Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* _(The Unknown Rich Man)_ Na *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Ubangiji mad'aukakin sarki. Tsira da aminci su 'kara tabbata ga fiyayyan hallita Annabi Muhammadu S.A.W *MAJANUNI* 'Kir'kirarran labari ne wanda ba'ayi don a ci zarafin wani ko wata ba. duk wanda ya ga ya yi dai-dai da rayuwarsa to a rashin sani ne. TSOKACI: Kasancewar Ubangiji ya halliceka da ji da ga ni tare da wadatacciyar lafiya, to kada hakan ya sanya ka d'auki kanka daban da sauran wanda aka hallita da wata larura makamanciyar wannan, Ubangiji ba yanda baya zartar da ikonsa, kuma yanda ya so haka shi yake faruwa. tabbas bawa baya shiryawa kansa rayuwa face wacce ya riski kansa a ciki. *_Da 'ko'kari da jajurcewarki wannan Littafi ya fita. Hasinatu (AUTAR MANYA💯) Binta tana godiya, rabbi ya tabbatar da zumuncinmu har gaban abada._* *Am Back Again* Allah ka bamu sa'a da rabo mai amfani. *1&2* *KANO STATE* *GADAR SALGA* Unguwa ce mai zaman kanta wacce take daura da kasuwar kurmi tsohowar kasuwa mai d'umbun tarihi a jahar *KANO.* Cikin rukunin gidajen yaku bayi na cikin unguwar. Matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha tara Zuwa ashirin zaune a kan kujera 'yar tsuguno da tarin wanke-wanke a gabanta tana wankewa tare da kifewa a cikin wani babban kwando. wanke-wanken take tun k'arfi da alamar sauri a tare da ita. Cikin rashin kintsi! Saliha Ta iso inda take, ba tare da tunanin komai ba ta kurma mata wani irin ihu! a cikin kunnuwanta! A Zabure! ta juyo har farantin dake hannunta yana fad:uwa a kasan gurin, idanuwanta sukayi rau-rau kamar zata fashe da kuka ta fara magana cikin yanayin na 'bacin rai! tare da yanayin hallitar da Allah yayi mata tace."Saliha menene haka."? Cike da rashin mutunci tace." Yo idan ba haka akayi miki ba ai ba za kiji magana ba, yaushe zan dinga wahalar da kaina gurin kiran sunanki ai ihu! kawai shi ya cancanta ayi miki tunda kunnuwanki a toshe! suke." Girgiza kanta kawai tayi tare da mayar da kanta 'kasa tana cigaba da wanke-wanken dake gabanta. A fusace! tace."Au! Shahida mahaukaciya kika mayar dani ina miki magana kinyi min banza to bari naje na shedawa wacce ta aiko ni kiran ki. Hanci ta shak'a ta sanya hannuna ta goge gumin goshinta cikin yanayin magana irin ta kurame! tace."Saliha kina dai ganin wanke-wanken nake ko." Saliha ta watsa mata harara da fadin." To ba zaki bar wanke-wanken ba ki tashi ki je kiran da take miki ba." A hankali ta ajiye sosan dake hannunta ta mike tsaye hanya ta nuna mata da hannu da k'arfi ta ce"Wuce muje." girgiza kanta tayi rai a b'ace tayi gaba Salihan ta rufa mata baya. Baba Asabe tana zaune a tsakiyar rumfa tana d'aura gishiri su ka yi sallama Saliha kai tsaye cikin uwar d'aki ta shige tabi lafiyar gado. Ita kuwa tsugunuwa tayi a gabanta cike da ladabi tace."Baba gani Saliha tace kina kira na." Ta ajiye d'aurin gishirin ta janyo jakarta dake gefe kudi ta dauko daure a leda ta kalleta da fadin." Bakin asibiti za ki je ki dauko min man gyda tun shekaran jiya ya k'are anata zuwa nema." bakinta kawai take kallo, nan ta fahimci abinda take nufi, tunda ba wai da 'karfi take maganar ba, shiyasa ta tsirawa bakinta ido, ta na ji amma ba sosai ba, shiyasa wani lokacin idan ana magana take bin bakin mutum. nan take fahimtar komai. Cikin saurin magana da yanayi na harshenta ta ce." Ban gama wanke kwanukan ba." Ta ce."Ki ajiye idan kin dawo ki k'arasa ai da sauran lokaci." Ta amsa da "To" Tare da mi'kewa. uwar dakin ta shiga domin dauko hijabi nan taga Saliha a kwance da waya a hannunta tana game. Girgiza kanta kawai tayi ta bude ma'ajiyar kayanta ta dau'ko hijabi tasa a wuyanta ta fito falon. Ta kalleta da fadin."Dubu arba'in da hud'u ne man gyada galan d'aya manja ma galan d'aya kafin ki isa zan kira Garba a waya na sheda masa zuwanki ya tari a daidaita sahu ya sanya komai a ciki. Tace."To shikkenan Baba sai na dawo." Tace." Ki kula sosai da kudin hannunki yau Juma'a akwai turmutsutsu na jama'a." Kud'in ta ri'ke da kyau da fadin." Zan kula insha Allah. Cikin nutsuwa take tafiya har ta fito bakin titi can tsallake ta hango mutumin ta zaune a 'karkashin tsohuwar motar da yake zama tare da tarkacen kayansa na mahaukata! Girgiza kai tayi tana me tsira masa ido yana kwance kan wani tattararran buhu ya takure jikinsa guri daya jikinsa duk yayi fururu! kasancewar lokacin sanyi ne shiyasa al'amarin ya tu'azzura. Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke tana sake jin tausayinsa na bin ilahirin jikinta, hakika da tana da yadda za tayi da ta taimaka masa ya daina kwana 'kar:kashin mota duk yanayin da ake ciki na ruwa da iska anan yake wanzuwa tsayin watannin da yayi a cikin unguwar tasu. Cike da tsantsar tausayinsa ta d'auke kanta daga inda yake ta fara laluben abun hawa Juma'a ce shiyasa abubuwan hawa sukayi k'aranci a kan titin. Ihu! da hargowar yara ya sanya da sauri ta mai da kanta gurin, nan taga yara masu yawa sunyi masa rumfa suna tsokanarsa sai ihu! suke tare da fad'in "Baban- baba kazami! Baban -baba mai annakiya Baban-baba mai kashi a wando."! Shi kuma Yana zaune yana kallonsu fuskarsa a sake kamar koda yaushe idan yara suna tsokanarsa sai ya yi ta murmushi koda kuwa cikinsu za'a samu masu jifansa da duwatsu! ba zai yi 'ko'karin 'kare kansa ba. Ranta ya 'baci mutuk'a ganin yanda manya mutane ke wucewa wasu a kasa wasu abubuwan hawansu amma a cikinsu an rasa wanda zai tsawatarwa da yaran akan abinda suke. Ba tare da tayi tunanin komai ba ta tsallaka titin kai tsaye gurin ta nufa. Tana zuwa cikin 'bacin rai irin na kurame take musu fad'a tana korarsu........Sai suka kwashe mata da dariya suna nuna ta da hannu da fadin." Mu bama jin abinda kika cewa ke din kurma ce ko kuma bebiya?" Abun yayi mata ciwo sosai ta sake d'aga muryarta cikin yanayin saurin maganarta da yanayin hallitarta take gargadinsu da fadin." Ita din kurma ce kuma haka Allah ya halliceta idan da wanda ya isa ya sauya mata hallita a cikinsu sai ya d'aura aniya. Suka dinga kyalkyala mata dariya sunayi mata ihu! kawai sai ta durk'ushe a gurin ta fashe da kukan 'bakin ciki a wannan lokacin ledar kudin dake hannunta ta fad'i ba tare da 'bata lokaci ba wani matashi dake can tsallake yazo ya d'auke yayi gaggawar watsa yaran ya gudu da kudin a daure a leda. Ido kawai ya tsira mata tana tsugune a kusa da shi kanta a tsakanin kafafunta sai kuka take. Sosai yake jin zafin kukanta a cikin zuciyarsa to amma 'kudirin dake cikin zuciyarsa shi ya hana shi rarrashinta tun ba yau ba ya san da yarinyar a duk sanda zata gan shi a hanya ko a gurin zamanshi yana hankalce da irin kallon da take masa 'kwayar idonta kadai ita ke nuna masa da cewar ta damu da shi, duk da cewa wata magana bata ta'ba had'asu ba to amma ya yi imani da cewa ita d'in mai 'kaunarsa ce, Abinda tayi a yanzu shine ya tabbatar masa da zarginsa. A nutse yace."Ki yi hakuri kinji ko." Shiru bata d'ago kanta ba, jim yayi yana nazari wani 'karamin icce ya d'auka ya zungureta dashi. a firgice ta d'ago kanta idanuwanta sunyi fululu fuskarta har ta kumbura! Tsigar jikinshi ce tashi ya mayar da kanshi kasa yana wasa da icce hannunsa. Tsaye ta mike tana karkad'e jikinta gabanta sai dukan uku-uku! yake! Ta kalli gabas ta kalli yamma kudu arewa sai kawai ta d'ora hannu a ka ta kurma ihu! tare da fadin." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una! Ya mike tsaye da sauri yana kallonta so yake yayi magana amma jama'ar da suka fara taruwa a gurin suka hana shi idanuwanshi kawai ya zuba mata. Haladu wanda ya kasance ma'kocinsu ya 'karaso gurin da fadin."Ke Shahida menene? me kike a gurin wannan mahaukacin."? Cikin kuka tace." Zuwa nayi na kori yaran da suke tsokanarsa shine suka sace kudin kuma Baba Asabe ce ta aike ni bakin asibiti na saro mata man gyada." Yace."In ban da shashanci irin naki da hauka yaushe zaki iya watsa yaran da suka dad'e suna tsokanar wannan shashashan mutumin nan wanda bai san ciwon kansa ba, shashahar banza kawai gashinan garin hauka kin janyowa mutane asara to kada kiji da wai sai na fad'a mata yanda akayi komai ya faru." Tana kuka take fadin." Don Allah kayi hakuri kada ka fada mata ." Tsaki yaja ya gyara zaman daddumar dake kafad'arsa ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Ganin haka yasa mutanan dake gurin suka watse. Komawa yayi ya zauna tare da rungume hannuwansa a kirji, Ta kalleshi da fadin." Baban- Baba Don Allah baka ga wanda ya daukar min kudi ba?" Girgiza kansa yayi alamun bai gani ba, hawaye suka sake zubo mata tace."To ko zaka duba min cikin takarcen kayanka ko Allah zai sanya suna ciki." Beyi mata jayayya ba ya fara dudduba tsummokaran dake gurin yana musu filla-filla babu komai sai tarin ledoji na pure water da sauran robobin lemo da yake tarawa. Ba tare da tsoron komai ba tazo ta tsuguna daf dashi tana sake hargitsa ledojin babban burinta ace taga ledar dake d'aure da kudin Baba Asabe. Sosai yake mamakin rashin tsoron yarinyar da yawa yara duk fitsararsu daga nesa suke tsayawa su tsokane shi, basa iya kusantar gurin da yake duk da cewa baya doke-doke amma hatta da manya basa iya zuwa inda yake amma abun mamaki ita ba taji tsoronshi ba tazo ta tsuguna kusa dashi duk da ta san cewa shi din ba mai cikakken hankali bane. Gabadaya jikinsa ya mutu wata iriyar kasala da kaunar yarinyar suka sanya shi kasa dauke idonsa daga kanta. Ta kalleshi da jajayen idanuwanta da karfi tace."Babu kudin sun sace ban san wane irin hukunci Baba Asabe za tayi min ba." Da yake ya fahimci kurma ce ita sai ya girgiza kansa ya had'e tafikan hannayensu guri guda alamun yana bata hakuri. Tsaye ta mike tana gyara zaman hijab dinta ta kalli hagu da dama babu motar data sako kai da sauri ta tsallaka titin tana had'a hanya. Cike da tsantsar tausayi yake kallonta har ta 'bacewa ganinsa, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi tare da sunkuyar da kansa 'kasa yana me cigaba da nazari da tunanin yanayi na rayuwa! _NA YI AMFANI DA SALO BIYU GURIN RUBUTA WANNAN LABARI, INA FATAN MASU KARATU ZA SU FAHIMTA_ *BINTA UMAR ABBALE* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi join don samun dama karanta littafin na d'aya. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) Na *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO... _____ _Fatan Alheri ga marubuta Amanar Binta💯🥰_ *Hasinatu (Autar Manya)* *Sadiya Rimi* *Binta Garba Saleh* *Matar ya sayyadi* *Real Esha* *Jamy 'Yar kankia* *Fatima Sunasi Rabi'u* *Dr Ms Agadaz* *Ummu Mahir* *Jasmine* *Zee Kumurya* *Shamsiyya Manga* *Autar Marubuta* *Indo Aisha* *Maman Teddy* *Zahraty Takwara* *xayyishatu Humaira* *3&4* Tsoro da fargaba! ya sanya ta kasa komawa gidan sai kawai ta samu kan dakalin wani gida ta zauna tana kallon masu wucewa da nufin zuwa massalaci domin gabatar da sallar juma'a. Har aka sakko daga massalaci tana nan zaune a gurin, Haladu yazo ya wuce ta yana girgiza kansa. itama kai ta girgiza tana kallonsa har ya karya kwanar layinsu, k'wafa tayi tare da d'auke kanta ta san duk wannan saurin da yake yana so ya je ya kai gulmar abunda ya faru babu shakka sai ta dauki mataki a kansa mutukar ya janyo mata 'bacin rai! dama sun saba tafkawa dashi a duk sanda yazo sayan abinci gidan nasu. Da yake gidan ya kasance gidan gandu( na kowa da kowa) ya sanya ba tare da neman iso ba ya kutsa kansa ciki tare da sallama a bakinsa. Ta amsa tare da fitowa daga kicin da wani kafcecen ludayi na juya miya a hannunta. Ta ce."A'a Haladu har an sakko kenan?" Ya amsa da "Eh wallahi" kai tsaye gurin zamansu ya nufa ya zauna tare da cire hular dake kansa. Ta ce." Gurasa da miya zaka saya ko kuma shinkafa da miya?" Hamma! ya saki ya sosa kansa da fadin." Yau dai shinkafa zan ci domin na gaji da cin kayan fulawa kwana biyu idan nazo bayan gida sai na rirri'ke kan famfo nake samun damar yi watarana har ihu! nake kurmawa! kai basir mugun ciwo ne wallahi." Saliha dake yanka salak ta fashe da dariya tana kallonsa, Fuskarsa ya murtuke yana muzurai! Ita kuwa sai tikar dariya take sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru. Sai da ya kai loma uku na abincin sannan yace." Uwar towo ina ja'irar yarinyar nan ta shiga ne?" Baba Asabe ta ce." Shahida kake nufi?" Yace."Eh kwarai kuwa." Tace."Kaga tun kafin tafiya massalaci na aike ta bakin asibiti shiru har yanzu bata dawo ba. Girgiza kansa yayi da fadin." Can na ganta gurfane gaban tsohon mahaukacin nan dake bakin titi tana kuka koda na tambayata sai take sheda min cewa...........Duk ya kwashe komai ya fada mata. Baba Asabe ta dafe kirjinta tana salallami! Ya ce."Wallahi kuwa ai wannan kudi kawai ki fitar da ranki dasu domin kuwa nayi imanin da cewar babu su an sace." Jiki a sanyaye ta zaune bakin rijiya da fadin.'' Amma kuwa wannan yarinya ta cuce ni dubu arba'in da hud'u ne wace irin kaddarace ta ritsa dani a yau." Ya ce." Hukunci mai tsauri zaki d'auka a kanta domin kuwa ita tayi ganganci har aka sace kudin idan ba haka ba mai zai sanya ta gurfana gaban mahaukaci irin Baban-baba wanda bai san kansa ba." Girgiza kai tayi cikin 'bacin rai tac e."Haladu ni fa ban yarda da wannan mutumin ba, wallahi ban yarda cewa mahaukaci bane tunda duk abun masu hankali yana aikatawa bayan haka kuma sallah bata wuce shi bana tamtama shine ya sace min kudina. Dariya yasa da fadin." In banda abinki Uwar towa ya za'ayi ki kira Baban baba mai hankali in da yana da hankali ba zaki gan shi a lalace ba. Sallah kuma da ki ke magana dayawa mahaukata irinsa suna daburawa amma ki daina sanya Baban-baba a cikin masu hankali. Tsaye ta mike da fadin." Haladu dole naje da kaina na duba kudina yau koni ko shi duk haukansa wallahi na fi shi sai ya fito min da kudina 'barawo kawai " Tsaye ya mike tare da zaro kudi daga aljihunsa ya mika mata da fadin." To ni dai ga kudinki zan shiga gida na huta zuwa yamma zan shigo domin naji a'ina aka kwana.'' Kudin ta kar'ba tasa cikin lalitar dake d'aure a kugunta da sauri ta shiga daki ta fito yafe da mayafi. Saliha ta kalleta da fadin." Baba kada kije ki tunkari mahaukacin mutumin nan kada garin neman gira a rasa ido ni dai na fada miki. "Sai naje d'in ba zan lamunci wannan al'amarin ba domin kuwa ban yarda da asara ba." Tana 'kare maganarta cikin zafin nama ta kama hanyar fita da kud'irin zuwa yiwa Baban Baba A tare a tare. Tunda ta hango ta gabanta yake faduwa sunkuyar da kai tayi har ta k'araso inda take, "Don ubanki abinda ki kayi min kenan? ta fad'a tana kokarin kai mata duka! tasa hannu ta kare tana kallonta da idanuwanta da suka taru da ruwan hawaye. cikin masifa ta ce."Tashi muje gurin mahaukacin daya sace min kudina." Cikin k'okarin kare kanta ta bude baki za tayi magana.......ta buga mata tsawa! wacce ta sanya babu shiri ta mike tabi bayanta tana me cigaba da aibata ubanta wanda bai san abinda yake faruwa ba. Har suka isa bakin titin tana surutai! jama'arta sai tambayarta suke abinda ke faruwa tana tafe tana basu amsa wasu dariya kawai suke su wuce wasu kuwa bin bayanta suke domin kashe kwarkwatar idonsu. Yana tsaye da wata jarka a hannunsa da alama gurin yake so ya bari, katamau! ta rike hannunta suka 'karasa gurin da yake. Tsira musu ido yayi yana kallo. ta kalleshi da niyyar yi masa tijara! dafin idanuwansa ya sanya jikinta mutuwa sai ta gaza furta komai kawai tayi 'kasa da kanta. Kallon yarinyar ya yi suka hada ido da ido, sai tayi gaggawar saukar da nata idon sakamakon mutuwa da jikinta ya yi a cikin k'wayar idonshi akwai wani sirri wanda shi kanshi bai san yana dashi ba. Can 'kasan ma'koshi ya ce." Menene ko za ku duba kudin ne?" Kai kawai ta iya d'agawa har yanzu kanta na kasa ta kasa kallonshi, Baba Asabe tayi namijin kokari gurin Fad'in." Kaga Malam dakata! ba mu yarda da cewa kai mahaukaci bane kazo cikin wannan unguwa ne da mummunar manufa don haka kud'ina dubu arba'in da hudu daka sace wallahi sai ka fito dasu ko kuma ka kwana a police station." Ya zuba mata kyawawan idanuwansa masu cike da kwarjini. Dalladi dake bayansu a tsaye yace."Uwar towo wannan magana ki barta kawai ko kin ta'ba ganin anyi sharia da mahaukaci ni na tabbata da cewa Baban-baba ba zai sace miki kudi ba, to yayi me da su? mutumin da ba shi da hankali idan kuma baki yarda ba sai ki dauki mataki amma ina mai tabbatar miki da cewa wahala zaki sha domin kuwa duk inda za ki je babu wanda zai saurareki. Ta girgiza kai nifa ba zan yarda ba wallahi." Yace."Shikkenan sai kiyi abinda za kiyi." Gurin ya bari bayan ya gama maganarsa, sai kawai ta hankad'a yarinyar kusa dashi da fad'in "Maza shiga k'arkashin motar ki duba min kud'ina idan zai kashe ki da duka bai dameni ba." Ba tare da wata fargaba ba ta shige k'arkashin motar ta fara dube-dube duk da tasan kudin basa gurin. Kallonsa tayi da fad'in." 'Yan sanda zan dauko maka yanzu ai gamu ga police station haukanka na 'karya ne" Cikin sauri ta bar gurin. Yana tsaye ya rungume kirjinsa da hannuwansa idanuwansa a kanta a lokacin da take karkashin tsohowar motar tana dube-dube. Jikinta ya jik'e da gumi ta fito daga 'kasan motar da 'karfi tace."Baba banga 'kudin b........Had'a ido sukayi yana kallonta jiki a sanyaye tace."Babu kudin a gurin." Kai ya gyad'a mata. sai ta matsa ta bashi guri ganin yana kokarin ture ta, ya shiga ya zauna tare da rungume gwiwarsa still idanuwansa na tsaye a kanta. Baba Asabe Cike da kwarin gwiwa ta isa station din duk ta zayyane musu abinda yake faruwa. Koda sukaji abinda take tafe dashi sai suka shashantar da maganar saboda sun riga sun san sharia da mahaukaci sai wanda ya shirya bayan haka kuma duk tsayin watannin da mahaukacin yayi a unguwar ba'a ta'ba kawo musu shi da sunan ya aikata mummunan aiki ba. saboda haka sai suka sallameta tare da kafa mata hujja da cewa ko don gaba ta daina cewa za ta yi sharia da mahaukaci domin kuwa al'kalami ya sauka daga kan duk wani mai matsalar k'wakwalwa. Jiki a sanyaye ta fito daga station din ranta duk a bace! tana tafe tana zancan zucci da irin hukuncin da za tayi wa yarinyar. Ita kuwa Shahida tana nan tsaye a gurin gabanta sai faduwa yake ta san halin Baba Asabe akan kudi babu shakka yau sai buzunta. A jikinta take jin yana kallonta amma tsabar fargaba ta kasa juyawa ta kalleshi ta fahimci a cikin haukan nasa harda kallo a ciki to idan ba haka ba menene abin kallo a tare da ita. Ya jima yana kallonta kafin ya sauke zazzafar ajiyar zuciya hannunshi yasa ya ja gefan hijab dinta. Cikin wani irin yanayi ta juya suka hada ido. muryarsa ya daga sosai da fadin." Wacece ita?" Zuciyarta ta karye hawayen da take ta tattalinsu suka su'bce. A raunane tace."Kakata ce." "Ina iyayenki?" ya fad'a still idonsa na kanta, kai ta sunkuyar jin tana shirin fashewa da kuka, ya sake maimaita maganarsa. Murya na rawa ta ce." Mahaifiyata ta mutu Babana kuma yana can unguwar Ja'in da matarsa da sauran 'yan uwana." Zama ya yi ba tare da ya sake magana ba. A sace ta d'an Kalleshi da gefen idonta, al'amarinshi akwai abun mamaki a ciki maganarsa cikin nutsuwa babu alamun ta'bin hankali a ciki ko dai akwai wani abu da yake 'boyewa ne? gashi ba yaro bane da shekarunsa yanda take ganinsa ma kamar zai yi shekarun mahaifinta, Kallonsa ta sake yi taga ya rungume gwiwarsa da hannuwa biyu yana girgiza kansa can kuma sai taga yana 'yar dariya. Cikin faduwar gaba Ta ce." Baban-Baba kana jin yunwa ko?" Ba tare da ya kalleta ba ya daga kanshi. Ta ce." Yanzu a ina zaka samu abinci?" Ya kalleta na second biyu kafin ya kauda kansa. Wata maganar take shirin yi masa ta hango Baba Asabe ta tsallaka titi, ya kalleta cikin tsawa yace."Ki tafi ki bani guri." da sauri taja gefe tana kallonsa, ya dauki iccen dake gabansa yana nuna ta dashi. "Na ce dake ki tafi ki bani guri ko ba kya ji ne? Saurin barin gurin tayi tana waiwayensa. Sai girgiza kansa yake tare da wasa da iccen dake hannunsa, Hawayen tausayinsa ta goge tana tunanin a inda zai samu abinci ya ci watakila kan bola zai je ya yi tone-tone ya samu lalataccen abinci ya ci tunda mafi akasari da haka mahaukata 'yan uwansa suke kawar da yunwar da ta damesu. A soran gidan ta samu ghana masgo kayanta kaf a ciki. Ta dinga jin masifarta daga gidan Saliha na taya ta. Jiki a sanyaye ta shiga da sallama a bakinta, ta kalleta da fadin." Na gama zama dake ki tafi duk inda za kije mara mutunci." "Baba kiyi hakuri tsautsayine kin san dai tunda kike aike na banta'ba zubar miki da kudi ba wannan ma kaddara ce." Tace." Ban san kaddara ba na fada miki na gama zama dake ki tafi can gidan Ubanki duk abinda za su yi miki dama tausayi yasa nake rike dake to tunda kin zama munafuka zama na dake ya 'kare Kije duk abinda Talatu za tayi miki ba zai dameni ba. Ta durkushe a gurin tana kuka da rokonta tayi hakuri tayi kunnan uwar shegu da ita kicin ta shige ta barta a gurin, ta kalli Saliha da fadin." Ki sanya baki tayi hakuri kinji." Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da abinda take, A fusace! ta fito daga kicin din ta nufi dakin sai gata ta fito da bulala a hannunta ta riga ta san idan tazo babu abinda zai hana ta doke ta. dan haka da gudu ta ruga a guje ta fita daga gidan tana jin lokacin da ta sanya sakata ta koma ciki tana surutai. Babu yanda ta iya haka ta kama hanya domin tafiya gidan mahaifinta dake can Ja'in Tafiyar 'kafa za ta yi tunda babu kud'i a hannunta gashi akwai tazara mai tsayi tsakanin Gadar salga da Ja'in. Koda ta fito bakin titin hankalinta na gurin zamansa, babu shi a gurin sai tarin tarkacensa , sai ta tsinci kainta da kasa tafiya har sai da ya dawo da ledar biredi a hannunsa taga ya shige karkashin motar ya zauna. Ajiyar zuciya ta sauke cikin zuciyata Tace."Watakila wani ne ya tausaya masa ya siya masa biredin. Sai da taje Sabon titi na gidan 'kankara a kasa kafin ta samu wani d'an kirki ya taimaka mata ya rage mata hanya. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. ____ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Kuyi join domin samun damar karanta littafi na d'aya. _Gaisuwa ta karamci zuwa ga iyaye na biyu._💯 *FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)* Tare da *USAINA ABDUL-MALIK KAITA (HAJIYA BABBA)* *5&6* Ta zo shiga gidan kenan ta yi karo da 'karamar k'anwarsu Walida tana d'auke da markad'an awara a kanta. kallon juna su ka yi sai kawai yarinyar taja tsaki ta wuce ba tare da tayi mata magana ba. Idan da sabo ta riga ta saba da irin wannan wulakanci da 'kas'kancin da 'yan uwanta suke mata duk da cewa itace babba a cikinsu amma mutum d'aya ce take ganin girmanta. Gabanta na fad'uwa tayi sallama cikin gidan. Talatu tana kicin ta baza kwanuka tana rabon abinci yayin da Hadiza babbar 'yarta ke yanka musu salak da tumatur. ita kuma Jamila tana shanya kayan makarantarta akan igiya. Itace ta amsa sallamar fuska a sake tace."Auntymu kece ki ke tafe da wannan ranar.?" Hadiza ta kalleta a watse ta mayar da kanta kasa tana cigaba da gyara salak din dake gabanta. Jamila tace."Talatu ga fa Aunty Shahida tazo." Ba tare da ta juyo ba tace."To Ubanta zan yi mata kome?" Jamila ta girgiza kanta ba tace komai ba taja hannunta suka shiga daki tana 'kokarin kawar da 'bacin ran dake damunta, ta tsani halin ko in kulan da mahaifiyarsu take mata a ganinta Shahida abar tausayi ce duba da maraicin da take ciki bayan haka kuma akwai nakasu na rashin ji a tattare da ita, babban damuwa yanda mahaifinsu yayi shakulatun 'bangaro da lamarinta da kuma lalurarta a matsayinsa na mahaifinta baya taimaka mata da komai gabad'aya ya sakarwa kakarta wacce ta haifi uwarta ragamar rayuwarta, bai san ci da sha da sutturarta ba, Uwa uba karatunta duk be san wannan ba, ta wannan fanni dole a jinjinawa Baba Asabe domin ita d'in maca ce mai kamar maza duk da nauyin ba akanta yake ba amma ta d'auka tana iyakacin 'bakin 'ko:karinta akan yarinyar. Tsaf Talatu ta gama rabon abinci amma babu rabon Shahida a ciki duk da cewar lokacin da ta zo gidan bata gama rabon abincin ba idan da ta yi niyyar sanya mata kwano zata san yanda tayi ta fitar mata da rabonta amma k'emagadas! tayi mirsisi ta rabe abincin kaf ta kira kowa ya d'auki nasa. Jamila a sanyaye ta nufi dakin da nata kason a hannunta. Kamar ta san niyyarta sai ta kira sunanta, taja ta tsaya tana kallonta, fuska a tsuke tace." Ki ka shiga da abincin nan ku ka ci tare sai na tsine miki albarka." Dama sarar ta kenan daga zarar 'ya'yanta sunyi mata laifi sai tace zata tsine musu. A marairaice tace."To yanzu ita Shahidan haka zata zauna Talatu kada fa ki manta itama tana da hakki a gidan nan tunda duk ubanmu d'aya." Ta ciko hannu da shinkafa 'yar manja wacce taji salak da yaji ta watsa a bakinta tana taunawa ta ce." Kafin ki san haka na rigaki sani ban yi niyyar bata abincin ba shiyasa nayi rabo babu ita idan kuma ki kayi wasa wannan na hannun naki zan k'wace na bawa almajirai kema kiyi asara." Hadiza ta kalleta da fadin." Banza mara kishin uwarta shin har kin manta labarin da Talatu ta ba mu a lokacin da suka zauna tare da mahaifiyarta yanda ta azabtar da ita amma shine saboda rashin kamun kai kike tausayin abinda ta tafi ta bari ai wallahi ni da wannan kurmar yarinyar har abadah." Jamila ta girgiza kanta da fadin." Ke Hadiza jahilci ne yake damunki wallahi ni ina ruwana da irin zaman da su ka yi kawai 'yar uwata na sani saboda duk rintsi ba'a sanjawa towo suna Shahida 'yar uwarmu ce dole ko mun 'ki ko mun so." Hadiza ta fusata! ta hau d'ura mata ashar wai ta kira ta da jahila. 'Kokarin tashi take taje inda take tsaye ta doke ta uwar ta hana ta. Sallama ya yi cikin gidan yana sanye da manya kaya sabuwar shadda mai uban surfani, kansa sanye da hula zanna bukar idan ka ganshi sai ka dau'ka wani hamsha'kin mai kud'i ne nan kuwa tsabar 'karya ce da fafar tsiya Jamilu kenan wanda abokansa suke kiransa da Ya hajuj! tsabar 'karya da nuna shi wani ne. ya sanya sunanshi ya 'bata a ko'ina ake kiransa da Hujaj! Ya kallesu da fuskar shannu "Menene na ganku a tsaye ke Jamila ya akayi?" Da sauri tace." Baba ka ga Aunty Shahida ce tazo shine Talatu ta raba abinci babu ita wai don na d'auki nawa zamu ci tare shine fa suka had'u suke zagina. Ya gyara zaman babbar rigarshi da fadin." Ina Shahidan take? Tace."Tana daki a zaune.'' Tsaki yaja da fadin." Shige ki je kuci abincin tare." da sauri ta shige dakin. Talatu ta kalleshi da fadin.'' Yau kuma? ba tare da yace mata komai ba ya bude dakinsa ya shiga ya turo k'ofa. Kasan kafet ya zauna ya cire babbar rigar jikinsa, hannu yasa cikin aljihu ya shiga fito da kudi daure da kyaure bandir biyar ne ya zube a gabansa yana wani irin murmushi babu shakka yau kura tayi nama ya tashi da Sa'a ko da yake dama sana'ar tasu ta gaji haka yau kai gobe wanin ka da yake shi akwai nasibi duk ranar da suka buga wasa baya fad'uwa, wasan yau yafi na kullum domin ya samu kudi masu yawa, burinsa a yanzu bai wuce siyan babur ba, zai sayi vespa d'an 'kasa irin wanda manya alhazawa suke hawa a duk lokacin da ba suyi ra'ayin hawa mota ba. Tura kofar dakin tayi sai yayi saurin boye kudin a bayansa. Tayi sallama tare da tsayawa 'kerere a gabanshi, yace."Kefa dadina dake rashin ladabi meye haka kin shigo ba tare dana nemeki ba kin tsaya min 'kerere a ka." Ta gyara daurin zaninta da fadin." Ka san kwanan zance ai bana so muyi hayaniya da kai a gaban yara saboda haka ka bani kudin dana ranta maka." Yaja tsaki da fadin." Wai shin har nawa ne kudin naki?" "Dubu biyu da dari hudu ne kada ka manta yau kwananka uku baka ba da ko kwabo ba tun daga safe har dare ni nake d'awaniya da gida to tunda Allah yasa yau ne cikar alkawarin da kayi min ba zan fita ba sai ki biya ni kud'ina." Kashingid'a yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa. Tace."Jamilu meye haka zaka dinga yi min murmushi kada fa kayi min wata magana don wallahi baza mu wanye lafiya ba." Ya sosa gemunsa da fadin." Ki je yanzu zan fito zan baki kud'inki ina jin shikkenan ko?" Kai ta girgiza da fadin." Ba fa zan fita ba sai da kud'ina a hannu. Ya mike zaune da fadin." Idan kika matsanta min wallahi zan ha naki ni nace kije zan baki idan na fito sanin kanki ne bana san takurawa." Ta yi jim tana kallonsa kafin ta gyada kai da fadin." Na kawo maka abincinka ne.? Sai da ya mula tukkuna ya ce."Aa ki bawa Jamila da Shahida suka 'kara ni na koshi." Ba tare da tace komai ba ta juya ta fita, koda ta fito daga dakin a maimakon tayi abinda yace kai tsaye kicin din ta nufa ta dauko abincin nasa tasa a gabanta ta dinga ci sai kace jaka, Walida dake sud'e hannu tace."Talatu d'an k'ara min wallahi ban koshi ba." Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kai loma bakinta, yarinyar dake mara kunya ce ta yatsine fuska da fadin." Talatu ki dai ci a hankali kada ki 'kware wannan loma haka." Bud'e baki tayi za tayi magana aikuwa ta shaki shinkafa ta hanci tari ya sar'ke ta ta dinga yi hawaye na zuba, yarinyar ta tashi ta bar gurin ba tare data debo mata ruwa ba. Shahida da Jamila haka sukaci abincin ba tare da sun 'koshi ba, suka fito domin wanke hannu nan suka ga Talatu tayi wurjajan ido yayi jawur har yanzu da sauran tarin amma saboda zulama bata daina cin abincin ba. Shahida ta banka mata harara ta wuce dama duk sanda tazo gidan abinda ke shiga tsakaninsu kenan harar juna, sai taso take gaishe da ita, Hadiza ta fito daga d'aki Talatu tace."Kinga 'yar iskar yarinyar nan saboda ban zuba mata abinci ba take hararata. Hadiza tace."Take harararki kamar sa'arki." Tace."Au! keda baki ta'ba gani ba? ai a duk san da zata zo gidan nan hararace take shiga tsakaninmu." Bagazan! bagazan ta nufi inda take ta juyo da ita suka fuskanci juna, murya ta d'aga da fadin." Don Uwarki mahaifiyarmu sa'arki ce?" Jamila tace."Hadiza neman fitina bashi da amfani me kuma tayi miki? Ta juya tana yi mata bayani yayin da ita kuma Shahida ta juya inda Talatu ke zaune ta dinga watsa mata muguwar harara tunda ta lura da abinda bata so to ta daura d'amarar 'bata mata rai. Talatu ta rike ha'ba da fad'in.'' Ni kike harara don Ubanki! ta dauke kanta tana jan tsaki tare da niyyar barin gurin. Hadiza ta fizgo kafad'arta tana nema ta kai mata duka, sai ta rike mata hannu cikin yanayin maganarta tace."Hadiza ki kiyaye ni wallahi ni nafi karfin ki dake ni." Ta fizge hannunta tana d'ura mata ashar!! Ya fito d'aga daki da yanayin bacci a tare dashi ya ce." Baku da hankali ne? sukayi shuru ya kalli Shahida da fadin." Me yasa duk lokacin da ki kazo gidan nan sai anyi rigima dake? Ido ta zuba masa, yaja tsaki da fadin." Ana magana kin tsare mutune da ido kizo ki tafi inda ki kafi wayo." Da yake da 'karfi yake maganar duk taji komai sai tace." Ai na dawo gidan ubana da zama." Talatu ta zabura! ta mike tsaye da fadin." A'ina.? Babu tsoro tace." A nan." Jikinsa ya mutu ya ce."Kinyi mata laifi ko?Fashewa tayi da kuka ta durkushe a gurin!. Talatu cikin masifa ta ce."Wallahi ko kukan jini za kiyi baki da gurin kwanciya a gidan nan aikin banza kawai." Ya kalleta da fadin." Kin san dai 'yata ce ko?" A fusace! Tace."Na sani amma wallahi ba zan zauna da ita ba." Ya girgiza kai da fadin.'' Duk lokacin da nayi ra'ayi 'yata zata dawo hannuna da zama." Tana numfarfashi! tace."Ni kuma a ranar zan tattara kayana na bar maka gidanka domin kuwa ba zanyi kishi da uwarta nazo nayi da ita ba. Murya ya d'aga gurin kiran sunanta, ta d'ago kai tana kallonsa fuskarta gaje-gaje da hawaye, Ya ce."Tashi muje ki fad'a min laifin da ki kayi mata." Ta mike tana share hawaye tabi bayansa zuwa dakinsa, kallon banza Talatu ta bisu dashi tayi k'wafa tana girgiza kanta. Duk abinda ya faru ta sheda masa tana kuka, ya ce."Kiyi hakuri kinyi sara a bakin ga'ba matsalar Baba Asabe kudi za'a biyata kud'inta" Cikin izzah! da nuna isa yayi maganar kamar wanda yake da burin biyanta kud'in dawainiyar da tayi masa daga farko har 'karshe. Yasa babbar rigarsa da fadin." Tashi mu tafi." Ta mike da sauri ta fito, shima ya fito yana kokarin kulle kofa tazo ta ta rike k'ugu tare da jan tunga a gabansa. Hannu yasa cikin aljihu ya zaro sabbin 'yan dubu-dubu uku ya watsa mata. Ta tsuguna tana tsincewa da fad'in." A banza dai duk abinda za kayi ni na rufa maka asiri." Ya gyara zaman hularsa ya kama hanyar fita ba tare da ya tanka mata ba. Ta kalli Jamila dake kan rijiya a zaune ta ce." 