[31/03 à 21:32] Sadjida: 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 Na *SAJIDA* 1 Zaune suke baki d'ayansu cikin fada, a kasa suke su dukansu saman tankadaden reran (kasa fara tas) dake tsakiyar fadar baki daya ba saman tabarma ba Su dukansu sun tantankwashe kaffafuwansu tun daga datijon dake zaune har zuwa yar karamarsu Kamaninsu du iri daya ne, sun kwaso kamar mahaifinsu wanda ya haife su wanda yake zaunen cikin shigar shada ruwan toka mai cike da kamala Sai matarsa dake zaune gefensa fara tas matashiya domin sam bata kai shekarunsa ba bayanta da goyo tana dan jijiga yarinyar dake dauke da wani irin gashi mai kyau a kanta wanda sun gado shi ne daga wajen mahaifinsu da yake bakin balarabe Manyan malaman fadar ne zazaune kusa da kujerar alfarma wace sarki ke sama zaune ya kura masu ido daya bayan daya yana kallonsu Dogarai ne hudu biyu gefe da gefen sarki, daya rike da wata irin bullalar dorina irin ta dukan rakumin nan murdadiya mai taurin gaske sannan mai lauyewa wace idan aka tsulawa mutun take zagaye jikinsa ta dannu da zafin gaske, dayan kuwa yana tsaye rike da wata jakar fata wace ke dauke da alkur'ani mai girma ya masa kyakyawan riko A hankali sarki ya dan daga kansa ya dan juya kan nasa hakan ya sa baban malamin da ya fi aminta da shi sannan ya fi kowa tsufa a fadar ya gyara cikin nutsuwa ya ce" Allah ya ja da rai, Allah ya jibanci lamuran sarkin garina, Allah ya huci zuciyar matashin sarkina mai cike da kamala, na miko gaisuwata ina kara jinjina da adu'ar gamawa da duniya lafia Sai da ya numfasa kafin ya ci gana cike da jin nauyin maganar da zai yin duba da abin na cikin gida ne ya ce" Yaran nan ne suka shigar da karan da ka bada rana yau a zo gabanka zaka wanzar da shara'a kwana biyu da suka shige Baki daya aka kwashi gyara kimtsi, sarki mai adalci, sarki mai zartar da hukunci a kan dukan wanda aka cuta Sai da ya lumshe idannuwansa cike da wani irin jan aji da wani irin cika da kamala sannan da jin kunyar datijon dake zaune wanda ke tafe da iyalinsa baki daya sun zo a masu shara'a kafin ya daga yan yatsunsa yana kallon baban yayan yaran da suka kawo karar mahaifinsu da kuma matarsa kan a saka masu alkur'ani a masu shinge kan aikata mugun abu a tsakani kama daga maganin asiri , zagon kasa dai da sauransu dukan abinda zai zama na cutarwa ne Da dan yatsansa ya yi nuni kan baban yayan nasu wanda kansa ke kasa yana cike da kunyar sarkin domin ya tabata ya shaka kuma a kansa zai sauke dukan haushinsa Da sauri na kusa da shi ya fadi cewa" Sarki ya baka damar fadin abinda ke tafe da ku a matsayinka na ja gabansu Sai da ya sada kansa sannan ya dago ya sauke ajiyar zuciya, shi kansa kana ganninsa ka ga jinnin sarautar domin maganar da zai yi sai da ya ringa motsa bakinsa kafin da kyar ya buda bakinsa ya ce" SUNNANa *DAYABU BINE MUTALAB,* mun kawo karar matar mahaifinmu ne wato MUTALAB da kuma matarsa MARDIYA domin muna so a yi mana shari'a ta adalci hakan ya sa muka nufo gidan adalci Gaskiya ne jangori, gaskiya ne yaro jangori a nan adalci shi ke janye da ragamar komai Ajiyar zuciya ya sauke ya ci gaba da fadin" ba wani abu ne ya kawo mu nan ba sai bukatar a yi mana tsakani da matar mahaifinmu wanda take uwa a wajenmu kan zamantakewar yau da kulun, kwarai muna fuskantar abubuwan dake gifata mana kala daban daban wa'inda suke saka mu a halin rashin nutsuwa da fadace fadace tsakaninmu da ita Mun zo gidan nan ne dan kaine uban kowa kuma mai zartar da hukuncin da ya dace bisa tafiar adinni, muna so a yi mana tsakani da ita kan maganar magani wato asiri, kar ta shiga tsakaninmu da mahaifinmu, kar ta shiga tsakaninmu da yan uwanmu, kar ta shiga hurumin aikinmu, ko matayenmu ko kannenmu kar ta hada su da lamari na rashin samun miji, a takaice dai dukan wani shinge da ake yi a gidannan mun zo da kokon bararmu kan a mana shi tsakaninmu da *Su* muma a yi masu tsakani da *Mu* koda wani ta ji zai yi idan bata tona ba, koda wani muka saka ya mana ya ci mu! Wasu kai suke jujuyawa, wasun kuwa cike da mamakin yau shara'ar ta cikin gida ce aman suka yarda ake yinta a fili gaban kowa, Jangori ne da kansa sai y'ayansa duda aun kasance fitatu kuma sananu a duniyar rigima sai dai abin ya bada mamaki gannin ya amsa kira shi dinma da kansa nan da nan labari ya fara fita waje harma yan jarida suka fara garzayowa suka cika kofar gidan sarki kowa na jiran fitowarsu domin komai abinka shara'ar gidan sarki baka isa ka fitar da ita waje ba sai dai ka tsinci abinda ka tsinta a waje Murmushi mahaifinsu ya yi a lokacin da DAYABU ya gama magana kafin ya dago jajayen idannuwansa da suka rikide sukai ja sakamakon bacin rai ya kali y'ayan nasa daya bayan daya sannan ya ce" *Na yarda nima a min tsakani da iyalaina, Sai kuma ya rage muryarsa a hankali ya kalli sarki ya ce" Aman banda soyayarmu, ina nufin ni dai ta min na fuskana wanda zamu ci gaba da zama lafia* Gaba daya aka shiga kallonsa, da yawa suka shiga sada kansu cike da kunya, wasun suka saki baki da jin abinda ya fada, matarsa kuwa ta rausaya kanta tana sakin murmushi tana jujuya kaffafuwanta A lokacin ne itama ta dago kanta da wani irin sauri ta kai dubanta wajen mahaifinsu Hannunta na hagu ta dago ta kai wajen bakinta da sauri tana mai ruruko manyan idannuwanta masu zagaye da kwalin kajal ta ce" *lah* Sai kuma ta maida dubanta wajen sarki wanda ya sauke mata kallon da zata iya kira kallon tsana wanda kwannan duniya ita rayuwarta bata san me ta masa ta tsare masa ba ya tsaneta yake kuma kan tsanarta kamar ya fida mata rai , ba wani haduwa suke da shi ba sai jifa jifa ko idan shara'a ta kawota ko ta rako wani aman daga irin kallon kyamar da yake jifanta da shi ta tabata da ace mai magana ne shi ko mai zage zage da ya mata zagin da bata taba jin irinsa a duniya ba Kanta ta yi gagawar mayarwa ta sada Sarki ya dan yi gyaran murya yana mai duban dogari mai rike da dorina a hannunsa, sannan a zuciyarsa ya ayanna" *Dama yaya za'a zo wajen fitina banda ke ke dai kin saka kanki a uku, mai yiwuwa yanda fatarki keda baki haka aniyarki azaluma kawai!* Da sauri mai rike da bulalar nan ya dagata ya mata wani irin duka a jikin wajen da na yi tunanin garu ne, ashe ba garu bane an masa wani irin tsarin shafa penti ne ya hade da garun Karan da abun ya yi ne ya saka baki daya mutanen wajen sada kansu sunna masu nutsuwa harma da hade kafafuwansu sunna kara kimtsa zamansu Sai da ya kuma dago kansa ya kara bin y'ayan da kallo lafin ya maida wajen mahaifinsu da kuma matarsa Su su goma sha uku ne, cikinsu ba wanda suke uwa daya kowane da uwarsa sai dai wani ikon Allah kamaninsu baki dayansu ya zo daya sai dai daga fata ne wani ya fi wani haske Kanta ya sauke dubansa, yanda take wasa da yan yatsunta kanta sade tamkar saliha Haka ya kuma furtawa a kasan zuciyarsa kafin ya maida dubansa wajen mai rike da alkur'annin Hannunsa ya nuna kansa Da sauri ya buda alkur'annin ya ciro shi Baki daya wajen suka kwashi kabara hakan ya sa du wanda ke wajen tsigar jikinsa tashi tana yam yam yam masu saurin hawaye kuwa suka shiga sharewa Kanta ta dago a hankali ta kai dubanta wajen alkur'anin Kafeshi ta yi da ido, har idannuwanta suka nuna mata abinda take zargi Da sauri ta kalli yayansu, sai kuma ta maida dubanta wajen mahaifinsu wanda shima ita din yake kallo ya zabga mata harara domin cikinsu ba wanda baya jin haushi, su dukansu suun cira bata nuna ba kuma daya bayan daya sai ya rama! Dan jan abin da ta ganni ne ya sakata tabe bakinta ta maida dubanta wajen sarki wanda ya gama hada gabas da yama kudu da arewa ya hade rai hakan ya tsoratar da dukan wani wanda ke zaune a wajen itama da gagawa ta sada kanta tana dan bubuga kafafuwanta kasan zuciyarta kuwa fadi take " *Azalumi mai wata fuska* Baban malamin dake zaune ne ya gyara zamansa cikin kamala ya shiga koro bayanan saka layar wanda du idan ya yi magana wajen sai an dauki kabara Irin abubuwan da aka gindaya habaici da baki ne kawai aka cire ciki kuwa harda duka aka saka hakan ya sa jikin DAYABU yin wani irin sanyi nan da nan dana sani ta ziyarce shi yana kallon kannen nasa da ya yi imanin du sai sun mutu ko sun kuturce a kan layar duka da aka saka masu dan wasu irin jarababun y'aya ne masu fadan balaki, domin idan ta hadoka da su har kirari suke yiwa kansu na idan baka jiyata mutumen ba kai ba jinnin MUTALAB bane! Cike da tausayi ya ajiye dubansa a kanta, ya tabata itace gawar fari domin kaf cikin kannensa babu wace ta kaita fada , a haka kuwa kamaninta sam bata da siffar mafadaciya, sam *Kamaninta basu yi nuni da wace zata iya yiwa wani illah ba* Ana gamawa wajen ya kwashi wani irin shiru, Sai da ya kuma jifan DAYABU da kallon zamu hade sannan ya gyara rawaninsa hakan ya sa suka gane zai mike ne, domin dama wannan shari'ar ita ta fitar da shi, ita ta tsayar da shi, baya kananun shari'a sai idan baba ce ko wace ta shafi ahalinsu Kowa kansa na kasa sakamakon tashin da zai yi A hankali ya sauko kafarsa ta dama mai dauke da takalmin fata irin na jinnin sarauta aman yana da kalar fukafuken dawissu bayan ya yi adu'a a kasan zuciyarsa Sai da ya gama sauke kafafuwansa sannan ya mike da wani irin isa da takama Yana mikewa da sauri sauran dogaran da suka karu suka shiga gyara masa rantsatsiyar suturar da ya saka ta yau wace sak irin fukafuken dawisu ne, harta da rawanin da ya sha wani irin rawani ne da akaiwa adon dawisu hakan ya sa baki daya ya dauke hasken wajen Da sauri suka lallayu shi kuwa ya shiga takawa a hankali yana bi ta tsakiyar mutanen da suka layu Kanta dake kasa hakama idannuwanta tana kallon kasa A lokacin da ya kawo kafarsa daidai ita ta kasan gilashin dake fuskarsa mai hasken fari ya ga yar igiyar abin sauraron kidan da ta saka a kunnayenta tana sauraro, hakan ya sa ya dan jima a tsaye a kanta har sai da ta yi saurin dago da dubanta sai dai bata karasa kallon fusakarsa dake lulube da rawani da gilas ta yi saurin sada tsumamun idannuwanta da kanta tana kallon takalminsa da ya tafi da imaninta baki daya Wata ajiyar zuciya mai zafi ya sauke yana ayanna tabas idan tana tunanin ta gagari kowa zai taka mata birki, a kulun ya hadu da ahalin gidansu yana mamakin irin zubin Halitar salihan mutane da akai masu sai dai tarin jaraba dake ciciyarsu, bare ita dake dauke da irin idannuwan nan masu lumshewa da wani irin lumtu lumtu masu tudun gaske da wani irin kumbura Kwafa ya yi a ransa ya ayanna: ita har ta isa ta saka abin sauraron kida a lokacin da take zaune a gabansa? A hankali ya kuma daga kafarsa ya ci gaba da takawa har ya bar wajen wanda barin wajen kadai sai da ya dauki kusan minti talatin tashinsa zuwa tafiarsa Sai da ya shige sannan dogarin ya shaida masu summa iya daga kai Kanta ta dago hade da harara ta sauke a fuskar dogarim wanda yake ta lulube kujerar sarki baima san tana yi ba Yayansu na mikewa suma du suka mimike , mahaifinsu kuwa ya duka sunna magana kasa kasa da malan Cike da bacin rai ta fara fita Tana fita ta saka dogon takalminta fari kal mai tsinin gaske ta rike tsatsonta tana girgiza Yayanta da sauran kannenta ne suka fito sai matar babansu a bayansu dauke da yarinyarta a goye Da wani irin sauri ta zagaye ta koma kusa da ita ta kama goyon da sauri ta kunce hakan ya sa suka shiga kokowar kar ta kunce mata goyonta ita kuwa sai da ta kunce shi ta yi sauri ta damkawa yayarta mai dan sanyin cikin nasu wace ke fadi" ke meye haka? Ki rufa mana asiri da laya tsakanninmu Bata tsaya ta saurari abinda take fada ba ta juya da sauro ta karasa kusa da matar mahaifinta wace ke tsaye da yan uwanta suma dangin balaki ta daga hannu ta wankawa matar mari da wani irin masifa ta aniya shigarta da duka Yan uwan matar babansu na gannin hakan summa suka shigeta da dukan domin ai laya tsakaninta da su aka yi ba da yan uwanta ba Yan uwanta na gannin hakan summa suka kasa hakuri domin familynsu wata irin family ce mai wuyar fasara, a tsakaninsu sunna cin kansu kamar me sai dai koda wasa basa bari a cuci dan uwansu idan kuwa aka yi gigin hakan sunna iya haduwa su lalasa mutun Wata irin kokowa ce ta kaure tsakanin dangin matar mahaifinsu da kuma su hakan ya saka baban yayansu dora hannayensa saman kansa a fili furta" shikenan, yau dai karshenmu ya zo, shikenan ta halakamu baki daya Da sauri ya karasa ya shiga janyo kannen nasa du wanda ya yi gardama kuwa hannunsa yake dagawa ya wankawa mutun mari nan da nan sai mutun ya bar fadan, mutane kuwa sunna kallon ikom Allah basu shiga ba domin kana iya shiga dan rabiya abin ya juye kanka su kuwa basa fatan fada da wannan ahali Yana damkar hannunta itane ta karshe sai da ya kaita kusa da motarta ya saketa Tana ta maida numfashi bata ankara ba ya daga hannunsa ya dauketa da gigitacen marin da ya sakata jin wani irin kauuu har kunnayenta suka yi kamar sun rufe tsabar saukar marin da zafi Cike da fada ya ce" kin kashe mu! Kin kashe mu! Ubanme ya kaiki marinta bayan yanzu aka mana tsakani da laya a gabanki aka dagata? A firgice sakamakon zafin marin da ya dada mata da dago shanyayun idannuwanta masu matukar haske da girma ta kale shi, kamar an mintsineta ta kwala ihu tana fadin" *karya ne! Ba cikaken bane! Bilahilazi sun daukeka wawa ba cikaken Alkur.anin bane suka saka yaya DAYABU!* Da sauri ya tsaya ya kura mata ido yanda aka yaga mata rigarta sai haki take tana hararan wajensu , sai da ya karyar da wuyansa ya sanyaya muryarsa ya ce" [31/03 à 21:32] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 2 A hankali ya ce" *NAJEEBA*? idannuwanta ta saka cikin nasa ta ce" Na'am yaya dayabu, na rantse maka karya yake sarkin ba na gaskiya bane suka saka, Aba ya fi karfinka kennan a kasar nan? Hannunsa ya dago ransa bace ya dafe gaban goshinsa Bai kuma yi mata magana ba ya juya ya ringa kama kannen nasa masu motarsu yana saka kowa cikin motarsa, baya yi maka magana sai dai ya nuna maka hanya kan ka tafi sha'anin gabanka Sauran biyun da basu da mota ya janyo hannayensu ya kawo su ya buda bayan motar NAJEEBA ya tura su kafin ya maido hankalinsa kanta Sai da ya kuma kallonta kafin ya ce" rigarki ta cire, kina kaisu ki tabatar kin koma gida kin saka sutura Kai ta gyada masa tana kara cije lebenta masu mugun kyau da haske tamkar fatarta bata da wani duhu Juyawa ta yi ta shiga motarta Da gangan ta ringa yin kamar motar ta ki tashi har sai da ta ga fitowar mahaifinta ta bi shi da kallo kafin ta yatsina bakinta ta turo bakin ta tada motar gannin yayansu ya karasa kusa da motar mahaifin nasu ta gyada kai ta tabata idan ya gane gaskiya ne ba zai yarda ba sai dai du abinda za'a yi a yi Gudu take falfalawa da su a baya a zaune sanye da kayan makaranta har ta karasa babar makarantar school mai hade da islamiya Budewa ta yi suka fito ta buda jakarta ta basu kudin kari suka juya suka tafi cikin makarantar Motar ta koma ta yiwa kys ta tayar ta kama tafia Tana tafe tana kara cije lebenta a haka har ta zo wajen danja Sojan dake cikin motarsa wanda tun ficewarta dazu polisai na tsayar da ita ta ki tsayawa ne ya fito ya zagaya wajen motar nata Fuskarsa a hade take, sam ba annuri, yana daya daga cikin mutanen da akaiwa sunna dan tsaurinsu da iko da mugun taurinsu a kan aikinsu, sunna kama mai laifi koma waye, sunna da haye basa yarda da raini Sai dai kamar yanda kowani dan adam yake da point faible hakama na Mala'ila wato sunnan da akai masa shine shagwababiyar mace Da sauri ta saka hannayenta ta buda gaban motarta Kayan kwaliya ta janyo da mugun sauri ta buda madubi ta dan duka dan kar a hangota daga gaba ta gyagyara kwalin idannuwanta, ta saka dan jan baki mai tafiya da kalar lebenta ya hadu sosai Rigarta ta ja ta gyara ya kasance wajen da aka cira matan ya fito hakan ya sa ana gannin dan saman mamanta kadan ba da yawa ba Zuge gilashin ta yi bayan ta yiwa fuskarta takwaf takwaf Da wata irin yanga ta dago dara daran idannuwanta ta sauke a kan fuskarsa, lokaci daya kamaninta na salihar mace mai fuzga ya bayanna a tare da ita Gaban goshinta kuwa kwonce yake da wani irin ni'imtacen gashi wanda ya yi luf luf da shi Sai da ta kara yin luuuuu da idannuwanta tamkar wace zata sume sannan ta dauki tissu ta ringa goge idannuwanta nan da nan kuma sai kwallah ta taru Tana kallonsa ta kara rage muryarta, dama mace ce mai karamar murya zazaga hakan ya sa sai da ya kara matsowa ya kashe kunne yana jin abinda take fadi" muryarta a sanyaye, sai dai yannayinta a hargitse ta ce" Allah ya huci zuciyarka sir, hatsari na yi ne cen baya hankalina tashe banma ga sunna tsayar da ni ba, ka gafarceni mai laifi ce ni, idan kuwa na sauka na bada motar bani da ja domin ba wanda ya isa ya ja da ikon da kansa Wani fadi ya ji kansa ya kara, gilashin idannuwansa ya dan yi kasa da shi hakan ya bayannar da idannuwansa masu jan gaske , Murmushi ya yi mata wanda ya bayanar da hakoransa masu tsawarya sannan iskar sigarin da ya zuga ta daki hancinta hakan ya sa da sauri ta kai tissu din nan wajen hancinta ta rufe tana kokarin danne tarin dake son taso mata Wayarsa ya miko mata yana kallonta da idannuwansa tamkar wanda yake daga maye ya ce" dora min numberki a nan yan mata, zan yi kiranki na fada maki yanda muka yi da su domin na fada masu su barni da ke ne, kin san akoy yan cikan dake son lalata mana gari Murmushin yake ta saki tana jin cikinta na neman hautsinewa sakamakon shakar warin nan dake fitowa daga bakinsa yana dukan hancinta, a duniya idan akoy abinda ke sakata gudawa to warin baki ne, bata san wani irin rashin lafia ne haka ba wanda idan ta shaki warin baki nan da nan cikinta ke murdawa ta nemi rikicewa harda juwa Tana faman lumshe ido ta dora masa numbobin da bata san ko na waye bama tana masa dan murmushi ta mika masa wayar Amsa ya yi ya kashe mata ido daya sannan ya bata hanya ta tayar da motarta ta halba bakin titi Tana yin nisa ta sauke ajiyar zuciya a fili ta furta" *Wawa kawai!* Maimakun ta je gidan kamar yanda yayanta ya mata kashedin cenza rigar jikinta, haka ta yi kwana ta je clinik, wato asibiti mai zaman kanta Tana zuwa bata yiwa kowa magana ba da yar farar jakarta da kuma farin dogon takalminta ta karasa bangaren likitan dake duba mararsa lafia Gannin yannayinta a wanke ya saka ba wanda ya tsayar da ita, ita kuwa kai tsaye ta karasa ta dan yi knocking Yana kokarin saka farar rigarsa ta likitoci ya bata damar shigowa domin a tunaninsa nurse din da zata kawo masa liste din mutanen da zai duba ne yau Kamshin turaranta ya saka shi juyowa da sauri Lokaci daya fuslarsa ta fadada murmushi yana kallonta Gannin fuskarta ba murmushi da alamun baci bacin rai ya saka shi saurin kara juyowa yana kallonta ya ce" oh angel, waye ya taba min ke da safe haka na ga fuskar ki a hade kamar wace aka batawa ko baki da lafia ne? Jakar hannunta ta ajiye saman fararan takardun table din tana kara yatsina fuskarta ta ja dan kwalinta baya gashinta ya kara bayana ta sauke ajiyar zuciya ta kale shi Sai da ta ja wata yar shasheka sai kawai hawaye ya shiga bin kuncinta Lokaci daya ya rikice, ya bi ya daburce, ya kai hannunsa da niyar kama hannunta sau uku yana fasawa sannin da ya yi cewa a duniya ta tsani a taba jikinta, du irin yanda take da iya wankar samari kana yin wannan kokarin na kwatanta zaka tabata zaku bata , batawa kuwa wace ba zaku shirya ba Kansa ya dafe yana jin zuciyarsa na bugawa, a duniya yana son yarinyar nan, idan kuwa ya ga ranta bace yakan fita a hayacinsa, bai san wani irin so ne yake mata mai tsanani haka ba, dalilinta ya sa ya daina fade fade a garin domin tana da kawaye kai bama maganar kawaye ba saloon dinta du wata mai ji da kanta a cen take gyaran kai ne, gyaran jiki ne, ko kunshi, ko mak up shi yasa ya nemi biye biyen matan da yake ya ajiye gefe, matarsa kanta yana kiyayewa kar ta san yanada aure domin shifa a kanta yana iya sakin matar tasa, Baban burinsa ya sameta, ya cin mata ta aure ko ba aure, sai yana gannin abu ne mai wuya ba auren domin har yanzu baban abinda ya fi bashi mamaki a kanta du irin wayewarta da tarin shagwabarta ko soyayar shan minti ba'a yi da ita, mutane da yawa na mata muguwar fasara, shi dake tare da ita shi ya san wacece ita Agogon hannunta ta dan kunce tana kallonsa ta ce" kudin jakana sun kare shine hankalina ya tashi domin yau ba zan bude saloon ba kai kuwa ka san inada kashin kudi shine na zo Kabsa ya dafe cike da kulawa ya ce" Angel, kuma shine sai kin taso? Haba baby idan kika yi kirana ko ina ne sai na zo na kawo maki aman shine zaki taso har ki zubar min da tsadadun hawayenki? Mikewa ya yi yana maganar ya dauko jakarsa ta laptop ya buda bayanta ya ciro kudi masu kauron gaske ya buda jakarta ya zuba mata Catin Airtel ya ciro ya buda jakar nata ya kuma saka mata sannan ya dubeta ya ce" kin karya? Idannuwanta ta juya masa cikin yannayi na lumshe su kafin ta dan cije lebenta na kasa ta kuma sake shi Jin an kuma buga office din ya saka ta tashi ta dauki jakar nata ta sakar masa murmushin da ya saka saman kuncinta cen sama kamar kusan idannuwanta lotsawa kadan wanda hakan ke kashe masu begenta, ta kara yi masa wani warwar da idannuwanta sannan ta kuma gyara tsayuwarta ta ce" jarumina, ka kula da kanka, sai mun hadu Bai iya amsawa ba sai wani irin sakai da ya yi da bakinsa ya rakata da kallo tamkar ya janyota ya maidota ya rukunkumeta a jikinsa yake ji har ta fice a office din Wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki a fili ya furta" dole na malaki babyn nan, tawa ce ta ni kadai! Ita kuwa daga nanma direct shagonta ta nufa, wato saloon dinta Motarta ta parker ta sauka bayan ta ciro gilas dinta pink coler mai yannayin heart ta dora ta dauki jakarta ta nufi cikin wajen da tun daga kofar take hangen da alama sunna da mutane sosai yau bayan ta hana a dauki mutane da yawa yau sakamakon amaryar da zata shirya Tana shiga wajen ya dauki ihu, domin kawarta ce bahija da kuma Ramlat suka kawo mata ziyara, kai ziyarar tafe take da son jin abinda ake cicirawa a gari wai sun kai mahaifinsu kara gidan sarki Itama da murna ta karasa wajensu ta zauna tana kallonsu Sai da suka gaisa, masu aikinta suka kawo mata jus da ruwa, da sauri dayar ta je ciki dan gyara mata abin kari ita kuwa ta sakarwa Bahija murmushi ta ce" bahija ina zuwa bara na cenza kaya Bahijarma murmushin ta sakar mata sannan ta dauki Iphone dinta ta danna kira Shiga ciki ta yi ta cire abayar nata ta dauko wata doguwar riga marar nauyi ta saka mai dan gajeran hannu Gashin kanta ta hade ta yi sama da shi ta saka masa dan karamin ribom ta daure shi hakan ya sa yake ta reto da cikarsa da kuma tsayinsa ga bakinsa Tana fitowa gaban madubi ta je ta shiga bin aiyukan da akaiwa mutanen, Biyu ne atach din da aka saka masu bai yi mata ba domin ya yi tudu da yawa dan haka ta sa a kunce ta shiga hada zare a jikin katuwar allura ta harhada da yawa su kuwa suka shiga sauke masu sai da aka gama na fari ta kama cike da kwarewa da kaunar aikinta ta gyara masu ya yi tsaf tsaf da shi ya kwonta kafin ta caje masu ta masu yanda suke so da shi Sai da suka gama suka biya kudin da aka yanke masu na aikinsu cike da farin cikin samun biyan bukata suka tafi Sai da saloon ya rage mace daya ta maida hankali ta saka mata gashin ido ta gyara mata girarta sannan ta saka mata akaifun nan da ake kira natural masu tsadar nan ta gyara mata su sukai wani iri kamar nata domin an rage tsayinsu sosai da sosai sun bada kala Itama biya ta yi ta tafi cike da farin cikin sakin fuskar NAJEEBA Sai da suka gama tafia ta je jikin madubin ta juya takardar dake nuna a bude suke zuwa a rufe suke ta dawo wajen ma'aikatan nata Fuska tamke ta ce" Nadia yaushe kika zama uwar gidana? Nadia da ta san ta yi laifi ta ce" aunty dan Allah ki yi hakuri, walahi tun jiya suka tambayeni yau zasu zo a masu aiki, kuma ke baki ce min kar na bude ba sai dazu a lokacin tuni sun zo na yi na yi na ce da su su tafi suka kiya, clients dinmu ne aunty ke ke hana mu wulakanta clients dinmu Wani huci ta sauke ta ce" to maza maza a gyara wajen a tatare komai a tsaftace, minister ya yi amarya nan za'a kawota nan da awa biyu, ku tanadi komai domin tun daga kurkun zamu silleta dan uban mama zata gani ba tace ba za'ai mata kishiya ba? Daria kawarta ta fashe da shi tana kallonta ta ce" NAJEEBA, wai waye ya taba ki yau du kike hawa uwa fulawa? Murmushi ta sakar mata kafin ta gyara zama kusa da ita ta dauko gashin idon da zata sakawa kanta bayan natama masu tsayin gaske ne da baki, aman da yake tana da bako yau za'q kara firgita shi Abin sakawar ta dauka bayan ta saka masa col ta shiga dan hura shi tana kallon yanda Ramlat ta huda hancinta Murmushi ta yi ta ce" Ramlat idan na kale ki hanci a huje kamar saniya Ramlat ta hade fuska ta harareta ta ce" bana son wulakanci NAJEEBA ke dake son a huda maki gwfen lebenki fa, nan har cewa kika yi a huda maki harshenki kina tsoron kanwar dad ne ya sa kika fasa wancen aman ai jira kike a kawo maki dan kunnen zinarin da kika saka a maki a huda maki lebe uwa wata yar hannu Idannuwanta ta jujuya tana dan rawa da kanta ta kalli madubin ta dago shi sosai a hannunta tana kallo ta kasa kasa ta daidaita ta dora na gefen dama Dayan ta dago shima ta shiga dan matsa masa kadan a sama ta shiga yarfe shi dan ya sha iska kafin ta dora, kunnayenta ne suka jiyo mata muryar bahija na cewa" wai me kuka je yi fada yau ne? NAJEEBA ta dan saci kallonta ta daga kafadunta ta ce" matsalar cikin gida ne Baki ta tabe ta ce" ku dai cikin gidanku kulun matsala, to Allah ya sawaka, aman yaya kuka kwashe da mai damagaram yau? Sai da ta kuma gyarawa ta dora ta daidaita da kyau, tana dago idannuwan nata sun kara wani irin girma da fuzga ta sauke su samanta ta ce" yau na ji jaraba wai ke ina ruwanki da son sannin abinda ke tafe a gidanmu? Kar ki manta kowa da sirrinsa wanda yake gannin sirri ne haba! Da sauri ta ce" aa, Allah ya baki hakuri, ni ba wani abin ya sa nake tambayarki ba gani na yi ke ke zaginsa kice ya damu mutane a kasa ya hanna mana rawar gaban hantsi ya tsane ki Allurar da ta dauko tana kara daidaita kashin idon dan ya yo das kar a ga col din da ta saka da shi ta shiga aiki da shi cikin kwarewa ta ce" ba zaki gane ba, ni ina iya zagin ahalina! Aman ke ya haramta a gareki Ramlat ce ta yi gagawar cenza zancen ta hanyar sako wani, daidai lokacin kuma yayanta ya yi kiranta cewa gimbiya na nemansu bayan salar isha'i Sai da gabanta ya fadi, lokaci daya ta shiga aiki cikin rashin kuzari gashi aiki ne jajir a gabanta shirya matar minister guda amarya wace kuma ta yiwa kanta alkawarin sai ta mata kwaliyar da zata firgita uwar gidan domin uwar gidan ce abokiyar gabanta wace suke fada da ita Ba ita ta bar saloon ba sai da magariba ta shige sosai, bayan ta yi sallah ta kama hanyar gidansu da wani irin gudu Tana zuwa a kofa ta bar motarta ta yi bangarensu da gudu tana lalubar kys din dakinta Budewa ta yi ta afka bayi ta shiga wanka da wani irin sauri Tana fitowa sallah ta yi domin tun tana hanya akai isha Sai da ta gama ta shiga ciro kayan sif dinta tana ta zubarwa a nan da kyar ta iya daukan wata jar abaya irin na dubai din nan ta zira Sai da ta zira ta dauki pant ta saka da sauri sauri ta caje gashin kanta ta warci turaranta tana gudu gudu tana fesawa da wayarta a hannunta da wata jakarta baka wace ta dauki takalminta baki a hannu Ba wanda ta nema dan ta san sun tsufa a gidan Gimbiya da gudu ta fada motarta ta tayar ta warceta ta nufi cikin gida (Gidan sarki) Ta kofar baya ta bi domin ta san idan ta bi ta gaba zasu kara tsayar da ita ne Bangare bangare ta ringa ratsawa, gidan dauke yake da gilas wani irin ginni mai haukata bawa Tana ratsawa har ta karaso bangaren da akan hada su a masu nasiha wanda a nan gimbiya ke hada su Sai da gabanta ya yanke ya fadi sakamakon hango takalma hakan ya shaida mata kowa na nan ita kadai ce bata zo a kan lokaci ba Sai da ta dafe zuciyarta a hankali ta furta" woyo Allahna na kara laifi Da sauri ta saisaita nutsuwarta ta karasa Hannayenta ta saka ta buda kofar madubin dake rufe mai nauyin gaske wace take goge kal kal duda dare ne kana gannin kanka tar a jiki Dan dakata ta yi ta ciro jan bakinta ta shafa tana kallon madubin ta saki murmushi, wanda baki daya hakan ya faru ne a kan idannuwanta kanwar mahaifin nasu wato Gimbiya da kuma yan uwanta, sai matar mai martaba da kuma yaronsa prince, dan kuwa madubin irin wanda idan kana gannin kanka daga waje ne kai kuwa ana ganninka daga ciki kuma baka gannin masu ganninka, ita kuwa rashin lafiar dake damunta idan ta ga madubi sai ta amsa tayinsa ta hanyar dan kara gyagyarawa Hannayenta ta kuma saka ta tura kofar ta shiga da salama kasa kasa Gabanta ne ya yi tsale ya yi luguden kidi ya fadi , hakan ya sa ta saki jakar hannun nata tana raraba ido jikinta na dan rawa rawa Yayanta da yayunta da kannenta ta ganni laye a layi daya kowane kansa a kasa kamar sun zo neman gafara Gefe data matar sarki ce ta sha wata mahaukaciyar kwaliya mai daukan hankali sai walwali take gata fara ce sai haskawa take Gimbiya ce tsaye a tsakiyar falon itama ta sha wata irin nitsatsiyar kwaliya jikinta sanye da alkyaba Da sauri ta kara kallon yan uwanta ta ga kowa da alkyaba a jikinsa, ita daya ce bata saka ba, hakan ya kara bata ran maman nasu Du bata kara firgicewa ba sai da ta sauke dubanta kan MAI DAMAGARAN, SARKI SARKIN SARAKUNA SARKI MAI MULKI CIKIN AMINCI, ZAKI BAYA DAUKAN WARGI, MAI GARI MAI KAUYUKA DAN *ABDUL MALIK ALI BUZU* *SHAHID* yake aban prince *ALI SHAHEED ABDUL MALIK ALI BUZU* miji a wajen *ZINARIYA ZULAIHAT* yar sarkin agadez, D'A daya kwalin kwal a wajen GIMBIYA *BILKISSU MAI GADON ZINARI* Kansa ya juyar daga kallon tsanar da ya gama jifanta da shi ya maida kan matarsa dake zaune tana ta sakin isa da takama da sarauta Yar yatsarsa ya daga ya yi mata nuni da ta fita Idannuwanta ta lumshe, dama ta san ba zai barta ta ji abinda ya faru ba, baya taba barinta jin ainahin sirrin da ya shafe su, bata san wani irin mutun ne shi mai shegen zurfin ciki da boye laifin yan uwansa Mikewa ta yi ta kara sakin shigar jikinta alkyabarta ta sauka sosai ta shiga takawa a hankali har ta karaso kusa da NAJEEBA dake tsaye baki daya jikinta ya yi wani kalau kamar ba ita ba Cikin murya kasa kasa sosai ta kara rabar NAJEEBAR ta ce" kauce min a hanyar yar talakawa! NAJEEBA ta dago da sauri sannan a hargitse ta sauke kakausan kallo a saman kanta, kafin ta ankara ta..................... [31/03 à 21:32] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 3 Kafin ta ankara ta cire lafiyayiya, kwontaciya, farar fatar matar sarki da wani gigitacen mari wanda hakan ya saka baki daya wajen hankalinsu ya dawo kansu Yaya DAYABU ne ya zabura ya mike tsaye sai dai hararan da Sarki ya Zabga masa ya saka shi komawa ya zauna jikinsa na rawa hankalinsa tashe Kai Gimbiya ke jujuyawa a hankali ta saci kallon d'anta, kuma sarkin garinta Ganni ta yi idannuwansa lumshe tamkar wanda bai ga abinda ya faru ba Dubanta ta mayar kan yar dan uwanta, mafi soyuwa a cikin zuciyarta sannan wace ta fi horawa a kan laifukanta Cikin tafiar takama da ta zame mata jiki ba da gangan take yi ba ta tunkaro wajen da suke tsaye wanda sai da NAJEEBA ta yi marin ne kuma baki daya jikinta ya kara kwasar rawa ta shiga jin kamar zata kurma ihu, sai kawai ta shiga yarfe hannayen nata tana matso kwalar da ta yi mata tawaye ta ki zuwa a irin wannan lokacin Tana zuwa tsayawa ta yi tana kallonsu, idan ta kalli wannan sai kuma ta kalli wancen Muryarta ta buda, kamar wace idan ta fito zaka ji wani tashin hankali da kururuwa, aa sai muryar ta fito da wani irin sanyi sannan tana kalkaltu irin na larabawa ta ce" Ya salam, yayarki kika mara? NAJEEBA ta ringa matso kwallah aman ina kukan ya ki zuwa dan ta san tana yin kuka yanzu zata manta fadan ta dawo rarashinta domin ita kanta ta san uwar tasu na matukar son ta A hankali lebenta na rawa ta ce" *ANMY* (wato mama), ta taba martabar iyayena ne Gimbiya ta kalli Zulaihat dake tsaye dafe da kuncinta, a hankali ta ce" rama Sarki dake jin dukan abinda ke faruwa ya kara dan muzkutawa yana sauraronsu Kamar jira take ba wani kauce kauce itama ta daga hannunta ta dauke NAJEEBA da mari Karar marin nan shi ya saka kanwar NAJEEBA mai bi mata wato Khairat zabura tana ruko idannuwanta da niyar tashi Da sauri DAYABU ya saka hannunsa ya mayar da ita ya ringa yiwa kannen nasa gargadin kar wanda ya tashi, ya kara sada kansa kasa Tun da ta mareta ido kawai ta rintse tana jin yanda jijiyar kanta ke harbawa Da mamaki ta buda idannuwan nata ta sauke a kan hannun Zulaihat, gata dai farar mace, kana kallonta ka ga laushi sai dai hannunta wani irin tauri ne da shi kamar dutse wanda ba komai ya janyo haka ba sai mayukan bleating din da take shafawa fatarta dan karin haske a kan nata kamar yanda wasu buzayen ke yi ya hadasa mata taurin tafin hannu kamar mai kwaba suminti da hannun nata Da sauri kuma ta maida dubanta wajen Gimbiya wace itama karan marin ya sakata saurin rintse ido da jin wani irin ciwo da daci a ranta, sannan mamakin rashin kunyar Zulaihat ya darsu a cikin zuciyarta, haka kawai take ayanna Zulaihat ba kara? Ba zaki yafe ba ko dan ni? Juyawa ta yi bata kuma kallon fuskar NAJEEBA ba dan ta san zuciyarta zata karye ne NAJEEBA kuwa kallon tsana ta bi Zulaihat da shi wace ke binta itama da kallon tsana harda na kyankyami kafin ta motsa labanta ta ce" kin mari *SHAHID* kuma sai na rama a kan *ALI*! ido ta ruruko tana kallonta sai dai ba damar kuma tofawa da sauri ta juya ta fita tana jin zuciyarta kamar zata bale , ta yi rantsuwa ta maya ba'a yi yar talakawan da zata zagar mata miji da kuma yarima ba! Sai ta ga bayan wannan tsinaniyar bakar yarinyar mai bakar zuciya! Kusa da yayanta ta je ta zauna wanda ke bin kuncinta da kallo zuciyarsa na karyewa, walahi baya son abinda zai taba masa kannensa, ko dan ya kasance baba a cikin gidansu, ko dan du yawancinsu iyayensu na fita sunna kannanu ne su bar masa yar jarirai ya raina? Du cikinsu ba wanda uwarsa ta rufa shekara hudu da shi, da wuri take tafiarta inda za'a bar masa shi kuwa ya raina domin mahaifinsu mai tafiye tafiye ne, sunna da masu raino aman baya iya motsawa yana tare da su hakan ya sa yake masu soyaya daya tak tamkar mahaifinsu, gani yake yama fi mahaifin nasu son su domin baya tunanin da shine wata mace ta isa ta shiga tsakaninsa da su ba! Sai da ta saisaita nutsuwarta daga tsayen da take kafin ta karasa gabansu ta aniya neman zama a kasa saman kafet din Da wani irin sauri SARKI wato mai martaba ya zabura daga zaune a saman kujerar falon ta alfarmar da yake ya tashi tsaye, da wani irin sauri ya karasa ya saka hannunsa ya tare ta A tare suka tarota da sauran y'ayan Sai a lokacin kukan ya zo mata ta fashe da kula tana rike da hannun Gimbiya ta ce" ANMY a kasa kuma? Irin yanda zuciyarsa ke bugawa gannin majaifiyarsa zata zauna kasa bayan shi yana sama ya saka shi lumshe idannuwansa DAYABU dake rike da ita shiga ta gabanta ya ce"ANMY ki rufa mana asiri kar ki zauna a kasa Itama fuskar ta kwabe, wanda sai a nan na gano kwabewar fuskar nan ta NAJEEBA tata ce, A hankali ta ja shashekar kuka ta ce" ku barni mana, ku barni na zauna kasa nima ya zo ya saka min layar, ku barni ya zo ya mana tsakanin nima kar a je na cuce ku a zamantakewar yau da kulun Kanta take girgizawa da sauri ta shige jikin Gimbiyar ta rukukumeta ta cusa kanta a kirjinta tana ta juya kanta tana nufin aa, aa Gimbiya ta kara riketa da kyau a jikinta, ga hannunta na dama dake cikin na SARKI ga kuma DAYABU da ya koma gefen hagu shima ya riketa da kyau, ga sauran yaran du sun zagayeta kowane ya kama kunnensa ya rike Idannuwanta lumshe ta ce" so kuke ku kashe min shi shima ya kasance bani da kowa? Ai gwara ku hade mu ku kashe sa8 ku huta ya ku y'ayana Du kansu suke jujuyawa cike da dana sani Gimbiya ta ce" yaya zaku kawo karar mahaifinku a cikin bainar jama'a? Koma me kuke tsoro shin baku yarda da Allah zai kare ku bane ko kun fi yarda da tozarcin? Yaya ina tashin tsakiyar dare ina rokan Allah ya raba ku da bakin duniya irin yanda kuka sha jinnin rigima aman kunna kara janyowa kunna hada kanku da su? Kai kuwa da na yi hannin ku tozarta mu sai ka nunan ai adalci aka nema ka je ka yi gaban kanka ka zaunar da yayana a gabanka ka bashi laya? Da sauri NAJEEBA ta kara riketa ta ce" Anmy, Layar fa ba a cike take ba, ya zare abubuwa a cikinta Da sauri ya kai dubansa keyarta da dan kwalinta ya zame ya fadi sai gashin kanta dake waje wanda yake daure da dan ribom a sama sama ya zubo sosai Mamaki ne ya kama shi na yanda aka yi ta gane Alkur.anin ba a cike yake ba, ko wani ne ya fada mata? Kai ina da wuya a cikin mutanensa wani ya fitar da sirrin, hasalima liman baba ne ya cire abinda ya cire a ciki daga baya kuma ya mayar da shi yanda yake , wanda sun yi haka ne daga shi sai shi sai Allahn dake kallonsu Idannuwansa ya lumshe yana jin mamansa na tambayarsa wai gaske ba cikaken bane? A hankali, a karon fari kennan da ya budi bakinsa tun farko cikin wata irin murya mai dadin sauraro da nitsar da firgitace ya ce" Na'am Wata ajiyar zuciya ta saki a hankali ta janyo shi ta hade shi da NAJEEBA dake jikinta ta gefenta ta kuma janyo DAYABU ta dayan gefen ta hade su ta rungume su tsam a jikinta wanda hakan ya sa kwabrin hannunsa na gogan wajen wuyan NAJEEBA Ajiyar zuciya ta ringa saukewa na samun nutsuwa kafin ta sake su Juyawa ta yi da NAJEEBA rike a hannunta du ta yiwa sauran nuni da wajen zama Baki dayansu a kasa suka zauna, Banda Sarki da ya koma kujerarsa ya lume ciki ya lumshe idannuwansa A hankali ta ce" yaya zaku biye mata koma me take maku ku fitar da sirrin cikin gidanku waje? Yaya kuke so hankalinmu ya kwonta a yanzu da tsufa ke riskarmu na zamu iya tafia kowani lokaci mu barku bari na har abada bayan kuna kokarin lalata kanku? Ko da gaskiyarka a lokacin da aka saka maka shi sai jijiyoyin jikinka arba'in sun tsinke Shine kai da girmanka ka tashi ka yi ja gabar kannenka da ka san cewa ko me za'a yi idan dai fada ya tashi sai sun yi ka zo ka tsugunna aka saka masu layar fada? Wato baki dayanku ku mace ko ku lalace shikennan ko? Kansa ya kara sadawa ya ce" Allah ya huci zuciyarki Hannunta ta buga gefen kujerar ta ce" ba wannan na tambayeka malan ka bani bayanin uban me take maku da ya karfina ni ka fada min na magance maku shi? Rintse ido sarki ya yi a ramsa kuwa fadi yake" subahannalah, itama zata fitan kennan? DAYABU ya kara sada kansa ya ce" Anmy, tana zargin ko mu ke hada mata fitinar da take yawan samun matsala da Abih, tana tunanin ko zamu hadewa yarta kai ne mu cuce ta, yajin nan da ta yi ta dawo ne da abubuwan nan wa'inda suka birkita mana lisafi Yan uwanta sun zo har gida da laya za'a saka mana iya mu aman banda ita, mune kawai za'aiwa shingen nan kuma ABIH na kallo bai hanna ba saima fadi da ya yi cewa a core duka, a cire fada, a saka mana iya na magani kar mu yi mata magani domin ya yarda da tarbiyar y'ayansa, bama bin boka bare malan Anmy to idan itafa ta mana? Sasauta muryarsa ya yi ya dago yana kallonta da idannuwansa da suka cika da kwallah ya ce" idan ta lalata rayuwar kanena fa? Idannuwanta ta rintse tana jin har wata zufar bacin rai na keto mata, a saka masu alkur'ani kuma yayanta ya yarda? Ta yayama za'ayi yo shi ya yarda bayan shima ya girma ga kuma soyayar kannensa da yake? Gyaran muryar da SHAHEED ya yi ne ya saka kowa yin shiru harma suka kara sasada kansu, inda NAJEEBA ta lafe jikin Gimbiya ta dora kanta , a zuciyarta kuwa fadi take mai tsamin bakin ya samu da kyar zai yi maganar ko? Sai da ya sha fama da mulkin dake cikin jinnin jikinsa kafin ya ce" samu gaskiya ne, haka kuma neman tsari ta hanyar adu'o'i da kiyaye sabon Allah da kadaice kai wa ibada gaskiya ne, Sai da ya kusan minti biyar bayan wannan maganar yana sauke numfashi kafin ya dora da fadin" ba abinda ke samun nagartacen bawa face kadarar da Allah ya hukunta zai same shi, sannan na yi imanin zai zo masa da sauki a kan wanda bai rike adini ya yi imani ba Dubansa ya maida wajen yaran baki daya ya ce" baku tafasa bama bale ku kone Wani kakausan harara ya saukewa NAJEEBA wace ta yi gagawar lumshe idannuwanta daga kallon kyawawan idannuwansa dake bayane tun da ya fara maganar take binsa da kallo, a hankali ya ce" rashin jin magana kuma baya haifar da abin alkhairi Dubansa ya kara maidawa wajen DAYABU ya ce" haba yaya, kai ka san menene girman hukucin alkur'ani kuma har ka yarda a saka a cikin gidanku? Ajiyar zuciya ya sauke ta girgiza kansa ya ce" ba zan iya sakawa ba, ba dan na yi zabunta ba, sai dan Abu ne mai hatsari wanda bana garajen sakawa wanda bai malaki hankalin kansa ba Numfashi ya yi ta saukewa yana hutawa doguwar maganar da ya yi sai ya kuma kallonsu ya ce" hukuncin bulala zata tabata ga du wanda ya fitar da maganar cewa ba cikake bane aka saka Lale hukunci zai tabata ga duk wanda ya kara kokarin fitar da sirrin cikin gidanmu waje! Du kawunansu suke gyadawa , sai da ya gamsu da hakan kafin ya maida dubansa wajen mahaifiyarsa ya sada kansa sosai ya ce" ALLAH ya huci zuciyar ANMY, Su duka suka shiga maimaitawa a hankali sunna fadin" ALLAH ya huci zuciyar ANMY Ajiyar zuciya ta sauke tana mai jin dadin yanda suke da biyaya a gare su du kuwa da irin yanda suka kasamce masu fada da taurin kai da taurin hali Da daidaya suka ringa tafia, inda Dayabu ya fara tserewa da yan kannensa uku domin baya son a barshi daga shi sai kanninsa kuma warinsa sannan sarkin garinsa a wajen nan, dan ya tabata yanzu zai titsiye shi ya karasa sauke masa laifukan da ya aikata Kanta ta kara shafawa ta ce" daga nan ina zaki je ne NAJEEBA? NAJEEBA ta kara kwontar da kanta a jikinta a hankali cike da kasala ta ce" ANMY, zan je gida ne kawai Murmushi ta yi ta dago habarta, hakan ya sa ta dago manyan idannuwanta masu dauke da kwali da kuma karin girar ido, dan bakinta kuwa dauke da jan baki kalar lebenta da dan man lebe daidai da ita yana sheki Hannunta ta saka ta kara goge mata dan hawayen da ta zubar saman kyakyawar fuskarta da bata da digon hodo ko daya a jiki Cike da kulawa da kauna ta ce" ki rike mutuncin kanki kin ji? Darajar mace mutuncinta yarinyata Shi kuwa a kasan zuciyarsa ya furta " wani mutuncin kuma? Ko dama akoy matan dake da mutunci sama da daya ne? Kanta ta daga a hankali tana jin kaunar maman nasu, Gimbiya ta shafa wajen da ZULAIHAT ta mareta ta lumshe idannuwanta a hankali ta mana mata kiss a goshinta ta ce" Allah ya tashe mu lafia Mikewa ta yi ta dauki jakarta, bata dauki dan kwalinta ba ta juya abinta da niyar tafiarta hakannan ba abinda ya shafeta Gimbiya ta dan daga muryarta ta ce" mayafinki fa? Juyowa ta yi ta dawo kusa da shi, domin mayafin nata ya take shi da kafarsa mai sanye da safa fara kar Dukawa ta yi bata ce masa ya daga ba ta janye abinda harda dan kadewa ta yafa a kanta ta yi gaba tana juyinta yanda take so Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai ya kalli Mahaifiyarsa a hankali ya ce" kin shagwabata, zata sha wuya kafin ta samu mai daukan haukanta, sannan marin matana fa da ta yi? Murmushi Gimbiya ta yi ta ce" ku kai kararmu, sai mu fada cewa ai itama ta mare mu Kansa ya girgiza yan murmushi kafin ya mike tsaye ya kara sada kansa ya ce" ALLAH YA HUTA GAJIYA GIMBIYA Tana murmushi ta ce" [31/03 à 21:33] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 4 Tana murmushi tana kallon yanda sarauta ta karbi yaron nata, yanda sarauta ke kara masa wani irin nutsuwa da kamala a hankali ta ce" Allah ya tsare gabanka, Allah ya tsare bayanka, ya tsare makwoncinka, ya tasheka da kansa Allah ya yi maka albarka Idannuwansa ya lumshe sakamakon jin dadin adu'ar da mahaidiyarsa ke yi masa har sai da ta dasa Aya sannan ya juyo ya kara dukar da kansa ya furta" amen Anmy Cike da tafiar kasaita ya fito daga bangaren mahaifiyarsa Bai zame ko'ina ba sai baban dakin karatun da suke raba dare sunna karatu da kuma ayukan sirri shi da mutanensa na sirri ciki kuwa harda yayan mahaifiyarsa da baban liman din fadar baki daya Sai da ta tsaya a baban wajen saida abinci ta sayi pizza wajen gida goma inda ta bayar da jaka hamsin cif aka zuba mata a cikin motarta Tana tayarwa ta karasa gidansu, Mai gadi ne ya bude mata kofar ta idasa shiga da motarta Yabi daya daga cikin masu aikinsu ta saka kwaso mata pizzar tana kai mata bangarensu da kannenta mata Sai da ta gama kwashewa ta rufe motarta da dan kwalin nan a hannunta tana dan wasa da shi ta shige cikin falon nasu Ja ta yi ta tsaya sakamakon gannin yayanta na bangarensu sannan kannen nata da kuma yayunta har sun yi wanka sun sasaka kayan baci Wani dan malalacin murmushi ta saki tana idasa shiga ta ce" aa, me kuke a zaune? Dubanta sukai gaba dayansu, gannin sai wayancewa take ya saka yayarta mai sunna Umakhulsum girgiza kanta ta ce" ai dole ki ce haka, dole ki ce haka Najeeba bayan ke kin iya tankwalo masifa tana baci! Da sauri NAJEEBA ta ce" toh fa Dayar mai sunna Zahrau wace itace mai sanyinsu ta ce" yanzu Najeeba kennan nima kina iya daga hannu ki wanke ni da mari? Kuma kin sani sarai da ba barinki zai yi haka ba koda kuwa Anmy ta yi dabarar sakawa ta rama sai ya maki wata muguwar muguntar marin masa matarsa ko? Da Sauri DAYABU na dan dago hannayensa ya dunkule guda ya ce" fisabililahi idan ba jarababiyar y'a ba bilahilazi da ta wanka mata marin nan sai na shiga neman na tashi ni ba fifike ba, NAJEEBA a gaban sarki ki mari matarsa dan kina yar yayan mamansa? Gaban goshinta ta dafe tana karasa shigowa Sai da ta zauna tana kallonsu ta ce" meye hukuncina? Cin uwani zaku yi yanzun ko yaya? Tasowa yayansu ya yi da sauri ransa bace ya nufota Da sauri ta rufe fuskarta domin wajen da bata so a kuma taba mata a yau kennan , Sai da ya karaso ya daga hannunsa ya yi ya yi ya bambarw hannayen nata aman sai kara shigewa cikin jikinsa take, nan fa tumurtu ya tashi gannin zata wahalar da shi a banza ya saka shi sakinta yana maida numfashi ya zauna ya ce" shegiya mai ilimin kokowa, kin ci sa'a fuskarki a boye da yau na fitar da sahun hannuna a jikinta Kanwar NAJEEBA dake dariya ne ta ce" wai ku ji fa, kamar wanda yaya zai mata wani duka mai karfi abinda nan zaka ringa zanen idan ka kamata ka fara kwalo da ita, tana zuwa gabanka sai ka bige da yi mata nasiha Da sauri ya kaleta yana zaro ido ya ce" kin ga wannan mai sunnan Gimbiyar sam bata da kirki, idan ta tashi magana sai ta ringa yiwa mutun shari ba gashi ba na jijigata kuma ki bari ki ga ta kuma marin matar sarki zara ga abinda zan mata Su dai du murmushi suke ita kuwa NAJEEBA ta hade fuska sai kara turo baki take wai sun hade mata kai sunna mata fada Sai da suka gama yi mata kashedin ta kiyayi yiwa sarki hayen nan ta sada kanta ta ce" kennan sai na kyaleta ko? Kun san me tace ne? Cewa fa ta yi *ke kauce yar talakawa* Ido Umulkhair ta zaro ba shiri ta ce" kan ubancen, shi yasa na so zuwa na ji a kan me zata maida maki mari yaya ya rikeni ashe iyayenmu ta zaga? Yayansu ya yi shiru shima ransa na kunna Zahra ta ce" kin min daidai dan ubanta ya kashe mu! Su masu yi mata kashedin kar ta kuma sai gasu sunna fadin ai ko sunne sai sun rama, nan da nan suka shiga zanen idan ya kama su ya kashe su sun yi, yayansu kuwa ya rafka tagumi yana kallon dan karamin kanensu wanda su biyu ne kawai maza sauran su goma sha biyar baki dayansu mata ne kuma ko daya ba'a yiwa aure ba tukunnan Ajiyar zuciya kawai ya kuma saukewa ya janyo pizzar ya shiga bubudewa yana raba du gida guda a biyu yana mikawa yaran kannanu Sai da ya yi sauran manyan ya basu guda guda har NAJEEBAR sannan suka shiga ci sunna dan taba hirarsu Sai da suka gama yar karamarsu mai sunna lalla wace bata kai shekara shida ba ta je ta langwabe a jikinsa tana hamma, a hankali ta ce" yaya Dayabu, ina Abihna? Gashin kanta dake dadaure da tsakiya masu shegen kyau wanda NAJEEBA ta mata kitso kananu sosai ta jera mata su ya ringa shafawa a hankali bai bata amsa ba Kamar minti biyar har ta yi baci hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya kalli ZAHRAU wace ke bi masa ya rage murya ya ce" Zahra yau a dakinki zata kwana dan Allah dan ki kular min da ita, kin ga Abih fa fushi yake da mu baki daya yau ko ita bai nema ba Kanta ta gyada ta mike da wayarta dake ringin saurayinta ne wanda aka saka masu rana ta duka ta dauke kanwar nata ta nufi dakinta da ita Tana kaita ta shinfideta ta hade kitson cen sama ta daure shi dan kar ya dameta wajen baci Ta yi mata adu'ar neman tsari kafin ta tsareta da ido a cikin ranta kuwa fadi take" inama Abih zai maido mahaifiyarki ke, ki tashi da jin dumin uminki a cikin jikin ki, ki rayu irin na kowata yarinya mai shekaru kananu irin naki? A hankali ta ja abin rufa ta rufe mata daidai kirjinta ta duka ta mana mata kiss a goshinta ta kuma ayanna" ya Allah, kar ka jarabemu da aure aure, wato ka sa dukanmu idan mukai aure ya zama mijinmu shine wanda zai birne mu, Allah kar ka kama mu da halayan mahaifinmu na yawan auri saki, ka sa mu zauna komai rintsi mu rayu da y'ayanmu Jikinta sanyaye itama sanye da kayan bacinta dogon wando sakake sosai da riga budadiya sosai ta fada saman bed din ta kara rungume kanwar nata kafin ta amsa kiran saurayin nata dake ta maido kiran Yana nan zaune sai da kowace ta shiga dakinta domin dare ya tsala sosai har sha biyu kafin ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya fita ya ja kofar bangarensu ya nufi nasu shi da kanninsa Tana shiga dakinta ta cire rigar jikinta Shafafen cikinta da ta gama cin pizza aman sam bai tasa ba ta kala tana shafawa ta ce" Alhamdulilah na koshi Mika ta yi ta shige bayi Wani wankan ta sake daurowa da alwallah sannan ta kuskure bakinta Tana fitowa eigar sallarta ta saka ta yi shafa'i da wutiri ta yi adu'a ta shafa Cire kayan ta yi ya rage mata daga ita sai pant, ta dauko bras kadai ta saka domin a rayuwarta sam bata iya baci da kaya masu nauyi, ta fefeshe jikinta da turare ta shafa humura Madarar da ta kwaba da tumatur din danye ta shashafa a fuskarta kafin ta haye saman lafiyayan bed dinta mai sasaukan shinfida Sama take kallo kanta saman matashin kan dake ajiye dan kar ta goge abin domin bai bushe ba Gefe daya kuwa wayarta ne ta shiga shating da tarin samarinta wa'inda ita kanta ba zata iya irgasu ba Dakinsa daya da kanninsa dan sam bai raba daki da shi ba, gadonsu ne dai daban daban Sai da ya shinfide shi domin ya yi baci Sannan shima ya shiga bayi ya yi dukan uzurinsa ya fito Baki daya yayan MUTALAB sunna da wata irin tsafta da kuma rikon adini, shima sai da ya yi raka'a biyu domin ya yi nafilarsa kafin ya kishingida da wayarsa a hannunsa Message ya tura kamar haka" Allah ya huci zuciyar kanina Har ya cire rai da zai bashi amsa domin lokacin karfe kusan daya na dare ne, sai dai cen ya ga amsarsa kamar haka" wata biyu ne ka bani DAYABU Murmushi ya yi dan ya san dama baya so ya kire shi da kanninsa, Wani message din ya dora kamar haka" na san ba zaka kulaceni da yawa ba idan ka yi duba baki daya kanena tamkar y'ayan cikina na dauke su, ina kokarin basu kariya da dukan karfina....ka gafarce mu Nanma ya jima sosai kafin ya bashi amsar cewa" Allah ya shirye mu Da sauri DAYABU ya dora" amen ya Allah Sai kuma a kasa ya dora" ka yafe mata, yarinta ce, na mata fada ba zata kuma kai hannunta jikin Zinaria ba Ya buda message din, ya karanta sarai, aman sai ya ki bashi amsa Hakan ya sa hankalin DAYABU ya kasa kwonciya, yana rike da wayar a hannunsa ya kasa samun baci, yana tsoron yaki yafe mata ya rama ta wani wajen, yana matukar tsoron shirun Sarkin nasu wanda ake kasa gane inda ya dosa Shi kuwa sarki dama ba sauka yake ba domin sam baya kashe data , wayar ya ajiye gefen abin bed ya koma a hankali ya kwontar da kansa ya lumshe idannuwansa yana tunnani Murmushi ya yi yana girgiza kai da takaicin yarinyar cinkushe a kasan zuciyarsa Kwarai ya ga karfin halinta, ya kuma yarda cewa bata da kunya Ya kara yarda da shawarar da ya yiwa kansa cewa sai ya koya mata hankali a duniyarta Zinaria dake falo yana jiyo shashekar kukanta, domin yana zuwa zai kwonta ta zo ta tsaya tana kukan a gabansa aka mareta aman ya kasa datse hannun wanda ya maretan? Hannunsa kawai ya daga mata ya yi mata nuni da ta tafi, domin sam baya iya hakurin jiyo koke koken nan Wani murmushin ya yi a kasan zuciyarsa ya ayanna" bayan batawa zuri.armu sunna da take faman yi a cikin garina, yana jaza mani zagi dan kawai mahaifiyata na kanwar mahaifinta ana kiranta da kanwata na zuba mata ido tana tabara, irin yanda wasu ke tunanin samun dagin kafa dan sunna soyaya ko watsewa da ita, shine yau zata nuna gwarjinina baya kaiwa gareta? Shine yau zata nunan ita jinnin shuwa arab ce ta hanyar daga hannunta ta mari matana a gabana? Kansa aya girgiza yaumshe idannuwansa yana tunanin tafiar da zai yi ya kai yaronsa waje, Aliyu bashi da lafia yana fama da rashin lafia mai tsanani mai tashi lokaci zuwa lokaci Yaron kan fita a hayacinsa ya mimike ya ringa wani irin zabura wani sa'in harma ya sume Yaron na fama sosai yana jin jiki wanda hakan ke matukar dagwa mahaifin nasa hankali da kuma mahaifiyarsa wace ta dora dukan so da isarta a kansa cewa yarima ne mai jiran gado..................... DAYABU kam sai da ya gaji da zaman jiran amsa ya fara gyangyadi ya ajiye wayar bayan ya kasheta ya kwonta a hannunsa na dama da tunanin da izinin Allah gobe daga wajen aiki zai koma cikin baban gidan ya same shi ya bashi hakuri Tun da asuba kiran sallar fari mahaifinsu ya ringa bi daki daki yana dokawa da karfin gaske Baya tsayawa su bude yake yin gaba domin yana cikin fushi da su, da da ne sai ya shiga ya ga tashinsu sun dauro alwallah yake barin wajen Haka kowace ta dauro alwallah suka fito falonsu suka tayar da sallah Bayan sun gama sun yi adu'o'insu du suka mike suka yi bangaren mahaifinsu zuwa lokacin har karfe bakwai ta yi Du zama suka yi kamar yanda suka tarar da yayansu kansa sade A hankali suka shiga gaishe shi, sai dai sam baya amsa masu yana ta danna carbinsa ya kure waje daya da ido DAYABU ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" ABIH fushi zaka yi ta yi da mu ne? Ba zaka yafe mana ba bayan ka san bamu da inda zamu nufa mu ji sanyi? Da haushi haushi ya dago ya kale shi ya ce" makaryaci! Makaryaci kawai, karya ne , ni zan matse maku waje ku kai karana a saka min laya? Ba ruwana da ku ba ruwana ku je ku tafiarku Yar karamar cikinsu ce ta mike da dan karamin hijab dinta cikus cikus tana takawa ta je jikin mahaifin nata ta dora kanta a jikinsa ta yi luff tana sauke ajiyar zuciya Shima hannunsa ya sa a hankali yana dan talabeta sannan yana bin y'ayan nasa da harara wa'inda suka sasada kawunansu kowane bai ce komai ba Cen matarsa ta shigo ta dauki kwaliyar safe hannunta dauke da wani irin plat mai yannayin kifi marar nauyi mai kyan gaske da natsakaicin girma Cikinsa gasashen kifi ne da soyayan dankalin turawa ta rufe shi da farar leda irin yanda ake nadewar nan Cike da kissa ta duka ta ajiye gaban Abih Ta koma wajen frij ta dauko ruwa ta dawo ta kuma ajiye masa tana ta takama irin ga matar ubansun nan ta zauna tana kokarin bude masa Da kallo du suke binta ciki kuwa harda shi da kallon mamaki yake binta Tsarin gidansa a irin wannan lokacin da y'ayansa ke zuwa gaishe shi a lokacin ake gabatar da kayan karin kumalon da ma'aikatan gidan ke girkawa tun da asuba Nan suke haduwa su karya kafin du su watse kowane ya je ya shiga shirin tafia wajen aikinsa ko karatunsa A hankali ya ce" ama yaya haka na ga iya wannan? Sai da ta juya idannuwanta masu girma da kyau sannan ta ce" iya shi na basu umarnin dafawa Da wani mamakin ya ce" aman ina abincin *Y'AYANA?* Itama da wani irin mamaki ta kale shi kafin ta budi bakinta ta ce" y'ayanka fa Habiby? Y'ayan naka da suka kaika suka baka laya a gaban jama.a suka tozarta ka suka wulakanta ka? Y'ayan naka da basa tsoronka basa yi mani biyaya a matsayina na matar ubansu wato uwarsu? Na gaji da wahalar zuwa kicin ina ta faman fadin kowane irin abinda yake kari da shi, na gaji da jido masu kayan kari na kawo masu tun daga kicin su karya kulun, na gaji da rashin kunyar y'ayanka Habiby! Da mamaki yake kallonta, ransa ne ya shiga tsale yana kunna, y'ayansa ne ta yi tsaye tana wulakantawa dan kawai an samu wannan yar matsalar? Ba ita zata dafa ba, ba kuma ita zata kawo din ba domin daga bakin bangarensa suke kawo mata ita sai ta idaso da shi ciki dan ba yar aikin dake shiga bangarensa A hankali ya rintse idannuwansa yana kokarin control din haushin da ya kama zuciyarsa domin so yake ya nunawa y'ayan nasa fushinsa a fili dan ko gaba su kiyaye irin abin tozarcin nan da suka yiwa kansu da kansu wanda idan duniya ta ji su za'a zaga bale su matan da suka fi yawa harma suka kawo mizalin aure Sai da ya samu ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau hudu kafin a hankali ya budi bakinsa ya ce" 🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺 [31/03 à 21:33] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 5 A hankali ya ce" Mardiya, aman ai y'ayanki ne ina kike so su je su ciyo abinci? Gannin kamar ta samu dama ya sakata kara juyar da kai gefe ta ce" su je waje mana Murmushin karfin hali ya yi yana gannin yanda idannuwan NAJEEBA tamkar zasu fado kasa yanda take zaro su tana son gaskata shin Abih dinsa ba zai wanketa sa mari ba? Wai mamansu kan uba yarinyar fa sa'arsu ce, kuma wai abincin me zata hana masu yau kuma? Murmushi Abih ya yi a hankali ya ce" tashi ki je ki saka a dafa ma y'ayanki abinci Mardiya Dubansa take, sai dai sam bata gano abinda yake dannewa ba, hakan ua sakata fadin" ai suma sun girma su je waje su ci Da sauri ya ce" to dauke wannan din, nima yau tunda amaryana zata min rowar abincin ai sai mu hakura mu duka Wani malulun bakin ciki da mamakin mahaifin nasu ne ya tsaya masu a zuciya Zahra ce ta sada kanta tana jinjina lale sun bata ran mahaifin nasu da har yau ya nuna halin rashin damuwa a kansu , bayan sun san irin tarin kaunar da yake nuna masu wada dalilin hakan yawancin rabuwarsa da wasu matan nasa su ne sila Yayansu kuwa kure Aban nasu ya yi da ido yana hango irin yanda yake danne bacin ransa Bilkisu kamar ta ciji matar mahaifin nasu, Najeeba a hankali ta kalli mahaifin nasu ta ce" ABIHNA Wani hararan ya zabga mata kafin ya ce" NAJEEBA MUTALAB, meye? Idannuwanta lumshe nan da nan suka cika da kwallah a hankali ta ce" kar ka hore mu da fushinka Abih, ba abinda muka yi Da karfi ya ce" makaryaciya, marar kunyar banza kawai! Ke ba har marin matana kika yi ba?? Da gadara gadara Mardiya ta ce" marina ta yi sannan ta shaki wuyan aunty Ummulkhair ta ce" ita ba zagin mahaifiyarta kika yi ba? Ummu kulsum ta ce" zaginta kennan kulun sai tana zagin mana iyaye bayan mun san ciwonsu muna son abinmu Da haushi Abih ya ce" ai dama na san su ke zuga ku shine zaku mi rashin da'a a nan? Kai DAYABU ya girgiza ya kalli kannensa ya ce" ku tashi mu je waje mu siya Du mikewa suka yi , wanda hakan ya saka zuciyarsa tsinkewa sai dai ya ki sakar masu yar karamar da DAYABU ya miko hannu ya bashi A hankali DAYABU ya ce" saketa mu je na shiryata kar mu yi lati ka ga sai mun sayi abinci kafin mu tafi Hannunsa ya bige ya ce" da kaniyarka y'arka ce? Na ki na sakin Hannunsa ya janye yana dan yatsine fuskarsa ya ce" kanwata ce, kuma dole a bani abina domin ni tana gaba da dukan wata katuwa, kuma walahi idan y'a ta kuma cewa ita uwata ce wannan karon ba marin kanwata zata sha ba, zata dauki mari ne daga hannuna! Yana gama fada ya juya ya shiga tura su du suka fito kowane ransa bace A hankali ta kamo hannun DAYABU ta sanyaya muryarya ta ce" domin Allah meye laifina a cikin nan yaya? Ido ya tsura mata da mamakinta, yanzu tambaya take meye laifinta bayan ta wankawa mace biyu mari a jiya matan dake da fada a ji a cikin garin baki daya? A gaban sarki ta mari matarsa sannan ta tsinkawa matar mahaifinsu mari Kansa kawai ya girgiza ya ja hannayensu Sai da ya kaisu bangarensu ya ce" maza ku shirya bara na sa a kawo mana abin kari daga restaurant abusa maza ku shirya kowa ya karya a hanya Sunna fita Abih ya mike ya ajiye yar saman kujera Juyowa ya yi rai bace ya nunata da yatsarsa ya ce" ke, aman baki da hankali ko? Yaran a cikin gidan ubansu ki ce ba zaki basu abincin da ba ke ke na ba ba kuma ke ke girkawa ba? Look Mardiya, bana hada y'ayana da kowa , bana iya jure rashin mutunci a kan yarana bayan su kadai malaka duniya Na rabu da ke ba wani abu bane , lale y'ayana basu kyauta ba aman ki sani ke suka baiwa laya ba ni ba, kuma ke kika tabo har haka ya faru da ke, da baki ringa wulakanci kina jifansu da kalamai kina zagar masu iyaye ba, da ba'a nuna sune masu iya asiri ke aa ba, da du haka bata faru ba Da kakausar murya, ya jirgice mata tamkar ba shi ba ya ce" Daga yanzu, daga rana mai kamar ta yau, ki kiyaye hannawa y'ayana abinci, ki kiyaye shiga hurumin da ba naki ba idan ba haka ba Mardiya gorin da kike masu cewa kin fi baki daya iyayensu jimawa da ni zai zo karshe Walahi bana hada y'ayana da kowa! ............................................. Kai kawon da yake ya fi a kirga, hankalinsa a matukar tashe, ransa sai suya yake yana kara gwada number da ta dora masa Wayar ya wurga jikin bango yana dafe kansa Yaronsa dake nemo masa mata ne ya yi gagawar zuwa ya dauko wayar yana kallon ogan nasa da tarin tambaya da kuma mamakin irin budurwar nan da ta dauki hankalin ogansa har haka Da sauri ya ce" oga, ka yi hakuri ka kwatanta min kamaninta, ni kuwa zan bazama na samo maka ita koma yar waye na kawo maka ita ko na kawo maka numberta na gaskiya dan da dukan alamu ba numberta bane ta baka dan ana fadin number nan babuma ita wato ba'a dorata daidai ba Sai da ya sauke huci ya dago kafcecen bakin hannunsa ya ce" isa, yarinyar idan ka ganta tama dauke da idannuwan mage Ka san yaya idannuwan mage suke? Sunna da girma da wani irin lu.u lu.u a cikinsu wanda idan har ka shagala zaka iya zubar da salabe tsabar kyansu da dukan zuciyarsu Bakinta madaidaici ne, lebenta na kasa ya dan fi na sama girma sannan lebenta yanda ka ga ruwan kasa haka yake yana sheki kamar wani diamonds Fuskarta yar doguwa ce, mai dauke da gashin gira wadatace wanda yake gyare kamar na yar tsana Hancinta dogo ne sosai sannan da dan fadinsa kadan Gashinn idannuwanta dogaye ne sannan bakake ne sidik ga cika wa'inda suka karawa fuskar nata wani irin kyau da haske Gashin kanta wanda ya leko sosai ta kasan dan kwalinta baki ne sidik yana wani irin kyalkyali Wani kanshi da take shi ya kara fuzgata zuwa gareta A zaune take a cikin mota ba zan iya fadin yannayin jikinta ba aman abinda na sani ta tara hips domin irin yanda cinyoyinta suka baje a cikin bakar doguwar rigar dake jikinta Fatarta kalar bak'a ce, bakin nan mai hasken gaske, ta shafa mai mai dan maski wanda ya saka fatar nata yin wani mus mus tana kara fitar da sirrin kyanta Da mamaki ya ce" oga bak'ar mace fa kace? Aman oga ina ce ka tsani bak'ar fata domin ka sha fadin kai ko haukacewa ka yi ba abinda zaka ci da bakar mace dan ba zaka iya kayan haushi ba Murmushi yana girgiza kansa ya ce" to ka dauka na sheka maka karya a wancen karon, ka dauka du da nake fadin hakan ban hadu da ainahin mace bak'a wace ta san darajar bakinta harma ta saka min sha'awarsa daga kallo daya Ka dauka cewa wannan yarinyar ko nawa zan biya dan ta zama malakina zan iya biya Ba soyayar shan minti ko na dare daya nake so da ita ba So nake na kawota gidana ta sama min iri irinta na hada da jajayen buzayena na cika gidana da jarina Shiru ya yi yana tunanin irin kukan shagwabar da ta dan sakar masa hakan ya sa tsigar jikinsa baki daya tashi da karfi karfi ya ce" rashin bani cikaken numberta kuwa ya nuna min cewa ita din mai tsada ce, kuma na yarda na siya Shi dai baki daya ogan nasa yau ya rikita shi, dan haka ya ce" Oga na ji kace a mota take ko? Wace irin mota ce? Juyowa ya yi ya ce" hilux ce baka sidik, sabuwa ce mai number Nigeria dan ko awo bata mata ba Da sauri ya kale shi, ido ya zaro ya ce" Oga, ko dai *NAJEEBA* kake magana a kai? Ogan nasa ya ce" wacece haka? Ya ce" Najeeba mai saloon NAJEEBA MUTALAB, wannan baban saloon din da ake magana baki daya garin nan Da kace mota baka Hilux sabuwa na tuna ba'a yi sati biyu ba da zakariya ke fadin ta dauko sabuwa domin budurwar uban gidansa ce Da sauri ya ce" kana nufin yarinyar da na gama zana maka ce budurwar csp Jibril? Da sauro ya ce" oga ai idan dai *NAJEEBA* ce, ita da kanta *MAGE BA, MAI KWONCIYAR DAUKAN RAI* wannan shine kirarinta Budurwar juju isma'il ce, Budurwar Elhaj razak ce wannan baban dan kasuwan Shiru ya yi sakamakon irin yanda ogan nasa ke kokarin bige shi Bakinsa mai dauke da hakora mai tsawargna ya hade da kishin NAJEEBA cikin zuciyarsa ya ce" kana nufin yar hannu ce? To koma yar hannu ce ni zan kwasheta Ai allura ce cikin ruwa Ka je ka samo min asalin numberta ni kuwa zan nuna masu su kauce idan basa iyawa Wata daria ya yi ya ce" zan yi mata bulala da tarin kudina Zan wanketa wankin da zai haukatata Zan gabatar mata da maganar aure na shinfide mata sadakin millions goma Zata gigice ne ta amshi aurena ta kawo kanta dakina Da sauri ya juya ya fita , shifa nan take ya ji tausayin ogan nasa ya kama shi Sai kuma ya daga kafadunsa yana fadin" mai yiwuwa y'ayan mutane da kake lalatawa ne kaima zaka hadu da ciwon zuciyarka, dan na tabata baka taba haduwa da mai wanke aljihunka a lokacin da kai kanka baka ankara ba sai yanzun dan tas zata cinye maka tanadinka Wuni ya yi yana yawo yana bin kama daga yan matan garin masu ji da kansu har zuwa yan daudu Aman du wace ta santama bata bada number sai dai ta fada masa ya je ya amsa Cike da gajiya ya dawo yana tunanin yanda zai yi Yama na yi ya shirya da wuri ya fita wajen gudu, wajen da ake basket ball, da hand ball, da dai sauransu Ya jima zaune, harma an fara buga kwallon har an tafi sallar magariba an dawo Har ya cire rai da zuwanta sai hango bak'ar motarta ya yi ta danni kai Hamdallah ya yi ya kara gyara zamansa Daga cikin motar bayan ta kashe ta ziro kafarta guda A hankali ta ziro dayar kafafuwanta dauke da wani takalmin basket fari tas mai nike ja Kana gannin takalmin ka san babar harka ne zai kai dubu tamanin a kadan Karasa fitowa ta yi daga cikin motar hannunta dauke da ball dinta ta rufe marfin ta shiga takawa Yawancin samari da kuma yan matan wajen sun bada hankakinsu kanta wasun kuwa satar kallonta suke Da yawa samarin sunna jin inama ace budurwarsu ce? Wasun kuwa sunna mangarin irin kayanta na sport wa'inda ko wace rana zata zo da sabin yayi masu motsi Da yawan yan matan wajen sunna mangarin irin yanda idan ta saka kaya ke mata kyau, wasu na son yin kawance da ita wasu kuwa na matukar jin haushinta da kishinta duba da irin yanda take dauke hankalin manyan mazan dake wajen manyan ma'aikatan dake fitowa motsa jiki da yawansu sum girmeta girma ba na wasa ba aman kuma ta fi su farin jinni Idan kudin ne akoy wa'inda suka dameta suka shanye aman an fi hangota kansu Da tarin nutsuwa ta karasa jikinta sanye da dogon wando wanda ya kama duwawunta dan irin girmansu sai dai ya saki daga kasa Sai rigarta ta gudu mai dogon hannu wace tana zuwa ta cireta sai ta kasa ja wace ke dauke da karamin hannu Baki daya kalar fatarta iri daya ce kama daga wuyanta, fuskarta, hamatarta idan ta daga dan amsar ball din a aske tas kuma ba wani baki kirin ko yannayi mai nuna rashin kula tas tas tas haka take A hankali ta shiga gudu dan ka'idane idan ka zo sai ka zagaya terrain din sau hamsin kafin a raba da kai a hau buga basket din Tana gudun ne tana dan buga hannunta da du wanda ta tarda dan gaisuwar ne haka, sai dai idan ta tardo namiji bata hade hannunta da shi sai dai ta daga masa hannun kamar zasu hade sai ta wayance ta kauce tana daria Sai da ta gama aka raba da ita ta hau saman filin basket din Sun kora da bugawa, ball din na hannunta tana gudu tana dokata da kasa ball din na dawowa tana neman wanda zata ba kawai sai ji ta yi an rukunkumeta daga bayanta wanda sam ba haka a basket idanma amsar ball ne zaka yi sai dai ka tinkari mutun idan ka yi sa'a ka amshe halas idan kuwa ka kasa wani ya kuma tarbansa ko ta gefen mutun aman sai gashin an rukunkumeta kuma namiji ne domin daga hannunsa da irin rikon da kuma warin zufar da yake ya shaida mata hakan Da wani irin firgici ta saki ball din, tana juyowa ga mamakinta dan wajensu ne bama dan dayan bangaren bane Wato ya yi haka da gaya ko? Ranta ne ya yi kololuear baci duba da yau itace wannan bakon ba'adaren ya tabawa jiki harda kwonto mata a jikinta ya dora hannunsa afatar jikinta harma saman hannunsa ya goge kasan mamanta Baki daya jikinta ne ya dauki rawa....ka ku manta NAJEEBA nada rashin ji, aman fa ba ta inda ake zato ba Ba zato ba tsamani ta daga hannunta ta....... 🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕 [31/03 à 21:34] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 6 Ba zato ba tsamani ta daga hannunta ta sauke saman fuskar garjejen ba'adaren da ya rungumota jikinsa Bako ne, shi bako ne sannan dan baba da rai ne Ya saba life, yana gannin NAJEEBA ya yi tunanin yar life din ce hakan ya sa ya fara isar da sakonsa ta haka dan ta gane ta yi sabon kamu Sai dai abinda ko ubansa bai taba yi masa ba ya ziyarce shi a lokacin da bai shirya ba Idannuwansa ya waro da karfi da mamaki wanda sakamakon marin ya saka baki daya hankali ya yo kansu Bata taba tunani ba, bata taba shiryawa ba sai ta yi ya daga dafkekiyar kafarsa ya daga mata bugu a cikinta Wata irin razananiya kara ta saki kafin ta tafi luuuuuuu a sume Gaba daya wajen hautsinewa ya yi ya hargitse Zaratan mazan dake son malakarta suka hayayako inda zaratan yan matan dake hasada da ita suke kokarin tare masa Shima cike da sangarta ya kara fitar da idannuwansa yana fadin" ni bani da rai da ta mare ni ne? Da wani irin sauri wani baban soja dake wajen Captain ne ya daka tsawar da ta saka du suka fara shiga taitayinsu harma wasu suka shiga silalewa dan kar abinda basu taka ba su kwashe Hannawa ya yi a tabata, ya kirayi ambulance sannan ya tsare wanda ya yi dukan ya yi kiran police dan shi soja ne baya kamu sai police Nan fa wajen ya hargitse aka shiga yada maganar ta waya da kuma wa'inda suka rigaya suka silale A lokacin DAYABU na zaune a katon falon SARKI , sun gama cin dadadan abincin da aka gabatar masu , ya kwontar da muryarsa yana kokarin kara bashi hakuri kan ya manta marin da NAJEEBA ta yiwa Zinariya Sai da ya surbi lipton din da aka hada masa mai dauke da lemun tsami da na.a na.a sai turiri da kanshi yake kafin ya kale shi A hankali ya ce" kana nufin na manta, na yi kamar ba'a yi ba? Da sauri DAYABU ya gyada kansa ya ce" mun mata fada sosai, ita da kanta ta yi nadama, tana kuma bada hakuri sosai Bakinsa da ya dan leko dan shan lipton din ya dan tabe ya yi dan murmushi sai da ya jima sannan cikin magana kasa kasa sosai da ba dan yana sauraronsa sosai ba da ba zai ji ya ce" to ta zo ta duka ta baiwa Zinariya hakuri Kallonsa DAYABU yake, lokaci daya kuma yana tunanin maganar , yana shirin yin wata maganar wayarsa ta shiga vibrating a aljihunsa Da sauri ya saka hannunsa ya lalubo ya fitar yana duba wanda ya yi kiran Gannin sunnan abokinsa ne ya saka shi dagawa Abinda ya fada ne ya saka shi zabura ya tsaya, a tsorace ya ce" what? Yaushe? Ita da wa? Me ta masa? Ina take? Dukan tambayoyin nan a tare ya jero su kuma hankalinsa tashe hakan ya saka SHAHEED kafeshi da idannuwansa masu kalar na zaki yana kallonsa Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une ya fada hankalinsa tashe yana fadin" gani nan tafe Da sauri ya kashe kiran ya juyo wajen SHAHEED dake dubansa da duba irin na tambayar meye Hankalinsa tashe ya ce" NANANAJJEEBA ce , sukai fada da wani ya daketa a ciki a wajen sports, yanzu haka dai an tafi asibiti da ita a summe Irin duban da ya yi masa , ba tare da ya nuna alamun zai tanka ko zai tayar da hankalinsa a kan lamarin NAJEEBAR ba ya saka DAYABU dubansa da duba irin na haba dan uwa Dan zamewa ya yi ya zauna yana kallonsa ya ce" haba SHAHEED maimakun ka zabura ka tashi ka bada umarnin a fitar da motar sirri a ja mu je ka ga yar uwarka sai ka yi min duba irin na tamkar an daki makiyiyarka ko tankawa ba zaka yi ba? Duban da yake masa dai ne bai daina ba, hakan ya sa DAYABU mikewa ya kara kallonsa ya girgiza kansa a hankali ya ce" da hakuri, da kawar da kai, da adalci aka san saraki, sannan basa bambanci a kan kowa, sukan talabi mai ji da marar ji, sukan yi yafiya a kan kowa Sasautawa ya yi ya ce" ban san me yasa taurinka ya tsaurara a kan yar uwarka ba Sada kansa ya yi ya ce" Allah ya huci zuciyar sarkina, a huta lafiya Yana gama fada ya juya da mugun sauri har kamar ya kifa ya fice daga fallon wanda dogarai ke tsaitsaye a kofa sunna gannin fitowarsa suka shiga yi masa fatan alkhairi da adu'ar sauka lafiya Sai da ya ga tafiarsa sannan ya lumshe idannuwansa, tun da ya lumshe bai kuma budewa ba sai ajiyar zuciya da yake saukewa a hankali ya afka duniyar tunani A firgice ya karasa asibitin Sai dai abinda ya bashi mamaki ya kuma dakatar da shi kafin ya shige shine gannin docter Jibril da kuma mala'ika wato baban sojan da NAJEEBA ta baiwa banzar number a hanyarta na dawowa sunna tsaye kowane na muzurai Ganninsa ya saka su saurin tarbo shi sunna kokarin rige rigen gaishe shi Fuska hade sojan ya ce" ai na hana kowa shiga sai na kusa da ita, ta farka kuma wanda ya daketan yana hannunmu ko uban waye ubansa sai ya amsa laifinsa na dukan matana! Doctern ya kale shi da sauri da mamakin matarsa kuma? Shima a matsayinsa na docter ya matso ya ce" barka da karasowa yaya, Alhamdulilah ana kawota na saka manyan docters abokannan aikinmu sun yi mata dukan kulawar da ya dace Yanzu haka maganar da nake maka ta farfado cikin hankalinta, sakamakon dukan ya mata a cikinta wanda take nisawa kuwa mun saka a yi mata dukan gwaje gwaje, ka san dare ya yi du an tashi da aikin gwaje gwaje aman da yake asibitin tamu ce ita kuwa matar docter ce ya saka har gadonta aka ringa turo kayan aiki ana aunata yanzu haka dai ana iya tafia da ita gida dan ta fada min bata son kwana a asibiti bata san irin halin da yan uwanta zasu kasance ba ya sa na bada damar a tafi da ita gida ko mu bada sabuwar ambulance a kaita har kifar dakinta Wata uwar harara sojan ya watsa masa Shima ya yi masa wani kallo irin na shiga gabankan nan Murmushi DAYABU ya yi yana kallonsu daya bayan dayan kafin a hankali ya ce" Allah ya saka da alkhairi Ba'a hana shi shiga ba domin docter na tare da shi Sunna shiga ya karasa da sauri wajen bed din da take kwonce idannuwanta lumshe gashin idon da ta saka sun yi mata luf luf sun kara girman idannuwan nata Lebenta kuwa du azabar da ta sha yana dauke da kalarsa na pink color iya na kasan na saman kuwa da dan duhunsa Karasawa ya yi da sauri yana yaye abin rufar da aka rufa mata har daidai kirjinta yana talabota Nan danan tabararta ta tashi, shagwabarta ta motsa ta langwabe masa ta saki kukan shagwaba tana kara langwabe masa Cikin zazakar muryarta take fadin" ya, cikina, a cikina ya dakeni bayan shine da laifi haka kawai ya taba min cikina da hannunsa dan na mare shi ya dakan kafarsa a cikina A hankali ya kara riketa ya ce" NAJEEBA, sannu, sannu kin ji? Kuma langwabewa ta yi tana wani irin far da idannuwanta ta ce" ba zan iya yafe masa ba Kansa yake gyadawa kafin ya bata amsa muryar sojan nan ta daki kunnayensu yana fadin" ni kaina ba zan iya yafe masa ba tunda ya taba min kafiarki, ashema shine marar gaskiyan? Ya dauka jikin ki abin banza ne da kowani banza zai iya tabawa? Likitan ya kale shi da sauri, sai ya girgiza kansa ya juyo yana kallonta Har kasan zuciyarsa yake jin kishinta sannan baya so ko da wasa ace tana son wani fiye da shi Shifa sonta yake kuma ba son a watse ba Gannin hankalinta ba a kwonce ba ya saka shi yin hakuri ya shanye kishinsa ya kara dudubata ya rubuta magungunnan da zasu kara kwontar mata da ciwon cikin da take ji ya fita da sauri ya bada a amso masa a cikin asibitin kafin ya zo da kansa su kamata da likita daya su dorata kan gadon marar lafia na turawa a tura gadon har wajen ambulance aka daga aka sakata dan tsabar gata ba dan bata iya tafia ba Sai da ta ga da gaske ciki aka sakata ya saka ta mike zaune tana yatsina fuskarta ta kalli yayanta dake ta aikin jera mata sannu hankalinsa a matukar tashe A hankali ta ce" ya, da sauki fa ni kar a kaini a cikin ambulance din nan hankalin Abih ya tashi, duda yanzu ya tsane mu Murmushi ya yi ya kamata ta sauko daga bayan a hankali yana rike da ita suka karasa wajen motarsa ya buda baya ya sakata sai kokarin riketa suke son yi shi kuwa yana tarewa ta kwonta a bayan sannan ya juya ya amshi magungunnan da aka kawo Kudi ya ciro a aljihunsa masu yawa ya mikawa likitan Da mamaki ya girgiza kansa ya ce sam shi ba zai karba ba DAYABU ya dube shi da kallo irin na yana son ya fahimce shi ya ce" ka yi hakuri, ni ina matsayin tamkar uba ne a wajenta Da sanina, ba zan yarda wani ya yi dawainiya da lafiar kanwata wace na raina bayan na san ba'ai maku baiko ba Alhamdulilah in dai inada rufin asiri zan yi iya yina a kan rayuwar kanaina Ba mayar da kyauta ko kyautatawarka na yi ba Ba raina maka na yi ba Hasalima na ji dadin irin kulawar da kuka bata baki daya Sai dai ka sani hidimar tsakaninku na soyayarku daban wanda ko shi da zata ji maganana ba zata amshi kudin saurayinta ba har sai ya zama miji a gareta Sai dai zamani ya zo mana da abubuwa daban daban, a yanzu dan saurayi na yiwa budurwarsa hidima ba wani abin bane, hasalima shi ke kara aminci tsakaninsu Sai dai ba zai kai har fannin lafiarta ko cimar da zara ci ba Ka yi hakuri ka amshi wannan a je a cike dukan abinda ya dace a cike Murmushi sojan nan ya yi da jin dadin abin a ganninsa an wulakanta likitan da ya bi ya kanainaye masa waje run dazu ya ce" aa yayanmu, ai kawai ka mayar da kudadenka, shima ba shi zai biya ba, wanda ya daketa shi zai biya komai dan shine da laifi shi ya fara shiga huruminta har ta mare shi Ita dai idannuwanta ta lumshe tana jin haushin ubanda ya fadawa malaikan nan cewa tana asibiti Lale ta fara yarda cewa an saka mata ido a garin nan Idannuwanta ta kuma budewa ta kalle shi Bakinta ta tabe a ranta ta ayanna" anya kuwa yana sallah? Yo sam ba annuri a tatare da fuskarsa sai duhu da warin baki! Jin haka ya sa shima likitan sauke ajiyar zuciya domin shi dai ba zai karbi kudin nan a gabanta ba, haba shi da yake so ya yi mata wanka da kudi ta yanda sai shi Shima sojan murmushin da yake yi yana ayanna ina zan yarda ka yi bajinta ka biya bayan na zo ne na rufe baki daya bakin yan gidansu da shagun? Ai zan saki bakin aljihunna na wankesu da yayan banki ta yanda zasu miko min yar koda ba fatiya na je na kara buda rigar nan nata na kali na cikin rigar nan dake hararena da kyau Salama DAYABU ya yi masu bayan ya yiwa sauran likitocin da kuma masu tsaron kofar urgence din alkhairi wanda suka ji dadi sosai harma suka shiga bayanin ko shi waye cewar yan uwan sarki ne fa, kowa kuma ya san waye sarkin wanda idan ka samu kadaicewa da shi ka warke da izinin Allah Sunna zuwa gida tun a hanya ya yi waya cewar a kawo masu Burger adadin da ya san zasu koshi kafin ya karasa shiga da motar Talabeta ya yi a jikinsa har suka karasa shiga cikin falonsu sai kara kwontawa take tana raki tana rigima shi kuwa sai sannu yake mata tamkar ya fashe da kuka Sunna shiga hankalin yan uwanta dake zaune ga abinci da yawa sun kasa ci sakamakon jin shiru yayunsu uku basu dawo ba wato DAYABU, NAJEEBA, DA ZAHRAU Gannin Najeeba langwabe tana kara sakin kukan tabara ya saka su tashi a firgice sunna rige rigen karasowa wajensu Hankalinsu tashe suke tambayar me ya sameta, ahin ko accident ta yi? Ita kuwa sai kara lafewa take a saman kujera baba ta ki amsawa Abincin da aka kawo ya kalla Bakinsa ya tabe ya tambayi ummu kamar haka" ke ummu wa ya kawo abincin nan? Sai da ta tabe bakinta itama ta ce" mai gidan ce ta kawo Bai ce komai ba sai zama da ya yi ya shiga balo maganin Najeeba ya amshi ruwan da Bilkissu ta dauko ya bale ya mika mata Fuskarta ta yiwa takwaf takwaf hakan ya saka shi fadin" Najee, kin ga ki amshi magannin nan walahi idan kuwa ba haka ba zan dura maki shi katuwar banza kina yin amai kuma zan kara maki wani Rauda ta ce" ya wai me ya sameta ne? Ko ciwon cikin ne? Na ga kuma ai ba karshen wata bane Yayansu ya ce" a wajen basket aka daketa ta summa Ido du suka zaro kafin karaminsu mai shekara bakwai ya bushe da daria ya ce" yaya an rama min dungure min kan da ta yi a school Hararansa ta yi ta ce" NAJEEB zan wanka maka mari Da tausayi kulsumu ta zauna gefenta tana dafa gefen wuyanta ta ce" wani dan iskan ne ya dakar min ke bayan ba'a dukan min kanwata Langwabewa ta yi a jikinta ta saki shashekar kuka ta ce" bako ne, kuma walahi na daku baki ji yanda har yanzu nake juwa ba, ya kashe min kwayayen haihuwa Khairy ta kai hannunta ta buge mata baki ta ce" shegiyar banza mai mugun fata, idan ya kashe maki kwayayen haihuwa ni ba sai na rike mar makogwaro ba? Yayansu da ya shigo da manyan ledojin burger ya ajiye inda yaran suka fara tsale, sufa a dasha dan du idan manyan sukai fushi haka ake koda yaushe zasu ringa cin dadi ne, duda na gidansuma mai dadin ne aman kun san irin gashin nan na waje mai tonka akoy motsa kunne (aminiya kawar arziki maman jaririna ga kaza🤣🤣🤣) Dubansa ya kai wajen magannin gannin bata sha ba ya saka shi yin wajen da sauri da niyar dauka ya dura matan Sai dai bai kai ga karasawa ba Zahrau ta shigo da gudu tana kuka sama sama tamkar ranta zai fita NAJEEBA dake langwabewa tana kamar ba zata iya tafia ba tana raki ita ta fara zabura ta yi wajenta hankali tashe Baki daya suka zagayeta sunna tambayarta meye ita da, wa ya mutu, me aka yi take kuka? Cikin wani irin kuka tamkar zata sike ta budi bakinta ta ce" *wai wai wai an fasa aurena* Ta karsashe tana mai kife kanta a kirjin NAJEEBAR da ta fara karasowa sannan ta fi kusanci da ita a durkuahen da take Shin kuna so? Idan kuna so ina comment ne mai nunan kuna bi? Free ne mutanena ku zagine mu je tare 😄😄😄😄😄 [31/03 à 21:34] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 7 A hankali NAJEEBA ke shafa lallausan gashin yayar nata da dan kwalinta ya fadi sakamakon kukan da take shekawa Du a firgice suke, aman sun rasa wace irin tambaya zasu yi mata Hannunsa ya saka ya janyeta daga jikin NAJEEBA ya jata saman kujera ya zaunar da ita sannan ya shiga sintiri Baki dayansu suka koma suka zazauna Yar budurwar cikinsu mai shekaru goma sha biyu ta ce" shikenan yanzu anko din shada da lesh da komai din da akai mana an fasa auren? Hararanta Bilkissu ta yi hakan ya sa ta yi shiru ta rafka tagumi cike da zulumin an fasa aure shikenan ba zasu yi sabga a gidansu ba Hannayensa da yake hadewa yana kara budewa ya kuma hadewa ya ce" wani irin ya fasa aurenki? Wani abu kikai masa? Tana kukan dai ta ce" aa, dazu ne da ya zo yake tambayana wai me ya kaimu gidan sarki ne? Sai nace masa ziyara Shine ya ce min" Zahrau karya kike, ashe abinda momy ke fada min gaskiya ne? Ku dangin jaraba ne baku da aiki sai masifa da fada? A gaskiya zahrau ba zan iya auren macen da ta kai karar ubanta aka bashi laya ba, kuma a gaban mutane kanwarki ta mari matar ubanku maimakun ku horata sai kuka tare mata fada, to gaskiya wace kika shakar nan aminiyar momy ce kud da kud, da ita aka kawo kayanki ita ta je tana kuka ta zayanewa momy komai ashe ku dai dangin jaraba ne? Ummulkhair ta zabura ta mike ta rike kugunta ta ce" mu ne dangin jarabar? DAYABU ya harareta hakan ya sa ta koma ta zauna tana gunguni ZAHRAU cikin sanyinta ta ce" nima nace da shi ya yi hakuri, abinda ya kai mu gidan sarki sirrin cikin gidanmu ne, kuma fadan nan da aka yi suna da yawa fa suka rufawa NAJEEBA ita kadai, ta yaya yake so na kyale ina kallo a dakar min kanwata? Shine shine.....sai ta fashe da kuka tana kara dora kanta a kirjin NAJEEBA wace du ta manta ciwonta jikinta sai rawa yake dan walahi a duniya sun rayu da rayuwar jin ciwon dan uwansu a cikin jinnin jikinsu Ana fadin maganar dan ubanci a duniya, su basu san da wannan kalmar ba Sunna fada tsakaninsu fa, aman idan kana son ka ga hadin kai da tsantsar soyaya wani abu ya samu dayansu DAYABU da hankalinsa ya kara kololuwar tashi ya ce" shi ne me? Dagowa ta yi tana kallonsa ta ce" shine ya kara kiranmu da jarababu harma yake ikirarin ko Abanna zai bashi hakuri ba zai hakura ya iya zabawa y'ayansa uwa irina ba dan sam ban samu tarbiya ba bare na tarbiyantar da yaransa Nima raina ya baci shi ne shi ne..... Kara tsareta ya yi da ido ya ce" shine me ZAHRA? Ta sada kanta kasa ta ce" shine nima nace masa mu ai du da sauki, shi da yake shege wanda uwarsa ta haifa ba aure bayansama ta haifi uku kannensa baki daya su ba'a zage su ba sai mune zai saka gaba yana ta zagi Idannuwansa baki daya ya rurubo lokaci daya ya tafa hannayensa ya ce" MAHAMADU rasululahi salalahu alaihi wa salam Da wani karfi karfi UMMULKHAIR ta ce" kin min daidai, ai walahi da kika kai karshe baki fada min ke kuwa me kika ce masa a kan irin zaginmu da ya saka ki a gaba yana yi ba da sai na dauke ki da mari walahi, dama sam bai min ba mutun ne sai shegen taurin hannu idan zai maki kyauta sai kaf danginsa sun sani Namijin dake buga gem kuma yana kallonsu a wayar yayansu wato Najeeb ya ce" lalala, ba yaya ya hana karami yace zai daki baba ba? Yayansu kam dake salalami dubanta ya yi ransa bace ya ce" sau nawa zan maku magana kan koda ranku ya baci ku ringa tauna magana kafin ku fadeta? Yaya zaki masa gori Zahra dan ya zage ki? Ke baki da bakin rama zagin da ya maki koma wani kala ne aman banda irin wannan gori? Shin shi ya saka mahaifiyarsa haihuwarsa haka ko me? Ko ke kina tunanin an maki albishiri din zaki gama da duniya lafiya ba tare da wata jarabawar da zaki ringa jin kunyar kanki ta same ki ba? Ina gannin kece mai hankalin cikinsu aman sai ki bani mamaki har haka? Na tabata da Najeeba ce da ake gannin ta fi ku rashin hakuri ba zata yi haka ba sai dai ta cire masa bakinsa dan gobe kar ya kuma Sanyi ya yi gannin du sun zuba masa ido shi kuwa yana fada sama sama Yatsarsa ya dago ya shiga nuna su daya bayan daya ya ce" ku yi kokarin gannin kun rufe naku sirrin, Ku sanni, bana so, bana son ku kasance masu izgili da kuma son daga fitina a duniya Domin kunada baban tabo Kuna tare da baban tabon da mai tabon kansa bai san na san yanada tabon ba Bana son abinda zai taba min nasabarku Bana son a fara da haka a kanku cewa ana fasa aurenku Bana so abin ya yi nisa Wata iska mai zafi ya furzar yana kallonta ya ce " to in ba rashin hankali irin na dan fari a wajen uwa ba me ya kaiki buda baki ki yi wannan shirmen? Ita dai kukanta ne ya tsaya a lokacin da yake bayannin suma sunnada sirri, tabo! Wannan kalmar sau uku kennan tana jinta daga bakinsa idan ta tsare shi sai ya nuna sam shi ba wani abu yake nufi ba yana nufin dai ita mace ce ya dace ta kasance mai taka tsantsan Baki Najeeba ta tabe tana hade mata gashinta Ta riga ta shaka, ta shaka iya wuya hakan ya sa ta kasa kida tofa ufan ne sai irin yanda take ayanna yanda zata yi da shi Ummukulsum ta ja tsaki ta ce" shine kike kuka? Kike kuka dan namiji yace ya fasa aurenki? Da me kuke jira ku a duniyarmu? Koda mun yi auren za'a sako mu ba tare da an waiwayemu ba, idan mun fito da ciki za'a irga mana ranakun haihuwarmu muna haihuwa za'a dauke dan a kaishi nesa da mu Me kuke jira? Me kuke tunani a rayuwarmu? Yanda ya yiwa y'ayan wasu, yanda ya ringa wulakanta y'ayan mutane yana saki a kan dalilinsa na son zuciya dole sai muma an ringa sako mu ana laya masa zawarawa, Dole sai mun cika masa gidan nan mun tsufa tare mun mutu tare...... Wani gigitacen marin da ya sauka a kan fuskarta wanda ya tsorata yan uwanta ya saka su zabura sunna kallon wanda ya yi marin a firgice ya sakata dantse harshenta har jinni ya fito na walaha Kafin su yi wani abu ya warci igiyar cajin dake ajiye ya shiga laftar du wanda hannunsa ya kai...kun san balarabe idan ya tashi dukan yaro yakan yi masa duka kamar zai kashe shi Mahaifinsu baya duka a banza, aman du randa hannunsa ya daga sai ya daka Da wani irin tsinanen gudu DAYABU ya warci kananun biyu ya fada dakin NAJEEBA wace ta rigayi kowa guduwa Yana shigowa suka dantse kofar wanda hakan ya saka uban nasu dukan kofar ransa bace yana jijigawa Ransa a matukar bace ya ce" bude min, marar kunyar banza marar kunyar wofi, bude min ki fada min maganar banza a gabana Ummu ni ne zaki yiwa fatan na maku aure a sako ku? Kennan ni jarabawar sake saken mata ba zata iya samuna ba ko? Zahrau shine kika zagar masa uwa kika ce masa shege? DAYABU shine ka saka su gaba sunna munanan kalamai a kaina ba zaka tataka su ba? Khairy shine kina ji ta zagar maki uba baki mareta ba? Najeeba me ya hada ki fada da dan gidan docter Basheer? Hannunsa ya saka ya kara dukan kofar NAJEEBA wace ita ta fi kusa da shi kafin ya zame ya zauna a jikin kofar yana sauke ajiyar zuciya Dawowarsa kennan ya tarar da wanda ke neman auren Zahra da mahaifiyarsa da kawayanta biyu a kofa sunna jiransa mai gadi ya hanna su shigowa sai kunfar baki suke wai sai ta fada masu a inda ta ga ta yi shegu Dama tun a hanya inda ya tsaya siyan fruits ya tsinci maganar fadan NAJEEBA harma ta summa Daga cen ya nufi asibiti aka shaida masa yayanta ya daukota an sake su Shine ya shigi ya tarar da Ummu na fadin irin wadinnan magangannun wai koda sun yi aure za'a sako su ne da ciki ko daga sun haihu a sake su Idannuwansa ya lumshe ya yi shiru yana tunanin rayuwa A jiya ya so kwarai ya saki Mardiya, sai dai gannin yanzu y'ayan nasa kansu sun fara fada masa magana a kan auri sakinsa ya saka shi kyaleta domin ba'a taba masa y'aya a wanye lafia Idannuwansa ya kuma lumshewa yana tunanin inda zai bi ya yiwa tufkar hanci, ya zama wajibi ya katse hanzarinta, ya zama wajibi ya yiwa tufkar nan hanci idan kuwa ba haka ba lale watarana y'ayan nasa zasu yi abinda zasu zubar da hawayen jinni, zasu ja sirrin da yake binnewa ya fito fili Zasu saka baki daya su tatara su bar kasar a lokacin da suka zama abin kyamata sannan abin gori a cikin kasar nan A hankali ya ce" ku fito Du sun ji shi, aman ba wanda ya yi yinkurin fitowa Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya ce" ku fito, ba zan daki kowa ba Zahrau ta fashe da kuka ta ce" ABIH, dan Allah ka yi hakuri Muryarsa ya dan daga ya ce" magana nake so mu yi ku fito na fada maku ba zan daki kowa ba Shiru suka kuma yi, wanda hakan ya saka shi sada kansa yana jin zuciyarsa ba dadi Sam baya jin dadi a kasan zuciyarsa Karar bude kofar da yake jingine ya saka shi sauri dagowa harma ya mike tsaye ya juyo yana son gannin wanda ya iya fitowa A hankali ta fito tana matsowa kusa da shi hankalinta a kan fuskarsa Shima idannuwansa ya sauke a nata fuskar Lokaci daya ya ji wata kauna irin ta da da uba na mamaye zuciyarsa A hankali ta daga kanta tana kallon fuskar nasa, idannuwanta da ta gama sannin sunna da effet a kan mahaifin nata koda ya tashi duka sunna saka shi dakawata ta kara masu girma sosai sannan ta yi masu kwal kwal Nan da nan kwallah ta cika su, bakinta take son budawa aman ta kasa A hankali ta shiga kokarin riko hannayensa muryarta na rawa tana son fitar da lafazi ta kasa, sannan hannayen nasama ta kasa rikowa dan sai take gannin sun mata nisa sosai Idannuwansa ya rintse sakamakon jin wani irin tausayinta ya gama halaka bacin ran nasa Tsantsar kaunar y'ayansa yana matukar yin tasiri a rayuwarsa Ko dan sun kasance mata da yawa wa'inda ya dauki son duniya ya dora masu? A hankali ya kama habarta ya dan dago yana kallon kwayar idannuwanta Muryarsa ya sanyaya ya ce" kuka zaki yi? Jin ya sauko hawayenta suka samu damar zubowa tana kallonsa sai a lokacin kuma bakinta ya bude cikin sanyin murya sosai ta ce" kar ka dake mu Abih, ka ga an summar da ni bayan bani da laifi, ka ga ya zazageta dan kawai an fada masa abubuwa Abih ina zamu shiga mu ji sanyi ne? Da sauri ya kama hannayenta ya karasa kusan dakinta sosai Muryarsa ya dan daga ya ce" ku zo gare ni, ku zo kun ji? Jin irin yanda muryarsa ta sanyaya ya saka du suke budewa sunna fitowa Du kusa da shi sosai suka zo suka zazauna wasun su har sunna dora hannunsu saman jikinsa Murmushi ya yi yana kallon ZAHRA ya ce" Zahra, daga yau kar ki kuma zagin mutun da nasabarsa, ko dukiya, koma menene kin ji? Na gwamace ace da ni gaki cen kun daku da mutun na je na raba da ki yi irin wannan abin, kin san me ya sa? Kanta ta girgiza tana kallonsa, hakama sauran Hannayenta ya riko ya ce" abinda ya sa shi mutun ba'a gama halitarsa, baya fasa gannin jarabawar rayuwa har sai ranar da aka saka shi cikin kabarinsa Eh lale yin fari ne kadara, na biyu ganganci na uku kuwa da gangan Aman koda y'aya goma ta haifa na hane ki yi mata gorin hakan domin ko ke kin tsufa zaki bar baya kin ji? Kanta ta ringa gyadawa Ya maida dubansa wajen Ummu ya yi murmushi ya ce" haba Umana, idan inada mumunan hali ai bana tunanin zaki kulaceni haka, na fi tunanin zaki min adu'a sannan ki yi fatan kar Allah ya jarabeni da ku, wato ya dora hakan a kanku dan na rantse maki ban san wani hali zan shiga ba, ki ringa kyakyawan fata kin ji? Kanta ta ringa gyadawa itama tana share hawayen fuskarta Hannun NAJJEBA dake cikin nasa ya kara rikewa yana kallonta, murmushi ya yi ya ce" ni ko dai kece jinnin abuna ba ni ba? Yaya aka yi da wahala safia ta yi dare ya yi baki yi fada ba? Allah ya shirye ki Kanta ta kifa saman cinyarsa Ya kai dubansa wajen DAYABU dake tsaye da NAJEEB a hannunsa wanda ya ki yarda ya sauka daga hannun nasa tun da ya tsorata kar aban nasu ya dake shi Murmushi ya masa mai tsayawa a rai kafin yana kallonsa ya ce" wa ya ce maku baku da wajen da zaku je ku ji sanyi? Kunada wajen da zaku je ku ji sanyi sosaima Ina raye, a doron kasa ai zan kasance maku katifar da zaku zo ku kwonta Tunda shi ya fasa aurenta, dama yana neman hanyar silibe mata ne, da izinin Allah, Allah zai fitar maki da miji na gari Murmushi DAYABU ya yi gannin du sun dodora kansu jikin Aban nasu Dan haka ya karasa da najeeb a hannunsa ya ringa dauko ledojin dake dauke da burger din yana kawowa yana ajiyewa Nan fa suka baje abincin, inda mahaifinsu ya fita ya je ya dauko yar karamar wace ta kai shekara uku a haife wajen uwarta ya dawo da ita bangaren y'ayan nasa inda uwar ta ringa cika tana batsewa ya zaunar da ita tsakiyarsu suka hadu sunna cin abincin sunna hira sunna wasa da daria tamkar ba sune suka shiga hali na matsananciyar damuwa yanzun ba ...................................... Da wani irin karfi ya diro daga saman bed din da yake kwonce a mike idannuwansa lumshe ya kai dubansa kan yaronsa da mamansa ta shigo da shi tana kuka tamkar ranta zai fita ta ajiye masa shi saman bed din hannayenta saman kanta sai jujuya kai take Irin yanda zuciyarsa ta buga gannin yanda yaron ya mimike sannan jijiyoyin kansa sun yi rado rado sun yi tsanwa sharr idannuwansa na kallon sama sam baya motsi ba allamun motsi a tatare da shi Hannunsa ya kai wanda ke wata irin rawa a hankali ya juyo yaron Zinariya ta kara fashewa da kuka hankali tashe ta ce" ya mutu ko? Ya mutu? Shaheed ya kalleta da sauri haka kuma zuciyarsa ta kara bugawa da karfi ya kara riko yaron ya ce"...... [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 8 Da wani irin karfi ya juyo shi yana kuma kallon fuskarsa Idannuwansa ya lumshe cike da tausayin kansa da kansa kafin ya rage tsayinsa ya shiga dodora hannayensa dan tabatar da abinda yake ganni a gabansa Tsintsiyar hannunsa ya kama ya saurara da zuciyarsa dan kara tabatarwa kansa Jikinsa a mace ya juyo wajenta inda ta yi tsaye tana jiran jin amsa Wani ihu ta so saki, sai dai ta sake shi a cikin zuciyarta sakamakon rufe mata baki da ya yi da hannunsa na dama sanann ya talabeta da hannunsa na hagu A hankali ya jata ya nufi falo baba da ita inda ta saki jikinta tamkar sumamiya tana gunjin kuka Sunna fitowa falon a kujera ya zaunar da ita still bai saki bakinta ba Yana dubanta har sai da ya rage tsayinsa ya kasance sun daidaita da junna a hankali ya ce" ihu zaki yi masa? Gunjin kukan da take har jijiyoyin wuyanta da kanta sun fito rado rado ya saka shi janyota ya bata kyakyawar runguma Hakan ya sakata kara sakin kukanta tana mai tambayarsa" shikenan ya tafi ya bar ni? Idannuwansa ya lumshe yana shafa bayanta, baki daya ta yi jajajir ta rikice Ta kuma fashewa da kuka ta ce" sai da na hana shi yin wankan nan na dare, ina shafa mai ya shige bayi har yanai min gwalo ya shiga kasan shower ya sakarwa kansa ruwa a kansa Sai da ya ga raina zai baci ya fito ya bude min Sai dai tuni jikinsa na rawa hancinsa na zubar da jinni Fashewa ta kuma yi da kuka tana rike hannunsa da ya tsurawa fuskarta ido yana sauraronta ta ce" shikennan sai ya fara karkarwa sosai da sosai har hakoransa na hadewa waje guda sunna bada sauti hakan ya tsoratani na yi gagawar rufa shi da bargo na je dakinsa na shiga binciko magungunnansa tare da wasu kayan darin dan na saka masa Ta rushe da kuka tana nunawa ta ce" ina dawowa da na daga shi na ganshi a haka, baya min murmushin, baya cewa" ki yi hakuri Anna Baya barin jikin shine nace ko summar ce ya kuma yi? Idannuwansa ya rintse yana jin wani irin yanda yake jin kansa ba karfi ba dabara A yau ya samu kansa cikin wani tashin hankali mai gigitawa a tarihin rayuwarsa A mutanen dake makale a cen cikin zuciyarsa yau ya shafe mutun na biyu kennan, bayan shafe idannuwan mahaifinsa da ya yi da kannanun shekarunsa Hasbunnalahu wani.imal wakim Sosai ya barta a kirjinsa ta samu kukan ita wanda hakan ya saka ta dan ji saukin zuciyarta Sai da ta ci kukan har ya so zarce misali kafin ya dago habarta yana kallon fuskarta A hankali ya kai bakinsa daudai nata, idannuwansa ya rintse kafin ya damki lebunnanta ya shiga tsotsa yana jin zuciyarsa ta yi masa nauyi Bashi da kalaman da zai nuna mata ta yi shiru Baya so gawa kwonce ta ringa irin wannan kukan Sai da ya san ya kashe bakin kukan sannan ya dubeta ido cikin ido cikin yannayin tausasawa domin ita uwa ce, ba wanda zai kaita jin ciwon rabuwa da yaron nan shi ya tabata da hakan, shi yasa yake jin bashi da kalmar da zai iya rarashinta sai dai ya tunatar da ita cewa itama yau ko gobe, ko watarana sunnanta gawa, wannan kira na mahalici ba wanda ya isa a manta da shi ko a yafe masa, an halice mu ba tare da mun roka ba, zamu mutu ba tare da mun shirya ba Tabas shi daya suka malaka a duniya sai bari biyu da ta yi bayansa, aman kuma wanda ya halice shi ya fita son sa Dan haka cikin tausasa kalamai da iya yinsa dan gannin shi ya jure ya bata kwarin gwuiwa ya ce" ki daina kuka haka zinaria Ki yi masa adu'a irin ta bakin uwa na tabata mala'ikun rahama zasu yi rige rigen zuwa amsarsa Ki yafe masa har cikin zuciyarki tun daga daukan cikinsa, naludarsa, shayar da shi da kika yi, da hakurin tarbiyantar da shi, ki yi kokari daga yanzu idan kin buda bakinki dan ki yi salatin annabi ne sai ko ki yi ta yi masa shinfidar kabari har a kai shi Wannan ita ce kaunar da zaki iya nuna masa a matsayinki na uwa Wannan itace babar kaunar da zaki nuna masa zinaria Kar ki manta *dukan mai rai mamaci ne* (Allah jikanka babyna😔👏) Gani take du da ya samu bakin yi mata magangannun nan dan ba shi bane ita Gani take sam bai san irin zafin ciwon da take ji a kasan zuciyarta ba Yaya zai hanata kuka da daga murya? Yaya zai hanata ihu da birgima? Yaya yake so yarensa na shiru ya kasance a kanta a irin wannan bakar rana a gareta? Bai san zafin da take iya ji ba, bata tunanin zai iya sanin karfin zafin da zuciyarta ke mata ba dan ba zai haihu ba kasancewarsa namiji Wannan lamaru kuwa shi zai sa har ya mutu ba zai ji jrin yanda baki daya zuciyarta ke tsartuwar jinni ba Zaunar da ita ya kuma yi sannan ya juya cikin irin tafiar nan tasa ta kasaitacen bujimin sarki Sam bai iya sauri ba , wannan shine saurin nasa domin har yana kokarin kauce sawunsa na kafar gaba Dakin ya koma, A hankali ya karasa wajen bed dinsa Cike da jin lamarin a kasan zuciyarsa ya langwabe kansa yana kallon gawar yaron Ko jiya har kusan karfe goma yana zaune gefensa, abinda ya fi tsaya masa a rai irin yanda yaron ya nace sai ya ga fuskarsa sai ya cire masa rawaninsa a wajen karatu Bai barshi ba har sai da ya ga ya fara gyadi gyadi ya dauko shi ya taho da shi nan bangarensa ya shaidawa mahaifiyarsa ta zo ta dauke shi yana jin baci A lokacin ne kuma ya dauke rawaninsa wanda hakan ya saka yaron yin murmushi yana shafa gefwn fuskar mahaifin nasa sai kuma baci ya dauke shi Ashe farkawa ya yi har mai afkuwa ta afku da shi? Cikin nutsuwa ya shiga shirya shi Yana yi masa wanka ne hawaye ya shiga zarya a saman fuskarsa Shikenan mutun din kennan, shikenan an kare kana kwonce sai yanda aka juyaka A hankali ya ringa llaba shi dan raunin fitar rai A hankali ya gama tsaftace shi ya kimtsa shi Ruwa ya watsa a jikinsa ya saka farar jalabiya irin ta saudiya sannan ya fito Hannunsa ya mika ya dauke shi a hannayensa ya rungume shi ya karasa saman bes dinsa da shi ya dora shi Alkur'ani ya dauko ya zauna ya buda ya shiga karanta masa murya a bude a bayanne Irin yanda yake karatun zaka gane zuciyarsa a cikin wani yannayi mai rauni da tashin hankali take Cikin nutsuwa ya samu ya yiwa yaronsa dukan abinda ya dace kowace gawa mai sa'a ta samu, ya samu adu'o'i kamar me Kiran sallar fari akai a baban masalacin gidan sarki wanda yake cikin gidan Shiru bai fito ba, a na biyu ne har hankalin liman ya fara tashi sai gashi ya fito Sallah aka gabatar, ana gamawa ya fadawa liman cewa idan an jima a samu a leko rakiyar yarima, Allah ya yi masa rasuwa Da mugun mamaki liman ke kallonsa irin yanda ya sanar da rasuwar cike da nutsuwa wada a irin ahekarinsa da yawa zaka same su da rashin nutsuwa har haka Tabas ya yarda abin sarauta ya gama ratsa sarkin nasu sai fatan Allah ya tsare Nan da nan ya sanar, wanda rasuwar ta matukar fifita mutane harma aka yi ta kokarin son ganninsa dan gabatar masa da gaisuwa sai dai ya shige da sauri ta kofar da yake shigowa Direct bangaren mahaifiyarsa ya je A hankali ya cire takalmansa ya karasa shiga ciki Tana lazumi zaune saman salayarta, sanye da wata bakar riga mai hade da hijab har kasa rigar kuma budadiya ce sosai wace take sallah ne da ita Yana karasawa gabanta ya je ya zauna wanda hakan ya sakata saurin dago kanta tana dubansa Rawanin kansa ya shiga warwarewa a hankali da sauri ta maida dubanta sosai a kansa Yana gama warwarewa ya kamo tafin hannunta ya dora a gefen fuskar nasa sannan ya lumshe idannuwansa Da sauri ta kai karshe tana kallonsa , zuciyarta kuwa ta shiga tsintsinkewa Muryarta na nuna tashin hankali ta ce" me, me ke damunka? Me ya faru a masarauta? Sai da ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa da kyar kafin ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa ya ce" ALIYU, ya amsa kiran mahalincinsa Da wani irin sauri ta zabura tana furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une Yaushe? Ciwon ne ya tashi? Ina yake? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une Sai ga hawaye a kan fuskarta Cikin matsanancin tausayinsa take kallonsa tana nin mutuwar dan jikan nata, sai kuma lokaci daya ta ce" ina mahaifiyarsa? Ina zinariyar take ne? Ya salam, wani rudun ta shiga sakamakon tunawa da ta yi irin yanda zinariya ke takama da yaron nan Takan daki kirji cike da gadara ta furta wata rana itace gimbiyar masarautar nan domin ta rigaya ta haifi magaji Koda jikin yaron ya motsa takan tirsasa shi fita ya zauna kusa da mahaifinsa wai dan ya koyi yanda ake tafiar da sharia Akoy ranar da ta yi wata magana a gaban amarya cewa" ya dace a ringa kiran yarima da mai martaba, dan ko a yanzu ba'a iya cire rai da hawansa kujera, bale idan mahaifinsa ya yi kaira da wuri Wannan magana ta matukar girgiza amarya harma ta kasa riketa take sanarwa Gimbiya Hannayensa ya saka ya maidota ya zaunar da ita yana dubanta a hankali ya ce" tun wajen karfe biyu da rabi ya rasu Anmy, tana bangarenta ta yi salama da shi na yi mata kiran likita ne ta dubata domin ta fara zubar da jinni sakamakon tashin hankalin da koke koken da ta ringa yi gashi cikin bai yi kwari sosai ba Sosai mutuwar nan ta daki Gimbiya, ta kara tsoron Allah sannan ta tausayawa mahaifiyar Aliyu da mahaifinsa Mahaifiyarsa ya kasance tana ta kuka a fili, mahaifinsa kuwa ba wanda ya ga kukansa sai dai ya sada kai sannan ya sauke ajiyar zuciya Nan da nan masarautar ta cika makil da jama'a, yan uwa da aminan arziki kowa da kararsa Da wuri wuri aka kaishi makwoncinsa sannan aka shinfida tabarmi dan amsar gaisuwa inda wajen ya cika makil ana ta amsar gaisuwa Baki daya ahalin gidan Mutalab sunna wajen rasuwar tun da sasafe Gaba daya matan sunna bangaren Gimbiya, nan du aka taru da yake falon ba karami bane harta Zinariyar nan take da yayarta sunna zaune sai kuka take har bayan magariba sam ta ki ta kwontar da hankalinta ta bi yaron da adu.a, idannuwanta sun kasa gane mata irin suturar da Allah ya yiwa yaron nata irin yanda aka taru ana amsar gaisuwa Lakada lakadan kafet uku ne shinfide, daya GIMBIYA ce zaune da tarin y'ayanta wato su NAJEEBA Daya Zinaria ce da yar uwarta da abokanansu dake ta shigi da fici Dayan kuwa idan baki sun shigo nan suke zama a amshi gaisuwa Bangare bangaren gidajen kowa ya tara jama'arsa yana amsar gaisuwa Sai yanke yanke ake ana sadaka, rasuwar dai taro na mamaki tamkar wani tsohon magidanci ne ya rasu Babu wace ta koma gida, a nan bangaren suke kwana wajen Anmynsu wace ke shiga tsakaninsu su layu du su lalafe mata domin baki daya wayoyinsu ta karbe ta kashe dan ta lura wayar NAJEEBA bata daina kuka gashi ita kuwa ta jima tana son ta kasance da y'ayan nata haka Iyayen daidaiku sun zo har masarauta sun yi gaisuwa, mahaifiyar NAJEEBA dake saudiya ta yi vidio call sai dai sam NAJEEBA ta ki amsarta, sai da Anmy suka gaisa Yau akaiwa yarima adu'ar uku Yau ne jama'a ta ringa ragewa tun bayan adu'ar Kafin ake cewa azahar ta shigo kai ya kasance du sai na kusa wato na kud da kud A yaune kuma jirgin mai martaba sarkin agadez ya sauka da abokannan tafiyarsa suka yi tataki da kansu dan zuwa gabatar da gaisuwa wa sirikinsa da kuma yarsa na rashin dansu daya cilo da sukai An masu tarba irin ta bajinta An sauke su a bangaren Mai martaba Sarki SHAHEED, ya sauke su tare da mutanensa na arziki su ABIH, su DAYABU, su liman Baba, Dogarai kuwa sun cika ko'ina sai kai kawo suke sun tatare ko'ina Cike da kamala ta mike ta kai dubanta wajen ZAHRAU, da UMMULKHAIR da UMMUKULSUM, da NAJEEBA Cikin nutsuwa ta ce" ku tashi ku min rakiya mu gaishe da mahaifin ZINARIA Mimikewa sukai yan matan reras , baki dayansu sanye suke da bakaken abayayoyi yan saudiya masu shegen kyau da tsari ga tsada Wani sirrin kyau ne da y'ayan nan tamkar idan kana kallonsu kar ka daina Bakin fatarsu irinsa ne ke wartar farar fats harma ta yi mangarin idan ta samu kalar nan ai sai yi Ga najeeba dake anfani da roger cavalais, sannan sabululukanta na anfani tana hada kayanta ne da kanta ciki kuwa harda su kurkum da sabulun victago da zuma da su kankana da dai sauransu hakan ya saka fatarta ita kadaima sheki take tana haskawa, sai haskenta ya fi na sauran ya kasance bakin nata irin na American din nan ne mai kyan gaske Ko yanzu da take zaman makokin bakinta baya rabo da dan jan bakin nan, hakama idannuwanta bata cire abin nan ba, gata da kallon kasa kasa sai ta lumshe idannuwan nata Anmynsu ce gaba Su kuwa sai sukai biyu a bayanta, biyu a bayan biyun wato sun jeru sunna wata irin tafia mai cike da kasaita idan ta ajiye kafafuwanta sai ta dauke su zahrau dake bayanta ke ajiye nasu, sannan su Najeeba su ajiye nasu Jakadiya na tafe tana shelar fitowarsu hakan ya sa du wani bawa ko wanda Anmy ta girma ya ja ya tsaya ya sada kansa dan girmamawa ga uwar gidan marigayi sannan uwar mai martaba Fuskarta sake take daga kanta a hankali sannan da dan murmushi tana amsa irin gaisuwar da ake ta jefo mata, da yawa cikin manyan samarin gidan sukan bi y'ayan dake bayanta da kallo, da yawa sun dauri niyar isar da sakonsu dan a kara kulla zumunci, wasun kuwa na masu kallon sha'awa da tsoro domin su din dai ba dai kyau ba sai dai masifa! a haka har suka karasa wajen shigar Dogaran kofar dake tsaitsaye da jakadiyoyin ne suka kwashi summa nasu kirarin da kawo mata gaisuwar da adu'ar Allah ya jikan yarima karami da fatan Allah ya jawo masu zama Babar jakadiya, tsohuwa ce ta shiga ta duka ta sanar da isowarsu Tana fitowa anmy ta shiga da bismillah sannan kanta a sade dan girmama sarkin garin agadez duda tana kyautata zaton ta girme shi domin shima ba wani tsoho bane Saman kujera ta zauna kafin ta ja alkyabarta ta gyara Baki dayansu kasa suka zazauna kusa da kafafuwan Anmy, Tun da suka shigo ta lumshe idannuwanta sakamakon kanshin turaran nan dake matukar kasheta a duniya Sunnan turaran *MUSKI-JAH* sakamakon jinsa da take a wajen wannan bawan Allah ya sakata nemansa a lokacin da suka fita waje a paris A ranar baki daya tanadinta ta saka ta siyo turaran nan, tana bude shi ta ga wata yar karamar kwalba sannan ba'a cike ba dan ko rabin kwalbar bata kai ba aman kuma yakeda muguwar tsada mai rikitarwa Daga ranar ta nemi waje ta ajiye maganar turaransa, yanzu abinda ta fi sakowa a gaba irin yanda yake saka tufafinsa Tana son ta ji wai du suturarsa daya zata kai nawa? Ba dan komai take son gane wasu al'amura nasa ba sai dan ta gane shin gayunsa da sarautarsa na bagidaji ne ko ya waye? (Ji fa rigima) A hankali ta dago da idannuwanta a lokacin da dogarin nan ke ta fadin" saraki sun amsa gaisuwarku jinnin MUTALAB, saraki sun ji dadin kulawarku ..... Bakinta ta tabe tana ayanna ko a ina mukai magana? Idannuwanta ta sauke a fuskar mahaifinta wanda akaiwa sasaukan rawani Irin yanda yake dan murza goshinsa ya sakata sakar masa murmushi domin kwarai ta fanr ya takura da rawanin nan ne Dubanta ta maida wajen DAYABU, hararar da ya sakar mata ta sakata yi masa murmushi har hakoranta suka bayana domin ta san hararar baya wuce numbersa da wasu daga cikin samarinta zasu dama dan ta tabata zai sha kira domin akoy masu numbersa a cikinsu idan sun sha mata kai ta hada su da yayanta takan basu ba abinda ya shafeta Kalle kallenta ya kai fuskar sarkin Gadez , a hankali ta bi wajen da ya kurawa ido Zahrau ce ke kallon Dogarin dake ta zuba ta san tausaya masa take a cikin ranta, sai dai irin kuretan da ya yi da ido ya saka NAJEEBA sakin murmushi har tana dan dantse lebenta na kasa Idannuwanta masu kale kale suka kaita wajen fuskarsa Irin yanda sukai ido hudu ya sakata da saurin gaske ta sada kanta sakamakon kallon nan na tsana da ya wurga mata wanda ke sakata jin faduwar gaba da tambayar kanta shin me ta masa? Sam bata iya kallon cikin idannuwansa, dan bakinta ta murguda a kasan zuciyarta kuwa fadi take" wai shi hala dan daudu ne da yake saka kwali? Kara bin fuskarta da ta sada ya yi da ido, lebensa dake cikin rawaninsa ya datse da hakorinsa na sama A kasan zuciyarsa ya furta" wani rashin jin maganar kika shirya da ya saka ki sakin murmushi Majanune? Dubansa ya maida wajen Dayabu, sai kuma ya lumshe idannuwansa yana ayanna ya zama wajibi a koya mata biyaya da bambancin sarkinta da yan iskanta! Irin yanda ta tsinke fuskar Zinaria da mari a gaban sarkinta ta yi rashin kunya mai tsauri! Muryoyin dogarai da jakadiyoyin dake kofa na shaida karasowar Zinaria ya saka NAJEEBA kara janye kafamfafuwanta domin ita ta fi kusanta da hanya ta kuma tabata idan har ta shigo ta ganta a bakin hanyar nan zata baje tafiyarta ta yanda zata taka mata kafa ne ita kuwa ta kara mata na biyu a gaban ubanta! Za ina tsalake ranakun posting idan har baku daukaka comment dinku ba😔 [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 9 Cike da wata irin kasaita da alkyaba a jikinta ta sanyo kai, bayanta kuwa jakadiya ce, sai bayi mata uku du suka duduka sannan suka dukar da kawunansu kasa A hankali ta ringa takawa har ta karasa kusa da Anmy ta samu waje saman luntsumemiyar kujerar dake nan ta zauna hakan ya kasance Zahrau na zaune kusa da kafarta ne Sai da ta sada kanta a hankali ta gaishe da Anmy, sannan ta juya ta yiwa sarakan gaisuwar tare domin ba wanda zata fara gaishewa ta bar daya dan rabonta da mijin nata kusan kwana uku kennan Sarki SHAHEED ne ya dubi dogaran dake tsatsaye kansu dan su san maganar tasu ce Da yatsunsa ya yi masu nuni kan su fita Da sauri suka ringa zagayowa sai su zube har kasa su kara neman afuwa sannan su fice a haka har ya zama daga su sai su a dakin Kanta dake kasa ta dan dago ta dubi mahaifinta dake dan nesa da ita A hankali ta saki kukan da ta aura harma ya zama abokin yinta ba dare ba rana kan rasuwar yaron nata Mahaifinta yana gannin yanda Anmy ta girgiza kai ta sada kanta hakan ya saka shi yin gyaran murya yana kallonta A nitse ya ce" shin baki yarda ba a maido maki yaronki ne ZULAIHAT? Da sauri ta sada kanta dan a kausashe ya yi maganar wace ke nuna ransa ya baci da irin kukan nata, wanda ya tabata kafin ya zo sarakuwarta da mijinta ba zasu kasa rarashinta ba harma su nuna mata adu'a ya fi bukata ba kuka ba Muryarsa ya kuma budewa a dake wanda hakan ya saka yan matan Anmy baki daya dagowa suka zuba masa ido wanda idan sarki baba na magana haka du kowa kansa yake sadawa Da sauri Anmy ke saka kafarta tana dan zungurinsu, ta hakan suke tunnawa sunna mayar da dubansu kasa Sai dai Zahrau haka kawai ta kara kure rawaninsa da kallo kafin ta sada kan nata Cikin wata kakausar muryar ya ce" wannan ai aikin banza ne bayan kema kin san idan yanzu wanda ya halice ki ya yi kiranki koda duka duniya ne gatanki bamu isa mu tare maki ko mu hanna ki ba ko a dadaure ko a nitse sai kin amsa dan shi ya amsa zaki auri kuka ki ringa yi masa kina hanna shi sukuni a inda yake, shin a kanki aka fara rasa yaro ne ZULAIHAT? A hankali , cikin tatausar murya Anmy ta ce" Zulaihat na neman afuwa Allah ya huci zuciyar sarki mai adalci Dubanta ta kai wajen Shaheed wanda ya dace ya nema mata afuwa aman ya yi biris, san hararansa Anmy ta yi hakan ya sa ya kawar da dubansa daga kanta Abih ne ya dan gyara zamansa shima a nitse ya ce" Allah ya huci zuciyar adalin sarki DAYABUma ya kara sada kansa cike da girmama sarkin ya furta" a yiwa zinaria afuwa mai martaba Anmy ta ringa zungurin su NAJEEBA, Najeeba ta saki murmushi ta ki yin magana, a hankali ZAHRAU ta sada kanta ta ce" Allah ya huci zuciyar sarkin abzin Haka su Ummu suka ringa furtawa a hankali aman cikin ikon Allah NAJEEBA sai ta sada kanta kawai tana murmushi a saman lebenta wanda bata boye ba Da yake basu da yawa a dakin dole a fahimci wanda ya yi magana da wanda bai yi ba, gashi maganar a nitse ake yinta ba da hayaniya ba, sannan ba a tare ake yin maganar ba idan daya ya yi sai ya ajiye harma ya saka sekwani sannan wani ya yi cike da biyaya Da sauri ta zamo kasa ta dukar da kanta ta ce" Allah ya huci zuciyar Aba SHAHEED ya kawar da dubansa daga kanta, ya maida wajen sarki, da idannuwansa ya risinar da idannuwan nasa sosai sannan ba rufe su ya yi ba haka kuma ana gannin samansu da gashin girarsa Hannunsa na daman ya dan daga daga ajiyen da yake ya dan dunkule shi sannan ya kara sada kansa Murmushi sarkin garin Agadez ya yi da kansa ya iya amsa masa shima kafin cike da farin cikin kasancewarsa sirikinsa sarkin da ko cikinsu sarakunna suna maganar irin yanda sarauta ta zauna masa a jinnin jikinsa Dubansa ya kai wajen Zulaihat a hankali ya ce" na san da kin san cewa dukan mai rai mamaci ne, sannan kin san cewa mamaci baya son kuka Ba za'a hana ki zubar da hawayen rasa gudan jinninki ba, aman kuma ba za'a barki ki zubar har zubarwa ta dawo ta zama ba kyau Idan kika tuna shi, ki yi gagawar yi masa adu'a Idan soyaya ce nuna masa ta hanyar adu'a Sannan ke kanki ki shirya naki zuwan inda ya tafi Kanta take gyadawa hakan ya sa NAJEEBA ta kara dagowa ta tsura mata ido Sai yau ta ji tausayinta, gaskiya ta ji tausayinta har cikin ranta Kwana ukun nan koke koken da suke a bangaren Anmy sai ta dauke shi kawai na a ringa basu hakuri ne a hadu a lalace, tabas mutuwar Aliyu ta daketa domin yaron ba wanda ya batawa, yaro be mai shiru shiru sosai sai idan kun hada ido yakan sakar maka murmushi To baima yi maganar ba bale ka ce ya maka ba daidai ba Sannan koda yaushe yana wajen mahaifinsa sunna zaman fada, bai cika zama a gida ba dan mamansa bata barinsa zama a gida kulun korarsa take ya je ya koyi irin yanda ake juya kujerar da wata rana zai mulka Idannuwanta ta lumshe ta maida kanta ta sada har ya gama sannan du suka shiga fadin godiya take da dai sauransu NAJEEBA kuwa abinda ya fi bata daria kennan, irin yanda sha'anin sarauta yake tafia, irin yanda sarki ke zaune magana na masa wahala aman wasu na ta faman Allah ya huci zuciyarsa To waima me aka masa da za'a ringa neman afuwar mutun? Anmy kadai take iya yiwa wannan kazagin itama sai idan ta tabata cewa ta bata mata to fa takan yi gagawar zubewa kasa ta ringa Allah ya huci zuciyar Gimbiya Sai da komai ya nitsa Sarki ya nemi da yaran su fita Du mimikewa suka yi, Zinaria ta fara godiya sannan ta juya ta fita Su Ummu da zahra dukansu sai da suka yi godiya sannan suka firfito aman NAJEEBA kanta kawai ke kasa a hankali kuma cikin tafiarta wace ake gannin yanga ce ko takama da isa ce bayan haka take tun kankannuwarta bata iya sauri ba a haka ta fita a falon Kansa kawai ya girgiza......bata nemi afuwar sarki ba, bata yi godiya ba, sannan da zata fita bata gode ba DAYABU kansa duka abubuwan nan yana hankalce da ita harma ya gama ganewa NAJEEBAR so take ta jaza masu baki daya tashin hankalin Mai Martaba wanda hakan ba zai masu da sauki ba Sunna tsakiyar tafia NAJEEBA ta ja ta tsaya, sai kawai ta shiga daria tana girgiza kanta UMMU ta harareta ta yi tsaki ta ce" ke dai, ke dai akoy fitinaniya, wai ke mai martaba sa'ankine da zaki ringa kokarin kawo raini kai tsaye tsakaninku? Kin ga sarai dai yaya ya girme shi aman yake masa biyaya, kin ga Anmy mahaifiyarsa ce aman kasancewarsa sarki idan tana gabansa a lokacin da yake saman mulkinsa takan sanyaya kalamanta sannan ta tafiar da lokacin cikin sada kai NAJEEBA kina ji kowa na rokar afuwa ke ba zaki yi ba ko? Ummulkhair ta ce" kin ga, ni kaina dan Anmy ta min wani mintsini ne ya saka ni magana, haba dan Allah matar nan ta Mai martaba bata da mutunta mutane, kunna fa ji ranar nan yanda ta zagi Najeebar ZAHRAU ta ce" ku dai ku daina irin haka, ina anfanin masifa wai? NAJEEBA ta ce" ku dakata ni du ba wannan ba so nake ki auri ubanta Zahrau ta zabura, dan har ga Allah gabanta ne ya fadi jin abinda NAJEEBA ta fada Ummulkhair dake tare mata ta girgiza kai ta ce" zuwa yanzu na yarda baki da hankali NAJEEBA Gaba suka fara yi hakan ya sakata itama daga kafarta tana biye da su bayan ta turo bakinta Sai da suka shige uwar dakan ANMY NAJEEBA ta fada saman bed da baya tana murmushi Juyawa ta yi tana kallon ZAHRAU ta ce" aunty, yaushe rabonki da ki ga fuskarsa? Zahrau ta waigota ta ce" wa fa? Najeeba ta ce" shi SHAHEED din Da sauri ZAHRAU ta zaro ido, Bilkissu kuwa ta tura kofar da sauri ta rufe wace shigowarta kennan itama da mamaji ta ce" aunty NAJEEBA sunnansa ne kika kama kai tsaye haka? NAJEEBA ta dubeta ta tabe baki bata bata amsa ba UMMUKULSUM dake cire mayafinta ta dubi Bilkissu ta ce" ke fice mana a nan muna tataunawa yara sai shiga maganar manya UMMULKHAIR kuwa itama bakin gadon ta karasa ta zauna tana fadin" walahi aunty ko, nima inaga a yanzu ba zan iya nuna kalarsa ba dan rabona da shi fuskarsa a waje tun kafin a nada shi sarauta NAJEEBA ta ce" sai dai a yi masa hoto a boye a fitar da shi bayan mun san hotuna yanzu ana iya kara masa haske ko a kara masa girma bayan yaro ne karami Da sauri Zahrau ta kai hannunta ta buge bakinta ta ce" ke dai neman fitinarki zai saka watarana a yanka maki bakin nan naki gutsi gutsi, ni ba zan manta lokacin da suke hawa dawakai da yaya ba, a lokacinma ya girmi yaya a girman jiki sosai har yaya na nemansa da rigima yana ce masa an hura shi shi din kyankyasar inji ne, shi kuwa yakan ce da yaya shi kuwa dan tamowa ne Sannanma ina ruwanmu ne muna cikin gidansu muna irin magangannun nan idan ya ji kun san da zai iya sakawa a dauke mu ya halaka mu shikenan ko? NAJEEBA ta koma ta kwonta tana kada kafarta ta ce" ina tausayawa talakawansa ne, kin ga ya ci ya cinye ya tayar da kai Turaran nan da yake anfani da shi sai da ya cinye min tanadina na shekara biyu a paris bayan kun san nima mai kudi ce Ta karashe tana kanne ido daya ta ci gaba da fadin" ku duba ku ga irin yanda fallonsa yake, Ac ban san adadin ko nawa bane, labulayen da karafunnan labulayen dakin nan sai ka rantse ba a africa bane, Cafet din falon, da kujerun falon kadai ya isa ya haukata wanda bai taba fita ba Duba ki ga irin dankara dankaran TV da windows da maficin nan dake kyali wanda aka ce da ruwan zinari ake wanke shi Kausasa dubanta ta yi ta ce" ku kun san me nake nufi da ruwan zinari dan irin tsadar da wankin sarka yake a kasar nan! Zobunnan hannunsa, da agogon hannunsa da takalmin kafarsa da shadar jikinsa da zubin da ake yiwa suturunsa kan sakani tunanin anya y'ayan mutane dake bata ba mafiya mai garin garin yake ba? Zuwa lokacin Ummulkhair mayafinta ta dauka ta ce" kun ga, ba'ai min aure ba bale na haihu na haifi mai min adu'a, haka kawai na zauna a je wani tsanwan kuda ya kai labarin nan kunnayen fadawansama ba shi ba walahi sai sun ci ubanmu ko kannensa muke ba cousins dinsa ba Tsakaninki da Allah NAJEEBA mutumen da ake yiwa maganar adalci wanda mutane suka shaida ake yabonsa ke jarababiya har kika iya kurewa rayuwarsa kallo kina neman masa shari? NAJEEBA ta mike zaune tana kallon Ummulkhair ta ce" Ummu, wata uku fa kika bani a duniya kin ga yaya baya nan idan kika kuma zagina Allah sai na mare ki! Kuma ai ba shari na masa ba gaskiya na fada da yake hararena yana min kallon tsana me na masa yo ni bayan shi da kudaden talakawa yake takama? Ni kuwa neman na kaina nake walahi! Zahrau ta girgiza kai ta ce" Allah ya shirye ki NAJEEBA, aman shi yaya SHAHEED din ne zaki ce ya dogara da kudin masarauta? Mutumen da shi ke zuba dukiyarsa dan gyaran gidan nan da kuma talafin gajiyayu da talakawansa? Najeeba kin kuwa san meye aikinsa? Kin kuwa san shagon kasuwanci nawa ya malaka wanda idan aka siyar da daya zai isheki rayuwar duniya? Kuma ma wannan falon ai ba ainahin falonsa na dayan bangaren da yake hutawa bane Baki san a wancen bangaren yaya yace harda su picsine, da wajen hutawa rikake? Da jardin da komai, shi ke fada min Sarki Shaheed sarki ne mai adakci wanda idan zai kwonta yake cike da damuwar shin yaya talakawansa zasu kwonta baci? Ke ba kyau tone tonen alkahairain mutun idan har yana yi domin Allah aman mutumen nan ya yi nisan da ba zaki iya fita cikin garinsa ki zage shi baki samu wani ya dauke numfashinki ba dan sunna kishinsa A gidan redio kin ji me ake fada kuwa? An jima ba'a yi sarkin da talakawa ke kishinsa suke kishin komai nasa suke kare komai nasa irin sarki SHAHEED, ke ina alfaharin kasancewata yar uwar bawan Allahn nan dan kasaitarsa ba ara ya yi a jinninsa take! Bakinta ta tabe ta koma ta kwonta saman bed din ta yi lamo A hankali ta ce" kun san shan koko bukatar rai, abin dauka dauka ne Sai da ta ja numfashi kamar zata yi baci ta buda idannuwanta ta ce" *ni sam bai min bane, sai nake jin na tsane shi sosai!* Itama Zahraun mikewa ta yi a kusa fa ita tana juya kanta ta lunshe idannuwanta inda Ummulkhair ta fita ta shiga zaga gidan ita kuwa Ummukulsum ta he ta harhada sauran baki dayansu sukai cikin falon cin abinci ta shiga zuzuba masu dan su ci abinci Aba ne biye da Anmy sai yaya DAYABU a bayansu suka shigo falon Mutanen Falon suka ringa gaishe su sunna fita dan sun ga yannayin na Anmy da alamun magana zasu yi da dan uwan nata da kuma y'Ayansa Zama suka yi ita kuwa ta shige ciki wajen yaran dan ta san sunna ciki Karar bude kofar ya saka su tashi da sauri NAJEEBA ta saki murmushi ta ce" Anmy ki rufa min asiri ki bani wayata na bude na ji yaya shagona da jama'ata kin ji? Anmy ta zabga mata harara ta ce" ku fito Tana fada ta juya ta fita suka kalli junna Zahrau ta ce" Allah dai ya sa ba laifi kika yi ba NAJEEBA NAJEEBA ta tabe baki tana sauko da kafarta ta fara fita Du an tataro sauran sun layi kamar yanda suke yi idan sun san sun yi laifi ko sun ga iyayen nasu a hargitse Anmy ranta bace ta ce" NAJEEBA shine wani dan iska ya dake ki a ciki ba'a fada min ba? Cikin mace fa nan ne yaro ke kwonciya, idan ya jiwa yarinyar nan ciwo walahi Yaya sai na daure ubansa! Najeeba ta shiga sakin murmushi tana gyada kanta tana kallon Anmyn nasu, sai a lokacin ta tuna da ciwonta ta sada kai gannin Aba na hararanta Ta kai dubanta wajen ZAHRAU ta ce" ke kau an yi wata irin y'a, shine kika tsaya yana zaginki baki dauke min fuskar shege da mari ba? Aba ya sauke ajiyar zuciya ya ce" ya ilahi BILKISSU ke da zaki hane su fada ke ke fadan sun ki duka? Yanzu zaki gindaya sharudan abinda ya kawo mu ko sai kin sa sun kara raina mutane? Bakinta ta dan zumburo tana kallonsa ta ce" aman ai kaima kana da wani laifi ko yaya? Ina matarka ne da bata zo gidannan ta zauna da mu ba ko kyankyaminmu take? Ummulkhair ta yi carab ta ce" Anmy, uhum nan kuwa da kanwarta ta haihu har aka yi sunna tana gidansu aman da yake ta raina mu mu....... Shiru ta yi sakamakon juyowa da Anmy ta yi ta ce" na koya maki? Tambayarki na yi? Ni na kiya maki tsegumi? Yi min shiru a nan my daughter! Kansu suka sada su duka jin ta fara hawa da gasken Tsayawa ta yi kansu tana dubansu murya a kausashe ta ce" *MUTALAB ND BILKISSU FAMILLY*! su duka suka shiga dago kansu a hankali sunna kallonsa, Sai da ta dago dan yatsarta manuniya ta nuna su ta ce" [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 10 Ku kiyaye ni, na fada maku ku kiyaye ni! Shin ku manya idan baku baiwa kannenku abin koyi mai kyau ba so kuke tun kafin mu mutu a ringa cicira maganar tarbiyar da muka yi maku? Zahra ke ce baba fa, me ya kaiki ke mace budar baki ki yiwa mutun gorin tabon rayuwa bayan ke bakima fara taki rayuwar ba? To ku sani, duniyar nan ba matabata bace, kar na ji kar na gani ko bayan raina na soke maganar yiwa mutun gori a rayuwarku idan kuwa aka yi ban yafe ba Kai suka ringa gyadawa, Hannunta ta saka ta dauki yar karamarsu dake son bare chocolate tana dubansu ta ce" da zai yarje min da a hannuna kuke, da zai iya da ya barmin ku dan na tabata tarbiyar y'aya a hannun mace take Numfashi ta sauke ta ce" sai dai hakan ba zai yiwu ba domin yana da shakuwa da ku mai tsanani Nan saman cafet din da suke zaune ta nemi waje ta zauna gabansu tana dubansu sunna dubanta Murmushi ta yi masu ta ce" ina son ku sosai, kun san da haka? Yannayin farin ciki ne ke wanzuwa a fuskokinsu Itama da tausayi take dubansu duba da ba wanda ya girma da iyayensa, wasun laifin iyayen nasu ne wasun kuwa laifin mahaifin nasu ne, hakan ya sa take matukar tausaya masu take kuma jinsu a ranta A hankali ta ce" Allah ya shiryar min da ku ABIH ya dubi DAYABU, DAYABU ya sakar masa murmushi domin kafin su shigoma kamar zata kama da wuta ta tanadi sai ta mari wani yau a cikinsu, dama DAYABU ya san tana samun kanta gabansu zata kasa tabuka komai, saidai ta dawo rarashi da adu'a Abih ya girgiza kansa yana ciro wayarsa yana duba whatsup dinsa domin ya jima rabonsa da ya duba tun zaman makokin da suke Sannu fa, Allah ya masa rahama.....mesage din da ta iya aiko masa kennan Ba salama ba wani doguwar magana, rasuwa akai masa ta masa gaisuwa fakat Dubansa ya kai wajen NAJEEBA dake kallon Anmy Wani sa'in wasu abubuwan yarinyar sak mahaifiyarta ta kwaso Irin jan ajin mahaifiyarta da sauransu idan ya ga ta yi yakan tuna da, sai kuma haushin maman nata ya lulubeshi harma ya tabe bakinsa ya kawar da kai yana furtawa a kasan zuciyarsa cewa kudi ko? Ki kara neman kudi , ki yi ta neman kudi, idan kin mutu a nadeki da rigar kudin a kaiki! Sarkin Garin Agadez ne ya zo da maganar cewa yana son auren Zahrau Gaba daya yan matan da aka bari ne suka kara dubanta sunna masu firfitar da idannuwa Itama kuresu ta yi da kallon bale Zahrau da ta dafe kirjinta tana kallonta baki bude NAJEEBA kuwa sai kawai daria mai dan sauti ta kufce mata, dariar ta fara saki sai ta karasheta da tari tana tari kamar tari ne ya taso mata Zahrau ta ce" na shiga uku Anmy, sarkin garin Agadez fa? Anmy matansa nawa? Anmy jajayen buzaye? Anmy sirikin yaya fa? Ta sada kanta ta ce" kuma ma tsoho ne Murmushi Anmy ta yi ta ce" matansa biyu, zai yi ta uku da ke Maganar sirikin yayanku sai me? Kin ga kema kin zama sarakuwarsa Maganar tsufa kuwa ajiyeta gefe ba tsoho bane Ido ta ringa kikiftawa ta rarafa ta je jikin Anmy ta dora kanta ta ce" Anmy, ni kuma? Anmy kin san inada tsoro fa, ba zan uya rigimar gidan sarauta ba kar ki kai ni kin ji? Murmushi Anmy ta yi tana gannin yanda Abih ke hararanta , karshema sai ya yi kwafa ya mike ya fita Ai kuwa kamar jira NAJEEBA take ta mike ta kwaso shoki ta jefawa ZAHRA wace kanta ke saman jikin Anmy tana shafa kanta Daria take kasa kasa ta juya ta nufi dakin Anmy, au kuwa suka rakata da kallo Anmy ta yi murmushi tana girgiza kai, Tsakiya suka sakata sunna ta rarashinta tare da fada mata dadadan kalamai da fada mata cewa idan tana so za'a mata idan kuwa bata so ba za'a yi mata dole ba Najeeba kuwa na shiga daki ta bar dariarta ta fito tana juyi har ta karasa gaban madubi Idannuwanta ta lumshe a fili ta ce" Anmyma tace kema kin zama sarakuwarsa Wayo dadi mun zama sirikansa (ta zama dai hajia🤣) Sai da ta gama dariarta ta nemi waje ta kwonta ta nemi baci dan ta yi niya yaufa sai ta tari bako ko daya ne Bacinta ta sha isashe har kusan salar la'asar sannan ta farka Bayi ta shiga ta yi wanda da brosh ta fito ta zauna tana shafa man ta Tana gamawa ta dauki wando da riga cikin kayanta duda wandon a dan sake yake rigar ce ta dan dameta ta saka abinta ta yi lamo tana kallon faratunanta da kunshin jikinsu ke son fita Kusan magariba Anmy ta shigo da wayarta a hannunta ta mika mata tana hararanta ta ce" anmatana, sai na gwada amshe wayarki na wata guda na ga yaya zaki yi? Murmushi ta yiwa Anmy tana sada kanta dan ta san idan ta yarda da gatse sai ta amshe din, ita kuwa babar damuwarta ace an rabata da waya Kallon Anmy ta yi gannin bata bata karamar ba Anmy ta buda bangaren kayanta ta ciro mata sahari dinta ta wurga mata shi sabo ne sannan ta ciro alkhaba sabuwa fara kal mai yan duwatsu a gaba ta ajiye mata gefenta ta rage muryarta ta ce" ku shirya bayan salar magariba ku je ku yiwa sarki salama Najeeba, ki kula, yayanku zai kasance a wajen nan ni kuwa bana nan ki kula na fada maki Gabanta ne ya fadi jin wai zasu je su yiwa sarki salama, to ita yanzu tsakani da Allah ina ita ina zuwa yiwa sarki salama? Taga dai Zahrau yake so, me zai hana a turata da jakadiyoyi? Walahi tana tsoron haduwarsu da wannan bawan Allahn da ta dasawa sunnan dunkum! Sai da ta kusan fita ta juyi ta ce" karamar wayarki tana wajen SHAHEED Wani irin kululu cikinta ya yi kamar wace ta sha abinda zai sakar mata ciki daga jin cewa karamar wayarta na wajen SHAHEED Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une Ta fada a fili tana mikewa da gudu ta yi bayi Bata zane ko'ina ba sai saman WC tana rike cikinta dake juya mata Bil haki ta shiga gudawa tsabar faduwa da gabanta ya yi da kuma irin yanda cikinta ya juya daga jin wayarta na hannun SHAHEED Me hadinsa da wayata? Me ya kai wayata wajensa? Na shiga uku Anmy kin kashe ni kin kare, da ya amshi wayar nan gwara ya amshi babar ya rotsara da kas, Anmy kin san neman shari yake a kaina shine kika bashi hanya, wannan tsanata da nake hangowa a idannuwansa shine kika bashi abinda zai idasa tsanar tawa? Sai da ta gama gudawar zufa na karyo mata ta tsaftace jikinta ta wanke ta fito ta zauna kasa ta kunna babar wayar nata Wayar na kunnuwa kamar jira ake network ya hau sai ga message rututu Bata tsaya dubawa ba ta shige wajen Call Da sauri ta ringa tura message cewar kar a nemeta a numberta airtel ta yarda wayar ne a kirayeta a numberta MOOV Da sauri take ta tura message din sai da ta gama ta fara sauke ajiyar zuciya a tunaninta ta toshe hanyar kiranta Wajen message din ta shiga, nan ta fara cin karo da message din samarinta kala daban daban Ciki kuwa harda masu shaida kata sun kasa hakura sun je gidan ake shaida masu rasuwar yarima ashe dan yayanta ne Wasu sun tsaya iya gaisuwa Wasun kuwa cikin ikon Allah ta ringa bin message dinsu tana zaro ido jin sun je har fadar gaisuwa Bata san lokacin da ta furta" uban wa ya aike ku? Da sunnan wa? Kuka ce wajen wa kuka zo? Kafafuwanta ta mike ta mayar da kanta baya, gashin kanta du ya bazu saman bed din tana kikifta ido Cen ta yi tsai da ranta, a hankali ta ce" NAJEEBA shin ubankine da zaki ringa rikicewa dan kawai ya amsar maki waya ko dan kawai ya samu ribar an zo an masa gaisuwa? Nan Abih ya san kinada samari, Dayabuma haka sun yanka ki ne? Dago kanta ta yi da irin duban nan na basawa ta juya kwayar idannuwanta masu girman gaske kafin ta furta" ke allura kike cikin ruwa, dole sai kin yi samari zaki iya fitar da gwaninki, bai huce yace ya hada kananun wayoyinmu zai yi bibcike kamar yanda ya saba lokaci zuwa lokaci Ko kuma dan sirikinsa na son aunty Zahrau zai hada dan ya goge du wata alakarta da wani? Huci ta furzar ta ce" ke koma menene bashi da hurumi da tarin samarinki! Idan kuwa yauma zai bi ki da kallon kyama da tsanar ne halas kema ai kina da idannuwan! Haka ta yi ta zama har kusan magarib Lokacin ne Zahrau ta shigo ta karsa inda take zaune itama ta zauna jikinta a sanyaye Dubanta ta yi, sai ta ji itama jikin nata ya yi sanyi A hankali ta dora hannunta saman hannunta na dama ta kara sanyaya muryarta ta ce" idan har kin san bakya so, idan har kin ji bai maki ba, idan har bakya ra'ayin aure ki zauna a gidan sarauta, idan har maganar yanada mata biyu ke kayar maki da gaba har ya kai kina jin ba zaki iya jurewa ba Dan shiru ta yi kafin ta tsareta da ido ta ce" *Kar ki amince* Ajiyar zuciya Zahrau ta sauke ta ce" aman sai na ga su Abih sunna murna da hakan, idan na tashi kai tsaye na nuna bana so yaya kike gannin zasu ji a ransu? NAJEEBA ta yi kara fuskantarta ta ce" kwarai ba zasu ji dadi ba duba da yanzu abinda suka sako gaba burinsu su yi mana aure da daidaya Hannunta dayan ta riko tana dan murzawa ta ce" to aman ina anfanin ki je ki kasa zama ki dawo? Koda hakuri kikai kika zauna kina shan wahala kina tunanin zasu ci gaba da jin dadin hadin nasu ne? Hannunta ta kai wajen habarta ta dan dago ta ce" Aunty, baki dayanmu ina mana fatan mu auri mazan da muke so kuma suke son mu Na tabata su ne zasu fi gannin darajarmu, zasu ji tsoron rasa mu, zasu kula da lamarinmu Mu kuma na tabata tare da su ne zamu yi hakuri mai inganci, zamu yi biyaya ke aunty mu bautu ba tare da mu kanmu mun ankara cewa vautuwar muke ba cike da farin ciki da nutsuwar zuciya Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" abin ne akiy gigita Kin ga zinaria yanda take a hakama ta tsane mu ina da na auri ubanta? Kin dai taba gannin mahaifiyarta matar kyankyamin bakin mutun take ita kanta ta cenza daga buzuwa ta koma balaraba dan ta tsanu jinsin baki Murmushi NAJEEBA ta yi tana lakatar mata hanci ta ce" wannan du bana so su zamo damuwar da zasu hanna ki auren Mai martaba sarkin Agadez ZULAIHAT da kike magana a gaban idannuwanki idan ubanta na magana tana iya daga kanta ne? To da izinin Allah idan kika auri ubanta ta nuna ba zaku yi zaman lafiya ba dolenta zata yiwa uwarta biyaya dan ba ke ba ko ni nan na zama auntynta Ta karashe tana dage mata gira guda hakan ya saka Zahrau sakin yar daria tana jan kuncin Najeeba Najeeba ta yi murmushi ta ce" matarsa kuwa meye hadinki da ita? Idan ita tana kyankyaminki, mijinta kuwa ya ga abin so kuma sai ta yi mamakin bakar fatar nan jinnin shuwa arab ta firgitata a lokacin da mijinta ya zama baya iya yi sai da yar duma dumar Abih Ta karashe tana mai shigar Zahraun da cakulkuli Ai kuwa nan suka cakule sunna cakulkuli sunna kyakyata daria kamar ba su ba Sai da sukai sallah suka ringa shiga wanka Kayan mak up ta baje saman cafet din dakin Anmy Cikin nutsuwa ta ringa gyarawa yayun nata fuskokinsa cikin simple mak up mai tafe da tsarin kalar fatarsu daidai da kowace Nan da nan sirrin tsarin kyansu ya fito Baki dayansu Lafayar ce suka nanada wace ta sha turaran wuta mai balakin kanshi Wajen saka alkyabar kuwa NAJEEBA ta yi tsaki ya fi a irga sannan ta dora nata Yan matan fitowa sukai reras su hudu da su kamar ka sace su ka gudu Tsayinsu ya kasance da kadan kadan suka fi junna, Yannayin jikinsu ne ya bambanta da kalar fatarsu dan wata ta fi wata haske, bakin wata ya fi na wata fizga aman fuskarsu kamarsu daya ciki kuwa har irin lebunnansu daya Jeruwa sukai NAJEEBA ta kashe masu hoto da Iphone dinta suka fito das da su a hoton kamar wasu amaren sarakuna wato gimbiyoyi Zahrau jinta take cikin nutsuwa cikin alkyabar, dadinta take ji sosai A haka suka firfito sukaiwa Anmy salama Message din Ambassador din Niger wanda ke zaune a kani ne ya shigo wayarta cewa ya zo fadar yana zaune da mutane ita kawai yake jura yau ba zai iya baci ba sai sun hadu Murmushi ta yi bayan ta karanta bata bashi amsa ba, sannan sam ta sha'afa shi din bata masa kashedin kar ya kirayi numberta na Airtel ba, hasalima saka wayar ta yi a jirgi dan bata so a gaban manya ta yi ta samun kira dan ta tabata tana dagawa abin zai zama magana Sunna tsakar FADA ne, wajen ya dauki hasken fitilu ne ga kuma hasken sarakunnan dake walwali Wajen a zagaye yake su kuwa su biyu sun tsaya dan nesa sunna zantawa Tun daga nesa dogarai ke sanar da zuwansu da kirari da komai tamkat su dinma y'ayan sarautar A hankali ya juyo dubansa wajensu dan gannin shin sun saka alkyabar yanzu ko basu saka din ba? Gannin sun saka ya saka shi maida dubansa wajen mai martaba Ga mamakinsa sai ya ga ya fi shi bada hankali kansu Murmushi ya yi a ransa yana furta ikon Allah A dazu karara Abih ya nuna masa irin rigimar da ta faru tsakanin Zahraun da tsoron manemin aurenta Cikin ikon Allah yana buda baki sai ya yi murmushi ya ce" dama ba mijinta babe shi yasa Allah ya kawar da shi daga rayuwarta kafin mai wajen ya iso Kuma dubansu ya yo kadan gannin sun dakata , sai da ya sha iska ya dan dago hannayensa ya yafito su NAJEEBA ta tabe baminta a ranta fadi take" irin ga yan gidansan nan, ahi ba zai yi mana magana ba mai dunkum kawai! Irin yanda suka nemi zubewa kasa dan gaishe da su ya kara birge sarkin garin Agadez Sai dai sam bai barsu ba ya hanna hakan Irin yanda du suka layu suka sada kansu daga tsayen da suke ya saka SHAHEED lumshe idannuwansa yana murmushi fadi yake" yanzu mutun yanzu ba mutun ba, dan ya tabata a wajen nan aka jata fada walahi zata kwabe alkyabar nan ne ta nuna hali , shi dai mutun marar kamun kai me ake da shi? Itama baki take yatsinawa daga kasa tana fadin" na tsani raini, na tsani Raini! Tun da suka tsayan yake kallon Zahrau, A hankali ta dago dubanta ta sauke saman fuskarsa Irin murmushin da ya sakar mata a bayanne yake shi ya sakata dan saka idannuwanta cikin nasa kafin ta lumshe su ta kawar da su a hankali tana jin zuciyarta na dokawa Ko ba komai ya iya kallo Ta furta a kasan zuciyarta Dogarin dake cen nesa rike da sakonsu ya yafito Yana karasowa cike da bada umarni a tausashe ya furta" idan su gimbiya sun koma bangaren GIMBIYA uwa, ka bi su da sakon nan A hankali ya yi maganar dogarin ne ya ringa takadi yana furta su Gimbiya sun gode da sauransu Wayoyin dake cikin aljihunsa kasan babar rigarsa ne suke ta vibrate Wayar wajen Zahrau ne da ta Najeeba da ta su ummu, ya amshe su ne a wannan karon bama dan bincike ba sai dan ya daidai du wani shigi da ficin da zai hada zahrau da wani, dan tuwon girma miyarsa nama Sai dai tun da ya amsa yar karamar fara kar din samsung din ciki ake ta kira Hannunsa ya saka ya lalubi wayar ya cirota Yana kallon screen din sai ya ga sunnan kamar haka" Ambasador zumana Wayoyin du farare ne, bai dai tantance wace marque dinsu ba hakan ya sa ya kasa gane ta waye Sunnan sam bai masa, sunnan ya saka shi dubansu daya bayan daya dan sunnan nan ba sunnan mutunci bane, koda soyaya ne me ya kawo zumma a ciki? Haka kawai ya tsayar da dubansa tsakannin ummulkhair da NAJEEBA, sun fi masa kama da wa'inda basu san meye jin magana ba Jin an maido kiran ya saka shi dagawa sannan ya kara a kunnayensa *haba baby, haba hearty, me yasa zaki ringa bani wahala haka ne? Kin san mutun nawa ke iya saka dukiyarsu dan su ganni? Kin san mace nawa ke faman na zama abokin gaisawarta? NAJEEBA na yi missing din ki, shi ya sa na taso na zo har masarautarku da alama baki ne da ku dan da kyar na iya gannin su liman babama, ki fito ina bakin zagayen kwanar gidan sarki dan Allah, idan ban ganki ba yau ba zan iya rintsawa ba* Dukan ratabi maganar nan ya yishi ne ba tare da ya ji muryar wanda ya amsa kiransa ba, shi dai dama faman da yake ta daga tunda ta gadaga kuwa zai fada mata gaskiya ne ta zo, ta zo fa idan bata zo ba ba zai bar wajen nan ba A hankali ya shiga cire wayar daga wajen kunnensa Zuwa lokacin kuwa irin jin abin ana kallon kan nan ya saka NAJEEBA dago dubanta dan tabatar wa ke kallonta ne? Da sauri da kuma tsoro ta mayar da kanta kasa ta sada sakamakon irin duban nan dake sakata jin babu dadi da ya tsareta da shi Ne ya sa ya tsane ni ne? Ta tambayi kanta Yana kokarin mayar da wayar message ya shigo kamar haka" kin kuwa san irin tsarabar da na kawo maki? Na zo maki da iPhone 12, na siyo maki wata gown, na siyo maki wata sarkar zinari a dubai *Baby ko nawa kike da bukata a yau zan baki in dai zan samu biyan bukata* Biyan bukatar ne ya kasa karasa cewa na son ganninta, sai ya tsaya a iya biyan bukata A dole yau ya gama yarda cewa yarinyar nan ta gama wulakanta su, Karshen wulakantawa a yanzu har nan cikin gidan nan mai daraja take baiwa samarin nata zuwa, sannan har a zo har nan a yi kokarin yada lalatar da aka saba? Bayan su ke hukunta wanda ya aikata lalata? Tabas a yau sai ya kamata turmi da tabarya da kansa ta yanda zai yi mata hukunci baki daya garinsa ya sani dan akan baiwa gawa kashi ne dan mai rai ya ji tsoro Ya san bai isa ya hukuntasu ba tare da huja ba Zai nuna mata yaro yaro ne, zai bi ta da kansa idan ta kama! Zai yi mata kamun da ba zata musa ba, zai yi mata bulalar nan a tsakiyar gari sannan shi kuwa katon banzan zai haka rami a cikin gari a jefe shi! Baya son zina! Baya son mazinaci A hankali ya fara jin tashin zuciya yana jin wani masifafen haushinta Tir da ke! Ke kuwa bayan rashin jin magana sai kika auri aikin da zai rarake ki ya tsufantar da ke a wulakance ya hada ki da cuta ko ya hada ki da tabo? Mace da zata ji, da ta kilace kanta a dakinta komai muninsa dan samun sakamako mai kyau zuwa gaba Dubansa ya kai kan Ummulkhair Da hannunsa ya yafitota Tun da ta ga haka a hankali ta tako ta dan tsaya dan nesa da shi kanta a kasa Wayoyin saura ya hada ya mika mata yana mai nuna mata ta koma Da murnar samun wayoyinsu ta juya ta koma kusa da yan uwanta, Najeeba fa nan da nan tsayuwar ta isheta, tun da ta ga wayarta a hannun Ummulkhair sai kafafuwanta suka fara yi mata kaikayi harma ta ringa jin kamar wace take jin fitsari Ta gaji da tsayuwar iskancin nan da irin duban da su Zagra ke aikawa junnansu da mai martaba da kuma irin kausasashen kallon da mai garinsu ke aika mata na kiyaya wanda ya kara fitar mata da tsayuwar kallon kallon a rai ya sakata a hanakali ta ringa dan matsowa kusa da Ummulkhair Raf ta kai hannunta saman nata ta damki mai wayoyin wanda tsaf a kan idannuwansa harma ya yi murmushin samun nasara domin dama burinsa ta karbi wayar dan ya aiwatar da aikinsa a yau ba sai gobe ba! ..............more comment aminan arziki😄😄😄😄😄💞💞💞💞💞💞💓💓💓💓💓💓💓 [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 11 Sakar mata wayoyin ta yi baki daya ita kuwa ta koma wajenta tana mai ci gaba da tsayuwa irin na yan uwanta Sai da suka kuma yin magana wace iya su ke jin abinda suke fada tsakaninsu sirikan kafin SHAHEED ya kai dubansa wajen su ZAHRAU Muryarsa kasa kasan nan ya buda bakinsa a hankali ya ce" ku koma ciki, sarki na godiya Kamar jira take a salamesu, ita ta fara daga kafarta tama manta da sai sun risina sun kara godiya ta yi gaba a hankali ta shige ciki Suma bayanta suka biyo sai dogarin dake tafe da wata katuwar ambulope dauke da sako dan nesa da su A nan tsakiyar gidan suka tsaya NAJEEBA na ta dadana wayarta tana duba sakwonnin da ta bari, irin kirate kirayen da ta samu wa'inda du ba'a daga ba aman an daga na yau na yanzu Sai tarin messages din da suka cika wajen ajiyar message suma sun cicika wajen wanda ta ringa bi da gagawa tana karantawa Tsaf ta ga na yanzu an bude shi, kuma ta ga sakonsa Zahrau ne ta ce" mu je mana meye wai kuka tsaya a nan bayan kun ga da mutun a bayanmu? NAJEEBA ta waiwaya ta ga Dogarin nan ne Karasawa ta yi wajensa shi kuwa ya sada kansa yana gaisheta Murmushi ta yi ta ce" baba dan Allah daga kanka, ku kam bakwa gajiya da wannan gaishe gaishen? Kawo sakon ka koma abinka ka ji? Da mamaki ya dago yana dubanta jin ta kireshi da baba Tabas shi din datijo ne, aman kasancewarsa a karkashin gidan sarakan bai taba ji ab kireshi da sunna baba ba Ko baki akayi in dai sun samu shiga ciki shikenan suma sun samu hanyar wulakanta mutane a bayan idannuwan manyan Sam sarkin bashi da hayaniya baya anfani da sarautarsa dan wulakanta mutane, aman na kasa da shi sunna anfani da damar nan Kwarai ya ji mamakin gannin kanwarsa ce, aman ta kiraye shi da baba Sai ya ji darajar yarinyar ta shiga idannuwansa nan take harma ya sakar mata murmushi yana kokarin risinawa dan godewa Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" ba dai zaku daina dukawar ba baba sai an jima Gaba ta yi ta karasa kusa da yan uwanta Tafia suka shiga yi suka nufi bangaren Anmy Hat sauran sun samu shiga ta tsaya Hannun Ummulkhair ta kamo ta saka mata sakon a hankali ta ce" eyah auntyna zan je na dawo wollah bako gareni Ummulkhair ta yi murmushi jin yanzu kuma ta zama aunty bayan dazu ta gama cewa zata wanka mata mari, Itama a hankalin ta ce" aman ai kin san ba'a zance a gidannan ko? Najeeba ta ce" ai nima ba a gidan zan yi zancen ba Kanta ta gyada har zata juya ta damko hannunta Tana juyowa ta sanyaya muryarta ta ce" kar ki manta abinda Ya ke fada mana, mutuncinmu darajarmu kin ji? NAJEEBA ta yi murmushi ta shafi gefen fuskarta sannan ta juya tana kalle kalle kamar munafuka ta kama hanyar fita Ta jina tana leke har sai da sahun mutane ya fara daukewa sannan ta samu dam dam ta bi ta daya daga cikin kananun kofofin gidan ta fice da sauri Tana fita ta cire alkyabar nan ta haska da hasken karamar wayarta ta samu waje ta ajiyeta sannan ta gyara lulubin lafayarta ta shiga takawa a hankali tana tafia Idannuwanta take tafe tana lumshewa dan jin wata sansanyar iska na busawa ta ko'ina Irin yanda wajen gidan yake da fadi da shukoki abin gwannin sha'awa, nan ne ake gudun dawakai Tun da ta tunkaro babar kofar fita gabanta ya fara dari dari ta fara tunanin yanda za'a yi su barta ta fita Wasu irin dafka dafkan mutane ne tsaitsaye a kofar fuskarsu harhada kamar basu san yaren fara.a ko sakin fuska ba Me zan ce masu dan su barni fita? Ta tambayi kanta tana mai dan ja ta tsaya tana hangensu Idannuwanta ta kuma lumshewa gannin bafa dare ya cika sosai ba ita kuwa niyarta ta je har saloon dan ko kiransu batai ba ta ga shin idan bata nan zasu iya kulawa da wajen yanda ya dace? Rufar jikinta ta kara gyarawa kafin ta hade ranta Tana zuwa ta ratsa tsakanin na faro, ta ratsa na biyu, ta zo na uku ne wata gabjejiyar murya ta dakatar da ita ta hanyar tambayar inda zata je a irin wannan lokacin? Sai da ta juyo ta kalli mutumen, sarai ta san ya santa ya kuma ganeta dan haka ta masa karyar ba yar cikin gidan bane bama bai taso ba Dubansa ta yi da kyau ta ce" sako zan karbo wajen Abih da suka fita dan rakiyar sarki Sannin cewa sarki ya tafi kuma ta tabata mahaifinta na cikin yan rakiya ta samu wannan amsar duda tana da shakun idan har zai yarda Ga mamakinta sai ya saki abin karewar ya bata damar fita kennan Hakan ya sakata dan kure shi da ido tana mamaki, sai dai gannin ya hade rai shima yama daina kallon nata ya sakata daga kafadunta har tana ayanna lale gidannan sun fara sasauta tsaro Shi kuwa tana fita ya juya ya danna kira ya shaidawa mai bayar da tsaron fada cewa eh ta fita A hankali take takawa tana gannin yanda garin ke walwali idan dare ya yi Manyan fitilun bakin hanya masu bada jan haske sun gama ko'ina sun haske garin Motoci da mashin da keke da masu tafiar kafa kowa na kai kawonsa tamkar ba dare ba Shagunna du a bubude Shagunnan atampopi ne, na dogayen rigunna ne, na jakunkunna ne abin dai ba'a cewa komai garin nada yannayi mai dadi da tsaro koda dare ya yi Bata da fito da ko sisi ba, dan haka ta yi niyar takawa a kafarta duda wajen sa dan nisa ta tabata ba zata rasa mai rage mata hanya ba Wayarta kuwa ta kunna ba zata kiraye shi ba sai ya kuma kira idan yana nan sai ta fada masa inda take idan kuwa baya nan ya yiwa kansa Har ta gifta tankamemen shagon da ake siyar da kayan kwaliya da su atash da turaruka na yan gayu masu jiji da kansu ta dawo Da wayo ta ringa hangen ciki Gannin yau Elhajin ne da kansa ba yaron nasa ba ya sakata hawa yar matatakalar kofar shagon ta tura baban madubin kofar dake kofa ta shiga Irin sanyi da kamshin yannayin shagon ne ya buso mata baki daya jikinta hakan ya sa ta lumshe idannuwanta sannan ta kuma budewa tana kallon shagon Bata yiwa kowa magana ba kamar yanda kowa ke sha'anin gabansa yana siye siyensa A hankali ta ringa bin wajajen tana dudubawa Abin turawa ta dauka ta shiga bi waje waje tana zabar manyan hodoji da su turaruka masu kyan gaske da tsada tana sakawa Sai da ta ga an rarage mutanen cikin shagon sosai sannan ta nufo wajen Elhajin tana tura keken daukan kayan Tana zuwa ta sakar masa murmushi cikin sansanyar muryar nan tata ta ce" barka da warhaka Elhaj Elhaji dake zaune da katon tumbinsa a gaba shima ya sakar mata murmushin yana fadin" barka dai yar budurwa sannunki da zuwa Bata amsa ba sai dauka da ta shiga yi da daidaya tana dora masa a saman table din bayan ba nan ake kaiwa ba akoy masu amsa su irga komai su fada maka nawa ne ka biya a zuba maka a leda a raka ka har wajen abin hawanka Daya daga cikin yaran ne ya taso da sauri yana fadin" Hajia ba nan ake kai kayan ba cen ake kaiwa Da sauri ta ce" eyah, ban sani ba ai Hannayensa ya saka zai kwashe kayan sai ya ji muryar Elhajin na fadin" aa kai bubakar barsu a nan nima ai ba wani abu nake ba zan irga mata Bari yaron ya yo ya koma suka ci gaba da kulawa da mutannen Sai da ta gama ajiye masa komai sannan ta dan taka karfen jikin kujerar dake gaban table din ta hau tana lumshe idannuwanta Ajiyar zuciya ta sauke tana yarfe hannunta ta saci kallon Elhaj ta ga ita yake kallo dan haka ta dube shi ta dan yatsina fuskarta ta rage muryarta sosai a hankali ta ce" na gaji sosai Kamar wani wawa ko yaro karami haka Elhaji ya saki daria yana fadin" sannu hajia ai da kin sakani dauko maki da kainama sai na yi aikin gashi kin sha wahala bayan kin fi karfin shan wahala Murmushi ta yi tana kara sauke ajiyar zuciya Muryarsa ya dan daga ya ce" kai dahiru dauko faro maza Da sauri saurayin da aka kira da Dahiru ya juya ya dauko ruwan faro ya ajiye har biyu a gabanta Kayan Elhajin ya shiga warewa yana sakawa cikin manyan ledojin kampanin yana yi yana kallon Najeeba wace ta kawar da dubanta tana danna wayarta Kiran gangan ta kara a kunnayenta ta shagwabe fuskarta sosai ta turo dan lebenta na kasa sannan ta lumshe shanyayun idannuwanta ce" yaya Irin yanda ta fadi yayan dole ko ke mace ki kaleta harma da sakin baki, domin jan yayan da ta yi sannan ta idasa da wani dan gurnanin kukan shagwaba Yan kafafuwanta dake jikin table din ta shiga dan bubugawa ta ce" yaya ina kampanin fa, har na zo na zabi abubuwan da nake so ka yi ka zo ka kawo kudin mana...... Ta kasan ido ta saci kallon elhajin, irin yanda yake sakin murmushi baki daya hakoransa a waje hakan ya baiwa kumatunsa damar kara girma, micik micik din idannuwansa suka kara dan shigewa sai dai kamshi kam yana ta fitar da kamshin miski kansa kuwa sanye da huka Hular dake kansa ya kara turowa gaba yana kallon shagwababiyar yarinyar Tashin hankali ya furt a kasan zuciyarsa Yo wannan na sameta nima na koma danye sharaf, dan na tabata idan muka fara wasan yar tserenmu a cikin falo ta dora tabara tana bubuga kafa ta ce sai na goyata Murmushi ya kara saki ya shiga zube mata kayan a cikin ledar Gannin haka ya sakata dan zaro ido ta kara fadin" aman yaya kace na fito sai mu hadu kuma kace yanzu an kirayeka wajen aiki? Shikenan ba komai Yi ta yi kamar ta kashe kiran ta dubi Elhajin Hannayenta masu tsararun yatsotsi ta hade, bakinta ta kara zumburowa ta kyabe fuskarta ta ce" ka yi hakuri Elhaji ka ji? Ka ga dama a kafa na fito motana ta samu matsala na yi tunanin mu hadu da yayana ya maida ni gida idan ya biya kudin kayayakin nan , sai dai kash ka ji wai an kirayeshi aikin gagawa ka san likita bashi da lokacin kansama Dan Allah ka yi hakuri Elhaj na bata maka lokaci da tsarin kayan nan Har yana inda inda ya ce" aa aa, idan yayanmu bai siya ba ni kuwa aikin me nake? Idanma da karin wasu a kawo su nan Hajia ai ke din baba ce Kikifta idannuwanta ta yi ta ce" ban fahimta ba Elhaj Wayarsa ya dora saman table din yana dubanta yana murmushi ya ce" ki dora min numberki nake nufo yan mata sannan ki bar maganar wai kudin kaya bayan shagonku kika shigo Murmushi ta yi a kasan zuciyarta tana ayanna zaka fada ne Sai kuma ta dan zaro ido tana girgiza kai ta ce" aa aa, ka rufa min asiri idan na je da kayan nan na ce wa ya bani? Yayanmu baya bari bayan nan yaya daga shigowa dan fita da kaya haka? Aa ba zan iya amsar kayan nan ba gaskiya Elhaj Kamar da wasa sai ga Elhaj na lalabar Najeeba cewa ta amshi kayan nan ba wani yawa kuma ai ita mace ce tana iya adana kayanta a dakinta Da kyar ta yarda aman tana ta dafe gaban goshi irin ya takurata amsar nan Cike da kulawa ya kara turo mata wayarsa ya ce" wanenen yayan nan namu mai sa'a a duniya da ya zama yayan wannan kyakyawar shagwababiyar budurwar? Wayar tasa ta kala kirar samsung ce babar gaske sannan sabuwa ce dal sai walwalin sabunta take aman bata dauka ba ta lumshe idannuwanta tana masa murmushi ta ce" sunnansa Ibrahim Adam , likita ne a baban asibiti na kashi Kansa ya ringa gyadawa cike da murnar jin hakan, nan take ya kuma tambayarta mahaifinmu fa? Dubansa ta yi duba irin ja wai Allah? Ta tabata wannan mutumen ya girmi Abih, aman da yake irin abihn ne gashi sai kira yake mahaifinsu sannan Yaya DAYABU yayansu ko me? Oh duniya yanzu du wace ta dan yi masa shagwaba kennan sai ya fada ya karba da gudu gudu shi kuwa? Sauka ta yi daga saman kujerar tana ganni yaronsa na jidar kayan yana fitarwa sannan tana gani ya saka kudi a leda guda irin kar ta gannin nan ta ki amsa Byron dake ajiye ta dauka ta duka ta rubuta masa number kanninta Najeeb ta ajiye masa tana murmushi ta ce" na gode Elhaj Shima murmushin ya yi da sauri ya saka takardar a aljihunsa har ya fara tunanin sauka da wuri yau dan ya je gida ya loda number ya yi kiranta Gasgi bata fada masa sunnan mahaifinta ba, aman ba komai koma yar gidan waye zai sani kuma shi ba da wasa ya zo ba da girmansa ba zai tsaya bin layi da kannanun yara ba dan ya san wannan samarin na zamani sunna yiwa wannan yar cakwai din layi Tana fitowa ta harhada kayan ta tsayar da dan adaidaita Yaron ne ya ce" an ce a kaiki fa Ta juya ta kalli wanda zai kaitan Kanta ta girgiza masa kawai ta shiga adaidaita sahun nan Direct sunnan shagonta ta fada masa sannan ta shiga lalubawa ta zaro kudin nan Murmushi ya saki tana gannin masu aku biyu wato jaka ashirin cif sababi Kanta ta gyada tana ayanna" yanzu haka baya fitar da zakah! Dan sahu na ajiyeta ta bashi kudin nan , nan ya shiga neman cenji dan haka ta amsa ta shige ciki ta saka a kawo masa Saloon din a cike take , sai aiki ake kuma a tsaftace take dan haka ta ji dadin hakan sosai Kayan aikin ta bude ta shiga lolodawa abinta wajen kayan siyarwarta, a hankali ta furta" halal na ci Zuwa ta yi ta zauna lokacin kuma karfe tara ta yi kuma a lokacin kiran ambasador ya shigo wayarta Bata daga a kira na fari ba sai a na biyu Zuwa lokacin ta amshi takardar tana duba wa'inda ke son kwaliya Byro ta amsa ta shiga dangwala ok a kan wa'inda zata iya yiwa a cikin satin nan sannan tana dora lokaci Sauraronsa take yana ta surutun dan me take bashi wahala ne Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" ka san dai na yi missing dinka a lot ko? Shima ajiyar zuciyar ya sauke yana jinta Ta ce" ina saloon ka zo na ganka ka ji? Tana gama fada ta kashe kiran ta kara fefesa turare ta kara duban kanta a madubi sannan ta ci gaba da kimtsa abinda ba lalene su kimtsa shi yanda take so ba Bai dauki wani lokaci ba sai gashi ya tsaya a kofar shagon Mikewa ta yi ta fita Bude motar ta yi ta shiga, sai dai tana shiga wata ta fito tana kallon numbobin bayan motar Kanta ta gyada ta koma da sauri ta dauki wayarta tana neman number kawarta Da gagawa ta ce" kin kade kawata, kin kade, kin san da ambasador ne ya fita daga shagon NAJEE? Kawar nata ce ta zabura daga zaunen da take tana ciye ciyen naman da aka gasa mata rusheshiyar mata da ita bata da aiki sai ciye ciye, itane matar ambasador kuma uwar y'ayansa uku ta ce" wace najee din? Saloo? Amsa ta bata cewa" kwarai yanda na gansu haka Allah datar da ni gannin annabi kiri kiri Ji ta yi zuciyarta ta shiga bugawa da sauri ta shiga neman abinda zata yafawa kanta tana fadin" gani nan zuwa Su kuwa tafia suka yi mai dan tsayi ya tsaya wajen masu gashin kaji Siya ya yi ya shigo motar da su ya tayar ya karasa wajen stade, wajen da yawanci samari ke zuwa su kebe da yan matansu su yi hira cikin aminci Sannan wajen akiy duhu hasken bashi da yawa sosai Kashe motar ya yi ya dauki wayarsa ya haska yana duban fuskarta A hankali ya ce" ina son ki Najeeba, ke kuwa kina wahalar da tsufana Murmushi ta masa ta ce" ka daina kiran min kanka da tsoho, ka fi yaro karami a wajena kai din jarumina ne na yarda da hakan Kansa ne ya ji na huruwa ya kawo hannunsa a hankali ya shafi gefen fuskarta wanda hakan ya saka ta dauki hannunta ta bige hannunsa har wayar nasa ta fadi Ranta ne kuma ta bata ta ce" meye haka? Ka san dai ba kyau ko? Kansa ya dafe yana kallonta ya ce" wai wani irin ba kyau? Yaya kike son ringa cutata ne a rayuwa? Ni bance zan je cen ba, na adana zuwa cen har mu yi aure aman kuma dan taba jikinki ba zaki barni ba sai ki ringa hanna min ko dan ba ni ake yiwa son auren ba? Idannuwanta ta lumshe cike da rakaicin soyayar zamani, Soyayar zamani na bada gudunmuwa sosai wajen kokarin tatsar mazan zamanin da take Dan me maza suke kokarin nunawa mace iskanci koda kuwa da nikaf suka ganta? Yanzu har fadi ake masu nikaf din sun fi masu yawo ba hijab munafurci shin laifin matan ne ko mazan? Hannunta ta saka zata bude motar da sauri ya ce" hala har kin yi fushi? Kin ga kar ki min fushi dan Allah dawo mu ci kazarmu ki amshi tsarabobinki kin ji? Najeeba ta juyo tana kara hade rai ta ce" bude min na fita Hannayensa ya saka gaba daya ya janyota jikinsa yana fadin" come on baby meye na fushi bayan ko dan shan mintin nan baki taba barina na yi ba Sosai ya riketa a jikinsa ita kuwa ta saka dukan karfinta ta hankade shi ta mika hannunta da sauri ta danna mabudin dake gefensa ta bude motar ta fito da wani irin karfi Wani kukan takaici ne ya zo mata lokaci daya lafayarta ta warware Bayanta ne ta ji ya daki wani abu Da sauri ta juyo jin an rike damtsen hannunta Kamshin turaran da ta shaka ne ya so halaka tunaninta da sauri ta saka hannunta da lalube ta lalubo jin jikin baya dauke da babar riga hakama fuskar ba nadi Wata mota ce ta hasko wajen Idannuwanta ne suka sauka a fuskar wanda ya riko hannunta Idan ana fadin an yi gamo takan dauka a wai ne sai yau da ta yi gamo da kanta Wannan mutumen aljani ne , aljanninma mai aljanin kyau Girarsa biyu a hade take kamar ransa a bace sai dai kyan fuskarsa ya batar da bacin ran Wani dogon hanci ne da shi da lebunna jajaye uwa na macen da ta san kanta take gyaran kanta Kamshi yake mai dadi da sanyi Kirjinsa wasu rikakun pecto biyu daka daka ne suka gaje wajen Damtsen hannunsa kuma tamjar zasu fasa rigar jikinsa baka wace ta dame shi Tsayinsa sosai ya yi mata tsayi hakan ya saka gaba daya kanta ke kallonsa sama sama Rigar jikinta ta kasan abayar fara ce mai dogon hannu aman ta dameta sosai Ya take dayan hannun lafayar nata hakan ya sa take kara karkacewa Bata taba jin mutun mai karfinsa ba, irin damkar da ya yiwa hannun nata ya sakata jinta ficik a hannunsa Gaba daya jikinta ne ya kara daukan rawa tana dubansa shima ita din yake kallo yana son gane shin abinda ya fitar da shi ya ganni ko ba haka ba? Takaici, haushi, tarin tsanarta ne yake ji a ransa hakan ya sa ya kara matse tatausan damtsen hannunta Bakinsa ya buda a kausashe ya ce" To fa, waye wannan? Ina sarki? Zai samu damar hukunta NAJEEBA kamar yanda yake fata? Najeeba gamo fa kikai mun shiga uku😲😲😲😲😲 [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 12 Bakinsa ya buda zai yi magana, sai dai ta rigaye shi ta hanyar juyawa ta waiwaya ta kuma juyowa wajensa A rikice take, hankalinta a tashe yake hakan ya sa a hargitse ta nuna masa motar ta ce" zai zai taba min jikina Idannuwansa ya kausasa yana dubanta, Sai da ya yi iya yinsa ya kara matse damatsunnan hannayenta dake cikin dafin hannayensa ya ce" ba abinda ya kawo ku nan kennan ba? Magana ne ya yi mata a kausashe, a kidayance , Iskar bakinsa dake kusa da ita sosai ne ta fito ta daki hancinta A hankali ta lumshe idannuwanta tana jin zafin rikon da ya yiwa hannayenta Kanta ta ringa girgizawa da sauri ta ce" aa, aa, ni ba yar iska bace Idannuwansa da sukai ja ya kai dubansa wajen motar, gannin na cikin motar na kokarin fitowa ya saka shi yi mata wani ja tamkar ya ja dan karamin yaro sosai Sai da ya kara yin cikin duhun da ita ya sasauta mata rikon karshe ya saki hannayen nata Da yake ya jima cikin wajen, ya fita ganninta sosai duba da ita a rikice take sai abin ya mata yawa take ta neme nemen inda zata saka ranta Bakinsa ya tabe ya juya da sauri zai tafi Da wani irin karfi ya ja ya tsaya hakan ya sa ita da ta tarbi gabansa dukan kirjinsa da goshinta Hannunta ta kai gaban goshin nata tana sosawa a hankali ta ce" aushhhhhh Tsayawa ya yi kawai yana kallonta Sai da ta sosai sannan tana dubansa ta ce" dan Allah ka taimaka ka fitar da ni daga wajen nan, walahi ban taba zuwa ba kar wancen mugun ya cin min Ji yayi gaba daya ta gama raina masa wayo, itane take gudun kar namiji ya cin mata? To ko ta danfaro shi wasu kudade ne take gudun ya kamata ya amshe? Sai dai irin kallon da yake mata zai iya gannin yar karamar wayarta a jikinta ta cikin rigarta sakamakon rigar a matse take sosai Bayanta baya gannin kudi ko abin kudi idan dai ba a cikin sket dinta ta saka ba Shi zata kalla ta rainawa hankali? Kansa ya girgiza ya ce" ba saurayinki bane? Najeeba bata taba zuwa wajen nan ba, sannan zata iya rantsewa bata taba samun kusanci da namiji irin yanda Ambasador ya yi mata a yau ba Hakan ya sa baki daya jikinta ke rawa takaici ya gama rufe mata zuciyarta Hannunsa ya kai ya damki hannunta ya juya ya shiga janta Bin bayansa kawai take Bata san shi, bata taba haduwa da shi, bata san mutun ne ko aljan ba, bata san shima zai cutar da ita ko akasin hakan ba abinda ta sani daya ne tana son ta yi nisa da motar Ambasador Tana so ta yi nisa da shi baki daya dan tana da muradin kasancewa ita daya Gani take ko ina ta bi idan ta zo wucewa yana iya ganninta, gani take zai kuma yin yinkurin aikata mumunan aikin nan da ya yi na hada jikinsa da ita Sai da ya fito bakin titi da ita ya saki hannunta Juyawa ya yi yana tafia cike da wata irin kasaitar da ta sakata zubawa bayansa ido Tsalaka titin ya yi wanda har sai da ta rintse idannuwanta sakamakon wani mai mota da ya so kade shi cikin ikon Allah maimakun ya tsere da sauri ko ya yi gudu dan tseratar da rayuwarsa sai ya zama mai motar ne ya take birki har hakan ya yi kara sosai Tana buda idannuwanta ta ga ya tsalaka, bai kade shi ba mai motar ya leko kansa yana fadin" ka ga malan rai zaka yiwa kwombo? Ka wani hau bakin hanya kana tafe da takama tamkar *mai DAMAGARAM?