AISHAH-SIDDIQAH 3 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com TUNASARWA/JAN HANKALI Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba. Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa. Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu. Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde. In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi Atqaakum”. Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna. Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada. –Takori Sumayyah AbdulQadir. SADAUKARWA Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga mambobin TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki. KIYAYEWA Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali. GODIYA DA JINJINA Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aishatu Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira. In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH. (INA TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. Takorinku April, 2024 AISHAH - SIDDIQAH 3 A isha-Siddiqah na cikin farin ciki mai yawa a yau, kasancewar yau ne ta zana paper dinta ta karshe a sakandire lafiya. Kuma ga dukkan alamu mahaifan Abdulrasheed basu yi asarar makudan kudadedn da suka kashewa Aisha ta jona karatunta na sakandire ba a makaranta mai tsada da yaransu ke yi, har yau da Allah yasa ta kammala cikin kudurarsa. Lokacin tafiyar Nenne aikin Hajj na wannan shekarar ya kusa, ta fara shirye shiryen tafiya, wannan karon tareda Nanin Gombe zasu tafi Hajjin bana, wato mahaifiyarta Hajiya Oummana, don haka za’a dauko Nanin daga Gombe, zuwa Lagos, sai su hadu su tashi ta Lagos State Pilgrims. Sun yi waya da Haj. Zainab ta gaya mata batun tafiyar tata, nan Umman Siddiqah take gaya mata suma acan Gombe suna shirin tasowa, kuma cikin ikon Allah wannan shekarar ma har da ita Umman, ta kara samun kujera daga ofishin su Malam Yunus. Nenne tayi murna sosai da sake haduwarsu a Saudi, karo na biyu, har take cewa cikin tsokanar Umman. “Abin Allah sai kiga wata shekarar kuma war haka, saimu sake haduwa a masarautar Ilorin, muyi wankan jegon Petel dinki”. Dariya Haj Zainab tayi cikin jin kunya, na Nenne tace “to ta share dakin Petel, tayi wake da da shinkafa da salad da yajin maraba, Petel zata zo musu sallama, don itama wajen mijinta zata koma kafin tashin nasu aikin Hajj, tunda ta gama makaranta. Da wannan Nenne da Umman Siddiqa suka yi sallama cike da kaunar juna. Haj. Zainab ta gayawa Malam Yunus maganar zuwan Petel ganin gida da sallama, wai zata koma inda mijinta yake zaune. Malam Yunus ba karamin dadin hakan yaji ba, a take ya ce maza Sunusi almajirin dake zama da Umma tun bayan auren Siddiqah, ya gyara dakin Petel ya share ya goge. Lokacin da za'a taho daukan Nani Ummana sai Nenne ta gayawa Siddiqa ta shirya zasu wuce Gombe tare, ta gaya mata zata kaita ganin gida ta gaida su Ummanta, in yaso ta yi kwana uku, suyi sallama da su Ummanta saboda sunaso zata bi bayan mijinta (Hamma) cikin watannan, wato lokaci yayi da zata tare a gidanta. Duk da Nenne ta yi mata wannan bayanin na dalilin da zata je sallama gida Gombe, Siddiqah bata damu ba, murnar zuwa ganin gidan ya take fargabar maganar tarewar, wato sawun Giwa ne ya take na Rakumi, ta hau murna da giringidishin shirin tafiya gida baji ba gani, kamar ta sume don dadi. Yaushe rabonta da Umma da Abbanta? Ji take kamar ta shekara Goma rabonta da gida da iyayenta. Nenne dai bata yi mata bayanin yadda tarewar tata zata kasance kai tsaye ba, ta barwa Haj. Zainab, don ta san Haj. Zainab zata fita iya lallashinta da convincing dinta ta tafi cikin dadin rai ba tareda ta daga hankalin ta ba. Kuma tun farko Haj Zainab taso daman a barta ta shirya Siddiqah tun kafin zuwanta Lagos wato tayi mata gyaran aure amma basu bata damar yin hakan ba a lokacin. Nenne tana ganin yanzu in taje gida kome Haj. Zainab takeso sai tayi mata yanzu ne yafi dacewa. Tsaraba sosai tasa Seun da Firdausi suka hadowa Siddiqah, wanda zata tafi dashi gida, turamen atamfofi da lesika na Ummanta da kannen Babanta mata dake Kumo, da shaddoji da yadikan Maza masu daraja da turare na Babanta da Yayansa madaurin aurenta Baba Barau. Itada Nenne da Firdausi suka taho Gombe ranar Asabar. Da suka shigo gari kuma tun kafin su tafi masarautar Gombe saida suka fara sauke Siddiqa a gidansu dake Jeka da Fari. Umman Siddiqah dama ta san da zuwansu, tuni ta shirya musu karba ta girma yadda ta saba yima bakinta na musamman, Umma akwai karrama bako balle suruka irin Haj. Sappah, ta tarbesu da abinci mai tsari da abin sha mai sanyi. Saida su Nenne sukayi kat, sukayi sallah suka huta, suka kuma sha hira sannan suka fara shirin wucewa fadar Gombe. Umma na tsokanar Princess Firdausi da cewa, "yau dai gata ga Gimbiyar tagwaye kuma auta sannan shalelen Nenne". Princess tayi murmushi tana sadda kai tace “Umma ai tuni Siddiqah ta kwace min wannan fadar”. Aisha-Siddiqah-Petel 'yar Ummanta, wadda tayi mul-mul da ita don kyau da koshi, na abincin yarbawa mai gina jiki, wanda ya hade da samun gyaran jiki na subulai da mayuka masu kyau da gyara fata, tana lafe jikin Ummanta sai zuba sassanyar kamshi take irin na matan manya, ko minti daya taki sakin Umma ta tashi, duk kunya ta ishi Umman, in tayi korafi sai Nenne tace. "Don Allah barta kusa dake taji duminki Zainaba, ai Aisha tayi kokarin da ban zata ba, wata nawa rabonta dake? Kin yi tsammanin zata iya wannan kokarin data yi? Petel ce fa! Kuma Siddiqahr nan ‘yar Ummanta! Yanzu kuma gashi kasar bakidaya zata bar miki, ai ta cancanci a barta taji dumin data yi kewar ji". Hajiya Zainab abin ya bata dariya sosai saida suka dara a tare. Petel ta sake sunne kai jikin Ummanta. Bayan wucewar su Nenne fadar Gombe, Malam Yunus ya dawo daga aiki ya tadda babbar bakuwar tasu AISHATU INDO SIDDIQAH, shima Abban na Aisha ya hau tasa murnar, yana cewa, "halan cusa ake miki da tebar yarbawa da Amala da Iyan, wannan kumari da kikayi a ina kika samo shi Indona? Keda kike kamar a bushe ki". Dariya suka sa itada Umma, ya mikama Aisha kunshin balangun da yayo mata guzurinsa, mai zafi da ruwa-ruwansa, yaji yajin balangu irin yajinnan mai citta, da yankakkiyar albasa da kabeji abin sai wanda ya gani ko ya dandana. Da doki da kewa Aisha ta karbi balangun Ayuba mai nama ta soma ci tana fadin, "kowa ya bar gida Umma gida ya barshi. Nayi kewar balangun Ayuba sosai, nayi kewar Arewa gabadaya". Yau dai Aisha da iyayenta kwanan farin ciki sukayi, sun sha labarin Lagos kamar ba gobe, itama ta sha nasu labarin. Na surutun da aka yi tayi akan aurenta. Musamman da Ishaq ya dawo daga bautar kasa ya tarar an yi mata aure. Abba yace Ishaq kuka yayi tayi a gaban su kamar karamin yaro kuma ya gaya masa bashi da laifi da yadda suka yi da mahaifinsa duk ya gaya masa. Yace tun daga lokacin Ishaq ya bar Gombe don yayi bakin ciki da abinda Babansa yayi masa, ya koma zama hannun Kawunsa a Kano. Shikuma ya saka shi a harkar kasuwancin da yake yi a Kantin Kwari, na sayarda atamfofi. Yace zuwa na karshe da Ishaq yayi Gombe kayan abinci ya kawo musu turum! Yace yana jin dadin zaman Kano kuma yana neman aiki acan sannan kasuwancin da yake taya kanin Babansa yana garawa sosai. Aisha taji wani irin yanayi na tausayin Ishaq na ratsata, amma bazata ce komai ba kada Abba ya daina bata labarinsa. Tun a daren Umman Siddiqah ta dama tukudi mai kyau ta soma baiwa Aisha da sabaya don nononta ya kara cikowa. Auren ne yazo mata ba shiri. Amma tuntuni tanada niyyar bata ‘sabaya’ in za'a yi mata aure don nononta data bige don ya tsahirta ya cicciko. Kwanciyar hankalinta da Aisha bata tare ba har lokacin ashe, tun lokacin karatu take yi. Koda Nenne tace zata yiwa Aisha gyara irin nasu, ita tafison ta bata tukudi da sabaya shine nasu na gado. Umma ta gaya mata da kyakkyawan lafazi cewa da sun koma Lagos zata tare gun mijinta, sukayi mata nasiha mai shiga jiki kuma mai ma'ana. Suka bata kwarin gwiwa mai yawa suka karfeta. A karshe suka nemi yarda da amincewarta kan hakan. Cewa ta yarda zata tare? Ko tukunna bata amince ba su gayawa Haj. Sappa a kara mata lokaci kan wanda aka bata? Aisha taji dadi a ranta iyayenta basu yi mata dole ta tare ba, basu tursasata ba kamar da, yanzu lallabata suke, don haka ita kuma tayi kudurin zata kasance mai biyayya ga dukkan umarninsu. Ta yarda zata je duk inda aka umarceta don tayi zaman aure, ko bangon duniya ne zata je ta zauna da wanda bata sani ba, bata san halinsa ba. sannan take da tabbacin Bayerabe ne kabilar da bata so din. Duk da cewa tasan in ta tafi yes, tabbas zata yi kewar Ummanta da Abba, zata yi kewar Nenne kuma. Kai har Dade dinsu Firdausi ta san zata yi kewarsa, mutum mai kirki, mai sake mata da janta a jiki kamar surukuwarsa ba, shi dasu Fatima da Firdausi ba wanda bazatayi kewa ba. Duk da ba shiri suka cika itada Fatima ba, amma sun zauna tare tsayin lokacinnan da dadi ba dadi sun zauna tare a gida daya, ta san zatayi kuka na barin gida da sabon data yi da gidan Nenne da daukacin mutanen cikinsa su Femi chief cook, Seun driver da sauran ma'aikatan gidan data saba dasu duka. Amma hakan bazai hana reality na cewa su duka ba zamansu take ba, zaman aure na wanda zataje wajensa. Kwanan su uku suka juyo Lagos, tareda tsohuwar Nenne wato Nani Ummana. **** **** **** Nani Oummana ta iso gidan surukinta Engnr. Idris Akanni lafiya, saboda soyayyar Kaka da matar jika ko kuwa soyayyarta da Prince Nani yi take kamar ta hadiye Aisha-Siddiqah, tsohuwar mai ran karfe komai takeso bata saka kowa a gidan tun isowarsu saidai kaji tace. “Indo jikata miko min kaza, ko yimin kaza”. Da daddare kuma da Nenne tasa aka gyara mata dakin ita Nenne inda ta saba sauka in tazo gidan, aka zo daukar kayanta za’a shigar dasu dakin Nenne. Ummana tace “ai kawai ki rufe dakin ki, ki tafi turakar mijinki, ki barni nida Indo-Siddiqah zan kwana”. Siddiqah taji dadin son nan da Oummana ke gwada mata. Don haka gladly ta barwa Nani Ummana gadonta tana murnar yau taga na gida bayan Nenne (bafullata) ita kuma ta shimfida Dunlop a kasa ta kwanta. Har dare ya raba suna hirar gida Gombe, Aisha ta samu kanta sosai da sakewa da tsohuwa Oummana, tana bata tarihin masarautar Gombe. Aisha kuma tace tun suna yara suke zuwa kallon hawan sallahr idi gidan sarki. Nani Oummana an sosa mata inda ke mata kaikayi don lokacin da Aisha ke fadi lokacin mulkin maigidanta ne uban kasar Gombe Sarki Ahmadu Jalloh Umar, nan ta hau baiwa Aisha labarinsa da irin girman abokantakar dake tsakaninsa da Sarkin Ilorin, wato Sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni, har da bata labarin yadda taki yarda da auren Sappa da Waziri Idrisu a baya, saboda a ganinta Yarbawane, tace “amma Uban Kasa Allah ya jaddada rahma agareshi bai saurareni ba”. Oummana tace, “sai gashi yau kaf! Cikin zuri’ar sarkin Gombe da ‘yan uwan Sappa da suke uba daya babu wanda yayi dacen aure da soyayyar miji irin wanda Sappa tayi. Tace “Bayeraben mutum akwai rikon aure akwai iya soyayyah”. Daga nan ta koma bata labarin gwagwarmayar data sha da kishiyoyi da kwarkwarori. Daga nan ta gangaro ga baiwa Siddiqah labarin yarintar Prince Abdulrasheed a matsayinsa na jikan farko a lIorin Emirate, da son hawa Dokinsa. Anan ma Siddiqah ta kara gane cewa Hamma Abdulrasheed, favourite jika ne again a gurin Kakarsa ta wajen Uwa da Kakansa na wajen Uba. Washegari ta raka Nani da Nenne wajen finger print na visar tafiya aikin Hajjinsu, akasa itama tayi a wani wurin daban bayan an gama nasu. Siddiqah ta soma tunanin da tarewar da akace zatayi gidan mijin dama aikin hajjin suka tafi da ita don ta kula da Nani Oummana, kasancewar komai ita take mata a gidan tsohuwar bata da kwari. Har ta fara hango kanta ta sako hakorin Makkah ta dawo Gombe da tsarabar Umma rankatakaf! Makwabta nata shigowa barka da zuwa bayan ta dawo. Sunanta ya tashi daga Siddiqah zuwa Hajiya Aishatu-Siddiqah Indo. Ashe dai duk hasashe take yi, kuma bata hasaso daidai ba. Domin an yi haka da kwanaki kadan rannan da daddare Nenne ta shigo mata da manyan trollies guda biyu babba da karama da zata tafi dasu, tace ta hada kayanta da duk abinda ta san zata bukata a gidanta a cikin jakunkunan data kawo mata dinnan. Da mutuwar jiki mai yawa Aisha ta karba ta mike ta hau hada komai nata a trollies din, hatta brush da soson wankanta bata bari ba. Amma dai kwarai taso aje da ita Hajjinnan, ta dade tana fatan ziyartar Shabbakin Ma’aiki SAW. Da kuma Masjid Haraam da Masjid Nabawy, wato dakin Allah mai alfarma da hubbaren ma’aiki SAW. Tazo shigowa daki taji Nenne da Nani suna magana kus-kus, bata so ta katse su, sai ta dan dakata, da nufin su gama sannan ta shiga ba da nufin yi musu labe ba, duk da kuwa har sunanta taji ana ambata ga alama very sensitive magana suke yi akanta. “To haka zaku aikata baku shiryata da komai ba? Ina nufin bakiyi mata shiri irin naku na yarbawa ba, ga shiri namu na Fulani da ya kamata duk a hada ayi mata a samu a Abdulrasheed ya karbeta da kima? Wannan da ya tuzurance ba aure sai hawa Doki ai matarsa sai an shiryata da kyau”. Nenne tace cikin jin kunya “Nani! Nifa babu ruwana cikin sha’anin nan ‘yar kallo ce, rigimar Dade dinsu ne tafiyar Aisha fa, amma ni tuni na zare hannuna daga lamarin nan wanda nasan bazai taba haifar da Da mai ido ba, in dai aka yiwa Abdulrasheed kutse da mace cikin rayuwar Polonsa. In don ta ni, Siddiqah ta gama zaman Kehinde a gidannan. Ina mata addu’ar samun wanda ya fi shi komai da komai ne, ba za’a lalata kuruciyarta tayi zaman gadin gidan gona sanadina ba”. “Akul!” inji