'Yar uwata na tafi na gode da zumunci." Jamila tana murmushi tace."To Aunty Shahida ki gaishe da Baba Asabe da kyau." Tace." Za taji da kyau." Hadiza tace."Banzaye kawai wannan munafurcin naku babu inda zashi." babu wanda ya tanka mata a cikinsu. Shahida tabi bayan mahaifinsu ita kuma Jamila ta shige daki tana jiyo irin zagin da sukewa Shahida tamkar maguzawa! *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO... _____ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Kuyi join domin samun damar karanta littafi na daya. *Marubuta* _Nimcy luv (Sarauta)_ _Hassana Bamalli_ _(OmApanan)_ _Sa'adatuBintuAbdullahi_ Ina godiya 'kwarai💯 Kyautar feji zuwa ga: _*Ummul-Khairi Shaik*_ _*Muhammad (Kairatu)*_ Binta tana godiya da k'auna tare da k'warin gwiwa🥰 *7&8* Jamilu Ya hujaj! mutum ne mai fara'a da wasa da dariya shiyasa yake da jama'a yara da manya duk inda ya gifta za ka ji ana fadin "Ya Hujaj! Shi kuma ya dinga washe baki kenan yana dariya idan da kudi a jikinsa ko nawa ne sai sun k'are domin bai iya gwaninta ba kyautar dubu biyar a gurinsa ba abu ne mai wahala ba, mutuk'ar yana da kudi to na bajinta ne amma fa gidanshi sai godiyar Allah domin da k'yar! yake bayar da kudin awo watarana matar gidan itace take cefane da yake tana awarar siyarwa shiyasa suke raba daidai. Da yawa mutane suna mamakin yanda yake sanya manyan sutturu da bajinta a waje amma 'ya'yanshi suna yawo babu sutturar arziki babu makaranta mai kyau, uwa uba kuma matarsa na sana'ar siyar da awara wannan dalilin ya sanya wasu ke zaginsa suna ganin arzikinsa ya tashi a banza tunda ya kasa sauke nauyin iyalinsa sai dai ya fita yana neman suna a gurin jama'ar gari. A zahiri sana'ar sa wacce kowa ya san shi ida ita sayar da takalma a cikin kasuwar wambai shago guda ne dashi yake bada sarin takalma na roba dana fata amma irin wanda akeyi a cikin kasuwar bayan wannan sana'ar tashi akwai wata wacce ya jima yanayi a 'boye kuma itace take kawo masa ma'kudan kudin da yake facaka dasu. Yau zaka gan shi da sabuwar mota amma idan aka kwana biyu sai gan shi cikin a daidaita sahu ko kuma a kafa yana tafiya idan ka tambayeshi sai kawai yace motarsa tana gareji ta samu matsala 'karya kamar kudin guzuri a gurinsa, wannan dalilin ya sanya jama'a suke d'aukarsa a matsayin mai rariyar hannu ko kuma d'an bariki har yanzu babu wanda ya hasaso irin sana'ar dake sanya abubuwan hannunsa suke salwancewa. Ko a cikin a daidaita sahun ma sai jan 'yar tashi yake da wasa yana tsokanarta wai lallai sai ta fada masa sunan saurayinta. Ita dai Shahida murmushi kawai take tana mamakin halayyar mahaifin nata, kwata-kwata baya jin nauyi da kunya idan yana wasu abubuwan. Da yake yamma tayi ya sanya titin ya cunkushe da ababan hawa bayan jama'ar dake kai kawo a gurin. Duk wanda yake cikin garin *KANO* ya san cewa titin *JAKARA* yana bukatar gyara daga mahukunta, amma anyi shakulatun 'bangaro dashi duk da irin gudumawar da matasan unguwar ke bayarwa a lokocin za'be amma ko wane d'an takara daga zarar ya samu abunda yake so sai ya manta da wad'anda suka sha masa wahala. mai adaidaita sahun yace."Alhaji ko zaku sauka anan ne yamma tayi gashi gowslow nan yaki sauki. Yace."Aa akwai sauran tafiya kayi hakuri ka shiga damu ciki, Yace."To shikkenan amma zaka 'kara min wani abu." Yace."Babu damuwa." Da karfi! tace."Subahanallahi." hankalinsu ya dawo kanta kokarin fita take daga babur din ya rike hannunta yana tambayarta, ta nu na masa shi wanda yake can tsallaken titi wani mai babur ya kusa buge shi jama'a har sun taru a kansa. Hawaye ta share tana fadin." Allah ya kiyaye da tuni mai babur ya buge shi Allah sarki Baban- baba." Yace."Ke wai baki da hankali ne kike magana ke kadai. Mai babur din yace."Alhaji baka lura bane ai mummanan al'amari ne ya kusa faruwa akan wancan mahaukacin dake tsallaken titin can.'' Yaja tsaki da fadin." Ni ai ban lura wallahi ba kaji yanda hankalina ya tashi ba ke ina ruwanki da mahaukaci Shahida." Yana kallonta yake maganar. Hawaye ta share da fadin." Haka kawai nake tausayinsa." Tsuke fuska yayi da fadin." Malama shige mota mu tafi bana son shashancin banza a garin tausayi ake cutarku wancan mutumin da ka gani ba mahaukaci bane akwai manufarsa. Ta share hawaye da fadin." Eh Baba nima bana masa daukar mahaukaci tunda wani sa'in duk abu na masu hankali yana aikatawa rashin galihun da yake cike ne yake damuna, da za'a samu wasu masu imani da tausayi su taimaka masa da abin yi Abbah ka duba fa kaga kayan jikinsa duk daud'a duk sun yage fuskarsa bakikirin takalmin kafarsa ya sud'e ya tsinke kullum karkashin mota yake kwana rana zafi iska ruwa babu wanda ya damu dashi da ci da shan sa." Yace."Shahida Irin wad'annan mutanan da kike gani basu da gaskiya shiyasa Allah yake mayar dasu haka watakila akwai wani mugun abun da ya tafka wanda yasa Allah ya nuna masa kuskuransa saboda haka idan za ki yi tausayi da imani ki tausayawa 'kananun yara ko kuma marayu ko nakasassu irinki amma ba irin wad'annan mutanan ba." Direba yace."Gaskiya ne Alhaji nima na jima ina mamakin mutumin nan da yake ina yawan shigowa unguwar nan ina ganinsa sai nayi ta mamakin yanda akayi rayuwarsa ta lalace haka koda yake duk mutumin da bashi da gaskiya yakan 'kare rayuwarsa a firgice ba tare da ya san ina ya dosa ba." Hawaye ta share tana jin zafin magangansu tace."Abbah ku dai kuyi masa Addua dashi da masu lalura irin tashi watakila kuma babu d'aya daga cikin abunda kuke zargi mybe jarabtace daga Ubangiji." Murmushi yayi ya dauko tafkekiyar wayarsa yana dubawa yace." Shahida irin halinku daya da mahaifiyarki Allah ya gafarta mata." Ta amsa da ameen tana goge fuskarta. Suna zaune a tsakar gida ita da Saliha suna gyaran kayan miya suka shiga gidan. Koda ta amsa sallamarsu sai kawai ta mayar da kanta kasa ta cigaba da abinda takeyi tai bala'in shan kunu! Da yake ya iya Siyasa sai ya cire takalmansa cikin ladabi da 'yar dariya a tare dashi yace."Baba sannu da aiki." Ciki-ciki ta amsa ita kuwa Saliha ko kallonsa ba tayi ba ballanatanta ta gaisheshi hakan ya 'bata mata rai sosai sai itama ta kudiri aniya a zuciyarta kan cewa duk sanda babanta yazo gidan ta daina gaishe shi. Da fara'a a tare dashi yace."Ai dawowata kenan na samu yarinyar nan a gidan shine take sheda min abunda ya faru har kika kore ta daga gidanki haba Baba ai hannunka baya ru'bewa ka yanke ka yar." Hannu ta d'aga masa da fadin." Dakata! Jamilu kazo ne kayi min dadin baki ko kuma kud'ina kazo ka biya ni bana son neman gidin zama ko kuma dama can hakkin rike yarinyar nan a hannuna yake?" Maganar ta 'bata masa rai amma sai ya basar yace."Haba Baba ki kwantar da hankalinki muyi magana ta fahinta mana ake rasa mutum ma ballanatana kudi." Tsaki! taja tana cizge alayyahun dake gabanta ta ce." Mutuwa dole ce amma da gangan yarinyar nan tayi min wasarere! da kudi har 'barawo ya sace saboda haka ka tashi ka bani guri bana bukatar tsari da dadin baki mutukar ba biya na kudi za kayi ba." Ya girgiza kai har ila yau da murmushi a fuskarsa yace."Wai shin ma nawa ne kudin naki.?" Ta kalleshi she'ke'ke! kafin tace."Kaji fa! kamar gaske har wani tambaya kake kamar wanda zai iya biya." Dariya yasa baka ta'ba ganin 'bacin ransa saboda ya iya siyasa yace."Ko ba zan iya biya ba ai yana da kyau na sani." Ta'be baki tayi da fadin." Babu amfanin na fad'a maka tunda ba iya biya za kayi ba." Ya gyad'a kanshi yana kallonta minti biyu ya giciye yana gyara babbar rigarsa ta zuba masa ido tana kallonsa ya zaro yan dubu-dubu sabbi kar dasu har wasu na zubewa a kasan gurin. Cike da mamaki take kallonsa yana irgawa cas ya cake mata dubu hamsin a gabanta ya gyara zaman babbar rigarsa da fadin." Gashinan duk da na san ban isa na biya kudin hidimar da akayi min ba ayi hakuri da ni da hali na na san anyi min kokari." Kunya ce ta rufe ta sai ta sunkuyar da kanta ba tare da tace komai ba har ya gama maganarsa ya fita daga gidan. Ganin haka yasa Shahida shiga daki ta kwanta kan gado abu biyu suka dame ta irin rayuwar k'as'kancin da take a tsakanin 'bangare biyu da kuma al'amarin *Baban- baba* daya tsaya mata a cikin rai. Hawaye masu zafi suka dinga karakaina a saman fuskarta hakika maraici bala'i ne tabbas da uwarta tana raye a duniya ta san ba za tayi irin wannan rayuwar ba, Baba Asabe itace ta haifi mamanta itace kuma ta haifi Kawu Musa mahaifin Saliha kenan amma ba tasan me yasa take fifita Saliha a kanta ba, Gashi dai duk ita ta haifi iyayensu amma tafi son Saliha a kanta duk abinda Saliha za tayi daidai ne a gurinta amma ita abu kad'an idan tayi sai ya zama laifi. Ta shigo dakin ta sameta tana kuka, sai jikinta ya kara sanyi murya ta d'aga da karfi ta ce."Kukan me kuma kike bayan ubanki yazo ya fanshe ki ashe dama yana da kudi mugunta ce take sa baya zuwa ya bani wani abu duba da irin dawainiyar da nake dake ko tausayin tsufa na ba ya ji." Ta mi'ke zaune cikin 'bacin rai da masifa irin ta kurame! tace."Wai shin Baba ni d'in bare ce a gurinki? ko kuwa bake kika haifi uwata ba?" Ta rike baki tana kallonta da fadin." Ni kike wa tsawa yau kuma tambotsan naki a kaina zaki sauke shi?" Tace"Ni tambayarki nake ina so ki bani amsa? Tace."Ni ce na haifi Uwarki na kuma Haifi Musa su biyu kacal Allah ya ba ni sai me kike so kiji.? Tace."To me yasa kike 'bakin ciki don kin kula dani kin ciyar dani kin tufarta dani don kinyi min d'awainiya shine kike gorantawa ubana ai sai yana dashi zai zo ya baki." Cike da dumbun mamaki tace."Shahida yau ubanki kike fifitawa a kaina.? Tace."Kada kiyi min mummunar fahinta Baba ina so na nuna miki Kuskuran da kike aikatawa kada ki d'auka bana fahimtar komai duk abinda kike ina lure dake kin fi k'aunar Saliha a kaina meye dalili? ko don ita ubanta yana baki kudi ni kuwa uwata ta mutu bata raye babu abunda take tsinana miki shine kike gallaza min saboda kawai tsautsayi ya ratsa an sace kud'inki shine har zaki tattara min kayana ki watsa waje wai kin kore ni Haba Baba ke baki ji kunya ba." Baba Asabe bakinta ya mutu kallonta kawai take ta cigaba da cewa." Tunda kika dasa sayar da man gyada a gidan nan ni nake zuwa na saro miki kuma bant'ba zubar miki da kudi ba sai wannan karon amma saboda rashin tawakkali kika fita duniya kina zage-zage kowa yana kallonki ai wannan abun kunya ne." Baba Asabe ta fashe da kuka tasa gefen zaninta ta fyace hanci ta ce."Lallai Shahida wuyanki ya isa yanka ni kikewa rashin kunya ko kuma dai Jamilu da Talatu sunyi miki hud'uba akaina." Tace."Ni ina ruwana da Talatu itama ai ba k'aunata take ba kuma Abbanmu ba zai zuga ni nayi miki rashin kunya ba." Ta goge fuska da fadin." To babu laifi tunda a karan kanki ki kaga dacewar hakan na gode." Tana 'kare maganarta sai ta kama hanyar fita tana goge fuskarta. Komawa tayi ta kwanta tana jin wasai a cikin ranta dama abubuwan da ake mata a gidan yana damunta yau dai ta amayar da abunda yake cikinta ta samu sa'ida. Ta shigo d'akin ta tsaya a kanta cike da tsageranci ta d'aga murya da fadin." Shahida ke marakunyar ina ce da zaki dinga farfad'awa Baba magana kamar wata sa'arki." Dama a ciki take da ita sai ta zabura! ta mike tsaye jikinta har tsuma! yake cikin yanayin maganarta tace."Mara kunyar gidanku ce! nace mara kunyar gidanku ce idan kina da mataki ki dauka." Saliha ta tsorata domin ta san halinta idan tana cikin bacin rai! bata lank'wasuwa kuma idan fada ya ratsa a tsakaninsu da wuya take kai labari domin lilis! take mata. Sai taja baya, bata daddara ba tace."To mara kunya Da kika mike tsaye kina wani zabura! duka na za kiyi ne kin san dai ni ba sa'arki bace." Tace."Ki fita ki bani guri bana bukatar ganinki ni duk wanda ba zai ja girmanshi ba to zan hau kai na taka kuma ke baki cancanci na baki girma ba saboda kema baki da ladabi." Tace."Don Ubanki ni ce mara dalabi.'' Tace."Ubanki dai domin uba bai fi uba ba ehe.! Saliha ranta ya 'baci kawai sai ta fitar da hannu ta kai mata duka, ai kafin kice me! ta cukumeta ta matseta jikin bango! tana dukanta ta ko'ina." Saliha ta dinga ihu! tana kakari tare da kiran sunan Baba wai tazo ta ceceta. Ita kuwa Shahida dukanta kawai take sai kace wata mai iskokai. Hankali a tashe ta shigo dakin tana fadin." Sai da nace ki kyaleta saboda kinfi kowa sanin halinta idan tana irin wannan halin babu maganar wanda ta ke ji kuma 'karfi ku ba daya bane kin girmeta amma ta fiki 'karfi duka take miki." Saliha na ihu! take fadin." Ki janyeta ni ba surutu za ki yi ba ta matse min wuya zata kashe ni." Cikin rarrashi da kwantar da kai tace." Yarinyar kirki yi hakuri ki saketa ai ta daku kada kiji mata ciwo kinga k'arfinku ba daya bane kiyi hakuri ta daina yi miki katsalandan a cikin al'amuranki." Banza tayi mata ta cigaba da dukanta tana mintsininta! Baba ta cigaba da banbanki tana kwantar da kai da 'yar murya tace."Shahida kinga bani da lafiya kada wannan 'bacin ran yasa ciwona ya tashi yau da 'kyar zan iya bacci sakamakon wannan al'amari banji dadin maganganun da ki ka fad'a min ba." Ta fashe da kuka tana cigaba da maganar daso ta tabbatar mata da cewa abun yana ci mata towo a kwarya. Ganin yanda take kuka ne yasa ta saketa ta koma gefe tana mayar da numfashi, Saliha data samu kanta sai ta wawuri! wani gwangwani da Baba ke ajiye-ajiye a ciki ta kai mata duka dashi da fadin." Shegiya mayya 'yar mai dattin hula." Da yake 'kasa-'kasa tayi maganar yasa ba taji ba, Baba ta buga mata tsawa tare da nuna mata hanyar fita, tana numfarfashin wahala ta fita d'aga dakin. Baba ta rufa mata baya ba tare da ta sake wata magana ba. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi join domin samun damar karanta littafi na d'aya. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *9&10* Kwana biyu da faruwar al'amarin Shahida ta samu sau'kin tsangwama! gami da aikace-aikacen da aka d'ora mata, Yanzu Baba Asabe tana k'okarin kamanta adalci a tsakaninsu, tunda ta fahimci cewa yarinyar na yi mata. mummunar fahimta. Tsakanin Saliha da Shahida babu mai magana da d'an uwansa gaba su ke yi duk da laifin na Saliha ne tunda a daran ranar da al'amarin ya faru ita Shahidan tayi mata magana amma taki amsawa. Sai kawai itama ta watsar da ita ta cigaba da sabgoginta ita kad'ai, Ita kuwa Baba Asabe jira take Kawu Musa yazo ta sheda masa abinda yake faruwa tunda ita basa jin maganarta. Baba Asabe na daga cikin rumfar kwanon da take zama domin sayar da abinci, gabanta babban baho ne cike da shinkafa fara da gurasa a ciki gefe guda kuma manya-manyan tukwane ne a kan murhu cike da miyar tattasai da taushe da nama tare da 'kashi a ciki, miyar sai k'amshi take. Baba Asabe ta jima tana sana'ar sayar da abincin shiyasa tayi suna a unguwar kowa ya santa a kan sana'arta kayan miya mota guda ake sauke mata, bayan sana'ar sayar da abinci tana sayar da man gyada da manja da sauransu, mijinta ya kai shekara ashirin da mutuwa tunda ya mutu ta kafa sana'a da ita ta dogara take rufawa kanta asiri har ta taimaki wani d'anta Kawu Musa da ya rage mata a duniya tana masifar sonsa shiyasa take fifita 'ya'yansa akan kowa kuma duk rabin abinda take nema nasa ne kullum idan yazo gidan kamar k'aramin yaro sai ta 'dauki kudi ta ba shi, shi kuma saboda rashin tausayi yasa hannu ya kar'ba, Kawu Musa babu yanda be yi da ita ba akan ta mayar da Shahida gidan ubanta tace A'a ba zata mayar da itaba tana kallonta a matsayin mahaifiyarta, A ransa baya son zaman Shahida a hannunta a ganinsa ba itake da alhakin d'aukar nauyinta ba shiyasa duk sanda yazo gidan sai ya zuga ta akan yarinyar watarana ta d'auki maganarsa sai su had'u suyi ta caccakar uban yarinyar a gabanta don ma dai kurma ce ba taji sosai amma dai duk ranar da suka so ta ji zagin da sukewa ubanta da 'karfi suke maganar Sai dai kawai ta shiga daki tayi kuka, Wannan damar Saliha ta samu take yi mata iskanci iri-iri. Kabewa take ferayewa ita kuma Saliha tana gyara Alayyahu, Haladu yayi sallama a gidan, kai tsaye gurin da'aka tanadar musu ya nufa ya zauna tare da cire hularsa ya kifa a gwiwarsa. Ta kalleshi da fadin." Haladu da alama yanzu ka dawo daga kasuwa.? Yace."Kwarai kuwa uwar towo dawowa ta kenan ko gida ban shiga ba na garzayo gurinki domin na 'barje gumi na." Baba Asabe tasa dariya tana gyara zaman lalitar dake rataye a wuyanta, tace."Hohoho! Haladu ba dai son dad'i ba ina jin dai kana adalci a gidanka ma'ana kana yi musu kyakykyawan cefa ne." Gemunsa ya sosa cikin inda-inda ya ce."Sosai nake musu cefane mai kyau amma shashashan babu abunda suka iya sai rage kudin cefane gabad'aya babu wacce ta iya abinci a cikinsu shiyasa nake zuwa nake cin kud'ina anan." Tana 'yar dariya ta ce." To Allah ya rufa asiri me zaka siya shinkafa ko gurasa da miya?" Ya ce."Shinkafa da miya da rabin kaza." Da yake da dan 'karfi yayi maganar yasa tayi saurin kallonsa tana girgiza kai dama haushinsa ta ke ji ta san abinda za tayi masa. Baba Asabe ta had'a masa komai ya juya bayansa yana ta kai loma. Saliha ce kad'ai ta lura da fitarta to da yake ba magana suke da juna ba shiyasa bata tambayeta ina za ta je ba. Minti biyar ta dawo ta cigaba da aikinta, ba tare da damuwar komai ba. Lokacin da Haladu yake ya gar cinyar kaza lokacin suka shigo gidan hayaniyarsu tasa cinyar kazar ta su'bce ta fad'i kasan gurin, ya lashi 'kasan bakinsa yana bin su da kallo. Indo Uwar gidansa tabi cinyar kazar da kallo kafin ta kalleshi sai muzurai yake kamar kace kyat ya ruga a guje alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare dashi. Lubabata amaryarsa ta sunkuya ta d'auki cinyar kazar tana nuna masa da fadin." Ashe abinda kake kenan a bayan fage Haladu wai me yasa kai azzalimi ne? Kullum sai kace mana kasuwa babu ciniki ashe nan kake zuwa ka baje kolinka mu ka barmu da wahalar yara da da'wainiya dasu. Indo tayi 'kwafa tana girgiza kai tace."Yau Allah ya tona maka asiri Haladu daga nan gidan sai gidanmu dama na gaji da zaman wahalar nan." Baba Asabe tace." Haba Indo ai ba za'ayi haka ba idan rai ya 'baci hankali ake sawa ya duba shi kiyi hak........"Ke kin ga dakata Asabe!" Lubabatu ce ta katseta tana hura hanci ta ce."Ai dole ki fadi haka mana tunda kullum ke yake zuwa ya yi wa ciniki saboda haka kawai ki ja bakinki kiyi shuru. Baba Asabe ta rike baki da fadin." Lubabatu rashin kunya zaki min daka gyara kayanka sai ba'kar magana. Cikin borin kunya ya ce."Ki rabu dasu Uwar towo duk in da za su je su tafi dama meye amfaninsu ku tafi din, amma ku aje min yara na domin ina da yanda zanyi dasu kudi kuma dole na ci abuna tunda ba uwar uban wani ne ya nema min ba." Fadin wannan magana da ya yi sai ya fusata! su suka shiga ci masa mutunci da gore-gore! Baba Asabe hankalinta ya tashi mutuka tsoronta Allah tsoronta Annabi kada Haladu ya saki matansa akan wannan dalilin. Da kyar ta rarrashesu suka fita daga gidan, shi kuwa Haladu har bayan magariba yana gidan ya kasa tafiya ashe duk fuffukar 'karya yake ya aika yara har biyu domin su duba masa sai su dawo suce gidan a bude yake Indo da Lubabatu suna nan babu inda su ka je Jikinsa yayi masifar sanyi fargabarsa d'aya kada ya shiga gidan su ci 'kwal ubansa dama kansu a had'e yake duk kisan mummu'ken da yake musu basa fad'a da junansu k'o'karinsu ya za'ayi su rufawa kansu asiri. Tsaki ya ja ya cire hularsa ya ajiye ya cigaba da zare ido akan jama'ar dake shige da fice a gidan. Sai da jama'a su ka yi sauki kana ta kalleshi da fadin." Haladu kayi jugum! ka tashi kaje gida komai yayi zafi maganinsa Allah amma don Allah ka sauya halinka ban ji dadin abinda ya faru ba kaga yanzu ni kaina a cikin zargi nake tunda a gabanka matarka Lubabatu take nuna ni da ya tsaya tana so ta dauki laifin kacokan ta dora min alhalin ni ban san abinda kake aikatawa ba na san dai kullum babu fashi za ka zo ka sayi abinci a gurina wannan shine abinda na sani." Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki hularsa yasa a sanyaye ya kama hanyar fita jikinsa duk a sa'bule, Shahida kamar ta fashe da dariya duk suka bi shi da kallo yana tafiya zugwi-zugwi kamar wanda k'wai ya tashewa a ciki. Bayan fitarsa dariyar da take boyewa ta sub'ce a fili ta ce."Karshen munafiki jin kunya." Saliha ta kalleta kamar za ta yi magana sai kuma ta ja bakinta tayi shuru tana girgiza kai. Ita kuwa Baba Asabe surutai take ita kad'ai akan maza masu irin wannan hali ko meye abin burgewa a gurin mazan dake ganin k'yashin ciyar da iyalinsu oho! **** Bayan kwana biyu ta fakaici idon Baba Asabe tasa hijibi ta fita, kai tsaye bakin titi ta nufa, idonta a gurin zamansa babu shi babu dalilinsa sai tarkacen kwaran-kwacamansa! ta jima a bakin titin tana kalle-kalle gabad'aya jikinta ya mutu saboda rashin ganinsa idanuwanta suka cika da ruwan hawaye. Wani yaro dake tafiya ta tsayar dashi tana tambayarsa. Yaron yayi mata wani irin kallo kafin ya ce."Ni ina ruwana da wani Baban- Baba ki je ki tambayi 'yan uwansa mahaukata" Yana gama maganarsa ya shige ya barta a gurin, taji kamar ta janyoshi ta gaura masa mari ta tsani a dangantashi da mahaukaci domin ita a ganinta ba taga haukan da yake ba tunda baya doke-doke. Wani kuttun! abu yazo ya tsaya mata a wuya ta juya domin komawa gida tamkar mara jini a jika haka take tafiya salo-salo! har ta isa gidan bata daina tunane-tunane a kansa ba. Kai tsaye uwar daki ta shige ta kwanta kan gado kai tasa a cikin hijabi ta fara zubda hawaye. Baba Asabe dake kokarin hura wuta ta ce."Saliha tunda ta dawo daga gantalin jeki ce tazo tayi wannan wanke-wanken. Saliha ta amsa da "To." Kai tsaye dakin ta shiga ta tsaya a kanta, "Ke! ki je ki kiyi wanke-wanke inji Baba." Tana jinta tayi mata banza, Tasa hannu tana kokarin fizge hijab din data rufe fuskarta dashi, Cikin zafin nama ta doke hannun! har sai da yayi 'kara. Saliha ta fita da hannu a sage! murya na rawa tace." Baba tana jina sai magana nake tayi min banza 'karshe ma hannuna ta buge duba sai zafi yake min." Tace."Rabu da ita zan shiga dakin na sameta." Saliha ta koma ta zauna da fadin." Wallahi Baba akwai ranar da zan sanya bulala na zane ' Yar iskar yarinyar nan na gaji da abinda take min." Tana kokarin fitowa daga kicin din tace."Idan kina ganin zaki iya da ita bisimillah ni babu ruwana to ka ji." 'Dakin ta shiga sai kawai taji shashshekar kukanta A sanyaye tace."Saboda na ce kizo kiyi wanke-wanke shine kike kuka?" Shuru tayi mata, Baba ta sake daga murya gami da maimaita maganarta. Ba tare data bude fuskarta ba tace." Me yasa kullum ni nake wanke-wanke a gidan nan idan gaskiya ne itama Saliha tayi saboda kinfi sonta shine kika bata aiki mai sauki ni kika bani aiki mai wahala ni wallahi na gaji haka kawai sanyi ya kamani idan gaskiya ne ki dauki 'yar aiki mana." Baba Asabe ta ji kanta yana juyawa da ita a gurin al'amarin ya bata mamaki mutu'ka. Ta ce."Shahida ni kike fad'awa wannan maganganun yaushe kika lalace?" Tana kuka tace."Ni kuskuranki nake so na nuna miki abinda kike ba daidai bane." Baba Asabe ta fashe da kuka da fadin." Mariya kin tafi kin bar baya da k'ura ni na haifeki a cikina amma baki tozartani kamar yanda 'yarki take tozartani ba, ni ba zan hofintar da zuriarki ba koda kuwa yarinyar nan zata dauko abin duka ta dake ni ba zan damu ba duniya ce ta ishi bagaruwa jima." Kuka take sosai wanda ya sanya Saliha ta shigo dakin hankalinta ya tashi sosai! sai rarrashinta take, A fusace! ta fita daga dakin, Ashe Kawu Musa ta kira a waya, ta sheda masa abinda yake faruwa, yace." Gashinan kan hanya. Baba Asabe na raku'be a jikin gado tana kuka da fyace hanci ita kuma Saliha tana tsaye a tsakiyar dakin sai Zaginta take da gore-gore! "Shegiya ai idan ba ki yi haka ba to ba ki cika 'yar gado ba, wannan mahaifin naki ai butulu ne masu ba'kin hali wai ace matar dake tallafarki ita kike wa rashin kunya ai yau zaki gane baki da wayo! Baba ta daga mata hannu da fadin." Saliha yi shuru da bakinki Ni tayi wa rashin kunya bake ba kada na kara jin maganarki. Gefe ta koma tana huci! Shi kuwa Kawu Musa yana zuwa ai bai yi wata-wata ba ya zari wayar redio ya fara lafta mata yana d'ura mata ashar! ,Fadi yake." Wallahi ba'kin cikinki ba zai kashe min uwa ba don ubanki yau sai kin bar gidan nan domin dama hakkin ri'ke ki ba a hannunmu yake ba. Da 'karfi yake maganar yana dukanta. Baba Asabe ta rike wayar tana janye shi daga gurin, "Ka daina dukanta kada kaji mata ciwo." Ita kuwa Fad'i take." Ki k'yale shi ya cigaba da dukana ya kasheni Kawu Musa idan baka kasheni ba wallahi baka cika dan halak ba." Maganar ta dinga yi masa kuwwa! a kunne! Ya nuna kirjinsa da hannu! " Ni kike fadawa haka? Tana kuka tace."Me yasa kake nuna min 'kiyayya! me yasa baka 'kaunata? me yasa kake fifita 'yarka a kaina? duk abinda kake min ina fahinta baka kaunata kullum idan kazo gidan nan cikin zuga Baba kake akan ta mayar dani gaban ubana, duk da ba naji sosai watarana na kan tsinkayi abinda kake fad'a akaina saboda haka nima bana sonka tunda baka kaunata." Kawu Musa jikinsa yayi sanyi, ya jefar da wayar redion ya kama hanya ya fita daga dakin kunyar duniya ta ishe shi. Ita kanta Salihan ganin yanda jikin babanta yayi sanyi yasa ta kasa daga kai ta kalleta simi-simi ta fita daga dakin. Tana kuka ta fara hada kayanta, Baba Asabe da sauri taje ta rufe sif din da mukkuli ta fita daga dakin.......Gabadaya haka suka kwana suka wuni cikin bacin rai mai tsanani, kuma tun daga ranar Baba Asabe take takatsantsan! da yarinyar bata tilasta mata kan cewa dole sai tayi mata aiki, Ita da kanta take tashi tayi abinda ba'a rasa ba amma ta daina aikin ruwa saboda tana gudun sanyi ya kamata, dama tayi wannan boran ne don ta samu sassaucin aikin ruwan da ake sanyata kullum ta Allah.*MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Fejin na yau na ku ne 'kannena biyu🥰* _Jamila Jamy 'Yar kankia_ Tare da: _Ummu-Hanifa_ Kuna da matsayi mai girma a gurina💯 *11&12* *WAIWAYE* Shekarun baya da suka wuce Baba Asabe da mijinta Malam Almu sunyi zama na mutunta juna gami da girmama juna, haihuwarsu biyu mace da namiji Musa shine babba tsakaninsa da 'yar uwarsa Mariya akwai tazara amma ba mai tsayi ba, A lokacin da Baba Asabe ta auri Malam Almu ya tsufa sosai bai ta'ba haihuwa ba har ya fitar da rai sai gashi cikin ikon Allah yana auranta Allah ya azurtashi da zuria, yayi farin ciki sosai ya dauki son duniya ya dorawa yaran ashe ba zai jima tare dasu ba Allah ya dauki rayuwarsa. Uwargidansa dama bata haihu ba wannan dalilin yasa ana raba gado ta tattara kayanta ta tafi garinsu. Gida ya rage Baba Asabe da 'ya'yanta, Tun daga lokacin ta kafa sana'ar sayar da abinci wanda da yawa mutane da dama suka dinga ganin rashin hankalinta a ganinsu ai bata wuce aure ba amma zata zauna ta lalata 'kuruciyarta a banza a wofi, To Duk zantukan dake yawo a gari suna dawowa kunanta, tayi banza da surutan mutane ta cigaba da sabgarta da kula da yaranta. Da yawa wasu mazan da biyu suke zuwa sayan abinci gurinta domin su kafa gwamnatinsu, cikin ikon Allah Alhaji Haruna ya samu shiga a gurinta ta kudiri aniyar auransa domin tana yi masa kallon nagartaccen mutum ashe kallon kitse takewa rogo auran beje ko'ina ba ya lalace a sakamakon nuna kyara! da hantara! da yake akan 'ya'yanta. Da farko ta nuna masa kuskuransa akan abinda yake ta kuma gargad'eshi ya daina. Sai shi kuma yayi kunnan uwar shegu da maganarta duk sanda yazo gidan to fa yaran basu da walwala sun dinga takurewa kenan gabadaya sun tsorata dashi domin kuwa wani sa'in har fakaitar idonta yake ya doke su, mahaifinsu kuwa dake karkashin 'kasa yana shan zagi! Sosai Alhaji Haruna yake *(Kishin kushewa)* akan yaran. Baba Asabe data gaji da iya shegen da yake mata sai kawai ta fito masa a mutum tayi masa wankin babban bargo, 'Karshe tace dashi babu lallai babu dole idan ba zai juri zama da 'ya'yanta ba to ya saketa domin kuwa ba zai zo har gida yana cin arzikin yara ya takura musu ba.'' Alhaji Haruna ya fusata! ransa ya baci a ganinsa babu amfanin auran macen dake da 'ya'ya tunda duk tsiya watarana sai ta tuna ubansu kuma soyayyar da take nunawa yaran ai kamar ubansu take nunawa, kawai sai ya yanke shawarar sakinta domin dai shi yana kishin ya budi ido yaga yaran a matsayin 'ya'yan wani ba nasa ba, Sai kawai ya rubuta mata saki biyu ya kama gabansa. Baba Asabe ranta ya baci sosai tayi kuka😭 mai yawa ta share hawaye ta barwa Allah lamarinsa, amma a zahirin gaskiya abin ya jima yana cin ranta ace wai shikkenan daga zarar mijin mace ya mutu ko kuma mace ta rabu da mijinta kan wani dalili shikkenan ita da 'ya'yanta sun zama abun 'kyama da wulakantawa a gurin wasu mazan, wannan ba daidai bane wallahi maza kuji tsoron Allah ku tausayawa mata mutukar mace zata sadaukar da rayuwarta a kanka da 'ya'yanka meye abin gudu a tare da ita, 'Ya'ya ne abin gudu kai ma kana dasu, kuma ba dole akace ka rike 'ya'yan da ba naka ba, *(Maza idan zaku auri bazawara to kuyi adalci kada kuso zuciyarku kan wani dalili shi aure na mutum biyu ne yarda da aminci shike janyo har a kulla auratayya amma sai kuga wasu mazan suna gudun mace mai 'ya'ya sai kace ance dole suyi wa yaran d'awainiya da d'an mutum da dukiya ba ai musu mugunta kuma ita rayuwa juyawa take wanda kake gudu sai ya taimake ka watarana)* Tun daga wannan lokaci Baba Asabe ta cire rai da aure kawai ta cigaba da neman kudinta, Allah kuwa ya shiga cikin al'amarinta tafi karfin yau da gobe da duk wani abunda ba za'a rasa ba. ******* Manyan mutane masu mutunci da dattako suka dinga turereniya gurin zuwa neman auran Mariya amma funfurus! ta shafawa idonta toka ta kore su, al'amarin daya fusata! Baba Asabe kenan ta rufeta da fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ta cigaba da cewa"Shi wanda kike kulafuci shin kina da tabbacin zai aureki? Babu wanda be san halin Jamilu ba gurin yaudarar yaran mutane me zakiyi da Jamilu manyan mutane masu mutunci suna tururrubi akanki! Ko kin dauka kinfi karfinsu ne? to bari kiji bayan kyawun jikin da kike dashi to baki da komai sai tarin muni duk ga 'yan mata nan masu kyau a gari wanda suka fiki komai basu dauki kansu wata tsiya ba sai ke to mutukar ni na haifeki ba zaki auri Jamilu ba." Da jin wannan magana sai ta dora hannu aka ta kurma ihu! tana kiran ta shiga uku ta lalace! Makota suka shigo suna tambayar ba'asi. Takaici da bakin ciki yasa Baba Asabe kasa magana ta koma ta zauna tana me cigaba da sabgoginta. Mariya ihu! take tana fadin." Ban ta'ba yi miki rashin kunya Baba ban ta'ba bijirewa umarninki ba duk abunda kike so shi nake so, ke kika zama gatana ban taso da ubana ba amma kin share min hawayen maraicin uba ina so kiyi min adalci a rayuwata kiyi hakuri na auri wanda nake so Jamilu shine rayuwata!" Jama'ar dake tsaye a gurin suka shiga mamakin al'amarin, Baba tace."Kun dai ji da kunnuwanku abunda take fada, Shin kuna da tabbacin Jamilu auranta zaiyi ko kuma yaudararta yazo yayi sanin kanku ne kafin yazo gurinta ya yaudari 'yan mata da yawa a cikin unguwar nan to me zai sanya ina ganin kashi da rana na taka auran Jamilu bashi da fa'ida tunda shi bashi da hali uwa uba kuma bashi da sana'a" D'aya daga cikinsu mai suna Huwaila tace."Ki yi hakuri ki barwa Allah al'amarin domin kuwa shi aure nufi ne na Allah kuma naji kina maganar Jamilu bashi da sana'a Aa yana da sana'a domin shago guda ne dashi a kasuwar wambai kawai dai aure ne be yi ba ya tsaya shiririta amma ki bari ni nayi miki alkwarin zuwa gidansu domin mu tattauna da mahaifiyarsa idan da gaske yake to ya fito ayi magana idan yana yaudaran yaran mutane to mu ba zai yaudare mu ba." Baba Asabe ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Shikkenan Huwaila Na gode Allah ya jishshemu alkairi." Huwaila ta amsa da ameen kafin ta rungume Mariya tana rarrashinta. Koda Huwaila ta samu mahaifiyar Jamilu da maganar kai tsaye tace ita sam bata ma san da maganar ba, amma idan ya dawo zata tambayeshi duk yanda ake ciki zata zo har gida tayi mata bayani. Bayan sunyi maganar da mahaifiyarsa ya nuna mata shi sam be san da wata Mariya ba ballantana ya je neman auranta saboda haka ta daina yarda da jita jitan mutane akansa aure nufi ne na Allah idan lokacinsa yayi to ko yana so ko baya so sai yayi. Sai jikinta ya mutu tace."Anya Jamilu ba zaka nemi maganin baki ba kuwa na fahimci cewar mutanan unguwar nan sun sanya maka ido." Dariya kawai yayi ya shashantar da maganar. Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin ya zauna yayi dogon tunani akan al'amarin a zahirin gaskiya Mariya bata da wani kyawun azo a gani amma kyawun jikinta yana mutukar rud'arsa yana masifar son cikakkiyar mace amma kuma yana so ya dawo gida yaga kyakykyawar fuska nayi masa sannu da zuwa. Murmushi yayi lokacin da ya tuna ai Ubangiji Allah ya hallata masa auran mace fiye da d'aya saboda haka zai auri Mariya saboda kyawun jikinta nan gaba kuma idan ya samu fara kyakykyawa sai ya aura ya samu ta shiga cikin taron jama'a wacce zai sanya a gaban mota yana zagaya gari da ita. Ya shedawa mahaifiyarsa shawarar da ya yanke kan cewa taje ta shedawa Huwaila cewa Eh tabbas da gaske yake zai auri Mariya domin ma yanzu ma shirye-shiryen kawo kudin aure yake. Farin ciki ya lullubeta aikuwa ba taja dogon lokaci ba taje ta shedawa Huwaila halin da ake ciki Huwaila cike da farin ciki ta yafa mayafi domin zuwa ta shedawa Baba Asabe abinda yake wakana. Baba Asabe addua kawai tayi ta barwa Allah amma daga can 'bangaran 'yan uwan Malam Almu an dan samu matsala domin sun so su hana faruwar al'amarin mussaman da sukayi binkice suka tabbatar da munanan halin Jamilu wanda ya zama abun gudu ga ko wane managarcin mutum. Jamilu yana ganin haka sai ya shiga musu facaka da kudi lokaci guda ya toshe musu baki. Kuma ba'aja dogon lokaci ba akayi komai a ka gama. amarya ta tare a gidanta dake unguwar ja'in. Jamilu ya ga fa'idar auran Mariya domin daga sanda aka daura auransa da ita k'ofofin samu suka bude daga gareshi Allah ya albarkaci kasuwancinsa, a maimakon ya nutsu ya yi abinda zai taimaki rayuwarsa ai sai kawai ya hau shiririta da shirme, burni yake sosai ya sayi sabuwar mota kana kuma duk bayan wata biyu yake fitar da tufafinsa ya zuba wasu takalma da huluna gami da agogona kamar hauka a dakinsa, turare kam be yarda da mai arha ba mai tsada yake fesawa, Mariya tana ganin ikon Allah domin duk irin shawarar da take bashi baya dauka idan ta matsanta masa sai ya rufeta da fada da fadin kudinta ne ko nasa! Haka ta naji tana kallo ta zuba masa ido sai dai labarin duk abinda yake aikatawa a gari yana dawowa kunnanta tana da labarin yanda yake kashewa matan bariki kudi. Sosai al'amarin yake cin ranta gashi har sunyi shekara da aure amma babu labarin haihuwa ta fahimci kuma shi sam abun bai dameshi ba harkar gabansa kawai yake. Ta sameshi da maganar tana so ita dashi suje asibiti a dubasu domin a tabbatar musu da lafiyarsu. Yayi funfurus! ya ce shi babu inda za shi lafiyarsa lau don haka kada ta 'kara yi masa maganar zuwa asibiti. A ranar taci kuka ta koshi kuma yanzu ta fara nadamar auranta dashi dama wannan badakalar mahaifiyarta take guje mata, yanzu da kunya ta tunkareta da maganar domin kuwa tun farko itace ta za'bi auransa dole tayi hakurin zama da mugun halinsa. Haka ta cigaba da hakuri yau fari goma baki don ma dai yana kokari ta fannin ci da sha daba don haka ba da ba zata ganu ba. Tana kokarin warware matsalarta sai wata ta matsalar ta shigo domin kuwa mijin nata aure ya rakito ashe tuntuni har an kai kudi dasa rana bata sani ba sai ana saura kwana biyu daurin aure yazo ya ajiye mata leda viva da kayan fadar kishiya a ciki. A ranar kwanan kuka tayi ta kudiri aniyar gari na waye wa zata tafi gidansu domin kuwa ba zata iya ganin wannan ba'kin cikin ba. Yana d'akinsa yana shirin fita kasuwa ta fita daga gidan, koda ya fito yaga bata nan be wani damu ba dama yayi tsammanin faruwar haka, aure zai yi babu wanda ya isa ya hana shi. Baba Asabe ta rufe idonta tace sam! bata yarda ba don haka tayi maza ta tashi ta koma dakinta ai duk wanda ya sayi rariya ya san zata zubda ruwa don haka ita bata da gurin kwana. Haka nan tana ji tana gani ta koma gidan Jamilu koda ya dawo ya sameta a gidan, a maimakon ya rarrasheta ai sai ya tsiri gaba da ita ya dai nai mata magana har aka daura auran baya kulata. Ta sake shiga halin ni 'yasu ta ko'ina babu sassauci sai ta mayar da hankalinta gurin ibadah da ro'kon sauk:i daga rabbis-samawati. Jamilu da amaryarsa suka dinga sheka amarci ayi wanka tare aci abinci a tare sannan kullum da daddare idan ya dawo daga kasuwa ya sata a gaban mota su tafi su zaga gari ko ranar girkinta ko ba ranar girkinta ba. Amarya Hafsa ta dinga jiji da kai a gidan tana zubar da habaici ita ga matar da akeso, ita kuwa Mariya ta tattara komai ta barwa Allah ta zuba musu ido. Aikuwa tafiyar ba tayi nisa ba amarya ta samu ciki, yana fahimtar haka sai yaje ya samo mata maganin zubar da ciki ya tsaya a kanta sai da tasha. A daran ranan cikin ya zube. Taci kuka ta koshi domin ita taso ta haihu ko don tayi wa Mariya gadara da hujja. Koda ya fahimci amaryarsa tana da saurin da'ukar ciki sai ya daina kusantarta kai tsaye sai yasa kwaroron roba(condem) sannan yake auratayya da ita, Hafsa amarya ranta ya b'aci mutuka sai ta daina amincewa dashi, aikuwa be ji kunyar ci mata mutunci ba domin tsakar gida ya fito ya dinga zazzaga mata tujara da fadin." Dama lalurace tasa ya aureta ba wani gamsar dashi take ba ta dubi matarsa Mariya cikakkiyar macace me zai yi da ita idan ba kaddara ba. Hafsa ta dinga kuka tana mamakin halin d:a namiji. Ita kuwa Mariya ba tayi mamaki ba domin ta san abunda yafi haka zai iya aikatawa ita tafi kowa sanin halinsa Tun daga ranar ya mak'ale mata ya dinga rarrashinta da kalamai masu dadi har da fadin kaddarace ta sa shi aure amma me zaiyi da wata bayan yana da ita. Ita dai jinsa kawai take ta san ba komai yakewa dadin baki ba sai ni'imar da Allah yayi mata duk daran duniya baya iya hakuri sai ya kusanceta. Tsayin wata biyar haka rayuwar take tafiya Jamilu ya watsar da amaryarsa kamar bashi ya ajiyeta ba, sai kawai ta tunkareshi domin taji matsayinta, ya kalleta sama da kasa kafin yaja mugun tsaki ya ce."Wallahi ban san dalilin da yasa na aureki ba dubeki don Allah guntuwa dake hanci k'ato in banda farar fata baki da komai." Hafsa ta fusata! ta daga masa hannu da fadin." Kaga ya isa haka ka fada min matsayina a gidanka dama ai kafin na aureka sai da aka fada min halinka amma tsautsayi yasa na aureka. Ya sosa gemunsa yana mata wani irin kallo ya ce."Kwad'ayin abun duniya ne yasa kika aure ni ai tun kafin naje neman auranki na gane ke din mayyar kudi ce shiyasa na rud'eki dasu kuma na samu nasara, saboda haka yanzu baki da wani amfani a gurina kije na sakeki saki biyu." Hawaye suka k'wace mata ta ce."Sai Allah ya saka min wallahi kuma abunda kayi min sai anyi wa 'yarka." Ko a jikinsa ya rubuta mata saki a takarda ya bata harda kudi dubu biyar akan takardar, a fusace! ta watsa masa kudinsa ta fita daga d'akin tana kukan bakin ciki. *TAFIYAR TANA DA TSAYI😃* Ku karanta littafin a sannu a hankali, amma kada ku manta na fada muku cewa nayi amfani da salo biyu gurin rubuta littafin, sai a nan gaba za ku fahimta *BINTA UMAR ABBALE* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi Join domin samun damar karanta littafi na daya *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *13&14* Ya hujaj! bayan ya rabu da amaryarsa da wata uku sai ya hango wata 'yar dumur-dumur! mai cikar kirji fara tas da ita amma ba ta cika kyau a fuska ba dan Mariya ma ta fita kyawun fuska, to da yake yana da kudi a hannu bai sha wahala gurin siye zuciyar Talatu ba, dama ubanta talaka ne basu da komai koda yaje neman auranta basu wani tsananta binkice ba suka dauki 'yarsu suka bashi. Wannan karon ba'kin cikin da Mariya ta had'iya yafi wanda ta had'iya a lokacin da ya auri Hafsatu, Talatu fitinanniya ce ta ajin karshe gabad'aya ta kanainaiye shi ta hanashi gane fari da baki ita kadai yake gani a gabansa, iskanci iri - iri suke a gidan, Sai ya kasance Mariya ta zama 'yar kallo domin tunda Talatu ta shigo gidan shikkenan ta kar'be girki da mijin gabadaya tsayin wata shida itake juya gidan sai abinda take so za'ayi. Sai dai abinda Talatu bata sani ba shine duk ranar da ta tafi Unguwa shi kuma a lokacin yake samun damar shiga dakin Mariya yayi abinda yake bukata domin duk gigin da yake akanta ba wani cikakkiyar gamsuwa yake samu da ita ba, Yafi samun gamsuwar da yake bukata da Mariya. Cikin ikon Allah ciki ya samu kuma bai bayyana kanshi ba sai da yayi wata biyar, ita Mariyar ta san da zaman cikin a jikinta. kawai tayi masa shuru ne saboda tana gudun ta fada masa ya zubar dashi tunda tana ganin irin k'wayoyin da yake dubgawa matayensa. Aikuwa bala'i ne ya tashi a lokacin da Talatu ta farga da cikin tana kuka tana fadin." Ashe dama yaudararta yake yana kusantar Mariya gashinan har yayi mata ciki amma ita saboda mugunta duk sanda ta samu ciki sai ya bata magani cikin ya zube to dan haka wallahi ba zata yarda ba sai an zubar da cikin Mariya. Budar bakinsa sai yace."Ta kwantar da hankalinta shi wannan ciki ba nasa bane domin shi rabon da ya hada shimfida da Mariya har ya manta. Mariya tana share hawaye ta fito daga dakinta tana kallonsu a tsaye a tsakar gidan sai rarrashinta yake, Tace."Jamilu kaji tsoron Allah kaji tsoron ranar haduwar ka dashi, kai ka san