[6/3, 4:13 pm] Takori: **** Karfe goma na safe su Ummi suka yi shirin tafiya taren su Bashir a filin jirgi. Tun asuba da na yi sallah fuskata babu walwala, kallon kowa kawai nake zuciyata a cunkushe da bakin ciki da bacin rai maras dalili. Hajjah yau ko gaishe ta ban yi ba, babu wanda na yiwa magana. Na zubawa allon talabijin ido kuri kai ka ce program din nake saurara, amma ina! Zuciyata ba ta tare da gangar jikina, abubuwa masu ban al’ajabi da ban tsoro kawai take wassafa min masu shirin faruwa dani. Kafin karfe goma na safe gidanmu ya cika ya batse da dan Adam, sai busa algaita ake ‘yan daurin aure suka fara layin shigowa gai da Hajjah suna fita, ‘yan’uwa ne da abokan arziki. Kafin Babanninmu su shigo sun sha ankon farar shadda (getzner) sai sheki suke. Suka zube a falon Hajjah suka kwashi gaisuwa suka fita. Ina daga uwar daki ina hango ficewarsu ta taga daya bayan daya. Mintina talatin bayan fitarsu na ji gabana YA FADI! A dai-dai lokacin da dakikar agogo ya nuna karfe goma sha daya na rana, a lokacin ne aka daura aurarrakin masu ban mamaki, da suka ajiye kundin tarihi da wani aure bai aje ba cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa. Wani maroki mai zakin muryar tsiya yake fadi da murya mai karsashi da kwarzantawa cikin babatun magana “ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!!” Sai da ya fada har sau uku. “An daura auren FA’IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA da FA’IZU MUKHTAR ABUBAKAR GIWA. HADIZA da MUHAMMADU BASHIR, a kan sadaki lakadan ba ajalan ba. Allah yasa anyi a sa’a, yasa anyi sai bakin rai, Allah ya sanya alkhairi ameen.....”da sauran babatu irin na maroka. Maimakon in kira yi sunan Allah sai na kwarara ihu da iyakacin muryata na zube a wajen a sume. Ban kara sanin me ke faruwa a duniyar ba. *** Jirgin Boeng 708 ya sauka a filin jirgin saman Mal. Aminu Kano da misalin karfe daya na ranar da ta kasance Asabar, wato awanni biyu da daura auren. Jirgi ne da ya taso daga Ukrain zuwa Nigeria bayan shafe awanni masu yawa yana keta hazo, kafin ya wulwulo kasa ya tsaya a cyprus ya sha mai sannan ya keto kasarmu mai dimbin albarka. Sai da passengers kaf suka gama fita kafin Pilots din su fito cikin fararen uniform dinsu. Shine na karshe a saukowa. Fari sol! Mai madaidaicin jiki, zai fi kyau ka ce ba shi da kauri sai fadin kirji wanda da ka kalla za ka san gym ya samar da shi. Ma’abocin wasu ilhamomi da nasibobi da dama da ba duk maza Allah ya mallakawa ba. Ya saya fararen idanunshi cikin gilashi mai duhu ainun samfurin ‘KAREN MILLEN. Sajen da ya zagaye gefe da gefen fuskarsa baki sidik kwantacce wanda a da baya da shi bai boye tsagin mallacinsa ba. Sai ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa ya fiddo cikakken Bamallen sa, kuma Bafillace. Dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ya dama, ya kutsa cikin ilmummukan zamani daban-daban. Dogon hanci gare shi kamar ruler aka sa aka ja shi aka daidaita shi a tsakanin idanunsa. Idanunsa dara-dara wadanda suka dan shige loko kadan farare tar masu sheki da maiko (oily eyes) wadanda duk cikin zuri’arsu maza da mata shi kadai aka ya yiwa wannan ilhamar. Idan lissafin da yake yi dai-dai ne yau shekarunsa takwas da barin gida ba tare da ya sake ko da waiwayarta da sunan hutu ba. A zubin halitta da kirar jiki ya fi kama da Ahmadu A.B, a halayya kacokan Abubakar Giwa ya kwaso ba wani cikin zuriyarsa ba. Don haka, ka ce ga hakikanin halayyar FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA, abu ne mai matukar wuya. Za ka san halinsa ne kadai idan ka zauna da shi, zaman ba na kwanaki ko watanni ba, sai dai shekaru. Shekarun ma sai idan kwana kake tare da shi daki daya ka kuma tashi tare da shi, halin da ake kira halin MAZAN JIYA ba na YAU ba, and difficult to be studied by sociologists and psychologists. Idan aka ce su karanci irin pilot Fa’iz za su yi placing dinsa ne kawai (upon hypothesis) but not a dependent variable. Daga fitowar shi daga jirgi har shigewar shi wani ofishi (pilots changing room) idanun Khadija-Ummi na kansa, tana mai yiwa Allah tasbihi da godiya mara iyaka da wannan miji da Allah ya ba ta wanda ke ninkaya cikin zuciya da mafarkinta, ba ta taba tsammanin akwai ranar zahirantar mafarkin nata ba. A hankali ta ji danshi a kan fuskarta, wanda ba ta ko tantama hawayen farin ciki ne. Har zuwa lokacin da ya gama shige da ficensa a (airport) din tare da abokan aikinsa, ya canza kaya zuwa kaftan na farar lallausar shadda (Hilton) da ruwan kasar hula a kansa, takalmin fata dake kafarshi shima ruwan kasar ne. Ya janyo trolley dinsa zuwa inda ya hango fuskokin masu kama da tasa fuskar, wanda komai daren dadewa suna gilmawa cikin idanunsa, wato fuskar zuri’ar Abubakar Bamalli, wanda ya fi so da gani shi ya fara ganin, wato Aliyu Na’ibi. Da sassarfa Aliyu ya karaso suka rungume juna shi da Fa’iz, rayuwarsu ta baya ta dinga dawo masa tar-tar kamar a majigi. Abubuwa da yawa ba zai manta dasu ba. Cikin taron nan kaf na mata da mazan Bamalli, manya da yara, wadanda ya sani da wadanda bai sani ba, musamman kananan yara, ya hanga ya duba bai ga Zahrar cikin taurarin ba. Ya ga Zanirah, ya ga Ummi, Mus’ab, Junior Yahya, Shu’aib, Walida, Abdallah da wata karamar yarinya mai tsananin kama da Fa’izah (Khausar), da sauran kannensa ‘ya’yan Baba Barau, Sadi, Salisu, Sani da Na’ibi. Mutum daya ce kawai babu, wato KANWAR kuma abokiyar fadan da a yau ta juye ta rikide zuwa matarsa ta sunnah. Ko da wacce irin fuska za ta karbi al’amarin? Ko da wace irin fassara za ta fassara shi? Ko da wanne irin hannu za ta karbe shi? Abin da ya sani ya kuma kwana da da sani ne cewa, Fa’izah! Ba ta da makiyi a duniya irin sa!!! To amma ai shi sonta yake yi tun can din ma. Har kuma gobe son ninkuwa yake yi irin kaunar da bai taba yiwa kowa a duniya ba, in ka dauke Mama da Baban Kaduna wato iyayensa. This is his own style of love! To amma da wane language (yaren) zai yiwa Fa’izah bayanin hakan har ta yarda ta fahimce shi, ta karbe shi a matsayin miji a gareta? Ya kuma wanke wancan dattin da ya dade yana yabawa kansa a idanunta? Don haka kallo daya za ka yiwa pilot Fa’eez ka karanto matsananciyar damuwa cikin fararen kwayar idanunsa. Duk da yaken da yake yiwa Aliyu da sauran ‘yan’uwansa. Yasa hannu ya karbi little Fa’izah hannun Zanirah ya dora a kafadunsa yana murmushi, kallo daya ya yiwa Ummi ya bude baki yana mamaki, ganin yadda kibarta ta zaizaye gaba daya, abin da babu wanda ya taba tsammani. Shi da ita murmushi suka yiwa juna, wanda ga Pilot Fa’iz murmushin ‘yan’uwantaka ne. Kuma ba annuri a fuskarsa har suka shisshiga motocinsu, yana motar Aliyu ne, Aliyun na tuki shi yana gidan gaba, Ummi da Zanirah da ‘yarta a baya. Sai dai tunda suka hau titin Zaria Road dodar wanda zai sada su da garin Zaria, kowa ya fahimci Pilot Fa’iz Bamalli cikin matsananciyar damuwa yake. Ya sanya fuskarsa cikin tafukansa Allah kadai ya san me yake tunani a zuciyarsa. Ummi ta yi tagumi a kujerar owner side da take zane. Wane irin mutum Fa’iz ya koma? Wane irin ango ne wannan babu wani alamar kulawa ko kwayar murmushi ga amaryarshi da aka daura musu aure yanzu-yanzun nan? Wane irin mutum ne shi da zai bar kasar haihuwarshi shekaru har shida da wani abu ya dawo babu alamun farin ciki a fuskarshi? Me ke damun shi? Anya Fa’iz na farin ciki da dawowar sa cikin ‘yan’uwansa? Anya Fa’iz lafiyarshi kalau? Anya Fa’iz na murna da auren su kamar yadda take tsammani? Ta jerowa kanta duka wadannan tambayoyin lokaci guda, ba ta da amsar ko daya, don haka ta sunne kanta cikin cinyoyinta ta soma kuka a hankali. Daga Aliyu, Zanirah da sauran kannensu dake cikin motar zuwa uban gayyar, babu wanda ya tambayi Ummi dalilin kukanta. Ga Aliyu shi kam abin ne ya zo mishi wani irin banbarakwai cikin sarkakiya. Bai san irin bayanin da zai ma kowannensu ba. Babbar fargabarshi yadda Fa’izah za ta karbi zancen aurenta da Fa’iz. A karo na farko ya ji haushin kansa kan munafuntarta da ya yi jiya, don me bai gaya mata gaskiya ba? Don me ya rufe mata? In kowa ya rufe mata shi bai dace da hakan ba. Ita kuma Ummi tunaninta da Fa’iz aka daura mata aure amma ganin halin ko in kula da ya nuna mata ya sanyata kuka. Shin da wane yare zai yi mata bayanin cewa da Bashir ne? Ya ya Ummi za ta tallafi maganar bayan yana da masaniyar cewar ta tsani halayyar Basheer fiye da kowa? Ta ya ya nitsattsiyar yarinya ‘yar kauyen Giwa ta cancanci tantirin dan duniya irin Yaya Basheer? Kaico da tunanin Hajjah! Kaico da bahagon tunanin iyayensu wurin hada irin wannan rikitacciyar auratayyar zumunci ko bata zumunci? Su kam sun haye! Yanzu na ‘yan bayansu yake ji. A zuciyar Zanirah cewa take yi, “Ina ma ban zo garin ba kwata-kwata balle in ga wannan rikitacciyar rana......!” A dai-dai lokacin da Aliyu ya karya kan motar cikin tafkeken (gate) din ABUBAKAR BAMALLI HOUSE.....” **** WANE NE NAZIRU GALADANCHI? Major General Sani Galadanchi shine mahaifin Dr. Nazir. Da na farko wurin iyayenshi, kamin haihuwar shi sun kwashe shekaru masu tsaho basu samu haihuwa ba. Da Allah ya kawo Naziru sai hakan ya zamo musabbabin nuna mishi tsantsar gata wanda babu kwaba ko tsawatarwa a cikin sa. Nazir ya tashi yaro dan hutu tun yana sakandire, sune samarin da ake kira ‘yan (high life) a lokacinsu. Haka nan bayan haihuwar Nazir sai da suka kwashe shekaru takwas zuwa tara kafin su samu haihuwar Haulatu. Daga Haulatu yara ne maza uku daya na bin daya duk bayan shekaru uku. Duk da jin dadi da sakewar da Nazir ke samu bai sa shi yin wasa da karatu ba, domin ya ga amfanin ilimin wurin mahaifinshi. Ya so ya tafi soja don ya gaji ubansa amma Baban ya dage kan harshen Larabci yake son ya karanta, baya son shi da aikin soja, babu kwanciyar hankali a cikinsa. Su shan sigari wannan duk a wurin Larabawa ya koya, sai dai sam in ya zo hutu baya sha a gida sai ya koma. Bai fara neman mata ba sai da ya kammala degree ya fara masters a zuwan shi bautar kasa garin Lagos, inda ya yi wani aboki Tim ya koyar da shi mu’amala da mata, don haka da ya koma Taiwan sai idonshi ya bude da hakan. A can ya kammala PHD ya dawo Kano ya fara aikin da yake yi a Bayero. Rasuwar Tim ta hanyar muguwar cutar (SIDA) Aids bai sanya Nazir Sani kintsuwa ba sai haduwar shi da Fa’izah A.A Giwa. Bai taba neman kowacce diya mace da niyar aure ba sai a kan Fa’iza, kamar yadda bai taba son wata diya mace tsakani da Allah ba baya ga Fa’izah. Bai taba tunanin zai bar yaudarar mata ba sai a kan Fa’izah. Daga ranar da ya dora ido a kanta, bai kara kula wata yarinya da sunan iskanci ko yaudara ba, domin yana ganin kintsattsiyar yarinya kamar Fa’izah ba ta dace da watsattsen miji kamar shi ba. Don haka ya kimtsa kansa, tun hakan bai zamo dalilin da za a hanashi Fa’izah ba. Tunda ya tabbatarwa kansa aurenta zai yi domin Allah da soyayya. Ya yarda ya amince da duk zargin da ake masa na cewa shi din dan iska ne, ya yarda ya kuma amince bai taba musantawa ba, kamar yadda bai taba cewa yana da wani hali na kirki ba. To amma wanda duk yake tarayya ta jiki da Naziru Sani, zai yi shaidar cewa mutum ne wanda baya wasa da sallah, kuma zuciyarsa daya ce da ita yake zaune da kowa, sannan ba shi da tsoro. Baya tsoron uban kowa, sannan abin hannunshi bai rufe mishi ido ba sam. Daga ranar da suka yi magana da Abdullahin Haulatu, ranar ba ta zagayo ba sai da Dr. Nazir ya gabatar da maganar Fa’izah ga iyayenshi, ya kuma roke su da aje mishi neman auren ta sati mai kamawa. Hajiyar su Haulatu ta yi matukar farin ciki da Allah ya nuna mata ranar da Nazir ya kawo mata zancen aure da bakinsa da ranta kafin mutuwar ta. ‘Yammata iri-iri ta sha nemawa Naziru yana fitittikewa, shi aure ba yanzu ba sai ya ci lokacinsa matarshi ma ba a haife ta ba. Da farin cikinta da rawar jikinta ta isar da sakon Nazir ga General, shima ya yi farin ciki sosai, suka yi ta yiwa Allah godiya. Tabbas addu’ar iyaye ba ta faduwa kasa banza a kan ‘ya’yansu, ko ba jima ko ba dade. A washegari ya tura kanin mahaifinsa da kanensa biyu da wan Hajiyarsu wurin iyayen Fa’izah. Haulatu ce ta ce dasu Kaduna za su wurin Alh. Muntari don shine madaurin auren su, ta karbi address wurin Aunty Rabi. Tarba ta girma da mutunci Mama ta yiwa iyayen Nazir ita da Baban Kaduna da suka ce daga Kano suke neman auren Fa’iza wa dansu Naziru, malami a inda Fa’izar take karatu. Sai mama ta kalli Baban Kaduna shima ya kalle ta aka rasa mai yin magana. Tun daga nan jikin dattijan ya fara sanyi. Da kyar Baban Kaduna ya ce, “Na yi mamaki da kuka zo neman aure ba tare da kun yi bincike a kan gidan su yarinyar ba. Ban da haka duk wanda ya san zuri’ar Abubakar Giwa, ya san basa auren bare. Ban fadi haka don yaron wajena ne mijin Fa’izah ba, sai don cewa ka’idar gidanmu kenan da muke bi tun iyaye da kakanni. Ina mai bai ma Naziru hakuri, ya yi hakuri, ya yi hakuri Fa’izah TA YI AURE!!!” Da wannan bakin labari Hajiyar Dr. N ta tare shi a dawowarsa daga wajen aiki. Labarin da ya yi masa bugun da wani labari bai taba yi masa ba. Ya dauki mukullin motarshi ya nufi kofa Hajiyarsa na kira, bai juyo ba yake fadin “Barni in je Hajiya, Giwan za ni in tambayi Fa’izah dalilin da yasa ni ban yaudareta ba ita ta yaudare ni...... ta san auren gida ake musu amma ta yi min haka.... me na yiwa Fa’izah da za ta zabi ta yi min wannan yankan kaunar ta yi dai-dai da zuciya da farin ciki na?” Gudun da yake shararawa a kan titin da zai kai shi garin Giwa ya fi kama da na ‘yan sumogal. Zagin duniya ya sha shi daga motocin gaban shi da bayanshi. A dai-dai kwanar da zai karya ya shiga Giwa suka yi arangama da motar shanu ta bi ta kan motarsa ta murkusheta irin murjewar da sai wani babban ikon Allah za a fidda mai rai a cikinta. **** GIWA Ban motsa daga inda nake ba, tun daga lokacin da na fadi na suma. Karar da na yi ya janyo hankalin Hajjah da sauran mazan dake zarya a tsakar gidan. A guje Hajjah ta shigo har tana tuntube da kofar daki tare da su Baba Barau da suka shigo a lokacin da ‘yan kanzaginta su Inna Kubra. Hajjah ta tsugunna da hannuwanta biyu ta girgiza ni tana kirana “Fa’izah...... Fa’izah!!” Baban Giwa (Barau) shi ya fita ya zo da ruwa a kofi ya shiga yayyafa min amma ban motsa ba, ga idanuna a bude ina kallon su tarrr! Hajjah ta shafi fuskata zuwa idanuna shima ban motsa ba, ta kama hannuna ta ji shi sanyi kalau, jijiyar ta saki. Ta dubi fuskata babu alamun rai a tare dani sai ta rushe da kuka. Inna Kubra ta soma karanto addu’a tana tofa min a fuska. Ya yin da Baban Giwa ke tofawa cikin kofi, ya kammala ya shara mini duka a kaina, sai na kwanto sharaf jikin Hajjah kamar matacciya. Ko dan yatsana na kasa dagawa, babu wata gaba dake motsi a jikina. Wannan ya tabbatar musu da cewa dogon suma na yi, irin wanda shock ke sanyawa, mai wuyar farfadowa. Hajjah ta rungume ni tana kuka ta ce, “Na shiga uku ni Hadiza, me ya yi zafi Fa’izah? Muddin kika mike Hafizi na isowa za a warware auren nan, ba zai yiwu garin neman gira a rasa ido ba. Wayyo ni Hadiza, wallahi na manta shaf da kiyayyar Fa’izah da Fa’izu da ba a yi auren nan ba”. Baban Giwa ya zauna gefe ya zuba min ido duk sunyi tsuru-tsuru, ya ce, “Uhm! Ai na fada Hajjah babu wanda ya saurare ni, yanzu in ta mace ai shi kenan hankalinki ya kwanta. Tun lokacin na Aliyu na gaya miki kada a kara aurarrakin nan kin ki ji. Yanzu ai an dau darasi ko?” Baban ABU wato mahaifina ya daga labule ya shigo yana cewa, “Zancen banza kake Barau, ba suma ba, ko mutuwa Fa’izah ta yi babu mai karya dokar Abubakar Giwa ko bayan ran Hajjah, mu zamu tsaya a kan wannan principle har karshen rayuwarmu. Tashi ka fita ka baiwa mutane wuri sakarai matsoraci girman wofi tun ranka bai baci ba wallahi”. Baba Barau ya kwantar da murya ya ce, “Nima ban ki hakan ba, amma a dinga duba soyayya tsakanin yaran nan kafin a kara kulla kowanne aure tsakaninsu. Fa’izah da Fa’izu basa ga amciji tun tali-tali har zuwa girmansu. Baban ABU rai! Yana gaba da komai, sai da shi ake komai”. Fa’izun ne ya bankado labulen dakin ya shigo a sukwane kamar an jefo shi tare da Yaya Aliyu, don tun fitowarsu mota Khalid yaron Baban Giwa ya ce dasu wai Fa’izah ta yi kara ta mutu! Bai iya ya ce komai ba duk da ya ji kadan daga abin da suke tattaunawa, illa bin Fa’izar da ke yashe a kasa mushe ko mai rai da kallo. Manyan fararen idanuwanshi gaba daya sun fito waje sun yi jawur, har wani brown-brown suka koma. Jikinsa sai mazari yake bakinshi na motsi, amma ya kasa magana. Aliyu ya ce “Shin Baba me kuke yi haka dukkanku tun dazu da aka rasa mai kaita asibiti? Fa’izah ba mutuwa ta yi ba!” Sai ya sunkuya ya ciccibe ta gaba daya, Fa’iz ya hade girar sama da na kasa ya ce, “Ko da ban karanta ba na san maganin wannan suman...” Da sauri Yaya Aliyu ya dire ni gefen gado ya yi baya, ya ce, “To likita mai mata Bismillah” Ya yi waje abinshi. A ranshi kam dariya ma abin ya ba shi yana ta yin ta ciki-ciki, wai matar dake tsakanin rai da ajali ake ma kishi? Bai san gara ta dauwama a suman ba da ta farfado ta ganshi. Ya karbi diyarshi da ke ta tsala ihu hannun Ummi a falo ya yi waje. A hankali su Baban ma suka shiga ficewa daya bayan daya ba tare da kowannensu ya sake tofawa ba. Hajjah ta share hawaye ta ce, “Yanzu Hafizi ya za ayi Fa’izan ta farfado?’ Fa’iz cikin jin haushinsu duka ya ce, “Ban sani ba Hajjah”. Ita ma a fusace ta ce, “Amma ka hana a kaita asibitin?” Ya fiddo ido ya ce, “Hajjah bakya gani daukarta ya yi ne?” Hajja ta hasala ta ce, “Zancen banza zancen wofi, yau ga sakaran kawai. Sannu mai mata, hala gawa za ka aura? To in gaya maka gaskiya auren nan kunce shi za ayi ba zai zama sanadiyyar rasa ran Fa’izah ba. Da na san haka abin zai zama tun farko da ban saurare ka ba.....” [6/3, 4:13 pm] Takori: Ranar litinin din nan rana ce da ba zan taba mantawa da ita a tarihin rayuwata ba, domin wani dan karamin bangare da ta taka cikin tarihin nawa. Na shigo aji a makare ainin domin sai da muka biya muka ajiye Yaya Rabi a asibitin Malam wajen awon tsohon cikin da take dauke da shi, muka kuma mai da ita gida sannan Yaya Mufty (sunan da Yaya Rabi ke kiran mijinta Muftahu) ya kawo mu ya ajiye ya koma (office). Jikina har bari yake domin na ji jiya ‘yan ajinmu na fadin anyi sabon lecturer mara daukar wargi, madadin Farfesan dake daukarmu darasin. Sanye nake da shudiyar danyar atamfa (exculusive) mai ratsin ruwan hoda da mayafi launin sararin sama mai haske. Bayan wannan babu komai a fuskata sai farar powder da na muttsika da vaseline (lip balm) a siraran labbana wanda ya kara musu taushi da kyalli. A rayuwata bana rabo da zizara kwalli a idanuna, kwallin (kajal) baki yana kara lafiyar ido, yana kuma kara fiddo min da gazar-gazar din gashin idona. Ina kokarin zama a kujera ya ce, “Get out please..... (fita waje don Allah)”. Wata kunya ta taso ta lullube ni ganin yadda idanuwan maza da matan ajin ya dawo kaina. Malam ya sake daga murya ganin na yi kasake! Na kasa zama na kuma kasa fita. Ya ce, “Get out I said (fita na ce)”. Na daga ido cike da kwalla a hankali na dube shi. Baki ne mai kyau na a buga a kalanda ko ayi tallan advertisement board da fuskarsa. Bai da tsayi can-can, yana tsaka-tsaki. Fatarshi goge da zuzzurfan ilimi a kananan shekaru. Gwiwoyina suka sage tamkar an rarrade su da murfin kwano haka na cira kafa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na yi tattaki a hankali na bar ajin. Wani abin mamaki sai ya kasance ban ji haushin mutumin nan ba a bisa korar karen da ya yi min a kan lattin awa daya. Sai ma haushin kaina mai tsanani da na bar Yaya Muftahu ya fara kai Yaya Rabi awo maimakon ya fara kawo ni. Haka nan na samu kaina da gwada yadda yake magana a sarke “get out.... get out I said!” Na yi murmushi na kwashi takarduna na yi (main library) don in yi assigment maimakon in zauna zaman tunanin malami mara daukar wargi, mai magana a sarke da in’ina. **** A gida nake bai ma Yaya Rabi labarin karonmu da sabon laccara mai tangardar harshe. Ummi ta ce, “Na ko so in ganshi, baki dan kakkaura mai yanayi irin na Yaya Bash yana driving wata (vauxhall) shudiya. Gaskiya gayen ya yi a rayuwa Aunty Rabi. Sai dai na yi mamakin yadda karamin yaro kamar wannan ya kai ga matsayin senior lecturer?’ Rabi ta ce, “Meye abin mamakin a ciki? Mai first class ko 2.1 zai iya zama lecturer komai kankantar shekarunsa. In kuma a waje ya yi karatun speed din ba daya bane. Mufty shekara daya kacal ya yi masters a Aston University”. Ummi ta zaro ido ta ce, “One year Aunty Rabi?” Ta ce, “Baki bina bashin rantsuwa ki shafa ki ji wai shafa-labari shuni”. A washe gari ma cikin ikon rabbi na yi latti. Malamin jiya shine a ciki, sai na ji hantar cikina na rawa, kafafuna suka fara hardewa. Tun ganina na farko jiya da mutumin nan wani sabon al’amari ya bakunci ruhi da zuciyata, ba zan ce so bane, zan iya cewa kwarjini yake mun, kuma yana razana ni da kwarjinin. Yadda zuciyata da hantar cikina basu bar karkarwa ba, haka kafafuna basu bari ba. Yau ma dai ta jiyan aka kwata, wato ya koroni waje. Wannan karon kam raina ya baci, domin karkarin lattin nawa na mintuna goma ne kacal. Muna cin abinci a (Al-Amir) na aje cokali na ce, “Wallahi Ummi wulakancin dan iskan malamin nan fa ya soma isata, asarar lacca biyu kenan ya yi mani”. Haulatu ta ce, “Wai wane ne?” “Oho! Na san sunan shi? Yana nan wani dan kakkaura”. Ummi ta ce, “To mu ji alkhairi tunda tsiwar taki ta iso kan malamai. Wani ya ce ki makaran?” Wannan ta wuce. Haulatu ta gayyace mu cin abincin dare a gidansu a washe gari ta taya Abdullahinta murnar kammala (Law-School) lafiya. Muka shirya tsaf muka cakare muka cancare cikin swiss lace ruwan kwaiduwar kwai (beig) da ratsin silver. Haulatu ta riga ta gaya mana za ta turo direban gidansu ne ya tafi damu, don ya Mufty ya je Giwa, matar gidan kuma tana fama da kanta ba ta (driving). Don haka da Abdoul ya shigo ya ce, “Wai wadanda Haulatu ta turo a dauka su fito”. Sai na zuba mishi rankwashi aka, muka zari mayafi muka yiwa Aunty Rabi sallama muka fita. Ni dai na ga mota ‘Vauxhall’ (one door) ba Honda din gidan su Haulatu ba. Kofar direba a bude ya zuro kafafunshi waje, sautin Abdurrahaman Sudaith na tashi a hankali a motar, ya sanya (ear piece) yana bi idanunshi a rufe ya jingina bayansa da kujerar kamar mai barci. Kamshin turaren ‘oud’ na mota na tashi kadan-kadan. Ganin bai da niyyar bude idon, bai kuma san da tsayuwar mu a wurin ba sai na yi masa sallama a hankali. Tare da cewa, “Mun fito”. Duk idanun ya bude wal! A kanmu. Hasken lantarkin farin bulb din da ya haskake harabar gidan ya haska mishi fuskokinmu. A sannu a hankali ya dauke ido a kanmu ya yi dan murmushi yana yiwa motar key yana fadin “Bismillah ku shiga muje, kamar ma na taba ganin daya daga cikinku”. Tuni zuciya da ruhi suka shiga aikin da suka saba a duk lokacin da suka yi arba da wannan bawan Allah. Lecturer dinmu ne (Mr. No name), don ban san sunan shi ba, mai kora ta a bainar jama’a in na yi latti. Meye hadin sa da Khaulatu? Ganin na tsaya na kasa shiga motar saboda mamaki sai ya dago ya dube ni muka hada ido na yi hanzarin russunar da nawa domin sun zama masu rauni kwarai a cikin nasa. Ya ce, “Ki shigo mu tafi, tana jiranku, o.k?’ Na bude bayan mota na zube. Ummi ta shiga gaba. Ya rufo kofar side dinsa cikin taushin murya ya ce, “FA’IZAH NAKE SO TA DAWO GABA BA UMMIN AUNTY RABI BA!” Wani sauti kululuuuu! Da cikina ya bayar kenan na mamaki, tsoro da tu’ajjabi. Ummi na dariya ta bude kofar gaba ta fito ta dawo baya ta zauna tana min alamar in fita ina girgiza mata kai alamar a’a. Ya ce, “Bana sayar da kai Fa’izah, ni aminin Barister Abdullahi Turaki ne. Shi ya turoni in taho daku an aiki Malam Saleh, ina fatan Fa’izah ta gamsu?” Ni da Ummi duka sai da muka murmusa. Na bude mota na fito na koma gaban. Ya ja motar a hankali muka bar harabar gidan, ya hau titi dodar. Daga ni har Ummi mun yi tsit kamar a ce kyat! Mu bude murfin mota mu arce. Sunayenmu da ya ambata wai har ma da Aunty Rabi. Na yi murmushi kadan daga aikin ( talkative ) Haulatu. Mun yi nisa da Gadon Kaya mun hau titin Audu Bako, jefi-jefi yana karkata mudubin shi don hango motocin dake bayan shi. Da danja ta tsai damu sai ya juyo sosai ya dube ni ,”Are you o.k?” Daga mishi kai na yi. Har muka zo ‘Yankaba bai kara magana ba, sai ni da Ummi kan yi magana na abin da ya shafe mu. Haulatu da Abdullahi ke zaune a harabar gidan bisa fararen kujerun roba suna hirar su hakora na shining (dariya). Kai da ganin wadannan ma’aurata ka ga masoyan da ke ji da juna. Har dai-dai inda suke ya yi parking, ya yin da duk suka mike suka nufo motar suna dariya. Ya zagaya ya budewa abokinsa, Haulatu ta bude mana ni da Ummi. “Mr. and Mrs”. In ji lecturer. “Na cika uzurinku, kyawun alkawari cika shi”. Abdullahi ya ce, “Wannan lazim ne Sadiqy (aboki)”. Haulatu ta ce, “Ni dai ba ruwana, kada ku shafa min kashin kaji, daman ta ce Dan iska ne”. Na dafe kirji da hannuwa biyu na ce, “Ke Haulatu!” Yadda na yi din da irin fiddo idon da na yi cikin razana ta gaske ya sa gaba daya har Ummi suka tuntsire da dariya. Abdullahi ya ce, “Kada ki jawo mata ‘carry over’ Sweetie”. Ya ce, “Ko spill over’ ba ta karasa a gidan mijinta”. Da wadannan hirarrakin muka rankaya dakin saukar bakin su Haulatu. “It’s a get together dinner of five....” Haulatu ta fada tana wara yatsunta biyar tare da janyo warmers guda biyar Arabian cuisines, kabsa, kebabs, manakees cikin biredin (pita), sai mankees, shawarmah da burger. Ta bubbude kowanne tana serving a plate, cewa take “I did it to you with my naked hands my dear Abdullahi! Congratulation on becoming a Lawyer”. Gaba dayanmu bamu san sanda muka zuba tafi ba, ni Ummi, da Mr. Lecturer. Shi kuwa Abdullahi murmushi yake bakin kamar ya tsage. Na kasa sakin jiki ko kadan abubuwan duk sun daure min kai. Sanda Mr. Lecturer ya bude wata foil paper ya turo gabana saura kadan in saki fitsari don mamaki. Gasasshen naman saniya ne mai romo da ya ji tumatir da albasa, har da cabeji sai turiri yake. Ya kuma dakatar da Haulatu daga serving dina shi ya yi serving dina da kansa, wannan gasasshen naman da ‘kebabs’ (tsire) plate dina wato har appetite dina ya sani, wa ya gaya masa ina son gasasshen nama? A yadda ya saki jiki a gidan na fahimci ba bakon zuwansa bane. Har wajen su Hajiyar Haulatu tare da shi muka je muka gaishe su muka dawo falon. Ya dauki tambulan ya cika da lemun matsattsun kayan itatuwa (tropical juice) ya miko min cikin lumshe ido da bude shi duka a lokaci guda. Ban iya na yi musu ba na karba, amma kurba daya na kasa saukewa saboda gardin lemon, ko ko in ce gardin hannun da ya fito daga gare shi. Cikin duka (Arabian Dishes) din nan gasasshen naman da ‘kebabs’ kawai na iya ci saboda na zama bakuwar zuciyata. This is the exact stranger I’m dreaming of. Sannan actions and emotions dinsa sun nuna abin da ke karkashin zuciyarsa, tun kafin ya furta, he care too much, sai shisshigi yake yi mun. Shishshigin da ba zan iya tankwabewa ba. Zuciya da gangar jiki duka sunyi amanna, sun karbi shisshigin sun dora a kan kujera mai matsayin da baya kwatantuwa. Watakila da zai iya lashe ni zai yi saboda kulawa. Hakan yasa duk na bi na takura na kasa sakin jikina daga sanya baki cikin hirar shi da Ummi, wanda duka tambayoyi ne a kan abin da ya kawo mu Kano. Haulatu ta ce, “Fa’izah fa ta bi ta takurawa kanta saboda malaminta”. Gaba daya suka maido hankalinsu gareni suna murmushi. Ta ce, “Dama kin saki ranki, kin saki jikinki wannan malamin....” Ya yi hanzarin cewa, “Abdullahi killace bakin matarka kafin in bubbuge shi”. Abdullahi ya miko hannu ya rungumo kwibin matar shi yana fadin “Kada ki kara magana Honey. A yiwa Yaya Malam biyayya don tare zan tafi in barku. Sai dai ban goyi da bayan a buge min bakin amarya ba tun ban biya farashinsa ba (siyen baki)”. Ban san sanda na yi dariya ba, ni dai haka nan soyayyar Haulatu da Abdullahi ta ke burge ni. A gaban kowa basa iya boye su masu begen junansu ne, sai dai in ba za ka iya gani ba ka kau da kanka. Haka yake yi in ya je wajenta a makaranta ya yi ta bamu kunya, wani zubin su bamu sha’awa, wani zubin su bamu dariya. Tattalin Haulatu yake kamar kwan da aka nasa yanzu-yanzu. Haka ita ma. Ganin dariyata sai Abdullahi ya ce, “Ko ke fa? In ya sake ce miki ‘get out’ ki zo nan ki gaya mun ni dashi ne kin ji Fa’izarmu”. Cikin dariya na ce, “Ai ban ga laifin shi ba Yaya Abdullahi. Ni ya dace in nemi afuwar shi a bisa lattin da nake mishi, wallahi ba halina bane yin latti akasi da uzuri aka samu. I’m sorry Malam”. Wani irin lumshe ido ya yi bai ce komai ba. Ya kara kwanciya a cikin kujerarsa. Wannan karon wayar hannunshi yake latsawa kamar bai san bikin da muke yi ba. Haulatu ta cika baki da shawarma cikin tsokana, “Wallahi Ummi wulakancin dan iskan malamin nan fa ya soma isata? Ko kin san asarar lecture biyu ya yi min? Oho! Ina na san shi? Yana nan wani baki dan kakkaura mai in-ina”. Na kai tafukana da suka sha adon jan lalle na rufe fuskata suna ta dariya. Shi kuwa murmushi kawai ya yi. Ya ce, “Haulatu ba a sirri dake?” Na ce, “Daman kin san shi ai kika rufemu a bai-bai?” Ta ce, “Ah toh! Ba ga shi yanzu na baku mamaki ba”. Abdullahi ya ce, “Lallai dan iska, yau kuma ‘yan iskan idanun bisa aminiyata suka fada?” Ya dago kai daga kan wayarshi ya ce, “Ya ishe ka haka nan Abdullahi! Kai ka tashi ma ka tafi lokacin tafiyar ya yi ko a nan za ka kwana yau?” Ya ce, “In na kwana na yi laifi ne?” Bai kula shi ba, suka ci gaba da kwasar girkin Haulatu sai da kowa ya yi kat. Shi da kansa ya yi serving dina. A yadda yake sarrafa hannayensa wajen serving din za ka fahimci lallai namiji ne wanda zai tattala matarshi matuka, wanda zai lallaba matarshi fiye da Abdullahin Haulatu. Abdullahi ya mike yana fadin “Haulatu zan wuce, zo ki ji mana”. Ummi ma ta mike ta ce, “Ni toilet za ki nuna mani a cikin gida”. Gaba daya suka fice. Daga ni sai malamina Mr. no name. A sannan ne na fahimci sun fita ne duka don su barmu mu biyu. Ya dan motsa a cikin kujerarshi sannan ya ce, “Fa’izah!” Wannan kira ya dade yana amsa kuwwa a sassan jikina. Ban iya na amsa ba sai kara dukar da kai ina murza zoben hannuna. “Har yanzu ban yi abin da zai sa a sake dani ba? Ko sai na kai ga durkuso bisa gwiwoyi na? Domin wannan afuwar Fa’izah?” Na dan fiddo ido, “Ta ya ya malami zai durkusawa dalibinsa?’ “Ta dalilin yana SON dalibar soyayya mai yawa.....” Ya fadi cikin kwaikwayar muryata. Da a ce ban ga yadda yake ciccijewa yana cin magani a aji ba, sai na rantse cewa ba shi bane. Lallai so ba dama ne. Jin na yi shiru ina tauna maganarsa sai ya katseni da cewa, “Shin Fa’izah ta tsai da gwani ne tsakanin Giwa, Zaria, ko Kaduna?” Sai na yi dariya cikin jin kunya, “Don me ka yi tunanin wannan? Mu ‘yan Giwa bama hada taura biyu a baka”. Murmushi ya yi tare da girgiza kai, “Mu ‘yan Kano muna hadawa, kenan rabon kanawa ne ya hana?” Murmushi na yi cikin jin shauki. “Fa’izah I’m serious. I’ve interest on you. Shin za ki iya auren malamin makaranta?” Dagowa na yi na dube shi da dukkan idanu, “Babana ma malamin makaranta ne”. “But you are born with a silver spoon in your mouth (kin fito daga gidan masu hannu da shuni), kaman hakan zai zama takura”. Ya fadi cikin murmushi. “A’a, ban fito daga (silver spoon) ba, na fito daga BABBAN GIDA (point of correction) mai babban suna”. Tafi ya yi min sau uku, “Mene ne bambancin guda biyun?” “Akwai bambanci da yawa. Babban gida kudi bai yi yawa ba, amma babu yunwa babu rashin suttura a cikinsa. Sannan masu shi dattijan kwarai ne masu magana daya. Idan kuma ka ce tajirin gida kana nufin gidan hutu”. Wannan karon dariya yake yi sosai wadda ta sanya ni shagaltuwa a kallon sa, kyawunsa na kara kayatar da zuciyata. “Na yarda dake Fa’izah, to amma fa sai kin ki ji kin ki gani a tafiyarmu. Abin da na gani ina so da zuciya guda ba zan iya munafuntar shi ba, ina da tabo Fa’izah, wanda na san as soon as an fara ganinmu tare za a kawo sukar sa. Duk da an ce waka a bakin mai ita ta fi daxi, ina jin kunyar kaifin idanunki....” Ya yi dan murmushi.... “Ina son mata Fa’izah, ina son su da yawa..... na yi amanna da cewa har gida za a biyo ki a gaya miki wannan, sai in ba a ganmu tare ba. Amma na yi miki alkawari Fa’izah tsakanina da mahaliccina from you it will cease to exist (son matan) na yi miki alkawarin bari har abada in har kin amince ki zamo uwar iyalina. Daga ganina dake na farko zuciyata ta gaya min ke ce (life-companion) dina mafi cancanta. Kaunarki ta fara ne daga ganina dake na farko (love at first sight) na rasa nutsuwar zuciyata a tsayin wunin ranar da daren baki daya. Da nake kwatantawa Haulatu kamanninki da level din karatunki take ce min ke best friend dinta ce tun a secondary, da take yawan bani labari. Shine ta hada mana wannan dabarar ta dinner (to dine here together) ta kuma turani in dauko ku. Gaba daya tarihinki na jishi wurin Haulatu, na kuma kara tabbatarwa kaina INA SON FA’IZAH! Shin Am I accepted Fa’izah?” Kaina na sunkuyar ina murmushi. Abin nan da masu iya magana ke cewa, labarin zuciya a tambayi fuska, don zuciyata ta yi na’am tun ma kafin ya furta. Har nake jin cewa, ba son mata ba ko mata dari gare shi zan iya zama ta casa’in da tara in har nice uwar ‘ya’yanshi. Domin yanada duk abubuwan da za a so shin a kansu. Ga dai ilimi, ga kuruciya, ga kyau na a manna a jarida, ban ga makusarsa ba. “Ko da ban furta ba, kallo daya za a yi min a tabbatar da na fada a matsananciyar kaunar ka. Daga lokacin da idanuwana suka fada a kanka Malam”. Magana nake a zuci, ban san cewa a fili nake yi ba. Ganin ya lumshe idonsa ya bude ya ce, “Na gode”. Ya tabbatar min ya ji abin da na ce. Wannan sai ya tuna min da lokacin da na karbi tayin soyayyar Yaya Aliyu a Zaria, ga shi ban ci ribar waccan ba, na amsa ta biyu, kada Allah ya kara dandana min dacin ta. Cikin dan lokacin nan mun tattauna abubuwa da dama mun kara fahimtar juna. Har zuwa lokacin na kasa tambayar shi sunan shi. Sai wurin karfe goma Haulatu ta fargar damu, da kyar muka katse hirar muka fito zuwa mota. Ina ganin Ummi da Haulatu na gulma suna rada da dariyar shegantaka ko kula su ban yi ba. Don na san da ni suke. A kan hanya ma hirar muke yi. Ya gaya min ya yi dukkan karatunshi ne a Taiwan inda ya karanta harshen Larabci ziryan. Shi da Abdullahi ‘ya’yan family friends ne, haifaffun garin Dambatta. Da kyar muka iya yin sallama don sai da Ummi ta shige ta barmu. Sai shigowar hancin motar Yaya Mufty ne yasa muka yi sallama ya jira fitowar shi da yin parking din shi suka yi hannu, sannan ya shiga motarsa ya tafi. Har zai fita get ya dawo ya yi min horn na juyo “Phone no na manta Fa’izah”. “Ni da Ummi bamu da waya”. “Saboda me?” “An hana mu rikewa ne”. Hannu yasa ya dauko tashi a gefe, “Ki rike wannan saboda ni Fa’izah. Na yi alkawari ba zan zamo mai hana ki karatu ba!” Ya cire layin ya miko min (Sony experia) sabuwa dal. Na rasa abin da ya hanani kin karba, na kuma rasa wanda ya sani yin godiya. Wala’alla soyayyar kenan? **** Fada na duniya babu irin wanda Aunty Rabi ba ta yi min ba a wannan daren. Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har sai da na saka kuka. Na farko daren da muka yi, na biyu tsayawa a waje da namiji tsayin karfe sha dayan dare. Na uku wayar da ta ganni da ita, da izinin wa na karbo ta? Don bakwa gaban iyayenmu ba zan ci amanarsu ba. Abin da ya zaunar daku gidana shine karatu ba (flirting) ba. Wannan wayar dole ki mai da masa abarsa gobe. Gaskiya ba dani ba, ba a gidana za a karya dokar A.B House ba, gara ma ku sake tsari. Gobe abu na farko da za ki fara da zarar kun shiga makaranta shine mayar da wannan wayar. Yaya Muftahu bai ce komai ba. Haka na kwanta zuciyata ba dadi da haushin Aunty Rabi. Duk kula mazan da Ummi ke yi ba ta taba yi mata fada ba sai ni da na yi sau daya, ni da nake da niyyar aure ma ba flirt irin na Ummi ba. Da zuciyata daya nake son malamina, da gaske auren shi zan yi in Allah ya yarda. I love you. If you hate it, kill with an arrow. But please not in the heart because that’s where you are. Gud night. Sakon da ya fara shigowa cikin wayar kenan da na saka layin da ya bani cikin kwalinsa. “Why will I hate it?” Na tambayi kaina cikin murmushi. “I do love it too!” Na baiwa kaina amsa. Don haka na baiwa Malami na amsa. “You inspire in me a love so deep and powerful that cannot be destroyed by any arrow! How I wish there is a way you could see into my soul. My love on you is far to strong Mallam!” Daga wannan na kashe wayar gaba daya. **** Washe gari tun asuba nice farkon yin wanka a gidan. Ban jira Ummi ba balle Yaya Muftahun dake sauke mu ya wuce office, na yi tafiya ta ni kadai saboda fushin da nake yi da Aunty Rabi, ban yi ko tunanin wani abu wai shi kalaci ba. Babban burina in dora idona a kan lecturer. Kusan nice farkon shiga laccarsa ta karfe goma ta safe. Kai! Ni Fa’izah na shiga uku!!! Don I become infatuated to him fiye da kima. Akwai wani sirri dake cikin kwayar idanunsa da ba duk maza Allah ya mallakawa ba. Sai dai kuma cikin rashin sa’a bayan ajin ya cika (class-representer) din ya ce ya mai da ita (fixed) karfe biyu na rana. Kamar na fashe da kuka dai-dai lokacin da wayar da na jefa a jaka ta kama tsuwwa. Cikin rashin kuzari na amsa da tunanin yadda zan yi in mayar da ita din kamar yadda Aunty Rabi ta yi umarni. Muryar mace ke tambaya, “Dacta ne?” “A’a, ba shi bane, wace ce?” “Ke me maganar wace ce?” “Matarshi ce!” Sai ta kyalkyale da dariya ta ce, “Ki ce Haulatu Sani Galadanci na gaishe shi, kuma inda hali yana jiranki a office dinsa. Saboda ke ya dage laccar ku zuwa anjima. He can’t wait to see you.... cross sword....!” Kunyar Haulatu ta kama ni ainun yadda ta yi ta canza murya ta shammace ni na yi tabargaza, na yi shuka a idon makwarwa. Jiki babu nauyi na nufi inda Haulatu ta kwatanta min cewa nan ne ofishin nasa. A ofishin akwai hoton gwamna mai ci a lokacin da na shugaban kasa, sai na Alh. Dr. Ado Bayero. Sanda na yi sallama rubutu yake yi amma bai kasa amsa min ba. Na samu kujera na zauna har ya kare, sai ya turo min folder din da yake rubutun nasa hannu biyu na amsa. Ko da na duba (note) dinsa ne da na yi missing har guda biyu cikin hand-writing dinsa mai kayatarwa da ban sha’awa. Idona ya kai ga dan karfen dake like saman kofar shigowa ofishin da ban rufe ba. Sunansa ne radau DR. NAZIRU SANI GALADANCI. Wato Dr. Yayan Haulatu ne uwa daya uba daya ta yi min irin wannan ninkewar? Kai abin da mamaki. Har mun yi sallama na kai bakin kofa sai na juyo na ce, “Na yi mantuwa ne”. “Ta me Fa’izah?” Na dawo a nutse na ciro wayarsa daga jakata na mika masa, yasa hannu ya karba yana fadin “Ya kika dawo min da ita?” “Aunty Rabi tana ta fada ne, ita ce ta ce na dawo maka da ita, ba za a barni na rike waya ba sai na yi aure”. Ya yi kasake cikin kallona da murmushi, “Sai na ji na kara son ki, na kuma kara yarda da cewa da ki kai ke din ‘yar babban gida ce. Abin da ban taba ji ba a wannan zamanin ‘yammata kamar ku a jami’a iyayenku sun hanaku rike waya, kuma kun bi, anyway. Ki ce ma Aunty Rabi ta yi hakuri, ba za ki sake rike waya ba sai kin zama matar Dr. Nazir insha Allahu” [6/3, 4:13 pm] Takori: Da sassarfa na karasa ficewa daga ofishin ina murmushi. Yinin ranar zungur na kare shi ne cikin tunanin Dr. Nazir da maimaita ambaton sunansa cikin zuciyata sakan bayan sakan, minti bayan minti, awa bayan awa son Dr. Nazir karuwa yake yi a raina. Yana kara habaka a birnin zuciyata. **** Soyayyarmu da Dr. Nazir ta yi nisa da karfin da ta zama sananniya a tsangayarmu. Tsegumi kam iri-iri an kawo min a kan yawan ‘yammatan da Nazir ke dasu cikin makarantar. Na kan toshe kunnuwana ne kamar yadda ya ce, ko in yi hannun riga da duk wanda ya kawo min tsegumin. Dr. Nazir ya ware muhimmin lokacinsa wurin yi min (extra class) bayan kowacce laccarsa. Nazir ya iya koyarwa. A dalilin koyarwar da yake yi min ‘points’ dina a jarrabawa ya kara karfi fiye da na baya. Nazir ba shi da karfin idanu (short sight), a dalilin hakan yake amfani da farin gilashi mai kara karfin gani (lenses) ya yin rubutu ko karatu, ko ba da lacca. Amma in ba fadi aka yi ba za ka yi zaton na kwalisa ne. Don yana mai kyau sosai. Nazir mutum ne da ya iya tsara magana da hafizin harshen da Ubangiji ya hore masa. Iya maganarsa da kirkinsa ya taka rawa mai yawa wajen sanya zuciyata ta zamo kangararra, bana ji bana gani. Da kaina in ban ganshi ba sai na bishi office, har sayayya mu kan fita wasu lokutan. Tun Ummi na hana ni har ta gaji ta rabu dani. Wai ni Fa’izah tsatso daga A.B House nice mai bin saurayi har office, nice mai fita da saurayi. Wannan ba karamin kona ran Ummi yake ba. Har ta gaji ta tseguntawa Aunty Rabi. Aunty Rabi ta samu Yaya Mufty take sanar da shi, inda ya ce, “A kawo mishi sunan Nazir cikakke zai yi bincike a kansa. In mutumin kirki ne a kyale ni, kwana nawa ne zamu gama karatun mu koma gaban iyayenmu? Domin Hajjah ta soma fadan mu dawo gida haka karatun ya ishe ta. Abu ya ki ci ya ki cinyewa tamkar cin kwan makauniya”. Aunty Rabi ta ce, “In kuma ba mutumin kirkin bane ba fa Mufty?” Ya ce, “Zan san abin yi a kai”. Ni kam duk surutunsu da harare hararen su basa damuna, na yi nisa a son Naziru. Wani irin so nake dandana mai wuyar fassarawa, wanda ya zarta na Yaya Aliyu fintinkau! Idona ya rufe a son Naziru, lokutana baki daya na Dr. Nazir ne. Tambayar da jama’ar dake tare damu ke wa Ummi shin Fa’izah ta san Dr. Naziru (use and dump) ne? Ta ya ya yarinyar ‘yar gidan mutumci wadda ta san ciwon kanta irin Fa’izah ta yarda cewa Dr. Nazir auren ta zai yi? Shin Fa’izah ta san yawan ‘yammatan da Dr. Nazir ya yaudara ya watsar a Kano? Shi fa dama duk inda kyakkyawar mace take nan idonsa yake, zai nuna mata so ya yi ta yi mata facaka, amma da an ce ya fito ayi aure ba kya kara ganin keyarsa”. Ummi ta kan girgiza kai, don bakin ciki ta rasa me za ta ce, sai dai ta ce, “Fa’izah kam ta yi nisa ba za ta ji kiran ba”. A yammacin wata talata mun dawo daga Ado Bayero Mall (Shoprite) ni da Nazir ya sauke ni dai-dai inda ya ga su Ummi a zaune a (seaters) na dalibai karkashin wata bishiyar dalbejiya mai inuwa, bai ko tsaya sun gaisa da su Ummi ba don ya san Ummi ba ta goyon bayan tarayyarmu daga ita har shakikiyarshi Haulatu, ita ma ta bi sahu don tsoronta na kar mutuncinta ya zube idon su Aunty Rabi dake matukar ganin mutuncinta, ranar da Nazir ya yi (dumping) dina. Ko ba don wannan ba Nazir baya sakar ma dalibanshi fuskar da raini zai shiga tsakani. Ko mata da yake nema tamkar bunsuru ba dai cikin tsangayarmu ba can a wasu tsangayoyin ko waje yake neman abinshi. Na yi musu sallama duka suka amsa min a sanyaye, na aje ledar hannuna gefen Haulatu ina fadin “Wash Allah! Na gaji da yawa. Dr. N (sunan da nake kiransa) ba dai yawo ba, shi dai a je shopping burinsa kenan”. Suka dubi juna suka kau da kai. Cikin nutsuwar da ban san tana da ita ba Ummi ta ce, “Fa’izah rayuwar da kika zabawa kanki kenan? Tarayya da maza irin su Dr. Naziru? Yau da Hajjah za ta ji wannan mummunan labari ina kike tunanin za ta tsoma ranta? Da kin sa zuciyarta ta yi bugawar farat daya. Wallahi-wallahi tun wuri ki sake hanya tun dare bai yi miki ba. Nazir ba dai-dai yake da tsarin rayuwarki ba, kuma aurenku ba zai taba yiwuwa ba. In kin manta kin fito daga zuri’ar A.B ne nake tuna miki”. Haulatu ta cafke “Ina mai matukar jin kunyar ranar da Yaya Naziru zai yi dumping din ki, (as if you had never been in existance), shi yasa nake so ki kwaci kanki tun kafin zuwan wannan ranar, domin mai hali baya fasa halinsa, kuma sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba. Nazir dai dan uwana ne, karewa ma shi ya sha nono ya saki na kama, uwarmu daya ubanmu daya. Amma bana goyon bayan ki mallaka mishi soyayyarki. Abin dai da baki son a ta da to dole ne a fadi, ba auren ki zai yi ba”. Na yi murmushi na ce, “Kun gama? Shin ina kaunar da kuke ikirarin kuna yi min din Haulatu da har ba za ku so abin da nake so ba don cikar farin cikina? Kuna kina da Dr. N ne don tsoron kada ya yi min yadda yake yiwa sauran ‘yammatan da ya nema a baya, shin ku Allahn musuru ne? Kun san gaibu? Kuma shin shi halin dan Adam baya canzawa ne? Dr. N ba munafuki bane irin yadda kuke zato, tun ranar da muka hadu ya gaya min abin da kuke gudu din, ya kuma tabbatar min daga kaina ya daina, ina rokon Allah ya taimake shi ya dainan. Manzo mai tsira da aminci ya ce, ‘ku kyautatawa mutum zato domin zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya’. Kuma duk iskancin da kuke tsammana mishi wallahi bai taba kai hannunshi jikina ba ko bisa kuskure. Bai taba ba. Wannan ya nuna Dr. N son Allah da Annabinsa yake yi mun, ba kuma zai gwada iskancin nasa a kaina ba saboda ba yaudarata yake da niyyar yi ba. Zancen mutuncina da kuke, kada Allah yasa a ga mutuncin nawa in har sai na bar Dr. N. Ke kuma Haulatu yadda kike aibata dan uwanki don tsira da naki mutuncin wallahi kin bani mamaki, in kin yi ne don ki burge wallahi baki burge ni ba. Ai naka-naka ne komin lalacewar shi, hannunka baya taba ribewa ka yanke ka yar. Ku zuba ido tunda duk kun zama ‘yan adawa da yardar Allah kunya za ku sha”. Na suri ledar shopping dina na bar musu wurin, na barsu suna kallon-kallo a junansu an rasa mai karfin halin musawa ko maida martani. **** Abdullahi ya ce, “Ka rufa min asiri Naziru, Haulat ta zo min tana kuka in rokeka ka rabu da kawarta in ba auren ta za ka yi ba. Naziru ka yiwa Allah ka rabu da yarinyar nan ko don zumunci da sanayyar dake tsakani”. Dr. Nazir Sani Galadanci sai ya yi murmushi yana harhada takardun daliban dake bisa tebirinsa. “Wata fuskar..... ta fi gaban mari. Za ka sha mamaki na Abdullahi”. **** Ranar da muka kare zana jarrabawar zangon karshe na aji uku (300 level), ranar muka yi shirin tafiya Giwa, a dalilin dan uban aiken da Hajja da Baban ABU suka ishemu da shi lallai mu zo gida ana neman mu. Mun yi sallama da Aunty Rabi da alkawarin ita da kanta za ta rako iyayen Nazir Giwa a duk lokacin da suka bukaci hakan, domin Aunty Rabi ta tsinke da irin kaunar dake tsakanina da Dr. N, duk da binciken da Yaya Mufty ya yi ya nuna cewa Dr. Naziru Sani Galadanci yana layin samarin da iyaye ke tsoron ya dora mayaudaran idanunshi bisa ‘ya’yansu a fadin garin Kano da jami’ar Bayero. To an ce fadan da ya fi karfinka sai ka mai da shi wasa. Don haka dukkaninsu suka koma lallabani da bina da siyasa. Ashe abin da ban sani ba a nufin Hajjah karatun daga iya nan an barshi kenan mu da Kano sai zuwa da yawo babu wanda ya gaya mini. Na ga dai Ummi cikin damuwa, da zamu tafi kuwa sanda Yaya Mufty ya kunna mota kuka take yi wiwi har da sharbe, ni kuwa sai na ji gabana ya yi wani irin mummunan faduwa a sa’ilin da Yaya Mufty ya hau kan titi. Kaduna muka fara isa. A sa’ilin da Yaya Mufty ya sanya hancin motar cikin gate din gidan Baban Kaduna, a sa’ilin ne na ji wani irin faduwar gaba da ban taba ji ba a rayuwata. Muka yi sallama a babban falo, duka ‘ya’yan Hajjah in ka dauke Rabi auta dake Kano babu wanda babu a falon. Suna zaune duk sunyi jigum-jigum. Da na juya ido zuwa mahaifina Ahmadu A.B sai na ganshi cikin jan ido kamar gauta. Babu abin da ya zo raina face mutuwa ga tsohuwa Hajjah. Idanuna suka yi kwalkwal na dubi Maman Kaduna cikin hawaye. “Hajjah ta mutu ko Mama?” Na rushe da kuka bana ji bana gani, kuka mai tsananin gigitar da zuciya ma’abociyar imani. Wata irin tsawa Baban ABU ya daka mini, “Ke bama son sakarcin banza. In mutuwar ta yi abin da za ki yi mata kenan? Sakayyar da za ki yi mata kenan zubar hawaye?” Baba Barau ya ce, “Ita Hajjah din za ta so ta mutu Fa’izah ba ta rungume ‘ya’yanku ke da Ummi ba tunda ta rungume na Zanirah?” Sai ga mai kuka na dariya bayan ga hawaye shabe-shabe a fuskar “Zanirah ta haihu Mama?” Gaba daya na basu dariya ban da Baban ABU. Na ce, “Amma Mama shine baku gayawa Aunty Rabi ba mun zo mun ga danmu?” Mama ta ce, “Mace ce, ai abin bana yau bane. Ita Rabi ta sani lokacin kuna jarrabawa shi yasa ta ce ba za ta gaya muku ba murna da doki za su hanaku karatu in kun zo kwa gani, to kin ji. Yau shekarar (FA’IZA) daya tana gudunta ko ina”. Na yi shiru cikin tunani, wato sunana Yaya Aliyu ya sanyawa diyarsa da Zanirah. Na ce cikin murmushi, “Allah ya raya takwara, zuwa Lagos ya kama mu kenan”. Ni sai a lokacin idona ya kai ga huhunan goro da alawa dake jingine gefe guda wani a kan wani. Na ce, “A’a, wannan kuma fa? Auren Maryam za ayi ko Hanifa?” Baban Kaduna da Baban ABU suka kau da kai kamar basu ji ni ba. Baba Ibrahim ne ya ce, “Auren Ummi ne ya tashi gobe insha Allahu, don haka makaranta ta kare babu sauran komawa Kano”. Ummi ta zare ido cikin firgici da kaduwa. Ni kuwa sai na rungumeta ina murna ina fadin “Don Allah Mama waye angon?” Mama ta ce, “Da masoyinta mana mai sonta tun tana karama”. Babu wanda zuciyata ta kawo min sai FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!” Ban san sanda na ce, “Amma a rasa wanda za a bawa Ummi sai Fa’iz?” Sai bayan na fada ne na tuna cewa, UWA da UBAN da suka tsugunna suka haifi Fa’iz ne a gabana. Suna zaune ne idanuwansu cike da kauna, kuma suna son dansu kwatankwacin yadda kowanne iyaye ke son dan da suka haifa duk munin shi ko munin halinshi. Ya yin da ni nake kokarin aibata musu shi a gabansu. A sanyaye na ce, “Allah ya sanya alkhairi”. Cikin sanyin jiki na wuce daki zuciyata cike da sake-sake. Wani bangaren tausayin Ummi nake ji. A ganina sun cuce ta sun aura mata mutumin da bai cancanci a hada auren shi alkhairi ba. Sai na tuna Ummi fa na son Fa’iz, kuma so hana ganin aibu. Yadda nake son Dr. N da tabban da yake da shi, haka Ummi ke son Fa’iz da kowanne tabo mai alaka da shi da halinsa. Iyayenmu suka bini da kallon nazari ganin yadda yanayi na ya sauya gaba daya a lokaci daya. Wajejen karfe hudu na yamma masu aikin gidan ke ta kaiwa da komowa sun kasa zaune sun kasa tsaye. Suna diban katon-katon na lemuka suna jerewa a firizan dake dakunan Baskwata (boys quaters) guda biyu dake like da juna. Na dan matsa na leka, ko falon dan ‘Prince Charles’ sai haka. Kwata-kwata falon bai yi kama da sauran falukan da na saba gani ba a wurare daban-daban. Komai na falon cream colour ne in ka dauke kayan kallo bakake samfurin SONY, hatta ‘curtains’ (labulaye) cream colour ne. Haka sauran kayan alatun dake falon. A.C har biyu, ta tsaye (standing A.C) da ta manne a bango (split), sai sassanyan kamshin (Bakhour) da Yahya ya sanya a dakin ke tashi. Kujerun (leather) ne suma cream colour masu laushi. Yadda wannan dakin yake, haka na kusa da shi yake komai da komai, sai bambancin kala. Na daya dakin ruwan makuba ne (grey). “Shin Yahya Baba amarya ya yi ne?” Sai ya kyalkyale da dariya, “Mama ce za ta bari Baba ya yi amarya?” “Yo ina na sani? Na san dai ba naku bane, duk da gasu a Baskwata”. Ya kara kyalkyala dariya, “Kin manta ne gobe su Yaya Bashir da Yaya Fa’eez za su dawo? Sai dai Bashir ya kammala, Fa’iz ma’aikaci ne ganin gida kawai zai zo”. Na ce, “Hummm! Lallai. Ni za ni in kwanta, anjima in su Baba za su koma Giwa kasa a tashe ni don Allah”. Ya ce, “Insha Allah”. Na juya zuwa cikin gida zuciyata cike da sake-sake. Da mamakin kaunar da Baban Kaduna yake yiwa ‘ya’yansa (beyond comment) sunan wani ganyen shayi. Abin haushin dukkansu babu na gari, don gara ma Bashir din shi shaye-shaye kawai yake. Shi dayan munin hali har ba a magana. Sai dai duk yadda na so in yi barcin Ummi ba ta barni ba. Hakika tana cikin farin ciki da ban taba ganinta cikin irin shi a duniya ba. Murnar auren ta da masoyinta Fa’iz Allah ya cika musu burinsu. Ta yi kukan dadi, ta yi na sosai. Duka dalilin daurin aurenta da Fa’iz gobe......” Na yi murmushi na ce, “Ki yiwa Allah ki barni in yi barci, ki bari ya dawo sai ku yi tare tunda karfe daya baya amo. Ki barni da abin da ya dame ni fargabar zuwan iyayen Dr. N, don ban san irin tarbar da Hajjah za ta yi musu ba”. Ta ce, “Matsalarki ce wannan”. Karfe bakwai na magariba muka bi Baban Giwa sai Giwa, Yaya Mufty ya wuce Kano. Tun daga gate din A.B Estate gaba daya komai ya canza, an sake fasalin ginin an mayar na zamani sosai, haka cikin gidan Hajjah an canza komai sabo dal kamar gidan amarya. An sake fenti gida kamar ba a cikin garin Giwa ba kamar a Lagos ko Abuja. Irin wannan sauyin na A.B Estate na faruwa ne a duk lokacin da A.B family za su yi wani gagarumin biki. Na ce, “Uhm! Ummi ana ji da aurenku tabbas”. Ta ce, “Fadi da babbar murya”. Abin da ya bani mamaki yadda su Inna Kubra, Indo da su Kaltume da sauran kannenmu na Giwa ke min oyoyo da (AMARYA).... Ka ga amaren sai kyallin goshi suke.... ni dai murmushi kurum nake ina cewa cikin raina “Auren Ummi guda ai dole a kiramu Amare, tunda mune Amara kirazan biki”. Idona bai hasko min kowa a falon ba sai Zanirah, rungume da buleliyar ‘yarta tana shayar da ita. Yaya Aliyu na gefenta yana waya. Habawa! Da Zanirah ta cizge ‘yar a nono ta dangware masa a cinya ta yi wani tsalle muka dire a tare muka makalkale juna bayan mun shararo a guje muka shiga juyi a tsakar falon Hajjah. Wai! TAKORI ta ce, TUNA BAYA SHINE RIKO! Yaya Aliyu ya mike rike da ‘yarsa ya hau Zanirah da fada..... “Wai ke baki da hankali ne? Kashe min ‘yar za ki yi? An girma ba a san an girma ba, kuna abu kamar kananan yara? Ko su Hanifa ba za suyi wannan shirmen da kuke yi ba....” Zanirah aka kwantar da kai aka shiga lallashin maigida... “Haba Baban Fa’izah! Shekaru uku currr! Ni, Fa’iza da Ummi???” Yaya Aliyu ya yi murmushi yana ci gaba da jijjiga Fa’izar don ta koma barcinta da hayagagar mu ya katse mata, don shi dama fadan shi baya nisa. Ya koma ya zauna ya ce, “Fa’izah ya karatu? Shi kenan an kare ko?” Muka dubi juna ni da Zanirah da Ummi duka muka yi murmushi. Na mika mishi hannu ya bani diyata kuma takwarata Fa’izah. Na dauke ta na sumbace ta na kura mata ido. Allah kareem dani yarinyar take kama sosai, ko da yake dukkanmu kamar tamu daya ce. Na ce, “Ya Allah ka raya mana little Fa’izah”. Kowa ya yi murmushi ya ce, “Ameen”. Yaya Aliyu kallona kawai yake, na san ba zai wuce mamakin kyakkyawan girman da na yi ba. Na samu Yaya Aliyu a kofar gida kan fararen kujerun roba yana yiwa ‘yar shi wasa, na labarta mishi zuwan dangin manemin aurena Dr. Nazir gobe. Yaya Aliyu ya yi shiru yana mai nazarin zancena. Akwai wani yanayi a tare da shi ya kada min ‘ya’yan hanji, wani yanayi da na kasa fassarawa. Yanayi ne mai nufin “BA ZAI TABA YIWUWA BA!” Na yi zugum! Ina dubansa hannuwa a kumatu zuciya cike da taraddadi. Ya yi ta maza in ji mata ya ce, “Fa’izah kin yi babban kuskure da kika saka soyayyar Dr. Nazir a ranki, alhalin kina sane da cewa babu auren (na gani ina so) cikin zuri’armu. Balle auren bare, wanda ba a taba ko da wasan kwatantawa ba. Tun bayan na mahaifiyarki wanda ko shi tunda ran A.B ne. Shin abin da ya faru a baya ni dake bai ishe ki ishara ba? Ki guji mu’amalar soyayya da kowa ki baiwa Allah zabi cikin al’amuran rayuwarki baki daya?” Idona ya cicciko da kwalla kadan ya rage su shimfido a kundukukina, na ce, “Yaya Aliyu ka taimake ni ina son Naziru, ina tsoron halin da zan shiga in na rasa shi. Fadar A.B ba fadar Allah ba! Bani da wanda zai taimaka min ya shige min gaba idan ba kai ba. I cannot afford losing him...” Yaya Aliyu ya zuba min ido na san mamakin halinmu na mata yake yi, a raina na ce, “Har an fika Aliyu Haydar?’ Ya saukar da kai bisa yatsun Fa’izah karama dake bisa cinyarsa, ya ce, “To ni dai Fa’izah babu abin da zan iya a kan wannan rigima da kika je kika jajibo. Zan yi dai iya kokarina in ga cewa ba a yiwa dangin Nazir wulakancin da za su tafi damu a baki ba idan sun zo. That is all. Ki jira hukuncin Hajjah a gobe”. Tun daga nan jikina ya kara yin la’asar. Na tashi na bar Yaya Aliyu don a ganina ba shi da abin da zai iya yi min din da gaske kamar yadda ya ce. Karfe tara na dare na kira Maman Kaduna nake sanar da ita zuwan dangin Nazir a gobe, don na manta ban sanar da ita a Kaduna ba. Na kare da cewa (cikin murya mai ban tausayi) “Mama na san ko da kowa bai goyi da bayan in auri Dr. Nazir ba, to ban da ke don ke uwa ce mai son duk abin da ‘ya’yanta ke so. A ganina lokaci ya yi da za a kawo CANJI a kan auren zumunci da ake tilasta mu yi, domin ZAMANI YA CANZA. A duk lokacin da zamani ya canza, dolen al’umma ne ta tafi tare da canjinsa in har tana so ta ci gaba. Auren zumunci ba laifi bane amma idan akwai son ran ma’auratan, in ko babu na daya daga cikinsu ya zama auren MUGUNTA, domin dole za a zalinci daya. Ke kadai kika rage min da zan kawowa kukana ki share min hawaye...... ki taimake ni Mama su amshi maganar Dr. Naziru da muhimmaci da karramawa. Wallahi ina sonshi Mama ba zan iya hakura haka in barshi ba a kan tsarin Hajjah... Ki taimake ni Mama don Allah, he’s the stranger that I’m always praying for!” Mama shiru ta yi na lokaci mai tsawo, kamin ta aje wani gwauron numfashi wanda ya kara samun suspence ya sagar da gwiwoyina. Domin numfashin da Mama ta sauke na nufin ba za ki taba cin nasara a soyayya ba Fa’izah. Ba za ki cimma ko daya cikin burarrakinki a rayuwa ba. A karshe ta yi tashin gwauron zabi ta murje jin nauyi da kawaici ta ce, “Fa’izah! Sai dai ki yi hakuri kam. Amma wannan yaron BA ZA KI AURE SHI BA! An riga an yi muku mazaje ba tun yau ba”. Da maganganun Mama na kwana zuciyata jagule ta kasa sukuni. Wadanne irin mazaje Mama ke ikirarin an mana? Mu bamu sansu ba? Mama na nufin ba zan auri Nazir ba? Mama na nufin ba zan taba cimma burirrikan rayuwata ba? Ya ALLAH ka sa kada shima in rasa shi kamar yadda na rasa Aliyu-Haydar. Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar..... ranar da za a ce shima Dr. N na rasa shi. Ni sai yanzu ne ma na san ina son Dr. N, hankalina ya yi matukar tashi da al’amarin dake shirin faruwa dani. Ya ya zan yi iyayena su amshi Dr. N? Na yi tunani iyaka tunani bani da mai mara min baya cikin dangina kakaf, kowa tsoro yake kada in shafa mishi kashin kaji. Na yi kuka na yi kuka har na ji babu dadi, idanuwana suka shiga yin wani yaji-yaji saboda kuka. Tunanin halin da Dr. N zai kasance in ya tsinci labarin ba za a bashi ni ba, da wanda nima zan kasance da abin da iyayena ke nufina da shi, shine babbar damuwata. Shin me ya mantar dani matsalar gidanmu tunda fari? Na yi zurfi a son Naziru? Me ya mantar dani rigimar gyatumar mu mai ran karfe? Babu ko tantama SO ne, SON NAZIRU ne. Ya makantar dani ya kurmantar dani har bana iya tunanin me zai je ya zo, har bana tuna baya balle abin da gobe za ta haifar. A wannan rana na yi fatan a ce ina ma ban fito daga A.B family ba! Ina ma ban kasance cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa ba [6/3, 4:13 pm] Takori: Surutun Hajiya kara kular da shi yake. A kufule ya ce, “To na ji Hajjah, in ta farfado din sannan ki san abin yi ko ba yanzu ba da lafiyarta ake nema ba komai ba”. Hajjah ta wuce tana fadace-fadacen ta da mita wanda Fa’izu bai saurari ko daya daga cikinsu ba. Pilot Fa’iz Giwa babu abin da ya gama shi da asibiti. Amma tsabar kishin kada Aliyu ya daukar mishi mata ya gwammace kada a kaita asibitin. Shi kam yanzu ya fara son Fa’izah ma da damarar rayuwa da ita. Sai dai ta mutu su je lahira suyi aure su zauna tare, amma Hajjah ta canza masa farat daya kamar ba Hajjar shi ba wadda ta fi kowa son shi a duniya including iyayenshi, ta fi shi son duk abinda yake so, ta fi kowa farin ciki da ya ce a aura mishi Fa’izah ba. Ta yi murna, ta sa mishi albarka har da kukan farin cikinta. Amma da ya dubi halin rai kwakwai mutu kwakwai da Fa’izar ke ciki sai ya yi mata uzri. Firjin dake gefe ya bude ya fiddo ruwa mai sanyi ya zuba a kofi ya tsugunna ya karanto Ayatul-Kursiyyu, Falaqi, Nasi da Ikhlas. Ya karanto karshen Suratul Al-Imran wato daga (Rabbana faghfirl lana wa af-anna) ya karanto ayoyin karshe na suratul Hashri tare da addu’ar Yusuf (A.S) a lokacin da ya shiga kunci a kurkuku, da addu’ar Yunusa (A.S) duka ya tofa a cikin ruwan, duk wata addu’ar yayewar kuncin zuciya da ta zo bakinshi ya tofa a ciki. Ya shafe min fuska da ruwan har cikin kirjina dai-dai santar zuciyata. Na lumshe ido a hankali amma ban motsa daga yadda nake ba, Fa’iz ya samu kanshi cikin tsananin rudewa da firgita, bai san sanda ya kwalawa Ummi da Zanirah kira ba. Dama suna falo suna ta tsuma. Zanira a guje Ummi da sassarfa suka fado dakin. Ya ce, “Shi kenan da gaske ne ta mutu, ku ce da su Baba su zo su binneta....” Fa’iz kuka yake sosai da hawaye da zuciyarsa. Haka Ummi da Zaneerah. Ko kusa da Fa’izar sun kasa karasawa. Aunty Hauwa ta shigo dakin da saurinta, da alama zuwan ta gidan kenan. Tana ta fada kamar ta ari baki, “Wane irin hauka ne wannan Fa’iz? In ka hana Aliyu kai Fa’izah asibiti me kenan ka yi? Ko meye ribar ka cikin hakan? Wai ma tukunna Fa’iz da na sani ne kuwa? Crying for the sake of Fa’izah’s unconsciousness?” Ta yi murmushi, duk ita daya ta ciccibeni gaba daya ta yi waje. Fa’iz bai ce komi ba, illa rakamu da kyawawan idanunsa dake cike da hawaye sun kuma kada sunyi jair. Sai kuma ya tashi da hanzari ya bita. Aliyu ya yi dariya ya aje little Fa’izah ya bisu ya ja motar zuwa asibitinsu wanda ke bayan gidan duka cikin A.B Estate wato A.B Clinic and Maternity. Likitoci biyu ne suka rufu a kaina suna kokarin ceto numfashina. Fa’iz ya shiga kai kawo tsakanin gabas da yamma, kudu da arewa. Ya yin da Aliyu ya jingina da kofar (Emergency Room) da nake ciki yana hango fuskata cikin (oxygen) da aka makala mini. Aunty Hauwa ta yi tagumi a kan kujera ta rasa abin da yake mata dadi. A haka jama’ar gidanmu da ‘yan daurin aure duka suka taddamu wannan ya harari Fa’iz wannan ya tausaya mishi, babu wanda ya iya ce masa ko da sannu da zuwa bayan shekaru masu dama da suka kwashe basu sanya shi a idanunsu ba. Shi kam Babana kujera ya samu ya kame yana kallon kowa daya bayan daya. A lokacin Baban Kaduna wato Alh. Mukhtar ya iso asibitin. Da Dr. Habib ya fito ya nemi son ganin daya daga cikinsu Baban Kaduna ne ya shiga. Ya ce, “Muddin Fa’izah ba ta farfado ba nan da awanni uku, to zai yi wuya in ba coma bane ta shiga. Sannan jininta ya hau, mugun hawa kuwa, zuciyarta ta tabu. Kokarin da muke yi yanzu shine na jininta ya sauka, numfashinta da bugun zuciyarta su dawo dai-dai. Na roke ku idan an samu Fa’izah ta farfado ku guji gaya mata awkward incidence ba ta hanyar da ta dace ba. Domin sudden unpleasant shock ya kan harbi kwakwalwa har ya haifar da depression’. Baba Muntari ya shiga sharar zufa, babu shakka ya shiga tashin hankali. Ya ce, “Ba komi likita, shi kenan ai in an samu ta farfado din shi kenan. Kuma ni ban san abin da aka gaya mata na tashin hankali ba, aurenta kawai aka daura da dan’uwanta yanzu-yanzun nan, bayan wannan ban san komai ba, dama can tana da makamancin ciwon hawan jini ko (something associate) ne bamu sani ba?” Dr. Habib ya ce, “Lafiyarta kalau. Sudden shock ne wanda zuciyarta ta kasa karba kawai. To ko auren ne ba ta so?” Baban Kaduna ya ce, “Mai yiwuwa. Biri ya yi kama da mutum, domin wasu daban sun zo neman auren ta. Bari in je in same su in ji”. Ya mike ya firto fuskarshi babu annuri sam. Barau ya kira gefe suka yi magana don da shi ya fara cin karo, ya kuwa gaya masa komai a gurguje cewa, Fa’izah ba ta son Fa’iz tun tana kankanuwa, Fa’iz ya tsani Fa’izah, tunda aka haifeta basu taba zama a inuwa daya ba dai-dai da sakan daya. Aliyu ta so ta aura kuma da bata samu ba ta dangana saboda Zaneerah. Tun sanda Hajjah ta fara fito da zancen ya same ta cikin sirri ya ce kar a soma wannan kada gyara zumunci ya zama bata zumunci. Su da aka yi musu haka suka zauna lafiya, to fa in babu soyayya a tsakani haka babu kiyayya, kuma su na jiya ne ba na yau ba, zamani kullum canzawa yake yi. Zai fi kyau a dinga karbar canjin da ya zo da shi idan babu sabon Ubangiji ko halaka a cikinsa”. Jikin Baba Muntari sanyi kalau kuma ransa ya baci domin shi ba haka Fa’iz da Hajjah suka gaya mishi ba kafin ya karbi waliccin auren nan. Ya dauka cewa ko da hakan (doctrine) din su ne kuma umarnin Hajjah ne, to babu wani abu makamancin wannan tsakanin Fa’izu da Fa’izah. Ofishin Dr. Habibu ya koma ya dauko takarda da biro ya fito ya doshi Fa’iz wanda ke tsaye gefe yana kallon su cikin dimuwa, don ya amince ba ALHERI Baba Barau ke gayawa Baban Kaduna ba, ganin yadda fuskarsa ma’abociyar kamala ke tattarewa tana yamutsewa. Don haka ganin ya nufo shi da takarda da biro fuskarshi babu alamun rahama, sai ya ji hanjin cikinsa suna dunkulewa wuri guda. Fa’iz ya daga dara-daran idanunshi da suka kada suka yi jawur ya dubi Baba kallon rashin fahimta, ya motsa baki zai yi magana amma ya rasa me zai ce ne. Baba ya ce, “Karbi ka rubuta min saki uku yanzun nan Fa’izu”. Fa’iz ya ja da baya ya soma hawaye ya ce, “Baba Fa’izah za ta farfado ne, amma ni ba zan yi saki ba....” Baba ya ce, “Fa’iz har ka yi kaurin wuyan in fadi ka musa min? In ka kashe ta za ka auri gawarta?” Fa’iz ya shiga girgiza kai ya ce, “Shin Baba a kan me za ka yanke wannan danyen hukuncin gare ni? Ka sani muddin ka takurani na rubuta takardar nan shi kenan, in na tafi ba zan kara dawowa kasar nan ba, kuma ba zan.....” Wani irin mari Baba ya share shi da shi, sai ga habo ta hancinsa. Ya kai hannu zai sake sharara mishi Babana ya rike hannun tamau. Suka juyo suka fuskanci juna su biyun, kowanne zuciyarshi na tafasa, inda Baban Kaduna ya yi amfani da gadarar shekaru biyu da ya tserewa Baban ABU da su ya ce, “Ni sa’anka ne Ahmadu? Ko ko akwai irin wannan wasan tsakaninmu?” Babana ya ce, “Babu ko daya, amma a nan kam ka yi zalunci in ka takurawa daya don amfanin daya. Aure kuma Fa’iz ba zai saki ba in dai a kan don kar wannan yarinyar ta mutu ne. Mutuwa lokaci ne kuma tana kan kowa, sannan lazim ce baka isa ka kara mata dakika daya daga wanda Ubangiji ya riga ya rubuta mata ba. Ni dai ni na haifi Fa’izah in kuwa ni din ne to in ta mutu na yafe, zan dawwama da farin cikin cewa da igiyar auren Fa’iz ta mutu cikin cika burin mahaifinmu Abubakar Bamalli. Sai dai fa abin bai kai da duka ba, Fa’iz ya wuce duka! Sai dai in Fa’izah ta kashe kanta a kan shirmen banza ta mutu kafira ba ruwana, amma aure ko ka kunce sai na sake daurawa. Ba a haifi dan da ya isa ya ki bin umarnin A.B Family ba, ba a haifa ba in dai ina da rai, ba kuma za a haifan ba. Fa’izu jeka abinka sai na neme ka, kada ka kara wahalar da kanka zuwa asibitin nan”. Fa’iz ya juya da sauri ya fita duk gaban rigarsa ya baci da jinin dake fita daga hancinsa. Ya dauki motar Aliyu da suka zo a ciki ko rufewa bai yi ba ya yi ribas da gudu ya fita daga estate din baki daya ya bar garin Giwa baki daya ya nufo Kaduna. Yadda ya shigowa Mama falo ya firgitata, sai dai kuma ba ta yi mamaki ba sam, habon ne da bacin da rigarsa ta yi da jini ya daga mata hankali, amma ba ta nuna ba. Tozali na farko da Abubakar Fa’iz dinta bayan shekaru takwas. Amma ta ganshi cikin wannan halin mara dadi da kyawun gani. Ta yi tagumi ta zuba mashi ido sai zufa yake. Daga bisani ya mike ya ware karfin A.C falon gaba daya da fanka, ya yi kwance rashe-rashe a tsakiyar falon yana lumshe ido yana budewa a hankali, shi kadai ya san abin da ke cin zuciyarsa, sai ko Ubangijin da ya halicci zuciyar ya sirrantata ya sanya mata hijabi don ta zama sirrin dan Adam da Ubangijinsa. Ita Mama zato take ma Fa’iza ce ta fasa masa hanci, ta ce cikin ranta, ai tayi da sauki da ba kan duka ta rotsa maka ba. Ta shige kitchen ta sakar masa labule ta janyo masa kofa. **** Karfe biyar na yamma agogon dake dakin asibitin ya nuna, wanda ya yi dai-dai da lokacin da na ja dogon numfashi tare da ware dukkanin idanuwana kan likitoci biyu dake kaina. Dr. Habib da Dr. Imoh suka dubi juna suka yi murmushi tare da zare na’urar da suka makala mini. Kwata-kwata na mance komi, ban san abin da ya faru dani ba da har ya kawoni gadon asibiti. Dr. Imoh ya ce, “Ya ya dai Fa’ija?’ Na yi murmushi na ce, “Bani da lafiya ne na ganni a clinic?” Dr. Habibu ya ce, “Of course Fa’izah! Za ki dinga fama da migraine (ciwon kan barin kai guda) lokaci zuwa lokaci. A duk lokacin da kika ji ya tashi, akwai kwayoyin da zan baki ki dinga hadiya kin ji ko?” Na gyada kai. Suka juya suka fita suka jawo min kofar. Nurse ta shigo ta gyara min kwanciya ta fita. ‘Yan’uwa da iyayena suka shiga shigowa mutum uku-uku suna duba ni suna fita. Shigowar Ummi da Zaneerah daga karshe ya tariyo min abin da ya faru awanni shida da suka gabata. “....... An daura aurena da FA’EEZ, FA’EEZ BAMALLI.!..... Fa’izun gidan Baban Kaduna...... Fa’iz Yayan Zaneerah, Fa’iz mugu, azzalumi, makaryaci, maketaci mai cin amanar ZUMUNCI da tozarta shi a gaban ko a bayan idon kowa... Munafuki, masharranci.... Fa’iz da na sani? Fa’izun Hajjah? Fa’iz da na tsana tamkar mutuwata...... Fa’izun da ya nuna min tsanar da a duniya babu wanda ya nuna min kwatankacinta, mai cin mutuncin mahaifiyata! Fa’iz! Fa’iz!! Fa’iz Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa......!!!” Na mike zaune sannu a hankali ina bin Ummi da Zanirah da kallo, wadanda bayan kalmar sannu da jiki basu kara ko tari ba. Na kai hannuwana duka biyu na rike kaina dake juyawa yana sarawa tamkar ya tsage. Idanuwana suka kada suka yi jajawur suka kankace, na dubi Ummi, Zanira, Yaya Aliyu da Babana da suka shigo daga baya. A lokacin ne hawaye suka soma zuba min tarara! Na bude baki zan yi magana na kasa. Wani kunci da bakin cikin da ba zan iya fassarawa ba ke azalzalar tsakiyar kirjina, na kai hannuna na dafe kirjin na ce cikin rishin kuka, “Baba anya kana sona kuwa? Da hadin bakinka aka yi min haka? Da saninka aka daura min aure da Ya Fa’iz? In kun hanani Nazir ku rasa wanda za ku lika min duk cikin zuri’armu sai Hafizin Hajjah? Baba kana sane da tsakanina da Fa’iz tun tali-talin kuruciya har girma! Baba Fa’iz fa ya tsaneni nima haka!! Makiyinka baya taba rikidewa ya zama masoyinka, har abada Baba. Don me baku hada shi da Ummi dake son shi yake son ta ba? Ya ya kuke so na yi da nauyin so, kunya da alkawarin da na yiwa Dr. Naziru?” Na shiga rurin kuka mai tsima zuciyar duk mai imani, balle MAHAIFI. Amma Baba bai ce komi ba, karewa ma fita ya yi daga dakin baki daya. Su Aunty Hauwa duk suka sake shigowa, ashe suna kofar dakin basu tafi ba. Yaya Aliyu ya dubi Aunty Hauwa cikin bacin rai ya ce, “Gaskiya-gaskiya ba a kyauta ba”. Aunty Hauwa ta harare shi ta ce, “Saboda me baka gayawa wanda ya fita ba? Ko kuma kana so ka kara da ta biyu ne?” Ya yi tsaki ya girgiza kai ya ce, “Ki bar maganar wasa Aunty Hauwa, ko kadan babu wannan tsohuwar ajiyar a zuciyata, illa gaskiya duk inda take dole in fade ta, ba a kyautawa Fa’izah ba! Ko babu komi yanzu Fa’izah matar Fa’izu ce, kinga kuwa ai babu sauran zance”. Aunty Hauwa ta yi murmushi, ban ga alamar ba a kyauta min din ba a fuskarta. Yaya Aliyu ya ce, “Fa’izah bani da ilimin (psychology) amma ina da tabbacin yadda kika ki auren nan haka Fa’iz yake kin shi ko ma fiye. Haka na dauka kafin ya dawo tun sanda iyayenmu suka fito da zancen. Amma Fa’iz ya zo da wani sauyi mai ban mamaki da na kasa fassarawa, he’s completely a changed person, unpredictable. Hajjah kanta yanzu ba ta son zancen auren ganin halin da kike ciki, haka Baban Kaduna da Baba Barau. Baban ABU da Baba Na’ibi da sauran hadin sune kawai, kuma su kadai ke son abin a yanzu. Yanzu Baban Kaduna ya gama fada da Baban ABU a kan a raba auren tunda yanzu ya fahimta abin da babu wanda ya fahimtar da shi a baya. Don haka ki kwantar da hankalinki ki saki ranki ki koma cikin nutsuwa da walwalarki, babu inda auren nan zai je tunda kaso mafi rinjaye kuma (most powerful) yanzu basu so. Ki bisu da duk abin da suka umarceki da dadin rai, ki kwantar da kai ki roki Fa’iz in har baya sonki ya baki takardar saki, na rantse miki in har yanzun baya sonki zai baki ko don maslahar kansa, ni kuma idan har ya baki, ni kuma na yi alkawarin duk yadda zan yi zan yi in ga kin auri zabin ranki, wa ma kika ce yake da suna?” Maimakon kalaman Yaya Aliyu su faranta mini ji na yi sun bakanta mini kamar akwai rainin hankali a cikinsu, musamman da na ga Aunty Hauwa ta bamu baya tana danna waya, ba shakka dariya take. Na dubi Yaya Aliyu a hankali da rinannun idanuna jage-jage da hawaye. Akwai wani irin yanayi a tattare cikin kwayar idonsa wanda ban saba gani ba in yana magana. A duk sanda Yaya Aliyu ke magana, kwayar idanunsa kan nuna gesture wanda ke tabbatar da abin da yake fadi. Amma a yau, ina shakka, Ali Na’ibi ya ki mu hada ido in hango wancan gesture din dake cikin kwayar idanunsa, ya juya wani bangaren ne daban baya kallon idanuna, kuma fuskarshi ta yi jawur abinki da farin mutum, farin Bafillace, Bamalle. Tsagin Mallacin ya fito rada-rada a gefen fuskarsa, kamar wanzamin A.B ya tisa. Idona a kanshi bana ko kiftawa na ce, “Yaya Aliyu ka rantse min da Allah ba da yawun Fa’iz aka daura mana aure ba”. Yaya Aliyu ya dan rikice kafin ya ce, “To Fa’izah me ya kawo rantsuwa, baki yarda dani ba kenan? Za ki dora min kaffara a kan abin da bani da tabbacinsa”. Na ce, “Duk ba haka bane Yaya Aliyu.....” Aliyu ya dubi su Ummi da su Aunty Hauwa kowacce sai ta sunkuyar da kai aka rasa mai yi min rantsuwar da nake so ya yi min din, duk da na san basu da masaniya a kan komai, musamman Ummi. Aunty Hauwa ta ce, “Fa’izah ki saurare ni, duk kin bi kin ta da hankalinki a kan abin da bai kai ya kawo ba. Fa’izu dan’uwanki ne ko babu aure tsakaninku ba zai cutar dake ba, ko baya son naki aure Ibada ne ba don biyan bukatar rai ake yinsa ba ko soyayya kadai. Ki dubi girman zumunci da nonon da iyayenku suka tsotsa tare ki kwantar da hankalinki ki manta da kuruciya..... daban take da GIRMA! Dukkaninku jiya ba yau ba!! Babu wanda bai mallaki hankalinsa ba, abin da kuke yi a da duk kuruciya ce.....” Wani irin kallo na yiwa Aunty Hauwa wanda ita kanta ya tsoratata. Ya kuma ba ta mamaki a yadda dai matsayinta yake a gare ni da yadda muke girmama su. Na ce, “Uhm! An daura fa! Nima shaida ce a kan hakan. Sai dai wallahi yadda aka daura haka za a sunce. Wallahi-wallahi in har ina numfshi babu inda auren nan zai je daga kaina ba zaku sake ba A.B. Da in yi zaman aure da Fa’iz na gwammace in kare rayuwata haka nan single! Da in zauna da Fa’iz gara min zamana a kabarina, gara na ga mutuwata, gara min zama da bakin kumurci.... gara na rasa rayuwata dungurugum!!!” Wani irin juyi da barin kaina ya shiga yi ya tabbatar min (migraine) da likita yake magana ya tabbata. Na dafe kaina na shiga kuka sosai. Na ci gaba da fadi cikin gunjin kuka. “Ya ya ma hakan zai taba faruwa? Wallahi ba zai yiwu ba!” Ni kadai kamar mahaukaciya nake ta wannan sambatun sun yi min shiru. Wannan ya kara tunzura zuciyata. Tunanin halin da bawan Allah. Dr. N zai kasance a ciki idan ya tsinkayi wannan labarin ya kara sanya ni tsandara kuka da kara duka a tare. **** Kwana biyu kacal duk na rame fiyet na zabge na fita a hayyacina. Sai ka rantse na yi shekara ne a kwance. Likita ya bamu sallama tare da kashedi iri-iri ga su Babana. Baban Kaduna ya ce, “Af! Ai aure ba makawa za a kwance shi me ya yi zafi?’ Wata sabuwa in ji ‘yan caca! Hajjah ta dawo ta girgije ta sanya ranar biki kwanaki bakwai masu zuwa, kasancewar ana jiran Basheer da zai dawo kwanaki uku da zuwan Fa’iz. Ashe daman rudewar ganin halin da na shiga ya sanyata canza alqibla a baya? Uhm! Zan ga wanda za su yiwa bikin kuwa. Babban rangwame ga zuciyata ban sa fuskar azzalumin ko sau daya a idanuna ba balle keyarshi. Wannan ya tabbatar mani lallai ne shima yana tsoron haduwar mu which I believe must be the most dangerous approach bayan gushewar shekaru masu dama. Ummi kam ta rungumi kaddara, ta bi umarnin iyayenta, a cewarta, iyayenmu ba za su taba zaba mana abin da zai zama cuta garemu ba. Ba za su taba kaimu mahalaka ba (Ummi fa ba ni ba). Karfe tara na dare na kadaice kaina cikin (store) kuka nake kamar raina zai fita. Irin shirye-shiryen da na ga A.B baki daya na yi ya tabbatar mani biki babu fashi za su yi shi. Ba ruwan kowa dani, ba mai shiga sabgata don da alama basu ma dauke ni a cikakkiyar mai hankali ba. Da na yi na gaji, babu mai rarrashi, babu kuma abin da kukan zai tsinana mini, sai na daura dukka hannuwana biyu a ka na shiga kwarara ihu tun karfina, ina bubbuga hannuwana jikin buhunhunan masara da shinkafa dake lode a store din. Jama’ar gidan duk suka baro abin da suke yi suka taru a kaina ban ga alamar akwai mai shirin lallashi na ba ko tambayar ba’asin ihun da nake yi. Kallo na suka tsaya yi tamkar masu kallon talabijin. Ummi ta yi tsaki ta ce, “Allah wadaran rashin tawakkali da rashin hankali da sakarci wallahi! Shin cikinmu don wa kike wannan haukan Fa’izah? Aure dai baya wurinmu kuma bamu muka daura ba balle mu warware miki, don haka ki kyale mana kunnuwanmu su huta”. Hajjah ta fito daga kitchen ta ce, “Don son Annabi wanda duk ke son gamawa da duniya lafiya ya tafi a wurin nan ya kyale Fa’izah!” Na sake sheko ihun tun karfina, na ce, “Hajja kun cuce ni, ku doke ni ku hanani kuka? Ku kulla min igiyar aure da mutumin da na ki jini a duniya fiye da mutuwa ta, bayan kin raba ni da wanda nake so da farko da na karshe, sannan ki ce ba zan yi kuka ba? Shin in ban yi kuka ba ya rage min radadin da zuciyata ke yi kashe kaina kike so in yi don bakin ciki ko me?” Baban Giwa ya ratso mutane bayan ya karyo reshen dalbejiya ya ce, “Uwar waye ta cuce ki ba dai uwarmun ba ko? Ja’irar yarinya har nake daga hakarkari nake son ayi miki son ranki don a zauna lafiya, ashe baki da mutunci baki da da’a? Hajjah kike cewa ta cuce ki?” Ya zuge ganyen baki daya ya shiga dankara min dukan da ake kira dukan mutuwa, wanda tunda nake a rayuwata ko makamancinsa ba a taba kwatanta min ba, amma bakina bai mutu ba, bai huta ba da fadin “Hajjah kin cuce ni.... kin raba ni da burin da na ciwa rayuwata.... ba zan taba yafewa ba muddin rayuwata.....” Hajjah ta soma kuka da idonta a yayin da ta kama hannun Barau ta ce, “Kyale ta haka nan, Fa’izah ba ta cikin hankalinta, ka kyaleta na ce kada ka yi abin da za ka zo kana nadama, in kuma baka bari to ka sauke zuciyarka a kaina ka karasa min dukan”. Baba Barau ya yar da tsumagiyar ya yi waje fuuuu! Kamar kububuwa, jikinsa har tsuma yake. Na tabbatar da Babana ne yau sai dai a dauki gawata in ya so shima a kashe shi. Hajjah ba ta yi fushi ba ta kama ni za ta mikar dani, cikin kurarin kuka na ce, “Kada ki kuskura ki taba ni..... Daga yau ba zaki sake ganina ba balle ki yi iko dani. Ki tuna Ubana kika haifa ba ni ba, don haka ko kashe ni aka yi babu ruwanki......” Zaneerah da Ummi suka saki kuka, “Fa’izah kina da hankali?” Na ce, “Kwarai, Baba Muntari da Aunty Hauwa ke rabon ciwon hauka har na je Kaduna na samo. Ko me za ku ce ku ce wallahi banni zaman aure da Fa’izou......” Jini ke bulbula ta hancina yana shiga bakina inda Baban Giwa ya shauda min dalbejiyarshi a kan hanci. Na kai hannu na share a yayin da na zaro jajayen idanuna suka kumbure suka suntume suka yi luhu-luhu jajir. Na ce, “Ku bace min da gani ko in kakkarya ku na rantse yanzun nan, manyan munafukai algungumai, ai daku aka kulla komai amma babu wadda ta gaya mini. Tsakanina daku sai Allah ya isa!” Ai kamin in rufe bakina na nemi kowaccensu daga yaran har manyan na rasa. Na ci gaba da gunza kuka ban ko damu da radadi da zugin da jikina ke yi mani ta ko ina ba. Muryar Yaya Aliyu daga tskar gida ya tabbatar mani ya shigo gidan. A yayin da Ummi ke fadi mashi cikin kuka........ “YAYA ALIYU FA’IZA TA HAUKACE!” Wadannan sune kalamai mafi firgitarwa da Aliyu Na’ibi ya taba ji a tsayin rayuwarsa. Baya ga dogon salati da ya ja ya dire ya tsarkake Ubangiji ya yiwa Annabi salati, sai ya sanya hannu ya zare hularsa da takalmi ya ce, “Tana ina?” Hajjah dake sharbar kuka zaune a kofar kicin ta yi mashi nuni da hanyar store. Aliyu ya shigo a hankali ya kunna fitilar da na kashe ya zauna gefena a hankali, ya dubi yadda na yi jina-jina, face-face cikin hawaye, jini da majina, ya matso kwallar da ta tarar masa cikin ido. “Shin wane ne da wannan danyen aikin haka Fa’izah?” Na ja shesshekar kuka cikin dusasshiyar muryar da ta dushe gaba daya, “Kadan kenan tun yanzu kan DAN DA KOWA KE SO. Nan gaba in na batawa Fa’iz mai yiwuwa a nakastani ko a hura wuta a babbaka ni Aliyu? Ba dukan kawo wuka ba, ko yankani A.B za ku yi gunduwa-gunduwa ba ni auren nan. Na gwammace in bi yawon dandi, da dai in yi karashen rayuwata a matsayin matar FA’EEZ BAMALLI!” Aliyu ya kaskantar da murya ya ce, “Fa’izah! Abin bai yi zafin haka ba ai. Kash! Ki bar furta kalmar nan ta “DANDI” ba don ni ba, ba don halina ba, ba don halinsu ba su duka iyayenmu. Sai don darajar da Allah ya yi miki ta ‘ya mace mai cikar mutunci ‘yar manyan mutane, kuma ‘yar gidan mutunci kamar A.B. Su wadannan da kika bi kika tadawa hankali meye ruwansu ne? Me ya shafe su? Aure dai sun yi kuskuren daurawa. Amma igiyar warware shi da kwance shi ba ta hannunsu balle su kwance ko su warware. Duk wannan kakabi da zagi da tashin hankali ba nasu bane, ba su ya kamata ki yiwa ba tsakaninki da Fa’iz ne can. Amma ina ruwan Ummi, Hajjah ko Zanirah?” Na galla masa harara na ce, “To shin ina na ganshi balle in yi mishi Yaya Aliyu? Ni kam yadda nake ji a zuciyata baki dayan A.B nake jin haushi. Har kai din wallahi”. Murmushi ya yi, ya rausayar da kai, “Ta ina laifin wani ke shafar wani? Har da Yaya Aliyu? Fa’izah” Fa’eez shi ya nemi aurenki da kansa domin gyara zumuncinku da ya gurbata a baya”. Ban san sanda na lailayo ashar ba na ce, “ZUMUNCIN me? In dai wannan shi ake kira gyara zumunci to ba shi bane, sai dai kara lalata shi. Na ji zan iya yafewa Fa’iz dukkan abin da ya yi mani, amma ba ta hanyar aure ba. In dai har an yarda a raba auren nan in auri Dr. N na YAFEWA FA’IZ DUK ABIN DA YA YI MANI A BAYA!” [6/3, 4:13 pm] Takori: Aliyu ya ce, “A da har an tayar mani da hankali da aka ce dani wai “Fa’izahna ta haukace! Ashe lafiyar kanwata lau. To share hawayenki ki bar ta da hakarkari tunda kin ce haka shi kenan. Yanzu abin da za ayi Fa’iz za ki yiwa wannan bayanin ta lallama da salama da kwantar da kai. Kin san an ce..... mai nema shine a kasa har kullum. Don haka kada ki ji komai don kin roki Fa’iz wani abu wannan hakkinsa ne a yanzu. Shi ke da ikon yi ko ki. Don haka dole ki aje rawanin kiyayyar gefe ki roki Fa’iz. Yanzu Fa’iz ya canza, ba shi da wannan muguwar azzalumar fuskar da kike fadi, ke tsoronki ma yake ji! Kin san an ce abin da ya baka kuka wata ran shi zai baka dariya. Haka abin da ya baka tsoro wata ran shi zai baka dariya. Baki ga ya kasa zuwa ba? Amma ina ruwan su Zaneerah, Ummi da tsohuwar Allah HAJIYA HADIZA?” Na girgiza kai hawaye na zuba na ce, “Yaya Aliyu kai kadai ke sona a cikin gidan nan tunda har ka goyi da bayana ka gane abin da nake so su gane suka kasa ganewa, wato Fa’iz ba mijin aure bane, ba masoyi bane abin neman tsari ne. Don haka na dauki shawararka, ka je ka baiwa su Hajjah hakuri domin na zage su sosai”. Aliyu ya yi murmushi ya ce, “Har na ji dadi, ni Aliyu Baban Fa’izah! Allah yasa nima tawa Fa’izar ta yi min biyayya haka tamkar mai sunan ta. Share hawayen nan duka A beg...” Nasa habar zanina na share hawaye tas, duk jikina rawa yake da karkarwa. Aliyu ya ce, “Kada ki damu da su Hajjah, su tunaninsu kin samu motsi a kanki ne. Don duk kuka suke miki na tausayawa. Ni kam na san babu yadda za ayi Fa’izata ta haukace a kan Fa’iz, faruwar hakan na nufin kenan FA’IZ ya yi galaba a kan FA’IZAH!” Na ce, “Never. Idan har na yi hauka saboda Fa’izu na ji kunya na fadi babu nauyi, kuma ban haifu cikin Maimunar da yake zagi ba tunda ban rama komai ba, tunda na bar Fa’iz cikin nasa hankalin. Wata ma zai je ya auro wadda ta fini ya ci gaba da rayuwarshi normal ni ko in kare a pyschiatric da Asylum”. Cikin murmushi sosi Yaya Aliyu ya ce, “Yauwa, ashe dai kin gane. Amma in ya baki takarda kika yi auren ki da Dr. Nazir kinga ai kin tusa mishi haushi ko baya sonki zai ji kishi, tunda akwai igiyar aure da ta taba gittawa a tsakanin ku, ko ya ya ne. In hakan ta faru da kyar ma zai iya zaman kasar ko ya kika ce?” Na yi murmushi da kumburarriyar fuskata na ce, “Shin Yaya Aliyu ina zan ga FA’IZ BAMALLI?” Yaya Aliyu ya ce, “Fa’eez na cikin kasarmu mai dimbin albarka yanzu haka. Za ki ganshi yau, gobe, jibi ko gata. Muddin ranakun nan suka wuce baki ga Fa’eez ba, to kirayi auren ku da suna tabbatacce na muddin rai. Domin sune ranaku na karshe da za a kammala bikinku a kai ki gidansa kina so ko bakya so. Don haka ki yi duk kokarin da za ki yi ki ga Fa’iz cikin kwanaki uku”. Na yi zugum ina kallon sa, na ce, “Shin don me ka boye min tun a daren ranar Yaya Aliyu? Wallahi-wallahi da duk yadda za ayi ba zan bari a daura auren nan ba......” Na ci gaba da kuka. Aliyu ya rasa me zai ce mini? Shi kam dabararsa ta kare kuma. Sai ya ce, “Ni kaina Fa’izah yanzu ba na ce miki ga hakikanin inda Fa’iz yake ba, rabona da shi tun ranar da ya dawo”. Da lallami da ban baki gami da dabara irin na Yaya Aliyu yasa na tashi daga store na je na kwanta a gadon Hajjah. Daga Ummi har Zaneerah babu wanda ta yi gigigin shigowa don kam su tsorona ma suke ji. Yarinyar da za ta bude baki ta zage Hajjah cikin A.B ai abar tsoro ce, balle nasu iyayen karan-kada miya. Yau da Baban ABU ya ji kalaman nan da na kade har ganyayyakina. Cikin daren na dinga shesshekar kuka ni kadai ina watangaririya a kan gadon Hajjah, daga wannan gefe zuwa wancan. Na turza na turza cikin kowanne lungu na zuciyata wurin bin shawarar Yaya Aliyu ta ki amince min da hakan, wato in kwantar da kai in roki Fa’iz Allah-Annabi amma na kasa. Ya ya zan iya zub da mutuncina ga Fa’iz in nemi wani abu daga gare shi, ashe ma ya isa kenan! Never (fau-fau). Dole ne ma ya bani, in ba ta tsiya ba ta tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarsa ba! Shima ya sani ko a lahira ba zamu yi makwabtaka ba balle zaman inuwa daya a duniya ko a lahira!!! Wai ta ya ya ma Fa’iz zai nemi aurena, kamar yadda Yaya Aliyu ke cewa? Ni fa Fa’izah da ya tsana? Ni kazama dakikiya ‘yar Maimuna? Uhm! Ko don yanzu na yi idon gani na zamo abar kwatance cikin mata? Da da nake a ‘yar’uwarsa kankanuwar yarinya mai rauni da bukatar kulawar yayyu irin sa me ya hana ya kauna ce ni? Ta ya ya yake tunanin ni Fa’izah zan mance kiyayyar da Fa’iz ya nuna mini tun ina ficiciyata har na kawo yanzu? Sanda yake aikowa su Ummi kayayyaki BAN DA NI. Ya tambayi lafiyar kowa BAN DA NI. Ya nuna banbaci kiri-kiri da fifiko tsakanina da sauran ‘yan’uwana...... Ya yabesu ni ya kushe ni..... ya zagi uwata a duk sanda ya so, ya dauko Ummi daga makaranta ni ya barni a jeji ko in mutu ko in yi rai ba damuwarshi ba ce. Ba don komai ba sai don saboda tsabagen tsana da kiyayya! Shin meye dalilin auren yanzu? Don na yi girma na yi kyau na zama kyakkyawa..... Don na yi kwakwalwar karatu wadda a da bani da ita..... Don na yi kyawun da duk cikin A.B babu kwatankwacina balle tsarana! Kaico da masu halin son zuciya irin Fa’iz Giwa. Wani da shan wahalar raino, ilmantarwa tare da real kauna ga Fa’izah shekara da shekaru bai samu ba sai shi. Wani da kwashe shekaru yana hidimtawa Fa’izah da inganta rayuwarta positively ba a bashi ba sai shi. Ga masoyi na gaskiya irin Dr. N mai wuyar samu a wannan lokacin, mai sadaukarwa so da kauna dukkan hakkokin da Allah ya ce a basu bai samu ba sai shi. Tabbas muddin na yarda na zauna da Fa’iz ko na saurari wata kalma daga gare shi ko da guda daya ce na tabbata wadda ba ta san ciwon kanta ba, ba ta san darajar kanta ba, ba ta san darajar wadda ta dauki cikinta wata tara ta haife ta shayar cikin wahala da kakani-kayi. Muddin ban auri Dr. N ba na cika butulu duba da tarin kauna da soyayyar da ya mallaka mani, na zama mayaudariya. Ya zama dole kenan in kaskantar da kaina ga Fa’izu ya warware igiyar da aka zarga a tsakaninmu? Juyawar da barin kaina yake yi ya tsananta cikin ‘yan dakiku, a yayin da zuciyata ta halarto min da cewa, rokon Fa’iz a bisa abin da bani da iko a kansa wannan dole ne! Kaskantar da kai ya zama dole gare ni, tunda durkusawa wada ba gajiyawa bane. Amma ba don ni ba illa don farin cikin Dr. Nazir Sani Galadanci. **** A washe garin ranar idanuwana na bisa kofa, yinin ranar zungur ban ko leko falo ba, illa kunnuwana da na kasa suna zuko min duk mai shigowa da mai fita a gidan Hajjah ko zan ji muryar Fa’izun? Shiru! Har yamma. Kafin in ji Aliyu na ce da Hajjah “Fa’iz ya je Kano dauko Yaya Bashir”. Hajja ta shigo dakin da nake kwance hannunta rike da kwano shake da gasasshen nama da ruwa-ruwan shi, an kuma barbade shi da yajin daddawa wanda ya ji kayan kamshin gargajiya mai dadi, ta zauna gefena a hankali da gani a darare take. Allah sarki Hajjah! Duk zagin da ta sha bai sa ta yi fushi dani ba don ina ji da safe tana gayawa bakinta ‘yan taya murna da suka zo mata daga Zaria, kada wanda ya shigo ya ta dani barci nake a barni na huta. Ita kanta ta fada fiyat! Kamar wadda ta tashi daga zazzabin kwana biyu. Ta ce, “Fa’izah ki yiwa Allah ki bude ido ki ci naman nan, na san kina jina ba barci kike ba, tun asuba nake aikin gasa miki don na san shi akdai za ki iya ci tunda kin ki cin komi tun jiya, shin baki tsoron