Nani Oummana, kada in kara jin wadannan kalaman sun fito daga bakinki Sappah! Masu nuna kin yi fushi dashi yaje ya cigaba da abinda ya ga dama. Kin sani zuciyarki kadai Allah zai kalla ya hukunta shi da fushin cikinta. Ki sani Abdulrasheed yana cikin jarabawar ubangiji akan sha’anin aure, ba yin kansa bane ba jifa bane, sannan ba shafar jinnu bane, amma da yardar Ubangiji ya kusa cinye jarrabawarsa. Dade dinsu ya fi ki gaskiya. Ki tura masa matarsa daga nan ki fita sha’aninsu, in yaso ko gunduwa-gunduwa zai yi da ita ya kawo muku ruwansa, idan ta shekara babu ciki shine zamu tabbatar aljana ta aureshi da gaske, ko mu yarda babu lafiyar mazantaka a tare dashi. Amma nima bana bayan ki bata komai na mata yanzu, kada a bar 'yar mutane da ciwon mara. Don ba lallai ya kulata tashi guda ba wannan uban kasaitar da bunkasar. Barta taje haka yanzun, can gaba in kin fahimci komai yayi daidai a tsakaninsu sai kiyi mata babban shiri na yarbawa ". Aisha duk ta rude, ta rikice don bata dai gane takamaimai shirin me Nani da Nenne suke ta magana akai ba, sannan ta kasa gane inda rabin wadannan zantukan nasu ya dosa, data gaji da tsayuwa a wurin kuma taga basu da niyyar saka aya a maganganunsu, sai kawai tasa kai a dakin gabagadinta, bakinta dauke da sallama. Sai duk suka yi shiru suna amsa mata. Ta karasa gaban Nenne jiki a sanyaye tace “Femi tace an gama WARA din da kikasa aka yi miki". Da far’a Nenne tace "Kai madallah da Femi sarkin masu Himma. Warar ai taku ce, kice ta yi packaging dinta da kyau, ki karba ki sata cikin kayanki,". A zuciyar Siddiqa tace “Allah ya suttura taci Wara, wannan sai asalin yarbawan Ilorin. Har gobe ita sai fura da nono. Kowa ya bar gida gida ya bar shi”. Tun kafin kwana biyu tafiyarta Nenne ta gaya mata komai na shirin tafiyarta ya kammala, ta gaya mata jibi zata tashi, kuma tace tayi hakuri cikinsu babu mai rakata. Haka Dade da Emir suka tsara tafiyar tata. Duk kokarin Siddiqa na boye rashin son tafiyar nan yau ta kasa boye karayarta cikin idanunta, jin cewa ita kadai ma zata tashi daga Lagos zuwa wata kasa da bata ko sani ba. Nenne ta bar wurin da azama don bata son Siddiqah taga tata karayar. Ranar tashinta zuwa Argentina Nenne tasa Siddiqa ta fiddo trollies dinta waje, Dade na jiranta a mota zasu tafi airport, shi da kansa zai sata a jirgi. Masu aiki suka daukar mata jakunkunan suka sa a bayan mota Lamborghini wadda asalinta motar Abdulrasheed ce da yake hawa idan yazo gida Lagos. Nenne tazo har daki tace da Siddiqa idan ta gama shiryawa ta fita parking lot Dade na mota yana jiranta. Nenne da wayau taki yarda su hada ido yau, kada taga karayar dake cikin kwayan idanunta. Ta miko mata wayar hannunta dake jikin caji tace ta kula da wayarta sosai. Sannan Nenne ta matso kusa da ita kamar bata so wani yaji me zata ce, ta fadi wani abu, da ya kara daga hankalin Siddiqah. "Ki yi hakuri da duk yanayin da Zaki riski rayuwa dashi a inda zaki je. Bai taba zama da matar aure ba a gabadaya rayuwarsa tun ta samartaka har girma, he will find it difficult to cope with you at first. Idan na bata miki a hada wannan auren a bisa sani ko rashin sanina ki yafe min Siddiqah. Na yi ne da kyakkyawar niyya saboda kaunata da mahaifiyarki. Aure ya gaji haka, ba inda baya kai diya mace kada ki damu da duk inda zaya kaiki. Ki dinga yi masa uzuri kullum, uzuri na cewa duk shekarunsa shi yaro ne a hannunki tunda bai taba dandana rayuwar aure ba, ba kuma sabida mu zaki dinga yimasa uzuri ba a’ah, sai don kasancewar sa shima Dan Adam ne, ajizi, kuma miji a gareki mai tarin nakasu kamar kowanne Dan adam. Idan ya bakanta miki bisa sani ko rashin saninsa, ban horeki da gayamin ko mahaifiyarki ba, a'a ki gaya masa face-face tsakaninki dashi yanzu babu hijabi, ku fuskanci matsalar komai tsaurinta, mijinki ya zama best friend dinki, confidant dinki, ya zama ba tsoro ba shakka a tsakaninku sai yarda da cewa kowa zai iya batawa daya a bisa sani ko rashin sani. Ki kuma dinga gayawa Allah a kowacce sallahr farillarki ya huwwace miki soyayyarsa. Ki ce “Allah ga AbdulRasheed dan Idris Abdullateef Akanni, ka sanya masa soyayyata mai girama". Wata irin kunya ta kama Siddiqah. Nenne bata damu ba ta cigaba da cewa. "Sannan ki hada da yin hakuri. Sabida shi wannan hakurin da nake ta jaddadawa a auren na gani inaso ma shi ne ke tafiyar da rabin auren, balle aure irin naku da bashi ya gani yace yana so ba, mu muka gano masa dacewar hakan. Don haka hakurin da zakiyi da Abdulrasheed mai yawa ne Siddiqah, shine kuma zai zame miki ginshikin zaman auren bakidayansa. A sanin da nayi masa ko baya sonki bazai taba cutar dake ba, sannan bazai wulakantaki ba saboda mu muka kawo ki cikin rayuwarsa, amma zai iya yi miki silent protest! Saboda mummunar fahimtar da yayiwa mata gabadayansu. Na roke ki Siddiqah, kiyi kokarin da zaki share wannan mummunar fahimtar da yayiwa mata daga zuciyarsa, in kowa nasa ya rainaki saboda shekarunki da wayewarki da karancin ilminki ni mahaifiyarsa ban raina ki ba, na yarda kema mace ce kamar kowacce mace mai fasaha da hikima da iya tata kissar. Abdulrasheed ya riga yayiwa mata kudin goro, inaso ki nuna masa har yanzu akwai nagari, akwai kuma masu soyayya ta saboda Allah. Wannan tarbiyyar da Haj. Zainab ta jima tana baki yanzu ne zata yi miki rana, ki fiddo ta sarari kiyi amfani da ita a gidan aure, ki fahimtar dashi cewa ba duka mata ne a cikin rigar da yake kallon su ba, komai lalacewar da zamani yayi, har gobe akwai mata masu kyawun hali. Na san bazaki samu cimma wannan nasarar a lokaci guda a tare dashi ba, sai kin yi HAKURI mai dimbin yawa Siddiqah, na dameki da kalmar hakuri ko? Kada kiyi mamaki, shi hakuri baya yawa, ribarsa ce kawai mai dimbin yawa. Ki kauda kabilancin nan naki da kika bari ya samu muhallin zama a zuciyarki, in har kinason a zauna lafiya, ina kara gaya miki Abdulrasheed Bayerabe ne, ki maida al’adarsa taki, shima sai ya maida al’adarki tasa. Aure babu cikin kabilar da baya kai mace a addinin musulunci, ni dinnan na isheki misali, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi Aishatu-Siddiqah, ya albarkaci aurenki da zuri’a salihah, dayyibah”. Nani Oummana tace “kisa himma kinji ko Indo wajen kula da mijinki, Aishoshi himma garesu ta wannan fannin. A fannin iya kula da shimfidar miji ma basu dana biyu, sannan a komai sai kinga sun zama zakaran gwajin dafi a wurinsa saboda albarkar sunan NANA AISHA, sannan ababen buga misali ga mazajensu a duk inda suka shiga. Ina fatan Allah yasa shekara na zagayowa in ganki goye da magajin sarkin Ilorin, ko mai sunan marigayi Uban kasar Gombe, kinji ko Indo Aisha?” Siddiqah sai ta soma hawaye. Ko dai su Nenne sun gaji da zamanta tare dasu ne saboda tana musu halin kabilanci? Shine zasu kaita inda suka san bazata taba iya zama ba, don kabilancinta bazai barta ta iya zama da Bayerabe ba. Zuciyarta na tunasar da ita kada ta taba yaudarar kanta, da tunanin ko mijin nata ne ya bukaci zuwanta, Hamma Abdulrasheed, (Prince), mai sunayennan guda uku, bashi ya bukaci ta je inda yake ba. Nenne bata iya cigaba da tsayuwa a dakin ba ta yi maza ta fice, ganin tashin hankalin da ya bayyana baro-baro akan kyakkayawar fuskar Aisha-Siddiqah karara. Princess Firdausi ta yi kamar bata fuskanci halin da Siddiqah ta fada ba, saboda tausayin da ya kamata, ta kama hannunta zuwa (parking lot) na gidan inda Dade da Seun ke zaune cikin mota suna jiran fitowarta. Firdausi ta bude mata kofar bayan motar, jiki a salube Siddiqah ta shiga. Firdausi ta rufe kofar motar tana cema Dade dinsu. “A dawo lafiya Dade”, cikin harshen Yoruba. Dade ya daga mata hannu kawai. Princess Firdausi na daga mata hannu itama haka har suka fita gate din gidan. Seun, ya zaburi mota ya bar shiyyar Banana Island da Siddiqah Yunus da mahaifin mijinta kwance a bayan mota. **** **** **** Suna tafe Siddiqah na tuno tun farkon zuwanta Lagos, daga zuwa ganin likitan Asthma ace komai ya jirkice mata haka, sai kaddarar aure wannan na tarad da waccan. Aurenma na masarautar Yarbawa, yarbawa da bata so tun bata san meye ma’anar kalmar Yoruba ba. Rayuwarta ta juye rana daya (upside-down) ta kutso cikin ta gaggan kabilar yarbawa din. Zamanta a birnin Lagos ta san daga yau ya kare kuma. Yanzu ne zata fara rayuwar reality da bayeraben miji, wanda shine hakikanin abinda ya kawota cikinsu, ya rabota da kowa nata. Ko wace sabuwar kaddarar ke jiranta? Ko wadanne sababbin abubuwan kuma ke kiranta yanzun Allah masani. Bayan ta riga ta fara sabawa da duniyar Yarbawan data fado ciki rana daya, wadda zuwa yanzu ta dade da bin jikinta. Ta na sunsuno cewa wata sabuwar rayuwar ce ta dumfarota, wato rayuwar aure gabagadi. A baya tana amsa sunan auren ne ba tareda taje cikinsa ba, yanzu kuwa kacokam an daukota ne an cuso cikin rayuwar Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni, ta karfi da yaji ba tareda ya bukace ta ba. Ko wacce irin tarba zata samu daga PRINCE ABDULRASHEED din? Ko zai yarda ya hada rayuwarshi da ita? Ko zaiyi maraba da zuwanta cikin rayuwarsa? Akan karan kanta shin ko zata iya sakewa ta rayu da wani da namiji a duniya ba Ishaq ba? Wadannan sune tambayoyin da Aishatu-Siddiqah ke yiwa kanta a kan hanyar su ta zuwa Airport, ba tareda ta san amsar ko guda daya ba. Sannan bata kuma da wanda zai amsa mata. “Bashi da lokacin kowa a duniya irin Dawakansa. Ba abinda ya baiwa muhimmanci a duniya bayan ibadah irin hawa Doki. Abdulrasheed yana matukar son Dawakansa, lokacin shi nasu ne. He enjoys riding horses more than anything in his life!”. Siddiqah ta tuno wasu daga cikin kalaman mahaifiyarsa akansa, a lokacin data ke yawan gaya mata ko wanene dan ta Prince Abdulrasheed Kehinde da halayensa, wannan har mijin da yake da lokacin mace ne a rayuwarsa, balle ita karan kada miya Siddiqah Yunus? A wancan lokacin da Nenne ke yawan bata wadanna labaran nasa, ta kan zama bored da sauraronsu, har ta tambayi kanta ko meye alaqarta da labaran da Nenne ke yawan bata akan shi da rayuwar shi? Yanzu ta gane cewa Nenne na bata labarannan ne don ta san cewa ko ba dade ko bajima, tana raye ko bata raye tunda aure ya riga ya shiga tsakaninta da Prince, watarana irin wannan na zuwa, wato ranar da rayuwarta zata shige sukuf! Cikin ta Dan Nenne wato Hamma Abdulrasheed (Prince), a daidai lokacin da bata zata ba kuma bata shirya ba, shima kuma ta tabbata haka tarewar tata zata zo masa bagatatan. Bata gushe ba tana ta wadannan tunane-tunanen har suka iso iyafot din Murtala Mohammed. Seun, shi yayi tsayuwar tsayin daka akan kayanta, har aka gama checking aka aunasu a jirgi. Ya rage dan lokaci jirginsu zai tashi, sannan ne Dade ya bata tikitinta da Fasfo dinta a hannunta. Yace da ita “nan da awanni 22 zaku sauka a kasar Argentina. Kada ki damu, na riga na gaya masa karfe nawa zaki taso, da lokacin saukarki. Kina sauka zai zo ya daukeki da kansa a filin jirginsu. Inji dai zaki gane kamannin Yayannaku? In ma baki gane shi ba na tura masa hoton ki, na jikin pasfo dinki, na tabbata shi zai gane ki”. Siddiqah ta gyada kai, tana fakar kallon Dade tana hadiye hawaye har wasu suka ballo kan kuncinta suka ki hadiyuwa, ta sharesu da gefen gyalenta. Dade ya lura kuka Siddiqah take yi kasa-kasa, yaji babu dadi a ransa, nan yaji duk guilt ya kama shi da bazai kama hannunta ya kaita har gaban Abdulrasheed da kansa ba, ya hada su yayi musu nasiha ya bashi amanarta, amma Emir ne ya ce masa kada yaje, ita kadai ya yarda a tura, in yaso a gaya masa ta taho, yaje ya dauketa da sun sauka, dattijon Bayeraben mai ran karfe shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan. Amma anya ba Prince din ya kamata su takurawa ya tako ya zo ya dauketa da kansa ba? To amma basu da mafita sai wannan guda daya, don iyaka tunaninsu sun san ba zai zo ba din, duk iya kiran da zasu yi masa in dai akan mace ne. bazai ce bazai zo ba amma zai yi ta zamewa ne cikin hikima ba tareda ya bata musu rai ba har sai sun gaji sun rabu dashi. Dade ya dafa kafadun Siddiqah a hankali yace “Be strong my daughter. Allah yana tareda ke kin ji, addu’o’inmu na tare dake, daga tashin ki har ki sauka ba matsala. In sha Allah. Ki fuskanci mijinki da karfin zuciya kada ki karaya da komai zaki gani akansa, kullum ki tuna cewa zaman jihadi ne zaki yi babba, na gyara rayuwar Abdulrasheed ya karbi rayuwar iyali. Ke ce kadai zaki sa ya goge tabon da yayiwa mata daga ransa, ko yaci gaba da yi muku kallon da yake yi muku bakidaya. Siddiqah ke kadai zaki sa Abdulrasheed ya gane ya kuma banbance cewa yana missing wata rayuwa mafi girman daraja daga wadda ya baiwa amanna a rayuwarsa; wato tsakanin rayuwar aure da tara iyali da kowanne dan adam mai lafiya ke yi, koko ta neman duniya babu wadanda zasu taya shi ci da morar duniyar, ke zakisa ya yarda akwai abinda zai bashi pleasure in this life fiye da hawa Dawakansa. Wuce ki shige ana kiranku, Allah yayi muku albarka bakidaya”. Da baya da baya take tafiya tana kallon Dade, mutum mai tarin karamci da kulawa a gareta, hawaye fal idanunta, shikuma Dade bai bar wajen ba, haka bai gushe ba yana aika mata murmushin karfafa gwiwa har ta shige cikin boarding passengers. ***** ***** ***** Lokacin da jirgin Argentinian Airways wato (Aerolineas Argentinas) ya daga da SIDDIQAH YUNUS tana daga zaune jikin tagar barin dama na jirgin, idanunta a lumshe, tayi kukan har ta gaji, sai ajiyar zuciya take yi yanzu kuma, zuciyarta ta cunkushe da tunaninninka marassa dadi; muhimmi cikinsu shine ganewa data yi iyayen Abdulrasheed bakidaya sun dora hope din daidaituwar rayuwar tilon