KULSUM 2 Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com SADAUKARWA SADAUKARWAR littafin Kulsum bakidaya taki ce A'ISHAH MAHMOUD SHAFI'I (MARUBUCIYAR ZANEN DUTSE, BAYAN NA MUTU, KOMAI NISAN DARE da WAYE SHI?). Sabida gudummuwar ki a dukkan al'amurana. Allah ya bar zumunci a tsakaninmu har 'ya'ya da jikoki. Yayar ki, TAKORI 7/11/2020 GODIYA Godiya ta musamman ga Nura Sada Nasimat sabida jimirin sa na bin rubutuna kafin bugawa da bada shawarwari. Allah ya raya mana Yusuf Nura Sada rayuwa mai albarka. JINJINA Ga daukacin mambobin TAKORI'S ONLINE FORUM, littafin Kulsum ya jinjina muku, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ba tare da izni na ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. KULSUM-2 Tunda Kusulmu ta ke a rayuwarta ba ta taba tafiya mai dadi da ni'imar wannan ba. A.C na buga ta ko ta ina, wanda ya cakude da kamshin (car fresh) wato turaren mota mai dadin kamshi, ya bada wata irin iska mai dadin shaqa a cikin motar. Ta taba zuwa Gombe ita da surukar ta Hajiya Rakiya, amma ko daya lafiyar injin motocin da yanayinsu ba iri daya ba ne. Wannan mota ce ta zamani lafiyayya ta mukami sosai. Ba su isa Birnin Tarayyah ba (garin da Haj. Nasara take) sai yamma lis, kai tsaye direban ya dauke hanya ya nufi kebantacciyar unguwar nan (Brains&Hammers). Kusulmu ta makure a jikin kofa cikin matukar gajiya wanda zaman mota fiye da awanni biyar ya haddasa mata, domin tunda suka taho banda gidan mai basu tsaya a ko'ina ba, sai kallon ikon Allah ta ke yi na abubuwan mamaki cikin babban Birnin Tarayyar Najeriya. Dogayen gine-gine na zamani a ko'ina da motoci kala-kala bisa titina wadanda bata san da irin su a duniyar subhana ba. Ga gadoji na sama da kasa (fly over) wadanda bata taba gani ba. Don haka ta saki ido, baki da hanci duka tana shan kallo abinta. Ko kwakkwaran motsi bata yi kada a wuce wani abun bata gani ba. Lokacin da direban ya tsaida motar a kofar gidan Hajiya Nasara daga farkon unguwar kasa amincewa idanunta ta yi cewa, wadannan gidaje ne, gidaje irin wadanda mutane suke rayuwa a ciki. Ita dai ko a fina-finai na hausa da suke kallo ita da Batulu ba ta taba cin karo da gidaje masu kyau, tsari da kayatuwar na unguwar su Hajiya Nasara ba. Ga shi gidan nata bai cika girma ba (pent house) kamar yadda turawa ke kiran sa. Mai aikin Hajiyar wata kabila ce budurwa 'yar kabilar Igala, ta karbi jakar hannunsu su duka, tare da russunawa ta yi wa Hajiya Nasara barka da zuwa cikin harshen nasara, ta dubi Kulsumu tace "welcome Ma" Kulsumu ta yi mata murmushi. Don ta gane barka da zuwa take mata. Hajiya tace da ita cikin turanci. Serah, kai ma ya ta jakar ta dakin can na kusa da na Nasma. Ki tabbatar ta ci abinci ta yi wanka ta huta. In ce ko dakin a gyare yake? Ban jima da gyara shi ba tsaf, Ajiya. In ji Serah. Hajiya Nasara ta dubi Kusulmu wadda ke tsaye tana zare ido kamar tsohon da yayi wa sarki karya, tsoron Ubangiji duk ya cika ta, tana mamakin yadda aka yi Goggo ta ke da alaka da Hajiya Nasara, don dai ita tun tashinta ba ta san a duniya akwai gidaje irin wadannan ba. Iyakar arziki da daula a wajen kowa a garinsu to ya kare ne gidan Sarkin Gaya. Ba don Goggo ta sha ba ta labarin Nasaran ba kafin ta ganta, kuma ta dade da sanin ko wacece ita a wurin Goggo, za ta iya rantsewa batan kai Nasara ta yi ta zo gidan su. Serah ta kama hannunta ganin ta tsaya kikam, sai aikin zare ido ta ke yi, ta ce, Lets go to your room ka yi wanka kafin in kawo abinci, ka ji? Cikin ran ta tace "ni mace ce ba namiji ba, ka ji min mata da wata hausar ta marar fasali". Dakin da ta kai ta matsakaici ne, ga lafiyayyen gado ya sha shimfida mai taushi da duvet shimfide iya rabinsa, ga sif ta jikin bango, madubin kwalliya da stool a jikinshi. Fararen labulaye zagaye da dakin da farin tiles shimfide a koina. Kauyancin ta bai tuke a koina ba saida ta shiga toilet din da Serah ta nuna mata wanda ke manne da dakin don ta yi wanka. Ta bata lokaci ba abin da ta ke yi sai kallo da kissime-kissime, ta kasa amfani da komai na bandakin. Serah da ta shigo don kawo mata abinci ta jima tana jiran ta har ta kai da bin ta bandakin don shirun ya yi yawa. Dan kwankwasawa ta yi, sai Kulsumu kamar jiranta ta ke, ta ce mata cikin damuwa, “Ki zo ki nuna min yadda zan yi wanka, na kasa kunna famfon, idan na kunna famfon sama ne yake zubowa (shower)” Serah ta ce, “Ba dai har yanzu ba ka yi wankan ba?” Hararar ta Kulsumu ta yi ta gefen idanu, ta ce, “Na fada miki, na rasa yadda zan yi in tari ruwa ma”. Serah ta fahimci ‘yar kauye Hajiya ta kawo musu, amma a fuska ba za ka ce tana da kauyancin ba. Gata nan fes da ita ruwan 'yan birni. Nan dai ta nuna mata komai har yadda ake (flushing), sannan ta fita, ta ce in ta gama ga abinci nan ta ajiye mata. Kulsumu na wanka cikin (bathtube) dumin ruwan yana ratsa fatar jikinta. Tana lumshe ‘yan idanunta cike da tunani da taraddadin sabuwar rayuwar da ta samu kanta a ciki. Ba ta san cewa akwai mutane masu falalar rayuwa irin haka ba. Gabadaya exposure dinta ya tsaya a fadin kauyen Gaya ne da kauyen ‘Yanleman. Tana rokon Allah ya ba ta ikon karfafa imaninta, ibadarSa da bautarSa, kada canjin rayuwa ya raunata mata su. Domin ta fahimci rayuwar da ta shigo ta yi mugun sabawa da tata, ga dukkan alamu jin dadin da ke cikinta har ya so ya yi yawa. Da daddare bayan ta idar da sallar isha’i Hajiya Nasara ta shigo ta same ta. “Ina fatan kin yi sallah Kulsum, kuma babu wata matsala?” Ta fada tana mai zaunawa a gefen gadon dakin. Kulsumu da ke zaune bisa sallaya tana saka da warwara ita da zuciyar ta bayan idar da sallahrta ta amsa a sanyaye da cewa, “Eh, na yi sallah Hajiya, kuma babu matsala”. A ranta tana mai jinjina saukin kai irin na Hajiya Nasara. Ko kusa ba ta yi tsammanin cikin daular da ta ke ciki ba ke nan a ganin da ta yi mata na farko har ta iya ta yi kwanaki a gidansu na kasa, babu busa ba hura hanci ba daga hannu. Hajiya Nasara ta ce, “To saurara, magana za mu yi mai muhimmanci”. Ta tattara dukkan hankalinta ta mika wa Hajiya Nasara, ita kuma ba tare da bata lokaci ba ta soma yi mata bayanin da ta ke son yi mata. “Kamar yadda ki ka sani sunana Nasara, mijina Alhaji Muhammad Bello haifaffen garin Kano ne, da mahaifiyata mai rasuwa Yakumbo Sa’a da Goggonki uwa daya uba daya suke. An yi min aure tun ina da shekaru goma sha biyar a jihar Kano, na haifi Da na na fari ina da shekaru goma sha bakwai. Ina da shekaru ashirin na haifi mai bi masa Sakinah. Daga nan na dauki shekaru bakwai kafin Nasma ta biyo baya. Bayan haihuwar Nasma na samu matsalar Fibroid a mahaifata, wadda ta yi sanadiyyar cire min mahaifar bakidaya. Maigidana Alhaji Muhd. Bello tsohon ma’aikacin NNPC ne. Inda yake cikin staff dinsu a babbar headquater dinsu da ke birnin London. Mun dade a birnin London don a can na haifi Sakeenah da Nasma, babbansu kawai aka haifa a garin Kano inda muka fara zama, kafin maigidana ya samu aiki da Nigeria National Petroleum Corporation da aka fi sani da (NNPC). ‘Ya’yana sune sirrina Kulsum, akwai shakuwa da fahimta tsakanina da su, su ne abokan shawarata. Dangi babu duka sun kare, zan iya cewa Goggonki kawai ta rage min a dangin mahaifiyata. A yau na dauko ki na kara cikin ‘ya’ya na, buri na ki yi karatun da zai amfani rayuwarki. Kulsum ki tsaya ki yi karatu, bakin cikin Da namiji ba naki ba ne a wannan gabar ta rayuwar ki sabida kwata-kwata ba ki kai munzalin da za a kira ki mace ba. Ki kwantar da hankalin ki mu yi zaman mu cikin aminci. Ki zauna da kowa da za ki hadu da shi cikin amana da zuciya daya. Ni kuma zan tsaya in ga cewa kin samu ilimi mai inganci kamar sauran ‘ya’ya na. Allah ya hada mu da dukkan alkhairin da ke tare da junan mu”. Cikin sanyin murya Kulsumu ta amsa da, “Ameen”. Shiru-shiru tana jira Hajiyar ta yi mata zancen lalurar ta, amma ta ji ba ta yi zancen ba. Ta shiga tunanin to ko dai Goggo ba ta fadi mata ba ne? Don haka cikin sanyin jiki ta ce, “Hajiya ina da lalura, ko dai Goggo ba ta gaya miki ba ne?” Murmushi ta yi tana danna wayar hannunta ba tare da ta dago ba. Ta ce, “Ta gaya min, kuma insha Allahu za ki warke. Waraka ta har abada, diyata Sakeenah babbar likita ce, likitar mata, za ta duba ki da yardar Allah da zarar sun dawo Nigeria ita da mijinta nan da sati biyu. Da yardar Allah karshen wannan matsalar taki ta zo, na so daukar mahaifiyarki Sugrah ne a wancan lokacin tun tana kamar ki, Baffanku ya hana ni, ya ce aure zai yi mata, shi ya sa yanzu na dage su ba ni ke. Allah ya ji kanta da rahama”. A fili Kulsumu ta ce, “Ameen”. Shauki da kewar mahaifiyar da ba ta taba gani ba ya kamata. Cikin kowacce sallar farillar ta ba ta manta yi mata addu’a. Kafin su taho Baffa ya sanar da Malam Hadi maganar tafiyar Kulsumu tare da Hajiya Nasara, babu musu ya amince tun ba da ya ji an ce Kulsumu karatu za ta yi. Shi ma yana so Kulsumun ta samu sauyin rayuwa ko yaya ne, don ta cire wa kanta damuwar auran da bai je ko ina ba. Ta je ‘Yalleman sun yi sallama kafin su taho, amma ba ta kwana ba a ranar ta dawo, washegari kuma suka taho Abuja. Kulsumu ta juya ta kalli lallausan gadon da ya sha shimfida ta alfarma na wani lallausan bedsheet hade da duvet dinsa pink colour da ratsin light blue. Ta soma tunanin yadda za ta malala masa fitsari. Tausayin kanta ya kamata. Da gaske ita abar tausayi ce don matsalar fitsarin kwance babbar matsala ce kuma nakasa ce. Musamman ga diya mace. A lokacin Hajiya Nasara ta rigada ta bar dakin. Da sauri ta tashi ta bi ta dakinta, ta taddata zaune gefen gado tana waya, ga dukkan alamu da daya daga cikin ‘ya’yanta ta ke magana. Don haka ta tsaya a gefe har ta gama wayar tana kallon dakin da kyawunsa da tsarinsa ya zarta tunani. Sai da Hajiya Nasara ta ajiye waya ta dube ta da murmushi, “Ya aka yi ne Kulsum? Ina magana da rigimammen Yayan ku ‘Tawfeeq’ ne, wai shi ma aikinsa zai bari ya dawo gida, ba zai zauna shi kadai a UK ba, bai saba da kadaici ba. Ban da abin Taufeeq ai shi namiji ne, yana da abin yin sa kwakkwara, don me zai aje ya dawo inda bai da abun yi? Ga babanshi ma ya yi ritaya su taru duk su zauna a gida?” Kulsumu da ba fahimtar zancen da Hajiyar ke yi ta ke ba kanta a kasa cikin jin kunyar abin da zata ce, ta ce, “Kayan shimfida nake so”. Hajiya ta dan yi jim, kafin ta ce. “Ni ba zan barki ki kwana a kasa ba, kada ki yi ciwon baya, idan kin ji fitsarin ki ki narka abun ki, ki malala shi iya yadda ki ke so, gadonki ne, dakinki ne. Idan kin ga dama gobe ki gyara, idan kin so ki barshi ya yi ta zarni na ga kalar kazantar ki”. Kulsumu ta kai hannu ta rufe fuskarta tana dariya, sabida yadda Hajiyar ta yi maganar dole ya ba ka dariya, beauty point din ya lotsa ciki sosai. Ta ce, “Kai Hajiya! Balle ma ina gyarawa sosai, ba ki ji dakin Goggo sumul ba ya zarni ba?” Ta ce, “Oho miki! Ki je ki san yadda za ki yi. Kulsum mai amalala!” Sai ga Kulsumu na kyalkyala dariya, wadda ta taho tare da tausayin kai. Indeed sunanta ke nan a harshen Hausa (Mai amalala) a shekaru goma sha takwas ba kadan. Ina kuwa maza za su iya zama da ita, balle Turaki dan kwalisa? Zuciyar ta mai yawan so ga Turaki ta ci gaba da yi masa uzuri, uzurin da har abada ba ta jin za ta daina yi masa, duk kuwa da mummunan kullacin da zuciyarta ta yi masa. Zama da ita sai wadanda ta zame wa dole, irin iyayenta da kakannin ta da daidaikun mutane masu babbar zuciya irin Hajiya Nasara. Hajiya Nasara ta dube ta cike da jin tausayi da kuma jin dadin ganin ta fara sakin jiki da ita. Da ma haka ta ke so, ta saki jiki. Shi ya sa ta kawo raha, ta ce. “Kada ki damu, ke dai wasa nake miki, katifar ta ruwa ce (water mattress) ba abin da zai same ta. Da safe sai a yaye zanin gadon a sa shi a (washing machine) injin wanki a wanke”. Ta ce a sanyaye, “Ni da kaina zan wanke, babu wanda yake wanke min”. Ta juya za ta fita fuskarta a sake, zuciyarta ma a sake, wanda rashin nuna kyama da nuna kauna daga Hajiyar shi ne silar yayewar damuwar ta. Hajiyar ta bi ta da kallo cike da tausayi. Har ta kai bakin kofa za ta bude handle din ta tsinkayi muryar Hajiya Nasara. “Nasma na gaishe ki. Ta ce she can’t wait to see you in Abuja” Ta fadada murmushin fuskarta hadi da juyowa ta ce, “Gobe in ta kira ki ba ni mu gaisa”. Hajiya Nasara ta ce, “Insha Allahu. Mu kwana lafiya, kada ki manta da azkar yayin kwanciya barci, ungo wannan littafin azkar ne ki dinga karantawa safe da dare, za ki kasance cikin kariyar Ubangiji insha Allahu”. Hannu biyu ta sa ta karba ta yi mata sai da safe. Ji ta ke kamar mahaifiyarta ta dawo duniya. Da ta bar gidan Sarkin Gaya, ta dauka ba za ta kara samun mai son ta a duniya bayan kakanninta da mahaifinta ba irin Laraba mai aikin ta. Ta kara yarda da kalaman Hajiya Nasara inda ta ce, ‘duniyar Allah fadi gare ta’. Hajiya Nasara tun ba a je ko ina ba, ta fara cike wani babban gibi a rayuwar ta, wato gibin UWA, wanda kaka ba ta iya cike shi. Ta maye mata gurbin Uwa, mahaifiya. *** *** *** Satin Kulsumu uku kenan a gidan Hajiya Nasara, ta yi sumul da ita, ta murje ta yi haske, har wani irin glowing na musamman fatarta ke yi. Hankalinta ya kwanta ba ta da damuwa ko kankani. Hajiya Nasara ta fada mata sai nan da watanni uku za a fara daukar dalibai a makarantar da zata je. So ta ke ta yi medicine ba Nursing da ta kwallafa wa rai ba. Amma Kulsumu ta ce ita nan duniya Nursing kadai ta ke so. Yau ne Dr. Sakeenah diyar Hajiya Nasara da mijinta Engr. Farouq za su sauka Nigeria amma a garin Lagos za su sauka, can inda mijin Sakeenahr ya samu aiki a hukumar haraji ta kasa (FIRS) wato Federal Inland Revenue Service. Tare suka taho da Nasma, wadda ke karatu a jami’ar Nottingham, za ta yi hutun karshen shekara tare da iyayenta. Daga Lagos suka sako Nasma a jirgin Abuja, Hajiya Nasara ta tura direbansu Yusha'u tare da Kulsumu su taho da Nasma daga filin jirgi. Alhaji Muhammad Bello ya yi tafiya zuwa Port-hearcourt tun kafin zuwan Kulsumu Abuja. Satin ta daya a gidan ya dawo, shi ba mai yawan kula mutane bane kamar matar sa, amma duk da haka sosai ya yi mata barka da zuwa cikin family dinsa. Hajiya Nasara ta yi masa bayanin komai a kan Kulsumu, amma ta sakaya rashin lafiyar ta. Ta ce ta daukota ne kawai don ta yi karatu, in ta gama zata koma Gaya kamar yadda ta alqawartawa su Goggo. Kulsumu ta sha ganin hoton Nasma a wayar Hajiya, don haka ba ta sha wahalar gane ta a fili ba. Nasma za ta girme mata da a kalla shekaru hudu don kuwa shekarunta ashirin da biyu ne. Tana shekarar karshe a jami’a inda ta ke karantar accountancy. Ita ma Nasma ta gane Kulsumu don Hajiya Nasara ta sha tura mata hoton ta. Tana ganinta ta sakar mata murmushi tare da rike hannunta, ta ce. “It is nice meeting you Kulthum. Ganinki ya fi jin ki, you are really beautiful”. Murmushi Kulsumu ta yi, murmushin jin dadi irin wanda dan adam ke yi in an yabe shi, ta ce, “Barka da zuwa Aunty Nasma”. Ta karbi jakar hannunta daidai lokacin da Yusha'u ya zo ya dauki trolley dinta suka rankaya zuwa mota. *** *** *** Nasma ta fito kanta babu kallabi, gashi gare ta ba na wasa ba na fulanin usli, ta dunkule shi cikin hair bound ta nufi dakin mahaifiyar ta. Ita da Kulsumu ne a dakin, Hajiya na amsa waya a gefen gadonta yayin da Kulsumu ke tsaye jikin closet dinta tana jera mata kayanta da aka kawo daga wanki da guga, ta zauna gefen Hajiya Nasara wadda ta ajiye wayarta ta bata hankalinta. “Har kin gama cin abincin ne Nasma?” “Sai anjima zan ci Mum, Kulsum ta dinga kwana dakina mana, ni ban iya kwana ni kadai kin sani. A gidan Aunty Sakeenah ni da su Waleed (‘ya’yan Sakeenah) muke kwana”. Hajiya ta yi dan jim, kafin ta ce, “Kin fiya rigima Nasma, da girmanki ki ke wani tsoron kwana ke kadai? To ba za ta taya ki kwanan ba, ki koma gidan su Waleed din”. Nasma ta marairaice, “Don Allah Mum, at least ko na sati daya ne zuwa in saba da dakin, ya yi min girma”. Kulsumu kirjinta sai duka yake sabida fargabar amincewar Hajiya ta kwana daki daya da Nasma, what of idan ta yi mata fitsari? Nasma ma’abociyar gayu na karshe, duk wannan son da ta ke mata ta sani da zarar ta gane ita mai fitsari a kwance ce zai koma kyama. Abin farin cikinta sai Hajiya ta kori Nasma, ta ce ba ta amince Kulsumu ta taya ta kwanan ba. Ta yi shirin kwanciya ke nan za ta karanta azkar din dare ta kwanta, sai ga Nasma ta shigo buguzum-buguzum niki-niki rungume da duvet dinta, ta ce, “Kulsum mu kwana tare, ban iya kwana ni kadai Allah, duk yadda na yi kokari”. Ba tare da ta jira cewarta ba ta haye gadon ta dukunkune cikin duvet dinta. A wannan ranar yadda Kulsumu ta ga rana haka ta ga dare a zaune don tsoron kada ta kwanta barci ya dauke ta ta yi fitsari Nasma ta sani. Cikin matsanancin tashin hankali. Sai da Hajiya ta zo tashinta sallar asubahi ta ga Nasma na sharar barci akan gado, ita kuma Kulsumu na jingine jikin gadon tana gyangyadi tana farkawa. Tausayi ya yi mugun kamata, ta sakar wa Nasma duka a cinya, ba shiri ta zabura ta mike zaune. Hajiya ta ce, ta koma dakinta yanzun nan ba ta ganin Kulsumu a kasa ta kwana? Ta zo ta takura mata saboda tsoron ta na banza da wofi, me zai cinye ta in ta kwana ita kadai din? Kada ta kara zuwa ta takura mata. Hajiya Nasara zaune bisa stool a washegarin ranar, waya ta ke da ‘yarta Sakeenah da ke Lagos, ta gaya mata komai game da Kulsumu da halin da ta ke ciki na lalurar fitsarin kwance tun haihuwar ta. Sakeenah ta ce a sako mata Kulsumu a jirgi ta zo Lagos za ta duba ta na ‘yan kwanaki, amma za ta yi akalla wata biyu a hannunta. Hajiya Nasara ta ce, ba za ta iya barinta ta zo har Lagos ita kadai ba sabida ba wani wayewar kai ne da ita sosai ba, sai dai ta hado su da Nasma, amma ta lura Kulsumu ba ta son Nasma ta san lalurarta. Ita ma kuma ba ta son ta sani din, kowa yana da sirri a rayuwarsa. Sakeenah ta fahimta, ta ce da mahaifiyarta kada ta damu, ta sako ta a jirgi kawai, ita da kanta za ta je ta dauke ta. Insha Allah ba za ta bata ba. Da haka suka yi sallama. *** *** *** Tun a daren Hajiya Nasara ta yi wa Kulsumu bayanin tafiyarta Lagos gidan Dr. Sakeenah. Da farko Kulsumu ta dan ji tsoro na yadda za ta tafi har Ikko ita kadai, amma Hajiya Nasara ta kwantar mata da hankali, ta ce, insha Allah lafiya lau Sakeenah za ta dauke ta. Hakan kuwa aka yi. Washegarin ranar ya kama Asabar, tun karfe bakwai Kulsumu ta yi wanka ta shirya tsaf. Allah ya taimake ta yau ba ta yi fitsarin ba. Ta dau duk abin da za ta bukata da isassun kayan sanyawa ta saka a trolley din da Hajiya Nasara ta ba ta domin ta yi tafiyar da ita. Nasma ce ta kula da komai na sayen tikiti da sauransu, ba ta bar filin jirgin ba ita da Yusha'u sai da suka tabbatar jirgin da Kulsumu ta shiga na ARIK ya daga ya bar kasa. Ta sauka a filin saman Murtala Muhammad na garin Lagos da rana tsaka, misalin karfe biyu na rana. Sanye ta ke da doguwar rigar atamfa batik dinkin fitted gown da yalwataccen mayafi kalar atamfar, wato deep green, wannan ne karo na farko da ta hau jirgin sama a rayuwarta, kuma ta yi fama da fargaba da zullumi iri-iri, har Allah ya sauke su lafiya. Bayan fasinjoji kawai ta ke bi don ba ta san inda za ta nufa ba, har suka dangana da inda mutane ke haduwa da wadanda suka zo tarbarsu. Ba tun yau ba ta san ganinta mai rauni ne. Ba ta iya gane mutane daga nesa-nesa. Sannan ba ta san Dr. Sakeenah a fuska ba, don haka raunanan kwayar idanunta ke ragaita akan fuskokin mutane, ko Allah zai sa ta gane 'yar uwar ta Sakeenah. Ba ta yi aune ba ta ji an rungume ta daga bayan ta. Ta juya a tsorace don ganin wadda ta rungume tan. Kamanni da Nasma da yanayi da Hajiya Nasara, su suka sa ta gane ‘yar uwar ta Sakeenah a tashin farko daga kallo na farko da ta yi mata. Ta sake ta daga rungumar da ta yi mata ta kama hannayenta fuskarta fal murmushi, ta ce. “Barka da zuwa Kulsum, if I’m not mistaken” (idan ban yi kuskure ba). Sakeenah ta fada tana rike da hannayenta. Ba ta yi saurin yarda Sakeenah ba ce, sai da ta bude jakar hannunta ta zaro hoton da Hajiya Nasara ta ba ta, ta kalle shi ta kara kallon Sakeenah, tabbas ita din