[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS Page 1 GIDAN ALI Lokaci zuwa lokaci take kallon agogo tana ƙwafa, kana kallon fuskarta za ka gane cike take da ɓacin rai, ƙarfe tara tana cika cif ta ɗauki hijjabi ta saka ta ɗakko mukullin gidan ta fita ta kulle, ta ja tinga ta tsaya a ƙofar gidan, ba ta yi minti goma ba ta jiyo ƙarar babur, tana juyawa ta ga shi ne ya shawo kwana kamar yadda ta yi zato, ta ƙara haɗe gira hannunta harɗe a ƙirji. Ali ya ƙaraso yana haɗe fuska "Maryam idan ba za ki buɗe mini ba na koma inda na fito!". Ya faɗa ganin ba ta da niyyar buɗe gidan tana binsa da kallo, ta girgiza kai ta buɗe sai da ya shiga sannan ta bi bayansa ta saka sakata, cike da mita yake cewa"Wannan wane irin hali ne, ki dinga cewa kina jin tsoron zama ke kaɗai, saboda tsabar raini sai ki fito ƙofar gida ki tsaya masu wucewa suna kallonki kina kallonsu wannan ai raini ne!". Maryam tana cire hijjabi ta ce"Duk yadda ka ɗauka, ni dai ba zai taɓa yiwuwa ka fita tun safe sai dare ba kuma ace daren ma wai ba ka da lokacina sai ka gama fira a majalisa, ka ɗakko ni a gidanmu mai cike da jama'a ana raha ana dariya ka zo nan ka kulle ni kai kana majalisa? Kar ka ga ina tsayawa a ƙofar gida, wallahi duk ranar da ka yi sake na gano majalisar nan taku sai dai a fara zaman da ni..." Ransa ya ɓaci ya ce"To bisimillah ai ga hanya nan, wallahi Hamza sai ya kai sha biyu a waje, amma dayake shi yana da ƴanci matarsa ko waya ba ta isa ta yi masa ba, ke da nake dawowa takwas da rabi ba za ki godewa Allah ba?" Ta taɓe baki ta ce"Ita ta ga za ta iya, don ni wallahi duk ranar da ka kai ƙarfe goma a waje ka saka a ranka babu kai babu kwana a gidanka, don wallahi tabarma zan kai maka shago kafin ka dawo!". Daga haka ta fita ta ɗauki bokiti ta zuba masa ruwan wanka ta kai masa banɗaki tana ci gaba da mita "Ni an isa a dawo min gida sha biyu, sai ka ce ƴar iska mutum ya ajiye? Tab". Kafin ya fito daga wanka ta kawo abinci falon, ta zuba musu, suna gamawa nefa suna kawo wuta, ta ɗauki wayarta ta jona, za ta ɗauki tashi ya ce ta bar shi yana da caji, ta kunna kallo a ƙaramar tv dake falon, tana kuma jansa da fira yana mazewa, ganin hankalinsa ba ya kanta ya sa ta tattara hankalinta kan tv. Shi kuwa Aliyyu jinsa yake tamkar a kan ƙaya, hankalinsa sam ba ya gidan da yake a zaune, fargaba ce fal zuciyarsa, saboda sanin halin Reza wacce ya karya mata alƙawarin haɗuwar da za su yi yau don ya ba ta rabin kuɗinta ya kuma ba ta haƙuri kan sauran kuɗin, amma saboda sanin halin Maryam dole ya haƙura ya dawo gida, wayar ya ɗauka ya saka a silent, babu jimawa kuwa sai ga kira yana dubawa ya ga Rezar ce, gabansa ya faɗi, ya ɗan tura wayar ƙarƙashin kujera, amma hankalinsa yana kanta yana ta ganin haske na kawowa yana ɗaukewa, sai jan tsaki yake cike da fargabar furucin Rezar na cewa yau har gidansa sai ta zo akan kuɗinta. Maryam wacce tsakin ya fara ba ta mamaki, ta juyo tana haɗe gira ta ce"Wai ni kam Love tsakin me kakr ta jerowa ne? Na lura tun da ka dawo ba ka da nutsuwa". Ya sauke numfashi ya ce"Wallahi Love mantawa na yi ban siyo biredi ba, shi ne duk abin ya dame ni". Lokaci ɗaya ta haɗe rai, don ta san indai ya fita siyan biredin nan fa sai an gan shi, ta ce"Ka bar shi kawai, a dafa indomi". Ya ce"Ai kuma shayin nake son karyawa da shi, wallahi minti biyar ya yi yawa, kin ji?" Ta juya kai ba ta ce komai ba, hakan ya sa ya gane ta yarda ya fita amma ba da son ranta ba. Ya tashi zai fita, ta ce"Ara min wayarka". Ƙirjinsa ya buga, ya ce"Ai fa yau ƙaraf na dawo gidan, transfer zan yi wa mai biredin". Ya fice yana jin salama a ransa, sai da ya yi nisa da gidan sannan ya kira lambar Reza, tana ɗagawa ta fara masifa"Wai kai Ali ni za ka rainawa hankali saboda ka yi aure ko? To idan ban kashe auren ba Allah Ya..." Kafin ta ƙarasa ya katse ta da faɗin"Subhanallah! Haba Reza, ke me yasa ba ki da uzuri? A ina za mu haɗu?" Tana faɗa masa gidanta zai kai mata ya kama hanya jiki na rawa saboda da ɗan nisa, kamar zai yi kuka saboda takaicin fitar da kuɗin ya ba ta dubu biyar yana ba ta haƙurin gobe zai cika mata dubu biyar, duk da ya san ba zai taɓa yiwuwa ya bata a goben ba, don wannan biyar ɗin ma da ƙyar ya haɗa ta, ya bar gidan zuciyarsa fal ƙunci, a hanya ya tsaya ya sayi biredin ya koma gida da ƴar fargaba. Har ta yi bacci saboda an ɗauke wuta kuma ya daɗe, ya ɗauki radionsa dake kan mudubi, ya haska ta a ransa yana cewa'fitinanniyar yarinya', sosai yake jin daɗin saurin baccinta, saboda daren ne kawai yake da lokacin wayarsa inda yake cin karensa babu babbaka da ƴan matansa, falo ya koma ya kwanta ya kunna radion ya ajiye, don haka yake yi idan Maryam za ta takura masa kan ya zo su kwanta, sai ya ce shiri yake ji, ko ta yi zaman jiransa jin radion ba ya ƙarewa, sai ta haƙura ta je ta kwanta. Data ya kunna ya shiga chart da Baby Farha wacce jiya suka haɗu da ita a wani group ɗinsu mai suna ƴan hutu, sosai jiya ya ji daɗin haɗuwarsa da ita kuma daga ganin hotonta ƴar hutun ce da gaske, saboda haka bai yi ƙasa a gwiwa ba ya shiga sharara mata ƙarya da nuna shi ma ɗan hutun ne kuma babban ɗan kasuwa, suna ta fira idan zai yi mata voice sai ya kashe radionsa ya narke murya yana iyayi kamar mace, shi a dole ɗan hutu. Sai ƙarfe ɗaya Maryam ta farka, yana jin ƙarar ɗaukar buta ta shiga banɗaki, ya yi maza ya kashe wayar duka ya baje a ƙasan kafet yana jan munshari. Ta leƙo ta haska shi tana mai jin tausayinsa, ta san a gajiye yake saboda yanayin aikinsa na kafinta, ga shi wuni yake a can, ta kira sa da 'Love' Ya tashi a firgice yana mirtsika ido ya ce"A...wai bacci na yi a nan? Ikon Allah kin ga fa radio nake ji ashe bacci ya ci ƙarfina". Ya kashe radion da ke ta shuuuu don tuni sun rufe gidan radio, ya kulle falon. Kafin ya shiga ɗakin gadon har ta kwanta, ta baje don ci gaba da baccinta, a hankali ya kai hannunsa jikinta, wanda ta ji saukar hannun kamar saukar wuta a jikinta, idan da abin da ta tsana a aure to wannan fannin ne, tsam ta cire hannunsa daga jikinta ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, wai sau nawa zan faɗa maka duk wani abu da ya biyo bayan bacci haramun ne?". "Hmm!" Ya sauke ajiyar zuciya, yana matsawa gefe, don shi dai ba wani zurfi ya yi a islamiyya ba, ganin ita kuma ta yi karatun ya sa shi zaton wannan hadisi ne, cewar ba a tashin mace a neme ta idan ta riga ta yi bacci, ajiyar zuciya ya sauke, ya juya mata baya, a zuciyarsa yana ta hango surar Baby Farha wacce yake so yana samun wasu kuɗi da yake jira ya ziyarce ta, idan Allah Ya taimake shi ƴar hannu ce sai ya san yadda zai ɓullo mata. GIDAN SADIQ Riƙe yake da hannun ƴaƴan nasa biyu mata wanda ya karɓo su daga maƙota, Afna har ta fara bacci aka tashe ta, ita ma Fanan daga gani baccin ne a idonta, ya buɗe gidan suka shiga zuciyarsa sam babu daɗi, kaca-kaca ya tarar da falon, ya yi ƙwafa ya kalli yaran ya ce"Kun ci abinci?" Suka girgiza masa kai alamar ba su ci ba, ya shiga kitchen, nan ma ya tarar da wanke-wanke a zube, nan ya duba kuloli da tukwane ya fahimci ba ta yi girki ba ta fita, idan da sabo ya saba da yin girki, don haka ya kunna gas sai ya ga ashe ya ƙare, tsaki ya yi ya ɗakko flas ya ga wayam babu ruwan zafin ma"Allah na gode maka!" Ya faɗa yana buɗe wani ɗan bokiti ya ɗauki plate ya zuba cake ɗin da ke ciki, ya dawo falo ya buɗe firji ya ɗakko lemo ya zauna yana janyo yaran jikinsa, ganin duk sun noƙe yasa shi ƙirƙirar murmushi ya ce"Ku zo mu ci ko". Fanan da ita ce babba ta ɓata fuska ta ce"Daddy da rana ma fa shi muka ci, da safe ma da shi muka je makaranta, kuma ma Afna ba ta so, ni ma ya ishe ni". Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Ku yi haƙuri ƙawayena ku ci kun ji? Babu kyau kwanciya da yunwa". Da ƙyar ya lallaɓa su, Fanan ta ci, ita kuwa Afna sai shayi ya haɗa mata da ruwan sanyi, shi ma tun safe babu komai a cikinsa, don haka ya ci cake ɗin, yana son duba littafansu ko da home work amma ya san bacci suke ji, ya yi musu shimfiɗa a ɗakinsu ya kwanta a ƙasa su suna gado, bayan ya yi musu addu'a sun fara bacci, ya janyo wayarsa ya kira lambar mahaifiyarsu. "Hello Masoyi sorry yanzu nake shirin kiranka". Ta faɗa ta cikin wayar cike da kulawa. Jin ya yi shiru ya sa ta sake cewa"Ina yaran, ka dawo gida?" Ya ce"Yusra me yasa gas ya ƙare ba ki faɗa min ba?" Ta ce"Oh my God! Wallahi na manta, na so ma na aiko Nura ya ɗauka sai na sha'afa". Ya ce"Amma me kike yi tun da rana a gidan?" Cike da gajiyawa ta ce"Oh! Yau fa na zauna sosai a kemis, kuma na je wani gida karɓar haihuwa, sai magriba ma na shiga asibiti a latti". "Ok sai da safe" Ya faɗa yana shirin katse kiran. Ta ce"Na gode Masoyi". Ya ajiye wayar yana tunanin kalar rayuwar gidan nasa, da haka bacci ya kwashe shi, yana dawowa daga sallar asuba ya ɗora musu abin karyawa a electric kasancewa akwai nefa, shi ya shirya yaran suka ci abinci ya saka musu wanda za su tafi da shi, ya bar mata nata, ya jira mai mashin ya zo ya tafi da su makaranta, shi ma ya tafi shagonsa na provition da babu nisa da gidansa. Bakwai da rabi Yusra ta koma gida, don ta tsaya jiran wacce za ta karɓi dutyn safe, saboda tana bawa wata mai naƙuda kulawa sosai, ba ta so ta barta sai ta damƙa ta a hannun wacce ta san za ta kula da ita, duk saurinta ba ta tarar da su a gidan ba, bacci ne fal idonta amma haka ta haƙura tana ajiye jaka ta shiga kitchen ta fara wanke-wanke, sai da ta gyara ko'ina gidan ya dawo hayyacinsa ya ɗauki ƙamshi sannan ta ci abincin da ya ajiye mata, ta yi wanka ta ɗauki waya ta kira shi, "Ina kwana?" Ta gaishe shi bayan ya ɗauki wayar. "Kin dawo?" Ya tambaya ba tare da ya amsa gaisuwar ba. Ta ce"Na dawo". "Ok anjima kaɗan zan kawo cefane". Ya faɗa yana sauke numfashin da ta san fassarsa. Ta ce"Ka bar shi, wake da shinkafa zan yi ai, kuma Nura zai zubo gas". "Zan zo dai" Ya faɗa. Ta ce"Masoyi da ka haƙura dai, wallahi jiya ban samu bacci ba, yanzu ina dawowa na hau kan aikin gida, bacci zan yi kafin na tashi ɗora girkin rana, kaina har ciwo yake". Yana haɗiye ɓacin ransa ya ce"Amma yau ma fa dutyn dare za ki fita, ba kya tunanin..." Ta katse shi da faɗin"Don Allah Masoyi, gobe ina gida fa". "Ok" Ya faɗa, yana katse kiran. Ita kuma ta gyara kwanciyarta ta fara bacci hankali kwance. Sai sha biyu ta tashi, ta kira yaronta Nura ya sako mata gas, har ma da cefanen kayan miya, don ba ta son zuwan mijinta shi yasa ta ce masa ba sai ya kawo cefane ba, saboda ta san idan ya zo hana ta bacci kawai zai yi, shi ma ya katsewa kansa kasuwa, a gurguje ta yi shinkafa da miya, tana saukewa ta ɗora tuwon dare don shi a son samunsa kullum ya ci tuwo da daddare, amma ba kullum take samun damar yi masa ba, saboda aiki, ƙarfe ɗaya aka dawo da yaran daga makaranta, suka ci abinci ta yi musu wanka, sai da suka saka unifom ɗin islamiyya sannan ta fito da littafansu suka yi home work, tana sauke tuwo ta yi wanka, ta shirya ta ɗauki abincin Sadiq ta haɗa kansu ta kai su makarantar da babu nisa da gidansu, sannan ta wuce shagonsa don kai masa abincin. Gefe ta tsaya sai da na ciki suka fita, sannan ta ƙarasa murmushi ɗauke a kan fuskarta ta ce"Sannu da aiki Masoyi". Ya yi guntun murmushi yana kallon yadda ta yi kyau tana zuba ƙamshi duk da ba kwalliya ta yi ba ya ce"Na gode". Ta ajiye masa kular tana cewa"Ya kake, komai ƙalau ko?" Ya gyaɗa mata kai yana ta kallonta. "Kemis?" Ya tambaye ta. Ta gyaɗa kai ta ce"E zan je na ɗan zauna, na gama aikin gidan, har tuwo na yi maka". Ya ce"Kin kyauta kuwa, sai goben". Ta yi murmushi ta fice, yaran sun sani daga islamiyya maƙotansu za su shiga, sai ya dawo bayan sallar isha'i ya ɗakko su, duk da ranar da ba ta nan ne yake katse kasuwar, amma a ƙa'ida goma da rabi yake tashi. GIDAN HARUNA Ƙarar alarm ne ya karaɗe ɗakin, hakan ya sa Halima tashi a firgice, ta janyo wayar da ke kusa da ita ta latsa alarm ɗin ya mutu, bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci ta miƙe zaune, ta dafe kanta tana jin yadda ya sara mata, tun dare ta kwanta da ciwon kan, ga shi har yanzu bai sauka ba, sakkowa ta yi daga gadon ta fita tayo alwala ta dawo ta canza kaya ta kabbara sallar da ake yi ta asuba, tana lazimi tana gyangyaɗi har bacci mai ɗan nauyi ya kwashe ta daga zaunen, a firgice ta tashi ta ga gari har ya yi haske, ga kukan tsuntsayen da suke faɗa mata lokaci ko da babu agogo, da sauri ta fita ta kunna murhunta na gawayi, sannan ta dawo ɗaki ta fara firfito da kayan sana'arta ta wainar fulawa, wata matashiya ce ta fito daga ɗakin dake kusa da nata tana cewa"Ashe kin fito, yanzu nake cewa yau Halima ta makara". Halima ta yi murmushi ta ce"Zainab ina kwana? Wallahi yau baccin ya yi mini nauyi ga ciwon kai tun jiya". Zainab ta ce"Ai ke ce ba kya hutawa Halima, sai ki sha magani kafin ki hau suyar nan". Jin ba ta bata amsa ba ya sa ta san ba ta da maganin, ta shiga ɗaki ta fito hannunta ɗauke da kofi da kuma maganin, kunun alkama da ta saba damawa ne ta miƙawa Halima tare da maganin, ta karɓa tana godiya, ta kwankwaɗe sannan ta sha maganin, Zainab ta ce"Zauna ya ɗan tsarga miki Halima bari na fifita miki wutar". Ba don kan ya daina ciwo ba ta tashi ta hau suyar wainar, mutane suna ta shigowa suna siya, yawancinsu ƴan makaranta ne, sai da ta gama tsaf sannan ta saka a farantai biyu ta miƙawa Zainab ta leƙa ɗakin da Zainab ɗin ta fito wanda kakarta ke ciki tana jin radio ta miƙa mata, suna gaisawa. Ta dafa shayi ta juye a flas ta ɗauki wainar da ta zuba a wata ƴar kula ta kai ɗaki ta ajiye, tana nan zaune a tsakar gida tana wanke-wanke yaron da yake kai mata tallar wainar makaranta