Dan su a wuyanta, wato samuwar farin cikinsa da canzuwar rayuwarsa ta hanyar aure. Dade da Nenne, Sun bata dukkan ‘trust’ dinsu, da duk wani fatansu nagari na cewa ita din a yadda take da kuruciyar nan (in her teens) zata ita iya canza Prince Abdulrasheed mai shekaru sama da arba’in daga rayuwar data sameshi a ciki, ya kuma karbeta ya bata gurbi tare dashi ko yanaso ko baya so. Gashi tasan bata taki komai ba, bata da idea bata da wata fasaha akan zama da Dan su Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni, wanda alamu sun gama nuna ba ita Siddiqah kadai ba, baya maraba da kowacce mace cikin rayuwarsa balle ita diyar Mallam Yunusa. Ko abubuwan nan da Kiki tace su suke gigita maza su so mace, ita Siddiqah bata dasu bata mallaki ko dayansu ba (frontward-backward) ta bakin Kiki. Taji da kunnenta sanda Murjanatu (Taiwo) take kusheta, Ya Allah! Murjanatu ma kenan wadda tafi kowa kusanci dashi, tafi kowa saninsa, ta san abinda zai iya so da wanda bazai taba so ba, balle ita Siddiqah da ba sidi ba sadada! Tsabar tunani irinna rashin self-confidence, lack of motivation da inferiority complex da suka bi suka dabaibayeta yasa har aka ajiye mata abincin jirgi a gabanta bata sani ba. Abu daya take da kwarin gwiwa akansa har gobe, idan ta tuna cewa ita bafullatana ce a kansa, tanada wannan ego din na cewa kabilar data fito tafi tasa daraja (a tunaninta). Kabilarta wato (Hausa/Fulani) babu ya ita a kabilun Najeriya wannan kadai idan ta tuna shi yake bata karfin gwiwa. Kenan ethnocentrism dinta har yanzu yana nan, bazai taba barin zuciya da kwakwalwar Siddiqah ba har abada wato perception dinta na (alfaharin kabila). Tana cikin passengers masu tafiyar dare, da suka tashi zuwa babban birnin (Beunos Aires) din Argentina, kai tsaye tun daga Lagos, tafiya ce suke yi mikakka ba tareda transit (dakatawa a wata madakata ba). Lokacin da jirgin su ya sauka a ‘Aeropuerto Ezeiza’, wato filin jirgin (Buenos Aires), saida kowa ya gama ficewa amma still har lokacin Siddiqah tana zaune a mazauninta kamar an kafe ta, ta rasa inda zata tsoma zuciyarta da rayuwarta taji daidai. Har saida ma’aikatan jirgin suka ankarar da ita cewa kowa ya fita ya barta. Sannan ne ta mike ta saba Jakarta, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta dinga jan kafa, jaye take da trollies dinta guda biyu da basu cika girma ba. Aisha sanye take da ruwan makubar Abayat da mayafinta kirar Taiwan, mai adon manyan stones da suka maida rigar mai dan nauyi, ba tareda Siddiqah ta san ina zata dosa ba kawai ta tasa kai a gabas take tafiya. Ita tasan ba wata shaida da take da ita da Hamma zai ganeta, kamar yadda Dade yake zaton itama zata iya gane shi, bata tsammanin ko kamannin fuskarta Prince ya sani. Kodayake Dade yace wai hotonta zai tura masa na jikin pasfo ko yaya dai? Itama kuma bazata iya tuna kamanninsa ba, don kallon shifcin gizo tayi masa a asibitin Lagoon lokacin da aka kwantar da Nenne, abunda zata iya tunawa game dashi guda daya ne zuwa biyu; na farko turarren tabon sallahr dake saman goshinsa, wanda ya ciza sosai ya nuna cewa Sajidi ne (mai yawan sujjadah). Na biyu kuma ingarman jikin sa murdadde da tsayayyun kafadunsa, wadannan ko ya juya baya ne ta gansu zata ganeshi dasu, don ba duk maza Allah yayiwa baiwar halittar da yayima Hamma ba. Ta cigaba da wuce mutane tana tafiya a ba tare da ta san ina zata dosa ba. Don haka ba jimawa Siddiqa taji wani marayan kuka ya zo mata, ba don ta rasa Uwa ko Uba ba, amma jin kanta take yau a marainiyar karfi da yaji, mara gatan kowa. Tana ta kokarin hadiye kukan da hawayen, tana gayawa kanta Allah na nan, kuma shi zai zama gatanta a nan inda bata da kowa. Hannayenta hagu da dama jaye da jakunkunanta ta wuce cikin terminal. Tana tafe idanu a rufe duk hawaye ya jika fuskarta, ba tareda ta san ina take jefa kafa ba saboda rudanin zuciya da kwakwalwa, Siddiqah tafiya kawai take kanta tsaye har ta kan kusa bige jikin mutanen dake wucewa ba tare ta kula ba, sabida idanunta sun rufe ruf! Da hawaye, sai ji tayi gab! Tayi wani uban karo da mutumin dake tahowa direct gabanta. Kawai sai ta samu kanta da dagowa a hankali, da bude ido jikakkun idanunta da suka kankance don kuka ta dubi mutumin, bata san sanda ta saki marikin jakunkunan hannunta kasa ba. Don kafin taga komai ta hango tabon sujjadar dake saman goshinsa, kafin ta sauko da rinannun idanunta akan faffadan kirjinsa wanda shine ya bashi suffar da za’a kira shi da INGARMA… A yawan hirar Kiki akan Kawunta, ta kan ce mata wai mazan duniya aji-aji ne su, a kamanni na halitta da kasaita, amma cikinsu da wuya a samu irin Uncle dinta…. Kiki tace “Uncle dinta zatinsa da kyawun surarsa ya zarta yadda duk zata misalta mata su ta gane baiwarsa mai yawa ce, ta dauka Kikin koda Ubannata kadai take yi a wancan lokacin, don ita bata ga komai da zata iya noticing har ta karar a tare dashi ba, a dan ganin data yi masa. Amma yau ta ga zahirin maganar Kiki-Ruqayyat, saboda ta yi masa kallo ne sak na rahma da salama, bana cikin halin taraddadi ba (ba irin wanda tayi masa a ganinta na farko dashi a asibiti ba). Ga cikar zati da kamala irin na jinin sarauta tsantsa da Allah ya yi masa, sannan kwarjinin fuskarsa a bayyane yake duk da a hade ta ke tamkar hadarin da ya nausa yayi gabas, sun nuna cikakken basarakensa, bayeraben usuli mai surki da ruwan jikin fulanin Gombe, wanda shine ya hadu ya maida shi tamkar ruwa biyun kasar Habasha, wato kamar dan kasar bakar fata ta Ethiopia, wannan kadai da kallon kyarr da ido da yake mata ne yasa ta gane cewa ba kowa bane a gabanta; HAMMA PRINCE ne…… Bata bukatar sai wani ya fada mata cewa ya ganeta, ko sai ya gabatar da kansa cewa shi dinne kafin ta yarda ta bishi. Shima kuma bai ce komai ba, sai kawai ya sunkuya yana daukar jakunkunan da ta saki a kasa …. Kafin Prince ya dago daga sunkuyon da yayi don daukar jakunkunanta, Aisha Siddiqah taji mararta ta cika taf! Da wani fitsarin razana da ke shirin balle mata daga yanzu zuwa kowanne lokaci, saboda tsabar kidima hade da rudewar da ta sameta lokacin da Prince ya dago manyan maganansa ya dubeta suka hada ido. Hamma ya wara manyan idanunsa a kanta, kallon da yake mata kamar yana son karanto dalilin wannan bewilderment din da ya gani a tare da ita. Ga hawaye na babu gaira babu dalili dake ta tsere a fuskarta wani na korar wani, Aisha ko damuwa bata yi data sharesu, ga jama’ar dake wucewa suna kallonta. Prince ya dan juya hagunsa da damansa a sace, kamar yana son ganin kota jawo masa hankalin mutane da wannan kukan nata, a dauka ko bata son binsa ne, ko batan hanya tayi. Sa’arsa daya sai yaga ba wanda ya basu hankalinsa wucewa kawai ake yi hagu da dama ba tareda an kula da ita da koke-kokenta ba. A cikin jikakkun idanunta kadai ya karanci cewa ta ganeshi, domin bayan rudewar ganinsa daya mamaye idanunta har da kallon sani dana bakunta a gareshi, da kuma kallon rashin sanin kalmar data dace ta furta masa mai nuna cewa ta gane shi din. Don duk wata kalma data kama a kan halshenta don furta masa, sai taga bata yi daidai ta furta masa itaba, har gara ma tayi shiru ta bishi da ido. Sai kawai taga ya juya dauke da jakukunan nata a hannunsa yayi gaba abinsa, ya kasa furta kalmar "biyoni" ko "follow me" don bai san yaren data ke ji sosai ba, tsakanin hausa da fillanci ko ingilishi, ya san dai Nenne tace daga Gombe ta ke, balle yayi mata tsammanin yarbanci. Kalarta da shigar jikinta da komai nata yafi nuna na ‘yan garinsu Nenne din, wato typical 'yan matan arewacin Najeriya. Aisha ta kasa cira kafa tabi bayan Hamma Prince tunda dai bai mata umarnin hakan ba, kada ta bishi ya zama ta zaqe, ita kuma a rayuwarta ta tsani zaqewa, kawai taga ya dau jakunkunanta ne yayi gaba. Ba tareda yace mata komai ba. Har sai da ya dan yi nisa ne ya ankara da cewa ashe bata biyoshi ba. A sannu ya juyo don ya tabbatar, sai ya ganta kuwa tsaye standstill a inda ya barta, bata ko cira kafa ba. Prince ya dakata yana tambayar kansa wannan wace irin yarinya ce kamar ‘yar goye Nenne ta kawo masa? Domin koda ya juyo gani yayi tana ta share ido bata taho ba din, tana jiran sai ya gaya mata me ya kamata tayi ita bata san facial expression ba? To idan kuma bai iya yaren data ke ji bafa, don shi ba wai ya kware da Hausa bane. Bayan dama cikin haushin an masa katsalandan da zuwanta gareshi ya wuni, alhalin yazo Argentina ne yin dogon hutun karshen shekara don ya samu ya huta, ya rage stress, yanzu ga rainon 'yar goye an kawo masa, yo raino mana! Don wannan a shekaru ai bata fice sa’ar Kikinsa ba. Budewar ido kawai Kiki ta fi ta. Ko Kiki fama yake da ita har gobe akan shirmen kuruciya, balle wannan mai ruwan ‘yan fulanin cikin garin Gombe. Dawowa yayi inda take tsaye yana kokarin hadiye fushinsa, don yasa a ransa cewa ba laifinta bane zuwan da tayi, umarnin iyayensa ta bi. Prince ya dan hade giran saman idonsa ya cure su, yace. “Are you waiting for my command? If yes, then follow me!”. (Kina jiran umarnina ne? In haka ne ki biyo ni toh). Aisha ba wai bata jin turanci bane ko yaya, tanada turancinta ba laifi tunda ‘yar makaranta ce, amma wannan karon kwakwalwarta ta kasa fassara turancin nasa, domin sak yake furta shi kamar na turawan yamma, wato accent din bata saba jin irinsa ba ko yaya ne dai ita dai bata gane me yace ba. Shikuma Prince sai bai kara cewa komai ba ya juya ya cigaba da tafiya, jinin mulkin ya motsa, yana cewa a ransa in bata biyoshi wannan karon ba baisan ya zaiyi da ita ba kuma. Don kuwa ya tabbata ta ji shi saidai in shakiyanci ne kuma abin nata, tunda ya tabbata ba kurma bace ai ya santa a zuwan da yayi Lagos tana gidansu. Tafiya yake a nitse akan marbles din wajen da jakunkunanta, bai kara waiwayota ba, ya barta a wurin tana zare jikakken idanunta ta rasa me zata yi takamaimai, don rudewa tasa ta kasa fassarawa kanta umarninsa ba rashin jin turanci ba. Kafin ta baiwa kanta shawarar kawai ta bi shi, shi ya fiye mata alkhairi fiyeda cigaba da tsayuwa a wajennan. Idan ya bace mata cikin mutanen da batasan kowa ba sai shi, tabbas zata gayawa aya zakinta. Sai kawai ta cira kafa da hanzari ta bi bayan Prince, harda hadawa da dan gudu-gudu, domin ya fara yi mata nisa. Prince sai jin motsin gudun-gudunta da sassarfarta yayi a bayansa, ya dan tsaya har ta cimmasa, kafin su jera tare zuwa parking lot na filin jirgin, yana gaya mata ta tafi a sannu akan santsin wurin, kada ya kada ita. Motar da Prince yake budewa Siddiqah ta bi da kallo domin da fari ta dauka ba mota bace wani abun ne daban, domin gani tayi murfin ya dage sama da kansa, wato kofar motar ta daga sama automatically, sannan samanta a yaye yake. (Sport Car, Toyota Supra) duk iyaka dauriyar Siddiqah da dakewarta na kada ta nuna kauyanci ta kasa karfafawa kanta gwiwar ta shiga motar nan, ba don komai ba sai don tsoron ganin cewa samanta a bude yake gabadaya. Idan iska ta daukota tayi wurgi da ita akan titi Ummanta kadai za'a yiwa asara. Shi a gatan da yake dashi a gobe za'a auro masa gomanta. Goman Siddiqah harda kwarori. Don haka shiga wannan motar ai tsautsayi ne da ganganci a ganin Siddiqah. Sai ta kara jin tausayin kanta na wannan rayuwar bakon wuri, da kasaitaccen basaraken bayeraben mijinta data samu kanta rana daya. Siddiqah ta kasa tsayar da hawayen ta sam. Prince bai lura da halin da take ciki ba ya sanya jakunkunan nata a bayan motar, sannan ya bude bangaren direba ya shiga ya zauna, har zuwa lokacin tana tsaye kikam. Shi tunda yake bai taba sanya mace a gidan gaban mota ya tuka ta ba inka cire Fatima ko Firdausi ko Kiki. Amma haka ya daure ya mika hannu ya budewa Aisha kofar barinta ta hanyar danna wani madanni a jikin allon motar, yana lallashin kansa da kansa, yana gaya ma kansa yarinyar nan taci albarkar DADE dinsa da NENNE. Iyayen da bai hada alfarmar su data kowa. A komai ma zata cigaba da cin albarkacinsu, tunda sun zabeta gareshi sama da kowacce mace, har gobe sun kasa gane uzurinsa na bashi da gurbin adana kowacce ‘ya mace a ransa da cikin rayuwarsa. Amma Siddiqa ta ki shiga don kauyanci da rashin sabo na shiga gaban mota daga ita sai katon namiji, gani take motar babu sirri, kowa yana ganinsu, sannan yadda take babu nauyin nan iska zata iya daukota ta jefota waje in aka fara tafiya. Prince ya fara zama bored da kauyancin Aisha don kiri-kiri kana iya karantar tsoron motar take ji a kwayar idonta, bayan kasancewarta cikin takurar zuciya har a kan fuskarta, har ila yau, kana iya ganin kauyancinta baro-baro. Shi bai ga dalilin kukanta ba ko sau daya, tunda da yardarta akayi komai, koda yake ya kamata yayi ma kukan nata uzuri, rabuwa da kasar haihuwarka rana daya da iyayenka bakidaya da danginka zuwa inda baka san kowa ba baka taba zuwa ba ba wasa bane. Amma in banda haka ai ba’ayi wa bakunta kuka in ma bakunta ce. A ganin Prince shi ya dace ya dora hannuwa aka yayi ta rafsa ihu yau ba ita ba, shi da aka turo masa mace bagatatan, macen da ya riga ya rufe babinta aka sako yau cikin gidansa da rayuwarsa. Watakila kuma tana kuka ne kan an aura mata tsoho kamar shi, yarinyarta da ita danya sharaf, gata nan santaleliya son kowa kin wanda bai samu ba. Amma ya kamata ta duba cewa bai je inda take da kansa yace yana sonta ba, balle ta yi kukan auren dole dashi. Inda wanda zata tuhuma akan hakan to nata iyayen ne da suka yarjewa nasa iyayen, ba tareda sun ko gan shi ko a hoto ba balle a zahiri. Ya tuna abinda ya faru jiya. Yana zaman zaman sa Dade ya kira shi a waya. Inda cikin raha Dade din yace. “Kehinde, me kake yi daga yau zuwa gobe ne?” “Dade it's