irin ciwon Aliyu ne?” Na yi mata banza na kara cusa kaina cikin filo na bude sabon kuka. Hajjah ta yi zugum da kwano a cinya, daga bisani ta aje shi a kasa ta ce, “In kin kin cin abinci wanka fa Fa’izah? Rabonki da wanka yau kwana hudu. Shin Fa’izu ya san wainar da kike toyawa ma, in don shi kike yiwa kanki wannan ukubar?” Ban san sanda na zaro kai daga cikin filo ba na yi kutubal da shi na mike zauna, na ce, “Hajjah don na yi kyau, don na yi haske na daina kazanta na zama abin gani har a so ayi sha’awa Fa’iz ya ce miki yana son aure na ko? To daga yau duk wani abu da ya shafi gyaran jiki zuwa wanka na barshi har abada! Na koma Fa’izar da ya sanni a baya, kazama ‘yar Maimuna!!! In ce dai in na shiga warin hammata da warin baki ya ce baya so, ya je ya auro ‘yar Rasha ni kuma a barni da mai sona tsakani da Allah ba don wani abu da na mallaka ba....” Na ci gaba da kuka na gasken-gaske. Hajjah ta ce, “Ayya Fa’izah, kin yi kuskure babba, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya. Daga ranar da Hafizi ya bar Najeriya bai kara ganinki ba ko a hoto sai ranar da ya dawo bayan an daura muku aure”. Da hanzari na tari numfashinta, “Tunda haka ne ki kwance auren mana ko dole ne? Na ji ko da ban auri Dr. Nazir ba na yarda na amince ki hada ni aure da Malam Hassan maigadin gidan Baban Kaduna, ko Isa direban gidan nann....” Hajjah kam ta koma yi min dariya, ta ce, “Yo ai shi kenan, wannan abu mai dan karen sauki. Sai ki je wurin Hafizin ki amso takarda ki kawowa Ahmadu da ya kulla auren ku, ni kuma na yarda ayi aure da Malam Hassan maigadi tunda ai mutumin kirki ne bawan Allah, ko ba jinina bane na san asalinsa da tushensa, na zauna da shi tun ba a haifeku ba, babu cuta ba cutarwa”. Ta mike ta fice ta bar kwanon naman a wurin yana ta turiri da kamshi. Na dade ina juya maganar Hajjah bayan fitar ta. Don me kowa na ce ya rabani aure da FA’IZU ABUBAKAR sai ya bude baki ya ce in amso takarda wurin sa? Bayan suna da masaniyar cewa ba zan taba iya rokon Fa’iz wani abu ba, ko kalma ta hadani da shi a kafatanin rayuwata? Ni na kai masa auren da zan je na karbo ba su suka kai ba? Don me su ba za su je su karbo ba in har da gaske suke suna son gyara kuskure da laifin da suka yi mini wanda ba zan iya taba yafe shi ba ko in amince da shi? Don me sai na karbo takardar aure zai warware ina ce in an maidawa Fa’iz sadakinshi shi kenan aure ya warware? Cikin kuka na fitar rai mai soya zuciya na ce da Hajjah, a lokacin da na mike na bita har uwar dakin barcinta tana shirin ta da sallar walha. “To ki bani sadakin mana ki gani in ban mayar mishi ba?” Tana kokawar sanya hijabin sallarta ta ce cikin alamun nuna gajiyawa da magana daya, “Shin ni Hadiza meye nawa ne cikin lamarin nan Fa’izah? Sadaki dai Barau ya karba, bayan daurin aure kuma ya dankawa ubanki na Zaria. Saboda haka su za ki je ki yiwa wannan tijarar da kike yi mini amma ni in kika sa min hawan jini Allah zai saka mini....” Ta soma kokarin fashewa da kuka. Na juya na fice da gudu na bar mata dakin tun Allah bai jeho wani cikin ‘ya’yanta ya aika dani lahira ba tare da na kara sanya N.S a idanuna ba. **** BIKI-BIDIRI Ga al’adar mutanen Giwa da yammacin Laraba ne muke kamu, washe gari alhamis kuma ayi budar kai. Don haka ban yi mamakin jin hargowar jama’armu ba daga ko ina cikin garin Giwa, Zaria, Kaduna da makotansu sun cika A.B Estate. Masu kidan kwarya sun soma wasa korai da gyaran murya cikin lasifaka, masu guda na yi, maroka na ma Hajjah kirari duk inda ta gifta. Na tabbatar dai al’amarin nan da nake dauka almara nema yake ya tabbata, za su hadani rayuwa da Ya Fa’iz ne ko babbaka su zan yi. Lallashin ma babu mai lokacin yi min shi, shima Yaya Aliyun tun ranar da yasa kafa ya bar gidan ban kara jin ko tashin muryarsa ba. Ummi da Zanirah babu wacce ta kara shiga sabgata, na kan ga dai Fa’iza ‘yar Zanirah ta rarrafo dakin da nake tana wasanta, ta yi ta gaji ta fita ko sanin da halittar dan Adam bana yi a dakin, domin ruhina da kulliyar tunanina baya wannan duniyar tamu, yana cikin wata duniya ta kunci, azaba da tafasar zuciya da zabalbalar kwallah. A yau na yi amanna da cewa, zan zama matar Fa’iz in na bari tsofaffin nan suka shafa min lalle. Na yi tunani iyaka tunani bani da mafita, bani da mai mara min baya, babu mai duban hujjata da idanun basira in dai a kan Fa’izu Abubakar ne. Wani yaro cikin ‘ya’ya da jikoki da suke matukar so duk da tarin aibobinsa. Don haka na yakewa kaina mafita ta karshe. Na janyo (travelling bag) dina na shiga shirya kayana da ba za suyi min wahalar dauka ba a gurguje. Adda Hanne kanwar Maman Kaduna da tawagarsu suka yane labule suka shigo da guda da sallama, duk suka cika dakin taf! Tsokanar duniya babu irin wacce basu yi min ba, in gadon dakin ya daga ido ya dube su to nima hakan. Kaya nake ninkewa daga sif ina dannawa a jaka. Adda Hannatu ta yi kwafa ta ce, “Ke ‘yar tawaye, mun zo kama ki ne kinyi kamar baki ganmu ba saboda kin isa”. A yayin da ta bincire hancin kwalbar turare “intimately beckham” suna ta raha suna darawa cike da unexpressable nishadi da farin ciki bayyananne a zuciyar su da fuskokinsu. Na dago jajayen kumburarrun idanuna na yi musu wani kallo a kaikace ta kasa-kasan ido a hankali na ce, “Ku kama uwarku dai”. A yayin da na sunto dankwalin kaina na yi damara a kugu gashina dake daure cikin (bound) ya sunce gaba daya ya cika fuskata da wuyana baki daya, ban damu ba, ban kula ba, jikina har tsuma yake ina jiran mai kwarin kashin da za ta fara matsowa gare ni. Adda Hannatu ta ce, “Eye! Dambe za ki yi damu Fa’izah! Lallai da aka ce kin haukace ashe ba ayi kuskure ba. To bismillah ma ga mai kwarin kashi tsakanin ni da ke”. Zaneerah cikin zafin cewa da na yi su kama uwarsu ta ce, “Eh, uwarmu zamu kama mana, tunda dai babban Yaya uba ne kamar yadda matar babban Yaya ta zama UWA...... wadda za ta cika mana gida da ‘ya’ya ta sauke tukunya ta dora mana abinci...... ta sa mana kula ta sabe mana babbar riga ta yiwa ‘ya’yanmu tarbiyyah irin ta gidanmu ba irin tata ta rashin neman albarkar iyaye da son gamawa da duniya lafiya ba.......” Daga haka suka shiga kwararo min turaruka ta ko’ina gaba da bayana har tsakar kaina zuwa yatsan kafata, har kuma cikin idanuna. Ashe dama kowaccensu da guzurin abinta cikin mayafi, ba Adda Hanne kadai ba. Azabar turare cikin kwayar idona ta rudani ta gigita ni na soma kara ina murza idanun da dukkan hannuwana, ina fadin “Idona.... idona..... wayyo Hajjah sun fasa min ido”. In sun fasa to ke da baki nan kin fasa karatun nan, sai dariyarsu suke. Kasa na sulale na kwanta ina birgima ina murzar ido dake neman tsiyayewa. Sai da suka kusa karar da kwalabensu kana na sha duka kitif-kitif-kitif daga hannun kowaccensu, wai ban yi wanka da kwalliyar tarbarsu ba sai zagin da na yi musu guzuri da shi. Kai wannan rana na ga wulakancin duniya da takaici da bakin ciki wanda ke kokarin fin karfin juriya da karfin halin da nake tinkaho da su. Nake amfani dasu ko yaya ne wajen ganin na kwato hakkina daga iyaye da dangina na A.B baki daya. Sai da idanuna suka lafa daga zugin da suke yi min na kuma tabbatar da basu tsiyaye din ba kamar yadda nake tsammani. Na shiga toilet dinmu wanda dama like yake da dakin barcinmu na wanko fuska da ruwan famfo mai sanyi, tuni zuwa lokacin an kece da kidan kwarya mai dadin amo da dadin sauraro. Wanda sautinsa ke amsa kuwwa cikin kwakwalwata yana zabalbalar min da ita. Ji nake shine amo mafi rashin dadin sauti da na taba ji a rayuwata tunda uwata ta haife ni. Mawakiyar waka take yi cikin lasifika tana kiran sunana tana hadawa da na Fa’izu Abubakar-Hafizin Hajjah, angon Fa’izah sanyin idaniyar Hajiya Hadiza Giwa..... Kin isar, kuma kin cika, baki taba gazawa ba uwar zuri’ar Abubakar Bamalli.... Allah ya ja kwananki ya kara miki lafiya ki ci gaba da kulle tsintsiyar Abubakar Bamalli. Takawarki lafiya uwar maza uwar Muntari, uwar Na’ibi uwa ga Ahmadu, uwar Ibrahim, Sani, Salisu da Sadi. Ki bani mota ki kaini Makkah Hajjah Giwar mata, Giwar mutanen Giwa..... Da gudu na fito daga bandakin ba don komi ba sai don tagarsa tana tsakar gidan dai-dai inda tsohuwar ke zaune tana wakar mai kama da banbadanci tana rawa daga zaune, saboda ba ta iya mikewa saboda kibar da ta yi mata katutu. Sai na ji kamar tana amfani da wakar tata ne da karin (tune) ko kuwa (melody) mai gaya min cikin tsakiyar kaina cewa, abin da Hajjah ta yi dai-dai ta yi, ina so ko bana so kuma ba zan taba yin nasara a kan A.B ba, sune suka riga suka yi a kaina. Wannan tunanin kamar anyi min wata irin allura mai kashe lakar jikin dan Adam ta karar da kuzarinsa, ta raba shi da BURIN sa da duk wani buri da ya ciwa rayuwarsa. Hawaye na malala ta kowacce mabubbuga ta idanuna yana kwarara a kan fuskata na tube kayan jikina dake kamshi na fita hankali ma zan ce ba na tashin hankali ba na canza wasu. Sai da na saurara na tabbatar su Adda Hanne da iyalanta su Zaneera da ‘yan kanzaginsu sun shige gidan Baba Na’ibi dukkaninsu don su kama Ummi, na sulale ta gareji ina jan trolley dina wadda ban cika da kayan da za su wahalar dani ba na bi ta baskwata inda babu ‘yan biki, mazan kuma duk basa nan, na bi ta hanyar da suke bi zuwa masallaci na fice daga gidan. Maigadin yana can yana baiwa tantabaru abinci. Tafiya nake bana ko waiwaye da wata irin sassarfa mai hade da gudu-gudu kamar zan tashi sama, bana ko ganin abin da yake gabana, ban kuma damu ba wai don mota ko babur sun buge ni ba, gara su buge nin in mutun in huta da nufin A.B a kaina. Don dai ba zan iya kashe kaina bane tunda na san abin da zan tarar idan na aikata hakan, babu mai kamasho ciki da za a raba bana mutuwar kafirici tare ni kadai zan dauki dakon abuna. Amma shiga ta duniya ba ni kadai zai yiwa illa ba, zai yi laga-laga ne da zuciyar duk wani da ya kwana ya tashi cikin zuri’ar Abubakar Bamalli, su rasa kwanciyar hankali da nutsuwarsu irin wanda na rasa tunda kowannensu cikin farin ciki yake da yankan kauna da kisan mummuken da suka yi mini, ni kadai ce cikin halin kaka-nikayi. Nema na su rasa alhalin sun san ba mutuwa na yi ba shine kadai kokari na karshe da zan iya, tunda kalmar fatar bakina da duk wani bore na ya gaza, abin dariya ne ma abin a zauna ayi ta dariya. Tunda su dai burin su ya cika, gara in mutu da su tausaya mani, su dubi al’amarina da zuciyar hankali da tunani. Da wannan tunane-tunane da zancen zuci da tafiya a kan hanya da kan titi bayan horn da zagi iri-iri da ga motoci da babura na bude ido na ganni cikin tashar motar garin Giwa. Ni da kaina na tabbatarwa kaina bani da wurin zuwa cikin danginmu kaf din su a karbe ni, in ka dauke gidan Baban Kaduna. Sai dai kuma ai abin da kunya da nauyi, gudun auren dansu nake yi da suka tsuguna suka haifa, kiyayyarsa ke neman kashe ni da raina. Kuma su zamo sune mafakata idan ina da kunya? Bugu da kari wanda ake bata kashin domin sa ba zai wuce can din ba, tunda baya Giwa wanda na rantse da in ga azzalumar fuskarsa na gwammace in yi arba da (arm robbers) cikin talatainin dare zai fiye min alheri da kwanciyar hankali fiye da sake arba da Fa’iz a sabuwar duniya da nake rayuwa bayan ta kuruciya ta shude da shi a ciki da duk wani al’amarinsa da na sani. Duk da na san babu jituwa ko kankanuwa tsakanin Hafizin Hajjah, Fa’izu Abubakar da iyayensa da suka haife shi, Baba Muntari da Maman Kaduna, wani sako na kololu zuciya da kwakwalwata ya tuna mini da cewa DA har gobe sunansa DA a zuciyar iyayensa, ko da kuwa Hitler ne mai daukan rayukan al’umma babu dalili. Da wannan tunanin sai na fada motar garin Zaria, wadda za ta kai ni har ABU in har DA shine DA a zuciyar iyayensa komin muninsa ko munin halinsa da munin ayyukansa, to kar in nemi gidan Baban Kaduna gara in koma ga tawa uwar wadda bana baiwa muhimmanci cikin rayuwata da hujjata ta banza mai cewa, ita ma ba ta bani kulawar da Allah ya ce ta bani. Na tabbata idan duk duniya ta taru ta ki ni ta juya min baya a lokacin da bani da kowa, bani da gata, uwar da ta haife ni ko ba za ta kulani ba, ba za ta kore ni ba. Wadda ta sunkuya ta kawo ni duniya Fa’izun ke kamo sunanta yana zagi a duk lokacin da ya so, a dalilin ta haife ni kuma bare ce ba ta hada jini da iyayensa ba. Bayan wannan ba ta yi masa laifin komai ba. Babban abin da ke damuna a wannan duniyar hujjar Fa’iz ta aure na? Har ya iya bude baki ya furta hakan bai ji kunyar kowa nawa ba? Duk da ba a auren na gani ina so cikin zuri’armu shi ya furta kuma an ba shi saboda fifikon da yake da shi a zuciyar Hajjah! Ko da zan mutu, zan so kafin isowarta (mutuwar) in samu amsar wannan tambayar, mene ne dalilin Fa’iz na aure na? Tunda na amince an halicce shi ne da kiyayyata ya girma ya rayu cikinta, ya bar kasar Nigeria cikin rainonta (kiyayyar), ya kuma yi gammon abarsa ya tafi da ita Rasha, ya kare shekarun da ya yi baya gida cikin soyayya da Ummi..... da kiyayya gare ni. Na ce, kyawun da na yi ne wanda a da bani da shi, da tsabtar da na yi a yanzu wadda yake goranta min bani da ita a baya, yake kyara da hantara da wulakanta ni a kanta, su suka sa ya zo yanzu ya ce zai aure nin. Hajjah ta ce ba su bane, ta kuma kafa hujjar ta da cewa, tunda Fa’iz ya tafi har ya dawo tsayin shekarun nan ko hotona bai taba gani ba, balle ya ga canzawar da ni nake ikirari. To mene ne? Mene ne hujjarsa? Yana nufin alkhairi gare ni? Yana yi min tanadin alkhairi? Yana nufina da alheri da wannan auren ko ko ya yi shi ne don karasa cimma mummunar manufarsa a kaina ta ganin ya raba ni da duk wani farin cikin rayuwata? Na wulakanta na tozarta na tagayyara a rayuwa? Ina ruwan Fa’iz da duniya ta da burinsa kawai ya raba ni da jin dadina dake cikinta? Tunaninnikan da nake ta yi kenan suna ci gaba da soya min zuciya, fuskata jage-jage da hawaye, domin iyaka tsinkaye da dan tunanin da Allah ya hore mini sun kasa bani amsar tambayoyina ko da guda daya daga ciki, har mai tasin da nake ciki ya hau kan titi dodar ya kama hanyar Zaria. Mu karasa a A littafi na 3 Takorin ku ce. [6/3, 4:13 pm] Takori: ZUMUNTAR KENAN?-3 Mai taxin ya gaji da gaya min gamu cikin Zaria, ina zamu dosa? Na zama kamar mutum-mutuma, kurma, makauniya don tunani, saida ya bubbuga kujerar danake zaune nace masa gida mai lamba tamanin cikin gidajen malamai na jami'ar Ahmadu Bello. Gidan da ya zamto mahaifata, dandalin quruciyar rarrafe da tata-ta ta, kafin in gujeshi zuwa inda nake ganin ya fishi farin ciki da walwala, a yau gani na dawo da qafafuna, na kuma gwammace in qarashe sauran rayuwata cikinsa ko da ace yafi kurkuku rashin Dadi da taqaita farin ciki. Wata irin doguwar ajiyar zuciya na saki, na ciro kudin da suka rage min kaf ko qirgawa banyi ba na baiwa mai tasi, ya fitar min da jakata daga bayan motar sa, ya yi min godiya mai yawa ya ja motarsa ya bar harabar wajen. Zan iya kimanta lokacin da qarfe takwas na dare sanda nake tsaye qofar gidanmu, domin ina iya hangen tanqareren agogon falonmu wanda hasken qwan lantarki ya wadata, kuma an dage labulen wawakekiyar tagar falon. Rashin motar Baba ya tabbatar mini bai shigo cikin gida ba, ya shiga cikin (city) kamar yadda ya saba duk bayan sallar isha'i. Don haka naji dan sanyi da qwarin gwiwar cira qafa da tura jakata. Sai dai a take wani irin tsoro da shakka suka lulluve ni, idan Momi ta yarda ta qyaleni in zauna Baban ABU zai qyaleni ne bai gayawa iyaye da 'yan uwansa ba? Kuma wane mataki zai dauka a kaina tunda ga dukkan alamu bai dauki al'amarin nan da sauqi ba? Hakan dai nayi shahadar quda da yin qarfin halin danna qararrawar qofar shiga falon (door-bell), sai da na danna sau uku kafin a buxe. Walida ce, zata yi magana nayi hanzarin kai hannu na rufe bakinta, muryata na rawa na ce. "Ki rufa min asiri Walida, shin Baba na gida?" Ta girgiza kai. "Momi fa?" Ta nuna min (kitchen). Na ce, "To don Allah Walida kar ki gayawa kowa ina cikin gidan nan, zan zauna xakin Abdallah, ai yana makarantar kwana ko?" Ta gyada kai tare da leqawa ciki ta tabbatar momi firar doya take, tayi min alamar in shiga. A hankali ta murda qofar dakin Abdallah na shige wanda ke daga can gefen tafkeken falon, ta mayar ta rufe kenan Momi ta qwala mata kira. "Walidaa!". Ta ruga a guje tana faxin. "Yes Momi". Momi ta ce, "Ke da wane a waje ku ke magana?" Ta dan diririce na rashin sabo da yin qarya, kafin ta ce. "Joseph ne yake neman Cinyere na ce bata zo ba". Ba tare da ta juyo ta dubeta ba ta ce. "Ga abincin ku can kan leda ki ta da Walid ku ci, ya yi bacci ko?" Ta ce, "Kai Momi, ki qyale shi ya fa sha kunun tsamiya mai yawa kafin ya yi baccin". Ta juya don ta kira Kausar ta tarar tayi bacci akan litattafanta itama, ta gayawa Momi kana ta dauki plate din ta bude qofar a hankali ta shigo. Nayi tagumi ne a gefen gadon Abdallah na zubawa kayana ido, da 'yar muryarta mai sanyi ta ce. "Yaya Fa'izah". Tare da zama a kusa dani, ta dora hannunta bisa cinyoyina. "Wai shin me ke faruwa ne? Duk akan auren ki da Ya Fa'iz ne?" Na share hawayen da suka cika mini ido, na ce. "Shin Walida kin mance sanda Fa'iz ke azabtar dani ne? Sharri kala-kala da azabobi iri-iri wanne ne Fa'iz bai min ba, bai kuma gana min ba? Qiyayyar duniya wacce iri ce Fa'iz bai min ba? Amma ki ga don zalinci ya zo ya kalallame Hajja da su Baba suka xaura mana aure...". Wasu azababbun hawaye suka mirgino akan kundukukina. "Don haka ni kam Walida anan zan ci gaba da voyewa har zuwa sanda suka gaji da nemana suka warware auren nan, ko kuma su kai gawata idan baqin ciki ya qarasa ni, da dai in zauna ayi bikin nan jibi...". Na ci gaba da share hawaye ina fyace majinar dake ambaliya daga hanci na. Walida tayi zuru tana kallona. Da alamun tayi nisa a tunani. Ni na san Walida yarinya ce mai kaifin basira duk da kasancewarta mai qarancin shekaru, kwata-kwata bana ji ta cika shekaru goma sha huxu. Wala'Allah abinda take saqawa ya zam mai amfani a gareni. Ta ce, "Yaya Fa'izah, ban zauna a Giwa ba ko kaxan balle in san halin Ya Fa'iz a da can, ko rayuwar da ku ka yi tare, bana ma kuma marmarin zaman, sai dai nakan ji ana labarin a cikin 'yan uwa ko in munje gidan Baban Kaduna ko yaro ne ya takurawa xaya sai kiji manya na faxin, "Kada ku zama Fa'iz da Fa'izah mana, kuyi riqo da ZUMUNTAR ku". Sai dai wallahi a yadda Baba ke son auren nan naku ya kuma dage ya tsaya wajen ganin wanzuwar sa na rantse duk inda ki ke sai ya nemo ki, balle cikin gidansa. Ni kam banga abin ta da hankali da qin Ya Fa'iz ba, da kin xora idonki bisan Pilot Fa'iz Giwa a akwatin talabijin sanda aka nuno shi a tashar CNN, ranar da wani jirgi ya faxi a Mozambique da kinyi alfahari da kasancewar shi miji a gare ki. Wanda ba isarki ko cancantar ki ce ta baki shi ba, face darajar Zumuncin da kasancewar ku JINI XAYA. Miji ne na liqawa a goshi, kuma abin tinqahon kowacce xiya macen da ta san ciwon kanta. Da kinyi nadamar wannan azabtar da kankin da tada haqarqarin da kike yi kan wai ba kya son sa. Ko kin san Ya Fa'iz na yanzu bai yi kama da Fa'izun gidan Baban Kaduna ba na da can da kika sani a baya? Wallahi in banda Fa'iz ke son ki, da na ce yafi qarfinki a halin yanzu kam! Umm!! Ni dai ina baki shawarar ki haqura ki fauwalawa Allah al'amarinsa da yinsa, kada ki zamo mai shisshigi cikin iyakar Ubangiji, wato yarda da qaddara mai daxi ko mara daxi. Wallahi Yaya Fa'izah ni shaqiqiyar ki ce, don haka ba fata nake miki ba, muddin yaya Fa'iz ya barki ba za ki samu ko da wanda ya kama qafarsa ba...". "Ni kam na shiga uku!!!". Abinda na faxi kenan a fili kamar in xora hannuwa aka in fasa kururuwa. Me yasa kowa ba ya ganin hujjata da qima, girma da muhimmanci? Me yasa kowa ke son Fa'iz? Me yasa kowa ya buxe baki yabon Fa'iz yake yi? Sun manta cewa maqiyinka baya tava dawowa ya zama masoyinka? Wanda ya ce bai son ka jiya, gobe ya ce yana sonka to tabbata wani abin ya hango. Na dubi Walida cikin matsanancin vacin rai a ido da zuciyata, na ce. "Yau na amince kina daga cikin maqiyana Walida! Kin nuna min ba ki qaunata Fa'iz kike so kamar sauran dangi, kema kina cikin sahun su Ummi, Hajja da Zaneera... Yaya Aliyu kaxai ke sona har gobe cikin A.B, kin kuma nuna min kema......". "...Walidaaa!". Momi ke qwala kira. Walida ta miqe a razane, a kixime muryarta na rawa ta ce. "Wallahi-wallahi daga yau ina bayanki Yaya Fa'iza... tunda har baki son Yaya Fa'iz har haka, nima daga yau na tsane shi... na tsane shi!!!". Wani irin murmushin qaunar 'yar uwata ya suvuce a fuskata irin wanda ke fitowa tun daga qarqashin zuciya, itama murmushin tayi mini. "Daure ki ci abinci Ya Fa'iza, zan ke kawo miki abinci ko yaushe. Don Allah ki daina kuka. In kinga ban shigo ba to ina makaranta ne boko ko Islamiyya. (Toilet) xin Abdallah a buxe yake, kuma famfo yana zuwa". Ta fice da sauri ta ja qofar ta tadda Momi, ina jiyo Momi na faxin. "Me kike a xakin Abdallah tun xazu ina ta kira?" Ta ce, "Momi littafina da ya ara nake nema "An African Night Entertaiment" nake jin ma ya tafi da shi". Shigowar Baba ya katse su. Na xauki kwanon abincin da Walida ta kawo mini nayi loma guda na sakwara da miyar Ugu. Tamkar nayi loma da curarren maxaci duk da zaqin nama da na mai tauraro da miyar tayi cau. Yadda zuciyata take baqiqqirin haka bakina yake xaci xau. Na runtse ido na a hankali na kishingixa bisa gadon Abdallah tare da jan bargo har kaina, sakamakon wani irin sanyi da naji yana ratsa qasusuwana, yana son shiga har cikin bargo na alamar shigar zazzavi. Zuciyata na wani irin tuquqi, maqaqi da azalzalar baqin-cikin da ba zan iya kwatantawa ba. ***** A GIWA Acan Gida babu wanda ya farga da rashina a gidan har garin Allah Ya waye, duk jama'ar gidan baqi da 'yan gidan kowa harkar gabansa yake yi, ana ta shirye-shirye. Musamman kasancewar ranar ta Alhamis a matsayin ranar buxar kai. Aliyu ne ya shigo falon Hajjah tare da xan uwanshi kuma babban abokinshi, wato Muftahun Yaya Rabi da ya zo a lokacin don su gaisa da Hajja, isowar shi Giwa kenan. A babban falon dake shaqe da A.B family maza da mata, Muftahu ya zo ne da labarin rasuwar Dr. Nazir Sani Galadanci, manemin auren Fa'izah. In banda Salati babu abinda Yaya Aliyu keyi yana mai qara jinjina wannan mummunan labarin, tare da qara tsinkewa da al'amarin Ubangiji. Muftahu ya nemi ganina don yi min bayani, Ummi dake kokawa mutuwar Naziru haiqan har kamar ta shixe ta yarfe hawaye da majina, ta ce. "A wannan halin da Fa'iza ke ciki ne zaka ba ta labarin rasuwar Dr. Nazir Yaya Muftahu? Ka rufawa kanka asiri, idan Fa'izah bata ce kai ka kashe mata Nazir ba, la-shakka zata ce haxa baki ku kayi aka kashe Naziru don ta yarda da auren Ya Fa'iz". Muftahu ya ce, " amman dole ne ta ji?" Ummi ta ce, "Ji kam ya zama dole ko ba jima ko ba daxe, amma ba yanzu ba, kuma ba daga bakin kowa ba sai na wanda zai iya ma haukar Fa'izah tamkar Yaya Aliyu ko Ya Rabi, amma ba kai ba". Da sauri Aliyu Na'ibi ya ce, "Wallahi babu ruwana, ba a bakina ba nima, indai har ka dage sai ka faxan Muftahu ga hanya, tana uwar xakinsu tana neman kashe kanta don bala'i da qin auren Fa'iz ko falo ba ta fitowa". Muftahu ya ce, "Bari inje, inji dai ba zata bugeni ko ta zage ni ba?" Suka ce a tare, "Uhm!". Hajja ta ce, "Muftahu ka qyale Fa'izah don Allah, shin Fa'izar da ta rufe ido ta zageni tas kan Naziru kai waye da bazata zage ka ba, zaka je mata da labarin mutuwar Nazirun?" Muftahu bai tsaya ba a yayin da ya danna kanshi a xakin bakinsa xauke da qatuwar sallama. Ya yi dube-dubenshi ya fito, ya ce. "Au, ai ma bata nan". Ummi ta ce, "Ko dai ta shiga bayan gida?" Ya ce, "Ga bayan gidan nan a hangame, ai babu kowa a ciki". Ta ce, "Duba sosai dai can qarshen gado ko ta naxe cikin bargo". Muftahu ya yi dube-dubensa har da duba qasan gado ya kuma haxa da kira. "'Yar Zaria a Kano!!!". Shiru ta ziyarce su, sai ma amsa kuwwar muryarsa da ta dawo cikin kunnensa. Ya ce, "To wataqila dai idona ne, Aliyu zo ka duba". Baki xayansu suka miqe suka shiga xakin inda Fa'izah ta ce xaukar ni inda ku ka ajeni. Zaneera sai da ta qara shiga (toilet) ta duba bayan qyaure da cikin baho, ta ce. "Kai! Tikisa!! Da qyar fa idan Fa'izah na cikin xakin nan". Leqa nan leqa can cikin A. B Estate baki xaya babu Fa'izah. Hajja ta tuna kalaman Fa'izah. "Daga yau ba za ki sake ganina cikin gidanki ba balle ki yi iko da ni...". Hajja ta fashe da kuka tana faxin. "Ni Dijah na shiga uku, wace irin zuciya ke da yarinyar nan wadda babu ahuwa da rangwame a cikinta? Tabbas Fa'izah ta gudu ne, ba ta gidan nan, ba ta garin nan". Zaneerah ta ce, "Ina! Babu inda Fa'izah za ta iya zuwa da ya wuce Kaduna, Kano ko Zaria. Bayan waxannan wurare na tabbata Fa'izah ba zata yawon banza ba, kuma ba zata kai kanta mahalaka ba duk rintsi duk kuwa abinda ke damunta". Aliyu ya zaro waya daga aljihunshi, haka Muftahu. Muftahu Aunty Rabi ya kira, ya ce. "Maman Abdul 'yarki wurin ki ta iso ko?" Ta ce, "Wacce 'yar tawa Mufty? Kasan 'ya'yan nawa yawa ne da su". "'Yar rigima mana matar Fa'izu!". Da fari Rabi kam dafe qirji tayi kafin ta ce. "Ni Rabi'atu, rabona da Fa'izah tun ranar da suka haura qafa suka bar Kano, amma gani nan tafe. Nima shirin kayana nake yi yanzu haka". A sanyaye Muftahu ya zura wayarsa a aljihun gaban rigarshi, ya ce. "Fa'iza ba ta Kano fa". Zanira ta fashe da kuka, "Ni kam wannan aure dole ne? Me ya yi zafi ne haka da ba za a haqura ba? Wallahi ni nasan Fa'izah da kafiya da taurin zuciya, tunda ta ce bata auren nan wallahi bata yi xin ne, babu wanda ya isa ya tanqwasa ta". Cikin alhini Aliyu ya ce, "Haka Fa'iz Giwa, tunda ya ce bai sakin auren Fa'izah yanzu ya saka xamba a aurenta, na tabbata ko duniya zata taru akansa ba zai saketa ba, sai dai mutuwa ta raba su A wannan gava ni na saduda Hajjah, dabarata da tunanina sun qare wajen tanqwasa Fa'izah tunda har anzo gejin da Fa'izah ta soma zartarwa rayuwarta hukunci ba tare da shawara dani ba, ya tabbata cewa nima ta sanya ni a rukunin sikelin da ta xora kowa. Sai ki yanke hukunci na qarshe, in har bata Kaduna ko Zaria". Yana faxi yana kiran Maman Kaduna. Ita xin ce ta xaga suka gaisa cikin matsananciyar girmamawa ta 'ya'yan A.B ga iyayensu maza da mata, Aliyu nauyin Mama ya dabaibaye shi, shin yaya zai yi ya tambayeta yarinyar da ta bar gida domin qiyayyar xanta? Jikinshi na bashi yaqinin ba yadda za ayi Fa'izah taje Kaduna, shin giyar wake ta sha ma? Ya yi ta maza jin shiru ta ratsa a tsakaninsu, ya ce. "Shin Mama ina Pilot ne?" Ta ce, "Yana vangarensa yana shirya kayansa, wai shirye-shiryen tafiya yake yi jibi can Russia, anyi masa kiran gaggawa kan wani muhimmin aiki. Yaya Fa'izar? Ince ko ta ware?" Gaban Aliyu ya bada damm! cikinsa ya ba da sauti, ya ce. "Don Allah Mama yi min magana da shi yanzun nan ko Yaya Bashir". Mama ta ce, "Na ce lafiya dai? Bashir yana kan hanyar tahowa na san ma ya kusa isowa yanzun, ka gaya mini mene ne? Me ya faru Aliyu?" Tausayin Mama ya kama Aliyu, daga jin muryarta kasan ta daxe bata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk akan Fa’iza. Aliyu ya rasa yadda zai yi don ta wuce ya yi mata qarya, ya ce. "Wallahi Mama Fa'izah ce bata kwana gidan ba, gamu nan a Giwa kowa hankalinsa a tashe". Mama tayi murmushi mai fitar da sauti, ta ce. "Ina da kyakkyawan zato da shaida akan xiyata, ba zata iya wuce Zaria zuwa Kano ba duk nisan da zata yi". Ya ce, "Wallahi bata Kano, yanzu Ya Rabi ke faxa". Mama ta ce, "Ka jarraba Zaria mana. Yanzu kam bai kamata mu faxawa Fa'izu ba tunda Zariyan yake shirin zuwa gaida Maimuna wataqila ya tadda ta can". Aliyu ya sake neman gidan baban ABU, momi ce ta xauka suka gaisa tana tambayar Little F. Aliyu kam duk gaisuwar ta gundire shi, ya ce. "Shin momin Walida, please Fa'izah Zaria ta kwana?" Da farko Momi Maimunatu shiru tayi sakamakon mugun faxuwar gaban da ya dirar mata. Ta samu ta haxa sauti wanda zai ba da ma'ana, ta ce. "Ko da zancen nan bai shafeni ba Aliyu da Fa'izah ta zo gidan nan da tuni na sanar daku ko don gudun tashin hankalin ku. Rabona da ganinta tun zuwansu daga Kano da suka zo suka kwana biyu nan ita da Ummi". Aliyu ya ce, "Ya Salam!!". Tare da tura wayarsa a aljihun baqin wandon (jeans) mai matuqar qwari dake jikinsa. Ummi ke tambayar, "Bata je ba ko?" Sai kuka, kazalika sauran 'yan uwa da 'yan buxar kai da suka ci kwalliya kyawu na bugun kyawu, duk hawaye ya vata kyakkyawar fuskar Bamallin su. Muftahu kam girgiza kai yake. Ali Na'ibi, ya jingina da bango, yayin da maganganun da suka yi da Fa'iza ke nausar kunnensa tamkar a lokacin ne take yi. "...ko yankani za kuyi A.B bani auren nan... na gwammace in bi YAWON DANDI... da dai in qarashe rayuwata a matsayin matar FA'EEZ BAMALLI!!!". Aliyu ya kama kai, ya ce, "Kash! Kinyi kuskure babba Fa'izah, ko masu yawon dandin basu da aure akansu, kada kiyi kuskuren da ba zaki iya gyarawa ba mana...". Ya fisgi hannun Miftahu suka yi waje inda ya xauki motarshi aguje suka bar garin Giwa. Allah Sarki Aliyu xan uwa na gaskiya, gidan karuwai ya riqa bi kala-kala da Miftahu wai yana neman Fa'izah, yana mai suffanta musu ita tare da nuna hoton ta. Amma babu wanda ya ce ya ga gilmawar ko mai kama da Fa'izah, amma babu alamar gazawa a tare da shi. Miftahu kam ko fitowa daga mota bai yi ba, tausayin Aliyu kaxai ya ishe shi. Haka ya zage gidajen karuwan garin Kaduna da Zaria kaf yana cigiyar Fa'izah har duhun dare ya shigo, ya ba da cigiya a ofishin 'yan sanda da kafafen yaxa labarai masu yawa. Ya ja birki dai-dai titin Sir Kashim, ya xaga waya ya kira Fa'iz Giwa, a fusace Aliyu ya ce. "Ka ji daxi ko xan gata! To tunda baka fasa auren nan ta ruwan sanyi ba, zaka fasa in an kawo maka gawarta. A yanzu Fa'izah kwata-kwata bata a Kano, Giwa, Zaria ko Kaduna, sai ka san inda zaka nemo ta". Bai bashi damar yin magana ba ya kashe wayarsa, shi kuma bai kira