* idannuwanta ta yiwa luuuu ta ga ya shige kwanar hakan ya sakata daga kafarta a hankali tana gyara rufar lafayarta Ta sha cika dare a shago dan takan kai har sha daya idan aiki ya mata yawa Aman yaya DAYABU ke zuwa ya tarbota su tafi gida Yau sai ta ringa tafia tana hankalce da mutane cike da tsoron daren Da haske ko'ina ba wani duhu ya game garin ba Mai mashin ta tsayar ta hau ta fada masa ya kaita anguwar gidan sarki Yana kaita ta bashi mai akun nan guda dake bayan wayarta Ido ya zaro ya ce" haba dai Hajia yaya zan samu cenjin wannan? Bata yi masa magana ba ta juya ta nufi ciki tana tafe cikin nutsuwa Baki da hanci ya saki yana kallonta har ta shige babar kwanar gidan sarki A hankali take tafe tana jin zuciyarta na dokawa dan bata san yanda za'a yi ta samu shiga ba Motar da ta hasketa ne ta sakata rintse idannuwanta ta rabe waje daya Kusa da ita aka tsaya tana jin jikinta ya dauki rawa dan sam bata son aikata laifi a wannan waje Wanda ya fito daga motar ya sakata sauke ajiyar zuciya Da gudu ta karasa ta fada jikinsa lokaci daya ta saki kuka tana kara dora kanta a jikinsa Kiransa Anmy ta yi cewa bata ga NAJEEBA ba, maza ya samo mata ita Gabansa ne ya fadi ya shiga kokarin cireta a jikinsa sai dai ta ki bada dama tana kara shiga jikinsa tana hawaye Muryarsa a cakule ya ce" NAJEEBA, meye? Me ya faru? Me ya same ki? Ke da wa? Kukan take tana jin ciwo a ranta , gannin ya bambareta daga jikinsa tana kallonsa ta ce" yaya, me me yasa kowani namiji yake son nuna min shi dan iska ne? Yaya me ya sa suke son nunawa mutun iskanci? Gabansa ne ya kara faduwa hakan ya saka shi kurewa fuskarta kallo Muryarsa na rawa rawa ya ce" Najeeba, kar ki fada min abinda zan tsani kaina , kar ki fada min abinda zai sakani yin gaba da ke Mutuncinki kika zubar? Da sauri ta rintse idannuwanta dan jin maganar da girma sosai a kunnayenta Sai kuma ta bude tana girgiza kanta tana kokarin rungume hannayenta a kirjinta Hannunta ya kamo ya sakata cikin motar ya tayar ya juya cikin gidan A hankali yake tafe har ya karasa wajen ajiyar motoci Yana dakatawa ya kashe motar a hankali yana sauke ajiyar zuciya Sai da ya sanyaya muryarsa sosai sannan ya ce" da me kike jiran ganni bayan kin ce zaki amshi abubuwan hannayensu? NAJEEBA ke baki yarda sun san gidanku ba, wanda ya san gidanku ya tabata mai naci ne ya kai kansa gidanku Najeeba ke baki yarda sun san kina da mahaifi tsayaye da kuma yayan da zasu ringa shaku ba Najeeba, kin mayar da aljihunsu wajen wasanki , kin kware wajen iya juya tunaninsu su fitar da dukiyarsu su kashe maki Dubanta ya yi ya ce" me kike jira? Me zasu so su kuwa a wajenki? Bayan sun san ba su kadai bane, sun kwana da sannin basa layin wa'inda zaki aura Me zai hanna su yi tunanin iskancin kike so bara su nuna maki ba? Kansa ya sada gannin ta kure shi da ido kuma harga Allah du ta fi su magana ga shegen karfi da idannuwanta ke gare su A hankali ya ce" kin san wani namijin na nuna irin haka dan ya gane shin matar ya kilace ce ko matar a watse ce? Wanin kuwa da kika gansa dama dan a watse din ne NAJEEBA, shi irin haka a haka ake rasa na kirkin Tsorona a haka na kirkin ya sulube maki ke kanki baki ankara Hannunta ya kamo ya dago yana dubanta ya ce" idan kika kare mutuncin kanki, kon kare mutuncinki ne a farko, kin kare na y'ayanki, sannan kin kare namu NAJEEBA, kin fito daga tsatson da ya yo sunna, Allah ya daukaka Abu kankani ake jira karamin abu ya zaga gari Shi yasa nake maku nasiha cewa ku kama kanku ku rike mutuncin kanku NAJEEBA ta lumshe idannuwanta a hankali ta ce" ya, kai ka san ni ba yar iska bace ko? Kansa ya daga yana dubanta A hankali ta dantse lebenta na kasa tana jin ciwon abin a kasan zuciyarta Dan kawai na so abin aljihunsu sai su so jikina? Ta tambayi kanta da kanta Sai ta girgiza kanta tana mai bawa kanta amsar cewa" da ya kare aikatuwa a duniya, da na gile shi da hakorina na kashe shege! Kudinka sai na ci idan har kana iya saki aman fa ba zaka zo ajiyata ba karya ne! Hannun yayan nata ta kamo ta ce" zaka raka ni wajen Anmy? Kar ta min fada Murmushi ya yi ya bude motar suka fita Sunna tafe tana tsara irin abinda zata yiwa Ambasador, sai na ci ubansa na rantse! A haka har ta dauki alkyabarta da ta ajiye ta dora ta kara gyarawa suka nufi ciki ........................................... Karfe biyu na dare Alkyabarsa yake cirewa a hankali Sai da ya cireta sannan ya shiga warware rawanin kansa A hankali ya gama warwarewa sannan ya kama babar rigar ya sauketa Sai wata riga dake ciki baka ta kama jikinsa sosai sai wandon shadar dake kasan rigar Mikewa ta yi tana karasawa inda yake tsaye ya baiwa wajenta baya Sai da ta dawo gabansa ta daga kanta tana kallon fuskarsa A hankali ta kai hannunta wajen sajen fuskarsa ta dora A hankali ta shafa tana kallon yanda idannuwansa ke lumshe Hannunta ta saka ta shiga kokarin cire masa rigar sai dai tsayinsa ya saka sai dadafe take ta kasa cirewar Dan murmushi ya sakar mata ya tayata ta hanyar rage tsayinsa Rigar ta cire masa sannan ta kai wajen hancinta tana sinsinawa tare da lumshe idannuwanta A haka har ta kai hancinta wajen bakon turaran da ta ji a hancinta A hankali ta kara rintse idannuwanta jin yannayin kanshin Princsss a jikin rigar Tana kallonsa ya shige bayi ita kuwa ta zauna saman lafiyaye tatausan bed dinsa da rigar a hannunta jikinta a mace ranta a bace hankalinta a tashe Ya jima sosai a bayin kafin ya fito yana tsane ruwan wankan da ya yi Turarensa yake shafawa yana hangenta ta madubin dake gabansa Ya so ya yi nafila, sai fai gannin ta zo harka tana zaune har warhaka ya saka shi karasa kimtsa kansa ya saka kayan baci riga da wando mai dogon hannu sannan ya karasa saman bed din Hawa ya yi ya kwonta yana kallon sama A hankali ta karasa ta haye saman kansa ta dora kanta saman kirjinsa Kamar wace take fada ta sada kanta sosai ta ce" Allah ya ja zamanin sarkina, Allah ya karawa mai martaba lafia da jisan kwana, Allah ya tsare mulkinka mai gidana Idannuwansa kawai ya lumshe, bai san yaya aka yi yake jin kalaman nan a waje sannan ya ji su a dakansa ba, yana son jin wasu kalar kalamai na kulawa ba irin wadinnan ba masu zafi yake son ji wasu kala daban aman sai ya fita waje ya ji kirari ya dawo daka ya kebance da macen da ta fi kowa sannin sirin jikinsa wace suka rigaya suka zama daya itama sai ta bi shi da kirari Hannayenta ta kai ta kashe wutar dakin, yar karamar dake gefen bedma ta saka hannunta ta kashe Sannin cewa bai taba mu'amalantar mu'amala da ita da haske ba ya saka ita da kanta ke kashewa a irin wannan lokacin, kwarai ta fi kowa kiyasta sanninsa domin ba idannuwanta suke gane mata ba, jikinta ke daidaita mata irin girmansa Idannuwansa ya lumshe yana jin kwarai yana da bukatar hakan, A hankali ta shiga zamewa ta kwonta sannan ta janyo hannunsa tana sauraron kulawarsa Ta kasance a kulun sai dai ta yi kwonce abinta shi kuwa ya bada kokarin komai Hannunsa ya kai jikinta a hankali, sai dai ya ji laushin riga a hannunta Rigar ya amsa ya ajiye gefe kafin ya shiga kokarin gannin sun samu nutsuwa baki dayansu Ta fi so su yi ta romance, ta fi ganewa hakan , Tana samun hakan, mai sakata samun nutsuwa kuwa sai dai sam gogan nata shi baya samun nutsuwa a iya hakan Sai da ta kankame jikinta cike da tsoro jin zai kai gareta Hakan ya saka shi sasauta mata rikon da ya yi mata a hankali ya ce" ki saki jikin ki dan samun gamsuwa cikin salama Ajiyar zuciya take ta saukewa tana son sakin jikin nata sai dai ta rigaya ta saka tsoronsa da tsoron abin a kasan zuciyarta hakan ke bata wahala matuka Ta gurzu sosai dan sai da ta biya kwanakin nan kafin ya saurara mata Bai koma saman bed din da dauda ba sai ya nufi bayi Sai da ya tsaftace kansa sosai sannan ya fito ya dawo ya tarar ta cenza zannin gadon kamar yanda ya gindaya mata Sai da ta gama ta dauke wancen zannin ta nade shi sosai ta mike bayan ta mayar da kayanta jikinta Rigar dake ajiye ta karasa ta dora hannunta zata dauka Sai dai bata kai ga dauka ba ya saka hannunsa ya rike rigar hakan ya sa ta sakar masa ta kara sada kanta tana dan murmushi ta ce " ka huta lafiya sarkina, Allah ya hutar da gajiyarka uban y'ayana Cike da kasaita ya sakar mata murmushi yana kallonta ta juya ta fice Me yasa bata iya zama a bangarensa komai dare bata iya kwonciya saman gadonsa sai dai ta je falo ta kwonta? Kafadunsa ya daga yana baiwa kansa amsa cewa bata da ra'ayin hakan ne Rigar d aya lura ta yi ta sinsinnawa da nishadi sai dai daga baya fuskarta ta cenza ya kai wajen hancinsa yana mai sinsinawa Da sauri ya maida baya baya kusan ciki inda idan ya saka zata kawo masa daidai cikinsa ya shinshina Da sauro ya cire daga hancinsa yana mai dafe gaban goshinsa Kanshin turaranta ne wannan Wani irin turare take anfani da shi mai kamshi mai tsayawa a jikin mutun haka? Bakinsa ya tabe yana ayanna" idan har kere na yawo.....zabo na yawo na tabata wata rana zasu hade........................ Tun da sasafe suke kinkimtsawa Sai da suka gama kimtsawa suka hadu a saman tafkeken table din wajen du suka zazauna Cike da farin ciki ta shiga zuzuba masu abinci da kanta tana yi tana dubansu Inama ace su dawama da ita haka? Gashi yau har zasu koma gidajensu inama ace mahaifinsu ya iya bata koda matan ne ya rike mazan? Abincinsu suka ci cikin nutsuwa kafin ta dauko ambulope din nan ta budeta Abubuwan ciki ta zubo wanda hakan ya saka su baki daya zazaro idannuwansu ciki kuwa harda GIMBIYA Da sauro ta dauki farar takardar dake ajiye ta buda, a fili ta karanta" *ina rokon alfarmar daga yanzu du wata dawainiyar gimbiyata ta dawo hannuna, idan nace kowace ina nufin kowace ciki kuwa harda kudin kari da kati.....fatan zaki rike wannan catin na banki sannan ki faranta min ta hanyar anfani da shi a kowani lokaci daga ni mai ke in sha Allah* Wani ihu ihu yan matan suka kwasa sunna dariya, NAJEEBA dake firfito ido ta daga hannayenta duka biyu tana sarawa ZAHRAU ta ce" *AN BASHI DAMA, AN YARDA* Zahrau kam kanta ta sada da mamakin kalaman ciki, dama zai iya neman wata dama a wajenta maimakun ya bata umarni? Ashe sarakai na neman dama maimakun su bada umarni ko dai shine mai saukin kai? Irin kallon da ya ringa yi mata jiya ta tuna hakan ya sakata saurin kara sada kanta tana murmushi kafin ta sauke dubanta saman makudan kudadan da suka zubo wai na karinta ne da kuma katin da yar agogon azurfa kamar dai soyayar yara masu ji da kansu Kanennta ta bi da kallo tana gannin yanda suke shoki Sannan ta sauke dubanta saman Anmy Ganni ta yi Anmy harda su tagumi tana kallon NAJEEBA wace ke murmushi tana kada kai tana hangota ta zama aunty Anmy ta dubi kananun ta ce" ku tashi ku je falo Bayan sun bar wajen Anmy ta dubeta cikin nutsuwa ta ce" bana so ki amince masa dan dukiya daughter Na fi so ki ji kin amince masa duda kin ga ba yaro karami bane da zai zauna yana soyaya irin naku na yara, sannan ba zaman jiranki zai yi ba duba da irin darajarsa Aman ko da wasa ba zan yi maki auren dole ba kin ji? Kanta ta ringa gyadawa a hankali sannan anmy ta dubi su NAJEEBA Murmushi ta yi masu ta ce" kar ku manta, ku ringa kiyaye darajarku ku rike mutuncinku kun ji? Su duka suka amsa mata da nutsuwa kafin du su tashi su tafi bayan sun gama yin salama da ita ............................................. Kansa a sade yake gaban mahaifiyarsa Kunyarta ne ya ji ta lulube masa zuciya sai wani irin takaicin zinaria da haushinta da mamakin ashe har yanzu bata da hankali? Yarinta ce ko raini ne ya shiga tsakaninsa da ita? Cikin tausasawa Anmy ta kara tambayarsa kamar haka" *SHAHEED, SHIN ZAKA IYA FADA MIN KAMSHIN TURARAN WA MATARKA TA JI A JIKINKA KAFIN ZARGI YA SHIGA TSAKANINKA DA ITA DA NI KAINA MAHAIFIYARKA KO BA ZAKA IYA BANI AMSA BA?* Me zai ce mata? Ce mata zai yi ga mai turaran ta tambaye shi me ya kai turaranta jikinsa? Ko fada mata zai yi ga abinda ya kawo turaran nata jikinsa ta titsiye shi kan a kan me? Aman yana tunanin ya yi girman da zai iya tara mata hudu shine zinaria ta masa gangancin kawo irin maganar nan kunnen mahaifiyarsa? Ta kuwa san irin yanda yake kiyaye lamarin mamansa shine ita zata masa wannan shirmen? Anmy ta shiga girgiza kanta a hankali sannan ta ce" [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 13 Kansa ya kara sadawa sosai kafin a hankali ya ce" Allah ya huci zuciyar Anmy Zamanta ta maida ta gyara tana mai girgiza kanta, kennan ta tabata wata yake ganni har kamshin turaranta ya zauna a jikinsa? Cikin nutsuwa ta ce" kar ka manta kai ne mai hukunta laifin da ya kai hukunci, shin aikata abin hukuntawa ka yi? Sai da ya kuma lumshe idannuwansa ya bude a hankali ya girgiza kansa Ajiyar zuciya ta sauke jin aa, dan haka cikin nutsuwa ta ce" bana gane gabanka bare batanka SHAHEED, bana fahimtar me kake boyewa a cikin zuciyarka Maganarka ta kasance kadan Wata ajiyar zuciyar ta sauke sannan ta ce" koda kai sarki ne, ni mahaifiyarka ce Ka yi kokarin yin shawara da ni idan bata girmi kwakwaluwana na mace ba ka ji? Kansa ya ringa gyadawa a hankali sannan ya dan dago ya dubi fuskarta Muryarsa dai cikin nutsuwa ya ce" ALLAH ya huci zuciyar mahaifiyata Murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta ta ce" idanma wacece ka aureta Wannan karon da idannuwansa ya bata amsa yana kara sada kansa a gabanta Murmushi ta yi ta furta" Allah ya yi maka albarka A hankali ya amsa da amen Bai tashi daga gabanta ba sai da ya cike lokacin da yake dauka a gabanta sannan ya mike ya yi mata salama ya koma bangarensa dan yau ba zai fita fada ba su waziri na cem sunna gabatar da shara'ar garinsa mai mutane masu rigima da saurin kawo kara Kamar wace ta jima bata zo dakin nata ba irin ta shekaran nan Da murna da komai ta shiga tana ta kara kallon dakin Jingina ta yi da jikin garun dakin nata, kai a duniya fa tana ji da dakin nan nata domin rabin tanadinta a cikinsa ya kare Bata tunanin ko dakin wata mai kudin mai auren zai nuna mata wani abu shi yasa take gannin idan ta tashi aure za'a kwashe komai a kai mata gidan mijinta ne Kalmar miji ta sakata buda idannuwanta *Mijina* ta furta a hankali Ina ka buya? Ina kake ? Yaushe zaka zo? Ko a ina kake na san baka da aure, Idanma kana biya yan mata kana da budurwa ka yi gagawar salamarta Zama ta yi saman kujerar dakin nata wace take da yannayin takalmi mai tsini ta dan talafe kuncinta A hankali ta ce" bana so ka zama farin mutun, dan rike NAJEEBA sai tsayayen namiji Farin mutun kuwa ya cika son jiki da sanyi sanyi Murmushi ta kuma saki ta dora kafa daya kan daya ta daga kanta kadan tana dan wasa da habarta ta ce" sannan ina so ka kasance mai lebe pink iya na kasan na saman ya zama baki....bai dameni ba idan an ce dan shaye shaye mai baki ja aman fa bana so ka zama dan shaye shaye ka ji? Hannunta ta dora wajen kirjinta tana kara dora kafa daya kan daya ta ce" kirji fafada, askin yan tasha........murya irin ta zaki, damtse mai taurin gaske Idannuwanta ta rufe da hannayenta irin ta ji kunyar nan ta ce" fafadan kirjin da zan iya kwonci na yi isashen baci da juyi Wani murmushi ta saki tana fadin" na san sai ka so mata, ....na san sai an so ramawa a so min kai abinda na fi sani shine ba zan yarda a karya min kara a ido ba! Ke NAJEEBA! Muryar zahrau ta sakata zabura tana kallonta , a rikice ta ce" meye? Zahrau ta ce" kin haukace ne kina zaune kina magana kasa kasa kina ta murmushi kina wani irin abu a saman kujera lafiarki kalau kuwa? Yanzu da nace kowace maza ta gyara dakinta ke ko kakaba baki fara ba bale shara bale guga kina zaune kina uban meye? Da sauri ta mike tana hararan Zahraun ta shiga yaye zannin saman gadonta ta ce" yaya ake so mutun ya yi kiba idan akoy irinku a waje? Shikenan ba zan zauna na hasaso yanda nake son gannin mafarkina ba sai an samu mai dirowa ciki ya katse ta hanyar sako nasa maganar? Yaya ake so mutun ya iya labewa ya samu lokacin kansa idan ba wada bashi da kys din dakin wani? Ni gaskiya ana takura min Zahrau ta tabe baki ta ajiye wayarta ta shiga tayata gyaran dakin tana fadin" yaya ake so a yiwa gandamemiyar budurwa aure a kaita dakin miji ta aikata abin kirki idan gyaran dakinta kawai na daukan mata awa biyu? A yi mata a ga ikon Allah, aunty ta yayama zan ringa aiki a cikin gidan ni daya bayan na gama tsara zan rayu da mijina tamkar abokan junna? Zamu raba aiyukanmu ne, mu rufe dakinmu mu saka kida muna yi muna casu abinmu, aunty ba zan iya auren namijin da bai iya rawa ba, ba zan iya auren namijin da bai iya sakani daria koda bana so ba, ba zan iya auren namiji mai tsare gida ba....Najeeba ta fada tana cilowa auntyn nata babyn nunus na zaki Cafewa ta yi utama ta jefa mata tana daria ta ce" gidan aure zaku gina ko gidan shedanu? Mace ai ita zata yi aikace aikacen gida , ta tsaftace ko'ina ta kimtsa ko'ina Bayan kin san da Abih ya fada da ihu ya fada a nasiha cewar ba zai taba bari a daukar mana yan aiki ba har sai mun tara y'aya? Ban san nufinsa a kan hakan ba ni sam Najeeba ta ce" ban ga aibu ba dan mun gyara datin da muka bata tare da kai! Maza da suka amsa sunnayensu na maza Mazan da suka rayu da adini a jikinsu, sukan taya matayensu aikace aikacen cikin gida Bana gannin walwala da sabo a wajen namijin da zai gimshe min fuska shi ga mai gida ni ina dauke cen goge cen gyara cen wanke cen shi ko gani baya yi bale ya yaba Aunty ni zan koya masa sannin zafina, ya kama min mu taru mu rufawa junna asiri Kina son sannin dalilin Abanki na hanawa a kawo maki yan aiki? Ba komai bane face shi burinsa ki gina gidanki, ki shaku da mijinki, ki san kanki ki san wa kike aure kafin a kawo maku masu sangartar da ku ta hanyar kuna zaune kafa mike ku ringa saka su dauko maku ruwa, kawar da plat din abincinku Zahrau ta zauna bayan ta jefa mata tsintsiya ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" nima na so haka a tare da ni sosai NAJEEBA ta duka ta shiga share dakin tana dukawa har kasan bed dinta kasancewar kasansa a bude yake tana sharowa sosai ta dago tana dubanta Murya a sanyaye ta ce" bai zama lale ki amincewa rayuwar gidan sarauta ba! Bai zama lale ki auri mutumen nan ba Farin cikin ki na gaba da komai Idan har zuciyarki ta ki amince maki da hakan ba dole bane! Dan murmushi ta yi tana share dan karamin cafet din wajen ta dan dago ta ce" sannan kina iya mayar da lokacinku naku wanda zaki saka sarkin Agadez shara a daka, a lokacin da ba masu yi maku hidima, babu idannuwan bafadanku Ta karashe tana kashe mata ido da yannayi na shakiyanci Daria ta yi tana girgiza kanta , NAJEEBA ta ce" namiji, ya kasance namiji a gaban wasu bakin fuska, aman amini a cikin gidansa Zahrau ta karkato sosai tana dubanta ta ce" ta yaya? Ta yaya kike tunanin zan iya aiwatar da wani abin da zai zo masa sabo a rayuwarsa? Ke kin sha gannin vidion gimbiyarsa inda take takun kasaita, wuyanta hannayenta kafarta dauke da zinari Kin ga irin yanda take zuba kudi Ke kin ga kalar fatarta kin kuma ga kalar kyawunta Bayanta akoy wata guda dake taka rawarta itama Wacece ni da zan iya jerawa da su? Kin ga kalar fatana bak'a ce, Bani da wani kyan da zan iya dukan kirjina na jera da matan nan Jikina ke mutuwa NAJEEBA NAJEEBA ta yi sakalau tana kallonta A hankali ta ce" da ba dan ke yayata bace, da sai nace ki tashi ki fitar min a dakina domin a duniyata bana son macen dake raina kanta ko wacece! Muryarta ta dan daga tana kallonta da tsintsiya a hannunta ta ce" shine me dan kina bak'ar mace? Ita bak'a ba zata je gidan sarauta ba kennan sai fara? Kin manta halayan mace ke siyan mata mutunci idan mutuncin ne , soyaya idan soyayar ne? Meye aibunki a jikinki meye baki da shi? Meye laifinki a fuskarki me ya gaza na mace? Kina nufin fatar naki ce ta fara baki haushi a yanzu kuma bayan mun kasance masu takama da kalar fatarmu? Bakinta ta turo ta ce" kudi kuwa, kudi aunty, kina tunanin sunna da wata matatsa ne ta fi aljihunsa? Zaki amshi kudin mijinki da dabara ki kashe da hikima ba tare da shi kansa ya gundura da tunanin kina da kashe kudi ba Wani gwauron numfashi ta sauke tana kallon NAJEEBA , idan Najeeba na fadi sai take jin abin ba wahaka, sai ta shiga aunawa sai ta fara tunanin anya kuwa? Anya hakan zai zo da sauki kamar yanda kanwar nata ke fada? Wayarta dake saman bed din NAJEEBA NE TA FARA KUKA duban wayar suka yi a tare NAJEEBA ta dauko tana kallon number Zahrau ta ce" waye? NAJEEBA ta daga kafadunta ta ce" nima ban sani ba ba sunna ai ZAHRAU ta juyar da kanta ta ce" tun da safe ake kirana da number ko ba mai 00 karshe ba? NAJEEBA ta gyada kanta tana kara kallon number A hankali ta ce" aman number nan batai kama da irin number yan cenken numbobi ja Tana fada ne tana dagawa ta kara a kunnenta Dan shirun da akai yi ne ya saka Najeeba kuma kallon number ta ga ba'a kashe ba A handsfree ta saka ta ajiye sannan ta yi mata nuni da su yi shiru Sharar da take ta ci gaba da yi tana gyarawa da kyau Sai da ta gama sharar ta kwashe ta zubar ta dawo ta shiga ciciro kayanta tana gyara masu ninkinsu tana mayarwa a muhalinsu Wata kamilaliyar murya ce ta yi magana kamar haka" Asalamu alaiki gimbiyana Dan shiru ya yi kafin ya dora da fadin" ki ja ajinki da kyau sarauniya ....aman yaya aka yi baki nemi number mijinki kin ji inda jirgi ya wurga maki shi ba? A tare suka zazaro ido a lokacin da suka fahimci mai sanyaya maganar nan ba kowa bane face sarki Wata wuntsilowa Zahrau ta yi tana kara firfitar da idannuwanta Da gudu NAJEEBA ta warto byro da takarda ta janyo wayar tsakiyarsu Da wani irin sauri ta yi rubutu sannan ta nuna mata Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta sanyayar da muryarta sosai da sosai kafin ta ce" amincin Allah ya tabata a gareka Murmushin manyan mutane ya yi jin da kyar dai ya samu jin muryarta a karo na hudu tun bayan nemawa Zinaria afua, da godiyar da suka yi masa Ya tabata yarinyar ba sai an bata lesson din jan aji kafin magana ba, da alama saraurar a jinninta take ba sai an koya mata wani abin ba Shima shirun ya yi mata, domin shi dai ai sarki ne abin nan a jinninsa yake ba wai hawa ya yi daga sama ba Wani rubutun ne ta nuna mata dan haka a hankali ta yi dan murmushi ta ce" yaya hanya? Ya gajiya? Shima murmushi ya yi kafin ya bata amsar cewa" gajiya ba zata kau ba sai na kilace ZAHRA ZAHRAU ta kuma zaro ido hakama NAJEEBA Da gangan Najeeba ta rubuta " to wai shekarunka nawa? Ta nunawa Zahrau Allah ya taimaketa sai ta karanta take maimaitawa dan haka bakinta ta cije tana wurgawa Najeebar fillow Lokaci daya ta ce" NAJEEBA bakya jin magana walahi Murmushi ya yi jin kamar kokowa suke, shima ya maimaita sunnan Najeeba Zai iya cenko ko wacece Najeebar nan, yana ga itane wace suka fiya dunguri a boye idan sunna tsaye tare da yan uwansu Tana mintsinnin Najeeba tanai mata cakulkuli ne tana fadin" baki da kunya Najee mijin nawa zan yiwa wannan tambayar? Sai kuma ta yi dif ta yi saurin kallon wayar Da wani irin sauri ta sauka tana fadin" na shiga uku, da sauri ta warci wayar ta kashe tana zaro ido Shi kadai ya ringa daria a bayane na kuruciyar yaran, Da yake ya shigo hutun yama ne sai kawai ya rubuta mata message ya tura sannan ya ci gaba da abubuwan da yake Da mamaki ta ringa bin message din da kallo, hakan da suka yi bai bata masa rai ba, saima magana irin ta tsokana Dama saraki na da raha haka? Ta kuma tambayar kanta Da baya baya ta fada saman bed din tana daria, a hankali ta ji dan tsoho na raf da zuciyarta.............. ............................................. Sannin cewa a gobe zai yi zaman fada ya saka shi gama komai nasa da wuri sannan ya kwonta saman bed dinsa ya shiga jan carbi Ta shiryawa yauma, ta gama sabawa da irin jarabarsa hakan ya sa a yanzu idan bata ji shi a tare da ita ba take jin sam ba dadi Tana wani irin kishinsa wanda ya zarce misali bale a matsayinsa na sarkin garin ta tabata ko tana so ko bata so wata rana sai wata ta so shiga rayuwarsu Abinda ba zata iya aminta da shi ba kennan Irin yanda ko mahaifiyarsa take jimawa bata ga kalar fuskarsa ba bale wata cen yar banza ta gane mata sirrin dake haukata zuciyarta a kansa? Tana godewa Allah da yake rufe fuskarsa wanda mutane da yawa sai dai su shaida hotonsa aman basu taba ganninsa a fili ba Wannan na kara daukaka darajarta ko a cikin gidan sarautar cewa itane macen dake gannin fuskarsa a duk lokacin da hakan ya raya mata Salama ta ringa yi, a hankali ya amsa mata ya maida kansa ya ajiye A hankali ta ringa takawa dan karasawa wajen da yake sai dai bata kai ga idasawa ba ya dago ya sauke idannuwansa a saman fuskarta wanda hakan ya saka ta ja da sauri ta tsaya tana jin gabanta na faduwa Me ya bata masa rai? Irin kallon iyakantarta da shi kennan Gabanta ne ya yi wata irin yankewa ya fadi, tsoro ta ji kan kar dai a je mahaifiyarsa ta fada masa cewa ita ta fada mata ta ji kamshin turaren da ba nasa ba a jikin rigarsa? Gannin ya koma ya kara kwontawa ya saka jin kafafuwanta sun fara yi mata rawa rawa A hankali ta juya ta koma falonsa ta zauna hankalinta tashe tana jiran fitowarsa ta ga idan zai amsa gaisuwarta?................... Kansa kawai ya dan girgiza ya maida ya ci gaba da jan carbinsa A ranar NAJEEBA bata fita saloon ba, sai washe gari wajen karfe goma Ta gama shiryawa cikin tsararan shirinta A yau riga da sket ta saka na atampa Bata daura dan kwalin atampar ba sai wani dan kwali ja irin takalmin kafarta da jakarta ta dan yafa a gefen kafadarta Hannunta dauke da agogo dan siriri yatsotsunta kuwa basu da zobe ko daya Kanshin turare take bazawa mai dadin gaske ga turaran wuta da ta turarawa kanta sosai take baza dadadan kamshi Ta zo tsakiyar gidansu ta hadu da yar kanwarta wace ita daya ce ta rage a gidan sauran du sun tafi makaranta masu aiki sun tafi aiki, itama dan karama ce Murmushi ta saki ta karasa wajen yarinyar ta duka ta dagota tanai mata wasa Yarinyar kuwa sai daria take tana dora kanta saman kirjin Najeebar Najeeba ta duba kitson kanta ta ce" heyi an mata kitson nan ya tsufa mu je saloon a tsefe shi a sake sabo Daga nesa da su kadan ta ji muryar matar babansu na fadin" kar ki daukan min y'ata ta saka ta ringa ramewa dan datin dake jin ki! Ajiye min yarinyata malama Dagowa ta yi tana kallonta Ta ga tana fadi ne tana nufota wato zata zo ta amshe yar Mikewa ta yi da sauri ta sungume yarinyar ta karasa wajen motarta wace ta sha wanki dan da sasafe dan saurayin mai gadin ya amshi kys dinta ya wanke mata ita tas domin Najeeba nada kyauta sosai hakan ya sa kowanensu ke son kyautata mata koda bata nema ba Cikin motar gidan gaba ta saka yarinyar ta rufe ta koma ta zauna itama ta rufe motar Sai da ta danne horn sannan ta tayar ta yi baya baya da matsiyacin gudu wanda take hango matar baban nasu na ihun ta bata y'arta aman ta tabe baki ta fita a gidan da baya baya Gashin kanta ta take birki ta nade shi dan ya fara damunta sakinsan da ta yi sannan ta dauki hanyarta tana tukin tana yiwa yarinyar wasa Cikin nutsuwa ta karasa kofar shagonta Sai dai irin motocin da ta gani ya sakata dan yin tsam tana bin su da kallo Tas ta gane motar dake gaba ba motar kowa bane face ta matar Ambasador domin motar tare ya siya masu ita tata ta siyar dan su yaya ba zasu barta hawa motar kato haka kawai ba Dama sun taba message da junna inda take mata kashedin bin mijinta har tana kiranta cewa" an koro su daga kasarsu sun zo sun samu arziki sunna bibiyar mazan mutane, abin ai gado ne ga kanwar ubanta ta amshe sarki kiri kiri , ga mamanta ta tafi yawon neman kudi ko karuwanci ba! Hannayenta ta hade ta dan murza su, ta dauko turaranta ta kara fesawa ta kara gyara girarta sannan ta dauko kanwarta tana kara yi mata wasa ta fito daga motar aman bata dauko jakarta ba dan kayan hannunta sun mata yawa ........cikin nutsuwa take takawa har ta karasa kofar shagon................. Hannunta ta saka ta kwonkwasa dan a bude mata tana kara kallon kofar shagon ta ga tsaftarsa ta yi mata sosai Sai da ta yi murmushin dama ke nake jira ta kalli kawayenta ta nuna masu da bakinta sannan ta mike bugudum bugudum bugudum ta karaso wajen kofar ta dora hannunta ta............ [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 14 Bude matan da aka yi ya sakata saka kafarta da bismillah ta shiga shagon Sai dai bata kai ga idasa shiga ba ta ji wata murya sama sama ana tafa hannu aka ce" oyah, gata fa ta shigo, karuwar yar dake zuwa nan ta amshe kudadenku kuma ta raba ku da mazajenku Da sauri ta dube ta Duba irin na tsanaki nan ta tabatarwa kanta cewa wannan itane matar Ambasador din Ko karya na yi maki? Idan karya na yi maki ai sai ki musa ko kunya bakya ji yarinya karama da ke kin mayar da kanki karuwa kina bibiyar mazajenmu Yarinyar dake hannunta ta kara rikewa dan kar ta fadi tana kallon matar Zata iya rantsewa idan auren kauye ne matar nan tana iya nakudota ta haifota ba tare da an talafa mata ba Gata ta wani zama wata kantamemiyar mace ba wani waje dake rabe ko'ina a hade yake Gaske, shi ya sa mijinta ke haukacewa ko wani dan karamin tabara nata Fuskarta ta dan yatsine ta juya a hankali ta nufi ciki Mayafinta ta warto tana fadin" ke dan ubanki ki tsaya min a nan dan ko uban wa nake magana da shi bai isa shigewa ba sai na gama! Zuwa na yi ki fada min karuwancin naki a kan mijina zai tsaya ne ko me? Da sauri Najeeba ta karasa saka kanwarta ciki ta zaunar da ita ta mika mata wayarta wace bata da wani code ta fito tana janyo kofar cikin Mai aikinta babar ce ke ta raraba ido hannayenta saman kanta , fadi take" Hajia dama abinda ya kawo ki kennan? Ki yiwa girman Allah ki yi tafiarki kar ki rikita mana wajen aikinmu dan mu aiki muka fito Wata bagwariya da ake dinkawa atash kuwa ta yi saurin fadin" jesus, wannan yalinya da gaske ne? NAJEEBA ta dubeta, ta kuma kallon mutanen cikin shagon Kafadunta ta daga ta karasa da karfi ta warce mayafinta dake hannun matar ta ce" eh haka ne, ni karuwarsa ne, nice nan mai haukata maki miji ya je gida yana ihun kiran sunnan NAJEEBA NAJEEBA NAJEEBA a tare da ke! Dan ubanki karya kike, ke nan har mace ce? Ina wajen da zai rike har ya haukata shi? Ta fada a zabure Najeeba ta yi far da idannuwanta ta ce" meye kuwa ba zai rike ya kasa zaburar da shi ba tunda har yake iya banbance sama da kasa, teba da mazaunai? Ke ko jiya a wajena ya raba dare mijinki! Tabas a jiyan kuwa ya raba daren domin shi dama mutun ne mai yawan yawace yawace ga cika dare a waje, ga uwa uba a jiyan ya nemi Najeebar kamar me dan ya jima wajen shagonta bai sameta Najeeba ta dora da fadin" kin ga kuwa idan har baka iya kiwo ba, baka iya daure akuyarka ba dole ta fita waje ta ci! Hakan na nufin ba'a karuwa daya shima mijin naki namijin karuwi ne Abin da ake busar da gashi na kusa da ita ta kinkima wanda ke jikin abin jonawa a jone ta shanmaci NAJEEBA ta tafka mata shi daga gefenta wanda hakan ya sakata yin tangal tangal ta je ta daki garun dake kusa da ita Ta saurin balaki ta sabule takalman kafarta ta rike guda a hannunta da yake mai dan tsini ne kadan Da gudu ta karasa ta shigi matarnan da wani irin masifa tana doka mata du inda hannunta ya kai Kawayenta da suka rakota basu shiga fadan ba sai rabawa da suke, wanda hakan ya fi yiwa Najeeba ciwo gannin mace kusan hudu ta ririketa Su dukansu kallonsu take , sai a lokacin ta gama fahimtar tare suke mace kusan shida dan hudun sun riketa sunna bata hakuri biyun kuwa sun rike Hajiar sunna tausarta sunna fadin ya isa hakannan ta bari haka NAJEEBA ta ringa kokowar kwacewa aman du sun saka mundula mundulan hannayensu sun ririketa hakan ya sakata sakin wani irin kukan takaici A rayuwarta ta tsani tana fada a riketa, ta fi so a barta idan akai mata jina jina zara rabu dan kanta, ta fi so a barta ta ji jiki ko wanda suke yi ya ji jiki da haka raini zai rabu tsakaninsu Tana ihun kukan take fadin" ku sake ni! Ku sake ni! Idan baku sake ni ba na rantse da wanda raina yake hannunsa kuma kun jazawa kanku fitinar da ba zaku iya dauka ba Dan walahil azim ko mazajenku kushewa ne a tsufa, ko a masalaci suke kwana tsabar musulunci ya ratsa su, ko mata maza ne sai na birkita lisafinsu, sai na rikita maku gidajen aurenku, sai na fitine ku ba dare ba rana! Walahi sai na koyawa mazajenku cika dare, sai n koya masu bibiyar mata! Sai Na gwada maku bariki iyawa ce! Dayarsu ta saketa da sauri cike da tsoron kalamanta Wada ke kusanta ta ce" ke ki riketa mata idan muka saketa zata koma wajen hajia ne kin ga fa ta fasa mata goshinta sai jinni yake Kanta ta girgiza da sauri ta ce" to ku saketa hakanan mana zaku kama riketa mu tafi, kunna fa jin abinda take fada kuma ni na san wacece ita dan haka ba ruwana Wa'inda ke tare da hajiar ma sun tsorata da hakan, dan haka suka ringa turata waje sunna fadin kawai ta kai kara gidan sarki a mata tsakani da ita da mijinta kar ta rabata da mijinta haka kawai da y'ayansu Da wannan shawarar suka samu suka tura hajiar waje Sai da ta fita sauran suka saketa Da wani irin masifa ta ringa wawurarsu tana jufansu hakan ya sa du suka fice a guje Dukewa ta yi wajen tana kukan takaicin bata yiwa hajiar yanda ta so yi mata ba, Da gudu yarinyarta ta duka tana fadin" aunty, dan Allah ki yi hakuri, walahi talahi ban san abinda ya kawosu wajen nan kennan ba, ki yafe mini ki daina kukan nan Dago dubanta ta yi tana kallonta Idannuwanta ta lumshe wasu hawayen suka zubo a hankali ta ce" kin ga wadincen? Baki dayansu sai na saka su a uku! Yanda suka tozartani bayan bani da laifi ko? Sai na tozartasu daidai da laifinsu! Mikewa ta yi tana goge fuskarta da tissu tana gannin yanda ake ta bata hakuri Murmushi ta yi tana kallon mutanen dake zazaune ana ta masu aiki aman an dakata sanadiyar fadan ta ce" saloon dina a bude yake daga safe har zuwa dare Zakunna zuwa nan ne muna amshe kudadenku muna gyara maku abinda ya dace mu gyara! Inaga kun san cewa mace sai da gyara ko? Ta kara lumshe idannuwanta ta ce" irin haka ke kara min gwuiwar fitowa daga gidanmu Idan bana samun masu jirana dan su fada min cewa lale ni din wata kwaro ce mai bada wuta a duniya da ba inda zan je sai na boye a daka Murmushi ta yi tana kara fadin" tawa sallon daukakar kennan kwacewa du wace ta yiwa mijinta rikon sakainar kashi da wace bata tashi tsakiyar dare tana adu'ar Allah kar ya hada mijinta d aalshe money idan dai ba matar aurensa bace Wata yar daria ta yi tana dage gira ta furta" du Alhajin da ya saki bakin aljihu zan kwasa ne! Ihu ihu saloon din ya kwasa ita kuwa ta juya ta shige ciki ranta du a bace tana jin haushin irin yanda bata wanwanke fuskar banzar matar nan ba Zama ta yi kusa da kanwarta ta janyota ta shiga tsefe mata kanta da dabara dan kar yarinyar ta yi kuka, tana tsefe mata tana mata cakulkuli nan ta samu ta ji sanyi a ranta sakamakon wasan da ta ringa yi da kanwarta Aiyukansu suka ci gaba da yi, duda a darare suke aman sun san da zata yi fushi da su nan take zata yi shi ne Itama cikin nutsuwa ta gama gyara kan kanwarta ta yarfa mata kannanun kitso ta saka mata tsakiya sukai kyau sosai a kanta ta shinfideta sannan ta saka a kawo mata abinci Kanta ta fita suka wanke mata tas ta shiga wajen busar da gashi Bayan ta gama ta zauna babar yarinyarta ta shiga yi mata wani irin kitso manya manya kwara hudu kawai, wanda ake yinsa kamar zane ya tafi baki daya baya Da yawan lokuta an fi yinsa da atash, Kasancewar tana da gashi sosai sai ake mata da gashinta hakan ya saka kitson ya yi tsayi ya yi tudu sannan ya yi wani irin kyau mai tsarin gaske tamkar ka kwace ka dora saman kanka Tana gama yi mata ta je ta zauna ta shiga gyara kwontacen gashin dake gaban goshinta tana nanade shi tana gyara shi da gel, a haka har gefe da gefen fuskarta ta gyara shi sosai Gashin ido ta fitar da wani sabon kala wanda ya fi zama natural, ga tsadar gaske da yake da shi Zama ta yi cikin nutsuwa ta saka abinta tana kallon yanda yake a idannuwanta Wata budurwa mai ji da kanta ce ke kallonta tun dazun, ita kanta ta lura da kallon sai ta share dan ba magana ta mata ba gashi kana ganninta zaka gane irin yan matan nan ne masu jiji da kansun nan Sai da ta gama ta dauki jan baki a cikin kayan mak up din ta shafa kalar lebenta ta juyo Wauh budurwar ta fada a lokacin da bata shirya ba tana kallon Najeeba Murmushi ta sakar mata ta mike ta mika mata hannu Itama hannun ta bata suka gaisa kafin ta dan sakar mata murmushi Budurwar ta ce" kina da kyau sosai, na yaba Wani dan murmushin NAJEEBA ta yi mata tana kallon kafarta Irin sarkar da ta gani da kuma zobe a yatsarta ya shaida mata ko wacece ita Dan rabata ta yi kusa da kunnenta kasa kasa ta ce" sorry, na haramta bin mata Budurwar kadai ta ji sai ita da ta fada , tana fada ta shige ciki ta daura alwallah ta gabatar da salar la'asar sannan ta ci gaba da zama da carbinta irin na hannun nan tana dan dannawa a hankali a hankali Sai da dare ya yi ta dauki kanwarta, ta gama hada kan kudaden da aka samu a ranar ta hada da takardar gidan wuta da ruwa da aka kawo masu ta salami sauran baki daya sannan ta rufe ta yi adu'o'i ta totofa sannan ta tayar da motarta ta nufi gida A kofar dakin mamanta ta sauketa tana mata byby, yarinyar ta ringa nokewa ba zata je ba dan ba karamin dadi ta ci a wajen Najeebar ba ga wasan da suka yi ta yi na goyo a dakin ga ta bata wayarta ta yi ta dannawa Daukan yarinyar ta yi ta nufi bamgarensu da ita dan sam ta ki ta shiga wajen mamanta Sunna shiga ta yi turus sakamakon gannin yayunta du sunna tsaitsaye da alama ita akae jira Yayanta ne da fada fada ya ce" daga gidan ubanwa kike Najeeba? Da mamaki take kallonsa ta ce" yaya, daga saloon nake mana ina zan je ni kuwa yau? Ummulkhair ta ja tsaki ta ce" a saloon din naki ne kuka yi fada yau? Gashi har an kai kararki gidan sarki ga samaci an kawo wai ke kam me ke yawo a cikin kwakwaluwarki na masifa ne? Me ya hada ki fada da matar ambasador? Gaban goshinta ta dafe a lokacin da Bilkissu ke fadin" aunty, me yasa kika tafi da Nusaiba kin ga mamanta ta yi ta zage zage da fada tana fadin zaki lalata mata yarinya har a gaban abih NAJEEBA ta ringa gyada kanta a hankali ta ce" inaga sai na sha magannin baki yaya, ka ji fa kowa ni na masa laifi yau harda kai? Yaya to ka san me ta min ne? Koma me ta maki sai ki duba yannayin da Anmy ke ciki, gashi shara'ar karfe hudu za'ai maku da wahala ace sarki baya nan! So kike a kara zuwa a fada mata cewa gaki cen yauma wata ta kawo kararki? Ke bakya tsoron kur'anin da ake saka maki ya lalata ki ne? Ina dalili wai ke kamar yar agunla? Bani y'ata! Bani y'ata Kuma daga yau kar ki kuma daukan min y'ata ja fada maki, haka kawai kin fi karfin uban da ya haife ki ki koyawa y'ata irin fitintinun ki? Tana fada tana warce Nusaiba dake hannun Najeeba Najeeba ta sakar mata yar, tana kallonta Zahrau ta ce" subahannalah, ke kuwa meye hadinki da shiga tsakaninmu da yar uwarmu? Kin taba gannin mun sakota a cikin matsalarmu da ke? Dan Allah ki daina zagar mana yar uwarmu, yau koda Najeeba yanda kike fadi ne ai bai dace ki ringa zaginta haka ba Kema fa macen kika haifa, kuma kema mace ce, bale kanwata ba yar iska bace walahi, ki fita a harkar shiga tsakaninmu da Nusaiba, Najeeba ba zata taba cutar da Nusaiba ba, na san ko baki daya mun mutu koda dako ne Najeeba zata yi ta rike kanwarta dan Allah ki shafa mana lafia hakannan mana kema? Sai da ta harareta sama da kasa ta yi daria irin ta wulakancin nan ta ce" wai kililin kasau macijin kumba Wace ake kawo sadakinta ana fardewa ne zata nemi ta bani shawara? Munanan halayanki sun hana maki samun mijin aure kina wani kumbiya kumbiya ke ga ta kirkinsu ko? To bari ki ji, a tafin hannuna kuke baki dayanku kuma ma rantse maku baku isa ku raba ni da gidan nan ba Ko a irin yanda na fi sauran iyayenku jimawa da mutumen nan kun san ya mace a so na Matar ubanku nake dan haka dole a kira ni mama Ummukulsum ta budi baki zata yi magana da sauri Dayabu ya dubeta duba irin na ido cikin ido Muryarsa har rawa take ya ce" Mardiya me yasa kike mana haka ne? Yaya kike tunanin cin riba idan har kika shiga tsakaninmu da yar uwarmu? Kin tabata zaki kai girmanta zaki iya tarota zaki iya rayuwa da ita ke daya kin iya mata? Tana zaro idannuwanta irin masifa na cinta ta ce" eh, ba abinda ya shafeku da y'ata ba domin baki dayanku kun kasance jinnin masifa karku koyawa y'ata Daria ya yi yana girgiza kai ya ce" haka ne, aman masifar inaga itama jinnin nata ne idan kika yi la'akari da ubanmu ne daya baki daya MARDIYA, ba dai NUSAIBA ba? Nusaiba dai ce ko? Ki rubuta ki ajiye daga yau daga kaina har zuwa wannan yar karamar dake kusana Yana nuna yar kanwarsu wace bata fi shekara shida ba Ya daki kirjinsa ya ce" Ni DAYABU MUTALAB idan har na isa da kannena daga bakin zahra har zuwa ummi na kankare mana wannan yarinyar daga cikinmu, yarki ko? Ki rubuta ki ajiye bamu isa mu tatse jinninta daga jikinmu ba aman mun isa mu kankareta daga cikinmu! Ko a titi, ko a cikin gida ba mu ba ita! Gaba daya yaren mutuwar tsaye suka yi sunna kallon irin yanda ran yayansu ya gama baci, Yana gama fada ya juya ya yi ciki ransa a matukar bace ya je ya gyara shinfidar kananu du ya kora su daki Manyan kansu silalewa kowace ta yi, zuciyarta da mugun rauni, me ya sa ta yi wannan aika aikar ne? Me ya sa sai da ta kai mutun mai hakuri da kare yan uwansa bango har ya aiwata haka yau? Ya fi su saukin hali da kawar da kai ko dan ya kasance mamiji? Aman a yau ta kaishi bango har haka ta faru Sun yi baci hankalinsu ba a kwonce ba Da sasafe ta rigayi kowa barin gidan ta zarce saloon Yau da kanta ta ringa yin aikace aikacen ta jirga zaman kujerun ta kakabe atach din dake tare ta wanwanke abubuwan wanke kafa ne, ta goge du wajen da ya yi dati Sai da ta yi aiki jina sannan ta zauna tana maida numfashi Da wuri wuri aka ringa cika wajen Nan ta shiga aikinta tana yi tana duba time Ba abinda ta ci sai da karfe uku ta yi ta bara masu ta shiga ciki Wanka ta yi mai tsari ta gyara jikinta tsaf ta fito sanye da wata abaya mai ruwan ja mai duhu da bakin hannu Dan kwalin abayar ta rataya a wuyanta ta fita ta shiga motarta Bata zame ko'ina ba sai fada Tana tsayawa ta saka gilas dinta fari dan siriri ta fito a motar Cirko cirko ta gansu su biyar a tsaye Ido ta zaro ta karasa wajensu a hankali ta ce" me ya kawo ku nan ku kuwa? Yaya DAYABU ya harareta ya ce" baki da kowa ne da zamu barki ki zo ke daya? Fuskarta ta sanyaya ta ce" eyah, na ga du na bata maku rai ne Zahrau ta kamo hannunta ta ce" mu je lokaci ya yi Najeeba, komai bata mana da zaki yi ba zamu barki ke daya gaban mutane dubu ba Wani sanyi da kaunarsu ce ta ji a ranta, nan suka rankaya da su ummu suka shiga bayan sun cicire takalmansu Tun da suka zauna yake yi mata mayatacen kallo Matarsa ta shiga bayanin a yi mata tsakani da mijinta ba ita ba shi Da sauri ya ce" aa, Allah ya taimaki waziri ni kam ba da yawuna ba, yarinyar nan ni na je na ce ina son ta, idanma laifin ne ni na yi mata dan haka bana cikin maganar a rabani da ita dan aurenta nake son yi! Gaba daya wajen ya yi tsit, sai Najeeba da ta kara sada kanta dan kunyar da take ji na irin kallonta du da ake Daga inda yake tsaye ta wajen tagar dakinsa yake hango komai Irin yanda ya fahimta yauma itace aka kawo kara Juyawa ya yi ya karasa wajen wayarsa karama ya danna kira, idan yana son jin abinda ake fada yake hakan sai a ajiye yana jin komai Zama ya yi ya yi zamansa na sarki ya bude litafi a hannunsa na hadisi yana dubawa still yana sauraron abinda ake fada Kansa kawai yake girgizawa a lokacin da ya ji ambasador na neman yin sakiyar da ba ruwa ta hanyar sakin matarsa har yana daga muryarsa cewa idan har ta yarda aka sakawa Najeeba wannan layar to ta tabata a bakin aurenta Karshe dai sai itane ta dawo bayar da hakuri cewa a bari kar a saka Abinda ya fi bashi takaici da haushi shine yarinyar ko A bata furta ba mutanen wajen ne ke ta hayaniyarsu tun dazu, ita ga isashiya Karshe dai kashewa ya yi a lokacin da ya ji shara'ar ta koma neman sasanci tsakanin matar ambasador da kuma Najeeba, inda aka shiga sasanta su da gindaya masu sharudan kar wace ta kuma tarban wata da neman fada, shi kuwa aka yi masa kwakwaran kashedin ya zama namiji ya tsawatarwa iyalinsa sannan idan auren Najeeba zai yi ya maida hankali ya aureta ba ya ringa neman fitina da girmansa ba Sai kusan magariba aka sake su Ranta kwata kwata a bace yake a yau din nan dan haka ta zarce wajen da ake siyar da shawarma Siya ta yi isashiya sannan ta karasa wajen hutun da takan je lokuta da dama Wajen bai cika mutane ba, idan ka ga mutane a wajen tabata irin manyan yan gayun nan ne Salaya ta shinfida ta gabatar da sallarta a wajen da hijab dinta dake cikin mota Haka ta yi ta isha ta shafa fatiya Mikewa ta yi ta adana komai ta dauko shawarmar ta zauna saman daya daga cikin kujerun wajen a lokacin duhu ya shigo sosai ta shiga harba yan kafafuwanta tana bude takardar shawarmar A hankali ta rike a hannunta tana fadin" Aikin banza! Aikin banza aikin wofi! Shirme shirme shirme kawai! Ta karashe tana murguda bakinta A hankali ya furta" ke da wa? Da sauri ta dago dubanta, sai dai bata idasa dagowa sosai ba gabanta ya fadi haka kawai ba tare da ta san dalili ba Wannan mutumen ne na ranar, wanda ya taimaketa ya fitar da ita Yauma wani irin turarensa ne ya fara yi mata salama kafin ta sauke dubanta saman jajayen lebunansa Irin yanda tsarin haliyar jikinsa take kuwa shi ya fi komai bata tsoro Haka kawai ta ji jikinta na yi mata wani yam yam yam dan irin yanda take gannin idannuwansa da girma ga kwali sai ta ji tsoron kar dai aje aljani ne? Bata idasa tunanin da take ba ya karasa saman kujerar dake daf da tata ya zauna yana jan dan karamin tsaki a cikin zuciyarsa yana mai dannar kansa cewa ka yi hakuri, ta hanyar nan ne kawai zaka iya cinma burinka! Ka yi hakuri. a fili kuwa sai ya furta" kema an kona maki zuciyar ne? Ya Allah ban san menya sa mata suke haka ba! Gaba daya sai ta ji kanta a takure, abincine fa zata ci ya wani sakota gaba, to wai wayema shi? Ina ruwansa da ita ne? Ita dake boyon cin abinci idan ba da yan uwanta bane sai anmy sai abih Haka kawai wani garjehen kato ya wani shiga yi mata bayanin da bata tambayeshi ba? Yanzu haka da budurwarsa ya yi fada, shirme! Shirme! Aikin banza kawai! Da yannayin tsiwa ta dube shi ta ce".... ...... Commetn comment na sis Ina jin dadin comment dinku, karo min zai karan karfin gwuiwa hajiyoyina😌😌 [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 15 Da yannayin tsiwar nan ta ce" ka sanni ne? Kwarai hakan ya bashi mamaki, ya matukar bashi mamaki, shi? Shine yau mace macenma wace ya fi rainawa take furta masa magana haka kai tsaye? Saurin kawar da hakan ya yi yana kirmiro murmushin da bai yi ba baki daya wunin yau ya miko mata hannu irin su gaisa din nan yana fadin" je suis desoler ( i'm sorry), ban gabatar maki da kaina ba, FARID ELHAJ BASHIR by name, ni dan Abuja ne ina shigowa garin nan ne dan kawowa yayana ziyara Elhaj Muctar Garba mai gold, ni matukin jirgi ne sannan dan kasuwa ne Du wannan jawaban da ya yi Najeeba ta yi sakalau da abincinta a hannunta tana kallonsa Tambayar da take yiwa kanta shine, to ita ina ruwanta ko tambayarsa ta yi ne? A hankali ta bi hannun nasa da ya miko mata yana nufin su gaisa ko me? Wani sakaran murmushi ta dan sakar masa ta maida hankalinta kan ledarta ta dan duka ta dauke sannan ta mike tsam ta koma kujerar dake nesa da shi ta barshi nan sakaye da hannu baki da hanci bude cike da mamakinta Wai bata ganninsa sa kyau ne? Duba da irin shigar da ya yi tau ya yi shiga ne irin ta yaran atajiran nan, ya saka riga da wando na wani mahaukacin yadi wanda koda baka san yadi ba idan ka gansa a idannuwanka zaka gane ba fa na wasan yara bane Ya dora yar hula a kansa wace ta kara kashe kyansa ta fitar da dogon hancinsa zuwar sannan ta kara masa kima Rigar ba wata mai budadan hannu bace, dinkin ya kama hannayensa sosai har kana iya gane hannayen nan nasa bafa na wasa bane Sai ya ringa dan kara kallon kansa a kaikaice kafin ya yi gagawar karyata abinda yake tunani ta hanyar fadawa kansa kalamai kamar haka" ranta ne a bace, shi yasa ta ki baka hannu, idan ba wannan ba yarinyar dake jira a tayata ta karba a guje? Tuna hakan da ya yi ya saka shi kara baiwa kansa hakuri ya mike cimak ya koma kusa da ita, wannan karon face dinta ya zauna yana dubanta ya ce" i'm sorry plz Na bata maki rai ne? Nima ina cikin damuwa ne shi yasa kika ga ina yi maki magana haka sannan kamar na taba ganninki Sai kuma ya dan zaro ido ya ce" oh yes, ke ce, ranar nan na fitar daga stade kun je ke da saurayinki nah? Tsatsareshi ta yi da ido ga abincinta ta cira ta fara taunawa hakan ya saka ta kasa ci gaba da taunawa sai kawai take kallonsa Ko maye ne? Abinda ta tambayi kanta Idan ba raini ba shi a nan bai gane ni ba sai yanzu? Ta kuma tambayar kanta Sai da ta juyar da kanta ta labe fuskarta ta karasa taune abin bakinta sannan ta juyo tana dubansa ta ce" aman bawan Allah fisabililahi me na yi maka ne? Ka dai san tunda na baro gidanmu na zo nan kadaicewa nake da bukata kuma shikenan sai ka shiga zayano mon magangannun da ya shafeka? To waima an rubuta a goshina cewa ga NAJEEBA maganin damuwarka ne? Plz ka girma ka je ka iya da matsalar budurwarka haka kawai ka wani matsa min , to ni ba ni ka ganni a inda kake tunanin ka ganni ba Tana gama fada ta mike ta bara masa ledar a nan ta yi gaba da sauri ta karasa wajen motarta tana jan tsaki ta fada ta rufe ta tayar ta warceta da gudu gudu ra bar wajen Zuwa wannan lokacin har sai da ya talabi habarsa dan mamaki Wato ita bata tsoro ga tashen iskanci ko? Bata tsoron ko shi wani mugu ne ya fafalawa fuskar nan tata mari ta zo ta saka abin idannuwan nan dake mayar da ita tamkar wata aljannah ta tata masa rashin mutunci ta tafi Kansa ya girgiza ya kai dubansa wajen ledar Dauka ya yi ya buda ya ciro abinda ke ciki Jujuya abin ya ringa yi kafin a fili ya furta" da na halal din ko da na haram din aka siye ku? Mayarwa ya yi ya ajiye a nan ya mike yana tafe kamar mai jin tsoron taka kasar ya bi ta cikin duhun da ya ratso ya shigo wajen yana mai ayanna" sanu sanu dai bata hanna zuwa, zaki yi bayanni ne daga bakin lokacin da na kama ki da laifinki, na rantse maki sai na fitar da ke waje zan hukunta ki a wajen da ba wada zan iya kallo na daga maki kafa marar mutunci kawai! ....................................... Hotunnan y'an matan da aka turo masa ne yake bi ta compte professional dinsa A gajiye yake tilis, ga kallon hotunnan da yake yana son a yau a yau din nan sai ya fitar da yarinyar da za'a kawo masa a matsayin mace ta biyu gidansa Yana son kara auren nan ba yau ba sai gashi da banzarsa ta buda masa hanyar yi Ya yi hayaniya mai yawan gaske hakan ya hadasa masa da gajiya mai yawa sai kawai ya dawo juyawa a saman bed din yana sauke ajiyar zuciya Shi kam a kan hitunnan wasu yan mata uku ya tsaya Ba dan komai sai dan irin shigarsu ta kamala sannan iyayensu mutanen kirki ne Biyu y'ayan hausawa ne sak, dayan ce bafilatana Turawa wanda ya turo masa ya yi, kafin ya mayar da kansa har ya turo masa da message kamar haka" *Su duka ukun uban gidana?* Tambayar ya kurawa ido, su duka ukun? Sai ya ji wani abu na ce masa me zai hana ka dauke su su ukun? Idan ka yi hakan ka gama cikewa sai ka koma gefe ka karbi salon kowace Bai bashi amsa da gagawa ba, shi kuwa ya yi ta jiran amsar karshe shima ya bar wayar a kunne ya kasa kashewa dan gudun ya sauka a je ya turo amsar bayan ya gama salar asubah ya dawo bangarensa ya kwonta yana duba agogon dakinsa ya lumshe idannuwansa Irin yanda zinariya ke ta tsatsareshi da ido aman ta kasa tambayarsa abinda ta masa ke bashi mamaki Me ke damun kwakwaluwar yarinyar? Shin sarautar ce ko sakarci ne? Yakan cika da mamakin wasu abubuwan nata Tabas shi mutun ne mai son sauki a rayuwarsa bai san dalilin da ya saka mutane da yawa ke tunanin ya cika son zafi ciki kuwa harda abokiyar rayuwarsa wace ya dace ta fi kowa sanninsa da fadin halayansa Yana so ace matarsa ta san cewa shi mutun ne mai son shakuwa da mace Yana son ya gabatar da rayuwar aure irin yanda ma'aiki ya koyar Yana so koda bai cika komai daidai hakan ba ya kwatanta Ya so ace shi din mutun ne marar nauyi a kansa, da ya rantse abinda zai hana shi zuwa ga matarsa lalle baba abu ne Sun yi auren biyaya ga iyayensu da zinariya, ya sameta a matsayin cikakiyar budurwa, sai dai a kulun abinda yake nema ido rufe ya rasa shine kasancewarta irin matar da yake so Yana so idan ya fita ya bayar da umarni idan yana daka a umarceshi cikin kissar da shi kansa ba zai gane umartarsa aka yi ba Yana so tsakaninsa da matarsa idan da ido ta yi bayani ya fasara abinda take nufi koda a cikin duban mutane ne Yana so tsakaninsa da matarsa ace idan akoy wani abu mai sunna kirari to fa ta yi shi ne a lokacin da idan ta yi shi zai kara kaimin faranta mata ya farantawa kansa ya lula da su a cikin duniya mai dadin gaske Sai kawai aka samu matsala tasa matar takan kwashi kirari ne kamar wata jakadiyarsa a duk lokacin da suka hadu Shin sai ya koya mata ne ko sai ya karo auren ta ga yanda wata zata wakanar sannan itama ta dauki hannu? Murmushi ya yi yana adu'a dan samun hutu, ya gaji walahi yawan maganar nan ta jiya ba karamin gajiyar da shi ta yi ba hakan ya sa ya takaita maganarsa daga jiyan zuwa yau a wajen gaishe da mahaifiyarsa ta hanyar sirrinsa ne kawai ya budi baki ya yi wata maganar Bai waiwayi wayarsa ba sai da garin Allah ya waye sosai har kusan karfe goma sha biyu Yana gama daura agogonsa ya janyo wayar nasa Direct cikin message dinsu ya shiga ya rubuta" halayanta su zamo nata ne ita daya, ta kasance mai halayan dawissu Ina son wace ta san kanta Ina son wace ta rufe kanta A yanzu ka ware daya a cikinsu ka tabatar komai ya gama a yau dan ina so nan da kwana hudu a gama komai ba zan ja ba, ba zan yi wani gangami ba dan ba aurena ne na fari ba! Yana gama turawa ya zauna bakin bed dinsa yana jin wani haushi haushi Ya tabata bai isa ba, komai yanda zai kiyaye tara mutane sai sun taru an masa yawan magana da tsarewa Shi kuwa alkawari ya yiwa kansa sati ya baiwa kansa sai ya ajiye wata macen a saman bed dinsa wace zai raya sunnar ma'aiki da ita, Wace zata cike zargin zinariya, ta faranta ran Anmynsa ta hanyar bin umarninta, Ajiyar zuciya ya sauke duba da bata lokacinsa ne yake sannan ya mike ya koma dakin da yake hangen abubuwan dake wakana a masarautar Kansa kan daukan caji fiye da tunanin mai karatu Matsalolin cikin gidan marauta a gaban idannuwansa suke, da yawa sun fi karfin titsiye su tashi daya dole ta sannu yake binsu ya ruguje su, da yawa rainin hankali ne yakan yi kamar bai ji ba bai gani ba Shi dai a matsayinsa na sarki mafi yaro a wannan karni yana iya yinsa dan gannin yana kare wasu abubuwan Shi mutun ne mai son motsa jikinsa kamar me, motsa jiki a wajen da ba wanda zai zo kallonsa ko ya san shi waye hakan ya saka yake fita da mutun kwaya daya tak su je wani tafkeken filin LAKD ya bale a guje ya yi ta gudu son ransa Idan ya yi ya gama ya yi pompe mai yawan gaske sannan su je wajen da yake shan dadar iskar garin ya zauna ya saje da kowa ya sha iska ba tare da ya yi aboki ko budurwa ba Ya saba fitarsa ba yau ba, idan bai yi fitar sirrin nan ba tabata wani abu mai karfi ne ya hanna masa yin hakan...... Wannan kennan ............................................ Kallon sarkokin Abih yake daya bayan daya wa'inda Dayabu ya saka aka yi masa tun daga kansa har zuwa kannensa Irgawa ya yi ya kuma irgawa ya kalli DAYABUn, to ko ya manta su goma sha takwas ne? Sai abin ya so bashi dariya da ya ambaci hakan a zuciyarsa Me zai hanna shi mantawa kai kuwa? Ya kuma tambayar kansa Abih ya kuma daya sarkar ya kalle shi ya ce" to kaima sakawar zaka yi? Murmushi ya yiwa abih ya ce" hum Abih rigimar y'arka ce wai yo sai na saka mana kamar wani dan daudu ko wani dan duniya Daria Abihn nasa ya yo yana bin yan siraran sarkokin zinarin da kallo Tabas yana godewa Allah da samun baban d'a mai hankali da nutsuwa wanda yake iya yinsa dan gannin yana gyara irin barnar da shi ke aikatawa Koma meye dalilinsa na sakin mata bashi da kyau domin saki Allah ya halata shi aman shi kansa baya son sa Shin y'ayansa sunna jin haushinsa ko? Irin yanda yake korara matansa haka kawai Akoya matarsa da ya saka wace zai iya rantsewa bai kamata da laifin komai ba, ya saketa ne dan ya wayi gari da maganar cewa a kan me ita zai barta bayan ya rabu da iyayen sauran? Sai mahaifiyar NAJEEBA wace ta maka shi a kotu sai ya saketa Murmushi ya kuma yi yana kallonsa ya ce" yayansu ka manta ku goma sha takwas ne y'ayana na cikina? DAYABU ya dago ya kurawa fuskar Abih ido, a hankali ya ce" aa mu goma sha tara ne Abih Gabanta Abih ne ya yi wata irin yankewa ya fadi wanda hakan ya saka shi saurin zabura yana kallonsa Su goma sha tara ne? Ku goma sha tara ne? Ya maimaita masa da sauri ya dora da fadin" a ina ka samo ta cikon sha taran? Fuskarsa dai ya kuma kurewa da ido yanai masa kallon nan da ake fadin kai ka san na san da hakan Sai ya yi gagawar basarwa yana murmushi ya ce" Abih, na manta ne, wani sa'in fa garin magana har cewa na yi mu goma sha uku ne sai da zahrau ta yi ta min daria Wata biyayiyar ajiyar zuciiya uban ya sauke sai dai sak ya kasa sakin jikinsa su ci gaba da hirar kamar yanda suke a dazu Sarkokin ya kuma rikewa yana fadin" ina ta NUSAIBA? duban mahaifinsa ya yi ido cikin ido a karo na biyu ya buda bakinsa ya ce" ban yi da ita ba Uban ya tsare shi shima da ido, kamar yaya bai yi da ita ba? Amsar ba wata a boye take ba a bayanne take cewar bai yi da ita ba A kan me bai yi da itan ba? Mantawa ya yi ko yi ne bai yi da ita ba? Aa ai ba cewa ya yi ya manta ba, cewa ya yi sak bai yi da ita ba Sai ya ji wani shaku da tsoron son jin abinda ya saka yaron nasa na farko a rayuwa yin wani abin kyautatawa wa kannensa banda daya a ciki Hakan ya saka shi fadin" gaba kuke da mahaifiyarta har yanzu wanda ya shafeta ko wani abu mahaifiyarta ta yi maka ne? DAYABU ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi ya ce" Abih, ka san bamu taba zuwa muka kawo maka karar matarka ba Da yawa wasu matan ka sake su ne dan kawai idannuwanka sun kama wani abinda bai dace ba a kanmu Ban san girman laifukansu ya dame nata ya shanye ne? Ban san ita din lale gaskiyarta ne itace rayuwarka ba? Abinda na sani shine na gaji da sakin mata da kake, kuma bana so ka kuma sakin mace dan a yanzu na lura lalefa kanena sun taso har sun fara gabatar da mazajen aure wanda nake fatan idan sun shiga sai dai a fitar da gawarsu fita na har abada Abih abin zai yi matukar wahala sai dai ikon Allah kawai zai kubutar da su Shine nake so ka yi kokari ka yi zamanka da matarka , in sha Allah idan dai mune damuwar ba zamu kuma zama damuwa ba aman fa Abih muma a kiyaye namu rayuwar dan kai ka san cewa ba zan iya lamuncewa mutun shiga hakin yaran da nake yiwa kallon marayu Basu rayu da baban jigo na rayuwa ba wato uwa Hakan ya saka nake yi masu uzuri a rayuwar yau da kulun, hakan ya sa nake kara jin tausayinsu Abih kam ba amsarsa ya samu ba, sai dai gannin yaron nasa ya daure shi da jijiyoyin jikinsa sai kawai ya yi masa shiru bai kuma tofa komai ba aman ya kuduri niyar tambayar ita natar tasa dan ya tabata bafa zasu fada masa komai ba tunda har yayansu ya hana............................ Sarkokin ya mike da su ya nufi cikin dakansa DAYABU na zaune yana kallon ikon Allah, Abihnsa zai fito ya bashi sarkokin ko ba zai fito ba? Har ya kusan cin rabin awa karshe ya mike yana murmushi ya girgiza kai ya yi gaba dama ya yi hakan ne dan ya isar da sakon cewa ya cire y'arsa a cikinsu! Ihu ta saka bayan ta kashe kiran da suka gama da Anmy Da wata irin daria ta ce" jama'ar gidanku wannan karron ina gayya, ina gayya ne da kaina kuma sai na buga wasa a kofar gidan sarki Ummulkhair ta dago daga yankan akaifunta tana yiwa kanwar nata kallon anya Najeeba baki haukace ba kuwa? Najeeba ta ce" ke ke aunty, wallahi du jarabar da za'a yi sai na kirawo ANNABO MAWAKI ya kada min waka da orchestre na shiga na cashe domin kuwa *DUNKUM* zai kara aure inji Anky, kuma auren nan da kwana biyu ne taxe maza maza mu je wajen mai dinki ta tura sakwanninmu mu zabi kalar da muke so Zahrau ta fito da waya tana daria itama ta ce" haka fa sannan Anmynki ta ce kar ki yarda ki dauki dinkin da bai mata ba dan ba sakashi zaki yi ba! NAJEEBA ta waiwaya tana kallonta ta ce" wai kin san aurensa mai yake nufi? Hehehe, yana nufin za'a kawo wata yar rainin hankalin ta biyu wace zata ci min uwar wace ta raina halitar Allahn ta farko ta dane min kan banza ta daki bakin mai bakin shegun nan, zamu ga karyar zagi da takama za'a yiwa zinariya kishiya da gold🤣🤣🤣🤣 Hum a dai a slow najee [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 16 Hakan ne ta kasance abu na manya nan da nan abubuwa suka kankama cikin dan kankannin lokaci a wajen mutanen da suka iya aiki da lokacinsu Nan da nan mutanen da anmy ta ringa fadawa suka fara halara cikin masarauta Su Najeebama sun tare a gidan ne tun ana gobe daurin aure hakan ya sa gidan ya ringa yiwa Anmy dadi ga uwa uba irin yanda Najeebar ke ta yi masu kitso da kunshi cikin nutsuwa a daka Idonsa cikin nata ya ce" in sha Allah gobe za'a dauran aure ZINARIA Irin yanda maganar ta daketa ta sakata baki daya yin luuuuu zata kifa hakan ya saka shi yin taku biyu ya damki damtsen hannunta ya tareta a jikinsa ya yiwa bayanta mazauni a kirjinsa A hankali ya kuma fadin" ki daina yi min garage da yaron cikin nan, dan shine abinda zaki yi mafi ganganci a rayuwarki wato barar min da shi da gangan Tabas ta gama yarda cewa kwananta ne ya kare a wannan rana a irin wannan lokaci a tare da sarkinta Kukan da take rikewa ne ya samu damar kufce mata da karfin gaske har tana cicije lebunnanta Me ya sa? Me na yi? Me na gaza? Kyauna ya rage ne ko hasken fatana da ya saka aka min lakabi da zinaria ya disashe ne ya mai garina? Ta fada tana rike hannayensa baki daya ta kuma fadin" kar ka yi auren nan, idan ka yi na koma baya, idan ka yi ko a cikin kawayena na daina tinkahon kaf cikinmu nice bani da kishiya, idan ka yi min haka ko a masarautar AZ za'a kafa tarihin lamarin domin mahaifiyata ta jima kafin a yi mata kishiya kuma daga ota ta rantse ba kari! Kar ka min haka dan kishiya mafisa ce, balaki ce, Shin y'ar gidan wani sarki zaka aura? Wani sarki ne ya baka y'a? Wata gimbiya ce ta yi gigin hada aurenka da y'arta bayan ta san wada ke cikin gidanka? Ikon Allah shine abinda ya tsaya ganni a tare da Zinariya A yau sai yake gannin ta fi sako reputation dinta a kan gaba fiye da ainahin kishinsa da ya dace ace ta furta kalaman tana son sa tana kiahinsa tana kishin hada shinfida da shi Da karfi ya juyota sunna facinha din junna inda ta sada kanta kasa jikinta na bari tana mai ci gaba da kukan nan Ya so kwarai da gaske ya rarasheta koda kuwa itane silar karin auren nasa a yanzu Aman irin kalamanta sai suka nuna masa ita tana tunanin wani abu na ta isa ya jinkirta masa karin aure? Ashe har takamar mahaifiyarta kennan cewa wancenma da ta shigo da kyar ne kuma daga ita ba kari? Murmushi ya sakar mata daga cikin rawaninsa wanda rabonta da gannin fuskarsa kiri kiri tun randa ta shigo ya yi mata gargadi da idannuwansa A hankali ya furta" sai ki ce da du wanda ya yi maki tambayar yanda aka yi aka maki kishiya cewa *komai ai mai shudewa ne, ko ya bace bat ko a cenje shi* Yana gama fada ya juya yana tafe cike da kasaitarsa da mulki ya shige cen ciki domin dama a falonsa baba ne suka yi maganar Wani ihun kukan ta saki tana ta rike kanta mai sanye da hular alkyaba Da sauri ta juya dan komawa bangarenta, ya zama wajibi ta yi kiran mahaifiyarta ta sama mata mafita Baban abin takaicin auren gobe? Me ta masa? Shine abinda ta fi maimaitawa hankalinta ba a kwonce ba Ashe shine dalilin tarewar wadincen yan iskan yan uwan nasa a bangaren uwarsa ko? Shine dalilin zuwan mutane a yau din nan sosai gidan ko? Har ta fita tana takama ta bi ta gabansu ashe su daria suke mata sunna kallonta ne kawai??????? ?.................. Tana zuwa ta samu ta yi kiran mahaifiyarta tana kuka ta fada mata labarin da ya zama mumuna a wajensu Ranta bace ta daki gefen bed dinta ta ce" ke, ki nutsu, ki saki ranki a yi komai da ke Aman yanda na hakura mijina ya rabi wata y'ayana na haramta masu *ZINARIYA na rantse maki ba dai shi ya rabi wata ba in dai ina raye!* Da wadinnan kalaman ta samu jin dan sanyi a ranta sai dai cikin bacinta ta ringa jin mararta na kulewa, tana farkawa ta ganta cikin jinni, wanda dama an daure mahaifar ne dan kar ya zube tunda Aliyu ya rasu ta ringa dan zubar da jinnin nan Washe gari Abin da akai a kuraran lokaci sannan mai auren ya nuna ba zai yi taro ba aman bai hana cikar fada ba Sosai ake shagulgula an yanke sa dankara dankara wasu an shiga gashinsu wasu an yi madafa wajen masu aikin abinci aun dora su sai yi suke Masu busa na yi kamar ba da bakinsu suke busar ba, hakama masu doka gangar kidan barebari da makadan larabawa Kidan barebarin ya kasance kidan gado ne na mafi uawancin mutanen dake cikin garin damagaram *DAMAGRAM* Ko sunnan Damagram ya samo asali ne daga yaren bare bari wato barbarci hakama zinder dake nufin zindir Wajen ya dauke su, dangin mahaifinsa sun halarta du mata ne sai baza kamshin turaren wuta suke da takama da mulki...dama an san babarbare da dan karen isa koda kuwa ba jinnin sarauta bane Fararen barebari ne da suka samun farin a wajen mahaifiyarsu Allah ya jikan rai, mahaifinsu kuwa tsabar baki har wani shuni shuni yake Maakadan bare barin na yi ne da busa inda manyan mata masu ji da kansu ke dan takawa kadan su yiwa jinnnin sarautar kara Bangaren Anmy kuwa itama daga waje ne masu harkar larabawan ke yi wata mata ce ke wakar da makadanta sunna karkada wani abu yana yin cas cas cas Tun dazu a nan Najeeba ta fi auki, idan ta mike dan ta amsa kira ne da sauri ta dawo tana kallon dukan yanda suke yi Sai da ta gama fahimtar takun rawar nasu da irin yanda suke juya kugunsu da wani karfe a kugun nasu mai dauke da yan kannanun karafuna farare tass sunna kara yas yas yas ta mike ta zagaya wajen daya daga cikin marayan Da murna ta cire abin ta daura mata saman watsetsiyar shadarta da akaiwa wani irin zubi tun daga sama har kasa Na kafar ta amsa shima ta daura da kanta sannan ta kunce irin daurin dan kwalin da ta nada ta samu ta dora shi sama kadan ta dan soke shi ya bada kalar ture ka ga tsiya Ana gama dayar wakar aka saka wata, A hankali ta shiga karasowa wajen rawar tana kada iya kugunta banda saman jikinta tana dan juyi a hankali a hankali sannan na kafar natama tana kadashi da dabara hannanenta su duka biyu tana wasa da su ta hanyar juya su tamkar na macijiya tana wasa da su sak irin rawar kwararun larabawan nan Gaba daya wajen ya hautsine da buda da daria , Ido Zahrau ta zaro cike da mamaki tana kallonta, Bilkissu kuwa ta shige da gudu itama tama biye da yayarta sunna yi tare abin dai ba'a cewa komai Da sauri Anmy ta mike da alkyabar jikinta ta shiga takowa cikin nutsuwarta ta fito dan gannin da gaske ne abinda abinda Rukayya ta fada cewar ai ga Najeeba ta shige filin rawar Ai kuwa itama sai da ta zaro ido dan rawar da take din bata san a ina yar ta koya ba, uwa uba ita din kanwar sarki ce, gashi sarkin yana cikin gidan yana falonsa , falon da yana iya hangen du abinda yake wakana ta nan ta droon din dake yawo yana daukan dukan rahoton wajen ko ta windows dinsa wanda tana fitowa droon din kuwa na daidai ita Ajiyar zuciya ta sauke gannin gaba daya mawakiyar ta nufota tana ta kodata da larabci hakan ya saka har wani yam yam take ji Abin fa ya karkato da hankula dan harta kannen mahaifinsa sun maido hankalinsu, wasu daria suke sunna tafi wasu kuwa cike sa takama sula cire kai sunna dan tabe baki irin abin ya basu haushin nan Yarinyar baiwar dake bin Anmy da jakarta ne ta bi bayanta a lokacin da ta nufi wajen kidan Ido ya kura a hankali daga kwoncen da yake yana biye da droon din daidai anmynsa dan shi har ga Allah baima ga abinda ke faruwa ba ya dai ga fitowarta ne Gannin tana nufar wajen kidan nan ya dan lumshe idannuwansa a ransa ya furta" anmy, me zaki je yi wajen nan ne? Bai karasa tunaninsa ba idannuwansa suka sauka a kanta Irin yanda take kada kugunta tana yiwa anmy murmushi gefenta kanwarta ce itama tana kokarin yin irin na yayar wato mai sunnan gimbiya Aubahannalah Shine abinda ya furta a fili a hankali Fuskarsa ne ya shiga hadewa yana mai bin abin da wani kakausan kallo kamar a gabansa take Tunaninsa Anmy zata janyota ne ta fitar da ita, sai ya ga ta yi mata magana a kunnenta kafin ta kalli yarinyar dake rike da jakarta Buda jakar yarinyar ta yi ta duka sosai gaban Anmy Anmy ta saka hannunta ta dibo wani irin damin kudi dami har hudu masu aku ta dora saman kan NAJEEBA mai dauke da dan kwalin nan Bata gama hautsina wajen ba sai da ta ciro sarkar zinari ta dora sama Ai kuwa mawakiyar nan me zata yi banda kara kwarin muryarta da rangada guda sannan suka duka Najeeba ta sauke masu karinsu Hannunta Anmy ta riko suka fice a hankali suka fita baki daya Sunna fita ya kuma binsu da droon din Anmy ta juyo ta kalli abin Yar karamar yatsarta ta nuna ta ce" kin kyauta Najeeba, kin san sarai yayanku ya tsani rawa ko? Shine yau kika cashe a gabansa domin wannan abin da kike ganni yana nufin a hannunsa abin sarafashi yake Wani mukut ta yi da yawun bakinta ta matsa kusa da Anmy ta rage muryarta ta ce" Anmy ai kina nan ba zaki bari a min komai ba, kuma anmy alkawari ne na yi idan zai kara aure sai na yi rawa ni so na yi fa na kirawo Annabo Gaba daya ya zaro ido domin baki daya wani motsi da magana idan kana son ji zaka iya dannawa ka ji hakan ya saka shi dannawar dan jin da me zara kare kanta sai ya ji ashe ita so ta yi ta dauko makadin nan dake kade kade a cikin garin ta kawo shi wannan gida na alfarma ya kada mata me? Sai kawai ya ji yana sakin wani kakausan murmushi yana girgiza kansa Shi kadai ya san da abinda zai yi masu daga ita har makadan sai kamaninsu sun sauya Anmy ta ringa gyada kanta tana kallon yar tata A hankali ta ce" Najeeba, maza zo cenza kayan nan ku je tare da yan uwanki ku yiwa amaryar kwaliya domin daga an shiga salar magariba za'a shigo da ita ta baya Kanta ta gyada ta yi gaba abinta Sai da sukai salar la'asar suka fito su hudu reras cikin wani irin danyen lesh kowace da kalar da ta dauki fatarta Wasu tsadadun alkyaba ne suka dora sama wanda dole ka kale su ka kuma kallo sannan ka yaba koda baka shirya hakan ba Bayan wata dankareriyar mota fara kar suka shiga su dukansu Direba ne gaba da wani bajimin dogari zaune fuskar nan tasa uwa an zagi mamansa sam ba fara'a Da wani irin gudu yake ratsa manyan titunnan garin fit fit fit Kasancewar motar da number gidan sarki ne ya saka sojojin dake hanya da polisai sam basa gigin tsayar da ita duda ba sarkin ne a ciki ba A hankali NAJEEBA ta ce" *kudi* masu gidan rana kuna gannin mutannen mu da su sai kallo basa tsayar da motar dan tambayar takarda Ummulkhair ta yi murmushi ta ce" aa Najeeba, sarauta dai Kudi ai kowama yana iya yinsa Sarauta kuwa gado ce Ko baran gidan sarki wani ne a cikin garin sarki bale ka shiga wannan mota? Inaga ko kwaya ka dauko zaka samu hanyar shiga da ita je ba tare da an san ko meye a motar ba Najeeba ta lumshe idannuwanta ta furta" *Sarauta* wani sa'in sai ma ga sarauta ta cika izgili Kun ga cewa a fada aka daura auren nan? Maimakun gidan su budurwar tasa? Zahrau ta yi murmushi tana kallonta ta ce" baba da karamin kennan Najeeba ta yatsina fuskarta ta ce" ai shi girma ko wani iri ne hawa yake yana sauka Akoy wajen da zaki ga girman zai samu yaya wanda dole zai sada Idan har sarki nada zuciya a cikin kirjinsa.......to tabas zai saurari kidan wace ke motsa masa ita Ummukulsum dake kallon wajen da suka tsaya ne ta yi murmushi duba da irin wajen da sarki ya dauko mace Tabas ta yarda a yanzu cewa sarkinsu baya mu'amalantarka dan kana mai kudi ko talaka Yana mu'amalantar kowa ne bisa tsarin da ya zo masa Ashe da wata motar a bayansu wace ke dauke da wasu yan matan bayi su su shida Irin kayan gidan sarautar ne a jikinsu sun yi kwaliya daidai misali Hannayensu dauke da sako du suka layu a bayan su NAJEEBA A hankali suka ringa takawa inda Dogarin nan ke ta fama wajen ture yaren dake son taba su Najeeba, wajen kaiwa du wani wanda ya janyo waya dan yi masu hoto ba tare da sun amince da hakan ba Gannin gidan cike da jama'a ya saka dogarin sada kansa da neman alfarmar su koma mota ya fitar da mutanen ciki Da sauri Zahrau ta girgiza masa kai a fili ta furta" zamu cudu da su dan bama kyamatarsu Murmushi Najeeba ta sakar mata da ido ta jinjina mata Duda hakan sai da ya fara shiga ya shela cewa a bada hanya kannen mai martaba na tafe Sannan ya dawo da sauri ya koma gefensu da zabgegoyar bulaliyarsa a hannunsa yana kuma sama masu hanya sunna ratsawa a hankali a hankali Kallo fa ana binsu da shi gaba daya sun mimike sunna faman yi masu sannu Wani daki aka nufa da su wanda suke tunanin a ciki amaryar take Zaune take da zumbulelen hijab dinta da kawayenta su hudu Ba kujeru a dakin sai tabarma su kansu sunna zazaune ne saman wata yar katifa wace take ta kanninta domin dakin kanninta ne Kanta a sade yake tana jin gabanta na faduwa cike da tsoron dago da kanta dan gannin kannen mijin nata Har yanzu ta kasa gaskata cewa ita Bintu itace ta zama matar mai damagaram Zata iya rantsewa cewa bata taba gannin fuskarsa ba ko a hoto, haka kuma idan dai ta hange shi to sun fita kallon hawan sarki ne da yake yi ana gobe sallah wanda ke shaidawa al'umar garin cewa sallah ta kama a washe gari ne Takan hangi hannunsa daya tak dake rike da igiyar dokinsa dayan kuwa a cikin alkyabarsa Farin hannun wanda ke dauke da wasu irin jijiyoyin sai idannuwansa dake dauke da kwali wa'inda idan ya juyo yana mai bin jama'ar garinsa da kallo sannan yana dan amsa gaisuwarsu da ihun kiran sarkin da suke sunna biye da tawagar Wai yau ita Bintu yar gidan malan sulaiman itane Allah ya yi zata tare a gidan sarki? Ko a baiwa bata taba hasaso kanta ba Hakan ya hadasa mata rawar jiki cike da tsoron kannensama kafin a kai kansa Tana cike da zulumi da tsoron matarsa da aka yi tataki a jiya aka zo aka baiwa iyayenta labarin wacece Zinaria Ta san cewa ita tana kasa da ita ne, ita talakarta ce, dan haka zata nemi masalaha da ita tun kafin ta gagari zama a damagram Daburcewa yan matan suka yi wata na faman bara ta samo kujeru, wara na kallon abin shansu da cinsu da baki daya suka kare saura kadan kadan dan sun yi taro kamar me duda a kure lokacin ya zo ko anko basu samu sun yi ba Da sauro dayar ta ce" bara na je shagon kalamu na samo jus Da kallo Najeeba ta bita har ta fita Kujeru ne dogarin nan ya ja daga kofa ya yi salama yana rike da su Bashi da hurumin shiga wajen da matar sarki take kai tsaye hakan ya saka shi tsayawa daga kofa da kujerun da ya fita da gudu ya sauke mutane ya dauko Najeeba ta bi hannunsa da kallo Kujerun da alama zasu yi nauyi gashi itane karama a cikinsu Matsalar bata daukan abu mai nauyi gaskiya dan haka ta juya ta koma cikin dakin da du suka bubude windows din dakunnan ta kakabe tabarmar nan ta dube su da murmushi a fuskarta ta furta" bismillah Ba tare da wani damuwa ba yayun nata suka zazauna baki dayansu NAJEEBA kuwa ta kai dubanta wajen amaryar A hankali ta shiga takawa ta karasa kusa da bed din Baki baki ta zauna cikin nutsuwa ta saka hannunta ta dago habarta wanda hakan ya saka baki dayansu jin gabansu ya fadi Ita Najeeba gabanta ya fadi ne a kan dalilin da bata sani ba Ita kuwa gabanta ya fadi ne jin wani irin lalausan hannu ya taba fuskarta wanda zata iya rantsewa hannun nan ya fi fuskarta laushi Da sauri ta sada kanta, yar karamar muryarta na rawa rawa ta ce" Barkanku da isowa Subahannalah Najeeba ta furta a kasan zuciyarta Bata so haka ba! Sam bata so haka ba! Ta yaya za'ayi wannan ta iya kwatar kanta a wajen Zinaria? Yarinyar kamaninta sam basu nuna yannayi na wada ta iya fada ko ta san tsatsaya a rayuwarta ba Yarinyar gaba dayanta yannayi na wata irin saliha ne a tatare da ita Haka kawai ta ji ranta na bacewa domin ita ba haka ta so ba, ta so ace wada ya auran nan ta ci ubam Zinariya a iya iskanci sai su ga ta iskanci Muryarta a sanyaye ta ce" yaya sunnan ki? Bintu ta kara sada kanta ta ce" sunna na Bintu Najeeba ta gyada kanta ta kai dubanta wajen kawayen nata Su kansu basa yannayi da yan iska Aman a kan me zai tashi ya wani dauko saliha haka? Wannan ai wulakanci ne salon banzar matarsa ta wulakanta yar mutane? Cikin nutsuwa Najeeba ta ce" ku dakata daga kofa, lokaci na tafia zamu kimtsa gimbiya Gaba daya suka yi waje bayan sun risina sun kara gaishe su Tabatarwar da suka yi cewa ta yi wanka mahaifiyarta na zaune tana kallo Najeeba ta buda akwatinta na kayan mak up Cikin nutsuwa ta shiga gabatar da aikinta cikin wata irin kwarewa wace a dan kankannin lokaci yar budurwar ta kara wani irin fresh da ita ta kara wani irin kyau hancinta ya fito zuwat sa shi yana wani irin sheki Gaba daya yarinyar kanta ce mai kyau, wani irin nutsatsen kyau mai birgewa Turaran wuta suka shiga yi mata ita kanta kafin su dora kayan da suka zo da su suka shiga turare mata su baki daya Mahaifiyarta na rike da turaren ruwan da suka bata concentrer mai wani irin dadi tana shafa mata lungu lungu na jikinta Daidai da pant dinta sai da suka turara mata sannan suka bata baya ta saka sabuwar bra din da pant din Taimaka mata suka yi wajen suturta mata jikinta da suturar da aka zo mata da ita wani farin lesh ne mai wani irin laushi Dinkin ya karbi Bintu sosai Nan Najeeba ta kuma zaunawa da agraf dinta tana kashe mata daurin dan kwali tana dantse shi yanda zai zauna Dole yarnan ta birgeka Saima da suka rufa mata alkyabarta mai dauke da wani irin ado tamkar dawisu da ta kalli kanta a madubi sai kawai ta fashe da kuka ta fada jikin mahaifiyarta tana jin gaban kirjinta na dokawa Ashe zata ga irin wannan daukaka daga Allah kafin ta mutu? Mahaifiyarta na mata murmushi ta rasa inda zara ajiyeta domin sai ta ga katifar nan ba zata zaunu da alkyabar nan ba Zahrau ta kamata tana murmushi itama ta zaunar da ita suka sakata tsakiya suka kashe hoto nan suka fito reras da su tamkar ka sace su ka gudu Sakwanin aka ringa ajiyewa kala daban daban kafin su yi masu salama a lokacin har an shiga salar magariba suka fito Tuni kuma motoci sun fara layuwa dan daukan amaryar mota hudu ce kawai dan ba'a so a ga shigarta ta kofar baya idan ya so daga baya sai a kawo mutane Su dai daukansu ya yi ya maida su fada Sunna fita Najeeba ta tserewarta dan tana son zuwa ta shaki iskar duniya ta ji sanyi na ratsa mata jikinta Motar yaya Dayabu ta shiga ta tayar abinta ta tafi siyan ice cream Zuwa lokacin da ta nufi wajen hutunta wanda rabonta da wajen yau kwana hudu kennan tuni an kira isha Da piyawatanta a mota da kuma abin sallah Tana sauka daga motar ta dauki piyawatan Gefe ta koma ta daura alwalarta sannan ta dawo cikin motar ta dauko salayarsa ta dauko alkyabarta A nan ta shinfida cikin nutsuwa ta tayar da sallarta Sai da ta gama baki daya sannan ta mike ta mayar cikin motar ta cire alkyabar ta dauko ledar ice cream dinta da wayarta Tun da ta tinkaro wajen ta dan ja ta tsaya sakamakon gannin mutumen nan zaune kansa sade Yau kuma irin shigarsa sai ta sakata kara kallonsa da kyau Dan waigawa ta yi ko zata ga motar da ta kawo shi? Sai dai hata ga mota ba Adu'ar neman tsari ta ringa yi da miyagu Kasancewar ya saka shada marron sai gaba daya hasken fatarsa ta kara fitowa Daga sajensa zaka gane mai summa ne sosai sannan baka ce sidik summar Kwalin idannuwansa dake nuna kansu ko a cikin dare ne sun kuwa nuna kan nasu da taimakon fitilun dake kukune Karasawa ta yi ta zauna a wajen da take zama hakan ya sa suke facing din junna Shima bai yi tunaninta a wajen nan a irin wannan lokacin ba kasancewar ya san cewa ita din kirjin biki ce du inda ta ji da maganar biki ko ba na gidansu ba zuwa take bale yau nasu? Kura mata ido ya yi gannin ta kasa bude abinda ke ledar sai dan jujuya cokalin hannunta take Shin dama tana da kunyar cin abu a gaban bakon ido ko cikin salon yaudararta ne da neman janyo hankalin namiji a kanta? Basarwa ya yi ya ki yi mata magana a yau din ya daga kansa sama yana gannin yanda farin wata ke kara haske Kasancewar ta rasa nutsuwar hutawar ya sakata kallon wajensa Sai da ta yatsina bakinta a hankali ta ce" hi Dagowa ya yi daga kallon saman ya sauke a saman kanta Da sauri ya cire idannuwansa domin dinkin lesh din nata daga gaban kirjinta an yi kata wani heart ne an cire wajen an zagaye shi da kyalkyali aman kuma an baiwa mararabar kirjinta damar bayannuwa sosai Kai kam ina ne gidanku kake zama a nan koda yaushe? Ko a saman bishiya ne? Ta fada tana nuna masa bishiyar dake wajen Shima bishiyar ya kalla, sai ya ji murmushi na zo masa, wato da alama a tsoracema take da shi ko? Kafadunsa ya dan daga a hankali ya ce" daga wajen auren sarkin garinnan nake, na gaji shine na zo nan na huta Bakinta ta dan tabe ta daga kafadunta Muryarsa mai sanyi ta kuma jin ya ce" daga ina kike haka? Me kike zuwa yi nan? Ko kema daga wajen auren sarkin kike ne? Dago idannuwanta ta yi ta sauke saman kansa a hankali ta ce" ban san shi bama ni sarkin nan, sannan wajen nan wajena ne ban san dalilin da zaka tambayen me na zo yi ba Wajenta ne? To ka ji ya fada a ransa Mikewa ya yi cike da isa ya dawo kusa da ita ya zauna inda take binsa da kallo har zamansa A hankali ya ce" freind? Hannun nasa dai ya miko mata yauma, shi kam ko a inda ya fito haka yake gaishe gaishe da mata? Duda yanzu abin ya zama ruwan dare dan gaisawa da mace ba wani abu bane da namijin da ba muharaminta ba bayan ba kyau Murmushi ta yi tana hararan hannun nasa a hankali itama ta ce" zan yi tunani Haka yauma ta bara masa hannun sakaye yana binta da kallo har ta shige motarta sannan yauma bata dauke abin cikin ledar nata ba nan ta bara masa su ta yi tafiarta Kansa ya gyada yana ayanna" du salonki, sai na ga ainahin wacece ke! Du iya tsare tsarenki na kwana da sannin ke din *MAGE CE MAI KWONCIYAR D'AUKAN RAI* da wani irin sauri amintacen dogarinsa ya karaso wajen da yake zaune ya zube kasa kansa kasa jikinsa na rawa ya ce" Allah ya ja da kwananka, Allah ya taimaki mai damagaram kiran gagawa ya samu daga wajen Gimbiya Allah ja da rai Da sauri ya kalle shi ya waiwaya baya ya ga har ta tafi Kira daga wajen gimbiya da gagawa? N Mikewa ya yi yana takawa ya nufi motar Bai shiga ba sai da ya mayar da rawanin kansa ya dora alkyabarsa ya cenza takalminsa ya rige sandar girmansa sannan ya shige baya ya lafe Jan motar yake gabansa na faduwa duba da irin abinda aka fara fada masa A haka suka samu shiga ta baya suka shige suka karasa wajen da Gimbiya ta umarci a kawo shi Du mutannen wajen dukawa suka yi a lokacin da aka shiga shelar shine Cikin taku irin na kasaita ya ringa daga kafarsa daya na korar daya har ya karasa wajen da GIMBIYA ke tsaye tare da y'ayan yan matanta Yannayin tashin hankalin da yake karanta a fuskarta shi ya saka shi kara rage hanzarin tafiarsa Motar da ya bada dan kawo amaryar nasa ce ya ganni a bubude Wasu mata ne ya ganni a duke nesa kadan aman kuma kuka suke A hankali ya kai dubansa wajen motar Idannuwansa ne suka sauka kan wasu fararan kafafuwa da aka fitar Irin yanda kafafuwan suke ajiye ne zai shaida maka mai su idan dai ba barci yake ba to yana cikin halin rashin lafiar da baya iya motsa su Da alama kuma mutumen dake ciki ahi daya ne Haka kawai ya ji zuciyarsa ta doka da wani irin duka mai tsanani A hankali ya karasa gaban mahaifiyarsa Kansa ya dula sosai ya ce" Allah ya ja da ran Anmy Anmy ta dago tana dubansa cike da fargabar abinda zata fada masa da tausayin yarinyar dama shi kansa da iyayen yarinyar Me zata ce masa ne? Ce masa zata yi su kansu yan rakiyar yarinyar basu san cewa ta rasu a cikin kotar ba har sai da aka zo aka kamo hannunta dan fitar da ita a sadar da ita da dakin mijinta? Ko kawai ta ce da shi SHAHEED ALLAH YA YIWA YARINYAR DA KA AURA YAU RASUWA? SAI TA RASA KALMAR DA ZATA IYA HADAWA DAN SAMUN WANNAN BAYANI BAKINTA NE YA SHIGA RAWA A LOKACIN DA TA BUDA TA CE" YAU NA YI DA YAWA😓 [31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 17 A hankali yan matan suka marmatsa bayan sunna dan dukawa sunna nan afuwa suka barshi tsaye gaban Anmy A hankali ya jinginar da sandar hannunsa ya saka hannayensa biyu ya dago fuskar mahaifiyarsa Irin yanda kwayar idannuwanta ke cikowa da kwallah ne idan wani abu mai rikitar da zuciya ya faru ya ganni Kwonce kwalar take a kurmin idannuwanta hakan ya sa fuskarta yin wani iri Sauran matan tsohon sarki biyun ne suka karaso suma da yannayin juyayi a fuskokinsu Fulani ce ta dora hannunta saman na sarkin dake gefen fuskar mahaifiyarsa A hankali ta girgiza masa kai wanda hakan ya saka shi saurin rintse idannuwansa domin wannan lamari shi ya faru a lokacin da ya rasa mahaifinsa Sun ringa dafa hannunsa ne sunna girgiza masa kai Da sauri ya maida dubansa wajen motar nan Kafarsa ya daga zuwa wajen motar nan bai ko dauki sandar ba ya karasa kusa da kafafuwan dake sanye cikin wani fari kar din silifas irin shirin da ake yiwa amare dai hakan ya saka Gimbiya saurin rike hannun Fulani ta lumshe idannuwanta tana tunanin irin abinda yaron nata zai iya ji, dan ta tabata yarinyar nan yana sonta duba da har aka ji kamshin turaranta a tufafinsa kuma bai musa ba har aka bashi damar aurenta ya amsa da murna ta zama matarsa a dan kankannin lokaci ashe ba zasu raya zaman auren tare ba? Fararan hannayensa ya saka da suke dake ya dora saman fararan kafafuwan nata A hankali ya idasa saka hannunsa ya saka kansa cikin motar baki dayansa Daidai lokacin da kunnayensa ke jiyo masa kukan tsofafin da suka rakota dakinta kamar haka" ashe ba zaki ga dakinki ba Bintu, Allah ya jikanki da rahama Binta, Allah ya haskaka makwoncinki salihar yarinya mai hakuro da nagarta Zuciyarsa ce ta doka da sauri ya saka hannun nasa ya yaye rufar da akaiwa fuskarta Fuskar nata ya tsurawa ido Fara ce sal, sannan fuskar nata ya amshi mahaukaciyar makup mai iya doka zuciya ta saka a ji an kamu da son mai dauke da ita Irin gashin idon nan natural ta saka mata shi ya yi mata wani irin gazar gazar duda idannuwanta a rufe suke ruf domin Anmy ta rigaya da ta shafe mata ido Dagowa ya yi a karo na farko ya bi mutanen sake wajen baki daya da kallo Muryarsa a saukake ya ce" ku je Daga ku je din bai dora komai ba, sai dogarai dake faman aikinsu Ya rage daga Anmy sai y'ayanta sai manyan datijan dake wajen Kansa a kasa ya furta" iyayenta sun ji? Anmy ta gyada kanta ta ce" yaya ya tafi wajen mahaifinta dan na jima ina kiran layinka bana samu, sai daga baya na kirayi amintacenka Kansa ya gyada a hankali ya kuma fadin" zan kimtsata da kaina, zamu kwana yi mata adu'a, Anmy in sha Allahu zata samu sutura nagartaciya zata yi makotaka da Abih da kuma Aliyu, ina fatan da kuma adu'ar ta kasance a fadar ma'aiki Salalahu alaihi wa salam suka amsa a hankali Anmy ta ce" a ina zaku yiwa gawar karatun? A ina zaka kimtsata? Ajiyar zuciya ya kuma saukewa mai zafin gaske ya ce" a bangarenta Hannunsa ya kara mikawa ya kamo na mahaifiyarsa ya ce" Anmy, ku je bangarenki, ba komai ku yi ta adu'a Kanta take gyadawa ta maida dubanta wajen motar ta kuma kallo So take ta fashe da kuka, so take itama ta saki zafin da take ji ta yi kuka sosai, sai dai ba halin hakan, an jima da horar hawayenta da tsayawa a lokacin da ya dace ta zubo su, an jima da horar zuciyarta da wata irin dakiya wace ke ritsa zuciyar ta yiwa zuciya lahani Hakama yaronta ya taso da horo wanda ya fi wannan tauri a matsayinsa na d'a namiji kwalin kwal a wajen mahaifinsa wanda ya rayu, ba wai ba'a taba haihuwar wssu mazan bane, no, an haifa du basu zauna ba sai mata da suke yayunsa du ba a nijer din bama suke aure hakan ya sa basu halarci auren kannin nasu ba bama kowace ta ji zai kara aure ba dan shi din ba mai magana bane kuma basu yi waya da anmy ba, shirye shiryen zuwansu da suke na su yi jajen rasa Aliyu ne Baki dayansu suka rankaya suka tafi bangaren Anmy Yana nan tsaye da dogaran yana ta dube duben cikin motar da komai mahaifinta ya karaso da mahaifiyarta Sosai mahaifiyarta ta yi kuka ta rungumeta a jikinta ta furta" kamar yanda kika kasance yarinya mai faranta min, mai yi mana biyaya, Allah ya karbe ki da ni'imarsa Bintu, Allah ya yafe maki kurakuranki mu kam mun yafe maki dukan laifinki Kansa a sade yake yana dauraron irin adu'ar iyayenta a kanta, kwarai ya kara tabatarwa kansa cewa ya yi rashin mace mai daraja, irin yanda du bakin da ya bude tun zuwansa wajen yabonta ne da fatan alkhairi a gareta sai ya ji yana mangarinta, sai ya ji yana mai adu'ar Allah ya sa idan tashi ta riske shi ya samu irin wannan shaidar ta duniya wace itace ta lahira Mahaifiyarta ta dora kanta a gefen hannun mahaifinta dake dan dadaba bayanta a hankali dan ya rarasheta ta ce"ta rayu da son gannin sarki a rayuwarta, tana son ta ganta gata ga sarki, Sai gashi yau Bintu gaki ga shi aman baki san yana wajen ba, Maganar ta kuma dukansa, dan haka sai ya nemi da su je ciki a kaita ciki kawai Sai da ya gama dukan abinda yake na bincike sannan ya kamata, ya cicibata ya dorata a gadon bayansa dan kuwa ya ki dogarai su kama masa du irin nauyi na gawa ya dorata a bayansa ya nufi bangaren da aka kawata mata Shinfideta ya yi saman cafet ya zauna a hankali ya cire babar rigarsa Karatu ya saka ya shiga cire mata takalman kafafuwanta, ya ringa cire mata komai a hankali sai da ya cire mata komai ya dauki sabuwar zanin rufar da ya kawo ya rufa mata shi har kanta Mikewa ya yi ya je ya yi waya da anmy sannan ya karasa ya bude ya amshi likafanin da ya bukata har an kawo masa, a lokacin yake son shiryata Dukan abubuwan bukata ya kawo kusa da shi ya shiga binta a hankali a laluma yana lalabata yana yi mata alwallah Dakatawa ya yi dan dole sai an cire masa abin idannuwan nata da kuma su sarka da yan kunnayen dai da sauransu Gaba daya jikinta rawa yake, tun da ta dawo ta tardo wannan lamari ta ji gaba daya hankalonta ya gama tashi jikinta kuwa ya kwashi rawa yanda ka san mazari Bata furta komai ba, tafe dai suke ita da Zahrau har suka shigo falon Gabanta ne ya yanke ya fadi a lokacin da ta gansa zaune a kasa ya sada kansa gaban gawar yana karatu muryarsa a bayanne aman a hankali kuma a sanyaye haka kuma bai cire rawanin dake jikinsa ba aman baya dauke da babar rigar Gaba daya zaka fahimci yana cikin tashin hankali ne idan ka kalli jijiyoyin hannunsa irin yanda suka mimike suka yi wani irin tsanwa da su abinka da farin mutun Hannun Zahrau ta damka wace ta jata suka karasa baki dayansu Bai dube su ba, sai hannunsa da ya saka ya bude fuskarta ya kasance fuskar ta bayanna Irin yanda fuskar ke fitar da annuri dole ka ji hankalinka ya tashi, gata dai kamar wace take bacin gangan Sai a lokacin ya dago ya dube su Ya san cewa itace mai iya fitarwar dan haka ya nuna mata kusa da kan Bintun yana nufin ta karaso ta cire mata Jikinta na ci gaba da rawar ta karasa ta tsugunna Dan man dake hannunta ta lakuta hannunta na rawa ya kai wajen idannuwan bintun A hankali ta shafa mata a idonta na dama ya dan dauki dan time ta janye shi ta cire shi a hankali ya biyo hannunta ba saura ko daya a jikin Dayanma ta saka hannunta ta shafa sai kawai ta ji ta kasa rike kukan nata a wannan karon Hakan ya sa ta zabura ta mike tsaye da niyar guduwa waje ta ci kukan dake wuyanta, shikenan? Yanzu shikenan? Yarinyar da ta je dazu ta yiwa kwaliya har sunna tsokanarta wajen turara mata turaran wuta itane kwonce haka gawa? Sai an juyata sai an kwontarta? Hannunta da ta ji an damka ne ya sakata saurin juyowa Bai bata damar fahimtar komai ba ya risinar da ita kusa da shi sosai har ya kasance sunna gugan jikin junna Sakin kukan ta yi da karfin gaske hakan ya saka shi janyo kanta shima da karfin ya dora saman kirjinsa ya saka hannunsa ya tare keyarta da shi har yana hade hijab dinta da shi sannan ya shiga girgiza kansa a hankali ya ce" yaya zaki yi irin kukan nan a kan gawa? Kar ki kona min jikin matata Muryarta cikin kuka ta ce" ta mutu? Shikenan ta mutu? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une Zahrauma ta janyo kafafuwanta ta hade da gwuiwarta ta fashe da kuka tana mai tausayin kanta da dukan musulmai Ya zama dole dai sai an mutu? Kowani mai rai mamaci ne , ya zama dole kowa ya dandana zafin mutuwa Jin ta sasauta kukan ya saka shi cire kanta daga kirjinsa yana yi mata wani kallo mai cike da fasarori irin na jin haushinta, na gannin rashin dacewar ta yi masa ihu a ka ga kuma gawa haka kawai, ya dauki hannunta ya nufi wajen fuskar domin ba idasa cire abubuwan ta yi ba shine zata wani tsere ita ga mai neman balaki! Hannunta na rawa tana dan cije lebenta na kasa ta idasa cirewa Gannin ya nuna mata yan kunnayen da sarkar ya sakata zaro idonta Mikewa ta yi da sauri ta fita da gudu tana kara sakin kukanta Da ido suka bita daga shi har zahrau, dan haka sai ya nemi da Zahrau ta cire dan shi baima san yaya ake saka abubuwan nan ba Zahrau ta taimaka masa suka cire yan kunnayen Sun zo cire na wuyan ne suka ga wani bakin abu ya bushe a wuyan nata Da sauri ya saka yar auduga a ruwa ya shiga goge wajen Wasu yan hudoji ne biyu rak suka bayanna a gefen wuyanta Hannunsa ne ya shiga dan rawa a lokacin da wani tunani ya darsun masa a zuciyarsa dan haka bai yi kasa da gwuiwa ba ya kama wajen ya matse da karfin gaske dan gannin idan har abinda yake zato ne Irin ruwan da ya fito, kafin wani bakin jinni ya ci gaba da fita ne ya saka shi rintse idannuwansa yana jin wani irin zafi da ciwo a zuciyarsa Bai ce da ita komai ba sai salamarta da ya yi Bai yi mata wankan ba sai da ya tabata saran na wani kalar maciji ne sannan ya kimtsata tsaf cikin suturarta ta karshe kafin ya tatare komai ya yiwa malaman dake jira iso suka dukufa suka shiga sauke mata alkur'ani mai girma, sannan liman ya je masalaci ya yi shela da kuma raraba kulhuwalahu dan yi mata shinfida ( ya Allah ka bamu irin gatan nan ) Sai da aka yi saukar fari sannan ya fito ya kara komawa wajen motar nan Da hasken wayarsa ya kara hahaskawa tare da amintacen dogarinsa Gaba da baya basu ga komai ba dan haka suka buda boot A tare suka zabyra sakamakon gannin wani dan saurayi dake daya daga cikin yaran gidan dake gyara wajen dawakai, yaron maraya ne gaba da baya yana aiki ne a gidan sarki a mace shima da kuma macijin nan a raye ya nanade jikinsa sai kansa dake dan gilo a sama kadan Da sauri amintacen mai martaba ya so matsa mai martaba gefe dan kare shi daga macijin nan Sai dai ya tare shi ta hanyar bashi wayar hannunsa Cike da kwarewa ya damki macijin nan ya yi masa rikon nan da ake yiwa makogwaron maciji ya janyo shi inda macijin ke ta fitar da dan harshe yana wani irin kara sssssssssssssss Yar yatsarsa ya saka bayan ya kara tabe bakinsa sosai ya cire abida ke watsa dafin sannan ya mikawa amintacensa ya maida dubansa wajen yaron Harbin bindiga ne kansa harbi daya tak wanda ke fasara komai wato yaron ya yi aikin kashe amaryar mai martaba wanda ya saka shi aikin kuwa ya kashe shi Sai da ya yi kiran asibiti aka tafi da yaron dan aune aunen bulet din da sauransu sannan ya wanke hannayensa ya koma ya har amintacensa da macijin nan inda ya nufi cen cikin fada da shi dan ganno na waye domin akoy yaren dake wasa da macizai a cikin gidan sannan da masu koya masu yanda zasu tafiar da maciji .......................................... An yi sututar bintu cike da daraja da tarin al'umah Ta samu adu'a'u, tana cikin samu domin mijinta ya dauri niyar jerota a cikin mutanen dake samun adu'ar nutsuwar kabari har karshen rayuwarsa bayan kuluhin musulmai da yake bi da shi Gidan ya kuma daukan haramar jama'a, mutane zuwa suke ta kowani gefe ana yiwa sarki da ahalinsa ta'aziya ciki kuwa harda yayunsa da kanwarsa daya kwal dake garin Niamey wajen yayarta Yana zaman makoki ne hankalinsa a rabe, sosai ya kara sakawa rayuwar gidan ido inda bincike ke tafia ta kasa yana son sannin abinda ya kawo maciji da mai wasansa cikin sabuwar motar da ya ware a boye dan dauko masa matarsa motar da ta kasance mutun shida kawai suka samu ganninta suka san da ita su ne : Sarki, Anmy, amintacen sarki, Zinaria, Abih, sai liman baba Gidan bai samu sasaucin jama'a ba har sai da aka yi satin Bintu Daga lokacin gidan ya fara samun daukewar sahu kadan kadan sai masu zuwa ziyara masu zuwa gaishe da sarki daidaiya Zaune suke kowane da yamutsen zogalensa a cikin plate sun saka Anmy gaba sunna dan ci kadan kadan Daya daga cikin kawayen matar ambasador ce akayiwa iso tare da mijinta zasu yiwa Anmy gaisuwa duda ita ba sanninsu ta yi ba aman da yake sun saba sai ta umarci a shigo da su dan Ajiye nata plate din ta yi sannan ta dan fito daga cikin yaren nata ta zauna inda take karbar baki Tun da suka shigo suka zube sunna gaishe da Anmy Mijin nata ba wani tsoho bane, hasalima Ambasador ya girme shi a shekaru Anmy na amsawa tana mai nuna masu jin dadinta Matar ce ta dago da yannayi na iya yi , kana ganninta ka san wannan kamar itane mijin shi kuwa matar dan ita ke ta yawan magana shi kuwa kamar mai jin kunya kansa a sade kawai yake Tun da suka shigo Najeeba ta shaida matar Itace take kakabewa matar Ambasador jikinta tana nuna mata ta bari haka gamuwa ta biyu zata kara daukan fansa Da iya yi matar ta ce" na jima ina son samun shigowa nan Gimbiya Allah bai nufa ba sai dai mu tsaya daga waje idan mun zo, wannan mijina ne sunnansa MOUSTAPHA likitan zuciya ne baban likita ne da ake ji da shi a kasar nan Ni kuwa sunna na AISATA yar kasuwa ce ni ina hada kayan lefe da komai da komai masu kyau na manyan mutane Gimbiya na gyada kanta kawai, dan bata son ta ga mace na zubar nan kamar wace aka tambaya, ita da ta zo ta'aziya sai ta bige da tallah? NAJEEBA ta ringa juya dan spoon din hannunta dan karami mai yatsu wanda take dibo zogalen da shi tana kara juya shi tana kallon matar da kallo irin na....ta kawo kanta har gida Cike da sarauta Gimbiya ta juya wajen y'ayan nata A nutse ta ce" NAJEEBA ta'al Mikewa Najeeba ta yi daga zaunen da take Hijab ne ja a jikinta mai tsayi har kasa sai hannayenta da ta fitar ta jikinsa ta shiga takowa a hankali Tun da ta taso matar ta kai dubanta wajenta Kamar wace aka yiwa kidan maruka a kumatu haka ta ji zuciyarta na yi mata balin balin Idannuwanta ta kara fitarwa dan tabatarwa kanta shin itace ko mai kama da ita ce? A lokacin ne kuma NAJEEBA ta idasa karasowa falon tana dan yatsina fuskarta da yannayi na sangarta ta rage muryarta sosai ta shagwabe yannayinta sosai sannan ta ragewa idannuwanta girma ta ce"""""": ..........to fah.... ..... ...... ...............mu je zuwa [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 18 A cikin wata irin sansayar murya ta ce" Anmy, zuciyata ke min zafi ban san dalili ba tun jiya da safe Anmy ta dubeta da duba irin na kula sosai ta ce" subahannalah wani irin ciwo ne haka Najeena? Tun yaushe? Zo mu ga? Karasawa ta yi ta dan duka gaban Anmy ta dora hannunta saman mamanta na hagu daidai zuciyarta ta ce" Anmy, nan ne, sai yana min zafi , yana sukana yana min ciwo, ni dai tun da gabana ya fadi rasuwar matar yaya nake jin haka Sosai hankalin Anmy ya so tashi tana ta dora hannunta daidai wajen ta ce" idan na danna akoy zafi? Da sauri ya ce" aa kar ki danna Allah da ja da rai, ba'a dannawa da garage har sai an je an yi mata gwaje gwaje, inaga tunda daidai zuciyarta ne ta samu ta leka clinik dina gobe da dare bake hawa in sha Allah sai na yi mata dukan binciken da ya dace Gaba daya matarsa ta zazaro ido ta aniya zazago girmansu da rawar lebe Gashi dai a gaban idannuwanta komai ya wakana wanda ta rantse da Allah karya ne Gabanta ne ya kara faduwa a lokacin da kalaman Najeeba suka dawo kunnayenta da irin rantsuwar da ta yi kan sai ta rama baki dayansu Kafin ta ankara tuni an yi mai yiwuwa domin wayar mijinta ne a hannun Najeebar har ta dora number Anmynta wai dan ta yi serving, a haka cikin gagawa ta dora nata number ta yi dialing, yana shiga ta kashe sannan ta mika masa wayar harda dan risinawa Sai kawai matar ta zama wata wawa sai zarar ido take har suka mike suka fita Tun kafin su karasa fita ta ja ta tsaya ta ce" bani wayarka Dubanta ya yi da mamakinirin yanda ta yi tambayar wayar Du tsakaninsu basa taba wayar junna, sam basa daukan wayar junna dan gudun fitintinnun yau da kulun sai gashi haka kawai wai ya hata wayarsa? Karasowa ta yi ta ce" ka ga aban Barira wayar nan taka walahi ko ka bani ko yau na fasata na karya layinka dan karuwar nan ba zata daukan min numberka haka kawai ta tayar min da hankali ina zaman zamana dan nan kawata ta kawo kararta da yake gidansu ne sai aka bige da daure mata karshe sai kawar tawa ta dauki laifi an shanye mata miji ita ba aurensa ta yi ba sai tatikarsa kudi take, shi bai zauna a gida ba sai yawon binta yake sunna yawon iskanci! Girarsa ya gama hadewa ya juya yana tafia da wani irin sauri Har sai da ya fita sannan ya duka ya dauki takalmansa ya saka ya karasa wajen motar Da yannayin karkamba ta karaso tana ihun sai ka bani wayar nan idan ba haka ba kowa ya mutu Motar ya ja ya mako da karfin gaske tana tsaye a waje ya sauke madubi ya ce" ki nemi ubanda zai maida ke gida, kin san ko ji waye na rantse maki zan lalasa maki jiki na daki kodadiyar fatar nan taki, idan ba jaraba ba mata bi danki ne da zaki ringa yi min ihu? Kin san ko ni waye kin san irin tashancina, sannan idan har y'ar na ja haka zamu ja sai ki yi ubanda zaki yi Wata ashar ta lalayo ta afka masa tana dukan motar ta ce" motar banza gareka? Ka je sai me zan nemi mai kawonin kuwa , kuma komai jarabarka a gidanka zan kwana sannan in dai una rate ba dai bakar y'ar nan ta kwace min miji ba kawayena su zageni Yawun bakinsa ya tofa mata har zuwa gaban rigarta ya ce" da ace ke farin naki ba na kanti bane da sai ki zagi wani da cewa baki, ke na rantse da ace ta aureni ko? Zan sake ki ne da ke da y'ayan da ban yarda cewa nawa bane ku kara gaba na huta da jarababiyar mace mai warin jaba! Sannan zaki dawo gidan zamu gwada karfi ne da ke mu ga wanda ya fi wani banza mahaukaciya mai kai kamar baro Yana gama fada ya tayar ya fice da wani irin gudu kamar ba shine yanzu a gaban gimbiya kansa a sade kasa ba, kamar ba shine shiru shiru da lafia ba, kamar ba shine mai yin shiru ita na magana Dama sun zo ne dan su kula alaka da ahalin gidan, sai yau suka samu gannin Gimbiyar dan su kula alaka duba da ita babar yar kasuwa ce shi kuwa likita ne yana so idan da hali ya zama likitansu na cikin gida fannin zuciya Sai gashi sun samu nasarar kula hakalar domin har number Gimbiya ya samu yau a wayarsa aman shine matarsa ke cewa ya fasa wayar ya karya layin? Yo shi ko ubanwa ya fito masa da maganar nan ai bama zai dube shi ba zai yi ya gama ne ya bashi lafia yau ya ga iskanci A takaice dai wannan mutane da suke mata da miji dama haka suke, sukan tayar da balaki su daki junnansu har titi ne Tabas matar bata zauna dam ba, shi kuwa mijin hakan ya saka ya zama wani irin marar tausayi da daga mata kafa a rayuwa Idan ba yan anguwarsu ba a wajen anguwar ana zaginta cewa ta fi karfinsa ta hanna masa zaman lafia Yan anguwar kuwa sun san waye shi domin mutun ne mai dukan mace kamar ya samu ganga, yaka daketa ta rama daidai gwargwadon iyawarta su yiwa junna gori sannan su koma cikin gidansu, Y'ayansu ba mai mutuntasu, yawonsu suke son ransu ba matan ba mazan ba wanda ya isa ya hana su ko ya saka su a cikin iyayen nasu........................... Wayarta ta ciro ta nemi layin wani farkanta ta koma gefe tana juran karasowarsa dan ba zata je gida a yanzu yanzu ba a yanda ta zage shin nan ta san a irin lokacin nan sai ya kusan kasheta Anmy kam ko bayan tafiarsu sai ta kasance mai baiwa Najeeba kulawa duda ta ga ta dan warware ta shige cikin yan uwanta sunna cin abincisu aman sai ya kasance tana yawan tambayarta yaya take ji har suma suka so tayar da hankalinsu sai ta basar ta nemi zuwa kwonciya A ranar da Bintu ta cika kwana tara da rasuwa da safe ya kasance du an watse sai masu hidimar gidan sai yan matan Anmy da basu tafi ba sai an yi sati biyu zasu koma gida A yau da safen ne kuma suka soya fara, sukai mata suya mai dadin gaske suka zauna a nan falo tare da Anmynsu itama tana cin kambolinta basu saka mata yaji ko daya ba Sunna yar hirarsu falon sai ya su ya su, hirar ba wani ta shan dariya bane aa, aman lokacin sunna raba shi ne da wani irin shakuwa da kulawa da junna Maganar da jakadiya ta duka tana fadi ne cewar matar Abih na neman iso ya saka Gimbiya kallonta da kallo irin na son ta maimaita Kara sada kanta ta yi ta maimaita maganar Dago kanta gimbiya ta yi daga kallon Jakadiyar ta sauke saman yaran Ta dan jima kamar second talatin tana kallonsu sannan ta cire kanta a kansu ta gyadawa Jakadiya kai Mikewa Jakadiya ta yi ta juya, dan ta gane amsar cewa eh aman ba yanzu yanzu ba Cike da kauna Gimbiya ta kalli yaran ta dan gyara muryarta ta ce" kunna ji? Du dubanta suka juyo yi Gimbiya ta yi masu murmushi ta ce" bana so a raba hali Du sun fahimci inda ta nufa aman dan ta tabatar cewa sun fahimtar sai ta masu shiru daga haka itama ta ci gaba da dan daukan kambolin farar tana dan ci har tana mamakin kanta yanda aka yi take cinsa da yawa haka ko dan tare da mutane ne An dauki kamar minti goma zuwa lokacin Har Gimbiya ta wanke hannunta, yaranma kananun ne basu gama cinye fararsu ba Da salama suka shigo falon Masu yi masu jagora ke amsawa da karfi karfi sunna fadin" ku shigo a hankali, Gimbiya na falo Ku sada kanku kasa ku gaishe da mace daya tamkar da goma mama a wajen sarkin damagaram Ku tako sannu sannu Bakinta ta dan tabe tare da yayarta suke wace ke biye da jakadiyar dan aiwatar da abinda ake nuna masu Sunna zuwa du suka nemi zama a kujera Sai dai basu kai ga karasa nufinsu ba da sauri Jakadiya ta tare tana nuna masu wajen da ya dace su zauna domin idan ka ga Gimbiya na sama wani na sama toh sarki ne, sai y'ayanta dake hayewa jikinta su dora kansu a saman kafarta, su kansu idan ka ga sun layi da ita to a saman diner ne Ko yanzu Zahrau ce kwonce kanta saman cinyarta ita kuwa tana shafa mata gashin kanta Daga kasa kuwa Najeeba ce ke gyara mata akaifunta tana ta kankare mata su tana yanke mata duda ba wani datin dake jikinsu aman ta saba idan tana zaune ko ta dora rigimar sai ta yi mata kitso, ko ta kama gyare gyaren mata su akaifu ne da sauransu Komawa suka yi wajen suka zauna domin wajenma waje ne mai alfarma dan ba kasa ne dabas ba aman duda haka ita ta so ta hau kan kujera dan a ganninta ai ita matar yayanta ce Yayarta ta fara mika gaisuwa, kafin itama ta buda bakinta cike da yatsina ta ce" Fatan kun wuni lafia, yaya aka ji da hakuri? Gimbiya ta dan dauki lokaci kafin ta lumshe idannuwanta, hakan ya sa Jakadiya fadin" Alhamdulilah, Gimbiya ta amsa Hakuri an gode Allah Da kallo ta bi Jakadiyar sannan ta sauke kan Gimbiya Sai ta ji shakarta ta shigeta domin irin kamalar dake tatare da fuskar gimbiya ba zaka iya takata kai tsate ba komai rashin kunyarka dan ba lalenema ka ji muryarta ba idan ba hakan ta so ba Idannuwanta ta dago ta sauke a fuskar Zahrau wace ke iya gannin hakan Dan mukewa Zahraun ta yi tana gyara gashin kanta ta bi kannenta da kallo baki dayansu, kallon nan da ake kallonka kuma a kalli mutun Du yawanci sai da suka dan turo baki kafin a hankali da daidaya suka shiga gaisheta, gaisuwa kamar haka" barka da yamaci, fatan kun zo lafia? Bakinta ta tabe tana dan jijiga yarta dake bayanta wace ke ta ihun a sauketa tun da ta ga yan uwanta aman uwar ta ki kunceta dan haka sai take kukanta irin kannanun kukan nan Basu wani jima sosai ba, ko gaisuwar yaran ba yanda ya dace ta amsa ba yayarta dai ce ke amsawa kafin su mike su juya su fita Sauri sauri take har suka karasa fita waje sannan suka shiga cikin motarta da suka zo da ita Sai da ta kama hanyar gidan iyayenta dan cen suka nufa tana ta jan wani uban tsaki Ita dai yayarta tana ta jijiga yar da ta ki yin shiru tana kiran sunnan yayanta dan saurayin Sunna karasawa suka sauka suka shiga ciki Mamansu dake shanya hijab din yar yarinyarta ce ta dago tana dubansu ta ce" aa, me ya samu kishiyar ne haka take wantsala kuka tun daga waje? Yayar Mardiya ta mikawa mamansu yarinyar ta zauna tana dan tabe bakinta ta ce" mama, anya kuwa Mardiya ba tana hada mu da y'ayan mijinta da kanwar mijinta dan ta kasance mai son kanta bane? Da sauri Mardiya ta dubeta ta ce" wani irin ina hadaku da su? Hararanta ta yi ta ce" kwarai kin ji abinda na fada! Mardiya du irin rashin mutuncin dake tsakaninki da yaren nan sai na ga da sauki tunda har zasu budi bakinsu su gaishe ki, sannan ke maimakun ki yi masu amsa irin ta uwa ko dan idannuwan mamansu sai kike wani binsu da harara Ke dai kece mai neman fitinar a bayane domin ni dai ba fada min aka yi ba ni na raka ki Mardiya ta zaburowa Nusaiba tana fadin" zaki min shiru ko sai na ci uwarki a nan yarinyar nan? Yar ta yi shiru tana kwontar da kanta saman kirjin kakarta ta kai dubanta wajen yayarta da yannayin fada ta ce" malama kar ki wani fada min haka dan ke baki san abinda nake ciki ba! Yanzu dai a gabanki zuwa muka yi zamu hau kujera aka hanna mu aka nuna mana kasa muka zauna Sannan kina ganni mu muka buda baki muka fara gaisheta bayan mune ya dace ta gaisar! Da kike maganar yaran ba sai da ta harari katuwar guzumar ba sannan suka gaishe mu ba? Itama idannuwan ta ruko mata ta ce" kin fa san bana tauye gaskiya ko a gaban waye, ba zan boye gaskiya dan kina kanwata ba Me kike so? Ki hau kujera ki layu da Gimbiyar Damagaram? Uwar sarki ce fa Mardiya baki da hankali ne? Ke ki kasance da ita a waje dayama ai arzikin arziki kika ci! Kuma maganar kujera ba a kasa aka sauke mu ba, na lura wajen saukewar an dora mu mafi karamci ne a cikin waje uku ne Da kike maganar sai da ta harari yara sannan suka gaishe ki inaga ashema da tarbiyarsu yaran dan har an isa a sakasu ko a hanna su duda kuna cikin haki na gaba da tsanar junna? Ke ki rufawa kanki asiri ke kin san cewa Allah ya baki dama, na rantse da Allah da ace kin sada kanki da matar nan da na tabata kun samu kusanci da fahimtar junna yanda ya dace, da ke ya dace a je a yiwa gaisuwar nan ba wai na tirsasaki na kaiki mu yi dan zama mu tashi ba Haba Mardiya, ke kin san waye mijinki, igiyar aure daya ta tsinke tsakaninku, ke kin san kafin ki shiga gidansa da manufarki ta yin hakan, kin shiga gidansa ne dan ki rama kwace maki saurayi da y'arsa ta yi, kin shiga ne dan ki muzanta rayuwarta ki hanna mata zaman lafia da kwonciyar hankali Baki shiga dan ki haihu ba Baki shiga dan ki jima da shi ba, Da biye biyen abokansa suka shunna masa ke ya aura Ke kin san kina cin ribar baba malan ne Ki kiyaye Mardiya, ki kiyaye dan wannan kadai ya isa ya shaida maki cewar Allab na tare da shi, kwarai kina haye masa da izgili kala kala aman Allah ya hanna rabuwarku, ke kanki nan da ya sake ki saki daya a nan kika ringa zuba mana hauka sai da muka neme shi aka mayar da ke Kin je kin saba da rayuwar gidansa idan kika ce zaki balo ki fito kece da shan wahala Ki duba ki ga jikina, kwoncen kayan da kika bani ne aman ni kaina na zama abar kwatance a cikin sa'a dan kina bani su ina ketawa ina shiga cikin jama'a har fadi ake kanwarta ce ke auren MUTALAB fa, me kika rasa a gidanki? Mijinki ba ke ba ko mu idan ya tashi tsokanarsa zai sako mu gaba ne sai an sha wasa da daria, Kudi sai dai ki ba wani A wajen kwonciya ya gaza maki ko a me? Mardiya idanma muzgunawar ne fa kin masu , ya dace ki gane cewar kece da faduwa idan kika ci gaba da rayuwa a haka domin ko a irin yanda kansu ke hade zaki gane mai shiga tsakaninsu fa walahi ba dai mutun ba sai dai Allah! Mardiya ta zauna tana hucin maganar yayarya bayan baki daya gaskiya ta fada mata Sai a lokacin mamansu ta kawo kujerar zama irin tayani tsegumin nan ta zauna tana kallonta ta ce" ke kuwa, rashin wayo ne ko rashin hankali ke saka ki aikata abubuwan nan? Jiya yayarki ke ce min wai kin yiea yaren iyaka da taba Yarinyar nan Ashe baki da hankali? Ke din kin isheta tuwo da miya ne? Ke yau ace mijinki na raye har ta kai aure yaran nan suka fita a harkarku yaya zaki ji? Ko macen nan ta isa ta yiea yarki kayan daki idan kina da hankali ai y'ayan miji abin so ne abin a jawo a jiki ne domin baka san waye wane ba, koda baka kwadayin lada ai kana kwadayin duniyar tunda ita ta rufe maki ido har kike tafka iskancin nan Mardiya zan fada maki, ba zan kuma barin yarana shiga fadanki na iskanci ba Da ace kece da gaskiya kin san wacece ni ko ni ba zan yarda a wulakanta min ke ba, aman na lura dadi ne ya maki yawa kike ihun Allah ya kasheki ki huta Bana son ki yi nadamar haka, Aman kuma dahuwar mutun mai kosai Ita dai sauraronsu kawai take, ita ita ta san me take ganni da yaren nan Yaren dake tunanin ita tsararsu ce? Yaren dake kiran sunnanta kai tsaye? Muryar yayarta dake idasa shanyar mamansu ta ji da haushi haushi tana fadin" wai wani ita ya dace ta gaishe mu, matar da idan haihuwa ne ta haife ki dan kawai kina auren yayanta kuma tana matsayin shugabar garinkima sai kawai ta wani gaishe ki? Ai da na rainata kennan, ke da ko bakinta ta buda ta ringa mana zuba ni sai na raina mata wayau! .......................................... Tsuru ne ta yi sanye da hijab baki har kasa mai hannu ta saka Anmy a gaba tamkar ta fashe da kuka tana kallonta Muryarta na rawa ta ce" Anmy mana, dan Allah a bar tafiar nan na yafe Anmy ta juyo da mamaki tana kallonta ta ce" NAJEEBA, a kan me za'a bar tafia gannin likita bayan zuciyarki na maki suka? Mai martaba zai yi fitar boye dan dole sai ya ga wani bincike a tsaye a gaban idannuwansa dan bai yarda da kowa ba, gashi kuma clinik din daya ne zaku je shikenan da daren nan sai na barki ki tafi ke daya ko a fasa? Ki fita a idona na rufe ba za'a fasa ba kuma tare zaku je kima dauko alkyabarki dan kin san ba zaki bi shi haka daga ke sai hijab ba ko? Gabanta ne ya kara tsinkewa ya yanke ya fadi har tana dafe gaban nata, ita? Ta shiga motar sarki? Ta zauna a ina? Wato ya makure mata wuya ya karya mata kai ya halakata ya kasheta dama abinda yake nema kennan ya ga ta mutu? Bama wannan ba, ita da zata je wajen cen dan ta yi neman magana ta hanyar samun kula alakar soyaya da mijin matar nan idan suka je aka yi mata binciken a gabansa aka shaida masa lafiyarta kalau yaya zasu kwashe? Ita kam ta rasa meye aikin wannan jarababen! Idan ba jaraba ba ko abin aunawar ka nemi a kawo maka ai kawo maka shi za'a yi har dakinka na baci ka yi aune aunen aman shine zai wani je da kansa? Fuskarta ta kara shagwabewa ta ce" Anmy, to ya bani sakon mana na yo masa ni, ko kuma ki ce da shi ya tafi kawai ni fa na warke Anmy ta dago daga danna watar da take tana magana da mahaifiyar Najeebar kan Najeebar ne kuwa uwar na so ta hasko mata ita a hoto ta ganta aman ta rasa ta yanda zata daukar mata ita ta harareta ta ce" [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 19 Sai da Anmy ta harareta ta ce" NAJEEBA MUTALLAB, tashi ki dauko min alkyabarki Najeeba ta kara turo bakinta ta mike jikinta a sanyaye ta dauko alkyabarta fara aman kuma adon baki ne ya fi yawa a jikinta ta saka sannan ta bade jikinta da turare ta dauki yan cenji da wayarta ta dawo falo Jakadiyar dake duke ne ta shaifa mata cewa har sun fito ita suke jira Kollan Anmy ta kuma yi, sai ta ga Anmy din ta dauketa hoto da wayarta tana dan murmushi ta ce" ki fan saki fuskarki mana kema an mata Bakinta ta kara turawa gaba ta juya tana tafe a hankali tamkar wace kwai ya fashewa a ciki jakadiyar na biye a bayanta tana nuna mata inda zata bi din hanyar da zai bi ya fita ba budadiyar hanya bace Gabanta banda faduwa ba abinda yake, har sai ta fara jin da gaske wani zazabi na son kamata da karfin gaske ba da wasa ba Ita dai ta san ya tsaneta, duda bata san falilinsa na tsanar nata ba Takan kama mugun kallo daga gareshi, harma da kallon da zata iya kiransa na kyama Tun fa ta nuna mata motar sai ta ja ta tsaya kanta sade Najeebarma ta tsaya tana kallonta, muryarta na dan rawa rawa ta ce " mu, mu je mana Da sauri Jakadiyar ta dago, sai kuma ta mayar da kan nata tana dan girgiza kai ta ce" Allah ya huci zuciyarki amintacen sarki kadai ke shigowa wannan waje ko ZINARIYARMU bata taba saka kafarta a wannan hanya ba, domin hanyar boyayiyar fita ce ta sarki Sai ta ji ta kara tsorata da bayannin jakariyar, hanyar boyayiyar fita? To a kan me za'a zo da ita nan? Ko dai a nan ne ya yi niyar kasheta ya huta? Idannuwanta ta rintse tana jimke wayarta a hannunta Najeeba mana, meye haka ne? Ki je, ki je kawai, ki yi tawakali da Allah, ba zai kasheki ba ......zuciyarta mai karfin ke karfafa mata gwuiwa, nan take matsoraciyar shawararta ta ce" aa, ki rubuta message ki bari a wayarki, idan aka ga kin bace shine! Dan mutumen nan shi kansa kama yake da aljannu! Hannayenta na rawa ta fitar da wayar ta rubuta message ta yi seving a wayar nata sannan ta shiga karasawa jimin motar jikinta du a mace Mutumen dake tsaye ne ya saka gabanta yankewa ya kara faduwa Wani irin girma ne da mutumen tamkar wanda ya fi ka'idar tsayin dan adam Gashi da wani irin jiki mai abin tsoro, fuskarsa kuwa zata rantse bai taba sallah ba dan ba annurin hasken sallah a tatare da ita ko daya! Bude mata motar ya yi ba tare da ya furta ko A ba Da sauri sauri ta daka dan tsale ta shige motar gabanta na faduwa ta zauna tana ta waige waigen tsoro Wata kwalba ce ajiye saman kujerar daga tsakiya haka, kwalbar mai duhu ce sannan ga duhun cikin mota hakan ya saka sam bata gane ko meye a ciki ba Cikin motar ba kowa sai wani irin sanyin AC din dake kunne da kuma wannan dadadan kamshin turaran nasa Hannayenta ta dora saman cinyarta ta jingina da jikin kujerar ta saki wawuyar ajiyar zuciya da tarin sarewar dake adabarta A hankali ta ringa furta kalamai kamar haka" ke kuwa ta haka zaki mutu ashe Najeeba? Koba motar zai yi ya ce na yi hatsari ko wannan katon zai saka ya dane min hanci sai na daina motsi? Wayo su auntyna zaku yi rashina, wayo yayana kana ina? Yau du ban ganka ba kuma ban nemeka ba, yayana ka yafe min irin rashin jin da nake maka Wayo Anmyna ki gafarta min ba zan kuma yin karyar ciwo ba kin ji? Ya Allahna ka bani ikon mutuwa da kalmatus shahada , Allah ka yafe min laifukana ka rufa min asiri A kadan ta dauki wasu mintina talatin gaba daya ta gama hada zufa ta gama ficewa a hayacinta harda yar kwalarta, jira ai ko na result din exam bashi da dadi bale jiran kila wa kala za'a kasheka ne ko za'a wujijigaka a yarda banza? A yan sekwanin sai ta samu kanta da wata irin nadamar rayuwa, Yo ita me ta masa? Duk irin sufanta shi da take da abubuwan da ba su ba sai ta ringa fadin" wasa ne, ban taba tunanin hakan a cen cikin zuciyata ba, na tabata kai ha barawo bane kar ka kasheni ka rufa min asiri Bude gefen damar da aka yi, da murya kasa kasa ana fadin" takawa sannu sannu dan sarki jikan sarki, takawa sannu sannu mai damagaram ikon Allah, gabanka haske, bayanka haske d'a daya kake mai ja da arne Kamshin turaran nasa da ya fara shigowa motar mai yawan gaske ya sakata sauri kara buda idannuwanta sannan ta rabu da jikin kujerar ta yi gagawar gyara zamanta ta nutsu ta sada kanta tamkar wace ta zo makaranta Kafin ya daga kafarsa ya shiga motar ya jima kamar wanda zai hau mahaukacin doki Shigowa ya yi cikin motar ya yi wani irin zama irin na hamshaki sannan aka mayar da marfin aka rufe Mutane biyun nan sune suka shiga cikin motar , gabjejen nan shine amintacen sarkin shi ya ja motar a hankali sai wanda ke dan kurarin a gefensa rike da abubuwan makamai kamar wanda zai yi artabu da mugun abu a gabansa Kwalbar nan dake ajiye wace ta gaje wajen harma tana gogar jikinta ya dora fari kar din hannunsa mai dauke da jijiyoyi a jikinsa manyan gaske ya bude marfin kwalbar Hannunsa ya zirawa safar hannu ya saka cikin bakin kwalbar ya janyo abinda ke ciki Wani irin kuuuuuu da cikin Najeeba ya yi a lokacin da wutsiyar macijin ta dan hau gefen cinyarta har tana wani irin yawo da dan karfi tana neman a saketa Wuyansa ya rike raf sannan ya dan gyara muryarsa kasa kasa sosai ya ce" *bani matacen* Da wani irin gagawa na gefen direban ya buda wata kwalbar, ashe ita kuwa tana dauke da abin sanyi ne wanda zai hanna macijin rubewa ya yi tsami ya lalace ba tare da an yi binciken da ake son yi da shi ba Amsa ya yi ya dago kansa ya daidaita da mai ran Irin yanda yake dilo harshensa yana yi masa tamkar giftawar mashi ya sakata sakin wata wawuyar ajiyar zuciya gaba daya jikinta ya dauki rawa Irin yanda ya rike macizan a hannayensa sai shi kansa ya zama wani abin tsoron a gabanta Kamar mai cutar asthma haka ta ringa jin numfashinta na yi mata rawa Kallon macijin yake kallo irin na tsanaki Sai da ya gama a kasalance sannan a gajarce ya ce" *aman yaya aka yi shi wannan yake da kiftu a gefen kansa dayan kuwa bashi da shi?* Allah ya huci zuciyarka wannan kiftu da kake ganni shine kawai abinda ke bambance macizan da aka kyankyashe a rana daya Shi kiftun nan kala biyar ne, Irin wannan dan siririn shi ya kara shaida min cewa shine abokin haihuwarsa sannan kalarsa ne tak tak , du abinda wancen zai yi wannanma yana iya yinsa, Allah ya kara maka lafiya Ya karashe yana dan kara dukawa Bai kuma yin magana ba sai mika masa matacen sa ya yi ya karba da hannu bibiyu yana gagawar mayar da shi cikin kwalbarsa, sannan ya kara dago mai ran yana yi masa kallo irin na kurullah Tabas idan a da wasa ta yi karya ta yi cewar zuciyarta na suka a yanzun kam sukar take, gaba daya jikinta ya mace ya yi mata nauyi har bata iya daga dan yatsarta Idannuwanta kawai take yawo da su a kansa ta yi wani kasangar tana hangen gashi har ya sakar mata macijin ya kasheta Aman dan me yake son kasheni da maciji? Ya kasheni da hannayensa mana? Take tambayar kanta a kasan zuciyarta ga zufa ta gama wanke mata duban wani waje na jikinta Wutsiyarsa ya kara dokawa a saman cinyarta yana neman a sake shi ya kwaci kansa, irin yanda maciji ke wutsil wutsil dan kwatar kansa Hakan ya saka ta saki ajiyar zuciyar da ta kara sakata jin tamkar cutar nan mai shanyewa mutun jiki ya zama baya jin yana iya anfanar da komai na jikinsa da kansa ne ya sameta wato cutar hawan jinni da ilolinta Sai da suka yi tafia mai dan nisa suka samu wani waje mai dan duhu duhu sannan direban ya taka birki ya tsaya Wani shirun ne ya biyo baya na kamar minti goma, NAJEEBA ta ringa maimaita kalmar shahada daga yannayin da take dan ta dauka an zo wajen da za'a kashetan ne Gannin yanda take wani ringeshe a cikin motarsa ya kara bata masa rai, me ya sa Anmy ke yi masa haka ne? Yau da ace cikin kannenta ko yayunta ne bashi da damuwa sai ya fita da su a cikin motarsa da su din ya yarda da su cewar koda basa jin magana to fa basu wulakanta kansu ba Aman sai ta saka shi daukota a motarsa mai tsafta, ta shigo masa mota tana garwaya numfashinta da nasa mai tsafta haka kawai ta zauna a wajen da yake ringesa kansa dan ya huta? Ya zama wajibi ya batar da motar nan sunna dawowa domin ba zai kuma shigarta ba Da ta san irin yanda yake kyankyaminta, da bata yi gigin yarda ta shiga wajen da yake ba Halayenta sam basu yi masa ba Muguwa ce, azaluma ce, makaryaciya ce, mazinaciya ce! Idanma bashi da tabas shi zai samowa Anmy shaidar da ba zata iya hanna shi hukuntata a bainar nasi ba! Ya yiwa kansa alkawarin a kanta zai tsoratar da matasan samari da matasan yan mata da manyan yan iskan garinsa domin sai ya yi mata hukunci bulalar da ta hau kanta na zina da aurenta komai yawanta shi yasa yake so ya yi mata damka irin na gani da gani Muryarsa a dake ya ce" *ki fitar min a mota!* Maganar nasa rairai a cikin kunnayenta domin dama sauraro take Dan zabura ta yi ta dago tana ta zarar ido Amintacensa ne ya fita dan bude mata bangarenta domun dama bai hude bane dan yana jiran umarni Yana budewa SHAheed ya watsa mata damin kudi a jikinta muryarsa still a dake ya ce" *nan da awa biyu ki tabata mun sameki a nan* Yana gama fada ya kuma komawa ya gyara zamansa Ai da wani irin sauri ta fita a motar da kudin a hannunta dan a saman cinyarta suke, ita a yanzu bata da bakin da zata iya budawa ta ce wani abu ko ta meni yin wani abu na rashin kunya Tana fita ya mayar da mitar ya rufe ya zagaya da sauri ya shige suka daga Gaba dayanta ta idasa zaro idannuwanta ta dora hannayenta saman kanta a fili ta furta" wayo wayo wayo innalilahi wa'ina ilaihi raj'une yau na ga masifa ido da ido yau na yi mota daya da arne marar mutunci marar tausayi mai cin danyen nama! Na rantse macijin nan ka fito da shi ne dan ka je ka kashe wani, yo waye bai sani ba cewa kashe kashe kuke a tsakaninku dan kujerar nan da kuke sama Allah ya isana da ka tsoratani, kuma na rantse sai ka sauka sarki mai adalci ya hau kujerar nan annamimi mai ido kamar na mujiya! Sai a lokacin ta kalli kudin da ya zuba mata Dami guda ne na manyan kudi sabin bugawa domin yanda suke mike suke hade zai nuna maka cewa sababin fitowa ne daga banki yan jika goma goma je da zara iya rantsewa ba karamin kudi bane Abin dake jikinsu ta kunce ta watsar a nan sannan ta bi su da yawu tana cire alkyabar nan da ta hana mata sukuni tana ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Allah ya tsareni da cin haram! Kai ko abincin fada ina cin wanda na san Anmy ta bada kudin aka kawo domin ban taba cin cimar da ta shafi shinkafa, ko wani abin da na san daga aljihunka zai iya fitowa! Yanda ka tsane ni, ni nama fika tsanarka azalumi kawai mai cinye kudadenmu mu talakawa Ta saman kudin ta bi tana tafiyarya da dan sauri dan a lokacin da ta duba agogon hannunta har ta ci minti goma a kan wanda ya barta Saloon dinta ta je suka gagaisa da masu yi mata aiki sannan ta kara duduba komai ta ware kudadenta ta bara masu na anfannin yau da gobe kafin ta dawo nan da kwana hudu Daga nan sai ta nemi mai babur ta dane tace da shi ya kaira wajen Hashimu mai nama Agashe ta bashi ya amso mata mai ruwa ruwa har na jaka biyar tukunya ce sannan ta suka kuma daukowa suka nufi wajen saida ice cream Haka take murmushi gannin yau zata sha mutumen nata wato ice cream dan ta kwana biyu bata sha ba domin Anmy bata barinsu yawan shan sanyin nan ko zaki Siya ta yi har roba biyu tace da shi ya kaita stade Yana ajiyeta ta dauki har jaka biyu ta bashi sannan ta ringa takawa a hankali a kafarta har ta karaso wajen mai gadin wajen suka gaisa da mutunci sannan ta samu ta shige cikin nutsuwa ta nufi wajen zamanta wajen hutunta Tana zuwa ta zauna tana gannin yanda daidaikun mutane kowa ke sha'anninsa, a wajenfa babu yaku bayi, du manya ne kowa kuma na sha'aninsa Ledarta ta buda mai dauke da naman nan ta fara ci a hankali tana lumshe idannuwanta dan tana mutuwar son tukunya Sai da ta ji ta yi hani'an sannan ta dauko ice cream dinta roba daya ta buda ta gyara zamanta ta saka yar cokalinta tana dan diba kadan tana sakawa a bakinta Wayarta ta dauka ta rubuta message kamar haka" *Na so zuwa dan gannin likitan zuciyana, sai dai na cika da fargabar irin yanda ya kasance mau cike da kwarjini a idannuwana, na yi masa kallon tsaf din da har na lura da irin hararar da matarsa ke jefa min wanda ya sakani jin tsoron zuwa wajensa a wannan rana Shin likitan zuciyana zai yi kin alfarmar fadawa gimbiya cewa na zo ya auna ni? Zai taimaka ya hada ji da wani likitan wanda zai auna ni? Domin ina tsoron tsumamun idannuwansa su sakani tsumewa na lume a cikin kogin da ba zan iya fitowa ba.....sako daga NAJEEBA MUTALAB* Tura sakon ta yi ta ci gaba da shan ice cream dinta Ta kuwa harbo a daidai, domin a lokacin ya gama shiryawa tarbanta, matarsa kuwa ta gama shiryawa cin ubanta a kofar clinik din domin zuwan wani bako a cikin bakar mota sidik ya saka baki daya aka fitar da kutanen dake ciki sai majinyata da masu jinyarsu daidaya, hakan ya sakata dakatawa a kofa ita da babar y'arta wace ta rakota su ci uban NAJEEBA! (HOUM) har tsuma hannunsa yake a lokacin da ya karanta mesage din da sai ya rantse bai taba karanta mesage mai dadinsa ba ya shuga bata amsa kamar haka *bukatunki, ki tabatar da amsasu ne hannu bibiyu a wajen likitan zuciyarki, wa kike so ya duba maki zuciya da ya fi ni? Ni zan kula da ke na ririta zuciyarki na yi mata fadan da ba zata kuma yi maki suka ba, zan sanarwa mamanmu cewa kin zo, aman zan biki bashi ko ki zo na duba ki ko na zo na duba ki, domin bana wasa da zuciyar mai dauke da zuciyata!* Samun kanta ta yi da sakin murmushin mesage dinsa, lale ba laifi kalamansa zafafa ne da har suka sakata kwafarsu Lale yana da tsumamun kalamai kuma ta yaba To yaya fagen aljihunsa? Ta tambayi kanta tana murmushi Sosai take jin dadin iskar wajen harma ta cika da mamakin ina mai kwali ne yau? Dan bata gansa ba, ko ya shige wani wajen ne? Ko ya koma abujar? Lokaci na shige mata bata sani ba domin ta dukufa tana amsa mesage din tarin samarinta kowane daidai da takun tafiyarsa ciki kuwa harda sojanta da likitanta, da ambasador dinta Sosai take nishadi harma yannayi tsoro da firgici suka barta Bakinta take tabewa idan ta ga wani mesage din, Takan girgiza kanta idan ta ga sakon kowani gara sai ya daki kirji ya turo mata sako Wata yar dariya ta yi a bayane a lokacin d ata tuna maganar yayanta da yake cewa, mace idan ta zama ita kowama saurayinta ne, zata ringa haduwa da samarin kala daban daban, su gajale, su zinataile su wawaye, su mahaukataye da sauransu Najeeba, ki kula a garin damagaram, domin mai damagaram ba zai hukunta wani dan ya maki laifi ba..... Wannan maganar ita ta tunatar da ita da maganar dunkum cewar awa biyu ya bata Wata irin zabura ta yi ta duba agogo Karfe goma ce ta gota harda minti arba'in Wato ta dauki awa biyu da minti talatin da bakwai Wata irin dirowa da ta yi ta mike a guje ta saki ledar naman da ta yi niyar kaiwa yan uwanta da uce cream din ta aniya dankara gudu da alkyabarta a hannunta tana ihun kiran kabu kabu Tana tsayar da dan acaba ta bashi jaka biyar hakoranta har sunna hadewa ta ce" ka falfala gudun mutuwa da ni ka kaini magama gudun hanyar gidan sarki Mai yin na banzama bale harda kudi da kuma rokon mai hawan? Ai kuwa ya buga babur ya tayar ya warcu babur a dubub lamba ya nufi wajen da aka bukata Adu'a kawai take tana saka alkyabarta jikinta na rawa tana fatan Allah ya sa bai zo ba Na mutu ta fada a dan fili a lokacin da ta ga motarsa tsaye a wajen da suka ajiyeta, sannan daidai kudin nan da ta watsa da yake dare ne Allah bai kawo wanda hankalinsa ya kai wajen ba Shikenan ta kuma fada tana son dirkowa aman sai da dan acabar nan ya sadata gata ga motar yana washe mata baki irin ya mata abin kirkin nan Sai kawai ta ji ita kam ta gama yawo, Dokar Anmy ce kiyaye acaba wace shi ya dora ita kuwa ta dorawa y'ayanta Yakan fadawa Anmy cewa, bai ga daraja a macen da zata wara kafarta ta hau acaba ta zauna jikin mai mashin ya jata ba Tuki da ya gaji birki da sauransu komai na iya faruwa a babur din nan Gaba faya jikinta na rawa ta shiga kiciniyar saukowa Kyar ita yake kallo, tun da suka karaso kusan minti talatin kennan ya ga kudadensa da ya bata a zubde a kasa Wato ita bata cin halal shine ta je ta nemo haram dinta? Sai kuma irin jiran da ta saka shi yi, zai rantse da Allah ko mahaifiyarsa bata saka shi jira daga lokacin da Allah ya kara daga darajarsa ko mamansa ke bashi daraja ta kiyaye lokutansa Sai gata kuma an kawota a babur har kusa da motarsa Karasa sauka ta yi tana yiwa mai babur ihun" ka yiwa Allah ka yi tafiyarka na ce ka bani cenji ne? Sai hajia ya fada yana sara mata sannan ya tayar ya juya abinsa Ja ta yi ta tsaya a wajen da take ta kasa karasawa wajen motar bale har ta shiga Gaba daya ta gama yankewa kanta hukuncin idan dazu Allah ya kubutar da ita yanzun fa? Zabura ta yi a lokacin da ta ga yana......... More cmnt mr pag😌 [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 20 Zabura ta yi a lokacin da ta ga ana sauke madubin bayan wanda ta tabata a nan yake zaune Sosai aka zuge shi sannan ya sauke dubansa kakausan duban nan mai abin tsoro a kanta Fitsarine ta ji zai zubo mata daga mararta Da sauri ta juya ta matsa sosai tana dan rawar nan dan ta rike shi kar ya zubo Haska wajen ta yi ta yi bismillah ta janye wandonta kasa kadan ta duka ta shiga fitsarin nan domin idan bata yi shi ta tabata zata yi shi a motar cen Kansa ya yi saurin kawarwa daga wajenta, amintacensa kuwa dama kansa a sade yake yana cike da mamakin lalle yarinyar nan ta isa Su suke tare da sarki SHAHEEd , wato gurnanin zaki Su suka san waye Sarki SHAHEED Yaya aka yi ta taka doka haka har haka? Sai da ta kusan karasa fitsarin ta tuna bata da ruwan kama ruwa Gaba daya ta ji jikinta ya kwashi wani yamyamyam na kyamar kazanta Bata wasa da tsaftar wajen nan ko da wasa gashi yau ta yi fitsari a wajen nan sannan a gaban sarki gashi babu ruwa Sai da ta gama sosai ta cire wandonta dan ba zara iya mayar da shi ba ta mike a hankali jikinta na ci gaba da rawa Tana tunkaro motar ya kuma dagowa yana yi mata duba irin na mamakin fitsarine ta yi d agaske haka gabansu ? Lalee ta cika rashin kamun kai da rainin hankali Kara datse lebensa ya yi na kasa yana gannin lokacin da ta karasa isowa ta ja ta tsaya daga nesa gaba daya jikinta na rawa hankalinta a matukar tashe baki daya wani kuzarinta ya bace sai tarin tsoron dake cin ranta Dubansa ya cire daga kanta ya kalli wajen amintacensa Sai da ya dauki mintunna kafin ya ce" bani faro Da sauri ya buda wajen da ake saka ruwan ya dauko ya juyo gaba dayansa ya dan risina ya mikowa sarki SHAHEED ya mika hannunsa na dama ya amsa yana rike da ruwan Cen ya saka hannunsa zai bude hakan ya sa amintacensa saurin kokarin budewa dan ya bude masa Bai bashi damar yin hakan ba ya dakatar da shi da hannunsa A hankali ya bude kofar Ziro kafarsa da ya yi ne ya saka NAJEEBA daga hannayenta duka biyu ta dora saman kanta Gaba daya ta ga wajen ya masu kadan idan tace zata gudu ta rantse ba inda zata je zai kamata Ruwan nan masu sanyin gaske sannan babar butali ne ya yi tsaye daga jikin motar Da hannunsa ya yafito ta Kafafuwanta ta shiga dokawa a hankali tana jin uwa ta ce na ki, sai dai gannin daga ita sai shi fa sai mai shigar masa taraya sai kawai ta ji kafafuwanta na kaita inda yake tsaye Daga dan nesa ta ja ta tsaya ta sada kanta Kansa ya kara gyadawa gannun bata zube ta ringa yi masa fadanci ba Rabonsa da ya ga mutun ya yi tsaye haka kansa da kansa ba tare da ya bashi izinin hakan ba tun barin garin sarkin agadez , sai Anmy wace take mahaifiyarsa Ko matarsa takan zube ne kafin ta nemi wani lamarin a wajensa Yatsarsa baba da ta tsakiya ya hada ya dan bada wani sautin da ya sakata dagowa Kudaden daje zube a kasa ya nuna mata da idannuwansa Itama kudaden ta bi da kallo domin wutar motar a kunne take Da sauri ta karasa ta duka tana tsintsincewa Sai da ta gama dauke dukan wa'inda take ganni ta harhada su ta karaso kusa da shi wannan karron ta miko masa su Hannayen nata da kudin duka ya bi da kallo, Wa shi? Take mikowa kudi haka? Sai abin ya so bashi daria a kasan zuciyarsa Idab ya fahimta yarinyar banda rashin kunya harda rashin hankali ke damunta Yau gashi da rigar sarautarsa a tsaye a gaban yar yarinyar nan marar kunya tana miko masa kudi hannu da hannu a tsaye kikam Baban goran ruwan nan ya saka hannunsa ya bale cikin dakiya ya mika mata muryarsa a kausashe ya ce" *ki tsaftace najasar dake tare da ke* Najasa? Ta tambayi kanta, ko fitsarin da na yi? Ta kuma tambayar kanta Amsar gioran ruwan ta yi ta matsa gefe kadan ta duka ba abinda ya dadata da kasa domin ita ai ganni take dare ne yayama aka yi ya gane fitsari na yi? Take tambayar kanta Ruwan sanyi ne da shi, gata bata saba anfani da ruwa masu sanyi ba sai dai ita kanta yanda take jin jikinta na yi mata kaikayi dole ta yi anfani da ruwan tana kara matse hikinta ta mike tana ajiyar zuciya Ruwan ta riko ta juyo sai dai ganshi a tsaye a wajen da yake Dan bakinta ta tabe a ranta tana ayanna wato bayan cin haram ko dai kwarto ne? Yo wannan saka ido har ina? Karasowa ta yi kanta a sade a kasa dan nesa da shi kadan Gannin bata yi abinda ya yi jiyar sai ta yi a yau a waje a bakin titi ba ya saka shi juyawa kusa da tagar amintacensa Murya a kausashe ya ce" bani biyu Dauko masa biyun ya yi masu sanyin balaki ya miko masa Amsa ya yi wannan karron ya ringa takawa cike da kasaita da isa har ya karasa inda take tsayen Buda goran ruwan ya yi cikin dakiyar fuska ya ce" ki dauri niyar yin wankan janaba a zuciyarki Da sauri ta dago kanta da wani irin tsoro da mamakin jin abinda ya fada Sai dai kafin ta gama fahimta tuni ya shiga tsiyaya mata wannan ruwa mai sanyin balaki tun daga saman kanta mai dauke da alkyaba da hijab a kasa ruwan na ratsata har cikin jikinta ga yannayi na sanyi ga kuma tana da cutar huka wato athsma Gaba daya ta rikice jin saukar ruwan nan hakan ya sakata kwala kara tana furta" ANMY kafarta ta daga da niyar kwatar kanta sai dai abin ya gagara dan wata damka da ya yiwa hannun nata da hannunsa daya ya kuma bale dayan da hakorinsa shima ya daga tun daga kan nata ya shiga bulbule mata shi Da karfin gaske ta fincike Alkyabar dake saman kanta da dayan hannunta, ido rufe ta yi cikinsa ta rukunkumeshi gaba daya jikinta na rawa tana jin numfashinta na neman fara bugawa Bakinta ta buda zata bashi hakuri sai dai ta gaza sakamakon jan shedarta da ta fara har numfashin ya fara wani kara sama sama yana hiiiiiiiiik, hiiiiik tamkar wace ta zo fitar rai Sarai ya san cutarta kuma ya san ta tashi ne aman bai daina ba sai da ya gama bulbule mata yana son bambareta da jikinsa aman ta mane masa tamkar cingan Yana gamawa ya saka hannunsa ya dago fuskarta Muryarsa a kausashe yana yi mata duba irin na tsana ya ce" me ya sa kika zabi zubar da mutuncinki? Idan na iyayenki bai dameki ba naki fa? Ke kin kasance sakarya a cikin mata Ban taba jin kyamar halita irin yanda nake kyamar halayanki ba, na tsani na ji a cikin kanena akoy ki! Ki sani tsakanina da ke ba alfarma ko tausayawa! Magana ta karshe da zan maki bayan ta idannuwana da nake maki kan ki kiyayi hada hanya da ni, sarkinki nake ba tsaranki ba! Idan ke takamarki *Mage ce* ni kuwa *kaifin wuka ne NAJEEBA MUTALAB!