month end ai ka sani (kuma ya kama Asabar din karshen wata), so nafi zama a gida a duk rana irin wannan, Pareto yayimin lissafin abubuwan da suka kare a gidan, da abincin dabbobi da sauran bukatunsu, muna checking lafiyarsu kuma, sannan in biya ma'aikata albashinsu na wata, sannan muna yin lissafin abincin Horses da zamu ajiye na tsayin wata guda. So I will be busy the whole day, daga yau zuwa goben har in samu in kammala da duk wannan”. Cikin tsokana Dade yace "kawai kace min “The Prince and his ranch activities dai, to Allah ya taimaka, inaso yanzu ka ajiye komai ka sa a shiryawa Aisha-Siddiqah dakin da zaka sauketa, jirginsu ya taso zuwa Argentina yanzu daga Lagos, zasu sauka a (Ezieza International Airport Bueunos Aires) nan da awanni ashirin da biyu”. Saida ya baiwa kwakwalwarsa aiki na wucin gadi yana son gane me Dade ke magana akai, kuma wacece Aisha Siddiqa din, har saida ya ga cewa ya gaza wajen ganewar ya tambaya cikin girmamawa mai hade da mamaki. “Dade wacece Siddiqah kuma wajen wa zata zo?” Sai Dade ya juya harshe zuwa (native language) yana masa bayani don dai Prince ya yarda cewa seriously yake magana dashi yanzu. Cikin harshen Yarbanci yace ma Prince din. "Na gaji da jiran zuwanka na sako maka matarka Siddiqah a jirgi, ta taho, so nake ku rayu tare rayuwar sunnah a gidanka da duk inda zaka shiga, daga nan har karewar numfashi. Tunda naga alama baka san zuru ba, da irin sacrifice dinda iyayenta masu dattaku suka yi mana, suka baka aurenta ba tareda sun ko gan ka ba". Sai Prince ya tsaya sakatoto! Da waya a hannu, jin Dade ya kashe wayarsa ba tareda ya bashi damar kara yi masa tambaya ko neman karin bayani ba. Ya koma ya zauna a hankali bisa kujerar da ya mike daga kai lokacin da zai amsa kiran mahaifinsa. Prince bayan gama sauraron Dade sai ya kasa cigaba da aikin da yake yi, zufa sai yanko masa take yi daga goshi, ya koma ya zauna yayi tagumi da hannu bibbiyu, yana ji kamar yayi ihu. Domin wannan shine (hukunci mafi tsanani da tsauri da iyayensa suka taba yi masa). To amma ya kamata yaga laifinsu? Sun bi duk ta hanyar data dace don ya kawo mata da kansa, don yayi aure ya cika mutum a lokacin da ya dace, sun yi fadan sunyi lallashin, sunyi barazanar aura masa guda hudu daga danginsa, Nenne har kuka tayi a gabansa, akan zarge-zarge marassa dadi da ake masa, Emir ne kawai yake yi masa uzuri, har kauracewa Baffanninsa yayi akan suna so yayi aure don radin kansa da zabin kansa, ya cika tarbiyyar gidansu abu ya gagara, don haka kada yaga laifin kowa a kan zabin da suka yi masa yanzu wanda shine hukunci na karshe da ya biyo baya, na biyo shi da yarinyar har inda yake finally. Kamata yayi ya ga laifin kansa, bana yarinya ba, wadda aka katsewa rayuwar kuruciya itama aka turo ta aure inda bata da kowa ba da son ranta ba. Ko kusa bai kamata yaga laifin iyayensa ba. Sun bi duk hanyar daya kamata su bi donbashi hakkinsa a addinance da al'adance. Yarinya ita akafi cuta ma, kasancewar da kuruciyarta an hadata da tsohon tuzuru kamar sa. Nenne ta gaya masa maganar auren tunda jimawa amma ya gudu ba tareda ya damu ba, in zai iya tunawa daga lokacin bata kara yi masa zancen yarinyar ba, ta koma normal rayuwarta ita da shi. Ashe ba hakura suka yi ba dungu suka yi masa. Yau dai ga matar nan an biyo shi da ita hara Ajantina, ba kwabonsa babu darinsa, a wurinsu karshen gata sun gama yi masa, a wurinsa karshen katsalandan da takurawa an yi masa, in ba Dade din ba wa ya isa yayi masa wannan karan tsayen a rayuwa? Ko Akannis tara bazasu fara ba. Kai ko Emir ba zai masa hakan ba. Shi tunda ya koma Qatar bayan rashin lafiyar Nenne, lokaci-lokaci maganar yarinyar na fado masa, yakan tuna wai yanzu an masa aure, sai kace wani a zamanin da. Tabbas za'a gaji da ajiyar matar nan kuwa, a karshe a maidawa iyayenta don ba zai taba dauka ba. Sai kuma ya tuno kamannin yarinyar, wanda ko bai rike hakikanin kamannin ta a ransa ba, hakika ya rike kalar idanunta masu kama dana kwan zabo, wadanda suka nuna tsantsar damuwar rashin lafiyar Nenne cikinsu da wani irin innocence. Ya dade a zaune kafin ya yanke shawarar takamaimai me ya kamata yayi? Gashi an ce ta rigata taho. Ya bi bayan kiran Dade ne yace ta koma sai ya shirya ko yace bai shirya iya zama da iyali ba har yanzun a kara masa lokaci? Har zuwa sanda yake jin ya shirya? Ya riga ya saba da rayuwarsa ta kadaici ayyukan cigabansa, and his horses always makes him busy, baya maraba da duk wani abu da zai canza masa tsarin rayuwar nan da ya riga ya saba da ita. Kamar ya kira Taiwo, ya gaya mata abinda Dade ya kira shi yanzu ya gaya masa in yaso ya nemi shawararta kan abinda ya kamata yayi, don gaskiya Dade ya shammaceshi, sai kuma ya fasa kiran nata. Dalilin tunawa da yayi cewa Taiwo tun rana ta farko da tazo Lagos taga yarinyar ta yi masa korafin yarinyar da Nenne ta aura masa bata yi mata ba, because they are so much different from the grounds of age and social class. Bai taba tanka mata ba don shi bai dauki zancen ma da muhimmanci ba. So yanzu ya kirata yace an sako yarinyar a jirgi ta taho masa, bai san abinda Taiwo zata ce ba, banda ta sa shi ya maida ita. Ita dama ta saba rikici da iyayensu in sun yi hukuncin da baiyi mata daidai ba. Wata zuciyar tace to ko Kiki zai dauko daga Ilorin su zauna tare? Nan ma yaga hakan bazai yiwu ba musamman kasancewar Kiki na makaranta kuma watarana itama aure zata yi. Shi kam! Yayi duk iyaka tunaninsa bai ga ta yadda zai iya zama gida daya da mace da sunan partner ba. Bayan tsanar su da yayi, har gobe duk kallo iri daya yake yi musu, koda da wace niyyar alkhairi suka dumfaro shi. Uwarsa da ‘yan uwan sa na ciki daya kadai ya kebance daga cikisu. Gidan nasa babban ‘Ranch House’ ne hade da gidan gona (farm house), tsarin ginin flat ne aka gina a can tsakiyar ranch din. A cikin wannan flat din akayi babban (sitting room) dake kunshe da dakunan gidan, falon gidan (is kitchennette) wato hade yake da budadden kitchen na zamani da ake yayi yanzu da dining area. A cikin wannnan babban (sitting room) din ne masterbedroom din Prince Abdulrasheed yake. Sai wasu (two extra two bedrooms) din, kowanne da bathroom a cikinsa, wanda asali ya tanadi dakunan ne domin ‘ya uwansa mata da haularsa dake zuwa hutu wajensa akai-akai. Daga harabar wajen flat din nan ne Ranch na Dawakansa, suna cikin stable dinsu a jere abin gwanin ban sha’awa. Ko ka samesu sun watsu cikin korran ciyayi a ranch house din suna ci daga garesu, suna kuma sha daga ruwan dake tsiri sama yana sauka kasa (katon swimming na gidan gonar), inda anan ake kiwon fararen Agwagin ruwa, Dove, Babba da jaka, Kangaroos, Jimina, da Gada Mai tsalle, a can karshen gidan kuma wajen kiwon Shanu ne irin na turai masu yawan haihuwa akai-akai inda ake milking danyar Madara. Prince har ila yau yana kiwon tsuntsayen gida irin su kajin gidan gona jajaye, farare da bakaken tantabarun Ingila, Dawisu da Argentinian Parrots (Aku-kuturun Argentina) manya-manya masu magana. Duk a cikin wannan kasaitaccen ranch din. A can karshen gidan gonar ne sassan Pareto da sauran ma’aikatan gidan gonar yake, da babban (store house) na ajiye abincin Horses dana sauran dabbobin. Yana zaune still yanata tunani ya ankara lokaci na tafiya, ya dade a wannan halin na zama shiruuu, ya rasa ta ina zai fara. Cika umarnin mahaifinsa ko bin hukuncin zuciyarsa? Kararrawa ta gaya masa ana magana dashi a kofa, da kyar ya iya mikewa don kafafunsa sun masa nauyi, zuciyar sa ko tayi nauyi sosai, da kyar Prince ya isa ga kofar ya bude. Pareto ya gani tsaye rike da kayan sa da ya wanke ya goge, ya bashi hanya ya wuce ya ajiyesu akan daya daga cikin (three seaters) din (sitting room) din, don a ka'ida Pareto baya shiga (master bedroom) dinsa. Kawai sai Prince ya samu kansa yana ce ma yaron gidan nasa. “Bude daki daya cikin biyunnan ka gyara, ka karbo abincin da nayi order, ka ajiye a dakin, zan kawo baki daga gida Lagos anjima”. A gidan gonar Prince, Prince ruwan zafi kawai yake iya dafawa da kansa, duk abinda zai ci daga ‘African Cuisine Restaurant’ dake kusa da gidansa yake saka order ake kawo masa, kullum sau uku, in har yana Argentina kuma yana gida bai je tournaments ba, to 'El Buen Sabor Africano' su suke bashi abinci na al’adarsa wato (traditional Yoruba food). Pareto ya bi umarnin ubangidansa ya je ya fara gyara dakin wanda dama a gyare yake, sai abinda ba'a rasa ba don baya sati biyu bai gyarashi ba, ko su Fatima sun zo ko basu zo ba yana yawan sharewa ya goge, dama dai Taiwo ce tafi sauka a cikinsa don yafi girma, ko ita ko Nenne. Dayan twin Princesses da Kiki ne ke sauka cikinsa. Pareto Yana feshe dakin da room freshener bayan ya gama mopping, yana yi yana tunain ko su wa Boss zai kawo? Ya san da ba lokacin hutun kannensa bane ba, ko Twin Sis dinshi Mrs Taiwo. Da ya kammala ya fito sai ya samu Prince har lokacin a zaune inda ya barshi da alama yana cikin tunani. Ya kasa yankewa kansa shawarar zuwa Airport din ne don cika umarnin Dade ko a’ah? Saida ya rage bai fi mituna talatin jirgin ya sauka ba ya mike cikin zafin nama ya suri mukullin mota ya fita. Kuma yana isa wajen ya hango yarinyar tana tahowa kanta tsaye, duk da dai Dade ya kara da turo masa hotonta ta waya da ko budewa bai yi ba, yana ganin ta jikin sa ya bashi, zuciyarsa ta amsa, yayinda kwakwalwarsa da idanunsa kuma duk suka shaidata. **** **** **** Aisha nata tunanin shiga motar ne ko yaya zata yi? And the Prince is patiently waiting for her to decide, kamar yasan shawara take yi da zuciyarta tsakanin binsa ko a’ah. A ransa yace baida matsala kan duk abinda ta zaba. Shiga motarsa ko kin shiga zabinta ne, shi dama dan cika umarni ne kawai. Ya mika hannu ya bude mata kofa, wani privilege da bai taba yiwa wata mace ba bayan Nennensa, a iyaka saninsa tun tasowarsa sai dai shi a bude masa. Ya kunna injin motar wanda baya making any noise ko kadan, kasancewarta lafiyayyar motar tsere (Sport Car) ta zamani, sa’annan mai lafiyayyen sabon inji, Siddiqah ta gayawa kanta gaskiya idan Prince ya gaji ya tafi ya barta a wurin nan ina zata je a wurinnan da batasan kowa ba? Inda ko kallo kowa bai ishi kowa ba, kada ma taje Police su kamata a wurin a bisa tuhumar rashin yarda da ita, don gasunan birjik cikin fararen kayansu suna ta shawagin tsaro a filin wurin. Ko me ya bata tsoro? Prince sai gani yayi bakuwarsa tayi kundumbala ta shigo motar da sauri. The way and manner da Siddiqah ta sako kai ta shigo motar ma kamar mai shiga daki ya saka Prince yamutsa fuska, domin ba ta haka ake shiga motar ba. Ya dan kalleta kawai ta gefen ido yana so yace ta rufo kofar, mulkinsa na gaya masa yayi mata banza, ita bata san ya kamata ba? Komai sai an gaya mata zatayi? Shi baya son yawan magana a nature dinsa, don sai ya wuni bai yiwa kowa magana ba in ba SAHEEB ba, ko zai baiwa Pareto da ma’aikatansa umarni ba kullum bane. Amma wannna bakauyar yarinyar ya ga alama a komai tana jira a bata command ne, in kuma an bata din ba kasafai take ganewa ba. Sai kawai ya mika hannu ta gabanta ya rufo kofar da kansa, a hankali ya hau kwalta suka soma tafiya, nanma ya ga bata da niyyar daura belt, haka kawai zata jawo masa attention din road safety. Da wata murya kamar yayi kuka don tausayin kansa, na aikinda Dade ya hadashi dashi Prince yace da ita. “Please, fasten your belt!”. Siddiqah ta dago tana duban Hamma Prince da ‘yar rudewa, cikin alamu na son ya fassara mata, don har ga Allah wannan karon ma bata gane me Hamma yace ba. Don haushin data bashi Prince bai kara maimaitawa ba, sai kawai yasa hannu daya yayinda yake tuki da dayan yana daura mata belt din a bayan kwibinta, saida Aisha ta janye numfashinta sama kadan, sakamakon kakkarfan kamshin masculine turaren Prince “Boss Intense” daya bakunceta. Don da farko bata fahimci me yake kokarin manna mataa kugu ba, wanda hakan ya sata ‘yar karamar kidimewa, don haka har Prince ya gama zura mata, ya cigaba da tukinsa numfashin Siddiqah ya ki komawa daidai yadda yake, sakamakon tsoro da kidimar data shiga kafin ta gane belt ne Hamma ya saka mata. Ko irin kalle-kallennan na bakin hanya na bakunta da bako ke yi in ya zo bakon wuri, banda Aisha-Siddiqah. Titi kawai ta kurawa ido ba abinda yake burgeta duk kyau da kyatuwar birnin. Hankalinta da tsinkayenta duk basa jikinta a yanzu, suna ga irin rayuwar data tunkarota, a kasar Polo ta Ajantina, amma ta san ko babu komai tana da Allah, tana kuma da albarkar iyayenta tareda ita. Kuma Umma da Malam suna sane suka kawo ta don ta rayu da dan Nenne, sabida darajar iyayensa, amma ko me yasa ba ruwan kowa da feelings dinta akansa wane iri ne? Shima din kuma yana sonta ko a'ah? All they care for shine dansu yayi aure da mace mai tarbiyyah yar masu dattaku, ya samu ya cika martabarsa da tasu. Ummanta da Abbanta kuma damuwarsu akan ta samu iyayen miji na kwarai ne, Nenne da Dade kuwa sun hada wannan, burin nata iyayen shine suyi mata aure cikin lokaci, sannan su kaita inda za’a rike musu ita da daraja. A ganin Aisha Siddiqa lamarin is far beyond this only, ya kamata ayi la'akari da zuciyarshi a kanta, ita tata mai sauki ce tunda ta rasa Ishaq, to bata da sauran zabi akan mijin aure. Ishaq kadai takeso. Don haka a rashinsa kowa aka zaba mata sunansa Umma ta gaida Aisha, wato sammakal, don bata da ja akai. Tun Daga kallon data yi masa suka hada ido a filin jirgi bata kara yarda ta dube shi ba balle ta kalli cikin idanunsa masu tsananin kwarjini. Ta kan dai dan saci kallon gefensa yana tukin. Tafiyar mintuna kusan talatin ce ta kawo su gidan