shi ba. **** [6/3, 4:13 pm] Takori: Fa'eez da ya tafi dauko Yaya Bashir a Airport a washegari wanda ya sauka ta Kano, qarfe hudu na yamma suna kan hanyar Kaduna daga Kanon. Bashir ya yi kwance a bayan (Henessy) yana kwarara hamma, yayin da Fa'ez ke ta tuqi kamar Allah Ya aiko shi ba mai magana da dan uwansa cikinsu. Tun can Fa'iz da yayanshi Bashir ba sa ga maciji. Bashir ya fiddo taba ya cinna mata (lighter) wadda aka yi da qarfen azurfa ya soma fesar da hayaqi. Sanye yake cikin (Italian suit) baqaqe, da gani kaga baqon Russia cikakken Injiniya a vangaren wutar lantarki Eng. Bashir Mukhtar Abubakar. Fa'iz ya yi maza ya toshe hanci da hannunshi, yayin da ya rage gudun motar ya sauka bakin kwalta ya kashe motar gaba xaya, ya fito ya mai da qofar ya rufe ya zauna a saman bannet xin motar. Tunanin halin da ya baro Fa'izah a asibiti jiya yake yi, wata zuciyar na ce da shi kawai in ta farfaxo ya haqura ya saketa. To amma abin tambayar anan shi ne, idan ya biye ta zuciyar ya saketa yaya zai yi da soyayyar da ta zamo masa qaqa-nikayi? Shekaru dai-dai har goma sha... yaya zai yi ya dinke zumuncin iyalin Abubakar Giwa da ya yiwa givi saboda wauta da quruciya? Yaya zai yi ya xinke varakar da ya wanzar a A.B House? idan ya saketa tayi nasara kenan akansa wannan karon? (She's always a loser on him and so she will remain till eternity.... Wata rana na zuwa insha Alla da Fa'iza zata san babu mai sonta duk duniya kamar shi da ta riqa maqiyin da babu ya shi a duniya. Shi kam ya tabbata alhakin mahaifiyarta ne da nata Allah Yake hukunta shi da shi ta hanyar xora mashi azabar SOYAYYAH... soyayyar kuma ba ta kowa ba ta Fa'iza Ahmad Abubakar Giwa. Wata yarinya da ya addaba, ya kyara, ya hantara babu gaira babu dalili sai a dalilin KABILA NCI, wauta da quruciya. "To in ka qi sakinta ta mutu fa a dalilin qiyayyar ka?" Wannan kam bai san makomar shi ba a wurin Ubangiji. Bai tava faxawa a soyayya ba, bai tava son mace ba a kafatanin rayuwarsa, mata kala-kala kuma iri-iri ya gani a rayuwarsa musamman abokan aiki da ke qarqashinsa da ake kira 'yan matan jirgi (Caterers) na qasashe daban-daban, musamman yankin Asia inda yafi yiwa jigila da suke binshi da tayin soyayya ta banza ko ta aure, amma tunanin kucakar qanwar nan da ya baro a qauyen Giwa, ya dishe hasken duk wata diya mace daga qwayar idanunsa. Har zuwa tahowarsa yanzun, bai manta da Alicia ba, wata (caterer) dake aikinsa shi kaxai ransa, da zai iya cewa ya tava kulawa da soyayya a dalilin abotarshi da Yayanta pilot Johari, mutanen Berlin ne. Da qyar ya samu ya taho gida shi kadai a dalilin kafewa da tayi sai ta biyo shi Nigeria sunyi aure a garin nasu Giwa, iyayenshi su Musuluntar da ita. Alaqar shi da Johari, ta faro ne tun daga karatu a (Ukranian Institute of Aviation) wanda shi yazo karantar tuqin jirgi Rasha daga Berlin ne, shi ne kuma ya samar mishi aikin da yake yi yanzun da kamfanin tashin jirage na mahaifarsa (Berlin Airlines) aka xauke su take, abinda ya hana shi dawowa gida kenan bayan kammala karatunsa. Don haka zai iya cewa idon Johari ne yasa yake kasa (ignoring) Alicia har kowa dake tare da su ya xauka soyayya yake yi da ita. Shi kuma yana biye mata ne don Johari yafi qarfin komai a wajensa in yana da iko. To sai dai mutum bashi da iko da ZUCIYA, barta akan abinda take so, komin munin shi da wahalar samunshi. Abubuwa da yawa sun faru wadanda zai ce su ne silar soyayyar da yake yiwa Fa'iza ko ba sune ba. Muhimmi a cikinsu shi ne, bayan SO na haqiqa akwai son ya gyara wannan qasaitaccen zumuncin na A.B family da yasa almakashi mai kaifi ya farka ya zama wound wato (gyambo) a zuciyar FA'IZAH AHMAD ABUBAKAR, yana so ya warkar da wannan gyambon ne da SOYAYYAH. Ko da zai rabu da Fa'izah zai rabu da ita ne (only) in ya yi nasarar warkar da wannan gyambon da shi ne silar samuwarsa a zuciyarta, wadda itama bata da ikon sarrafata, domin SO da QIYAYYA duka halittar Allah ne da basu tava zama wuri guda. Wani sashe na zuciyar Fa'iz Giwa ya ce. "Shin me Fa'iza take taqama da shi ne haka da yasa ta ci galaba mai yawa haka a kansa, in ba don sharrin SO ba? In ba don son ta ba da ya sameshi rana xaya baiga abinda ma zai sa shi yin aure a halin yanzu ba, bai shirya masa ba (at all) yana cin kuruciyarsa ne. In ba don so da ba ya shawara ba, bai ga dalilin da zai sa ya baro aikinshi wanda kullum ranar Allah samu ne mai xumbin yawa a gareshi, ya zauna yana ganin baqin ciki ba. Ko ma me zata yi tayi ta gama, however, yana son matarsa, saki a tsakaninsu yana ganin wataqila shi ne abu na qarshe da ba zai tava yi ba a rayuwarsa, sai in mai yanke hanzari ce ta cika umarnin Ubangijinta (mutuwa). Mutuwar tashi ma, zai so ace daga hannun Fa'iza ce ba don Allah baya yafe haqqin rai ba, a ganinsa in tayi hakan wataqila gyambon zuciyarta zaya warke. Tunani na qarshe da ya ziyarce shi, shi ne ta gama suman, qafarshi qafarta, kwas xin nan da zai tafi Amsterdam sati uku masu zuwa, tayi ta suman tana farfaxowa yana da ruwan da zai yi ta yayyafa mata, indai ba mutuwa zata yi ba Falillahil-hamdu. Bai kai qarshen tunaninsa ba Bashir ya bude murfin motar da qarfi, ji kake butt! Ya fito yana fadin. "Kai, don ubanka ance ma ni bawan gidanku ne da za ka tsaida ni a gefen titi zafin rana na duka na?" Fa'iz ya yi tsaki ya ce, "Kada ka sake zagar min uba Yaya Bash! Ta yaya zaka kunna min hayaqi cikin mota in zauna ina shaqa, na tayaka sha kenan? Iyaye kuma tunda ba ka ganin darajar su ni ina son kayana, kada ka sake ka sake zaginsu a gabana, na rantse ba zai yi maka dadi ba". Bashir ya dubi Fa'iz sosai yana cikin wani irin yanayi na tashin hankali da bai tava ganinsa ciki ba, har wata rama ya yi, kafin ya baro Russia ba haka ya sanshi ba sam. Jikin Bashir ya yi sanyi, ya koma mota ya zauna ba tare da ya yi magana ba sai da Fa'iz ya mula, ya kammala shan qamshinsa da harare-hararensa kana ya ja motar aguje tare da sakin qira'ar Abdurrahman-Sudaith a rediyon motar cikin Suratul Nisa'i. Wannan ya taimaka wajen sanyaya zuciyarshi dake tafarfasa babu gaira babu dalili. Bashir dai binsa yake da ido, da zuciya, ya kasa shiru, bayan sun jima suna tafiya yana kallon Fa'izun wanda idanunshi suka kaxa suka yi jawur. "Wai kai me ke damunka ne?" Fa'iz ya harare shi ta cikin madubi, "Ai ni babu abinda ke damuna face tawa matar da ta tsane ni tamkar mutuwarta, duk da bani da wani hali abin qi, baya ga shirmen quruciya na can baya, wanda da ace zata saurare ni ta saurari kalaman dake qunshe cikin baki da zuciyata da ta fahimce ni, kai kuwa ke da damuwa. Baya ga baqin munanan xabi'un da kayo guzuri, shan giya, taba da bin matan bariki tamkar tsohon bunsuru, kai da wai an kaika ne domin ka zama ubana, mai dorani bisa hanya sahihiya, ka rikide ka zamo tantiri, wacce irin qiyayya ce ba zaka gani daga taka matar kamila Hadizatu ba?" Bashir ya tashi zaune daga kishingidar da ya yi a kujerar baya tare da wurgi da abinda ke hannunsa ta taga gaba daya, ya antayo ashariya cikin harshen (Ukrain) wadda Fa'izun a duk zamansa a Russia shekaru goma vai tava jin wani ya yi ba, haka ya lailayota da turanci wadda Fa'izun bai san akwai ba ma, sannan ya shimfidota da Hausa ji kake. "Abu kazan uban nan! Uban waye ya xaura min auren? Sharrin da zaka je kayi min a gida kenan Fa’iz? Wato dama ido ka sa min a duk motsina ko me? Duk tambadar da kake yi da Alicia na tava daga ido na dube ka da zaka ce ina neman mata? Ai dama gwano baya jin warin jikinsa...". Fa'iz ya yi saurin miqa hannu ya kashe qira'ar da ya kunna na karatun Alqur'anin dake tashi, ya juyo ga Bashir bayan ya kashe motar baki dayanta. Ya yi rantsuwa da Allah ya sake rantsewa ya ce. "Wallahi-wallahi ka sake zagar min iyaye sai na sauke ka a dajin nan yaya Basheer!". Basheer ya dubi qwayar idon Fa'iz sosai har wani blue-blue take, jijiyoyin kansa sun tashi rada-rada saboda fushi da mazantaka, ya ce a ransa. "Anya Fa'iz qanina ne?" Fa'iz qato ne qwarai murzajje mai wasu irin qarfafan damatsa da ginannen jiki na Bamallin usli tamkar (Late) Abubakar Giwa a sanda yake nashi tashen quruciyar, yana nome manyan gonakinsa da hannunsa ba tare da ya nemi mai tayashi ba. Irin mazan da jarumtakar su ce kadai tasa duka rabin rayuwar su cikin iska suke yinta, ruwa, hazo, zafin rana, sanyi ko duhun dare baya hana su lulawa cikin sararin samaniyar Subhana. Wanda duk ya yi qoqarin dambe da su, mace ko namiji labudda uwarshi ta haifi wani kawai amma ba shi ba. Savanin shi Basheer da (gulder), hayaqi da zina da ya jefa kanshi a Russia rana daya suka haxu suka tsotse masa jiki da kuzarinsa. Sai dan banzan bakin tsiya da kaudi wanda ba a kashe shi a magana. Inda suka bambanta da Fa'iz kenan, wanda kafin ya yi qwaqqwarar magana ma aiki ne jawur, sai lokacin da ya sa kansa. Bashir ya ja bakin (glass) ya mannawa idanunsa, ya koma yadda yake da, wato kishingida, yana ta huci shi kadai kamar kumurci, bai qara magana ba. Fa'iz ya ja motar a guje, bai tsaya ba sai a qofar gidansu dake unguwar Jabi Road cikin garin Kaduna. **** A uwar dakin Mama take lallashin Bashir yana kunkuni cewa yake. "Aure? Aure?? Wane irin aure yanzun nan haka sabida Allah, mutum yana tsaka da cin kuruciyar sa, ko an gayawa Hajjah zamanin da irin na yanzu ne? Kuma a rasa wanda za a aurawa wannan lukutar yarinyar mai shegen qarfin tsiya sai ni? Salon in na mata ba dai dai ba ta hau ruwan cikina yadda take danne su Zanirah? To ni yanzu ma daga gama karatu ban kama aiki ba anzo an dora min aure, ku ne za ku dinga yi min dawainiyar auren? Sannan ni wallahi ba zama nazo yi ba, na zo ne kawai in ganku in koma. Dama ace 'yar siririyar ku ka aura mini 'yar wajen Baban ABU sai in karva da godiya, me ma take ne da suna Fa'eez?" Fa'eez dake gefe ya juya musu baya yana kallon tangamemen hoton Fa'izah da Zaneerah, sun sha goggoro ranar bikin Zanirah da Mama ta kafa a falon, ya wani irin juyo cikin (slow-motion) ya qwalalowa Bashir kyawawan idanunshi, ya ce. "Yaya Bash! Ahir! 'yan iskan idanunka bisan matata! Na gaya maka, na qara (warning) dinka, o.k?" Mama ta dafe kai, "Fa'iz, yaushe ka koyi rashin kunya ne for Allah's sake waye baya kuskure a bisa rashin sani? Ka bari Bashir ya dora idonshi bisan ummi kamin ya yi wadannan sambatun banzan mana. Bashir, kana magana ne akan wasu kwailayen yara mitsi-mitsi daka tafi ka bari shekaru takwas a baya da suka wuce. To wadannan...". A yayin da ta miqe ga daya 'enlargement' din dake can hanyar kofar fita na Zanirah da Ummi, shima ranar bikin Zanirah ne sun sha ankon beig swiss laces mai ratsin silver da goggoro kalar adon leshin, wato (silver), wanda in ba ka daga idonka sama ba baza ka hango shi ba saboda anyi (placing) dinsa da nisa, ta taka kujerar cin abinci, ta dauko ta sauko fuskarta cike da annuri ta dora ma Yaya Bash akan cinyarsa. "Ga Ummin Hajjah". Bashir ya kurawa Ummi ido na 'yan dakiku yayin da kalmomin da suka shiga fita daga bakinshi bai san dasu ba... "How does this girl turn to slim?" Duk da tension din da Fa'iz yake ciki wanda Bashir din ya hada masa sai da dariya ta kama shi, ya yi murmushi cikin takaici ya tashi ya bar dakin yayin da Mama ke kyalkyala dariyar jin dadi tana kallon idanuwan Bashir da ke neman zazzagowa akan hoton. A ranta ta ce. "In banda anfi karfin Ummi me zata yi da Bashir don Allah? Ita kam tana fatan Ummi ta zam silar kimtsuwar xanta daga halin da ya tsunduma kanshi babu gaira babu sabar, don duk komi yana dawowa kunnenta, duk da Fa'iz ba duka yake gaya mata ba sai dai ya ce tayi masa addu'a, ya canza hali rana daya. Ta daga hannu sama ta godewa Allah Al-khaliku sarkin qaga halitta da ya suranta Ummi kirar da ta fi karfin namiji ya wulakantata. Ta sani da yawa kamilallun mata 'ya'yan gidan tarbiyya suke shirya mazajensu masu mugayen dabi'u irin na Bashir, don haka ta kara godewa Hajjah tare da binta da kyakkyawar addu'a a zuciyarta na Allah Ya ja kwananta cikin zuri'arta har kansu (junior) ko ana so ko ba a so. Allah Sarki Maman Kaduna, a wannan ranar bata yi bacci ba, kwana tayi akan kafafunta tana kai sunan Fa'iza ga mai duka, kan ya karkato da hankalinta taso Fa'izu. Mama hawaye take da idanunta, a yayin da take rokon mai cusa soyayya da ya cusa soyayyar Fa'iz a zuciyar Fa'izah. Soyayyar da babu kamarta a duniya wadda ta fi gaban wadda take yiwa Nazir Galadanchi. Babu abinda ke damun Mama irin ganin yadda Fa'iz ke neman ya susuce kamar baya ji sosai, sai kayi magana sau uku kafin yasan da kai a gabansa, tunani yake ko da yaushe. Tun dawowar shi bai iya ya tsaya ya ci wani ginannen abinci ba kullum sai tea, lemo, snacks. Jiya kam da ta shiga boys qutarers nemansa yana wanka ta tadda hotunan Fa'iza sunfi kala goma anyi enlarging dinsu an kafa a kowanne kusurwa na daki da falonsa, musamman cikin bedroom, tayi tunanin ina ya samo hotunan? Da ta tambayi Yahya ya ce shi ya aika ya karba mishi wurin Walida. Mama kam ta tabbatar hakkin Fa'izah ne ya kama Fa'iz. Babu mamaki in ya tuka jirgi a wannan lokacin ya saito shi cikina garin Giwa wanda hakan babu makawa zai murkushe musu dan garin na iyaye da kakanninsu da bai taka kara ya ba balle ya karye. Mama ta tabbatar nutsuwar Fa'iz kawai samun zuciyar Fa'izah, ko da bai furta ba bai kuma nuna (weakness) dinsa ba, har gobe Fa'iz Abubakar, namiji ne mai amsa sunan namiji ko a cikin daruruwan maza baka fiya gane (weakness) dinsa ba, balle akan mace. Ita din ma don ta sa mai ido ne, amma da fatar bakinsa bai furta mata ba. Wanda hakan kuma (samun zuciyar Fa'iza) ba shakka ba karamin aiki bane ga duk wanda yasan Fa'izah da Fa'izun wurin kafiya da taurin kai. Wadannan sune halayen da Hajja ke hange har take ganin hada masu irin halayyar gamayyar aure shi ne dai-dai. A yau kam Mama ta qalubalanci tunanin Hajjah akan-kanta. Hada masu halayya daya aure cikin A.B ba dabara bace so-karvau. Zanira da Aliyu kam hadi ne na Allah, laushi na dukan taushi. Amma masu taurin zuciya da kafiya ba dai-dai bane hadasu aure, in daya ya taso daya ba zai sauka ba, haka in daya ya hau daya ba zai yarda ya fado kasa ba yayi lallami ya kaskantar da kai ba ga dan uwansa. Yadda Fa'izah ke ganin ta watsar da kanta inta kwantar da murya ta roki Fa'iz SAKI, haka Fa'eez Giwa ke ganin zub da kima ne da aji, muddin ya kwantar da kai ya baima Fa'izah haqurin abinda ya yi mata a baya. Duk da abin ya zo ya zame masa jidali, ya hana shi ci, sha da sukuni da jin dadin komai dake cikin rayuwar duniyar baki daya. Ya hana shi barci da walwala balle komawa bakin aikin shi. Don haka Mama ke addu'ar Allah Ya sauke na Fa'izah, domin muddin Fa'izah ta sauke dole ne shima Pilot din ya sauka. To a washegari ne kuma Aliyu ya kada mata 'ya'yan hanji da albishirin gudun Fa'izah. Bata iya ta fadiwa Fa'iz ba sai dai shi a lokacin ya damu da ya ga Fa'izah ko da gani da ido ne a kalla zai samu sauki daga azabtuwar da zuciyarshi ke yi a dalilin rashin ganin nata, inyaso ko ganinta ya yi kawai daga nesa ya haura takalmansa ya bar mata garin da kasar baki daya, in ta rage bala'in ta bishi Amsterdam su zauna. Indai sun kasance gida daya ai maganar kafiya da kiyayya sai ayi ta yin mai dalili, ba yanzu da ko harararta baya hange ba. Ya kurawa jerin jakunkunan da ya danqara dalolin shi ya sayo da sunan lefe ido. Shin wacce Fa'izah yake tunanin za ta daura zaninshi? Ko da yake a lokacin yana kan aiki a Istanbul ne, giyar son ta buge shi, ya shiga hada su a kasuwar (AKMERKEZ Shopping Mall) ba tare da ya yi shawara da kowa ba ko yasan 'size' da take amfani da shi a yanzu. Ya dubi shekaru ne kawai ya kintata, kuma da ya ganta bata zarce yadda ya kintatan ba. Ya bude yana duba su a hankali har da (underclothes). Fadin abinda ya kashe akai bata baki ne, amma ta wace hanya zai bata ta karba tunda a zuri'ar su ba'a lefe? Shi ne abinda ke damunsa. Ya mayar ya zuge ya koma ya jingina da filo ya lumshe idonsa, abin duniya ya bi ya dame shi, ya rasa ta hanyar da zai bullowa matsalar aurensa. Hausawa kan ce, "Tun ran gini ran zane". Haka "Juma'ar da za tayi kyau tun daga Laraba ake ganeta". Sannan "Kowa ya sayi rariya yasan zata zub da ruwa". Kuma "Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka". (So he has to bear the outcome of his wrong doings...) Ya nisa "Ba abinda lokaci ba ya magani". Wani sashi na zuciyarsa ya yi (whisphering) wato rada. Dai-dai lokacin da wayarsa dake kan bed-side take ta tsuwwa. A fusace ya dauka domin bai son wani abu ya katse tunanin nan da yake yi, tunanin kaxai sassauci yake saukar mishi tunda ba zai iya gayawa kowa halin da yake ciki ko abinda ke damunshi ba, sai dai su tattauna shi da zuciyarsa su baiwa juna shawara, su kuma lallashi juna tunda babu mafita sai jajircewa, ya rike igiyoyin aurensa gam-gam har zuwa lokacin da Allah zai tausasa zuciyarta wadda babu wanda ya san yaushe ne? Sai Zuljalali wal ikrami. "Na'am!". Abinda ya ce kenan ba tare da ya duba fuskar wayar ya ga wane ne mai kiran ba. "Ka ajiye duk abinda kake yi haka ka taho gobe. Yanzu na samu sakon ana kiranmu (interview) jibi da British Airlines. Ka sani wannan dama ce ba ta wasa ba, don Allah Abubakar ajiye komai ka taho don Allah. Night flight na gobe zamu bi zuwa Great Britain". Abokinsa ne Ba'indiye Maajid Abduljalal ke magana kamar zai fashe da kuka. "Amma Maajid za ka cuce ni, ka san abubuwan da suke gabana kuwa?" "Zan cuce ka ko zan taimake ka? (This is a life-time opportunity) Abubakar, ina shawartarka (don't miss it...) koma mene ne ke a gaban naka ajiye shi, ba Fa'izah bace? Don Allah kada ka ba da maza (achievements are greater than women). Ka yarda dani, ka karfafa zuciyarka muyi wannan fafutukar tukunna, sai ka dawo ka ci gaba. Na yi maka alkawarin (I'll stand by you) inga cewa kun dai daita da matarka idan mun dawo (and I promised to help you to the end of the battle my friend, be a man) Fa'iz, ina jiranka. Akwai (morning flight tomorrow) daga Abuja, nima shi zan bi daga Berlin zamu hadu a Airport din Wales, ina jiranka". Ya kashe wayar ba tare da ya bashi damar ya yi korafi ko musu ba. Ya ajiye wayar cikin matuwar jiki, sai kuma ya daga ya kira British Airlines ya yi 'booking' duk da jikinsa a mace yake. Wani sashe na zuciyarsa ya yarda da Majid babu tantama zai halacci wannan (interview) to amma wani iri yake jin jikinsa kamar in ya tafi ba zai dawo ya tadda Fa'iza ba. Halin rai da karfen nasara. Ya duba agogonshi 'Jovial' mai ruwan kasa-kasa ya tadda karfe uku na yamma. Dole ne yaga Fa'izah ko daga nesa ne kamin ya tafi Birtaniya. Domin a yadda yake jin jikinsa da zuciyarsa da kyar ne in zai dawo ya tadda Fa’iza. Don haka maganar ginshira da jan aji babu su yanzu, zai fuskanci Fa'izah (no matter what!) Ya mike kamar wanda aka yiwa allurar kuzari ya fito da sauri ya kwalawa kaninsa Shu'aib kira. "Ka rufe kofar nan ka kwashi jakunkunan nan dake daki na ka zuba min a boot ka aje mukullin, zanyi tafiya sai na dawo". Ya isa sashen Mama yana yi mata bayani a gurguje, sai ga hawaye a idon Mama. "Ni dai raina baya son tukin jirgin nan Fa'iz, hankalina ba ya kwanciya, kullum kana kan iska. Me zai hana ka dawo gida kwata-kwata ka nemi wani aikin mai sauki kayi?" Ya yi dariya ya ce, "Kai mama kenan, insha Allah ba abinda zai faru. Ki bar mutum da zuciyar sa akan abinda suke so, kiyi addu'a Allah Ya tsare, Ya dafa mana, Ya kare miki mu a duk inda muka shiga. Ki cire duk wata fargaba da tsoro, mutuwa daya ce tak! Hanyoyinta ne yawa gare su, amma inevitable ce (mara makawa). Yanzu ina zan ga Fa'izah inje Mama ko da babu gaisuwar arziqi?" Mama gabanta ya ragargazo ya fadi. A irin wadannan kalaman masu tsinka zuciya da Fa'izu ke furta mata da halin da yake ciki a fuska da zuci zata iya kara masa damuwa da sabon labarin gudun Fa'izah? Ko da yake wani sashe na zuciyarta na gaya mata wai Fa'izah na Zaria, amma ya akai tasan hakan? Ya za'ayi ta tabbatar da hakan? Yadda Fa'izah taki jinin auren nan ina ne ba zata ba don ta guje masa? Fa'iz ya sha jinin jikinshi da shirun Mama, ya ce cikin raunanniyar murya. "Mama Fa'izah ta kashe kanta saboda kiyayyata ne ki ke jin nauyin gaya mini? Na tabbata Fa'iza in akwai abinda yafi haka zata yiwa kanta, indai akaina ne Mama...". Ya kasa karasawa, muryarshi na karkarwar da ta baiwa Mama tsoro akan wanda take ciki. Tayi hanzarin katse shi. "Lalalala! Fa'iza ta warke tuntuni. Hasalima ka samu sauqin tafiya domin tana A.B.U". Ta hasaso ne kawai ta fada, domin ta rantse ba za'a ji mutuwar sarkin nan daga bakinta ba, ya je wani ya gaya masa. Tayi saurin dauke kanta daga kansa, saboda hawayen da ke neman fallasa ta sun ciko idanunta, kiris suke jira su malala. Ya yi dan murmushin tausayawa kansa, amma yafi tausayin Mama da matsalar shi ta zo tayi mata karan tsaye bata ji ba, bata gani ba. Ya juya ya doshi kofa, a zuciyarsa babu tsoron Fa'izah ko miskala-zarrah. Babu tunani ko fargabar abinda zata yi masa. To me zata yi masa da ya wuce zagi na fatar baki tunda dai a doke ba zata doke shi tayi nasara ba, sai dai hannunta ya yi ciwo. Zagi yana tofo? Ko yana tsiro a jikin dan Adam? "Kuskuren Pilot Fa'iz Giwa kenan na farko, da ya sani da ya tafi neman aikinshi salin-alin shi ya fiye mai ALHERI". Inji Sumayya Abdulkadir (Takori). [6/3, 4:13 pm] Takori: *** A ZARIA Yaya Rabi da suka taso daga Kano ita da direban Ya Muftahu ta yiwa direban umarnin ya tsaya a Zaria zata ajiye tsarabar Momi na ta Gurasa data yo mata daga Kano kamin su wuce Giwa su hadu ita da su Yaya Aliyu su shiga neman Fa'izah. Malam Garba direban Muftahu yayi (parking) dai-dai kofar shiga falonmu kasancewar gidajen malamai na Jami'ar Ahmadu Bello falo zaka fara taddawa da ka zo gidajen. A dai-dai wannan lokacin na kammala cin abincin rana da Walida ta lababo ta kawo min ne. Na daga labulen dakin Abdallah ina kallon daidaikun motocin dake giftawa suna wucewa ta kofar gidanmu da yake titi ne a shimfide wanda in ka bishi zai shigar da kai cikin makaranta don ko kusa nasan ba lokacin dawowar Baba bane, don shi sai wajejen taran dare yake shigowa. Nikam wannan zaman kadaicin ya fiye mani zaman Giwa ina kallon bakin ciki kala-kala. Sai dai tunanin halinda N.S ke ciki ya addabeni ko a wane hali ya samu kansa da jin wannan bala'i da ya fada mana babu zatonmu ba tsammani? Naji haushin barin wayata da Nazir ya bani da nayi a Giwa, ko banza da yanzu ina magana da N.S muna neman mafita. Ko da yake ko da na taho da ita din babu katin da zan ke saka mata tunda ko giyar wake nasha ba zan aiki Walida wani waje ba balle har Momi tayi (spotting) dinmu. Shin a duniya ina da masoyin da ya kai Walida a yanzu? Tun bullowar bakin al'amarin nan gareni ita kadai ta tausaya min, ta taimaka min ta kuma bani goyon baya don ita ta yarda nice tata, kuma farin cikina take so ba na kowa ba. Duk da itama da fari ta so ta tirje amma Hausawa sunyi gaskiya da suka ce ce naka sai naka. Na sa hannu na share hawayen da suka zubo min. Babu zato babu tsammani naga shigowar motar su Ya Rabi, kafin inyi wani motsi na neman buya munyi ido hudu da ita, tana rungume da jaririnta Sadiq mai sunan A.B da ta haifa. Wai sai na saki labulen da sauri na kwanta a kasa ina haki. Yaya Rabi ta fito daga mota tayi kofar falo tana danna kararrawa, Momi tazo ta bude, ta ce. "A'ah! Manyan baki daga birnin Dabo, saukar yaushe?" Rabi ta ce, "Ke tsaya Momin Walida, ina Fa'izar da aka ce ta gudu?" Momi ta ce, "Wai 'yarki? Ai, ashe gurinki ta gudu?" Yaya Rabi ta dubeta shekeke abin har da alamun raini a ciki, ta ce. "Wurina ko wurin ki? Amma Aunty Maimuna baki kyauta ba, kina ganin yadda hankalin bayin Allahn nan ya tashi musamman Hajja, Baiwar Allah me tayi muku da zafi haka, don ta nufe ku da alheri? Shin dama tsakanin Fa'iz da Fa'izah akwai bambanci ne da za ki goyi bayan Fa'izah ta ki zaman aure da Fa'izu? Ai dama shi bare a cikin A.B har abada sai ya nuna shi bare ne. To sai dai ki bar naki auren akan na 'yarki, amma wallahi baki isa komai ba. Mtsw! Ni bani hanya in wuce". Momi na ta dubeta galala kamar ta ga hauka sabon kamu, duk da maganganunta sun mata zafi amma ta danne zuciyarta, a tausashe ta ce. "Shin Rabi ina ruwana da harkar Fa'izah balle aurenta? Tukunna ma da kika zo kika sani a gaba kina zagi Rabi ina kika ga Fa'izar a gidana da har nake goyon bayanta?" Rabi ta doka tsaki ta ce, "Yanzu fa naga Fa'izah da idona, yanzu nayi ido hudu da Fa'izah, kina tunanin ina da matsalar ido ne?" Momi ta ce, "Kayya Rabi, ba dai gidana ba, in kuma kina musu to ga hanya shiga ki duba ko’ina" Rabi tayi tsaki ta shige har tana bige kafadar momi tana fadin. "Biyo ni in nuna miki Fa'izar". Ba musu Momi ta bita salaf-salaf kamar ana janta, yayin da Rabi ta murda marikin kofar dakin Abdallah, sai gani kwance a dandaryar kasa bisa (carpet) nayi flat duk na jeme nayi zuru-zuru nayi baki kamar ba ni ba. Momi ta shiga salati da sallallami tana fadin. "Na rantse da Allah ban san da Fa'iza cikin gidan nan ba, bansan ta ina ta shigo ba, bansan yaushe ta shigo ba". Yaya Rabi kam bata bi takan momi ba, kallona take cike da takaici, yayin da nake barware wani irin kuka, ta ce. "Amma kin bata wayonki Fa'izah. Yanzu kan mutumin da ya kusan sati a makwancinsa ki ka kode, kika moje, kika sukurkutar da kyawun halittar ki haka alhalin baki san iya nisan taki rayuwar ba? Kaicon kafaffiyar zuciya mara amfani irin taki. Dr. Naziru kam ya amsa kiran mahaliccinshi tuni, don haka baki da sauran hujjah ta kin karbar aurenki da hannu bibbiyu kuma baki da sauran kaunar da zaki baiwa Nazir bayan binshi da kyakkyawar addu'a". Kwakwalwata ce ta debi wata 'yar hayaniya, tana yi min hargagi, tana yi min ihu-ihu, kararraki har da rugugi da taratsi da kalaman dake fita daga bakin Ya Rabi. Rarrafe na shiga yi akan gwiwoyina zuwa inda take tsaye ina tambayarta cikin kwanciyar hankali. "Ke Rabi, wanne Nazirun ne kike cewa ya mutu? Naziru Galadanci na?" Na fashe da dariya duka a lokadi daya, na dubi Momin Walida. "Kiji muguwa Momi, wai taje sun hada baki sun kashe min N.S don in auri dan uwanta. Ta lallabo nan tana fadin bani da sauran madafa ko hujja ta kin danta. To ko babu Naziru kina zaton zan bar shima Fa'izun da rai ne? Idan har babu Naziru kisa a ranki Fa'iz zai bishi ne duk ranar da ya shigo hannuna... na rantse, na kuma rantsewa da wanda raina yake hannunsa Rabi, shima Fa'iz sai na kashe shi idan da gaske ne kina ikirarin Naziru ya mutu". Na kara saka dariya har da hawaye, a hankali kuma sai na koma kuka tun ina yinshi a hankali da shassheka har muryata ta dushe ta daina ba da amo. Na ciro dankwalin kaina na rufe fuskata da shi. "Wayyo Naziru, wayyo Nazir me yasa kayi min haka a dai dai lokacin da nafi bukatar ka? Ka tuna alkawarurrukan da kayi mani baka cika ko daya ba? Kana so ka tabbatar min da gaske ba zan taba cimma duk wani burina a rayuwata ba? Kana so in tabbatarwa kaina banzo duniya cikin masu sa'a ba? Kana so inyi amanna da cewa ba zan taba samun duk abinda nake so a rayuwa ta ba? Kana so in rasa imanina na cewa nima Ubangiji na so na kamar sauran bil'Adama da Ya halicce mu tare? Ko ko ni Allah baya so na...". Da sauri Momi ta juya man baya tana hawaye. "Yi maza ki gyara furucinki Fa'izah, ce ne Astagfirullah, fadi da babbar murya na tuba Ya Ubangiji, na tabbata Kana sona, son da kake yi min ne ya sanya baka barni da dabarar kaina...ba". Rabi ta fashe da kuka ta kama ni zata rungume ni, na ingijeta da karfi. "Kada ki kuma zuwa kusa dani, yau na tabbatar ba Fa'iz ne kadai mai kina da mahaifiyata ba har da ke Ya Rabi". Na soma ja da baya, Momi ta miko hannu. "Ji ni nan Fa'izah, ki daina fadin maganganun da kike fada, Rabi tayi abu ne akan rashin sani, Allah baya kama laifin da aka yi bisa rashin sani, kuma babu mai laifi sai ke, ko me Rabi ta ce min ke kika jawo min, ke ki ka shafa min kashin kajin da bani da yadda zanyi in goge shi cikin danginku. Baki kyauta min ba, kin sani cikin bala'in da ba zan iya fitar da kaina ba". Ta soma kuka, Ya Rabi ma kukan take da na durkusa na saki wata kururuwa dukkansu ficewa suka yi daga dakin da gudu. Fa'iz Mukhtar Abubakar Giwa, ya yi parking mota kirar 'Sienna' ta Baban Kaduna da ya tuko daga Kaduna zuwa Zaria. Ya fito sanye cikin wata shadda-shadda boyel-boyel ruwan madara kirar (filtex) kanshi babu hula, sakamakon hakan, tarin sumar kanshi ta bamallin usli wadda bai fiya tajeta ba sai dai kula da ita ta kwanta tayi linkif a kansa sai sheki take bakikkirin, murdaddiya kuma kamar yana (relaxing) dinta, kamar kuma haka take a halicce. Ya yi sallama a falon gidanmu inda ya tadda Momi da Ya Rabi na kuka da girmansu da komai. Da sauri Rabi ta ce. "Ka koma Fa'eez, Fa'eezah TA HAUKACE! Muddin kaje inda take a halin yanzu abin ba zai yi kyau ba. Duk ni na jawo da na fada mata rasuwar Dr. Nazir, ni Rabi'atu wa ya aike ni?" Fa'iz ya yi dan dawurwura da manyan idanunshi akansu. "Waye haka Nazir?" Ba kuma tare da ya tsaya jin amsarta ba ya murda kofar dakin Abdallah gaba dayanshi ya shiga gaba gadi ba tare da tunanin komai ba ko wata fargaba cikin ransa. Durkushe nake akan gwiwoyina na aza kaina bisa gadon Abdallah ina sharar kuka babu ji babu gani, fatana kawai adai-dai wannan lokacin nima mutuwar tayi min adalci ta zo ta dauke ni, ta sada ni da masoyina, muyi aurenmu a kiyama ya fiye min wannan rayuwar da bani da sauran masoya a duniya sai rundunar makiya da burinsu a duniya shi ne zubar hawayena da shigata cikin kaka-nikayi, wato iyaye da 'yan uwana na jini. Na dago ido shargab da hawaye, jajur kamar gauta, don naji alamar tsayuwar mutum a kofa, ya kuma jima cikin dakin ba tare da ya yi motsi ko magana ba. Ban tabbatar ba, amma wannan matashi mai jini a jika ya yi min kama da FA'IZ BAMALLI dana sani wasu shekaru masu yawa a