* gaba daya ta idasa sikewa ta tafi luuuuu ta fada a jikinsa sumamiya Baya tare da wani damuwa ko firgicin gannin ta summe masa Hasalima idasa rikota ya yi ya turata motar sannan ya shiga gidan gaba domin ko suturar jikinsa kyamatarta yake bare zama kusa da ita a karo na biyu bayan ta gama wannan wulakancin Amintacensa kansa a kasa, magangannun sarki tas a kunnayensa sai dai bai san wanka ne ya mata da kayanta a saman titi ba A hankali ya tashi motar zai nufi cikin gida, muryarsa a cinkushe ya ce" Degza da allura Yana gama fada ya maida dubansa bakin titin yana mai bale agogon hannunsa A nan ya yarda agogon , ya kuma bale botiran rigarsa daga ciki Da gudu ya shiga pharmacy ya amso maganin da allurar Yana kawo masa ya duka ya mika masa sannan ya juya ya shiga wajen direban Ruwan Allurar ya fashe kanta ya tsira tsinnin allurar ya zuki ruwan ya saka kwalbar cikin ledar Sunna karasawa cikin gida hanyar sirrinsa ya fito da kansa cikin takamarsa ya buda bangaren da take Hijab din nata ya kama ya cire dan samun wajen da zai mata allurar Rigar dake kasa ta atamfa ce mai damamen hannu Jikinsa ya laluba ya ciro wata yar siririyar wuka mai kaifin balaki ya kama rigar ya yaga wajen hannun Allurar nan ya caka ya tsira mata ba tare da ya bi ka'idar a hankali ba domin zafin tsiya ne da ita Yana gama tsira mata ya dauki ruwa ya dan warwatsa mata A zabure ta farka daga summar wahalar da ta yi, idannuwanta ne suka sauka a kan macijin da ya cire masa dafinsa suka zuki abubuwan bukata a jikinsa hakan ya sa ya kasa motsawa sai ya ki mayar da shi cikin kwalbar dan bashi da niyar kashe shi, zai mayar da shi wajensa ne Gefen fuskarta na gogar jikinsa hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya ta koma duniyar summa daga kwoncen da take Tsaki ya ja a cikin zuciyarsa gannin summan fa ta kuma yi Dubansa ya kai wajen amintacensa Ba zai iya tura shi ya kaita bangaren Anmy a irin wannan lokacin ba, idan kuwa shine zai kaita dole ya bi ta hanyar da zata sada shi da fallon Zinariya sannan ya bi ta fallonsa ya bi ta doguwar hanyar da zata kaishi bangaren Anmy din ba tare da ya bi ta hanyar da kowa kan iya ganninsa Hannunsa daya ya mika ya daukota Dauka irin na yara ya yi mata a hannayensa bai rufe motar ba bai masa magana ba ya juya ya nufi bangaren Zinariyar A daidai lokacin tana zaune a fallo ita da yayarta sunna cin abincin da ta saka aka masu wato gasashen naman rago ya ji kayan hadi sai turiri yake sunna ci sunna hirarsu hankali kwonce Kasancewar hanyar ta sirri ce, ba'ai masa iso ko ta saka ran zai iya zuwa a irin wannan lokacin Jin karar bude wajen ya sakasu waigawa a tare Da yake kofar mai dauke da dan haske ne sai suka ga yannayin tsayi da fadinsa hakan ya sa da sauri suka mike yayar nata ta warci hijab dinta ta saka haka itama Kofar ya turo da kafarsa Kasancewar tafiar nan tamkar ta giwa a jinninsa ne ko yanzu ba sauri yake ba a hankali yake tafia da uta a hannunsa Gaba dayansu suka zube kansu a kasa har sunna hada baki wajen furta" barka da war haka mai martaba Bai iya amsawa ba, da kansa kawai ya dan gyada kai, Jin kamar zai wuce da kyakyawan takalminsa ne ya saka Zinariya dago kanta a hankali Gabanta ne ya kwonci kwonci ya yi faduwar da ita kanta ta kusa zubewa daga duken da take Ya shige ciki hakan ya sa ta kara zabura ta mike Da sauri yayar tata ta riko hannunta ta ce" ina zaki je? Warve hannun nata ta yi ta ce" baki ga waye a hannunsa ba? Yarinyar nan da nake fada maki nace da ita yar talakawa ta mari fuskana itace a hannun mijina mai daraja me ya kawota bangarenmu? Me ya hadata da shi? Me ya sa ya dauketa da hannayensa masu matukar daraja da kima a duniya baki daya? Aman idan kika je me kike son yi bayan kin san sarkinki ne shi kuma kanwarsa ce? Ta fada tana son tareta Hannayenta ta kuma warcewa tana kallonta ido cikin ido ta ce" shi ya sa kika kasa gagarar kishiya! Koda kare jinni biri jinni ni Zinariya sai na kafa tarihin zama daga ni sai mijina Babu shegiyar da ta isa ta hau hannunsa haka ya bi ta falona na barta da hankalinta da ranta koda kuwa zan yi yawo tsirara ne! Tana gama fada ta juya da sauri tana bin bayansa, yayar tata kuwa ta yi gagawar daykar waya dan kiran mamansu Tun da ya shigo Anky dake zaune da su Zahrau suka zabura sunna kallonsa Da sauri Anmy ta karasa dan itace kawai zata iya tarbansa Har hade maganarta take wajen fadin" sususubahannalah, Shaheed me ke damunta kar dai ciwon zuciyar ya yi tsanani Irin yanda ta rikice yake kallo, da ta san shagalinta ta je ba asibiti ba zata rikice haka? Anmy ta ce" likitan ya yi kurana yake ce min da sauki aman zata koma ya kara bincikata, wai summa ta yi ne Shaheed? Ta fada tana rungumota jikinta a lokacin da ya ajiyeta saman kujera Tsayawa ya yi yana kallonta, yayaunta kuwa du suka duduka kansu sunna faman yi masa barka da warhaka Bai baiwa Anmy amsa ba ya juya a hankali zai tafi Har ya kusan fita ya juyo, muryarsa a hade ya ce" ZAHRAU, ki shirya aurenki karshen watan nan idan Allah ya aminta Yana gama fada ya juya ya fice a dakin Kicibis dukai da ZINARIYA wace ta labe dan jin abinda ya hada shi da ita har ya rungumota haka, sam bata ji takun fitowarsa ba Bai kulata ba ya fice ya barta kai sade tana fadin" a huta lafia mai damagaram Yana fita suka rikice, kan mai dankarawa da gudu ya daukowa Anmy ruwa, sai mai kara rungumarta Da gudu Anmy ta yi ciki dan kiran likitansu , Tana shiga Najeeba ta ja dogon numfashi Idannuwanta a rintse tana jikin Zagrau bata bude ba ta furta" *BAN TABA TSANAR HALITA IRIN YANDA NA TSANEKA BA! NA RANTSE SAI NA RAMA A KANKA KO A KAN ALADEN MATARKA!* a tsorace suke kallonta, Zahrau ta dora hannunta gefen fuskarta a hankali ta buda bakinta zata yi magana sai ga Anmy ta fito da wayar a kunnenta tana fadin" ...............😓 [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 2 1 A sume ne take docter ki zo yanzun Da sauri ummulkhair ta ce" Anmy ta farfado Anmy ta ajiye wayar tana karasowa itama ta duka ta kamo Najeeba ta rungumeta a jikinta tana fadin" Najeena, meye? Jikin ne ya saka kika suma? Likitan ya nuna min da sauki kar na damu kuma yayanku ya shigo da ke a summe meye ne? Najeeba kam irin yanda zuciyarta ke kunna bata da bukatar komai sai na kadaicewa Ga jikinta du a jike yake gashi zuciyarta na yi mata zafi tamkar ta ciji babu Anky, zan kwanta Tsurawa fuskarta ido Anmy ta yi na dan lokaci kafin ta shiga taba jikar jikinta da cirar hannun rigarta sannan ba alkyaba a tare da ita ba hijab dinta Tana kallonta ta ce" me ya fari da ke kika dawo min ba a yanda kika fita ba? Najeeba ta ja numfashinta da kyar ta ce" Anmy, athsmana ne ya tashi, Anmy ta kara jin tausayin yarinyar fiye da sauran yan uwanta Kamata suka yi suka nufi dakinsu da ita Saman bed din suka shinfideta Anmy na ta shafa kanta tana kallonta A hankali ta ce" Allah ya baki lafia bara na je na fadawa yaya cewar da sauki Mikewa ta yi ta juya ta fita Tana fita da sauri Zahrau ta riko hannayenta ta ce" me ya faru da ke? Me ya maki? Waye kika tsana? Me aka yi? Gaba dayansu hankalinsu a tashe yake su duka Najeeba ta cije lebenta na kasa tana jin wani irin kunci a zuciyarta Muryarta a kausashe ta ce" SHAHEED NE, Shaheed ne ya min wankan janaba Da karfi suka kusan fadi a tare kan me cewa" quoi? (What?), sai me cewa Me? Idannuwansu a zazare a waje cike da tsoron abinda ta fada din A hankali ta ja hancinta ta tashi ta dan jingina tana kallonsu, sai da ta kuma lumshe idannuwanta ta bude , a hankali ta kabarta masu abinda ya faru Kwarai sun ji tausayinta sai dai Zahrau na budar bakinta sai ta ce" Najeeba, rashin jin maganarki ke jaza maki fitina Ke da ya sauke ki ya ce ki je ku hadu a lokaci me ya hana ki zuwa ki yi jiransa? Ummulkhair ta ce" bama wannan ba, tsakani da Allah ciwon zuciyar nan dama karya ne Najeeba? Ke kam bakya jin magana ban san me ke kwakwaluwarki ba Ummukulsum ta ce" NAJEEBA, kudin da ya baki kika watsar? Sannan kika yi fitsari a gabansa a gaban yaronsa? Me kike so ya dauke ki? Najeeba ko bai yi tunanin baki da kamun kai ba ai kema kin san baki da shi ko? Najeeba ta lumshe idannuwanta a hankali ta ce" eyah, me zai hanna ku taru ku min dukan tsiya dan na taba dan gwal? Dagowa ta yi ta firfito da idannuwanta ta dauki hannunta ta nuna kanta ta ce" na rantse da wanda raina ke hannunsa bashi da mutunci, kuma bai sani bane irin yanda ya yi ikirarin ya tsane ni na fi shi tsanarsa, zan nunna masa a aikace, ba dai ni Najeeba ba? Nice ya kwontar jikin maciji? Kallon Ummukulsum ta yi ta ce" ji wani kililin kasau da ita kamar ta Allah ke nan kyankyaso ne ya shiga rigarki kika cire rigar da wasu kannanun nonuwanki kina ihu a gaban kannenki, Ummukulsum ta ce" ai dai ni ban yi fitsari a gaban mazan da ba maharamaina ba Ta buda baki zata rama Zahrau ta ce" kun ga ku saurara mu ji da abinda ya sha mana kai mana haba da Allah, ku kawai baku da aiki sai fitina? Maganar zaki rama bata taso ba! Ki rama me? Ta yaya? Ki bari ki mutu maza su kaiki ba mata ba dan walahi da zaki ji tarihin bawan Allahn nan sai jinninki ya hau, baki yi mamakin yanda aka yi yake damkar maciji da hannunsa katon maciji ba wani jariri ba? Ke ki kiyayi maza walahi bana son fitinar da zata saka ransa ya bace ya batar da ke Najeeba! Ke kin san albarkar anmy kike ci, kin san albarkar su Abih kike ci, aman kina da izgili a abinda ya shafe shi, ke idan ba rigima ba ina ke ina tsayawa kafada da kafada da shi? Ai ko ba sarautar dake yawo a jinnin jikinsa ba shi din yayanki ne, yaya aka yi kike girmama yaya DAYABU ne? Bale ko a cikin mutane akan yi wani halayensa daban! Najeeba mutumen nan adali ne, aman kuma inaai tabatar maki ya fi macijin nan da ya sumar da ke balaki idan kika tankwalo hakan zaki samu domin mu yan uwanki ba abinfa zamu iya yi maki NAJEEBA! NAJEEBA dake kallonta ta yi murmushi tana dan girgiza kanta, a hankali ta dan yi atishawa tana dafe daidai kirjinta ta ce" tabas shi din wani ne na yarda, shi din ya girme ni kuma na yarda Dubansu ta yi ta yi murmushi ta ce" sai dai ni din kamar yanda ya ce ne *MAGE ce ni mai kwonciyar d'aukan rai* zan dauki ransa a lokacin da bai ji ba bai gani ba bai san da zuwan lamarin ba Tunda ya yi saken na kasance mace......zan nuna masa irin girman karfina a kansa! Shi da takobi take suka, ni kuwa da kalamai nake suka idan na tashi harbi da tawa kibiyar nakan harbi wajen da baya jin magani! Ummulkhair da ta bude victago ta lakuto ta nufi wajen kirjinta tana shafa mata a hankali ta ce" ki dai bi a hankali, kar kibiyar ta kasance mai zuwa ta dawo ce Ummukulsum wace itane ta fi su tsoro ta ce" ni dai dan Allah ki yi hakuri, a bar maganar wata ramuwa dan ba wajen bane, ko dan Anmy ai ya isa ya taka ki ki sada kanki, kinafa ji NAJEEBA yanzu yace auren aunty Zahrau karshen watan nan, ke kin ga Anmy kanta sai da ta zabura ta kale shi hakan na nufin ita kanta bata san da maganar ba bale Abih kuma ya zama wajibi su masa biyaya, ke kina kasa zaki wani ce ke aa? Da yake ta fi rainata dama yan watani ne ta bata ba shekara ba sai ta ce" Ummukulsum ni abin ya fi maki ciwo dan nace zan rama ko? To na fada dan Allah ki dakeni ki huta mana tunda na ta a abokin tagwaitakarki! Dawowar Anmy da waya a hannunta ya saka su yin shiru Wayar ta mikawa Najeeba tana mai tsareta da mugun kallon idan bata amsa ba komai na iya faruwa Wayar ta amsa da hannunta na hagu tana kallon saman screen din Wauh na ce a lokacin da na ga wace ke zaune itama tana kallonta Kallon kallo suke yiwa junnansu, har sai da matar ta dan saki murmushi ta lumshe idannuwanta ta bude cike da isa ta ce" ke yar Mutalab sai uwarki ta gaisheki ne? Ta kasan idannuwanta ta kalli matar aman bata furta ko A ba Murmushi ta yi tana yi mata kallo mai hade da madaukakiyar soyaya irin ta d'a da mahaifi Ita kam ta ina zata bi y'ar tata ta dawo mata yanda take so? Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" yaya jikin ki? Najeeba dai bata ce komai ba, Anky kuwa bata takurata ba ko amsar da ta yi ai ta yi kokari, hakama yan uwanta Zahrau ce ta leko tana daria ta daga hannunta ta ce" Mama i miss u Warcewa Ummulkhair ta yi tana ihun cewa" Mama, ni ke missing din ki Ummukulsum ta amshe ta ce" mama ba ji ce tagwayenki ba? Daria itama take a hankali ta dan juya idannuwanta wa'inda sukai wani farr da su gasu da girma masha Allah ga gyaran da suke dauke da shi ta ce" an matana, baku san irin yanda nake missing dinku ba, ina kewarku fiye da tunaninku, ina so na zo na ganku, na rungumeku, na ji me kuke ciki, ina son halartar auren Zahra, ina nan ina yi maku tanadin abubuwan da idan kuka saka baki daya damagaram sai ta girgiza Bakinta ta tabe ta mike kwonciyarta tana lumshe ido, a kasan zuciyarta kuwa tana fadin" abinda kika fi kauri a kai kennan, abinda ya fi maki ni kennan wato abin duniya! Anmy ta karasa kusa da ita ta ja bargo ta rufa mata, dan zaunawa ta yi gefenta a sanyaye ta ce" NAJEEBA Kallonta ta yi da kallo irin na wanda take iya yiwa mahaifiyarta Dukawa Anmy ta yi wajen goshinta ta yi mata kiss a goshin nata a sanyaye ta ce" ki huta kin ji? Dan ina so mu fita da ku duka gobe in sha Allah Kanta ta dan gyadawa Anmy kafin ta maida idannuwanta ta lumshe Su kuwa hira suka sha da mahaifiyar Najeeba wace du wasu abubuwa irin su wani lumshe ido, su shan iska, su shagwabe yannayi baki daya nata ne Najeeba ta kwasa, ba wai tana yi dan ta birge namiji bane, abinda dai ta kara a kai shine ta fahimci yana tsuma mazan sai take kara sakar masu shi Kayan nasa ya tsurawa ido kafin ya watsar da su cikin kwondon kayan wanki Kasan shower ya tsaya ya dora hannayensa jikin garun wajen yana jin saukar ruwa a jikinsa Sai da ya gama ya darje jikin nasa da sabulu da soson wankansa kafij ya fito daure da tawul mai tsayi A hankali ya karasa wajen miror ya tsaya Turarensa ya dauko ya yiwa jikinsa bari da shi kafin ya jefar da kwalbar dan ya kare sai wani Idannuwansa ya dan kurawa ido, yar yatsarsa ya kai wajen da bakin abin ya yi yar kwana tamkar wanda yake saka kwali An haife shi ne da kwali a idannuwansa, shi kansa baya yiwa kansa kallon tsaf domin kwalin nan na tayar masa da tsigar jikinsa shi yasa baya matsewa mutun duba ko yace zai buda girman idannuwansa a kanka domin bai san yaya zaka ga idannuwan nasa ba Juyawa ya yi ya ciro wata farar jalabiya marar nauyi sosai ya saka a jikinsa sannan ya saka dan gajeran wando Wajen bed dinsa ya karasa ya kwonta yana mai adu'ar tsari dukan motsinsa Rmt din Ac ya laluba ya dauka daga kwoncen ya kara masa karfi ya sada shi daidai kansa sannan ya lumshe idannuwansa Tunanika ne birjik a cikin kwakwaluwarsa shi har ya yi watsi da abinda ya faru tsakaninsa da Najeeba domin ya ajiye hakan a fagen bata da kunya ne zai koya mata hankali a nitse Baci ne ya sandeshi ya dauke shi , irin bacin nan wanda ke dan fizgarka sama sama Irin abin nan dake zaburar da mutun a yayin da irin bacin nan ya zo masa ne ya zowa SARKI Abin sai ya hade da a lokacin da ta kai masa damkar nan ta saka gwuiwar kafarta ta daki wajen da bai dace kafar tata ta kai ba, hakan ya saka shi kara jin wannan balakin da ya ji wanda da ba dan ya rintse idannuwansa ba a lokacin zai iya kurma ihu ne A zabure ya farka yana mai kai hannunsa wajen ya damka yana mai rints ido domin sak mafarkin kamar a da gaske ne abin zai sake faruwa da shi Da sauri ya kai dubansa wajen, idannuwansa ya mayar ya lumshe a cikin zuciyarsa ya furta" azaluma, na jikata da ruwa shine ta dakar min wajen da idan ta kasarani na gama wata takama a duniya ko? Ta Allah ba taki ba macuciya da lamarin maza ya gama bude maki ido! Kuma lumshe idannuwansa ya yi yana tausar kansa Bai taba nunawa Zinariya ta zo gareshi ba, ta yi kadan ba zinariya ba bai ga macen da zai je ya lalaba ko ya tura mata yar muryar cewa ta dube shi ba! Idan ta kawo kanta ne sannunta idan bata zo ba ko me zai ji yakan taushi kansa ya tirsasa kansa ne ya dane kamar yanda ya iya danne abubuwa da yawa a rayuwa .......................................... Wajen karfe goma tuni sunna makeken fallonsa, Fallon da ya saka yan matan daga kawunnansu sunna bi da kallo, falon da ya gama haduwa ya hade ya harhade Sunna zaune ne saman maka makan kujerun falon na alfarma, kujerun kansu nishi suke sunna murmusmus a ido domin ba kananun kujeru bane baki dayansu irin na gidan sarakai manyan sarakai Maka makan Ac din ne ke kara huro sanyi a falon wanda sakamakon zaman minti goman da suka yi har jikinsu ya gama daukan sanyin Fitar da Anmy ne hakan ya sa dole kowace ta bi tsari na saka Alkyaba NAJEEBA ta saka wata watsetsiyar atampa ja, an yi mata dinkin sket da riga ne , sket din daga baya an yi masa tsaga mai dan tsayi domin ta haye sama kadan sannan sket din ya kamata daga wajen duwawunta tsam sai ya tafi zuwat bai bude din nan ba Rigar kuwa an yi mata dinkin zamani, an mata baban wuyan nan ne wanda ke saukowa kafada sannan daga gaban an dan yi yar tsaga an fitar da V Hannayen kuwa an saka masu roba daga sama sun bude sosai daga cen kasa kuwa sun tsuke sakamakon robar da aka saka Kanta kuwa dauri ne ta kashe na Zahra buhari Ta rigaya ta saba da rashin zama fuskarta ba a gyare ba hakama ko fita zata yi sai ta tsuke ta gyara fuskarta tas Hakama yanzun fuskarta a gyare take da simple mak up, idannuwanta kuwa ta yi masu sabo da dora natural gashin ido masu tsayi sukan karawa idon wani sirrin kyau da fuzga ne A hankali ta sada kanta ta ce"Anmy, me zai hana mu bari gobe mu yi fitar nan? Duba da bai fito da wuri yau ba Anmy ta buda baki zata yi magana jakadiya ta yi salama Dukawa ta yi a hankali ta ce" Allah ya kara lafia, Elhaj Mutalab ya karaso Kanta ta gyada mata dan haka ta mike da sauri ta fita Tana fita bata jima sosai ba Abih ya shigo da salama Murmushi ne kwonce saman fuskar Anmy tana amsawa kafin ta mike tsaye ta ce" yaya shigo zauna mana muma jiran fitowarsa ne muke Karasowa ya yi ya zauna, yaren baki daya suka hadu sunna gaishe shi da yannayin murnar ganninsa Hannunsa ya dora a gefen fuskar NAJEEBA ya ce" yaya jiki? Murmushi ta yi ta dan dora gefen fuskar nata a hannun nasa Ci gaba ya yi da shafa jelar gashinta dake yawo, dayan hannunsa kuwa Ummulkhair na rike da shi tana dan masaging daga kasa kuwa Zahra ta rike kafa daya tana masaging Ummukulsum kuwa tana daidaita masa ruwa daifai misalin shansa Zamansa ya gyara ya ce" kin san me nake gani kuwa Anmynsu? Anmy ta girgiza kai bayan ta ajiye masa abinci a plat domin komai a jere yake Abih ya ce" sarka DAYABU ya saka aka yiwa yaren nan har shi aman banda NUSAIBA Anmy ta dan yi turus tana kallonsa ta ce" kamar yaya banda Nusaiba? Me ta yi uta Nusaibar da ya wareta? Abih ya dan yi murmushi ya ce" na tambayi kannen du sun ki fada min abinda aka yi, koma meye na san mai girma ne, aman kuma sun ki fada min abinda ya faru Dubansu Anmy ta yi daya bayan daya a hankali ta ce" eyah, eyah, ashe zan ga haka da raina tun kasa bata rufe idannuwana ba? Shigiwarsa da kamshin turarensa da ya shigo du kuwa da irin yanda dakin ke dauke da kamshin turaren wuta ya saka Anmy waigawa wajensa Fuskarta ta sada, hankalinta ya tashi jin haka, Yan matan ne du suka mimike aman Najeeba sai ta langwabe a jikin Abih ta lumshe idannuwanta tamkar bata san da fitowarsa ba Da sauri Zahrau ta saka hannayenta ta mikar da ita inda ta sakar mata harare ita kuwa ta jinginar da ita a jikinta Ya saka wata shigar ce mai birkita lisafin alhazai Ya gama kashe shigarsa ne cikin shiga mai daraja Ya fito a sarkinsa ga rawaninsa mai girma mai kayata sarautarsa Ja ya yi ya tsaya gaban makeken abin turaran wutar da ake yi ana karawa kafin ya kone ake cirewa a zuba wani yana tashi a hankali domin ba garwashi bane a ciki toka ce mai zafin gaske Hannunsa ya dora saman dokar wace ke dauke da zafin gaske domin ita ke saka turaren hayaki a hankali a hankali Da yan yatsunsa ya marmatsa turaren dan ya isa haka sannan ya maida dubansa wajen mahaifiyarsa wace ta fi daukan hankalinsa gannin yannayinta A hankali ya karaso har kusa da ita kafin ya rage tsayinsa sosai kansa sade ya furta" barka da safiya Anmy Anmy ta dago ta sauke idannuwanta a saman kansa Hannunsa ta kamo ta rike tana yi masa duba irin na ido cikin ido, a hankali ta ce" na kawo karar yan uwanka, ina so a mana shara'ar cikin gida , ina so ka zaunar da DAYABU MUTALAB tare da kannensa baki daya ka yi masu tambayar a kan me zasu ware daya daga cikinsu? Najeeba ta lumshe idannuwanta, tabas itama tana son a hana wannan gaba tsakaninsu da yar kanwarsu, yarinyar zata baka tausayi ne idan ta ga daya daga cikinsu tana rarume rarumen ya dauketa tana kukan ya dauketa sai dai ba hali domin maganar dayabu maganar uba ce a wajensu, sai dai a yanzun fa ta ji azalumin nan ne zai yi maganar sai take jin a kan me? Idannuwansa ya lumshe wanda hakan ke nufin amsarsa ne na ya karbi bukatar mahaifiyarsa Agogon hannunsa ya duba a hankali ya furta" karfe tara na dare a falon karatu Abih ya sauke ajiyar zuciya yana mai jin kanwar tasa a ransa, yana godewa Allah a kulun da ya bara masa ita, ita daya ta rage masa sai y'ayansu Anmy ta dubi yan matan a hankali ta ce" na san ba zaku fadi laifin yayanku ba, kuma ba zaku fadi abinda kuka yi tsakaninku ba, aman ku sani idan kun ga kun samu wariyar kai to kasa ta birni idannuwana ne Shi dai yana tsaye ne sai da ta gama ya kama hannayenta ya nufi wajen zama da ita Yana zaunar da ita ya dawo suka gaisa da Abih kafin ya samu waje ya zauna Du yan matan uku kasa suka kara zubewa Aman Najeeba sai ta karasa saman kujerar da Anmy ke zaune ta dane gefen kujerar sannan ta dora kanta a kafadarta Wannan karron kam komai a kan idannuwansa, mamakin yanda aka yi ta mike kan kafafuwanta da sauri haka da mamakin yanda aka yi ta manta gargadinsa da sauri haka suka saka shi tsaida dubansa a kanta Lebensa na kasa ya dantse da hakoransa kafin a sanyaye ya buda bakinsa bayan ya gama harhada kalaman da zai yi anfani da su ya ce" [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 22 Cike da iza ya buda bakinsa ya kai dubansa wajen Abih, a hankali ya ce" Abih, in sha Allah auren Zahrau karshen watan nan na tsayar da shi Abih ya ringa gyada kansa, tabas ya yarda da abinda ya yanke domin shi din uba ne a wajen yaren baki daya sannan shi da kansa ya isa da shi bale yaren Sai da ya kara mintunna yana jin sai sanya albarka Abih da Amih suke, yaren kuwa du sun sada kawunansu Anmy kuwa tana shafa bayan Najeeba, lalabata take domin bata da lafia konda safe da ta farka sai da ta sha maganinta na athsma domin numfashinta ba wai wani daidaituwa ya yi ba Bakinsa ya buda a karo na biyu ya kaisasa muryarsa ya ce" sai dai ina so hakan ya zamo sirri Ko da wasa bana so maganar ta fita tsakar gida bale waje domin BINTU kasheta aka yi Gaba dayansu a zabure suka kale shi Najeeba kuwa kamar wace aka jefo daga kan Anmy zuwa kasa sai gata ta wuntsilo tana kallonsa a tsorace Abih ya yi gagawar furta" innalilahi wa ina ilaihi raj'une, wani irin kasheta aka yi? Wa ya kasheta? Anmih ta kafeshi da ido, subahannalah kasheta? Wani irin kasheta? Gaba daya sai ta ji hankalinta ya tashi da maganar sannan ya sako cewar kar a fitar da maganar Zahrau kennan yana cikin tsantsamin wani ne ya yi hakan a tatare da shi? Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Abih sannan ya kalli Anmih A hankali ya ce" Allah masani, sai dai kowa ya yi taka tsantsan sawayen kowa a kirge yake Gaba daya ta sha jinnin jikinta daga zaunen da take kafin ta maida dubanta wajen yan uwanta Suma yanzun sarkin suke kallo a tsorace su duka Yana gama magana ya mike tsaye Baki dayansu suka sada kawunansu, a hankali suke furta" a huta lafia Anmih cike da kaunar d'an nata kwaya daya da kuma tsantsar tausayin halin da yake ciki itama ta furta" a huta lafia Sai da ya shige du suka dago da kawunansu Rarafawa Zahrau ta yi da sauri ta dora kanta saman cinyar Anmih Muryarta na dan rawa rawa ta ce" anmy, tsoro nake ji, kamar wanda ya kasheta yana iya kashe ni? Anmy ta yi sauri girgiza kanta a hankali ta ce" ba zai kashe min ke ba, ba zai kashe min ke ba in sha Allahu Allah zai hana, itama ki kadara lokacinta ne ya yi A hankali Najeeba ta kama hannunta ta rike a nata itama cike da tunanin da ya gama hadasa mata zufa daga cikin jikinta Fitar da suka fasa kennan, domin dama ta yi niyar fita da su ne su je wajen likita a kara duba Najeeba sannan su je wajen batuba wace ta yi niyar damka mata shirin Zahrau dan duka duka auren bai fi sati biyu ba A dole suka koma bangarenta suka hadu ta saka a kawo mata kayayakin shirya amare a boye Tun a ranar ta shiga baiwa Zahrau shiri irin na gyaran jiki da hade haden tsumi kala daban daban Sai take jin dadin yannayin, dan ta tuna da, dan haka ta titino abubuwa irin na da wa'inda ta rike wuta sosai a zamanin mahaifin mai martaba ta ringa kawo dukan abin bukata Kara kayan gyaran jikin ta yi sosai domin tana darzar fatar Zahrau sauran na darzar nasu da kansu Tsumin nan ne kawai basa sha, sun rufe a falon Anmy na biyu sun shinfida katuwar tabarma sun dora mata leda du sun saka kannanun kaya sai raha suke, itama Anmy din sai daria takewa shirmensu har tsalen itama sai ta shafa suke hadin madara da kurkum fir ta ce ba zata shafa ba Turaren wuta mai dadin kamshin ne ta zuba a dan kasko ya ringa ratsa jikin Zahrau, Tana gamawa Ummulkhair ta dauko masu suma suka hadu a cikin abin rufa su uku suka zuba Anmy ta bisu da da kallo ta yi murmushi tana girgiza kanta, fatanta Allah ya nuna mata nasu suma haka ta kimtsa su Da sauri Najeeba ta cire abin rufar tana ta numfarfashi sama sama Ummukulsum ta warce ta kara rufa su tana fadin" ke ja cen zaki wani bude mana dama mai numfashin kadangaru kawai Najeeba ta matsa tana sauke numfashi, Anmy ta miko mata sansanyar madarar da ta kadawa Zahrau tana mata dariar itama ta ce" idan ba neman magana ba mai ya kaiki saka kanki ke mai cutar huka? Amsa ta yi ta kafa kanta ta shanye tas sannan ta kalli anmy ta ce"Anmy ina son na turara jikina nima Anmy ta ce" to zo nan Mikewa ta yi ta karasa wajen da aka yiwa Zahrau Zama ta yi saman kujerar Anmy ta rufa mata bargon aman kanta a waje ta zuba mata turaran mai sanyin kanshi ya shiga bin jikinta Kafafuwanta ta wara cikin dabara ta kara matsa turaren wajen sosai harda rintse ido dan zafi ta ji na dukan wajen domin da pant a jikinta, tana ji su Nadia na fadin aba turara wajen da turaren wuta ko a yi matsi, to ita me hadinta da matsin? Aman wannan kam sai ta yi ((😲)) Sun jima a wajen kafin suke fitowa shima yama ta yi suka fito dan amsar baki Bayan salar isha'i yaya Dayabu ya shigo tare da NAJEEB, Sunna sanye da shada ne a jikinsu wando da riga iri daya sun yi tsaf da su Ya gaishe da Anmy yana dan murmushi irin yana neman gyaran nan, sai Anmy ta hade fuskarta ta kawar da kai Murmushi ya yi a kasan zuciyarsa, bai ce komai ba Sai da lokacin ya yi du suka nufi bangaren harda kananen Ta lungun da zai sada su da dakin karatun suka bi suka karasa dakin karatun A dakin nabar kujera daya tak ce sai shinfidun cafet na alfarma Sai manyan kur'anai, da alo manya Maka makan tableau ne dauke da sunnanyen Allah da ayatul kursiyu, da sunnan Muhammad (sallalahu alaihi wa salam), su Alhamdu Ac hudu ne a dakin sai manyan panka tafka tafka dake kunne suma sunna aikinsu Tun kafin su Zauna muryar Abih ta shigo da salama Ba shi daya bane tare yake da matarsa hakan ya sa Anmy kallonsa da kallo irin na me ya sa zai zo da ita? Kawar da kansa ya yi ya nemi waje ya zauna Yanda aka yi zaman Abih ya zauna ne tare da Dayabu da Najeeb a bangare guda Gefen daya kuwa Anmy ce tare da yan matanta kananun du sun dadane mata jiki da yan kananun alkuabarsu sun yi tsaf kamar ka sace su ka gudu Manyan kuwa kowace na gefe gefenta , su kam yanzun basa sanye da Alkyaba sai zumbula zumbulan hijabai har kasa irin mai habar nan Mardiya kuwa na zaune gefe guda itama ita daya, ga yarinyarta sai tsala ihun kuka take tana so ta saketa aman ta ki sakin nata Ta sha wani rantsatsen lesh sai kyalkyali yake yarinyartama ta shiryata cikin wata riga doguwa mai shegen kyau, kyanta zai shaida maka kudinta Sai ihu take tana kallon Najeeba, dan kaf a cikin yayun nata babu wanda ta shaku da shi irin najeeba dan goyata take ta yi ta mata doki , sannan du idan zata shigo sai ta shigo mata da tsarabar sweet Wani uban tsaki ta ja ta dangwarar da yarinyar saman cinyarta ta dale keyarta ta ce" zan ci ubanki Nusaiba ki zauna min yau ga jaraba ba inda zaki je Da sauro Najeeba ya kama bakinsa yana kallon yayansa, a fili ya ce" yaya Mardiya na zagin kanwata bayan ka hanamu zagi walahi Duban Mardiyar ya yi ya ce" walahi ki bar zagar min kanwa Mardiya da a cike take irin yanda Abih ya tasota ya tiso keyarta ya kawota a zaunar da su kan laifin da bata san me ta yi ta harareshi ta ce" sai ka hanani zagin nata shege mai katon kai Da sauri ummulkhair ta dubeta ta ce" aman me yasa kika cika son neman fitina ne ke? Anmy ta yi mata wani kakausan kallon da ya sakata sada kanta aman kasan zuciyarta a bace yake Ai kuwa Bilkissu da ba kallon Anmy take ba ta ce" to fa, an tabota Ranta ya kara baci ta ce" ke bilkisu an taboni ni ga mahaukaciya ko? Yan iska kawai da iyayenku kuke kuma du irin rashin hankalina na fi su domin ni na fi uwar kowa cikinku jimawa da ubanku Da sauri Anmy ta dago kanta a karo na biyu ta sauke dubanta a kanta Zahrau ta sada kanta tana jin hawaye na son zubo mata Ummukulsum ta ce" me yasa idan kin tashi masifarki kike sako iyayenmu? A kan me zaki ringa koya mana muguwar tabi'a ne? Kin dai san uwa ba fin uwa ta yi ba ko? Kuma yai da gobe sai Allah kin san watarana zaki ji kunya? Kar ki manta a damagaram muke idan wannan bai san sirrinki ba wani ya sani balema a tafin hannuna sirrin naki yake Rufe min baki shashasha, siriin nawa da kika sani meye? A ciki akoy cikin shege ne? Ko akoy yawon ta zubar ne? Da sauri Dayabu ya dubeta, da yake mahaifiyar Ummukulsum bata zama waje dayan nan ba kennan gori ne ta mata na hakan NAJEEBA ta kara sada kanta tana jin zuciyarta na yi mata tukuki, sam bata so ta furta ko A a wajen nan domin ba a ko'ina take son raba hali ba Ummukulsum ta ce" Alhamdulilah, haka ne, na sani na kuma yarda uwata haka take, ke fa ubanki kafin ya zama malami meye bai yi? Ta fada muryarta a dan dage Fuskarta da Anmy ta tsinke da mari ne ya saka du suka firgice sunna kallonta Sai a lokacin Anmy ta buda bakinta a hankali ba a tashe ba ta ce" ashe lalacewar tarbiyar naku har ta kai ina zaune a waje kuna tozarta kanku ta hanyar sakarwa harshenku linzami? Kun san ikon harshe a tare da mutun kuwa? Harshe kan saka bawa ya zama sakarai a cikin al'uma, Idan baka iya rike harshenka ba zai fada maka maganar da zata saka ka da na sani a cikin duniya baki daya! Ku shikenan a wajen da ya dace a ji muryarku da wajen da bai dace bama sai ku saki baki ku furta kalma daya? Ummu a gabana kike rashin kunyar nan? Ummu ni zaki tozartawa iyali? Wuyanki ya yi kwarin da ya isa yankan da zai jazawa mahaifiyarki zagi daga bakin mai nemanki da fitina? Abih da kansa ke sade yana cike da mamakin rayuwa irin yanda yau shine mace, matarsa take budar baki tana zagin y'ayansa a gabansa aman ya kasa furta mata komai Sunnayen Allah ya ringa kira ido rufe domin baya so rashin kunyar Mardiya ya kaishi wajen da zai kuma aikata kaifin rabuwa da mace, irin yanda ya rabu da matansa ya yiwa kansa alkawarin ita wannan ta birne shi ko ya birneta, sai dai kash ya yo hakan a lokacin da yake aure da matar da bata san darajar kanta ba, ya yi zama da mata kala daban daban, har yar bariki da ustaziya, bai tashi daukan wannan niyar ba sai a kan wace zata tarwatsa masa nutsuwar zuciya Tun da Anmy ta fara magana sauranma suka kara sada kansu Ummukulsum kuwa sai ta fashe da kukan nadamar sakin bakinta da ta yi har haka ta faru Kanta ta dora a gefen kafadar Najeeba tana kukan inda Najeeba ta rintse idannuwanta tana jin kukan yar uwar tata har cikin zuciyarta Bata taba jin tsanar matar abih irin na yau ba, tabas bata zo wajen nan dan furta kalma daya ba aman ta rantse a yau b sai gobae ba sai ta tardata du gidan ubanda ta shiga ta ci uwarta! Sanarwar shigowarsa ya saka Anmy sada kanta tana jin kamar ta fashe da kukan itama, kai ina, dole ne ya bara mata yaren nan dan walahi ba zata yarda ya kara tafia da su ba ya kaisu tarbiyarsu na kara shiga hatsari! A haka zaa aurar da mace a kaita gidan miji a kai me? Ta tabata irin yanda ummu ta kasa dane bacin ranta ta nuna shirme ko miji ya fada zata fada ne! Ya kai minti ashirin kafin yake karasa shigowa cikin shigarsa ta kamala Da hannayensa ya dakatar da amintacensa kan ya tsaya a kofa domin shara'ar ta cikin gidansu ce Direct wajen kujerar ya karasa yana tsaye yana bin kowa da kallo Yarinyar dake sheka kuka kamar zata sike ya bi da kallo, mahaifiyarta da ta riketa gam ya kuma bi da kallo kafin ya maida dubansa inda yarinyar ke nunawa tana son a saketa ta karasa wajen Najeeba aman an hana Murmushi ya yi a kasan zuciyarsa domin nan take ya gama fahimtar matsalarsu baki daya sai dai kamar yanda ya kasance sai ya saurara to fa zai sauraran ne dole A hankali murya a tausashe ya ce" *KI SAKE TA TA JE WAJEN YAN UWANTA* A hankali ya yi maganar, sai dai kasancewarsa mai cike da kwarjini da bulaliyar dukan magana ya sakata tunkudo yarinyar a biye wanda ita a boye ta yi aman du an gani Yarinyar kuwa da gudu ta karasa jikin Najeeba Tana zuwa ta ringa dora kanta a jikinta tana rukunkumeta, sai dai Najeebar bata riketa a jikinta ba itama Zuciyarta na mata tsale, so take ta riketa ta rungumeta aman ba hali a hankali ta saci kallon yayansu wanda komai a kan idannuwan sarki, shima duban nasa ya kai wajen DAYABU sai ya ga idannuwansa a rintse suke, ya gama hawa stage din da ba zai iya furta kalma daya ba tare da ya yi maganin matar nan ba! Murmushi ya yi ya idasa gani kan matsalar kafin a hankali ya kai zaune Sai da ya zauna ya gyara zamansa sannan ya yi sakama a hankali Baki daya suka dago kawunnansu daga sadawar da suka yi, Dubansa ya kara kaiwa wajen yarinyar dake ta wawuwar Najeeba dan bata yi shirun ba so take ta kulata ta yi mata wasa ta rarasheta aman ta ki yi mata hakan A tausashe ya ce" Abu hauraira Allah ya yarda da shi yana cewa" ka so masoyinka daidai gwargwado domin zai iya zamowa makiyinka, haka kuma ka ki makiyinka daidai gwargwado domin zai iya zama masoyinka wata rana Numfasawa ya yi ya shiga binsu da kallo tun daga kan Abih har zuwa mahaifiyarsa A hankali ya kuma furta" *ME KE DAMUN AHALINA NE? ME KE DAMUN SHUGABAN CIKIN GIDAN BIYU NE?* *YAYA AKA YI YA YARDA KIYAYA TA YI ZAFI HAKA A CIKIN GIDANSA BAYAN YANA DA IKON KATSETA KODA KUWA TA HANYAR KAWAR DA MAI HADASATA NE A WAJE?* [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 23 Baki daya wajen ne ya dauki shiru , kawunnansu du a sade a kasa haka kuma NUSAIBA bata daina kukan da take ba Sarki ya kuma buda bakinsa ya ce" mazon Allah tsira da amincin Allah su tabata a gareshi yana son yin alfahari da mu a gobe kiyama Aman ta yaya? Shirun dai ne ya kara tabata a wajen hakan ya saka ya dago yar yatsarsa ya yi nuni da Zahrau a tausashen dai ya furta" Bismillah Zahrau ta kara sada kanta a hankali ta ce" Allah ya kara girma, ya umarcemu da mu hayayafa dan gobe ya yi alfahari da mu Kansa ya gyada a hankali kasa kasa ya furta" barakalahu fihk, Kansa tsaye ya nuna Najeeba dake dan janye Nusaiba daga jikinta ya furta" meye ilar gaba a musulunci? Dungurar da Anmy ta yi mata ya sakata dagowa domin ta so ta yi kamar bata gane da it ake ba , sai dai ba hali domin a irin yanda Anmy kanta ta nutsu a gabansa abin sai wanda ya gani, A sanyaye ta furta" *Allah yana yiwa mutane afuwa, aman banda masu gaba da junna* Dubansa ya maida wajen DAYABU da kansa ke kasa shima kafin ya ce" shin me ya dace shugaba ya koyar tsakanin hakuri da rashinsa? Yaya DAYABU ya dago yana dubansa kafin ya furta" Hakuri, Hakuri shine ya dace da kowani bawa, mai hakuri zai ci riba Sarki ya gyada kansa ya furta" Mai hakuri zai kai ga ci Dubansa ya maida kan iyayensa daga Abih har Anmy A sanyaye ya furta" shugaba, ya dace ya kasance mai matsanancin hakuri, ya ringa shanye abinda da yawa ba zasu iya shanyewa ba Shugaba koda na wasan yara ne, ya dace ya zama mai yanke hukunci cikin aminci, da kawar da kai Dubansa ya maida wajen Mardiya, sunna hada ido ta yi gagawar sada kanta, a hankali ya furta" ka karfafa zumunci, ka yada zumunci, kar ka zamo wanda zai yi silar yanke zumunci Shiru ya kuma yi kafin ya furta" mai magana bismillah Anmy ta sauke ajiyar zuciya tana dubansa kafin ta maida dubanta wajen yayanta, a hankali itama ta furta" burina, bai fi zumunci ya dore ba Allah ya ja da ran sarkin damagaram Shaheed ya lumshe idannuwansa ya maida dubansa wajen Abih Abih ya buda idannuwansa da sukai masa jajajir , a hankali ya furta" Allah ke bada girma, koda kuwa yaranmu sun zamo shuwagabaninmu mu masu biyaya ne, Allah ya kara datako Mai damagaram Kuma lumshe idannuwansa ya yi sannan ya maida dubansa wajen DAYABU Kansa ya sada , a hankali ya furta" na yi kuskure, baki daya ni na ja ragamar wanzuwar wannan fitina,Allah ya ja da rai daga yanzu daga kan DAYABU MUTALAB, har zuwa NUSAIBA MUTALAB bamu da wariya, Allah ya huci zuciyar sarkin garina Da sauri Najeeba ta kankame NUSAIBA a hankali a jikinta sannan ta sakar mata dan murmushi tana shafa kitson kanta wanda tun wanda ta mata ne ba'a tsefe shi ba kusan sati uku a kan ko wankin kirki ba'a masa ba hakan ya sa ya tsufa duba da sunna da izgar gashi nan da nan gashi ke tohowa a kansu shi ya da du sati sauran ke yawan kunce kansu domin kitso ko saloon a gida ba wani wahala shi ya sa kawunnan nasu ke kara albarka Murmushi ya yi wanda iya zuciyarsa ne sam bai bayanna a fili ba A hankali ya kuma furta" Allah ya yi mana jagora Baki dayansu suka amsa amen banda Najeeba dake kara buda bakin Nusaiba tana kallon hakoranta da suka yi dan duhu hakan na shaida mata bata wanke mata baki har gashi ya kama hakoran yar yarinyar Shirun da ya dauki wajen ne ya sakata dago kanta dan gannin har ya gama maganar ne? Idannuwansu ne suka sarke da na junna a lokacin da ya kusan karasowa inda take zaune , da sauri ta mayar da kanta kasa ta sada sakamakon faduwar da gabanta ya yi da kuma irin kallon tsanar da ta ga ya yi mata A ranta kuwa fadi take" azalumi, ashe harfa fuska biyu ne da kai? Gaka yanzu ka gama maganar wa'azi da masalaha ni kuwa ka tsane ni? Ba damuwa, zaka gane ne dan yanda ka tsane ni ni naka fi ka tsanarka! Sai da ya fice a fallon da kamar minti goma sannan du suka mike Irin yanda ta karaso ta warci yarta ta juya buguzum buguzum ya saka baki daya suka zaro idannuwansu Da sauri Abih ya daga kafarsa zai bita sai dai maganar da Anmih ta yi cewar" idan ka bita yaya zaka rarasheta ne ta maido y'ar? Ya saka shi dawowa da sauri inda take tsaye da yarensa Muryarsa har tana hadewa da junna ya ce" yanzu domin Allah Bilkissu ba zaki yi min adalci ba kema? Kema a yanzun ganni kike ni ke daure mata tana haka? Ko so kike na yanke igiyoyin da sukai saura a tsakaninmu ne na jara dauko wata? Ita watar idan na daukota kin san meye halayanta? Wani sabon zama ne za'a kara dorawa da y'ayana shin da me zata shigo? DAYABU ya yatsina bakinsa yana girgiza kansa, lale ta samu damar da take tunanin har zata iya taka sawun kafarta ta fita da y'ar da sarki ya gama nasiha a kanta Fitarta kawai suka ganni, hakan ya saka Zahrau kallon Anmy, sanyaya muryarta ta yi ta ce" Eyah, Anmy Najeeba ta fice da sauri Anmy Anmy ta kallota da sauri, sai kuma ta kalli Ummulkhair ta ce" maza ku bita Sai da suka fita ta kuma kallon DAYABU ta ce" wai Ummulkhair na tura ta bita, ko ta je ta tayata ba, bi min su ka maido min su ka ji? Irin yanda take sauri ya yi daidai da Mardiya ta buda gaban motar Abih ta shiga kennan zata rufe ita kuwa ta karaso da wani irin mahaukacin sauri ta tare marfin kofar ta hannata rufewa Hannunta daya ta saka ta finciko yarinyar ta direta kasa cen gefe sannan ta maida hannayenta ta finciko uwar waje Da ihu ihu uwar ke fadin" ke baki da hankali ne? Ke wata irin karamar yar iska ce? Dauke fuskarta ta yi da mari, ta maimaita mata wani sannan ta saka hannayenta ta hankadata jikin motar nan ta rike mata wuya A masifance ta ce" ke wawuya ce Mardiya, kin so ki ci darajar uwa koda kuwa shekarunmu daya da ke, sai kika bata rawarki da tsale! Tanas gaskiya kika fada babu wace ta zauna ta yi hakurin zama da shi har zuwa wannan lokacin kamar ke gashi yarki har zata ryfe shekara hudu nan da sati uku da kwana biyu, Kin san me? Dalilin wannan ni kaina na so na ga mutuncinki, domin a duniya du macen da ta iya jure zaman waje domin y'ayanta nakan bata wani waje mai daraja a cikin mata wanda ba kowa nake ba shi ba Sai dai ke din kin kasance wawuya a lokacin da kike anfani da kadarar wani ko dama da kika samu na zama matar MUTALAB kina taka mu son ranki! Warto hijab dinta da Dayabu ya yi da murya a dan dage yana fadin" Najeeba me kike haka? Sakar mata hijab kin san da labari na iya iske sarki har yanzu a cikin gidansa kike fa kin manta a wajen ajiye mitoci kike Fuzge hijab dinta ta yi, Ummulkhair kuwa na gefe rike da yar ta juyar da ita gefe guda tana dan jijigata har ta yi shiru daga kukan da take na rabota da su ta kwonta a kirjin Ummulkhair duda ita Najeeba take so ta dauketa aman ko a Ummulkhair din aka tsaya da dama domin mamanta ta cika duka da fada da zagi abu ga yaro inda ta fi jin dadi nan ta fi zuwa Gannin sai kakari Mardiya take ya saka wannan karron ya fardota baki dayanta daga jikin Mardiyar da ta yiwa shakar mutuwa Yana rike da ita tana tirjewa sai da ya matsar da ita gefe ya riketa a hannunsa da karfi karfi ya ce" zaki dawo hayacinki ko ba zaki dawo ba? Wata tirjewar ta so yi ta hanyar kuma ridar Mardiya dake tsugune tana rike da wuyanta sai dai bai bata dama ba ta hanyar dauke fuskarta da marin da ya sakata saurin ja ta tsaya tana mai dafe kuncin nata da hannayenta bibiyu dan walahi bata son mari, kai ina dalili za'a maren mata fuska? Ita bata son mari ko kadan Randa bace ya ce" ke baki isa na tankwasa ki bane ko ke idan ranki ya baci mahaukaciya kike zama? Na fada maki ki daina, na maido ki da laluma , na nuna maki hanya sai tirje min kike kinai min tijara? Wani irin iskanci ne wannan? Sarki sa'ankine da zai tasheki daga magana yanzu yanzu ki fito ki aikata? Ke din banza ke din wofi? Da kakausar murya ya ce" ki kiyayi haye a wajen da wargi bai samu wajen zama ba! Yana gama fada ya hade su da Ummulkhair ya ha su da Nusaibar suka yi ciki Tana nan tsugune har Abih ya karaso Yana kallonta ya san an yi ba dadi da y'ayansa, gannin yannayin da take ciki ga kuma ba y'ar a tatare da ita Shima da nasu da yake jira da ita dan haka a kausashe ya ce" tashi mu je Mikewa ta yi ta je kusa da motar zata shiga Waigowa ta yi ta kalli baban filin wajen Zata nemi gannin sarki, zata labarta masa irin marin da Najeeba ta yi mata komai dadewa, sannan ta daukarwa kanta Alwashin yanda Najeeba ta kasance mai tara samari sai dai ta mutu a haka, domin kuwa ta rantse da Allah sai ta wulakanta rayuwarta Ba ta taka dokar layar da aka saka masu ta kai hannunta kanta na biyu kennan ba ? Itama zata dawo daga zagon kasar ta bi ta hanyar kasa! Abih kuwa yanzu ta fara zama da shi bata ga ubanda zai rabata da mijinta ba, zumunci ne tsakanin mararsa kunyar y'ayansa da y'arta ta haramta! Har yanzu hannunta dafe da kuncinta suka shigo Fallon Anmy Sai da suka shigo ta ja ta tsaya sannan ta waiga dubanta kan yayanta wanda shima yake jin zafin marinta da ya yi A hankali ta ce" yaya, aman ka san ba dadi marin fuska ko? Yayanta ya ce" ke kuwa kika mari matar ubanki? Marar kunya? Kanta ta sada sai ga hawaye masu zafi sun fara fita daga cikin idannuwanta a hankali ta kuma furta" yaya, ka ga irin rashin kunyar da ta aikata a gaban sarkin da kake cewa kar ni na yi ya ji labari? Yaya ka ga yanda take son rabamu da Nusaiba bayan ni ina sonta? Hannunsa ya saka ya kama hannunta suka karasa ciki, a lokacin kuma Anmy ta fito daga dakin yan matan da ta kai ta shinfide tana kallonsu ta karaso Zaunar da ita ya yi ya zauna , shima sanyaya muryarsa ya yi ya ce" koma me ta yi, baki ji abinda ya maimaira cewar shi shugaba shine wanda zai iya shanye komai ba? Najeeba ba dan bashi da zuciya ba Sannan ke da ita idan nace da ke ba faya bane zaki fahimci bambancinku? Ke kanwarsa ce, wace ya isa ya saka belt ya yi maki dukan tsiya koda kuwa babu rawani a kansa Ita kuwa matar Abihnsa ce, wace koda da rawani a kansa zai iya daga mata kafa ya kawar da kai ya bita da nasiha yau da gobe har ta fahimta Najeeba kamar yanda kika fada cewar tana anfani da damarta hakan ne, Kwarai Mardiya ta taki sa'a a rayuwarmu, ta yi nasarar auren ubanmu dan haka uwa take a wajenmu koda kuwa bata dauki girman hakan ba Anmy ta yi murmushi a ranta kuwa tana mamakin irin yanda yaron ya kasance tamkar mahaifiya, zai hukunta kannen nasa ya kasa samun nutsuwa Bambancinsa da mahaifiya daya ne, du irin karfin soyayar uwa tana iya cire kanta ta nuna maka laifinka ta kawar da kanta ta labe ta yi jinyar zuciyarta, aman shi sun gano lagonsa koda ya daga hannu a kansu shi ke dawowa ya zauna ya yi ta rarashi Sarai ta ga anfanin hakan a yau, sannan ta gane dalilin da ya sa maganarsa take da karfin tasiri a wajensu Shi din uba ne kuma uwa ne a wajen kannen nasa Irin yanda yake shanye duka dominsu ya saka shi zamowa shugaba a cikinsu Hannunsa ya kai wajen fuskar nata da take rike da wajen idannuwansa ya rintse kadan a hankali ya dubi Anmy ya ce" Anmy, ki yi hakuri ki yafe mata bin bayanta da ta yi ta aikawatar da fada a cikin gidan sarki, dan Allah ki yi hakuri Murmushi ta yi masa tana gannin girman yaron a idannuwanta, ta tabata zai iya zama adali koda a cikin gidansa ne Shima murmushin ya yi ya mike ya kara tsugunawa ya furta" Allah ya kara girma uwata Anmy ta ji wani yamyam da wani dadi ya ratsa zuciyarta, a sanyaye ta furta" Allah ya yi maka albarka yarona Hannun Najeeba ya kuma rikewa kadan kafin ya saketa ya juya ya nufi wajen Ummulkhair dake goye da Nusaiba Tsayawa ya yi yana kallon yarinyar har ta yi baci Murmushi ya yi ya dan duka ya mana mata kiss a goshinta sannan ya kalli Ummulkhair a hankali ya ce" Khairiya, kar ki bari khulsum ta yi kukan maganar da ta fada mata kin ji? Sannan kar ki yarda bacin ran mamanta ya saka khulsum tsanar Nusaiba Ummulkhair ta gyada kanta itama tana rike da hannun yayan nata ta ce" yaya auntu Zahra na tare da ita a dakinmu, tama ce na goya Nusaiba idan ta yi baci a wajen khulsumbdin zata kwana Kansa ya gyada yana mai jin nutsuwa ta shige shi, dan baya so laifin mahaifiyar yarinyar ya saka kannen nasa gannin bakinta Yaya, wayar tawa fa? Gaban goshinsa ya dafe ya ce" ke ba na manta ba, aman kin san meye yayarki ne tace ita zata siya shi yasa na manta zan tambayo maki ita yayane an siyan ne ko yaya? Murmushi ta yi tana jin dadi a ranta, tap, idan aka ce auren yayansu ne bata san irin abinda zasu yi ba, fatansu Allah ya sa yanda yarinyar ke nuna masu kauna a waje har cikin gidan haka ne, Allah ya sa matar yayansu ta zamo uwa a garesu baki daya Sai da ya kara shafa bayan yarinyar ya furta" kaita ki shinfideta ki yi mata adu'a sannan ki ajiye wani dan abin ci a kusa dan kar aje ko tana tashin tsakiyar dare neman abinci Amsa masa ta yi ta nufi ciki Kanta sade yake a kasa tana tsoron dagowa sakamakon irin kakausan kallon da Anmy ke binta da shi A hankali ta furta" Anmy ki yi hakuri Anmy ta yi dan murmushi ta ce" wani abin kikai min ne NAJEEBA Mutalab? Najeeba ta kara sada kanta a hankali ta ce" Anmy, a gabanku fa take wannan rashin mutuncin Anmy ta dan daga kafadunta ta ce" eh na gani, ke kuwa sai kika zaneta a bayan idannuwanmu aman a wajen da duniya zata iya gani ba, ai haka ne danka dama ka zane shi kawai Najeeba ta kara sada kanta dan ta san yaufa tana hannu A hankali ta budi bakinta zata yi magana Anmy ta ce" ai ban yarda cewar, bayan rashin kunya, rashin sannin ciwon kai, rashin kawar da kai yanzun harta da darajar kanki baki sani ba? Da sauri ta ringa girgiza kanta ta ce" Anmy Anmy ta ce" ki yi min shiru malama! Idan ita ta nuna halayen tarbiyarta ta marar kunya da rashin sannin girman na gaba da ita da raini ke sai kika nuna taki tarbiyar wace kika gada ta masifa? Kanta ta kara sadawa kasa Anmy ta ce" ina sannin ciwon kai ga macen da zata yi anfani da karfin damatsunnanta ba dan ta yi ibada ba? Ina hankali ga macen da zata kai hannunta jikin wata da niyar zu gwada karfi bayan ta san wani abu na iya faruwa a wajen ko ita a ga tsiraicinta ko a ga na abokiyar fadan nata ta hanyar yage mata hijab ko zannin dake daure a jikinta ko rigarta haka kawai ta jazawa kansu abin kunya domin na tabata du wace ta san kanta zata ji kunyar a ga tsiraicin yar uwarta mace bale nata! Yaushe kika raina gida mai daraja irin gidan nan da zaki yi dambe a cikinsa bayan wanda bai san irin darajarsa bama ya kiyaye ya girmama shi bake ke da kike cikinsa kika san meye shi? Yaushe kika raina haduwarki da yayanki wanda nake iya yina dan rufe izgilinki? Ina kika zubar da class dinki da har zaki mike ki tarbi mutun da fada bayan kin san ance shiruma amsa ce ga mai hankali? Allah ya huci zuciyarki....Najeeba ta fada tana kara sada kanta Anmy ta dago dan yatsarta guda ta ce" zaki nutsu ko bakya so ne Najeeba Mutalab! Tashi ki je dakinki ki yi nafila ki shirya yin baci Sai da ta kara dukawa ta yi godiya tana kallon fuskar Anmy din da ata daure mata sannan ta shige ciki Washe garima sun wuni ne sunna gyare gyaren fata, sai dia har zuwa lokacin ba wani sake masu baki dayansu Anmy ta yi ba, idannuwanta a kansu, tana ta daukan dukan abinda bai mata ba tana rubutawa a litafi da byro sannan tana dora question mark a sama, kan neman yanda zata biyo da su Sai irin dabi'un da ta shiga koya masu na rayuwar gidan sarauta, wace da yawa sun iya sai dai kuma da yawa basu iya ba dole sai an zauna dan ba karamin aiki bane Irin magana da ido, magana da kai, sasauta kallo ga sarki , irin kallon da zaka masa a cikin jama'a a matsayinsa na sarki, irin wanda zaka iya masa idan daga kai sai shi ne, irin yanda zaka ringa kiran sunnansa a waje da kuma idan dqga kai sai shi ne Murmushi Najeeba ta yi tana lumshe ido da anmy ta furta" MAI GARINA, a daka kuwa tana iya yi masa special sunna kamar MAI NI Bayan salolin su magariba da isha ta fito dauke da Nusaiba Sai da ta duka har kasa ta ce" Anmy, ina son zuwa saloon na dauko abin kitsonta Anmy ta dubeta, a hankali ta ce" ki dauki kys din motana, ku je ku dawo Najeeba ta kara yin godiya ta dauki kys din Tana cikin tuki mesage din Anmy ya shigo Sai da ta tsaya a saloon ta dauko abubuwan bukatarta sannan ta dawo motar ta duba mesage din *ki kula* Murmushi ta yi tana kallon Nusaiba ta ce" wa ke son ice cream? Ai kuwa Nusaiba ta ringa daga hannunta tana ihun ni ni ni Daria ta yi ta karkata ta nufi wajen mai Ice cream Siya ta yi sannan ta sayan masu kilishi ta nufi wajen hutunta dan bata son komawa yanzu yanzu Tun da suka tsaya daga inda yake tsaye yana hangen motar gidansa mitar Anmynsa har suka fito ta fitar da darduma ta kawo wajen da take zama ta shinfida Wayarta ta kunna wakar hausa ta breaker ta ajiye a gefe sannan ta zaunar da Nusaiba dake dan rawa rawa ta buda mata takardar naman tana kallonta ta ce " sai kin ci wannan sannan ki sha ice cream Ai kuwa yarinyar ta maida hankalinta ta fara ci din domin ice cream din shi ta fi so a bata Kara gyara tsayuwarsa ya yi ya dan matso kadan dan jin abinda suke fada Ta dauka ta saka a bakinta tana dan taunawa sai kuma ta ja tsaki a hankali ta furta" idan ya san wa'azin zumunci ko ya san na zalinci? Sai ta yatsina fuskarta ta mayar da muryarta tamkar tasa wato ta sanyayar da ita ainun ta furta" meye ilar gaba a musulunci? Ta murguda bakinta a hankali ta furta" yana magana tamkar mace, yanzu haka sarautar samunsa dai ta yi aman sarki ai zaki ne! Idannuwansa ya zaro da mamakin wai ashe wannan abin du shi ake yiwa? Kansa ya girgiza a hankali ya karaso ya zagaya ya zauna yana masu salama Tun da ta gansa sai ta hadiye na bakin nata da sauri sannan ta cire hannunta daga cikin takardar tana mai binsa da kallon mamaki Hannunsa ya saka ya dauki naman nan duda yana tunanin da wahala ya iya ci domin a rayuwarsa baya son dabi'ar cin abu a titi sam bai iya ba bai saba ba ya daure ya kai bakinsa bayan ya yi bisimillah Yana ayanna idan ba shaidaniya ba me zai hada ki da kunna waka da dare a wajen nan duda da haske da kuma mutane aman ai ka kiyaye kawai! Ita kuwa hannun nasa ta bi da kallo irin yanda ya dan jujuya naman sannan ya saka a bakinsa Da mamakin rashin yi mata salama, da haye mata darduma uwa uba ya kamo kanwarta ya rike a jikinsa sannan ya ci mata namanta take kallonsa Dagowa ya yi ya kai hannunsa ya danna wajen kashe wakar sannan ya hada idannuwansa da ita Ido daya ya kashe mata ya dage mata gira daya hakan ya saka ta yi gagawar cire dubanta a kansa tana furta" meye wannan kuma kamar wani dan iska kana kashewa mutun ido, ko dau a yar iska ya daukeni? Shi bai san ko kawance bana yi da mace farar fata ba shine zai ringa damuna shi wani garjejen fari, yo farin mutun ai sangarta ta kare a wajen, kayan tsantsane kawai Dubansa ta kuma yi ta ga yana son bude ice cream din, hakan ya saka Nusaiba yin dare dare a saman kafarsa har tana masa daria tana nuna masa Kai yaro, yaro, bashi da hankali, ta fada a kasan zuciyarta A fili sai ta tsinci kanta da furta" Me ya sa kake saka kwali a idannuwanka sai kace wani dan daudu ko boka? Kansa ya dago jin yanda ta yi tambayarta kai tsaye , abin sai ya zame masa wani banbarakwai, sai yake jinsa normal mutun kamar kowa Tambayar baba ce, sannan ta rashin kunya ce Aman sai ya ga ai tambaya ce dan haka sai ya mayar da dubansa wajen Nusaiba ya ce" Bonjurno [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 24 Mayar da dubansa ya yi wajen Nusaiba wace ya hudawa Ice cream ya saka dan cokali ya dan dibo ya kai bakinta, A hankali ya furta" kennan ba bambanci tsakanin abinda Allah ya zana da kansa da wanda mutun ke iya sakawa? Da sauri ta kuro ido ta yi gagawar furta" astaghrullah Shima yana kallonta ya ce" sabo na yi? Nifa tambaya na yi Sai a lokacin ta yi kokarin tsurawa idannuwan nasa ido, sai da ta ji har tsigar jikinta na tashi domin wannan kwalin wani kwali ne mai matukar tasiri, kwali ne mai kayar da gaba da saka mutun sada kansa koda kuwa bai so ba, kwali ne dake matsayin fatar mutun ba wai saka shi aka yi ba , hakan ya sa wajen ke daukan du yannayin da cikin kwayar idannuwan ke da shi Kwalin a yanzu kyalkyali yake duda hasken duhunsa ya dan risina sakamakon gajiyar dake tatare da shi Da sauri ta kawar da kanta tana jin wata boyayiyar ajiyar zuciya na kwace mata har ta dan sosa gaban goshinta Cikin nutsuwa ya kawar da dubansa shima a ransa yana fadin" marar kunya na so na ga shin ke bashi da karfin saka ki kasa kallonsa ne ko me? Nusaiba dake wasa da ice cream din ta lakato ta nufi wajen bakinsa Shi kansa bai yi jiran zuwan hakan ba domin ya kuma ciran kilishin nan da ya yi masa dadi a bakinsa yana dan taunawa a hankali Kawo abin ta yi wajen sajensa tana son lakata masa a bakinsa sai ta lakata masa shi a wajen gemunsa Idannuwansa ya dan zaro yana gannin abin ya bata daria, dan haka sai ya kalli Najeeba Gani ya yi kanta na wajen wayarta tana dadanawa Lakuta ya yi itama ya kai mata bakinta hakan ya sa yarinya ta ringa kaucewa ita wasa ne yake mata A hankali ya ji zuciyarsa na tunzura shi kan ya yiwa yarinyar wasa, dan haka sai ya bada hankalinsa a hankali ya shiga yi mata cakulkuli Ihun dariyar da take ne ya saka Najeeba dagowa da sauri tana kallonsu Ido ta zaro gannin yanda Nusaiba ke zaune dare dare saman cinyar bakon mutumen da bata sani ba sai faman wangala masa daria take Fuskarta ta hade ta ce" Nusaiba Da sauri yar ta juyo tana kallonta Najeeba ta ce" meye haka? Me na ce da ke? Bakya jin magana ko? Da sauro ta sauka daga saman cinyarsa ta koma jikin Najeebar ta zauna tana kallonta ta ce" aunty ba zan kara wasa da namijin da ban sani ba, ki yi hakuri kar ki fasa yawo da ni Bata kuma yi mata magana ba sai kokarin mikewa da take ta kama hannun kanwar tata Bata bi ta kan Ice cream din, da naman da kuma dardumarta ba ta nufi motarta Sai da ya dan bi su da kallo kafin ya mike cikin izarsa ya dan duka ya dauke kayan harda dardumar aman bai ninke ba domin shi dai zai iya rantsewa yau ya fara yiwa wani aiki bayan mahaifiyarsa, ko mahaifiyar tasa aikin ba wani bane sai irin idan sunna zaune yakan dan masaging din hannayenta, ko ya miko mata abinsha ko abin ci, ko ya gyara mata zaman takalmanta dai haka Sai gashi ya dauko ledar nama, da su ice cream ya bi bayan yarinyar da yake dakon kamata da abinda yake sane da tana aikatawa haza yake son ganni dan hukuntata a fili ba a boye ba ya bita da kayanta Bayan motar ya saka hannunsa ya bude ya zuba kayan a ciki yana gannin yanda ta juyo tana kallonsa da mamaki Bata ce da shi komai ba saima jan motar da ta yi bayan ya rufe ta yi gana tana kara yiwa Nusaiba fadan wasa da maza ko waye Bayan motar ya bi da kallo har suka bacewa ganninsa Kansa ya girgiza yana dan murmushi, wato da ake cewa wanzam baka so a jikinka haka ne ko? Ita tana yawonta aman tana yiwa kanwarta fadan kar ta ga tana wasa da maza Fuskarsa ya kara hadewa ya juya ya nufi wajen zaman domin bai gama hutawar da ya fito yi ba, Zama ya yi ya dora kafa daya kan daya Dan gishiri gishirin da ya ji a lebensa ya saka shi dan kallon hannunsa Da san abin mai a jiki irin maikon kilishin kadan sannan ashe abin ice cream din har a rigarsa Mikewa ya yi ya nufi motarsa Hannunsa ya mika ya janyo abin goge baki da goran ruwa ya matsa gefe ya ringa goge du inda ya san zai samu abin Sai da ya gama gogewa tas tas sannan ya mika hannunsa ya amshi kayansa da amintacensa ke miko masa ya koma gefe ya shiga kimtsawa Yana gyara rawanin kansa ya kuma girgiza kansa a ransa yana ayanna" ita ga salihar mace mai tarbiya? Lale da bakone ni a rayuwarki da hakan ya birge ni, sai dai Zan iya rubuta labarinki a tafin hannunki harda wanda ke baki sani ba! NAJEEBA zaki zamo aya a garina, a kanki zan yi maganin kananun yan tsageran garina! Ya kasance a wannan dare cikin nishadi da dan sanyi a zuciyarsa wanda ya jima bai ji ba a kala tun rasuwar yaronsa Tabas wasa da Nusaiba da ya yi ya saka shi jin sanyi a zuciyarsa dan yarinyar sosai ta rukunkumeshi sai da ta saka shi yi mata murmushi mai sauti sannan ya bita da cakulkuli duda sakaryar yayarta ta rabata da shi dan iyayi nata Adu'a ya yiwa kansa da sauran musulmai baki daya na Allah ya basu masu albarka baki daya Sai a lokacin ya tuna da cikin jikin Zinaria, cikin na nan ko ta barar da shi? Duda da irin zubde zubden jinnin da ta ringa yi shi kuwa rabonsa da ita an jima, bai san me ke dauke hankalin yarinyar nan ba kamar itace sarkin ba shi ba, Uzuririkanta sun yi mata yawa, uzururikanta kamar wace keda nauyin talakawa a kanta? Har ya zama uzururikanta sun fi shi mahainmanci Shi kennan haka zai yi ta rayuwa ne? Sunna kusa da macen da suka fi nisa da junna Sunna karkashin innuwa daya aman tafiarsu nada tsayi Bai san me yasa ta dauki wasu lamura da zafi ba Ya dace ya ringa samun kulawa ta miji da matarsa wace ta amsa sunnanta a cikon dakansa Takan saka shi jin nauyinta idan tana masa kirarin nan Wani sa'in har sai ya dubeta da sauri da mamakin shin mata ya aura ko baiwa? Sam mace bata da lamari irin na tafiar da soyaya yanda ya dace? Shi dai ba mai kallon film ko sauraron labarun soyaya bane Yana anfani ne da ilimin da ya karanta na islamiya Kwarai adininsa ya koyar da yanda zaka gudanar da rayuwar aurenka koda kiwa kai din shugaba ne Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wa salam , shugaba ne na duniya baki daya, aman irin yanda tsarin tsaftataciyar soyayarsa da matayensa ta kasance dole mutun ya yi sha'awar gudanar da irinta Idannuwansa ya mayar ya lumshe yana jin wani takaici guda gefe guda dake yawan zo masa Ko tunani take yanda na iya dane tarin rigingimun talakawana zan iya dane rigimar dake jikina? Ko ni din bana tare da sha'awa ne? Gannin kamar tunanin ya sako shi gaba ya saka shi mikewa ya shiga nafila, zai fi kyau ya samu ladan nafilar tunda dayan ladan ba zai samu ba, ba zai fita ya je bangarenta ya lalabota ba, idan har ba'a nuna mata mahinmancinsa a islamiyarsu ko a gidansu ba ba damuwa, zai kuma kwatanta wani auren! Dinkuna masu rai da lafia ke shigowa daga wajen telan Anmy na yaran baki daya Sai dinkunnan da aka ware tela biyu aka kilace suke zuba aiki na gimbiya Zahrau Aure har ya zama saura kwana daya tak wanda tun fitar nan ta su Najeeba Anmy bata kuma barinsu fita ba baki dayansu Abincinsu su ke shiga kicin bisa jagorancinta su girka, Hirarsu sunna dakanta daidai da masu yi mata hidima ta dakatar, su kuwa basu sako komai a ransu ba domin takan yi haka dama idan y'ayan nata suka zo yi mata yan kwanaki Bakin da suka zo gidan a daren yau ne suka dan fara daukan hankulan mutane Sai dai ba wanda ya kawo wannan lamari a ransa Wayewar garin safiyar juma'a, tun da sasafe ana ta karatu da sadaka a baban masalacin juma'a na gidan sarki Sosai ake kara gyare gyaren masalacin da zagayensa an saka turaren wuta mai wani irin dadin kamshi ya zagaye ko'ina har cikin anguwanin kusa da gidan sarki Lokacin sallar juma'a na yi wajen ya gama daukan musulmai Ko'ina ka duba sune cikin shiga mai tsafta tarin musulman garin damagaram ne sun fito ba yara ba manya ba tsofafi, kowa ya fito cikin tsafta da turare a jikinsa ya zo da karfin gwuiwarsa da tarin son kasancewarsa a wannan waje mai albarka wajen da zai gabatar da sallar juma'a Dawakai biyu dake tafe da ado irin na sarakuna ya shaida cewa yau zunna da baki bayan sarkin garinsu harda wani sarkin Sosai aka ringa bada hanya ana miko gaisuwa har suka idasa shiga ciki sannan fogaren dake kakare da dawakansu suka rike dawakan aka rurufe saukarsu Sallah aka gabatar cike da nutsuwa, kafin a ja doguwar Adu'a sai kuma sanarwar a dakata za'a daura auren SARKIN GARIN AGADEZ Da yake akan yi daure dauren aure wasu har sun fara tashi sai dai jin daurin auren ya saka su komawa suka zauna Abih ya saki murmushi a lokacin da yake bayar da auren Zahrau, sai kuma wata nutsuwa da farin ciki ya shiga cikin zuciyarsa a lokacin da ya amshi sadakinta a hannayensa Daurin aure ya tafi cikin tsarin islama, ya amshi adu'o'in manyan malamai Lasifikar dake ajiye ce ke sanarwar daurin auren da ya saka zuciyoyi da dama neman tarwatsewa Daga kwoncen da dake a saman doguwar kujerar falonta daga kasa bayi ne ke yi mata hidima wasu na yi mata tausa wasu na hada mata abin bukatarta ta wuntsilo ta fado daga saman kujerar sannan ta ruruko idannuwanta tana kara kasa kunnayenta dan jin abinda ke fitowa daga spiker masalacin gidan mijinta Alhamdulilah, Alhamdulilah muryar liman ta furta a lokaci daya ya kuma maimaita kalmar" An daura auren SARKIN GARIN AGADEZ TARE DA GIMBIYA ZAHRAU BISA SADAKIN JAKA HAMSIN TARE DA DOKI MAI KWALIYAR ZINARI WANDA YA ZAMA HALALIYAR GIMBIYA ZAHRAU wani irin ihu ta saki daga tsayen da take Bata tsaya ta dauki alkyabarta ba ta juya da gudu ta nufi bangaren Anmy ta biyayiyar hanyarsu Hanya ce dake boye, wace ba kowa ya san da ita ba aman a yau ta tashi tonata bata tsaya wata wata ba ta bude kofar ta fada falon Anky dake dauke da Anmy da zuga zugan yan matanta da suka fito a gimbiyoyi reras a jere abin ba'a cewa komai Tana shiga hannayenta saman kanta ta furta" Anmy, me nake ji? An daura auren mahaifina da Zahrau wacece zahrau? A kan me sarki zai yarda a zo garin nan a yiwa mahaifiyata kishiya? Anmy kin san irin yanda Aya ta tsani maganar kishiya shine zai jaza min bakin jinni a wajen mahaifiyata? Walahi ba zai yiwu ba Anmy, Anmy wannan wani irin abu ne bai jima da tozartani ya min kishiya ya bara min abin fade a duniya baki daya ba shine yanzu zai jagoranci tozarcin uwata?? Baki dayansu idannuwansu a kanta suke Shigar jikinta riga ce diguwa irin ta shan iskar nan domin bata da kauri ko kadan sai malalalen gashin kanta dake daure da dan ribom Ga cikinta nan ya tasa sosai dan kamar ba cikin watani shida ba sosai ya fito dama alkyaba ke boye shi Anmy ta cire kanta daga dubanta a hankali ta furta" subahanallah Zulaihat, auren ne tozarci? Dama auren da mai martaba ya yi tozarci ne a wajenki ke a matsayinki na uwar gidansa? Sannan a yanzu kin ga halin da kike ciki kika fito a haka kina irin magangannun nan muryarki a sama sama tamkar ba ZINARIYAR Sarkin Danagaram ba? Dama haka kuke ko a yau ne abin ya sameki ? Kallonta Najeeba ta yi ta kuma kalli Anmy ta ga Anmy ta kawar da dubanta wato ita kunyar kallonta take ji a haka ita kuwa ta tsaya kikam sai surfa tambayoyi take da sakin zance haka Dubanta ne ta kai har wajen cikinta sannan ne ta ga shatin pant din dake cikin jikinta Itama da sauri ta cire kanta tana kallon Zahrau, Gani ta yi Zahra'un ta hade hannayenta ta rike da dan karfi Bata hannata ba, bata kuma yi gigin rarashinta ba, dan bata so tun yanzu ya zamanto ta ringa shiga wani hali bayan bata ga komai ba Juyawa ta yi ta shige ta bugo kofar da ya saka Anmy dago kanta da sauri ta kai dubanta wajen kofar Idannuwanta ta lumshe, a hankali take tambayar kanta....shin itane Zulaihat ta bugawa kofa a yau? Lale idan kana raye ba abinda ba zaka gani ba Yau itane aka bugowa kofa haka Idannuwanta ta kara rintsewa tana mai taune lebenta na kasa Aure? Abinda ta kwana da sannin cewa sai an mata shi ita dake auren sarki? Shine zata yi ikirarin an tozartata? ZULAIHAT kar ki saka ni zarginki mana? Zaihat kar ki saka zuciyata kin aminta da ke mana bayan hakan bai dace ba zato zunubi ne Zulaihat a kan auren ne kike aikata haka? Idannuwanta ta lumshe ta ji zuciyarta na furta mata" *MAI DAMAGARAM ZAI YI AURE, ZAI SAKE WANI AUREN KWANA KUSA KUWA ZULAHAT DOMIN NA IN DAI YARON YA GAJI MAHAIFINSA TO BA ZAI IYA ZAMA DA KWAYA DAYA TAK BA* Gaba daya hargitsewa gidan ya yi da hayaniya da gude gude da murna domin sai da aka daura auren ne aka shiga shigowa da abubuwan yanka ana yin waje da su dan za'a yi sadaka ne da su Ba'a jima ba gidan ya kwashi shiru sakamakon dogaren da suka fitar da kowa aka saki hanya aka kara gyara hanya Cike da nutsuwa da kasauta suke takowa har suka idasa shiga bangaren Anmy Tunda suka shigo gaba daya yan matan suka zube kasa kawunansu a kasa cike da girmamawa Waje suka samu suka zazauna kafin suke amsa gaisuwar Anmy Sai da wajen ya dan dauki shiru kafin cike da muryarsa mai nagarta ya buda bakinsa cikin nutsuwa ya koro adu'a Ya yi fatan alkhairi kafin ya dora da wata zazafar nasiha wace ta kare a aure bauta ne, zaman raya sunna ta je, Ya karashe da kausasa muryarsa yana fadin" kar na ji, kar na ga abinda zai saka ni taka kasar garin agadez ba da sunnan zumunci ba ya Zahrau Kanta dake kasa tana ta hawaye ta kara sadawa tana dan gyadawa Anmy ta yi musmushi da dan guntun hawaye a gurbin idannuwanta Najeeba ta kara rike hannunta dan zuwa lokacin hannunta daya a cikin na Najeeba dayan kuwa a cikin na Ummu Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya furta" ANMY, zan kaita da kaina ne Anmy ta gyada kanta ta sanyaya muryarta ta furta" zan so a je da yan uwanta su yi mata kwana biyu Allah ya ja da kwanakinka Kai tsaye ya furta" zamu je da UMMULKHAIR da UMMUKULSUM ANMY ta tsare shi da kallo da mamakin jin abinda ya fada, Abihma dake cen gefe yana amsa waya kasa kasa hankalinsa na kan yaren nasa, sai ya kebance da su sun zanta tare da yayansu, Dayabu kuwa yana zaune dan nesa da su shima a kasa ya tankwashe kafafuwansa ANMY ta ce" ai su uku ne, akoy NAJEEBA dubansa ya kara kaiwa wajen Anmy, da duba irin na kar ki min haka, kafin ya zafafa dubansa zuwa ga Najeeba wace tun da ya nuna banda ita ta dago da mamaki tana kallonsa itama cike da jin haushin kalamansa Irin duban da yake mata na tsananin tsana da wanda ta masa wanda tsaf duba me mai hade da harara kafin ta sada kanta tsaf a idannuwan Anmy Da mamaki ta kara dubansa ta kuma kalli Najeeba Murmushi ne ya kubuce mata kafin itama ta maida kanta ta sada tana jin wani tunani na son ta yi shi yanzu yanzu Muryar sakin Agadez cike da kamala ya furta" Allah ya ja da ran mai Damagaram, zan so a je da kanwata domin na tabata zata debewa Gimbiya kewa Yana fada ne yana nuna Najeeba hakan kuwa sai ya baiwa kowa mamaki ciki harda ita kanta Najeebar Yaya aka yi kike da farin jinni a wajen manyan mutane bayan ke din baki dace da samun hakan ba *MAGE?* Ya ayanna a ransa kafin yake cire dubansa daga kanta ya maida wajen Abih dake dawowa yana dan murmushi, shifa yau wani fayau yake jinsa, yau wani farin ciki yake ji mai girman gaske, yau ya aurar da daya Tun dazu yake samun kiran mahaifiyarta da kuma Mardiya wace ya ajiyeta gefe ya yi watsi da ita Yana karasowa shima kansa ya sada a gabansu, domin koda kuwa yana uba a wajen SHAHEED sannan siriki a wajen sarkin Agadez to fa shi din yana kasa da su ne daga indalah, Allah ya umarceshi da ya yi masu biyaya a matsayinsu na shuwagabanin kasarsa A hankali ya buda bakinsa yana kallon Abih ya ce""""" [31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 25 Cenxa harshensa ya yi zuwa harshen larabci, ya tausasa muryarsa ya kara sada kansa yana kallon yayan mahaifiyar tasa wanda ke zaune kusa da y'ayan nasa mata shima zuwa lokacin yannayin rashin son rabuwa da su ya bayana a tatare da shi A hankali ya furta" Allah ya saka da alkhairi Abih, Allah ya biya da dukan bukatu na alkhairi ya kara girma ya kara rufa asiri Yanda ka bani ragamar komai Allah ya fitar da ni da kai da kowa kunya a lamarin Kuma dagowa ta yi da mamakin jin irin yanda larabcinsa ke son yi mata wahalar fahimta bayan larabcin yarenta ne, kasancewar larabci ya shiga cikin junna sai ya yi anfani da baban mai wahalar wanda shi Abih din shi ya koya masa shi ya yi magana, a ciki abu kalilan ne ta fahimta Abih ya yi murmushi shima ya dauki yaren wanda ya tabata ko Anmy bata iya shi ba, shima kasancewar a saudiya ya yi karatu tun yana karami ya kasance yaren larabci kala biyu yake ji, da na wajen mahaifiyarsa da kuma wanda ya zame masa na makaranta ya bashi amsa kamar haka" nagartarka ta shaida kanta, bayan kasancewarka sarki sai kuma kyawawan halayenka suka sayan maka biyaya daga wajenmu iyayenka, Allah ya yi maka albarka, ya baka zuri'a dayiba A kasan zuciyarsa ya amsa da amen amen amen Kasa kasa ya yiwa Anmy bayanin ta inda zasu fito su shiga motar da zata sada su da aeroport nan da minti talatin Mikewa suka yi suka fita ta hanyar da suka shigo Anmy kuwa ta mike da sauri ta shiga hada hadar harhada mata dukan abubuwan bukata A lokacin ne Abih ya samu damar kadaicewa da su baki daya Kansa ya sada kafin ya dago yana dubansu Sun yi masa wani irin kyau mai birgewa sannan sun yi masa girman da sai yau ya yarda y'ayan nasa masha Allah sun fa girma Su dukansu sunna cikin wani danyen lesh ne, wanda ya tabata da kudinsa zai tambaya sai ya kalli Anmynsu a firgice hakan ya saka shi kin tambayar kudin domin abinda ya saka ya gansu da shi ya tabata ya kece kudin shada! Tun daga yan kunnayensu kuwa har zuwa sarkar wuyansu zinari ne da abin hannayensu, ta zahrau ce kawai ta banbanta ta kasance baba sosai da wani irin kira mai ban tsoro domin ba karama bace a girma da tsayi da fadi da kuma kyan fasali Alkyabobin dake jikinsu kadai abin kallo ne, ta Najeeba ce ta kasance shara shara mai shegen kyau A hankali ya ce" ban san da wace kalma zan yi anfani dan nuna maku irin tsananin farin cikin da nake ciki gannin Allah ya fitarwa da daya cikin miji nagartace mai daraja a doron kasa a lokacin da na fara shiga rudanin anya irin rikon da na yiwa iyayenku Allah ba zai jarabceni ta fannin zamanku a gabana haka ba?, sai na ringa kai kukana wajensa ina fada masa cewar kar ya kunyatamin ku, kar ya jarabeku da laifukana, ya dora min jarabawar a kaina komai girmanta ya sanyaya maku domin ku din baku ji ba baku gani ba hasalima halayana sun kasance masu saka ku fita a hayacinku lokuta da dama Murmushi ya saki ya dora da fadin" ina fatan yanda na ga naki, na ga na sauran har zuwa kan Nusaiba Ina adu'ar gidan aurenki ya kasance gidan da idan kin shiga in sha Allahu ba za'a fitar da ke ba har sai dai idan gawarki ce zata fito Da sauri Ummulkhair ta kalle shi da mamakinsa, sai kuma ta mayar da kanta ta sada Murmushi hakan ya bashi har ya kasance ya furta" ummu, dole na so kaina, ban san haka iyayen matan da na ringa yankawa tikiten zawarci suke ringa ji ba sai da na ji an shafa fatiyar daurin auren y'ata, sai abu biyu suka diro min lokaci daya tarin girmamen farin ciki da matsanancin faduwar gaban idanfa aka maido min ita? Sai na samu kaina da kebancewa na kai sujada na godewa Allah sannan na roke shi aa, ni kam kar na ga haka a ahalina Ya kara tausasa muryarsa ya ci gaba da fadin" Zahrau, kina da saukin hali da biyaya, ki kara jajircewa dan gannin kin kai ga ci a gidan mijinki, ki rike adininki, kar ki yi wasa da ibadarki in sha Allahu komai zai zo da sauki Kar ki yarda ki yi sake da su azkhar dinki duda na san dama ba mai wasan bace aman ki kara a kan na da, ke kin san rayuwar gidan sarauta daban take da rayuwar da ba ta gidan sarauta ba, yau ko dan zaki kebance a wajen da ba yan uwanki ba ni ba anmy dinku dole abin ya zo maki da wahala Aman idan kika kwontar da hankalinki haka ne aure ya gaji haka ba inda baya kai mutun Kanta ta ringa gyadawa kafin ya miko masu hannayensa Baki daya suka karasa jikinsa suka dodora kawunansu a jikinsa shi kuwa ya lumshe idannuwansa yana hangen abubuwa a gabansa masu yawa, da farko dai yana jin wani abu na kayar masa da gaba haka kawai, sai kuma burin da ya ci dan gannin ya gyara rayuwarsa shi kansa kafin a kai ga y'ayan nasa, dan kuwa ya dauki hanyar da zai gyara irin zamansa da kowama , in sha Allahu zai je ya kara bibiyar matan da ya saka idan ya samu wa'inda basu yi aure ba har yanzu ya kasance sunna da kyawawan halaya zai nemi aurensu ya dawo da su cikin ahalinsa su zauna Tabas ba zai saki Mardiya ba domin ya tabata Mardiya kam kadararsa ce A haka Anmy ta idasa fitar da abubuwan da ta tanada sannan suka mike du suka dadauka Kuka ne ya kwacewa Zahrau ta jimke hannayen Anmy Anmy bata hannata ba sai kara sakata a jikinta da ta yi, a hankali ta shiga rada mata" mamanki na agadez, tana anguwar kara kara na saka an binciko min cewar a cen ta yi aure tana zaune da y'ayanta uku, abin farin cikin mutumen da take aure jajirtacen mutun ne mai tsoron Allah sannan shi ke bada karatu a fada, in sha Allahu kin fita daga cikin dangi zaki je wajen dangi ne, mun gama magana da uta yanzun dan ta fadan tana ta kiran Abihnki ya ki yarda ya daga , na gama bincikena in sha Allahu ba komai ku je kawai Sai ta samu kanta da jin sasauci duda ba wata uwar shakuwa bace suka yi da mahaifiyar tata, aman sukan dan gaisa lokaci zuwa lokaci, bata san inda take aure ba sai yanzu hakan kuma ya mata dadi dan ko ba komai ta san ba zata rasa wasu yan uwan a cen ba duda family MUTALAB ba wanda zai kai zuciyarta irinsu Mota daya tal ce, ba tambarin shaida ko su waye a cikinta kamar yanda motocin suke dauke da tamburan gidan sarki da farin sunnansa Motar baka ce wulik sai sheki take sannan madubanta bakake ne wulik ba'a gannin na ciki ko kadan Bayan motar suka bude aka sakata a tsakiya yan uwanta du suka shige gefe da gefe Hannun Najeeba Anmy ta damko a sanyaye ta ce" na zuba masu tarbanku, na zuba datijan da nake baiwa amana sun bazu a cikin gidan Kar ku manta gidan sarauta na dauke da hatsari, kar ku manta inda zaku je ku din baki ne sannan bakin dake tafe da abinda kila wa kala ne idan ana so Ku kasance masu saka ido da adu'a, NAJEEBA kar na ji labarin fada a cikin tafiar Kanta ta ringa gyadawa tana ta murmushi har Anmy ta gama fada mata abinda ta tabata Ummu ce ya dace a fadawa aman da yake utane uwar fada sai ake fada mata Tana juyi kanta dan rufo motar sai da gabanta ya tsinke ya fadi Wanda ke zaune wajen direba ne idannuwansu suka hadu , a ranta ta furta: *DUNKUM* Gefensa kuwa sarkin garin Agadez ne Da sauri ta sada kanta tana mai kara nutsuwa, lalle a yanzun ta yarda akoy gagarumin abinda ya saka Dunkum biye wannan aure da tarin taka tsantsan Sai ta kara rike hannun yar uwarta tana mai tofa adu'a Wayar Ummu ce ta yi kuka DAYABU ne da ya rigayesu zuwa aeroport din dan tabatar da wajen zamansu a jirgin da zai tashi nan da yan mintuna ne ke tambayarta sun fito ne? Ta tabatar masa da sun fito sannan ya kali shugabar wajen dake tsaye dan hanya za'a buda sai sun dangana da cikin wajen da baban wajen ne ke zuwa da motarsa kafin su fito sannan sai an zuba dukan passinger sannan su shiga VIP dan gudun ido da daukan hankali kansu Tun da ya dauki hanya ya shiga falfala gudu da motar kamar wani gagarumin direba Sarafata ya yi cikin kwarewar da zai iya sarafa kujerar mulkinsa har ya sada su da wajen shiga jirgin Sun kai minti ashirin a zaune kafin suke fitowa Kukan dai take du sun damu da kukan nata sosai shi dai gaba ya yi sarki na biye da shi suka gama magana da Dayabu sannan suka shiga hawa Dayabu kasa tsayawa ya yi su yi salama domin shi dama mai rauni ne a kan yan kannen nasa sai kawai ya yi masu nuni da zasu yi waya ya gudu wajen motar da sarkin ya zo da ita yana hangensu sai da suka shige aka dan samu minti goma sannan kofar ta daga ta rufe sai fatan sauka lafia Basu wani jima ba suka sauka lafia a garin Agadez Nanma a wata motar suka nufi masarautar wace sunna karasawa aka basu damar shiga dan da waya ya shaida masu a bude hanya Direct bangarensa ya nufa da motar da su baki daya a ciki Sai da suka gama zama su dukansu zama irin na hutu a tafkeken falonsa mai adon Abzinawa sannan ya aika sako wa matansa biyu kan yana falo su same shi Mahaifiyar Zinaria ce ta fara zuwa da kuyanginta tana tambayar yaya aka yi ya dawo bata sani ba a cikin zuciyarta domin zinaria dai bata iya fada mata abinda ke faruwa ba hasalima tana cen ta gama shiryawa nufinta da ita za'a juya dan ta rantsewa mahaifiyar tata cewar bata san da maganar auren ba, tana cen tana jiran jin za'a tafi kai amarya ne Turus ta yi a lokacin da ta karaso falon da salama a hankali tana kallon yan matan dake jere saman kujera mai tsayi daya da kujerar mijinta wanda ta tabata wanda ya yi wannan gangancin to fa ba karami bane a wajen mijin nata Sai hakimtacen, nutsatsen, zakaran sirikinta dake zaune a dayar kujerar sarakan da idan sun zo sukan zama , sai mijinta gefensa sunna zaune tamkar abokai Dan murmushi ta saki, nan da nan jakadiya ta shiga miko gaisuwa da gaisuwar sarki ta musaman kafin ta karasa saman babar kujerar uwar gidan sarki ta haye ta hakimce ita ga hajia baba Sai ga mai dakin tsakiya itama ta shigo cikin shigarta ta alfarma Ita kam bata tsaya turus din ba saima gagawar karasawa ta zauna da take dan bin umarnin maman Zinaria cewar ta kiyayi neman waje a wajen mijinsu! Sai da suka gama zama kafin da hannunsa ya salami mutanen dake tare da su Sai da ya sha iska irin ta sarakai sannan ya budi bakinsa cikin tausasawa ya ce" ina farin cikin dawowata gareku iyalaina, Ina fatan na sameku lafia, Kawunansu suke amsawa sai irin kurema yan matan ido da ta yi ta kasa kwakwaran motsi Ci gaba ya yi da fadin" Alhamdulilah, tafia ta yi kyau, ina mai gabatar maku da kanwarku, abokiyar zamanku, yar uwarku GIMBIYA ZAHRAU a matsayin matata ta uku wace aka dauran aure da ita yau yau din nan a masarautar DAMAGARAM Baki dayansu sai da suka zabura da jin kalamansa, sai dai irin yanda fuskar ta tsakiyar ta nuna farin ciki karara da sakin murmushi da sada kai dq sauri ya sha bamban da irin yanda firgici tashin hankali, tukukin bakin ciki ya nuna kansa a fuskar maman Zinariya kafin take aro abinda ta fi iyawa wato kirsa ta yafa ta ringa kokowar danne bacin ranta ta yi iya yinta ta sasauta numfashinta har ya kuma furta" KANWA ce a wajen sarkin DAMAGARAM, Dubanta ta kai wajen mijin yar tata, wada take matukar shaku da tsoro, zata iya rantsewa idan sun yi magana da wannan mutumen bai fi a irga ba, domin yawancin lokuta koda maganar ta hado su da kai ne zai bata amsa ko da firgitatun idannuwan nan nasa ko da yar yatsarsa, idan kuwa abin ya kakare ya zama dole sai ya yi magana zata iya rantsewa a rasuwar dansa ko a wani gagarumin jajen da ta masa ne ya iya furta mata kalmar *ALHAMDULILAH* kawai Kafin ta maida dubanta kan yan matan Bata taba gannin bakar fatar da ta kayar mata da gaba irinta yaren nan baki dayansu ba, bata taba jin gabanta na dukan tara tara a gaban mace yar uwarta sai da ta ganta gaban yaren nan Me hakan ke nufi? Me auren sirrin da mai martaba ya yi ke nufi? Yaushe haka ta faru Zinaria bata sanar mata ba? Yaya aka yi sarkin ne da kansa ya kawo amaryar? Wa'inda suke tare kuwa su waye? Kara danne abinda ke damunta ta yi tana mau yiwa kanta alwashin ba abinda zai faru, zata kawar da ita kamar yanda take kawar da sauran kudirinsa na auren! Wato da ta bara masa wannan shahsashar bata ishe shi kwalamarsa ba sai da ya jara hango wata? Watarma kanwar sarki bama yar sarkin ba? Kanwarma ba ta jinni ba ta tabata yayan nan ne da Zinaria ta tsana gashi yau yau yarima yake dawowa daga tafiar da ya yi zai zo tare da matarsa da yarsa, Murmushin da ta saki karara zai nuna maka irin murmushin nan ne da ake yi iya laba kafin ta furta" masha Allah, Allah ya bada zaman lafia, bismillah ta tashi mu je ciki a yi mata shirin amare Sai a lokacin SHAHEED ya dago da dubansa ya sauke saman fuskarta, irin kallon da ya yi mata ne ya sakata saurin sada kanta ta yi shiru Sai da Sarkin garin Agadez ya shirya magana sannan ya furta" an gama yi mata komai, harta wajen zamanta an tanada, Allah ya sakawa gimbiya da alkhairi Wannan lamari ya kara girgizata, haka dole dole suka juya suka koma Sai da ya sadata da bangarenta wanda cikin ikon Allah bangaren ya kawatu da bangare biyu ne, kiri kiri SHAHEED ya zarce dayan ya saka kys ya bude ya shiga Da baki bude suka raka shi da kallo kafin suke kallon junna Hannayenta Zahrau ta kama a sanyaye ta ce" eyah, kin ga wace ake tunanin zata zubar da hauka sai ta zama wace ta fi kirki a cikinsu NAJEEBA ta yi sakalau da baki tana kallonta kafin ta ce " wato dai ke kunanyenki ke anfani a jikinki aunty? Zahrau ta kara tsareta da kallo Najeeba ta girgiza kanta ta ce" to ki saurara, idannuwanki nake so su kasance masu taka tsantsan, sannan bara na je na sanyo mamanki tana waje da kannenki tun safe, oh ki ce harda Dunkum a bangarenki? Da sauri du suka zaro ido har sunna rige rigen shigewa ciki jin alamun zai fito A hankali ya furta" ya zama dole mu zauna har kwana biyu a nan, dan ba zan tafi na barku a nan ba Yana gama fada ya fita da kansa dan gannin wa'inda ake so su shigo Nan da nan fadar ta dauka Farin ciki ne karara a fuskokin mutanen fadar da mamakin ashe dama zai iya kara aure? Farin cikin ya gama tarunma matarsa ta tsakiya wace ke tare da madaukakin farin cikin da ta kasa boyewa sai sanarwa yan uwanta take sunna tayata murna har fadi suke ya fara sakuwa itama zata samu yanci da yin adu'ar Allah ya basu zaman lafia Ita kuwa tana komawa ta kama kiran nunber zinariya wace nakudar dole ta kamata take ta gunjin kuka jin wai har sun tafi kamar zata haukace sai hauka take zubawa a gaban kuyanginta sunna biye da ita ga likita an kirawo ga Anmy a gefe a tsaye ta harde hannayenta tana kallon ikon Allah .......................................... Sun gana da yan uwa da bakin da ya yarda da su kafin yake zarcewa wajen sarki suka sake zama Irin adu'o'in da ya kara koyawa sarki ya saka shi kara jin nutsuwa da jin dadin auren, a haka yaronsa ya sauka da matarsa da yarsa Kana ganninsa zaka gane mutun ne dan gayu, sannan ya samu sangarta domin sai da ya karasa ya rungume aban nasa duda kasancewar katon namiji ingarma Sunna gamawa suka koma bangarensu da matarsa wace suke cikin masifa kusan sati biyu kennan rabonta da ta yarda da shi yana cikin tashin hankali da bukatar mace kasancewarsa mabukaci dan kawai ya yi budurwa a cen ta sakoshi gaba gata dama mahaifiyarsa ce ta daure mata take tsula iskancinta son ranta Shi dai ba mazinaci bane, aman a irin yanda yake jin kansa komai zai iya faruwa da shi idan bai samu mace ba shi yasa yana zuwa bangarensa ya sake neman lemun tsami ya sha duda yana kwadayin zuwa ya zauna da sarkin Garin Damagaram domin a rayuwarsa yana son idan Allah ya kara daukaka shi ya zamo yaron SHAHEED ko dan ya koyi kasaita da sarauta wace take zane a jinnin jikinsa Raba dare suka yi sunna ta hira suna wasa sunna daria Du sun saka kayan amarya na baci a jikinsu, daga mai wando da riga sai mai yar riga sunna ta shagalinsu sun samu pizza sun yi abinsu da kansu sai ci suke sun raba dare duda ita zahra'un carbinta ke hannunta tana ta ja a hankali tana neman kariya a wajen Allah domin mahaifiyarta ta zo mata da karin adu'o'in da mijinta ya bata ta kawo mata ga su rubutu, ita dai ta sha dan a yanzu bata da damar nuna ita ba zata sha rubutu ba, koda yake cen dama ita ba mai gardamar hakan bace Har karfe biyun dare ya tsala UMMUKULSUM ta mike ta nufi baya dan fita saman baban wajen da ya hada da na yariman gidan wanda wajen hutu ne sannan ta saman wajen kana iya hango garin yanda ake fadi idan dare ya yi yana da kyan kallo Ba wanda ya kula da ita har ta tafiarta Tana zuwa ta karasa ta yi tsaye tana wara hannayenta bata ko tsoro tana kallo tana sakin murmushi mai dadi da jin wata sansanyar iska na kadawa Ta dauki minti hudu a haka lokaci daya ta ji an rufe mata bakinta ruf da hancinta kafin ake juyota da karfin gaske Rigar dake jikinta da wandon dake jikinta aka yi anfani da karfi aka yage mata su kafin ake kaita kasa nan saman wajen da ba ko shinfida aka bi bayanta aka dane ruwan cikinta Fuskarsa kawai ta iya gani sai sumewa da ta yi tsabar firgici, shi kuwa yana furta" na shiga uku wayo zan mutu ya afka mata ido rufe yana neman nutsuwar dake neman saka shi kurma ihu tamkar mahaukaci a irin wannan dare haka Gaba dayansa yake kara shigarta gashi kuma yana gunjin kukan wahala da tsoro yana furta shi ba mazinaci bane ta yafe masa Irin yanda suka ga shiru ummu bata dawo ba ya saka NAJEEBA mikewa daga ita sai yar rigarta dake jikinta wace bata fi daidai duwawunta ba domin duwawun nata sun kwasheta gashi rigar pant kawai ta saka a ciki ba rigar mana, gata fara ce rigar mai santsin gaske ta labe ta fitar da shatin mamanta wanda kawunansu ke tsaitsaye sun kara tauri sakamakon irin sanyin dake hurawa a garin wanda ke saka yannayin mutun daukan lamarin Du iran ta daga kafarta sai yannayinta ya cenza salon takun duwawunta na yin sama da kasa kamar wace ke yi da gangan Ummulkhaire ta mata daria tana fadin" dubita ku dawo mu kwonta kun ga muna so mu yi safia mu kara cenza zaman gadon nan na zahrau ni sam zamansa bai mun ba, ga abinda Anmy ta fada cewar mu fafarke katifar mu lalubeta tas kar ta kwonta a sama kafin mu lalubetan Amsata ta yi ta idasa fita ta nufi wajen da tun dazu Ummukulsum ke fadin ita dai yau sai ta ga abinda ake fadi cewar ai idan dare ya tsala wajen kan daukan wani irin haske tamkar parisss ko karyar yan makarantarsu ne? Sai da ta yi mika ta yi hama a hankali ta furta" Ummu ya isa haka kallon Paris din ki zo mu je mu kwonta dare fa na yi kuma kin san Zahrau ba zata barmu mu kwonta bamu yi nafila ba Karasa hayewa saman ta yi, lokaci daya kunnayenta ke tsinkayo mata magangannu da gurnani, kukan namiji da yanda yake ihun shi ba mazinaci bane, da irin yanda yake fadin wayo dadi zai kashe shi ya sakata saurin juyawa wajen dan ta tabata yayarta dai nan ta shigo, wannan kalamai kuwa sun so tarwatsa zuciyarta Inda idannuwanta suka sauka sakamakon hasken farin watan da ya yi dau tamkar an kunna fitila mai hasken gaske ya sakata jin fitsari na neman fitowa daga mararta Hango bayan katon namiji da hannun yayarta a kasansa ya sakata jin numfashinta zai bar gangar jikinta Du fitsararta, du tarin samarinta bata taba gannin bayan namiji haka ba, bata taba gannin tsiraicin namiji ba, uwa uba a kan yayarta Gaba daya ta zabura ta kwala wani irin firgitatacen ihun da ya saka shi rintse idannuwansa a lokacin a kansa ke sade ya dora sujada yana adu'a Da sauri ya tashi ya yi tahia a gagauce ya salame ya mike ya warci rawaninsa Yana fitowa da wani irin karfi da sauri yana kuma nada rawaninsa hakan ya yi daidai da sauranma sun firfito Ihun da take kwalawa ya saka a tare suka nufi hanyar, sai dai irin tsawar da ya daka masu na cewar su yi baya ya saka su saurin yin bayan aman kamar zasu summe su biyu sai kama sunnanta suke sunna ihun meye?? Wayo na shiga uku, wayo na mutu na lalace, tana ihun ne tana jan numfashinta dake sama sosai Yana shigowa ya hangeta tana daka tsalen albarka baki daya jikinta na tafia da ita hannayenta saman kanta kafin ta duke tana kallon wajen da ya yi gagawar zarewa ba tare da ko ya samu ya kawo ba aman mai afkuwar ta gama afkuwa domin dai a yau ya mayar da UMMU cikakiyar mace ta hanyar ratsata da gararia first night din yayarta ita ta kawo budurci Da sauri ya karasa ya saka hannunsa ya dagota, muryarsa a cinkushe ya buda bakinsa zai tambayeta uban me take ma ihu Sai dai bakinsa ya yi dif a lokacin da ta kamo hannunsa ta dora saman kirjinta gefen zuciyarta ta hagu wanda ya yi daidai da saman mamanta das ta dora da karfi ta damki wajen tana ihun fadin" zata fashe wayo zuciyata zata fashe, wayo ya kashe mu, ya kashe mu, wayo yayata ya wulakantata ya halakata Sai kuma ta idasa zubewa dif ta gama sumewa Inda ya ji alamun motsi ya kai dubansa Da sauri ya rintse idannuwansa da wata irin faduwar gaba mai balakin karfi ga kuma NAJEEBA a jikinsa ta sume inda ya talabeta baki dayanta a hannunsa daya, idannuwansa kuwa tun da ya ga abinda ya gani ya rintse da karfi yana fatan Allah ya sa ba abinda yake ganni bane wato Yarima tsugune gaban UMMU zigidir baki daya jikinsa na rawa harta da hannayensa da dukan gabai nasa da irin kalaman da yake fadi yana talabota da hannayensa yana fadin" Barka da safiya [31/03 à 21:39] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 26 "Innalilahi wa'ina ilaihi raj-une! Wacece wannan? Daga ina ta fito? Na halaka kaina na halaka yar mutane, wayo Allahna na kashe rayuwar yar mutane na kashe kaina, wayo na shiga ukuna yau na tafka kuskure mafi muni a rayuwana, wayo ni ba mazinaci bane zanen k'addarata ne, wayo matata ce ta janyo min ta hana min kanta bayan ina da ita, na shiga uku na lalace." Hannunsa na dama ya saka ya tare hanyar da Ummulkhair ke son lekowa sakamakon kalamansa da suke daukaka girman fitowar furucinsa Wani ihun ta saka itama hakan ya saka shi daukan NAJEEBA dauka irin na jarirai ya fito Hannunta ya damka kafin da idannuwansa ya yiwa ZAHRA nuni da ta biyo bayansa Gaba daya bari jikinta yake Dukan gabanta kamar ba nata ba haka ta ringa hada hanya ita tama rasa me take ciki har suka idasa shigowa falonta ya shinfide NAJEEBA nan kasa saman cafet sanan ya yi masu nuni da su zauna Juyawa ya yi da sauri ya koma, lokaci daya mazan dogaran sun fara farga har an fara nufi wajen sannan tuni an kaiwa sarki kabarin ana jin murya na kuka sama sama kamar ta yarima da kuma wata mace hakan ua saka shi fitowa da saurin gaske bayan ya warto sharbebiyar wukarsa ta yaki mai sunna Babarbara Yana komawa ya saka hannunsa ya karbeta a hannunsa, kafin yake rufa mata mayafin da ya shigo da shi a wajen sirrinta Haske ya kunna hakan ya saka Yarima saurin wartar wandonsa jikinsa na bari ya shiga kokarin sakawa Wajen wuyanta ya shiga dora hannunsa, lokaci daya yana waigen bayan da yake sama ne suke yana hangen yanda gidan ke ta kai kawon dogarai wasu na tambayar daga inda ihun yake sai kokarin karasowa suke Matan sarki ne suka fito a firfirgice du sunna kokarin yin inda ake fadin ihu na fitowa Giftawarsa da dogarai majiya karfi sai kirarin yaki suke a bayansa ya saka jikin matan nasa kwasar rawa Da sauri suka bi bayansa kowace da irin abinda take sakawa a kasan zuciyarta, fatan Gimbiya ta tarar da amarya ce ta mace! Dakatawa ya yi duba da falon amaryarsa ne za'a shiga ya tsayar da baki daya dogaran waje daya sannan ya shige da saurin tsiya Saurin kawar da kansa ya yi daga kansu gannin du jikinsu da shigar baci ne sannan sun zagaye yar uwarsu Wajen da yake jin muryar yarima baban dansa ya nufa da sauri babarbararsa a hannunsa Yana hankada kofar wajen ya shige da sauri yana tambayar abinda ke faruwa da yaren buzanci Abubuwan da yarima ke kara maimaitawa da irin yanda SHAHEED ya gyara mata kwonciya tamkar mataciya ya saka sarki zaro idannuwansa baki daya jikinsa ya kama bari Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une Da wani irin bacin rai ya nufe shi da wukar nan yana dagawa a fili ya furta" tirr da kai FARID, gwara na kasheka da hannuna na huta Da sauri ya yi wata irin dira ya tari gaban mai martaba kafin yake saka hannunsa ya tare wukar nan da hannu daya ya janyeta daga hannunsa ya riketa taf a hannun nasa Ihun kukan da ta saka tana dora hannayenta duka biyu a saman kanta ne ya ankarar da fitowarta hakama mahaifiyarsa gaba daya jikinta ya dauki wani irin bari itama ta dora hannayenta saman kanta tana jin abinda ke shirin riskarta duka a zuwa bakaken halitar nan! A yau ta ga balakin da ko mutuwar ubanta bai girgiza mata kwakwaluwa irinsa ba Tashin hankali ya risketa na mamaki kafin ta gama fahimtar wani ko baci ya ki daukanta ga wani ya sameta yau itace tsaye a gaban tarin abin kunyar nan Sai kawai ta dafe kirjinta ta silale kasa Muryarsa a dake ya furta" idan har magana ta daukaka ta fita tsakar gida ba abinda zan iya yi maku baki daya! Ku sanni sirrin masu mulki, da manyan malamai ya fi tarwatsa al'umah, ya fi lalata tarbiya! Ku sani idan har waje ta dauka haka ya faru da yariman garin agadez to kuwa matasan garin agadez zasu dauka su mayar da hakan abin yi! Ana iya tankwasa rigima idan bata yi yawa ba! Yana gama fada karasawa ya yi ya sungumeta ya fito da ita Dakin Zahrau ya nufa da ita kafin ya kuma fitowa ya sungumi NAJEEBA itama ya nufi dakin da ita sannan ya yiwa sauran alamun su biyo shi Saman bed du ya jera su kafin ya yi tsaye ya kura masu ido Ta ina zai fara? Me zai ce? Tabas sun shiga rudani mai girman gaske, shi kansa ji yake kamar zuciyarsa zata samu matsala a irin lamari An dauki kamar mintunna ashirin sai ga bugawar kofar, du a zaune suke sunna ta kuka su biyun, Ummu ta dawo hayacinta aman bata iya komai waje daya kawai take kallo sai hawayen dake bin gefen kumatunta Shi kuwa yana tsaye ya kura ma waje daya ido Karasawa ya yi ya bude kofar Likita ce ta shigo Sarki kuwa na tsaye daga baki baki bai shiga ba domin ya san ko a yanzu basu saka kaya ba, irin yanda yake zufa sai abin ya baka tausayi ya koma ya jingina da kofar yana kallon yanda iyalansa suka rikice NAJEEBA dake sume ta fara baiwa taimakon gagawa Ai kuwa ta farka a rikice tana ta waige waige, sai ta kwala ihu mai karfin gaske ta fashe da matsanancin kukan da ya saka yan uwanta suma fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya da zafin gaske sunna ririke junna Karasowa ya yi ya saka hannunsa ya bambare hannun Zahrau daga jikin Najeeba kafin ya kuma saka hannunsa ya k'ara cicib'arta. Bai zame ko ina da ita ba sai cikin bayi direct ya idasa wajen bath da ita. Zaunar da ita yayi sai ihun take tana kuka kamar ranta zai fita ga gazar gazar din gashin idannuwan nan nata sai kara far suke. Bata tsamaci jin ruwa ba sai saukarsa ta ji a kanta hakan ya saka gashin kanta gaba dayansa ya yi lingib a bayanta da wani karfi ta so zabura ta tashi sai dai ya saka hannunsa ya maida ita cikin ruwa ya zaunar da ita sannan ya riketa tam a ciki. Tun tana gunjin kukan har ya zama ta ringa rage sautinsa tana yi sannu sannu har ya dawo na zuci ne take yi sai hucin da take furzarwa. A hankali ta langab'e a saman damtsen hannunsa shima ruwan ya jik'a masa jalabiyar jikinsa cikin wata shak'ak'iyar murya dake cen ciki ta furta" Ya halakamu, ya wulak'antamu, ya goga mana penti, me mukai masa? Ya ketawa yar uwata hadi." Gani yake ta d'aukaka firgicinta, gani yake ta zurfafa firgicinta bayan ba haka ya dace ta nuna ba duba da ita din aikinta kennan, harkar maza ya zame mata abinda ta fi k'warewa a kai, akan me zata ringa irin wannan abu? Sai yake tunanin tana pretending ne, sai yake gannin kamar so take ta raina masa hankali Jin rawaninsa na son jik'ewa ya saka ya ringa janye jikinsa a nata Idannuwansa ya sauke a kanta da niyyar yi mata magana sai dai da kansa ya kawar da kansa da wani irin sauri yana mai rintse idannuwansa domin ruwan nan da ya jik'a mata jiki da shi baki daya ya lafe mata da rigar nan mai santsi a jikinta a yanzu ne hallitar k'irjinta ta wani irin bayanuwar da ta saka shi ji gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa. *(mai damagaram yana ruwa, kusa da kada inji breaker🤣)* Mik'ewa yayi da sauri ya juya ya fita a bayin. Yana fitowa ya tarar da su sun saka suturun da suka rufe masu suturarsu, sannan sunna zazaune gefen kanta likitar kuwa ta bata maganin da zata sha dan rage rad'ad'in dake damunta na bak'on lamarin daya ziyarceta bayanshi bata samu wani mugun raunin da zai saka a kaita asibiti ko a mata d'inki ba, tana shiga ruwan zafi komai zai dawo normal sai dai abinda aka yaye din da ba za'a iya maido shi ba. Tawul ya d'auko ya mik'awa Ummu ya nuna mata bayi hakan ya ganar da ita abinda yake nufi. Wasu kayan ta d'aukar mata ta nufi bayin da su. Kamata tayi ta fitar da ita daga cikin ruwan dan har lokacin tana ta zubar da hawaye wani irin ciwo take ji a zuciyarta domin a rayuwarta idan akoy abinda ke tayar mata da hankali, ya sakata a firgici to fa irin abinnan ne. Kayan ta saka jikinta a mace suka fito tare. K'arasawa tayi ita ma ta zauna ta d'ora kanta gefen wuyan Ummu Muryarta a sanyaye ta ce" Ummu, kiyi magana mana, dan Allah ki ce wani abu mana." Suma hawayen suka ringa sharewa shi kuwa yana kallonsu. Sun d'auki kamar minti goma a haka kafin a hankali ta bud'a bakinta, hawaye ne wasu ke korar wasu cikin disashiyar muryarta ta furta" Dama me kuke jira da rayuwata? Kun manta wacece mahaifiyata? Yanzu haka idan kuka je tudun jamus layi na biyu babbar k'ofa mai ruwan blue gidanta ne, zaune take tana amsar kud'in wannan." "Ki yi min shiru!" Ya bud'a bakinsa tun d'azun ya fad'a da wata murya ta tsawa wace ta saka du suka rintse idannuwansu suka sada kawunansu Muryarsa ya kuma bud'awa yana cijewa yace" ku tashi baki d'ayanku mu fita!" Da sauri Najeeba ta d'ago tana kallonsa, sai dai ba damar yin magana domin har ya juya ya fara fita. Zahrau kam bata da katab'us, baki d'aya duniyar ce ta yi mata zafi ta rasa wani tunani zata yi da irin wannan lamari, aman tsawatarwar daya yiwa ummu ta sakata jin dama dama domin idan har haka zata ringa fad'i idan bakinta ya bud'e tana iya idasa halaka masu tunani su yi ta kuka. Kamata suka yi ta mik'e da k'yar tana rintse idannuwanta kafin ta sauko. Kamata suka yi a hankali tana tafiya suka fito domin basu san inda zai kaisu ba, su kuwa basu isa su k'i fitowar ba. Irin yanda suka ga duk mutane ne a zazaune kama daga Sarkin Agadez, na damagaram, Gimbiyoyin, yarima da matarsa sai du suka ji hankalinsu ya k'ara tashi. A hankali suka k'arasa da niyyar zaunar da ita a kasa, sarkin garin Agadez dake kallonsu ne kamar zai fashe da kuka shi kam ko rawanin babu a kansa yau an yi abinda ya cujewa buzu nad'i ya nuna masu doguwar kujerar dake ajiye." Nufar wajen suka yi suka zaunar da ita kafin su zauna kusa da ita sosai a jikinta. Najeeba irin kallon da take bin yarima da mahaifiyarsa da shi irin kallon nan ne wanda zaka ji kamar ka kashe mutun. Yayi d'agowar kansa ya fi a k'irga sai zai bud'i baki sai ya kasa hakan ya saka Gimbiya saurin zamowa kasa ta had'e hannayenta tana kallonsa muryarta na rawa ta furta" dan girman Allah a rufa mana asiri, kar ku manta yarima shine mai jiran gado, sirrinsa ya fita tamkar sirrin baki d'aya gidan nan ne zai fita, Allah ya huci zuciyarka a rufawa yarima asiri a gafarta masa." Tayi gaggawar juyar da kanta wajen SHAHEED ta d'an k'ara rarafawa hannayenta a had'e ta ci gaba da fadin" Ku rufa mana asiri, wannan sirri namu ne baki d'aya, dan girman Allah ku rufa mana asiri." Du wani motsin kowa yana hakimce ne yana bi da kallo, bai furta ko A ba. Kansa dake kasa ya dago, irin kukan da yake sai ya baiwa mutun tausayi. Da sauro ya rarrafa ya nufi wajenta hakan ya sa sarki sakar masa tsawar da ta saka bai idasa idasawa har inda take ba aman ya ja daga d'an nesa. Hannayensa ya had'e ya kara duk'awa sosai yana ta kuka kamar zai mutu yace" Dan girman Allah ki yafe min wannan lamari da na aikata maki, na rantse maki da Allah ni ba mazinaci bane na je d'akin iyalina ne ta fito ta bar min d'akin sai na biyo bayanta a tunanina inda kike tsaye itace a tsaye domin idannuwana sun rufe, satina biyu kennan tana guje min a shinfid'ata, zaki ga na rufe maki ido da bakinki ba dan komai ba sai dan sannin tana iya k'wala min ihu ta tara min jama'a ni kuwa na yi alk'awarin a daren sai ta bani hakk'ina, ban san cewa ba da ita nake mu'amala ba sai da na kai ga shiga wajen da ba nawa ba, wallahi wallahi ni ba mazinaci bane, sannan ba mai afkawa mutane bane, na kasance ina koyi da halayen nagartatun mutane dan na kasance nagartace, ban tab'a aikata zina ba ko a lokacin da bani da aure, dan girman Allah ki yafe min wannan b'arna da na aikatawa rayuwarki sannan na aikatawa rayuwata, ki maka ni kotu a yanke min hukunci daidai da laifina ko ki kaini kotun musulunci a yanke min hukuncin jifa domin ba zan iya rintsa ido da hak'inki irin haka a kaina ba." Mahaifiyarsa ce ta fashe da kuka mai tsanani. Da sauri ya juya ya k'arasa kusa da SHAHEED ya duk'a ya kama k'afafuwansa yana gunsheken kuka ya shiga fadin" Dan Allah yaya ka saka baki ta yafe min, ka saka baki ta gafarta min kar abin nan ya tab'a d'iyan d'iyana, ka ga wannan dake zaune zata iya maimaita abinda ya faru tsakanina da ita kafin ta baro d'akina, hakan yasa na biyota da sauri ban san inda ta lab'e min ba na fito da gudu ina nemanta sannan itama wando ne a jikinta da rigar baci na rufe bakinta da hanuna da idanuwanta dan kar ta min ihu ko ta fad'a min abinda zai fitar min da son zuwa gareta a raina hakan ya sa na afka mata, ba zan iya fahimtar ba da matata nake ciki ba, hankalina ya gama tafia burina na samu nutsuwa." Gannin ya k'ura masa firgitatun idanuwan nan nasa masu matuk'ar abin tsoro ya saka shi sakinsa ya juya wajen mahaifinsa ya karasa ya kama k'afarsa. Kafin ya fara magana ya hamb'are shi da k'afar tasa hakan yasa ya fad'i gefe aman bai gaza ba ya kuma tashi ya kara ruk'unk'ume k'afar tasa yana wani irin kuka murya a cakule ya furta"BABA." Sarki ya saka k'afarsa yana kiciniyar kuma hamb'are shi aman ya gaza dan baki d'aya jikinsa yayi sanyi lamarin ya shige shi a lokacin da bai shiryawa hakan ba. Muryarsa ya bud'a a birkice ya furta" Inna lillahi wa'ina ilaihi raj'une." Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une! Sai kawai muryarsa ta shiga rawa sai kuka ya k'wace masa, hakan ya saka SHAHEED saurin rintse idanuwansa ya sadda kansa. Muryarsa na rawa ya shiga furta" Lalle kana wasa da adininka, kana wasa da ibadunka, idan kuwa ba haka ba kaima k'addararka mai tsauri ce domin kamar yanda ka fad'a saina hukuntaka! Wani irin rayuwar aure kake da macen dake gudunka har cutuwa ta shiga tsakaninku haka mai tsanani mugun raini ya shiga tsakaninku har ya kaika ga neman afka mata da tsiya ya kasance ka fad'a kan wace ba ita ba?" Dubansa ya kai kan matar tasa dake kukan ita ma cike da dana sani ya furta" Anyi haka? Mijinki ya zo maki kin fito da suturar da tayi kamanceceniya da ta baiwar Allahn nan? Idan waje ya ga kin nufa ina kika lab'e masa ya fito waje nemanki? Kina ganni ya aikata haka baki katse masa hanzari ba ko baki gani ba?" Fashewa tayi da kuka tana k'ara sada kanta muryarta na rawa ta ce" Allah ya huci zuciyarka a yi mana afuwa, a gafarta mana, a ji k'anmu, tabbas hakan ya faru daidai da abinda ya fad'a, kuma a lokacin da na zo fita lab'ewa na yi dan ina jin haushinsa ya hana min wasu kud'ad'e, dan ina so yana fita na koma na d'auka domin mun jima muna gaba tsakaninmu sakamakon mahaifiyarsa ta nunan cewa kar na yarda ya yi yan mata ko ya yi tarayya da 'ya'yan turawa a waje shi kuwa yayi budurwa shine ni kuwa nake nuna masa fushina ta hanyar hana masa abinda yake buk'atar." Sai kuma ta k'ara sadda kanta tana kukan da na sani da tarin nadama. Kansa yake girgizawa ya ma rasa me zai ce? A hankali ya furta" Ga irinta nan, ga irinta nan, kin yiwa sarakuwarki muguwar hud'ubar ita ma kar a mata kishiya ga inda abin ya kaiki, lalle ke ba uwa ta gari bace, ke ba mata ta gari bace sannan ke ba shugaba ta gari bace, tabbas kema hukunci zai hau kanki domin ba zan iya ci gaba da zama da ke a matsayin matata ta aure ba." Baki d'ayansu a zabure suke kallonsa sai a lokacin SHAHEED yayi gyaran murya yana kallonsa ya furta" Allah ya huci zuciyarka, Allah ya ja da zamaninka tuba muke." Baki d'aya suka ringa maimaitawa banda su NAJEEBA. Kansa ya k'ara sadawa ya shiga fadin" Tabbas wannan lamari idan ma da ganganci a ciki to fa zanen k'addara ce, abin ne ya zo a harhad'e, shi ga abinda ya fitar da shi daga d'akinsa ita ma ga irin lokacin da ta kai tare da yan uwanta suna shashanci maimakun su kasance a cikin bautar ubangiji!" Sasautawa yayi ya kuma d'auka da cewa" Tir da matar dake gudun shinfid'ar mijinta, tabas kina cikin tsinuwar ubangiji sannan kina da naki kason a cikin wannan lamari." Dubansa ya maida wajen yarima ya kausasa muryarsa ya furta" Tir da namijin da ba zai iya rige arzizimun wandonsa a lokacind a fitinarsa ke harbinsa ba!" Sai kuma ya maida dubansa wajen Gimbiya ya sasauta muryarsa ya furta" Kaico ga uwar da zata ringa shinfid'a hanyoyin b'araka a cikin ahalinta, domin kuwa wannan uwa ta d'auko hanyar tarwatsa iyalanta da al'uma mai yawa, dan kuwa mu dukanmu muna samun tarbiya ne daga iyayenmu, daga bakin lokacin da aka samu gurb'attaciyar tarbiya lamarin b'atanci zai yawaita a cikin al'umah." Sassauta muryarsa yayi yana kallon sarki ya furta" Rud'ani, tashin hankali ya hana min kallonsu a cikin idannuwa, sai dai ya zama dole zamu hau wata shari'ar a yau a wajen nan dan danne wata b'arakar, amar yanda na fad'a cewar a duniya baki d'aya babu mumunan sirrin da fitarsa ke haifar da mugayen sakamako irin sirin masu mulki da kuma manyan malamai da masu iko, akan d'auki hakan da fuska biyu, masu d'aukarsa da mummunar fuska ta hanyar kwaikwaya sukan yi yawa a cikin duniya baki d'aya, k'alilan ne ke yi masa kyakyawan fahimta har su gane b'atancinsa." Kuma kausasa muryarsa yayi ya furta" Ba'a kyauta ba, an tafka abinda Allah ya haramta, sannan an shiga hakin baiwar Allahn da bata ji ba bata gani ba." Shiru ya kuma yi kafin ya dubi wajensu. Muryarsa ya sanyaya sosai kafin ya furta" UMMUKULSUM, shin zaki iya jurewa, ki jajirce, ki d'auki hak'uri ki yafewa bawan Allahn nan duba da irin abubuwan da suka gabata da shaidar wace abin ya faru a sanadiyarta ? Zaki iya yafe masa har cikin zuciyarki? Ki tuna Allah na yafewa bayinsa masu yafiya ya Ummu." Kanta dake kife a jikin kafad'ar Najeeba tun daya kama k'afarta yana gunsheken kukan nan ta ji wani irin tausayinsa ya tsirga mata haka kawai sannan wani irin tsigar jikinta ta ringa tashi, bata k'arasa jin tausayinsa ba sai da ta ji kalaman mahaifinsa da kukan mahaifinsa da shi kansa. Gimbiya ce ta k'ara duk'awa tana kallonta muryarta na rawa ta furta" Ki rufa masa asiri, ki rufawa kanki Ummukulsum, kar ki manta kema mace ce, fitar sirin nan tamkar fitar da sirrinki ne, ki rufe shi dan girman Allah." Cire dubanta ta yi daga kanta, muryarta na rawa ta furta" Na yafe masa." Sai kuma ta fashe da kukan da ya saka Najeeba wace jikinta ya d'ume da zafi kanta na sarawa ita ma fashewa da kukan tana k'ara rungumeta, Zahrau kuwa ta zama wata mutun mutumi sai juya kai take baki d'aya ta rasa me take ji. Hamdallah yayi kafin ya maida dubansa wajen sarki a sanyaye sarki ya ringa sakin ajiyar zuciya, muryarsa a sanyaye ya furta" ina neman alfarma, ina neman alfarmar a bar min ita a nan gidan, ta yi istibra'i a d'aura masu aure, domin na rantse shi zai gyara abinda ya lalata." Daga Gimbiya har matarsa a tsorace suka kalli sarkin da ya watsar da su yana cike da jin haushinsu, sam tamkar basa wajen tun da ya masu tambaya yayi watsi dasu. Da baya ta kai zaune tana mai d'ora hannayenta saman kanta a b'oye, kishiyarta kuwa bayan tarin tausayin yarima domin yaron yana da mutunci sosai, sai kuma tarin al'ajabin abinda ke shirin faruwa, auren yarima da matarsa aure aka yi na zobe, yar k'awar gimbiya ta k'ud da k'ud wace ak'idarsu d'aya cewar ba za'a yi masu kishiya bace ya aura, hakan yasa Gimbiyar ke taya ta yak'in maganar kishiya sai gashi a yau abu biyu ya faru da su baki d'aya, wato wanzuwar *KISHIYA* a tsarin da basu ajiyeta ba. Kansa ya kuma sadawa yarima ya k'ara duk'awa shima yana rok'an hakan. Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya furta" zamu juya gida a jirgin safe in sha Allahu, zan yi kira na sanar da abinda ake ciki." A haka dole aka tashi, sarki na zaune saida kowa ya tashi sannan ya bi bayan Zahrau dake son shiga d'akin jikinta a mace. Hannunta ya kamo ya maidota baya A hankali ya sakata cikin jikinsa ya rungumeta yana buga bayanta kad'an kad'an kafin ya jata suka koma saman kujerar Sai a lokacin ta samu kuka ya kubce mata cike da tsoro take nuna masa ba zata iya zama ba yan uwanta a wannan gidan da ya gama tsoratata ba. Sosai yayi anfani da hikima ya ringa rarashinta har ta dawo nutsuwarta ta ringa sauke ajiyar zuciya da kansa ya mata alk'awarin zai nemi alfarmar malan ya bashi y'aya biyu k'annenta su tare da ita su tayata zama kafin a kawo mata Ummu. Da wannan ya samu ta kwontar da hankalinta kafin ya rakata har d'akin suka ci gaba da gabatar da sallah baki d'ayansu suna godewa Allah da irin wannan ranar. .................................... Zabura ya yi tsaye sai kuma ya yanke jiki ya fad'i zaune saman kafet d'in hannayensa aje saman kansa muryarsa na rawa ya furta" innalilahi wa'inna ilaihi raj.une, hasbunnalahu wani'imal wakim aya ta tabbata a kaina ni MUTALAB gashi, abinda na aikata ya kamo ni da wuri haka a kan yarinyata." Sai ya fashe da kuka yana kallon yanda D'AYABU ya tsurawa sarki ido kamar wanda ya suma a zaune. Da sauri Anmy dake kukan itama ta kaleshi a firgice jin zai tona asirin da suke lullub'ewa kansu da k'afarsu, zai tonawa kansa asiri a cikin irin rud'anin nan da suke ciki zai k'ara masu wani. Duban da Ummu ke masa ne ya saka shi k'ara sada kansa yana hawaye Ummulkhair ta kalli Najeeba wace ita ma ita take kallo kafin Najeeba ta bud'a bakinta a hankalì tana kallon Ummulkhair tana dan yatsine fuskarta tace" eyah, eyah, yau kin yarda da ayar tambayar da na d'ora a kan maganar da Abih kan fad'a wani sa'in?" Maida dubanta tayi wajen Abih a sanyaye ta furta" *ABIH, WACE AYA CE TA TABBATA A KANKA?* komawa sarki yayi ya jinginar da bayansa jikin kujera yana lumshe idannuwansa, ta faru kuma ta k'are, rikicin cikin gidansu zai k'ara kunnuwa a yanzu, ya tabbata wani tashin hankalin ne zai k'ara kunno kansa hakan ya saka ya idasa had'e fuskarsa da dukan wani abu wai shi annuri ya lumshe idanuwansa a lokacin da Anmy a firgice ta kallesu tace "... Happy juma'at [31/03 à 21:39] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 28 Bata motsa daga yanda take ba tana dai kitson tana kallon yanda yake iya yinsa dan gannin sun barshi ya shigo wajen Kasancewar saloon dinta, sun kwana da sannin maza kan shiga ya saka ba wace ta wani damu dan sun hangi namiji na son shigowa domin akoy mazan dake zuwa takanas a yi masu manyan kitson nan na irin samarin nan na zamani Wasun kuwa sukan rako yan matansu ne wasu kuwa su kawo matayensu Nadia ta mike tana daukan dan kwalinta ta ce" a gaskiya wannan sabon tsari na tare mutun a waje ba zai haifa mana d'a da ido ba, ni banma san a kan wani dalili zaki yarda da irin lamarin nan ke da bakya so Ita dai bata ce komai ba sai dan sauran gashin da ya yi saura take son idasa kitsewa Fita ta yi ta shiga kokarin gannin an barshi ya shigo, sai dai dogarin nan na buda baki ya ce da ita" MAI MARTABA YA FADA MANA CEWAR BA WAJEN SHIGAR MAZA BANE DAN HAKA BA ZAI SHIGA NAN BA Da mamaki ta koma ba tare da ta yi gardama ba jin ashe mai martaba ne ya saka dokar hakan a kan kannensa? Najeeba bata ce da ita komai ba bayan ta shaida mata, sai da ta gama kitson nan sannan matar na murnar an gama mata ta cire jika ashirin ta mikawa Najeebar tana ta godiya kudin kunshi ne da kitso da gyaran faratuna da gashin ido tamkar wace aka yiwa kyauta Itama Najeebar cike da fara'a sukai salama matar ta tafi Gurin da take wanke hannaye ta je ta wanke hannayenta tas tas tana murmushin jin darun wata budurwa dake fadin ita gaskiya ita zata yi mata gyaran gashinta idan ya bushe yarenta kuwa sunna fadin ba kananun aiki take yi ba, zasu iya yi mata ko wani kala take so domin ta koya masu kuma sun kware sosai Sai dai ta kiya ta ce ko nawa ne zata biya ita dai NAjeebar take so ta yi mata Hijab dinta mai ruwan ash color ta saka mai hannaye sannan ta kara fesa turare ta juya ta fita daga shagon kafarta sanye da takalmi mai ruwan hijab din aman kafa ciki ne mai dan tsini a kasansa Tana fitowa suka shiga bun bayanta hakan ya sa da mamaki ta dakata ta juyo tana kallon su Du kawunansu a kasa a lokacin da ta juyo sannan sunna fadin" Allah ya ja da ranki, Allah ya huci zuciyarki Bata iya basu amsa ba sai karasawa da ta inda ya kafeta da ido kamar ya dauketa da idannuwansa yana kallonta fuskarsa dauke da wani irin murmushi mai girman gaske Tana isawa ta dan harde hannayenta tana kallonsa A sanyaye ta ce" menene? Murmushi ya yi yana shafa kansa daga gaba zuwa baya, a hankali shima ya furta" kauna ce, dan Allah ki bani dama Motar da ya zo da ita ta kalla, motar nan zata yi kudin hudun tata gata baka sidik mai shegen kyan tsiya Bakinta ta dan tabe kafin ta ce da shi" mu je Tare suka juyi suka nufi cikin saloon din Da sauri baban dogarin ya ce" Allah ya taimake ki, an hanna maza shiga ciki Dakatawa ta yi ta juyo tana jin uwa ta ce da shi da ubanwa suka yi tarayar siyan wajen da har zai ringa shiga sabgar da ba tasa ba? Sai dai kasancewar kwakwaran gargadin da ta samu daga wajen Anmy a lokacin da ta nuna ba wanda zai bita ya saka ta cire dubanta daga kansa ta furta" harda mijin da zan aura? Da sauri ya girgiza kai yana bashi hanya, shi kuwa wani mahaukacin dadi ya saka shi saurin cin mata suka jera suka shige saloon din tare Sunna shiga sanyin Ac din dake busa saloon din ya dake shi, kanshin turaran wuta fa kuma tarin turarukansu na siyarwa dake cikin wani katon waje mai dauke da madubai ya hade ya saka shagon zama cikin wani kamshi unik da sansanyan sanyi Juyowa ta yi tana kallonsa a hankali ta ce" ina fatan baka dauki maganar da na fada da mahinmanci ba domin dan ka samu shigowa na fadeta Matsota ya yi yana kallonta kafin ya furta" zan tabatar da ita ne, domin ba wanda ya cencenci amsa kiran sunnan mijin princss sai ni Irin yanda ya yi maganar ya sakata dan juya idannuwanta sannan ta idasa shiga tana mai cire hijab dinta dan itafa idan tana ciki tana aiki gaskiya bata saka komai a kanta Waje ya samu ya zauna kusa da Nadia saman kayataciyar kujerar zaman mutun hudu kafin ya shiga binta da kallo Budurwar nan ce ta hau saman kujera Nan NAJEEBA ta karasa ta shiga ciro atash din da za'a saka mata a boye cikin gashin kanta ya zama tamkar gashinta Sak sak irin gashinta ta ciro maroon mai duhu sosai, sannan yannayin santsintama ya zama irin na gashin matar Col (gam, wannan abin dai mai danne atach din ) Ta fitar sabo ta ajiye Sai da ta kara busar da gashin sosai sannan ta shiga fitar da wadatacen da zai boye atach din baki daya zagayen kan budurwar Cikin nutsuwa ta warware atach din nan ta wari daidai misali ta tsaga wanda zata hadewa ta hade sauran ta soke da yar wukar kitson sannan ta shiga shafa col din nan a jikin atach din Sai da ta shafa ta dan hura da bakinta ya dan sha iska sannan ta daidaita ta dora shi gaba kadan da tsagar sannan daidai tsiron gashin kafin ta hade da gashin cen kasa ya kasance ya zauna das da shi ta kuma tsaga wani Nan da nan ta idasa sakawa shi kuwa ya wani irin kura mata ido tamkar zai cinyeta yar uwarsa tun tana masa magana har ta yi shiru ta rafka tagumi ta zubawa sarautar Allah ido Wanda ta ware din nan ta kunce ta hade su , mai ta lakato ta shafa sama sama dan col din baya son mai sannan ta saka abin cajewa ta ringa caje gashin har ya hade da atack din ya hade sosai da sosai kafin ta dago daga bayan matar hakan ya kasance ta baiwa su Nadia baya kennan Da sauri ya koma saman kujerar yana daga hannayensa ya dora saman kansa ya kara zubawa kugunta ido kafin ya cire dubansa da sauri a fili ya furta" takwarankwatsa sonta nake kuma sai na aureta Du yawancin yan matan wajen shi suke kallo, babar yarinyar Najeeba ta kawar da dubanta daga kansa ko jus din da aka ajiye masa bai taba ba, Najeeba kuwa tana jinsa ta yi kamar bata san me yake fada ba sai da ta tsaga gaban kadan ta saka wata yar na'ura mai saka gashi ya bi umarni ta ringa bi a hankali tana kara kwontar da shi ya yi lumbuk a gefe guda ya kwontar da hankalinsa waje daya sannan tsagar ta fito sosai Dan gel ta bude ta ringa lakata da broch cike da kwarewa ta ringa dan kwonto da kananun da suke gaban goshin hakan ya sa nan da nan budurwar ta kara wani shegen kyau tamkar gashinta ya yi mugun hadewa da gashin nata domin kalar daya ne sannan yannayin santsinsama daya ne Dan ribom sabo ta siya a nan aka daure mata shi a tsakiya sai murna take kamar me kafin a saka mata gashin ido a gyara mata girarta Itama ta ci kusan jaka goma sha talwas da rabi sannan ta roki idan zata samu mak'up gobe domin auren yar uwarta ne ake Sai da Najeeba ta duba time din da take so ta amshi numberta tana mai sheda mata zata duba ta gani zuwa safe zata bata amsa idan har zata samu i.a Kudin da ta bata ya mike ya dauko ya zauna yana kallo, budurwar ya bi da kallo har ta fita kafin ua maido dubansa wajen NAJEEBA da ta dawo ta zauna tana dan matsa yatsutsanta Nadia ya kalla ya ce" Nadia, yanzu duka wannan tsayuwar da matata ta yi tana faman aikin nan sun tashi a wadinnan yan kudaden? Duba fa ki ga yanda ta kayar da wancen budurwar kamar gashin kanta ji yanda ta zama wata mai kyan gaske wannan tana fita ta fara wankar maza aman kuma sai kudin aikin matata ya zama ko jika ashirin bai rufe ba? Sansanyan ruwan da daya daga cikin masu gyaran wajen ta bude ta zuba a tsaftatacen kofin gilas ta miko mata ta amsa ta sha ba mai yawa ba ta mika mata ta dora kafarta daya kan daya kafin ta kai dubansa wajensu Nadia sai kwatanta masa take cewar ai haka aikin yake kuma ina laifi kana samun haka ko a wuni ne baki daya bale kafin a tashi za'a samu kudade na mamaki domin saloon dinta ya zama saloon din da sai manyan mata ko yan mata masu ajin gaske ke zuwa domin akoy kashe kudi sosai sai dai aikinta daban ne ko a waje Dubansa ya maido kanta ya ga su take kallo Kudin ya ajiye yana dubanta ya ce" me yasa ba za'a bani dama ba? Bana tunanin zan iya bari ki ci gaba da zuwa wajen nan, zan sama maki aikin ofice ki kasance a kilace Najeeba, idan wata ya mutu ki dafe manya manya dan na san takardunki, Nadia ta fada min irin takardun da kike dasu Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce" waye ya ce maka aikin office ke birge ni? Ka ga aikin nan, shi na tashi da shi a cikin abubuwan da nake son yi a rayuwana shi yasa ka ga na ware nan Da kake maganar aikin office, kidaya min zan iya samun nawa a wata? Huzaifa da gagawa ya ce" zaki iya samun jaka dari hudu, ke har akoy na dari biyar din da zan iya zuwa na samu abokin mahaifina ya sama maki gurbi a wajensu domin idan ya ji matata ce zai samo mana da guduma Murmushi ta masa ta ce" a ranakun da ban yi kwaliya ba, nakan tashi da jaka dari da arba'in, ko dari da hamsin, idan ba'a samu isasun mutane ba nakan tashi da jaka saba'in ko tamanin Idan na samu yan kwaliya, amare nakan yi masu kwaliya a jaka hamsin, kawayen amarya kiwa jaka ashirin masu zuwa wajen biki jaka goma Akoy ranakun da nake tashi daga shago da zunzurufun kudade kusan jaka dari hudu ko sama domin idan aka ce maka juma'a ce, asabar da lahadi wajen nan cika yake da mata da yan mata, amaren ne da uwayen gida, Wayarta ta janyo iPhone tana kallonsa ta ce" irga min, ka dauka a jaka dari dari kulun zan iya tashi da nawa a wata? Nadia ta ce" million uku Najeeba ta yi murmushi ta ce" ba ruwa nake biya ba, ba ni ke biyan wuta ba sai idan na yi ra'ayi, Abih ke biyan duka Idan kayana sukai kasa Anmy ke min oder ta cika min shago Idannuwanta ta kara kura masa ta ce" shine zan je office na yi me karkashin ikon wani? Murmushi ya ringa yi , a ransa kuwa ya yarda cewar ashe dai kasamcewarta babar yarinyar ba iya iya kwaliya da kyaun tsari ta tsaya ba, aljihunta nauyi ne da shi, rikakiyar boyayiyar mai kudi ce , to aman yaya aka yi ta zama lashe money? Shi fa ko gara ce ita wace take iya karar da dukiyarsa ya ji ya gani yana sonta Rage muryarsa ya yi ya ce" ina son ki NAJEEBA Sai da ta ji wani dan ras, tabas zuwansa kai tsaye da kalamansa na sakata kallonsa da duba na daban Cire dubanta ta yi daga fuskarsa hakan ya saka ya kara matsota sosai yana kallonta ya ce" ina son na aureki Najeeba, dan Allah ki yarje min mana? Kuma duban fuskarsa ta yi, tabas Huzaifa namiji ne mai kyau bakar fata ne shi mai tsafta, Yana da fara'a sosai gashi mai tsayi daidai misali, yana da kakauran jiki sannan yana da dan tumbi na jin dadin rayuwa Murmushi ta yi tana cire idannuwanta daga kansa, Wayarta ne ta dauki kuka da wakar su akon wace yake fadin For ever i love for ever........ da yake ta kuma ajiye wayar a saman kujera ya saka du suka kai dubansu *LIKITAN ZUCIYATA* , shine ke haskowa a saman sunnan mai kiran Bata damu ba ta mika hannu ta dauko sannan ta daga Salama ya yi mata kafin ya furta" ina cike da begen ranar da zan ganki, shin kina Niger kuwa? Sai da ta dan saci kallon Nadia ta ga kamar zata dauketa da mari sannan ta dan yi murmushi tana satar kallonsa sai ta ga fuskarsa ta dan cenza daga yannayin fara'a zuwa sad A hankali ta ce da shi" zan taboka Likitana Shima murmushi ya yi ya kashe yana fatan ta tabo shin Idan kana da time, ranar Wednesday ka zo fada Farin ciki ne kuma ya mamaye zuciyarsa harma ya kasa boyewa da yatsunsa ya irga cewar....nan da kwana uku ko? Kanta ta daga hakan ya sa ya mike, chek din da ya rubuto makudan kudi ya ajiye kusa da wayarta sannan ya juya yana murmushi ya masu salama Da sauri Nadia ta dauki Chek din tana dubawa sai da ta yi dan ihu kafin ta ce" ke, wai kin san nawa ne? Najeebama tana ta daria tana kallon chek din ta ce" da alama dan uwanki banar harka ne Nadia ta ce" Najeeba ina fada maki ko waye shi kennan baki yarda ba? Babar harka ne, Najeeba ta ce" na san waye shi, abinda ya sa na bashi matsayin babar harka nawa suke da kudi aman basa iya cirewa su yi kyauta da su? Sai ki ga sun tatare budurwa ita ba ga wani ba sai su kadai aman dan iskanci kudin zuwa saloon sunna bakin cikin bata? Gaskiya irin mazan nan basu da Mutunci! Nadia ta ninke ta soke mata ita cikin jakarta tana fadin" bana tunanin zai kasance irin mazan nan, domin ni kaina dominki kwana biyun nan hajia ce bale ke Ita dai Najeeba litafin da ake rubuta wa'inda suka nemi mak'up ta dauka tana ta dubawa dan gannin wanda zasu samu Sai d yama ta yi sosai wajen ya kuma fara saukan mutane masu fitar dare Ita dai zuwa lokacin sai ta kilace kanta sunna hira da yar uwarta wace ke magana kasa kasa bata jin dadin jikinta domin a jiya dai sarki sai da ya karbi sadakinsa NAJEEBA ta zaro ido tana ganni uwar sarkar da ya baiwa Zahrau da makulin mota da hoton motar da kyautar wasu kuyangin amana kafin ta ce" Zahra wai kyautar meye wannan? Zahrau ta yi murmushi kawai ta ce" zaki san ko ta meye, ba yanzu ba Itama murmushin ta yi tana kallon uban badon da ta markada ta zabga masa madara da karanfani fiye da adadin da aka bukata ta kafa kai ta shanye Zahrau da suke vido call ta zaro ido ta ce" Najeeba, ba zaki daina shan kayayakin gayran jikin nan ba ko? Gashi wa'inda kike dura min sai da na raina kaina , Najeeba sai da na ringa maki Allah ya isa Najeeba ta yi murmushi tana gyara kayan gefe guda sannan ta rufe frij dinta ta koma ta zauna ta ce" aunty, ko gobe na ji abu naturel wanda zai sharen fage ya gyaran jiki zan yi na sha abina dan a gaskiya ba zama zan yi sai an tashi yi min aure a shiryani ba Zahrau ta girgiza kai ta ce" anya ba babar mai jaraba bace ke kuwa? To yanzu idan kika auri mijin da hakan bai dame shi ba? Najeeba ta yi murmushi ta ce" aunty ai shikenan, kin manta ban saba ba bale hakan ya wahalar da ni? In sha Allahu ko wani kalar miji na samu shi zai horani ta yada yake so na zame masa Zahrau ta yi murmushi ta ce" wa kika tsayar? Dayabu ya fada min komai, dazu mai martaba ya turon sakon na tura number Ummu yarima na tambaya zai kirata , ke da Ummulkhair ku na sako gaba yanzun Najeeba ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" ni kaina ban sani ba, abinda nake son yi zan tsaida kwara biyi, a cikinsu sai na kaiwa Allah kukana kan ya zaba min daidai da ni Zahrau ta gyada kanta daga ringeshen da take, tana mai adu'ar Allah ya basu mazaje na gari, kwari ta yi mamakin irin yanda Najeeba ta yarda zata fitar da miji haka cikin sauki, sannan a yanzu ta kara jin nutsuwa ta shigeta jin cewar Najeebar da kanta ta kara jadada mata har Najeeba ce zata fitar da miji? Lale ta yarda kanwar tata ta fara zama mutun mai nutsuwa Sun sha hira kafin suke katsewa ta barta cike da tunanin abinda ta fada cewar su janyo yar uwarsu jikinsu To ita ta ina zata fara wannan lamari bayan Abih bai san cewa sun san da maganar ba? Yarinyar kanta menene halayenta shin tana da ra'ayin kasancewa da su a matsayin yan uwanta? Bayan salar magariba ta shirya cikin wando da rigarta na spot ta saka takalmanta tun a nan kafin ta dora hijab dinta dogo har kasa ruwan ja mai duhu Salama ta yiwa yaren shagonta ta harhada kudadenta cas sannan ta fito daga ciki Bude mata daya ya yi da gudu sannan dayan ya zagaya ya shiga wajen direba ita kuwa ta shiga baya ta zauna daya ya zauna gidan gaba suka dauki hanya A hankali ta masu bayanin inda zasu fara zuwa Sunna zuwa ta ciro jaka goma ta mikawa na zaunen ta umarce shi da ya yo nama leda biyu a saka tukunya a dayar mai zafin gaske Fita ya yi ya siyo naman ya dawo yana kokarin ajiye mata Mai dauke da tukunyar ta ware ta mika masu dayar ledar, dan murmushi ta yi ta ce" na san baku ci komai ba ko? Ku ci abinci mana kuma ina dalili wai wannan kamewar? Kun ga dai ni kanwarku ce ba ruwana ba abinda zan maku ku ci abincinku mu je stade bangaren basket ball a cen zan buga ball yau Kasancewar ta yi bayanin sport dinta harma Anmy ta amince sai dai ta fada mta cewar lokacin da aka yanke mata kar ta saki ta wuce shi a waje ya saka basu yi gardama ba, sannan alkhairin da ta masu ya saka suka ji dadi dan walahi yinwa suke ji an basu kudin abinci fa kawai ba damar su motsa ne yau suka fara aikin nan dole haka suka wuni da yinwarsu Sunna karasawa ta cire hijab dinta daga cikin motar take hangen wajen Terrain din bashi da dati ko daya, shi terrain din ne bai cika samun mutane a ciki da dare ba, da yama aka fi basket a samansa idan dare ya yi sai ya zamana yan gayun yan kata da samarinsu ke zuwa su yi zancensu a nan Daidaiya zaka ganni a saman wajen sun zo buga basket Shi daya kwal ta gani da wata irin ball a hannunsa Irin yanda yake juyawa ya daka tsale ya jefa ball din cikin raga ya sakata shagala da kallonsa *Freind* ta furta a hankali Ashe kana basket? Ta kuma tambayar kanta Sai ta ringa jin wasan na kara shiga ranta irin yanda yake bugawar sai kace wani jordan A hankali take karasa takawa har ta isa Bata yi masa magana ba sai gudun da ta fara shi kuwa tun da ta tinkaro amintacensa ke sheda masa ga wata na matsowa idan kar a barta ta karaso a tare ta, Yana fahimtar itane ya furta" barta Gudu ta ringa yi cikin nutsuwa da earpiece a kunnenta tana sauraron kidanta mai tashi a cikin sanyo ba kwaramniya Sai da ta hada zufa jinna sannan ta shiga cirewa ta ajiye saman abin zama A hankali ta ringa karasawa inda yake buga ball din shima ya hada zufar kamar me aman ya kasa bari dan ba yanzu yake bari ba sai ya gama bugawar yake zuwa wajen hutunsa ya dan huta kafin ya tafiarsa Yi ya yi kamar a lokacin ya ganta ya juyo yana dan doka ball din tana dawowa hannunsa yana kallonta Shamatarta ya yi ya cilo mata, da sauro ta cafe ball din itama ta shiga dan dokawa tana tunakararsa Fahimtar da ya yi cewar tana son ta tsineshi ne ta je ta saka ya saka shi kokarin karewa yana tarewa ita kuwa tana neman hanyar bu tun karfinta Sai da ya bari ta sha wahaka sannan cikin sauki ya karbe ball din ya juya ya yi wani tsalen da ya sakata zaro ido cike da mamakinsa daga inda yake ya cila ball din ta shige zuruf wato 3 point Abin ya kayatar da ita, hakan ya saka ta shiga tafawa tana yar dariya cike da mamakinsa Ai kuwa nan wasa ya bale suka ringa yi sunna kasawa da gudu sunna kilkila dariyar da su kansu basu san ta yi nisa har haka ba su dai dariyarsu suke sha idan ya amshe ball din Ball din na hannunta ya dagata sama da hannunsa daya yana mata daria kadan kadan Irin yanda take daka tsale tana fadin ya tsaya dai ya ga ikon Allah sai ta kamo ya shagaltar da shi harma ya kasance idan ta daka tsalen kanta na dukan kirjinsa sannan da hannayenta ta saka ta daki kirjin nasa tana fadin" in ba tsoro ba baki korere mana Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa ya sakar mata ball din Warta ta yi da gudun tsiya ta nufi ragar Sai da ta karasa ta wurga ball din Ai kuwa ta shige ciki hakan ya sakata sakin dan ihu na murnar ta saka sannan ta juyo ta shiga kwaso shoki tana watsa masa Daga inda yake bai motsa ba sai hannayensa da ya harde yana kallonta Murmushi ne ya subuce masa a lokacin da take kwasar shokin nan kafin ya dan girgiza kansa ya cire kansa daga dubanta yana gannin yanda mutanen dake zaune sunna zamcensu suka dauki hankalinsu harma suke kyakyata dariyar lamarin da masu yi mata tafin ta saka daya kwal bayan tun dazu yake ta sakawa ta kasa sakawa Kansa ya dan girgiza ya juya ya nufi wata lafiyayiyar kujerar da aka ajiye masa da ruwan gora da abin goge zufa fari kart sai kamshin fitinanen turaran nan nasa yake ya yi ya karasa ya zauna Ba din ta dauko ta kara jefawa sannan ta kuma daukowa tana kallonta ta gane ba karamar ball bace irin wa'inda ake kawowa daga americar nan ne masu tsadar gaske da karko Wajensa ta karaso tana jin mugun kishi dan kana gannin fuskarta zaka gane ta sha wahala sai shasheka take sosai Goron ruwan da ya bude ya kafa kansa ya dan sha kadan take kallo Gannin ya sha sai ta cire kanta a wajen tana gannin yanda yake dan goge zufar jikinsa har wajen wuyansa Ball din hannunta ta nuna masa ta ce" ball din nan ta kanpani Kapto ce? Ko copy ce? Shima kallo ya yi kafin ya yi dan murmushi, wai copy wato ba zai iya siyanta ba take son sani ko? Sai ya dan daga kafadunsa ya ce" ita ce, yayana ya siyan min Bakinta ta dan tabe tana son ajiye masa ya miko mata ruwan dake hannunsa yana dan lumshe idannuwansa ya shafa shafefen cikinsa wanda ke dauke da wani irin gida gida masu tauri irin na masu sport din nan yana fadin" yinwa nake ji, gashi daga nan zance zan je Ruwan ta tsurawa ido, ta dan makale kafadarta ta ce" ka kafa bakinka fa, kuma sai kawai nima na kafa? Da mamaki ya kalli ruwan ya kuma kallonta Murmushi ya yi ya ce" da zan fito fa sai da na yi broch kuma kin ga ban ci komai ba, sannan bakina baya wari Itama murmushin ta yi tana kara makale kafadarta ta ki amsa Juyawa ta yi ta daga hannunta Su dama ita suke jura sun ci sun yi hani'an Ledar ya fito da ita ya karaso ya kawo mata sannan ya koma ya zauna sunna jiran ta gama su tafi dan su kansu an masu gargadin daga bakin inda lokacin zuwanta gida ya yi koda a sume ne su maidota gida Yannayin mamaki ya nuna a lokacin da take miko masa naman ya ce" aman, kika ce min baki san sarkin garinnan ba kuma na ga dogari guda ya kawo maki abu ko dai ke din y'arsa ce? Da sauro ta kale shi, sai kuma ta yatsina fuska ta ce" ni kuam zai haifa? Yaro ne fa! Bayan wannan ai ba lale na sanshi ba, ni ban taba ganninsa ba kuma ko na ganshi ban sanshi ba tunda baya cikin tsarin mutanen da nake son mu san junna Dan Anmy dina ne! Tun da take maganar ya tsura mata ido da mamakinta, kai, shine yaron? Innalilahi sai kawai ya ringa jin me zai hana ya wanka mata marin da zata fita hayacinta har ta buda wannan muryar tata mai kwari ta fasa ihun nan kamar an kasheta? Yau shine wannan ficiciyar yarinyar ke ce masa yaro? Amshi mana, Ta fada tana kara mika masa naman Shima kafadarsa ya makale kafin ya ce" nima bana ci, na san ko kin saka a bakinki? Da mamaki ta wangale baki tana kallonsa, Sai da ya dan hade fuska ya ce" aman me yasa kika raina sarkin garin nan bayan na ji irin yanda ake tsoronsa? Kafadunta ta daga ta ce" nima raina ni ya yi ai Ido ya kara zarowa yana jin har kamar kirjinsa ya fara zafi yana kallonta , tabas ya tabata dole ya shaketa ya kara summar da ita a karo na uku a wajen nan Bai idasa jin lale dole ya hukuntata ba sai a lokacin da ta kara dan gyara tsayuwarta tana duba agogon dake cikin wandonta dan tafia zata yi ta ce" [31/03 à 21:39] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 27 A firgice, a rikice, a tsawace Anmy ta ce" yaya muna cikin wannan tashin hankalin zaki yi mana wata tambaya kina mai kokarin tirke mun tamkar kece uwarmu mu kuwa y'ayanki? Baki daya yan matan sai abin ya basu mamaki, yannayin Anmy din ya saka jikinsu ya yi sanyi harma du suka zuba mata ido da wani irin duba na mamaki Anmy ta kawar da kanta tana jan hancinta tana kara rintse idannuwanta da sukai mata luhu luhu ranta hade ta ce" ku tashi ku je dakin ku Jiki sanyaye du suka mimike, Najeeba ta kara waigowa ta kalli mahaifinta ta ga kansa a kasa sannan hannayensa sai rawa suke, ta kai dubanta wajen yayansu ta ga shima kan nasa a sade shi kuwa kuka ne yake a hankali ta saci kallon mai martaba ta ga ya yi wata kwonciya a jikin kujerar ya daga kansa sama idannuwansa lumshe rawanin dake kansa ya kara fadi sakamakon yannayin kwonciyar nasa, shigar alkyaba ne a jikinsa mai ruwan duhu wace ke da igiya wajen wuyanta, fari kal din hannunsa daya ne a waje yana rike da sandar girmansa dake ajiye a kusa da kafarsa, sai dayan dake dafe da gefen zuciyarsa Da sauri ta cire dubanta a kansa ta juya da wani irin sauri ta bi bayan yan uwanta Sunna shiga da sauri Ummulkhair ta zube a kasa tana mai dora hannunta saman kanta tana dubansu a rikice ta ce" shin kun fahimci abinda na fahimta? Kun gane cewar akoy wani gagarumin sirin dake damun mahaifinmu wanda da alama mahaifinmu ya shafa wanda nake kyautata zaton idan har ya fito fili mun kade? Najeeba ta jefar da iPhone dinta saman kujerar dake ajiye ta cire alkyabar jikinta ta jefar ta zauna a kusa da Ummukulsum ta shiga cakuda gashin kanta Dagowa ta yi da wani irin yannayi ta ce" aya ta kasance a kansa da wuri? Bai fadi haka ba sai da ya ji cewar wannan tsautsayi ya afku da Ummu? Me ke faruwa da mahaifinmu? Wace aya ce wannan ta kasance a kan ubanmu? Ummukulsum dake share hawaye itama ta budi bakinta a hankali ta ce" sai jake jin tsoron abinda zuciyata ke fada min, sai nake jin tsoron abinda nake tunani Ummulkhair ta ce" me kike tunani ummu? Ummu itama ta dora hannunta a kanta ta ce" sai zuciyata ke ce min bayan mahaifiyata mai amsar kudin zina ce mahaifinama ya taba fadawa wata Da sauri Najeeba ta matso kusanta tana daga hannunta da ihu ihu ta ce" ke ke, yi min shiru, walahi zan tsinka maki mari idan kika fadi cewar Abih ya taba yiwa wata fyade Ummulkhair ta shiga yarfe hannayenta tana fashewa da kuka ta ce" Najeeba ai ba haka ta fada ba, abinda kike tunani ne kika fada kuma nima abinda nake tunanin kennan innalilahi wa'ina ilaihi raj'une me ke faruwa da mu? Itama Najeebar baki daya kafafuwanta ne suka gaza daukanta Tana kokarin zubewa kasa Dayabu ya shigo Da wani irin sauri ya karaso ya tareta a jikinsa suka kai kasan tare Da rarafe sauran suka karasa wajensa suka rungume shi sunna kuka baki dayansu Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, yake maimaitawa hankalinsa a tashe ya shiga fadin" tabas kadara, mumunar kadara ta faru da kanwata, sai nake jin ba wanda ya kaini jin ciwo duda irin yanda aka fada min lamarin cewar ba da son ransa ba, duda na san Allah ya kadarto hakan, sannan har an yanke hukunci zai zama mijinki aman zuciyata ta kasa daina hawaye Tsoro nake ji , walahi tsoro nake ji Idan ita ummu ta faru da ita a wajen mutunci wajen da aka isa a tankwasa karfe komai taurinsa ku fa? Shin wace irin kadara ce ta afkawa mahaifinmu ya aikata mana haka? Da sauri Najeeba ta dago kanta tana kallonsa DAYABU da hankalinsa ke tashe ya shiga fadin" ba zan iya kuma zuba maku ido kuna yawo haka ba, du ku fitar da mazan aure a cikin manemanku a yi maku aure ku tare a gidajenku hakan zai saka mani nutsuwa a cikin zuciyata, walahi idan ayar nan ta kuma kasancewa a kan wani a cikinku bana tunanin zan iya yafewa Abih! Lebunanta ke hadewa da junna sai jimkesu take tana kara budewa A rikice ta ce" me me ya yi ne wai? Me ya yi? DAYABI ya sasauta masu rikon jin du sun dago shi suke kallo Kansa ya sada ya kasa magana hakan ya saka Ummukulsum dora hannunta a kai ta shiga zunduma ihu tana son mikewa ta yi burgima ko zata ji sanyi, cikin muryarta take fadin" shikenan uwa karuwa uba karuwi ko dai ni shegiya ce ban sani ba? NAJEEBAma dake kuka tana kallonsa ta ce" yaya waye shege a cikinmu? Ummulkhair kam sai ta kame, gaba daya ta kasa kuma motsa hannayenta tambayar da yan uwanta ke yi take jiran amsarta Hannunsa ya saka ya rufe bakin Ummukulsum sannan ya ringa bin Najeeba da kallo wace ta zama uwa wata wada ke son tashi sai tsale take tana kai kawo sai kuma ta tsaya tana kallonsa gashi kanta baki daya ta balbaza shi hannunsa ya saka ya jata kasa da karfi hakan ya sa ta yi wani irin zama dabar a gabansa gabanta na yi mata wani irin tsalen albarka kamar zai bale ya fito daga kirjinta Wayarsa ya dauko ya shiga galeri Hoto ya fitar saman wayar tasa ya mika masu Har rige rigen amsar wayar suke suka tsurawa hoton ido Yannayinsa a kansu ya ce" sunnanta *HUWAILA* , sati daya ne tsakaninku ita da Najeeba, Tana nan garin zaune gidan kannin mahaifinta tana karatu a lycee Du da iein tarin kamanin da take kamar an tsaga kara ita da su bai hanna Najeeba cewa " yar gidan waye? Me hadinmu da ita mu kuwa? Murmushin takaici ya yi yana kallonta ya ce" NAJEEBA MUTALAB idannuwanki sun samu matsala ne? Wannan da kike ganni yar gidan MUTALAB ce, jinnin MUTALAB ce wace ya samu a zamanin da baya jin magana! Kamar ya kuma dima masu guduma haka suka kasance du sunna kallonsa Sai cen Najeeba ta yi ihu tana zazaro ido a firgice ta ce" lalle akoy tashin hankali a gabana, ina tare da wannan lamari a tsatsona nake tata rashin mutunci a garin damaram? Ashe nima da nama lamarin a boye a tare da ni ban sani ba? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une Ummulkhair ta ringa share hawayenta tana jan hanci ta ce" ko shine abinda yake saka matarsa yi mana wata magana cewar y'ayan yan iska? Ummukulsum ta yi murmushi, ita abin sai take ganninsa wani iri, ashe ba mahaifiyarta kadai ce ke tare da wani mugun lamarin rayuwa ba? DAYABU ya sasauta muryarsa ya ce" ku zauna Irin yanda ya yi maganar ya nuna masu gabansa ya saka suka zazauna sunna kallonsa A sanyaye ya ce" a kadan zai kai shekara shida da na san da yarinyar nan Na bibiyi rayuwarta da ta mahaifiyarta har na samu cikaken bayani a bakin kannin mahaifinta wanda ke rikonta Ya ki amsar yarinyar a bayane ya amsheta a boye ne Komai nata shi ke mata , karatunta bukatunta aman kuma hakan na nufin kar ta yarda ta fitar da ko waye mahaifinta a garin nan, Ban san nufinsa na yin hakan ba, Yana yi ne dan ya boye sirinsa saboda idan sirrin nasa ya fita zai shafi y'ayansa, mutuncinsa ko yana yi ne dan son ransa?? Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" abinda na sani shine kasata kasar hausa ce, mai dauke da al'umar da idan irin haka ta faru yakan zama matsala, yakan shafi y'ayan mutun, abin ya zama na gori, idan mata ne ka ga har ana gudun aurensu bayan ba su suka aikata ba kuma shi kansa wanda ya aikatan na tabata da ya san abinda zai je ya dawo da ya hanna kansa aikatawar Kamar yanda na fada maku, ni DAYABU MUTALAB, na baku umarnin fitar da mijin aure kwana kusa ba nesa ba! Sannan Abinda aka yanke shine.....Anmy ta roki Mai martaba alfarmar hadaku da masu tsaro sakamakon abinda ke faruwa a cikin gidan wanda yake cikin bincikensa Ya zama dole ku dawo nan da zama sanadiyar abinda ya faru da Ummu, ta rantse ba zaku bi Abih gida ba shima kuma sai bai ja ba na tabata yana tsoron kadaicewarsa da mu yana gudun tambayoyinmu hakan ya sa aka dora dokoki a kan shiga da fitarku baki dayanku Zaku ringa zuwa wajen neman iliminku a kan lokaci ku dawo a kan lokaci Zaki bude saloon dinki wajen karfe goma na safe ki rufe goma na dare ku dawo gida tare da masu tsaronki Tap.....shine abinda Najeeba ta fada a zuciyarta kennan, masu tsarona? Ana nufin za'a hada ni da wasu langayayun dogarai su ringa bina ko police? Ta yaya zan samu mijin na ware da wasu karti a bayana? Hala ba zan ringa zuwa wajen hutuna ba? To yaya, zance fa? Ka san da dole sai mun ba wanda ke neman aurenmu dama zamu iya aminta da shi ko? Idannuwansa ya zaro ya ce" Ummulkhair, ni da ni aka bi ba zaku yi wani zance ba! Sai Anmy ta kuma rokar cewa kuna iya baiwa mutun dama ya zo nan, ku gana da yama ya koma inda ya fito a falon da mai martaba ke saukar baki Da sauri Najeeba ta ce" kana nufin falin da yana iya ganninmu sannan ya ji du abinda zamu tatauna da saurayin yaya? NAJEEBA ko baki da gaskiya ne? Ya tambayeta yana mai kallonta da son jin amsa Kanta ta ringa girgizawa ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, wani irin zance zata yi ita kuwa bayan ta san wannan mutumen da ya tsaneta na iya ganninta yana jin abinda zata fada? Sai kuma wani abu da ya diro mata shine yayan banki! Yanzu idan aka ce ta zauna da saurayi daya ana nufin nauyin aljihunta zai rage? Aby daya da ta sani shine lale lale zata samo mijin aure, zata tsayar da daya kwalin kwal wanda zai zama mijin Najeeba Bai bar dakin ba sai da ya kara kwontar masu da hankali, shi kansa ya samu hankalinsa ya kwonta da damuwar da yar uwarsa ta tsinci kanta a ciki kafin ya mike ya fice a tankamemen dakin nasu Su duka sun yi shiru ne a kwonce, a hankali Najeeba ta lalubo wayarta ta turawa Zahrau message kamar haka" me kike ? Zahrau dake zaune kunyar Mai gidan nata na neman kasheta sai hira yake mata yana kara son ta saki jikinta ita kuwa tarin kunyarsa ta lulubeta da tsoron yannayin kusancin da suke ciki ya hanna mata daukan wayarma bale ta ga message din hakan ua sa Njaeeba ta fita a wajen Zahrau ta shiga contact dinta ta ringa bi daya bayan daya sunnayen samarinta tana kallo tana tuna yannayin mutun da halayensa da komai da komai Zaune yake bayan ya fito daga bangaren Zinaria wace ya taka yau da kansa ya kai mata ziyara dan gannin yaya yannayin jikinta yake? Ciki dai ya lalace domin bai kai lokacin haihuwarsa ba a dole aka fitar da shi akai mata wankin mahaifarta hakan ya sa take kwonce cikin damuwa da tsoron daga wayar mahaifiyarta Ko da ya je ganninta ta yi mamakin ganninsa a bangarenta sai dai bata iya bashi wata kulawa ba har ya bar wajen dan hankalinta bama a jikinta yake ba Sosai yake jin ba dadi na lalacewar cikin jikinta, sai dai ya dauki dangana ya barawa Allah tare da fatan samun wasu masu albarka masu zama Alkyabar jikinsa ya saka hannunsa a hankali zai cire, Da sauri ya dakata sakamakon wani abu da ya fado masa a rai Idannuwansa ya daga ya kai dubansa kan agogon dakin......................... Da sauri ya mike tsaye yana sauke Alkyabar kasa ya shiga taka kyawawan kafafuwansa saman lalausan cafet din wajen ya nufi wajen kujerar dake ajiye Zama ya yi ya dora kafarsa daya kan daya ya shiga warware rawanin dake kansa Sai da ya warwareshi tas sannan ya kuma tsurawa waje daya ido A cikin ransa ya shiga ayanna : *IDAN FA BA BINTU AKA ZO KASHEWA BA, NI AKA ZO KASHEWA?