Prince tsakiyar garin Buenos Aires (capital of Argentina). Tausayin yarinyar ya dada kamashi ganin ta kifa kai a jikin allon motar tana sauke ajiyar zuciya ita kadai bayan tayi kukan ta gaji. Ya kashe motar yace da ita cikin sassauta sa “mun zo. Ko zaki iya shigowa ciki?” Da sassaukan turanci ya fada. Wannan karon bata isa tace bata gane ba, domin kuwa Prince yayi lowering accent dinsa da voice tone dinsa sosai. Pareto ne ya iso da hanzari ya budewa ubangidansa kofa kafin ya zagayo ya budewa Aisha. Ya umarceshi da ya shigar da jakunkunan ta ciki. Yana fatan kuma ya karbo mata abincin da yace ya karbo mata. "Master abincin tun kafin fitarka na karbo shi, na shirya shi a dakin". Aisha ta fito tana zare kyawawan idanunta a gidan gonar Prince Abdulrasheed (Kehinde). Wani babban ranch house ne wanda tun daga nesa zaka hango daidaikun Dawakai na alfarma farare da jajaye da bakake, sun watsu jefi-jefi suna cin korran grass, wani abun sha'awa da ko a talbijin bata taba gani ba sai yau a zahiri. Prince ya wuce gaba, Aisha ta hadiye kauyancin ta da tsoronta ta bishi a baya zuwa ainahin (sitting room) din dake cikin ‘ranch house’ din. Da suka shigo tsakiyar falon, Prince sai ya maida kofar ya rufe yayi gaba ya barta a wurin. Siddiqah ta cira kai a hankali tana kallon wannan kayataccen muhalli wanda saidai taga kwatankwacinsa a finafinan larabawa dana turawa, shigifa ce ta alfarma mai hade da karamin madafi na zamani da akeyi a cikin falo (kitchennett). Girman falon da fadinsa yasa kujeru kala-kala saiti uku kosassu na musamman yaci, batare da kowacce ta san da zaman ‘yar uwarta ba. Dole tsarin komai na sitting room din Hamma Prince ya burge bako, har dai in wanda ya san kimar muhalli mai daraja ne, ba kamar Aisha-Siddiqah ba, wadda iyakacinta Gombe da Billiri. Sai ko yanzu data dan samu 'yar gogewa a zaman ta na gidansu Prince a Lagos tareda Nenne. Ita kyawun falon da dukiyar da aka zuba a cikinsa firgitata yayi, maimakon ya bata sh’awa, ya kara kidima 'yar nutsuwar da ta fara samu. Tsayawa tayi a tsakiyar falon harde da hannuwa a kirji, tana jiran ya bata umarnin zama, ko ya nuna mata kujerar data dace ta zauna. Ta kwaso gajiya ba ‘yar kadan ba kafafunta har mintsininta suke, ba abinda take bukata a lokacin irin ruwa mai zafi a kwami ta shiga ta wartsake wannan gajiyar zaman data kwaso, sannan ta samu ta sauke sallolin farillar dake kanta don lokacin duhun dare ya fara shigowa. Prince bai tsaya a sitting room din ba balle ya gane halin da take ciki, da bukatarta na yada kafada, tafiyar awanni 22 Siddiqah tayi a jirgi daga kasar Najeriya zuwa Ajantina. An raine shi da zama mutum mai karrama dan adam ko yaya yake, don haka tuni yasa Pareto ya shirya mata abinci mai rai da motsi a dakin tun kafin fitarsa. Kusan koda ace Prince bai da duka halin humility din mahaifiyarsa Nenne Sappa, to yafi duk sauran ‘yan uwansa mata kamanta halinta na kirki da kyautatawa mutane, yana da kula da humanity din kowanne dan adam dake zaune karkashinsa. Kai ba dan adam kadai ba har dabbobinsa da yake kiwo sun shaida karamcinsa da kulawarsa garesu. Wannan ne dalilin da yasa bai ji a ransa zai iya wulakanta yarinyar nan ba, in anbi salsala meye laifinta? Bata san shi ba, bata taba ganin shi ba ko a hoto, aka je har gaban iyayenta aka aurota da kima don haka inma da wanda zai yi blaming dalilin zuwanta katsahan cikin rayuwarsa ai iyayensa ne ba itaba. Su din kuma ya tabbata masu cikakken iko ne a kansa, sunada ikon canza masa rayuwa zuwa wacce hankalinsu yafi kwanciya da ita. Don haka ya shanye komai na damuwarsa a fuskarsa, haka ya boye bacin ransa a cikinsa, ya dawo daukan abu a kitchenette ne ya ganta har zuwa lokacin a inda ya barta, mamaki ya kama shi, ita komai sai an mata umarni? Sai ya nuna mata dakin dake gefen nasa yace. “Kiyi amfani da wanan dakin”, ba tareda yace komai ba ya bude mata dakin suka shiga, ya nuna mata wajen kunna wuta da wajen kunna room heater, da yadda zata kunna shower da tap na toilet sannan ya fita, ya dauki snacks dinda da ya fito dauka a firij yasa kai ya koma master bedroom dinsa. Yana shiga dakin tun bai kai ga zama ba kiran Dade ya shigo wayarsa. Da rashin kuzari Prince ya zauna a gefen gadonsa yana amsawa Dade, suka gaisa, ya gayawa Dade ta iso lafiya, kuma har ya daukota, tana tare dashi a ranch house already. Dade don farin ciki hamdala ya saki a fili kuma da karfi, har abin ya baiwa Prince mamaki. Sai ga Dade yanata shiwa Prince albarka kwando kwando, yana roka masa alkhairori na rayuwa, zuria mai dayyiba da falalar Ubangiji. A karshe yace “yadda yayi musu wannan biyayyar Allah ya bashi masu yi masa ninkinta da gaggawa”. Jikin Prince Abdulrasheed ya idasa macewa murus, dan sauran shirin silent protest dinsa akan zuwan Siddiqa ya karasa tsiyayewa, ya rasa wane irin son yayi aure ne haka a zuciyar iyayensa, irin addu’o’in da Dade yayi ta jero masa yau, bai taba yi masa irinsu ba, Dade ya umarceshi da ya karbi wayarta ya hada mata layi ya loda mata credit don ta rinka kiran kowa nata a Gombe dasu Nenne. Prince yayiwa Dade alkawarin tunda yanzu dare yayi tana bukatar ta huta, gobe in sha Allah zai bata daya cikin wayoyinsa dake hade, ba sai ya karbi ta hannunta ba. Ina zani Dade ya goya Prince! Don farin cikin sa ya gaza boyuwa. Bai san sanda yace. “That’s my son Kehinde! Master of all my children, the great Prince of the Ilorin Emirate!”. Ya kare wayar tasu da cewa cikin harshen yarbanci. “Nenne mhi Iya agba opeo toba se die”. Ma’ana Nenne da Kakarsa Nani sunaso zasu kirashi yanzu domin su bashi tasu albarkar. Suna gamawa da Dade kuwa Nenne ta kira, ko daga yadda take magana yau dashi a sake kasan cikin farin ciki take. Cewa take cikin Fulfulde. “Allah wanne albarka Hammansu!”. Wato (Allah yayi albarka Yayansu). Shikuma ya amsa da “Amin Nenne, Allah beddu sabbungo!”. Wato Allah ya kara girma. Sannan tace “na baiwa Aisha WARA mai yawa ta taho maka da ita, tana cikin kayanta a duba a cire a dumama”. “Godiya nake Nenne, madallah!”. Uwar da Dan cikin shaukin juna suka yi sallama, ko ince Nani Oummana ta amshe wayar ba tareda ta barsu sunyi cikakkiyar sallama ba. Cikin fulatanci Nani Oummana ta shiga koda masa halayen kwarai na AISHA-SIDDIQAH wadanda ta nakalta a dan zaman da tayi tare da ita na gajeren lokaci. Tace "bafullatanar usul ce don haka bata da tsoro saidai kunya. Kada kayi tsammanin zata dinga jin tsoronka duk shekarun nan naka idan ka uzzura mata, amma idan ka tausasa mata zata yi maka biyayya sannan zata ji kunyarka". Da wannan sukayi sallama shida Nenne da Nanin Gombe. Wayar gabadaya ya kashe ya jefa ta a tsakiyar gado, kansa har sarawa yake kasancewar yayi Magana mai tsayi, a karshe yace da kansa “so Oummana ma na son Siddiqah kenan”. Dama can bata son ya auri kabilar Babansa, ta sha fada masa yazo wajensu yayi aure ya more mata. Yanzu kuwa tunda ta samu an aura masa 'yar Gombe ai shikenan kuma kaya ya tsinke a gindin kaba. Gara ya kashe wayarsa gabadaya don yana so ya zauna ya nutsu, ya saurari zuciyarsa, ya nemi zabin Allah sannan yayi tunani mai kyau akan zuwan Siddiqah rayuwarsa, ba wanda zai sa shi nadama daga baya ba. Wanka ya fada ya sakarma kan shi shower mai dumi. Yana wanka amma yana zufa, don iyayensa sun gama daureshi da jijiyoyinsa. Da ya fito daga wankan ya zabi kayan barci farare marassa nauyi ya saka ya sha zazzafan chamomile tea dinda ya saba sha kullum kafin ya kwanta, don chamomile din yana bashi barci na nutsuwa duk daren daya sha shi. Prince ya kwantar da kai a wuyan kujerar da yake zaune yana tunanin me ya kamata yayi akan zaman Siddiqah tare dashi a gidansa? Ya duba ya hanga ya ga ko ta ina babu wata mafita bayan mika wuya ga hukuncin Ubangiji da Kuma abinda iyayensa ke so yayi, hukuncin su na karshe kenan akansa, don ga dukkan alamu basu dauki al’amarin rashin aurensa da saukin da yake zato ba, ta yadda zai tunanin mayar da ita ba tareda sunyi mummunan sabawa shi da su ba. To amma shi ina yaga lokacin zama da mace a rayuwarsa. Abar ta tsanarsu da ya riga yayi bakidayansu, da kudin goron da ya riga yayi musu na maha'inta, marassa godiya, marasa tarbiyya, marasa tsoron Allah, mazinata, masu kwadayi da rashin halacci, sannan (gold diggers). Kullum a tafe yake kamar tsuntsu daga wannan kasa zuwa waccan, in ba jela zai mayar da Siddiqah ba yaya zai yi da ita? Yadda Prince Abdulrasheed yayi kwanan zaune yana tunanin mafita da wadda zata fishsheshi, haka Aisha Siddiqah ma tayi kusan rabin kwanan zaunen akan kujerar sofa kwaya daya dake dakin da Hamma ya sauketa. Ta kusan kwana a zaune dangargar tana kewar gida da iyayenta da Nenne. Amma a karshe ta lallashi kanta ta baiwa kanta baki tunda bakin alkalami ya riga ya bushe, gata ga Hamma Prince a cikin gidansa. Ta baiwa kanta shawarar daina takura zuciyarta akan komai ko asarar hawayenta, ta fuskanci reality din dake gabanta kawai, wanda shine zaman aure na fisabilillah tsakanin ta Abdulrasheed Kehinde wanda shi Allah ya zaba mata madadin Ishaq, iyayenta suka ga shi yafi mata alkhairi akan nata kabilan, alhali sun san bata son wannan kabila ta Yoruba ko digo. Tace tunda iyayenta shi suka zaba da saninsu na cewa Yoruba dinne, ta kuma gane ko su waye kabilar yarbawa yanzu a dan zamanta dasu a Lagos da makaranta, it will be easier for her to live with this arrogant Prince. Ya kamata ta baiwa kanta farin ciki ta maida komai ba komai ba, ta kuma baiwa kanta ‘yanci a zama da Prince. Abu na farko kada ta yarda ya raina ta wai don ita yarinya ce sosai a kansa, ta girmama shi yadda Allah yace a matsayinsa na mijin ta kuma babba sosai a kanta, ta shiga duk inda take so a gidannan ai gidanta ne da aure ya riga ya bata, ta kuma cire duk wani tsoro-tsoron nan nasa wanda take dan ji a baya dalilin rashin sakin fuskarsa gareta. Zata fara rayuwarta cikin sukuni da walwala daga safiyar gobe, ta daina bari kwarjinin Prince Abdulrasheed yana yi mata dabaibayi. Saka kai a damuwa kan abinda baka da maganinsa aikin banza ne, gara ma ta nemowa kanta farin ciki da sukuni a cikin gidan, ta hanyar yin duk abinda taga zai bata nishadi. Tunda auren Baban Kiki yanzu aka fara, kuma ya zama dolen da bazata iya gujemawa ba har illa masha Allahu. Aisha Siddiqa ta mike bayan gama wannan tunanin, ta shiga bathroom ta daura alwallah sai ta kintaci inda hakalinta yafi kwanciya da cewa shine gabas, ta tada sallah, ta sauke duk sallolin da suka risketa a hanya. Sannan ta koma tayi wanka da ruwa mai zafi sosai ta sanya wata doguwar rigar barcinta sabuwa kar mara hannu da dan kauri. Ta zauna taci abinci ta koshi don yunwar cikinta kadai ta isheta kasancewar bata ci abinci a jirgi ba. Data kammala ta dauko wayarta ta saka a caji, ta ce ita kadai "bari in roki Baban Kiki ya karba ya hada min network". Amma koda ta fito don duba shi babu shi a falo bata tadda shi a sitting room din ba, ya dade da kashe wutar lantarki da duk kayan wutar dake falon ya shigewarsa dakin barcinsa. Komawa dakin tayi ta maida wayarta ta saka a caji, ta cigaba da kallon ko’ina a dakin tana tazbihi, don ita dai bata taba ganin gida mai shan kai irin Ranch House din Hamma Prince ba, wanda tun saukarta ta kudire daga yau ta daina kiransa Hamma sai Uncle AK. Ba don komai ba sai don kwana daya da sukayi yau a gida daya yasa kwarjininsa da kamalarsa sun karu a idanunta. An kashe dukiya da lokaci wajen tsara wannan gidan gonar Dawakan nashi ba kadan ba, komai na gidan daban yake daga wanda ta sani, ko ta saba gani a Gombe da Lagos. Ga caji ta samu waya ta cika full, kuma bata jin barci, amma bata da password din da zata yi amfani da WiFi din gidan. Sannan bata da kudi a wayar ma balle tayi kira na kai tsaye, kwarai take son kiran Nenne da Ummanta ta gaya musu yadda ta sauka lafiya. Son samu har Dade mai sonta da son kwanciyar hankalinta ta kira don ya tabbatar ta kwantar da hankalinta. Anan kan kilishin da tayi sallah da waya a hannu barci mai nauyi ya dauke Aisha Siddiqah Yunus a gidan Prince Abdulrasheed (Kehinde). Barci take yi na gajiya da tsamin jiki wanda zaman jirgi na awanni masu yawa ya haifar mata, ba ita ta samu farkawa ba sai asubahi. Ta saba ji a jikinta idan asubah tayi, ba tareda kowa ya tasheta ba ko taji kiran sallah. Yau dinma jikinta ne ya bata cewa asubah tayi, Siddiqah ta bude ido a hankali tana salati da mika. Ta fadawa kanta; “Kwana na farko a gidan Bayeraben miji na!”