baya. Fari sol, har da surkin jaja-jaja kamar Bahurghade, ingarman mutum dan asalin garinmu Giwa, kuma jika ga Hajja Da ga Baban Kaduna da mama Asma'u. "Yau ko ni ko kai tunda Dr. Nazir ya tafi kai din zaman me zaka yi a duniyar banda zaman ka ci gaba da kuntata mini?" Da na mika hannu ga bangaresn dama na sai naji ya fada kan kwalbar lemo (7up) da Walida ta kawo mini na gama sha dazu,, na riketa katamau ina kallonshi kallon kura taga nama, kallon tsintsu daga sama gasasshe. Ya soma daga min hannu yana fadin cikin lumana. "Ki saurare ni tukunna... (just once) Fa'izah, kada ki aikata abinda zai sa kizo kina da kin sani. Na roke ki, ki saurari kalaman fatar bakina tukunna, daga nan na yarje miki ki zartar da duk hukuncin da ya yi miki....". "Ko uban da ya haifeka ban sauraron shi balle kai, kai da duk wani dan A.B ma kwansu da kwarkwatar su indai akan na karbi aurenka ne". Na daga kwalbar nan na wulwula na faskara mashi a goshi, ya yi saurin sunkuyawa ta wuce ta saman kanshi ta daki tsakiyar kansa. Kan kace meye wannan jini ya wanke shi tun daga tsakar kansa, goshinsa har zuwa wuyansa, amma don rashin zuciya zance ko bakin naci Fa'iz bai fasa dosoni ba, sake dosoni yake yana fadin. "Ashe da gasken kin haukace? Fa'izah (are you lunatic?)" Ya warware hannu ya shimfida min mari. Wani irin marin da ya tafi da ji da ganina na wucin gadi, na kuma ga gilmawar taurari goma. Amma bakina bai mutu ba. "Muddin ka iso gareni sai dai wani ba kai ba, baka ba da saki amma idan ka tafi inda Nazir ya tafi na saku ko babu takaba, iyakaci nima a kasheni. Na gwammace mutuwar da zama da kai wai a matsayin miji sau dubu gara mujiya da kai Fa'izu Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa". Wani irin karfi da ban zata ba ya shigeni, na isa ga madubin dogon yaro dake like jikin bango wanda Abdallah yasa kusoshi shida ya kafa a dakinsa na soma kokarin banbaro shi daga jikin bangon, ban damu da yankewar da tsokar hannuna ke yi da gilashin ba har na samu nayi nasarar raba shi da kusoshin da suka tokare shi suka zame masa garkuwa daga fadowa kasa. Fa'izu Abubakar, ya tabbatar tsandara mishi mudubin nan zanyi, wanda hakan na nufin tsattsagewar jikinshim ta ko ina, alhalin ba karfinsa nafi ba, don haka yayi amfani da wani irin zafin nama wurin isowa gareni, ya kama mudibin ya yi mishi fisga daya ya wancakalar dashi a gefe ya kwankwatse, na sake doka tsalle don isa ga fashasshen gilashin in samo wani bangare daga jikinsa, ya isheni farkewa jikan Hajja ciki babu nadama, na jini baki daya cikin murdaddun damatsan Fa'iz Giwa, ya rungume ni gaba daya katamau cikin faffadan kirjinsa. Ban san sanda na tsala ihu ba. Wani irin ihu shi ba na karaya ba, shi ba na razana ba, haka shi ba na mika wuya ba. Ni kawai ban san na mene ne ba, ko mene ne ma'anarsa. Saboda wasu abubuwa ne naji cikin jikina masu kama da jan wutar lantarki (shocking) tun daga tsakar kaina har (toes) wato babban dan yatsan kafata shocking din azaba ne ake yi min irin wanda kiyayya ke haifarwa. Gam-gam Fa'iz ya rike ni. "Fa'iza saki dai kike so daga gare ni ko?" Zuciyata na bugu tashi na lugude, cikin masifa da bala'in da ba zai kwatantu ba na ce. "Indai kai dan halak ne cikin uwarka da ubanka... to ce ne an sake ki Fa'izah!". Fa 'iz yayi shiru yana gwama numfashi, kafin da ya tattara dukkan karfinshi yayi watsi dani gefe guda. Yana girgiza kai ya ce. "In aka yi hakan za'a zauna lafiya?" Cikin gyada kai mai nuna tabbatarwa. "Har da kwanciyar hankali, za'a zauna cikin A.B family gaba daya, (no more crisis... no confrontations...)". Murmushi yayi, wani murmushin da na kasa fassara ma'anarshi ko abinda yake nufi, ya ce. "Kin san ba'a saki cikin tashin hankali, ko cikin fushi, in aka yi hakan sakin bai saku ba. (Words and promises made in anger are like fire... you cannot reverse the damage they have done). Don haka share hawayenki, kije kiyi wanka ki fito kiyi sallar la'asar, ki kawo min biro da takarda. Shi kenan Fa'izah?" Haba! Ai ban san sanda na mike nayi toilet ba na sunce na sakarwa kaina shaya, sai a wannan lokacin ne radadi da zugi daga goshi da tsakar ka ya isowa Fa'iz. Ya kai hannu tsakiyar kanshi ya fitar inda yaga yadda jininshi ke ambaliya. Ya murda kofar dakin da sauri ya fito falo inda Momi da Ya Rabi ke zaune jigum-jigum. Momi ta mike tayi salati, ta tsarkake Ubangiji, tayi masa tasbihi, ta kadaita shi. Ta ci gaba da fadin. "Ba lafiyarta kalau ba, kuzo ku fitar min da ita daga cikin gida, ku kaita (psychiatric) kada tayi mana lahani cikin dare". Fa'iz ya samu kujera ya zube juwa da hajijiya suna kwasarsa. Ya yi murmushi. "Momi da hankalinta fa, bacin rai ne. Kuma tana da gaskiya da babu wanda ya tsaya ya kalla, amma shi kenan komai yazo karshe ai". Yaya Rabi ta cire dankwalin kanta ta daure mai goshin, ta sa mayafinta tana share mishi jinin wuyanshi da keyarsa, yayin da Momi ta dauko akwatin taimakon farko (first aid box) da yake ma'aikaciyar jinya ce, ta gyara wurin, ta cire kwalbar da ta nitse a wajen, ta dinke inda ke bukatar dinki duka idanun Fa'iz na lumshe har ta gama. Ta goge duk wani jini da auduga da ruwan (hydrogyn) tas. Ya mike tsaye sanda ya jiyo murda kofa daga (toilet) alamar na gama wankan na fito, yana ce da Momi ta kai min wasu kayan in sanya. Momi tana girgiza kai ta ce, "Wanda ke neman kashe mutum za'a kaiwa kaya ya sanya? Ni kam bana kai kaina mahalaka ina ji ina gani ba, kai dai kace kaji ka gani, bari in dauko maka ka kai da kanka, sai ince ga su". Ta shiga dakinta ta dauko doguwar rigarta da dankwali na shadda ta kawo masa, ya amsa ya murda kofar Abdallah ya shiga. Na takure can kuryar kuskurwar dakin ina mai kallon ceiling da zani kawai daure iya kirjina. Yau sati biyu kenan rabona da wanka, don haka ji nake ta ko ina wata iska mai dadi tana ratsani. Tsami da tashin da jikina ke ta yi kwana da kwanaki duk na samu saukinsa. Gashin kaina da na jika jagab da ruwa ya taimaka wurin suturta fatar bayana, ya kwanta lamban akan dogon wuyana ya sauka a kafaduna. Bai yi magana ba ya mika min rigar na amsa. Fa'iz ya kalleni na 'yan sakanni, ya ce. "Ina takardar?" Na mike na nufi littattafan Abdallah kan (study-table) dinsa na yago takarda harda daurawa akan littafi, na dauko biro. Ya zauna gefen gadon ya karbi littafin, ashe ma yana da nashi biron a gaban aljihun rigarshi kyakkyawa dashi (biron) ya dora akan takarda ya soma rubutu. Na koma jikin bango na tsaya hannuwana biyu sarke a kirjina ina kallonshi kasa-kasa. Ya ce a hankali, "Nawa kike ganin ya kamata in rubuta?" Na dan fiddo ido, da sauri kuma na ce. "Uku mana!". Har sai da na bashi dariya, ya yi murmushi, ni kuma na sake hade rai. Sai ya mai da fuskarsa ya kintsa ta. "Har uku, kina ganin su Baba ba za suyi fada ba?" "Akan me za suyi fada kai da abinka?" Murmushi yayi ya kalleni ya maida kai ya ci gaba da rubutu, ya kammala ya ninke ya maida bironsa aljihunsa ya mike ya iso har inda nake, ya miko mini. Hannu biyu nasa na amsa kamar wadda aka bawa damin kudi don rashin ta ido har da cewa. "Na gode". Ko da yake ni wannan ta fiye min gida da mota dole in gode in kara godewa. Ya yi murmushi ya dauki hanyar fita, har ya kai bakin kofa ya juyo. "To yanzu kin yafe mini?" Na ce, "Ni me kayi min? Dama auren ne bana so da kai". "Ba wannan nake nufi ba Fa'izah.. Na can baya nake nufi, shekaru goma da suka wuce a gidan Hajjah". Nayi shiru cikin TUNA BAYA...Wai TAKORI ta ce TUNA BAYA SHI NE ROKO. Fa'iz ya wahalar dani da yawa har yadda mai karatu ba zai fahimta ba. Ya ki ni, ya nunan kiyayya, ya nunawa uwata, ya yi mata izgili kala-kala da kalamai na raini a wancan lokacin wadanda 80% su suka rura wutar kiyayyarsa gareni fiye da wanda ya yi min ni kaina. Uwa tafi gaban wasa, haka ba'a hadata da komai, ni tawa mai sauki ce tunda na yar da kwallon mangwaro na huta da guda. Fa'iz ya cuce ni sosai, ya vata min sosai (he so much hurt me heart and soul) ya bata min baka da zuci ta yadda a wancan lokacin har nayi furucin BAZAN TABA YAFEWA FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI BA! To amma mutumin da ya hakura da auren da yayi don yana so duk da mugun rotsen da ya sha ai ya cancanci yafiyar tunda dai daga yau shi kenan da kyar ma in wata hulda zata sake hadamu baya ga gaisuwar zumuncin da ta zama dole ko a lahira sai anyita. Sai na daga jajayen idanuna na dubi dan uwana Abubakar (Fa'iz) har zuwa lokacin idanunsa akaina yake. Wani irin yanayi ne cikin kwayar idanunshi mai nuna gajiya, damuwa da matsananciyar yunwa wadda ta ci karfin mutum ta nuna cikin kwayar idanunshi. Ban taba ganin Fa'iz ba tun bayan tafiyar shi ko a hoto sai yau, ya kara wani irin girma da kyau da haiba mai ban mamaki. Ya zama (giant) ma'abocin kwarjini da kamala da alamun samun (exposure) na rayuwa cikin kowanne fanni a fararen kwayan idanunshi. Fa'iz ba Fa'iz ba, in ba don halin ba me zai hana ni inso wannan kyakkyawan kammalallen matashi? Na kau da wannan bahagon tunanin na ce cikin taushin murya. "Ka je kawai, babu komai". Fa'iz ya tura duka hannuwanshi cikin aljihu, ya ce a tausashe. "Baki yafe din ba kenan?" "Abinda ya wuce ya wuce a wurina, bana son TUNA BAYA...". Ya lumshe ido, "Har yanzu baki fadi ba da bakin ki Fa'izah cewa kin yafe mini". Na ce, "To Ya Fa'iz, NA YAFE MAKA DUNIYA DA LAHIRA!". A hankali Fa'iz yake lumshe idonsa yana bude su, ya yi shiru ya kasa cewa komai. "Show me in another way... na kasa gasgata kunnuwana Fa'izah". “Like how? (Ma'ana, ta yaya?" Na tambaye shi. Sai ya zaro hannunshi na dama dake sanye cikin aljihun rigarshi kaftan na yadin (filtex) ya miko mini (yana nufin muyi musabaha). Abinda bana so din shi ne ya dawo min, wato TUNA BAYA..., "Ba don komai Baba ke son in tafi ba sai don Mama da ta tsane ni kan shegiyar yarinyar nan Fa'izah!!!" Ban iyawa! Hada hannu da Fa'iz Bamalli... Wani kwayan mutum guda daya da ya takurawa zuciyata a lokacin da bata da kwarin daukar kunci da kuntatawar. Wata zazzafar kwalla ta shiga tsatstsafo min. Fa'iz idanunshi suka kada, jikinshi ya soma dan shaking a sanda yake fadin. "Baki yafe min ba, wallahi Fa'izah yafiyar ki bata kai zuci ba. Akwai abinda baki sani ba, ban taba kin Momi ba, ban rainata ba, kuru... kuruciya ce da yarinta amma babu komi a raina a game da Momi ko da take (outsider) amma na yarda nayi kuskure kuma babu wanda ya san gobe sai Allah, kuma kana naka ne Allah Yana nashi. Yanzu babu lokaci, ina kan uzuri da na baki labarin abinda ya faru tun kafin a haife ki...". Ya tsuguna a gabana ya dora hannu bisa tafin kafata, amma ya kasa sake furta komi, wani ajin yana motsawa yana so ya maida shi Fa'izun shi yana so har gobe har gaban abada kada Fa'izah ta juya shi ko ta ga (week-point) dinshi. (Na yaushe kuma Fa'iz? TAKORI). [6/3, 4:13 pm] Takori: Sai ya mike a hankali yaja da baya ya juya ya doshi kofa, sai da ya kai bakin kofar sai ya juyo kadan cikin fadin. "Allah Yaji kan NAZIR S.". A lokacin ne mutuwar da Ya Rabi ta ce min Dr. Nazir yayi ta dawo min danya sharaf, tuni hawayen dake makale cikin idanuna suka tsinke baki daya. Addu'a ce mai kyau ya yi ga masoyina na hakika, wato Dr. Nazir Sani Galadanci. Don haka na ce. "Ameen Ya Rabbi". A yayin da ya sanya kafarshi waje zai fita daga dakin. Wani sauti ne ya fito tun daga karkashin zuciyata na zuciyar 'yan uwantaka va tare da yayi shawara dani ba. "Haka zaka fita kayan ka duk jini?" Sai bayan na furta ne naji kunya da alamun nadama, sosai idanunshi ke nuna cikin juwa yake karfin hali kawai yake na duk maganar da yake yi, a hankali yayi murmushi ya dan juyo ya dube ni. "Za suke tuna min da irin kyakkyawar sallamar da muka yi da matata (a da) kanwata FA'IZAH A.A GIWA. Don haka kada ki damu da su, ko nazo sanya (uniform) ba zan zubar da su ba, zan tafi da su har Great Britain". Yayi murmushi (a karo na biyu) “ki sanya kayan da Momi ta baki” ya fice da sauri. Oho kuma wai inji wohoho! Kai ya shafa, ni dai tunda na rabu da alakakai falillahil-hamdu. Dama abinda yasa ni tambaya ganin yawan jinin ne tunda haka yake so meye ruwan Fa'izatu? Momi ta dube shi a yayin da ya kai kofar fita zuciyarshi a jagule, ta ce. "Yanzun Fa'izu haka za ka shiga cikin mutane kaya duk jini? Ka zo ga na babanku ka saka sai ka tafi". Ya yi murmushin da Hausawa ke kira yake. "Babu komai Momi, da naje (Airport) canzawa zanyi zuwa (uniform) ai". Rabi ta ce, "Daga nan sai ina?" Ya ce, "Ina da (interview) ne Aunty Rabi a kasar Birtaniya". Idanun Rabi sukai rau-rau, hawaye na son zubowa ta ce. "Haka zaka yi tukin jirgi Fa'iz da rauni a cikin kanka?" Cikin kosawa da son ya tafi kafin likin da yayi ya balle, ya ce. "Babu komi Ya Rabi, bi'izinillahi Rabbi". Ta ce, "To baka hakuri da tafiyar zuwa sati mai zuwa kafin nan Fa'izar ta sakko ku tafi tare? In ta zauna nan me zata yi mana?" Fa'iz ya sake murmusawa cikin takaicin kalaman Aunty Rabi, ya ce. "Shin cikin ku Ya Rabi wa ke da jan wuyan sanyata ta bini ba ma gidana ba har wata duniya a yadda take ji da taurin kan nan? Yanzun ma dabara nayi mata muka rabu lafiya, ki rufa min asiri in tsallake in bar Nigeria Ya Rabi". Yasa kai ya fice abinshi. Bai isa (Airport) ba sai ana kiran sallar magariba, a yayin da ya karya motar ya shiga filin jirgin ne zugin da radadin da tsakar kanshi ke yi ya tsananta. Ya kashe motar a wuri na musamman ya fita ya dauko jakar kayanshi na (boot) ya rufe motar, cikin sauri ya gama cike-ciken takardun da zai yi. A yayin da ya shiga (pilot's changing room) domin sauya kayan jikinsa zuwa na matukan jirgin sama ya tuna da abinda ya ce da Fa'iza, ya yi murmushi. A lokacin ne cikinshi ya soma kugi, wani irin kugi da bai taba yi mishi ba, yana tuna mishi rabon shi da kwakkkwaran abinci tun dirar shi Nigeria daga Russia. Yanzu kam da zuciyarshi tayi sanyi, hankalinsa ya kwanta da samun kalami mai dadi daga Fa'izah yana jin zai iya hadiyar abinci ko abin sha. Abinda bai taba samu ba tun tasowarsu (kalami mai dadi daga Fa'izah) ko da yake shima din haka bata taba samun rana irin ta yau daga gareshi ba. Don haka ya yi (marking) ranar (as precious). Wata rana mai dumbin tarihi a cikin ranakun rayuwarsa. Fa'izah tayi kuskure da take tunanin zan iya sakinta koda daya ne balle uku rigis, saboda shima haukan da ake zaton mata ya sameshi ko me? A yadda yake jinta a zuciyar nan tasa, yake jinta a ko'ina na ruhi da bargon jikinsa? Shi kam bai san ma yana son Fa'izah ba sai yau din nan, ashe ada hasashe yake, ba don wani kyawunta ko kyakkyawan girman da tayi ba, a'ah yin Allah ne kurum, shi ya daura masa ta yadda bashi da harshen da zai fassara soyayyar Fa'izah a zuciyarsa, tun ranar da ya bar Giwa zuwa kasar Rasha. Ya tuna rotsen da tayi mishi, sai ya girgiza kai ya yi murmushi. Kuruci dangin hauka kenan. Fa'izah na ganin hargaginta da (power) dinta shi zai kwatar mata 'yancin da take so, har yaji tsoronta ya sake ta? Tsoron sa Allah-tsoron sa ranar da zai dawo gida Nigera daga wannan tafiya da zai yi wanda ya tabbata idan taji tsiyar da ya shuka mata a takarda ta nemi tsire shi da mashi, wannan ne hukunci na karshe da yake tunanin Fa'izah zata yanke masa in ya dawo. Bai kai karshen tunaninsa ba (computer) ta shiga ankarar dashi lokacin tashinsu yayi. Za su tashi ne karfe uku na sulusin daren ranar ta Alhamis daga (airport) din Abuja zuwa Wales din kasar England ba kamar yadda ya kintata da farko ba, wato karfe goman dare, don haka lokacin haduwarsu da Majid ma ya canza don sunyi 'transit' a ‘Scotland'. Karfe sha biyu na safiyar washegari suna Wales. Kowa dake cikin jirgin ya fita in ka dauke (pilot) Fa'iz Giwa, yayi shiru shi kansa bai san me yake tunani ba har saida wani abokin aikinsa ya ankarar dashi za'a rufe jirgin, sannan ne ya daura idon shi akan jakar kayanshi ya dauka ya mike ya fito. Monica da kawarta Divya, suna daga cikin fasinjojin jirgin da Fa'izu Abubakar ya biyo zuwa Scotland, zai sake kwasa zuwa Ingila. Sunzo ne musamman daga Abidjan domin halartar kallon wasan kwallon kafa na gani da ido a (Chelsea UK). Ta gabansu Pilot din ya gifta a (reception) jaye da 'yar jakar kayanshi a hankali akan (marbles). Tsakanin Monica da Divya, an rasa wadda zata fara dauke ido a kansa har ya kulewa ganinsu ya bi (lifter) zuwa (underground). Monica ta tabo Divya. "Kin sanshi ne? Irin wannan kallo haka?" Divya ta girgiza kai, "Kamar nasan fuskarsa, ya taba debo mu daga Paris zuwa Ukraine". Divya ta ce, "Bahaushe ne fa tamkar mu ba Balarabe ba, sai dai ta ko ina babu fuska". Monica ta hadiyi miyan da ya tsaya a makoshinta, ta dafe kirji ta rufe ido tana ta faman gyada kai kamar kadangaruwa, wata irin soyayya na cinta Fa'izun bai san suna yi ba wai kunu a makota. Sun hadu da Majid a filin jirgin saman Wales, ba abinda Majid ya fara hangowa sai lafceciyar (plasta) akan Fa'iz da goshinsa. Hannu ya mika ya rungumo kafadunsa suka karasa wani dakin hutawa na musamman dake cikin filin jirgin, suka zauna a tare cike da gajiya da tsamin jiki na kwanan zaune. Majid Abduljalal Balaraben Syria ne wato (Shaam), tare suka yi karatu da Fa'iz a Russia da Johari da wani bakar fata Solomon Bayaraben Nigeria (they are very close to each other) don haka sun san tarihin juna, sun kuma san damuwar junansu. Majid bai tabbatar ba, amma jikinshi ya bashi anyita ba dadi da Fa'izah. Hasashen shi ya hasaso mishi ita ce ta yiwa Fa'iz wannan raunin. Fa'izu ya ja numfashi ya sauke, da gasken-gaske cikin damuwa yake mai yawa, wadda ta kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskar shi. Maajid ya bubbugi kafadunshi, ya yi murmushi ya ce. "WO-MAN! Inka fahimci kalmar ko? Tana nufin Wo! MAN ka shiga uku kenan!". Duk halin da Fa'iz yake ciki sai da Maajid yasa shi dariya, ya yi mai isarsa kafin ya ce. "Maajid! Maajid!! Ya aka yi kasan cewa Fa'izah ce ta rotsa ni?" Ya ce, "Oho maka wannan kuma! Ni dai na san kai ba makaho bane balle ince faduwa kayi ka ci da baka ka fasa goshi ka fasa kai, na kuma san ba dambe kayi ba aka fi karfinka da (giantness) din nan naka Fa'iz. Na kuma tabbata ba gidan giya kaje wani yasha ya bugu ku kayi rigima ya rotsa maka kwalbar ba". Sai ya sake tintsirewa da dariya, ya ce. "To amma saboda Allah me yasa ka kirani adai-dai lokacin da kasan ina tsakiyar yakin neman soyayya a tsakiyar rikici da Fa'izah? Shin ko kasan wannan kadan ne da ace ban yi mata karyar saki ba da ta kwankwatse ni gaba daya da gilasai?' Majid ya yi tsaki ya ce, "Kai ka so duka wannan shirme na Fa'izah. Ni kam yana daga cikin abinda ya hanani aure yanzu, wato fargabar irin macen da zan debo ma kaina, don ni dai ba zan auri matar da bata so na ba wallahi. Idan wani ya ki ka da wuni, wani da kwana zai soka. Ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare, don haka mu bamu fara cin tuwon ba ma balle miyar ta kare, yanzu ne muka fara laluben har sai mun lalubo mai son mu. Mu matuka jirgin sama, muna bukatar mata masu matukar son mu, wadanda kullum muka fita sai sun kai goshinsu kasa sun roka mana kariyar Ubangiji saboda kullum rayuwarmu cikin sadaukarwa take, za'a dawo ko ba za'a dawo ba. In zamu fita su faranta mana, hakazalika in mun dawo. Sannan ba nymphos ba (masu yawan bukatar Da namiji) ka gane? Don haka ne naga wautarka da rashin azancin ka wurin nemo auren yarinyar da tun fil'azal kai tafi tsana sama da komai a rayuwarta wai a matsayin (life-time partner) dinka. Kada ma kayi gigin kawo mana Fa'izah a yanzu, ta hada maka zafin da zaka tura rayukan al'umma cikin (solar-system). Ka barta tukun, zuwa wani dan lokaci har ta sauke zafin kanta". Ya yi murmushi mai hade da sautin dariya. "Yau Majid so kake ka kasheni da dariya. Da alama kana da (good experience) akan WOMEN din nan. To ga tambaya, shin ya za'ayi Fa'izah ta so ni? Ni dai (I can't do without her no matter what). Ko kasan duk haukan kiyayyar da Fa'izah ke yi a kaina bana jin ciwo? Ka san cewa har iyayena Fa'izah ta zage su tas akan idona ban ji komai ba, me yasa?" Da sauri Majid ya amsa. "Don kana sonta mana, so irin na halaka ga maza, wanda ya zarce halastaccen so ya hada da ribatar zuciya, so na fiye da kima don iyaye ba'a hada su da wata abar banza (mace). Duk da ance so hana ganin laifi to amma banda iyaye. (They made us what we are today! They are, therefore, incomparable to any worldly material). Ka farka daga gigin son nan Fa'iz ka zama jarumi akan Fa'izah kamar yadda kake jarumi akan komai. Sai dai in kiyayyar Fa'izah ta ci gaba wata rana zaka kita kaima. Kiyayyar Fa'izah a gareka ta yi yawa, tafi wadda ka ce kayi mata. Ni dai in ni Maajid ne bazan jure ba, mace ta fasa min kai... ta zagar min iyaye, mace! Mace!! Mace!!! Woman, Imra'ah! Ana maa Adhry!!! Macen ma wata karamar yarinya Fa'izah da ta tashi a kauye irin Nigeria? Ba zan dauka ba". "Baka taba fadawa a son Woman din da ka rainawa kura bane Maajid shi yasa kake duk wannan cika bakin da kake yi. Nima da irinka ne, haka nake da wannan akidar. Ban taba zaton akwai macen da zata sani zub da kaina ba sai da Allah Ya dora min lalurar ciwon son Fa'izah. Ko kasan har kasa na dire gwiwoyina ga Fa'izah? Maajid SO BA KARYA BANE. Sai dai ta wani bangaren ina cizawa ina hurawa. Iyaye duka iyaye ne a zuciyar kowanne Da na halak Maajid. Na zagi uwar Fa'izah yafi sau shurin masaki akan idonta a kunnenta kawai don bata fito daga family dinmu ba, ban taba tunanin yaya take ji a ranta ba, duk da yarinyar ce a lokacin. Kuma kasan saboda mene? Ba wani abu bane kawai Maman nata (we are not bloodly related). Babanta yaje bautar kasa yayo (secret marriage) da ita daga Taraba da yake na gaya maka a zuri'armu ba'a auren (outsider). Bayan wannan Aunty Mainuna bata yi min laifin komi ba, baya ga ALHERI. Ko kallon banza nayi mata murmushi take mayar min a da can tana fadin yarinta ce, idan na girma zan gane wani baya auren matar wani, itama bata taba zaton zata auri bazazzagi ba tana cikakkiyar bafulatana. Da Allah Ya tashi saka mata Maajid rana daya sai Allah Ya yiwa al'amarin nawa juyin waina da kaunar abinda ta haifa tun ranar da aka haifeta.......". Labarin mai tsaho ne Maajid, (just bear in mind I have reason to love and respect Fa'izah and her mother to such an extent, and I'm ready to do everything to undo the hurt I caused to them). In kuma ci gaba da jajircewa ga rike igiyoyin auren Fa'izah da duk iya karfin da Allah Ya halicceni da shi har sai na dinke ZUMUNCIN A.B family ya koma yadda ABUBAKAR BAMALLI ke son ganinsa, hakan kuma zai ci gaba ko babu tsohuwa Hajjah (to the last journey) insha-Allah, ni na lalata ni zan gyara, duk da ance ba'a bari a kwashe dai-dai, jikina na bani ni zan kwashe daidai Maajid, sai Fa'izah ta so ni fiye da sonda nake mata in Allah Ya bamu tsawon rai da lafiya". Jinjina kai Maajid yayi, ta wani bangaren ya yarda ta wani bangaren bai yarda ba. "To da ka dire mata gwiwoyin a kasa, ka roketa me? Ta so ka?" Ya yi dariya ya ce, "Ina! Karewa ma kwarjini tayi min na kasa fadin abinda nayi niyya". Maajid bai san sanda ya fashe da dariya ba. "Amma ka ba da maza Pilot. Zan so ganin wace ce Fa'izar nan da zata ki namiji kamar ka ko yankar naman jikinta yake yi kullum, sai dai in ba mace bace. Tukunna ma cewa nake shekarun yarinyar basu fi ashirin ba? In har kana da tsokar zuciya a jikinka Abubakar, kuma kana son in yarda kai namiji ne mai mazakuta a jikinsa ba bonono kake mana ba mata-maza ne, ka share Fa'izah kayi kamar ka manta da al'amarinta kada ka koma inda take sai nan da (atleast) watanni uku. A kalla Fa'izah tayi haukarta ta gama ko da bata bari duka ba to 80% zai ragu tunda ta zame maka mutu-ka-raba daga kai har iyayenku. Sannan ne zaka neman sulhu cike da juriya da kai zuciya nesa, ka hadiye duk wani borenta so zallah zaka yi ta (portraying) ka zama kalar tausayi ka nuna baka da katabus sai yadda aka yi da kai, ka kwanta kace “in takani za kiyi to ga bayan taka”. Amma yanzu abinda yafi haka ma Fa'izah zata yi maka indai labarin da ka bani can baya da yanzu gaskiya ne, UWA ba abin wasa bace, ai na dauka ita kadai kayi ta yiwa shakiyancin. Tunda kace ita Maman (have reason with you) baka da matsala da ita kun fahimci juna tuntuni. Wacece Fa'izah? Me take takama dashi da zata ce bata son ka Fa'iz baya ga kyawun da take da shi? Me aka yi aka yi ta? Sai dai in muna-mata ce ba mace ba wadda tasan me ake so a namiji. Takamar diya mace kowacce iri ce kafin a daura mata aure ne, amma yanzu Fa'izah ta zama nama, bata da sauran abin tinkaho. Duk yawan kiyayyar ta fa muddin ta dauki ciki Fa'iz ta kare, domin a lokacin ne zata shiga fargabar ba zata so danta ya yi maraici ba, kuma ba zata so a kirata bazawara ba, ko kada ku rabu ta rabu da 'ya'yanta, Zata shiga tunanin yanzu fa ta zama (second-hand) ba zata je gidan da babu mace ba, kuma kasan ba son kishiyar nan suke yi ba, kuma idan ta fita, ba zata samo yaro kamar ka ba ko da ta samu mara mata din. Zata shiga fargabar me zata je ta tarar gidan mutumin nan dama ta zauna da wanda bata so din ita azo a tadda ita tunda ku zama da mace fiye da daya al'adarku ne. Kiyayyar diya mace tana da wasu magunguna guda uku wadanda in kana dasu, wallahi sunan kowacce diya mace "sorry" ko ko ince (finished product). Na farko mace na son yawan kyauta na abinda tafi so daga hannun mijinta, kyauta wadda zata ratsa mata zuciya ba gayan kudi ba. Sannan mace Allah ya yi ta da son a nuna an damu da ita, duk inda kake, ka nuna mata tana ranka kana tuna ta da so da kauna. Tana kuma son a darajja ta (kada ka nuna mata danginka sun fita, suna kuma kada ka nuna musu ta fisu) ka barwa kanka wani sirrin na zuciyar ka. Tana so ka kwantar da kai ka bata hakuri in ka bata mata rai. Da fari zata nuna shariya ne, amma zuciyarta sanyi take, tana hucewa a hankali. Idan ka matso 'yar kwalla zaka ji ta ce, "Shi kenan, ya wuce". In ka kawo kyautar nan in ranta yana bace zata ce, "Ni bai dameni ba" ko "bana so ka bar abinka" amma a cikin zuciyarta sonka karuwa yake yana fidda rassa. Haka kayi kokarin ka fahimci duk wani (likes and dislikes) dinta shima ka dage da gujewa/aikatawa. Ka rike amanarta, kada ka dinga zancenta da kowa ko da 'yan uwanka. Duk inda kake, ya zamanto kana yawan nemanta tare da nuna mata ita kadai ce a gabanka saurin mata basa burgeka ko da ba hakan bane (in reality) a zuciyarka. In kayi riko da wadannan Fa'iz kiyayyar Fa'iza komin girmanta babu inda zata je. Fa'eez ya dube shi cikin mamaki. "Who taught you all these?" Maajid ya yi murmushi. "Matar Yayana (psycologist) ce muna dasawa da ita sosai. Tana yawan bani 'theory' akan mata da abinda suke so. Ko baya ga haka ni ba irinka bane da inji kadai kasa gaba. (All work without play make jack dull boy) ina karance-karancen Novels domin samun nishadi (mostly authorized by women). Kuma ina soyayya da mata kala-kala a kasar mu. Ina zaunawa da kanne na mata ina jin hirarrakinsu da damuwoyin da suke ciki da mazajen su, ina sakar musu fuska ni ba (terror brother) bane irinka". Fa'iz ya kyabe baki ya ce, "In ka gama surutunka don Allah tashi muje mu samu (hotel) in kwanta in huta. Zazzabi ke neman rufeni sabida jinin dana zubar. An gaya ma Fa'izah na kamar sauran matan da ka fahimta ne? An gaya ma Fa'izah zata tsaya ta saurari mutum har yayi mata wani dogon sharhi in ta tsane shi? Koko an gaya maka Fa'izah abin hannun maza ya dameta da zan bata abu, ta amsa bata kwada mini ba? (Above all) ma ta yaya kake tunanin ni Abubakar Mukhtar zan yiwa mace kuka har in tsaya lallashinta ta samu kafar wulakanta ne?" Maajid ya kunna sigari ya dasa ma lebbansa, ya ce cikin murmushi. "Meye kuma ya rage baka yi ba? Yanzun nan fa ka gama ce min ka durkusa da gwiwoyinka a gaban Fa'izah ba matse maka baki nayi ba". "Tsugunno daban, kuka daban. Ko da na tsugunnawa Fa'izah bance mata komi ba balle inyi mata kwallah. Da in yiwa Fa'izah kwallah don ta so ni wallahi gara mun dauwama a haka. In na sami sararin aiki inje gidansu ko ta taga ne in leka in ganta in dawo bakin aiki na kada Allah Yasa ta biyonin, an gaya maka a matse nake da mace kamar ka?" Maajid ya fashe da dariya, ya ce. "Ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu. Amma da ka tabbata sakarai, haka kawai Allah Ya halatta maka abu ka haramtawa kanka? Fa'izah dai mace ce dake shekarun shekarunta na (teenager) ba abinda tafi bukata a yanzu irin kasancewa da namiji da zama gidan mijinta, musamman da kace duk tsararrakinta an kaisu dakin aure. Ka zauna nan kayi ta rikon aure, ta yi saurayi mai debe mata kewa koda da hira ne asarar wa?" Ya kai mishi wani mugun kutufo a kwibi, ya ja jakarsa keey...! Ya taka da gudu ya shige (lifter) ya barshi a baya. Fa'iz yayi tsaye kafafunshi harde da juna yana bin (lifter) da ta dauki Maajid zuwa sama da kallo har ya daina hango farar fatar Maajid da fararen kayansa da kwantaccen bakin gashin kansa na Larabawan Syria, yana mai auna maganganun da suka fito daga bakin Maajid din cikin ma'auni na hankali da tunani. Ya tabbata duk abinda Maajid ya fadi gaskiya ne, to amma ta yaya zai bullowa Fa'izah su kasance tare? Bama a gida Nigeria ba a duk inda ya sanya kafa? Barma (bomb) din da ya taho ya barota dashi ya fashe me zai je ya tarar bayan fashewar (bomb) din? Dole ya bi shawarar Maajid na tilasta kansa kin ganin Fa'izah da dosarta har bayan watanni uku kamar yadda Maajid ya ce. "Kai to kuma har wata uku! Wata uku fa ba kwana uku ba!! Fa'izah zata iya yin saurayi a tsayin lokacin. Yadda take kin shi din nan zata iya yin saurayin da zai debe mata kewar mataccen nata. Ya rike kanshi da hannunshi biyu yana girgizawa da sauri... "No! Babu mai barinta, iyayensu ba zasu bari wani abu ya taba mishi aure ba tunda tana tsakiyarsu. To itama bata da hankali ne? Ai aure yafi gaban wasa". A wannan