* Ba zai manta ba, ana zaune a dakin karatu a lokacin da aka gama daurin aure du kawunansu a sade sai ya so yin raha da su, domin mutanen dake wajen daga amintatunsa, sai iyayensa wa'inda suke tsofafi da datijai ne Ba zai manta kalmar da ya fada ba, wace ya ce" *NI ZAN JE DAUKO FADIMA BINTU* Ya fadi kalmar ne dan ya saka su sakin raha, sai dai maganar ta so ta bada armashi a lokacin da mahaifin Bintun ke godiya cike da farin cikin jin shi da kansa zai je daukota An rarage mutanen dake ciki sai ya kasance saura mutun shida Amintacen bafadensa ne ya kuma tambayar maganar cewa" ALLAH YA KARA MAKA LAFIA, SHIN A WACE MOTA ZAMU JE DAUKO GIMBIYAR? Ba zai manta amsarsa da ya bada a bayane ta hanyar fadin : Sabuwar motar nan a ita zamu je dauko gimbiya.........................ya katashe yana mai sakin murmushi mai dan sautin da ya saka du mutanen wajen suma sakin murmushin sunna jinjina maganar cewa wai da gaske zai je ne da kansa? Da sauri ya mika hannayensa ya janyo farar takarda da byro ya dora sama Sunnayen mutanen dake wajen ya shiga rubutawa daya bayan daya Sai da ya gama rubutawar aman bai saka na amintacensa ba Bin sunnayen ya shiga yi da kallo Idan akoy abinda rayuwa ta koya masa shine jiran komai daga kowa ........ya jima yana wannan tunanin har ya ga dare na tsalawa A kan sunayen ya ringa dora number tun daga 1 har na karshe kafin ya mike ya nufi bed dinsa dan samun hutu komai kankantarsa domun rabonsa da ya huta har ya manta tun ihun fitinaniyar yarinyar nan Wata irin mika ya yi a saman bed din , bukatar kebewa da mace yake, hakan ya saka baki dsya jikinsa ya mutu wata irin kasala ta dirar masa Tsintar kansa ya yi da kiyasta irin abinda ya dace da damkarsa Da sauri ya rintse idannuwansa sakamakon hotunnan da suka shigo zuciyarsa Korar shedan ya ringa yi ido rufe dan samun nutsuwa kafin ya mayar da kansa ya kara dannawa a saman fillow din yana jin yanda bugun zuciyarsa ya cenza Dolema ya auro uku ya jera! Daga bakin lokacin da ya fahimci cewa daya ba zata iya da shi ba ya san cewar sai ya kawo, zai karo uki ne a kwana kusa ko dan ya ringa zagaye su A cikinsu ya tabata ba zai rasa wace ta dace da bukatar zuciyarsa ba! .......................................... Aiki take da kanta yau, tana kitsa gashin wata bafulatanar mata mai son gyaran kanta, ana yi mata kitso kananu masu kyan gaske Idan tana kitso a tsaye take yinsa wanda take yiwa kuwa sai ta hau kujerar saloon sunna yi tana kallon abinta A saman gashinta ta totse abin caje kan, sannan abin tsagawar daya a kan matar daya kuwa a cikin gashinta domin gashin nata hade shi ne ta yi ta kame shi a sama Hira suke da Nadia tana yar daria NADIA ta ce" NAJEEBA, ni da yau na maki abinda bakya so, Najeeba Huzaifa ya matsa min walahi, kin ga ko yau da sasafe shi ya tasheni a baci ya rantse cewar ba zai iya hakuri ba Najeeba meye laifin Huzaifa ne? Idan kudin ne ke kin san waye HUZAIFA a damagaram, yaro ne mai kudin balaki Idan kyan ne meye laifinsa? Gashi baki ne kamar yanda kike so mijinki ya kasance me ya sa ba zaki amsa shi ba? Shi fa a shirye yake da yau kika ce ya fito zai fito Tsaga wani kitson ta yi ta dauka sannan ta dubeta ta ce" numberna kika bashi hajia ko me kika min? Nadia ta dan kebe bakinta ta ce" walahi na bashi numberki, na fada masa inda kike bi, na fada masa harda da food din dake birke ki Najeeba ta ringa gyada kanta tana idasa kitse jelar kitson matar, domin har karshe take kitse mata shi ya kwonta yar yar da shi shi yasa matar ke masifar son ta zo saloon din, bata barinsa sai an yanyara mata kitso da kunshi an wanke mata kafarta sannan ta sayi dadadan turarukansu masu birge mijinta ainun Najeeba ta ce" kin san meye, ya cika daria wa kowa ne, Nadia ina son namiji mai wasa da yawan yin daria aman fa ni kadai nake so ya ringa washewa hakora ba kowace mace ba haka kawai Kwonkwasa wajen da ake ne ya sakata kai dubanta kofar Gabza gabzan dogarai har biyun da aka hadata da su ne suka tarewa wanda ake maganarsa hanya Saurayi ne jikake, ya jiku har ya jike da cefa ga iya kwaliya Yana da kyakyawan nasaba, gashi da fara'a HUZAIFA dan kasuwa ne sannan yana karatunsa wanda ya fi baiwa kasuwancinsa karfi domin karatun mamansa ce ke matsa masa aman ya malaki abubuwan rayuwar da ba shi ba ko wani masa ya huta A duniyarsa yana son mace mai irin halayen Najeeba, Ya santa ne dalilin cousine dinsa Nadia, NAJEEBA na kashe shi, shagwabarta na haukata shi, idannuwanta na tsuma shi, uwa uba tafkeke kugunta mai kara masa yardar cewa yes shi namiji ne sakamakon idan ya ganta yakan rasa nutsuwarsa ke kara haukata shi da son malakarta ta kasance tasa Yakan je wajen da take buga basket ball ya zauna a motarsa yana hangen yanda take wasanta ransa na tafarfasa da kishin mazan wajen Yakan sakin murmushi idan ya ji wajen manya manyan maza irin ana hirar yan mata an yi katari wani ya sako zancen babyn Irin yanda take wawusar aljihu na kashe shi hakan ya saka yake so ta shigo nasa aljihun domin yana kara kaimin nemansa dan ya bude mata bakin aljihun nan ta shiga ta yi burgima ta yi jina jina ta wanke kafa ta fito Sai dai abinda ke damunsa ta kasa bashi dama Ta raina shekarunsa, ta kuma raina yannayinsa Ya kwatanta tashi daya amsar da ta bashi shi je" murmushin sangarta kafin ta dora da fadin" aman tsokanana kake ko? Ka dai san koda ka girme min bai fi da shekara biyu ba, gaka mai arhar daria a kowa, yaya kake so na maka wayo ka hada ni da hukuma?????? Happy weekend people💓 [31/03 à 21:39] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 29 Ta ce" ni banma ga dalilin da zan nuna na san shi ba, bai min ba, ko a layin mutanen da zan iya jin nauyinsu ba, Sam mutumen bai min a cikin tsarin rayuwana ba Mikewa ya yi tsaye hakan ya bayanar da irin tsayinsa, SHAHEED ya kasance namiji daya kwal da babu irinsa Yana da tsayi daidai misali, Shaheed ba shankalale bane kuma ba rubdede bane Jikinsa ya kasance jiki kamame mai tsafta Kirjinsa yana da fadin gaske sannan cikinsa ba a shafe bane yake luwai kamar na mace aa, a shafe yake aman da wani gida gida irin na masu daga karfen nan Ya kasance mai hannaye masu tsayi da kauri, damatsunnan hannayensa tamkar na dan dambe wanda baka gane hakan sai ya saka irin rigunnan nan na gudu Irin yanda ya kware wajen sarafa doki haka ya kasance tamkar doki a kowani fani, sam bashi da wasa ko laso laso Fuskarsa dauke take da gira mai yawa wace har ta kusan hadewa da yar uwarta baka sidik, Idannuwansa kuwa manya ne ba fici fici ba masu dauke da gashin ido mai yawa baki sidik, sannan sunna dauke da kwali mai ruwan maroon mai duhu wanda yake kyalkyali ko a cikin duhu ne Hancinsa yana da dan girma sannan yana da karan hanci mai tsayi Lebunansa masu fadi ne kadan sannan pink color ne yas da su ga taushin tsiya Yana da cikar gashi irin na larabawa domin ya dauko gashin Anmy ne wanda yake yawan aske shi sai dai duda haka ya ajiye kyakyawan sajen da ya je masa har wajen habarsa ta fitar da san gemun da yake dan ragewa yana gyara shi yana kara hawa fuskar yasa das da shi ga baki ga kyalkyali Cinyoyinsa sunna da tsayi da wani irin tauri irin na wanda ya sabawa jikinsa da sport sannan kaurinsa masu kauri ne da tauri suma a rike suke a jikinsu Yana da manyan tafin kafafuwa irin na manyan mutanen nan na da duda basu da tuwo sosai Cike da kasaita ya ringa takowa ya yi taku uku ya kasance tsaye kikam a gabanta hakan ya saka ta zama wata yar firit da ita tamkar wace zai yi kujera da ita Kirjinsa ta dan kurawa ido kafin ta dan matsa kusancinsu ta dago da kanta tana kallonsa da dan mamaki ta ce" kanshin turaran nan, a ina ka samo shi? Idannuwansa ya lumshe ainun a kanta a kasan zuciyarsa yana furta lale na yarda baki da kunya ko daya yarinyar nan, muryarsa da ta dan fara kausasa ya buda ya ce" kin san shi ne? Fuskar tasa ta dan kurawa ido kafin ta cire dubanta daga kansa ta mayar gefe tana mai sakin ajiyar zuciyar da bata san dalili ba sannan ta ringa dan girgiza kanta Fitowar dogarin dake tare da ita baban ya saka shi cije lebensa na kasa yana son kara kawar da fuskarsa irin na dazu don kar a je ya gane shi a hankali ya furta" na yayana ne na dan fesa, turaran ne na birge ni Dan murmushi ta yi, bata ce komai ba, karamar eayar dake aljihunsa ya ciro ya mika mata yana kallonta ya ce" tunda yau kin aminta da abotakata, saka min number ki Wayar ta kai dubanta sama, wata irin waya ce yar karama mai sulbi sannan fara ce kal kamar hannu bai taba tabata ba bale a yi tunnanin ana ajiyeta a wani waje Tabas mutumen nan yana da tsafta, yana kanshi uwa uba saukin kansa ya saka eh lale zata iya zumunci da shi Kwarai ta ji dadin da ba soyaya ya nuna mata zai yi da ita ba, domin kuwa a tsarin rayuwarta farin mutun baya cikin tsarin namijin da zata iya soyaya da shi ko na second daya Kuma kai dubanta ta yi kansa, mutumen na tare da wani irin kwarjini, girmansa ya bata mamaki irin yanda farinsa kuwa yake har ya zarce matan nan masu karin mai a kan nasu Wayar ta amsa ta saka numberta wace idan an kirayeta ana samunta ko wani irin time kafin ta mika masa ta juya tana daga masa hannu Daga inda yake tsaye ya bita da kallo inda dogarin ya koma da gudu ya bude mata wajen zama ta shiga ta zauna Wani uban tsaki ya ja yana yin kwafa ya koma ya zauna da wayar a hannunsa wada ta saka numberta Ni SHAHEED ni ne yaro? Sam halitata ce bata yi mata ba? Wani murmushi ya saki yana dan kara cije leben nasa na kasa cike da takaicin abinda ta fada Haka kawai ya ji yana jin haushin kalamanta Kansa ya dan kara girgizawa yana mikewa dan karasawa ya huta a ransa kuwa fadi yake" sannu sannu bata hanna zuwa yarinya, abinda na yi niya a kanki sai na cinma burina marar kunya! Sun hade a falo sun yi hira kamar yanda suka saba, Anmy na tare da su tana jara hankalcewa da yannayinsu baki daya, sai Ummu da ta wuni da ita tana ta kokarin gannin ta fitarwa da yarinyar abin daga ranta , ba laifi ta dan kara sakuwa kan yawan shiru da kukan da ta dauka na kwana biyu Da sasafe wajen karfe tara, Najeeba ce tsugune kusa da kafar Anmy bayan sun kara gaisawa cikin kara sada kanta ta ce" Anmy, dama saman maganar tsayar da mutumen da aka ce din nan ne, akoy mutane biyu da muke tare nake son a rokar min alfarmar su fara zuwa a cikinsu sai a ware guda in sha Allahu Da sauri ta dubeta, da wani yannayi mai cike da rashin jin dadi, saurayi? Zance? Kennan tana da wanda take so ko me? A hankali ta ce" Najeeba, kina da wanda kike so ne a cikinsu? Najeeba ta kara sada kanta irin kana jin kunyar nan ba zaka iya yin magana ba, hakan ya kara sanyaya gwuiwowin Anmy Muryarta kasa kasa ta ce" ki basu dama Kara sada kanta ta yi ta yi godiya kafin ta mike daga ita sai rigar bacin dake jikinta wace ta kafe a jikinta , rigar bata da shara shara sai dai kasancewar ta velour sai ta lafe a jikinta ta yi mata dass ta fitar da tsarin halitarta Da kallo Anmy ta bita har ta shige dakinsu dan zuwa ta shirya ta fita wajen aikinta kafin take sauke wata nanauyar ajiyar zuciya Shin da wa zata iya yin irin maganar nan wanda zai bata kyakyawar shawarar da mutane ba zasu ga ta yi son rai ba? Da wa zata zanta wanda zai dubi lamarin da duba irin na fahimta ba zai bi bayan dayan biyu ba ya bata shawarar da ta dace? Tabas ba zata iya tauye yarinyar kai tsaye haka ba, Waye wanda zai bata hanyar da zata bi cikin ruwan sanyi ta samu cikar burinta? (ya mama ta ce ku shige daka tana da kyakyawar shawara Anmy😆) A yau da ta tashi sai ta yi shiga cikin wando na jins irin wanda ke dame kafar nan daga cen kasa sannan ta saka riga ruwan pink color mai dogon hannu da botira daga gaba Da ta zo bala botiran sai ta bar daya bata bale su dukansu ba sannan ta caje gashinta da kyau ta daure shi a tsakiyar kanta Turare ta bulbulawa jikinta kafin ta dauko wata abaya baka sidik wace sam bata da siri domin tamkar sange haka take ita dai an sakata ne dan kar a ce ba'a saka abin rufa ba ta dora abinta ta dora abin kan saman tarin gashinta mai tsayi da baki Kusa da Ummu ta je ta rage tsayinta ta mana mata kiss a kumatunta sannan ta buda Jakarta ta ciro kudi kimanin jaka hamsin ta mika mata tana kallonta ta ce" kin rage fara'a yayar Najeeba, hakan kuma na saka ni aiki da rashin kuzari Da murna da kuma mamakin yau ta bata kudi daga tambayarta ta dauki kudin tana kallonta ta yi yar dariya ta ce" yau nice yayar taki? Kin yarda kennan? Najeeba ta yi daria har fararan hakoranta suka bayana ta ce" idan har zaki saki ranki, idan har zaki daina tunani kina dorawa kanki abubuwa zan yi ta kiranki aunty na rantse Murmushi Ummukulsum ta yi tana saka kudin cikin jakarta ta mike itama ta dauko hijab dinta dogo ta saka ta ce" mu je, nima yau zan yi aikin Ai kuwa da murna Najeeba ta kama hannunta suka fito, Takalmi ta saka mai ruwan pink sai jakarta itama yar karama pink mai kyan gaske suka jero Salama sukaiwa Anmy dake zaune tana neman wayar maman Najeeba ta kasa samu suka fito A yau masu tsaron sun kasance har mutun hudu hakan ya baiwa Najeeba daria ainun Mota biyu suka fita da ita dole, motar Najeeba da motar Ummukulsum har zuwa shago Ta yiwa mutane kwaliya sosai, ummu na tayata hakan ya saka ta saki ranta har tana ta murmushi inda kira ya wuni shigowa a wayarta aman ta ki dauka domin Najeeba ta tare ta hanna ta ce" tabas ba zai samu lamarin da sauki ba! Sai bayan magariba suka zauna inda suka samu indomi da kwai da kif8n gwangwani suka gwongwaje Mikewa najeeba ta yi ta dauko masu wata gora ta dauki kofi ta cikawa ummu ta miko mata Ummu ta amsa ta kafa kai ta shanye tass kafin ta yi yar gyatsa Najeebama ta cika ta kwankwada sosai ta rufe ta mayar frij Ummu ta ce" Najeeba da me da me kika hada wannan kuma ke dai akoy fitinaniya Najeeba ta yi murmushi ta ce" baki ga hadin da maman Zahrau ta kawo mata ba? Shine na saka ta tambayeta me da meye a ciki Ai sabuwar tatsa ce ta rakuma sabon haihuwa na hada mata karanfani mai yawa da kuma zuma sabuwar saka ke ni idan na sha dadi nake ji a zuciyata Ummukulsum ta ce" walahi kuwa, nima ai wani sanyi na ringa ji a zuciyata sannan abin kamar yana ratsa gaban jikina Sai da dare ya yi suka fito suka kama hanyar gida yau ba inda zata je domin sun cika dare a saloon din Tun daga bakin kofa suka ga wani lamari, yau su da kansu sai da suka fito aka duba motarsu kafin su samu shiga ciki Sunna shiga suka samu Anmy su take jira, sai da ta ga shigowarsu sannan hankalinta ya kwonta Cike da kulawa take basu amsar tambayarsu kamar haka" wasu manyan barayi ne aka kawo dan a yi masu nasiha, shine baban cikinsu ya fitar da layar zanarsa ya so ya bace a gaban mai martaba Hakan da ya yi ya saka Shaheed gane abinda yake nufi tun kafin ya saka layar bakinsa ya zabura ya damki hannunsa ya kaishi kasa sannan ya take hannun nasa ya saka masa layar a bakinsa ya kuma rike masa numfashi har ya hadiyeta sai dai abin mamaki bai bace din ba Hakan ya saka Shaheed yin fada mai tsauri a fada domin baki dayansu sai da ya saka suka fitar da asirinsu ya take kafin ya shiga fadin" ashe idan har karyar asirinku zata ci a gabana ni ba jinnin marigayi bane! Ya daki kirjinsa ya furta" na rantse da wanda raina ke hannunsa daga yau kuna ji kuna ganni sata zata gagareku domin kun hadu da faduwar gaba kennan in dai zaku ayanna sata a ranku! Sai kuma ya kai dubansa wajen amintacensa ya umarci a je da su gidan horo sannan an bazu neman sauran da suka aikata satar gidan Elhaj Hamza domin sai da suka yiwa y'ayansa biyu fyade sannan suka kwashe komai na matarsa ita kuwa suka sumar da ita Najeeba ta zauna dabar kusa da Anmy ta ce" Anmy, aman shima mai martabar yana da asiri ne? Ummulkhair ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Najeeba, daga nan muka yi kallon abinda ke faruwa, Najeeba kin ga irin yanda ya murde jikeken katon nan kuwa? Dogarai suka zaburo da polisan dake tsaitsaye aman da hannunsa daya ya dakatar da su ya kuma murde masa hannun sai da ya hadiye layar da balaki wanda layar ana sakata a baki ake bacewa sai gashi dar a tsaye ba inda suka bace , Najeeba wai kin ga wani irin abu da ya ringa bin jikina na tsoro wani yam yam yam, ni walahi baki daya sai na ga kamar ba uaya shaheed da muke gani a nan dakin Anmy ba, kike maganar asiri, ai da uban asiri yake takama shine ayar Allah Anmy ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" na san shi da zafin zuciya, aman ban san cewa yana da karfi irin wanda idannuwana suka gani a yau ba, baki daya dogaransa sai suka bude filin kirari maganar da nake maki da kyar yan jarida suka watse suka barshi ya shige ciki dan yin sallaj, tun dazu ina son shiga na kasa Najeeba ta yi wani malalacin murmushi, a kasan ranta kuwa fadi take, oh yanzu haka wani sarkaci ne ya samu marar karfi, in ba haka ba mutumen dake cikin malunmalunma bashi da wani girma sai tsayi me zai iya yiwa gagarumin barawo? ............................................. A yau kam cike da wani irin takama ta sadar da kanta da dakinsa, baki daya yau tun da abin nan ya faru aka zagayeta ake mata wani irin kirarin da ya sakata jin du duniya kai babu matar sarkin da ta kaita isa da takama, mijinta jarumi ne a kowani fani, irin yanda ya nan da nan labarin yanda ya yiwa wannan barawo da ya gagari gida da waje, barawon dake tsinkawa manyan alhazawa mari idan ya yi niya, ko kuwa sai ya yi kiranka ya shaida maka rana da lokacin da zai maka sata yana takama da layar zanarsa zai shiga kuma ya dauka ya kuma tafi ba yanda zaka yi da shi, shine yau ya shiga hannun SHAHEED wanda ya jima yana jiran irin ranar da zai kasance gashi gashi su gwada ga da ga su ga wanda zai ci Wannan lamari ya saka gidanjen TV da radio suka dauka, nan da nan labarai ya shiga gama garin sai murna ake ana shewa ana fadin" wane yaro wane uwar yaro! Wane dan karamin tsagera da tarban babansa, Gurnanin zaki mai ban tsoro yake, shine sarkin sarakuna, tabas a shekarunsa ya kasance yaro ne a kan karagar mulki wanda a lokacin hawansa da yawa sun shiga zulumin yarintarsa zai hau karagar mulki? Da yawa sun shiga tsoro da firgicin lamarin , sannu a hankali suka dawo suke dukan kirji su fadi cewa" su yan kasar damagaran ne, sarkinsu na nan ya kwana lafia, kuma du wanda ya taka su zai taka shi! Har yanzu bata yi waya da mahaifiyarya ba, hasalima wayar ta kashe ta fi so ta je gata gata su yi wace zasu yi Cikinta ya fice, tun a jiya kuma jinnin da ta dan zubar ya tsaya duda ba samun karfin jikinta ta yi sosai ba aman ta yi niya zata je ta mika gaisuwarta Ta san bata isa ba, bata isa ta kawo masa wargin a kan me ya daurawa mahaifinta aure ba, aman ta rantse sai ya yi dana sannin auren da ya daura daga shi har du wani wanda yake tare da shi! Amarya kuwa ko? Zata dawo gidansu da kafarta ko a kawota...... Tun da ta shigo tana binsa da kallo bayan ta zube ta gama yi masa kirari da gaishe shi Agogon da ya ciro yake dubawa ya dan dakatar yana kallonta Har ta dan fada, ya san barin da ta yi ne ya hadasa haka ko? Da kansa ya ringa takowa har inda take Hannunsa ya saka ya mikar da ita tsaye Cikin nutsuwa ya janyota jikinsa ya bata kyakyawar rungumar da ta sakata jinta a cikin nutsuwa nan da nan A hankali ya ringa dan kawo hancinsa jikinta har wajen kunnanta na dama Muryarsa ciki ciki ya furta" shin jinnin nan ya barki ko yana nan? Sai da ta ji gabanta ya fadi, a hankali ta so girgiza kanta dan irin yanda take da sarau din haduwarsu a bed abinda ya saka kennan har a yi a gama take a takure da kasa sakin jikinta sai dai jin da ta yi da gwuiwarsa ya gane bata saka abinda zai tare mata daudar ba ya saka shi tun daga tsayen ya shiga haukatata ta hanyar yin anfani da sajen fuskarsa da dan gemunsa yana giga mata shi a wuyanta Alkyabarta ya sabule ya yar nan kafin ya saka hannayensa duka biyu ya dauketa cimak ya yi saman bed din da ita Shinfideta ya yi kafin ya bi bayanta ya shiga cire mata tufafin jikinta, yana yi yana kara kallon yannayinta idannuwanta a rintse suke sannan ta yi aikin da ta saba ta kwonce masa luf ya kasance ko cire tufafinsa ba zata taya shi ba dan ta kara saka masa abin a ransa Haka ya dane ya shiga dan kokarin gannin ya samu nutsuwar dake matukar damunsa Ba wani wasa mai armashi, domin du inda ya kai hannunsa ya taba maimakun ta bashi dama sosai ko ta nuna masa tana jin dadi duda ta fi son romance fiye da komai aman ba hali ta sandame idannuwanta rufe Bai yi kasa da gwuiwa ba ya ringa damkarta yana son ya ringa jujuyata ya samu stl kala daban daban ko zai samu ya samu nutsuwa da wuri, aman abin ya ci tura dan kwonciya daya tak take iya hakuri itama ba wai a daneta da kyau a raraketa ba aa sama sama Shi da kansa sai da ya wahala bale ita da take wani irin shashekar da ya skaka shi jin abin du ya tsaya masa a rai Da kyar ya iya kawowa ya sauka a kanta dama ko rigarsa bai cire ba iya abinda ya san zai anfanar mata ya fitar domin ko ya cire din aikin banza ne ba shafa masa jiki zata yi ba bale ya ji dan dadin da yake hasashen ana iya ji idan an yi hakan Bayi ya nufa yana jin wani iri a cikin zuciyarsa, shin ko zai samu wata malamar dake wayar da kai a irin wannan fannin ya kirawota ta shiga ta wayewa Zinaria kai ne? Ko zai samo irin shawarwarin hakan na wa'azuzuka na waya ya zaunar da ita ya kunna mata ne? Irin yanda idan yana neman agajin ya samu nutsuwa yake nuna mata cewar ta rike shi, ta shafa masa jikinsa ta taya shi, aman sai ta ringa rintse ido kamar wace ke shan wahalar kasancewa da shi? Shin ya fi karfinta ne take boyewa suke zaune da cutarwa haka ko ita a rayuwarta bata dauki sex da mahinmanci ba? Ko bata da lafia ne? Ruwa ya kunna ya shiga wanke najasar dake tare da shi da niyar ya yi ya fito ya sameta ya zaunar da ita Yau kam zai yi mata tambayoyin da yake son idan har ta bashi amsoshinsu ta nan zai fahimci abinda ke damunta, in sha Allahu zai zauna ya yi doguwar magana da ita ya nuna mata shi fa yana son macen da zata zama yar bariki a cikin dakinsa Idan yau zata daka cinyarsa da kafarta dan ta haukata shi zai bude mata ya yi mata rashe rashe ta taka Idan yau zata haukata shi da salonta da ya rantse ya gama samun nutsuwa Abubuwan sun masa yawa Rigimar cikin gidansu, rigimar waje, ga kuma rigimar cikin jikinsa! Zai so ya samu nutsuwar jikin nasa dan ya san idan har fa baya tare da nutsuwar nan yana yawan dauke wuta Da tawul daure a kugunsa ya fito ya kai dubansa saman bed din Sai dai wayam ba ita ba alamunta Wani irin takaici ya saka shi bin kofar falonsa da kallo Ya tabata ta tafi! Haushin hakan ya saka shi daukarwa kansa niyar koda ta zo da bukata ba zai kulata ba! Yama gama yankewa kansa hukunci a yau aure zai daura a kwanannan, dama abinda ya saka shi dan jinkirtawa rasuwar Bintu ...................................... Bayan kwana Biyu Ya kasance yau laraba ce, ranar da yake zuwa fada tun karfe uku dan a cen yake gabatar da salar isha'i, sai dai yana zaune a falonsa na ciki carbinsa karami a hannunsa yana ja hankalinsa kwonce yaka dauke da abin droon dinsa mai hasko masa komai dake wakana a cikin gidan dama dakunan Tun sunna daka ran fitowarsa har karfe biyar na yama ta yi, su dai basu motsa daga wajen da suke tsaitsaye dan jiran fitowarsa ba Tunda yaron ya zo ya ga zuwansa kusan minti talatin yana zaune a wajen da aka sauke shi an kayata masa zaman nasa da komai na bukatar bako aman wace ya zo din dominta bata fito ba Wayarsa dake haskawa kadan kadan ua kai dubansa, Dauka ya yo ya shiga amsa kiran domin mai martaba ne da kansa Cike da mutunta junna suke gaisawa kafin ya gabatar da bukatarsa na son a kara baiwa Ummukulsum hakuri ta daga wayar yarima domin har zuwa yau bata daga wayarsa ba Yana shirin bashi amsa ya kai dubansa kan abinda ke nuna masa abubuwan dake wakana a cikin gidan Bai san lokacin da ya zaro idannuwansa yana kallon ikon Allahn dake haskowa a alon tablette din Sosai ta gurfana da juss din dake cikin kofin glass tana murmushi ta kai daidai bakin saurayin nata dake ta sheka daria yana wani irin lamari kamar zai rungumota jikinsa Irin suturar da ta saka a jikinta kuwa sket ne da rigarsa sun mata wani irin cifcif daidai da halitarta abayar da ta dora a sama tana shiga ta cire ta yar saman kujera mai cin mutun daya sannan cike da son rigima ta tunkare shi ta tsiyaya jus a cikin kofin da gangan ta kai bakinsa dan gannin abinda zai faru hakan kuwa ya yi daidai da dawowar idannuwan SHAHEED WAJEN... *Alhamdulillah* [31/03 à 21:41] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* *SADAUKARWA GA* *SAMIRA HARUN (YA MAMA😉)* *BILKISU KANAR* *YAGANA* *AYSHER* *JALILA* *MA NAZIFA* *RAHIMA* SADAUKARWA GAREKU BAKI DAYA GRUP MAGE DA FANS MAGE......ina matukar jin dadin kasancewa da ku 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 30 Daga b'angaren mai martaba cikin kamala da datijantaka yake furta" Allah ya taimakeka kana ji na kuwa? Ko dai matsakar network d'in nan ne." Ya k'arashe yana mai duba wayarsa da yarima dake gurfane gabansa. A hankali yake sauke wayar daga kunnansa sam baima san yana yin hakan ba. K'ara k'ura mata ido ya yi da duba irin na son ganin abinda zata aikata, sannan a kasan zuciyarsa kuwa fad'i yake" Acikin gidan nan zata aikata aikin nata? A cikin falona? Tabas idan har haka ya kasance yau ba sai gobe ba sai na zartar da hukunci a kanki a kasata!" Sai da Najeeba ta kawo kofin kusa da bakinsa , ya sakankance zai damk'a ta janye ta mik'e tana murmushi. Juyawa ta yi ta bashi baya ta ajiye sannan ta koma ta zauna a wajen zamanta ta d'ora k'afarta d'aya a kan d'aya tana d'an karkad'awa tana kallonsa. Saukowa yayi da sauri ya nufota yana d'an shagwab'e fuskarsa, sai da ya zauna saman cafet d'in ita kuwa tana saman kujarar ya sakata gaba kafin ya furta" na so ki fara cika aikinki na lada amaryata, ta hanyar shayar da ni da wannan kyakyawan hannun naki mai d'auke da k'unshi ja." D'an tsura masa ido ta yi kafin ta cire dubanta daga kansa, d'an murmushi ta kuma yi hakan ya saka dimple d'in kumatunta da na kusa da idannuwanta suka lotsa, yar siririyar wushiryar bakinta ta bayyana ga haske da hak'oran ke yi, leb'enta kuwa baya d'auke da komai sai dan man leb'e kad'an da ta goga saman leb'unan hakan ya saka na k'asan mai ruwan pink color k'ara shek'i haka ma mai duhun shima ya k'ara shek'in. Fuskarta ce ta yiwa kwaliya ta hanyar shafa hodar ruwa daidai da kalar fatarta yar kadan kafin ta caje girarta da kyau ta saka kwali mai kyau mai baki ta ja dan ail liner sannan ta dora gashin idonta mai tsayin da ya girmi na idannuwanta hakan ya saka idannuwan nata kara yin sidik da su abin dai ba'a cewa komai Dinkin jikinta kuwa wata lafiyayiyar chiganvy ce aka yiwa dinkin sket da riga cif cif da jikinta Najeeba na dauke da wata irin kira abin birkita lisafin du wani da namiji sannan abin mangarin ga y'aya mata Ta kasance mai matsakaicin tsayi, domin tsayinta ba cen cen bane, Najeeba bata da rama sam, tana da dan jikinta mai dan kwabri wanda ke tafe da wasu mama masu dan girma sannan a tsaye suke cirr domin irin masu fadin nan daga kasa ne dauke da yan kawuna bakake sidik masu dan tsini da dan fadi tamkar wace ke cikin sha'awa koda yaushe yannayinsu kan zama a haka basa shafewa haka halitarsu take shi ya sa bata saka body a waje domin idan ta saka sukan nuna kansu ne koda da rigar mama a ciki, Cikinta munafukin ciki ne da baya nuna ana cin abinci a cikinsa, ko dan tana gudu tana sport tana abdo a cikin gidansu, hakan ya saka cikinta ke lafe sosai saman wani irin tafkeke, fafadan kugunta mai dauke da wasu irin duwawu da suke da girma sannan suka hade da cinyoyinta suka kara masu fadi ga tudu hakan ya sa take dauke da yannayi na Niki minaj daga kasan Tun fil'azal Najeeba tafiarta ta kasance irin tafiar nan ta tsokalo rigima, haka halitarta take ba da gangan take yi ba aman da yawa kan kokarin kwaikwaya dan a ganninsu tana sane take yi kuma gannin abin ya karbeta sai su yi kokarin kwaikwaya aman ba hali domin tafiar kasaita tamkar wata sarauniya a jinninta yake tana yi kuma jikinta na motsi daidai misali, shi yasa idan halin ta yi rawa ya kama take anfani da kugunta wajen saka mata sakin baki sunna kallonta bale maza tsabar yanda ta iya juya shi da gadara Tana dauke da dan dogon wuya sai fuskarta mai dauke da saje sakamakon tarin gashin da Allah ya basu na mahaifinsu da ya kasance shuwa arab Gashin kanta baki ne sidik har gaban goshinta hakan yake haska copy choko color din fatarta mai santsi da kyalkyali, Gashin girarta tamkar ta SHAHEED take sai dai ita tana daidaita tata tana gyarata koda yaushe daidai da tsarin da take so a fuskarta Tana dauke da dara daran idannuwa masu tsaga tamkar na damisa, sunna dauke da gashin ido masu yawa da tsayi wa'inda ko a haka wasu na tambayarta idan ta yi kari ne? Hancinta kuwa dan daidai mitsali ne, bata da karan hanci mai tsayin nan aman kuma ba a duke hancin yake ba, dan karami ne daidai da fuskarta Lebunanta sun kasance na kasan ya fi na saman girma da kadan, sannan na kasan tamkar wanda akai masa yannayi na heart domin daga tsakiya ya fitar da yannayin nan gashi idan ta yi niyar shagwaba sai ta kara nitsar da shi sai kawai ka ji ka afka a shaukinsa da son cinye shi Lebunanta sunna da dan duhu kadan, na kasan ne yake da dan hasken pink sakamakon irin yanda take bashi kulawa ta hanyar saka brosh dinta tana dan gurza shi a hankali a hankali har sai ya fara zafi zafi sannan ta wanke ta kawo hadin zuma da lemun tsami da man haba dinta da take hadawa ta dan shafa kadan sai ta kwonta, sai ta wanke da asusuba sannan ta kawo maganin bushewar lebe da saka lebe ya yi wacila wacila wato *Sabarob* ta shafa kadan kafin take tafia wajen aikinta ta wanke hakan ya saka yannayin lebenta ya zama wani unik saman ya dan fi na kasan duhu na kasan ya zama mai ruwan pink shi ba orange ba, sannan suke da wani irin laushi da santsi wanda ko da ido idan ka kala zai tafi da kai ne Daga kasan lebenta gefen hagu kadan, wani dan kurji ne dan karami mai haske irin wanda ake cewa na masasara ne ya fitowa mutun, to ita dai ya fito mata tun tana karamarta kuma bai bace ba, wannan dan kurjin sai ya zama wani cikon sirrin kyan fuskarta, dan tamkar ta yi yar huda ne ta saka abu mai kyalkyali a wajen, har akan tambayeta yanda ta yi ta fitar da shi a kusan lebenta domin idan ta tashi sangartarta takan yi rawa rawa da lebenta sannan ta dan cije wajen kurjin nan idan ta sake shi sai ya kara haske da walwali kafin ta yi wani irin farrrr da idannuwanta Dafe daidai zuciyarsa ya yi da hannunsa na dama yana kallonta a sanyaye ya ce" me kike so na malaka maki? Me kike so na baki? Ki kama daga kaina har dukiyata duka naki ne Najeeba, ki bani kulawar da nake bukata na roke ki Najeeba ta dan yamutsa goshinta kadan kafin ta dan fitar da harshenta ta dan lashi lebenta na kasa as usual, a hankali ta ce" me ya sa kake tunanin dan ka malaka min wani abin zan iya yarda da soyayarka? Ka zo da shirin baje min haja ne Elhaj? Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce" da haja, da ni mai hajar, baki daya nake son baje maki ki taka ki yi abinda kike so da su Najeeba, ni dai burina ki wanke ni son ranki aman ki aureni kwana kusa dan ina mai tabatar maki a matse nake da ke Idannuwanta ta dan rintse dan jin kunyar wai a matse yake din da ya fada, kafin kuma ta bude tana dan kaucewa kallonsa Hannunta ta saka daga sama wajen rigarta ta janyo chek din da ya bata a saloon shi kuwa yana kallonta, ba kalacin shi ba, harta wanda ke jiran su fara ya samu huja a kusa na kallonsu ta miko masa gefen damtsen hannunsa A hankali ta dan ragewa idannuwanta girma ta ce" shi ya sa ka fara marina da yayan banki? Kafin ya bata amsa ta kara rage tsayinta, Kanta ta waiwaya cikin dabara ta kurawa wajen dake dauke da abin camerar dake nuna cewar ta nan ake iya ganninta Shima idannuwansa ya kura a kan nata tamkar sunna kallon junna da mugun kallo, Cire kanta ta yi a wajen ta ja tsaki a ranta tana furta, wani irin hira ne zan yi da mutun bayan mai yiwuwa matarsa marar mutunci na kallon mu? Ko kuwa cikin barorinsa? Ko kuwa kawayenta yan iska da suke jirana su gane min miji ko me? Gaskiya da sake Haka kawai sai ta sauko itama ya kasance sunna zaune ne a saman cafet din zama irin na kusa da kusa kadan kafin ta rage muryarta sosai ta ce" ban san yaya aka yi ba daga nan da kwana uku lamarin wankar maza ya fara fice min a rai Ka san wani abu? Kansa ya girgiza yana kallonta, ta ci gaba da fadin" na fi kwarewa wajen wankar aljihunnan mazan da suka ajiye mataye a gida suka zo suke bin mu, sukan bude bakin aljihunsu su kashe mana kudaden da a shekara ba zasu iya anfanar iyalansu da su ba, Ina matukar jin dadin karbar kudin wanda matarsa ta tarbe ni ta zageni Shin ka san cewar sunana bashi da kyau a waje? Dan bakinta ta yatsina ta ce" kama sani ne domin wa'inda ke zagin nawa da irin haka da yawansu matan da na zame masu tashin hankali ne, sai samarin da na raina shekarunsu irinka Ban san yaya aka yi na raina mai kananun shekaru ba Ni din ce mai rigima Ina famma da fitina da yawa hakan ya sa nake tunanin anya kuwa namiji mai kananun shekaru zai'iya hakurin halayana? Matsota ya yi sosai yana dubanta ya ce" kannanun shekarunna ba su zasu hanna na kasa hakuri da halayanki ba Najeeba Baki san cewa babar kadara ita ke saka biyaya dole ba? Najeeba.... Ya fada a sanyaye yana mai kara dora mata takardar nan tare da wata takardar itama ta bankin ce sannan ya hade hannayensa ya ce" ba rokona kika yi ba, ban kuma nuna zan iya da dawainiyarki dan kin kasance mai son kudi ko wani abin ba Abinda na sani *MACE* yar gyara ce, dole a gyara mace, dole a kashe mata kudi idan ana so a ganta tsaf tsaf tsaf da ita, ba wai abinda ya fi karfina na tarka ba, kowani mutun kan yi daidai karfinsa ne Najeeba, da kwaliyarki, da kyan tsarinki na ganki, a yanzu da nake son kasancewa da ke ina so ki zauna da ni daya kwal, hakan ya sa nake jin zan iya maye maki gurbin sauran samarinki ta kowani fani, zan iya da kowace lalura taki ta yau da kulun, ki yarda da ni ki amincewa motsina hakan zai saka na kara gyara tsayuwana na faranta maki Murmushi ta yi har cikin ranta, itafa ta mayar masa ne dama dan ta ga iya gudun ruwansa sannan ta nuna masa kudinsa basa gabanta, aman ina ita ina nuna bata son kudi? Ta fada ta kara tana son kudi yanzu tana son su gobe Ba wanda bai fito nema ba Ba wanda idan aka mika masa baya karba ba Halal take ci ba haramun ba Domin bata je ta baza haja an kwasa an biyata ba Da dabararta take samun kudi a wajen du wanda ya saki bakin aljihunsa Da wayonta suke wanyewa lafia da mutun Bata taba zina ba Bata taba kusanta kanta da zina ba Ko rayuwar shan minti ba'a yi da ita Takan saka kaya wanda ranta ya so aman idan ka yi gigin tab'a jikinta zaku samu matsala kai da ita koma waye kai aljihun gara kuwa zata wanka har zuwa lokacin da zata shige daga daka. D'an murmushi ta masa sannan ta k'ara gabatar masa da abubuwan da aka kawo masa dan tarbarsa aman ina shi ya shagala bin motsinta yake da kallo yayama za'a yi ya shigo da wasa ne shi? Tabas bai shigo da wasa ba, kuma sai ya daki wannan sha'ani da zafi zafi. A hankali ya saka hannunsa yana shafa wajen hancinsa, ji yake har kamar wani hucin zafin balaki na cin k'owata gab'a ta jikinsa har zuwa cikin k'wak'waluwarsa, shin ina kunya da kawaici irin na y'a mace? Ina girman daraja da mutunci irin na y'a mace? Ita bata da su tun haihuwarta ko daga baya ta saka k'afa ta shure? Wani dalili ya sakata shurewar saboda kud'i ko dan wata buk'ata da ta kasa hakuri? Shi ya sa a rayuwarsa yana addu'ar idan Allah ya bashi y'aya mata zai aurar da su tun sunna k'ananun shekaru ba dan komai ba sai dan kar su zama gandama gandaman yan matan da ko sun je da budurcin to fa ya samu rauni. Sai yake jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa na lamarin, yana jin abin har cikin k'ok'on ransa, me ya sa a cikin yan uwanta ta kasance wace ta fi sauran irin wannan halayya? Tabbas suma Dayabu ya shaida masa suna da samari, sai dai shi idanuwansa basu tab'a kama masa su da wani lamarin da zai zargesu ba, me yasa take irin shigar nan sannan take sakin jikinta da kowani k'ato ta yi hira ba damuwa ba wani d'ar? Me ya sa ta b'ata rayuwarta da yarintarta take harkar maza ido rufe? Me ya sa kika yi abinda kika yi har ya kasance na mayar da ke abinda nake harin na kama tsamo tsamo da laifi? A bayyane sannan a sanyaye ya sada kansa muryarsa da rauni ya furta" Haba *NAJEEBAT*, me ya sa kika saka min madaukakiyar tsanarki ta hanyar zubar da mutuncinki a wajena kasancewata yayanki sannan sarkin ki? Meye ribar da zaki ci a nan gaba cikin gidan duniya? Waye zai iya aurenki ya rik'e ki da amana bayan ya san wacece ke? Kaico da zamanin da zina ta zamo ado ga al'umma, kaico da wannan zamanin da mutane kan iya dukan k'irjinsu su taka da tink'ahon su d'in yan iska ne. Ajiye tablette d'in ya yi ya mik'e daga wajen, domin ya had'u da b'acin ran da yake gudu, tabbas yana jin zafin irin abubuwan da take yi ba dan komai ba sai dan ta kasance yar uwarsa, y'a a wajen auntynsa aminiyar anmynsa wace take matuk'ar k'aunarsa, taa d'in k'anwar DAYABU ce d'an uwa kuma amininsa wanda suke hirar sirri da junna harma ya haye masa, ita din y'a ce a wajen Abih d'insa, daga ita har yan uwanta yanai masu soyayya ta yan uwantaka, shi d'aya amynsa ta mallaka, yana da yan uwa yan mata wajen sauran matan mahaifinsa sai dai babu wata shak'uwa sosai a tsakaninsu ko dan sunna nesa ne? Yana jin zafin du abinda za'a ce su suka aikata domin yana masu kallon y'ayan da Anmy ta haifa. Hira suka sha har bayan magariba ita da aka ce ta salame shi kafin sallah magariba. A daidai lokacin da ta zo shiga b'angarensu ta ringa jin hayaniya da kuka sama sama hakan ya saka gabanta ya yanke ya fad'i ta afka da gudu dan gannin abinda ke faruwa. Mai martaba ne zaune a kujerar da idan ya hau kowa kan zauna a k'asa. Yau ma Abih ne zaune, matarsa gefe tana rusa kuka da Anmy cen gefe tana jan carbi, sai yan uwanta dake zazzaune kawunansu du a k'asa kusan su dukansu. Tunda ta afko d'akin a tsorace sai da ta bi kowa da kallo, hakan ya saka sukai ido hud'u da shi. Gabanta ne ya kwanci kwanci ya fad'i sakamakon irin yanda idanuwansa suka kad'e sukai jajajir ya kuma b'alla mata kakausan hararan da ya sakata jin tana jin fitsari. Da sauri ta kai k'asa a wajen da take tsaye kanta a k'asa tana jin har jikinta ya d'an fara rawa rawa dan irin fad'uwar da gabanta yayi sakamakon tsagwaron b'acin ran data gani a tattare da shi sai ta shiga taitayinta ta sadda kanta baki d'aya ta had'e hannayenta a saman cinyarta bata kuma d'agowa ba. "Allah ya k'ara maka lafia wani irin zama ne wannan? Wace irin rayuwa ce wannan? Daga na fad'i gaskiya shikenan ya tsintsinka min mari, ya hankad'a ni na fad'i gaban goshina ya tsage bayan ya d'auki kusan kwana goma yana min gabar da ban san abinda na masa ba nice ya dace na masa gaba dan a gabansa NAJEEBA ta shak'e min wuya ta marar min fuska yar uwarta na rik'e da y'ata da na haifa, yayansu na kallo aman bai d'auki wani mataki a kansu ba bayan a ranar da ka mana shara'ar nan ne. Daga na tambaye shi inda Zahrau ta je wai da gaske ta auri sarkin agadez shine yake ce min eh Allah ya yi, ai ta Allah ba tawa ba?" Sasautawa ta yi tana k'ara sada kanta domin ba ido da ido take maganar ba ba zata iya kallon idanuwansa tayi bayanin nan ba, cikin kuryar kukan da son lalle sai ta fasa k'won daya tsaya mata a wuya ta ce" Allah ya taimake ka, shine yau MUTALLAB zai bud'i baki ya ce min na daina sheganta masa y'aya dan ba shegu bane sai dai na nemi shege wa wajen ubana?" D'agowa tayi tana kallon yaren daya bayan daya ta ce" *Allah ya ja da ranka shi ya manta tasa shegiyar ne?"* A firgice du suka dago sunna dubanta banda wa'inda ta yi hakan dan su ji sai yan uwansu da ko a ka basu damu ba , tun daga DAYABU, DA UMMU, DA UMMULKHAIR, DA NAJEEBA wa'inda suka rigaya suka mallaki hankalin kansu wa'inda ta d'aukaka rigimarsu ne dama dan tana so sai ta fasa sirrin da ya fad'a mata ya rok'eta kan ta b'oyewa y'ayansa dan yana jin matsananciyar kunyarsu, yana jin kunyar ranar da zasu ji irin abin nan su kale shi da shi, ya boyewa duniya da y'ayansa yarinyar nan ba dan komai ba sai dan gudun a goranta masu, ya san mutane da izgili da neman fitina, gashi Allah ya bashi y'aya mata har goma sha shida baya so sakamakon hakan su ringa samun matsalar rayuwa, ya fad'a mata ne dan ya d'auka ita d'in tunda ta kasance matarsa to fa sirrinsa ce. Ya fad'a mata maganar nan ne dan kar ta ji a gari ta tuhume shi da b'oye mata babbar magana irin wannan, kawai daga jin labarin an d'aura auren Zahrau fitintunnu suka tashi kamar zata kama da wuta, saima da ta ji wanda ya aureta nan fa hankalinta ya k'ara tashi idanuwanta suka rufe ta ko wace hanya neman abinda zata lalata lamarin take, shine ta ringa tak'ale tak'ale ganin dai b'angaren Zahrau yarinya ce mai matuk'ar biyayya da matsanancin kamun kai, hakama mahaifiyarta sai kawai ta shiga yada masa magana cewar yanzu da sarkin ya ji ya aikata haka yaya za'a yi ya so had'a zuri'a da shi? Shine fa shima ya ce da ita "In banda abinki Mardiya ni kuwa na had'a da ke?" (Wato idan baki ya san abinda zai fad'a bai san amsar da za'a bashi ba) shine fa ta ringa fad'e fad'en maganar da idanuwansa suka rufe ya wan wanka mata mari domin fadi take" yanzu haka ba ita kad'ai bace shegiyar har sauran duba da irin yanda suke da halayya na shegu." Kamar wani wanda shege yake da halayya tasa daban, hakan ne ya saka Abih hankad'ata yana nunata da yatsa ya ce ta daina sheganta masa y'aya. Sai aka yi rashin sa'a ta kaiwa madubi duka, dama abinda zai kaita gidan sarki take nema sai kawai ta fad'a motarsa ta nufi gidan sarkin, tun da aka fito daga sallah ta tsaya a hanyarsa dogarai na kakarewa aman sai da ta yi yanda ya gane itace kafin ta fasa kuka ta yi hanyar b'angaren Anmy. Burinta ta fasa wannan sirrin y'ayansa su san abinda ya aikata, ta wanzar da tashin hankali tsakaninsu da mahaifinsu da su kansu. A hankali Anmy ke girgiza kanta kafin ta ringa furta "Innalilahi wa inna ilaihi raj'une." Da sauri ta shiga tatara k'annanun da su suna cike da tsoron ganinsu zaune gaban mai martaba dan su tsoronsa ma suke, sai Nusaiba dake ta mak'alar wuyan DAYABU tana wasa. Anmy du ta tattara su ta tura su ciki tana jin kamar juwa zata kifata da k'asa. Shi Kansa sarki sai ya sada kansa k'asa yana jin yanda kansa ke sarawa, ayau yana tare da b'acin ran da wannan fitinaniyar ta haddasa masa, sai ga wani gagarumin da ya tabbata Anmynsa sai ta shiga matsanancin tashin hankali, uwa uba Abih. Abih gaba d'aya jikinsa ne ya ji ya fara masa wata mijirya kafin ya d'ora hannunsa daidai zuciyarsa ya rintse idannuwansa wasu zafafan hawaye suka shiga biyowa gefen kumatunsa. Anmy ta sada kanta sai kawai ta fashe da kuka tana girgiza kanta tana b'oye fuskarta dan kunyar da take ji da irin maganar Mardiya. Baki d'ayansu hankalinsu ne ya k'ara tashi, hakan ya saka du suka rasa ina zasu nufa, wajen Anmy din ko wajen Abih? Da rarafe wa'inda suka fi kusanci da Anmy suka yi kanta suka ruk'unk'umeta, wa'inda suka fi kusanci da Abih kuwa Ummukulsum ce da Dayabu suka yi wajensa da Nusaiba suka had'e a jikinsa. Mamakin hakan ya saka Anmy d'agowa hannunta na rawa ta kai dubanta wajen SHAHEED ta ga kansa a sade, aman ya damk'i sandar dake kusa da k'afarsa da damk'a mai tsananin da ya hadasa jijiyoyin hannun nasa k'ara yin tsaye rad'o rad'o. A rikice take tatab'a jikinsu ta shiga fadin" baku yi mana fushi ba? Wallahi zan fad'a maku yanda aka yi, kun san k'adarar bawa bata fice shi kar ku yiwa mahaifinku da ni kaina da na taya shi b'oye sirrin nan fushi." DAYABU dake dafe da hannun Abih wanda ya dafe daidai zuciyarsa muryarsa na rawa rawa ya ce" ABIH, kar ka kashe kanka a irin wannan lokacin da matarka take son tona asirinka dan manufarta da mu kanmu bamu sani ba, Abih mun san da maganar nan dan girman Allah ka sassauta kar ka had'iyi zuciya domin idan ka mutu mu mukai asara ba ita ba." UMMUKULSUM ta ririk'e hannayensa tana dannawa ta ce" Abih zafi nan ke maka? Idan yana zafi mu je asibiti, Abih wallahi wallahi bama jin kunyar ubanmu ko haushinka domin a haka muke son ka." NAJEEBA ta k'ara rik'e Anmy tana b'oye fuskarta a jikinta tace" Anmy, meye na kukan? Kanmu aka fara ko kanmu za'a rufe?Anmy, koda mu dukanmu ne shegun shine aka ce zamu zo mu shak'e maku wuyan a kan me hakan ta faru? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Anmy ba shege bane abin gudu, d'an halal d'in aman mai halayan shege! Anmy, ai ba daga yannayin da aka haifeka kake nuna halaya ba, halayanka na nuna wanda ya baka tarbiya." "Anmy, kowani tsuntsu kukan gidansu yake yi! Koda dubu ya tara mu ubanmu ne, babu wata hallitar da zata zagar mana shi bamu sauke hak'oranta k'asa ba na rantse!" Ummulkhairma kukan take tana kara share hawayen Anmy ta buda bakinta ta ce" Anmy, ku daina kukan nan haka, kin ga fa Abih sai rike daidai zuciyarsa yake Najeeba ta saketa tayi wajen Abih ita ma ta d'ora kanta gefen k'afarsa tana jin kamar ranta ne ake wasa da shi, irin yanda iyayen nata ke zubar da hawaye sai ta ji tsoron Allah ya k'ara shigarta, wai kunyar duniya kennan, duniyar ma yayanka, ina ga kunyar Allah? (ALLAH, ALLAH, DAN GIRMANKA DAN SOYAYARKA DA FIYAYEN HALITA ALLAH KA SHIRYE MU, KA YAFE MANA, KA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA, KA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA KIYAMA). Anmy da Ummulkhair ma da rarafe suka k'arasa wajen Abih, Anmy ta d'ora hannunta inda hannunsa yake tana hawaye tace "Ya isa, daga yau nauyin sai ya tafi ya baka lafia, yaya sun ji, sun sani sun sani." Sai ta had'e kanta da su suma sunna ta hawaye, shi kuwa da hannunsa yake daddab'a su yana jin wani irin a cikin ransa. SHAHEED kuwa abu d'aya ya hana shi tashi daga zaunen da yake shine shara'a, ya hau kujerar nan ne dan ya yi shara'a tsakaninsu tana zaune ta kawo k'ara ne, du irin kukan da mahaifiyarsa ke yi tamkar ana narka dalma ne ana zuba masa a k'irjinsa. Mardiya kuwa baki da hanci duka a bud'e suke ta yi wani fik'i fik'i tana ganin abin na neman juyewa a kanta. Anmy dake kuka tayi saurin d'agowa, hannun Dayyabu ta damk'o sannan ta damk'o na yayanta tana hawayen nan ta ce "Insha Allahu ba zamu yi kunya ba, insha Allahu Allah zai yi ta rufa mana asiri." A hankali ta kuma fad'in" *YAYA, DAYABU, SHIN ZAKU BAIWA MAI MARTABA AUREN Y'ATA?* *INA BARAR AUREN YARINYATA WA SARKIN DAMAGARAM, INA BARAR AUREN Y'ATA WA YARON KA*?" Ta karashe tana mai hade hannayenta da nuna Abih. Tunda ta fara neman auren ya d'ago da rinanun idanuwansa ya tsura mata daga ita har yayan nata da kuma y'ayan nata, suma y'ayan mata biyu da suka yi saura sai ya zamana kukan nasu ya d'auke d'if sai kallonta da suke da kallo irin na son ta idasa maganarta. Anmy ta k'ara kamo hannun Abih na dama tana mai k'ure shi da kallo, gwara a yita ta k'are, gwara ta nunawa Mardiya a lokacin da ka so wulak'anta bawa Allah kan rufa masa asiri, gwara ta fad'i muradinta idan ya so ko wace wace, idanuwanta a kansa, su kuwa idanuwansu a kanta inda zuciyoyi suka shiga bugawa tamkar zasu b'allo su fito daga k'irjin da dama a wajen. A sanyaye tace " _Idan kun yi comment zafafa, zaku samu zafafa🤣, wasan fa yanzu ne ya fara._ NADIA ta yi murmushi tana kallon Auntynta ta ce" a ranar da suka suka yi fada a kan abin nan sai da ta ringa maimaita kalmar nan sai sitin da uku ina irgawa Hannun Auntyn ta riko ta ce" Happy juma'at🥺 *Yan uwa ina k'ara gode muku, Allah ya bar k'auna.* [31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 31 Irin yanda NAJEEBA, da UMMULKHAIR suka dago suka tsatsare Anmy da ido tamkar zasu dauketa da idannuwansu dan yannayin girman maganarsu masha Allah Hakan ya saka Anmy daburcewa ta juya ta kalli SHAHEED Ganni ta yi shima ya dago kansa daga duken da yake ya kura mata duban da ya sakata jin gaban jikinta sunna kara mutuwa tsoron abinda ta yi niyar fada ya darsu a cikin zuciyarta harma ta ringa dan kokarin sakin hannun Abih Hannunta Abih ya riko da kyau yana kallonta ya ce" ki fadi muradinki kai tsaye kan yaren nan, kin isa da ni ubansu bale su, BILKISSU ki fadi koma me kike son fada kai tsaye, idanma ba zaki fada ba ki saka rana da lokacin da kike son a daura auren da ko wa kika zaba cikinsu ina mai tanatar maki mutuwata da mutuwar wace kika zabar kawai zai hanna wannan lamari Mardiya baki daya jikinta rawa yake hakan ya saka ta shiga kokarin matsowa Hankalinsa ne ya kai kanta Sai da ya dan girgiza kansa kafin ya ce" MARDIYA, ki fita mu yi maganar sirri da masu rike sirrina, domin ni a yanzu ko lokacin cin abincina da izinin Allah ba zaki kuma sani ba kar ki je waje ki saka speaker ki ringa ihun na cika ci Irin kallon tsanar da DAYABU ke mata da kallon gargadin dake shaida mata idanfa ta yarda ta matso kisa da su sai dai wata ba ita ba ya saka tana dogon wiya jikinta na rawa ta mike ta kai dubanta wajen mai martaba Sai dai irin yanda ta ga idannuwansa ya saka ta fice da sauri ta tsaya kofa hankalinta tashe sakamakon rashin jin da waye kuma za'a daurawa sarkinsu aure a cikin y'ayan da ta tsana? Fatanta kar ya kasance da wace sanadiyarta ta shigo rayuwarsu Domin kuwa ta rantse da Allah idan har aka aurawa sarki Najeeba ta tabata gaba ta ci ba baya ba dan kuwa shi kansa saurayin nata ba wani uban mai kudin bane bale mulkin da zai yarda ya kama kafar Mai martaba Kennan ta yi a banza ko me? Alkawarin da ta yi cewar sai dai ta ji ana yiwa wata buda sai ta tabatar da shi koda kuwa hakan zai yi sanadiyar rabuwar nata auren Waigawa ta shiga yi dan samun mafita Da sauri ta nufi bangaren ZINARIA domin ta san wacece a halin kishi dan irin haukan da ta zuba a auren bintu ko a gari fadi ake ita ta kasheta!, ta yi niyar zata fara fada mata maganar da sarakuwarta ke shirin aikata mata idan ya so sai ta zama makiyarsu ta gasken gaske Anmy ta kara kallon Najeeba kafin ta kuma sada kanta, a sanyaye ta ce" yaya, ina so cikin su biyun nan da suka kawo, a hada auren SHAHEED da daya Wata wawuyar ajiyar zuciya ce Najeeba ta saki wace ta saka Anmy sauke dubanta jiki a mace Ajuyar zuciyar ta kuma saki tana kamo hannun Anmy, irin zata yi convincing dinta ta ce" Anmy, Alhamdulilah, dama Anmy Ummulkhair ce bata da saurayi, Anmy kin ga ni ai na maki maganar Huzaifa ga kuma likita, a cikinsu koma wa kika zabar min na yarda zan zauna da shi Anmyna Jikin Ummulkhair har rawa yake a lokacin da ta ji abinda Najeeba ke fada Hakan ya saka baki daya ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce" Eyah Najeeba, Eyah Najeeba, wace irin magana kike haka bayan kin san cewa kaf cikinmu na fi ku rauni? Ni a gidan sarauta? Ko sujada na kai ina fadawa Allah ya hada ni da kunu huce in sha ka domin ina matukar tsoron ringingimun yau da kulun , Najeeba ke kuwa kin sha fada ke ai su kike so ko? Najeeba ta yi gagawar fadin" ke, ki rufa min asiri, ki rufa min asiri da wata fitinar gwara na san salar gawata ake yi, bayan wannan ni Huzaifa nake so, yanzun nan tafiar da ya yi mun tsayar da maganar zan kawo maganar gida ne fa DAYABU dake kallon su da matsancin mamak8n shin sun manta cewar sarki na zaune ya daka masu tsawar da ta saka du suka zube jikin Anmy Ransa bace ya ce" lale baku da kunya da kawaici Gardama kuke a kan maganar da aka yi ko me kuke nufi da maganarku? Ku tashi ku bacewa mutane a wajen nan, kuma magana ta riga ta yita a yanzu yanzu zamu yanke wace ta dace idan ya so in an yi auren dan Allah ta kashe kanta! Hankalinsu du a tashe suka shiga mikewa , du sai suka shiga gware da junna tsabar rikicewar hanyar da zasu bi Sunna shiga daki Najeeba ta karasa da sauri ta rukunkume Ummulkhair ta saki kuka tana fadin" ashe ba zaki ringa daukan girma irin na aunty zahrau ba? Ashe kin manta irin tsanar da wannan bawan Allahn ya min har zaki nuna kina jin tsoron zaman aure da shi? Ummu, a titi ya min wanka da ruwan sanyi cewar na dauki niyar yin wankan jannaba shin karuwa ce ni? Kaf cikin mu ku kun fi kowa sannin ko rigima ta kawo mu fada ya kama hararana tamkar zai kashe ni da idannuwansa da mugun kallo Ummu, kin fi kowa sannin a duniyata ina jiran damar da zan rama irin cin wulakancin da jifana da mugayen magangannun da ya yi nake nema ko? Kafin aunty zahra ta bar gariin nan sai da ta sakani rantsuwar fita a harkar matarsa Ummu, me na mata? Du idan mun hadu ko ta zartar da yawu ko ta kirayeni banza talaka Ummu wace irin rayuwa kike son saka yar kanwarki a ciki bayan kin san a duniya *SULTAN SHAHEED MAKIYINA NE?* UMMULKHAIR ta yi gagawar rufe mata baki ta kara janta ciki ta dungurar da ita saman kujera Tana kallonta ta ce" ohk laifi na yi da na zilewa auren mutumen da ya kasance ko hauka nake idan na ji sunnansa nake wartsakewa? Kaf cikin namu waye yake dago kansa ya yi masa duban ido cikin ido a lokacin da kowa ke rawar jiki? Kaf cikinmu waye ya daga hannu ya wankawa matarsa mari ya kwana lafia bayan nan muka ringa nafilar Allah ya sa kar a sace ki a je a datse hannayen ki? Najeeba, a gaban Anmy kika nuna mata ke kina da wanda kike so? NAJEEBA yaya kike tunanin zan iya zaman kishi da matar da nake tsoro kamar raina? Kin taba gannin na gaishe da matarsa a tsaye ba tare da na duka ba? Ke kin taba gaisheta tun da kike? Najeeba ni, ni Ummulkhair auren Sultan SHAHEED? na tabata maki tsoronsa zai saka nima a tardo gawata a ajiye kafinma a sadani da dakinsa NAJEEBA a kan mema Anmy zata so hadin nan? Me ya sa zata nemi wannan abin bayan mu tsakaninmu da shi ubane sarki ne a wajenmu? NAJEEBA waye ke bibiyar matar da yake aure? Idanfa wani ne ke kashe masa mata? Najeeba ta ringa binta da kallo kafin ta ce" idan fa ZINARIA ce ke kashe masa mata? Da sauri Ummukulsum dake tsaye hannayenta rungume a kirjinta ta matso ta ce" kai, ku yiwa mutane shiru kar garin haukan ku ku yi kokarin kauce hanya! Zato? Zato irin wannan? Wai da kuke ba ni ba , ba ni ba, an fada maku shi yana da ra'ayin aurenku ne? Banda masifa, rigima, fitina, tara samari, iya shege me muka iya ne y'ayan mutalab? Ikon Allah ne ke giftowa yana hada mu da na kirki, idan ba wannan ba ku fada min a samarin tsayuwar titin waye ba dan airs ba? Najeeba ta ringa gyada kanta ta ce" ka ji uwarmu ta yi magana, ke Ummukulsum na rantse kika kuma ce mana yan iska sai na fafala maki mari malama a nan, kuma ba dai sarki ba ? A kai kasuwa, ko ina numfashin karshe aka daura min shi zan mike na murje ido na ce bana so! Gaba dayansu da mamakinta suka kura mata ido, lale ta cika mutun mai karfin hali, Yanzu itane ke fadin haka a kan sarki? Ummulkhair ta ce" aman an fadi ba nauyi, an ji kunya Na tabata yau Anmy ba zata iya rintsawa ba idan ta ringa tunowa kin nuna kin fi son wani dan daudu a kan yaronta! Najeeba ta yi shiru jikinta du a mace tana kallonsu idannuwanta suka ciciko da kwallah A sanyaye ta ce" Ummu, Huzaifan ne dan daudu? Ummu Huzaifa ba dan daudu bane na rantse Kuma kin ga, ban taba sannin yaro zai juri iya shegena sai da na zauna na ringa masa yana taro ni Ummu, ina son Huzaifa har raina, ya jima yana fama da ni Meye laifin Huzaifa?, saurayi tsayaye yaro mai jinni a jika Ummu, Huzaifa ya iya sangarta ya iya hira ya iya yi min kallo irin na mutun mai daraja Ummu me ya sa zaki zagar min shi bayan shi zan aura nake so na zama uban y'ayana? Ummu, kin manta irin namijin da nake so? Huzaifa du ya hada abubuwan nan Ummu, shine tsakani da Allah dan ki tayar min da hankali zaki zage shi ki ce da shi dan daudu kuma ummu dan kawai na nuna aa ba ni ba sai ki ce na tayarwa da Anmy hankali? Ni yaya kike so na iya yin bacin ne? Ummu aunty Zahrauna kan sadaukar da farin cikinta domina Na tabata da itane ake magana a kanta, da ba zata taba kawo sunnana kusa ba dan ta san idan na tsani abu na tsane shi, zata amsa ne koda kuwa hakan na nufin karshen numfashinta Ummu, a hannayenku ta barni ashe ta yi aikin banza shine kuke tayar min da hankali fisabililahi? Ta karashe wasu irin hawaye na zubowa daga idannuwanta kafin ta juya da gudu ta yi cen ciki Kafarta ta daga zata bita hankalinta tashe Da sauri Ummukulsum ta riko hannayen nata Maidota ta yi kusa da ita kafin ta bata kyakyawar rungumar da ta sakata itama fashewa da kukan tana girgiza kanta ta ce" walahi zan amshi auren nasa koda kuwa matarsa zara kashe ni, ta daina kuka ina sonta ban yo haka dan son kaina ba Ummukulsum ta ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" zata fito ne, ta yi mana haka dan ta saka mu, mu kwana muna kuka hankulanmu tashe Barta zata fito ne ummu, aman in sha Allahu rigimar Sultan da mutanen dake tare da shi kaf cikinmu ba mai iyawa sai Najeeba Shin baki ga tsarin tafiarta ba? Tamkar dawisu haka take tafia cike da takama tana baza albarkatun jikinta ba tare da tana yi da gangan ba Shin baki ga irin yanda take iya saka idannuwanta cikin nasa ba? Waye yake da wannan kokarin bayan ita din? Shin baki ga ranar da ta daga hannu ta wankawa Zinaria mari a gabansa ba? Hakan na nufin koda a gabansa ne ba zata taba bari a takata ba! Tabas tsana, ko na ce wani baban lamari na faruwa tsakaninsu wanda mu kanmu mun kula da irin rashin daidaituwar yannayinsu dake faruwa a tsakaninsu Aman wannan lamari kam, inaga na Allah ne! Ummulkhair ta ce" idanfa suka yanke ni ce zan aure shi? Ummukulsum ta ce" haka Allah ya tsara, koda ke ce zaki je ki rayu da su in sha Allah babu abinda zai same ki face wanda Allah ya kadaro maki! Baki dayansu shi suka saka gaba a lokacin da suka roke shi shin ya amince su je su fadawa Allah kan zabi biyun nan Allah ya dora su a kan wada ta fi dacewa da shi Ya san da sannin cewa ba zai kubucewa auren yar gidan Mutalab ba domin an rigaya an fadi maganar, abinda yake son bakinsa ya buda ya fada shi ne" *NA ZABI UMMULKHAIR* , sai dai lamari na kasancewarsa baba a wajen na mulki ya saka shi harshensa yin nauyi Gannin abin yake wani iri, Ba zai iya buda baki ya furta masu zabinsa ba domin shi, shine mai danne zuciyar wasu, shine mai daukan dukan wasu, shine mai shanye damuwar wasu Abu daya ya san zai yi shine, zai roki cewar a saka auren da za'a masa tamkar wani yaro da zabinsa shima Mahaifinsa ya masa auren fari Ya yi na biyun da kansa ba'a je ko'ina ba ta rasu Gashi mahaifiyarsa zata masa auren uku da matar da shi kansa yake cikin faduwar gaban kar ta masa zabin da zai saka shi mutuwa dan bakin ciki Yana so a bashi damar daukan mace biyu a rana daya, zabin da suka yanke da wace zai zabowa kansa ya aureta a cikin sirri Sam Zinaria ba zata iya da lamarinsa ba, so take ta kashe masa lamari yana da karfinsa da kokarinsa haka kawai Auren da za'a daura masa kuwa idan Ummulkhair ce itama me zata iya masa? Yarinyar da shekarunta duka duka ba zasu zarce ashirin da hudu ba,? Sam baima kawo maganar idan kuwa Najeeba ce ba, sai dai kura masu idon da ya yi wanda hakan ya saka Anmy sanyaya muryarta ta kara kallonsa ta ce" SHAHEED, ko kaima ba zaka auri y'ata ba? Da sauri ya kalleta, sai kuma ya maida dubansa wajen DAYABU Kansa ya kara sadawa a hankali ya buda bakinsa ya ce" ko wani zabi kukai min, in sha Allah zan yi biyaya Sai dai, ina da wani muradin auren wata yarinya, ina fatan za'a hada su biyun a rana daya Namijin duniya kennan, haka Dayabu ya fada a kasan zuciyarsa Abih kuwa murmushi ya yi a fili ya furta" wannan ai abin murna ne, Allah ya tabatar mana da alkhairi Su duka da amen suka amsa kafin su mimike Dayabu ya nufi dakin Anmy da Nusaiba dan ya shinfideta domin ba zai kula kannen nasa ba, ya kula idan ba ya nuna masa da zafi zafinsa ba zasu kawo raini a lamarin A lokacin da suka zo tafia gida sai Abih ya shiga motar Dayabu Har ya tayar ya fara tafia Abih ya yi murmushi yana girgiza kansa ya ce" ina hangen rigima a wajen yan biyuna, NAJEEBA, ko UMMU? sai dai da son kai irin nawa sai nake jin bana so a kara yi masu kishiya duda na kasance ni ina balawa mata tikitin zawarci bama na basu damar yin zaman kishin Dayabu ya yi murmushi ya ce" Abih, ka manta Ummu, sun yi zama da maman Bilkisuu fa Sai da ya lumshe idannuwansa a lokacin da ya ji sunnan *UMMU* mahaifiya a wajen NAJEEBA, shi yakan kirata da UMMU, sauran kuwa sukan ce mata mama Murmushi kawai ya yi yana tuna lokacin, zamanin nan ya kasance tamkar wani zaburaran doki a tsakanin matan nan biyu Ya ga rayuwa ya yarda cewa mata sunna suka tara Murmushi ya yi a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake" me ya yi zafi haka da aka guje ni an matana? Na kai zuciyar cikin duhun da ta kasa yafe min? ............................................. Ba yanda bata yi da dogaran dake tsaron kofar bangaren ZINARIA kan su barta ta shiga tana da sako wajenta mai mahinmanci, sai dai sam suka ki amoncewa domin ita da kanta ne ta nuna ba zata karbeta ba tana hutawa Haka dole ta samu ta kwana gefen fulani domin idan dare ya yi haka ba mai fita daga fada sai da kwakwaran dalili ............................................. Sam bata samu ta rintsa ba, sakamakon maganar yar uwarta cewar ta saka Anmy a cikin bacin rai Idan ta juyo daga kan gadonta ta hange su sai ta ji uwa ta je ta cicije su ko zata huce, sai kawai ta ji baki daya kewar yayarta ya hana ta rintsawa domin ta tabata da ita ce da ba zata taba yi mata fushi haka ba Suma bangarensu sun matukar yi kokarin gannin sun watsar da fushinta gefe, domin idan har suka biya tabas zata saka su a damuwar da zasu kwana sunna kuka ita kuwa da safe ta warware ta yi tafiyarta! Kiran salar fari a kunnayenta ya sauka Dira ta yi daga gadon ta yi bayi ta dauro alwalah Sai da ta zo ta saka doguwar riga saman ta bacinta sanann ta yane kanta ta shiga gabatar da sallah Tana nan zaune har aka kira sallar asuba ta kuma gabatar da ita cikin nutsuwa ta shafa fatiha da sauri ta mike ta yi bangaren Anmy bata kula yayun nata ba Tana zuwa ta shige da salama kasa kasa kafin ta karasa da dan saurinta wanda ita ganni take sauri ne take yi ta duka gaban Anmy wace ta gama sallah tana jan carbi Kanta a kasa tana jin hawaye na son zubo mata ta kamo hannayenta ta dora a gefen fuskarta a sanyaye ta ce" Anmyna, wai da gaske na bata maki rai wai har kin kwana baki yi baci ba? Anmy dake jin kaunar yar a ranta ta ce" in ji wa? Najeeba ta ce" ba aunty Ummu bace ta fada? Dan murmushi Anmy ta yi jin ta ce da ita auntu Ummu, yau ummun ce auntyn, Kanta ta dan girgiza tana murmushi ta ce" aa, ma baby girl ba zata bata min ran da zan riketa haka a zuciyata ba, Me ya samu idannuwanki suka kunkumbure haka? Murmushi ta yi ta ce" ban yi baci bane Anmy Anmy ta kara shafa gefen fuskarta a sanyaye ta ce" tashi ki je ki kwonta cen ki huta maza Mikewa Najeeba ta yi tana jin hankalinta ya dan fara kwonci dan yannayin da Anmy ta nuna mata ta tabata an bar maganarta Doguwar rigar ta cire ya mata sauran wata yar rigar baci baka wace bata idasa rufe cinyoyinta ba sannan daga saman mai gidan mama ne wada ake kira rabin nono ya kasance saman a bultse suke rabin ne suka rufe Ba abinda ya shafeta dan ta san ba mai shigowa bangaren Anmynta, kuma gaban Anmy kuwa zir ne kawai bata yi Hayewa ta yi saman lafiyayen bed din Anmy mai sansanyen kamshin turaranta ta yi kwonciyarta tare da rungume yar kanwarta dake ta baci ......................................... Kamar yanda ya saba da duhu duhu yake shiga dan gaisheta Hakan ne ya faru, a lokacin da ya daga labulen dakinta ya sanyo kansa Idannuwa masu neman fitina suka sauka a kan fitsarariyar yarinyar nan wace ya yi mata kallon shari'a daya tak ya yi gagawar cire idannuwansa yana jin wani nishi na kwace masa kamar mai cutar athsma Da sauri ya saki ya juya ba tare da ya shigan ba, domin gani yake sam bai dace ya shiga a irin wannan lamarin da mace ke kwonce da irin wannan shigar bayan ba muharamarsa bace! A wannan rana Najeeba bata fita saloon ba, sai da aka yi salar magariba ta fito cikin shirin abayarta lurub har kasa ta cewa Anmy zata dan leka ta dawo a tsaitsaye Da adu'a ta bita tana mai yin dan murmushi Irin yanda yarinyar ta fi sauran yan uwanta kulawa da ita ya saka take mata so daya tak da babu irinsa Kwana bakwai dai suka dauka zasu sake zama su dukansu tana adu'ar Allah ya yi zabi na alkhairi Tun da ta zauna a wajen yau ya fahimci halin da take ciki Shima zaunen da yake hotunnan tsala tsalan yan matan da aka turo masa ne yake bibiya yana son gannin wace zata iya da shi? Kuma dago shanyayun, lumsasun, idannuwansa masu shige da na mashaya da kuma dauke da kwali ya yi ya kai dubansa a kanta a karo na bakwai Haushinta yake ji sosai, ta zo ta wani zauna masa a wajen da ya rigayeta kamawa a nan yake zama, bayan yana cike da haushinta na har wani ta ja mahaifiyarsa na hada sunnansa da nata, yo shi Allah ya tuba idan aka ce za'a aura masa wannan yarinyar a ranar zai cire rigar sarautar ya je da gudu ya tari katuwar mota ta murje shi da ya ga takaici! Me zai yi da masifafiya, yar balaki, balagazar mace? Ai shi auren nan da zai yi na hutu ne ba na jazawa kai balaki bane! Sai da ya dani zuciyarsa kafin a sanyaye ya furta" *wa ya taba ki? Sai nake ga hankalinki tamkar ba a kwonce ba, hakan kuwa kwata kwata ya dauke min nutsuwata* Dagowa ta yi tana kallonsa, yauma da alama ya yi gudu ne dan da kayan gudun a jikinsa sai mahaukacin basket din takalmin dake kafarsa wanda yannayinsa zai tsadanta maka tsadarsa A hankali ta cire kanta ta dan daga kanta tana kallon taurarin wajen Muryarta a sanyaye itama ta furta" *ina cikin tsaka mai wuya ne, ashe haka zaman juran amsa yake? Ina cikin gararin rayuwar da kila wa kala ne idan har zan kai labari, domin kuwa da na yarda da abinda zai iya kasancewa da ni gwara a ce bana duniyar!* Da matsanancin mamaki yake kallonta, aurensa ne take fadin da ya kasance a kanta gwara ta rasa ranta? Ita din wacece da har take tunanin tana da girman matsayin da shi zai yarda ta amsa sunnan matarsa? Ashe aurensa zai iya kuntata mata rayuwa har haka? Tabas da ace zai iya da ya je da kansa ya roki a aura masa ita ko dan ya ringa kallon yanda zata yi har ta mutun Sai dai ina, irin yanda yake jin kyankyaminta ba zai iya wannan kasadar ba Sai da ya dan cije lebenta na kasa kafin ya furta" me ya yi zafi haka NAJEEBA? wani irin abu ne wannan dake damunki mai tsanani? Ki fada min ni zan yi maki maganinsa domin Najeeba ina jin ki har cikin zuciyata yanda na dauki kanwata haka na dauke ki Juyowa ta yi tana kallonsa Sosai ta ji dadin maganarsa, wada ta so a ce yayanta ne yake fada mata dadadan kalamai haka Kanta ta sada a hankali ta mike tsaye Kuma dubansa ta yi a sanyaye ta ce" wannan rigimar cikin gida ce, ni din, bana iya fadin sirrin Ahalina Tana gama fada ta yi gama cikin wani taku na ban tausayi domin gaba daya jikinta a sake yake hakama tunaninta ba a jikinta yake ba ........................... Bayan sati daya Da yamaci ne suka hadu a bangaren mai martaba, A tsakanin wannan sati dayan baki daya y'ayan sun cika da zulumi da tashin hankalin abinda zai faru Ko a yau basu san cewa za'a yanke abinda aka yanke shawara ne hakan ya sa suke cen wajen harkokin su, Najeeba na saloon, Ummu na wajen aure Tun da aka yi maganar nan Dayabu da kansa ya dakatar da Huzaifa kan ya bari zai waiwaye shi idan hakan zata yiwu Likita kuwa ba'a bashi damar shigowa bama sai dai a waya suna soyewarsu tamkar ba gobe Abih du suke kallo a lokacin da ya gama adu'a, kafin a sanyaye ya dago dubanza cike da gamsashiyar amsar da zuciyarsa ta bashi, haka kuma malaman da ya rarabawa kan a taimaka suka shaida masa ya budi bakinsa cikin nutsuwa da kamala ya ce" ALHAMDULILAH, ba wanda ya isa godiya sai Allah Alhamdulilah da Allah ya dora mu kan amsar da ta tara mu a yau Dubansa ya kara kaiwa wajen Anmy dake zaune tana sauraro a hankali ya ce" BILKISSU, du wajen wanda na yarda da kamalarsa, da datijantakarsa , da irin shaidar adininsa da na kaiwa maganar nan ya nuna min ya yi abin a cikin kwana shida, ya yi kwana uku da sunnan kowace Wasun kuwa sunnan Ummu kadai na basu Wasun kuwa na Najeeba Tabas Allah ya kawo amsa, Amasar nan kuwa ita ce *NAJEEBA* BALIN BALIN BALI BAL BAL 🤣🤣🤣🤣🤣 wata wakar indiya [31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 32 Irin yanda yayi wani dum a zuciyarsa na lokaci d'aya ya saka shi rintse idanuwansa da k'arfi. "Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une! Me ke shirin faruwa a tarihin rayuwarsa? Shi? SHAHEED, shine da auren wannan yarinyar?" Bud'a idanuwansa da suka rigaya suka cenza kala yayi da niyyar budar bakinsa ya furta masu magana kamar haka" *Aa, ba zan lamunci auren fasik'a ballagazar mace ba, ku yi hak'uri ku nema mata wani*." Idanuwan nasa ya fara saukewa kan DAYABU DAYABU kansa na sade ne, ya kasance zuciyarsa ta cika bugawa mai tsananin gaske domin ya tabbata ba zai amshi maganar Najeeba ba yana da damar k'iyawar, kuma idan ya k'iyan ba abinda za'a yi sai dai sai ya kasance ya had'e hanayensa biyu dake rawa rawa cike da tsoron amsarsa yana ta adu'a a k'asan zuciyarsa. A hankali ya kai dubansa wajen Abih Sai ya ga Abih ba a zaune dangalgal yake ba, shi bai san yar tsamar dake tsakaninsa da yarinyar ba hakan ya saka farin ciki ke kwonce a kan nitsatsiyar fuskarsa amsarsa kawai yake jira. Dubansa ya maida kan Anmy. Irin yanda ta bi ta marairaice fuskarta zaka rantse cewar jira take ta ji amsarsa ko ta suma ko dad'i ya sakata kai sujada k'asa, irin kallon da take masa na jiran jin amsarsa ne, hakan ya saka ta d'an langab'e kanta sannan ta k'ura masa ido tana sauraronsa. Sau biyu yana k'ok'arin gyaran murya dan ya furta abinda ke cikin zuciyarsa cewar ba zai yiwu ba, Alkhairin ta kai shi wajen wani, sai dai ya kasa d'aga ya d'ora dubansa kan mahaifiyarsa sai ya ji du ya tsintsinke. " *SHAHEED*." Ta fad'a muryarta har tana d'an rawa rawa. A sanyaye tace "Sai nake ganin jinkirin amsarka tayi yawa SHAHEED, ko dai ba zaka auri yarinyata ba?" "EH ba zan iya aurenta ba Anmy..." Zuciyarsa ke fad'a a lokacin daya kasa magana. ANMY ta ta budi baki da d'an k'arfi tace "SHAHEED?" Idanuwansa ya lumshe kafin ya kuma bud'ewa kansa ya cire daga dubansu da k'yar ya bud'i bakinsa ya b'amb'aro maganar dake ciki ya furta" Allah ya tabatar da alkhairi Anmy." Ajiyar zuciya ta sauke tana maida dubanta wajen Abih da yanayin farin cikinsa ya fara raguwa. A hankali ya ce" SHAHEED? Anya kuwa mun yi maka adalci a maganar nan? Ya dace ka fad'i ra'ayinka domin kai dai yanzu ba wani yaro bane da za'a saka ka gaba a tirsasa maka wani abin ba." Kansa ya d'an girgiza cikin nutsuwa kafin ya ce" Allah ya sanya Alkhairi Abih." Abih ya sauke ajiyar zuciya ya d'an saci kallon DAYABU ya ga yanzun ya d'ago kansa yana kallon sarkin. ABIH yace "Yaya maganar d'ayar yarinyar?" Saida ya d'an jik'a leb'unansa da suka bushe kafin yace "Insha Allahu idan kun tsayar da ranar d'aurin auren ita ma zan gabatar da danginta sai a yi komai a had'e." Albarka sosai suka sakawa lamarin, Anmy ta k'ara dubansa , a sanyaye ta ce" Alkhairi ne, insha Allah SHAHEED." Murmushi ya k'ak'aro mata kafin suke mik'ewa su masa sallama. A baya ya tsaya sai da suka fita ya dawo da sauri. Wajen da ya tashi ya koma ya zauna. Kansa sade ya k'ara had'e hannayensa kafin ya d'ago yace "Dan Allah, ka amsheta da zuciya d'aya domin kai d'in mai zuciyar adalai ce, ka zame mata bango, ka zame mata uba, ka zame mata farin ciki ka zamo sanadiyar shiryuwarta, tabbas na san cewar kana yawan tuhumanta kan harda sakin hannuna a yanda take sangartarta, ka yi hak'uri, ka rufa min asiri ka dubi baiwar Allahn nan da idon rahama." Saida ya gama maganar sannan SHAHEED ya lumshe idanuwansa ya k'ara gyara kwoncinsa a saman kujerar da yake hakan ya saka DAYABU k'ara godiya sannan ya mik'e ya fita. Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une ya ringa maimaitawa a k'asan zuciyarsa. Me ke shirin faruwa da rayuwarsa wanda bai tab'a hasashen kawowa a cikin tsarin rayuwar tasa ba? Meye wannan? Yarinyar nan itane zai aura? Waye bai ce yana sonta ba waye bata amsa tana sonsa ba? Waye bata yiwa kwaliya ta yiwa rangwad'a ba? Waye bai ganta da dan wando tana tsalen gudu da ball a hannunta wai ita ta tafi sport? Wani sakarai ne baya son tab'a jikinta? Wani irin zaman aure ne zai yi da ita bayan yana da dar da irin kasancewarta mace marar kamun kai? Aure fa aka ce, Idannuwansa ya kuma rintsewa yana jin wani irin haushinta a kasan zuciyarsa Me ya sa kika gama iskancinki zaki kare a gidana? Har kansa ya ringa sarawa a irin wannan tunani da ya yi. Kwonciyarsa ya gyara yana mai lumshe idannuwansa da suka yi ja sannan sukai nauyi yana tunanin rayuwa A yau bama zai je wajen gudu ba dan baya tunanin idan ya fita zai iya aiwatar da wani abu Tabas Anmy na cikin farin ciki madaukakin farin ciki, hakama yayanta da kuma DAYABU Sai dai basu cika nunawa ba domin zaune suke sunna kara tsara ta inda zasu hayo mata Anmy kan ji har gabanta ya fadi idan ta tuna yanda za'a sha fama da ita Farko, harkar saloon, Biyu harkar fita Uku auren kansa da wanda za'a d'aura mata bayan tana tsalen fad'in ai ita ga wanda take so *HUZAIFA* Abih ya dubi agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa na hagu ya kalli Anmy ya ce" Bilkissu, wai karfe nawa take dawowa ne, na ga lokacin ace ta dawo ya yi gamu dare dare a zaune shiru Anmy ta kalli agogo itama, mikewa ta yi tana fadin" k'warai, zuwa yanzu ya ci ace sun dawo duba da tun da na dora mata dokar lokaci bata taba kaiwa lokacin bama take dawowa dan wataran har sai ta rigayi Ummukulsum wace ke zuwa wajen lesson da Professor Wayarta ta gwada kira shiru, hakan yasa ta nemi layin SHAHEED. Ta jima tana ringin kafin ya d'aga. Anmy a tausashe ta ce" ALLAH ya taimake ka baci ka yi?" SULTAN dake zaune saman sallaya ya d'an girgiza kansa yana fitar da hucin zafin dake cikin zuciyarsa ya dan girgiza kai tamkar tana ganninsa sannan ya d'an furta" Ummu." Anmy ta k'ara tausasa muryarta ta ce "Dama, so nake ka bani number amintacenka, zan yi kiransa ya yi kiran dogarin dake tare da Najeeba, shiru basu dawo ba." Idannuwansa ya k'ara rintsewa a k'asan zuciyarsa yana fadin" yaya zata yi ta dawo yanzu? Sai ta gama bi kwararo kwararo tana siyen naman bakin titi ta je wajen da ta nasa k'wai ta zauna daga cen kuma idan ta raya mata ai sai ta nufi wani wajen? Yanzu Anmy wannan ce kika zaba min matar aurena?. Du a k'asan zuciyarsa yake bayaninsa kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya furta "Ina zuwa." Kashewa ya yi ya mik'a hannu ya d'auko wayarsa mai d'auke da numbobin du wasu dogaran gidan. Abin layo layo ne, DOG NAJ ya kamo kafin ya danna kira. Daga b'angaren da suke cikin tashin hankali kira ya shigo masa sam bai duba ba ya d'aga ya kai kunnnensa a lokacin kuwa d'an uwan nasa na fadin" Bayan nan ina zamu nufa nemanta? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une." "Hello? Hello?" Ya ringa maimaitawa. Shaheed kuwa na sauraron irin yanda dayan ke ta ambatar" Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une." Hankali tashe yana fadin "Kuma wajen mai nama bata nan, mun je wajen mai ice cream bata cen, mun je stade bata cen, to wai ko dai tana cikin saloon d'in nata bamu duba da kyau bane." Shima hankalin nasa a tashe ya ce" ba ka ga suturar da ta fita da ita bace a jikin yar aikin nata? Yaya aka yi ta fita bamu ganeta ba?" D'ayan ya furta" baka gannin yau abin ya kasance da wani irin cinkoso gashi dare ya yi mutane wasu sai fitowa suke wasu na shiga ta yaya kake so mu ganeta bayan yau ko fitilar kofar saloon din ba'a kunna ba." " *INA TA SHIGA?*" Ya fad'a a dake wanda sai a lokacin dogarin nan ya ciro wayar daga kunnensa da wani irin fad'uwar gaba ya lek'a sunnan da ya kira shi " *GURNANIN ZAKI*." Wayar ce ta sub'uce daga hannunsa yayi wani irin sama da hannayensa kafin ya furta "Mun mutu." Wayar ya bi ya wawura dan kuma kaiwa kunnansa yana mai zubewa k'asa tamkar yana gaban Shaheed d'in hakama d'an uwansa na ganin wannan lamari yayi tunanin lalle wani babba ne a fadar yayi kira idan ba amintacen sarki ba to fa wani babba ne shi baima kawo cewar sarkin ne ba. "A kashe , ya kashe, Attahir shikenan, dawama a cikin gidan kurkukun k'urya ya tabbata a garemu, GURNANIN ZAKI ne ya kira wayana da kansa kuma hankulanmu tashe ban duba ba na daga du ya ji abubuwan da muke fad'a." Zuciyarsa ya dafe cikin tashin hankali yana jin cikinsa na murd'awa dan mad'aukakiyar tashin hankalin da ya hangowa kansu harma bakinsa ya kasa furta komai. Mik'ewa yayi ya damk'i hannunsa yace " Tashi mu kuma bin waje wajen da ta saba zuwa, dan ina mai rantse maka ba zamu taba komawa fada ba tare da ita ba!" Murmushi tayi da jus d'in dake ajiye saman lafiyayen table din da aka jera masu kayan k'walam da mak'ulashe. Cikin wani irin shauk'inta yake , cikin dabara yake d'an k'ara kusanta kansa da ita yana mai kasheta da kallon soyaya. Cike da farin cikin ganinta yace "Ban san a kan wani dalili yayanmu ya hana mu ganin junna ba, yace min zai waiwayeni har yanzu shiru, Najeeba ina jin tsoron kar a je ya hana min ke?" Najeeba ta dan yi murmushi bata ce masa komai ba, hankalinta du yana kan agogonta so take ta mike aman kuma kar ya ga tana wulakantashi da yawa bayan uban nacin da ya ringa mata su hadu koda wani wajen ne bukatarsa ya ganta ya yi missing din kyakyawar fuskarta fiye da tunaninta hakan ya sa ta tsara fitarta yau du ta ringa yarda da yan kwaliya da masu gyaran jiki tun safe take cin wahalalen aiki wajen ya rikice sai shiga ake ana fita sannan ta ki kunna fitilar waje, sai da wajen ya zama sun daina duba wanda zai fita ko wada zata shiga tana hankalce da su kafin suka cenza sutura da AIDA ta fice fittt tamkar Aidar ce ta fita dan takan aiki Aidar siyo wani abin "Lokacin komawarki ya yi ko?" Ya tambayeta cike da kulawa. Najeeba ta sakar masa murmushi tace " Ka san doka ce, kayi hak'uri ina ji a jikina zai waiwayeka soon." Murmushi yayi yana mai jin dad'i har abokansa ya gayyata su ganewa idanuwansa dan su yarda cewar shi d'in fa ba k'aramin k'waro bane, yau shine ya kawo NAJEEBA restaurant. Mik'ewar da tayi da doguwar rigar AIDA jikinta du bata jin dad'in kasancewarta a cikin rigar mutane ya saka shi mik'ewa shima yana kallon table d'in yace "Baby baki ci komai ba fa?" Najeeba ta d'an girgiza kanta da jus d'in hannunta tace "Ba ga Jus na sha ba? Ka san bana iya cin abu a gaban mutane haka bana jin dad'in ci." Murmushi yayi ya d'auki wani croissant ya nufi bakinta da shi. Sai kawai ta kula kamar an yawaita kallonsu ba mazan ba matan wanda bata san dalilin hakan ba ko dan bata saba zuwa irin wajen takanas ta zauna ta ci abinci bane? Takan zo Abusa restaurant aman ba dan ta zauna ba, daga cikin motarta ake mik'o mata dukan abinda ta buk'ata , aman yau ita Najeeba dan ta farantawa saurayi ta shigo d'are d'are ta zauna saman kujera, hakan ya hanna mata nutsuwa jinta take tamkar a saman k'aya du bata fahimtar abubuwan da yake fad'a. Murmushi yayi, shi baban soyayya ya kai bakinsa ya gutsura ya tauna ya had'iye yace " Ko tsoro kike a je na saka wani abu a ciki?" Najeeba tayi yak'e tana d'an zama gefe tana d'an waige waige a sanyaye tace "Huzaifa tafia zan yi dare fa ya yi." Murmushi yayi yace "Dan Allah manta da wani dare yayi, babbar yarinya da ke za'a wani d'ora maki dokar dawowa gida da wuri sai kace wata yar daji?" D'an tsai tayi tana kallonsa, a k'asan zuciyarta kuwa fad'i take lallai baka da wayo, ai wayewar tawa bata kai wajen da zan iya bijirewa Gimbiya ba, sai ta daki hak'oran banza a zauna k'alau. Ambatar Gimbiya da tayi ya sakata jin gabanta ya fad'i, firgigita tayi ta shiga wawurar jakarta mai d'auke da wayarta. Dubawa tayi dan ganin ina wayar? Sai dai cikin ikon Allah bata ciki, hankalinta ne ya tashi ta mik'e da sauri ta kama hanyar fita. Shima mik'ewar yayi yana mik'awa abokinsa wayarta da ya zare, ya yiwa kansa alk'awarin zai je ya binciki wayarta du wani d'an iskan saurayinta dake mata magana ya d'ud'ura masa ashar da zumar itace sanan ya masa kashedin sake shiga hanyarta, zai shiga wajen hotunanta da vidos dinta ya tura wa'inda sukai masa kafin ya yarda wayar ya siya mata sabuwa _(HATARA dai yan matanmu, waya ta zama balaki, tashin hankali, fitinar dake hanna kwonciyar hankali a wannan zamani, wasu yan matan kan yarda su ringa d'aukan hotunan wasu sasa na jikinsu haka kawai suna bari a cikin wayarsu wasun kuwa samarinsu suke turawa, zaka ga budurwa ta yi hoto rabin nonowanta a fili harshe a waje tamkar wata karya da k'walelen kai a fili tana wani langwab'ewa ita ga kyakyawa ta ajiye a allon wayarta, shin k'anwata, yayata, y'ata idan wayarki ta fad'i a titi ya kasance wani mugu ya tsinceta ya je ya yi anfani da abubuwan dake ciki, ciki kuwa harda munanan hotunan nan naki ina zaki shiga da ranki? Wani saurayin ya zo gidanku ne dan ya lalata tarbiyar iyayenki ya yi tafiarsa, wani ya zo ne dan ya wulakanta ki ya kara gaba, ciki d'aid'aiku ne suka zo dan soyaya idan wayarki ta fad'a hannun wanda kike wulak'antawar nan ya je ya fitar da vidio d'inki kina wasu irin abubuwa ke ba yar bariki ba ke ba mahaukaciya ba yaya kike tunanin zai yi da su? Dan Allah mu rufawa kanmu asiri da lamarin nan, wallahi, wallahi idan wani abu bai tona mana asiri ba wayoyinmu zasu tona mana Allah ya kare mu baki d'aya)._ Bayanta ya biyo da sauri. Kusan motarsa take tsaye tana son bud'ewa. Ta bayanta ya zagayo ya rungumeta a jikinsa hakan ya saka gabanta ya yanke ya fad'i harma jikinta ya fara b'ari b'ari. Da sauri ta ringa kiciniyar k'wacewa hakan yasa ya k'ara ruk'unk'umeta a jikinsa a sanyaye yana furta " Baby meye haka? Ki tsaya na ji d'umin jikinki a jikina, ba wani abu zamu yi da ke ba sai an mana aure aman irin yar rungumar nan ba zan samu ba? Ki duba fa ki ga irin yanda wasu ke tsotsar bakin junna wa'inda basuma kaimu wayewa ba aman ke sai ki ringa guduna?" "Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une ..." Najeeba ta fad'a da k'arfin gaske kafin ta tura shi tayi baya baya ya gamu da jikin motar. Da sauri ya saketa gannin zata tara masa mutane yana kallonta da mamaki. Rasa me ma zata yi ta yi, yanzu Huzaifa ne ya ruk'unk'ume mata jiki haka ya d'ora mata kai a wuyanta Idannuwanta ta lumshe tana jin wata tsanarsa na mamaye gurbin birgetan da ya fara. A sanyaye tace "Wai ko wani namijin ma d'an iska ne, ko dai nice mai sifar yan iskan da bana iya tarayya sai da d'an iska? Wai kowa haka yake soyaya ko matar da zaka aura sai ka nuna mata akuyanci?" "HUZAIFA." Ta fad'a a sanyaye hawaye tuni ya fara wanke mata fuskarta tace "Dama dan ka d'ana jikina ka shigo jikina har ka saka na kamu da soyayarka?" Huzaifa yayi gagawar girgiza kansa ya mik'o hannunsa dan tab'a nata aman sai ta kauce da sauri tana kallonsa, shi yama rikice sam bai d'auki haka a matsayin wata damuwa ba, a kan me zata wani damu daga yar runguma, yo yan matan yanzu meye ba'a yi da su? Aman ita daga yar runguma ta kama kuka haka me take nufi da shi? A sanyaye yace "Najeeba, ba fa wani abu na maki ba, rungumeki na yi a jikina wanda yanzu hakan ba wani abu bane , Najeeba aurenki fa zan yi ko kin manta?" Najeeba ta d'an lumshe idanuwanta tana d'an girgiza kanta a hankali tace "Da ace ina yarda da rungume rungumen nan da baka tardo ni a haka ba, Huzaifa da ace ban d'auki irin haka a bakin komai ba da ina ga cikin biyu an yi d'aya, ko duniya ta d'ad'a ni da k'asa ko kuwa ina wani wajen da kai baka isa ka hango ni ba, dan na rantse maka tun ina da shekara goma sha hud'u nake tara samari, Huzaifa da ace na biyewa samari mun ringa soyayar zamanin da kake fad'a da na tara y'aya da yawa a duniya, duniyar ta gama yayina ko na zama rik'ak'iyar yar barikin da ba dai k'ananun yara ba sai manya." Tana gama fad'a ta juya a hankali ta shiga tafia a k'afarta. Huzaifa ya waiga ya ga abokansa biyu na lek'e hakan ya saka ya ji kamar ya k'urma ihu a wajen ( kai, ta zo maka da sauki baka sha mari ba?) Me ya sa ta masa haka? Shi sam bai ga wani abinda yayi na laifi ba, koda yake zai je ya gama aiyukan da zai yi a wayarta sannan ya je saloon dinta gobe ya shiga koda da gudu ne ya bata hak'uri, zata sauko ne abinda ta fad'a da bakinta cewar ta kamu da son sa?. Sam bai bi bayanta ba, itama hakan ya fi mata alkhairi tana tafe tana share hawaye ta bi ta gaban comisaria ta kama tudun poste a k'afarta tana tafe tana had'a hanya tamkar zata fad'i k'asa. Ficewarsu biyu ta hanyar da take bi aman sun kasa ganeta, sai da suka dawo da wani irin gudu suka lura da budurwar dake tafe tana had'a layi kasancewar hanyar itane hanyarta ta bi kullum idan zata koma fada. Wani irin birki suka ci a gabanta, da sauri d'ayan ya fito hankalinsa tashe ganninta tana ta hawaye gashi ba kayanta ne a jikinta ba. Bata kula irin rikicewarsu ba ta bud'a baya ba gardama ta shiga ta kwontar da kanta jikin kujerar *da ban je ba, da ban ga wulak'anci ba, da ban ba da hanya ba, da bai rungumi jikina ba, ni Najeeba, ni ba yar iska bace* wannan abubuwan take fad'awa kanta a cikin zuciyarta har suka k'araso fada. Su sun fita shiga damuwa domin sun san cewa an san basa tare da ita gashi sun d'ora lokaci sosai a kan lokacin dawowarta. Tun daga yannayin Amintace suka k'ara sarewa har suka gama parking da motar ta bale ta fita ta nufi b'angaren Anmy su kuwa sun kasa fitowa daga cikin motar domin tsaye yake hakimce hannayensa rungume a k'irjinsa da yanayi irin na zaku ci ubankun nan yana jiran su gama k'umbiya k'umbiya su fito su tarkata su yo b'angaren SULTAN. *Masha Allah* [31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 33 Tana shiga ta tarar da Anmy zaune tana rike da wayarta DAYABU na tsaye da wayarsa shima yana dokawa haka Abih na zaune aman kansa a kasa Tana shigowa Anmy ta fara ganninta hakan ya saka ta mike da sauri tana fadin" NAJEEBA, daga ina kike? Waye ya daga wayana yake ce min na shafa maki lafia na bar kiran ki? Ina wayarki take? Me ya same ki? Dayabu ya juyi da sauri yana kallon yanda ta yi wani irin turus sannan kukan da take ga kuma irin yanda jikinta ke bari gabansa ne ya fadi hakan ya saka da wani irin sauri ya karaso ya kamo hannayenta ya yi ciki da ita Sai da suka shige daki ya zaunar da ita har jikinsa na rawa ya ce" daga ina kike? Kukan me kike? Anmy da ta biyo bayansu ji take kafafuwanta sai bati suke kamar zasu rabu da gangar jikinta dan tsoro da fargaba A kidime ta karasa shigowa tana fadin" wani ya maki wani abu? Wani abu ya same ki? Fashewa ta yi da kuka tana zumburo bakinta ta ce" Anmy, wayata ce ta bata Ba anmy ba, shi kansa sai da ya ji ya sauke ajiyar zuciya duda ba wani yarda ya yi da maganarta ba Abih ne ya shigo ya zauna bakin gadon yana kallonta A sanyaye ya dubi Anmy ya ce" Bilkissu, mu je Anmy sai da ta kamo hannun Najeeba ta rike tana kallonta a sanyaye ta ce" wannan shine alfarma ta fari da zan nema a wajenki nurul khalb Najeeba ta kurawa fuskar Anmy ido aman ta kasa tambayar menene har suka fita Sunna fita Anmy ta ringa sintiri ta kasa zama, dama sun yanke sai dai Dayabu ya tarbeta da maganar dan shi kawai zai iya fatatakarta kuma ta saurareshi Cikin daki Na san karya kike da maganar dan an sace wayarki kike kuka, ki fada min abinda ya saka ki kuka tun raina bai baci ba DAYABU ya fada yana kuma mai jin tsoron abinda zata ce ya sakata yin kukan Sai da ta rintse idannuwanta wasu hawayen suka kara zubowa daga gurbin idannuwanta, cike da jin kunyar abinda zata fada ta shiga kwatanta masa abinda ta aikata wanda ta tabata sai ya babala mata mari aman kuma da ta rike ita daya ta yi ta jin haushi gwara ta fada masa ya wanwanka mata mari ko zai huce Da mamaki yake kallonta kafin ya girgiza kansa a sanyaye ya ce " Najeeba, kin san irin darajar da Allah ya yi maki har kike aikata halaya irin na wasu sakakun mata? Najeeba kin kuwa san irin daukakar da Allah ya maki har zaki je ki zubda kanki haka? Najeeba kin kuwa san irin matsayin da Allah ya maki har zaki yarda wani sakarai ya rungumi jikin ki? Yaya aka yi kika kasance mai saurin sakarwa maza fuska bayan ke din kadara ce da ta fi lu'u lu'u daraja? Najeeba nan da kwana goma idan Allah ya yarda za'a zafa fatiyar daurin aurenki da mutun mafi daraja da mutunci, mai girman mulkin da Allah ya nada tun a kannanun shekaru, mai zamani mai takawa da Alfarmar Annabi, mai watsa taron yan daba mai rikita taron tsageru, Najeeba zaki kasance daya daga cikin mata masu girman daraja wa'inda idan sun zo ficewa ake sada kai ba'a hada ido da su tsabar yanda Allah ya daukaka su ya darajanta su ya fitar da tarmamuwarsu ko da rana take kyali? Najeeba zaki kasance hakima, gimbiya, wace zata zama daya daga cikin wa'inda ko sarakai na jinjina mata kasancewarta matar daya kwalin kwal din sarkin da ya kafa tarihi, Najeeba yaya zaki yarda ki je wani sakaran da ko baran gidan nan ya fi shi mukami a damagaram ya kai hannunsa jikin ki? *NAJEEBA, ZAKI KASANCE DAYA DAGA CIKIN MATAN MAI DAMAGARAM NAN DA KWANA GOMA KACAL* kike faman saka mu a uku? Tun daga wannan kalmar kunnayenta suka dode ta daina fahimtar abinda yake fada har sai da ya dasa aya ya ga ta kurawa bakinsa ido kamar wace ta suma a zaune Hannunsa ya kai wajen kuncinta dan gannin yana furya sunnanta a sanyaye ta kasa amsa shi ya shiga dan taping a hankali ta ce" Najeeba kina ji na kuwa? Sai a lokacin ta yi wani firgigita ta farka daga summan zaunen da ta yi kafin ta kurawa fuskarsa ido a karo na biyu Wani irin hantsilowa ta yi daga saman bed din ta fadi kasa har tana take doguwar rigar dake jikinta ta kuma dagowa Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta kafin ta takarkare ta kwala wani firgitacen ihun da ya saka Dayabu saurin kai hannayensa wajen kunnensa ya dode lokaci daya kuma yana nufarta dan rufe bakinta daga wannan ihu da ta saka daya kwal ta ja shi da wani irin jan da ake yi kamar wace ke kiran sallah... Happy juma'at jama'atul musulmi😲 [31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 34 Hannayensa dode da kunnayensa ya diro ya karasa inda take ihun nan Yana zuwa ya saki kunnensa ya damke bakinta da hannunsa sannan ya saka dayan hannun nasa ya riketa da kyau Sikewa ta yi, lokaci daya numfashinta ya dauke ta tafi luuu a jikinsa Ido ya zaro cike da tsoro da mamakin suma ta yi? Lalle ya dauki abin da wasa ashe har ya kai cen? Jikinsa na bari ya samu ya kaita saman gadon ya shinfideta sannan ya mike ya karasa wajen kofar dakin A hankali ya bude hakan ya saka Anmy saurin juyowa a lokacin da Abih ya rike hannayenta yana lalabata cewar kar ta shiga ta bari har su fito Ummu da Ummulkhair dake tsaye jikin kofar ne suka kutsa kawunansu cikin dakin hakan ya saka ya basu damar shiga sannan ya maida kofar da sauri ya datse dan ya ga Anmy ta zaburo ta nufo wajen Dakatawa ta yi kusa da kofar hankalinta tashe ta kalli Abih, a sanyaye ta ce" me ya sa ya hana min shiga? Baka jin shirun ya yi yawa ko wani abu ne ya sameta? Abih ya kara kamo hannunta suka koma falo suka zauna, a sanyaye ya ce" mu yi jira, idan yana irin wannan hali da kannensa nakan basu dama, idan na saki mace na dauko wata haka muke shiga da su du su rikice, shi ke rufe kofa daga shi sai su, ban san ta yanda yake lalaba su ba, in sha Allahu zai lalabata (Ya Allah, du wani yaya da ya dauki girma ya kasancewa kannensa tamkar bango, wajen da suke kai kukansu ya share masu, wajen da sun san uba ne a gare su, Allah ka dafa masa, ka masa albarka, ka kare shi, Yayana JAMILU Allah ya kara daukaka baban yaya👏👏👏) ........................................ Cike da tashin hankali Ummulkhair ta yi kanta, ita kuwa Ummukulsum ta yi bayi da gudu dan dibo ruwa A rikice Ummulkhair ta ce" yaya, summa fa ta yi? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une daga fada mata ta summa yaya zamu yi da ita ta nutsu? DAYABU ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Ummulkhair, kar ki yi kuka, kar mu saki ta ga rauni a tatare da mu idan ba haka ba na rantse zata botsare mana ne ya kasance mu dake son tirsasata ta amince da maganar nan mu zamu dawo mu goya mata bayan bata so,abinda bana fata sam, kun dai san wacece Najeeba, tana da karfi a cikin zukatanmu, rigimarta ta fi ta NUSAIBA girma dan haka na roke ku kar na ga wace ta wani zubar da hawaye UMMUKULSUM ta share hawayenta ta shiga tofa adu'a a cikin ruwan sannan ta mika masa ta jingina da jikin gadon a sanyaye ta ce" eyah, Najeeba ta cika daukan abu da zafi, in ba wannan ba na zata zata kama ihun murna ne, meye a cikin auren Mai Damagaram? Ka ga kamar kaza yanzu ta zama daga abu ya dan daga mata hankali sai kawai ta summe Zuwa ya yi kusa da fuskarta a hankali yana shafa mata ruwan nan Kamar second goma yana dan shafa mata ruwan ta ja wata irin doguwar numfashi ta sauke kafin ta buda idannuwanta a tsorace Ido hudu suka yi da yayanta, sai yayunta da du suka matso sosai kusa da ita Da sauro ta janye hannunta daga na yayanta ta kai saman hannun Ummulkhair da take yiwa fushi aman tashin hankalin nan ya saka ta manta da wani fushi, hannunta ta damko tana kallonta ta ce" Ummu, mafarki na yi ko? Ki yiwa Allah ki samo wani faskare ko ki dauko wani birgi ki kima min na farka dan mafarkin nan sam bashi da dadi kar na mace a cikinsa Ummulkhair ta sada idannuwanta tana jin kamar ta mayar da hannun agogo baya ta ce ita zata aure shi da wannan tashin hankalin da kanwar tasu ta shiga, shin tsoronsa ne take har yaka ko menene? Dama rashin kunyar tata a boye ne take yi ko meye? Jiki a sanyaye ta saki hannun Ummu kafin ta kai hannayenta biyu duka saman kanta ta ce" kennan da gaske ne? Da gaske ake za'a min aure da shi? Da gaske kuke zaku yi min wannan abin? Yaushe aka fara auren dole a familly dinmu da za'a fara a kaina? Kun san ina da wanda nake so, har na gabatar da shi a gidan nan aman shine za'a min haka? Ku ce da shi bana son sa! Ku ce da shi kar ya soma halaka min rayuwa wayo Anmy, wayo Abih zaku halakani da kanku? Da tsawa tsawa DAYABU ya ce" zaki mana shiru da fadin shirme a wajen nan Najeeba ko sai na tataka ki? Sasauta muryarta ta yi tana kallonsa ta ce" yaya? Kai da kanka? Kai fa uba ne a wajenmu, kai din uwane a wajenmu yaya yau kaine kake son turani rami da kanka? Idannuwansa ya lumshe yana control din emotion dinsa kafin ya bude ya ce" kin taba gannin uwa ta tura yaronta rami ne cherie (dear) ? Kin taba gannin inda uba ya kai dansa ga halaka kansa kalau? Na san kin san ba dukiya ko mulki ya saka mu yanke wannan hukuncin ba, ke kin fi kowa sannin ba wani kyale kyale na duniyarnan ne ya kaimu ga haka ba, me yasa ba zaki nutsu ki saurari kalamaina ki yi masu kyakyawar fahimta ba? Najeeba dai kuka take har jikinta na rawa tana jan hanci ido rufe A hankali Umulkhair ta dora hannunta gefen kafadarta ta ce" Najeeba? Dagowa ta yi ranta a bace ta ce" ki bar kiran sunna na, kina kallo za'a min wannan abin ba zaki iya hannawa ba? Kina ganni aka ce ko ke, kin san sarai irin tsanar da ya yi min aman shine kika yi shiru aka dauke ni bayan kin san bakin cikine zai kashe ni a gidansa A hankali take girgiza kanta tana jin tamkar zata fashe da kuka Bakinta ta buda zata yi magana sai kawai ta kasa da sauri ta yi cikin bayin dakin ta duka tana kuka, a gaskiya bata san me ya taso mai tsananin girman da ya hadasa tsana a zuciyar Najeeba ba, ta rasa me ya sa zata yi tunanin dan ya halakata, dan an tsaneta ne, aka hadata aure da shi maimakun ta yi tunanin alkhairi Tabas akoy wani lamari na rashin dadi da yake nuna mata ita sai ta fi ajiye hakan a matsayin dan tana yawan fitar da rashin jin maganarta a fili ne hakan ya saka yake mata irin haka NAJEEBA a gabansa fa ta mari matarsa, NAJEEBA sau nawa zata kacame da fada a cikin gidansa ko a kofar gidansa a yi ta tashin hankali da ita bayan ta san labari zai kai masa? Idanma ya ji haushinta ai kamar ita take take dokokinsa ne mana, Allah ya taimaketa ta kasance wace Anmy ke yawan rokar Alfarmar ya kawar da kansa daga yarta? Akoy wata shara'a da ya taba zartarwa wace ta raka makociya, a wannan ranar Amintacensa ya yi mata wani duba wanda sai da hanjin cikinta suka motsa kafin ya furta" Hatara yarinya, ki saku daga mayen da ya kama ki idan ba haka ba zaki samu kanki a kabari domin kuwa ba'a hada ido da mai damagaram, ana ganni a gaban kowa ya daga masa hannu, hakan ya saka shi yin gum da bakinsa cike da gannin rashin kunyar yarinyar sannan an nuna a barta kar a hukunta ta DAYABU ya kurawa fuskar Najeeba ido, gaba daya zufar tashin hankali da ta sakawa ranta ta jike mata fuska da abin hwaye tun daga gaban goshinta har fuskar baki daya hakan ya saka du wani gashi dake fuskar ya kwonta luf luf Hannayenta ta hade tana kallonsa ta ce" ban san kamaninsa ba, wace kalar fuska ne da shi? Tsoho ne ko yaro ne karami? Wani irin mutun ne? Dan karami ne ko yana da girma?, yaya kai ka san bana son farin mutun, burina kulun shine na auri mutun mai lokacin kansa, wanda yake da lokacina kowani time, wanda zamu yi wasa da daria da shi, wanda zai mayar da cikin gidanmu filin nishadinmu, filin kwonciyar hankalinmu, filin samun nutsuwarmu, yaya...ta kuma fada a sanyaye ta ce" ina da burin mijina ya zamo abokin wasana, idan na yi niyar ganninsa koda a tsakiyar dare ne bani da wani shingi tsakanina da shi, babu wani abu da zai hana min ganninsa. Yaya, ka san bana son mai mata, ina ji a cen kasan zuciyata cewar idan har na auri mai mace ba zamu zauna lafia ba domin ina da madaukakin kishi a kan abinda yake nawa Idannuwanta ta kuma lumshewa ta kara sanyaya muryarta ta ce" ya tsane ni, ban san me na masa mai girma har haka da ya tsane ni ba, yakan min kallon da ba zai yiwa kashinsa ba, ya jefe ni da mumunar kalmar dake nuna yana zargina, shin yaya dama ana aure da zargi? Hannayensa ya saka ya janyota jikinsa, ya kasance kanta saman kirjinsa hannunsa kuwa saman gashin kanta Ummukulsum na rike da hannunta ta kara matsowa sosai kusa da ita suka sakata tsakiya A sanyaye ya ce" ba kulun bawa ke tsara rayuwarsa kuma ya ganta yanda ya tsarata ba, Shin kin san lokacin mutuwarki? Ko da za'a halice ki an maki shawara ne? A hankali yake dan shafa gashin kanta dan ya samu ta rage kukan da take yi, Ta sasauta kukan ba dan komai ba sai dan ta ji ya furta mata cewa" NAJEEBA, dan wannan ne kike kuka? Ba zan iya gannin kanwata na kuka haka ba dan haka an fasa maki auren hadi da mutumen dake jiran hanyar halaka ki ba! Sai kawai ta ji ya ci gaba da fadin" Njaeeba, ba kai tsaye muka tunkari abin nan ba, haba Najeeba meye a tatare da dan uwan naki wanda har kike irin wannan dan an ce za'a aura maki shi? Najeeba shine kike hada soyayar wani dan duniyan da yake maki ta karya da girman darajar auren nan? Ina yanzu kika gama fada min abinda shi saurayin naki ya saka ki yi, take dokarmu, ya ingizaki kika yi satar hanya kika tarda shi, sannan harma ya so ya wulakanta ki? Najeeba shin bakya mamakin irin yanda Allah ya ringa kare ki har zuwa wannan rana? Zaki butulce masa ne? Ina so ki kwontar da hankalinki kin ji an kanwana? Ya karashe yana dan taping din bayanta Kanta ta dago tana girgiza kanta a hankali ta ce" ka kasa ganewa yaya, ni fa ba wai butulci zan yi ko wani abin ba, ni kawai sonsa ne bana yi shi yasa na ce ba zan aure shi ba, sam bai min ba, sam bana son sa, baki daya ya saba halin irin mutumen da nake so Hannunsa ya saka a gefen damtsenta ya riketa da kyau kafin ya ce" Najeeba Mutalab, bismillah! Yana gama fada ya mike ya saketa ya daga muryarsa a zafafe ya ce" ke wace irin mai taurin kai ce? Ko kunya bakya ji? Yau ke zaki nuna bakya iya auren dan Anmy na cikinta? Koda yana dauke da cutar da zata iya halaka ki, koda yana dauke da cutar hauka ina ga ido rufe zaki amsa tayin aurensa balema ba daya? Ke Najeeba kin san alfarmar da Allah ya saukar a kanki kuwa? SULTAN SHAHEED kike tambayar yaro karami ne ko tsoho ne shi ya sa za'a hada aurenki da shi? Murmushin takaici ya yi yana gyada kansa, ya ci gaba da fadin" Ke gani kike roka ya yi? Najeeba da ace kadarar da ta samu yayarki a kanki ta fada kice da du mun mace da damuwa zuwa yanzu? Gatanan gabanki zaune, tana cikin jin ciwon abinda ya sameta aman ta dane ta shanye take cudanya da kowa dan ta san Allah ya dora mata ba wani ba kuma shi zai bata mafita Najeeba????? Sai ya rasa me zai kara furtawa daga cikin bakinsa A hankali ya kai zaune ya sada kansa kasa Ya tabata wannan lamari ne kadai zai yi ta saurareshi Kansa na kasa ya rintse idannuwansa ya yi forcing din kansa hawaye ya shiga bin kumatunsa Dago fuskarsa ya yi da muryar kuka ya ce" na zata na isa da ke, na zata idan na haka rami na nuna maki na ce fada zaki fada ne ba tare da kin tsaya tunanin komai ba, Sai gashi Najeeba, saboda maganar aure, maganar aurenma mai daraja kike tunanin zan cutar da ke ni DAYABU? Najeeba Anmy da Abih kike tunanin zasu cutar da ke? Baki daya jikinta ne ya kara daukan rawa Da sauri ta diro ta nufo shi aman sai ya mike yana mai dakatar da ita da hannunsa Yannayinsa a hargitse ya ce" Najeeba, ba komai ki yi hakuri na yi katsalandan a rayuwarki ashe ban isa da rayuwar taki ba Hannayenta ta kara dorawa a saman kanta ta karasa da gudu tana neman fada masa Kuka take bilhaki tana furta" da wane kake so na ji yaya? Da wane kake so na ji? Nima kai din kaine zan fadawa tashin hankalina, walahi ina cikin tashin hankalin da ban san iyakarsa ba, yaya zuciyata zafi take , ban taba zaton haka a rayuwata ba Idannuwansa ya lumshe jin ta fara sasauta muryarta a kan tasa Da hannu ya yiwa Ummu nuni kan ta gyara shinfidarta Da hanzari ta gyara wajen kwoncinta sannan Dayabu ya nufi bed din da Najeeba A hankali ya shinfidar da ita sannan ya kamo kafafuwanta ya dora sama Safar dake jikin kafafuwanta ya cire mata sannan ya karasa kusa da kanta a hankali yana shafa gashin kanta ya ce" *FA'INAMA AL USRI YUSRA*, na fi so ki fadawa Allah , ki ringa fadin" ALLAH, idan alkhairi ne ka tabatar min da shi cikin kwonciyar hankali da kosashiyar lafia Idan kuwa ba alkhairi bane, ka saka a fasa koda ana gobe daurin auren ne Idannuwanta ta lumshe a kasan zuciyarta tana furta wani alkhairi? A ina yake? , tana jin Ummulkhair ta fito daga bayi ta ci kukanta ta koshi ta wanke fuskarta ta aro jarumta ta kara nufo wajen kanwar tata a hankali ta kwonta gefenta ta rike hannunta na dama, Ummukulsumma ta dawo gefenta na hagu ta hau ta kwonta itama ta rike hannunta na hagu a cikin nata Tamkar wasu kannanun yara sai da ya masu adu'ar tsari , ya kara tsayawa a wajensu har ya ga ta daina kukan baki bude sai hawaye dake bin gefen kumatunta, sosai abin ke damunsa aman zai jure dan idan bai nuna mata ba wani abu dan tana kuka ba tabas zata rikita su Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fita ya ja kofar yana kara sauke ajiyar zuciya tare da goge hawayensa Cikin nutsuwa ya yiwa su Anmy bayanin cewa a ci gaba da shirye shirye! Nan take Anmy ta dauki wayarta ta koma gefe ta yi kiran mutanen da ita suke jura, mutanen da ta yiwa wannan lokacin tanadi, wa'inda zasu saka Najeeba daka har sai lokacin ya yi su fito, mutanen dake kula da gimbiyar saudiya, tun da aka fadi maganar ta kakabe dukiyarta ta shiga shirye shirye, ta dauko su ta sauke su a wani tankamemen gidan SULTAN, jiran yau suke dama su taho Tun da suka zube kawunnansu ke kasa jikinsu ke bari basu iya dagowa ba haka kuma bakinsu bai daina furta kalmomin ban hakuri da neman afuwar saken da suka yi har ta bace masu Amintacensa ne ke fada tamkar zai kai masu bugu tare da nuni cewar zai cenza su ya maida su filin horon dogarai domin a irin abinda suka nuna ba za'a iya bugun kirji da su ba a filin daga ba! Sai da ya kara lashe lebensa na kasa da yake jin a yau ya cika bushe masa kafin ya buda bakinsa a hankali ya ce" a ina kuka hadu da ita? Tana cikin wani yannayi? A ina ta cenza suturar da ta fita da ita? Baban ne ya kara sada kansa ya nemi afuwa sosai kafin ya kora bayanin abinda suka sanni da inda suka ganta da kukan da take Komawa ya yi ya jinginar da bayansa jikin kujerar da yake zaune ya mayar da idannuwansa ya lumshe Da yan yatsunsa ya yi masu nuni cewar su tafi Da sauri suka kara dukawa kamar zasu kwonta sunna ta neman afuwa kafin su fito daga falon Kara zubewa Amintace ya yi kansa kasa ya shiga neman afuwar Sultan , domin du horon dogarai na gidan nan a hannunsa yake haka kuma idan suka aikata laifi yana da baban kaso a ciki Idannuwansa da suka kara yi masa nauyi ya buda da kyar yana kallonsa Sai da ya furzar da huci mai zafi kafin ya ce" daga yau, bata da wani mai tsaronta sai kai, du inda zata saka kafarta ka saka, du abinda zata ci ka fara tabawa, du wanda zai mu'amalanceta ka hana Da mamaki kansa a kasa yake amsawa, ya cika da matsanancin mamakin jin cewar shi, shine zai tsare wannan yarinyar? shi rantsatsen mai baiwa Sarki tsaro ne, ko Gimbiya bai taba baiwa tsaro ba baban yaronsa ke bata tsaro aman yau shine aka wakilta da maganar baiwa wannan yarinyar tsaro? Kara tasowa ya yi daga jikin kujerar yana kara dunkule hannunsa ya kara kakausa muryarsa ya ce" *hukunci zai hau wuyanka ne daga bakin lokacin da ta zile maka ka nemeta ka rasa, shu'uma ce, zata iya shiga duban mutane ka lalubeta ka rasa, hakan zai wanzar da tashin hankali a rayuwarka!* Yana gama fada ya mike tsaye ya shiga takawa shi kuwa amintacensa kansa a sade a kasa yana fadin" Allah ya huci zuciyar mai damagaram, Allah ya huci zuciyar zaki, namu sarkin sarakaine na gida da dawa, Allah ya kara maka lafia da nisan kwana Dakatawa ya yi, bai juyo ba daga inda yake ya furta" ka saka a binciki wacece *NADIA MOCTAR a UNIVERSITY* Daga haka ya shige ciki yana jin wani irin al'amari mai girman gaske dake damunsa Ta ina zai bi ya horata? Ya je ya zubar da kansa ya shiga jikinta dan ya samu kusancin da zai kamata tsamo tsamo da laifin da take aikatawa sai gashi a lokacin da ta aminta ta bashi numberta harma suka fara sakarwa junna fuska ta hanyar yin yar doguwar hira da junna shine za'a katse? Shi ne zai auri yarinyar nan, nan da kwana goma? Kansa ya daga ya kai wajen agogo, Idannuwansa ya lumshe a lokacin da ya ga har karfe goma sha biyu ta gifta a ransa ya furta *aa ba kwana goma bane, kwana tara ne* Lebensa ya kara cijewa na kasa yana mai ajiye rawaninsa Hannunsa mai cike da yannayin karfi ya daga yana yamutsa summar kansa da ta taru wace yake so ya shiga ya aske kayansa da kansa Idannuwansa ya kuma budewa a kasan zuciyarsa yake furta" da ace kin kilace kanki, da ke din babar harka ce da ba dai yaro ba sai dai baban yaro Sai gashi kin banzatar da kanki, Idannuwansa da suka dauki kalar ja dan bacin rai ya kara budawa yana furta" Zaki zama matana ne, sai dai rayuwarki zata zama cikin kunci Abinda kika saba da shi, kina ji kina ganni zai gagare ki, sai ya zame maki fiye da zinari domin zaki nema ruwa a jalo ki rasa shi, zan saka maki matakan tsaron da ko dan jaririn namiji ba zaki gani ba bale ki hadiyi yawunki a kansa Zan kasance maki fitinar da baki taba tunanin zata shigo ratuwarki ba! (Ma ji ma gani) Sai da ya shige sannan ya dago kansa Ransa bace ya mike ya fita daga falon yana cike da matsanancin bacin rai Du darajarsa? Du girmansa za'ace yanzu an nada shi kula da yarinya karama irin wannan? To wai, meye girman darajarta da za'a nada shi, shi ya bata kula? Meye tsakaninta da shi? Sai kuma maganar Nadia Moctar, ta ina zai fara bincikenta? Nadiar nawa ce a cikin University? Dole zai dauki wayarsa ya yi aikin, tunani yake me hadinsa da wata Nadia? Wani murmushi ya yi yana girgiza kansa, wani auren zaka sake? Halitarka ba ta mace daya bace, Kansa ya girgiza yana kara wani murmushin a kasan zuciyarsa ya furta *Ga fili, ga mai doki* Idannuwanta bude suke har goshin asuba Ta kasa yarda cewa itane haka ke shirin faruwa da ita Ta kasa tsayar da takamaimai abinda zata yi da rayuwarta elle n'arrive pas a y croire (ta kasa yarda), cewar ita Najeeba, itane haka ke shirin faruwa da ita Lokaci daya ta ringa da ta sannin rayuwa Ashe du irin tara samarin nata zata kare a auren dole ne bata sani ba? Sai kuma ta ji zuciyarta ta raunata, a hankali zuciyarta ta ringa kara rufeta da fada kamar haka" dole Allah ya kama ki Najeeba, ke ce zalinci wancen, yiwa wannan karya, cin kudin wancen, mazan da kika saka hawaye yawa ne da su ashe ke banza bami san cewa haka zaki kare ba? Ta tabata idan har ya yarda ya amshi aurenta ba dan wani bane sai kawai dan ya idasa nufinsa na son kasheta Wani irin shakarsa take ji a kasan zuciyarta, zata iya rantsewa rabonta da ta shiga harkar matarsa ko shi din kansa tun da ta ganni ido da ido yana rike wuyan maciji harma ya saka yar yatsarsa a wajen bakinsa ya ringa fitar da wani ruwa mai duhun gaske Tana kallonsa yana kallonta ya yi mata wanka da ruwa masu sanyin gaske bayan ya san tana fama da cutar athsma A haka, bata yi masa komai ba ina da ta yi masan? Sai goshin asuba barci mai wani irin nauyi ya kwasheta wanda sam bashi da dadi sai mafarkai mararsa dadi sosai a cikinsa Da duhu duhu mata shida suka shigo har dakin da yan matan Anmy suke, wa'inda suke saman salaya sun gama sallah aman sun raba adu'a sunna yi dan Allah ya tankwasa yar uwarsu Saman bed din Anmy ta kai dubanta bayan ta amsa gaisuwarsu A hankali ta furta" bata yi baci ba jiya? Ummulkhair ta gyada kanta kafin ta sada kanta Matan nan fararen larabawa ne, kusan su duka farare ne tas tas sai wani irin shu'umin kamshi suke ga fatarsu kamar ka kali kanka a ciki Anmy ta kai dubanta kansu a sanyaye ta ce" ban san ta inda zamu fara ba, bana iya yi mata tsawa ko na rufeta da fada, abinda na sani idan ta farka ta ganni zata so tayar da rigima, gashi dole a yau za'a sakata dakin dumin cen da gyara ku kanku ba zaku kuma fitowa ba bale ita sai ana gobe daurin auren, ban san ta yaya zata amince da abubuwan nan ba, ga wajen aikinta, ga .................. Hannunta da datijuwar ciki ta rike ya saka Anmy sauke numfashi a maganarta tana ta lumshe idannuwanta domin sam bata so ta ga Najeebar a cikin wani yannayi na rashin jin dadi Cikin harshen larabci ta ce" kin san cewar wannan ranar mun ci alwashinta, muna jiranta ko? Kin fi kowa sannin mun shiryawa wannan ranar ko? Kukanta, ko ihunta, ko summarta ba zai hanna mu wanketa ciki da bai ba, domin kuwa shinfidar da zata taka mai daraja ce! Dole zata koyi rayuwa da yanda zata tafiar da sarkin mu! Mace na iya shanye wuyar nakuda, hawayen da zata zubar sune samun sasauci a zuciyarta! Maganar so kuwa Murmushi ta yi ta kai dubanta wajen Najeeba dake kwonce ta rungume fillow a jikinta gashinta ya warwatsu ko'ina, rigar aida ce a jikinta har yanzu sai shaf din pant da kafafuwanta masu tsananin hasken tafin kafa da wani shap a jikinsu ta maido dubanta kan Anmy ta kara sakin murmushi a hankali ta ce" lokaci zai nuna mana idan har ta isa ta kaucewa zuciyar *GURNANIN ZAKI* ..................salam alll........ [31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 35 Ajiyar zuciya Anmy ta kuma saukewa ta koma gefe tana kallon su Karasawa babar cikinsu ta yi ta saka hannunta a hankali ta yi bismillah Sauran du dukar da kawunnansu suka yi har sai da ta saka hannayen nata cike da kula ta talabo Najeeba Idannuwanta ta buda a hankali kafin ta ware su da sauri tana kallon matar A dan zabure ta so mikewa tana fitar da idannuwanta waje sannan muryarta da ta disashe dan kukan da ta sha ta ce" lafia? Menene? Wacece ke? Bata daina kokarin tayar da ita zaune ba kafin ta mika hannunta a miko mata alkyaba wata iri ta veloor kalar baki sidik Tana daga zaunen sai zaro ido take matar nan ta rufa mata shi a jikinta ta dora mata shi a saman kanta A hankali cike da nutsuwa cikin harshen larabci ta ce" a kowani hali shugaba ta farka daga baci ta kiyayi saurin buda bakinta ta yi magana ba tare da ta shiga bayi ha ta wanke bakinta, domin baban abinda zata aikata na bada hanyar da Uban gidanta zai ji zuciyarsa ta hautsine da tashin zuciya shine ya ji warin bakinta, shi kuwa baci idan aka tashi daga shi koda na minti talatin ne baki kan daukan wari marar dadi, irin warin nan na saka ciki ya rikice ko mutun ya yi gagawar kawar da kansa daga wajenka NAJEEBA ta kara zaro idannuwanta tana gannin wasu biyu sun zo sun hadu sun mikar da ita tsaye, cikin nutsuwa wace du ta fi su yarinta ta matso, sannan kana ganninta ka ga kakarfar mace Hannun Najeeba ta damka ta kamata ta cicibata suka kama suka dorata a bayanta Baki hangame Najeeba ke binsu da kallo ta ga an goyeta a baya luf ta aniya neman dirowa da ihu ihu ta ce" Anmy, Anmy meye wannan? Su waye wannan? Anmy ta matso da sauri tana son kamo hannunta tana fadin" Najeeba, ba wani abu bane zamu koma wancen bangaren ne kin ji? Ki nutsu kar su nutsar da ke Wannan kalma ta kar su nutsar da ita ya sakata yin wani irin sakalau tana bin kowa da kallo du a firgice Kara rufa wani zani mai kamshin gaske suka yi a saman kanta hakan ya saka ta daina gannin komai sai tafiar da ake yi da ita Kwata kwata aka fita daga bangaren Anmy aka yi bangaren da aka tanada domin gyrare gyaren Dakuna hudu ne a wajen, baban dakin nan suka shige da ita Mafarin barowar Najeeba daga cikin yan uwanta, mafarin shigarta sabuwar rayuwa mai cike da abubuwan ban mamaki, A wannan ranar tana ji tana ganni sai da aka tubeta zindir kafin a saka mata wata yar yololuwar riga baka kirin wace aka fara yi mata darzar fatar jikinta da ita Dakin wani irin dumi ne yake dauke da shi wanda da farko ta ringa zufa sosai sai daga baya zufar ta shanye a jikinta a lokacin da suka yi mata wata irin darzar da ta kusan fitar da ita daga hayacinta Sosai suka bi lungu lungu na jikinta suka darji fatar Najeeba da wasu irin abubuwa dake dame masu fitar da kanshi abin nan basu barshi iya fatar jikinta ba har fatar kanta sai da suka darza Da ruwa mai dumin gaske mai hade da ruwan turaren nan mai mugun tsada wato sandal FLEUR aka darwaye jikinta tas Sabon broch da maclean aka bata ta wanke bakinta sai kakare kirjinta take da kuma kasanta tana biye da su da wani kallon mamaki irin yanda du yanda take neman botsarewa sai su tarota idan ta so nuna karfi sai a barta da wannan matashiyar ta maida ita zaune Alwallah ta dauro suka fito Rigar sallar da aka ware aka miko mata ta kabarta sallah cikin nutsuwa ta gabatar Ta jima kanta a kasa tana hawaye, tama rasa me zata ce? Ta ina zata fara, abinda ta fi fada shine Allah kar ka bari su min auren nan dan kasheni zai yi Tana dagowa ta yi tahiya kanta sade ta ja carbinta ta gama Sai da ta gama sannan aka mikar da ita Rigar tata suka kama mata ta cire hakan ya saka ta tsare su da kallo ranta a yannayin bace ta ce" wai zir zan yi ta zama ne ko me? Datijuwar nan ce ta girgiza kanta tana kallonta cikin ido ta ce" idan mace zata yi magana, ya kasance ta ragewa idannuwanta tsauri da yawa, irin ta sada su kadan ita bata rufe su ba ita bata bude su sosai ba Idan maganar fada ce zata yi ya kasance ta sada idannuwan sosai idan ta faro a sanyaye sai ta bude su baki dayansu, bafa daga murya zata yi ba, aa, idannuwan nata ne zasu nuna yannayin da take son isar da sakonta Hannunta ta saka ta ja Najeeba ta zaunar da ita bakin bed mai dauke da zani mai duhu Wasu oil ne dake hannunta ta raba zamanta ta shiga tsaga gashin kanta a hankali tana dan shashafa mata shi ta ce" idan kuwa zata yi tambaya ne, ya kasance da kwayar idannuwanta zata dasa question mark din, wato ta yi yawo da su ta dasa su ta hanyar kai kwayar idannuwan nata kasa Manyan kitso ne ta fara yi mata irin da ake kira zane kwaya hudu ne ta yi niyar yi mata dan haka ta ringa yin kitson a hankali tana lalumata tana tufke har karshen gashinta A sanyaye ta ce" bale ke din daga yanzu kin zama uwar talakawa, nauyi mai girma ne ya hau kanki wanda yake a wuyan mijinki, zai kasance ke ce mai tarbarsa a du halin da ya shigo maki Shugaba kan daukan abubuwa, yana shanye duka a waje, yana shanye du wani tashin hankalin talakawansa, Daga bakin da ya shigo wajenki, sai ki ga ya gaza, a gabanki ne zai iya fitar da bacin ran da ya shaka, a gabanki ne zai iya fitar da tarin yannayi na tausayi, tsoro, ko firgicin da yake hange a tatare da talakawansa wanda hakan zai taba shi sosai, harma ya nuna maki hakin da zuciyarsa take ciki Ke kuwa *Kece mai shanye damuwarsa*, zaki mayar da shi a gabanki tamkar yaron dake da kiwya kike son ke kuwa sai ya saba da ke, hakan kuwa zai faro daga yannayin idannuwanki Zaki kasance idannuwanki dauke da haske da kwali, zaki kasance mai sada dubanki a gaban kowa bale a gabansa, zaki kasance mai lumshe idannuwanki a gabansa Dan saurarawa ta yi tana tsaga na karshe ta ce" sai movement din hannayenki da jikin ki baki daya Zaki kiyaye irin motsinki a gabansa, ba daga ya nuna maki bacin rai ba zaki tarbi magana da" wa ya isa? Aka yi haka? Ina ba'a isa ba? Ta hanyar maganarki zaki daukaka muryarki har ki ji maganarki ta girmi tasa, Daga bakin lokacin da muryarki ta girmi tasa zaki ga ya yi lakwas yana jin zuciyarsa na kara ruruwa yana son kara daukan abin da zafi Ke din nan, ke ya dace ki sanyaya muryarki ki sada kanki da dubanki Muryarki ta kara sanyi, ki nuna kin fi shi shiga damuwar da ya shigo maki da ita, a hankali ki nuna masa kowani tsanani yana tare da sauki kafin ki nuna masa cewar idan har yana fadarki, farin ciki mai dorewa shine abinda zai wanzu a tatare da shi Dago kanta ta yi ta kalli matar, sosai take jin abubuwan da take fada tana kuma anfani da su, idan ta nuna a wanda zata aikatawa ne sai ta yi murmushi karara ta dan girgiza kanta Za dai ta anfanarwa HUZAIFA, domin ta tabata Allah zai amshi adu'o'inta Kanta ta mayar ta sada matar ta karasa kitse mata gashin kanta tas sannan ta bi shi da wani man mai dadin kamshi Mikar da ita ta yi da rigar nan ta jikinta sannan ta kwontar da ita saman bed din Ji take gajiya sosai na damunta sakamakon irin darzar da aka mata, abu da rashin sabo Wani hadi ne ta nufota da shi wato APKI da MAN KADANYA cakude da wasu graine kannanu maroon Hannayenta ta kama ta tayar da ita zaune Cikin nutsuwa ta ce" cire rigar Ido Najeeba ta kura mata da mamaki, bata yi magana ba aman yannayinta ya nuna kwari ba zata iya kallo ana ci gaba da wani yi mata zirr ba Zama matar ta yi da abin a hannunta ta ce" kin san shekarana nawa? Shekarana sitin da biyar a duniya Da mamaki Najeeba ta zaro ido tana kallonta, sam bata yi kama da wace take da wadinnan shekarun ba Matar ta ce" wannan din, shine aikina, sannan ban taba yiwa koda yar sarki bane sai matar sarki, matar sarkin ma, sai wace Allah ya yi, Dan sasautawa ta yi ta ce" SUNNA NA PRINCESSS FADIMATU MUHAMAD, nice yar farko a wajen sarki MUHAMMAD, Na yi awani a jirgi dan zuwa nan dan mutuncin Mahaifiyarki da kanwar Abihnki Bani da jiyar juyawa sai na gama abinda ya kawo ni Kuma lumshe idannuwanta ta yi kafin ta dan buda idannuwanta da yannayin gargadi wanda sam a muryarta babu aman idannuwanta sun nuna ta ce" zaki cire rigar ko na cire maki? Hannayenta ta saka tana jan rigar cike da mamaki, a hankali ta bada hankalinta kan macen ta ringa gannin yanda take du wani motsinta, Wannan hadin ta kawo wajen mamanta ta shafa mata a yan mamanta da basu da girma sosai ya kasance ta shafa masu sosai sannan aka kawo wata bra wace ana iya rageta ko a karata aka daure mata su dam Sakata ta yi ta yi ruf da ciki sannan ta ringa shafa mata shi a wajen duwawunta masu fadi da girma, duda haka ta kara mata domin shi anfaninsa dama shine ya kara cika waje, shi yasa aka shafa shi a mamanta dan ya jara girma sai kuma duwawunta Wani pant aka bata ta saka sannan aka cenza mata wajen kwoncin Dayar matar ce ta shigo da wani man mai tsarara ta shiga shafa mata shi a jikinta baki daya tana masaging din jikinta a hankali a hankali har kafafuwanta da tafin hannayenta ko'ina cikin nutsuwa da kula Sai da ta gama lumdeta sannan aka kuma tayar da ita aka rufa mata wani abin rufa aka saka wani mahaukacin turaran wuta mai wani irin sanyayan kamshi ya shiga ratsata domin a saman wata kujera ce mai hudoji direct ya ringa ratsa jikinta yana hawa ko'ina na jikinta yana kamawa sosai da sosai har ya gama sannan aka ciro wata wata riga fara kar aka bata ta saka mai dan tsayi kafin a bata safar kafa da ta hannu duka ta saka sai hula aka rufe mata kanta da ita mai dan gashishika mai laushin gaske Anmy ce ta shigo tare da dayar matar wace ita kuwa aikinta shine hade haden tsumi kala davan daban Tunn da ta ga Anmy sai ta ringa binta da kallo Anmy kuwa tana kiyaye abinda zai saka su kadaice har sai da ta amshi abinda matar ta daho tantabaru ne da wani sirri ta dawo kusa da ita ta zauna Budewa ta yi ta saka hannunta ta ringa bismillah tana ciyar da ita tana kiyaye bata da kasusuwa har ta cinye sannan ta saka cokali tana bata romon nan a hankali har ta shanye shi Wata madara mai dan dumi ce Anky ta miko mata cike da bol mai dauke da sinadarai ta bata ta shanye Sai da ta shanye tas ta mika mata Mikawa matar ta yi ta juya ta koma domin rubutu ne take a allo tana rubuta yusufa da kanta dan hadin kankanar da zata yiwa Najeeba Anmy zama ta yi a kusa da ita ta kamo hannayenta tana gannin yanda fatar Najeebar har ta wani irin daukan harama ga abin man nan ya saka hannayenta sunna santsi Idannuwanta ta lumshe a sanyaye ta ce" Najeeba, zaki yi hakuri da abinda Allah ya hukunta? Najeeba ta ringa kallon fuskar Anmy hakan ya saka Anmy jin wani iri, so take ta san me take tunani a zuciyarta, kar ta dauketa mai son kanta da yawa Matar nan ce ta dawo ta ja abin zama ta zauna tana kallonsu Murmushi ta yi ta nuna anmy da hannunta ta ce" ki rungumeta a jikin ki, ki fada mata dadadan kalamai Ta kai dubanta wajen Najeeba ta sakar mata murmushi ta ce" kunya, da tsananin soyaya su rinjayi rigimarki a irin wannan lokacin Anmy a hankali ta rungume Najeeba a jikinta tana dan taping din bayanta ta furta" i love u Najeebana, kin san me? Mamanki na hanya yau ko gobe zata zo Najeeba ta rintse idannuwanta wasu hawaye masu dumin gaske suka zubo mata, mamanta? Zata zo? Ta zo ta yi me? Rabonta da Niger shekarun da dama, ahine yanzu zata zo ta mata me? Bata dai ce komai ba har Anmy ta gama ta shinfideta da kanta sannan ta mike ta fita Wani baci ne kai nauyin gaske ya dauketa na gajiya da kuma rudani Bacin bata yi mafarkai a cikinsa ba, hasalima kamar wace ta mutu bacin kawai take du jikinta a gajiye ....... Haka ya kasance a wuni za'a yi mata irin gyaran nan sau biyu, da dare kuwa za'a ringa koya mata yannayin magana da kuma yannayin cin abinci, da komai da komai wanda a gannin Najeeba kallonsu kawai take bata san cewa tana daukan yannayinsu ba domin su sun ga sosai tana daukan darusan su duda ba amsa take basu ba Bayan kwana hudu mahaifiyarta ta zo, sai dai tun da ta zo ko da wasa idannuwansu basu hadu ba domin kuwa idan ta shigo dakin Najeeba koda a zaune take zata lumshe idannuwanta ne, ita kuwa zata tsaya ta yi murmushi daga nesa kafin ta juya Tana azabtuwa da yannayin yarinyar nata Sai dai bata da wani iko na tirsasata, Ta samu DAYABU ta roki idan an fitar da ita ya rokar mata sasauci, Abih kuwa sam baya son abinda zai hada shi da ita domin matar tana da tasiri a rayuwarsa, zata haye masa ne a lokacin da bai shirya ba Yau sauran kwana uku daurin aure A yau da sasafe ya saka aka kira masa Zinaria Sai da ya gabatar mata da tarin abubuwan arziki irin na fitar kishiya kafin cikin nutsuwa ya bata hakuri dan gannin ya samu bata yi irin na wancen karon ba sannan ya shaida mata cewar zai daura aure da mace biyu nan da kwana uku Wani abin aka ce ya girmi hawaye, sai kawai ta ji zuciyarta ta dauki wani irin suka da zafin da ta yi gagawar dukewa Hannunta na dama ta dora daidai wajen ta damka sai kawai ta tafi numfashinta ya dauke Sosai ya shiga wani yannayi na ganninta a haka, meye wai a su kishiya? Meye dan zai yi aure sai ta ringa fmhayacinta? Ta san bata so ya yi aure aman sam bata iya bashi kulawar da yake da bukata? Subahannalah, subahannalah shine abinda ya ringa furtawa a kasan zuciyarsa Sai da ya kira docter ta dubata ta bata taimakon gagawa kafin take dawowa hayacinta Wannan karon kam ta kasa dane kukanta da ihunta, sosai take kuka ta rikice masa tana neman a hayacinta ta zauna jikinta du yana bari ta ce" me na rasa? Me na gaza? Mutuncina, darajata zasu zube ne a kasata, me ya sa kake son sai ka zubar da dukan wani tinkaho namu a duniya? Mahaifiyata ka ja gaban yiwa kishiya, yanzu zaka kara yi min du a cikin shekara daya? Kishiyarma ba daya ba har biyu? Ba zan iya lamunce raba mulkin garin nan da wata ba, ba zan iya lamunce tunaninka da wata ba Sai kawai ta sauka da gudu ta fita ta yi bangarenta tana jin kamar zata mutu dan bakin ciki Wayarta da ta kashe ta kunna hannunta na bari ta shiga neman layin mahaifiyarta Tana dagawa muryarta a hade ta shiga koro mata bayani Mikewa tsaye mamanta ta yi daga zaunen da take har tana gannin wata innuwa innuwa na son rufe idannuwanta Me ya shirya yiwa rayuwarta ne da ta y'ayanta? Tana nan tana fadi tashin yanda zata kawar da maganar auren danta daya kwal namiji da wannan bakar yarinyar, da kuma yanda zata yi da yarinyar da rabinta da ta ganta tun shara'ar da aka yi masu da Yarima domin ganninta ya zama aiki a gidan baki daya, sam bata zuwa gaisheta bake ta samu ta wannan hanyar ta gama da ita shine zancen za'a yiwa Zinaria kishiyoyi har biyu ya fado? Kashe wayar ta yi ta nufi dakinta da wani irin sauri a bayane ta furta" *ka ci nasara a mu ta hanyar shigar da wasu cikinmu, sai dai baka isa ka sako mana wasun ba ta bangarenka, ko wadinnan din zan fitar da su ne ko ta wani hali!.............. Ta wuni cikin tashin hankalin da ko abinci bata ci, Yayarta ce ta zo ta tare a wajenta suka shige daka sunna tsare tsaren yanda zasu fitowa lamarin ........................................... Bayan salar Isha yana zaune da jarida a hannunsa Amintacensa ya shigo masa da wata ambulope Dukawa ya yi ya bashi sannan ya fita daga dakin ya koma wajen da ya rasa me suke yiwa yarinyar nan a ciki, hasalima bai san wajen na meye ba bayan kuma a cikin gidan yake ba wanda zai ce ga abinda ake yi a wajen Sai da ya gama komai sannan ya buda ambulope din nan mai girma Hotunna ne birjik, hade da takardar haihuwa, da adress complet Hoton yarinyar ya kurawa ido, masha Allah Nadia akoy cikar mama sosai domin ko a hoton ana ganewa Ajiye hoton ya yi gefe ya dauki takardar da aka yi bayani a ciki Tabas kawarta ce, kawarta kuma ta yarinta domin tun makarantar secondary suke tare Murmushi ya yi ya ninke komai ya mayar kafin ya dauki wayarsa Mesage din da ta bara masa sun fi karfin irgensa dan haka ya goge su baki daya kafin ya yi shiru da wayar a hannunsa Irin yanda take zumudi da kayan da aka kai na aurenta du ta yada maganar duniya wanda sam bai so haka ba, sosai an dauka cewar itane matar da zai aura uwa uba irin yanda take neman aminiyarta ido rufe dan ta shaida mata wannan dadadan labarin sai dai kash ta rana ina *NAJEEBA* ta shiga Sai da dare ya raba sosai sannan amintace ya yi satar hanya ya fice Bai zame ko'ina ba sai fadar da HUZAIFA ke zama Yana zuwa ya yi masu salama kafin ya nemi ganninsa Mikewa ya yi suka yi nesa da mutane sosai Wata yar karamar wuka ya shafa masa a gefen cikinsa cikin kakausar murya ya ce" ina wayarta? Wayar zata bani, ka kiyaye idan ka yi wani yinkuri na rantse zan huhuda hanjin cikinka na yanke harskenka har sai ka ringa rokon mutuwa ta daukeka! Kasancewar du inda zai je da wayar yake yawo yana kirta iskanci da ita har ya yi saken da Sultan ya saka aka yi tracenshi aka san wajen zamansa da komai bisa tirsasawar Anmy ya saka a amso wayar a hannun Huzaifan Jikinsa na bari ya ciro wayar ya bashi Kafin ya ankara ya masa wani bugu a keyarsa hakan ya saka ya tafi kasa summe sannan shi kuwa ya juya ya hau babur din da ya yi bada sau yana tuki yana sin fahimtar abinda ke faruwa, Kwata kwata Sultan yana nisanta kansa da shi domin shi kansa yanzu bai san shigarsa ko fitarsa ba, abinda ya sanni shine wani abin na faruwa wanda sarki yake boye masa Bukatarsa ta gaba shine sannin meye? Sai al'amuran auren nan, sam bai san yaya za'a tafiar da komai ba! Abinda ya dace ya sani dan sannin abinda zai yi! Yau ta kama sauran kwana daya jal daurin aure, wato gobe za'a daura auren Cikin nutsuwa ake takawa da ita ita kanta bata san inda za'a kaita ba A rurufe komai sannan ba waje aka nufa da ita ba ta wani lungu ake ta tafia mai nisa da ita har aka isa inda za'a kaita Sanyin safia ne, su hudun nan ne suka sakota tsakiya hakan ya saka kanta ke kasa suke jan hannunta a cikin wata irin tafia tamkar yar yaye Sosai a yau da ta kalli madubi ta firgita da irin cenjin da ta ganni a jikinta tun daga fatar jikinta, gashin kanta, mamanta, duwawunta, kamshin jikinta kai harta da laushi santsin jikinta sai da suka bata mamaki mai tsananin gaske Ta tabata a yanzu suturunta ba zasu shigeta ba ta wajen duwawunta da kuma mamanta domin sun kara cika ne sosai mamanta har ya yi girman da zai kai girman mangwaro mai dan girma kasanta kuwa tabas ta fi Niki minaj Shigar da akai mata doguwar riga ce ta lesh wace aka yi wani irin dinki mai jan kasa daga baya sannan aka dora mata wata irin alkyaba mai ruwan ashh kala mai haske ta fi lesh din haske domin shi lesh din duhu ne da shi Wani irin dadadan sanyi ne ya ratsa fatar jikinta da wani irin nutsatsen kamshi Idannuwanta ta lumshe dan rabonta da ta ji sanyi haka na ratsa jikinta tun satotan da suka yi Ji ta yi sun kamata sun gurfanar da ita zaune kasa sannan datijuwar nan ta karaso gabanta ta kama hannunta na dama ta kara durkusar da ita ta fitar da hannun mai dauke da wani irin kunshi mai shegen kyau a sanyaye ta furta" *ALLAH YA JA DA RANKA, MUN ZO NE NEMAN ALBARKAR AURE, ALLAH YA TAIMAKE KA* wani irin tsintsinkewa gabanta ya yi ya dagargaje ya fadi hakan ya sa ta fago kanta da sauri dan tabatarwa kanta wani ranka ya dade din ne? Lokaci daya ta mayar da kanta ta sada sakamakon ido hudu da suka yi da shi, idannuwan nan nasa sam ba alamun hutu domin har yanzu a rikide suke da fitintinnun da Zinaria ke gabatarwa na tayar da hankalinta da ta yi, ga abubuwan dake kansa, ga tunanin auren nan kamar da wasa Idannuwansa ya lumshe yana jin kamshin da suka zo da shi, wacece mai kamshin nan a cikin su? Kuma buda idannuwansa ya yi yana kallonsu du kawunnansu a kasa a gabansa, su dukansu jinnin sarauta ne yaushe suka zo? Me suka zo yi? Sai da ya furzar da huci sannan a sanyaye ya buda bakinsa yana kallon Fadimatu A hankali ya daga yatsunsa biyu ya yi nuni da wata ambulop yar karama fara karrr sannan ya lumshe idannuwansa ya dan jimke hannun nasa ya dan jinjina mata Mikewa ta yi ta dauko ta duka ta ringa godiya da abin arziki duda basu buda sun ga meye a ciki ba, wannan shine kyautar da zai mata kafin aure bayan akwatunnanta da sauransu Sai da ta kara tabata sannan Najeeba ta buda bakinta da take ji ya mata nauyi a sanyaye ta furta" *AN GODE* da sauri suka kalleta jin AN Gode din da ta ce tamkar wace take magana da wani sa'anta bayan a hardace suka koya mata irin gidiyar da ta dace ta ringa yi masa a gaban mutane Ta buda bakinta zata yi magana ya daga mata hannu hakan ya saka ta sada kanta ta ringa neman afuwa Da yan yatsunsa ya nuna su tafi Du mikewa suka yi basu kamata ba, domin kuwa iya su ya yi nuni da su fita Tana jin alamun sun tafi ya saka ta dago da sauri dan gannin abinda ke faruwa A yanzun kam ba iya zuciyarta kadai bace ta fadi harta da ita kanta sai da ta ji zata zube a wajen kafin ta yi gagawar mikewa tsaye nufinta ta juya ta tafi, sai dai ta tsinkayo muryarsa kamar ba shi ba a hankali ya furta" zo Jikinta ne ya kara daukan bari Ta juyo tana kallonsa A zaunen da yake bai motsa ba sai dai irin kallon da yake mata ya isa ya halakata da tashin hankali Kafafuwanta ta ringa jin sunna kaita wajen da ta tabata zai summar da ita idan ta idasa Tana zuwa ta zube kasa hakan ya saka dubansa sadawa wajen da take tsugune Kallo ya kare mata, shi kadai ya san irin hukunce hukuncen da zai mata a rayuwa Bai ce komai ba sai da ya gama yi mata kakausan kallon da ya sakata jin zata fashe da kuka kafin a hankali ya furta " *TAFI* ai kamar jira take ta mike da sauri ta fita , tana fita ashe sunna jiranta suka kuma daukan hanya suka koma Ambulope din suka mikawa Anmy da Ummu dake zaune kafin ta shiga tube mata shigar nan tana mai yi mata maganar shin yaya aka yi ta furta iya kalmar nan a gabansa? Anmy ta saki murmushi a lokacin da ta gaakudan kudaden da aka rubuta a kan chek, da kyautar gida da kuma kyautar zinarin da aka fadi irin kirar kafin ta mikawa Ummu Murmushi itama ummu ta yi kafin ta mayarwa Anmy domin sam bata rike komai Na Najeebar dan ba zai yiwu ta diro kai tsaye a yanzu ta nuna itace uwar Najeeba ba Ita dai Najeeba shigewa ta yi ko tsayawa bata yi ta ga abinda suke mamaki da murnarsa ba, alwallah ta kara daurowa ta zo ta shiga sallah, kuka take har kanta da jikinta suka dume da wani irin zafi da ciwo, fadawa Allah take aa ita bata so kar a daura ........... (HOUM) *BABAR RANA* Ranar da zata haukata zukata da dama, ranar da yan jarida zasu samu abin yadawa, ranar da zukatan maza da dama zasu ji wani iri da madaukakin tashin hankalin jin inda ta fada Lale da yawa zasu ji inama, da yawa zasu ce dama ai yannayinta sai manyan ciki kuwa harda ambasador da soja da likitocinta uwa uba HUZAIFA, Ranar da labari zai hadu a waje uku, tun daga bangaren ZINARIA, NADIA, DA KUMA NAJEEBA, Jin labarin daga sama zai gigita da yawa, .........ku biyoni yar mutan niger Idan comment ya cikan gida zan yi na gobe, idan bai cikan ba sai nace Allah ya sada mu da alkhairi i.a *Masha Allah* [31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 36 A yau ta kasance ranar asabar ce, Garin damagaram bai taba daukan harama irin na yau ba Samari da yan mata, datijai da tsofafi, kar harta yara kanana idan suka samu hanyar fita sun fece zuwa baban filin da ake babar tadar wasan kaho An shirya wasan kaho da sukuwa takanas saboda auren nan An yada maganar daurin auren nan ne a gidan redio da TV cewar Sarki zai kara auren yan matala tsala tsala kwaya biyu duda yan matan ba'a fadi ko su waye ba, sai dai maman NADIA da Nadia du sun baza cewar itace dayar, su kansu sun kasa kunne su ji wacece dayar Gaya kuwa ba sai an gayata ba, domin wajen ya samu halartar manyan baki na mamaki gidan sarki kara cika yake tun a jiya har zuwa yau cikin bakin kuwa harda su *MAI MARTABA SARKIN AGADEZ, DA MATANSA BAKI DAYA, DA YARONSA YARIMA* Tun da suka zo, GIMBIYA mahaifiyar ZINARIA ta tare a bangarenta suka kile tare da sauran y'ayanta mata suka shiga hada hadar sa ji sa ganni sai dannar Zinaria suke wace take neman ficewa a hayacinta maimaitawa take ba zata iya raba mijinta da sarautar nan da wata halita ba Yayarta guda kuwa ta fita cikin mutane dan ta samo rahoton dayar kuwa yar gidan waye? Domin tuni Nadia ta tona kanta ita da uwarta wa'inda basu san tana cikin amaren da za'a kawo gidan sarauta ba daidaiku ne domin ta karbi abin da hannu bibiyu, bata taba tunanin ita Nadia zata tare a matsayin amaryar mai martaba, ita zata ga fuskar mai martaba, takan yi daria ta furta" Najee, ina kika shige, yau daukaka ta tardoni a gida ni zan zama matar abokin gabarki, kar ki damu kawata zan shirya ku! Bangaren Anmy hankalinta ya so rabuwa biyu, sai dai mahaifiyar Najeeba ta kaleta ido cikin ido ta ce" idan har kika yarda shiriritar yarki ta saka maki damuwa to fa ta samu nasara a kanki, ki gane tana kara langwabewa du idan kin shigo ne, ki zo ki kula da baki ki barta ta gama shan karin ruwan, idan lokacin fitar da ita ya yi za'a fitar da ita koda a sume ne a jinginar da ita, ban taba gannin bataciyar ya irin yarku ba! Kun wani rikice dan tana abu nan Abihnta har ni yake fadawa magana wai ina ruwana da ita, han Murmushi kawai Anmy ta yi, domin a lokacin da aka basu damar su shiga su duka su kara ganninta a jiya ne suka yi kicibis da Ummu, du daburcewa Abih ya yi sai neme nemen kys din mota yake a aljihun rigarsa har sai da Dayabu ya yi murmushi ya kama hannunsa ya ja shi, har ya gifta ta ya juyo ya ja tsaki kamar wani yaro ya ce" an ji kunya, me kuma ya maido ki nan? Ki koma mana wajen neman kudinki, ki barmin y'ata babu ruwanki da ita *FADA* ta rikice, ta hautsine wajen ya dinke da jama'a, dogarai ne sun sha rawani daidai misali du sun bazu sunna bada wani irin tsaro sai sojojin da suka barbazu suma sunna bayar da tsaron Tsaye yake a cen sama ta wajen window dinsa mai duhu wanda shi yana iya gannin na waje aman daga waje ba zaka iya hango shi ba Bashi da riga a jikinsa, ya gama moysa jikinsa ne da wani dan tawul karami yana goge zufar jikinsa yana kallon du wasu shagulgulan dake kai kawo a cikin fadar Hannayensa masu taurin gaske ya daga ya dan dora a jikin garun ya kara kurawa wajen ido Tabas ya jima rabonsa da ya ga taro haka, ya tabata Anmy ta bada babar gudunmuwa dan tana aurar da y'a Murmushi ya yi yana girgiza kansa ya juya cike da kadaita ya nufi bayi da kansa Ya jima ciki yana wanka da dukan uzurinsa kafin ya fito Agogo ya kaiwa duba, nan da awa daya da rabi za'a gabatar da daurin auren dan haka sai ya zarce wajen tarin kayansa ya buda ya tsaya yana kallo Saka sababin kaya ba yau ya fara ba, sannan ba sai ana wani abin yake sakawa ba, sai dai na yau din a sabinma bugagu ne wa'inda suka amsa kiransu Da hannunsa ya ciro su da sabon rawaninsu hade ya ciro duka ya ajiye gefen gadonsa Zama ya yi ya dauki karamar wayarsa ya danna kira Tana fara ringin aka daga ana mai aiko da salama da neman fara kirari Da sauri ya furta" yi shiru, abinda nake so da ke ki saka a yiwa yan mata kamar goma kwaliya ya kasance an laya su a matsayin amaren nan da ake yi, ina so ku ringa gardamar ba zaku bayar da amarya ba, Ina so ki saka mata simple shiri ki bata hijab da nikaf ta fara fita ta tsaya ki a cikin kwanar gidanku kafin ki sandi mutane ki fito Akoy dan sahun da zai dauko ku ya kawo ku Idan kun zo yau gidan ba'a hanna shiga ko fita, zaku samu hanyar shigowa Idan kun shigo zan wakilta macen da zata sada ku da bangarenta sai ku gabatar da abinda zaku yi Dan shiru ya yi yana sauke ajiyar zuciya kafin ya dago yar yatsarsa guda ya ce" ku kiyaye, rayuwarta ko nace rayuwarku baki daya ke cikin hadari, idan har kuka kuma falasa wani abin ko me ya biyo baya ku kuka da kanku Yana gama fada ya datse kiran sannan ya dan dane lebensa na kasa Kuma mikewa ya yi da tawul din dake jikinsa ya nufi wajen window din Abubuwa da dama sun shiga idannuwansa, irin yanda ake waje waje ana kuskus daga inda yake ba zai fahimci komai ba sannan a yau ba zai fitar da droon ba har sai an fara hawa dokunna domin a yanzun ana cen ana hawan kaho ne ana ta zubda maza Suturarsa ya ringa sakawa cikin adu'a da iya daukan wanka Sai da ya saka abinda zai kara rufa asirinsa duda wandon shadar ba karami bane aman gwara a kara daurewa dan kar a ji kunya A lokacin da ya dora babar rigar shi da kansa sai da ya tofawa kansa walahaula wala kuwata ila bilah domin dinkin ya dauke shi ya amshe shi sosai haka kuma kalar ta karbe shi sosai Sai da ya saka farin yadi mai haske a fuskarsa mai shara shara kafin ya yiwa masu jiransa umarnin shigiwa dan gabatar da nadin rawanin da suka takanas dominsa Su biyu ne, kwararu ne, aikinsu ne, nadin za'a hauda shi daidai yanda zai bada kalar tsuntsun da aka yi dinkin irin kalarsa wato Dawisu mai hasken fari kar kar kar sai dan kalar blue mai haske jefi jefi Sosai suka gabatar da aikin nadin da ya dauki lokaci kusan minti talatin kafin su saka masa safa fara kar su saka masa takalmi kafa ciki shima farin ne kar kar mai kyan gaske domin fata ce akaiwa adon fari tas tas Dawisu ya gama bayana a lokacin da suka miko masa sandar sarautarsa, Sandar baka ce mai adon zeba daga sama Sandar wata irin sanda ce mai shegen kyau ga tsada Rike sandar da ya yi a hannunsa na dama a lokacin da ya mike tsaye ya kara masa wani irin cika da girma Baki daya ya haske wajen har ya kasance su da kansu suka shiga kirarin dole domin kuwa wani yabon zaka yi shi ne a lokacin da kai kanka baka sani ba Irin yanda karamar wayar da zai rike ta sha masa kai da ringin ya saka shi dubawa Idannuwansa ya lumshe, bai san yaya aka yi suka cika takura ba , auntyn Nadia ce wace take kanwar mamanta uwa daya uba daya, da kansa ya amshi numberta bisa kwakwaran gargadin kar ta yarda wasu su san yana magana da ita sai Nadiar sai mamanta Dagawa ya yi ya kara a kunnensa bai yi magana ba Sai da ta kara sada kanta sosai sannan ta yi tambayar zuwa wani lokaci ne? Idannuwansa ya daga ya kai wajen agogo, daurin auren a yanzu bai fi saura minti goma na, dan haka sai ya sada idannuwan nasa a hankali ya ce" bayan awa biyu da komawar *GUDGE MOCTAR* Amsawa ta yi ya kashe wayarsa Dubanta ta maida wajen yayarta da suka yi tsuru tsuru ita da Nadia sunna jiran amsar Amsa ta basu dan haka suka shiga neman nikaf da bakin hijab domin kaf a cikin gidan babu ba mai sakawa! Cike da kasaita ya ringa tafia Yana fitowa dogaran dake laye a cikin katon falonsa suka kwashi wani irin kirari mai saka tsigar jiki tashi Busa ce ta karade wajen irin ta sarakai hakan ya saka shi lumshe idannuwansa kafin ya bude ya sauke dubansa kan sarakai hudu da suka halarci taron da manya manyan mutanen da suka zo dan taya shi zaman wannan ranar Da kansa da kuma idannuwansa ya yi anfani wajen gaisar da kowa ta hanyar dan sada kansa da kuma idannuwansa sai baban dogarin dake isar da sakonsa ya isar yana jinjina da hannayensa, sauran kuwa sai su kwashi kawo gaisuwa sunna fadin Sarkin garin maradi ya amsa gaisuwar *MAI WUKAR YANKA*, yana yiwa *GURNANIN ZAKI* fatan alkhairi A haka dai har suka kara cinye wasu lokutan masu mahinmanci kafin a fita baki daya a bijiman dawakan dake dauke kwaliya ta mamaki da wata bazara a gefe dogarai majiya karfi suna ririke da ita Sai da ya taka hannun Amintacensa kafin ya dora kafarsa daya a abin dokin sannan ya hau da kyau indo dogarai suka kare hawan nasa Sai da ya zauna ya rike sorsin dokin sannan da kafarsa ya dan daki gefe da gefen dokin a hankali, nan fa dokin ya shiga wata tafiar kasaita domin yanda yake tafe fari kar da shi ga irin yanda yake daga wutsiyarsa mai dauke da yalwatacen gashi itama tana sama tana yawo irin ya koshin nan ya gaji da koshi kamar ya fashe tafiarsa ta koma ta kasaita Haka aka layu anna ta rangada buda ga busa ga yan rakiya har suka fice daga fadar wada ba wanda bai fito gannin kwaliyar sarki da fitar sarki ba Yayar Zinaria ta juyo tana gyada kanta ta ce" a gaskiya, da kamar wuya SULTAN SHAHEED ya iya zama da mace daya, koda bai je nema ba za'a zo neman alfarmar aurensa Zinaria, ki duba ki ga yanda baki daya ya haske wajen cen, da ace nice ke, zan yi kwaliya irin tasa na bashi goyon bayan da zai saka ko wa ya karo sai dai ta biyo bayana! To ke Zinaria yaya kike tunanin mutun har haka ya zauna da ke daya? Kin yarda da kanki har haka ne? Wace irin kula kike bashi wace zata saka shi haka? Kar ki manta Aba da Abihnsa suka maku auren hadi, kar ki manta a zamanin nan mutun ko dan rufin asiri yake da shi shikenan ya kama hange hange bare wannan? Zinaria mijinki sarki ne, kuma mai kudi ne....yaya zaki kasa yiwa kanki adalci ki ringa summa dan zai yi aure? Mahaifiyarsu ce ta daka mata wata irin tsawa ta hanyar fadin" kilishi anya kuwa ke jinni na ce? Baki san mulkinsa da dukiyarsan ne ya saka lale lale zamu tanadesu dan kanmu da y'ayanmu ba? Baban bakin cikina ace har yanzu babu wani abu da take da shi da zan iya fara dora rai a kansa, kilishi, ko ki min shiru, ko na hautsina kwonciyar hankalinki sakarai ke da kika ne kike yiwa kishiya bauta ai ke kika gani! Shiru ta yi ta koma ta zauna domin ba zata furta wani abin ba kuma cibi ya zama kari, gani take da wannan zaman da suke sunna sake sake da kiraye kiraye da tsare tsare, da mikewa suka yi suka saka akai mata shiri irin na wanda ake yi, suka tarbi amaren nan da kansu da sai sun fi girgiza mutane, aman sun tare a nan sun hadu sunna ta abu kamar wasu jahilai Ita kam gaskiya ko yanzu zata mike ne ta je wajen kiahiyarta domin tare suka zo da mijinsu sarkin tsatsunburun ne su shirya a tarbi amare da su, ita kam Alhamdulilah tana zaune da kishiyarta lafia, ita ta je ta sameta a gidanta da y'ayanta , matar tana da hali na datako hakan ya saka cikin nutsuwa suka hada kawunnansu suke zaune kalau, ko irin asiran da Gimbiya ke bata ta zuba a abinci dan ta raba su ita kam bata taba anfani da shi ba, tana amsa dan su zauna kalau da mahaifiyarta aman ko nisa bata yi take zubarwa ya bi iska domin ita dai bata dauki duniyar da zafi ba, kuma iliminta ya fi gaban wannan gaskiya, ta gane cewar idan ba kanka ka sauke, ka nemi zaman lafia da kowa ba to da dan da ka haifa ma sai dai ya bika dan dole! Ana gama salar azahar aka gabatar da daurin aure Auren da aka fara daurawa shine auren da ya saka zukata da yawa zabura da jin tamkar an dika masu guduma a kansu A lokacin da aka furta kalmar sunnan nan wato *NAJEEBA MUTALAB* sosai zukata suka rikice, da yawa kuwa suka hangame baki cike da mamaki HUZAIFA bai iya tsayawa ya ji sauran daurin auren ba ya fita daga cikin tanfatsetsen masalacin yana jin tamkar numfashinsa zai bar gangar jikinsa Kuka ya fashe da shi a cikin abokansa yana son sai sun barshi ya doka kansa da madubin motarsa Yana kukan yake fadin" ta cuce ni, ashe dama bata so na? Ashe dama mai gida zata aura shine ta yaudare ni? Dama ashe aurenta za'a daura na dinka sabuwar shada na zo ni ga sirikin sarki? Dama ashe aurenta za'a daura na zo nan? Nadiama ta cuce ni, ashe ta san haka ne ta barni nake ta fama da soyayar Najeeba a zuciyata? Hannun abokinsa latif ya rike ya ce" Abdul latif, ka taimaka ka kaini wajen Nadia, ka kaini na ji me na mata a duniya? Walahi du rashin jin maganata na ajiye dan kar Najeeba ta kubuce min, ina nan ina ta neman inda zan ganta kulun a kofar shagonta nake wuni dan na sameta ta yi hakuri da abinda na mata, ni ban yi dan bata ranta ba Ku shaida ne nan wayarta a hannuna na ringa korar du wani mai kiranta dan bana so idan na zo malakarta wani ya zame min matsala Kune shaida summar da ni aka yi kan wayarta ni kaina ban san mutumen ba aman shine yau zan ga daurin aurenta? Shi dai Abdul Latif kama shi ya yi domin kwarai ya san yana son Najeeba da gaske, dan haka bai tsaya yi masa shakiyanci ba ya taimaka masa suka shige mota Yana shirin tayar da motar docter ya fito yana langwui Tsayawa ya yi ya dafe habarsa ya furta" kan uba, lale na yarda cewar *MAGE, MAI KWONCIYAR DAUKAN RAI CE NAJEEBA* da ta tashi kawo mana dukan sai ta kawo da wajen da ko mun sha kwaya ba zamu tunkara da salon iskanci ba Soja ne ya fito har ya zarta ya dawo yana kallon Docter Daria ce ta kubce masa kafin ya girgiza kansa ya yi gaba, lale ya san yarinyar nan ta fi karfinsa kuma ya yarda Allah ne ya kareta domin matar manya ce, shi irin ya dan yi hira da itama bai samu ba sai dai daga nesa Da yawa sun ji jiki ciki harda likitan zuciyarta, da ambasador Ambasador kansa ya sada a cikin masalaci idannuwansa sukai masa wani irin jajajir gashi kuma shi a cikin masalacin yake ba a balbalin masalacin ba bare ya mike ya fita, sai ya zama a lokacin da ya dago dubansa sai da gabansa ya fadi domin yana kallon sarki sai baki daya ya raina kansa, shima shaheed din shi ya kalla kafin ya cire kansa yana sauraron haramar daurin aurensa da Nadia kasan zuciyarsa kuwa haka kawai ta hanna masa sakat, gani yake du inda ya kai dubansa ba zai rasa samarin yarinyar ba, kai da ba dan an masa kwakwaran bincike kan kawar nan tata ba, da ba zai aureta ba, an fada masa cewar yarinyar girman kanta ya saka samari da yawa ke tsoron tunkararta, har fadi ake cewar tana da nauyin jinni, sosai iyayenta ke faman ta tsayar da miji domin kawancen nasu da Najeeba shekara uku ta bata, Nadia na dauke da shekaru ashirin da hudu tana cikin ta da biyar, ita kuwa fitsarariyar na dauke da shekaru ashirin da daya tana cikin da biyu Idan ya kalli Ambasador ba abinda ke fado masa irin maganar.....ina so na ganki, na zo maki da dukan abubuwan da kika ce kina so na tsarabarki, ina so na ganki ko zaki bani nutsuwa! Lalle uwa uwa ce Bai yarda da iyaye a kasar musulmai sun isa da y'ayansu ba sai a kansa Gashi dai ya kai inda ya kai Alhmdulilah aman kuma gashi a karo na biyu an daura masa aure da zabin da ba nasa ba Idannuwansa ya kuma lumshewa ya maida hankalinsa wajen da ake kara raraba su goro ne ba kadan ba mutane sunna ta amsa a bokitai anna ta fita da su kafin a shiga haramar wani daurin auren, ga Dayabi, ga ABIH, ga sarkin agadez, ga yarima a kusa da shi sai ya shiga salatin annabi da fatan a watse lafia.......... Hi mutanen arziki, Zan yi posting na biyu yanzu, idan kuka fitar da shi za'a janye dokar bibiyu🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 [31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 37 Yana langwui ya shige dakin da Nadia ke zaune da kawayenta da auntynta da kuma daidaikun yan uwanta, dakin mai girma ne hakan ya sa kowa ke sha'aninsa an fi raja'a wajen daukan hotunna Nadia ta sha kyau domin aida ce ta zo ta mata mak'up har gida tana shaida mata cewar Najeeba bata fita kwana biyu yayarta ke fita saloon aman da ta fito zata shaida mata, ita kuwa ta dauki niyar ai Sai an nemo mata Najeeba ta tsantsara mata firgitaciyar kwaliyar da zata haukata mata sarkinta A lokacin tana shirin shan wasu magungunnan hausa ne da auntynta ta dama mata da nono mai tsami, sosai fa Nadia ke amsar tsumi daga wajen iyayenta domin suma wayayun mata ne duda ba'ai mata gyaran jiki ba sun bar hakan a zuwan sai ta tare dan lokaci ya kure yawon neme nemen abubuwansu ya ishe su Yana zuwa ya zube , mamanta da ta ga yannayinsa ta tsame daga mutane ta yo dakin Auntynta kuwa tun da ya fashe da kuka ta shiga korar mutane cike da tashin hankali tana kallonsa Su hudu suka yi saura sai tambayarsa ba'asin kukansa ake Yana dago kai cike da muryar kuka ya ce" ashe Nadia ta san haka ta barni na yi ta hauka a kan kawarta? Ashe ta san wacece kishiyarta ta kyaleni na ringa barnar zuciyata da dukiyata ina hauka? Nadia ta ringa kallonsa tana son ta ji abinda yake son fadi Sai da ya share hawayensa ya ce" Allah ya isa tsakanina da ke Nadia, shine kika kyale ni ina haukan Najeeba ashe da ita za'a daura auren Sultan? Nadia dake ta kallonsa ta yi wani dan tsam kafin ta taso da sauri ta juyi fuskarsa ta ce" hei dan uwa, me ka ce? Hannunta ya janye daga fuskarsa cike da jin haushi ya ce" tambayata kike abinda nace? Nace kin ji kunya son kudin naki ya rasa wa zaki cuta sai ni jinnin ki? Da sauri ta ce " bla bla bla, ba shi din nake son ji ba, auren Najeeba da sultan? Waye sultan kuma? Lalle kin iyabiskanci Nadia, ya fada Mamarta ce ta ce" kai Huzaifa wai meye haka? Me kake fada haka? Huzaifa ya juya wajenta ya ce" mama, ni Nadia zata boyewa Najeeba kawarta ce kishiyarta da za'a daura aure da Sarki yau? Yanzu ina zaune aka daura auren Najeeba da sarki kafin na baro wajen Nadia ta zazaro ido kafin ta dora hannayenta saman kanta, a rikice ta kara yiwowa kusa da shi ta dafa shi da hannunta da ya kwashi rawa ta ce" yanzu domin Allah me na maka zaka zo min da zancen dake iya halaka ni Huzaifa? NAJEEBA fa tana gida kwonce bata da lafia inji aida da ta zo ta min kwaliya, kai kuwa sai kace wai Najeeba Najeeba Najeeba ce aka daura aurenta da Sarki? Daria ya fara yana kallonta hade da hawayen dake zuba a idannuwansa Nunata ya ringa yi da yatsarsa ya ce" wawuya, meye ya tayar maki da hankali? Kema kin san zaki ci kakanki ne? Kema kin rikice ina ni? Kin min bakin ciki yarinya kuma sai Allah ya saka min! Wani irin ta kurma hannayenta saman kanta ta zube ta shiga burgima fadi take" mama bilahilazi ku yi kiran baba na fasa, walahi na fasa auren mijin Najeeba, dama Najeeba ce dayar? Mama kin kuwa san Najeeba? Mama Najeeba fa kawata wace muke zuwa nan wani sa'in wace kike cewar yarinyar nan tana birge ki dan bata shafe shafen nan na yan matan zamani gata saliha mai kyan hali Mama na rantse maki da Allah Najeeba kililin kasau ce, kanta a kasan nan take harbi irin na bakin maciji ko harbawa ba'a yi ake macewa Mama Najeeba ce fa? Walahi halaka ni zata yi, idan wani bai kashe ni ita zata kashe ni dan na tabata sai ta ci uwani da na auran mata miji! To wai me hadinta da shi bayan a duniya ko maganarsa bata so ina mata, irin idan zance ya kawo zance sam bata so a kawo maganar sarautar garin nan bale sunnansa ? Mama ni ke zaune da Najeeba tun safe har dare a saloon dinta, ni ganau ce ba jiyau ba mama da ubwan waye bata dakuwa idan ka kawo mata simple raini bare ni da zan auri mijinta? Mama ki rufa min asiri tun ina numfashi ki hanna abin nan Da mamaki mamanta ke binta da kallo hakama auntynta ke tareta tana fadin" ke meye wannan, rage muryarki kar ki sa a fara taruwa mana, ki bari mana Mamanta ta ce" ke yanzu ai abin murna ne ace Najeebar nan dai da na sani ce kishiyar taki, yarinyar da bata taba gaisheni a tsaye ba sai ta duka, yarinyar da in tsintsiya na dauka zata amshe ta share wajen da nake son kimtsaya? Yarinyar da nan in ta zo sai ta baiwa kannenki abin dadi ni kuwa du da ina aiki sai ta min kyautar kudi masu yawa? Yarinyar abin mangari wace nake fadin da Ibrahim dina ya girma sai na aura masa ita domin a duniya tarbiyarta na birge ni shine ke marar kirki zaki ringa fadin kalamai irin haka munana a kanta? Haba Nadia , Haba Nadia nan abanku baya so kina kawaye aman yarinyar nan da kansa ya furta eh lale wannan tana da tarbiya ya yarda ki yi kawance da ita aman shine Nadia zaki fadi haka a kan yar mutane? Ni walahi sai yanzu hankalina ya kwonta zan fita na ci gaba da bikina cikin farin ciki Nadia ta zabura ta mike tana neman wayarta a haukace ta ce" ina, ina ba zaki gane ba mama, ba zaki gane ba, a daki kike mama, mama baki fita kin san me duniya take ciki ba, mama a zamaninku babu kililin kasau, kai ko akoy ta yanzu nata salon daban ne, mama ki manta wata maganar cewa wai zan je na shinfida sarauta ko na je na yi tinkaho ko na je na kwace miji a hannun zinariya, walahi walahi sai na zama uwa akuya a gaban Najeeba Kai ina, a watse, walahi a watse an fasa auren nan Kokarin fita take dan watsar da taron mamanta da kanwar mamanta suka rikota suka yi ciki da ita sunna fadin Huzaifa ya kama masu Bakinsa ya tabe yana jan hanci ya kama hanyar fita, komawa zai yi wajen auren dan mahaifinsa na cen, zai je na fada masa ashe matar nan da ya fara kekyarawa palas itace aka yi masa wuf da ita Dannata suka yi ciki suka rufe kafin auntynta ta zaunar da ita tana kallonta ta ce" ke dallah banza zaki mana shiru ko sai na ci ubanki a wajen nan? Dan ubanki kishiyar ce kike yiwa haukan nan? Ke ba mace bace ko ba abinda take da shi kike da a jikinki ba? Dan hauka ko wacece ita zaki nuna ne har ki ringa fadin wai a fasa aure? An ce mana an kashe matarsa kin ce kin ji kin ganima bale wai zama da kishiya? Kishiyarma mamanki na fadin tana da halaya shine zaki zo kina mana hauka a nan? Idan gabdancin ne ke ba zaki iya kwatar kanki a gabanta ba? To Nadia ko a dadaure sai na kaiki gidan nan yau, dan walahi sai an dama da mu, me aka fi mu? Yarinya ke da zaki amshi girma kan girma? Tun da abin nan ya samu nake takawa ina daga kai da bakin gilas a garin damagaram, kin san da rububin kawance ake da ni dan yar yayata zata auri sarki? Zan ci uwaki idan kika raba ni da farin cikin nan walahi! Idonki idonta zaki mata murmushi ki ce da ita" hello yar uwa ki bata hannu ku gaisa! Sai me? Ke ko yar uwarki ce idan halal ne ku jera an fada maki zamu tsaya ne? Yarinya ko ni uwarki yace yana so idan halal ne bara ki ji zan zo mu jera ne bale wata kawa Dallah warware mana maza shiga wanka mu fita mu yi jiran dan sahun dan na ga take taken ki yar iska ce ke kina iya saka min hawan jinni! Mahaifiyarta kam mace ce mai sanyin gaske, kuma ita bata ga wani abin tashin hankali a nan ba, wai Nadia bata ji tsoron an ce ana iya kasheta ba sai tsoron dan za'a mata kishiya kawarta mai mutunci? Du irin yanda suka ringa fadawa mutane auren nan? Ita kanta sanadiyar auren nan yau mai gidansu baki daya ya zo daurin aure tun da safe da shi aka rankaya gidan sarki har ce mata ya yi ta sama masa number sarkin shine wai Nadia zata yi mata haka? Karshe dai tun a lokacin auntynta ta gama shiryata ta fita ta samu hanya ta ce ta fita gatanan Ta san sarai wacece auntynta, tabas kamar yanda ta ce ta kiyayeta zata ci kaza kazancinta zata aika dan haka da nikaf din tamkar munafuka ta fice a gidan ba tare da an farga cewar amarya har ta fita ba Sai da ta bushi kasa ta ce zata je ta karbo dinki da dabara ta fice a gidan banda yayarta ba wanda ya san nufinsu sai mahaifin Nadiar wanda shima sarkin ne da kansa ya masa bayani bayan an gama daurin aure Bakin titi suka samu suka zauna, Nadia kam wani irin murdawa cikinta ke yi, ita fa kallonsu kawai take, ba zasu taba fahimtar abinda take nufi ba, baki daya wani zumudinta, wani farin cikinta, wata takamar da ta dauko ta yi mata sanyi, abu daya take furtawa auntynta shine" aunty, ni na zauna da Najeeba, Najeeba uwata ce a iya bariki, ki barta kawai inda kika ganta dan na tabata kema zaki so ta idan kika hadu da ita bare mai Martaba, ita fa ba wai bakin hali ne da ita ba, aa, abinda zata aikatawa du wace ta kalar mata sahibi ne mai yawa, takan ce na tsani kishiya, ba zan auri mai mace ba, idan kuwa mijina ya kali wata sai na mata *salatu* irin na maza Daria auntyn nata ta yi tana gannin yanda ta rikice, lale zata tsaya har a sada Nadia da dakinta domin a irin yanda du irin firiritar Nadia ta haukace din nan daga jin maganar daurin auren nan ina da an kaita gata gata? Kallonta ta yi ta ce" kin ga, zuwa an jima zamu cika fadar nan kwonmu da kwarkwatarmu, du abinta zata ganki zagaye da dangi dan haka ke da ita sai dai kallo, idan ta zo da mutunci a yi, idan kuwa ta zo da rashin mutunci a yi Nadia ta dago kanta tana gannin wani adaidaita sahu da bashi da number a jikinsa, sannan sabo ne dal ua tsaya a kusa da su bai masu magana ba aman su yake jira ta ce" baki san su waye MUTALAB FAMILLY BA? ai inda zamu je din gidansu muka je, zamu tardata tatare da iyayenta da yan uwanta danginta, aunty idan ta kama a zane mu za'a zane mana jiki ne tasss walahi Itama zuea lokacin jikinta ya yi sanyi, sai dai bata nuna ba, ta jara karfafa mata gwuiwa ta ce" Nadia, ai yanzu ba ke ba, ko ni zane ni sai ruwan sama walahi domin na zama uwar matar Mai Damagaram, tashi mu je, mijinki na kare lafiarki kina hauka, na tabata sonki yake a yanda ya damu kar a kashe ki Haka suka tafi cikin dan sahun nan su duka da nikaf Abinda aka bincika kawai shine idan basa dauke da wani mugun abun kafin su shige ciki Sunna shiga kuwa Jakadiya da Anmy ta turo tarbarsu, ita kanta bata san ko su waye ba ta ja su bangaren Amaryar sarkin ta buda masu sannan ta yi baya A nan suka zauna sunna karewa tanfatsetsen falon kallo cike da wani yannayi Kai da ace hankalinta a kwonce da idan ta fara daukan hoton wajen nan? Yau itane zaune a cikin gidan sarki, a cikin daki, malakinta, a matar sarki? *Akoy shagali* A lokacin da karfe hudu ta yi na yama, a lokacin Anmy ta bada umarnin a kai ZINARIA, da NADIA dakin gyaran amaren da tuni aka shige ciki da Najeeba aka shiga gyarenta , dan kimtsa su domin baki dayansu za'a fitar da su ne babar runfar da a nan za'a hadu da MAI MARTABA bayan salar isha'i dan a gabatar da junnansu a babar runfar wace ake cen ana ta kara kawatata domin ba kowa zai kasance a wajen ba sai shakikan amaren da kuma su Anmy din da shi kansa sarkin Shirin ba na wasa bane, dakunnan duka aka shige da amaren da kuma Zinariya ya kasance kowace da wada ke tsaye kanta Sai da kyar aka samu Zinariya ta yarda da shirin nan, shima sai da Anmy ta yi hakuri ta kara tura masu jakadiyar sarki kafin mamanta ta yarda a fita da ita a je wajen shirin amaren Shiri ake masu mai tsafta, shiri mai class, shiri mai daukan hankali Mai mak'up ce ta fara zane masu fuskokinsu da royal mak'up mai shegen kyau da tsari lafin masu gyaran kai su shiga kiciniyar yi masu abinda suka zaba a yiwa gashinsu duda Nadia bata da gashi sosai aman a haka akaiwa kanta wani irin coiffure ba tare da an saka atach ba ya yi kyan gaske harma ta ringa ayana dama gashinta na kwaliya? NAJEEBA kam kallon mutane take, masu gyaranta a yau sunna yi ne sunna rarashinta, wani girma ta dauka a yau wanda suke girmamata da shi, ko magana zasu yi mata da wani yannayi na daban mai matukar girmamawa suke yi mata shi A daidai wannan lokacin ta fi daukan shiru a kan ta ringa zubar da hawaye A jiya zatonta ba zata waye ba, irin yanda jikinta ya tsananta zafi, a tunaninta za'a fasa, sai dai tana ji tana gani aka ci gaba da dura mata abubuwan dake kara saka mata kasala , tana ganni Abihnta ya ringa murnar gannin yanda fatarta ta dawo da irin yanda ake kula da ita, tana gannin yanda yayunta ke wani irin farin ciki harta da Nusaiba an yanyara mata kitso kannanu an shiryata cikin yar rigarta ta barbi mai kyau Tana kallon yanda yayanta ke amsa waya hakoransa waje yana ta fara'a yana shaida yana gaiyatar daurin aure gobe a fada zai aurar da kanwarsa Daga nan ta kara sarewa lamarin sai kawai ta aro shiru ta yafawa kanta, tsakaninta da kowa ido ne bata cewa um bare um....um Irin yanda take fitar da kamshi ko fitsari ta yi baki daya kamshin turaran ke fita a jikinta, irin yanda suka mayar da fatarta ita kanta takan ji a yanzu take mace mai classs Irin lesson din da suke bata kamar da wasa ya zama attitude dinta, domin a yanzu a cikin idannuwanta zaka fahimci halin da zuciyarta ke ciki Suturunsu duka masu ruwan sararin samaniya ne, sai alkyabobi farare kar masu dauke da duwatsu da wasu irin kwaliya Zinaria, har zuwa wannan lokacin bata san wa aka aurawa mijinta ta biyun ba, domin yayarta da ta fita neman rahoto tsaf ta ji ko wacece aman tsoron ta kai labarin nan da bakinta ya sakata nuna kai ita bata fahimci ko wacece ba Abinda ya sa kuwa shine, ba yau ba Najeeba ta zama makiyiyar zinaria da mahaifiyarsu , idan har suka ji wannan bayani ta tabata ba za'a yi da kyau ba abin zai shafi har ita Yannayin zinaria har yanzu a bayane ranta a bace yake fiye da tunanin mai tunani Sai dai ta fasa ihun kukan domin ta wuni yi a jikin mahaifiyarta, sannan itin alkawarurukan da mamanta ta mata cewar ta zuba ido ta gani ba wata shegiya da zata yi kishi da ita ya sakata yin shiru tana sauraron ana mata kwaliya ana shiryata Sallah kawai ke tashin su, har zuwa lokacin da aka gama shirya su A lokacin da Anmy ta ringa bin dakunnan su ita da Ummu sun ga kwaliya Sosai Zinaria ta fito a hajia matar sarki hakorin makarta ko yaya ta juya ta dan daga bakinta yana walwali A haka suka ajiye sarkar da suka shigo da ita dan a saka mata sannan suka nuna cewa ita za'a fara rakawa dan ta tarbi kannenta Ita dai kallonsu kawai take har suka fita kafin ta ja wani uban tsaki har mahaifiyarta ta yi gagawar banka mata wani kallon da ya sakata sada kanta domin masu kwaliyar ba tafia suka yi, su kansu da mamaki suke kallonta haka kawai sai suka ji girmanta ya zube a idannuwansu domin mahaifiyar mijinta ne ta yima haka, yo kishi hauka ne? Bale gidan sarauta ai ta san da za'a mata kishiya! Dakin Nadia suka shiga Irin yanda ta sada kanta abin ya basu sha'awa, gaishe su ta yi kanta a sade sosai Ummu ce ke kallonta, kwarai ta so shaida ta sai dai sam sai ta ki yarda ko wacece, a haka itama suka ajiye tanfatsetsiyar sarkarta suka fadi cewa nan da minti ashirin za'a shigo a tafi da ita Daga nan sai suka yi wajen Najeeba A lokacin da suka shiga, ZAHRA ce tsaye tana ta yi mata vidio tare da wani sauti mai sanyi da ratsa zuciya su duka tana daukansu vidion ne har ita da yaya Dayabu wanda shima ya shigo a karo na uku a yau yana hankalce da kin maganar Najeeba sai dai ya yi murmushi kawai ya kyaleta, gwara ta yi shirun da ta ringa ihun kuka haka kawai kan abinda ba za'a fasa ba Tun da Anmy ta shigo sai ta ji idannuwanta sun cika da kwallah Ta kasa yarda cewa Najeebanta ce zaune a wajen nan, saman wata kujera mai alfarma an rufa mata alkyabarta a saman daurin dan kwalin da ta sha mai tsari da kyan fasali Karasawa suka yi su dukansu sunna kallonta Anmy ta fi kusanci da ita inda yan matan du suka kara rukunkume Ummu, hakama yaran da ta yi yan kwanakin nan sun matukar sabawa da ita kamar wata mamansu Anmy ta kamo habarta kadan ta dago dubanta Sunna hada ido Najeeba ta yi raurau da idannuwanta Kai Anmy ta ringa girgiza mata a hankali ta ce" kar ki bari su zubo su bata kwaliyar nan an matana, kin ga yanda kika yi kyau? Kar ki bari wannan rana ki yi hawaye Najeeba kin san farin cikin da nake ciki kuwa? Da kin san yanda nake jin nutsuwa da auren nan da sai kin fi kowa murnarsa Kuma juyota ta yi sosai tana amsar sarkar da Dayabu ya bude ya ciro ta zinari ce su dukansu iri daya A hankali ta shiga daura mata kafin ta ce" abinda muna tare, ina nan fa, ina tare da ke fa Najeeba ta ringa sauke ajiyar zuciya Mahaifiyarta ce ta matso kusa da ita Itama idon ta kura mata, wai ita ta haifi santaleliyar yar nan? Lalle Allah ya mata kyauta ta saka kafa ta shure ta tafiarta? Murmushi ta yiwa Najeebar dake kallon fuskarta, mamanta sam bata tsufa , bata da kaurin jiki hakan ya sa bata wani zaune ba, sannan cikinta bashi da yannayin wace ta haihu dan mace ce mai matukar kula da kanta A hankali ta dan lumshe mata ido bata cire dubanta da karfin nan ba hakan ya saka Ummu sakin ajiyar zuciya a boye tare da saka ran watarana zata dubeta Nan suka lalace sunna ta daukan hotunna da vidio, Ba wanda ya dauki maganar nasiha, Anmy ce ta katse hakan cewar su bar mata y'a zata yi mata a nitse, to nasihar wacece ba'a mata ba, har mai wa'azi aka kirawo ta mata sosai sai dai abinda ba za'a rasa ba Sai da aka dauki kusan minti arba'in sannan su Anmy suka fara tafia A lokacin da suka nufi runfar aka shaida masu Sarki ya hana zama a nan ya umarci a je falonsa na kurya mai dauke da su camera da sauransu Nan suka nufa cike da ayar tambaya, sunna cike da mamaki Kasancewar tuni yana cen ciki ya saka Anmy na samun waje suka hakimce ita da Ummu tana hangen su Gimbiya kusa da zinaria da wata yayarta, hakama Nadia tana tare da aunty da wasu yan uwansu biyu manyan mata du sunna zazaune ne saman manya manyan kujerun falon sun cika sosai sosai kowace na dan murmushi idan sun hada ido da wata, su kuwa matan kowace kanta sade da alkyabarta Wayar da ta dauka umarni ta bada kan a rako Najeeba da zahrau, da dayar matar sarkin Tana kashewa ta kuma kiran SHAHEED A lokacin an gama masa wani nadin ana ta binsa da turaruka ne Tambayar da ta masa kan me yasa ba'a zauna a rumfa ba? Amsa daya ya bata a hade cewar" Eumfar na dauke da hatsari ne Ajiyar zuciya ta sauke, gaske ta ga dogarai da mai wasan maciji sunna tsaitsaye sun tsare ko'ina da alamu hayaki zai yi Ajiyar zuciya ta kuma saukewa tana mai bin wajen da kallo Waye? Waye ke son gannin bayan auren yaronta? *Shin yaron nata ake son gannin baya ko kuwa matan da zai aura?