wannan cikin na jikina kai ne ubansa amma ka ke shegenta shi. Ya nuna ta da yatsa da fadin." Rufe min baki munafurka Allah ta'ala har yaushe na kwanta dake da zanyi miki ciki ban yarda ba tun wuri kije ki nemi uban danki." Wani irin hawaye masu tsananin zafi suka shiga zuba a saman fuskata, ta dinga kokarin magana amma tsabar bacin rai ya hanata furta komai, a daddafe ta shiga dakinta, tasa hijabi ta fito. Ya kalleta ya watsar da fadin." Duk in da zaki tafi kije domin kuwa ba zan yarda da wannan cikin ba. Talatu zuciyarta tayi wasai dama babban burinta Mariya ta fita ta bar mata gidan ita kad'ai. Tsakanin Baba Asabe da Hujaj! rigima aka tafka ba kad'an ba! domin kuwa Baba Asabe cewa ita ba zata yarda da wannan 'kazafin ba sai ta maka! shi a kotu a maimako ya risina ya bata hakuri domin su samu daidaito a tsakaninsu, sai ya k'ara fusata yace idan kotun k'oli zata kai k'ararsa taje ta kai babu abunda ya dame shi. Baba Asabe kai tsaye kotun musulunci ta nufa ta d'auki lauya ya tsaya mata suka fara bugawa, da yake ita gaskiya duk inda take sai ta nuna kanta a take asirin Hujaj! ya tonu domin kuwa duk wanda zai bud'i baki a gurin ba zai fadi alkairinsa ba sai sharrinsa. Alk'ali ya tabbatar da shedu daga bakunan jama'a a take ya yanke hukunci kan cewa dole Hujaj! ya amince da wannan ciki domin addinin musulunci ne ya amince da hakan, koda bashi yayi cikin ba tunda har ya kasance a gidanshi a ka sameshi dole ya dauki d'an da za'a haifa a matsayin d'ansa, bayan haka kuma dole ya cigaba da kula da matarsa da cikin da take dauke dashi, Ci da sha da kula da lafiyarsu duk yana rataye a wuyansa. Mai sharia ya gama yanke hukunci ya buga katako alamun hukuncin ya tabbata, ya mi'ke. kotu ta tashi kowa na fadin albarkacin bakinsa. Bayan kwana uku ya samu takarda da biro ba tare da tunani da tsinkaye ba ya rubuta saki har uku da kansa yaje ya har gidan ya bada takadar ya futo abunsa. Baba Asabe ba ta iya karatun hausa ba, ita Mariyar ita ta karanta takardar a take a lokacin ta fadi a gurin, hankalin Baba Asabe ya tashi a wahalce aka kaita asibiti taimakon gaggawa akayi a kanta domin kuwa jininta ya kai k'ololowa gurin hawa. Haka Baba Asabe ta dinga kai kawo ita kad'ai dan ma dai tana da kudi a ajiye shiyasa ta samu saukin wasu al'amuran. A takaice sai da Mariya tayi sati uku a kwance a asibiti ta samu sauki likita ya dora ta akan magani tare da sharad'ai masu tsauri domin kuwa. hawan jini ga mace mai ciki babban matsala ne. Baba Asabe ta sake yun'kurin shigar da kara kotu domin tun sanda alkali ya yanke hukunci Hujaj! bai ta'ba zuwa ya kawo naira biyar a cikin abunda alkali ya yanke masa ba. Kawu Musa d'anta shine ya hanata yace ta bar maganar kawai su barshi da Allah domun duk yanda take tunanin Hujaj! ya wuce haka shaid'anin mutum ne, Sharia dashi bata da amfani. Baba Asabe ta hakura ta bar maganar suka kyaleshi da mugun halinsa, Bangaran Mariya kuwa sai addua domin ita kadai ta san irin kuncin da take ciki bata ta'ba tsammanin Jamilu zai tozartata irin hakaba. Allah al-musauwiru wanda bashi da tamka, ya fara saukar da ishara akan Hujaj! kasuwancinsa ya tsaya duk abinda ya ta'ba sai ya lalace ta kai ta kawo idan ya fita kasuwa haka zai wuni babu wanda zai zo gurinsa da niyyar sayan kayansa, Idan zai tafi gida sai ya ci bashi domin kuwa idan yaje gida babu kudi a jikinsa zasu kwana suna tafka rigima da Talatu. Wani abokinsa ya jashi gurin wani malami domin yayi masa duba acikin al'amuransa yaga abunda yake kai kawo. Kai tsaye malamin yace."Matarsa da ya rabu da ita itace mahad'in arzikinsa saboda haka idan yana so arzikinsa ya dawo tilas yaje ya dawo da ita gidansa. Jin wannan magana sai hankalinsa ya tashi ya dinga share zufa yana tunanin yanda za'ayi ya cigaba da zaman aure da Mariya bayan yayi mata saki uku. A hanyarsu ta dawowa gida Alhaji Shu'aibu ya kalleshi da fadin." Ya hujaj! naga duk ka tashi hankalinka wannan al'amarin fa duk mai sauki ne." Ya kalleshi cikin damuwa yace."Alhaji Sha'aibu ya kake kiran wannan al'amari me sauki saki uku fa nayi mata ta yaya zan aureta dole sai ta auri wani sannan zata hallata a gareni." Alhaji Sha'aibu yayi murmushi da fadin." Yanzu dai mu bari ta haihu akwai shawarar da zan baka." Yace." Alhaji zama cikin kuncin talaucin nan ya isheni wallahi." Yace."To ya za kayi kaine kayi ganganci ai irin wannan ba'a yanke hukunci kai tsaye sai mahukunta sun duba maka abunda ya dace da rayuwarka gashinan ka saketa ba tare da ka san itace abokiyar arzikinka ba." Hujaj! ya girgiza kai da fadin." Wallahi sharrin zuciya ne amma nan gaba dole na kiyaye a yanzu dai burina ta dawo hannuna ko arzikina ya dawo." Yace."Ka kwantar da hankalinka komai zai zo da sauki insha Allah. ***** Alhaji Sha'aibu shi ya cigaba da kwantar masa da hankali, amma duk da haka kullum cikin lissafin wattanin cikin yake sai da ta haihu sannan hankalinsa ya kwanta. Alhaji Sha'aibu shi ya bashi bashin kudi wanda yayi wa 'yar da aka haifa siyayya, sannan kuma shine ya jagorance shi zuwan gidan, kunyar duniya ta isheshi sai sunkuyar da kai yake, Alhaji Sha'aibun ne mai k'ok'arin magana Baba ta kalleshi da fadin." Da dai banyi niyyar yi maka magana ba amma ta kama dole sai nayi inaso ka bude idonka sosai ka kalli wannan 'yar dake hannunka." Yayi ta maza ya daga kai ya kalleta da fadin." Ai tunda na kalli yarinyar nan na tabbatar da cewa ni ne ubanta saboda haka don Allah Baba ayi hakuri kada ayi tone-tone duk abubuwan da suka faru a baya tsautsayi ne amma na san ban kyauta ba. Ta girgiza kai da fadin." To naji maganarka wane suna kake ganin za'a sanyawa yarinyar ."? Da murmushi a fuskarsa yace."Sunan mahaifiyata nake da niyyar sanya mata Maryama kenan." Tace."Shikkenan Allah ya raya ta yasa cikon addinin musulunci ce." gabadaya suka amsa da ameeen ya Allah." Da zasu tafi ya ajiye mata dubu biyar da fadin duk hidimar da ta tashi tayi da kudin kafin ranar suna." Ba tace komai ba har suka fita daga gidan, Ta girgiza kai da fadin." Kullum yana fama da malin-malin(babbar riga) sai kace limami amma shaid'ancisa yafi karfinsa. Itama Mariya dake uwar dakin maganar da take kenan, idan yana magana kamar mutumin kirki amma mugun halinsa yafi dubu! gabad'aya yanzu bata kaunar ta bude ido ta ganshi ta tsaneshi don dai kawai kaddarar aure ta ratsa a tsakaninta dashi babu yanda za tayi tunda ya kasance uban 'yarta dole tayi hakuri ta manta da abubuwan da suka faru a baya. Ashe rigima ce take jiransa a can gidansa. Ya shiga gidan cikin nishadi da walwala domin kuwa gani yake kamar Mariya ta dawo gidansa ta gama tunda Alhaji Sha'aibu ya fada masa shawarar da ya yanke kan cewa shi din ya amince zai yi *(Auran kisan wuta)* da ita zai saketa idan tayi wata daya ko biyu a gidansa, To tunda ya fada masa wannan magana yake farin ciki tabbas ya san Alhaji Sha'aibu ba zai cutar dashi ba. A tsaye ya sameta a tsakiyar tsakar gidan sai kace wacce aka dasa! tsoro ta bashi da sauri ya kira sunan Allah kafin ya fuskanci itace yaja mummunan tsaki da fadin." Talatu ke wace irin jahila ce zaki tsaya tsakiyar tsakar gida sai kace aljana ko wani siddabarun kike min a gida."? Ta fusata! dama a wuya take ta hayayya'ko! masa tana kumfar baki tace." Rufe min baki algungumi! munafiki duk halin da kake ciki na sani tsohuwar matarka daka saki ta haihu har kana siyayya kana kai wa jaririyar data haifa bayan da bakinka ka furta cewa ba kaine ubanta ba." Ya daga mata hannu da fadin." Kinga saurara min! idan kuma kin 'kiya zanyi maganinki ni ba shashashan namiji bane da zaki titsiye da maganganun banza ni ne nan Uban yarinyar da Mariya ta haifa kuma a yau nayi mata hud'uba da sunan mahaifiyata Maryama saboda haka ki hadiyi zuciya ki mutu." Ihu! ta kurma! taje ta cikwikwiye masa riga tana zaginsa da fadin." Ya cuceta wallahi ba zata yarda ba sai ya sake ta. Ya fizgeta daga jikinsa ya yar! a gurin yana fadin." Dama ai ke din baki dace dani ba saboda tunda na aureki komai nawa ya lalace baki da amfani a gurina a halin yanzu, Mariya ce mahad'in arzikina kuma zata dawo gidana babu gudu babu ja da baya, sannan wannan maganar da nake miki itace ta farko kuma itace ta karshe duk sanda kika sake cewa na sake ki to wallahi na gama auranki har abadah ni ba'a haka dani mace tamkar riga take a gurina.'' Yana maganar yana buge! babbar rigar dake jikinsa. Tsallake ta yayi yaje ya bude dakinsa ya shiga ya barta a gurin cikin wani irin hali mai wuyar fassara! babu abunda ya dameta a halin yanzu sai ganin ta samu haihuwa dole ta dauki mataki akan irin cutar da yake mata ta daina yarda yana dubga mata kwayoyi kuma ba zata sake yarda yasa condem (kwaroron roba) idan yazo auratayya da ita ba, dole itama ta haihu tunda har ya amince da 'yar da Mariya ta haifa a matsayin 'yarsa. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *15&16* Hujaj gabadaya hankali da tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin Mariya ta dawo gidanshi, domin shi kansa yanzu ya kara tabbatar da maganar malaminsa Mariya itace taurarinsu suka daidaita domin tunda ya aureta k'ofofin samunsa suka bude, ko wace harka ya buga yana samun nasara amma tun sa'ilin da ya rabu da ita komai nasa ya lalace ya rasa gane kan al'amuransa, saboda haka shawarar abokinsa Alhaji Sha'abu itace dai-dai da abinda yake zuciyarsa ya tabbatar da cewa abokin nasa ba zai cutar dashi ba. To cikin ikon Allah akayi suna yarinya taci sunan mahaifiyarsa Wato Maryama kamar yanda ya fad'awa Talatu, sosai yayi bajinta Alhaji Sha'aibu ya bashi aron kudi yayi duk abinda ake bukata na haihuwa dan ragon suna manya guda biyu ya sayawa maijego bayan uban naman 'kaurin daya siya mata, duk wannan facakar da yake Talatu tana da labari, hankalinta ya tashi ainun! lokacin ta shiga sauke samirun dake kan kwabarta ta kulle a dankwali ta nufi kasuwar bakin asibiti. Talatu na siyar da Samirun ta hada kan kudin tsaf ta nufi gurin malaminta domin ya taimaka mata akan al'amuran da suke faruwa. Yamma likis ta dawo cikin tarin gajiya da yunwa ta kwanta a tsakar gidan tana tunanin abinda za taci domin kwayar shinkafa basu da ita, gashi tayi ragwan azanci gabadaya kudin dake hannnta ta tattare ta bawa Malamin babban burinta ace Mariya ta lalace ta kuma yi nesa da ita. Sallamarsa ce ta dawo da ita hayyacinta. Ko kallonta bai yi ba ya kama hanyar dakinsa yana baza babbar rigar sabuwar shaddar dake jikinsa, tunda ya shigo gidan ya game da Kamshin turaransa, a zahiri ka ganshi zaka dauka wani babban hamshaki ne wanda yaci ya tada kai saboda yanayin sutturun da yake tu'ammali. Ta hadiye kakkauran yawun dake bakinta gatsal ta ambaci sunansa."Jamilu." Ya juyo yana kallonta fuskarsa a murtuke! mugun haushinta yake ji yana ganin duk ita ta janyo masa shiga talauci dan dai kawai Malaminsa yace kada ya sake ta amma da tuni ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda." "Kasan tun safe haka nake zaune banci abinci shin baka tsoron hakkina ya kama ka." Cikin taushin harshe tayi maganar. Yaja tsaki da fadin." Talatu ashe kin iya kwantar da murya ai na d'auka karfinki ne zai kwatar miki." Murmushin takaici tayi tace." Jamilu kenan ai ni yanzu na daina kishi da Mariya babban burina ka dawo da ita mu zauna tare tunda na fahimci cewa itace farin cikinka. Murmushi yayi yace." Kin ci albarkacin Mariya." Hannu ya zura cikin aljihu ya dauko kudi duba daya ya zara a ciki ya cilla mata da fadin." Gashinan da yau da gobe kici abinci, sannan magana ta karshe da zanyi miki shine ki iya bakinki akan zama na da Mariya kuma ki zauna lafiya da ita domin itace mahadin arziki na." Ba tace komai ba tasa hannu ta dauki kudin da ya jefa mata tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta. Bai bi ta tanka ba ballanantana ya duba halin da take ciki dakinsa ya shiga ya sayo k'ofar ya kashingida yana hutawa kafin dare yayi ya nufi in da yafi wayo. **** Hujaj shige da fice ya cigaba dayi tsakanin gidansu Mariya da kuma zauran malaminsa wanda yake sake tabbatar masa da cewa lallai yayi kokarin ganin Mariya ta dawo gidanshi mutukar yana so arzikinsa ya yalwata, aikuwa ya tashi hankalinsa, sai da yaga tabbutuwar auran kisan wutan da abokinsa sannan hankalinsa ya kwanta. Alhaji Sha'aibu yayi murmushi tare da godewa Allah, babu shakka dami ya tsinta a kala, babu yanda za'ayi Allah ya azurta shi da mace kamar Mariya ya rabu da ita, auransa da ita mutuwa ce kawai zata raba, dama can yana jin abokin nasa ne, bai auri Mariya dan ya sake ta ba. 'Bangaran Mariya kuwa hankalinta ya kwanta, a yanzu ne ta san tayi aure domin kulawar duniya Alhaji Sha'aibu nayi mata tare da 'yarta wacce suke kira da Shahida, ita kanta Baba Asabe sai yanzu hankalinta ya kwanta ganin yanda Alhaji Sha'aibun yake kulawa da 'yarta wannan shine babban burinta ace 'yarta tayi dace da miji nagari. Mariya tayi shar abunta tayi kyau da kiba haka nan Shahida tayi wayo rayuwarsu sukeyi mai tsafta dukkaninsu sun amince da juna babu nufin auran kisan wuta a zuciyarsu. Yana can sake da baki yana ta lissafin wa'adi (kwanaki) ya cika Abokin nasa ya cika masa alkawari kamar yanda yayi daukar masa. Bonono rufe kofa da barawo kenan. Lokacin da Hujaj ke lissafin wa'adi ita kuma Mariya ta samu ciki da Alhaji Sha'aibu. Shahida nada wata takwas a duniya Ganin yanda cikin yake wahalar da ita ne yasa Baba Asabe tazo ta dauki Shahidan ta tafi da ita can gidanta domin kula da ita, aikuwa cikin ikon Allah yarinyar tayi lafiya ta manta da nono, Baba Asabe ta cigaba da kula da ita tare da bata magungunan gargajiya. *** Sau uku kenan yana masa maganar cikar wa'adin amma yana shakulatun 'bangaro dashi, yau ne karshe dole ne ya saki Mariya ko yaso ko yaki. Koda ya isa kasuwar bai zauna a shagonsa ba, kai tsaye shagon abokin nasa ya nufa, fuskar nan tasa a murtuke. Alhaji Sha'aibu na ganinsa sai gabansa ya fadi, ya san dai labarin gizo baya wuce na koki. Babu walwala suka gaisa da juna. Ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu ban ta'ba tsammanin cewa za kaci amanata ba wallahi yanzu haka mu kayi da kai? wata biyar fa mukayi da kai cewa za ka sakar min matata amma duba wata takwas kullum idan nayi maka magana sai kayi shuru ko kuma ka dinga raragefe, Alhaji Sha'aibu kai kanka kasan cewar yarinyar nan itace kashin arziki na mai zai sanya kayi min haka."? Hular dake saman kansa ya cire ya ajiye gefensa ya kalleshi da fadin." Alhaji Jamilu ni fa ba jahili bane ina da ilimin addini daidai gwargwado dama can ban auri Mariya dan na sake ta ba, kuma duk kudin da na baka kayi mata hidima wallahi saboda tsananin son da nake mata ne, bana bukatar komai a gurinka, 'Yarka Shahida kuma zan cigaba da daukar nauyin ta domin duk abinda Mariya ta haifa ina sonsa, babban Albishir din da zanyi maka shine Mariya na dauke da juna biyu ni ne kuma ubansa." Wani irin gumi ya dinga yanko masa! a take wuyan rigarsa ya jike jagab! bakinsa yana rawa yace." Alhaji Sha'aibu cin amanar da za kayi min kenan? sharadi mukayi da kai cewa babu mu'amular aure a tsakaninka da ita, amma me yasa za kayi min haka." Shuru yayi masa domin duk maganar da zai fada masa ya riga yayi masa bayani duk abinda zai biyo baya mai sauk'i ne. Ya girgiza kai bala'in bakin ciki kamar ya kasheshi ido jawur! ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu idan ka san wata baka san wata ba ka mance waye Jamilu ko."? Murmushi yayi da fadin." Alhaji Jamilu duk in da zamuje fa nafika gaskiya idan hukuma za kaje ka sanar dasu, to kanka zaka tonawa asiri watakila ma alkali ya daure ka, saboda haka hakuri kawai da dangana za kayi." Yaji kamar ya dora hannu aka ya kurma ihu! saboda takaici babu shakka Alhaji Sha'aibu yayi masa bazata. 'Kwafa yayi tare da girgiza kansa ya kama hanya ya fita daga shagon yana sa'be babbar riga, duk ya zauce ya fice daga hayyacinsa, kasa zaman kasuwar yayi ya nufi zauran malaminsa duk ya zube masa abinda ya faru, Arrama ya buga kasa ya zana ya kuma zanawa ya kalleshi da fadin." Ka rabu dashi kawai na duba naga zamansa da yarinyar na 'kan'kanin lokaci ne, yanzu ka kwantar da bankalinka ka zuba masa ido kawai ka cigaba da harkokinka, akwai wasu layu da zan baka wanda zaka samu kwalba mai murfi kasa a ciki, ka jefa cikin tsohowar rijiya, sannan akwai turaran da zan baka kullum kafin ka turara jikinka sai ka kalli gabas yamma kudu arewa ka kira *Arziki har abadah! talauci kada yazo inda kake."* sai ka turara jikinka da hannayenka, ina mai tabbatar maka da cewar kai da talauci har abadah." Hujaj yayi farin ciki sosai da irin taimakon da yake samu daga gurin malaminsa, sosai yayi masa alkairi kana sukayi sallama, ya nufi gida hankalinsa a kwance yana da tabbacin cewa duk abinda malaminsa ya fada masa zai tabbata. Wannan shine abinda ya faru. Hujaj ya dauke hankalinsa gabadaya daka kan Mariya ya cigaba da fagauniyar yawan malamai domin samun sa'a ta duniya arziki kawai ko ta halin yaya. Bangaran Talatu kuwa kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki dama babban burin ta Mariya tayi nesa da ita, duk abinda yake faruwa tana da labari kuma idan taje gurin malaminta yana sake tabbatar mata da magana, wannan dalilin yasa ta kara gazgata al'amirin malamin nata, ya iya aiki kamar yankan wuka. Cikin wannan halin ta samu ciki domin sai da ta shiga ta fita ta janyo da hankalinsa kanta, kuma bata yarda ya kusance ta da k'waroron roba(conderm) **** Mariya na cigaba da samun kulawa da mijinta da kuma mahaifiyarta, cikin ikon Allah cikinta ya shiga watan haihuwarsa, sai kuma lalura tayi yawa , yau da lafiya gobe babu, ta kai ta kawo har sai asibiti suka bata gado domin kula da ita da abinda ke cikinta, Allahu akbar ashe abokin tafiya ne, daran juma'a nakuda ta tashi, kafin asubah, ta haihu 'ya mace sai da babu rai! mahaifa kuma tayi gardama likitoci suka rufu akanta domin ceto rayuwarta, duk abinda Allah ya kaddara babu makawa, suna tsaka da taimaka mata mahaifar tayi sama, a take ta dinga wani irin nishi! idonta na rufewa da wata irin jijjiga, da kalmar shahada Allah ya dauki rayuwarta. Sun shiga rudu mai tsanani mussaman mijinta da mahaifiyarta, bangaran Jamilu kuwa ko a jikinsa domin yanayin sa ma ya nuna kamar yana farin ciki da mutuwarta, domin koda yazo gaisuwa babu alhini a tattare dashi, kwalliya yayi sosai yana uban kamshin turare kamar sabon ango! komai na jikinsa mai tsada ne. Wannan shine abunda ya faru a baya, Shahida ta cigaba da zama gurin Baba Asabe tana kula da ita ci da sha suttura harkar karatu da kula da lafiyarta duk Baba Asabe ta dauka. sana'a take sosai domin macace mai kamar maza. Hujaj mantawa ma yake yana da wata 'ya a wani guri mutukar ya tuna da ita to yaje gidansu ne, mahaifiyarsa tayi masa maganarta, anan zai girba 'karya yace ai yana zuwa ya duba yarinyar har kudin abinci yana kaiwa, alhalin tun bayan haihuwarta bai sake zuwa gidan ba. gabadaya ya manta da ita, domin ko lokacin da Kawu Musa yaje kasuwa ya sameshi domin ya sheda masa lalurar yarinyar, sai da ya gama sauraransa tsaf sannan yasa hannu a aljihu ya dauko dubu daya ya bashi da fadin." Suyi hakuri insha Allahu zai zo ya dubata.'' Takaici yasa Kawu Musa ya fita daga shagon ba tare da ya karbi kudin ba. Tun daga ranar Baba Asabe tayi al'kwarin cewa ta daina neman komai a hannunsa, za ta cigaba da kula da yarinyar da ikon Allah babu abinda zai gagare ta. *Abubuwan da suka faru kenan a baya, yanzu zamu cigaba da labari* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin nan. Su yi joining domin samun karanta littafi na d'aya. A yi hakuri a daina bi na pravite Na gode* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *17&18* *AIRPORT* babban filin tashi da saukan jirage na Malam Aminu dake Kano. A hankali nake bin su da kallo sun jeru tsaf dasu cikin uniform gefen maza daban na mata daban, suna tsaye kowanne da 'yar jakarsa a hannu da alama screening ake musu kafin shiga cikin jirgin. Na dinga ayyanawa a raina cewa wata shekarar insha Allahu dani cikin masu hauke farali. Ajiyar zuciya na sauke a hankali na gyara takardar da biron dake hannuna nayi saurin matsawa gefe jin horn na mota a dab dani. Motar na zubawa ido tare da ayyana wani abu a raina. Da sauri na kalli jiragen dake daukar fasinja. sunan mutumin dake bayan motar irinsa ne a jikin jiragen dake d'aukar fasinjan domin zuwa kasa mai tsarki. *'DANGASKE AIR LINE* sunan dake tambare a jikin jiragen kenan. *'DANGASKE41* shine a rubuce a jikin hamshakiyar motar da tayi parking gefan da nake tsaye. Ido na zura akan motar domin ganin wanda yake kokarin fitowa. kafarsa sanye cikin brown din takalmi mai gidan yatsa da kafar da takalmi duk abin kallo ne. Ya fito bakinshi na dan motsi yanda na fahinta kamar addua yake. direban ya mayar da murfin motar ya rufe ya dan bashi hanya, kira kuma sai ya shigo wayarshi dake rike a hannunsa. A sace nake kallonsa ina sake nazari a kansa. babu shakka shine hamshakin attajirin mutumin nan da sunansa ya mamaye ko'ina a fadin Najeria da ma kewayenta. Yana sanye da milk din shadda 'yar gasken dinki tazarce rigar har kasa da aikin rumi a wuyan rigar kanshi sanye da brown din hula (dara) ya nad'e hular da farin hirami, hannunshi daure da wani irin agogon sarka white colour, a irin kallon kurrula irin nawa na fahimci cewa shi din ba yaro bane kamar dai yanda jama'ar gari suke maganarsa, babban mutum ne kamili mai shekarun da suka wuce arba'in, a kalla dai shekarunsa na haihuwa zasu kai hamsin da biyu zuwa da uku. da akwai tsalli-tsallin furfura a kwantaccen gashin da yake zagaye da bakinsa. Yana wayar ina kallonshi tare da nazartarsa tabbas ya cika cikakken mutum mai kima da mutunci gami da daraja dan adam ko ga yanayin kalamansa a waya, a nutse babu baragada da hayaniya. Escort dinshi uku suna tsaye a kusa dashi, sai kuma wata matashiyar budurwa dake d'an kama dashi kad'an a gefensa a tsaye sai zumbura baki take tana dauke kai tana sanye da jallabiya baka mai duwatsu tayi roling da pink din gale hannunta rike da wayoyinta da kuma handbang dinta. Murmushi yayi ya dan gyara zaman gilashin dake sakaye da idonshi yace." Yanzu dai ni already ina airport tare da Shukura da Hajiya bana tsammanin kan wannan dalilin zan janye abinda nayi niyya saboda haka duk abinda ya dace ayi ina gari ko bana gari duk abinda kayi dai-dai ne Sule a cigaba da duk abinda aka saba kada a sauke min tukunya a gida " Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Okey to hakan yayi Allah yasa albarka a ciki sai mun dawo." daga haka bai sake wata magana ba ya kashe wayar ya mayar da ita gaban aljihun rigar dake jikinsa. Ya juya yana kallonsu a nutse yace."Ina Hajiya.? Shukuran ce tayi magana. "Tana cikin mota wai kafafunta ke ciwo." Girgiza kai yayi ya san za'a rina dama ko a gida ma kuka take da kafafun amma saboda rigima tace lallai sai taje aikin hajji tunda da iko to duk shekara ba za tayi fashin zuwa ba. Hannu yasa ya bude motar gyangyadi take. sai abin ya bashi dariya yayi kadan kafin ya fara kiran sunanta. Firgigit ta bude idonta tana kallonsa, da sauri tace." Wane irin baccin asara ne yake nema ya kwasheni a mota nida nake da niyyar zuwa gaban ma'aiki SAW." 'Kokarin fitowa take tana cigaba da surutai." Wannan kafa ita kadai ce damuwata a duniya amma Allah yayi min komai saboda haka babu abinda zan fasa na ibadah." Duk wani bayani da k'auli da zai kawo mata ba zata yarda ba, shiyasa yaja bakinsa yayi shuru kawai yabi ra'ayin ta akan duk abinda takeso babban burinsa su rabu lafiya. Yace." Ki zauna kada ki fama kafafun bari akawo keke a sanya ki a ciki. "Wa za'asa a keke?" a tur'bune tayi maganar tana hararsa." Shima ya gyara fuska babu wasa yace." Ke mana ko kin dauka idan mun isa can ma zaki iya d'awafi da kanki.? Shuru tayi tana tunani. da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa domin wani irin ciwo kafafun nata ke mata. Ya d'an juya tare da kiran daya daga cikin Escort dinsa. Ya risina cike da ladabi yana sauraransa. "Adamu kaje ciki ka fito da keke za'a dora Hajia a kai." Ya amsa da sauri cike da bin umarni ya bar gurin. Ina nan tsaye a raka'be kamar wacce tayi wa sarki k'arya har wanda aka tura ya dauko keken ya dawo suka dora ta akan idona suka shige Ban samu damar bin bayansu ba saboda akwai securities (masu tsaro) sai na dinga leken su ta tsakanin 'karafuna anan ne naga yanda ma'aikata da jama'a fasinjojin dake gurin ke bashi girma, fuskarsa ba 'boyayya bace idan akayi duba da yanda jaridu da gidajan television media ke nuna hotonanshi. Yanzu ma dai tunda ya shiga gurin masu daukar labarai sai d'aukar hotonshi suke da duk wani motsinsa. Cikin kamala da dattako yake dagawa jama'ar dake gurin hannu yana amsa gaisuwarsu fuskarsa a sake saboda daraja dan Adam har sai da ya cire farin gilashin dake sakaye da idonsa. wannan ya bawa gidan television din NTA dama daukar vedio sa lokacin ya juya da niyyar shiga wani kebantaccan jirgin da ya kasance na mussaman dashi da iyalinsa. Kamar yanda mane ma labarai ke bin diddinginsa nima haka ban dauke idona ba har sai dana tabbatar da cewa sun shiga jirgin sannan na janye idona, gumin dake goshina na sharce kafin na sauke wata irin ajiyar zuciya, gaskiya na jinjinawa wannan mutumin da ace duk haka masu hali suke da sun ji dadi, ya zama koda yaushe a fadi alkairinka kafin a fadi sharrinka. *Wannan kenan* ***** Takwas na dare suka kawo wutar nepa cikin unguwar wanda jama'ar dake zaune a cikinta suka cire tsammanin samun wutar sakamakon faruwar matsalar data janyo shud'ewar wattani rabonsu da samun wutar lantarki. Unguwar ta rikice da ihu! ba yara ba manya mata na cikin gida ma ihu! suke kananun yara sun fito waje sai ihu suke da fadin." *NEPA!!.* Baba Asabe dake zaune a tsakiyar rumfa tana daura man gyada irin wanda take siyarwa, tafi kowa farin ciki da samuwar wutar dalilin sana'ar ta, bata samun lokacin daure-daure sai da daddare, fuskarta da fara'a tace." Allah ya taimake mu, jama'a mai za'ayi da duhu ko a kabari Allah yayi mana tsari dashi." Saliha data fito daga uwar daki tace." Ameen dai ai Baba na fi kowa farin ciki kinga na huta wahalar kai waya ta gurin chaji." Tana maganar tana kokarin sanya wayar hannunta a chaji. Tace." Aikuwa ai yaran nan sun cutar damu wallahi ace saboda tsabar mugunta da bushewar zuciya mutum abu ba shi ya aje ba kayan gwamnati amma sai abi dare a sace ko tsoro ba sayi watarana injin wutar ya tashi dasu, kai Allah dai ya shiryi yaran yanzu." Ta amsa da "Ameen tana kokarin kunna Tv tace." Baba kin manta ai ba wannan ne na farko ba kusan sau uku 'barayi na bin dare su sace abubuwan dake da muhimmanci a transformer amma dai wannan karan naji ana cewa anyi kwamiti akwai kuma 'yan bijilanti da zasu sanya ido sosai." Tana cigaba da abinda yake gabanta tace." Ai hakan shine abinda ya dace suyi dama can rashin hadin kai ne na cikin unguwa." Shahida ce ta katse maganar da suke. rumfar ta shigo hannunta rike da plate da abinci a ciki. Can gefe ta zauna babu walwala a fuskarta, kallo guda kayi mata zaka fahimci cewar akwai abinda ke damunta. Ta kalleta da fadin." Akwai miya amma me yasa zaki sanya manja a cikin abinci, kina so wani ya shigo yaga kina cin fara da manja ya fita ya zage ni ko? dama kwana biyu naga sai nukufurci kike wai shin me akayi miki ne."? Hawaye suka fara gudana a saman fuskarta. kawai sai ta ajiye cokalin ta kifa kanta tsakanin gwiwarta tana rusa kuka." Ta bude baki kawai tana kallonta gabanta in banda faduwa babu abinda yake, rikon maraya akwai matsala babba. Saliha taja tsaki da fadin." Baba don Allah ki kyaleta ke kike rarrashinta shiyasa ai take duk iskancin da takeso idan bata bukatar zama a gidan ba sai ta hada kayanta ta tafi gidan ubanta ba." Duk da tana da matsalar kunne hakan bai hana ta jin irin kausasan maganganun da Salihan keyi a kanta ba, ta rasa me yasa Saliha bata kaunarta, tun suna yara take nuna mata kiyayya, bayan mahaifinta shine yasha nono ya bawa mahaifiyarta, amma kiyayya karara take nuna mata. Baban tace." Saliha wace irin magana ce wannan? ba na san tashin hankali da neman fitina, saboda kina ganin tana da matsalar kunne shine kike cin mutumcinta a fakaice, kin fi kowa sanin halinta, duk sanda kike kure hakurinta to zan kyaleki da it........Ta katse ta da fadin." Ki kyaleta Baba ta cigaba da maganganu a kaina jikinta ne zai yi tsami yanzu yanzu." cikin dashewar murya take magana. Baban tace." Magana dai ta wuce ke Saliha babu ruwanki da ita ki kama girmanki." Tsaki taja ta gyara wayar ta dake chaji ta tashi ta bar gurin tana kunkuni." Duk suka bi ta da kallon mamaki, Saliha sam bata da tarbiya wai a hakan ma gwara Shahidan tunda ita duk rintsi tana jin maganar kakar tasu. Gurin yayi shuru sai tv dake aiki. Kallonta tayi tana juya abincin har yanzu ta gagara saka loma daya a bakinta, da d'an 'karfi tayi maganar." Shahida sanja min tasha ki kai NTA KANO na saurari labarai." Ajiyar zuciya ta sauke ta rarrafa ta isa gurin Tv fa fara kokarin sanja tashar Tv ce irin ta da sai shuuuuuu! take mutane ma basa fita sosai, a haka suke kallon. Dai-dai lokacin da ta kai tashar NTA din yayi daidai da lokacin da aka haskoshi a filin jirgi yana gaisawa da mutane tare da cikakken bayani a kansa amma kuma da turaci ne. Murya ta karo ita da Baba Asaben suka kurawa Tv ido suna ganinshi haza-haza domin tv ba clear saboda rashin Area mai kyau. Baba Asabe tace." Shahida wannan mutumin ne mai taimakon mutane ko.? A sanyaye ta daga kai da fadin." Shine wai suna bayani a kanshi zai je aikin hajji da tare kakarsa da kuma 'yarsa tilo guda daya." Karaf tace." To bashi da mata aure ne.? Itama tace." To ina zan sani Baba nima na dan tsinci wasu abubuwan ne ba komai na fahimta a kanshi ba, amma dai gaskiya ba zai rasa matar aure ba tunda ga budurwar 'yarsa nan." Tace." Eh gaskiya kam amma kuma surutai marasa kyau suna yawo a kanshi jama'a da bin diddigi da ganin kwaf da yawa mutane nayi masa zargin auri saki wai a kalla ya auri mata sama da goma ya saki saboda yana da kudi." Ta kalleta da fadin." Baba ki iya bakinki wallahi, na lura mutane ke kawo miki gulma iri-iri kada aji wannan maganar daga bakinki babu ruwanki." 'Yar dariya tayi tace." Yo 'yar nan ai maganar duniya bata 'buya, ko na fada ko ban fada ba, idan halinsa ne, Allah zai tona masa asiri watarana." Tace." Eh duk da haka dai babu ruwanki wannan al'amari domin na san ki da magana watakila wasu na iya zuwa siyan abinci ki basu labarin da baki da tabbas akai, daga haka kuma sai al'amari ya lalace! sunanki yayi ta yawo gari." Uffan ba tace ba, saboda ta san duk maganganun Shahidan akan hanya suke, sai kawai ta cigaba da abinda ke gabanta. abincin take cusawa a bakinta tana had'iye wa da 'kyar! ita kadai ta san abinda ke damun ranta, kwana uku bata sanya shi a idonta ba, taje bakin kasuwar ya kai sau biyar bata ganin gilmawarsa, sai dai tarin tarkacensa a karkashin tsohowar motar da yake kwana, ko yana ina oho! wasu zafafan hawaye suka zubo mata a kumatu, tayi saurin gogewa! tana satar kallon in da take zaune, hada ido sukayi sai tayi saurin sunkuyar da kanta tana juya sauran abincin da ya rage da cokalin hannunta. Ta ture bokitin man gyadan da ta gama daurawa, a nutse take kallonta kafin ta d'an bud'e murya yanda za taji tace." Shahida idan baki fada min damuwarki ba waye zaki fad'awa? duk halin da kike ciki na fahimta kwana biyu kamar baki da lafiya, shin ko dai wani abu yana damunki ne."? Tasa hannu ta goge hawaye dake ta gudana a saman fuskarta, murya na rawa tace." Baba zuciya tana tausayin wannan mutumin na bakin kasuwa wallahi haka kawai nake tausaya masa, kullum dashi nake kwana dashi nake tashi a raina yau kwana uku kenan babu labarinsa sai dai tarkacensa a karkashin motar da yake kwanciya.'' Baba Asabe ta tsira mata ido cike da tsantsar mamaki tace." Baban- baba kike nufi.? Kai ta daga. Mamaki ya cika ta tace." Ke kuma meye damuwarki da mahaukaci Shahida kada fa garin tausayinki ki jefa kanki a wata musifa watakila ma ba mutum bane, aljani ne domun babu wanda ya san daga wace duniya ya fito." Gabanta na faduwa tace." Wallahi mutum ne kamar kowa kuma ba mahaukaci bane, tunda yana sallah kuma baya doke-doke watakila damuwa ce ta mayar dashi haka." Baba tace." To ai shikkenan yanzu wane irin taimako za'ayi masa." Wani dadi ya ratsa zuciyarta, cike da farin ciki tace." Ki sanya masa kwano na abinci tun daga safe har dare, tunda Allah ya baki yanda za kiyi wallahi zaki samu lada." Tace." To shikkenan zanyi yanda kikeso amma kada na kara ganin kin shiga damuwa a kansa, kuma kiyi kaffa-kaffa dashi tunda na lura baki da hankali." Tana 'yar dariya tace." Baba kenan, Baban-baba ba zai cutar dani ba nayi imani da hakan, tunda na jima ina bashi sadaka kuma bai ta'ba yunkurin kawo min duka ba, sai dai yace ya gode." Shuru kawai tayi mata ba wai dan bata da abun cewa ba, tsabar takaici ne ya isheta, yanzu yarinyar ta zama hukuma sai da rarrashi! za tayi kokarin ganin tayi mata duk abinda ta ke so. *BINTU* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin suyi joining domin samun damar karana na d'aya A yi hakuri a daina bi na pravite Na gode.* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *19&20* Duk da Baba Asabe ta amince da abinda ta ke so hakan bai sanya ta kwantar da hankalinta ba, kullum cikin damuwa take duk saboda rashin sanin takameman gurin da mahaukacin ya sauya da zama, don ita duk a tunaninta tsokanar da yara ke masa ya sanya ya bar gurin, a rana ta kan je bakin kasuwar sau uku ko fiye da haka tayi ta dube-dube ko Allah zai sanya ta gan shi, babu shi babu dalilinsa sai tarin tarkacensa dake k'ar'kashin matacciyar mota (a kori kura) da yake kwanciya a 'karkashinta. Da azumin arfa a bakinta daf da za'a sha ruwa ta faki ido ta fita daga gidan kai tsaye bakin kasuwar ta nufa. Baba Asabe ta fito daga kicin da muburgi a hannunta, Saliha ce kad'ai a zaune a tsakar gidan tana had'a musu lemo, tace." Ina Shahida ita kuma sai tazo ta soya mana awara kada asha ruwa mu rasa abunda za musa a bakin salati." Tabe bakinta tayi ta ce." Yanzu ta fita." Cike da mamaki ta ce." Ta fita kamar yaya ina taje?" Ta ce." To ni kya tambaye ni, nima ban sani ba, na san dai sa'i da lokaci tana fakar idonki ta fita." Baba Asabe bata kawo mummunan abu a ranta ba, tafi tunanin cewa Shahidan bakin kasuwa take zuwa gurin mahaukacin data d'auki son duniya ta d'ora masa. A fili ta ce." Allah yasa ya tafi kenan ba zai dawo ba domin kuwa na fara zargin mutumin nan idan ba aljani bane to babu shakka maye ne." Ta d'aga labulan d'aki ta shiga tana cigaba da maganar da alama al'amarin yana damunta. Yau ma ba sa'a domin kuwa gurin zaman nashi ma dabbobi (awakai) ne a kwance a gurin duk sunyi masa kashi ga ruwan saman da akayi jiya ya jika masa wasu kayan nasa, babu shi a gurin sai dabbobin da suka maye gurbinsa. Wasu zafafan hawaye suka ciko idonta, ko'ina mutumin nan ya shiga? "Watakila ya mutu a wani guri." Zuciyarta ce ke raya mata hakan. Ta girgiza kai gabanta na wani irin fad'uwa! "Insha Allahu bai mutu ba." Ta furta hakan a fili. Da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo ta kira wani yaro da hannunta. Yaro yazo ya tsaya gabanta da ledar kankana da lemo a hannunsa da alama aikensa akayi kuma da azumi a bakinsa yana sauri ya isa gida yace." Gani." A sanyaye tace." Don Allah ko kasan inda Baban-baba ya koma da zama?" Cike da rashin fahimta yace." Waye Baban-baba?" Ta nuna masa tsohuwar motar da fadin." Mutumin dake zama a waccan motar." Ya kalli gurin da take nuna masa ya juyo da tsoro a tare dashi ya ce." Ni ma ban sani ba.'' bai jira jin abinda za tace ba yayi saurin barin gurin yana waiwayenta. Ba ta ha'kura ba ta sake tarar wani yaron tana tambayarsa, yaron irin marasa kunyar nan ne, kawai sai ya fashe da dariya yana gwada irin maganarta ta kurame! "habbbaba! ya nu na ta da yatsa yana kyalkyala dariya ta bishi da kallo tausayin kanta da kanta ya lullubeta, wai shin ita din abar tausayi ce ko kuma Baban-baba? Hawaye masu zafin gaske suka ciko idonta, tayi namijin k'okarin hanasu zuba, da saurin gaske ta bar gurin tana addua a zuciyarta. Koda ta koma gidan ma 'bacin rai ne! don fad'a ta riska, Baba Asabe ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa idan ba tayi a hankali ba to za ta kai ta asibitin dawanau a duba kwakwalwarta, to itama a lokacin da Baban ke fadin hakan ba taji haushi ba domin ta fara zargin kanta anya kuwa bata samu matsalar kwakwalwa ba. Washe gari aka tashi da sallah, jama'a nata walwala da farin ciki mussaman wanda Allah ya hore wa abin layya ciki har da Baba Asabe domin babban (rago) na dubu sittin ta saya tayi layya dashi, wadatar zucci ne da ita tare da 'ko'karin faranta ran jikokinta dake gabanta. Uku ga sallah ta shirya tsaf fuskarta babu walwala ta fito daga d'aki da hijab dinta a hannuta. Baban ta kalleta da fadin." Kin shirya kenan? ai da nace Saliha ta shirya kuje tar.....Salihan ta katse ta da fadin." Ni babu in da zani bacci zanyi na huta, sannan kuma da yamma Kamalu zai zo muje gidan yayarsa ziyara." Kamalu shine saurayinta wanda akayi musu baiko. Baban ta ce." Ayyo! to shikkenan Shahida kinji abinda ta ce." Babu damuwa a tare da ita ta ce." Babu komai.'' Hanyar fita ta nufa da fadin." Sai na dawo." Ta ce." Ki gaishe su ba dan halinsu ba, maganar naman sallah kuwa ba zan ce ki tafi musu dashi ba dalili na fi kowa sanin waye Jamilu da burgar tsiya yanzu idan baki take ba yana nan ya kayar da manyan shanu yana neman suna a unguwa." Bata tsaya taji 'karshen maganar ba tayi saurin fita daga gidan, a ranta tana jin haushin irin cin mutuncin da Baban ke wa mahaifinta. Ilai kuwa tana shiga gidan taga zahiri domin kaca-kaca ta samesu suna ta aikin suyar nama tare da daka dambu a k'aton turmi Hadiza ce mai wannan aikin. Can gefe kuma ganda ce tare da kan sah! da rago a babbake akan buhu an shanya k'udaje sai tashi suke a gurin da wari mara dadi. Jamila ce kawai ta amsa sallamarta tana fara'a tace." Aunty Shahida ashe kece dama kwana biyu kina raina." Ta saki fuskarta da fadin." Nima saboda ke nazo gidan." Hadiza ta kalleta da fadin." 