. Tun daren jiya ta yi wa kanta alkawarin bazata kara kuka ba, ta karbi auren Prince a matsayin kyakkyawar kaddararta. Ta amince babu nadama kuma babu kaico a cikin bin iyaye kowanne iri. A can dakinsa Prince Abdulrasheed shi ko baccin ma bai samu ba, yadda ya ga rana haka yaga dare. Bai samu mafita ta yadda zai mayar da Aisha Lagos ba, in yaso shi ya takura kansa ya dinga zuwa akai akai. Babu mai yarda da wannan shawarar tasa tsakanin Nenne da Dade don sun san bazai jure zuwan ba, su basa rabuwa da juna sai dole don haka suke so shima ya mayar da Siddiqah abokiyar rayuwarsa. Don haka ya qudurce raino zaiyi musu in sun gaji sun san nayi da ita don shi kalubalantar lafiyarsa ma yake yanzu akan mace. Da talatainin dare yace bari kawai ya gayawa Allah, yafi shi sanin yadda zaiyi da Siddiqah a cikin gidansa da rayuwarsa. Ya dauro alwallah yayi cikakkiyar nafila raka’a biyu ya roki Allah ya sassauta zuciyarsa akan tsanar da yayiwa mata, idan yarinyar nan alkhairi ce a gareshi, rayuwarsa da addininsa, ya roki Ubangiji ya bashi juriyar zama da ita, don maganar mayar da ita bata ma taso ba, ba idea bace karbabbiya wa iyayensa illa wadda zata tarwatsa zaman lafiyarsa da su. Don haka koda wasa ba zai yi ganaganci ko kuskuren mayar da ita Lagos nan kusa ba. Sai da yayi sallahr asubah da mintuna kusan talatin kafin ya samu barci, bai kuma farka ba sai wajejen karfe goma na safe. A sannan ne ya tuna da mace cikin gidansa, kuma bai bata breakfast ba. Don ko Pareto ya kawo bazai buga masa kofar ba sai ya tashi don kansa. Prince ko dabbobinsa da tsintsayensa baya so a bari da yunwar safe, balle Dawakansa, balle kuma mutum dan adam mai amsa sunan matarsa. “Ya salaam!” Prince ya furta a fili, a gurguje yayi wanka da brush, da riga da wando three quarter na barci a jikinsa ya fito zuwa kitchenette, yana tunanin me zai bata taci mai sauki kafin yayi order a kawo breakfast. In yaso zuwa yamma sai yasa Pareto yayo mata cefane ta dinga dafawa da kanta, in tanada ra'ayin hakan, don ya san mata bisa al'ada su suke girkin abinci da kansu, ko daga mahaifiyarsa wadda duk matsayin ta na sarauta, bata bari a yiwa iyalinta da ita kanta abinci bata saka hannu wajen girkawar ba. Kasancewar shi ba ma'abocin ajiye abinci bane. Yana saya ne a sanda yake da bukata kawai yaci ya tashi. Ko Pareto ya karbo ya kawo masa gida. Ya tuna cakes dinsa da baya rabo dashi a firinjinsa da choculate doughnut, sai ya jona ruwan zafi a butar dafa shayi ya hada duk wasu kayan shayi na kasaita akan tray, ya juye ruwan zafin a karamin tea flask ya hada cakes din da doughnut din waje daya, yana aikin yana gayawa kansa rayuwa mai juyi, yau shi Abdulrasheed (Kehinde) ne ya zama boyi-boyin mace. Siddiqa ta ko kasa hawa gadon dakin ta kwanta tun bayan idar da sallarta take zaune a inda tayi Salah din, kwarai take son yin magana da Ummanta da Nenne har da Dade da Firdausi, ta gaya musu tazo lafiya tana cikin kewarsu. Idanunta suka yi tarwai bata ko jin komawa irin barcin safennan da Prince ya samu don bata saba komawar ba, anan kan kilishi ta kishingida tana latsa wayar hannunta tana karanto azkar din safiya daga cikin (Muslim Muna Application). Sai taji alamun ana taba mata handle din kofa. Da sauri ta daga Ido ta dubi kofar, kasancewar ko kwan lantarkin dakin bata kashe ba, haka ta kwana cikin tsananin haske abinta. Prince ya murda kofar kadan, ya fara shigowa ya aje tea flask, kafin ya koma ya shigo da tray din hannunsa, ba tareda ya kalli inda take ba ya dora farantin kan centre table. Yana dagowa daga sunkuyon ajiyewa da yayi suka hada ido ta cikin hasken kwan fitilun da suka dallare dakin. Kwarjinin Prince da kamshin turarensa da ya cika dakin yasa Siddiqah bata iya ta amsa masa daga kwance ba, with respect ta tashi zaune daga kishingidarta, tana amsa sallamar da yayin. Irin dan durkuson su da Nenne ta koya mata na gaida maigida ko Uba tayi daga inda take zaune, tana ambatar kalmar gaisuwa da ake yawan amfani da ita a gidansu Nenne, har itama yau da gobe yasa ta tsinta wasu daga cikin kalmomin Yarbanci masu sauki ta rike wato tace dashi. “Ekaaro”. Don dai ita Hamma din, ko kusa bai yi mata kama da mai jin harshen Hausa ko fulatanci ba, kamannin sa basu nuna ya san kalmar “Zo” ba, ta san dai zai kasance daga native language sai kuma turancin nan nasa mai sarkakiya da yayi tayi mata jiya. Shima ya mayar mata, fuska babu walwala, sannan babu yabo ba fallasa. “Yaya gajiyar hanya? Thank you, and good morning”. Sannan yace mata “please manage this tea, (yi maleji da wannan shayin kafin a kawo karin kumallo)”. Ya juya ya fice ba tareda ya jira amsawarta ko ya dubeta ba. Har ransa tausayin Siddiqah yake ji. Aisha sai ta samu kanta da bin umarninsa, ta tashi ta shiga toilet ta kunna famfon wanka (shower), tayi wankanta fes da kalkale jiki da sabulu, kasancewar akwai sabulai na ruwa (bath gels) kala-kala a wurin wankan masu tsananin kumfa da dadin kamshi. Saida tayi wanka ta ji ta sakayau ta zauna shan tea din da ya aje mata. Ta ci cakes din sosai da dadin rai, kunnenta har motsi yake don dadin dandanonsa. Domin cake ne na musamman da Prince ke sawa bakery suyi masa mai dan yawa, sai ya aje a firji yana ci kadan kadan in baya son cin abinci mai nauyi. Zaka samu Sau tari yana cinsa da yamma haka yana korawa da ruwan gahwah mai zafi (hot coffee). In kuma da dare ne yafi shan chamomile ko lavender tea. Ta gayawa kanta bazata ke tambayar Prince ya koya mata amfani da wani abu a gidannan mai sha mata kai ba kada yaga kauyancin ta. Da kanta zata koyi amfani da komai ta hanyar amfani da basirar ta, na yadda zatayi surviving in this amazing and wonderful Ranch House. Wanda ya hada da budewa kanta kofar fahimtar amfani da komai na gidan, ko in ta samu ya hada mata wifi ta dinga tambayar google yafi mata sauki akan ta dinga yawan tambayar sa watarana yace mata 'yar kauye. Aisha saida ta tabbatar ta koshi, kafin ta zauna ta fidda kayanta daga cikin jakunkunan da ta zo dasu tana mayarwa tana jerawa a wardrove, zuwa lokacin in ka ganta kamar ba itace mai kuka face face da hawaye jiya ba, ta samu duk wata damuwa ta bar ranta. Self-confidence ya maye gurbin ta. Ta yanke hukuncin karbar kaddarar ta da hannu bibbiyu, na reality din rayuwar ta kenan, wato rayuwa da Bayeraben basaraken mijinta Hamma Abdulrasheed (Prince), wanda shi Allah ya ga damar su rayu tare. Iyayenta kuma suka ga dacewar shine mafi alkhairi a gareta akan Ishaq data qallafawa rai, shikuma ya wahaltawa soyayyarta da jiki da zuciya da aljihunsa. Bata so take tuna Ishaq ko kadan, (he's her past), Ishaq wanda basa taba haduwa su rabu batare da ya gaya mata adadin son da yake mata ba, ba tare da ya gaya mata muhimmancin da take dashi cikin rayuwarsa ba, ba tareda ya gaya mata tanadin soyayyar da yayi mata in sunyi aure ba. Kalaman Ishaq kadai da kulawarsa gareta ke sawa take dada ninkaya a sonsa kullum a wancan lokacin, har zuwa lokacin da Allah yaga damar raba su. Bata sanin lokacin da tunanin nasa yake sadadowa cikin kwanyarta ba, tana kwatanta shi da Prince. Sai taga ma kwatantawar bazata yiwu ba, domin ratar dake tsakanin comparison din auren ta da Prince da soyayyar ta da Ishaq mai yawa ce. Tunda Prince bashi yaje har inda take ya ganta yace yana son aurenta ba, ba da kwabonsa ko darinsa ya aurota ba, a'a auren gata aka yi masa da ita. Don haka kada ta tsammaci komai daga gareshi bayan cin darajar iyayensa a gunsa. Itama kuma bata saka aka ba. Babu komai a ranta game dashi banda girmansa da take gani saboda kwarjini da kamalarsa mai sawa taji shi kamar wani kanin Babanta. Duk da Siddiqah ta san bazata taba samun mai sonta a duniya kamar Ishaq ba. Prince ba ajin aurenta bane ai wutsiyar rakumi ne da tayi nesa da kasa. Wannan tunanin data soma in bata yakice shi ba yana son bata mata juriyar ta da yakanarta data riga ta kudurta na karbar kaddara, don haka da karfin tsiya ta yakice tunanin Ishaq ta jefar, ta cigaba da ninkewa da jera kayanta a wardrove din dakin ta jikin bango. Tana cikin fidda kayan ne ta ci karo da sakon Nenne da akayi packaging a leda da kyau, wani nau’in abincinsu ne wai shi WARA da Nenne ta ce mata na Hamma dinne, sai ta fitar ta ajiye gefe da kayan girkin da Nenne ta hadota dashida kwalaben turaren wuta masu daraja sosai. Aisha ta fiddo wata gogaggiyar atamfarta super Holland cikin dinkunan da Nenne tayi mata riga da zani da kallabinsu ta saka, ta yafa mayafin da ya shiga da atamfar wato orange kamar mai shirin fita unguwa, ta saka wani flat shoe dinta dan Italy da ya dace da mayafin jikinta, ta fito das-das da ita, tana taku a hankali zuwa sitting room din Abdulrasheed domin ta gaisheshi ta kuma bashi sakon Nenne. Tana fitowa kuwa ta hangi Prince din a zaune a dining yana karya kumallo. Ya daga manyan idanunsa yana kallonta tana takowa zuwa gareshi dauke da kunshin leda. Kallon da yake mata babu komai a cikinsa sai tausayinta. Aisha ta koma bashi tausayi na yadda da kuruciyarta aka aura mata tsoho kamarsa (in his forties), yaji sassauci sosai a ransa tun wayewar gari bayan da yayi addu’ar musamman akan lamarinta, da neman Allah ya bashi mafita, ta iya zama da ita ba tareda ya cuta mata cikin gidansa ba. Daga jiyan yaji a ransa bazai taba iya wulakantata bisa saninsa ba, tunda kuwa koba komai zabin Nenne da Dade ce. Da kuma darajar cewa iyayensa ne sukayi tattaki zuwa ga nata iyayen suka auro masa ita cikin mutumci da karamci. Don haka shigowarta rayuwarsa a lokacinda bai shirya ba duk ba laifinta bane tunda ba ita ta tsara hakan ba, iyayensu ne. Ya tabbata ko rantsuwa yai bazai kaffara ba itama fin karfin ta akayi da bazata yarda ta auri tsoho kamarsa ba sai yaro sabon jini dan uwanta. Don haka shima kallon Kiki yake mata zai taya su rainonta, ya ajiye musu ita tare dashi yadda sukeso har zuwa sanda suka ga ya kamata su karbi ajiyar tasu. Don shima yanzu yana tababar cikar lafiyar mazantaka a tare dashi, don bai ji komai akan Siddiqah ba wai don an ce matarsa ce, duk kyawun nan nata kuwa. Ga kugunta ya ciko kirjinta ya daidaita komai nata masha Allah irin yadda Yoruba Demons ke son ganin mace. Komai nata das, kamar ita ta zaba, amma hakan baisa yaji wani abu ya darsu a ransa gameda ita ba ko yaji yayi mata wani kallo bayan normal kallo irin wanda yake yiwa Kiki ba Ya aje mug cup din da yake sipping tea daga ciki, ya yima Aisha alama da hannu data zo inda yake ta zauna, ta karasa a hankali ta isa gareshi, russunawa tayi akan guiwarta irin yadda taga mahaifiyarsa nayi in zata baima Dade dinsa abu, ta mika masa kunshin sakon Nenne kamar yaro ya kawowa Ubansa aike. Yaji wani iri da wannan ladabin tsofaffin da take masa, kafin ya karba sai da ya tambayeta da turanci. “Menene a ciki?” “Sako ne daga Nenne”. Sai ya karba yana juyawa kafin ya fara kokarin budewa, sai kuma yace mata ta hau kujerar dake fuskantarsa ta zauna ta karya kumallo. Ba yau ta fara hawa (dining table) tare da mutane ba a gidan Nenne, don haka sai bata ji hakan a sabon abu ba, ta ja kujerar dake fuskantarsa ta zauna, duk da dai taji kamar tayi rashin kunya yana bisa tebir itama ta haye bisa tebir. Saita tuna Dade dinsa ma ana hawa bisa tebir din cin abincin iyalinsa aci tare dashi. Tun daga kamshin abinda ke ciki Prince ya gane cewa WARA ce, his very own Wara, tafiyayya tun daga Lagos din Nijeriya, Nennensa mai kula da abinda yakeso ta aiko masa. Warar ta soyu da kyau, murmushi ya subuce masa don rabonsa da cinta tun zuwansa gida. Ya kamata ayi warming dinta kafin yaci, but he can’t wait, a hakan ya dauko guda daya ya gutsura ya tauna, sai suka hada ido da AISHA SIDDIQAH. Aisha tayi saurin sunkuyar da kanta tana kokarin zuba ruwan zafi a kofi. “Ko kin iya cin WARA in sammaki?” Prince ya tambayeta da karamar murya kadan. "Naga kina satar kallona ina cin Wara, ko kin sanni?". A ranta tace “nikuwa na sanka. Labarinka buhu – buhu kwando - kwando gareni daga mahaifiyarka da ‘yar gaban goshinka, Kiki”. A fili kuma sai ta kada baki tace “ai bana iya cin Wara nikam, duk kuwa da cewa nasan da Nono ake sarrafata, bamu yinta a Gombe, da dai Awara da yaji ce, itane abincin Hausa Fulani”. Tayi maza ta kai hannu ta rufe bakinta bayan fitar furucin, domin sai bayan ta fada ne ta tuna Nenne ta haneta da wannan nuna kabilancin a zama dashi, haka Ummanta, domin koda Prince bai yi kama dasu ba, tofa ba’a canzawa tuwo sunansa na cewa shi din Bayerabe ne jikan Sarkin Yarbawa kuma. Prince yayi murmushi ya shafa lallausar gashin habarsa. Fatima ta taba gaya masa something like that wasu watanni can da suka gabata akan wata bakuwa ta Nenne data dauko daga Gombe mai nuna musu kabilanci, komai aka bata sai tace wai bata iya cin abincin yarbawa, baya raba dayan biyun wannan yarinyar dake gabansa ce, mai amsa sunan matarsa. Sai cewa yayi da ita cikin dage giransa sama “kin manta cewa Bayerabe din kika aura? A proud one! Dole ki koyi cin WARA, har wani lokacin ki zabi Wara ki bar Awara” Ya karasa da dan guntun murmushin motsawar sarauta. “Me zaki ci for lunch in bada order tun yanzu? Suna da Gbegiri ko Efo Riro with Iyan, ko Oka da Ewedu ko Eresi Eyin (Jollof rice with chicken)?” Dan cije siraran lebbanta Siddiqah tayi, duk bata ji tana sha'awar cin su ba yau, ko don tayo nesa da gida ne? Duk da babu wanda bata iya ci a ciki ba a Lagos, sun kuma taimaka mata sosai wajen cikowar jukinta musamman kugunta, ita yau tuwon Semo da miyar kuka take sha'awa. Prince ya zuba chips da plaintain akan faranti yana ci hade da boiled egg, a gefe ga kofin mug dinsa sa cike da tea mai zafi, bai yi aune ba sai kawai Siddiqa ta sako masa Atishawa duk da dai tayi kokarin karewa da hannunta. Itama kuma bata san da zuwanta ba, kwace mata tayi unexpectedly sakamakon sanyin AC dana kasar da suka hade suka cakude matawaje daya a hanci suke bugarta, wanda ga alamu shi baya ji sam, saboda sabo, shi ya kunna AC dinma da kansa. Tasa tissue kuma ta fyace hanci, bayan wucewar atishawar, saura kadan Prince ya saki kofin tangaran din dake hannunsa don bayason a face hanci ko atishawa a gabansa, kuma a take hakan yasa ya kware da abinda yake ci a makogaronsa. Ya dubeta cikin takaicin abinda tayi masa dinnan (atishawa da face hanci) yana dan tari irin na wanda ya kware, saida tarin ya lafa masa silently yace mata, “Go back to your room, please!”. Siddiqah ta dan russunar da ido cikin yanayi na rokon afuwa, tana fadin “kayi hakuri Uncle AK. Subucewa kawai tayi ba bazato na, please kayi hakuri!”