Sanadin Boko 3-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:29 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Jikin abubakar sai bari yake, lokacin da suka shigo mota shida Hashim ne a baya, yayin da sagir ke tuki. Yace, innalillahi wa ina ilaihi raji'un, lallai na fada cikin jaraba. Dama Hafsat karuwa ce? Ya kifa kanshi ta baya. Hashim yace cool down my broos. Ka bi ahankali. Yace, Hashim daina cewa inbi a hankali, ka dai san promise da nayi dasu lamido kafin su yarda in aure ta, kuma ko yanzu ina kar kashin dokokin ne. Me kake zato in suka tashi bincike suka gano wanan matsalar? Sagir yace, amma sai dai in da ne tayi karuwancin, yanzu dai bisa tarin alamu batayin harkar. Abubakar yace, zazzabi nakejifa, ku kaini Asibiti. Hashim yace please Hamma kayi cooling mind dinka mana, wane irin Asibiti kuma? Yace Sagir dan Allah muje zazzabi nake ji. Sagir yace naso muje gurin Rahama, zamuji gaskiyar magana. Abubakar yace please, ku daina min zancenta, bana sonta, ba zan auri karuwa ba,zuwa wani lokaci bacci ya dauke shi, suka je office din likitan dan amsa kiran shi. Bayan sun zauna ya dube su a natse yace, ya shiga wata damuwa ne wadda lokaci 1 ta kumbura zuciyarsa, kokuma ya tsorata. Ya dan saurara, kafin ya cigaba da ce musu zai kwanta na dan kwanaki don kauce ma abin da zai biyo baya, sanan dole ne ya kaucema duk wani abu da ka iya tashin hankalinsa. Suka ce, to in sha Allahu za‘a kula. Suka dawo gurin shi suna dan tau tauna maganar Hafsat. Sagir yace, nayi zaton Hafsat tayi haka ne don Abubakar ya rabu da ita. Hashim yace, anya? Ni kam ina ganin rabon ba za akai mana bara gurbi cikin zuri‘a bane. Iyayenmu ba zasu amince da wanan auren ba. Sagir yace, amma Abubakar zai shiga wani hali in kayi la‘akari da matsanancin son da yake mata, dube shi fa lokaci kan kani yanda ya zama? Baka ganin zai iya mutuwa, zai fi masa sauki, in dai akan ya auri karuwa ne,zuri‘ar mu suna da tsuri, auran shinnan shine na farko da za‘ayi auren bare, kuma in yazo da matsala zasu kafa shi hujja ga yan baya. Sagir yace, hakane. Kusan 11 saura sagir yaje mota ya fito musu da dardumar sallah, sannan ya tafi taredacewa sai dasafe. Kusan karfe 4 dare Abubakar ya farka, jikinshi lakwas yake jin shi, kansa da kirjinsa kuwa sun masa nauyi. Ya dora hannu a kirjinsa, sam baya san tuno abin da ya faru ko kadan. Amma zuciyarsa ba zata iya amincewaba ko na sakon. A fili ya furta Hafsat! Hafsat!! Karuwa!!! Yai juyi ya kwanta akan hannun damansa. Allah ya cire min sonta, don ina da matukar kishi a kanta. Tabbas yana kishinta dayawa, da ya tuno ta taba aure sai yaji kuna a ransa, ina ma shine mijinta na fari! To ashe ma ba haka bane, ita Dattice, Bolace da kowane kazamin zai zo yazuba shararsa. Tir! Tir!! Da shi ya aureta. Ya sake juyawa. Tabbas nasan cewa idan ina son abu ina yimasa so tamkar rai, amma in naga zai bani matsala ina hakura dashi, nasan zuwa jibi zanji ta fita daga raina.Da wadannan tunane tunanen ya jiyo tada sallah daga massallacin da ke cikin Asibitin ya kai hannu ya dafa kan Hashim wanda ya jingina kansa bisa gadon yana bacci a zaune kan kujere Hashim ya bude ido Abubakar ya ce cikin fulatanci an kira sallah shima ya yunkura zai tashi sai yaji jiri yana diban shi ya komaya zauna bayan fitan Hashim da kyar ya lallaba ya tashi ya nufi toilet ruwa ya sakar ma jikinshi kafin yayi alwala sallar ma a zaune yayi ta don bazai iya tsayuwa ba kafin ya idar zazzabi ya rufe shi da likitan ya shigo ya yita masifa meyasa zai watsa ma jikin shi ruwan sanyi da safen nan? Lokacin da sagir ya isa gida Rahama na zaune, don duk ta damu sunyi dare. Ya shigo jiki babu karfi, ta dubeshi Hafsat takiko? Ya zauna yace, dauko mun ruwa in sha. Ta kawo tare da tsiyaya masa a kofi ya sha, sannan ya dube ta. Dama Hafsat ba yan uwanku bane? Tace, me kagani? Yace, ta fada mana cewa ita karuwa ce, zaman kanta takeyi. Rahama ta zabga salati, mai ya kai Hafsat yiwa kanta shairi? Ta rike haba cikin al‘ajabi. Yace, ga dai Abubakar can a gadon asibiti sakamakon furicin da tayi. Rahama tace, kuma? Yace, to wai menene labarinta? Nasan kinsan komai tunda tayi wanan furucin yanzu ke kadaice zaki wanke ta a gurin Abubakar, domin ance magana zarar bunu, in ta fito ta fito kenan. Rahama tace, gobe zaka yarje min inje gidanta dan muyi magana, idan ta bani izini to zakuji komai, ina zaton tace haka ne don ya rabu da ita. Sagir yace, in ko sun rabu zasu sha wahala, don itama ko da bansani ba yanzun haka tana cikin damuwa. Rahama ta shigo gidan, shadad tagani kan tabarma lamo da alamu yunwa yake ji, ko kuma damuwa bai da lfy. Tace, yau babu makaranta ne? Ina antyn taka? Yace, tana ciki. Ganin halin da take ciki ya tsorata Rahama, har tadau waya ta kira sagir, tace ta tashi su tafi asibiti, tace a a ta bari mutuwa zatayi, amma ga amanar yaron ta nan. Tace, in kinje kaduna inda na fada miki lokacin da nake baki lbrina, zaki sami lbr iyaye na, ko da baki samesu ba kice suyafe mun. Ki nuna musu dana shima ya san dangina. Rahama tace, haba hafsy, kitashi wanan ba ciwon mutuwa bane, ciwon son Abubakar ne, kuma in sha Allahu zaki sameshi. Ta fita, sagir kazo kayi mata magana. Da kyar ta yarda ta bisu saboda magiyar da sagir ke yi mata. Asibitin da yake suka kaita, likita ya dubani wai nima zuciyata ta motsa, kuma jinina ya hau.daga nan sagir ya tafi dakin da Abubakar ke kwance ya sami Hashim na waya, shi kuma yana kwance. Yaba hashim hannu suka gaisa. Sanan ya nufi gun abubakar bashi hannu shima suka gaisa. Duk da cewa abubakar din da kyar yake magana, yace Sagir kasa Rahama ta kawoma Hashim abun karyawa, saboda yana da ulser. Sagir yace, Rahama tana gurin Hafsa a nan asibiti, ta je tasamu halin da take ciki takirani muka kawota nan. Da sauri ya mike me ya sameta? Sai kuma yaja tsaki ya koma ya kwanta. Sagir suka bari suje suyi take away. A hanya sagir yake ba hashim labarin abin da ya faru har suka kawo hafsa nan . Hashim yace yanda za‘ayi yanzu zamu samu Rahama ta bamu duk abin da ya faru. Sagir yace, kaji batu. Ko kallon inda suka ajeyi abincin da suka suyo mashi bai ma yiba, ya damu kwarai. Wayarshi dake hanun hashim tayi kara, hashim din ne ya dauka. Abba ne. Yace tuk da kuka kiramu da kuka sauka har yanzu shuru, ko lafiya? Hashim yace, Abba akwai matsala fa. Da sauri Abubakar ya duro dakarfin da bai san yana dashi ba, a hankali yace kada ka fada mashi komai game da Hafsa please. Hashim yace, abba kace me? Bana ji? Abba yace me ya faru nace, kun samu wata matsala ne game da yarinyar? Hashim yace, Abubakar ne bashi da lafiya, yanzu haka anbamu gado muna asibiti. Subuhanalilahi!Me yasameshi har haka? To likitan dai yace ciwon zuciya ne, zuciya ne e dan kumbura. Inji hashim. Abba yace, ikon Allah! In sha‘Allahu gobe muna zuwa. Hashim yace to Abba sai kunzo. Abubakar yace kace da sauki, ni kam ba sai sunzo ba. Duk da haka Abba yace zasuzo. Zuciya ai ba abun wasa bane, da suka gama wayar Abubakar yace, kai dai banza ne, wa ya fadanmaka ana fadin ciwo? Hashim yace, da fa zan fadan mishi matsalar Hafsa ne kace a a ba dole in fada mishi ciwo ba, tunda bani da mafita na riga dai na fara fada.Abubakar yace, ko sunzo kada kayi musu maganar hafsa, na san yanda zan warware matsalar, domin insukaji Hafsat karuwace to fa zasu kara reke wanan al‘adar da hannu biyu. Kaga kokarina na baya ya zama banza, har yan gaba ba zasu amfana da komai ba. Amma in munyi shuru koni banyi ba kannan mu zasu iya yi. Hashim yace, shikenan. Amma itama zamuyi bincike. Abubakar ya kalleshi da sauri, zakuyi binciken me? Bana son wani bincike, ni na hakura da ita. Hashim yace, gama malam bana son gadama, yanzu bagaka a gadon asibiti kana ciwon so ba? Abubakar yace, inji uban wa yace maka ciwon so ne? Ai ni tun jiya na daina sonta, ciwon daga Allah ne, sai kace wani wawa zan tsaya ciwo akam mace kamar a film? Film din ma na indiya? Sagir da ke jinsu yayi dariya tare da cewa, kai da ita duk cutar so ke damun ku, don haka ku nutsu zamuyi bincike. Abubakar ya hade rai kunsan Allah, wlh na fasa. Hashim yace harda rantsuwa? Abubakar yayi tsaki ya kwanta. Washegari su Abba suka iso su 5, harda dada, amma yan da suka ganshi duk sun damu. Bawai jikinsa ya tsananta bane, amma yana cikin damuwa. Likita ya fada musu matsalar zuciya tana da girma, subishi a hankali, kuma damuwar da yake ciki suyi kokari su kau da ita, sukace basa zaton yana cikin wata damuwa, aMMA zasu zauna dashi. Abba da baffansa guda 2 da dada da kuma gogonsu kuma surukarsa, wato gogo jami, suka sashi gaba bayan sun gama cin abincinda Rahama ta girka musu. Sukace ya sanar dasu damuwar shi, nuna musu yayi ba komai, ciwo ne kawai.Goggo jami tace, ina hafsatun? Da sauri yace taje kaduna, dama nan ai karatu tazo, to bamu sameta ba, amma zata zo gobe don ban fada mata bani da lafiya ba. Hashim ya saki baki yana kalon Abubakar, amma bai ce komai ba. Sagir shine ya sauke su yayi dawainiya dasu. Su dada gidan Rahama suka kwana, yayin da maman rahama ta zauna dani. Dada ke tam bayan rahama game da halayane, wai ance ni kawarta ce. Rahama tace tana da tabbacin ina da halaye masu kyau da biyayya. Washegari suka juya tunda yana tare da Hashim, ni kam ban san yana Asibitin bama, bana ganin kowa daga maman rahama sai sagir da rahama.shadad ma yana can gidan su maman rahama da mahaifiyarta. Hashim da sagir sun fita sun bar abubakar kwance yau har kwana 3, amma baiji son Hafsa ya girgiza daga zuciyarsa ba, sai ma son ganin halin da take ciki da yake. Tunda aka ce mashi bata da lafiya tana kwance a Asibitin. Yaji ranshi ya kasa kwanciya, gashi tun da yace masu sagir baya son jin labarinta suka daina zancenta. Dan haka bai san koyaya jikin nata yakeba yanzu. Ya mike jiki babu karfi yafita, da nurse suka ci karo yace mata wane daki ne aka kwantar da wata Hafsa? Ta nuna mishi ta wuce. Ya nufi gurin, ta window ya tsaya yana kalonta tana bacci. Ta rame matuka. Gadonta na jikin window ba kowa a dakin, tamkar ya shiga a fili yace, me yasa kika cuceni? Me yasa kika zama kazamar rijiya wanda kowane kazami zai jefa kazamar gugarsa? Ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Ina sonki Hafsa, ban taba ganin abin da nake so ba irinki. Ya juyawa window din baya, wasu kananan kwala masu dimi suka biyo gefen idon shi,kin cuceni. Ya sa hannu ya share idon sa, dai dai lokacin da ya hango su Hashim, nan take ya soma tafiya dan barin gurin. Sagir yace, ina kaje? Ko gurin Hafsa kaje? Tsaki yaja, inje in mata me? Na dai dan taka ne. Suka kalli juna sukayi murmushi, Sagir da Hashim. Sannan sagir yace, Abubakar ba‘a yiwa so miskilanci, ka nutsu a warware komai. Hashim yace, daga gurin Rahama muke, tayi mana bayanin gaskiyar lamari. Abubakar ya dubeshi da sauri ta taba aure ko? Tana tsokana tane dan na barta ko? Hashim yace a a bata taba aure ba Abubakar yaja tsaki. To ba zan saurareku ba, in bata taba aure ba ina ta samo yaro? Agurin karuwanci? Ya nufi cikin daki yana fadin ada na tsani inji an ce ta taba aure, duk da ina matuka son danta, amma yanzu har fata nike so nake inji an ce auran ta taba yi. Sagir yayi ma Hashim alama da hannu, wai ya kyale shi. Ni kam dama ina da tsohon ciwo na a jiki bai taso ba, sai yanzun da yaji ni a gadon asibiti. Yau in likita yace nan ne ciwo kaza ne, gobe sai yace har da kaza ma, yau da ya shugo kuma ya gama duba ni, wai zama asamin jini. Na bude ido da kyar, jini? Na fada a hankali, yace, eh mana, jininki ya tsotse, dama tunda kukazo baki da ishashen jini. Maman su Rahama tace, saya za‘ayi ne? Yace, eh to, da dai tana da wasu yan uwa haka sai su bata, in da wanda zai iya bata, don ba mu cika son siyan jini ba. Mama tace, to bari su shigo muji. Bayan yafita nace, mama wai wanene ke dawaibiya dani? Mama tace, to ni dai ban sani ba, ko wanene cikinsu? Oho! Ni dai likitan bai taba kawo kaza ba. Zai kawo magani, kuma zaizo ya dubaki, don haka bansan wanene ke daukar nauyinki ba. Lokacin da sagir suka shugo da hashim, mama tace likita yace sai an sa jini a jikinta,suka ce, sagir yayi mana bayani, anjuma zamuzo a gwada jininmu. Nace nifa zanfi son ku barni in mutu. Mama tace, kuje ku kyaleta. Aikinta kenan zancen mutuwa, kuma nasan da zataga mutuwa guduwa zatayi. Su sagir suka sa dariya, ina so in tambaya shi wanan dan uwa Abubakar dama a nan yake in kuma tare suka zo in Abubakar din? Ina son sanin halin da yake ciki, ina ma wayata? Bansan cewa a fili nayi yambayar ba, sai da naji mama tace. Wayarki tana hannun rahama, ta kira gurin aiki ma ta fada musu ma. Shuru nayi ina tunanin tare da fatan bataji sauran zantukar zuciyar tawa ba. Suna fita suka nufi gun Abubakar, can kusan minti 30 likita ya shugo ya dubi Abubakar yace mishi ina ganin kai zuwa gobe zamu sallame ka. Yace, Allah ya kaimu. Ya dube Sagir, ku kuma muje a gwada jininku din. Abubakar ya dubesu da sauri, lafiya? Hashim yace Hafsat tana bukatar jini. Abubakar ya tsurawa Hashim ido, jini kuma? Kikita yace kwarai kuwa. Daga nan bai sake magana ba, ya dauki wayarshi yana dan danawa, amma cikin zuciyarshi a rikice take, kadafa ta mutu! Suna fita yaga sun nufi gefab dibar jini da gwajin su, nan da nan ya nufi dakin da take. Bai shiga ba ta window ya tsaya yana lekenta. Tana kwance, amma da alama idonta biyu. Rahama tana zaune tana cin abinci. Yayi tamkar ya shiga, amma sai ya fasa. Ya fita harabar asibitin ya nemi guri ya zauna karkashin wata bishiya. Ya saka fiskarshi cikin tafukan nannayenshi, yanzu ya gama gane cewa soyayayarsu