'Yar iska bebiya kawai." da yake a hankali tayi maganar ba ta ji ba ta dai ga bakinta na motsi a lokacin da take maganar amma Talatun da sauran 'ya'yanta duk sun ji." Babu wani 'kulli a cikin ranta ta ce."Talatu ina kwana anyi sallah lafiya? A dakile ta amsa ta cigaba da juya zallar tsokar naman dake cike da kaskon suya. Jamila ta shimfid'a mata tabarba tana zama ya shigo gidan fuskarsa a tur'bune! kamar koda yaushe yana sanye da tsadaddiyar shadda wacce taji uban aiki irin na manyan mutane, hula da takalmi da agogo duka babu na banza kamshinsa kuwa tuni ya cika gidan. Gabad'aya su kayi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala ya bud'e d'akinsa ya shiga babbar rigar ya cire ya rataye ya zauna kasan kafet zugum! da ka gani yana da damuwa. Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya amsa yana bin ta da kallo har ta samu guri ta zauna tana sake gaishe shi. Ya amsa yana mata wani irin kallo kafin yayi kwafa da fadin." Sai yau ki kayi ra'ayin zuwa gurin da nake?" Shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Ya cigaba da cewa." Maganar aure ce ba kya so na yi miki shiyasa ki ka d'auke k'afarki daga gidan nan ko?" Ta kalleshi da fadin." Baba aure nufin Allah ne idan lokaci yayi zanyi aur......ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu da fadin." Ni zaki fadawa lokaci? zaman me kike kin zama uwar mata shekara ashirin kanwarki Hadiza saura wata shida bikinta ga Jamila nan itama nayi magana da yaron da yake son auranta mun tattauna da mahaifinsa, ke da kike babbarsu kina zaune to wannan itace magana ta karshe da zanyi miki wata biyu kacal na baki ki fito da mijin aure tunda kin kammala secondary kinyi saukar al'kur'ani to kuma me ake nema?" Tana shashshekar kuka ta ce." Wallahi Baba tunda nake babu wanda ya ta'ba cewa yana sona, duk wanda yake so na yi aure ba kamar ni ba, na dai fi tunanin saboda lalurata maza suke gudu na." Ya girgiza kai da fad'in.'' Mace bata kwantai matsalar ki ba zai hana ki auruwa ba, ki na da duk abinda ake buk'ata saboda haka ni ban yarda da wannan maganar taki ba." Sai ta kasa ce masa komai domin duk abinda zata fad'a masa ba zai yarda ba, bahaushe ya ce." Mai d'aki shi ya san inda yake masa yoyo, gaskiya ne tunda ta taso babu wani namiji da ya taba cewa yana sonta. Hannu tasa ta goge hawayen fuskarta, ta kalleshi har yanzu fuskarsa bata sassauta ba." "Zan tafi Baba." tafad'a tana k'okarin tashi. ya ce."Ki bari sai yamma idan an kammala soya naman ki tafi da naki." Ya sosa mata in da yake mata 'kai'kayi cikin fargaba ta ce."Baba ina ka samu kudi ka yanka *SAH!* har da *Rago?"* Ya kalleta yana sake tamke fuskarsa." Ke ni kikewa wannan tambayar don ubanki." Ya fada yana zazzare mata ido! A sanyaye! ta ce." Kayi hakuri." Hanyar fita ya nuna mata da hannu cikin tsawa! yace." Tashi ki fita ki bani guri." Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo yayi bajinta da burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai kudi ne. Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi *SAH!* da Ragon a gurinsa. Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba. Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai da aka 'kwamushe haka ya dawo gida a motar haya. Kwabo yanzu babu a cikin asusunsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa. Talatu ta shiga d'akin tana gyara d'aurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take fuskarta na maiko. 'Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada." A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin." Ta juya ta fita bagazan-bagazan! Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu. Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma?" Bai saurareta ba ya cigaba da loda zallar tsoka da k'ashi cikin buhu yana fad'in gidajan da za'a kai musu. Talatu kamar ta dora hannu ka ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a kai kuma?" Ya ce." Na bayar sadaka dama haka Allah ya ce ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya ishe ku." Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba. Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan k'aunar da mahaifin nasu ya yi musu. Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata bu'kata ta siyan icce ko man gyad'a da makamantansu. *BINTU* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi Joining domin samun damar karanta littafi na d'aya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *23&24* Cikin nutsuwa yake musabaha da jama'a bayan idar da sallar asubahi a massalacin dake jikin gidansa wanda ke unguwar giginyu, cikin kamala ya fito daga massalacin da cazbaha a hannunsa yana sanye da farar jallabiya mai k'aramin hannu kansa sanye da hula mai raga-raga irin ta larabawa kamar ko da yaushe ya nad'e kansa da farin rawani. Can tsallake ya hangi wasu matasan samari a tsaye, jikinsa ya bashi cewar shi suke jira ya fito daga massalacin, aikuwa dai gabanshi suka zube suna gaishe shi, ya saki fuskarsa tare da basu umarnin tashi. Bayan sun gaisa sai kuma su kayi shuru suna sunkuyar da kai dukkaninsu da alamun magana a bakinsu. Gyaran murya yayi cikin kamala da dattako yace." Ko meye yake tafe daku kada kuyi shakkar fada min ina sauraranku." Na farkon yace." Alhaji Taimako nake nema a gurin ka, kayi min suttura kamar yanda Allah yayi maka, tabbas nazo gurin da za'a share min hawaye na." Da rawar murya yake maganar. Ya dafa kafadarsa da fadin." Menene bukatarka? fadi kanka tsaye." Yaji kwarin gwiwa a tare dashi yace." Mata ta ce ta haihu yau kwana bakwai kenan bani da abin hakika da goro da Alawa hankali na ya tashi sosai Alhaji domin maula ba hali na bane, kawai don bani da yanda zanyi ne kasancewar gwamnati ta yanke min albashi na, babu laifin tsaye bare na zaune wannan dalilin yasa wahala tayi min yawa yara na biyar gashi karamin ma'aikaci ne albashin duka dubu talatin da biyar nake dauka amma yanzu tsayin wata shida kenan da gwamnati ta zabge rabin albashin ya koma dubu goma sha bakwai, to wannan dalilin yasa duk wani karamin ma'aikaci yake cikin tashin hankali." Ya dinga girgiza kansa yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. ido ya tsurawa mutumin yana tunanin wani al'amari daya faru a cikin shekarun da suka gabata lokacin ma da duniya take kwance kenan Malam me za'ayi da mulkin Najeria. Numfashi ya sauke kafin yace." Kada ka damu komai yana da sanadi kuma kowane bawa akwai hanyar abincinsa saboda haka ni zan taimaka maka daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri." Gabadaya suka amsa da "Ameen." Ya kallesu kafin yace."Abokansa ne ko kuma tafiyar kowa daban?" Hada baki sukayi gurin bashi amsa da cewa." Abokansa ne." Sai yayi murmushi wanda yake fitar da zahirin kyawunsa ya umarce su da su bi bayanshi zuwa gida. Dubu dari cash ya bashi da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai. Shi da abokansa suka rasa bakin godiya. To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu. **** Yau haka kawai ta tashi da kwad'ayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin Jakara take. Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai bata sha'awa ba, wainar geron dai take 'kulafuci. Ta kalleta da fadin." Baba bani naira d'ari zan sayi waina yau kwadayinta nake ji." Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika mata. Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta 'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma. Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da ta yi dashi a kwance a k'asan mota akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da k'azanta har da kashin awakai." Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da annuri. Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci. Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana mamakin abinda ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki da maik'o sai ka rantse da Allah cewa 'kafafun ba'a jikinsa suke ba. Tsoro yasa ta d'an ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba. Ya bud'e idonsa tare da k'okarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta. Bakinta na rawa ta kirayi sunansa. Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta dake k'asan motar yasa bakin kazantacciyar butar da ko arzikin murfi babu a bakinsa ya gumtsi ruwan ciki ya fesar dashi har sai da ya same ta a kafafu. Ya sake kafa bakinsa a bakin butar yana kokarin shan ruwan dake ciki. Cikin rauni da tausayi tace." Kada kasha wannan ruwan bashi da kyau zai maka illah.'' Ko kallonta bai yi ba ya kafa baki ya sha ya ajiye butar a gurin da take. Tsigar jikinta gabadaya ta tashi, sam bata san kallon butar saboda yanda take da 'kyankyami Komawa yayi ya kwanta ya rufe idonsa yana takure jikinsa, taji wasu zafafan hawaye suna kokarin kwace mata, wallahi da tana da yanda za tayi akansa da tuni ta samar masa nutsuwa da makwanci mai kyau. Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta sayi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba. daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, ta ce." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar. Ta fara k'ok'arin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi ka ci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a." Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba. Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka ta ce." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.'' Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne. Hannu yasa ya 'karbi wainar a takaice ya ce." Na gode." A hankali ya yi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata. Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo." Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta. Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu. Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko?" Ta ce." Eh saura naki a kadai gashi can a jug." Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.' Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya." Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi." Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita. Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa ba sai wannan mahaukacin.' Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar." Tana 'yar dariya ta ce." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa." Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri. "Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci." Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bud'e kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai k'amshi yake. Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba. Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba. A sanyaye ta ce." Sannu ko baka da lafiya ne?" Ya d'aga mata kai alamun ."Eh." gabad'aya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka ta ce." Zazzabi ko ciwon kai.? Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa ya ce." Babu ko d'aya jikina ne yake ciwo." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwa'ke amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka." Shuru yayi bai ce komai ba. Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa! a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so kin dame ni da surutu." Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya d'auki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin. Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya. 'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata! Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka! Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.? Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta. **** "Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi ya yi sallama da Hujaj. Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa." Ta ce." To za'a fada masa. Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai biya. Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha na shi gobe ya koma da wata kadarar tasa domin samun nasara tare da nin ka abinda ya bayar. *BINTU* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin su yi joining domin samun damar karanta na daya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *27&28* Ha'ki'ka duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, zahiri kuma wanda ya hau motar kwad'ayi to babu shakka za ta sauke shi a tashar dana sa ni, Hujaj cikin rashin k'ima da rashin arziki ya nufi gidansa da gashi sai singlet da gajeran wando domin ko da sanya tufafin jikinsa don ganin kamar zai samu nasara, sai gashi cikin hukuncin Allah an k'wamushe shi, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko haka ya nufi gidansa cikin rashin kuzari da rashin 'kwarin gwiwa, in da Allah ya rufa masa asiri ma dare ya tsala babu wanda ya ga ne shi a hanya sai da ya zo shiga gidan ne su ka yi arangama da mak'ocinsa mai suna Malam Habu yana nannad'e tabarma zai shiga gidansa, da sauri Hujaj din yayi nufin shiga gidan, ya ji Malam Habu din yana magana amma saboda kunya bai saurare shi ba, ya yi saurin banko kofar gidan ya sa sakata ya kulle kana ya ja tsaki da fadin munafiki kawai. Malam Habu ya girgiza kai ransa a 'bace da irin zubda mutuncin da ma'kocin nasa keyi a gari, ko shakka ba ya yi daga can gurin sana'ar tasa ne aka wulakanta shi irin wannan, in banda zubda mutumci da son duniya mai za'ayi da sanar cha-cha! jahili shine ya d'auke ta sana'a har yake fankama da ita, gidansa ya shiga da tunanin yanda zai tunkari ma'kocin nasa da maganar zuwan Saminu Abbatuwa sannan kuma dole ne ya nuna masa kuskuran abinda ya ke aikatawa wannan shine zaman amana a tsakaninsu. Fitowar ta kenan daga d'aki da buta a hannunta za ta kama ruwa. ya shigo gidan kamar wani 'barawo sai sand'a yake, shi kansa kunyar kansa yake tunda ya fara sanar ca-ca! bai ta'ba wulakanta irin yau ba. Ta kalleshi da mamaki a tare da ita ta ce." Mai zan gani ni Talatu?" Bai saurare ta ba ya nufi dakinsa da saurin gaske, ba ya so tayi kwakwazo har 'ya'yansa su tashi a bacci su san abinda yake faruwa. Ta ja mutsiyacin tsaki da fadin." Allah ya shirye ka Jamilu wallahi na yi nadamar auranka." ranta a 'ba ce ta shiga bandakin tana tur! da halin mijin nata. Wa she gari ya tashi zuciyarsa a 'kuntacce fargabarsa kada Saminu ya zo ya ritsa shi a gidan sai sauri yake fita. "Wai ana sallama da mai gidan." Wani ne yaro ne yake magana a gidan. Gabansa ya fad'i! wai shin ya zai yi da wannan mutumin ne? Luf yayi a d'akin bai ce komai ba yana jin lokacin da Talatu ke fadi'n." Ka ce gashi nan zuwa." Ya nemi gefan gado ya zauna yana tunanin k'aryar da zai girbawa mutumin. Ta shigo babu sallama ballanatana gaisuwa, ta ce." Ka ji ana sallama da kai a waje ko?" Ya kalle da dan firgici a tare da shi ya ce." Na ji zan fita na same shi." Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta. Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya samu Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah." Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ?" Yayi shuru bai ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana hura 'katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni." Cike da burga da rashin gaskiya ya d'aga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi k'arfin haka." Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na mai'ko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi idan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali." Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa mak'ocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj d'aya na k'okarin d'aura masa ankwa a hannu. "Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.'' Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun mak'aryaci ne, saboda haka hukuma ce zata raba ni dashi." Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba. Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da k'ima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari. Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis da shi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya." Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba. Wai a kace labarin duniya ba ya 'buya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar. Shahida kam d'aki ta shiga ta ci kukanta ta k'oshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani. *** "Ranka ya dad'e iyakar ha'kuri nayi kawai abinda na ke so ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani." Officer ya ce." Saminu kaje ku yi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto." Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure na ke so nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin ma'karyaci ne na daina yarda da maganarsa." Ya kalleshi da fadin." Saminu ni ne fa nayi alkawari cewa 'karshen wata ana bani kudin gidana zan biya ka kudin ka amma cin mutuncin da kake min ya isa haka muna gaban hukuma anyi komai a rubuce da kuma sharad'i ka kwantar da hankalinka zamu rabu lafiya insha Allahu." Ya d'an sassauta amma bai saki fuskarsa ba tana tanan kamar hadarin dake dab da zubda ruwa, ya kalli Officer din da fadin." Na amince da hakan amma ayi komai a rubuce da sanya hannuku sannan kuma a fada min ranar da zai bani kudi na domin nima na shiryawa hidimar dake gabana." Officer din ya kalleshi da fadin." Hujaj kaji bayanin Saminu yana bukatar sanin rana da kuma kwanan watan da zaka biya shi hakkinsa." Yayi jim yana nazari wannan maganar kawai dai ya shata ne ya fad'a amma babu wani dilalli da su ka yi cinikin gida dashi kawai ya fadi hakan ne saboda ya kubtar da kansa yana kuma hasashen kafin zuwan lokacin sa'a ta fad'o kansa a gurin sana'ar tasu. Ya ce." ashirin da takwas ga watan uku ya kama ranar lalata kenan insha Allahu zan biya Saminu kud'insa." Officer ya rubuta ya sanya hannu, ya mika masa shima ya sa hannu. Ya kalli Saminun dake tsaye ya sa k'aton ciki a gaba, ya ce."Kai ma kasa hannu akan wannan yarjejeniyar ni ne sheda." Ya kar'bi zungureriyar takardar ya yi jagwlgwalonsa a kai domin dai bai san me ake nufi da singing ba. Bayan kwana biyu 'kura ta d'an lafa ya nufi can abbatuwan in da Saminu ke kasuwacinsa na siyar da nama ya same shi da wata sabuwar magana. Bayan ya gama sauraransa sai ya hau shafa 'katoton cikinsa yana dan murmushi wargajejen wawulonsa ya bayyana ya ce." Eh to Hujaj ban k'i maganarka ba zan iya amincewa da manufarka mutu'kar yarinyar ta kwanta min a raina, saboda haka zan je na duba ta na gani idan ta cancanta sai mu fanshe kawai." Ya sanya dariya da fadin." Ai wannan yarinyar tawa ba ta da makusa cikakkiyar maca ce san kowa k'in wanda ya rasa, matsalar kunne kawai ke da ita amma bata da wani nakasu." Shima yana dariyar ya ce." Ai ni babu ruwa na da matsalar rashi ji daga gare ta, idan tana da abubuwan da nake buk'ata daga jikin mace falillahil hamdu.'' Ya bashi hannu suka tafah! kafin ya ce." Kawai ka je ka same ta a can gidan kakarta dake 'yan gurasa ai gidan ba 'boyayye bane Baba Asabe kowa ya santa a kan sana'arta." Ya ce." Babu damuwa insha Allahu gobe da daddare zan je na duba ta yanda ya kamata." Su kayi sallama cikin barkwanci kamar ba su ta'ba samun matsala ba, Hujaj ya nufi kasuwa cike da farin cikin rabuwa da nauyin Saminu dake kansa, yana da tabbacin cewa yarinyar za ta yi masa kamar yanda yake bukata, tunda duk in da ake bukatar cikakkiyar mace to ta kai gurin. *Turkashi!* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *25&26* Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki ya ji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai ya ce." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? ta'be baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi mu su, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu. Babu ladabi a maganarta ta ce." sai ranar da akayi hankali ni ma zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo. Ta ce." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi." Yana kokarin tashi zaune ya ce."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan." "Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne?" Yana k'o'karin magana su ka ji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje." Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni. Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, ta ce." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka." Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa. Ta ce." Kai har mai ka saya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bu'katar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji." Ya ce." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri." Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai. Jallabiya yasa ya fita. Wani shirgegen k'aton mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne. Ya mi'ka masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo." Ba tare da ya ri'ke hannun da ya mika masa ba ya ce." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba." Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna ka ji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka." Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wad'anda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin." Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa. 'Yar dariya yayi irin wacce ya saba ya ce." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina na fi so mu yi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka." Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah." Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli d'igon gashi babu kan sumul sai uban 'kyalli yake. Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin nan hakkinsa. **** Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har da su zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya. Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa. A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara." "Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci." Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane." Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi ta ce." Shahida ba wai bana so bane. A'a ni bana son kina zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba wallahi." Ta ce." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri a kaina." Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake." Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba. Ta kalleta da fadin." Ki d'auko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin." Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta. Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado. Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa ta zuba masa har da manshanu. Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta d'auki abincin za ta fita, Baban ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba. Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa. Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar. **** Saminu Abbatuwa ya yi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda ya yi masa alk'awari, shiru malam ya ci shirwa, b'angaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye. Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a k'iyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli al'kalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa. Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa. *Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce😳* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *31&32* "Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar. Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karon dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita. "Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fad'a ba ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa! Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan! Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake k'okarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali. Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse? Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata k'arfin iko na a kan 'ya ta." Ta ce." Me take nufi to? Yana k'okarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana." Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke." Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa. Dama ta shirya masa ko da ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya. ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa. Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya." Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shiryawa zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa!" Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga k'okarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki." Ta ce." Jamilu cin mutuncinka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai inda karfi na ya 'kare akan hakan." Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta." Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya d'aya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai Allah yayi muku hisabi." Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.'' Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa. Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata. Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici! Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake k'okarin hada aure da Shahida bai cancanta ba." Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu." Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddin tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba. Tana fitowa daga kantin Lurwanu ta hango shi ya fito daga gidan. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa. Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a tur'bune ya k'arasa in da take. sai ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba. Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai fad'uwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaya gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta." Kallo guda ya yi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shak'i'ki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu. Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya d'auko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.'' Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Ina zaka kai min mata ta?" Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku! "Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun. 'Kin 'karba ya yi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min mata ta?" Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.? Da yake da 'karfi ya yi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci." Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau." Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa. Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai! mahaukaci kawai." yana kai k'arshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu. Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke...... ***** "Ranka ya dad'e ina sauraranka. d'aya daga cikin yaransa ke wannan maganar yayin da yake tsugune a gabansa. Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa Ja'in a cikin garin nan.?" Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka na sumunti dake sharad'a." Ya ce." To ai ta kwana gidan sau'ki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa. Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin?" shuru yayi na minti biyu, sunansa Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa sunansa da kuma unguwar da yake zaune. "Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi wahala ba." Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi k'okari sanin wanene mutumin domin kawo maka cikakken labari a kansa." Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe. Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota domin cika umarnin maigidan nasa. Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a zahiri da bad'ini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da cewa ya san abinda yake. *Binta tana mik'a sak'on gaisuwa ga ilahirin masoyanta💯❤‍🔥* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi joinig domin samun damar karanta littafi na d'aya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *29&30* Da wuri ya dawo gidan, ya umarci Jamila cewa ta shirya da sauri kada magariba tayi ta je ta kira masa Shahida maza su zo tare yana nemanta. Tunda Talatu ta ji haka ta san da wata a kasa. sai ta bishi dakin ta same shi a kishingide yana zan can zucci. Gefan sa ta zauna da fadin." Na ga ka aika a kira maka wannan yarinyar a jikina na ji ruwa baya tsami banza." Ya kalle ta na second biyu kafin ya ja tsaki da fadin." A nan ki ka fi kauri gulma da tsugudidi dube ki don Allah kamar ba mace ba, wannan tufafin na jikinki idan ban mance ba yau kwanansa hudu a jikinki." Hannu ta daga masa da fadin." Ya isa kada ka ci min mutunci, shin da kake wannan maganar ka siya min sabulun wanka ko omon wanki ne."? Shuru yayi mata banda hararar ta babu abinda yake. Tace." Da fatan dai yarinyar nan ba gidan nan za ta dawo da zama ba domin wallahi ba zan iya rike ta ba nima naji da nawa." Tsakaninta da Allah take maganar. Ya gyara zamansa da fadin." Aure zanyi mata itama ta huta da wannan cin mutuncin naki." Tabe baki tayi kafin ta ce." Au ashe ta samu mijin aure amma babu labari." Ya ce." Wannan mutumin ne da yake bina bashi zan bashi kyauta a madadin kudinsa, kin san yarinyar nakasashiya ce za'a sha wahala kafin a samu mai auranta shiyasa na yanke shawarar aura mata Saminu tunda dai shi din ma kansa d'aya da rabi ne. Farin ciki ya cika zuciyar Talatu, babban burinta a duniya a ce Shahida ta wulakanta, a maimakon ta nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa sai ta cigaba da karfafa masa gwiwa cewa hakan da yayi daidai ne, domin shi yake da iko da 'yarsa. Cikin wannan halin Shahida da Jamila su kayi sallama a gidan. Talatu ta fito daga daki tana washe baki, abin mamaki cikin sakin fuska ta amsa gaisuwarta, ita kanta Shahidan abin ya bata mamaki mutuka. Durkushe take a gabansa gabanta in banda faduwa babu abinda yake, tun kafin yayi mata magana ta karanci komai a fuskarsa, labarin gizo baya wuce na koki saura kwana uku wa'adin da ya bata ya cika, wasu zafafan hawaye suka shiga tsere a saman fuskarta. Fuska a murtuke ya daka mata tsawa! da fadin.'' Ba kuka na ce kiyi min ba Shahida ki saurare ni da kyau! kina jina ko."? ya k'arashe maganar da karfin gaske wanda har sai da su Talatu su ka ji sautin muryarsa. "Ina fatan baki mance magana ta dake ta karshe ba."? Murya na rawa da yanayin maganarta ta ce." Ban man ce ba Baba." Ya ce." Wa ki ka tsayar a matsayin wanda za ki aura."? Kai tsaye ta ce." Babu kowa." Ya jima yana kallonta kafin ya ce." To ba zaki mayar da ni mutumin banza ba, kina yawo godai-godai a gari ni ba shashashan uba bane, tunda kin kasa tsayar da mijin aure ni a matsayi na na wanda ya haife ki zan aurar dake ga wanda ya cancanta, saboda haka ki zauna cikin shiri ki kuma shedawa kakarki cewa nayi miki miji zan had'a ku tare da Hadiza na aurar daku a lokaci guda." Wani irin kuka ne ya k'wace mata murya a sarke ta ke fadin." Baba ka da kayi min haka mana kayi min adalci ka sake bani dama a karo na biyu insha Allahu zan fito da wanda na keso." Kafin ma yayi magana Talatu ta bankad'o dakin ta shigo domin duk abinda ke faruwa suna ji ita da yaranta, ta ce." Wa ne irin adalci ki ke so ayi miki ? ai ki godewa Allah tunda har ki ka samu wannan bawan Allah ya amince da cewar zai aure ki a matsayin ki na muskiniya, ki daina daukar kanki cikakkiyar mutum kamar kowa." Maganganun Talatu sunyi mata zafi sosai! a shari'ance ma sunyi tsauri da yawa, jahili ne kadai ya ke bambamce jinsin mutum wanda Allah ya hallita mai lafiya ko mara lafiya, duk wata hallita da Allah yayi akwai manufa kuma ba don baya sonka ya hallicce ka hakan ba, shi ya fi so ya gan ka a hakan ne. Da k'yar ta iya yunkurawa ta tashi. hanyar fita kawai ta nufa hannunta kunshe a bakinta kukan da take dannewa ya'ki dannuwa sai fita yake hawaye kuwa a saman fuskarta sai tsare suke. A bakin titi adaidaita sahu ya sauke ta, yanayin tashin hankalin da take ciki ya sanya ba ta lura dashi ba, yana daga can tsallaken da jarkar ruwa a hannunsa zai je ya samu ruwan alwalwa a tuka-tuka! shi ya gan ta a firgice! hankalinsa kuma ya tashi ainun! ganin yanda take kuka! ya bi ta da kallo lokacin da take karya kwanar layin gidansu, sai da ta k'urewa ganinsa sa'an nan ya tsallaka titin cikin damuwa ya nufi in da tuka-tukar take yana tunanin abinda ya ke damunta. Cikin matsanancin tashin hankali da damuwa ta shiga gidan, kai tsaye rugume kakar tayi tana rera wani irin kuka mai tsuma zuciya! duk da ta kasance nakasashiya ba zata so ayi mata irin wannan auran ba, gabadaya al'amarin bai kwanta mata a rai ba wannan shine dalilin da yake sanya ta zubda hawaye. Baba Asabe ta rike ta suka shiga daki a tare, ita kuwa Saliha ko a jikinta ta'be bakinta ma tayi ta cigaba da aikin gabanta. Da kyar Baban ta rarrasheta ta dora da fadin." Dama tun da naga wannan kiran na gaggawa na san akwai abinda zai faru, Jamilu ba shi da kirki ko kadan kiyi shuru ki fada min abunda sukayi miki." Tasa hannu ta goge hawayen dake gudana a saman fuskarta, ido jawur! ta kalle ta da fadin." Wai aure zai yi min ." Baban ta zuba mata ido cike da mamakin maganar "Aure kamar yaya ."? ta sake tambayarta domin jin cikakken bayani. Murya na rawa da yanayin maganarta ta fara sheda mata hukuncin da baban nata ya yanke a kanta cewa lallai zai had'a ta aure da wanda yayi ra'ayi. Baba Asabe tayi tsalle ta dire! ta fara surfa bala'i ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce." Wato yanzu ne zai nuna iko a kanki saboda bashi da kunya an gama yi masa wahala kin girma kin zama mutum shine zai shigo da wannan maganar to wallahi bai isa ba mutukar ina raye ba za'ayi wannan auran ba." Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba. Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar." Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na aikata wannan abu." Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar al'amarin ba." Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so." Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake. A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana! Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa." Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan." Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa. A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci! Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata. Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani! Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido. Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta. Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin. Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin. ''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta. Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."? Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka." Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."? Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci. Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."? Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa." Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza! Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin." Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi." Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin. Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya. Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin......*MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. *33&34* *KANO* Unguwar giginyu. Shukura cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafad'arta wanda dashi gwara babu. hannunta rike da mukkulin mota tare da handbag tana wani irin k'amshi mai fizgar hankali. Shukura karatun low ta yi yanzu haka ta kammala, tana ta fafutukar aiki, mahaifinta ya ce ba da yawunsa ba, domin dai babban burinsa bai wuce a ce ya aurar da ita, duba da yanda ta kai munzalin auran, bayan haka kuma tana aikata abubuwa marasa kyau irin wanda ba ya so, hakan kuma baya rasa nasaba da sanya hannun uwarta akan dukkanin abunda take. Ganinsa a zaune a gurin hutarsa ya sanya jikinta ya yi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai! Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje. Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko? A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah." Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida." Sai ta fashe da kuka da fadin "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take maganar. Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar magariba. Ya ce." Ina za ki ji? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara." Girgiza kansa ya yi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka! Ta zube a jikin kakar uban tana gursheken kuka. Hajiya Saude hankalinta ya tashi a duniya ta tsani 'bacin ran yarinyar dalili ita kad'ai ce babu wasu. shiyasa take lallabata. ta dinga rarrashinta kan tayi shuru ta fada mata abinda yake faruwa Ta ce." Daddy ne ya ha na ni zuwa kuma kin fi kowa sanin yanda nake da Samira 'kawata ce sosai ai bai kamata Daddy ya hana ni zuwa bikinta ba. Ta ce." Aikuwa bai kamata ba wallahi, shiyasa wani lokacin bana son zamansa a gida saboda yana matsanta miki da yawa bari ya shigo na ji dalilinsa. Tana rufe baki ya shigo da niyyar d'aura alwala. ta dakatar shi ta hanyar kiran sunansa "Alhaji Habu." Ya amsa tare da tsayawa yana sauraranta. "Meye dalilin da ya sa zaka hana yarinyar nan zuwa bikin 'Kawarta kana fa matsantawa yarinyar nan Alhaji Habu." Babu wasa a fuskrasa ya ce." Hajiya wane irin biki ne wannan ? wanda sai magariba za ayi shi, to ba zan lamunci wannan shashanci ba, bayan haka kuma dubi sutturar da take jikinta tuntuni na hana ta sanya dinkuna irin wannan amma taki ta dai na wannan dalilin ya sanya na hana ta zuwa kowane irin biki ta hakura dashi tunda ba ta jin magana." Ta kwantar da kai da fadin." Ai ba za ayi haka ba yarinyar nan Samira 'kawarta ce tare su ka yi karatu ya kamata ace Shukura ta halarci bikinta kayi hakuri ka bar ta taje ba don halinta ba sai dai ni nake nema mata alfarma." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To shikkenan amma ta sanja kaya lallai kuma ki sanya hijabi a jikinki kafin ki fita." Da sauri ta daga kanta da fadin." Insha Allah Na gode Daddy." ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Kamar gaske ta fito da k'aton hijab har k'asa tayi wa hajiyar sallama ta fita, tana shiga mota ta cire hijab din tana jan tsaki ! karamin mayafin dake ciki jakarta ta fito dashi ta rataya a kafad'arta sannan ta kunnar motar fige ta da karfin gaske ta fita daga gidan, kai tsaye rijiyar zaki ta nufa gidan Hajiya Zaliha domin sunyi waya da Mamanta ta ce ta sameta a gidan domin itama ba ta jima da sauka a garin ba. **** Tashin hankali kenan! tun a bakin titi a ka tare shi aka sheda masa abinda yake faruwa, bai gazgata ba sai da ya karya kwanar layin gidan ya ga zahiri! tun daga nesa yake hango jama'a cike a kofar gidansa ga katakwaye da katifu da sauran abubuwan amfaninsu nan a watse a gurin, tonan silili Saminu ya zo yayi a gidan bayan fitarsa yasa zaratan Samari suka dinga watso musu kayan su waje, Hadiza da sauran 'yan uwanta sai kuka suke, ita kuwa Talatu tana zaune a kofar wani gida abin duniya ya dame ta, ma'kota da 'yan uwanta sai bata baki suke, Saminu yasa k'aton kwado (dan mukkuli) ya kulle gidan yayi tafiyarsa. Hujaj tunda yake bai ta'ba tozarta irin yau ba, ya rasa da wane ido zai kalli Jama'ar dake gurin, kawai sai ya huce! fushinsa akan Shahida ya dinga gaura mata mari yana fadin." Kin ga irin abinda ki ka janyo min ko? kin ga tozarcin da ki ka janyo min ko."? ya dinga kwashe ta da mari yana haurinta da kafarsa har sai da ta durkushe a gurin tana wani irin kuka! da kyar aka janye shi daga gurin ana bashi hakuri. Malam Habu makocinsa ya ja shi gefe yana bashi baki da fadin ." Haba Alhaji Jamilu ka nutsu mana ita kuma wannan yarinyar da kake dukanta meye laifinta da zaka huce fushinka a kanta dama tuntuni nake fada maka ka gyara kuskuranka saboda irin wannan rana to yanzu ga abunda ya faru." Ya cire hular dake kansa yana firfita da ita ya ce." Malam Habu wallahi ban taba tunanin Saminu zai yi min wannan tozarcin ba, amma babu komai tsinanniyar yarinyar can ce ta janyo min domin da ta amince da bukata ta da tuni haka ba ta faru ba kamar ni a ce an tozartani irin haka.'' Malam Habu Ya ce." Yanzu dai mu bar wannan maganar insha Allahu komai zai daidaita, akwai daki da rumfa a cikin gidana zan baka aro ka shiga ka zauna kafin mu ga abunda Allah zai yi." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke da fadin ." Na gode sosai Malam Habu Allah ya saka da alkairi." Ya ce." Babu komai bari yanzu nasa yara su kwashe kayan su shiga dasu Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba .'' Ya amsa da "Ameen yana bin gurin da kallo, manya da yara sun cika sunyi dafifi a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa. **** "Ranka ya dade wallahi na dauka binkicen da ka sanya ni zai bani matsala sai gashi cikin hukuncin Allah komai ya zo da sau'ki don lokacin dana shiga Unguwar ban sha wahalar sanin waye Alhaji Jamilu ba." Zamansa ya gyara a nutse ya ce." Sule nima nayi farin ciki da haka ina fatan zan samu kyakykyawan labari daga gare ka." Fuskarsa ta sauya da alhani da kuma jajantawa. Ya ce." Yallabai al'amarin mutumin dai babu arziki babu kuma kima da mutunci.'' "Ina sauraranka." Ya fada tare da mayar da hankalinsa gare shi. Cikin rashin jin dadin abubuwan da ya gani da idonsa ya shiga warware masa abunda ya faru ya kuma dora da bashi labarin da ya samu daka bakunan mutane da sauran jama'ar dake makotaka dashi, domin ya tabbatar masa da gaskiyar binkicensa ya nuna masa hotonan da ya dauka a lokacin da yake ta zazzabgawa yarinyar mari ana ta bashi hakuri. Ya karbi wayar yana duba hotonan ransa yayi masifar 'baci ganin yanda yake dukan yarinyar har da kafarsa, babu shakka wannan mutumin bashi da mutunci kuma bai san darajar dan adam ba, kuma jahilci shike da damunsa ba wani abu ba, hakika ya ji ciwon yanda ya ke tozarta yarinyar a gaban jama'a amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, ya mika masa wayar da fadin." Goge hotonan daga wayarka." Da sauri ya goge gabadaya kamar yanda ya umarce shi. Ya kalle shi a nutse ya ce." Da safe idan Allah ya kai mu ka je ka nemi shi mutumin da yayi tozarcin domin jin cikkenan karin bayani daga gare shi, ina so ya tabbatar maka da iya adadin kudin da yake bi daga baya sai mu ga ya za'ayi ." Ya ce." Insha Allahu zanyi kokarin ganin hakan ya tabbata." Ya ce." Ma sha Allah ka tashi ka je kawai sai Allah ya kai mu goben ." Ya mike yana godiya sannan yayi masa sallama ya tafi. A daran ranar bai kwanta ba sai da yayi Istahara akan al'amarin, ya wayi gari da yarinyar a cikin ransa, yana tausaya mata sosai yana kuma so ya aure ta amma yana tunanin wani abu a cikin ransa, duk da hakan ba haramun bane amma yana ganin kamar yarinyar tayi masa 'kan'kanta da yawa idan anyi duba da matakin shekarunsa, yayi mata girma domin yana kallonta ne kamar 'yar sa Shukura a zahiri shekarunsu na iya zuwa d'aya. **** Sule ya zo masa da cikakken bayani akan Saminu ya warware masa komai da yanda Hujaj din ya dinga yaudararsa har yayi masa alkawarin bashi auran 'yar sa, daga baya kuma ya dinga yi masa yawo da hankali wannan shine dalilin da ya sa ya yanke wannan hukuncin. Ba a ja dogon lokaci ba ya Umarci Sulen da kudi dubu dari hudu ya je ya kai wa Saminun domin kashe wutar yace koma lallai ya je ya bude gidan ya kulle. amma ya gargadi Sulen cewa kada ya kuskura ya sheda masa cewa ga wanda ya biya kudin. Saminu ganin har da riba akan kudinsa yasa da saurin gaske yasa rigarsa ya fito kai tsaye gidan Hujaj din ya nufa, lokacin ya fita yawon Malamai burinsa kawai a daure bakin Saminu sannan ya wulakanta a duniya kamar yanda ya wulakantashi. Sai Malam Habu ne ya kar'bi mukkulin ba tare da ya bi ba'asin komai ba ya bude gidan, yasa yara suka dinga kwashe kayan suna shiga dasu. A gari ya ji cewa Saminu ya dawo da mukkuli har iyalinsa sun koma ciki, sai ya sake gazgata karfin aikin malamin da ya taimaka masa, domin duk a ganinsa aikin malamin ne yayi tasiri. 'Bangaran Baba Asabe kuwa da kyar ta wayi gari, domin tunda Lurwanu mai kanti ya sheda mata cewa Hujaj ya tafi da Shahida hankalinta ya tashi mutu'ka! har tayi niyyar zuwa gidan suyi wacce za suyi Kawu Musa ya hana ta yace a rabu dashi su ga iya gudun ruwansa. Kasa hakuri tayi washe garin ranar da yamma ta shirya ba tare da tayi shawara da kowa ba ta nufi gidan, domin bata tsammanin zata zubawa mutumin ido yayi abinda ya keso a kan marainiyar Allah, dole sai tayi masa karakare! sannan za su daidaita. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi joining domin samun damar karanta littafi na daya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ Pege 37&38 'Kamshi turaran ta ne ya tabbatar masa zuwan ta gurin. Cikin nutsuwa ya d'ago kansa daga barin karanta jaridar da ke hannunsa. 'Bata fuskarsa ya yi yana yi mata wani irin kallo na tuhuma. Lallausan murmushi ta yi masa ba tare da tace komai ba ta fara kokarin zama a kujerar dake fuskantar sa. Cikin tsawa! ya dakatar da ita daga abinda take shirin yi. "Ka da ki sake ki zauna anan gurin.'' Ya fada yana zare mata gabad'aya idanuwansa yanda ya tsani mutuwarsa haka ya tsane ta Fatima tayi masa illah a rayuwarsa. Da hannu ya nuna mata hanya da fadin." Fita ki bani gurin tun kafin ranki ya 'baci." Ta girgiza kai still da murmushin a fuskarta ta ce." Ai ko babu komai ka tsaya ka saurare ni domin kaji da abinda nake tafe, idan ban ci albarkacin Shukura ba sai na ci arzikin zumuncin dake tsakaninmu domin dai ni ba zan yi gaba da kai ba." Tsaki ya ja ya koma ya zauna tare da cigaba da karanta jaridar dake hannunsa. Gurin yayi shiru na minti biyar kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta kalle shi wani irin bala'in son sa na ratsa dukkan sassanan jikinta, ita ce tayi wauta a wancan lokacin, gashi yanzu ya yi mata nisa tayi-tayi ta shawo kansa ta kasa, saboda babu wacce ya tsana sama da ita.'' "Maganar Shukura nake tafe da ita." Ta yi maganar idonta a kansa. Shuru bai d'ago kansa ba ballananta ya bata amsa. sai ta d'ora da fadin." Aiki na samo mata a babban kotun birnin tarraya ina fata ba zaka watsa min 'kasa a ido ba." Babu walwala a fuskarsa ya ce." Babu wani aiki da Shukura za tayi, buri na na ga na aurar da ita ga wanda ya da ce, saboda haka wannan maganar ki ajiye ta a gefe.'' "Me kake nufi kenan.? ta fada d'a b'acin rai a tare da ita. Ya ce." Ban amince da kud'irin ki ba." Sai ta fusata! "Amma dai ka san ba kai kad'ai ka ke da iko da ita ba ko? "Yes na sa ni da ni da ke muka haife ta amma abinda nake so shi za a yi idan kuma akwai matakin da zaki d'auka bisimillah." Fuska a tur'be ta mi'ke tsaye! "Shikkenan tunda haka ka ce zan nuna maka nawa ikon a kanta." Fuuu! ta bar gurin ranta a mugun b'ace! Dogon tsaki! ya ja ya bita da mummunan kallo har sai da ta fita daga gurin. Ya d'auke kansa yana jan ajiyar zuciya tare da tuno kuttun 'bakin cikin da ta k'unsa masa a can baya. ******* Da azama ta shiga d'akin sai dai me? tuntube tayi da ita a raku'be jikin dirowar gado ta hada kanta da gwiwa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Gabanta na fad'uwa ta ambaci sunanta a sanyaye ta ce." Shahida ba zaki fada min abinda ke damunki ba ko? kullum sai ki 'buya a daki kina kuka idan maganar Saminu ce ai ta mutu ki daina damun kanki mutu'kar ina raye ba zan bari mahaifinki yayi miki auran dole ba." Jin yanda take tausar ta da kalamai masu sanyi ya sanya ta sassauta kukan da take yi ta sa hannu ta goge hawayen dake gudana a fuskarta ta ce." Baba ba zaki iya magan ce min matsala ta ba, watakila ma idan na fad'a miki damuwa ta ki kira ni mahaukaciya, shiyasa na gwammace damuwar da nake ciki ta zama ajali na." Maganar ta doke ta sosai! kafafuwanta su kayi sanyi sai ta nemi guri ta zauna tare da fadin." Shahida wace irin damuwa ce wannan ? wacce har ki ke ikirarin ta zama ajalin ki, kada dai a kan mahaukacin mutumin nan ki ke nema ki kashe kanki?" Jin abinda Baban ta ce yasa ta 'kunshe bakinta da tafin hannunta domin ta hana kukan dake k'okarin kufce mata fita. Ta dinga girgiza kanta zafafan hawaye na sharara a fuskarta, murya a sar'ke da yanayin harshenta ta ce." Ki daina kiran sa da wannan sunan domin bai cancanta ba wallahi shi din ba mahaukaci bane kuma zan iya sadaukar da farin ciki na akan sa." Jikinta ya 'kara yin la'asar jin furucin da yarinyar ta yi. ya kamata ta daina tsawwala wa domin ba ta san abinda Allah ya lullu'be ba amma babu shakka al'amarin yana bata tsoro mutu'ka! Ta ce.'' To na ji na daina kiran sa da mahaukaci ko za ki iya fad'a min abinda ya same shi domin tabbas ruwa baya tsami banza Shahida baki ta'ba shiga damuwa ta kwana da kwanaki ba irin wannan ko shakka ba nayi akansa ne." Hanci taja tana jin wani irin rashin dadi a tare da ita ta ce." Yau tsayin kwana goma kenan ban sanya shi a idona ba tun bayan korar da akayi masa daga mazauninsa shikkenan ban sake ganinsa ba, ko na je bakin kasuwar haka zan dawo gida gabad'aya ma mutane sun watsar da kayan sa a bola sai filin gurin tunda mai motar ya d'auke abar sa." Wani irin sanyi ta ji a zuciyar ta amma ba ta nuna a zahiri ba, sai ta shiga girgiza kai cikin alhini da damuwa ta ce." Ayya! Allah sarki shi yasa ashe kwana biyu na ga ba kya kai masa abinci ashe abinda ya faru kenan amma na tausayawa mutumin nan wallahi." Zuciyar ta ta 'kara yin rauni! kukan da take dannewa ya kufce! ta ce." Ni yanzu ban san ya zanyi ba zuciyata tana so ta gan shi ban san a wane hali yake ciki ba, ya kamata a taimaka masa." Kallon tausayi takewa yarinyar domin kuwa Allah ya jarabce ta da soyayya a in da bai da ce ba sai dai addua kawai. Ta ce." Ki share hawayen ki ki daina kuka insha Allahu zan taya ki da addua kuma zan sanya ayi miki saukar al'kur'ani a kan lamari idan da rabon zaku sake had'uwa sai Allah ya had'a ku a wani guri na daban." Hannunta ta ri'ke da fadin." Na gode Baba Allah ya saka miki da alkairi, insha Allahu nima zan dage da addu'a Allah ya bayyana mana shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." ******* "Alhaji Sammani mai leshi wani d'an kasuwa ne wanda ya kasance abokin hurd'ar Hujaj ta 'boye! shima yana caca kuma yana samun alkairai sosai yana kasuwancin ne kawai domin kawar da hankalin jama'a daga kansa. Tarin kud'ad'an da yake bin Hujaj ba za su lissafu ba, domin dai Hujaj! gabad'aya duniya ta juya masa baya komai nasa ya tsaya cak! sai buge-buge! yake yana yawon malamai k'auyuka da zaurukan malamai ba irin wanda bai je ba domin a duba masa me yake faruwa da rayuwar sa. Kimanin miliyan biyu da rabi Alhaji Sammani yake bin sa, kuma a wannan lokacin ya bu'kaci da ya bashi kud'insa domin yin wata bu'kata! Ya rasa ina zai tsoma rayuwarsa ya yi nan yayi can fagau-fagau! ya zama wani shashasha! har ya fara surutai a hanya, shawarar da ya yanke shine sanya gidansa a kasuwa domin ya biya bashin kudin da ake bin sa! Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin su yi joining domin samun damar karanta na daya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Mutane masu karamci da mutunci ina godiya da adduarku tare da 'kwarin gwiwa💯❤‍🔥* _*JAMILA YUSHA'U*_ _*FAUZIYYA MU'AWIYYA*_ Tun a farkon fari muke tare. ina ro'kon Allah ya had'a fuskokinmu da alheri🙏🏻 *35&36* Lokacin da ta isa gidan baya nan, amma kuma daf yake da dawowa domin ya yi shiri na mussaman na zuwa mahad'arsu. Babu yabo babu fallasa Talatu ta karbe ta. suka gaisa sama-sama kafin ta bar ta zaune a gurun. Jamila ta shigo gidan hannunta rik'e da 'bakar ledar dake dauke da kayan miya gwalagwaji. ganin ta yasa ta washe baki da fadin." Baba ke ce a gidanmu?" Ta saki fuska da fadin." Ni ce Jamila ai na jima da zuwa ina zaune ina jiran dawowar babanku." Ta ce." Aikuwa yana kan hanya domin lokacin dawowarsa yayi." Talatu ta fito daga kicin ranta a 'bace ta harare ta da fadin." Sarkin shishshigi da cusa kai a maimakon ki kawo min aiken da nayi miki shine ki ka tsaya kina neman suna ko.?' A sanyaye ta ce." Ki yi hakuri." Tsaki taja da karfi ta fizgi ledar dake hannunta aikuwa ta ya ge kayan miyan suka watse a gurin, sai kawai ta hau d'ura mata ashar! ranta a a b'ace ta yi saurin barin gurin tana turr!! da halin mahaifiyarsu sam bata da d'abia mai kyau. Shahida ta fito tsakar gidan da alamun bacci a idonta, Jamila ce da ta shiga dakin ta tashe ta daga baccin tana sheda mata zuwan Baba Asaben. Ganinta yasa zuciyarta karyewa sai kawai ta zube a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai sosa zuciya. Jin kuka ya cika gidan ya sanya tayi gaggawar Fitowa daga kicin da ludayin miya a hannunta nan ta iske Baban na rarrashinta da fadin." Tayi shuru ta share hawayen ta mutukar tana raye babu mahalukin da ya isa yayi mata auran dole. Karaf ta bude baki ta ce." Wannan fa ba hurumin ki bane Baba kina nema ki wuce gona da iri a akan wannan yarinyar." Ta daga mata hannu da fadin." Saurara haka kada kiyi min rashin kunya ba gurin ki na zo ba gurin mijinki na zo kuma shi nake zaman jira saboda haka kada ki kuskura ki kara wata magana a cikin wannan al'amari." Ta ja dogon tsaki tana surutai kasa-kasa ta juya ta shige kicin domin cigaba da aikin dake gabanta. A gaggauce ya shigo gidan. sai kawai yayi tozali da ita a zaune tare da yarinyar a kusa da ita, kallo daya yayi mata ya san da abinda ta zo. A tsaye ba tare da ya risina ba ya gaishe ta. itama fuska a daure ta amsa, da sauri ya nufi hanyar dakinsa sai ta dakatar dashi ya tsaya tare da soka hannuwansa a cikin aljihun rigarsa. Ta ce." Ba wani abu ne ya kawo ni gidan ka ba sai wannan yarinyar domin na zo ne na tafi da ita saboda ba zan ta'ba yarda ka cutar da ita ba." Ya ce." Kin taba ganin uban da ya cutar da abinda ya haifa?" Ta ce." Sau nawa kuma sai dai idan ba a sa son zuciya ba." Ya girgiza kai da fadin "Shikkenan Baba ni ba naso mu dinga jayayya da juna, zan baku dama da lokaci dake da yarinyar domin ni ba mutumin banza bane nayi nufin yi wa 'ya ta aure kin hana to wannan ce dama ta 'karshe a gare ku sati uku kacal ya rage bikin Hadiza kuma so nake na had'asu duka na auran, a cikin wannan satikan nakeso Shahida ta tsayar da miji idan ba ta tsayar ba wallahi tallahi zan had'a ta aure da duk wanda nayi ra'ayi. Cike da alhani da jajantawa yarinyar Tace." Wai shin Jamilu kai wane irin uba ne mara tausayi da jin kai? shin baka ganin halin da yarinyar nan take ciki ne, bata da koshin lafiya wane namiji ne a wannan zamanin zai iya da lalurarta" Ya ce." Tunaninki daban da nawa, ni a ganina duk wannan ba matsala ba ce kuma wanda zan bawa auranta zan sheda masa matsalarta cewa kurma ce to sai kuma me? tana da duk abinda da namiji yake bukata a jikin mace matsalar rashin ji ba zai ha na komai ba, saboda haka wannan shine hukuncin dana yanke." yana kai karshen maganarsa yayi gaggawar bude dakinsa ya shiga. Jiki a sanyaye suka koma gida, duk da cewa ba duka taji komai ba amma ta tsinci wasu maganganun, hawaye kawai take sharewa ta je ta kudindine a kan gado zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta. Kawu Musa ne ya kai ta chamis aka duba ta tare da bata magani, a wannan lokacin ya tausayawa yarinyar sosai amma ya za suyi da abinda yafi 'karfinsu Jamilu shi yake da iko da 'yarsa ko'ina aka je shiyasa da ya ji Baba Asaben tana ikirarin kaishi kotu ya hana ta ya ce tayi hakuri kawai kanta za ta bawa wahala Jamilu ya fi su rinjaye da yarinyar. Kwananta biyar a kwance tana jinyya kafin ta warware ta rame fuskarta tayi haske da tafin kafarta da hannunta alamu sun nuna tana bukatar ruwa a jikinta. Ta fito da hijabi a wuyan ta. Ta kalle ta da fadin." Shahida Na ce ." Ki bari yara su kai abincin nan tunda har yanzu jikinki bai gama dawowa daidai ba kiyi hakuri ki koma ki kwanta. Zum'bura baki tayi cikin yanayin da Allah ya halliceta Ta ce." Ni dai idan kin zuba masa kawai ki bani na tafi na kai masa." Tayi murmushi da fadin." Shahida ko dai wannan mutumin dashi za ayi ne.? Murmushi tayi tana kawar da fuskarta. Wani irin tausayin yarinyar ya lullube ta idan ba sharrin zuciya ba mai zai ja hankalinta kan mahaukacin da bashi da asali kawai ganinsa akayi rana tsaka, wannan yana daya daga cikin sharrin *SO!* dole tayi wa yarinyar uzuri. Ta mika mata kwanon abincin da fadin." To gashi nan amma kada ki ce zaki zauna a gurinsa kamar yanda ki ka saba zaki janyowa kanki jifa da tsokanar yara domin dai duk wanda ya gan ki tare dashi zai dauke kema irinsa ce." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Yanzu zan dawo insha Allahu." Hanyar fita ta nufa, sai ta bita da kallon tausayi da jimami! **** Yana can cikin k'arkashin motar a kwance kafafunsa kawai take hangowa sunyi 'kura sosai amma babu kaushi ko faso! a tafin 'kafar sai dai daud'a. Da d'an karfi ta kirayi sunansa "Baban-Baba." Jin muryata a cikin kunnansa yasa da sauri ya bude idonsa ya fara kokarin fitowa daga kasan motar. Ido ya tsira mata yana mata wani irin sihirtaccen kallo, kaunarta yake har cikin kokon ransa. Murmushi tayi ta dan tsuguna kusa dashi ta ajiye kwanon abincin a gabansa, a nutse Ta ce." Ina wuni." 'Kin amsawa yayi kawai ya kafe ta da kwayoyin idanunsa wanda ta so ta fuskanci wani abu a tare dashi, sai kawai ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannnunta. Ba zato ta tsinkayi maganarsa." Kin tafi kin barni da tunaninki." Kallonshi tayi tana so ta tabbatar da maganarsa. Ya lumshe ido tare da daga mata kai "Nayi kewar ki My dear." Gabanta ya fad'i ta dinga kallonsa tana mamakin kalaman dake fitowa daga bakinsa kamar ba wannan mai tabin hankalin ba. A sanyaye Ta ce." Ga abinci nan kayi hakuri nima kwana biyu bani da lafiya shiyasa ban zo ba." "A jiki na naji hakan domin tare muka kwanta ciwo nima bani da lafiya my dear amma ganinki a yanzu ciwon ya tafi." A d'an tsorace ta ce ." Don Allah waye kai nifa har yanzu zuciyata bata amince min da cewa kana da tabin hankali ba, haka kawai nake tausayinka. Shuru yayi bai ce mata komai ba. A lokacin ta fahimci sauyawa daga gare shi, sai ma ya shige 'kasan motar ya bar ta a tsugune a gurin. Ta mike tsaye tana 'karkade jikinta tana juyawa taga yara sun fara taruwa a gurin, da sauri ta tsallaka titi ta shiga layinsu cikin sassarfa. Washe gari ma da safe ita ce ta kai masa abin kari, sai dai lokacin da ita isa bakin titin baya nan, sai dabbobi a kwance akan buhun da yake kwanciya duk sunyi kashi da fitsari! gurin sai wari yake ga shara nan birjik da bawon lemo da sauran tarkace! Tsigar jikinta ta tashi! ta tsani ganin kazanta a rayuwarta, wai yanzu a ce mutum mai rai! wanda Allah ya daraja shike kwanciya a gurin, ta girgiza kai tana kokarin mayar da kwallar dake kokarin zubo mata, kofin kunun ta ajiye a can gefe in da babu k'azanta! ta juya gaba da baya tana duba gurin, da yake yanzu garin ya waye babu mutane sosai amma dai wandanda ke sana'a a bakin kasuwar sun fara fitowa yara 'yan makaranta da wanda ke cikin ababan hawa suna ta wuce wa suna kallonta lokacin da take kokarin korar dabbobin dake kwance a kan shimfidar buhun nasa. Wani almajiri ya zo ya tsaya da roba a hannunsa. Kallonsa tayi idonsa cike da 'kwansa da alama tashinsa kenan daga bacci ya fito neman abinda zai sa a bakinsa. Cikin yanayin da Allah ya halliceta take masa magana." Ya ce." A she baki sani ba ai jiya da daddare wani mutumi ya zo wai ashe shine mai wannan motar." Ya fada yana nuna katuwar akori kurar da ta jima a gurin. ya cigaba da cewa." Ya gargadi Baban-Baba cewa lallai ya kwashe tarkacensa daga gurin zai turo kanikawa su kwance motar ya siyar da ita. Gabanta ya dinga dukan uku-uku! baki na rawa." Ta ce.'' Yanzu ina yake."? Cike da rashin fahimta ya ce." Waye? Murya a sama ta ce." Baban-Baba." Wata hanya ya nuna mata da fadin." Ni dai waccan hanyar na ga ya nufa." A take hawayen da take dannewa suka 'kwace suka fara gudana a saman fuskarta, jikinta sai rawa yake tana bin hanyar da kallo! "Shin ina yake ne a yanzu? wane irin hali yake ciki? wannan tunanin take a zuciyarta idonta kurr! akan hanyar da almajirin ya nuna mata. A sanyaye Ya ce." Kiyi hakuri ki daina kuka nima nayi nawa kukan na gaji." Ta kalleshi da ragowar hawaye a fuskarsa ta ce." Saboda me zan daina kuka d'an Malam ina tausayin mutumin nan." Ya ce." Yana da kirki kullum sai ya bani abinci na ci na 'koshi, shiyasa da aka kore shi daga gurin nan ban san ya zanyi ba." Hannunta tasa a kafadarsa Ta ce." Kayi hakuri ka ji ko insha Allahu Allah zai sake had'a mu dashi, maganar abinci kuma ni zan cigaba da baka ai kasan gidan Asabe mai abinci ko?" Da sauri ya daga kai da fadin." Eh na sani." Ta ce." To kullum ka dinga zuwa kana karbar abincin. Cike da murna da farin ciki Ya ce." Na gode sosai Allah ya shi albarka. Ta ce." Bude robar abincin naka." Da sauri ya bude ta juye masa kunun da zafinsa da sugar sannan ta bashi fulas da kosai a ciki ta ce." Idan ka gama karyawa sai ka kawo fulas din gida." Ya dinga godiya kamar zai fashe da kuka. Cikin mutuwar jiki da muguwar damuwa ta tsallaka titin ta shiga layinsu cike da jimami da fad'uwar gaba. *Jama'a tafiya tana kara nisa kada dai ku manta cewa wannan littafin na kudi ne adalci guda da nayi muku tsawaita free peges har book1 ina fatan za ku yi kokarin sayan littafi na biyu, domin karanta cikakken labarin.* Hanyar da za a biya kudin mai sauki ce...#500 Vip 1k 0542382124..Binta umar gtbank, idan kati za a turo sai ki dauko hoton katin mtn ki tura mini ta WhatsApp, mutanan nijar kuma za ku turo da dala dari Vip jakka daya, katin airtel za ku tura min da shi ta wannan number 07084653262 Allah ya ba mu sa'a da rabo mai amfani. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ Pege 41&42 Cike da fuffuka! irin ta rashin gaskiya ya nuna ta da yatsa da fadin." Kada ki yi min maganar banza da wofi mana; don uwaki ni za ki zauna kina tsarawa magana, ke din guda nawa kike? me ki ka sani a rayuwa da har zaki zo kina kawo min 'kabli da ba'adi, to wannan shine gargadi na dake na karshe! kada wani abu ya sake faruwa ki zo kina min wasu zantuka ranki sai yayi mummunan 'baci! wallahi." A sanyaye ta ce." Kayi hakuri Baba." tsawa! ya daka mata ya nuna mata hanyar fita da fadin." Fita ki bani guri shashasha kawai." Da sauri ta fito tana share hawaye! Talatu ta ja tsaki da fadin." Aikin banza yarinya kina wahalar da hawayenki a wofi wannan mahaifin naku ai ya riga yayi nisa domin ba zai ta'ba gane hanya ba, don haka kowacce ta nemi madafa don duk wanda ya dogara da Jamilu 'bacin rai ne zai kashe shi." Hadiza ta ce." Talatu duk lalacewarsa ubanmu ne babu yanda za mu yi dole mu shiga damuwa." Ta ce." To ai sai ku yi karo karo ku biya masa bashin da ake bin sa shashashai kawai ana nusar da su suna baud'ewa." To in ban da rigima irin ta Talatu ya za su yi ? za su je su rufe shi da duka ne? ai ya riga ya gama yi musu illah! a rayuwarsu dole kuma su yi hakuri su cigaba da yi masa addu'a domin ba a canzawa towo suna. A na kiran sallar isha'i mai adaidaita sahu ya sauke ta a bakin titi. Kud'insa ta bashi ta fara kokarin tsallaka titin da nufin shiga layinsu, dan gabadaya Hankalinta yayi gida ganin garin yayi duhu, gashi babu wani cikkaken haske akan titin. tana kokarin tsallakawa kawai ta ji ana jan gefen hijab d'in ta. A razane! ta juyo sai tayi saurin ja da baya tana kallonsa gabanta na wani irin fad'uwa! Yana nan yanda yake sai dai an samu sauyin tufafi a jikinsa, amma fuskarsa tana nan cike da 'kasumba sumar kansa duk a cukurkud'e! Yana sanye da tazarce na shadda bulu sai dai ta kod'e sosai tayi haske sai wani takalmi sosa a kafarsa shima ya sud'e! amma babu datti a tare dashi. Murmushi kawai yake mata yayin da yake mata wani irin kallo. Ita kuwa gabanta sai bugawa! yake tana kallonsa tana so ta tabbatar da cewa shine ko kuma aljani ne domin al'amarin ya 'bata tsoro mutuka! Maganarsa ta dawo da ita hayyacin ta. "Shahida ni ne Baban-baba kina mamakin gani na ko?" da d'an k'arfi yayi maganar saboda ya san lalurar ta. Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke har yanzu da ragowar tsoro a tare da ita ta ce.'' Baban Baba kai ne da gaske ko dai idona ne yake min gizo." Ya sake matsowa kusa da ita a nutse ya ce." Ni ne dai masoyinki na san kin yi kewata ko? nima ina can hankali na yana kan ki." Wasu hawaye masu zafi suka 'kwace mata ta ce." Alhamdulillahi Allah Na gode maka daka 'kar bi addu'a ta." Yana murmushi ya ce." Ai d'azu akan idona kuka fito tare da wata abokiyar ki sai na ga fuskokinku cike da damuwa! ganin haka ya sa jiki na yayi sanyi na ce lallai akwai abinda yake faruwa, wannan dalilin ya sa na ce sai na zauna na jira dawowarki kafin na tafi." Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta. Ya dan sake matsowa daf da ita da fad'in." Ko ba zaki iya fad'a min damuwarki ba?" Ta kalle shi tana girgiza kai. Ya tausasa murya da fadin." Ina sauraranki ki sanar dani abinda yake faruwa domin ganin ki cikin damuwa da tashin hankali ya sanya ni cikin wani hali." Ita dai a tsorace take dashi dan sai waiwayen bayanta take. Shima ya fahimci hakan ya ce." Kina jin tsoro na ko? Zuciyarta ta karye sai kawai hawaye suka shiga gangarowa ta sanya hannu tana sharewa wasu na biyo baya! sai jan majina take. Wani irin ciwo zuciyarsa take masa. tuntuni ya tsani zubar hawayen ta ita ce ba ta fahimci hakan ba. Ya rasa yanda zai yi a gurin yana jin kamar ya rungume ta ya rarrashe ta, sai dai ya daure ya shirya kalaman rarrashi ya fara kwantar mata da hankali har ya samu ta daina kukan. Ta kalle shi; nan ta fahimci cewa yana cikin damuwa da kukanta, sai ta sassauta fuskarta ta d'an yi kasa da kanta ta ce." Ka fara fad'a min ya akayi rayuwarka ta sauya ? wani almajiri dai ya tabbatar min da cewa an tashe ka daga gurin da kake rayuwa to tun daga lokacin ba a 'kara ganin ka ba. shin dama kai din ba mahaukaci bane?" Murmushi yayi, ya ce." Ni ba mahaukaci ba ne Shahida." Da sauri ta kalle shi tana mamakin furucinsa, koda yake ba abun mamaki bane a gurinta tunda dama can ita ba ta yi masa wannan kallon. Ya cigaba da cewa " Rayuwa ce ta mayar dani haka amma yanzu alhamdulillhi na gode Allah tunda ya mayar min da alkairi ya had'a ni da uban gida wanda ya dauke ni aiki a garin abuja, ina masa gadin gidansa ni nake kula da masu shiga da fita! wannan shine ya sauya min rayuwata na dawo cikkaken mutum kamar kowa tunda bani da fargabar ci da sha da kuma gurin kwanciya komai ya d'auke min, nutsuwa ta zo min ban yi tunanin kowa ba sai ke domin ina ganin zaki iya amincewa mu rayu a inuwa d'aya." Hannu tasa ta rufe fuskarta kunyarsa ce ta rufe ta. Ya raunata murya da fadin." Ko kina ganin nayi miki tsufa ne? ko kuma kina gudun kada 'yan uwanki da 'kawayenki su yi miki dariya."? Hannunta ta cire tana girgiza kai ta ce." A'a wallahi bana shakka kuma bana jin kunyar mutane su gan ni tare da kai! so na gaskiya nake maka, kuma wallahi zan iya rayuwar aure da kai a cikin kowane hali, ina rokon Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninmu." Ya amsa cike da walwala da farin ciki. Ya ce." To yanzu ya za a yi nayi magana da mahaifinki domin jibi nake so na koma bakin aiki na." Shuru tayi tana Nazari! Ya ce." Shahida akwai matsala ko?" Kanta ta d'aga murya a sanyaye ta ce." Mahaifi na yana cikin matsananciyar damuwa da rashin lafiya! gashi bama jituwa da juna kullum cikin yi min tsawa! yake tunkararsa da wannan maganar zai yi wuya domin bashi da fahimta, ita ma Baba Asabe tana da tata matsalar. Ya ce." Ko zan iya sanin matsalar.?" Shuru tayi tana jin nauyin fad'a masa! dole duk d'an halak yayi kishin iyayansa. Ya ce." Ki daina shakkar fada min damuwarki Shahida ni dake mun riga mun zama d'aya." Shuru tayi ta kasa magana. Ya d'anyi murmushi da fadin." Ki fad'a min kada kiji komai, ni mai rufa miki asiri ne a kowane yanayi." A sanyaye ta fara bashi labarin abinda yake faruwa. Shuru yayi na minti uku kafin ya ce." Ina ganin wannan ba a abun damuwa bane insha Allahu, ni zan yi iyakar bakin 'kokari na akan al'amarin ina da alfarma sosai a gurin maigida na zai nemi alfarma a gurinsa insha Allah ba za ku tozarta ba." Ta ce.'' Kudin fa suna da yawa." yayi murmushi da fadin." Ba zai gagara ba insha Allahu rabbi.'' Ta dinga kallonsa ta na tunanin yanda za ayi har a samu a biya wannan kudi masu yawa, to amma tunda ya ce Allah ya gama magana. Har 'kofar gida ya rakata suna tafe suna hira ta fahimtar juna sosai ta saki jikinta dashi, ta kuma samu sassauci a kan fargaba da tashin hankalin da take ciki. Sai dai har yanzu tana mamakin sauyawarsa. Cike da farin ciki biyu ta shiga gidan. Sai kawai ta riske su a tsaitsaye a tsakar gidan har da kawu Musa a cikinsu, da alama akwai maganar da suke. Gabanta ne ya fadi! ganin fuskokinsu babu walwala ko kad'an! Kafin ma tayi magana ya rufe ta da fada! ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Sai kawai ta fashe da kuka ta durkushe a gurin tana shashshe'ka! Baba Asabe ta ce." Ka kyale ta haka tunda dai Allah yasa ta dawo lafiya shikkenan magana sai ta wuce." Ya ce." Idan gidan uban nata take so ta koma ai sai ki had'a mata kayan ta, amma idan ba haka ba mai zai sanya ta dinga wahalar damu, kawai ina zaman zamana an taso ni a tsaye 'karfe goma na dare idan ba shashashan uba ba waye zai bar 'yar sa tana gantali a hanya irin haka." Ta ce." Na ce ya isa haka don Allah kada mak'ota su ji abinda yake faruwa, tunda dai ta dawo magana sai ta mutu." 'Kwafa! yayi da girgiza kai ya kalle ta da fadin." Ni zan tafi gida sai da safe." Ta ce." To Allah ya tashe mu lafiya" Ya kama hanya ya fita da takaicin abin a cikin ransa. Saliha kuwa bayan fitarsa tsaki ta ja ta shige daki tana surutai! Ya rage da ita sai Baba Asabe a tsakar gidan. Ta ce." Ai sai ki tashi kuma kukan da kike bashi da amfani domin sai da na ce miki kada kiyi dare duba da yanayin garin da kuma lalurarki idan shi Jamilun bashi da hankali to mu muna dashi" Cikin b'acin rai na yanda suke cin fuskar mahaifinta ta ce." Baba ku daina daukar alhakinsa haka don Allah." Sai ta ri'ke baki da mamaki a tare da ita ta ce." 'Karya akayi masa kenan?" Girgiza kai tayi ta ce." Tuntuni na dawo fa babu ruwan Babanmu shine ma ya ce na tashi na tafi kada dare yayi min." Ta ce." To a ina kika tsaya har goma na dare." Kai tsaye ta ce.'' Ina tare da Baban Baba." Gabanta yayi mummunan fad'uwa!" Baki na rawa ta ce'' Baban-Baba kuma?" Ta amsa da "Eh." tana kokarin tashi tsaye. Ta cigaba da cewa." Ya zo ne saboda ni, kuma mun tattauna maganganu masu muhimmanci! wallahi Baba baki ga yanda rayuwarsa ta sauya ba dama na ce miki ba mahaukaci bane." Baba Asabe jikinta yayi sanyi sosai kawai ta dinga kallonta ta gaza cewa komai, mamaki da al-ajabin al'amarin kawai take. A daran ranar dai da 'kyar Baba ta iya rintsawa tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki na al'amarin yarinyar da wannan mutumin da take zargin wani abu a kansa. Mamakin ta ya kara tsananta lokacin da Shahidan take sheda mata irin maganar da suka tattauna dashi. wato Maganar aure da kuma taimakawa mahaifinta da zai yi." Ta kalle ta da fadin." Shahida anya kina da hankali kuwa.? Kafin tayi magana Saliha ta kyalkyale da dariya da fadin." Ras! take tsabar iskanci ne wallahi! amma Baba ki kyale ta kawai jiki magayi ta je ta aure shi jikinta zai gaya mata." Baban ta girgiza kai da fadin." A'a Saliha ba za ayi haka da ni ba, domin yarinyar nan amana ce a hannuna ban bari ta an aura mata Saminu abbatuwa ba to kuwa ba zan bari ta auri mahaukaci ba." A hankali suke maganar dan kada ta ji." Ta kalle su ranta a masifar 'bace ta ce." Baba na san duk kokarin ki kada nasha wahala a rayuwa! wallahi nayi imani da Allah mutumin nan ba zai azabtar dani ba, yana sona ina sonsa mai zai sanya ki dinga mugun tunani akan al'amarin, ni dai mutukar kina so ki ga farin ciki na to ki amince da abinda nake so kuma ki bini da addu'a. Sai kawai tayi shuru tana kallonta gabadaya jikinta ya mutu ta rasa yanda za tayi ta kamo bakin zaran. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ WANDA BAI JI BARI BA...! 39&40 To ko da ya sanya gidan nasa a kasuwa bata canza zani ba. Domin kuwa duk dillalin da yazo domin ya duba gidan ba ya yi masa 'kima ta mutunci. duba da yanayin unguwar ta gargajiya ce. bayan haka kuma gidan irin ginin taka haye ne irin ginin 'yan kanci! duk fulastar ta zaizaye! ramuka ciki da wajan gidan, sannan kuma duka d'akuna uku ne sai tsakar gida madaidaici da kicin da band'aki. Wannan dalilin yasa gidan bai yi wani daraja ba. sai wanda yazo daga k'arshe ne ma yayi wa gidan 'kima ta mutunci ya saya miliyan daya da dubu dari biyu, amma duka na bayan sun taya ne a wula'kance! Ganin ba yanda zai yi ne ya sanya ya sallama gidan a hakan, idan ya so sai ya biya bashin miliyan d'aya tare da alkawarin cika sauran a cikin 'yan kwanaki kad'an domin akwai wasu kudi da yake sanya rai a kansu duba da cewa malaminsa ya tabbatar masa da samuwar su. Alhaji Sammani ya nu na rashin amincewar sa akan hakan. A cewarsa ya za ayi yai masa wasa da dukiya duba da cewa shi a dunkule ya bashi, amma zai tsinka masa kud'i a cikin miliyan biyu da rabi an bashi miliyan d'aya mai zai yi da ita a wannan lokacin da yake bukatar kud'in masu kauri da zai yi order amma za a zo masa da wasa! ba tare da 'bata lokaci ya nufi police station. domin shigar da 'kara mutukar akan kudi ne baya saurarawa kowa ciki kuwa har da 'yan uwansa. "Alhaji Sammani ban yi tunanin za kayi min haka ba wallahi, yanzu ni ka kawo police station? na d'auka ai kai mai rufa min asiri ne a kowane hali. Alhaji Sammani me akayi akai miliyan biyu da rabi da har zaka tozarta ni." Murmushi ya yi ya ce" Alhaji Jamilu ni kaina ban so hakan ba amma duk kaine ka janyo duba da ganin yanda kake min yawo da hankali alhalin na sheda maka cewa ga bukatar da zanyi da kudin nan. shin wai ko so ka ke ka talautani ne kamar yanda ka talauta kanka." Murmushin takaici ya yi ya ce." Kana da damar da zaka fad'i duk abinda kake so, amma ka sani sai kayi nadamar abinda kayi min.'' Ya zakud'a kafad'arsa da nuna alamun bai damu ba ya ce." Kud'i na kawai nake bu'kata a yanzu gani a zaune ga kuma Yalla'bai shi zai zama shaida zan kar'bi miliyan d'aya ba don raina ya so hakan ba sai don samun maslaha a tsakaninmu, sabida haka ka fadi lokacin da zaka cikan kud'i na." Shuru yayi gumi sai karyo masa yake. D.P.O Ya ce." Alhaji Jamilu kai muke saurare." Kansa ya d'ago ido jawur! ya ce." karshen watan nan insha Allah zan biya Alhaji Sammani Kud'insa." D.P.O yayi rubutu cikin wata takarda ya bashi ya sanya hannu. Ya kalle shi da fadin." Wannan shine 'karshen magana Alhaji Jamilu, iyakar adalci anyi maka kada lokaci ya cika ka zo da wata magana, hukuma ba zata saurare ka ba idan baka cika al'kawari ba to zamu d'auki mataki na gaba." Ya ce." Babu damuwa Allah zai rufa asiri." Daga haka bai saurari jin wani abu daga gare su ba ya tashi fuuuuu! ya fita daga ofis din. Duk suka bi shi da kallon mamaki! **** A shirye ya fito ya same ta zaune a falo tana kallo. kafin ma ya yi magana ta riga shi da fadin." Ranka ya dade ina son magana da kai." Tunda ya ji haka sai yayi murmushi ya nufe ta ya samu guri ya zauna tare da fuskantar ta. cikin zuciyarsa yake raya cewa maganar dai d'aya ce amma ba zai yi saurin yanke hukunci ba tukkuna. Ta gyara zaman ta da fadin." Hajiya Fatima ta kawo k'arar ka akan Shukura wai ta samo mata aiki amma ka hana shine nake so na ji dalili." 'Bacin ransa ya danne ya ce." Hajiya ki cire kan ki a cikin wannan maganar don Allah. domin ba ni da wannan ra'ayin, babban buri na shine Shukura ta samu miji nayi mata aure amma ni ba zan yarda da wannan tsarin ba." Ta ce." Sabode me? kenan karatun da tayi ya tashi a banza?" Ya ce." Bai tashi a banza ba mutukar za tayi amfani dashi ta hanyar da ta dace. nufi na anan shine ta tarbiyan tar da yaran ta sannan tayi biyayyar aure." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Hakane kai ma kana da hujja amma ai har yanzu ba ta samu tsayayye ba, mai zai hana ka bar ta domin ta ci gajiyar karatun da tayi." Girgiza kansa ya yi, alamun bai amince ba. ya dan kalli agogon dake daure a hannunsa ya ce." Wannan maganar mu bar ta kawai Hajiya kawai ki cigaba dayi mata addua'a." Ta ce." To shikkenan Allah ya za'ba mata miji nagari." Ya amsa da "ameen." Kallonsa tayi lokacin da yake kokarin tashi ta ce." Yanzu kuma ina ka nufa? kwana biyu dai na ga ka zauna a gida ka huta sosai na ji dadin hakan." Ya ce." Kano zan tafi amma iyakaci na kwana biyu zuwa uku zan dawo saboda akwai tafiyar da zanyi zuwa Spain insha Allah." Ta ce." To Allah yayi jagora ya tsare ka a duk in da zaka shiga. Sai dai ba zan fasa yi maka maganar aure ba, Alhaji Habu mutukar ka naso ka cika cikakken mutum to dole kayi aure idan ba haka ba to jama'a ba za su daina zargin ka ba." Murmushi ya yi ya ce." Na kusa aure Hajiya insha Allahu kiyi min addua." Fuskarta cike da annuri ta ce." Alhamdulillahi haka nake so na ji to ubangiji Allah ya baka tagari.'' Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina." ******** Tsabar fargaba da tashin hankali ya haddasa masa matsanancin ciwon kai! wanda duk dauriyarsa sai da ya kwanta! hankalin Talatu ya tashi domin ko banza idan ya fita ya samo wani abu yana rage mata wata wahalar gidan! ta shiga nan, ta fita can. yawon cin bashi domin samun abinda za su ci da yara. Ganin saura 'yan kwanaki wa'adin ya cika ya sanya ya yanke shawarar sanar da ita halin da ake ciki ko da taimakon da za tayi akan lamarin. Tashin hankali kenan! maimakon ta tausaya masa halin da yake ciki sai ta shiga surfa masa rashin mutunci da tsiya iri-iri da tozarci! a cewarta shi ya sayi hakan da kud'insa saboda haka ita babu wani taimako da za tayi masa domin shi kadai yake cin kud'insa hakkinta da na yara baya saukewa! saboda haka matsalarsa ce! a halin da ake ciki 'ya'yansa ne kawai suke tausaya masa domin sune suke jinyarsa! Talatu ba ta bi ta kansa harkokin gabanta kawai take. Jamila ce ta yanke shawarar zuwa ta fad'a mata halin da mahaifin nasu yake ciki na rashin lafiya, da kuma irin tashin hankalin da suke ciki. Kasa hakuri tayi hawayen takaici suka k'wace mata! ko shakka ba tayi fargaba da tashin hankali ne suka janyo masa ciwo! me za ayi da wannan hali irin na mahaifinsu, duniya ta sani suma 'ya'yansa sun sheda cewa abinda yake aikatawa haramun ne, anyi anyi dashi ya bari ya'ki! kullum sake tsunduma kansa yake a masifa! yau shine cin bashin wancan. gobe shine cin bashin wannan. kuma kudi ba kad'an ba! to yanzu dai yayi kankat! gidan da yake tutiya dashi ya sarayar dashi kuma bukatarsa ba ta biya ba, dama karshen kwad'ayi jin kunya! Mutumin da ya sayi gidan ya bada notice saura 'yan kwanaki, kana kuma ga wani can a gefe yana jiran miliyan daya da rabi wannan wane irin tashin hankali ne? Ido jawur! ta fito tsakar gidan da hijab a hannunta, Jamila na biye da bayanta itama kallo d'aya za kayi mata ka hango damuwa a tare da ita. Baba dake tsige alayyahu ya kalle su tana girgiza kanta, babu shakka ruwa baya tsami banza duba da yanayin fuskokinsu, bayan haka kuma ta zargi wani abu ne yake faruwa da mahaifin nasu duba yanda ta ji suna magana 'kasa-'kasa kamar ba sa so wani ya ji abinda suke tattaunawa. Cikin dushewar murya! da yanayin harshenta ta ce." Baba zan je na duba babanmu bashi da lafiya shine Jamila ta zo ta fad'a mini." Cikin alhini ta ce." Allah sarki to ai ba kuka za ku yi ba addu'a za kuyi masa Allah ya tashi kafad'arsa ai cuta ba mutuwa ba ce; shin wai me yake damunsa ?" ta karasa maganar tana kallon jamilan dake kokarin mayar da k'wallar idonta. A sanyaye ta ce." Ciwon kai ne mai tsanani! amma da likita ya duba shi ya tabbatar mana da cewa jininsa ne ya hau?" "Allah sarki! ai abinda ake ta fama dashi kenan. Allah ya bashi lafiya." Gabad'aya suka amsa da "Ameen." 'Dari biyar ta mi'ka wa Shahidan da fadin." Kuyi kudin mota amma ki dawo da wuri kar ki bari dare yayi miki kin ji ko ." A sanyaye ta ce." Insha Allahu." Hanyar fita suka nufa ta ce." Jamila ki gaishe min da mai jikin kinji ko." Ta ce." Insha Allahu zan fad'a masa." Girgiza kanta tayi bayan fitar su, tausaya musu take na rashin samun nagartaccen uba! idan Jamilu bai yi hankali ba yanzu ba to yaushe ne zai yi ? gashi Allah ya bashi zuria duk mata wannan shine abin dubawa. Lokacin da suka isa gidan yana bacci shi kadai a dakinsa, ita kuwa Talatu sai sabgoginta take, Hadiza bata nan ta je bikin 'kawarta, gidan a bushe 'kamas! yanzu ne Talatun take kujuba kujubar d'ora girki bayan ta je tayi fafutukar ciyo bashi a mak'ota! Babu arziki ta kalle su da fadin." Au! ita ki kaje kika jajibo me za tayi? ko kuma za ta iya biya masa bashin dake a bin sa ne." Ta ce." Haba Talatu wannan ba magana bace dani da Anty Shahida duk d'aya muke kuma itama tana da hakki na je na fada mata ne domin ta zo ta duba shi saboda yana matsayin mahaifinta. Tsaki! ta ja ta shige dakin girki ta bar su a tsaye a gurin da takaicin ta. To sai gefin magriba ya tashi daga baccin babu laifi da dama-dama jikin nasa. fitowa yayi domin daura alwala nan ya gansu a zaune a tsakar gidan sunyi jugum jugum! jikinsa ya k'ara yin sanyi! kunyar had'a ido yake dasu, da sauri ya dauki buta ya kama hanyar band'aki. Sai suka dinga rige rigen yi masa sannu! kansa kawai ya iya daga musu yayi saurin shiga band'akin Talatu ta bishi da zabgegiyar harara! "Baba ya jikin naka?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce." Da sauki alhamdulillhi wanene ya fada miki bani da lafiya?" Ta goge hawayen da ya zubo a fuskarta ta ce." Jamila ce ta je ta fada min shine na ce bari na zo na duba ka, Baba Asabe ma ta ce ayi maka sannu.'' "Ina amsawa ai na ji sauki ki tashi ki tafi kada dare yayi." Ya fada yana dan kallonta ganin yanda take kuka sai abin ya bashi tsoro lallai baya shakka ta samu labarin abinda yake faruwa; sai kawai ya sunkuyar da kansa 'kasa ya san takaicin abin ke damun zuciyarta. Aikuwa ya tsinkayi maganarta. "Baba wace irin rayuwa ka jefa kanka a ciki? wace irin rayuwa kake so ka jefe mu a ciki shin wai baka tausaya mana ne?" Shuru yayi bai ce komai ba. Ta ja majina! tare da cigaba da cewa ." Gabadaya ka zubar da kima da mutumcinka a gari, babu wanda bai san irin harkar da kake ba, shifa arziki na Allah ne, wallahi ubangiji ba zai ta'ba azurtaka da haram ba! ko ya azurtaka din 'karshen nadama da jin kunya! shin meye ribar abinda kake? gashi ka jefa kanta cikin masifa da bala'i ka jefe mu a ciki, a yanzu ina muka ga miliyan daya da rabi? babban tashin hankalinmu wannan gidan da ya rage maka shima ka sarayar dashi yanzu da mu da kai ina zamu kama?" *BINTU**MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ pege 43&44 "Ranka ya d'ad'e wannan mutumin da ka sa na yi maka binkice a kansa har ila yau magana d'aya ce kamar dai wancan lokacin; ma'kotansa da jama'ar unguwa ba su ba da kyakykyawar sheda a kansa ba, duk wanda zai bud'e baki yayi magana baya fad'in alherin sa, ranka ya da'de wannan shine labarin da nasa mu a kansa cewa d'an ca-ca ne wasu ma suna zargin yana harkar bariki." Cikin ladabi Sule ya 'karasa maganar da yake tafe da ita. Jaridar dake hannunsa ya ajiye a gefansa, ya mayar da hankalinsa gare shi ya ce." Sule ka tabbatar da Gaskiyar maganar nan? kasan duniya ta lalace mutane basa kunyar sharri! yarda da amincewa ne yasa na sanya ka gudanar min da wannan binkicen, ba naso daga baya wata magana fito." "Ranka ya dad'e hakane wallahi ba za a ta'ba had'a baki dani a cutar da kai ba, duk maganar da na fada gaskiya ne akan Hujaj sai dai ma'kotansa sun bada sheda arziki akan mahaifinsa, sun tabbatar min da cewa shi mutumin kirki ne domin har ya rasu bai ta'ba aikata alfasha ba." Ya ce."To godiya nake Sule za ka iya tafiya." Har ya niyyar tashi sai ya koma ya zauna yana d'an shafa 'keyarsa tare da sinne kai. "Sule Ya akayi ne? da alama akwai magana a bakinka ." 'Dan murmushi yayi ya ce." Ranka ya dad'e na jima ina mamakin al'amarin tun a karon farko da ka sanya ni wannan aikin, sai nake tunanin wani abu, na ce kodai mun kusa samu uwar d'aki ne?" Maganar ta sanya shi dariya ya ce." Sule ai na d'auka za ka bukaci zuwa gida ne domin dubo iyali ashe ba hakan bane.?" Da murmushi a tare dashi ya ce." Da wannan maganar ma Alhaji amma ina bu'katar ka bani wannan amsar idan babu damuwa." Shuru yayi na minti biyu kafin ya ce." Hakane maganar ka Sule, yarinyar mutumin nan nake so na aura insha Allahu." Da walwala a tare dashi ya ce." Ma sha Allah Alhamdulillhi ranka ya d'ade Allah ya sanya alkairi yasa za ayi damu Allah kuma yasa abokiyar arziki ce." Ya amsa da "Ameen suma ameen." Shuru gurun yayi na minti biyu kafin ya ce." Amma Alhaji baka ganin hakan zai janyo maka wata matsalar duba da cewa uban yarinyar bashi da kirki! akwai ma'kiya wad'anda suke jiran 'kiris su samu abun yayatawa a gari." Murmushi yayi ya ce." Sule kada ka damu da hakan, insha Allahu alkairi ne zai biyo bayan al'amarin, ba mu nufi kowa da sharri ba, duk wanda ya nufe mu dashi to babu shakka sharrinsa zai koma kansa." Ya ce." Wannan haka yake fatan alkairi Alhaji tabbas idan hakan ta kasance za mu fi kowa farin ciki." "Ma sha Allah." Abinda ya fada kenan; ya dauki jaridar da ya ajiye ya dan kishingida kan kujerar da yake zaune, ya ce." Ina fatan ka shedawa Labaran cewa bayan sallar la'asar za mu fita." Yana k'o'karin tashi ya ce." Eh Alhaji na sheda masa umarinka tuntuni." To bayan fitar Sule da minti goma kira ya shigo wayarsa. Koda ya ga wanda yake kiran sai ya ajiye ya cigaba da abinda yake. Sai da ta kira sau uku tukkuna ya daga, shuru yayi bai ce mata komai ba. "Daddy ina kwana." ta fada cikin rawar murya. A dakile ya amsa. Sai ta fashe da kuka tana bashi hakuri "Daddy don Allah kayi hakuri ka ji." Gyaran murya yayi babu walwala a tare dashi ya ce." Shukura kin zama mara ji ko? Fatima ta na yi miki hud'ubar banza kina dauka, kamar ni ubanki na baki umarni ki tsallake! ki fita ba tare da izini na ba, har na fita baki dawo ba shin me kike so ki zama?" A sanyaye ta ce." Daddy wallahi ba 'kin bin umarnin ka nayi ba, tsoro nake na fad'a maka gurin da zan je, na san ba zaka bari ba shiyasa na tafi amma ai Hajiya ta sani na fad'a! mata. "Shukura saboda kin san bana tsallake maganar Hajiya shiyasa ki ke had'a ni da ita ko?" "Ba haka bane Daddy." Ya ce." Nayi 'karya kenan." "A'a Daddy ba kayi 'karya ba kawai dai na ga itama Mamana tana da hakki a kaina babu laifi idan na je in da take." Ya ce." Ok to ki tattara kayanki gabad'aya ki koma gurinta kada na dawo na same ki a gidana." Tana kuka take bashi hakuri! Ya ja tsaki! da fad'in." Wallahi kiyi hattara da wannan uwar taki bata da kirki! sannan magana ta dake ta 'karshe shine kiyi gaggawar fito da mijin aure a cikin masu sonki domin ba zan lamunci sakarci ba." Yana gama maganarsa sai ya kashe wayar ya ajiye ransa a 'bace! Shiru tayi da wayar a hannunta tana tunanin abinda zai biyo baya, ta san halin mahaifin ta kaifi daya ne, baya magana biyu, mutum ne shi da bai yarda da shiriri ta ba, ita kuwa a yanzu dai babu wani wanda zata nuna a matsayin wanda za ta aura domin har yanzu ba ta samu wanda yayi dai-dai da rayuwarta ba, tunani mai zurfi ta shiga domin nemo hanyar warware matsalarta. **** "Baba yau fa zai zo da daddare ku gaisa sannan kuma mu je da shi can gidanmu su gaisa da Babanmu domin gobe yake so ya koma gurin aikinsa." Ta ce." Waye zai zo?" domin ita har ga Allah ta manta da maganar da sukayi da safe. Ta d'an 'bata fuska da fadin." Har kin manta ko?" Girgiza kanta tayi ta ce." Ke shahida magana mai muhimmanci ita nake ajiyewa a cikin raina domin abubuwan da suka dame ni suna da yawa." Ta 'karasa maganar tana kokarin kwance lalitar dake d'aure a k'ugunta. Sunkuyar da kanta tayi idonta yayi ja! alamun ranta ya 'baci! Ita kuwa Saliha dariya kawai take mata tana 'yan 'kananun maganganu wanda ta san ba za ta ji ba. Wutar nepa a ka kawo Saliha da sauri ta kunna musu fanka domin zafi ake a garin. Ita kuma Shahida ta je ta dauko hijaban ta domin ta goge. Ta kalle ta da fadin." Kin san dutsen gugar nan yana da jan wuta Shahida da ki bari na gama kallon labarai idan an gama sai kiyi gugar ki." Ta ce."Baba idan su ka dauke wutar fa.''? Ta ce." A'a ba zasu dauke ba insha Allahu, ke Saliha kunna min talabijin din NTA KANO zaki kai." Ta ce." To." da sauri ta janyo 'yar yawo (cover socket) ta jona kayan kallon tana kokarin gyara Area domin hoton ya fito. Shahida d'aki ta shiga ta kwanta ta shiga tunanin masoyinta. An gama labaran, 'karshen kawai suka riska. A in da mai gabatarwa yake fad'in kanun labaran 'karshe, cewa wannan Attajirin d'an kasuwar Alhaji Saddiku wanda aka fi sani da *'Dan gaske* zai yi rabon shinkafa a babban company sa dake sharad'a, za a fara rabon abincin da karfe hudu har zuwa karfe goma na dare. Baba Asabe ta ce." Wannan karon ma sai na je ko Allah zai sa na da ce." Saliha ta ce." Da rabon kiyi asarar kudin motarki, har kin manta 'bakar wuyar da ki kasha a wancan lokacin" Ta ce." Wuya ai mai shigewa ce 'yar nan a wannan zamanin shinkafa 'yar gwamanti babban buhu ai ko kwana zanyi a gurin ba zan damu ba mutukar zan samu, saboda haka yanzu ma zan tashi na shirya sai ki kula da masu shige da fice. Girgiza kanta tayi a zuciyarta ta ce." Wanda ya 'ki sharar massalaci ai yayi ta kasuwa! samun shinkafar nan ai sai mai tsananin rabo. "Baba ina za ki je kuma?" ta fada tana kokarin tashi zaune. Tana gyara hijab din dake wuyanta ta ce." Unguwa zani amma ba zan dade ba insha Allah." Ta ce." To don Allah kiyi sauri ki dawo kada kuma ya zo ba kya nan." "To." kawai ta ce ta kama hanya ta fita da sauri tana mamakin wautar yarinyar. **** Gurun cike yake da mata da maza dattijai da matasa matan aure kai harda 'yan mata, dama irin wannan na faruwa mutane babu uzuri sai su tarkato 'ya'ya da jikoki a zo a bi layi kowa kansa ya sani idan kai ka samu ba zaka bari d'an uwanka ya samu ba, wannan shine abinda yake cutar damu wato son kai. Gurin yayi cikar kwari! hayaniya ce kawai take tashi wasu ma fad'a suke yi akan bin layi mussaman mata wasu babu kamun kai! don ma da akwai masu tsaro (securities) da abinda za ayi a gurin sai yafi haka. Duk yana kallon abinda yake faruwa ta cctv camera ya umarci yaransa cewa su je su raba number kowanne ya san matsayinsa lokaci yana cika afara rabo." Abinda ya faru kenan mutum goma ke raba number 'bangaran maza mutum biyar 'bangaran mata mutum biyar. Baba Asabe dai ita ce ta dari hud'u da talatin da shida😂 ta tambayi cewa ita ce ta nawa ? ya fada mata cewa sai an bawa mutum dari hudu da talatin da biyar kana za a zo kanta, amma bata sare ba! ta gyara tsayuwarta a gurin tana adduar Allah yasa tana da rabo. Wasu na fita wasu na shigowa haka ake ta turmutsutsu! a gurin, duk wanda rabo ya zo kansa ana bashi yake jan buhun ya fita daga gurin da yake kan titi ne abun hawa baya wuya. Gefin magriba ya sauko 'kasa yana sanye da farin yadi dinkin tazarce, yadin mai taushi ne wanda kallo d'aya zaka san mai tsada ne, kansa sanye da farar dara irin ta larabawa ya nade da farin hirami sai k'afarsa dake sanye da bakin takalmin mai gidan yatsa. bai yarda ya fito haka ba sai da ya sakaye idonsa da farin gilashi. Da sauri Sule ya je ya bud'e masa mota! tunda ya ga ya fito ya san fita za su yi. Duk saurin Sule sai da wasu daga cikin mutanan dake gurin suka ganshi. Kafin ki ce kwabo sun yanyame! motar! wani za'kwa'kuri a cikinsu ya 'bude murya sosai dan da alama maro'ki ne ya fara yi masa kirari. *"Damuna uwar albarka." Alhaji Saddiku mai dubun nasara! kai ne 'ki gudu sa gudu mazan fama! bangon sukari kowa ya jingina sai ya lasa! Allah yayi maka arziki muna amfana dashi! Allah ya 'kara suturtaka 'DAN GASKE!* *'Dan da aka haifa da kyakykyawar Aniya."* Da murmushi a fuskarsa yake d'aga musu hannu cikin nuna alamun jin dad'in addu'onin da suke masa! Sule da Labaran suna ta k'ok'arin ganin sun kori mutanan da sukeyi dafifi a jikin motar, da 'kyar suka matsa sannan ya samu ya shiga motar ya zauna amma duk da haka hannu yake daga musu cike da jin dadin adduarsu. Motar tana daf da fita ya hangi dattijuwar matar da ba zai ta'ba mance fuskarta ba. tana tsaye ita ce a kusan 'karshen layi. Baba Asabe ganin yana kallon gurin da suke da sauri ta d'aga masa hannu tana fadin." Alhaji Allah yayi maka albarka hakika kana aikata alheri muna rokon Allah ya kai mizani, Allah ya yi wa dukiyarka Albarka." Ya amsa da "Ameen ya rabbi." Ya kalli Laraban da fadin." Ka fita ka samu daya daga cikin yaran dake wannan aikin, cewa su ware Dattijawa maza da mata a sallame su duba da raunin da suke da shi." "An gama ranka ya d'ad'e." Da sauri ya fita daga motar ya je ya cika umarni ya dawo ya zauna a mazauninsa, Sule ya ja motar suka fita. Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce." Ranka ya dad'e "Gadon 'kaya za mu nufa ne?" Ya ce." A'a Adakawa za mu je." Gabad'aya sukayi shuru babu wanda ya sake magana, sai dai Labaran da Sule cikin tunani suke! a duk lokacin da suka shigo garin KANO maigidan nasu sai ya je unguwar Adakawa kuma baya yarda su shiga dashi cikin unguwar a bakin titi yake sauka ya ce su tafi zai dawo gida da kansa. Wannan abu na nasu mamaki mutu'ka! *Tafiya tana kara nisa book1 yana daf da k'arewa! masu himma suna ta biya domin samun damar cigaba da karanta labarin. #500 ba zata gagara ba in sha Allahu. ga account din da za a tura kudin....0542382124...Binta umar gtbank.. idan kati za a turo sai ayi mini magana ta whsap 07084653262 mutan nan nijar za ku tura dala dari katin airtel ku tura mini ta WhatsApp* Allah ya yassare🙏🏻 *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ [ 47&48 To a daran ranar Talatu dai da kyar ta iya rintsawa, domin ta jima tana tunani akan al'amarin, ka da fa tana zaune baki a sake yarinyar da ta tsana! tayi mata zarra! tunda gashi tun kafin aje ko'ina Hujaj ya fara yi mata habaici ita da 'ya'yanta, dole ta je ta bincika domin sanin ainihin mutumin da ya ke neman auran yarinyar. Shahida da 'kunci! da 'bacin rai ta tashi. tsakanin Baba da Saliha jira take wani ya ce mata kule tace cas! domin gabad'ayansu a ciki take dasu, saboda suna kiran masoyinta da mahaukaci. Ta shiga d'akin ta same ta a kudindine a cikin bargo amma ba bacci take ba. kawai ta tsirawa rufin dakin ido! Ta d'an bud'e muryarta ta ce." Shahida ki tashi ki karya kummalo mana kina kwance kina tunane tunane mara amfani ko?" Ta mike zaune tana kallonta ta ce." Baba ina neman alfarma a gurinki." Kallonta tayi tana ayyana wani abu, labarin gizo dai baya wuce na koki, amma sai ta ce." To Allah ya sa zan iya. Ta ce." Don girman Allah da darajarsa ki kar'bi wannan al'amari da zuciya d'aya! wallahi nayi imani da Allah cewa alheri ni, nayi istahara akan al'amarin, Baban Baba ba zai cutar dani ba, mutumin kirki ne kuma ba mahaukaci bane kamar yanda ku ke zato, yau ce kawai ta mayar dashi haka, amma tunda ya samu ubangida ya koma mutum kamar kowa, arziki da rashi duk daga Allah suke, kiyi min addua kawai Allah ya sa hakan alheri ne. Gabadaya ta gama kashe mata jiki da kalamanta, a yanda ta shirya ta kuma kudire a ranta cewa sai bayan ranta wannan al'amari zai tabbata, amma wannan maganganun da tayi gabadaya gwiwarta tayi sanyi, babu shakka akwai wani abu da Allah ya rufe, kuma sha'anin aure irin wannan ba'a tsawwala wa domin idan ka tsananta sai ayi babu kai. Ta ce." Shikkenan Shahida na rabu dake da abinda ki ke so Allah ya sa hakan alheri ne dake damu baki daya. Cike da tsantsar farin ciki ta ce." Na gode sosai Baba insha Allahu za muyi farin ciki gabadayan mu, amma ki shirya an jima kadan yana tafe zai zo ku gaisa kafin ya tafi Abuja gurin sana'arsa. Ta na kokarin fita daga dakin ta ce." Shikkenan Allah ya kawo shi lafiya. Zama tayi kan kujera 'yar tsuguno jikinta duk a mace! Saliha ta ce." Baba Lafiya dai?" A sanyaye ta ce." Lafiya lou Saliha al'amarin Shahida da wannan mutumin ne yake ban tsoro. Ta ce." Tuntuni na ce miki ki daina damuwa amma kina kokarin janyowa kanki matsala! duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka." Ta ce." Na yi fatan alheri ai Allah ya ba su zaman lafiya." Shuru tayi ba ta amsa da ameen ba, kawai ta cigaba da feraye kabewar dake gabanta. ** To kamar yanda Talatu ta kudire a ranta cewa za ta je tayi tambaya a kan lamarin, da asubah zakara ya bata sa'a ta fita can wani 'karamin k'auye ta nufa gurin wani malami, wanda ya duba mata al'amarin ya kuma tabbatar mata da cewa shi bai ga komai ba face alheri domin kuwa babu da na sani ko bak'in ciki a cikin al'amarin, sai farin ciki. Jikinta a sa'bule ta dawo gida da tunanin yanda za tayi ta wargatsa auran. *** Cikin nutsuwa ta fito ta same shi a tsaye a soran gidan, sosai tayi farin cikin ganinsa tsaf dashi cikin shadda bulu mai duhu tazarce har k'asa da hula da takalmi ya dora rigar sanyi a sama saboda yanayin garin sanyi ya fara busawa, ta tsuguna har kasa tana gaishe shi, ya amsa a nutse yana mata wani irin kallo wanda ya sa ta jin kunyarsa ta kasa tashi tsaye. Ya ce." Kin yi min kyau fiye da tunaninki. Murmushi tayi ta ce." Ni ma haka idan na gan ka cikin suttura cike da kamala sai na yi ta mamaki kamar ba kai ba, wanda da yawa mutane suke maka kallon mahaukaci! lallai babu shakka wannan ubangida naka dole a jinjina masa domin ya taka muhimiyyar rawa a rayuwarka, ya sanya ni cikin farin ciki mara mislatuwa domin ni yayi wa tagomashi yayi wa bajinta ba zan gushe ba face na cigaba dayi masa addu'a har karshen rayuwata." Ya dinga jin wani irin farin ciki na kwarara a zuciyarsa, ya ce." Za ki gaisa da maigidana insha Allahu sai kiyi masa godiyar alherin da yayi miki, duk da cewa yana da labarinki amma lokaci kad'an ya rage ku gaisa da juna da ikon Allah." Ta mi'ke tsaye tana gyara mayafinta da ya sauka a kafadarta ta ce." Ina fatan zuwan wannan rana. Kawu Musa ne ya shigo da shirin zuwa kasuwa a tare dashi. Ya tsaya suna gaisawa babu yabo babu fallasa yake kallon mutumin, shima mamakin sauyawarsa yake, kamar bashi ne wannan mahaukacin ba mai yagaggun kaya da kwanciya cikin 'kazanta. Ya ce." Ai babu damuwa mu je ciki sai ku gaisa sosai tsayuwa a soron bashi da amfani." Cike da jin dadi ya ce." Na gode sosai Kawu." Ita kuwa Shahida babu wanda ya kai ta jin dadin ganin yanda Kawu Musa ya saki fuskarsa su gaisa da Masoyinta cikin farin ciki. Babu yabo babu fallasa ta shimfida masa tabarma ya cire takalminsa ya zauna a nutse ya ke gaisata, ta amsa babu walwala a tare da ita domin dai har yanzu zuciyarta ba tayi na'am dashi ba kawai dai ta hakura ne saboda samun farin cikin yarinyar. Ita kuwa Saliha a fakaice take kallonsa tana k'unshe dariya, hular kansa da takalminsa soso da ya cire a gefanta su takewa dariya. wanda duk abinda take yana kallonta kuma yana mamakinta a zuciyarsa. Kawu Musa shi yake masa tambayoyi, cikin nutsuwa yake bashi amsa daidai da tambayar da yayi masa. Kawu Musa ya ce." To Allah ya tabbatar da alheri a cikin al'amarin. tunda ka riga kayi magana da mahaifin yarinyar ai shikkenan, dama shike iko da 'yarsa, tunda ya baka mu kuma za mu zama masu addua da fatan alheri, amma mun baka amana ka rike ta da kyau, marainiya ce bayan haka kuma ka duba lalurarta. Ya ce." Nayi alkawarin haka insha Allahu. Baba Asabe ta ce." Da zai yiwu sai ka kama haya a cikin unguwa ka ajiye ta a kusa, idan yaso ka dinga zuwa daga can abujan. Ya ce" Hakan ba zai yiwu ba Baba, ni dai buri na ku yarda dani, ku amince cewa zan rik'e amanarku, ni kuma nayi alkawari insha Allahu idan ban rik'e ba Allah ya hukunta ni". Ta ce." To ai shikkenan Allah ya sa mu dace amin." Gabadaya suka amsa da "Ameen ameen." Da zai tafi ya ajiye mata dari biyar, ta ce."A'a zo ka dauki kudinka bawan Allah ka 'kara guziri, kai da za kayi tafiya" Yayi sauri yasa takalmansa ya kama hanyar fita Shahidan ta bi bayansa da sauri. 'Yar 'karamar waya tacno ya bata ya ce ta ri'ke zai dinga turo mata sak'on gaisuwa, saboda ya san lalurarta, ta kar'ba ta na godiya sai murmushi take ganin yanda aka samu daidaito ta kowane b'angare! a yanzu burinta bai wuce ace sun mallaki juna ba. **** "Eh ni ne Alhaji Sammani mai leshi kasuwar wambai.'' Ya fad'a yana gyara wayar a kunnansa. Daga daya 'bangar ya ce." Ma sha Allah. dama na kira ne akan maganarka da Abokinka Jamilu Hujaj." Ya ce." Eh hakane to ina sauraranka, Allah yasa alheri ne. Murmushi yayi a nutse ya ce." Alheri ne insha Allahu." Yayi shuru na second daya kafin ya ce." Nawa ne sauran kud'in naka ne?" Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya ce." Ba saura bane ai domin a miliyan biyu da rabi an bada miliyan daya ka ga kuwa ya wuce saura." Ya ce." 'Kwarai kuwa, yanzu idan na fahimta cewa kudinka da suka rage a hannun abokinka Miliyan daya da rabi kenan?" Ya ce." 'Kwarai kuwa." ya fada yana gyara tsayuwarsa a cikin shagon. Ya ce" Babu matsala ka tura min account number zan sa maka insha Allahu." Mamaki ya rufe shi! ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ya ji wayar ta tsinke! ya dinga kallon fuskarsa wayar yana mamakin in da Alhaji Jamilu ya samu wannan hanyar, shin waye wannan mutumin? amma bari ya tura account din ya gani, domin bai gama amincewa da maganar mutumin ba, ya na so ya tabbatar ne kawai. Ko minti biyar bai yi da tura account d'in ba ya ji alert kudi sun shigo, yana dubawa ya ga kud'insa cif miliyan biyu da rabi! Cikin tsantsar mamaki! ya nemi guri ya zauna jikinsa sai kyarma yake dama Jamilu ya sha sheda masa cewa shi ba 'karamin mutum bane. Text ne ya shigo wayarsa ya bude yana dubawa. Sai jikinsa ya 'kara mutuwa karanta abinda yake k'unshe. _"Ga kud'inka nan Alhaji, ka mayar masa da miliyan dayan da ya baka Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba."_ Hannu na rawa ya fara kokarin kiran wayar sai dai sai kash a kashe take, ya kira ya kai sau bakwai bata shiga ba, sai ya hakura ya fara laluben lambar abokin nasa domin fada masa halin da ake ciki. " Na san da hakan, domin kafin a tura maka kudink'a sai da aka sheda min, Yau ka tabbatar da cewa ni din ba 'karamin mutum bane ko?" ya fada cike da izzah da ginshera! Alhaji Sammani ya ce." Wai don Allah ina ka samo wannan mutumin domin daga jin muryarsa bai yi kama da abokanan hurd'ar mu ba." Murmushi yayi kafin ya ce." Haihuwa ce tayi min rana saboda haka mu bar maganar kawai, kai kayi nufin tozarta ni Allah bai nufa, sai ka tura min abinda yayi saura nawa dake hannunka, daga haka ala'karmu ta yanke." Ya na gama maganarsa ya kashe wayar yana jan tsaki, account number ya tura masa yana jiran ya ji alert. Cike da kwarin gwiwa ya fito daga d'akinsa! ya bankad'a labulan dakin yana kiran sunanta. Ba ta amsa ba sai ido kawai da ta zuba masa. Ya ja mugun tsaki kafin ya ce." Na yarda ke ce ki ka karya ni, ba tun yau ba malamina ke sheda min hakan, rabon wad'annan yaran nake zaune dake, amma ki sani, Mariya ta fiye min ke duk da bata raye ina alfahari da ita, domin ta haifa min yarinyar da ta share min hawaye, ba zan ga ji da sheda miki cewa ke da yaranki baku da amfani a guri na ba." Yana gama maganarsa ya saki labulan ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa fes! gabadaya duk wani damuwa da lalure-lalure da yake sun tafi sakamakon shigowar kud'i, a maimakon ya je ya mayar wa da dillali kudin ya bashi takardar gidansa, kawai sai ya cigaba da fantamawa da kud'in, ya gwammace ya zauna a matsayin d'an haya a gidan, domin zuwa yayi ya bashi kudin hayar shekara biyu dubu dari biyu da ashirin, yasa abinda ya rage a aljihunsa ya cigaba da buga barikinsa. Baba Asabe tayi-tayi dashi kan cewa a je ayi binkice a can garin nasu amma fafur! ya'ki a lokacin har ya so yayi mata rashin kunya! Kawu Musa ya ce kawai ta kyaleshi kamar yanda ya fad'a mata cewa uwarsa da ubansa ne kawai za su fad'a masa magana ya ji akan wannan al'amari to tunda basa raye babu wanda ya isa domin dai yarinya 'yarsa ce shi yake da iko da ita! Baba Asabe har kuka tayi saboda tsabar 'bacin rai tana jin takaicin abinda mutumin yake mata, wato ita ta gama yi masa wahala yana nuna mata iko. kawai sai ta barwa Allah al'amarin, ta tsananta da addua. 'Bangaran masoyan kuwa sun sha'ku sosai ta waya domin kalaman soyayya suke aikawa da junansu babu dare babu rana. Ranar juma'a 20/3/2021 aka d'aura auran, babu laifi d'aurin auran ya tara mutane, amma duk yawancinsu mutanan Hujaj din ne, sai wakilan ango guda biyu da suka bada sadaki, kuma suka kar'bi auran bisa yarjewar addinin musulunci. *Littafi na daya yana daf da 'karewa, ina fatan masoya za ku goya mini baya gurin sayan littafi na biyu domin cigaba da tafiyar tare. hanyar da za a biya kudin mai sauki ce Normal group #500 Vip group posting sau biyu a rana 1k za a tura kudin ta wannan asusun. 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku tura dala dari Vip jakka daya katin airtel za ku turo min dashi ta lambata. Allah ya yassare* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE🌳* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ 45&46 "Wai ana sallama da Shahida." Yaron ya fad'a yana wasa da garegaran dake hannunsa. Saliha dake zaune a tsakar gidan tana kula da masu shige da fice domin sayan abinci ta hararin yaron tana shirin magana sai ga Shahidan ta fito daga daki. Sai tayi shuru tana yi mata wani mugun kallo. Yaron ya ce." Yawwa Shahida ki zo ana kiran ki a waje." Da dan 'karfi yayi maganar. saboda ya san lalurarta. Da sauri ta ce." Ka je ka ce gani nan zuwa." Yaron ya juya ya fita cike da wasa a tare dashi. Dama tayi wankata tsaf ta shirya cikin atamfah mai sauki kudin, sai kawai ta fesa turare mai dadin 'kamshi ta sa hijabi a jikinta, ta fito cike da farin ciki a tare da ita. Saliha ta bi ta da harara da fadin." Shashasha! mara hankali kawai." Yana tsaye a soron gidan ya shirya babu laifi doguwar jallabiya ce a jikinsa ruwan madara amma ta kod'e sosai, da ba'kar hula mai raga-raga a kansa, kafarsa sanye da takalmi d'an madina kore sai hannunsa dake makale da carbi mai madannai! yayi mata kyau sosai, ta tsuguna har 'kasa tana gaishe shi. Ya amsa yana mata wani irin duba mai tattare da abubuwa da yawa. Cikin nutsuwa ya ce." Ki tashi mana." Ta mi'ke tsaye tana murmushi, a hankali ta ce." Yau kafi koda yaushe kyau." Murmushin farin ciki yayi ya ce." Na gode sosai Gimbiyata." Tana wasa da yatsun hannunta ta ce." Baba Asabe ta je unguwa ya za ayi kenan?" Ya ce." Hakan ba matsala ba ce idan babu damuwa sai mu je can gidan naku nayi magana da mahaifinki." Ta ce." Shikkenan hakan yayi." Suna fitowa kofar gidan. adaidaita sahu yana sauke Baba Asabe da 'katon buhun shinkafarta. Ta fito da kudi ta bawa direban da fadin." Don Allah ka taimaka ka shigar min dashi gida." Ya ce."To babu matsala Baba." Tana juyowa ta gan su a tsaye. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! Wani irin kallo take musu fuskarta babu annuri ko kadan. A sanyaye ta ce."Baba sannu da zuwa." A dakile ta amsa tana kokarin shiga gidan, ya zube gwiwa a 'kasa yana gaishe ta. wuce shi tayi ba tare da ta amsa gaisuwarsa ba. Sosai ya ji babu dad'i amma sai ya danne! ya tashi tsaye yana buge rigarsa! Shahida kuwa idonta sun ciko da ruwan hawaye ta ji ciwon wulakancin da tayi masa. "Kayi hakuri don Allah." Ta fada tana kokarin mayar da hawayen dake kokarin kwace mata. Ya ce." Babu komai kada ki damu. zubar hawayenki shine damuwa ta, saboda haka kiyi kokarin hana su zuba." Ta daure tana kokarin mayar da hawayen ta ce." Bari na je na sanar da ita." Ya ce." To babu matsala. Gidan ta shiga ta same su suna mayar da magana. Baban tana cewa." Ai mutumin nan yana da kirki sosai wallahi shine ya bada umarnin cewa a sallami dattijai irinmu saboda raunin da muke dashi, da ba don haka ba da tuni ina can cikin 'kila wa 'kala." Saliha ta ce." Ai ya taimaka wallahi ban yi tsammanin zaki samu ba." Tana kokarin magana Shahidan ta katseta ta hanyar fadin." Baba wannan fa ba rayuwa ba ce, tunda ubangiji ya girmama dan adam babu wanda ya isa ya wulakanta shi, a matsayinki na mai hankali bai kamata kiyi masa haka ba, ban ji dadi ba wallahi." ta kai karshen maganar cikin rawar murya. Ta ce." Rashin kunya za kiyi min Shahida?" Ta girgiza kai "A'a ni ba nufi na kenan ba, kawai kuskuran ki nake nuna miki." Ta ce." Ai ba tun yau ki ka saba nuna min kusukura na ba Shahida ki cigaba da yi min abinda ranki yake so. Ta share hawayen da ya soma fita ta ce." Allah ya baki hakuri! dama zan fada miki ne cewa. Za muje can gurin Babana tare dashi." Ba tare da ta kalle ta ba ta ce." Sai kun dawo." Ga mamakinta sai ta ga ta juya ta fita. Suka kalli juna ita da Saliha ta ce." Gatse fa nayi mata." Saliha ta ce." Don girman Allah Baba ki kyale 'yar iskar yarinyar nan da mahaukacin mutumin nan jiki magayi." Baban ta shiga girgiza kanta tana tu'ajibun al'amarin. Gidan duhu sosai! babu haske. dukkaninsu suna rumfa a zaune yunwa na sasakarsu! yau Talatu dai ta ranste tace kowa ya ci aljihunsa! domin ta gaji yawon cin bashi gashi babu mai ko anini a cikinsu, tunda ba sana'a suke ba, bahaushe ya ce duk lalacewar mutum yana da rana. Talatu tana iyakar bakin ko'kari a kansu, yau dai ta gaji! 