* Ajiyar zuciya ta sauke haka kawai ta tsayar da dubanta kan mahaifiyar Zinaria wace fuskarta ba yabo ba falasa tana yake dai irin kar a ga kasawarta aman sam abin bai kai zuci ba A kansa zuciyar Anmy kuwa tambaya take *GIMBIYA, shin abin iya kishin ya tsaya ko kun saka kanku a ukun rayuwar duniya da kiyama?*, da sauri ta ringa kore shaitan tana cire maganar daga ranta daidai lokacin da aka shiga shelar za'a shigo da NAJEEBA Du dubansu suka kai banda Nadia, da kuma zinaria da suke nitse kawunnansu sade Da mamaki Gimbiya ke kallon wa'inda suka shigo da ita, su biyu ne kawai wato kishiyoyinta sai jakadiya da wasu bayin dake tafe sunna zubar da flowers pink da fari a hanyar da take takawa A haka har suka karaso wajen zamanta suka zaunar da ita sunna mai gyara mata abin rufarta kanta sade alkyabarta ta rufe gaban fuskarta Kamshin turaranta tuni ya ringa kaiwa hanci hanci, du kuwa da falon kansa yana da kamshinsa aman kamshin nan nata ya rigaya ya gama kama jikinta sandal Rose na ruwa Gaban Nadia ne ke dukan tara tara , a hankali ta rike hannun auntynta kanta sade tana jin zuciyarta na mata rawa sosai Ita dai Gimbiya ta ki dauke idannuwanta, burinta ta san wacece a rufen nan? Dan yanda ta damu ta ga fuskar wace kiahiyoyinta suka shigo da ita ko Nadia bata damu da gannin kamaninta ba! Ina danginta? Shine abinda take ayannawa a ranta Cen ta yatsine fuska a lokacin da ta yi tunanin yanzu haka wata diyar wani kasurgumin talaka ce aka lulube dan kar a gane A hankali ta kai dubanta kan takalmin kafar Najeeba Takalmin fari ne kal kal da shi mai dan gashishika kadan a samanta, sau ciki ne takalmin irin babuche, kyalkyalin dake samansa suma fararen ne sannan ya yi yar kwana kadan Kana ganninsa ka san babar harka ce Kuma daga idannuwanta ta yi tana juya su suka hada ido da Ummu Irin yanda Ummu ke binta da kallo, ita kuwa sai ta kakaro murmushi ta sakarwa umu Ummu ta yi murmushin itama kafin ta kara gyara zamanta ta kuma daga dubanta ta sauke das a kan y'arta, lalle yanzu ta yarda yarinyarta ta shigo cikin mata, ko Najeeba na so ko bata so sai sun zauna sun yi magana! Ya kara wasu mintunnan sun kai talatin kafin a shiga fadin" *GYARA KIMTSI, GYARA KIMTSI, A GYARA ZAMA A NUTSU, MAI DAMAGARAM ZAI SHIGO, DAN SARKI JIKAN SARKI, SARKI MAI WUKAR YANKA, SARAUTA GADO CE, DAN MUN GADA BA DAN HAYE BA, GYARA KIMTSI GA GURNANIN ZAKI TAFE, GYARA KIMTSI GA FARI MAI FARAR ZUCIYA FARAR ANIYA NAN TAFE, JINNI NA BAREBARI DA SHUWA ARAB, KAI DAYA MUKE DA KAI TALLL TAMKAR GOMA* Irin abubuwan da aka ringa fada kafin ya sanyo kansa ya shigo cikin nutsuwa A shigowarsa ne baki daya du wani turare ya risina, Du irin kamshin amaren sai nasa ya doke su domin an masa wankan turare ne kamar ba gobe Tun da ya shigo du suka sada dubansu Cike da takun kasaitar da du takunsa daya sai zuciyoyin matansa sun amsa har ya kai ga kujerar da ta fi kowace alfarmar ya yi bismillah sannan ya samu ya zauna Sai da ya ringa bin wajen da kallo daya bayan daya, da hannunsa ya yi umarnin dogaran su juya Suka juya a tatare sannan ya ja numfashi a hankali ya furta" *ASALAMU ALAIKUM* Wannan salama tasa , itace sanadiyar da ta saka du wata halita a wajen dago kanta A daidai wannan lokacin ne idannuwa suka ringa garwaya da junna, da yawa sun dauko amsa salamar ta katse daidaiku ne suka kaita har karshe kafin idannuwan matan nan uku su sarke da junna Kamar hadin baki, koda yake idan abu ya dakeku haka ne, a tatare suka zabura a wajen da bai dace su zabu tsayen ba, kowace cike da tsoro da mamakin abinda idannuwanta ke ganni a zaune A rikice ZINARIA ta nuna yatsarta kan NAJEEBA wace hular alkyabarta ta fadi kan kafadunta itama kamar sauran bakinta na rawa ta ce *KE?* Najeeba ta kalleta na second biyu ta juyi wajen Nadia cike da matsanancin mamaki ta nunata da yar yatsarta itama ta ce *NADIA?* Nadia kam gaba daya mikewar da ta yi na tsoro ne, domin bata san zasu ga junna a nan kusa ba hakan ya saka ta tsorata da ido hudun da suka yi da Najeeba bakinta na rawa sosai ta budi baki ta ce" Morning people😌 [31/03 à 19:24] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 38 A rikice Nadia ta ce" NAJEEBA, dan girman Allah ki saurare ni na maki bayani." Auntynta ta ja hannunta da karfi Warce hannun nata ta yi ta ce" aa, kin ga, ki bari na fad'a mata, walahi tallahi da na san mijinta ne zan aura da ban yarda na yi wannan gangancin ba." Irin yanda take bayannin hankalinta tashe , sannan har ta fara takowa zata k'arasa kusan Najeebar da saurinta. A wajen kusan kowa hankalinsa na kanta banda Zinaria da mahaifiyarta da suka gama mutuwar tsaye a lokacin da suka gama fahimtar a yau wata bak'ar fatar, daya daga cikin cousins din Mai Damagaram, y'ayan Mutalab , wace suka fi takun sak'a da ita ta zama mata a wajen mai Damagaram, ZINARIA ta juya wajen mamanta, a fili cike da kidima ta ce" ashe wannan ce ya aura? Ya rasa wace zai had'ani kishi sai wannan marar kunyar yarinyar yar wulakanci? Ya rasa wa zai d'auko min sai wannan bak'ar yar mai idanuwa kamar na mujiya?" Kuka ta fashe da shi a fili wanda da sauri yayarta ta kamata ta aniya mayar da ita saman kujerar A rikice mahaifiyarta ma ta kamata kasa kasa take fadin" ki min shiru, ki bari mu fita walahi ba zai yiwu ba!" Kamar wa'inda suka samu TV dubansu ya dawo wajen NADIA da ta karaso kusa da Najeeba. Hannunta na rawa ta kamo hannun Najeeba, auntynta kuwa kamar zata k'urma ihu dan takaici. A birkice ta ce" ke kin san na san cewar bakya son kishiya, ke kin san nima haka ne, kuma ke kin san ke kika min alk'awarin rabani da kishiya ko da na auri miji mai ita, Najeeba, kin san ba zan taba auren mijinki kaina sane ba, koda maye nake da sani ba zai taba faruwa ba, ni ba maciya amana bace." Najeeba ta lumshe idanuwanta tana jin yanda suka yi mata wani irin nauyi. A hankali ta ringa satar kallon mutane Kyam idannuwansa a kansu. Du abinda ke faruwa da ido kawai yake bi tamkar baya wajen. Haka su Anmy har baki Anmy take saki tana bin ikon Allah Zinaria kuwa sai danarta ake kamar zata hau bori. Idannuwanta ta maida wajen Nadia Sai da ta lumshe su sukai wani luuu sannan ta bud'e su. A hankali ta ce" ke, daina irin haka mana, meye a ciki dan kin auri miji? Na ce maki na damu ne? Bayan kema ya d'auko Barira, ina taya ki murnar malakar abinda kika jima kina marari, ke kin san ba nawa ra'ayin kennan ba dan haka kar ki bani kunya kin saka ana kalona!" Maganarta a fili ta yi ta, cikin kwonciyar hankalin da ya zama jikinta, duda daga kasa wani irin jimkar hannun Nadia ne ta yi wanda ya saka Nadiar shiga wani rud'un Ta ce babu komai, irin magangannunta sun bayana karara ita auren kansa baya gabanta, aman kuma irin rikon ta mata ta tabata akoy wata a kasa. Hannun nata ta saki ta koma ta zauna tana mai gyara alkyabarta da kyau kafin ta kuma dago dubanta ta sauke kan Nadia dake tsaye kanta *Zaki ci ubanki!* shine abinda zuciyar Najeeba ke ayannawa Na tsaye shi, baya gabana, aurensa baya gabana, aman ko kashin da na yar ya haramta gareki domin aminci ba karya bane! Ta kuma furtawa zuciyarta Ji take baki daya ta gama muzanta a idannuwan mutanen dake wajen, du wanda ya santa, to fa ya san Nadia Anmy da baki daya jikinta ya yi sanyi ta kai dubanta wajen Sultan Irin kallon da yake ramkar kallon jin dadi, irin yanda ya maida hankali a kallon dramar da ta wakana, ko take kan wakana kamar wanda abin ya masa dadi A hankali ta sada kanta Ba'a taba hayaniya mai yawa haka a gabansa ba, baka isa ka yita haka a gabansa ba tare da ya maka abinda zai firgitaka ba, aman sai gashi ya yi shiru ya kyale har Najeeba ta fadi maganar da bata so ta fadeta a gaban kishiyoyinta ba, kwarai karara ta nuna bata yi auren da zata yiwa kishi ba! Me ya sa Shaheed? Me ya sa ka auro aminiyarta? Shin amsa min ka yi dan baka da yanda zaka yi da ni ne ko me? Ni kiwa zan nuna maka ba sarauta ba,, ko me ke kanka ni na haife ka! Ummu kam da kallo take bin kowa, har lokacin da auntyn Nadia ta karasa ta kama hannunta ta ja ta ta mayar da uta wajenta tana jin inama idan ta wanke fuskar Nadia da mari ba abinda zai faru? To da yau sai ta fafale fuskarta da mari sannan ta yi tirr da ita, bata taba bata kunya ta sakata jin ashe Nadia sakarai ce bata taba sani ba irin na yau, lalle Nadia sakarai irinta babu Ashe yarinyar da take haukan tsoron ita batama damu da mijin ba? Ga alamu karar sun nuna kamar auren dole ne akai mata? Zaunar da ita akai Sai a lokacin ya dauke idannuwansa daga kanta Kwarai da farko, wani murmushi ne ya subuce masa a lokacin da ya hangi dukan da gannin Nadia ya yi mata, irin yanda su duka biyun suka rikice da ganninta a gabansu kuwa ya bashi mamaki duda ya san Zinaria basa shiri aman bai taba tsamanin kawar tata tsoronta take ba, aman a kan me take tsoronta? A hankalo kallonsa ya koma na son karantar ainahin abinda take ciki maimakun wanda yake fitowa daga bakinta Murmushi ya kuma saki irin na yake din nan a lokacin da sak kunnayensa suka jiyo masa irin yanda ta yi magana da nuna bata damu da gannin kawarta aminiyarta a matsayin kishiyarta ba, wace suke raba mafarkin kasancewa su kwalin kwal a gidan miji Dubansa ya maida kan Zinaria, kanta sade yake, sosai an janyo alkyabarta an rufa mata dan kar a ga fuskarta Tausayinta ne ya ji har cikin ransa, irin magangannun da ta yi kwarai sun bashi mamaki, meye ilar bak'ar fata ne? Bai san me ya sa idan hankalinta ya tashi take barin bakinta ya ringa fadin du abinda ya zo zuciyarta ba Ya tabata da ba dan mamanta ta rufe mata baki ba, da zata dora wata kalmar mai zafi ne a kan kalamanta, menene a kishiya ne da mata ke tashin hankali dan za'a yi masu? (Han, baka yi rayuwar neman aure da wani bane, a wajen da kake soyaya ranka shi dade) Kuma kai dubansa ya yi wajen da aka zaunar da Nadia, tsuru Najeeba take kallo hakan har ya so ya bashi mamaki, ta yaya mace zaki yi sake har a ga rauninki haka? Kansa ya girgiza sai kawai idannuwansu suka sarke da na Anmy Irin kallon da ta masa ya saka shi sada nasa idannuwan wanda hakan ke nufin yana tausarta ne Matar sarkin agadez ta tsakiya ce ta duka sosai ta kama hular alkyabar nan ta dora saman kan Najeeba, Kanta kasa ta zagayo ta kama hannayenta, hannunta dayan suka kama ya kasance tana tsakiya Anmy na kallonsu, sarai ta san abinda zasu yi, ita dai Najeeba bata musa masu ba , binsu ta yi a hankali suka nufi wajen da yake zaune Sunna zuwa da hannayensu suka kaita kasa ya kasance ta duka a gaban kujerarsa A sanyaye Zahrau ta ce" Allah ya huci zuciyar Sultan, Allah ya huci zuciyar mai damagaram, Gimbiya Najeeba na neman afuwar daga murya a gaban uban gidanta A hankali da mamaki fal ramta ta dago ta hangi fuskar Zahrau, iyeah, yaushe ta koyi irin abubuwan nan? Kishiyarta ce ta budi baki itama cikin kara sada kai kamar yanda suka tsugunar da Najeebar ta ce" Allah ya huci zuciyar mai wukar yanka, Allah ya saka sasauci a hukunci takawa, sannu da karin hakurin halayan mata , Allah ya kara maka lafia Gimbiya Najeeba na neman afuwar mikewa a lokacin da baka bada izini ba Idannuwansa kawai ya lumshe masu bai ce komai ba suka mike a hankali suka koma Sunna zama su Zinariama suka mike da ita suka nufi wajensa Baki dayansu suka zube suma, cike da kwarewa a lamarin bada hakuri da kirari mahaifiyarta ta taushi zuciyar sarki da neman afuwa Idannuwansa a kan Zinaria A hankali ya budi bakinsa kasa kasa ya furta" Allah ya sanyaya zuciyar uwar gidan SHAHEED Idannuwanta ta lumshe jin dadadar muryarsa a kanta, mahaifiyarta kuwa har sai da ta kara jinjina ta kara daga murya tana fadin" Zuciya ta sanyaya Gurnanin zaki, Allah ya kara girma, uwar gidanka ta amsa ta gode rarashi Da biyu ta yi hakan, wa'inda take so su jin kuwa sun ji, a haka suka koma Sai da Aunty ta kamata ta mikar da ita, ita kanta kafafuwanta rawa suke, sai wata datijuwar daje gefenta suka saka Nadia a tsakiya suka nufi wajen baki dayansu a tsorace domin basu taba kusanci irin haka da sarki ba, sannan basu san al'adun gidan sarautar ba Sai da suka karasa suma suka tsuguna Hannayensu du suka hade kamar sunna adu'a kafin su shiga hadin baki wajen maimaita abinda suka ji ana fada masa Murmushi ya yi kafin ya gyada masu kansa Auntyn Nadia ta ringa sauke ajiyar zuciya, a ranta kuwa fadi take" Allah ka sa mu tashi da wuri lafia daga wajen nan, Gannin basu mike ba ya saka ua rage muryarsa sosai ya furta" ku koma mazaunin ku Sunna komawa suka zazauna tadar gaba wace a cikinta ne ake fadawa junna magana ta hanyar firgitatun kyaututukan da matayen zasu yiwa junnansu Wannan tada, zinaria ta san da ita, kuma ta shiryawa hakan, sai dai a yanzu a wajen mahaifiyarta ta kara ninka kyautar dan tana son ta fara kai mari da firgitatun kyaututukan da zata gabatar ba dan komai ba sai dan ta nunawa y'ayayn talakawan nan kudin kansa hawa hawa ne, sannan sarauta fa gado ce! Yayar ZINARIA ce ta fito cikin shirin wata mahaukaciyar shada ruwan pink, an cancada mata mak'up tana baza kamshi sosai Da alkyabarta baka mai shara shara wace ta fitar da tsarin gashinta karara Cike da yanga dauke da jaka ta karasa Tsakiya Jakar nan ta buda ta duka kadan ta ciro wata katuwar sarka ta zinaria kafin ta hada da chek mai dauke da kimanin kudi cefa millipn biyar biyar ya zama sarka biyu da million goma Sai da ta dadaga ta nununa sannan ta buda bakinta da hausar buzayen da bata zauna ba ta ce" *Alhamdulilah, ZINARIA na yiwa Amare barka da sauka da fatan sun shigo lafia, Zinaria ta sauki Amare da ruwa sansanya da wajen zama harma da kyauta a ja jari* Karin chek din shine karin da suka yi, sai maganar a ja jari da suka d'ora wace sarai magana ce cikin hikima. Murmushi Anmy ta yi kafin yayar Zinaria ta dauka ta je gaban Anmy ta tsuguna ta ajiye sak'on ta k'ara gaishe da Anmy din sannan ta koma mazauninta. Dubansa ya kai wajen su Nadia, Sai kici kici Aunty take da jaka ita batama san inda ta zuba chek din da ya bada Jakadiya ta kawo masu ba, sarai ya san a wannan wajen za'a so nuna hali na wulakanci shi ya sa ya bada chek biyu wanda ya tabata wannan uwar handamar ba zata taba iya ciro kudi irin haka ba. A lokacin da ta fitar da takardun sai da ya lumshe idannuwansa sannan ya ci gaba da kallo Sai a lokacin ta kalli takardar, sai da ta zaro ido tsabar kad'uwa har da yan yatsunta ta kara irga ziro din dan tabatarwa. Ajiyar zuciya ta sauke ta nufi wajen itama Tana inda inda ta ce" NADIA na godiya, sannan ta bada kyauta a baiwa kishiyoyinta kamar haka, million muraran million har million ashirin ashirin... *su ja jari* (kar ku manta ita ba sannin me ake fad'a ta yi ba, kokari ta yi ta kamanta) Itama ta nufi wajen su Anmy, sai da ta duk'a da hannu biyu ta mik'a masu sannan ta mik'e ta nufi wajen Nadia da baki d'aya ta zaro idanuwanta da mamakin kud'in, kan ubancen kaya sa, wani abin sai manya, wani abin sai kishi, yo ita uban wa zai bata wannan kud'in ta yi wasa da su? Ko hauka take, ba dai dan ta birge kishiya ba walahi, kai, inama inama daga ita sai Zinaria ne suka shigo? Inama inama hakan ne? Kwarai gwuiwar Zahrau ta yi sanyi a lokacin da ta tuna kudaden da suka zo da su kwata kwata million hudu hudu ne, suma Anmy ce ta bada chek din tana fadin akoy tadar nan, suma zamaninsu an yi, idan an kawo amarya kowa na yiwa kowa kyauta, sai dai su nasu da sauki domin zamaninsu idan ka bada million dayama ka yi kokari bare har sama, su kam ba ta nan suka zuba kishi ba, aman sai ga wani tashin hankali kiri kiri ana wasa da kudi kamar jaraba yanzu haka kowace iya abinda gareta ne ta kakabe dan kawai kar a rainata? Anmy dake yaki da zuciyarta kan ita zata je wani duban ta kuma kaiwa wajen Sultan Ta sani, farin sani cewar shi ya bada kudin Nadia Aman why ya yi haka? Shin tsana ce mai tsanani tsakaninsa da Najeebanta har ta kai haka ko me? So take ta shiga idan ya so sun dade basu ce ta zabi Najeeba a kansu ba! Sam ba zata iya bari a shiga da yan kudaden nan ba, lalle yau ta yarda yanzu irin tadar nan ta zama hauka, gaskiya mahaifiyar zinaria bata son zaman lafia , a kan me zata bada irin hanyar nan? Sai kuma shi kansa dole sai ta tuhume shi da kudaden nan idan kiwa shi ya bayar sai ya ba sauranma! A hankali ta ajiye ambulope din ta dan mizguta zata tashi Hannun da ya mayar da ita ne ta bi da kallo Murmushi ta sakar mata kafin ta idasa mikewa gaba dayanta Ina sam ba zaka ce matar nan ta haifi najeeba ba, Doguwar riga ce a jikinta ta shada an mata makeba wace ake fitar da wuya kawai Rigar ta sha handwork mai tsadar nan irin wanda ake yi a dubai Rigar ta hadu, ita kadai abin kallo ce sannan aka yi mata dauri das irin na zara buhari a saman kanta Ashe itama gashi ne da ita?, hakan ya sa daurin ya kawata sosai a kanta Sam babu irin cikar nan irin tumbi daban mama daban, rigar ta bi shafafen cikinta sannan mamanta ta saka bra das sun zauna a muhalinsu Kafarta kuwa sanye take da takalmi mai tudun gaske baki sidik wanda ya haska fatar kafar tata, Ummu ba baka bace tana da hasken fata aman kuma ba fara bace Hannunta dauke da yar poss dinta ba kudi ba abin kudi ko daya a hannunta Sai da ta tsaya a tsakiya kafin cikin harshenta wanda larabci ya kwonta muraran ta furta" Asalamu alaikum Idannuwansa ya lumshe cike da jin kunyar wace ta fito mata, Ummu uwa ce a wajensa, ya so Zahra ta shigo dan ya kula da motsin son shigowarta, sannan ya ga Anmy ta so shigowa duda ya yi niyar dakatar da Anmy din domin a nan a yanzu ba a matsayin maman Najeeba take ba, aa , a matsayin mamansu su duka take, sai ya ga Ummu ta fito Amsawar da suka yi sunna kallonta ya saka ta yi murmushi a hankali bayan ta daga idannuwanta da ta saka masu karin gashin idon da ya zame mata jiki ko a yanzu da ta baiwa shekaru arba'in baya sam bata sake da gyare gyare ko dan ta yi zaman saudiya ne? Ita dai bata sake Cike da sanyin murya, dauke da tsararen murmushi har hakoran makarta biyu na azurfa suka bayana kansu ta furta" Alhamdulilah Godiya ta tabata a gareku adalan yan uwa Allah ya saka da alkhairi da kyauta masu girma da tsari A hankali ta kai dubanta wajen Sultan. Sai da ta k'ara sakin murmushi sannan ta ce" Allah ya taimakeka, kyautar *GIMBIYA NAJEEBA* zuwa ga yan uwanta su ne tagwayen gida da kuma shop place." Shi da kansa sai da ya k'ara kallonta da kallo irin na *DA GASKE KIKE?* Tagwayen gida dai, gidaje ne da ahalin sarauta suka kashe k'atuwar anguwa suke tanfatsa gidaje kala daban daban a ciki, mahaifiyar Najeeba ta yi dank'ara dank'aran gidajenta masu firgitarwa har k'waya bakwai, gidajen sun ginnu, k'asa ta ci kud'i sannan shop place d'in nan wajen da ake gabatar da kasuwanci ne, shagunna ne a laye har k'waya shida kowane da sunan shop place ba abinda ba'a siyarwa suma malakinta ne. Idanuwanta ta d'an bud'a masa sannan a hankali ta ce" har abinda ke ciki." (tana nufin kowace gida d'aya da shago d'aya da abinda gidan da shagon suka d'auka). Lalle ta kai duka murmushin nasarar da yayar zinaria ke yi na sun ci fadan sai ya ka ciki, ita bak'uwa ce, aman ta san gidajen nan babu na wasan yaro, sannan ta san shop place. Ai Nadia gaba d'aya ta ji wani girma ya hau kanta, ita ina ruwanta da wani duka, sam bata san mahimmanci hakan ba, ikon Allah take kallo a dan kankanin lokaci ta zama hajia (🤣 k'awata kennan) Murmushi ya yi daga cikin rawaninsa, tabas iyayensa sun gama magana, wato idan sauran sun bayar da kud'in jari da sarkar kwaliya, su sun bayar da muhali da uwar jari? Kansa ya ringa dan girgizawa a hankali , du ita d'in nan ce suke tarawa kasa? Da sun san, ko baki daya garin nan zasu bayar dan k'watar martabarta ita din ta gama zubarwa da basu yi wannan k'ok'arin ba, da sun san sun siyarwa kansu kunya ne kan kunya da basu yi irin wannan lamari ba. Sai da ya bushi iska yana gannin ta koma wajen Anmy ta zauna, fuskar Anmy ta fad'ad'a da farin ciki da annashuwa ya sauke ajiyar zuciya. Bayan sallamar nan, dama zai yi shiru ne du su gama gabatar da kyautarsu wa junnansu, idan sun gama mahaifiyarsa zata yi nasiha , sannan ta fad'i wace zata fara zuwa turaka kamar yanda abin yake a tsare. Anmy ce ta bud'a bakinta cikin sanyin murya, da mulkin dake cikin jinnin jikinta , cike da aji, da aiki da ilimi ta shiga yi masu nasiha. K'warai ta yi nuni da girman igiyar da ta rataya a kansu a yanzun, sannan ta yi masu nasiha da su yi koyi da kishi tsaftatace domin kuwa kishi halal ne aman idan har bai zarce ka'ida ba, ta yi masu nuni kan kowace ta girmama ta gaba da ita, su wanzar da zaman lafia a zuciyar mijinsu. A hanki ta dago ta ce" a yau *NAJEEBA* zata fara tarewa bisa k'a'ida, sannan Nadia dake amarya." A zabure ta d'ago dubanta da kanta dake kasa, ita kanta a cikin hali take na damuwa, tabbas ta lura idan ba da gaske ta yi ba tana cikin tsakiyar tashin hankalin ne da ake kira gaba k'ura baya damisa. Rabonsu da wani magana ta shiga tsakaninsu tun a bakin titin nan, sai dai irin kallonsa kan isar da sak'on zuciyarsa. A yau da ya d'auko mata Nadia a matsayin kishiya sam ta k'i aminta cewar soyaya suka yi, sai ta d'ora hakan a matsayin da saninsa, wata hanya ce ta ya nuna mata cewar ita ba kowan kowa bace, abinda take jin haushin kanta irin yanda abin ya mata ciwo, k'warai abin ya daketa harma fiye da kishiyar da take zaune cikakiya k'osashiya, fitinaniya wato Zinaria, Tabbas abin ya daketa, sam bata tab'a kawowa kanta cewar zata wayi gari ta ganta a irin rayuwar nan ba, yau gata ita najeeba zaune ga kud'i ga mulki aman sun kasa sakata kwaso shoki saima cikin tunani kala daban daban, shin tsoronsa nake? Shine tambayar da ta cika yiwa kanta. Eh ina tsoronsa, domin tamkar dodo haka yake a wajena, ban san kamaninsa ba, ban san zuciyarsa ba, ban san laifina a gareshi ba, idan dan ina kallonsa ne, ba wani abu bane sai son ganin wai kullum shi sai ya saka kwali? Wani sa'in kuwa idan na ga ana ta magana shi bai yi nakan kale shi dan na ga wai yana wajen kuwa? Fad'ana da matarsa bai shafe shi ba, ita dake zagina da munanan kalamai fa? *SHIN ME NA MASA DA YA SAKA YA FI TSANATA DA KOWA A DUNIYA?*, ni nake da abubuwan da zan tsaneka har mutuwarka, ka d'oran karan tsana kana tsargina? Sannan ka haye dukiyar marayu kana wasa da ita? An ce wai kasuwanci yake, yaushe yake fita kasuwar? (Kam Najeeb, kasuwa zai je? To sarkin wasan karan yara ne ba?), an ci an tayar da kai! Jin maganar bakin Anmy ya sakata jimk'e hannayen Zahrau, Ita? Ita fa? Zata tare a ina? D'akin wa? Turaka? Saima kalmar turaka ta b'ace mata b'at a bakinta,tabbas aurenta aka fara d'aurawa kafin a d'aura na Nadia, sannan idan maganar wace aka fara kawowa ne ita a gidan ta kwana, sai dai sam ba zata tare a turakar kowa ba! Idanuwansa a lumshe suke a lokacin da wannan magana ta fito daga bakin Anmy. Rintse idanuwansa kawai ya k'ara yi yana jin yanda yanzun ne zuciyarsa ta fara tafasa da abubuwan dake faruwa. A kan me za'a ce ga wace zata fara shiga d'akinsa? Shi sam, bai ajiye wannan a gurbin wace zata zo gareshi ba, ba an d'aura ba? Su barshi ya zartar da yanda yake so aurensa ya tafi. Anmy ta k'ara gyara zamanta tana hangen yanda Zinaria ta jinginar da kanta jikin kujerar da take zaune. Sosai take tausayin yarinyar, tana tausaya mata da irin kishin dake damunta, irin wannan kishi, abinda ya dace ta samu wace zata ringa tausarta tana saka ta a hanya tana tarota, sai dai ga dukan alamun mahaifiyarta wace ta fi kusanci da itan ba zata taimaka mata ba, sai yanzu ta fara cire zafin reaction d'inta na jin an d'aura auren Zahrau da mahaifinta, tabbas uwar gijiyarta na bada gudunmuwa wajen k'ara tunzura zuciyarta, tatanta d'aya ne, irin zargin da ya shiga zuciyarta a kansu ya zamo k'arya, idan har ya zama gaskiya ita kam bata da abinda zata iya yi sai zuba ido, kisa? Kisa fa? *Allah ya baku zaman lafia* A fili aka ringa amsawa kafin ta bada damar ana iya tafia. Talafota suka yi suka fara bi ta corridor d'in da zai kaita falonta suka fara fita. Sai su Nadia suma suka yi b'angarenta, sannan su Zahrau suka kamata suka fita da ita, ita ko b'angaren nata bata je ba suka nufi b'angaren Anmy da ita dan su shiryata a rakata. Suna shiga ta zame ta zube a k'asa a baki bakin shiga falon kafin ta saki kuka mai zafi mai cin rai. Wace ta yi mamaki kad'ai kishiyar Zahrau ce, domin ita bata san wannan launin kissar da ta gabatar ta dnane abinda ya daketa a cikin zuciyarta wato wai Nadia. Hannayenta take yarfewa a rikice ta ce" Wai Nadia? Aminiyata? Me na masa?" Da sauri su Ummu dake jira suka yo kanta, har rige rigen tambayar me ya samu Nadiar suke? Najeeba ta k'ara d'ago kanta ta ce" walahi basa soyaya, yaushe rabona da ita? Da sunna soyaya nice ta farkon da zata fara fad'awa domin ita rayuwar nan birgeta take, na tabbata daga baya ya saka haka dan kawai ya k'ara wulak'anta ni." Da mamaki kishiyar Zahrau ke kallon Najeeba kamar me. Najib dake zaune cen yana game da wayar Anmy ya dakata tun da ta fad'i yana ta kallonta, yanayinsa na nuni da hankalinsa a tashe ya ce" aunty Najeeba zaki b'ata kwaliyarki fa." Zahrau ta kalli kishiyarta ta sakar mata murmushi ta ce" aunty, ki je ki huta kin kwaso gajiya." Itama dacewar hakan ta gani, dan haka ta sakar mata murmushi kafin a sanyaye ta ce" Najeeba, ki yi hak'uri kin ji? Idan harma hakan ne ki d'auka hukucin Allah ne kasancewarta matarsa, ki yi hak'uri ki sanyaya zuciyarki ki rage kishinta kin ji?" Tunda take maganar bata wani baiwa abin importante ba, sai da ta ji kalmar *kishi*, Nimporte quoi! Ita zata yi kishi dan kawai ya yi aure? Kishi? Na me? Auren so ake yiwa kishi, mutumen da aka sani ake kishinsa, mutumen da ya gama kafa soyayarsa shi ake kishi ba wai haka kawai ba, ita ba kishi take ba, sam ba kishi take ba, tana jin haushin a mata kishiya da aminiyarta ne, me ta yi? Meye laifinta? Nadia ba abokiyar gabarta bace aman shine za'a had'ata gaba da ita? Wani ihu ta tak'ark'are zata saki sai dai abinda ya d'auke mata shi saukar yan yatsu biyar a fuskarta. A firgice ta d'ago dan ganin waye ya mata wannan hukunci a saman fuskar da ta gama shan gyare gyare? To mema ta yi na marin? Sama sama ta ji muryar kamar ba tata ba tana fad'in" Zaki min shiru ko sai na b'ab'ala maki k'afa a nan? Shirme! Shirmen banza! Maza mik'e ku saketa, maza mik'e zaki fice a kimtsaki ki je ne b'angarensa idan ya so dan Allah a kawo ki gunduwa gunduwa *Najeeba MUTALAB!* Yarinya an wani shagwab'aki kina iskanci? Ke kin san wanda kika bud'i baki kika yi magana sama sama a gabansa ko uwarki da ubanki ba zasu iya yi ba aman alfarmar Gimbiya ya biki da kallo? Au ke ga marar kunya, ga isashiya ga mai bakin magana ko?" Du a wannan lokacin kamaninta ne suka dawo wa Dayabu dake tsaye ya hard'e hannayensa. Tabbas ba'a tab'a kawo mace mai laushin da ta ringa kwana da su a saman katifa d'aya tana cencana su ba irinta , sannan ba'a tab'a kawo macen da idan ka yi abin hukunci zata hukuntaka ko a gaban ubanka ne irinta takan kashe dukiyarta domin baki d'aya y'ayan, bata tab'a ware tata ba, idan ta tashi wanka d'aya bayan d'aya take wanke y'ayan daga shekara zuwa shekara ne, da d'an girmansa yana hankalce da ita bata tab'a dan ta zo kan tata yar ta fi wanketa ko ta fi binta a laluma ba. Hararan da ta sakar masu ta cire d'aurin da akai mata na zarah Buhari sannan ta dakatar da Anmy ta ce" Wallahi, walahi da ba dan idan na fita na tatakata ba nima na raba rashin kunya a gaban SHAHEED ba, da sai na tataka banzar yarr nan! Ke har tunani kike dan yana son ki ya aure ki?" "Ummu?" Anmy ta fad'a da d'an k'arfi. Ummu ta ce" Oho shiiiiit, Anmy pls ki barni haba, wai ita uban wa ta fi zuciya ne? Ke? Ke najeeba? K'anwar bayansa zaki bud'i baki ki wani nuna baki damu ba dan an maki kishiya Nadia? To ki yiwa Allah kar ki damun idan kina so ki k'aro masa da Barirar! Aman fa ki sani, ko Ubanki MUTALAB da ya d'aure maki gindi kike iya shege, ko uwar taki gata a tsaye, ko su yayun naki nasu isa sultan Shaheed gurnanin zaki na zaune su ringa iya shege ba! Yau na ga ikon Allah! Dan an d'aura maki aure da shi ba yana nufin har kin kai wajen da zaki masa iskanci bane! Ke ko murza namiji zaki yi ki murza a k'uryar d'aki aman ba wai a gaban mutane ki nuna ke kin isa ba!" "Zaki daina bina da idanuwa kina wik'i wik'i da su ki mik'e Najeeba ko sai na nuna maki wacece *MARIAMA BIN ABDALLAH* *UMMU?*!" Zabura ta yi daga zaunen da take a kasa ta mike tana kara zaro idannuwan da sauri ta aniya kokarin yin wajen Anmy sai kara kallon Mahaifiyar nata take [31/03 à 19:24] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 39 Har waiwayen Ummu take tana hada kafa wajen sauri Anmy ta kamata ta juyo ta kalli Ummu ta yi kwafa ta jata suka shige ciki Dama wace ta yi saura datijuwar nan ce kadai wace zata kimtsata wato Fadimatu Hankali kwonce ta sakata cikin wani ruwa mai kanshin gaske da sanyaya zuciya Tana fitar da ita ta kara bin jikinta da wani mai lalausa mai sanyin kamshi Wasu kayan baci dake cikin kwalinsu ne ta ciro, rigar fata ce doguwa da pant dinta da bra dinta Rigar mai shegen kyau ce abin ba'a magana, iein mai santsin nan ce hakan ya sa take bin jiki masha Allah Cike da nutsuwa ta zauna ta kara gyara mata gyaran gashin da akai mata Wannan uwar kwaliya baki daya an wanketa an zubar da hodar Kamaninta natural shine a tatare da ita Baby face dinta ta bayana, ga lebenta mai kyan tsari Man lebe mai wani irin kanshi aka bi da lebunnanta Kwali kawai aka saka mata kafin a rufa mata bargo wani sansanyan kanshin turaran wuta ya shiga bin jikinta baki daya Har gashinta da kalar turaran gashin da aka mata anfani da shi A yau dai Najeeba kanta ta san ko wa ya sameeta a haka ya samu gata mai matukar girma da tsayawa a zuci Hijab fari kar, hade da Alkyaba wata kalar blue mai duhu sabuwa dal aka luluba mata a saman suturarta Zaunar da ita ta yi tana kallonta A hankali ta ce" Najeeba, ko me zaki tarar ki kasance mai yin biyaya da Hakuri Ki sani ko me kike ji a zuciyarki ki dane shi, domin kuwa idan har kika ringa falasa shi to fa kece a matsala kin ji? Kanta ta daga a sanyaye, domin baki daya jikinta ya gama mutuwa ne, wata faduwar gaba take ji, takan yi tunanin wai da gaske zata je dakin mutumen dake miji a gareta? Wannan shiri da ake mata shin hasashen da take ne zai faru da ita? Wannan rakiya ba kowa ya yita ba sai Jakadiya A lokacin da aka yi kiranta itace mafi datijantaka, ita ta raka Anmy, yau gata zata yi rakiya ta uku a matan sarki Cike take da fargaba, ta so ta ti tambayar aa, yaya za'a raka masa mace biyu? Sai dai ba hali domin ta san idan da ba da sanninsu ba, ba za'a iya kai masa wata kuma a kara kai masa wata ba A hankali suke takawa sunna kara kusantar dakin Yanzu yanzu ta dawo daga rakiyar Gimbiya NADIA bisa umarnin amintace ya shaida mata umarnin mai wukar yanka ne Ta shiga rudu, mace biyu zai tare da ita ko me? Jiki sanyaye ta karasa da ita tafkeken falon da ya kasance shine falonsa na karshe wato na sirrinsa, wanda matayensa ke shiga, daga su sai dakinsa na baci Ta jima tsugune kanta kasa tana jiran uban gidansu Najeeba dake zaune saman kujerar da ta yiwa kanta masauki ta daga kanta cike da nutsuwa tana bin falon da kallo Tabas bata taba gannin wajen da ya birgeta irin wajen nan ba Tsarin falon nan ya sakata yin saranda cewar lalle sarkin Damagaram ba karamin mutun bane Sanyin Ac din ya sakata yin lakwas tana sauraron yanda cikinta ya dan fara neman agaji domin a gaskiya yinwa take ji rabinta da abincin kirki har ta manta, sai kima mata abubuwa suke, Dubanta ta maido wajen Jakadiya Kanta a kasa tun gurfanar da ta yi, Hakan ya bata mamaki tana dubanta ta ce" aman mama ki daga ki huta mana Da sauri Jakadiya ta kara sada kanta ta shiga Fadin" ALLAH ya taimakeki ai ban gaji ba, Allah ya kara maki lafiya Gimbiyar Gimbiyoyi, sannunki da zama uwar gidan Mai damagaram Murmushi Najeeba ta yi tana kara kallonta ta ce" to tashi ko tafi idan ya zo zan ce da shi kina gaishe shi Jakadiya kam abin ya gama kasheta da mamaki, kai? Tana gaishe shi? Ita wa? Kara sada kanta ta yi ta ringa neman afuwa da fadin ba sai an ce tana gaishe shi Wannan lamari ya baiwa Najeeba Nishadi har kara kallonta take tana so lale lale sai ta dago kanta kamar wara wace take gaban sirikinta? Ita dai Jakadiya cike take da tsoro da al'ajabin Najeebar, so take ta bata damar da zata kara gurfanawa aman Najeebar ta hanna Najeeba ta kara sakin murmushi ta ce" ki tashi ko ki bata min rai fa? Na salame ki Ai kuwa da sauri ta kara gurfanawa tana Allah ya huci zuciyarta, kafin ta mike ta yo waje da sauri Najeeba ta zaro idannuwanta a fili ta furta" kai? To meye dan kin bata min ran? Lalle gifan sarauta na tare da wani lamari mai girma Komawa ta yi ta kara zaunawa da kyau ta shiga tunanin rayuwa Saloon dinta, yaya yake tafia? Kudadenta ina aka kilace mata? Kayan aikinta shin ana kular mata da su? Domin fa, zata koma bakin aikinta, zata nemi kudinta kamar yanda ta fara, auren sarki ba zai hannata nema ba! Kamar wasa zama ya sameta Tun tana daga kanta tana kallon agogo har karfe dayan dare ya yi bata ga alamun kowa ba, bata ji motsin kowa ba A hankali ta cire kafafuwanta daga cikin lalausan takalmin da aka saka mata na baci ta dora kafafuwan nata saman kujerar nan ta juya ta yi kwonce ta mike kafafuwan nata sannan ta sauke alkuabar daga jikinta baki daya dan ta ji dadin baci A kasan ranta ta furta" ai da gannin jajayan idannuwan nan nasa na mashaya ne, mai yiwuwa an labe wani wajen ana aiki marar kyau Kafadunta ta daga tana ayanna ta fi nono fari, sannan ita kuwa da ta mareni sai na fadawa Abih! A hankali ta lumshe idannuwanta tana mai neman baci, baci take so ta yi ta huta, ta ajiye matsalolinta gefe zata waiwayesu ne daya bayan daya domin a yanda ta fahimci rayuwa zuwa yanzu idan ba ita da kanta zata daukarwa kanta mataki ba, to fa bata da wanda zata fadawa ya shige mata gaba A hankali ta ringa lumshe idannuwanta tun tana cike da tunanin duniya da matsalolinta har ta fara gyangyadi Cen cikin gyangyadinta ta ji wani ihu daya tak wanda ya sakata zabura a firgice har tana gurdewa ta fado daga saman kujerar da take kwonce A tsorace ta kai dubanta wajen agogon dakin mai dauke da gilass Karfe uku har da minti arba'in da bakwai, wato hudu dai ta kusa A tsorace ta kara saurarawa dan jin shin ihun ta ji ko kuwa mafarki take cike da mamakin har ta yi bacin awa kusan uku? Murya ce ta shiga kunnenta a galabaice ana furta" *wayo Allahna zan mutu, wayo na tuba ka sarara min haka, wayo dan Allah kar ka kara turawa zafi nake ji kar ka yaga ni biyu, innalilahi wa'ina ilaihi raj'une wahala* A hankali ta kifta idannuwanta sukai mata dan luuuuuu sannan ta kuma budawa Irin kalaman da kunnayenta suka kuma tsinto mata sune kamar haka" *ta fi karfina, wayo zan mutu wayo ni Allahna ka taimakeni Sarki* Wani irin ras, hade da kamewar bayan kai ne ya sameta lokaci daya, Mikewa ta yi tsaye ta juya wajen da ta fi jin magangannun na fitowa Muryar kawarta ce, aminiyarta ce, wace take tamkar yar uwarta ce ke fitowa daga cikin dakin cen wanda ya fi kowane nuni da shine dakinsa Irin magangannun dake fitowa ko mahaukaciya ce ita sun kai su nuna mata ga abinda ake nufi da su, aman sai zuciyarta ke karyatawa take ce mata" ke kuwa, yau din ai ranarki ne Wata zuciyar ta furta" ranata kuma? Wata ta bata amsa da cewar" kwarai , ai a gaban kowa aka tsayar da hakan, sannan har aka kawo ki dan karbar ranar taki To ko dai an cenza ne basu sani ba suka kawo ni? Kai ina, wani cenji? Irin kalaman dake kara fitowa suka saka a hankali ta ringa jin hannayenta na yi mata rawa, gaban jikinta na kwasan rawar hakama zuciyarta na yi mata barazana da tarwatsewa *WULAKANCI NE, HAKA GIDAN SARAUTA YAKE NE, KO KUWA IYAKANTARWA CE?* a hankali tun tana jin kukan sama sama har ya ringa ragewa Sam ko sannin cewa a tsaye take ko a zaune bata yi ba, abinda ta sani ita dai kunnayenta na jiyo mata abubuwan da zuciyarta ke bata fasara nan take An kuma daukan wani lokacin a haka har ta daina jiyo kukan Nadia, da magiyarta Tana nan tsaye har kunnayenta suka fara jiyo kiraye kirayen sallar farko Kafafuwanta sam bata jin su a jikinta, abinda ta fi ji a yanzun shine irin yanda zuciyarta ta cinkushe da baki sannan idannuwanta suka rufe da zubar da hawayen da bata san sunna fitowa daga gurbin idannuwanta ba Kofar take kallo A lokacin da aka shiga dan kusur kusur din son bude kofar Kara tsurawa kofar ido ta yi tana kallo har aka gama budewa Bayan budewarma an dan dauki yan mintuna kafin fuskar ta fara bayannuwa a idannuwanta Fuskar nan mai haske, mai walwali, mai dauke da kyakyawan saje, mai yalwatacen gashin gida da ido, mai dan fadi , mai dauke da dogon hanci mai dogon karan hanci, mai dauke da idannuwa masu zanen Kwalin Allah ne ta bayana a gabanta A yanzun, tana tunanin cikin biyu daya, ko ta samu matsalar gani har amininta ya fara yi mata gizo a gidan aurenta, ko kuwa ta haukace, ko kuwa ta samu shanyewar barin jiki Tun tana hangensa daga nesa, har kusancinsu ya kara tsananta har ya kasance ya bayana gashi gata face to face sunna kallon junnansu a daidai lokacin da ta tabata shi ne a gabanta a tsaye Lebunnanta ne suka kwashi rawar da hannayenta ke yi a lokaci daya ta dago da yar yatsarta ta yi nuni a kansa Ta jima tana barin lebe kafin da kyar ta samu kalaman su fito daga bakinta ta ce" *KAI? ME KAKE A GIDAN NAN? WA KE KUKA?* fuskarta yake kallo tsai har cikin kyawawan idannuwanta masu dauke da eye ball masu shegen kyau da gashin idonta natural domin an cire mata karin sai nata da suke cike da baki sidik, sai lebunnanta dake rawa rawa tamkar ba nata ba da kalaman da suka fito daga bakinta A zabure kamar an tunzurata ta daga kafarta da ta mata nauyi sannan ta dauki mujirya ta damko hannunsa na dama wanda hakan ya saka shi sada dubansa wajen da ta riko hannun nasa da nata hannun ta dago sosai tana kallonsa Muryarta a yanzu ta hadu da kamar zata fashe da kuka ta ce" dan Allah, ka taimaka kar zuciyata ta tsaya, ka fada min abinda ya kawoka gidan nan, har dakin nan, har cikin dakin cen, sannan nake jin muryar aminiyata a ciki? *Kai din wanene?* Da hannayenta bibiyu ne ta rike masa hannunsa guda, tuni jikinta ya dauki wani zafi na firgici da tashin hankali Idannuwansa ya lumshe kafin ya vude yana kuma kallonta Wannan karon a hankali ya ringa cenza kallon da idannuwansa ke mata masu laushi zuwa wanda ya saba yi mata Kasancewar fuskar tasa take kallo, sannan cikin idannuwan nasa, a lokacin da idannuwansa suka rikide zuwa wanda ya jima yana binta da shi, wato kallon tsanar nan sai kawai mai rawani ya fado tar tar a kan hakan A yanzun kam ba kanta aka soka ba, aa, guduma ce aka duma mata baki dayanta wanda hakan ya sakata yin luuuuuuu tana daukewa kamar injin da ya mutu a mota ana faman sai ya tashi Tareta ya yi baki dayanta ta fada jikinsa, kamshin turaranta, santsin fatar jikinta da rigar nan wace ta yaye domin dama mai tsaga ce ta yi gefe da irin yanda gashin kanta ya yi luf luf a kan fatarta mai masifar kyau da tsari suka sauka baki daya a jikinsa a lokacin da bai shirya ba A hankali ya yi kasa da ita saman tiles din dakin ya kasance tana saman hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuwa ya kara talabeta da shi Wani gurnanin kuka ta dan saki kafin ta furzar da iska tsai kuma idannuwansa take kallo A hankali ta dago hannunta na dama baki daya jikinta na rawa ta kai kusa da fuskarsa A hankali ta shafa fuskar dan kara tabatarwa idan wai shi din ne? Kafin ta saki wani dan marayan kuka tana jan numfashinta Baki daya abubuwan da suka ringa faruwa tsakaninsu daki daki suka ringa fadowa cikin zuciyarta A hankali ta kara shafa fuskarsa wace tuni idannuwansu sun yi ja haka kuma saman goshinsa ya fitar da wata jijiya wace bata san ko ta meye ba Muryarta a cen ciki, idannuwanta na daukewa , zuciyarta na son yin karfin hali aman ta kasa ta kara damkar hannunsa a hankaki ta furta" *NA TSANE KA*! Ban yaba jin tsanar mutun irin...........sai kawai hannun nata ya saki luuuuu ta dauke wuta Fuskarta yake kall9 da wani irin kallo mai cike da son gane wani abu Kamar wanda yake so ido rufe sai ya ga shinfidar fuskarta ya ga abinda aka hada aka yi fuskar tata A hankali ya dago hannun nasa dake wajen cikinta ya kawo wajen fuskarta A sanyaye ya shafa gefen fuskar tata still yana kallon fuskar tata, lokaci daya kuma gabansa ya tsananta faduwa kan abinda bai san dalili ba A hankali ya ringa kara kusanta kusanci da fuskarsa da tata Idannuwansa ya tsinci kansa da lumshewa kafin ya kai wani lamari mai girman da bai san me ya aike shi ba Lebunansa ya dora saman nata masu dauke da man leben nan ( lips) din nan mai kanshi da zaki zaki da sulbi Harshensa ne ya dan lashi abin lokaci daya kuma ya zabura ya mike bayan ya saketa ta idasa kwonci a wajen Kafafuwansa ya mikar ya zauna a kasan shima, a hankali ya sada kansa kasa Tabas ya yi wannan lamari dan ya hukuntata, hukuncinsa gareta kuwa shine ya nuna mata idan ka rike mutuncinka irin abinda kake gani a wajen mijinka, ya yi haka ne dan ta kara jin tsanar rayuwar da ta aikatawa kanta Alkawari ya daukarwa kansa sai ya hukuntata a waje, sai gashi ta zama matarsa, hakan ya kara bashi bacin ran da yake son hukuntata Sai abu na gaba ya san cewa daga an jima kadan za'a zo neman zanin kwananta, domin tun a jiya wace ta yi masa message din zata turo sai ya yi mamakin hakan dan kuwa zinaria ce, ya yi haka dan a kai zannin nan da gaske domin ya tabata ba haka kawai ta nemi dauka ba, ya san da sannin ita bata da shi a tare da ita shi ya sa ya amshi na Nadia bayan ya fada mata bukatarsa Me ya sumar da ita? Me ya sa ta furta masa kalaman tsana? Bai yi tunanin zata farka ba, so ya yi tana bacin nan ya kaita saman bed din ya maye gurbinta a cikin shaidar budurcin nan sai gashi ta farka, harma ta yi tsaye ta ga fuskarsa a yanzu lokacind a bai so ta gani da wuri wuri haka ba Idannuwansa ya kara lumshewa ya mije tsaye Haka kawai yake jin babu dadi a ransa, ba dan komai ba sai dan kasancewarsa mutun mai son fita hakin mutane Kwarai ita din wata halita ce da ta masa katutu a kwonciyar hankalinsa, aman yana so ne ya gasata da kansa ba wai ta hanyar cin fuska haka ba! Daukanta ya yi cimak a hankali ya nufi dakin da ita Nadia dake baci saman kujerar da ya ajiyeta ya kai dubansa, ko kotsawa bata yi ba Shinfide Najeeba ya yi saman shaidar budurcin Nadia sannan ya dauki Nadiar ya nufi dayan dakinsa da ita Itama shinfideta ya yi ya kunna mata Ac, sannan ya janyi kofar ya rufe ya koma wajen da Najeeba take Ya jima tsaye yana binta da kallo Cen ya sauke ajiyar zuciya yana tabe bakinsa ya nufi dardumarwa ya dauka ya shinfida ya shiga gabatar da sallah A lokacin da ya gama yana zaune yana jan carbi har kira ya shigo wayarsa Mikewa ya yi ya dauko ya kuma kai dubansa wajen Najeeba, sarai ta farka, aman kuma idannuwanta rintse ne suke ba baci take ba, ta kasa katabus da jikinta ne zazabi ya rufeta, ga irin kunnan da ranta ke yi kamar zata mutu take ji Wayar ya danna ya kara a kunnensa Kar a min wannan al'adar SHAHEED, Muryar Anmy ta doki kunnensa a hankali ta ci gaba da fadin" Jakadiya ce ta yi safiya wai daga bangaren ZINARIA an turota daukan zani? Ina jin ko ita ba'a yi mata daukan zanin nan ba bare yanzu ta saka a yiwa yarinya? Wannan abin sam bashi da wani tsari, a kan me za'a dauki zani a je ana yawo da shi? Jinnin yarinyata haka kawai har a je a yi mata wani asiri da shi? Bana so, kar a dauka, a bar min , kai Shaheed ka wanke min da kanka bisa amana Wannan karon idannuwansa ya lumshe, domin ta buda nata idannuwan tana jin muryar Anmy dinta ras dan kuwa ba wani hatsaniya adakoy ba, sanyin safia ce, gashi sosai a kusa da ita yake yana binta da kallo Anmy ta ce" kana ji na kuwa? Idannuwansa ya sake budewa yana kallon Najeeba, ido cikin ido suka kalli junnansu wanda hakan ya haifar masu da faduwar gaba, Da sauri ta cire dubanta a kansa, so take bakinta ya rage mata nauyi ta budi baki ta fada masa maganar dake cin zuciyarta Lale ta yarda *ya tsane ta*, kamar yanda ya fada a kusan mota bai taba kyanar halita irinta ba, A yau itama ta rantse sai bakinta ya furta masa irin girman tsanar da ta masa Hannunta ne ya kai kan lema lema, hakan ya sa ta kai hannun ta shafo da kyau sannan ta dago hannun nata A hankali ta ringa kallon abin, sai a nan kalaman Anmy suka fasara mata abinda take nufi Kwonce ne take a saman saman lemar budurcin wata? Sai da tsigar jikinta ta tashi kafin ta kwala karan da ya saka shi saurin katse kiran Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une! Ta fada da karfinta tana janye jikinta cike da kyankyami da tashin hankali Allah ya isana! Allah ya isana! Na tsaneka, na tsani Nadia, tabas ni Najeeba koda maza sun kare ba zan taba kallonka a matsayin wanda zan iya rayuwa da shi ba! Ka raba ni da masoyina, ka raba ni da du wani masoyina,, zaka sakeni ne na je na auri HUZAIFANA Idannuwansa lumshe yake sauraron rashin da'ar da take masa *HUZAIFANA* Zaka sake ni ne Idannuwansa ya buda a karo na ba adadi ya kuma kallonta A hankali ya ja zif din rigarsa doguwa wace ya yi sallah da ita dan ya samu ya cire rigar cikin salama Sama ya yi da rigar ya cireta baki daya daga jikinsa ya yar a nan kasa Gajeran wando ne kwal a jikinsa baki mai rige cinyoyin nan Hannunsa ya mika daya tak ya damkota kafin ya saka dayan ya daukota cimak ya saukota daga saman bed din, domin shima ba zai iya kuma anfani da bed din ba dan kazantar dake sama Rigar jikinta fara da ta gogi abubuwan ya kama ya daga ta sama ya cire mata ita a lokacin da yake karasawa saman doguwar kujerar dakin Baki daya ta zazaro idannuwanta tana kallonsa, daga shi sai wandon nan, gaba daya du wata halitar karfi da firgitarwa ta bayana a jikinsa A hankali ya saka hannunsa daya ya mayar da ita kafin ya kama bra din dake jikinta da karfi ya cirata ta gaba hakan ya sa du suka fito a bayane Kafarsa ya kuma sakawa ya mayar da ita sannan ya ringa son daidaita bugun zuciyarsa tamkar mai cutar athsma Nonuwanta dake fili ya ringa kallo kafin ya kai dubansa saman fafadan kwonkwasonta da cikakun mazaunanta da shafafen cikinta Yanzu a nan ne ta kai ta banzatar? Idannuwansa suka rufe, hankalinsa ya tashi, Magangannun ambasador, maganarta na ta je ta auri Huzaifanta du suka ringa yawo a kwonyarsa Lokaci daya ya saka hannunsa wajen PANT dinta ya ja....................... To madallah Sai atinin kou?😌😌😌😌 [31/03 à 19:24] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 40 Hannunsa na dama ya saka ya janye dan siririn igiyar wandon da bashi da wani fadi sai wata igiya da ta rike shi Sam baya risina dubansa ko kawar da idannuwansa a kan halitarta Maimakun ya ji a ransa baya son kallon wani waje nata sai baki daya komai ya zame masa abin kallo Yana dane da ita ne da kafafuwansa hakan ya saka yake kallon yanda take son karfi da yaji ta amshi kanta idannuwanta rintse tana ta kokowa A hankali, sannan farkon budar bakinsa tun da aka fara shagulgulan nan a hankali ya ce" me yasa kike son kwace kanki bayan zan baki abinda kike so ne? Najeeba idannuwanta rintse kawai suke, hawaye ne ke bin gefen kumatunta a hankali yana gangara wajen kunnayenta wani kuwa ya zarce abinsa A hankali ya saka hannayensa ya rike nata hakan ya sa take dagowa da kirjinta tana komawa yarab ta fadi saman kujerar Mamanta dake dauke da tsini ya tsurawa ido Duba irin na tsanaki, irin yanda kawunnan suke da dan tsini sannan suka dan baje ya ringa kallo A hankali yana rike da hannayen nan nata kafafuwansa matse da cinyoyinta ya sado da fuskarsa Sai fa ya rintse idannuwansa dan abinda zai aikata din sosai yake jin takaicinsa A hankali ya dora lebensa sama, cikin nutsiwa ya shiga yagaya leben nasa a sama yana karawa A hankali dumin lebunansa da na harshensa ke sauka a saman mamanta abinda bata taba gani ko hasashen zai faru da ita ba Wani irin dogon numfashi ta dauka wanda da kyar ya dawo jikinta na tsabar firgici da tashin hankali A hankali, ba da mugunta ba, irin lamarin nan wanda zai shiga jikin mutun ya kasara zuciyarsa ya ringa zuwar mata a nufinsa na ya horata, a nufinsa na ya ringa kwadaita mata haka a kulun yana barinta cikin wahalar abin Ka'in da na'in ya ringa tsotsarsu ta hanyar baiwa kowane hakinsa a tsanaki Idan ya kama wannan ya zo saki har sai ya dan ja shi kadan sannan ya sake shi ya kama wancen A hankali da harshensa ya ringa yin sama har ya kai wajen wuyanta Hadewa ya yi da harshen nasa da kuma gashin fuskarsa da habarsa ya ringa binta slowly, passionately, a hankali ya kama habarta ya ringa tsotsa sannu sannu kafin ya karasa wajen bakinta Irin yanda baki daya abin ya zo mata ya girmami tunaninta A hankali ta ringa jin tamkar ana zare mata lakah Du wani dan kuzarinta sai ya koma iya zuciyarta aman ta kasa kwakwaran motsin da zata iya hana wannan tashin hankali wanzuwa a rayuwarta Idannuwanta ta rintse da sauri sakamakon jin lalausan lebunansa saman nata A hankali ya kai idannuwansa ya lumshe sakamakon jin dumin bakinta da kuma kamshin da yake fitarwa Kara lumshe idannuwansa ya yi ya damki harshenta ya ringa tsotsa yana karawa har sai da ya yarda cewar ta gama mutuwar jiki sannan ya sasautawa matsetan da ya yi A hankali ya ringa kai harshensa du wani lungu da sako na jikinta wanda duda kasancewarta bakon shiga sam bata ji ciwo ba sai wani irin madaukakin abu dake mata yawo a ilahirin jikinta sannan tana jin kamarma wace take yin fitsari A hankali harshensa ya dira a saman zumbulkon cibinta domin cibiyarta bata da rami dan zumbulko ne da ita dan karami Da lebensa ya ringa yawo a kan wajen hakan ya saka ta kara rintse idannuwanta a hankali ta furta" innalilahi wa'ina ilaihi raj'une Tana mai kankame jikinta da take ji yana daukan wani ikon Allah daban Tabas Sultan ya san kan tsiya domin a wannan lokacin du wani sako da lungu na jikinta sai da ya yi kokarin ajiye lebensa da bakinsa da harshensa cike da wata irin kulawar da shi kansa bai san abin ya kai cen ba A hankali ua saka hannunsa ya damki cinyarta da babar forme dinta wace ke kara shiga idannuwansa A lokacin da ya raba kafafuwanta a lokacin ya ga irin ikon Allahn dake zuba daga jikinta Idannuwansa ya tsura sosai duda kokarinta ta rufe jikinta aman ta kasa domin karfin ba wani bane a jikin nata sannan du in ta yinkura dan rufewar yakan karewa ya hanna ne da hannayensa Yar yatsarsa ya saka ya dangwalo abin a hannunsa, Yaukinsa da kaurinsa ya tabatar masa lalle shi din ne Lahauli wala kuwata ila bilah, Ko tarayar da ya yi da Nadia a yanzu sai da ya yi anfani da liquide wanda zai bashi damar shiga jikinta, asalima a kulun yana ajiye da su ne a kusa da matasan kansa domin Zinaria ce ta koya masa anfani da ire iren abin nan dan kulun sai ya matsa a jikinta yake iya anfanuwa da ita, to hakan ce ta kasance da Nadiama domin ya yi iya kokarinsa dan gannin ta sako sosai ya samu yanda yake so , ba laifi tana da ni'imarta aman dole sai da ya zuba domin idan har ya kisanceta a iya ni'imar jikinta tabas zai mugun ji mata rauni ne A yanzu abinda ke zuba daga jikin Najeeba ya saka shi kallo har sai da ya ji jikinsa na harbawa Da sauri ya saki yana hade kafafuwan nata yana jin jikinsa na kara rikice masa, daukanta ya kuma yi tamkar marar lafia ya maida ita saman bed din sannan ya janyo abin rufa ya rufa mata har kusa da wuyanta yana jin harta hannayensa rawa suke Kara rage tsayinsa ya yi yana kallonta , ita kuwa sai rintse ido take kamar zata yi hauka a cikin zuciyarta, she cnn't believe it, A yau gatanan kwonce, tsirara haihuwar uwarta , kato, Namiji ya gama sideta tas tas Namijinma mutumen da suka ringa zama wajen hutu tare, sunna hira tare, har suka buga basket ball Uwa uba namijin da shine SULTAN SHAHEED, Yau shine ya gama gannin jikin nan nata da take matukar boyewa tun karfinta Yau ya gama kalleta ciki da bay, zata iya cewa ya fita sannin me jikinta ya kumsa a yanzun domin ita dai ba zata iya fadin wanni wajen na jikinta kama da me yake ba domin a rayuwarta mutun ce ita mai matukar kunyar ta kali wajen da yake da nauyi a jikinta , sam bata cikin yan matan dake daukan hotunnan jikinsu ko ta tsaya fama da madubi dan ta ga yannayin jikinta A yau, itane bayan tana ji tana ganni ta zama shaidar me namiji ya gama yi da wata mace, sannan ya dawo ya rike mata hannu ya aiwatar da abubuwan nan a jikinta aman cikin ikon Allah ta rasa kuzarin da zata iya kwatar kanta a gabansa? Sai da ya dora hannunsa a gefen fuskarta hakan ya sa a tsorace ta kuma buda idannuwanta ta sauke a fuskarsa: Daf da daf suke da junna ashe Idansa guda ya kane mata ya sakar mata wani irin murmushin da bata taba gannin namiji na yin irinsa ba kafin ya mike tsaye Da sauri ya juya dan kar ta ga yannayin da ya shiga, itama gannin dan gajeran wandon ya sakata saurin rintse idannuwanta cike da tsoro tana jin inama zata iya yin ihun da baki daya gidan sai ya girgiza? Da ta yi da sunnan Anmy dan ta zo ta rabata da dakin nan kafin ta mace Sai ta ringa neman ta kuma sumewa aman abin ya gagara Sai ta ringa neman inama ta farka ta ganta a falo ace baci ne take mai tsanani Ba bugu, ba zagi, ba muguwar magana, a sanyaye ya samar da kusanci da jikinta ya shige ya barta a halin da bata san yaya take ciki ba Cikinta take ji ya kule mata kamar wace ta hadu da kumburin ciki kafin mararta ta kara daure mata sai ciwo ya fara a hankali a hankali yana bala mata sama sama (haba dole, wannan uban tsumi a barka a halin kaka nakayi?) Idannuwansa ya rintse da sukan karfinsa a lokacin da yake tsarkake jikinsa Maida hankali ya yi ya gama ya dauro tawul tare da riko wani a hannunsa Direct wajen suturarsa ya karasa ya buda ya ciro tufafinsa Ba tare da wani damuwa ba ya kimtsa jikinsa, sannan ya nada rawaninsa A lokacin da ya zo fita kusan sumewar ta kuma yi, ashe shi ne? Wayo shi ne! Lalle najeeba an yi gaula wawa mahaukaciya ta bugawa a jarida Idannuwanta ta mayar ta rintse tana jin yanda suke mata zafi sosai, Yana fitowa ya koma inda Nadia ke kwonce Bacinta take har zuwa lokacin dan haka bai tasheta ba sai ya nemi waje ya zauna da waya a hannunsa Auntyn Nadia ya fara yiwa test mesage cewar ta zo, kafin ya shiga tunnanin wanda zai nema ya zo ya tafi da Najeeba Tun da ta farka ta kimtsa jikinta ta yi wajen yaren Daya bayan daya ta ringa binsu tana tsayawa ka yi wanka ka fito , tana tsaye ta ga shirinka kafin ka fito wajen cin abinci Sai da ta zo kan NUSAIBA ta shirya yarinyar tsaf sannan ta dorata a bayanta ta fito da ita Ido hudu suka yi da shi zaune dare dare a saman daya daga cikin manyan kujerun falon Anmy, gefensa DAYABU ne shima cikin shigar sabuwar shada yana zaune yana kallon yanda kannensa suka yo fes fes da su daga inda yake zaune yana fadawa Bilkissu ta tabatar kowa ya samu abinda yake son ci NUSAIBA na jin muryarsa ta shiga kokarin dirowa tana fadin" yaya Murmushi ya yi ya mike da sauri ya amsheta a hannunta ya rungumeta yana sinsina kamshin da take ya ce" kai, wa ya fesa maki turare mai dadi? Ummu ta mika hannu ta dauki hijab dinta ta saka tana yatsina bakinta Dayabu ne ya fara dukawa har kasa ya gaishe da Ummu Cike da kulawa ta ringa amsawa kafin ta ce" DAYABU a nan ba ka kwana? Abih ya hade rai ya kawar da kansa daga kanta yana turo bakinsa Anmy ta ce" yaya, walahi tana daga hannu ta wankawa yarinyata mari, abin nan kwana na yi ina zabura, ashe dai bata fasa mari ba? Abih ya kaleta da sauri ya ce" mari? Anmy ta ce " kwarai kuwa Dubansa ya maida wajen Ummu, a dake ya ce" Nana me ya sa zaki dakar min fuskar *y'ata?*, kin san da saboda y'ayana ina iya yin shara'a da mutun? Baki ta yatsina ta ki bashi amsa hakan ya sa ya kara hasala ya ce" marar kunyar banza kawai malama kin zo kina wani cika fuska ko gaisheni kin kasa yi a gabanki sai dan cikinki ne ya gaishe ni! A hasale ta dube shi ta ce" MUTALAB wai ina dalili ne ni kake nemana da masifa haka? Haba a barni na huta za'a wani dameni da neman tashin hankali mutun ya girma sai neman fada haka kawai? Abih ya kureta da kallo, yanda take maganar tana ruko idannuwanta sai ya ji murmushi ya subuce masa a bayane, da sauri ya gimshe fuskarsa ya mike yana dan sosa kansa yana satar kallon Anmy da DAYABU Gannin shi suke kallo kuma sun ga abinda ya yin ya saka shi hade fuska ya ce" dama abinda ya kawo ni dan mu yiwa baki rakiya ne Bilkissu, na ga kin tara fitsararu a gidan naki na yi nan Ummu ta kara turo baki tana kallon bayansa ya juya da sauri, Har sai da ya kai kofa ya juyo, ai kuwa suka yi ido hudu da ita Wani irin shanye dubansa ya yi a kanta kafin ya dan motsa bakinsa kasan makogwaronsa ya furta" *Ki min rai* Da sauri ta kawar da dubanta tana jin wani iri a kan jarumin uban y'arta, tunda ta rabu da aurensa bata taba yin wani auren ba, ita ba tsufa ba, ita ba rashin lafia ba, kawai zaman da ta yi da shi ya saka ta kasa gane wani yaren, ta saba sa rayuwa da shi da irin garajensa da fadansa da hayaniyarsa uwa uba da tsarin soyayarsa Dubanta ta kai wajen DAYABU da Anmy da niyar tambayarsu wai zaman me suke ne? Sai ta ga tsuru ita suke kallo Sai kawai ta daburce a dan rikice ta ce" Kai meye kake kalona? Sai kuma ta sosa goshinta ta ce" ka yi ka kai min su makaranta ka wuce aikinka fa? Bana son shashanci ka zo ka wani zauna ana tausarka sai ka ga kanwarka da ka kai gidan miji jiya ba! Tana fada ne tana kokarin shigewa ciki Da ido suka rakata har ta shige kafin su kali junna su sakarwa junna murmushi Zahrau ce ta fito sanye da hijab tana dan sauri ta ce" Anmy, ina zuwa zan je bangaren SULTAN Anmy ta dan zabura ta kaleta sai kuma ta koma ta zauna a hankali ta gyada mata kai Ficewa ta yi hankali kwonce ta nufi bangaren A lokacin da ta shigo abinda ta ganni ne ya bata mamaki, auntyn Nadia ce rike da hannunta sunna tafe a hankali zasu bi ta corridor su shige ciki Irin tafiar da take Zahrau ta bi da kallo kafin ta kai tsugune ta shiga gaishe shi Kamar yanda ya saba amsawa hakan ce ta faru kafin ya yi mata nuni da dakinsa Kanta ta kara sadawa kafin ta mike a hankali ta nufi dakin, zuciyarta kuwa cike da sake sake da son sannin abinda Nadia ta yi a bangarensa da irin tafiarta Saurin korar abin ta yi a ranta dan gudun kar zargin ya yi yawa ta shiga dakin Irin yanda ta yi karo da bra, da pant da rigar Najeeba ya sakata saurin shiga nemanta a cikin dakin Idannuwanta ya sauka a fuskarta hakan ya sa ta nufeta da sauri tana kiran sunnanta a hankali Najeeba ta buda idannuwanta da sukai mata nauyi ta sauke a fuskar yayarta Zahrau ta yi saurin dago kanta cike da tausayi ta ce " NAJEEBA, sannu, sannu kanwata Najeeba ta kara dora kanta a hankali saman cinyarta , a lokacin wasu hawayen suka kara balewa a idannuwanta Muryarta a raunane ta ce" ban taba sannin Ahalin Mutalab zaku ki saurarena ku min auren nan bayan ina fadi a sannu ina fadi da ihu cewar kar a mun hatsari ne ga rayuwata ba, sai gashi a kaina an fara inda yaya ya nuna min idan na ki zai yi kuka, su ummu suka nuna min ai alkairin kennan, Anmy bata zauna mun zanta ba, Abih bai bani lokacinsa ba, ke kina nesa idan na kira bakya dagawa, sai ga bakuwar da ta zo ta wanken fuska da mari du a kan auren nan? Zahrau ta ji zuciyarta ta karye, a hankali ta ringa shafa kanta ta ce" Najeebana, zafin ciwo ne ke damunki, idan kika shiga ruwan zafi kika sha magani zaki ji ki garas, ki yi hakuri kin ji? Ki daina fadin magangannun nan a kanmu, Najeeba ba zamu taba juya baya a wajen da zaki cutu ba, kuma iyayenmu ba zasu taba yi maki shiru da gabgan ba, sunna tsoron su saurareki ne ki ci galaba a kansu har su janye auren nan, Najeeba Ummu kuwa kin san halinta, idan tana waje ki kiyayi abinda zai kaita makura, kin mantata ne? Bata son irin halayan nan kin sani sarai a kan zumunci bata saurarawa, Ummu idan muka yi fada zata hade mu ne ta bamu punishment din da da kanmu zamu dawo nemawa junnanmu hakuri, kin manta a lokacin da yaya kan yi fushi da mu irin yanda take zaunar da shi ta ringa nuna masa mahinmancin junnanmu? Ki daina jin haushin ummunmu, domin uwa ce a wajenmu baki daya NAJEEBA ta cije lebenta tana jin ciwo a zuciyarta ta ce" ba zaki fahimta ba, Zahrau, ba zaki fahimci abinda ke faruwa da rayuwata ba, kin ga, ashe shine muke zama a stade, kuma shine muka buga basket ball, Zahrau, ya wulakanta ni, ya nunan ba kowa bace ni, ya kawo Nadia ya kwo........ Rufe bakinta Zahrau ta yi, a hankali ta ce" ki yi hakuri Iya kalmar da ta fada kennan kafin ta shiga kokarin kamata Du irin abinda take Najeeba na kallonta ne kawai, domin a tunaninta wannan bacewar shinfidar da har ya bushe nata ne Shirun ta mata dan ta lura bata so ta yi mata bayanin abinda ya faru, Lebenta ta kara cijewa a lokacin da Zahraun ta fita dan zuwa ta samo wata suturar kafin ta tafi da ita Aman Allah ya taimake ka, tun jiya ka bani amsar eh zan dauki abin shinfidar amaryarmu, dan me zaka hanna a yanzu bayan kai ka fada? Muryar Zinaria ce kw bayani a sanyaye Shaheed kuwa na sauraronta Wayarsa ta kara yin vibration din mesage Yana dubawa ya ga sakwon eh za'a samu waje sosai a jirgin da zai shigo daga niamey sannan ya wuce agadez Amsa ya turawa yaron nasa wanda ke kula da shagonsa na kayan gini cewar a je a ciro tiket na iya adadin mutanen da ake bukata Dubanta ya yi yana karantarta, A hankali ya ce" na wanke abin shinfidar, yana hankalce da ita Da karfi ta ce" Meh? Ka wanke? Wani irin wankewa? Kai ne zaka yi wanki? Ko dai bata kawo budurcin nata ba? Duban da ya sauke a kanta ne ya sakata saurin yin shiru da maganarta sama sama Da sauri ta dan duka ta nemi afuwa sannan ta mike ta nufi hanyar bangarenta kamar zata fadi Tana zuwa ta karasa da saurin jikin mahaifiyarta tana kuka ta ce" wai ya wanke, wani irin wankewa? Shine zai wanke? Mahaifiyarta na shafa kanta tana cije lebenta, ya wanke? Idan har ba'a samu jinninta ta haka ba, bata tunanin akoy yanza zasu yi su samu Sai dai zasu kwatanta ko yayane Yana nan zaune har Zahra ta dawo ta shige ciki Bata jima sosai ba ta fito sunna tafe a hankali kan Najeeba na saman wuyanta Tsayar da ita ta yi ta karasa ta duka ta dauki alkyabarta ta dawo a hankali ta rufa mata kafin ta kara kamata su nufi hanyar fita Idannuwansa ya dago daga kallon gefen da yake ya sauke a bayanta, wani yam yam ya ji a jikinsa hakan ya sa ya cire dubansa daga kanta yana kallonsu har suka fita sannan suka dauki hanyar coridor din da zai kaisu bangaren Anmy Haka kawai ya dan kurawa waje daya ido, ba abinda yake gani sai abin nan da yatsarsa ta dangwalo Nan da nan ransa ya ringa baci Bacewa mai tsanani A kasan zuciyarsa kuwa ya furta" *ta zo ta baka nutsuwa, shin haka ta mike a gabanka ka tana wajen da ka yi niya?* idannuwansa ya kara rintsewa da karfin gaske yana jin kansa na neman kwasan ciwo Mikewa ya yo da sauri yana koran tunanin nan ya nufi hanyar fita Rumfa zai je wace aka kama macizai har uku a cikinta a jiya, Mugayen macizai ne masu baban dafi Macizan na cikin gidan ne, a yau dai zai gansu da ransu, a yau zai dauki hannu na mai su Tabas tun yana yaro aka koya masa harkar wasa da maciji, zai iya cewa a kusa kusan nan a cikin gidan sarautar du kalar macijin da aka yarje a shigo da shi to fa sai ya san wanda yake da damar iya kula da shi dan kar a shigo da wanda zai bace ya jiwa mutane A kaf masarautar nan basu san cewa yanda ya lakanci abin har ya fi karfin tunaninsu, domin bayan koyon da akai masa ya kara zurfafa iliminsa ta hanyar karantarsu da komai ta computersa Tun da ya fito ya ja turus ya tsaya sakamakon irin busar da aka kwasa Ashe fa akoy hawa dawakai? Irin yanda ya ga matasa na laye sun sha damara da manya manyan mutane harda datijai kowane na tsaye ne rike da linzaminsa ya saka shi sakin dan murmushi Hannunsa ya daga ya yafito amintacensa dake tsaye kusa da wani ingarman doki ya sha kwaliya yana rike da linzaminsa, wato dokin da zai hau ne Tunkaro wajensa yake yana karantar irin tsayuwarsa *Hala har ya tare da mace ne a cikin matan?* shine tambayar da ya yiwa kansa *HALA JAR YA SAMU NUTSUWAR DA YA HANA MASA SHI YA SAMU?* yana karasowa ya kai kasa ya hade hannayensa ya sada kansa ya furta" *JA GABA KAKE JAN GWARZO, FARO KAKE MAI FARAR ZUCIYA, YA KAI MIJIN ZINARIA, MIJIN GIMBIYA NADIA DA GIMBIYA NAJEEBA, SANNUNKA DA FITOWA HASKE, HASKENKA HASKE NE MAI HASKA DUNIYARMU, SANNU DA FITOWA NAMIJIN MAZAJE, SANNU DA FITOWA MAI GIDAN RANA, SUN BUGU SUN BUGA SUN KASA, GURNANI KAKE MAI TARWATSA TARON MAZA, KAI NE DAYA TAK MAI WUKAR YANKA MAI DAMAGARAM SARKIN SARAKUNA, MATASHI NE MAI ABIN MAMAKI, MAI MOTSA ZUKATA KODA BASU SHIRYA BA* Murmushi ya saki yana lumshe idannuwansa, kansa ya dan sada da dubansa ya sauke a kan Amintacensa Namiji ne gabjejen gaske wanda yake ji da shi, Wannan shine babar kyautar da masarautar Garin Agadez ta taba masa wace har gobe yake jinta har cikin ransa, kyautar Amintacensa kyauta ce da ba zai iya mantawa ba, a da soja ne, ya sadaukar da haka dan bauta masa, shi kam me zai iya bashi ne dan ya gode masa? Shi ba bawa bane, ya bashi sarautar dogaran Fada baki daya, yana da salary wace ta ninka ta sojojin har uku, yana da gida a waje da fada da mota har biyu kyautar sarki ne Dan rage muryarsa ya yi da niyar ya tsokane shi kasa kasa ya ce" yaushe zan maka wankan ango? Shima murmushin ya yi ya kara sada kansa hannayensa jimke bai daina yannayin kirarin da yake ciki ba A hankali ya ringa takawa manya manyan dogaransa na yi masa kirari, da sauri amintacensa ya janyo dokin ya nufo shi da shi Danndukawa ya yi dan ya taka ya hau kamar yanda aka saba Sai dai ga mamakin duban jama'ar wajen wani uban tsale ya daka ya dane saman ingarman dokin nan Ai kuwa zo ga ji wani irin busa da ihun gardawa da kirari, nan fa tsumi ya motsa aka haukace aka dane dokunna Lalle Sarkinsu ya fito a shirye, dan haka du suka haye suka yi baban filin sukuwar Fada aka shiga gabatar da sukuwa cikin tsari da zaburar da zuciya inda wajen ya cika makil ana ta kai kawo ana murna A hankali ta je ajiyeta saman gado, sai dai ta kasa zama ta kwala yar kara tana mikewa tana kara wara kafafuwanta da muryar kuka ta ce" Aunty, barkono a kasana, ki yiwa Allah mu je asibiti kar a je na farke Auntynta ta juyo tana daria tana kallonta, a fili a bayane ta ce" sakaryar wofi, NADIA, kin bani mamaki, wai ki budi baki kina hauka gaban kishiya? Ni yanzu da Allah tsaya min na taimaka maki NADIA ta kaleta da kyau ta yi murmushi ta ce" Aunty kennan, ni NAJEEBA ba kishiyata bace, kuma na rantse da Allah zan yi ta zuwa ina gaisheta ina neman afuwarta har ta sauko, Aunty, ni ? Ba zaki turani na yi mata gaba ba, ni? Zan mayar da ita kishiya? Idan har na yarda na shiga layin kishiyarta kin ganni nan ko? Sai kin kasa gane wacece ni! , a jiya har fada kike ashe bata damu da shi ba? Ni kuwa ina da tambaya Aunty, *MENENE AINAHIN DASA TSANARSA A ZUCIYARTA?* kin san menene? Aunty zan baki mamaki idan na furta maki dalilin madaukakiyar tsanar da ta fara yi masa harma ta ringa neman makusarsa ido rufe shine daga wani fada da suka yi da matarsa ta budi baki ta ce da ita *BAK'A, MAI BAKIN ANIYA, KIN MATSAWA RAYUWATA KAMAR WATA KISHIYARKI, BAYAN MIJINA KO A KAFARSA AKA KULA BAK'A ZAI CIRE YA YAR NE, BAKYA GABANSA HAKAN YA SA NAKE TAUSAYA MAKI!* NADIA ta yi murmushi tana kallon Auntynta ta ce" a ranar da suka suka yi fada a kan abin nan sai da ta ringa maimaita kalmar nan sai sitin da uku ina irgawa Hannun Auntyn ta riko ta ce" Happy juma'at🥺 *Yan uwa ina k'ara gode muku, Allah ya bar k'auna.* [31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 41 Ta ce " Aunty, a kan me zai mata zafi har haka? Bayansa, su ranar da aka ce ana taro na gidansu zaki ga ta rasa me zata saka, a saloon ta saka wannan ta cire Mitarta daya ce" ka je ya ringa hararanka kamar wanda ka fito tsirara Auntynta ta girgiza kai ta ce" ke dai ta baki tsoro ne, ai Nadia komai isarka da tunanin kai din wani kwaro ne ai akoy gabanka, so nake y'ata ta kasance jarumar Sarki Shaheed, so nake baki daya ki doke su! Nadia, wai kin ga fuskarsa? Yaya kamaninsa suke? Nadia ta yi wani irin tsam kafin ta saki murmushi ta saka hannayenta ta dafe kumatunta, a bayane ta ce" tabas rabo ya kaini zama matarsa, in ba haka ba ban isa na shigo layin wace zai iya duba ba Me kike nufi? Auntyn nata ta tambaya cike da zakuwa Nadia ta ce" Aunty, walahi rawanin nan da yake shine rufin asirinmu, da ace buda fuskarsa yake da kirarsa da mun shiga uku da mata, Aunty, Shaheed baki ba zai fadi kamaninsa ba, Murmushi ta yi ta mike ta nufi bayi dan tara mata ruwan wanka da gashi Da kallo ta bi dakin a karo na biyu, Ac sai yi yake dakin sanyi sosai Aunty na fitowa ta ce" Aunty, ba'a kashe Ac din nan ba tun jiya? Kamata ta yi ta mike suka nufi bayi Sunna shiga ita da kanta ta cire zanninta ta ajiye, auntyn nata na jiranta dan ta san sai sun sha kokowar zama a cikin ruwan dumin ta ce" wato Nadia bacina na jiya, wani irin baci ne na yi mai salama Daidaya nake fada maki Nadia na yi a dakin cen Ac na hura kofofin fatana, Nadia baci ne na yi da salaba , lokacin sallah na yo tar tar a cikin kunnayena kiran sallar tamkar a dakin nan, Na so na ki tashi na kara juyawa sai dai cikin ikon Allah irin karatun da aka yi tamkar a azumi ya hana min rintsawa Nice yau da bin masalaci sallah? Lalle Nadia wannan gida baban gida ne A yanzu na daina zagin dangin kishiyarki, koda kuwa suma daga gidan sarautar suka fito aman na daina zaginsu da suka zo wajenta suka tare Nadia, ba yinwa, ba kishirwa, ba shara, ba wanke wanke, ba wanki bare guga, Nadia ba zagi ba duka, ba zafi, Nadia wajen kwonciya a gyare ga wani kamshin turaran wuta da basa gajiya da sakawa Nadia ina mike ina shating ina hasko kaina Haba ina, zan je na duka na yi masu salama na dawo na taya ki zama, Nadia ni dai ko cin uwar taki Najeebar zata yi ko? Ba inda zaki, maganar tafia ki bara mata mijima bata taso ba Nadia na daria tana dan tsoma kafarta a ruwan da ta ji ya yi zafi sosai ta ce" Aunty, ni sulhu nake nema da Najeeba, ni kaina a jiya kafin na san waye shi nake fadin na bara mata Aunty, ni kam zaman lafia nake so da Najeeba, aman ba zan iya barin SULTAN ba Daria ta yi ta ce" ko ke fa yar, wato kin ga maza kin kasa kawar kai ko? Wahalar bata firgitaki ba? Nadia ta ringa daria ta ce" ta firgitani, aman kuma ta kara min kwarin gwuiwar zama a shashena... ........................................ Ruwa masu zafi ta hada itama kafin ta yi kokarin kama Najeeba Tun daga yanda take kin son cire doguwar rigar jikinta ta dan fara kokonto Bata kawo komai kanta ba dai har ta talafa mata ta shiga ruwan nan Irin zaman da ta yi a cikin ruwam ya saka gaban Zahrau mumunan faduwa Da sauri ta mayar da hannunta na hagu ta kara taba zafin ruwan dake dauke da abubuwan kamshi Tabas yana da zafin da ko lafiarka kalau zaka ji tsoron shigarsa bale ita da take tunanin miji ya zo mawa Da sauri ta kalli Najeebar, abubuwan da ta gani saman shinfidar a bushe fa? Sannan ita kanta a jikinta ta ga abubuwa su fa na meye? Duban fuskar Najeebar ta ringa yi kafin a sanyaye ta ce" gardama kikai masa Najeeba ko me ya faru da ke? Najeeba ta kai dubanta kan fuskarta Haushi ya sakata kin yin magana a wannan lokacin sai da Zahrau ta kuma fusta"kin ga, ki rufa min asiri ki bani amsar dake min yawo a raina, ki rufa min asiri ki bani amsa yaya zan saka ki cikin ruwan zafi haka baki ji zafi ba? Bayan na ga alamun da suka nuna min mijinki ya zo gareki? Shirun da ta kara yi ne ya saka Zahrau kara shiga yannayi na damuwa, fuskarta na rikidewa zuwa kalar wace zata fashe da kuka ta budi bakinta a hankali ta ce" meye damuwarki? Hala ba ke ya zowa ba? Hala da wata ya tara a ranarki? Najeeba ta yi rauraurau ta budi bakinta da yannayi na bacin rai kasa kasa ta ce" me kike son ji? Yawan maganana da bacin rai na? Me kike son ji? Na kuma maimaita maki shirmen da ba yanda zaki iya yi min? Hannayenta dake kusa da nata ta riko ta dago tana kalonsu ta ce" ban taba gannin wulakanci irin na jiya ba, tabas ya gama anfani da Nadia ya dorani saman datin jikinta Ido Zahrau ta rintse da karfi tana kawar da kanta A sanyaye ta lumshe idannuwanta tana jin du wani waje da harshensa ya ringa bi a jikinta kafin ta ce" Zahrau, kin san wani abu? *NA TSANE SHI!* Zahrau ta lumshe idannuwanta itama kafin ta janye hannunta ta mike a hankali ta ce" ina jiranki, ki gama ki fito Da sauri ta juya ta fita, ita kuwa ido ta lumshe ta kara zama cikin ruwan nan, tabas ya ci galaba a kaina a yau, Ya bi min jikina da kallo, Idanma da gangan ka lashi fatar jikina SHAHEED na maka alkawarin sai na saka ka son lasarta da hauka hauka, Idanma da zumar wani lamari na zuciyarka ka hade lebena da naka Shaheed, Na maka alkawarin sai na haukata yawun bakinka Shaheed sai na zabura mafarkin ka, Shaheed sai na hana maka sukuni! Na rantse matanka ba su ne abokan gabana ba! Domin na yi imanin WA MAN TASHA'UNA ILA AN YASHA ALLAHU RABUL ALAMEN. Zahrau na fita ta ci karo da Ummu zaune tana kallon kofar Ido hudu suka yi da junna, Zahrau ta sada kanta ta yi niyar fita a dakin Ummu ta yi murmushi ta ce" Zahra, zo mana Zahrau ta fasa fitar ta karasa wajen Ummu tana kallonta Ummu ta kuma yin wani murmushin ta ce" ina zaki je ki fadi matsalar yar uwarki? Ba dai Anmy zaki fadawa ba? Zahrau ta dago tana son goge hawayen dake cikin idannuwanta a sanyaye ta ce" Ummu, tana cikin damuwa, yaya DAYABU ya fada mana sai mun kai zuciyoyin nesa mun kawar da kawunnanmu, inaga shima dan ya kauracewa haduwa da ita ne yake iya hakurin gannin hawayenta Ummu, meye mai karfi tsakaninsu haka? Na zata Najeeba zata iya hakuri, aman Ummu aminiyarta Nadia fa ya aura, sannan a jiya Nadiar a bangarensa ta kwana, ba abinda ya faru da Najeeba Ummu ta lumshe idannuwanta tana kokarin murmushi a bayane, a sanyaye ta ce" Eyah, shine zaki je ki fadawa Anmy haka? Zahrau ta bar hawayenta sauka a fuskarta sosai ta ce" na gaji ne da gannin yannayinta a haka, kanwata ta kasance macen da a wajenta nake daukan darusan kecewa da daria komai bacin raina, ita ke kara saka min kaunar na rayu a zuciyata, ita ke kara saka min nutsuwa idan har hankalina ya tashi, Ummu, na gaji da ganninta tana hawaye a kan auren nan, na ga alamun shima ba so yake ba, itama haka to a kan me zasu yi ta wahala har haka? Murmushi ta yi ra kamota ta zaunar da ita tana hangen yan kafafuwan Najeeba daga wajen kofar da alamu ta karu tana jin me za'a ce A hankali ta ce" shine zaki fada mata ta raba auren? Zahrau ta kuma sauke ajiyar zuciya harda yar shashekarta ta ce" ashe shine wanda ke tafia suke haduwa a stade wajen da take zuwa shan iska? Shin bibiyarta yake yi ko menene? Ummu, idanma aurensu ba mai mutuwa bane a sama mata yancinta, ba zan iya motsawa nan da cen ba har sai na ga abinda zai faru ya faru da kanwata, Ummu, a wajen Najeeba muke koyon murmushi komai bacin ranmu, ba zan yarda farin cikinta ya gushe daga rayuwarta ba, walahi su Ummulkhair jiya kuka suka yi kamar me, Ummu yaya kwana ya yi muna mesage da shi hakan ya sa tun karfe shida yana gidan nan , mun yi niyar yau mu hadu mu duka mu sakata murmushi sai gashi ya kara bata mata? Ummu ta yi murmushi dai kafin ta ce" Zahrau, sai nake gannin kamar kun so kanku da yawa, idanma wani abu ya hada su fushi da junna me zai hanna ku yi bincike dan gano kusababin wannan rashin jituwa tasu ta hanyar zama ku tambayi kanku da kanku wacece kanwar ku? Wannene Sultan Shaheed? Bara na fada maki waye SHAHEED,.SHAHEED mutun ne mai son kare martaba da mutuncinsa da na duk wani wanda ya sani bare na dan uwansa Shaheed a duniyarsa ya tsani mace mai rawar kai da neman fitina Shaheed ya kasance mai son mace mai wahalar ganni ga maza Zahrau, Shaheed fa shugaba ne Zahrau SHAHEED yana da dama da yawa a rayuwa, sannan idan yau ya ki kallon Najeeba meye dalili? Inaga baban dalili a nan shine yana jin haushinta, yana jin haushin halayanta, a abinda na fahimta kennan Ke kin san wacece kanwarki a fannin tara samari Wayarta na hannuna , labarinta na kai mini daga inda na fito Dan shiru ta yi ta ce" bama wannan ba, zaki fita kanki tsaye ki tarbi Anmy ki nuna mata Shaheed na takura yar uwarki Zahra ko kunya bakya ji bakya jin nauyi? Kin san irin yanda ta ci burin auren nan da irin lokacin da ta jima tana son haka ya kasance kuwa? Kin san burin anmynku kennan kuwa? Kin san baban tashin hankalinta a yau ta ji wani abu na faruwa tsakaninsu ne, bare har abin ya fito daga wajenku? Zahrau idan da amana ruwa ba zai ci gwani ba, idan har da kunya ba zaku iya daga kai ku nuna wani lamarin ba, Anmy wacece a wajenku? Ko kuwa sangartar da ku da tsananin soyayar da ta nuna maku ne zaku saka mata da shirme? Najeeba ta lumshe idannuwanta a hankali ta ja jikinta ta koma wajen wankanta Darzar jikinta ta shiga yi cikin nutsuwa Sai da ta gama sannan ta koma gaban madubi ta yi tsaye *ANMY* tabas idan har su din y'ayan halal ne zasu so saka alkhairi da alkhairi, ANMY, uwa ce a wajensu mai kuka da damuwarsu ta yi farin ciki da farin cikinsu Ta kasance mai sadaukar da farin cikinta dominsu mai rungumesu a kowani hali Du irin fitintinnun su bata taba gajiyawa ba , takan tarewa ta dauki jifan da akaiwa kuka Gashin kanta ta warware ta shiga yin wanka dan ta tsaftace jikinta Sai da ta gama ta dauko dan karamin tawul ta nade kan nata kafin ta kurawa madubi ido Murmushi ta yi a bayane tana gannin yanda fuskarta keda kumburin kuka da rashin wadatacen barci Lale ta yi mantuwa guda, ta manta su waye Y'yayan mutalab, ta manta idan ta tayar masu da hankali sosai ba zasu iya rikewa ba, au kuwa zasu tayarwa da Anmy ne Lale ta manta girman alkhairin Anmy a rayuwarta Murmushi ta yi tana dauke dan guntun hawayen da ya dan leko ta gefen idannuwanta kafin ta nuna yar yatsarta ta kausasa dubanta ta ce" NAJEEBA MUTALAB, na hana maki zubar da hawaye a gaban kowa! Daga yanzu zaki yaki du wani mai shirin yakarki da salon takun da ya zo maki ne! Tawul ta daura a kirjinta kafin ta nufi hanyar fita A hankali ta rufe bayin, tana juyowa ta gansu su uku zaune su Ummu sun shigo sun hadu su hudu kennan Murmushin da ta jima bata masu irinsa ba ta sakar masu Du sandarewa suka yi sunna gannin yanda take takowa ta karasa wajen kayanta dake dakin ta ciro na sallah ta saka ta juya ta tayar da sallah Tana gamawa Anmy na shigowa da zazafan dahuwar dake ta tiriri da kanta a hannunta wanda ta shige kicin da kanta ta dafa da kanta ta karaso tana fadin" an yi sallah? Da wani murmushin ta mike tana fadin" Anmy, yinwa nake ji sosai cikina Murna, farin ciki ne ya lulube su baki daya, Ummu dake amsa waya kuwa ta yi murmushi a ranta tana furta" yanzun na yarda ni na haifo ki yarinya! Kamar da wasa Najeeba ta zauna tsakiyarsu suka ringa cin abincin nan sunna ta raha tsakaninsu Anmy ta kalli Zahrau ta ce" me ya sa ba zaki bi yan uwanki ku juya ba? Ita maman Zinaria an ce tace zata bi baya sai jikin Zinaria ya daidaita, ke kuma kin ce ba yanzu ba, shin akoy wata matsala dake faruwa a gidan naki ne? Zahrau ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Najeeba dake cire rigar nan ta dauko yar yololuwa ta saka ta dawo da sauri tana fadin" kar ku cinye mai dadin Murmushi ta yi ta kalli Ummu dake dan kallonta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta kan Anmy dake nazartarta ta ce" Anmy, lafia kalau, ina so ne har Najeeba ta tare bangarenta, kin ga kin ce sai ta yo satinta sannan, kuma mun yi magana da shi ya amince Anmy ta gyada kanta tana murmushi suka ci gaba da cin abincin Sai cen bayan sun gama ta kalli Ummukulsum ta ce" ummu, ki yi kokarin kula yarima, ya jima a falon nan , tabas na fahimci wani abu a tatare da yaron, na kuma yarda da gaskiyarsa Ummukulsum ta gyada kanta tana dan sadawa irin na jin kunyar nan....... Tana gama ci sosai ta mike ta yi saman bed dinsu Kwonciya ta yi tana warware gashin kanta Dubanta ta maida wajen Anmy , sai da ta shagwabe fuskarta ta ce" Anmy, Saloon dina fa? Anmy ta kaleta da sauro, ta kalli Ummu, ta kuma kalli yan uwanta Sai da ta kikifta ido a hankali ta ce" sai bayan sati biyu zaki koma in sha Allah Najeebana, fatana ki kwontar da hankalinki Najeeba Murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta Ummu kuwa ta mike ta kama hannun Anmy sukai waje Tana dubanta ta ce" wani irin zata koma saloon? An taba yi daba? Anmy ta ce" Ummu, ba zan iya hanata aikinta ba, kuma shima ba zai hannata ba walahi, sai dai wajen aikin ne aka cenza mata, ana gina mata wajen ne a nan cikin fada daga wancen hanyar fitar, sai a buda mata kofar a saka masu tsaro, mutanenta zasu iya zuwa nan su yi aikinsu su tafi, ranar da take sha'awa tana iya shiga ta zauna, ranar da bata sha'awa ta yi zamanta masu aikinta su mata, Ummu ta ringa jin kaunar Anmy a ranta, ita kam bata da wani dan uwa ko wani makusancin da ya kai mata wannan baiwar Allah Irin kaunar da take yiwa yaran daban ne, hakan ke saka mata gannin girmanta da kimarta a idannuwanta Da yama kusan karfe biyar Najeeba ta yi salama kofar dakin Anmy Anmy ta dago ta amsa mata cike da kulawa tana dubanta Karasawa ta yi ta zauna kanta kasa a hankali ta ce" Anmy, a jiya sam bamu rintsa ba, sakamakon ciwon ciki da ya tashi Nadia, dole sai da aka nemi Sultan, hakan ya sa na nemi alfarmar a kawota bangaren Sultan dan ko menene shi din zai fi gagawar kulawa da ita Dan numfasawa ta yi tana hankalce da yanda Anmy din ke kallonta kafin ta ce" karshe dai Anmy bamu rintsa ba har safia, nice ma na ringa dan barci hakan ya sa ya sakani zuwa na kwonta shi kuwa ya kwana yana kula da ita Anmy ta ce" Subahannalah, yaya aka yi haka? Ko wani abu ta ci? Yaya aka yi bai fada min ba? Najeeba ta kamo hannunta a sanyaye ta ce" ni ce nace kar a tashin min ke daga bacin gajiyar nan, ni na hanna a tada maki hankali dan na san kin gaji da yawa Anmy Dan murza hannun take ta ci gaba da fadin" tana dan fama da irin hakan, lokaci zuwa lokaci, shine na nemi alfarmar ta yi satin nan, idan ya so sai na yi na gaba Anmy ta kura mata ido ta ce" an fahimta ba, kina nufin ke kika sadaukarwa wata kwanakin ki a wajen mijinku? Najeeba ta shagwabe fuskarta sosai ta yi raurau da idannuwanta ta ce" Anmy, Nadiata ce fa, kuma yayan kansa sai da ya nunan bai amince ba, ni na yi ta magiya har ya aminta da hakan , *ki yi hakuri Anmyna* Anmy rasa abin fada ta yi, sai take gannin zancen kamar wani shiririta, wannan wani irin sake ne zata yi haka da gagawa? Amsa mata ta yi tana mai mata nuni kan ta je ta huta zata waiwayeta Sai da ta kara godewa sannan ta mike ta nufi wajen yayunta cikin ranta kuwa ita ta san me take nufi da hakan..... Sai da ya gama sallar isha'i tare da jama'a kafin ya nufi bangarensa Cikin nutsuwa ya karasa yana tube kayan jikinsa kafin ya dauki wayarsa ya zauna ya danna kiran number amintacensa *Macizan nan, shin sunna ina?* Cike da rikicewa a muryarsa ya furta" abinda ya tayar min da hankali kennan, yanzu haka gamu tsaitsaye da baban liman muna ta nema, an neme su a wajen da aka ajiye su an rasa sama ko kasa Ba tare da wani firgici ba, a nutse ya ce" kai da wa, da wa ke neman? Kai tsaye ya furta" Ni da baban Liman, da Dogari mai rike alkur'ani Kansa ya gyada a hankali kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kashe kiran kittt Hankali tashe amintacensa ya saka suka ci gaba da nema a wajen da suka boye su, Liman ya ringa fada kamar me, dogari ta rikice sai kai kawo suke baki dayansu sun hargitsa wajen .... ............................... *AMINTACENA, LIMAN, DOGARI, MATATA* Ya furta a kasan makoshinsa Har zai mikr dan dauko litafinsa wayarsa ta dauki tsuwa Hannunsa ya mika ya dauka gannin Anmy ya daga nan take *Me ya sa zaka yarda da shawararta bayan ka san yarinya ce SHAHEED?* sunna gaisawa abinda ta fada kennan hakan ya saka shi yin tsai yana tunanin inda kalamanta suka nufa Iskar da ta fesar me ta ci gaba da fadin" idan har ciwom cikin ya yi wani mugun tsanani ne a kirayi likita sannan a fada mana mana mu sai mu zo mu kula da ita baku daya aman sai ka yarda da maganar Najeeba cewar ta sadaukar da satinta a wajen aminiyarta dan kawai bata da lafia kai ne kadai zaka iya kula da ita ko me? Idannuwansa ya buda daga lumshewar da yake ya kurawa waje daya ido Haka ta fada? Ya tambayi kansa, maganarsa da sarkin Agadez ce ta fado masa a rai inda yake fadin" da kyar in zan iya baci, ban taba sannin darajar mace mai fatar Zahrau ba sai da na hadu da zahrau, lalle zan ringa begenta na lokutan da ta dauka Sultan, ka riki matarka, ina mai tabatar maka zaka yi bayani Saurin korar zancen ya yi yana tunanin meye kuma na tuna zancen? Wayar ya duba ya ga ba'a kashe ba, wato dai a kunne Anmy take kan karyar y'arta? Murmushi ya yi a sanyaye ya furta" Allah ya huci zuciyar Anmy Anmy ta girgiza kanta kawai tana kashe wayar ta dubi Ummu dake sauraron du abinda ya faru ta shiga yi mata bayani To a wannan darema ya rabu da Nadia, ya rabu da n'imarta, sun raya daren duda ita din damuwarta daya ce daga ta ga alamu sai ta kama hawaye da magiya ...................................... A haka suka ringa raya darensu tare, A daren da ya kama na biyar a garesu ya yi kokarin kunna fitila dan kallon Nadia a fili Idannuwansa ya mayar ya lumshe da sauri sai kawai kamaninta suka fito a fatar idannuwan nasa Tun daga kanta har kafafuwanta ne suka saka shi saurin buda idannuwan nasa daga lumshe yana kallon waje guda A hankali ya mike tsaye ya nufi bayi cikin zuciyarsa yana dauke da adu'ar kore shetan Baki dayama sai ya dauro alwallah ya fito daga bayin ya nufi darduma Ya raya daren ne a nafila kafin ya nem8 wajen hutawa ya kwonta Washe gari, ahine ranar da zasu kuma haduwa a bangarensa baki daya Ranar ya kasamce kwana shida da farin kwanan daya a bangarensa kwana akwai kuma da daurin aurensu Tun karfe bakwai ta shige daki da niyar kimtsawa ta cewa iyayenta tana zuwa wa'inda suka shiga hada hadar fitar da suturar da zata saka dan wannan rana............. A ci weekend lafia [31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 42 Ba wata kwaliya ta yi ba, ko daya bata sakawa fuskarta wani lamari na kwaliya ba sai gashin idon da ta zauna ta dora shi das a idanuwanta kafin ta idasa gyara fuskarta ta hanyar gyara sajen gefe da gefen fuskar nata ta hade gashinta waje daya ta d'aure. Sket da riga na shada color blue mai duhu ne suka ciro mata Ta zo saka sket din ya shige aman zif d'in da k'yar ya janyu har Anmy na fadin ko a cenza wasu ne? Rigar ta saka mai dogon hannu budade sosai an yiwa rigar gidan mama dan ko bra bata saka ba kafin ta d'auki dan kwali ta sasauta gashinta kasa sosai ta d'ora masa daurin Zarah buhari das das a saman kanta. Wata yar siririyar sarka da dan kunne siraru ne aka bata ta saka kafin ta amshi alkyabar da aka miko mata ruwan pink domin zubin jikin shadarma ruwan pink din ne. Takalma masu tsini sosai ta saka a kafarta kafin a wanketa da turare mai k'amshin gaske. Murmushi ta yiwa Su UMMU dake biye da ita sunna hira kasa kasa , ba komai suke son sanni ba sai wai yaya kamaninsa suke? A daidai kofar shiga ta juyo tana kallonsu ta ce" dan Allah ku tsayani mana? Kun ji An ce k'arfe takwas ake zaman , na tabata ba za'a jima ba ni na tsani ina bin hanyar nan ana wani gaisheni uwa wata shugabar kasa. Ummulkhair ta ce" aa, ke kuwa wani irin jira tsakani da Allah? Ki rufa mana asiri kar a je a ganmu tsaye a kofar nan a zata wani abin ne." Murmushi ta yi ta dan tura kofar mai dauke da maduban da ba"a hango na ciki aman tun tsayuwarsu su suna ganinsu daga ciki. Sai da ta dan shige kadan kafin ta saka hannunta ta cire alkyabar nan ta jefowa Ummukulsum da ta fi kusa da ita tana daria ta juya kasa kasa ta ce" sai ku tafin ai na gani." D'ago idanuwanta da take suka sauka a saman fuskokinsu. Sai da gabanta ya kwonci kwonci ya fadi kafin da sauri NADIA ta sada kanta tana jin gabanta na dukan sitin sitin. A hankali ta yi kasa kasa da dubanta kafin ta cije ta kuma dago idannuwanta tar ta sauke a cikin nasa A hankali ta ringa takowa, kafarta sanye da takalminta bata cire , sannan idannuwanta a cikin nasa Murmushi ne yake kokarin subuce masa sannan tar yana mai kallon idannuwan nata yana son ganin iya gudun ruwanta. Ji take kamar za'a dauketa a nanata da kasa , ji take ta fara jin wata irin juwa mai karfin gaske sanadiyar kallon junnan da suke Ji take idannuwansa na zama kamar wani mashi sunna son sukar nata A hankali ta ji kwalah na taruwa a cikin idannuwan nata A hankali ta lumshe su domin ta yarda , idannuwansa sunna dauke da wani sirri na daban sai dai gagar jikinta ba zata tsaya daga kusantarsa ba Sai da ta kusa gareshi kafin ta cire dubanta daga wajensa ta maida wajen Nadia Murmushi ta kakaro a hankali ta furta" *Asalamu alaikum* Da sauri Nadia ta dago dan duban fuskarta, kuma sada kanta ta yi kasa sosai dan jin tsoronta take har ranta Muryarta na rawa ta furta" Amen wa alaiki salam Dubansa ya cire daga kan NAJEEBAR ya kai wajen Nadia , kwarai ya yi mamakin yanda a bayane take barin jikin tsoron kalonta, kuma kallon NAJEEBA ya zo yo a tunaninsa stil tana tsaye somin kamshin turarenta na nan, sai dai ya ga ta je wajen zama ta zauna, kafafuwanta ya bi da kallo, takalman dake jikinsu ya bi da kallo Neman izinin shigowar da ake ne ya saka shi lumshe idannuwansa ya maida dubansa bakin hanyar Sai da aka dauki minutes kamar biyu kafin ya yi gyaran murya. Jakadiya ce ta bayanna a duke sosai ta furta" ALLAH ya taimake ka, ZINARIA na kwonce zazabi ke damunta, shine GIMBIYA ta umarceni na isar da sakon gaisuwa sannan na shaida cewar ba zata samu halartar taron yau ba, tana neman alfarmar a matsa shi zuwa gaba Kansa ya maida ya jinginar jikin kujerar da yake zaune, Idannuwansa ya lumshe a kasan zuciyarsa yana furta" Ba zata kwontar da hankalinta ba?, me ya sa ta cika daukan lamarin duniya da zafi? Shi bai ga abin tada hankali dan an maka kishiya ba, kishiyoyinma yara kanana zata wani fitini kanta, zuwansa biyu da kansa har bangarenta, sai tarota yan uwanta suke ta saka sun tare bayan du da mazajensu aman sun kasa tafia domin nunawa take kamar zata mutu, Idannuwansa ya bude da yan yatsunsa ya salameta hakan ya sa ta yi ta godiya kafin ta tafi. Sai da ta zauna ta ji wata irin kunya ta lulube zuciyarta hakan ya sa ta kama lebenta na kasa ta lumshe idannuwanta tana dan tsotsa Jin shirun ya yi yawa ya saka Nadia dago dubanta A kan Najeeba ta fara dorawa Lale ita tana dauke da farar fata, Najeeba kuwa bakar fata aman bata taba gannin kalar fatar dake birgeta irin ta Najeeba ba, yanzun sai take gannin Fatar tata ta kara wani fasowa Inama ace zata saurareta? Inama ace zata iya samun kwarin gwuiwar tunkararta? A hankali ta kai dubanta wajen Sultan, Ita kam rayuwar sarauta ta fara bata wahala ba magana, shiru d'in nan na menene? Tana kai dubanta ta ga idannuwansa kamar a lumshe suke aman kasa kasa a kan Najeeba suke, wannan kallon, wannan kallon shine kallon da Najeeba ke yawan fadi cewar yana tsareta da kallon tsana ko wani kallo ne daban? Ita sai take fasara kallon nan a matsayin irin kallon da yake mata idan yana cikin hali na zai je gareta Kanta ta k'ara sadawa ganin daga yanda yake, idanuwan nasa a kan Najeebar ya budi bakinsa a hankali ya furta" *Zaman yau ba zai yiwu ba, sai dai zuwa lokacin da Zinaria ta samu lafia*." Dan saurarawa ya yo kafin ya dago dubansa ya cire daga kanta ya d'ora kan Nadia , wanda hakan ya fadar mata da gaba domin tuni launin idannuwansa sun canza kala Ya furta" *Zaku iya tafia*." Yana kai Aya ita ta fara mikewa, a hankali kasa kasa ya kuma dora idannuwansa a kan bayanta, Da sauri ya rintse lokaci daya kansa ya sara masa *WHY? WHY? ZALAMARKI TA HANA MAKI HAKURIN LOKACIN DA ZAKI MORI HAKAN YA ZO GAREKI?* Ya tsinci zuciyarsa na tambayarsa Bai iya cire dubansa ba sai da ya ga ta amshi Alkyabar nan kafin ya cire kansa ya mika hannunsa ya rike na Nadia Gabanta ne ya fadi, yau take kare kwana a bangarensa, aman ji take dama ya sawake mata kwanan yau Ta kasa sabawa, kwata kwata ta kasa sabawa Bata yi rayuwar biye biyen maza ba, tabas sun kasance masu saka kannanun kaya aman sam rayuwar bin maza ba nasu bane Ita, bata fiya kallon BP ba, sannan ba mai karance karance bace Kwarai lamarin nan ke bata wahala, har yau kuwa tun kallo daya da ta masa ta kasa kuma masa wani irin kallon na tsanaki Idan ya yi tsaye a gabanta nan da nan take rikicewa, tsoronsa take ita kam kwarai da gaske Bayan komawarsu wani zaman hiran suka bude kafin ta amsa kiran Anmy ta sakata bacin wuri wand ata yi hakan ne dan gobe itace da daukan girki Lamo ta yi saman bed, a hankali take shafa gashin jikin matashin kan dake ajiye Idannuwanta ta lumshe kafin ta kuma budewa ta kai dubanta saman yan yatsunta Hawaye ne suka bi gefen idannuwanta a hankali ta furta" *Yau gani da auren farin mutun, mai sarauta, mai takama, mai jin wahalar magana, wanda ya tsane ni, mai mata biyu bayana* Dan murmushi ta yi tana juyawa cikin bargonta a hankali ta furta" *ABIN DARIA* A yau da safe da murna Nadia ta bar bangaren Sultan, duda a jiyan ba wani tabata ya yi ba domin haka ya kwonta sukuku da shi , kwata kwatama a zaman da ta yi a bangarensa na sati daya cif sau uku kadai ya zo mata,kwanakin da ta sha matukar wahala a wajen angon nata, domin kuwa ya kasance du idan zai kawo mata ziyara gabanta ke kwonci kwonci ya fadi ita kuwa sai ta kasa rufe bakinta ta yi ta kurma ihu tana neman agaji da neman yanda zata yi ya sauka da wuri Sannan tabas ta yarda sarauta wani lamari ne na Allah mai girman gaske da wuyar fasara. Komai da ido, da hannu ko da kansa yake nuni Sai idan yana son nuna ya ji dadi yakan dan yi wani killer smile Bayan ta koma bangarenta Aunty ta amsa kiransa Wani dan akwati ne ya bata a hankali ya furta" Allah ya bamu zaman lafia Da amen amen ta amsa kafin ta baro bangaren cike da farin ciki da annashuwa, tana tunanin yanda zata yi ta koma gida, itafa walahi ta ga waje A cikin satin nan ba abinda suke tsakaninta da yan uwanta sai zama sunna debewa junna kewa Wani irin karfin gwuiwa ta ringa ji yana kara shigarta, wani irin tabacin decision dinta na kara zama a kasan zuciyarta Bangaren anmy bata daina tsumamata ba wanda hakan har mamaki yake bata, domin akoy lokacin da ta ce" Anmy, shi abin nan yaushe za'a daina shi? Sai Anmy ta ce" Jannuh, ba za'a taba daina shi ba koda kuwa Allah ya albarkaceki da samun ciki, domin bashi da matsala ga lafia, sai dai ma ya kara maki lafiar, Najeeba, mace ko me take takama da shi sai da gyara, baki ga yanda yanzu Zahra ke dauka da kanta ta kimtsa kanta ba? Ai sannin darajar abin da ta yi ne Ita dai murmushi kawai ta yi wai ciki, ciki fa? Da wa? Ko kare mata kallo da ya yi ya shamaceta ne, macuci kawai azalumi mai fuska biyu!, sam ta fasa gardamar amsar gyara ko shan dadadan nonon rakumin da ake mata hade hade a cikinsa, Takan maida kai da fata ta karba a ranta kuwa fadi take, tanadin wani ne, domin yana sakina zan maka auren rashin mutunci wanda Damagaram zata girgiza Mijin zahrau ya kasa hakuri ya shaida masu cewar zai zo su tafi, daka ta shige ta yi kiransa ta kwontar da muryarta, sai da ta gama rarashinsa tamkar wani yaro da dadadan kalamai kafin ta furta masa ya bata kwana uku kawai, in sha Allah zata zo koda bata gama abinda take yi ba Kwarai ta rike wannan abu a ranta, ta yiwa kanta tambaya....yaya aka yi yake zumudi a kan yayar tata? Gashi dai Gimbiya na nan, rabonsu da ita tun haduwar da aka yi wai tana jinyar Zinaria, sun hadu sun dinke a bangaren Zinariar ita kanta ko barorinta rabonsu da su ganta sati dayan kennan, Anmy da Ummu da su ummu da Zahraun zuwansu biyu aman Gimbiyar kadai suka gani ita din wai baci take. *Ranar tarewarta* Zaune suke a falo su biyar, UMMU na kitse kan Zahrau da wasu irin kannanun kitso masu bala'in kyau tana yiwa Anmy Daria Ba dariar komai bane face irin yanda tun dazu takan dan rafka tagumi sai kuma ta cire ta kai dubanta agogo ta furta" yaya zamu yi da y'ata? Yau ranar zuwanta turaka ne, gashi har an yi magariba." Wani irin sansanyan kamshi, mai hade da kamshin turaran wuta, da takun takalmin mai dan tsini ne ya saka su dan juyawa. Ya Subahannalah, NAJEEBA ce ta bayyana cikin shigar wata abaya bak'a sid'ik mai dan ado fari fari Tsaf ta zane fuskarta da simple mak'up kafin ta gyara gashin kanta ta yane dan kwalin rigar bak'i mai shara shara. Irin yanda rigar ta bi shap dinta abin ba'a cewa komai. Hannunta kuwa dauke da wata jaka mai dan girma fara kal itama wace ta zuba abubuwan buk'atarta. Wauh, Ummulkhair ta fada tana mikewa da yannayin tsokana ta ce" Najeeba, wannan kwaliyar du ta oga ce?" Murmushi ta yi ta ajiye jakar tana rufe fuskarta da hannayenta bibiyu. Wani farin ciki da sanyi ne ya ratsa zuciyar Anmy har ta kasa boyewa, UMMU ta dan cije lebenta na kasa tana murmushi a kasan zuciyarta kuwa mamaki ke son kasheta, ya salam, wannan yarinyar ba abinda ta bari nata ko meye? Bangaren halaya bayan ba tare suka rayu ba? Farin cikin Anmy ya kasa boyuwa hakan ya sa ta mike da matsanancin farin ciki ta yi cikin dakinta da wayarta, dan zata yi kiran Jakadiya ne, sannan ta dauko dahuwar da UMMU suka yi da ZAHRAU wace da kanta ta shaida masa cewar yau ita zata tura masa abinci, sannan ta nemo Alkyabar da zata hau da irin shigar yarinyar nata. Cike da Tausayi zahrau ke kallonta, bata san dalilin da ya saka UMMU ta saka maganin nan a cikin abincin da za'a kaiwa SULTAN ba, abinda ta sani shine tana da dalilin son dole dole hakan ta tabata. Hannunta ta kamo ta janyota kusa da UMMU sosai kafin ta kaleta, muryarta ta sanyaya ta ce" yau tsal, ina so na ji kun yi magana." Najeeba ta kaleta, aman sai ta dan cure lebunanta masu shegen kyau ta kasa cewa komai. Ummu ta yi murmushi tana jin tamkar ta ciro zuciyarta ta buda mata ita ta nuna mata irin ilar da soyayarta ta yi mata, shin yaushe zata dubeta? Yaushe zata yafe mata? Sai kuma wani tausayinta da take ji na daren yau wanda ko wace uwa take iya kasancewa, wato cikin zulumi da tsoro da tausayin y'arta, Ta tabata abinda ta je ta siyo ta zuba a abincin SULTAN ko dokine shi sai ya motsa shi bale mutun dan adam mai rai da lafia tabbas ba zata iya fitowa ta nuna rashin jin dadinta a abinda ya faru da y'ar tata ba, aman ta yiwa kanta alkawarin gyara auren yarinyarta ta kasa Yanda kowata mace cikin matansa ta samu kulawarsa a lokacin da ya yi niya, to fa zai kalli Najeeba koda bai shiryawa hakan ba Kwarai bata kulaceshi ba, aman kuma zata saka shi ya fara cire zargin dake damunsa, duda ita kanta bata da tabacin idan har zai cire zargin. Najeeba na zaune tana kallon yan yatsun UMMU. Tsoro take ta kasa ci gaba da gaba da matar, tsoro take karfin soyayar matar ya yi rinjaye a rayuwarta bayan ta yiwa kanta alkawarin in sha Allahu itama ba zata kulata ba. D'an d'ago dubanta ta yi sai idanuwansu suka sarke da junna tsantsar kauna, had'i da yanayin tausasawa take hange a idannuwan matar, da sauri ta cire dubanta. Ummu ta sauke ajiyar zuciya tana gannin an fara fitowa da kulolin gidan sarautar sababi masu mugun kyau. Yayunta ne suka amshi kayan, Jakadiya ta rike jakarta Ta coridor suka bi suka tafi UMMU ta lumshe idannuwanta a kasan zuciyarta tana furta" I'm sorry JANNUH." Anmy ta zauna a hankali gefenta kafin ta kamo hannunta ta ce" MARIAM, ki kara mata lokaci kadan kin ji? Na tabata ita kanta karfin hali take, shi yasa na daina mata maganar na zuba mata ido, zata zaburo ne a lokacin da bamu yi zato ko tsamani ba. Murmushi UMMU ta yi ta dora kanta saman cinyar Anmy, a sanyaye ta furta" da na sani, da na zauna komai wahala, da na sani da na zauna komai tashin hankali da bacin rai, Aunty Bilkiss na tafi, yanzun na dawo du irin dukiyata, mutanena, na kasa samun nutsuwar tunanina. Cike da tausayawa Anmy ke k'ara tausarta. Dayabu da ya sanyo kai sai ya juya dam ya koma, ba zai shigo ba a irin lokacin nan, dama yau yana da wajen zuwa budurwarsa ta dawo daga karatu zai je su ajiye magana a yita ta kare, dogon karatun nan ya ishe shi haka. Basu jima wajenta ba suka juyo, su Ummulkhair sai santin falon suke , ita dai Zahrau ta yi gum abinda ke zuciyarta na zuciyarta. Mikewa ta yi bayan ta cire Alkyabarta a hankali ta nufi dayan dakin da ya saka Nadia wancen lokacin Hannunta na hagu rike da yar wayarta karama wace rabonta da dubata har ta manta Jikin kofar ta tsaya tana k'arewa irin kofar kallo. Bakinta ta yatsina ta saka hannunta a hankali da niyar budewa Sai dai ta yi ta yi kofar ta ki ta bude A fili ta furta" Munafurci! Juyawa ta yi wajen dayar kofar ta karasa Idannuwanta ta lumshe sakamakon jin wannan turaren du ya cika dakin harta da kofar idan ka rabo sai ka ji shi butu butu Fasa budewar ta yi ta juyawa kofar baya tana gannin kira na shigowa wayarta A tsanaki ta daga kiran ta yi salama Aida ta ringa ihun murnar jin muryar uwar gidan nata a rikice ta ce" Aunty wai dan Allah da gaske yanzu Sultan SHAHEED kike aure? AUNTY wai aure kika yi da gaske? Aunty yaushe zamu zo mu ganki? Aunty shago fa? Najeeba ta dan dafe goshinta a hankali ta ce" Aida wannan ihun fa, sannan wace kike so na amsa maki cikin tambayoyin? Sam bata ji budewar kofar ba, sannan bata ji fitowarsa ba, domin Aida ta kasa daina ihunta sai murna take ta ce" Aunty ba zaki gane bane, mutane da yawa sunna zuwa wai a taya su murna kin yi aure, su yanzu so suke su koma yar mutunci da ke kin zama gimbiyar garinmu , wai harda matar Ambasador ta zo gyaran kai fa tace ita so take ta zama mai classs yanda mijinta zai daina fade fade, ta zama client dinmu daga yau tana so a ringa kula da ita a shago Murmushi Najeeba ta yi a bayane, kafin a sanyaye ta furta" waye ya ce mata zan bar mata mijinta ya huta ne? Ai ba zan taba barin mata shi ya huta ba dan ba dan ita kadai aka yi shi ba Da mamaki Aida ta ce" aman ba an ce kin yi aure ba? Kin auri Sultan? Aunty Ummulkhair ce ke fada mana da kanta fa Najeeba ta ce" ke, tsokanarku take, ni ba wani sultan da na aura, Aida HUZAIFA ya zo kuwa? Idannuwansa ya mayar ya rintse daga tsayen da yake, du hirarta yana ji hakama ta wace ta kirayeta domin Aida tana magana ne da karfi karfi so excited, ita kuwa Najeeba duda yanda take maganarta a hankali a sanyaye cikin voice dinta mai fita lafazi by lafazi bai hanna shi jiyo maganarta ba domin Allah ya hore masa ji A hankali ya tako har zuwa inda take tsaye Hannunsa ya saka a hankali ta wajen tsatsonta Lokaci daya ya janyota baya ya kasance ta hade bayanta da jikinsa, ta yi masauki a fafadan kirjinsa ta baya Gabanta ne ya yanke ya fadi a hankali ta kai dubanta wajen hannun Ta yannayin girman hannun ta gane ko na waye sai kamshin turaransa da ya mata dirar sauri a hancinta A hankali ta lumshe idannuwanta sakamakon jin sajensa a wajen dokin wuyanta hade da hancinsa yana sinsinawa Boyayiyar ajoyar zuciya ta sauke tana hangen takunsa karara da abinda yake nufi da kusanta jikinsa da nata har haka A hankali ta dora hannunta saman nasa ta saka dan karfinta da niyar bambare hannunsa daga tsatsontsa muryarta cen ciki ta furta " Assshhhhhhhhhhhhhhhhhhh, ka bari mana, Maimakun ya barin sai wani irin yar yar yar da ya ringa ji baki daya jikinsa ya fara amsawa sakamakon maganar da ta tashi yi sai da ta yi yanda iskar bakinta ta sauka a gefen wuyansa , irin jan maganar da ta yi ya sakashi rintse idannuwan da bai shiryawa ba Bai tantance ba ya ji ta kuma buda bakinta a hankali ta ce" ina da saurin kaiwa du katon da ya kai hannunsa jikina marrrrr.....i Dan murmushi ne ya ji zuciyarsa na yi, MARI? lolz ya fada a cikin zuciyarsa Sai da ya kara yin sama sama kadan da hannunsa kafin ya yi kasa da su duka wajen fafadan kugunta ya dora saman manyan cinyoyinta a hankali ya furta" baki san maza sunna suka tara ba? Dan yawo kadan ya yi da kugun nata a wajen dogon wandon yadin dake jikinsa a hankali ya furta" har yanzun dai ban hadu da wace ta kai marin nan fuskana ba,.......... Dan jan iska ya yi ya saki dan murmushin gefen kuncinsa a hankali ya furta" kin zo amsar hakin ki ne? Da sauri ta buda idannuwanta kafin ta saka hannunta ta janye nasa ta matsa gaba kadan sannan ta juyo ya kasance yanzun sunna kallon junna Sai da ta lumshe masa idannuwanta sannan ta furta" *NI AI BANA RABA NAMIJI DA WATA* Tana gama fada ta dauki wayarta da ta fadi ta juya da dan sauri ta koma saman kujerar nan Kansa ya d'an jujuya yana mamakin furucinta, Bata raba Namiji da wata? Ya kai bata jin kunyar abinda take aikatawa?. Direct wajen abincin ya nufa, saman k'aton diner irin na gidan sarauta, fari k'al da shi sai d'aukan ido yake ga kujeru na alfarma. Zama ya yi saman kujera kafin ya bi kwanukan da kallo Kwanukan sun bashi sha'awa tun daga yannayin kyansu da tsarinsu hakan ya saka shi sha'awar buda su. Cikin nutsuwa ya buda kulolin, murmushi ya yi gannin irin cimar da aka kawo masa. A dan plate ya zuba, sai dai ya zuba miyar da yawa domin shi akoyshi da son miya bare wannan miyar ta murjajiyar malofiya ta sha kayan had'i su dadawa da nama da kifi sai tashi kamshin yake ga curry ya saka shi jin sha'awar yin hani'an. Sosai ya ci abincin nan har yana kara surb'ar miyar kafin ya mik'e ya nufi d'akinsa. Sai da ya fara yin brosh sannan ya koma saman bed dinsa ya kwonta yana mai lumshe idanuwansa haka zaki yi ta fama, a yanzun da na tabata kin san lamarin, sai dai ki gani ana yi da wasu! Cije leb'ensa ya yi ya juya ya kara gyara kwonciyarsa da kyau yana jin dacin irin abinda ta fadawa wata, wato shi ga sakarai ko? Da aurensa a kanta aman ta furta wasa ne, *Huzaifa* sunan nan yana masa yawo sosai a cikin kunnensa, yana tune da yaron, sannan ya san yaron shine wanda ke daukan mai a gidan mansa mai sunna SHAHEED SS, yana sane da manya manyan mutanen da yake kasuwanci da su domin idan ana zaman fada da yawa kan zo su kawo gaisuwa harma su kawo shawara a irin ci gaban garin Damagaram. Kansa ya d'an jujuya ya mike zaune ya dauki laptop dinsa ya shiga aiki da ita, ba komai yake had'awa a yan kwanakin nan ba sai tarihin mutane hud'u da suke tsaye a ransa wa'inda ya saka ayar tambaya a kan lamuransu harma ya aniya saka ido a dukan motsinsu hotunansu ne, na iyalansu ne, na muhalansu, da dukan wasu dama na rayuwarsu. Yana zaune shi daya sai ya ringa jin baki daya tsigar jikinsa na tashi. A hankali ya ringa gyara zamansa, tun abin na haye masa kasa kasa har ya ji sosai wani lamari na gundurar zamansa harma yana neman hautsina tunaninsa. Dawowa ya yi kan turbar da ya kasa gane abinda yake aikatawa a computer, harma ya fara hada sak'o da sak'o. *Mai damagaram fa da magana.* [31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 43 A hankali ya janye yan yatsunsa ya kashe computer ya rufeta Saman kujerar ya kara gyara zamansa yana dan balancing kadan kadan yana sauraron wani irin al'amari dake ta harhada kansa a tatare da shi Baban tambayar da yake yiwa kansa shine" *Shin zan iya shiga hakinta ta hanyar kiran wata daga cikin matana na sauke gajiyata dan kawai ina tare da kyankyamin kasancewa da ita?* A hankali ya buda idannuwansa da suka cenza launi sunna karbar amsawar da jikinsa ke yi Ko a wancen ranar na yi haka ne dan na san inada damar fara zama da wace na yi niya ne A yau da yake ranarta ne, dole dole ranarta ne, Idonsa ya rintse dan kawai ya gwada idan har zai iya jurewa? Mintuna kamar ashirin tsakani ya gama gane cewar a yau baya jin wani yaren daniya ko jurewa idan har ba rage abinda ke mararsa ya yi ba A hankali ya mike yana kunce arzuzumin wandonsa cike da mamakin yannayinsa Me ke damuna haka? Ni ba wani abu na sha ba, sannan sam lamarina baya min haike irin haka Bayi ya shiga ya sakarwa kansa ruwa , ruwa masu sanyi sosai Sai dai maimakun ya samu lamarin ya lafa aa, sai ya kara daukan damarar ko wace wace A hankali ya dan rabawa kansa tawul kafin ya shiga takowa sannu sannu hannunsa dauke da remote din da yake iya control sin hasken wutar dake falon baki daya Abu daya ya fito da shi a kasan zuciyarsa, shine zai je gareta ya samu dan sauki ta hanyar romance A hankali yake takawa inda dariarta ke dan tashi sama sama kadan a lokacin da take amsa waya, Wa ya fada maka? Shine abinda ta fada kasa kasa, kafin ta ce" kai bana son hauka, ka ga zan tura maka komai a detail yanda zaka je ka bugo min sabuwar takardar da zan baka ka kaiwa client dina, Amsar da ya bata ne ya sakata fadin" kai ajo bana son iskanci ka ji ko,? Ai ba zaki daina ce min kai din ba? Ai dan kin san du wannan aikin ba wanda zai cika maki shi irina ne ya sa kike lalabani yau, yanzu Najeeba ba zaki fada min gaskiya ba cewar wai da gaske ogan oganni kika yi mana wufff da shi? Kai Najeeba akoy babar Haja na rantse da Allah, kuma shine ko ki kira mana makadin zabi ya wuni yana mana casu muna murza duwawu? Waima fada mini wata magana Kawar, wai dan Allah da gaske Harda aminiyar nan taki da na tsana mai shegen girman kai ya hade ya yi quf da ku? To ta yaya aka yi ita dan ubanta zata ci naman da kika ci? Ko bata san wacece ke a garin Damagaram ba? Kitttt ya ji an datse kiran da take sauraron dan daudun dake mata aiki ta hanyar raba katinanta na shagonta Da sauri ta dan yinkura dan gannin abinda ke faruwa sai dai bai bata dama ba ya karasa gaba dayansa saman kanta lokaci daya yana mai hade bakinsa da nata Ido ta zazaro ta yi saurin janye bakinta tana maidawa gefe da sauri ta saka hannayenta da niyar tunkude shi muryarta na rawa ta ce" *SHAHEED, SHAHEED, ME KAKE SON YI HAKA MARAR MA'ANA?* idannuwansa ya sauke a kan lebunnanta dake ta rawa sosai tana kama sunnansa haka kai tsaye gatsai gatsai Bai iya yi mata magana ba sai saka hannayensa da ya yi da karfin Allah ya riketa ya fincike rigar da ta saka din dama gun dazun ta wancakalar da dan kwalinta sai ya mata saura daga ita sai bra da dan gajeran wandon da ta saka irin mai dame cinyoyin nan baki sidik sabo fill gashi ya sha turaran wuta A yau bata tsaya jiki mace ba ta bashi damar kashe mata jiki, hannayenta duka take sakata tana tare fuskarsa du inda ya yi niyar kai harshensa sai ta tare ga hayaniyar da take kan ya barta kar ya taba mata jikinta meye haka yake son yi? Meye wannan din? Shima a yau din cike da kokowar son ya kai inda yake so yake dan kai hancinsa yana sinsinarta ko'ina Idannuwansa lumshe a hankali ya furta" *ki nutsu, ni kaina ba zan je na rabi gonar da wani ya raba ba! Ina cikin halin son a tabani ne, idan kika min gardama zan kama hannunki da karfi na juye maki komai a cikin bakinki* Da sauri ta kawar da fuskarta daga nufota da ya yi, muryarta na rawa sosai ta ce" *ka ga, wannan abin bana so! Ka daina, na san ba zaka ci abincin da wani ya ci ba, Shaheed wa'inda suka cin yawa ne da su dan Allah kar ka fara* Idannuwansa ya rintse cike da jin wani daci a kasan zuciyarsa, wai shine matarsa ta sunnah ke fada masa kalmar cewa kar ya rabeta dan ta rabi wasu bama daya ba? Fasa neman hada bakinsa da nata ya yi da karfi ya fincike wandon nata hade da pant din dake ciki Ido ta rintse tana mamatse kafafuwanta a lokacin kuma ya samu damar janye bra dinta Bai tsaya wani kuma kulata ba, ko binta a laluma ba, da sauro sauri yake dadamkar jikinta burinsa daya ne kawai ya samu nutsuwarsa Abin ne ya gagara, a lokacin da ya gama bayanar da ita a gabansa ya yi dana sannin fitowa gareta, domin gaba daya neman makancewa da kuma kurumcewa yake Hannunta na dama ya kama ya kai wajen da ya fi adabarsa duda har yanzu tawul dinsa na jikinsa ya dora da dan karfi ya danna a hankali idannuwansa rintse ya ce" ki kula min mana, ahin ba aikinki bane? Ki kula min mana? Baki daya ji ta yi ta mutu daga zaune, gabanta ne ya kwonci kwonci ya fadi lokaci daya jikinta ya kwashi rawa A rikice ta ce" kai ina ina wayo na shiga uku meye wannan? Wayo hannuna Idannuwansa ya dan daga ya sauke saman kanta, baki daya bai taba yarda da yarinyar ta gama raina shi ba sai yau Gannin idan ya hakura zata iya halaka shi a irin yanda farashinsa ke kara hauhawa sai kawai ya janye tawul dinsa ya duka da sauri wajen da take kwonce ya dora kansa cikin rawar jiki da son samun nutsuwar kansa ya shiga lamarin da ya sakata baki daya rikicewa Fashewa ta yi da kuka a lokacin da take jin yana kai harshensa wajen nan, Ji take fitsari take gaba daya jikinta ya gama birkicewa ya rikice tsoro ya gama halakata Idannuwansa ya rintse yana jin juwa na dibansa Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une me ke damuna haka wanda ban tana tsintar kaina a ciki ba? Ni ban taba shan wani abu ba, ban tana jin bukatuwa da son aiwatar da sex irin na yau ba, kuma sai da na kasance da ita? Mikewa ya yi ya jirgata da kyau, a hankali wani hawaye mai zafi ya shiga cika kurmin idannuwansa Fuskarsa daidai da tata, yana gannin tana hawaye Kukan me kike? Zuciyarsa ke tambayarta , Kin cuce ni Zuciyarsa ta ayana wanda hakan ya sakashi baiwa idannuwansa damar kara kadewa sosai sannan kwalar ta idasa cike su makil aman bai basu damar zubowa ba Lebenta yake kallo kafin ya kai dubansa cikin idannuwanta *Me na maki da zafi haka? Me ya sa kika wulakanta min kanki?* du yake bayanin nan a cikin zuciyarsa sannan idannuwansu sarke da junna Abinda take ji mai d'an lema lema yana yawo tsakankannin kafafuwanta da cinyoyinta ne ta kai hannunta da sauri cike da tsoro tana turewa sannan a rikice tana dubansa ta furta" *ka rufa min asiri, ban shiryawa haka ba, idan har ka yarda ka yi haka ka kara sakani a cikin halin kunci, a yanzu wannan abin shi kadai ya yi min saura wanda nake son malakawa wanda ya dace, idan har ka kwace shi bayan tsanarka da ka saka min a zuciyata ina mai tabatar maka ka jazawa harta matanka, sai na ringa neman fitintinnun da hankalin kowa zai tashi a garinka* Idannuwanta yake kallo, kalamanta na shiga kunnayensa ta wata fasara daban da wani haushi da wani d'aci, bayan halin da yake ciki ta k'ara wata gudunmuwar da ta saka shi cikin rawar jiki da mugun rufewar ido, lokaci d'aya ya yi watsi da k'yank'yami kaiwa ziyara gonar da yake hasashen wani ya noma. Lokaci d'aya yana kallon idanuwanta tana kallon nasa a saman babar kujerar dake ajiye a falonsa, kujerar alfarmar da yake kishingida lokuta da dama. Karkashin talatainin dare, ta dirtsa faratunanta jikin damatsunan hannayensa ta kara kukuro manyan idannuwanta masu dauke da gashin gira da kwalin Kajal Bakinta mai fitar da dadadan kamshi na huro kalamai a kan fuskarsa wanda ta dago kan nata da karfi ta mayar da karfi ta buga a saman kujerar lokaci daya cikin muryar kuka tana son matse kafafuwanta ta ce" *KAR KA YI, KAR KA BUDE MIN, BA NAKA BANE*.......... Tashi daya ya k'ara wara kafafuwanta kafin ya idasa bakin wajen da tsananin santsinsa da sulbinsa ke saka amarinsa sulubewa yana jin santsi da laushin wajen na kai duka a cikin kwakwaluwarsa. Ganin wajen na wasa da hankalinsa ya k'ara daidaita yar hanyar dake rufe ruf cikin zuciyarsa ya karanta adu'ar saduwa da iyali kafin ya tura kansa da wani irin karfin da ya sakata k'wala k'ara mai matuk'ar k'arfi da ciwo sakamakon bak'on yanayi mai ciwo da tashin hankalin da ya ziyarcewa wanda hakan ya saka shi saurin bud'a idanuwansa ya sauke a kan fuskarta. Gabansa ne ya shiga wani irin fad'uwa lokaci d'aya ya k'ara gyara zaman kansa a jikinta dan idasa tabatarwa. A hankali abubuwa suka shiga kwonce masa, fuskarsa a kan nata, yana kallonta abubuwa na shiga kwakwalwarsa a bud'e shi dai ba yau ya fara taraya da mace ba, ya kai bambancin da zai iya gane macen dake vude da wace bata bude, kai harta wace ta haihu. A hankali ya lumshe idanuwansa yana jin bugawar zuciyarsa ya had'u kala hud'u ne, na buk'atuwa, na abinda ya riska a wajen da bai taba tsamani ba, na irin kaikaita masa lamari da ake, da kuma irin duniyar da ya samu kansa a ciki. Maida maganganunta gefe yayi a hankali ya ci gaba da wadatar da abinda ya je yi aman wannan karon hannunsa na hagu daidai goshinta yana yi yana share mata zufar dake zufa daga goshinta da kuma wace ke taruwa a kanta. Mafarki ne wannan ko zahiri? Ko kuma dai wata matar ce a suffar Najeeba? In kuwa ita d'in dai ce, to lallai bai san sunan da zai iya kiran kanshi da shi ba, Najeeba! Ita ce yau ya shigeta kuma ya zama na farko, me hakan ke nufi? Me yasa ya dinga zarginta akan abinda bai da hujja akai ta bad'ini? Wane irin mutum ne shi? Ya Allah! Gashi a kanta yau, zuwa wanda bai shirya masa ba, zuwan na k'eta da son dole saiya cutar da ita, amma ga dukkan alama shine zai cutu, me yasa ya wa yarinya haka? SHAHEED ka farka, tabbas wannan da kake wa kallon watsatsiya ita ce ta kawo maka abinda yafi komai daraja, duk abubuwan daka gani a game da ita kururuwar shed'an ce, duk abinda ido ke gani ne, kuma shiyasa hausawa suka ce *k'azantar da idonka bai gani ba tsafta ce*. A hankali ya bud'i bakinsa jin irin ganimar dake zuba a wadace wada ke saka shi yawatawa duk da bak'on wajen daya ziyarta a matse yake aman a wadace santsin wajen ya saka shi kwacewar magana ta hanyar furta" *MASHA ALLAH, SUBAHANNALAH, LA'ILAHA ILALAH, YA RAB, YA RAB, YA RAB...",* Sai kuma ya sasauta muryarsa cen kasa ya furta *wayo ta rik'e ni , wayo dad'i....* (🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈 ni dai ba luwana wollah) .....Bara dai na gudu, bara na gudu kar lamarin nan ya kaini furta kalmomin sunnayen da zan kasa lek'owa MAGE HAUSE. Ya d'auki lokaci yana mai gabatar da wannan lamari a kan Najeeba, wace tun da ya fara take kukan bakin ciki, kukan takaici, kamar zata sike, tana neman suma ido rufe, burinta hukarta ta tashi a yau ta kasheta, kiri kiri take kallon mutumen da ya mata wankan janaba a bakin titi, wanda ya wulakantata yake jin haushinta kan laifin da bata sani ba, a yau kuma ya nuna mata karfi ya k'wace abinda take tutiya da shi du rayuwarta bayan ya k'wace mata aurenta na fari? Kukanta ya kasa tsaiyawa har zuwa lokacin da ya sakar mata nauyinsa a saman kanta. Tarin wahala take tana kara rik'e jikinta dan kar ta shak'i k'amshin jikinsa. A hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya kafin ya saka hannayensa ya k'ara rik'eta a jikinsa sannan ya d'an sasauta mata nauyin jikinsa idanuwansa lumshe yana mai jin yanda ake hauhawa da nutsuwa da farin ciki a k'asan zuciyarsa. *"BATA JIN MAGANA, TANA TARA SAMARI, TANA SHIGAR BANZA, TANA CIKA DARE, TANA WASA DA MAZA, TANA DAMBE DA MATA, AMAN KUMA BA MAZINACIYA BACE*." Wannan kalamai su ke yawo a k'asan zuciyarsa, sai dai wani abu da yanzun yake jin shi a game da yar yarinyar, wanda a ganinshi babban abun kunya ne ma tattauna hakan da zuciyarshi ma, abun kuwa ba komai bane face wata *kunyarta* da yake jin tana wani sauko mishi a gabb'an jiki, duk da bai tab'a furtawa kowa halayyarta da yake zargi ba, amma dai yau kam abun kunya ne gareshi, sai dai ko ya k'i ko ya so dole ya yarda *NAJEEBA MUTTAB ta bashi mamaki*, mamakin da zai iya kira da mad'aukakin mamaki. Shi kad'ai ya sakarwa kansa b'oyayyan murmushi a k'asan zuciyarsa ya furta " *Lallai d'an hakin daka raina, shi ke tsokale maka ido."* Bugu da k'ari yan magana sunce " *Raina kama...ka ga gayya."* A hankali ya kai dubansa kan fuskarta , idannuwanta rintse, hawaye jage jage bakinta na rawa take furta kalamai kamar haka" *me ka yi? Ka shiga hakin HUZAIFANA, bayan shiga rayuwana ka shiga hakinna? Da wani ido zan kalli HUZAIFANA?* *Mai damagaram yi ta kanka.*🏃‍♂️ [31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 44 Sai da ya rintse idanuwansa kamar ta doka masa wani irin abu mai nauyi a kansa haka maganganunta ke sauka a cikin kunnuwansa. Murmushi ya samu ya saki a hankali kafin ya idasa dagata baki d'aya. Dubanta yake, ko hannayenta bata iya d'agawa aman bakinta ya kasa mutuwa, tana fada masa maganganun da yake ji kamar zai kifa a irin wannan lokacin. Abinda bai tab'a yi ba, abinda bai tab'a kulawa shi sultan SHAHEED ba, shine yau ya yi, du irin dattin dake tare da ita bai duba ba, haka ya mike ya d'aura tawul a kugunsa kafin ya cicibata a jikinsa, wata kyakyawar runguma ya bata ya nufi dakinsa da ita. Sai da ya shige dakinsa da ita ya nufi wajen abin zama ya ajiyeta a karkace har idanuwanta na hadewa dan azabar da take ji sannan sai had'e jikinta take irin kar a gane mata jikin nan. Murmushi ya kuma saki kafin ya nufi bayi. Sai da ya tara ruwa masu zafi , sannan ya cire tawul dinsa. Wanka ya fara yi dan tsaftace jikinsa ya cenza wani tawul din sannan ya fito cikin nutsuwa. Dan tsayawa ya yi gannin ta sauko k'asa tana ta son mik'ewa. A hankali ya k'arasa inda take ya kuma dan dukawa dan d'aukarta uwa wata yarinya k'arama. Najeeba da idanuwanta ke bud'e ta kuma rufewa da sauri jikinta bai daina b'ari ba, muryarta a ciki ciki ta ce" dan Allah kar ka tab'a ni, ka barni zan iya da kaina." Bai dai ce da ita komai ba daukanta ya yi ya nufi bayin da ita. Kallon ruwan yake yana tunanin ciki zai sakata? Bai tab'a dan ya samu mace a budurwa ya gasata ba, bai taba dan ya wahalar da mace ya kula da gashe gashenta ba, yakan yi kokarin ya kirayi wani baba naki ya taimaka maki, aman yau sai yake jin me zai hana ya kwatanta? A hankalo ya idasa ya rage tsayinsa kafin yake tsumbulata cikin ruwan. Wani ihun ta saki tana ririk'e hannayensa had'i da k'irjinsa. Tun jikinta na wani irin bari har ruwan ya idasa ratsata kafin take sasauta masa rik'on da ta yi masa cike da muryar kuka ta ce" Ban tab'a jin kyamar rayuwata irin ta yau ba." Idanuwansa ya lumshe yana sauraronta Idonta ta bude da kuka da dan ihu ihu ta ce" ka daina kallona, ban san me na tsare maka a duniya da kake yiwa rayuwata katsalandan ba, ka sake ni na roke ka." Idanuwansa dake kanta ya kara d'orawa a leb'unanta. A hankali ya kai hannunsa cikin ruwan ya ji ya rage zafin, bude wajen gudadar ruwan ya yi ya tafi kafin ya kamo mesar ruwan ya kunna na ruwan zafin. Sai da ya zuba a hannunsa ya ji tana iyawa sannan ya yi kasa da shi ya ci gaba da cika jakuzi d'in. Ita kam kuma hade kanta ta yi da gwuiwarta, so take ta kukurma ashar kala daban daban aman ta kasa domin dai ashar dai yaya DAYABU ya hanna su yiwa ko k'annensu bale baba. So take ta dago kanta ta fafad'a masa magangannu ta k'asa, kwata kwatama ya cika bayin baki daya ya gaje ko'ina ita ko numfashin kirki ta kasa. A hankali ta ji ya ce" me yasa kike so na sake ki?" Dago dubanta ta yi ta sauke kakausan kallo a kansa ta ce" Dan na tsani aurenka, bana son ka!" Sai da ya sauke yar ajiyar zuciya kafin ya ce" toh fa, nima ai ba son naki nake ba kau?" Kuturun kare, tabdijan, sai ta ji abin ya mata ciwo, yo ita tunda take anya wani namiji mai lafia ya tab'a furta mata baya sonta? Sai da ta firfito idannuwanta ta budi baki a hasale ta ce" kan...... A sanyayen ya ce" ki rage k'arfin muryarki mana, kar ki fad'i wata muguwar maganar da zata saka na cenza shawarar k'yaleki a wannan daren." Ido ta ringa binsa da shi, a sanyaye yake budar bakinsa ya yi magana, a sanyaye yake binta da wani sansayen kallo. Shima ita d'in yake kallo, *bana son ka*, kalmar nan ta masa nauyi a cikin ransa, bai san dalili ba aman ta masa tsauri da yawa, yafa san cewar bata son nasa, ya kuma san wanda take so aman du idan ta kara jadada lamarin sai mamakin abin ya tokare makoshinsa. Me ya yo zafi haka? Yau gashi zaune, a arha a irin lokacin nan ya zauna yana kallo ana furta masa ba'a sonsa? Idanuwansa ya kuma budewa a kanta, maganganu ya yi a lokacin da yake saduwa da ita, tabas ya kayatu da wani lamari mai girma wanda a kallon da yake mata a haka da ace zai iya kuma damkarta idan har zata masa shiru da kalaman tsana kuma zata iya d'auka, ba abinda zai hana shi mayar da ita doki daga nan har safe. Hannayenta da ta hade ya saka shi tsayar da tunaninsa. "Tunda kaima ba sona kake ba, tun fil'azal nake ganin k'iyayata a tatare da kai, nima inada wanda ke jirana, me zai hanna ka sawake min?" Sai da ya aika mata da killer smile kafin ya ce" saboda bana so ran su Anmy ya b'ace, kin kuwa san irin yanda suka ringa rokon na kawar da kai a yarintarki?" Kai? Kai? Kai? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une ta fada tana mai fashewa da kuka. Mik'ewa ya yi daga tsugunon da yake lura da ya yi ta fara kawo hankali yanzu so take ta nuna masa taken rashin kunya, so take ta hargitsa masa tunani, ao take ta hanna masa kyakyawan nazari bayan yana so ya kadaice kansa, so yake ya zauna ya yiwa kansa fada So yake ya idasa baje lamarinta a rubuce ba a cikin kwonyarsa ba So yake ya faro labarin daga tarihin rayuwarta So yake ya gane, meye sirrinta? Me yasa ta ringa fade faden samari? Me yasa take nunawa duniya ita din wata aba ce da ya dace duniya ta kyamata? Me ya sa ta mayar da namiji wani abin da take iya takewa? Idannuwansa ya rintse a lokacin da ya zo fita kunnayensa suka jiyo masa muryarta sama sama tana fadin" walahi, sai ka sake ni! Koma me zai saka ka sake ni sai na aikata! Ba ance zina da kisa ke sakawa ku yi saki ba? Sai ka sake ni, ni bana son farin mutun mugu mai cinye kudin talakawa! A irin juyowar da ya yi ya lura cewar a tunaninta har ya fice domin kanta cikin cinyoyinta ruwan dake diga sosai yana kara jikata. Irin yanda bak'ar fatarta mai haske ke haske wajen da yanda ruwan ke hauhawa jikinta da irin tsugunninta ya sanyaya cije leben da ya yi da niyar karasawa ya dagota da wuyanta ya hadeta da garun bayin dakin nan ya bambance mata sokayen da take farfadawa magana da shi! Tabas shi mijinta ne, aman karyarta ta sha karya ya zamo bawa a daka, shi sarki yake a kowace fada yana fatan hakan ya dore har ya daina numfashi A hankali ya dawo, wannan karron maimakun ya tsuguna sai ya dan dafa abin, a hankali ya ce" da ace zaki iya aikata zina, da kin aikata kin rabawa gayu domin kuwa sosai kin karci wuyan shashashai, Dan numfasawa ya yi yana gannin yanda ta zabura irin ta tsoratan nan da jin muryarsa a kanta ya kai hannunsa a hankali wajen idannuwanta hakan ya sa ta rintse idon nata da karfi. Murmushi ya yi ya ce" ko wani irin aure ke kan matar da na aura, zan so ta kiyaye abu guda, *had'a ni da wani* dan cije lebensa ya yi ya ce" ki gane, Allah ya killaceki dan zai malakawa wanda yake killatace! .......Sai da ya kara cije lebensa ya kara rage muryarsa ya furta" kuma ma ni bana iya k'yale mace ta ringa min magangannu haka *koda ina sonta*!" Gashin idanuwanta ya ringa shafawa a hankali yana kallon kyakyawar fuskarta wace a yau ta idasa k'awatuwa a idannuwansa A sanyaye ya ce" hakama da haram d'in zan ciyar da ke." Kara matsawa ya yi ya kai harshensa mai dan dumi dumi hade da leb'unnansa ya mana mata kiss mai zafi kafin ya furta" *nima bana son bak'ar mace ai*" Yana gama fad'a ya kara mikewa yana jin kansa har sarawa yake, shara'a yake irin mai rikicewar nan , aman ya fi magana da hannayensa da gangar jikinsa da, idannuwansa haka kawai fitsarariyar yar nan ta wani saka shi maida mata martani kamar mace? Har zai fita ya juyo ya ce" saura na dawo na kuma yi maki wankan Janabar idan har kika kara d'aukan lokaci!" Baki ta saki ta raka bayansa da kallo, wannan karon a kasan zuciyarta ta ayanna" Allah ya isana mugu, ai nima me zan ci da farin mutun? Nan da nan ka wani koma ja uwa k'osai, daga an yo abu fuska ta zame maka ja, ko rana ka shiga sai ta dafe maka fata, Allah na tuba na ci me a farin mutun banda mugunta me ka iya, ka ci nasara ta biyu a kaina aman ba zaka kuma gannina bama bale har ka wulakanta ni! Kuma na fada mai cinye kudin talaka, yo in ba cin haram ba ji bayin da ake wanka ko na Anmy albarka, sai na yi girki a wajen nan na ci, to na godewa Allah nima ba mabaraciya bace, da sana'ata bale har kaka naka yi ta kawo ni neman taimako." Wankan take da ruwan masu zafi tana ta fadace fadacenta a kasan zuciyarta har ta gama ta dauki sabon tawul ta lulubama jikinta tana jin kirjinta na mata nauyi domin bata saba wanka tsakiyar dare haka ba gata da ciwon huka. A hankali take takawa, du irin ruwan da ya ringa sakata ji take uwa ana tsikarinta da allura, haka kuma wani fayau take jinta uwa an wawushi wani nama mai yawa a kasanta. A hankali ta idasa fitowa daga bayin tana sando, so ta yi ta ficewarta komai ahirun fadar da abubuwan tsoro yau a wajen Anmy zata idasa wayewa. Sai dai tana fitowa ta ji an kama tawul din nata an shiga gogoge mata ruwan dake jikinta. A tsorace take binsa da kallo har ya gama ya karb'e ya yi gaba da shi. Da sauri ta nufi wajen da take gannin abin rufa dan rufe jikinta sai kuma ta rage tana furta" aushhhhhhhh!" A k'asan mak'oshinta D'akin ya d'auki dumi mai dad'in gaske sakamakon abin dumama daki da ya kunna ya kashe AC din domin ya san tana da ciwon Athsma ga garin ba laifi garine wanda daukan zafi du kiwa da irin manyan duwatsunsu Lulubawa ta yi ta yi zaune a bakin gadon tana binsa da kallo dan gannin karshen gudun ruwansa Shima saman kujerar dake facing din bed din, inda take zaunen ya hau ya zauna, sai da ya dan gyara zamansa irin na sarakai sannan ya kura mata ido irin yanda take kallonsa Furtawa take" mugu, azalumi, mai kwacen abinda ba nasa ba, sai Allah ya saka min irin hararan nan da kake min, kuma na rantse daya bayan daya sai na tarda matanka na daki banza har dakinsu idan ya so ka kule ni a dakin kaji! Shi kuwa fuskarta kawai ya kurawa ido, yana furta" inama ace baki da taurin kai? Da na kwatanta mayar da ke yanda nake son ki kasance, idan dare ya yi ki kawata min lokacina ta hanyar wankeni da bakon yannayin da kika sakani, shin me kike tunani? Yanda zaki yi da ni ko? To nan gani nan bari, kuma ba dai saki ba? Ba zan sake kin ba, tunda na ci wake a lambun nan, ba wanda zai ci irinsa, MAGE KAWAI MAI KWONCIYAR DAUKAN RAI! ...........ma ji, ma gani, ma gane waye Magen tsakanin mutanen nan biyu........baci dai ya iya sata........kuma baya yafe bashi. Talatainin daren nan ya faru cikin wani lamari mai wuyar fasara Mutun biyu ne tsaye a cikin duhu, sunna magana wace bata fi a irga ba aman yannayin taba hannayensu ya fi yawa A shafe nake, tun shekarar da aka so shafe shi ta same ni, gashi ya ajiye har uku yana bin daya bayan daya bayan ni nawa iyalan sun barni Dayan ne ya furta" kai naka iyalan ai ka tara, ni ban tara ba, ba kuma zan tara ba har sai na rama! Abubuwan hannayensu suka cenza kowane ya dauki hanyarsa suka shige ciki ......................................... Kowa da irin shiryawar da ya fi ganewa da ita Kamar yanda magaifiyarta ta fantsama neme nemen malaka, abubuwan da zata kasance ta malake shi sai yanda ta yi da shi, tana zuba tsabar dukiya tana amso yan kuli bisa yarda da ta yi cewar wanda ya bata kulin ya isa ya zartar da hukuncin abinda take so ita da yarinyarta ta dawo ta kuma dukufa ta ci gaba da dadaure Zinaria da kalamai irin na....ki turara, ki tsuguna, ki yi wanka, ki kurba, mu binne inda aka ce a binne, ina mai tabatar maki na lungu baya karya Cike da kalaman nan har hankalinta ya fara dawowa jikinta, hakan ce ta kasance a yau tsakiyar dare suka fito suka yo bine binen, kafin ta bude mata abubuwan turaren ta saka mata A lokacin da ta fara turaren ne ihun NAJEEBA ya karade wajen, wanda in dai ka kusanci bangaren tabas zaka jiyo sai dai ka yi kamar baka jiyo din ba Wannan ihun ya kusan summar da ita harma ta shiga kuftayar son zuwa dan ta ga ko menene Janta uwar ta yi, a lokacin suka hade da munafukin nan Murya a kausashe Gimbiya ta furta" ko da rai, ko ba rai, ko da hankali, ko babu, ko da yarda ko da karfi sai sun bara maki fillin mulkin ki! Tana maganar tana idasa janta cikin bangarenta ne hankalinta du a tashe domin kuftaya Zinariyar ke yi kan lale lale sai ta je bangaren Sultan dake zazagaye da dogarai Niyarta daya ta idasa shigewa falon da ita tana kara rike abinda ta amsa a hannun mutumen kafin ta shiga kai kawo yayun Zinariar na tambayar abinda ke faruwa Rai bace ta ce " wani irin rashin mutunci ne za'a ringa jin ihun mace a bangarensa? Ba zai iya hannata ihun ba sai ya buda an san abinda ke faruwa da ita ko sallon iskanci ne tsagera ce itama wace yake taren da ita? Wacece? Me ta zo da shi? Tabas zan nemi mu je Agadez da Zinaria, dole zan kai y'ata na shiryata a wajen da zan yi abinda na ga dama ba tare da an dakatar da ni ba, dole zan nemi layin Sarki na fada masa rashin lafiyarta sai mun zo gida! Su dai yayun nata sunna son danarta ne, aman sun san da kamar wuya mahaifinsu ya yarda da a zo da ita gida, Zinariya kuwa bata taba jin tsana mai tsanani irin ta yau ba, bata san da wace yake tare ba aman abu daya da ta sani koma wacece sai ta ga bayanta, har ya kai ga zuwarma wata? Gujin kuka take ido rufe hannayensa a daidai kirjinta Hasko irin tsarin mijinta, sansanyan kamshin jikinsa, ni'imatacen laushin fatar jikinsa, takamarsa mai kara sakata macewa a kansa, kamshin bakinsa mai sanyi da saka nutsuwa, du ya anfanarwa wata? Sam bata son kawowa ranta cewar zai iya kusantar Najeeba, qbu daya take son tabatarwa cewar Nadia ce, idan kuwa ita din ce ta rantse sa hannunta zata kwakule mata du wani abin anfanuwa na jikinta! Ta tanata a irin yanda ta lura sam Najeeba bata cikin wa'inda zasu iya samun alfarmarsa, hakan ya sa ta yarda da maganar mahaifiyarta cewa ta sada kanta, ta yaki lamarin a hankali ta kasan kasa, .................................... A hankali wani baci mai nauyi ke fuzgarta , ga ciwon da jikinta ke mata , a zaunen nan da take ita kadai ta san irin azabar da take ji a kasanta , ta luluba sosai har kuma zafi ya fara damunta aman ta ki sararawa jikinta sonin tsoronta Allah gudunta ta kuma rufe ido wa'innan idannuwan nasa masu dauke da kwali da wani irin launi da ya tsaida tar a kanta na sakata cikin yannayi na shaku da taka tsantsan Daga inda yake zaune, bai taba kasancewa a nishadi irin na yau ba, dadin kallonta yake ji a kasan zuciyarsa, murmushi yake a boye wanda sam ba'a gani Sarai ya san tana jin wahalar zaman nan, aman yana kallonta dan ya ga irin jarumtarta, ai ko da yar yatsa aka kaiwa wajen nan zihara za'a ji jiki bale uwar yatsa Muzgutawa ta yi , baci na rinjayarta, kanta na kara nauyi ga ciwon da yake mata ta kwonta a karkace tana hangensa Tun tana ganninsa har ya kasance kamar ta sume, ta daina fahimtar komai ta daina gannin komai, ta shige wani irin baci mai tsananin nauyi Ajiyar zuciya ya sauke ya kai dubansa wajen agogon dakin Gannin karfe biyar ce ke shirin yi ya saka shi mikewa a hankali ya nufi wajenta. Hannunsa ya saka ya gyara mata kwonciyar da ta yi ya kuma zubawa fuskarta ido na dan lokaci " *Who are u NAJEEBA?"