ya zo ya ɗauka ya tafi, bayan ta share tsakar gida ta shiga ɗaki ta auno shinkafar da take dafawa ta siyarwa ta fito ta fara tsince ta, sai da ta gama ta ɗora tukunya ta saka wake, sannan ta koma ɗaki ta tarar mijinta ya tashi, ta kalle shi cike da takaici ko sallar asuba bai yi ba, sai yanzu zai yi idan har an yi sa'a yana da niyyar yi a ranar, ta kalli yadda daga tashinsa har ya ɗauki waya duk da ta san halayyarsa ce amma tana takaicin abun. "Ga wainarka da shayi" Ta faɗa tana tura kayan gabansa Ya ce"Ki ɗan dafa min taliya da ita zan karya, wannan wainar kuma ki samu leda ki saka min". Ta ce"Taliya ai ka san ta ƙare". Ya yi tsaki ya tashi ya fita don yin wanka, daga shi sai gajeren wando, wanda har zuciyarta ba ta son hakan, ko don Zainab da ke zaune a tsakar gidan kullum daidai wannan lokacin, ta yi masa ƙorafi har ta gaji, ta lura abun ya bi jikinsa ne. Yana gama karyawa ya fara sosa kai, tsaki ya ja fuskarsa ta nuna alamun damuwa, Halima da ta san kwanan zancen ta ce"Lafiya kake tsaki?" Haruna ya ce"Wallahi Halima jiya zero na shigo gidan nan, wannan shinkafar ma bashi na karɓo ta, kin ga bai kamata yanzu na fita ban bar miki komai ba". Ta yi guntun murmushi ta ce"Haba kar ka damu, Allah zai rufa asiri, watarana sai labari, ga wannan ka hau babur". Ta ƙarasa tana miƙa masa ɗari biyu Ya karɓa ya ce"Na gode, kai ni kam na yi sa'ar mace ta gari, Allah Ya shi miki albarka". Ta amsa da amin, shi kuma ya fice. Ta yi shiru tana tunanin kalar rayuwar auren da take yi, sam Haruna ba shi da zuciyar nema, dududu wata uku kenan da auren amma kullum a haka ake, dama a wurin da take siyar da abinci suka haɗu har ya aure ta, don haka da ta lura da irin mijin da ƙaddara ta zaɓo mata, sai ta fara sana'o'inta, tun da idan ya kawo abin da za a dafa shi kenan, babu ruwansa da mahaɗi, ita ce gawayi, mai, magi, kayan miya, omo, sabulu da siyan ruwa, sai dai duk ranar da ya samu yana ba ta dubu ɗaya, saboda haka take ƙara dagewa a kan neman na kanta don ta rufawa kanta asiri. A zaure suka yi kiciɓus da Zainab ta sha gabansa tana cewa"Haruna ni me kake nufi da ni wai? Jiya ko biyar ba ka ba ni ba yau ma..?" Tana direwa ya ce"Ki yi haƙuri Zee, wallahi jiya ban shigo da komai ba, shi yasa ma kika ga na yi dare, saboda shinkafa ma a tata na ɗiba na saka a leda na ajiye kawai, saboda ta yi zaton da ita na shigo, amma yau dole zan shigo miki da wani abu, ai za mu haɗu ko tawan?" Ta ruƙo hannunsa ta ce"Ko na karyawa fa ba ni da shi". Ya sauke numfashi cikin sarewa da halinta, ya ciro ɗari biyun da Halima ta ba shi ya ba ta, ya fice. Ta soke a hularta, ta shigo gidan tana gyara rigarta da ta zame ta don ta ɗauki hankalinsa, ta shigo ta fara fifitawa Halima wuta tana ɗan ɗaga murya ta ce"Halima fito da barkonon na daka miki". Tana murmushi ta fito da shi, a ranta tana jin daɗin irin kirkin Zainab da kakarta wanda yau satinsu uku kenan da tarewa a gidan, amma har sun saba. 08028966015 [7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS PAGE 2 Da ƙyar Maryam ta iya tashin Ali ya tafi masallaci sallar asuba, saboda nauyin da bacci yake yi masa, amma da ya idar da sallah sai da ya zauna a masallacin ya kunna data, ya dudduba saƙonni, lambar Baby Farha ya duba ya ga ba ta hau online ba, ya yi murmushi yana ayyana tana can tana bacci a cikin AC. Lokacin da ya dawo tana zaune a sallayar da ta idar da sallah, ya kwanta yana jira ta gama ita ma ta zo ta kwanta, ganin shiru ba ta da niyyar tashi ya sa shi cewa"Love me kike yi ne? Jiranki fa nake" Nan take ta haɗe rai, dama ta san kwanan zancen shiyasa ta zaɓi ta yi zamanta har gari ya yi haske ta fita ta dafa shayi, sai ga shi dai ba ta tsira ba, ita kam tana son mijinta, tana kishinsa sosai, amma ta tsani ya neme ta a shimfiɗa, wannan shi ne babbar matsalarta, a zatonta rashin sabo ne da farko amma yanzu ga shi har auren ya yi wata shida a haka ake, ta sani ba ta ba shi haƙƙinsa yadda ya kamata, kawai yana ƙyale ta ne saboda a zauna lafiya kuma ta san yana shakkarta, hakan kuwa ya samo asali ne ta yadda yake bala'in sonta, sannan ya kasa maza da dama kafin ya same ta, ciki kuwa har da waɗanda suka fi shi komai na rayuwa, a lokacin an zuga Maryam sosai a kan aurensu, masu rufin asiri suna sonta amma za ta auri kafinta wanda zai kai ta gidan haya, ta ce ita ta ji ta gani. "Ko ba zan samu ba?" Ya tambaye ta yana karaya da lamarinta, shi mutum ne mai ƙarfin sha'awa, wanda har yake ganin hakan shi ne ƙaddararsa, don tun da ya fara sana'a yake samun na kashewa ya fara neman mata bisa shawarar abokai, a yadda suke faɗa masa, ai shi saurayi ne ko a shari'a idan an kama shi ma bulala ce kawai, kuma yana yin aure zai daina, hakan ne ma ya sa shi dagewa ya yi auren don ya samu cikakkiyar nutsuwa da halalinsa, sai kuma Allah Ya haɗa shi da mace mai gudunsa, sosai abun yake ci masa tuwo a ƙwarya, don haka ya kasa yakice wa kansa wannan halayar, ko chart ɗin batsa duk yana yi ne saboda ragewa kansa damuwar nan da kuma sabo. Haka dai ta je gare shi ranta babu daɗi, kuma ya san yau a haka za ta wuni da ƙuncin nan, shi yasa idan aljihunsa da nauyi yake gwammacewa ya tafi wurin matan banza inda za a faranta masa ya biya, a haka ne har bashin dubu goma ya shiga tsakaninsa da Reza, wanda ba dan haka ba da dubu biyar ɗin da ya ba ta jiya sai dai ya yi musu buƙatun cikin gida, ita kuwa ƙarya da yake yi wa ƴan mata a waya dama halinsa ne, ba ma zai taɓa iya dainawa ba. Suna gama karyawa ya tafi aiki, ita kuma ta shiga harkokinta na cikin gida, tun tana gida sana'arta ce kitso da ƙunshi kuma har yanzun ma tana yi ba ta watsar ba, gidan nata ba ya rabo da mata, maƙotanta masu sana'a ma duk nan ne majalisarsu, ana kitso ana kitsa gulma, don ma dai ana shakkarta don ba ta da wasa, sai dai ko ba ta gama ba magriba tana yi ta rufe sana'a, ta gyara gida ta ɗora girki sannan ta yi wanka ta yi kwalliya, ta jira dawowar mijinta, idan da abin da ta tsana bai wuce duhu ya yi ta ganta ita kaɗai ba, da ƙyar ta amince da cewar sai takwas da rabi zai dinga dawowa gida, kuma tana gotawa za ta fara mita tana kiransa a waya, idan ta gaji sai ta rufe gidan ta jira shi a ƙofar gida. Yau ma kamar kullum, ta gama komai ta idar da sallar isha'i, ta kame tana jiran dawowarsa. Tun da Ali ya fita da safe, wajen aikinsa ya wuce, ya shiga aiki tuƙuru, babu zancen kula kira da plashing ɗin da ƴan mata suke yi masa, yawanci waɗanda ba su daɗe da haɗuwa ba ne suke kiransa, amma duk wacce suka daɗe ta san da cewa Aliyyu ba ya haɗa aikinsa da komai, idan yana office ba ya ɗaukar wayarsa sai ya fito, da haka yake neman na kanshi domin ya samu asirinsa ya rufu, wajen aikin babu nisa da gidan iyayensa, a nan yake zuwa ya ci abincin rana ko a aiko masa, sai magriba ya tashi daga aiki, sallah ya yi ya shiga gidansu suka taɓa fira da ƴan'uwa, sannan ya tafi majalisar unguwar bai jima da zama ba Reza ta kira shi, ya ɗauki wayar kamar zai yi kuka ya ce"Reza idan kin yi haƙuri ma ai zan kira ki". Ta ce"To ina jiranka...". Ya katse ta da faɗin"Ki ƙara min haƙuri don Allah, wallahi ba su samu ba, sai dai ko gobe". Ta ce"Ali kar fa ka mai da ni ƴar iska". Ya yi dariya ya ce"To da mece ce?" Ta ce"Dariya ma kake yi kenan! Wallahi idan ban zo gidanka na tona maka asiri ba shegiya ce ni, ɗan iska ka yi auren ma ba ka daina cin bashi ba". Ali ya ce"Ni dai ki yi haƙuri, tsautsayi ne ya ja ni, da ba ki zage ni ba". Ta ce"Ka nemi kuɗina ka ba ni". Ya ce"Gobe zan kawo miki in sha Allah!" Suka ajiye waya. Ya fito daga sallar isha'i kenan sai ga kiran Maryam, yana ɗauka ta ce"Na ji shiru, wallahi yunwa nake ji yau, don Allah ka dawo da wuri". Bai ce komai ba ya kashe wayar, ya buga babur ɗinsa, abokansa suna ta yi masa tsiya, Madam ta yi kira, shi dai ya ɗauki hanyar tafiya gida, yana takaicin yadda take kafa masa takunkumin nan, sai ta ce ba ta iya cin abinci ita kaɗai, kuma ta yi ta kiransa tana ce masa yunwa take ji, ya dawo su ci. Tana zaune tana kallo a waya ya same ta, ta yi masa sannu, ta kai masa ruwa ya yi wanka, sannan ta kawo musu abinci, suna cikin ci sai ga kira a wayarsa, sai da gabansa ya faɗi saboda harƙallar rashin gaskiya da yake yi, indai aka kira shi a gaban Maryam sai ya ji faɗuwar gaban nan, da ya ga abokinsa Hamza ne mai kiran sai ya ji dama-dama, ya ɗaga yana cewa"Hamza ya ne?" Daga can ɓangaren Hamza ya ce"Wallahi aboki wani kaya ne mai zafi ya samu, sai ka gani dai ka fito muna bayan layinku". Ƙirjinsa ya ba da rass, ya kalli Maryam wacce ta dakata da cin abincin ta kafe shi da ido, don duk a abokansa ta fi tsanar wannan Hamzan, tun da ta lura ya fi maƙale masa, kuma tana jin sautin wayar ta ji ana magana da kurman baƙi, ta fara tunanin wane kaya ne me zafi mijinta zai siya? Tsam ya tashi zai fita, yana hello hello, alamar babu network, bai ankara ba ya ga Maryam ta ruƙo rigarsa ta zaunar da shi, ta yi masa nuni da abincin dake gabansu. Cikin karaya ya ce"Hamza wai katakon ne aka samu masu kyau?" Hamza ya ce"Kai dalla Malam ina yi maka zancen kaya kana ce min katako, wata mai zafi aka samu fa, kuma wallahi babu tsada..." Da sauri Ali ya katse shi da faɗin"Au shadda? Ai sai ka ce min wannan shaddar da zan siya wa Maryam an samu, ka tsaya kwana-kwana?" Hamza ya ce"Kana gida ne?" Ali ya ce"Ina gida, amma ka ajiye min gobe za mu yi magana, duk da ba ni da kuɗin ma". Suka yi sallama, ya kalli Maryam yana sauke ajiyar zuciya, suka ci gaba da cin abincin tana auna maganganunsu a zuciyarta. Yau ma dai gajiya ta yi da ƙarar radionsa ta je ta kwanta, hakan ya ba shi damar dulmiya duniyar wayarsa, ya yi mamaki da har Baby Farha ta fara yi masa zancen yaushe zai je gidansu? Hakan ya ba shi tabbacin ba ƴar ƙarya ba ce, don ƴan ƙarya yana cewa zai je suke kawo masa uzuri har a bar zancen, ya faɗa mata zai zo cikin satin, sai kuma ya fara tunanin kayan da zai saka, don hotunan da ya tura mata sun kwana biyu, yanzu kayan sun sha wanki, ya fara tunanin dole nan gaba ya fara aron kayan sakawa kafin ya ɗinka sababbi, da wannan tunanin ya yi bacci, bayan ya gama tashin kan ƴan mata da ƙarya. GIDAN SADIQ Yau tun magriba ya rufe shagon, ya je ya kwaso ƴaƴansa, saboda ba ya son barinsu a maƙotan nan don dai babu yadda zai yi ne kawai, gida suka shiga ya canza musu kaya, ya wanke unifom ɗin, sannan ya saka musu tuwo, shi ma ya saka, suna gamawa ya ɗakko littafansu babu home work sai ya yi musu bitar karatu, ya kunna musu surar da suke a islamiyya, suna saurara har bacci ya ɗauke su, a gida ya yi sallar isha'i, ya yi musu shimfiɗa suka kwanta ya tofe su da addu'a, sannan ya kira lambar Yusra har sau uku ba ta ɗauka ba, tun jiya yake cikin yanayi na buƙatuwa, amma babu yadda zai yi kamar dai gwauro, sau da yawa yakan yi tunanin duba shawararwarin da mahaifiyarsa take ba shi akan aikin Yusra, ko dai ya mata tilas ta ajiye ta kula da gidanta, ko shi ya ƙara aure, amma idan ya tuna yadda take da kishi sai ya kau da zancen, saboda yana ƙaunarta, ba ya son abin da zai kawo rabuwar kai a tsakaninsu, duk da ya san ba za a taɓa dawwama a haka ba, don hanyar da gidansa ta ɗakko ba mai ɓillewa ba ce, da wannan tunanin bacci ya ɗauke shi. Sai wajen sha ɗaya ya ji ringin ɗin wayarsa ya duba ya ga ita ce, kamar ya share sai kuma ya ɗaga don wataran takan dawo cikin daren ta ce ta gudo, jin tana tambayarsa ya gidan yara sun yi bacci? Kawai sai ya kashe wayar ma duka ya ci gaba da baccinsa. Da safe shayi ya dafa musu da ɗumamen tuwo, ya yi musu wanka ya shirya su suka tafi makaranta, shi ma ya tafi shago. Tana dawowa ta gyara gida, ta sha sauran shayin da biredi, ta yi wanka ta zauna har za ta kira wayarsa ta fasa, don kar ma ya ce zai zo, ta yi kwanciyarta, da wuri ta yi girki, ta zuba na yara ta kai musu maƙota, sannan ta zuba na shi ta bawa yaro ya kai masa, ta zuba nata a kula ta tafi kemis, daga nan ta wuce asibiti. Yau dab da magriba ta dawo, kusan lokaci ɗaya da yaranta, ta shiga ta taho da su, suna ta farin cikin yau Momynsu tana gida, sosai suke kewarta idan tana yin aikin kwana, don ma wani lokacin tana zuwa har islamiyyar ta gansu, cike da farin ciki suke ta ba ta labarin makaranta, su suka zaɓi abincin da za a dafa, ta ɗora, suka yi sallah tare, sannan ta yi musu wanka, tana taya su home work har ta gama girkin, suka ci a faranti ɗaya cike da ƙauna irin ta uwa da ƴaƴanta, bayan sun gama ta ba su wayarta suna ta kallon bidiyoyin yara na ilimi har suka yi bacci, ta gyara shimfiɗa ta kwantar da su, sannan ta yi wanka ta shirya cikin kayan bacci. Tana kwance tana ɗan taɓa chatting ya dawo, wajen tara da rabi, ta je ta karɓi ledar hannunsa tana yi masa murmushi mai cike da ƙauna, ta kai kitchen ta taho da abincinsa, kafin ta fito har ya shiga wanka, a bakin gado ta zauna ta ɗauki wayarsa da ke ajiye, wacce ta san babu ruwan shi da saka cord, ta duba call long ta yi murmushi ganin duk amintattun kira ne babu na zargi, haka ma massages, shi babu ruwansa da chart, babu ma App ɗin whatsApp a wayar, sai facebook da yake da tsirarun abokai, wannan tana yawan dubawa ta wayarta don ta ga abokansa, tun da nan ma bai wani saka tsaro ba. Tana ajiye wayar yana fitowa daga banɗakin, ta sakar masa murmushi, ya yi mata murmushin gefen baki, jikinta ya ɗan yi sanyi, don ba haka suka saba ba, a hankali ta ƙarasa inda yake tsaye a gaban sif yana duba kayan da zai saka, gabansa ta je ta tsaya ta riƙe duka hannuwansa daga ɗaukar kayan, ta shiga jikinsa ta kwanta, ya shafa kanta bai ce komai ba, ta ce"Na ga kamar kana cikin damuwa". Kai tsaye ya ce"Ai ke ce". Ta ce"To ka yi haƙuri, yanzu ba ga ni ba?" Ya ja hannunta zuwa gadon, tana ta narke masa, har suka samu nutsuwa cike da ƙaunar juna, sun yi wanka sun fito suna cin abinci ta lura da yadda har lokacin ba ya cikin shauki kamar da, ta tattara hankalinta gare shi ta ce"Masoyi akwai abin da yake damunka bayan kewata, don Allah kar ka ɓoye mini". Ya yi saurin girgiza kai, ya ce"Babu komai Masoyiya yanayi ne kawai, kwana biyu kamar zan yi zazzaɓi, kuma kewarki ce take haddasa mini irin hakan, ina da mata amma na kwana da kewa kamar mara gata...". Ta katse shi a shagwaɓe ta ce"Don Allah kar ka ce haka, yanzu ba ga shi kewa ta tafi ba?" Ya ce"Amma haka zan rayu ba kodayaushe zan samu kulawarki ba?" Ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, yanayi ne ya zo da haka". Ya ce"Amma idan na ce miki yanayi ya saka ni son ƙara aure za ki fahimta?" "Sadiq! Aure za ka yi?" Ta tambaye shi a tsorace Ya girgiza kai ya ce"Sam, kawai tambayarki na yi". Jiki a sanyaye ta ce"Wannan bai kai dalilin ƙara aure ba, kuma ma na ga..." "Ya isa, gwada ki na yi fa" Ya katse ta. Ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi ba don ta yarda da cewar gwajin ba ne, da wannan tunanin ta kwana a ranta. GIDAN HARUNA Kasuwa Haruna ya nufa kai tsaye, don yaron shago ne, kasancewar babban shago ne ana biyansa daidai gwargwado, sai dai wannan halayyar tasa da ta zame masa katankatana ita ce take lamushe duk wani abu da zai samu, duk a zatonsa idan ya yi aure shi kenan matsala ta mutu, da farko kamar gaske sai daga baya ya ji ya rage samun nutsuwa da Halima, sannan ma sam ba ta da wayewa ta wannan fannin, ta ƙi sakin jiki da shi, su na bazan sun fi ta iya komai da yake so, shi yasa ya fi samun nutsuwa da su. A duk inda ɗan bariki ya haɗu da ɗan'uwansa ba ya ɓuya, don haka tun a satin farko da su Zainab suka tare a gidan ya gane ita ma ƴar hannu ce, kamar da wasa wataran zai shiga wanka tana zaune ya tsaya yana kallonta, sai ya ga ta ɗage masa gira tana kashe ido, ya yi murmushin jin daɗi don tun a ranar farko da ya fara ganinta ya kwaɗaita da ita, bayan an kwana biyu yana ƙofar gida ta zo za ta shiga kawai ta shafa bayansa za ta shige, ya taso da sauri yana miƙa mata wayarsa, ta saka masa lambarta, kuma tana shiga gida ya kira ta, su ka yi ta waya kamar sun saba, daga nan suka fara chart na musayar kalaman banza don kar ta san kar babu wani abun ɓata lokaci, sautari idan zai shigo gida yakan taho mata da leda tsire ko balangu ko dangin kayan sanyi, kafin ya ƙaraso sai ya yi mata waya ta same shi a zaure, ya lalube jikinta ta karɓi leda ta shige gida, sannan shi ma ya shiga kamar ba a yi komai ba, duk ranar da bai taho mata da komai ba ba ya faɗa mata ga shi nan zai shigo, ita kuma da safe sai ta daidaici fitarsa sun haɗu a zaure, don tana da mugun son banza, irin matan nan ne ma su yi wa maza kankat idan suka shiga komarsu. Yau ma hakan ce ta faru, ya samu alheri a kasuwa babu laifi, don haka ya ƙunso mata balangu mai zafi da yogurt, ya sayi taliya leda uku, sabulun wanka da omon wanki, don ya ragewa Halima. A zaure ya tsaya ya kira ta ba ta ɗaga ba, don lokacin tana tsakar gida wayar tana ɗaki, tana ganinsa ta taho da sauri za ta rungume shi, ya kauce yana kallon ɗakinsa ya ce"Haba Zee mene ne haka?" "Naki yana zaure" Ya faɗa yana saurin shigewa ɗaki. Ita kuma ta je ta ɗakko ledar ta shiga ɗaki, ta baje ledar cike da zumuɗi, Baaba ta ƙure ta da kallo ta ce"Ke Zainab a ina kike samo balangun nan ne?" Ta haɗe gira ta ce"Haba Baaba ai kin san saurayina ne yake kawo min". Baaba ta ce"To me yasa ba kwa zancen ne sai dai ki leƙa ki karɓo ya tafi?" Ta ce"Aiki ne yake yi masa yawa wallahi, kuma shi dayake aure ne a gabansa ba ya son ma dogon zance, sai ya ce duk ƙarya ce ake shararawa". Baaba ta sauke ajiyar zuciya tana karɓar balangun da Zainab ta ɗibar mata ta ce"Ni dai don Allah ki kama kanki Zainab, kin ga dai amana na karɓa, ki taimake ni na aurar da ke kar ki sake jajibo mana wani abun kunyar a nan, na bar waccen unguwar saboda ke, nan dai kin ga mu baƙi ne babu wanda ya san tabonki ballantana ki rasa miji, ki nutsu don Allah kin ji?" Ta ce"In sha Allah Baaba ba zan ba ki kunya ba". 08028966015 [7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS PAGE 3 Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h GIDAN HARUNA Halima ta tashi daga ƴar kwanciyar da ta yi a sallaya bayan idar da sallar isha'i, idonta fal bacci, saboda gajiyar da take kai wa dare da ita dalilin kujiba-kujibar da take wuni tana yi na sana'o'inta, ta yi murmushi tana yi wa mijinta sannu da zuwa, Haruna ya zauna yana amsawa, ya bata ledar hannunsa, da dubu ɗaya, ta karɓa tana yi masa godiya, sannan ta kawo masa abinci ta shige ɗaki ta kwanta, kafin ya gama har ta yi bacci. Ya ɗauki wayarsa ya kira Zainab suka yi fira, don ya san Halima tana da nauyin bacci ba za ta farka nan kusa ba. Can wajen ƙarfe goma har ya kwanta, Zainab ta kira shi ta ce ya kunna data, jansa ta dinga yi da maganganun banza, har ta tabbatar ta tada masa hankali sannan ta roƙe shi kan ya zo ya taya ta wanka, da farin ciki ya tashi tsam ya fice daga ɗakin, duk da yana fargaba, a tsakar gida suka yi kiciɓus suka yi wa juna murmushi ta cikin duhun, tana shiga banɗaki ya mara mata baya, ba su daɗe da shiga ba suka ji muryar Baaba tana cewa"Da mutum?" Lokaci ɗaya ƙirjinsu ya buga, suka fara muzurai, jin ana ƙoƙarin buɗe ƙyauren Zainab ta yi saurin cewa"Da mutum, ina ciki Baaba". A hankali ya ce"Yanzu ya za mu yi kenan?" Ta ce"Idan ta gaji za ta koma". Ya ce"Ta ya za ta koma tana buƙatar shiga banɗaki, kema wallahi kin fiya jaraba, ga shi za ki tona mana asiri". Ta ce"Tsautsayi ne, wallahi na gaji da marmarinka..." "Ni uwar me kike yi ne Zainab?" Baaba ta faɗa a fusace. Ta ce"Ina masai kuma yanzu na shiga". Suka ɗauki lokaci a haka kowa tsuru-tsuru musamman Haruna, sai Zainab ta tuna da ai da waya a hannunsa, da sauri ta ce"Ka kira lambata wayar tana ɗaki". Yana kira, ta ɗaga murya ta ce"Baaba ga wayata can tana ringing don Allah ki ɗaga kawo ne". Baaba da fitsari ya matse ta, a fusace ta ce"Ke buhun ubanki, wai kwana za ki yi a banɗakin?" Ta ce"Don Allah Baab, kuɗi ya ce zai turo, kin san kuma ba ya kira biyu, don Allah je ki kar ta katse kafin na fito". Baaba ta koma ɗaki tana tsaki, wuf Haruna ya fito ya yi zaure da sauri, sannan Zainab ɗin ta fito, ta tarar da Baaba tana kokowa da wayar, don ba ta iya ɗagawa ba, ta karɓi wayarta Baaba ta koma banɗaki tana mita, ita kuma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, sosai take son Haruna don haka dole ta san yadda za su ɓullowa lamarin nan, ta riga ta saba da maza yanzu jinta take tamkar a keje, don tun da suka dawo gidan nan ba ta haɗu da wani namijin ba, kuma a satin da za su dawo ɗin aka cire mata cikin da wani saurayinta ya yi mata, dalilin hakan ne ma kakar tata ta ce a bata Zainab ɗin su bar unguwar, saboda kowa ya ji zancen zubar da cikin nata, ta san idan Zainab ta ci gaba da zama a unguwar ba lallai ƴan ba ni na iya su barta ta yi aure ba. Shi kuwa Haruna sai da ya ji Baaba ta shiga banɗaki, sannan ya shiga ɗakinsa ya saka sakata, tashin Halima ya yi ya ragewa kansa zafi, saboda Zainab ta gama kunna shi, daga nan bacci mai cike da nutsuwa ya kwashe shi, saɓanin Zainab. GIDAN SADIQ Washegari da damuwa Yusra ta tashi, idan ta tuna maganarsu ta jiya sai gabanta ya faɗi, sosai ta shiga tsoron kar Sadiq ya ƙara aure, tana da kishi sosai, ba ta jin za ta iya raba mijinta da wata macen, a yadda take ji indai ta tabbata Sadiq zai ƙara aure ita za ta iya haƙura da aurensa bakiɗaya ma, ta je ta yi wani auren ta rayu ko da babu ƴaƴanta a kusa da ita, muddin za ta rayu babu kishiya kuma ba za a hana ta aikinta ba ta amince, a sanyaye take yin komai har ta kammala abun karyawa ta kai dining ta jera, sai da ta yi wanka sannan ta tashi yaran daga bacci, kasancewar yau Asabar ce babu makarantar boko, ta yi musu wanka, da suka ƙaraso dining ɗin shi Sadiq har ya gama cin nashi abincin ya tashi, yana kallonta ya san tana cikin damuwa, sai ya ɗauka ko yanayi ne jikin da jini, tun da ya tashi ba su haɗu ba sai yanzu, don tana idar da sallah kafin ya dawo daga masallaci ta koma ɗakin yaranta ta kwanta. "Zan fita, me za a kawo?" Ya tambaye ta yana yi mata kallon tsaf. Hankalinta a kan abincin da take zubawa ta ce"Ba sai ka aiko komai ba, yau ina gida me za a dafa maka?" Yana tafiya ya ce"Ki dafa zaɓinki kawai ya yi". Ya fita yana mamakin sauyinta, ko a dawo lafiya ba ta ce masa ba, ballantana ta raka shi, ya sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin kau da abun. Da rana bayan ta gama komai yara sun tafi islamiyya, ta kwanta tana ta tunanin wannan maganar tasa da take neman tarwatsa mata farin ciki, idan ta tuna za su rabu sai idonta ya ciko da ƙwalla, kanta ya kulle ta rasa abun yi, saboda haka ta kira Sister Sumayya a waya, babbar ƙawarta tun ƙuruciya, kuma abokiyar aikinta a yanzu, ba sa ɓoyewa juna sirri damuwar ɗaya ta ɗayar ce, bayan sun gaisa Sumayya ta ce"Sister na ji kamar akwai damuwa a muryarki, ba ki da lafiya ko daga bacci kika tashi?" Yusra ta sauke ajiyar zuciya ta kwashe duk abin da yake damunta ta faɗa mata. Sumayya ta yi murmushi ta ce"Haba ƙawata, ke daga wannan kawai sai ki yi zargin Sadiq zai iya ƙara aure?" Yusra ta ce"Kamar ba ki san butulcin namiji ba?" "Butulci?" Sumayya ta tambaya da mamaki, sannan ta ɗora da faɗin"Don zai yi abin da Allah Ya halatta masa sai ki kira shi da butulu? Haba Yusra ki dawo cikin hayyacinki...". Ta katse ta da faɗin"Wallahi Sumayya ba zan zauna da kishiya ba, don haka zan ba shi zaɓi, ko ya sake ni ko ya manta da ana ƙara aure a duniya". Cike da mamaki Sumayya ta ce"Da gaske duk son da kike yi wa Sadiq za ki iya rabuwa da shi saboda zai ƙara aure?" Yusra ta ce"Ƙwarai kuwa, wannan abu ne mai sauƙi a wajena, saboda na tsani kishiya". Sumayya ta yi makirin murmushi mai ɗauke da manufofi da dama, wannan wata dama ce da ta jima tana neman hanyar samunta, domin kuwa ko maye ya manta uwar ɗiya ba za ta manta, amma za ta biyo mata ta bayan gida, kuma daki-daki har ta cim ma burinta. "Sister ya zan yi? Duk na damu". Yusra ta faɗa kamar za ta yi kuka. Sumayya ta ce"Dole cikin uku a yi ɗaya, ko dai ki haƙura da aikinki kamar yadda yake so, ko kuma ki samo ƴar aiki wacce za ta dinga zama tana yi miki aikin gida, idan kina aikin kwana ta kwana da yara ko kuma ki haƙura ya ƙara auren". Yusra ta yi shiru na sakanni tana nazari, sannan ta ce"Ba zan iya ajiye aikina ba fa, zan gwada yi masa zancen ƴar aikin dai ko zai amince". Sumayya ta ce"Idan ya amince sai ki yi min magana, zan samo miki mai hankali da nutsuwa, kin dai ƙi kishiyar ko? Ni ba ga shi ita ce take kula da ƴaƴan ba idan ba na nan?" Yusra ta taɓe baki ta ce"Zuciyarmu ba iri ɗaya ba ce Sister". Daga haka suka ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama, da wannan matsayar ta samu sauƙin damuwar da take ji. Da daddare bayan sun gama cin abinci, yana lura da yanayinta na rashin sakewa da shi har yanzu, amma ya share, sai da ta gama jujjuya maganar tana tunanin karɓuwarta a wajensa sannan ta ce"Masoyi ina da magana mai muhimmanci". Ya ce"Ina sauraronki". Ta gyara zama ta kama hannunsa tana wasa da shi, ta ce"Na san ba na sauke duka nauyin da ya rataya a wuyana ta ɓangaren kula da gidan nan, ni ma ba na son zaman yara a maƙota, ga shi kai ma ana katse maka kasuwa, da safe a katse maka bacci ka tashi ka shirya su, su tafi makaanta..." "Ai duk na san wannan Yusra, ki tafi gaɓa ta gaba" Ya katse ta da faɗin hakan. Ta ce"Dama tunani na yi, na ce me zai hana na samo mana ƴar aiki, sai ta dinga kula da gidan idan ba na nan ko?" Ya yi shiru yana nazari, saboda bai taɓa zaton jin haka daga bakinta ba. "Ka amince na samo?" Ta tambaye shi jin ya yi shiru. Ya girgiza kai ya ce"Yusra ba na son ƴan aikin nan, kuma ma gidan nan bai yi girman da za a buƙaci ƴar aiki ba, indai don kula da yara ne, zan duba yiwuwar duk ranar da kike yin aikin kwana a kai su gidanmu su kwana a can, ni kuma zan kula da kaina, sai ki taya ni addu'ar Allah Ya ba ni ikon riƙe kaina, idan kuma na ga hakan duka bai yi daidai ba to ina ba ki haƙuri, don gaskiya zan iya ƙara aure..." "Wai da gaske?" Ta katse shi da tambaya, idanuwanta sun kawo ruwa, ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. Ta ce"Sadiq ka san zan iya haƙura da aurenka saboda kishiya?" Ya yi guntun murmushi ya ce"Ban sani ba, kamar yadda ke ma na tabbata ba ki san zan iya ƙara aure saboda na tsare mutuncina da tarbiyyar yarana ba ko?" Tashi ta yi za ta bar wurin, ya ruƙo hannunta, ta fizge hawaye suna sakko mata, ta shige ɗaki ta kwanta, tana kuka mai cin rai. ALI Bayan sallar isha'i yana shirye-shiryen komawa gida kwatsam sai ga Reza ta zo har majalisarsu, ya haɗe rai duk da yana ɗan fargaba saboda ya san ba ta da kirki, gefe ya ja ta don kar ta yi masa tonon silili a cikin mutane, ya ce"Haba Reza don Allah ki sakar min mara na yi fitsari!". Ta ce"Kai dalla can, ni harkar arziƙi ce na zo maka da ita, kana so na ka biya ni kuɗin?" Ya ce"Wallahi ina so, rashin kuɗin ne kawai, idan akwai ai ba zan bari ki yi ta bibiyata haka ba". Ta ce"To albishirinka". "Goro!" Ya faɗa cikin ƙosawa. Ta dafa kafaɗarsa ta ce"A daren nan za ka iya biyana cikin daɗin rai, wataƙil ma ka samu jari sanadin hakan". Ali ya ce"Don Allah Reza ta fi kai tsaye, sai kwana kike sha". Ta ce"Wallahi wata ƙawata ce take neman mai ɗauke mata kewa, ta kira ni ta ce na lalubo mata mai jini a jika, za ta ba shi dubu biyar, sai na ga tun