da Hafsa wata mai wahalar fassara ce. Muhimmiyace kuma hamshakiya. Ba zai taba daina sonta ba har abada. Menene mafita? Wata zuciyar tace mafita kenan, ka aureta. Hashim ya fada a bayan shi. Abubakar ya dago kai, idonshi jajir. Hashim yace, don Allah ka sama kanka salama, kana son Hafsat ka aureta. Abubakar yace, ba zan iya kwantar da hankalina ba, kasan kuma aure da zargi yana bata aure ko? Please, bar maganar aurenan ba zan iya ba. Ya mike ya bar Hashim a gurin, cikin ta kaicin rashin sauraran shi da Abubakar baiyi ba. Kai-tsaye ofishin likita ya nufa, yana zaune kan katon tabirin shi yana ta hada wasu fayal. Ya dubi abubakar. Ranka ya dade ya kakara gyagijiwa kenan? Abubakar ya zauna kan kujera batare da ya nemi iziniba. Ya dubi likitan. Likita wai me ke damun yarinyar nanme? Likita ya tatara hankalin shi gurin Abubakar, kana nufin sister dinka? Abubakar yace, eh. Likita yace, gaskiya bata da lafiyap gaban Abubakar ya fadi. Me ke damunta? Likita yace, tanada hawan jini, ga zuciyarta ta dan tabu, typoid ma tana dashi, dan muna zaton shinema ya tsotse jininta. Yanzu haka tana bukatar jini, muna gwada na sauran yan uwanka ba zai yi ba, amma da irin naka ne zaka iya ba kowa jini. Sannan mun sami jininta dan da ya hau ya sauka. Abubakar yace, likita ina so kudibi jinina kusa mata. Likita yace, kaima baka da lafiya, don haka ba zamu dibar maka jini ba. Yace, bani da ishashen jinin ne? Likita yace, kana da jini don jini. Yace, to a diba saboda ko ba ku diba ba zanje wani gurin su dibain kawo,in ma shi kenan ya rage min zan hakura ita ta rayu.shuru likitan yayi, can yace in na diba zan fasa sallamarka gobe. Yace dama ko ka sallameni sai na jira ta. Likita yace, matarka ce? Abubakar yace, ina fatan haka in Allah yaso. Sanan don Allah kada ka fada ma yan uwa na nine zan bada jini, shi kuma abu na gaba, inaso kayi mata gwajin (H I V) don Allah. Likita yace, in sha Allahu zanyi. Yace to jinin yaushe za‘a diba? Likita yace, gobe ne. Yace to in Allah ya kaimu sai adiba. Amma jikin nata yana sauki ko likita? Ya cigaba don Allah aluran min da ita sosai. Likita yace, tunda ka fadamin ko ita wacece to za a duba ta fiye da da. Yace to na gode, game da kudi ba matsala, na fada maka ai. Yace, nasan haka. Washegari sai dai sukaga basu ganshi ba da safe. An dibi leda 2 suka tace, duk da sunce ba komai a cikin sa. Aka bashi magun guna ya sha, suka rubuta mashi wani tare kuma da ya rika cin abubuwan kara jini tare da shan na kara ruwa Hashim yaji mamakin ganin shi sharkaf a kwance, ba wai ciwo bane, a a jikinshi a sanyaye yace, ina kaje tun dazu? Ya kali Hashim na dan fita na motsa jiki, shine nagaji. Hashim yace mai makon kayi mana magana mufita tare? Har nace kodai kaje ka bada jinin ne? Na tambayi likita yace an siyo jinin. Abubakar ya daure fuska, in bata jini a kan me? Ko su samu ko kada susamu ina ruwana? Hashim yace matsalaka kenan kin fahimta, kana son yarinya har a gidan karuwai ana dauko mace a aureta bare ita wanan da kadara ta fada mata. Abubakar yace, kada ka daurewa karya gindi, wanan ba kaddara bace. Ita kadara ma kanta mace ta kama karuwanci sanan ace kaddara? Hashim yace, zan so ka aje wanan kishin ka saurara muyi maganar. Abubakar yace, amma tuni na fada maka banson jin ko? Haushi ya kama hashim kada ka so zancenta, amma ka iya labewa ka lekata ko? Abubakar yace me zan leka? Hashim yace, zakaga kamar banganka ba ko? Ya tashi ya nufi dakin Hafsa, lokacin har jinin Abubakar ya soma diga cikin nata. AL‘amarin so babu karya acikin shi, amma shi amma shi kanshi Abubakar yana al‘ajabin irin son da yake ma Hafsa. Likita ya tabatar bata dauke da cutar kanjamau, domin tunda abubakar yace ayi mata gwajin (H I V) hankalinshi yafi da tashi. Kamar jinin take jira, gari na wayewa ta soma samun sauki, har tana tashi zaune, kuma har da sallah. Mama da Rahama suna tayi mata tsiya dama jini kike bukata, gashi har kin gyare. Itama ta danyi yake, tace Rahama ina wayata? Rahama tatashi ta balle jakar ta ciro wayar tana cewa. Ke wayarki da ita da babu duk daya ne. Na dubeta da alamun karin bayani. Tace, to tun da natafi da wayar nan babu wanda ya kira ki. Na amsa ba tare da ce mata uffan ba, sako nasamu kaina da rubutawa. (ABUBAKAR SADEEQ) NASO IN MUTU SABODA NA SAN BA ZAN TABA SAMUNKA BA, KA YAFE NI. INA SO KA SANI CEWA INA MATUKAR SONKA, KUMA HAR IN KOMA GA ALLAH BA ZAN DAINA SONKA BA. DON ALLAH KADA KA MANTA DANI, DUK LOKACIN DA KA TUMONI KA MIN ADU‘A ******** natura masa ne zan katse sakon ashe yariga yaje. A zatonshi fadi ce, don kullun zata kira shi sau kusan 4 banda tex na kalaman so da kauna tare da bege. Sai dai shi bai taba jin haka ya burge shi ba ko acikin ranshi, sai dai bai taba nuna mata bai ji dadi ba. Sai kusan minti goma sha 2 sanan ya karanta kusan sau 3, sanan ya yarda ita ce. Yayi ajiyar zuciya sauki ya soma samuwa kenan. Da dare yayi yaje ya leka su ta window kamar yan da ya saba duk dare in hashim ya yi dan bacci sai ya saci jiki yaje yayi lekensu. Hashim yasha ganin sa, amma bai taba nuna masa yasan yana zuwa ba. Zaune kan salaya ya hangeta, hunnuwanta a sama hawaye na ...... Zaharaddeen shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-02 Posted by ANaM Dorayi on 10:53 PM, 26-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Hannuwanta a sama hawaye na sauka a kan kumatunta. Lallai duk wanda ya ganta ya san tana cikin damuwa. Maman rahama tana gefe kan tabarma tana bacci tamkar yashiga yaga me tak ma kuka? Menene matsalar ta? Ba shi da mai bashi amsa, haka ya cigaba da tsayuwa yana kalonta har ta gama ta jin gina da bango, fiskarta na kalon saitin window din. Da zata kula sosai zata hangoshi, amma batayi tunanin da mitinin da zai fito cikin sulisin daren ya zi ya tsaya ba. Yana kalon ta, tadago ido sama alamun tana tunani, bakinta kuwa yana motsi, ga alamu istigifari takeyi. Wayarta tana gefenta, ya koma ya jin gina da bango, ya curo wayarshi yana karanta sakonta. Nan take ya rubuta karya kike bakya sona, kuma daka ki kara min tex. Ni kuma bana sonki, ba zan aureki ba. Da ya tura sai ya koma leketa, da sauri ta dauki wayar, ganin labar shi tayi dan mur mushi, amma da ta gama karanta dan sakon sai yaga ta toshe baki da da hannunta tana kuka tare da sake daga hannunta sama tana fada ma Allah. Ya jingina da bango tare da rintse ido. Hakika tana son shi, to me yasa ta fada mishi ita karuwa ce a gaban Hashim? Sam baiji takun sawo ba. Ya de idanun shi a hankali yana me fatan ace hafsa ce,ganin hashim yasa shi yin kame-kame don baya so su fahimci har yanzu yana sonta. Hashim yace, mr. Man ka amince haryanzu kana son Hafsa, kulun ina jin fitarka kana zuwa lekenta. Aure a gurinka yake in ba zaka saurari ainihin kaddarar da ta hau kanta ba, to ka amince muje gurin iyayenta don tautana batun aurenka. Abubakar ya nufi dakinshi yasan dare ne kila tana ji. Hashim ya biyo bayan shi suka zauna suna fiskantar juna Hashim yace, na fada maka Rahama ta fada muna komai. Ta tabatar muna fyade akayi mata. Yace, agaban Rahama akayi? Ni dai kawai ina sonta zan aureta. Sannan ina son kai ka rufa min wanan asirin, mubar shi a tataba aure, don Allah kada ka bari dangi suji zancen nan, amana na baka. Abu na gaba kuma muje gurin iyayenta kafin mu koma gida. Hashim yace, haba nawan, yaya ma ba zan rufa wanan asirin ba? Koda ban santaba ai zan rufa mata, balantana kaddara ce ta sameta. Zuwa washegari na kara samun sauki, har da wanka ina canja kaya. Wayar Rahama tayi kara, tace min tana zuwa, Sagir yana kiranta, tana zaton yana harabar asibiti. Nace, to. Su 3 ta samesu cike da murmushi tace, Abubakar jiki yayi kyau. Yace, wlh gashi ma an sallame ni. Hashin yace, Rahama dama muna so ne kiyi mana cikkaken kwatancen inda zamu samu iyayen Hafsa. Rahama tayi shuru tana dan nazari, can tace ni dai a kwatancen da tamun acikin labarin da tabani, ta ce mun a kaduna, sunan unguwarsu rigasa. Layi kuma ko abuja road tace min? Na dai manta. Sagir yace, ni anawa ganin Abubakar ka bari ta kara samun sauki sai aje gaba daya da ita. Hashin yace, shinema zaifi zuwa da sauki. Abubakar yace, a a, ina da nawa dalilin zaku fahinci nufina daga baya. Rahama abinda nake so kafin gobe ki dan tambayeta cikin dabaru muji koda sunan layinsu. Rahama tace to. Ina kwance da wayan rahama a hannuna ina kalon hotona, yawanci duk hotunan bikin ta ne tasa a ciki. Na tsaida ido na a kan hoton abubakar me yasa ban fada mashi gaskiyar lamarina ba?Me yasa nace mashi ni karuwa ce, alhalin nasan wanan mumunan sunan da na kira kaina dashi zai iya bina? Ko dayake inma ban fada mishiba zaiji a wani gurin, cewa nayi ciki na gudu, tunda babu wanda yasan cewa fyade akayi min. Wasuma zasu ce masa ni karuwa ce. Amma da yaji abakina fa? Ko da ya sake ji a wani gurin bazai ji komai ba. Rahama ta ka tsemin tunani da cewa, hafsat ki tuna min kwatancen layin ku, wai in kai shadad. Na dubeta banyi maki kwatancen layin mu ba? Tace, kince abuja road, nace Allah to ban san nace ba. Rahama tace, har sunan layin kika ce ko me? Gidan wanene? Atake layinmu ya bayyana a idona, ban san na furta gidan 12 layi na 3, wasu suce gidan yawa. Na kali Rahama ina tuno rayuwar da nayi a wanan gidan, ina kewar gidan ina burin in sake zuwa gidan. Rahama tace mai zai hana in kin sami sauki muje? Nayi kokarin in tare hawayena, amma ba zasu tsaya ba saboda girman bakin cikin dake zuciyata. Nace rahama lokacin zuwa na gida baiyi ba, tace saboda me? Na sha fada maki abaya sai na kama aiki ko na sami mijin aure. Rahama tace, yaushe har kika saki fuska bare ki samu mijin aure? Taci gaba. Ba ma wanan ba, me yasa kika cewa abubakar ke karuwa ce? Nace, Rahama duk wanda zai aureni sai ya nemi asalina, kuma na tabbata duk wanda yaje unguwarmu don neman labarina za a fada mishi na shiga duniyar karuwanci,nakuma tafi da cikin shege, wanene ma yasan munnir fyade yayi min? Bale ma a dan kare ni? Shiyasa na fadi haka. Rahama tace, kamata yayi ki bashi asalin labarin abinda ya faru yanda zai fahimta, in sha Allahu zaya taimaka miki. Nace nifa kinsan Allah rahama? Bana son amaimaita min na baya, naga babu wata hanya da zan kori Abubakar da ya wuce in fada mishi hakan dan ya rabu dani. Duk da yanzu ina na damar hakan. Na dubeta sosai yanzu bana jin kunyar in furta ina son Abubakar, don bansan ina sonsa ba sai yanzu da na koreshi. Rahama tace kila kiga ya dawo, amma in yazo kada ki kuma kuskuren da kikayi a baya. Nace, Rhama na rokonki dakada kimin karya don hankalina ya kwanta, na tabata ko Abubakar yana shaye shaye ba zai dawo gareni ba. Tuni na dangana dashi, tun ranar da na tura mashi wani sako da dadare, kin ga amasar da ya bani nan acikin wayata. Na sauke ajiyar zuciya tare da share wani hawaye da ya biyo kan karan hancina yayi min dan maimayi. Rahama na gane kuskurena da nasani nabi innata nasan ba zan tozarta ba, zasuyi hakuri dangin uwata zasu rikeni da ko na hadu da Abubakar bazanji komai ba. Lallai barin gaban iyaye matsala ce katuwa. Rahama tace, ita dama mace guri 3 yakamata ta kasance, in bata gidan ubanta to a sameta a dakin mijinta. Idanto ya kasance baki can to a sameki a kabari, ta cigaba da cewa, duk inda mace take a sameta a karkashin wani uba ko miji, ko wa, ko kani, ko daki. Idan aka sami mace bata kar kashin ko 1, lallai ba wanda zai ganta da kima ko daraja. Kare da doki suna iya kawo maki hari tunda ke yar kanki ce, don haka duk lokacin da Allah ya kawo maki miji to kiyi aure zafin da kika dauka kan maza ba inda zaya kaiki, tunda sune a bokan rayuwa.Rahama tayi wa abubakar text din kwatancen da na ambata cikin hiran mu don haka washegari suka dunguma suka nufi kaduna har da sagir inata yi wa rahama mitar sallama in likita yazo ta fada mishi saboda sagir na kashe kudi wanda a zatona shine me kashewa ta ce min in nutsu in warware tas,sun isa kaduna shekaru masu yawa bai tsaya a garin kaduna ba tun daya bar ta sai de ya wuce ta a mota tambaya suka yi aka nuna musu rigasa haka ma abuja road sai dai sun sha wahala da ta sama suka yi mamakon ta kasa sun shiga layi na ukusun tambaya gidan yawa amma babu shi sun zaga sun gaji har sun fita daga abuja road sun fada makarfi road Abubakar ya ce mu dai koma kan abuja raod din mu sake yin tambaya daga bisani suka yi tambaya a wani masallaci da ke layin na ukun bayan sun idar da sallah nan mutane suka basu shawaran suje ta kasa Ikon Allah suna shiga layi na uku Abubakar ya gane gidan su Hafsa domin tsawon shekaru gidan yana nan yanda yake baa kara komai ba saidema kara lalacewan da yayi suka tsaya kusa da gidan yara nata wasa a kofar gidan cikin kasa sagir yace kana da tabbacin cewa nan ne gidan yaya ma akayi ka sani abubakar yace nazo shekaru da dama bayan fitowar yarinya daga gidan yasa su yin shuru yar doguwa marar jiki tana sanye da doguwar riga ta farin yadi da kore kalar tutar nigeria gadukkan yan kaduna duk wanda ya ganshi yasan cewa yadi ne na makarantar primary ta gwamnati tana rataye da yar jaka ta buhu mai dauke da littattafanta na makaranta kafarta sanye cikin sandal na roba wanda igiyoyinsa suka ciccire,Abubakar gabanshi ya fadi, tamkar hafsat a shekarun baya. Yace yanmata zo mu tambaye ki mana. Ta tsaya nesa dasu, abubakar yace nan nan gidan su hafsat? Ta maimaita sunan hafsat? Yace, eh. Tayi shuru tana son tunano wacece hafsat a cikin gifan nan? Ta dubeshi karama ce? Yace, baba ce, suman mamanta inna ta zaro ido inna? Yace eh. Duk yan dakinsu suna da labarin hafsa yayarsu, duk da itace karama kwarai a lokacin da abubuwan suka faru ba zata mance da sunan hafsa ba. Sai dai kamanin hafsat sun bace mata. Inna kuwa ai uwarsu ce, wace babansu ya kora sanadin abin kunyar da akace hafsat tayi. Ta dubeshi tace, hafsat bata nan, hakama inna. Yace, ina suka je? Cikin kagara tace, nima ban sani ba. Inna dai tana funtuwa. Yace, to baba fa? Ta nuna gida da yatsa, yana ciki bashi da lafiya, sagir yasa baki. Kice masa yana da baki. Tace, saidaifa ku shiga, don baya iya fitowa. Hashim yace, to fada masa sai mu shiga. Tana juyawa, sagir yace, wanan yarinyar tana matukar kama da hafsa. Abubakar yace, donma baka santa tana karama ba, da cewa zakayi itace. Tafito tace, yace in shugo daku. Suka rufe mator suka bita. Lallai gidan yawa ta sunan nanshi inji sagir. Kansu a kasa saboda yawan matan gidan da yaransu, wasu kuma suna wasu ayyukan. Sun dan gaisa da wadanda suke bakin hanyar zuwa dakin, yarinyar da ta shugo da tabarma ta shinfida musu a gefe suka zazzauna suna fuskantar tsohon. Yana kwance kan tsohuwar katifar shi, wadda ta lakume. Suka gaisa, dakin yayi shuru lokacin yarinyar ta kara dawowa da kwanan sha na silba mai dauke da ruwa ta dire masu. Baba yace, kai cema babarku ga baki. Itama ta shugo su gai sa. Baba yace, kin shaida su? Tace, a a yace samari daga ina? Abubakar ya zunguri sagir, nan take sagir yace."Baba mu baki ne daga Kano." Baba yace, "Kano gurin wa kenan?" Ya ce, "Ba za ka shaida mu ba, ni sunana Sagirn wannan kuma Abubakar. Sai kuma wannan Hashim." Sagir yayi dan shiru saboda tunanin ta inda zai fara maganar. Can ya ce, "Wato Baba za ku ji mamakin cewa mun zo neman auren Hafsat ne." Baba ya yunkura ya zauna wanda baisan lokacin da yayi hakan ba, domin in zai irin wannan zaman sai an kama shi. Ya ce, "Hafsatuna?" Hashim ya ce "Ita" A rude Baba ya ce, "A ina kuka ganta? Don Allah ku fada min, kun ganta ne?" Tausayi da kaunar tsohon ya ratsa zuciyar Abubakar, ya ce "kada ka damu Baba, Hafsat tana nan lafiya." Ya ce "Alhamdulillah, Allah yasa ba irin mafarkin da na saba yi bane, tare kuke da iata? Hashim ya ce "Ba mafarki bane Baba, kuma ba tare muke ba." Ya nuna Abubakar. "Ga mai sonta da Aure nan, mun zo ne mu sanar da kai magabatanmu za su zo. Sai dai matsalar da muke tunani kada su zo kuma wani ya basu labarin cewa ta bar gida. Kila sanadin hakan iyayen mu suki amincewa." Baba ya ce "Wannan ba matsala ba ce, in sha Allahu, Amma kafin nan ina son Hafsat ta zo gida, yarinya tafi daraja idan tana gaban mahaifanta."suka ce To Insha Allah za su kawota, ko kuma su tafi da wani ya ga inda take. Baaba ta ce, "Kai amma wannan abu ya yi dadi, amma ku jira wanta yanzu sai ku gaisa, batun zuwa kuwa nice zan biku, ko kuma muje tare da Umar wansu din." Suka ce A kira shi. Sagir ne ya dauki lambar, bugu daya ta shiga ya dauka tare da Sallama, Sagir ya amsa ya ce, "Mu baki ne daga Kano, gamu nan gurin Mahaifinku, zamu samu ganinka?" Ya ce, "Lafiya?" Sagir ya ce, "Lafiya lau." Umar ya ce, "To gani nan zuwa, zan shigo layin da fasinja." Sagir ya ce, "To."Suna zuwa kan layin Umar ya cema kwandastansa ya kara dasu shi zai shiga gida, ya basu hannu suka gaisa sannan ya yiwa Baba sannu da Jiki. Cikin doki Baba ya ce, "Jiki da sauki, sun zo ne da labari akan Hafsatuna, abin dadi har da mai son aurenta, gashi nan tsakiya." Da tsananin mamaki ya ce, "Da gaske kun ga Hafsa? Allahu Akbar!!! dama tana raye?" Sagir ya ce, "Tana raye." Umar ya ce, "Ikon Allah!" Baba ya yiwa Umar bayanin komai da yanda suka yi. Umar ya ce, "Baaba ki zauna ni zan je naga inda take kafin, in yaso kwaje daga baya." Baba ya ce, "Haka ma yayi Umar." Umar ya ce, "Shawarata anan ko za a ce bakin suje can Funtua wajen Inna a karbi auren?" Sai Baba ya ce, "Ba komai nan ma yayi Umar. Allah shine mai yanda ya so."Umar ya shiga motarsu, inda suka je gidanshi suka ci suka sha, sun huta sosai, sai karfe 5 suka ce zasu tafi. Abubakar ya kasa hakuri ya ce, "Yarinyar can tana kama da Hafsa." Umar ya ce, "Ummi, 'yar autarmu ce." Ya ce, "Masha Allah." Duk yaga sauran kannanta yanzun saura Inna, suna gidanma Umar ya kira wayarta, bayan sun gaisa ne yake fada mata cewa cewa Wadansu bayin Allah ne suka zo da labarin Hafsatu, cikinsu har da wanda zai aureta. Cikin tsananin mamaki ta ce, "Da gaske kake?" Ya ce, "Gasu nan ma." Ta ce, "Harda Hafsat din?" Ya ce, "A'a, zan dai bisu muje in ga gurin da take." Ta ce, "Ko zaku biyo mu je?" Ya ce, "Kada ki damu Innarmu ni kadai na isa, tunda gida zata dawo." Inna ta ce, "To."Biyar da rabi suka dauki hanyar Kano su 4 ne. Suna hira a nan Umar ya samu wadan su labaran game da Hafsat, nan ne ya ji cewa bata san sun zo ba, bata da lafiya don haka ya ce, "To in mun je ku bari in fara shiga."Kusan karfe 8 suka iso Kano, sai da suka yi Sallar Isha'i sannan suka isa gidansu Rahma. Tana ganin Umar ta gane dan'uwan Hafsa ne, saboda kama ta jini. Da sun ce a bari sai da safe a je gurinta, Umar ya ce shi kam yanzun yake son zuwa. Dole suka tafi, daga bakin kofa suka tsaya Umar ya shiga da sallama.Mama tana sallar Isha'i, ni kuma ina bakin gado. Ina jin a jikina tamkar wani bakon al'amari zai same ni. Muryar Yaya Umar ta katse ni, da sauri na dubi kofar, zumbur na mike tsaye jikina yana kyarma na ce da sauri, "Yaya Umar! Yaya Umar kai ne ko mafarki ne?" Ya yi murmushi, "Ni ne Hafsa." Na zuba masa ido, ya sake zama magidanci, ya tako ya rike hannuna, na ce, "Kai da wane ne? Wa yace maka ina nan?" Ya zaunar da ni a bakin gado ya ja kujera ya zauna dai dai lokacin da Mama ta idar da Sallah.Na ce, "Mama ga Yayana Umar." Ta juyo suka gaisa, su Sagirr suka shigo har da Abubakar. Shi na zuba ma ido tamkar wadda na warke makanta. Shi kuwa ya hade rai kamar wanda zai fadi sakon tashin bom. Mama kadai ya gaisar, bai kalli inda nike ba ya ci gaba da karanta wata takarda da aka lika a jikin bango, ta masu gargadin ciwon kanjamau. Hankalina ba ya tare da su, don haka ban san me suke tattaunawa ba, yau wane irin mafarki nake yi? Ga Yaya Umar ga Abubakar? Mutumin da na cire rai da sake ganin shi, ya dawo ne? Ko kuma daman yana nan? Ashe wai a fili nayi zancen, sai na ji Sagir ya ce, "Wa?" Na dube su cike da damuwa ina zare ido. Na kalli Abubakar, "Don Allah ku fadi min ina mafarki ne?" Sagir ya ce, "Hafsa mune muka zo da Umar." "Kun je gidanmu ne? Wa ya kaiku?"Nan take na mike don watsa ruwa na fito na jawo jakar Rahma na murza hoda. Ta ce, "Iye! Har da su hoda? Kina son birge Abubakar." Na ce, "Ina ruwana da shi?" Mama ta ce, "Sauki ya samu ta 'ki saka hoda? Har da kwalli radau kayanki." Na ce to. Sannan na ce Rahma ta dan hada min tea. Lokacin da Sagir ya isa masaukin nasu, ya same su suna karyawa, hira suke yi inda Umar ya basu labarin barin Hafsa gida, ya ce kowa ya sha mamakin faruwar matsalar saboda Hafsa nitsatstsiya ce, ko yawace- yawacen nan na 'yan mata bata yi, bata ma da kawaye, son bokonta ne yasa wannan saurayin ya yaudareta har ya kai ga yi mata ciki, kasan mata da karamar kwakwalwa, idan saurayi na kashe musu kudi babu wuya an yaudaresu. Hashim ya ce, "Labarin da Rahma ta bamu fyade yayi mata shi saurayin." Umar ya ce, "Ta yiwu haka ne, don lokacin da abun ya bayyana Babanmu bai kwantar da hankali an ji yadda lamuran suka faru ba, kawai ya kore su ne." Abubakar ya ce, "Ta bakin Umar ne mace idan tana son namiji ta hadu da Shaidani, to ba zata yi wuyar bada kai ba." Sagir ya ce, "To duk dai komai ya wuce. Allah ya tsare mana zuri'a kuma ya rabamu da rudin shaidan." Ameen ya Rabbi, suka amsa. Ran Abubakar fa a bace yake amma bai nuna ba, a nashi ganin ba wani fyade, ita dai dan tana son shine taje don sakarci ta bashi kanta, har saida yayi mata ciki sannan za tace yayi mata fyade, dan ta kare kanta ne kawai, wa ma yasan adadin kwanciyar da tayi da shi. Ya ja tsaki.Sun shigo ina shan tea, na ajiye ina kallon Yaya Umar na ce, "Ina kwananku?" Suka amsa amma ban da Abubakar wanda ke latsa wayarshi, a raina na ce, "Mutumin nan fa har yanzu bai huce ba." Na dubi Yaya Umar na ce, "Ina Baba da su Baaba?" Ya ce, "Suna nan... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-03 Posted by ANaM Dorayi on 09:35 PM, 27-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya ce, "Suna nan, Baba ne dai ba lafiya, ya fi shekara baya fita." Idanuna suka ciko da kwalla na ce, "Allah ina zaton halin da na saka su a ciki ne ya sa shi rashin lafiya." Umar ya ce, "A'a lalura ce kawai." Na ce, "Ina Ummi?" Ya ce, "Ummi ta yi tsawo, sai kin ganta." Na ce, "Inna fa?" Ya ce, "Inna tana Funtua." Na tsura mishi ido, "Me take yi a can? Ko suna da dangi ne?" Ya ce, "A'a, tayi aure can da Yaranta ma 2." Nan take na dafe kirji, kuka ya kuma kwace min na ce, "Ban yiwa Iyaye na adalci ba, sun soni, sun min dukkan abinda iyaye kewa dansu daidai karfi, amma ni sai na tarwatsa su." Yaya Umar ya ce, "Komai mukaddarine kada ki damu." Tsaki Abubakar yayi tare da tabe baki, ni dai na kauda kaina gefe. Likita ya shigo a nata 'yan hirarraki ya bani sallama. Daga nan Sagir ya kwashemu mu 6 banda Abubakar, don yace muje kawai, muka fice zuwa gidana. Mama dama ita bata shiga ba gidansu ta wuce, sai ga Shadad ya rugo da gudu, Mama ta ce mishi na dawo shine ya taho. Mama tana barinshi gida ne saboda rigima da yake yi a asibiti, ya fada jikina yana min oyoyo Aunty. Umar ya zuba mishi ido, shi kam sai yanzu ya tuna fa ashe da ciki na bar gida, ya ce, "Dan da kika haifa kenan?"nace shine, sunansa shadad, idanuna suka soma kawo ruwa, nace jeka gurin kawunka, yamike yaje gurin umar, umar yace tabbas wannan dan munnir ne, kamarsu ta baci, kinga ko dolensa ya amshi danshi, nace ai yaya wlh baxan bashi yaron nanba, koshi ya bukata, inkuma kunsan zakuce in kaishine tobazan koma gdaba, daganan gabama zanci.... da sauri umar yace, toshikenan anbar maganar, kusan karfe 1 har sagir da hashim sunyi mana sallama, sai kuma gasu sun shigo da kayan abinci, karamin buhun shinkafa ne da taliya, sagir ya mikoma rahma kudi batare da yayi mata mgn ba, yafita. sannan ya kirata a waya, wai tabani inji abbkr ne, amma tace inji sagir, rahma kuwa tabani tace inji sagir, nace kaiba zan amsaba kashe kudin yayi yawa, dubi kwanciyata a asbitifa, tace a'a asbitinki ina ganin hashim ne, na amsa tare da cewa, ko wanene ma dai nagode.Rahma ce tadafa mana abinci mukaci, misalin karfe 3 yaya umar yashirya tafia kd, nace yasakebi ta gidansu maman rahma yayi mata godia, don tun bayan fitarsu sagir na bashi labarin komai, tundaga tafiyata har iyanzu har tsakanina da munnir ban boye masa komaiba, yacemin yana ganin munnir shima a wata jibgegiyar mota lkc zuwa lkc, yafadamin dukkanin abubuwan da suka faru bayan barina gda, nayi kuka sosai, yace karna damu komai yafaru da mumini daga Allah ne, kuma sakayya tana nan tafe tsakanina da munnir, insha Allah sai kowa yagane fyade ya miki, nidashi da rahma mukaje gdansu mama inda yayi mata godia bisa godiya bisa rkon datayimin, yayi addu'a ga likita hindu wadda tamin gata, munayi masa rakiya saiga sagir da abbkr, yace da umar yadan jirashi.suka shigo gurin rahma ashe sallama yayo mata, suka kira umar gefe sukayi sallama dashi, sannan abubakar yabashi kudi tare da tabbatar mishi da cewa tsakanin gobe zuwa jibi iyayensa zasuzo, don haka yasanar dasu, bansan mesuke tattaunawaba, yazo dai yacemin zasu saukeshi a gareji, nace to saimunyi waya, don nakarbi lambarshi, yasoma yakira inna muyi mgn nace mishi a'a baxan iya mgn awayaba, washe gari naje skul, ashe na danji sauki, kuma yanzun na rage kuncin zucia kamar da, ina zaune ina krt wata baiwar Allah tayimin sallama, nakalleta tanamin murmushi tare da sallama, na amsa mata nima cikin sakin fuska, tace nadaina ganinki kwana 2 lfy, naga kindan rame, nace banda lfy ne, har na kwanta asbiti, taxauna tare da cewa eyya, Allah yasauwake, saita danyi shiru daga baya kuma tacemin sunana sa'adatu sulymn, kekumafa? nace sunana hafsa, tacemin inaso muzama kawaye inba damuwa, nace bakomai, mun danyi hira, sannan tatafi, abinda yafi cizon raina yanzu a wane matsayi abk ya ajiyeni? da nayi zaton yabarni har abada, amma sai gashi yazo asbiti, duk dabaimin mgn ba, kuma naganshi a layinmu yazo gidan mama yakira yaya umar, kenan har yanzu yana sona? bari in isa gda in kirashi, ta gidan rahma nabiya, ban boye mata komaiba abinda ke raina, itama ta amince da cewa inkirashi mu gaisa na masa godia, donfa gaskia shine ya nauki nauyin asbitinki, tace, hatta jinin da aka karamin nashine yabada, amma baisan cewa su sagir sun saniba, tace keko shinkafar nan da kudin nan shine yakawo nace sagir ne don kada kiki karba, bayan tayi shiru, sai kuma takara da cewa, abk yana sonki, matsalar karuwancin dakika dorawa kankine, kinsan maxa sunada kishi, kuma gaskia yana kishinki, yakuma ki sauraron kowa cikinsu sagir bare suyi masa bayanin danayi musu, nace, kinbasu lbr komai game dani ne9 tace, sun bukaci nafada musu, shine kawai yaki sauraro, na jinjina kai nace, toba ance shima bashida lfy ba? tace eh, saidaya bada jini ko sallamarshi ba'ayiba, wani sanyi naji cikin raina, jinin abk yana gauraye da nawa? na sauke ajiyar zucia na kalli rahma, anjima zan kirashi, to waima in nakira nace masa me? rahma tace kirashi yanzun, nacije nace to bari nakira, nalatsa lambarshi ta tafi, nace to rahma mexance masa ne don Allah? wayar tasoma ringing, daidai lokacin yana zaune a babban falonsu, yana tare da wasu daga cikin danginsa sunzo dubashi, aciki harda fadima, ya kalli number dake jikin wayar, tamkar yashare, amma saiya kasa, don lokacin ma itace azuciyasa, ya amsa sallama ta bayan ya daga wayar, na kalli rahma mexance? ( amma da hannu nayi mata alama) ta harareni, ku gaisa mana, ta fada a hankali, nace ina yini, ka isa gda lfy? ba zato naji yaja tsaki, sannan yakashe wayar, na dubi rahma nace, tsaki yaja sannan yakashe, tace duk kece kika jama kanki, yaxa'ayi ki dora ma kanki halin daba nakiba? nace magana zarar bunu, na riga nafada ta fito bamai iya maidata, wasu zafafan hawayen son abk tsantsa suka soma sulalomin, ina sonshi rahma, idan yabarni dakyar in zan moru, bansan hakaba sai bayan dana furta kalmar datajamin tsana a gurinsa, tace kidaina kuka, duk abinda yasamu bawa daga Allah ne, kuma abk yana sonki, na tabbata zai aureki, na sauke ajiyar zucia tare da share hwy, koba gaskebane zancenki nadanji sanyi, kitayani da addu'a, rahma tace, tuni nake tayaki, nace ngd, Allah yabar zumunci, bari inje in dauko shadad in wuce gda, nasan yana jirana, tace to saimunyi waya, na daukoshi sannan na nufi gda, raina cunkushe, kunnuwana basu daina amsa kuwwar tsakin da abk sadiq yaminba, duk da tsananin son danake masa amma baxan juri wulakanciba, ban taba tunanin wata rana zatazo da namiji zaimin hakaba, domin banmayi tunanin cewa zan kalli namiji a matsayin mutum ba, tun bayan abinda munnir yayimin, ina yan aikace aikacena, lkc zuwa lkc inajan tsaki sbd abinda abk sdq din yayimin, dakuma tunanin cewa nidashi mun rabu kenan? Sallamar mamansu Rahma naji nafito daga kitchen ina amsawa turus na tsaya na tsaya ina kallon matar da suke tare, itace ko kuwa dai mafarki ne? bakina ya furta Inna! sai kuma na juya daki da gudu na zauna ragwaf,na kifa kaina cikin cinyata, kuka na saki wanda ya farkar da shadad daga bacci Mama tace ji wani sakarci shigo daga ciki" ta umarci inna,inna ta shigo ta zauna itama ta zauna shadad ya taso yazo ya dafa bayana yana son yayi kuka yana cewa Anty wanene ya dukeki? mama tace kyale wannan antyn taka mai kukan tsiya harsai an doketa? mama ta ci gaba to wannan kukan na menene? inna tace na rashin son gani nane, don haka ma yanzun zan tafi Da sauri na fada kanta ina cewa inna ki yafeni inna ban kyauta miki ba, inna na tuba natuba" inna kawai sai tasa kuka, mama tace haba maman hfsa, yaya kuma zaki taya ta?Da kyar ta lallashe mu. Na kasa hada ido da inna,duk da dadin da naji na ganinta. shadad na zaune a cinyarta, muryata a dusashe nace "yaya umar ne ya kawoki? tace ehh shine amma ya juya sbd suna da bakin da zasuje kd din gobe. Lkcn da muka zo kina mkrnta, shine yace bari ya kaini gdan maman taku" Na sauke a jiyar zucia, ina su kawu?tace kowa lpia. ina nan ina malumfashi kika ki nemanmu shekara da shekaru? Ina cikin bakin cikin kunan rai yanda kika gudu yafi bata min rai abisa cikin da kikayi. abinda ya kona min rai dake kenan Allah yasani hfsa banso kika guje min baNace inna bazan iya hada ido dake bane abnda kike min fada akanshi kullum na kiyaye ban kiyayeba. Amma wlh ba da gangan na aikataba munir fyade yamin ta karfi inna " inna tace umar ya fada min komai,Allah zai fidda ke ta shafa kan shadad Allah yayi maka Albarka ya tsareka da hali irin na munir, shi kuma Allah shine yasan yadda zaiyi da shi, mama tace komai dama mukaddari ne ga bawa Allah ya shige mana gaba. sannan game da yaron nan mai sonta kuyi mata fada,dan mutuncine tayi auranta tare da yin karatunta adakinta. Aure da haihuwa basa hana neman ilmi, yanzun baga rahma ba! da bamu bata goyon bayan taci gaba da karatu ba Amma yanxun da tayi aure mijin yace shifa matarsa fa makrnta zata koma, Nace dama rahma nason karatu gashi ta samu" mama dai ta tafi gda ta barmu. ranar kwana mukayi hira nida inna hirar bayan rabuwa, munyi kuka mun gaji. Da safe muka je makaranta nida shadad muka bar inna,duk wanda ke makarantarmu yau yasan ina cikin farin ciki, shi kuwa Abbkr lkcn dana kira dinnan ya min tsaki, yana kashewa ya mike ya nufi dakinsa ya kira umar suka gaisa. yace, umar don Allah idan iyayenmu sun zo gobe kada ka bar wata baraka da zata nuna cewa yarinyar nan ba a gda take ba" umar yace To insha Allahu ba wata matsala yace sannan ku amshesu da karamci suna son haka" umar yace insha Allahu, haka nan da dare suna tare da hashim yana sake fada masa cewa "Don Allah in sunje kada ya bada wata kofa da Za a gano yarinyar nan ciki tayi" hashim yace Haba nawa, Insha Allahu komai zai zo da sauki, ka kwantar da hnkalinka, babu wanda zai fahimci komai, Tunda yaya umar ya dawo daga kano ya sanar da baba zuwan baki, don haka baba yace ya kira masa Amininsa Malam garba da malam mamman. suna zuwa ya shaida musu komai,suka ce To insha Allah goben bazasuyi nisa ba, sannan sukayi masa murna da dawowar yar'sa HAFsat.Sun shawarta a amshi bakin A shagon gdan malam garba ,don yana da girma,don haka tun ranar yasa ya'yansa su gyara shi,umar kuwa kaji ya siyo da cefane akayi sa'a matarsa murja tana 'yan karance2 ltattafai don haka taiya grki. ya siyo lemuka kaloli aka zuba a ckin frdge.tun safe Babah ta kimtsa baba,yanxun ma yakan dan kokarta wanka da kanshi tun baya n da akaga hafsa ta fito masa da kayan sallar da umaryayi masa lkcn yana cikin ciwo bai sasu ba, yar ciki da malum malum yasaka an shimfida manya manyan tabarmi. umar yakawo chines carpetdinshi aka shimfida. Babah kuwa harda turaren wuta ta zuba a kasko tace akai shagon da za a sauki baki,Tun asubahi Abbkr ya rbuta txt ga baffa sa'adu, bayan gaisuwa ta girmamawa yace"Baffa ina fatan zakuyi hkri da yanda zaku samu gdansu hafsa, ina nufin talakawane.Da fatan wannan ba zai zama matsala ba,ka yafeni innayi rashn kunya" murmushi baffa yayi lkcn da ya karanta sakon,yayi kiran layin Abbkr. ckin grmamawa ya dauka tare da gaishe shi ,Baffa yace "Hamma kada ka samu damuwa, talaka da mai kudi duk dayane a gurn Allah,in talaka yafi mai kudi tsoransa ma to yafi mAi kudi agurinsa, Lura da cewa kudi ba komai bane face jarabta,duk da mafi rnjaye cikin zurarmu masu kudine amma muna da talakawan,so kada kadamu" Abbkr yace, Na gode BaffA Allah yakai ku lpia ya dawo da ku lpia" shi kuma yace ameen, shi yasa yake son baffa sa adu akwai saukin kai ba irinsu Baffa magajiba. Hashim yazosunyi sallama a inda ya sake sanar da shi damuwarsa, bayason suji cewa tayi ciki, ko ta bar gda,Hashim yace kada ka damu" tun da suka tafi yake cike da fargaba,tafiyarmaitsawo ce tsakanin yola zuwa kd. duk da sammakon da suka doka sai kusan mmagrb suka iso, don haka baFfa sa'adu yace da hashim bari ya kira amininsa dake zaune kd don su sauka gurinsa. washe gari sai su shiga gdan da suka zo,Hashim yace to. A nan take baffa ya kira abokinsa, basu samu matsalaba don yace gashi nan zai zo ya taho dasu da kansa. direba ya jawo shi har zuwa by-pass,shi ne ya gano su dai dai inda yace su tsaya. baffa da abokinsa sunyi murna da ganin juna,don sunfi shekara goma basu hadu ba sai dai waya sbd yanayin aikin kowannensu, Tare suka yi karatu a jami'a (ABU) a gdan shi da ke makarfi road ya saukesu a sashin baki, umar ya kira HAshim yace to "to yanzu ya zamuyi da abincinku? ko ka sanar daniunguwar da kuke sai na kawo maku"Hashim yace makarfi road dai naji ance amma bari in tmbyi yaran gda ya fada wa su baffa sai baffa yace.To ba laifi, in ankawo din dama su nan ba su san da zuwanmu ba,Baffa ya sanar da abokinsa sai yace haba dai su barshi yanzunnan za a yo musu take away, Yace a a bari dai su karboan nan take hashim tare da direban gdan suka nufi layinda hashim ya fada masa ashe babu nisa, umar ya fito suka gaisa,sannan ya fito musu da kulolin tare da samiru har da kayan shaye2 marmari masu dan dano, Baffa magaji yace ashe babu nisa da nan?sai da sukayi sallah sannan suka zauna zaman cin abncin. duk da babu wanda ya furta koMai amma kowa ya yaba wannan sauka tare da dadinn grkin, sunci sunyi kat har sun rage. nan gdan ma matar gdan ta gabatar musu da ciye ciye, sun dai dan taba sannan yace hashim yaje gdan dansa munir ya hada shi da direba yace ya kaishi shi can. sannan su baffa su ka zauna zauna zaman hira. inda abokin baffan yace sai kaji rasuwar 'ya'yanka ko? baffa yace suwa? su munir? yace a'a su bashir, banayi maka txt ba? baffa yace subhanallah, wlh ban ji ba,banga kuma txt ba duk tsawon lkcn nan ,baka ga banyi maka ta'aziya ba,tun yaushe ne? yace sun kusa shekara 2 baffa yace Allah ya jikansu hadari ne? yace a'a kasan yaran nan da rashin jin mgna can ne a malesia gurin karatu suka yi ri gima suka harbi junansu,yanzu saidai munir kadai, baffa yace auzubillah Allah ya yafe musu,mukuma ya kyautata tamu. Daddy ya ce Amin, Baffa ya ce, "Shi yasa fa nafi son mu dinga barin yaranmu suna karatu a gabanmu, saboda irin wadannan matsaloli shaye-shaye da harbe-harbe bashi da amfani gurin matasa, ba 'afi mu jami'oi ba, amma sai mu dage mu dinga raina namu, mu daukesu mu fita da su ba maisa muna ido a kansu, mu tura musu kudi, kuruciya tana dibansu, dole ne su ringa sheka ayarsu san ransu." Dady ya ce, "Nima sai yanzu na gane haka, kaga shima Munnir din gurin bin matanshi yanzu haka yana fama da (HIV/AIDS), matan ne kawai na tsira da su." Baffa ya ce, "Allah ya kyauta. Amma ya kamata mu farka, boko tana da kyau matuka, amma mu daina sakin 'ya'yanmu sakaka saboda tana da nata illolin, mu tsaya mu gyara skul dinmu na gida, kuma mu bar 'ya'yanmu su yi karatunsu a nan a gaban mu. Haka zai basu damar ci gaba da karatun addininsu, muna yin wani kuskure." Dady ya ce, "Wane iri?" Baffa ya ce, "Muna fifita boko kan na Islamiyya." Baffa Magaji ya ce, "Sosai kuwa, in ka yi la'akari irin kudin da muke kashe wa karatun boko, Islamiyya bama kashe mata, duk da cewa kudin Islamiyyar baifi kudin takardun Bokon ba, sai muke kyashin biya." Baffa ya ce, "Kuma in munyi kokari sunyi wannan 'yar saukar ta zamani shikenan sun gama, maimakon nan ma mu dafa musu su ci gaba."Dady ya ce, "Um!!! ai nayi kuskure Sa'adu sosai, don kuwa Bokon zalla yarana suka yi, sam ban damu suje Islamiyya ba." "Kash!!!" Inji Baffa Magaji, "Kayi kuskure, Allah fa baya turo mu duniya mu yi boko bane, ya turo mune dan mu bauta masa, to baku nemi ilmin bauta masa din ba bare kusan yadda zaku bauta masa din, don Allah kayi kokari har kai kanka ka shiga Islamiyyar manya." Baffa ya kara da cewa, "Ubangiji ya umurcemu da mu kare kanmu da Iyalanmu daga wata wuta, to Basu san Allah ba, ba ka koyar da su yanda zasu bauta masa ba, kenan kare su daga wannan wutar ba. Wadda aka ce makamashinta mutane ne da duwatsu." Haka dai sukai ta masa fatawa har yace ya gane kuma zai gyara sosai, zan dauki malami harda ita Mominsu ana koya mana. Baffa Magaji ya ce, "Da kuwa ka kyauta."Dady ya ce, "Sa'adu danka ne zai yi auren?" Ya ce, "Eh dan kanina ne, suka hadu da ita a Kano tana Makaranta." Dady ya ce, "Yaushe kuka soma auren waje?" Baffa ya yi dariya ya ce, "Wannan ne karo na farko." Dady ya ce, "Lallai to, shi wannan dan gurinka ne naga kuna kama?" Ya ce, "Hashim dana ne, shi tuni yana da Iyalansa harda 'ya'yanshi." Dady ya ce, "Lallai kaji dadi, nima dana bar wadan can sunyi aure yanda suka nuna min suna son auren, aida tuni ina da jikokina., to me zai hana ga yara nan cikin 'ya'yanka Sa'adu a samu wani ya duba?" Baffa ya ce, "Ai kusan duk wadanda suka isa auren suna da matansu, sai dai nan gaba in Allah yasa da rabo." Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-04 Posted by ANaM Dorayi on 06:15 AM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Shi kuwa Hashim da suka je gidan Munnir yaron Dady yana kallonshi gabansa ya fadi, domin suna matukar kama da Shadad, a ransa ya ce, "Ko dai wannan ne Munnir din da yaci amanar Hafsa?" Sai yaron Dady ya cewa Munnir Dady ne yace na rako shi nan, wai dan aminin nan nasa ne na Adamawa. Munnir ya ba Hashim hannu suka gaisa, sannan ya ce da direbaa ya tafi, su kuma suka shiga.Matar Munnir wadda ya kira da Baby ta mike ta ce, "Angel bako muka yi ne?" Ya ce, "Eh." Suka hada ido da Hashim ya yi sauri ya kawar da kansa gefe, domin tana sake da gajeren wando da ya dame shape din mazaunanta, da kuma karamar riga da ko cibinta bata sakko ba, ga wani karin gashi buzu-buzu, kumbarta duk farata zako-zako. Hashim dai a ransa ya ce, "In dai wannan ce wayewa to gaskiya bata da wani amfani." MUnnir ya cema Hashim, "Ga matata Hasina." Itama ya ce mata, "Ga Hashim dan abokin Dady na yola." Suka ci gaba da magana cewa daman ku ne Dady yaketa bani labarin Yola yana da amini, amma saduwa tayi wuya? Ya ce, "Wallahi, haka ne daman." Hashim dai a dadare yake saboda sam ko ruwa ya kasa sha, kyankyamin farata da gashin Hasina yake, da ya gaji dai ya ce masa yana so ya huta, shine ya kaishi masauki. Yana shiga ya fada toilet domin watsa ruwa, sai da ya gama sannan ya kunna wayarsa saboda Abubakar, ai kuwa yana kunnawa sakon Abubakar ya fara karo da shi na cewar sun isa lafiya? Kuma ya yi masa bayanin yanda ake ciki.Ai bai gama karanta sakon ba sai ga waya daga Abubakar, ya daga tare da Sallama, Abubakar ya ce, "Iskanci ne ya saka kashe waya ko me?" Hashim ya ce, "Na sani saboda kai na kashe, domin zaka dame ni." Abubakar ya ce, "Ai hankalina ya fara tashi saboda ina tunanin likin da nai ya balle." Hashim ya ce, "Ko daya, domin ko gidan ma bamu je ba." A nan dai ya gaya masa yadda aka yi. Abubakar ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Shi kenan, sai Allah ya kaimu. Pls abokina ka tsare komai." Hashim ya ce, "Kai Malam sa Allah a ranka." Abubakar ya ce, "Da kai na sa a ran? -ya ce- Pls ka dan yimin kokari nasan zaka iya komai." Washegari misalin karfe 10 na safe bayan sun karya, sun kintsa Hashim ya kira Umar cewa suna tafe, nan take ya iso gidan Babansu, Umar ne yayi jagora har shagon da za'a karbe su, sun gaisa cikin mutunta juna inda suka nemawa Abubakar auren Hafsa akan sadaki dubu 10, sannan suka sanar dasu Matan 2 zai aura nan da kwana 23, don haka suka ce ahada Iyayen Hafsa. An yi komai cikin mutunta juna, sai dai suka fito Dady ya ce, "'Yar talakawa haka? Ai da kun sani kun zo gidana kun duba." Baffa Magaji ya ce, "Kai yaron nan da rore- rore yake, dubi Anguwan nan kasan talauci yayi katutu a cikin ta." Baffa Sa'adu ya ce, "Tarbiyyarta ya yaba, sannan na fada muku gwagwarmayar da akai akan auren nan da yakin da Abubakar yayi, don haka kawai ku bar zancen nan. Allah dai ya shige mana gaba." Suka ce Ameen Koda suka dau hanya Hashim yana ta yaba musu halayenta, lokacin da Abubakar ya kira Hashim sun yi nisa a titi, ya ce, "Hashim yaya?" Ya ce, "An gama komai, muna hanya yanzu, an baka auren Hafsa." "Masha Allah." In ji Abubakar, yanzu kam baya da wata matsala. Ni kam zuwan Inna gurina ya dawo min da farin cikina ta wani bangaren, musamman ma dana dawo school na samu har girki tayi mana, sai da nayi kukan dadi, gashi yau ina cin abincin Innata, ashe zan sake cin abincin Inna ta? Kwananta 3 Umar ya zo suka tafi, sannan ya sanar da ita zuwan Iyayen Abubakar.Hafsa ta ce, "Yaya Umar ya fa fasa aurena, me zaya kai Iyayenshi gidanmu?" Umar ya ce, "Kawai abinda zan fada miki shine kibi Iyayenshi, sannan ki amince masa ki rufawa kanki asiri, mutum ne nagari dan mutunci, mafi yawan Mazan yanzu suna yin auren tamore ne, basa bin abinda addini ya ce, ka aureta dan addininta, nasabarta, dukiyarta, kyanta, wannan samun Abubakar sai an tona." Inna ta ce, "Samun miji kamar Abubakar dace ne, dan haka ki nutsu." Suka min nasiha suka tafi, sun barni cikin kewa, nan da nan naji kaunar gidanmu ta isheni, don haka na hada kayana da cewa wani satin zan tafi Kd. Gidan Maman Rahma na kai Shadad, ni kuma na tafi, a hanya gani nake KD tafiyar tamin nisa, ganin nisar hanyar na yi, tunda na zo garin ban kuma bin hanyar ba. Ina sauka tashar Kawo na samu motar anguwarmu, ina shiga layinmu na ga canje-canje daban-daban, na yi Sallama a gidan aka amsa. Wanda suka sanni suka fara fadin, ""Hafsa ce yau a gari?" Sai suka shiga kallon kallo tsakaninsu, wasu suka fara shiga daki kai gulmata na dawo. Baaba ta fito da gudu ta rungumeni, sai naji wasu suna cewa, "Wannan ita ce Hafsan?" Labarin duk ya bazu cewar na zo, ana ta min sannu da zuwa, naga yara kanana da na tafi na bari duk sun girma, abubuwa duk sun canza.Dakin Baaba na shiga muka gaisa, nace mata ina Baba ta ce, "Yana dakin shi, sha ruwa ki je ku gaisa." Na tashi na shiga wajen Baba, ina zuwa naje gare shi ya ce, "Hafsatuna ke ce?" Na ce, "Ni ce Baba, kayi hakuri ka yafe min, nice duk na jawo muku." Ya ce, "Hafsa laifina ne da nayi miki baki, da ace ban miki baki ba da haka bata faru dake ba, maimakon nasa miki albarka akan abinda zaki yi sai na biki da mugun fata, na yi da- na-sani, tunda na koreku bani da kwanciyar hankali, lafiya bata isheni ba, ki yafemin Hafsatuna." Sai kuka shima Baban, itama Hafsa sai kuka, ta ce, "Ka yafe min Baba." Ya ce, "Na yafe miki 'ya ta.Na ce masa, "Baba ya jiki?" Ya ce, "Jiki da sauki, daman akwai ciwon rashinki, amma yanzu gaki kin dawo Alhamdulillah." Na sauna na ci abinci cikin jin dadi da ganin gidanmu, na kira Umar nace masa na sauka lafiya, ya ce to yana nan zuwa gare ni. 'Yan gulma an fara shigowa gana Hafsa wai ta dawo, akwai wata kawar Innarmu sai gata ta zo, "'yar nan ke kuwa mai yayi zafi haka zaki tafi kawai a wayi gari baki nan? Ina kika tafi? Ina cikin da kika tafi da shi? Me kika haifa?" Raina ya baci da tambayoyin ta amma sai na ce mata, "Yana can inda yake yaron." Baba ya ce, "Tabawa ai komai ya wuce tunda ga Hafsa gare ni, kuskure ne aka samu." Ta sake cewa, "To yanzu ina ki ke?" Cikin kosawa na ce, "Kano kuma karatu nake yi." Maza na shiga kiran wayar Rahma don bana son wadannan tambayoyin, na kara wayar a kunnena ina ji tana cewa, "To gun wa kike? Kuma duk tsawon lokacin nan baki yi aure ba?" Na yi mata shiru, Rahma ta daga na ce mata ga Babana, ta ce haba? Na ce, "Kina shakku ne? Gashi ku gaisa." Na mika masa tare da cewa, "Rahma ce wadda nake tunanin ka samu labarinta a gurin Umar." Ya ce, "Kwarai kuwa, mutanen arziki." Suka gaisa, daga nan na tashi na koma dakin Baaba, na bar Tabawa nan zaune tana damun Baba da tambayoyi, anan ne yake fada mata cewar zanyi nan da lokaci kankani, ta fito tana cewa, "Abu yayi dadi, ai gwara tai auren." Ta fito tana maganar, matan gidan suka ce ai gwara auren ina amfanin zaman bariki? Su a zatonsu yawon dandi nake, raina na ce kanku ake ji Lokacin da nazo fita ni da Faty zata rakani gidan Yaya Umar, ina jin Ade tana cewa, "Duk yanda aka yi dan Bariki ne irinta, ko kuma kara da kiyashi za'a yi." Asabe ta ce, "Daukar mara sani kenan." Na wuce ban tanka musu ba. Gaskiya Baaba mutum ce domin bata shaida musu batun aurena da zuwana ba, gidan Yaya Umar na kwana, da safe na zo gida Ummy ta makale min dan itace wadda muka shaku, sauran kuwa basu dokin zuwana, domin an gaya musu nice sanadin tafiyar Innarsu, Ban ga laifinsu ba don kuwa ni ce naja musu, duk zancen da muke da Baaba da Baba tare da Yaya Umar, duk magana ce akan na daure na yiwa Abubakar halacci, na rike shi amana, dan mutum ne mai sona, yayi jihadi a yadda nake ya aureni, har suna cewa samun kamarshi sai an tona. Sai nake tambayar kaina, "To wai saninshi suka yi suke masa haka? Ko kuwa zuwan da yayi ne suka yanke masa wannan hukuncin?" Haka na shirya na koma Kano, inata karatu da zuwa aikina. Wata ranar Juma'a ina zaune gaban computer ina latse- latse na gurin aikina, kawai sai naga Manaja ya miko min doguwar takarda, na ce, "Me ya faru?" Ya ce, "Masu gurin ne suka buka ci a sallame ki." Na ce, "Ni kuwa me nayi za'a sallame ni? Me nai musu?" Ya ce, "Wannan kuma sai ki tambaye su." Na ce, "Shike nan." Na tashi nayi bankwana da su Musa.Gidan Rahma na je da kuka na, dan aikin da nake ji dashi yake rufan asiri an tsigeni akai, dariya ta saka min wai gurin fa na Maman su Abubakar dinki ne. Na ce, "Ai nawane ma Abubakar din?" Ta ce, "Eh mana, jiya ya zo nasan dai kun sasanta." Na ce, "Ni ban ganshi ba."Cikin mamaki ta ce, "Bai zo gurinki ba?" Na ce, "Ban ganshi ba." Ta ce, "Dazun nan yayi sallama damu ya koma." Na ce, "Um, to don Allah a haka zaka auri mutum?" Rahma ta ce, "To har bikinku ya kusa don haka sai ki soma shiri." Na ce, "Rahma abubuwan da suke faruwa a kaina tamkar a mafarki, to yanzun auren dole za'a min ko kuwa? Ban san komai ba akan auren." Rahma ta ce, "Saura sati 2." Na ce, "Um!!! Ni dai zanga ikon Allah." Ina zuwa gida na tarar an canja min kwadon kofata, na yi turus! Na jiya na nufi gidansu Rahma, cikin fara'a Mama ta tareni muka gaisa, ta turo min kwanon danwake tana cewa, "Maza ki ci mutumin naki." Na ce, "Mama ba ta cin danwake nake ba, na zone naga an canjamin makulli." Ta ce, "Yaron nan Abubakar ya kawo, ya gaya min ai kunyi sallama ko?" Na dubeta ina so na fahimci Abubakar ya zo ne? Ta ce, "eh, harma ya bani dubu 2 kyayi masa godiya ma." Na ce, "To, amma nifa ban ganshi da idona ba." Mama ta ce, "Ya hausar baki ganshi ba? Ya ce min kun zanta yanda bikin zai kasance saboda lokaci ya kure." Na ce, "To bansan an yi ba." Mama ta hauni da fada, wai in dai nutsu ina sone in kishi. Na dai ce a bani Makulli, ta bani na nufi gida na bude kofar, buhun shinkafa ne karami sai sabulun wanka da na wanki, sai kayan tea da kudi dubu 5 na gani, sai takarda akan kayan, ga abinda takardar take cewa, "Na san cewa kin san komai game da auranmu dake gabatowa, wadannan kayan abincinki ne, na san zasu isheki kafin bikin, sannan na haramta miki zuwa gurin aiki, Makaranta kawai na aminta ki je."Duk son da nake yiwa Abubakar sai da naji haushi ya kamani, wace irin kaddara ce wannan? Wane irin iko ne Abubakar yake min? A haka zan je gidansa yana min wulakanci? Ni fa Allah ya sani ba zan dauki wulakanci ba. Ni kadai na dinga Jaraba ina mita, daga bisani na yanke shawarar kiransa a waya, sau 2 tana yi tana katsewa yaki dauka, na kara cika dan takaici, na zauna na rubuta masa text, "Ka sani fa bana son ka, sannan ba zanyi auren wulakanci ba, don kawai kana sona saika dinga nuna min iko? Don kasa an sallameni a gurin aiki ko kana takama naku ne? To zan nemi wani, kuma ban ce ina neman taimakoba har da zaka kawo min abinci tare da karfin halin canzamin kwadon kofa." Ina kammalawa na tura masa sakon text din, zuciyata cike da fushi da takaici.yana jin shigowar sakon amma bai duba ba, domin yana zaune gaban Dadarsu, yana so yayi mata batun dake tare da shi, ta ce, "Ina jinka." Ya ce, "Daman Dada ina so nayi magana ne akan kayan lefen da za'a kai, inaso idan naje Dubai na karo wasu." Dada sai ta saki baki kawai tana kallonshi, lallai Abubakar ya zo da sabon salo, sai ta ja tsaki ta ce, "Kai yanzu yaron nan har kayi girma da kudin da zaka zo kace zaka hada kayan aure? Ka manta kenan duk abinda Lamido yake yi kai bai ma be kenan? Sanin kanka ne duk wanda zai yi aure a cikin zuri'armu Lamido ne yake mishi komai, shine ni zaka zo kace wai zaka yi wani kaya, to shike nan kaje kayi amma ba da yawuna ba, kai baka da tunani ne? Wace irin yarinya kake nema da kake rawar kafa a kanta haka? Ni dai ba zaka jawon magana ba, ka tashi ka bani wuri."yal tashi jiki a sanyaye, tare da cewa, "Ki yi hakuri." Ya ce, "Kuma duk abinda kuka yi daidai ne." "Sai ka zuba ido kaga abinda Lamido zai yi, shike nan jeka." Yana fita suka hadu da Hashim, yake gaya masa yadda suka yi da Dada, ya ce, "Kaima ka yi laifi, kana so ka jawowa Hafsa tsana a dangi ko? Ka bari kaga iya gudun ruwansu, ai sun san komai a kai." Ya ce, "To shikenan to!!" Tabbas familyn Lamido auren farko yi maka za'a yi, in kuma ka cika zakewa yanzu za'a ce maka rashin kunya, balle Hamma da yayi fice tunda ya dauka 'yar waje (bare). Bayan sun gama magana da Hashim, yana kashewa sai yaga text din, ya bude ya duba ya ja tsaki, ya mike ya zauna bakin gadon tare da dauko wayarshi, nan take ya ga ya dace ya bata amsa don haka ya rubuta cewa, "Ban damu ki soni ba, asiri fa zan rufa miki, in bani ba dinma wa zai auri 'yar gagara? Zancen aiki kuwa, kya iya komawa, baki ji maganar Iyayenki ba ni zaki ji tawa? Kya iyayin duk abin da kike so tunda kina da 'yanci, barikin kenan."Lokacin da sakon ya shigo wayata kuka na saka, Mijin da zan aura ke fadamin haka? Na kira Rahma ina kuka wiwi na fada mata komai, ta ce, "Ki yi hakuri zan kirashi." Na ce, "Kada ki yi masa magana, illa kawai ana daura aure zan kama gabana." Rahma ta ce, "Ki yi hakuri ina nan zuwa." Su da Sagir suka zo da dare, lokacin na idar da Sallar Isha'i kenan, Shadad yana kwance kusa da ni, ko abinci na kasa ci. Suka yi sallama na amsa, suka zauna Rahma ta ce, "Wai mai ya faru?" Na ce, "Rahma duba text din nan." Na mika mata wayar ta karanta, tana gamawa sannan ta mikawa Sagir, shima ya ce, "Ki yi hakuri, wallahi ni nasan Abubakar yana sonki, kiran kanki Karuwa da kika yi shine silar fushinsa." Rahma ta ce, "Kuma yaki ya saurari kowa ya ji yanda abubuwa suka faru." Na ce, "Ni dai gudu zanyi matsawar aka ce yau shine mijina, duk da cewa nasan ina son shi." Sagir ya ce, "In kin gudu me Iyayenki zasu dauka? Wace rayuwa zaki samu a gaba? Kuma zaki sake samun wanda kike so kamar shi? Duk wadannan tambayoyin ya kamata ki yiwa kanki su, sannan ki amsa su duka." Na fashe da kuka, bani da zabin da ya wuce hakuri, domin Sagir gaskiya ya fada min, Allah ka shige min gaba. Rahma ta ce, "Ya zo ne akan batun wane irin shagali zamu yi saboda katin da za'a bugo, na san dai baki wuce Walima ba shiya sa na fada masa haka." Na ce, "Wa na sani da za'a buga kati? Ni walimar ma ba zanyi ba." Rahma ta ce, "Ka jita ko? Shiya sa nake ta gaban kaina, na san ba zata bada hadin kai ba." Sagir ya ce, "Yanzu dai Hafsa a shawarce ki zuba mana ido, naki bine kawai." Na ce, "A'a, kun zo da abinda ya sabama shari'a ba zan baku goyon baya ba." Suka yi dariya, haka suka yita lallashina tare da kare Abubakar har dai na danji sanyi suka tafi, bayan Rahma ta yi delete din text. Ana saura kwana 10 biki, danginsa suka nufi Kaduna da lefe, saitin akwati mai 5 dauke da kaya masu tsadar gaske, Goggonninsa sunyi mamaki gadin gidan da Abubakar ya nemo aure takalawa ne lis, sai dai an karbesu cikin karamci, da kayan abinci da nasha masu kyau wanda Murja Matar Yaya Umar ta yo. Dakin Baba aka share aka shimfida darduma, bayan sun ci sun sha sukai sallah, sannan aka bude kaya. Matan gidan suka shigo sunata yabawa saboda irin wannan kaya haka, daya daga cikin 'yan kawo kaya ta ce, "Ina amaryar ne?" Baaba ta ce, "Tana can Kano tana karatu a can." Umar ya kawo dubu 10 na tukuici tare da cewa su yi hakuri sun gode. Ko da suka dawo sun ce an karbesu hannu bibbiyu, kuma suna da karamci Iyayenta sai dai talakawa ne lis. Dada ta ce, "Shi dai ya sani kuma ya jiyo." Waya Rahma ta kira Sa'adatu ta makarantarmu, take gaya mata batun aurena yadda zasu shirya, sannan ta ce don Allah gobe zata zo har makaranta ta bata kati dan ta rabawa kawayenta. Sa'adatu ta ce, "Allah ya kaimu." Rahma ta dubeni ta ce, "Kin ga illar kin shiga jama'a, wallahi ki canja hali, dan family din da zaki shiga suna da yawa." ...... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-05 Posted by ANaM Dorayi on 05:56 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Abubakar ya zo gurin Rahma ya kawo mata katin biki da duk wani abu da zamu bukata, sai hotuna da yace ta bashi dan can dangin sun matsa a kawo hotuna saboda suna son kalanda da memo. Rahma ta kirani a wata ta ce na shirya zan rakata gidan Matar kwamishinan ilmi, ta ce pls na kure adaka saboda sutura itace mutum. Ban kawo komai a raina ba, na ci kwalliya na saka after dress akai, ita ce da kanta ta ja motar tare da yi mata tsiwar cewar har kin kware da zaki cire (L) din? Ta ce, "Hannuna ya fada kinsanni da karambani." Muka tsaya wani gidan hoto mai kyau, anan ta ce min, "Hoto zamu karba ki shigo." Naje wajen hoton muka shiga, Rahma ta je tai magana da wani mai hoto na ga suna magana amma ban san me suke cewa ba, na dai tsaya a ciki. Da ta zo na ce mata, "Ina hoton?" Sai ta ce, "Wai sun kone sai dai a sake wani." Ina zaune gefe aka yi mata wajen kala 5, ya nuna mata ta ce yayi. Ya ce to nifa? Ta ce, "A'a, Hafsa ai ita bata hoto." Ya ce, "To shike nan." Na ce, "In gani Rahma." Ta ce, a'a ba zan gani ba, muka zauna zaman jiran karba, akai editin dinshi na ce, ka wanke mai kyau sosai fa. Muka karba muka fito. Muna hanya na ce, "Ina gidan Kwamishinan?" Ta ce, "Daman hoto ne, nasan idan nace miki ki raka ni ba zaki ba." Na ja tsaki tare da cewa, "To kai ni gida." Bayan la'asar lis ina duba wani littafin masu fasaha wanda yake burgeni na Ikilima, Shadad na gidan Mama na tura shi dan in nutsu ina son in samu wani abu da zan karu da shi cikin halayen Ikilima. Duk da ciki-ciki ya yi sallamar sai da kunnena ya dauko daddadar muryarsa, hannunsa rike da Shadad, na dan kauda kaina na ci gaba da duba littafin dun da na kasa fahimtar komai a cikinsa. Shadad ya rugo yana cewa, "Aunty ga Uncle." Na ture shi tare da cewa, "Waye haka? Da Allah ni matsa can." Ya bata fuska, "Aunty kin ganshi nan fa." Don kada Shadad ya fahimci wani abu sai na ce, "Sannu da zuwa." Bai amsaba sai ya bata fuska tare da tabe baki, "Na zo ne kawai in ganki, tunda kina lafiya shikenan ni na tafi." Ban motsa daga inda nake ba na ce, "A gaishe su."Ya ciro kudi ya bawa Shadad, "Je ka zauna sai na dawo." Ya ce, "In ka dawo zaka tafi da ni?" Ya ce, "Sai kayi hutu." Ya juya ya fita, na bishi da kallo hatta tafiyarshi ta lafiyayyun maza ne, komai nashi birgeni yake yi. Daidai soron ya juyo idanunmu suka kalli juna har ciki, ya zare nashi idanun ya kalli gabanshi, sannan ya bude kofar ya fita. Na lumshe ido tare da shakar kamshinsa, tsam! Na mike na nufi kofa ina leken shi, ya mike da nufin fita daga layin ina zaton ba da mota ya zoba, na bude kofar ina lekenshi har sai da na dena ganinshi. Shadad na samu yayi wada-wada da kudin da ya bashi, 'yan dari 2-2 ne guda goma, na kwashe su na koma daki na zauna bakin gado ina tunani, damuwa ta ban san zaman da zamu yi ba. Cikin kwanakin shagali na karatowa kuma karatuna na kara daukar zafi, don mun kusa mu fara Jarabawa.Rahma ke shirya komai na game da walima, ana gobe daurin aure na dawo Makaranta wujiga- wujiga, na iske gidana dam da jama'a. Rahma ce da makota har da dangin mijinta suna ta aiki, wasu na wankin naman kaji, wasu na wankin kayan miya. Turus! Na yi yayinda makota suka soma fadin ga AMARSU, guntun murmushi nayi tare da gaishe shi sannan na shige daki, a zuciyata na ce, "Kai su Rahma da karfin hali." Ita kuma sai hada murhu take yi. Ta zo daki ta sameni, "Don Allah kada ki nuna fushi ko wata alama da za'a gane da wata matsala." Na ce, "Wai ni duk ba wadannan ba, a ina kika samu kudin yin wannan shagalin?" Ta ce, "Daga taskar ango." Na ce, "Shagali, Allah ya baku sa'a."Dazu Inna ta kirani tace min tun jiya suna Kaduna ita da danginta, tace min ya kamata na taho." Rahma ta ce, "Mama ta ce gaskiya can ya kamata a tafi, to sai dai mu bar walimar sai ranar lahadi, ko me kika gani?" Na ce, "To ni dai gobe sammako zan yi." Kafin dare an gama suyar kaji an yi miya, duk ta ba wadanda suka tayata aiki. Da duku-duku muka gama shiri ni da Shadad, sai ga Rahma da direbansu, Mama ma ta shirya, Rahma ta ce, "A dibi naman da drink a tafi da su ko?" Na ce duk yanda ta gani, tunda kajin da yawa, sai ta debo sosai, goma daidai muna Kaduna.Allah Sarki Baaba! Ashe har anko suka fitar, gidan cike yake da mutane ban zaci ganin haka ba, ashe Baaba gayya ta yo, dakin Baba nan Inna ta sauka da danginta, na ji kunyar ganin 'yan uwanta, amma ganin basu nuna komai ba sai na saki jikina, suka gaisa da Mama, Baaba ta shigo muka gaisa, ta ce, "Ga fa abincin 'yan daurin aure can nasa a dafo shi a gidan wata mata da ke yin na kudi." Baaba ta ce, "Ko ko za'a sayo 'yan holokon nan ne da dan cokali na robar nan a zuzzuba a ciki?" Na ce, "Oho." Rahma ta mike, "Baaba kin tambayi wannan ita dake jin haushi sai kace wadda za'a yiwa auren dole? Bari inga abincini." Suka tafi. Inna ta ce da Mama, "Baiwar Allah nan tana kokari, Allah ya saka mata da alheri." Su Mama suka ce Amin. Rahma ta dawo tana cewa, "Abinci yayi kyau, ta zuba wadatattun kayan lambu, yanzu bari a dauko naman nan a zuba a kai, na bada kudin take away din." Nan suka zuba abincin da naman kaji, ga drinks, Innarmu ta ce, "To shi Babanku kinje kun gaisa?" Na ce, "A'a." Ta ce, "Yana dakin Malam Garba ki je." Nan na fita, Shadad ya biyoni na rike masa hannu, ina jin lokacin da wasu ke cewa, "Hala wannan shine dan nata?" Ban damu da in juya inga ko su waye ba, na fita. Mun gaida da Baba, ya dauki Shadad tare da cewa, "Muhammadun ne wannan?" Na ce, "Shine." Ya ce, "To Allah ya yi masa albarka." 'Yan daurin aure sun zo ance nan suka kwana gidan aminin waliyyinsa ko?" Na ce, "Eh." Duk da ban sani ba, ya ce, "To Hafsatu, ke dai ba kankanuwar yarinya ba ce, Allah ya kawomu lokacin auranki, don Allah kiyi hakuri ki zauna da Mijinki lafiya tare da ladabi da biyayya, ni dai in kin min haka kin gama min komai." Yayi mata nasiha sosai, ya ce, "To Alhamdulillah, Yayanki Umar shine ya sai miki gado da kujeru daidai karfinsa, Baabarku kuma ita ce ta sayi duk abinda aka dafa, sadakinshi da shi aka sai miki katifa da fuloli. Sai dai Innarki da tace ta zo da kudi sai kin zo za'a shawarceki, nima ta gefena dangi sun zo daga Maiduguri sun bani gudummawa dubu goma ce na ba Umar." Na ce, "Oh Allah! Mai rufawa bawa asiri, Allah ya saka da alheri." Ya ce, "Amin, Allah ya baku zaman lafiya." Na dawo gida na bar Shadad gurin Baba, Innarmu ta ce, "Ya miki bayanin komai ko?" Na ce, "Eh." Ta ce, "To ni nan gurina kawunanki da sauran dangi sun hada dubu hamsin, ni kuma nayi adashi na dauki na dubu sittin, sai na bada hamsin, goma kuwa na basu Ummi saboda anko da suka ce tunda Yayanki hidima ta masa yawa.Sannan ta ce, "Shi kuma Babansu Rabi'u (mijinta kenan) ya bada dubu hamsin, nan dubu dari da hamsin kenan gaba daya sai asan yadda za'a yi da su." Na ce, "Ni dai Inna duk yanda kuka yi daidai ne." Muryata ta soma rawa zanyi kuka, "Ban zaci zaku kula ni kumin wannan gatan ba, dan na riga na watsa muku kasa a ido." Kanwar Innarmu ta ce, "To komai ya wuce Hafsat." Innarmu ta ce, "Kayan kicin zaku je ke da Rahma kasuwa ku sayo yanzu tunda an ce ana gama daurin aure zaku wuce da kayanki." Na ce, "Da an sani ba'a sai kayan anan ba, don tafiya yola da kaya aiki ne, in naje can a siya." Inna ta ce suma sai da aka siya sannan suka zo, amma an ce su zo da motar dibar kaya, dan Umar ya fada ma angon cewa su zo da ita. Na ce, "To yanzun me za'a siyo?" Ta ce, "Ke kika san abinda ya kamata." Na ce, "Tab, to ni ai bani ma da komai tunda Karatu nake yi banyi tunanin auren nan kusa ba." Ta miko min kudin nace Rahma ta karba. Mun fito zamu tafi muka ga Sakina kanwata 'yar wajen Baaba nace ta zo mu tafi. Muka je a motar Rahma nan kasuwar bacci, na sai kayayyaki su TV da kayan kitchen duk na amfanina da su blender da sauransu. Mun kashe dubu chasa'in, ragowar kudn na sai kayan gara dan ma Inna ta yi cincin, dubulan da alkaki. Muka sai shinkafa buhu 2, taliya 3, semi 4 manyan galan na manja da na man gyada 2-2. Nan dai muka kashe kudi, sannan muka nufi gida. Mun samu ana loda kaya wai motar kaya zata yi gaba, don haka Rahma tace ma Yaya Umar ga wasu a saka a tafi da su. Ya ji dadin ganin garar da nayi ya ce, "Dama ita yake ta tunani ina zaya samu kudi ya saya?" Ni kam na shige gida guri tunda ya soma cika.Misalin karfe biyu aka daura aurenmu da Abubakar, lokacin da wata marokiya ta shigo tana rangada guda, jikina yayi sanyi lakwas, yau na zama matar aure, sai dai nayi missing din al'adunmu, kamar sa lalle, kamu, ko fulawa ba'a zana min ba bare gyaran kai. Na watsa ruwa na zo na zira Jallabiyyar cikin akwatin da mayafinta. Rahma ta zo ta sani sai da nayi kwalliya na shafa turare, sannan ta taya ni na zabi sarka da 'yan kunne da abin hannu zuwa zobuna, nan take na yi kyau. Jallabiyyar ta sha ado. Ta ce, "Ki zo ku gaisa da su Hashim da Sagir za suyi Yola, mu sai gobe da Asubahi. Kinge kenan muna da lokaci yau da yamma sai muje muyi gyaran kai tare da yin fulawa.Na ce, "Ke nifa in dai da Abubakar ba zan fita ba don kada ya yarfani a cikin mutane." Ta ce, "Suna wani shago can da Umar ya kaisu, suna cin abinci." Muka nufi shagon gurin su Hashim, Abubakar bai zo ba Sagir ya soma min tsiya, "Gata ango, gata Ango, cancadin shagali." Hashim ya ce, "Yi ma Umar waya ya turo mana mai hoton nan dole Ango ya ga hoton wannan shiga, sai kace Balarabiyar Sudan Masha Allah!" Na ce, "Kuna dai zagi na ne, kuma na gode." Muka gaisa Hashim ya ce, "Baffanmu sun tafi don Jirgi zasu bi mu kuma da ku Asubanci zamu yi." Na ce, "Gaskiya mun fa shirya Walima a Kano." Rahma ta ce, "To sai dai randa kika dawo kuyi." Na dubi Rahma, "Gobe zamu bar Yola ko? Don ina son yin karatu nan da kwana goma zamu fara zana Jarabawa." Hashim ya ce, "Ture batun komawa Kano gobe don Yola goben ne zamu soma namu biki." Sagir ya ce, "Mu ma sai an gama biki zamu wuce, na fada gurin aikina." Na ce, "Um!" Tunani na daya ban dinka komai ba, waton bani da sabon kaya, Rahma ma tayi wannan tunanin, amma bata ce komai ba lokacin wayar Hashim ta yi ruri ya daga kawai sai na ji ya ce, "Yawwa Munnir, ka shigo layin? In ka shigo layi na 3 din muna nan a wani shago jikin masallaci." Tsigar jikina ta soma tashi, kafafuwana suka yi rauni har na kasa rike kaina, na jingina da bango. Duk sakamakon sunan da naji an kira "Munir." Duk da bani da tabbacin akan cewa wanda na sani din ne. Ban ankara ba na ji muryarshi a kofar shagon yana sallama, numfashina ya yi sama da kyar na kwato shi, yana shigowa gurinmu ya soma jeho idanu shima mutuwar tsaye ya yi yayin da muka kalli juna ido cikin ido.Hashim da bai kula ba fadi yake, "Abinda ka makara, tuni an daura auren." Sam Munnir ya kasa kauda kanshi daga dubana, ban san nufin kallonshi gareni ba, amma ni kallon tsana ce da kiyayya mai tsanani nake masa, zuciyata ta shiga fadi min cewa, "Tashi ki shake shi, wanke shi da mari." Tsam na mike na fice a fusace, Hashim ya ce, "Zo mana Hafsat lafiya?" Rahma ta mike ta kwala min kira, "Hafsat! Hafsat!" Sam ban saurara ba ko ganin gabana bana yi, da ganin Munir gara ganin mai daukar raina. Na share zufa bayan na zauna, sam ban ji me su Innu suka cewa ba, ashe wai ina ta tsallake mutane ina wucewa.Rahma ta zauna tana tmbyata "menene? sai alkcn hawaye suka soma sin tiri akan fuskata. ckin kunnena tasa tana cewa shine baban shadad ko? naji sunansa munir tunda hashim ya ambata" Ban tanka taba, sai da nayi kukana ma'ishi, tun mutan dakin suna tmbyata har suka hkra. Rahma tace, fada min idan shine' nace shine me zaki masa? ta mike nace koma ki zauna" tare da riko ta. Na sauke numfashi Rahma barshi, abu daya nake son san menene dangantakarsu da abbkr? indai yan uwane to fa in sama da kasa zasu hadu ba zan zauna da shi ba, Rahma tace daina msalin nan babu kyau yanzun ki bari zan kirasu gashim anjima Na ce ki barsu kawai zan bncika a sannu, sukam su sagr mamakin hafsa ne ya cika su,sai dai shi hashim ya zargi wani abu.Lallai shadad yana matukar kama da munir ya dubi munir wanda ya kasa zaunawa yace zauna mana ranka ya dade, ga abnci, munir ya zauna bayan ya ciro hankici yana share zufa,sagr ya mika masa hannu suka gaisa, haka ma hshm. Nan dai suka juya hira,ya nuna sagr "wannan ne angon? Hashim yace a'a yana yola, kasan na fada maka mata 2 zaya aura. shadad na rike a hannun yaya umar, dawowarsu kenan daga gdan yaya umar din. yace kawu bari in je gurin antyna, tana can dakin? umar yace "Ehh don shigarsu dakin ne yAya umar ya fita shi da shadad sai yanzu suka dawo. ya shiga da sallama jikin sagr ya nufa yana me fadin Uncle ina antyna? sagr yace tana gda. munir ya tsurama yaron ido,gabanshi yana wata irn faduwa ya bi yaron da ido lkcn da yaron ya fita a guje. tamkar ya cafko yaron yakeji don ya sake kallonshi da kyau,ko kuma duk cikn firgicin ganin hafsa din ne? ya mike cikin tashin hnkali,yace to Hashim Allah yasanya alkhairi, nizan tafi. Hashim yace da sauri? munir yace em inada dan wani uzurine, suna fita yi masa rakiya sai waiwaye2 yake,ya shiga motarsa ya tada tafe yake yana zantuka shi kadai, tmbayr kansa yake" shon wannan yaron mai matukar kama da shi dan hafsa ne? cikin sane kenan ta haifa?a fili yace lallai zan amshi dana dubi yanda kaunarsa ta zirga ckin jinina,amma kuma.... ya doki kan styarin motar tare da cwa tab nasan za'ayi rigima,yanxun wama zan tunkara da wannan magnar? tunda iyayena ba wanda yasan zancen? ko gdansa yakasa zaune da tsaye,duk ya damu gashi badama ya fadawa matarsa. sai dai ya yanke shawarar dadynsu da zancen, Nikam ban da tursasawar Rahma bazan yi wani lalle ba,amma haka tasa sakinarmu da ummi suka nemo mai zanen fulawa ta yarfa min a hannuwa. tasiyo man shamfo sbd anwuce da akwatunana (lefa) dama kayan dangi daban suka kawo wai suddaje. don haka ba'a taba nawa ba,tayi min don tayi tayi nace bazani saloon ba, na manta da wani abn takaicin da rahma tamini tarkacen mata ne wai sai nasha. Nace matama gwara takwashe tarkacenta inba hakaba zatayi asarar kudinta, don zubarwa zayi, tace gashinan cikin jakata in naso naje nazubar, inkuma na shirya sha to inkirata taimin bayani yadda ake amfani dasu, nace kanki akeji, gdan yaya umar mukaje kwana, sam na kasa bacci, gaskia bansoba naga munnir sai naji nakara tsanar maza, Allah ya sani indai dan'uwan abkr ne toba zan zauna cikin zuri'arsuba, ke amarya tashin manta doguwar tafia ke garemu? Wanka kawai nayi don ina fashin sallah, na kintsa jikina sosai muka fita tare dasu ya umar, ummi da matar ya umar duk tare zamu tafi dasu, dangin inna duk tare muka tafi dasu, nida sakeena da rahma a motar hashim da sagir, harda shadad aka tafi, lallai yola akwai nisa, tun muna tafia ina hira har nai bacci dan bantaba doguwar tafia irin hakaba, bamu isaba sai gaf da magrib, tunda karfe 6 na safe, kuma wai haka dinma sai naji ana cewa munyi sauri, dankareren gate ne muka dosa, sai kace na gdan yari, muna shiga gdan dam da mutane haske ko'ina, mayafi naja na rufe fuskata, lkcn naji gdan yadauki guda anata fadin gasu nan sun iso, rahma ce take rungume dani, har zuwa kofar shiga tace, kishiga da kafar dama kiyi addu'a, hakan nayi, sannan aka zarce dani can dakin, nan da nan zugar dangin suka cika falon, har dakin da nake, sai fillanci ke tashi, daidaikune suke mgn da hausa irin wadda bata goge din nanba. wata ta duko kaina, amarya bude fuskarki muganki, ke kam wane irin kyaune dake har hamma yafita hayyacinsa danke? Na sake sunne kaina cikin cinyoyina, wata tace, nana ke kam baki ganta acikin hotunan kalanda ba? Tace nagani, sonake inganta afili, rahma tace, sai kingaji da ganinta, tunda nan zamu bar muku ita, ankawo kulolin abinci, shinkafa da miya da nama, sai kunun gyada da sauran drinks, suka dan rage nan muka shiga cin abinci, nikam wanka na mike zanyi, bayina acikin dakina yamin kyau, nafito na zura kayan bacci, sukuma suka shiga sallah, rahma tace, shine zakisa kayan bacci? Nace ina naga sabon dinki, tsofaffinma banzo dasuba, na saka katon hijabi, sukuma cikin daren nan suka hau yin jeren dakina, sun saka kujeru a falo ina juyosu suna tababa, anan za'asa, anan zaifi kyau, suka dawo daki suka hada gado, suka dibi na kicin sukaje suka jera wanda shima kenan falon, matsayina na yar talaka amma iyayena sunyi kokaro, suka hau gado suka kwanta nikuma nakwanta kan kafet dan nasaba da kwanan kasa, rahma tazo kusa dani takwanta, sai wayarta tashiga ruri, nace to masoya ga angonki nan, ta fito da wayar tana cewa, yanzun nanfa muka gama dashi, kurum sai naji tana cewa, ango_ango, munyi fushima, baka kira ba muna hanya, mun iso tuni ka sharemu, ina jiyo muryarshi ....... Zaharaddeen shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-06 Posted by ANaM Dorayi on 05:57 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO yana cewa, ai munata yin waya dasu sagir, sun tabbar min kuna lfy, na tabe baki yace, to yaya kuke? Tace lfy, mungama shirya muku komai, gobe asubanci zamuyi gda, yace au, kuna nufin baxaku tsaya ayi budan kaiba? Tace ai mun gama budan kai tunda munkawoma ita. yace to nawa zan fansheta? Rahma tace mekenan? Nima na tashi zaune tare da kara matsowa, sannan na kara kanga kunnena, yace, toni kam bansan yadda zan muku bayaniba, amma zaifi kyau ku tsaya dan kar kubar mata abin gori, kunsan halinku dai mata, rahma tace, to zamu tsaya, sai daifa mu bamusan yanda kuke gabatar da al'adunkuba, sannan amarya bata da dinkakken kaya, yace meya hanata dinkawa? Kodai bata shirya aurenaba? Tunda tun asali bani takesoba? Rahma tace, wannan batun aiya wuce, don dama bata da wanda takeso, zuwankane kakoya mata soyyaya, yace rahma kenan! Ai ina zaton soyyayar da kawarki ta iya niban kai gurinba, amma dai ya wuce ta bakin naki, sannan kuma za'a kawo mata kayan sawa, mu nan garin dama haka ake kai kaya, don amare basa amfani da kayan akwatin sai dai ayi musu a gidajensu, rahma tace, hali keyin haka, mukam talakawa irinmu kuwa lefen muke amfani dashi, ta canza batun da cewa, ina angona? Yace mun saidashi, tace tabdi! Ba'a kake, da kunga gayyar kanawa, don Allah yana kusa banishi inji muryarsa kona samu nai bacci, ya saki daria, na lura kin shagwaba sagir dayawa, shiyasa yadamemu da tadinki, na sulale a hankali na kwanta, da alama bata fahimci abinda yake nufiba, suka gama surutunsu da mijinta sannan sukai sallama da hirar soyyayarsu, dare ya tsala, kowa na kwasar baccin gajia, amma niban dani sbd hakikanin gaskia kalaman abkr sun soki zuciyata, mutsu mutsu nane yatashi rahma, tace a hankali lfy? Nace rahma mekika fahimta da mgnr abkr? tace namefa? Na juyo da cewa, yace damacan bashi nake soba, sannan yace soyayyar dana sani shi baikai gurinba? Lkcn dakikace zuwanshine ya koyamin soyy, rahma tace, kinsan nifa bakoda yaushe nake zama nazarin mgn irin hakaba, amma ke mekika fahimta? Tace wlh rahma koyaya mutum yai zance nasan meyake nufi, inada wata baiwa tadaban akan karantar mutum, ko zolaya yayi ina gane manufarsa, nufin abkr damacan munnir nakeso bashiba, sannan na iya soyyayar da baikai gurinba, to sbd soyyaya nasakarwa munnir kaina har na samu ciki shiko bai taba hakanba, rahma tayi shiru itama ta fahimta, amma don kada na tashi hankalina agane inada damuwa sai tace, kada kiyi masa wani zato, ta yiwu ba nufinsa kenanba, (kai abkr na gasawa hafsa mgn gaskia, yan'uwa kuja mai kunne mana) nace hum! Rahma tuni na hararo irin zaman da zamuyi da abkr shiyasa nake gudun aurena, yanda na fahimci halinsa, shi mutum ne mai tausayi dason kyauta, sannan mai jajircewa ne akan abinda yakeso, wanda bai kaucema addini, sai dai kash! Yanada naci tare da mita idan an masa laifi, sannan baya bincike bare saurare, kinga kozansha wuyar zama dashi in nayi la'akari da irin halayen nan, sannan zai dinga jefamin mgn, hwy suka soma zubomin tare da sintiri afuskata, Rahma tace, duk wannan hasashen nakine, don haka kibar mummunan zato a kanku, kiyi fatan alheri, nace to Allah yaxaba mana mafi alheri, sai kusan assalatu sannan nasamu bacci ya daukeni, da safe karin kumallo mai kyau mukayi, kunun gyadane da lafiyayyen kosai, da kuma kayan tea gamai muradi.natashi nashiga wanka bayan mungama, kayan rahma nasaka cikin sabbabin kayanta, rahma tace bari tadan fita cikin gdan tagani, jim kadan tadawo tace, wai gaskia babban gdane, gasu da tarin zuri'a, nace hum! Allah yasa mudace, rahma tace amin, can saiga wasu yanmata 3, 2 manya, 1 karama, ina zaune bakin gado suka shigo har ciki, biyun sunyi kama da abkr, duk yanda akayi kannensane, duk suka tsuramin ido, bayan mun gaisa, su kuma sai mgn suke cikin fillanci harda daria, (nidai nagane gulma suke) karamar cikinsu ta matso kusa dani tana cewa cikin harshen turanci, aunty sunana ummi, wannan kuma sunanta rukayya, yayatace, wannan kuma sunanta husna, abokiyar wasanmuce, dukkanmu kannen hamma ne, nace to sannunku da zuwa, ta dubi sauran tana sauraron abinda suke cewa, sai naga tahade rai, sanna itama taci gaba dayi musu mgn cikin fillancin, abinda nake zargi ni suke kushewa ita kuma bahaka tasoba, saina samu kaina da tsarguwa, su 2 suka tashi suka fita suna daria, nace musu sai anjimanku, sukace to, ita kuma ummy tadawo kusa dani tazauna, tacemin hammansu yana sona da yawa, dan Allah na kula dashi, nayi yar daria nace to ngd ummy, kuma zanbi shawararki, sai naji yarinyar tashiga raina mai hankalin manya, tace kinyi kyaufa, anjima za'ayi budan kai nace, ya akeyi? Tace kubakwayine? Nace a'a, tace yanada kyau, zaku zaunane sai a bude fuskanki inkin rufe, anayi ana gada, daga nan sai dangi suyi fansa, nace mekenan? Tace kudine za'ayi ta zuba muku, sai kuma a kawo faute daga gidan amare, nace shikuma mene faute? Tace ba ankai muku suddajeba? Na tsura mata ido, mene suddaje? Tace kayan dangi mana, ba ankai mukuba? Nace eh, tace toshine suddaje din ai, nace to menene faute? Ina nufin me akeyi dashi? Tace kayane su kuloli dasu. Kaya dangin amarya suke badawa wasuma harda gado sukeyi, nace to, rahma tace in kuma mutum bai sanibafa? Tace ai duk zuri'armu sun sani, rahma nace abinda mukeyi acan zamuyi sai mubasu hkr muce bamusan sunayin hakaba, tace, ai baza'a damuba, tunda an sani cewa baku saniba, karfe 4 daidai lkcn gdan yacika dam kidan sarauta ke tashi, kai zuri'ar abkr akwai kyau, sunata shigowa kallona, ummi taje kiran da abkr yamata, don tuni sunyi waya yasan cewa tana gdan, ta shigo dauke da katuwar leda, tace anty canza kaya donga adda fadi nan sun iso, kuma nasan hamma da abokanshi ma sunata shiri, shine yace in baki kayan nan, muka bude nida rahma nace, kila dai a dinken yasiyo, rahma tace, daga gani don gasunan a ledarsu, nace Allah yasama to sumin daidai, daya leshine da aka hada da swis, dayan kuma leshine zalla, sai shadda doguwar riga taji aiki, sai atamfa, nace toni wanne zan saka? Rahma tace kisa leshin nan, ummi tace aunty kisa shaddar nan mana gata ja tunda keba fara bace, zakiyi kyau, nace rahma duba akwatii akwai takalmi ja cikin kayan can? Saiga ja takalmi gami da mayafi, ummi tace kiyi amfani da bakake, kuma hamma yanason jan abu ga mata, don in zai saya mana zani dole saikaga ja aciki, na sake yo wanka na zauna gaban madubi nadauki kwalliya, harsu ummi suna cewa gaskia nai kyau, na saka sarka da sauran tarkacen karau, suk su rahma da sakina kowa yayi kwalliya, zuwacan abokan wasansa suka shigo sunamin tsiya wai in fito, yan'uwana suka takamin baya muka nufi gurin. Katuwar darduma ce shimfide, tun kafin mu karaso na hangi hamma sanye da shadda blue mai kyau da tsada sai sheki take, gefenshi fadima ce wato kishiyata, tana sanye cikin wani yadi, tsananin kyan yadin ne yake bayyana tsadarsa, taci gwargwaro, ga gwala gwalai, gabana ya fadi don kyawunta ya wuce misali, ina isowa kanshinsu yadaki hancina, duk sai na jini na zama wata ga daini nan, donko nasan ko a kyau baxan kama kafa da itaba, muka kalli juna nida ita ido cikin ido sannan na dauke kaina na zauna, guda ta soma tashi, sai aka umarcemu da mu rufe fuskokinmu da kyau, duk muka rufe sai aka kira kannenshi wai su fara bude uwargda, rukayya ta bude fadi, mai guda tafarayi sannan danginta suka shiga zuba kudi, daganan saini, ummi ce ta bude fuskata nima, nima dai dangina sukadan watsamin abinda ke garesu, bandamu da kudin da aketa zuba musuba, musamman abkr don al'adace da addiniba, (inama ni suka bawa kudin nan) can kuma saiga iyayen fadi sun kawo faute wajen dangin abkr, kayan gado dan italy na kwali, da kuloli da sauransu, aka shiga sanarwa, rahma ta duko kusa dani tace ya za'ayi? Nafito musu da garar nace suma abasu, buhunan shinkafa talia, dasu dubulan da alkaki da yan samirun damukazo dasu, haka kuwa sukayi, basuce komaiba da aka basu, rahma tace suyi hkr bamusan yadda suke abubuwansuba shiyasa, nan naga anata raba kalandu zuwa jakunkuna da memo da jota, dadi sauransu, hotuna nake mamakin inda akasamu nawa, kamar tare muka dauka? To suna nufin tare muka dauka? Yana tsakiyarmu ya kwanta bayan fadima, nikuma na kwanta a bayanshi, dukkanmu muna daria. ina sanye da jallabiya, al'ajabi ya cikani, sai daf da magrib aka tashi, muka koma dakina, dama na kosa mu koma, na janyo daya daga ciki jakunkunan da akaba dangina nace, yaushe ne har mukai wannan hotunan ni hafsa? Rahma tai daria tace lkcn daxamuje gdan kwamishina, idan nace kizo muje baxuwa zakiyiba, shiyasa nahada baki da mai hotan yamiki baki saniba, computer kuma tatsara abubuwa, daman fuskarki kawai muke bukata kuma gashi munsamu, rahma tabude jakarta tace ga hotunan yanzu kigani, tabani na kalla, amma nace Allah ya isana amma, nace dubi yanda nayi acikinsu kamar wata yar aikinsu, badai shine yaji kuma ya ganiba inji rahma? Nace ga yanmatan nan kannenshi zasuyi rainin wayo, rahma tace, kedai tsakaninki da kowa mutunci, nace shima sai wani shareni yake, shiyasama da ana hotunan nan da danginsu ban cusa kainaba ciki, nayi zugum ina kallon fadima, kishinta nacin raina, nace rahma, fadima tana da kyau, ina zaton abkr yafi sonta, me kamar wannan mezai damu kansa dani kila ya aurenine don wata manufa, rahma ta mike cewa, saikiyi kuma, nikinga tafiyata zan sallah, gara ke hutu kike, saiki zauna kiyi tayi ke kadai, bayan sallar isha'ine aka kawo mana abinci cikin kuloli, nan aka shiga ci tare da lbrn karamcin mutanen yola, dan bikin nasu ya burge dangina, tabbas yola nima zance sunada karamci, ina kwance tunanin yanzu abkr yanacan tare da matarsa, sai mukaji sallama, rahma ta amsa, tace rufe fuskarki ga angonki nan, nace mezaizo yayimin? Rahma tace inya shigo saiki tambayeshi magulmaciya, koda baki fadaba nasan tunaninshi kikeyi, nace kada kimin sharri, tunanin me zan tsayayi? Kafin tace wani abun sun shigo, hashim yace sai mun sayi bake kenan? Naga amaryar tasha lullubi, rahma tace dame kake zato? Nan dai sukayi addu'oi tare dayi mana nasiha, sannan suka mikawa rahma kudi da ledar kaza, daya daga cikin wadanda bansaniba yace, to tunda anbiya saiki bude mana fuskarki mugani, nayi musu shiru, haka nan naki bude fuskar sugani, nayi shiru sannan