. Ya mike ya dauki ledar Wararsa zai bar wurin yana cewa, “in dai ke kazama ce mai atishawa da fatar hanci anyhow bazamu shirya ba”. Murmushi Siddiqah tayi, bayan wucewarsa daga wurin, tasa a ranta ko kusa bazata dinga jin tsoron Hamma don yana takamar sarauta ba, zaman aure ne ya kawo ta ba zaman Oga da yaronsa ba. Ko yana nufin (as a human) shi baya Atishawa ne ko baya fyace hancinsa idan bukatar hakan ta kama? Da rana kuwa abinda ya ambata dazu su Iresi Iyan (Jollof rice with chicken) sai lafiyayyen Gbegiri soup da Eforiro su aka ajiye mata bisa dining, sai wankakkun kayan marmari a yayyanke da casserole, to su kadai ta iya ci ta bar masa sauran abincin. Siddiqah tana sallahr la'asar a dakinta Pareto ya shigo da kwandon kayan cefane da yayo, yana jera kowanne a muhallinsa, na firji wato su kifi da nama da kayan gwari ya saka a freezer ya fita. Bayan ta sallame sallahr tayi addu’a ta shafa, bata manta da rokon Allah ya cire mata shakkar Prince Kehinde ba, ko ta samu damar zama dashi cikin sukunin zuciya yadda iyayensa keso ta kasance tare dashi. Tana bukatar shiga WiFi dinsa bata san ina zata je ta same shi ta fada masa ya jona mata ba, ya shige masterbedroom dinsa ya rufe yana ramuwar barci, da bai samu yayi ba daren jiya saboda rudun zuwan Aisha da ya kwana a ciki. Shikuma barcin ba’a cin bashinsa a zauna lafiya. Ko motsinsa bata kara ji ba, tun bayan gama break fast dinsu. Ta mike da zummar taje kofar dakin nasa in yaso tayi masa sallama, ko tayi knocking ta gaya masa bukatarta na ya hada mata wayarta ko ta samu ta kira gida. Sai gashi ma ya fito da kansa cikin shirin fita shan iska, ya dau wanka iyakar dauka (casual wear) da yafi sawa a gida, riga da wando marasa nauyi masu saukin sakawa ne a jikinsa. Wadanda kullum suke taimakawa wajen zaftare adadin yawan shekarunsa. Kai tsaye inda take tsaye ya nufo, cikin takunsa na kasaita. Ya mika mata daya daga cikin wayoyin da yake amfani dasu. “Nenne ta min maganar in baki waya tun jiya domin ki rika kiransu kina gaisawa dasu". Hannu biyu Aisha tasa ta karba da jin dadi a fuskarta sosai sannan da girmamawa tace. “Nagode Uncle”. "Gashi bansan yadda ake amfani da ita ba ko zaka hada min tawa?" Hamma ya dan dakata yace "wannan din nayima Nenne alkawarin zan Baki. In kin bi komai a hankali zaki gane". Daga haka ya fice. Ficewa yayi kawai ba tareda ya bata amsa ba. Amma kwarai ta burgeshi domin bayan son mutum mai zurfin ciki da nuna iya abinda bai iya ba. Siddiqah bata ji gwiwarta tayi sanyi ba, wai don Prince bai tsaya ya koya mata operating wayar ba, ita kanta ta jinjinawa karfin halinta na yin doguwar magana dashi haka. Tana kuma addu’ar ta dore da karfin halin nata, don bata son tsoro da jin shakkarsa su zama su suke jagorantar mu’amalarsu itada shi, tunda yanzu mu'amala ta riga ta zama dole tsakaninsu. Yana fitowa Pareto ya far hangowa daga can nesa dashi yana yiwa Doki Saheeb wanka. Sai yayi tsayuwar da ya saba daga nesa yana kallonsu. Pareto ya kula dashi ya bar abinda yakeyi ya wanke hannunsa ya iso gareshi, don in yaga ubangidan nasa yayi irin wannan tsayuwar daga nesa yana kallonsa yasan magana yake so zai yi dashi. Sahib ya ankara da fitowar mamallakinsa nan da nan ya soma haniniya da zambarwa. Koda Pareto ya iso gareshi ce masa yayi. “Wancan sabon Criollo Horse din mai ciwon kafa an duba shi? Pareto ya amsa cike da girmamawa cewa tun jiya ya kira vetrenary doctor dinsu ya duba shi, kuma ya bashi magani tun a lokacin ya fara warewa. Pareto yana so ya tambayi ubangidansa ko matarsa ce wannan din ya auro daga Nigeria? Don dai bata yi masa kama da irin masu biyo shi har gida ba, haka bata yi kama da mutuniyar banza ba, ko ‘yan uwanshi mata dake zuwa wadanda duk ya sansu farin sani. Amma Prince kaman ya san haka, sai ya hade giran sama dana kasa ya daure fuska sosai, ta yadda babu fuskar ma da zai jefe shi da tambaya akan Siddiqar, don shi a wurin shi karshen abin kunya nema yace da Pareto wannnan ‘yar kankanuwar yarinyar da bata fice ‘yarsa Kiki ba; matarsa ce. Prince ya isa ga Saheeb yana masa gaisuwar yammaci irin yadda ya saba da yarbanci, ta hanyar yi masa hira cikin native yaren nasu, yana yi yana shafa kwantaccen gashin wuyansa, dokin yana haniniya yana zambarwa irin yadda ya saba in yana tareda Prince. Daya bayan daya yake duba lafiyar sauran dawakan dake cikin stable. Pareto na biye dashi a baya suna zaga tsakannin Dawakan suna maganarsu kadan-kadan cikin yaren kasar Argentina, ya gaya masa zai tafi kasar France yin Wani tournament kuma zai dauki akalla sati acan kafin ya dawo. Pareto da karambani da wuce gona da iri sai ya jefo masa tambayar data fado a ransa. “Boss, bakuwa fa? Yaushe zata tafi ko tare zaku wuce kasar France din?” Wata harara da Prince ya juyo ya zabgawa Pareto tasa ba shiri Pareto ya kai hannu ya rufe bakinsa yana bada hakuri. “Amma ka san abinda zai kai ni can tournament ne ko? Tukunnama meye business dinka da zaman bakuwa a gidannan? Ko akanka take zaune? Na yi maka zancen ka taimaka mata da wani abu ne? Kayo mata cefanen duk wani abu da zata bukata, final. Inma akwai abinda babu cikin kayan daka sayo tayi magana sai a karo". Pareto ya amsa a ladabce da "an gama Master". Ko ba’a ce ta fara girki ba ta yanke shawarar daga gobe zata fara dama. Don da daren ranar tazo cin abincin dare again ta ci karo da Ekele, Moi-Moi da Akara. Koda dai ta iya ci duka a Lagos, to fa tana ci ne ba don ra’ayi ba, sai don ta samu yayi mata maganin rama da cikowar kasusuwa. Amma a nan kam bazata ci ba sai dai yaci abinsu shikadai, abinda ranta yakeso zata dinga dafawa na kasar haihuwar ta. In yaso tunda Nenne ta koya mata yawancin girke-girken da Prince ke ci din kuma tayi mata guzurin kayan girkin duka, to zata fara gwada yiwa Uncle AK girki da kanta, ko don ta gwada kwarewarta a iya girkin yarbawa data samu gun Nenne. Washegari Siddiqah data fito kitchen cefanen da aka jibge mata kowanne a muhallinsa da wadanda ke cikin freezer ta fara zuwa tana duddubawa, ta sha mamaki da taga kusan duk abubuwan da aka sayo din kamar ta bada list, don yawanci ire-iren abincin da Hamma yake ci dinne aka kawo kayan dahuwarsu. Bata san cewa restaurant din da yake karbar abinci Pareto yaje ya karbi lissafin komai ya sayo mata ba. Ta maida komai inda ya dace ta canza daga yadda Pareto ya ajiye shi, tazo da guzurin spices dinsu na yarbawa da sauran kayan kara aroma din girki. Nenne har yajin borkono da tasan bata rabo da cinsa ta sa an daka mata ta hado dashi cikin kayan ta, sai ta dauko su duk tayi musu mazauni a ma'adanan kitchenette din. Daga nan Siddiqah ta zage ta hau girki. Tana yin abinta cikin dadin rai domin sosai take jin dadin aikin da take yi din. kafin awa daya ta kammala duk abinda tayi niyyar yi ta taimakon injinan saukaka girki. Ta ajiye masa nasa anan kan dining da yake zama yaci. Ta debi wanda zata iya ci ta shige dakinta ta rufe. Prince sai sakkowa yayi ya tadda breakfast mai rai da lafiya an shirya masa, plantain, chips, da moi-moi, sai kunun acca da yaji madara wanda shima Nenne ta koya mata. Bayan ya san ba abunda ya baiwa Pareto order kenan ba. Amma wannan din ya bashi sha'awa sosai don haka ya zauna da kyau ya soma ci. Har yaci ya gama bai san ita tayi ba, saidai tabbas yaji dandanon abincin ya canza a bakinsa, sannan kunun ya bashi mamaki, tunda bai taba odarsa anan ba. Nenne ce kawai take yi masa, kuma wani ikon Allah bai tambaya ba. Yaci yayi nak, with excitement ya mike, tana hangoshi daga bayan curtains din dakinta sanda yake cin abincin har ya gama ya fita jogging din safe cikin gidan gonar inda acan zaiyi excercise dinsa. Aisha da tayi wanka wajen karfe 10 na safe wata riga t-shirt mara nauyi da dogon siket baki ta saka ta haye gadonta ta dauki wayar da ya bata tana danne danne. Kamar yadda Prince yaki bata lokacinsa ya koya mata amfani da wayarsa ta yarda komai sai in baka sa kanka ba, amma yanayi (condition) na bukatuwarka da abin zai sa ka koya komai wahala ko rashin wahalarsa. Don kuwa a hankali tana bin umarnin wayar sai gashi ta gane yadda zata saka lamba tayi kira, da yadda zata yi chatting ta whatsp da sauran social media platforms. "Umman Siddiqa" wato Ummanta Haj. Zainab Yunus ita Siddiqah ta fara kira (with nostalgia). Haj Zainab ko da taga lambobi rankatakaf na kasar waje data kasa gane ko daga ina suke jikinta ya bata matafiya an sauka lafiya a kasar Argentina. Tun tafiyar Siddiqa take ta binta da addu'a tun komawarta Lagos daga sallamar da taje musu kan duk inda ta samu kanta a gidan aure Ubangiji ya zama gatanta, ya huwwace mata tausayin mijinta, tarbiyyarsu ta zame mata jagora. Tana dagawa din kuwa sai taji muryar Petel dinnata. Tana fadin “Ummana kina ina? Petel dinki nata kewar ganinki tun jiya. Na sauka lafiya a Argentina Ummana”. “Petel dina am miyelwa mi, kada ki damu da tunanin kowa, duk muna lafiya cikin alkhairi, aure neya gaji haka kinji ko Petel dina?” Kukan shagwaba ya zo. Aisha ta soma sheshsheko shi, Umma tayi maza tace “lala-lala Petel, in haka ne zan daina daga kiranki, Petel din Umma. Ko bangon duniya suka tura ki kije ki zauna da mijinki lafiya kinji Petel dina. Banda rashin karar nan taki da nasanki da shi da keke da kekenki, watarana ‘ya’yanki zasu yi miki fiyeda wannan biyayyar da kika yi mana in sha Allahu”. Da kyar ta samu Petel ta hadiye kukan shagwabar suka koma hira. Ta tambayeta ya ta samu bakon wurin da maigidan nata?” Siddiqah ta soma magana cikin tsananin gaskiyar dake ranta cikin fulatanci. "Uncle AK yanada kirki Umma. Kinga har wayarsa ya bani, don in sake in ji dadin zaman gidan, kuma in nayi masa magana yana amsawa. Amma Umma idan na tuna shi din bayerabe ne, duk kyawunnan nasa irin na Nenne, sai inji wani iri a raina….”. Bada niyyar labe Prince yazo dakin nata ba, yazo ne ya tambayeta koda abinda babu na cefane da shoppping yasa a karo mata saboda zai yi tafiya har ta tsayin sati daya. Sai kawai ya tsinkayi tana fadar hakan ga mahaifiyarta a waya cikin harshen fulatanci. Bai fasa shiga dakin ba yasa kai ya shigo da sallama, duk kunya ta kama Siddiqah. Umma na fadin. “Akul Petel, ko Allah hoddiri fe’an, be tagu fe’an (wato abinda Allah ya riga ya rubuta mata kenan wanda babu makawarsa). Zaman aure ba ruwanshi da kabilanci. Tayi maza ta kashe wayar cike da fargabar ko Uncle yaji me take gayawa mahaifiyarta akansa? Sai kuma ta cewa kanta ai ba lallai ya zama yanajin fulatanci ba yarbanci da turanci kawai ya ke ji. Da wannan Siddiqa ta karfafi kanta ta mike daga kwanciyar, ta boye wayar a kasan filonta duk guilt ya baibaye fuskarta. Hakika Prince yaji abinda take fadi din don shi yama fi jin fulatanci sosai har fiyeda harshen Yoruba, don dashi Nenne ke masa magana tun yana yaro har girmansa haka Nani Oummana. Har ransa yaji wani iri shima, kwatankwacin abinda kanwarsa Fatima ta gaya masa kenan akan Siddiqah wato har yanzu kabilancin nata da saura. Ba tareda ko a fuska ya nuna mata yaji ba, sai kawai yace, “Madam din gidan nazo in miki sallama, koda abinda kike bukata? Zan dan yi balaguro na wani lokaci". Siddiqah wadda ke ta fama da kayan guilt dinta, wanda ya kusa nutsar da ita cikin kasa don kunya kasa amsawa tayi. Nan dai ta hau 'yan mutsu mutsu na rashin sanin abin cewa, da ya ga ta kasa bashi amsa duk ta takura da guilt, sai yayi murmushi kawai ya juya ya fita abinsa. Kai tsaye dining ya nufa, ya zauna yana kokarin hada coffee, amma koda ya hada din ya kasa kaishi bakinsa sai juyawa yake da cokali a hankali. Tambayar kansa yake ko ta yaya zaman aure zai yi dadi tsakaninsa da Siddiqah tunda ita ga alkiblarta akan kabilarsa? Ya tambayi kansa yaushe ne za’a daina nunawa juna kabilanci tsakanin hausa Fulani da yorubawa ne? Yoruba da yawa da ya sani ko a cikin Akannis akwai wadanda basa cin abincin hausawa, da an ambaci bahaushen mutum kallon wani jaki, dakiki suke yi masa. Shikuma a matsayinsa na bilingual babu wanda zai ce ya fifita tsakanin wadannan kabilun, duka yana girmama kowanne saboda Nenne da kuma Dade dinsa da suka fito daga cikinsu, don haka Hausa/Fulani da Yoruba, basu da banbanci a wurin Prince. Sai ga Siddiqah ta fito falon kamar mara gaskiya. Prince don ta saki ranta da kansa ya ja mata kujera yace ta zauna. Zamanta keda wuya ya juya harshe zuwa fulatanci gangariya, yana tambayarta me zaya zuba mata cikin kalolin abinci na kasaita da yasa aka kawo wajen dake jere bisa tebir? Shikuma Prince abinda yaji ta fada ne yasa yake son tabbatar mata yana jin fulatanci fa, ba ita kadai ce bafullatana ba, yanaso dai ta sabawa ranta da kasancewar asalinsa Yoruba ne ba canji. Yanada kyau tasan cewa Bayerabe ta aura (a proud one)!”