da kana ta ƙoƙarin biyana awon shinkafa ya hana me zai hana ka je kawai, ka ga sai na riƙe kuɗin da za ta ba ka, ka biya ni kenan?" Ali ya ɗan sosa kai yana tunani, yana son zuwa yana fargabar kar ya daɗe ya shiga komar Maryam, amma wannan wata babbar dama ce, ko babu komai zai sauke duka kewar dake tattare da shi, sannan ya huta da nacin Reza na neman biyan bashinta, ya sauke numfashi ya ce"Ina ne gidan?" "Biyo ni!" Ta faɗa tana wucewa gaba, ya kai wa abokinsa Hamza mukullin babur ɗinsa yana faɗa masa yana zuwa,ya bi ta a baya zungui-zungui, suka shiga adaidaita sahu suka ɗauki hanya. Suna fara tafiya sai ga kiran Maryam ya shigo wayarsa, ya ƙi ɗauka don bai san me zai ce mata ba. A ƙofar wani babban gida suka tsaya, suka fito ta ɗauki waya ta yi kira, babu jimawa wata babbar mace ta fito ta ba wa Reza kuɗi idonta a kaina, sannan muka shiga Reza ta koma, sai ƙarewa gidan kallo nake, wanda nake mamakin a ce mace ce ita kaɗai take rayuwa a cikinsa, haka dai nake biye da ita har cikin babban falon da ya ji kayan more rayuwa, sanyin Ac sai ratsa ni yake yi, babu wani tsayawa bayani ta nemi gudanar da abin da ya kawo ni kai tsaye, ni kuwa ban yi ƙasa a gwiwa ba wurin faranta mata, har ban san tsawon lokacin da na ɗauka ba. Kafin na fito daga wanka ta kawo min abinci mai rai da lafiya, dama yunwa nake ji, na ci na ƙoshi na kora da lemo mai sanyi, sai a lokacin ta kalle ni ta ce"Ya sunanka?" "Aliyyu" Na ba ta amsa ina murmushi. Ita ma murmushin ta yi min ta ce"Gaskiya na ji daɗin haɗuwarmu, nawa Reza ta ba ka?" "Dubu biyar" Na ba ta amsa. Ta ce"Ni zan ƙara maka dubu biyar yanzu, sai dai babu cash a hannuna, kuma ATM ɗina ya samu matsala, ka kwanta ka huta bari na shiga maƙociyata ta ara mini, ko na daɗe kar ka fito". Ya jinjina mata kai cike da farin ciki, sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga sha ɗaya saura mintuna, ga miss call ɗin Maryam rututu har da massages, tsoro ya kama shi, gabaɗaya hankalinsa ya tashi, Allah Ya taimake shi ba ta daɗe ba ta dawo, ta ba shi dubu biyar, sannan ta shiga kitchen ta fito da leda ta ba shi, ta ce"Ga mai adaidaita nan zai kai ka sauke ka, ka ga dare ya fara yi". Ya ce"Na gode sosai Hajiya". Suka yi musayar lamba, ya fita ya shiga adaidaita sahun yana yi masa kwatance har suka ƙarasa. A sanyaye ya ƙarasa gidan nashi, yana tura ya ji shi a rufe kamar yadda ya yi zato, ya ciro waya ya kira ta, bugu ɗaya ta ɗauka "Ki zo ki buɗe min, ina ƙofar gida". Ya faɗa da fargaba. Yana jin motsin buɗewarta, ya mayar da ledar hannunsa bayansa ya ɓoye, tana buɗewa ko kallonsa ba ta yi ba ta juya ta koma, ya rufe gidan ya ajiye ledar a zaure, ya shiga yana karanto la haula wa la ƙuwwata a hankali. 08028966015 [7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS PAGE 4 Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 GIDAN ALI Ɗakin gado ta shige kamar kububuwa, kafin ya ƙarasa har ta kwanta, ya ƙaraso ya zauna a sanyaye ya ce"Love ba ki san mene ne ya tsayar da ni ba..." Ta katse shi da faɗin"Babu ruwana da ko mene ne ya tsayar da kai, ka raba dare a waje, ni dai ba zan iya ba, don haka gobe ƙarfe shida a gidanmu za ta yi min in sha Allah!". "Innalillahi! Haba Maryamata, ai ya kamata ki ji hanzarina, wallahi aiki ne ya sha kaina, ganin ga azumi yana matsowa kuma ban tanadi komai ba, shi yasa na ce bari na dinga ƙara lokacin tashi saboda na linka samun kuɗin, amma tun da hakan bai yi miki ba, shi kenan na haƙura kawai". Ko juyowa ba ta yi ba, ballantana ta nuna ta san yana yi. Ya zaro dubu biyu yana miƙa mata ya ce"Ga wannan kya sayi hoda". 'Ko uwar hoda ba!' Ta faɗa a zuciyarta, tun da ba ta ga amfanin yin kwalliyarta ba, kafin ta yi wanka yake fita, sai dare ya dawo, da daddaren za ta yi ta zambaɗa hoda kamar wata aljana? Ta yi ƙwafa a bayyane. Ya tashi a sanyaye ya canza kaya, ya kashe wayarsa ya kwanta, sai kuma ya ba ta tausayi ganin bai ci abinci ba, bai yi wanka ba, duk da gajiya da yunwar da ya kwaso, kuma duka saboda ita yake yi, ya nemo mata abin da za ta ci ta sha da sutura, sai ta ji ba ta kyauta ba, to amma mazan zamanin nan ne sai kana saka ido sosai a kansu, idan ka ce za ka ɗaga musu ƙafa sai su fanɗare maka kana ji kana gani. "Baka yi wanka ba kuma abincinka yana falo" Ta faɗa ba tare da ta juyo ba. Ya ce"Babu komai, zan kwana a hakan". Ba ta sake cewa komai ba, ta tashi ta fita, ta ɗauki a bincin ta kai kitchen ta buɗe ta rufe da kwando saboda kar ya lalace, shi kuma yana ta fargabar kada tsautsayi ya sa ta leƙa zaure, wata fitinar ta ɓallo, sai da ta dawo ta kwanta sannan hankalinsa ya kwanta. Yana lura ta yi bacci ya tashi tsam, ya tafi zaure, ya ɗauki ajiyarsa ya buɗe, snacks ne da dangin kayan zaƙi su alawar madara da chocolate kala-kala, sai robar wani lafiyayyen yougurt, ya zauna a zauren ya buɗe yougurt yana sha, sannan ya kunna data yana duba sakwanni hankali kwance, ya kai minti talatin kafin ya tashi ya tattara sauran kayan, saɗaf-saɗaf ya shiga ɗaki, ya ɗakko wata babbar rigarsa ta shadda ya bazata ya jure su a ciki, ya ƙudundune ya cusa a sif, ya nemi waje ya kwanta bacci mai daɗi ya kwashe shi. Yana farkawa ya ga gari har ya yi haske, ya kalli agogo ya ga bakwai saura, ya tashi da sauri ya fito, falo ya leƙa ya tarar da Maryam zaune tana cin abinci ga kuma babban akwati a kusa da ita, gabansa ya faɗi, ya dai fita ya yi alwala ya dawo falon, a bakin ƙofa ya shimfiɗa salayya saboda kar ta fita yana sallah, yana idarwa ya ce"Maryam yanzu duk fushin ne ya sa kika ƙi tashina sallah har gari ya waye?" Ta ce"Ai dama ba dolena ba ne, kai ne yake dole ka tashe ni". Ya ce"To shi kuma wannan akwatin fa na mene ne?" Tana ajiye farantin hannunta ta ce"Gidanmu zan tafi Ali, don ba ƴar iska ka ajiye ba da har za ka kai ƙarfe goma sha ɗaya a waje! Gara na tafi idan ka gama tara kuɗin na dawo, idan kuma ka samu wata ma shi kenan". Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar hijjabi za ta saka. Ya ƙarasa ya riƙe hijjabin kamar zai yi kuka ya ce"Haba don Allah Maryam, ai na san na yi kuskure tun da na ba ki haƙuri ya kamata ki yi min uzuri, ki gani ko zan ƙara? Naga jiya ne kawai hakan ta faru, kuma na faɗa miki dalilina, tun da ba mu fahimci juna ba na haƙura da aikin daren, wallahi haka ba zai sake faruwa ba, yi haƙuri mana kin ji kyakkyawar matata". Ta koma ta zauna tana ɓata rai ta ce"Wannan ya zama na ƙarshe, don idan ka ƙara kai wa irin haka a waje ba zan fahimce ka ba, wa ya faɗa maka zafin nema yana kawo samu?" Ali ya ce"Ba ma zai sake faruwa ba in sha Allah". "Ina ka bar babur ɗinka jiya?" Ta jefo masa tambaya. Ya ce"Ai da na ga na yi dare sai na bar shi a gidanmu saboda kar masu ƙwacen babur su tare ni". Sai da ya tabbatar ta haƙura sannan ya tafi wajen aiki, bayan la'asar sai ga wannan Hajiyar ta kira shi a waya, ya ɗaga suka gaisa take ce masa yau ma idan da dama tana son ganin shi, da sauri ya faɗa mata babu dama, suka yi sallama yana jin rashin jin daɗi, saboda yana son zuwan amma yana son zaman lafiya a gidansa don haka ya kau da kai, ya ci gaba da aikinsa. Sai bayan magriba Maryam ta ɗauki akwatinta ta mayar da kayan ta jere a sif, buɗe nashi sif ɗin tayi, don ta kwana biyu ba ta gyara ba, tana kwaso kayan ta ji motsin leda, da mamaki ta shiga bincikawa, ai kuwa tana zazzage babbar rigar nan sai ga kayan ciye-ciye sun bayyana, gabanta ya faɗi ta hau duba su cike da mamakin yaushe suka fara haka da Ali? Abun har ya kai ya sayi kayan daɗi ya ɓoye a sif yana ci shi kaɗai? Gefe ta yi da su, ta kwashi kayan ta mayar sif don ta fasa linkewar, ta kwashe kayan ƙwalam ɗin ta je ta baje a falo, ta dinga ci kamar babu komai, sai da ta cinye komai ta sha ruwa ta zubar da ledojin tana ta mamaki, tana kuma jiran dawowarsa don ta ji dalilin wannan sabon salon da ya tsiro da shi. Ƙarfe takwas tana yi Ali ya kamo hanyar gida, har kwakwa da dabino ya siya mata a hanya, saboda ya san tana so, ya tura ƙofar ya shiga da babur ɗinsa, ransa fes ya shiga ɗakin, ta kalle shi babu yabo babu fallasa ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa yana miƙa mata ledar kwakwar, ta karɓa ta yi godiya tana jinjina rainin hankalinsa, wato ya siyo kayan ƙwala har da dambun nama, ita shi ne zai haɗa ta da kwakwa, ta maze ta kai masa ruwa ya yi wanka, ya fito ta zuba masa abinci ta koma kujera ta kame tana cin kwakwa da dabinon. Da ɗan mamaki ya kalle ta ya ce"Ya dai Love! Yau kin ci abinci kafin na dawo kenan". Ta girgiza kai ta ce"Wallahi ban ci ba". Ya ce"To me yasa?" Ta ce"A ƙoshe nake, nan da ka gan ni cikina babu masaka tsinke tura kwakwar nan kawai nake don ina so". Ya yi ƴar dariya ya ce"To ke kuwa me kika ci?" Ta ce"Abubuwan da ka ci jiya ka ƙoshi har ka kasa cin abincin dare". Gabansa ya faɗi ya dake ya ce"Kamar ya? Me na ci jiyan?" Maryam ta ce"Au har ka manta ka yi saura ka ajiye a sif kenan". Ya ji ƙirjinsa ya ba da sautin dumm! Ya kasa cewa komai. Ta ce"Hmm! Na yi mamaki wallahi, yaushe muka fara haka da kai? Kuma idan za ka ci kai kaɗai ai da sai ka ci abunka a waje, ban gani ba ballantana na saka maka rani..." Ya katse ta da faɗin"Wallahi ba haka ba ne Maryam, wata yarinya ce take ta bi na a kwanakin nan ba na kula ta, to shi ne jiya ta bawa Hamza ya kawo min wannan kayan, kuma na san idan ma ban karɓa ba wallahi ba zai mayar ba, kuma zuwa zai yi ya ce mata na karɓa, shi yasa kawai na karɓa ɗin, to da yake na san ba za ki ji daɗi ba shi ne na ɓoye saboda kar ki gani, amma ba wai manufata na yi miki rowa ba wallahi". Maryam ta yi murmushin takaici ta ce"To mene ne abun ɓoyewa? Kenan jiyan a wurinta kake har sha ɗaya ko?" Ya yi saurin girgiza kai ya ce"Wallahi ban taɓa kula ta ba ma, ba faɗa miki ai aiki na tsaya, kuma tun da zai kawo mana matsala na daina, ba ga shi yau na dawo da wuri ba?" Ta ce"To shi kenan magana ta wuce". GIDAN SADIQ Sanda Sadiq ya gama uzurinsa ya je zai kwanta, sai ya same ta zaune a kan gadon, yana shiga ta sakko ta fice daga ɗakin, har bacci ya fara fizgarsa ba ta shigo ba, hakan ya sa ya fito don ya lallashe ta, a falo ya tarar da ita kamar yadda ya yi zato, saboda halinta idan suka yi faɗa ta ce za ta kwana a falo, zama ya yi a gefen kujerar da take kwance, yana shafa kanta ya ce"Yusra!". Ta juya masa baya, ya juyo da ita ya ce"Ni fa ban ce miki zan yi wani auren nan kusa ba". Ta ce"To me yasa ka hana ni samo ƴar aikin?" "To ki samo mai hankali" Ta ji furucinsa a bazata. "Da gaske?" Ta tambaye shi tana jin daɗi sosai. Ya ce"Da gaske mana, ba shi ne dalilin fushin ba?" A gabansa ta ɗauki waya ta kira Sumayya ta faɗa mata ya amince da ɗaukar ƴar aikin, cikin jin daɗi ta ce mata gobe za ta kawo mata ita har gida. Sai ga Yusra ta ware har tana yi masa firar yadda za ta kasance da ƴar aikin, suka kwanta tana cike da farin ciki. Washegari da kuzarinta ta gama komai na gidan, shi kuma ya tafi shago, ƙarfe tara Sumayya ta shigo gidan tare da wata buduruwa, Yusra ta tare su da murna, suka gaisa tana kallon yarinyar da take a nutse daga gani ba ta da hayaniya, Sumayya ta ce"To ga Kursum nan na kawo miki, ban fiya yabon wani ba, amma ina da tabbacin za ki ji daɗin zama da ita, ba ta da gandar aiki, kuma tana da hankali". Yusra ta ce"Ai na lura da hakan, ke dai Allah Ya saka ƙawata". Sumayya ta ce"To ya kika tsara yanayin aikin, a nan za ta zauna duka ko zuwa za ta dinga yi tana tafiya?" Yusra ta ce"Idan ta gama aikinta za ta jira na dawo gidan sannan na tafi, ranar da nake aikin kwana kuma za ta kwana a nan, ta kula da yaran ko dan saboda tashin sassafe ta shirya su su tafi makaranta". Nan Sumayya ta faɗa mata unguwar da gidan su Kursum yake, sannan ta ɗora da faɗin"Kursum ki yi abin da ya kawo ki shi kaɗai, ki kular mata da yaranta ki rungume su hannu biyu-biyu, sannan idan za ki yi girki ban da almubazzaranci, magana ta ƙarshe babu ruwanki da mijinta! Gaisuwa ce kaɗai za ta haɗa ku, idan kin yi girki ki ajiye a dining, yana dawowa ki shige ɗakin yara a nan za ki na kwana, kar ki sake ki fito babu hijjabi ko mayafi idan yana gida, kin dai ji ko!?" Ta ƙarasa tana ƙanƙance ido alamar gargaɗi sosai. Kursum ta ce"In sha Allah zan kiyaye komai". Yusra cikin jin daɗi ta ce"Na gode sosai ƙawata". Sannan ta ce"Yau babu aikin komai, tun da ina gida, sai dai gobe ki zo da safe, zan bar miki mukulli a wurin mijina, sai ki dinga zuwa kina karɓa a shagon, kin ga gobe aikin safe zan yi, to kafin ki zo mun fita dukanmu, idan kin karɓo mukulli sai ki yi wanke-wanke ki gyara ko'ina, kafin sha biyu ki yi girki idan yara sun dawo su ci ki shirya su su tafi islamiyya, shi ma ki zuba ki kai masa nasa, sai ki zauna a gidan, wajan ƙarfe uku zan dawo kin ga sai ki tafi ko?" Kursum ta jinjina kai ta ce"In sha Allah babu matsala". Suka yi mata sallama suka tafi, a hanya Sumayya ta ce"Don Allah Kursum kar ki ba ni kunya, na faɗa miki kuɗin da zan biya ki idan aikin nan ya yi kyau, ki kwantar mata da kai, shi kuma ki san ta inda za ki ɓullo masa". Kursum ta yi murmushi ta ce"Ni fa dama can yana burge ni wallahi, ballantana kuma za mu rayu a inuwa ɗaya? Hmm Allah Ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya yi ɓarna". Sumayya ta ce"Allah Ya shi miki albarka Kursum, idan komai ya tafi daidai, wallahi sai na yi wata shida muna raba daidan albashina da ke". Kursum ta kwashe da dariya cike da farin ciki, ta ce"Riba biyu inji sauro". 