karon hawayen kawai yake ganin idan ya yi (shading) zai samu sassaucin kishin da ya tokare shi ya hana shi hadiyar miyau. In kuma ya sake ya bari suka zubo ya tabbata Fa'izah ta maida shi kamar sauran maza da Maajid yake misali masu yiwa mace kuka don ta so su. Kada Allah Ya nuna masa wannan ranar. *** [6/3, 4:13 pm] Takori: A ZARIYA Na fito falo fes dani cikin doguwar rigar Momi, baki na kamar gonar auduga, ban zauna a ko daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya ba sai a tsakinin Momi da Ya Rabi, suka dan matsa gefe suka bani fili a darare duk da ita Momi babu alamun jin tsorona a fuskarta, ta bani filin ne kada in dire akan cinyarta. Duk sai suka bani dariya, ga Aunty Rabi mai yi min kallon hauka sabon kamu. Na tsugunna gaban Momi da gwiwoyina biyu, na ce. "Don Allah Momi kiyi hakurdi ki yafe ni, duk bacin ran da na sanya ki da kashin kajin da na shafa miki na zama cikin gidanki ba tare da saninki ba. Wallahi ni kaina wani abin idan ina yi ban san sanda nake yinsa ba, ji nake kamar ana kitsa min shi a tsakar ka, bana cikin hayyaci na. Ya Rabi kema don Allah kiyi hakuri, kuma wallahi Momi bata san ina gidan nan ba". Nan suka dubeni baki bude kamar sunga wadda ta warke daga cuta. Yaya Rabi ta muskuta ta ce. "Yanzun kin kyauta kenan da abinda ki ka yiwa Yayanki da yazo miki sallama zai yi tafiya? Fa'izah kisan kai za kiyi? Kisan ma na mijinki dan uwanki, rabin jikinki? Fa'izah kina son gamawa da duniya lafiya da kike ta da hankulan rayukan iyaye da masu kaunarki akan sanin kanki?" Na kara kwantar da kai da kaskantar da murya sai ka rantse duk duniya ba za'a samu mai kirki na ba. "Kiyi hakuri Ya Rabi, komi ya wuce bi'izinillah. Tsakanina da Ya Fa'iz yanzu sai gaisuwar mutunci da mutuntawa, na bashi hakurin ciwon da na ji masa tunda YA SAKENI!". Rabi ta shiga salati tana sallallami tare da tafa hannuwa, kafin ta kai karshen salatinta take direwa ta dauko sabo. Kafin ta fashe da kuka ta ce. "Kin cuci kanki kin cuce mu Fa'izah, hakkin iyayenki da na Hajjah ba zai taba barinki zama lafiya ba. Kin bata wayonki, kin fita zakka cikin A.B, kin zame mana bakin bunu bata baibaya. Bace min da gani tun ban lallasaki ko na tattaka ki ba...". Ko a jikina wai an tsikari kakkausa. Sai na sa hannu biyu na mika mata takardar, Rabi ta mike tsaye kamar an fisgota ta fisgi takardar daga hannuna, na tabbata in na tsaya tabbas zata tattakanin, sai na mike tsam koma daki na murza key. Na shige cikin bargon Abdallah tunani dubu dari da hamsin ya aureni 70% na Dr. Nazir ne. Mutuwar shi ta dawo min danya, inama ana mutuwa a dawo! Ga damar da nake nema kwana da kwanaki ta samu, amma wanda nayi ta hakilon akansa mai sawa da hanawa ya yi ikonsa akansa. Na rufe ido ina kuka, tunanin kyakkyawar soyayyar mu cikin Jami'ar Bayero da wajenta ke gifta min filla-filla. Na yiwa Allah godiya da na zamo silar kimtsuwar Nazir Sani, ya kuma mutu akan niyyar AURE. Babu abinda zanyi domin nuna soyayyata a gareshi bayan nema masa rahma da gafarar Ubangiji a halin yanzu. Momi dai ban san halin da take ciki ba don bata yi magana ba, sunkuyar da kai tayi, sai Ya Rabi ke ta fadace-fadacenta wanda ko a kwala ta. Kukan rashin Nazir nake baka da zuci, na jiyo muryar Ya Rabi na cewa. "Shima Fa'iz ya yi karamin tunani, ba'a biyewa mace, da maza na biyewa mata da cikinmu babu wadda ba bazawara ba. Idan hankali ya bata shi ake sawa ya nemo shi, haka nan komai aka yi shi cikin fushi, sai anyi nadamar aikata shi". Ashe Momi na hawaye take yi, can na jiyo tata muryar tana fadin. "Yo ai shi kenan, sai ta yi ta zama idan zaman gidan iyaye dadi ne ga baligar mace. Duka sa'o'inta babu wanda ya ba da kunya sai Fa'izah Bakin Buni Bata Baibaya a cikin A.B. Fa'izah bata dauko zuciyata ba sam, zuciyata mai tsafta ce da ban taba kwana da wani a cikinta ba balle in tashi da shi tsayin shekaru a cikinta. Duk wanda yayi min ba dai-dai ba ko nice da gaskiya uzuri nake yi masa da ajizanci irin na dan Adam. Dukkanmu masu kuskure ne da gazawa a wani bangaren, balle Fa'iz akan Fa'izah ne kawai za'a ce bashi da kirki. Na kuma yi mishi uziri tun a wancan lokacin da rashin haxuwar jini ne kawai, ko cikin 'ya'yanka ba ma 'yan uwanka ba sai kaji wani yafi kwanta maka. Da babanta ya ce min Fa'iz ya ce Fa'izah yake so da aure jikina ya bani akwai wani al'amari mai girma tsakanin Fa'iz da Fa'izah da babu wanda ya sani sai Allah. Nayi addu'ar Allah Ya hadasu da alherin dake tare da junansu, Ya rabasu da sharrin juna Ya kuma sanya albarka a cikin aurensu. Amma ga abinda Fa'izah taga ya fiye mata, titsiye miji ya saketa. Ba zan yi mata baki ba sai dai duniya kanta makaranta ce mai azuzuwa kala-kala. Kuma na roke ki Rabi, kada ki sanya sunana cikin sha'anin nan, har gobe ni 'yar kallo ce a cikin al'amuran ku, ki bar iyayenta suyi hukuncin da ya dace da ita". Momi ta share hawaye. "Babu wadda ta baiwa uwarta kunya a cikin A.B sai Fa'izah don ta tabbatar muku da gaske ni bare ce a cikin ku...". "Ki bar fadin haka Aunty Maimuna". Rabi ta katseta cikin jin tausayi. "Dole ince haka Rabi, shin da me zan doshi babanta da shi yau ya yarda ban san da zaman Fa'izah cikin gidana ba? Duk muna zaune aka yi saki akan idonmu, wallahi duk mu za su dorawa laifi...". Bata idasa maganarta ba tayi shiru saboda sallamar Baba. Prof. Ahmadu A.B, ya shigo da sallama, duk ya rame yayi duhu saboda tashin hankalin rashin sanin halin da nake ciki, da kuma ina na shiga. Ya samu kujera gefen Momi na ya zauna, ya ce. "Wash Allah! Taimaka mini da ruwa mai sanyi Mainmunatu". Momi ta mike tayi (kitchen) don ta kawo masa ruwan, sai a lokacin ne ya lura da autar Hajja a gefe, ya ce. "A'ah! Rabi yaushe a garin? Kin zo kuma kin tadda tashin hankalin da diyarki ta saka mu ciki ko? Fa'izah ta bani kunya, ta bada min kasa a ido. Ban taba zaton tana da wannan halin ba na kafiya da kekasasshiyar zuciya wanda ba'a taba samun irinshi a zuri'ar A'B ba. Sai dai ta wani bangaren na yi mata uzuri tunda ance Barewa bata yi gudu danta ya yi rarrafe ba, kuma duk abinda ka yiwa iyayenka ko bajima ko ba dade naka 'ya'yan za suyi maka (auren Momi da yayi ba tare da yardar nashi iyayen ba). Allah Ka bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya, ameen. Rabi ta ce, "Ai tana nan cikin gidan dakin Abdallah, ba wani waje taje ba. Sai dai Fa'iz din yazo ya saketa har nan". Baba ya zabura ya mike, "What! Shi Fa'izun ne ya yi mana haka? Duk ta da hakarkarin da nake yi akan auren nan, tunda aka fara maganar auren nan bamu ci abinci ni da ubansa ya fada mana ba, shi ne ya biyewa shirmenta?" Momi ta karaso da gorar ruwan 'Rogolis' da tambulan din karau a hannunta da gorar lemon (5alive) ta aje a gefe don tasan bacin ran da Baba ya samu kansa a ciki ba zai barshi ya sha ruwannan da yake son sha ba. Bacin ran ya kashe kishirwar. Ta ce, "Kada kaga laifinsa Baban Abdallah, ta nemi rabashi da ransa in bai saketan ba me zai yi mata ya ceci kansa? Rotsa masa kwalba tayi aka fa?" Baba ya mike yana salati, ya kara da. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Tana ina tambadaddiya ku gani in babballata itama jikinta ya gaya mata, kisan kai zata yi? Shi kuma ya tsaya yana kallonta?" Rabi ta tabbatar muddin na shiga hannun Baba a wannan lokacin sai tarihina yadda komi nashi yake tsima kamar ana kada mishi gangi, don haka ta tare kofar dakin Abdallah tana fadin. "Yo Yaya in ka daki Fa'izah a yanzu aikin me aka yi? Wacce riba za'a ci? Baka huce ba tunda aikin gama ya gama, bakin alkalami ya bushe. Mu duba takardar idan ya yi na Musulunci ayi kokarin gyarawa". Ta shiga wurga ido neman inda ta cilla takardar saboda tashin hankali, kafin ta ganota a tsakanin kujerar da take zaune. Baba da kyar ya zauna a kujerar da ya mike sai wata irin zufa yake yi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, duk ilahirin jikinshi rawa yake. Ya karbi takarda daga hannun Rabi ya warware, ga abinda dansa Fa'izu Abubakar ya rubuta cikin takardar. Baban Giwa ko Baban A.B.U. Fa'izah ta takura min in saketa alhalin ban iya hakan ko giyar wake na sha. Igiyar aure dai kowa ya sani uku ce, to ni Fa'izu Mukhtar Abubakar na ninka (ribanya) igiyoyin aurenmu da matata Fa'izah Ahmad Abubakar ukku sau uku =(9) kenan. A kara tausar Fa'izah don Allah kada wanda ya kara dukanta indai akaina ne, domin nayi mata laifin da na cancanci horo daga gareta fiye da wannan da take mani. Ko kun manta baya? Na tafi kasar Ingila saina dawo a san abin yi. Danku, mai neman albarkar ku. Fa'eez Giwa. Nan da nan Baba ya washe baki yana dariya, ya kuma mikawa Rabi takarda. Cikin zumudi ta karbi takardar tun kan ta gama taya yayanta dariyar farin-cikin da yake yi, tun kafin ta kare karantawa take dariya har ta gama. Kana ta mikawa Momina itama ta karanta duk suka sa dariya. Rabi ta ce, "Aje a hakan, kada wanda ya ce mata ba haka ba. In ya dawo ya fada mata da kansa ". Baba ya yi dariya a zuciyarsa hamdala kawai yake yi. Ya dauki ruwansa da Momi ta aje masa wanda ya kasa sha ya shanye tas, ya dau mukullin motarsa ya fice zuwa masallaci. Ya Rabi ta kalmashe takarda cikin jakarta ta shigo dakin da nake tana yatsina fuska. "To Gimbiyar bala'i, in kin ga dama ki taso mu wuce Giwa tare ko hankalin gyatumar bayin Allah Ya kwanta, jininta da ya hau ya sauka saboda kaunar ki alhalin ke din ba kya son kowa sai kanki, har kuwa da iyayen da suka yi nakudar ki suka haife ki. Gobe ake yinin Ummi bai kamata ace babu ke ake yi ba koda yake ke zakka ce". Na yunkura ina fadin, "Zuwa kai kamar da kasa, sai dai wallahi ba zan kwana gidan Hajjah ba sai dai gidan Baba Na'ibi?". Ta ce, "Yanda kike so ai haka za'ayi miki don kam kinfi karfin kowa". *** A GIWA Washegarin ranar ya kama yinin bikin Ummi. Ni, amaryar kanta da Zanirah da sauran kawayen amarya duka gidan Baba Na'ibi muka kwana. Babu wanda ya nuna min wani canji ko a fuska ko a mu'amala kamar komi bai faru ba, ashe Ya Rabi ta bi ta bayan gida ne ta yiwa kowa bayanin yadda abin yake. Duk da babu wanda ya nuna min wani abu ko alamar jin haushi ko ta da abinda ya gabata ni din akan kaina jina nake wani irin sukuku! Duk jina nake kamar bare a cikinsu, kuma kenan ashe abinda nayi din ban kyauta ba kenan tunda nake jin kaina matsayin mai laifi a garesu da babu wanda ya budi baki ya ce nayi laifin. Gani nake kamar dukkansu A.B kallon tsana da kyama suke min tunda na ki dan uwansu na kawo sauyin al'amari cikin zuri'ar su wanda tun Ahmadu A.B shekaru ashirin da uku a baya ba'a samu kwatankwacin sa ba. Ummi sai faman ja na take a jiki, dinkuna ma duk iri daya tayi mana, wanda duk tasa nima shi take takura min in sanya, dai-dai da kalar agogo bata bambanta ba. Zanirah kam wani baya-baya take dani tare da yi min wani gani-gani, ni dai naki yarda in biye mata tunda ta samu labarin cin zarafin da na yiwa Yayanta ta koma min haka. Ba na yarda in nuna nasan tana yi ma duk da raina baya yi min dadi. Allah wadaran surutun Ya Rabi. 'Yan uwa da abokan arziki kowa yazo yadda yake kiran Ummi da "Amarya" haka nima suke kirana, amsawa nake da karfin gwiwata tunda nasan ina da 'guarantee'. Su Walida, Hanifa, Maryam manyan kanne kirazan biki sun kasa zaune sun kasa tsaye, sunyi ankon shadda ruwan zuma da bakin gwaggwaro sunyi kyau matuka. Walida idan muka hadu da ita ta takarkare tana rabon abinci sai ka rantse da Allah bikinta ne ko nawa, saboda rawar kai da rawar kafa. Ashe Walida tasan komai, ni ina mata dariya itama a ranta ni take yiwa. Ummi ce ta gargadeta kada ta sake aji mutuwar sarki a bakinta. Da yamma can goshin magariba muna sanye da wani (swiss-lace) mara nauyi ni da Ummi (turquise blue). Jama'a sun fara bajewa don gab ake da kiran sallar magariba a falon Aunty Zainab, Ummi zaune a gefe tare da sauran kawayenmu, hatta Haulatu ta halarci bikin Ummi, Naja'atu da Zubaida duk suna falon ana ta zuba hira. Ni ina gefe kwance a doguwar kujera, Fa'izah ce akan ruwan cikina diyar Yaya Aliyu ina mata wasa tana ta dariya. Yayin da Zanirah tana zaune da zungureren cikinta a gaba tana faman zuba (souvenirs) a leda ita da su Haulatu, kowacce da abinda take zubawa a leda wata kek, wata meat pie, wata cincin, wata soyayyen nama suna dai yin kullin nasu cikin tsari mai burgewa. Walida ta shigo ta ce wai muje inji Yaya Bashir duk mu ukun yana dakinsu na da na gidan Hajjah. Gaba daya muka mike, Ummi aka sake gyara goggoro aka duba madubi aka dauki (spray) aka feshe jiki, tuni dakin ya dume da kamshi mai dadi. Aka sa hoda aka fente fuska, nan da nan ta hau sheki. Nayi dariya na ce, "Iyen ba! Kaga amaren babban Yaya, haduwar ba sauki". Ta kyabe baki ta ce, "Ohon miki! Kece gwauruwa, sai ki zuba mana ido in munyi 'ya'ya kunyi kai daya sai ku ci naku zamanin tare dasu ko?" Na ce, "Ina! Ta Allah ba taki ba. Allah Ya kiyaye insha Allah nima bazan kara shekara gidan iyayena ba Allah Zai kawo min nagari na kowa, kuma zabin zuciyata". Da hirarrakin da muka karasa dakin su Yaya Bashir kenan. Ummi ta faki idona tayi min gwalo. A tare muka yi sallama Yaya Bashir ya amsa, kowaccenmu ta samu kujera ta zauna. Yaya Bashir na fadin. "Ummi tawa dawo nan mana". Yana nuna kusa dashi. Tayi murmushi tana sunkui da kai, bata amsa tayin nashi ba ta zauna a gefena, shi da Yaya Aliyu ne, wanda tsam ya taso daga inda yake zaune ya zauna a masangalin da Zanirah ke zaune ya zauna cike da kulawa yake tambayarta. "How is my baby kicking?" Cikin murmushi ta amsa, "Gashi nan yana ta yi kamar zai kwance min zani". Murmushi yayi suka ci gaba da hirarsu. Bashir ya taso daga inda yake ya nuna min kujerar da ya mike. "Ke gwauruwa, ja jiki ki bani wurin zama kusa da mata ta mana". Sum-sum-sum na mike na bashi kusa da matarshi, a zuciyata ina da na sanin biyo su don kamar da gayya suke yi, don su ci min fuska. Sai dai tun can ina girmama Yaya Bashir, saboda yadda baya nuna bambanci tsakaninmu da Zanirah da kowa cikin gidan Hajjah. Na hada hannuwana biyu na tallabe haba ina kallon su suna barkwancinsu suna dariya, babu wanda ya damu da ni, kamar ma sun manta da ni a dakin. Takaici ya isheni, na mike zan fita, Aliyu ya ja gefen zani na zan gifta su. Na juyo amma ban yi magana ba. "Dama ba wani abu yasa aka yi kiran tare da ke ba, maganar liyafar Kaduna ce ta gobe, mu zamu sa ankon shadda (hilton) da su Ummi, ke kuma tunda kin saki naki auren (don bana ce an sake ki ba) sai kisa wannan". Ya nuna min leda bacco shake taf da kaya. "A wajen Maman Kaduna na amso miki cikin kayan da tsohon mijinki yayi niyyar baki tsiya ta hanaki kwantar da kai ki ci arziki, ya tattara ya barki bayan ya dankara miki sakin wulakanci tara rigis! Wai 3x3 =9. In basu yi miki ba ki fada aje a buda a canjo miki don babu abinda zai yi da su, in zai yi sabon aure na tabbata sababbi zai yiwa sabuwar matar duk da nasan ko zai yi ba nan kusa ba, don kinsan matuka jirgi mata ba damunsu suka yi ba, kullum a tsaye suke kwana cikin iska, ba lallai ya damu da yin aure nan kusa ba". Suka kwashe da dariya baki daya. Kallon Yaya Aliyu kawai nake yi ina lissafa shi cikin sahun boyayyun makiyana wadanda ke sanye da fatar damisa suna (pretending) ta akuya ce. Yaushe Yaya Aliyu ya koma haka? Yaushe ya zabi Fa'iz ya barni? Hawaye suka zubo min wadanda duk kokarina na kasa maida su. Naso insa kai in wuce ba tare da na ce dasu komai ba, amma zuciyata ta ki amincewa ko da ban iya na rama ba, bazan nuna karaya ba. "Koda bani da wanda zan aura a halin yanzu, nafi karfin suturar da zan sanya a jikina. Allah Ya hore min abinda zan dinka ma kaina inyi fitar bikin Ummi ko da bai kai nasu tsada ba a kalla dai ba za'a ce an ganni tsirara ba. Don haka ba sai na daura na Fa'izun ba, ko a sanda yake mijina bai yi arzikin da zai dinka min sutura ba, ya baro yi min sutura a sanda nake da bukatarta balle yanzu da igiyar ta tsitstsinke, alakar ta bi rariya. Don haka Yaya Aliyu, ina ganin ku nemo wanda za kuyiwa gorin sutura ba dai ni Fa'izar ba". [6/3, 4:13 pm] Takori: Suka sake kwashewa da dariya alamar 'game' din nayi masu dadi dukkansu. "Sai Hajiya Fa'izah!!!". Suka ajiye jinjina da hannayensu. Ganin sun mai da ni mahaukaciya na fito na barsu ina matsar hawaye zuwa falon Aunty Zainab. Fa'izah baby ke ja min zani, ban san sanda na tureta ta fadi gefe tana kuka ba. Aunty Zainab Maman Yaya Aliyu ta tare ni tana tambayar me ya faru nake kuka? Ina kuka na zayyane mata wulakancin da suka yi mani dukkansu. Ta ce, "Fa'izah duk ke kika jawowa kanki. Da kin kwantar da hankalinki da Fa'izu da duk hakan bata faru ba. Kin san dai duk cikinsu Fa'iz ya fisu komai har shi yayan kobon (Aliyun). Amma ki ka rufe ido ki ka badawa idonki toka da bala'i da rashin arziki har ya gaji ya tafi ya barki. Don haka baki da hujjar jin haushin su Ummi ko mazajensu anan". Kokari nake in danne tasirin maganganun Aunty Zainab a zuciyata ta hanyar turawa gidan Hajjah a dauko min wani tsalelen leshi na (pitch colour) asalin shi marigayi N.S ya dinka mani kudinshi sun kai Naira dubu tamanin da biyar, ya dinka min shi ne wai inyi fitar fatin bikin shekarar haihuwar wani abokinsa da aka yi a Kano mai suna Dr. Gadanya. To a lokacin a ranar sai na tashi da zazzabi, dalilin rashin zuwana kenan na linke na goge leshin na boye can kasan kayana. Ina da takalmi da jaka 'yan (Thailand) suma mahadin leshin duk ban taba sanyawa ba. Abinda yayi mani cikas inda zan samu goggoro ba tare da na kula wadanda muka yi amfani dasu a yau ba. A take na dau mayafi na fita, naje saloon aka gyara min kai da (setting) na burgewa na kuma je aka nado min goggoron yadda nake son shi (light pitch) aka yi min gyaran akaifa da wankin kafa nayi sumul da ni. Na dawo gida na kulle kaina cikin kallabi kai ba zaka ce an taba shi ba na hada kayan da goggoron na boye a sif din Aunty Zainab. Wurin sha biyun dare barci ya soma fizgata sannan su Ummi suka shigo ina kwance a gado, ta cire goggoronta ta kwado min, shi kansa goggoron kamshin turaren Bashir yake yi. Na ja wani wawan tsaki na ture goggoron daga kusa dani, ko me zan jiwa haushin oho! Tana so ta gaya min ne ta hada jiki da namiji, ko me zan jiwa haushin oho! Banza an bata sidin turawa shi ne zata zo ta yiwa mutane fiffika, har warin tabar da aka ce yaya Bashir yana sha take yi. "Banza mahaukaciya". Ban san sanda furucin ya amayo daga cikina ba. Tayi dariya ta ce, "Duk haukana ai ban kai ki ba. Yaya Bash ya ce a gaya miki kada ki samu damuwar rashin (partner) gobe don 'couple evening' ne za'ayi miki mijin roba da yaya Sa'id Ibrahim Bamalli". Ashariya naso danno mata, amma sai na fasa. Ta cancanci bakar magana itama, don haka nayi gyaran murya daga kwance. "Babban hauka ya wuce ka kaiwa miji kanka a soron gidan iyaye? Don haka ban fiki hauka ba, ke naki salon na zamani ne, nawa kuwa (old-fashioned) ne. Ni kam ku bar mijin robar ku na yafe ba a matse nake da namiji ba da har sai nayi riga malam masallaci. Party ba don kowa zani ba, sai don kar ku dauka wulakancin ku da cin fuskar ku ya hana ni sakewa ne ko ina bakin cikin rashin miji har hakan ya hana ni shiga mutane, ina fatan kin gane?" Ummi ta tafa hannu tayi dan fitoo, ta ce. "Yeho! Yarinya wallahi kinci a baki kyautar amsarki. Indai wannan shi ne hauka, don Allah a nada min sarautar mahaukatan duniya akan umarnin iyayena nake ba kuma zan taba ganin ba dai-dai ba, tunda na bisu, su nakewa biyayya. Ke kuma mai hankalin da yafi na kowa da kika tasarma kisan kai fa? Waima tukunna ina hankali ga matar da ta titsiye mijinta da duka da zagi ya saketa? Matar da ta dauki kwalba ta rotsawa mijinta ai ta tabbata tsinanniya". (Baki kasan me zaka fada baka san me za'a mayar maka ba-TAKORI). Zaneerah ma aka cire mayafi aka jefo min. Eh naji kamshin (212) din yaya Aliyu kam babu shakka amma itama ta cancanci a tanka ta duk dai da ban san ita din dame zata mayar min ba. "An dai ji kunya wallahi, tsofai-tsofai ga goyo ga tirtsetsen ciki amma ba'a fasa jaraba ba, shima Yaya Aliyun...". Daga labulen dakin yayi yana fadin. "Zaneerah ina wayata da na baki ki sa min caji?" Dif! Kake ji na dauke wuta, kamar ba ni ce mai magana ba. Ya dube mu suna ta sheka dariya kamar sun samu motsatstsiya ya ce. "Me take cewa ne?" Na mike gaba-gadi na dauki dankwalina na daura na bar musu dakin. Ina jinta tana cewa dashi. "Zaginmu take yi". Ya ce, "Baya tsiro ai, da tuni jikin nata mijin ba masaka tsinke". *** Washegari tun safe su Ummi ke shirin wucewa Kaduna liyafa, sai shirya kaya ake ana zuge (troller). Motocin da za su kwashe su zuwa Jabi Road basu zo ba sai bayan azahar suka shiga suka tafi da kawayenmu duka daga can ne za su shirya zuwa wajen da aka tanada don yin liyafar. Ina kwance a doguwar kujera ban ko motsa ba ina kallon fitarsu daya bayan daya. Yaya Aliyu ya shigo yana balle 'links' din hannun rigarshi ya ce da Zanirah. "Madam, muje ko?" Ta tashi wata tikisa da ita kamar alkubus, shi kuma aka sakalo hannu kugunta aka tallafeta, a haka suka fice ko kallona basu yi ba, suka fice. Inda ya bude mata gaban 'Porsche' dinsa ta shiga, ya rufe ya zagaya shima ya shige. Bashir aka kama hannun amarya mai kama da Princess Diana don kyau da daukar ado suka fice. Har sun kai kofa ya juyo yana ce da ni. "Af, gwauruwa, mijin robarki fa yana jiranki a waje Yaya Sa'idu, an baki kaya don kidifiri kin ki amsa. No worries, na jikinki ma inaga ba laifi, kya samu waje ko tebirin iyaye da su". Wani gululu yazo ya tokare ni yaki wucewa, ya tsaya min a makoshi, amma Fa'izah (is always) Fa'izah, ina da 'ki-fadi' sai na ce. "Allah Sarki Yaya Bashir ka sallami mijin robar Fa'izah ko babu shi Fa'izah (can survive), kasan mace Allah Ya yi mata juriyar iya rayuwa ba tare da namiji ba, namijin ne bai iya rayuwa mai dadi sai da mace. I.e namiji zai saki mace, ta zauna gidan iyayenta ba tare da ta yi wani auren ba kuma ta zauna lafiya. Amma shi namiji a ranar da yayi sakin ma zai iya kawo wata, ka gane?" Ya ce, "Ohonki kuma! Tsoron shan kunya ya hanaki zuwa (party) baki da sauran bakin surutu". Da haka ya fice. Na mike tsam bayan fitarsu nayi wanka, na dauko lesi na na sanya, na saki dogon gashina a gadon bayana, na karkata goggoro na tsayar dashi dai dai goshi na. Na janyo takalmi da jaka na cikin kwalinsu mai tudun dunduniya siririya da siririyar igiyar daurewa na fitar na sanya, na rike 'purse' din mahadinsa wadda kudin mota kawai na zube a ciki. Nan da nan na hau walkiya kamar wata dan daren goma sha hudu. Na kawo (fashion earing) kalar adon lesin na daura (shimmering pearls) hannu, wuya, kunne da idon sawu sai walainiya nake duk motsin da nayi. Ni kaina yau nayi mamakin yadda nake, ban taba tunanin haka Allah Ya kyautata surata ba sai yau. Na fito harabar gidan Baba Na'ibi babu kowa don haka na tura wani almajiri yayo min hayar taxi kafin minti goma sai gashi ya dawo cikin motar tare da mai taxin. Na ce da mai taxin ya yi duk iya gudun da zai iya ya kaini (Indoor-sport hall) na garin Kaduna cikin awa daya, ko nawa ne zan biya shi. Nan da nan ya ce in shigo mu tafi. Dakin taron ya cika ya batse babu masaka tsinke da kyawawan iyalin A.B tabbacin a yau mallawan na biki kasurgumi da basu taba yin kwatankwacinsa ba. A cikin tafiyar nutsuwa na shiga ratsa taron jama'ar suna kallona tabbacin basu tsammaci zuwana ba ma balle wannan shiga ta firgitarwa. Ashe wajen cike yake da abokan Fa'eez na Kad-Poly irin su Surajo Nuhu wanda a halin yanzu ma'aikaci ne a Central Bank da wasu daga cikin abokan su da yawa suka mike suka tarboni muka jero tare sai tafi suke yi da dariyar farin ciki, yayin da Sa'adu Bori dake cin kasuwarsa a wajen ya karkatar da akalar wakarsa gareni ya kyale su Ummi, cewa yake. "TAKAWARKI LAFIYA GIMBIYAR ABUBAKAR FA'IZU GIWA... AMARYA FA'IZA AMANAR FA'IZ GIWA...". Suraj tunda na tako kafata cikin (hall) din yake min (spraying) da dollers madadin Fa'izun su kenan. Ni kam ko a jikina, a raina fadi nake wahala ce bata ishe ku ba, ko kallo basu isheni ba. Wajen ya hautsine da kirarin abokan Fa'iz masu video da masu camera suka juyo da akalarsu kanmu gaba daya abokan Fa'iz daukana suke hotuna wasu vedio da wayoyinsu. Ina kallon bakin su Yaya Aliyu dake (high-table) yaki rufuwa, haka Mama da tarin hamshakan matan Kaduna da ta gayyato. Anan Yaya Rabi, Aunty Hauwa da Mama da kanta suka taso suka tarbeni suka hana ni isa ga mazaunin su Ummi. Girgiza kai nake cikin son kecewa da kuka ina yi musu nuni da ka su barni in wuce, amma sunki hakan. Mama ta rikeni gam-gam, haka Ummi da Bashir, Zanirah da Yaya Aliyu tasowa suka yi daga mazauninsu ya saura babu kowa a gaban Sa'adu bori cikin filin sai mu 'ya'ya da jikokin Hajjah da kawayen Maman Kaduna sai ko Surajo da ya rufa min asiri suka shiga yi mana "spraying" ni da Surajo sai ka rantse da Allah shi ne angon nawa, kazalika Ummi da Bashir, Zanira da tirtsetsen cikinta da Yaya Aliyu rungume da ita, duk suka bude bakin jaka suka shiga yi mana 'spray' tako'ina. Dadi ne ko mene ne ya yi min yawa, sai gani kuka ya kece mani. Tausayin Mama har kokon raina da jinjina kaunar da take mani na kasa jurewa nima ban san dalilin tausayin nata da ya rufeni ba, na zame da gudu na karasa mazaunin su Ummi na zauna na kifa kaina a tebirin na shiga kuka mai yawan gaske wanda ni kaina bansan dalilinsa ba. Suraj ne yazo ya zauna a kujerar Yaya Bashir ya ce. "Fa'izah, Fa'iz bai kyauta ba na sani, don me ya yi mana haka? Rana irin wannan mai dumbin tarihi ka tsallake ka tafi wani aiki kai kafi kowa aiki?" Haushinsa ya kara kamani da shisshigin da yake ta yi mini tunda na sako kafata a filin wajen nan shi bai yadda ba asiri ya rufawa abokinsa, kuma abin kirki yayi. Na dago idanuna jike jagab da hawaye, "Kada ka kuma yi min zancen wani Fa'iz, nazo (partyn) nan ne don Ummi da Bashir, don me zaka zo kana tambaya ta wani Fa'iz bayan mun rabu tuntuni?" Dariya Surajo ya yi, "Aradu bonono Fa'iz yayi miki wai rufe kofa da barawo, waye ya ce miki Fa'iz zai iya sakin ki? Ko jiya shi ya kirani daga England ya ce in taimake shi inzo in tsaya tare da ke, bai yarda da kowa ba cikin abokanmu sai ni. Wane irin saki babu ko dadin ji? Kina hauka ne?" Wani irin rugugi naji cikin kwanyar kaina, da kyar in ba motsin kwakwalwa bane. Na zazzaro ido ina duban Surajo ina auna abinda yake fadi cikin hankali da tunani. Nasan Surajo mutum ne mara wasa, na sanshi da can don ya so Ummi aka nuna ba za'a bashi ba ya hakura. Abubuwan da suka faru suka shiga dawo min sabbi kar, wato yanayin Fa'iz bai nuna damuwa ko bacin rai ba a sanda yake min rubutun cikin takarda, babu wata alama ta nuna damuwa a fuskarshi. Me ya hana Baba bai lallasa ni ba, kuma su Aunty Rabi babu wanda ya yi fushi dani a lokacin? Sai ma cewa da tayi in taso mu tafi bikin Ummi Giwa? Me ya hana ni karanta takardar da kaina abin kamar tsafi?" Raina ya yi mugun baci, hankalina ya jirkice, idanuna suka kada suka yi jawur suka wani irin cicciko da kwalla. Suraj Nuhu, ya yi danasanin karambaninsa, ya tabbatar ya yi babban kwafsi, kuma abinda ba'a aike shi ba don son ya burge. Ya shiga in-ina yana fadin. "Fa'izah da gangan nake, na rantse miki bamu yi maganar komi da Fa'iz ba, ni na kawo kaina...". Ina! Surajo ya barota domin kuwa mikewa nayi gaba dayana tsam nayi hanyar fita, yayin da ya biyoni yana magiyar in saurare shi, amma kurar da ta debo shi ban kalla ba. Su Ummi suka dakata da abinda suke yi suka biyo mu da idanu. Aliyu ya saki hannun matar shi ya biyo bayanmu, ya riqo hannun Suraj ya ce ya rabu dani, kana ya haushi da fadan. "Don me yasa ka gaya mata Surajo? Wa ya aike ka yi mata zancen Fa'iz? Ka san haukar Fa'iza kuwa? Muna zaman zamanmu lafiya ka sayo mana tashin hankali". Surajo cikin matsananciyar nadama ya ce. "Ni ina na sani? Na gaya mata ne kawai Fa'iz ne ya yi min waya cewar yana Wales inzo in tsaya da ita, shi kenan abinda na fada". Yaya Aliyu ya dafe kai yana fadin, "Shi kenan Surajo ka baro mana likin, sai gyaran Allah. Wallahi ko lallashi ba zan je ba ta je can duk inda zata je zata dawo da kafafunta, ai ba yau ta fara ba”. Da daren washegari aka raka Ummi gidanta a Kabala Custain. Washegari Zanirah da Aliyu da ‘yarsu Fa'izah suka wuce Lagos, na Giwa suka nufi Giwa, na Zaria ma haka, haka na Kaduna. Miftahu da Ya Rabi suma suka dauki hanyar Kano da yaransu biyu, amma Ya Rabi ta ce da Yaya Mufty su tsaya Zaria su ga halin da nake ciki. Hajja kam ta ce da su don Allah kowa ya kyale ni inyi kida na da rawata ni kadai, kada wanda yaje inda nake balle ya wani lallasheni in bata masa rai a banza. Amma Ya Rabi ta kasa jurewa. Ko cikin 'ya'ya Fa'iza ta daban ce a wurinta, tana da matsayin da babu mai shi cikin tarin 'ya'yan nata. *** Da na baro Indoor Sport Hall Zaria na nufa a taxi bana ko ganin abinda yake gabana don tsananin takaici da tashin hankali. Fatana inga takardar sakin nan nawa da idanuna in karanta abinda ke ciki. Har aka zo kofar gidanmu ban sani ba ina sharar hawaye da dankwalin leshi na, sai da mai taxi ya ce. "Hajiya, ba nan ne gidan ba?" Na bude na fita na fiddo kudin da ban tsaya kirgawa ba na dai tabbatar yafi abinda zai nema na zube mishi a kujerar gaba nayi ciki. Na danna kararrawa (door bell) Momi ta zo ta bude duka hannuwanta cude da fulawa ina jin alkubus take yi. Ganina haka hajaran majaran fuska babu alamun rahama ta tabbatar cikin ranta da kyar in ba (bomb) din ne ya tashi ba. Ta matsa min hanya na shige, ta koma kicin ta ci gaba da aikinta. Gidan babu kowa sai Walid autan Momi, duk suna Kaduna cin biki. Na fadi nan bisa carpet na shiga kururuwa kamar na rasa iyayena biyu a lokaci daya. Momi bata ce min cikanki ba, haka ko lekowa bata yi ba. Wannan ya kara kunna ni, na mike na shiga tamaula da kayan falon su filillikan kujera, flower rose. Ganin ina shirin yi mata