* Karasawa ya yi bayi ya kuma dauro alwallah ya fito. Kad'aice kansa ya yi ya shiga bautar ubangijinsa cike da nutsuwa mai girman gaske. A inda yake zaune sai da haske ya fara nuna kansa kafin ya d'ago kansa daga dukufar da ya yi yana jan carbi. Adu'a ya yi ya shafa sannan ya mik'e ya koma d'akin. Tun kwoncinta ne dai bata juya ba, da ka ga kwonciyar ka san a takure take, a gajiye take. Ya saba komai gajiya a irin lokacin nan yake shiryawa, du irin bacin da yake ji kuwa ba zai iya zama bacin ba. Wanka ya tsalo ya dawo ya shirya kansa cikin shiga ta alfarma kafin ya fita ya yi zaune saman kujerar dake facing d'in wace komai ya wakana tsakaninsa da ita a tsakiyar daren nan. Idanuwansa ya lumshe yana girmama lamarinta a cikin zuciyarsa. *"SHAHEED, BANA SON KA, MUGU, BANA SON FARIN MUTUM, SAI KA SAKE NI, HUZAIFA."* Kalaman nan ya yi wani waje mai girman gaske ya ajiye su, zai iya rantsewa ko Anmy sai ta kakare take fad'in sunansa kai tsaye. Ko da ranta a b'ace yake zata sanyaya muryarta cike da rarashi ta kwatanta masa. A fannin mace kuwa, bai tab'a had'uwa da macen da ta kalleshi shi SULTAN SHAHEED ta kama sunansa gatsai haka ba, sannan a irin damk'ar da ya mata ta kuma duban idanuwansa ba. Murmushi kawai ya yi, idan har bai zurfafa a sanin wacece ita ba , akoy damuwa. ..................................... Hannunta da ta tokare gefen kumatunta UMMU ta kama ta cire tana kallonta ta ce" yaya wai meye wannan dan Allah?" Anmy ta sauke ajiyar zuciya ta kai dubanta wajen agogo ta ce" MARIAM, karfe goma ta gota bai yi kira a je a rako min yarinya ba, Maryam ko dai zuwa zan yi?" Idanuwanta ta zaro cike da mamaki ta ce" Anmy, ki je ina? Sai ki je ki ce me ya tsayar maki da yarinya? Kin ga fa su Zahrau du sun yi wani iri yau na ga ikon Allah, ita Zahrau tun dazu jake fama ta tashi ga mai kitso da kunshi a shiga yi mata domin gobe walahi zata juya gidanta aman ta ki tashi da waya a hannu wai ko zai kirayeta? To cinyeta zai yi ni NANA MARYAMA? kun ga Bayan kun san yau DAYABU ke kawo yarinyar da yake nema kuma du sai ku wani baje a nan? Dan Allah ku tashi hakanan." Jakadiya ce ta shigo ta duk'a ta shiga kwasar gaisuwa. Du Anmy ta yi tsai tana jiran ta ji labarin NAJEEBA ne sai kawai ta ji wai MARDIYA ke neman iso Da sauri ta kai dubanta wajen Ummu, ta kai bayan UMMU tana goye da NUSAIBA ne wace ke dan zazabi tana dan rigimar zazabin Mardiya? Ta tabata yarinyar a yanda bata da kunya zata iya yin wani abin na rashin kunya, du abinda ke faruwa ita dai tana kiyaye abinda za'ace an yi da ita, du tsakaninta da yara suke fadace fadacensu Aman tana tsoron idan har UMMU zata iya hadiye wani iya shege duda yanzun UMMUN ba irin ta da bace aman duda haka tana shakun UMMU. A hankali Anmy ta ce" ita da waye?" Jakadiya ta k'ara sada kanta sosai ta ce" Ita da wata mata ce wace zasu yi sa'anni, inaga ana yawan zuwa shara'a da matar wannan wace ake kira da wudiliya." ANMY ta kuma kallon UMMU sai ta ga ta koma wajen Zahrau ta karb'e wayar hannunta ta nunata da yatsa a kausashe ta ce" ZARA MUTALAB , ko ki mik'e ki cire hijab d'inki a maki kitson nan ko na jibgeki na rantse a wajen nan!" Da sauri Zahrau ta mik'e tana cire hijab d'in, muryarta a raunane ta ce" Ai da wuri yake kira a d'auko wace ta fara kwana b'angarensa, ai da wuri yake kira tun da duhu duhu, *ina NAJEEBANA? LAFIA HAR YANZU BA'A NEMI A ZO A RAKOTA BA KAR DAI A JE ABIN YA MASA YAWA NE UMMU?"* Ummu ta saki baki gannin zata tona masu asiri dan kawai ta firgice. Anmy ta kalli jakadiya ta shiga tunanin me zata ce mata? Baki daya y'ayan na nan, Dayabu na hanya uwa uba UMMU, NAJEEBA na iya shigowa yanzu ko idan an jima, Shin zata yarda ta shigo bayan ta santa da neman fitina ta tada mata rigima a irin wannan lokacin ko zata hannata shigowa ne? A sanyaye Anmy ta kuma kallon jakadiya dake jiran amsa kafin ta bud'i bakinta ta ce"... [31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 45 A sanyaye Ammi ta ce "Ki shigo da ita" Har ta mike za ta fita Ammi ta kuma faɗin "Ki kai gaisuwata ɓangaren Sultan" Kuma ɗukawa ta yi cike da ladabi da biyayya ta amsa kafin ta tafi. Ba'a ɗauki lokaci ba suka shigo. Wata irin kwalliya ce jikin Mardiyya, ta sha wani rantsatsen lesh an yarfa mata mak'up Tunda suka shigo hankalinta ya tafi wajen yaran, Bayan wacve ke goye da Nusaiba kawai take iya hangowa, Ummu kuwa na tsaye ne tana nuna irin kitson da za'a yi wa Zahrau. Zama suka yi saman kujera sannan suka shiga gaishe da Ammi Ammi ta amsa masu cike da kulawa tana ɗan satar kallon yaran , sam ba wadda ta yi yunƙurin gaishe da Mardiyya, ko damuwa basu yi da ita ba Kwarai bata ji daɗin hakan ba duk da mutum shi ke janyowa kansa mutumci ko akasin hakan, amman ai tarbiyyarsu fa? Sai da ta sadda kanta a hankali ta ce "Allah ya taimake ki, dama kan maganar Abban Nusaiba ne na zo, kwata kwata ya zubar da ni, ya yi block din numbobina ba gabaɗaya da nake samunsa, hatta Mama sai da ta saka a neme shi amma ya ki zuwa, gashi ni ba sakina ya yi ba" Dan saurarawa ta yi ta dan dago dan gannin shin tana sauraronta? Gannin Ammi na kallonta da kyau ya saka ta ci gaba da faɗin "Idan laifi na masa tsakanina da shi ai ya ci ace ya yafe, idan kuwa fadana da yara ne ba ruwansa ya fita a ciki domin tsakanina da su ne" Da mamaki Ammi ke kallonta a kasan zuciyarta kuwa faɗi take 'Ikon Allah, wai ita a gidansu ba'a fada mata ka so mutun ka so d'ansa ba?' Dubanta ta kuma kai wa wajen Ummu dake dan jijjiga Nusaiba, ko nauyinta bata ji haka take jibgata a baya ta yi ta jijjigawa, a yan kwanakin da ta yi da yarinyar ta matukar sabawa da ita domin yanzun Mama sak take kiran Ummu da shi kamar yanda sauran yaran ke faɗa. Mikewa ta yi ta nufi wajen Muryarta a dan dake ta ce "Sannu fa?" Dakatawa Ummu ta yi ta juyo daga wajen yaran dake ta mata surutu Ido cikin ido suka kalli juna, ita dai bata santa ba, sam bata taɓa haɗuwa da ita ba, ko hotonta bata sani balle ta shaida ta. Ba wata shigar firgita mutum ce a jikin Ummu ba, domin riga doguwa ce sakakkiya baka a jikinta Sai dai yannayin tarin kamalar da fuskarta mai cike da yalwataccen gashi da ɗan murmushi ya saka Mardiyya jin shakkun yi mata magana a gatsai gatsai Dan haka sai ta dan kakari murmushi ta ce "bani ita na rarrasheta ko zata yi shiru? Kallon da Ummu ke mata dan ta fahimci ko wacece ita, sarai ta san matar ta hoto amma ko ita bata taba haɗuwa da ita gata gata ba A hankali ta ringa kunce goyon kafin ta juyo da Nusaiba ta mika mata ita Da farko idon yar a rufe yake, hakan ya sa ta yo lufff a jikin Mardiyya, sai da Mardiyya ta ce "A'a, bata da lafiya ne? Jikinta zafi haka me yake damunta?" Jin muryar ya sakata buda idannuwanta Kallonta take kafin ta fara rigimar sai ta koma wajen Ummu (idan baku manta na Nusaiba yarinya ce karama, ko a haka Mardiyya ta kasance mai yawan zaginta hantararta da yawan faɗa, a rayuwar yanzu ko ɗan naka ya mallaki hankalin kansa sai da addu'a da kawar da kai, bare yar yarinyar da ta samu mai rarrashinta da nuna mata soyayya hakan na iya haifar da son nisantar mahaifiyarta da ta haifeta, karamin abu ne hakan) Da mamaki ta kalli Ummu, da yanayin shashanci ta ce "ke ko har kin canza uwa ne haka zaki ringa kuka a hannuna?" Ummu kam wajen ta bari ta koma saman kujera ta zauna tana mai bin Wudiliya da kallo wace ke zaune tana bin kowa da kallo itama Wani murmushin ta yi ta kuma maida dubanta wajen yaran Da idannuwanta take gallawa duk wanda sukai ido hudu harara, sai dai a yanayin yanda ta lura sun rigaya sun hade kan nasu na iya shege wato kar wanda ya gaishe da Mardiyya? Sallamar Dayyabu ne ta saka su duban wajen Shine ya fara shigowa cike da yalwatacciyar fara'a a fuskarsa Bayansa wata yar budurwa ce kyakyawa fara tas , ta saka abaya baka har kasa ta yane kanta da mayafinta Du sai yaran suka shiga murnar zuwansu Zahrau ta mike tana yafa dan kwalinta cike da nuna kulawa suke yiwa budurwar yayan nasu barka da zuwa Kasa ta zauna kanta kasa tana murmushi tana dan murza yan yatsunta, shi kuwa yana zaune kusa da Ummu yana mata magana kasa-kasa, haka kuma kannansa duk sun zagaye shi ban da Zahrau da ta shiga hidimtawa bakuwar cike da fara'a Hannun Bilkisu ya dan doke ya ce" Mairama ki barni da tsegumi wai ba yayarku bace ku je mana ku tambayeta" Jin abinda ya fada ya sakata dan dago dubanta tun bayan gaishe su da ta yi Dan murmushi ne a fuskarta kafin ta mika hannu a hankali ta furta "Ku zo" Sai da suka kara kallon iyayen nasu kafin duk su yi wajenta Ai kuwa ta ringa cafe hannayensu suna gaisawa duk da ba sakin jiki suka yiwa juna ba amma fuskarsu da mawadacin farin ciki Baki ta tabe kasa-kasa ta ja tsaki sai kokowa take da Nusaiba dake son zuwa wajen Ummu Ammi ta kai dubanta wajenta ta ce "Mardiyya, barta ta je wajenta mana, mamanta ce fa, mahaifiyar Najeeba ce" Da sauri ta dago ta kai dubanta wajen Ummu, Sam Ummu bata kallonta, hasalima dariya take yiwa maganar DAYYABU na irin rigimar da suka sha kafin budurwar tasa ta yarda ta zo gaishe da su A hankali ta furta "Na ji dadin jin haka, hakan na tabbatar min da tarbiyyarta, har ma na ji ina zumudin kasancewarta matar yarona" Tana maganar tana kai hannunta gefen fuskarsa ta dan shafa a hankali sunna dariya a tare Wani irin abu ne ya tokare kirjinta kokowa take da abinda zuciyarta ke tambayarta, dannewa take dan kar ya fito fili tana kara kallon su UMMU da DAYYABU ga kuma AMMI dake ta sakin murmushi da alama ta manta abinda ya kawo su gidan ko meye. Zuciyarta ce ta ci gaba da fadin 'What? Meye wannan? Wani irin abu ne wannan? Ko dai yar uwarsu ce? Meye tsakaninsu mai karfin da take zaune rashe rashe a gidan Ammi haka? Goye da Nusaiba ga kuma yaran sai wani hira suke uwa wace ta haife su da cikinta?' Daga dogon corridor din dake hadawa da bangaren SULTAN iso ya ringa shigowa cikin maganar mutun kamar biyu Da sauri Ammi ta kai dubanta, hakama Zahrau da du wani wandake wajen Ita ce ta sanyo kai, cikin shigar da ta tafi da ita wato alkyabarta ce sai dai kamshin turaran ba wanda ta je da shi bane, kamshin turaran SHAHEED ne ya fara dukan hancin duk wani wanda ke wajen Da sauri yayunta suka yo kanta, domin ja ta yi ta tsaya tana mai jin kunyar kallon su ido cikin ido Wani irin farin ciki ne ya lulube zuciyar Ammi a lokacin da ta fahimci komai Ummu ta sadfa kanta tana murmushin cin nasara DAYYABU ne ya mike shima cike da farin ciki ya yi wajensu A hankali suka kamota suka nufo ciki da ita Budurwarsa da kallo take bin su, tabbas yau ta kara yarda da irin soyayar dake tsakaninsu, cike da mangari take dubansu, a ranta kuwa ji take inama ace sune haka? Ita bama yan uba bane aman ba wani kulawa da junna da suke da yan uwanta A ranta take jin zata dauri niyyar kusantar yan uwanta koda kuwa ba zasu kulata ba har su samu fahimtar juna Kanta a sade yake baki daya yau kunyarsu take ji, ji take duk sun gane abinda ya sameta hakan ya sa ta kasa hada ido da su sai kara sada kanta take DAYYABU ya ce "Ke wai menene?" Jakadiya da babar baiwar bangaren SULTAN ne kawunnansu sade JAKADIYA ta furta" Allah ya ja da rai , Allah ya taimake ki , Sarki na gaishe ki, yana mika sakon gaisuwa da godiya, yana neman afuwar jinkirin zuwan GIMBIYA" Ammi ta kara yin murmushi kafin ta gyada masu kai suka mike suka fice Mikewa UMMU ta yi ta karasa ta kama hannun Budurwar DAYYABU Cike da kulawa ta mikar da ita tsaye ta kara matsota kusa da Ammi sannan ta dan dago habarta a hankali ta ce "Allah ya albarkaci rayuwarki yarinyata" Kanta kasa tana kara sadawa domin ya sanar mata mamansa ce, cike da jin kunya da kaunar Ummu take kara sada kanta Dubanta ta maida wajen su DAYYABU , a hankali ta furta "Ku tashi mu shiga ciki" Duk mikewa suka aniyar yi suna kama hannun Najeeba ta mike kafin su nufi cikin Wudiliya ta kalli MARDIYYA da ta yi mutuwar tsaye ta gyada kai cike da mamaki Mardiyya ta karaso ta zauna tana kallon Ammi ta ce "Ammi baki ce komai ba, ko ya sake ni ne bani da labari ya auro wata? Ammi ta kalleta, bata gane ta mata shiru ne dan ga bakuwar fuska? Sannan bata so maganar ta yi nisa irin haka a gaban yaran? A hankali ta furta mata "Mardiyya, kar ki damu zan kiraye shi yau, idan ya so zai zo koda kuwa da ni ta kama zuwan zamu zo" Yar dake kuka ta dire mata ta mike ta fara kama hanya Da sauri Wudiliya ta mike ta bi bayanta Sunna fita Mardiyya ta ja ta tsaya ta keta wani ashar tana fadin "ldan na yarda ya banzatar min da aure shegiya nake" (shi ya banzatar maki ko ke?) Wudiliya ta ce "Yau na ga bariki gannin idona, kina zaune za'a yi maki sakiyar da ba ruwa? To ko danginsu ce ita wannan matar dake goye da Nusaiba? Ke anya baki yi sake ba za'a maki sakiyar da ba ruwa? Anya ba wasa kike da lamarin MUTALAB ba?" Mardiyya ta kalleta, da kallo irin na son karin bayani Wudiliya ta ce "dubi yanda y'ayansa suka nuna basu san da wata halitta wai ke a wajen ba, kuma suna kiran wancen da sunan Mama, dubi fa yanda babban dansa ke hira da ita kamar wace ta nakudo shi? Anya ba wasa kika tsaya yi ta fi ki iya bariki ba har ta fi ki fada a wajensa?" "Ke kika san dalilin rabuwarsu? Kin ga kar ki wani raba min hankali, ina ce kin rakoni ne dan ki tayani sakawa ta masa magana? Nima ba zan yarda ba, wannan tsohuwar da na tabbata ta haife ni na rantse a yanda na san MUTALAB na tabbata ba zata dauke hankalinsa a kaina, inaga yar uwar tasu ce kuma kin ga bama zan bi ki ba zan koma na nuna hankalina ya ki kwonciya saboda jikin Nusaiba, zan jira shi ya zo ya fada min matsayina a wajensa a yanzun ehe, maganar y'ayansa basu gaisheni ba kuwa ban damu ba, dama me kike jira da fitsararri tambaɗaɗɗi yan iska?" Mardiyya ta ida sa zuciyarta cike da wani tsoro da jin wata fargabar gannin Ummu, kwarai irin yanda ta ga yaran sun sake da Ummu ya daketa, irin yanda Ummun ta wani nuna ita din isasshiya ce a gidan ya daketa, ta jigata, accnt dinta ya yi kasa sosai, motarta tana bata wahala, ta je gidansu ya ce zai waiwayeta ya manta da ita, ko auren Najeeba sai a redio ta ji da kuma yanar gizo, ana ta yi mata barka wai ita matar ubanta, kwarai a yanda ta san MUTALAB da kwakwar mace ya bata mamaki, aman zai zo ba inda zata motsa wallahi kafarsa kafarta da tsiya tsiya! (Ko? Tsiya tsiya fa? Namijin? Ko kannin kemenka ne ka bishi a laluma domin yana dauke da igiyar da idan ya tsula maki ita sai kin rasa gane hanyar gidanku ko wacece ke!) Kasa ce mata komai ta yi tana binta da kallon wawuya, idan ba wawanci ba ko Mutalab mahaukaci ne ai ita bata ga ubanda zai cireta daga gidansa a haka ba, bale mutumen a tsaye? Da alama Mardiyya sai ta sha bulaliyar duniya zata yi hankali Du irin yanda suke so ta fada masu abinda ke damunta kallonsu kawai take, sai da ta ja iska a hankali ta kalli UMMU Idannuwanta cike da kwallah, muryarta a raunane ta ce" me ya sa kika tafiyarki a lokacin da muke cikin rayuwar bukatar ki? Me ya dawo da ke a yanzu?" DAYAyBU ya furta "NAJEEBA, meye haka?" Najeeba ta dube shi ta ce "Yaya? Kai baka ssn sanin dalilinta na tafiya ne ko ka san dalilin nata ka ki fada min? Tsananin son kudinta ne ya hanata zama tare da mu ko kuwa bata dauki aurenta da mahinmanci bane? A yanzu da take son tirsasani zama da auren da bana so a matsayinta na wacce ta tafi ta tsinke nata auren tana tunanin zan mata biyayya ne?" Da mamaki ya zaro ido, muryarsa kausashe ya ce "kina hauka ne? Mahaifiyar taki kike yiwa irin maganar nan, titaiyeta zaki yi kan abinda ba dolene sai ta fada maki ba ko fada zaki yi mata kan rayuwarta a matsayinta na mahaifiyar ki?" Dan murmushi ta yi tana janye hannunta daga cikin na Ummulkhair, da yar yatsarta ta nuna Ummukulsum a sanyaye ta ce "abu nawa rashin uwa a kusa da ke ya tauye maki?" Juyawa ta yi wajen Ummulkhair ta ce "har gobe cikinmu wa ke kukan da ace mamansa na nan?" Zahrau ta nuna ta ce "yaya kika ji dadin zuwanta kusa da ke a yanzu?" Ta koma wajen DAYYABU ta ce "da ace da daya wace ta rungume mu da yanzu ka haifi y'aya biyu ko uku, amma kasancewar kaine uwarmu a kulun tunaninka idan ka yi aure kar ka kawo wace zata daga maka hankali a kanmu" Daga idannuwanta ta yi zata kuma yin magama suka sauka a kan ABIH, tsaye yake yana kallonta, duk basu san da zuwansa ba wanda tun da Mardiyya ta shaida masa zata je a message ya azamar ajiye abinda yake dan ya tarda ita kar ta je a yi rigima domin ya san wacece Mardiyya haka kuma ya san wacece NANA MARIAMA idan aka kawo mata raini DAYYABU ya budi bakinsa a sanyaye ya ce "kennan har yanzu baki daina jin haushin auren nan naki ba?" UMMU ta buda idannuwanta da suka cicika da kwallah Karasawa ta yi ta zauna kusa da su sosai Idannuwanta a kan Najeeba wace ta sada kanta tun da ta ga ABIH a tsaye A hankali ta lumshe idannuwanta ta kuma budewa a kanta A sanyaye ta furta "Ban taba aikin da na yi nadama irin tafiyar da na yi na barku a lokacin dakuke da bukatata ba, bayan sanin da na yi cewar y'a mace na samun tarbiyya ne daga mace yar uwarta, na san wa nake aure a lokacin, na saka kafa na shure y'ayan dake kallona su kirayeni *MAMA*, ya kara doke yaron dake zama ya dora kansa saman cinyata ya ce da ni *UMMU*, na tafi dan kawai fushin zuciyata bayan na kawo rantsuwa na gifta mai girman gaske da zafin kishin da ya rufe min ido wanda ya saka ni dana sani, na juya na tafi bayan na kunce goyonki a bayana ke da na haifa da cikina, ban ko waiwayoki ba na tafiyata da passport dina da visata na yi jiran jirgin da ya zo ya dauki passinger ciki harda ni ina hura hanci rai bace da kudadena da katina na banki na tafi na bar kasar haihuwata" Sasautawa ta yi sakamakon hawayen da ya fara zubo mata daga gurbin idannuwanta A hankali ta ci gaba da fadin "sai dai kashh, da na sani, da na kawar da kaina, na hadiye wulakanci da neman fitina da tashin dukiya da irin yanda kudi ke dukan kansa ke saka shi aiwatarwa a gareni na rungumi yan dagwai dagwai dina na rayu da farin ciki, domin kuwa daga bakin lokacin da na sauka, na fara kokarin ciyar da kaina, tufatar da kaina, neman abinda zan yi dan inganta rayuwata duk da tarin takardunna, da dukiyar da na tafi da ita ta gadona da iyayena suka bara min, sai rayuwata ta zamo wata sabuwar rayuwa mai cike da duhu duk inda na ga yaro ko yarinya sai na saki murmushi sai kuma hawaye ya biyo baya Idan na zo kwontar da hakarkarina wani sa'in idan nonona ya soke ni sai ki fado min a raina Nakan zabura ni kadai a dakin hotel dina ina jin kamar muryarki kina fadin *"MAMA, ZAN YI FITSARI"* Na rayu cike da burin zama wata abu, da son goge ku a rayuwata na manta da ku na sake wani auren na haifi wasun Sai dai me? Ashe na yiwa kaina mugun illah ta hanyar shakuwa da ku, Makwoncinmu daya A tsakiyarku nake kwanciya inai maku tatsuniya kunna hayewa jikina kuna kokoyi, Idan kukai fada nakan ji hankalina ya tashi, zan saka ku shirya ta hanyar nuna maku ilar abin Na saka shakuwa mai tsanani a tsakanina da ku, da yayanku har ya kasance na zabi kulawa da yara a matsayin karatuna" Sosai take hawaye hakan ya saka ta saka hannayenta ta toshe bakinta dan kuka take son yi sosai Dayyabu kansa da yake mai saurin hawaye ne idannuwansa sun cika da kwalla, hakama sauran du hawayen suke zubarwa ciki kuwa Harda Najeeba dake hango duk abubuwan da take fada a zahiri kamar a lokacin komai ke faruwa da rayuwarsu Mikewa ta yi da sauri ta juya da nufin tafiya, domin ita dai da bakinta ba zata iya furta masu dalilin fushinta ba Karron da ta ci da shi ne ya sakata kokarin zubewa Sai dai bai bata damar hakan ba ta hanyar tareta sosai da hannunsa kafin ya maidota dakin da kyau kusa da yaran ya aniya zaunar da ita yana kallonta a sanyaye ya ce... [31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 46 A sanyaye ABIH ya ce" ina zaki je bayan ina jiran wannan ranar shekara da shekaru dan na baiwa Najeeba amsar tambayarta wace du sauran yan uwanta ina iya basu amsa kai tsaye na dalilin da iyayensu suka bar gidana aman ita na kasa bata amsar?" A tsorace take kallonsa, bakinta na rawa ta ce" amsar? Wace amsar kake tunanin zaka iya fada masu?" Abih ya dan yi mata murmushi mai ciwo a hankali ya furta" haba *SIRRINA*, baki san sun san wani *Sirrin* rayuwata mai tsanani kuma suka hakura suka ci gaba da mutuntani ba? Yaya kike so ki ci gaba da fuskantar irin wannan shariya da abubuwan da y'arki kwalin kwal ke maki a kan namijin da ya kuntata maki? Kina da bukatar samun girmamawa, soyaya, kallon daraja daga wajenta, tabas kina samu daga wajen yan uwanta aman ita din ke kika haifeta fa? Dan Allah ya isa haka, ki barni na fada" Har bakinta rawa yake ta furta" aa, ba ruwanka da abinda ke damuna, ni ban rokeka fadin wannan abin ba, ina fadawa Allah idan lokacin ta dubeni ya yi zata dubeni dan kanta" Murmushi ya yi yana dubgure kanta ya karasa da sauri ya zauna gaban y'ayam nasa ya ce" ba ga irinta ba, ci gaba zata yi da boyewar, tana kakare laifina, ita dai a haka take so ta kare?" Najeeba, na auri mata goma sha bakwai a rayuwata Cikinsu ba wace ban haihu da ita ba, kuma ba wace ta ga girman y'arta take fecewa Na birne mace uku a gidana wa'inda suka rasu a hannuna, sauran goma sha ukun nan du rabuwa muka yi, banda mardiya ta sha hudu Najeeba, kamar yanda kuka sani, wasun dalilin na tarda su sunna dukanku ne, wasun rana tsaka zaku tubure da rigimar bakwa son su, wasun zasu nunan ba zasu iya rike y'aya birjik haka kawai bane, wasun zalamarsu ta saka, wasun kuwa sun aikata abinda ya hana min yafe masu ne ya saka ni rabuwa da su aman banda *NANA MARIAMA* Sai da ya kalli UMMU dake kallonsa da mamakin wai da gaske bayanin zai yi ya yi murmushi ya ce" aminiyar BILKISSU ce, wato Ammi dinku, ita ta yi mata gorancen aurenta, sun kasance masu raba ayya daya, sunna rike sirrin junnansu duda BILKISSU ta bata shekara UKU a haife wanda hakan ya saka idan ta yi niyar tsokanarta ko idan tana cikin yannayi na tashin hankali takan kirayeta AUNTY domin takan ce da ita "Bani da kowa sai Allah sai ke" Min sasanta kanmu da NANA MARIAMA a lokacin da nake amsa sunnan Yaro da kudi, ina jin wani irin tashen kudi dake daukana yana yawo da ni yana dadani da kasa Na tara y'ayan sai dai ba wai takamaiman su din ne a gabana ba, ina dai da wani irin kaunarsu a zuciyata wada ke sakawa idan aka yi katari na dan zauna na ji damuwarsu to fa ko wace iri ce zan dage na magance masu banda zama da su da kukawa da tarbiyarsu da kuma gane irin ilar sakin iyayensu da shigowar bakin fuska a matsayin sababin iyayensu ke janyo min Sai da na auri NANA MARIAMA na fara gane meye ma'anar zuri'a, Tanadinta zuri'arta, burinta zuri'arta, farin cikinta zuri'arta, abokannanta zuri'arta a lokacin ta shigo ta tarda mahaifiyar Ummukulsum da tsohon cikin Ummukulsum Zamansu bai yi nisa ba na sawake mata a lokacin da ta haifi yar jaririyarta sakamakon gannin itama ta haihu yanzun zata fara ware nata daban sauran daban wanda na kamata da hakan sau uku karshe dai na sawake mata na ci gaba da koyon rayuwa a wajen NANA Mariama Fadace fadace, rashin zaman lafia, rigingimu na tsakanin miji da mata kan hada mu, sai dai wani ikon Allah daga lokacin da zan tabo ku zata zube a kasa gwuiwoyinta a kasa tana kuka ta ce" ka yiwa Allah ka yiwa Annabi muhamadu salalahu alaihi wa salam ka barni na huta, ka barmin yara su huta, kai baka gannin yarintarsu, soyayarsu, karfin zuciyarsu? Kar ka hargitsa min tarbiyarsu ko ka birkita min zaman lafiyarsu, yaren nan sune farin cikina, kai ka san ba dukiyarka ko kyanka ya saka nake hakurin zama da kai ba sai dan yaren nan" Abinku da wanda shedan ya rigaya ya buga min ganga sai na sheke da daria sai na kalleta a kaikaice na ce" ku ji shishigi malan, yara ina ruwanki da su? Su tashi a tashama mana na san tarbiya ta Allah ce ba ta wani ba, dan haka idan kin gaji da zama da ni ki kama gabanki!" Zata kawar da kanta, ra mike ta tatara ku ta yi vangarenku da ku, ta hanna yan aiki zuwa inda kuke da cikinta a jikinta ta yi ta kulawa da ku, har sai na kasa jurewa dan kaina na dawo na lalabata domin du abuna nakan kasa nutsuwa idan muka yi fadan da ta min fushi har ta kaurace min, zaku ga na dawo ina lalabata mu shirya" Dan murmushi ya yi ya ce" har zuwa lokacinda yar uwarta wace ta kasance yar mahaifinta ce ta bayanna, Wannan itace rayuwar da na yi mafi muni a cikin rayuwar da giyar kudi ta kaini ta baro ni" Kallonsu ya yi da kyau ya ce" a lokacin bata fi wata hudu da cikin Najeeba a jikinta ba, murna farin ciki haka take bugawa mutane tana fada masu ashe tana da yar uwa? Kuma itama yar uwar nata da danginta bangaren mahaifiyarta, wato dai ta samu dangi Sosai ake shige da fice ana tayata murna, harta da dangin na yar uwar tata sun zo sun taya murna, inda yar uwar tata ta tare a gidanmu suke zaune kalau A hankali yau da gobe, kadara da haduwa da wata irina wace ta sako duniya a gaba muka shiga fandarew, munna watsewa, munna aikata alfasha a boye a cikin gidanta na aure cikin du dakin da hakan ta kama" Subahannalah, Ummu ta fada da karfi ta ce" wai wa ya tambayeka?" Hararanta ya yi ya ce" ko dai bakin ciki kike na huta da nauyin dake kaina ne?" Ci gaba ya yi da fadin" tun bata sani ba, har Allah ya sanar da ita, Ta ci kuka, ta yi dana sanni harma ta so bara min gidan sai dai a lokacin da DAYABU ya riki kafarta yana ihun UMMU UMMU, sai kawai ta fashe da kuka ta rungume shi ta bara mana wajen wato gamu ga duniyar" Kunya ta hanna min zama sai na bara masu gidan na tsayin sati, ashe aikin gama ya gama har ta dauki ciki na tsayin wata uku, UMMU kuwa na dauke da nata wata bakwai Dole na waiwayo iyalaina, dole na waiwayo matata da y'ayana, Sai dai kash bayanuwar cikin ya kara hadasa mata tashin hankali Na takaice maku, ni da kaina sannu a hankali na ringa haifar da dalilan da suka ringa kara nisanta ni da matata ta rufin asiri wace du abubuwan nan da nake mata ko kanwata daya kwal wace ta ragen a duniya kuma aminiyarta bata sanarwa ba, sai dai ta rufe daki ta ci kuka ta fito a yi abinda za'a yi Akoy ranar da ta tasheni tsakiyar dare ta ce da ni" MUTALAB, na aureka ne domin Allah, ina zaune da kai dan Allah ya saka min kaunar y'ayanka, Mutalab a da ina tunanin ina iya hadiye komai dan yarenka, aman a yanzu na gane harta NAJEEBA dake da shekara uku ina iya bara maka na tafiata idan har baka bar rayuwar nan da kake ba, idan har baka takawa zuwan uwar yarinyar nan da take takenta birki ba zan wanke kafa na je na daki mamanta na daketa na yi kason haka, MUTALAB idan ka kai zuciyata makura zan halaka ka na halaka kaina, dan walahi walahi irin yanda nake maka magiyar ka aureta idan sonta kake ka nuna min yaya zaka kuma iya auro bara gurbi a cikin gidanka to fa ka kiyayi du wata mu'amala da ita, idan ba haka ba MUTALAB zan halakamu baki daya mu shiga uku, na roke ka ka sawake min na yi tafiata" Sai kawai na fi ta hawa dokin zuciya, na rufe na ringa shiga ina fita ina fadin" Mariama, kin jima baki halakani ba, ki gwada idan kina yiwa Allah ki gani! Ni zaki nunawa zuciya? Kin san ni gaba da baya ko waye, kuma idan takamarki kina da kudi kin san na dame ki na shanye, ki zubar min da y'ayan mana, sai na auro wata ta zo ta kularmin ai kin san ba ke na fara aure ba, kai ni banma yarda da rashin aurena har yanzu ba, na tabata kin asirceni ne malama" To fa ranta ya bace, muka ringa sakawa muna fidawa wannan karron har gaban sarki da kuma BILKISSU, Ko a nan kin fadin dalilin fadanmu ta yi, Sarki na mata nasiha sai da aka tambayi musababi ba kunya na fadi dalilin kai tsaye wanda ban taba jin kunyar abinda nake aikatawar ba sai da ya ringa yi min nasiha yana tino min rayuwa da mutuwa, a lokacin na furta walahi walahi walahi sau daya tak ne, yarinyar ce ta cika neman fitina har take nuna kamar wani dinkewa muka yi da ita, Sai da aka shirya mu da *SIRRINA* kafin muka dawo gida Shekara kamar uku tsakani kamar komai ya wuce, ba wai yan mata na daina yi ba, ba kuma take taken masu kudin zamani na daina ba kaina sama da isata da komai gefena ga hajiata tana kawar da kai ga jiginiyar y'ayana da suke dauke da wata irin tarbiya ta shakuwa da junna da soyayar junnansu bale DAYABU da ya kasance ya iya tafiar da tarbiyarsu daidai gwargwadon iyawarsa, Wata ranar asabar, wace ta kasance ranar da ta kai bango, ina katon shagona na buga madara suka kawo mata ziyara da yar da aka haifa min da siyaya rigijib dan neman fitina A lokacin tana da saurin rama mari, dan haka a gabansu ta masu dan karamin hauka, ta nuna masu halaya na mata, suka ringa raba haki har hayaniyar ta kawo inda nake Kafin na mike sai da wani abokina elhaji Saley ya ce" lale kura ta yi lafia, yo ni mace ta isa ta ringa yi min abinda matar ELHAJ MUTALAB ke yi masa ban lakada mata duka ba na nuna mata ita ke kasa da ni na koya mata hankali ko dan gaba ba? Da wannan hudubar ta shaci fadi da bacin na isa gidana rai bace jinnina a sama ga oga ya zo ga ogan da zai zartar da hukunci wato mai gida tamkar kububuwa na fada gidan Ina zuwa ido rufe na tsayar da su, Rai bace na dubeta, a matsayinta na wace na kilace matata mai daraja, a gaban mutanen da suka ci amanarta, ni kaina wanda na ci amanarta dan rashin kunya irin tawa na murje ido irin ga boss din nan na kai na kawo sunna bina da kallo kowace na jiran ta ji kalaman bakina sai kawai na dubeta ido rufe na daga hannuna na kai mata marin biyar zazafan da ya sakata dafe kumcinta cike da mamaki, da firgicin rashin adalcina na kuma daga yar yatsana na nunata na ce" banza jahila! Da ke kadai zan rayu hala da kike nuna halin mahaukata ne? Ke har kin isa ki tare min budurwara ki daka har ki cira mata riga? To wannan da kike ganni ki saka a ranki sai kun yi zaman kishi da ita domin sai na aureta na kawota gidana kun zauna kin dafa mata ta ci kuma ta je shinfidata a karo na biyu! Yau na ga matar balaki dan kawai na aureki ban isa na dubi wata ba? Ba'a auren ke na aureki ko ni zaki nunawa hauka a nan? Ke ki je inda zaki je na sake ki saki daya domin ni ba sakarai bane da zaki ringa zuba min shirme kin bi kin tatare min gaba da baya na kasa aure to yau dai asirin bokan naki ya karye sai a kara gaba malama!" Hawayen da bata yi idan muna fada ne ya bale mata, Tana dafe da kuncinta ta matso kusa da ni sosai, A hankali ta ce" *sakayar soyayar kennan MUTALAB?, ka yanke min zama da y'ayana? Ka sake ni a karshe dai a kan son zuciyarka bayan ka san iyayena sun rasu ina kake so na je na yi zawarci? Ba asirceka na yi ba, kai ka hanna kanka aure, sai dai kash Mutalab, kash, walahi da ka san koda zaka maido ni ni ba zan dawo ba domin na haramta hauranka, Mutalab na rantse da Allah na kare da y'ayanka da du wani abu da ya fito daga hannunka! Kishi da wannan? Ta nuna matar, kafin ta tsartar da yawu ta kunce goyon Najeeba ta saketa daga tsaye hakan ya saka Najeeba zabura ta wawureta tana kukan MAMA, sai dai ina kuma hankadeta ta yi ban aune ba ta bala min mari ta kuwa ci damara da dan kwalinta ta ja baya ta ce" idan ka isa bismillah, walahi ko a da ban mari fuskarka ba dan kana dauke da igiyar aurena a yanzu da kai da bola du daya, Mutalab bismillah, da kai da dadiron taka sai nai maku jina jina a gidan nan* Mamaki ya hanna min motsi, ita kuwa karambani ya sakata tunkararta, lalle kuwa sai da ta mata jina jinan ina tsaye tamkar gaula domin marin nan da ta min ya aniya maido min maganar sakin da na mata Da gudu ta shige dakinta , dan kwali da dukan takardunta da jaka daya tak ta dauka ta fito DAYABU na kuka yana riketa haka yan uwansa sai kawai ta kubce ta fice da gudu ta fita Idannuwansa ya bude wa'inda sukai masa jajajir, ya ce" kun ji abinda ya faru tsakanina da NANA MARIAMA, tabas wani sa'in Allah kan baiwa mutun mace ta mutunci sai dai irin rikon da zai mata ke hadasa cenzawar lamarinta UMMU dake dafe da kanta dake sara mata ta kalle shi ta kuma kalli yarwn sai kuka suke Dubanta ya yi wannan karron maganar tata ce, sai da ya sanyaya muryarsa ya ce" bayanta na auri mata, daya bayan daya ina kara saki domin ido rufe uwar y'ayana nake nema wace zata kuma daukan dawainiyar gidana da y'ayana tamkar ita ta haifa Tun ina saki da karfina har na dawo ina saki da hawayena A hankali na ringa dana sani, har na je na zauna gaban kanwata na zayane mata gabli da ba'adin zamantakewar da na yi da matata, Sai dai kash, a lokacin ta so ta maido min da farin cikina sai Nana mariama ta gindaya rantsuwar cewa" ai kuma ita da mutalab sai a lahira Kuma sada kansa ya yi ya ce" walahi na sha wahala, ina cikin shan wahala Ina ta kame kame ido rufe Yarana na ta gararamba zuciyata na ciwo Du irin tarbiyar da suke samu ba ta mace tsayayiya gashi na kasa bada su wajen kanwata kwata kwata domin idan na shigo gidana burina na ga layin motocinsu, na tsinkayi kwaramniyarsu na zauna mu yi hira mu yi goyo goyo da kannanuwan, manyan na daukanmu a hoto Sai nake kwatanta irin macen da nake so, sai na fadawa Allah Sai da na dangana da auren wace nake zaune da ita a yanzu, sai malan liman na baba ya ce da ni" *kar ka saketa, koma meye halayanta, ka jure, idan ka kuma sakinta wace iri zaka kuma daukowa y'ayanka? Kar ka manta y'aya mata masu barin gaban iyayensu da wuri ne, kai kuwa goma sha biyar gareka mata masu rai da lafia a ciki baka aurar da ko daya ba, shin wai baka tsoron sake saken nan a sako maka naka? Bana so ka ji ciwon sakin y'aya a zuciyarka, domin ba uban dake so ya budi idannuwansa ya ga yarinyarsa a gabansa na zawarci*" A hankali ya kuma maimaita" *NA SHA FAMA, INA CIKE DA TSORON RANTSUWAR MARYAMA* Da sauri UMMU ta kuma kallonsa, zuciyarta na kara dokawa, Mikewa ta yi tsaye tana jin zata fashe da kuka Kafarta ta daga zata gudu ABIH ya kuma furta" *Marayu ne mu, daga ni har y'ayana, walahi ba zan kuma rayuwar dadiro ba ba zan yarda na hada SIRRINA da dadiro ba* Da gudu ta tafi wannan karron tana mai barin kukanta fitowa Abih ya mike tsaye da sauri , sai dai riko hannunsa da ya ji an yi ya saka shi juyowa A hankali NAJEEBA ta furta" *ABIH*" idannuwansa ya lumshe wasu hawayen suka ci gaba da zuba a idannuwansa Da sauri ya koma ya zauna kansa kasa Dagowa ya yi ya ga irin kukan da suke A sanyaye ya ce" da na san rayuwa haka take da daci, da na roki takaituwarta a kaina daga bakin lokacin da na rasa matar kwarai, Mariam ta kasance mai hakuri, da juriya da kawar da kai, ni sai na bazantar na ringa tunkudata har na kaita wajen da ta fashe ta kasa da ni, ni da kaina na yiwa kaina mugunta waye ba zan yiwa ba? DAYABU, UMMULKHAIR, UMMUKULSUM, ZAHRAU, NAJEEBA, *SHIN ZATA DAWO GARENI?* Tabas tsakanin da da iyaye sai Allah, tausayin iyayen nasu ya saka su hawaye sosai da sosai kafin su aniyar kwontar masa da hankali NAJEEBA jikinta a mace yake tana kallon Abinta Gaskiya Abih ya aikata ayyuka kala daban daban sai hamdallah Bata iya cewa komai ba har suka wawatse aka barta da zahrau Zahrau ta ringa kwontar mata da hankali tana kara nuna mata cewar UMMU bata da laifi Cike da hawaye ta ce" Auntu Zahrau, ashe shima ya tsani bak'ar mace aka aura masa ni?" Da mamaki ta ce" wata irin magana ce haka, SULTAN din ne ya tsani bak'ar mace? Me aka yi? Me ya sa ya fadi haka? Wani abu kika ce masa?" Sai da ta kara shahsekar kukanta sosai sannan ta ce" *Da karfi ya kwace min abinda nake tanadarwa waninsa Bayan wannan, ya ringa min hararan nan na tsana Na zata ya tafi ni kuwa kaina a sade nake fadin ai ba son farin mutun nake ba, mugu azalumi mai cin kudin talakawa* Sai da ta zaro ido kafin ta zauna da sauro tana kallonta ta ce" ya ji? Kina nufin ya ji?" Najeeba ta gyada kanta tana kallonta itama ta ce" ya ji, shine abinda ya saka shi fada min shima ai ba son bak'ar fata yake ba" Cike da madaukakin mamaki, da ayar tambaya Zahrau ta furta" lalle akoy wani lamari a tare da shi wanda yake da girman gaske Ke yanzu, kece kika fadi haka a gabansa sannan gaki a zaune daram da ranki? Lalle na tabatar da du wayonki wani sa'in baki da wayo, ko kuwa rashin hankali ne? ALLAH masani" Zama ta yi gabanta tana kallonta ta ce" na zata zaki iya tafia ke daya ba tare da shawarana ba? Sai dai na kula a kan matsalar wani kika iya samo mafita a kan karan kanki kina zama wawa Najeebana" Kuma kallonta ta yi gannin itama ita din kawai take kallo ta ce" abinda ya saka ya kasa tataka ki ko ya karya maki kafa sakamakon maganar da kika fada a gabansa ya shanye shi zamu dauka mu yi anfani da shi ta hanyar buga wasan nan" Kumatun NAJEEBA ta dan riko ta ce" baya son bak'a? Zamu gani idan har furucinsa shine gaskiyarsa, idan har idanniyarsa ba zata karyata sakonsa ba, idan har gangar jikinsa ba zata rikita lisafinsa ba!" Mikewa ta yi ta kama Najeeba ta ce" zo mu je ki kuma shiga ruwan da AMMI ta hada, domin babu ne kawai bata tanadarwa wannan ranar ba Abih na fitowa ya karasa Fallon, nan ya kuma tarar da Mardiya zaune ta kumbura kamar zata fashe sai karkada kaffafuwanta take cike da balaki Yana son ficewa ta mike da yannayi na raini ta ce" ji mana? Meye ka shiga dakin cen ka zauna tun dazu ana cin amanata ne ko meye? Hala ji kake ban san wacece wancen matar da ta wani ja su ciki ba? Malan na gaji da irin abubuwan nan gaskiya amanata za'a ci ido na gani?" Good morning all [31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 47 Alhamdulilah na dawo😁 Cike da kulawa, da yannayin da kwata kwata baya nuna mamakinsa a irin halayarta a yanzun, domin ta shayar da shi lamarin da lamarinsa ya fasa bashi mamaki ya dubeta duba na tsanaki ya ce" da gaske kuwa kin san wacece?" Karasawa ta yi sosai kusa da shi tana dan jijiga jikinta, irin ga mata an batawa mata rai ta ce" eh mana, ba uwar NAJEEBA bace? A kan me zata zo.nan ta tare ko yar uwar BILKISSU ce? Ko kuwa dan kai take zaune?" Idannuwa baki daya UMMU ta zaro daga wajen diner da suke zaune ita da Ammi , domin tun fitowarta Ammi ke zaune da ita tana tausarta, baki daya hankulansu ne ya dawo, irin rashin kunyar da matarsa ke tatawa ta saka UMMU zaro idannuwanta cike da mamaki Abih ya ce" dama haka ne, dama ace zaman da take a nan nawa ne? Ke da na fi kowa farin cikin hakan, da ace zata kuma dubana bayan rashin adalci irin nawa da na yi farin cikin hakan na godewa Allah" Yana gama fada gaba ya yi ya barta nan tsaye, maimakun ya nemi wajen su UMMUN sai ya bar gidan baki daya Kwata kwata hankalinsa a tashe zuciyarsa bata da nutsuwa Tunda ta fito daga wankan nan wanda ta ji dadinsa fiye da na dazu ta zauna ta saka pizzar da Zahrau ta kawo mata mai zafin gaske wace aka sarafata da naman kaza Sai da ta koshi sannan ta kuma mikewa ta koma bakin gadon da Zahrau ke zaune tana kunce kitson da ala fara yi mata sannan ta mika mata abin kitson ta sauaka kasa ita kuwa ta fara kunce mata a hankali, Basu yiwa junna magana ba har sai da ta gama mata ta caje kan sosai sannan ta raba shi gida uku cen saman ta fitar da kadan na tsakiya sai ma karshe ta dadaure kafin ta fara tsagawa a hankali ta kuma yiwa na gaban gida gida sannan ta fara daukan wani irin kananen kitso masu kwana kwana da shiga cikin junna sannan har karshe take kitse kitson duda irin yanda bata jin karfi sosai a jikinta aman ta ci burin sauke kitson a kan har uwarta A hankali Zahrau dake ta harhada yanda zata bilo mata ta ce" tsoho ne?" Najeeba da sarai ta san wa take nufi aman sai ta kasa bata amsa Zahrau ta yi murmushi ta ce" matsalarsa dai farinsa da kuma sarautarsa ko?" Najeeba ta sauke ajiyar zuciya, a hankali kamaninsa suke dawo mata , da sauri ta saki ajiyar zuciyar da ta kwace sakamakon irin yanda kamaninsa suka kawatu a idannuwanta Wani murmushin Zahrau ta yi, domin a rubuce sai dai ta rubuta labarin kanwar tata ta baiwa wani tsabar yanda ko da ido ta yi magana take gane gaskiyar ciki da kuma wanda ta fada dai ne A sanyahe ta furta" sai kike ce min na yawaita shiru a kan yawan magana, nan kika nuna min daga mijin da na aura har matansa kar na zake wajen buda bakina ina magangannun da ni kaina zasu gundureni domin kuwa a irin haka ina iya bada kofar da za'a gane raunina, tashin hankalina, sakarcina, jin tsorona" Najeeba ta ci gaba da kitse gashin Zahrau, itama Zahraun sai ta yi shirun tana sauraronta dan kuwa ta san kitson nan ba na karewar yanzu yanzu bane Sai cen kamar bata wajen, kamar ba zata tanka ba ta ce" Ban taba shiga halin firgici da tashin hankalin da na shiga ba, Dan jan iska ta yi ta ci gaba da fadin" just ki kwatanta abin a gabanki, mutumen da tun bana biyewa maganarsa har ta kai min buga wasa daga ni sai shi, Lebenta na kasa ta cije da hakoranta na sama kafin ta ci gaba da fadin" ya yawaita yi min tambaya a kan gidan nan, sai na nuna masa ni ban san gidan ba, ban san kowa ba, karshe na furta masa ni fa bai min ba" Tsagawa ta yi da dan karfi har Zahrau na fadin" Aush" Najeeba ta furta" Du a kan me ya min basaja yake hira da ni? A kan me ya ringa yi min tsmbayoyin da suka shafe shi? A kan me ya ringa hakuri da fadana? A kan me ya ci gaba da janyoni jikinsa ina fadin maganar da ta raya min a kansa?" Sai da ta ja numfashi ta sauke , irin abu ya dake kan nan ta ce" sai kawai na ganshi a lokacin da ya shirya wulakanta ni shi ne a gabana da kamaninsa da komai sai dai fuskarsa na dauke sa kallon tsanar nan da ya zamo ayar tambaya a wajena!" "Kun ban amsar hasashenku, sai dai zan kuma yi maki wata tambaya Aunty Zahrau, kasancewarsa baban mutumen dake mu'amala da mutane kala daban daban, har ya kasance ya iya basaja ya shiga gari ya yi lamuransa, shin bai taba sannin menene halayar yan matan zamani hade da samarin zamani ba ko kuwa yana nufin du yan matan yanzun ba soyaya ce suke yi da samarinsu ba aa zubar da mutuncinsu ne suke?, kina so ki ce min Aunty ya taba kamani da namiji turmi da tabarya ne ya saka shi wareni daban a cikin yan uwana ya sako lamarin tsana a tsakanina da shi? Ko tsabar rashin yancin kai ne zai saka matarsa marar tarbiya du haduwata da ita ko yan uwana da ita tun bana kulawa har ya kai kimarta da shakunta suka zube a idannuwa sakamakon mamakin kalar fatata da ta yan uwana da jifanmu da kalmar y'ayan talakawa ya saka har ta kaini da daga hannuna na fara jin dadin sauke iskancina a kan fuskarta shikenan mu ba zamu iya ramawa ba dan bamu da yanci? Shi mutun idan ba sarki bane shikenan sai ya zama talaka? Anya kuwa ta san menene talaka? Ba narar arziki bane talaka, mai mataciyar zuciya shine talaka! Aunty kina son ce min dan muna samun matsala da sakarya nunar ranar matarsa ce ya tsane ni ko me na tare masa ne ni? Na ga dai gidan nan wajen kawo kara ne, na tabata ban kasance wace aka fi kawo karana ko na rako gabansa dan shara'a ba a cikin garin DAMAGARAM! Ko shima so kike ki ce min shine dalili?, Aunty kadara cewar wai na bata rayuwar tawa, na zama fitinaniyar na gagari kowa a kasarnan, ina ruwansa da rayuwata da zai sakota gaba?" Ta karashe maganar tana huci sosai ranta a matukar bace Murmushi Zahrau ta kuma yi a hankali ta ce" NAJEEBA kitsa min sannu sannu dan Allah zafi fa" Bata bata amsa ba, dan kuwa ta gama shaka mata ba dadi a ranta Aunty Zahrau ta ce" Tambayata Najeeba a kanki shine: shin ke zaki tsara rayuwarki ne ba Allah ba?" Najeeba ta ce" Me hakan ke nufi Zahrau, na isa na tsara rayuwata ne?" Zahrau ta yi murmushi ta ce" Good, kin san da wannan shine kike haushi dan Allah ya wanzar da ikonsa a kanki? Daga ni har ke har Ummukulsum shin mun san rayuwa zata kasance haka a kanmu? Kin taba tunanowa cewar ni Zahrau zan auri sarki, sarkinma mahaifin ZINARIA kuma dansa namiji kwalin kwal ya tafka aikin da zai shigo zanen kadarar ahalina?, wa ya taba kawowa kansa cikinmu wace ta fi mu tsoron harkar maza take gudunsu tun karfinta hakan ne zai risketa? Me ta yi? *HAKURI* ta yi, tana kallon ikon Allah a lokacin da ta gane bata isa ta zana zanen rayuwarta ba" Dan dago kanta ta yi tana kallon NAKEEBA ta ce" Kina nufin kina son nuna min cewar ke din daban kike a cikin halitun Allah da har kika kai matakin da zaki samu aure mai daraja mai mutunci dan kawai ya kasance mutumen da kike naki zato yana nasa kuma ya zama fari sannan yana da mata ciki harda wace haka kawai kuka tsani junna shikenan kin isa ki nuna ba'a maki adalci ba, Najeeba har ta kai da ke da bakinki musulma kike kina kallonsa dan kin rikice ki ce masa ya sake ki ko auri HUZAIFA?" Najeeba dake kallon yannayin yanda Zahrau ke magana a sanyaye ta ce" Aman" Zahrau ta ce" Aman me? Idan bamu isa ba, iyayenmu baasu isa ba, kina son ki nunan bakya tsoron Allah?" "Aunty wani irin baku isa ba?" NAJEEBA ta fada tana dan nuno hannunta fuskarta na nuna yannayi na tashin hankali Zahrau ta yi dan murmushi tana dan girgiza kanta ta ce" bamu isa ba NAJEEBA, meye bamu gwada ba? Meye bamu nuna maki ba? Ciki harda mamansa wace ta haife shi ta roke ki, ba wai dan kin fi sauran matansa daraja ko wani abin ba a wajen Allah, aa, sai dan tana yi maki so daya tak fisabililahi sannan ta rayu da son samun iri daga tsatson kawarta aminiyarta? Du kika watsa wannan, yanzun ta kai har kina kallon mutun mai daraja, da mutunci, mai nagarta, mutun wanda Allah ya daukaka, ke dan kin samu dama kike furta masa ka sake ni? Idan har da gaske kike ba zaki iya rayuwa da SHAHEED ba, gwara a yau mu samu Ammi a san yanda za'a yi, ki tashi kawai ki je ki sameta, ki fada mata gaskiyar cewa ke fa ba zaki iya zama da shi ba dan haka a sawake maki, kin san aure Najeeba idan ba so, ba yarda akoy matsala, idan har mace ta tsani namijin komai na iya faruwa, tunda har shi ya amince zai zauna da ke a gaban mahaifinki da yayanki da kuma mahaifiyarsa ke kuwa kin kasa hakura da hakan sai a dauki mataki, ya sake kin ki koma wajen Huzaifanki, mai yiwuwa shine abokin rayuwar taki aman sai kin bi ta kan Sultan kafin ki karasa hannunsa" NAJEEBA kawai galala ta yi tana kallonta, 'ita? Ta tashi ta je ta samu Ammi da maganar nan? Sannan ita ta rabu da shi ta komawa Huzaifa? Ita kanta tana wannan furuci a kan Huzaifa ne a kan dalilin da bata sani ba, aman yau ko dan dan abinda take taka iya shegenta dan ta kwana da sannin a kilace yake da ya kwace me kuma ya mata saura?' Kanta ta dukar muryarta a raunane ta ce" Aunty, shi din da ba so na yake ba fa?, ki duba ki ga wai ni ya cewa baya son bak'a, kuma ya auri Nadia Aunty NADIA fa?" Zahrau ta yi murmushi ta dukar da kanta ta bata damara tsagawa sannan ta kuma daukan wani kitson A sanyaye ta furta" me kika ji a zuciyarki a lokacin da kika ga wata fuskar a matsayin matarsa bale Nadiarki? Yaya kika ji da ya furta maki baya son bak'a?" A hankali saurin kitsonta ya ringa ragewa sakamakon irin zafin da ta ji ya ringa dawo mata sannu a hankali, Tabas ta ji wani irin zafi mai girman gaske, faduwar gaba, da jin an gama wulakantata Ajiyar zuciya ta sauke tana jin irin yanda idannuwanta suka cika da kwallah, a hankali ta furta " *RAINA YA BACI SOSAI* wani murmushin Zahrau ta yi a bayane ta kuma aiko mata da wata tambayar da ta sakata tsayar da kitson harma ta kurawa wajen da ta tsaga da tsirarun gashin kan na Zahrau ido, ZAHRAU ta dago kanta tana kallonta ta ce" Tall me an mata, zaki iya beman sakin ki ne a hannun Ammi, ki fito ki yi zawarcinki, ki samu bakin mutumen da kike hasashe ya aureki a matsayinki na bazawara ku je ku samu irin rayuwar da kike tsarawa kanki ki barawa NADIA da ZINARIYA mijinsu?" *MIJIN SU?* Abinda ya fi tsaye mata a kasan zuciyarta, 'aman a kan me Aunty zata ringa yi mata irin wannan? Dan ta tayar mata da hankali ne ta sakata kuka ko dan ta birkita mata lisafi ne? Mijinsu? Ita har ya saketan ne da aunty zata kirayi namijin da ya gama karbar du wani tanadinta ya kare amshe du wani guzurinta sannan ya shiryata kafin ya sakata a jikinsa ya bata rungumar da ya kusan minti biyar a tsaye da ita a hakan ya furta mata kalmomi kamar haka :Ki kula da kanki, ki tsaftace harshen ki, Allah ya sa ki wuni lafia....: ya karashe yana mai kara matseta a jikinsa wanda tuna hakan da ta yi sai da ta ji wani irin yarrrrt a jikinta na ba gaira babu sabar Du tunanin nan da take, sam bata san har Zahrau ta janye kanta tana kallonta ba Kwalar da ta cika mata ido ce ta samu damar zubowa a hankali saman fuskarta Zama ta yi kusa da ita hakan ya ankarar da ita Dumin da ta ji a fuskarta ta laluba cike da mamaki tana kallon lema lemar da ta lalubo Zahrau ta harde hannayenta ta ce " zan fada maki gaskiya, kin taki sa'ar samun miji haka mai tsada bayan kina zaune a waje daya, a gaskiyar magana a irin wannan zamani koda kuwa da gasken baya son bak'ar fatar ba zan ga laifinsa ba, domin kuwa yanzu zamani ya zo da wani irin kida wanda ya saka mata hawa suka cenza salon takun kidan Ba komai bane sai irin yanda yawancin maza suka fi son farar fata kan bak'a, Zaki ji namiji ya furta shi fa farar ko maya ce, ko mahaukaciya ce yana so, koda bata da nasaba!, hakan ya bada gudunmuwa sosai wajen shafe shafen yan matan zamani, Najeeba, ke shaida ce irin yanda kawarki burinta ta taba magana da shi, sai kawai Allah ya malaka mata shi, Wa'inda basu kaishi bama daraja sun samu ana wawarsu bale shi? Ki cire masa rawanin ki ajiye shi ba ko sisi na tabata jinnin Ammi da mai martaba zai kawatu a idannuwan da zasu furta: ko bashida ko sisi sunna so!" Hannun Najeeba ta kamo ta rike a nata ta ce" zaki iya zama da shi?" Najeeba ta kasa budar bakinta, du kuwa da irin yanda take son yin magana, sai ya mata nauyi na gaske Zahrau ta ce" zaki amshi abinki cikin ruwan sanyi! Bakya son sa? Ai kin fahimci an wuce wajen so ko? Baya son ki? Zamu jaraba mu ganni......, matansa? Zasu yi yaki ne dominsa, kema kuma zaki yaki abinki .......kowa salonsa ya fishe shi" Najeeba ta kifta idonta a sanyaye ta furta" bana son hada bawa da wata, ban taba tunanin kasancewata a gareshi ba, lalle Allah shi ke da byro da takardar bawansa" "Hakkun, kuma a yi masa biyaya koda ba'a so a hakan za'a samu rabauta" Zahrau ta karasa fada Da sauri Najeeba ta kamo hannunta tana kallonta, a sanyaye ta furta" ta ina zan fara? Ta ina zan iya wannan yakin? Aminiyata da kuma ZINARIA, wa ya fi so cikinsu? ta yaya zai dubi bak'ar fata bayan ga farare nan a gabansa?" Zahrau ta yi yar daria tana jin sanyi a ranta, sannan a lokacin ta ga tsantsar yarintar NAJEEBA, wai ita nan ta yarda da kalamansa cewar ya tsani bak'ar fata? Sai ta tsinci kanta da kuma yin yar daria, tun a yau zata fara gwadawa, ita kanta ta fi so mijinta ya dawo da kansa su koma dan kawai ta maidawa Gimbiya maganar da ta yi cewar ya halarci auren nan dan zumuncin dake tsakaninsu na sarauta ba wai dan zai kara aure ba, bayan auren kuma ta furta mata lalle bakake kun fara kasuwa fa, aman ki koma mu gani.....tana son ya zo da kansa su koma sai ta tabatar cewa lalle bakaken sun yi kasuwa A hankali ta ce" kan abinda kika fi kwarewa, ina so ki buga wasan da kike bugawa a kan kowa, idanma yana tunanin karantarki ya yi ya san ko wacece ke to zamu yi anfani da sannin nasa mu gwada masa bai san komai ba! Najeeba kallonta dai take, Zahrau ta mike tsaye tana mai kokarin kwontar da ita ta ce" abinda nake son ki kula wanda da alama idan kina tare da shi yake bale kansa shi ne *Harshen ki*, ki kiyaye furucinki, ki tsadanta muryarki da kalamanki Kallon yayar tata take cike da wata kaunarta, tabas ita kanta da ta irga irin abubuwan da ta ringa furtawa sai ta ji wani iri, kamar wata wace aka kunna? Abin rufa ta ja ta rufa mata har wajen wuyanta kafin ta yi murmushin tsokanarta ta ce" zaki iya jure kwana shida baki je turaka ba?" Ido Najeeba ta zaro a dan rikice ta ce" Aunty fa" Zahrau ta yi daria ta ce" yeah, zan rikita iyayenmu, da yan uwanmu dan fara gannin zargin da nake yi idan har gaskiya ne? Ko kuwa hasashena ne Najeeba kam bata iya cewa komai ba sai rakata da kallo da ta yi kafin ta maido dubanta waje guda, wani irin dukan jikinta ke kwasa du idan ta hango shi a kasan idannuwanta, gaba daya jikinta sai ta ji wani irin yar yar yar take iya bude idannuwanta da sauri ....................... SULTAN Yana cikin aiki da computersa bayan ya gama da taron mutanen da ya gama da rigimarsu yan kasuwa ne sannanu da suka kawo karar junna kan a masu tsakani da junnansu bayan sun kasance makota ne sosai, wannan shara'a sai da ta saka aka kirawo manya manyan malaman da suka zo suka ringa kawo manyan ayoyi bisa hakan, dayan ne ya kasance mai neman fitina ko rufe ido ne? Sun hada makotaka da junna, layi daya aman sana'a ta zamo tak tak iri daya, kuma abin kamar da gangan yake yi domin baya tashi siyan abu sai ya ga dayan ya siyo ya zuba shima sai ya kawo da yawa ya zuba sannan da neman fitina ya rege kudinsa sosai ta yanda zai kwacewa wancen mutanensa sai daidaiku, yana yi masa haka sosai da sosai har asara yake saka sho tafkawa wanda karshe ya gane da wata a kasa, domin shima ba wani uban kudi yake sakawa kayansa ba, yar ribar da zai bi shi sai ya ki dorawa ya bada kayan a yanda ya sara, hakan ya matukar saka masa tashin hankali duba da shi din yanzu ya fara tashi yana ta kokari ne dan ya ciyar da iyalansa ya fi karfin yan matsalolin rayuwa, shi kuwa dayan shagonsa cike yake makil sannan zai kai ukun na dayan kuma sana'arsa wace aka fi saninsa fa ita saifa kayan abinci ne, aman tsabar neman fitina a yanzu ba abinda baya saidawa domin daga makocin nasa ya saro wani abin shima sai ya saro ya kima karya, sam baya so ya ga yana samun na rufin asiri shi kuwa abin ya kaishi bango ya maka shi a gidan sarki Lamarin ya so ya ja daga sosai sakamakon mutumen da aka baiwa damar magana ya nuna Niger din shin ba kasa ce ta republic ba?, yana da yancin yin sana'ar da yake so da zarra ba satar kudin ya yi ba, ya dora da fadin ya san yancin kansa ba zai kawo shi kara kan wannan ba Wannan lamari ya saka sai da ya yi kira ga manyan malaman fada da na garin baki daya, suka amsa kira kafin a fara gabatar masa da nasiha mai ratsa jiki, da manyan hujoji da ayoyin da suka zo da maganar haka, kafin ya samu ya gabatar da shara'ar Hakan ya saka kansa ya dauki zafi sosai ga harkar kasuwancinsa da yake son zama ya hada kan irin abubuwan dake shigowa da irin abubuwan da aka fi muradi wa'inda yaronsa baba zai je shaina da kansa ya yi oder su A hankali ya mika hannunsa ya dauki cofin glass mai dauke da jus din ananas ya kai bakinsa ya dan sha kadan kafin ya ajiye ya ci gaba da dane danensa Yar karamar wayarsa wace yawanci ahalinsa ke nemansa ta layin ce ta dan motsa alamar vibration Dauka ya yi ya duba Sakon Zinaria ne, rabonsa da ita yau zai kai kwana hudu, sako ne tana son zuwa bangarensa idan ya gama hutawa Amsa ya tura mata da ok kawai kafin ya ci gaba da aikinsa Yana nan zaune a falon nasa kamar da minti talatin, har ya gama dane danen ya rufe ya daga kansa sama ya lumshe idannuwansa ya tsinkayo tafia daga corridor din dake kawota bangarensa Bai daga kansa ba, har ta shigo ta karaso dan kusa da shi kadan Kamar yanda ta saba ta zube kasa kanta a kasa ta jimke hannunta guda ta sanyaya muryarta ta budi bakinta ta fara magana kamar haka" ...................... [31/03 à 21:56] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 48 Ta budi bakinta ta fara magana kamar haka" Allah ya taimaki sarki, Allah ya ja da rai ya ara maka nisan kwana, sannu da hutawa zakaran gwajin dafa, sannu da warhaka takawa"................... Lafuzanta ne suka yanke sakamakon hannunsa da ya dora daidai bakinta yana kallonta Idannuwanta ta dago tana kallonsa itama da duba irin na tarin soyayarsa da tarin jin haushinsa da tarin jin tsoronsa Dayan hannunsa ya saka ya kama hannun nata dake jimke ya ajiye saman cinyarta kafin ya saka hannayen nasa baki daya ya dagota tsaye shima yana mikewar ya kasance sunna mikewa a tare Wajen doguwar kujerar falon ya kai dubansa, sai dai yana kallo sai da aka hasko masa lamarinta mai girman gaske a idannuwansa A hankali ya lumshe idannuwansa ya samu kansa da jin zuciyarsa na rike sunnanta a ciki ciki Dubansa ya kai saman kujerar da kyau, idannuwansa sun hasko masa abinda ya sha'afa bai goge da kansa ba, dan murmushi yake jin na son kwace masa sai dai ya ki barin hakan ya faru ya gimtse fuskarsa da kyau A hankali ya karasa wajen zama da ita ya zaunar da ita, sai kara sada kai take irin na girmamawa tamkar wace ta zo gaban sarakuwarta farin haduwar nan Hannunsa na dama ya saka a nitse ya dago habarta yana dubanta Muryarsa ya sanyaya sosai, sannan a rarabe a hankali irin ya yi niyar cadin da ita yau ya ce" haba Zinariana, shin bakya gajiya da kirarin nan da kike min bayan daga ni sai ke?" Da mamaki take kallonsa, shi kirarin ne baya so? Ai ita kirarin nan shine karin fasa kanta da sakawa ta ringa taku daidaya, idan ana kodatan nan ko dogon fushi bata iya yi, kai ita da ko shi zai mata kirarin zata washe masa hakora ne! Shaheed ya kuma dago dubanta ya ce" ki dubeni cikin ido, ki min magana da girmamawar da miji kan iya samu a wajen matarsa, yaya zan zama sarki a waje haka kuma a dakina? Oya yi min zancen soyaya" Gaba daya wannan karron ta idasa kuro idannuwanta tana kallonsa, muryarta a dan rikice ta ce" zancen soyaya kuma? Da kai?" Shima abin sai ya bashi daria a kasan zuciyarsa, sai dai bai yin ba ya ce" Zinaria da wa zaki yi idan ba da ni ba? Na maki tsufa ne?" Sai kawai ta ringa kakare hada ido da shi, tana ta kare fuskarta cike da wani lamari na mamakinsa, shi sarki guda yake magangannun nan? Su an hore su da yi masa kirari da koda shi da fadin ya yi kaza ya fi wane, haka mahaifiyarsu ke yiwa mahaifinsu ko a gaban waye, ahine shi zai kawo wasu magangannu? Sai kawai ta ringa jin zuciyarta ba dadi sakamakon tunanin da ta saka mata a cikin kwakwaluwarta, 'yaya aka yi a da bai ce yana son soyaya ba sai yanzu? Ko dai wannan karuwar bak'ar yar ya fara kulawa?' Sai da gabanta ya fadi kafin ta kale shi a tsorace, shi kuwa kallon irin yanda du ta rame, an yi mata kwaliya kamar yanda ta saba zuwar masa da kwaliya sai dai raka sosai ta bayana kanta a tare da ita A hankali ya kai hannunsa, domin ya rigaya ya yiwa kansa alkawarin zai ta lalabata har ta saki, dan kuwa ya ga wani labari da aka yi posting na irin yanda mata ke ji idan za'a masu kishiya, da irin shawarwarin da namiji ya dace ya bi dan gannin ya kwontarwa da matarsa hankali ta dan nustu a kan maganar, a sanyaye ya furta" yaya jikin ki?" Zinaria ta kara kikifta idannuwanta sai ga hawaye, a hankalin itama ta ce" jikina gayanan dai, shine na zo neman alfarma a wajenka, ina so mu je gida tare da AYYA a yi min magani sannan hankalina ya kwonta kafin na dawo" Hankalinsa a kanta sosai ya ce" wani irin magani ne da ba zan iya nema maki shi a nan ba? Ko fita ta kama ni mai kaiki ne da kaina, wani irin kwonciyar hankali kike so wanda sai kin yi nisa da dakin mijinki?" Du magangannunsa na yau, da irin tsayinsu, da irin yanda yake yinsu cike da kulawa na cutar da ita, domin har baki take saki tana kallon jajayen lebunansa da yake dan motsawa a hankali, da idannuwansa da suka cenza launi sakamakon gajiya yana dan lumshe su yana bude su a hankali, sai kawai ya ringa birge idannuwan ganninta Ita kanta bata san lokacin da bakinta ya furta" NAJEEBA ta tare ne?" Kama sunnanta da ta yi ya saka masa jin gabansa ya fadi kamar wani wanda aka kaiwa wawan dukan bazata, A hankali ya kuma kallon fuskarta, a yanda ya kula ko a haduwarsu ta farko ita ba NADIA bace a gabanta Najeeba ce, Haka kawai sai yake jin ransa ba dadi sakamakon rashin jituwarsu, yau kuma ya fara jin abin a cikin ransa, sosai da sosai A hankali yar fara'ar da ya ringa saki ya shiga harhadeta, ba dan komai ba sai dan kawai ba zai iya barawa wata cikinsu daman kawo masa maganar wata ko tambayoyi a kan wata ba, idan sunna so sun hadu su yi kishin su, shi abin daria yake bashi sosai domin ranar da aka yi dramar nan har wani hura hanci ya ringa yi daga bayan rawaninsa a kasan zuciyarsa kuwa ya ringa tunanin dama hudu ya jera ya ga iya gudun ruwansu Fuskarsa a hade aman bai daga muryarsa da karfi ba ya ce" shin ina iya saka tsorin kar zafin kishin ki ya kaiki wajen da zaki kasa gano hanyar dawowa?" (Lauje) Idannuwanta kawai ta kura masa tana kallonsa, sam ta kasa bashi wata amsar kuma, zafin kishi ne? Inama ace ana yiwa namiji kishiya da ta gwada yiwa SULTAN ta ga irin nasa kishin, shin shi baya jin kishi a ransa ne? ( to fah ) Hannunta ya kamo ya rike a nasa ya ce" ke ce babba, ba zan taba bada kofar da wata zata wulakanta ki ba, ba zan iya wulakanta ki ba domin ke din ke na fara sanni, ina mai rokonki a yau kan ki sanyayawa zuciyarki, ina da abubuwan yi masu girma da yawa, idan har kika talafa min ta hanyar kwontar da hankalinki kika ja yan uwanki a kan akida guda wato zaman lafia da zaman aure, ina mai tabatar maki zaki fi kowa jin dadin zama da ni" Ya dan tsagaita yana ta sauke numfashi kafin ya dora da fadin" idan kuwa kika kiya Zinaria, ban san a wani kalar zaki iya wayar gari ki ganni ba, ban san idan zan iya fama kamar yaro ba, ban san idan zan iya zubar da shirme kamar wani wawa ba domin sunna na raya" Yana gama fada ya saki hannun nata da ya riko , ya yi kokarin tashi ya mike tsaye, hakan ya sa ash color din jalabiyarsa sauka kasa Da ido take kallonsa, ta tabata, ta tabata kennan ya tare da yarinyar nan? Sam bata wani tsinci wasu abubuwa a cikin bayanansa ba A hankali zuciyarta ta ci gaba da yin kunci sosai da sosai, Tabas shawarar da wannan mutumen ya kawo masu koda kuwa sun kiya da farko zasu yarda yanzun, Ba zata iya yarda ya tara da wannan banzar ba! Da sauri ta kara neman alfarmar tafiyarta garin agadez Yana jinta sai kawai ya yi biris tamkar bai ji ba, ya shigewarsa cikin dakinsa mai dauke da harkar takardunsa da abubuwan nemansa Baki daya sai ta ringa cika tana hawa tana jin idannuwanta na neman kara rufewa, sam bata wani yi yinkurin binsa ko neman kara lalabashi cikin ruwan sanyi ba, saima ta ji ai wannan tsana ce da nuna halin rashin damuwa da ita Ranta bace again ta fice a fallon nasa ta nufi wajen mahaifiyarta Tana zuwa ta udasa ta zauna kusa da ita Wayar da Gimbiya ke yi ne ta ajiye ta ce" yaya ya yardan ne mu saka a kawo mana tkt ?" Da yannayi na zata iya fashewa da kuka ta ringa girgiza kanta tana daga idannuwanta ta kai kan yayarta daya da ta rage wace itama mijinta a yau ya mata magana ta karshe cewar idan ba zata dawo dakinta ba ta zauna, tana kallonta ta ce" baki daya ya cenza, kamar ba Sultan dina ba, yau ni yake cewa na daina yi masa kirari na masa hirar soyaya, karshema kan maganar bai tanka min ba tun bayan da ya nunan shima yana iya sama min ko wani irin magani na lafiata!" Gimbiya ta ce" wani irin kirari kuma? A cikin dakin naki da shi kike masa kirari?" Da mamaki ta kalli mahaifiyar tata, ta ga dai tsakaninta da mahaifinta kirari babu lokaci, to wace irin magana ce wannan? Gimbiya ta ja tsaki tana fadin" shashashar banza, to ba dole ya gama rainaki ba? Wai ke daga ke sai shima hirarki tsakaninki da shi kirari ne? Arrrrrrr da ke walahi" Yayarta kuwa banda daria me zata yi ta ce" Auta wai Allah da gaske kike?" Du sai suka daure mata kai, maimakun kuma su zaunar da ita, su fahimci ai ga matsalar baba da take kara nisantata da mijinta harma su nemi maganceta cikin ruwan sanyi sai abin ya shashance a daria suka shiga neman layin mai martaba dan su bi ta kansa ko zai amince masu da tafia da Zinariar, sai sheda mata ake yana kan waya wanda ya makale da wayar Zahrau yana karbar caji da lamura dan ya kara mata kwanaki cike da shagwaba ........................ Cike da shagwaba Zahrau ta kara rike wayar hannunta tana hangen yanda du yan uwanta ke ta kai kawo dakin NAJEEBA tana dan murmushin gannin zasu ci galabar abinda suke so ta kara rage muryarta ta fan saki kukam rigima ta ce" ur excellency my happiness, idan har ka amince min ne, idan baka amince ba zan taso a yau yau na zo gareka, domin du duniya babu aikin da ya kai min naka daraja wanda ba zan iya takewa saboda kai ba" Sai kuma ta dan ja shashekar kuka ta ce" Duda nice babba mace a cikinmu, kuma ina son na ga na bara masu du wani farin ciki kafin na yi nesa da su, bale Nusaibana yar jaririya da ita abin tausayi, ina so na je da kaina wajen mamanta mu sasanta huby" Ido kawai tsoho ke lumshewa yana sauraron wani salo na son rokon alfarmar ta zauna a gidansu ta kara yan kwanaki, shi abin sabo ya zo masa Tabas a matansa Gimbiya takan tsiri tafiar shakatawa a kadan ta yi wata haka kawai ta je wata dubai ko london ko hawai.....gari dai da zata more rayuwarta ta jima a cen ga kashe kashen kudi ga abubuwa dai sai hamdallah kafin ta dawo, ita kuwa dayar sai ta shekara bata fita ko kofar gida ba, aman itama idan ciwon gida ya kamata takan lula a kadan ta yi kwana hamsin wai tana hutawa domin tana samun balewa daga kusa da Gimbiya bata yiwa abun rikon wasa, tana morewarta daidai gwargwadon iyawarta Sai gashi ita daga sati daya, duda ya damu ainun domin kuwa shi kadai ya san irin farin cikin da yar karamar cikinsu ke saka shi, aman sai gashi tana neman alfarmar kara sati daya tak a gidansu, ba irin abinda ke birge shi sai idan tana fadim kaf duniya a yanzu yana gaba da kowa da komai nata, sai kuma cikin hikima ta nuna masa yan uwantanma sunna da nasu darajar wada ba zata iya samun farin ciki idan har daya daga cikinsu ya ce washhhhhh Murmushi ya yi yana dan shafa gemunsa da ya fara furfura farare kal a sanyaye ya ce" Sati daya tak, daga shi kin yarda ba zaki kara ba?" Itama murmushin ta yi jin sautin muryarsa kafin a sanyaye ta ce" In sha Allah ogana" Wani murmushin ya kuma yi a bayanne yana jin kansa sai kara fadi yake , Sunna yin salama ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta karasa kusa da Ammi dake danna wayarta tana rubuta message Allert ne ya shigo wayarta, tana dubawa ta ga kudi ne zunzurutu daga mijinta Wani murmushin ta yi ta shiga rubuta masa messafe din godiya, hade da kalaman soyaya ba wani dar ta tura masa sannan ta juyo tana sauraron Ammi Ammi ta ce" yaya bai kyauta min ba, yayya zai tashi kai tsaye ya yiwa NAJEEBA maganar nan a yanzu bayan ba lafiar kirki gareta ba tsakani da Allah? Gashi du ta rikice min ban san ta inda zan fara ba anya ban shiga hakkin yarinyar nan ba kuwa? Zahrau ta ji Tausayin Ammi a ranta sosai, sai dai bata da niyar ja da baya dan haka ta kama hannun AMMi ta ce" Ammi, ba wani abu fa, idan har ta samu kulawarmu baki daya zata mike ta warware ne, kin ga abubuwa masu girma har biyu ne suka sameta a yau kadai, dole sai an rarasheta an lalamata Ajiyar zuciya Ammi ta sauke kafin ta saki murmushi a sanyaye ta ce" ta ji ciwo ko?" Zahrau ta dan sada kanta dan kunya, a hankali ta ce" Ammi, kin san tana da saurin warkewa a kan ciwo ko wani iri, bata da kam jiki in sha Allah nan da kwana uku zaki ga ta ware" Ajiyar zuciya Ammi ta kuma saukewa a sanyaye ta kuma fadin" na so a kira likita kun hanna, bana so ciwo ya hanna mata nutsuwa fa" Zahrau dai bata gushe da murmushi da son kwontarwa da Ammi hankali ba, har sai da kiraye kirayen salar isha.i ya tashe su Tabas abinda ta kudiri niya ta samu, domin kuwa ita kanta wace suke tsoron yau hankalinta ya kasu kashi da yawa sannan ita kanta so take ta ga fara'ar Najeebar, uwa uba Ammi dake nan nan da ita, ita kuwa ta karbi jawabi ta langwabe sai shagwaba take sosai, lale tana jin ciwo a jikinta sai dai tunda ta wuni shiga ruwa da anfani da ruwa abin da sauki sosai, sannan lamarin mahaifinta da mahaifiyarta ta yiwa kanta shawarar zata cire wata damuwa, ita dai abinda ba zata yi ba shine ta lalabata ta koma masa, idan ta yi ra'ayi dan kanta halasss Nana suka hade a dakin sunna ta hira da wasa da daria harda DAYABU da ya fito daga zance, Mardiya kuwa tana dakin da aka kaita ta yada zango da waya sai karbar banzayen hudubobi take daga wajen kawayen duniya, ita a dole miji zai saurareta, kasancewarta a gidan sarki kusa da tsohuwar matar mijinta kuwa ta yishi ne dan ta nunawa shegiyar Najeebar nan cewa uwarta bata isa ta dawo gidan MUTALAB ba! .......................................... Karfe goma ce ta gota a agogon bangon dakinsa Kwonce yake saman lalausar shinfidarsa mai dauke da zanin gadon ruwan ashe color irin manyan zanin gadon nan ne da ake dorawa bayan an shinfida bargunnan nan na lybia manya manya masu nauyi da kyau Jikinsa sanye da riga da wando farare kar na baci, wandon mai dogon kafa ne rigar ce mai yankaken hannu aman itama baba ce rigar domin budadiya ce sosai A irin gajiyar da ya yi yau, ya hau gadon nan ne da burin rinyse idannuwansa dan ya samu ya shiga baci, Sai dai tunda ya kwonta din sai ya kai idannuwansa kan kofar shigowa wajen bacin nasa ya kura ido kawai yake kallo Lokaci zuwa lokaci sai ya maida duban nasa wajen agogo sai kuma ya kalli kofar Juyawa ya yi ya baiwa kofar baya ya shiga adu'o'in tsari Ya jima yana yi ya tofa ya shafe jikinsa, sai kuma ya kuma juyo dubansa ya kai kan kofar Mikewa ya yi zaune a hankali ya sauka daga saman bed din ya kama hanyar fita Yana fitowa ya shiga bin falon da kallo Shiru ne falon ba kowa sai kamshin turaran wuta da sanyin AC Fitilar dake kara haske ya kunna ya kuma bin dakin da kallo Idannuwansa ya dan kikifta gannin har karfe goma sha biyu ce ta gota A hankali ya karasa wajen doguwar kujerar falon ya hau sama ya kwonta hannayensa tokare da keyarsa kafafuwansa daya kan daya yana kallon bakin hanyar coridor din bangaren Ammi Irin motsin da ya yi jin kamar kiran sallah ya saka shi idasa bude idannuwansa da kyau Hannayensa sun yi tsami sosai ya kai dubansa da mamaki wajen agogo Tabas lokacin salar asuba ne har ya yi Da sauri ya kara kai dubansa falon sama ko kasa abinda yake son gannin bai ganni ba Lebensa na kasa ya tsinci kansa da dan cijewa yana jin kamar damuwar son sannin dalilin hakan na son kutsowa cikin lamarinsa Tabe bakinsa ya yi ya mike ya nufi bayi dan shiryawa ya gabatar da sallah A wunin ranar ya yi ta tunanin lamarin duba da Ammi bata yi masa maganar ba, shi kuwa sam bai nemi jin ba'asi ba, sai ya ci gaba da harkokinsa da yau da kulun Wasa wasa sai da ta kwana uku bata waiwaya turaka ba, domin tun tana na wasa har ta hadu da na gasken domin athsmanta ne ya ringa tashi gadan gadan sakamakon kurar da aka yi ta bude window din dakin da suke Ammi kuwa ta shaka ne, a ganninta ya dace ya bi bayan Najeeba, ko dan a yanda aka rakota daga bangarensa dan haka itama ta ki kawo masa maganar ko irin gaisheta da yake na asuba bata taba kawo masa maganar Yau ta kama kwana hudu, a yaune Zahrau ta yi niyar garin Allah na wayewa zata je anguwa wajen Hajia Hadiza Awilo , matar dake gyara kala daban daban Kamar yanda ya saba zuwa da asusuba yauma hakan ce, AMMI ce da UMMU zaune a dakin AMMI din, a yau tataunawa suke na lamarin da ya shafi AMMI din da kanta Cike da damuwa take gabatar mata da abubuwa irin na halayan da Zinaria da mahaifiyarta ke nunawa, irin na Nadia da ta shigo jiya tsal itama ko sau daya bata zo ta gaisheta ba, da yannayin damuwa ta furta" ki duba ki ga yaron nan tun da aka rako NAJEEBA bai waiwayota ba, me ke damunsa? Me ya sa matansa basu dauke ni da mahinmanci ba? Ko dai laifin daga shi ne baya saka su a hanyar da ya dace su bani girmana? UMMU ta ce" eyah Ammi, inaga lamarin nan dole sai da adu'a, bana so ko daya ki ga laifinsu, shima haka ina so ki masa uzuri, kin ga fa abubuwan kansa da yawa, wani abin yana iya shige masa a duhu ne bai san da shi ba Aman in sha Allah ni zan nemi kusanci da matansa dan na gane meye matsalar, sannan shima zan zauna da shi daga ya samu lokaci A hankali ya yi salama muryarsa a ciki aman kuma kunnaye zasu iya jiyowa Amsawa suka yi baki dayansu shi kuwa ya karasa har inda suke zaune wato bakin bed Hannayensu dake rike da junna ya saka hannunsa ya raba sannan ya shiga tsakiya ya zauna Da yannayin sakin fuska ya saka hannunsa ya dago, dubansu ya yi da yannayi mai tarin kaunarsu da jin wani irin girmansu a zuciyarsa , a hankali ya furta " barka da asuba ummani" Murmushi ne ya wadata fuskokinsu, cike da girmamawa, fa kaunarsa suka amsa gaisuwarsa A hankali UMMU ta ce" Yaya fama da al'umah?" Sai da ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya furta" ALHAMDULILAH " mukewa UMMU ta yi cikin dubara ta furta" zan leka kicin na ga idan an gama Ammi " Har sai da ta kusan fita ta ji muryarsa cike da kamala yana fadin" shin zan samu dan kwano tare da kowa Umani? " Dakatawa ta yi ta juyo da dan yannayin mamaki, AMMI ce ta ce" kana nufin zaka karya a nan tare da ni, ko tare da mu? Murmushi ne ya mamaye fuskarsa gannin yanda wani irin yannayi na farin ciki dake mamayar kamilaliyar fuskar mahaifiyar tasa, yana kallonta ya ce" du wanda zai kara daukaka wannan ni'imatacen farin cikin da nake ganni a kan Fuskar da ta fi kowace fuska tsada a zuciyata " Mikewa Ammu ta yi tana ta murmushi, sai ta kalli UMMU ta kuma ta kalle shi, idan ba zata manta ba rabonsa da ya zauna ya ci abinci da ita har ta manta, kai an jima, gashi yau yana nufin harda yan uwansa? Sai kawai ta manta dan fushin da take ji a zuciyarta nasa du wani farin ciki ya maye gurbin hakan UMMU ta fadada murmushinta tana jin wani irin farin ciki ita kanta har AMMI ta karaso da sauri ta rike hannunta Muryarta kasa kasa ta furta" zaki iya ke daya kuwa? Me ake girkawa yau a kicin ne? Table a goge yake? Yara du sun farka kuwa? An kawo alkyabar kowa kuwa? Shin zasu shirya a kan lokaci kuwa? " Daga inda yake zaune sai ya tsinci kansa da sakin wani irin murmushi, wai dama haka jin zai kasance da ita ke sakata a farin ciki? Sai ya ringa jin wani irin dadi zuciyarsa A hankali ya ce" *AMMI, ki bar ahalina su fito cin abinci da ni a kan lokacin da suka saba, a irin shigar da suka saba fitowa, UMANI zan zauna a table din cin abincin falonki ba tare da rawani ba "* Wannan karron ita kanta UMMU sai kawai ta ringa dan yarfe hannu tana jin wani yam yam yam na bin jikinta, kasa magana ta yi tsabar farin ciki ta juya da sauri dan nufar kicin, domin kuwa abincin kawai zata iya tsayawa ta tabatar an kawata shi Cike da wani irin farin ciki AMMI ta dawo wajensa, hannayenta ta saka daidai da fuskarsa ta talabo tana kallon kamilaliyar fuskarsa mai dauke da saje, farin fatarsa da kamani na mahaifinsa na tatare da fuskar tasa, hannunta na dama dauke da carbin nan irin na dannawa baki mai dauke da dan abu na yawo a jikinsa mai hasken gaske yana walwali Idannuwanta cike da kwala ta budi bakinta ta ce" [31/03 à 21:56] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 49 Idannuwanta cike da kwallah ta budi bakinta ta ce" ka gani SHAHEED, walahi ina da bukatar zama da kai haka, ka gani ko SHAHEED rabona da jin farin ciki haka an jima sai jin daurin aurenka da NAJEEBANA, sai ko wannan zaman da zaka yi da mu, fuskarka ba tare da rawani ba, ka ga SHAHEED sai nake ji kamar idan muka zauna zan iya yin magana da kai kai tsaye, sai nake sakawa raina dama idan muka zauna zaka yi daria wa shirmen kannenka, ka saurari bukatunsu, ka tambayi muradinsu, harma ka yi wasa da su irin na kowa, sai nake hasaso zamanin mahaifinka, yakan ware lokaci ya zauna da mu baki daya ba rawani a fuskarsa, yakan zauna ana wasa da daria da mu baki daya, sai sai nake jin kamarma ace ba rawanin nan a tsakanin mu, sai nake tunanin rayuwa ba sarauta? Shin zan kasance koda yaushe a irin farin cikin nan na yau ne ko zai kasance gundurare a gare ni? " Hannunsa na dama ya dora saman nata na hagu dake saman kuncinsa, a hankali ya karkata fuskarsa wajen hannun nata ya mana mata kisss a tafin hannun nata mai sanyi hade da zafin kaunarta dake zuciyarsa tare da lumshe idannuwansa sannan ya dago dubansa yana kallonta, idannuwansa ba yannayi na kuka aman tarin tsagwaron kaunar mahaifiyar tasa ya saka su cenza kala, A hankali ya furta" Ammyna, a koda yaushe kike da bukatar hakan, koda ina nesa da gari ki turan texte, just write t mom, ko a saman rakumi nake, ko a cikin jeji nake, koda an daure ni da sasari zan kunto, zan zo gareki, zan duka gabanki, AMMI ke ce duniyata, ke ke kawata min duniyata " Murmushi ta yi mai sanyi da sauri ta kama shi ya mike ta ce" je, je ka yi wanka ka zo, ka yi gagawa ka zo karfe takwas muke breakfast" Shima cike da farin cikin ganninta a farin ciki ya juya ya fice yana mai takunsa na kasaita da kamala sanye da rigar sallah UMMU kam a kicin ta gama rikita kowa, an fitar da wasu sababin abubuwan zuba abinci na alfarma, an kara kawata abincincikan, sannan ta baza ma'aikata da wuri wuri su kara bin goge goge da sharen sharen da suka yi duda wajen ko a haka a mugun gyare ne a wajena (😅), baki daya ta bi ko'ina ta kara zuba turaren wuta a manya manyan abubuwan saka turaran wutar dake gigirke a kowani lungu na tankamemen falon Nan da nan suka ringa jera manya manyan kulolin dake shake da abincicika, AMMI ce ta fito sanye da abaya baka har kasa mai dauke da ado madaidaici, Cike da murna take bin ko'ina da kallo, kafin ta sauke dubanta wajen agogo Karfe bakwai da minti talatin ne na safe dan haka Direct ta karasa wajen kujerar da UMMU ke tsaye tana kara gogewa da kanta tana ta kara kyalkyaleta Da murmushi a fuskarta ta ce" UMMU, kujerar nan ta gogu kamar wace kika wanketa haka take kyali fa haba ki je ki huta haka dear" Da murmushi itama ta dubeta ta ce" kin san ni tunda asuba nake wanka na kimtsa tun kafin na yi sallah, shi ya sa kawai na tsaya na ga komai ya shirya BILKISU ce ta fara fitowa sanye da wando da riga na baci , dogaye ne sakaku sosai a jikinta , Tsayawa ta yi tana kara bin dakin da kallo, domin aiki sai mai shi harta da labulaye sai da aka cenja nan da nan dakin ya dauki sabon tsari Idannuwanta ta dan zazaro a lokacin da ta hangi saman table din, irin yanda aka kawata shi Da sauri ta karasa ta duka har kasa ta gaishe da iyayen nata Da yannayin mamaki batama tsaya ta ji amsarsu da kyau ba ta ce" AMMI, MAMA baki aka yi ne? " Ummu ta yi daria kawai Ammi kuwa ta mika hannu ta tasheta tsaye ta ce" takwara, ba baki aka yi ba, kawai dai an cenza ne , maza je ki tashe sauran dan yau weekend ne shine ba'a shirya ba ko? To lokacin hawa table ya kusa oya a je a shirya cin abinci " Ai kuwa da zumudi ta juya ta koma dakinsu na yaran tana ta gumtsa masu irin tarin kulolin da ta ganni a falon AMMI gashi kuma ba birthday din wani ba, kuma ba baki aka yi ba cike da zumudi du ta ringa tashinsu domin bayan gama salarsu da wanka da broch du sai suka nemi waje suka kwonkwonta dan yau din weekend ne malaminsu na islamiya kuwa sai karfe goma yake zuwa Zuwa karfw takwas du yawanci sun halara a saman table din cin abincin falon sai dai yau maimakun a fara kai tsaye sai suke ta amsa gaishe gaishen iyayen nasu ya kasance saura mutun uku kawai ne basu karaso ba, su ne wanda ake jiran, sai NAJEEBA da UMMUKULSUM Du yawanci da kayan bacinsu ne jikinsu, wasu doguwar riga har kasa da dan kwali, wasu kansu da yar hula ta baci, mutun daya ce bata fito ba ita kuwa dama ba fitowar take ba sai idan ta ji maganar mijinta Kusan da minti goma sha bakwai ya bude a hankali ya shigo falon, ya yi daidai da fitowar NAJEEBA da dan gudu gudu tana fadin" AMMI, walahi ki yi mata magana dan kunnena ne fa a zuwanmu Abuja na siyi abuna a chopclass, shine zata ce nata ne?" UMMU ta ce" karya ne, walahi karya ne wannan yan kunnayen ba nata bane ni na sayi abina a Niamey da kudina a shagon wannan matar SAJIDA mai sunna JADAH na neme su na rasa sai yau tana zazage jakarta ya fado" Tsayawa ya yi a daidai wajen da ya sanyo kai suka shige da gudu ta yi bayan Ammi tana ta gwalo tana kuma fadin nata ne Dif ta yi baki bude hannu sangale ido waje tana kallonsa hakan ya saka UMMUKULSUM waigawa a tsorace domin irin kallon nan ne dake nuna karara wani abu ka gani da ya firgitaka har haka UMMU ce ta waiga itama sai wa'inda ke kallon Najeebar suma du suka waiga dan gannin meye? Lokaci daya Ammi ta saki murmushi tana kallonsa, kwata kwata bata iya boye farin cikin fanar nan Shada ce jikinsa, dinkin wando da riga , rigar tsayinta daidai gwuiwarsa, kansa ba hula hakan ya sa tsadaden askin kansa da gyarn fuskarsa bayana karara, jikinsa kuwa sanye da bakar shada ne sai dan agogo a tsintsiyar hannunsa ta hagu Cikinta ne ya bada wani irin kurrrr , lokaci daya jikinta ya dauki bari ta aniya neman dukewa dan boyewa ita kuwa jikinta sanye da rigar baci ne doguwa ruwan hoda mai siririn hannu sannan ko rigar mama babu sai pant dinta da ya bi rigar ana gannin shatinsa Cirw dubansa ya yi daga kanta ya nufi UMMU da ta mike da farin ciki gannin yaran du sun zuba masa ido gannin daga inda ya fito, gashi ba sannin fuskarsa suka yi ba banda Zahrau da karara fuskarsa ta dawo mata a idannuwanta ta mike itama tsaye da sauri har jikinta na daukan rawa rawa domin da wayonta ta manta ranar da ta ganshi ba rawani, tun kafin a yi masa nadin da Abih ya je da su dan taya shi murna da adu'a A lokacin da UMMU ta gabatar masu da shi, baki daya sai suka ringa zaro ido, harma suka rasa inda zasu saka ransu, abu daya suka yi a tatare shine mikewa, sannan cike da yannayi na sunna tsoron hada ido da shi du suka ringa kawar da dubansu duda tsantsar son karewa kyakyawar fuskarsa kallo da suke son yi Murmushi ya saukar a kan fuskarsa kafin ya mamayeta da fara'a ya idasa wajen da UMMU ta bude na zama Zama ya yi da bismillah sannan ya kara bin mutanen wajen da kallo, 'MASHA ALLAH' yake ayannawa a kasan zuciyarsa, ashe haka yan uwansa suke da yawa da kyan kallo?, yaren du sai suka shige masa idan ka cire daga bakin marar kunyarsa sai namijin sai yar karamar da ta shiga ransa sakamakon wasan da ya ringa yi da ita harma ya rike sunnanta Ta kasan ido ya saci wajen da ta duke, ganni ya yi sunna yar kiciniya ita da uwar kafin ta dagota tsaye ta dan harareta sai kuma ta waske ta janyota ta zaunar da ita kusa da ita wanda hakan ya zama ta fi kisa da shi a gefensa na dama A tausashe ya ce" ku zauna mu ci abinci mana " Du bin umarninsa suka yi, wanda shi kansa ya kula umarninsa ne suke bi kai tsaye domin yar hayaniyar da ya tarar sunna yi sun yi gum sai kallon junna da suke a sace du sun nutsu Murmushi ya kuma yi, a lokacin da kamar an budi bakinsu da Zahrau ta kawo masa gaisuwa du sai suka ringa yin irin nata sunna fada a tatare Ba na wace ya amsawa, sai dubansa da ya kai wajen Ammi ya sakar mata murmushi a hankali ya ce" Ammi, y'ayan naki hala makarantar gaisuwa kika saka su? Na ji sai maimaici suke uwa wa'inda suke kawo harda" Ammi ta yi yar daria a lokacin da ta fahimci ya tsokani yaren ne, hakama UMMU dake ta bubude kayan abincin Ummu ta ce" aa fa SHAHEED, kar a haskawa my stars " Shima dan murmushin ya kuma yi, Ummu ta kai dubanta wajen yan matan da suke serving tare a da, tun daga kan Zahrau har kan Najeeba aman a yau du sun nutsu irin kamar sunna tsoron su motsa su mutun nan Da kulawa ta ce" yan mata yau ba za'a zuba ba? Oya maza ku tashi ku yi serving dinmu " Du sai suka kuma mikewa su hudun nan, sai ya kasance sunna hada ido da junna kowace na son fashewa da yar uwarta da kuka Ammi cikin jin dadi ta ce" Ke NAJEEBA, ki zubawa mijinki " Gaba daya sai suka waiwaya suka kalleta, hakan ya saka ta dan zaro ido ta kikifta su a kan yan uwan nata da kuma lokaci daya suka dauke dubansu a kanta kafin ta maida kan Ammi, Ganni ta yi sam bata kuma bi fa kan maganarta ba, gashi shi din kansa ya yi wani irin zama kamar wanda ya lumshe idannuwansa yake barci bayan idannuwan nasa a kanta suke, kare mata kallo yake haka kawai ya tsinci kansa da tambayar kansa 'yanzun da wani ne ya zo gaishe da Ammi haka zata fito a gujen nan da irin shigar nan kanta ba ko dan kwali' (ta hade gashin kan nata cen sama irin idan zaka yi bacin nan ta daure hakan sai ya kawatata sosai) Korar tunanin ya yi, ya ci gaba da bin yan uwanta da kallo ya ga yanda suka yi serving din kannensu baki daya bayan sun bubude sunna tambayar kowane abinda yake so Ajiyar plat a gabansa ya saka shi bin hannayenta da kallo, kamar da wasa sai da ta ajiye har hudu wanda hakan ya saka shi bude idannuwan da dan mamaki yana binta da kallo Komawa ta yi kujerarta tana maida numfashi kamar wada ta yi tsere kafin ta ja nata da Zahrau ta zuba mata da har cokali mai yatsu ta shiga dan cacaka aman sam ta kasa ci Na gabansa ya kuma bi da kallo, harda gayya wannan lamari sai kace wanda mutun shida ne zasu ci abincin? Du ta zuba iya kokarinta sannan babu abinda bata zuba ba ta ajiye Ammi da Ummu kam summa cike da farin ciki suka shiga kokarin jan nasu, a sanyaye Ammi ta yi adu'ar cin abinci a bayane wanda hakan ya saka da sauri wa'inda suka sha'afa suka kama aka idasa da su kafin du a fara cin abincin Ina iya cewa yaren da su Ammi su ke gwagwarmayarsu ta hanyar cin abincinsu hankali kwonce, Sauran yan matan da suka dan fara tasawa da wa'inda suka tasa din sam sai suka kasa cin wani abin kirki sakamakon irin yanda tarbiyarsu take na kasa cin abu a waje gaban wani bakuwar fuska , hakan sai ya zame masu wani irin cin abinci su din nan gaban SULTAN SHAHEED Shima a hankali yake tsakurar wanda ya janyo gabansa yana hankalce da yanda NAJEEBA ke ta wasa da spoon din cikin salak zala da aka zuba mata wai ita ba zata ci mai nauyi ta zama katotuwa ba Hannunsa ya mika a hankali ya dauki yan kunnayen da suke rigama a kansu, hakan ya sa ta dago da ta sauri ta bi hannun nasa da kallo har ya maida kusa da plat dinsa ya ajiye sannan sam baya kallonta kamar bai yi wani abu ba ya gimtse abinsa Satar kallon su Ammi ta yi, sai ta ga su ta farin cikinsu suke, duda ba mai magana aman sun kasance masu yalwataciyar fara'a a fuskokinsu Hannunta ta mika ta dora saman yan kunnen, ba zato tana shirin daukewa ta ji nasa a saman nata A hankali ya shafa saman hannun nata wanda hakan ya sakata zare ido da zare hannun nata da sauri tana kallonsa Da sauri Zahrau da su UMMU suka kawar da kai cike da mamaki, ita kuwa sai ta harhade fuskarta kamar zata fashe da kuka sannan sunna hada ido ta murguda bakinta gefe tana kara tura bakin haka kuma tana son zare hannun nata aman jin nasa take ya riketa taf Ido ya zaro gannin rashin kunyar da take masa, sai ya dan yi murmushi yana gannin su Ammi har sun kamala hakan ya saka a hankali ya kara murza bayan hannunta sannan ya yi aiki da yan yatsunsa biyu ya zare yan kunnayen ya mayar gabansa ya ci gaba da dan cin abincin Baki ta turo gaba sosai ta ringa kallonsa, shi kuwa sam baya kallonta, su Ammi kansu sun kula da yannayinsu aman ba wanda ya nuna ya ga wani abin Nan da nan kowa ya gama cin abincinsa banda Najeeba da ta yi ta cika tana batsewa Ammi ta kalleta ta ce" Najeeba, ya haka? Ki ci abincin mana na ga baki ci komai ba" Najeeba ta kara takwakwafe fuskarta sai kawai ta saki dan kukan shagwaba ta ce " Ammi, yan kunnayena ya dauka bayan da tsada sosai na siye su fa " Shi kansa da mamaki yake kallon fuskarta da lebunnanta da take hadawa tana kukan tabarar da su, haka kawai ya samu kansa da kara tsare fuskarta da ido yana jin wani irin abu tamkar tabarar tata na birge shi Dan tissu ya ja yana goge bakinsa ya tabe bakin nasa bai ce komai ba Ammi ta kale shi, ta ce" eyah yayansu bata abinta mana baka ga itace karama, ai ummuna ta bar mata ko?" Ummu ta turo baki itama ta ce" Ammi, to tace na bata sai na bata aman ta daina yin karyar wai ita ta siya " Najeeba ta gala mata harara ta ki yin magana tana kara matsar kwalar dole sannan baki daya ta saki jikinta rigar jikinta bata dameta ba tana ta kara tura bakinta da yannayi na rigima take ji Dan murmushi ya yi a lokacin da ya mike tsaye, tura yan kunnen ya yi a aljihunsa sannan ya kai dubansa wajen su Nusaiba Hannunsa ya mika mata a hankali ya ce" Nusaiba zo" Nusaiba dake kallon fuskarsa da yar dariyarta ta yi wajensa ta kama hannunsa ta rike tana ta kara kallon fuskarsa so take ta tina inda ta sanshi Murmushi ya kuma yi mata ya dauketa baki dayanta sannan ya yi wajen babar kujerar fallon ya zauna yana ajiyeta gefensa kafin ya shiga yi mata wasa Da yannayin farin ciki iyayen suka karasa wajensa gannin da gaske zama ne zai yi tare da su du sai suka bar yaren nan zaune Kasa kasa Bilkissu ta ce" auntyna dan girman Allah wannan shine sarki?" Ummukulsum ta gyada mata kai tana murmushi Bilkissu ta ce" wauh, walahi haka yake da kyau? Kuma ashe ba tsoho bane auntu Najeeba ke cewa za'a aura mata tsoho, kuma Aunty ya fita kyauma ko?" Najeeba ta ringa share fuskarta ita a dole fushi take, kuma Ammi bata amso mata yan kunnen ba, ita haka kawai take son yan kunnayen ba wani na zinari ba karfe ne sak aman an masu tsari ne sosai, Yar dariya Ummu ta yi tana kallonta ta ce" SORRY sis, ba zan kuma ba na bara maki yan kunnayen kin ji kanwata?" Zahrau da ta gama amsa waya kasa kasa ta kashe tana binsu da kallo a hankali ta ce" ta ina zamu fita ne? " Ummulkhair ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsu ta ce" gaskiya gwara ya ringa rufe maku kansa, ina wannan da budewa yake ai da rikicin mai yawa ne, lalle Najeeba baki da kunya wannan ne kike cewa ke bakya son fari waye waye? Tap, yanzu dai Aunty Zahrau tashi mu je kawai kar mu yi da sanyi, walahi mu je, kai ni daga yau na daina jin haushin kishin Zinaria a barta ta yi kishin mijinta walahi" Su dai kannanun karasawa suka yi suka hadu da shi da su Ummu sunna wasan su Da yake AMMI ta san da fitar salamarta kawai suka yi suka tafi su uku tare da dogaran da zasu dafe masu baya har mutun hudu Sai da ta gama zamanta saman table din sannan ta mike bayan ta yiwa yaya DAYABU mesage cewar tana son ya shigo mata da babar waya da layi Niyarta ta ratsa ta yi shigewarta daki domin yayunta fu sun fice, kannen nata kuwa kowane ya shiga wasansa kafin malamin makarantarsu ta islamiya ya zo A tausashe, yana sauraran hirar iyayensa da suke bashi labaru kala daban daban ya bi bayanta da kallo kasa kasa har ta bacewa ganninsa Ajiyar zuciya ya sauke ya dago dubansa ya dora saman AMMI, a sanyaye ya ce" *SHIN LAFIA UMANI AKA RIKEN MATA YAU KWANA HUDU BATA ZO INDA NAKE BA?* Ammi ta kale shi da sauri tana kara jin dirara magangannunsa a kunnayenta, UMMU kuwa sai ta kaida kanta a kasan zuciyarta tana murmushi, AMMI na kallonsa da kulawa ta ce" *SAKON GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI ZUWA GAREKU A DUK INDA KUKE, NA SAN KUN SAN DALILIN SHIRUNMU BAKI DAYA YAN NIGER, ALHAMDULILAH MAY BE KOMAI YA DAIDAITA, SOSAI NA TARAR DA SAKWANI MASU MATUKAR YAWA YAN UWA DA AMINAN ARZIKI, DA YAWA NA NUNA TASHIN HANKALIN RASHIN JI NA, DA YAWA NA NUNA KULAWARSU DA SAKON GAISUWA, NA GODE ALLAH YA BIYA ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKHAIRI YA BAR KAUNA, HAKAMA WA'INDA SUKA RINGA SAKWONNINSU NA KYAUTATAWAR DA SUKA YI NIYAR YI MIN DAN JIN DADIN WANNAN NOVEL NAWA SAKWANNINSU SUN SHIGO KUMA AN SHAIDA MIN ALLAH YA KARA ARZIKI YA BIYA, MASOYA, A DUK INDA KUKE SAKON GAISUWATA ZUWA GAREKU, ALHAMDULILAH GRUP MAGE BANI DA TAMKARKU, ALLAH YA BIYA YA KARA DANKON ZUMUNCI, GASU FA, KADAN NE....AMAN IN SHA ALLAHU MUN DAWO BAKIN AIKI😅😅😅😅, daga taku ce SAJIDA* [31/03 à 21:56] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 50 Cike da basarwa AMMI ta ce" eh ta dan yi rashin lafia ne" Idannuwansa masu girma da ladaftar da mutun ya zubawa mahaifiyarsa yana kallonta, bai ce komai ba aman a yannayin kallon da ya kurawa fuskarta ya fasara irin tarin tambayoyi ko nace tarin son karin hasken da yake, Cire kanta ta yi daga dubansa ta maida wajen tanfatsetsiyar tV din dake jikin bango wace ke kashe tana dan girgiza kafarta daya ta dora da fadin" idan kuwa ita dinma gaba za'a yi da ita a hanna min ganninta sai na ji karin bayani " Dan murmushi ya yi yana sauraron Nusaiba na tambayar ya saka mata Game a wayarsa bayan shi ko kwaya babu a cikin wayar, ya maida dubansa wajen UMMU, Cikin yannayin wadatacen murmushin fuskarsa ya ce" UMANI, me ke damun kawarki ne daga farin ciki sai na ga kamar kawarki zata bata ranta fa ko menene?" Itama dubansa ta yi, ta yi dan murmushin zata bashi amsa Mardiya ta fito daga dakinta, Karar rufe kofar da dan karfi ya saka UMMU yin shiru bata ce komai ba Niyar Mardiya ta fice ta karasa diner, ta gaishe da Ammi kawai, sai dai hango wani mutun mai girman jiki, kyakyawan gaske, uwa uba tarin tarin kwarjinin dake fita daga jikinsa, tarin haske da lamari mai girman dake hanna tunkararsa kai tsaye, irin tarin hasken Azhkar da salar asuba, da tarin nafilfillu dake dakushe du wani karamin tsagera, sai ko wadinnan idannuwa nasa masu zabgawa tsagera mari da suka hadu suka sakata rage saurin da ta kwaso da niyar shigewa Da dan mamaki ya yi mata kallo daya ya cire idannuwansa a kanta, domin kuwa ya ganeta matar Abih ce, sai dai abinda ya bashi mamaki irin shigar dake jikinta da kuma ganninta kamar wace ke zaune daram dakam haka a gidan? Tana karasowa ta dan rage tsayinta ta gaishe da Ammi Ammi ta amsata da kulawa ta ce" Mardiya, mijin NAJEEBA ne ai ku gaisa" Da wani irin firgici da mamaki ta dago dubanta ta yi niyar kara kallon fuskarsa, duda ba ita yake kallo ba sai ta kasa yin hakan ta tsinci kanta da saurin sada kanta idannuwanta na kara zazarowa tamkar zasu balo su fito waje, what? Mijin wa? Idan bata manta ba SULTAN SHAHEED ne ya auri Najeeba, Sultan din da take tunanin wani margayaye ne bayan rawanin nan dake kansa koda taushe, da yawa a cikin gari na tunanin wai ko dai wata kama ce da fuskarsa dake sakashi kin son bude fuskarsa ko ya ringa yin sasaukan rawani irin na sarakan zamani komai zafi? Bata taba jin du abinda take aikin banza bane irin na yau, ashe haka yake? Tana gannin ta samu galaba a kanta tunda ta aurar mata uba hakan na nufin ta rama rabata da saurayinta da ta yi, sai kuma a yau ta ga wannan bawan Allah da bata san da wani sunna zata sufanta shi ba ace shine SULTAN? Muryarta na rawa rawa ciki ciki ta kai gaisuwarta kafin ta mike ta juya da sauri ta nufi ciki , wato ta koma tama fasa zuwa table din, sam bata da karfin iya cin wani abu, kwata kwata bata da karfin hakan, a yanzun jin zuciyarta take tamkar zata fashe, ji take tamkar zata hadiyi zuciya ta mutu, bata taba kawowa kanta Najeeba zata samu irin wannan mijin ba, bata taba tunanin zata kasance a irin wannan ranar ba, itafa bata da makiyiya sai Najeeba da uwarta, wayarta ta warto tana sintiri tana tunanin me ya dace ta yi? Wa ya kamata ta yi kira? Ko dai shawarar bin bokayen take dauka ta fara ne? Domin kuwa a da ta yiwa kanta alkawarin ba ita ba harkar boka ba dan komai ba sai dan ta kawo rantsuwa ta gita kamar yanda Najeeba ta ce da ita ba boka ba malan zata yo andani da lamarinta na mace ta zartar da hukunci ta hanyar haramta mata soyaya da saurayinta, itama ta kawo rantsuwar ba boka ba malan ita kuwa sai ta auro ubanta kuma sai ta hanna mata kwonciyar hankali karshe sai ta yi sanadiyar da ubanta ya kore ta! , Sai dai kash, a yau sai ta fara tunani cikin daya biyu.......anya kuwa zata iya ci gaba da gogaya da Najeeba da Uwarta ba tare da ta bi ta kasan kasa ba? Wayarsa ce ta dauki kuka a hannun Nusaiba Amsa ya yi ya kara a kunnensa, a tausashe ya amsa gaisuwarsa Abih dake tsaye kofar dakin ya ce" Allah ya taimakeka, na shigo ne tanzun zamu gaisa da su Bilkissu, shine nace yau ko zaka fita fada ne? Zancen aminin nan nawa dake kwonce wanda nake maka bayanin matarsa ta tashi hankalinta bisa maganar da ta ji makocinsu na yi a waya tsakiyar dare wanda ya saka mata tsantsamta da saka hannunsa kan rashin lafiar mijinta, shine na ce ina so da kanka ka yi shara'ar nan, walahi ciwo gaba yake ya ki ci yaki cinyewa gashi asibiti basu ga komai ba, ana ta na hausa wannan ya ce matabiya ce, wancen ya ce jifa ne, kai dai ka san lamuran kwashe kwashen mutanenmu, shine nace dan Allah a shigar mana lamarin nan" SHAHEED ya dan gyada kansa, a hankali ya ce" ABIH yau ba zan fita fada ba, ama ka saka a fada masu gobe in sha Allah mu yi zaman karfe tara a cikin gida " Godiya Abih ke ta yi har ya sanyo kansa falon, sai kuma ya dan yi turus da mamakin Gannin wai da gaske SHAHEED din ne yake ganni a zaune tsakanin UMMU da BILKISSU ba RAWANI?? Murmushi ne ya fadada a fuskarsa kafin ya karaso shima yana kara kallonsa da kallo mai nuni da yannayin farin cikin da ya tsinci kansa a ciki ya mika masa hannu suka gaisa kafin ya samu waje ya zauna yaran du suka shiga dane shi sunna gaishe shi da murna da ihun fadin ABIH ne ABIH ne Wannan abin shi ya saka Mardiya zabura ta ajiye wayar da suke da kanwarta fitinaniya wace a yanzu haka ta kai wajen da bama a gida take ba ta tafiarta Maradi wajen wani Alhajinta da ya kama mata gida, sam bata ji yarinyar ko a lokacin da mahaifinsu nada rai, da adu'a kawai yake binta , a yanzu da kasa ta birni idannuwansa sai da ta yi bikin bayana cewar ta zama rikakiyar yar bariki sannan ta faso gari da lasisinta take fantamawarta hankali kwonce Da sauro ta warto hijab dinta maroon ta saka ta bude kofar ta fito Daidai ta kusa karasowa UMMU ta ajiye masa ruwan da ta zuba masa a cikin copin glass mai dan tsayi mai sanyi ta koma wajenta ta zauna duda tunda ya zo ba wani magana da ta hada su daga gaisuwa sai ruwan da ta dauko masa ta ajiye masa Du irin yanda Sultan ya cika wajen bai hanna Mardiya karasawa ta dauke kofin ruwan ta je saman table ta ajiye a ranta kuwa fadi take 'karya ne walahi , ba zaki zauna kina gwada min bariki a wajen da mijina yake ba ' Tana dawowa ba ko dar sai ta samu waje dan kusa da Abih kadan ta zauna, ita bata gaishe shi ba, ita bata bar wajen ba, sai binsa take da kallo , sai kawai take ga kamar wanda ya cencara kwaliya domin ya sha sabuwar shada ne ya hade abin dai ba'a cewa komai, hakan ya sa ko dan datijantakar tasa ke son boyewa sai yan tsirakun furfurar dake jikin gemunsa dake iya shaidawa da ya dan kwana biyu da kuma fuska irin ta baba daban take da ta yaro Sai da ya ajiye wayarsa ya dan matso da zamansa ya hade hannayensa biyu ya dora gwuiwoyin hannayen nasa saman rigar shadarsa da ya dan ja baya kadan yanna kallon Abih, muryarsa a dake kadan tamkar ba sirikinsa ba, ya dauko muryarsa da yake magana da ita a kausashe a wajen shara'a ya ce" *Meye anfanin zaman iyalinka a gidan nan bayan ba wata sabga ake ba ABIH?* ABIH ya kale shi, sai ya maida dubansa kan Mardiya da sai da ajiyar zuciya ta kwace mata jin abinda SHAHEED ya fada, dama hanya take nema ido rufe dan haka ta samu nauyin da zuciyarta ta yi mata ta fara ragewa Abih ya maida dubansa kan SHAHEED, a hankali ya ce" gata ai SHAHEED ka tambayeta" Sultan ya maida idannuwansa dake dauke da yannayin kausasa ya ce" Mardiya, me kike a nan zaune tamkar wace bata da aure?" Mardiya ta hadiyi wani yawu jin wai a tambayetan da Abih ya ce, kafin muryarta na rawa rawa karshe ta fashe da kuka ta ce" wai yaya kake na yi ne MUTAKAB, yaya kake so na yi? Bayan kana min gabar da ban san a kan me ba dan kawai na fadi gaskiyana shikenan?, ni bani da damar nuna fushina shine zaka nunan na tafi gidanmu? Da zaka ce a tambaye ni a kan me nake zaune a nan so kake na yashi na kara komawa gidan namu ka hadu da wannan kunna cin amanata? Wannan din da ta ce da wada ta nuna ya saka da SHAHEED, da AMMI, da ABIH baki daya suka kai dubansu wajen UMMU dake zaune Ga mamakin SHAHEED wanda ya yi jiran jin irin hukuncin da UMMU zata dauka ta hanyar ramawa sanninta da ya yo cewar bata da hakuri da daukan raini, sai ya ga ko nunawa bata yi cewar ta san zancen da ake ba, hasalima abin yanke farce ta dauna ta duka tana dan karkare karamin farcenta na yatsarta karama, Juyowa ya yi da yannayin mamaki, lalle dunia ta yi sanyi, sannan ya yarda idan ba auren ba babu abinda zai saka ka kalli mutun da girmansa da komai ka farfada masa magangannun da sukai maka dadi dan kawai ya taba auren mijinka bayan ya girme maka nesa ba kusa ba "Haba Mardiya, me yasa kike da saurin daukan fushi a kan lamarin duniya harma ki rufe ido ki ringa magana na neman magana ne? Me ya hada zamanta da mijinki ne? Me yasa kike ta shigota da gudu bayan tana iya yinta tana kauce maki da dukan karfinta ne?" AMMI ta karasa tana mai kallon Mardiya Mardiya ta ce" Haba maman Sultan, tsakani da Allah karya na yi ne? Meye hadinta da mijina da zata ringa dauko masa ruwa daga ya zo? Meye zai sa ta zo nan ta tare bayan na san ba danginku bace?" Da wani mamakin Ammi ta budi baki zata yi magana , Abih ya rigayeta yana dan murmushi ya ce" in ba Mardiya ba macen da ka haihu da ita a yi maganar meye hadinka da ita?" Da sauri ta tare shi tana dan fido masa manyan idannuwanta ta ce" kana nufin du iyayen y'ayanka sunna iya zuwa nan su tare dan kawai aun haihu da kai?" Mutalab ya dago idannuwansa da sukai masa ja ya kalleta, ya dauke dubansa ya kai kan UMMU, sai da ya lumshe idannuwansa kafin ya cire ya dora kan SULATAN dake bin du wanda ya dauki magana da ido yana jira su gama, dan murmushi ya yi ya dan cije lebensa ya ce" ka ga ilar rashin zama waje daya ko? , Shaheed a da ce mata na yi ta je gidansu, aman a yanzu ina so ta koma dakinta sai dai da sharadi, dan Allah Shaheed ka rokar min Nana ashuwa ta koma dakinta, ina mai roko da kokon barana uwar y'ayana ta koma dakinta" Shaheed ya kurawa Abih ido, lokaci daya Mardiya ta zabura , baki daya jikinta ya kwashi rawa, tana mai kukan nan sama sama ta ce" walahi ba dai da ni zan yi kishi da macen da ta girmeni ba, matar da ta haifeni ne za'a hadani kishi da ita? Me yasa ake son kai a wajennan? Kowa idan ya budi baki sai dai ya goya mata baya ni kuwa a kwaye min? To walahi ba zan hada kishi da ita ba sai dai ka sake ni MUTALAB," UMMU ta dago daga gyaran farcenta da take ta kai dubanta kan Mardiya a karo na farko kennan, sai da ta rintse idannuwanta ta saki bakinta da ta cije da karfi tana kallonta ta nunata da abin yanke farcen nan ta ce" sannin cewar ke yarinya ce ya saka nake kawar da kaina a kanki MARDIYA! Yaya kike son sai kin kureni wajen da zan iya hukuntaki tamkar yar da na haifa da cikina ta hanyar dane ruwan cikinta na matse bakinki na zaneki da bulala?, ki kiyayi shiga sabgata, na rantse maki zan iya matse hancinki na rufe numfashinki! MARDIYA ke yarinya ce, kuma a duniyar kishi ke yar kauye ce ki je ki zauna da mace ta koya maki kishi, ki bambance MIJI da KISHIYA , ki iya yiwa MIJI magana, ki iya tafia a gaban miji kafin ki dawo ki tantance ni din abokiyar gabarki ce ko makashinki ce!" Abin yankan Farcen ta ajiye da karfi saman table din glass din wanda hakan ya saka wajen yin kara ta mike tsaye, sannan ta dan duka ta dafa hannayenta bibiyu saman table din tana kallonta da idannuwanta dake nuna tsantsar bacin rai ta ce" zama da tsoho ai ya kare tunda kika auri tsoho da yarintarki dan son zuciya kika zauna, shirme ai ya kare a macen dake tunanin zata ci galaba a wajen namiji bayan tana kin y'ayansa, ke kam wawuya ce tunda har kike yiwa mijinki hauka a gaban kowa, ke din sakarai ce tunda har kike tunanin ihunki zai hanna wani abun rayuwa! Mazan nan da biyayarkima yaya kika gama da su? Bale ke tsagera karamar kwari?, shin mahaifiyarki ta rasu da kika rasa magaya ne ko me?" Baki Mardiya ta daga zata yi magana da yannayin tsoron da ya darsun mata na yannayin UMMU, sai dai kafin ta yi UMMU ta zabura ta idasa matsawa kusa da ita sosai ta ce" dis, idan bakinki ya furta min A ba cikin kalmar da zaki hada dan gaishe ni ina maki rantsuwa da wanda raina ke hannunsa sai na sauke maki hakori irin yanda zan hukunta dan cikina, domin ke din y'ar cikina ce!" Wuki wuki ta shiga yi da idannuwanta Ummu ta juya ta fara tafia ranta a matukar bace, sai kuma ta tsaya ta juyo ta kalli MUTALAB da MARDIYA ta dan daga muryarta ta ce" me zan yi da aurensa? Bana so, ki kwontar da hankalinki in dan wannan kike hauka!" Wannan kalmar ita ta fi batawa Abih rai, ya muke da sauri ya taka yana biye da UMMU wace ta kara saurinta zata shige dakin su NAJEEBA ya ce" NANA nine bakya so? Nine bakya so Nana? Sai me dan bakya so na, idan baki aureni ba mutuwa zan yi yo? Aman walahi ba wanda zaki aura in dai ina raye , mu zuba ni da ke" UMMU ta juyo ta zazaro idannuwanta ta ce" mu zuba MUTALAB, idan an zo daura aurena ka hanna! " Tana kokarin rufe bakinta sukai ido hudu da NAJEEBA wace yar hayaniyar ta fitar da ita, irin kallon da take mata ya saka jin kafafuwanta sun yi mata nauyi, A hankali ta furta" NAJEEBA" NAJEEBA ta lumshe idannuwanta zafafan hawaye suka zubo a kurmin idannuwanta, itama a hankali sannan a sanyaye ta furta" *sai kin aure shi MAMA, idan kuwa ba haka ba mu zuba*" Tana gama fada ta juya da sauri ta yi dakin kannenta da aka kora su da niyar labarta masu abinda UMMU ke yiwa Abihnsu Wani irin farin ciki ne ya saka UMMU jin saukar hawaye mai dumi a gurbin idannuwanta, Ba na komai bane sai na wannan kalma da take ji daga bakunnan y'ayanta goma sha shida banda dayar, a yau ta fito daga bakinta cike da rigima ta hanyar turo dan bakinta mai kyau ta ce *MAMA* , Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta da sauri ta bi bayansu dan a yi komai a gabanta Murmushi Abih ya yi ya juya da sauro da takamarsa ya zo wucewa ya jiyo ihun kulan Mardiya da ta yi dakinta da gudu tana maimaita ba zata yi zaman kishi da UMMU ba ya mikawa SHAHEED da ya talabe kuncinsa yana kallon ikon Allah hannu ya ce" a tayamu da adu'a su kara rikice mata har ta aminta sai ka daura mana aurenmu" Shi kam Shaheed sai ya samu kansa shima da yin murmushin ya mika masa hannun suka gaisa ya juya ya yi ficewarsa Dubansa ya maida Kan AMMI dake ta kalle kalle ya sakar mata murmushi ya mike ya karasa kusa da ita Hannunta ya dauka na dama ya manawa bayan hannun nata kiss a hankali ya ce" AMMI, i lv u" Murmushi AMMI ta yi tana kallonsa cike da kaunarsa, Ya ce" zan je, Ammi zan dawo idan har ban samu gamsuwa da irin hukuncin Umani ba" Ita dai tana mai binsa da murmushin har ya tafi Kamar yanda ya fada masu hakan ne ya kasance, a zaunen ya tarar da matansa biyu su duka sun sha kwaliyarsu sai kamshin turare dake tashi, aunna zaune a kujeru masu nesa da junna ba wada ke yiwa yar uwarta magana Da mamakin ganninsa ba rawani, da shiga irin ta jaruman maza du suka bi shi da kallo Sunna jira ya zauna ya hakimce su kai gaisuwa sai suka ga ya ja ya tsaya a tsakiya, Muryarsa a dake ya ce" shin daga baya kika fasa ko menene dalili?" Zinaria dake kallonsa gannin maganar da ita yake ta kara buda kunnayenta dan jin a kan abinda yake magana, Sai kuma ta ga ya juya wajen NADIA itama a kausashen ya furta" Daga baya kika fasa ko tunda kika zo baki san wannan shine abu na farko a cikin layin abinda zaki yi dan samun dorewar zama da ni tare da kwonciyar hankali da nutsuwa ba? Shin baki san shine dalilin da ya saka na yi dogayen hanyoyin da zasu kai kowacenku wajen ba tare da ta fito ta bi cikin baban gida ba?" Kara sada kanta ta yi itama cikin rudu, aman ta kasa furta komai domin a ganninta Zinaria itace baba itace ta san kan mai gidan gannin bata ce komai ba sai itama ta yi shirun ta kara sada kanta sosai SULTAN ya ajiye wayarsa saman table a hankali ya ce" ku kiyaye" Gannin yana niyar shigewa ciki ya saka ZINARIA kara saukowa ta rage muryarta sosai ta ce" Allah ya taimake ka, shin a kan me kake magana?" Ja ya yi ya tsaya na dan sekwani sai kuma ya juyo ya ce" ina magana kan zuwa gaishe da MAHAIFIYATA, kowace safia kafin ku gaishe ni ku tabatar da kun fara gaisheta sannan ku biyo hanyar gaishe ni, domin kuwa albarkarta nake nema" Yana gama fada ya yi gaba, hakan ya saka su bin bayansa da kallo Ficewar Zinaria ya saka Nadia zabura itama tama sauri ta yi gefenta cike da tunanin bata san ana hakan ba, sai dai ta cika da tsoro, tsoron haduwa da Najeeba domin ta tabata a wajen take, tana tsoron abinda zata iya yi mata idan suka kasance a waje guda! Zinaria kuwa bakinta ta tabe a kasan zuciyarta tana ayyana 'ai an yi walkiya na ga komai walahi, matar da ta wanke makiyiyata ta baka shine zan ci gaba da jerangen zuwa da zowa dan gaisheta? Ba zan je ba' ................................... Wasu irin fararen jigida masu dauke da duwatsu kananu yas yas sannan sunna ta zuba kamshi ne Zahrau ta yi cinikinsu har kwaya goma sha biyu biyu gida hudu, hakan ya saka aka zuba su a cikin kwalabensu masu dauke da wani irin ruwan turaran shafawa aka mayar da su gefe bayan ta caje kudadensu masu yawan gaske Cike da ladabi Zahrau ta ce" Balaba, dan Allah ki taimaka mana da sirrikan sabulan wanka na fatoci kala daban daban mana, kama daga fatar farar mace har zuwa bak'a, Harta da irin wanda wace ke shafe shafe ke oya anfani da shi dan samun farar fata mai kyau da santsi da tsari ba tare da ta shafa mayukan nan masu kona jiki ba?" Hamshakiyar matar dake zaune cikin madaidaiciyar kwaliya tana zuba kamshi bakinta dauke da hakoran maka biyu sai kyalkyali suke ta dan yi murmushi ta gyara zamanta ta ce" yaya kike so na baki sorrin sana'ata Gimbiya Bilkissu bayan na san kanwarki Gimbiya Najeeba nada saloon? Idanfa ta mayar da wannan sana'arta tawa ta kare domin ina mai tabatar maki da zata kwacen kwastoma, a yanzu haka da wadinnan kawai nake kara kwatar kaina a kan shagonta" Murmushi Zahrau ta yi ta ce" ba zata mayar da yin sabulai sana'arta ba, na maki alkawari balaraba, ina son ki bani wadinnan sirikan ne dan ina nesa, sannan ina son kanena su uku su lakance su dan yiwa kansu" Balaba ta kara yin murmushi ta ce" idan akai haka kennan ba zasu zo na ringa hada masu ba?" Zahrau ta yi wani murmushin ta ce" bayan a yanzu a gabanki na mayar da ke wace zata ringa hada turaran wutar fada? Kin san da mun iya hada turaran wuta irin namu tsumamun turaran wutar da kuke so ruwa a jalo aman kuma na baki wannan damar ai kin san dan mun iya hada sabulai ba zai hana mana zuwa ki hada mana ba idan hakan ta taso, juste ina son na san sirrin nan, ina matukar mamakin matan da suke anfani da sabulun wanka na ruwa da na sabulu fatarsu na daukan yannayi na kwailin dake hanna masu yin bakin nan na hannu da kuma kafafuwa, ina mamakin irin yanda fatarsu ke yin santsi da sulbi , sannan irinmu masu bak'ar fata ina matukar son sannin wai menene sirrin dake sakawa fatarmu na daukan yannayi na sheki , santsi, da wani irin ni'ima tamkar wa'inda bama shiga rana ko ba zafi a garinmu?" Murmushi Balaba ta yi ta mike ta dauko litafi da byro ta dawo ta mika mata, a hankali ta ce" tabas zan baki sirrikana, bismillah ki rubuta daifai misali, aman kafin nan zan fada maki wani sirrin, wato *zafi*, zafin rana davan, gumi daban, Zafin rana shine abinda fata bata so, aman gumi daifai misali shine abinda fata ta fi so dan karbar gyara.....misali........ Shin kuna son sirrikan nan ne?😁🤣🤣🤣🤣, idan kuna so ku lalaba ni na yi tunani sai mu ga abinda za'a yi🤣😆😁, amanfa iya gyaran fatar zqn bayar, domin kuwa shi baban gyaran cen ai kowama ya iya😌🙈 Taku ce SAJIDA [31/03 à 21:56] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 5 1 GUMI daidai misali na gyara fata, yana sakawa fata karin laushi, yana saka fata karbar ko wani irin gyara, ke harta da JESIKA (HQ) na bukatar jiki ya kasance da dumi dan hakan ke sakawa itama ta kasance cikin dumin Sannan masu shafa man bleating, ba wai masu garwaye nake maki magana ba, aa, manyan masu shafa bleating wa'inda suka san darajarsa sukan shafa mai ne sai su rufa da abin rufa mai kauri , hakan har ya daina wahalar da su domin kuwa sun saba sukan yi bacinsu a haka, lale fatarsu na karbar mayukan nan fiye da wanda baya shigar Da farko dai zan kawo maki ire iren hadin da muke yi na sabulun wanka na macen da bata Bleating da kuma wace ke son fatarta ta koma fara (a gaskiya zan fada maku gaskiya, zan kawo iya na bak'ar🤣 kar yan Allah tsine su ce na kiyawa y'ayansu shafa man bleating) Da farko zaki samu sabulun VICTAGO ana so a same shi isashe domin kuwa shi wannan sabulun anfaninsa a jikin fata shine kashe kuraje da du wani fari fari da sauransu na fata, ko wace irin fata kuwa ki gwada zaki bani amsa, sai ki samo hade haden sabulu irin su carotte, na zumar nan, su Mon savon, su la vie belle, su savon de Marseille, su Roger Cavalaisses, idan kika hada wadinnan sabululukan sai ki sayi zuma mai kyau sosai wadataciya, ki sayi madara peak, ki sayi dankalin turawa ba da yawa ba wanda zaki dan yanyanka shi ki dake shi ko ki markada shi yanda dai zai narke, ki sayi resain shima murje shin zaki yi a ciki, ki sayi kankana wace ita kuwa zaki cinye saman sai kasan nan zaki yanyanke ki markade, idan kina son fatarki bayan bakinta ta dan kara haske kadan kina iya saka kurkum yellow ba da yawa ba, sannan ki saka dilka ita kina iya daketa sosai sai ki zuba kadan dan warin nan nata, haka kuma ki je wajen masu hada turaruka ki ce da su na hada sabulu kike so, sai ki zabi kamshin dake kwontar maki da hankali ki sayi madaidaici ki kawo ki hada a hadin sabulun ki , idan kin gama hade sabulun nan baki daya da kayan nan sai ki samu turmin karfe baba ki kara wanke shi ki kara dake hadin nan sai ki zuba a bokici ki dadane shi sosai sannan ki ringa bude shi dan ya kara hade jikinsa. Iya wannan kika rike matsayin sabulun wankanki zaki rabu da kuraje da wasu kananun matsaloli na fata in sha Allah (na Bak'ar fata kennan, sannan da farar fatar da take so fatarta ta kara laushi da santsi kennan, aman fa ba na wanda ke son na bleating bane, na bleating dinma akoyshi dan dai ina tsoron iyayen y'ayanmu😅) Zaki iya markada tumatir danye ki hade shi da colgate ki ringa shafawa, yana gyara fata da sakata sulbi Ruwan Alovera yana kashe kuraje, aman kafin ki shafa ki goga a gwuiwar hannunki, idan baki ji zafi ba zaki iya shafawa fuskarki , idan kuwa da zafi kar ki shafa bai karbi fatarki ba Dan tsagaitawa ta yi a lokacin da Zahrau ta gama rubutawa ta ce" ba dai za'a bamu na bleating din ba?" Dan murmushi Balaraba ta yi ta ce" ku dai na san bakwa shafa man bleating, baki data gidanku bakwa wannan, bakwa sabulun bleating to me zaku yi da shi?" Itama murmushin ta yi, ta so ta fada mata ko dan gaba, shi ai ilimi ne sani ne sannan ita du farinta ai tana anfani da sabulun na bleating shi yasa tamkar kwai kulun haka take sheki gashi dai da shekaru a kanta aman sun boye , Zahrau ta ce" to mayuka fa?" Balaraba ta ce" kin san shi mai da kika gani daukan fata fata ne, zan iya baki wanda ba shi ke karbar fatarki ba shi yasa idan ka tashi siyan mai to ka san wani meye baya son fatarka wanda ke iya saka maka kuraje ko wata matsalar daban, kin ga ni ko ido rufe aka bani carass zan jefar da shi domin ko a miya na ci shi sai na yi kuraje, shi ya sa ko siyan mai na tashi bana siyan wanda aka hada da carass komai kyansa, aman akoy dangin su Roger cavaills, su secret de teint da dai sauransu mayuka ne masu kyau dake kama yawancin fata Ummulkhair ta ce" abinda ke bani mamaki Balaba, yanzun an rage shafa mai dan samun hasken fata sai ki ga sabulu kawai ya wadatar ko kuwa sabulun nan na ruwa da ake hade hade ki ga baki daya jikin mutun ya dauka ba bambanci harta da kafa da take da taurin kai" Balaba ta ce" haka ne, kin san shi mai idan ba iya shafa shi ka yi ba yana haifar da matsala ta hanyar saka maka jiki ya yi daban daban, ka samu bakin gurbin ido, bakin kunne, wanin hannunsa baya taba jin mai ko wani irin ne, duda shi mai idan kana so ya kama maka jiki zaka ringa shafa shi da dare ne idan ka gama komai ka yi wanka sai ka shafa ka bi lafiyar gado, a lokacin da ka tashi salar asuba kuma sai ka yi wanka, sannan saka tube a mai ke saka fuska ta yi bakin gurbin ido domin a lokacin da rana ta daki wajen an gama in dai ba nikaf zaka ringa anfani da shi koda yaushe ba, su sabulan ruwan da na wanka shi yasa suka fi anfani a yanzun, domin sabulun ruwan nan mu ba na yanda bama hadawa a shagon nan dan kuwa su baki daya suke kama fata basa barin wani wajen daban" Ummukulsum ta ce" ni dai ba wannan ba, kin ga du cikinmu nice marar gashi mai tsayi da kuma kyau, sannan tafin kafata tana min wani mugun abu ta cika yin kaushi idan sanyi ya zo har tsatsagewa take, ki taimaka Aunty balarabarmu" Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsu, kafin ta ci gaba da fadin" dan gyaran gashin ki ki samo *kwai, sabulun salo, ruwan tumatur* ki hade su waje guda ki shafa a kanki, zai sa gashinki ya yi kyau da shikin, sannan ki ringa markada albasa idan har zaki jure warinta kina wanke kanki bayan ki shafata zaki dan jima da ita a kanki sai ki wanke da sabulun *salo da yodo*, Kina iya hada man gashinki da abubuwa kamar haka *Man kwakwa, man albasa, man zaitun, Man Oil, Man kadanya, Man alayahu, wadatacen man shannu* hade su zaki yi ki ringa shafawa a kanki Idan kuwa na mutanenmu na gida zaki iya jurewa sunna anfani ne da iya dungulen mai, wato man shannun nan mai wari danye, anai masu manyan kisto a lafta sai su kawo bakin dan kwali su nade kan😆, akoyfa wari aman akoy result mai kyau, Sannan *Gyaran kafar* kuwa kina iya samun Man shanu, Man kwakwa, Man ridi, Man Alayadi , zaki hade su ne waje daya da dare ki shafa koda a wajen kaushi ne ki saka leda sai ki dora safa a kai, da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi" Wadatacen murmushi ne ya wadaci fuskar Zahrau bayan ta gama rubucewa ta ce" kwanaki kin min magana a kan na kiyaye cushe cushen magungunnan nan na zamani, harma kin ce min garin neman gira kar na rasa ido, kin nunan cewa yawanci magungunnan nan na zamani su ke haifar da cutar sanyi, sannan wasun sunna hadasa ila a mahaifa, gashi kuma lamarin nan fa yanzu na shigo aman na gama gane cewa idan ba gyara akoy matsala, dole sai da gyara, me kike iya gabatar min dan na ringa anfani da shi? Idanma ke ke siyarwa muna so" Balaraba ta gyara zamanta tana kallonta ta ce" Gimbiya Zahrau, ba duka magungunnan gyara suke da matsala ba, sai dai ganewar da mutane suka yi cewar mata mun haukace idannuwanmu sun rufe kan wannan lamari sai kowa ya tashi kai da fata shi mai magani ne, ina iya rantse maki wata mai maganin ita ke saidawa aman bata taba anfani da shi ba domin ita kanta bata san me ya kunsa ba bata yarda da shi ba, A ganina a yanzu da kuke yaran mata me zai hanna bayan irin taimako da na tabata Gimbiya zata tsaya maku kansu irin na su kankana da ake yi da yusufa da sauransu, da su daguwar kaza da tantambaru, sai ku rike sasaken baure da karanfani da mazarkwaila, walahi Zahrau zan fada maki du girman nan nawa haihuwata uku ko? Bani da wani siri da ya dara wannan, domin ina jina sakayau, marata bata daurewa, ni'ima daidai misali alhamdulilah, sai ko ruwan dumi da karanfani idan na ji ina bukatar na dan kara matsewa ne nake saka karanfanin da gishiri kadan idan bana bukatar hakan iya ruwan dumin nan shine nake yi du asubar Allah na zuba a baban flask dina na rufe, da shi nake wuni ina sirkawa ina anfanina, ban ce maki idan na hadu da wani sirrin da na yarda da shi bana aiwatarwa kaina ba, domin kuwa mace dai yar gyara ce ko wacece dan kuwa ko satin da ya shige sai da na yi tataki har garin maradi wajen Hajia SAMIRA HARUNA ta yi min tukunyar nan da ta taba yi min, na maganin zafin da garin dahuwar, na zauna na cinye tas kafin na juyo idan kin kula na cenza mota, to a washe garin ne oga ya min kyautar nan" Murmushi bayanane Zahrau ta yi, domin kuwa Tukunyar nan yau kwana biyu kennan da UMMU ta yi masu ita sai da suka cinye tas tas, gaske ta ringa haduwa da yannayi na jika haka kawai Kudade ne masu yawa suka cakewa Balaraba kafin suke mikewa zasu tafi Har sun zo bakin mota dogarai sun bubude masu da sauri sai Balaraba ta ce" Gimbiya Zahrau " Dakatawa Zahrau ta yi ta dawo tana kallonta, Balaraba ta kamo hannunta na dama ta ce" Dan Allah kar ki fadawa Najeeba na ji tsoron bada wasu daga cikin sirikana, bana so ta ji haushina a kan hakan domin ita din ita ta koya min kitso da kunshi" Murmushi Zahrau ta yi ta ce" ba zan fada ba " Bangaren UMMUi kuwa cike da mamaki take kallon Bilkissu da suka gama sauraron Najeeba na fadin wai bata son auren mahaifinsu, hakan ya saka Bilkissun kama hannunta tana kallonta ta ce" MAMA, me ya ba zaki auri ABIH ba? " Rasa mai zata ce da yarinyar ta yi, sai kawai ta shiga kikifta ido, NAJEEBA ta koma ta yi kwonce saman bed din tana kallon sauran sam basu wani damu ba kasancewarsu yara sosai, ita kanta Bilkissun dan shekarunta sun kai goma sha uku haka shi yasa ta fahimci abinda ake nufi harma ta ji kwata kwata ba dadi a ranta, dan tsaki ta yi ta cire kanta, haka kawai take jin haushin mutumen, wai haka kawai ya kwace mata yan kunnayenta? UMMU ta kara kama hannun Bilkissu tana kallonta a sanyaye ta ce" Biki, ki yi hakuri kin ji? Ba kin mahaifinku nake ba aman ina bukatar ku min adu'a idan alkhairi ne Allah ya tabatar" Kai ta gyada a hankali ta shiga jikin UMMU ta dora kanta, hakan ya sa NAJEEBA lumshe idannuwanta sannan ta mike a sanyaye ta fita ta koma dakinsu Wata kwonciyar ta yi ta kuma lumshe idannuwanta tana ta tunanin rayuwa, a haka har yayunta suka dawo bayan sun gama nunawa AMMI abinda suka siyo da UMMU suka sameta a dakin tana kokarin yin baci To dai bacin da bai samu ba kennan domin kuwa sai da aka saka jigidar nan tsaf aka tare nan ana ta training din tafia da ita a jiki sunna daria abinsu Bayan salar isha'i UMMU ta kalli AMMI da kulawa ta ce" AMMI, ban ga yarinyar nan ta shirya dan zuwa wajensa ba" AMMI ta yi murmushi kadan ta ce" kin san meye UMMU, sam ban ji dadin ranar nan da bai biyo bayanta ba, na san da kamar wahala na samu abinda nake so kai tsaye da SHAHEED, aman fa koda a kwatance ne ina so ya ringa kokartawa......u see ko waya bai bugo ya yi wani bayani ba, kamar wanda ya baro wata uwar mata aka kawo min ita nan, sarai na gane ta samu lafia , abinda ke faruwa nima ina son samun bambanci , a gaskiya ina son ya fara gane lamarin nan kala daban daban ne, sannan ina so koda kuwa cenza namijin da ka samu bisa tarbiyar da matarsa ta dora sa nada wahalar gaske cenza shi......aman ina son kwatantawa. Believe me na san a kan me nake magana, nd trust me sai na ga kul uwar daka!" Dan murmushi kawai ta yi ta kada kanta ta ci gaba da jan carbinta Cen kusan karfe tara UMMU ta yada zango a daki ta zauna kusa da yan matanta da suka fara kitson Zahrau Kasancewar kannanu ne sosai, gashi kuma Dayabu ya ce a jibi jibi zata koma dakinta shan nonon ya isa haka ta dan dubi yanda Najeeba keda saurin kitso ta yi murmushi tana amsa sannun da suke mata inda Ummulkhair ta mirgino daga kwoncen da take ta dora kanta saman cinyar UMMUN ita kuwa Ummukulsum sai fama take da ruwan albasa da kumb a hannunta UMMU ta kuma yin murmushi, ba karamin dadi take ji a rayuwarta idan ta ga yanda kan yaren nan ke hade ba, takan godewa Allah harma ta ji wani hawayen farin ciki na son silalo mata a lokacin da bata shirya ba tsabar jin dadi Dubanta ta maida wajen sif ,cen sama ta ringa hangen sauran jigidar da suka rage kafin ta maido dubanta tana dan shafa gashin kan Ummulkhair a sanyaye ta ce" ina son magana da ku " Su dukansu sai suka maido hankulansu kanta harma Zahrau ta mike itama sunna sauraronta, UMMU ta ce" ina so ne mu yi magana a kan rayuwa, duda ku biyu baku je dakin auren ba tukunnan aman du ba mai bacewa bace dan koda Allah ya yi bana nan kuka je dakin aurenku ina so ku rike wannan" NAJEEBA ta kalleta da kyau, bata nan? Ina zata je kuma? Ummu ta ci gaba da fadin" Tabas aure ya ginu ne da rayuwar Sex, sai dai baban abinda nake so ku gane kyakyawar mu'amala tsakaninka da mijinka shi ke sakawa a fi jin dadin komai, ina so ku yi kokarin jajircewa dan gannin kun wanzar da kyakyawar mu'amala irin ta shakuwa da fahimtar junna tsakaninku da mazajenku, ba wai dan kuj auri masu mata ba wanda ke kanki Ummukulsum zaki tare da mai matar ne halayansu ya saka ku hau kuma ku bi, ko kuwa ku ce da karfi da yaji zaku cenza su......aa, ita rayuwar baki dayanta yar dabara ce, yar siyasa ce, hakuri, da kuma fadawa Allah. Ba ina nufin kowani namiji ya saba da gim gim gim da matarsa ba aa, wani namijin matar tasa da ka zo ka tarda mace ce da ta san kanta, ta gane cewar idan har ya ci gaba da irin halayan nan na komai ba ruwansa ba ita kadai zai shafa ba harta da y'ayan da zasu haifa yana iya shafar su sai ta jajirce har Allah ya sa suka kasance aminan junnama ba tsorata zaki yi ba, zaki shige ne kema, zaki damki damar nan sannan ki dan kara naki salon da zuciya daya ba dan ki cutar da ita ko y'ayan mijinki ba. Idan kuwa namijin nan kin tarar da shi da halaya tamkar fan dambe kamar yanda na fada maku dole sai kin bi a hankali sannan kin bi da zafi zafi, kuma sai kin jure kin saka hakuri a zuciyarki a hankali har ki samu sasauci.....sannu sannu har ki fi karfin wulakanci a wajensa, irinsa ne sai ki ji ana cewa wane ai ya dauko ruwan dafa kansa, zafin nan du babu, mutumen nan idan yana gidan amarya hum zaka ga ya shige ne da wuri fitiwa ta gagara, zai je ya lafe abinsa ko me suke yi a gidan? Lolz abubuwa dai ire iren haka............." Dan nisawa ta yi tana kallonsu ta ce" komai tsufan namiji, komai yarintarsa idan har ya hadu da mace zata iya daidaita abinta irin yanda take son rayuwarsu ta kasance, aman fa ban ce da ku wai zai zama mijin kan tace ba, kai ni kaina bana son namijin da lokaci zuwa lokaci ba zai botsarewa maganana ba domin hakan na bambanta min ni ba mamansa bace sannan a karkashin ikonsa nake, tunda muka samu kyakyawar fahimtar junna koda kuwa mun samu sabani shiryawarmu abu ne mai matukar sauki, mai yiwuwa daga idannuwanmu sun sarke da junna komai zai wuce, ko idan na zo wucewa yana iya riken tafin hannuna shikenan na huce, ko ya yi anfani da wani sunnan dake sakani nishadi, idanma nice na bata masan da nawa salon da ina yi zai sauko komai hawan da ya yi, abinda dai nake so shi ne *KAR KU KASANCE KU KOMAI FUSHI, KAR YA ZAMANTA IDAN HALIN NUNA FUSHIN NAKU YA KAMA A RINGA ROKAR KU ANA LALASHIN KU KU KI SAUKA HAR KU GUNDURE SHI YA YI BANZA DA KU, SANNAN KAR KU KASANCE KU BAKWA FUSHI EHE*" Wasa wasa a nan UMMU ta tare da y'ayanta, tun sunna jin kunyar wasu magangannun har ya zamanto sun fara yi mata tambayar ta yaya hakan zai kasance? Har ya dawo sai su yi murmushi su kalli junna, a haka har Ummukulsum ta samu kwarin gwuiwar duba wayarta, irin tarin sakwanin da Yarima ke turo mata ta ringa karantawa Ummu da yan uwanta a hankali cike da nutsuwa har ta kai karshe wanda sakwannin tun sunna nuna tsagwaron ban hakuri da neman yafiyarta, har suka dawo kamar da wasa yakan dan sirka kalmomi kamar haka" kin tsaya min a zuciyata, na kasa cire wannan rana " , har ya dawo dora harafi a cicire kamar haka "i lv u", karshe dai baro baro ya doro shi a hade cewar "walahi i love you", har da irin yan yayan wayan nan dake nuna idan mutun na cikin halin sad da dai sauransu Abinda ya fi birge Ummu bai taba tsalaken rana ba, hakan ya sa ita kanta a yau ta ji tana iya yafe masa harma ta dubi Ummukulsum ta umarceta da tana iya rubuta masa amsa dan gannin idan har ta fara daukan darusan da take masu a yau Cike da nutsuwa ta dora kalamai kamar haka" *Asalam Alaikum, fatan an wuni lafia? Dan na kawo gaisuwata ne da fatan a yi baci lafia* Bayan ta gama ta karantawa Ummu , ta yi murmushi domin kuwa kwarai hakan shine daidai, sam bata so ta nuna zumudinta ta hanyar bashi amsa ta farko ko ta nuna masa kamar shi take jira, sannan rashin ambaton sunnansama nada nasa wajen, tana turawa ta sakata kashe wayar dan ta tabata idan ya gani yana iya beman kiranta ita kuwa ta hane su amsa wayar saurayinsu mai mata a irin lokacin nan, dan kuwa ba dadi idan ka yiwa wata kaima za'ai maka! Murmushi kawai NAJEEBA take har tana dan rage girman idannuwanta irin tana dan kausasa kallonta tana hangen abubuwa da dama, ta tsinci kanta da jin zata kwatanta abubuwan nan, tabas zata kwatanta abubuwan nan. ........................................ Baki daya a falo ya yada zangon aikinsa a yau, ba komai ne yake hadawa a computernsa ba sai binciken da ya saka wani kwararan police abokinsa ya yi masa a kan rayuwar mutanen nan uku komai da komai da ya shafe su A hankali ya ringa nazartar irin abubuwan da aka kawo masa har ya tsaya kan Amintacensa Ya maimaita wani waje ya kai sau uku, wanda abinda ya samo da gaskiyar lamarin ba haka bane Kan soyayarsa ne da ita, an nuna ya so ya yi soyaya da ita sai dai mahaifinta ya dakatar da kamarin bayan ba haka abin ya kasance ba, soyaya sak suka yi mai zurfin gaske daga baya suka rabu a lokacin da mahaifiyarta ta fito karara ta nuna masa shi din ba dan wani bane, ba jinnin sarauta bane kwarai zai yi rashin kunya idan ya nuna yana son yar sarki, dan haka ya kiyaye takunsa ya bar matar manya wa manya Hakan ya hanna masa zaman garinsa ya dawo DANAGARAM, karshe ya ajiye aikinsa harma ya samu kusanci da sarki ya samu karbuwa, wannan shi ne gaskiyar lamarin abinda ya kawo shi garin DAMAGARAM har ya zama gagara badau a cikin masarautar ta hanyar samun kusanci mai karfi da SULTAN A hankali ya ji ya kasa cire ayar tambaya a kansa, *WACECE* a cikin y'ayan sarkin? Sai a kan Liman baba, wanda shima ya samu wasu karin bayanai kan wa'inda yake da su a kansa Sai kuma mai bulala, wato baban dogarin zabga, wanda shi ke tsaye da babar bulala a fada......labarin *Dandatsa* da akai masa tun a shekarun mahaifinsa, ya kasance ya afkawa mata har shida hakan ya sa akai masa hukuncin dandatsa aka jefa shi a gidan yari na dan lokaci A lokacin da ya fito sai ya samu matansa biyu sun barshi, y'ayansa kuwa ba maganar su yi masa biyaya, dan haja sai ya koma wajen sarki Allah ya jikan rai da koke koke da komai da alkawarurukan ya shiryu, Sarki sai ya amince, ya janyo shi jikinsa dan ya kara shiryuwar, ya nuna masa kyakyawar hanya da komai karshe har ya samu mukamin nan, sai dai har yanzu shi da mace sai dai kallo, shi a yanzu matan nema sam basa bashi sha'awa sai dai ya kalla ya cire kansa. Kansa ya dago ya kuma kallon hanyar da ta nan ya dace a ce ta shigo tun dazun, sai dai yanzunma ba alamunta Dan murmushi ya yi a bayane yana dan girgiza kansa, wato dai AMMI ta shirya? Bakinsa ya tabe irn bai dame shi ba, sannan ya mike da computern nan ya yi ciki Sai da ya daura alwallah kafin yake hawa Bed sinsa bayan ya yi wanka Idannuwansa ya lumshe a hankali ya cije lebansa na kasa Baki daya jikinsa ne ya amsa masa a lokacin da ya hango kogin nan, tabas wannan shine kogin zuma A hankali ya buda idannuwansa da har suka fara amsar sakon nan ya sauke dubansa kan AC din dake kusurwar dakin, a fili saman lebensa ya furta "Bacin zaki hana min yauma?" Sai kuma ya lumshe idannuwansa yana hasashen irin haduwarsu ta gaba, zata amshi tukwuicin tsagerancinta ne a hannayenta! Wato dai yar fitsarariyar AMMI ba zata shiryu da neman magana ba? Jikinsa ya ringa hadewa ko zai samu dan sasauci cike da wani takaici dake taso masa, wai yana da mace uku aman yau kwanansa hudu rabonsa da Mace dan kawai yana tare da amarya? Hum! Ai kwanakin amarcin saura gobe kawai zasu zo ne a yita ta kare walahi shi ba waliyi bane! Wani tsakin ya kuma yi a hankali sannan ya mike ya shiga cire rigar bacin da ya saka ya koma bayi Sosai ya ringa zubawa kansa ruwa sannan ya fito ya zauna saman kujera da karamar wayarsa a hannunsa, shi kadai ya ringa tunani shin kiran AMMI din ne zai yi ko me? Mtsssssss han hm, A hankali ya ringa jin ransa ya fara bacewa sakamakon wani tunani da kalamanta da suka fado masa a ransa Na tsane ka! Bana son ka! Ka sake ni na auri masoyina! Ni bana son farin mutun Huzaifana nake so! Idannuwansa ya rintse da dan karfi a lokacin da ya ji wani abu mai karfi ya soke shi a kahon zuciyarsa, kamar da wasa ya ringa jin abin ba dadi a ransa harma ya tsinci kansa da fadin" *Yanzu fisabililahi me ya yi zafi a maganar nan da har zan ringa tunota ina jin tamkar wani mai ciwon athsma zuciyata na tafarfasa bayan na san gaskiya ne tana da saurayinta aka raba su ai kau?, kuma shine hankalina zai ringa tuno min shirmen nan? Idanma bata so na ai inada masu so na! Nima kuma ai ba son nata nake ba!* Lebensa na kasa ya kuma dan cijewa, da gaske zafin maganar yake ji kamar a yanzu ta fada masa Sunnan Huzaifa ya yi masa katutu a zuka yana jin wani irin daci a kan sunnan da wani tunani daban Gannin zai cutu ta hanyar tinane tinanen nan sai kawai ya nemi kusanta kansa da Allah ta hanyar dora nafila, domin kuwa ba zai yarda yana ji yana gani kamar wani yaro karami ya tinga tino maganar yarinyar nan da bata jin magana mai fadan tsiya gabansa na faduwa haka kawai! Morning people😁, ga breakfast😌 [31/03 à 21:57] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 52 Tun karfe bakwai su Najeeba suka gama kitson nan, kitson da akai masa wani irin kannanun tsinta har sai da Zahrau ta ce yanzu Najeeba haka kikai min kannanun kitson nan wa zai tsefe min? Sai kawai Najeebar ta yi murmushi abinta ta janyo sabuwar wayarta IPhone da yaya DAYABU ya kawo mata a jiya ta kunna Whatsup din da ta riga ta yi installed ta shiga, tarin numbobin mutanenta da take yiwa gyara wa'inda Habu dan daudu ya tuturo mata ta shiga saving kafin ta yi message daya mai dauke da gayatarsu gidan Mai Damagaram cewar saloon dinta ya koma nan, za'a ci gaba da aiki kamar yanda ake budewa a da, da sasafe sannan a cika dare kafin a rufe, daga kasa ta saka sunnanta da kowa zai iya ganewa kafin ta fita a whatsup din Instagram ta shiga ta yi posting din hotunnan talar kalolin mak'up din da take yi masu ita da yan uwanta sannan ta dora da albishir din dawowarta Hakama ta shiga Facebook da tsohon cmpte dinta shima ta yi posting din bayani wa mutanen da suke hira a ciki A kwoncen nan hankali kwonce ta ringa aikinta ta hanyar posting din tarin hotunanta masu matukar kyau da tsari, A haka take samun tarin tambayoyin mutane masu son sannin wai da gaske tana gidan sarki? Wai da gaske Mai damagaram ne ya aureta?, Sai tarin masu turo mata invitation din son ta zamo kawarsu a Facebook Cikin sabon posting dinta harda numberta na whatsup wanda ta jadada ga mai son kwaliya da gyaran jiki yana iya tuntubarta a number ta tura A haka ne wasu daga cikin tsofafin samarinta suka ringa bata nishadi ta hanyar turo mata habaici, zata karanta ne ta yi daria kafin ta yi block din mutun ta je ta maka numbersa a black liste Number Aida ta dannawa kira Kamar wace ke jira ta daga tana salama NAJEEBA ta ce" Aida, goben in sha Allah ku fito da wuri fa, yanzu su aunty Zahra sun je su ga yanda aka yi wajen, ni ban je ba in sja Allahu sai goben, ina so ku fito da wuri ku yi dukan gyare gyaren da ya dace kafin na fito domin na tabata wajen nan namu sai ya cika ko dan masu son gannin kwakwaf" Da sauri Aida ta amsa cike da ladabi kafin su kashe, itama ta shiga kiran ma'aikatansu tana shaida masu sakon mai gidansu inda suka cika da farin cikin tashin aikinsu kai da fata ga mai gidansu a gefe gasu a fada, sukan hasaso yanda abin zai kasance ne, sun tabata ci gaba ne Isashen Baci ta samu a lokacin da yan uwanta suka yada zango a saloon dinta Sosai wajen ya mugun tsaruwa ya birge su, haka suke yiwa wajen vidio cike da mamakin irin tsarin ginnin da akai a dan kankannin lokaci aka shake shi da kaya cikin tsari Kaya dai gasunnan, an zuba sai fatan samun ribarsu Da farin ciki suka yada zango dan yiwa Ummukulsum gyara tsakaninsu har sai da kusan yama sannan suka firfito sukaiwa masu tsaron kofar salama domin kuwa wannan karron bama dogarai AMMI ta saka a kifar shagon NAJEEBA ba, haka kawai tsoron dora dogaran take dan haka ta tura takarda wajen commissioner yan sanda aka turo mata mutun biyu ginanu ta ware masu mota daya da dukan abibda zasu bukata hakan ya sa su kansu farin cikin wannan aiki domin kuwa ci gaba ne suka samu mai girma Vidion kawai take ta kallo tana karawa, sai wani zumudin zuwa ta gani ya shiga zuciyarta, wata irin kaunar iyayenta ta kara shiga cikin zuciyarta hakan ya sa cike da farin ciki ta duka har kasa ta shiga koro masu adu'o'in gamawa da duniya lafia da dukiya mai albarka Da farin ciki Ammi ta mikar da ita ta ce" Najeeba, bafa mu mukai abin nan ba, wannan din da kike ganni daga mijinki ne domin da na kai masa maganar ne ya samu mai zane ya zana yannayin ginnin ya zuba ma'aikata sannan ya zuba kudin kayan da za'a zuba a cikin" Sai ta ji abin wani bako a wajenta, aman kuma farin cikin da take ciki ya hanna mata jin abin sosai din nan sai kawai suka ci gaba da farin cikinsu, ita kanta UMMU ta sha mamakin wajen, lalle an dankara dukiya ba laifi sai adu'a da fatan a mora Zama sukai sunna hirarsu domin yama ne Hanyayoyin dake jere su uku ne aka shiga kokarin bude daya da kys hakan ya sa suka dan dakata dan gannin ko waye sai dai ba dukansu ba, A hankali ta fara leko kanta kafin ta sanyo kafarta muryarta kasa kasa ta yi salama tana karema mutanen fallon kallo Dukan Alamau sun nunna a tsorace take da shugiwa wajen hakan ya sa take ta rabe rabe har idannuwanta suka sauka kan NAJEEBA da ta dago dubanta daga kan wayarta tana amsawa mutane maganarsu ta sauke a kanta Da sauri Nadia ta sada kanta haka kuma da dan sauri ta karasa wajen su UMMU ta duka har kasa harta da muryarta na dan rawa ta shiga gaishe su ta hanyar fadin" barka da safia mama" Ummu ce ta saki murmushi ta mika hannunta ta kama na Nadia , da kulawa ta ce" ki karaso daga nan Gimbiya, barka da yamaci" Baki daya ta kasa samyn nutsuwa ko sakewa, du tsoro ne bayane karara a fuskarta, yau tun da safe take shan gumurzu da kanta kan shin zata zo ne ko kar ta zo? Gashi dai ba yan rakiya , ita daya zata zo, a yanzun da maman Najeeba ta kama hannunta sai ta jara jin tsoro, itafa tsoronsu take gaskiya Dosanuwa ta yi kanta kasa ta shiga gaisar da su daya bayan daya Ga mamakinta sai suka ringa amsata da kulawa, har tambayarta UMMU ke yi yaya bakunta fatan komai lafia bata da wata matsala Ajiyar zuciya ta sauke ta jin sanyi sanyi a ranta, dan kuwa sai da auntynta ta rakota har kofar ta turota kafin ta iya shigowa domin zuwanta uku har sai da ta sha stop diarhee tsabar rikicewar da ta yi dan kawai ta saka tsoro da tunanin idan ta yarda ta zo zasu hadu su yi mata jina Baki dayansu sun amsata, hakan ya sa a hankali ta dago dubanta dan satar kallon NAJEEBA Sai da gabanta ya kuma tsinkewa ya fadi, da sauri ta sada kanta kasa ta rike hannunta da dayan hannun nata tana fatan Allah ya fitar da ita lafia, Gata dai zaune itace farar mace kaf a wajen nan aman baki daya da ta sauke dubanta kan Najeeba sai ta ji ta muzanta, munnin kanta ta ringa ganni a bayane, irin yanda NAJEEBA ta kara zama ne ya bata mamaki, a gaskiya ta kara zama wata irin babar yarinya, gashi dai ba kwaliya ko dis a fuskarta, sannan suturar jikinta doguwar sakakiyar riga ce irin ta shan iska, kanta kuwa a kunce yake ba kitso sai tasubala da ta soka a ciki da alama tana shirin gyara kan ne, tarin gashin nan nata sai ya yi uwa tukunya a saman kan nata hakan ya sa gaban goshin ya kuma yin luflufluf Abinda ya kara kayar mata da gaba ido hudun da suka yi, irin kallon da Najeeba ke binta da shi ba zata iya fasara ko me ke cikin zuciyarta gane da ita ba, kamar mai yi mata kallon ta bata mamaki, ko macuciya, ko zata hadu da ita, hakan ya sa ta ringa jin fitsari na mintsinar mata mara A hankali ta kara rage tsayinta bayan ta dan mike ta yi masu salama Da mukawa Ammi ta yiwa su Ummu magana cewar su yi mata rakiya Ai kuwa da ido NAJEEBA ta bi su har suka bacewa ganninta suka shige lungun da zai sadata da bangarenta Bakinta ta tabe a hankali ta mike tana mai jan tasubalarta daga kanta tana kwonce daurin da ta yiwa gashinta ta nufi cikin dakinsu Du da kallo suka bita, sannan a bayane AMMI ta saki murmushin da ita kadai ta san ko na meye, Zahrau kuwa ta mike ta bi bayanta dan tana son ta kama mata su gama hada abinda zata tafi da shi gidanta .................................. .......... Bayan salar isha, GIMBIYAR garin Agadez ce zaune da waya kage a kunnenta tana sauraron kalaman kamilin mijinta, a sanyaye yake maganar sai dai abinda ke neman kasheta shine irin kashedin da ya yi da irin alwashin da ya ci a kanta, bata gama farfadowa ba ya dora da fadin" ban san yaushe zaki yi hankali ba, abinda na sani shi ne ni ba tsohon banza bane, na zuba maki ido na zata zaki yi tunani? Sai na ga kin kara bani mamaki a karo na ba adadi a lokacin da kika tare a gidan sirikinki da sunnan kina jinya, shin ina iyayensa? Ina yan uwansa? Ko ba su shi kansa bai isa ya kula da matarsa ba? Ki sani na san me ke damunku ku duka, daga ke har Zinaria idan baku farka ba zan saka maku hukunci mai tsananin da zai firgita du wani mai kaunarku, idan a gobe baki biyo jirgin da zai fito daga garin Niamey ya yo damagaram daga nan ya yo Agadez ba komai na iya faruwa da mulkinki, idan nace maki komai ina nufin komai!" Kitt ya kashe kiran da ya sakata zabura har hannayenta na rawa tana kallon screen din tanfatsetsiyar wayarta Ta kasa yarda cewar shi ne, yau ita ce mai martaba ya yiwa magana a haka? Ita ce ya yiwa fada a haka? Sosai kanta ya dauki hayaki ta cika ta batse, ina ai dole ta je ta ganshi gashi ga ita ya maimaita magangannun nan, zata je kuwa ko dan ta gani da idannuwanta abinda ke shirin samunta ita kanta, me hakan ke nufi? Shin yarinyar nan bayan yarta har ita sun gama da ita ko meye? Da sauri ta mike ta yi dakin Zinaria dake kwonce har ta fara baci bayan ko salar isha bata yi ba wai ta gaji dan kawai an mata wankin kafa bama ita ta yi da kanta ba gannin tana baci ya sakata fitowa ta shiga kiran number babar yarta, ina ba zai yiwu ba, walahi ba'a yi su ba! ....... . . .. . ........................... Tarin gajiyar da ya dawo da ita a yau ta hanna masa tunanin komai, yana gama dukan abinda ya zame masa jiki, ya gama waya da lauyan da ya dora kan binciken abubuwan da suka tsaye masa a rai, domin shi dai ba lauya bane, irin halin tsantsamtun da ya shiga ya hanna masa fita neman bayanan da kansa, domin a yanzun fitarsa sai idan ta zamo dole ne, ya daina fitar daren da yake ya dakatar har komai ya warware masa Yana gamawa bayan ya gama nafilarsa sai kawai ya nemi waje ya kwonta dan samun hutu, Sosai shara'ar da ya yi a yau ta caza masa kwakwaluwa, ya hadu da mutane ne masu matukar taurin kai dan kuwa du yanda ya so a gama shara'ar cikin masalaha da junna sai da suka saka shi mikewa da kansa ya kawo kur'anin da sam baya son yawan saka shi a garinsa ya ajiye a gabansu kan su rantse domin mutun ne kwonce ba ta yada yake, sai bin mutane da ido, bayaj a da shi din shi ake so da gani sai gashi a yanzu komai sai an masa, ga mata ga y'aya, rayuwa dai tai masu zafi sai hamdallah....cikin fadawa Allahn da ake ne matarsa ta tashi tsakiyar dare dan dauro alwallah sai ta ga babu ruwa baya zuwa, niyarta ta zagaya baya dan samun ruwan a butar makiciyarta, sai dai a nan ne ta ringa jin magangannunsa kan lalurar mijinta Sosai aka yi rigima domin Abih kansa ya ja ya tsaya kan sai sun fadi komai idan kuwa ba haka ba kur'ani ya ci su Ajiyar zuciya ya shiga saukewa a hankali wanda ke nuni da ya samu baci kennan (Asuba ta gari SULTAN) a yau ne ya kama ranar da iyayenta sukai mata alkawarin zata koma bakin aikinta zata je ta fara gabatar da aikin da ta fi kwarewa a shi wato harkar saloon Shiri ta yi na mamaki, domin ta sha wata rantsatsiyar shada ne doguwar riga sannan da kanta ta aminta ta dora alkyabar nan dan ta san ba za'a bata lafia ta yi tafiaarta haka ba Daurin da ya fi fitar da sirrin kyanta ta kafa a saman kanta simple sai jelar gashinta dake dan yawo a gadon bayanta wanda ta saka masa biboudi sai nanadewa yake a gadon bayan nata masha Allah Takalmi ta kafa mai dan tsini, sannan kafa ciki bayan ta saka safa suka yada zango a falo sunna jiran yaya DAYABU su karasa wajen sannan daga cen su yi salama da Zahrau wace ta sha wani irin rantsatsen mak'up itama sai kyali take daidai da kalar fatar jikinta Yana zuwa cikin shigarsa ta Gizner ya gaisar da iyayensa sannan suka tashi dan karasawa bayan sun yi masu adu'a Cike da nutsuwa suke tafia, hakan ya sa du hankali ya yi kansu Du inda suka zo sai an duka an kawo masu gaisuwa, sannan kowa so yake ya bambance wacece amaryar sarkinsu? Aman a yau sun kasa bambancewa dan irin kamar da y'ayan Abih suke, gashi sun saka Alkyaba ne su dukansu, haka kuma tafiarsu cikin tsari Yaya Dayabu ne ya hango tarin takalma a kofar wajen hakan ya saka shi dan zaro idannuwansa ya ce" ke NAJEEBA hala mutanen nan du sunna cikin wajen cen?" Najeeba dake sakin murmushi gannin irin yanda aka kawata wajen ta ce" yaya, sunna ciki, to aman bana gannin abubuwan hawansu fa?" Yaya DAYABU ya ce" ai a kofar shigowa aka umarcesu ajiyewa, akoy dogarai dake baiwa abin hawan mutane tsaro, kema yaya za'a yi kowama ya shigo gidan nan da mota sai kace wani karamin gida?" Murmushi ta kuma yi, lokaci daya droon din SULTAN ya ringa yawo a wajen, du kawunansu suka daga suka bi shi da kallo, haka kawai ta ji a jikinta kamar ana kallonsu ne, sai dai gannin yan uwanta basu damu ba sai itama bata damun ba Karshe dai yaya Dayabu kasa shiga ya yi domin tun daga waje zaka gane fa yau sun hadu, mata ne birjik a wajen baba da babarta Ita kanta ta yi mamakin wasu fuskokin mutanen da ta gani a wajen nan, ba dan komai ba sai dan da yawansu irinnan san junnan nan ne aman gaisuwa kawai ke hadawa, da yawansu irin sunna yiwa mutun kallon sun fi karfinsan nan ne, ciki kuwa harda matar ambasador da ta rangada guda lokaci daya tana fadin" gata fa ta shigo, Allah ya yi mana maganinta, Allah mun gode maka, yanzun kam sai dai a je a karata da Zinaria, Zinaria kuwa ta ci dubu sai ceto, zamu ga wa zai fadi a wasan" Da mamaki Zahrau ke kallonta gannin irin yanda wajen ya bada kala daban daban, a ranta ta furta 'To fah, kar dai a dora daga inda aka tsata' NAJEEBA na murmushi tana kara bin kowa da kallo, masu tafe dan taya murna ta gane haka kuma masu son ganewa idannuwansu komai a bayane yake dan haka sai ta cire alkyabar dake kanta, baki daya ta idasa cirera a jikinta hakan ya sa Hadimarta da sauri ta amsa ta yi dakin da aka ware dan hutunta ta kilace ta fito tana risinawa da tambayarta inda zata fara zaunawa dan hutawa Murmushi ta yi mata bata ce da ita komai ba, ta shiga bin bakinta daya bayan daya tana gaisawa da su tanai masu lalle marhabin Bayan ta gama ta umarci su Aida kan su bubude kayan aiki a fara aiki, aman aikin yau ba za'a amshi kudin kowa ba, sai dai zuwa gaba Ai kuwa wajen ya idasa rikicewa da murna da gudar mata Sai a lokacin ta ga Habu dan daudu, sai da ta zaro ido dan mamakin yaushe ya shigo, Idannuwansa ya yiwa far far ya tafa hannu ya ce" ci ubansu kawata, takawarki lafia mata a wajen mai damagaram, karya ne a tankawa uwar dakina na kyale ko a gaban dubu sai nai motsi sai dai a dinken baki, kin san wanda ya gama tsorata da maciji ko igiya ya gani firgita yake, kin jijiga matan gwamnoni, kin tarwatsa zuciyar dakakiyar macen da take gannin ita mace ce, kin zaburar da yan mata, kin watsa kannanun kwari kin mike kin mana raf da wuyan MAI DAMAGARAM uban gidan ZINARIA, tabas ke din sai sarauta, domin manyan kaya kike janye da su da mai tuka su sai OGA, sitiyarin kan motarki ba kowani hannu zai iya juya shi ba, dole ki firgita mana fara mai takama da hakan, da Allah muka dogara ba da uban wani ba, mun tabara mun sha yasin mun motsa da adu'ar iyaye dan alkur'ani makiyanmu fadawanmu" Ihun aka kuma sakawa hakan ya bata ran wa'inda akaiwa habaicin, ciki kuwa harda matar doctor wace itaka ta zo tataki ne yau dan ta ga wannan NAJEEBAR sannan ta san Habu farin sani ta ce" kai Habu habaici kake mana ne?" Habu ya kuma juya ido ya ce" kar ki ce min kin ji kamar da ke nake?" Zahrau ta girgiza kai tana kallon yanda wajen yake, ita ta rantse da Allah har a cikin zuciyarta baki daya ta tsorata, aman cikin ikon Allah NAJEEBA a tsaye take hannayenta sake fuskarta bata nuna alamun mamaki ko tsoro saima bin kowa da take da kallo daya bayan daya, ko shewar nan da ake du masu yi tana bin su da kallo, ga uban jus jus da ake rarabawa inda su Ummu ne suka ja ragamar rabe raben da sauransu, A sanyaye ZAHRAU ta ce" ni dai dan Allah a bar wannan abubuwan haka, wai shin kaima kitson ka zo ne?" Sai da Habu ya kaleta sama da kasa ya ce" ke kuwa baki san inda suke ina nan ba? Ai a jikinsu nake ci, sannan da kike cewa a bar haka kin taba gannin gidan kitso ba runguntsumi?, dubansa ya maida wajen NAJEEBA dake kallonsa, ita kanta a kasan zuciyarta uban mamakin ta inda ya shigo a yaushe ya shigo take, idan bata manta ba tun da aka dora masu zama da dogarai aka hanna masa shiga shagonta, Habu yana yi mata aiki ne ta hanyar kawo mata mutane sosai da sosai, idan ya zo waje kuwa zai zauna a sha hira da shi ne ya yi tafiarsa, bayan wannan ba wata alaka tsakaninta da shi domin ko irin biki nasu na yan daudu bai taba fada mata dan ta fada masa gaskiya itafa wannan abin baya bata sha'awa nema kwata kwata shima tana masa fatan shiriya Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" to in bama gagawa irin ta dan adam ba, MUTALAB fa goma sha shida ya kyankyashe mata, ciki kuma biyu kawai ya kilace a dakin miji, suka san ko na tausayawa wahalar yan tsofafin mazajensu na mika masu wata jinnin MUTALAB din? Kun san abinda ya yi yaya shi ya yi kanwa" Daya daga cikin kawayen Mardiya, wace ta bata wannan rana takanas tare da fada mata sirrin nan, bama kawarta bace kawar kanwarta ce wace ta turota takanas dan a kunna masu , rikakiyar yar bariki ce kana ganninta ka ga wace ta auri duniya auren zobe ta yi kas kas kas da cingan ta ce" kwarai kuwa hajiyata, ai MUTALAB ya iya haihuwa, aman ba ku goma sha shida babe matan, ku goma sha Bakwai ne ko kin manta wace aka samu *KYAUTA?