08028966015 [7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS PAGE 5 Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 GIDAN HARUNA A ranar tun tsakar dare zazzaɓi ya rufe Halima, dama tun da rana take ciwon kai, ta kasa bacci, sai gabannin asuba ya ɗauke ta, amma da alarm ɗinta ya buga haka ta daure ta tashi ta yi sallah, sai dai ta kasa komai ta kwanta a sallayar tana ta rawar sanyi, yayinda Haruna yake ta baccinsa bai san halin da take ciki ba. Zainab ganin har bakwai ta wuce Halima ba ta fito ba, ya sa ta ƙarasa ƙofar ɗakinta tana sallama, ta amsa mata da ƙyar tana tashi zaune ta ce"Zainab". Zainab ta buɗe labulen, ta ce"Halima yau lafiya kuwa ba ki fito ba?" Halima ta ce"Wallahi ba ni da lafiya, zazzaɓi da ciwon kai tun jiya, yau ba zan iya ba ma". Zainab ta ce"Ai kuwa babu daɗi a zo nema a ga ba ki yi ba, yau ɗaya da sai na yi miki". Halima ta ce"Za ki iya kuwa Zainab? Kar ki wahalar da kanki". Ta ce"Haba wace wahala, ɗakko min kayan, bari na haɗa wuta". Ta fita tana kunna mangal, ita kuma Halima ta tashi ta ɗakko mata kayan wainar, Zainab ta dawo hannunta ɗauke da kofin kunu ta miƙa mata, har da paracitamol ta ce ta sha kafin a kaita asibiti, ta yi mata godiya, ita kuma ta koma ta fara aikinta. Wajan ƙarfe tara Haruna ya tashi daga bacci, turus ya yi ganinta kwance a daidai wannan lokacin, ya fice don shiga banɗaki, sai dai ya tsaya ganin Zainab a bakin murhu tana ta fifita wutar wake da shinkafa, don har an fita da waina, jikinta ne ya ba ta ana kallonta, ta ɗago ta kalle shi, ta yi masa farr da ido, ƙasa-ƙasa ya ce"Ke dai kina son wahalar da kanki, ki yi ta taya matar nan aiki". A hankali ta ƙaraso kusa da shi ta ce"Kai ka tattarata ka kai ta gida ta yi jinya, ka ga mun samu ɗaki kafin ta dawo". Zai yi magana kenan Baaba ta fito daga ɗaki don ta duba jikin Halima, suka waske ya wuce banɗaki, a ransa yana ta tunanin maganar Zainab, domin tabbas shawararta abar dubawa ce, saboda haka yana komawa ɗaki ya tambayi Halima kwanciyar me take yi, ta faɗa masa yanayin jikinta, ya ce"Allah Ya sawaƙe, to ina abun karyawata?" Ta ce"Ban fita ba fa yau kwata-kwata". Ya ce"Kuma don ba ki da lafiya ba zan ci abinci ba kenan?" Takaici ya kamata, tana tabbatarwa kanta lallai Haruna ba miji ba ne, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ji muryarsa ya ce"Daurewa fa za ki yi ki dafa min taliyar nan". "To!" Ta amsa tana tashi zaune, ta huta na sakanni sannan ta fita ta kunna mangal ta ɗora. Tana fita ya kira lambar Zainab, tana ɗagawa ya ce"Na koro ta ta min girki, kar ki taya ta, ni abincin ma ban so kika karɓar mata ba, idan ta ji wahala za ta nemi zuwa gidan da kanta". Zainab ta yi dariya suka kashe wayar, tana leƙen Halima ta gefen labule. Zama ta yi a bakin wutar bayan ta haɗa komai na jollop ta ɗora, ruwan yana tafasa ƙamshin ya daki hancinta, nan take cikinta ya fara rugugi, yawu ya taru a bakinta da gudu ta ƙarasa bakin makwarara ta fara kwara amai babu ƙaƙƙautawa, Zainab ta yi kamar ba ta ji ta ba, haka shi ma Haruna, sai Baaba ce da ta ji abun ya ƙi ƙarewa ta fita tana cewa"Subhallah! Sannu Halima, har da amai?" Halima ta gyaɗa kai a galabaice, Baaba ta miƙa mata buta ta wanke bakinta, ta wanke wurin tana ta yi mata sannu, Halima ta koma ta zauna a wurin girkin, tana buɗewa don ta zubar taliyar wani aman ya sake taso mata, haka ta dinga yi babu ƙaƙƙautawa, wannan karon Baaba cewa ta yi"Zainab je ki ki ƙarasa mata girkin can, ina ga ƙamshin ne yake saka ta aman nan". Zainab ta je kan girkin, Baaba ta yi sallama a ɗakin Zainab tana kiran Haruna, ya fito yana gaishe ta, ta ce"Haruna wannan yarinyar kamata ya yi fa ku tafi asibiti, ka ga duk ƙarfin halinta ta galabaita lokaci ɗaya". Ya ce"To Baaba bari ta shirya sai na kai ta". Ɗaki ta koma ta kwanta, ya kalle ta yana taɓe baki ya yi mata sannu, ta gyaɗa masa kai, Zainab tana gama girkin ta yi sallama a ɗakin, ta ɗauki kula a kwando ta juyo taliyar ta kawo musu, suka faki idon Halima suka kashewa juna ido. Yana cikin cin taliyar yake cewa"Halima asibiti ya kamata na kai ki, ga shi da ɗari biyar kawai na tashi, kin ga kuwa ba ta fi kuɗin adaidaita ba, yanzu ya za a yi?" Ta ce"Babu komai, ai na sha paracitamol". Ya ce"To me zai yi miki? Ba ki ga har da amai ba? Ko ciki ne da ke ma?" Cikin ƙosawa ta ce"Allah masani". Ya ce"To yanzu dai tashi za ki yi, ki lallaɓa ki shirya, ki saka kayanki ko kala uku ne a jaka sai na raka ki gidanku, idan jikin ya yi dama-dama kya dawo". Cikin rashin son hakan ta ce"Gaskiya da ka bar ni a nan ɗin..." "A hakan ba kya iya aikin komai? Daga dafa taliya kin yi amai sau biyu, ina za ki iya wani moruwa? Duk aikace-aikacen gidan waye zai na yi miki?" Hawaye ya zubo mata, ta san gaskiya ya faɗa mata, saboda haka ta ce"To shi kenan mu tafi ɗin". Tana jiri ta ɗakko ƙaramin akwatinta, ta zuba kaya, ta saka hijjabi ta kwanta a kujera tana jiransa, yana gamawa ya ce ta tashi su tafi, sanda suka fito Zainab tana daka yaji, Baaba tana zaune a tsakar gida, Halima ta ƙirƙiri murmushi ta ce"Baaba za mu tafi". Baaba ta ce"Asibitin ne? Ya na ga akwati?" Haruna ya ce"Ai daga can gida zan kai ta, kin ga yanayin jikinta a gidan sai ta fi hutawa". Baaba ta ce"Haba ɗan nan! Irin haka ai babu daɗi yarinya tana fara laulayi ka kwashe ta ka kai gida, ban da abunka ba ga Zainab ba? Komai za ta yi mata, ga ni kuma zan dinga kula da ita, idan zazzaɓin ya sauka ai shikenan ma, ka dai duba". Ya ce"Ai Baaba wannan duk wahalar da ku za a yi, ita ma ta fi son zuwa gidan, ko kwana biyu ne ta yi sai ta dawo, kin san halinta idan tana nan ba za ta huta ba". Baaba ta ce"Ai shi kenan, kuma abincin da Halima?" Halima ta ce"Zainab ta dinga yi, sai ta dinga cire ribarta ta ajiye min uwar kuɗin, har mu ga yanayin jikin". Ta yi mata godiya, Zainab ta raka su har ƙofar gida, tana farin ciki. A ƙofar gidansu ya tsaya ko shiga bai yi ba ya ba ta ɗari biyu ya juya ya tafi, ta shiga da sallama tana jin jiri kamar za ta faɗi, nan ta faɗawa mahaifiyarta halin da ake ciki, Umma ta taɓe baki ta ce"Ke kuma ta ki ƙaddarar kenan Halima, wannan mijin naki sam ba mutum ba ne wallahi, amma babu komai lokaci ne". Ta haɗa mata shayi ta sha da biredi, ta dafa mata ruwa ta yi wanka, ta fita ta siyo mata magunguna ta sha, ta kwanta bacci ya ɗauke ta. Haka Zainab ta gama abinci ta siyar ta ware ribarta, ta yo cefanen wanda za ta yi gobe. Tun kafin dare sun tsara yadda komai zai kasance, saboda haka dukansu babu wanda ya iya yin bacci, ƙarfe ɗaya na dare Baaba ta yi nisa a bacci, Zainab ta tashi ta zare sakata a hankali, ta fito ta tura ɗakin Halima da yake a buɗe babu sakata, dama yana zaune a falo yana jiranta, ya tashi da farinciki ya saka sakata, ya ja ta suka shiga uwar ɗaka, har kan gadon Halima. GIDAN ALI Washegari ƙalau suka tashi da Maryam komai ya wuce, ya ci abinci ya tafi aiki, wajan la'asar Hajiya ta kira shi, take tambayarsa yau zai samu lokacinta? Ali ya ce"Wallahi Hajiya ina wajen aiki ne..." Hajiya ta ce"Haba Aliyyu aikinka ai babu abin da zai tsare maka, idan ka tashi ba sai ka zo ba? Na ji daɗin haɗuwa da kai ne fa, shi yasa ka ga har ina nemanka, dubu goma zan baka wannan karon". Ali ya yi jimm yana jinjina dubu goma, da dubu goman nan fa zai rage aiki, don haka gaskiya ba zai bar wannan damar ta wuce shi ba, ya ce"To zan zo idan an yi sallar magriba, sai dai gaskiya ba zan daɗe ba". Ta yi murmushin jin daɗi ta ce"Babu damuwa, Allah Ya kawo ka lafiya". Yana aiki yana tunani, ga Baby Farha ma ta takura masa sai ya je gidansu, sai kaucewa yake don so yake ya yi sabon ɗinki, idan kuwa yana so da wuri dole ya jajje wurin Hajiyar nan idan ya tattara ya gama buƙatunsa ya watsar da ita daga baya, ana idar da sallar magriba ko gidansu bai shiga ba, ya buga babur ɗinsa ya tafi. A ƙofa ya tsaya ya faɗa mata ya zo, ta fito ta shiga da shi har babur ɗinsa, cike da farin ciki ta buɗe firji ta ba shi lemo me sanyi ya sha, sannan ya ce mata zai yi wanka, ta ce ita ma za ta yi dama, ba dan ya so ba suka yi wankan tare, ta kawo masa kayan ƙwalam yana ci tana kallonsa, sosai yaron ya shiga ranta, ta ce"Aliyyu kana burge ni sosai, kuma ina hango faruwar wasu muhimman lamura a tarayyarmu da kai, ga ka matashi mai jini a jika, a ina kuka haɗu da Reza?" Ya sosa kai ya ce"Hajiya kenan, Reza a ƙasan layinmu take, mun daɗe da ita". Ta ce"Waye kai? Ka ba ni labarinka, me yasa ka zaɓi neman mata a maimakon aure?" Ya ce"Hajiya ai ina da auren, wannan ana yin sa ne saboda nishaɗi kawai". Da mamaki ta ce"Da gaske kai ma kana da auren?" Ya ce"Wallahi ina da mata, yanayi ne kawai ya sa ban daina harkar nan ba". Ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ni ma ina da miji..." Ya zaro ido da mamaki ya ce"Yanzu haka maganar nan da muke yi da auren wani a kanki?" Ta ce"Ƙwarai kuwa, amma ga ni nan ina dai amsa sunan matar aure ne kawai". Ya ce"Amma Hajiya me yasa kika zaɓi wannan rayuwar?" Ta yi murmushin takaici ta ce"Aliyyu Wani Auren ba ya amfanar mutum da komai sai cutarwa, wani auren na jeka-na-yi-ka ne, wani auren sai dai ya kai mutum ga halaka, wani auren ana yinsa ne saboda mugunta da ƙuntatawa, wani auren ana yinsa ne saboda asiri ya rufu, kamar dai nawa auren, ina zaune a gidan nan ne kawai saboda asirina ya rufu, tun ina yarinya a haka rayuwar take, an aura min wanda ba sa'an aurena ba, ya rufe ni a gida saboda mugunta yana can yana yawon ƙasashe da sunan aiki, ko yana nan babu abin da yake iya taɓukawa, girma ya kama shi duk ya gajiya, kuma a hakan mu uku ne matansa, cikinmu babu wacce ta taɓa ko ɓatan wata, rashin haihuwa daga shi ne, ga shi zan tsufa babu ɗa ballantana jika, gani yake tun da ya bar min dukiya ya sallame ni, ya manta ni mai lafiya ce ba kamar shi ba, ina buƙatar abokin rayuwa, shiyasa nake amfani da kuɗin da yake taƙama da shi ina yin abin da ya kasa yi min, Aliyyu ka ga laifina?" Har zuciyarsa ya san ba a kan daidai take ba, hujjarta ta yi rauni, tun da ai akwai hukuma, za ta iya kai shi a raba auren tun kafin abun ya yi nisa, amma dayake ya san ba wa'azi ya zo yi ba, sai ya ce"Gaskiya Hajiya ban ga laifinki ba wallahi, ai wannan shi ne daidai, mace sai da namiji, tun da har ya bar kuɗin ki ji daɗinki kawai, sai ki ta istigfari Allah gafurur rahim ne". Ta yi murmushin jin daɗi ta ce"Na gode sosai Aliyyu". Sun ɗauki tsawon lokaci suna aikata masha'a, shi kansa ya yi mamaki, saboda ya manta rabon da ya yi irin wannan daɗewar da mace, yau kam wasai ya ji shi kamar ya gama juye duk wata damuwarsa ta wannan ɓangaren, wani abu da bai sani ba Hajiya ta faki idonsa ta kashe wayarsa, Maryam har ta gaji da kira tana ji a kashe, sam ƙin ba shi damar tashi Hajiya ta yi, shi ma ya gaji sosai, don haka da taimakon sanyin AC bacci ya yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai ƙarfe biyu na dare. A firgice ya tashi zaune tunowa da inda yake, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi lokacin da ya kalli agogo, ya ɗauki wayarsa yana mamakin yadda aka yi ta mutu, ya kunna gabansa yana faɗuwa, ya sakko daga gadon, ya zura kayansa sannan ya tashi Hajiya. Ta tashi tana mirtsika ido ta ce"Aliyyu ina zuwa? Ka kwana a nan don Allah". Da sauri ya ce"Ina? Ba zai yiwu ba wallahi". Ta tashi zaune tana narkewa kamar yarinya ta ce"Don Allah ka kwana, zan ƙara maka dubu goma". Ya ce"Ba ki san masifar da take tunkaro ni ba ne, wallahi ko a dubu ɗari ba zan kwana a nan ba". Ta tashi ta ɗakko masa dubu ashirin ta ba shi, ta ce"Amma ka san ba za ka keta unguwar nan a babur ba cikin daren nan". Ya ce"Wallahi zan tafi ko a ƙafa ne, iya wuya dai a gidana zan kwana". Hajiya ta ce"Ina zuwa" Ta ɗauki wayarta ta kira wata lamba, ta faɗa masa ya zo gidanta yanzu da sauri, tana sauke wayar ya ce"Waye?" "Ɗan sanda ne". Ta faɗa tana ajiye wayar ta zauna tana dafe kai, don ta tsani a katse mata bacci. Ba ta lura da daskarewar da Aliyyu ya yi ba, sai da ta ji cikin tashin hankali ya ce"Ɗan sanda fa kika ce! Hajiya me na yi miki?" Ta kalle shi ta kwashe da dariya ta ce"Aliyyu kenan!" ANA TA TAMBAYATA WAI WANI AUREN NA KUƊI NE? E NA KUƊI NE, A KAN NAIRA 300 KACAL! 