ce, sannan ta mayar mata da murmushin tare da gaisuwa irin ta malam Bahaushe ta hanyar russunawa. Sosai ta bai wa Sakeenah dariya da ta tsaya duba hoton nan. Ta hana ta durkuson ta dago ta, Sakeenah sanye ta ke da doguwar riga da veil dinta kirar Oman da farin gilashin idanu irin na likitoci. Ta kama hannun Kulsumu suka nufi motar da ta zo a ciki. Wani kyakkyawan mutum ma’abocin kamala Kulsumu ta tarar a mazaunin direba, wanda kallo daya ta yi masa ta ba shi matsayin mijin Sakeenah. Yara biyu ne a motar mace da namiji, macen ba ta fi shekaru hudu ba, namijin kuma zai yi shekaru shida, suna zaune a kujerar baya ta motar. Hannu ya mika ya bude wa Sakeenah kujerar gaban motar bayan ta sanya jakar Kulsumu a booth din motar, ta kuma bude mata kujerar baya ta shiga ta rufe. Bai bata lokaci ba ya ja motar suka bar harabar filin jirgin saman. Kulsumu ta gaida mijin Sakeenah da ke tuki. Ya amsa very respectful tare da ce mata, “Da fatan kin iso lafiya, ya ya ki ka baro su Nasma?” Ta ce, “Nasma na lafiya, tana gaishe ku”. Ya ce, “Madallah”. Daga haka bai kara magana ba sai shi da matarsa suke hirarsu jefi-jefi. Yaran na ta yi mata surutu har suka iso gidansu da ke a Victoria Island. Dr. Sakeenah ta kai mata jakarta dakin da ta ware mata, ta nuna mata toilet da ke ciki da sababbin bath kit. Kafin ta fito ta kawo mata abinci mai rai da motsi, jallof din macaroni ne wadda ta ji kayan lambu da naman kaza, sai farfesun kayan ciki da fruits a wani bowl na tangaran. Sai da ta sallaci azuhur ta sauya kayan jikinta, sannan ta zauna cin abincin. Har motsi ta ji kunnenta na yi sabida dadin girkin Dr. Sakeenah. Da ta kammala ta koma bisa gado ta kishingida tana hutawa, tunanin Goggo, Umma da Batulu ya zo mata. Sosai ta ke kewarsu a wannan lokacin. Dr. Sakeenah ta shigo dakin da sallama rike da hannun karamar ‘yarta Walida. Ta sakar mata murmushi ta ce, “Kulsum ya ya dai? Ina fatan babu wata matsala?” Murmushin ita ma ta mayar mata, a ranta ta ce, dukkansu kirki da son mutane kamar Hajiyarsu. “Ba wata matsala Aunty Sakeenah, ina hutawa ne. Na gode sosai”. Sakeenah ta zauna a gefenta, ta ce, “In barki ki huta zuwa gobe ki ba ni labarin lalurar ki, tun daga farkonta har karshenta, ko za mu iya farawa yanzu?” Ta ce, “Mu bari zuwa goben Aunty Sakeenah, jirgin nan ya wujijjiga ni, duk ya hautsina min ‘ya’yan hanji na”. Sakeenah ta yi dariya, ta ce, “Ai kin yi kokari ma, na zaci ba za ki iya zuwa ke kadai ba, kasada na yi na ce a turo ki ke kadai. Kasar tamu ba tsaro. To ki fito falo ki yi kallo maimakon ki yi ta zama ke kadai”. Tare suka fita zuwa falon. Engr. Farouk ya fita, suka zauna a kujera daya, Dr. Sakeenah ta murdo musu tashar MBC 3 suna kallon shirin da suke yi a lokacin. Ba jimawa la’asar ta yi, suka tashi kowacce ta nufi dakinta don yin sallah. Sun yi waya da Hajiya Nasara da daddare inda Sakeenah ta hada su suka yi ta hira. Hajiya ta turo wa Sakeenah lambar Goggo Shatu ta ce ta kira ta ta gaishe ta, ta kuma hada su da Kulsum. Sakeenah ta yi yadda mahaifiyarta ta umarce ta, Goggo ba ta waye da ita ba sam sai da ta yi mata bayani "Sakeena ce ‘yar wajen Hajiya Nasara". Zo ki ga farin ciki gurin Goggo, sun dade tana mata bayanin family dinta, Goggo ta sa mata albarka, sannan ta hada ta da Kulsum. “Goggo kuna lafiya? Ya Baffa? Babana ya zo?” Goggo cike da farin ciki ta ce, “Lafiyarmu kalau Kulsumu, sai kewar ki. Babanki satinsa daya da zuwa, duk siyayyar da ya saba yi miki ni ya yowa ya kawo min. Hajiya Nasara ta gaya min kina wajen ‘yar ta za a yi miki magani, Allah ya sa a dace. Ina fatan ba ki da matsala da iyalin nata?” Kulsumu ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Allah sarki Baban ‘Yanleman, da na samu kudi shi ma zan saya masa wayar hannu mu dinga magana da shi. Iyalin Hajiya masu karamci ne Goggo, ni dai ba abin da zan dorar a kansu sai alkhairi”. Goggo ta ce, “Masha Allahu, duk sun debo halinta ke nan, ai da ma barewa ba ta gudu ‘yarta ta yi rarrafe. Allah ya kara zaunar da ku lafiya”. Suka ci gaba da hira, can Kulsumu ta ce, “Goggo ya labarin wajen su Umma?”. Goggo ta ce, “Kwana uku da suka wuce ta turo Batulu ta kawo min sukari da kilishi. Batulu har kuka ta yi da na ce mata kin bar gari”. Kulsumu ta ji idanunta sun ciko da kwallah, ta ce, “Allah sarki Batulu na, watarana Allah zai hada mu insha Allahu”. Daga nan suka yi sallama da Goggo, ta kai ma Sakeenah wayarta. Washegari Dr. Sakeenah za ta je interview da asibitin da za ta fara aiki. Ta samu Kulsumu a daki ta fito daga wanka tana shafa, hannunta rike da mukullin mota, ta ce, “Kulsum zan je interview, watakila in kai har 12 noon. Walid da Walida za su zauna tare da ke, ki dafa muku ko noodles ne anjima kafin in dawo, suna da saurin jin yunwa”. Kulsumu babu nuku-nuku ta ce, “Aunty Sakeenah ni fa ban iya kunna (cooker gass) ba”. Sakeenah ta ce, “Hajiya ba ta koya miki ba?” Kai tsaye ta ce, “Hajiya ba ta sa ni girki, komai wannan kabilar ke yi”. Sakeenah ta ce, “Ai kuwa ba zai yiwu ba, daga yau tare za mu dinga shiga kitchen, har girkin gidan nan nan da sati biyu ke za ki dinga yi mana”. Kulsumu ta yi dariya ta ce, “In dai na gargajiya ne babu wanda ban koya a wurin Umma ba, da yake wani lokacin ni da Batulu take sawa mu yi wa Maimartaba girki, amma irin naku da sauki”. Sakeenah ta ce, “Wace ce Umma?” Kulsumu ta ce, “Babar sa”. “Shi wa?” A nan kuma sai ta yi shiru tana tauna sunan TURAKI a ranta. Wani kwayan mutum guda daya da ya yi mata babakere a zuciya, ta kasa manta komai nasa, duk nisan watanni da na shekaru. Sakeenah ganewa ta yi Kulsumu ta lula a duniyar tunani. A hankali ta dafa kafadarta da hannun damanta. Cikin taushin murya ta ce, “Kulsumu are you married? (Kulsumu kina da aure)?” Firgigit ta yi ta dubi ‘yar uwartata Sakeenah, ta rasa amsar da za ta ba ta. Sakeenah ta sake nanata tambayar ta, wannan karon hadi da girgiza ta. Kulsum ta ce, “Dogon labari ne Aunty Sakeenah, in kin samu lokaci zan gaya miki”. Sakeenah ta ce, “Abu daya nake so in sani kafin in tafi, kina da aure ko a’ah?” Ta sunkuyar da idanunta kasa, cikin jin nauyi. “Na taba yi, amma yanzu ba ni da shi”. Mamaki ya kashe Sakeenah, har nawa Kulsumu ta ke da za ta amsa sunan bazawara? Da ta tuna da matsalar da Kulsumun ta ke ciki kuma sai mamakin nata ya ragu, sanin halin mazan zamani. Ajiyar zuciya ta yi, ta ce, “Mu je kitchen in nuna miki yadda ake kunna gass da kashewa. Ta nuna mata komai kuma ta fahimta, sannan ta yi mata sallama ta tafi. Bayan fitar Aunty Sakeena ta ja yaran suka nufi dakin da ya zam nata, suka kwaso toys dinsu suna ta wasansu kamar sun dade da saninta. Ba'a fi one hour da fitar Dr. ba suka ce yunwa suke ji, ta ja su suka tafi kitchen, cikin tsanaki da tsananin kula ta kunna cooker din ta dafa musu noodle da dafaffen kwai suka zauna bisa Island din kicin din suna ci tana firfita musu. A haka Babansu ya zo ya same su, kanta a kasa ta gaishe shi ya ce, “Sakeenah fa ba ta dawo ba?” Ta ce, “Ai ba ta jima da fita ba ma”. “O.K”. In ji Engnr. Farouq sannan ya juya ya dau abin da ya dawo da shi ya fita ya sake komawa ofis. Sai karfe daya Dr. Sakeenah ta dawo, yaran suka rungume ta suna mata oyoyo! Kulsumu ta karbo jakar hannunta zuwa dakinta, ta ce, “In ce ko ba ku yi wa Aunty Kulsumu rigima ba?” Har suna hada baki wajen cewa, “Ba mu yi ba Mummy, ta dafa mana noodle da egg mai dadi mun ci mun koshi”. Ta dubi Kulsumu da fara’a ta ce, “Good, na ga alama Kulsum kina da kokari. Na gode sosai”. Dan murmushi ta yi ta ce, “Lah Aunty me na yi na godiya?” Ta ce, “Kula da yara mana, bari in yi girki sai mu samu mu zauna. Amma tare za mu shiga kitchen din”. Tare suka shiga madafin tana ba ta kananan ayyuka tana taya ta, tana yi tana mata bayanin komai. Nan ta fahimci Kulsumu yarinya ce mai saurin daukar abu dakaifin basira, kuma ba ta da kauyanci duk da cewa daga kauyen ta fito. Komai ta gwada mata sau daya ta gane, har tambayoyi ta ke yi mata, wannan duka zan yanka ko ya ya? Ana motsawa ko ba a motsawa? Maggi dunkule guda nawa za a zuba? Da haka har suka gama girkinsu mai rai da motsi. Sakeenah ta ce ta dauki warmers din ta jera a dinning ta je ta yi sallah, sai ta zo ta dau abincinta ta ci. Ita sai mijinta ya dawo za su ci tare. Dr. Sakeenah ba ta samu zama da Kulsumu officially ba sai washegarin ranar sabida Kulsumu ta kara sakewa da ita sosai, kuma ta samu hakan, don cikin kwanaki biyun da suka yi tare Kulsumu ta saki jikinta da Sakeenah sosai. Yau da dare wajejen karfe takwas ta shigo dakin nata, ta yi sassaukar kwalliya sai kamshi ta ke da alama mijinta yana gida. Kodayake ta lura ko ba ya nan Dr. Sakeenah kullum cikin ado da kamshi ta ke, dazu ta ba ta wasu (deo sprays) masu sanyin kamshi har guda uku ta ce ta dinga amfani da su. Ta tadda Kulsumu na gyara kayanta da ke cikin trolley tana jera su a wardrove don Dr. ta gaya mata komawarta Abuja ba rana. Da sallama ta shigo, Kulsumu ta amsa. Ta ce, “Aiki ake ta yi ne Kulsum?” Ta yi murmushin ta mai kyau, har dimples din suka lotsa cikin kumatunta sosai, ta ce, “Kayana nake mayarwa wardrove zan fi jin saukin daukansu a can”. Sakeenah ta zauna a gefen gadon tana bude kofofin hancinta sosai ko za ta ji sauyin atmosphere a dakin, amma ba ta ji ba. Kulsumu tana kula da kanta sosai da muhallin da ta ke zaune, ba ta bari a ji wani sauyin atmosphere ko ya ya a tare da ita mai alaqa da lalurar ta. Dr. ta ce. “Bar aikin ki zo mu yi magana mai muhimmanci in mun gama sai ki ci gaba”. Ta ajiye rigar da ta dauko ta dawo gefen Sakeenah ta zauna, ta kuma tattara dukkan hankalinta ta mika mata. “Tun yaushe ki ke yin fitsarin kwance?” Ta sunkuyar da kai cikin jin nauyi. “Abin da zan iya tunawa gaskiya tunda aka haife ni”. Dr. ta ce, “Kamar ya ya ki ke ji kafin ki yi shi?” “Mafarki nake na tsugunna a toilet zan yi, daga nan sai kawai in ji ni cikin laima”. Dr. Sakeenah ta dan kura mata ido, sannan ta nisa ta ce, “Kulsum sunan matsalarki a kimiyyance 'NOCTURNAL ENURESIS’. Ana kuma kiran sa 'bed-wetting' da harshen turanci. Wasu tun haihuwa sai sun girma suke dainawa. Treatment din sa guda biyu ne; pharmacological and non-pharmacological. Na farko da zan dora ki akai 'is non-pharmacological' ni da ke za mu hada gwiwa mu yi shi. Da farko dai daga karfe shidda na yamma kar ki kara shan ruwa ko wani abu mai ruwa-ruwa. Sannan kafin ki kwanta ki tabbatar kin yi fitsari. Da tsakar dare zan dinga zuwa na tashe ki ki je ki yi fitsari, sai kuma da asubah na sake zuwa na tashe ki ki je ki yi. A hankali system din jikin ki zai saba da hakan, zan saita alarm da zai dinga tashi na ina zuwa tashin ki at interval. In ya ki bari bayan watanni kamar biyu zan yi referring dinki ga 'kidney and bladder specialist/nephrologist' akwai maganin da za su rubuta miki bayan sun yi examining din ki”. Kulsumu ta gyada kai cikin fahimta, Dr. Sakeenah ta kara da cewa, “Muna fatan ya tafi after this non-pharmacological treatment, ba sai mun kai ga shan maganin ba”. A sanyaye ta ce, “Insha Allahu Rabbi”. Dr. ta ce tana mai mikewa tsaye, “In kin gama jera kayan sai ki je ki yi fitsarin ki kwanta, Allah ya tashe mu lafiya”. Ta amsa da, “Ameen Aunty, nagode”. *** *** *** Tun daga wannan ranar suka fara wannan excercise din, Sakeenah ba ta yi kasa a gwiwa ba, kuma ba ta kuskure wa wajen tashinta a kan lokaci sau biyu cikin dare da kuma asubahi ta je ta yi. In ta bushi iska kuma ta zaga gari da ita ta ga garin Lagos ta yi mata sayayyar kayan amfani tare da su Walid. Hajiya na kira akai-akai ta ji development (cigaban) da ake samu haka Goggo, Dr. Sakeenah na yawan kiranta ta hada su a waya, har Baffa ma in yana gida. Kulsumu sai kara mulmulewa ta ke boyayyen kyawunta na bayyana sarari. Garin Lagos ya karbe ta har fiye da Abuja. Dr. Sakeenah ta samu aiki da Lagos Specialist Hospital, don haka zamanta a gidan sai ya karanta. Duk hidimomin gidan da kula da su Waleed sai ya dawo kan Kulsumu. Ba ta da kiwa ko kadan da jikinta da zuciyarta ta ke taimaka wa Dr. Sakeenah. Wannan ya sa ta shiga ran Sakeenah sosai, ta kuma dage wajen koya mata duk abin da zai amfane ta, kama daga girki, tsafta, turanci da sauransu. Da daddare sukan zauna duk gidan su yi hira kafin lokacin kwanciya barci, amma Kulsumu ba ta sakewa sam in Engnr. Farouq na wajen, Dr. Sakeenah kuma ba ta barinta a daki ita kadai in har suna gida sai ta takura mata ta zauna a cikinsu. Ta kan ce, “Kulsum in kin tafi zan yi kewarki!”. Rabon da ta yi fitsari cikin barci har ta manta. Ita kanta a jikinta tana jin ta fara samun lafiya, ko ko ta ce ta samu lafiya daga lalurar fitsarin kwance. Duk da haka basu bar fargabar ko zai dawo ba. Ilai kuwa, bayan wata biyu da rabi suna murna lafiya ta samu kawai rannan ta kuskure bacci ya dauketa ba tareda ta je ta yi fitsarin ba, ai kuwa ba'a jima ba ta ji ta cikin danshi. Washegari hankali tashe ta gayawa Dr. Sakeenah, inda ba bata lokaci tace ta shirya su wuce asibiti tare. Asibitin da take aiki ta kaita, da kyar suka samun appointment na ganin 'kidney and bladder specialist' wanda shi kadai ne duk fadin asibitin. Kuma visiting Doctor ne a wata sau daya yake zuwa, sun yi sa'a sanda suka samu appointment saura sati daya ya zo asibitin. Ranar da suka samu ganin nephrologist din ya dade yana yiwa Kulsumu tambayoyi, ta dinga amsawa da taimakon Dr. Sakeenah. Ya ce da Sakeenah "urinary incontinence (another medical name for bed-wetting) among adults is now rampant. Wato lalurar fitsarin kwance ga manya matsala ce da ake samu sosai yanzu. A karshe ya hada ta da wasu magunguna (tricyclic antidepressants) wato tofranil (imipramine), da kuma DDAVP (desmopressin acetate) bayan series of gwaje-gwaje, wadanda Kulsumu zata dinga sha based on prescription. (A bisa ka'ida). In ta zauna sai ta yi ta tunanin wahalhalun da kakanninta suka yi shekara da shekaru suna sha wajen nema mata lafiya, yawo tsakanin kauyuka bukkokin masu magani, ashe ciwon ta maganinsa na asibiti ne Allah bai taba ankarar da su ba. Domin tuni jikinta ya saba da system din da Dr. Sakeenah ta dora ta a kai kuma yana karbar medication din da take sha babu kuskurewa. Cikin ikon Allah suna saka ran ingantacciyar lafiya ta samu ga Kulsumu. Wasa-wasa yau ta kwashi watanni hudu gidan Sakeenah, Hajiya Nasara ta yi-ta yi Sakeenah ta dawo mata da Kulsumu, tunda ta tabbatar mata ta samu lafiya kamar yadda babban likitan ta ya tabbatar mata a ziyarar karshe da suka kai masa amma Sakeenah ta ki, kullum da uzurin da ta ke bai wa Hajiyar. A zahiri kuwa ta saba da Kulsumu ne, ba ta son rabuwa da ita. Ita ma Kulsum ta saba da Sakeenah da yaranta sosai, amma ta fi so ta koma wajen Hajiya ko sabida Nasma, sun saba sosai kullum suna tare a wayar Sakeenah. Rannan da Nasma ta bugo mata waya, Dr. Sakeenah ta kawo mata daki, sai ta ce, “Ni dai bari in dauki salary dina, waya zan saya miki, ko kwa bar ni in huta ke da Nasma”. Nasmah ta gaya mata hutunta ya kare cikin satin nan za ta koma makaranta. “I will be calling you when I get back to Nottingham. I wish you all the best Sis". (Zan din ga kiran ki idan na koma Nottingham. Ina miki fatan alkhairi). Wannan ce sallamar su ta karshe da Nasmah, kafin ta bar gida Abuja zuwa U.K. ***** Dr. Sakeenah ta cika alkawari, tana daukar albashinta ta saya mata ‘yar karamar waya samfurin Siemens, zo ki ga murna wajen Kulsumu. A ranar Goggo da Baffa suka san ta yi wayar kanta, domin kuwa raba dare suka yi suna hira. Washegari kuma ta kira Nasmah, “Nasmah albishirinki, Aunty Sakeenah ta saya min waya”. Nasma ta ciji yatsa, “Shi ne ta riga ni? Ya Taufeeq na tahowa wannan satin, na ba shi waya mai kyau ya kawo miki”. “Allah sarki Aunty Nasma, ke da Aunty Sakeenah ban san wa ya fi kirki ba. Kada ki damu, zan aika wa Babana daya ‘Yalleman, ni kuma in yi amfani da daya, ba ki yi asarar kudinki ba. Na gode ‘yar uwa”. Cikin ranta ta ke tambayar kanta, tsakanin Hajiya Nasara da ‘ya’yanta wa ya fi son kyautata mata??? *** *** *** UNIVERSITY OF READING, UK Yana sanye da bakaken Japanese suit, ya daura farar rigar likitoci a kai, baki ne dogo, tun da can ba shi da kiba kamar yadda ba shi da rama. A duniya akwai kyayawan bakar fata wadanda kyawunsu kan sanya nationality dinsu cikin kokonton daga kabilar da suka fito. Hakika wannan matashi yana cikinsu, domin kai tsaye ba za ka gane daga kasar da ya fito a (Africa) ba in har ba shi ya bude baki ya fada ba. A babban dakin taron malaman jami’ar 'Reading' wato ‘seminar room’ duk ciki su biyu ne bakar fata. Dakin Seminar din a cike yake da malaman jami’ar daga tsangayoyi daban-daban na faculty of medicine. Kowanne daga ciki yana wakiltar tsangayarsu ne (delegates). Babban teburi ne mai tsayi da fadi wanda aka zagaye da kujeru, a gaban kowanne delegate dan karfe ne mai dauke da sunan mamallakin kujerar da sunan tsangayar da yake representing hadi da matakin ilminsa. Tattaunawa suke a kan sabuwar tsangayar da za su fitar cikin faculty of medicine na jami’ar ta 'Reading' wanda a baya babu shi a jadawalin koyarwar jami’ar, wato Ophthalmology Department (tsangayar karatu a kan likitancin ido), sun kuma cimma matsaya guda a karshen tattaunawar tasu. A lokacin da suka rufe tattaunawar kowa ya mike ne don barin dakin taron abun ya faru kamar yadda ya saba faruwa da shi lokaci zuwa lokaci. Yana mikewa kansa ya sara, mummunar sarawa, jiri ya debe shi, gumi ya lullube shi. Daga nan kuma bai san abin da ya sake faruwa ba, sai farkawa ya yi ya samu kansa a gadon asibiti. A gefensa babban amininsa ne, wanda suka fito kasa daya, wato Abdul’Ahad Maikano zaune a daidai saitin kansa ya kura masa ido. Ruwan da aka makala masa a jijiyar hannunsa ya bi da kallo kamar mai kirga saukar kowanne digo na ruwan zuwa cikin jikinsa. Amma a zahiri ba ruwan yake kallo ba, innocent and naïve fuskarta ce ta ke gilma masa. Wani mummunan scene da ya kasa bace masa, a rana ta karshe da ya tsallake ya barta, bayan ya karbe mata alfarmarta cikin wani yanayi da duk mai imani ba zai yi irinsa ba. Muryar ta ce ke yi masa amsa-kuwwa cikin roko, tana rokonsa da ya tausaya mata, al’amarin da ba shi da maraba da rape ban da igiyar aure da ta lullube shi. Tun daga ranar kuma, har izuwa inda yau ke motsi, bai zauna lafiya da zuciyar sa ba, bai samu farin cikin da yake hasashen samu in ya guje ta ba. Ya samu cikar kowanne cikin burikan sa, amma ya kasa samun kwanciyar hankali, zuciyar sa kuma ba ta huta ba. Wani irin maganadisu ne ke jan zuciyar tasa zuwa gare ta...., da wani irin extraordinary feeling mai wuyar fassarawa. Feeling din da har gobe bai san ma'anar sa ba, bai gaya wa wani ba, balle ya samu fassarar sa. Ya san dai daga ranar zuciyar sa ba ta kara hutawa ba. Ruhin sa bai bar azabtuwa ba da tunanin ta. Girman laifin da ya san ya aikata mata kuma, daga ita har iyayen sa, ya hana shi samun karfin gwiwar komawa gida ya fuskanci iyayen sa. Sannan tunaninta ya ci gaba da yi masa dabaibayi irin wanda ya hana shi jin dadin komai. Ga dai ilmin da ya fito nema ya samu yadda ya kamata, wanda a take bayan kammalawar sa jami’ar ta dauke shi aiki a Teaching Hospital dinta amma duk da wannan achievements din, ya kasa samun farin cikin da ya kamata ya samu. Ya kuma kasa samun contentment din da ya kamata mai nasarar rayuwa irin sa ya samu. Girman laifinsa ga iyayensa da kullum yake hangowa, ya hana shi zama lafiya yaji dadin nasarorin nasa; sun yi masa gatan da yake ganin takurawa ne a gare shi, ya bula musu kasa a ido ta hanyar kin komawa garesu, tare da kin waiwayar wadda ta kasance a karkashin alfarmarsa. Ga shi sakamakon hakan yawan tunani da damuwa ya haifar masa da ciwon kai na barin kai guda (migraine) wanda a duk lokacin da ya tasar masa, sai ya fidda shi daga hayyacinsa, kuma sai ya sha drip a asibiti. “Are you okay Man?” Abdul’Ahad ya tambaye shi. Lumshe idanunsa ya yi daga kan ruwan da ya daura su ya kasa daukewa. Abdul’Ahad ya kama hannunsa na hagu wanda babu ruwan a jiki. “You better be careful da lafiyarka Aboki (sunan da yake