'kokari take ma ta biya bashin da ta ci a baya wanda kullum ta Allah ake mata sallama ba dare ba rana. Motsin shigowarta gidan ya sa Hadiza tayi saurin kunna fitilar wayarta tana fadin." Waye?" Ta ce." Ni ce Shahida." Talatu tayi karaf ta ce" Wa ce Shahida kuma. ba dai kurmar yarinyar nan ba, domin na ji kamar muryarta." Hadiza ta ja tsaki mai tsayi ta tashi ta shiga daki ta kwanta. tunanin yanda za a yi ta samu abinci kawai take, tana ganin saurayinta kawai zata kira a waya ta fad'a masa halin da take ciki. A wulakance ta kalle ta kafin ta ce." Ke kuma daga ina da wannan daran?" "Da ga gida nake." tafada a takaice. Ta ce." Ayyo! to ina fatan dai lafiya?" "Gurin Babanmu na zo tare da wanda zan aura za su yi magana." Gabanta ya yanke ya fad'i! ta ce" Waye wanda zaki aura din? wane sakarai! asararran ne mara mafad'i." Jamila ta ce."Haba Talatu abinda ki ke fa bai dace ba, kefe uwa ce idan ba zaki fadi alheri ba to kiyi shuru." "Rufe min baki ba'kar munafuka algunguma." ta katse ta a zafafe! Jamila ta mik'e ranta duk a 'bace ta kama hannunta suka fita tsakar gidan. "Don Allah Aunty Shahida kiyi hakuri da abinda Talatu take miki wallahi ba na jin dad'i." A jiyar zuciya ta sauke ta ce."Jamila Mahaifiyarku ba ta k'aunata ban san abinda nayi mata ba. amma ki sani wallahi ta na cin albarkacin ki, da ba don haka ba da tuni na dauki mataki a kanta." Ta ce.'' Ki cigaba da hakuri watarana sai labari yanzu ina mutumin da ku ka zo tare?" Ta ce." Yana can waje a tsaye kuma wallahi da gaske ya ke aure na zai yi." Ta ce.''Amma na ji dadi wallahi. mu je na gaishe shi kafin Baban ya dawo" Tare su ka fita suka same shi a tsaye a jikin bango (garu) yana danna 'karamar waya nokia da aka d'aure ta da kyaure. Jamila wani irin kallo take masa a tsorace! kwata-kwata mutumin bai kwanta mata a rai ba, ganinsa wani iri babu sutturar arziki gashi tsoho gemunsa da tsalli-tsallin furfura! "Ina wuni." Ta fada tana dan sunkuyar da kanta. Ya amsa fuskarsa a sake yana dan tsokanarta. Tana 'yar dariya ta ce." Ga aunty na nan; don Allah ka rike mana amanarta! kaga tana da lalura ta rashin ji a kula mana da ita. Murmushi yayi ya ce." Kada ki damu 'kanwata zan ri'ke amana insha Allahu; yanzu ina so ne nayi magana da babanku domin da gaske na ke." Tana k'okarin magana Hujaj ya k'araso gurin! kallonsa yayi sama da 'kasa da fadin." Malam menene? ka tsaya min a kofar gida tare da yara na." Ya d'an rusuna da fadin." Barka da dare Baba." A takaice ya amsa da "Barka dai" Gurin yayi shuru dukkaninsu jikinsu yayi sanyi! Ya kalli Shahidan da fad'in."Waye wannan ki ka kawo min?" Ta ce." Shine wanda nake so na aura, mun daidaita junanmu shine ya ce yana da kyau ya zo ya gaishe ka, kuma akwai alherin da yake tafe dashi." Bud'ar bakinsa sai ya ce." Ni da kai na nace ki fito da mijin aure, amma kin san dai a yanzu ba ni da kud'in da zanyi miki wata hidima ko? don haka maganar aure a tattara a ajiye a gefe guda. idan kuma zai aure ki babu kayan daki falillahil-hamdu." Ya ce."Babu komai Baba Shahida nakeso ita kanta ba wani k'yale-k'yale ba, buri na kawai ka bani ita. Wani irin kallo yake masa yana raya abubuwa da yawa a ransa! wannan mutumin da yake gabansa da ka gani talaka ne duba da yanayinsa, amma kuma ya yaba da nagartarsa kuma ba 'karamin yaro bane, Shahida 'yarsa ce mai rangwamin ga ta, shiyasa bai wani ci buri a kanta ba, amma zai so nagari ya aure ta ko dan ya kula da ita saboda lalurarta. Ya ce." Na baka yarinyar nan amana. sai abu na gaba wane alheri ne yake yafe da kai bayan wannan." Fuskarsa cike da annuri ya ce."Alhamdulillhi na gode sosai insha Allah zan kula da amanarka. bayan haka kuma Shahida ta shaida min irin halin da ka ke ciki na rayuwa, zanyi iyakar bakin kokari na akan lamarin. Ya ce." Wane irin taimako za kayi min? da ka ganinka dai talaka ne, wanda baka ajiye ba, baka bawa wani ajiya ba, shin ko akwai wata hanyar da ka ke samun kudi a b'oye kake yawo a tsiyace! kana da hanyar miliyan biyu da rabi ne?" Ya girgiza kai cikin rashin jin dadin maganganunsa ya ce." Eh insha Allahu, ina da alfarma a gurin maigidana, mutum ne shi mai tausayi da taimako insha Allahu zai duba uzuri na." Nan da nan fuskarsa ta washe ya ce." mutukar kuwa hakan ya tabbata baka da matar aure sai wannan yarinya na baka ita halak malak." Bai yi mamakin jin haka daga gare shi ba, ya ce."Shikkenan Baba na gode sosai, yanzu abinda za ayi shine ka bani number wayar mutumin da yake bin ka bashin kud'in koda maigidana zai bukaci magana dashi idan na koma can abujan." Ya ce." Don ta lamabar waya ai babu matsala sai na baka yanzu. Ya shiga fad'a masa lambar shi kuma yana d'auka a 'kwara'babbiyar wayar dake hannunsa da aka d'aure ta da kyaure. Sai bayan ya gama fada masa lambar wayar ne ya kalle shi da fadin." Da gani kai ba yaro bane ga alamun shekaru nan a tare da kai. shin kana da aure ko kuma yarinyar nan ita ce matarka ta farko?" Ya ce." Nayi aure shekarun baya har 'yata ta girma ta zama budurwa amma tana can garinmu." Ya ce." Ina kenan?" "Katsina a cikin karamar hukumar jibia, nan ne mahaifata. Ya ce." Ma sha Allah. kayi kokarin ganin ka fitar dani a wannan masifar ni kuma nayi maka alkawari sati guda yayi yawa gurin daurin auranka da yarinyar nan. Ya ce." Insha Allahu zanyi kokari." Gidan ya shige zuciyarsa fes! yau haihuwa za tayi masa rana. A tsakar gida ya same ta a tsaye. kamar wacce take jiran shigowarsa babu sannu da zuwa ta ce." Maganar da Jamila ta zo fad'a min gaskiya ne?" A lalace ya kalle ta kafin ya ce." 'kwarai kuwa yau haihuwa za tayi min rana dake da yaranki kun zama yuyuyu! sakarkaru kawai." Yana 'kare maganarsa ya bude dakinsa ya shiga ya bar ta a tsaye a gurin cike da d'umbun mamaki! A hanyar su ta komawa gida take tambayarsa ashe ya ta'ba aure har da haihuwa, ya tabbatar mata da gaskiyar magana ya ce." Amma yarinyar ta na can garinsu kamar yanda ya shedawa mahaifinta. Cike da 'kauna da begen juna su kayi sallama da juna tare da alkawarin cewa gobe da wuri zai zo ya gaisa da Baba Asabe kafin ya tafi. Lokacin da ta shiga gidan, muryoyinsu ta ji a can cikin daki harda Kawu Musa. gabanta ya fad'i! jin kawu Musa a gidan ba alheri ba ne. Saliha ta fito tsakar gidan ta sameta a tsaye ta kasa shiga dakin. Ta dan d'aga muryarta da fadin." Matar mahaukaci kin dawo kenan?" Kallonta kawai tayi amma ba tace mata komai ba, ba don ba taji haushin kalaminta ba. Suka fito daga dakin a tare, Baba Asabe na sake jadadda masa matakin da zata dauka akan al'amarin, ya yin da shi kuma yake nuna mata cewar tabi a hankali domin ba ta da k'arfi akan yarinyar kamar ubanta. Ya kalle ta suka had'a ido! sai tayi saurin sunkuyar da kanta kasa. Ya d'an bud'e muryarsa da fad'in." Shahida wannan rayuwar ki ka za'bawa kanki ko?" Shuru tayi hawaye na 'kok'arin kufce mata. Ya cigaba da cewa." Shin me ki ka hango a tare da wannan mutumin wanda shi ba mai hankali ba kuma ba mahaukaci ba, a matsayin ki na mara lafiya zaki za'bi wannan rayuwar da mara galihu. wanda ba a san asalinsa ba." Baba Asabe ta d'ora da fadin" Yo idan ba rashin hankali ba ina ke ina auran mahaukaci mutumin da ba a san daga ina ya ke b......gurin ta bari tana wani irin kuka! duk suka bita da kallon mamaki! lallai al'amarin yarinyar ya fi karfin tunaninsu. *An fara biyan kudin littafin masoya* *Hanyar da za a biya kudin mai sauki ce #500 Vip 1k 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Dubbun Godiya zuwa ga:* *Hajiya Hadija Marad'i (Nijar) Ina godiya da abin alheri Hajjaju🥰🙏🏻* 49&50 'Yan Allah ya sanya alhari da 'yan gulma sai shige da fice suke a gidan, ita dai Baba Asabe kallonsu kawai ta ke yi saboda ta san mafi akasarinsu, ba alheri ne ya shigo dasu ba, domin da kunnanta ta ji wasu mata suna maganar cewa; ai auran kawai aka d'aura amma babu lefe babu komai, asali ma angon yana da matsalar k'wak'walwa sannan ba shi da wani cikakken asali. ire-iren wannan zantukan jama'a suka ke'be guri guda su na yi. Amarya kuwa sam ba ta sanya damuwar komai a cikin ranta ba, ta na ji ko babu lefe za ta iya zama da masoyinta burinta ya cika za su rayu cikin inuwa d'aya. Kitso akayi mata 'kananu irin na bare-bare sai k'unshin salatif da makociyarsu tayi mata, ta sanya sabuwar atamfa wacce ya kawo mata a din'ke da mayafi da takalmi, Rabi makociyarsu wacce tayi mata k'unshi itace tayi mata kwaliyya dai-dai gwargwado tayi kyau tana ta murmushi, mutane na ta'ba ta suna mata Allah ya sanya alheri. Saliha kuwa sai dariya take mata addua take a zuciyarta Allah yasa mahaukacin ya nuna mata tumasanci! Can gidan Hujaj kuwa Talatu kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ganin yanda al'amarin auran ya kasance, babu lefe babu wata hidima da ango yake wa amarya. babban farin cikin ta da ta samun labari cewa ai angon ma bashi da hankali asalinsa mahaukaci ne kawai ya d'an samu sau'ki ne! wannan al'amari yayi mata dadi sosai, kawai sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da sabgoginta, ko gidan bikin ba ta je ba, Jamila ce kawai tayi wanka ta shirya ta tafi. ita da sauran yaran suna gida duk wanda ya shigo sai sun labarta masa abinda yake faruwa domin ita Hadiza ma yawon gantali ta tafi da saurayinta. Da magariba Hujaj ya shigo gidan; 'kalau dashi cikin sabuwar shadda babba riga da 'yar ciki, komai sabo ne a jikinsa sai walwala yake kamar bai ta'ba shiga wani rikici ba. A tsiyace! ta kalleshi kafin ta ce." 'Karya banza da wofi ina zaune labarin komai ya same ni da har kake wani fuffuka kana murna ka dauki 'yarka ka bawa mahaukaci wanda ba a san asalinsa ba." Ya ce." Ai gwara ita akan ke da 'ya'yanki, Talatu daf ki ke da ki bar gidan nan, ki rubuta wannan ki ajiye mutsiyaciya kawai duk kin tsiyata ni, zan dai auro wacce take dai-dai da arziki na." Ta buga cinya da fad'in" Ai wallahi 'karya kake Jamilu, ai na ci gida ko ka sake ni ba zan fita ba ina nan daram dam." Ya ce." Tunda gidan ubanki ne ai sai ki zauna sakarai shashasha! kawai." 'Kwallah ta ciko idonta tana rawar murya ta ce. " Shashasha ba, ai ka santa. A sukwane ya gaura mata mari! wanda sai da ta ga gilmawar taurari! ya nuna ta da yatsa da fadin." Wallahi ki ka sake wata magana a bakin auranki domin dama na ga ji da zama da ke mahaukaciya kawai." D'aki ta shige tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Bayan sallar isha'i Hujaj ya dira a gidan, Baba Asabe. ta shimfid'a masa tabarma suka gaisa kamar abin arziki. Shahida ta fito ta gaishe shi, ya amsa kafin ya ce ta nemi guri ta zauna. Gurin yayi shuru na minti biyu yayi gyaran murya da fad'in." To Alhamdulillhi, bu'katata ta biya gurin ganin na auran da yarinyar nan a in da ya da ce! wannnan mutumin ya fitar dani kunya saboda haka ko da yana tsince-tsince ne akan bola zan iya bashi auran 'ya ta saboda yayi min abinda ba zan mance ba. Shahida 'ya tace, ni ne ubanta ni nake da iko a kanta, saboda haka babu wani mahalukin da ya isa yace ga yanda zan yi da abinda nake da iko a kansa. Ta ce." Dakata! Jamilu." Ya kalle ta ido cikin ido. Ta cigaba da cewa." Ai na dauka arziki ne ya kawo ka gidan nan ashe rashin kunya ka zo kayi min." Ya ce." A'a ba nufi na kenan ba. Ta ce." Idan ba nufinka kenan ba mai zai sanya ka dunga wasu maganganu masu kama da jirwaye." Ya ce." Surutai nake ji a gari cewa wai na d'auki 'yata na bawa mahaukaci wanda ba a san daga ina ya fito ba, naga dai ni na hai fi abata, kuma wannan maganar nasan daga gidanan ta fito." Ta tsira masa ido kawai tana kallonsa, ya cigaba da cewa."Kamar yanda na fada da farko cewa." Mutumin nan sanadiyarsa na fita daga cikin rud'ani, to wallahi ko doke-doke yake yana tsince-tsince a bola hakan ba zai hana ni na bashi yarinyar nan ba, dalili ya rufa min asiri na a lokacin da yake daf da tonuwa". Jiki a sanyaye ta ce Allah ya sanya alheri. Ya amsa da "Ameen ya cigaba da cewa." Gobe da sassafe zai zo ya d'auke ta su tafi can abujan inda yake aiki, yayi alkawarin cewa bayan an kwana biyu, zai zo ya dauke ni domin na je naga mazauninsu, na amince da maganarsa dari bisa dari! ke Shahida wannan mutumin daga yau shine uwarki shine ubanki! kuma mijinki, yi nayi bari na bari, ke ki ka ganshi kina so ki ka amince da auransa, saboda haka kada naji wata magana ta biyo baya wannan shine abinda zan fad'a miki." Ta d'aga kanta da fadin." Insha Allahu zanyi kokarin yi masa biyayya Baba a cigaba da yi mana addua'a." Ya kalli Baba Asabe da fad'in." Ko akwai nasihar da za kiyi mata domin tafiya nake so nayi da ita can gidana da wuri za su wuce." Ta ce."Ai ka riga ka gama yi mata nasiha Jamilu ni kuma a suwa! a matsayinka na ubanta ai ka gama komai.'' Ko a jikinsa, ya kalli Shahidan da fad'in " Ki shiryo ki fito ina waje ina jiranki." Ya mi'ke tsaye tare da zura hannu cikin aljihu, dubu uku ya d'auko ya ajiye a gabanta da fadin " Allah ya ba mu alheri.'' Cike da rashin kuzari ta bishi da kallo tana Allah wadai da mugun halinsa. Ta juya ta kalle ta tana zaune ta kasa tashi ballantana ta shirya kamar yanda ya umarce ta. Ta d'an bud'e muryarta da fad'in." Ki tashi ki sanyo mayafi ki bishi Shahida ai magana ta 'kare, ni dai nayi iyakar bakin kokari na akan lamarin, ba zanyi miki baki ba sai dai adduar Allah ya tabbatar da alheri." Wani irin kuka ya kufce mata sai kawai ta rungume ta a jikinta tana fadin." Baba don Allah ki yafe min kada ki k'ulla ce ni, ki cigaba da yi min addua." Tana kuka sosai ta ce " Shahida addua a kanki ai yanzu na fara, ba zan daina ba har sai ranar da Allah ya dauki raina, amma har a cikin raina ban so kiyi wannan rayuwar ba, na so ki auri miji nutsatstse mai hankali d'an gari mafi kusa dani wanda zai kula min dake da lalurarki, amma hakan bai samu ba, sai wannan kaddara to ina rokon Allah yasa ta zama alheri." Sosai suka rungume juna suna ta kuka! Saliha ta dinga kyalkyala musu dariya tana yi musu vedio, da 'kyar suka rabu da juna kowanne zuciyarsa babu dadi, mussaman Baba Asabe da har yanzu abin bai kwanta mata a rai ba. Ita kuwa Shahida kukan rabuwa da ita kawai take, amma a cikin zuciyarta ba ta tunanin komai face alheri domin ba ta tsammanin cewa masoyin nata zai cutar da ita. **** To tun a mota ta sha jinin jikinta gabad'aya sai tayi sanyi jikinta ya mutu! ta dinga kallonsa a fakaice! tana jin wani irin tsoro a cikin zuciyarta. Gabad'aya kamar tunda aka hallice shi bai ta'ba dariya ba, fuskarsa murtuk! sam ya ma'ki yarda ya kalle ta ballanatana ta samu sararin yi masa wata magana, tun bayan da ya d'auko ta daga gaban mahaifinta ya rikid'e! ya zama mara farin ciki ko a motar ma bai yarda ta zauna a kusa dashi ba, cewa yayi taje can ta zauna cikin mata 'yan uwanta. Ta dinga tunane-tunane marasa kyau a cikin zuciyarta! amma ba ta bari abinda take rayawa a ranta yayi tasiri ba, kawai sai dinga nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Tunda take bata ta'ba doguwar tafiya irin wannan ba shiyasa gabad'aya! jikinta ya mutu! ta gaji sosai! sai addua take Allah ya sa su sauka lafiya! ko ta samu ta mi'ke k'afafunta! Matar dake kusa da ita ta bata pure water "Kar'bi ruwa 'yan mata naga kamar kin gaji." Ba ta ji maganarta ba kawai dai ta ga tana mi'ko mata ruwa. Da sauri tasa hannu ta kar'ba ta bud'e baki za tayi magana, ya juyo daga mazauninsa wata muguwar harara ya daka mata fuskarsa a mugun had'e! Sai tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na wani irin fad'uwa ta mayarwa da matar ruwan da sauri! jikinta sai rawa yake. Matar ta bi ta da kallon mamaki! sai kuma ta ta'be bakinta ta ajiye ruwanta da fadin."Kin yi wa kan ki." A galabaice suka isa abuja! yanda ta fahimta kamar tafi kowa galabaita watakila saboda rashin sabo ne. Ya riga ta fita daga motar yana tsaye yana jiranta ta fito. a gajiye likis ta fito, nan ta ga yanda ya sa bakin gilashi a idonsa tare da rufe kansa da bakar hular sanyi. ta dan tsaya a gefansa tana bin tashar da kallo! ga rana ta k'wallare! jama'a kowa na gabatar da abinda yake gabansa. Hannunta ya ri'ke! ya jata suka nufi wata rumfar kwano gurin wata mai sayar da abinci bayerabiya. cikin harshen turanci suka gaisa kafin ya shedawa matar cewa ga ajiyar yarinya ya kawo mata ta bata abincin da zai isheta anjima zai turo a d'auke ta, wanda zai zo ya d'auke ta sunansa Sule." Ta Amsa da "to kafin kalle ta da fad'in." Zo ki zauna." tana nuna mata wata kujera. Gabanta ya dinga duka yana daka! hawaye suka ciko idonta! ita dai ba ta ji abinda suke cewa ba amma ta fahimci kamar barin ta zai yi a gurin ganin yanda matar ke kallonta tana nuna mata gurin zama. Ta ri'ke hannunsa tana girgiza masa kai! wasu zafafan! hawaye suka kufce mata. Saurin d'auke kansa yayi ya cire hannunsa daga nata ya kalli matar da fad'in." Tana da matsalar kunne ba sosai take ji ba." Da kansa ya ja hannunta ya kai ta ya ajiye a kan kujera, fuska a murtuke ya ce" Zan je wani guri ne shiyasa na kawo ki anan na ajiye amma zan turo a dauke ki kada ki damu." Bai jira tace wani abu ba yayi saurin barin gurin ko waiwayenta be yi ba. Duk kyawun abincin bai bata sha'awa ba, gabadaya ma ba ta cikin nutsuwarta, tsoro da fargaba sunyi mata dabaibaiyi, tunani ma ta rasa wane kala za tayi, sa'i da lokaci ta ke share hawaye tana bin tashar da kallo da nazarin wace rayuwa za ta fuskanta a nan gaba. Ekeke matar dake sayar da abincin kenan, ta kalleta a karon da ba zai lissafu ba, domin tun tana lallabata ta ci abincin har ta gaji ta zuba mata ido! sai dai haka kawai take tausaya mata idan ta tuna cewa kurma ce ba ta ji sosai, ta yi tunanin abubuwa da yawa akan yarinyar, ta tunanin mutumin yayi kawalcinta ne domin ya dinga biyan buk'atarsa! Sai daf da magariba Sule ya je domin d'aukarta! Ko kusa ko alama bai gane ta ba ballantana yayi tunanin wani abu, ko da yake can baya da ya je binkice lokacin da abin ya faru duhun dare ya shigo da kuma cikowa ta mutane shine dalili. Su ka gaisa da Ekeke kafin ya sheda mata shine Sule ya zo tafiya da yarinyar." Ta ce." To kud'in abinci dubu biyu sai kudin jira dubu uku, duk da ba taci abincin ba ita wannan ba damuwarta bane. Sule bai ja doguwar magana ba ya ciri kudinta ya bata. Jiki a sanyaye take binsa tana ta addua a cikin zuciyarta. ba ta 'kara firgita ba sai da ta ga shirgegiyar motar da ya bude mata wai ta shiga. Ai sai hawaye suka fara zuba kuka sosai take! tana waiwaye a gurin, ta tsorata don gani take kamar sa ce za ayi." Yayi -yayi da ita ta shiga amma fafur! ta' ki shiga sai kuka take tana nema ta tara musu mutane a gurin. Wayarsa ya fito da ita ya kira maigidan nasa ya sheda masa halin da ake ciki. Ya ce ya bata wayar su yi magana. Nan ma da kyar ta karbi wayar jikinta sai rawa yake. Da muryar da ya aro yayi mata magana da k'arfi yanda za ta ji. "Shahida ki shiga mota Sule zai kawo ki gidan da nake aiki wato gidan maigidana kamar yanda nayi miki bayani a can baya. zamu zauna a gidan ne a wani sashe da aka ba mu, ina nan ina jiran zuwanki." Hankalinta ya kwanta jin muryarsa, a sanyaye ta ce." To." ta mika masa wayar tana godiya a cikin ranta domin wallahi tayi tunanin Sule sace ta zai yi. *Normal group #500 Vip group 1k via 0542382124..Binta umar gtbank. idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262...Mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel. Vip gruop jakka daya.* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE🌳* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ 51&52 Girman gidan da tsaruwarsa ya firgitata sosai, sai ta 'kara shiga rud'ani zuciyarta ta cigaba da yi mata tunane-tunane marasa kyau! wani 'bangaran na zuciyarta na nuna mata cewa Baban- Baba mutumin arziki ne ba zai cutar da ita ba. Tafiya mai tsayi su kayi a cikin gidan domin kwalta ce a shimfid'e har sai da suka kusa kai wa karshen gidan, sannan taga yayi parking, sai ta dinga kalle-kalle a gurin, tsit! sai shuke-shuke da kukan tsintsayen dake sauka a kan ciyayi gabanta ya cigaba da fad'uwa, cikin zuciyarta take ta nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! ya bud'e mata 'kofar motar, alama yayi mata ta fito da hannunsa. 'Kin fitowa tayi ido jawur! take kallonsa kafin ta bud'e baki cikin yanayin maganarta tace." Ina ne nan din.? Ya ce." Gurin da zaki zauna ne maigida ne ya ce a kawo ki nan" Sai ta kasa fahimtar inda maganarsa ta dosa. kawai dai ta zuba masa ido tana ayyanawa abubuwa da yawa aran ta. Cikin wayo da dubara ya ce." Ai yana ciki yana jiranki kamar yanda ya fad'a miki a waya." shima ya fadi maganar ne kawai! ba tare da ya san abinda ke faruwa ba. Jin abinda ya ce yasa ta d'an ji 'kwari a jikinta, ta fito daga motar, yayi mata jagora zuwa wani ke'bantaccen sashe, ya bude mata ta shiga da bisimillah a bakinta! tare da jin fad'uwa gaba a tare da ita. Tana shiga ya mayar da k'ofar ya rufe da key. ya bar gurin da saurin gaske. Shuru falon babu alamun motsi! sai dai tsaf ko'ina a tsare babu datti a ko'ina. Falo ne mai girma da kujeru masu kyau da labulaye! sai dak'in bacci guda biyu da kicin da bandaki duk a falon. a hankali ta zauna kan kujera mai cin mutum d'aya tana sake nazarin falon, gefe guda kuma zuciyarta sai bugawa take, shin ko daga ina mijin nata zai fito oho! "Yallabai komai ya kammala, yarinyar tana wannan sashen daka umarce ni dana ajiye ta." Sule ne ke wannan maganar lokacin da yake zaune a gabansa. Ya cire farin gilashin dake sakaye a idonsa ya kalleshi sosai kafin ya ce."Matata ce Shahida." Da sauri Sule ya kalle shi da dumbun mamaki a tare dashi ya ce." Matarka Yallabai?" Yayi murmushi da fadin."Kwarai kuwa a jiya nan aka daura min aure da ita, itace yarinyar mutumin nan da nasa kayi min binkice a kansa." Sule ya dinga jinjina al'amarin ya ce." Wallahi Yallabai ban gane komai ba, ita kanta yarinyar ban gane ta ba, sai dai nayi ta mamakin dalilin da yasa ka 'kebance ta a gidanka, sai na ce to ko da wani abu ne wanda kake shiryawa." Ya ce." K'warai kuwa Sule kai din yaro na ne amintacce wanda na yarda dashi, nasan cewa ba zaka mance wahalhalun da nasha a can baya ba, auren farko ban yi dace ba, na biyu ma haka, wannan dalilin yasa gabad'aya nake tsoron duk wata 'ya mace saboda kaidi da sharrinsu, da yawa 'yan uwa da abokanan arziki suna fad'in ai ba duka suke da mugun hali ba, bahaushe yace wanda maciji ya sara idan ya ga bakin tsumma dole ya razana! a cikin zuciyata na cire aure gabad'aya daga raina! sabida samun zaman lafiya na, daga baya surutai na jama'a yayi yawa a kaina cewa ba girma na bane na zauna babu aure! wannan dalilin yasa na janye kudirina, auran wannan yarinyar nayi shi ne da manufofi da yawa. saboda haka kai kad'ai ne a gidan nan kasan wannan yarinyar matata ce, akwai wani shiri da nake akan lamarin duk don na gwada ta, da tarbiyarta." numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Matata ce, amma za ta zauna a matsayin matarka na d'an wani lokaci, ina nufin ko da wani daga cikin iyali na zai tambaye ka sai ka amsa da cewar matarka ce, shikkenan, amma babu ruwanka da zuwa sashen, sai dai idan ni na aike ka gurinta." Sule ya sauke zazzafar ajiyar zuciya, a sanyaye ya ce." To shikkenan Alhaji Allah ya sa a dace da tagari, ina yi maka fatan alheri ubangiji Allah yasa anyi kenan." Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina Sule za ka iya tafiya sai na neme ka." Godiya yayi sosai kafin ya tashi ya tafi cike da mamaki a tare dashi, ko da yake bai ga laifin maigidan nasa ba, duba da cewa a can baya mata sun wahalar dashi don yayi hakan ba laifi bane. Kuka taci sosai! ganin duhu dare ya shigo gashi babu haske a falon, ko'ina yayi duhu! sai labulan tagogin dake falon ta janye haske ya shigo, hakan yasa iskar sanyi ta dinga shigowa, jikinta ya dinga kyarma! da sauri ta takure jikinta akan kujera tsoro na sake kanainaye ta, bud'e tagogin da tayi sai idanunta ya dinga yi mata gizo ta dinga ganin gilmawar abubuwa da yawa. da sauri ta je ta sauke labulayen ta koma ta zauna, babu abinda ya fi damunta irin sallar magariba da isha'i! ga yunwar da take mugun sasakarta! Jin motsi kamar ana ta'ba 'kofa ya sa gabanta ya tsananta fad'uwa! ta tsirawa kofar ido! duk da bata da tabbacin ganin fuskarsa saboda duhu amma a jikinta take jin shine zai shigo. Ya shigo da sallama ciki-ciki. ba ta ji ba amma ta ga inuwarsa. Tsaye ta mi'ke! har yanzu jikinta bai dawo daidai ba. Ya kunna hasken 'karamar wayarsa, nan ya hangeta a tsaye ta tsura masa ido, lokaci guda ya fahimci firgici da tsoro a tare da ita. Sunanta ya kira babu walwala a fuskarsa. Ta amsa cikin rawar murya. Ya ce." Zo ki kar'bi wannan ledojin kayanki ne a ciki." A sanyaye ta 'karasa kusa dashi tasa hannu ta kar'bi manyan ledejojin dake hanunsa. Bayansa ta bi ganin ya nufi d'aya daga cikin d'akunan dake falon. Ya juyo ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya ce." Nan d'akina ne kuma ina bukatar sirri! ki d'auki wancan dakin ya zama naki." ya fada yana nuna mata d'aya dakin. Yana gama maganarsa ya bud'e ya shiga ya barta a tsaye da ledoji a hannu. Ta jima a tsaye a bakin kofar dakin tana tunane-tunane! daga bisani ta fara laluben hanya tunda ya shige dakinsa da hasken sai falon ya dawo inda yake duhu sosa! ta nemi kan kujera ta zauna ba tare da tayi tunanin shiga dakin ba, saboda tsoro take ji tana ganin gwara ta zauna a falon shi yafi mata alheri, amma haki'kanin gaskiya Baban-Baba yayi mata bazata! ba ta ta'ba tunanin zai mata wannan wulakacin ba, hawaye masu tsananin zafi suka shiga kwaranya a saman fuskarta. Fitowa yayi daga d'akin ya ji shashshekar kukanta! Tausayi ta bashi amma bai nuna ba, ya d'aga muryarsa sosai!" Ke menene? ki ke wa mutune kuka" A zabure! ta juyo tana kallonsa! sai kuma ta sunkuyar da kanta amma ba ta fasa zubar da hawaye ba. Ya ja tsaki! da fad'in." Ko yunwa ki ke ji ?" Kai ta daga masa alamun hakane sannan tayi namijin 'kokarin fad'in." Ina so nayi sallar magariba da isha'i." Ya ce." To waye ya hana ki? da duk zaman da ki ke a gidan ba kiyi sallar ba?" Ta ce." Duhu ko'ina babu haske." Ya ce." Ki bud'e wannan ledojin da akwai fitila da batiri a ciki sai ki kunna." Da sauri ta fara dubawa, ya kunna mata hasken wayarsa har ta saita fitilar ta kama, sannan ya kashe wayarsa, ya kama hanyar fita, ta bishi da wani irin kallo zuciyarta sai bugawa take. Tana d'aura alwala a bandakin dake cikin falon ta dinga jin motsinsa kamar yana shigowa da abu, sai da ta fito ne ta fahimci cewa kayan abinci ne. Nan falon ta gabatar da sallolinta, ta jingina jikin kujera tana kallon shiga da ficensa tsakanin kicin da dakinsa. Gani tayi ya zo ya zauna a daya daga cikin kujerun dake falon, ido ya zuba mata, sai ta kasa jure hada ido dashi, domin yanzu gabadaya tsoro yake bata, ya sauya sosai! ya dawo Baban-baba na asali wanda ta san shi a lokacin da yake kwanciya a 'kasan mota! Gyaran murya yayi kafin ya kira sunanta yanda za ta ji.'' Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba. Ya ce." Nan ne gurin da maigidana ya bani domin na zauna da iyalina. bayan haka kuma sa'i da lokaci za ki dinga zuwa kina gaisawa da kakarsa wacce take zaune a cikin gidan, za ki dinga taimaka mata da wasu abubuwa duk da cewa akwai masu aiki amma kema zaki shiga sahun su, akwai kayan abinci a kicin komai da komai na bukata maigidana ya bani kudi nayi miki sayayya! a cikin ledojin nan akwai kayan sawarki kala hud'u da mai na shafawa da sabulun wanka da wanki da sauran tarkacen ku na mata, abinda babu kada kiyi 'kwaron baki sai ki sanar dani, amma ina so ki zauna da masu gidan nan lafiya! mussaman maigidana domin shi ya mayar dani cikakken mutum kamar kowa, wannan dalilin yasa nake so kiyi masa biyayya kamar yanda za kiyi min, duk wani abu da yake bukata kiyi masa.'' A sanyaye ta ce." Insha Allahu zanyi iyakar bakin kokari na, ni dai buri na ka ri'ke ni amana kamar yanda kayi alkawari! Tsaki ya ja kafin ya mi'ke tsaye ya ce." Wace amana kuma? ki daina wannan maganar, domin kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, saboda haka ki daina wannan maganar." Wani irin kallo take masa tana jin maganganunsa na amsa kuwwa! a kunnanta "Kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, don haka ki daina maganar amana." Wannan magana ta jima tana yi mata yawo a k'wa'kwalwarta. Jin yunwa na nema ta halaka ta yasa babu shiri ta dauki fitila ta nemi hanyar kicin ta je tana laluben abinci, aikuwa ta samu fulas cike da dambun shinkafa wanda yaji kayan had'i! ga ledojin ruwa nan pure water ta dauka ta fito da fulas din abincin a hannunta. *BINTU*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ 53&54 A ta'kaice dai Shahida ita kad'ai ta kwana, domin tun da yayi fitar nan, bai dawo ba, tun tana jin tsoro har ta hak'ura ta barwa Allah al'amarin, sai dai bakinta bai daina addu'a ba har san da bacci 'barawo ya sace ta. Motsin shigowarsa da asubah ya tashe ta, sai ta mik'e zaune da sauri tana laluben fitilar da gurin bacci ta fad'i a gurin, batiran duk suka watse Shigowarsa yayi daidai da lokacin da ta gama gyara fitilar haske ya mamaye falon. Ya kalle ta babu walwala a tattare dashi ya ce." A nan ki ka kwanta ne?" Kanta ta daga masa alamar ."Eh." ya kama hanyar d'akinsa ba tare da ya sake wata magana ba, wannan ya sake tabbatar mata da cewa ba a gidan ya kwana ba. Jiki a sanyaye tayi alwala ta fito anan falon dai ta gabatar da sallah, ta jima tana addu'a tana kuka sosai take neman sassauci a gurin mai duka domin ba ta ta'ba tunanin cewa zata fuskanci irin wannan matsala ba. Sai da gari ya waye sosai ya fito cikin shiri ya d'ora rigar sanyi babbah da sabuwar hula irin ta sanyi ya rufe kunnuwansa sannan ya rufe idonsa da gilashi b'aki, tsira masa ido tayi domin gani tayi kamar yayi haske ba kamar can baya ba sai dai har yanzu wannan k'asumbar tana nan duguzaza! tare da tsalli-tsallin furfura. Ganin yanda take kallonsa sai ya sha kunu! ya ce." Na zama tibi ne?" Ba ta ji abinda ya fad'a ba amma yanayin yanda ya yi maganar yana tsatstare ta da ido ta fahimci cewa ransa a 'bace! sai ta d'auke kanta tana mamakinsa a cikin zuciyarta. Gyaran murya yayi sosai ya bud'e ta domin ta ji abinda zai fad'a mata. "Zan tafi can kudu wani aiki kamar yanda maigidana ya umarce ni, don haka za ki cigaba da zama anan babu wata matsala tunda akwai ci dasha saboda haka ki kwantar da hankalinki, amma ban amince ki je ko'ina na ba, abinda na aminta dashi zuwa gaishe da kakar maigidan kamar yanda na fad'a miki da farko. Tsoro ta cire a ranta ta kalle shi sosai kafin ta ce." Shi maigidan naka bai san cewa kai ango bane zai tura ka wata uwa duniya, kada fa ka manta amana ka d'auko ni a gaban iyaye na mai yasa tun kafin tafiya tayi nisa ka sauya hali, wallahi ban yi tunanin haka daga gare ka ba." Hannu ya d'aga mata da fad'in." Za kiyi min rashin kunya ne?" ta girgiza kanta. ya cigaba da cewa; idan na zauna a gidan me zanyi miki da har ki ke wannan maganar." Sunkuyar da kanta tayi tana mamakinsa. Ya cigaba da cewa'' Ai ban ta'ba ganin makwad'aicin uba irin naki ba, wanda bai san k'ima da mutumcin 'ya'yansa ba. domin ya ba ni auranki ne a matsayin fansa a gare shi, ke da bakinki kuma ki kayi al'kawarin girmama maigidana saboda alherin da yayi miki keda mahaifinki, amma har kina da bakin fad'in wata magana a kansa, to ki iya bakinki idan ba haka ba ranki zai yi mummunan 'baci! Kuka take sosai! ta ce." Yanzu mai ya kawo wannan maganar? wato ka naso ka nuna min cewa maigidan ka ya fi ni kenan, kada fa kamanta bani da kowa a wannan gari sai kai, ban san ko'ina ba, sannan akwai rashin sabo wannan shine dalilina na fad'in wannan maganar amma bada cin mutunci ba. Tsaye ya mi'ke tare da fad'in" Ni dai na fad'a miki ki kiyaye! kuma ki iya bakin ki, maigidana ya fi kowa daraja a guri na ciki kuwa har dake, mutukar kina so na shirya dake to ki girmama shi kuma ki san irin maganar da zaki dinga fad'a a kansa. Cikin shashshe'kar kuka ta ce." Kayi hakuri zan kiyaye insha Allah, yanzu kwana nawa za kayi?" Ya ce."Sati biyu zanyi." a sanyaye ta ce." To Allah ya kiyaye hanya ya bada abinda aka je nema." Ya amsa da amen kafin ya d'ora da fadin." Akwai komai na bukata, idan wani abu ya 'kare to kiyi wa Sule magana wanda ya kawo ki nan, abokina ne zai yi miki komai kafin na dawo" Ta ce." To shikkenan.'' hanyar fita ya nufa, sai ta mi'ke domin yi masa rakiya ya dakatar da ita da fadin." Koma ki zauna bana bukata." Ta koma ta zauna tana kallo ya bud'e kofa ya fita tayi saurin zuwa ta bud'e labule tana le'kansa, juyo wa yayi suka had'a ido, sai tayi saurin sauke labulan gabanta na cigaba bugawa. Kamar yanda ya sanar mata da cewa akwai komai na bu'kata hakane. koda ta duba kicin din komai da komai da akwai, sai ta kunna karamin gas din da ta gani a ajiye. ta d'ora ruwan shayi, sannan ta feraye dankalin hausa ta soya dai-dai cikinta, a kicin d'in ta had'a shayin ta zauna tana sha tare da had'awa da dankalin da ta soya. Tunani ne yayi mata yawa, gabad'aya ta rasa a ina zata ajiye wannan al'amari! ashe Baban-baba mayaudari ne ba ta sani ba? ita dai har ga Allah ta ke k'aunarsa take kuma yi masa kallon mutum mai mutunci da amana, ashe kallon kitse takewa rogo, tun ba aje ko'ina ba ya fara gwada mata wasu dabi'u marasa kyau! hawaye ta share! tana tunanin Baba Asabe, watakila dama abinda take ta guje mata kenan shiyasa hankalinta bai kwanta da al'amarin ba, tabbas duk abinda ya fad'a akan mahaifinta gaskiya ne, beyi masa sharri ba, domin ita kanta ta san ba suyi sa'ar uba ba, sai yanzu take sake gazgata maganarsa, domin duk uban arziki mai kishin 'ya'yansa ba zai dauki aure ya baiwa irinsu Baban-baba wad'anda basu da asali ma'ana ba a san daga inda suke ba. Sosai ta ci kuka ta koshi a kicin din, ta ajiye al'amarin a matsayin kaddararta, domin a yanzu duk abinda za ta fito ta fad'a a banza babu wanda zai saurare ta. Wanka tayi ta shirya cikin atamfah riga da siket daga cikin kayan da ya kawo mata jiya, tasa hijabi a jikinta ta kama hanyar fita, tana so ne ta je ta gaisa da masu gidan kamar yanda ya umarce ta kafin ya tafi. Sai da tayi tafiya sosai sannan ta fito harabar gidan, nan taga mutane rukuni-rukuni a wata rumfa yawanci maza ne matan basu da yawa, suna zazzaune, daga can bakin gate kuma ma'aikata ne masu tsaro sun kai bakwai harda masu bindigu a hannu. Da sauri ta d'auke kanta. tana jin fad'uwar gaba, lallai duk yadda akayi wani abu ne zai faru a gurin, da alamar suna jiran fitowar maigidan ne. Wata hanya ta bi duk da cewa bata san ina za ta shiga ba kawai dai tayi hasashen nan ne hanyar da zata shiga cikin gidan. Wani lafiyayyan k'amshin turare ya daki hancinta. da sauri ta d'ago kanta tana kallon hanyar lokacin da suka fito tare da escorts dinshi guda biyu. ido suka had'a da saurin gaske tayi kasa da kanta jikinta yayi bala'in mutuwa! "Wannan ai shahararran attajirin nan ne da ake nuna fuskarsa a tibi." sake kallonsa tayi a karo na biyu cikakken mutum kamili mai halin dattako! yana sanye da farar shadda kal dinkin tazarce da jar dara ya nad'a farin rawani a saman hular. as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi, yayi kyau sosai ba'a magana domin gabad'aya shekarunsa sun 'buya sakamakon gyaran fuskar da akayi masa wanda ya sake k'ayata fuskarsa, gemu kad'an ya bari wanda ya kwanta luf da furfura kad'an-kad'an. Duk sai ta dabarbace! domin wani irin kwarjini yayi mata, tun kafin ya k'araso gurin da take ta zube 'kasa tana gaida shi da yanayin maganarta. Bai amsa ba sai dai ya yi mata alama da hannunsa ma'ana ta tashi, kasa mi'kewa tayi kanta yana 'kasa tana kallon kyakykyawar kafarsa cikin ba'kin takalmi maigidan yatsa. Ganin ta kasa tashi yasa ya wuce ya bar ta a gurin, yaransa suka rufa masa baya. Tashi tayi tana buge jikinta zaninta duk ya kwashi ciyayi! a sanyaye ta juya tana kallon bayansu har suka 'kurewa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya mai zafin gaske. A hankali ta tura kofar falon wacce ta kasance ta gilas. sallama tayi a nutse da yanayin maganarta. Hajiya Saude tayi saurin kallon bakin k'ofar tare da amsa sallamar. kallon rashin sani take mata, ita kuma duk sai ta daburce! ganin kallon da matar take mata. A sanyaye ta isa har gurin da take ta zube 'kasa tana gaishe ta, Cikin wani irin yanayi ta amsa gaisuwar tana mamakin daga ina yarinyar take, domin ita duk a tunaninta irin nakasassun da suke zuwa gidan neman taimako ne, da jin yanayin maganarta ta kurame ba sosai take fita ba. Ta sauke ajiyar zuciya cike da d'an tausayin yarinyar a tare da ita ta ce." Ai yanzu maigidan ya fita idan taimako ki ka zo nema yana waje can zaki tsaya." Ganin tayi shuru ba ta amsa ba, yasa ta bud'e muryarta ta sake maimaita maganarta . Cikin jin nauyi ta ce." Sunana Shahida ni ce matar Baban-baba." Jim tayi kafin ta ce." Ayyo! amaryar Sule ce ashe. sai tasa dariya da fad'in ai jiya nan yake sheda min cewa ya k'ara aure har maigidan ya bashi gurin zama a cikin gidanan Allah ya sanya alheri ai mu nan da Sule muke kiransa." Murmushi tayi ba tace komai ba, sai dai cikin zuciyarta take ta auna maganganun matar ashe dama sunansa Sule na gaskiya. Hajiyan ta cigaba da cewa." Ai Sule mutumin kirki ne sosai ki ri'ke shi da kyau sosai! kuma ki zauna da kishiyarki lafiya." Gabanta ya fad'i jin maganar kishiya, ta dinga kallonta lokacin da take jaddada mata nagarta da kyawun halinsa, sai ta ji wasu zafafan! hawaye suna nema su kufce mata. Da k'yar! ta iya danne damuwarta, ta ce." Hajiya ko da akwai wani abu da zanyi miki?" Girgiza kanta tayi ta ce." A'a babu komai, sai dai ki zauna ki d'ebe min kewa ai na ji dad'in zuwanki gidan nan saboda zaman kad'aici yana damuna, Shukura kuma ba gwanar zaman falo ba kullum tana daki da waya a hannu." Sunkuyar da kanta tayi tana nazarin maganganunta, to shin maigidan bashi da aure ne? ko kuma ba a gidan yake zaune ba? bata da mai bata amsa sai kawai tayi shuru, tare da tsirawa tv ido kallon kawai take amma ba sosai take jin abinda ake fad'a ba. Cikin riga da wando na bacci ta fito daga d'akinta. ganinta a zaune yasa tayi turus! tana kallonta babu annuri a fuskarta ta kalleta da fadin." Hajiya wannan wacece kuma?" ta fada tana nuna ta da yatsa. Tana shirin bata amsa ya shigo, duk sai su kayi shiru suna kallonsa, a nutse ya zauna kan kujera yana kallon Shukuran dake tsaya da alamun rashin gaskiya a tattare da ita. "Kin yi sallah?" tambayar da ya yi mata kenan. Sai ta hau diri-diri kafin ta ce." Daddy bani da tsarki ai." Shuru yayi be ce komai ba, da shagwaba ta ce" Daddy don Allah ka bari na je gidan bikin nan, kamar hakan bai dace ba tunda Aunty Samira 'kanwar mommy ce kuma kai ma 'kanwarka ce ka taimaka Daddy don Allah." ta 'karasa maganar tana karyar da kai. Shuru yayi bai ce uffan ba, ta kalleta da fadin." Hajiya kisa baki don Allah" Kallonsa tayi da fad'in.'' Alhaji Habu ina nema mata alfarma." Yanda ta fad'i maganar cikin 'kaskantar da kai ya bashi dariya! Ya ce" Na amince amma ba don halinta ba, kuma ban yarda da kwana ba, aje a dawo." Tsalle ta buga da fad'in." Daddy na gode Allah ya 'kara girma." Duk abinda suke tana takure a gurin tana kallonsu, sai dai ba sosai take jin abinda suke tattaunawa ba. ita gabad'aya zaman sa a gurin shi ya 'kara firgitata! ta kasa gane wane yanayi take ciki, haka kawai mutumin yake cika mata ido. Hajiya ta nuna ta da yatsa da fadin." Yallabai wannan ita ce amaryar Sule fa, wallahi da farko na dauka irin masu zuwa neman taimako ne, sai da ta gabatar min da kanta tukkuna na tuna amma ga dukkan alamu tana da matsalar rashin ji kurma ce" Kallon da yake mata ne yasa duk ta tsargu! ta kasa 'kwakwkwaran motsi. A hankali ya kalli Hajiyan da fadin." Ya sunanta?" "Shahida sunanta, ai na ce na samu abokiyar hira duk da cewa ba ta ji sosai hakan bai zai hana ta d'ebe min kewa ba." Ya ce." 