08028966015 [7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS PAGE 6 https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 ALI Sosai ya shiga tashin hankali, kamar zai yi kuka ya ce"Hajiya me na yi miki don Allah za ki saka mini da wannan?" Ta yi dariya ta ce"Ni kuwa ko butulu ce ai ba zan saka maka da sharri ba a yau, ko don faranta min da ka yi, haka kake da tsoro? Idan ka fita yanzu za a iya kama ka da laifin yawon dare, shi yasa zan saka Ɗan sanda ya mayar da kai har gida". Ya sauke ajiyar zuciya duk da haka bai samu nutsuwa ba, Hajiya ta ce"A gaskiya Aliyyu wannan matar taka ta yi dace, ina ma ina da damar yin wani auren! Ai da kai zan aura, don Allah gobe ma ka zo ka ji?" Ya ce"Hajiya kenan, ki bar ni na fara fita daga bala'in da na shiga yau, kafin komai ya biyo baya". Ta ce"Bala'i kamar ya?" Ya ce"Daga baya zan ba ki kabarin wace ce matata". Suka yi shiru, har Ɗan sandan ya kira ta ya ce ya ƙaraso, suka fita tare Ali ya hau bayan babur ɗinsa ya kai shi har ƙofar gida, ƙirjinsa yana ta bugawa ya ɗakko waya ya kira lambar Maryam yana haɗawa da ƙwanƙwasa gidan. Maryam da ba ta daɗe da yin bacci ba ta tashi a firgice jin ƙarar wayarta, tana dubawa ta ga shi ne, ƙwanƙwasa gidan da ake yi ne ya tabbatar mata da dawowarsa, ta duba lokaci ta ga ƙarfe biyu da mintuna, ta yi huci mai zafi zuciyarta tana ƙuna, ta sakko ta buɗe loka ta ɗakko mukullin shago ta shiga falo ta ɗakko tabarma tana buɗe gidan ta watsa masa ta mayar da sakata. "Maryam!" Ya kira sunanta yana buga ƙofar, amma ko waige ba ta yi ba, ta koma ɗakinta, zama ta yi a kan gadon tana tunanin wace rayuwa mijinta yake son faɗawa? Zargi ne kala-kala yake ɗarsuwa a ranta, ciki har da na neman matan, amma ta saka a ranta ko ma mene ne ya zo ƙarshe daga yau, ta share hawayen da ya zubo mata, duk yadda yake buga gidan ba ta sake bi ta kansa ba, ta kwanta da baƙinciki tare da fargabar sabuwar rayuwar da ya ɗakko. Shi kuwa Ali sosai ransa ya ɓaci, don tun da take cewa za ta ba shi tabarma ya kwana a waje bai taɓa zaton za ta iya aikatawa ba, sai ga shi ya ga zahiri, haskawa ya yi ya ɗauki mukullin ya buɗe ƙaramin shagon dake manne da gidan, ya shiga da bisimillah, duk ya yi ƙura don ba a taɓa kwana a cikinsa ba ma, haka ya shimfiɗa tabarma ya zauna, ya yi jugum yana nadamar wannan rayuwar da yake yi, ga shi aurensu ko shekara bai yi ba za su fara samun matsala, ya san gobe Allah ne kaɗai ya san irin bidirin da za su sha da Maryam, sai dai duk rintse ba zai yarda ta tafi gida ba, idan ta je ta faɗi dalili a ka titsiye shi da tambayar inda ya je me zai ce? Da wannan tunanin ya kwanta ya yi matashi da hannunsa, sai dai ya kasa bacci duk da babu sauro, tunani yake yi yanzu ya baro lafiyayyiyar katifa a makeke gado cikin AC, cikin abin da bai fi minti talatin ba rayuwarsa ta canza ga shi kwance a tabarma cikin ɗaki mai ƙura. Tashi zaune ya yi, ya lumshe ido yana tuna duk abubuwan da suka wakana a daren na yau, tsakaninsa da Hajiyar da ko sunanta ba ta faɗa masa ba, yana buƙatar kuɗi kuma ya ga alamar zai samu alkhairi sosai ta wajanta, muddin ya kwantar da kai, saboda haka dole a yi ɗaya cikin biyu, ko dai ya nunawa Maryam dole ta yarda da cewar ya samu sabon aikin dare na gadi a wani kamfani ko kuma ita Hajiyar ta yarda ya dinga zuwar mata da rana, sai ya dinga tashi daga aikinsa da wuri, idan ya tara abin da yake nema sai ya rabu da ita, da wannan tunanin zuciyarsa ta nutsu, ya ɗakko waya ya kira ta don ya sake yi mata godiyar kuɗin, sai dai ba ta ɗauka ba, ya kunna data yana duba saƙonni, sai wajen uku da rabi ya yi bacci. Da safe ƙarfe shida ya farka, ya fito ya ci gaba da buga gidan, ta ƙi buɗewa, ya kira wayarta sai ta ɗauka, ya ce"Maryam ki buɗe min alwala zan yi". Ta ƙashe wayar, ta zo ta buɗe, ya shigo a sanyaye ta kalle shi ta kau da kai, ya yi alwala ya yi sallah, yana zaune a falo ya ga ta ɗora tukunya, sannan ta koma ɗakin gado, ya tashi ya bi ta, yana shiga ya ga tana birkito kayan cikin sif tana watso su kan gado, ya ƙarasa ya tsaya a gabanta ya ce"Maryam mene ne haka? Wai me yasa kike sha'awar yin yaji ne? Ko ba ki san abun kunya ba ne? Yanzu ko cewa na yi ki tafi gida sai ki tafi ɗin? Sai ka ce kin manta da muna da magauta masu jiran su ga ranar da za ki yi nadamar aurena? Haba Maryam, komai fa nake yi dominki ne, na san tun farko na yi kuskure da na ɓoye miki abin da ya kamata a ce kin sani". Ganin ta ba da ni nutsuwarta, ya sa na zaunar da ita, ni ma na zauna na ci gaba"Maryam tsakani da Allah wani aiki ne na samu, na gadi da za mu dinga yi ni da a Hamza a wani kamfani, mu ne masu night duty, to shi ne dalilin kai wa daren da na yi jiya, ba a tashi ba ma na gudo saboda na san ba za ki samu nutsuwa ba, tun da ba ki san inda nake ba". Har yanzu ba ta ce komai ba. Ya ce"Gani na yi kuɗin da za su dinga biya da kauri shi yasa, kin ga fa kullum dubu uku, kin ga ai za mu toshe wani wajen ko?" Sosai ta yarda da shi, amma ba ta jin za ta yarda da wannan aikin daren, ta kalle shi ta ce"Yanzu saboda dubu uku za ka dinga kwana a waje kullum? Da rana kuma ka tafi wani aikin? Shi kenan ba ka da lokacin hutu? Shi baccin da wane lokaci za ka dinga yi? Tara shi za ka yi ya zame maka matsalar da sai ka sha maganin da ya ninka dubu uku sau goma? Ina ta faɗa maka zafin nema ba ya kawo samu, saboda haka ka kwantar da hankalinka, indai ni ce kar ka damu, ba ga shi ina sana'ata ba? Idan nauyin gidan ne ya maka yawa zama ya kamata mu yi mu tsara komai na san ta inda zan rage maka nauyi, ko magi da kayan miya ne, ba wai ka ɗauki wannan matakin ba". Ya ji daɗin yadda ta yarda da shi sosai, ya ce"Na gode Allah da ya ba ni mace ta gari, Maryam Allah Ya biya ki da gidan aljanna, yanzu dai aikin ne ba kya so ko?" Ta ce"E gaskiya ban yarda da shi ba". Ya ce"Dama shi komai ɗan maslaha ne, in sha Allah na haƙura, sannan Maryam ni ban amince ki taimake ni da abin da yake nauyina ba, zan dinga yi miki komai daidai ƙarfina, fatana dai mu samu zaman lafiya da farinciki mai ɗorewa". Tana murmushi ta ce"Allah Ya dawwamar mana". Ya ce"Yanzu dai tun da komai ya wuce shi kenan babu sauran rigima ko?" Ta ce"Da saura fa". Ya ce"To me kuma ya faru?" Ta ce"A gaskiya wannan majalisar taku ba na sonta kwata-kwata, kawai ana idar da sallar magriba ka dawo gida mu zauna ina buƙatar ganinka, mu yi fira na yi maka kwalliya kuma ka samu isasshen bacci". Ya yi dariya ya ce"An gama ranki ya daɗe, in sha Allah yau ana magriba za ki gan ni". Daga haka ta fita ta sauke shayinta, suka karya ransu fes, ya fita aiki cikin kwanciyar hankali. GIDAN SADIQ Da Sadiq ya dawo ta yi masa bayanin duk yadda komai zai kasance da ƴar aikinsu, ya amince ba don ransa yana so ba, sai dai a zauna lafiya kawai. Washegari da safe Yusra ta tafi aiki, don ta riga yaran fita a gida ta bar su da Sadiq, wajan ƙarfe takwas yana shago sai ga yarinya ta shigo, ta gaishe shi, ya yi zaton ma wani abu za ta siya, ganin ta yi shiru tana sunkuyar da kai ya ce"Me kike so?" Ta ce"Mukulli na zo karɓa, ni ce Kursum, sabuwar mai aikinku". "Ok" Ya faɗa yana kallon yanayinta, sannan ya ɗakko ya ba ta, ta duƙa ta karɓa ta ce"Na gode, sai anjima". Ta fice. Tana shiga gidan ta cire hijjabi ta yi gefe da shi, tana ƙarewa ko'ina kallo, mukullan ta fara gwadawa tana buɗe ɗakunan, sai ta lura babu na bedroom ɗin Yusra, ta taɓe baki ta shiga kitchen ta yi wanke-wanke, ta fito ta share ko'ina ta goge, ta share tsakar gidan har da wanke kayan su Afna duka, sannan ta ɗora girki, a cikin jakarta ta fito da leda mai ɗauke da magi, curry kala biyu da niƙaƙƙen nama soyayye, ta tsara haɗalliyar jollop, sannan ta kunna ɗayan gas ɗin ta ɗora wani girkin, ta saka magi da curryn da ta tarar a gidan, kafin ya dahu ta yi wanka ta ci kwalliyarya ta canza kaya, don da wasu kayan ta taho, tana gamawa ta zuba ta ci ta ƙoshi, ta juye ɗayar tukunyar wacce ta dafa kaɗan don Yusra, ta zuba na Sadiq ta rufe gidan ta tafi kai masa, a lokacin sha biyu saura kwata, tana zuwa ta ga ƙofar shagon a rufe, ta jira har shiru bai dawo ba, ganin har sha biyu ta yi ya sa ta koma gida saboda kar yaran su dawo, babu jimawa kuwa suka dawo, da saurinta ta tare su ta rungume su, suka tsaya suna kallon juna, duk da Momynsu ta faɗa musu ita za su dinga tararwa a gidan, kuma sun ganta ranar da ta zo. Hannunsu ta ja suka ƙarasa ɗaki, tana cewa "Sannunku ƙawayena kun gaji ko?" Suka gyaɗa mata kai. Ta cire musu unifom, ta yi musu wanka suna ta bin ta da ido, ta saka musu kaya marasa nauyi, sannan ta zubo musu abinci a faranti ɗaya, ta zauna tana ba su a baki tana yi musu murmushi har suka ƙoshi, sun ci sosai, saboda canjin test ɗin abinci da suka samu, ba irin wanda Yusra ta saba dafawa ba, ta ba su ruwa suka sha, sannan ta ɗakko jakarsu ta taya su home work, suna gamawa ta saka musu unifom ɗin islamiyya ta ɗakko alawowi ta ba su, ta zauna tana musu tatsuniya, har lokacin makaranta ya yi, da yake babu nida da yaran maƙota suke tafiya, ta ce daga yau ita za ta dinga raka su, sai da ta sake gyara fuskarta sannan ta ɗauki abincin babansu suka tafi, ta kai su makarantar ta ƙarasa shagon, wannan karon a buɗe yake, ta tsaya a gefe har mutum biyu da suke ciki suka gama, sannan ta ƙarasa da murmushi ta gaishe shi, ya amsa babu yabo babu fallasa, ta miƙa masa abincin ta ce"Ga shi, ka yi haƙuri na kawo a makare, tun kafin sha biyu na kawo maka, sai na tarar shagon a rufe, na jira wajan minti goma sha biyar sannan na koma saboda su Afna kar su dawo babu kowa". "Ok, na je kasuwa ne" Ya faɗa bayan ya gama jinta. Har ta juya ta tafi ta dawo ta ce"Kenan kullum daidai wancen lokacin kana kasuwa?" Ya ce"Ba kullum ba". Ta ce"Me zai hana ka ba ni lambarka, idan zan zo sai na dinga tambayarka ko kana nan, ko kuma ranar da ba ka nan ka kira ni ka faɗa min ko?" Ya ɗan yi jimm, sai kuma ya ga tana da gaskiya, hakan zai fi mata sauƙi, ya miƙa mata wayarsa ta saka lambar, tana ce masa"Kursum, na san ka manta sunan" Ta ƙarasa da shegen murmushi. Tana fita ya yi saving lambar, sannan ya ɗakko abincin ya fara ci, cokali ɗaya ya yi, ya ji girkinta ya bambanta da na Yusra, ɗanɗanon ba ɗaya ba ne, sai ya bar shi a kowa da irin hannunsa, amma abincin ya yi masa daɗi, ya cinye tass ya sha ruwa. Kursum ba ta jima da komawa ba Yusra ta dawo, dama ta wanke fuskarta kafin ta dawo, kuma ta ƙara wanke-wanke ta gyara gidan tsaf har da turaren wuta, Yusra ta ji daɗin yadda ta tarar da gidanta, a ranar farko har ta fara jin daɗin ɗaukar ƴar aiki, yanzu da tuni yadda ta dawo a gajiyen nan aikin gida za ta hau da girki, yanzu kuwa Kursum na tafiya abinci ta zubo ta ci, ta yi wanka ta kwanta ta huta, sai la'asar ta tashi don tafiya kemis. A shagon shi ta tsaya ta shiga da sallama murmushi ɗauke a fuskarta, ya yi mata murmushin shi ma yana amsawa "Kin dawo?" Ya tambaye ta. Ta ce"Ga ni kuwa, ta kawo maka abinci ko?" Ya gyaɗa mata kai. Ta ce"Na ga alamar za mu shirya da yarinyar, ba ta da son jiki, har da kayan yara ta wanke, gida fess". 'Kuma ta iya girki' Ya faɗa a zuciyarsa. A fili kuma ya ce"Madallah! Kemis za ki je?" Ta ce"E, zan ɗan leƙa, Nura yana can, da wuri ma zan dawo na yi maka tuwo". "To na gode, sai na dawo" Ya faɗa yana ta kallonta, har ta tafi. Ana kiran sallar magriba ta koma gida sai da ta ɗakko yaran a maƙota suka shiga tare, ta ɗora tuwo ta yi alwala suna idar da sallah suka fara bata labarin Anti Kursum, kamar yadda ta ce musu sunanta hakan, ta ji daɗi sosai da yaran suka saki jiki da Kursum ɗin, har ta kira Sumayya ta ba ta labari ta sake yi mata godiya sosai, Sumayya ta ce "Babu komai, ai yi wa kai ne" GIDAN HARUNA Sosai Haruna ya yi mamakin yadda Zainab ta ƙware, ashe karuwar gida ce zaune, duk da babu wani gyara a jikinta amma salonta ya gigita shi, da ƙyar ya bari ta koma ɗakinsu, don roƙonta ya dinga yi ta kwana a nan ɗin, ta ce ba zai yiwu ba, Baaba tana farkawa fitsarin dare, haka ya kwana ransa fess shi bai ƙi Halima ta yi wata ɗaya a gida ba ma. Washegari da safe Halima ta kira shi suka gaisa sai ya ji bai kyauta ba, don tun da ya kai ta gidan bai kira ta ba, ya ce"Ki yi haƙuri Halima wayata ce babu kati, shi yasa ban kira ki ba, ya jikin naki?". Ta ce"Babu komai, jiki Alhamdulillah, yanzu za mu je asibiti da Umma". Ya ce"To Allah Ya ƙara afuwa, da daddare zan zo, Allah Ya sa dai na samu abin da zan siya miki wani abun". Ta ce"Amin, idan ba ka samu ba ma ka zo, zuwan naka ya fi muhimmanci fiye da abin da za ka kawo, ka ga idan ba ka zo ba Umma ba za ta ji daɗi ba". Ya ce"Zan zo in sha Allah! Na gode Halima Allah Ya ƙara miki lafiya, gaskiya zan yi kewarki kafin ki dawo". Ta yi murmushi ta ce"In sha Allah ba zan fi kwana uku ba ai". Gabansa ya faɗi, shi da yake fatan ta yi wata ɗaya sai ga shi tana zancen kwana uku? Ya ce"Haba Halima lafiyarki tana da muhimmanci a gare ni, saboda haka ki zauna ki warware sosai, babu komai zan jure kewarki". Ta ce"To, sai dai yadda ta yiwu". Da daddare da ya dawo daga kasuwa, ya sayi lemo, kankana, madara, milo ƴan saches, suga biredi da maltina ya haɗa da dubu biyu ya kai mata, bayan sun gaisa ta ce"Ga shi ba ni da lambar Zainab ballantana na ji ko tana fita a abincin nata?" Cikin suɓutar baki ya ce"Ai ina da lambarta". Da mamaki ta ce"Lambar Zainab ɗin? Yaushe ka karɓa?" Sai yanzu ya san kwaɓar da ya yi, nan take ya fara in'inar da bai san yana da ita ba. LITTAFIN WANI AUREN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 300 KACAL! 