kiransa), Dr. Andrew ya ce kana tsanantawa kwakwalwarka tunani ne, shine silar migraine din ka, as a medical doctor ba sai an tsaya gaya maka illolin hakan ga lafiyarka ba. Har gobe ba ka dauke ni yadda na dauke ka ba Aboki, ba sai ka yi haka zan san ba ka yarda da ni ba. Sannan ban kai matsayin da zan zamo amini a gareka ba. Ka ki gaya min damuwar ka ta shekara da shekaru. Tunda muka zo a haka nake ganin a. Ni ba abin da ba ka sani a kaina da iyayena ba, amma har gobe ban san komai a kanka ba. A kalla in ka gaya min damuwarka ko ban yi maka maganinta ba, zan ba ka shawara, shawara wadda in ka bi ta za ka samu sassaucin damuwarka. Na yi-na yi ka hada ni da mahaifanka ko sau daya ne mu gaisa a waya tsayin shekarun nan Aboki, ka ki yin hakan. Kullum da uzrin da zaka bani. Har yau ba ka yarda da ni ba ne, ko kuwa ba ka ba ni matsayin aboki na gaske ba?” ABUBAKAR (TURAKI) ya sake lumshe kyawawan idanunsa. Duk inda ake neman aboki na gari, to Abdul’Ahad ne. Ya rungume shi kamar dan uwansa na jini tun zuwansu garin (Reading Barkshire). Ba wai bai amince masa ba ne, kawai bai taba sharing al’amuran rayuwarsa da kowa ba, sannan ya sani shi mai laifi ne ga iyaye abin tinkahon kowanne dan Adam, watakila har wajen Ubangijinsa! Ba ya so Abdul’Ahad ya bar ganin mutuncin sa. “Okey, tunda hakan ka zaba wa kanka, da yardar Allah ba zan sake tambayarka komai a kan rayuwarka ba. Abin da nake so kawai shi ne, ka kula da lafiyarka, ka kare ta daga cututtukan zamani wadanda ba mu da maganinsu. Aboki, me ce ce rayuwa? Komai da ke cikinta mai wucewa ne, idan har mun dauke shi da sauki”. Daidai lokacin likita Andrew ya shigo dakin. Ruwan ya cire masa, ya ce suna iya tafiya yanzu, amma yana kara jan hankalin Dr. Aboubacar da babbar murya ya raba kansa da damuwa da tunani. Abdul’Ahad ke tuka su cikin motar Aboubakar Turaki kirar Acura. Suna tafe a kan titin da zai sada su da gidan Abubakar-Turaki da ke cikin jerin gidajen malaman jami’ar 'Reading'. Turaki ya rasa me ya sa yau zuciyarsa ke neman wanda za ta raba dimbin damuwar nan da ke nukurkusarshi da shi ko da kadan ne? At least ya samu sassaucin damuwar nan in yayi voicing dinta ga wani, someone caring like Abdul Ahad. Yana gefen Abdul’ahad yayin da Abdul’Ahad din ke tuki cikin nutsuwa, bakinsa ya motsa kadan ya fadi abin da bai ta furtawa ba tsayin shekarun da suka yi tare. “I am married Aboki”. Ya fada daga can kasan makoshin sa. “What?" Maikano ya tambaya kamar bai ji daidai ba. “Aure ka ce ko me?” “Aure aboki, I’ve a wife at home (inada mata a gida), ina cikin tasku, domin na yi wa iyayena laifi, na kasa zuwa in ba su hakuri don ban san da kalamin da zan wanke kaina ba. Na yi musu babban laifi, na kin waiwayar su all these while a kan bana son auren da suka yi min. Tun bayan na taho kuma tunanin yarinyar ya kasa barina, sabida ita ma na yi mata wani babban laifi. I lack the courage na fuskantarsu su duka ukun, in ce su yafe min”. A wannan lokacin ya kwashe labarin sa kaf ya gayawa Abdul Ahad, garin su, inda ya fito da matsayin mahaifin sa. Cikin mamaki Abdul’Ahad ya ce, “Kana nufin tun tahowar ka ba ka kara waiwayar gida ba?” Cikin jin nauyin abin da ya aikata ya ce, “Duk halin da suke ciki na sani. Wani abokina a garin mu yana gaya min, na san lafiyar su kalau. Ina bibiyar lafiyar su. Da farko ina kira, daga baya ne na daina, ba don komai ba sai don kada su takura min in dawo wajen matar da suka aura min. I thought I don’t like her anymore Aboki, saboda tana da lalura... I thought I escaped, auren da bana son, amma tunaninta ya hana ni sakat a duka shekarun nan, something like infatuation… emotional disturbance.... I just..... cannot express…, kawai ji nake zan iya zama da ita da lalurar tata against all odds”. Abdul’Ahad ya yi wani mischevous murmushi ya ce, “Man, ka dawo hanya kawai, tell me you love your wife right now (kana son matar ka yanzu), shawarar da zan baka itace ka koma gida ka taho da ita, ka kuma nemi afuwar iyayenka bisa kaurace musun da kayi alhalin su da alheri suke nufin ka, in ba haka ba, ba za ka taba zama lafiya ba na gaya maka, kuma ba za ka ga albarka cikin rayuwar ka ba. Babu iyayen da suka san ciwon kansu da zasu so dan su ya tafi Turai ba aure. Da ka kwantar da hankalin ka da ka fahimci manufarsu tuntuni. Ba sun yi ne don su takura maka ba. Shawarar da zan baka ke nan, ka je gida, ka karbi duk wani punishment daga gare su, sannan ka dauko matarka!”. “Kana ganin za su yafe min Aboki? UmmuKulsum za ta kara kallona da kima bayan duka laifuffukan da na yi mata? Ban taba kallon ta da matsayin mata ba! Aboki har raping dinta na yi don kawai in nuna rashin kaunata gare ta. This is the worst moment da nake tunawa a kanta, kuma abin da ya canza zuciyata zuwa alkhairi bakidaya a kanta. Ba ta cancanci duk abubuwan nuna rashin kauna da na yi mata ba tunda ba ita ta zo ta ce tana sona ba, iyayena ne suka je suka nemo min aurenta har gaban iyayenta kamar yadda ake neman auren kowacce diya ta mutunci. Ban kyauta ba Aboki, watakila Ubangiji ke hukunta ni da feelings a kan UmmuKulsum, wadanda ke kassara ni a yanzu, suka kuma hana ni jin dadin kowacce nasara da ta same ni”. Abdul’Ahad ya ce cikin tausayawa, “Don’t ever say you raped her again, tunda igiyar aure ta hada ku. Matarka ce. Sai dai ka ce, ...not in a nice way...! Mace kuma mai rauni ce a halittar ta, ban hakuri, kulawa da nuna soyayya tareda nuna ka amshi laifin ka kadai zai wanke laifinka komai girman sa. Iyaye kuwa tsakaninmu da su akwai afuwa, yafiya da jin kai, wanda Ubangiji Subhana ya sanya a tsakaninmu da su. Ka je gida ka kwantar da kai, ka amshi kowanne laifinka. Ka karbi punishement komai tsaurin sa. Sannan ka ba su hakuri, ka dauko matarka kusa da kai ina tabbatar maka hakan kawai za ka yi ka wanke kanka a wajensu, kuma ka samu nutsuwa da zaman lafiyar cigaba da gudanar da al'amuran rayuwar ka”. Turaki ya yi na’am da shawarar amininsa, cikin satin gabadaya ya maida hankali wajen shirin dawowa kasar haihuwarsa, soyayyar da bai san cewa ita ce ke nukurkusar sa ba tana kara masa azama ga son dawowa gida, da burin ya dora ido a kan KULSUMU. *** *** *** GAYA Batulu na markada abarba cikin blander a kicin din Umma, yayin da Umma ke turara alkubus a kan wuta, ga dukkan alama ita ce da turakar Maimartaba yau. Don girkinshi matansa ne kadai ke yi mishi da hannunsu. Suka jiyo hayaniya daga tsakar gida, wani suna yana tashi daga bakin jama’ar gida, kamar TURAKI! Umma tayi sak! Daga abinda take yi, ba ta gaskata kunnuwanta ba don haka ta mike ta leka tsakar gidan ta tagar kicin. Ba ta yi nasarar hango wanda jama’ar gidan suka yanyame ba, amma tabbas ta ji suna fadin, "Turaki", komawa ta yi ta zauna ta ci gaba da turara alkubus dinta, amma hankalinta ya rabu biyu. Batulu ta kashe blander ta ce, “Umma kina jin me ake fadi kuwa? Kamar Yaya Turaki na ji suna cewa…”. Kafin Batulu ra rufe bakin ta Umma kuma ta samu zarafin amsa mata, kamshin turaren Turaki (one man show) ya ziyarci hancin su, daga nan kuma sai sallamarsa, cikin muryar nan tasa mai cike da haiba da ginshiran sarauta, kafin ingarma kuma kyakkyawa Abubakar (Turaki) ya sako kai ta hanyar rage tsawon sa a kofar kitchen din Umman sa. Sanye yake da kaftan na wata lallausar farar shadda (filtex), hular kansa ruwan kasa ce mai haske, haka fatar agogon hannunsa samfurin RADO itama ruwan kasar ce, a kafarsa budadden takalmin fata ne dan kasar Italy. Kallo daya Umma ta yi masa ta dauke kanta, amma sai da zuciyarta ta buga sosai da sßganinsa. Ban da uwa-uwa ce da ba za ta yarda Turaki ne ba, domin gabadaya ya canza ya zama wani gogaggen matashi, wheather din kasar England ya amshe shi ba kadan ba. Ya kara kyau da ilhama, ga wani lallausan saje da ya tara a gefen fuskarsa wanda a da ba shi da shi. Batulu ta hangame baki sannan ta sheka da gudu ta rungume shi tana fadin. “Yaya Turaki kai ne? Ashe za mu sake ganinka?” Shi ma ya rike ta a jikinsa yana fadin, “Autar Umma kin kara girma, me Umma ke ba ki hakan?” Dariya ta yi tare da riko hannuwansa duk biyu kamar ta hadiye shi don farin ciki, sai fargawa suka yi babu Umma a kicin din babu alamarta. Shi da Batulu suka bi bayanta zuwa dakinta, zaune suka same ta a gefen gadonta ta kifa fuska cikin tafukanta tana share hawaye. Jikin Turaki ya kara yin la’asar, fiye da wanda yazo a cikin sa, a kan gwiwoyinsa ya tsugunna a gabanta. “Umma na san ni Abubakar Turaki mai laifi ne, mai tarin laifuffuka a gare ku, Umma duk laifin da ku ke zargina da shi na karba, kuma na san na yi. Amma don Allah Umma ku ba ni dama in gyara kuskurena. Don Allah Ummah. Ajizanci ne irin na dan adam. Umma cikin tarin alfarmomin ki na uwa, wadanda ba za su taba karewa a gare mu ba nake rokon ki da ki yafe mini, na tabbata na yi muku laifi wanda in ba ku yafe min ba ba zan taba zama cikin kwanciyar hankali ba. Na kwashe shekaru ban zo na gan ku ba, ban nemeku a waya ba, ban ji lafiyar matar da kuka zaba min ba wanda ba akan haka muka rabu ni da ku ba. Mun rabu ne akan duk shekara zan zo, kuma zan dinga kiran waya. Ummah a yau gani a gaban ku, durkushe akan gwiwoyi na, na zo in tabbatar muku na karbi zabin da ku ka yi min da hannu bibbiyu. Ki taya ni ba ta hakuri. Ba zan kara maimaita kuskure na ba”. Umma dai ba ta ce komai ba, amma kalamansa sun shigeta, yana ta magiyar sa, ita kuma tana aikin share hawaye. Wuni guda ya yi cur yana bin Umma da neman gafarar ta, amma uffan ta ki ce masa komai, Batulu kadai ke kula da al’amarinsa. Ita ma in ta tuna babu Kulsumu a gidan duk sai ta ji wani irin haushin sa ya rufe ta. A haka dai ta yi masa girki mai kyau, ta kuma shigar masa da kayansa sashen sa. Bayan ta sa an share an goge ko'ina. Yana so ya tambayi Batulu Kulsumu, ya rasa ta ina zai fara. Sabida yadda take sha masa kamshi. Kwarai hankalinsa ya dugunzuma ya tashi da ya fahimci babu ita a sashen nasa, babu komai nata, kai da alama ma an dade ba a yi amfani da sashen nasu ba. Amma ya kasa tambaya. Saboda fargabar abinda za'a gaya masa. Bai samu ganin Maimartaba ba sai washegari da safe yana kalaci. Mai girki wato Hajiya Saratu ta yi masa iso turakar mahaifinsa. Maimartaba ya amsa gaisuwar sa kadaran-kadahan, amma daga gaisuwar bai kara ce masa komai ba. Hankalinsa ya kara yin kololuwar tashi. Ya gurfana gaban Maimartaba yana ba shi hakuri tare da jaddada cewa ya amince ya karbi dukkan laifuffukansa. Ya karbi zabin su da hannu bibbiyu. An dauki lokaci kafin Maimartaba Sarki ya ce da shi. “Mu kam ai mu za mu ba ka hakuri Turaki, tunda mun takura rayuwarka ba da sanin mu ba. Har dalilin hakan ka zabi ka kaurace mana a wannan lokaci na tsufa da muka fi bukatar kulawarku da komai. Ka kwantar da hankalinka, kuma ka daina gudun mu in dai a kan yarinya Kulsumu ne, tuni mun maida wa iyayenta ‘yar su, bayan mun sa Alkali ya raba auren bisa doron shari’ah”. Wani gumi ne ya keto wa Turaki tun daga tsakar kansa har zuwa yatsar kafarsa. Ya san Maimartaba ba ya zolaya, kuma ba ya fadin abin da bai aikata ba. Idan mafarki yake yana rokon Allah ya farkar da shi, Maimartaba ya janye abin da ya gaya masa yanzun nan. Maimartaba ya ci gaba da cewa, “Muna fatan yanzu za ka daina gudun mu, tunda mun bi ra’ayinka, mun yi maka yadda ka ke so? Wato zama babu aure?” Hawaye suka zubo daga idon Turaki, ya rasa da bakin da zai yi wa mahaifinsa bayanin cewa; gabadaya shekarun da ya yi, ya yi su ne cikin son Kulsumu, da nadamar abin da ya yi musu. Sannan ganin girman laifin sa ne ya hana shi dawowa har sai da Abdul’Ahad ya karfafe shi. Ba fitsarin kwance ba, ko kashin kwance ta ke yi a yanzu kam ya daura dammarar zama da ita cikin so da kauna. Sannan as a medical doctor zai nema mata magani iyakar iyawarsa, idan ma ba ta samu lafiya ba ya alkawarta wa ransa ci gaba da zama da ita da lalurar da Allah ya dora mata. Har bincike na musamman ya yi a kan lalurar ‘Eneuresis’ kasancewar ba fanninsa ba ne, ya kuma samu kwarin gwiwar cewa, da ya dawo zai kai ta inda za ta samu magani. A wannan halin Umma ta shigo ta same su. Dukkan su babu wanda zuciyarsa ba ta motsa ba ganin Turaki yana kuka. Daga yarintar sa zuwa yanzu za su iya kididdige sau nawa ya yi kuka a rayuwarsa. Amma ba su yi saurin nuna karayar su ga laifin da ya yi musu ba tukunna, domin ya jawo sun cutar da yarinyar mutane, sannan ya nuna wa duniya ba su isa da shi ba. Wannan shi ne babban abin da ke kara fushinsu a kan dan nasu. *** Washegarin ranar Kiru ya tafi wajen Yayarsa Hadiza. Hadiza ta karbe shi kadaran-kadahan don ita ma ya bata mata rai ba dan kadan ba. Allah ya gani tana son Kulsumu! A zaman shekaru hudu da suka yi da yarinyar ba za su taba cewa ga aibunta ba. Ta shiga ran su sosai sabida kyawawan halayenta. Amma yadda Turaki ya kwantar da kai yana ba ta hakuri tare da rokonta ta shige masa gaba ya shawo kan iyayensu su dawo masa da matarsa su kuma yafe masa laifin sa, dole ta tausaya masa. An ce naka sai naka, don duk cikin kannenta Turaki ne favourite dinta, tana sonshi sosai a matsayin sa na namiji daya tal a cikinsu. Dole ta hakura ta karbi uzurinsa ta ce ya tafi gobe za ta zo gidan insha Allahu za su shawo kansu, amma tana mai kara gaya masa bai kyauta musu ba, kuma ya yi babban kuskure. Kulsumu duk da kasancewar ta tashin kauye, mace ce cikin dubu ba zai samu kamar ta da sauki ba. Turaki ba ya ja, akan ko me aka ce ya yi, ya karbi laifinsa, shi mai baiwa kowa hakuri ne da dukkan iyawarsa. Washegari Hadiza ta zo Gaya, Umma ta yi mamakin ganinta ko waya ba ta yi ta ce za ta zo ba. Bayan sun gaisa ta ce, “Umma wajenku na zo ke da Maimartaba, kuma a tare nake son ganinku”. Ko kusa Umma ba ta kawo zancen Turaki ba ne, don ba ta san jiya ya je Kiru ba, ta ce, Maimartaba yana da baki, in sun tafi sai mu je. Allah ya sa dai lafiya”. Hadiza ta ce, “Lafiya kalau, sai alheri Umma”. Bayan tafiyar bakin Maimartaba suka je suka same shi a falon da yake ganawa da iyalinsa. Ya dubi Hadiza ya yi murmushi, ya ce, “Fulanin Kiru ku ne tafe?” Hadiza ta zube ta gaida mahaifinta yana tambayarta ‘yan jikokinsa, ta ce, duk a gida ta baro su, ita kadai ta zo. Sannan ba ta bata lokaci ba ta dora da abin da ya kawo ta, wato nema wa Turaki afuwa daga gare su, ta ce ba komai ya hana shi dawowa ba illa iyaka yana hango girman laifin da ya yi muku ne, yana jin nauyi har sai da abokinsa ya ba shi shawararar ya ture hakan ya fuskance ku, ya karbi laifinsa komai girman sa. Don Allah Umma ku yi hakuri ku maida masa matarsa tunda shi da kanshi yanzu ya zo ya ce yana son ta, na kuma fahimci wallahi da gaske yake, kuma wannan shi ne karo na farko da ya taba saba wa umarnin ku. Sannan karo na farko da Turaki ya taba bude baki duk kawaicin sa ya ce yana son mace. Ni na tabbatar su Goggon Kulsumu ba za su ki dawo da ita dakinta ba tunda dama ba su suka nemi a mayar musu da ita ba, daga gare mu ne”. Maimartaba ya ce da Hadiza shi ai tun jiya ya yafe wa Turaki, amma ba zai zama karamin mutum a idon talakawansa ba, ba zai yi masa bikon Kulsumu ba, ya je da kansa in iyayenta sun gamsu da nadamar sa su sake bashi aurenta, kada kunyarsa ta sa su yi abin da ba sa ra’ayi. Umma ma ta ce tana bayan ra’ayin Maimartaba. Hadiza ta samu Turaki a sashensa ta yi masa bayanin yadda suka yi da iyayen su. Ko ba komai hankalinsa ya kwanta tunda sun yarda sun yafe masa, ya sa a ransa wannan karon shi da kansa zai dawo da Kulsumu rayuwarsa. Zai yi amfani da hikimarsa ta Da namiji wajen sabunta rayuwar su, zai nemi soyayyar Kulsumu, ba tare da taimakon kowa ba!!!. Washegari Hadiza ta koma Kiru gidan mijinta. Turaki ya kira Batulu sashensa. Batulu sarkin hidima ga Yayanta, tana shigowa niki-niki da tray da ta jero warmers a kai, ta ce, “Yaya Turaki guess what? Yau Burabuskon gero na yi maka da miyar ganye”. Ya gintse fuska ya ce, “Fatima, in ya shake ni fa?” Ta tuntsire da dariya ta ce, “Taste it first, bayan haka ma ga lemon abarba a gefe na hada maka, na zuba kankara a ciki sai ka dinga yi kana korawa”. Ya yi murmushin sa mai aji, he is not in the mood na yin rahar, ya ce, “Na gode Fatima, Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki miji na gari. Zauna magana za mu yi”. Ta zauna a gefe tana murmushin addu’ar da ya yi mata. Ya ce, “Fatima game da kawarki ne, ai ke za ki taya ni biko ko? Ba za ki hukunta ni da laifina ba?” Fatima-Batulu ta fadada murmushinta. Amma sai ta ga ya kamata ta kare wa Kulsumu martabar ta, an ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. Balle Kulsumunta. Ta ce, “Yaya Turaki ina sonka da Kulsum, amma gaskiya yanzu na fi son ta auri wani daban wanda yake son ta”. Lumsassun idanunsa ya bude sosai a kan Batulu, ya ce, “Fatima na taba ce miki bana sonta?” A zuciyarta hamdala ta ke yi, amma a fili sai ta ce, “Ai ba sai ka fada ba, action speaks louder than voice”. Wani dan murmushi ya yi, ya dora habarsa a kan hannayensa da ke sarke cikin junansu. Cikin sanyin murya ya ce, “That was then… Fatima ke kanwata ce, ba zan iya gaya miki komai ba, alfarma kawai nake nema daga gare ki ki ba ni goyon baya, ni da ke mu hada gwiwa mu dawo da Kulsum cikin rayuwar mu, duk son da ki ke da ta auri mai sonta ai ba ya ni Fatima. Tunda masu iya magana sun ce, naka sai naka…”. Batulu ta wani harare shi ta kasan ido, ta ce, “How can I believe kana sonta yanzu Yaya Turaki? Ba don ka faranta wa su Umma ba ne ka ke son dawo da ita? Gaskiya auren soyayya nake son Kulsumu ta sake yi, irin wanda nake fatar wa kaina”. Turaki ya tsura wa kanwarsa Batulu ido, yana mamaki, ya ce, “Fatima I’m old enough in zaunar da ke ina fada miki abin da ba shi ne a raina ba. Sannan su Umma sun cire hannnsu cikin maganar nan, ke kadai ce support din da ya rage min if you didn’t trust your brother, who will? So ki ke dai in fito fili in ce miki sonta nake yi ba dan kadan ba, don Allah ki taimake ni Batulu”. A wannan gabar, Batulu ta karaya, ta amince da gaske yake yi. Sai ta ji ba za ta iya gaya masa ma Kulsumu ta bar garin Gaya ba, zuwa inda ita kanta ba ta sani ba. Domin Goggo ba ta fada mata ba. Hajiya Nasara ta nusar da Goggo kada ta gaya wa dangin mijin Kulsumu inda ta ke, domin ta fahimci har gobe Kulsumu na son Turaki, ba abun mamaki ba ne in ya dawo ya nemi kome ta ce ta fasa karatun, tunda an ce ba shi ya sake ta da kansa ba. Don haka Batulu ba ta san garin da aka tafi da Kulsumu ba, Goggo dai ta ce da su ‘yar Yayarta ce ta tafi da ita birni, ita ko sunan garin ba ta sani ba. Don haka Batulu ta ja bakinta ta yi shiru, ta ce da shi in ya shirya za ta raka shi biko. Ya ce ai shi a yau yake so su je ba sai gobe ba. Suna tafe a gefen hanya zuwa gidan Malam Jibo, garin ba wuta sai hasken farin wata. Turaki na yi wa Batulu tambayoyi a kan Kulsumu, Kulsumun da har aure ya hada su bai san komai a kanta ba. A yau ba abin da yake son ji irin zancenta, Batulu ta lura hirar Kulsumu kawai yake son su yi, ko ta yi niyyar share shi ba ta iyawa, domin Ubangiji da ya nufe su da fitowa daga ciki daya shi ya sanya kaunar juna a tsakaninsu. Ya ji abubuwa masu yawa a kan Kulsumu daga bakin Batulu, wadanda suka kusan fiddo hawaye daga idanunsa. Ta ce, “Ita Kulsumu ai mai hakuri ce, duk shekarun nan da ka diba ba ka dawo ba, ba ta korafi. She never complain. Tare muke zuwa makaranta mu dawo, babu wanda ya san tana da aure. Rannan ta ce min, "Batulu Allah ya sa Yayanki lafiya yake, ni dai in yana lafiya zuwa ne kawai ba zai yi ba, to falillahil hamdu, zan ci gaba da jiransa daga nan har gaban abada!. Sai dai in shi ya dawo ya ce ba ya aure na”. Turaki ya kauda kai sabida hawaye da suka ciko idonsa. Ya ce, “Wallahi Batulu, ban taba kinta ba, ban taba jin tsanarta a zuciyata ba. Kawai aurenta ya yi min wuri kuma ina son in ji ina son mace kafin in aure ta, sai aka yi min aure na gaggawa, sannan ban samu nutsuwa da isasshen lokacin da za mu fahimci juna ba ina tsaka da shirye-shiryen tafiya ta. Bayan na tafi kullum da tunaninta nake kwana nake tashi. Ban taba kawo wa a raina Maimartaba zai taba tunanin raba