ta'adi da kayan kallonta ta fito a fusace ta nuna ni da yatsa. "Wallahi-wallahi ki kiyayeni cikin gidan nan, kinga dai babu kowa, babu mai kwatar ki don haka sai inyi miki dukan tsiyan da zai taimaka ya dawo dake cikin hankalinki, don da alama Fa'izah ke dabba ce, dabbar ma ta daji wadda bata san ciwon kanta ba. Allah Yasa Fa'izu yankan kai yake yi, ya yanke naki kowa ya huta wannan bala'in". Na hade kaina cikin gwiwa bayan nayi fatali da goggoron. "Momi bai kamata kice min haka ba, duk abin nan da nake yi saboda in kare mutunci da martabar ki ne daga idanun wanda bai san kina da su ba, don ni ta tawa mai sauki ce ban dauki kaina a bakin komai ba balle in dauki wulakancin da Fa'iz ya shekara yi mini abinda zai hana ni shakar numfashi a duniya. Ba zan taba son shi ba Momi, ba zan taba ganin farinshi ba tunda ya wareki daga cikin iyayensa. Duk abinda yayi min a baya kin manta Momi...". "...Na manta don ubanki, sai ki sani in tuna! Wallahi ki ka sake yi min kururuwa a gida sai na kakkarya ki, kin kuma koma inda ki ka fito kinji na gaya miki". Sai na tura kai cikin kafafuna nayi ta rasgas kuka a hankali, babu mai lallashi balle wanda zan yiwa in huce. A kuma yanayin Momi na na tabbata zata aikata abinda ta fadi na sake na sake daga mata sauti. A haka Babana ya taddani, ya zauna cikin kujera yana fadar. "Kiyi kukanki mai dalili, yi kukanki da babbar murya Fa'izu bai sake ki ba! Da yake shi ya haifu cikin uwa da ubanshi ya san darajar iyayenshi da karfin ikon su a kansa. Allah Ya dawo dashi lafiya kafarki kafarsa, inda duk ya sanya kafa na rantse da wanda raina yake hannunsa". *** Kwana biyu aikina kenan ina abinda naga shine rangwame a gareni wato (kuka) duk na koma jemammiyata ta baya a dakin Abdallah. A haka ne Ya Rabi da Ya Mufty, kan hanyarsu ta komawa Kano sai gasu a Zaria, Aunty Rabi ta shigo ta iskeni dakin Abdallah, ta aje mayafinta da babynta akan gadon Abdallah, ta ce. "Kai! Fa'izah bakya gajiya, zuciyarki bata gajiya da kuntatawa kanta a banza a wofi alhalin hakan ba zai sa ba, kuma ba zai hana ba! Shin duka wannan na kiyayyar ne, ko na haushin Fa'iz dan albarka bai yi saki ba?" Nayi banza da ita, can kuma na ce. "Ki bani takardar in gani da idanuna". Da murmushi fal a fuskarta ta ciro takardar a jakarta ta ce. "Gata". "Don haka in zaki hutar da kanki da zuciyarki to ki hutar, in kuma kina ganin kukan ki da tayar da hakarkari da hankalin ki shi zai sa Fa'eez ya yi saki to anan kam kinyi kuskure. Haka in ma duka da kwalba ne shima aikin banza za kiyi tayi don kuwa Fa'iz jinin Hajjah ne, rabin zuciyarta, magajinta. Idan ya ce 'eh' baya taba dawowa ya ce, 'a'ah'. Shin don Allah in tambaye ki, meye abin ki ga Fa'iz?" Na dago sharkaf da zufa, kashirban da hawaye da majina bayan na karanta takardar. "Ai ba zaku taba gano aibunshi dani nake hangowa ba tunda danku ne, ba kuma ka taba ganin aibun danka komin muninshi ko munin halinshi. To tunda ba zaku gani ba da duk hujjar da na kawo to ni na tsane shi ne, bana sonsa, fakat! Da inyi zaman aure dashi gara min zama a dokar daji da bakin-kumurci. Allah da Ya halicce ni Shi Ya daura min kiyayyarsa da duk wani mai irin halayyarshi. Yadda kuma ake ikirarin shi jinin Hajja ne baya magana biyu sai a gaya min in ni tawa uwar shege na tayi ta kawo muku". Ya Rabi ta jinjina kai cikin kidima tana fadin. "Babbar magana. Ni na kawo kaina, dama ba yadda Hajja bata yi dani ba kar nazo ke mahaukaciya ce amma banji maganar uwata ba dole naji wohoho! Sai ki mutu kuwa! Muddin Fa'iz ya dawo kafarki-kafarshi zuwa Russia, wallahi nima na daina lallaminki, mu zuba mu dake aga wanda ya haifi wani. Dabba kawai, shashasha, mara hankali". Na ce, "Ko uwar Rasha ne ba zani ba, wallahi ba zani ba ko gunduwa-gunduwa za'ayi dani". Rabi tayi dariya, "Ai har uwar Rashar ma zaki, tunda matukin jirgi kike aure ina ne ba za'a saka ki a jirgi a kaiki ba?" Na ce, "Koda na rasa bawan Allah Dr. Nazir, mai ilimin da ya amsa sunan ilimi, banga me zanyi da direba ba Ya Rabi. Kamar ni in kare a mutumin da bai da ilimin komai sai na tuki? Direban tasha, wallahi na yi asara!!!". Rabi ta ce, "Kin kuwa yi asarar. Yanzu ke ko babur zaki iya tukawa ne balle aje ga mota zuwa jirgi? Ke kinga shegen bakin ki baya mutuwa, ni na gaji da magana don ba malamar jami'a bace. Ranar da ki ka bi Fa'iz daga ke sai shi na tabbata murus bakin zai mutu mu don kin raina mu ne ki ka cika mana kunne da babatu. Don haka sai anjima, mijina yana jirana. Sai mun zo rakiya filin jirgi...". Tamkar ta soka min mashi a kirji haka naji. "Ko kuma an aiko muku da sakon mutuwar danku kunzo zaman makoki ba? Ki sani, ranar da duk Fa'izu ya yi gigin sake sako kafarshi cikin gidanmu kamar yadda na dauke kafata daga nasu gidan, wallahi sai buzunsa Ya Rabi!". Ta ce, "Ko? Lallai kin fitsare, inama ina nan za'ayi wannan (BOXING)? Kai da na kadawa (Winner) tuta. In kuma kanwar ta kar tsamin ne sai kiyo min waya inzo jinyarki". *** Zaman Zaria fa yayi min zafi, Walida, Abdallah duk suna makarantar kwana. Kausar da Walid makaranta suke zuwa safe da yamma. Babu Ummi babu Zanirah balle tsohuwa Hajjah mai samu farin ciki. Ko da yake Hajjah ni na gujeta don a ganina ita ce ummul-haba'isin sanya rayuwata cikin halin kuncin da take ciki bayan shafa min bakin jini da hakan ya yi a idanun iyaye da 'yan uwana. Daga uwata har ubana kowa fushi yake dani, Walida kadai ke kula ni a gidan, haka nan kullum Baba zai fita sai ya ce. "Tunda haka kike so, wato ga dakin uwarki ga naki, inta wuce dakina ki bita da ido kina kissime-kissime ai sai kiyi ta zama". Wannan magana ba karamin kona min rai take yi ba, tun ina kuka har na saba. A zuciyata kuwa Allah Ya isa ga Fa'iz tafi dubu biyar. Na rame, na fige, na zama 'yar firit dama jikin ba wani jiki ba. Nayi niyyar komawa Giwa amma na kasa saboda kurarin da nayi a baya cewa ba zan sake zuwa gidan Hajjah ba. Wuri daya ne nake tunanin idan naje zanji sanyi, wato wurin Maman Kaduna, to amma in ina da kunya ai bana dosheta ba alhalin kiyayyar danta na neman zauta ni. Ko babu komi ranar da Fa'izun ya ga damar dawowa me na isa nayi mishi akan idon uwarsa? Gara dai ya kwaso jiki ya kawo namu gidan. Haka Zanirah da Aliyu suka yo min waya wai hakuri suke bani abinda suka yi min ranar bikinmu a Giwa su wasa ne suke min. Tsaki nayi na kife wayar nayi tagumi da hannu bibbiyu. Bayan kwana biyu kuma, sai Ummi da Bashir suma suka bugo, amma su ba hakurin suke bani ba, korafi suke wai naki inje inga gidansu, to inzo in raka Ummi awo tana da ciki dan sati biyu. Na ce, "Sai ku bari ya cika wata daya tukunna mu fara zuwa awo, kunji ko 'yan abu kazan uba marassa kunya". Ummi ta ce, "Da fatan (this very big) ashar (is for me alone not with my husband) don mu albarkar miji muke nema ba ma zaginsa". Watanni biyu suka shude tun ana zuba ido har kowa ya gaji babu Fa'iz babu duriyarshi, babu ko wayarsa. Don haka na yanke shawarar tunkarar Baba da shawarar da na yanke, wato komawa karatuna a Kano. Da farko baban ya fara ne da zunduma min zagi bayan ya gama saurarona, kana ya ce. "Sai dai in karuwanci kuma za ki sannan in barki, tunda kin ki zaman aure. Sannan ina mai tabbatar miki muddin ya kasance wani mummunan abu ne ya samu Fa'iz sakamakon raunin da kika yi mishi da kwalba, to ki tabbata sai na rotsa miki kwalbar 7up a wannan kodaddiyar fuskar da kike tinkaho da ita. Kazalika in Fa'iz yayi zuciya ne yaga cewa gara ya fasa auren, sai na dauke ki ke da kayanki na kai mishi sadaka, ko aikace-aikacen gida ne kiyi masa. **** A WALES (UK) A bakin wani (swimming pool) dake cikin hotel din da suke ciki cikin birnin Wales din kasar Ingila, bisa fararen kujeru da ‘yar jar lema da tayiwa kujerun inuwa ta rage hasken hantsi daga idanuwan wadanda ke zaune cikinta. Pilot Fa'iz Giwa ne da Maajid da Johari tare da wasu abokan su wadanda duka matuka jirgin sama ne ke zaune suna karya kumallo bayan sun fito daga (interview) din da ta kawo su kasar Ingila da British Airlines. Maajid na shan (tea) cikin wani kankanin kofi, amma hankalin shi naga Fa'iz dake faman juya cokali cikin (coffee) mai zafi idon shi na kan wata siririyar baturiya dake sanye cikin dan kamfe da 'bra' kadai, tana tafiya lange-lange kamar zata karye saboda rashin kauri da kumari ko kuwa kamar da an busheta da baki zata fadi don sirinta. Amma a zahiri, idan ka dubi cikin kwayar idanunsa ba ita yake kallo ba, idanunshi ne kawai a saitin da take, tsabar tunani ke jagwalgwala kwakwalwarshi wanda kuma ke neman fitar da shi daga duk wani jin dadi da yake ciki ya kuma zamo barazana kuma ga walwala da farin-cikin sa, harma da nutsuwarsa da hayyacinsa cikin duk al'amuran da yake gabatarwa tun barowarshi gida wanda ba wani abu bane face kanwarsa/matarsa FA'IZAH A.A GIWA. Wadda damuwa da al'amarinta da neman sanin hanyar warwarewar damuwar al'amarinta da shi ya zamo wani abu kadai da ya tsaya ya yi karantsaye ya addabi rayuwarsa. Har yake neman zautashi ba don ya kasance jarumi akan komai ba musamman wajen shanye damuwa komin girmanta. (Still) idanunshi na kan Ba'ireshiyar cikin rashin sanin abinda yake yi ya dauki attaruhun kwalba ba tare da ya ankara ba ya zuba cikin kofin Gahwarsa ga zatonsa sukari ne yake zubawa. Maajid na kallon shi bai hana shi ba sai ido da ya gwalo kamar za su fada cikin kofin shayinsa. Pilot Javed Saddyqy ya dubi Maajid cikin yamutsa fuska tare da nuna Fa'iz din da abinda yake yi da baki. Maajid ya kada masa ido alamar ya kyale shi. Idon shi daina kan Baturiya wadda ke ta faman yi mishi gizo da Fa'izah surarta na rikidewa tana zama Fa'izah. Ya sake daukar cokali ya motsa shayin yana shirin kaiwa bakinsa. Anan ne Suhayl Khan mutumin India ya ce da Saddiqy wanda shima Ba'indiyen ne cikin harshen Tamil. "Fa'iz ya samu makuwa ne halan?" Alama Saddyqy yayi mishi ta yayi shiru ta hanyar daura dan yatsarsa bisa lebensa, a lokacin yana rike da kofin ne a hannunsa amma tsayin mintuna uku bai kurba ba idanunshi akan Baturiya. Anan sai Javed ya sanya kafa ya dan take mishi yatsun kafarshi dake kusa da tasa, ya ce. "Ba zaka sha bane?" Fa'iz ya kai kofi da azama bakinshi ya yi mishi kyakkyawar zuka. Ba shiri ya saki kofin a kan tebirin ya ce. "Aaah!". Suka kwashe da dariya gaba daya, wadda zafin gahwah da zafin attaruhu suka hadu suka hana Fa'iz jinta duk da karfinta (dariyar tasu). Maajid ya samu abinda yake so, ya buga tebirin da hannunsa da karfi yana fadin. " Woman na nufin WO! MAN, ka shiga uku kenan. In har baka dauko Fa'izah ba kun zauna a garin nan tare Fa'iz kai ba namiji bane ungulu ne da kan zabo, duk wannan cika da batsewar naka [6/3, 4:13 pm] Takori: **** A ZARIA A wannan rana wadda ta kasances asabar din karshen watan Agusta cikin 'Area One', Walida da Abdallah duka suna gida sunzo hutun karshen zangon karatu na biyu daga makarantun su daban-daban. Ina kwance cikin dakin Walida wanda yanzu ya zama nawa tunda ita ba zaman gidan take ba, sanye da riga da zani na atamfa mai karshen tsada (Exclusive Sharaton) ruwan ganye mai ratsin hoda, kaina ban daura kallabin atamfar ba yana dai ajje gefen gadon, na hade gashin kaina cikin tafkeken 'hair-bound ina karanta sabon littafin Takori ne mai suna 'KWANA SITTIN'. Zuciyata ta tafi gaba daya cikin rayuwar (schezophrenic_Safeenah) mai tsananin ban tausayi. A wani bangaren, ba Safeenar nake tausayawa ba kamar Kabir Danbatta, na rasa shi da Dr. Dangi wa yafi dacewa da amsar ragamar rayuwar Safeenah? Kowannen su masoyinta ne na hakika. Muryar oyoyon da Walida ke yi ya katse min karatun, na bi hadaddun jakunkunan da Shu'aib ke shigowa da su dakin namu yana dora daya kan daya da kallo ina kissimawa cikin raina, wane irin baki ne muka yi masu tafe da jakunkuna 'classic' haka kuma har dozen? To kwana nawa suke nufin za suyi a gidan namu? Kamshin sassanyan turaren (212) na maza ya sirnano cikin hancina, wani irin kamshi da ban taba jin mai sanyi da dadinsa a duniya ba. Wadanne irin baki ne momi tayi haka? Abinda nake tambayar kaina kenan. Daga inda nake kwance na jiyo muryar ma'abociyar ginshira, na tambayar Walida ina Momi da Baba? Walida ta ce, "Momi na gurin aiki, Baba na cikin makaranta. Amma Yaya Fa'izar tana ciki tana karatu". Da murmushi fal a fuskarsa ya ce. "Karatu? Ko dai kuka Walida?" Ta ce, "Wallahi karatu take, kullum ma karatu take, ta je kasuwa ta sayo littattafan TAKORI na da dana yanzu, su take karantawa kullum, ta daina kukan tuni...". Muryar FA'IZ, FA'IZ GIWA, FA'IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA! Da kwarin gwiwarsa ya yi sallama a dakin cikin 'husky voice' din da Allah Ya yi musu baiwarta zuri'ar Abubakar Bamalli Giwa bakidaya. Ya samu wannan kwarin gwiwar ne daga labarin da ya samu a bakin Walida masu nuna na kwantar da hankalina tunda har ina karatu? Duk da kwakwalwarsa bata fahimci littattafan TAKORIN da Walida take bayani akai ba, ya dai fahimci NOVELS ne wanda ba zai ce na Hausa ne, na Turanci ko na Larabci ba, tunda bai san mene ne ma'anar TAKORIN ba, bai ma taba jin kalmar ba cikin kowanne yaren. Abinda ya fahimta shi ne TAKORIN 'is an author' tunda yaji ance NOVELS dinta. Banda wannan kwarin gwiwar da ya samu ya samu karin na Momi da Baba duka basa nan yadda zasu ji dadin babbaka juna a wuta idan ta kama. Babu mai ceton dayansu. Yau za ayita ta kare (he can no longer tolerate it anymore!!! Kamar yadda ya ce da Mama ne ya zo daukar aurensa (dead or alive) haka yake har zuciyarsa. In har littafin labarin SAFEENAT MAHMOUD ALKALERI wato KWANA SITTIN na Sumayyah Abdulkadir ya amsa, to nima Fa'izar da ake yiwa sallamar na amsa. Ya shigo kansa tsaye Walida na biye dashi kamar bakinta zai tsage don murnar ganinsa ta iso har gadon da nake kwance, da murnarta take fadin. "Aunty Fa'izah ga Yaya Fa'iz!". Wani irin kallo nayi mata wanda nake jin tunda Momi ta haifeta babu mahalukin da ya taba yi mata shigensa, ba shiri ta juya har tana cin karo da (stool) din madubi, saura kadan ta kifa. Da sauri Fa'iz ya riko hannunta ya rike gam. "Ina zaki matas? Ke da nazo muyi zance? Zauna hira za muyi kafin su Momi su dawo". Walida a daburce take, ya jata suka isa har gefen gadon da nake kwance suka zauna har rigarshi ta rufe min kafa kadan. In banda kamshin sassanyan turaren shi ba abinda ke tashi a dakin. Ya bige da tambayar Walida sha'anin makaranta tana bashi amsa a darare, kokarin zamewa take ta barmu yana kara shimfido mata tambayoyi akanta da kannenta su Waild, Kausar da yayanta Abdallah da nasu karatun. Ganin ba zai barta ta tafi ba ta ce, "Yaya Fa'iz bari in kawo maka ruwa da lemo in kaiwa yaya Shu'aib abinci falo". Ya ce, "Kada ki damu Walida, na cika cikina a Kaduna, haka shima Shu'aib. Yaushe Momi za ta dawo?" Walida ta kalli inda nake bamu hada ido ba, amma taga yadda kwayar idanuna suka kada suka yi jajawur, numfashina ke sauka da sauri-da-sauri har wani irin huci nake kamar mesa babu rahma cikin su dai-dai da kwayar zarrah. Walida ta kara rudewa ta ce, "Na jona ruwa a (heater) Yaya Fa'iz ka barni inje in kashe kada ya kone fada Momi zata yi min". Ya ce, "To kiyi sauri nima ba zama zanyi ba, sako zan baki wurin Momi sai mu wuce". Ta ce, "Toh". Da saurinta ta fice har tana sake tuntube da dokin kofa. Ya girgiza kai ya mike ya sauke ido a kaina, tsayin mintuna biyu yana kallona kawai babu ko kiftawa. Nima kallonsa nake, wani irin kallo da ni kaina na kasa fassara shi, na takaici ne ko na kiyayya koko na gara da Allah Ya kawo ka? Ni kaina ban sani ba. Daga ni har shi babu mai niyyar daina kallon, duk da shima na kasa fassara nashi kallon. Shi ba kallon so ba, ba na kiyayya ba, ba na jin haushi ba. Yafi kama da kallon iko da raini. Ta wani fannin tamkar kallon, "Baki da yadda za kiyi dani" koko kallon "Nafi karfinki da ke da duk abinda kike takama da shi. (In another notion) kallo ne na "Yarinya na ci dubu sai ceto, kiyi duk abinda za kiyi" Sai da ya mula don kansa ya ce. "To ni Aunty Fa'izah zan wuce Giwa, tunda na iso Hajjah bata ganni ba, lefenki na kawo miki, wanda kowa ya kasa kawo miki tunda kin zama Faskari, mai faskarawa mutane kai. Sai tsarabar da nayo miki a tafiyar da nayi, tunda babu gaisuwa ko ta Musulunci a tsakaninmu. Daman nazo ne in shaida miki zaman nan ya isa haka! Ranar (monday) kwana ki shidda kenan masu zuwa ki kimtsa kayanki da duk abinda kike bukata za ki tare a gidanki kamar sauran 'yan uwanki, don gaskiya fisabilillahi kin takurawa su Momi da alama har su Walida kin takura musu, nima kuma kin takura min. Haka kawai ina da mata amma bani da maraba da gwauro. Gara mu kauce haka muma mu manta komi, da duk abinda ya faru a baya, mu fuskanci sabuwar rayuwar dake tunkaro mu, muka kuma bude ido rana daya muka ganmu cikinta. Wato rayuwar aure. Sai mu rungumeta, mu kasance cikin godiyar Ubangiji da neman dacewa duniya da lahira". Da ace Fa'iz yasan tashin hankali da bala'in da kalaman dake fita daga bakinsa suke kara jefani da ko da wuka a makoshi bai yi gigin furta su ba. Domin kalamai ne da ban taba jin mafi muninsu a duniya ta ba. (Hada rayuwa ta har abada da shi FA'iZ-ABUBAKAR) koko ince makiyina. Mugun dan uwa da kullum ketowar alfijir da faduwar rana sai nayi dakacen INAMA ban hada jini da shi ba. Wani kwayan mutum guda daya da ya maida mahaifiyata marainiyar wayonsa, ya maida ni kwallon takawarsa a duk sanda ya so, ko gare-gare abin wasan yara. Mikewa nayi gaba daya na littafin KWANA SITTIN ya fado daga ruwan cikina, na ce. "Da uwar wa zaka tafi wurin direbancin?" Tsalle daya nayi sai gani a bakin kofar dakin nayi maza na rufe na murza 'key' na zare shi na cilla shi waje ta taga cikin wani irin zafin nama da ni kaina ban san inada shi ba. Ya yi maza shima ya cafe mukullin cikin irin nashi (exceptional) zafin naman wanda yafi nawa kafin ya kai ga ficewa ta tagar. Ya shiga sosa keya da (key) din ya daure fuska sosai kamar ba shi ne ya gama maganar da yayi cikin raha ba. "Meye haka? Gafara ki bani hanya na wuce". Na ce, "Wucewa kam zaka yi ta, tunda har ka yi nasarar amsar mukulli. Amman fa bayan rubutun saki uku ris a gareni FA'IZA A.A GIWA". Murmushi ya yi, "Wannan ne kuma ba zaki samu ba har abada Fa'izah, har kuma yaumil-ardhi. Domin ban aureki don in saki ba. In haka ne tun farko ba zan fara ba. Karewa ma, ni ba lallaminki nazo yi ba kamar wancan karon, UMARNI ne ki hada kayanki ranar litinin za ki tare a gidanki kamar kowacce mace mai aure. Ba kuma neman afuwarki ko kiyi min uziri nazo ba tunda ke abu ba ya karewa a wajenki kamar cin kwan makauniya. Ki matsa na ce, tun hannuna bai kai fuskarki ya yi mata tabon da bata da shi ba...". Sunkuyawa nayi kafin ya kai karshen maganarsa na dauko littafin da Walida ta kammala rubutu dasu, na yago takarda a ciki na mika mishi. "Ko da can babu wani wasa makamancin 'game' ko 'April-fool' da ya taba shiga tsakaninmu balle yanzu da kowannen mu ya mallaki hankalin kansa. Za ka wuce din babu haufi, kuma babu makawa, amma fa bayan ka yi rubutun nan". Na sake mika masa takarda. Fa'iz ya sanya (key) cikin aljihun kaftanin shaddar dake jikinsa. "Kenan har wani hankali kika mallaka yanzun? Ko daya! Kina nan yadda kike; Jiya 'i yau, kazama, dakikiya, 'yar kauye, mummuna. Don haka daina cewa wani wai kin mallaki hankali, ina hankalin yake nan kana tura kanka cikin jahannama kana ji kana gani?" Na ce "In shiga wutar mana, tunda ba tare za'a sanya mu ba ina ruwanka?" Ya ce, "Naga alama abin naki nema yake ya wuce na rannan, to ba zan rubuta ba kiyi duk abinda za kiyi". Anan kam dankwalina na janyo nayi dammara dashi a kuguna kamar wata sabon hauka, na doshi Fa'iz da takarda har na iso gabansa. Sai dai kuma zuciyata cike da taraddadin murdaddun damatsan Fa'iz da na hango ta cikin kayan jikinsa. Ina tunanin idan ya cafke ni da su wa zai kwace ni? Babu kowa a gidan sai yara na kuma kama kofa na kulle? Da alama shima ya shirya yau. Idona ya kyallo min biro a aljihun gaban rigarsa, na cizgo shi, na matsa gabanshi sosai har muna iya jin hucin numfashin juna. Kallon zakaru masu shirin dambacewa muka tsaya muna yiwa juna. Sai na samu kaina da ganin wautata anan, shin in nayi duka ta ina zai shigi wannan 'giant' din? Fa'iz kato ne sosai mai tsayi da kauri, kaurin da ba kiba ke haifar dashi ba 'diet' ne da hutu na yanayin rayuwa mai nagarta. Don haka na fashe da kuka tabbacin Fa'izun yafi karfina kamar yadda ya ce, babu yadda zanyi dashi. Sai na ce a raina. "bari kawai kaifin harshe na ya zama makamaina". Cikin kuka na ci kwalarshi amma fa kada ki so ki tona bugun da zuciyata ke yi, na ce. "Idan har ka haifu cikin uwa da ubanka ka rubuta min takardar nan Fa'iz...". Ban kai karshen kalamina ba ya fidda hannu ya shimfida min wasu irin gigitattun mari hagu da dama. Na nemi ji na da ganina na wucin-gadi na rasa. Naga giftawar wasu taurari masu hasken dake tafiyar da ganin dan-Adam na lokaci mai tsawo, ji kake fauuu! fauu!! fau!!! Yasa tsayayyun kafadunshi ya ingije ni gefe guda na fadi warwas akan dandagaryar kafet. Ya nufi kofa ya zaro dan mukullin a aljuihunshi yana kokarin sanyawa jikin kofar, nayi kukan kura na wawuri abin zaman kwalliya (stool) na jefe shi dashi, ya same shi a baya. Yasa hannu ya rike kafadarshi ya kuma juyo cikin dan bude ido ya ce. "Kin gama?" Na tsala ihu na taso nayi kanshi da duka da duk iyakacin karfina da hannayena hagu da dama. Ganin duka wannan bai min ba, domin kamar ba jikinsa nake duka ba, sai na kai kaifafan hakorana damtsenshi shi, cewa yake. "Fa'izah baki da hankali ko?" Irin bude kofar da aka yi ba zato ya sanya Fa'iz hankadani tsakiyar gado wanda ke nufin da can dukan nawa da cizon nawa bai dameshi ba sai gudun kada a shigo a ga ina dukanshi. Gaba dayanmu muka bi kofar da kallo cikin firgita. BABA NE! Ya ce, "Kai amma Fa'izu anyi sullutun banza! Ka tsaya kanwar bayan ka na lallasa ka kana tsaye sororo, shashasha, sahorami". Cikin kuka na ce, "Baba shi fa ya mareni, yayi min dukan tsiya har da rufe kofa don ma kada wani yazo ya taimakeni, dubi yadda ya dauki tebirin nan ya kwada mini a baya...". Baba kam bai tsaya saurarona ba ni da karerayi na ya dauko dorinar da yakewa su Walida barazana da ita in sunyi laifi yayo kaina. Fa'iz ya kama bulalar da karfi ya rike, ya ce. "Haba Baba! In Fa'izah na haukan shirmenta bai dace kowa ya biye mata ba". Na ce cikin gunjin kuka, "Kai ne shirmammen, mahaukacin, amma ni lafiyata kalau". Baba ya yi salati, ya fisge bulalar daga hannun Fa'iz ya shiga tsula mini ta ko'ina ina ihu ina zagin Fa'iz ban fasa ba. Fa'iz ya sake damke bulalar ya ce, "Baba ya isa haka nan. Ka yiwa Allah da darajar marigayi kayi hakuri". Idanun Baba sun rine da bakin ciki da takaici, ya ce. "Fa'iz ko ka cikani ko in kakkarya Fa'izah da hannuna, ina amfanin wannan jarababbiyar yarinya cikin A.B?" Ya fisge bulalar daga hannunshi, ya ci gaba da shimfida mini da iyakacin karfinshi. Da Fa'iz yaga Baba na shirin illata ni (and he has no regret for it) Sai ya fado kaina gaba daya yayi min rumfa da faffadan kafadunshi, ya zagaye ni da hannayenshi ya rungume ya ce. "Sai dai ka nakasta mu tare Baba! Amma ba zan zuba ido a kashe Fa'izah akan gaskiyarta ba!!". Baba ya yada bulalar ya fice yana fadace-fadace, bai dai yi min baki ba, sannan bai yi tir da haihuwarta ba amma ya ce ni zakka ce a cikin A.B, wake daya mai shegen doyi, mai son bata musu zuri'a, to nayi kadan, ba'a haifeni ba. Na tattara dukkan karfina da yayi mini saura wurin ture Fa'iz da lullubar da yayi mini da jikinsa, na mike duk jikina yayi rudu-rudu yayi birdin-birdin nayi hanyar kofa. Fa'iz mikewa yayi ya riga ni isa ga kofar ya rufeta da nashi mukullin, cikin kuka na ce. "Ko kai maye ne Fa'iz ka saki kurwata hakanan! Bar ganin ka hadani da iyayena, Hajjah da dukkan 'yan uwa na har yanzu ina da sauran mai mara mini baya wajen ganin ka rabu dani ka sakeni da ka ki da ka so. Shin wai ni kadai ce mace a duniya ne? Koko cewa akayi daga kaina an daina haihuwar 'ya'ya mata? Ka matsa ka bani hanya in wuce tun baka jawo an fitar min da raina daga gangar jikina ba". Fa'iz yayi murmushi hadi da rausayar da kai cikin ginshirar tasa, ya gyara tsayuwarsa hannuwansa duka biyu zube cikin aljihu ya ce. "Ba ke kadai ce mace a duniya ba Fa'izah, kuma ba'a ce daga kanki an daina haihuwar 'ya'ya mata ba. Karewa ma, akwai mata da suka fiki komai a ko'ina cikin duniya. Sai dai ke kadai ce wadda aka jarabci zuciyata akanta, aka jarrabeni da sonta da kaunarta. Don haka ina mai baki hakuri ki saurari abinda nake son bayyana miki, ki daina daukar fansa a bisa abinda baki sani ba...". "Mene ne abinda ban sanin ba? Na kwana na hantse da sanin cewa ni ce mutum ta farko da ka fi tsana a rayuwarka. Dalilin ka na zuwa kace kana son nawa yanzu ne ban sani ba, ba kuma na bukatar sani. Abinda nayi amanna dashi shi ne... makiyin ka baya taba dawowa ya zama masoyinka sai in yana da wata boyayyar manufa akanka. To ALLAH YA FI KA!!!". Na karashe cikin rishin kuka wanda ke tafe tun daga karkashin zuciyata. Shiru Fa'iz yayi, bakina kawai yake kallo cikin mamaki, nawa da na kansa. Wata zuciyar na gaya masa ya hakura da Fa'izah ko ita ce autar mata, wata na tankwabe hakan. Cikin wannan halin kalamaina suka ci gaba da dukan dodon kunnensa. "Wanda duk ya baka shawarar wadannan gayyar tsiyar da tarin akwatunan shirgin ka za su sayi zuciyata wallahi yayi maka karya, domin ba tsirara ka ganni ina yawo ba, ka baro gini tun ran zane. Wanda duk ya ce maka hadani da iyayena suyi ta dukana shi ne zai sa in soka ya yi maka hudubar banza, domin babu abinda dukan Baba ke karamin baya ga TSANAR KA...! Aure kuma kaje ka rike, kayi ta rikewa. Ka ninka shi ba sau uku ba, sau dari. Sai dai fa kama daina mafarkin zan bika ko kofa ta kashi. In Allah Ya yarda, insha-Allah ba zan sake cewa ka sakeni ba. Sai dai jikin Fa'izah da ya kwadaitar da kai ga AURENTA ba zai taba zama mallakin ka ba. Ya gwammace ya zama na arnan bariki, 'yan daudu da 'yan ashana...da dai ya zama mallakinka". Ban rufe baki ba daga furucin naji saukar tafukan Fa'iz a fuskarta, mari ta ko'ina hagu da dama. Ya fisgoni ya angiza ni na fadi akan kafafuna, kamin in wartsake in gane abinda ya ci gaba da gudana babu Fa'iz a dakin sai takalman shi. Kamin inyi tunanin abin yi (next) Fa'iz ya shigo tare da Baba fuskarshi tayi jajawur idanunshi sun rine har wani blue-blue suke cikin bala'in da ban taba gani ba. Ya ce, "Fa'izah ga Baba, maimaita abinda ki ka fada mini yanzu a gabansa". Na fashe da kuka, "Ni me na ce? Na ce ne ba inda zani, ba zan bikan ba". Baba ya ce, "To-to ya isa haka". Ya duka ya dauki dankwalina dake yashe a kasa ya rufa mani aka, ya ce. "Oya, ku tafi kusan nayi, kada wanda na kara ganin kafarshi cikin gidana, in ba harkar arziki ta kawo ku ba. Tunda ka hana a dake ta me zan iya yi mata? Ni wannan yarinyar ta isheni jarabarta ta isheni, Ku wuce ku tafi gidanku don Allah don kiyayya kusa masu ku soke junanku, aure ba za'a kwance shi ba. Ke kuma Fa'izah inji kin saka kafarki wani wuri ba inda Fa'iz ya aje tasa ba sai na tsine miki albarka... Sai na yafe ki!!!". A firgice na cira kai na dubi Baba. Kuka nake har naji babu dadi, na gyara dankwalina, bana ko batun takalmi balle mayafi, tuni na riga Fa'iz kaiwa bakin mota, na bude baya na shige. Na kifa kaina jikin kujerar gaba ina rusa kuka na gani kasheni! A can cikin gida kuwa gardama ce tsakanin Fa'iz da Baba. Ya ce shi ba zai tafi dani ba a yanzun ya fasa. Ayi duba da halin da nake ciki. Wane farin ciki zai tsinta a tare dani?" Baban ya ce, "To Fa'iz in ka saki auren ne kamar yadda take so ka bani takarda wadda zan nunawa Hajjah da sauran dangi Fa'iza tayi zama mai dalili a gidana, domin Hajjah har ta fara nuna fushinta da zaman Fa'izah tare da mu bamu mikata Kaduna ba. In kuma kana aure, to Fa'izah bata kara zamar min gida ta kara kwana daga yau. In baka tafiya da ita inda kake kasan inda zaka ajeta amma ba dai gidana ba! Yarinya daya tal na neman zautar dani kamar ita kadai na haifa? Na gaji wallahi". Fa'iz ya sake kwantar da murya ya ce, "Baba Fa'izah ta rantse ba zata zauna dani ba. Ta yaya zan kaita inda ake ganin mutunci na ake girmamani ta dizgani ko ta rufe ni da duka don Allah Baba? Ni kam a kyale Fa'izah, ayi mata addu'a ta samu saukin bacin ranta kafin mu tafi. Amma bai dace in tafi da ita cikin wannan hali ba". Baba ya ce, "Na gama maganar nan Fa'izu, Fa'izah ba zata sake kwana mini cikin gida ba sai in baka aure. To wannan kuwa, bani da yadda zanyi da ita". Fa'iz ya fice fuuu shima nashi ran a bace. Ba haushin Baba yake ji ba, zuciya yayi mai cewa ya yiwa Fa'izah duk abinda take so don a zauna lafiya. Kamar yadda Baba ya gaji shima ya gaji. In so cuta ne to hakuri ma magani ne. Bai taba ganin yarinya mai taurin kai da taurin zuciyar Fa'izah ba da kullaci wanda baya jin lallashi. Ya bude kofar motar ya shiga ya zauna, har ya tayar da ita ya juyo yaga ban rufe kofar ba. Ya fito yazo ya rufe ya sake ta da motar aguje, ban san inda ya nufa ba sai dai jikina ya bani ba Kano bane, ba Kaduna bane. Ya manta shaf da Shu'aib dan rakiyarsa. Shima Shu'aib din yana kallon mu muka fita bai yi gigin binmu ba. Nayi kuka nayi kuka har na gode Allah, na kuma ba uku lada. Hawaye sun kafe, murya ta dishe, haka idanuna sunyi luhu-luhu. Don haka nayi shiru na zubawa sarautar Allah ido ta hanyar kurawa tsirrai halittar Ubangiji ido dake giftamu aguje suna tsere da junansu (bishiyoyi da dazuzzuka). Ko ma mahalaka Fa'iz zai kaimu, a wannan lokacin ban damu ba. Domin na fidda rai da rayuwar farin ciki tunda iyayena da suka haifeni ma basa so na, na kuma tsani rayuwar ita kanta muddin tare da Fa'iz zan yi ta. Na kuma tsani wani abu wai shi farin ciki ya sake ratsowa cikin rayuwata..