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL [7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS PAGE 7 Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Ya ce"Na yi zaton Salma kika ce ƙanwarki, ban ji sosai ba". Ba ta kawo komai ba a ranta, suka yi sallama ya tafi. A ranar ma haka Zainab ta je ɗakinsa suka ƙara haɗuwa. Sanda ta kwana uku a gida Baaba ta ce masa ya yi musu kwatance za su je gidan, sai ya kwatanta musu ya kuma ba su lambarta, suka je suka duba ta, Baaba ce take cewa Umman Halima"Tun da jikin nata da sauƙi ai dama komawa ta yi, kin ga Zainab babu abin da ba za ta yi mata ba, ni kuma zan dinga saka ido akanta". Umma ta ce"Gaskiya ne, mun gode Baaba, to in sha Allah ko gobe sai ta koma, ai jikin nata da sauƙi kam, aman ma ya tsaya". Sun ɗan jima suna fira sannan suka tafi, takaici kamar ya kashe Zainab ganin Baaba ta dage sai Halima ta dawo sai kace ita take aurenta, suna hanya ta ce"Wai ni Baaba me yasa kika damu sai ta koma? Ko mijinta bai damu ba sai ke?" Baaba ta ce"Kar ki ishe ni da shirmen banza da na wofi, shi mijin nata ne ya faɗa miki bai damu ba?" Daga haka aka yi shiru da zancen, har suka ƙarasa gida Zainab ranta a ɓace. Ranar ce masa ta yi ba za ta je ɗakinsa ba ma, tun da har ya yarda Halima ta dawo bai damu da ita ba, gara ta yi zamanta, ya dinga rarrashinta ta ƙi sauraronsa. GIDAN ALI Sai da ya yi kwana uku bai je gidan Hajiya ba, duk yadda take kiransa kuwa, saboda ba ya so su sake samun matsala da Maryam kwana kusa, yanzu ana yin sallar magriba yake dawowa gida, kwana uku bai yi zaman majalisarsu ba, sai dai a ganin Maryam an gudu ne ba a tsira ba, tun da kullum sai Hamza ya biyo shi gidan, su zauna a ƙofar gida sai su kai ƙarfe tara, ganin an jera kwana uku a haka ya sa ta fara yi masa ƙorafi, ta ce gaskiya Hamza ya daina zuwa yana hanata fira da mijinta, Ali ya ce shi dai mutum ba zai zo wurinsa ba ya kore shi, watarana Hamza ya zo, Maryam ta tashi ta tare hanya tana haɗe gira, da mamaki Ali ya ce"Maryam mene ne hakan? Ba ni hanya don Allah" Ta ce"Babu inda za ka fita, ka faɗa masa kana buƙatar ganawa da matarka shi ma ya tafi wurin tasa matar". Ali ya ce"To ai shi yanzi ya saki matarsa, shiyasa idan ya koma gida da wuri sai daren ya yi masa tsayi, kuma kin ga nine dai abokin, dole wurina zai zo, na ga nan a ƙofar gida ne kina leƙowa ma za ki ganmu". Ta ce"Idan na ganku zan jiyo irin huɗubar da yake yi maka ne? Wato ya saki matarsa kai ma yana yi maka huɗubar ka saki taka ku zama ɗaya ko?" Ali ya ce"Subhanallah! Haba Maryam wannan wace irin magana ce?" Ta ce"To ni dai ban amince da wannan sabuwar majalisar ba, saboda haka ka faɗa masa ya daina zuwa ba ka so!". Ali ya ce"Wallahi ba zan iya korar shi ba". Ta ce"To wannan abokin naka ya zama kishiyata, saboda haka daga yau ka fara raba mana kwana, ranar kwanana ana magriba ka dawo gida, ranar kwanan shi ana magriba za ka dawo ka tarar da tabarma a ƙofar gida, don ba zan iya ba!". Cikin takaici Ali ya ce"Wai me yasa kike haka ne? Gabaɗaya kin kanainaye ni, sai ka ce ke ce mijin, na faɗa miki shi kaɗai ne a gidan shi ya saki..." "Ya je ya hau sallaya ya fuskanci alƙibla!" Ta katse shi har da ɗaga murya. Ya juya zai fita, ta ruƙo rigarsa ta dawo da shi, ya ce"Maryam wai mene haka?" Ta ce"Da gaske fa nake wallahi, ka bari ni na je na same shi na faɗa masa ina buƙatar mijina a kusa da ni". Ganin ta shiga ta ɗaki ta ɗakko hijjabi Ali ya ce"Bari na je na faɗa masa". Ya fita, bai jima ba ya dawo yana ɓata rai, har lokacin tana tsaye da hijjabin a hannu, ya ce"To ga ni sai ki kwaɗa ki cinye. Ta yi dariya ta ce"Ni da ana kwaɗon ma ai da tuni na cinyeka na huta da matsalolin da kake tara mini". Daga haka suka shiga ɗaki, har ta kunna kallo ya kashe yana cewa"Wucewa za ki yi mu je mu kwanta, ai tun da kin hana ni fita dole ki rage mini daren". Nan take fara'arta ta ɗauke, ta ce"Ni fa tun rana nake jin kasala da ciwon kai, kitso ma yau mutum ɗaya na yi wa". Ya taɓe baki ya ce"Ai wallahi ko karkarwar zazzaɓi kike sai kin wuce mun tafi ɗaki, ai tun da kika kafa mini doka na yi miki sam'u wa ɗa'a ni ma dole ki bi tawa doka, ni wannan dokar ma ai gana ta kai ni gobarar Titi a Jos, babu zancen cewa kin fara bacci, idan da rabo ma sai ki ga cikin satin nan Allah Ya kawo mana babban rabo, kya samu ɗan tayin fira nan da wata tara ko?" Ko kallonsa ba ta yi ba, ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, fargaba duk ta addabe ta, sai ta ji da ta sani ma ta bar shi da Hamzan, haka dai ta miƙa kai kamar ta yi kuka don takaici. Kwana uku suna yin haka, Maryam gabaɗaya dauriyarta ta ƙare, saboda haka ta fara ƙaryar rashin lafiya, kafin ya dawo sai ta shige bargo ta ce zazzaɓi take yi. Ana haka ne kuma Hajiya ta dame shi da kira kan ya kamata ya zo ko awa ɗaya ne, to shi ma ya yi kewarta, kawai yana dannewa ne ganin yanzu yana yi wa Maryam fin ƙarfi, to da ya ga ta narke da zazzaɓin da ya san na ƙarya ne sai ya ƙyale ta, ya yanke shawarar zai je gidan Hajiyar yau. Yana idar da sallar magriba ya kira Hajiya ya faɗa mata ga shi nan zuwa, ya kama hanya ya tafi, yau ma da kanta ta shigar da shi, kafin su ƙarasa ɗaki yake ƙara kallon gidan, ya ce"Hajiya wai duk girman gidan nan babu mai gadi ne?" Ta ce"Akwai mai gadi, aikensa nake yi idan zan yi baƙo". Ya ce"Kenan dai Hajiya akwai wasu baƙin bayan ni". Ta ruƙo hannunsa a lokacin da suke ƙarasawa ta ce"Wallahi tun ranar da ka fara zuwa har yau na kasa sake kula wani, kai na musamman ne Aliyyu, ni fa da za ka dawo gidan nan da zama gabaɗaya wallahi zan so haka, kana ɗaki kawai a cikin AC, ka zaɓi abin da za a dafa maka ka ci ka kwanta, sannan kullum dubu goma". Ya yi ƴar dariya ya ce"Kin ga kuwa da har ƙiba fa sai na yi". Hajiya ta ce"A to! Ka dai duba wannan damar". Ya sosa kai ya ce"Ai Hajiya matata nake tunani, kin san fa amarya ce ko haihuwar fari ba ta yi ba, kuma wallahi tsaye take a kaina, tana lura da duk wani motsina, shi yasa amma da ni ma zan so hakan wallahi". Hajiya ta ce"To kai kuwa Aliyyu ya aka yi ka yi sake matarka take juya ka har haka? To me zai hana ka ce mata ka samu aiki a wani garin, sai ka zo mu yi zamanmu, duk kwana biyu ka dinga tura mata kuɗi ka kashe bakinta, ko ba zai yiwu ba?" Aliyyu ya ce"Kuma fa kin kawo shawara Hajiya, zan yi tunani, ke zai yiwu ma in sha Allah!". Ta ce"Ko kai fa, na gode, sosai nake sonka Aliyyu, ji nake kamar na kashe auren nan na aureka wallahi". Ya yi murmushi ya ce"Habawa Hajiya wane kare da ɗaukar gara? Wani kayan ai sai amale". Daga haka ta kawo masa abinci ya ci, ya yi wanka, ya fara abin da ya kawo shi, ƙarfe tara ya baro gidan, yana ta sauri saboda Maryam, a hanya ya tsaya ya kira ta, tana ɗagawa ya ce"Maryam ki yi haƙuri ga ni nan zuwa". Ba ta ce komai ba ta kashe, sai da ya tsaya a hanya ya siya mata kwakwa da dabino sannan ya ƙarasa gidan. Yana zuwa ya ganta fuskar nan kicin-kicin. Ya yi murmushi ya ce"Hajiya Maryam kenan, uwargidana amaryata, sarautar mata daga ke babu ƙari..." Ta ɗaga masa hannu ta ce"Don Allah dakata, ya isa haka, na san dai duk siyan baki ne kake yi, babu komai Ali duk yadda ka tsara rayuwarka ka je ka yi ta yi, ni dai Allah Ya sani na yi iya ƙoƙarina don na ga na kula da kai, tun da kana ganin kamar takura ne shi kenan, ka je ka yi". Ya zauna, ya janyo ta jikinsa, yana cewa"Haba Love, wallahi ba takura ba ne ba, na sani ƙauna ce, kuma ina jin daɗin yadda kike kulawa da ni ɗin wallahi, yanayin aiki ne kawai, ga kwakwa na kawo miki, na san za ta wanke laifina ai ko?" A zahiri shi take kallo, amma sam ba ta gane inda maganganunsa suka dosa, ta yi nisa a duniyar tunanin da zuciyarta ta ɗarsa mata, dalilin kusancin da suka samu, sakamakon zamanta a cinyarsa, wani kalar ƙamshi ta ji na wata shegiyar humra mai daɗin ƙamshi, kuma ta san Ali idan zai fita da safen nan ba ya wani fesa turare ma, ko ma yau ya fesa ai ba su da irin wannan turaren, kuma ma fa wannan humra ce, kamar ta yi masa magana, sai ta bar shi a kan za ta yi bincike kafin ta tuhume shi. GIDAN SADIQ Rayuwar gidan Sadiq ta samu ci gaba a nasu ganin shi da Yusra, yanzu hankalinta ya kwanta sosai, tsakaninta da Kursum sai godiya da fatan alkhairi, idan tana aikin kwana ko fargabar ta bar mijinta da wata a gida ba ta yi, domin ta yarda da su, su biyun, yayinda Kursum matakan da ta tanada don shayar da Yusra maɗaci suke ta tafiya hawa-hawa. A yanzu dai ta riga da ta gama da Sadiq da yaransa wajen girki, ya yarda a kan Kursum ta fi Yusra iya girki, don sosai Sumayya ta kashe kuɗin wurin siya mata kayan ɗanɗanon girki, wanda Yusra duk ba ta san wainar da ake toyawa ba, duk da ƴaƴanta sun sha faɗa mata girkin Anti Kursum yana da daɗi sosai, ita ba ta kawo komai ba, tun da ba ta ji wani bambanci da nata ba. Abu ɗaya ta sani Kursum tana taimakonta. A ɓangaren Sadiq tsakaninsa da Kursum babu yabo, babu fallasa, kullum za su gaisa tana murmushin da ya gane ɗabi'arta ne, sai dai yadda ba ta gajiya da kwalliya abun yana burge shi, saboda shi mutum ne mai son kwalliya sosai, duk da bai taɓa faɗawa Yusra ba tun da ya lura ita ba ta da ra'ayin wannan zane-zanen, sai kuma tsafta da take da ita sosai abun yake burge shi, uwa-uba kuma yadda take kula masa da ƴaƴa, abun sha'awa, sun shaƙu da yaran sosai ba su da zance sai na Anti Kursum ɗinsu, saboda haka shi ma yanzu aikin Yusra ba sosai yake damun shi ba. Sai dai wani baƙon lamari da yake faruwa da shi, wanda tun yana damunsa yanzu ya zame masa jiki, ta wani ɓangaren ma abun ɗebe kewa ne a gare shi. Wata yarinya ce take turo masa massages kala-kala, na kulawa, tun yana sharewa har ta kai ya fara mayar da hankalinsa a kan saƙonninta, duk ranar da ba ta turo ba sai ya yi ta tunanin dalili, akwai lokacin da ta yi kwana uku ba ta tura masa saƙo ba, duk ya kasa sukuni, motsi kaɗan ya duba wayarsa, ranar na ukn sai ya kirata a waya, sosai ta nuna farincikinta, kuma ta faɗa masa ba ta da lafiya ne, jiya aka sallamo ta daga asibiti, kamar wasa tun daga ranar suka fara yin waya da yarinyar da ta ce sunanta Ummu, ta iya kalamai masu tsayawa a rai, sosai yake mamakin kansa, don bayan Yusra bai yi tunanin zai sake iya soyayya da wata ba, sai ga shi cikin sauƙi ya faɗa soyayya da wacce bai santa ba, kuma ko hotonta za ta turo masa sai dai ta rufe fuskarta, to shi ma a yanzu bai shiryawa wani auren ba, shi yasa ya bar ta a je a hakan, amma yarinyar ta yi masa har zuciyarsa, sosai suke waya musamman ranar da Yusra take aikin kwana. LITTAFIN WANI AUREN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 300 KACAL! 2526907490 Aisha Abdulrazaƙ Zenith bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015 KO KATIN Airtel NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL. [7/30, 5:34 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN* BY SADIYA ABDULRAZAƘ FIRST CLASS WRITERS PAGE 8 Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 GIDAN HARUNA Ƙiri-ƙiri Haruna ya ƙi cewa Halima ta dawo, duk da ta faɗa masa jikin da sauƙi sosai, ita kuma mahaifiyarta tausayinta take ji, shi yasa ta ƙyale ta ta dinga hutawa, Halima har mamaki take yi yadda kullum idan zai zo ganinta sai ya taho da leda sannan ya ba ta kuɗin kashewa, sosai hakan ya yi mata daɗi, ta fara tunanin mijinta ya fara samu sosai a kasuwa, amma ta saka a ranta duk da haka ba za ta dakatar da sana'arta ba, za ta ci gaba da yi don a taru a rufawa juna asiri. Bayan kwana uku suka shirya da Zainab, har ma suka shirya yau ma za su haɗu a ɗakinsa, don haka da daddare ƙarfe ɗaya Zainab ta tashi saɗaf-saɗaf, ta shige ɗakinsa, ta saka sakata, suka fara sha'aninsu, bai fi minti goma da shigarta ba Baaba ta tashi don yin fitsari, ta ji ɗakin a buɗe duk da ta san da kanta ta saka sakata, kuma Zainab ba ta tashi fitsarin dare, sai ta yi tunanin ko yau ta tashi ne tana banɗaki, ganin butarsu a yadda ta ajiyeta ma bai sa ta yi wani tunanin ba, ta ɗauka ta je ƙofar banɗaki ta tsaya tana jiran fitowarta, jin shiru ba ta da niyyar fitowa ya sa ta cewa"Da mutum?" Ta ji shiru, ta bubbuga ƙofar nan ma shiru, sai ta leƙa a hankali tana haskawa ta ga wayam babu kowa, ƙirjinta ya bada sautin rass ta fara tunanin ina Zainab za ta tafi cikin daren nan? Ta shiga ta yi fitsarinta, ta yi zaure ta ga ƙofar gida a rufe tsaf, gabanta sai faɗuwa yake yi, ta dawo ta shiga ɗaki wai ta ƙara dubawa ko idonta ne ya nuna mata Zainab ba ta nan, amma ganin ko bargo babu a kan shimfiɗar ballantana a yi tunanin ta lafe a ciki ya sa ta saddaƙar wani abu ya samu jikarta, tuni ta fara hawaye, zuciyarta tana bugawa. Kamar ta tashi Haruna ta faɗa masa halin da take ciki, sai kuma ta fasa, don tana tunanin samari ne suka hure mata kunne ta gudu bariki, sai ta miƙe zumbur ta shiga ɗaki ta duba kayan sakawar Zainab, ta gansu tsaf babu alamar an ɗauki wani abun, har hijjabin da ta yi sallar isha'i ma yana nan a inda ta bar shi, Baaba ta dawo tsakar gida ta zauna a kujera tana matsar ƙwalla. A firgice ta ɗago jin an buɗe ɗakin Halima, ta miƙe tsaye don ta samu damar da za ta faɗawa Haruna, ya je ya dubo ko ba ta yi nisa ba ya faffalla mata mari ya dawo da ita, sai dai ta yi turus ganin mace ce ta fito, cikin sakan ɗaya ta yi tunanin ko Halima ta dawo tana bacci? Amma ganin wacce ta fito ɗin ta doshi ɗakinta gadan-gadan ya sa ta yi saurin kunna fitarta hannunta na rawa. A firgice Zainab ta juyo ganin an haskata, ƙirjinta ya buga da ƙarfi ganin Baaba ce a tsaye. Baaba kuwa sakin fitilar ta yi, ta dafe ƙirji, cikin razani ta ce"Zainab! Me kika yi a ɗakin Halima?" Cikin inda-inda ta ce"Caji na saka fa Baaba". Baaba ta ce"Bantan ubanki ke da cajin" Sai ta ƙaraso ta rufe ta da duka, kafin ta saketa ta fashe da kuka, ta shige ɗaki. Ita ma Zainab ɗin shigowa ta yi, ta zauna rakuɓe a gefe tana hawayen nadama, can Baaba ta ce"Zainab yanzu shahararki a iskanci ta kai har da na gida? Har cikin gida, da mijin maƙociyarmu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!". Zainab tana kuka ta ce"Ki yi haƙuri Baaba, wallahi iya yau ne kawai, kuma mun yi na farko mun yi na ƙarshe". Baaba ta ce"Amma wannan yaron an yi ɗan banza, Allah sarki Halima ashe ba ta yi dacen miji ba, kaico! Da halinku ke da shi ɗin, sai Allah Ya sakawa Halima". Sai kuma ta tashi, ta je ta fara ƙwanƙwasa ɗakin Haruna, don Zainab tana fita ya saka sakata, ya yi lakur saboda yana jiyo tattaunawarsu sama-sama, gabansa ya faɗi da ƙarfi da ya ji ana buga ƙofar, kamar kar ya buɗe sai kuma ya daure zuciyarsa ya buɗe, cikin karaya ya ce"Baaba ce da daren nan?" Baaba ta ce"Haruna ka ji tsoron Allah! Ka sani akwai mutuwa, akwai hisabi, sannan zina bashi ce, kuma duk wanda yake cin amanar aure ba zai yi kyakkyawan ƙarshe ba in sha Allah!". Cikin ƙarfin hali ya ce"Mene ne ya faru ne Baaba?" A fusace ta ce"Uwarka ce ta faru da ubanka! Me ya kawo Zainab ɗakinka da daren nan?" Ya ce"Wai Zainab? Wallahi zuwa ta yi, ta ce min wayarta babu kuɗi, na kira mata Halima za ta tambaye ta wani abu, akan sana'ar da take taya ta". Baaba ta ce"Ita kuma ta ce caji ta saka, babu komai Haruna duniya ce ta fi bagaruwa iya jima! Idan ni da Halima muna da hakki akan cutarwar da kuke yi mana Allah Ya saka mana tun a duniya". Daga haka ta shige ɗakinta, ta bar shi riƙe da ƙofa, jiki a mace kamar kazar da ta taka wuƙa ya dawo ya zauna a kujera yana dafe kansa, ya jima a haka sannan ya