auren mu ba ko shekara goma zanyi ban dawo ba. Da ban yi wannan dadewar ban dawo ba. Abin da raina ke gaya min kullum aurenmu na har abada ne, babu abin da zai raba shi, kuma dukkan obstacles din da ke cikinsa da sannu zan shawo kansu. Zan bai wa kawarki mamaki Batulu, wannan sabon Abubakar ne, ba wanda ta sani a shekarun kuruciyarta ba”. Batulu ta san duk abin da yake fadi, har zuciyarsa yake nufi. Amma can a kasan ranta ta san ta yi masa nisa, nisan da ba ta san ranar da Allah zai hada su ba, don kuwa Goggo ta ce mata, ita ko sunan garin da ta ke ba ta sani ba. Daidai lokacin da suka kawo gidan Malam Jibo, ta ce ya tsaya a kofar gida ta fara shiga. Ba ta jima da shiga ba ta fito, ta ce, Goggo ta ce ya shigo. Sabuwar tabarma Goggo ta fiddo ta shimfida masa, ta rasa a wane yanayi ta tsinci kanta. Yau Turaki ne da kansa ya biyo sawun Kulsumunta! Ko ya ya za ta ji in da a ce tana nan? Ita shaida ce kan cewa har gobe Kulsumu na son mijinta. Ba ta da zabi ne cikin hukuncin da iyayensa suka yanke musu, sannan kawaicinta ba zai bari ka san abin da ke zuciyarta ba. Muryar Turaki ta yi sanyi a lokacin da yake gayar da Goggo. Ya rasa me ya sa jikinsa ya yi la’asar, watakila hakan na da nasaba da alamun babu giftawar Kulsumu cikin gidan da ya gani. Goggo ta ce, “Matafiya an dawo kenan? Da fatan an samu nasarar abin da aka je nema?” Yana cikin amsa mata Baffa ya yi sallama ya shigo gidan. Da tocilan din hannunsa ya haska Turaki amma bai gane shi ba, domin bayan girma da Turaki ya kara ya ajiye kyakkyawan sajen da ba shi da shi a baya. Fatarsa ta wanke ta yi smooth sannan ta kara yin fresh da ita. Ya ce da Goggo, “Baki muka yi ne? daga ina, ban waye da su ba”. Batulu ta yi zaraf ta ce, “Baffa Yaya Turaki ne fa”. Kan Turaki na kasa, ya rasa inda zai sa kansa da kunyar wadannan dattijai. Baffa ya ce, “Turaki dai? Turakin da na sani? Na Kulsumu?” Ba zai iya fadin yadda wannan sentence din ya taba zuciyarsa ba (Turakin Kulsumu). Wasu hawaye marasa dalili suka sake ciko idonsa. Ya gurfana gaban Baffa ya soma ba shi hakuri a bisa laifinsa na kin dawowa gida kamar yadda ya alkawarta wa iyayensa. Sannan ya ce, “Baffa ni da bakina ban saki Kulsumu ba, amma tunda shari’a ce ta raba auren, kuma Kulsumu ta yi min idda na zo da kokon barana ina rokonku ku dawo min da Kulsumu dakinta. Insha Allahu ba zan ba ku kunya ba, zan rike Ummu-Kulsum da soyayya da amana har karshen rayuwarmu. Baffa Maimartaba da Umma sun ce ba za su sanya baki ku dawo min da Ummukulsum ba, kada su tirsasa ku. Baffa ni a kan-kaina na zo bikon matata, ku yi min uzuri ku karbi hanzarina, ku ba ni dama ko da ita ce alfarma ta karshe da za ku yi min a kan Ummu-kulsum”. Baffa da Goggo suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Batulu ma hawaye ta ke yi, ta ce. “Baffa don Allah ku yi wa Yaya Turaki alfarma, ni shaida ce a kan cewa yana son Kulsumu, ko da ma can Baffa shi fa ba wai ba ya sonta ba ne, kuruciya ce da kuma karatun nan da ya sa a gaba, don Allah Goggo ki ba wa Baffa hakuri”. Goggo ta nisa ta ce, “Batulu sarkin manyance, mu ai ba mu yi fushi ba, kuma ba mu muka ce a dawo da Kulsumu ba, hukuncin na Maimartaba ne”. Batulu ta ce, “To Goggo ku barsu su shirya da kansu. Idan suka shirya kansu Maimartaba sai ya fi kowa farin ciki”. Baffa ya dubi Turaki, duk sai ya ba shi tausayi, ya ce, “Abubakar, shi sha’ani na tsallake maganar iyaye da ma karshensa nadama. Na ji dadi da ka fahimci ka kuskurewa iyayenka, kuma ka dawo ka nemi afuwarsu. Har kake son gyarawa. Amma zancen nan da nake maka Kulsumu ba ta gidan nan…”. Da sauri Turaki ya dago lumsassun idanun sa ya dora a kan tsohon, hasken farin wata na kara musu walainiya. Baffa ya karashe zancensa da cewa, “Kulsumu ba ta garin nan ma bakidaya!”. Dukkansu babu wanda bai ji nannauyar ajiyar zuciyar da Turaki ya sauke ba. Ya ce, “Tana ina Baffa? Ko ina ne zan bi ta”. Da muryar da Batulu ta kasa amincewa cewa tasa ce. Goggo ta yi saurin cewa, “Ai an ce ma sun bar kasar, ‘yar Yayata ce ta tafi da ita. Ni kuma ban ma rike sunan kasar ba, Baffa ya ma sunan kasar?” Baffa ya ce, “Ke ba ki rike ba balle ni? Ko Yagwaslabiya ne ko me? Oho!” Saura kadan Batulu ta yi dariya ganin Goggo da Baffa sun dage suna son tunawa juna kasar da Kulsumu ta tafi, amma an rasa mai tada daya. Turaki wanda ke jin wani tukuki a ran sa kamar ya hadiyi zuciya ya huta ya ce, “Babu lambar wayar wadanda suka dauke ta din?” Goggo ta ce, “Yo mu ina muka ga waya? Suna da waya kuwa, don da ta zo na ga tana magana da ita, amma ban yi azancin karbar lambar ba. Amma Turaki ka kwantar da hankalinka, duk karshen shekara za ta kawo ta gida hutu”. Turaki ya ce, “Goggo idan ta zo ba na nan fa? Ni din ba mazauni ba ne, a can inda na yi karatu na samu aiki, da ma zuwa na yi in dauke ta mu koma tare”. Baffa ya ce, “To insha Allahu duk ranar da Allah ya kawo su za a karba maka lambar waya a ajiye. Ko yarinyar nan Batulu za a kira a ba ta”. Jiki a salube cikin mutuwar jiki da yankewar buri Turaki ya baro gidan su Kulsumu, Batulu ta tausaya masa halin da ta ga ya shiga. Har suka zo gida bai iya ce wa komai ba. Batulu ta kwashe duk abin da ya faru gidan Goggo ta labarta wa Umma. Tana mai tausaya wa halin da dan uwanta ke ciki. Umma ta yi dan murmushi, ta ce, “Daga baya ke nan!”. Daga wannan ba ta kara tofawa ba. *** *** *** Washegari Goggo ta kira Hajiya Nasara ta ce, “Nasara jiya sai ga mu da babban bako, mijin Kulsumu daga Turai ya zo biko”. Hajiya Nasara ta ce, “Ina fatan dai Goggo kin bi shawarata ba ki gaya masa inda ta ke ba?” Goggo ta ce, “Ai na fahimci abin da ki ke nufi Nasara, cewa muka yi ma ba ta kasar, daga ni har Baffa kuma ko sunan kasar da ku ke ba mu sani ba. Amma gaskiya Turaki ya ba ni tausayi, sai da na ji kamar in ba shi lambar wayarta, amma na ce bari in fara shawara da ke tukun kada in bata lamari. Amma mai zai hana mu maida mishi matarshi ta yi karatun a dakinta Nasara? Aure fa yana gaba da komai, kuma na san ba za su hana Kulsumu karatu ba”. A tsanake Hajiya Nasara ta ce, “Goggo, kada ki yi saurin karaya. Mijin Kulsumu yana bukatar a ba shi lokaci ya tantance tsakanin fari da baki a cikin aurensa da Kulsumu. Ma’ana, baki da tabbacin zai maida ta ne don ya faranta wa iyayensa ko don yana sonta. Sannan ita ma Kulsumu akwai bukatar ta kara hankali, wayewa da nutsuwa kafin ta zaba wa kanta hukuncin komawa gidan mijinta ko yin sabon aure. Goggo ki daure ki ci gaba da ba ni hadin kai tukunna, ki cire tausayin Turaki a ranki. Shi bai tausaya wa jikarki ba ya tafi ya barta shekara da shekaru a dakinsa ba sako babu kulawa? Ni ban yarda yanzu sonta yake ba, na fi yarda da cewa so yake ya gyara tsakaninsa da iyayensa. Ki kyale Kulsumu na dan lokaci ta kara sanin kanta, ta samu lafiyar jikin ta, ta yi karatunta sannan ta auri mijin da ke son ta ta ke son shi. Ra’ayi da tunanin su ya zo daya. Koda kuwa Turakin ne amma a can gaba. Sannan Turakin nan fa ba shi ne autan maza ba, ba'a ce bayan shi Kulsumu bazata auru ba wai don lalurar ta, kuma duk abin da ki ke hange a tare da shi akwai shi a sauran maza. Ki fahimce ni Yaya Aishatu, ba nufi na in hana Kulsumu aure ba, amma don Allah ki kara mata lokaci. Na yi miki alkawarin ranar data zama cikakkiyar Nurse zan dawo miki da ita ta zabi mijin aure. Alhamdu lillahi ta samu lafiyarta wadda ya guje ta a kanta bai kamata don ya zo ya marairaice muku tashi daya ku yi saurin amsa masa ba, gara ya san Kulsumu mace ce mai daraja ya kuma san cewa akwai bambanci tsakanin mai lalurar da ya guda da wannan ta yanzu”. Goggo ta rausayar da kai, ta ce, “Duk na fahimce ki, na kuma yarda da shawarar ki. Sai dai ba mu da hujjar cewa Turaki ya guji Kulsumu ne sabida lalurarta. Sun auri Kulsumu a kan sanin cewa tana da lalurar. Aure ne dai in Allah ya kawo karshensa dan Adam bai da dabara, amma na yarda da hujjojin da ya bayar kwata-kwata ba su da alaka da lalurar ta”. Hajiya Nasara ta ce, “Shi ke nan. Allah shi ne masanin gaibu, amma maganar komen nan ki manta da ita Goggo, cikin watan nan Kulsumu za ta fara karatunta, ina rokonku don Allah ku manta da Turaki. Can gaba in suna da rabon komawar sa koma idan tana son shi yana sonta cikin nutsuwa da cikakken hankalin su, Allah ya yi wa Kulsumu zabi mafi alkhairi”. Goggo ta ce, “Amin Nasara, insha Allahu yadda ki ka ce, haka za a yi”. *** *** *** Umma ta shiga turakar Maimartaba a daren ranar a matsayinta na mai girki a ranar. Bayan ya gama cin abinci ta ke labarta masa yadda Batulu ta ba ta labarin zuwansu gidan Malam Jibo ita da Turaki, Maimartaba ya gama sauraronta tsaf! Sannan ya yi murmushi ya ce. “Kin ga hikimar da na yi ta zare hannunmu daga cikin maganar ta fito zahiri ko? Sun dauke ‘yar su zuwa inda za ta samu kwanciyar hankali ta yi karatun da suke so ta yi, ta auri miji mai sonta tsakani da Allah. Yau da mun saka baki da mun shiga hakkinsu, kunyarmu tasa su dawo da ita ya zo ya sake ba mu kunya, ya sake tafiya ya barta, don ya ce min ashe aiki ya samu a can din amma bayan shekaru uku zai dawo gida gabadaya. Rakiya raba kanki da sha’anin Turaki, in ya damu ya je ya nemo ta a inda iyayenta suka boye ta. Ya karbi aurenta a hannunsu da kansa, in sun amince mu sai mu bi su da addu’a, amma kada ki sake sa baki a sha’anin Turaki, wanda muka yi a baya ya bula mana kasa a ido, Allah ya ba mu lada”. Umma ta ce, “Ai na cire hannun nawa ranka ya dade, na dai kasa cire yarinyar a raina ne. Ni na san na yi asarar surukar kwarai mai son Turaki da zuciya daya. Zan bi su da addu’a Allah ya yi musu zabin alkhairi dukkanninsu. Allah ya sa watarana Kulsumu za ta dawo min”. Murmushi Maimartaba Sarkin Gaya ya yi, ya ce, “Mata kuna son kanku da yawa, sannan kuna saurin manta girman laifin ‘ya’yan ku. Ni kuma na fi yi mata addu’ar Allah ya ba ta miji mai sonta ba Turaki ba, har yanzu ban gasgata wannan sabuwar soyayyar tasa ta dare daya ba, ya ce tunda ya tafi ya soma sonta, me ya hana ya dawo ya gyara laifinsa a lokacin da ya dace?” Umma ta ce, “Haka Allah ya rubuta masa ranka ya dade, ko mun yi niyyar yin abu sai Allah ya nufa, ko ni ka shammace ni ban taba zaton za ka raba auren nan ba komai dadewar da Turaki zai yi. Sabida jikina na ba ni komai daren dadewa Turaki zai so Kulsumu, domin na mika lamarin su ga Ubangiji, kuma na tabbatar da ya karbi budurcin ta ranar da zai tafi. Kuma Alhamdulillah inada yaqinin wannan ne ya zama silar canzawar zuciyar sa a kanta”. Maimartaba ya tsura mata ido, bai ce komai ba, amma can a karkashin zuciyarsa ya fara nadamar tsatstsauran hukuncin nasa, da ta yi masa wannan bayanin tun farko da ya yi wani hukuncin da bai kai raba su tsauri ba. Bai san cewa Turaki ya bi umarninsa ba ya tabbatar da auren sa kafin ya tafi. Ya soma zargin kansa da yin zalunci ga karamar yarinyar da ya mayar bazawara a kananan shekarunta. Amma da ya tuna ya yi ne bisa kyakkyawar niyya ta adalci ga talakawansa sai ya rage zargin kan nasa. *** Watanni biyu Turaki ya kwashe cikin iyayensa da ‘yan uwansa. Duk wata ‘yar uwarsa da ke gidan aure sai da ya kai mata ziyara. Wajen aikinsa na ta nemansa, don haka ya kara neman izinin iyayensa kan ya koma U.K, ya kammala consultant ya baro aiki da su ya dawo gida bakidaya. A kan wannan alkawarin suka amince masa ya koma. Batulu har kuka ta yi sosai da zai tafi. Bai tafi ba sai da ya je ya yi wa Goggo sallama ita da Baffa, yana kara yi musu tunin lambar waya idan su Kulsumu sun zo, ya yi alkawarin ko a wacce kasa suke zai bi Kulsumu. Baffa dai sai da ya ji kamar ya ba shi lambar, amma ya tuna rokon da Nasara ta yi ta yi masa a waya kan kada ya bayar din. Ya sani ita mai nufin alkhairi ga Kulsumu ne. Ta yi hakan ne da kyakkyawar manufa ba don ta hana ta zaman aure ba. Ranar da ya tafi ne kuma aka sauke musu buhunhuna da katon-katon na kayan abinci. Sai da aka cika dakin da Baffa ke ajiye shirginsa. Sako ne daga Turaki, da kudi masu yawa cikin ambulan. Baffa ya ce da ‘yan aiken su mayar masa da kudin ba zai karba ba, inda suke gaya amsa ai Turaki ya riga ya bar garin Gaya zuwa inda ya fito. Haka ya wuni da jimamin abin. Goggo ta ce za ta je ta yi wa Hajiya Rakiya godiya, Baffa ya yi hakuri kawai ya karba don bai kamata su mayar wa Hajiya Rakiya ba. Ko da ta je yi wa Umma godiyar cewa ta yi, “Haba Hajiya Shatu, Turaki ai dan ku ne, don ya yi muku alheri ba sai na sani ba. Don Allah kada irin haka ta sake faruwa ki ce za ki yi min godiya, tsakaninku ne da Dan ku, ni babu ruwana”. *** *** *** LAGOS Saukarsa ke nan a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke garin Lagos. Wankan tarwada ne makimanci ga kyau. Ma’abocin yalwar murmushi, irin mutanen nan ne masu jovial personality. Babu ta yadda za a yi daga kallo na farko ka sanya shi a jerin kyawawa, amma annurin fuskarsa da cikar zati ya isa misali. Sanan yanayin fatar jikinsa abin so ne ga duk namijin da Allah ya baiwa. Alamun yawaitar murmushi, wani personality ne da ba kasafai ake samun maza da shi ba. Navy Officer TAWFEEQ MUHAMMAD BELLO yana saukowa daga matattakalar jirgin yana kokarin roaming layinsa domin ya samu ya kira ‘yar uwarsa da shi. Ya sanar da ita saukar sa. Waje ya samu ya zauna a reception na filin jirgin yana ci gaba da danne-danne a wayarsa. Sanye yake da grey suit da jan neck-tie a wuyansa. da kyar ya samu ya yi roaming layin. Ya dannawa ‘yar uwarsa Sakeenah kira. “Kin shanya ni, and you know na tsani jira, ban da Hajiya da ta ce in tsaya in tafi mata da sako a wajenki ko kyalli na ba za ki gani ba, kin sani”. Cike da damuwa Dr. Sakeenah ta ce, “I’m so sorry Yaya Taufeeq wallahi I’m on call. Amma yanzu Baban Waleed zai zo ya tafi da kai, na gaya masa kuma ya taho”. Ya ce, “Ni ba zan kwana a gidanku ba, ki gaya masa hotel zai kai ni, bana son jayayya da wannan kafaffen mijin naki”. Murmushi ta yi cikin lallashi, don ta saba da rigimar Yayan nata, ta ce, “Amma at least ka shigo gidan nawa ka ci abinci ka huta. Na shirya maka better, my king brother, my very own Bachelor Brother”. Dole tasa shi yin murmushi. Sakeenah is his favourite sister. An san sako da sako da rigima da juna, amma shi Sakeenah kullum lallaba shi ta ke, duk abin da ta san yana so shi ta ke masa, ko ya yi fushi da ita fushin ba ya zuwa ko’ina. To yau ma hakan, ta kare zancenta da cewa. “Zan iso gida kafin awa daya, kuma gidan akwai mutane. Na sa Kulsum ta shirya maka table. Please smile at me (ka yi min murmushi). I assure you zan hango shi daga nan inda nake a dakin haihuwa”. Murmushin ya yi ba don ya shirya yinsa ba, ya ce, “O.K, see you then”. Ya kashe wayar da ya hango Engnr. Farouq na karasowa. Mikewa ya yi ya tadda shi suka kama hannun juna cikin musabiha. Farouk ya dauki jakarsa wadda ba ta cika nauyi ba suka nufi motar da ya zo da ita suna kara gaisawa da tambayar lafiyar su Waleed. Kararrarwar shiga falo Farouq ya danna, daga ciki ta amsa da siririyar muryarta. “Ana zuwa”. Cikin nutsuwa ta murda mukullin tare da yi wa Baban Waleed barka da zuwa, ba ta lura cewa ba shi kadai ba ne. Ya ce, “Ina ‘ya’yan naki na ganki ke kadai?” Dan murmushi ta yi, ta ce, “Muna homework da su duk suka yi bacci”. Sai a lokacin ta ankara da bakon da ke bayansa. Ta kara nutsuwa tare da ja da baya ta ba shi hanya tare da cewa, “Barka da zuwa”. Taufeeq ya kalle ta sau daya ya dauke kai, ya sako kafa cikin falon. Ko kadan ba ta ji dadin yadda ya yi mata ba. Ba ta san cewa shi naturally haka yake ba, ba ya sakar wa mata fuska. Sannan baya yi musu kallo na biyu. Daga uwarsa sai kannensa biyu. Duk yawan murmushinsa ya san a inda yake yinsa. Wucewa ta yi dinning tana kara gyara musu komai kafin ta wuce daki. Amma tana shiga Engnr. Faruoq ya kwala mata kira, “Kulsum!” Ta amsa tare da fitowa a tsanake tana sanye da doguwar riga ta atamfa (Hitarget) mai ruwan jinin kare, ya ce, “Zo nan”. Ta matso har inda ya kira ta ya nuna mata farfesun naman Sa da taliya da miya da ta aje musu, ya ce, “Taufeeq vegetarian ne, ba ya cin nama, ki hada masa salad da orange juice kada ki sa sukari. Kwashe wadannan din ki tafi da su”. Gabanta har faduwa yake sabida wani kallo da Taufeeq din ke mata shi ba na raini ba, shi ba na mutunci ba. Tana shiga kitchen din ta debo lemon zaki (orange) guda shidda manya ta yanka ta soma matsewa a juicer kamar yadda Sakeenah ta koya mata. Nan da nan ta gama. Allah ya so ta iya hada salad din, nan ta yanka shi manya-manya ta yanka cocumber, tomatoe, cabbage da karas ta yi masa hadi yadda Sakeenah ke yi, tana so ta saka mayonnaise tana tsoron kada ta yi ba daidai ba, ga shi ba za ta iya tambayarsa ba, don yadda ta ga wannan Taufeeq din ba sauki kuma ba wargi ba kamar Baban Waleed ba. Haka ta dauko salad din da mayonnaise din daban ba ta zuba a kai ba ta kawo musu. Ta koma ta dauko juice din cikin jug din da ta juye shi ta jefa kananan kankara a ciki ta kawo ta aje, Taufeeq na dannan wayarsa bai kalleta ba har ta gama, ta tambayi Baban Waleed ko suna bukatar wani abu? Ya ce babu, ta je sun gode, Allah yai mata albarka. Ta wuce daki tana amsawa a zuciyarta. Suna fara ci Sakeenah ta shigo, kai tsaye Taufeeq ta dosa tana ta zuba murmushi. "My king brother Ya Taufeeq, ina fatan ka zo lafiya, kayi hakuri bai kamata in je ofis ba yau tunda na san za ka zo, believe me.... emergency call ne" (ka yarda da ni kiran gaggawa ne). Bai ce mata komai ba sai shan lemonsa yake yi. Ta narke fuska. “Ya Taufeeq, please smile at me, saboda kai fa na baro aikina na taho”. A nan ne ya daga ido ya dube ta. “Kin ce kin shirya min better, wannan ne bettern? Kin sa ‘yar aikinki ta kawo min nama, juice an zuba kankara bayan kin san ni ne zan ci”. Sakeenah ta zaro ido, “Ya Taufeeq ba ‘yar aiki ba ce, niece dinmu ce, ina sauri an kira ni on emergency (kiran gaggawa) na bar mata girkin, and she don’t know your problem (bata san matsalar ka ba), don Allah ka yi hakuri”. Haka dai ta samu ta lallaba shi. A ranta tana fadin, “Rigimamme”. Har dare suna falon suna ta hira, Kulsumu na kicin tana musu girkin dare, lokaci-lokaci Sakeenah na zuwa ta duba aikin nata. Sosai ta ke jinjinawa kwazon Kulsumu don duk abin da ta koya mata sau daya ta dauke shi ke nan. Wayar Hajiya biyu tana jaddadawa Sakeenah kafar Taufeeq kafar Kulsum zuwa Abuja, ta hado su su taho tare. An fara sayar da form na School of Nursing Kulsumun za ta cike nata (FCT School of Nursing, Gwagwalada). “Ka tashi ka kai ni Hotel in samu in huta, gobe asubanci zan yi. Na matsu in gan ni gaban uwata”. In ji Taufeeq yana kallon Engnr. Farouq. Farouq din ya ce, “Babu fa inda zan kai ka, alhalin ina da dakin baki”. “Sai in zauna kuna ba ni abincin ‘yar aiki?” Sakeenah ta dube shi cikin takaici. “Na fa gaya maka ba ‘yar aiki ba ce Ya Taufeeq, jikar kanwar Babar Hajiya ce da Hajiya ta dauko a Gaya. Don Allah kar ka sake fadi, in ta ji ranta ba zai yi dadi ba. Tunda ka zo ba ta zauna ba tana ta hidima da kai, amma kana kiranta ‘yar aiki. Haba! Haba Ya Taufeeq ban sanka da wulakanta mutane ba”. Jikin sa ne ya yi sanyi, duk da bai fada ba, ya ce, “Dauko min sakon Hajiya in wuce, Allah ba zan kwana gidanku ba. Haba suruki ne ni fa!”. Dariya Farouq ya yi, ya ce, “A inda babu surukai ko?” Sakeenah kuma ta ce, “Ai Kulsum din ita ce sakon da za ka daukan”. “Ban gane ba?” Ya fada yana hararar ta. Ta yi murmushin mugunta don ta san halinsa ba ya hada hanya da mata. Ta ce, “I mean Hajiya cewa ta yi ka tafi mata da 'yar ta Kulsum Abuja, kafarka-kafarta”. “Da tare muka zo?” “Sai ka tambayi Hajiya, in ba za ka dauka ba sai in gaya mata”. Mikewa ya yi tare da daukar wayarsa bai ce komai ba. Amma har zuciyarsa ransa ya baci. Da ya san sakon kenan da ba zai tsaya gidan Sakeenah ba. Farouq tashi ya yi don ya kai shi inda yake so, ya san sarai ba zai yarda ya kwanan ba tunda an bata masa rai. Dr. Sakeenah ta shigo daki ta samu Kulsumu na hada kayanta, tun safe Hajiya ta gaya mata yau za ta koma Abuja, an fara saida form din makarantar da za ta shiga. In ta ce ba za ta yi kewar Sakeenah da iyalinta ba ta yi karya, musamman Waleed da Waleeda. Sun yi zama na mutunta juna da amana ita da Dr. Sakeenah, kuma Sakeenah ta yi mata gata da taimakon da har abada ba za ta manta ba. Ita ce silar samun saukin ta daga lalurar fitsarin kwance, lalurar da ta yi ta fama da ita tun haihuwar ta, ta hana ta jin dadin rayuwar aure. Don haka ba za ta taba mantawa da wannan taimako da iyalin Hajiya Nasara suka yi mata ba. Sakeenah ba ta tsaya a taimako ga lafiyarta kadai ba, har ga sauran fannonin rayuwar diya mace ta taka rawar gani wajen inganta mata. Girki, tsaftar jiki da ta muhalli, kwalliya da duk abin da zai amfani mace Sakeenah ta koya mata. “Wato Kulsumu farin ciki ki ke za ki bar mu shi ya sa ki ke ta faman tattare inaki-inaki”. In ji Dr. Sakeenah tana mai zama a gefenta. Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai, sai ga hawaye sun zubo. Ta kama hannun Sakeenah ta rike cikin tafukanta, ta ce, “Doctor, na gode. Na gode, wallahi bana farin ciki, zan yi kewarku sosai. Musamman su Waleed”. Sakeenah na dariya ta ke share mata hawaye ta ce, “Ni ma na gode Kulsum, Allah ya ba ki ilmi mai amfani ya kuma ba ki abokin rayuwa na gari. Na ji dadin zama da ke. Insha Allahu duk sanda ku ka samu hutu zan roki Hajiya ta ba ni ke, mu ma in mun samu sararin aiki za ki gan mu a Abuja insha Allah”. Ta je dakinta ta shigo da akwati shake da kaya, ta ce, “Ga kaya na sa an dinka miki kala goma ne, za su yi miki amfani, saboda zuwa makaranta, kowanne da gyalensa, ga takalma da jaka set biyar ki yi amfani da su”. Duk sai ta rasa da bakin da za ta gode. Aunty Sakeenah ba ta da abin da za ta gode mata da shi sai addu’ar alkhairi gare ta da zuri’arta. Washegari Baban Waleed ya je ya dauko Taufeeq don ya yi kalaci, sannan su kai su airport. Kafin su gama Kulsumu ta kimtsa komai nata. Da ma tun bakwai na safe ta yi wanka. Daya daga cikin swiss laces din da Sakeenah ta dinka mata ta saka mai ruwan zuma da ratsin coffe. Lokacin da ta fito falo jaye da katuwar jakarta. Taufeeq ya daga kai ya kalle ta, sai ya ga jiya ashe kallon tsoro ya yi mata. Duk inda ake neman kyakkyawar mace ta kai, iyakaci a ce ba ta da wayewa irin ta matan birni. Baban Waleed ya karbi akwatin daga hannunta bayan sun gaisa. Tana so ta gaida Taufeeq babu fuska. Dr. Sakeenah ta ce, “Kulsum ba ki gaida brothernki ba”. A sanyaye ta ce, “Barka da safiya”. Irin gaisuwarsu ta gidan Sarkin Gaya. Ta riga ta saba ba ta iya gaisuwar ina wuni ko ina kwana ba, sai dai ta ce barka da asubah, barka da yamma, ko barka da rana. Ko ya amsa ko bai amsa ba ita ba ta sani ba. Sai da suka ajiye su Waleed a makarantarsu suna fadin, “Aunty Kulsum yau in mun dawo tuwo za ki yi mana irin na rannan”. Ta juya ta share idonta ta yi musu murmushi, sannan ta ce, “Toh insha Allahu Waleed. Ka yi karatu mai yawa, ka zama Doctor irin Mummy”. Suna waving dinta, ita ma tana waving dinsu, Engnr. Farouq ya ja motar suka bar filin makarantar yaran zuwa filin jirgi. Sun yi sa’a akwai jirgin da zai tashi zuwa Abuja nan da awa daya, Taufeeq ya yankar musu tiket guda biyu, Sakeenah da Farouq suka yi musu sallama suka tafi don duk wajen aiki za su. Suka zauna a waiting lounge ba mai ce da dan uwansa komai. Taufeeq wayar hannunsa yake daddannawa, da alama he is addicted to that, ita ma wayar ce a hannunta, amma game ta ke yi. Daga baya ta bude jakarta ta jefa ta. Ta dauko dan karamin littafin Alma’asurat tana karantawa. Ba jimawa aka kira su kowa ya tashi, wayar Taufeeq ta zame daga aljihunsa ta fadi kasa ta tarwatse. A tare ita da shi suka sunkuya suna tsincewa. Ta dago tana mika masa battery din wayar ne suka hada ido. Kallo kai tsaye cikin idanunsu. Taufeeq ya rasa me ya hana shi janye idonsa daga na Kulsum, samun kansa ya yi da ci gaba da kallonta. Ita ta fara dauke idonta ganin kowa ya fita daga lounge din sai su biyu. Ya daga kafa ya bi bayanta yana tambayar kansa, “What’s wrong with me? Wannan kallo haka!” A kujerun da ke daura da juna suka zauna, tana daga jikin taga yana gefenta, tana zama tasa ear-piece a jikin wayarta tana sauraron kira’a. Ana ta fadin a daura belt Kulsum ba ta san ana yi ba, sai bude ido ta yi ta ga hannayen Taufeeq zagaye da ita yana fastening mata belt din. Kamshin turarensa ya sa tsigar jikinta tashi ta yi catching breadth dinta sharply. Har jirgin ya bar kasa ba ta yi regaining mood dinta ba. Ji ta yi duk jikinta ya saki. Ba ta taba zama so close da namiji ba irin haka. A take wani tunani ya fado mata a rai, "TURAKI" da abin da ya faru tsakaninsu… that fateful day...... Sosai ta matsa jikin taga ta takure jikinta, ta runtse idanunta. Ta kara sa wa a ranta ba ita ba MAZA! Dukkansu mugaye ne. Amma hakan bai hana wani sako na zuciyarta lakewa a gefe ya yi tunanin Turaki ba lokaci-lokaci. Zamanta daura da Taufeeq a cikin jirgi, duk memories din Turaki ya kawo mata. Ganinsa ta yi ma yana rikidewa yana komawa Turakin. Ta rasa wane irin masifaffen so zuciyarta ke ma Turaki. Ta tabbata zuwa yanzu shi ya mance da ita, amma ita ta kasa manta shi, ko ta yi kokarin hakan ba ta cin nasara. Idan maza sun yi dubu a duniya Turaki ne kadai karbabbe ga zuciyarta. Duk tarin laifuffukansa zuciyarta uzuri ta ke masa a lokuta da dama. Sai dai ta san ko a lahira suka sake haduwa ba za ta sake bari ya shigo cikin rayuwarta ba. Ya yi mata laifin da ba za ta iya yafe masa ba, wanda sai yanzu da hankali ya kara shigar ta ta gane hakan. Ta gane ya kwanta da ita ne out of hatred. Sannan bisa dole. Ya raba ta da tinkahonta na diya mace, sannan ya tsallake ya barta cikin wani hali na neman agaji, amma bai tausaya mata ba, sannan bai agaza mata ba, still tunda ya tafi bai kara waiwayarta ba. Duk da haka zuciyarta mara mafadi is craving for him… ai ko shi ya saura Da namiji a duniya za ta yi yaki da ita wajen ganin ta fidda shi daga cikinta. Har suka sauka a Abuja tunanin da ta ke ta yi kenan. Yusha'u Hajiya ta turo ya dauke su zuwa gida. Taufeeq na lura da mood dinta, tunda suka taho ba ta walwala, kamar ta fi son ta zauna a Lagos din ne ko mene ne? Bai sani ba shi. *** *** *** ABUJA Tarba ta musamma Kulsumu ta samu daga Hajiya, har ta fi murna da dawowarta a kan ta Taufeeq. Abinci kala-kala ta sa Serah ta shirya musu a dining. Hajiya ta aika Serah dakinta ta ce ta kirata ta ci abinci in ta huta. A lokacin ta fito wanka tana shafa mai Serah ta iske ta da sakon Hajiya. Doguwar riga kawai ta saka ta yafa veil din rigar ta bi bayan serah. Ta zauna kenan ta fara zuba fried rice a faranti, Taufeeq ya shigo falon. Kai tsaye dining din ya nufo ya ja kujera mai fuskantarta ya zauna. Shi ma ya yi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa T/Shirt DKNY ruwan goro da bakin wando chinose. Da ka ganshi ka ga Alhaji Muhammad Bello, wanda asalinsa bafullatanin Adamawa ne, kuruciya kawai ya fi shi, kwata-kwata ba ya kama da su Nasmah, ya fi su dogon hanci da kwantacciyar suma, su kuma sun fi shi haske. Tunda ya zauna sai ta samu kanta da kasa cin abincin da ta zuba, sai juya cokali ta ke cikin shinkafa, tana kallonshi yana ta loda vegetables a kan 'yar shinkafar da ya zuba. Ya gama ya fara ci, yana satar kallonta. "Yanayin yarinyar mai sanya tausayi ne," Taufeeq ya fada a ransa, sam ba ta da rawar kai irin wanda 'yammata tsararrakin ta ke da shi, sannan akwai tarin nutsuwa tattare da ita da wata irin kamala da bai taba gani tare da mace ba. Yana kallo ta dauke farantin abincin ta ta nufi dakin ta. Wannan na nufin; ba za ta iya cin abinci a gaban shi ba. Wanda ya nuna ita din mai kamun kai ce. Ya ji yana son yi wa mahaifiyarsa tambayoyi a kanta, yana son sanin komai na rayuwar ta. Shi da Hajiya ne a uwar dakin Hajiyar a daren ranar suna hirar abubuwan da suka baro a UK, Hajiya ta ce, “Don me za ka ajiye aikinka Taufeeq? Idan ka zo nan ka zauna me za ka yi mana? Ga Daddy shi ma tunda ya yi ritaya ba wani abu yake yi ba da pension dinsa kawai yake amfani”. Taufeeq ya ce, “Mum I cannot endure the loneliness (ba zan iya jure kadaicin ba). Baban wani abokina ya sa an yi min transfer zuwa NIGERIAN NAVY, ina jiran su kira ni”. Hajiya Nasara ta ce, “Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi”. Taufeeq ya ce, “Amin Mum… ita wannan yarinyar da na dauko daga gidan Sakeenah wace ce dinki? Ko ita ce yarinyar da Nasmah ta ba ni waya in kawo mata?” Hajiya Nasara ta ce, “Kulsum ba, ita ce. Jika ta ke ga kanwar mahaifiyata ta Gaya, ai ka san Goggo Aishatu da nake ba ku labari? An yi mata aure ne da Dan Sarkin Gaya, auren bai je ko’ina ba, shi ne na dauko ta don ta ci gaba da karatu nan a gabana. Gobe da safe za ka kaita ta sayo form din school of Nursing, Gwagwalada”. Taufeeq ya ce, “Kamar ya ya auren bai je ko’ina ba? Mijin ya sake ta ne?” Hajiya ta girgiza kai, “Bai sake ta ba, iyayensa ne suka raba auren. Ya tafi karatu Turai ya ki dawowa”. Taufeeq bai kara magana akai ba, wani zancen daban ya koma yi. Amma cikin zuciyarsa sai ya ji yana tausaya wa Kulsumun, karamar yarinya da ita an maida ita bazawara. Matsalar 'ya'yan sarautar nan kenan. Washegari da safe Kulsumu na yi wa Hajiya Nasara gyaran daki, ta ce da ita ta shirya Taufeeq zai kai ta sayen form. Haka nan dai ita ba ta son hada hanya da Taufeeq dinnan, kallon idanunsa na sa wa ta ji wani iri a ranta. Za ta so a ce ba shi zai kai ta ba, Hajiyar ce da kanta ko direba ko Serah ta raka ta, amma ba za ta iya yi wa Hajiya musu ba. Dole ta shirya cikin daya daga kayan da Sakeenah ta bata ta nemi hijab cikin kayan da ta zo da su daga Gaya ta dora a kai. Ta je ta ce da Hajiya ta shirya, ita kuma ta kira Taufeeq a waya, ya ce ta same shi a cikin mota yana waje. Suna tafe cikin motar Daddy (Honda 2015 model) babu mai cewa komai tun bayan da ta gaishe shi ya amsa. Sai da suka iso makarantar ya yi tambaya aka nuna musu inda za su je. A mota ya ce ta jira shi, ya je ya sayo ya dawo ya dora mata a cinya. A hanyarsu ta dawowa ya tsaya ya sayi abu a supermarket, sannan suka karaso gida. Ta bude kofar motar za ta fita, ya kira sunanta. Da dumbin mamaki ta juyo don ba ta san ya san sunan ta ba. Wani dan karamin farin kwali ya miko mata. Cikin taushin murya ya ce, “A message from Nasmah (sako daga Nasmah)”. Hannu biyu ta sa ta amsa, ta yi masa godiya ta shige cikin gida. Ya bi bayanta da kallo. Wani irin kallo da ya tabbata bai taba yiwa kowacce diya mace ba. A falo ta tadda Hajiya, ta ce, “Har an dawo?” “Mun dawo Hajiya, kin ga sakon da Nasmah ta aiko min”. Ta zauna gefen Hajiyar tana kokarin bude kwalin wayar. Murna fal kumatunta, Hajiya ta ce, “An gode wa Nasmah”. Ta fiddo wayar mai kyau da ita. Ta ce, “Hajiya ki aika wa Baban ‘Yalleman, ni sai in ci gaba da amfani da ta wajen Aunty Sakeenah”. Hajiya Nasra ta ce, “Ba za a yi haka ba, tunda ta saya da sunanki ki hada duka ki yi amfani da su, insha Allah zan bai wa Yusha'u wata ya kai masa har Gaya, sai Goggo ta ba shi”. Kulsum ta ji dadi sosai, wai ita ce mallakin wayar hannu har guda biyu rus! Na nunawa sa'a. Taufeeq Hajiya ta sa ya taimaka mata ta cike form din ta online. Babu jimawa admission ya fito, an dauke ta a FCT Nursing School. Duka wani shige da fice da Taufeeq suka yi shi, har ta fara shiga aji. Malam Yusha'u direban Hajiya ya ci gaba da kaita yana dauko ta, sabida shi ma Taufeeq din aikinsa ya fito ya yi joining Nigerian Navy, ya tattara ya tafi Lagos inda suka ajiye shi. Sai dai kuma ya tafi ne da Kulsum manne cikin ransa. Wani al’amari da bai taba faruwa da shi ba a kan diya mace. Tun daga ranar da Hajiya ta hada su zuwa sayen form ya kasa mallakar kansa a kan Kulsum. Sosai ta zauna cikin zuciyarsa, da ya ji labarinta kuma da yadda mijin ta ya tafi ya barta sai feelings dinsa a kanta ya karu. Da ma kuma tausayi yana taimakawa wajen kimsa so. Ya bar wa ransa komai don ya san yadda Hajiyarsa ta sa wa ranta son Kulsum ta yi karatu ba za ta taba aminta ba. Amma ko da ya kama aikinsa a Lagos sai nutsuwa ta gagare shi. A duk abin da yake yi Kulsum na gilma masa, tunaninta ya hana shi sakat, yana mamakin wane ne ya auri Kulsum ya kuma sake ta cikin hankalinsa? Wannan shi ake kira sauta ga wawa. Hajiya ba ta fito fili ta gaya wa Taufeeq lalurar da Kulsum ta yi fama a baya ba, kuma ba ta kafa hujja da ita a kan dalilin rabuwar aurenta ba, tunda su Goggo kansu ba su da tabbas a kan hakan. Ta barshi a yadda su ma suka barshi, wato ya tafi karatu ya ki dawowa, iyayensa suka raba auren. A rayuwar Taufeeq Muhammad Bello, bai taba haduwa da abin da ya tsaya masa a rai irin Kulsumu ba. Kulsumun da ba ta san yana yi ba, karatunta ta dumfara with much enthusiasm. Karatun kadai ta sa a gaba, shi ne goal dinta, ko ta so ta yi tunanin Turaki tana yakice shi ne da dukkan karfinta. Hajiya Nasara ta cika alkawarin da ta daukar wa Kulsum, ta aika wa Malam Hadi waya, don haka Kulsum ta zamo ba ta da damuwa, kullum tana tare da iyayenta da kakanninta a waya, in ta dawo gida. Ga Nasmah da Aunty Sakeenah su ma suna kiranta akai-akai. Sati uku da tafiyar Taufeeq sai ga shi ya dawo ba zato ba tsammani. Hajiya ta ganshi at a smart pace (afujajan), gabadaya ya zama tamkar ba shi ba. Duk ya birkice ba nutsuwa sam a tare da shi. Da Hajiya ta nemi ba’asin dawowarshi ba lokacin da ya kamata ya dawo ba, sai ya ce lafiya kalau. Ba ta kara maida hankalinta ta kanshi ba, sai ta sa Serah ta shirya masa vegetarian meal dinsa, lokacin Kulsum na makaranta. Taufeeq ya samu Daddy dinsa a falonsa yana shan gahwah, ya shigo falon ya samu wuri gefen Daddyn ya zauna, Alhaji Muhammad Bello ya dubi dan nasa cike da kulawa ya ce, “Ya aka yi ne Taufeeq? Na ganka ba'a yadda na saba ganinka ba, is anything wrong a wajen aikin?” Taufeeq ya sunkuyar da kansa yana tauna kalaman da zai furta wa mahaifinsa. Daddy bai katse hanzarinsa ba har sai da ya mula don kansa ya yi magana. “Daddy aure nake so!” Daddy ya hadiye mamakinsa ta hanyar murmushi, kafin ya ce, “Ka samu matar ne?” Taufeeq ya kara yin kasa da kai, ya ce, “Daddy, Kulsum nake so, ka roka min Hajiya ta ba ni aurenta. Na yi alkawarin zan barta ta ci gaba da karatu har sai ta ce ya ishe ta, aurena ba zai zama barrier ga neman iliminta ba, insha Allahu. Ka yi min alfarma Daddy ka roka min Hajiya, in ni na yi mata magana ba za ta amince ba”. Daddy ya gyada kai, ya ce, “Wai yarinyar nan da ta dauko a Gaya?” Taufeeq ya ce, “Ita Daddy”. Alhaji Muhammad Bello ya ce, “Da kyau, na yaba da hankalin yarinyar, ga ta ‘yar uwarka. Ka bar komai a hannuna in dai yarinyar ta amince Hajiyarku za ta fi kowa son al’amarin”. Amma ko da Daddyn ya furta zancen ga Hajiya Nasara, budar bakinta sai cewa ta yi. “Ba zai yiwu ba. Na dauko Kulsum don ta yi karatu ne ba don in aura wa dan cikina ita ba. In auren yake so ya nemo wata, amma ban da Kulsum, iyayenta sai su zarge ni da son kai. Don yanzu haka tsohon mijinta ma na ta bilinbituwar nemanta da kome, ni na ce kada a gaya masa inda ta ke, don dai mu samu ta yi karatun nan. Sai kawai yanzu in je in ce musu Dana zai aure ta ko shekarar farko ba ta rufa a karatunta ba?” Daddy ya dan tsura wa matar tasa ido, kafin cikin sanyin murya ya ce. “Can we wait for her?” Murmushi ta yi sabida yadda ya yi maganar cikin lallashi. Ta ce, “Za ku iya jira har ta kare Nursing School sai ku shiga jerin manema, in Allah ya sa ku ne da rabo sai ku samu, in kuma mijin ta ke da nasara sai kuyi hakuri”. Murmushi mai sauti Alhaji Muhammad Bello ya yi, kafin ya ce, “Alright. Insha Allah mu ne da rabon. Zan lallashi Taufeeq ko zai fahimce ki, don a yadda na fahimta soyayya mai zafi ce ta kama shi. Ki duba kunya da kawaici irin na Taufeeq, amma ya fito fili ya ce min aure yake so. Ta nan za ki fahimci ba da wasa yake ba. Amma muna neman alfarmar ki barsu su fara fahimtar juna kafin ta gama karatun ko don ya samu nutsuwa”. A nan ma Hajiya Nasara ta ce ba ta yarda ba, zai kasa wa Kulsum hankali, karatu za ta yi ko soyayya? Ya kyale ta kawai ta yi abin da ke gabanta ya nemo wata ya aura. Daddy ya ce, “Nasara ki fahimta, Taufeeq ba aure yake so ba, yarinyar wajenki yake so. Ki zama mai tausayi mana? Kuma zan ja masa kunne ba ko yaushe zai dameta ba. Don Allah ki yi mana alfarma”. Hajiya Nasara ta san yadda Alhaji Muhammad Bello ke son Taufeeq fiye da kowa cikin ‘ya’yansa ba lallashin da ba zai mata ba. Sai ta ce a ranta za ta gwada Taufeeq don ta fahimci ko wane irin so yake yi wa Kulsum. Ta ce da Daddy za ta yi magana da Taufeq din kafin ta amince ya soma kula Kulsum. Da daddare bayan sun gama cin abincin dare su uku, ita, daddy da Taufeeq, Kulsum na daki ta ki fitowa. Hajiya ta lura tun zuwan Taufeeq ta koma daddawar daka, ko falo ba ta zama. Ita Kulsum a kan-karan-kanta ta rasa me ya sa ta ke jin nauyin Taufeeq? Idanuwansa ne manyan (magnet) din da ke takura zuciyar ta. Yana da wasu irin idanuwa tamkar maganadisu masu jan zuciyar diya mace, tamkar jan wutar lantarki. They makes her feel unease, shi ya sa ta zabi kebe kanta muddin yana wuri. Hajiya ta dube shi bayan Daddy ya tashi ya koma tsakiyar kujerun kayataccen falon ya murdo tashar CNN ya kure sautin yana sauraron labarai. Ta dago ido ta dubi dan ta Taufeeq, a tsanake ta kalle shi na ‘yan sakanni, kafin ta ce. “Na ji sakon ka wajen mahaifinka, amma ko ka san Kulsum na da lalura? Dalilin da ya sa na dauko ta ma ke nan bayan karatu, za ka iya aurenta a haka?” Taufeeq ya daga kyawawan idanunsa ya dubi mahaifiyarsa, a tsanake ya ce, “Wace irin lalura ce Mum?” Hajiya Nasara ta dube shi, tana son fahimtar yanayinsa, ta ce, “Fitsarin kwance ta ke yi, tunda aka haife ta”. Taufeeq ya zuqi numfashi ya fesar, (a bit confused) ya ce, “Fitsarin kwance as in tana barci ta yi fitsari cikin barci?” Hajiya ta ce, “Shi fa”. Ya yi dan jimm! Kafin ya ce, “Mum, ai ni ita kawai nake so, bana jin hakan zai hana ni aurenta, zan kuma nema mata magani har Allah ya sa mu dace. Idan kuma ba ta warke ba zan zauna da ita a haka, to the very end. Ni dai ki yi min alfarma ki ba ni aurenta”. Jikin Hajiya Nasara ya yi mugun sanyi, domin ba amsar da ta tsammata daga gare shi ba ce. Danta ko cikin ‘yan gayun samari ajin farko ne. Ko cikin masu tashen ilimi shi Navy Officer ne (sojan ruwa). Bai taba ce mata ga yarinyar da yake so ba a tsayin shekarunsa talatin da uku da haihuwa. Ya tsallake duk ‘yammata a UK ya zo ya ce ‘yar qauyen Gaya yake so, kuma mai lalurar fitsarin kwance. And he is willing to stay with her cikin lalurar tata ba tare da ta warke ba. Don haka ta yarda ciki al’amarinsa gaskiya ce ziryan. Amma ita wane bayani za ta iya yi wa iyayen Kulsum ba tare da sun zarge ta da son kai ba? Ga maganar tsohon mijinta da ke bibiyar nemanta har gobe, kuma ta sani su Goggo na son zancen sa, don dai sun bi abin da ta ce din ne kawai don sun san ta yi ne don amfanin Kulsumu. Yanzu kuma ta je ta ce musu Dan cikinta zai auri Kulsumu ai ba ta da hujjar kare kanta daga zargin su na kasancewa mai son kai. Kwarai za ta so Kulsumu ta zamo suruka a gare ta domin a dan zaman da ta yi da ita ta gama yarda da kyawawan halayen ta. Sannan ta shiga ranta yadda ba a zato. Abin farin cikinta ne Taufeeq ya aure ta, to amma ba dai yanzu ba! Ta yi ajiyar zuciya ta daga kai ta dubi Taufeeq din, ta ce, “Ka yi hakuri mu bi lamarin nan a sannu, babu bukatar gaggawa a cikin sa. Ka bai wa Kulsum lokaci. Aure ko soyayya ba nata ba ne yanzu. Ka bar wa Allah lamarin ka yi addu’a. Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakanin ku”. Taufeeq ya ce, “Na ji abin da ki ka ce Mum, sannan na fahinta, amma don Allah ki bar ni in nemi yardar ta a hankali. Na yi alkawarin ba zan hana ta karatu ba”. Hajiya Nasara ta ce, “To Taufeeq na amince, sannan Kulsum amana ce a hannun mu, na rabo ta da iyayen ta ba don ba su da yadda za su yi da ita ba, ko don sun gaza a kanta, a’ah, sun ba ni ita ne sabida yarda da suka yi da ni. Don haka sai ka san irin mu’amalar da za ta kasance a tsakaninku. Wadda ba za ta zamo ta Allah wadai ba”. Taufeeq ya kwanta a kan gadonsa a wannan daren, ya lumshe idanunsa yana tunano maganganun da suka yi da mahaifiyar sa a ranar a kan Kulsum. Maimakon abin da ya ji na lalurar fitsarin kwance ya sagar da gwiwarsa a kan Kulsum, sai ya ji his feelings for her heightened. Da ma har yanzu akwai masu irin wannan lalurar a duniya? Ina ma shi likita ne? Likitan ma wanda ya yi specializing a kan lalurar Kulsum. To ko dalilin da ya sa Mum din sa ta kai ta wajen Sakeenah ke nan? Allah Sarki Kulsum! Ubangijin halitta ya kyautata halittar ta da halayyar ta ta kowanne bangare, amma sai ya jarrabce ta ta wannan bangaren. Fitsarin kwance nakasa ne ba kadan ba, musamman ga diya mace. To ko wannan ne dalilin da ya sa mijin nata ya guje ta? Shi ji ya yi hakan ya kara sanya masa son ta da tausayin ta. Wahegari Kulsum na kicin tana kwaba wa Hajiya fulawar da za ta yi cincin da ita, Taufeeq ya shigo kicin din, kayan barci ne a jikinsa farare ‘yan gidan Ralph Lauren da alama ko wanka bai yi ba. Da Kulsum ya kwana a zuciyarsa da ita ya wayi gari, ya san kuma kicin shi ne wajen da zai ganta a daidai wannan lokacin. Ilai kuwa yana shigowa ya yi tozali da ita. Wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki, ya jingina da cabinet din kicin din yana kallon ta. Hankalin ta gabadaya yana kan fulawar da ta ke murzawa da hannunta ba ta ma lura da shigowar sa ba. Taufeeq ya shagala sosai da kallon ta har bai san adadin mintunan da ya bata a tsaye ba. Daga bisani ya kira sunanta cikin taushin murya. Da hanzari ta dago dara-daran idanunta ta dube shi. “Barka da kwana, kana son wani abu ne?” Don dai ita ba ta taba ganinsa a kicin ba. Ya ce, “Ba abin da nake so. Na zo ne in taya Kulsum hira”. Dan murmushi ta yi, a ranta ta ce, da sassafen nan? “Ga shi kuma ina yi wa Hajiya aiki”. Kulsum ta fada cikin sanyi. “Ba matsala, sai mu yi tare”. Taufeeq ya ba ta amsa. Dan murmushin ta sake yi har dimples din suka lotsa ciki sosai. Taufeeq ya rungume hannayensa a kirji, yana kallon ta keenly, ya ce, “Na zo ne mu kulla abota ni da kanwata Kulsum”. Murmushin ta sake yi har yanzu ba ta ce komai ba, kuma ba ta dago ba. So ta ke ta ce da shi, ai mace da namiji ba sa abota, amma ba za ta iya doguwar magana da shi ba. Tsoron maza ta ke ji, sannan tana jin nauyin sa sosai fiye da komai, ba ta son kallon kwayar idanunsa. Ya kara kankan da murya, ya ce, “Kulsum please, can we be friends? Sabida ke na baro aikina na taho. In ban zama abokin Kulsum ba ba zan iya aikin ba”. Wannan karon da dumbin mamaki ta cira kai ta dube shi. Anya Taufeeq ne Yayan Dr. Sakeenah da ta sani? Mutumin da a farkon zuwansa yake mata kallon kaskanci? To ya yi abota da ita ya samu me a cikin abotar? Ita Kulsumu jikar Goggo ‘yar kauyen Gaya wadda ba ta aje ba, ba ta kuma ba wani ajiya ba? Taufeeq ya fahimci ba ta da abin cewa, sannan he is not welcome in dai Kulsumu ce. Don haka ya sauya akalar hirar tasu ta koma ta karatu, ai kuwa nan da nan ya samu bakin Kulsum. Shi dai burin sa ta sake da shi, sai ta saki jiki da shi ne zai samu damar bayyana mata manufar sa a hankali. So yake su fahimci juna sosai, ya shiga rayuwarta ta yadda duk ranar da ya bayyana mata manufarsa a fili za ta fahimce shi. “Me ya sa duk fannonin karatun medicine ki ka tsallake su ki ka zabi zama Nurse Kulsum?” Zuwa lokacin ta gama kwabin da ta ke yi, tana wanke hannunta a sink. Ba tare da ta dube shi ba, ta ce, “Sabida in taimaka wa ‘yan uwana mata da kananan yara. Bana jin dadin yadda ake treating dinsu a asibitoci, musamman asibitocinmu na karkara, sai na zama Nurse ne zan iya bada gudunmawata fully ga mata da yara. A can gaba ina so in yi specializing as a Professional Perioperative”. Taufeeq ya jinjina kai, sannan ya ce, “Amman kuma zai hana ki samun cikakken lokacin mijinki, ba karamin mai hakuri ne zai yarda matarsa ta dinga kwana a wajen aiki ba”. Da sauri ta ce, “Yaya Taufeeq ni ai ba zan yi aure ba!”. “Sabida me?” Taufeeq ya tambaya curiously. Dan jim ta yi kafin ta ce, “Saboda na yi ban ji dadin sa ba”. Taufeeq ya ce, “Me ya hana ki jin dadin nasa, bayan an ce Dan Sarki ne ma mijin naki?” Kulsum ta kasa dagowa ta dubi Taufeeq, don ba ta san bayanin da za ta yi masa ya gane ba. Turaki bai kasance mai adalci a gare ta ba ta kowanne bangare. Wanda hakan ya sa ta ke alakanta gabadayan maza da halin Turaki, wanda in sun fahimci mace na son su kamar ta mutu sai su yi amfani da hakan su cutar da ita, su barta da karyayyar zuciya, sannan su guje ta. Kada Allah ya maimaita mata aure in dai duk maza irin Turaki ne. A fili ta ce, “Ba ya sona! Bai taba sona ba!!” Magana ta yi a zuci, ba ta san cewa a fili ta yi ta ba. Taufeeq ya tsura mata ido, zuciyarsa na racing ya ce, “Kuma sai aka ce duk mazan duniya ba za su so ki ba, sabida dan Sarkin Gaya ya ki ki?” Kulsum ta ce, “Daga na gaba ake gane zurfin ruwa! Ina da abin da zai ki ni a kansa. Don haka ban ga laifinsa ba da ya kasa zama da ni”. Ta rasa abin da ya sa ta ji zuciyar ta ta yarda da Taufeeq har ta ke fallasa masa sirrin zuciyarta. Abin da ba ta taba fada wa kowa akan Turaki ba. Taufeeq ya fahimci in yana son zama very close to Kulsum sai ya janye zancen soyayya a tsakaninsu. Ba karamar illa Turaki ya yi wa zuciyar ta ba. Kuma duk da hakan har gobe she has some kind of strong feelings for him. Which makes him jealous…..(wanda ya sanya shi kishi). Ya ce, “Kulsum, ba ni labarin auren ki, ki ba ni labarin Turaki”. Dan murmushi ta yi, ta ce, “Babu wani abin karaswa a kai. It is a very short marriage, which ended abruptly kamar kiftawar ido… he don’t like me at all…”. Taufeeq ya cusa hannunsa cikin tarin kwantacciyar sumar kansa yana kokarin boye kishin da ya harzuqo masa, domin ya gane zance in na Turaki ne Kulsum na maraba da shi. “Ke kuma kina son shi… har ba ki ji dadi ba da ya rabu da ke… har kike alaqanta sauran maza dashi, sabida shi ne autan maza…”. Bude baki ta yi tana mai dafe bakin da yatsun ta tana dariya, dariyar data sa Tawfeeq shagala cikin kallon ta, ta ce, “ ba haka bane Yaya Taufeeq…”. Taufeeq ya ce, “Haka ne mana! Tunda ga shi har kina fadin ba za ki yi aure ba tunda ya rabu da ke…”. Ta yi saurin gyara masa da cewa, “Ba shi ya sake ni ba… Maimartaba ne ya raba auren…”. Taufeeq ya hadiye wani kullutun kishi da ya sake tokare shi a makoshi… ya yi ta maza in ji mata, ya ce, “Well, idan na fahimce ki Kulsum ba aure ne baki so ba, sauran maza ne ba ki so, amma kina son tsohon mijin ki. Ni kuma sai na ga gara ka auri wanda ke sonka, a kan ka auri wanda ka ke so. As a brother, (a matsayin dan uwa) shawarar da zan ba ki ita ce, ki bude zuciyar ki ki kaunaci masu kaunar ki. Ni a wurina Turaki ba shi da uzurin da zan karba wanda zai tabbatar min ya na son ki. Ya tafi shekara da shekaru ba sako ba aike kamar yadda Hajiya ta gaya mini, so do away with him from your life Kulsum kamar yadda iyayen sa da kan su suka hango miki, Turaki ba ya sonki!” Ta san iyakar gaskiyar ke nan, amma ta rasa me ya sa ta yi mata daci? Ba shi ne mutum na farko da ya fada mata hakan ba zuciyar ta ta sha fada mata, Hajiya Nasara ma ta fada, amma sai ta ji ta Taufeeq ta fi ta kowa yi mata daci. Ta ya za ta yi ta fahimtar da su son da ta ke wa Turaki ba yin kanta ba ne? Wani al’amari ne daga Allah wanda ba ta san musabbabinsa ba? Hawaye suka ciko idonta, amma ta yi kokarin maida su. She don’t want to shed tears for Turaki… Faduwar za ta yi mata yawa. Taufeeq ya tako har gabanta ya tsaya, hannayensa biyu zube cikin aljihu, ya ce, “Na ba ki assignment Kulsum, ki je ki yi kokarin da za ki yi ki cire tunanin ba za ki yi aure ba, saboda dan Sarkin Gaya. Rayuwa ba haka ta ke ba, every disappointment is a blessing. In wani ya ki-ka da wuni, wani da kwana zai so ka! Ki ba wa wani daban dama ya shigo rayuwarki bayan Turaki, ki sa a ranki abin da ya sa ki ka baro Gaya ba don ki yi karatu ne kadai ba, har ma da samun sabon abokin rayuwa, wanda zai kaunace ki against all odds. Na barki da wannan. Mu wuni lafiya”. Wunin ranar zungur ta yi shi ne da tunanin maganganun Taufeeq Mohammed Bello, wadanda ta auna ta ga cewa gaskiya ce zallah ya gaya mata. Ta amince za ta bi shawarar sa, za ta ci gaba da kauda Turaki daga kan hanyar ta. Matsalar ikon hakan ba nata ba ne. Ko ta yi kokarin hakan ba ta cin nasara. Ta amince an halicce ta ne domin ta rayu da soyayyar Turaki, soyayyar wanda bai san tana yi ba. Washegari Taufeeq ne ya kai ta makaranta da kansa. Ya yi hakan ne domin ya samu damar yin sallama da ita. A gobe zai koma Lagos, kokarin sa na son ta sake da shi ya fara yin nasara. Suna tafe a hanya ya ce, “Kulsum me zan samu? Gobe zan koma Lagos”. Dan murmushi ta yi, ta ce, “Me nake da shi da zan ba ka Yaya Taufeeq?” Ya juya kan motar ya shiga harabar makarantar, sannan ba tare da ya juyo ya dube ta ba, ya ce, “Your phone number”. Ta fadada murmushin ta tare da cewa, “Don dai wannan ba ni wayarka in sa maka”. Hannu ya mika ya dauki wayar daga inda ya ajiye ta a aljihun motar ya ba ta. Ta juya kyakkyawar wayar samfurin Iphone a hannunta, sannan ta soma dialing lambobinta a ciki. Ta yi saving da (Sister Kulsum) ta mika masa. Daidai lokacin da ya yi parking a parking lot (wurin adana motoci) ya kashe motar ya juyo ya dube ta with affection (cike da kauna) cikin kwayar idanunsa. “I will call you tonight, (zan kira ki da dare) Yusha'u zai zo ya tafi da ke, ni akwai inda zan je. Gobe in na tafi zan yi kewar abokiya ta Kulsum”. Ta yi ‘yar dariya, abokiyar nan da yake fada yana amusing dinta. Don dai ita ba ta san mace da namiji na wata abota ba. Ya kwantar da kai a kan sitiyari, murya can kasa ya ce, “Kulsum za ki yi kewata?” Yadda ya yi maganar loving and romantic kamar ba Taufeeq ba. Tafukanta ta kai ta rufe fuskarta, ta rasa me ya sa ta ji kunya. Watakila yadda ya yi maganar ne. Ya bude mata kofar side din ta ta fita tana saba jakarta. “Yaya Taufeeq na gode”. Ta juya ta soma tafiya, shi kuma ya bi ta da kallo. Ya rasa irin son da zuciyarsa ke ma Kulsum, mai mamaye zuciya haka farat daya. Sai da ya daina hango ta, sannan ya yi reverse ya bar makarantar. ****** University Of Reading, UK. Har ya shigo ofishin ya zauna bai sani ba. Ya dora haba a kan hannayensa yayi zurfi a tunani. Dr. Abdul’Ahad Maikano, ya sa hannu ya kwankwasa tebirin da yake tsakaninsu. A hankali ya dago ya dube shi, idanunsa sun kada sun yi jazir. Abdul’Ahad ya ce, “Dr. Abubakar ko lafiya tunda ka dawo ban ganka ba? Ban ji feedback na zuwan ka gida ba?” Ya sauke hannayensa bisa tebirin tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. A hankali ya ce, “Abdul’Ahad na rasa Kulsum, sakaci na ya jawo min babban da na sani. Maimartaba ya raba auren da kansa, sun maida UmmuKulsum ga iyayenta, su kuma sun bar garin da ita. Na tashi a tutar babu, ma’abocin da na sani. Hakika bijirewa iyaye babu inda zai kai mu sai ga rashin albarka da rashin kwanciyar hankali. Ina ma na karbi auren Kulsum da kyakkyawar manufa da ban kasance cikin kuncin da nake a yanzu ba”. Maikano ya tausaya wa abokinsa, ya san irin wannan nadamar, ita ake kira ‘NADAMA MARA AMFANI’, ya ce, “Amma tsakaninka da su fa? Ina nufin iyayen ka?” Ya ce, “Sun yafe min da kyar da sidin ludayi, sannan Maimartaba ya ba ni shekaru uku in kammala duk abin da nake yi a nan in koma gida, su kuma kakannin Kulsum sun ce ko sunan kasar da aka tafi da ita ba su rike ba, mun dai rabu a kan in sun zo end of the year za su karba min lambar wayar marikan nata. Su kuma su Maimartaba sun ce, in mun daidaita tsakanin ni da ita shi ke nan za su amince mu koma auren mu”. Abdul’Ahad ya ce, “Ni kuma ka san wani abu? Ban yarda kakannin Kulsum ba su san inda aka tafi da ita ba. they just want to teach you a lesson or something else… in za ka koma next year zan raka ka mu je tare, kuma insha Allahu ba za mu dawo ba sai tare da Kulsum. Game din yanzu tsakanin kai da Kulsum ne babu interference na iyaye. Idan ka maida kanka dan soyayya Aboki ka samu Kulsum ka gama”. Murmushin gefen baki Turaki ya yi, murmushin kasaitar sa da ginshirar sa da ya saba. Wannan kuma wani abu ne da bai san ya yake ba (lallashin mace da soyayya), ya saba shi ake cewa ana so har a yi ta husumar kishi a kansa. Yau Abdul’Ahad na fadin shi zai koma neman soyayya. A yadda yake jin son Kulsum ta dawo cikin rayuwarsa yana jin ba abin da ba zai iya ba, in dai zai same tan. Ya fara tuna rayuwarsa, bayan shigowarsa UK, ya fara karatun medicine a jami’ar Reading Berkshire, ya kammala da kwali mai daraja inda kai tsaye ya tafi specializing a Ophthalmology wato fannin likitancin ido. A dukka wadannan shekarun yana rayuwa ne with the guilt na laifin da ya san ya aikata wa Kulsum, yana kuma cike da taraddadin komawa ga iyayensa don ya san cewa ya yi musu laifi. Sannan tsaurin karatu irin na medicine ya hana shi samun lokacin komawa gida. Daga ranar da abun ya faru (ranar da ya karbe wa Kulsum alfarmarta) kamar an sa igiya an zarge zuciyarsa da soyayyarta. Everything happens like a magic, kuma kamar an tsara shi ya tafi a hakan. Abin da bai sani ba shi ne, Maimartaba ya tsara din, kuma komai ya tafi a yadda ya tsaran. (Kulsumu ta zauna a zuciyarsa koda ya tafi, idan ya san ya tafi ne ya barta a cikakkiyar matar sa). Ganin girman laifin da ya aikata wa Kulsum a ranar da zai taho ya san Umma ta dau zafi da shi, shi ya sa ya ki kiran waya, kullum kokari yake ya kammala abin da ke gabansa ya koma gida bakidaya ya fuskanci kowanne irin hukunci daga iyayensa. Da wannan damuwar ya rayu a dukkan shekarun da ya kwashe yana karatu. Yana gama karatunsa kuma university din ta rike shi ya yi mata aikin koyarwa temporary sabida kyawun takardunsa. Tun a shekararsa ta farko ya hadu da Abdul’Ahad Aminu Maikano. Babansa diplomat ne, ‘yan asalin jihar Katsina. Abotarsu mai ban sha’awa ce, sai dai Abdul’Ahad bai san komai a kan Turaki ba sabida zurfin ciki da rashin son magana irin nasa. Sai fa lokacin da ya rasa yadda zai yi da damuwarsa har ta soma sabbaba masa rashin lafiyar ciwon kai mai fitar da shi hayyacin sa da Abdul’Ahad din ya samu ya bayyana masa komai nasa. Kuma bisa shawarar Abdul’Ahad din ne ya zo gida har abubuwa suka kwana yadda suka wakana. Madallah da aboki irin Abdul’Ahad mai fitar da abokinsa daga damuwa. Ya ji dadin shawarar sa, don haka ne yanzu ba ya boye masa komai da ya shafe shi. Tunda ga shi ya samu ya shirya da iyayensa. Tunda ya dawo duk bayan kwana uku sai ya kira gida, secretly kuma suna waya da Batulu tana gaya masa har yanzu ba bayani, ta je wurin Goggo sau ba adadi ko za ta ci karo da wani abu a kan Kulsum din, amma sai dai su yi hira ta taho, kullum zancen Goggo daya ne, ita ba ta san sunan kasar da aka tafi da Kulsum ba. Baffa kuwa ba abokin zancenta ba ne da ma. Ga Kulsumun babu kawa balle aminiya, ita ce da ma kawar tata. Kuma aminiyar ta. She is very anti-social. Amma tunda Goggon ta ce za su zo karshen shekara ita kuma ta yi masa alkawarin kawo masa labarin Kulsum idan ta zo gari, sannan Goggo ta yi alkawarin bada lambarsu. *** *** *** Tana kwance da daddare a tsakiyar gadonta washegarin komawar Taufeeq Lagos. Wani textbook ta ke nazari NURSING ETHICS IN EVERYDAY PRACTICE (Connie M. Ulrich). Wayarta da ke karkashin filo ta yi kara. Ko da ta daga babu suna, bakuwar lamba ce a wayarta. Da ma contacts din nata ba su fi shidda ba, Goggo, Hajiya, Aunty Sakeena da Baban Yalleman sai Nasma da wata abokiyar karatun ta Grace. Don haka da sallama ta amsa cikin siririyar muryarta. Daga daya bangaren Taufeeq ya kira sunanta, “Ko ki bugo ki ji yaya abokin ki ya isa Lagos?”. Murmushi ta yi, don ta gane mai magana. Ya ce, “Na kira kawai in miki sai da safe. Kada ki manta da ni cikin wadanda za ki yi mafarki. Also put me in your Du’as, ina da bukata muhimmiya wurin Ubangiji. Wadda nake so ba ta so na”. “Kamar ni da Turaki”. Zancen zucinta ya fito fili ba tare da ta sani ba. Taufeeq ya runtse idonsa. “Ya Allah! Kulsum me ki ka ce?” Da sauri ta ce, “Ban ce komai ba Ya Taufeeq, zance ne irin na zuci”. Ya yi murmushi cikin jin tausayin kansa, ya ce, “Ko?” “Eh, amma me ya sa ba ta sonka Ya Taufeeq?” “Watakila ban yi mata ba ne”. “Kai din? Ita kuwa wane irin miji ta ke so bayan kai?” Murmushi mai sauti Taufeeq ya yi, ya ce, “Kin san an ce shan koko daukar rai”. Ta jinjina zancensa, sannan ta ce, “Yanzu yaushe za ka zo gida?” Ya ce, “Kina so ki gan ni ne Kulsum? I thought bayan Turaki ba kya son ganin kowa?” Ta kai tafin hannunta ta rufe idonta kamar yana ganinta. “Ya Taufeeq na yarda da abin da ka ce… do away with him… amma ji nake har abada ba zan iya kara aure ba…”. “Sabida kin rasa autan maza?” Ya katse ta. Ta lumshe idanunta, ta ce, “Ba haka ba ne. Ban gane komai a cikin auren ba, sai bacin rai. Bana so a maimaita”. Taufeeq ya yi ajiyar zuciya, ya ce, “Kulsum ko ni ne?” Wayar ta cire daga kunnenta na ‘yan sakanni, kirjinta na bugawa sabida dukan da kalamansa suka yi mata. Cikin kasa da murya ya ce, “Ina son ki Kulsum, na ba ki lokaci ki yi tunani, tunanin abin da ya dace da ni, da ke. Ki karbe ni a matsayin miji ko a'ah. Duk matsayin da ki ka ba ni Kulsum zan karba da godiya. Sai dai idan ki ka sake ambaton Turaki a kunnena..... zuciyata za ta buga Kulsum!”. Bai kara cewa komai ba ya katse wayar. A wannan daren Kulsumu kwana ta yi tunani, mamakin mutum kamar Taufeeq dan gata gaba da baya ya ce yana sonta. Ba ta taba kawo hakan a ranta ba ko da wasa. Ta rasa a matsayin da zuciyarta ta amshi batun nan. Shi kuma Taufeeq tun daga ranar bai barta haka ba. Text din safe daban, na dare daban mai jaddada kaunar shi gare ta. Ba ta da abin da zata ce mishi, ta tattara komai ta mika wa Ubangiji. A karshen wannan watan Nasma ta kare karatunta, Hajiya da Daddy za su je graduation dinta a garin Nottingham din kasar Ingila. Kwarai Hajiya ta so su tafi tare da Kulsum, amma tana da jarabawar karshen zangon karatunta na farko. Don haka Kulsum da Serah kawai aka bari a gidan sai maigadi da ke bakin get. Yusha'u da ke kai ta makaranta sai da safe yake zuwa ya kai ta, in ta tashi ya koma ya dauko ta. Sai ta yi amfani da kadaicin wajen yin karatu yadda ya kamata. In abu ya shige mata duhu sai ta kira Aunty Sakeenah a waya ta warware mata. Ana saura kwana biyu su Hajiya za su dawo, dawowarta daga makaranta ke nan ta zauna a dining tana shan ruwan sanyi sabida gajiya da kishin da ta kwaso. Aka danna kararrawar shigowa falon gidan. Ta tashi a hankali ta je ta bude, ba ta tsammaci ganinsa a wannan lokacin ba, don haka ta dan bude baki cikin mamaki, wanda ke hade da murmushi. Taufeeq ne cikin fararen uniform dinsa na Nigerian Navy. Ya yi kyau har ya gaji. Ya daga mata gira ya ce, “Hello, Nurse”. Ta rufe baki tana dariya, ta ce, “Ya Taufeeq kana hanya, amma ba ka gaya min ba in shirya maka better?” Ya sa kafa ya karasa shigowa cikin dakin, ya ce, “Ai ke ce bettern. Ni ba ni hanya in wuce. Ya ya na ji gidan shiru haka?” Ta ja da baya tare da karbe masa jakar da ya goyo a bayansa suka isa ga kujerun falon suka zauna. Ta ce, “Hajiya da Daddy ai ba sa nan, sun je graduation din Nasma, sai jibi za su dawo”. Ya ce, “Oh, yes Daddy ya gaya min na manta ne. How are you managing ke kadai toh?” Ta ce, “Ba ni kadai ba ce, Serah tana nan. And my textbooks also”. Ya yi murmushinsa mai aji, “To me zan samu express yunwa nake ji Aunty Nurse”. Ta mike da azama ta nufi kicin tana fadin, “Ka ba ni minti sha biyar in ga abinda za'a samu". Murmushi ya sake yi, ya bi ta da kallo admiringly har ta shige kicin din. Cikin mintuna sha biyar din da ta ce kuwa ta hado masa vegetarian meal dinsa. Har gabansa ta kawo ta ja karamin tebur ta dora. Taufeeq ya dube ta da murmushi, ya ce, “Thank you”. Sannan ya kara da, “I’m here just to see you, Kulsum kin hana ni sakat, kin hana zuciyata sukuni. Don Allah ki tallafe ni ko na samu sa’idah”. Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi. Ya ce, “Kulsum?” Yadda ya fadi sunan a hankali kamar mai rada sai da Kulsum ta ji shi har ranta. Ta dago ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta kai dubanta gare shi, kwayar idanunsu ya sarke ta yadda ba za ta iya janyewa ba in ba shi ya ba ta damar hakan ba. “Kin amince in gabatar da ke ga su Daddy a matsayin matar aurena? Zan barki ki yi karatun ki har sai kin ce ya ishe ki. Zan mantar da ke tsohon mijin ki har sai kin yarda shi din ba autan maza ba ne. Zan ba ki soyayya da kauna har sai kin amince cikin matan duniya ke ta musamman ce. Ki ba ni dama Kulsum, Kulsum don Allah!”. A hankali ta kai tafukanta ta rufe fuskarta, kawai ji ta yi ta yarda da Taufeeq, ta amince da kowacce kalma ta bakinsa. Ba ta san sanda wadannan kalaman suka fito daga bakinta ba. “Yaya Taufeeq ina da lalura wadda ta sa na cire aure daga zuciya ta. Tunda aka haife ni nake fitsarin kwance har girma. A yanzu haka ba ni da tabbacin na daina ko ban daina ba. Ka yi hakuri ka nemi mai lafiya kamar ka ka aura, bana so in zame maka lalura. Har yanzu magani nake sha”. Taufeeq yana da kima a idanunta, ba ta so ta fito kiri-kiri ta ce da shi, Turaki kawai ta ke so a duniya. Hakan zai zama cin fuska kuma zai gane cewa, duk abin da ya fada mata, iyayenta ma suka fada mata na ta manta da Turaki ta bayan kunnenta yake bi. Turaki bai shig rayuwarta don ya fita a sanda ta ke so ba. Amma ga mamakin ta budar bakinsa, sai cewa ya yi. “Kulsum, ina son ki da dukkan lalurar duniya da ke tare da ke. Zan kuma zauna da ke a haka. Kin amince in gabatar da zancen mu ga manya?” A wannan matakin, ba ta da wani tunanin yi, ta yi duba ga wane ne Taufeeq da gatan da yake ciki, ta kwatanta da nata gatan, amma ga shi ya nace yana binta da kokon barar soyayya. Duk da lalurarta abar kyama data sanar da shi. Ta tuno tarin alkhairin mahaifiyarsa da ‘yan uwansa gare ta. Ko ita butulu ce ya kamata ta duba halacci. Don haka ta samu kanta da daga masa kai alamar ta amince. Da yana da dama a wannan lokacin rungume ta zai yi don ya nuna mata iyakar farin cikin sa. Da ba shi da damar hakan sai ya rausayar da kai tare da lumshe idanun sa ya ce. “Na gode Kulsum, kuma insha Allahu ba za ki taba yin nadamar zamantowa ta mahadin rayuwar ki ba!”. A kwana biyun bakidaya yana like da ita, tana musu girki yana taimaka mata, ko ya zauna ya yi ta mata hira. Sosai suka shaku ta kuma fahimci Taufeeq mai matukar saukin kai ne ba kamar yadda ta dauke shi a baya ba. Idan yana son abu yana mishi so ne da dukkan zuciyarsa, haka idan yana kinsa ba ya iya boyewa. Shi ya je ya dauko su Hajiya ranar da za su dawo lokacin ita tana makaranta. Sai dawowa ta yi ta tadda Nasma a gida, dakin Hajiya ta fara zuwa ta yi mata sannu da zuwa. Hajiya ta ce, “Sannu da gida Kulsum, da fatan mun same ku lafiya, ya ya jarrabawar?” Ta ce, “Alhamdu lillah, gobe insha Allah za mu gama, za mu samu dan hutu, ina son zuwa wajen su Goggo”. Hajiya ta yi dan shiru sannan ta ce, “Zuwan ki Gaya ba yanzu ba Kulsum, ki bari sai can gaba. In dai Goggon ki ke son gani kawai zan sa Yusha'u ya dauko ta ta kwana mana biyu”. Kulsum har da dan tsallenta don murna, ta ce kuma a dakinta za ta sauki Goggon. Ta fice cike da murna ta samu Nasma a falo ta dora kafa daya kan daya tana kallon talabijin tana shan ice-cream, ta ce, “Kulsum me Mum ta ke ba ki ne? Kin yi girma kin kara fari sai wani glowing ki ke yi idanunki na sparkling?” Dariya ta yi ta zauna kusa da ita ta ce, “Ai dai ban kai ki ba Aunty Nasmah”. Ta ce, “To ya karatun? Ina fatan ba ki da matsala?” “Alhamdu lillahi ko da matsala Aunty Sakeenah na kokari a kai”. Nasma ta ce, “To masha Allah, have some ice-cream”. Ta debo a cokali ta nufo bakinta. Dariya ta yi ta bude bakin kenan za ta karba suka yi ido hudu da Taufeeq da ke shigowa, ba shiri ta rufe bakin sai kuma ta kware ta soma tari. Nasma ta juya don ganin abin da ya kwarar da ita, ta ga Taufeeq ne. Ya zuba hannayensa biyu a aljihunsa yadda ya saba ya zuba mata lumsassun idanunsa. Ta sake juyawa ta dubi Kulsum nan da nan ta fahimci akwai wani abu. “Ya Taufeeq, ice-cream zan ba ta fah, ta ganka ta kware”. “To me ye wani za ki ba ta ice-cream, ita jaririya ce?” Ya samu kujerar da ke kallon ta Kulsum ya zauna. Ai da sauri ta tashi ta yi daki, ya ce, “Tafi a hankali kada ki yi tuntube mana”. Nasmah ta ce, “Ai kawai ka goyata ka kai ta dakin”. Ta bi bayan Kulsum da gudu kada ya make ta. A washegari da zai koma Lagos ya samu Hajiya a daki ya gaya mata sun daidaita da Kulsum ta amince masa. Hajiya ta yi mamaki kwarai don ba ta zaci hakan zai zo da sauki ba, ta san Turaki Kulsum ke so, don an fi karfinta ne. Ba ta so ya kasance Kulsumu ta amince da Taufeeq ne albarkacin ta. Sannan ita a wannan lokacin ba ta shirya yi wa Kulsum aure ba. Ta kyale ne sabida Taufeeq bai iya sanya abu a ransa ba, idan ba hadin kan Kulsumun ya samu ba ba zai maida kai ga aikinsa ba. Ta nisa, ta ce, “Taufeeq na yi murna, amma kamar yadda na ce a baya ina so ka ba wa al’amarin nan lokaci. Ka yi hakuri har Kulsum ta kare makaranta, sannan ne za mu ba ta damar fidda miji, yanzu ba ta da nutsuwar da za ta zabi mijin aure, kuma ba auren ta ke son yi ba. Ina rokonka, ka ba ta lokaci”. Taufeeq ya nisa, “O.K Mum, zan bi abin da ki ka ce. Ki taya ni addu’a Allah ya sa in jure jiran, kuma Allah ya sa ina da rabon samun Kulsum a rayuwata”. Abin ki da Da da mahaifi, sosai ta ji zuciyarta ta tabu, ta ce, “Insha Allahu inda alkhairi Allah zai ba ka ita. Kuma ba ga waya ba? Ko ka tafi ko yaushe kana iya kiranta, sai dai bana son abin da zai hana ta maida kai a karatu don Allah”. Dan murmushi ya yi, ya ce, “Mum zan kiyaye, zan tafi gobe ki sa min albarka”. “Albarka kullum cikin sanya muku muke. Allah ya kara wa rayuwa albarka”. Kulsum da Nasma a dakin Nasman, ta tura mata akwati shake da kaya, ta ce duk tsarabar ta ce. Ta bude tana daga English wears din daya bayan daya ‘yan gidan Marks & Spencer, duka babu mai fidda tsiraici za ta iya zama gida da su. Tana daga su daya bayan daya tana yabawa. “Aunty Nasmah, duk ni kadai?” Nasmah ta yi murmushi, ta ce, “Sai a yi ta tsantsarawa Yayana kwalliya”. Rigar da ta daga ta sa ta rufe fuskarta. Nasmah ta yi dariya, ta ce, “Ai kallon ku nake kar, kun dauka ban gane ba ne ko? Sai ki yi hakuri Yayan nawa akwai fada, akwai rigima. Ban sani ba ko ni da Aunty Sakeenah kadai yake yi mawa? Ke kam ai lallaba ki zai yi na sani, tunda shi ne mai nema”. Kulsum ta shuri jakarta ta bar dakin Nasmah na fadin, “Sai fulako sai ka ce tashin Ruga”. Ko da Taufeeq ya koma duk dare sai ya kira ta, komai yake yi sai ya sanar da ita. Tun tana jin kunya har ta saki jikinta da shi. Ita ma takan fada masa me ta ke ciki a kan harkar karatunta. Hatta Aunty Sakeenah da ke Lagos ta san zancen Taufeeq da Kulsum. Kusan ta fi kowa farin ciki da al’amarin don dai ita haka nan ta ke matukar son Kulsum. Hajiya Nasara ta cika alkawarin da ta yi mata, kwanansu uku da yin hutu kawai rannan tana gyaran kayanta a closet dinta ta tsinkayi sallamar Goggo. Goggon da ke zuwa kullum cikin mafarkinta, Goggon da ta ke kewa, kewar da ba za ta misaltu ba. Sakin kayan hannunta ta yi ta buga wani uban tsalle ta rungume Goggo. “Yi min a hankali, tsohon kashi ne”. Goggo ke fadi. Da kyar ta bambaro ta daga jikinta, ta kalle ta ta sake kallonta cikin fulatanci ta ce, “Kulsumu am ondo (Kulsumu na ce wannan)?” Dariya ta yi, ta kama hannunta zuwa bakin gado, Goggo na fadin, “Halan wankan inji na sake fata Nasara ke yi miki?” Dariya sosai Kulsum ke yi, ta rasa inda za ta saka Goggo don murna. Ta zaunar da ita gefen gado, ta bude dan bedside fridge dinta ta dauko gorar fresh milk da ruwan sanyi na gora tana ta rawar jiki, ta ce, “Goggo wanne zan zuba miki?” Hajiya Nasara ta shigo, a bayanta Serah ce da tray din abinci. Ta ce da Goggo, “Ai yau kuma ba kanta tunda ga Goggo ta zo, ina jin ko runtsuwa Kulsum ba za ta yi ba”. Kulsum ta ce, “Kamar kin sani Hajiya, kwanan zaune za mu yi”. Hajiya Nasara ta ce, “To don Allah barta ta huta ta ci abinci, son samu ta watsa ruwa ma, sun sha hanya”. Nasmah ta shigo ta gaida Goggo, Goggo ta ce, “Ita ce auta ko?” Kulsum ta ce, “Goggo kada ki sa Aunty Nasmah ta kara shagwaba akan wadda ta ke yi, idan ta ji kina kiranta auta”. Dariya suka yi, Nasma ta ce, “Ni ce nake shagwaba ko? Zan gamu da ke ne. Goggo ki je ki watsa ruwa ki yi sallah, ki huta ki rabu da ita”. Goggo da Kulsum ba su samu kebewa ba sai da daddare, Kulsum ta dage a dakinta Goggo za ta kwana bayan already Hajiya Nasara ta gyara mata daki. Goggo ta sha labarin zamanta a Lagos gidan Dr. Sakeenah da hanyoyin da Dr. Sakeenah ta bi ta hana ta fitsarin kwance. Da kaita babban asibiti data yi ta ga kwararren likita. Ta ce tun daga lokacin har yau ban kara yi ba. Idan na ji fitsari ko cikin barci ne sai na ji kamar ana alerting dina har cikin kwakwalwata. Amma har yanzu likita bai dauke ni daga shan magani ba. Idan na tuna wahalar da ku ka yi ta sha ke da Baffa, sai in tausaya muku, ashe lalurar tawa ta asibiti ce”. Goggo ta ce, “Godiya ta tabbata ga Sarkin halitta, shi magani ai dama dace ne, ciwo kuma warakarsa lokaci ne. Kulsumu Allah ya kawo miji na gari tunda lafiya ta samu”. Ta rufe fuska da hannayenta tana fadin, “Kai Goggo, ni karatu nake yi. Kuma har yau likita bai ce na warke ba”. Ba ta gaya wa Goggo Taufeeq ya fito yana sonta ba, haka ita ma Goggo ba ta gaya mata dawowar Turaki ba da komenta da ya ke so. Sun yi shawara ita da Hajiya Nasara su bar zancen a tsakanin su kada a raba mata hankali. Ita kuma Kulsumu kunya ce ta hana ta gaya wa Goggo zancen Taufeeq da kuma kasancewar har yau zuciyarta ba ta bai wa soyayyar Taufeeq kwakkwaran matsugunni ba. Ta fi kallonsa a wanda ya fi karfinta, dan gata, amma mutum mai tsananin kirki. Washegari Nasma ta ce za su kai Goggo ta ga gari ta mike kafa. Kowaccensu ta sha kwalliya, amma ko daga nesa ka san Nasmah ta fi Kulsum aji nesa ba kusa ba. Yayin da Kulsum ta fi Nasma kyau mai fizgar hankali. Nutsuwarta na kara wa kyawun nata ado, yana bayyana kwarjininta. Nasmah ce ke tukin motar su shiga nan su fita can cikin garin Abuja, suna ta gaya wa Goggo wurare. Sai goshin magriba suka dawo gida. Kwanan Goggo Shatu bakwai tare da su ta koma Gaya da tsarabar Abuja rankatakaf! Nasmah ta yi shirin zuwa Lagos za ta yi sati biyu, Dr. Sakeenah ta roki Hajiya su taho tare da Kulsum tunda suna cikin hutu. Hajiya Nasara ta ce, hutun ai ba shi da yawa, nan da sati daya za su koma. Sakeenah ta ce, ko sati dayan ne a bar mata aron Kulsum. Sosai ta ke murna da wannan tafiyar. A daren ta shirya kayanta, kuma a daren sun yi waya da Taufeeq amma ba ta gaya masa za ta zo Lagos ba. Washegari jirgin Azman na safe ya daga da su zuwa birnin Ikko. *** *** *** READING Turaki ne tafe cikin kankanuwar motar sa kirar Acura akan shimfidadden titin da zai sada shi da gidan aminin sa Abdul'Ahad Aminu Maikano, misalin karfe biyar da rabi na yammacin ranar Talata bayan ya taso aiki daga jami'ar ta Reading. Kamar kullum sanye yake cikin bakaken suit masu kauri, ya tsuke wuyan sa da ruwan tokar tie fatar shi tayi santsi har wani sheki take yi na musamman. Ta earpiece din dake makale a kunnen sa yake magana da Abdul'Ahad din "i am on my way Aboki....nan da mintuna ashirin zan karaso". Sati biyu kenan da angwancewar Abdul'Ahad da amaryar sa wata hazikar dalibar sa Dr. Sajidah wadda 'yar kasar Eritrea ce. Iyayenta Refugees ne a United Kingdom. Sanda ya iso gidan nasu mai cike da korran shuke-shuke daga sama har kasa, har lokacin sallar maghriba ya gabato. A kofar gidan ya tadda Abdul'Ahad da Sajeedah din suna jiran isowar sa, ya faka motar ya fito Sajeedah na yi masa barka da zuwa, tare suka rankaya su duka zuwa cikin gidan. Gidan nasu bai cika girma ba amma cike yake da duk wani nau'in kayan alatun jin dadi da saukaka rayuwar dan adam. Abdul'Ahad ya gayyato shi cin abincin dare ne kamar yadda su kanyi lokaci zuwa lokaci. Kuma su tattauna akan matsalar Turakin wadda ba komai bace banda 'UmmuKulsum' kamar yadda Turakin ke kiran ta in full. Sallah suka fara yi, kafin su idar Sajeedah ta gama shirya musu tebir, bayan sun idar suka nufi dining din Abdul'Ahad na cewa Sajeedah "in ji dai kin cika tukunya da kyau, kinsan gwauraye ba'a sa musu sanwa kadan". Dariya Sajidah tayi tace "shima Dr. Abubakar ya kusa tashi daga gwauro don nayi masa kamun kanwata, Fadwa, jira nake ta samu hutu in dauko ta su ga juna". Turaki na dan murmushi bai ce komi ba. Abdul'Ahad yace "wane Abubakar din? Yana da matar sa a gida fa, Allah ya kashe ya bata, ya gama mutuwa a kanta, ki dai taya shi biko shine za ki yi gwanin ta, Kulsum yake jira ya dawo da abar sa, kuma insha Allah zamu yi nasara". Cikin mamaki Sajeedah ta tambayi mijin ta cikin harshen turanci "dama yana da mata?" Turaki wanda ke zuba abinci a plate kansa a kasa, cikin kwantaccen sautin sa yace "Sajeedah, rabu da mijin ki kin ji, i am all alone, living alone, ta riga ta kubuce min, bisa sakaci da kuskure na, bansan ina zan nemo ta ba, duk wata hanya da zan samu labarin inda take bani da ita, keep praying for me kin ji, ita kadai nake so!" Cikin mamakin abinda take ji yau daga bakin Dr. Turaki Sajeedah tace. "Kun rabu ne?" "An raba mu dai, don ba ni na saketa ba". Ya bata amsa. A gajarce Abdul'Ahad ya bata labarin komai. Sajeedah ta rasa abinda zata ce, a karshe tace "hakkin iyaye dana Kulsum ne ya rikide ya koma maka soyayyah Dr. Abubakar. How i wish zan ga Kulthum da na yi kokari na bata hakuri ta dawo". Murmushi Abdul'Ahad yayi cikin zolaya ya ce "to ka karbi wadda ake ma tayi mana ka rage zafi? In ya so in Kulsum ta bayyana sai ka hada biyu? Sanyin garinnan without a wife is terrible". Hararar Abdul'Ahad yayi, sannan ba tare da ya tofa ba ya mike yana duba agogon swatch blustery dake daure a damtsen hannun daman sa. "Zan tafi gida, akwai marking din takardun dalibai da zan yi. Sajeedah, you cooks nicely, thank you once again". Sajeedah tace "ai fa ka kore shi, inama zan ga Kulthum dinnan in gaya mata how lucky she is! For winning this precious heart of Turaki. Ta dawo wa mijin ta mai kaunar ta. Dr. Abubakar duk ranar da Kulsum ta dawo mana zan zama babbar abokiyar ta, ko don in gaya mata irin son da muka wanzu muna yi mata, a lokacin da ta kubuce mana". Murmushin dai kawai yayi, sai dai bai ce komai ba, tausayin kansa yake ji don gani yake kamar ya rasa Kulsum har abada, wani abu da ya tabbatar zuciyar sa komai juriyar ta bazata karba ba. Gaban sa har wani irin faduwa yake yi idan ya tuna Kulsum zata iya auren wani a halin yanzu. Idan kuma hakan ya tabbata shi da aure sai ranar da Ubangiji ya nufa. Zai kare rayuwar sa a haka. Sannan zai fasa komawa gida. Duk wani tanadin rayuwar sa ta gaba, ya tsara shi ne tare da Kulsum. Duk abinda yake tarawa don ta ji dadi ne ita da 'ya'yan da zasu haifa. Yayi wa Kulsumu tanadin rayuwa mai gardi, da soyayya irin wadda ko a hikaya babu duk don ya wanke laifukan sa na baya. Ya sa kai ya fita ya nufi motar sa Dr. Abdul'Ahad ya biyo bayan sa. A jikin motar sa suka tsaya yayin da Sajeedah ta koma gida. "Any development?" AbdulAhad ya tambaya. "Aboki ina cikin damuwa mai tsanani, i'm just pretending to look okay. Bana iya barci, ko na yi barci mafarkin ta nake yi tare da wani na, na kira Batulu ko sun samu wani labari ta ce har yanzu babu, har makotan su data sa su gaya mata da zarar sun ga tazo wajen Kakannin nata sun ce har yanzu bata zo ba. Na tabbata su Goggo sun boye UmmuKulsum ne kuma ba don kowa suka boye ta ba sai don ni. Idan ta auri wani ba ni ba na tabbata karshen farin ciki na ya zo Aboki. Su Maimartaba sun ki sanya baki har yanzu. Ina cikin yanayin da nake bukatar aure, in kuma ba ita na samu ta dawo min ba bazan iya auren kowacce mace ba, ka bani shawara, domin kwarai na ji dadin shawararka ta baya, na kuma amfana da ita". Abdul Ahad ya nisa yace "a yanzu dai bamu da zarafin zuwa gida har sai mun hada abinda ke gabanmu (zama cikakkun consultants), na maka alkawarin ni zan taya ka nemo Kulsum kuma kakannin ta da kan su zasu gaya mana inda take, na san abinda zan ce musu su karbi nadamar mu, ai da ciwo abinda ka yin, it's not easy ka dawo yanzu ka ce kana son ta su yarda da wuri, zasu yi ta tsammanin ka dawo ne don ka samu ka farantawa iyayen ka ba don kana son 'yar su ba, in aka yi la'akari da yadda komai ya wakana". Sun dade suna tattaunawa Abdul 'Ahad na kwantar masa da hankali, har yana fadin "Turaki believe me..... Kulsum bazata iya auren kowa ba bayan kai, u are her first love, her first husband, duk wanda zata aura da fargaba zata shiga gidan sa tunda ta san ita ba budurwa bace, ko zata yi aure a gaskiya ba yanzu ba, abinda zata fi maida hankali a kai yanzu shine neman ilmi don ta gina rayuwar ta". *** *** *** Dr. Sakeenah ta daga waya ta yi kiran lambar Taufeeq, “Yaya Taufeeq guess what?” Dan tsaki ya yi, “Ke fa haka ki ke, sai mutum yana tsaka da aiki ki ishe shi da shirme, komi ba za ki fada kanki tsaye ba sai kin yi ta kumbiya-kumbiya”. Sakeenah ta ce, “Tunda ba za ka saurare ni ba ka yi wa kanka, na fasa gaya maka albishir din”. Ta kashe wayarta. Ya kira ta ki dagawa, ya sake kira ta kashe wayar gabadaya. Don haka da ya tashi aiki ya dauke kan motarsa ya yi Victoria Island gidan Sakeenah, duk da ya san ba wani abu ba ne mai muhimanci za ta gaya masa. Amma me? Wadda ta bude kofar a lokacin da ya danna door bell bai yi tsammanin ganinta a garin Lagos ba. Baki ya bude sakaka! Yana kallonta. Murmushi ta yi ta ba shi hanya ya wuce, yana fadin. “So this is the albishir, sorry Doctor, wannan har goron albishir zan ba ki ai. Kulsum in town, what a surprise!” Sakeenah ta ce, “Rike goronka tunda ka gwale ni”. Engnr. Farouq ya shigo falon, ya mike ya ba shi hannu, ita kuma Kulsum ta wuce dakinsu. Nasma da ke taje dogon gashin kanta ta ce, “Kamar muryar Yaya Taufeeq nake ji a falo?” Ta amsa mata da, “Shi ne”. Nasmah ta ce, “To fa shi ke nan yanzu ba sauki, ga shi muna da wajen zuwa, gidan su wata course mate dina za mu je”. Ya karaso har kofar dakin nasu, ya ce, “Kulsum, abin ma haka ne ko? Za ki zo amma jiya ba ki gaya min ba?” Tana kawar da kai daga gare shi, ta ce, “Ni ma ban san da tafiyar da wuri ba, don da Aunty Nasmah ita kadai za ta zo”. Nasmah ta ce, “Ba wani nan, ko sanda ku ke waya jiya ai kin dade da kulle jakar kayanki”. Ya jinjina kai, ya ce, “Na gode Kulsum, na kwana da sanin ba ki damu da ni ba ai. Ni kadai nake bilinbituwa ta…”. “Yanzu dai Ya Taufeeq ka dauke mu ka kai mu Lekki gidan su kawata Iftihal, sai ku yi soyayyar a hanya kada ku shiga lokaci na”. In ji Nasmah. “O.K, ku fito ina jiranku”. Bakar Abaya ta fiddo za ta dora a kan kayan jikinta, wadanda english wears ne ba masu kama jiki ba, cikin tsarabar da Nasmah ta kawo mata, amma sai Nasmah ta karbe. Wata dakakkiyar shadda dark pink wadda aka yi wa dinki Senegalese ta fiddo mata cikin dinkunan da Sakeenah ta yi mata, tana faman mitar, “Ban san yaushe za ki shigo gari ba Kulsum, kullum ana fiddo ki kina nokewa”. Kwalliya sosai ta yi mata, sannan suka tadda Taufeeq a mota bayan sun yi wa Dr. Sakeenah sallama. Suna tafiya zuwa Lekki, Taufeeq na tsokanarta. “Ka ga amaryar Taufeeq M. Bello ta kashe kala”. Ta sha kunu sosai sannan a shagwabe ta ce, “Wallahi Aunty Nasmah ce ta takura min na yi kwalliya”. Ya ce, “Tana so ki burge Yayanta ne, kuma kin burge shin. Duk kin dusashe hasken sauran mata daga idanun sa”. Ya daga wayarsa ya kashe ta da hoto. Ta yi narai-narai da ido sai hoton ya bada wata irin kala mai kyau. Tarba ta musamman Iftihal kawar Nasmah ta yi musu. Ba su dade sosai ba sabida Taufeeq da ke damun Nasmah da waya. Sai da ta gwammace ba ta sa shi ya kawo su ba. Ta san arzikin Kulsum ta ci da har ya yarda ya kawo su din. A hanyarsu ta komawa gida, shopping sosai ya tsaya ya yi wa Kulsum, Nasmah na taya shi zabe. A kwanaki bakwai da suka yi a Lagos, kullum sai Taufeeq ya zo wajen Kulsum in ya taso daga aiki, a gidan yake cin abincin dare. Kullum kokarinsa Kulsum ta sake da shi, ta yarda za ta ba shi martanin soyayyar da yake yi mata, amma kullum jiya-i-yau, Turaki ya yi wa zuciyar Kulsum babbar illah, duk da ta cire shi a ranta, ba ta da hope a kansa, amma ba ta jin bayan shi za ta iya kara sanya wani Da namiji a zuciyar ta. Sai dai tana martaba Taufeeq sabida mahaifiyarsa da ‘yan uwansa da ke rikonta bilhakki. Ta dawo gida ranar lahadi, litinin ta koma makaranta. A can ta baro Nasmah wadda za ta kwana biyu kafin ta dawo. *** *** *** BAYAN SHEKARA HUDU Kamar kiftawar ido, haka shekarun suka zo suka mirgina, abubuwa da yawa sun faru a cikinsu. A shekaru hudun Ummu Kulsum Abdulhadi Yalleman ta fiddo da HND in Nursing. An yi bikin Batulu shekaru biyu a baya, tana garin Kaduna tare da mijinta Abdulkadir ma’aikacin GT Bank, yaranta biyu mace da namiji twins. Wannan ne lokacin da Hajiya Nasara ta deba wa Taufeeq na jiran Kulsumu, don haka zuwa yanzu kusan kowa nata ya san da zaman Taufeeq, ya je har Gaya da 'Yalleman ya gabatar da kansa. Yanzu burin kakanninta shi ne kawai ta yi aure. Amma Kulsumu kullum tausarsu ta ke yi kan su barta ta yi hidimar kasa, ta fara specialization dinta. Daddyn su Taufeeq ne ya sa hannu aka barta yin hidimar kasa a Abuja, inda bayan camping suka tura ta National Hospital. Shekara daya baya suka sha bikin Nasma da masoyinta Mujaheed dan abokin Daddynsu, Mujaheed ma’aikacin Shell Company ne, suna zaune garin Port-Hearcourt. Kulsum Abdulhadi, cikakkiyar ma’aikaciyar jinya mai shekaru ashirin da hudu, a wannan lokacin komai nata ya kai ya kawo. Ta samu wayewar kai irin wadda zurfin ilimin boko ke sabbabawa mai shi. Wayewa mai tafe da rikon addini. Ta canza gabadaya daga Kulsumun Goggo zuwa Kulsum din Nasara. Ba abin da Goggo Shatu da mijinta za su ce wa Hajiya Nasara sai addu’ar alheri, domin ta zama bayan da ya goya marainiya Kulsum ta tsaya da kafafunta, ta cika burinta na zamowa mai amfani ga al’umma. Zuwa wannan lokacin ko ta ki ko ta so, ta tsayar da Taufeeq a matsayin mijin da za ta aura, sabida dalilai masu yawa da ba za su kidayu ba. Muhimmi shi ne mahaifiyarsa, sannan ‘yan uwansa mata da suka ba ta kaunar ‘yan uwantaka irin ta 'yan uwa na ciki daya wadda ba ta taba samu a rayuwarta ba. Ta manta ita din marainiya ce. Turaki ya zama wani rufaffen kundi (littafi) wanda ba a bukatar a bude shi. Ya zama past, wani irin past da ba ta ko son tunawa, domin babu wanda ya taba barin tabo a zuciyar ta kamar sa. Ba ta taba hasaso future dinta da shi ba. He is her past and Taufeeq her present. *** *** *** Tana kammala hidimar kasa su Goggo ba su biye mata ba, suka saka ranar aurenta da Taufeeq watanni uku masu zuwa, in don ta ita ne a barta ta je Yola ta yi shekara daya don zama cikakkiyar Perioperative Nurse. Zumudi a wajen Taufeeq abin ba a cewa komai. Zuwa yanzu ya daina damuwa da son martanin soyayya daga Kulsum, mu’amalarta da shi saffa-saffa. Ba ta zafafa a ciki ba, shi ma kuma ya ja girmansa bai cika takura mata ba. Amma daga lokacin da aka sanya musu ranar aure gabadaya ya canza, soyayya yake nuna mata a sarari kamar ya cinye ta. Ita kuma in ta tuna cewa ba a budurwa zai aure ta ba duk zumudin nan da yake nunawa a kanta, sai jikinta ya kara yin sanyi. Ita bazawara, shi saurayi, wannan abu yana damunta a rai. Amma shi ko a jikinsa. Ta lura ba karamin shiri yake yi wa aurensu ba. Gidan da za su zauna a Lagos ya gama gyara shi, ya wadata shi da komai na rayuwa. Biki saura sati biyu, Goggo Shatu ta ga ya kamata ta je ta sanar da Umma auren Kulsum, amma nauyi ya hana ta. Ta ga cewa kuma in ba ta sanar da ita ba, hakika ba ta kyauta ba, alakar da ke tsakaninsu ba Turaki da Kulsumu ne suka hada ta ba, don haka bai dace a ce su za su raba ba. Ta san ta yi musu babban laifi, amma ba ta da yadda za ta yi ne, ta kuma ji dadi da har gobe Umma ko Maimartaba babu wanda ya taba saka baki a kan komen Kulsumu, wannan ne ya ba ta karfin gwiwar amincewa da maganar Dan Nasara. Shekaru biyun baya Abubakar Turaki ya zo tare da abokinsa, ban hakuri na duniya babu irin wanda ba su yi ba, amma ta yi abin da har gobe yake damunta; kafewa kan bata san inda Kulsumu take ba, wanda sanadin hakan ne ya sa watakila Turaki bai sake takowa kofar gidansu ba. Ta hanga ta duba ta ga ba mafita, dole Umma ta san da auren Kulsumu, don haka ta kwashi kunyarta a tafin kafarta ta tafi gidan Sarki. Umma na lale marhabin da zuwan Goggo kamar yadda ta saba, kuma ta cika gabanta da kayan makulashe. Sun dade suna gaisawa, sannan suka barke da hira, inda Umma ke sanar da Goggo nan da sati biyu za a yi bikin Nana babbar ‘yar Yaya Hadiza a garin Kiru, ko Goggon za ta samu zuwa? Goggo ta yi dan jim! Kafin ta ce, “To ai ni ma gayyatar bikin ce ta kawo ni, auren Kulsumu ne ya tashi da dan marikiyarta, shi ne na zo in gaya miki”. Wani irin rikicewa Umma ta yi, amma ta yi kokarin rike kanta a gaban Goggo ba ta nuna dukan da maganar auren ta yi mata ba. In suna da matsala a yanzu kan ‘ya’yansu, to matsalar Turaki ce, ya ki aure har gobe yana jiran dawowar Kulsum rayuwarsa, Turaki ya dangana da neman Kulsumu ne ba don ya hakura ba, sai don fahimta da ya yi cewa, iyayenta ba sa bukatar sauran alaka a tsakanin su. Har gobe ba ta fidda rai da dawowar Kulsum cikin iyalinta ba, domin Allah ta ke son yarinyar ba kuma ta yi wa Turaki sha’awar kowacce mace bayan Kulsum. Ashe babu rabon sake shigowar ta cikin rayuwar su? Wani guntun hawayen tausayin Turaki ne ya zubo mata, ta yi kokarin dauke shi da dan yatsanta, ba ta bari Goggo ta gani ba don kada ta karya mata zuciya. Ta ce, “Masha Allahu, Kulsumu aure ya zo! Allah ya sanya alkhairi Ya bada zaman lafiya da zuri’a mai albarka”. Goggo a zuciyar ta ta ce, “Amin”. Ta kasa amsawa a fili, saboda ganewa da ta yi Hajiya Rakiya hawaye ta ke yi. Ba ta jima ba suka yi sallama, kowa jiki a sanyaye. A daren Umma ta samu Maimartaba ta gaya masa maganar auren Kulsum. Ba ta fahimci komai a tare da shi ba. Washegari da ta shigo kawo masa karin kumallo ya ce, “Na bada umarni a yi wa yarinyar nan kayan daki kamar yadda na alkawarta a baya. Sai ki samu wadanda za su je su kai wa iyayenta. Allah ya sanya alkhairi”. Umma don takaicin sa tashi ta yi ta fita ba tare da ta ce komai ba. Saura sati daya biki Nasma ta zo Abuja tana tura tsohon cikinta. Aunty Sakeenah ta roki Hajiya Nasara amarya ta je Lagos a can za ta sa a yi mata gyaran jiki. Kuma a can za a yi dinner din ango da abokansa wadda Nigerian Navy suka shirya masa kafin daurin aure. Hajiya ba da son ranta ba ta yarda ita da Nasma da mijin Nasma Mujaheed suka tafi Lagos. Mai gyaran jikin da Sakeenah ta dauko ‘yar Sudan ce mazauna Lagos, tun washegarin zuwansu ta fara aikinta a kan Kulsum. Sakeenah ta hana Taufeeq ganin amaryarsa ko da wasa, ya zo gidan ya fi a kirga ta hana shi ganinta. Shi kuma ya hada baki da Mujaheed mijin Nasma kan ya san yadda zai yi Nasma ta kawo masa Kulsum, shi dai ya ganta ko na minti biyu ne. Mujaheed ya tausaya masa, ya dau waya ya kira Nasma. “Sweety har yanzu ba a gama muku gyaran jikin ba ne?” Nasma ta ce, “An gama na yau, saura na gobe. Wani abu?” Ya ce, “Ba wani abu, Yayanki ke son amaryarsa ta zo su je wajen telan da zai dinka kayansu na dinner, telan ya ce dole sai ta zo da kanta kayan za su fi fitting dinta. Amma don Allah kada Sakeenah ta san kun fito, ba za ta bari ba”. Nasma ta ce, “Ba wani abu, we will be there in 25 minutes, Aunty Sakeenah sun fita da Engnr, amma ba za mu dade ba ko?” “Ko minti talatin ba za ku yi ba insha Allahu”. Nasma ba ta gaya wa Kulsum inda za su ba, har ta yi parking a kofar gidan Taufeeq. Wani kyakkyawan mansion mai kyau da tsari a Lekki. Har suka shiga falon farko inda ta ci karo da hotonta window size. Ba a dade da yi mata dilka da halawa ba, sai sheki ta ke yi, ga wani sihirtaccen kamshi da ke tashi daga jikinta. Tana juyawa daya barin ta tadda the same window size na hoton Taufeeq, nan ta gane inda suka zo. Suna ta sallama shiru, sai Nasma ta ja hannunta suka kutsa har bedroom din Taufeeq, amma ba ya nan, kuma babu Mujaheed, ta ce da ita ta zauna ta duba su a backyard, ta kira wayar Mujaheed bai dauka ba. Nan Kulsum ta samu wuri ta zauna a kan sofa kwaya daya da ke dakin. Wata irin kishirwa ce ta dameta tun kafin su taho. Tana juyawa ta yi arba da bedside fridge din Taufeeq. Mikewa ta yi a hankali ta isa ga dan karamin firjin ta rage tsawon ta tana addu’ar Allah ya sa ta samu Maltina. Best drink dinta kenan. Sai dai me? Kwalaben da ta gani a jere a ciki ba ta taba ganin irin su ba, wasu dogaye da su masu fadi daga kasa. Da sauri ta zaro kwalba daya, ta bi rubutun jikin su da kallo "whisky" baro-baro. Wato “GIYA" ga su nan kala-kala na zamani, masu karshen tsada. Jin takunsu ta yi ana nufo dakin, da sauri ta mayar da kwalaben yadda ta gansu, ta koma bisa sofa ta zauna, kirjinta na wani irin bugawa da sauri da sauri. Numafshin ta na neman daukewa. La-shakka da tana da asthma da hawan jini ba abinda zai hana su tashi a wannan lokacin. Wannan duhun da ya kan mamayi idanunta ya zo ya lullube idonta. Allah ya so ta a zaune ta ke, da babu shakka faduwa za ta yi. Daidai lokacin da Taufeeq da Nasmah suka shigo dakin. Runtse idanunta ta yi tana tasbihi ga Allah, ba ta ko son bude su don kada ta ga fuskar Taufeeq. Kujerar da ta ke zaune ya zo ya zauna dab da ita. Kamshin sassanyan turarensa ya bugi hancinta, ta kara runtse idonta, ta ki yarda ta bude. Ya sa hannu zai taba ta, ko me ya tuna kuma ya fasa. Da ganinsa ka ga wanda ke cikin madaukakin farin ciki, shaddar jikinsa fara kal, sai maiko ta ke yi tana nuna tsadarta. Ya yi wani irin fresh da shi, da ganinsa ka ga sabon ango wanda ya gama samun duk wani farin cikin rayuwarsa. Tunda ya zauna yake tsokanar ta. Sai a lokacin ya lura Kulsum hawaye ta ke yi, hawayen da bai san dalilin zubarsu ba. Hankalin sa yayi mummunan tashi, bai san sanda ya dora hannunsa a kan nata ba ya kira sunanta muryarsa na sarkewa. Har yanzu ba ta bude idonta ba, don bata son ganin sa, amma hawaye ne ke zuba ta gefen idonta. Da ya dora hannunsa a kan nata ji ta yi tamkar ya dala mata garwashin wuta. Ta soma kokarin janye hannunta, amma ya hana ta damar hakan. Yau mashayin giya Allah ya nufe ta da aure, ita Kulsumu jikar Goggo? Astagfirullah! Ita ko wane laifi ta yi wa Ubangiji ya hada ta da wannan kaddarar? Tayi saurin yin istigfari ga kalamanta. Mikewa ta yi da niyyar barin dakin, amma Taufeeq bai saki hannunta ba. Wata zuciyar ta gargade ta da cewa, kada ta yi wani action wanda zai sa ya fahimci ta ga sirrinsa. Don haka ta bude idanunta a jigace, ta zube su a kanshi, kana iya hango zurfin kololuwar tashin hankalin data ke shimfide cikin idanunta, ta ce, “Yaya Taufeeq ka sake ni gida zan tafi”. Yana kokarin kallon tsakiyar idanunta data sake runtsewa ya ce, “Laifin me na yi miki haka Kulsum?” Da sauri ta ce, “Ba ka yi min laifin komai ba, na ga bai dace in zo nan ba ne, kuma bana jin dadi”. Ya ce, “Na biya sadaki, fatiha kawai ya rage a shafa, shi ne ki ke cewa bai dace ba don kin zo gidanki?” Wasu hawayen suka shimfido mata, ta ce, “Wallahi bana jin dadi, don Allah ka bar ni in je in kwanta”. With concern ya ce, “Ban ji komai a jikin ki ba na alamun zazzabi, ina yake miki ciwo?” Da sauri ta ce, “Ido na”. Don dai ta samu ya kyaleta. Ya ce, “Then let us go ki ga ophthalmologist”. Ta katse shi da hanzari, “Ba fa ciwon yau ba ne, tunda na taso da shi na taso”. “Kuma ba ki taba ganin likita a kai ba? this is silly, ki wuce mu je kawai”. Za ta yi musu ya dora yatsansa a kan labbansa, tare da jan hannunta suka bar dakin. A haka suka tadda Nasmah da Mujaheed a falo, wadanda ke zaune suna shan coffee. Su duka biyun suka dago ido suna kallonsu, Nasmah ta ce, “Lafiya?” Ya ce, “Mujaheed ya maida ke gida, zan kai Kulsum ta ga likitan ido”. Ta ce, “Haka ake zuwa ganin likitan afujajan ba shiri ba appointment?” Ni dai gaskiya kada ka hada ni da Aunty Sakeenah". Ya harare ta yace, “European Hospital zan kai ta, sabon asibitin ido ne, na hadin gwiwar European Union (EU), ko yaushe ka je za ka ga likita”. Kulsum wadda duk rawar jikin da yake a kanta ya daina burge ta, kwarjininsa ya zube daga idanunta, ta ce, “Don Allah Ya Taufeeq ka barmu mu tafi gida, ma je asibitin daga baya, idan Aunty Sakeenah ta dawo ta ga ba ma nan za ta yi mana fada”. Ya ce, “To hell with Aunty Sakeenah, kina zaune da ciwon ido shekara da shekaru ba ki taba ganin likita a kai ba ki ce wata Sakeenah? Wuce mu je kada ki bata min rai”. Nasmah ta ce, “Ni dai ka san yadda za ka yi ka fidda ni wajen Aunty, sai kun dawo”. Har ya tada motar suka hau titi Kulsum hawaye ta ke yi, hawayen da ya danganta da ciwon idon nata, ko on fadan da yayi mata. Da kuma rakin ta, haka ta ke da raki kamar kankanuwar yarinya, abin kuka ba ya mata wuya. Kulsum ta daga kai ta dubi tankareren asibitin da Taufeeq ya kawo ta. European Specialist Eye Hospital. Ya samu wuri ya yi parking ya bude mata kofa. Tare da cewa, “Mu je ciki, ko sai na dauke ki ne?” Ba ta ce masa komai ba, don yanzu komai nasa ya daina burgeta, ta sa kafa ta fito. Tana zaune ya je ya yanki kati ya yi komai ya dawo. Aka nuna musu ofishin da za su ga likita. Mutum biyu ne a gabansu, daya na ciki bai fito ba, daya na kan layi daga waje. Suka zauna, Taufeeq ya ce da ita, “Ba sa bata lokaci su, kana zuwa za'a duba ka, sunada kwararrun likitocin ido, duk Nigeria babu kamarsu a fannin ido, don haka ne tsadarsa ba ta dada ni da kasa ba”. Ita dai jinsa kawai ta ke yana kara sire mata. Abun ba kama! Wai Taufeeq mashayin giya. Allah Sarki Hajiya! Ko ya ya za ta ji duk ranar da ta samu wannan bakin labarin? Tana alfahari da ‘ya’yanta, tana bugun kirji da tarbiyyar da ta ba su. Kullum burinta shi ne su zame mata ‘ya’ya na gari. Musamman Taufeeq da yake namiji tilo shi kadai da Allah ya ba su. Daddy na son Taufeeq yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba! Ya ya za su ji idan ta zo gabansu ta ce ta fasa auren Taufeeq, saboda giya yake sha, ana saura kwana hudu daurin aurensu? In kuma suka karyata ta fa? Suka ce sharri ta yi wa dan su? Anya za ta iya yi wa Hajiya Nasara wannan sakayyar ta fasa auren Taufeeq kwanaki kadan gabanin aurensu? Duk wani shiri na duniya sun gama shi, har kayan aure su suka yi mata, da wane bakin za ta zo ta ce ta fasa auren Taufeeq a yarda da hujjar ta? To amma haka za ta bari tana ji tana gani a aura mata mashayin giya ya zama uban ‘ya’yanta? Tana wannan tunanin mai matukar soya zuciya mutumin da suka tarar ya fito daga ofishin likita, Taufeeq ya wuce gaba ta bi shi a baya. A jikin kofar ofishin an rubuta (Consultant Ophthalmology), ta bi bayan Taufeeq cikin mutuwar jiki da ta zuciya suka shiga. Sanyin Iya kwandishan ne ya fara bugun jikkunan su. Kulsum ta kai dubanta ga mamallakin ofishin wanda ke zaune cikin kujerar sa mai juyawa dama zuwa hagu, ya baiwa kofar shigowa baya, idon sa na kan file din ta. Sanye cikin grey-black Italian suit. Gabadaya ya juyo da kujerar sa ya fuskance su, amma idon sa na kan file din gaban sa. Ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane TURAKI ba, Turakin ta .... Her Ex-Turaki, kowanne irin canjin rayuwa ya samu kuwa, sai dai ya tara suma a kansa wadda a baya ba shi da ita, ta kwanta luf a kansa sai sheki ta ke ta fulanin Gaya. A jikin dan karfen da ke kan teburin sa cikakken sunan sa ne cikin ruwan gold, DR. ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI GAYA..... ta wani irin zuki numfashi ta fesar. A hankali ta soma maida kafafunta baya don barin ofishin. Cikin tsananin taka-tsan-tsan na kada takunta ya bada sauti. Abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun ta.... Alaqar da ke tsakaninsu, wata irin alaqa ce ba mai kankaruwa daga zuciya ba!!! Saura taku biyu ya rage mata ta fice ya dago kansa gaba-gadi don ganin masu shigowa… Bayyanannen canjin da ta samu cikin shekaru takwas da doriyar watanni bai hana shi gane ta farat daya ba, kamar yadda itama nashi canjin da nauyin shekarun da suka hau kansa, suka bashi suffar cikakken mutum wanda ke cikin ganiyar cin ilmin sa, ya kuma san ciwon kansa a halin yanzu, bai hanata gane shi ba. Ya kafe ta da idanunsa ta cikin farin gilashin da ke manne a idon sa,... idanun nan na Turaki da ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu... A lokacin da ita kuma ta bude kofa ta fice da dan banzan sauri… har tana tuntube, saura kadan ta fadi! Mu karasa a littafi na uku. Kuma na karshe insha Allahu. Kulsum 3 zai biyo bayan sa bada jimawa ba. Nayi muku alkawarin cigaban bazai jima ba. Gundarin labarin Kulsum yana cikin littafi na uku. Taku har abada:- SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI. JANUARY, 2021. Ga masu bukatar tsofaffin littafaina zaku iya mallakar su a softcopy ko hardcopy (based on order idan hardcopy ne), a tuntube ni a whtsp ta wannan lamba 07030137870. DANDANO DAGA KULSUM 3 "Malam lafiya?" Tayi tambayar tana dojewa kallon idanunsa. "Na zo fita, ka sa securities din ku sun tare ni, na ci bashin ku ban biya ne?" Bata yi aune ba ta ji hannun ta cikin na Turaki, kafin ta tantance meke faruwa ya jata tana tirjewa ya bude motarshi ya sanya ta, tare da rufe kofar da key din hannunsa. Ya zagaya ya shiga mazaunin sa ya tashi motar. Masu gadin suka wangale masa kofar ya fice suna daga masa hannu cikin girmamawa. Tafiya kawai yake bisa shimfidaddun titunan garin Lagos ba tareda Kulsumu ta san inda aka nufa ba. "Malam sace ni zaka yi? Malam ina ruwan ka da ni ne? Malam ni matar aure ce ko baka ganni tare da mijina ba!" Idan sitiyarin motar ya bata amsa, to mai tukin motar ma ya bata. Inda take wannan bai kalla ba, tukin sa kawai yake cikin nishadi, sai sharara gudu yake amma murmushin dake kan tattausar fatar bakin sa ya kasa bacewa. Kulsumu ta soma bugun gilashin motar da duka hannayen ta, fatan ta gilashin ya fashe koda zai yanke ta ne, tayi ihun da mutane zasu ji su kawo mata dauki. Amma ta lura gilashin motar ko sound baya badawa kuma ko zata shekara tana bugun sa bazai fashe ba. Kawai sai ta fashe da kuka tana kiran Goggonta da Baffanta. Abinda yayi matukar baiwa Turaki dariya, ya dubeta ta gefen idanunsa, "saura Batulu da Ummah". Idanun cike da kuka amma hararar shi take yi. Har suka shiga unguwar Ikoyi Kulsumu bata bar kuka ba, don ta gane in ma sata ce Turaki ya gama sace ta. Sun wuce gidaje kamar guda biyar kafin su shiga wani kyakkyawan 'lodge' mai hawa daya. Mai gadi ya zo ya bude, Turaki ya zura hancin motar sa cikin gidan. Yayi parking a rumfar adana motoci wadda ke dauke da wasu motocin guda biyu, ya kashe motar tare da sakin nannauyar ajiyar zuciya. Ya dubi Kulsumu wadda ta ki dagowa daga cinyoyinta, balle ta san inda ya kawo ta. Sautin kukanta kadai kake ji a motar, kamar wadda aka fadawa sakon mutuwar iyayen ta. Kirjinsa ne kawai yake dagawa yana sauka da sauri da sauri. Ya yarda wani lokacin 'excitement' zai iya haifar da bugun zuciya. To hakan ce ta faru ga Turaki. Wanda ke ganin komai dake faruwa dashi yau kamar a mafarki..... wai shine da Kulsumu a gabansa! Idan mafarki yake yana rokon Allah kada ya farkar dashi daga wannan mafarkin, har sai ya ga karshen sa. Har sai ya gan shi tare da Kulsumu matsayin ma'aurata a karo na biyu. Ashe duk mahaukacin neman nan da yake wa Kulsumu tana cikin kasar Nigeria, a Najeriyar ma a garin da yake rayuwa!. Allah shine shaida kan babu abinda ya wahalar dashi a duniya irin neman da yayi wa Kulsumu, shekaru dai-dai har guda hudu. Shi Allah da yake Gafurun-Rahimu ne, yau gashi ya tankado keyar Kulsumu ya kawo mishi ita har cikin ofishinsa. Shin shi wane irin wawa ne da zai yi saken da zata sake kufce masa? "If u are done the cry (idan kin gama kukan) ki wuce mu karasa ciki". A matukar fusace ta dago ta dubeshi.... "Nima bansan meye hadin nawa dake ba.... I just want to confirm ko Kulsumu na ce wannan. I just want to confirm....idan matata dana rasa nake nema ce. I just want to confirm....idan reaction din ta sabida ganina a inda bata yi tsammani ba yana da alaqa da ta gane ni ne itama, ko kuwa wani abu ne daban ya firgitata take neman mafaka.....". Kulsum 3. Kada ku bari a baku labari. Akwai Dambarwa ba 'yar kadan ba. -Takori