* (irin sararsu ne, zaka ji an cewa yaron da Allah ya yi aka same shi haka KYAUTA) Sai da Zahrau ta kusan faduwa daga tsayen da take, a tsorace ta kai dubanta wsjen wace ta yi maganar hakama su UMMUKULSUM , Najeeba kanta sai da ta rintse ido, aman kuma dama walahi ta shiryawa irin ranar nan, ta san da a irin yanda ta tarawa kanta neman magana sai an binciko sirikan rayuwarta dan a nemi tozartata, tama yi mamakin sirrin gidansu da ya jima haka ba tare da an jima da bankado shi ba, shi yasa ko ba komai take gannin ba laifi Mardiya fa ta yi hakuri, domin tsayin lokacin nan bata fada ba sai yanzu ai kuwa ta yi kokari Kannanun magangannu ne suka shiga girmama, harma wasun na neman karin haske da maganar KYAUTA Najeeba ta girgiza kanta ta ce" kai dan duniya, dan duniya bai yi ba, wato shi ko yaya ka yi da shi hakan take gareshi, kwarai kuwa mu goma sha shida ne kamar yanda na fada hakan ne, domin duniya ta san MUTALAB ya haihi y'aya goma sha bakwai ne, maza biyu, mata goma sha biyar, a yanzu da na gano munada yar uwa sai nake fadin sha shida, abin farin cikin alfahari nake da Ubana da bai zubar da yar kanwata ba, ya haifo abinsa santala sannan ta samu kilacewa wace zata yi min wuf da mijin daya a wajen nan alkawari ne........ta karashe tana mai sakin murmushi ta kai dubanta wajen Aida ta ce" ina take?" Da sauri Aida ta shiga dakin hutun NAJEEBA ta fito da wata budurwa kyakyawa mai tsayi irin na yan uwanta, kamarsu daya sai dai ita din fara ce, sannan hijab ne jikinta yannayinta ya nuna tana da dan tsoro domin sai rarabewa take Su kansu yayunta sun sha mamaki, a hoto suka san yarinyar yaushe Najeeba ta santa har ta kawota? Da sauri Najeeba ta fincike hannunta da take jijimkewa ta ce" Jinnin Mutalab Allah kawai yake tsoro, jinnin Mutalab dokokin Allah yake karewa, haduwa da shi kawai yake tunani, idan ba dan haka ba da ya yanka dan mutun sai dai uwarsa ta haifo wani ba shi ba! Sakar min hannunki ki kalli du wace ta bi ki da kallo daidai misalin wanda ta yi maki, idan yar mutunci ce ki yi mutunci da ita, idan ba yar mutunci bace kika daga mata kafa walahi sai na tsinka maki mari, kema ganninki kika yi, suma wa'inda suka same ki daga ke basu kara wata ba hakan na nufin kadara ce ta afka masu wace ba yar shegiyar da ta fi karfinta, ina alfahari da ke, ZAHRAU na Alfahari da ke, Ummulkhair na alfahari da ke, Ummukulsum na alfahari da ke, mu kam muna alfahari da ke a ahalinmu" Zahrau ta matso kusa da su su hudun, tana kallonsu ta lumshe idannuwanta ta ji wani dadi a kasan zuciyarta, burinta dama itama ta dawo cikinsu ashe yar rigimarsu har ta kawota gidan nan? Hannunta ta kama a hankali ta dan murza sannan ta sakar mata murmushi wanda ya sakata fashewa da kuka ta shiga rungumarsu cike da wani irin farin ciki, ashe zasu karbeta? Ta sha labewa ta kalle su tana son su a ranta aman kuma tarin tsoron ta kusance su ya saka kulun take kara hangensu daga nesa, tunaninta kar ta kusance su, su fatataketa dan ta kasance ba da aure aka haifeta ba, ko a message din da suke da NAJEEBA walahi gani take wasa ne, ashe dai da gaske ne? Ita kam ina zata saka ranta dan murna da farin ciki? Habu ne ya ringa kikifta ido yana gannin yanda wajen yake kara daukan haramar rikicewa a fili ya ce" toh fa" Zahrau ta dan zunguri keyar NAJEEBA a hankali ta ce" itace surprise din da kika ce min kin adana mana?" Najeeba na satar kallon budurwar nan tana kokarin fita ta gyada kanta da wani irin sauri ta saki hannun yan uwanta ta finciko hannun budurwar da ta kasance karya uwar fada, domin dai ita sanadiyar fada du an yayage mata fuskarta da reza an yi mata dinkunna hakama a wuyanta tafka tafkan dinkunna ne na ciwo ga kuma wajen girarta Ai kuwa a shirye take, ita ta fara kokarin kaima NAJEEBA bugu, cikin ikon Allah wajen ya nemi harfitsewa domin kuwa da kyau NAJEEBA ta ware take rama rigimar da bata yi ba na satitika dan kuwa har ta tsigewa budurwar nan kitson kanta jinni ya fara zuba hakan ya sa itama cike da bacin rai ta ciro rezarta ta nemi yanke mata jiki, daidai polisan nan sun shigo da gudu dan Zahrau ta kirasu tana ihun su taimaka, Najeeba kuwa ta saka hannunta ta tare rezar sai aka yanketa a hannunta yanka mai girman da jinni ya bale mata Yanda suka ringa hankado du wani mai rigimar waje ne ya saka shi kara tsaida abin a kansu yana kallo Su kansu sai a nan suka ankara da Habu, shima sukai waje da shi Kokowa ce ake tsakanin NAJEEBA da yayunta, ihu take su saketa sun tatare sun riketa sai tirjiya take ja hakan ke sakawa suke kara matsowa waje ga hannunta da Ummulkhair ke ta kokarin daurewa sunna mata ihun ta tsaya ta tsaya aman firrr ta ki idonta ya rufe ji take baki faya zuciyarta ke son tsayawa idan har bata janyo makoloton yarinyar cen ba Police din ne ya umarci su saketa, dan kuwa su sunna wajen nan dan su hanna du wata fitina da shigar du wani fitinane ko namiji, sai gashi yau ranar farko an fara a haka? Sunna tunanin hutu ne ya same su ashe dai zasu motsi motsi na arziki? Zahrau ta ce" ba zaka gane ba, ka bamu hanya mu koma gida da ita idan muka saketa mu muka san wa muka saki" Irin jarumin nan, sannan yana so su gane shi ko zuwa gaba dan idan ana son tsaro su nemi sunnansa a masarautar ya ce" Gimbiya ki yi hakuri ku saketa , mun san aikinmu zamu iya da komai" Zahrau gannin Yaya Dayabu yana tahowa da wani irin sauri sai ta saki Najeeba, domin kuwa ta tabata a irin yanda yake jefa kafar nan tasa idan ya iso su kansu sai sun sha mari dan haka ta shirya karbar nata, ita dai kam ta shiga uku, dama Najeeba sai da ta fada mata yau ta tabata sai an yi rigima domin haka ne idan ta jima bata fito ba takan tarar da an shiryawa fitowarta, shine harda fadin ita kuwa ba zata kula kowa ba Sunna sasauta mata rikon da wani irin karfi ta yi ciki da police din nan, wanda hakan ya saka SUKTAN kara rintse idannuwansa yana jin bugun zuciyarsa ya karu kashi casa'in, numfashinsa ne ya ringa doka masa da karfi yana fita da sauri, idannuwansa suka kara yin ja a lokacin da ya ga ta daki police din nan da hannayenta uwa uba ciki ta yi da shi wanda hakan ya zo masa a ba zata ya nemi riketa ta damki damtsen hannunta da karfi dan ya samu ya hanna mata ficewa, Dan daudun nan na nesa kadan yana ta dira yana ihun a saketa ya tare mata matsiyaciyar nan shegiya busashiyar karuwa Juwa ke daukan NAJEEBA dan da gaske jinni take zubarwa mai mugun yawa aman zuciyar ta shuwa ta tashi, idannuwanta sun gama rufewa sai ta cire makwogwaron karuwar cen Baki dayansa ya mike tsaye, jikinsa har rawa yake tablette din a hannunsa ya saketa sakamakon gannin da gaske Police din nan so yake ya rungume masa mata ta baya dan ya ci karfinta ya hannata zuwa wajen fadan ita kuwa tana son fin karfinsa, gashi dayan kuwa du yana ta fitar da kutane yana fadin kar wanda ya dawo sai da katin gidan sarautar da za'a buga a rarabawa du wani client dinta DAU kake jin karar wani mahaukacin marin da ya saka NAJEEBA dauke wuta lokaci daya , domin gaba daya hayaniyar nan ce ta dauke mata ta daina jin maganar kowa, sai kuma fatar idannuwanta sukai mata nauyin tsiya a saman lebenta take son furta kalmar nan kwaya hudu wato *yaya ka mare ni?* Aman fir maganar ta ki fitowa a lokacin da ya warci hannunta dake cikin na Police din nan ya yi mata wani irin ja ya karasa kusan yayunta da du suka aniya kare fuskokinsu sai dai cikin ikon ALLAH da hannun nasa na hagu ya shiga sauke masu tankadeta mareta ciki kuwa harda bakuwar yau tau, wace yau yau ta fara irin haduwar nan da su haka, hakan ya sa ta kwala wata kara idannuwanta waje ta dafe kuncin nata tana zazaro ido cike da mamaki da tsoro da tashin hankali harma ta ringa jin zata saki fitsari Luuu take yi daga bayan DAYABU wanda bai cika hannunta ba ya aniya zazaga masifa, sai dai lokaci daya ya yi tsittt sakamakon irin yanda jibga jibgan dogaran Fadar suka shiga cika wajen da wani irin bulaloli a hannayensu sunna dakatar da du wanda bai rigaya ya baiwa kafarsa mai ya kara gaba ba, sunna gurfanar da su Lokaci daya Amintace ya ware babar muryarsa fuskar nan tasa a hade ya furta" ku zube a kasa, ga MAI DAMAGARAM zai karaso, kowa ya kai gwuiwarsa kasa ya sanda dubansa ko kuwa na rantse da wanda raina ke hannunsa zan saka babarbara na yanke kafafuwan mutun sannan na kwakwale idannuwan shege domin ga MAI WUKAR YANKA NAN TAFE Cikin ikon ALLAH tun daga kan polisan, har zuwa su yaya DAYABU da sauran mutanen dake wajen du suka zube kan gwuiwoyinsu, a nan ne NAJEEBA ta tafi luuuuu ta kusan faduwa kasa, sai dai Yaya Dayabu bai bari ba ya saka hannunsa ya tarota jikinsa yana kallon fuskarta gabansa ya fadi, a hankali ya dora kansa saman goshinta hawayen da yake ta rikewa dan marin kannen nasa da ya yi suka samu damar fitowa, Zahrau kuwa hannunta na rawa kasa kasa ta kara tauke kullin hannun NAJEEBA kafin ta saci kallon dogaran nan da baki dayansu suka yi wani irin gurfanawa hannayensu a jijimke sunna masu kawo gaisuwa sai dai ba magana, wajen kuwa ya yi wani irin dif ba magana sai ajiyar zuciya kala daban daban dake tashi, sai kuma takun tafiyar dake shaida koma waye ke yinta yana yinta ne da fushi, da kuma karfi Zuciyoyi ne suka shiga tsintsinkewa a lokacin da Amintacen sarki ya kai gwuiwarsa guda kasa dayar a tankwashe ya dago jimkaken hannunsa kansa a kasa muryarsa sama sama ya ce"""""" Hello mutanen yaya ne😊, sorry walahi yarinya ne ba lafia, godia nake da sauki yanzun Alhamdulilah [31/03 à 21:57] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 53 Sai da ya ware murya, wanda hakan zai iya tsoratar da wanda bai saba ji ba, ya nutsar da wanda ya saba ji, jikin mutun ya kwashi tsuma ba tare da shi aka koda ba amintacen sarki ya ce" Gagara badau kake dan sarki jikan sarki, takawarka lafia jarumi hamshaki barde, kai ne namu kai ne nasu kai din na kowa ne, tafiyarka ke shaida sahunka Mai wukar yanka, kai ne usulin Babarbara ba itace usulinka ba, daga kasa kake dagowa sai ka nuna sama ka saki, baka fito ba sai da ka shirya *SULTAN SHAHEED ABDUL MALIK ALI BUZU* Takawarka lafia miji a wajen *ZINARIA, NADIA DA NAJEEBA,* Idannuwansa da suka cenza launi ya daga a hankali ya sauke dubansa a kanta, gashin kanta da ta daure ribom din ya kunce gaba daya gashin ya sauko sosai yana walagigi Hannayenta a fili, dama dama rigar bata yaye ba sannan da safa a kafafuwanta Dan gyaran murya ya yi a sanyaye hakan ya sa amintacensa mikewa da sauri tsaye Da idannuwansa ya kai dubansa kan Habu dake ta rawar jiki ya dan dantse gefen lebensa sannan ya kuma duban police din nan Ba magana ya yi ba, aman irin kwatancen ya yi ya saka amintacensa fahimta Nan da nan aka shiga salamar mutanen banda su biyun nan Du kawunnansu a sasade suke ba wanda ya dago har aka fitar da mutanen nan baki daya sannan ya sauke dubansa kan bakuwar fuskar dake cikinsu Bai ce komai ba sai takawa da ya ringa yi har ya karasa wajen da suke tsugune Hannayensa ya saka ya dan rage tsayinsa Hannunsa dake talabe da ita ya cire sannan ya dauketa da hannayensa Muryarsa ciki ciki ya ce" ka kai Bilkissu aeroport yanzu Daga haka ya juya da NAJEEBA a hannunsa ba tare da ya kuma bi ta kan kowa ba har ya bacewa ganninsu Sai da Amintace ya basu damar dago kansu sannan du suka dadago a tsorace, dogaran nan ne suka kara korar kowa suka rurufe sannan suka dora gadi a wajen Kuka Zahrau ke yi bilhaki, domin ko gidan fir an hanna mata komawa , DAYABU ya dubeta yana tuki zasu karasa aeroport murya da fada fada ya ce" Zahrau, ko ki min shiru ko kuwa na baki mamaki a nan, aman kin ban mamaki, kin bani mamaki Zahrau, kina tsaye kina kallo? Da darajarku da komai ku zubar da wannan rashin mutuncin? Zahrau kin san waye SHAHEED a kan NAJEEBA? Lalle ina mai adu'ar Allah ya sanyaya fushinsa, ina rokon Allah ya sasauta masa damuwarsa, Zahrau SHAHEED ne ya fito da kansa a irin wannan lokacin ya dauki NAJEEBA da hannayensa a gaban dogaransa, Zahrau kun bani kunya" Wani kukan ta saka tana yarfe hannayenta ta ce" yaya dan Allah ka yi hakuri, ni kaina sai da na ga abin ya idasa rikicewa, yaya ban gane ban san SHAHEED a kan NAJEEBA ba?" DAYABU ya girgiza kansa kawai ya yi mata shiru, har sai da suka karasa gidan jirgin sunna zaune dan bai saura minti ashirin su daga ba a hankali ya ce" Harda dan daudu, ga maza nan sunna son rungumota a jikinsu, shin sake na yi da tarbiyarku har haka ko menene?" Sai kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga bin gefen kumatunsa, hakan ya mugu mugun kara daga hankalin Zahrau dan haka ta ririke hannayensa tana ta girgiza masa kai hankali tashe muryarta a rikice take fadin" Dan Allah kar ka yi mana kuka, ka dakemu, ka yi mana komai dan Allah kar ka tuhumi irin tarbiyar da ka bamu domin kuwa mu mun san kai din ubanmu ne" Kansa ya girgiza a hankali ya ce" Zahrau, Allah ya yi rayuwarmu wata iri, tabas na san ba wanda zai iya raba NAJEEBA da fada, aman ban yi tunanin a yanzu da take amsa kiran matar SHAHEED zata cike mayafinta ta nemi dakuwa da wata matar da bata kama darajarta ba, ZAHRAU kema dake dauke da taki darajar kika tsaya a matsayinki da kasancewarki yayarta kuke danbatuwa, to bara ki ji, wace aka turo din AMMI ta kama wayarta dazu kafin mu iso tana fadin ta tabata idan har aka tsokani NAJEEBA sai ta rama, idan kuwa ta zubar da hauka a cikin masarauta ga kishiyoyi ga mijinta mai zafi ana iya kilaceta a dakin horo, daga nan ko uban me take takama da shi an karya saura uwarta, Zahrau wato maradinku ba zai ji kunya ba? Me zai faru, me zai yi mata, Allah masani, aman kun cutar da zuciyata" Kanta ta dora gefen hannunsa tana hawaye, ita kanta zuciyar tata ta mugun raunana, shin Najeeba wace irin zuciya ne da ita mai karfi fada haka? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une idanfa aka sakata dakin horon? Idan labari ya kaiwa zinaria fa?" Motar shiru ta dauka a haka har lokacin tafia ya yi, nasiha ya kuma yi mata mai ratsa zuciya kafin su rabu tana ta hawaye, sai da ta shiga ta ga GIMBIYA hakimce a wajen VIP din, dama nan suke zama hakan ya bata mamaki matuka, ta gaisheta da mutuntawa aman ita sai ta cire kai kamar bata santa ba. Zaune yake ya cire rawanin, kansa sade kasa ya dafe kan nasa da hannayensa biyu biyu yana kallon kasa Da wani irin sauri AMMI ta nufi wajen NAJEEBA dake shinfide saman doguwar kujera, UMMU kuwa ta yi wajensa hankali tashe ta saka hannunta ta cire nasa tana kallon fuskarsa har sai da gabanta ya yanke ya fadi Idannuwanta ta lumshe tana jin wani irin daci a zuciyarta, tabas AMMI ta fada mata komai dangane da wayar Mardiya, ita ta hanna a shaida masu dan tana son gannin yaya zasu tafiyar da abin, sai gashi cikin sauki sun tafka rashin hankalin da abu daya take jira shine gannin farkawarta ta nadi jikinta tamkar an aikota A hankali ta ce da SULTAN" ka yi hakuri " Idannuwansa ya lumshe, ya kuma budewa a kan UMMU, ya kama hannun nata na dama ya rike a cikin tafukan hannayensa, a hankali ya kai wajen zuciyarsa ya dora yana kara cije lebensa na kasa Sosai ta kara tsorata tana kallonsa da dan saurin magana ta ce" subahannalah, menene wannan bugawar da zuciyarka ke yi? BILKISSU zo kama min" ta karashe tana azamar mikewa tana kara tataba jikinsa AMMI ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Dukanta ka yi ne Shaheed? A summe fa take ka barta kwonce haka? Menene ya yi zafi haka Shaheed, dan Allah ka yi hakuri ka sasauta, NAJEEBA yarinya ce sannan ka san rigimarta a hankali du zata daina" Idannuwansa da sukai masa mugun nauyi ya cire ya dora kanta, shimatt a kwonce take yar baby face dinta ta fito radau, AMMI na kokarin cire mata rigarta har sai da ta cire mata ita ta kai mata ita wajen cikinta hakan ya bayanar da bras din dake cikin rigar fara tas da lafafen cikinta Ammi na tofa mata adu'a bayan ta gama waya da likitan masarautar Kuma lumshe idannuwansa ya yi, a hankali ya furta" UMANI," Sai kuma ya dan ja numfashi yana ta hucin zafin abinda yake ji a ransa ya dora da fadin" UMANI alkyabarta ta cire, Umani a gaban wani kato dake hadasa husumar, Umani sannan ta fito kofar shagonta a haka, kuma Umani police din nan ya kama damtsenta da hannayensa biyu, ya juyar da ita yake son rungume min ita a jikinsa, Umani ta ja DAYABU ya mari fuskarta mai daraja, ta daga muryarta mai daraja kowani banza ya saurara" Sai kawai ya yi shiru idannuwansa rintse sosai sannan ya sada kansa kasa haka kuma bugun da zuciyarsa ke yi ba wani sasauci Da sauri AMMI ta cire kanta a kansa ta sada dubanta itama, UMMU ta cije lebenta na kasa irin yanda ranta ke baci da wannan lamari, a sanyaye ya kuma dagowa wannan karon har jijiyar gaban goshinsa harbawa take a kausashe ya ce" Na sha wahala Umani, Allah ne kawai ya kare min .........sai kuma ya yi shiru ya ki karasa abinda ya yi niyar fadan a hankali ya daki hannun UMMU ya mike tsaye ya kuma kai dubansa inda take Wajen frij ya nufa da kansa ya dauko ruwa ya dawo Budewa ya yi ya duka a hankali ya zuba ya shafa mata ruwan nan Yana yin na biyu ta ja wani irin numfashi ta sauke, lokaci daya ta buda idannuwanta tana ta sauke ajiyar zuciya A hankali ya kai dubansa wajen AMMI ya ce" Ammi, kar ki kira likita namiji kin ji? Ki kirawo mace" NAJEEBA ce ta fashe da kuka muryarta na fita kasa kasa ta ce" AMMI, ni ku barni na je na rama Ammi yaya Dayabu ya mare ni ban masa komai ba, Ammi kuma ta zagemu haka kawai bamu yi mata komai ba" Da wata irin murya mai nuni da daf ake da aiwatar da kowace irin hukunci UMMU ta ce" *NAJEEBA!* DA sauri Najeeba ta dago, sai a lokacin ta ga SHAHEED, sannan ta ga UMMU Ai kuwa da sauri ta ringa kokarin jan rigarta, irin ta rufe jikin nan nata, shi kuwa a tsaye yake kikam yana mai bin du wani take takenta da kallo, idannuwansa kuwa sam basu da dadin kallo a irin wannan yannayi Lebensa na kasa dake datse a bakinsa ya kuma turawa bakin nasa yana mai binta da kallon nan da ta rigaya ta gama gane na tsana ne Sai da ya lumshe idannuwansa a karo na uku sannan ya mika hannunsa daya ya damki hannun nata Da hannun nata daya ya mikar da ita da wani irin janta ne ya yi Bai tsaya kula daya cikinsu ba ya yi ciki da ita wanda hakan ya saka AMMI mikewa tana biye da su da sauri tana fadin" SHAHEED bani yarinyar nan mu koma bangarena, SHAHEED bani y'ata ka ji ko?" Da sauri Ummu ta saka hannunta ta riko na AMMI, hakan ya sa ta juyo da sauri tana kallonta ta ce" Mariam kar ya dakar min yarinya cikani na karbota" (🙄) Ummu ta girgiza mata kai ta ce" mu tafi, idan ta kama ya saka belt ya zane jikin banza da bata da hankali aman walahi ba zaki hana shi hukunta marar kunya ba ehe!" Da wani irin mamaki Zinaria ta mike tsaye, idannuwanta baki daya ta fitar waje dan tsabar mamaki ta kai dubanta kan amintaciyar baiwarta ta ce" kina nufin Mai Martaba da kansa ya shaida wannan fada?" Ai kuwa ta kara gyada kanta ta ce" kwarai kuwa Allah ya taimake ki, babu sanarwa sai zagayen su jan gwarzo a wajen, Amintacen sarki ya shela karasowarsa, zuwa lokacin ita kuwa ta summe, na kaiki karshe shi ya dauketa ya juya da ita" Jim ta yi jin wata magana kuma, hakan ya sa ta kankance idannuwanta ta ce" kikina nufin ba mari ya wanka mata ba ya yi umarnin a kwasheta koda a mace ne ba summa ba a watsata dakin horo?" Jin muryar uwar dakin nata ta fara baci ya sakata dan dago dubanta, sai dai da sauri ta maida muryarta na dan rawa rawa ta ce" aaaaaaa, Allah ya ja da zamaninki uwar gida kuma amaryar mai damagaram, a irin yanda ransa ke bace fuzgarta ya yi ya jata da karfi ya juya da ita, na tabata zuwa yanzu ya gama gindaya mata jawabin horonta ya saka a shiryata dan zuwa dakin horo , aman na saka a tare min hanyar horon ahalin gida, idan har ta tabata za'a yi kurana a shaida min" Katseta Zinaria ta yi tana fadin" maza tashi ki gano min, ina nan ina jiran dadadan maganar da zata sanyaya min" Mikewa ta yi da saurin gaske ta tafi bayan ta kara yi mata kirari, ita kuwa ta koma ta hakimce tana sakin murmushi a fili AMMI da UMMU tsuru sunna kallon bakuwar y'ar dake zaune a yannayi na takura, ba halin su bata wata kulawar da take da madaukakin girma hakan ya sa du suka tsura mata ido kawai Wata gwaurywar ajiyar zuciya UMMU ta sauke a hankali ra kai dubanta wajen yan uwan dake shashekar kuka, dan kuwa fada dai na gidan duniya sun sha shi har kamar zata dake su Maida dubanta ta yi wajen AMMI ta ga waje daya kawai take kallo, ta tabata a cikin zulumin Najeeba take, ita du ba wannan ba, tana cikin tunanin magangannun da suka yi ne da SHAHEED, me ke damunsa? Menene matsalarsa? Ummu ta kuma kallon AMMI a karro na biyu, ta kai dubanta kan NUSAIBA Dan murmushi ta yi a sanyaye ta ce" na amince da komawa dakina, idan da hali a gobe gobe" Da wani irin sauri Ammi ta kallota, hakama su UMMUKULSUM dake cikin halin tashin hankali Ammi ta ce" ki, kina nufin zaki auri yaya?" Ummu ta yi murmushi a bayane ta gyada mata kai, ai kuwa zo ka ga irin yanda su Ummukulsum suka rukunkume AMMI sunna rizgar kukan farin ciki, wayo MAMA, Ita kanta Ammi sai ta ringa jin wani farin ciki marar musaltuwa, a hankali ta mike ta nufi dakinta, tana da bukatar yin hawayen farin ciki, tabas ta godewa Allah da ya nuna mata wannan rana, ta tabata matar rufin asiri, arziki, hakin rayuwa kam bayan Ummu take, yau Allah ya yi wahalarsa ta zo karshe, dama ta sani idan har ta kaita makura zata shiga gidan ne in ya so sai su raba abinda bata so su raban UMMU kanta irin farin cikin da yaren suka nuna sai ta ji wani irin abu mai girma a cikin zuciyarta, a hankali ta kamo hannun yar uwarsu dake kallonta ta janyi yarinyar ta hade da hannun su Ummulkhair, lalle Allah ya yi zata rayu, gata kuma tsaf kama da ubanta sai dai hasken fata , murmushi ta saki tana jin wani irin farin ciki mai girman gaske na ratsa zuciyarta yana shiga dakin da ita rigar da take ta rikewa tana zaro ido ya dora hannayensa ya janyeta ja daya kasa Ido ta idasa fitarwa a mugun tsorace, da sauri ta kankame jikinta gaba daya jikin nata ya kwashi rawa Kanta a kasa dan matsananciyar kunyar tsayuwarta a gabansa a irin wannan shigar, bakinta na rawa cike da jin tsoron abinda zai mata a yanzun, dan kuwa ba zata taba manta ranar da ya fara kawo mata hari ba, wannan rana ta ajiyeta a wajen da ba zata iya hada komai da ita ba, kwarai ta ci azabar da ta kusan halakata sannan ta ga abinda ya kusan makantata, Bakinta na rawa rawa ta ce" dan Allah kar ka yi min ka ji? Walahi na wahala, walahi tsoro nake ji sosai" Ta sauke dubanta a kansa, gani ta yi idannuwansa kyam a kan gukunta dake kadawa sakamakon rawar da jikinta ke yi, ga kuma dan kukan jigidar dake dan tashi dan ko yaya ka motsa zasu shaida kansu ne Kafafuwanta ta ringa matsewa tana son rike su dan su bar kukan Bai bata amsa ba sai saka hannunsa da ya yi ya kuma cicibarta wanda hakan ya sakata zaro ido da tsoro da mamaki, domin na dazu bata san an yi ba a summe take Bayi ya nufa da ita, cikin halin dakiya ya sabeta da soso da sabulu ba tare da ya cire mata kananun kayan da kiri kiri ya hanna kansa cirewar Yana gamawa ya kuma nadota a tawul sannan ya tsayar da ita tsaye a tsakiyar dakin A lokacin da ya saka hannayensa cikin tawul din ya ja pant dinta sai kawai ta hangame baki tamkar wace ta summa tama kasa furta koda A ce , sai jikinta da ya kara kwasar rawa ga wani zafi da jikin nata ke dauka na tsoro Sai da ya cire mata shi a hannunsa ya zagaya bayanta a hankali ya ringa sabule bras dinta hakan ya sa ta kankame tana girgiza kai tana hadiyar wani wahalalan yawu hankalinta sam ba a jikinta ba ta ce" na roke ka, ka yi min rai bana so" Idan ya tankata to lalle dakin ya tankata, a haka ya idansa zare mata ita itama ya rike a hannayen nasa Idannuwansa dake da nauyi ya ringa nuna mata bed da su Hakan ya sa ta matso daf da shi sosai ta saka hannayenta ta riko hannunsa ta kai dubanta saman bed din ta maido saman fuskarsa, kanta ta langwabe ta ce" eyah yayanmu, dan Allah bana son hawa saman gadon cen ka rufa min asiri *yaya SHAHEED* na yi tafiata wajen Ammi kaina ciwo yake, hakama hannuna ka ga yanda ya tsage kuwa? Idan na ce zan yi komai zai yi ta zubar da jinni ne" Dan bakinta da take maganar kawai ya kurawa ido, shi bama fahimtar yarenta yake ba, a irin yanda yake jin kansa ne baya son yin wani kwakwaran abin da zai kara birkita masa lisafi, so yake ya kadaice ya huce, so yake kafin ya dauki kowani irin mataki ya huce sannan, baya son daukan mataki ransa bace ya zo ya yi dana sani, a hankali ya kai hannunsa wajen kugunta mai dauke da jigidar nan ya damki wajen da dan karfi hakan ya sa suka shaida sunna nan ta hanyar dan yi kara kadan sannan ya shiga tafia da ita a hankali wajen bed din Asalamu alaikum gidan Mage😆, Walahi ina ganninku, ina kuma biye da comment dinku, ku sani ina ji da ku ina kuma bin ku da adu'a, Alhamdulilah gashi na yau, fatan zaku karo min comment din ku zafafa, Kufa yi hakuri, kun san harkallar funiyar sai a slow walahi i'm vry busy😌, zan fa yi shara yau aradu masu mana labe a gidan nan ehe☹️ [31/03 à 21:57] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 54 Tirjewa ta shiga yi, lokaci daya ta fashe masa da kukan da ya saka shi ja ya tsaya kansa kuwa ya sara masa Da kyar ya kuma iya daga idannuwansa ya sauke saman fuskarta, irin yanda ta ririke tawul din nata da karfin gaske tana girgiza masa kai tana mamatse kafafuwa ya bi da kallo, a hankali ya furta" MENENE JEEBA?" Najeeba ta turo bakinta ta shiga dan buga kafarta aman bata yi gigin sakin tawul din ba, a raunane ta ce" ni bana son zuwa cen din ne " SHAHEED ya ringa bin irin yannayin bacin da ta yi magana, kamar wani mai son karantar bakon abin da bai taba gani ba haka ya zama sai bin fuskarta da yannatin jikinta kawai yake da kallo Kuma fara janta ya yi, da wani irin sauri ta si kubcewa ta gudu gannin rikon na yanzu ya dan sasaura mata shi Bata san daga ina ba, bata san a lokacin da ya damki dantsen hannunta ba ya juyota juyi daya ya kaita jikin bango ya hadeta Irin buguwar da ta yi da dan karfi ya sakata rinrintse ido tare da jiran jin saukar gigitacen marin da ta tabata sai ta saki dan fitsarin dake mararta A hankali ta ringa jin iska kadan na dan dukan fuskarta, bata iya buda idannuwan nata ba sai rawa rawa da suke na tana son budewa tsoron hakan ya hanna mata budewar Yar yatsarsa mai bima babar yatsa ya saka a kwonce, tun daga tsiron gashin gaban goshinta ya ringa shafawa a hankali har ya sauko da yatsar tasa wanen da ta daure tawul irin daurin da ake yiwa magani tam a faidai kirjunta wato ta yi taho na taho ta hade su a nan Yar yatsar tasa ya dora kan kukin ya ringa dan zagayawa Baki daya ta kuma rinrintse idannuwan nata tana jiran jin tashin hankalin nan dake shirin faruwa da ita A sanyaye cikin muryar da bata sanshi da ita ba ta ji ya ce" ke din yar kokowa ce?" Da mamakinta buda idannuwanta jin kamar da sanyi ya yi mata magana, da sauri ta cire dubanta a cikin idannuwansa sakamakin irin yanda idannuwansa suke da ja sosai, kuma yake shanye su yanai mata kallon nan na tsana gashi kuma yana magana a hankali, me kennan? Oh irin ya yi mata sanya sanya ya kashe banza ko? Habarta ya kamo a hankali ya dago dubanta sunna kallon junna, ya ce" bana son ina magana ba amsa JEEBA" Najeeba ta hadiyi wani yawu a hankali mukutt, a ranta kuwa fadi take ka ji karuwanci ni NJAEEBA, a fili ta ce" aa,aa walahi ba yar kokowa bace ni " Shaheed ya ce" karya ne Najeeba, ke ba yar kokowa ba aman kulun kike kokowa a waje? Yaushe ne shin zan huta da faduwar gaban hakan?" A yanzu kam ta rasa da wace kalma zata bashi amsa, amsar kanta ce ta rasa me zata ce masa, sai kawai ta shiga jin jikinta na son yi mata rawar dari, kai ina haba ina, yaya tana jira ya gagaura mata mari ya nemi yi mata fyade na biyu sai ya wani tsaya yanai mata magana salo salo bayan ta san cewar idan ya samu hanyar kasheta tsaf sai dauke kanta ya huta? SHAHEED ya kuma tsurawa fuskarta ido, kukan nan da ta ringa yi ba ko digon hawaye, ya Allah , yana cikin yannayi na damuwa , sone yake kawai ta je ta kwonta ya san da ya barta a kwonce aman kiri kiri tana saka shi yawan maganar da zai hadasa masa ciwon kai da tsatsauran tunani "Ummm? NAJEEBA ki je ki kwonta kin ji?" Ya fada a karo na biyu yana kallonta Da sauri ta saki tawul din ta kamo hannunsa da yake son kuma dorawa a kan fatarta bayan wahala hakan ke bata, sosai take jin wahalar hakan ko dan bata saba haka ba?, kuma wai SULTAN SHAHEED? tap, kai ta kuma girgiza masa a sanyaye ta ce" ka yi min rai na koma bangaren Ammi, shikenan sai kuma watarana ka ji SHAHEED? " da wani madaukakin mamakin ya kuma kallon bakinta mai kama sunnansa kai tsaye, zai iya rantsewa ko yana yaro yarinyar nan bata gama idasa iya magana bama aman dan raini kai tsaye ita ke kiransa da sunna shaheed duda ba daidai ta iya sunnan ba aman kasancewar Marigayi mai martaba yakan kirayeshi ne da sunnansa kai tsaye, gashi ita din tun tana yar kankannuwarta AMMI keda nacin daukota sai ta koyi sunnan take fadi abinta, aman duda haka a gaskiya a yanzu ta bashi mamaki da take iya kiran sunnan kai tsaye hankali kwonce abinta Dan girgiza kansa ya yi , muryarsa dai stil a sanyaye ya ce" ba zan iya ba, bama zan iya mayar da ke cen ba, kin ga ba yauba ita ke baki damar taka abinda bai dace ba, ba zan iya hada rigimar nan da wace ke kaina ba!" "Wawawawani irin ba zan koma cen ba? Wayo na shiga uku ina zan zauna toh? In dai fada ne ba zan kuma ba ni dai ka barni na yi tafiata" ta karashe tana turo bakinta gaba, baki daya ita dai so take kawai ya barta ta yi tafiyarta hakanan Boyayiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya dan ja da baya yana kallonta, da idannuwansa ya nuna mata tana iya tafia Ai kuwa sai da ta saki murmushi, irin ta ji dadin nan sannan ta rabo jikinta da jikin garun tana dan kallonsa ta raba shi ta fara tafia Sai da ta kusan fita ta ji an fi sama da ita a dawo da ita ciki Baki daya ta aniya son kwace kanta da yannayi na kokowa da tsoro aman an hanna mata wannan dama har sai da aka danganata da saman bed din nan, Sansanyan kamshin da abin rufar ke yi ya cika hancinta, laushin gadon kuwa ya sakata dan nitsewa kafin ta nemi tashi da dan sauri Bai bata damar nan ba ya kuma mayar da ita ya kwontar yana kallonta, irin yanda ta ringa kokowar da shiSHAHEED sai abin ya fara bashi nishadi, da gangan ya ringa biye mata har sai ya barta ta tashi sai ya mayar da ita baki daya, ita kuwa hakan ke kara tsoratata sai ta kuma fashewa da kuka du ta yaye tawul din garin kokowar kwatar kai Zaunar da ita ya yi dangalgal saman bed din ya zamanta sunna kallon junna sai sauke ajiyar zuciya take a tsorace tana masa wani kallon da bai san me yasa yake saka masa bugun zuciya ba A hankali ya kure dubanta, har ya dangana da lebunnanta Idannuwansa ya lumshe ya damki lebunnanta, iya su ya ringa yi masu wani irin horo mai zafin gaske, mai zuwa da zafi zafi wanda ya sakata baki daya zaro ido jikinta ya kara daukan bari, hannayenta na ture shi tun karfi aman abin ya gagara domin sai ta kula kamar idan ta tura shin kara mane mata yake a jikinta Tun tana kukan zuci har hawaye ya kama zarya a kan fuskarta, wata irin mugunta ce yake mata iya lebunnan bakinta da mamanta aman hakan ya sakata soma fita hayacinta domin kuwa irin yanda kan mamanta ke mata zogi kamar zata mace take ji hakan ya sa daga ya dan cika mata lebe sai ta aniya hada shi da Allah da kuka da komai kan ba zata kuma ba, sai dai baya bari ta idasa magiyar zai kuma damkarta Sam bai nemi hanyar da yake yiwa tanadi ba, hasalima du idan tawul din ya yaye har wajen yakan janyoshi ya rufe ne, aman hannayensa da hakoransa sun yi mata damkar da shi da kansa sai da ta dawo bashi tausayi Baban tashin hankalinta tun a haka ta gama ganewa bambancin tsagerancinsu ina ga ya kai inda take? Sai kawai ta bi ta idasa sarewa, kwarai bai mata ihu ko duka kp hargowar da zai tada mata jama'a ba, aman a iya hakan ta ringa dana sannin zuwa wannan waje Kansa ya dora a dokin wuyanta yana sauraron yanda take ta shasheka da ajiyar zuciya Idannuwansa ya rintse da karfin tsiya, domin kuwa a yanda ransa ke bace du irin yanda ya tayarwa da kansa hankali ba zai yarda ya zo mata a haka ba, dan kuwa ya tabata zai yi anfani da damar ne dan huce haushinta da yake ji, hakan ya sa ya mike a hankali ya saketa ya nufi bayi yana ta hada hanya tamkar zai kife a kasa Baki daya ta kasa tashin da take son yi, dan kuwa gaba daya hannayenta da jikinta ne sukai mata nauyi ta rasa dalili, sai hawayen da take idannuwanta lumshe dan ko tawul din ta ja ta rufe kirjinta ta kasa ga ajiyar zuciya wata na korar wata Tsayuwa ya yi kasan shower ya sada kansa Lebensa ya yi masa jajajir sai dan rawa yake masa sanadiyar irin halin da yake ciki Hannunsa na dama ne ya jimke ya kai duka jikin garun nan yana kara taune leben nasa dan so yake ruwan nan mai sanyi dake zubar masa ya bashi yar nutsuwa ko yayane " *ALLAH NE YA TSARE MIN ITA* " ya furta a hankali muryarsa a cinkushe, " *ya Allah ka kara tsare min ita* " ya idasa fada a saman labansa Baki daya mararsa ce ta kama ciwo, cikinsa ya aniya kulewa waje guda ya kasa kwakwaran motsi Bai saba da irin wannan matsalar har haka ba, idan ba dan ita ba ba zai taba sannin wannan maysalar ba, dan jarabar idannuwansa du ranar da ya ganta sai ya kurewa kallonta, haka zai zo ya yi ta fama Ajiyar zuciyar da ya ringa saukewa ce ta fahimtar da shi idan fa ya yi da wasa yana iya kwonciya rashin lafia Rausar zuciyarsa ya yi ta yi kan tinasar da shi abinda yake yawan fadawa kansa dan ya rarashi kansa koda a xen baya Sai da ya tabatar da ya rage bacin ran sannan ya juya a hankali ya fito mata hakansa Bata ga fitowarsa ba, bata san da ya nufota ba, sai ji da ta yi an kuma fara taba mata jikinta Sai dai a wannan karron a sanyaye ake taba mata jikin, ga sanyin ruwan dake haduwa da fatar jikinta, ga ji da take kamar za'a cinyeta ya sakata kasa buda idannuwanta sai barkewa da ta yi da wani sangartacen kuka Hancinsa yake ta kai kawo a wajen jigidar nan mai sansanyan kanshin sirri Kasancewar a yanzu yana mai binta a hankali, yana kokarin gannin ya baiwa komai hakinsa duda kasantuwarsa a yannayi na bacin rai da mugun bukatuwa da ita aman sai ya ringa bin du wajen da ya yiwa muguwar damka a hankali yana mai hura wajen da lalabashi Tsoronta, da zafin da guraren ke mata ya hanna mata karbar sakonsa yanda ya dace, duda haka nan da nan lamari ya kwace a jikinta domin kuwa a shirye yake da karbar sakon ko yayane Lokaci daya komai ya kwonkwonce masa, lema lemar da ya ringa ji ya saka shi kai dubansa, a fili ya furta" *Wayo ALLAHNA*, a hankali yannayinsa na son ya bita a sanyaye ya yi masa kaura wanda shi kansa bai san hakan ya bar kwakwaluwarsa da aikinsa ba, a yauma ya zo mata, zuwan da ya kusan sumar da su baki daya, ita kam ta gama sarewa duniya da abinda ke cikinta, ta yi dana sannin karbar abubuwan da auty Zahrau ke dudura mata , sannan ta yi dana sannin guje masa na kwanaki hudu domin kuwa a kalaman dake dan kwace masa idan ya juya kai ya kuma juyar da kansa zai ce" Me ya sa kikai nesa da ni har tsayin lokaci?" Wasa wasa cikinta ba komai, ta karbi kari mai sanya juwa idan ba'a karya ba, ta amshi bulaliyar da ta gwamace duka da ita, ta amshi wani irin horon da ta gama sakawa zuciyarta ba zata anfanu ba daga nan, ta kasa mugayen kalaman da ta yi a wancen ranar domin maganar da ta fi yi shine neman ya barta kar ya tsagata gida biyu, ya barta kar ta mutu, ya sasauta mata ba zata iya ba Har sai da ya kasance ya yi niya dan kansa sannan ya saki kansa ya samu nutsuwa Wata irin murya cen kasa mai nuni da mai dauke da ita na tsikin matsanancin hali Najeeba ta ja numfashinta da karshi sannan a wahalce ta ce" da ka halakani gwara ka sawake min SHAHEED, aikinka na nuni da burinka ka kasarani bayan nima BA SON KA NAKE BA" Shi kam bai iya bata amsa ba, hasalima gefe ya koma bayan ya yi irin kwonciyar da aka koyar dan gudun komawar lamari jikinsu, sai ya samu kansa da tsurawa fuskarta ido, kallonta kawai yake yana jin tsigar jikinsa na kuma tashi, baki daya lamura na son kara bijiro masa............... Farin ciki ne madaukaki ya dira a zuciyar ABIH a lokacin da ya ji wannan sako na UMMU, gashi dai a zaune so yake ya zabura ya je ya ganta ido da ido ta shaida masa da bakinsa aman ya kasa domin yaransa sun zagaye shi sai neman afuwar fadan da suka yi suke Da wani murmushi ya shafi gefen kumatunsu ya ce" kun ga, ku je dakunnanku kun ji? Yanda ta yi da mu maman naku nima idan harda ni a hukuncin ba laifi zan karba ne" AMMI dai daria kawai take sosai, dan Walahi irin yanda yayan nata ya yin ne ya bata daria, sai kawai take hango da cen, Kiran da Zahrau ta yi a wayar AMMI ta shaida mata ta isa ne tana falonta yanzu haka ya sakata sakin murmushi tana fatan alkhairi sannan ta shaida mata kayanta zasu zo Agadez gobe in sha Allah za'a kai a auna mata su a tura su Shi dai Abih kara buda idannuwansa kawai yake dan gannin UMMU wace da gangan ta yi zamanta a daki ta rufe tun da ta ji ya cewa AMMI gashi nan zuwa ...................... "Haba Nadia, yaya kike son ki saka ni asarar kudina, ki saka ni asarar likacina da tunanina ta hanyar mayar da kanki wawa kamar ba ke ba? Na ji na sanni mijin Najeeba kika aura wanda yake mijinki kema a yanzun sai me? Ina ce aure kika ce, kuma auren nan ba wai kin san za'a yi shi bane kika yarda, kuma ba tashi kika yi kika je kika auri mijin kawarki ba dan cin amana aman shine sai ki ringa irin abinnan kamar wata sokuwa? Me kike so yanzun? Da kike baya baya bakya anfani da koyarwar da akai maki dan mijinki ya san da ke so kike ki zama ta karshe a cikin matayensa? Kin san dai ba saki idan har ba kama ki aka yi da laifin zuna ko kisan kai ba, a kan me zaki ringa irin wannan abin?" Mahaifiyar Nadia ta karasa mata magana ta waya tana yi kamar ta shiga cikin wayar ta ganta gata ga ita Nadia dake cikin hali na tsoro, tun dazu da safe ta budi muryarta dake rawa rawa ta ce" Mama, ba wannan ne damuwata ba, ina tsoron a je na kawo kaina gidan halaka domin kuwa a dazu da safe na ga abinda bai dace a ce na gani ba, baban tashin hankalina zan je na samu sarki da maganar ne ko zan yi shiru ne? Wanda na gannin ya ganni ne? Idan ya ganni me zai min? Mama na shiga uku na lalace ana neman rayuwar sarkina ido rufe na je bangarensa na yi na yi wajen ya ki buduwa ban san dalili ba, ina tsoron wani abin ya same shi ko ni ya sameni, una tsoron ace wanda na kama shima ya kama ni? Magangannun da na ji dole sarkina ya sani ya kuma ji daga inda na ji su Hankalin mahaifiyarta ne ta ji ya tashi, dan kuwa a muryar yar tata kana iya gannin tsantsan tsoro da tashin hankali da kaka naka yi, da sauri ta mike tsaye tana kallon agogo ta ce" Kuka ce na baku shi a haka ko? To gashi☹️ ni dai oh sunna sai ya kare a bakin maman abdul, [31/03 à 21:58] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 55 Baki daya a rikice mahaifiyarta ta ce" kina ji na? Kar ki kashe wayarki, ki barta a haka Nadia gani nan zuwa" Nadia ta ce a sanyaye" mama, idan kin zo zaki samu shigowa ne? Ina tsoron ki rasa hanyar bi idan har magautan Sultan sun san da na san abinda ke faruwa, mama ina jin tsoro sosai" Ai kuwa hakan ya sa ta kara rikita mamanta, da gudu gudu ta fito da kys din motarta da wata wayar tana kiran number mijinta haka kuma dayar wayar bata kashe lasge ba, sannan sai maimaitawa Nadia take cewar kar ta kashe kar ta kashe Kira kan kira a irin wannan yamaci aman ta kasa samun mijinta, hakan ya sa ta nufi ma'aikatarsa duda bata da tabacin samunsa Sha'ani da waya, a lokacin da ta kusa karasawa kampanin wayar suka shiga shaida mata kudinta sun kare bai fi yan second a yanke layin ba, hakan kuma ya yi daidai da lokacin da Nadia ta zabura hankali tashe ta shiga furta" innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, muryarta sama sama, wanda hakan ya saka mahaifiyarta maimakun ta take birki kusan office din mijinta sai ta take accelerator motar ta je ta daki abin dake kafe da sunnan mijinta goshinta ya daki sitoyarin motar ta koma ta kuma dakar kujerar Goshinta ne ya fashe a lokacin ne kuma mutane du suka taso a guje ana ta fadin Subahannalah, ciki kuwa harda mijinta baban juju datijon da ya rike datijantakarsa Gabansa ne ya fadi gannin motar matarsa, uwa uba kafarta da ta fitar waje tana son karasa fitowa hankali tashe ya nufeta yana matsa mutanen dake son taimaka mata ta fito A rude yake tambayarta lafia, bata ji ciwo ba, me je faruwa ta fito haka daga ita sai dan kwali da doguwar rigar shan iska? A rikicen itama ta kama hannunsa, ido rufe fadi take" Nadia, Nadia, Nadia ce sun kashe min ita, Nadiata ta mutu, shikenan sun kashe min ita, dama tun da aka ce min auren gidan nan ba na Nadiata bane na nuna ta hakura, aman tsabar son sarauta da sarkin nan ya saka ta nuna ta ji ta gani, shikenan sun kashe ta" Gannin kamar bata cikin hayacinta ya saka mijinta kama damatsunnan hannayenta da hannayensa bibiyu ya shiga jijigata ya ce" ke Hawau ki nutsu, me kike son fada min haka? Waye ya kashe Nadiar?" Wani irin kuka take, ta shiga labarta masa abinda Nadia ta fada sannan tana ta nuna hanyar da ya dace a bi dan zuwa gidan Sarki, fadi take" sun kashe min ita " Shi kansa hankalinsa ne ya ji ya tashi, nan da nan ya fara jin zufa na neman karyo masa, rabonsa da barin jiki irin wannan har ya manta, da sauri ya koma ciki, iya wayarsa da kys din motarsa ya dauko ya bar yarensa a ciki ya fito da wani irin sauri Budewa sukai suka shiga, ya harba motar bakin titi yana yi yana gwada kiran Nadiar, sai dai tana shiga aman ba'a daga ba Gani yake kamar an ninka nisan wajen , du irin yanda yake sheka gudu kuwa sai yake gannin ya kasa karasawa, sau uku yana gwada kiran Shahees sai ya yi gagawar kashewa domin dai Shaheed ba mutumen zuben da zai iya dirowa kai tsaye haka bane, hakan ya saka shi ajiye wayar a lokacin da suka karaso gate na farko mai dauke da manyan dogarai Ai kuwa duda sun kasance sirikan gidan sai aka tsatsare su da tambayoyin da suka kara rikita mahaifiyarta So take ta furta an kashe mata y'a, sai dai mijin ya tatareta ya hanna mata magana, karshema sai ya nuna sarki ne ya basu damar zuwa Gannin irin kukan da Maman Nadia take ya saka suka nemi layin sarki wanda suke samunsa a kowani lokaci dan su ji daga bakinsa A lokacin ya gama gasa Najeeba ya dawo da ita saman bed din ya fito ya ja ya tsaya dan ya afka tunanin ta yanda za'ai ya sama mata tea mai zafi wayarsa ta shiga kuka wace take a kafe a falonsa wace dogaran kofa baba ke kiransa da ita ne Sai da ta katse aka kuma kira sannan ya karasa ya daga muryarsa a sanyaye ya amsa salamar da sarkin kofa ya yi masa a risine sannan ya shiga kora masa bayani cike da ladabi da biyaya da sada kai Jim ya yi cike da mamakin jin mahaifan matarsa ne suka zo, mahaifiyarta na kuka , mahaifinta ke tukawa sannan sun yi zasu hadu da shi Dan gyaran murya ya yi da fadin a basu damar tsalake get din Ajiye wayarsa ya yi ya koma dakin Da sauri ta mayar da idannuwanta ta rintse da karfi sannan ta yi lamo tamkar wace ta fara baci A hankali ya cenza tufafin jikinsa zuwa manyan kaya kamar yanda ya saka ko gajiya baya yi, sannan ya yi simple rawani ba mai girman nan ba sai dai ya rufe har hancinsa kamar yanda ya saba sai idannuwansa kawai ake gani Juyowa ya yi ya sauke dubansa a kanta, gannin fatar idannuwanta na motsi ya saka shi dan sakin murmushi a boye sannan ya shiga takawa har gaban gadon ya ja ya tsaya Jin shiru shiru ba motsin kimtsawa sai ta buda idannuwanta Ai kuwa da wani irin sauri ta mayar ta rufe har tana tura bakinta A hankali ya ce" shine zaki ringa kallona ina saka kaya ko baki koshi na?" Da sauri ta kuma buda idannuwanta, sai dai wannan karron ba kallonsa ta yi ba, gefe guda take kallo a tsorace take girgiza masa kanta, muryarta na rawa rawa ta ce" wajen AMMI nake son zuwa, ka ga yama ta yi gashi bani da kaya a nan " Bakinsa ya tabe ya dan daga kafadunsa sannan ya juya a hankali ya kama hanyar ficewa Da sauri ta so yinkurawa ta tashi, sai dai bata idasa hakan ba ta koma da wani irin saurin tana sakin yar kara tana rufe idannuwanta, du irin yanda ya gasata tamkar masa ya juyata ciki da bai bai hannata jin kamar zata mutu dan azaba ba, bata taba sannin wannan mutumen *MAGE* ne ba sai yau, da dariya da shafa da laluma ya yi mata damkar da zai iya halakata Ba zata iya yarda ya tafiarsa ya barta a wajen nan sannan ya dawo ya sameta ya idasa halakata a daren nan kwaya daya da ya yi mata saura na amarci, a gaskiya ta daina mamakin irin ihun da Nadia ta ringa yi, sannan ta ji takaicin Zinaria dake kishi da wannan abin, wahalar? Tashin hankalin? Azabar? Kai gaskiya bariki hauka ne, a haka yan bariki ke rayuwa da maza kala daban daban? Wani daidai su wani ya girme masu, a haka su kamu da cutar kaikayo da sauransu (Allah ka shirye mi, ka rufa mana asiri, ka shiryi zuri'armu , ba dan halayanmu ba, ba dan wata ibadarmu ba, Alfarmar fiyayen halita da alkur'ani, ka raba mu da zina koda ta ido ce, ko wace iri ce), ita bata ga abinda zata yiwa kishi ba in dai ba dan dan kyan nasa da dan kudin nasa da dan farin nasa ba, to meye abin kishin? An ce mata shi sukewa kishi, ashe kuwa mata basu san ciwon kansu ba? Ita kam gaskiya ya fi karfinta, gaskiya sam ya fi karfinta... A hankali ta idasa saukowa ta shiga bin bango bayan ta idasa zuge zif dinta ta rufe bayanta da kyau Zama ta yi waje guda ta ringa sauke ajiyar hutawa, zamanma ba wai rasras ne ta yi shi ba, baki dqyanta dan dosanuwa ne ta yi a babar kujerar dake da wani irin tsari ta dafa hannayenta suka tatareta tana kara rintse ido Sama sama ta ringa jin magana, ta yi dan tsai dan jin maganar ta dan lafa sai kuma ta ganshi ya shigo da wani irin sauri Da kallo ta bi shi a dan tsorace gannin abinda ya dauka a hannunsa ya kuma ficewa tamkar bai kula da ita a zaune ba Irin yanda yannayinsa ya nuna tashin hankali sai du hankalinta ya tashi A hankali ta kuma cicibawa da kyar ta mike tana jin wata irin juwa na zuwar mata na yinwar da ya gama cinye du wani dan abincin dake cikinta ta nufi fallon Bayansa take hange, yana tsaye hannunsa daya a goye a bayan nasa , sai mutane biyu da take jin kukan daya, dayan kuwa kansa sade yana ta murza hannayenta ya kasa wani motsi kirki A hankali take kara matsowa, sai dai bata idasa matsowar ba ta fara fahimtar matar dake zaune, hakan ya sa gabanta yankewa ya fadi Muryar jakadiyar sarki ke neman iso, Mai tsaya wata wata ba ya bada damar shigowa Mutanen da suka shigo dauke da mutun ne ya saka Najeeba ja ta tsaya gabanta na dokawa A lokacin da suka shinfideta a wajen da ya nuna sunna ta kakareta da alkyabarta ya saka Najeeba jin kafafuwanta sun fara rawa sosai da sosai Sai da suka fita sannan ya karasa wajen da mamanta ke son isawa aman mijinta ya riketa, ba dan komai ba kuwa sai dan kasancewarsu a gaban mai Damagaram, koma menene basu da damar idasawa wajen nan a irin wannan lokacin har sai an basu dama, duda kuwa y'qrsu ce ta cikinsu, shi din ai sarkinsu ne Alkyabar tata ya yaye, lokaci daya idannuwansa suka sauka a wajen kafafuwanta da suka yi wani irin sundum Da sauri ya shiga bin kafafuwan da kallo har Allah ya saukar da dubansa a wajen da ya ga wasu yan kannanun kofofi biyu da suke shige da yan tiloli kananu sosai A hankali ya kara kurewa wajen da kallo nan ya fahimci san hakori ne na macijin da ya yi sara, sara kuwa irin ta kokowa A hankali ya kara dukawa, bai taba daidai wajen ba sai kara kusanta dubansa da ya yi sosai da sosai, sam ba alamun rai a tatare da ita aman bai yi gagawar sarewa ba har sai da idannuwansa suka sauka a irin yannayin kofar Da wani irin sauri ya mike ya yi wajen jakar nan da ya dauko daga daki ya ajiyeta ya budeta Adu'a yake a kasan zuciyarsa Allah ya sa saran bai kai tsayin minti arba'in da biyar ba, sara be na maciji mai kala biyu, iein macijin nan mai kalar ash color da baki, irinsa ke dauke da hakora daya ya fi daya girma, hakoran daya ya dan fi daya tsayi , mai tsayin shike da tsini, wanda bashi da tsayin kuwa shine mai kakauran waje Hakan ke sakawa ana iya gane cizonsu idan aka ga yar karamar kofofin daya ta dan fi daya girma, sannan idan ya yi sara yakan sumar da mutun ne, summa mai tsananin dake nuna tamkar mutun ya mutu ne, sai dai a hankali mutun ke kara nisa, idan har aka dauki lokacin nan ba'a yi gagawar tsayar da dafin ba, ko aka sadaka da asibiti suka yi gagawar yi maka nasu dabarun ba lalle kana iya rasa ranka Wata aska ce ya ciro mai kaifin balaki sannan yar siririya ce Bai tsaya wata wata ba ya kamo kafar nan wajen gwabrinta ya daidaita askar nan tun daga gaban saran ya shiga yin baya baya da shi yana kara sauka Wani irin bakin jiki ne ke fitowa mai tsarara, har ya kai wajen da normal color din jinni ta fito sannan cikin wani saurin ya kuma huda dayar kofar har ya kai wajen da ya tsaya shima inda kamar yanda suke da bambanci haka yannayin yaduwarsu take a jikin dan adam Buda wata kwalba ya yi mai dauke da alcohol na asibiti ya dauki auduga da sauri sauri ya zuba alcohol din nan wanda hakan ya saka baki daya wajen ya shiga wani bori tamkar ana kone wajen kafin ya lafa sai wajen ya yi fari fat har ana gannin dan nama naman wajen hakan na nufin wajen ya wanku tas tas tas kennan Bai yi kasa da gwuiwa ba ya saka audugar nan ya ringa wanke wajen da wanki na kirki wanda ke darzar wajen sosai A hankali ya dago ya sauke dubansa a kan mahaifiyarsa, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" inaga kukan nan bana son sa" Da sauri ta kuma duban fuskarsa, aman sai ta mayar da kanta kasa sakamakon tsagwaron bacin rai da ta hanga a tatare da shi Shigowar iyayensa ya saka shi lumshe ido, dama ya san a rina domin ta wajenta suka bi kafin a karaso da su nan, harda Abih da UMMU Baki dayansu son su san abinda ke faruwa suke, shi dai shirun da ya yi kallon agogo yake yana kiyasta iya adadin lokacin da ya ci ace jikinta ya fara daukan dumi ya rage sanyin nan kau kamar gawa NAJEEBA dake tsaye sai a lokacin idannuwanta suka gane mata lale da gasken NADIA ce Baki daya sai ta ji ta kasa iya rike kanta, a hankali ta silale daga inda take a tsayen nan ta zauna saman cafet din kamar yanda baki daya mutanen falon suke ciki kuwa harda SUKTAN da ya zauna a kasan shima dan ya dubata da kyau Abih ne da yannayi na tashin hankali ya ce" SHAHEED mu kaita asibiti mana? Menene ya sameta? Meye wannan akai kamar an yanka ne? Me ke faruwa ne?" Sai da SHAHEED ya dauki kamar minti uku yana mai ci gaba da dan taba yannayin jikinta da yake jin kamar yana cenzawa kamar kuma baya cenzawa sannan ya kalli ABIH, A sanyaye ya ce" wannan din shi ne treatment din da zasu yi mata ko kun je, ku mu saurara kadan, idan har da sauran numfashinta zata farka" Ai Najeeba na jin haka sai ta fashe da wani kuka kasa kasa tana mai dora hannayenta saman kanta hankalinta tashe da jin kalaman SULTAN, me? Aida? Me ya same ta? Wani irin treatment ne wannan ya yi mata? Bakin jinnin nan na meye? Me ke faruwa ne da gidan nan da shi kansa SULTAN? Ammi da ta fi kusa da ita ne ta kamo hannunta irin ta karaso jikinta A hankali ta jarasa ta zauna a karkace ta dora kanta a gefen jikin Ammi, tana mai fitar da wani marayan kukan da ya saka cike da tausayawa, sannan jin irin yanda jikinta itana ya dauki zafi ta ringa dan taping din bayanta dan ta samu ta yi shiru, domin kuwa a irin yanda ya hade ran nan su kansu sun yi shirun ne sunna masu adu'ar Allah ya sa ta tashin Cen kamar minti goma sha uku sai kofofin fatar jikinta suka fara fitar da alamu da mutun mai rai ta hanyar fara fitar da zufa A hankali jikin nata ya ringa rage yannayi na sandadan din da fatar matace ke dauka ya fara dan rage sanyin da ya dauka sai dai sam bai dauki dumi irin na fatar yawancin mutane masu lafia ba hakan ya saka shi kai dubansa wajen mahaifiyarta, cikin nutsuwa ya furta" idan tana cikin halin rashin lafia takan yi nawa temperature din fatarta?" Mamanta cikin shakakiyar muryar wace ta ci kuka ta koshi ta ce" bai taba haura 38 ba, domin ita din sam jikinta baya daukan zafi koda kuwa bata da lafia" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya furta" da ranta, zata farfado in sha Allah dafin bai ratsata sosai ba" Dubansa ya kuma kaiwa a karro na shida kan NAJEEBA, ajiyar zuciya ya sauke a karro na ba adadi kafin ya mike yana dubansu kasa kasa ya ce" to ki daina kukan mana?" Su duka shi suka kalla kafin kuma su kalli inda yake kallon, Njaeeba ce ke ta shashekar kukanta, baki daya abin ne ya zo mata a lokacin da bata tsamata ba, tarin tsoro ya sakata neman sikewa da tuna Bintu Bai kuma kara wani lokacin ba ya juya ya fice a fallon Wannan karron ta babar kofarsa ya fita da kansa Tsayuwa ya yi yana bin gidan da kallo Muryarsa dake ya kai dubansa kan sarkin zabga, liman, amintacensa, sarkin kofa, da du wani dogarin da ya kwana ya waye a fadar dake tare bisa umarninsa, inda ya saka aka zubo masa polisai suka hau wajen aiyukan ma'aikatansa kafin ya gama abinda zai yi Ya yi kai kawo kamar sau hudu wajen nan yana kallon du wani wanda ke wajen kansa a kasa Sai da ya ja ya tsaya ya furta" kowa ya dago kansa ya kalle ni " Baki dayansu mamaki, tsoro, da al'ajabin a dago kai a dube shi ya dirar masu, wani irin su dago su dube shi? " Gannin du sun kasa ya yi wani murmushin yake a karro na biyu ya furta" umarni nake baku " Ai kuwa baki dayansu sai sauka ringa dago kawunnan nasu, sai dai da wani irin sauri suke sada dubans7 sakamakon arba da ainahin fuskarsa a bayane, rawanin ya mayar da shi iya kansa, baki daya kamanin mazan da suke hasashe ya bayana a gabansu, irin yanda suke hasashen daurewa irin na sarkinsu sai abin ya dame tunaninsu ya shanye hakan ya saka da yawansu jikinsu kwasar rawa sai daidaikum da suka kasance jaruman jarumai ne suka sada kawunnansu hankalinsu sam ba a jikinsu ba, baki dayansu sunna cikin fargaba da wannan lamarin da bai taba faruwa ba Affuwa dai Takawa, Allah ya huci zuciyar MAI DAMAGARAM, ALLAH ya sasauta fushin JIMINA, Allah ya huci zuciyar SARKINMU.......Amintace ya fada yana kara sada kansa cike da biyaya SHAHEED ya budi bakinsa a sanyaye ya furta " Menen laifin su da ake son daga na kawo su a ringa binsu ana kashewa tamkar kiyashi? Shin daukar fansa ne ko kwacen kujera ne? Menene ribar biyowa ta bayan fage bayan ni ake son kuntatawa gani a bagas ba zan iya yin komai ba ana iya koda gile kaina ne domin nima mutun ne kamar kowa, sai dai maimakun mai aikatawar ya biyo kai tsaye sai yake lungu lungu da ni yana cutar da y'ayan mutanen da basu ji ba basu gani ba" Dan sasautawa ya yi gannin da yawansu basu san inda zancen ya nufa ba, hakan ya sa sukai sakayau da su, a cikinsu kuwa akoy wa'inda suka san inda zancen ya nufa suma sai kara yi suke irin zancen basu gane inda ya nufa ba A hankali ya dora da fadin " baka jin tsoron Allah ne? Baka tuna akoy ranar tsayuwa ne? Wa'innan da kake kashewa dan son zuciyarka baka tsoron irin huja da hisabin da Allah zai wanzar a kanka a gobe kiyama ne, ko kai zuciyarka ta kekyashe ka zabi duniyar ne wace baka san iya adadin wa'adin da ya rage maka ka cika ba? Shin idanma Allah ya ara maka nisan kwanan ka tabata ita duniyar da kake tunanin yi domintan zaka samu abinda kake son samun ne? Idan *MACE CE?*, idan *LAFIA* ce, ko tunanin mulkin da Allah ya nada bawansa bai cencenta ba dan kannanun shekarunsa ne? Ko wani lamari naka na kanka da ka barawa zuciyarka?, shin ana anfani da damar da aka sani a kaina cewa ko jama'ar garina da inada hali da na hanna masu saka laya a cikin kasata ne ake son kasara min tunanina ta hanyar kashe min iyalaina?" *ALLAH ya huci zuciyar maza* aka ringa maimaitawa, kowane na tsarge da dan uwansa, sannan magangannun Sultan karara sun fito fili SHAHEED ya sauke ajiyar zuciya yana mai furzar da hucin bacin rai yana ayanna irin hukuncin da koma wate ya dace da shi ya ce " Ba zan saka alkur'ani mai girma dan samun mai yi min zafon kasa ba, sai dai ina mai shaida masa mumunan labarin cewa ya mayar da rigarsa ta zuwa makabarta dan birne Gimbiya NADIA bisa abinda ta jiyo, domin kuwa bata mutu ba, da ranta " Du yawanci mutanen wajen ne suka dago kawunnansu a firgice, mutuwa? Da yawansu tsananin mamaki da tsoron furucinsa ne ya saka masu dagowar nan, cikinsu kuwa mugun da ya aikata ne ya dago a firgice shima da jun wannan lamari, bata mutu ba? Tana ina? Da ranta? Me ta ce? Yaya aka yi bata mutu ba?" "Yaya wanda ya aikata aikin nan zai min daukan wawan da ban san abinda nake yi ba? Harma ya yi tunanin a lokacin da na wanki gawar matata da kaina na suturtata aka kaita ba zan lura da saran macijin da ya kasheta ba, ko kuwa ya yi tunanin da yake ni din wawa ne zan iyakance binkicena a kan macizai da irin hatsarinsu bayan na kasance jinni ga ABDUL MALIK ALI BUZU BA?, shin kun manta sanadiyar sararsa da maciji ya yi a filin daga ya saka shi zuba kiwonsu har sai da ya lakanci raba gangar jikinsu da hakoransu kafin ya iya fitar da karinsu, ya san yanda ake magance dafinsu idan bai gama shiga jiki ba, ya iya bin rawarsu har kuke tunanin zai iyakance sanninsa a kaina ni SULTAN SHAHEED?" ya karasshe da dan daga muryarsa sannan a kausashe ya kaiwa garun da yake tsaye suka mai karfin gaske sannan ya maido dunkulelen hannun nasa ya daki gefen kirjinsa ya ce" lungu lungu camera ce biyayiya a gidan wada ba kowa ya san da ita ba, sakwani tsakiyar dare, kulawa da kuncewa baki daya a tafin hannayena suke, droon kadai kuka san da shi a tunaninku shine kawai zai ringa aiki idan safiya ta yi ina zaune na ringa bi da shi yana dauko min rahitanni kamar wani gaula?" Dan murmushin takaici ya kuma yi a hankali ya furta" kunna iya tafia " Ba wanda ya iya koda kwakwaran motsi ne a cikibsu, shi kuwa a tsayen nan da yake idannuwansa kyam a kan mutun biyu da suka yawaita haduwa da junnansu a cikin masarautar idan dare ya raba, wa'inda yake gannin haduwarsu lokaci zuwa lokaci Shi ne ya fara juyawa, lokaci daya suka kwashi kirari hade da neman afuwarsa, basu su yi shiru ba har sai da ya shige baban falonsa Idannuwansa ne suka sauka a kan ZINARIA da ya aika kiranta Bai yi komai ba sai karasawa da ya yi wajen wayar cikin fada ya yi kiran comandan din da aka ajiye yake jan ragamar bada tsaro wa gidan A kausashe ya ce" ko karamin yaro ne kar ku bashi damar fita daga kowace hanya, ku zuba ido ku yi taka tsantsan dimin na zunguri wanda ya aikata, kuma ya san da shi nake daga yanzu zuwa dare komai na iya faruwa ciki kuwa harda barazana fadawa" A dake shima ya amsa kafin ya kuma zagewa ya kara tada jinnin ma'aikatansa ya gingindaya sharudan cewa ko mace ko namiji ko yaro ko tsoho ko a halin rashin lafia ko a halin hauka ko a mace kar a fita fa kowa daga masarautar DAMAGARAM! Ajiye wayar ya yi ya kuma juyowa gare su A hankali ya karasa ya zauna Gannin numfashinta ya dawo, hasalima baci take yi mai nauyin gaske wanda daga shi ne komai zai saketa ta farka ya maido dubansa wajen AMMI da ta aiko masa da tambayar da ya zama wajibi ya amsata Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" EH ba'a rufe wajen, haka ake barinsa ya bushe dan kansa ko ruwa ba zai taba wajen ba. Dan shiru ya yi na dan lokaci kafin ya dora da fadin " Ba'a taba raba gidan sarauta da abubuwan tashin hankali, zagon kasa, munafurci, hade hade, fitintinnu, rigingimu, da dai saransu, ciki kuwa harda kisa, Wanin kan tsinci kansa ne a wajen da bai dace da shi ba, wanin kuwa yakan kawo kansa wajen ne dan a ganninsa ai nashi da wani waje da ya fi nan din, dama dan irin rayuwar aka haife shi. Dubansa ya kai wajen UMMU dake rungume da NADIA, zuwa yanzun sun rage mata nauyin suturar dake jikinta sosai dan ta sha iska, hakama ya kai kan AMMI dake rungume da NAJEEBA wace du ta makalkaleta idannuwanta lumshe tana kwonce a samanta sosai sai ajiyar zuciya kawai take saki, Sannan ya kai kan Zinaria, sai ya ga sam ba wani yannayi na damuwa ko alhinin gannin yar uwarta kwonce sheme sheme a halin rai ko mutuwa, hasalima dan girgiza kai take irin idan mace na cikin neman balakin nan Ya kuma saukewa a kan iyayen Nadiar, mahaifiyarta na kusa da bayanta, tana rike da hannunta cike da yannayi na tashin hankali, mahaifinta kuwa kansa a kasa ya dan dafe kai malunmalun din jikinsa a dan tatare, hularsa ta yi gaban goshinsa kadan. A hankali ya ce" AMMI, kwanaki an kashe Bintu ta hanyar saran maciji, shine a yau ya sari kafar Nadia, Dan sasautawa ya yi ya sada kansa a hankali ya furta" Ina cikin zargin mutun biyu ne, duda na san cewa zato zunubi ne sai dai na fada a wannan zaton ne bisa hujojina, mutanen nan kuwa sune *Amintacena da kuma sarkin Bulala*, kara sada kansa ya yi kafin ya dago ya sauke idannuwansa a kan Zinaria ya ci gaba da fadin" faduwar gaban kar a je da iyalina a ciki ya hanna min gannin amsoshina a fili, sai nake ta zagayewa ido rufe sai na samo hujojin dake hada matata da shi, koda kuwa ya kasance tsoron saurayinta, koda kuwa ya kasance bawa a gareta a yanzun, aman kiri da muzu na kasa samun kakarfan dalilin da zai iya hadata da shi a talatainin dare a wajaje uku, harda mahaifiyarta,, me suke fada? Me suke amsa? Me suke aiwatarwa? Meye tsakaninsu da shi? Shin kishi ne ya rufewa iyalina ido har ta kaita haka ko son zuciya, ko kuwa ramuwar na shiga tsakanin soyaya da soyaya ne? " Ya karashe yana mai kara son dole ta dago idannuwanta da ta shiga wuwurgawa a tsorace dukan alamun rashin gaskiya ya gama bayana a tare da ita , wanda hakan ya sakata inda inda harma ta dauki magana a firgice cewar " Ni dai ba abinda na aikata " Idannuwansa ya rintse sannan ya bude ya kalleta, hakama dukan mutanen wajen,, a takure a birkice , a wahalce ya ce" Shin na kama sunna a furucina ne a nan? " Gannin ta sada kai baki daya jikinta ya kwashi rawa sai kawai ya mike tsaye, ransa bace ya shiga kai kawo Juyowa ya yi murya a kausashe ya ce" 😁 [31/03 à 22:00] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 56 Juyowa ya yi murya a kausashe ya ce" shin kin aikata abinda zai sakani a cikin halin tashin hankali, kunya, matsanancin bacin rai? " Kuma dago dubanta ta yi, baki daya jikinta bari yake ta rasa ina zata kalla, gani take ko'ina na dakin ya zama idannuwa ne, baki daya ta ringa gannin tamkar an tsatsarata a gaban alkali ne, duda kasancewarsa miju a gareta wanda ta yi rayuwar shekara da shekaru da shi aman sai ta tsinci kanta da kasa kallonsa sai tsabar tsoronsa da ya rufeta ta shiga barin jiki baki daya Kai ya dan juya a hankali ya juyo dubansa kanta a lokacin da ya rage tsayinsa Da dan karfi, zuwa lokacin muryarsa ta fara amayar da tsarin dake cikin zuciyarsa, tamkar zai hadiyeta danya dan bacin rai ya ce" Zaki budi baki ki bani amsa ko sai na aiwatar da abinda zai tayar da hankalin kowa a nan? " Da sauri AMMI ta dora hannunta na dama ta saman kan NAJEEBA da ta cusa kanta cikin jikinta sakamakon irin yanda amon muryarsa ya yi mata rashin dadi a cikin kunnayenta AMMI na shirin yin magana suka ringa jin maganar Nadia a firgice sannan muryarta a shake, sai ta shiga dan harbe harbe irin zata tare wani abin sannan ta kwala razananen ihun da ya saka baki daya akayi kanta Ido rufe take fadin" kar ya sare ni, ka dauke min shi zai sare ni, walahi ba wanda zan fadawa, tsoron maciji nake ka kama shi yana lauye min kafata innalilahi wa'ina ilaihi raj'une wayo Allahna, wayo zai kashe ni " A rikice mamanta ke ta girgiza hannunta dake cikin nata tana kama sunnanta sai dai kamar bata san ana yi ba Da sauri ya duko da wani abu a cikin kofin glass da ya jika ya dan yi gyaran murya hakan ya sa UMMU bashi damar kama kanta Bakinta ya gumtse da hannunsa sannan ya dura mata abin nan ta hancinta hakan ya saka baki dayanta ta yi wani irin tasowa a gigice sannan ta koma ta zube ta shiga amai ta hanci ta baki Lokaci daya kuma idannuwanta suka bude jajajir da su tana ta zubar da hawayen wahala baki daya jikinta rawa yake tana bin dakin da mutanen dake wajen da kallo Wani irin kuka ne Zinaria ta fashe da shi gannin Nadia ta tashi, Ba wanda ya kula domin Nadiar du aka fi baiwa hankali wace gaba daya jikinta na rawa sannan ba karfi ta shiga fadin" Ban fada ba ko? Bai bari ya sare ni ba ko? Ba zan tona asirin ba kar ya kashe ni dan Allah " Najeeba dake kallonta tana jin hawaye na ziraro mata daga gurbin idannuwanta zuciyarta cike da tausayinta, ta san za'a rina ne irin tsoron NADIA bare wannan abin ita kanta ta tsorata, ba zata manta ranar da ta ganshi yana ta damukar maciji ba, sai kawai ta shiga tsoron ko dai shima macijin ne? Sai da ya yi iya yinsa sannan ya dan sasauta muryarsa ya shiga kiran sunnanta Kanta take girgizawa tana maimaita ba zata fada masa ba Mahaifiyarta ce ta kama hannunta ta rike a cikin nata da kyau ta ce" Nadia, kale ni, na zo, na zo fa, ba na fada maki zan zo ba? Kin ganni ni ce, fada min meye? Me kika gani, me ake fada? Idan har kika ci gaba da boyewa kin san da sannin ba barinki zai yi ba, domin kuwa ba zai taba yarda cewar kin rufe masa asirinsa ne, zai dauka cewar kina son tona masa a kowani irin lokaci, ki sani da ba dan Allah ya yi kina da sauran numfashi ba da yanzun an jima da goge babinki a duniya, ki sani kafin ke an kashe wata, idan kuma kikai shiru kema zaki bita, Nadia koda kuwa Allah ya yi wannan shi nr hanyar da zaki mutu kin fi so ki mutu ba tare da kin fadi abinnan ba? Bale da izinin Allah an kare, ba wanda zai kuma taba ki, ki buda idannuwanki ga mijinki, ga mahaifiyarsa, ga mahaifinki, ga yan uwansa da iyayensa , ki fadi koma menene" Nadia ta dora kanta saman cinyar mahaifiyarta ta rintse idannuwanta, ta ce" Amintace ne, da kuma wannan mai rike katuwar bulala kusa da Sultan idan an zo shara'a, su ne suke zance, shi wancen ya ce shi dai baya cikin maganar kisa, abinda yake so kamar yanda aka hana masa jin dadin aure shima ya wayi gari Sultan baya iya jin dadin aure.......... Sai ta fashe da matsanancin kuka ta dora da fadin", shine Amintace ya ce" kamar yanda ya katse masa dukan farin ciki, ya dawo ya dauke shi a matsayin dogari ya ajiye komai nasa na farin ciki, to lalle shima sai ya kai ga ransa, kafin nan sai ya cikawa Gimbiya burinta na son raba shi da kowace mace ko ta halin kaka sannan ya kashe ya kashe Sultan" Wata irin faduwar gaba NAJEEBA ta ji, har ta yi gagawar kallon SHAHEED dake tsugune kusa da Nadiar yana kallonta tamkar TV Da sauri Zinaria ta sauko kasa hannayenta saman kanta ta ce" Na san a duniya idan akoy abinda na fi tsana shine mijina ya rabi wata macen, burina koma wacece ta bar min mijina koda kuwa mutuwa zata yi, aman ban taba gigin kashe kowa ba, ba ni nake kashe masa mata ba, ban taba zuwa dan kashewar ba, na san bakina na furta kalamai aman ban taba gigin kashewa ba, kuma haduwar da nake yi da shi ba wani abu bane sai taimakon da yake kawo min ba dare ba rana cewar na aikata ko na zubawa Sultan a abinci hakan zai saka ya tsani matan da ya aura, ni ban san maganar maciji ba, banma san cewar wai har ta kai shi ga haka, tabas ina da matsanancin kishi, ba zan iya raba mijina da kowace mace ba, aman ban taba aikata kisa ba....." ta karashe tana mai fashewa da matsanancin kuka Kamar wace aka kunna ta kuma zabura ta dora da fadin " kuma a jiya a jiya kirana ya yi, bamu hadu ba yake ce min zai saka ni farin ciki yau, zai fara rabani da daya kafin dayar, ni ban san nufinsa zai kasheta ba " Ammi kai kawai take girgizawa hawaye masu zafi suna zuba daga gurbin idannuwanta sunna sauka saman fuskarta, NAJEEBA kanta a zaune take ta zubawa mutanen nan uku ido, tun daga kan SULTAN, NADIA, uwa uba Zinaria Haka kawai take jin abin sosai a ranta, harma irin tsayuwar da ya yi na yan mintunna ya kura mata ido ya bata tausayi A hankali ya juya ya nufi dakansa wanda hakan ya saka du wani mutun dake wajen rakashi da ido, UMMU kanta hawayen take cike da mamakin wata amanar ta mutanen yanzu da sam basu da amana, shekara nawa kana tare da mutumen, du yawancin sirinsa da yardarsa ya yarda ya baka shikenan rana tsaka a kama irin wadinnan magangannun a kansa Bai jima sosai ba ya bayana, cikin shigarsa ta sarakai sosai ya fito a yanda yake fitowa da A yanzu sai ya zauna saman kujera ya dake Ya dan jima a haka sannan ya dago da dubansa ya sauke kan NAJEEBA dake zaune jikinta doguwar rigar nan ce kawai ba wani lulubin da ya dace , dan haka a sanyaye ya furta " AMMI da UMMU, a lulube GIMBIYA NAJEEBA da NADIA " AMMI na kallon yannayinsa cike da wani irin tausayinsa a zuciyarta ta janyo hannun NAJEEBA ta sakata a jikinta sannan ta lulubeta da alkyabar dake jikinta hakan ya sa sosai ta baza Alkyabar kasancewarta mai fadi da tsayi ga kauri sai ta wadace su ta baje da kyau ta rufe su su duka Hakama UMMU ta aiwatar ta hanyar mayarwa da Nadia tata jikinta bayan ta kara lulubeta Sandar dake hannunsa ta sarautarsa wace a yanzu a komawarsa ya daukota ce ya doka da karfi wanda hakan ya saka lokaci daya daga Zinaria, UMMU, AMMI, suka yi kasa da kawunnansu, Nadia da mahaifanta ne basu gama gane wasu sirinan maganar sarki ba hakan ya sa sai da suka kalli yanda su AMMI suka yi sannan suma suka sada nasu Budewar da aka yi aka shigo da salama ne ya saka gaban AMMI yankewa ya fadi, muryar Amintace ne ta bayana rikeken Namiji maji karfi, tsayaye mai yannayin tsayayen namiji, Sai da ya dan saci kallon mutanen wajen sannan ya yi irin gurfanar da yake dan kawo gaisuwa ga SULTAN SHAHEED SHAHEED kallonsa kawai yake, sai da ya jima a haka sannan ya ce " Ka kula da bata mutu ba, gatanan ta mike da ranta AMINTACENA? " irin yanda ya furta kalmar AMINTACENA din yana mai cije lebensa da karfi ya saka Ammi rintse idannuwanta cike da bacin rai da fargaba Kara sada kansa ya yi, du da irin yanda gabansa ya kwonci kwonci ya fadi, sai ya yi kokarin anfani da kwarewarsa ta wajen yaudarar mutanen dake tare da shi da zuciya daya wa'inda basu gama fahimtar shi din ko wanene ba ya kara tausasa kalamansa domin sam bai taba tunanin Zinaria wawuyar da zata iya sakarwa lokaci daya bane harma ta fadi abinda ke faruwa dan haka ya dauki aniyar karyatar da Gimbiya a gaban sarki duda hakan baban laifin da ake iya gurfanar da shi ne, sai dai zai yi anfani da tarin yardar da Sarkin ya yi masa shima ya kwatanta kwatar yancinsa, dan haka ya ce " wace bata mutu ba ya uban gidana " Shaheed ya kara lumshe idannuwansa cike da dacin zuciya ya dan saki murmushi yana kawar da kansa, ta yaya zai zauna su ci gaba da wulakanta junna? Dan haka dubansa ya kai wajen mahaifin Nadia ya ce" honorable, gashi a tafi da shi PeJi, ka sani wannan yaro horona ne, domin tun yana da yan dabarunsa na kasancewa police a da, na kara nitsar da shi na bashi horo kala daban daban na yau da kulun, sai kun yi taka tsantsan da shi, sai kun dora idannuwanku a kansa sosai, kar ku saka shi a daki mai kasa ko mai ruwa, ku kiyaye saka shi a daki mai duhu , ya kasance a kejin da hasken wata da rana ke iya haske shi, ya kasance koda mutun daya ne na ganninsa hakan zai hanna masa du wani yinkuri na gannin ya kubutar da kansa" Dan sasautawa ya yi gannin irin yanda ya dago a gigice yana kallon SULTAN SHAHEED ya maido dubansa cikin idannuwansa, ya kasance sun yi ido cikin ido da wani irin kakausan kallo da idannuwansa da suka dauki ja yake kallon na Amintacensa, da sauri ya sada nasa duban dan kuwa baba da babansa fa, sai dai baki daya jira yake ya karasa ya bashi damar yin magana aman sai ya ji ya dora da fadin " A bincika maganar Gimbiya NADIA, sannan a yi anfani da shaidar abokiyar aikatawar tasa, na baku damar ku shigo fada ku yi binciken da ya dace da su baki daya, du wanda ya taka doka ta taka shi koda kuwa *Gimbiya Zulaihat* ce ! Ya karashe yana mai doka sandar nan a kasa a kausashe ya furta " *Idan har ka yi gigin tashin da kake kokarin yi a wajen nan zan tashi mu gwada karfi da kai wulakantace mai wasa da Amanar Allah! Domin ina mai tabatar maka ba zan barka ka huta ba har sai ka samu naka hukunci daidai da laifinka, sai ka girbi abinda son zuciyarka ya kaika aikatawa!* Sakwat ya yi ya mayar da kafar tasa, ba zai yarda du haukansa Sultan shaheed ya ajiye alkyabarsa dominsa ba, shi kam ba yau ba ya ringa tunanin karfin Sultan Shaheed kamar mai iskokan dake doka mutun da kasa, irin mutanen dake kawo masa tsagerancin da wani sa'in dole sai shi zai iya tankwasa su bake wa'inda suka shigo da takamar asirinsu dake tatare da su hakan ke sakawa su gagari dogarai, daga ya fuskanci hakan yake gagawar yiwa tufkar hanci tun kafin a gane gazawar dogaransa da ba gazawa ce sukai ba, lale lale shi din ne ya san abinda ya taka shi yasa du wani kwaro mai jin kansa na hayaki yake yin lakwas a gaban Maza, dan kuwa makashin maza maza ka kashe shi ba shaka! Sojoji ne su hudu suka shigo, babansu ne da yara uku, Suma dukawar suka yi suka kawo gaisuwar sannan mahaifin Nadia ya kora masu bayani, da irin tsaron da ya kamace su da komai, sannan suka sakawa Amintace ankwa wanda ke ta fitar da huci yana son kallon Zinaria dake kuka ya kasa har suka fita da shi Sai da ya kuma rintse idannuwansa ya bude a sanyaye yana kallin iya mutanen da suka rage domin mahaifin Nadia an tafi da shi, sai mahaifiyarta , ya kai dubansa wajen AMMI ya furta" A kilaceta bangaren bayi " .yana gama fada ya mike inda baki daya Zinari ta idasa kara zubewa tana son kama kafafuwansa dan ta bashi hakuri, aman ina ya ki bata damar hakan domin na farko da ta rike irin yanda ya wancakalar da ita ne ya sakata idasa fashewa da kuka tana fadin ita bata yi kisa ba, bata yi zina ba za'a kilaceta a bangaren Bayi? Ita ba baiwa ba jinnnin sarkin Agadez, matar Suktan shaheed wace ta bashi d'a, itane yau za'a kai bangaren bayi? Dan ta yi kishi shikenan sai a wulakantata? Da zafi zafi AMMI ta ce" wato har yanzu baki ga ilar tarbiyarki da mashawarantarki da son zuciyarki ba har kike furta kalaman nan? Wato har yanzu baki gane alfarmar kin amsa kiran sunnan matarsa ya saka ba'a saka maki ankwa an fita da ke a gaban talakawanki ba? Wato har yanzu baki gane kina cikin matsala mai girman gaske dan kuwa ke kanki baki san irin abinda yake bakin ko na menene ba har sai sun gama bincikensu a kanki sun gano irin girman laifinki shin ya cencenta a barki a hora ki a sirri ko kuwa dole a fitar da sirrin ba? Ke baki gane cewar alfarmar mahaifinki kika ci ba?, Baki gane cewar a yau, a yanzu ke din nan ba kowa bace sai sakaryar macen da ta kasa yin hakatacen kishi ta tafka kuskure wa rayuwarta ta wulakanta kanta ba? Baki ji daga bakin wanda kika yi mugun abun dan ki malake shi naki ke kadai din kin cenza sunna daga ZINARIA zuwa Zulaihat ba?, kaicon ki ZULAIHAT, kaicon ki, ke kau kin shiga uku, ki rasa wanda zaki ci amana sai mijinki?, kishi ai ba hauka bane ZULAIHAT! Ke yau koda an samo gaskiyar lamarin cewa babu hannunki a maganar kisan nan kina tunanin SHAHEED zai sauko da wuri wuri ya dube ki ne? Zaki samu irin darajar da ya baki a da ta kasancewarki matar da ya fara aura, wace ya fara haihuwa da ita ne? Zaki yi asara ta yardar da mijinki ya baki, zaki yi asara ta irin gannin girmanki da kimarki da yake, zaki gani a aikace ke din ba wanda kika fi, zaki fahimci halayanka sune limamin dake jan ragamar rayuwar da zaka iya fuskanta da mutane tun a nan gidan duniya! Kin san kina son sa kika yarda aka aura maki SULTAN? Inace y'ayan zamani akoy gungiyar dake kare hakin ku, koda kuwa mahaifinki ne sai su hanna shi yi maki auren dole, ita mahaifiyar take da ta kasance babar banza ta isa ta hanna kanta zama da kishiyar ne? Yaya bata iya hanna komai da nata rayuwar gidan mijin ke kike gannin ta isar maki? Dan ta haife ki shikenan komai halayanta sai aka ce ki yi mata biyaya? Ke din sakarai ce da baki san abinda ya dace da rayuwarki bayan haihuwa guda da bari uku da yanzu y'ayanki hudu a gidan nan, da a gabansu zaki amshi hukuncin cin amana wa abihnsu? Yaya zaku yi auren gidan sarauta ku yi tunanin zaku kasance ku kadai jal?, ke a zamanin nan ko talakan da bashi da ko sisi ya samu damar jera mata hudu jera sun zai abinsa koda kuwa bashi da abinda zai ciyar da su ne, bale wanda Allah ya horewa? ke da kina da hankali, ko da kina tare da magaya masu nazari da sun nusar da ke cewar idan akoy mai dama a wajen mijinku ke ce, ke kika fi kowa sanninsa kafin wata, ke ce mai dauke da lakanin da zaki iya zuwa kai tsaye gare shi kafin wata, ke din nan da kin koya masa yanda a duniya koda ya so wata fiye da ke to fa tsananin girmanki, darajarki, kauna ta zaman tare zai hanna masa wulakanta ki, an fada maki matar farko abin wasa ce a zuciyar mijinta? Idan kin ga namiji yana abun kirkin da a da ba haka yake ba sai bayan aurensa tabata harda gudunmuwar matarsa, idan aka ce lalacewa halayansa suka yi tabata wace ta ja hakan ita ne, menene burinki? *MULKI, ARZIKI, KI KADAICE SHI IYA KE* dan kar KAWAYE SU ZAGE KI, ko a gazawarki? Sai gashi ina mai cike da tsoron kar a je kin rasa komai.......AMMI ta karashe tana mai share hawayenta sosai Dubanta ta mayar wajen mahaifiyar Nadia da Nadiar kanta dake zaune kawunnansu a kasa ta ce " Ku yi hakuri, a yanzu ba zai iya bayar da hakuri ba, ku tashi a raka ku bangarenta ta huta " Da sauri Nadia ta ringa girgiza kanta, a tsorace ta ce" AMMI, dan Allah aa, akoy maciji a cen " AMMI ta dam sauke ajiyar zuciya ta ce " to ku tashi ku je bangarena, nima gani nan zuwa " Ai kuwa mikewar suka yi ita ta yima mamanta jagora hanyar bangaren AMMI suka bi suka shige Dubanta ta kai wajen UMMU a sanyaye ta ce" idan yaya ya dawo zamu yi shawara da shi kan maganar wannan ware waren turakar, bana jin zan iya kuma barin hakan ta faru" Ita dai kai ta gyada kawai, domin baki daya jikinta ba karfi, harma mamakin irin karfin zuciyar AMMI din take, duda takan share hawaye lokaci zuwa lokaci aman sai kokarin gannin ta daidaita komai take Wayarta ta ajiye, tana kara taba jikin NAJEEBA Cen sai ga tsohuwar JAKADIYAR dake kula da kebantacen wajen da ake kebe ahalain gidan da wani abin ya ritsa da su Sosai ZINARIA ta fashe da wani irin kuka tamkar zata side a lokacin da suka kamata suka mikar da ita A kausashe Jakadiyar ta furta" Hatara dai Zulaihat, sasauta muryarki a falon mai damagaram kike " Ai kuwa ta yi kitttt tana ji tana ganni suka fice da ita duda an bi ta sirri da ita aman ina ta tabata wannan magana har ta gama yada fada, ita kam ina zata saka ranta? Ina zata tsoma ranta? A irin yanda take da wulakanci, yanda ta dauki masu yi mata hidima da sauransu tamkar wasu bayinta, sam ba maganar mutuntawa sai tarin wulakanci da tozarci, dan ta tofa maka yawu ta kireka dan talakawa bawanta ba wani abu bane, dan ta saka a yi maka bulaka ba wani abu bane, tana jin dadi idan tana wulakanci, takan ji kwonciyar hankali da nutsuwa a zuciyarta idan tana wulakanci, a ganninta wannan shi ne bambancinta da sauran, wannan shi ne bambancinta da talaka, sai gashi yau zata je kebantacen wuri, wajen da ba rasa ci, sha , sutura zaka yi ba, bambancin shine bata da wata alfarma a wajen sarki, bata da damar ganawa da shi, bata da damar dora doka ko taka wani, tana da yan hidima sai dai bata da damar wulakanta su domin inci ne da su, suma sunna wajem da suke fada a ji ne, zata je duniyar mahidimta ne, wajen da suke nasu sarauta ne, y'aya da jikoki ne, bata da damar sakawa ko hannawa sai abinda hali ya bada ne, hakan ya matukar razanata, ya hanna mata sukuni har aka karasa da ita fadi take a bata wata Basu hanna mata ba, suka bata wayar , nan da nan ta yi kiran mahaifiyarta ta shaida mata wannan labari da ya kusan saka maman nata jin zuciyarta zata tsaya Itama hankali tashe ta nemi gannin sarki a kusancin magaribar nan wanda a yau bangaren Zahrau yake, sai dai amsar da aka bata cewar ba zata samu ganninsa ba ya sakata yin zaman yan bori, a nan kasa inda kuyanginta suka rikice harda yar kazaginta wace ta fece da gudu bangaren Yarima dan kai masa labarin halin da mahaifiyarsa ke ciki Wannan kennan Sai da AMMI ta ja numfashi ya fi a irga sannan ta kara shafa kan NAJEEBA a hankali ta ce" tashi Najeebana " Da taimakonta da na UMMU ta mike tsaye Ammi ta kama hannunta da niyar tafia da ita bangarenta , duda ba haka take so a kasan zuciyarta ba sai dai gannin kamar NAJEEBAR nada bukatar taimako sai ta kasa barinta a nan din A hankali UMMU ta ce" AMMI, me zai hanna ita a barta a nan? Mai yiwuwa ta taimaka masa da wani abin?" Sai da ajiyar zuciya ta kwacewa Ammi, aman sai ta kada furta komai ta ja ta tsaya tana kallon yannayin NAJEEBAR Gannin kanta a kasa tana ta wasa da yar yatsarta sai AMMI ta lumshe idannuwanta ta juya a hankali ta yi gagawar kama hanyar tafia, kwarai tana son ya samu kadaicewa da mace koda kuwa ba abinda zai shiga tsakaninsa da ita, koda kuwa ba zai yi maganar abinda ke damunsa ba, koda kuwa ba zai kulata ba, tana son wani ya kasance a kusa da shi, shima fa mutun ne, mai rauni, mai tare da damuwa, mai son idan yana cikin damuwa ya samu mai taya shi, mai bashi shawara, mai nutsar da zuciyarsa UMMU ta kama hannun nata da take wasa da shi, a sanyaye ta ce" ki shiga ruwa masu zafi ki jima a ciki sosai, sannan ki sha ibuprofen" NAJEEBA ta dan gyada kanta tana hadiyar yawu masu zafi a makogwaronta cike da yannayin damuwa UMMU ta dago habarta a sanyaye ta ce" my BEEBA? " Najeeba ta kaleta jin wani sunna da ta fada Ummu ta yi dan murmushi ta ce" SHAHEED ne yake ce maki MY BEEBA, a lokacin da ake kawo ki wuni wajen AMMI din ki " Da mamaki a fuskarta, muryarta a sanyaye ta ce" Dama yana min magana ina karama? " Murmushi UMMU ta yi ta ce" yana son yara kananu, burinsa AMMI ta haifa masa kani shima, ganninki a wajenta sai ya samu abin nishadi idan ya baro fada da wajen horo da hawa doki, yakan yada zango a bangaren da aka zuba maki kayan wasa da masu kula da ke, sukan bara maku wajen shi kuwa ya ringa saka ki tatata kamar yanda kike tafiarki a hankali sai ya ce *ZO NAN MY BEEBA* , tun baki iya sunnansa ba, irin yanda yake zuwa da ke wajen mai martaba shi kuwa yana kama sunnansa ne kai tsaye har kika iya da maganar yara sai ki ce " JAHITT, wai SHAHEED " Wani murmushi ne ya dan subuce mata , sai kuma ta kalli UMMU ta ce" to me ya da daga baya ya tsane ni? Me ya sa daga baya na kasance babar makiyiyarsa? Kaf cikin yan uwana na dawo ni ya fi tsana? " Ummu ta lumshe idannuwanta, a hankali ta ce" ni kaina ina son sani, ko zaki yi kokari ki samo mana amsar nan?" .............hi............ [31/03 à 22:01] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 57 Kanta kawai ta sada bata iya baiwa mahaifiyarta amsa ba, a haka UMMU ta saki hannunta ta bi bayan AMMI Ta jima nan tsaye tana saka tana kwoncewa, Tana ta nazari ne a kan rayuwarta ita kanta, kafin ta daga kafarta da kyar ta shiga takawa ta nufi dakin da a ranar ta ga ya fito da Nadia daga ciki A hankali ta idasa saka kafafuwanta tana bin dakin da kallo, ba sanyi domin Ac a kashe, sai dai da kamshin sansanyan turatan wuta A haniali ta taka ta nufi bayi du kuwa da irin yanda take jin jikinta ba karfi kwata kwata Ruwa ta tara masu zafi ta rintse idannuwanta a hankali ta fara saka kafafuwanta sannan ta rintse ido ta zauna wanda hakan sai da tmya sakata kama abin nan ta rike da karfin gaske Idannuwanta rintse suke kakam, abubuwan rayuwa take ta tunawa, yau gata a gidan da ba saki sai ka aikata kisa ko zina, biyu daga cikin abubuwan da rana bata fitowa ta fada bata nemi da Allah ya tsareta daga mumunar kadarar da zata kaita aikatasu ba Yau gata a matsayin matar aure, matar farin mutun, Sai dai abinda ya ki barin kwakwaluwarta shine irin yanda yake son ya jata da dan wasa duda ba wai wani sakewa ya yi ba aman yannayin da yake nuna na kamar zai tsokaneta na bata matukar mamaki Kafarta ta riga dan wanawa a cikin ruwan tana kara hauda shi jikinta a hankali ya ringa salabcewa har zafinsa ya ragu sosai Wannan karron sai ta hada na sabulu mai kunfa sosai mai sansanyan kanshin da ya sakata lumshe idannuwanta, Ta jima a cikin ruwan nan har sai da ta ji kiraye kirayen sallah sannan ta dauro alwallah ta fito daga bayin da tawul din da ta gani Tsaye ta yi a dakin daga ita sai tawul, tunaninta kayan da zata saka A hankali ta fara leko kanta dan so take ta je wajen wayar cen dake ajiye ta yi kira bangarwn AMMI a kawo mata kayanta, sai dai tana lekowar sai ta hangi akwatinta wace take malakinta Da dan sauri ta fito ta kama tana janta har ta shige dakin sannan ta datse tana sauke ajiyar zuciya Bata buda akwatin ba sai da ta je wajen turarukan dake ajiye Ido ta buda sosai gannin turaran nan, sai kuma ta turo baki tana dan gunguni ta dauki guda ta buda ta shiga yiwa jikinta barinsa sosai har kai tana ta kara juyawa da daria a fili ta ce" Na rama cicije min nan da ka yi malan ehe" Sai da ta gama barnar da gangan dinta sannan ta koma wajen akwatin ta shiga bubudawa Wata doguwar riga mai hade da hijab dinta har kasa ta ciro wace ta tabata an saka mata ita ne dan sallar Pant da bras ta ciro sababi ta ajiye Sai da ta fesa masu tyraran nan son ranta sannan ta saka ta zira rigar ta shiga neman abin sallah Sai dai sama ko kasa babu, tana nan tana ta zagaye kamar da wasa ta tsinkayonkiran salar isha'i, hakan ya sakata zaro idannuwanta da sauri ta fito ko kashe fitilar da ta kunna bata yi ba tana son yin saurin sosai aman har yanzu ba wai ta saku yanda ya dace bane, ta dai rage jin azabar da take ji dazun aman kuma har yanzun wajen na sukanta Ba tare da tunanin komai ba ta tura dakin nasa da salama kasa kasa ta shiga Tsayuwa ta yi tana kallon dakin, ba kowa ciki aman da kanshin turarrn wuta da ya garwaye da turaran daki da kuma na jikinsa da ya fesa sai abin ya bada kamshin ya hade ya cika ko'ina na fakin Ga sansanyan sanyi dake dakin na AC din da bai kashe ba Dan tabe bakinta ta yi ta nufi kebantacen wajen da ake sallah a dakin Wajen a kawace yake, ga alkur'anai mai girma a saman wani dan sif fari kal a jefe da litatafan musulunci da carbunna dai masha Allah Sallah ta kabarta a hankali ta shiga gabatarwa, tun daga Azahar da bata samu damar yi ba, la'asar da bata yi ba, magariba, sannan ta dora da isha'i Tana salamewa ta ji muryarsa kasa kasa ya ce" du kina me kika tara sallah haka a kanki NAJEEBA? " sai da gabanta ya fadi, domin ita dai sam bata ji shigiwarsa ba bale takun tafiarsa, uwa uba kanshin turaran nasa dake shaida mata zuwansa waje itama shi din ne ta kilkila a jikinta ya kasance har hancin nata ya daina jiyo kamshin zabar ya shaka da yawa Sai da ta dauke numfashi kadan sannan ta dan sada kanta da carbin da ta dauka fari mai kyau a hankali ta ce" Nafiloli na yi " Dan murmushi ne ya kwace masa a kan labansa, bai ce komai ba ya koma ya gyara zamansa saman gadon ya jinginar da bayansa a jikin kan gadon kadan sannan ya ci gaba da binta da kallo kasa kasa yana mai jan carbin dake hannunsa Du sai ta kasa jan lokaci mai tsayi tana jan carbinta, tana ganawa ta daga hannunta a cikin zuciyarta ta yi adu'o'inta ta shafa sannan ta ajiye carbin ta mike ta dan ninka salayar ta bi wajen kur'anan nan da kallon sha'awa tana ji a zuciyarta inama ace nata ne duka? Kai da ta caba Dan satar kallonsa ta yi, sai ta ga ashe ya yi baci, dan haka dan ta yi murmushi ta juya a hankali da niyar tafiarta wancen dakin ta kwonta Kasa kasa ta ji ya furta " Baki ji ba? " Har sai da ta dan tsaya ta juyo ta kale shi, gannin bai motsa a yanda ta barshi ba sai kawai ta juya ta ci gaba da tafiarta a hankali Idannuwansa ya dan buda kadan ya ce" Najeeba idan kika fita ba zatai maki dadi ba " Juyowa ta yi tana turo bakinta gaba tana dan magana kasa kasa , cewar haka kawai ashema ka san sunana malan Shi dai kallon bakin nata kawai yake a yanda yake, sai kuma yanda ta tsaya masa wani kerere a tsaye a ka da yake mamaki Dan buda idannuwan nasa ya yi ya sauke duban nasa a fuskarta, irin yanda ta turo bakinta da tsayuwar da ta masa kamar wata yar baby sai mutsu mutsu take da bakinta Hannunsa na dama ya mika mata a hankali ya ce " Zo " Sai da ta bi hannun da kallo , a ranta fadi take, kawai mutun sai fari uwa wani aljanni, irinsu ne kana ta kanka a gida kana faman girki da tsantsara masu kwaliya sun fita waje wasu matan na wawarsu, haka kawai kana ta kanka a jaza maka abinda ba shi ba, sai wani yanga da wani langwui salon ka kara tara matan, to dai matsalarka ce malan idan kana so tara million ma A hankali ta dora hannunta saman nasa , tana kara shagwabe fuskar tata ita bata ki zuwa ba, ita bata yarda zata je har zuciyarta ba A hankali ya janyota gaba dayanta jikinsa ya dorata saman jikinsa ya saka hannayen nasa ya bata kyakyawar runguma Muryarsa sanyaye ya ce" yaya zaki gudu ki barni bayan kin ga matata ma cikin wani hali, nima ina cikin damuwar saka mai so na a wani hali? Duda na san ba so na kike ba aman idan kika zauna da ni zan rage zafi " Bakinta dake daidai wuyansa ta turo sosai tana tabewa, a hankali ta ce" to ka yafe mata mana, ai na ga ba ita ta kashe maka mata ba, kuma ba ita ta so kashe maka mata ba, bayan wannan ai dan tana son ka ta aiwatar da hakan, kishinka take shi ya sa " Idannuwansa dake lumshe ya dan kara lumshewa sakamakon abu biyu, gannin kamar maganarsa batai mata zafi ba, da irin hucin dake saukar masa a dokin wuyansa Sai da ya jima tamkar ba zai yi magana ba sannan ya ce" zan duba maganarki, kafin na yafe mata zan kara aure " A hankali take jin haushin magangannunsa, to a me wai ya dauketa ne? Ita ga wawa ko? Da dan zafi zafi ta ce " idan ka tashi ka auro farare tas tas tas bakakenma ka sake su SHAHEED " Murmushi bayanane ya yi gannin a yanzun maganarsa kamar ta mata ciwo, dan haka ya ce" sai nake gani kamar kin ji haushi? " Bakinta ta yatsina tana dan son tashi aman sai ya kara matseta a jikinsa hakan ya sa ta daina kiciniyar son tashin Itama sai da ta jima tana tunani sannan ta ce" ba biya ba bege me ya kawo jin haushin maganar abokin zama ?" "Haka ne kuma, aman ko ba komai zan duba shawararki zan kawo wata tsaleliyar fara, sai dai ni bana ajiye bayi a matsayin matan da zan ringa zagayawa, kema musulunci ai ya yi karfi yanzun ko " Shaheed ya fada yana mai kara rungumeta a jikinsa Sai da ta datse lebenta na kasa a dan kausashe ta ce" sake ni! " Kansa kawai ya dan girgiza mata bai sake tan ba bai kuma bata amsa ba Huci ta furzar kafin ta ce " Allahn da ya sa nima ba ni nace ina son farin ba! " Murmushi ya yi a bayane bai bata amsa ba, sai kawai ta ringa sauke ajiyar zuciya, sai da ta dan daga dubanta ta sauke a kan habarsa , gannin idannuwansa a rufe sai ta zabga masa harara harda murguda bakinta Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" Na yafe maki " Ido ta zaro da mamakinsa, wani irin karfin gani ne da shi haka?, wai kuma me yasa ya cika son yi mata komai cikin sanyin lamari bayan shi din mutun ne mai zafi? A hankali ya ce "BEEBAHHH?" dagowa ta yi da sauri dan jin muryarsa a wani irin sanyaye sannan irin yanda ya ja sunnan sai ta ji da bambanci sosai kan yanda UMMU ta fada, nasa har wani irin yamyamyam ya sakata ji a jikinta, sam sai ta kasa amsawa kiransa sai wani zuru da ta yi tana kallon wuyansa domin daf take da wuyan nasa numfashinta na sauka a wuyan nasa A hankali ya ce" BEEBAH ki janye hancinki daga wuyana, kin ga sai wani yannayi nake shiga kar na zo na kara kuma a ce ban kyauta ba " Idannuwanta ta lumshe a hankali, tana mai jin yanda maganarsa ke sauka a cikin kunnayenta, sunna samun wani muhali mai tsafta a cikin kwakwaluwarta, kasancewarsu ba zafi ba ihu ba kausasa sai take jinsu wani bambarakwai harma ta kasa tuna waye mai furta su haka a sanyaye, a rashin sani ta dan matse masa wajen mararsa da hannunta na dama ke sama hakan ya saka shi rintse idannuwansa a hankali ya furta " Washhh zata kashe ni " A dan tsorace ta dauke hannun nata, sannan ta yi gagawar janye jikinta daga irin mamukar da sukaiwa junna, cike da kunya gannin ya ki saka mata duwai ya mata wani damka ya sakata dam gyaran murya kasa kasa ta ce"....... .................🥳🥳🥳🥳🥳😎🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳 [31/03 à 22:01] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 58 Gannin ya ki sakar mata duwai ta dan gyara murya kasa kasa ta ce" ka sakar min nan, kana fa gannin inda kake saka hannayenka kana halaya kamar wani........." Sai kuma ta yi shiru a lokacin da ya kara janyota da dan karfi jikinsa ya mayar da ita irin kwoncin da ta yi dazun a jikinsa sosai, sannan ya rage muryarsa sosai da sosai ya furta " kamar wani kwarto ko?" Hannayenta duka biyu ta kai wajen bakinta tana rufewa tana zaro ido cike da tsoro da kuma mamakin furucinsa Sai dai kafin ta kai ga farfadowa sai ta ji ya dora da fadin " Ai ke kika lalata ni, gashi sai haye min jiki kike kina wani shan mur " " Ka ji tsoron Allah shaheed " ta fada a mugun sanyaye tamkar zata fashe masa da kuka muryarta na dan rawa rawa Murmushi ya saki ya mayar da fuskarta wajen kirjinsa a hankali yake shafa bayanta ba tare da ya kuma furta mata koda A bane Baki daya ta ringa kaea gyara kwonciyarta, har ta samu kwoncin da ta ji dadinsa sannan ta lumshe idannuwanta tana mai karanta adu'ar baci Bacin ne kuwa ya yi awon gaba da ita, hakan ya saka mata sakin nauyinta a jikinsa da kuma kara sakankancewa da jikinsa Murmushi ya yi a hankali ya juyar da ita saman bed din Cikin nutsuwa da lalama ya cire mata rigar nan dan ta ji dadin baci A hankali ya juyar da ita ya bale mata bras din nan ya cire baki daya Numfashi ya ringa fuzga da sauri da sauri, sai kuma ya ja abin rufa da sauri ya rufa mata har wajen wuyanta sannan ya kara yi mata adu'a ya mike yana gyara jikinsa sannan ya fito daga dakin ya nufi bangaren AMMI Kamar yanda ya yi tunani hakan ce ta faru, tana zaune saman abin sallah tana jan carbi aman baki daya hankalinta waje guda ta kurawa ido tana kallo hakan na nufin jan carbin ne kawai take aman damuwar da take ciki mai yawa ce Cike da rauni, rauni irin wanda bawa baya iya boyewa gaban mahaifiyarsa ya karasa ya zauna kusa da ita sosai yana kallonta Idannuwanta ta lumshe jin sa a kusa da ita, a hankali ta kura masa ido tana nazartarsa Kansa ya sada kasa yana ta dane halin da yake ciki hakan ya sa a hankali ta saka hannunta ta dago kansa Hannayenta biyu duka ta saka ta tare fuskarsa sai kuma ta janyo fuskar tasa hakan ya saka shi biyota ya dora goshinsa a kafadarta kamar yanda ta bukata A hankali ta shiga taping din bayansa, muryarta a raunane ta ce" cry, cry, cry my boy " Dan shiru ta yi sannan ta dora da fadin " basu kyauta ba, sun ci amanar zaman tare na shekara da shekaru bisa son zuciyarsu, ba laifi akai masu ba, ba tinzura su akai ba ta hanyar wulakanta su a zamantakewar da aka yi ba, niyarsu ne, jst cry SHAHEED , cry a jikin mahaifiyarka domin kaima mutun ne, dan kana sarki baya nufin zuciyarka bata anfani, dan kana sarki baya nufin baka jin rauni irin na kowa, ka zubar da hawaye ko zaka ji sanyi a zuciyarka sannan ka manta da lamarinsu, Allah ya gama saka maka tunda ya bayana maka komai, Allah ya gama yi maka komai tunda ya hanna su wulakanta ka a idannun duniya, CRY MY HAPPINESS " Ai kuwa, magangannun da take tamkar tana bashi damar kara hasko irin zaman da ya yi da su, sosai ya yarda da su, sai ga rayuwa ta zo masu a haka daga shi har su, kwarai zuciyarsa ta masa nauyi , bukatarsa samun hawayen, da zai samu ma ya rushe da kuka mai tsanani kawai, sai dai rashin samun hakan ya saka shi ringa sauke tagwayen ajiyar zuciya yana ta kara yiwa komai fila fila yana mai baiwa kansa amsa cewar dan adam kennan, ka shiryawa komai daga gare shi,, a hankali ya ci gaba da jin nauyin nan na ragun masa, a fili ya furta" harda aikata kissa? Lalle shi kansa bai san karamar kiyayata da ya saka a ransa ta yi girman da zata kaishi ga halaka AMMI " Ammi ta yi dan murmushi jin dumin abu a kafadarta, ta tabata abinda take so ya samu ne ya samun, wato zubar hawayensa dan ya ji sanyi a zuciyarsa, dan haka itama a sanyaye ta furta" Dan Adam kennan, mutun mugun ice kennan " A hankali ya dago kansa yana kallonta, hakan ya bata damar saka hijab dinta tana goge masa fuskarsa, a sanyaye ta ce" har na tsawon wani lokaci zaka kilace ZULAIHAT a bangaren horo ? " Sai da ya jima kamar ba zai yi bayani ba sannan ya ce " Idan aka gama bincike suka tabatar cewa laifinta kawai hada kai dan a kori kishiyoyinta ne ba dan a kashe su ba, idan aka tabatar ta hanyar vidios din da gareni a wajena cewar laifinta bai kai na aikata kissa ba, kuma kotu ta ga ba zata riketa ba ba zata yi kaso ba, zan yi kokarin turata masarautar Agadez ta gidan motar haya, zata sauka irin na kowa ta dauki abin hawan da zai kaita masarautarsu Zan sanar da mahaifinta ya saka jakadiya ta tarbeta daga bakin gate na farko a yi wajen horo da ita zan bata damar zama tare da bayi na tsayin lokacin da zata gane rayuwa, domin kuwa tarbiyar da ta samu sai ta samu wace zata nuna mata ba zahiri aka nuna mata ba, na tabata duniya ce kawai zata ladaftar da ita ta horar da ita, domin kuwa idan ba haduwa ta yi ta kwana ta tashi ta ci abincin mutanen da take wulakantawa ba, ba zata taba gane yaren ba, gidan horon garin Agadez ya tanadi horo ne sak ba dan sarki ba bawa, zata je ta hadu da sabuwar rayuwar da zata hidimtawa kanta komai, daidai da shiga bayi sai ta bi layi kafin ta samu shiga, ba tsaftacen waje ba tsaftacen kayan zuba abinci bare dandannon da bakinta ya saba, ba waya ba tv ba wuta bare ta samu AC ko panka, daga nan zata fahimci darajar ni'imar da Allah ya bata ta yi wasa da ita, zata gane darajar masu hidimta mata, idan na gamsu cewar horo ta samu ba son kai ba zamu yi zama da ita da mahaifiyarta da mahaifinta, idan da hali sai ta dawo ta zauna a karo na biyu , aman fa AMMI sai dai a yi hakuri domin kuwa ba a matsayin uwar gidana zata dawo gidana ba, sai dai a sake dauran aure da ita dan kuwa na rubuta mata saki daya, dukan abin kunyar da take gudu zata same shi da izinin Allah sai mu ga irin daukan da zatai masa " Ajiyar zuciya AMMI ta sauke tana kallonsa, sai kuma ta dan kawar da dubanta a hankali ta ce" mun yi magana da mahaifiyar Nadia cewar ta saka a kawo wanda zai kula da ita har kafarta ta warke, sannan ta tsorata matuka bangarenta ina ga ko a buda mata bangare na hudu, ko kuwa kawai ka mayar da matanka bangarenka Shaheed, idan Allah ya yi kun fara tara iyali sai su dawo bangarorinsu, aman a haka ni kaina na tsorata da mutun, dan kuwa su nasu ya fito, kamar yanfa ka fada ne gidan sarauta ba'a taba raba shi da ire iren abubuwan nan " Shaheed ya gyada kansa yana sauke ajiyar zuciya AMMI ta ce" yaya zaka yi da shi kuma sarkin bulala fa? " Shaheed ya dan yi murmushi a hankali ya ce" Da ace haushina ne kawai yake ji, bai ji za'a cutar da ni ya yi shiru ba, harma ya bada tasa gudunmuwa ba, da sai na manta da na ji sunnansa a cikin magautana sai dai kiyaya girma take, kuma na tabata karuwa take a cikin zuciyarsa, dan haka zan yaye shi daga masarauta , zan fitar da shi cikin gari sannan na saka ido a kan lamuransa, domin kuwa koda bashi da lafiar aikata mugunta ga y'ayan mutane shi abin a zuciya yake, hanyoyin aikata mugun abun kuwa yawa ne da su, zan kai shi rayuwa cen kusa da baban gidan kaso, sannan zan saka masa ido sosai " Cike da gamsuwa Ammi ke gyda masa kanta Gannin sosai ya saku kan dazu sai ta ji dadi, dama ta tabata idan suka zauna zai ji sanyi sanyi a ransa, dan haka sai ta yi niyar kara saka shi nishadi ta hanyar fadin" gobe yarinyata ke gama sati gudanta, a gobe zasu yi zama ko yayane? " Shaheed ya dan dago a hankali yana kallon AMMI, sai kuma ya yi dan murmushi ya ce" zasu yi zama aman ai sai Nadia ta samu lafia ko AMMI? " Ammi ta ce" an fada maka ta ce ba zata iya zuwa bangaren mijinta ba dan kawai kafarta na yi mata ciwo ? " Yanzun kam sai ya yi shiru aman fuskarsa a washe take ba a daure ba Ammi ta ce" ina yarinyata SHAHEED?" Murmushin da yake rikewa ne ya bari ya subuce masa Waje daya ya dan kurawa ido yana kallo, sai kuma ya dan girgiza kansa yana cije lebensa na kasa, kasa kasa ya ce" Bata jin magana, zata mayar maki da yaro mai magana , fada take nema ido rufe " Wani farin ciki ne ya dira a zuciyar AMMI, dan kuwa irin yanda yake maganar yana dan juya kansa ga murmushi kwonce a fuskarsa sai ta samu kanta da yin yar dariya har cikin zuciyarta, a hankali ta ce" ni dai kar wanda ya cutar mij da y'a, ehe " Fuskarta ya kurawa ido, a ransa kuwa fadi yake wace zata wani tsaya kallona na cuceta? Ban taba gannin tsaurara irin yarki ba AMMI zata tsareni da ido ta bani umarni ba ko shayina, wai Malan cika ni, wai je ka auro da yawa fararan, wai ni take murgudawa baki a gabana?, sai kuma ya saki murmushi yana ayana sai na cije leben mu ga abin yin tsiwar a gabannan, AMMI kam gannin sai sakin murmushi yake yana dan juyar da kai sai ta ce" tashi ka duba Nadia sai ka tafi bangarenka ka huta " Sai da ya kama hannunta kamar yanda ya saba ya dora shi a gefen kuncinsa na dama ya lumshe ido sannan ya kawo shi wajen bakinsa ya sumbaci bayan a sanyaye ya furta" Allah ya sa ki hama da duniya lafia ya datar da ke da shiga gidan aljannah, ya yafe maki laifukanki ya faranta maki zuciyarki, Allah ya nutsar da zuciyarki ya kara maki imaninki yah UMANI " Ammi dake amsawa da Amen , Amen a kasan zuciyarta kuwa ita kadai ta san irin adu'ar da take masa, har ya gama ya mike cikin nutsuwa ya fice a dakin Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi sai kuma ta ci gaba da jan carbinta har sai ta ji baci tukun zata ajiye Irin kwonciyar da ta yi zai nuna maka a takure ne ta yi shi Tun da Sultan ya shigo ya lura da idannuwanta biyu aman kuma kamar harda hawaye a gefensu Kasancewar ba wani kwakwaran motsi ya yi ba sai bata ji shigowarsa ba, hasalima ta hanna kanta rintsa ido dan ko a nan din tsoro take ta rufe idonta ta ga macijin idan ta bude Dan gyaran muryar da ya yi ya tsoratata , hakan ya sa ta zabura har ta bige ciwonta Fashewa ta yi da kuka tana rinrintse idonta Da dan sauri ya karasa yana fadin" hey, menene, meye? " Jin muryarsa ya sakata buda idannuwanta, baki daya hannayenta rawa suke ta kale shi ta ce" tsoro nake macijin ya shigo, wollah ka tambayi Najeeba ko laifi na mata kwari take kamowa ta ajiye min a gabana , ba zan motsa ba sai ta yi hakuri ta dauke, haka Allah ya halice ni da tsoron du wani abu bayan kuda , dan Allah a kaini gidanmu " Tausayinta ne ya ji ainun, wannan daukan alhaki har ina, gata ita bata mutun ba aman an barta da tashin hankalin tsorata har haka Hannunta ya kama ya tayar da ita tsaye, a hankali ya ce" ba kyau mutun ya cika tsoro har haka, ki rage ki yaki kanki ki rage sannan ki daina nunawa kina tsoron domin duniya ta ki lafia, baki san da wa zaki hadu ba, baki san inda rayuwa zata kaiki ba" Yana gama fada ya kama hannun nata ya fita da ita ya nufi dakin UMMU da ita, dan ya san idan ya kaita dakin Ammi to itama Ammin kunyarta zata hannata yin bacin, ita da Najeeba kawai take iya bacinta a cikin matansa Bayani ya yiwa UMMU, kwarai ta fahimta dan haka ta kamata ta kaita da kanta saman gadonta harma ta shiga dauko abinda zata gige mata dan jinnin da ya zuba a wajen ciwonta Ajiyar zuciya ya sauke yana dan girgiza kansa ya juya ya tafi Ummu kuwa da dabara ta saka Nadia ta cire uwar alkyabar dake jikinta sannan ta sakata ta kwonta Zama ta yi gefenta a bayane ta ringa tofa mata adu'o'i hannunta saman kanta, hakan ya sa ta yi ta jera ajiyar zuciya har jikinta ya shiga warewa ta shiga jin nutsuwa a cikin zuciyarta Muryarta na rawa ta ce" Mama, zaki kwana da ni a nan gefena?" AMMI ta yi dan murmushi ta ce" Eh, a nan zamu yi kwonciyarmu Nadia, abinda nake so da ke koda abin tsoron kika ganni idan dai ba waje ya kure maki ba bana so ki tsorata, ke ko waje ya kure maki ridarshi bige banza, ni bana wani gudu sai dai ya lahantanin ta haka aman fa sai na kar shi" Yar daria abin ya bata, harma ta yi murmushi ta ce" Mama, kennan a wajenki Najeebana ta gaji wannan abin, idan ta ga abu tana tsoro in ya nufeta maimakun ta gudu ko ta yi ta ihun a taimaketa sai kawai ta ride shi ido rufe, akoy ranar da wata irin tsaka katuwa bak'a kirin harda yan gashi a jikinta ta fado mata saman abin kwaliyarta a shago fa, ai kau aka ringa guje gujen guduwa itama tana tsaye jikinta na rawa, sai kayan ta kwashi ayatul kursiyu a bayane tana yi tun karfinta, kuma sai ta warci kwalbar wata hodar ruwa ta shiga dandatsar tsakar nan fadi take idan aljani ne ka bace na maka ayatul kursiyu idan kuwa tsaka ce dan ubanki ba inda zan je, kuma fa harda hawaye domin tana tsoron tsaka sosai fa " Ai kuwa abinda mama take so ne ta samu, wato ta ringa jin irin halayar gudan jinninta, hakan ya sakata wani irin nishadi, sai kawai ta kara sakin jiki da Nadia, itama ta saki jikinta sosai da maman tana ta bata labarunsu, kuruciyarsu, irin tabin maganarsu, zuwa yanmatancinsu, zuwa yanzun A haka ne mama ta ce" aman Nadia, me ya sa Najeeba ta tsani Sultan ne?" Nadia ta dan gyara kwonciyarta a hankali ta ce" Mama, ta dauki wani lamari ne ta sakawa zuciyarta cewar du idan ta motsa yana binta da harara, ya tsane ta, na rasa menene ya ja haka? Me ke damunsu ne baki dayansu, sai dai a yanzu ni ina da ja da maganar kallon tsana yake yi mata, qman ba komai na tabata a hankali ita da kanta zata ganni, zata fada min hakan kuma " Mama dai murmushi kawai ta yi, lalle ta ji Nadia ta shiga ranta sosai da sosai, dama yarinyar bata da duhun kai, haka sukai ta labari har baci ya dauketa sannan UMMU ta dauro alwallah ta shiga gabatar da nafilfilu domin dare ya yi sosai Sai da ya gama dukan kimtsawar da yake yi a kowani dare, ya gabatar da nafilarsa raka'a biyu kawai ya yi doguwar adu'a sannan yaike ya cire jalabiyar dake jikinsa Turare ya fesa a jikinsa sosai sannan ya shige cikin abin rufar da ta kanainaye take baci hankalinta kwonce A hankali ya janye abin ya maye gurbinsa ta hanyar hade jikinsu sannan ya lumshe idannuwansa ya shiga neman baci bayan ya yi adu'a Wani irin nutsatsen bacin da bai zata zai samu ba ya samu, a lokacin da ya motsa kiraye kirayen sallar asuba na biyu tuni har lokacin ya yi, da sauri ya diro ya nufi bayi dan kar ya makara Ko da ya kimtsa ya kai dubansa wajenta bata nan, sai kawai ya fice dan gabatar da sallarsa Ya jima sosai domin sai da ya leka ya ga kwannan su AMMI da Nadia da jiki, sannan ya dawo, a lokacin tuni takwas ce take neman yi Kasa kasa kunnayensa ke jiyo masa dan kida na tashi, hakan ya mugun bashi mamaki harda dan zaro ido Kida? A nan? Da safiyar nan wani iblis ne wannan? Da sasarfa ya nufi dakin da yake jin dan kidan ga carbinsa a hannunsa A bude dakin yake, ta baiwa kofar shigo baya, ta daura zani ta dage shi har wajen kwaurinta sai rigarta mai kananun hannaye sai gashin kanta ta hade su cen sama ta sike da kumb dinsa Zanin gadon nan ne ta yaye ta ciro wani tana shinfidawa, sai kuma ta saka wakar larabawa mubale, hakan ya sa take kada kugunta tana rawar larabawan haka kuma idan ta dan mike sai kawai ta cire da rawar ethiopian tana kada kafadun nan exactly yanda suke yi har ta dan yi kasa kasa da kan nata sannan ta tsayar da jikinta sai iya kugunta kawai ke juyawa da wani irin kwarewa ga shafafen cikin nan nata baki daya casun sasafe ne NAJEEBA ke hadawa a bangaren SULTAN, wanda ta tabata ba zai zo inda take ba, haka kuma bata wani kure volume ba bale har ya ce ta cika masa waje da ihun kida A hankali ya jinginar da bayansa, baki daya idannuwansa tamkar zasu fado ikon Allah kawai yake kallo Gannin har kamar da gaya, har kasa kasa take dan dukawa sai kuma ta kara ci gaba da cashewa ya saka shi murya cen ciki ya furta" *BEEBAHHHHHHH* " NAJEEBA kam kunnanta mai ji ne, sai dai wakar da ta saka ta hanna mata jin domib kuwa kwarai a ciki ya yi maganarsa A hankali ya ringa dan daga idannuwansa da sukai masa nauyi ya kuma furta" *BEEBAH, KI BAR BALAKI YA YI BACI NA ROKE KI* " Wannan karron kam ta ji, hakan ya sa ta yi turus ta tsayar da rawar tata, wajen da take kallo dai take kallo idannuwanta rintse, sai kuma nan da nan magangannun su aunty Zahrau suka shiga dawo mata sala sala, maganar aunty Zahrau da ta ce da ita" bana son iskanci Najeeba, ai so muke mu ga iya gudun ruwansa, zaki bani hadin kai na gaskata maganar da ya yi cewar baya son bak'ar fata ko zaki ci gaba da shirmen nan ne wai? " Yawu ta hadiye da kyar kafin ta dan duka ta dauki wayar dake kidan A hankali ta dorata saman kanta ta tataro dukan jarumtarta ta yafawa kanta Irin wakar nan ta falguni da suke rawa da abu a kansu, sai kawai ta dan wara hannayenta ta ci gaba da rawar nan da iya kugunta ta juyi gare shi Baki daya ya kwalalo idanniwansa yana kallon ikon Allah, a hankali ta ringa matsowa kusan shi tana mai bin wakar nan a sanyaye sannan da hannunta na dama tana mai nuna masa kan ya matso gareta tana dan tare wayar kar ta fado da kanta bata sana hannu ba hakan ya sa idannuwansa ke yawon binta du inda ta dan juya, uwa uba da gaya sai kawai ta dan juya ta kara kada mutanen da kyam sai ya bi su da kallo sannan ta juyo har ta idasa zuwa daf da shi A hankali ta dan kara tsayinta ta yo dadage duda bata kamo tsayinsa ba sai kawai ta dora yar yatsarta tun daga saman goahinsa kamar yanda ya yi mata a jiya ta shiga yawo da ita har ta kawo wajen lebunnansa, a hankali ta zazagaya lebunnan nasa sai kawai ta saka dayan hannun ta dan kamo bayan keyarsa ta yo kasa kadan da fuskarsa A hankali ta kusanta tata fuskar kusa da tashi, baki daya ya sakankance ya gama shiryawa harta da bakinsa ya saki tsabar masifafen mamakin dake shirin kaishi kiyama bai shirya ba sai kawai ta kawar da lebunnanta daga daf da fuskar tasa ta mana masa peck a kunci sannan ta yi wani irin zabura ta yar da wayar a nan ta shige bayi a guje wanda a lokacin da ta yi hakan bai san inda kansa yake ba ya sakankance ne jira kawai yake Baki daya ya kara kwalalo idannuwansa, murya a shake ya bi inda ta shige da kallo Hasbunnalahu wani'imal wakim ya fada a bayane yana dafe kirjinsa dake wani irin dokawa fat fat fat tamkar zai ballo ya fito masa A hankali ya ja kafafuwansa da sukai masa nauyi ya karasa kusa da bayin ya dan dora kansa a jikin kofar, muryarsa cen ciki ya ce" open the door Beebah " NAJEEBA ta dan zaro ido, sai kuma ta makale kafadunta kamar yana ganninta tama ki yin magana kwata kwata A sanyaye ya kara furta" plz " Bakinta ta dan tabe , sam ta ki nuna da ita a wajen SHAHEED ya kara dora kansa sosai , muryarsa na kara bacewa sai sanyin dake neman lulube shi , hannayensa na bari kadan kadan ya dora saman abin budewar muryarsa har rawa take ya furta" kina son kashe ni ne? " Tabatawar da ta yi ta kile kuma ta bar kys din a jiki ya sakata matsawa ta cire pant dinta ta haye masai abinta ta gyara zamanta SHAHEED ya dora hannunsa da dan karfi ya ce" ki bude min BEEBAh, ki bude min kar ki ilatani i beg u " Dan idannuwanta ta zaro jin muryarsa ta fara baci, ta kara gyara zama a hankali ta ce" ehem " Irin gyaran muryar nan idan kana bayi SHAHEED ya lumshe idannuwansa yana jin yanda kansa ke sarawa haka kuma bugun zuciyarsa na kara girmama, a sanyaye ya ce" idan har na shiga bayin nan, sai nai maki fila fila BEEBAhhhhhhh " Bakinta ta tabe tana kara kallon wajen da ta kile ta ci gaba da neman uzurinta ah tom Ransa a bace ya budi baki da karfi ya ce" Oh gidan nan, jama'a wani dan abu ne ya rike ni😭😭😭😭🙄🙄🙄 [31/03 à 22:01] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 59 Ransa a bace ya budi baki da dan karfi ya ce" BEEBAHHHHHHHHHHHH " Sai da ta dan zabura a hankali ta ce " Um? " Shaheed ya dan sasauta muryarsa ya ce" Bude min kin ji? " NAJEEBA ta makale kafadarta, a hankali ta ce" to ban gama ba ai " " Me kike yi? " ya tambaya idannuwansa a lumshe Ido ta zaro, sai kuma ta shiga guna guni Kasa kasa ta ce" kuma sai kawai na ce maka ga abinda nake yi fisabililahi SHAHEED , to wai idan na fitoma me zan maka ne da sanyin safiyar nan? " Shiru ya yi, shiru mai dauke da ma'anoni, sannan yana sauraron irin yanda zuciyarsa ke doka masa dan wani takaici A hankali ya juya ya shiga jan kafafuwansa yana dan dama bai shigo dakin nan ba, da da ya ji kidan nan daga kofa ya tsaya ya yi magana, aman sai kawai ya wani shigo kansa tsaye Tabas shi din ya jima da yin aure, ya jima da sannin mace, sai dai fa wani baban lamari na rayuwarsa a kalmar mace ba wai macen da zai yi wasa da daria da fahimtar junna da komai bace, aa , shi ya sa a yanzun da wannan yar ta AMMI ta masa wannan lamari sai ya shige shi ba haufi, Ya jima yana kai kawo a dakinsa kafin ya nufi bayi ya shiga kintsa kansa domin kuwa zai je fada ne yau su yi zama na musaman da baki daya fadawa , zaman da ya saja kowa ya amsa kira a kan lokaci idan ba haka ba komai zai iya samun wanda bai amsa kiran ba daga hukuncin cikin fada Sosai ya sha shirinsa ya bayana dawisunsa sai baza kamshi yake abinsa duda dan haushin yar gidan AMMI da ta rikita masa lisafi da sasafen nan, lebensa na kasa ya cije yana kallon kofar a ransa ya ayana 'zaki yi bayani ne' ya yi kwafa ya ci gaba da tafiarsa hankali kwonce ya fice Najeeba kam sai da ta tabatar sahu ya dauke sannan ta sauka ta yi wankanta tsaf tsaf abinta Akwatinta ta buda ta ringa dubawa da kyar ta samu atampa sket da riga, du sai aka zuba mata wasu manyan kaya shada, lesh, da alkyaba, sai kayan baci, da kyar ta iya ciro atampa Wajen turaren nan ta koma har washe baki take ta dildila abinta a jikinta sannan ta saka riga da sket dinta suka zauna dasss a jikinta Zuwa yanzun tafiarta ta daidaita sannan ta samu nishadin safiar nan abin ba'a cewa komai hakan ya sa ta kashe daurin zarah buhari mai hade da ture ka ga tsiya sannan ta zauna da wayar ta danna kira ZAHRAU kamar jira take, cikin kamilaliyar muryarta da a yanzu ita take magana da ita wa kowa ba sai iya mijinta ba ta amsa salamar NAJEEBA NAJEEBA ta ringa mata daria tana fadin "Aunty ba salama, hala wai ko kayanki baki dauka ba? " Zahrau ta yi dariar itama dan a yanda take shakiyancin sai da ta sakata dariar dole, ZAHRAU ta ce" ke ina Ummu suke ? " Najeeba ta ce" yanzu zan tarda su mu yita ta kare, rabonsu da ni tun da na farka na ganni a dakin SHAHEED, shine basu leko ni ba, ba waya har yanzu, irin sun manta da ni din nan ko sun goge ni a layin kanwarsu ko? " ZAHRAU ta ce" NAJEEBA yaya Sultan din ne kike kama sunnansa kai tsaye haka? Idan ya ji ki zaki yabawa aya zakinta " Najeeba ta yi yar daria , aman bata sanar mata sirrin abinda ta gama masa yanzu ba, sai dai kawai ta ce" Ba abinda zai min domin ni a Shaheed na san shi, ya buga kwalo da ni, ya ci namana , ya kwacen ice cream dina, dan haka sunnansa SHAHEED " Murmushi ZAHRAU ta yi itama, a hankali ta ce" Ke yarima fa yana aeroport, kuma su UMMU basu sani ba, hasalima ko mahaifiyarsa bata sani ba, mahaifinsa dai ya sani sai kuma ni, jiya har kusan karfe goma ya nemi izinin son ganninsa, to yana bangarena shine ya same mu a nan ya duka har kasa ya kara neman gafara sannan ya nuna ya gaji, ya kasa iya hakuri , shifa ba abinda ya zuba a jikinta da za'a ce sai an ga idan bata da komai na wata uku, shi a bashi matarsa , yana son ya kara neman yafiyarta gashi ga ita, tabas tana amsa sakonsa ba laifi yanzun aman shi ba haka yake so ba, magana sak yake so su ringa yi ta fahimta, shi kam a bashi damar zuwa zance , Walahi Najeeba baki ji yanda kunya ta titsiyeni ba, aman mahaifinsa sai ya ringa sakin murmushi harda su gyara zama ya wani ce" ka je abinka, ka lalabata Allah ya sanya alkhairi " , maganar da nake maki dai yanzun yana aeroport shi ke jiran jirgin da zai yi damagaran da shi, yau babuma jirgi fa aman na sojawa zai bi tsabar ya saka rigima a ransa " Murmushi NAJEEBA ke saki tana dan dage girarta, ta ce " muna jiransa, yanzu kuwa zan je na same su , baki san wani abu ba, ashe amintace maci amana ne ?" Ai kuwa Najeeba ta kora mata labarin yanda aka yi, wanda hakan ya matukar girgiza Zahrau, ta yi mamaki sosai, sannan ta masu fatan shiriya, ta jinjina karfin sarautar garin damagaran da rashin tsoron SHAHEED da ya iya yanke hukunci a kan yar sarki, jikar sarki kai tsaye haka, ta ji tausayin NADIA matuka, harma ta baiwa kanwarta shawarar dan Allah kar ta yi fada da Nadia NAJEEBA ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba har suka kashe Sai bayan sun kashe ta yi shiru tana nanata sunnan Nadia a saman lebenta Bakinta ta dan tabe ta mike ta dauki hijab ta saka ta kashe komai ta nufi bangaren AMMI hankali kwonce ko kari bata tsaya dubawa ba da ake ajiyewa karfe takwas Ai kau tana zuwa ta tarar da su yau a saman cafet suke sunna cin abinci hankali kwonce Gaishe da iyayen ta yi cike da kulawa suka amsata, ta cire hijab din ta yi wuli da shi saman kujera ta zauna hankali kwonce sannan ta zuba abinci a plate ta kai dubanta wajen yayunta ta ce " An gaishe ku " Daria suka saka kasa kasa jin irin gaisuwar nan ta bosawa wai An gaishe ku Sai dai basu gama dariar ba, da murya na yi mata rawa ta ce" iiina kwana NAJEEBA " Da mamaki Najeeba ta kaleta, kaikaikai Nadia ce ke gaisheta? Me hakan ke nufi? Sai dai bata nuna wani abu ba saima kallonta da ta kara yi Murmushi ta sakar mata ta ce" tsakaninki da Allah kunyar su ce ta sa kika gaida ni ko kin haukace? In ba iskanci ba Nadia yau kuma ni zaki gaida? Tunda Allah ya halice mu baki taba gaida ni ba, kin ga bana son iskanci ni walahi " Murmushin ne itama ya kubce mata, harda sauke ajiyar zuciya ta samu kanta da kai lomar abincinta wanda tun dazu ta kasa ci hankali kwonce sai jujuyawa take NAJEEBA ta ce" yaya kafarki? " Nadia ta amsata har wata kwallar farin ciki na son zubo mata ta yi gagawar kokarin mayar da ita gannin hararar da ta wanka mata wace ta tabata ta kwalar ce Kamar daga sama UMMU dake murmushin farin ciki ta ji NAJEEBA ta ce" wai lafia yau Mama ta yi wannan kwaliyar harda saka jan baki ko ni daya na fahimta? " Ummu ta zaro ido ta ce" NAJEEBA ina ruwanki? " Ai kau Ummulkhair da yake itama yar rigimar ce sai ta shiga kilkila daria ta ce" ke yau ne fa, ai na fada maki kin ga shadar da Abih ya saka yau tun karfe shida ya zo gidan nan" Najeeba ta zaro ido, UMMU ta rankwashi kan Ummulkhair ita kuwa ta rike kan tana kwalkwal da ido, yan uwan kuwa sunna ta kilkila daria AMMI ta ce" wato yau ku duka kun takan dokar cin abinci ko? Najeeba zaki min shiru a wajen nan har cikinki ya koshi kafin ki min surutu" Shirun sukai aman Najeeba sai sauri take ta gama Tana gamawar ta dauke plate din ta kai shi kicin ta wanke ta ajiye ta fito Tun kafin ta zauna ta shiga ratabo abubuwan da ta zo da su, maganar zuwan Yarima, fadan a kan me basu lekata ba, tambayar yanzun wace makaranta yar uwarsu take domin ta tafi school, ta idasa da fadin ya dace su kira makadin da zai masu casun auren soyaya Yanzun kam AMMI din ce da kanta ta kilkile da daria ta dauki dan filow din kujera ta jefawa Najeeba ta ce " ja'ira " Ummu kam wata irin kunya take ji, wace da safen murje idannuwanta ta yi tasss ta fito abinta aman yanzu NAJEEBA du ta sakata jin wata irin kunyarsu walahi ....................FADA................ An gurfanar da sarkin Bulala dake rusar kuka tamkar ransa zai fita yana magiya da fadin shi bai taba yarda da maganar kisa ba Sabon sarkin dogarai ne ya doke bakinsa cikin wata irin razananiyar murya da tsoratarwa ya ce" tuf, rufe mana baki maciji! Yi mana shiru mai fuska biyu, da na halak baya cin duduniyar uban gidansa koda kuwa za'a karsa idan bai bada hadin kai ba, tunda har ka rike shi ka kasa fada mar Sarkin Damagaran ai mai sauraronka ne, na so ace a nan za'a bara min kai da ka bambance horo shashanci " Kara hade hannayensa yake yana rusar kuka da magiya, Shaheed ya dago idannuwansa daga yannayin zamansa na saraki ya sauke dubansa a kansa, irin yanda suke nema masa aduwa da sauransu , suke fatan Allah ya huci zuciyarsa du gasu a zube a gabansa sai ya dan juya kai cike da haiba ya ce" Na yafe maka " Baki daya mamaki ya saka su dagowa, bai kasa da gwuiwa ba wajen furta" ku daina hantararsa, ku daina wulakanta shi, ku bar shi da halinsa " Da sauri sarkin Dogarai da yake wani irin jibgegen katon da ya ninka amintace a kirar da kamar mazan da dakiyar ya kai gwuiwarsa kasa ya hade hannayensa , cikin wata zaburariyar muryarsa ya shiga" Adali ne, dan halal ne, shi daya ne tak irinsa babu, Gafara dai malan dan malan jikan malan, gafara dai mai gida mai dawa, mun yarda cewar a saman hanya ka kwana, mun ruguje mai sauko min mangari mai harara, takawarka lafiya bijimi uban gaya, ya karba ya gode, Allah ke kare gabanka da bayanka, sannu sannu sarkin sarakuna, mai dogarai a baba dogarai ya gaishe ka ubana " Da kansa yake amsawa har aka kama sarkin bulala aka fitar da shi daga fadar Zama aka kara yi , zaman da aka gabatar da nasiha mai ratsa zuciya, aka gabatar da sharuda masu girgiza munafuki, aka tashi a kan magana daya cewar du wanda ya taka doka zata taka shi! Daga nan masalaci aka shige dan gabatar da sallah, bayan an gama ne aka mayar da auren NANA MARYAMA UMMU, DA ABIH WATO ELHAJ MUTALAB gaban dubin jama'a ciki harda yayan Mardiya da bai san da zancen ba, suka hadu kuwa suka ringa taya shi murna domin sam hakoransa sun kasa rufuwa murmushi yake abinsa hankali kwonce A lokacin da SARKI ya mike sunna dan takawa da kimah, dogarai na tafe da lema baba wasu da bulalai gaba da baya sunna tafe a hankali, haka kuma masu kira na yi Liman ya ce" ALLAH ya taimake ka, sai nake gannin kamar bai dace a saki sarkin bulala na da haka a cikin gari ba, idanfa ya kara aiwatar da wani cutar ta hanyar hada baki da wani a cutar da kai? " Sai da SHAHEED ya kara taku kamar biyar sannan ya dan ja ya tsaya, Hannunsa mai dauke da zobunnan azurfa biyu na dama ya mika ya kama hannun Liman cikin rawaninsa, a sanyaye ya ce" ALLAHN da ya fargar da ni kan wannan yinkurin cutar da ni din da suke, shi zai kuma kare ni Liman, na tabata ba abinda ke samun bawa face wanda Allah ya hukunto masa, ban raina mutun ba, na san ba abinda mutun ba zai iya shukawa ba, sai dai kuma na yarda cewar akoy wanda ya halici mutun, shi yasa nake kai masa kukana kan ya hanna, ya kare, ya kuma kiyaye jinnin ALIYU " Murmushi ya yi yana gyada kai, ba shi ya juya ba hat sai da suka karaso kusa da bangaren Ammi sai shi ya ja ya juya, aman kuma a lokacin Yarima ya iso, hakama da manyan mutanen da suke tafe dan su shigo su yiwa AMMI ALLAH sanya albarka Kasancewar shine a gaba sauran na take masa baya , sai da ya fara saka kansa Sai dai maimakun ya bada hanya jama'a su samu shiga sai ya juyo ya yi tsaye a kan kofar ya kasance mutanen suma du suka tsaitsaya sunna kallon sa Sarkin dogarai ne ya karaso ya duka sosai ya shiga tambayar ko da abinda ya manta ne a je a dauko? Sai dai bai ce uffan ba, hasalima lebensa na kasa a dan dantse yake ya yi shiru bai bada amsa ba Gannin haka ya saka sarkin digarai mikewa ya shiga salamar mutane, yana mai fadin sako zai ishe GIMBIYA , sarki na godiya Haka dai du aka watse saura Yarima da shi, SULTAN ya dan yi gyaran murya a hankali ya ce" dan dakata ina zuwa " Daga haka ya juya ya shige falon da tun shigowarsa ta farko yan matan suka nutsu, UMMU kuwa mikewa ta yi ta shige dakinta dan iya shegen yan matan nata kam yana beman hanna mata zama , AMMI sai daria take tika abinta nishadi take ciki sosai kasa suka zube suka shiga gaishe shi, Bai amsa ba daga tsayen da yake yake bin su da kallo A hankali ya ce" Ummu, ki tashi ki shirya, yar uwarki ta raka ki bangaren saukar baki ku gaisa da yarima, kar ku jima " Daga haka ya samu waje ya zauna ya maida hankalinsa wajen mahaifiyarsa Ciki suka shige su uku, aka bar Nadia zaune kanta kasa, da yar uwarsu wace ta taso daga school nesa kadan da su aman su dukansu sun nutsu sosai A cikin daki kuwa dama a shirye suke, sai kawai suka kara kawata shirin Ummukulsum, wace jikinta du a mace yake, karara ta nuna masu tsoronsa take ji, aman sun ki su bata dama hasalima suna karfafa mata gwuiwa ne A lokacin da suka fito sai baza kamshi suke Niyatsu tafia ne tatare su duka sai da AMMI ta yi kirran sunnan Najeeba NAJEEBA na tahowa da hannunta ta nunawa biyun su tafi, Boyayiyar ajiyar zuciya ya sauke, domin tun shigowarsa yake satar kallonta, a lokacin da du suka duka har ita har Nadia, haka kuma da suka tashi sukai ciki bayanta ya bi da kallo, a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake 'na shiga uku ni kau da yarinyar nan, so take ta masheni wani wawan namiji da alamu' Tana dawowa ta dan duka wajen AMMI daga gefe tana mai fadin" Na'am Ammina? " AMMI ta yi mata murmushi tana shafa gefen kumatunta, bata ce komai ba ta mike tsaye ta kama hannunta ta zaunarta a nan, sannan ta kamo na Nadia da Ummi ta zaunar da NADIAR kusa da ita kadan sai kuma ta tafi da ummi din rana dan masu murmushi dan kuwa maganar da ta gama masa kennan kan ya dace su yi zama irin wanda ake yi, su yi magana ya masu nasihar zaman lafia sannan ya raba masu kwanaki bisa shawararsu, idan ya so Nadia ta koma dakinta itama auntynta na nan tafe idan an jima dan ta yi waya ta fadi abinda ya tsayarta bata gama hada kayanta bane Shiru ne wajen ya dauka, tamkar ba kowa haka wajen ya dauka, su dukansu kawunnansu a kasa yake sunna kallon kas, shi kuwa tamkar bai san an yi ruwansu ba ya share su yana zaunensa dai kikam abinsa A hankali NAJEEBA ta dago dan walahi wuyanta ya sage ta kai dubanta wajensa, ido hudun da sukai da wannan kallo nasa na tsana da yake binta da shi ya sakat kawar da dubanta tana turo bakinta gaba, a kasan zuciyarta ta shiga fadin 'shin yaushe zai bar yi min kallon tsana ne ni ' Shi kuwa kuma binta da kallon ya yi, shima ayannawa yake 'kamar ba ita ta gama min rashin kunya ba, ko me ta yi a bayin ?' Ajiyar zuciya ta dan sauke a hankali ta dan yinkura ta fara mikewa Sai dai bata rigaya ta idasa mikewar ba muryarsa ciki ciki ya ce" idan kika tashi a nan sai na baki mamaki BEEBAHHHH " Bakinta ta kara turowa, wai me ya sa ya cika son takurawa rayuwarta ne? Ta ga dai ba maganar za'a yi ba, ai sai a barta ta kara gaba ko? " Yaya kuka tsara kwanakinku " ya fada yana kara juya dan zoben dake yatsarsa yana mai tsatsare su da ido tamkar zai dauke su da shi, barema NAJEEBA wace du ta takura ta gaji da hararanta da yake Nadia ta kasa yin magana, dan a tunaninta Najeeba ya dace ta yi magana, ita kuwa itama ta yi shirun dan kuwa bata tunanin wannan hukunci na matar karshe ne Shaheed sai ya fara tunanin shin raini ne ko me ya sa basu yi gagawar amsa shi sunna dukar da kai kamar yanda Zinaria ke yi ba? Sun wani dake sunna basarwa? Bayan ya yi magana daya dari suke jira ya masu? Hannunsa ya kai wajen goshinsa a hankali yana dan murzawa, kasa kasa ya ce" ya zama wajibima na maido matata sannan na dauko wata dan ba zan dauki wulakanci ba " Su duka suka dago sunna kallonsa, sai dai Nadia da sauri ta sada kanta, NAJEEBA kau dan kurawa fuskarsa da ta yi ja alamun gajiya na tatare da shi ta yi Muryar Nadia na rawa rawa ta ce" ka , ka yo hakuri dan Allah mun tuba, Najeeba ce ta dace ta fada ko ko ka zaba mana koma yaya ne ya mana in sha Allahu " A hankali Najeeba ta maida dubanta kan Nadia, zata iya rantsewa bata taba jin wani abu ya tsirga mata mai kama da wanda ya tsirga mata a yanzu a kan Nadia da furucinsa ba Idan bata manta ba a Jiyama ya yi maganar sai ya karo aure aman bata damu ba, sai a yanzu da ta lura da furucinsa kamar irin na serieus din nan ne sai ta ji wani irin lamari na kamar bata ji dadin jin hakan ba, sannan tana kallon Nadia sai ta ji wani iri, wai yanzu Nadia ce kishiyarta? Wace suka hada miji tare? Yanzu abinda ya yi mata a shekaran jiya Nadiama ya mata? Akoy wasu manyan kalamai da ya furta mata wa'inda har yanzun idan ta tuna sai ta ji wani irin yar yar yar, shin itama Nadia haka yake fada mata? A hankali ta fara watsi da kalaman, ta fara kushe su da rage masu karfi a zuciyarta bale har su lahantata Kuma duban Nadia ta yi, ta san wacece Nadia, a da Nadia kan cewa ita burinta ta auri mai mace ta yanda zasu gwabza rayuwar kishi, kowa halinsa ya kwace shi, ita kuwa sai tace bata son mai mata domin bata taba tunanin wani ya tauna nama ya bata ta tauna itama Idannuwanta ta lumshe, haka kawai sai ta ji wani irin abu na sukarta a cikin idannuwan nata, a hankali ta dago jin ya daga waya muryarsa kasa kasa yana magana da alama da Yaya Dayabu yake wanda ya shiga garin Niamey a jiya kafin ya ajiye ya dago subansa su yi ido hudu Janye nata idannuwan ta yi cike da jin haushinsa, haka kawai ta ji wani irin haushinsa ya tsirga mata, wai yanzu zaunar da su ne ya yi yake fada masu zai kara aure? Me yake so su ce da shi? Da su suka saka shi hukunta matarsa ne,? "Ohk, fine" abinda ya fada kennan kuma ya yi shiru na wani lokaci kafin ya dora da fadin" ki fada min yanda kike so Nadia " Kanta ta dago ta kuma kallonsa a karo na ba adadi sannan itama ta sauke ajiyar zuciyar, ta maida dubanta wajen NAJEEBA ta ce" dai daya ya yi ko Najeebana? " NAJEEBA ta lumshe idannuwanta ta komar da bayanta a hankali ta jingina jikin kujera, kanta ta iya dan dagawa a sanyaye sannan dake Sai Nadia ta ce" Alfarma nake nema Allah ya taimake ka, kafata bani da lafia bana iya komai da ita dole sai nai jinya, idan har da hali ina so idan auntyna ta zo mu je gida tare, ba dan na raina kokarin AMMI ko gazawarku ba, MAMA yanzun ba zata kuma zama da mu ba, ni kuwa na tsorata sosai, ina neman alfarmar na je koda sati daya ne na kara warwarewa....." Ta idasa maganar tana sada kanta kasa Shaheed ya kwashe minti biyar yana nazarin maganarta, ta gama sarewa cewar ba zai bata amsa a kan hakan ba, sai ji ta yi ya ce" wani wajen maman ta ce da ke zata tafi ?" Da sauri ta dago kanta tana girgizawa, sai kuma ta mayar ta sada cike da tsoro, ita a ganninta an maida auren mama me zai sa ta kuma zama a nan kuma? Shaheed ya lumshe idannuwansa yana kallon NAJEEBA, haka kawai yannayinta sai ya ringa taba nutsuwarsa, wannan dakewar da ta yi sai yake so ta dago koda tsokana ne ta yi yana kallonta Dan ya kara kular da ita, wanda ya tabata sai ta kale shi , haka kawai jikinsa ke bashi idan ya fadi haka zata kale shi Sai ya ce" Ni kuwa na yi baci ta yaya bayan kina nesa da gidana ? " Da wani irin madaukakin mamaki NADIA ta kai dubanta kansa, a lokacin kuwa ya yi iya yinsa ya cire dubansa daga cikin idannuwan Najeeba ya dora kanta ya sakar mata san murmushin da ya sakata jin wata irin nutsuwa a cikin zuciyarta Tana sada kanta ya maida dubansa kan fuskar Najeeba, ya ci gaba da fadin" idan ta zo zaku tare a bangaren da ba'a bude ba, na kusan bangaren BEEBAHH, a cen za'a baki dukan kulawar da kike so, sannan zan saka jakadiya ta kai maki kati biyar kina iya rabawa wa'inda kike son su ringa shigowa gannin ki, aman fa daga satin nan zaki dawo nan ladanki " Murmushi ta saki tana kara rage tsayi daga zaunen da take ta ringa gabatar da godiyarta A hankali ta kai dubanta wajen NAJEEBA, sai dai gannin idannuwanta a lumshe sai ta shiga kokarin mikewa dan zuwa ta amshi maganinta, sanan ta tabata zai bukaci yin magana da matarsa Tana tafia a hankali ya maida dubansa sosai kan NAJEEBA, kallonta yake da kallo irin na son dole ya karance ta A hankali ya ciciba daga inda yake ya koma kujerar dake kusa da ita ya zauna Hannunsa ya dora saman nata dake jimke kadan saman cinyarta hakan ya sa ta buda idannuwanta a karro na biyu sunna kallon junna Muryarsa ciki ciki sosai ya ce " sai na ga kamar ranki ya bace dan na yabi matata " Dan yawun da take tunanin ta bari a bakinta ta tatara ta hadiye da kyar sannan ta fuskance shi, itama a sanyayen ta ce" anya ba sai ka je asibitin idannuwa ba kuwa? Domin dai idannuwanka sun fara baka gannin da ba daidai ba " Kallonta yake bai bata amsa ba Sai da ta ja hancinta a hankali ta dora da fadin" yaya zaka yi tunanin zan bata rai a kan auren da biyaya nake kawai?, kamar yanda baka so inaga nama fi ka so, dan ka san yanke min nishadi aka yi rana tsaka " Bata karasa maganar da take ba ta ji saukar lebensa a kan nata, idannuwansa kulle sosai ya kama lebenta ya shiga basu wani irin horo mai zafin gaske wanda ya sakata saka hannunta tana ta son ture shi, aman ko gezau saima da ya ga dama dan kansa ya sake ta Bai yi nisa da fuskarsa a jikin tata ba ya tsatsareta da kakausar murya ya ce" dan ki gane idan mai wuri ya zo dole mai tanarma kan nadewa, beebah ko kina mutuwa kina farfadowa ne kin harmatarwa wani, koda kuwa zaki hadiyi zuciya ne sai kin dandani azabar da kika kwashe shekaru kina dandana min, beebah meye samari basa fada maki, wayarki a hannuna sakon tsohon cen ya shigo cewar ki bashi nutsuwa?, sannan baki dadara ba kike ci gaba da neman fitina a gare ni, ba zaki gane ba, ba zaki taba gane komai ba, aman ki sani ina daf da dauke numfashinki ki dawo na kuma dauke shi ta hanyar hade bakin ki da hancin ki na rufe ki suma harma ki leko kiyama idan ta kama, domin ni narka min dalma da kike a wajen da ba zaki taba hasashe ba a sannin kanki ya fi karfin sumarki, beebah ina maimaita maki ki bar balaki ya yi baci, idan ba haka ba zaki haka mana ramin da zamu rufta ya halaka mu !" Ya karashe maganar da kakausan murya tare da dantse lebenta na kasa da dan karfin da ya sakata fashewa da kuka ta saka hannayenta bibiyu ta shiga dokawa a kirjinsa ido ryfe ta ce" My kaina😓 [31/03 à 22:01] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 60 Hannayenta bibiyu ta shiga dokawa a kirjinsa idannuwanta rintse tana jin wani irin tashin hankalin take sukar mata kahon zuciya, meye wannan? Me ke damunta haka? Me ke kara gudun zuciyarta ya dada mata zafin jiki ya hasasa mata fitar numfashi da sauri ya sababa mata bacin rai a kan furucin farin mutun mai mata SULTAN SHAHEED ne? So take ta buda idannuwanta ta samu karfin gabatarr da fushinta a kansa, aman a irin abinda take ji da zufar da take fitarwa sai ta fara tunanin idan har ta buda idannuwanta tabas idannuwansa masu dauke da zanen kwali zasu hadiye nata hadiya irin wace maciji kobra ke hadiye dan uwansa a lokacin da suka tsinci kansu a waje na rashin abinci, zai hadiye su ne murus ta yada zata rasa idon duba a gabannan Tsoron hakan ya sakata idannuwanta a rufen nan muryarta a zafafe ta ce" Ni balakin nake so na tayar, ta yanda zamu rufta a ramin nan kasa ta rufe kawunnanmu kowama ya huta " ! Sai kuma ta sanyaya muryarta a hankali ta kai kanta saman kirjinsa, wanda ke rufe da riga ta ciki da malun malun sai fitar da dadadan kanshin nan yake, muryarta a sanyaye wannan karron ta ce" Kana shigo min da garaje, kana taka ni da takama, shin meye ya sa kake son nunan takama ne bayan ni ban san wani sarki ba a miji? SHAHEED na san cewa kake bani da kunya, na cika tsauri, bana so ka daina tunanin hakan domin bana tunanin zan kasance mai yi maka kirari" a sanyaye ta idasa tana mai dora dayan hannun nata a saman kirjinsa wanda hakan ya saka shi lumahe idannuwansa yana jin kalamanta, Wani irin yannayi yake jin kansa, tun daga kan kwakwaluwarsa har zuwa zuwa cen kasan zuciyarsa, lamarin mai girma ne mai tafe da abin kunce balakin da yake mata ikirarin ta barshi ya yi baci, wannan lamari ya kire ahi balaki ne tun daga ranar da ya samu fasarar abinda ke damunsa game da wannan yarinya mai halayen yan nanaye, sai ya dauki lamarin nan ya yi wani irin katon akwati mai matsatsen ciki ya saka shi, ya saka katon makuli ya rufe shi, ya yi ta kara jibga masa jibga jibgan laifukanta ta yada zai kara matsanancin nauyin da babu mahalukin da zai iya tashinsa harma ya bude shi ua falasa sirrin da ya boye a cikinsa Sai dai kash, gashi nan rana tsaka, a irin lokacin da bai shirya ba bayannuwarwa a rufe ruf ya watsar da kaso saba'in a kan dari na laifukanta, hakan ya sa du wani kusanci nasu ke girgiza laifukan nan harma ya fara jin barazanar dake son mayar da shi wani dan yaro, Lebensa na kasa ya dan cije a hankali yana jin yanda take sauke ajiyar zuciya, a hankali ya dan lumshe idannuwansa da sukai masa ja, ya kara bata kyakyawar rungumar da ta sakata yin lamo a jikinsa Bai ce da ita komai ba, sai mikewa da ya yi da ita a jikinsa Idannuwansa ya sauka a kan iyayen mazaunanta, masu wani irin tudu da fadi hakan ya saka shi lumshe idannuwansa a hankali ya kara riketa a jikinsa ya shiga dan tafia da ita ba tare da ya dauketa ko ya takura tafiar tasu ba Batai masa musu ba, haka kawai ta kasa yi masa musu din, ta yarda da binsa cikin zuciya daya har suka shige hanyar da zata sada su da bangarensa Bai zame ko'ina da ita ba sai saman kujera mai zaman mutun daya Shi ya fara zama kafin ya dorata saman cinyarsa ya kuma likata da kirjinsa ya mayar mata da kanta irin yanda ta yi da farko ba tare da ko ya cire malun malun din jikinsa ba A hankali ya ringa shafa ualwatacem gashin kanta, muryarsa ciki ciki ya ce" Yaya kike tunanin zan yi wasa wajen kawowa rayuwarki cafka?, ido rufe abokiya nake nema, koda kuwa zamu ringa fada ne, wace zata dube ni ta ce da ni SHAHEED nake marari, rashin kunyar NAJEEBA sai ta ringa sakani..........., Sai kuma ya yi shiru na dan lokaci wanda har shirun nasa ya sakata dan fara budaumsasun idannuwanta tana dan son dago da fuskarta dan ta kale shi, sai dai bai bata damar hakan ba ta hanyar mayar da kan nata a hankali ya ce" Ki yi komai ba komai yarinya " Dan murmushi ne ya subuce mata wanda daga cen kasan zuciyarta ne ya fito, harma aka ji dan sautinsa A hankali ta ce" zaka sakar min abokina? Bashi da wani laifi a fadan da aka yi ka sake shi, domin shi ke ciyar da mahaifiyarsa " Shiru ne ya biyo baya na lokacin mai dan tsayi harma ta cire rai da zata ji amsarsa sai ji ta yi ya ce" na tura shi daukan soja, idan ya fito sai na aura masa mata hudu, kin san ina son mutun mai son farantawa iyalina rai " Baki ta saki dan mamaki harma ta dago baki dayanta, irin yanda yake binta fa kallon kasa kasa ya sakata turo bakinta a fili ta ce" yanzu dan daudun ne ka kai daukan soja?" Bai bata amsa ba, a yanda yake kawai yake bin du wani motsinta da kallo har ta idasa mikewa gaba dayanta ta kara turo bakinta sosai a fili ta ce" Ba dai rigima kake so da ni ba? Zamu yi, zan fadawa Ammina a sako min aboki haka kawai? Malan walahi ni bana son tashin hankali, bana son fada da maza haba, ni kaucewa mutun nake aman ana bi na, garinka a dake yake a tankade daga kai har Nadiar , hasalima ba zan iya zama da mijin kawata ba! " Murmushi yake ta dokawa a kasan zuciyarsa, a hankali ya dan muzguta dan yana son cire babar rigar nan ya samu damar kallon drama girl din nan tasa hankali kwonce, sai dai hakan ya tsoratar da Najeeba a tunaninta mikewa ne zai yi a kanya sai kawai ta juya ta fala da gudun balaki ta shige dakinsa tana kokarin danno kofa Yar daria ce ta subuce masa ya raba bayanta da kallo har ta shige tana son rufewar, kansa ya ci gaba da dan jujuyawa a hankali a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake 'yarinyar ba dai kujera ba, ka ga sun hanna mata gudu yanda ya dace sai kwana take abinta yar rigimamiyar' Yana kokarin tashi ne wayarsa ta kuma daukan tsuwa Sai da ya cire rigar ya ajiye ya koma ya gyara zamansa a hankali ya ce" NAJEEBA, ki fito ki ciyar da ni na shigo da yinwa " Bakinta ta turo daga wajen da take, tana ta ayanna yanzu tsakani da Allah magana ne ya mata a hankalin nan kamar zata ciro daga bakinsa? To ita ta yayama yake so ta fito ta bashi wani abinci bayan yanzu ta gama zanenta hankali kwonce? Sai kawai ta yi mukus tana sauraron irin yanda ya amsa salama cikin nutsuwa kafin ya dan saurara Cen ya mike tsaye domin baya so ko da wasa su ji wani damuwa tsakanin junnansu, dan kawai yana gudun lamari na kishin mata ne A hankali ya ce" Allah ya ja da kwana, haka ne, kwarai laifin Zinaria ya kai wajen da ta ja har na bata saki " Ajiyar zuciya da wani huci mai dan zafi na takaicin gurbataciyar tarbiyar da y'ayan nasa mata suka samu daga wajen mahaifiyarsu, Muryarsa a dake ya ce" Gimbiya ki daina min ihu a kaina, idan ba haka ba zan dauki mumunan mataki a kan ki! " Shiru SHAHEED ya yi, domin ya fahimci muryar kukan da magana sama sama da yake ji na mahaifiyar Zinaria ne Sarkin Agadez ya ce" Alhamdulilah, Allah ya sa hakan ya zame mata izna da ita da dukan wani mai halayanta ko wanda halayenta ke baiwa sha'awa, Dan saurarawa ya yo kafin ya dan kara karya muryarsa ya ce" ina rokom Alfarmar a sasauta fushin, idan har da hali ta koma dakinta koda nan da shekaru ne " Sai da SHAHEED ya dan saki dan murmushi a hankali ya ce" in sha Allah, burina ta gane rayuwa, ta gane abubuwa kamar haka : Dan adam ba abin wulakantawa bane komai rashin arzikinsa ko mumunan kamaninsa, ina so ta bambance mahinmancin zaman aure da zama domin ta birge kawayenta, ina so ta koyi sannin cewa mulki ko sarauta kafin ta hau dubanta sula hau, kuma suka sauka suka bari, a yanzu a matsayinta na yar sarki matar sarki tana iya amsa kiran mai duka, za'a kaita ne daga ita sai farin likafani sai hali sai sallah, ta gane ita ba kowa bace ko a wajen Allah daga bakin sa'in da ta dage kai da fata ita ba zata bi dokokin Allah ba, ina so ZINARIA TA SAN RAYUWA : , ya dan nisa ya dora da fadin " hakan ne ya saka ni mikata ga gidan horo na ahalin cikin gida " Murmushi ya saki mai sanyi , kafin ya furta" Dama na san kai din adali ne, mai nazari ne, mai sowa dan uwansa abinda yake soea kansa, tabas na yi imani da cewa da ba dan ta samu gurbataciyar tarbiya ba da ta jima da fahimtar cewa adali, zababe, managarci ne Allah ya wanke ya bata, da ta jima da fahimta ta karba harma ta koyar da wata waye mijin da take aure, sai dai kash, sannan a gaskiya ka yi hakuri SULTAN SHAHEED, gidan horon Damagaran yar karamar aljannar duniyar mabukaci ne, ba zata taba shan wahala ba domin kuwa abubuwan da ta rasa kadan ne a ciki, zata dan hakura ne har a fitar da ita ta ci gaba da daukan banzayen hudubobi, ama idan har ta samu kyakyawan horo, zata je ta hada labari ne harma ta kwabi bakin du wani mai sakata aikata mugun abin, dan haka daga bakin lokacin da za'a samu sakamakon bincike cewar ba hannunta a rasuwar marigayiya da kuma kokarin son kashe yar uwarta za'a miko mana ita ne sai mu bata horon da ya dace ga marar kunya! " Wani murmushin SHAHEED ya yi, kafin ya shiga mika godiyarsa cikin jin kunyar sakar masa y'a da ya yi aman kuma shine har ya fahimce shi haka SARKI na ajiye kan wayarsa ya maida dubansa wajen mahaifiyar Zinaria dake ta rufe bakinta dan kar ta saki kuka tun karfinta domin kuwa bata so ko da wasa kishiyoyinta su yi gaba da ita Kai ya girgiza a kausashe ya ce" wato bawa ba zai taba yin asara irin ta yayi asarar uwar y'ayansa managarciya, tabas asarar kudi ko wata kadara ba zata taba kamo asarar rasa mata ta gari ba " Kansa ya dan girgiza a hankali ya warware nadin dake kansa sai da ya sauke ya ajiye ya ci gaba da fadin" meye wannan nadin? Me ke tatare da shi bayan tarin hatsari da tarin tashin hankali?, a wannan nadi bawa na iya haduwa da halakarsa, a wannan nadi kana iya kwonciya cikin fushin ubangiji, a wannan hadin zaka iya rasa lafiyarka, nutsuwarka, wadatacen lokacin kanka kai idan ka yi wasa harta sa ibadar ba zaka tsayar ba.....tabas nima wannan nadi ya min ilah, daga bakin lokacin da ya dauki girman kai, neman fitina, izgili, hayewa a kan matata da y'ayana mata, haka kuma ya hanna min wadatacen lokacin da zan ringa hankalta da irin abinda ke wakana da ahalina ta hanyar fahimtar yaya mu'amalarsu take da talakawana, da jama'ar garina koda kuwa sunna boyewa a cikin gida, a tunanina matar kirki nake aure da ita harma na kasa tunanin cewa tarbiya fa ba iya mace kawai ake sakarwa ba, dole ka kama a matsayinka na namiji, dole ka rintsa tsawatar da abubuwa da dama ciki kuwa harda iyalan naka....." Shiru ya yi ya sada kansa, cen ya dago yana bin su da kallo ya ce" sai gashi nima na baiwa mulki madaukakin darajar da iya shi kawai yake da lokacina, shi kuwa sai ya samu wannan damar ya yi min ilar da ya lalata min tarbiyar y'aya, ya kara baiwa matata kofar lalata tata tarbiyar ita kanta " Sai da ya share zufar dake keto masa sannan ya kausasa muryarsa ya tsatsare su da duban da du suka kara shiga hankulansu ya ci gaba da fadin"" Sai dai ba zan kuma sakacin nan ba, ina mai tabatar maku zan yiwa mulki rashin kunya ta hanyar kiyaye masa na yi masa jan ido na nuna masa mahinmancin iyalaina, da ni kaina, yarinyata mace ta aikata laifin da ya fitar da ita daga gidan miji, sanadiyar hakan zan kaita dakin horo na cikin masarauta cen cikin bangaren bayi! " Gaba dayansu abin ya dake su, ciki kuwa harda Zahrau da ta san da maganar rigimar aman bata san saki ba da kuma decision din mijin nasu Ai kam a yanzu sai Gimbiya ta kasa rike kukanta, a bayane ta fashe da wani irin kuka ta budi bakinta ta ce" me na yi da tsanani haka?, me ya sa komai ke son juye min kuma ake gannin laifina? Haba adalina, haba uban gidana me yasa a yanzu kake yanke hukunci mai tsanani a kaina? Haba aban yarimana, me ya sa kake son ido rufe sai ka wulakanta ni a gaban makiyana?, ka duba ka ga matar yarima yanzun ta sameni da kukan wai ya tafi Damagaram, shi SHAHEED din maimakun ya fara kiranka ya maka bayanin laifin da ta yi sai takardar saki ya turo maka maimakun kaima ka sakar masa kanwarsa sai ka bige da wani rarashinsa?, shin meye laifina ko na y'ayana dan mun ki kishiya?, kishi haram ne? " "Ki min shiru ko na sabauta maki halitarki na saba kamaninki na gigita kwakwaluwar ki a wajen nan ke Baratu!" Muryar Sarkin Agadez ta karade wajen ransa a bace ya dora da fadin" tir da matar dake takama a kan kowa, BARATU ni ne sarkin ama ko ni da kin samu da kin mulke ni, kar ki yi tunanin a zaunen