tashi ya saka sakata ya koma ya kwanta. Washegari safe Zainab ta tashi ta shiga harkokin wainarta kamar ba a yi komai ba, saɓanin Haruna da ya kasa fitowa sai da suka yi chart ta faɗa masa babu komai ya maze kawai, kuma haɗuwa yanzu ma suka fara, ta samo musu wata dabara, wannan ne ya ba shi ƙwarin gwiwa ya saki jikinsa, har ya fice daga gidan. Ita kuwa Baaba ƙarfe goma na safe ta shirya ta tafi gidan su Halima, suka gaisa ta cewa babarta ta zo tafiya da Halima ne, Umma tana murmushi ta ce"Ai Baaba gani na yi har yanzu bai ce ta koma ba, shi yasa na barta ta ƙara hutawa". Baaba ta ce"Haba ƴar nan, ku kuma ai ya kamata ku gane kara ce yake yi, sai ka ce laulayin kanta ne farau? Kuma fa ƴata Halima ai jaruma ce, ni dai yau da ita zan koma gidan nan Allah kuwa". Umma ta ce"To kin ji dai Halima, sai ki tashi ki shirya, bari na je kasuwa na yi miki ƴar siyayya, idan na dawo sai ki bi Baaba ku tafi, ka samu mai kula da lamarinka ma ai abun murna ne, mun gode Baaba". Bayan ta tafi kasuwa suka dinga fira da Halima tana ta jaddada mata ta riƙe mijinta, ta dinga saka ido sosai a kan shi saboda ƴan matan zamani ba su da kirki, a haka har Umma ta dawo, Baaba ta saka ta a gaba suka koma. Ita kanta Baaba sai da ta yi mamakin yadda Zainab ta nuna ko a jikinta, ita ta gyara mata ɗakinta fess tana ta yi mata sannu. Haruna bai san da dawowarta ba, da yake akwai mukulli a hannunta, sai dawowa ya yi ya tarar da ita, ya ɗan ji daɗi saboda dama yana shakkar dabarar Zainab duk da shi ma ya san ba abu ba ne mai sauƙi yadda ya saba da ita su rabu lokaci ɗaya, amma tun da Baaba ta san komai ya zama dole su canza taku idan ma za a kuma ɗin, da wannan ya saki jiki da Halima har suka taɓa fira kafin ta yi bacci. GIDAN ALI A cikin satin Ali ya zowa da Maryam sabon labari, na cewar wani kamfani a can Enugu zai ɗauke su aiki na sati ɗaya, kullum dubu goma, kuma su ne za su yi musu kuɗin mota,masauki da abinci bakiɗaya, ganin ta ɓata rai ya sa shi tausasa murya ya ce"Maryam don Allah idan na zo mana da abun alkhairi ki daina gwasale ni, ki dinga yin fatan alkhairi kawai, kwana bakwai fa kacal za mu yi, dubu saba'in ina laifi? Ba sai na yi miki kayan sallah a ciki ba?" Ta ce"Ni fa ba aikin ne ba na so ba, garin ya yi nisa, kuma har kwana bakwai". Ya ce"To ai haƙuri za ki yi, wanda ya tashi nema ai ba ya duba nisa Maryam, ni ma zan yi kewarki kuma na akwai masu tafiya su yi wata bakwai, ko shekara bakwai, to ina laifi don na yi kwana bakwai?" Ta ce"Haka ne, shi kenan Allah Ya kai ka lafiya, ya dawo mini da kai lafiya, Allah Ya ba da abin da aka je nema". Ya ce"Amin mace ta gari, ko kefa! Amma da kin tsaya kina wani tantama? Gobe da yamma za mu tafi, saboda haka yau kam duk rowarki sai kin bar min daren nan duka, kya dinga tunawa da ni ko?" Ta ce"Kai ai aikinka kenan, na rasa me kake ji, ni dama tun can babu wannan abun a aure da na ji daɗina" Ta juya kai gefe Ya ce"Maryam kenan, ke dai na rasa irin tunaninki wallahi, nan gaba za ki saba dai, ina ga sai kin haihu ko?" Ba ta ce komai ba, ta tashi ta kwashe kwanukan da suka ci abinci. Kafin ya shigo ɗaki ta yi luf kamar mai bacci, saboda fargabar furucinsa ta kasa baccin ma, ya yi abin da zai yi ya kwanta, yana kai hannu jikinta, ta ce"Na fa fara bacci, ga ciwon kai". Ya matsa gefe, don dama ba wai buƙatarta yake yi ba, kawai dai don ta sake yarda da tafiyar tashi ce, shi da zai je ya ɓarje guminsa a gidan Hajiya har ya tsaya ana kace-nace da shi? Daga haka ya juya ya fara baccinsa hankali kwance, har zumuɗin zuwan goben yake yi. Washegari bai fita aiki ba, da kanta ta haɗa masa kaya a jaka, har ta ce ya siyo fulawa ta yi masa cincin ya ce a'a ta bar shi, tun da kanta yana ciwo, tun azhar Hajiya ta yi masa tex ɗin tana ta jira, ya ce mata sai da yamma, ana idar da sallar la'asar ya ɗauki jaka yana yi wa Maryam marayan kallo saboda yaudara, sai ya ga ta tashi ta saka hijjabi, ya ce"A ina zuwa kuma?" Ta ce"Ai ya kamata na raka ka tasha ko?" Ya ce"Haba Maryam wace tasha kuma? Mu da za mu haɗa da yawanmu a ƙasan layi sannan mu ɗunguma zuwa tasha, kuma tsakani da Allah sai a ce ni ne kaɗai matata ta rako ni?" Ta ce"To mene ne idan ma an faɗa?" Ya ce"A'a wallahi ni dai ina kishin a gane mini kyakkyawar matata, duk sallamar da za mu yi mu yi ta a iya zaure, kwana bakwai ne fa, kamar yau ne, yi haƙuri kin ji?" Haka dai ya lallaɓata ya tafi, bai samu nutsuwa ba sai da ya gan shi a gidan Hajiya, sosai take farin ciki da zuwansa, jinta take tamkar wacce ta yi sabon aure, ɗakin mijinta ta buɗe ta kai kayansa ciki, ta faɗa masa nan ne masaukinsa, tun kafin ya zo ta sallami ƴar aikinta, ta ce mata tafiya za ta yi, sai bayan sati ɗaya idan ta dawo za ta neme ta, saboda haka da kanta ta yi masa girki sakwara da haɗaɗɗiyar miyar da ta zuba yajin maza a ciki ta yi lafiyayyen kunun aya shi ma ta watsa masa ƙwayoyi, Aliyyu ya kwashi abinci ya yi wanka, suka fara shagalinsu, bayan ya kashe wayarsa. Bai kunnata ba sai washegari shi ma sai azhar, don sosai ya kwashi ramuwar bacci da safe, ya kira Maryam suka gaisa yake faɗa mata yanzun nan suka sauka, ta ce"Alhamdulillah! Tafiya ta yi kyau, ina ta tunani wayarka na kikkira a kashe ashe sai yanzu kuka je, amma dai da nisa". Ya ce"Ke dai bari Love, kwana muka yi a hanya, ana sharara gudu, sai yanzu muka isa". Ta ce"Ma sha Allah! Da daddare za mu yi chart". Hajiya dake zaune tana jin duk wayar tasu, ta kaɗa masa ɗan yatsa alamar a'a, tana maƙe kafaɗa kamar yarinya. Ya ce"Ai Maryam chart dai yau ba zai yiwu ba, jiya fa ban yi bacci ba, yanzu caji zan bada wayata, a kaimu mu ga yanayin aikin, sai mu ci abinci a kaimu masauki, kin ga ina yin wanka sai bacci, tun da gobe sassafe za mu tafi wurin aikin". Cike da tausayawa ta ce"To Allah Ya tsare ku, Ya ba da sa'a Love ka kula da kanka sosai don Allah, ban da kai wa dare a waje ka ga dai ba ka san kowa ba". Ya ce"Haba ina ma na ga wannan damar? Mu da za mu wuni aiki, ai ina dawowa sai bacci, ke ma sai dai ki yi haƙuri ba za mu dinga doguwar waya ba". Daga haka suka yi sallama, ya kalli Hajiya yana washe baki, ta juya kai ta ce"Ina kishi da wannan matar taka gaskiya". Ya ce"A haba Hajiya, ai kin wuce ki yi kishi da Maryam". Ta ce"Ba ni labarinta, tana sonka sosai ko?" Kamar ta yi masa allurar tonon silili haka ya ɓarke ya fara ba ta labarin Maryam, hatta gidan iyayenta da yadda suka fara soyayya zuwa aurensu, da sana'ar da take yi, duk sai da ya faɗa mata, sannan daga baya ta nemi sanin unguwar da yake haya, ya kwatanta mata tsaf. Haka rayuwa take gudana tsakanin Hajiya da Aliyyunta, suna ɓarje soyayya, Ali sai dai a ci a sha a kwanta a yi bacci, daga shi sai gajeren wando za ka gan shi a falo yana kallon TV, AC tana ratsa shi, ya shiga kitchen ya yi ciye-ciyensa son ransa, kullum ya ji alert ɗin dubu goma. Kwanansa biyar a gidan, Hajiya ta ce masa za ta je unguwa, tun da ya zo bai ga ta fita ba sai yau, tana yin baƙi, idan za su zo sai dai ta ya shige ɗakinsa ya yi kwanciyarsa. Kai tsaye Hajiya ta bi kwatancen da ya yi mata, ta je har gidan Maryam, a buɗe ta tarar da gidan, ta yi sallama ta shiga, ta tarar da mata guda biyu suna fira, wanda kwarjinin Hajiyar ya sa suka yi zaton wata babbar baƙuwa ta yi, suka yi wa Maryam sallama suka tafi, Maryam ta tashi tana yi mata sannu da zuwa, Hajiya ta ja kujera ƴar tsuguno ta zauna ta ce"Yawwa Maryam, dama kitso na zo ko zan samu?" Ta ce"Za ki samu, bari na ɗakko tabarma". Ta shiga ɗaki, Hajiya ta bi bayanta da wulaƙantaccen kallo, ta fito ta shimfiɗa hannunta riƙe da kibiya ta ce"Bisimillah". Hajiya ta zauna a tabarma, Maryam ta fara yi mata kitso, tana ji ta ɗakko wayarta ta yi kira, ta ji tana cewa"Ali na samu gidan Maryam ɗin, ga shi nan ma har ta fara yi mini kitson". Can kuma ta ce"A babu komai wallahi, tana da kirki, bari dai idan na zo gidan ma yi magana". Maryam ta ɗan yi mamaki jin irin sunan mijinta kuma da alama mai sunan ne ya kwatanta mata har ta zo kitson, ba ta kawo komai ba har ta gama yi mata, Hajiya ta ɗauki dubu biyu ta bata, Maryam ta ce"Ai baiwar Allah bai kai haka ba, ungo kuɗinki har dubu biyu?" Hajiya ta ce"Haba ai yiwa kaine, ke da Ali ai duk ɗaya kuke a wajena". Cak Maryam ta tsaya ta ce"Wai wane Alin?" Ta ce"Ba sunan mijinki Ali ba, wanda ya yi miki ƙaryar ya tafi Enugu aikin kamfani? To idan ya dawo ki faɗa masa Hajiya Zuwaira tana gaishe shi". Daga haka ta fice tana murmushi, ta bar Maryam wacce mamaki ya daskarar da ita. Shi kuwa Ali yana falo ya yi ɗai-ɗai yana kallo a TV, lokaci-lokaci yana damƙar dambun nama yana ci, ya ga an buɗe ƙofa, da sauri ya miƙe tsaye ganin wani mutumi ne ya shigo ba Hajiya ba, kallon-kallo suka shiga yi da mutum, kafin Ali ya kwasa a guje ya yi hanyar ɗakinsa, mutumin ya bi sa ya guje yana cewa"Waye kai!?" Ali ya murɗa key zuciyarsa tana bugawa da mugun ƙarfi, ga shi ya bar wayarsa a falo. GIDAN SADIQ Yau ta kasance Asabar Yusra tana gida, don haka Kursum ba za ta zo ba, bayan ta gama duk ayyukan gida ta kwanta tana bacci, har ta makara sai da aka fara kiraye-kirayen sallah ta farka, ta fito ta ɗora girki, tana gamawa ta zubawa yara, suna yin cokali ɗaya suka kalli juna, Afna ta ce"Ni dai Momy na ƙoshi" Fanan kuma ta ce"Momy me yasa abincin Anti Kursum ya fi yin daɗi?" Da mamaki Yusra take kallonsu, ta ja abincin ta yi cokali ɗaya ta ji babu wata matsala, ta ce"Ita na Anti Kursum ba irin wannan ba ne?" Afna ta ce"Nata ya fi daɗi, kuma da wuri take gama yi mana, ta ba mu a baki". Yusra kanta ya kulle tana kallon abincin ta ce"Mene ne bambancinsu?" "Yara ma suka gane ballantana ke? Haba Yusra yanzu za ki ce duk tsawon lokacin nan ba ki gane canjin ɗanɗanon abinci da aka samu ba a gidan nan sanadin Kursum?" Sadiq ya faɗa wanda ba su san da shigowarsa ba Cak ta tsaya tana kallonsa da auna maganganunsa, ya ce"Wannan ba wani abun mamaki ba ne, kin san an ce dama kowa da irin hannunsa, ni ɗakko min abincina na koma, yunwa ce ta dawo da ni, Kursum kafin sha biyu take kai min abincina har na saba da ci da wuri, ke kuwa sai ƙarfe biyu, duk yunwa ta gama cinye mutum". Ai Yusra ji ta yi kamar an zare mata laka saboda tsananin mamaki, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ga ya shiga kitchen ya ɗakko abincin ya zauna zai fara ci, ta tashi ta je ta tankwaɓe cokalin hannunsa abincin da ya ɗibo ya zube, ya ɗago yana yi mata kallon mamaki, ta ce"Abincin da babu daɗi za ka ci? Ai sai ka jira Kursum ɗin ta dafa maka! Wai da gaske ni kake faɗawa wata ta fi ni iya girki?" Sadiq ya ce"Yaushe kika ji na ce haka? Don na ce an samu canjin ɗanɗano ba shi yake nufin nata ya fi daɗi ba, shekararmu nawa da nake ina cin abincinki? Idan ba ya yi mini daɗi za a kai wannan ranar ban faɗa ba? Inda kin zauna kina sauke hakkin gidanki ta ya ma Kursum ta kai na ci abincinta?" Ya faɗi hakan, don kuwa bai ga abin da zai sa ya yi sake Kursum ta bar gidan nan ba, don ko ta fannin girki kaɗai an samu ci gaba, shayi ma wannan idan ta dafa sai ya ji bambanci da na Yusra. Ta ɗan ji dama-dama a zuciyarta ta ce"Amma ai ka ce ita da wuri take kai maka abinci, mai yasa za ka yabeta?" Ya ce"Dole fa idan an yi min na faɗa, kullum ba kya kai min abinci sai kun gama ci ke da yara, ita kuwa kafin sha biyu ta gama ta kawo min". "Hmm!" Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ɗakko masa wani cokali ta koma ɗakinta ta zauna ta yi shiru, ba don tana son Kursum ba da babu abin da zai hana ta canzo wata, don ta san mijinta ba akan komai yake mayar da hankali ba, tun da ya fara wannan ƙananun maganganun akwai dalili, amma koma mene ne ta saka a ranta za ta fara kula. Daddare yana falo yana chart da Ummu, wacce take ta ce masa ya je ya kwanta yau Anti tana gida, shi kuma sun ɗakko maganar da ba ya so a katse, kwatsam sai ji ya yi an warce wayar hannunsa, ya ɗaga kai ya kalli Yusra wacce bai ji ko motsin fitowarta ba, da sauri ya kai hannu zai warce wayar ta riƙe ta ƙam cikin hargagi take cewa"Sadiq wace ce Ummu? Wace mai tsautsayin ce ta shigo mini rayuwata!? Sadiq!" Ransa a ɓace ya ce"Malama ba ni wayata". Tana huci tare da zazzare ido ta ce"Ba zan bayar ba!". Ya ruƙo ta, sai ga su suna kokowa har ya ƙwace wayarsa ya shige ɗaki, ya barta durƙushe a falo tana kuka. Zama ya yi a bakin gado ya dafe kansa, yana tunanin bai kyauta mata ba, sai dai wata zuciyar tana faɗa masa hakan ba komai ba ne, tun da ba haramun ya aikata ba, shi kam a yadda yake jin Ummu a cikin zuciyarsa babu me iya raba shi da ita, kuma ya ma saka a ransa ya zama dole ya nunawa Yusra ba yana ƙin kula mata ba ne saboda tsoron kishinta ko kuma ba shi da niyyar ƙarin auren ba, saboda haka dole a cikin satin nan ya san wace ce Ummunsa, kuma su daina wasan ɓuyan nan su fuskanci juna, kowa ya san the game is over. To fa! Kuna tunanin idan Sadiq ya san wace ce ɓoyayyiyar masoyiyarsa zai ci gaba da sonta? Sannan ya Yusra za ta yi idan auren ya tabbata? Ga dai Ali nan an tarfa shi a cikin gidan Hajiya, yana da hanyar fita? Ƙwan da Hajiya ta kai gidan Ali idan ya fashe ya za a kwashe tsakanin Ali da Maryam? Halima ta dawo, yaya alaƙar Zainab da Haruna za ta kasance? Shin dabarar da ta ce ta samu za ta kai musu kuwa? LAST FREE PAGES! ƳAR'UWA KI SIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI, YANZU AKA FARA TAFIYAR LITTAFIN WANI AUREN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 300 KACAL! 8028966015 Sadiya Abdulrazaƙ Opay bank KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN 08028966015/09060689001 KO KATIN AIRTEL NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL