[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 1* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_________________________________* *_Da sunan Allah me Rahama da jinkai ina godiya ga Ubangiji da ya yarda Zan fara sabon littafi na me suna ZAN FASA KWAI Ubangiji ka tsareni rubuta abinda ya kauce da tuntuben alkalami kasa ya zamo wa azi da izna_* *Gaisuwa ga masoyan GIDAN IKO na kusa da na nesa Ina gaishe ku* *_Sai Uwata haj Saliha abubkar abdllh Zaria gaisuwar ta muddin Rayuwa ce Allah ya dafa_* "Talai Wai Ina Talai ta shige don tsohon wulakanci ta barni ina ta yage bakin kiranta? Tsohuwar ta taho da sauri tamkar zata kifa saboda Jin Kiran uwar gijiyar ta akalla tsohuwar zata haurawa shekaru sittin koma fiye ta taho da sauri har tana cin tuntube kadan ya rage taci da kasa. Ta wurgo Mata harara lokacin da take zubewa agabanta. "Gani hajiya kiyi hakuri Ina bandaki naji kina Kira tun jiya Wallahi ciki ke murda min sai faman zagayawa nake...... "Ai nayi Zaton samun wuri ne yasa Kika fara nuna min kinaji Ina kwakwazon kiranki kikayi min kunnen uwar shegu dama ba Dole ciki ke rude Miki ba komai Kika samu wawab kin abkawa ciki sai kace jaka? Wani Abu ya daki zuciyar tsohuwa talai Jin Wai yau ita take Kira da jaka Amma ya ta iya tunda Ubangiji ya zano abincinta akar Kashin wannan Mata me masifar izza wadda ko saboda izzar tata ne ma aka rada Mata suna da izzatu? Ta katseta da wata tsawa tamkar zata fasa Mata dodon kunnen "Da Allah Ni tashi ki Kai min jakata mota Kika sakani gaba kamar kin samu wata TV" Tsohuwar ta Mike da azama ta dauki jakar ta hannu wadda Isa da izza ke Hana Mata dauka Wai sai an Kai Mata duk in zata fita. Tabi bayan tsohuwar tana sababi inda tsohuwar kamar zata fashe da kuka saboda Jin abinda ake fada Mata ba Diya ba jika ma tayi da ita Amma saboda kawai tana Yar aiki sai ake sauke Mata kowane kalar wulakanci tamkar ita ta kawo talauci duniya. Ta bude mota ta saka Mata jakar ta juyo zata dawo ciki inda ta maido ta. "Na sallame ki ne kike kokarin juyawa? Wai talai me kike daukar kanki ne a gidan Nan? Akwai gadon tsohonki aciki ne? Tsohuwar ta rusuna tana Bata hakuri "Nace akwai gadon tsohonki aciki? "A a Babu hajiya na tuba ki yafe Ni nayi Zaton kin sallame Ni ne Amma ba Zan sake ba . Ta wurgo Mata harara "Idan na dawo na samu wankin tile din Bai fita ba sai kin sauya shi wallahi duk wata sai an biyaki kudinki Amma saboda kin kware a ha inci wankin tile ma sai kinyi cuta "Zan kiyaye hajiya adawo lafiya Taja tsaki taja motar ta fice tana sababi Tsohuwa talai ta juyo ta soma aikin wankin tile tamkar zata sabunto shi yadda ya faro har dai ta tabbatar ya fita kafin ta Kama wankin kayan hajiyar inda Kuma ciwon cikin da tayi magana ya kayar da ita abin tausayi tsohuwar amai da gudawa ya sarketa ta Fadi Kan shinfida tana kwara amai zawayi na bin shimfidar inda harira ta me aikin girka abinci ta kawo Mata agaji da Dan ruwan gishiri ta Kuma tsabtace tsohuwar cikin ikon Rabbi Kuma amai da zawayin ya tsaya sai dai ta kwantsame Abu ga tsoho amai da zawayi ba Dadi Sai San maraice hajiyar ta dawo inda ta iske talai akwance Babu lafiya Amma sai me? Sai sababi da masifa Wai lambone musamman da taga wankin da talai din ta fara ciwo ya kaita kasa Aiko ta SHIGA zubar da ruwan tijara Wai akan Dole sai talai ta taso ta wanke Mata kayanta Harira ta kalleta "kiyi hakuri hajiya wallahi Bata da lafiya kwance ta wuni amai da gudawa ke damunta Bari Ni na karasa wankewa...... Ta zabgowa harira wata ashar "Na tambaye kine gwana yar ka iya? Kauce daga Nan ko yanzu ranki yayi Baki Yar iska me shiga shirgin wani.... Tsohuwa talai ta taso tana daura Dan kwalinta ta fito dai dai da shigowar hajiya Mama uwar me gidan wadda tazamo dodan izzatu saboda masifarta Tsohuwa talai ta Yi Mata barka da zuwa inda izzatu ta Sha jinin jikinta Hajiya Mama ta amsa inda take duban talai. "Baki da lafiya ne talai? Wallahi kuwa hajiya amai da gudawa ne.... Ta dubi izzatu fuska ahade tasoma zazaga masifa... "Kuma shine saboda Rashin sanin kimar Dan Adam bakiyi tunanin kaita Asibiti ba saboda ba uwar ki bace? Ke Wai wace irin Yar iskace ne ? Maza ki sa akaita Asibiti ko ruwa akara Mata me aiki Ba baiwa bace sun taimake ki ba kadan ba tunda ke agidan ku Basu koya Miki komai ba "Kiyi hakuri hajiya Bari asa akaita ko kyamis ne..... "Asibiti za akaita ke in kinji naki ciwon kyamis kike zuwa? Talai tace hajiya ai naji sauki ma ba sai munje ba..... "A a talai kuje ko ruwa akara Miki Baki ga yadda Kika kwaltse ba? Haka ko akayi direba ya dauki talai zuwa Asibiti inda aka Kara Mata ruwa da magunguna suka dawo gida Inda hajiya Mama ta balle hancin tsiyar da ya kawo ta gidan Dan nata "Ina da labarin duk irin cin Kashin da kikewa masu aiki izzatu kin mace ko wacece ke? Don me Zaki samu mutane kiyi ta cin zarafin su don kawai suna muku aiki? To Bari kiji abinda ya kawo Ni gidan nan yau shekarar ki goma Sha biyu Nan gidan Amma ko batan wata bakiyi ba to na gaji da gafara sa Banga kaho ba a yau nazo da magana wadda zanyi akan ke da mijinki don haka maza ki Kira min shi yazo yanzu Ina jiran shi.......... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 2* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *________________________________* ..Hawaye ya tararowa izzatu Jin abinda hajiya Mama ke Fadi wata zuciya ta kuleta taji kamar ta tashi ta rufe hajiyar da duka sai dai Babu hali hajiyar zaune take da kuturinta. "Kukan banza ne kike kukan wofi. Yanzu Nan daga gidan saminu nake Ina shiga yara suka taho suna min oyoyo abin farin ciki duk inda na waiga Yan dugwi dugwi ne ke hawa da sauka ajikina shi wannan haka zai lalace akan ki ba zaiyo aure ba ? To maza ki Kira min shi kice Ina jiranshi... Ta wurgowa hajiyar harara kafin ta bude Baki cikin gadara da izza ta fara magana "Hakan da kikayi yayi kyau hajiya ku sama mishi mafitar da zata bulle dashi don nagaji Nima magana ce kawai banyi ba to tunda har Anzo inda Kika gaji hajiya zanso ayau koma yanzu ki tsinke igiyoyin aurena sai ki kawo mishi wadda zata Rika haihuwa duk wata ....... Hajiyar ta dago Mata hannu "kar ki sake ki zageni don na Fadi gaskiya..... "Ba Zan zageki ba hajiya Amma Nima ba Zan yarda ki fada min maganar da zata dameni ba kija bakin Ni Kuma Zan fassara Miki kowane kalar ciwo Zan fada Miki kalar maganin tunda na kula shekawa jaki shayi aikin banza ne ba iya Sha zaiyi ba.... "Ki Fadi komai damar kice Amma na rantse Miki sai an kawo wata mace agidan Nan wadda zata haifa Mana yara wallahi na gaji da sai dai kici ki kasayar "Ai hajiya Ni tuni na gano kece Baki gano ba kice Rabon a bankado abinda zai saka zuciya tashi Baki taba tambayar ko shi Dan naki ne ke da matasala ba sai dai Ni kuke kallo? To za ayi duk yadda kike so tunda watan da za ayi magana ya Kama wallahi za ayi magana Don haka yanzu sai kiyi hakuri baya gari Yana can kasar waje neman lafiyar da zata bashi Yan dagwai dagwai din da kike magana idan ya dawo sai kizo kuyi maganar kafin lokacin Ni na Dade agidan mu tunda nayi kawaici nayi hakuri ba ku San nayi ba to Ak ya dawo Ni kuma ya sallame Ni Hajiyar tayi shiru tana tauna maganar izzatu kar dai matsalar daga AK din ne na Rashin haihuwar? Karfa allura ta tono garma Kai Bata zaton hakan Kuma ko daga gareshi ne ai akwai magani sai agwada. Da haka hajiyar ta taso inda talai tayi Mata rakiya har wurin motar ta suka tafi ita Kuma ta juyo inda Kuma izzatu tace dawa Allah ya hadata ba da talai ba? "Kinje kun zageni ke da hajiya to in zata burgeni Mata hudu ya kamata ta aurowa ak haihuwa Kuma sun Dade basu haife mishi singa da kasuwar kurmi ba Haka tayi ta sababi tamkar zata aro Baki ta hada da nata talai dai ta wuce daki ta barta Kwana biyu tana cikin takaici da bakin cikin da hajiya Mama ta guma Mata inda take ta jiran zuwan me gidan don ayi ta ta Kare Wai ramamme ya zagi maye Ya Kira wayarta yake sanar da ita kanwar shi asma,u ta haihu har gobe ake suna hajiya Mama ta kirashi ta sanar dashi inda ya bukaci ta dauki kudi dubu hamsin ta kaiwa asmau kudin aski "Gaskiya ba zanje ba ak sai dai na tura talai ko harira Amma Ni dangin ku nayi wuri na aje su gaskiya saboda nagane basa kaunata........ "Babu komai tunda har Kika iya fada min kinyi wuri kin aje dangi na na gode....... Dit ya tsinke wayar inda Kuma taji lallai Bata kyauta ba kamata yayi ta amsa mishi da to in yaso sai ta tura wani kawai don haka sai ta Kira wayar tana bashi hakuri cikin kissa da kisisuna har tana fadin tayi kuskure yayi hakuri da haka suka aje wayar t Washe gari ta nufi gidan Asma u inda ta tabbatar ba zasu kwashe da marar arzikk ba musamman dangin shi dake da burin yada Mata bakar magana to yau Suma zata nuna musu uwar su ma dai dai take da ita bare su kanan shegu Da haka ta fice ta iso gidan sunan Wanda ya ciki ya batse da Yan uwa da abokan arziki ta fito mota tana shakar iska dai dai inda ta hade fuska don kar su Raina ta....... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 3* *___________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *__________________________________* ...Sanye take da leshi me kalar ruwan kasa me cizawa wato coffee brown kafarta sanye da takalmi me tudu Wanda ya Kara Mata tsayi hannunta cike da warwaraye da zabban zinariya yayinda kwalliya ta taimakamata afuskar ta don in baccin kwalliyar to da ba zata kallu ba ahalayya Kam taci sunan ta izzatu don izgili da dagawa ba a magana hakama Bata Faye shiga mutane ba saboda tana ganin ta zarce hada kafada da mutane musamman idan Basu da kumbar Susa don kuwa mijin da take aure eng abdukarim fitaccen Dan kwangilar dake samu kwangila daga gwamnatin tarayya Wanda sunan shi ya tumbatsa aduniya shine barazanar ta da homar ta sai dai inda matsalar ta take shine tsayin shekaru Bata haihu ba inda har dangin shi ke yada Mata magana da habaici da arashi karshe ma said ga hajiyar shi da kanta ta wanko kafarta ta wanke ta soso da sabulu inda itama ta daura damarar yakar duk Wanda yace Mata kulle zata ce mishi Cass Ta shigo gidan sunan inda ta iske ana ta sabga ta dauke kanta tana hura hanci Da yawan Matan dake gidan suka bita da kallo suna kallonta awatse itama tana musu kallon sai dai aganni abarni ko Kuma bakin ciki ya kashe mutum. Kai tsaye ta shiga dakin me jegon Wanda yake cike da Yan uwa da dangi Tamkar wadda ta shigo cikin wata najasa haka take ta shakar hanci tana dauke Kai inda asmau take kallon ta tana mamakin daukar kanta Bata gaishe da kowa ba ta jawo kudin ta mikowa asmau "Gashi inji AK yace akawo Miki Yana Miki barka ta Mika mata tana dauke Kai. "Madallah na gode inji asmau ta fada tana Miko Mata jariri Shafa tace "Kai Yaya ak ya soma rage kyauta ba kamar da ba....... Samira ta karbe da fadin "Yaya eng ba zai rage kyauta ba wata Kil dai sauran kudin ne sukayi dimuwa Yar gidan ikon tashi ta na baza irin wannan ikon Allah yaushe zaiyi abin kuzo ku gani? Samira tace Ni wallahi Ina tausayin shi bawan Allah kowa da danshi Amma shi Babu Kuma an rufe mishi idon ganin gaskiya..... Ke dai Bari Yar uwa sai dai aci akima katon Kashi a hau mota ashiga gari ana hura hanci Ni wallahi har gobe mamaki nake yayun mu sunyi Rashin dacen Mata mu Kuma mazan mu sunyi dacen Mata.... "To ko kina da Sha awa ne akan yayan naki shafa? Cewar izzatu da tagaji da Jin shaguben su "Me kike nufi da ko Ina da Sha awa? Inji shafar, Izzatu tace "Wai ko ki aure shi nake nufi tunda Ni na tsare muku gaba na tsare muku baya tunda kina haihuwa kawai sai ki kaso auren ki kizo kuyi Maja Kinga sai kema ki biyo layin masu sa ar mijin harma ki yi abinda nakeyi. Sai suka harzuko Mata su duka tamkar zasu cinyeta. "Me kike nufi da wannan maganar? Dama kinzo don kici Mana fuska ? To aikuwa Wallahi jikin ki zai gaya Miki zakuma ki Gane karyar iskanci kike... Izzatu ta Mike tana aje jaririn "To Bari agano Yan iska tsakanin Ni da ku ai a yanzu dai dai nake da uwar mutum ma da uban shi bara ku gayyar na gayyaro "Eh kice dama da abinda ya kawo ki yau har hajiya ta samu tukwaicin zagi gareki ? Sai saka soma musayar yawu har an daura damarar dambacewa inda shafa ta rarumi izzatu suka soma dambe har suna yagawa juna sutura inda a karshe sukayi Mata taron dangi har suka fasa Mata goshi . Inda gidan suna ya hautsine wasu suka shiga tsakani izzatu ta taho da Alwashi kala kala Alwashin karshe shine rabuwa da ak Kwana biyu da yin hakan me gidan ya dawo daga tafiyar da yayi ayadda taso ba zata Kuma kwana gidan ak ba Amma wani Abu da ta kasa ganewa shine ak kwarjini ne gareshi Koko son shi ne takeyi da har in tayi arba da shi take mantawa da kanta? Ganin ak yasa taji ko za a dawo da bara bana ba zata Rabu da ak ba Ta tarbeshi cikin salon kissa da kisisina Wanda take siyeshi har ma ta mantar dashi tunanin wata ya mace. Washe gari ya fice zuwa gaishe da hajiya Mama inda acan ya karbo umarnin hajiyar na ya karo aure ko Kuma ita tayo mishi Ya dawo inda ta kula da Yana cikin damuwa duk da Bai fada Mata ba Amma ta San kwanan zancen don haka sai kawai ta fada mishi yadda sukayi da Hajiya. Ya dubeta "Ni kamar Ni ace za ayi min aure ai kamar an sarawa matar da aka aura min aiki. Ta Sha mur tana hade fuska "Nifa har yanzu kaki fito Dani duhu akan gwajin da akayi Mana Amma ko baka fada min ba na san an samu matsala ta bangarenka don da akaina aka samu matsalar da tuni ka bi bayan hajiya ka karo aure shine ka rufe min har kana tsallake kasa neman lafiya to kasani Nima hakuri na ya Kare tunda hajiya ma tazo har gida taci min fuska akan hakan bare su shafa dake fasa min goshi Lokaci yayi da ya kamata ka fito ka fada musu gaskiyar magana akan Kaine me matsalar don su sakar min Mara nayi fitsari idan Kuma na gaji da mugun halin su sai ka sauwake min auren ka kawai. Yayi murmushi Yana dubanta "Wa ya fada Miki magani naje nema India? Yo har sai an fada min ga Abu abude? Ai na San halinku ne maza na Rashin adalci da Akaina aka samu matsalar nan da tuni ka samawa kanka mafita to Nima na gaji Ya Kuma yin murmushi " to haka din ne Allah ya bamu lafiya Amma Ina so ki sani Ni haihuwa da ake ta maganar ta akaina ban wani damu ba saboda na San komai Allah NE ke yin shi idan Ina da rabon haihuwa Zan haihu idan Kuma bani dashi auren ne kawai ake da ikon yi min Amma haihuwa Babu me ikon bani ita in ba Allah ba So ki bar damuwa hajiya Kuma kiyi Mata uzuri Dole ne taji tausayina Amma ko ita ki Bari Zan fahimatar da ita zata Gane sai dai ki sani ba Zan lamunci Raini gareta ba duk abinda zatayi Miki saboda kin rabeni ne idan Kuma kina sona Dole ki girmam min mahaifiyata don su shafa in sukayi Miki zanci mutuncin su Amma akan hajiya komai zai iya faruwa Ta dubeshi cikin Jin haushi da takaici "Kana nufin sai don Ina sonka sai in Bari hajiya ta takani akan abinda ba laifina bane? Shima ya dubeta cikin Jin haushin abinda take kokarin fada akan mahaifiyar shi........ [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 4* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........."Me kike son ce min ne"? Ko hajiya Bata haifeni ba nayi Zaton girmanta zaisa ta ci albarkacin sa bare kuma Ni da kaina. To kar ki Fara don Zan iya jure komai akaran kaina Amma ba Zan jure ko kallon banza ga hajiya ba bare ki nuna Mata yatsa....... "Ohooo sai nice za a iske gida azageni in Kuma shiga sabgarsu su zageni saboda Ni ban San yanci ba ko kuma shago aka bude na fito ko Kuma daga sama na fado? "To na rantse maka Babu shegen da Zan Kuma yarda ya taka Ni in zuba ido in kyale shi don yanzu Kai nakewa Alfarma ba kamar Ni da suke zaton kayi min Alfarmar ba sai Kuma ka shirya sanar dasu Kaine da matsala ba Ni ba. Ya dubeta "Ina fatan cikin shegun da ba Zaki yarda su taka ki ba Babu hajiya? Kiji ki Kuma kiyaye Babu wani Abu da hajiya zata so ko ta sani Wanda ba zanyi shi ba don bani da wani fata ko buri sai na in rabu da ita lafiya. Ko auren take so nayi zanyi don zanyi biyayya agareta sai ki kiyaye. Tayi wata kwafa ta shige daki ta barshi da yi Mata rakiya da ido kafin yayi murmushi kishi manya kowace mace da kalar nata abinda ma yake tambaya shine shi kishi dabi a ce ko hali ne? Tunda sukayi haka sai izzatu ta fito da sabbin salo tamkar wadda ake zugawa Amma dayake Allah yayi mishi hakuri sai yayi Mata uzuri akan cewa maganar hajiya ce ta sa ta daukar Kai Sati biyu Yana gida Yana kallon idon mikiya a tashar farin wata shafa ta shigo ita da wata budurwa me shegen kyau ya tashi zaune inda izzatu ke kallon su awatse Suka zauna suna gaishe da shi inda ko kallon izzatu Basuyi ba Bayan sun gaisa shafa tace "Dama hajiya ce tace na kawo maka lubabatu gata nan kanwar mijin asiya ce idan Allah ya yi sai ku dai dai ta". Lubabatu ta sunnar da kanta kasa cikin Jin kunya inda yaji wani Abu marar Dadi in Banda hajiya yaushe zata turo mishi yarinyar har gida Mai makon ma ace yaje ya ganta. Izzatu da take kallon su cikin kaskanci ta tofa albarka cin bakinta. "Wane irin aure ne haka marar daraja da sanin kimar Kai? In ba lalacewa ba lubabatu yaushe za a turoki gidan mutum maimakon shi ya iskeki gidan ku in dai ba zubarwa Kai daraja ba? Shafa ta dubeta "Ai Rashin daraja ya Kare ga ci kasayas? Babu komai indai ta samu shigowa ai tayi daraja..... Ya dago Mata hannu cikin fusata "Ashe kema kin iya wannan iskancin irin na su Samira da asmau? Akan idona kike fada Mata haka? "To Yaya bakaji abinda tace ba? .... "Tashi kuje Zan zo in samu hajiyar muyi magana.... Shafa ta finciki hannun lubabatu suka fice daga gidan "Gaskiya ba Zan boye maka ba ak indai aure ake Shirin Yi maka Ni Kam sai dai ka sauwake min aurenka don ba Zan iya zaman hakuri biyu ba, ba zanyi hakuri da Rashin haihuwa ba Kuma inzo inyi da kishiya da dangin miji abarni inji da Abu daya Bai tankawa maganar ta ba ya ci gaba da kallon shi inda wayar shi tayi Kara ya duba ya dauka da sauri inda ake sanar dashi batun kwangilar da aka bawa wani Dan kwangila ne wato Kabir mashi Wanda aka karbo aka bashi don anfi yarda da aikin shi fiye da Kabir mashi din don haka ake son ya fara cikin watan Nan kwangilar shimfida tituna ce a wasu kauyuka wadda za a samu ALHERI sai dai baiji dadin karbewa daga hannun Kabir mashi ba don Babu me son ayi mishi haka Amma dai ya amsa sukayi sallama Washe gari sai ga hajiya Mama ta diro gidan ak na Shirin ficewa Ya zube gaban ta Yana kwasar gaisuwa "Jiya na turo shafa da lubabatu akace matarka tayi Mata wulakanci? A a hajiya Babu abinda tayi Mata dama Ina Shirin zuwa ne Kika zo. Hajiya ayi hakuri da maganar auren Nan don Allah. Auren ne kawai zamu iya hajiya Amma Babu me iya bani haihuwa sai Allah da yaso bani zai bani inko Bai zano ba to Matan kawai Zan Tara don haka hajiya na rokeki kiyi min addua abarwa Ubangiji komai Yana sane da Ni da matsala ta Hajiya ta sauke ajiyar zuciya, "To shikenan abdulkarim na fahimce ka Kuma maganar ka itace gaskiya na janye maganar lubabatu Ubangiji yasa kana da Rabon ganin naka diyan Amma gaskiya sai kajawa matarka kunne...... "A a hajiya tunda dai kin janye Taki maganar Ni Kuma yanzu ne zanyi tawa maganar "Wai hajiya Baki San shine da matsala ba kike kokarin yi mishi aure ? To Nima ba Zan iya auren Wanda baya haihuwa ba tunda ya Zama juya Nima Ina da muradin karawa gaba tsawon shekaru goma Sha inda haihuwa nayi yanzu da na kusa aurarwa tunda kun gama naku wulakanci Nima yanzu ne zanyi nawa Shekaru biyu kenan da suka wuce mukaje Asibiti akayi Mana gwaji Ni da shi inda likitan ya nemi in Basu wuri suyi ganawar sirri ban San me ya fada mishi ba Kuma har yanzu Bai sanar Dani ba inda ba gano an samu matsala daga gareshi shine ya boye min don kar in ce ba Zan iya ba inda kuka Dora min jakar tsaba to hajiya abdulkarim ne me matsala ba izzatu ba sai ku gaji ku hutas ku Kuma sakar min Mara inyi fitsari Hajiya ta dubeshi ta dubi izzatu cikin tashin hankali.......... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 5* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........ Hajiya ta dube shi da mamakin wannan magana ta izzatu. "Da gaske ne abdulkarim"? Yayi murmushi Yana mamakin izzatu akan yadda take kokarin butulce mishi "Hajiya mu rufe maganar Nan don Allah babu amfanin da tado ta zaiyi Mana mu barwa Allah ikon shi kawai sai mu zauna lafiya..... "A a abdulkarim idan har kasan kana da matasala kar ka rufeni fada min sai anema maka magani tunda Ubangiji Bai Saukar da cuta ba sai da ya Saukar da maganin ta. "Haka ne hajiya to anema Mana sai muyi amfani dashi Ni da izzatu........ "Adalilin me da Kare zai dauki Dame? Ai ba a taba karan ta min akan komai ba sai sai akan magani? Kuma Ni meye hadina da Shan maganin ka na matsala? Kai ne nasu Kuma Kaine da matsalar Nan meye nawa? Ni fa kasani wallahi na gaji da wannan zaman cutar don nazo karshe wallahi da zaka sauwake min zanfi farin ciki don yanzu Babu wani amfanin Zama da Kai Hajiya ta Mike da Shirin komawa "Zansa mas udu ya karbo min maganin sai kuyi amfani dashi mugani Allah ya sa mu dace Ya Mike shima suka fito don yiwa hajiya rakiya inda direban ta ya ke Izzatu ta rako hajiyar da harara tana Jin kadan ya rage ta make tsohuwar komai zai faru ya Dade Bai faru ba. Hajiya ta wuce shi Kuma ya dawo inda ya isketa sai cika da batsewa takeyi Ya soma rarrashin ta Akan tayi hakuri su barwa Allah ikon shi akan maganar haihuwa...... "Saboda ka Gane Kai ke cutata shiyasa zakace inyi hakuri Mana Amma ai ka Dade da sanin irin wulakacin da danginka harma da hajiyar ka suke min suna zaton nice da matsala har suka kasa yi min uzuri sai yanzu da Allah ya haska min na gano ka shine Nima za a cuceni? To kasani Kai namiji ne komai Daren dadewa zaka iya samun haihuwa Amma Ni da lokaci na ya wuce to yafa wuce kenan so abinda yafi kawai mu hakurewa juna don Allah ka sahale min aurenka tun lokaci Bai kure min ba. "Ni dai nasan duk kokarin me kokari Bai Isa ya samo abinda ba Rabon shi ko ya samo din kuwa zai sulale ya barshi don ba Rabo bane don haka Zan Baki shawara ki roki Allah abu mafi ALHERI a Rayuwar ki sai kiga ALHERI Yana samunki a ko ina Amma son zuciya Babu abinda yake haifarwa sai bacin zuciyar don haka don Allah don Annabin sa ina so daga yau ke daga yanzu ma mu rufe babin maganar haihuwa Ubangiji yayi Mana baiwa me yawa don Bai bamu haihuwa ba sai mu butulce mishi? Ina rokon Allah yasa Rashin haihuwar da Bai bamu ba ya zamo sanadin SHIGA ALJANNAH shi kenan magana ta Kare daga yau. Abinda ta kawowa ranta shine kawai Yana son taci gaba da Zama dashi Yana cutar ta tunda yasan shine bashi haihuwa Bata tanka mishi ba Amma fa tana Jin ba zata yarda da wannan cutar ba. Tundaga wannan Ranar sai zaman lafiya ya wanzu tsakanin ta da dangin miji su shafa duk da ba SHIGA sabgar su take ba haka ma hajiya Bata Kuma zuwa gidan ta ba inda Kuma ak yayi kwangilar shi ya gama ya samu ALHERI me yawa yayiwa hajiya da danginshi hidima itama izzatu ya Bata kasonta Wanda me yawa Wanda duk in yayi kwangila ya gama dama ka Ida ne sai ya Bata sai dai awannan karon Bata amsa ba tace ta gode ba zai siyi Ra ayin ta ba idan dai har son burgeta yakeyi to ya sauwake Mata auren shi ta Kara gaba inda itama zata haihu Yayi murmushi Nan ma rarrashin ta yayi Yana Bata hakuri shima tayi shiru ba don ta yarda ko ta aminta ba. Ranar wata alhamis ta kwanta barci inda tayi wani mafarki Wanda shine silar zamowa karshen auren su da AK ....... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 6* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .....Wani mutum tagani a matsayyin mijin aurenta Wanda ba AK ba kawai Kuma ta ganta da jaririya ahannu amatsayin yarta sai dai wani hayaki dake biye da ita ta rasa Gane hayakin meye akarshe ma sai hayakin Nan ya rikide ya koma wuta wadda ke biye da ita tana Shirin lasota aguje take gudu kankame da jaririyar inda ta hango ak Yana tafiya hankali kwance akan wani Abu me kama da jirgin kasa inda ta sheka aguje tana son ya taimaketa kar wutar Nan dake biye da ita ta lasota Amma ga mamakinta sai sai taga ko kallon ta baiyi ba ya wuce abinshi. Tabishi da kallo har ya kusa kurewa ganin ta inda ta hangi wata yarinya me kyau tana rungume da jaririya ta mikawa ak din ya karba Yana murmushi ya rungume yarinyar Yana murna inda ta ke kallon yarinyar da tabawa ak jaririya kamar lubabatu tana kallo Kuma ya dauketa cikin abin hawan shi me kama da jirgin kasa suka wuce suka barta ta shagala da kallon matar me kama da lubabatu har taji wani mugun radadi Yana binta ajiki kafin ta kwallara Kara inda Kuma taji an fizge jaririyar dake hannunta tana kallo akayi sama da ita Ta kuma kwallara Kara kafin ta farka.... Ta farka inda take jiyo hucin wutar na bin jikinta Babu batun ADDU A irin ta Wanda yayi mugun mafarki don gaskiya Bata iya ta ba sai ta shiga laluben fassara mafarkin ta Da taso gaskiya koma ace da Dan guntun sani akanta to zata Gane wa azi ne da izna akayi Mata tunda tagani ta samu yarinya Amma hayaki da wuta sun biyota akwai kura kenan Kuma lubabatu da tagani da ak in batayi sannu ba zata barwa lubabatun ak da filin gidan ta Amma sai batayi wannan hasashen ba sai kawai ta kalli mijin da tagani amatsayin Wanda zata haihu dashi sai ta haukace ta Kuma tada bular lallai sai ak ya sauwake Mata auren shi Ta nufi dakin shi don tuni suka Raba makwanci don tace bataga amfanin zuwa dakin nashi ba sai ta fito da tsiya taku kala kala inda Kuma tafi sauke tsiyar ta Akan tsohuwa talai. Ta shiga dakin ak din Yana tsaka da bacci yaji ta antayo mishi ruwan sanyi ajiki gashi lokacin sanyi ya farka afirgice Yana shissheka ya dubeta tana Kada jiki da son ta fashe Ya dubeta cikin sanyin murya "me ya farune izzatu",? "So nake ka tashi ka sallame Ni don na gaji gaskiya ba Zan Kare a auren da Babu tsiyar da zai tsinana min ba........ [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 7* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ......... Ya share ruwan dake yarari akan fuskar shi Yana murmushi Yana kallonta "Izzatu Allah ya sani Ina Jin tausayin ki Zan Kuma Kara hadaki da Allah da manzon sa ki bar maganar Nan haka...... "Kar ka Kuma Jin tausayi na Kai ne abin tausayi ba Ni ba don Ni na hango mafitata a mafarki don haka sallame Ni kawai in Kama gabana. Yayi murmushi "Abinda Kika gani a mafarki ba lallai ya zamo gaske ba sai dai nuni ko izna don Allah kiyi hakuri ki barni nayi barci na kaina ciwo yake, Ya kwanta ya barta tana jijjigar jiki idonta fal masifa ta fito tana sababi inda ta iske tsohuwa talai zaune tana Gyan gyadi sai kawai ta shara Mata Mari Abin tausayi tsohuwar ta farka afirgice "Wane irin dabban cine ki share wuri ki zauna kina min bacci da tsakar Rana? Ke Bari fa kiji in fada Miki idan kinji kin gaji da aikin Nan babu lallai Babu tilas na gaji da gayyar hakora in kin gaji sai na sallame ki Ta shiga zubar da ruwan tijara inda tsohuwa talai hawaye ya tararo Mata tana ta ahi da neman afuwa Jin Marin da izzatu tayi wa talai yasa ak fitowa ya na kallon yadda take Mata tijara ranshi ya baci matuka gaya don Allah yasaka mishi son tsohuwa talai don asali talai wurin hajiya Mama take aiki shine ya matsa da sai tsohuwa talai ta dawo gidan shi don ya Saba da abincin ta tun da sauran karfinta tayi aiki a gidan su shine mafarin tsanar da izzatu tayi Mata saboda tana ganin an turo tsohuwar ne don ta saka Mata ido ko da take wulakanta masu aiki tafi wulakanta Talai Ya karaso wurin ya kamo hannunta ya tada ita inda yaga hawaye na bin idonta "Kiyi hakuri talai Ni naji Miki Amma ban San haka kike muskanta ba . Ya dubi izzatu cikin wani irin fushi da Bata taba gani afuskar shi ba "Baki ji kunyar cire hannu ki Mari tsohuwa irin haka kamar talai ba? To ya zamo na karshe da Zaki Kuma yiwa wani ma aikaci a gidan Nan bare talai. Talai kamar Uwata ce daga yau kar ki Kuma sakata ko shara bare wani aiki na soke Mata duk wani aiki sai dai agirka abata...... "Wannan ne Kuma baka Isa ba wallahi muddin Ina gidan Nan to Dole ne tayi aiki ba tsufa ba ko mu kwana lafiya ce . Dama na Dade da ganota tsohuwar muna fukace wadda aka turo don tazo ta saka min ido to aiki ya Zama Dole tayi shi ko Kuma jikinta ya Bata Labari wallahi salon kasa ta kalli kanta a wata tsiya kace sai dai agirka abata ita a way? Bai San lokacin da ya faska Mata Marin ba karon farko a tarihin Rayuwar auren su da ya taba Kai hannu jikinta da sunan duka abinda bai taba yi ba. "Ba Zan taba Bari ki wulakanta tsohuwar da Ni ne na kawo ta gida na ba Akan talai ba sai kin roki saki ba Zan Baki shi jahilar banza wadda Bata San kimar tsoho ba. Idan har ka girmama tsohon wani to naka ka martaba don hak sai ki kiyaye ba Zan lamunci wulakanta mutanen dake kasanki ba...... Ta cakumo kwalar rigar shi ta tattare ahannun ta "Tunda har ka mareni akan wannan tsohuwar banzar ai kasan ta ballowa kanka aikin da ba zaka iya dashi in yaso sai ka auri talai ko hajiya mama....... Ya Kuma Bata kyakkyawan marika guda biyu ajere Wanda yasa taga wata koriyar walkiya Ya Kira duka ma aikatan gidan inda yace kar akuma saka tsohuwa talai aikin komai Koda dibar ruwa ne wankin kayan ta ma arika hadawa ana kaiwa shago a wanko Haka Kuma duk Wanda izzatu ta Kuma ciwa fuska ko wulakanci to ya fada mishi tunda ga wannan Rana tsohuwa talai ta samu cikakken yanci inda Kuma izzatu ta fice daga gida ta nufi nasu da sunan tagama auren dama sanadi take nema ta Kuma samu sai dai acan gidan Basu Bata samu goyon baya ba inda aka tuso keyar ta aka dawo da ita aka Kuma bawa ak hakuri inda ita Kuma take Jin ta gama auren shi Koda shi Daya yayi saura aduniya sai sun rabu inda Kuma ta fito da sabon salo na aunawa hajiya Mama da duk wani nashi zagi abinda yake Jin ba zai daukaba Tsawon sati biyu tana gurza mishi Rashin mutunci Yana dauke Kai inda washe gari sai ga hajiya mama da tarin magunguna ta diro gidan.......... [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 8* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* ...........Hajiya Mama ta shigo gidan tana sallama inda izzatu ke zaune tana chatt a wayarta ta dago kanta ta dubi hajiyar ba tare da ta amsa sallamar ta ba ta maida kanta ga wayarta taci gaba da chat dinta Hajiyar ta karaso ta zauna tana kallon izzatu da ta baiwa banza ajiyar ta. Tayi murmushi kafin tace "Ga maganin Nan ki ajewa abdukarim da Zuma ake Sha safe da maraice. Bata karba ba kamar yadda Bata nuna ta San da zaman hajiyar a wurin ba Talai da taji zuwan hajiyar ta karaso tana gaishe ta "Yauwa talai ga magani Nan ki ajewa abdukarim kice mishi sau biyu ake Sha safe da maraice Kuma da Zuma ake Sha Talai ta karba tana fadin insha Allah ba Zan manta ba hajiya Hajiyar ta Mike da Shirin ficewa inda talai tace "Hajiya ki tsaya ko ruwa Kisha Mana bare ki huta..... "Tunda gidan gyatumin tazo sai ki Bata ruwa gwana yar ka iya , cewar izzatu wadda ke wurgo musu harara "Ni in nagane mutum munafiki ne me zai hada Ni dashi da munafurcin sa? Wallahi a yanzu dai dai nake da anuna min yatsa na karya tunda tafiyar Babu mutunci Hajiya Mama ta Kada kanta "Allah ya shiryeki ya dawo dake hanya..... "Ameen in dagaske kike duk da kema kina bukatar shiriyar tsohuwar banza me bibiyar Matan ya'yan ta...... Kalmar tsohuwar banza ta fado akunne AK dake shigowa gidan wani Abu ya naushi kahon zuciyar shi ya dubi hajiya ya Kuma dubi talai da ta soke Kai kasa Yana son ya gano wadda izzatu ke jifa da kalmar tsohuwar banza amma ya kasa ganowa "Yanzu kike tafe hajiya? Yayi karfin halin tambaya "Yanzu nazo har Zan wuce dama magani na kawo maka gashi Nan wurin talai tayi maka bayani. Wannan saurin na hajiya shi ya alam ta mishi zagin tsohuwar banza da izzatu tayi ba da kowa take ba sai hajiya mama. Ya riko hannun hajiyar Yana fadin "hajiya don Allah me ya faru kike sauri haka? "Babu abinda ya faru ak Zan koma gida ne kawai ka tabbatar kayi amfani da maganin da na kawo maka.... "Ina fatan hajiya ba ke ko talai take Kira da tsohuwar banza ba? "To wacece Ni da ba za a zageni ba ...... Kafin ma hajiya ta dire zancen ta ya Cabo izzatu ya soma wanketa da maruka "Ayau Zan nuna Miki hajiya tafi karfin komai agareni Ina tausaya Miki Amma da yake jaka ce Baki San ana tausayin ki kije na sakek........ "Kar ka fara abdulkarim ! Hajiya ta katse shi da tsawa. "Ka rabu da ita Kai dai kayi ta hakuri..... "Ai dama da wannan manufar kikazo bakar munafuka annamimiya kin Kuma ci nasara don Ina me tabbatar Miki da yau wallahi aurena da abdulkarim ba zai Kuma kwana a duniya ba sai ya sakeni don in Kara gaba ko Zan haihu. Ta dubi ak "Idan dai Kai din Dan halak ne cikin wannan tsohuwar banzar da wancen tsohon banzan na kushewa ka sakeni saki uku.... Kafin ma ta dire zancen ya furta Mata kalmar sakin "Idan akwai sakin da ya wuce a lissafa shi fiye da uku to nayi Miki shi kije kije kije bana bukatar ganin bakar fuskar ki Arayuwa ta Ina fatan hakan zai tabbatar Miki Ni din Dan halak...... Ta dubeshi ta watsar "Sai ka auro hajiya Mama kasaka dakin da Zan bari....... Bata rufe Baki ba ya rufeta da duka sai da hajiya ta yi mishi tsawa kafin ya saurara Mata inda tafice aguje don ta tabbatar ba cikin hankalin shi yake ba "Baka kyauta min ba abdulkarim me zaisa ka biye Mata ? Zagi ai baya Kari don ta zageni sai menene? Naso ka lallaba matar ka kuyi zaman ku har Allah ya warware maka lalurar ka don ba kowace mace bace zata hakura da Rashin haihuwa shi yasa kaga Nima nake lallabata "Hajiya na gaji da halin matar Nan Kuma ba ayi wata mace da zata zageki ba in kyale ta ko Ruhin mu hade yake wallahi na gwammace in mutu da dai in Bari wani ya muzanta min ke bare izzatu dake home da barazana cikin rizgar arzina. Kuma Bari in fada Miki gaskiya hajiya da dai nayi nufin yin shiru har muddin Rayuwa akan matsalar Rashin haihuwa hajiya Ni lafiya ta kalau itace me matsalar ba Ni ba............. [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 9* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Hajiya Mama ta dubeshi azabure Jin Yana fadin ba shine me matsalar ba izzatu ce. "Dama lafiyar ka kalau abdulkarim Amma kaja Baki ka tsuke? Lallai na sarawa hakurin ka ka Kuma yi halacci Amma anyi maka butulci. "Tun tsawon wane lokaci ne kasan hakan? "Izzatu ta matsa min da son lallai sai munyi gwaji idan ma magani zamu soma karba sai mu karba inda na Gane manufar ta ta son agano me matsala ce. Munje Asibiti inda akayi gwajin sai dai akanta aka samu matsala don likitan ya fada min tayi shaye shayen magunguna na Hana daukar ciki Wanda suka haifar Mata da matsala a mahaifar ta inda ya bada magani don ta Sha Munyi ganawar sirri ne da likitan Wanda ya ce ta bamu wuri zamu gana inda ta fito ta dawo mota Ni Kuma ya sanar Dani matata ba zata taba haihuwa ba saboda illar da maganin Hana daukar ciki yayi Mata a mahaifar Ni Kuma nayi alkawarin Zama da ita da lalurar ta inda take min kallon nine me matsalar ba ita ba inda maganin da aka Bata ma Bata yi amfani da shi ba tace ita ta San lafiyar ta kalau Kuma tunda bataji nayi Mata wata magana ba to matsalar tawace Ni Kuma nayi nufin rufa wannan asirin don Ina tausayin ta gidan su ba komai bane bare Kuma duk ta wanke dangin da Rashin mutunci Kuma ma Bata San mijin da zata aura ba Wanda kalubalen dake tare da ita yafi na Nan shiyasa Kika da Ina hakuri da ita Amma tunda har lamarin ya soma shafarki Dole ne inyiwa tufkar hanci dama kwanaki ta Mari talai to ko akan Marin zanyi Mata hukunci sai gashi ta jawo abinda na gudar Mata na Kuma San zata gano hakan da kanta musamman idan ta Kuma yin wani auren Hajiya Mama ta sauke ajiyar zuciya "Allah ya shirye ta yasa ta Gane ko Babu komai dagawa da izgili aikin shaidan ne duk yadda kake tausaya Mata ita Bata tausayin kanta.... "Hajiya na yarda ki nema min auren lubabatu Amma ki Fara Jin Ra ayin ta idan nayi Mata sai ayi magana kawai... "To ko kaje da kanka kawai sai ku fahimci juna dama wancan zuwan shafa ce ta zanzame Ni akan ta kawo maka lubabatu don ita yarinyar cewa tayi kunya take ji Allah ya zaba abinda yake shine ALHERI ina fatan auren ku da lubabatu ya zamo silar farin ciki Kai da ita damu gaba Daya "Abu kamar was karamar magana ta Zama babba inda lubabatu ta amsa tayi na am da batun tuni aka tsayar da Rana cikin wata biyu aka Sha biki amarya ta tare inda Kuma can izzatu ta soma fuskantar kalubalen gidan su don tuni ta Gane Bata da uwa agidan sai dai Matan uba Wanda take wuni bauta musu Babu gode bare bare godiya ga Rashin abinci bare Kuma dare yayi sauraye su cika Mata kunne da guda har ta kasa barci Dawowar ta gida ko wata ba ayi ba taji shelar bikin AK da lubabatu Wanda acewar ta take barka da rabuwa da shi Amma sai da ta tsinci wata damuwa wadda ta rasa ko ta mecece Damuwar da Bata da maraba da kishi Amma sai ta maze taci gaba da harkokinta har ta fita daga idda inda Kuma zawarawa sukayo Mata sallama inda tayi nufin yin aure ko don ta nunawa ak ita din ba irin matar dake bandaro bace Wai don an saketa. Kayanta da ta baro gidan ak yasa aka kwaso Mata mota har gida ya kawo Mata inda ya Kuma Bata wata takarda yace taje ga likita Usman Wanda ya zamo musu family doctor Ada can wai zaiyi Mata bayani..... "Yo bayanin me zaiyi min tunda dai Allah ya Raba Ni da wahalar auren ka Wanda Babu komai acikin shi sai asara? Yayi murmushi "Kar kice haka don akwai wani Al amari da Usman din zai sanar dake Wanda zai haska Miki abinda ke cikin duhu Da haka ya juyo abinshi ya barota da yi mishi rakiya da ido tana hasaso wani Abu me kama da nadama Amma haka ta cije washe gari ta nufi Asibiti inda ta zarce office din doctor Usman............. [5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *page 10* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ....... Doctor Usman ya tarbeta cikin mutunci don Bai zaci sun rabu da AK ba bayan sun gaisa yake Mata fatan alkhairi akan auren AK din "Ashe eng ya angwa ce madam ? To Allah ya baku zaman hakuri da haka Mata ke goyawa mazajen su baya ai da ko Ni Nan na karo wata to Amma abin ne ba duka Kai ba sunan wata hula Izzatu ta kwabe Baki kafin tace "Shi dai Kam ai aikin banza ne yake Wai jefa agwagwa ruwa Wanda Bai ko Kai ga harara cikin duhu ba . Doctor Usman yayi murmushi "To madam na Gane karatun sai ayi ta hakuri dama shi zaman haka ya gada Amma da anyi hakuri sai komai ya zamo ba komai ba duniyar ma guda nawa ce? "Likita bama tare fa da AK ahalin yanzu don Allah ya sani ba Zan jure zaman asara agidan shi ba shekaru goma Sha biyu Babu haihuwa haka Zan Kare saboda Allah? Yanzu ma zuwa nayi ka fasa min wancen KWAN na gwajin da kayi Mana don har yanzu Bai fuskance Ni da sakamakon gwajin ba Wanda Ni da kaina na gano matsala daga gareshi don yadda dangin shi ke son saka min ciwon Kai da nice da matsala da tuni sun mishi aure shine kawai na zabi ya sauwake min auren shi in Kara gaba don kasar Allah me yalwa ce in kaji matsatsi ka Kara gaba shine nake son sanin sakamakon don in har da bukatar Nima adora Ni Kam magani ko ya sakar min wata cutar sai na Tara kusa. Doctor Usman ya zuba Mata ido Yana Mata kallon kinyi wauta. Ya tambayeta "Yanzu shi eng yasan Zaki zo Nan wuri na? "Eh yasani ta bashi amsa Amma duk da haka sai da ya Kira wayar shi don sunyi dashi shima zai Taya shi rufe sirrin Kara biyu ya daga bayan sun gaisa yake sanar dashi madam ce tazo da wata magana wadda muka Dade da haka Rami muka binne na Kuma yi maka alkawarin sai dai ta fito ta bakin ka ba dai Baki na ba. "Kar ka damu Usman baba tare da ita a yanzu ta nemi saki ne gareni don tana ganin nine me matsala bayan ta gama cinye fuskar hajiya ta tas inda na sauwake Mata Kuma tunda tazo gareka na yarda ka fada Mata gaskiyar magana don ta Gane kalmar tausayin ta da nake yawan nanata Mata Amma Bata taba daga kalmar tayi Mata duban fahimta ba So kar ka damu na yarda na amince ba ita ba duk wani ma me min kallon da take min ka sanar dashi na gode ya fada Yana tsinke wayar shi Radam tajiyo maganar da AK yayi inda taji wani ruwa na bin jikinta inda ta Gane zufa ce don ko Usman Bai fada Mata ba ta gano bakin zaren. Usman ya soma da yi Mata tambayoyi akan Shan kwayar Hana daukar ciki Kai tsaye ta amsa mishi da eh kwarai ta yi su. Inda shi Kuma ya Dora yi Mata bayani "Wadan Nan magunguna da Kika Sha sune sukayiwa mahaifar ki muguwar illah wadda ta kassara ta har kikaji babu batun ciki ko haihuwa Ranar da kukazo gwaji eng ya nemi sanin dalilin matsalar ku inda ta bangaren shi ba a samu matsala ba sai ta bangaren ki inda bincike ya gano illar da maganin yayi Miki Dalilin da yasa na ce ki bamu wuri kenan don ban San ya me gidanki zai fahimci zancen ba inda nayi mishi bayanin komai Amma ga mamaki na sai Naga ya tausaya Miki har ma yace mu haka mu binne Ni da shi baya son kowa yaji shine dalilin da Bai fuskance ki da maganar ba ya dai karba Miki magunguna Wanda ya sanar Dani Wai kinki amfani dasu wannan shine dalilin da kikji Bai sanar dake komai ba Amma banji Dadin abinda Kika sanar Dani ba gaskiya Kuma kin tafka kuskure ba karami ba Ta dafe kanta hawaye na zuba inda take Jin wani Abu me kama da nadama duk da Bata taba yin nadamar wani Abu da tayi a Rayuwar ta ba sai yau da taji inda ake halacci ba tare da an duba Kai waye Wanda akewa halaccin ba Bata cewa Usman komai ba ta taso ta taho Kai tsaye ta zarce gidan abdulkarim duk da ita Kanta Bata San me zai kaita gidan ba bare abinda zata yo............. [5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 11* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Ta shigo gidan cikin wani irin sanyin jiki da nadama tana tafe tana kunga kafa da son lalubo yadda zata dawo da bara bana Ta shiga gidan inda ta iske Lubabatu na aikin matsa katafun ak Wanda ke kwance akan kujera tree seater lubabatu ta amsa sallamar izzatu tana yi Mata sannu da zuwa inda ak ya tashi zaune Yana kallon ta Ta zube gaban shi tana sharar hawaye kafin ta kece da kuka tamkar wadda akayiwa mutuwa idan baka San ta ba sai ta baka tausayi "Me yasa baka fada min halaccin da kake min ba AK? Nayi nadama fiye da yawan shekaru na a yau na gano tausayin da kake fadar kana min a lokacin da damata ta barni Don Allah ka gafarce Ni abdulkarim yau Ni NA SHIGA UKU ina Zan sa kaina? Tsam ya tashi ya bar Mata gidan don Yana ganin Rainin hankali ne ma ya tsaya sauraren ta inda ta gama kukanta ta fito inda lubabatu ke Bata hakuri da haka ta fice tana tafe tana zancen zuci babu abinda yafi damunta irin yadda taga lubabatu ta murje har cikin ta ya bayyana ita kuwa har yanzu ba ta samu nasarar da take fadin asarace zaman gidan shi Mutumin da ta tsayar me abin hannun shi ne irin Yan bokon Nan Wanda duniya ke fadawa karya Wanda suke dadewa Basuyi aure ba saboda tsara Rayuwa da suke ai kuwa aka daura auren ta tare agidan shi Babu abinda ya sauya daga halinta sai ma abinda yayi gaba na wulakanta ma aikata da son dagawa da fangima . daular dake gidan Kabir mashi ta zarce ta gidan ak don shima Dan kwangila ne me zaman kanshi don shima Yana da communication da fadar shugaban kasa wurin karbar kwangila Hakan yasa ta ga ya Zama dole ta dakushe kaifin irin wancan garnakakin irin na gidan ak don ba zata yarda tarihi ya maimaita kanshi ba Dole ne ta samawa kanta mafita akan samun magaji agidan Kabir don haka ta lalubo lambar sister mero wata malamar Asibiti dake taimakon ta a lokacin da ta nemi maganin Hana daukar ciki Kara biyu sister mero ta daga wayar bayan sun gaisa take tambayar tana Asibiti? Ta amsa Bata Asibiti yanzu sai dai ko zuwa gobe su hadu a asibitin kawai don azaton sister mero maganin da ta Saba karba ne zata karba da haka sukayi sallama ta aje wayar inda take tunanin idan Bata yi kokarin samun Wanda zai gaji dukiyar Kabir ba idan ya kauce ai ta tabbata me asara to ba ma zata yarda tarihi ya maimaita kanshi ba daga gidan Kabir ta gama matsawa wani wurin don ta hadu da matsalar dangin miji ba Kuma zata yarda Rashin haihuwa ya Kara kawo Mata wani tarnaki ba don haka ta Matsu garin ya waye ta iske mero don taji yadda zasu faro da yadda zasu Kare Washe gari kuwa ta gillawa Kabir karyar cewa Bata da lafiya zata je Asibiti inda ya cika Mata Jakarta da kudi ta ja motar da Kabir ya siya Mata ta wuce Asibitin national hospital dake garin Abuja don ganawa da sister mero..... Bari muji yadda wannan ganawa zata Kaya tsakanin izzatu da sister mero [5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 13* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ...........Sister mero ta zakuda tamkar wadda kunama ta sakarwa harbi jin izzatu na ambato Mata milyon goma "Banji me kikace ba izzatu "Yadda kikaji hakan nake nufi milyon goma na ce Zan Baki idan har aikinki ya tafi daidai..... "Wane irin aikine zanyi Miki ki bani wannan kudin? Don Allah karki yaudare Ni izzatu ko cikin mafarki ban taba ganin milyon goma ba ...... "Zaki gansu ido biyu harma su zamo naki idan kinyi nasarar kammala aikin ki Babu kuskure ko sabani........ "To naji wane irin aikine kike ta fada haka? Fada min don Allah tun zuciya ta Bata buga ba. Izzatu ta dubeta tayi shiru kafin tace "So nake mu hada wata kwangila dake kwangilar da zata danka Miki milyon goma ahannu..... "Wace irin kwangila Ni ki fito amutum kiyi min magana ba alaye da kwane kwane ba. "Da ko Diya nake so ki samo min acikin karbar haihuwar da kike Ni Kuma Zan sanar inada ciki Wanda Dan da Zaki kawo min shine Zan batar da hankalin mutane Kan cewa nice na haifa......... "Dakata Allah idan na fahimce ki wata ta dauki cikin ta haife sai in dauko in kawo Miki? "Hakan nake nufi. "To tashi ki Kai kudin ki gaban da Kika San fin dubu zasu yi Miki Ni dai Kam albarka ban siyar ba. "Haba wannan ma ai Rainin hankali ne da son ki wulakanta min aiki kija akore Ni Haka kawai wata zatayi wahalar daukar ciki da rainon shi ta Kuma ketare hadarin na kuda ta haifa saboda son zuciya sai in sato in kawo Miki don Allah meye sunana idan nayi Miki hakan? Yaya zakiji idan ke akayiwa hakan? To mu rufe wannan maganar muyi wata Izzatu ta dubeta asheke "Dama fa ALHERI bai Faye karbar bakin mutum ba Amma ki sani kudin da kike kokarin yiwa arziki kullin da zai tarwatse har ki mutu ba Zaki taba mallakar su ba tunda Kuma ba Zaki iya ba zanje birnin gaba inda za ayi min Tana gama fadin haka ta Suri Jakarta ta fice tamkar kububuwa inda sister mero ta bita da kallo inda Kuma take Jin wani lissafin me kama da na dokin Rano ya sauko Mata akan bukatunta na son ta mallaki mota da son ta siyi gida Amma ta Yaya zata mallaki gidan da motar alhalin albashin ta ma kafin ta karbe shi bukatu sun targada shi? Amma Kuma ta Yaya zata iya wannan aiki me matukar hadari akanta da aikinta? Sannan Kuma Yaya zatayi da hakki da alhakin wadda zata sibarewa Dan? Ance mugun tunani shi ke abotakar shaidan sai sister mero ta ture wancen kalubalen ta hango bukatar ta inda tayi na am da aikin da zai mallaka Mata milyon goma wannan ai shine yiwa arziki kulli yaushe ne? Yaushe ne zata hada Kan wadan can kudin a wannan Nigeriar me jiya tafi yau gobe tafi jibi. Don haka tana tashi aiki sai ta Kira wayar izzatu ta nemi kwatancen gidanta...... "Me ye na neman kwatancen gidana Kuma? In ma shawara Kika sauya kin makara don Ni magana guda nake bana maimaici..... "Yi hakuri fada min inzo muyi magana Izzatu taja tsaki kafin ta Bata kwatancen Mero ta iso gidan Wanda ita da kanta ta San lallai Dole izzatu ke rudewa da son samun mafita Ta dubeta awatse "Meye Kuma na biyoni gida? "Kiyi hakuri shawara nayi Naga Bai kamata ace kizo da bukatar ki wurina ba in watsa Miki kasa a ido haka na yarda sai mu tsara yadda abun zai kasance. "Me yasa shi matsiyaci ko ya shiga tandun Mai yake fitowa kandas? Yaushe ne mero Zaki Tara milyon goma? Meye abin wuya acikin aikina? Wannan magana tayiwa mero zafi Amma ta hadiye "Ni dai yanzu muyi magana Yaya abin zai kasance? "Zan sanar da Kabir nazo Asibiti ance inada ciki Zan dauki acting din masu ciki ke Kuma ba ki Nan da wata bakwai ko takwas kiyi kokarin kawo min abinda yasamu namiji ko mace duk Wanda ya samu Ina so "To shikenan zanyi kokarin hakan in Sha Allah sai dai maganar kudin Zaki fara bani wani Abu ne kafin cikar aikin ? "Kare ya cijeni ne mero da zan Baki kudi Baki gama aiki ba? Ranar da duk Kika gama aikin ki Ina me tabbatar Miki da ko minti ba za a Kara ba Zan biya ki kudin ki cash Da haka sukayi sallama da mero ta fice daga gidan inda Kuma a wannan Rana lamarin ya soma Wanda ya kunshi wani KWAI da fasuwar shi zai tafi da Ruhin Al umma da yawa. Kabir ya dawo inda izzatu ke sanar dashi taje Asibiti an sanar da ita cikine da ita inda yayi murna tamkar ya mayar da ita cikin shi inda ita Kuma ta soma fito da salo kala kala inda Kuma izzatu ke baza izza inda Kuma akayi sa a Kabir Bai Faye bawa uwarshi muhimmanci ba inda izzatu ta Kara baza komar wulakanta uwar Kabir din wadda Allah ya zubawa tsananin hakuri da alkunya inda a yau ta nuko gari tundaga birnin Zaria ta iso gidan Dan nata don ta ga shi saboda shi dai yakan iya share shekara Bai lekota ba bare ya agaza Mata duk kudin shi da shaharar shi Bai bada Kai ga lamarin mahaifiyar shi ba inda Ni Kam gidan iko nace anyi asara kuwa indai haka ne........... [5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 12* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Ta faka motar me kololuwar daraja a farfajiyar Asibitin national hospital dake babban birnin tarayya Abuja inda ta fito fuskarta sanye da Derk spes ta soma takawa sannu ahankali tamkar me tausayin kasa hannunta sabe da jakar LV kafar ta sanye da takalmin LV mahadin jakar sai wani matsiyacin leshe Wanda ya lashe kudi ba kadan ba kamshin turaren ta ya bulale wurin ta kara daukar kanta yayin da ta ga wasu manyan Mata suna binta da kallo don gaskiyar magana shigarta Babu karya don ta samu Kabir mashi yadda take so Kuma ya rike Mata Kan macijin inda har take Jin kanta ame jinin arziki Ta iso ofis din sister mero wadda aiki yayiwa sauki suka gaisa inda meron ke kallon ta cikin Sha awa "Jiya kin Kira bana Asibiti naje gwarunfa duba wata abokiyar aikina da bataji Dadi ba Ina fatan dai ba kwayar pills din da Kika Saba karba Zaki karba don gaskiya lokaci yayi da ya kamata ace kin haihu ai kin Sha Miya haka Nan, "Uhum mero ai ba Zan kuma yarda insha wani Abu yanzu da sunan Hana daukar ciki don nayi nadama ba kadan ba...... "Gara dai Kam don abin in ya kazanta Babu kyau. To yanzu me za ayi Miki? Ta sauke ajiyar zuciya "Mero na rabu da mijina sanadin Rashin haihuwa inda ayanzu nayi wani auren Wanda bana fatan sake gamuwa da wani tarnakin irin na gidan AK shine nake son samun mafita daga gareki..... Mero ta tareta "Kin samu matsala ne halan? "Na samu matsala kuwa gagaruma wadda silar Shan maganin Hana daukar ciki ya haifar min har na samu bakin sakamakon ba Zan haihu ba shine nake gudun haduwa da irin waccan matsalar ta gidan AK shine nake so ki taimakeni da mafita. Sister mero ta sauke ajiyar zuciya "Gaskiya izzatu Babu wani taimakon da Zan iya yi Miki illa ki rungumi kaddara Kuma hakan ya zamo izna da Jan kunne gareki da masu irin abinda kikayi Shi Allah ba ayi mishi Dole ana yin tsari Amma sai an fara haihuwa anga yadda haihuwar ta faro misali yinta Kai da Kai ko Kuma inke da mijinki zaku iya haifar me cutar sikila idan kunyi tsari ba laifi bane don ku hutar da yaran daga wahala Amma da yawan ku Kuna SHIGA hurumin Ubangiji da son kuci gyaran wahayi........ "Kinga mero ban baro gida don inzo kiyi min wa azi ba in wa azi nake sonji zanje ne in siyi kaset ko in bude Sunnah TV ban kumayo wanka don inzo ki shaki kamshin turarena ba, A a nayo kwalliya ne don ina so ta biyani kudin sabulu...... "To naji hajiya izzatu me kike so nayi Miki yanzu? "Shine abinda ya kamata kiyi ba Wai ki saki baki kina neman shiga rigar malunta ba. "Ina so ne na mallaki Da ko Diya ta yadda Zan fita daga matsalar bana haihuwa shine kawai nake so ki taimakeni "Wannan me sauki ne inaga gidan marayu kawai ya kamata kije ki darzo duk kalar Wanda yayi Miki mace ko namiji sai kin zaba.... "Idan naje gidan marayu na dauko ai kowa yasan ba nawa bane Kuma bana son na gidan marayu gaskiya Kuma ai kowa zai kalle shi da sanin asalin sa, "To yanzu ya kike so ayi ? "Mijina na yanzu baisan bana haihuwa ba shiyasa nake so yin kauda bara da hankalin shi abinda nake so mero ke Nike so muyi magana ta fahimta don Zan biyaki kudi tundaga naira milyan daya zuwa goma akan bukatata idan har Zaki iya shiyasa ma na taho gareki don nasan aikin da Zan Baki akwai mutane fin dubu da in na Kai musu da gudu zasuyi min Sister mero da taji yawan kudin da izzatu ta ambato zata Bata akan aikin da bataji komeye ba sai ta rude ta kidime har take Jin ita ko ma Arayuwar ta ta taba Kama milyon guda ahannun ta? Yau sai ace za ta samu goma me take jira?.............. [5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 14* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Matar ta shigo da buhun bakco Wanda ta zubo kayan kadi dangin su kukar Miya daddawar kalwa da kubewa da karkashi ta shigo da sallama inda izzatu ke kwance akan kujera tree seater a Dole laulayi take Ta amsawa matar aciki ta zauna tana kallon ta ganin kamar Bata da lafiya "Babu lafiya ne halan? "Eh wallahi dungo cikine ke ta bani wahala , ta fada tana gatsina fuska tamkar dai ace cikin ne na gaske "Allah ya Raba lafiya ai haka laulayi yake Dole ne ake jinjinawa uwa akan wahalar samuwar danta Allah kayi Rahama ga iyayen mu ke kuma ya Raba ku lafiya ke da duk wata me dauke da Kaya irin naki. Ta amsa kamar ana Mata Dole. Amma abin mamaki ko ruwa ba ayi karar bawa ladidi ba me amsa sunan dungo ita da gidan danta bare abincin tarba Amma dayake Allah ya zuba Mata ruwan hakuri Bata damu ba daga karshe ma izzatu Nan ta barta yashe afalo ita Kuma ta shige daki tabi gado Wai ita me ciki Sai biyar na yamma me gidan ya shigo inda yayi arba da uwarshi yashe a falo ya zube suna gaisawa inda yake tambayar Wai lafiya tazo? "Eh lafiya Amma ba Lau ba ruwan da akayi kwana uku da ya wuce bango na ya Fadi Allah ya kiyaye Babu abinda ya taba sai Yar akuyata itama ba sosai taji jiki ba don na barota ma tana yawon ta. "To Allah ya kiyaye gaba zansa agyara shi ko zuwa Nan da wata me kamawa in Sha Allah. "To Allah ya bada iko Kuna lafiya dai ko? Nazo na samu izzatu ba lafiya inda take sanar Dani cikine Allah ya Raba lafiya Ya amsa Yana murmushi don shi kanshi Yana muradin yaran Kishin ruwa ya isheta har ta kauda alkunya ta tambaya ya dauko gorar ruwan ya Bata ya Kuma lariya ta kawo Mata abinci Amma tace ta koshi inda ta Miko mishi kayan kadin dai dai da fitowar izzatu tana shake hanci Wai wani wari wari take ji inda ya nuna Mata kayan da babar ta kawo inda ta toshe hanci "Haba Ashe buhunki ne baba yake wannan doyin don Allah jeki dasu zasu sakani amai bana ma amfani da irin su Wani Abu marar Dadi ya daki zuciyar dattijuwar Amma ta matse inda ta amsa da fadin ba komai Bata San basa amfani da su bane ta Mike da Shirin tahowa inda takewa izzatu fatan samun lafiya abin takaici Wai dubu biyu tayi kudin mota daga hamshakin Dan nata ta karba tayi godiya ta taho tanemo tashar mota kafin ta jirayi cikar motar da zata zo birnin zazzau inda sai dare sosai kafin ta iso gidan nata Wanda ta gada daga marigayin mijinta uban Kabir Wanda ta haifa shi kadai saboda yawan wabin da tayi sai da kyar ta sameshi inda ta zamo jajirtacciya wurin neman kwabo inda ayanzu ma hada rainon yara takeyi Wanda duk wata uwayen yaran Kan biyata dubu biyar inda take rainon yaran idan iyaye su zasu fita aiki su kawo Mata idan ta dawo Kuma su karbi abinsu yara biyar take raino inda suke biyanta dubu ashirin da biyar kenan shiyasa Kabir Bai damu da ya Bata kulawa ba Wai ai tana samun kudi sai Kuma akayi sa a ita din ba me son roko bace bare matsawa shiyasa idan taga ya Sharari lokaci Bai zo ba sai ita tazo ta ganshi ta koma Haka Kuma katangar da ta sanar dashi ta Fadi yace zai sa agyara Bai gyara ba sai dai itace ta siyi zana aka killaceta Izzatu ta bude fejin salo da firirita Wai ita adole ga me ciki inda shi Kuma yake biye Mata da tace uhum zai ce meye ko me take so? Tabara iri iri inda Kuma Yan aikinta suka SHIGA UKU da yawan aiki ta yi ta tofar da yawu da Aman karya suna faman wankewa da gogewa Inda Kuma kadan zasu kuskure tayi ta Danna musu ashariya sai dai su kauda Kai suyi hakuri Wata biyar dai dai da yin maganar su ta kwangila da sister mero lubabatu matar eng AK ta tashi da nakudar haihuwa ta biyu don wancan da ta haifa Bai zo da Rai ba kasancewar ta Sha wahala shiyasa wannan karon aka kawota asibitin national inda Kuma cikin sa a sister mero ce ke night duty inda tayi hikimar sakawa lubabatu ruwan nakuda dama tayi hakan don cimma kudirinta na son cika burinta ta kumayi sa a lubabatu tafita hayyacinta har Bata San lokacin da ta haife abinda ke cikinta ba........... [5/16, 6:07 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 15* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Wani ikon Allah da ya Saukar shine lubabatu ta haifo Yan biyu duk Mata batare da ta San tayi hakan inda Kuma sister mero take kallon lamarin tamkar cikin shirin film ko wani shiryayyen Abu inda kuma tayi maza ta aiwatar da wani shiri tamkar walkiya ko ibilishiya ta shirya yarinyar guda ta turo ta zuwa dakin hutu inda ta fito take sanar da wadanda suka kawo lubabatun ta haihu wato hajiya Mama da tsohuwa talai don AK baya gari inda Kuma mero ta sada su hajiya Mama da talai dakin da lubabatu ke ta sharar bacci saboda allurar bacci da ta zurkuda Mata da sauri mero ta zagaya bayan tagar dakin da lubabatu ta haihu ta Suri Jakarta wadda aciki ta saka jinjirar ta fice da sauri tana duba yarinyar dake tsotsar yatsun hannunta Ta jawo wayar ta ta Kira izzatu ta daga tana fadin ya akayi Kuma kike isata da Kiran waya... "Aikina Yana dab da cika ga kyakkyawar yarinya ahannu na ya za ayi kenan?..... "Ki Bari don Allah? Taho kawai gani Nan Zan bude Miki gida tunda Kabir na can Yana bacci Kinga sai mu kashe mu binne ba tare da ya sani ba Kinga asiri rufe kenan. To fito ki bude min don gani Nan daf da gidan don Ina so in koma Bakin aikina.. Duk dare ne kusan Sha Daya da mintuna haka izzatu ta taso tazo ta bude gate din inda napep ya sauke mero inda tace ya jira ya mayar da ita Asibiti Suka shigo da izzatu inda mero ta fito da yarinyar daga katuwar Jakarta ta mikawa izzatu dai dai da ta tsanyara kuka inda izzatu ta doka daki Kabir tana Kiran sunan shi ya taso Jin kukan jaririya ya fito da sauri inda yayi arba da sister mero cikin kayan aikinta "Kar dai Ina can Ina bacci har akayi haihuwar ban sani ba?, "Ai dayake ma ta samu nakuda me sauki shiyasa ta kirani na garzayo. Ya karbi yarinyar Yana kallonta kyawu Kam tamkar Hindu inda atake yayi Mata huduba Aisha humaira ya mikata ga mero Yana kallon izzatu Yana Mata barka. Mero ta Mike da Shirin komawa Asibiti inda Kabir ya debo kudi masu dama ya Bata tafito tana godiya ta shige napep ta koma Asibiti inda ta iske dakin da lubabatu take cike da Yan uwa suna ta yaba kyawun Yar inda mero ke musu kallon na Sha da ku. Talai ita tace zata kwana wurin uwar dakinta lubabatu don lubabatu Kam ta dauketa tamkar uwa ga kyautatawa da take Mata Kai kaf din ma aikatan lubabatu na kyautata musu shiyasa ma talai tace ita zata kwana hajiya Mama ta tafi gida ta huta Haka hajiyar ta taho kafin asubahi lubabatu ta farko inda mero ta tabbatar Babu matsala ta sallame su itama ta harlanta aiki ga Wanda zai canjeta ta taho gida tana fatan tayi baccinta zuwa Sha biyun Rana taje gidan izzatu ta karbo kudinta Sai karfe biyu na Rana ta nufi gidan izzatu inda Koda izzatu ta ganta sai ta hade fuska tana masifa "Me Kuma kikazo yi mero ? In don kudin kine ai Kya Bari ayi suna ko?...... "Bamuyi haka da ke ba indai ba Saba min alkawarin Zakiyi ba nayi cinikin mota kuma yau nace Zan bada don haka dauko min hakki na in wuce... "Bafa Zan Baki ko sisi yanzu ba wallahi sai bayan suna don haka karki tada min hankali, mero ta dubeta cikin sikewa da son ta nuna Mata halin Dan Adam na butulci "Bamuyi haka dake ba indai ba Saba min alkawari Zakiyi ba........ "Kije dai bayan suna ki zo ki karbi kudin ki don ai kin San nafi karfin kudin ki matsalar matsiyaci kenan Bai iya samun wuri ba.... "Karki Kuma zagina akan hakki na, na Baki kwana Sha hudu ma ba bakwai ba Zan dawo karbar kudina ina me tabbatar Miki idan nadawo wata magana me kamar irin haka ta sake faruwa tsakanina dake na rantse Miki da Allah ZAN FASA KWAI ! Mero tafice afusace inda izzatu ta bita da kallo tana tunanin lallai mero zata zamo Mata katon kalubale kuwa in ba sakin hannun juna suka yi ba To Bari mugani sati biyu ya wuce me zai faru?.................... [5/16, 6:07 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 16* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ............ AK ya samu wayar hajiya Mama take sanar dashi haihuwar lubabatu inda ya yi murna ba kadan ba washe gari Bai ko gama aikin da ya kaishi sokoto ba ya juyo gida ya iso Yana tambayar lubabatu Babu inda ke Mata ciwo ko? Ta amsa da Babu ta Miko mishi yarinyar wadda ya kankame tamkar za a kwace mishi ita inda yayi Mata huduba da sunan hajiya Mama wato bilkisu inda za a kirata da ummita Hidima sosai ak yayi tamkar Bai San zafin kudi ba tundaga Kan lubabatu har zuwa ummita inda akayi taro lafiya aka Kare lafiya lubabatu na kula da yarta wadda aka shiryawa gata da Jin Dadi ga Kuma kaunar Yan uwa da dangi na iyaye kasancewar an Dade ana jiran ganin ya'yan eng abdukarim din sai ummita ta zamo son kowa. Acan Kuma gidan izzatu tamkar ba gidan haihuwa ba saboda ta Raina ajawalin mutane ba kowane take ganin ya cancanci tayi Hulda dashi ba shiyasa Babu wasu mutanen kirki sai Yan uwanta suma ba kowa ba don yanzu ne zatayi maka Gori koma ta nuna maka iyakarka Ahaka dai akayi suna yarinya ta amsa sunan Aisha humaira inda izzatu ke kiranta fulani Wai alkunya ce irin ta Yar fari Sai dai abin haushi abin takaici Wai har akayi haihuwa har sai da aka kwana shida kafin Allah ya kawo dungo ba don ta San anyi haihuwar ba a a sai don ta duba izzatu don tunda tazo tayi mishi maganar zubewar katangar ta har yau din Nan Bai taka inda take ba Wai sai da tazo ta samu haihuwa har kwana shida gobe suna Ta cika da mamaki yadda Kabir ke kokarin mantawa da ita arayuwar shi Karin wani mamakin ma izzatu ta Hana dungon jaririya Wai bacci take yi Tayi Mata barka da sauke Kaya lafiya tayi nufin komawa gida don ko Kabir din ba zata tsaya gani ba Ta fito kenan motar shi ta faka inda yake ta shuga da fita akan hidimar sunan gobe sai kawai yayi karo da mahaifiyar tashi Wai sai yaji Bai kyauta Mata ba. Yafito Yana fadin yaushe tazo? "Yanzu nazo Kuma har Zan koma.... "Baba ba suna kikazo ba da Zaki koma?......... "Ina da wata martaba ne a idonka da zaka Fadi haka? Kuma ka fada min haihuwar ne da zaka zaci sunan ya kawoni? Atake ya Gane Yana Mata ba dai dai ba har ta Kai ga tankawa duk hakurin ta Da sauri ya soma tuba da Bata hakuri akan Wai ya shafa a ne duk da ranta ya baci Amma sai da tayi mishi uziri Kai lallai abar uwa da danta Da haka ya lallbota har ta yarda zata kwana ayi suna. Washe gari kuwa aka soma cin uban shagali Wanda Kabir ya Kashi kudi ba na wasa ba akayi taro aka Kare inda Kuma washe gari dungo tayi nufin wucewa birnin zazzau inda ya yi tsaye aka debar Mata nama me yawa acikin kattin Rigunan da ya yanka ya Kuma hadota da kudi masu dama ta wuto tana addua da sa albarka Haka humaira fulani aka ci gaba da rainon ta itama da shirya Mata ALJANNAR DUNIYA komai ya tafi daidai Sati biyun da sister mero ta diba Bata Kara ko awa da minti ba ta diro gidan izzatu wadda sai da akayi da gaske kafin a samo Mata maganin da zata Sha ruwan nononta ya Zo don ta gilla karyar Wai Bai zo ba ne inda cikin Yan aikinta wata ta sanar da ita agarin su da akwai me bada magsnin irin wannan matsalar a garin dutse ta jihar jigawa don haka ta hada Mata tafiya taje ta Kuma tako sa a har tayi amfani dashi Kuma ruwan nononta ya Zo don haka take shayar da fulani inda Kuma a yau sister mero ta diro gidan don karbar hakkinta Ta shigo gidan ta samu izzatu na bawa fulanin nono inda ta dubeta a sheke ta watsar ta zauna akan kujera tana duban izzatu dake Mata kallon ke kadai Kika San sirri na "Gani na biyo hakkina sati daya Kika bada Ni Kuma bayi biyu ai na daga kafa ko???......... [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *page 17* *_insha Allah zamu koma muku posting a Rana so uku safe Rana da dare in hakan Bai samuba zamu koma so biyu a Rana in Allah ya Yar da_* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .......... Izzatu ta dubi mero cikin Jin haushi da takaici . Mero ta dubeta yadda take Brest feeding din yarinyar tamkar itace asalin uwar ta ta gaskiya "Uhum kinganki kamar dai ace da gaske kinji yadda akeji sai kokarin feeding ya akayi ma maman yazo? "Ba damuwar ki bace Ni bansan haka kike ba mero da ban hada tafiya ta dake ba Ina amfanin tafiya da matsiyaci? "Na ma fi da haka matukar kikce Zaki dawo min da bara bana akan hakki na don haka tashi ki dauko min in wuce me motar da na siya ya isheni da na kawo mishi kudin shi Izzatu ta Mike tana Saba fulani akafada tana fadin Banga amfanin tarayya dake ba tunda Baki da mutunci Ta shige daki ta rubuto check na milyon biyar ta Miko Mata "Sai abi wani sarkin ba na garin mu ba Mero ta dubeta tana kallon ceck din da take Miko Mata "Ai bamuyi dake Zaki bani takarda banki ba cash kikace Zaki don haka koma ki dauko min kudi na daidai. "Banda su ajiye sai dai kije banki ki karba ta fada tana cillo Mata ceck din afuskar ta Mero ta dauki cack din tana duba inda tayi arba da rubutun milyon biyar Ta dubeta "Ya Naga kin rubuta min milyon biyar amaimakon goma? "Biyar din Naga damar Baki don ko ke Kika yi cikin Kika haife iyakar ta kenan Mero ta Mike tsaye tana kwabe gyalenta ta na cin damara a kugun ta "Bari kiji in fada Miki izzatu bafiki iskanci don ni har takardar shaida sai da na Kama don haka bini sannu ko yanzu in fasa kwai rubuto min cikon kudina in wuce in ko Kuma yanzu in iske Kabir mashi in fasa mishi Kwan kigani idan Baki kwana gidan ku ba Da gaske kuwa ta Kada hantar cikin izzatu inda har ta rubuto mata cikon kudin ta tabata . "Ai kuwa godiya ma ya kamata in Miki don kuwa kin yi min silar farin cikin da ba Zan iya manta shi ba na gode sosai Allah ya Kara daukaka "To ameen in da gaske kike in ma ba gaske ba ne Allah ya biye bakinki Nima na gode da samun abinda ban taba zaton samu ba sai gani na biyu..... "Bana bukatar ganin ki a gidana don Zaki iya Zama barazana ga Rayuwa ta mu hadu Nan mu Rabu Nan Sister mero tayi murmushi ta fice inda ta shige mota ta nufi banki don ta fito da kudi ta biya me mota kudin shi. Fitar sister mero ya bawa izzatu damar kamo bakin zaren wani mugun qulli da tayi nufin zargawa mero Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira wani Dan ta Adda da ta sani Wanda ya taba yiwa wata kawarta aiki har ta zarga nata mugun qullin Don haka ta Kira wayar gambo mafiyas Wanda ya kware a iya Sara suka da ta addsnci Kara biyu gambo mafiyas ya daga "Allah ya taimaki hajjyata ta samu ne? Kwarai kuwa gambo maza kazo Ina son ganinka.... "An gama hajiya dama Babu komai ahannu na.......... "To maza garzayo kasamu kudi yanzu Minti Sha biyar ya iso inda take fada mishi abinda take so yayi Mata "Ka Gane ko gambo wata ce nake so ka bi min bayanta zuwa first Bank zata fiddo wasu manyan kudi shine nake son ka karbo min su ka dawo min dasu zaka ganta cikin mota 206 jar kala me lambar katsina yi maza gambo ka karbo min kudin Nan kar ka yarda asamu akasi ko sabani......... "Babu kuskure acikin aikina hajiya Ina me tabbatar Miki da awa uku tayi yawa kisaka Ranki inuwa kudin ki sun dawo Miki sun gama Ya fice Yana fiyto izzatu ta zauna tana dariyar mugunta "Uhum mero kenan yaro yaro ne yaro Bai San wuta ba sai ya taka mero kinci karya kin kwana da yunwa Gambo mafiyas ya iso bakin ya labe a gefe Yana kallon mutane me SHIGA da me fita ba inda ya hango motar sister mero wadda aka kwatanta mishi Sai ya soma dakon jiran fitowar mero Mero da ta gabatar da cek din da zata fitar su kansu sun girgiza Anna da suka duba asusun izzatu sai Basuyi mamaki ba atake suka Bata takardar da zata cike ta cike aka fitar Mata da kudin duka sai ta raba su ta saka milyon biyar cikin asusun ta ta fito da milyon biyar don taje ta biya bashi sau Kuma ta aje don bukatu Ta SHIGA motar ta ta nufi gida don ta Kira me mota yazo gida ya amshi kudin shi saboda zai fi sirri Sai dai wani Al amari dake Shirin faruwa ya gigita sister mero inda wata mota ta Sha gabanta cikin azama ta taka burki don kadan ya rage ta banki motar da ta Sha gabanta Atake gambo mafiyas ya fito ya na bude motar mero Yana kanga Mata bindiga agoshi Yana tambayar ta kudi Bataja ba ta jawo buhun kudin ta Miko mishi ya amsa ya koma motar sukaja motar aguje suka bacewa ganinta inda mero take sauke ajiyar zuciya ta iso gida tana tunanin waye ya San zataje banki? Babu ko shakka izzatu na da hannu akan wannan abin da akayi Mata koma ita ta turo Mata bakaken mabiya sai Kuma ta tuna da yadda izzatun taso yi Mata dungu akan kudinta sai kawai ta gano mugun kulli ne izzatu ta kullo Mata inda Kuma wata zuciya ke Bata shawarar tashi kije kuyi ta ta Kare Babu Wanda yasan zakije banki sai ita to komai zai iya faruwa Aikuwa ta fice zuwa gidan izzatu inda ta badda sawu da saka nikabi ta tari napep ya kawota kofar gidan izzatu inda Kuma cikin sa a ta ga motar da tayi Mata fashi ta faka har katon basamuden da ya yi Mata atakin da bindiga ya fito Yana rike da buhun kudinta inda ta tabbatar dai izzatu ce me alhakin yi Mata hakan, to yanzu meye abin yi? Anya kuwa idan tace SHIGA zatayi gidan izzatu ba zata saka katon ya illatata ba????............ [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *page 18* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Wata zuciyar tace Mata shiga kawai ki karbo hakkin ki tunda ma gashi kin gani ya kawowa wadda ta sakashi Har ta cire kafa zata tunkari kofar shiga gidan sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta Akul Kika SHIGA gidan can yadda Dan ta addar can ya nuna Miki bindiga komai zai iya faruwa gara dai ki koma gida ki sako sabon lale Amma SHIGA gidan can ayanzu akwai matsala Sai Kuma ta karbi wannan shawarar da fuskar fahimta ta juya gida Gambo mafiyas ya direwa izzatu kudin a gabanta inda inda ta Gane kudin ba duka bane Amma dai an rage ta Zaria rafar dubu dari ta bashi ya karba Yana godiya inda yace da wani aikin ya samu ta kirashi Da haka ya fice Yana zukar tabar iblis din shi Abinda izzatu bats sani ba shine shima gambo mafiyas sai da ya wari wasu kudin ya boye don harkar duka Babu Amana Amma izzatu Bata Gane ba ta dauki kudin ta mayar daki Komawar sister mero gida ta doko wa izzatu waya inda tana ganin Kiran meron gabanta ya Sara dass ! Amma sai ta maze ta daga da salon bagararwa "Sister mero ya kike ya aikine? "Lafiya Amma abinda Zan fada Miki izzatu karki yarda kice irin wannan wasan zamuyi dake don na rantse Miki da Allah sai na kaiki kasa warwas.......... "Me akayi Kuma mero?....... . "Karki yaudare Ni don Ni ba yarinyar goye bace idan kudin ki kike so ai ba sai kin turo min babbakun mabiya ba sai in maido Miki in karbi Yar mutane......... "Nifa bangane Abinda kike nufi ba mero wani Abu ya faru ne? "Kin fini sanin abinda ya faru saboda Babu Wanda ya San zanje banki karbar kudi sai ke to Akan me Zaki turo min Dan fashi bayan Ni da ke taimakon juna mukayi? Kuma magana Kare nazo dazu na tarar da shi Wanda Kika sa yayi min fashin ya Zo gidan ki da buhun kudina to saurareni da kyau na rantse Miki da sarkin da ya huran numfashi da tassarufin lamurana sai kin biyani kudina Baki Nan da awa ashirin da hudu ki turo min kudina ga lambar asusuna Nan Zan turo Miki idan Kuma kina bukatar sauran kudinki Zan maido Miki in karbi Yar mutane duk shawarar da Kika yanke Ina jiran kiranki......... Dit ta yanke wayar tabar izzatu da kyalkyala dariya "Uhum mero kenan na kula in ba kwanji na na motsa ba Zaki zame min kadangaren bakin tulu to duk Zan hada in kashe da tulun da kadangaren don Banga amfanin su ba Akarshe dai ta yanke shawarar turawa sister mero kudinta don suna game wayar sakon lambar account din ta shigo wayar izzatu a take kuma tayi Mata transfer ta wsyar kudinta suka SHIGA inda sister mero tayi murmushi "Uhum izzatu kenan tunda wannan turbar kike son mubi to Zan nuna Miki Ni har gobe takadarci Yana min Rana Baki sanni bane Amma Zan nuna Miki kece karamar Yar iskace Nasha gabanki har abada ke gaba da abada ma na wuce da iyawar ki Zan Kuma waiwaye ki don wasan mu Bai ma fara ba karamar marar kunya dake bileja Itama izzatu anata bangaren Tasha mugun Alwashin akan mero saboda ta kula itace zata zamo Mata matsala to su zuba shege NE zai fasa Bata santa bane nata iskancin kawai ta sani Bata San nata ba Allah yasa tsautsayi ko azal ya sa mero Kiran wayarta ko ma zuwa gidanta taga yadda ake kera Rashin mutunci Tom Bari muga yadda Za ayi haduwa ta gaba da sister mero da izzatu waye zai FASA KWAI............. [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 19* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Wata irin Rashin lafiya ta Kama dungo uwar Kabir mashi ciwo irin Wanda Bata taba yin irin taba Amma da yake ta iya jarumta da hakuri haka take ta jaganiya da Yan yaran rainon ta yaran Babu Wanda ya shekara biyu ga Yar banzar rigima wancan yayi kuka ta rurruga wancan yayi fitsari ta wanke wancan yayi Kashi ta wanke ba zata taba samun sauki ba sai sunyi bacci ko iyayen su sun karbesu Amma Duk da haka ciwon da takeji Bai sa ta kwanta ba duk da kallo Daya zakayi Mata ka Gane Bata da lafiya matukar dai kana Gane lamarin Rayuwa sai dai Rashin kudi ya Hana Mata zuwa Asibiti inda ta Bari sai ta karbi kudin rainon ta idan anyi albashi sun karbi kudin su Sai dai kafin albashin ciwo yaci karfin ta har ta Fadi kwance ciwo riris inda har rainon ma ya gagara Wata daga cikin masu kawo yaranta me suna Jamila ta shigo gidan inda ta iske dungon kwance abin tausayi "Subhallah ladidi Baki da lafiya ne? Wallahi kuwa Jamila Ina Dan gidana fahat? Yaron da take raino ya SHIGA dago Mata hannu Yana son ta dauke shi saboda sunyi sabo me karfi da yaran Ta Mika hannu ya taho ta rungume shi inda Jamila ke kallon ta cikin tausayawa "Amma ladidi kinje Asibiti kuwa? A a Jamila banje ba saboda Babu kudi hannu na.......... "Karki damu taso muje in kaiki ai lafiya tafi komai Jamila ta kaita Asibiti aka dubata aka Bata magun guna suka juyo gida inda jamilar ta kashe kudi masu dama sama da dubu goma Sha biyar duka dawo gida gungo nata zuba godiya don gaskiya Jamila na mutunta ta ko abinci me Dadi tayi sai ta Aiko Mata bare ta dafa nama "Karki damu ladidi ai mun Zama Daya Babu komai ke dai Allah ya Baki lafiya Ta amsa da ameen ya Allah Haka Tasha magani har sauki ya samu Inda wata ya cika Jamila ta dauki albashinta ta kawowa dungo hakkinta Amma dungo tace Allah ya sauwake wallahi ba zata karba ba Amma Jamila tace wallahi sai ta karba..... "Haba Jamila don dai nice uwar marasa mutunci sai na karbi kudinki ?...... "A a sai kin amshe su wallahi banyi don komai ba sai don Allah da zaman tare Allah ya Kara Miki lafiya ta aje Mata kudin ta dauko danta ta fito inda ta bar dungo da zubar hawaye Wai yau Dan da ta haifa ta wahaltawa shi ke gudunta yayin da can wasu da Basu hada komai ba sai musulunci da mutunci suke wahala Mata har suyi Mata abinda danta Bai yi Mata ba Babu abinda yafi Kona ranta irin yadda ta taka har gida ta sanar dashi zubar bangon ta Amma har yau Bai tada Mata ba asalima an kusa shekara Amma har yau zuwan shi guda Kuma yaga yadda aka saka zana amma bai Kuma zuwa ba Kuma yanzu da mutuwa tayi ba lallai ya sani ba to in ta mutu ma Yana da asara ne? Amma dayake tana mishi uzuri sai ta bar abin ya wuce ko aranta Bata aje shi ba taci gaba da rainon yaranta Wanda ke debe Mata kewa fiye da zato inda makocinta malam Ali ya shigo ya duba jikinta inda yake tambayar ta Kabir ya Zo kuwa? Tayi murmushi "Bai zo ba malam Ali , to Allah ya Kara lafiya da haka ya fice Yana mamakin wannan yaro da duniya ke rudu duk shaharar shi Amma abin haushi ya yasar da uwar shi sai tayi raino ta ke ciyar da kanta Amma shi Yana can cikin katon gida daga shi sai matar shi suke hutawa Anya kuwa Bai dauko hanyar lalacewa ba? Uwafa? Uwar ma irin dungo wadda yasan yadda ta wahalta mishi har ya tako matsayin da ya tako? Babu wata riba ko nasara da ake samu ba ta silar uwaye ba koma an sameta to zata sulale saboda Babu albarkar iyayen sai yayi mishi adduar Allah ya shirye shi ya kuma shiryi Al ummar musulmi Baki Daya.......... [5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 20* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* Yara suka taso cikin kulawa inda ummita iyaye da Yan uwan uwa da na uba ke nuna Mata so da kauna da Kuma kokarin dorata bisa bigiren tarbiya me kyau inda tayi matukar sabo da ubanta eng AK Wanda ko yaushe tana hannun shi Yana Mata wasa har tayi sabo me yawa dashi don in har Yana gida to Bata Rabuwa da shi tafi like mishi fiye da Uwar ta shima Kuma Yana janta jiki don wani irin so yake Mata jinta yake tamkar Ruhin shi lokacin da ta Kara wayo ma dakin shi take kwana in kaga sun Rabu to baya gari shima sai da hikima in ko ta na farke ya tafi ya barta to zata wuni kuka sai da kyar zata hakura in Kuma ya dawo kaf abinda ya Riko natane ba kuma zata yarda ya kubce Mata ba Lokacin da ta Kai shekara biyu sabon ya Kara karfi da ta kula zai yi Mata wayo ya gudu sai tayi ca cumi rigar shi ta rike Taki saki sai anyi da gaske kafin akwace shi hannun ta Sai da ta shekara biyar kafin lubabatu ta Kuma haihuwa inda ta haifo Mubarak bayan Mubarak sai Ahmed sai Fatima daga kansu haihuwa ta tsaya inda yaran ke samun kulawa Amma duk tsananin so da kulawar da ake Basu Bai Hana atarbiyan ce su bisa tsari ba don gaskiya lubabatu tana da kokarin tarbiya Bata kuma yarda da sakarci ba ko don ta tashi da tata tarbiyar ne? Sai yaran suka tashi cikin tarbiya da girmama mutane duk inda suka SHIGA sai sun zamo abin so da Sha awa Sai dai soyayyar ummita da ban take azuciyar mahaifin su sai dai Yana kokarin saita Kan yaranshi ba tare da nuna wariya ba Amma duk da haka ummita na karbar girmama wa irin ta babban wa sai lamarin gidan eng AK ya zamo abin Sha awa akasin na gidan Kabir mashi Daular da ake tanadawa humaira fulani ta zarce afadeta don akullum shaharar Kabir karuwa take kwagiloli Kai da Kai suke zuwa inda izzatu tace haihuwar fulani ne tazo da goshi Wai da ma ummul khairi aka samata inda kuma Kabir ya yarda da maganar ta Kullum Kara shahara yake inda izzatu ke matukar kulawa da humaira wadda ta taso ba kwaba ba harara ko da ko zata yaga kudi Yan magana sukace nono alkalin Da ai kuwa hakan ta na Shirin tabbata domin kuwa nonon da humaira ta tsotso ajikin uwar goyon ta na Shirin tabbata domin kuwa ta taso da wata irin sangarta da tabara bama wannan ne abin ji ba tun tana Yar shekara biyar ta iya tijara da wulakanci hakama idan ta na kuka Bata Jin rarrashi inda Kabir ke matukar so da kaunar ta Amma batayi sabo da shi ba sosai kamar izzatu Amma duk wani gata tana samun shi Makaranta ma pravet aka saka ta me shegen tsada aka Kuma yi sa a tana da fahimta sai dai kullum sai tayi fada da yara Yan uwanta inda Kuma kaf din yaran da take fadan dasu Suma ya'yan wasu ne da yawan su ma sun fita matsayi da daraja shiyasa ake Zama lafiya Amma Wanda izzatu ta Raina ajawalin su yanzu ne zata fito ta wanke mutum soso da sabulu in ma taga Kai ba kowa bane to yanzu zata sa akulle ka Lokacin da fulani ta shekara goma izzar ta ta fito fili duk wani wulakanci na izzatu fulani ta kwashe shi kaf har ma tacewa izzatu Bata iya ba inda Kuma tace waje take so akaita tayi karatu ai kuwa izzatu tasa Kabir ya sama Mata makaranta a America ta Kuma dage ta tafi inda acan ne Kuma ta Kara koyo izza da dagawa har da jijji da Kai har Allah da ikon shi ta kammala karatun ta dawo gida Inda Kuma can ummita eng AK ya so fiddata waje tayo karatu Amma ita ummita tace Bata son abinda zai rabata da abban ta tafi son kullum ta ganshi Yayi murmushi "to sai kinyi min alkawari Zakiyi karatu sosai don so nake kiyi karatu me zurfi...... "Nayi maka alkawari Abba in Sha Allah ba Zan baka kunya ba kuma sai kayi alfahari Dani", Hakan kuwa akayi itama tayi nata karatun anan cikin garin Abuja har ta Kare inda ita Kuma ta taso cikin nuna irin nata alkalin da ta tsotso Babu hayaniya sai tsantsar irin tarbiyar da ta samu ita da kowa sai mutunci da mutuntawa da Kuma sanyin hali inda shima eng ya soma shahara akan kwagiloli Kan na kamfuna da Kuma na gwamnati komai dai cikin rufin asiri Rayuwa Kuma na tafiya cikin godiya da Kuma wadata..................... [5/16, 9:33 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 22* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* [ ...........Mutane suka soma fusata da wannan wulakanci da humaira ke yi kowa Yana son ya wuce gida amma saboda iskanci ta saka kida ta ware Kara ta bar mutane da danno horn Wanda ya cika kunnuwan mutane inda gayen da tayi hakan domin shi ya Gane tayi hakan ne domin ta Kona ranshi ai kuwa Yan ta wagarshi dake bayan shi suka fito daga motar dake bayan shi katti ne majiya karfi da ita da motar sukayi Mata dibar Karan mahaukaciya suka aje gefe Sai jinta tayi an fizgi motar an kaita gefe inda ashar din da mutane ke ta dura mata Kan Bata musu lokaci da tayi ya Kara Bata haushi inda ta fito taga yadda bayani motar ya bandare saboda dibar Rashin albarka da akayi Mata motar da ko sati batayi da kawowa ba haushi ya isheta ga Kuma zagin da ake ta sheko Mata abinka da Yar gata haihuwar Asibiti sai kawai ta bare da kuka shabe shabe ganin Babu Wanda ya kula ta sai ma kallon banza da ake jifar ta dashi ya sa ta shigo motar ta taho inda taji gaba daya motar ta sauya saboda bandarewar da tayi haka ta iso gidan Yana kuka inda izzatu ta fito da sauri tana tambayar ta me ya faru? "Momy dubi yadda ya mayar min da mota wallahi ba zan yarda ba...... .... "Waye da wannan aikin? "Wani dan iska ne momy bayan yayi min Bari Kuma yasa Yan iska sukayi min haka da mota wallahi sai ya biyani...... "Muje ki nuna min shi don ubanshi ko waye uban shi sai na saka an daure min shi Bai San ke ko wacece bane? Hana suka SHIGA mota suka fice izzatu na ta zuba sababi har inda abib ya faru sai dai ko me kama dashi Basu gani inda izzatu ta SHIGA sababi da dai ta Gane harara cikin duhu take sai tace su koma gida kawai "Dan iska Allah ya kure shi da ya Kare Rayuwar shi gidan sarka matsiyacin banza bai San ke din zaune kike da kuturinki ba? Haka suka dawo fulani na kukan ita motar ta ya zatayi? Izzatu ta rungume ta tana Bata hakuri tana fada Mata Wai za a gyara Mata motar ta...... "Ni momy sai dai asauya min wata wallahi bana sonta bama Zan sake hawanta ba.......... "Sha kuruminki Yar lele za a sauya Miki ko jirgin sama kike so ubanki na da kudin siya Miki bare wata mota can da kudinta ba zasu wuce milyon goma ba Haka kuwa akayi Bata Kuma hawan motar ba sai da Kabir ya sauya Mata wata wadda tace tagani ana talla a aljazira ai kuwa akayi Mata oder ta soma burkar gari Wata Ranar asabar ta nufi park don ta huta bayan tayi order abinda take so ta shimfida darduma ta zauna tana chat awayarta har uku na maraice inda ta nade dardumar tayi nufin tafiya gida tana tsaye zata bude mota ta SHIGA taji saukar bawon ayaba afuskar ta Ta dago da sauri don taga daga inda ya fito sai kawai idonta ya hasko Mata gayen da yayi Mata wulakanci har hawa biyu Har ga Allah baiyi da niya ba asalima Bai San ya watso inda take ba Ta tafi afusace Kan ta sauke mishi lodi abin haushi kafin ta Isa har yaja motar yayi gaba abinshi Haka ta juyo tana kuka izzatu ta tarbeta tana tambayar ta "Momy sai na wulakanta gayen can me na yi mishi yake min haka? "Ba dai Wanda ya lalata Miki mota ba? Shine momy yau ma sai da ya watsa min bawon ayaba afuska....... "Wai Dan gidan uban waye ne? Dame yake takama? To koma uban waye ubanshi duk Ranar da ya sake na Kama shi ga hannu sai na saka an daure shi ya Kare Rayuwar shi a kurkuku. Nan ma haka izzatu tayi ta masifa har dai suka Gane ba mafita sai yazo hannu. Ciwo ya dawo wa dungo sabo gal inda wannan karon ta nufi Asibiti inda aka yi Mata awo aka gano matsalar ta Abin ya firgita likitan Amma ita dungon Bata firgita ba don tuni ta soma hasashen hakan Likitan ya dubeta cikin rudani da tashin hankali don Yana tausayin ta tun wancen zuwan da tayi yake tausaya Mata "Baba matsalar kwada ce tare dake Kuma mun duba munga saura guda daya Tak shin kin taba bada kodarki ga wani ne? Ta amsa da eh kwarai kuwa nasan anyi hakan...... "To baba sauran gudar da tayi saura tana da matsala don haka ana bukatar sake dasa Miki wata kafin wannan gudar ta tsaya da aikinta don ko za a dawo kanta sai anyi aikin dashen Ta dubeshi cikin zafin ciwo 'to yanzu kamar nawa ake bukata wurin aikin likita? Yawan kudin da ya ambato Mata ya kusa sakata faduwa inda ta tabbatar da lallai sai ta nemi daukin danta Kabir don wurin shi ne kawai zata iya samun wannan kudin don haka tacew likitan zata yi iyakar kokarin ta har ta samo kudin kome kenan zata dawo da haka sukayi sallama da likitan ta dawo gida Ta sanar da malam Ali abinda akace ta Kuma ce zataje Abuja wurin Kabir ta sanar dashi abinda kenan...... "Inaga ki Bari naje tunda Baki da lafiya dungo ko Zaki iya zuwa? "Eh Zan iya malam gobe zanje in Sha Allah sai afadawa su Jamila naje abuja don yau lahadi na San gobe litinin zasu kawo yaran su "To Babu matsala Allah ya kaiki lafiya ya dawo dake lafiya yasa kuma adace ya tashi kafadunki.. Ta amsa da Allahumma ameen Washe gari ta bugi hanyar abuja............... [5/16, 9:33 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 21* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........A yanayin tsarin halitta humaira fulani farace Amma ba irin farin Nan me haske sosai ba da kadan tafi wankan tarwada sai dai akwai wani Abu Wai shi kyau ga Kuma diri me tsari don dirarriyace me daukar hankali Bata Faye son yawan kwalliya ba Amma duk shigar da tayi zata karbeta Kuma ta zamo Zara cikin taurari akwai yauki da yanga da Kuma nuna matanci sai dai tsabar dagawa da izgili har da izza to dama yaushe barewa ke gudu danta ya rarrafa? Agefe Daya Kuma tsarin halittar ummita ya zamo Fara ce tas har tana yellow yellow ita kuwa macece me son ado da kwalliya Kuma idan tayi kwalliya Kai kace Yar tsanace Bakinta dauke da siririn hakorin makka Wanda shekarar da ta wuce ne abban nata ya biya musu kujera su duka hada haj mama sukaje suka sauke farali dama hakorin makka na burgeta sai Kuma akayi sa a ta sanyo shi inda ya Kara fito da martabar ta inda samari ke ta kawo mata Hari Amma Allah Bai sa taji tana son tsayawa da su ba inda Kuma abbanta yace ba yanzu ne zata soma magana da samari ba sai dokar tayi Mata Dadi ta kulle su ta jefar da makullin Ta kwashi su Mubarak a motarta da abban ya siya Mata elements suka nufi sahad don Allah yayi ta me son kayan makulashe dangin Zaki shiyasa Bata sati Bata zo sahad ba yadda take son chocolate da biscuits Bata damu da abinci haka ba shiyasa take kwaso kannenta suzo sahad ko jifatu su kwashi abinda suke so Ta faka motar a parking space dai dai da da fakawar wata katuwar mota kusa da inda tayi parking cikin Rashin sa a kyauren motar ya gogi motar da ta faka kusa da ita. Fulani ta fito tana kallon yadda kyauren ya Dan gogi motar ta ta lailayo wata ashar marar tsarki ta antakawa ummita ta fito tana Bata hakuri.....Kafin ta cire hannu ta tsinkawa ummita mari "Ubawaye ubanki agarin Nan da Zaki gogae min mota.? Wannan shegiyar motar Taki me kama da amalanken shanu ita kike kokarin lalata min tawa motar da sai ta siyi Taki hudu ko biyar? Ummita ta dubeta tana dafe da inda ta mareta dayake ba me son tashin hankali bace sai ta kuma Bata hakuri tana fadin ba da gangan tayi Mata kuskure ba Haka fulani ta wuce tana sababi inda ummita ta sauke ajiyar zuciya taja kannenta suka shiga cikin sahad din inda Mubarak ke fadin shi fa sai yaci ubanta idan ta kuma zagin ummitan....... "Rabu da ita Mubarak Allah ya hada ta da daidai ita Ni bana neman tashin hankali. Haka suka SHIGA suka judo kayan kwalam din su fal ledoji inda itama fulani ta siyo ice cream da da wasu abubuwan inda suka fito kusan Atare ummita na mamakin ta Akan zafin Kai da zuciya Adaidai kofar fita fulani ke gaba su ummita na bayanta inda sukayi taho mu gama da shi, shi zai shigo ita Kuma zata fita suka gwabza wani irin karo Wanda har kayan hannunta suka tarwatse ice cream din ya watse ajikinta ga Kuma goshinta da suka gwabza karo ya daku sosai "Ya subhallah ya fada Yana dafe goshin sa da yaji Yana mishi radadi ya duka Yana tattaro Mata kayanta da suka zube kasa ya kwaso su Yana Miko Mata inda zuciya ta ciyota maimakon ta karba sai kawai ta gaura mishi Mari tana sababi "Dabba da Kai zakayi min Bari salon kayi min sata banza matsiyaci". Ya dubeta Yana shafa inda yaji tafin hannun ta kamar shi namiji me jini ajika ace mace kamar wannan ta cire hannu ta tsinka mishi Mari ? Sai yaga ai shi yayi Mata laifi Don haka yace ta Bari ya SHIGA ya amso Mata kayan da yayi Mata asara.... "Kaine matsiyaci kaje da sauran ma na bar maka tunda dama kazo kayi min sata ne... Ta wuce fuuu ta bar shi da yi Mata rakiya da ido , Amma lallai yarinyar can ta sameshi da yawa yadda yake da zafin Kai Amma ace har amare shi Amma bai dauki mataki ba? Yana kallonta ta fice aguje ta bar sahad din inda su ummita da kannenta suka fito Mubarak nacewa "Kinga Allah ya saka Miki anty . "Uhm na gani Mubarak Kai dai bi duniya a sannu don Bata da tabbas itama Ina rokon Allah ya shiryeta don wallahi naji Ina son ta duk da abinda tayi min...... "Wallahi Ni bana sonta anty tunda Bata da kirki. Ummita tayi murmushi tajawo mota suka dawo gida Inda Mubarak ke fadawa ummansu abinda ya faru asahad ummita tayi mata bayanin komai haj lubabatu yace Allah ya kyauta sai ki kula . Ita kuwa fulani ko da ta fito daga sahad sai ta zarce jifatu ta siyo abinda take muradi tana tafe tana sababi da tijara ita kadai inda tazo dai dai traffic light ta tsaida su. Nan ma said masifa take Akan jiran traffic din inda ta waiwayo bayanta taga dogon go slow din da aka hada inda motar dake bayan ta ta hango gayen da yayi Mata Bari abakin sahad Taja tsaki tana Jin tamkar ta fito ta shake shi inda kuma traffic ta Basu hannu Amma tayi kunnen uwar shegu Taki matsawa saboda Wai ta Rama abinda yayi Mata. Aka ci gaba da danno Mata horn Akan ta matsa gaba Amma ta share sai ma latsa kida a CD ta Kuma Ware kidan.............. [5/17, 10:10 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 23* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Cikin ikon Ubangiji ta iso garin Abuja sai dai zaman mota ya jigatata don haka da kyar da gano gidan Kabir inda take ta shessheka numfashi na neman daukewa tamkar me ciwon asma Fulani ta tarbota don wani ikon Allah jinin su ya hadu Ta rungumota tana fadin "Ya Kaka Baki da lafiya ne? Da kyar dungo take magana "Bani da lafiya Aisha ina mutanen gidan ne? Izzatu ta fito ta aunowa fulani harara don Bata so take shiga sabgar tsohuwar "Tashi ki bace min da gani kilbabbiya, ta fada tana hararen humairar Ta tashi ta nufi dakin ta tana tausayin kakarta Izzatu ta dubeta tana dafe da gefen cikinta alamar ciwo yake Mata "Baki da lafiya ne dungo? "Wallahi kuwa izzatu jiki yaki Dadi Allah yasa Kabir Yana gari ? Yana Nan sai dai inma kudi Kika zo nema bashi dasu don kwanan Nan lamarin sai godiyar Allah "To Allah ya rufa asiri dama cikon kudine so yayi min don Zan siyar da Yan awakina in nemi magani ........ "Ai da kin bugo waya ba ki wahalar da kanki ba yanzu irin haka ke Dadi kinzo kin Bata kudinki Kuma ba lallai ki samu kudin ba Sai izzatu ta SHIGA sababi tana fada Wai ba a haka sanar da mutum ake in za a zo wurin shi ba Wai azo ayi mishi tashi na kamaka ba in turawa ne in baka sanar dasu zuwanka ba ko ruwa ba zasu baka ba Haka Kabir ya dawo ya samu tsohuwar shi cikin halin ciwo Kuma ko ruwa ba a Bata ba bare abinci. Kafin ma ta sanar dashi matsalar ta izzatu ta rigata inda ta Dora da Wai Babu kudi yanzu Shima sai yabi bayan matar tashi akan dai Babu kudin don ya Gane izzatu batayi na am da bayar da kudin ba Dungo tayi murmushi "Babu komai Kabir ko aro ne anemo min ciwona Yana bukatar gaggawa....... "Gaggawa Kuma ? Yo dungo ko mutuwa ta shiga gidan da Babu ai dolenta ta fita Kabir ya dubi izzatu Yana mikewa inda ya nufi daki ta bishi "Gaskiya baba Bata da lafiya izzatu Bata taba tambayar kudi wurina ba So Zan Bata duk abinda take bukata........ "To kudin da zaka bani na bikin Barth day din fulani fa ? Shiyasa kaji tun farko na ce baka da kudi ka Bata kudin mota kawai ta koma gida zuwa wata me kamawa idan sun samu sai abata don hidimar zatayi maka yawa Haka kuwa akayi ya dawo ya sanar da ita ya buga waya ko rancen ya samu Amma abin ya gagara da haka ya aje Mata dubu biyar yayi Mata fatan samun lafiya Ta Dade zaune tana Kore sauro inda kuma har yanzu ba a Bata ruwa ba bare abinci Fulani ta fito ta dauko Mata robar madarar laban da abinci Wanda ta zubo Mata naman kaji zuku zuku ta dire gabanta "Ya Kaka Baki Jin yunwa kikayi shiru Baki Sha ko ruwa ba? Ta karbi madarar ta soma Sha kafin ta soma cin Naman inda wani ikon Allah sai taji kamar ana rage Mata ciwon Ni Kam gidan iko nace ko ciwo Yana son abinci me kyau Adakin humaira ta kwana cikin gidan sauro inda dungo ke ta saka Mata albarka washe gari ta hado kayan ta fulani ta kawo ta Tasha inda izzatu ke taksicin wannan kawa zuci na fulani ga jemammiyar tsohuwar Ai kuwa da ta dawo daga Kai dungo Tasha sai da taja kunnen ta kamar ta cire shi tana fadin Wai Babu ruwanta da tsohuwar "Haba momy kakata ce Kuma ace Babu ruwana da ita? ...... Ta gwabje Mata Baki "Baki hada komai da ita ba hanya ko ta rafi nono ko na gora meye hadan kifi da kaska? Fulani ta shige daki tana gunin Jan kunnen ta da akayi inda Kuma sister mero ta shigo gidan da sallamar ta me kwari. Arude izzatu ke kallon ta "Me ya kawoki gidan Nan mero? Me kikazo yi ? "Haba irin wannan tambayoyi tamkar na SHIGA kabari ko Dan ruwa ba za a bani ba ? Bakonka Annabin ka fa...... "Baki cikin layin bakon ka Annabin ka donke kallon tauraruwa me wutsiya nake Miki don haka Fadi abinda ya kawo ki kiyi ki bar min gidana.......... "Kai hajjaju makkatul mukarramina wannan dogon sharhin tamkar Baki San daga ina nafito ba? To dama matsalar kudi ce ta kamanni shine na tuna dake don haka milyon biyu kurum nake so ba yawa....... "Agidan ubanwa za a samo milyon biyun? Wace irin jaka ce ke ne? Kina bina bashi ne Zaki wanko tsantsaman jikinki kice na Baki kudi? "Karki Kuma zagin ubana izzatu arziki ya hadamu ba tsiya ba ke komai sai an biyo Miki ta bayan gida ake daidaita wa dake? Meye don nace ki bani milyon biyu Ina ce farin cikin da na Samar Miki ya zarta milyon dari? To bani in wuce don bana son ta kaimu ga cacar Baki in kuwa ba haka ba wallahi yanzu ne Zan fasa kwai ......... "Allah ya tsine Miki idan Baki fasa dangin kaji da tsuntsaye ba. Bari in gaya Miki mero na fiki tashanci da iya lalata ban San haka kike ba wallahi da ban yarda na hada hanya dake ba Amma ki sani duk Ranar da Kika kaini karshe na rantse Miki da Allah sai dai ki tsinci kanki kushewa Zan Baki milyon biyu Amma ki kaddara daga kanta ko a mafarki kar ki yarda kice kin sanni don sani na zai zo Miki da matsala.......... "To naji hajiya izzatu dauko min in wuce don sauri nake. Izztu ta rubuto mata cek ta Bata ta karba tana godiya inda izzatu ke Mata kashedi da idonta Sister mero ta Mike tana fadin Wai sai gani na biyu....... "To a gani na biyun ki tabbatar kin taho da likkafanin ki don Zaki zo inda Zaki gama yawo. Mero ta kyalkyale da dariya ta fice daga gidan inda izzatu tayi shiru tana tunanin mero da irin salon da take nufin kawo Mata Itama sai tayi murmushi"mero kenan muje zuwa Ni dake za agane waye gaba......... [5/17, 10:10 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 24* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Bai Kara tunawa da batun wata halitta Wai ita dungo ba asalima tun da ta tafi ya share da lamarin ta inda aka kashe kudi sosai wurin yiwa fulani bikin murnar cikar ta Sha bakwai da haihuwa akayi taro na manyan Yara ta Kuma samu kyaututtuka daga kawayen ta na karatu Kana biyu da yin bikin yake sanar da izzatu anyi mishi alkawarin bashi kwangilar gyaran wutar lantarki wadda zai samu manyan kudin na tashin zance inda ta cika da murna don duniyar su zata Kara haskawa Sai dai me ? Maimakon yaji Kiran daga fadar me bawa shugaban kasa shawara Kan abinda ya shafi aikin. Sai ji yayi Wai har anyi kwangilar an gama har ma an Dora da wasu manya har uku Kuma Babu wadda ta fito da sunan shi sai sunan eng AK Wanda a yanzu shike Kan gaba na karbar kwangila daga gwamnatin tarayya abinda ya girguza Kabir mashi har ya gurfana agaban me bawa shugaban kasa shawara "Ranka ya Dade na tuba don Allah a gafarce Ni idan har da kuskure a cikin aikina to asanar Dani Zan gyara ban San abinda nayi ba aka mayar Dani gefe anyi mini alkawarin bani kwangilar gyaran wutar lantarki Amma sai ji nayi har anyi ta angama menene laifina? Alh uba Dan yaro ya dubeshi "Agaskiya Kabir sunyi bincike ne akanka inda suka gano kana bada rata da yawa har aikin ya zamo Babu nagarta inda sukace aikin eng AK yafi naka nesa ba kusa ba shiyasa suka juya akalar Kan shi Amma idan zaka gyara ba damuwa bace sai nayi maka request wata ta gaba abaka don nasan wata Kil waccan akasi aka samu Ya zube Yana godiya da alkawarin zai gyara da haka ya taso ya taho Yana mamakin yadda eng AK ya samu SHIGA fiye dashi matukar kuwa hakan yake nufi to zai ware kwanji sai ya dawo da bara bana Akan harkar shi da ake son yi mishi fin karfi Izzatu ma tamkar zata fasa kuka Amma tace itama ba zata taba yarda wani ak can da tagama rufe babin shi ya ce zai Kuma sake shiga Rayuwar ta da mijinta ba da sakel wallahi Aguje fulani take gudu akan hanyar don dama haka take Bata tafiya sannu sai dai tamkar zata tashi sama Cikin sa a ta shawo kwana daidai da wata katuwar mota itama ta shawo kwana Kuma hanyar Dole sai daya ya kauce kafin dayan ya samu zarafin wucewa Su duka suka sunno hancinan motocin su alokaci daya sukayi kallon kuda Atare inda atake ta ganeshi gayen Nan ne da yayi Mata Rashin mutunci har sau biyu dama neman shi take sai gashi sun Kuma haduwa inda zai Gane itama Yar zafin Kai ce Tama fi shi zafin Kai don haka sai ta kashe motar Taki fitowa shima ya kalle ta Yana mamakin kaddarar dake hadosu Suka Kuma yin kallon kuda inda yaga har da harara take Aiko mishi inda yayi murmushi Wanda ya kular da ita shi yaki yin baya itama Taki yin baya kowa na takama da zafin kanshi sai akayi sa a itace akan hanya shi in za a kwana bashi da damuwa ta Gane hakan ne ganin yadda ya tada kida amotar ya bawa banza ajiyarta inda ita Kuma aka fara Kiran wayarta don tana Kan hanyar zuwa bikin kawar tane Kuma itace babbar kawa shiyasa ma ta fito aguje gashi Kuma akwai tazarar da zata iya takawa kasa ba don haka kawai sai ta fito don ganin ya Dora kanshi akan sitiyarin motar Yana lumshe ido tamkar me bacci Kawai sai ji yayi gilas din motar tashi yayi Kara tatssss Ya dago da sauri inda yaga ta sauke katon dutsin akan gilas din motar shi wadda ita da kanta ta Gane tafi karfin yaro shiyasa ma ta ke ganin Yana ji da kanshi Abin ya Bata mishi Rai matuka gaya har Bai San lokacin da ya sauke Mata Marika biyu afuska ba abinda ya haddasa Mata daukewar gani na wucin gadi Lokacin da ta dawo duniyar mutane ne ta soma wanke shi da manyan asharai kafin ta fasa kuka ta Kira wayar izzatu take fada Mata ga Wanda ke Mata wulakancin Nan ya mareta har idonta ya fice........ "Kina Ina yanzu? Ta kwatanta Mata aikuwa izzatu ta Figo mayafi ta fice tamkar zata tashi sama inda ta Miki hanya sai gata agaban su fulani nata rera kuka Aguje izzatu ta fito ta soma wanka mishi Mari hagu da dama tanayi tana antaka mishi ashariya amma da yake namijin duniya ne Bai ko motsa ba Yana kallon yadda izzatu ke sauke mishi lodin zagi kala kala................ [5/19, 7:15 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 26* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........."Babu komai Anwar Rashin sani ne Kuma itama ai tayi maka Rashin mutunci Zan Kuma ja kunnen ta kaima kayi hakuri. Atake Anwar ya Kira wayar yasa aka saki su fulani inda Kabir yayiwa Mr President sallama ya wuce station ya kwaso su izzatu Wanda sukayi firgai firgai inda fulani ke ta kuka izzatu na Bata hakuri "Wallahi momy ba Zan taba kyale gayen can ba yayi min wulakanci Kuma yasa an kulle ki saboda Rashin mutunci ? Ko Zan kyale shi Akan abinda yayi min wallahi ba Zan kyale shi Akan kulleki da yayi cikin zarnin fitsari ba ko waye ubanshi kuwa duk Ranar da muka sake haduwa dashi Wallahi sai ya Raina kanshi da haka suka iso gida ta wuce ban daki don tayi wanka acewar ta duk zaurin fitsari take Shigar ta bandaki izzatu ke tambayar Kabir waye wannan yaron da yasa akayi musu wulakanci? "Anwar ne Dan gidan Mr President....... "Koda naji gadarar yaron ta nuna ya Taki wani Abu Amma Yana da hakuri gaskiya don inda yace sai yabi kadin ashar din da nayi ta banka mishi Babu shakka da fitowar mu ba yanzu ba......... "Ai albishirin ki ma kiji wani Abu da yasa nace gara da akayi Wai Mr President din ke nemawa Anwar din auren fulani Wai salon soyayyar sune haka........... Izzatu ta rangado guda me karfi inda take Jin tafi Kabir farin ciki yau ace yarta na auren Dan gidan shugaban kasa ita me yafi wannan farin ciki? "Kace gara da akayi Kabir ko ba komai lamarin zai zamo Mana tamkar jari don Dole ma abaka kwangila tunda ka zamo surukin masu Abu da kansu ....... "Ashe dai kin Gane Nima hakan nagani Zan dawo da martabata da ake son yi min fin karfi... "To Amma wani hanzarin ba gudu ba ta Yaya kake ganin yuwar lamarin alhalin fulani ta kullaci yaron ba kadan ba Kuma shima Ni Banga wani Abu da zai nuna zasuyiwa juna uzuri ba? Wannan me sauki ne idan akayi auren can zasu shirya kansu shima namiji yayi biyayya bare ita mace? Ai Dole ne ma tayi biyayya ke dai kar ki sanar da ita ayanzu sai lamarin ya tunkaro sai ta San komai da haka suka aje magana Dungo baiwar Allah ciwo yaki Jin magani duk Yan dabarunta na Shan magani Amma ciwo yaki inda ta siyar da Yan awakinta ta hada kudin da Basu Kai ko Rabin abinda ake nema ba ta nufi likitan ta Yi mishi bayani ya tausaya Mata matuka inda tace ya ajiye kudin hannunshi idan ta Nemo cikon zata zo ayi Mata aikin Ya karbi kudin sukayi rubutu ya Kuma nemi address dinta ta kawo shi har gidanta inda yake ganin kokarin ta na son ta taimaki kanta da kaucewa roko da tumasanci sai yake Jin ko da cikon ne ma zaiyi Mata in ta kama don haka sai ya saurareta Zaman gidan yayiwa ummita yawa inda ta nemi shiga makarantar koyon computer Kuma eng ya Goya Mata baya ta shiga inda take Jin ta rage kadaici Sai ya zamo ta fannin shaharar aikin kwangila ya zarta Kabir mashi kashe arna don gudar da akace za a rokar mishi ma ba a bashi ba eng AK aka bawa ita , idan har baiyi kuskure ba kusan wata goma Sha daya kenan Rabon da ace mishi ga aikin kwangila don haka yake ganin eng ne yayi mishi shigar sauri abinda kuwa ba zai yarda dashi kenan ba Izzatu da take ta durawa ak din ashar tace ya zamo Dole yaje ya samu ak ya yayi gargadin shi Akan ya Daina karbar kwangila sai dai ya Bari idan anyi a Yan mishi wani Abu Ai kuwa ya sallamawa eng Wanda ya fito ya tarbeshi suka gaisa inda ya fito mishi ta hanyar siyasa "Eng nazo ne inji adadin kwangilar da akace za a bani Amma shiru har yanzu sai ji nayi Wai an baka kayi ta harma ka Dora da wasu shine abin ya bani mamaki. "Kwarai kuwa me gida nayi ta har ma na dora da wasu guda biyu Wanda nakeyi yanzu. Amma banji Dadin tada maka alkawari da akayi ba. Sai dai Zan baka shawara ka nemi dalili idan na kuskure ne sai agyara shi don gaba don yanzu haka akarshen shekara za a gabatar da wasu manyan kwangilolin har biyar kaga idan ka nuna bakaji dadin alkawarin da aka tada maka ba to Ina me tabbatar maka da acikin wadan can biyar din za a baka wasu inaga hakan ya dace kayi. "Kwarai kuwa eng ka kawo shawara na Kuma gode da haka sukayi sallama ya dawo gida Yana fadawa izzatu yadda sukayi........ "Rainin hankali ne kawai yake son shigo maka dashi ta Yaya zakaja kunnen gwamnati indai ba salon Dan sauran girmanka ya zubeba? Idan har irin wannan ta Kuma faruwa nagane shi ke son talauta ka to Zan sako gambo mafiyas atafiyar don in ba koya mishi hankali akayi ba to munaji muna gani sai ruwa ma ya gagare mu Kabir yayi na am da hakan inda suka ci gaba da zaman jiran saurare Amma shiru tamkar bawa ya leka garin su.............. [5/19, 7:15 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *page 25* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........."Kai Nan har Dan iska ne Kai da zaka saka shimfideden hannunka ka marar min yariya? Dama ina jiranka akan wulakancin da kayi Mata har sau uku saboda Kai Dan iska ne? Waye ubanka a duk fadin Nigeria? To zaka Gane karyar iskanci kake don sai ka Kare Rayuwar ka agidan maza. Kasan ko wacece ita da irin gatan dake gareta ? To bude kunnen ka kaji da ranta ya baci gara gara amaimsita yakin badar da tabuka ita kadai ce gayya zakuma ka Gane gatanta ya zarce ayi Mata ko harara bare kallon banza Izzatu tayi ta sababi da masifa tana wanke shi soso da sabulu Amma ko daga Kai baiyi ba bare ya tanka inda izzatu ta fiddo wayar ta ta Kira D P O na yankin ta sanar dashi tana son aturo Mata motar Yan sanda biyu suzo su wuce Mata da wani Dan iska da take son abatar dashi gaba daya Ta gama wayar tana mishi kallon banza inda ta dubi motar shi ta dora da sababi "Dan iska da Kai ka aro mota ka shigo gari shine zaka nemi shiga hurumin yarinyata shege da ganinka ma kayi Kama da masu wankin mota wata Kil wanki aka kawo maka shine ka shigo gari don kayi bagu da barazana da motar mutane don da ganinka matsiyacine Kai zaka Gane ka tabo abinda yafi karfin ka har iyayen ka sai an kulle min su tunda Basu iya tarbiya ba...... Baice Mata komai ba har tagama cinye fuskar shi tas inda Kuma motocin na Yan sanda suka faka har mota uku cike da Yan sanda tamkar zasu Kama Yan fashi "Kunga shegen Nan ku Kama min shi cewar izzatu inda taga kaf din Yan sandan sun wuce wurin Wanda take cewa su Kama Amma me? Sai gani tayi suna kamewa da sarawa abinda ya bawa izzatu haushi......... "Ku Kama min shege ku aje sai Naga ko uban waye yake daure mishi kugu.......... D P O ya dako Mata tsawa wadda Bata San ko ta wacece ba inda suke ta bawa Anwar hakuri suna sarawa abinda ya daurewa izzatu Kai Bata Sha mamaki ba sai da taji Anwar din na bada umarnin Kama ta ita da fulani kawai sai gani tayi suyo musu zummuwa Aka garkama musu ankwa ana iza keyar su SHIGA motar Yan sandar........ "Kafin ku wuce dasu kusa yarinyar tazo ta janye motar can Kuma kar abada belin su sai in Ni Naga damar hakan Kuma don yanzu kar a kirani sai Nan da bayan wata uku don inaso uwar da Yar su koyi darasi. Ita Yar Ina so ta koyi tarbiya ita Kuma uwar don idan ta sake haifar wani dan Nan gaba ta San irin tarbiyar da zata bashi Aka dakowa fulani tsawa ta fito jiki na rawa ta janye motar ta koma cikin motar Yan sanda akaja su aka wuce dasu inda izzatu ke kallon lamarin kamar wani mafarki ko Shirin film Wai ka dauko Dan sanda ya kama maka mutum Amma sai lamarin ya juye akanka waye wannan yaron da taga Yan sandan ma kamar tsoron shi sukeji? Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira Kabir take fada mishi abinda ya faru inda isar su station din ko minti Sha biyar ba ayi ba Kabir mashi kashe arna ya iso don yayi belin iyalan nashi Azaton shi ficen da yayi da sharar da kowa ya sanshi yasa yayi zaton da yazo ne za a bashi belin su izzatu Amma sai ya iske sabon Labari Wai babu batun beli sai Nan da wata uku Yayi mamakin wannan yaro da izzatu ta fada mishi to waye? Da ya nemi sanin yaron da yayi wannan aikin D P O ya sanar dashi Anwar ne, Mamaki ya Kama Kabir Jin Wai Anwar ne to Ina suka hadun da fulanin har sukayi wannan wautar? Da haka yayi sallama da caji ofis din ya nufi me bawa shugaban kasa shawara don ya zamo tsanin shi na ganin Mr President don ya San shi kadai ne zai saka Baki Anwar din ya fito mishi da iyalin shi don haka ya tunkari Alh uba Dan yaro Wanda ya sanar dashi abinda ya faru tsakanin yarshi da Anwar Wanda ya bada umarnin kulle su har sai bayan watannin uku shine yake son Isa wurin Mr President don asaka Baki Anwar ya hakura Ai kuwa alh uba Dan yaro yayi mishi jagora har sukayi nasarar gani Mr President Kabir ya zayyane mishi komai inda yayi murmushi Yana cewa "Yara ne su duka Kuma suna takama da zafin Kai kayi hakuri Kabir don Allah bansani ba Amma yanzu Nan zai zo Nan inji abinda yasa yayi hakan ya fada Yana dauko wayar shi ya latso lambar Anwar Kara biyu ya dauka inda uban yace yazo yanzu Yana son magana dashi ya amsa da gashi Nan zuwa ya aje wayar Ya dubi Kabir "Kabir fatan ba zanyi maka shisshigi ba idan na tambaye ka bakayiwa Yar tamu miji ba? Ya amsa da baiyi Mata miji ba inda Mr President yace zaiso su hada Anwar da ita fulanin aure don wata Kil wannan tsamar tasu salon tasu soyayyar ne. Wani Dadi da ya rufe Kabir tamkar ya shide don Yana ganin auren fulani zai zamo mishi auren jari da yadda zai dawo da kwangilolin shi da ake son yi mishi fin karfi don haka jiki na rawa ya amsa da Babu matsala duk yadda Mr President ke so hakan za ayi daga karshe ma yace ya bawa Anwar din auren fulanin idan an shirya azo ayi magana Mr President yaji Dadi sosai dama Yana neman Yar da zai hada da Anwar tunda shi har yanzu cewa yake Wai baiga wadda tayi mishi ba don haka ya zabi yi mishi haka don baya son yaron nashi ya bude Tasha shiyasa yake son yi mishi aure Mr President ya kawo kyautar girma ya bada yace akaiwa fulani ta siyi kayan kwalliya abind ya gigita Kabir mashi shi Kam zai iya cewa gara da akayi da haka Anwar yayi sallama ya shigo ya zube Yana gaishe da Kabir mashi don ya sanshi sosai Yana ganinshi agidan nasu sai dai har ga Allah Bai zaci shine uban yarinyar da tayi mishi gatsali ba. Mr President ya tambayeshi "Su waye kasa aka kulle a station? Ya fada mishi duk yadda abin ya faro har zuwan izzatu da irin tozarcin da tayi mishi duk ya fada musu inda Mr President yayi murmushi "To kanwar ka da uwarka kasa aka kulle don iyalan Kabir ne sai kaje maza kasa asake su............ Yazube gaban Kabir Yana bashi hakuri "Kayi hakuri Abba ban sani ba ne ka gafarce Ni yanzu ne zansa akansu har gida............. [5/19, 4:36 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 27* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Abinn tausayi abin kuka da zubar hawaye ciwon dungo duk me tsoron Allah Dole yaji zuciyar shi ta raunan bisa Dole ta aje raino don Bata iyawa ciwo yaci karfinta Makotan ta malam Ali da Jamila sun Mata karah matuka gaya inda malam Ali ke tur da Allah wadai da Kabir da duniyar dake Rudin shi Jamila Bata San dungon nada wani da da har ya shahara ba kallon da take Mata Bata taba haihuwa ba Amma da dungon ta fada Mata tana da Da Yana zaune garin Abuja...... "Kuma ke Kika haifeshi dungo? Kwarai kuwa Jamila baya son dai rabata Koko Yana ganin ya wuce akalli fakiriya Irina ace nice na haifeshiba? Oho "Amma gaskiya kiyi hakuri dungo indai ke Kika haife shi gaskiya Bai maida biki ba Kuma Bai zamo da abin alfahari ba tunda Bai damu da damuwar ki ba shi kuwa me yake nema cikin duniya da har take Rudin shi yake Miki hakan? Allah ya shirye shi yasa ya Gane Amma fa Yana da tarin kalubale gaban shi Wanda alhakin kadai zai iya tadeshi Shi kuwa malam Ali da ya shigo yaga dungon cikin halin ciwo ya tausaya Mata Ya dubeta "Dungo kabiru kuwa yasan Baki da lafiya haka? "Ya sani malam Ali tunda har gida na taka naje na sanar dashi "Ya Zama Dole akirashi yanzu don Dole Dole ce. Ya a karbi wayar ta ya lalubo lambar shi ya kirashi Wayar ta shiga tayi ta burari kamar ba zai daga ba sai da aka jera mishi Kira kusan bakwai kafin ya daga Kuma Yana gani ya kuma san me lambar Yana ganin dai idan ya dauka aiki zata Sara mishi shiyasa ya watsar da Kiran sai da yaga ba za a hakura da Kiran ba ne ya dauka akule "Kabiru kana lafiya? Cewar malam Ali ya amsa da lafiya "Dama don in sanar dakai tsohuwa fa ba lafiya har ana bukatar ganin ka da gaggawa in ma Babu wani uzuri me nauyi akanka to ko zuwa gobe ne sai ka Zo. 'to Babu matsala ya fada Yana aje wayar ba tare da yajira sallamar malam Ali ba Washe gari kuwa sai gashi ya iso da safe inda ya iske dungon cikin halin ciwo ta rame ta Kare abin tausayi ga me raunannar zuciya ma sai ya koka Amma dayake akwai karfin hali sai kwarara kanta take. Ya zube Yana gaishe ta Yana Mata sannu da jiki ta amsa tana tambayar shi iyali ya amsa da kowa lafiya Malam Ali ya shigo suka gaisa inda yake mishi bayanin ciwon da ya ke damun tsohuwar tashi Ya kadu ba kadan ba Jin Wai ciwon Koda ne matsalar ta Ya sauke ajiyar zuciya "Aikin gaskiya babba ne kudi ake kashewa ba kadan ba yayin dashen Koda Kuma Ni gaskiya yanzu bani da kudin da Zan iya biyan aikin. Sai dai ko a saurara zuwa gaba....... "Haba kabiru irin wannan halin da take ciki kake maganar a saurara? Idan har baka da kudin biyan aikin sai kuje a ciri taka a dasa Mata don duk Wanda zaiyi hakan bayanka yake "Nima fa ba lafiyar Nan gareni ba malam Ali a dai saurara din har zuwa gaba shi ciwo shi ke shiga da garaje Amma lafiya sai ahankali. Malam Ali ya bishi da kallon takaici da hasara da dai haihuwar irin wannan yaron gara abarar dashi a zauna Babu haihuwa don haihuwar irinsu in ba damuwa da bakin ciki ba Babu abinda suke gadarwa Kabir ya zura hannu acikin aljihun shi ya debo kudi dubu goma ya dire agabanta "Gashi inna a rike wannan Zan dawo bayan kwana biyu inga yadda jikin ya zamo......... "A a kabiru kaje da kudinka na gode Amma Zan so ka tsaya in FASA MAKA wani KWAI don kaji idan na cancanci irin wannan sakayyar a gareka......... "Inna yanzu sauri nake don akwai wata kwangila da aka bani yau Zan soma ta ki aje duk wata magana gefe sai na dawo..... Wayar shi ta dauki tsuwwa inda ya ga sunan alh uba Dan yaro ya dauka da sauri inda ake sanar dashi ana neman shi Kan kwangilar da zai Fara Da sauri ya fice daga gidan Basuyi cikakkiyar sallama da uwar tashi ba bare Mal Ali Hawaye ya zubowa malam Ali ya share Yana duban dungo "Anya kuwa ke Kika haifi kabiru dungo? "Uhum Ni na haife shi Mal Ali...... To ki tuna indai har a Asibiti Kika haife shi sauya Miki shi akayi Baba zaton Dan halak zaiyi abinda yayi Miki, mu da muka hada makotaka kawai dake muna Jin tausayin ki Amma ace da ya kasa Jin Kan uwar da ta wahalta maka? Dungo ta Mike cikin layi da jigatar ciwo ta hankado kar Kashin gadonta ta jawo wata katuwar mantimoti ta jawo wani kunshi kulle cikin tsumma ta kuma jawo wata tsohuwar takarda ta nufo malam Ali dake kallon ta da mamakin abinda take nema. Ta zube kunshin da takardar agaban shi "Malam Ali Bari yau in fada maka wata magana da ta zamo sirrina saboda Kai din ka zamo Dan uwana Kuma wannan sakon Ina so ka isar dashi ga kabiru don inaji ajikina ba zai dawo ya riske Ni da Rai ba don nasan zai wuce shekara Bai dawo ba..................... [5/19, 4:36 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 28* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ...........Malam Ali ya bita da kallo inda ta kwance kunshin tsumman sai ga kudi dumus Yan naira dubu dubu sabbi gal a daure da takardar banki malam Ali mamaki ya kashe shi daga zaune har dai yayi kokarin tankawa "Kina da kudin Nan dungo Amma Kika zauna da ciwo har Kika Sha wahala haka? ........ "Ba kudi na bane malam Ali wannan kudin kabiru ne na abinda ya gada kuma shine KWAN da nake cewa dashi ya tsaya in fasa mishi ya ki don haka ga Amana Nan dukiyar maraya ce ka isar gareshi dukiyar da mahaifin shi ya mutu ya bar mishi ce ba Zan taba mishi abinshi ba saboda Nima an bani nawa Ina Kuma Ina tsoron taba mishi dukiyar shi don nasan hadarin dake tare da cin dukiyar maraya aka Kuma sanar dashi na yafe mishi Amma yayi sannu da wannan Rayuwar. Ta Miko mishi tsohuwar takardar "Wannan Kuma sadaukarwar da nayi mishi ce wadda shi ya kasa yi min irinta itace rubuce aciki ya karanta ko don ya Gane Ni naso shi tun kafin ya shigo duniya Amma shi duniyar ta rudeshi ya watsar da lamarina . Ta fada da hawaye na bin idonta Malam Ali ya karbi kudin da takardar Yana dubanta "Lallai uwa da Da sai Allah dungo kina aje da kudi kina fama da rainon yaran da ake biyanki ki cida kanki kina tanadawa Dan da yake can Yana more Rayuwar shi baya ma sakoki a lissafi. Zan cika Miki wannan alkawarin Zan Kuma kiyaye da ko duba takardar ba Zan Bari wani yayi ba bare ataba mishi kudin shi ke Kuma Allah ya Baki lafiya Ta amsa da ameen "Nayi maka izini ka duba takardar Nan malam Ali ko don kaima ka San abinda nayiwa kabiru Amma shi ya kasa yi min irin shi na yarda ka duba ai Ni da Kai mun Zama Daya Malam Ali yaji Yana son duba takardar ko don ya fita daga zato Ya bude takardar ya soma bin rubutun cikin ta Yana karantawa dogon rubutu ne har ya gama karance shi tsab inda hawaye ya kece mishi Banda Yana da karfin hali da Babu abinda zai Hana shi kokawa Dungo ta dubeshi "Ban San lamarin zai motsa zuciyar ka ba da bance ka karanta ba......... "Dungo Anya kuwa kabiru na son gamawa lafiya? Anya kuwa Yana son DUNIYA da Rayuwa su barshi Zama cikin salama? Kinyi kokari Allah ya biyaki da ALJANNAH kin Kuma fita hakkin shi shine ya kasa fita naki Ya Mike ya fice tun Bai durawa kabiru ashar ba. Haka ya wuni Yana mamakin yadda wannan yaro da abinda ke Rudin shi Haka Jamila ta wuni zaryar dubata da girka Mata Dan abin tabawa inda da Rana ta girka Mata wake da Yar anta ta kawo Mata inda ta isketa ciwon ya taso abin sai da yasaka Jamila hawaye ta tallabota ta Dora kanta bisa cinyarta inda taga kamar tana Suma ta soma shafa Mata ruwa afuska har ta kawo numfashi ta farko cikin wani irin yanayi me kama da son wucewa kiyama inda Jamila ta tashi don ta taro mota su wuce Asibiti Ta samo me napep da kyar saboda wahalar da napep din keyi ta iso gidan inda ta iske wani bakon Al amari me kama da mafarki "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Ina dungon ta shige ? Ta duba gidan kaf Amma Babu dungo Babu dalilin ta Ta ci gaba da karade lungu da sako na gidan Amma maganar guda ce Babu dungo Babu dalilin ta Malam Ali ya shigo shima Yana son duba dungon Amma ya riski lamarin me kama da almara Jamila kuka take tana karawa inda malam Ali ke tunanin ko dai rijiya dungo ta fada saboda bakin cikin abinda danta ke Mata? Don haka yayi maza ya bude rijiya Yana dubawa Amma Babu ita Sai aka shiga nema da Jaje da duba asibitoci Amma Babu labarin dungo har dai daga karshe aka barwa Allah lamarin inda aka rufe gidan dungon Wanda hatta wayarta Bata dauka ba komai Yana Nan abinda ke Kara saka baba Ali zubar hawaye shine abinda ya dauki dungo shin wani ne ya dauketa Koko ita ta gudu da kanta ? Idan ita ta gudu ina ta tafi to? Idan Kuma wani ya dauketa meye hikimar daukarta? Haka malam Ali ya rufe gidan ya na tunanin Ranar da zai iske Kabir ya isar mishi da sakon uwarshi.................. [5/21, 5:47 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 29* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ......... Aguje fulani ta sheko akan titin tamkar zata tashi sama inda ta wuce wata hamshakiyar mota wadda ta rasa gano inda ta santa. Atake ta gano motar gayen Nan ce da yayi Mata Rashin mutunci Ai kuwa da sauri tayo rubos ta dawo inda taga ya faka motar shi zai siyi tuffa da inubi Ta fito tana sanye katon gilashin ido Wanda ya mamaye fiye da Rabin fuskar ta tana sanye da doguwar Riga ta yadin material lemon green anyi mishi adon fulawowi ja da Baki tayi kyau sosai ta yafa mayafi Dan karami Wanda Bai rufe Mata dogon goshinta ba Wanda iska ke kadawa tamkar kwallo Kai tsaye ta tunkar me kayan fruit din tana takawa tamkar me tafiya akan kwai. "Malam bani aybar Nan ta dari biyar ta fada tana Mika mishi gudar naira dubu Ya karba Yana saka Mata aleda ta Ciro guda biyu tana barewa inda Anwar ke kallonta Yana mamakin yadda take mishi kallon da wa ka shigo garin Abuja? In har ya fahimta dai dai ma sai da yaga bakinta na motsi duk da baiji abinda take fada ba Amma yayi sa ar jiyo tsakin da tayi Me fruit din ya Miko Mata cikon dari biyar dinta ta dubeshi ba tare da ta karba ba. Ta Nuno Anwar dake zaune cikin mota Yana kallon ta "Ka bawa wancan matsiyacin sadaka don nasan irinmu irinmu ya ke jira yayi maula ta fada dai dai da ta jefa mishi bawon ayabar afuskar shi Daya daga cikin masu biye dashi don bashi kulawa wato body guard dinshi da ya kula da abinda tayiwa uban gidan su ya daga hannu zai sharara Mata Mari Amma da sauri Anwar ya dakatar dashi. "Da dai ka barshi ya mareni ya Maro ajalin shi jaki da shi Yana biye da jaki Dan uwanshi, Ta bude motar ta tashige ta figeta aguje ta hau titi inda wani hamshaki da abin ya faru akan idon shi yaji ya mutu da son fulani don shi Allah yayi shi da son mace me tsiwa tana burgeshi don haka da sauri ya shiga tashi motar ya rufa Mata baya inda suka bar Anwar Yana mamakin wannan yarinya daga karshe dai yayi murmushi ya siyi abinda ya kawoshi ya wuce gida Sister mero tayi sallama gidan izzatu tana murmushi inda izzatu ta fito tana nunata da yatsa , "Ina fatan kinyo wankan gawa kin Kuma taho da likkafanin ki don Ina me tabbatar Miki dab kike da kushewa.......... "Wai Ni na mutu yanzu izzatu? Kai bana zaton Koda kuwa zanyi ido hudu da mutuwar to Zan roki tayi min alfarma in gama dake tukuna ta dauke Ni , ai Ni in kin ganni lahira kaini akai don haka SHIGA ki fito kudi nazo karba......... "Saboda gyatumin ki ya bani ajiya? "Ko daya gyatumi na Bai Baki ajiya ba Ni dai na Baki ajiya.......... "A gidan ubanwa Kika bani ajiyar? Ke mero ki fita idona wallahi na rantse miki in Kika kaini karshe Zan iya murde Miki wuya ki mutu murus ! "To Bismillah ai ke da kanki kinsan Ina da kaddara a wurinki itace humaira inda kikayi kuskure da tun farko kikace Lada Zaki biyani da cewa kikayi siyar Miki da humairar zanyi da ban bibiye ki don haka ladar aikina har in mutu ba Zan Daina karbarta daga gareki ba don haka dauko min kudi in Kama gabana idan Kuma Zaki iya siyenta ayanzu to muyi ciniki ki bani milyon dari in bar Miki ita har abada idan Kuma ba Zaki iya ba to Zan Rika zuwa ina karbar Yar milyon biyu ko uku idan bukatar hakan ta taso.......... Tasss! Ta dauke meron da mari.... Mero ta dubeta cikin mamaki na karfin halin marinta "Kika mare Ni izzatu?...... "So ma nake kice Zaki Rama Marin kiga yadda ake hawa hanyar lahira "Uhum bama Zan Rama ba saboda ke din jakata ce ko ince asusuna don haka dauko min in wuce milyon biyu da dubu dari biyar nake so yau don Ina Jin tausayin ki da uku zance ki bani...... Karar motar fulani da izzatu ta jiyo Wanda ya alamta Mata dawowar ta yasa taga Bari kawai ta sallami izzatu don Bata son ta fahimci komai don haka ta rubuta wa sister mero cek ta Bata Wanda yayi daidai da shigowar fulanin wadda ko kallon mero batayi ba inda meron ke Mata kallon tayi saurin girma "Momy na dawo cewar fulani dake Hawa Kan bene saboda taga momy tayi bakuwa . "To sannu da dawowa. "Sai ki tashi ki tafi Allah Ubangiji yasa tsautsayi ko kaddara su sake dawo dake Nan gidan inda Zaki Gane kinyi kuskuren shigowa duniya arashin dace Mero ta Mike tana murmushi "To na gode uwar dakina a huta lafiya ta fice daga gidan inda izzatu ta rakota da wata matsiyaciyar harara A kofar fitowa gidan sister mero taga hamshakiyar motar me daukar hankali tabita da kallo inda shi Kuma na cikin motar ya fito Yana tsaida sister mero ta tsaya suka gaisa inda yake sanar da ita wata yarinya ya biyo wadda ta shiga gidan yanzu . Atake mero ta Gane humaira yake magana "Allah sarki ai ya ta ce ince dai ba wani Abu tayi maka ba? "A no Babu abinda tayi min kawai na biyota ne don Allah ya jarabeni da kaunar ta ya fada Yana rusunawa don yaji tace itace uwarta "Karka damu Alh sai dai ka Kara hakuri don Bata tsayawa da samari Kuma ma ubanta ya ce ba yanzu zaiyi Mata aure ba Amma tunda Allah Ubangiji ya kawoka bani lambar ka sai muyi magana don Nan din ba gidan mu bane munzo wata hidima ne da an Kare zamu koma gida in yaso sai muyi magana "Ok to mama Babu matsala ya bude motar ya dauko Mata compliment card din shi ya Bata inda mero ta ga suna shi honorable bello Rimaye Bata tsinke da lamarin ba Sai da taga kyautar gieman da yayi Mata suka Rabu akan zasuyi waya ya tafi Yana Jin lallai yayi sa a Mero tayi murmushi "Kai lallai abar Allah da lamarin sa wannan yarinya uwarta ta iya haihuwa Ni Kuma na karbi haihuwar ta a sa a yanzune wasan mu da izzatu zai dauko sabon salon da zai kayatar da me kallo da saurare................ [5/21, 5:47 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 30* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Tunda Kabir yayi kwangilar Nan har yau ba a Kuma kiranshi an bashi wata kwangilar ba inda akayi ta cin burin kwangilar hako Sola da akace za ayi a kauyuka biyar da yake zaton zaiyi har Yana cin buri hatta izzatu ma ta ci nata burin inda Yar lele humaira fulani ma ta shigar da tata bukatar ta son asauya Mata mota wadda ta gani a tashar MBC fitowar shekarar 2019 inda Kuma akayi Mata alkawarin da anyi kwangilar an gama za a yi Mata oder ta sai dai me? Shiru ta bashi Labari inda ya Gane lallai an maida shi aljihun baya koma angama dashi A fusace ya zaro wayar shi zai Kira eng AK inda izzatu ta dakatar dashi 'zuwa ya kamata kayi ba Kiran waya ba na lura wannan mutumin so yake yaga bayan mu Kabir idan ba sako gambo mafiyas atafiyar nayi ba ba zai saurara Mana ba. Da sauri ya tashi mota ya nufi gidan eng AK don suyita ta Kare Eng ya kwashi iyalanshi suka fice country Moll inda suke ta jidar abinda ya kawo su duk da silar zuwan ummita ce wadda tacewa abbanta tana son zuwa don siyo biscuits da kayan makulashe inda shi Kuma ya kwaso su duka suka wuce don gaskiyar magana yanzu duniyar nayi dashi Ummita da Mubarak da Ahmed da Fatima suka nufi wurin kayan kwalam suna ta jidar abinda suke so cikin sa a ya shigo don siyen makilin da wayar iPhone kawai sai idon shi ya fada kanta wani Abu ya daki zuciyar shi ya zuba Mata ido Yana kallon ta har Bai San lokacin da kafar shi ta taka ta Isa inda suke ba ya Kai hannu Kan abin takai hannu suka dire hannu alokaci daya inda tayi saurin duban shi shima ya dubeta sukayi kallon kuda atare inda yayi saurin Miko Mata abida ta Kai hannu tayi saurin Jan hannun kannenta suka bar shi rike da biscuits din Yana musu rakiya da ido inda ya saki baki Yana kallon su har suka fice inda yake tambayar kanshi Anya kuwa yayiwa kanshi adalci ace Yana amsa sunan kirista yace musulma yake so? Gambo mafiyas da yaji shirun shi tayi yawa ya kwado mishi Kira inda ya dauko abinda ya kawo shi ya fito Yana waiwayen ummita har dai gambo mafiyas ya kula da kallon da yakewa ummita ya faske keyar shi "Lover boy kayo kamu ko kake zuba Mata ido? Wilson yayi murmushi Bai tanka ba suka bar wurin Lokacin da suka iso gida eng ya hango motar Kabir mashi afake inda ya Gane wurin shi yazo Don haka ya cewa iyalan shi su shigs ciki zaiga bakon shi ya budewa Kabir falon da yake karbar Baki ya karrama shi da ruwa da lemu Yana mishi sannu da zuwa "Ba ruwa ya kawoni Sha ba AK Jan kunnen ka nazoyi don na Gane Kaine ka ke kokarin gurgun Tani tun kafin ka Fara kwangila nake yi ba Kuma Zan yarda zuwan ka yasa ka kassara niba don haka ka janye jikinka in ko kaki ji to ba zaka ki gani ba AK ya dubeshi Yana karanto hasbunallahu wa Ni imal wakil don yasan wannan mutum yadda ya fito Yana fada mishi hska to Babu abinda ba zai iya yi ba "Kayi hakuri me gida Wallahi bani da laifi akan duk abinda kake zaton Ni nayi maka Wallahi ban da hannu Abu daya na sani ana fada Akan aikinka to Zan baka shawara ka gyara don ana fadin kana bada rata shiyasa aikin Babu nagarta wannan shi na sani Kuma me gida nifa kanenka ne komai ya samu bawa da sanin Allah Ni da Kai Babu Wanda yasan gobe sai Allah Ni ban Isa na tare Rabon ka ba duk inda ka shiga sai ka samoshi......... "Bance kayi min wa azi ba so nake kawai kace ka Daina aikin kwangila har abada ba Wai wani makararren wa azinka Wanda na Saba ji ba. "Gaskiya me gida ba zanyi maka karya ba don Bata cikin tsarins maganar gaskiya ba Zan iya barin kwangila ba tunda bani na tsara yinta Arayuwa ta ba Allah ne ya zano min ita don haka Ni ALHERIN Allah kawai nake roko ko da gwamnati ta daina yi Dani to zanyi ta mutanen dake can waje komai da lokacin da sa........... "To shikenan tunda haka kace Amma kar kayi kuka Dani akan abinda zai sameka ba Wai don na rasa yadda zanyi bane yasa nake ta binka a a don in fita hakkin ka Amma tunda ka kawo taurin Kai sai ince zakaga abinda zai faru...... "Me gida ai Babu abinda zai faru sai ALHERI................. "To shikenan tunda haka kace Ni na wuce Ya Mike Bai ko yi mishi sallama ba ya fice inda AK ya soma karanto addu oin nema tsari ya koma cikin gida Yana fadawa lubabatu yadda sukayi da Kabir mashi kashe arna inda itama ta bashi shawarar suyi ADDU A itace kadai mafita Amma mutum a yau Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro. "To Ubangiji yayi min katangar karfe da duk wani me sharri da abin cutarwa ta amsa da Allahumma ameen. Afusace Kabir ya koma gida izzatu ta tarbeshi tana tambayar yadda sukayi da AK din ya Kuma zayyane Mata yadda sukayi inda tace "Kaji ko ? Kaji irinta ko har ya dubeka ya fada maka Wai aikinka Babu nagarta? Duk yadda kake kallon lamarin da sauki bashi da sauki Kuma idan ba gambo mafiyas aka sako cikin tafiyar ba to sunanka ma ya kusa Daina motsawa.......... "Abinda ba zanyarda dashi ba kenan don haka maza ki Kira min gambon Nan yazo yayi min maganin wancan marar kunyar wato eng AK Izzatu tayi murmushi ta jawo wayar ta ta dokawa gambo mafiyas Kira Kara biyu ya dauka................... [5/22, 6:19 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 31* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ......... Izzatu ta jawo wayar ta ta dokawa gambo mafiyas Kira Kara biyu ya dauka "Allah ya taimaki hajjyata in karaso ne? "Kwarai kuwa gambo mafiyas maza kazo kayi min maganin wani tarnaki dake shirin konani taho da sauri don Allah......... "Angama hajiya gani Nan zuwa........... Minti talatin gambo mafiyas ya karaso inda Kabir ya dubeshi ya tabbatar da zai iya aikata kowane irin ta addancin Yayi gaisuwa wurin Kabir inda izzatu take Kora mishi bayani "Me Kaka so ayi mishi Kabir? Ga gambo Nan zai cika maka kowane irin aiki kake so don aikin shi Babu sabani bara kuskure fada mishi duk yadda kake so ayi mishi inma batar dashi kake so ayi nasan gambo mafiyas ba zai taba baka kunya ba. Kabir ya dubi gambo mafiyas "Gambo Ina so ayiwa eng AK abinda sunan shi zai Daina zagawa duniya inaso abatar min dashi ta yadda Zan dawo da duniya ta sabuwa tunda bayyanar shi ce take neman kaini kasa warwas "Angama me gida bamu address din gidan shi yau din Nan zamu kaddamar mishi Atake Kabir ya Basu address din gidan har da hoton shi sukayi sallama ya fito Yana cewa su saurare shi zasuji yadda abin zai kasance Sai dai wani akasi da aka samu Aranar shine gambo mafiyas ya samu Kiran wani abokin shi dake Lagos Kan wata harkallar wadda za a yo wata SATA ta manyan kudi don haka ya bar aikin su izzatu ya shilla Lagos inda ya wakilta ya ranshi su Wilson da zarto wadanda suka horu da aiki suka Kuma kware Amma Wilson din ya fi su kwarewa shiyasa gambo mafiyas yafi ji dashi duk da kasancewar shi mabiyin addinin almasihu Amma sauran duk hausawa ne su hudu sai Wilson na cikon biyar duk suna aiki da gambo mafiyas inda ake bin dare afasa shaguna ko su haura gidaje suyo sata atakaice dai Yan fashi Wilson ya yi shiri shida su zarto suka nufi gidan eng AK da son aikawa dashi kiyama don umarnin da aka Basu kenan Suka kumayi sa a suka samu haurawa gidan eng a wani dare suka Kuma tadoshi shi da iyalan shi suna bukatar kudi ya Kuma dauko ya Basu inda cikin sa a idon Wilson ya fada Kan ummita dake sharar kuka akan atak da zarto yayi Mata agoshi Sun rufe fuskokin su da face mask idon su kurum ake kallo inda ummita ta kula da kallon da yake mata shi Kuma atake ya tuno da ganin da yayi Mata a country mall da irin daukar da tayi mishi da mafarkan ta da yayi tayi har ya Rika zuwa country mall din Wai ko zai sake ganinta Amma ko me kama da ita Bai gani ba sai gashi Wai yau yazo har cikin gidan su da umarnin kashe mahaifin ta atake yaji zuciyar shi tashiga rawa ko babu komai ba zaiso abinda zai sakata zubar hawaye ba don haka ya yanke shawarar sama Mata farin ciki akasin cika umarnin da zai barta Cikin damuwa Tsini Wanda ya yiwa eng AK atek da bindigar yake fadawa Wilson shifa zai cika aiki ne ko suyi su wuce Da sauri Wilson din ya dakatar dashi inda yake fadin wrong address Suka dubi juna inda Wilson din ke fadin su fice kawai da sauri sukayi gaba inda Wilson ya dauko jakar kudin da gwalagwalan su lubabatu da ummita da aka karbe ya zube musu agaban su Yana Basu hakuri ya dubi ummita ya huro Mata kiss ya wuce da sauri suka bar gidan ida zarto ya dauko wata jaka me dauke da kudi wadda yace Wai ba a shiga arziki afita haka Nan Gambo mafiyas ya Kira Wilson da son yaji yadda aikin ya Kaya Amma Wilson ya sharara mishi karyar Wai wrong address ne aka bada Kudin da zarto ya dauko su suka rage musu zafi inda gambon ke fadawa izzatu wrong address ne aka sami inda izzatu taketa yiwa gambo sababi Wai ya fara saka wasa a aikinshi in ko hakane gaskiya ba zasu daidaita ba inda yace ta Bari zai dawo Nan da sati guda shi zaiyi Mata aikin da kanshi don ta San Yana Nan da hatsabibancin shi da haka sukayi sallama tace tana sauraren shi Nan da sati dayan ................... [5/22, 7:10 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 32* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Hajiya Mama tazo Jin abinda ya faru ga abdulkarim jikinta har Bari yake don Ubangiji ya hasko Mata lamarin amafarki inda gari na wayewa ta Kira abdulkarim take tambayar shi suna lafiya dai ko? Ya fada Mata suna lafiya sai dai abinda ya faru don haka hajiya Mama ko Karin kumallo batayi ba ta tashi direba ya kawo ta gidan AK Dukan su suka zube gaban hajiyar tana tambayar su "Basu dai taba kowa ba ko? "Basu taba kowa ba hajiya hatta kudi da gwalagwalan da suka karba sun maido sai Yan Wanda ba za a rasa ba................... "Alhamdulillah tunda dai Basu taba kowa ba sai mu dage da addua Ubangiji yakiyayeka dukkan sharri ya Dora ka Kan makiya suka amsa da ameen da haka hajiyar ta koma gida tana ADDUAR Allah ya Kare Mata danta. Hon bello Rimaye ya soma budewa sister mero bakin aljihunshi akan son auren humaira fulani inda meron ke shirya yadda zata tunkari izzatu Amma acewar ta sai ta tatsi hon yadda Koda izzatu zata nemi kawo Mata wargi Wilson kuwa ya kasa samun nutsuwa don muddin zai runtse idon shi to Babu shakka zai hango ummita bare kuma yace bacci zaiyi kaf burinshi da tanajin shi zai Kare ga mafarkin ummita abinda ya tabbatar sonta Bai Kama shi don ya sake shi ba yayi zaton abin nawasa ne amma ya Gane yafi karfin wasa Gaba daya ya fice hayyacin shi har ya Daina fita ko Ina ya kwanta jinyar ciwon so Zuciyoyin shi sukayi ta kawo mishi shawara bi da bi har dai ya yarda ya dauki shawarar karshe ta yaje kofar gidan su ummita ko da ganinta ne yayi ya rage radadin sonta Ai kuwa ya Mike ya fice sai gashi kofar gidan su ya faka motar can gefe ya dawo nesa kadan da gidan ya zauna Yana zubawa kofar gidan ido Zaman shi ko minti talatin ba ayi ba ta fito cikin motar ta tafice inda ya bi motar da kallo ko ba komai yaji sanyi tunda akalla dai ya hangota inda wata zuciyar ke fada mishi yabi bayan ta zuwa inda zataje ko ba komai zai Kuma ganin ta ai kuwa ya dauki motar yabi bayanta inda suka hadu a traffic wadda ta tsaida su ya juyo Yana kallon ta inda yaga tsantsar kwarjini da haiba inda ya tabbatar ita din me kyau ce Jikinta ya Bata lallai ana kallon ta sai ta waigo inda idon su ya hadu yaji wani Abu me kama da Jan shock ya fizgeshi ita Kuma tana kallon shi ta tabbatar shine me kallon ta sai ta dauke kanta danjar ta Basu hannu suka wuce inda bisa Dole ya koma gida inda yakejin ya samu hanyar rage kewa Da yamma ya fito da zummar siyo kayan shayi ya wuce ta kuki cafee inda ya hango ta tafito daga kukin rungume da takardu ta bude motar ta SHIGA ta ja ta nufi gida Atake ya Gane kuki ta fito zuwa dazun me yuwa computer take karanta Ya wuce abin shi itama ta wuce batare da tasan yanayi ba Satin da gambo mafiyas ya dawo daga Lagos ya Kuma samo abin duniya Wanda suke karewa ga Matan banza da kayan maye don basa tsinana abin arziki don haka ya Isa gidan izzatu Yana zukar tabar iblis wiwi Da sauri ta toshe hanci tana tofar da yawu "Haba gambo meye haka zaka shigo min da wannan shegiyar tabar me warin Kashin jaki? Don Allah koma waje ka zuke abinka ko dadin me kukeji acikin zukar hayaki hayakinma irin wannan da ko dadin Shaka Babu?..........."yi hakuri hajiya kan ne in Babu hayaki fanko ne Rayuwa ta in Babu mandular Nan akwai damuwa har Rashin lafiya nake kwantawa idan ban busa ta ba Ya murtsuke sauran ya saka aljihunshi "Yauwa to haka dai yafi don har kaina ya soma juyawa Nima ka sakani kwalewar Dole "Yauwa hajiya Ashe akasi aka samu wurin aiki? "Ai shiyasa nafi yarda da aikin ka yanzu Yaya za ayi kenan? Ki bar komai a hannu na hajjya Ina me tabbatar Miki Nan da Rana irin ta yau wancan mutumin ya SHIGA UKU ke dai ku tanadi kudi don kin San Ni bana tare da tsautsayi ko kuskure bare wani Abu Wai shi sabani....... "Karka damu gambo idan aiki yayi kyau ma za a biyaka kudi lunki uku Kai dai baje basirar ka kayi aiki me shegen zafi don ka samu sallama me kyau.... "Angama hajiya bani sati guda Daya kacal zakiji mugun albishir da haka sukayi sallama ya fito ya Kama gabanshi inda izzatu ta Kira Kabir take sanar dashi yadda sukayi da gambo mafiyas yace yayi daidai Kuma zai biya gambon lunki hudu ma ko biyar matukar dai aikin shi yayi sanadin fakuwar eng AK Cikar satin da gambo mafiyas ya diba yayi daidai da kammaluwar aikin shi inda ya Kira Kabir yace yaje wurin hukuma ya sanar da akwai wani da yake kisan yaran mutane yau ya kashe wata yarinya ya sako a motar shi don haka su tashi Jami ansu da binciken motocin mutane ta haka ne tarkon zai Kama eng AK. Aikuwa atake Kabir mashi kashe arna ya Kira wayar D P O ya sanar dashi abinda gambo mafiyas ya sanar dashi inda Kuma suka tashi Jami ansu aka soma checking point Wanda duk motar da zataje ko tazo sai me ita ya fito ya bude but sun caje komai kafin su bashi izinin tafiya Bawan Allah eng abdukarim ya taho batare da sanin mugun qullin da aka hada mishi ba ya taho inda ya iske dogon layin na checking point Wanda ake ta bincike motoci shima ya bi layi batare da sanin shi ake son ganin baya ba ba Kuma Wai idan yajuya zaiyi tafiya ba. A a ganin baya na har abada inda ake son kasa ta rufe idanun shi................ Ubangiji kayi Mana sutura kar ka Bari makiya suga bayanmu 🤔 [5/22, 7:24 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 33* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Sannu ahankali akazo Kan eng AK Wanda ke kallon yadda ake binciken motocin mutane har akazo gareshi "Ranka ya Dade muna son duba cikin motarka idan Babu damuwa....... "A a Babu komai yallabai Bismillah ya fito Yana daga musu cikin motar suka bincike ba su samu komai ba sukace ya bude musu but Ya kewayo ya soma kokarin bude but din Amma wani abun mamaki tamkar an sakawa but din kwado yayi yayi ya bude Amma yaki buduwa yayi iyakar kokarin shi Amma but ya ki buduwa ya dubi Dan sandan Yana sharce zufa "Ranka ya Dade wallahi yaki buduwa karfen nasara kenan ban fa Dade da budeshi ba Amma yanzu da yake so ake ya bude yaki da zaku yarda sai ince muku babu komai aciki............. "A a ranka ya Dade a dai bude don Rana tsaka aka tashe mu aikin Nan .............. Ya Miko mishi key din motar "Karbi to ka gwada kagani Ni dai na gaji gaskiya, Dan sandan ya karbi key din ya soma kokarin gwada tashi sa ar inda ya turza sosai kafin yayi nasarar bude but din cikin sa a Kuma ya hango wani Abu me kama da jini na bin wani tsumma dake kudun dune yajawo shi ya warware inda yaga wani Abu me kama da hannun mutum inda kafar mutum ta fado Kuma wani Abu ya fado me kama da kokon Kan mutum Eng AK ya zaro idanu Yana mamakin yadda wannan alamarin ke Shirin faruwa ta Yaya akayi wannan abin ya shigo motar shi Inda Dan sandan yake kallon eng abdukarim da mamakin wannan abinda da ya samu acikin motar inda daga can baya Kuma cikin masu jiran go slow Kabir masi ya fito daga tashi motar ya karaso wurin inda shima yaga abinda ake mamakin gani amotar abdulkarim "Wai abdulkarim Kaine da part din mutum a mota? Eh lallai da gaske kake har da tsafi kake hadawa shiyasa ka shiga gabana to Allah ya shirye ka ya fada Yana murmushi ya koma motar shi Yana kallo aka fidda motar eng abdukarim aka saka Mata key aka kulle shi Kuma aka wuce dashi sashen da zai bincike shi yayin da Yan sandan suka ci gaba da bincike motocin mutane Da wata irin dariya Kabir ya SHIGA gida inda izzatu ta tarbeshi tana tambayar dariyar Nan ta lafiya ce? "Ki tayani dariya don ya akan idona Dan banzan can AK ya shiga hannu shigar da ba zai taba fita a yanzu ba. Kai lallai na yabawa gambo mafiyas akan wannan aikin nashi Dole ne in mishi biya me kyau, Izzatu ta kyalkyale da dariya tana fadin nasan gambo mafiyas ya fi da haka Amma ya akayi har hakan ta faru? "Nima ban San yadda gambon ya shirya wannan makircin ba ya dai kirani ya fada min abinda Zan sanar da Jami an tsaro na Kuma fada musu sai gashi akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai Amma Bari in Kira gambo mafiyas din yazo ya karbi kudin shi kuma inji yadda ya shirya wannan makircin Ya dauko wayar shi ya Kira gambo ya ce yazo yanzu Ai kuwa ba a rufe awa guda ba sai ga gambo mafiyas Kabir ya daga mishi hannu alamar jinjina inda gambon ke murmushi "Me gida kaga aiki ne Hala? "Naga aiki gambo don akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai ya akayi ka shirya mishi hakan? "Ai me gida na Dade ina binshi sannu ahankali har na samu sa ar ya bude but din na fakaici idon shi na saka mishi hannu da kafar shiyasa nace ka sanar da hukuma don ta fara binciken motocin ta yadda Za a kamashi kaga idan aka samu wannan abin a motar shi Dole za a shiga bincike kaga daga Nan sai sunan shi ya baci har ya Kai Babu me kallon shi bare sunan shi ya motsa Izzatu da Kabir suka tafawa gambo mafiyas akan makircin shi Kabir kuwa ya bashi kudi masu yawa ya Kuma ce zai neme shi matukar wani zai yi mishi shigar sauri irin na ak to yanzu ne zai Kira shi don yayi mishi maganin shi da haka sukayi sallama gambo ya wuce Yana murna izzatu da Kabir ma suka wuni farin ciki sun jefa Rayuwar bawan Allah cikin garari.................... [5/22, 7:24 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 34* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ..........Bincike tamkar za a binciko yadda uwa tayi ciki har ta haife lamarin da yazo mishi da wani irin rudani har yakasa Gane inda mafita take bayan ta Allah Yasha tambayoyi har na tashin hankali inda lamarin ya koma hannun C I D inda kuma suka rikeshi Wai sai sunyi bincike agidan shi Wayarshi ma kasheta akayi don kar ya Kira wani ko wani ya kirashi, Lubabatu da sukayi dashi ba zai wuce shida na maraice ba gashi har takwas da Rabi tayi mamakin abinda ya tsaidashi don ta San baya son yayi sallar magruba a waje Ta jawo wayar ta ta doka mishi Kira Amma abin haushi matar Nan me zakin muryar tsiya na sanar da ita sai dai ta sake Kira lokaci na gaba yanzu Wai ba za a samu layin ba Haka tayi ta jaraba Kiran wayar shi Amma ta kasa samun shi Dole ta hakura ba Kuma hakura tayi ba tunanin abinda ya tsaidashi da kuma Rashin samun wayar shi don tasan ba lafiya ba don ta San wayar shi Yana da caji Ummita ta shigo Mami Ina Abba ya shige yau har yanzu Bai dawo ba? "To Ni kuwa ina Zan sani ummita? Gaba na dai na faduwa don na fara tunanin ba lafiya ba............ "Mami bara na Kira wayarshi naji inda ya tsaya................ "Wayarshi Bata shiga na Kira na kasa samun shi Ubangiji yasa dai lafiya. Hankali ya kasa kwanciya inda ummita tace zata Kira haj mama taji ko ta San inda abban ya shiga Amma lubabatu ta ce ta saurara tukuna Sai dai har Sha dayan dare Babu wani Abu ko da na samun wayar shi ne Dole lubabatu ta Kira wayar haj Mama wadda har ta fara bacci ta jiyo karar waya ta farka tana tambayar lubabatu lafiya kuwa? "Hajiya AK ne har yanzu Bai dawo ba Kuma duka layikan shi arufe shine ko ya fada Miki zaije wani wuri? "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Wallahi lubabatu bai fada min ko zaiyi tafiya ba Kuma kince duka layi kanshi basa aiki ? Eh wallahi hajiya Amma Bari na Kira abokin shi zayyan ko ya san inda yaje da haka lubabatu tayiwa haj mama sallama ta Kira wayar zayyan din take tambayar shi ko yaji AK din zaije wani wuri Amma ya sanar da ita Bai sani ba Rabon shi dashi tun la asar. Hankalin lubabatu da ummita ya tashi matuka gaya har dai bacci ya gagari idon su suka kwana salla suna fadawa me babbar rumfa me iko akan komai me tassarufin Al amura haka suka kusa kwana zaune inda Mubarak da Ahmed da Fatima ke ta sharar bacci abinsu saboda yarinta da kuruciya Wayewar garin na laraba yazo musu da wani irin tashin hankali domin ko Jami ai ne daga hukumar bincike ta C I D suka diro gidan eng abdukarim inda lubabatu ta rude da Ganin su suka Fara yi Mata bayani "Karki damu hajiya tambayoyi ne kawai Zaki amsa Mana da Kuma binciken da zamuyi agidan Nan saboda an Kama me gidan Nan da part part din mitane amota................ ",Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un hasbunallahu wa Ni imal wakil Allahumma ajirni fee musibaty haza wa ahalufnee khairan minha. "Abdulkarim din ne akewa wannan zargin? Ubangiji ka bashi mafita da mafitar ka........ "Kar ki damu hajiya bincike muke tukuna ba Wai an tabbatar ba abinda kawai muke so shine ki bamu hadin Kai mu gudanar da binciken komai zai daidaita da yardar Allah, Ta share hawayenta da habar hijabinta ta soma amsa masu duk tambayoyin su har suka Kare suka shiga bincike gidan shima Allah da ikon shi ko wata kakkaifar wuka Basu samu ba da haka suka kammala sukayi Mata sallama bayan sun sanar da ita Yana hannunku Kuka ummita keyi tamkar zata hadiye zuciyar ta inda lubabatu ma ta ke nata kukan sai yaran ma suka dauki kukan Babu Wanda yayi kokarin rarrashin wani inda Kuma haj mama ta taho gidan don taji ko AK din ya dawo don itama ta nemi wayar shi yafi akirga Amma Bata sameshi ba sai ta iske iyalan gidan sunata rizgar kuka Hankalin ta ya tashi inda lubabatu tayi shiru tana korawa hajiyar bayani abinda ya gigita hajiya Mama itama ta fashe da nata kukan sai da kyar lubabatu ta rarrashe ta inda tace ta bari yanzu zasuje su ganshi Suka hada mishi kayan kalaci suka tafi su duka inda hajiya Mama ke ta sharar hawaye inda suka taho har da talai itama hawayen takeyi Sai dai duk yadda suka so ganin abdulkarim din lamarin ya ci tura Wai ba zasu ganshi yanzu ba sai dai ko Nan gaba an dai karbi abincin an Kai mishi Amma ganin shi sunce ba yanzu ba Kuka hajiya Mama take tana rokon su su taimaka Mata ko hango shi ne tayi in ba zatayi magana dashi ba to su nuna Mata shi ta hango lafiyar shi.................. [5/23, 11:35 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 35* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Kukan da hajiya Mama keyi ne yaba wani Jami I tausayi inda yake girmama girman kaunar uwa ga danta lallai duk Wanda Bai kyautatawa iyayen shi ba shine asararre duniya da lahira Don haka sai ya ce abude musu su shiga aikuwa hajiya Mama tayi ta saka mishi albarka Inda yace ai albarkar ku muke nema mama duniya da lahira Suka shigs inda suka samu AK lafiya kalau sai dai zaman wuri Daya kawai ne damuwar Ummita ta makale shi tana kuka lubabatu da hajiya ma kuka suke inda yake ta Basu hakuri akan yadda kaddara ke saukowa bawa babu zato bare tsammani Kuma da anyi hakuri sai komai ya wuce . Mubarak da Ahmed da Fatima ma rungume shi sukayi inda hajiya ke tambayar yadda abin ya faro ya Kuma sanar da ita kaf abinda ya faru. "Ubangiji ya fidda ka kunya abdulkarim yau duniya wani baya so ko silifas ka sauya bare Kuma Ubangiji ya daukaka ka shikenan sai ashiga hassada da bin mutum ta karkashin kasa Amma Babu komai inda ADDU A ta zatayi tasiri akanka to Babu Ranar da zaka tozarta Kuma da ikon Allah kayi gaba gaban da ba za a iya cimma ka ba............. Wani Jami I ya shigo yake sanar dasu Wai lokacin da aka Basu ya wuce sai dai suyi hakuri sai wani lokacin na gaba Haka suka taho suna addu a da neman mafiita sai dai duk yadda suka dauki lamarin ya wuce Nan don kusan tsayin wata biyu Amma Babu bayanin komai Wai bincike ake duk yadda yan uwa da dangi ke shiga da fita Kan lamarin Dole aka saurara aka barwa Allah ikon shi Agefe guda Kuma Kabir mashi kashe arna fakuwar eng AK ya dawo da martabar shi dominko yanzu Dole tasa ake bashi aikin kwangila ya Kuma yi yadda yake so don da gaske son Rai yafi yawa cikin aikin shi Wanda yake zaftare kaso arba in cikin dari sittin shine za ayi aiki dashi ko Babu nagarta inda Kuma izzatu da fulani suke warwasawa yadda suke so don yanzu duniyar dasu take damawa kudi suna ta shigowa asusun izzatu ya cika ya tumbatsa yayin da fulani Bata da sauran damuwa komai ta nema tana samu don haka suke Jin Basu da sauran matsala Tsayin watanni shida Wai ana bincike inda daga karshe aka Mika batun gaban kotu don Alkali ya yanke hukunci Zuwa kotun ma Bai zo da sauki ba domin ko wasu Bakin fuskoki ne suka zo suka bada shidar zur akan eng AK Wai dama Yan unguwa suna jitajita akan shi game da lamarin shi inda wasu ke ganin Yana da hannu a kungiyar matsafa don an Sha gano yaran da suka Bata agidan shi don haka kotu ta yanke mishi humunci irin Wanda yake yankewa yaran jama a Sharri dai kala kala inda daga karshe Ubangiji ya kawo mishi dauki ta hanyar binciken da akayo gidanshi ba a samu wata shaida da zata nuna shi amatsayin me hannu a kungiyar matsafa ba haka Kuma duk tsayin lokacin ba akama shi da abinda zai alamta tabbatar zargin ba Abinda dai akayi mishi an karbe duk abinda ya mallaka don biyan diyyar ran da ya kashe na Wanda aka samo kafa da hannu har da kokkon Kai Haka aka sallamo shi ya dawo gida Inda murnar iyalai da Yan uwa ta kasa boyuwa acewar hajiya mama ita dukiya dama bakuwa ce Kuma raba bawa da arziki sai mutuwa inda take mishi nasiha da kar ya damu da abinda aka karbe mishi yanzu ne ma yake da damar sake samun wani arzikin fiye da Wanda yayi don ita hassada takin arzikice (Allah kajikan haj Saliha Zaria ita ke fada min hassada takin arzikice me hassada kuwa Yana cewa Allah Bai iya ba to Wanda yace Allah Bai iya ba ya kake zaton zai Kare?) Bai damu ba ya Kuma amsawa hajiyar da cewa komai ya samu bawa da sanin Allah Kuma bawa Bai Isa kaucewa kaddarorin shi ba ko da kuwa zai shige akasa ne don haka ya riki hajiya da tayi mishi ADDU A Allah yasa ya cinye jarrabawar shi Haka Yan uwa da abokan arziki ke ta zuwa yi mishi jaje kasancewar shi mutum me ALHERI kowa nashi ne inda Kuma yake matukar Jin kunyar mutane akan sharrin da aka kala mishi amma Allah shi zai wanke shi Rayuwa tayi wata irin sauyawa agidan shi Babu abinda ya tsira dashi sai gida hatta da motoci an karbe sai Yan kudin da sukayi saura abanki Kallon lamarin yake tamkar mafarki Wai yau shine a wannan bigiren Amma babu komai ya godewa Allah da ba imanin shi ya rasa ba sai ya karbi kowace irin Rayuwa da ta Zo inda ajalin shi ya riska Dole ya mutu Kuma Dole ayi hakuri Sauyin da Rayuwa tazo dashi har ta Kai an cire su Mubarak daga makarantar kudi zuwa ta gwamnati don ba za a iya biya musu kudin ba inda takai abincin da za akai baka ma na neman gagara sai dai dayake lubabatu macece me kokari itake Kara karfafa mishi gwiwa akan yayi hakuri dai kar yayiwa Allah butulci da sannu bawa ke cimma Rabo da arziki Haka Kuma da sannu kunkuru zaije inda jirgin sama yaje Hajiya da Yan uwa da abokan arziki wadan da Basu zamo kaza me ci ta goge Baki ba suke ta hidimta mishi don Suma ya hidimta musu lokacin tasu bukatar Amma fa da yawan su Wanda suka ci moriyar tashi suna Nan suna juya kudi Amma dayake Dan Adam ne me yin Abu don yabo ko ganin ido sun ma manta da tsiruwar shi zumuncin zamani kawai mutane suka Rika Amma duk da haka shi Bai rike su ba duk inda Rabon yake zai fito shiyasa ya ke zaune lafiya inda Kuma hajiya ke taimaka mishi har ta Fara siyar da kaddarorin ta tana bashi kudin don ita Kam ranta ma zata iya bawa abdulkarim don yayi Mata Hidima tana Kuma addu a Allah ya kawo mishi mafita ya Kuma bude mishi kofofin arziki Dare daya lubabatu ta soma kosawa da wannan Rayuwar ta talauci tun Bai Gane ba har aiyukan ta suka soma nuna mishi.................... [5/23, 11:35 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 36* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .......... Lubabatu tamkar wadda aka zuge dare Daya ta sauya sauyi kuwa me yawa abinda ya bawa AK mamaki Amma duk da haka yayi Mata uzuri don aganin shi Dole taji Babu Dadi musamman yadda ta Saba Rayuwa cikin iko da wadata yau Kuma lamarin sai sannu Bata fito fili ta fada mishi ba Amma ya lura da ita da take taken ta Amma duk da haka yayi Mata hanzari don abinda ya nuna mishi kamar tagaji shine kullum cikin bacin Rai take abu kadan Kuma sai ya fusata ta Koda ko ita da yarane sai kaji tana ta antaka musu zagi abinda ta San bayaso bare duka sai ya zamo yanzu duk ta hada tanayiwa yaran sai dai ya kalla ya kauda kanshi Idan Kuma ta hadosu shi da ita zata rufe idonta ta gurza Rashin mutunci son ranta Amma duk da hakan baya biyewa don ya San mafarin lamarin har dai wata Rana ya zaunar da ita Yana mata nasiha "Kiyi hakuri lubabatu komai Kika gani aduniya Yana da farko da Kuma karshe. Kar wannan canjin yasa kiji aranki ko Rahamar ta Kare ko babu sauran wani Jin Dadi Nan gaba . A a yanzu ne ma lamarin zai Fara duk bawan da Kika ga an jarrabeshi matukar ya cinye jarrabawar shi to matakin nasara ne ya hau . Hska Kuma Babu Wanda zaiyi hakuri Bai cimma rabar hakurin shi ba don haka don Allah da manzon sa kiyi hakuri babun da muke ciki in Sha Allah zamu samu kanmu cikin wadata wata Rana matukar dai munyi hakuri domin Allah. Na sani ba kowane zai jurewa Rashi ba to Amma ai bawan da yayi imani yasan Dole ajarabeshi sai mu godewa Allah da ya bamu wannan jarabtar me sauki kiyi hakuri ki Kuma jure ki koma hango baya yadda kika samu Kai sai ki godewa Allah shi Kuma sai ya dubeki ke da lamarin ki. Ta matse hawaye ba tare da tankawa nasihar sa ba inda yaji tausayin ta ya Kara kamashi Da hakan dai ake ta gurgurawa da Dadi ba Dadi kamar dai ta dauka ko ta hakura inda ake cikin Rufin Asirin Allah wani abun mamaki Kuma ba a Kara kiranshi Kan abinda ya shafi harkar kwangila ba shima kuma Bai nemi cusa kanshi ba ya tsaya matsayin shi Yana ta laluben hanyar da Asiri zai rufu inda Allah cikin ikon shi masu zanen taswirar gidaje Kan bashi aikin zanen kasancewar shi eng Wanda ya hada har da sanin makamar zanen inda Kuma kudi ke Dan shigowa Amma ba kamar yadda aka sababa Inda agefe Daya Kuma Kabir yayi wata irin shahara da tunbatsa akan harkar gwangila saboda ayanzu shine ke Kan kadamin shi aiki Kuma Babu nagarta haka za ayi shi agama kafin lokaci kadan ya lalace saboda an saka manuba da ha inci Malam Ali yayi ta Kiran wayar shi Amma kememe yaki dagawa saboda ya San maganar dungo za ayi mishi inda a yau malam Ali ya bugo hanya ya iso garin Abuja duk da Bai San gidan Kabir din ba Amma akace matambayi baya Bata kasancewar shi shahararre Bai Sha wuya wurin gano gidan ba inda ya tsaya Yana karewa gidan kallo Wai gidan dan dungo ne wannan Amma ta Rayu a wani gida da bashi da maraba da kufai saboda ruwan damuna da ya kayar dashi Anna Bata samu arzikin tadawa ba Amma dubi gidan da yazo garin Abuja ya Gina tamkar yayi wurin Zama aduniya Bama wannan ne abin ji ba irin yadda aka kirashi yazo ya samu mahaifiyar shi cikin halin ciwo da neman agaji Amma bawan Allah Nan tunda ya ufa ya tafi Bai Kara waiwayo ta ba bare yayi tunanin duba yadda ta karaji da jiki bare ya kawo Mata dauki ko agaji Yau tsayin watanni shida Babu dungo Babu labarin ta Amma ko dai dai da Rana guda Daya Tak Bai tunawa da uwar shi na cikin neman taimako da agaji bare Kuma ya ruko wani Abu irin na jinkai da ya'yan kwarai masu neman albarka kewa tsaffin su Kai wannan wace irin SHIGA UKU da asara ce? Ubangiji ka shiryi bayinka masu Bata kasa yaran musulmi su zamowa iyayen su sanyi idaniya irin su kabiru Kam da haihuwar su wallahi gara barin su don haihuwar su batayiwa Wanda yayita Rana ba Malam Ali ya share hawayen tausayin dungo yayiwa me gadin magana akan asanar da me gidan yayi bako Aiko sai gashi ya fito cikin shiga ta Wanda ya samu wurin Zama a duniya Kaya masu tsada Wanda kallo daya zakayi mishi ka bashi matsayin minister ko Dan majalissa Ganin malam Ali yasa ya ji wani Abu marar Dadi ya sauki she da ruwa da lemu inda yake tambayar shi "Kabiru baka tambayi me jiki ba bare ka Kira kaji ya ta Kare ji? "To ai lafiya ita ke fakuwa na San dai taji sauki.............. "Amma ko taji sauki ai tana bukatar kulawa mussamman Kai da kake dolen ta "Kabir kayi sannu da kidan da duniya ke maka kana taka rawa Wallahi Babu komai acikin wannan Rayuwar sai rudani Duk nasarar mutum a Rayuwa ya samota ne daga addu ar iyaye don su ke da mabudin kowace irin nasara... "Bama abinda ya kawo Ni wurinka kenan ba don kowa ya gyara ya sani banzo don nayi maka wa azi ba sakone dungo taba Ni ta Kuma ce in isar gareka gashi Kuma Allah ya Taya min na kawo maka sai dai abin tashin hankali da saka zuciya rawa shine mun nemi dungo sama ko kasa mun rasa..................... [5/24, 7:50 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 37* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ...........Arude yake kallon malam Ali Jin yace Wai Babar tashi ta bace an nemeta sama da kasa Babu ita Babu labarin ta............. "Malam Ali ba asan inda take ba kenan? "Abinda yake daurewa mutane Kai kenan don faruwar lamarin tamkar kiftawar ido Wai an nemi dungo Babu ita Babu dalilin ta "Shin wani ne ya sace ta Koko guduwa tayi???.......... "Allah shine mafi sani abinda kawai na kawowa Raina shine dungo tana ganin Bata da kowa sai kanta idan ta faku idanun Al umma batayi laifi ba shiyasa don nafi zargin guduwa tayi don bakin ciki Babu abinda baya sawa........... "Bakin cikin me malam Ali?........ "Bakin cikin ka kabiru me yuwa dungo tana kallon kanta a wadda batayi SA AR haihuwa ba don ban taba ganin Dan halak yayi irin abinda kayiwa mahaifiyar ka ba Kabir Abu Daya Zan fada maka shine ka saurari zuwan musiba don kuwa kajawo Allah fada.... Arikice kabiru ya Mike Yana duban malam Ali da ya fada mishi gaskiya Amma ya kasa abinda zaiyi don ya yarda ya amince lallai ya jawo Allah fada Malam Ali ya Mike Yana fadin "Ni na koma sai Allah ya kaddaro saduwar mu idan kazo inda nake ma gaisa idan kuwa ta Kama mun hadu shima ma gaisa don ba Zan yaudari kaina cewa zaka zo gidana sada zumunci ba Toni a wa? Da haka malam Ali ya fice ya bar Kabir da hada hudu da ukun da zasu bashi takwas Izzatu da taji batun itama taji Babu Dadi Amma sai tace addua kawai zasuyi itace mafita Yayinda humaira fulani taji ya kakar tata ta Bata kuka take tamkar dai izzatu ce ta Bata abinda ya Bata ran izzatu ta shiga zazzaga Mata masifa Kwana biyu Kabir ya watsar da batun dungo inda yace duk ma inda ta SHIGA zata fito idan Kuma tayi haka ne don ta tada mishi hankali to ta tada mishi Bai samu zarafin duba kunshin da takardar ba ya kwashe su ya watsa ciki kabit din ajiyar takardun shi Kwana biyu ummita na zuwa kuki cafee kasa saboda Babu kudin da zatayi transport din zuwa gashi saura wata biyu ta Ida ta karbi sakamakon Tana tafe anatse inda kamar daga sama Wilson ya hangota zata ketare titin da zai sadata da kuki cafee inda ya zuba Mata ido a yau ji yake tamkar idan baiyi Mata magana ba zaiyi Rashi na zuciyar shi sai dai kafin ya faka motar ya fito har ta shige Ya kasa tsaye da zaune zuciyar shi na kawo mishi shawarwari akan kawai ya jira ta fito in yaso ko mayar da its gidane sai yayi Aiko ya dasa zaman jira har uku na maraice ta fito ta soma tafiya inda ya kula tamkar Bata da lafiya Ta gota shi kadan ya ga ta dafe bishiya ta rike kanta Wanda alamu suka nuna ciwo yake Mata inda dabara ta fado mishi ya tashi motar ya karaso gareta Yana fitowa Ya tunkaro ta ta zuba mishi ido kallo daya ta Gane shine Wanda ya tsura Mata idon Nan a country mall Yayi Mata sallama cikin hausar shi da Bata fita Bata amsa ba ta dai dubeshi "Sannu fa Naga kamar kina neman taimako na?...... Tayi saurin Kada mishi kanta "No nagode zaka iya tafiya. "Kiyi hakuri nasan inda zakije akwai nisa kizo na kaiki Naga kamar kina headache ne ...... "Nagode sosai Zan iya komawa ba damuwa........... "Kiyi min alfarma ko ta kaiki gida ne tunda har Baki da lafiya.......... "Idan aka ganni a motarka nace me? "Ka ganka kuwa ? "Taimako wani abune da addinin mu ya koyar damu ga mabiyan sa shin kana daga mabiyan ne da zaka taimakeni? "To duhu da haske basa tarayya a wuri Daya Dole daya ke bawa Daya wuri idan haske ya bayyana to duhu yayewa yake don haka na gode da taimakon ka gareni "Na sani amma haka Nan naji Ina son taimakon ki tunda muma namu addinin ya koyar damu taimakon Kuma Bai saka kiyayya ga sauran addinan ba indai ba naku adfinin ya saka muku kiyayyar sauran addinan ba. Kiyi hakuri ki shigo na saukeki nayi Miki alkawarin Babu cuta tsakanin mu haka kawai nake son taimakon ki Azahiri ita kanta tana bukatar taimakon don Jin kanta take tamkar zai tarwatse Dole ma ta nemi abinda zai kaita gida don Bata sababa ga kuma yunwa da takeji wadda idan akasa tace zata tafi to ko shakka Babu sai dai akwashe ta amika gidan don haka ta sallama ta shiga motar yaja suka iso gida ya sauketa ya Miko Mata fakitin maganin ciwon Kai me tsadar gaske ta karba tana godiya Tun daga wannan Rana Bai Kara shiga cikin lamarin ta ba sai dai zai labe ya kalleta ya more ya koma gida inda kusan kullum sai yazo kuki internet cafee ya ganta batare da ya Bari ta ganshi ba Hajiya sabuwa first lady matar Mr President take sanar da Mr President din maganar da ta taba fada mishi ta samowa Anwar auren diyar kawarta matar soja wato kudusiyya ta taso don haka atura mutane su nema mishi auren Ya dubeta Yana murmushi "Kice auren gata za ayiwa Anwar ba na fada Miki Yar gidan Kabir mashi Nima na nema mishi ba? Ta kwabe Baki da zaka yarda sai ince ka bar maganar Yar gidan Kabir mashi kudusiyya macece daya tamkar da goma......... "Ba zanyi magana biyu ba tunda dai kema kin samo mishi wata sai ahada mishi biyu don haka itama Yar gidan Kabir mashi din sai muyi magana kawai Wannan abin ya Bata ran haj sabuwa don tasan idan matar soja taji haka ba zata yarda ba Amma kome kenan zasu San yadda sukayi suka lalata Shirin Yar gidan Kabir din don kudusiyya kawai suke son tayi Rayuwa a gidan Anwar din baza ta tabs Zama da kishiya ba bare har ta Zama Bora Sai dai da Anwar din ya shigo hajiya sabuwa ke mishi maganar kudusiyya da zaba mishi ita da tayi a matsayyin matar aure yayi saurin tareta..... "Bana son ta hajiya ku barni na zabo matar da Nike so da kaina tunda Kuma zabar kanku kukayi ke da dady ba hada ku akayi ba....... "Kayi karya ka bani kunya Wallahi Anwar Dole ne ka auri kudusiyya..... 'to shikenan haj duk abinda ya samu Yar mutane kar kiyi kuka da kowa...... Ya fice ya barta sake da Baki............... [5/24, 7:50 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 38* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........Anwar ya fito sukayi kicibus da mahaifin shi ya zube Yana rattaba mishi abinda hajiya sabuwa ta fada mishi akan Wai ta yi mishi Mata da kudusiyya wadda shi atsarin shi kudusiyya batayi mishi ba. Mr President yayi murmushi "In Banda abinka Anwar meye na damuwa don ta zabo maka matar girma ? Nima fa nayi nufin Yi maka gata kanaji? "Eh inaji dady. Yauwa ai kasan gidan Alh Kabir mashi ko? Eh gaskiya kamar na sani Amma dai akwatanta min . Yayi mishi kwatance ya Kuma Gane inda ya bashi rafar dubu hamsin hamsin guda biyu ta dubu dari yace idan sun gama magana ya bada amatsayin kyauta Ya dubi uban cikin Rashin Gane abinda yake nufi har dai ya tambaya "Dady wa za a ba wannan kudin shi alh Kabir mashi din? "A a kaje Zan kirashi zamuyi magana bashi zaka bawa ba ita wadda zaku yi maganar da ita zaka bawa amatsayin kyautar ka. Ba don ya Gane ba ya taho don har ga Allah shi Bai kawo komai aranshi ba yayi nasarar Gane gidan ya Kuma tura me gadin yayi mishi sallama da alh Kabir Atare suka iso inda Kabir kewa Anwar sannu da zuwa ya sauke shi a wurin da yake karbar Baki suka gaisa inda Anwar din yake sanar dashi dady ne ya turo shi "Eh ai ya kirani bayan ka taho Bari in turo maka ita. Ya Mike ya bar Anwar sake da Baki Yana maimaita kalmar Bari in turo maka ita, to itawa za a turo mishi? Sai ya zuba ido kowacece itan Fulani na zaune cikin ado da kwalliya tamkar me shiri fita party ta zubawa TV ido tana kallon India Wanda take son sanar da dadyn ta tana izuwa India don garin na burgeta sai Kuma gashi ya shigo Yana kiranta Ta dago da sauri "gani dady Yauwa dama bakone gareki Yana can masaukin Baki kije ku gaisa.......... "Bako Kuma dady? Ni yace maka yake nema? Gaskiya dady bani yake nema ba sai dai in wrong address ya samu don Ni ban ba kowa address Dina ba....... "Eh shi wannan din ma ba cewa ke Kika bashi ba Ni nace mishi yazo ku daidaita ke dai jeki idan kin dawo zamuyi magana. Ta motse fuska don Sam acewar ta Bata ga mijin Aure a yanzu ba sai gashi Kuma ana son shigs Rayuwar ta Tasa me aikin su talatu ta biyota da ruwa da lemu inda ta yi gaba don zuwa duba wannan marar kunyar da aka jajubo Mata Ta taho tamkar tana Jin tausayin kasar fuskar ta murtuk Wai don kar yaga hakoranta ta shigo Babu ko sallama inda idanun su suka hadu su duka tamkar wuta taja su suka ji bugun zuciya Atare inda ta zauna tana auno mishi harara tamkar idanunta zasu fado inda talatun ta shigo dauke da tire Wanda ta jero ruwa da lemu tana Shirin ajewa humaira ta doko Mata tsawa..... "Koma da ruwan Nan talatu wannan ba bako bane abokin Adawa ne..... Talatu tayi dabar dabar don Bata fahimta ba inda kuma humaira ta Kuma daka Mata tsawar "Nace ki koma dashi ko bakiji ba? Da sauri talatu ta dauki tiren ta koma ciki inda ta fusknce shi shima Yana mamaki abinda suke nufi da turoshi inda atake ya gano gatan da dadyn yace yayi nufin yi mishi har yayi murmushi don yasan ba zasu taba daidaita wa da wannan marar mutuncin ba Murmushin shi ya Bata haushi. "Au harma na Zama abin dariya agareka ? "Uban me kazo yi agidan mu? Ko Nan ma kazo ne don ka sake bawa Yan sanda damar su kulle Ni ? Ta fada tana Kada kafa alamar masifa na Shirin tashi Ya Kuma yin murmushi Wanda ke kuleta da haushi da takaici "Kiyi hakuri Ranki ya dade............ "Kai bari fa in gaya maka dama inajiran Allah yasake hadamu don in Rama abinda kayi min To Ni nan da kake gani wallahi uban kuturu ma ya Yi kadan bare na makaho da ba gani yake ba duk uban da ya daure maka..... Ya gaji da Jin zagin da take mishi don Babu abinda ya tsana a Rayuwar shi irin zagi don haka ya cire hannu ya tsinke ta da Mari Marin da sai da taga giccin koriyar wuta "Nafi karfin zagi agareki ko Zan zagu ba dai ga irin ki ba jahila marar tsinkaye wallahi ba Irina Mata ke zagi ba nafi zagi ga irinki dabba dake Kuma in har kece ake Shirin abinda aka shirya zanyi maraba da hakan ko don in koya Miki tarbiyar da uwarki Bata koya Miki ba Ya Mike afusace ya watso Mata kudin da dadyn ya bashi ya Bata "Gasu Nan ki kaiwa Kabir mashi don saboda su yayi tallar ki inda ya San zai samesu Ashe ke da uban naki duk nema kuke akarkashi na to ku biyo Ni Zan baku na cin abinci Tana dafe da inda ya zabga Mata Mari har ya fice ta kasa cewa komai Akan cin fuskar da yayi mata Me yake sanar da ita? Da gaskene tallarta dadyn yayi? Eh ai in Bata manta ba dadyn ya fada Mata shi ya turo shi don haka ta tabbata sai dai tanajin ba abune me yuwa ba matukar Kuma akace hakan sai ya yuwu to za ahaife da marar ido Ta kwashe kudin ta nufi cikin gidan inda take ganin karfin halin shi na zuwa har cikin gidan su ya zabga Mata Mari Kabir ya tareta "Yaya Yar dady Yaya Kika ganshi ? Yayi Miki? "Wai dady baka San shine yayi min wulakanci har sau uku ba? "To dady bana son shi don fansa ma Zan dauka akanshi ba Kuma Zan kyale ba don bashi da mutunci to nima Zan gwada mishi bani da mutunci..... "A a karkiyi haka Anwar Yana da kirki Baki fahimce shi bane don haka dama fada Miki ne bamuyi Anwar shine mijin da aka tsayar Miki Nan da lokaci kadan za ayi biki..................... [5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 39* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ........."A a dady wallahi bana son sa don ya gama saka min kiyayyar sa idan kuma kace Dole sai na aure shi to wallahi Zan bar gida ne kawai in SHIGA duniya........ "A a ba za ayi hakan ba cewar izzatu tunda dai Baki so an Bari. "To hakan dai yafi momy.... Ta fada tana hayewa saman bene inda Kuma Kabir yace "Ba fa Zan janye hadata aure da Anwar ba don auren su shine tabbata ta Akan aikina don auren ta zai zamo min tsani.......... "Nima ba zanso fasuwar auren ba Kabir na dai fada ne don kar ta gudu Amma ai gata can gidan Anwar din da haka suke rufe zancen Koda Anwar ya koma gida Mr President ya tambayeshi "ya ka ganta ne Anwar? Ya shafa sumar kanshi 'dady batayi min ba wallahi Bata da tarbiya......... "In Dan tarbiya ai me sauki ne Anwar sai ka dorata Kan irin taka tarbiyar munyi magana ne tuni da ubanta Kai ai Dan gata ne Mata biyu lokaci Daya? Tashi kaje zamuyi magana dashi Kabir din Kai dai ka zamo me adalci agare su Allah yayi jagora Ya tashi ya fito yanajin shi Kam baiyi sa ar aure ba don kaf Matan da ake Shirin bashi Babu wacce yake so Amma yanajin zaiyi biyayya tunda duka iyayen shi ALHERI suke nufin shi dashi don haka ya zari key din mota ya fice wurin abokin shi badamasi Wanda ya zamo Dan gidan Alh uba Dan yaro don ya sanar dashi irin auren da ake Shirin yi mishi Yana tafe kamar Wanda akacewa kalli can sai kawai idon shi ya hango mishi ummita wadda ke tafiya akasa zuwa kuki Gabanshi ya amsa inda ya kusa buga motar Amma Allah ya tsare ya dawo Kan doka da oda inda Kuma ya nemeta sama ko kasa ya rasa Haka ya Isa gidan su badamasi ya sameshi suka kashe inda badamasin ke fada mishi yanzu yake Shirin zuwa ya Kai mishi albishir din ya samo mata.......... "Kai Amma nayi maka murna don gara kayi aure da dai barikin da kake Kai ba mutumin banza ba Amma ka biyewa Matan banza nima dama nazo ne in fada maka yadda ake Shirin aura min Mata biyu Kuma duk cikin su Babu wadda nace inaso daya daga haj daya daga dady Amma yanzu tahowar Nan da nayi Allah da ikon shi nayi tsuntuwar soyayya Amma Wai kafin na kyafta ido har ta bace wa ganina Amma nayi alkawarin duk duniyar da tashiga sai na nemota nayi ta uku da ita......... Badamasi ya kyalkyale da dariya "Kai Amma wallahi su Dad sunyi min daidai Mata biyu lokaci Daya in ba irinku Yan gata ba Ya Mike da Shirin tafiya "Na lura ban baka tausayi ba badamasi Bari kawai in wuce tun baka sa zuciya ta bugawa ba.......... "A a malam Bari nazo na nuna maka yarinyar da nake fada maka na samu don ka ganta sai dai fa ban taba yi Mata magana ba saboda kwarjini da tayi min na dai binciko ance min Yar gidan eng AK ce na Kuma San baba ya sanshi shine kawai na fada mishi ina sonta yace in Bari zaiyi mishi magana Amma har yanzu na kasa yi Mata magana sai dai kawai na Zo inda Zan hango ta na kalleta na more....... "Amma dai ka kusa bada maza badamasi duk barikin ka ace tsoron mace kake? Ko dayake wata Kil kamila ce shiyasa kake shayinta kaga banbancin matar kwarai da ta banza inda abariki ne Babu wani kwarjinin da Matan bariki kewa Yan bariki tara ce ke dukan goma........... 'ban Yi maka gardama ba abokina muje in nuna maka ita... Haka suka fito har zuwa kuki cafee inda Kuma cikin sa a ta fito ta soma takawa domin komawa gida inda Kuma agefe guda Wilson shima yake lafe yana Kare Mata kallo inda Kuma gaban Anwar ya buga da karfi yarinyar da ta saci zuciyar shi itace masoyiyar badamasi? Lallai akwai hayaniya a gaba duk surutun da badamasi keyi domin Koda ummita Anwar baya cikin hayyacin shi da haka sukayi sallama ya taho Kai tsaye ya tunkari Mr President cewar yanzu ne ya samu matar aure idan zasu yarda ya auri Mata uku to ahada mishi da ita idan kuwa ba zasu yarda ba to abar auren duka Mr President yayi murmushi "Yar gidan waye ita wannan din ? Yar gidan eng AK ce ya bashi amsa "To kaje zanyi mishi magana ko ta hudu ka Kara hangowa kayi magana Zan cike maka su hudu dai dai ai Kai din Dan gata ne, Anwar ya tashi Yana murmushi yayiwa Mr President sallama ya wuce abinshi.................. [5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 40* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* .........Alh uba Dan yaro yazo har gida ya samu eng AK Akan Dan wurin shi badamasi yaga yarshi Yana so har ma suna rokon iri don hada ZURIA Eng yayi shiru don har ga Allah baya son yiwa ummita auren da ba itace ta kawo Wanda take so ba Kuma hasalima Yana da tarihin Rayuwar badamasi da yadda yake son sheke Aya da Matan bariki shi da kanshi ba zai yarda da auren badamasi ba don haka Bai boyewa Alh uba Dan yaro ba. "To alh na gode da kauna don me son hada ZURIA da Kai ya gama maka Dukkan kauna sai dai gaskiya alh bana son matsa Mata akan aure don yaran yanzu kana so ina so ma ya aka Kare bare anyi basa so? "Zan sanar da ita zancen badamasi ka Kuma turoshi yau ko gobe don su gana idan yayi Mata shikenan idan kuwa baiyi Mata alh sai yaro yayi hakuri...... "Kar ka damu abdulkarim koni ba zanso kayiwa yarka Dole a aure ba don wannan zamanin ba irin Wanda ake Dole a zauna lafiya bane Ina fatan alkhairi agaresu idan Kuma baiyi Mata ba sai ya nema agaba da haka sukayi sallama inda ya dire mishi kudi masu kauri akan Wai ya bawa Yar shi ta siyi kayan kwalliya sukayi sallama ya tafi Bai boyewa lubabatu ba dake ta Shan sharafinta da daukewa ak Kai ya zayyane Mata yadda sukayi da alh uba Dan yaro Amma ke da ke can in kin tanka ta tanka mishi don tana ganin awannan halin za ayiwa ummita aure cikin halin Babu? Bai bi ta kanta ba ya kira ummita dakin shi ya sanar da ita abinda ke faruwa na game da badamasi da ubanshi ya Zo neman aurenta ya Kuma nemi Jin Ra ayin ta Ta sunkuyar da kanta kasa tanajin kunya tana Kuma nazari............... "Kar ki kwari kanki ummita ba Zan taba yi Miki AUREN Dole ba Wanda kike so shi Zan Baki don haka idan kinji ranki Bai dauka ba Babu kunya tsakanina dake Zan Baki damar ki. "Abba na baka zabi wallahi zanyi maka biyayya muddin ka hango cancanta da dacewa akan shi zanyi maraba in Kuma roki Allah ya zaba min abinda yafi ALHERI Ya sauke ajiyar zuciya Yana godewa Allah da ya bashi ya me biyayya "Allah yayi Miki albarka ummita na gode da karrama Ni da kikayi Amma ki Bari zuwa yau ko gobe badamasi zaizo ku gana yadda Kika ganshi ko kikaji shi aranki kar ki boye min ta haka ne Zan yanke hukunci na adalci amatsayina na mahaifin ki Ta amsa ta fito Washe gari kuwa sai ga badamasi ya iso cikin shiga ta Alfarma da son ya siyo zuciyar ummita Amma Rashin sa ar da yayi kallo daya tayi mishi taji yayi Mata Kama da Yan duniya ita Kam Bata muradin auren irin su don wayewar su tayi yawa Sukayi fira ta Yan Mintoci duk yadda yaso ya yaudari zuciyar ta hakan Bata yuwu ba haka sukayi sallama Yana Bata kudi Amma Taki karba tayi godiya inda yake Jin lallai irinta yake so wace macece ke kin kudi a wannan duniyar? Sai yaji ta Kara burgeshi da haka ya taho Yana santin aurenta "Yaya Kika ga badamasi ummita? Shin yayi miki Koko akwai matsala? Tayi shiru kafin ta dubi abban nata "Kayi hakuri Abba ka gafarce Ni gaskiya Bai yi min ba wayewar shi tayi min yawa............ "Nima da kin zabi badamasi ummita to da Zan fada Miki aibin auren shi don Nima tarbiyar shi batayi min ba Amma tunda Ra ayin mu yazo Daya shikenan sai abashi hakuri dama ban rufeshi ba ke Kuma Ubangiji ya Baki miji na gari ta amsa ta fito Haka kuwa akayi ya iske alh uba Dan yaro ya sanar dashi yadda sukayi da yarinya ya Basu hakuri ya dawo gida Kwana biyu Wilson na kwance Babu lafiya abinda ya tabbatar ciwon son ummita ne ya kayar dashi inda ya hadiyi magani da allurai Amma duk abanza Babu wani sauki sai radadin zuciya Tamkar Wanda ya amsa umarni ya zaro key din mota ya fice zuwa kuki inda yayi nasarar ganin shigarta ya zauna zaman jiran fitowar ta Sai yamma ta fito inda ya shigo mota ya karaso inda take tafe akasa ya danno Mata horn Ta juyo Inda idonta ya hasko Mata shi sai tayi maza ta daure fuska yayin da shi Kuma yajefota da wani murmushi ya fito Yana fadin "Kice yau da kafar dama Kika fito gashi mun hade don hanyar gidan naku zanbi Ta sassauta fuskar ta "Ayya yau Kuma inajin Kaine baka fito da kafar damar ba don yau ba inda kasani zani ba......... "Sa ar takice take da yawa har nayi nufin kaiki duk inda zakije Ta dubeshi "Na taba fada maka duhu da haske basa tarayya a wuri Daya me kake nufi da SHIGA cikin Rayuwata? Ya shafi sumar kanshi Yana murmushi "Nagode da wannan damar da Kika bani manufata itace muyi musayar zuciya....... "A hakan zamuyi musayar zuciya kana a duhu? "Kasancewar mu mutane jinsi Daya shine kawai alakar mu ta kasanwa mutane Amma akwai banbanci me yawa tamkar nisan sama da kasa don haka kar ka Kuma bibiyata don abinda kazo dashi Kai da kanka kasan ba Mai yuwa bane na gode da taimakon da kataba yi min sai anjima Ta wuce ta barshi inda yake biye da ita Yana nacin ta shigo motar shi ya kaita gida Amma Bata saurare shi ba haka shima Bai fasa binta ba har ta karaso gida shi Kuma yayi zaman awa kusan biyar Yana son ganin fitowar ta Amma shiru har dai ya gaji ya dawo gida sai dai me? Yayiwa ummita tsaye arai bacci ma da ta kwanta mafarkin shi tayi tayi da ta farka ma Babu abinda take bege face ta saka idonta cikin nashi inda Kuma kwana biyu shi Kuma baije kuki ba ta damu matuka gaya har ta soma zubar hawaye ta dafe gurbin zuciyar ta "Kar ki yaudare Ni Mana zuciya? Ta Yaya Zaki sakani son abinda Bai dace Dani ba? Ko kusa haka Kuma ko alama ita kanta lamarin Bai burgeta ba to bare Kuma iyayenta suji Dole ta watsar da wannan gurbatacciyar dake nuna Mata mafarkin ido biyu ...................... [5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI* *NA* *HADIZA BARA'U GIDAN IKO* _Hakkin Mallakar na gidan iko ne_ *Page 41* *_____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ............Ta taho tana fatan ayau ta ganshi ko daga nesa ne Amma ko burbushin motar shi Bata hango ba har tsayin sati biyu inda ta bawa zuciyar ta magana Amma lamarin yaki yuwa Ta fito don komawa gida kamar ance Mata juyo sai ta hango shi ya zuba Mata ido itama ta zuba mishi nata idon inda take hango tsari da kyan halittar shi Farine tas har ya soma jajaja sumar kanshi baka manyan idanu masu cike da gashin girare baka wuluk sai Dan karamin bakin shi me siraran labba sai sajen dake fuskarshi Wanda Bai Kai kasumba ba a idonta Kam ta Dade Bata ga namiji irin shi ba me yuwa shiyasa ya kasa barin zuciyar ta ganin irin kallon da take mishi yasa ya tako ya karaso gareta "Amma nayi farin cikin ganinki don kwana biyu da ban ganki ba wallahi na rasa natsuwata Allah yasa ban shiga hakkin ki ba idan nace ki shigo mota ta na maida ke gida Bata San lokacin da murmushi ya kubce Mata ba ta dauke kanta "Kar ka yaudare Ni ka Kuma yaudari kanka. Babu hadin tutu da fura Kai da kanka kasan hanyar mu tana da banbanci so ka Daina kusanta kanka Dani don Babu Hadi......... "Ni kuwa a yanzu kusancin nake nema gareki don bana ko shakka munyi musayar zuciya don ko baki fada ba nagani a idonki so karki damu Ni dake zamu zamo Abu guda....... Bata jira ya Kare maganar shi ba ta soma tafiya Yana biye da ita da yaga bazata tsaya ba sai ya fito suka jeru suna tafiya Wai zaiyi Mata rakiya ai kuwa sai gashi ya kawota har gida ta shiga shi kuwa ya dawo tun daga wannan Rana yake biyota su taho tare ya kawota har gida shi Kuma ya juya Ta dawo inda ta samu eng AK yayi Baki Wanda Mubarak ke fada Mata Wai Mr President ne yazo wurin abban su Eng ya karbi bakuncin Mr President Wanda suka gaisa yake tambayar shi Ina ya shige aka Daina Jin duriyar shi ya bashi amsa da ya na Nan yanayin Rayuwa ne "To madallah Zan neme ka Amma kafin Nan wata Alfarma nazo nema idan har Allah yayi lamarin Dama yaron wuri na ne Anwar yaga Yar wurinka yake so shine yace nazo na Yi maka magana idan bakayi Mata miji ba ya shigo cikin masu nema Amma don Allah kar ka kalli girma na ko alfarma ta ka tursasa yarka akan auren Anwar don in har Bata son shi to zai hakura ne ko da kuwa zai mutu don haka kar kace zaka bawa Anwar yarka don Ni ba zanso hakan ba idan ta na sonshi zanyi murna idan kuwa Bata sonshi zanyi musu fatan ALHERI ne kawai don muna da Matan da muka zaba mishi Ni da uwar shi ya Kuma yi Mana biyayya to yanzu ne yaga wadda hankalin shi ya kwanta da ita itace yarka shiyasa zanyi mishi Alfarmar aurenta idan har Allah yayi wannan shine makasudin zuwana. AK yayi shiru kanshi akasa Yana nuna girmama wa ga Mr President inda yaji yayi na am da Anwar ya zamo mijin ummita don tarbiyar shi tana burgeshi tamkar ba Dan wani ba Kuma atsari ma yasan ummita zata so shi don yafi badamasi nesa ba kusa ba .har ga Allah ba don abin duniya yaji Anwar ya kwanta mishi fiye da badamasi ba sai don ya zabawa Yar shi miji na gari Amma ko shi din ummita zatace Bata so zai bawa Mr President din hakuri yaro ya nema agaba Ya dago kanshi Yana duban Mr President "Sir Babu matsala Anwar Nima Dana ne zanso ummita ta karbi auren shi duk da nasan Bata da matsala da nace ta karba zata karba Amma a turo Mata Anwar su gana su Kuma daidaita idan da Rabo Amma daga gareni ma Zan iya cewa na bawa Anwar auren ummita sai fa idan Allah ne Bai kaddaro hakan ba. Mr President yayi murmushi "Nagode sosai abdulkarim da goyon bayan da kabani Zan Kuma turo Anwar yazo su gaisa fatan Ubangiji yasa ALHERI zamu hada Da haka sukayi sallama yayi mishi rakiya har wurin motar shi sai ga kyauta ta girma anyi mishi Amma yace ba zai karba ba inda aka aje mishi motar ta fice ta barshi Baki sake Dole ya karba ya shigo cikin gida Yana fadawa lubabatu yadda sukayi da Mr President Akan son auren ummita Ta dubeshi azabure Cikin wani kallo me bayyana takaici "Shine suka Fara siye imaninka da dukiyar su? Ta fada Yana nuna kudin da hannunta abinda ya kona mishi Rai ba kadan ba ya dubeta cikin mamaki "Nayi Zaton ko wani ya fada Miki haka Zaki karyata lubabatu in siyar da yancin ya ta Akan kudi kike nufi ? "Ba Zan ma karyata ba abdulkarim don nasan talauci Babu abinda baya sawa ba zai zamo abin mamaki ba don ka siyar da mutuncin yarka akan kudi da abin duniya ba..... 'sai dai kasani Nima inada hakki akan ummita don haka ban yarda ba ba Kuma Zan yarda ba. Idan har kaci kudin su saboda aurenta to ka kwana da Shirin biyansu. Yaji wani yaji yaji Yana lullube kwayar idon shi Wai don ya talauce ne lubabatu ke son kece rigar mutuncin shi ne kokuwa akwai abinda yayi Mata Wanda ya fusata ta har take mishi wannan dibar albarkar? Ganin idan yace zai biye Mata Kan batun to rayuka ne kawai zasu baci sai ya fito daga dakin nata hakki dai da take magana nata ya Bata tunda ya sanar da ita Yana Duke Yana faman wankin kayan su Mubarak ummita ta shigo da sauri ta aje takardun ta "Abba da Ranar Nan kake wanki? To kawo na karasa maka Ta fada tana kwabe hijabinta Yayi murmushi "Jeki huta kici abinci ummita ai na kusa karasa wa Bayan ta nutsune ya ke sanar da ita "Ummita an sake zuwa da kokon barar neman AUREN ki Ni Kuma nayi alkawarin ba Zan taba matsa Miki Akan aure ba sai Wanda yayi Miki don haka Yaya kike gani? Ta dukar da kanta kasa "Abba na baka zabi duk Wanda ka bincika kaga tarbiyar shi da dabi un shi sunyi maka Wallahi zanyi biyayya duk mijin da ka zaba min Zan karbe shi don nasan ba zaka taba cutar Dani ba . Yayi murmushi "Allah yayi Miki albarka ummita idan har hakane abinda Kika fada to na yarda da tarbiyar Anwar Kuma zai zamo Miki miji abin alfahari don haka na yaba dashi da tarbiyar shi Amma shima zaizo kuga juna shima idan Kinga bai kwanta Miki ba ki sanar Dani kinji ko? Ta amsa da to Abba ..... Lubabatu dake tsaye kansu ta maganta "Kar fa kayi kokarin tabbatar da wanna maganar abdulkarim don na rantse maka da Allah ba Zan taba Bari ka kafa jari hujja da diyata ba don ba Zan Bari ta Rayu cikin Rashin yanci ba...................