da muke ban san komai a kanki da kan irin rayuwar da y'ayanki ke cakulawa a gidajen aurensu ba, idan baki manta ba a zaman da kuka yi a dakin Zinariya nazajen y'ayanki sun masu magana cewa idan suka kai gobe su kam kar su dawo masu gida, baki yi tunanin maganar mai tsauri bace? Ni na tura masu da sakon hakan aman sai kika kasa ganewa domin ke din banzar uwa ce!, kin kai ni wajen da zan dauki mataki a wajenki BARATU! Tabas ba zan zuba ki a cikin dakin horon bayi bisa hujata na kin yi sake da tarbiyar y'ayana ba, ama zan tura ki gida ki nuna masu halayanki, ki gwada masu wacece ke, su ga irin wulakanta sun da kike yi, na tabata mai martaba sai ya mayar da ke baiwa kaskantaciyar baiwar da bata da wata daraja domin kuwa sam baki da halayan y'ayan sarauta!" Yana gama fada a kausashe ya mike ya bar komai a nan ya nufi cikin uwar dakansa Gimbiya, wato BARATU ta rasa wani tunanin zata yi a zaunen da take, tabdijan, za'a turata gida? Da tsufanta gode gode da ita? Zuwa gidanma a matsayin a saka ido a halayanta? Ita kam ita ce zata he gidansu a haka? Lalle da ta gane bata da wayo domib kuwa yayanta dake kan sarauta sai ya nuna mata bata da wayo, mahaifiyarta kuwa dama mace ce da sam basa shiri tun bata kawo yanzu ha domin kuwa tun da ran mahaifinta take alwashi a kan halayanta, a yanzu haka sai su yi kwana uku basu gaisa ba, ba dan komai sai dan tana kiranta zara kama yi mata fada a kan rayuwa Tana nan wajen zaune har su Zahrau suka mimike suka bar wajen, domin su dai koda sun so rarashinta su nuna mata hanya ita din ba mai sauraronsu bace, idanma bata ce sun mata magani da mijinta ana son rabasu ba ai da kyau, hukunci sarki kuwa ya aiwatar da shi daidai yanda ransa ke so, dan kuwa kwarai hakan ne giyar sarauta ta dauki zuciyar Gimbiya da wasu daga cikin y'ayanta ta hura su ta yanda sun samu wani irin hauhawa da tunanin kaf duniya babu wanda zai iya kamo su ciki kuwa harta da mazajen aurensu dan haka sai suka yi gum suka kara gaba...... wuta ai ruwa ke kasheta! .......................................... Su UMMU basu dauki wani lokaci mai tsayi a wajen yarima ba, hasalima sun kasance masa wasu irin ababe masu daraja da wuyar gani, ya zamanta muryar Ummukulsum yake mararin ta buda baki ta yi ta masa bayanai masu dadin sauraro, sai dai bayan gaisuwar da ta shiga tsakaninsu sai kawai ta yi shiru abinta tana sauraron yanda suke gaisawa da Ummulkhair, Sai dai tarbiyar yan matan ta matukar tsaya masa a rai, jan ajinsu ya saka masa jin nutsuwa a zuciyarsa, uwa uba kunyarsu ta saka masa jin tausayin wace wannan lamari ya ritsa da su, sosai ya kara yarda cewa idan Allah ya taimake shi ya sameta a matsayin mata lalle ya samu nagartaciyar mace, zata tarbiyantar da y'ayansa, zata ja ragamar gidansa da kunya da kyakyawar mu'amala, shi dake dan sarkin sai yar bak'ar kanwar matar mahaifinsa ta zame masa itane sarauniyar, domin kuwa sai ya ringa dan takalo maganar da zata yi, har dai ya hakura suka rabu cike da begen son kara ganninta, aman ya shaida mata ba zai bar garin ba sai da amincewarta , wato ta bashi damar gabatar da magabatansa A daidai nan ne ta dan dago dubanta, ta kuma kallon zankadedwn yaron kafin ta sada kanta da sauro domin ya yi mata wani tsatsarewa da ido ne, a sanyaye ta ce" ai ba'a yi wata ukun ba " Dan murmushi ya yi ya bata amsa kamar haka" na san da ba sai an yi wata ukun ba, kema kuma kin sani " Hakan da ya fada ne ya sakata da sauro ta daga kafarta ta bi bayan yar uwarta har kamar ta ci tuntube, shi kuwa banda murmushi ba abinda yake harda sauke ajiyar zuciya Sunna karasawa kofar baban falo ne suka samu sakon su dakata Mai martaba na zaune da iyalansa, su kansu na kofar basu san cewa ya shige tuni da yar bak'arsa ba. ......................................... Mahaifiyar Mardiya dake zaune a saman tabarmarta a waje sansaya tana kallon yayansu Mardiya da ya kawo mata maganar daura auren MUTALAB ta sauke ajiyar zuciya ta kai dubanta wajen da Mardiya ta mike tsaye lokaci daya, Sai da ta kara sauke ajiyar zuciyar takaicin halayan yarinyar tata ta ce" Masha Allah, Allah ya basu zaman lafia, Allah ya bata ikon kula da y'ayanta bisa amana, ai ka gani hakurinsa ya masa magani, domin kuwa a labarin da na ji a kan ita matar nan tasa sun yi zaman amana, halin rayuwa ne da kuruci ya raba su, kadara dai ta Allah, tunda yanzun ta dawo gare shi Allah ya basu zaman lafia " Cike da datako ta karashe maganar, danta na murmushi ya ce" bakima sani ba ina, sai kin ganshi, kina gannin yannayin yalwataciyar fara'ar kan fuskarsa zaki gane yana cikin farin ciki, tabas mace ta gari ita ce sila ta zaman lafia " Su kam hira suke, basu san irin kokowar da Mardiya ke yi da numfashinta ba, basu san ta mike ba, basu ma san ta dan matso kusa da su ba, sai Karan ihunta da zubewarta kasa ne ya ankarar da su halin da take ciki Da gaske ta summa, summa ta yi, bata numfashi, Hankali tashe mahaifiyarta ta ce" Alhamdulilah ala kuli halin😊 [31/03 à 22:03] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 6 1 Cike da tashin hankali mahaifiyar Mardiya ke kallon yaronta ta ce" Summa fa ta yi da gaske, ka dauko mota wannan yaron mu kaita asibiti " Kansa ya girgiza ba alamun tashin hankali ko wani abin a tatare da shi ya ce" ina, idan har muka ci gaba da nuna mata ita din wata aba ce mai darajar da ta fi ta kowa to tabas ci gaba rashin mutuncinta zai yi maimakun ya tsaya, ki duba ki ga yanda rayuwarmu ta samu cenji sanadiyar aurenta da wannan bawan Allahn, mutumen nan bashi da bakin ciki, bashi da rowa, bashi da wariwa tsakaninmu, duba ki ga ya bani gida ga mota sannan ya nunan hanyar nema, a gaskiya idan har Mardiya zata ci gaba da haka da kaina zan nemi da ya salameta, domin kuwa darajarsa ta kai wajen da zan iya ture Mardiya na rungume shi, dan kuwa a duniya da mai mutunci nake iya zama, Mardiya kuwa idan tana so ta yi summa bakwai! " Baki bude ta raka shi da kallo, sai yayarta ce ta kama mata ita suka kaita daki suka samo ruwa suka shiga shafa mata Tana farkawa a firgice ta farka, bata tsaya adu'a ko wani matacen jiki ba sai wata ashar da ta luluka tana fadin" walahi basu isa ba, basu isa ba, daga ita har shi din basu isa ba, shine ba neman shawarana ba komai sai dai na ji a gari ya auri tsohuwar matar da ta je saudiya yawon kilakinta ta dawo, matar da tana magana idannuwa na mata rawa? Dama na san abinda ya kawota gidan nan walah8 dan ta asirce min miji ne, aman bata isa ba sai ya saketa shi dinma bai isa ba !" Mahaifiyarta ta girgiza kai ta ce" kaya, kaya, Allah wadaran naka ya lalace, to ki bi a sanny Mardiya kar ki manta igiya daya keal ta rage tsakaninki da shi, sannan da kike maganar bai isa ba ke a wa? Da acema matar mutunci ce ke sai a tausaya maki a kama maki harma ya ji tausayinki da nauyin fada maki zai kara aure, aman ai du mace mai irin halayanki sakamakonta kennan! Kuma da kike cewa ta je kilaki kar ki manta zato fa zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne, koda yake na kula ke din aikin zunubin ba yau ba kika bashi gaba ba baya ba, Allah ya shirye ki " Yayarta ta yatsina baki tana kallon yanda take cenza kaya bama sauraron maganar mahaifiyar tasu take ba har ta gama ta dauki yar jakarta ta fice bata tsaya jin komai ba Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta ce" inaga ban zame mata ishara ba, sai ta je ta kaso auren ta dawo mu layu idan wannan innuwar ta shige mu tarbi wata, kin ga ina bara na dauki yan cenjin nan na fara saro mana dan abubuwan batarwa dan kuwa na ga alamun yarki bata da hankali gwara mu fara nema kar abubuwa su cakude mana muna zaune yaya kuwa ga iyali sai hamdallah " Ita dai mahaifiyarta abin duniya ya isheta hanyar da Mardiya ta bi ta fice kawai ta kurawa ido To a wannan ranar du inda Mardiya ta san zata samu ABIH ta je harta da wajen abokannansa inda yake zama aman bata ganshi ba, karshe dai sai ta mayar da kanta dakinta ta tare tare da kudirin zaman jiransa dan kuwa ta tabata du abinda ba zai kwana waje ba, kuma a shirye take da su baki dayansu, zasu san su din kannanun mararsa mutunci ne, Wasa wasa tana zaman nan har karfe goma sha daya, karshema bacin wahala ne ya yi awon gaba da ita, a lokacin da Abih din ya dawo batama san ya dawo ba, shi kansa motarta ya bi da kallo ya tabe baki yana kara gwada kiran number UMMU dake masa wasa da hankali wai wani itafa ba wani dan soyaya ta dawo aurensa ba, dan mutuncin y'ayanta ne, dan haka karma ya wani yi tunanin dan wani abin ne ta dawo masa! Wannan takaicin ya saka shi bacin shima ba tare da ya ko kula bangaren Mardiyar ba. ....................................... Karfe dayan dare da yan mintunna kennan, du wani bawa mai dauke da gajiya yana kwonce a irin wannan lokacin yana dan hutawa koda kuwa mai yawan nafilfilu ne kafin lokacin motsawarsa ta yi ya gabatar da nafilar dare Sai dai kashh, banda SULTAN SHAHEED dake zaune saman kujera mai zaman mutun daya ya kurawa waje daya ido Ya kai ruwa ya kai tsaki, ya kuma kai kansa kasa ya roki Allah kan ya kama masa, domin yakan rasa baci a idannuwansa a irin lokuka irin wannan, yakan zama mai cike da tsoron Allah da tsoron haduwarsa da ubangijinsa, yaya talakansa zai kwanta? Shin yaya bayin Allah ke rayuwa a kasarsa? Ya jima rabonsa da ya yi bada kama ya shiga gari, ya zama wajiba ya koma rayuwar bada kamar da yake yi yana cakudawa da al'umar Damagaran, ta hakan yake sannin yawancin matsalolin dake faruwa a cikin garinsa, Bai ji motsinta ba, bai ji shigowarta ba, sai jin lalausan hannayenta ya yi ta sanyo ta bayansa ya kasance ta dora jikinta a bayansa hannayenta a wajen wuyansa sannan ta dora kanta a wajen dokin wuyansa idannuwanta lumshe Yannayin zafin jikinta ne ya saka shi dan kara gyara zamansa a hankali ya shiga dan shafa hannayen nata, muryarsa ciki ciki ya ce" Me ya hanna maki baci? " Dan bakinta ta turo itama muryarta ciki ciki ta ce" Ban saba kwana ni kadai ba ", ta ci gaba da wasa da sajen fuskarsa dake kwonce luf luf Idannuwansa ya lumshe a hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya kafin ya mika hannunsa ya maidota gabansa Bai tsaya jiran komai ba ya dorata saman cinyarsa ya mayar da bayansa da kyau baya ya jingina sannan ya dora kanta saman kirjinsa ya shiga shafa lalausan gashin kanta Lamo ta yi tana sauraronsa, a hankali ta ce" Kai kuwa mai ya hanaka baci? " Sai da ya tabe bakinsa a ransa ya furta ji tsegumi, a fili kuwa ya ce" Ina tunanin matata ne " Sai da ta dan dago ta kale shi kamar yanda ya zame mata sabo idan abu ya daketa zata dan dago dubanta ta kai wajen da ta ji abin, a hankali ta cire idannuwanta a cikin nasa du kuwa da hasken fitilar dakin mai duhu ne aman ras suke kallon junna Muryarta a sanyaye ta fe" Ka yafe mata mana, kar ciwo ya kama ka domin ciwon so bashi da magani in dai ba abin son mutun ya samu ba " Shafa gashin kan nata da yake ne ya dakata na yan sakwani kafin ya ci gaba, muryarsa na shaking kadan ya ce" ke kin san zafin ciwon so? " Lebenta na kasa ta dan dantse, a hankali ta lumshe idannuwanta, cike da jan aji kafin ta bashi amsa ta ce" Na san ciwon so, haka kuma na san zafin rabuwa da masoyi " A hankali ya lumshe idannuwansa yana mai jin wani irin daci daci a zuciyarsa, me yasa take son bata masa nishadinsa ne a kowani lokaci? Bata san irin abinda take hadasa masa na tashin hankali da bacin rai du a furucinta ba? Me ya sa bata tsoron irin abinda zai iya yi mata a kan furucinta? Me take nema a wajen Namiji ne ta rasa a wajensa? Idannuwansa ya kuma lumshewa a hankali ya kawo lalausan hannunsa ya saka cikin rigar bacinta doguwa ta kasa hakan ya saka ta dauke wuta tana mai jin gabanta ya yanke ya fadi Irin yanda ya ringa shafa kwontacen cikinta ne ya sakata fara sauke ajiyar zuciya sannan ta dan yi lamo tana sauraronsa A hankali yake kara sama yana mai tafia da dabara wanda sam ba zata ji tashin hankali ba Sai da ya dangana da mangwaron dake tsaye kikam ya tare hanya ne ya fara dan shafa shi yana dan lumda shi dan ya samu wadatacen ruwan da zai saka shi nishadi Idannuwanta ta lumshe sakamakon irin yanda yake baiwa y'ayan itatuwarta kulawa ba tare da ya girgiza da karfi ko ya tsinko da garaje ba Bata ankara ba sai jin dumi dumi da abin danshi danshi ta yi a baki bakin, hakan ya saka ta kwace ajiyar zuciya da dan karfi kadan sannan ta dana shanyayun idannuwanta ta dora a saman gefen fuskarsa tana kallonsa Baki daya jikinta ne ya dauki rawa, a hankali take dan matse damtsen hannunsa irin abin na shigartan nan Shima dake kokarin motsatan ya gama motsawa , jin idannuwanta a kansa ya saka shi dago nasa da suka cenza kala sukai ja ya sauke a cikin nata wanda hakan sai da ya saka shi jin wani irin yarrrr tun daga kwakealuwarsa har tafin kafafuwansa domin kuwa kalar da idannuwanta suka nuna ya matukar bada kokari wajen kara masa kaimin bukatuwarta Shanye nasa ya yi, ya kuma wara su a kanta, cikin nutsuwa ya kamo kumatunta ya hade bakinsa da nata A hankali ta amshi harshensa dake cikin bakinta mai fitar da kanshin turaren baki na menth ta shiga dan tsotsarsa ido rufe tana kara janyo rigarsa zuwa jikinta Gaba daya jikinsa ne ya kwashi wani irin rawa, a hankali ya ringa sauke mata numfashinsa a saman fuskarta, idannuwansa ruf a rufe ya kasa wani kwakwaran motsi, ita kuwa tamkar ta samu waji lolipop hankali kwonce take lamarinta har sai da ya ji zata haukata shi ya kwace bakinsa yana kallon fuskarta da dan bakinta da idannuwanta dake lumshe Muryarsa cen ciki, da nauyin tsiya ya ce" Me ya sa bakya so na? " A kurya ta tsinkayo maganar , hakan ya sa ta buda idannuwanta da suma suka cenza kala ga abin bacin da ta fara ji ga na jigata mata zuciya da ya yi tana kallonsa, Ido cikin ido suke kallon junnansu, wanda hakan ya haifar masu da wani irin felling, sun kara cadawa a kogin da suke ciki tsundum, har daidai lokacin da ta dan daga masa kafadunta, wato amsarta kennan bata sani ba Idannuwansa ya lumshe a hankali ya ciciba ya dauketa ya yi wajen bed da ita Wani irin zazafen romance yake bata wanda ya sakata mutuwar jiki da gabai baki daya sai wasu irin manyan kalamai da kunnayenta ke tsinkayo mata daga bakinsa wa'inda a saman lebensa yake furta su dan dai kawai Allah yai mata baiwar ji ne A hankali ta ringa kame jikinta tsoro ya fara darsun mata, muryarta na rawa rawa ta ce" kar ka yi akoy zafi " Sai da ya kara rarashinta ta yada ta idasa yarda da shi kafin ya yin, sannan sosai ya bita a hankali sai dai jimawar da ya yi, dan kuwa a yau bata ji irin azabar nan ta jiya ba, ba za'a rasa dan abinda ba za'a rasa ba aman ba wani azabar a zo a gani bane, sai dai lamari na ba saban ba dama sai a hankali Baci ne ya yi awon gaba da ita, shi kuwa ya kasa koda rintsa ido daya ne Tarin nutsuwar da yske samu a wajenta ta zarta tunanin bawa, haka kuma irin yanda kalamanta ke shigarsa koda da wasa ta fada ya zarce hasashen bawa A hankali ya raba jikinsa da nata ya dan matsa ta yada zai iya kare mata kallo Irin yanda zuciyarsa ke bugawa idan yana tare da ita ne ya tabatar komai karfin namiji ashe rago ne a gaban mace mai sunna mace Irin yanda yake kasa rike wasu lamura a zuciyarsa idan yana tare da ita shi kansa sai abin ya zamto yana bashi mamaki da matsananciyar kunya A hankali ya juya mata baya dan rage kayatuwarta a idannuwansa, sai dai baki daya zuciyarsa ta nuna bata san zancen ba hakan ya sa ya rintse ido dan nuna mata karfi kamar yanda ya saba daneta a kan son zuciyarsa Hakan ya hadasa masa zafin zazabi, domin baki daya jikinsa ne ya garwaye da zafi har hucin numfashinsa idan ya fitar ba normal bane Yanda ya ga rana haka ya ga dare idannuwansa bude shi bai samu kwarin jikin tashi nafilar ba, yana ta biyan gawon shanu, sai a wannan lokacin ya yarda babu sakaran abu irin abinda ke damunsa, gaba dayama shi so yake ta tashi a yita ta kare, aman kuma gudun jin amsarta ya saka shi yin gum da bakinsa a lokacin da Allah ya wayi gari Yana kan salayarsa kansa duke ta duka har kasa muryarta ciki ciki ta furta" Barka da safia " Dago dubansa ya yi da sauri ya sauke a kanta, Jin shirun ya yi yawa itama ta dago, sai dai ga mamakinta hararanta yake wanda hakan ya bata mamaki har ta dan zaro ido a kasan zuciyarta tana ayanna to fah Gannin ba amsar zata samu ba ita kuwa dama ba wai koshi ta yi da bacin ba sai ta mike a hankali ta yi kan bed, hijan din ta cire ta ajiye ta yi daidai abinta ta kuma neman baci, shi kuwa da ido kawai yake binta Lebensa na kasa ya dan cije yana jin jikinsa har yanzu da zafin nan sosai A hankali ya mike ya nufi hanyar wajen AMMI dan ya gaisheta kamar yanda ya saba Yana shiga ya tarar da su, su biyu sunna hirarsu kamar yanda suka saba Cike da kulawa suke amsa gaisuwarsa, sai dai kuma yannayin tashin hankali da yannayinsa ya nuna a fuskokinsu Da sauri UMMU ta ce" Me ke damunka? Ka ga yanda fuskarka ta yi ja hakama idannuwanka" ta karashe tana mai kai hannunta wajen wuyansa Ido ta zaro ta ce" Subahannalah Shaheed baka da lafia ne? ?" Dan murmushi ya yi a hankali ya dan girgiza kansa, AMMI kanta gabanta sai duka yake tana kallonsa UMMU kam da sauri ta mike tana fadin bara na kira likita na dan sama maka wani abin da zaka ji kwarin jikinka UMMU na fita SHAHEED ya matsa sosai kusa da AMMI yana kallon fuskarta, a hankali ya dora kansa a wajen kafadarta ya yi shiru idannuwansa lumshe AMMI ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwar yannayinsa, muryarta a sanyaye ta ce" Da zazabi ka tashi ne ko baka kwonta ba? " Itama kan nasa ya girgiza hakan ya sa ta kasa gane inda amsar tasa ta nufa A hankali ta ce" Me ke damunka ? " SHAHEED ya lumshe idannuwansa, ji ya yi to shi idan bai fada mata ba wa zai fadawa?, haka kawai ya samu bakinsa da furta " *SO NAKE TA MANTA DA WANI TA SO NI, NI NI KADAI, NA ZAMO DUNIYARTA, BANA SO NA BITA DA FADA KO TASHIN HANKALI, NA FI SO TA KASA KATABUS SAI DA NI DAN RADIN KANTA BA DAN WANI YA SAKATA KO YA TIRSASATA BA* " Ya karashe maganar yana mai lumshe idannuwansa, Tabas mamaki mai tsanani ya so halaka tunanin AMMI, what? SHAHEED?, idan ba mantawa ta yi ba da Najeeba ne akai masu auren hadi wanda Najeebar nada saurayinta aka rabata da shi, wai yau SHAHEED ne ke fada mata haka? Wai da gaske ne ko mafarki take? Lalle ta yarda ya fara gazawa, sai ta ringa jin wani irin dadi da kuma tausayinsu su duka biyun, A hankali ta ce" Kaine zaka sakata a yannayin nan a lokacin da ita kanta bata sani ba, SHAHEED ba'a yiwa mace sarauta a cikin gida, ina so ka yarda da wannan na tabata komai zai zo maka da sauki " Shiru ne ya kuma biyo baya mai tsayi har UMMU ta dawo dauke da tea sai turiri yake ta mika masa tana fadin Docter na nan zuwa yanzun Dan dagawa ya yi da tea din a hannunsa yana kallonta ya ce" Umani hala a gidan nan kika kwana? " Da mamaki ta kale shi, har tana zarro ido, ita kam ta rasa NAJEEBA da SHAHEED yanda zata yi da bakunnansu, to yanzu tsakani da Allah tambayar nan zai mata? SHAHEED ya dora da fadin" Ko abih din ya yi tafia ne? " Yanzun kam mikewa ta yi zurbat ta juya ta bara masa dakin hakan ya saka AMMI bushewa da daria har tana dan rike cikinta sannan ta harare shi ta ce" Kai ku shafawa kawata lafia kai da matarka tun muna iya mu! " Murmushi ya yi yana dan shan tea din nan ko zai ji dadin bakinsa, sannan ko zai ji jarabarsa ta kwonta masa, haka kuma so yake likitan ya yi ya zo ya duba shi ya koma bangarensa dan baya so ta fito a yau, ya fi so su wuni sunna baci domin ko shi ba inda zai je sai da yamma Sababul khair In SHA Allah saura kirisssss🤣💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 [31/03 à 22:03] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 62 Ba shi ya bar bangaren AMMI ba sai da likita ya zo ya gama yi masa tambaye tambaye da dauke dauken zafin jiki da su daukan jinninsa ya juya, suka gama maganar kudaden da za'a fitar dan cikin fada sannan ya yi masu salama ya bi ta hanyarsa ya koma Rigar jikinsa ya cire ya feshe jikinsa da turare sannan ya haye saman gadon A hankali ya shige cikin abin rufarta ya sakata a jikinsa ya lumshe idannuwansa Wannan lokaci shine na hudu da ya saka mace a jikinsa da niyar yin baci ba wani abin ba, domin Zinariya sunna gama abinda ya hade jikinsu take tafiarta kamar dai ka hayo yar bariki, Nadia kuwa hakan bai faru da su ba ko bayan sun samu kusanci da junna A hankali ya ringa lumshe ido har ya ji baya nan, wato barawo ya yi awon gaba da shi, bacin da yana tsakar yi ya ji alamun motsinta a hankali Tun yana dan rikota har ya ji tana son kubce masa da karfi hakan ya sa ya wawurota jikinsa da dan karfi ya riketa yana sauke ajiyar zuciya da buda idannuwansa da suke cike da wani baci mai dadi Ido hudu sukai da shi, ta masa kuri tana kallonsa, sai a lokacin ya ringa tsinkayo kabarar sallah wanda hakan ya bashi matsanancin mamakin da ya saka shi da wara manyan idannuwansa a kan fuskarta A hankali ta sada dubanta tana dan tura bakinta sannan tana kare bakin nata dan kar ta masa magana kai tsaye bayan itama kiran sallar ne ya farkar da ita kar iskar bakij mai baci ya dakar masa hanci haka kawai ta ce" sallah fa ake" Idannuwansa ya kara lumshewa da ita a jikinsa A hankali ya shiga tashi da su Sai da ya mike ya shiga takawa da ita a jikinsa ya nufi bayin Bai tsaya cire mata rigar bacinta ba, haka shima bai cire karamin wandin nasa ba ya kai su kasan shower suka tsaya Sunna tsayawa ta rintse ido domin ba sai an kunna shi ba, da kansa ya bude faaaaa ya ringa basu duka a jikinsu Sabulun ruwan da ya matso ya shiga shafa mata a gashin kanta zuwa wuyanta, zuwa cikin rigarta kafin a hankali ya sabule hannun rigar ya shiga janta kasa a hankali Ido ta kurawa fuskarsa da gashin kansa cike da matsanancin mamakin salonsa, wai dama yana da lokacin kasancewa da iyalinsa har haka? Gannin ya fi matsawa yan biyunta sai ta dora hannunta saman nasa sake a wajen ruf yana ta murzawa a hankali shi a nan wanke su yake Ido hudu suka yi da junna, a hankali ta cire idannuwanta ta kuma kaiwa saman cinyoyinsa Har sai da tsigar jikinta ta ringa tashi, cinyoyinsa kamar na yan kokowa mundil mundil da su a kame kam ba kamar tuwon laushi ba, saman har wani dan tozo suke da shi idan ya tsaya kikam, sai wani irin gashi da ya masu luf luf luf sannan ruwan da ya taba su sai ya zamana gashin sai sheki suke abinsu Gannin yana son daga hannunta niyarsa ya wanke mata hamata ya sakata dan zaro ido tana kallonsa Ai kau bata ankara ba ta ji ya fara mata cakulkuli Dan ihu ta saki ta fashe da daria da gudu gudu ta shiga kokowar kwacewa Shima dariar tata ta tafi da shi har ya shiga yin daria kasa kasa yana kara rikota jikinsa yana jin tana ihun sai ta rama tana masa cakulkulin shima hakan sai ya zama ta matso sabulun ruwan ta shiga wanke shi tana mumurza ko'ina hankali kwonce tana son sai ta taba wajen da zai saka shi daria kama daga lafafen cikinsa mai gida gida, da keyarsa, ta duka ta taba tafin kafarsa, ta mike ta kama hannunsa ita sai ta yiwa hamatarsa aman ta kasa daga hannun sai kawai ya shagala yake rakata da ido yana jin nishadin lokacin Kunnayensa ne suka jiyo masa salamar dake nuni da an gama sallar Ido ya zaro da wani irin sauri ya kamota gabansa ya nuna mata yannayi na ta yi alwallah dan har an gama sallah Itama alwalar ta maida hankali ta yi ta bi bayansa da tawul din da ta janyo a shanye a bayin Tana fitowa ta tsinkayo maganarsa yana fadim" haka kawai yarinya ki wani saka mu kokowa a bayi bayan ba kyau magana a bayi, kuma ki wani saka na rasa jam'i kai yarinyar nan bakya jin magana" Baki ta bude da mamaki tana karasawa inda yake miko mata doguwar rigarta ta sallah da har ya fice ya dauko mata Da sauri ta warwareta ta shiga sakawa sannan ta saki tawul din kasa Ita kanta ta manta da komai bale shi dake kallonta hakan ya sa a rashin tunawa ta duka ta zare jikaken wandon dake jikinta ta ciro shi baki daya Ido ya zaro gannin katon wandon da ya mata daidai, itama sai a lokacin ta ga abinda ta aikatan, ai da sauri ta matse shi a hannunta tana tura baki ta juya zata koma bayin Hannunsa ya mika ya kamota yana mai kara bin jikinta da kallon kasa kasa, hankali ya ce" Let's pray " Kai ta dan gyada masa, suka nufo kilatacen wajen sallah Lalle ta yabawa limancinsa, ta yabawa irin tsarin sallarsa harma ta ji a ranta zata kara dukawa ya kara koyar da ita adininta domin kuwa ita ko a ina ta hadu da wanda ta san ya fi ta ilimi a kan wani abin bata jin kunya ko girman kan duka masa ya koya mata bare adinin musulunci mai dauke da abubuwa masu girman gaske wa'inda wasun har ka koma ga Allah ba zaka taba saninsu ba Mikar da ita ya yi a hankali ya sakata gabansa shi kuwa a bayanta , bayanta mane da kirjinsa ya shiga takawa da ita suka nufi falon gidan Ita dai inda ya yi da ita take bi, sai ganninsu ta yi sun yi dakin cin abinci Kayatacen tankamemen table din diner ya nufa da ita mai dauke da wasu irin kuloli masu ado da zeba Kana gannin kulolin nan ka san na manya ne, ga fruit wanke tass a cikin wani bowel mai shara shara domin ana iya gane ko meye a ciki kuma a rufe da wani marfi Sai zug zug din da ta yi imanin jus ne a ciki Idannuwanta ta lumshe sakamakon jin hucinsa wajen wuyanta wanda ya zame hular doguwar rigar tuni , sai take jin jikinsa da dan gumi, aman ta kasa tambaya A hankali ya ce" ni yinwa nake ji " Dan murmushi ta yi wanda bata shirya ba domin irin yanda ya yi maganar sai da ta ji kunya walahi Kanta ta dan dago ta dube shi, sai kuma ta cire dan ita a yanzun irin duban nan nasa da sam baya barinta da shi ke rikitata, gashi dai maganar sanyi ke fitowa daga bakinsa zuwa gareta, ama kuma idannuwansa na jifanta da kallon tsanar dake ladaftar da ita! Wajen cin abincin suka karasa Kafin ta zauna ta dauki plat daidai cin sa Aman sai ta ga ya cenza mata da wani baba Yana kallon yanda take zuba abincin yana koya, domin dai sultan ko dafa ruwan zafi bai iya ba, inama ya samu damar dafe dafe shi da ya tashi cikin horon koyon abubuwa da dama ciki harda kasuwanci wanda bai fara harkokin mahaifinsa ba sai da ya kama masters a marketing dinsa sannan ya karbi komai yake tafiar da shi daidai da gwargwadon iyawarsa domin kuwa harta da takardar business communication sai da ya hada saboda tsaro Tana gama zuzuba komai ya mike ya dauki farantin ya yi gaba Bayansa ta bi da kallo, gane cewar ba a nan yake so su ci abincin ba ya sakata dan bubuda jus jus din Na aya ta dauka da abin zubawa ta bi bayansa Cikin nutsuwa ta karasa wajen da yake zaune yana jiranta ta ajiye sannan ta zauna itama Bismillah ya yi mata ya fara saka hannunsa ya fara ci , kafin ta fara ci itama Ta yi dagowa ya kai biyar tana kama shi da irin kalon nan, hakan ya sa ta yatsina fuskarta bayan ta hadiye abincin ta kura masa ido A sanyaye ta ce" Me ya sa kake jifana da kallon tsana tun shekarun baya? " Da mamaki yake kallonta, kallon tsana kuma? Wani irin kallon tsana ne yake jifanta da shi? Gannin tana son cire hannunta ta tashi sai ya riko hannun nata Idonta ta dora saman hannunsa dake rike da hannunta A hankali ya fitar da hannun nata sannan ya matsota sosai Hannun nan nata dake rike a nasa ya shiga sidewa daya bayan daya yatsotsin wanda hakan ya sakata shagala da kallonsa Sai da ya gama sannan ya maida nasa hannun, wanda dama ga vokali ta dauko aman sai ya saka hannu ya diba a hankali ya nufi bakinta da shi Dan langwabewa ta yi tana sauke ajiyar zuciya ta ki ta bude bakin nata Yana mai dubanta a sanyaye ya ce" Ki ci kin ji, ki yi hakuri ki ci ko zan iya ci " .............sai da na gama ya goge😭😭😭😭😭😭 [31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 63 Wannan karron sai d akirjinta ya doka, harma ta ringa jin tamkar zata fashe da kuka da tashin hankali, a hankali ta kuma kurawa fuskarsa ido tana kallonsa ta kasa karbar abincin, shima dai kallon nata yake harma yana jin bashi da wani abu mai dadin kallo irinta a duniya sai dariar mahaidiyarsa "Kin san kin ada kyau kuwa JEEBA?" Ya fada kasan makoshinsa yana mai shafa gefen fuskarta, bai bari ta dawo daga sumar da ta yi ba ya dora da fadin "Ina so idan Allah ya sa inafa rabon haihuwa a duniya y'ayana su ringa yin kamaninki da fatar jikin ki, da shahwabarki, ama banda fadan ki" A hankali ta furta" Na shiga uku, meye hakan kuma?" A kasan zuciyarta ta yi maganar, ama a fili ta bayana cikin sanyi da rarabewa, Bakin nata da ya yi furucin ya kurawa ido, da ba dan baya son matse mata waje ta hanyar nuna mata zanlar zalamarsa a kanta ba, da ya kara kusanci a tsakaninsu a wannan zaman ta hanyar mayar da su abu guda a irin wannan lokacin Buga kofar da ake a karro na ba adadi ne ya saka shi kai dubansa, haka itama Hannunsa ya mika ya dauki remote tare da tablet dinsa ya kunna ya shiga kallon mutanen dake tsaye a cen wajen dogarai Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ajiye wayar ya dauki jus din nan ya zubawa kansa ya sha sosai Kallonta yake kasa kasa kafin ya furta "zan je na dawo, ki ci abinci kin ji?" Kanta kawai ta iya gyada masa tana mai binsa da kallo har ya shige cikin baban dakinsa Ya dauki lokaci kamar minti ashirin sannan ya fito Gaba daya sai ta ji wani irin yam yam yam a jikinta a lokacin da kamilin sarkin, mai wukar yankan ya bayanar mata a Sultan SHAHEED Ajiyar zuciya ce ta kwace mata tana kallonsa sai ta ga wajenta ya nufo hakan ya sa ta ji zuciyarta na rawa Yana karasowa da gaya sai ya ja ya tsaya kamar yanda yake yiwa Zinaria ta kwashi kirari ko ta dukar da dubanta har sai ya fice Da farko kan nata ta dukar kasa kamar yanda idan aka kawora shara'a ko ta yi rakiya Sai dai kamar yanda ya yi tunani ko minti daya bata yi a hankan ba ta shiga dago dubanta a hankali har ta sauke saman fuskarsa Murmushi ya saki ya rage tsayinsa ya mikar da ita tsaye Hannunsa ya saka ya janye abin wajen bakinsa sannan ya kusanto fuskarsa da tata A hankali ya shiga kissing din lebunnanta har sai da ta bashi amsa son ransa sannan ya cikata ya sakata a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya Muryarsa ciki ciki ya ce" Yaya aka yi bakya jin tsoron hada ido da ni? " Itama sai ta ki bashi amsarsa, domin ai ita ta fara tambayarsa ya mata banza ko, sai da ya gaji dan kansa sannan ya cikata Har ya fara tafia ya ji ta ce" baka koshi ba kuma zaka fita? " Dakatawa ya yi ya juyo gareta, sai da ya mata kallon tsaf ya ce" ki tanadar min wani abincin, domin zan fita da matsananciyar yinwar ki, fatana kar na ringa magana ina ambatar sunnanki a lafuzana......." ya karashe yana mai kashe mata ido daya sannan ya juya yana mayar da rawanin wajen bakinsa ya fice Ta kai minti biyar a tsayen nan tana kallon kofar da mamaki A bayane ta ce" kan Uba," sai kuma ta juyo tana sakin murmushi Sai da ta dan jujuya ta kwaso shokiiiii ta juya wajen kofar nan ta sauke masa ita a fili ta furta" gayen zai halaka ni "......... Sunna fita daga nan waje suka samu mahaifin Nadia ya gabatar masa da dukan sakamakon binciken da aka yi, hakama lauyan da ya dauka da kuma police din da ya shiga cikin mutanen gidan sarautar ya yi basaja Sosai ya gamsu da bayanansu, sannan aka tafi da dukan wa'inda suke da hannu a ciki tun daga kan wanda ya ga lokacin da ake kama macijin ya ji labarin macijin ne ya yi kisan an bai fada ba, da wanda macijinsa ne, da sauransu Sai da aka gama hargitsa gidan sannan aka saka kowa kuble dan za'a fitar da Zinaria Da kansa ya saka aka fitar da ita aka kawota gabansa Gaba dayanta ta zube kasa har jikinta na rawa ta fashe masa da kuka tana neman afuwarsa, cewar ba zata kuma yarda ta hada kai da wani dan a cuce shi ba Ta dora da fadin" Haba ya mijina, ka gafarta min laifukana a gare ka, na san da ban kyauta ba, ama ba zan taba hada kai da shi dan na ci amanar aurenka dake kaina ba, ban taba cin amanar aurenka dake kaina ba " Ransa bace matuka , ya kalleta, muryarsa kausashe ya ce" Da kin san darajar kanki, da kin kilace min kanki, sai dai kashhhh........, shiru ya yi na dan lokacin kafin ya furta" idah ta hau kanki, na tura takatdarki wajen sarki" Yana gama fada ya juya ya shiga takawa, yana jin lokacin da ta kwala wani ihu duda muryarta a shake take ta zube kasa sumamiya, haka suka konkimeta suka sakata a mota, a hanya ne suka yi kokarin gannin ta farfado kafin tale gane komai sun sakata a motar hayar da akai mata shata zata dauki hanyar damagaran zuwa Agadez, hanyar da bata taba bi ba a mota tun da Allah ya haliceta, sai gata yau an sakata da ranar gari zata shiga garin agadez a motar haya, ita kam ko a haka aka barta ta gane rayuwa bale idan ta tuna mahaifinta na jiranta da takardar saki? Ita kam ta kawo abinda ba wanda ya taba kawowa gidansu, aman ta tabata mahaifiyarta zata tare mata (uhum, baki san itama an turata gidan ba😁) Daga nan bangaren su Nadia ya nufa domin ya yi niyar yau ba zai fita ba Yana zuwa suka gaisa da iyayenta, sannan ya mata yaya jiki da tambayar ko akoy abinda suke da bukata?, sun bashi gamsashiyar amsa sannan ya fice ya koma falonsa A nan ya tile, a nan ya kuma bajewa, a nan ya ringa shigar yarinya ta inda bata zato bata tsamani, a nan ya ringa kara yiwa kansa ilah da soyayar yarinyar Ammi, a wajen nan ya ringa baje kolinsa , suka ringa samun kusanci da shakuwar da bai yi da wani mahaluki ba....... Bayan kwana biyu da daurin auren su UMMU yaya DAYABU ya dawo daga tafiar da ya yi garin Niamey bisa aikinsa Farin ciki ba irin wanda bai nunawa Ummu ba, sannan ya shigi abin da karfi karfi dan kuwa kiri kiri ya nuna ba zata zauna a wancen gidan ba, dan haka aka shiga gyare gyaren rantsatsen gidan Abih dake anguwar jeune cadre Tsananin farin cikin da Abih ya shiga ba'a cewa komai, hakan ya sa shima ya shiga gabatar da bincike a kan yarinyar da DAYABUN ke nema, dan kuwa ya shiryawa bikin DAYABU, a duniya DAYABU ya kasance jigon rayuwarsa da ta y'ayansa, kowa dai rigimarsa shi yake zubawa, kowa shi yake kaima, shi kuwa ya dauka ya rungume ya nemi mafita , sam baya wasa da ahalin MUTALAB dan haka shima ya fara dukan lamarinsa da dukan katfinsa, dan kuwa zai masa biki na dan gata. A cikin sati gudan nan idan fitar SHAHEED ta yi yawa bai fi sau hudu ba, NAJEEBA kam tana ji tana ganni zuwa bangaren AMMI ya gagareta domin Shaheed ya wani irin kasawa ya tsare dukan motsinta a kan idannuwansa, ya zamana idan ka ga an neme shi to abu ne mai girman gaske wanda dole sai ya fita, ko harkar kasauwancinsa da yake yawan operat a dakinsa ya ajiye ya basu dama, ya kasance Najeeba ta gama salamawa zuciyarta da gagarumin abin dake dawainiya da tunaninta A yanzu kwata kwata ta daina yi masa maganar wani, koda ya yi dan ya nemi fitina takan yi murmushi kawai ta yi masa shiru Ta yi maganar fita saloon ya fi a kirga, da ta ishe shi ya nuna mata saloon dinta su Aida na aiki , da mutane ba masu wani uban yawa ba domin sai da aka buga bage, idan kana son aiki a wajen zaka ciri tikite ne ka yi jiran rana da lokacin da aka baka, Ta ji dadin hakan kwarai, harma ta tambaye shi yaushe zata koma bakin aikinta? Sai ya nuna mata zata koma idan ya ji hankalinsa ya kwonta da hakan A yanzu Najeeba na dawainiya da wani irin kishi a cen kasan zuciyarta, a yanzu take jin haushin du wata mace mai sunnan tasa ko wace suka taba maganar da ta zarce ta yan uwantaka ko ta aikinsa Ita kanta tana mamakin kanta , basu furtawa junna kalmar so ba, ama sunna wani irin kafa kafa da junna fiye da tunanin mai tunani Yau suka cika sati guda, kuma a yau ne zata bar aiki Nadia ta kama, haka kawai ta tashi da bacin rai sosai A cikin ruwan wanka take kwonce ta lumshe idannuwanta, ba komai ke mata yawo a kwakwaluwarta sai irin lamarin da ya wakana tsakaninta da mijinta a daren jiya Ta kasa cire wannan lamarin a cikin zuciyarta, A yanzun tsakaninta da shi abu daya ne kwal ya kasa furta mata, wanda zata iya rantsewa zuciyarta na bukatar jin hakan daga bakinsa Zuciyarta dake tashi ne ya sakata juyar da kanta ta tofar da yawu ta kora da ruwa sannan ta idasa wankanta ta fito tana mai jin wani irin baci Tana fitowa da gagawa ta karasa wajen kayanta da aka turo mata da su ta shiga kimtsa kanta dan bata son ya tardota har ta yi wanka ta tabata zai nuna bacin ransa ne Tana gama dora alkyabarta ta karasa gaban madubi da gashin idon da aka sako mata wanda ta sa su Ummu suka sako mata komai ta gyara ta shiga dorawa Fuskarta ta gyara kadan sannan ta saka jan baki kalar kasa kasa a dukan lebunnanta Turarensa ta dauka ta shiga fesawa, a haka ya shigo da waya a kunnensa yana amsawa Bayanta ya kurawa ido, alkyabarta, a hankali ta juyo ya zamanto sunna facing din junna Murmushi ta sakar masa , wanda shi kuwa fuskarsa ta nuna yannayi na ya shiga halin damuwa a yanzu yanzun A hankali ta taka har inda yake tsaye , tana zuwa ta shige jikinsa, tana jin muryarsa a sanyaye ya furta" zan tabo ka daga baya " Bai tsaya ya ji amsa ba ya kashe yana mai sakin wayar nan ya saka hannayensa bibiyu ya rungumeta a jikinsa yanna jin yanda zuciyarsa ke dokawa A hankali ya ce" Har gagawa kike ki bar ni? Shine har kika yi wankan ki bayan kin saba cuta min bayana? " Dan murmushi ta yi na karfin hali a ranta tana ayanna ai gara kai idan ba daya da daya, ni fa? A fili kuwa sai ta furta" ango fa kake mijin Nadia, na tabata zata yi maka fiye da hakan " Bai ce komai ba sai dan murmushi kawai da ya yi ya karasa saman kujera da ita suka zauna yanda suka saba dare dare tana saman cinyarsa Cikinta yake shafawa, ahi kadai yana adu'ar Allah ya sa kwalonsa ya gama shiga rijiya, yana da burina rayuwarsa, shi ne ya buda ido ya ga cikinta ya tasa, ko zata daina rigima daga ranar? Sunna nan zaune sai shiririta tafiarta yake, da kyar ta samu ta kubce masa Ta yi mamakin yan rakiyarta matuka, yayunta ne su biyu da jakadiya da bayi mutanen dai masha Allah Haka suka sakota tsakiya anai mata wani irin kirarin da ya sakata jin wani irin girma na hawa kanta, a haka har suka karasa bangaren AMMI AMMI, Yaya Dayabu, Abih, da kannenta ne cike a wajen ana ta hira ana daria Sai ta ji wata irin kunyar hada ido da su ta kama ta, bata taba jin haka irin na yau ba, ga bacin da take faman ji, ga tunanin barinsa da ya saukar mata da kasala Basu dai samu yanda suke so da kanwar kuma yarsu ba, dan kuwa sama sama ta tsaya kafin ta shige dakinsu tana sauri Tana shiga ta tarar da UMMU na ware jigidar nan da Zahrau ta ajiye sauran a saman sif Da sauri UMMU ta sha murr gannin Najeeba ce, ta idasa fitarwa ta saka a jakarta tana kallon Najeebar dake kallon jakar tara Daria kawai Najeeba ta yi ta haye bed din a hankali ta yi matashin kai da cinyarta tana mika Ummu ta yi murmushi ta shiga shafa lalausan kanta, haka kawai ta yi ra'ayin yi mata kitso dan haka sai ta gyara mata kwonciyarta ta dauko kayan kitson ta haye gadon ta gyarata yanda zata ji dadin tsara mata kitson ta shiga yanyara mata shi kannana sosai Ummulkhair kuwa ta dama masu lale na hausa , Ummukulsum ta je ta kawp skoth ta zauna tana yankawa sunna hirar su har baci ya dauke Najeeba...... YAYA DAYABU kuwa kayan UMMU ya ringa jida yana kaiwa motarsa har ya gama komai ya kulle motar ya dawo dan yana son ganawa da SULTAN yau yau din nan kafin ya kai kayan UMMU a kimtsa mata su dan an gama gyara an zuba kaya an gama jera komai mai dakin kawai ta yi saura, Mardiya kuwa tana wancen gidan na Abih __________________________ Washe gari ta tashi da rashin kuzari, haka ta yi wanka ta kimtsa kanta suka ci gaba da ayukansu da yan uwanta Wajen karfe goma suka yi waya da Zahrau da dukan yan uwansu hakan ya sa wayar ta dauki dan lokaci kafin su katse Garin dan wake suke gyarawa zasu jwfa dan wakensu shelar shigiwar Sultan ta karade wajen Ai kamar ana wuwurga su suka ringa tserewa kowa na shigewa ciki, hakan ya baiwa NAKEEBA daria har ta dara abinta ta ci gaba da hada garin da kanwa da miyar kuka ko foku A lokacin da ya shigo sai da ya gama da iyayensa sannan ya karasa wajen da yake hangenta ta dage tana kwaba garin hankali kwonce da muciya Zama ya yi yana kallonta, a ransa fadi yake hankalinta kwonce, yanzu haka ko tinawa da ni bata yi ba, dama fama take ta dawo ta zuba sangartarta Gaishe shi ta yi tana dubansa, a lokacin shi kuwa sai ya zame ya zauna saman ledar da suka shinfida dan kar su bata wajen Daga UMMU har AMMI ido suka zaro daga inda suke zaune da matsanancin mamakin gannin ya zauna a nan ba kan kujera ba, ba cike da takama ba A hankali ya ce" Na ji, ko ki kiraye ni ko? " A ranta ta furta'ina ni ina kiranka kana tare da matar so raina ya baci ', a fili kiwa baki ta dan tabe bata ce komai ba Zamansa ya gyara da niyar yi mata tambayar da ya zo da ita, Allah yana ganni yana matukar mamakin lamarinta, haka kuma bai taba sakawa ransa wai tambayar na iya kawo matsala ba, dan haka hankalo kwonce ya ce" BEEBAH " Dan dakatawa ta yi da motsawar tana kallonsa, jin ya yi mata irin kiran dake kasheta dan haka ta kura masa idannuwanta masu hadasa masa kasala Sai da ya ja numfashi sannan ya dora da fadin" Me zai hanna ki baiwa kawarki abinda kike sha kike kasancewa haka? Na san mata fa bakwa rabo da dan taimakawa kanku" Idannuwanta ta dan wara dan neman karin bayani, hakan ya sa ya dan kara matsawa kusa da ita a hankali ya ce" idan wani abu ne na sha kike sha , ki taimaka mata itama ta ringa sha, irin na saukar da ni'imar nan " Ya salam, wani irin faduwar gaba mai hade da bacin rai ne ya ziyarceta, idannuwanta ta saka cikin nasa tana kallonsa kafin ta cire muciyar tana nuni bangarensa ranta a bace aman kuma muryarta ba sama sama ba ta ce" Ai ba sai ka min haka ba zaka nuna min ka sadu da matarka ba Shaheed, koda baka fada ba na san matar so dole ka kula ta, waima yaya kake tunanin zan saka damuwa a raina dan ka kwatanta min ka kadaice da matarka bayan kiri kiri ka nunawa duniya ji din ba kowa bace ta hanyar karbar hadin da akai maka a fili aman a zuci ka hadani da aminiyata? Sai me dan baka so na? Allahn da ya sa nima ban rasa mai sona ba, kafin kai nima ina da mai so na, kuma nima ina son abuna dan haka kana iya...............................................................................................DIF maganarta ta dauke sakamakon wani azababen marin da ya sauka a gefen kumatunta da kunnenta kadan ya yi sanadiyar dauke jinta harma ganninta ya fara nuna mata biyu biyu uku uku Zabura AMMI ta yi tsaye ta furta" Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, SHAHEED lafia?" Tana fada ne tana yiwowa wajen da wani irin sauri NAJEEBA kam daga tsayen da take ta durkushe kasa saman gwuiwoyinta , dan kwalin dake kanta ya fadi, kitson da akai mata ya bayana kansa sai yar sarkar dake wuyanta mai heart ta shiga dan yawo kadan kadan a wuyan nata, still hannunta na jikin kincinta AMMI na karasowa da sauri ta duka ta kamata tana maimaita " meye haka? Me ta yi maka daga zuwa sai mari? Me ke faruwa? Me aka yi? " Du a rikice take fadin hakan , shi kuwa yana tsaye kikam idannuwansa sun kada sun masa wani irin ja, gaba daya jikinsa ya dauki rawa tamkar yana filin yaki, hannayensa kuwa ya jimke ya saki, nan da nan jikinsa ya yi ja irin na bacin rai, idannuwansa suka kara kadawa Kuma dagowar da AMMI ta yi ta ga yannayinsa a haka ya saka gabanta faduwa Da sauri ta kama NAJEEBA ta mikar da ita , bata kuma ce masa komai ba sai jan NAJEEBAR da ta yi da sauro ta turata cikin kicin ta janyo kofar ta rufe A tsayen nan da yake idannuwansa a kansu har AMMI ta rufo ta dawo ta tsaya nesa da shi tana kallon ikon ALLAH Sai da ta sanyaya muryarta daga inda take ta ce" Saura 😁😁😁😁😁💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 [31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 64 A sanyaye AMMI ta ce" Haba Shaheed, kai da kanka ne yau ke marin fuskar Najeebana? Bayan ka san ko musulunci yayi hani da marin mutun? Mari fa cin fuska ne, wani irin laifi ne ta yi mai tsanani haka? " Idannuwansa ya lumshe sakamakon zafin da yake ji a cen kasan zuciyarsa kafin a hankali ya zauna yana mai kara jimke hannun nasa Rawaninsa ya idasa warwarewa ya yar a nan kasa sannan ya ja babar rigar da yake jin ta masa nauyi a yanzu ya sabuleta daga jikinsa Hannun nasa na dama ya kuma kurawa ido, wani irin haushin hannun yake ji a kasan zuciyarsa A hankali ya kara sauke ajiyar zuciya ya dago idannuwansa da sukai masa jajajir, muryarsa a sanyaye ya ce" So take sai ta kashe ni ido rufe ne? Me na yi mata da zata ringa hada ni da wani dan iska? Me ya fi ni da shi da zata ringa cewa wai tana son sa? Ammi sai kawai ta ringa ce min an mata auren dole itama ba so na take ba? Me ya yi zafi tsakani da Allah da take so sai ta kashe ni cikin ruwan sanyi? Me ya yi min saura? Ta amshe komai, ta gama amshe komai, ran nawama so take ta ga ya fita ko so take na ringa daga hannu a kanta , ko kuwa so take na je na halaka yaron mutane ne? AMMI bana iya yawan maganar nan, ashe ba zata gane yarena ba? " AMMI ta kai dubanta wajen UMMU da ta taso ta taho, a hankali ta karasa ta zauna itama a kusa da su Ammi ta ce" Me ka yi mata da ta fadi haka? " UMMU ta ce" haba Bilkissu, harma tambaya zaki yi abinda aka mata? Fitsaririyar yarinyar nan shin bata san darajar girman igiyar dake kanta bane da zata ringa magana irin na jahila? Inma me ya mata ina hadin ta kwara masa ba sonsa take ba? An fada mata shi son nata yake? NAJEEBA ba sonki yake ba biyaya ya yiwa iyayensa dan an isa da shi, fitsararoyar malan! " SHAHEED ya kalli UMMU da mamaki, ba sonta yake ba fa ta ce? Kansa ya dan girgiza ya rage muryarsa ainun ya ce" UMMU ba haka zaki ce mata ba, kin ga yanda hankalinta ya tashi da marinta da na yi fa, ni bama wannan ba daga tambayarta ne fa sai ta kama fadan nan, ko sun yi fada da wani ne ni zata tada min hankali haka kawai? " Tausayinsa ne ya kama AMMI, kwarai yanzun bata da dar cewa yar tata ta gama yiwa yaron nata illah a zuciya, ransa a matukar bace yake, hankalinsa a tashe yake, baki daya jikinsa rawa yake aman kuma ya ji za'a fatataketa ya tare, kar a mata haka, kar a ce da ita haka A hankali ta ce" MARIAM, wace irin tambaya ce ya yi mata ne? " Ummu ta sada kanta, tsakaninta da Allah Allah tausayinsa take ji a kasan zuciyarta, kuma ba wai dan ita ta haifi Najeeba ba ko wani abun, sam kawai bata so ya zurfafa har Najeeba ta gane dan kuwa ta san wacece Najeeba Kansa sade a kasa ya ce" daga tambayarta abinda take sha ta taimakawa yar uwarta dan ta gyara kanta shine ranta ya baci har take fada min wasu magangannun banza" Su dukansu da mamaki suka kuma kallonsa, sai kuma kunya ta hanna masu hada ido da junna A hankali AMMI ta ringa murza gaban goshinta cike da mamakinsa, dama haka ne ko likita idan abu ya shafe shi ne yakan rikice ya kasa gane gabas bare yama, kudu bare arewa, to ita yanzu mai zata ce da shi ne? Ta ina zata fara kwatanta masa lamura ne? A hankali ta ce" SHAHEED, wannan wace irin tambaya ce zaka yiwa macen da ta san darajar kanta? Ai ko mace bata son ka zata iya jin zafin tambayar nan, kaima menene haka da girmanka? " Kallon AMMI kawai yake cike da mamaki, to wai shi menene laifin da ya aikata haka ne? UMMU ta ce" aa AMMI, shi din ko ba mijinta bane ai yayanta ne kuma ubanta, bai isa ya yi magana da uta ba dan rashin kunya zata mike tana nuna shi da muciya? Sa'an yinta ne? Ko mahaifinta ya isa ya nuna shi da muciya, ai daraja ce, Allah ya daraja shi dole a bashi darajarsa " Ammi ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce" haka ne, ban ki ba domin a yanzun ko ni da wahala na yi garajen nuno shi da muciya, sai dai dan abin danki ne kina son takewa ki rufe harma ki dorawa yarinya laifi salon gobe ya kara dora hannunsa a jikinta? Idan shi Allah ya bashi darajar kasancewa sarki, ita sai Allah ya bata darajar zama matar sarki, kina so ki ce min itama mulkarta zai yi? Da kuwa na yi tir da ita harma na rantse cewar ba jinnin mutalab da Mariama bace ita! " UMMU ta ce" AMMI, kar ki yarda ki fadi haka Najeeba ta ji, ki murje idannuwanki walahi a kan Najeeba, to ita waye da ba za'a hukuntata ba? " AMMI ta kara sada kanta kafin ta dago ta ce" zan fadi gaskiya, iya abinda nake gannin shine gaskiya a kan zancen nan Ku dai kunna so ku take sanni ku take gaskiya ne bayan ba'a kyauta mata ba, na yarda matar mutun kabarinsa aman an yi wasa matuka da yarinyar nan, an dora mata auren nan ta amince kuma aka hadata kishi da aminiyarta? Nadia fa ta sha kwana a dakin Najeeba, itama haka, su yi fadansu su shirya, shikenan dan ya kuntata mata a laifin da ban san ko na meye ba sai ya aikata haka, duda na san matar mutun kabarinsa, ama Najeeba ta yi kokari kuma har ga Allah ina gannin girman hakurin da ta yi dan kuwa ban zaci zata iya cire kanta ta mayar da komai ba komai ba da sauki haka , dan haka gaskiya a daina, sam bans so, idan kana haka zaka iya hadasa rigima fa tsana a tsakanin matayenka, sannan zaka rasa kwonciyar hankali a wajen du wace ta ji zafinka a zuciyarta, ina kara fada maka mace fa ba hula bace, ka daraja mace, ka kara mutunta mace ! " Ajiyar zuciya yake sauke a karo na ba adadi, a yanzun so yake ya ganta gashi iyayen nasa sun saka shi tsakiya sun ki barinsa Najeeba kam AMMI na kuleta sai ta samu kanta da yin shiru na dan lokaci hannunta dafe da kuncinta kafin ta silale kasa ta fashe da wani irin kuka maran sauti mai cin rai Kanta ta dora saman gwuiwowinta, idannuwanta rintse kukanta take kashirban ta kasa baiwa kanta hakuri A hankali cikin kukan nata take fadin" Why me?, me na rasa Shaheed da zaka ringa nuna min iyakata? Ka san cewar nima ba da gangan na shigo rayuwarka da matayenka ba, ka san cewar ko da na shigo rayuwarka ban so wata shakuwa ta shiga tsakanina da kai ba, aman shine zaka saka na ringa jin tamkar ni kadai keda kai kana wulakanta ni? Menene na nuna min ka tara da wata bayan ni? Na san dama tunda ka kula matar cushe ai wace ka aura dan soyaya sai inda tunaninka ya tsaya a kanta, na san cewar zaka kulata harma ta ji tamkar ta haukace, aman me yasa zaka nuna min hakan a bayane? ........" Wani kukan ta kuma fashewa da shi har tana girgiza kanta dake sara mata , sai wani irin yamutsawa da cikinta ke A hankali AMMI da ta baro su da UMMU ta idasa shigowa cikin kicin din Da sauri ta je ta kashe gaz din dake ci tukunyar ruwan ta tafasa sai bori take tana dan kukan nan dake nuna tukunya ta tafasa Wajen Najeeba ta karaso da sauri ta duka tana kokarin dagota Cike da tausayinta ta ce" Sorry baby am, sorry hearty am, ba zai kuma dukanki ba in sha Allahu, ba zai kuma gigin taba min fuskarki ko wani bangare na jikin ki ba" Kanta saman hannayen Ammi, sai ta shiga tariyo marin, kwata kwata ita bama marin take tunawa ba, mari dai ba yau ta fara sha ba, duda wannan marin sai da ta ji kamar ta fara sakin fitsari sai dai wani takaici da ikon Allah zafin maganarsa ta gyashe zafin marin da ta shigo tana juwa dan jinsa Bata yarda cewar ta zama jaka a duka ba sai yau A hankali ta kara lafewa a jikin AMMI tana ta sauke ajiyar zuciya, me ya sa? Me ya yi zafi? Me ya sa yake son yi min haka? Marin nawama da ya yi dan ita ya yi? A kan Nadia? Idannuwanta ta rintse tana jin dacin hakan a kasan zuciyarta, ba dai matarka ba? SHAHEED na yarda ni bani da wani power ban isa ba, kuma in sha Allah zan tatare tabarmata na daina yaudarar kaina na baiwa masu waje su shinfida, domin bani da karfin kokowa da kai, Shaheed ka gama yi min ilar da idan na tsaya jin bakaken magangannunka ina iya macewa bani da ja da zabinka, in sha Allah zan tsawatarwa du wani banzan tunanina a kanka! Jin jikinta da zafi ya saka AMMI lalabawa ta mike da ita a jikinta A hankali ta kama hannunta da kyau ta ce" Na jefa maki dan waken zaki ci? " Najeeba ta yatsine fuskarta ta girgiza kanta a hankali ta ce" Na daina jin yinwar Ammi, zuciyata ke tashi" Daidai sun zo fita daga kicin din Ammi ta dan kura mata ido tana kallonta, sai kuma ta cire dubanta tana jaye da hannunta a hankali suka ratsa suka wuce dakinta Tun da suka fito komai ya tsaya masa, kwata kwata ya daina gane yaren UMMU da irin tataunawar da suke, a hankali yake kallonta har suka bacewa ganninsa kafin ya sauke ajiyar zuciya, Kuka? Kuka ne ta yi fa , kennan marin ya yi mata mugun zafi a jikinta da har ta yi kuka? So yake ya mike ya bi bayanta ama ya kasa wani motsin kirki bale ya iya aiwatar da hakan Ummu ta ce" SHAHEED " Dagowa ya yi yana kallonta ya kasa amsawa ta ci gaba da fadin" Ka gane, ba zamu iya tunkarar matarka da wata magana ta gyara ba, bama haka, a nan ba'a haka, aman kai ke aurenta, kaima cikin dabara zaka iya kwatanta mata ba kai tsaye zaka fada mata komai ba, domin idan ka fada mata kai tsaye komai na iya faruwa tana iya daykan maganar ta kaita du inda fahimtarta ta nuna mata, hakan kuwa sam bashi da dadi, sannan ko da wasa ka kiyaye fadawa wata maganar wata, mata matsala ne da mu , kamar yanda ka ga kana fama da shara'ar kishiyoyi kala daban daban wace a kowace safia kafin dare ya yi sai an sha shara'ar abokanan zama to hakan ne, wata rigimar bata taka kara ta karya ba ama take zama baba a yi ta yinta har sai Allah ya yi mata tsawa, baban abinda ke daukaka kiyayar mata idan Mijinsu na nuna bambanci, fifiko, ko ya ringa zancen daya a gaban daya haka kawai, idan kana gaban daya ba ruwanka da takalo maganar kowata mace " Dagowa ta yi tana kallonsa, kawai waje daya ya kurawa ido, kuma cikin ikon Allah har zuwa yanzu a cikin yannayinsa barin jikin nan ne kawai ya daina aman baki daya yannayinsa ya cenza baya cikin nutsuwarsa Ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta dauko masa ruwa masu sanyi ta mika masa Ruwan kuwa ya kwonkwade kafin ya kuma dubanta ya ce" Umani ai ita ta ja har na mareta ko? " Shi fa dama ba damuwa ba ya iya, idan damuwa ta shafi cikin zuciyarsa yakan rasa madafa, idan abu ya shafi AMMI yakan rikice ne, ya iya dakewa a gaban mutane ama idan ya samu wanda zai iya fayacewa damuwarsa fila fila to fa yakan manta waye shi ya kasa rikewa, bare ta tabata Najeeba ta shiga wani hali ne, ta tabata a yanzun Najeeba ta afka a ramin da bata shiryawa hakan ba, ita kanta tausaya masu take su dukansu, dan sun zurfafa tsanar junnansu ne hakan ya haifar da zazafar soyayar da suke aikatawa junna aikin fushi da fasara maganar dan uwa AMMI ce ta karasa shigowa, rigarsa dake yashe a kasa ta dauke babar rigar sai fitar da fitinanen kanshin turarensa take , dakakiyar shadar mai tsadan gaske ta sha aikin sarakunna milk color ta ajiye gefe ta zauna ta ce" tashi ka je bangarenka SHAHEED " Duban da yake mata tun da ta fito sai yanzun ya kifta idannuwansa, ya je ina? A cikin wannan halin da ya wankawa Najeeba mari har ta yi kuka? Ammi ta kuma kallonsa tana hade rai sosai kamar wace bata taba yin daria a rayuwarta ba ta ce" ka tashi ka tafi bangarenka lokacin sallah na gabatowa kuka yaren nan dan wake ne zasu yi ka ga har kwabin nasu ya hadu " Wajen kwabin ya kai dubansa, robar da Najeeba ke tukawa da kwabeben abin da bai san ko meye ciki ba, sai muciyar da ta saki nan kasa sanadiyar shigar zazafan marin da ya sakar mata, sai kwalbar yaji da abin kwai da mayonaise da lemun tsami da magi Mikewa ya yi dan bin Umarnin mahaifiyarsa, cikin nutsuwa yake takawa har ya idasa ficewa aman ya bar rawanin nasa da babar rigar tasa a nan UMMU ta girgiza kanta ta ce" Gaskiya kawata kina takurawa Sultan haba, gaskiya ki daina biyewa wancen sangartaciyar yarinyar, meye lagonsa kuka samu ne zaku fara bashi wahala ko me ? " Yar daria AMMI ta yi, cike da farin cikin da ta fito da shi, da farin cikin gane idanma SHAHEED na cikin halin matsananciyar soyayar Najeeba to fa itama ta kamu da ita , domin abubuwa da dama sun nuna mata haka tun kafin su samu wannan sabanin, idan ka dauka irin yanda ta yi hakuri da maganar fita saloon, ta yi hakuri da fita yawo, Najeeba ce ke yawan murmushi idan ana maganar shaheed maimakun da, abinda ta fi tsana a yi maganarsa, uwa uba yanzun tana shinfideta saman bed ta bata goro ko zata daina jin tashin zuciyar sai ta yatsina fuska ta ce" AMMI, to ai ba sai ya ringa nuna min ya fi son Nadia ba ko? " sun taru sun sakata a farin ciki, AMMI ta ce" wai kin san wani abu nana, anya yarinyata ba tana da wani abu ba? " Ummu ta yi murmushi tana gyara zamanta ta ce" Ba yarinyarki kadai ta harbu ba, harta Nadia, dan a zaman da muka yi a dakin cen tare na tabata tana da wata kama " Idannuwa AMMI ta lumshe sakamakon jin wani irin farin ciki na lulube zuciyarta, Alhamdulilah, Alhamdulilah, Alhamdulilah, ta ringa ambata a fili, Shekaru nawa sunna dakon jiran samun wannan kyauta?, ashe dai bayan Aliyu marigayi yana da rabon samun wani? Ashe dai ba zai biyota ba daga shi dif haihuwa ta dauke ko sama ko kasa? Najeeba na dauke da junna biyu, hakama Nadia? To ita me zata ce da Allah ne da irin ni'imomin da yake lulube ahalinta da su? Zata kara ninka ibadarta ne, zata ringa barin goshinta a kasa ne tana yiwa mai gaya mai duka kirari, zata ringa kai gaisuwa ga fiyayen halita, sannan ta kara rokar Allah kan ya bara mata yan tayin nan, duda hasashensu ne a matsayinsu na datijan da suka ga yau suka ga jiya suka iya bambance abubuwa da dama na rayuwa Ammi ta mike tana fadin" Mariam, ki zo mu kira docter ya auna min ita Maryam " Kamo hannunta UMMU ta yi tana girgiza kanta ta ce" ki kyaleta Bilkissu, idan shi din ne da zai bayana kansa, sam bana so ta san da wani abun a yanzu kin fa san shi kansa cikin baya tashi ciwulwutarsa sai an ambace shi, yanzu zo mu jefa masu dan waken nan sun yi gudun tsira " Daria AMMI ta yi itama ta shiga tatara kayan tana fadin" Allah ya shiryi Shaheed, ka zo waje maimakun a ringa ihun murnar zuwanka aa, kowa fashewa yake abinsa, kuma ba wata magana yake masu ba da ido ne zai ringa bin su uwa ya samu sabuwar hakita " Itama UMMU dariar take, nan suka shiga shapter abinda ke faruwa idan yana waje da yaren sunna shan daria A wannan rana sallah kawai ke tashin Najeeba daga nanauyan bacin da ta ringa yi, sai dan waken nan da ta wuni ci, domin baki daya kwadayinta ya taru ya tare a kan dan wajen Cen dare wajen karfe biyu ta ga message da numbersa, abinda aka rubuta a ciki shi ne *NA KASA BACI* , ta karanta ya kai sau hudu kafin ta tabe bakinta ta kashe wayar ta ajiye ta juya ta ci gaba da bacinta hankali kwonce Da asuba ta makara domin har an gama sallar asuba sannan ta iya mikewa jiki du a mace ta shiga wanka A lokacin yan uwanta du sun fara aiyukan gidan da ya zame masu jiki, kowace ta kama aikinta, da farko tana jin hayaniyarsu dan sun share dakin sun cenza abin shinfidar, sai dai daga baya sai ta ji diffffffff a lokacin kuwa Ummulkhair na kakaba daria muryarta sama sama Idasa broshing din bakinta ta yo, dama ta yo wankanta ta daura alwallarta ta juyo a hankali ta fito daga bayin ta juya tana rufewa ta idasa shiga cikin dakin Turuss ta yi sakamakon ganninsa zaune bakin gadon, cikin doguwar bakar riga irin ta sallah, rigar ta kara haska shi ya yi wani freshh da shi, sajen nan nasa lufluf sai dara daran idannuwansa dake kabta kikam yana mai binta da kallo Cire kanta ta yi a sanyaye ta furta " Morning " Bai iya amsata ba, duda mamakin jin ta gaishe shi da ya yi bayan tana fushi da shi, yana kallonta ta karasa wajen kayansu ta buda ta ciro rigar sallah da pant da bras Bata saka pant da bra din ba rigar sallar ta fara sakawa sannan ta dauki turare ta shashafa du wani sasa na jikinta kafin ta shinfida darduma ta shiga gabatar da sallar asubahi Sai da ta gama salarta cikin nutsuwa sannan ta mike ta dauki pant dinta Juyawa ta yi ta duka ta saka wanda hakan ya saka shi kara yi mata kuriii yana kallonta Sai da ta gama sakawar kafin ta ciro doguwar riga ta atampa, rigar kuwa ba'ai mata gidan mama ba dan haka take son saka bras Rigar sallar nan ta dan sasauta ta kaita daidai kugunta sannan ta juya masa baya hakan ya sa dogon bayanta shafafe wanda baya dauke da lungu lungu ya tsatsare shi sai dan fadin mamanta kadan da yake hangowa har ta saka bra dinta sannan ta sabule rigar baki daya Dukawa ta yi irin dukawat rakumi kansa kasa jikinsa sama ta dauki rigar wanda hakan ya saka shi sakin ajiyar zuciya yana kara gyara zama yana mai binta da kallo Rigar ta saka ta juya tana jan zif dinta sannan ta dauko dan kwalin rigar ta daura saman kanta ta kashe irin daurin nan na ture ka ga tsiya Rigar bacinta da ta cire ta dayke ta ninke ta mayar da ita wajenta sannan ta koma wajen dardumar itama ta nade ta kaudata ta karasa gaban madubi ta ja ta tsaya tana bin kayan kwaliyar su Ummu da kallo Murmushin mugunta da neman fada ta yi kafin ta shiga uda turarukansu Ai kam wani irin wanka ta shiga yiwa jikinta da turarukan nan tana harhadawa har suka fara hawan mata kai dan tsabar barna ama bata daina ba sai da ta ji ta jika da turare sannan ta ajiye Juyowar da take kanta ya kusa gwaruwa da kirjinsa hakan ya saka kirjinta bugawa ta ja baya kadan ta dora hannunta kan abin madubin nan da ba kwari gareshi ba, gannin hakan ya saka da sauri ya sa hannunsa ya taro kugunta ya rikota jikinsa har sunna jin numfashin junna na garwaya waje guda Muryarsa a shake ya ce" Ni zaki nuna tamkar bana waje BEEBAH? " NAJEEBA ta hadiye busashen yawun makwogwaronta, so take ta masa rashin kunya ta mumurguda masa baki, sai dai walahi tsoron marin nan nasa na jiya ya mata katutu a rai, ama idan ya san wata ai bai san wata ba Fuskarta ta yatsine a hankali sai kuma ta saki wata irin shagwababiyar murya ta ce" Haba SHAHEED, me kake so? Ko na kara fada maka sirrin abinda nake sha dan samun ni'ima ka kaiwa kawata? To SHAHEEED abunuwan ne da yawa walahi, da ka je wajen su Ammi su suke bani sai su harhada maka ka kai mata ta ringa sha may be a dace " Bakinta ya kurawa ido da mamaki, furucinta yake aunawa bisa mizani, a hankali ya yi niyar yin magana sai dai bugawar da zuciyarsa ke yi ya saka shi lumshe idannuwa yana ayanna yau ya ga tashin hankali, ya yi gwa da gwa da maza masu abin tsoro basa kayar masa da gaba sai wannan ficiciyar yar? Najeeba ta dora hannunta saman nasa ta shiga kokarin kwace rikon da ya yi mata idannuwanta saman fuskarsa tana tsinewa zuciyarta da dukan wasu burikanta, yaya zuciya da buri zasu yi mata haka? Dama su din masu cenza ra'ayinsu ne suka sakata hawa kan turba yanzun suke son sakinta a tsakiyar filin daga? Wannan wani irin tashin hankali ne da bata shiryawa haka ba? Rayuwarta da shi ta dauri niyar ko a yaya ta zo mata hamdan, idan da dadi idan babu oho, sai gashi banzar zuciya da banzayen burika na k8n fari mai mata sunna neman tarwatsa mata shiri? A hankali ta kuma kallon kyakyawar fuskarsa wace ke wartar du wani tunaninta da nazarinta, murya a shake ta kama hannun da dan karfin da take tunanin tana da shi ta ce" KA CIKA NI NA KARA GABA! " buda idannuwansa ya yi da wani kallo mai tafe da sako, sakon ya kunshi magangannun ban hakuri, da rarashi, da roko irin na ki ji kaina ki tausaya min, Bakinta dake mutsu mutsu tana rike shi dan kar ta yi abinda zai kurumtata ta kuma budawa ta ce" Barka da juma'a jama'atul musulmi A gaskiya ba zan iya kwatanta maku irin farin ciki da nishadin da kuke sakani yan gidan Mage Grup, walahi na wuni ina shan dariar chafterku, harda masu rrrrrrrrrrr na ce ku yi hakuri kar ku yi amai😌😌😌😌😌 [31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 65 *SAKO ZUWA GARE KU JAMA'AR CIKIN GIDAN MAGE, JINJINA, GAISUWA, FATAN ALKHAIRI, ADU'AR GAMAWA DA DUNIA LAFIA, HAKIKA ADU'O'INKU SUKAN SAKANI NA RINGA JINA CIKIN MATSANANCI FARIN CIKI, UWA UBA IRIN KOKARIN DA KUKA RINGA YI A KAINA, SAKWANI SUN SHIGA WAYA KUMA AN GODE, TABAS ALLAH SHI KE HADA BAWA DA MUTANEN KIRKI, SANADIYAR RUBUTU NA HADU DA MUTANEN KIRKI WA'INDA NAKE FATAN KODA NA DAINA RUBUTU ZAMU CI GABA DA KUTUNCI TARE DA JUNNA, ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI YAN UWANA MA SAMIRA DA BILKISSU, SHAWARWARINKU GARENI KO A WANI LOKACI ZAN DAUKA DOMIN KU DIN AMINAI NE KUMA YAN UWA NE* *NA GODE* Ta kuma furta" ka sake ni Shaheed " SHAHEED ya dan girgiza mata kansa bai iya bata amsa ba yana kallonta Takaicin shirun nan nasa nukurkusarta yake har cikin hanjinta A rikice ta ce" Ka sake ni dan girman Allah ka bani lafia na huta da fitintunun nan, zuciyata ba zata iya dauka ba SHAHEED, me kake jira da ni ne? Wani wulakancin kuma kake shirya min ne? SHAHEED tun ban san yarenka a kaina ba ka yi min wanka a bakin titi da ruwa masu sanyi, athmata ta tashi tun ina jan numfashi har na sume ka dana min allura ka kawo ni ka watsar, Shaheed ka tashi ka hada ni aure da aminiyata zaman kishi?, Shaheed ka saka aka kawo ni bangarenka na zauna a daren da yake nawa kunnayena suka jiyo min du wani irin abinda ke faruwa tsakaninka da NADIA, Shaheed Nadia Wasu hawayen wahalar ne suka ziraro mata masu zafo ta dora da fadin" du bai isheka ba ka dauke ni ka kaini saman datin da ta zubar ka dora ni Shin ni ba mutun bace?, Shaheed kana nuna min ido da ido matanka, ai ba cewa na yi ba matanka bane ba ko? Sannan Shaheed du bai isheka ba ka tambaye ni abinda nake sha? An fada maka ina shan wani abin ne? Ba abinda nake sha, bai isheka ba sai da ka mare ni dan na ki fada maka abinda zaka kaiwa yar gwal?, A hankali ta shiga rera sansanyan kukanta kafin ta dora da fadin" Nima ba son naka nake yi ba ai kau ......... " ta idasa fashewa da kuka mai ciwo Shaheed ya ringa girgiza kai a hankali yana jin wani irin ciwo da zafi da tashin hankali a kasan zuciyarsa, a hankali ya ringa sasauta irin rikon da ya yi mata muryarsa cen kasan makoshi ya ce" Dan Allah, ki daina cewa bakya *So na*, ki daina BEEBAH " Yana fada ne yana idasa sakinta, har ya saketa baki daya ya dafe goshinsa da wata irin juwa dake son maka shi da kasa ya juya mata baya kansa na sara masa, a hankali ya shiga cira kafarsa yana neman hanyar da zai fita a dakin, baki daya jikinsa kuma rawa yake masa Bata dakatar da shi ba sai hannayenta da ta harde a kirjinta tana mai binsa da kallo har sai da ya bacewa ganninta sannan ta saki dan murmushi tana share hawayen da ta yi forcing ta fitar a gabansa ta karasa gaban madubin nan ta zauna A hankali take tsara kwaliya a fuskarta a kasan zuciyarta kuwa fadi take 'Zan zame maka mace wace ta fi kowace mace rauni da zubar da hawaye a gabanka, SHAHEED ba zan yarda ka cin min ina zaune ba' Da kallo Ummulkhair dake zaune goye da NUSAIBA a bayanta wace ke rigima ta bi shi da kallo domin ita daya ce a falon, itama an sakata zama ne dan ta duba Mardiya da aka gama shaidawa cewar gatanan zata zo domin abih ya yi kiran Ammi ya fada mata cewar Mardiya ta yi rantsuwar daga gidan cen zata zo wajenta Kanta ta sada da sauri sakamakon ido hudun da suka yi tana dan kara jijiga yarinyar, sam basa jin nauyin goyanta su kam, kansa ya cire ya fice a falon Tana shirin mikewa ta shige ciki wajen Najeeba ta ji an banko kofar an shigo falon Mikewa ta yi a tsorace tana kallon wace ta shigo a haka din MARDIYA da kanta ke hayaki sakamakon labarin da aka kawo mata cewar Abih ya gyarawa UMMU gidansa dake Jeune cadre ya zuba mata kayan alatu tamkar gidan zai tsage dan kaya, ga wani irin fita daban da ya yi a anguwar, bata yarda ba sai da ta je ta ganewa idannuwanta duda mai gadi ya hanna mata shiga aman daga inda take ta ga abinda ta gani shine ta koma masa ta same shi gadan gadan da tashin balagar rashin kunya, ya mata banza shine ta ce zata zo ta sammu Ummun su yita ta kare, ba zata amshe mata miji ba bata isa ba tsohuwar banza kawai Gadan gadan ta idasa gaban Ummulkhair ta ce" Ke ina tsohhuwar guzumar uwarki take? " Ido Ummulkhair ta zarro tana kallonta, ita dai bata da fada irin nasu, bata iya hayaniya sosai din nan ba, Ummukulsum ta fi ta iya maida martanin rigima, har solofiyo suke ce mata ita da Zahrau, hakan ya sa ta dan rike kafar NUSAIBA dake daidai cinyarta tana kallonta ta ce" Wace haka kuma Mardiya? " Mardiya ta matso da wani irin balaki ta hankadata, bata shiryawa gannin hakan ba hakan ya sa ta je baya gaba dayanta ta fadi da bayanta saman Nusaiba jikin karfen kujerar falon Wani irin tartsatsin ihu Nusaiba ta saki kafin ta dauke dif Da gudu suke firfitowa daga kofa daban daban A guje suke nufo yar uwarsu dake yashe a kasa tana ta kokowar son kwonto Nusaiba da ta kara nauyi a bayanta sannan gwuiwar hannunta na zubar da jinni Da wani irin gudu AMMI ta idasa wajen ta shiga son kama su hankalinta tashe bakinta ya kasa furta komai Da wani irin sauri UMMU ta ture NAJEEBA dake son karasawa itama aman sam bata iya gudu ko sauri ba hakan ya sa take wata tafia tingil tingil hankalinta tashe Mardiya dake tsaye idannuwanta rufe ta ce" Baki dayanku bakinku a hafe ko? Bayan auren cin amanar da son zuciya kuma shine za'a kaita sabon gida tana tsohuwa ni a barni a gidan da yara suka tashi suka lalata? Walahi ban ga yar iskar da ta isa ta shigar min gidan miji ba! " Tas , fuskarta ta amshi wani irin fitinane, mahaukaci, zazafan marin da ya sakata kwala ihu ta juyo tana kallon kantamin hannun da ya sauke mata biyar Bai wata wata ba ya kara dauke fuskarta da wani tsadaden, wulakantace, fitinanen marin da ya sakata yin luuuuu cike da mahaukacin mamaki da al'ajabi ta kwala ihu ta ce" Kan uban cen kaya sa, ni ka mara? Ashe kuwa zaka iya marin Mutalab da MARIAM? zaka iya marin uwarka mahaifiya? " Da wani irin hauka hauka ya shiga kunce belt din dake daure a kugunsa , gannin haka Najeeba, da Ummukulsum suka rigaye shi afka mata, kan kace meye wannan kanwarsu bakuwarsu da yake itama jinnin shuwan ne ke yawo a jijiyoyinta ta afka masu, yaren suka ringa neman wajen kai mata duka Ummu ce ta daka masu wata irin tsawa mai hade da gunjin kuka, AMMI ta dago da NUSAIBA a hannunta wace hannayenta ke yin lagai lagai muryarta cike da kuka ta ce" Ta kashe ta, ta kashe yarinyarta ta cikinta, ta kashe Nusaiba! " Gaba dayansu ne suka idasa juyowa wajen iyayen nasu a tare, cikinsu mutun uku ne suka zube a summe sakamakon gannin irin jinnin dake zuba daga keyar NUSAIBA, Abih da shigowarsa kennan a hankali ya silale a wajen zaune dabas ya dora hannayensa bibiyu Yaya Dayabu ya daga kafarsa ta hagu ya fara takawa tana masa nauyi ama a haka ya ringa janta har ya karasa wajen AMMI dake kuka ido rufe tana maimaita innalilahi wa'ina ilaihi raj'une A hankali ya dora hannunsa wajen jinnin yana kallon yanda idannuwan yarinyar suke kakafe sannan jikinta ya dauki wani irin sanyi harta da fatar jikinta ta yi fayau Da sauri ya saka dayan hannun nasa yana gurgusa gashin kanta , muryarsa hade da wani ihu ihun kuka yake fadin" UMMU, wayo mun shiga uku, Ummu ku tare jinninta kar ta mutu, Ummu wayo ta kashe mana kanwarmu, ku kama mana kar jinninta ya kare, wayo Nusaibata, ku tare jinnin nan ya bar zuba kar ya kare AMMI, wayo Abih, Wayo Ummulkhair, NAJEEBA, wayo Bilkissu, wayo Najeeb zo ku tare jinnin kanwarmu na zuba daga kanta" UMMU dake kuka ta saka hannayenta tana janye nasa, muryarta a ciki dan tsabar kukan da take ta furta" innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Allah ka yi mana maganin masifar da ta fi karfinmu, Allah ka jikan yarinyar nan, ka sa ta huta, DAYABU ka bar dannawa Nusaiba ta rasu fa baka gani ne? " Qi kamar wada ta kara rikita dakin, gaba daya wa'inda ke jijiga wa'inda suka summanma sai suka kara rikicewa, Najeeb kam ya rukunkume mahaifinsa ya cusa kansa cikin kirjinsa yana kuka dan shi tsorata ne ya yi da gannin jinnin dake fita daga kan kanwarsa wace shekara daya ce tak tsakaninsu yanzu haka da kokowa suka rabu ta fara rigimar da ta zame mata jiki kwana biyun nan, domin haka kawai zata kama kuka tana dora kanta a jikin du wanda ke kusa da ita, kuma jikinta lafia kalau ba rashin lafia ba ba komai ba, hakan ya sa Ummulkhair ta goyata suka fito falo shi kuwa ya kwonta ya shiga baci Wani irin ihu DAYABU ya yi, a lokacin da NAJEEBA ta fashe da wani irin kuka hannayenta duka biyu saman kanta tana nuna Mardiya da ta yi wani irin wuri quri hannayenta duka biyu a saman kanta tana maganar da ba'a jin me take fada, ama da alama ta zauce ne dan kuwa magangannu ne take ta saki tana kuma kallon du wani mahalukin dake wajen Kukan kuran da Dayabu ya yi ya damki wuyan Mardiya ya kaita kas hannayensa bibiyu a rike da wuyanta ne ya saka Abih zabura da wani irin gudu yana kokarin bambare Najeeb daga jikinsa Ummu da gudu itama ta yi kansa tana furta" Mun shiga uku ku kawo mana talafi, Dayabu saketa, saketa kar ka dora laifukanta a kanka " Shi kuwa ido rufe haka yake furza yawun bacin rai yana fadin" kema sai kin bita, zan kashe ki da hannayena kowama ya huta da jarabarki, sai na halaka ki " Ido ABIH ya zaro gannin Najeeba hannunta wuka ne ta warto daga kicin da gudun balaki, sai ya rasa inda zai nufa Da sauri AMMI ta juya ta ajiye Nusaiba kusa da Ummulkhair da ta summe tun da aka furta Nusaiba ta rasu ga jinni na fita a hannunta itama da gudu ta yi niyar tare Najeeba Basu ga shigowarsa ba, sai hannun Najeeba mai rike da wukar nan da ya tare Rike hannun ya yi da dan karfi hakan ya sa ta saki wukar Wukar ya mikawa sarkin dogarai dake tsaye jikinsa na tsuma kafin da wani irin sauri ya zagaya wajen da tuni Mardiya ta summe dan azaba ya kama hannayen Dayabu ya shiga kwalkwata da wani irin karfin da ya saka DAYABU dago da dubansa yana kuka kashirban yana kallon mai bambare shin Irin yanda zuciyarsa ke bugawa har ana ganni ta makogwaronsa ya ringa girgizawa SULTAN SHAHEED kai, bakinsa ya buda yana cracking ya ringa fusgar magana ya ce" Ta, ta kashe min kanwata, ka barni na kasheta........dama so take du ta hahahahalaka mu, shikennan nima sai a kash...................n" kasa karasawa ya yi, jikinsa ya ringa saki a hankali ya lumshe idannuwansa ya taho zai fada mata Tare shi SHAHEED ya yi hakan ya sa Sarkin dogarai da gudu ya karaso ya kama shi ya yi saman babar kujera da shi Sai da ya bi falon da kallo, daya bayan daya kafin a sanyaye ya furta" Ammi ku shirya ta , Allah ya sa mutuwa hutu ce a gareta" Ya maida dubansa wajen ABIH dake tsaye kansa sade kasa, a hankali ya karasa ya dora hannunsa na dama gefen kafadar Abij ya ce" ABIH " ABIH ya dago da kyar yana kallonsa, a hankali ya ce" ABIH ka yi hawaye, ka zubar da hawaye ko zaka ji sanyi a cikin zuciyarka, sannan ka yi hakuro, ka yi hakuri, ka yi hakuri ABIH, taka kadarar rayuwar kennan, ka salaceta ka sakata a makwoncinta da hannayenka sannan ka yafe mata, yarinya ce duda haka kowa ya yafe mata, muma namu lokacin muke jira, ba wanda ya san musababin abinda zai kaishi kiyama sai Allah, dukan mai rai kuma mamaci ne Abih " ABIH ya kuma busar da hucin dake cikin zuciyarsa Zuwan likitoci ne ya saka SHAHEED ya gyara tsayuwarsa ya shiga yi masu nuni da su duba mutanen dake zube a summe, duda irin yanda suke ta kallonsa da son gaskata wai da gaske kamanin wanda suke ganni a gabansu ne SULTAN SHAHEED? Najeeba dake tsugune kanta a jikin hannun Ummukulsum ce ta dago a hankali ta mike tsaye da niyar barin wajen, sai dai wani irin luuuuu da ta yi zata zube ne ya saka shi daga kafarsa da sauri ya karasa ya tare ta, lokaci daya kuwa Sarkin dogarai ya shiga buga tsawar kowa ya sada kansa Da kirjinsa ya hadeta, a hankali ya karasa saman kujerar dake da girma ya zaunar da ita Kafafuwanta ya rage tsayinsa ya dauke a hankali ya dora saman kujerar , kafin ya gyara mata kwonciyarta yana gyara mata kitson kanta A hankali ya mika hannunsa ya dauki hijab din da ya tabata na Ammi ne ya luluba mata Hannunta ya rike na dama, a hankali yana shafa gaban goshinta , muryarsa a sanyaye ya furta" Kar ki daga min hankali, ki karfafa min gwuiwa ta hanyar zama jarumata, ki yi mata adu'a idan ba so kike du mu kwonta ba BEEBAH " NAJEEBA t lumshe idannuwanta, hawayen da suka bushe ne ta ji sunna harhada kawunansu, a hankali suka bale mata ta kai dubanta kan fuskarsa ta ce" Shikenan ta kashe min kanwata? Nusaiba ta rasu? " Hannunta ya kara jimkewa ya furta" ki yi ta hailala BEEBAH " Idannuwanta ta mayar ta lumshe Sakin hannun nata ya yi ya mike yana kallonsu Sai da ya kara kausasa muryarsa ya ce" du wanda ya farka ya dawo kusa da kujerar nan ya zauna, bana son na ji ihun kuka ko magangannun da basu da tsari, soyaya kuke yiwa yar kanwarku? Ku rakata da adu'a, ita ta bara mana duniyar, da ta tafi bata yi gagawa ba, mu dake raye bamu yi jinkiri ba, du zata dauke mu ne koda kuwa bama so!" Dubansa ya maida wajen sarkin dogarai cike da juriya dan kar yan uwansa su ga gazawarsa abin ya lalace ya ce" ka bada sanarwar jana'izar NUSAIBA" Wannan mutuwa ta Nusaiba ta girgiza al'umar damagaram, daga bakin lokacin da aka gama zana'izarta aka dora zaman makoki gidan ya ringa dinkewa da al'umah na nesa da na kusa, mutuwar kankannuwar yarinya ta samu halartuwar jama'a tamkar zasu fasa gidan sarautar Dangin MARDIYA daga bakin lokacin da suka ji takamaiman abinda ya faru sai kunya ta hade su, mahaifiyarta ta yi kuka, ta yi kuka, ta sanarwa Allah, sun hadu su dukansu sun kai gaisuwa sun kuma nemi afuwa cike da jin kunya kafin mahaifiyarta ta kara yiwa Abih gaisuwa, ta nemi afuwarsa sannan ta dora da fadin" Tabas du wanda ya ce a duniya son ransa zai bi karshensa nadama, yau gashi Mardiya taurin kanta, da jajircewarta dan gannin wani ya halaka ta halaka kanta da kanta, a yau Marfiya ta tashi a banza babu gidan mijin babu yar da zata iya tunata ta yi mata adu'a, kaya, nima tawa kadarar harda haihuwar MARDIYA, ta tsananta kishi, abin ya dawo bakin ciki, ta zamanto bata san alkhairi ba, ta so duniya, duniya ta bata sakamako, tsakanina da ahalin Mutalab sai kyakyawar adu'a, har gobe ni din mai bin ku da kyakyawar adu'a ce" ta karashe tana mai fashewa da kuka, Abih da har yanzu bai samu kukan ba kansa kawai ya ringa dan girgizawa, sai dogarai ke bada amsa a haka suka bar gidan suka koma gidansu dan ba abinda zasu ci da Mardiya, hukunci ya hau kanta, hakan zai zamo ishara ga du wata mai taurin hali irin nata! Sai da suka dauki sati biyu sunna zaman makokin NUSAIBA kafin kafa ta dauke A wannan ranar ce Sultan ya bada umarnin UMMU ta fito ta je gidanta Basu musa ba, ama y'ayan nata yan matan ne kawai suka zauna domin baki daya sauran bin bayanta suka yi suka cika motar DAYABU ya tuka su har sabon gidan Sunna zuwa DAYABU ya shiga nununa masu kowa wajen da yake nasa, nan ya kara zubar da hawaye a lokacin d aya kawo kan gadon Nusaiba, sai da ya yi mai isarsa sannan ya share hawayensa ya yi mata adu'a .............morning.................... [31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 66 A hankali UMMU ta idasa bakin bed din da Abih ke kwonce, royal bed ne rantsatse wanda ya amsa sunnansa, idannuwansa a rufe suke tamkar mai baci, sai dai ba baci yake yi ba, Cikin nutsuwa ta saka hannunta ta janyo farar takardar dake ciki Warwareta ta yi ta karanta, Fuskarta dauke da yannayi na rashin jin dadi ta ajiye nan gefe domin igiya dayar da ta yi saura tsakaninsa da Mardiya ne ya tsinke Sannu sannu ta haura saman gadon Hannunsa daya dake kusa da idannuwansa ta kamo cikin nata, a hankali ta furta" Gani na zo Aban Dayabu, ka buda idannuwanka , ka fada min dukan abubuwan da suka faru da kai tsayin shekarun nan, ka fada min wanda ya bata maka ni kuwa zan je mu gwada karfi da shi komai girman tsayinsa da karfinsa" A hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya kafin ya kamo hannunta ya dora gefen fuskarsa yana mai kurawa fuskarta ido, sannan yana mai jin sanyi na ratsa dukan zuciyarta da tunaninsa, muryarsa a shake ya ce" Ki dawama da ni har karshen numfashina NANA, ki zame mana uwa baki daya Nana, walahi na ga rayuwa, ba zan sake fade fade ba Nana " Idannuwanta ta lumshe a hankali ta kara matsawa kusa da shi kafin ta shige jikinsa ta lumshe idannuwanta bata ce da shi komai ba Shima idannuwan nasa ya lumshe dan ya amsar kennan, wato ta aminta, kuma ta dawo gare shin kennan, baci ya shiga nema domin rabonsa da bacin har ya manta sai barawon dake fuzgarsa ya dan taba ya farka tsabar damuwa A washe gari aka tafi da MARDIYA, domin koda kuwa labarin mutuwar ya nuna ba da gangan ta kashe y'arta ba hukuma ta ki aminta da haka, sun tafi da ita sai yanda hali ya yi (Ku mu saba da dane zuciyoyinmu, ku mu ringa yiwa kawunnanmu adu'a kan Allah ya sa mu fi karfin zukatanmu) A hankali abubuwa suka fara komawa gurbinsu, du mutane suka kama gabansu ciki harda Zahrau da yarima da dayar kishiyarta Sosai yayan Ammi suka yi sanyi da rayuwa, barema Ummulkhair, ta jima tana nisa cewar a bayanta Nusaiba ta rasu, sai Najeeba da take dan fama da zazabin dare da kewar kanwarta Nadia a wajen take wuni sai dare take tafia bangarenta Sultan kam ido ya kawo ya zubawa ikon Allahn Najeeba, rabonsa da wani kusanci tsakaninsa da ita tun shinfidetan da ya yi a kan babar kujera Ya rasa ina take shiga da idannuwansa suke gaza ganninta, kwata kwata ta yiwa ganninsa tsada, yakan sauke ajiyar zuciya ya dan girgiza kansa kawai, domin yana yiwa al'amuranta uzuri, lalle tana da tata hujar Ita kanta Nadiar lokaci ya barta har ta kara warwarewa, iyayenta sun zo sosai haka kanwar mamanta na nan har zuwa lokacin A hankali komai ya dawo normal, ya rage samun mutane a kai a kai na gaisuwa Ya zamanta ya koma rayuwa yanda yake yi, a hankali komai ya ringa daidaituwa har du wani tunani nasa ya dawo jikinsa Sannu sannu rashinta a kusa da shi ya fara tasiri Sati uku kennan da rasuwar Nusaiba abin ya gama kama jinni da jikinsa Bilhaki a yanzun kewarta yake, idan ya tuna magangannunsu da ita kuwa irin furucinta yakan ji tamkar an dake shi da karfe mai karfi a dukan gabobin jikinsa, da ace zata kasance mai yi masa uzuri da ta gane ta taka matsayin da ba wace ta taba takawa a duniya, da ace zata iya ganewa da ta ture du wani abin sun zauna, bai je mata da wata magana ba sai dan ya yaba, bai je mata da rokon ta gyara kawarta kuma yar uwarta ba sai dan ya jita daban, ba cin fuska bane, yabo ne Yakan girgiza kansa, a hankali ya furta" Ban yi haka da sanina ba BEEBAH " Sai ya shafa gemun dake habarsa a hankali ya ce" da ace zaki yarda, da na furta maki irin ilar da kika gama yiwa rayuwata Beebah, kin kai wajen da nakan ji a kasan zuciyata cewar ba zan iya babu ke ba" Wayarsa ya dauko a karo na bakwai kennan da zai tura mata mesage ba amsa, shi kansa tun abin na bashi mamaki har ya dawo ya daina bashi mamaki irin yanda yake da naci a kan lamarinta, shine zaune da aikin yiwa mace message, shi da ko aurenki zai yi mai zuwa ya masa zancen daban shi kawai sai an kawo ki zaku hade, dan murmushi ya yi A hankali ya dora dogayen yatsutsansa ya shiga taping din message kamar haka" Kin manta da bawan Allah ne? Ki bani amsa alfarmar rasululah S.A.W " Sai da ta amsa da sallalahu alaihi wa salam, kafin ta tura masa da salama Ajiyar zuciya ya yi yana kallon salamar kamar wani dogon message mai dadi kafin ya dora da fadin" Ina muradin gannin matata, ko zan samu wannan alfarmar? " Bata maida masa da amsa ba sai kurawa Nadia ido da ta yi wace ke ta ciye ciye abinta, sam yanzun ta sake da mutanen gidan tana cudanya da su tamkar yan uwanta na jinni, sannan ko tsakaninta da Najeebar sukan taba hira, maganar sirri ce ta kau, basa wani sirrin junna irin na da Mikewa ta yi ta shige ciki Katon hijab ta sanyo hade da nikaf ta fito Wajen Ammi ta je ta dan duka ta yi mata magana sannan ta mike ta yi gaba Saloon dinta ta nufa Tana shiga ta je ta zauna su Aida suka saki aikin da suke yi suka bita dakin da ta shige Umarnin su gama ta basu sannan ta fara tsife kitson kanta da ya tsufa Sai bayan sun gama ne suka rufu a kanta, wasu na tsifar kan, wasu na wanke mata kafa da akaifu, daya na gyara mata akaifun hannu , mai kunshi na hada kunshin da zata yi mata dan kadan ba mai yawa ba iya hannayenta Ba ita ta bar saloon din nan ba sai da yama sosai kafin ta koma bangaren AMMI A cenma wanka ta shige cikin nutsuwa ta gama kimtsa jikinta cikin lalausan lesh ja mai adon baki a jikinsa kafin ta fito hannunta rike da dan mayafi ruwan baki sidik mai shara shara Ido kawai AMMI ta zuba mata, kalar fatar jikinta wani sheki take kara yi tamkar ta rihana, a yanzun sai ta kara budewa ko dan abinda suke zargin tana dauke da shi ne? Kiraye kirayen salar isha ya sakata daukan hijab din AMMI ta gabatar da sallar sannan ta zauna nan sunna dan taba hira Sai da karfe tara ta yi ne Ammi ta kuma kallonta a karro na ba adadi , muryarta sanyaye ta ce" NAJEEBA, tashi ki tafi mana " NAJEEBA ta dan yi murmushin, ita kanta ta kusan minti ashirin tana saka ta tashin to sai ta kasa tashin, dan haka ta mike Har ta fara tafia AMMI ta ce" Kar ki manta, k8 fada masa gobe in sha Allah zaki koma bangarenki kin ji? " Ita dai ta amsa ne kawai ama ba wai dan tana tunanin zata iya zaman wani bangarenta ba, ita kam me zata je yi cen ita daya kwal? Duda ta san tana kaura yan uwanta zasu bita ne aman ta fi son wajen da take jin shige da ficen jama'a, tana jin sasaucin abubuwa da dama idan tana jin motsin mutun a kusa da ita A hankali ta tura kofar glass din dake sadaka da falonsa Sansanyan kanshin turaran wuta hadi da kanshin turaransa da sanyin AC ne suka daki hancinta Dan lumshe idannuwanta ta yi tana jin zuciyarsa na yin sanyi A hankali ta fara bin fallon da kallo sai kuma ta ringa hasaso irin zaman da suka yi da mai falon Jikinta a mace ta idasa shiga, sai a lokacin ta ganshi zaune , ya kura mata ido yana kallonta bayansa jingine da kujerar falon wa'inda aka cenza su aka zuba farare tas tas, hannunsa daya a daudai kahon zuciyarsa, dayan kuwa ajiye saman kujerar, kansa sumar kan ta fito sosai ta yabanya Ajiyar zuciya ta sauke, gayen nan mai kyau ne......ta furta a kasan zuciyarta, sannan mai aji ne......ta kara baiwa kanta amsa Hannunsa dake ajiye ya dago a hankali yana miko mata Sai da ta bi hannun da kallo sai ta dauke kanta A hankali take karasawa inda yake zaunen, ama ba da niyar kama hannunsa ba Tana zuwa ta nemi waje ta zauna tana kallonsa Ido ya zuba mata yana jin yanda gaba daya hankalinsa, da tunaninsa, da nutsuwarsa suka tsaya cak a saman kanta Kanta ba dan kwali sai dan bakin mayafin nan karami mai shara shara hakan ya sa gashin kanta da aka wanke mata shi tas aka sakata a kask sannan aka yi mata dan ado da shi kadan ya bayana kansa yana ta sheki Yar madaidaiciyar kwaliyar da akai mata ta tafi da tunaninsa Shanyayun idannuwanta suka zuba masa kasala A hankali ya kara dora idannuwan nasa a gefen fuskarta da ya mara, Bai taba tunanin du irin tashin jinta watarana zai iya daga hannu a kanta ba Kuma lunshe idannuwansa ya yi ya kara budewa saman kanta, tun gaishe shin da ta yi sai ta raja'a hankalinta a kan wayarta sannan ta daure fuskarta tamau Haka kawai sai ya ringa jin shakar yar karamar kanwarsa, shima sai ya kasa ce mata komai aman ya dago kadan daga kwoncin da ya yi tun farko ya tsura mata ido tamkar zai hadiyeta da su Najeeba ta ji zaman nan ba zata iya shi a haka ba, idannuwansa kan yi mata girma har ta ji kamar zata zurme cikinsu, daidai da bugun zuciyarta ya cenza dan haka a hankali ta muzguta ta mike tsaye ta zagaya ta fara tafia da niyar shiga wancen dakin daya Bata ji motsinsa ba, batama san ya mike ba, sai jinta ta yi ya bata wata wawar runguma , ya rukunkumeta a jikinsa sosai yana shakar kanshin da jikinta ke fitarwa tun daga na turaran wuta zuwa na ruwa masu sanyin kanshi da kama jiki A hankali ta lumshe idannuwanta tana tatara du wata jarumtar da zata iya gasa shin, domin ta kamu da tsoron anya kuwa zata iya juya wannan tsadaden saurayin? A sanyaye ta furta" SHAHEED menene haka kuma? " SHAHEED bai ce da ita komai ba, sai juyota da ya yi ya kasance tana facing dinsa A hankali ya shiga romancin dinta, du inda hancinsa ya kai sai kawai ya gigice ya kara neman fita hayacinsa Sai dai abin mamaki sauraronsa ne kawai take ta ki ta maida masa da martani ko yayane bayan ba haka take tsaya masa kikam ba Tun sunna abin a tsaye har ya idasa kai su jikin bango ya yi mata majingingina kafin ya zamar da ita kasa Sosai ta dantse hakorinta dan hannawa kanta viye masa, iya karfinta ta ringa tare kanta dan kar ta biye masa, shi kuwa fama yake ido rufe, cen ya kamo hannunta ya dora saman fafadan kirjinsa mai dauke da laulausan gashi kadan ba da yawa ba a hankali ya furta" touch me Bab " Najeeba ta lumshe idannuwanta ta ki ta taba shin Bai hakura ba dai ya kuma janyota jikinsa idannuwansa lumshe yana ta faman lasar lebwnta da ta datse ta ki yarda wani abin ya samu a hakan Gashi dai bata hanna masa tabata ba, aman kuma ya kasa samun fuskar yin yanda yake so Gaba daya ya saketa, ama tana jikinsa ya shiga yamutsa sumar kansa da ta taru sosai idannuwansa rintse A hankali Najeeba ta ringa sauke ajiyar zuciyar jin ya saketa dan walahi kiris ya rage bata bada kai ba, Cikin nutsuwa ta ringa tatara gashin kanta da ya cire mata ribom dinta ta dunkule shi waje daya kafin ta janyo rigarta dake yashe ta shiga kokarin mayarwa fuskarta tamke kamar bata taba daria ba Mikewa ta yi tsaye, hakan ya saka shi binta da kallo har ta shige Kara yamutsa gashin kansa ya yi kafin ya mike ya shige wanka Ya jima ciki ya dauro alwallah ya fito Nafila ya dora cikin nutsuwa ko zai samu sasaucin tunani Sai da ya gama sannan ya shafa ya zauna yana jan carbi Sai da dare ya kara rabawa sannan ya mike ya nufi dakin da ta shiga yana jin ba zai iya raba gado da ita ba bayan gata a kusa da shi a ranarta ba Cikin nutsuwa ya haye saman bed din Cikin abin rufar ya shige ya janyota jikinsa sosai ya rungumeta Sai dai zafin da jikinta ke dauke da shi ne ya saka shi dakatawa yana kallon fuskarta duda cikin duhu ne Kara shigewa jikinsa take cikin dan magagin bacin dake fuzgarta a hankali ta dora kanta a damtsen hannunsa ta sauke ajiyar zuciya Kasa kwoncin ya yi, dan jikinta zafi ne da shi, sai ya ji hankalinsa du ya tashi A hankaki ya yaye mata bargon , sanyin da take gudu ne ya lulubeta dan haka ta farka tana mai wara idannuwanta da kyar Muryarsa kasa kasa ya ce" Beebah, baki da lafia ne? " Najeeba ta dan sasauta rikon da kuma shige masan da ta yi tana girgiza kanta Ajiyar zuciya ya sauke ya janyota jikinsa dan sam baya son wannan shirun da daure fuskar, muryarsa a raunane ya ce" Na jigata da yawa BEEBAH, kin ga kale ni, du na fita hayacina menene, me kike so na yi ne? Yaya kike so na yi ne? Baki san irin yanda damuwarki ke kashen du wani dalilin dake iya saka ni farin ciki ba? Gefen fuskar tata ya ringa shafawa a hankali kafin ya kamo hannunta na dama ya kai wajen fuskarsa, kasancewar bata jin karfin jikinta sai kawai ya shamaceta ya dan kaiwa fuskar tasa mari ya furta" ki rama ko zaki huce, mare ni ki huce Beebah, ki yi hakuri, ban san lokacin da na zarce haka ba............................., shiru ya yi mamakin kansa zai kashe shi, sai dai ya faro ba zai tsaya ba, dan haka ya dora da fadin" Ban san yanda zan kwatanta maki irin dacin da nake ji a duk lokacin da kika tunasar da ni ba ni kike so ba, harma ki yi kokarin furta min sunnan wanda kike so din Beebah, walahi nakan yi kokarin bara maki wajen dan ban san me zan iya aikatawa ba " A hankali ta dago da fuskarta tana dan buda hannayenta da ta jimke tana kallonsa, gefen fuskarsa ta dan shafa a hankali ta furta" Me yasa kake nuna min kamar ka damu da lamarina bayan ba haka bane? Meye dalilin da ya sa ka tsane ni ne a rayuwa? Me ya sa daga baya ka shiga jikina? Me ya sa ni ba zan taka matsayin da wata ta taka a rayuwarka ba? Me ya sa kake tunanin kai kadai ke iya jin zafin furucina? Me ya sa furucina zai maka zafi a kahon zuka bayan na san ba wani lamari dake damunka a kaina? " Murmushi ne yake mai ciwo, hannunta ya jimke cikin nasa muryarsa a sanyaye ya ce" Eyah, a yau bakin wace ta saka min damuwa shekara da shekaru nake fama da miki a cikin zuciyata ce ke neman furtan bata taka rawa a rayuwata ba? Cikin rawar wace take son takawa ne? Wace zata riken makogwaro na kasa hadiye yawu ko wace? " Sado idannuwansa ya yi yana kallonta , a hankali ya saki dayan hannun nata ya kawo yar yatsarsa wajen sajen fuskarta muryarsa sanyaye ya ce" Beebah, ni na san ba biye da ke da nake bane, wayona, fadana ko dabarata ya saka Allah ya kare min ke ba, Beebah yaya aka yi a lokacin da aka fitar da ni daga gidan koyon yaki ina buda ido na fara ganninki da saurayi a wajen danjar daje raba hanyar gidan Abih? Beebah hannunki cikin nasa kun gaisa ko meye oho, a lokacin da aka fice da ni a motar mai martaba ta sirri muna zaga gari a cikin tukin wahainiya ana nununa min yanda garina ke ciki da al'umar garina, sai kawai muka hadu da ke, wando ne a jikin ki blue da farar riga, ko nonon kirki baki fara ba aman kina tsaye da wani Beebah bayan ba haka na tsara mana ba? " Da mamaki ta kurawa fuskarsa ido tana kallonsa, Ido cikin ido ya ci gaba da fadin" Du wannan bai isheki ba , daga jin na fito sai kika dauke kafa da zuwa wajen AMMI sai idan ta saka an dauko ki, Beebah kowa na zuwa gaishe ni aman banda wace na riki gaisuwarta da mahinmanci, kowa na rububin son sanina banda ke, yar kankannuwa da ke kikai min katutu kika hanna min zaman lafia Beebah aka tashi aurena, a tunanina shakuwar da muka yi kina karama ya bara maki abinda ya bara min, aa , sai kika dauko makada kika dinka dinki mai tsada kika cashe a aurena, shin wannan bai isa ya batan rai ba? , bayan wannan da shekaru Allah ya amshi ran mai martaba, Beebah na maye gurbin kujerarsa, abubuwa suka kara matso ni sosai, fuskantar lamura suka sakoni gaba, a haka kika kutso da makamanki na son sai kin halaka ni Beebah ba'a sati ban yi shara'ar ki ba, abin takaici yawanci ko budurwa ta kawo kararki da saurayinta kar ki kwace mata, ko matar aure ta kawo karar a maku tsakani kar ki rabata da mijinta da y'ayansu A lokacin d akaina ke sarawa na buda idannuwana sai na ga yar kankannuwar kanwata ta zama cikakiyar budurwar da dukan mai Namijin dake amsa sunnan namiji zai iya mararin son samunta a matsayin wace take kusa da shi sosai, kusanci mai girman gaske, Beebah gaki da son saka kannanun kaya, gaki da son amsawa kowani dan banza Yaya kike so na yi da tunanina ne?" Ya kuma tsagaitawa yana shafa dogon hannunta ya ci gaba da fadin" Bayan wannan kika tashi da burin tsanar sarauta, kika dora da burin tsanar mai farin fata, karfi da yaji kika sakani boye kamanina wa duniya dan kar abinda ke raina ya falasa ki guje ni!, Ya kara lumshe idannuwansa ya ce" Beebah, ban taba jin ina zama lusari, wawa, wanda komai ke kuncewa ba sai kina daf da ni, idan ina shara'arki nakan yita ne zuciyata na aman jinni, nakan bayanata ne jikina na tsuma, hankalina a tashe, sai na kafe ki da ido dan ki fahimci yarena ki rufa min asiri ki kiyayi neman halaka ni, duda kuwa na san kallon nan naki da nake zai haifar min da mugun bukatar son na kebance da ke a matsayin matar aurena" Dan murmushi ya yi yana fadin" Rigimamiyata, ban koya maki sakankancewa da ni ba dan ki sakankance da kowani gardi, sai gashi abubuwa na zuwar min masu bata zuciya har ta kai na yi akwati na tatara damukarki na kule, na ringa neman laifinki ido rufe da yanda zan yi na kama ki a kan zargin da nake maki dan na hukunta ki na huta, ba zan boye maki ba da ace na kama ki da wani laifi abinda zai hanna min gabatar da hukuncinki a tsakiyar garin damagaran ba karamin abu bane, dan kuwa kin min ilar da ido rufe wajen maida duka nake nema duda a fahimtata bakima san ina yi ba, ke rayuwarki kawai kike, " Irin yanda take kallonsa ba ko kiftawa ya saka shi kara saka idannuwansa a cikin nata ya ce" Wai harda ce maki ki fito ki bashi nutsuwa?, da baki fito daga shagon Alhajin nan ba da sai na halaka shi, kina fitowa na shiga na biya du abinda kika kashe na nuna masa cewar matar aurece ke, hakan ya sa bai neme ki ba, aman baki dadara ba kika shiga motar tsohon nan har ya taba maki hannu, da baki fito a motar nan ba da ban san me zan maku ba!" Ya karashe yana mai cije lips dinsa na kasa irin abin ya masa ciwo sosai ya dora da fadim" Sai kika shirya ranar da zan hadu da ciwo irin naki wato huka ta hanyar gayato tsageran nan har fada, Beebah kika saka dinkin dake tona min ajiyata, kika ringa wasu abubuwan da suka kusan dauken numfashina dan kawai ki tada min hankali ina zamana ko tausaya min bakya ji ga rigimar gari ga ta cikin gida, ga kuma taki " Gaba daya wata mutun mutuni ce ta zama a kwoncen da take a jikinsa tana mai bin idannuwansa da lebunansa da kallo Baki daya komai ne ya yi mata nauyi harma ta rasa ta inda zata fara , da kyar ta iya furta" SHAHEED " SHAHEED ya kara sauke mata duban nan da ta yiwa lakabi da kallon tsana, a hankali ta dago hannunta ta kai wajen idannuwansa ta shiga shafa saman idon hakan ya sa ya dan lumshe su kafin ya kuma budewa ya kama hannun nata ya kai wajen bakinsa ya mana mata kisss mai zafi a kai A hankali ta ce" Ka min gwari gwari yanda zan fahimci yarenka, Shaheed wace irin shakuwa ce da saka abu a rai ta saka ka aikata haka? Wani irin nauyin baki ne ya hanneka tsawatar min?, Sai kuma ta kara sasautawa ta ce" zargin da kake min ba shine ya fi tsaya min a rai ba, dan kuwa zan iya cewa ko yayuna sunna min nasiha ne kawai, kasancewa mai fita nema a saloon wajen da ba abinda ban tatara ba, kawayen banzan ne, tarin yan daudun ne, yan bariki na bugawa a jaridar ne, uwa uba irin tarin samarina ya saka kowa ke min kallon na zubar, Aman Me ya sa ka dubi wata bayana? Me ya sa ka dauki aminiyata? " Shaheed ya ringa dan yin murmushi yana kallonta, cikin nutsuwa ya juyeta kasan sa ya dan dora mata jikinsa kadan sannan bai sakar mata nauyin jikinsa ba, muryarsa ya kausasa ya ce" Tsoronki nake " Da mamaki take kara kallonsa tana dan tare hannunsa dake son shiga cikin jikinta kafin ta dan dago da idannuwanta tana kallonsa, ido daya ya kashe mata ya ce" [31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 67 "Tsorona kuma?" Najeeba ta fada tana kallonsa da mamaki Murmushi ya yi yana shafa kansa a hankali ya ce" Da gaske nima sai da na zauna na gane tsoronki nake, kin ga abinda kike yi na fadace fadace ina da damar na kama ki na lakada maki duka na rufe ki, kaf Duniya ba wanda ya isa ya amshe ki, ama sai kawai na ringa kallonki ina fata a cikin raina....inama zaki rufa min asiri ki daina?, inama zaki daina biya samari?" Dan lumshe idannuwansa ya yi yana jin kansa na dan sara masa sannan bakinsa ya fara masa ciwo sakamakon wannan zuba da yake yi Jin lalausan hannunta a wajen sajensa tana shafawa ya saka shi buda nanauyan idannuwansa yana kallonta, A hankali ya kara kusanta kansa da ita, lebunnanta ya cafka ya shiga bata hot kissss, Idannuwanta lumshe ta kama harshensa a hankali ta ringa tsotsarsa a cikin bakinta hakan ya saka shi yin kasakai cike da mamakinta da wani irin tsuma da jikinsa ya fara A hankali ta saki sannan ta lume kanta a kirjinsa cike da kunya Wata irin ajiyar zuciya ya ringa saki ya mayar da hannunsa yana shafa gadon bayanta A hankali ya kuma zuge zif din rigar tata, A hankali ya zareta daga jikinta kafin ya kara hade jikinsu waje daya yana ta tatara kalaman bakinsa dan kokarin gannin ya bata amsa a dukan tambayoyinta ya ci gaba da fadin" Abokiya nake nema, wace zamu yi zama na fuskantar junna, wace zata yi rayuwa da ni ta matsayin miji abokin rayuwa abokin wasa, ba uban gidanta ba, burina nima na samu wace zata ce min NA KI! Ta nunan ita ga yanda take so ba wai kulun ni ke da gaskiya nine na isa ba, jtama ta nunan ta isa da komai nawa!," Ya dan rage sautinsa sosai ya ce" a gaskiya na hada ki da aminiyarki da farko bisa hukuncin Allah cewar matar mutun sai ta kasance matarsa koda kuwa baya so, na biyu na yi niyar hada ku ne dan na rama irin zafin ciwon da nake ji a duk lokacin da kike wahaltar da ni, sai dai ki sani BEEBAH, itama ina jinta a raina, sam bana so ki dauka ko bana son zama da ita ki wulakantata, Nadia tana da tarbiya da kyawawan halaya, da ba dan kin min illah ba da babu abinda zai tsayar da ni haukacewa a kanta!" Idannuwanta a lumshe suke tana sauraron dukan kalamansa a hankali cikin dadadar murya da sansanyan lafazi A hankali ta dago dubanta ta tsatsare fuskarsa da kallo, irin yanda fuskar ta dauki ja zaka fahimci ya gaji da maganar nan, ama sai ta kuma dakewa domin burinta ya idasa horuwa da yi mata labari dan kuwa ba zai zamanto ita ke zuba ba shi yana kallonta gata mutun mai kaikayin baki sam bata son zama bata dan labari A hankali ta ce" Tall me, kana son wasu ni baka furtan kana so na ba dan me? " Da mamaki yake kallonta, sai ya ga to du bayanin nan da yake na menene? Hala bata fahimci inda ya nufa ba, idan ya furta mata cewa ta masa illah bata gane wace irin ilar ta masa ba kawai so take ta bashi wahala? Kai ya girgiza ya yi saurin rike hannunta da take dan shafa kirjinsa a hankali ya ja numfashi ya ce"Idan kika tayar da rigima zaki iya dauka kuwa? " Murmushi ta yi tana kara shigewa jikinsa tamkar wata mage, shi kuwa hakan ke kara hautsina masa lisafi ya zamanto sai kakarewa take kar ta hargitsa shi har ya haike mata Kuma jefo masa wata tambayar ta yi cewa" sai nake ji a kasan zuciyata ban gamsu da cewar ka aureta dan ka rama bane " Murmushin ya yi shima ya ki bata amsar wannan magana, cen ya kara tare lebenta da take bin hannunsa da shi a hankali ya ce" BEEBAH " :Ummmmm?" Ta amsa shi tana dan langwabewa a jikinsa Kuma talafota ya yi ya ce" Jikinki zafi nake ji, baya sauka kara hawa yake " Idannuwanta ta lumshe, so take ita a yi kawai, haka take ji a kasan ranta wanda bata san dalilin da take son ya haukata mata jiki ba, Muryarta a sanyaye ta ce" haka yake min kusan sati biyar yanzun " Idannuwansa dake lumshe yana jin yanda ta saka yar yatsarta a bakinta, dumin bakin nata da irin yanda ta shiga tsotsa a hankali a hankali nan da nan jikinsa ya dauki rawa, da sauri ya buda idannuwansa sukai ido hudu da junna, irin yanda ta yi kalar jariri sai ya ji kamar zai summe daga zaunen nan da yake Da karfi ya sauke nanauyar ajiyar zuciya kafin ya birkitata baki dayanta ya yi mata runfa Da wani irin sauri yake gurzarta idannuwansa lumshe, idan ya birkitota nan sai ya birkitata cen, jikinsa na wani irin rawa rawa kamar zai hadiyeta ya maidata ita cikin cikinsa ya huta Hannayensa yake cikawa da mazaunanta sai kawai ya dan saki murmushi a fili ya furta" MASHA ALLAH " Sai da komai ya kankama ya ji shi tsamtsamtsam ga abu na bin lamarinsa, sai kawai ya rukunkumeta a jikinsa yana fitar da wani irin numfashi muryarsa a ciki ya furta" Da wani ya shigar min da ya halaka min farin cikina har duniya ta tashi, ban taba jin kishin abu, da Kaunar abu, da son kilace abu irin yanda nake jin naki ba NAJEEBA, NAJEEBA ina son ki, ina son ina son ki, ina son ki so na gaskiya da babu yaudara a cikinsa, ki min rai, ki agaza min, ki dube ni" Hawaye ne masu sanyi da wani irin tsuma ke ratsa fuskarta, fuskarsa da ta yi ja ta kurawa ido, a hankali ta kai hannunta ta shiga goge masa yan guntayen hawayen dake zirarowa ta kurmin idannuwansa Idannuwansa cikin nata yake furta" ki furtan kalmar so ko zan ji sauki a zuciyata " Zuciyarta ce ta kara bugawa, ta yarda cewar shi din Namiji ne cikake mai iya motsa zuciyar du wata halita, yannayin sarautarsa na kara masa wani irin girma da kwarjini a idannuwanta, yannayin shigarsa na haukata lamuranta, takan nacewa son kallon shigarsa, takan nacewa kanshin jikinsa harma ta taba gigin siyan irin turaransa ta karar da dan tanadinta, shi din mai tsada ne, komansa mai tsada ne, jajircewarsa, da irin tsayuwa kan kafafuwansa na sakata jinsa a cen kasan zuciyarta, sai dai ba zata furta ba, ba zata iya furtawa a yanzu kai tsaye ba, dole zata ja zarenta na mata wanda zai bashi bambancinta da watarta, dole zata kara tsayawa ya furta idan yana cikin hayacinsa kafin ta idasa aminta da magangannunsa ko ba komai namiji yake ehe Sun raya daren nan kamar ba gobe, hakan ya sa nanauyan baci yin awan gaba da ita Cen cikin bacinta ne ta ringa jin ana shafa fuskarta A hankali ta juya ta ci gaba da bacin tana fan yatsina fuska Bai hakura ba ya ci gaba da shafawar a sanyaye hakan ya sakata dan buda nanauyan idannuwanta ta sauke a kan ni'imtaciyar fuskarsa Wani irin murmushi ne a kan fuskar tasa, wanda kana ganni zaka fahimci yana cikin farin ciki Muryarsa a sanyaye ya furta" BEEBAH, ki tashi ki yi sallah, kin ga na fita tun da duku duki an ce Nadia ba lafia ashe baki tashi ba har karfe tara? Tashi likitan ya dawo na ce ya tsaya ya baki maganin zazabin nan na dare, kuma kin san me Nadia na dauke da junna biyu ki tashi ki ji abin farin ciki" A hankali ta idasa wara idannuwanta a saman fuskarsa, Allah yana ganni maganar junna biyun Nadia ya sakata sakin wani irin murmushin farin ciki, a hankali ta ringa jin kaunar aminiyar tata da son tayata farin ciki na bijiro mata, Fuskarta mai dauke da murmushi ya tsurawa ido, Hannayenta ya rike har ta idasa zama a saman bed din, kafin ta shiga mika tana lumshe idannuwanta Da sauri ya dan kawar da dubansa dan walahi idan har zai zauna kallon mikarta yanzu zata rikita masa lisafi yana zamansa kalau Kamata ya yi ta mike tsaye, kuma yanzun jikinta sam ba zafin ko daya, haka kuma bata kama da marar lafia A kofar bayin ta ja ta tsaya tana dan tura shi irin kar ya biyota Murmushi ya yi ya tsaya har ta rufe bayin sannan ya samu waje ya zauna yana jiran fitowarta Shi kadai yake godewa Allah irin baiwar da ya yi masa, Nadia na dauke da ciki har na sati uku , ta fara rashin lafia ne sosai yau har AMMI aka fadawa shine ta kiraye shi ya yi kiran likitar dake duba matansa ta zo ta dauki jinninta da fitsarinta ta koma, har ta dawo ta kawo result shine ya dakatar da ita cewa ta baiwa Najeeba maganin zazabin dare, s nan ne AMMI ta yi nuni da kar a bata ba'ai mata gwaji ba tukuna, domin ita dai ta san abinda take ganni a jikin Najeebar gashi ba kowani magani ba mai ciki ke iya sha ba Yana nan zaune ya jima sosai kafin take fitowa daure da tawul a kirjinta Cikin nutsuwa take kokarin karasawa wajen kayan salarta da abin sallah Duka yana kallonta har ta idasa sallar sannan ya kurawa fuskarta ido da ta yiwa takwaf takwaf tana karasowa inda yake zaune Sai da ta dare kan cinyoyinsa sannan ta sarkafo hannayenta a wajen wuyansa ta shiga zuba shagwaba tana kara tabe dan bakinta ta ce" Ni kiwuyar zuwa falon AMKI nake yanzun " Murmushi ya yi yana kallon yanda take yiwa fuskarta a hankali ya ce" Ni kuwa bana tunanin zan iya katabus jin kin jima kina kwana da zafin jiki " Kara langewa ta yi a kirjinsa ta ki cewa komai sai dan kukan shagwaba da take tana kara shiga jikinsa Idannuwansa ya lumshe, a yanzun ya fara tunanin yarnan zata zauta shi ne idan ya yi da wasa fa A hankali ya mike da ita a jikinsa ya shiga takawa yana mai kara gyara rikonta a jikinsa Idannuwanta lumshe tana shakar dadadan kanshin turaran dake fita a wuyanta har ta ji tsittt kamar hayaniya ta dauke Da sauri ta dago dubanta, ba shiri ta dirko daga jikinsa tana zazare ido gannin yayunta da kanwarta zazsune kawunnansu a kasa, wata datijuwa a gefen AMMI itama kanta a kasa, sai AMMI da ta kawar da dubanta kamar ba abinda ta gani zuciyarta kuwa wani irin mamakin SHAHEED din ne ke neman halakata, a da takan aunawa a ranta cewa shi din bai yi halayen mahaifinsa ba na kulawa da mace, aman a yanzu sai ta karyata wancen tunanin Cike da mamakinsa ta kale shi , bakinsa ya dan tabe ya kama hannunta ya ce" Mu je mana " Da sauri ta juya cike da wata irin kunya ta koma hanyar da ya biyo da su, ita ta yi nisan kiwo a sinsinar wuyansa ashe har ya kawo kofar bata sani ba har ya bude ya shigo da ita a haka tana nanakarsa ita kam me zata cewa yan uwanta da ta gama kurantawa bata son sa, da wani ido zata kalli AMMI ta ganta kwonce rashe rashe a jikinsa "BEEBAH, wai ina zaki je ne haka?" Ya fada yana saurin cin mata dan da gudu ta fala Birki ta ja ta ci a lokacin da ta saka kanta cikin dakin ta juyo tana dago hannayenta ta ce" Fisabililahi SHAHEED ka san su AMMI na zazaune da su Aunty Ummu ka shiga da ni a nanuke da kai salon su ce da ni munafuka, AMMI kuma ta yi tunanin na zama marar kunya? " Irin yanda take bayanin tana nunawa tana yawo ta kasa tsayawa waje daya hannayenta a sama ya bashi daria sosai, sai abinda ya kara birge shi gannin fada ake masa yau kuma, ikon Allah kala daban daban a wajen yarinyar AMMi, sai kawai ya hade bayansa da garun wajen ya harde kafarsa sannan ya dage mata girarsa ya kane mata ido daya ya ce" Zo nan " NAJEEBA ta yi sakalo tana kallon yanda ya yi da fuskar tasa, sannan ta kai dubanta wajen da ya nuna ya kuma daure gida A hankali ta karasa ta tsaya ta sada kanta, hakan ya kara bashi daria, wai kunya ta ji ko me? Lalema "Mu je a duba min ke" ya fada yana kallon fuskarta Tana murza yan hannayenta a hankali ta ce" Dama lafiata kalau nakan yi masasarar dare wani lokacin " Kansa ya girgiza ya ce" Bana so kina rashin lafia " Dago da dara daran idannuwanta ta yi tana kallonsa, cikin nutsuwa ta idasa jikinsa tana mai dora kanta a saman kirjinsa, muryarta ciki ciki ta ce" Ni allurar cema bana so a rayuwata, ka barni haka na tuba " Du idan ta kusanta jikinta da nasa sai ya ji kamar zai tsere domin abin bambarakwai yake zuwar masa, bai saba ba ko kadan bai saba ba ko Nadia bata shiga jikinsa, takan sada kanta a gabansa dai sannan takan damuwa da cin sa ko shan sa, ama Najeeba ta mayar da shigewa cikin jikinsa aikin yinta Hannun nasa na dama ya dora a bayanta, a sanyaye ya furta" Ki ce kina so na BEEBAH? " Shiru ta yi na lokaci kankani, hakan ya sa kirjinsa ya yi ta bugawa harma yannayin ya so ya dagule masa Yar karamar wayarsa ce ta dauki tsuwa , yana dubawa ya san AMMI ce ya daga Bayan ta yi magana a hankali ya furta" AMMI ta tafi, bata son allura " Ammi da ta yi zaman son gannin irin farin cikin da zai nuna itama idan aka tabatar mata irin farin cikin da zata ji sai ta yi turus da maganar da ta dauko ta ce" Shaheed, ka kawo kin ita nan, ko ta tsaya yanzu yanzu ana kawo mata abin fitsari maza ta yi a kawo min " Bai saka komai a ransa ba sai tsayuwar da ya ci gaba da yi da ita a jikinsa har kunnayensa suka tsinkayo masa tafia kafin ya ji an tsaya Bai bude idannuwan nasa ba ya furta" Bani " Ummulkhair da ta juya da sauri ta juyo har jikinta na rawa ta duka ta miko masa robar da aka bata ta kawo Najeeba kuwa sai ta kara boye fuskarta a kirjinsa ta kasa dagowa dan tana jin kunyar Ummulkhair da kuma irin abinda ta tabata zasu yi mata idan sun hade A hankali ya kuma shiga da ita yana janta a jikinsa har suka dangana da bayi Sunna shiga ya shiga son cire doguwar rigar dake jikinta ta sallah Bata iya yi masa musu ba har sai da ya cireta baki daya kamar wata wada zai yiwa wanka, ya mika mata abin muryarsa ciki ciki ya furta" Ki yi ki bani " Da bakinta ta ringa mutsu mutsu tana tunanin kuma a gabanka zan yi? Tsumamun idannuwansa da suka cenza kala dan rashin samun amsa daga gareta ne ya kura zuba mata hade da kakausan kallo A hankali ta juya ta nufi wajen WC Ta haka ta yi tabara ta zuba fitsarin ta cire hannunta kanta a kasa ta dago hannunta tana mika masa Idannuwansa a kanta har ya amsa sannan ya juya ya fita Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana cije lebenta na kasa tana shafa mararta tana jin irin fitsarin da take yanzu mai yawan gaske ne ya fi na da yawa, sannan idan tana yinsa har ji take mararta ta yi mata sakayau sannan ta dan kwashi dumi A hankali take huci mai hade da tsantsar kaunar bawan Allahn nan Acting dinsa na tsaye mata a zuciya, irin yanda baya kyankyaminta na halaka tunaninta Ta jima a cikin bayin wannan karronma domin tunani ne ya yi gaba da ita har sai da ta ji ta kage a zaunen da take sannan ta janyo ruwa masu dumi sosai ta kimtsa jikinta ta sake yin wanka ta ja rigarta da tawul ta fito Du a tunaninta ya jima da barin dakin domin a kadan ta dauki minti talatin a bayin nan fa, sai dai yana tsaye ne jikin bango kansa a kasa yana tunani, kwata kwata yarinyar ta iya dauke natsuwarsa da kwonciyar hankalinsa, bai san ta yada zai kwatanta irin yanda take tafia da shi ba, bai san ta inda zai bi ya samu ta furta masa kalmar nan ba, du ji yake komai nasa ragage ne, yaya zai yi ta yafe shi? Shin bata son sa? Me ya rasa ne? Kar dai har yanzun wancen din ne a ranta? Kar dai du wannan bata lokaci da falasa akwatin sirrinsa da ya yi mata ita din a banza take kallonsa? Hannunta mai danshi ne ya taba damatsunnansa masu cika, A hankali ya dakata yana kallonta Dan murmushi ta yi a sanyaye ta ce" Me ke damunka? " Bai bata amsa ba, sai hannayen nata dake rike da damtsensa, dayan kuwa na rike da tawul din da ta dauro da ya kurawa ido Sannu a hankali ta ce" Ina missing din buga basket, zaka je terrain mu je mu buga kwalo? " Leben nata yake kallo har ya saka hannu ya janyota gaba dayanta jikinsa Kyakyawar runguma ya bata kafin ya shiga aika mata da zazafan sako wa'inda suka saka jikinta ya dauki rawa idannuwanta suke marmarmar kamar zata side dan azabar shaukin da ya dauketa Ihu ne kawai bata yi na, tana rike da kansa idannuwanta rintse hakama lebenta dantse Dif ya yi sakamakon kiran da ake ana karawa, kuma kukan kiran AMMI ne Da sauri ya laluba idannuwansa na rufewa yana bude su da kyar dan jarabar dake cinsa ya daga kiran aman ya kasa yin magana domin komai ya ki fitowa daga bakinsa A hankali ya saki wayar sakamakon wani irin abu da ya tsirga masa tun daga kansa har kafarsa sanadiyar abinda AMMI ta fada tana ta daria tana ambaton Alhamdulilah Alhamdulilah Cikinta dake shafe ya kurawa ido, da duba irin na tsanaki, A hankali ya yi sama da dubansa har zuwa fuskarta, Sannu sannu ya mayar da ita saman bed din ya kwontar da ita Kasa ya yi sosai nd verry slowly ya dora jajayen lebunansa a saman mararta A hankali ya ciro harshensa mai dumi ya ringa lasar marar tata, hakan ya sakata rintse ido da karfi ta rike kansa tana jin jikinta na kara dauka Bai bari ba har sai da ya ji zata sume tana fadin" wayo Shaheed ka bari wayo wani yamyamyam ake min " Cikin gagawa ya ringa ruda mata jikinta, da kyar bakinsa ke kwacewa yana fadin" tell me you love me , kiss me baby, please lv me hearty " Rukunkume shi ta yi hawayen shauki na zirara daga gurbin idannuwanta muryarta na rawa ta ringa furta kalaman a rarabe " *i..........l................o........v.......e............JJJJJJJJJJJJJJJSHAHHHHHHHHHHHAD* " Kamar ky din kara kunce dokin jikinsa ne, sai da ya zabura baki dayansa ya saki hanniniya sannan ya ringa tafiar da su cikin salama idannuwansa na zubar da wasu irin tsadadun hawaye masu yawa da shauki, tamkar zai hadiyeta, ba tare da ya ji mata rauni ba yake nuna mata wata irin soyayar da ita kanta ta saki sansanya kuka mai ratsa zuciya tana rungume shi a jikinta, ta yi sadaranda ta zubar da makaman yakinta, ta yarda Allah shi ke dasa so a zuciyar bawa a lokacin da bai shiryawa hakan ba, yau gata ta zubar da komai a gaban dan fari mai mata mai sarauta, yau gata ta gane dan Namiji na saraki ba zai hanna masa nunawa matarsa soyaya da bata kulawa ba, a hankali ta ringa kara yarda da shi harma ta buda idannuwanta ta sauke a kyakyawar fuskarsa mai saje a lokacin da yake tatareta yana mai furta" Ki bi min a sannu kar ki sauka da karfi, dan Allah ki hau bayana na goya ki na kaiki falon mana to waina Sapni Suhani din nan a wace tasha ne ake yinta, ni banma san akoy tashar ko babu ba dan bana iya rabona da kallon TV BEEBAAH" Najeeba ta sauke ajiyar zuciya ta daidaita ta haye bayansa, ya mike da ita tamkar wata yar baby ya karasa falo da ita a jikinta gajeran wandonsa ne sabo da farar rigarsa, ta kame gashin kanta ta soke da macajin kansa Tana bin dukan motsinsa ne har ya gama hada TV din dake makale a bango wace rabonsa da kunnata har ya manta, kai shi mantawa yake akoy TV a duniya, ko labaru yakan dubawa ne ta yanar gizo Zama ya yi bayan ya dauko masu abinci ya sakata jikinsa da spoon yana ciyar da ita tana ciyar da shi cike da farin ciki da kwojciyar hankali sannan sunna kallon series din na indiyawa wato YOUNG LADY (SISINA GATA FA MUTUNIYAR TAKI) cikin shauki ............................................ Alhamdulilah maganar auren Yaya Dayabu ta kankama, an gama komai rana kawai ake jira wace aka tsayar nan da wata biyu da sati biyu domin mahaifiyar amaryar ce ba lafia an fitar da ita waje Zuwa lokacin cikin dake jikin matan Shaheed ya gama fitowa ya girma ya idasa bayana kansa, domin na Najeeba watansa takwas da sati uku Na Nadia kuwa watansa bakwai da sati hudu Rayuwar zamantakewar dake gudana tsakanin Nafia da NAJEEBA zan iya kiranta tsaftataciya, akoy kishi a tsakaninsu, sai dai tsaftatace, kishin yan gayu wato kishin cikin daka wanda kowace burinta fuskar mijinta, idan kuwa suka hadu sukan sha hira harda wasa da daria da matsanancin kulawa da damuwar dan uwa idan har damuwar ta bayana a fili Idan wani abu ake a familly dinsu Nadia duda baya son fitar Najeebar yakan kaita da dare da kansa a cikin motarsa, ta shiga ta yi barka ko jaje sannan su ja su yi wajen hutunsu, wajen da a da sukan hadu ne dan su yi fada, harma su buga basket ball wanda yake bin takunta a hankali yana tareta dan kar ta fadi takan yi sport dai amta haka kafin su biyo wajen mai kilishinta su siya sannan su shiga ta boyayiyar hanyar da sarkin Dogarai ya saka aka fasa yake gadinta da kansa idan SULTAN zai fita har ya dawo A gidan Abih ana zama ne na fahimtar junna, hakuri da junna, juriya da tarbiyar y'aya, dan kuwa Nana Maryama wato UMMU ta zame masu uwa, wace haihuwarsu ce kawai bata yi ba aman dukan wata dawainiya da su dariarsu ko kukansu a kafadunta suke zube su, inda mijinta ya zame masu uba tsayaye, mai basu kulawa ta musaman, mai gindaya doka a wajen da ya dace sannan baya tashi a kanta, mai saka ido sosai a kan tarbiyarsu, mai dafawa matarsa yana bata gudunmuwa a dukan abinda ta yanke masu na zaman rayuwa, hakan ya sa su dukansu suke tafe da rayuwarsu bisa aminci, kulawa da junna, ladabi da biyaya a tsakanin junna, sannan ko yanzu idan ka yarda ka taba daya a familly dinsu to fa ka janyowa kanka rigima ne da ahalin gidan MUTALAB......sannan a yanzu fadan ya cenza salo ne maimakun daga kan DAYABU sai ya faro daga kan MUTALAB ya zarto kan NANA MARYAMA ya dire kan NAJEEB! ........................................... Masarautar Agadez Wahalar da suka sha ta tsayin wata biyar biyar kowace a gidansu a karkashin ikon wanda ya isa da su ta saka sukai sanyi tamkar kazar da ta sha dukan ruwan sama Sun yi sototo da su harma suke labewa a lokacin da aka fitar da su aka gabatar da su suka dawo mutane sak kamar kowa Sarkin garin agadez ya yi duka da kyakyawar bulala ya gindaya rantsuwar cewa ba zai iya dagawa du wani mai wulakanta dan adam dan kawai Allah ya bashi dama ba, ya kawo misalai da ayoyi ya fasarce kan ko musulunci ya hanna da irin alkawarin azabar da zata tabata a kan masu irin halayen Gimbiya da zinariya kafin ya sanar da gayar daurin auren Yarima da Gimbiya Ummukulsum rana daya da yaya Dayabu, hakan ya saka Gimbiya kara rintse idannuwanta domin kuwa wannan lamari har ya taba lafiarta dan a yanzu fama take da hawan jinni mai karfin gaske domin bata taba tunanin zata wayi gari ita Gimbiyar sarkin garin agadez a gidan horo a gidansu ba, hakan ya sa sunna komawa ta salami masu hidimarta dan idannuwanta ganni suke daria suke mata, sun gama rainata sun gama ganninta a wulakance a yanzun kam bata da wata daraja da fada a ji a masarautar Agadez Inda Zinaria take kara daga mata hankali da koke koke da magiya da rokon a taimaka a mayar da ita dakinta ta tuba ba zata kuma ba A yanzun masautar na tafia ne bisa mutunta bawa, daraja dan adam, bayin masarautar kansu sun samu inci daidai misali, domin ba zaka kiraye su da bayi ba sai dai mahidimta haka kuma har salarry ne da su GIMBIYA Zahrau kuwa na dauke da cikinta wata hudu abinta, inda Sarki ke nan nan da dan cikin nan yana mai bata kulawa ta musaman ___________________________ A yau ya yi wani irin baci ne mai cike da mafarkai wai ana miko masa jarirai A lokacin da ya farka salar asubahi ne ya sauke dubansa a kan Nadia, baiwar Allah ta kara budewa ta zama wata irin rusheshiya, gashi yanzu bata samun wadatacen baci sai goshin asuba, a haka yake tashinta ta gabatar da ibadarta, mahaifiyarta ta nemi alfarmar ta koma gida ta haihu aman ya kasa bari Da sauri ya kimtsa ya gabatar da sallarsa, kafin ya zauna ya shiga tashinta Da kyar ta iya tashi ga nauyin jiki ga nauyin baci ya taimaka mata har zuwa bayin sannan ya dawo ya zauna da carbinsa a hannunsa yana ja Wayarsa ya dauka ya shiga dubawa dan gannin sakwanin da ya samu A yauma ya ci karro ne da message din Zinaria, bai duba ba ya goge shi ya ajiye wayar gefe Sai da ya ga ta tayar da sallar sannan ya mike ya nufi bangaren AMMI dan du idan aka ce ba kwanakin Najeeba bane hankalinsa kacokam na kanta, yakan kwana ya a mafarkai wani mafarkin har da su gudu zai kaita asibiti Tun da ya buda ya fara cin karro da yaran gidan, ga wani dadadan kanshin turaran wuta da ya daki hancinsa, sai shige da fice suke murna kwonce a kan fuskokinsu, hakan sai ya bashi mamaki domin su din ba masu tashin asusubar nan bane A hankali ya idasa kutsawa ya shige falon, nan kunnayensu suka fara jiyo masa muryarta a sanyaye ta ce" AMMI, ba zan iya shan kunnu ba ni dai , kin ga kunnu na busa mutun haka kawai na zama katotuwa a ringa yi min daria?" Ammi na daria ta ce" NAJEEBANA, ki taimaka ki sha kunnunki kin ga yaran nan da suke mutsu mutsu da baki, ina tsoron su yi tsotsau, idan kuwa babu ruwa za'a sha rigima a gidan nan" Wata irin zabura ya yi har yana jin zai fadi a kas dan karasawa wajen da suke hayaniyar Da sauri ya bayana a gabansu, gaba daya jikinsa ne ya dauki rawa harma ya rasa me zai furta a lokacin da ya ga NAJEEBA zaune saman katifa mai daukan mutun biyu gefenta sange ne irin na jarirai da wasu jajayen jarirai sunna kwonce lufff sai yan uwanta da suka zagayeta Ammi ta ringa murmushi tana gannin yanda ya rikice ya kalleta , ya kalli yaren , ya kalli Ammi, ya kalli yan matan da du suka sada kawunnansu sunna gaishe shi "Ammi yaushe yaushe? Ammi biyu ne? Ammi yaya aka yi ba'a kirani ba? Ammi wai da gaske ko daya daga cikin mafarkaina ne?" Ya ringa fadi bakinsa na rawa kamar zai fadi ya haye saman katifar Salamr su Yaya Dayabu da Abih ne ya saka su juyawa A lokacin shi kuwa ido rufe so yake ya shafa gefen fuskarta koma ya sumbaceta sai kusantarta yake tana dan kaucewa tana sada kanta Yaya Dayabu kansa sai ga hawaye yana ciro yaran yana mikawa yan uwansa da mahaifinsu sun kasa furta wata kalma mai nauyi, sai cen yaya dayabu ya ce" AMMI, wai dama ba wahaka haihuwar? Ni kulun da tunani nake kwana, irin yanda Najeeba take da son jiki idan ta tashi haihuwa du sai mun fita hayacinmu, wai sai kawai yanzu na ga message" Ammi da farin ciki ya kasa boyuwa a fuskarta tana daria ta ce" tun karfe daya take nakuda, shima ogan ai tun lokacin na gwada kiransa ama ba'a daga ba sai na masu uzuri kawai Muna tsaye muna kulawa da ita har abin ya idasa kankama, walahi Allah ya bata mai sauki tunda an sauka lafia, ama ai haihuwa haihuwa ce DAYABU" Yaya Dayabu ya ringa jejera mata sannu, shi kuwa Shaheed ya rike hannunta na dama yana kallonta, wani irin farin ciki, da madaukakiyar kaunarsu baki dayansu ya saka shi jin son ya rukunkumeta ya kwala ihun sunnansa ya yi ta murna Karshe dai a wajen nan har Nadia a nan ta same su, inda ta ringa santin babis din maza baki dayansu masu girma da kyau kamar zata hadiye su haka take ji a cikin zuciyarta Sun hade, sun cakule, harta da yaran sun saki jikinsu a gaban Sultan wanda ya kasa ya tsare yara a hannunsa haka kuma hannunta a hannunsa ya kasa saki sai faman murzawa yake a haka har aka zo maganar shayarwa nan ya kura mata ido cike da birbewa yana kallon yanda suke kiciniya ita da Ummulkhair Kansa ya dan girgiza yana murmushi ya mike ya bar wajen dan a baiwa masu son shigowa barka danar shigowa domin an dakatar da su a waje Saura daya kwalin kwal😁😁 in sha Allah [31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *68* *ND* *ND* *ND* *ND* *ND* *ND* An sha Sunna lafia, sunnan da idan na tsaya zane dole ne mu shekare a wajen nan, harka ce ta manya, manyanma saraki dan haka ki hasaso yanda lamarin ya wakana hajiata, yara sun ci sunnan ABDALLAH da MUHAMMAD Sunna yin sati biyu da kwana biyu auren yaya Dayabu ya rage saura sati uku Nadiama ta haihu, ta samu yaronta namiji fari tass shima kato da shi Nan aka kuma yin wani zaman sunnan, inda baki daya Najeeba ta hargitsa taron ta hanyar shigar da take sakewa, gata jegon ya karbeka fatarta ta kara murjewa , sai kawai take baza abin kallo da kanshi idan ta gita, haka kuma a tsaye take kan kafafuwanta a kan al'amura Uwa uba mawakiyar nan ce ta larabawa ta sake zuwa, wada a lokacin da kidan ya tashi SHAHEED sai da gabansa ya fadi da sauri ya bada umarni a kaiwa Najeeba karamar wayarsa dan ya san batama san inda tata wayar take ba Murmushi kawai take zubawa a lokacin da take jin kashedinsa na kar ta kuskura kar ta yarda, kar ta yi gigin yin rawa A hankali ta furta" Haba takawa, haba uban gudan Beebah......zan yi maka rawarka a daki ne zan juya maka har na kada maka kugu na yi maka rawar kalangu daga ni sai kai, na daina rawa ko dan su Abdallah " Murmushi ne ya subuce masa ya ringa dan gyada kansa cike da kasaita hakan ya sa dogarai sada kawunnansu sunna miko gaisuwa da kirari dan gannin Saraki na murmushi ya tafi duniyar shauki (😁) Gimtsewa ya yi yana mai kashe kiran tare da sauke ajiyar zuciya An watse taro lafia, bayan watse taro ne mahaifiyar Nadia ta zo har wajen Ammi ta duka ta nemi alfarmar Nadia ta je gida ta yi wanka, ba dan komai ba sai dan ita likita ce kuma Nadia ta karu sosai wajen haihuwar nan tana son kulata da kanta Duda ba'a yin hakan, ba'a zuwa wanka a gidan sarauta, ama sai Ammi ta yi mata wannan alfarma, domin kuwa tun saran da maciji ya yi mata suka so hakan aka hanna a yanzun kam sai ta basu wannan dama domin ko ba komai iyayenta ne ai kuma suna da karamci da kawar da kai _________________________ Shirye shirye ya kankama, Ummukulsum ta shige dakin gyara, inda Najeeba ke makalewa itama ana bata gyaran nata na musaman domin du wani abin da Ummu zata sha tare suke sha, harma ta fita mayar da hankali domin a yanzun ta fita sannin darajar abin auren kara karasowa yake , bai fi sauran kwana biyu kadai a daura auren Yaya Dayabu da amaryarsa ba, sannan na su ummu da Yarima A wannan rana ne su Zahrau, su Yarima ango da baban amininsa mai sunna Idriss suka yada zango a garin damagaran tare da yan rakiyarsu tun karfe goma na safe cikin jirgin air france da ya wuce dan sauka a garin Niamey Sunna sauka hadewa suka yi da yan uwanta suka harhada abinda suka ajiye a grup din da suka yi create iya su yan matan sukai shawara dan bada gudunmuwarsu ga yayansu abin alfaharinsu Zahrau kanta da take babarsu wace komai ya shiga hannunta sai da ta yi mamakin irin kokarin da suka yi, nan suka samu Ammi da Ummu wace itama ta zo gidan a yau domin a nan masarautar za'a gabatar da shagulgulan auren duka biyu suka zube masu tarin kudin da takardojin adu'o'in kananun da suka rubuta ciki kuwa harda takardar Najeeba inda ya rubuta kalamai kamar haka "YAYANA, INA MAKA ADU'A KA SAMO MIN BABIES MATA DA YAWA YAWA YAWA" Du daria suka saka , a lokacin da aka yi kiransa aka gabatar masa da irin kokarin kannen nasa sai kawai ya hade su baki dayansu a jikinsa yana dan bubuga bayansu, tabas ya ji wani irin dadi mai sanyaya zuciya sannan ya kara ji a cen kasan zuciyarsa cewa ahalinsa ahalinsa ne, jinnin Mutalab ba zasu taba zubar da dan uwansu ba A tsaye suke kan kafafuwansu kan shirye shirye Rana na yi suka kwasa a cikin motoci tare da dogarai yan rakiya wajen motar dogaran kanta mota hudu ce suka saka su a tsakiya cikin shiga ta alkyaba a rurufe masu ko'ina suka yada zango a gidan su amaryar yaya Dayabu Irin tarbar da suka samu sun ji dadinta sosai, iyayenta ba wasu masu arziki bane ama mutane ne masu wadatar zuci, an masu dahuwa an gyara masu waje an shinfida masu tabarmu da darduma an kawo masu sansanyan tukudi wanda ya ji damu da sansanyar solani ya sha siga da kayan kanshi ga uban cikwui din dake ciki Ai kau suka baje tamkar ba matar sarakai bane a wajen suka sha abinsu ana wasa ana daria inda mutane ke ta son su samu damar ganninsu aman dogaran nan sun kasa sun tsare dan kuwa kiran da sultan ke yi yana karawa ya kara saka sarkin Dogarai tsayawa kikam a kofar shiga sai muzurai yake ya kasa ya tsare domin uwar dakinsu na ciki Abinda ya kawo su suka shiga yi, wato kitso da kunshi, sun raraba aiyukan a tsakaninsu inda kanwarsu mami itama ta kware a wajen zana kunshi kamar wata aljannah haka ta ringa zane masu kafafuwa Najeeba kam ta cire alkyaba ta ajiye ta shiga yaryarawa Auntunsu kitso wace ta sake cikinsu take kara karantarsu da jin kaunarsu a cikin zuciyarta domin ita a duniya ta tabata Allah ne ya wanke ya bata wannan bayin Allah da ake tsoro a cikin gari, ita kam sam bata ga abin tsoro a tatare da su ba, abin kaunarta ne, farin cikin zuciyarta ne, mutanen rufin asirinta ne tunda suka nuna mata kauna du irin arzikinsu da sarautarsu suka rungumeta a jikinsu sai kawai take ji a kasan zuciyarta lalle adu'ar samun miji na gari da dangi masu saukin hali da ta taso tana yi tun tana yar karamarta ne Allah ya amsa mata Ba su su bar gidan nan ba sai kusan salar isha'i, shima kira ne ya shigo wayarta tana dagawa a dake ya furta" Zaki ja abinda zaki shiga kule ke da fita sai na maki wani cikin kin haihu, kin manta jariran da kika bari a gida ne?" Murmushi kawai ta yi tana sakawa kitson da aka kusan gama mata ribom suka mike sukai masu salama Nan suma suka yo masu bajintarsu daidai karfinsu inda aka hado su da uban tukudin nan cike da katon kula har biyu da kayan damunsa wanda hakan ya masu dadi dan kuwa sun ji dadin gumbar nan sosai walahi Sunna zuwa gidan ba zama ba suka yi, a nan aka gamawa Najeeba kitsontsa suka tarar UMMU ta ci karfin kitson Ummukulsum wace ake mata wasu irin kannanun kitso masu shegen kyau Ummukulsum ta yi wani irin fresh da ita, ta kara fitowa das da ita, dama du ta fi su hasken fata sai fatar ta kara haske sosai da santsi, ko a ido ka kaleta zaka so kuma kallonta domin abar sha'awa ce, a zaunen da take daga kasa wata yar kujera ce ta tsuguni wace balarabar ta ajiye mata, ana mata kitson tana kawo turaran wuta na tsuguni lokaci zuwa lokaci tana saka mata, wannan turaran da irin gyaran kasan da akai mata 6a saka ko yar yatsarta bata gigin gwada sakawa a jikinta domin kuwa ta yi wani irin matsewa abin ba'a cewa komai Nan Najeeba ta zauna bayan ta watsa ruwa ta shayar da yaranta, sannan ta mikawa masu kula da su ta kama kan AMMI ta shiga kitsa masu du kuwa da irin tarin gajiyar da suka shigo da ita Zahrau kuwa ta shiga kunsa mata lalle namu na hausa Ummulkhair ce ke ta turo baki tana hararar wayarta ta dago daga saka farcen da take yiwa Ummi ta kalli Ummukulsum ta ce" AMMI kin ga ba, walahi na san ita ta ba Yarima numberna ya ba wannan mutumen da suka zo tare, ni su fita a harkata ba zan iya ba gaskiya" Ammi ta ce" to wai meye aibunsa? Dan kawai yana nesa da gari Ummulkhair ai idan abin ki ga gidan ya kama zaki zo ki ga gidan ko? Ni walahi nutsuwar yaron ne ta birge ni, gashi kyakyawa mai ladabi da biyaya to meye aibunsa? " Dan bakinta ta kara turowa tana jin Najeeba na gyara zamanta tana tsaga kitson kan AMMI ta ce" Ammi, balema kudi ne da shi na rantse, kin ga fa a Abujar da yake zaune a cen aka haife shi, mahaifinsa ya rasu da wuri ne ya bara masa tarin dukiyar da shi kansa bai san adadinta ba, a haka mahaifinyarsa itama ta rasu, shine ya ki kula kudin ya je karatu , a waje suka hadu da Yarima har suka kula abota ke kam an yi solofiyo " Da mamaki Ummi ke kallon Najeeba wace itace bakuwarta, ba komai ya bata mamaki ba kuwa sai ta yanda aka yi Najeebar ta samu information a kan mutumen UMMU ta ce" Idon naira ta ce ki amince ke meye ki amince mana?" Ammi ta ce" kin ga dai kar ki yiwa y'ata, ai gaskiya ta fada, to tsakani da Allah meye aibu dan ka so kudi? Ke yar albarka kudi abin so ne ehe!" Ita dai mesage ta tura masa kamar haka" Ni dai ba zan iya auren mai yaren inglish a bakinsa ba, kai da baka da RRR a harshenka, kumama ni bana son mai kyau gaskiya " A lokacin da ya karanta sai ya saki murmushi yana kallon Yarima dake yi masa mitar shi bai ga anfanin hanna masa gannin mata da aka yi ba wai sai an daura aure bayan matarsa ce, ya dora yatsunsa ya rubuta mesage kamar haka" Ma ji ma gani, aman mai yaren RR din nan sai ya zamo uban y'ayanki da izinin Allah domin ba inda zan je Sarkin Damagaran uba ne ga kowa, ya kuma bani daki" Haka suka yi ta raha tsakaninsu har zuwa shiga kwonci kafin kowace ta labe da waya tana dan taba hira da mijinta, ciki kuwa harda Najeeba wace a irgenta bai fi kwana takwas zasu koma bangarensu ba, wato zata fara daukan duty Hotunnan dinkunnansa da aka kawo ne take ta bi daya bayan daya tana kallo, bakinta ta turo ta danna voice tana shagwabe muryarta ta ce" Ni du kayan nan na rasa wanda kyansa bashi da yawa, Ni gaskiya haka kawai ka saka masu kyau ka fita daurin aure Har ka samo mana wata? " Murmushi ya yi daga kwoncen da yake yana mai jin dadin irin yanda lokaci zuwa lokaci take nuna kishinsa a fili wanda hakan ke saka shi jinsa wani gingirigin, kafin ya danna ya shiga bata amsa daidai da maganarta Asubah alkhairi Fari mijin Najeeba A ranar dake gobe daurin aure sun wuni ne sunna tsaye kan harkar tsare tsaren tarbar baki da irin abincin da za'a girka wanda baki daya girkin larabawa ne za'a yi a wannan taron aure na y'ayan Mutalab Sai da magariba ta yi suka kile a baban filin dake zagayen wajen AMMI ya su ya su suka shiga gabatar da sister Days, wanda ya dauki larabawan da suka zo da tsuma su Ummu, da su Ammi da Ummu, sai yan matan da su Najeeba Kwaliya ce suka dauka irin ta larabawa, sun shirya shiri mai tsarin gaske ga turaran wuta sun jojona waje waje sun zuba uban turaren da ya ringa game masarautar ba iya nan ba, a wajen kuwa harda DAYABU wanda yake tare da kannen nasa tun da yama, sallah kawai ke tashinsa Raguna har uku aka gasa masu, irin gashin nan mai fita daidaya, aka gabatar masu da komai da komai sunna shan kidan larabawa sunna cin gasashen ragon nan sunna korawa da jusss Ai kau rawa suke sha abinsu iyayen na shan dariya Daga inda yake ringeshe da computer a kunne a gabansa da tablettt dinsa yana bin yanda suke gabatar da bikin nasu ya fi kurawa Najeeba ido, wace kugunta ke daure da irin abin nan na larabawa wanda sunna rawa yana bada sautin cas cas cas, hannayenta rike da wata yar igiya fara, gabanta kuwa wani kwanon silba ne karami, sai kafarta da ta dora kafa daya kan daya ita kuwa dauke da sarkar kafa mai walwali, kasancewar wajen da wadatacen haske sai ya zamanto komai yana ganni Hirarta take hankalinta kwonce, sannan ba abaya bace a jikinta, sket ne budade da wata bak'ar riga wace ta bi lafafen cikinta wanda ko shi da ba dan ya san shine ya yi mata cikin da ta raina a gabansa har ta haife shi ba da shi zai fara karyata cewar ta taba haihuwa a wannan shafafen cikin, sannan ko a zaunen da take duwawunta da cinyoyinta sun kara wani irin bajewa wanda ke nuni da kibar haihuwar a cen ta tare, sai mamanta da suke cike bam ga ruwan nono na shayarwa ga asalin halitarsu Ajiyar zuciya ya ringa saukewa yana jin wayarsa na ta tsuwa, kiran nan ya kai na tara a kadan, tun da magariba ake kiransa aman wannan da ya zamanto a kusa kusa sai kawai ya mika hannunsa ya dauko yana mai duba sunnan dake sama Dan kara kurawa sunnan ido ya yi da dan mamaki, dan gannin Gimbiyar garin agadez ce, Yana da numberta a wayarsa, ama kira bai taba hada su kai tsaye ba, koda jaje ne ko gaisuwa takan bi ta kan y'arta ne Rage sautin kidan ya yi ya dan gyara kishingidarsa da wayar a hannunsa da kuma tablettt din yana kallo ya amsa kiran ta hanyar salama cikin nutsatsiyar muryarsa mai kamala Mamaki ne ya dirar masa jin tana gaishe shi, bai idasa mamakin ba ta dora da kara neman afuwarsa sannan ta fara magana a sanyaye kamar haka" yara sun zo Damagaran wajen auren, aman mai martaba ya hanna masu sauka a fada cewar su sauka a gidan kanwata da safe zasu zo baki dayansu harda Zinaria , dan Allah a kara nema mana afuwarsa ko zai sasauta mana fushinsa" Shaheed ya dan kara buda idannuwansa a kan yan matan AMMI da suka fara tashi sunna yin rawa yana dan girgiza kai yana murmushi a hankali ya bata amsa da fadin " In Sha Allah " Gimbiya du sai ta kara dirircewa tama rasa ta inda zata bi dan fada masa abinda matar Yarima ke shirin yi, aman shi kadai ke iya tsawatarwa a masarautarsa dan haka fada masan ya zama wajibi A sanyaye ta dora da fadin" sai yarinyar nan ta wajen Yarima, wato matar tasa, itane ta tafi ashe itama, kuma da niyar rigima ta tafi dan haka ina neman alfarmar a katse hanzarinta " Shaheed ya kara buda idannuwansa da kyau, rigima? Zata zo wajen auren? Uhum Karshe dai haka suka yi salama bata samu wata gamsashiyar fuskar da zata kawo masa dayar maganar dole haka ta yi hakuri da kudurin cewa idan da rabo zata koma dakinta Shi kuwa ido ya zubawa Najeeba da ta dauki dan kwanon nan ta dora shi saman kanta bayan ta cire dan kwalin Ido ya kara zarowa yana kallonta a lokacin da ta mikar da hannayenta ta shiga kada kugunta su kuwa larabawan nan me zasu yi banda yi mata ruwan turare da buda sama sama Da sauri ya lalubo wayarsa yana cije lebensa na kasa yana mai furta" ya isa haka neman maganar, a watse tun muna shaida junna!" 😁😁😁😁ni ban ga laifin rawa ba wollah haka kawai a dai ringa jin tsoron Allah.....ah tom😊😊😊😊😊😁😁😁😁😁😁 ___________________________ An daura aure lafia, duban jama'a sun shaida bisa wakilcin Sarkin sarakuna Mai damagaran, da sirikinsa, amininsa, babansa sarkin garin agadez, da manya manyan sarakunnan da suka halarta bisa gayata da suka samu domin kuwa shi din mai zuwa taro ne hakan ya sa idan yana taro ake zuwar masa ta ko'ina ba iya Niger kawai ba An wuni cikin shagulgula, shagalin da ya dauki salo kala daban daban Matansa du sun halara, kwaliya da shiga ke ware yayar wane ko uwar wane😊 Zinaria ta halarta tare da yayunta ko ba komai auren dan uwansu ake suma sannan masautar biyu sun zama yan uwa hakan ya sa suka shiga mutane duda irin tarin mamakin da ake na ganninta irin yanda ta rame sosai ta kara wani fari fat kamar wace bata da jinni a jiki tsabar saka damuwa a ranta, sai dai ta ji dadi da iyayen mijinta basu nuna mata komai ba, kai harta da yarinyar da ta sako gaba da zagin cin mutuncin bata wani nuna mata wani abin ba saima gaisuwar mutunci da suka yi a tsakaninsu Bayan magariba du an fitar da tarin jama'ar nan sai na jiki sosai ke shigowa falon, su kuwa sun yayada zango, Zinaria na rike da Abdallah tana dan jijiga shi cike da begen yaron a kasan zuciyarta Najeeba na gefe guda lulube da wani jibgegen hijab mai nauyon tsiya wanda fitowarta kennan daga wanka ta hau kan yar kujerar tsugunon nan da jimkin abubuwanta da ta harhada ta ringa zubawa a hankali yana bin jikinta hankali kwonce tana hangen Zinaria daga zaunen da take, dan bakinta ta dan tabe, ita fa ba za'a hanna mata jin kishin mijinta ba, domin ya isa ne Tana gamawa ta shige ciki dan kwontawa, ta gaji, gajiyartama ta gaji, sai dai maimakun ta samu bacin sai kiran da mijinta ya yi mata na vidio call ya sakata kura masa ido tana kallonsa ta saman screnn din Bakinsa da yake dan dantsewa ta di baiwa hankali, kafin ta saki murmushin jin abinda ya ce , cewar ta zo gareshi A hankali ta ce" Na ki " Ido ya zaro yana kallonta ya dan nuno karamar yatsarsa ya ce" Beebah, satinki nawa rabonki da ni? Ke tunda cikinki ya tsufa kika ysane ni, a yanzun da kika haihu har kika fara sallah shikenan ba zaki zo gareni ba? Nine fa? " Murmushi ta kara yi a sanyaye ta ce" Kwana nawa ya rage mu hadu ne SHAHEED?" Idannuwansa ya kausasa jin ta kama sunnansa, kit ya kashe kiran yana kumburi, hakan ya sakata tashi ta zauna da sauri ta shiga doka masa kiran tana kallon wayar, ama fir ya ki ya daga hasalima kamar baya nan haka ya mata shiru bayan yana kallo A hankali ta koma ta kwonta ta shiga yi masa message sansanya mai sanyaya zuciya, ta dora da fadin" Fushinka na iya hanna min baci khalb, na tuba abin kaunana " Murmushi ya yi yana mai bin kalaman da shauki a cikin zuciyarsa, a hankali ya sake kiranta, Tana dagawa ya kura mata ido na dan lokaci har sai da ta kashe masa ido daya sannan ya yi murmushi, shi kadai yake ayana irin abinda zai mata, wato har sati take tunanin zata kara shi kuwa yana nan uwa wani sakarai ko? Zata gane bata da wayo, ta dai yi gigin zuwa bangarensa A washe gari tun karfe tara suka tashi da hayaniya, ba ta komai bace sai ta matar Yarima wace a yau ta shigo da sunnan ita din matar yariman ce harma ta samu sadawa da bangaren Ammi Kuka take cikin harshenta da baya fita da kyau tana mai nuni da Ummukulsum zata shigar mata gida ne dan ta rabata da mijinta kamar yanda yayarta ta raba sarakuwarta da mijinta hakama kanwarta ta raba Zinaria da mijinta Ba wani nan sulhu ba take, fada ne take wanda ya baiwa Najeeba daria tsayen da take cikin shiga ta wani danyen lesh mai kalar orang da ratsin fari ta dora farar alkyabarta har kasa sai baza kamshi take fuskarta dauke da nitsatsiyar kwaliya , hakama yan uwanta da du sun riga da sun dauki kwaliya sun shirya dan bikin da ake a cikin gidan du sunna kallon ikon Allah, sai hakurin da ake bata na ta zauna a yi magana , gefe AMMI na tsaye itama sai UMMU da ta tabe bakinta ita kuwa ba alkyaba bace a jikinta bubu ce ta babar atampa ta kashe dauri ita kanta fuskarta da mak'up simple, uwa uba Amaryar tsarin kwaliyarta ba'a cewa komai du sunna kallonta Karar buda bangaren shigowarsa ya sakata saurin kai dubanta wajen, haka kuma du wani mahalukin dake falon sai kake jin tsitttttttttt ya yo, yan matan har sun kai kasa dan girmama mai girma, wa'inda basu rigaya sun zube ba AMMI ce da Ummu da Najeeba, da matar Yarima, Ita Najeeba ta ki dukawar ne dan bata so ya bayana a cikin tsarin da ba rawani, a yau tana jin kishin du wata mace ta gane mata shi ba rawani ciki kuwa harda matar Yariman! Kanshinsa ne ya fara rufe kofofin hancinsu, kafin sandar girmansa ta fara shigowa baka mai lankwasa da adon zeba sai farin hannunsa mai dauke da zoben azurfa da agogon azurfa sannan jijiyoyin sun mimike rado rado ana ganni a jikin A hankali yake kara bayana lokaci daya ta ji wani irin abu na mata yawo a jiki da kwakwaluwarta da zuciyarta, Bayanuwarsa cikin shiga mai duhun haske ya sakata sada dubanta kafin itama ta zame ta kai kasa ta dukar da kanta cike da jin shayinsa da matsananciyar kaunarsa A SARKINSA YAKE, SARAKI NE, MANYANMU NE, MASU MULKINMU NE, UBA GA ABDALLAH DA MUHAMAD, BABA A WAJEN YAKUB MIJI A WAJEN NAJEEBA DA NADIA, cike da kasaita ya dan juyo da kansa bangaren mahaifiyarsa wace ta kai zaune itama cike da sada kanta domin kuwa ita ta kawo shi duniya aman ko ita takan bambance lokutan da take iya kama kunnensa ta ja, da kuma lokutan da take sada dubanta a kan nasa dan kuwa daukaka ce daraja ce da Allah ya bashi, Kansa ya mayar wajen UMMU, itama kan nata a sade yake a kasa Matar Yarima na idasa gane komai itama ta zube a kas wajen da su Ummu suke duke, AMMI kuwa a kan kujera ne take, Ummuma a kasan take kanta kasa Duban kowa yake daya bayan daya har idannuwansa suka sauka a kanta, Yana kallon nata kallo na kurullah, kallo na soyaya, kallo na bege, Salamar Yaya DAYABU da ya kwana a gidan amarya ne ya saka shi kai dubansa inda yake shigowa, yana karasa shigowa ya duka shima nan kasa da sauri yana mai kawo gaisuwarsa Shiru bai amsa ba, hakan ya sa ya kara sada kansa kasa A haka mutun uku suka shigo da salama, wato ABIH, YARIMA, DA AMININ YARIMA Bayanuwar yannayin wajen ya saka su zubewa suma sunna mai gaishe da MAI DAMAGARAM MAI WUKAR YANKA GURNANIN ZAKI Da sauri ya cire dubansa daga kansu bayan ya gama gannin bakin Yarima harda shi a wajen da matarsa take, ta dauki wannan kwaliyar da ta tsintsinke masa zuciya, tana baza kanshin nan da yake matukar kishi, sai kawai bakinsa ya kara yin nauyi ya kasa amsa gaisuwar sirikinsa da yariman da abokinsa A hankali ya kuma cirw dubansa ya dora shi kyam a saman kanta A hankali ta ringa dane idannuwanta dake son dagowa dan dubansa, har matse hannunta ta yi du dan ta hannawa kanta kallonsa sai dai ina, abinda ya zame mata jiki, ya rigaya ya zame mata sabo bata tunanin akoy wani hargagin da zai hanna mata dago da kan nan nata da take jin yanai mata balin bal A hankali ta idasa dago da dubanta ta zuba idannuwanta cikin nasa Irin TSADADEN kallon nan da ya saba yi mata wanda a da take dauka da na tsana, kallon nan mai yi mata nuni da tsantsar kaunarta da matsanancin kishinta da madaukakin bukatarta, kallon nan mai tsuma zuciyarta ya sakata lumshe idannuwa koda bata shirya ba ne ya kafeta da shi ko kyaftawa baya yi A hankali ta ringa jin zuciya da gangar jikinta na mikar da uta tsaye daga zaunen da ta yi Tana gama mikewa ta ringa takawa da kafafuwanta dake dauke da farar safa kal kal da alkyabarta har ta karasa gabansa Sakamakon ya darata a tsaye sai ta dago dubanta tana kallon idannuwan nasa Gannin a yau yan sarautar aka tashi da su, ga shara'a ta samu a irin wannan lokacin sai ta saka hannayenta a hankaki ta dan ja rawanin nasa kasa kadan ya kasance lebunansa a waje sannan da girarta ta yi masa tambayar menene? Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya dora hannunta na dama daifai kahon zuciyarsa sannan saman labansa ya furta" *KISHINKI NAKE, SON KI NAKE, ND I NEED U A SAMAN GADONA* " Murmushi ta sakar masa mai tsada kafin ta dube shi da kyau itama a kan lebenta ta ce" *BURINA NA DAWAMA A CIKIN JIKIN KA, ZAN JE NA YI JURANKA HAR ALLAH YA KAWO MIN KAI....* hannunsa ta ja ta dora a wajen mararta ta dan shafa ta kara tsura masa ido ta ce" *Marata a shirye take da daukan ajiyarka ko da kuwa mace na iya dauka sau billion a rayuwa.......zan amshi ruwa daga mai dauke da ruwa, zan baka hardar karatun da kake koya min fila fila KHALB* " Har ga Allah sai kawai ya ji jikinsa ya fara bari bari, yana kallonta kamar wani wawa har ta shige ta kofar da ya biyo Ji ya yi tsayuwa na neman gagararsa, da duba ya ringa bin jama'ar dake wajen du kawunnansu a kasa Wani yawu mai santsi ya hadiye ya ja ya mayar da rawanin har wajen bakinsa Muryarsa na crakin ya kai dubansa wajen Yarima ya dan limshe idannuwansa a kasam zuciyarsa kuwa fadi yake 'Ina, koda na ce zan gabatar da shara'ar nan ba zai yiwu ba, ta lalata komai ta tsatar da komai sannan ta tafi da komai', sai kawai ya dan kara gyara tsayuwarsa ya ce" *YARIMAH ABDUL JABAR, KA GABATAR DA SHARA'A WA AHALIN GIDAN SHAHEED ALIYU DA MUTALAB NA BAKA WUKA NA BAKA NAMA* Yana gama fada ya juya da dan hanzari ya shige ta hanyar nan, Ai kau ta dan dage alkyabar dake jikinta ta juya da niyar kwasawa da gudu tana daria dama ta dan tsaya ne dan ta ga shin zai zo ko sai ta yi jiran nasa? Shima dariar ce ta kubce masa ya shiga warware rawanin kansa ya kara hanzari dan cin mata domin kuwa shi Suktan Shaheed ya jima da gane cewa ifan yana daka shi din sunnansa Shaheed khalb din BEEBAH, sarauta na hannun *NAJEEBA MUTALAB* ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH Allah yaa nuna min kamalawar wannan labari nawa mai sunna MAGE, Mage kirkiraren labari ne, idan har ya yi shige da rayuwarki/ka an ci sa'a ne, dan haka a gafartawa yar mutan Niger Ya Allah ina rokonka da sunnayenka tsakaka ka yafe min kuraran dake cikin wannan labari da wa'inda na yi a baya da wa'inda nake tunanin yi idan har da raina, ya Allah ka bani ikon rubuta alkhairi da yan yatsunna ka hane ni lalata tarbiyata , Ya Allah ka jikan iyayenmu ka sa mu cika da kyau da imani Sakon gaisuwa *Zuwa gare ku daukacin al'umar da sukan nunan kulawa, soyaya, a aikace da aljihunsu a kan wannan sako more specially Mage grup fans, ku din nawa ne, nima taku ce, ina mai baku albishirin cewa in sha Allahu zan dawo da sababi har kwaya uku, da ba dan daukan sunna ba da na furta maku sunnayensu, sai dai ina mai rokon ku da ku kasance tare da ni bayan azumi idan Allah ya nufemu da gannin lokacin, ku ci gaba da bani kwarin gwuiwa da hadin kai dan kuwa na fada da karfin murya cewa ni dai ina rubutu ne domin ku, idan ba ku ba ni, Allah ya yi maku albarka, ya kara lafia, ya kara imani, ya kara arziki mai anfani, ya sa a gama da duniya lafia* Jinjinar ban girma *JINJINAR BAN GIRMA ZUWA GARE KU YAN UWANA, TAURARI WRITER MA YAR UWATA SAMIRA HARUN, MA Y'ATA RAHIMA, MA KANWATA NAZIFA, MA KAWATA HALISA WATO LISSA AND MA NUSEE, ALLAH YA BARMU TARE, YA KARA DANKON ZUMUNCI YA KIYAYE MIN KU AMEN* Alfaharina A duniyar yanar gizo ina alfahari da Allah ya hada ni da masoya, har suka kasance yan uwana *BILKISSU KANAR, ND SAMIRA HARUN* Zan iya dukan mai yi maku cune da baki Allah wallahi😁 Daaukaci DAUKACIN marurubuta na gaishe ku, na kuma gaishe ku, inai maku fatan alkhairi Sako zuwa ga jama'a MAGE ba na siyarwa bane, kyauta ne, idan kika biya kudi wani kato ya siyar maki kin yi kyauta ne😁 Dan ALLAH du wanda na batawa a wannan labari ya yafe min, domin mutun nake dan adam ban fi kowa ba ban isa na kamo kowa ba👏👏👏👏😁😊😁 *Alhamdulilah SAJIDA CE YAR MUTAN NIGER*