'Kwarai kuwa nima wannan ne dalilin da yasa na bashi guri a gidan nan, na ce ya zauna saboda ki samu walwala. Ta ce." Maganar auranka dai shuru Alhaji kullum sai kace kana kan hanya.'' Shukura da sauri ta ce." Hajiya ai daddy ba sabon aure zai yi ba, Mommyna zai dawo da ita.'' Wani irin kallo yayi mata kafin ya mi'ke ba tare da ya ce musu komai ba ya haura samansa. Hajiya ta ce." Shukura mahaifinki ya tsani ayi masa maganar Fatima mutukar kina so ki ga b'acin ransa to ki ambaci sunanta, wannan k'iyayyar tayi yawa." A sanyaye ta ce."Wai Hajiya me ya faru ne? na lura daddy ya tsane ta sosai kuma yana da ri'ko! kome tayi masa ai sai yayi hakuri tunda na shiga tsakani, sannan da dangantaka a tsakaninsu." Ta ce." Shukura labarin yana da tsayi sosai! amma babu shakka Fatima ta yi abubuwa da yawa marasa kyau a can baya! wanda ba su da amfani, saboda haka tayar da al'amarin yana nufin 'bacin ran mu gabad'aya. A sanyaye ta ce." Shikkenan to Allah ya kyauta." ta amsa da "Ameen ya rabbi." Shahida na zaune tana satar kallonsu, yanayin fuskokinsu da yanda suke magana a hankali cikin rashin walwala yasa ta gane cewa lallai abinda suke tattaunawa ba mai dad'i bane. **** To kwana d'aya biyu har ta saba! kullum idan ta tashi za ta gyara gurinta, kafin tayi wanka ta shirya jikinta tsaf! sai ta karya kummalo ta nufi cikin gidan a can take yini tare da hajiya, idan lokacin shiga kicin yayi ta je ta taimakawa masu aiki, sosai Hajiya take jin dadin zama da ita, wannan dalilin yasa ta umarce ta cewa duk abinda take bukata kada tayi 'kwauron baki ta tambaye ta, anan take cin abinci rana da dare. sai tayi sallar isha'i take tafiya gurinta, sai dai abinda yake damunta yanda Shukura ke 'kyamarta! hantara! kyara! wataran harda zagi! kuma kullum ita ke zuwa ta gyara mata d'akinta ta wanke mata bandaki da sauransu, amma bata ta'ba godiya ba, wannan abu yana damunta sosai! Kasancewar ta samu caji a wayarta yasa ta tura masa text na gaisuwa da kalaman soyayya! tana jiran amsarsa, shuru bai bata amsa ba, jikinta ya 'kara yin sanyi gabad'aya bata da wani kuzari, yau kwanansa tara da tafiya babu wata magana da ta ta'ba shiga tsakaninsu ta hanyar sadarwa. Cikin kwana goma da tayi a gidan ta sauya fatarta tayi luff! tayi kyau daidai gwargwado kuruciyarta ta sake bayyana, Shahida bata da wani kyau na ku zo a gani, sai dai tana da dirin jiki mai kyau akwai cikar kirji tare da kyakykyawan k'ugu ko'ina a jikinta a cike yake bata da rama kuma tana tsakatsaki ita ba doguwa ba sannan ba gajeriya ba, tana da yawan gashi cikkake irin na asalin hausawa, bakikirin! haka take d'aure shi da ribbon ya taru sosai a kanta, tana yanayi da Nafisa Abdullahi jarumar finafinan hausa, sai dai har taso tafi Nafisa cika da kwarjini. ba ta da makusa bayan matsalar kunne (rashin ji) da Allah ya hallice ta. Yau kwana goma sha biyu kenan da tafiyarsa, tana lissafi saura kwana biyu ya dawo,sai murna da farin ciki take, domin ita kad'ai ta san irin halin da take shiga a duk lokacin da za tayi bacci! tsoro take ji ita kad'ai a wannan gurin, koda wani abu ba zai shiga tsakaninsu ba, idan tana jin motsinsa a gidan rahama ne. Shuru lokacin da ta shiga falon, sai sallama take babu wanda ya amsa, cikin zuciyarta take tunanin ko Hajiyan na d'aki bata fito ba, sai ta yanke shawarar shiga dakin. a lokacin ne yake saukowa daga sama cikin pyjamas (kayan bacci) irin masu falmaran amma babu ta ciki kirjinsa wanda ya ke cike da kwantaccen gashi 'baki duk a waje! Da saurin gaske ta kawar da kanta! tana jin wani irin fad'uwar gaba, 'kafafunta ne suka shiga kyarma! ta zube a k'asa tun kafin ya 'karaso gurin da take. "Alhaji Ina kwana?" tafad'a cikin sar'kewar murya. Bai amsa ba da hannu yayi mata alamar ta tashi. Tashi tayi amma ta gagara kallonsa, gabad'aya ma tsigar jikinta ce take tashi ganinsa haka. Gurin cin abinci ya nufa ya zauna domin karya kummalo. Ita kuma jiki a mace ta kama hanyar fita, ya tsirawa bayanta ido, duk da cewa a cikin hijabi take hakan bai hana shi ganin 'kirar jikinta ba, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! yana danne abinda ke taso masa. muryarsa ya bud'e sosai kafin ya kira sunanta. Juyowa tayi tana kallonsa, yayi mata alama da hannu ta je gurinsa. Gabanta ya tsananta da fad'uwa, shin idan ta je me za tayi masa? abinda take rayawa kenan a zuciyarta. amma tuno gargadin mijinta yasa a sanyaye ta nufi gurin nasa kamar yanda ya umarce ta. *Littafi na daya yana daf da k'arewa ku yi hanzari ku biya kudin littafin na biyu domin cigaba da karanta labarin.🥰 Yanzu ne fa za a fara wasan. ina fata za ku yi mini kara gurin sayan littafi na biyu. Allah ya yassare.* *Normal group posting sau daya a rana #500... Vip group posting sau biyu a rana 1k. 0502382124...Binta umar gtbank. idan kati za a turo sai ayi mini mgn ta WhatsApp 07084653262.. Mutan nan Nijar dala dari Vip jakka daya katin airtel za ku tura mini ta WhatsApp* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *ABACHE POULTRY FARM*🐓🐓🐓 *Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.* *08069459550* *08039451082* _*'Karshen littafi na d'aya kenan, sai mu tara a cikin littafi na biyu, wanda ya kasance na kud'i #500 vip 1k za a tura kudin ta wannan account din...0542382124...Binta umar gtbank, idan kati za a turo sai ayi min magana ta WhatsApp da wannan numbers.. 07084653262.or 08089965176. BINTA UMAR ABBALE*_ 59&60 Ya jima yana jinyyar karan hancinsa kafin ya daina masa ciwo, sai dai sa'i da lokaci idan ya tuna abinda ya faru tsakaninsa da yarinyar sai yayi murmushi! cikin zuciyarsa yake addua'a akan Allah yasa ta cinye jarrabawarsa, domin d'an zaman da su kayi tare sonta da k'aunarta ya gama mamaye jini da gangar jikinsa. A na ta 'bangaran kuwa daina walwala tayi a gidan, motsi kadan za ta tsorata, domin tana fargabar kada ya kawo mata farmaki har gurinta. Bata sake saki jikinta ba sai da su Hajiya suka dawo sannan. ta warware amma duk da haka Hajiyan sai da ta lura da wani abu, sai take tambayarta ko akwai abunda ke damunta ta daina sakewa, da sauri ta ce "babu komai wallahi kaina ne kawai yake ciwo." Hajiya ta ce'' Ai fa na ga alama saboda ba haka muka tafi muka bar ki ba, to amma kin shedawa mijinki domin naga kina da k'wauron baki'' Murmushi tayi ta ce." Eh na fada masa har ya siyo min magani na sha." Ta ce."To Allah ya raba lafiya." domin ita Hajiyan a tunaninta ko ciki ne da ita. Ta ce." Ki je ki kwanta ki huta ai sai da lafiya ake komai." Sosai tayi farin cikin hakan, sakamakon ganin saukowarsa tasan tabbas idan yana gurin ba zata iya sakewa ba. Ya zauna kujerar dake fuskantarta. sai ta sunkuyar da kanta a hankali ta ce." Ina kwana?" ya d'aga mata hannu ba tare da ya amsa ba. Hajiya ta kalle shi da fadin." Yarinyar nan bata da lafiya har nake zargin ko ciki ne da ita?" Gabansa ya fad'i ya kalle ta da fadin." Wane irin ciki kuma Hajiya duka-duka yaushe su kayi auran?" Murmushi tayi da fad'in." Yo tsakanin mace da miji ai sai Allah, ai yanzu kamar tuntu'be akeyi dashi a hanya, shine nake tambayarta mijinta ya sani, ta ce" Eh har magani ya siyo mata." Ya kalle ta tare da bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce" Ke da gaske ciki ne dake?" Kunya duk ta rufe ta, sunkuyar da kanta tayi tana jin nauyi don gani take kamar maganar tayi kama da ta rainin hankali! kwana d'aya kacal da aurensu ya dauk'e mata miji ya kai shi uwa duniya, zai zo yana tambayarta sai dai idan shine yayi mata cikin. ita da zuciyarta take magana. Hajiya Saude tasa dariya da fadin." Kai ma dai da wani abu, to idan shine a tunaninka za ta fad'a maka ne? ni ma hasashe kawai nake. Ba tare da ya ce komai ba ya dubi agogon dake daure a hannunsa, ya kalle ta da fadin " Hajiya zan fita" Ta ce" To Allah ya bada sa'a." ya amsa da "ameen yana kokarin tashi. Shukura ta fito daga d'akinta. Sai ya tsaya yana kallonta, ta ce." Daddy ina kwana?" ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta ce."Hajiya ta fad'a maka sakon mommyna." Ya kalli Hajiyan domin jin 'karin bayani. Ta ce" Neman magana ne kawai irin na Hajiya Fatima, mun shirya dawowa gida ne shine take ba mu sa'kon gaisuwarta gare ka. Bai ce komai ba ya kama hanyar fita, sai suka bi shi da kallo jikinsu a sanyaye Hajiya ta riga tasan halinsa tun yana yaro mutukar ya bar abu to bar shi har abadah, wannan dalilin ne yasa take tausayawa Hajiya Fatima duba da irin wahalar da take sha a kansa ya'ki sauraranta, shekara da shekaru da rabuwar auransu, ta'ki aure ita lallai tana jira yazo ya mayar da ita d'akinta, in da shi kuma ya ci alwashin sai dai ya mutu babu aure mutukar sai ya zauna da ita ne. 'Yan uwa da ita kanta kakar tasa sunyi-sunyi har sun ha'kura, domin mai daki shi ya san in da yake masa oyoyo, shi kadai ya san irin wahalar da ta bashi a lokacin da suke tare. **** BAYAN KWANA BIYAR Tana zaune 'kasan kafet tana cin abinci wanda ci kawai ta ke yi saboda ta kori yunwa ba wai don abincin babu dadi ba, A'a sai don ta san mutukar ta kwanta da yunwa to tabbas zata tashi a galabaice! shiyasa take tuttura abincin tana had'awa da ruwa. Motsi ta ji ana kokarin bud'e kofar shigowa, gabanta ya yanke ya fad'i! ta tsirawa kofar ido tana addua a zuciyarta, domin ba ta kawo cewa mijinta bane ta fi tunanin maigidan ne da yake kai mata hari a duk lokacin da su had'u sai ya san yanda yayi ya ta'ba jikinta, wannan abu yana yi mata ciwo mutuk'a! ita ba abun ta zazzage shi ba tana cikin gidansa, sai dai duk sanda ya ta'ba jikinta ko ya cire mata dankwali sai ta yini tana share hawayen takaici wanda ya ajiye ta ma bai ta'ba ri'ke mata hannu ba amma shi kuwa har ya samu sararin rungumeta yana tatta'ba wasu abubuwa na jikinta. Da 'karamar wayarsa yake haske falon ya hange ta zaune kamar kace kyatt! ta ruga a guje! Ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah a cikin ranta da sauri ta je ta rungumeshi kawai sai ta fashe da kuka! tana sake matse shi a jikinta. Wani yanayi ya shiga amma bai bari yayi tasiri a tare dashi ba. yasa hannu ya cire ta daga jikinsa hanyar dakinsa ya nufa ba tare da ya ce mata uffan ba. A sanyaye ta je ta zauna tana kallon d'akin dake rufe don bayan shigarsa mukulli yasa ya kulle ba tare da ya tsaya ya saurareta ba. Kwanan 'kunci da 'bakin ciki tayi ido luhu-luhu! ta tashi don ba ta iya shiga kicin ba kwanciya tayi lamo kan kujera zazzabi na neman rufe ta. Tsayin kwanaki uku da dawowarsa uffan be ce mata ba, ko ta gaishe shi baya amsawa, fushi yake sosai! da ita. idan ya fita tun safe baya shigowa sai dare wajejen sha biyu. Sosai ta shiga damuwa matsananciya tun tana zazza'bi! sama-sama har ya kai ta 'kasa! ta dinga kwara amai, yana daki ya ji kakarinta! da sauri ya fito ya tarairaye ta bayan ta gama aman ya wanke mata baki ya kai ta kan kujera ya kwantar. Kicin ya shiga ya had'o mata shayi tea. da kyar ta iya shan rabin kofi ta koma ta kwanta tana lumshe idonta, gabad'aya yanzu ta daina sonsa tunda bashi da imani. Tsayin kwana uku yana kula da ita kafin ta warware sosai! sai aka koma 'yar gidan jiya, yana amsa gaisuwarta amma baya tsayawa suyi doguwar magana da juna ballantana ya ji damuwarta. Wannan abu yana mata ciwo sosai! cikin ranta sai nadamar auransa take. **** "Saliha jiya nayi mafarki da Shahida cikin wani yanayi mara dad'i." Baba Asabe ke wannan maganar lokacin da take d'ura man gyada a kwalba. Hankalinta na kan wayar dake hannunta Ta ce."Hum Baba Asabe kenan." Ta ce."Ko za ki yi mata magana ne da wayarki." Ta ce'' Baba raba ni da yarinyar nan don Allah na san dai mahaukacin nan ya fara cin ubanta." Ta ce." Saliha fata nagari lamiri, ba na jin dadin irin wannan maganganun da ki ke akan Shahida. Murmushi tayi kafin ta ce" Bari na tura mata text (sak'o) na san idan ta gani za ta bada amsa, tunda kin san dai idan an kira ta a waya ba lallai ne ta ji ba. Ta ce."To shikkenan Allah yasa mu ji alheri. Ba tare da ta bawa maganar muhimmanci ba ta amsa da "ameen" ***** _"Ke Shahida dama ba komai ne yasa na turo miki wannan text din ba. Baba Asabe ta dame ni wai lallai ta na so ta ji lafiyarki, saboda haka sai ki bata amsa."_ Wannan shine abinda Saliha ta rubuta. Tana hawaye take tura amsa kamar haka. _"Wallahi ina nan lafiya lou Saliha ki kwantar mata da hankali ki ce ina gaishe ta da kyau zan kuma zo ba da jimawa ba"_ Daga dakinsa ya fito ya ga tana kuka! sai tayi saurin share hawayen amma ba su daina zuba ba. Ya zo ya 'karbi wayar yana dubawa. Tausayi ta bashi ganin irin amsar da ta bayar, hakan ya sake tabbatar masa da cewa lallai zata ri'ke masa sirrin gidansa cikin ko wane hali. Bai nuna farin ciki a fuskarsa ba, sai ma yasa wayar cikin aljihunsa ya ci kunu sosai! ya zauna yana fuskantar ta. Zaman da yayi ta san DA WATA A 'KASA, sai ta sunkuyar da kanta tana neman sassauci gurin Allah. Ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji ya ce." Maigidana ya sake tura ni legos domin wani aiki! zan tafi yanzu don na kammala duk wasu shirye-shirye, saboda haka ina sake gargad'inki da kakkausar murya! ki kula da abinda zai 'bata masa rai! domin ya fi karfin komai a guri na, bayan haka kuma da kud'insa na aure ki, yana da iko dani da abinda na mallaka! duk abinda yake buk'ata kiyi masa, ki kula da kakarsa da kyau! wannan shine gargad'in da zanyi miki.'' Hawaye wani na bin wani ta ce." Don Allah kada kayi min haka, ka nema min alfarma a gurinsa ka tafi dani duk in da za kaje domin ina bukatarka a kusa dani, bayan haka kuma wannan mutumin bashi da hali mai kyau! farautata yake a duk sanda ya tura ka wani gari." Ya mi'ke tsaye! cikin fad'a ya ce" Sharri za kiyi masa? me zai yi dake? ina abin burgewa da sha'awa a jikinki da har zai farauce ki, to shikkenan misali a ce maganarki gaskiya ce, ni na amince ki bashi kanki a madadina domin bani da wata cikakkiyar lafiyar da zan kwanta dake, na fad'a miki wannan mutumin ya fi karfin komai a guri na, saboda haka na amince a duk lokacin da ya buk'aci wani abu a gurinki ciki kuwa harda kwanciya dake, to kada kiyi masa jayayya domin yin hakan na barazana da auranki, ki amince masa kai tsaye kuma ki sakar masa jiki sa'anan kiyi k'o'karin faranta masa, ki ji a ranki kamar kina tare dani, wannan shine abinda za kiyi ki faranta min rai. *WASA FARIN GIRKI!🥰* Ko ya zata kasance? ina fatan za ku biyo ni domin karanta cikakken labarin, don wannan sominta'bi ne, kada ku manta akwai labari a 'kasa jingim! don haka masoya kada ayi 'kasa a gwiwa gurin biyan kudi domin jin yanda za ta kasance. Ni ce taku a koda yaushe *BINTA UMAR ABBALE* MARUBIYAR *1-NANA KADIJA* *2-YARO DA KUDI* *3-GIMBIYA BALARABA* *4-BABBAN YARO* *5-MASHAHURI* *6-LADIDI KWADAGA* *7-RUWAN DARE* *8-SADAUKI OMAR* *9-NIDA YAYA SADAM* *10-YAR BANGAR SIYASA* *11-DA WATA A KASA* *12-MADADI* *13-KWARYA TABI KWARYA* *14- GA IRINTA NAN* *15-MATSALARMU A YAU* *16-GOJE* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *ABACHE POULTRY FARM*🐓🐓🐓 *Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.* *08069459550* *08039451082* 57&58 A tsorace take kallonsa a lokacin da yake 'kokarin zuwa gurin da take tsaye. Cikin wata irin tafiyar isa da ta'kama! ya tsaya daf da ita hucin numfashinsa na dukan fuskarta. hannu ya sa cikin aljihu. kafin yasa d'aya hannun ya rungumota jikinsa! rikon tsauri! yayi mata da hannu d'aya yana sumbatar gefen fuskarta. Wani irin hauka da buge-buge! ta shiga yi duk domin ta 'kwaci kanta daga hannunsa! ta samu gefen kafad'arsa ta gartsa masa cizo! wanda yayi sanadiyar sakinta, sai ta matsa gefe tana mayar da numfashi tare da wani irin kuka! mai ciwo! jikinta na kyarma! tsigar jikinta gabad'aya ta tashi. Kallonta yake da idanuwan da suka sanja launi! ta zabga masa muguwar harara! cikin tsananin jin ciwo da takaicin abinda yayi mata ta ce." Wallahi ka ji kunya! ashe dama baka da kirki ko?" Ya tsira mata rikitattun idanuwansa dake cike da tsantsar fitina ta shekara da shekaru! gabad'aya yarinyar ta gama tayar masa da hankali. Ta je ta rarumi gwangwanin turare a kan madubi ta jefa masa tana kuka ta ce." Sai Allah ya saka min abinda kayi min, kuma sai na fad'awa mijina." Ya 'bata rai! kafin ya bud'e muryarsa sosai ya ce" Kafin ki fad'a masa ni zan riga ki, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka ki fice min daga daki" Da k'arfi ya k'arasa maganar yana nuna mata hanyar fita da hannunsa. Ta sake d'aukar wani gwangwanin ta je fa masa wanda ya sauka a goshinsa, tana zubar da hawaye ta ce" Ban yafe ba daka ta'ba ni." yanda ta ke rawar jiki da yanda take kuka har cikin ranta ya tabbatar masa da cewa ta ji ciwon abinda ya yi. Sai ya mi'ke da azama ya nufe ta, ta zabura! a guje tayi hanyar fita, garin kici-kicin bud'e kofar ta zame ta fad'i a gurin, rintse idonta tayi ganinsa a tsaye a kanta ya yi mata rumfa. Ta rufe fuskarta da tafin hannunta "Don Allah kada ke ta min haddi, ka dubi darajar aure kada ka sake ta'ba ni." tafad'a jikinta na wani irin rawa. Hannu biyu yasa ya d'ago ta ta mi'ke tsaye, ya tsirawa fuskarta ido, hawaye sai tsare suke a saman fuskar, harshe yasa yana tsotse hawayen, gabad'aya k'afafunta suka kasa d'aukarta, sai k'o'karin zubewa take a gurin, yana tallafota. Yanzu ma haukan ta sake yi masa tasa dukkanin 'karfinta ta dinga dukansa a k'irji har sai da ya saketa, ta zube a gurin tana wani irin kuka mai cin rai! Tayi tur! da wannan rayuwa da take. tayi Allah wadai da ita. Ya tsuguna gabanta tare da k'okarin daidaita yanayinsa ya ce." Ko na kwanta dake mijinki babu abinda zai ce, saboda iko na ne, ke kuma baki da wata daraja! sannan na ji kina maganar aure! to ki daina daukar wannan auran naku da mutunci, domin duk ina da labarin yanda akayi shi, da kud'i na aka fansheki a gurin mahaifinki, saboda haka ina da iko da damar nayi duk abinda nakeso dake. Wani irin kallo take masa bakinta ya mutu murus! gabad'aya ta rasa a wane mizani za ta ajiye maganarsa. Ganin tayi sanyi ta gagara magantuwa yasa ya mi'ke tsaye, anan ne ta girmansa ya bayyana sosai! ya tashi, saboda yanayin kayan dake jikinsa masu kwanciya a jiki ne, wannan dalilin yasa girmansa fitowa, gaskiya ta tsorata! da yanayin, sai tayi gaggawar d'auke idonta tana kiran sunan Allah a zuciyarta, tunda ta ke, bata ta'ba ganin girman namiji irin haka ba sai akan wannan mutumin da yake kokarin keta mata alfarma. "Tashi ki fitar min a daki.'' Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta, da sauri ta tashi har dankwalin kanta yana fad'uwa, anan ne ya ga tarin sumar kanta, ya sake shiga rud'ani, domin a rayuwarsa yana masifar son mace mai gashi, kawar da kansa yayi daga barin kallonta ya nuna mata hanyar fita da fadin." Yanzu nan zan kira mijin ki na sheda masa irin zagi da cin mutumcin da ki kayi min." Ya fadi maganar ne yanda za taji. Muguwar harara! ta buga masa kafin ta ja dogon tsaki! ta fita ta barshi a tsaye da kwantaccen murmushi a fuskarsa. Jiki a mace ya nemi guri ya zauna tare da dafe kansa, gabad'aya jikinsa ya rikirkice sha'awa ta shekara da shekaru ta taso masa, bai san ya zai yi ba a halin yanzu. Yinin kuka da damuwa tayi, duk ta tsargi kanta da kanta, sa'i da lokaci idan ta tuna al'amarin sai gabanta yayi ta fad'uwa, adduar kariya kawai ta lazumta domin ita kad'ai ce magani a gare ta. Wajejan goma da rabi na dare ya turo mata text cewa ta kiyayi 'bacin ransa idan ya dawo domin ya ji labarin abinda tayi wa maigidansa saboda haka tayi gaggawar zuwa ta bashi hakuri. Amsa ta bashi kamar haka; "Da kasan abinda ya faru a tsakanina dashi ba zaka fad'i haka ba maigidanka mutumin banza ne don haka ni ba zan bashi hakuri ba. Sai ya bata amsa da cewa; Ashe kuwa auranki yana gargada domin kuwa mutukar ba ki je kin bashi hakuri ba wallahi zan iya sakin ki." Jikinta yayi sanyi jin abinda ya ce. sai tayi shuru tana tunanin yanda za ayi ta je ta bashi hakuri bayan tasan shine mara gaskiya. Ya sake turo mata da wani sakon, cewa; "Lallai kada ta tsallake umarninsa a daran nan taje ta bashi hakuri. Agogo ta duba sha d'aya saura na dare, ya za'ayi ta iya fita a wannan daran. gaskiya sai dai da safe, shima don ba yanda za tayi ne. Yau cikin hijabi har 'kasa ta shirya jikinta, babu walwala a tare da ita nufi cikin gidan. Zaune a falo ta same shi kan wani keke irin na motsa jiki, yana sanye da singileti da wando iya gwiwa, cigaba yayi da motsa jikinsa ba tare da ya kalle ta ba. Tsugunawa tayi a gefansa da fadin." Ina kwana?" shuru yayi be amsa ba ya cigaba da abinda yake gabansa. "Don Allah kayi hakuri." Tafada cikin yanayin maganarta, gabadaya duk tayi sanyi ta fara nadamar wannan auran. Ya cire 'karamin towel din dake rataye a wuyansa. fuskarsa ya goge! kawai ya jefa mata towel din a jiki. Sai ta bi towel din da kallo tana mamakin abinda yayi. kallonsa tayi. suka had'a ido sai tayi saurin kawar da fuskarta. Ya tashi daga kan keken ya nufi gurin cin abinci ba tare da ya ce mata komai ba. Ganin haka sai ta ajiye masa towel din ta kama hanyar fita tana neman tsari dashi. Sunanta ya kira tana daf da fita. Ta juyo tana kallonsa fuskarta sam! babu fara'a. "Zo ki zuba min abinci" hankalinsa na kan wayarsa yayi maganar. Girgiza kanta tayi ta koma da baya domin bin umarinsa. Ta had'a masa komai ta ajiye a gabansa kafin ta ce." Zan iya tafiya?" Kansa ya girgiza alamun A'a. sai ta tsaya tana kallonsa da jiran umarni na gaba. Sai da ya mula tukkuna ya ajiye wayar hannunsa kafin ya kalle ta a sakarce ya ce." Kinyi kyau cikin hijabi." Tayi shuru dai ba tace uffan ba. Gabadaya girmansa ya zube a idonta. Ya ce'' Na ga kina ta wani rufe-rufe me ki ke b'oyewa ne?" Ta ce." Babu komai." Girgiza kansa yayi ya ce."Ban yarda ba gaskiya, ba zaki fita ba sai kin cire wannan hijabin na duba ki." Taji wani irin fad'uwar gaba! ta kalle shi idonsa k'ur! a kanta kamar tsohon maye! Ta ce" Shigowata ban kai minti goma ba kuma iyakata nan falon me kake tunanin zan d'auka?" Ya daga kafad'a da fad'in." Ni dai ban yarda ba saboda haka ki cire idan kuma kinyi gardama to zan cire miki da kaina. Cikin rawar murya ta ce." Kai fa uba ne, ka haifa kasan mai kyau da mara kyau, yanzu idan akayi wa 'yarka abinda kake min za ka ji dad'i?" "Ba zan ji dadi ba gaskiya" Serious ya fadi maganar. Ta ce." To mai yasa ka keyi min haka?" Shuru yayi be ce komai ba illah kofin shayi da ya d'auka yana kur'ba! Ta ce" Zan iya tafiya?" Ya ta'be baki "A'a nifa har yanzu ban yarda dake ba, mutukar zaki shigo nan to ki dinga sa mayafi wannan hijabin akwai munafurci a ciki. Cike da takaici da mugun haushinsa ta ce." Ba hali na bane sata, kuma ba zan fara anan ba, don haka ka daina d'aukar alhakina. Bagarar da maganar yayi ya cigaba da kur'bar shayinsa. Yanda ya ke wulakantata hakan yana yi mata ciwo mutu'ka! sai kawai ta kama hanyar fita a karo na biyu ya dakatar da ita da fadin." Har yanzu ban baki izinin fita ba don haka dawo ki tsaya." Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta koma da baya ta tsaya tana facing d'in shi, ya 'kura mata mayunwatan idanuwansa masu je fata cikin tashin hankali. Sai da ya gama karyawa tsaf! sannan ya tashi ya fito daga tsakanin kujerun ya nufi gurin da take tsaye. Ta ji fad'uwar gaba sosai! amma ba ta karaya ba, domin kuwa tasan duk shaid'ancin mutum bai fi karfin addu'a ba, tana da tabbacin cewa sai ta samu rinjaye a kansa. Daf da ita ya tsaya yana lumshe mata shu'uman idanuwansa. Ta kawar da fuskarta tana cigaba da nanata addu'ar neman rinjaye a bakinta. Ya sanya hannu da nufin cire hijabin jikinta. Ba tare da jin nauyi ba ta buge hannunsa da karfin gaske! bahaushe ya ce ." Idan babba ya zubar da girmansa yaro zai iya hawa kai ya tattaka. Ya dube ta da fad'in" Ba ki ji nauyin abinda ki kayi ba?" Zum'bura bakinta tayi tana d'an ture shi da 'kokarin so ta fita daga tsakaninsa domin ya babbake gurin yayi mata rumfa. Ya sake kama 'kasan hijab din a karo na biyu, sai ta sake wancakalar da hannunsa, ta tsinci kanta da nuna shi da yatsa da fadin" Wallahi zan baka mamaki yanzu nan!" cikin zafin zuciya ta fad'i maganar jikinta na wani irin karkarwa! Bai wani tsorata ba, sai ma sake matse ta da yayi jikin bango (garu) ya tallafo fuskarta da hannunsa d'aya, aikuwa karan hancinsa dake daf da bakinta ta gartsawa cizo! tana nema ta gutsire masa saman hanci! babu shiri ya matsa gefe yana shafa gurin da ta cije shi wanda yayi sheda tare da rurucewa! Zazzafar harara! ta buga masa kafin ta ja masa dogon tsaki! tana 'kun'kuni! ta wuce ta bar shi a tsaye a gurin yana bin ta da kallo har ta bud'e 'kofa ta fita. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Ga hanyar da za a biya kudin littafin....Normal group #500 posting sau daya a rana, Vip group 1k posting sau biyu a rana. account number.... 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp da wannan lambar.07084653262....Mutanan Nijar za ku tura dala dari. Vip jakka daya, za a turo mini ta WhatsApp. Allah ya yassare.* 55&56 A nutse ta d'an tsaya a jikin daya daga cikin kujerun cin abincin, amma bata yarda ta kalleshi ba, kanta yana 'kasa, sai dai a jikinta ta ji yana kallonta. gabanta ya dinga fad'uwa tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! 'kadaicewarsu, a falon su biyu yana nufin abubuwa da yawa, saboda haka sai tayi ta maza! ta d'ago kanta ilai kuwa sai ta ritsa shi ya zuba mata ido wanda har ya fara sanja kala, ya 'kan'kance ya kuma yi ja! ta sake shiga rud'ani mara misaltuwa! cikin yanayin maganarta ta ce." Yalla'bai ko kana bukatar wani abu ne?" Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nuna mata tarin abincin dake shirye a teburin alama yayi mata wai ta had'a masa abin kari. Cikin rashin kuzari ta fara abinda ya umarce ta, gurin tsiyaya shayi (tea) ya zubo mata a hannu saboda gabad'aya ta kasa nutsuwa sakamakon kallon kurillan da yake mata. Yarfe hannun tayi, tana d'an ya mutse fuska! babu zato babu tsammami ta ji ya kama hannun yana dubawa! da saurin gaske ta k'wace hannunta tana d'an harararsa, gefe guda kuma k'afafunta sai rawa suke domin ba 'karamin tsorata tayi da abinda yayi ba. "Sannu.'' a hankali ya furta duk da ya san ba lallai ne ta ji ba. Ba tare da tace masa komai ba, ta juya da sauri ta bar gurin. kallo ya bita dashi yana ayyana abubuwa da yawa a tare da ita. Cikin mutuwar jiki da faduwar gaba ta isa sashenta, ta zube kan kujera tare da dafe goshinta. Sam 'kunar dake hannunta bata dameta ba akan abinda ya faru a tsakaninsu, shin wai mai yake shirin faruwa ne? gabad'aya mutumin bai kwanta mata a rai ba, duba da irin mugun kallon 'kurrila da yake mata, bayan haka kuma menene hujjarsa na ri'ke mata hannu a matsayinsa na babba mai hankali ai ya san hakan ba daidai bane, tunda yafi kowa sanin matsayinta a gidan, matar aure ce kuma matar yaronsa. Gaskiya al'amarin ya sanya ta cikin rud'ani haka ta yini tana tunane-tunane! Wajajen tara na dare text ya shigo wayarta, da yake tana samun chaji a can cikin gidan, tunda gurinta babu wuta haka take zama cikin duhu sai hasken wannan fitilar da ya kawo mata ranar da suka zo gidan. Farin ciki ya cika mata zuciya ganin mijin nata ne ya turo mata sa'kon, cikin rawar hannu ta bud'e domin karantawa! Hawaye ne suke 'kwace mata ganin abinda yake rubuce. _"Ba zan dawo jibi ba, saboda maigidana ya umarce ni na zauna tsayin sati uku na kula masa da wasu harkokinsa ."_ Tana kuka ta rubuta masa amsa kamar haka. _Don Allah ka dawo wallahi ina cikin matsala da kewarka akwai abubuwan da suke shirin faruwa."_ Ya dawo mata da amsa kamar haka. _"Maigida na ya wuce komai a guri na, ba zan iya yin jayayya dashi ba saboda haka kiyi hakuri kawai"_ Kasa bashi amsa tayi sai uban kukan da take shirga! wai shin ita ya za tayi ne? wannan lamari da faru ya fara sanya ta cikin shakku da fargabar zama a gidan. Kwana tayi cikin zullumi da tunani da kuma rashin madafa, amma tasa a ranta cewa Allah shine madogara a gare ta. Washe gari ta shirya tsaf cikin doguwar riga ja mai adon duwatsu tayi kyau sosai sai dai rigar ta d'an matseta daga 'kasa kasancewarta mai cikakken 'kugu, koda ta ga haka sai tayi tunanin cire rigar ta sanja wata sai dai duk kayanta sunyi daud'a wanki suke bukata gashi har yanzu ba ta ga Sulen ba ballanantana ta tambayeshi sabulu. hakanan ta yafa mayafin rigar ta nufi cikin gidan domin gaishe da Hajiya kamar ko da yaushe. Sai dai yau ma shuru babu Hajiyan babu Shukura! cikin zuciyarta take tunanin ina suka tafi, can taji motsi a hanyar kicin ta juya da sauri, sai tayi ido hud'u da Sule ya fito daga kicin din da wani abu a wuyansa, hannunsa rike da babban tire ya shiryo abincin akai. Gaisawa sukayi take tambayarsa masu gidan, nan yake sheda mata cewa sun je biki za suyi kwana uku ko hud'u kafin su dawo." "Eh hakane fa, ta manta shaf ta ji suna maganar biki wanda za suyi a cikin gari. 'Dan tsayawa tayi har ya gama shirya teburin cin abincin, sannan ta kalleshi tare da sheda masa bukatarta. Ya ce." Babu damuwa insha Allah zan kawo miki idan anjima. Tana shirin magana suka hangi sakkowarsa daga sama. yau ma yana cikin kayan bacci masu taushi masu kama dana sanyi domin har da hula. waya ce a kunnansa da alama da wani yake magana. Koda ya sauko kai tsaye gurin cin abincin ya nufa. Sule ya bishi gurin da saurin gaske. Da har tayi niyyar fita sai kuma wata zuciyar ta hana ta domin tana gudun 'bacin ran mijinta tana kuma so ta zauna lafiya dashi, wannan dalilin ne ya sa ta tsaya amma har yanzu tana jin haushin abinda yayi mata jiya. Sule ya risina tare da mi'ka gaisuwarsa, ya amsa hankalinsa na kan wayar dake hannunsa. Sule ya fara 'kokarin zuba masa abinci, sai ya dakatar dashi tare da bashi umarnin tafiya. Ya bi umarni cikin sauri ya kama hanya ya fita. Ta kai minti biyar a tsaye tana dawurwura! kafin ta yanke shawarar zuwa ta gaishe shi. Duk abinda take yana kallonta ta gefen idonsa. A nutse ta tsuguna da fadin." Yallabai ina kwana ka tashi lafiya?" Ya d'an saci kallonta da gefen ido kafin ya amsa a ciki, wanda yake da tabbacin ba lallai ne ta ji ba. Itama ganin bakinsa ya motsa yasa ta mi'ke tsaye zata tafi. Kawai ta ji sunanta rad'au! a bakinsa. Ta ja ta tsaya tana kallonsa gabanta na bugawa. Da hannu ya nuna mata gurin zama. ma'ana ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake gurin. Kasa zama tayi, domin tana ganin kamar hakan bai dace ba. Ya bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce." Ki zauna nace ko bana son gardama." Ganin yayi maganar da yanayi na bacin rai! yasa taji wani iri kwata-kwata ba taso ta 'bata masa rai! Ido cike da ruwan hawaye ta ce" Kamar hakan bai dace ba. "Ni na baki umarni." yafad'a yana tsatstsare ta ido! A sanyaye ta ja kujera ta zauna amma ta gagara kallonsa, bayan kwarjinsa sai mugun 'kamshin turaransa da duk ya cika gurin. sai jikinta ya sake mutuwa ta dinga wasa da hannayenta. Muryarsa ya bud'e sosai tare da kiran sunanta. Ta amsa tana d'an kallonsa, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraran abinda zai biyo ba. Ya ce." Ya hannun naki?" "Da sauki." tafada a ta'kaice! Gurin yayi shuru na minti uku. d'ago kanta tayi ta ritsa shi ya 'kura mata ido wannan karon ma idonsa ya sauya kala yayi ja! tare da 'kan'kancewa! sosai ta shiga rud'ani! sam bata 'kaunar wannan kallon da yake mata. Ta tsinkayi maganarsa yana cewa; 'Kin san kina da kyau kuwa ?" Shuru tayi ba ta iya magana ba, sai mugun mamaki! da yake kasheta. Ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! kafin ya sake bude muryarsa yanda za ta ji ya ce." Zuba min abinci." A hankali ta fara zuba masa abincin tana Allah wadai da wannan hali nasa. shi kuma sai kallon hannunta yake, wannan dalilin yasa duk ta daburce amma dai yau ba ta zubar da komai ba. Bayan ta had'a masa sai ta kalleshi, as'usul ita d'in dai yake kallo! 'bata fuskarta tayi kafin ta ce." Zan tafi Yallabai. Kai tsaye ya ce." Zauna ki ta ya ni ci." Ta kalleshi da tsantsar mamaki a tare da ita lallai ma wannan mutumin da alama bashi da kamun kai Fita tayi daga tsakanin kujerun. Ya kira sunanta, ta kalle shi ba tare data amsa ba. Babu walwala a tattare dashi ya ce." Hau sama ki gyara min gado na. Taji wani irin miyau! ya tsinke a bakinta tsabar tashin hankali. Baki na rawa ta ce." Yallabai kamar hakan bai dace ba, kana yin wasu abubuwan da basu cancanta da kai ba. Ya ce" Na san ke matar aure ce, kuma matar yaro na, to ina so ki sani; shi mijin naki a 'karkashi na yake, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka kada ki sake yi min jayyaya akan umarni na. Jikinta yayi sanyi tana sake tuno jan kunnen da mijin nata yake mata akansa. Abincinsa ya fara ci ba tare da ya sake kallonta ba. Ta saci kallonsa ta gefen ido, sai ta ga babu walwala a fuskarsa. A hankali ta kama hanyar matattakalar bene tana addu'ar neman tsari a zuciyarta. Tsaruwar d'akin sam bashi ne a gabanta ba, babban burinta ta gama abinda take yi ta fita. Tana tsaka da gyara shimfid'ar gadon ya shigo dakin. Gabanta ya tsananta fad'uwa! duk sai ta rasa abinda za tayi, ta dinga sauri tana jere filo sam ta'ki kallonsa sai sanda ta ji kamar yana murzawa 'kofar mukulli (key) sannan ta zabura! ta kalle shi, lokacin ya rufe 'kofar ya nufi inda take.