suka mike dukkansu, abkr ya dubi rahma, saiku zama cikin shiri, kunayin sallar asubahi in Allah yatashemu zaku dauki hanya, tace to, abokan suka fita, rahma ma tafice, saini saishi, duk mukayi shiru, yana dai tsaye, yace, inbaki da mgn nizan tafi gurin amaryata, uwargidanki kenan saida safe, da sauri na dubeshi bayan na janye mayafin kaina, shima ni yake duba, bansan me yake zuciyarshiba, nidai tawa zuciyar kishine fal, na kauda kai cikin takaici nace, to dama akwai wanda yace ba amaryarka bace? Allah yabamu alheri, na mike tare da tura kofar toilet na shige, banjin fitsari amma dole nayishi, don banason tsayawa kusa dashi, dana fito yatafi, ina jiyosu sunayiwa sauran yan'uwana sallama afalo, Rahma tashigo, har kunyi sallamar? Nace na lura bazaki rike mijinki da kyauba, kada dai kimanta cewa ku 2 ne, nace um! Niba shine agabanaba, kuma bazan wulakanta kainaba, don na lura bana cikin yan kayanshi, abinda nasani shine, duk zaman daya zaba shi zamuyi, rahma tace shikenan, in kinyi tunanin yanda zaki kama mijinki a hannu kya kirani a wayata, tajawo ledar gabanta, bari mu tayaki cin kajin tunda ba ango, nace ke ango ya dama, niko ajikina, tace, abakiba, nan tafito da kaza daya, nace su dauka suka tace a'a, bansan meya hanani bacci ba wannan dare, alwala na dauro nazo na duka inata nafila, sai naji raina yayi sanyi harma bacci yana dibana, kacaniyarsu rahmace ta farkar dani, sunata shirin tafia, nima na tashi nahau shiri, rahma tace, waike inazaki naga kina diban kaya cikin karamin akwati? Nace kano mana, karatuna zanyi wasa dashine? Tace kun shirya hakan keda mijinki? Nace um! Zancen kikeso.Sai gasu sun shigo, waisu fito yan kd, nace ni yan kn zanbi, damasu mama sun tafi da shadad sbd makarntashi, na zura hijabina, yan gdan sun shigo sunata godia ga yan kd, tare dayi musu alheri wai inji lamido, turaman zannuwa ne da kudi na shan ruwa a hanya, har sun shiga motoci saiga abkr akan mashin ya tuko, yana sanye da farar jallabiy mai gajeran hannu, dama ina cikin tunanin watonba zayazo yayi sallama da yan'uwanama, kallo daya nayi mishi nakau dakai, duk sai naji haushi yake bani, musamman da zuciyata take rayamin cewa daga ganinshi yasha amarci, ina kallo shima yaciro kudi ya mika musu, motarsu tatashi ta nufi gate, na juya nabarsu nan tsaye dasu rahma, ko karyawa na kasa, duk tsananin son masa (waina) danakeyi, sagir yana kiran rahma waita shirya, nima na hau kintsi, rahma sai daria takemin. Can suka shigo dasu abkr, sai kamshi tare da kyallin goshi yake, daga ka ganshi ango dai sosai, yasha boyil mai ruwan kasa, hula minista baka, takami ma haka, suna gaisawa rahma tace, waida hafsa zamu wuce kn? Na zabga mata harara, wai nema? Ya dubeni da mamaki, mexakije yi kn? Nayi farin rashin kunya tare da murguda baki, menakeyi da jarabawa na tahowa zaman me zanyi anan? Rahma tace zaman aure, nace hum! Sai naga yayi murmushi, sagir yace, kibari ai angon zai kawoki ida lkcn zana jarabawar yayi, nace nidai gaskia tafia zanyi, idanuna suka kawo kwalla, sagir yace to abkr amaryar nan shagwaba takeji, abkr yace, tayi son ranta, amma tafia sai nai niyya, rahma tace ni tunaninama Allah yasa miyar nan bata lalaceba, sannan walimarmu tasha ruwa. Nace in kinje kirabawa makota, rahma tace to, narigasu isa wajen motar, nakama murfin zan bude, abkr ya dallamin harara, na matsa ya bude musu suka shiga.bayan tafiyarsu rahma, ina tsaye na cije lebe ina kallonsu, zuciyata tana tukuki, da sauri na juya daki, nafada gado ina kuka tamkar yarinya, tausayin kaina nakeyi, bansan irin rayuwar dazanyiba, kamshin turarensane ya cikamin hanci, don haka saina zaci yana tsaye, da sauri na dago kaina tare da waiwayowa, shine kuwa, yace sbd kina zaton za'a cinyeki shiyasa kikeson tafia ko? Na zuba mishi ido ban tabkaba, shima ni yake kallo, ya dauke kanshi daga kallona, koda yake dama bani kike soba, na sunkuyar dakai, yace gaba, ance so dayane tak! Kuma tuni kin dorashi kan wani, na dago da sauri muka hada ido, na juya mishi baya cike da suyan rai, kana nufin bana sonka? Yace basaina maimaitaba, in kuma ba hakaba, menene dalilin kukanki? Nadubeshi, duk wata amarya tanayin irin wanan kukan a wannan ranar, dole nayi kewar yan'uwa, yace ko? Amma dana zaci ba yauce rana ta farko dakika soma rabuwa dasuba? Gabana yafadi don na fahimci mgn yajefamin, ka iya fadin duk abinda ranka yaso game dani, don naga kamar don hakan ka aureni, na zauna bakin gado cikin bakin ciki tare da tausayama kaina, yatako ya matso kusa dani, don haka na aureki, kuma zanci gaba da fada miki duk mgnr da tazo bakina, sbd baki iya tauna mgn ba kafin ta fito daga bakinki, duk sanda na kalleki saina tuna cewa ke karuwa ce ada, na mike a fusace, zamanmu bazai yiwuba matsawar zaka dinga kallona wa wannan fentin, ya zauna kan madubi yace, waya shafa miki fentin? Inace kece da bakinki kika shafama kanki? So yajaki kika zubar da kimarki, kuka ya kufcemin, cikin kukan nake cewa, nikam tafiya zanyi, kasakeni.Yayi yar dariya ' ina sonki tsakanina dake babu batun saki. Tafia ce dai in kince zakiyi ta bazan sha mamaki ba tunda mahaifanki ma kin tafi kin barsu bare ni. Yanzun ma kya iya tafia in kinso ya juya ya fita, nace 'subhanallah' wannan wace irin rayuwa ce? Nayi kukana na qoshi sannan na share hawayena babu me bani haquri. Na kira Rahma suna hanya cikin dusasshiyar murya nace Rahma Abubakar yazo yaci mun mutunci ni gsky bazan iya zama dashi ba. Rahma tace meya fada miki? na sanar da ita komai tayi shiru na dan lkc can tace kiyi haquri duk laifin kine da kika sanar dashi ta bai baishi kuma mutun ne mai mita tare daqin saurare. Munyi munyi ni da sagir kan cewa ya sauraremu dan muyi masa bayanin gsky lamarin sai yace"Ai kin gama magana shi ba zaya iya jin wata kwaskwarima ba sannan yayanki umar yace masa da soyayya ya yaudareki kika bada kanki don haka yanzun shawarata itace kiyi shiru da duk abinda zai ce kada ki tanka shi. Na kula yanada mugun kishi ne nace ko gidan karuwai ya ganni yace yana so bai dace yazo kuma ya dinga ca6a min magana ba. Rahma tace kada ki damu zai zo ya yi nadama nace kinga dai ga jarabawar mu tazo bana zaton zan zana ta. Na sake rushewa da kuka shekara ta ta qarshe Rahama tace ki daina damuwa addu'a itace kadai mafita Allah zai kawo sanadiyyar da zaya fahinci gsky nace shi kenan. Ranar har magriba ban kuma ganinshi ba abinci daga cikin gida ake kawominsanda saudatu ta kawomin na dare na rana ko bude shi banyi ba. Tace ke kam baki san cin abinci gashi kina ta kuka kiyi haquri aure kenan zaki saba damu in kin saki jiki. Mu kam bamu da wata matsala nace to nagode nayo wanka don na fara sallah. Nayi shafa'i da wuturi sannan nayi shirin bacci sam bana kojin yunwa na hau gadona kwanta. Text ya shigo cikin wayata na duba shine angon nawa. Yace bazan samu shigowa ba don fadi bata san in fitavqila sai gobe. Duk suyan da raina ke yi sai na rubuta cewa Allah ya kaimu ka gaisheta. Na share hawayen da ya zubomin sannan naje na rufe qafata. Abubakar dake kwance kan gadon shi tsararre tun da ya shigo daha salkar isha'i yake kai kwance. Gaban mudubin dakin fadi ce tana fesa turaruka shi masu qamshi sanye take da rigar bacci me shegen kyau tare da ma'ana. Daga inda yake kwance yana kallan ta zuciyarshi fadi take ina ma ace hafsat ce haka a gabanshi. Me yasa ta fadi mishi cewa ita karuwa ce? Me yasa ta kasa adana masa kantahar zuwa lkcn da zai aureta?.Shin maza nawane suka kwanta da ita? Abinda ke sashi ganin ba zaya kusanta kanshi da ita ba kenan. Dalilai 2 suka sa shi auranta na 1 tsabar santa da qaunarta na 2 kuma..... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-07 Posted by ANaM Dorayi on 06:01 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na biyu kuma yanda yayi yaqi da danginsa don ya samu ya aureta. To sai da damar ta samu sannan yaji wannan muguwar maganar ba abin yace ya fasaba lamido ya ce don me? In kuma ya fadi dalilin shi zasu qara qarfafa al'adarsu tare da kafa misali dashi. A duk lokacin da wani yayi yunqurin auro yar waje a cikin family kai yasan sai lamido yasa an rubuta shi cikin kundin tarihin family dinsu. Gsky bai so hafsat ta furta zancan nan ba gaba daya haushinta yakeji shine mafarin daya tura mata wannan saqon don ya qara bata haushi. Zaman Fadi a bakin gadon yayi daidai da shigowar amsar dana bashi koda ya karanta sai kuma tausayi ya kama shi tamkar ya rubuta ban baki amma sai ya fasa. Ni kuwa sallah ke nutsar dani a duk lkcn dana samu kaina cikin damuwa don haka ita na duqa yi har nisan dare sannan na kwanta zucita wasai. Gsky ko yaushe ina alfahari kasantuwa ta musulma kuma ina roqan Allah ya kashe ni cikin musulunci. Da safe bayan nayi wanka na rufe jikina da hijabi na nufi 6angaren mutanan gidan daki daki na gaida su. Tsohuwa gwagwal itace tace min lamido yana gefanshi inje mu gaisa.Kan kujera na sameshi da carbi a hannunshi na zauna gefe sannan na gaida shi cike da ladabi yace yarinya hafsat ko? Nace eh yace to kina jin dadin zama damu? Nace eh yace to madalla kiyi ta haquri har zuwa lkcn da zaki saba damu. Sannan in kinga wani abu baki gane ba ki samu gwagwal zata yi miki bayanin komai. Nace to nagode ya ce babu komai na tashi na nufi sashe na na samu abin karina Kunun tsamiya da qosai nakai kicin na aje da yake ya kawo kayan tea sai na hada ruwan lipton na sha. Ai kuwa tamkar na tsokano yunwar don haka sai na tsiyayi kunun na sha da qosai Na shiga gyaran dakina na tsaftace ko ina sannan na saka turaren wuta na koma gado na kishingida. Can wayata ta soma ruri na duba Rahma ce na dauka muka gaisa tare dayi mata bangajiya. Ta sake bani haquri tare da shawarwari sannan tace min miyar nan da kaji duk tabai maqota sannan ta basu haquri game da batun walima kan cewa bamu zaci zaa wuce yola ba. Nace shikenan muka dan zanta sannan mukayi sallama.Ummi ta shigo da sallama cikin fara'a na tareta. Ta gaida ni cikin girmamawa sannan tace Dada da Abba suna gaishe ni nace ina amsawa na ce ga kunu da qosai a kicin tace ta qoshi don yanzunnan ta karya muka zauna muna hira. Tace aunty hammana yana sanki da yawa kiyi kallan yanda yayi rigima a cikin family dinmu dan ya aure ki? Nace haba wace rigima yayi? Nan ta shiga bani lbrn na jima ina mamakin wannan irin al'ada Nace kenan ba kwa sona? Tace muna sanki mana sai dai yanzu aikin kine ki koyama danginmu sonki da son duk wani bare dazai shigo cikin mu bayanki,nakalli yarinyar qarama da hangen irin na manya nace ta yaya zan koya musu haka? Tace aunty ke zaki fini sanin hanyoyin da zaki bi don su soki kadan din dana sani shine halayen kirki yin kyauta tare da sakin jiki damu Saura kin fini sanin halayen da zaki nuna a gaba in mun kawo bare in munce zamu aura baza a hana mu ba tunda basuga wani mugun abu daga gareki ba Nayi dan murmushi ummi kenan insha Allah danginku ba zasuyi takaicin da kasantuwata cikin ku ba. Kusan qarfe biyu ya shigo lkcn ummi ta tafi ni kuma na soma bacci A jikina naji cikin bacci ana kallona ko nace ana tsaye a kaina a hkl na bude idona Qamshi turaren sa ya daki hancina sanye da qananan kaya yayi kyau matuqa, bai san cewa na farka ba Ni kawai yake kallo ba wai fuskata yake kallo ba amma a hkk na yunqura na tashi ya dubi fuskata kin dai yi sallah ko kike bacci? Nace nayi sannu da zuwa yaya Fadima? Ga mamaki na sai naga yayi murmushi tare da cewa lafiarta kalau kenan yafi santa? Wayata tayi ruri ko ban sani ba Rahma ce wayar tafi kusa dashi don tana kan mudubi ya daga ya duba sannan ya ajiye nazo na daga muka gaisa tace na jiki sanyi dayawa har yanxu dai? Nace Rahma me zqi canja ni dai ki tayani addu'a Tace insha Allah taci gaba dama na kiranki ne in fada miki cewa na rabar da duj niyar nan da naman kada ya lalace. Sai dqi na rage miki kadan a gidana in kinzo sai kiyi amfani da shi Nace ki barshi kawai Rahma ta yiwu nazo kenan sa'adatu sulaiman ma dazu ta kirani ta fadamin cewa wai tamin test dina da suka rage nace mata to nagode Sai dai bani da tabbacin zanyi jarabawar Rahma tace insha Allah zakiyi nace Allah yasa nagode ki gaida mama da shadad baya rigima? Tace ai yaqi zama tunda ya ganni yaqi mama nace Allah sarki to sai anjima mukayi sallama Na dubeshi bazaka xauna ba emm......akwai abinci ya tabe baki am okay ba zama zanyi ba ki shirya inkaiki kuga juna da fadimana,na maimaita fadimarshi? Amma sai na danne na miqe na fada bandaki wanka na soma shi kam dakin yayi ta bi da kallo tare da shaqar qamshin turaren dana turare dakin dashi tun safe idanunshi suka sauka kan rigar baccina wadda na ninke ta kan gadona Ya dagata ya warwareta ruwan hanta ce mai santsi kalar ta mishi kyau zaya so ya ganta sanye a jikin hafsat Ya kai rigar ya dorata a fuskar sa a hankali yake shaqar qamshin ta irin wanda yasoma ji tun ranar da suka rage mata hanya motsin qofa ne yasa shi jefar da rigar ya kuma juya ma gadan bayatare kuma da sake hade rai. Na zauna gaban mudubi duk da cewar kayan ne a jikina wato da nayi wankan ban fito ba sai da na saka rigata. Na janyo mai na soma shafawa yace wai wanka kikayi? Ni fa ba nazo dogon zama bane Na dubeshi ya wani tsare gida bance komai ba naci gaba da murza mai a qafata ina yan shafe shafen su eye pend ya kuma katseni Kada ki 6ata lkcn gurin yin wani shafe shafe don bazaki tsorata Fadima ba a kyau " turqashi mu hadu a kashi na "4" na qarshe" Alhamdulillah. Wannan shine karshen littafi na "3", godiya ta musammam ga masoya kuma mabiyan Hausa Novel Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100