. Abinda tayiwa kanta alkawarin ta daina a gidan Hamma, wato kuka, shine ya dawo mata yanzu domin tasan tayi kuskure. Siddiqah sai ta kifa kai a saman tebur din daya raba tsakaninsu ta fara rera masa kuka babu gaira babu dalili, wani irin kuka na zallar shagwaba da ya nuna kuruciyarta a fili, kukan wanda yafi kamata a kirashi ‘na borin kunya’, a dalilin ganewa da tayi cewa Hamma Prince ya jita tsaf, a lokacin da take cewa tana jin wani iri a ranta da kasancewar sa ‘Bayerabe’ ga Ummanta mahaifiyarta. Shi kuma gani haka wato ganin guilt yayi mata yawa sai ya saki fuska sosai, daga dan dauretan da yayi, don baya son kukan mace a gabansa taba shi yakeyi sosai, Hamma ya koma magana cikin turanci, da dan murmushin bagararwa a fatar bakinsa, don ya kwantar da hankalinta. “Me akayi miki na kuka? Share hawayenki ki ai bakin alkalami ya riga ya bushe miki, ki shirya zama na har abada da Bayeraben miji, don wani abu muhimmi a al’adar gidanmu babu ‘sakin aure’. In akayi anyi kenan har abada, da so ko babu. Munada kishi mai tsanani akan iyalanmu, kishi irin mai lasting har gaban abada. The Akannis’ sun san ciwon matansu sosai. Bama taba auren mace mu hada irinmu da ita, daga baya mu barta wani ya aura. Ke ko ko bamu hada iri ba wato ko ba’a samu rabo a takani ba in dai mun aureta bama taba sakinta. A takaice sai ince miki Bayeraben mutum yafi bahaushe/bafullatani kishi da rukon aure da kyau. A wurin bahaushe ne kawai zaki ga ana saki da sake-saken aure anyhow. Nima biyayya na yiwa Dade na karbeki a gidannan as a Fulani girl, but I never planned it. Duk da ni bani da preference na matar aure daga kowacce kabila. But honestly what Hausa/fulanis are doing to Yoruba tribe is extremely bad. Islamically (a musulunce) mun san cewa Ubangiji yace “Inna akramakum indallahi Atqakum”, above all kuma kalmar shahada ta riga tayi binding us together. Then why the disgust? Idan aka duba ta fuskar kishin kasa ma, ya kamata a daina kabilanci gabadaya tsakanin kabilun Najeriya. Mu yarda cewa mu din duka WA-ZO-BIA ne. Idan muka yarda muka karbi hakan zamu zauna lafiya cikin girmama darajar kabilar juna". A cikin muryarsa akwai maturity na yawan shekaru, akwai amo (tone) mai nuna sanin ciwon kai, sannan at the same time a cikin muryar Prince din akwai lallashi, sabida kukan data soma yasa yaji tausayinta sosai. Domin ya fahimci kalar nata kabilancin kamar nature dinta ne, tanada kabilanci sosai da ya kasa boyuwa a ranta. “Ai kuwa in baki yimin shiru haka ba, ni kuma daga yau zan fara yi miki magana da Yarbanci kullum, har sai kin kware kin fini iyawa". Dan murmushi ya subucewa Siddiqa tasa bayan hannu ta share hawayen, taji dadin yadda bai dauki abin da zafi ba shi kamar Fatima. Kodayake dama hankalin namiji irin Hamma dana yarinya mace kamar Princess Fatima ai ba daya bane. Suna haka hankalinsa ya rabu biyu sakamakon ana ta kiransa a waya ya kasa dauka sabida Siddiqah taki daina matsar ido, mai kiran kuma bai fasa kira ba, da kyar ya daga wayar ya amsa sai yaga ashe Aunty Murjanatu-Taiwonsa ce. “Kehinde wai da gaske ne?” Abinda Aunty Taiwo ta fara tambayarsa kenan. Ya ce. “Menene fa?”. “Fatima ta gayamin su Dade sun turo maka yarinyar nan har Argentina?”. Yace “Exactly, gata nan ma a zaune a gefe na”. Taiwo kamar ta kundumo masa ashar shida wadda yace take kusa dashi din, sai ta tuna Dade da kansa aka ce ya tura ta, karewa ma shi yaje yasa ta a jirgin Argentina ta tafi ga Prince din. Taiwo ta rasa me ya samu iyayensu akan yarinyar nan. Duk girman Dade ace shi da kansa yaje ya saka ta a jirgi. Taiwo tayi shiru kamar zata yi kuka, can kuma tace. “Kehinde kuma ka yarda ta zauna a gidanka? Harda wani gata a gefenka, to uwar me take maka a gefen naka, wannan bakauyar yarinya haka? Kehinde kada kace min zaka iya kwanciyar aure da kucakar yarinyar nan?” Dariya sosai da kunya maganar Taiwo ta baiwa Prince Abdulrasheed. To in bai yarda ya karbeta a gidansa ba yaya zaiyi da ita? Bayan saida ta taso ma aka gaya masa ba shawarar sa ko amincewarsa aka nema ba? Prince yace da Taiwo “wace irin Magana kike haka? A matsayin Dade da Nenne garemu, kin ga ya kamata in sakota a jirgin da ya kawota ne in maido musu ita? Kigayamin tsakanin Dade da Nenne waye abokin sa'in'sa na?” Taiwo ta kasa magana na ‘yan dakikai, don ta san Kehinde ya fita gaskiya, amma in itace zata iya yin bore ta maidata din, saidai suyi hakuri su bi ra’ayinta, Kehinde yanada gudun zuciyar Dade da Nenne fiyeda kima shiyasa iyayen nasu ke samun damar takura masa. Ita da yake sun san halinta ba irin nasa bane wa yake shiga rayuwarta ko ace lallai ga abinda zata yi har a nemi tursasata alhalin tana cikin shekaru in her forties? Tsoron da take daya ne da zaman yarinyar nan kusa dashi a gida daya, tasan maza basu da hakuri akan sex, balle Kehinde da ya kusan fita shekarun kuruciya ba aure babu sabon Allah ta wannan fannin, tana da yaqinin cewa Kehinde baya neman mata a waje, duk yadda suke binsa kuwa as a celebrity, Taiwo tana cikin fargabar kada tsautsayi yasa Kehinde ya hada jiki da yarinyar bisa rashin kauda kai da matsuwa da rashin sanin darajar kai akan sex irinna maza, yaje haka kawai su yi masa surkullensu na Fulanin kauye da basu waye basu san komai ba sai kwadayi, don bazata yi jimilla a fulanin ba, su wadannan wato (Siddiqa da iyayenta) irinna kauye take kallon su, haka kawai taje a mallake mata dan uwa, don dai bata tashi taga bangaren su Nenne na surkulle ba, gashi kuma dai ance itama yarinyar daga Gombe ta fito. Kafin ayi haka Taiwo taji wani mikakken tsaki ya kwace daga bakinta, tace. “Kabi a sannu dai, wannan yarinyar kwatakwata ba ajinka bace Kehinde, class matters a lot in marriage, know how to relate with her don gaskiya da sake”. Ta kuma kashe wayarta cikin kunan rai. Kamar ita aka yiwa auren dolen, auren zubar da class ta bakinta. Yadda Prince ya dauki al’amarin da sauki, ba haka twin dinshi Taiwo ta daukeshi ba, gani kawai take an cutar da Kehinde dinta. Yau ba don tana tsoron iyayensu ba, ko kuwa da ace ba su suka auro masa Siddiqah da kansu ba, sai ta raba aurennan ko ta halin kaka. Dariya sosai Taiwo ta baiwa Prince da daukar dumar magaji da nishinta. Ya tambayi kansa dama ashe aure yanada class ne? Shi bai taba sanin haka ba. A saninsa Sarakuna har bayinsu da ‘ya’yan bayinsu suna aura suyi (sa-dakoki) dasu su haifi ‘ya’ya kuma tare dasu. Eh toh, ita Taiwo tana nufin yarinyar irin ‘ya’yan malam Shehu ce, tunda kuwa yaji ance yariyar ba ‘yar sarauta bace, ba kuma ‘yar masu arziki ba, irin wadanda ya kamata ya aura a matsayinsa na Prince of the Ilorin Emirate, amma a saninsa duk ba wannan ne ya hanashi aure tuntuni ba shi, tunda kuwa ta kowanne bangare tafi Haseenah da yayiwa hakikanin SO na soyayya akan radin kansa cikar martaba, asali, da kyakkywar nasaba. Ko babu komai ita duk sanda aka ga dama za'a je aga iyaye da danginta, koda basu da komai ya tabbata sunada asali, tunda har Nenne da kanta ta ga dacewar auro masa ita saboda kwadayin wata nagarta data gani a tareda mahaifiyarta. A kwana shidda kadai da zuwan Aisha tsarin kitchen da sitting room din Prince ya canza, komai ta maida shi yadda tafison ya kasance. Aisha ta canzawa kanta da kanta rayuwa a gidan Prince Abdulrasheed Kehinde. Kullum zaka sameta cikin tsafta da wanka da shiga mai kyau kuma ta mutunci. Taga cewa zaman me zata yi in bata motsa jikinta? Koda take son cikowa bata son irin kibar Fatima. Ta soma koyawa kanta gyaran sitting room din da kitchennette din, da kawar da duk abinda suka ci abinci ta wanke ta goge ta kife. Sannan ta fara sanyawa gidan turaren wuta masu tsananin dadin kamshi da Nenne ta hado mata. Ba'a jima ba ta gane yadda ake amfani da daukacin electronic appliances na gidan su dish washer, kunna dispenser, washing machine don wanke kayan ta data yi amfani dasu, ta hanyar karanta manuals dinsu. Cikin kwana na bakwai da zuwanta Aisha ta fahimci da yawan abubuwan amfanin gidan, ba tareda an koya mata ba, ta fara goge kauyancin data zo dashi kaso hamsin cikin dari, sai dan abinda ba’a rasa ba. Idan Aisha tayi girki ta kan tambayeshi idan ya fito ko zai ci? Sai yace yayi order. Don Prince ganin Aisha yake bazata iya wani girki da zai iya ci ba har guda nawa take? Siddiqah bata wai damu ba, sai ta dafa iya na cikinta ta kwashe a warmer tayi shigewarta daki da abinta. Prince ya zo Argentina ne domin ya huta, don haka zuwan Siddiqah na bagatatan dinnan baya ciki abubuwan da ya tsara a hutunnan nasa, don haka satin siddiqah biyu kenan amma abubuwa sunki yi masa normal, na farko ji yake tamkar a kansa take zaune tsabar ya kasa sabawa da zaman matar aure da motsinta a cikin gidansa. Duk da ita Siddiqah ba abinda ya dameta da Prince a cikin gidan, harkar gabanta kawai take yi tsakanin kitchen da falo da dakinta, sannan ta riga ta kirkirarwa kanta abubuwa na debe kewa da zasu lallasheta cikin wayar da Prince ya bata, social media plarforms ta sauke iri iri ba wanda bata shiga ta ga me duniya ke ciki, bayan girke girke da take yi wa kanta don ta burge kanta da kanta kullum. Yo ta burge kanta mana, sanin da tayi Prince bazai ci ba, musamman ganin komai na girkin available kuma a wadace yasa take dafa duk abinda ranta ya kwanta dashi. Daga baya idan ta girka ta kan ajiye bisa dining din da yake zama don cin abinci, ganin cewa da kudinsa ake yo cefanen koda bazai ci ba hakkinta ne ta bashi, musamman lokutan data ganshi a gida, ko in ta ganshi ya fito zai fita unguwa ko kuma ya dawo, sai kaji tana gaya masa cikin ladabi da sasanyan fulatancinta. “Ga abinci Hamma Abdul, ban sani ba ko zaka daure ka ci?” A irin wanna lokacin da Siddiqah ta kwantar da kai tana masa tayin abinci cikin kwantar da murya, jin kansa yake on top, irin yanda maigida ke ji a gidansa, ya ji shi a ransa yanzu ya cika mutum, amma sai yaji sarautar ta motsa ta hana shi amsa mata da dadin rai, sai kawai yace mata “na gode, I am okay”. Ya kan ki kallon inda abincin yake, ya wuce ga abinda ya fiddoshi daga dakinsa, don kiri-kiri Siddiqah tasa Prince ya ragewa kansa zaman (sitting room) dinsa, bata takurawa kanta sam a zaman gidansa wai saboda shi ko don sanin cewa yana cikin gidan, tuni ta roki Ubangiji ya cire mata tsoro da shakkar Hamma, da kwarjininsa dake sata bare-baren jiki tuni Allah ya ji rokonta ya yaye mata. A halin yanzu shine ma za’ace Siddiqah ta takurawa, don saidai in bazai zauna a sitting room din ba yayi ta zaman daki, ba abinda ke hanata bajewa a falon gidan ta kunna talbijin, bai taba ganin yarinya mara tsoro da shakkar idanunsa wadda kwarjinin sa bai sawa ta bar wuri irin Siddiqah ba. In kaga yadda take sakewa a kitchen din tana kai komo domin shirya abinda zata ci kamar ta shekara a gidan. Sau da yawa sai ta ta gama abinda zata yi na ranar ta shige bedroom dinta ta kwanta yake iya fitowa ya zauna a sitting room din don yayi kallon labaransu na (PoloLine TV), yana kallon yana shan Chamomile Tea, wanda shine ke sashi yin barci na nutsuwa a yawancin lokuta. Prince baya so ya zauna daga shi sai ita a falon, don sau tari kallon Siddiqah kadai idan yayi tausayi take bashi, (no any other strange feeling) bayan wannan, tausayinsa akan wannan aure da aka yi mata ne jaririya da ita da tsohon bachelor kamar shi. An kuma rabota da kasar haihuwarta da kowa nata, sannan shikuma gashi bai ko iya hira da bare ba, baren ma mace, yawanci in kaji hirarsa na fita tar-tar da Kiki ne ko Aunty Taiwo. Koyaushe Aisha na magana da iyayenta suna kara karfafata, da kuma mutanen gidansu Abdulrasheed su kuma suna kyautata mata. Princess Firdausi ta taba turo mata lambar Aunty Taiwo tace ya kamata ta kirata ta gaisheta don taji tana yiwa Nenne korafin Aisha bata taba gaisheta ba, ko a waya, kamar bata san matsayinta ga Kehinde ba. Amma Aisha ji tayi ko da wasa ta kasa kiran Aunty Taiwo. Tana kiran kowa na gidan musamman Dade, harda Princess Fatima kuwa mai amsa mata sama-sama. Amma har lokacin bata kira Kiki ba saboda alkawarin da ta yiwa kanta na ba dai Kiki taji maganar aurenta da Uncle dita daga bakinta ba in duk gidansu an rasa mai gaya mata to aje a hakan. Haduwarsu cikin gidan ma ita da Prince ba sosai bane tunda baya zaman falon, wani lokacin da safe in ya fito karya kumallo in ‘yan saukin kan na kusa yakan je har kofar dakinta ya kwankwasa yace ta fito su karya kumallo tare, ta kance daga cikin dakin ba taredata fito ba Hamma ya ci, ita ba yanzu ba, don tasan na order ne in ita tayi ta bashi baya ci ai sabida ya dauka bata iya ba ko yayane oho. Daga nan basa kara haduwa sai ko da daddare in zai yi dinner tana zaune a sitting room din tana latsa wayar hannunta ko kallon tv, nan ma su kan hadu, kan ba yadda Prince zai yi, saidai yaci abincinsa tana zaune don baya iya cewa ta tashi. Ta fahimci duk yammaci daga karfe hudu zuwa shidda na yamma wato bayan yayi sallar la’asar, Hamman nasu Fatima, yana kasancewa a ranch dinsa ne ya karasa wunin ranar tare da Dawakansa. Mu’amalarsu shi da Dawakan mai ban sha’awa ce, don sau tari takan hango su idan ta daga labule don samun danyar iska (fresh air). Musamman wani babban doki a cikin Dawakan da ta ji Hamma yana kira da suna SAHEEB. Sau da yawa ta kan jiyo basarakiyar muryar Prince idan yana magana da dokinsa Saheeb, ko in Pareto ya tadda shi a wurin suna maganar da ta shafi lafiyar dabbobin. Ana I gobe zai tafi France din da ya shirya tafiya suka wayi gari da bakuwa a gidan ba zato, “Kiki”. Tun kafin kamo hanyarta ta komawa makaranta, Kiki ta yanke shawarar bari ta tsaya gidan Uncle dinta tayi kwana biyu yadda ta saba tare dashi, sannan ta wuce makaranta, tayi kewar Kawun nata sosai. Da niyyar kwana biyu kacal Kiki ta tsaya wato zatayi Asabar da Lahadi in yaso Litinin ta karasa Los Angeles daga Argentina, tuni a hakan tayi booking flights dinta tun farko. Ko da ta sauka ma bata kira shi domin ya daukota ba, taxi ta biyo zuwa gidan nasa duk don tayi surprising dinsa. Pareto ya tabbatar mata Master na nan, kasancewar ya san matsayin Kiki a gidan yasa ya barta ta wuce kai tsaye zuwa kofar shiga sitting room. Kiki (Ruqayyat Toufeeq) taci gayunta kamar koyaushe, ta fito a Kikinta tsaf, ‘yar gatan Prince (Uncle AK) inji ta, tana tafe kwas-kwas-kwas akan tsinin takalminta, sanye cikin wata ruwan zumar kampala Yoruba Traditional Attire mai ratsin baki data sha dinkin bubu don Kiki kam masha Allah bul take, shiyasa da wuya kaga tayi dinki wanda zai kama jikinta, ko English wears da take yawan sakawa zaka ga cewa sakakku ne, Kiki tayi kyau har ta gaji duk da bata make-up, da ganin ta kaga ‘yar hutun budurwa mai cin lokacinta da zamaninta, bayarabiyar asali gaba da baya. Wani dan share-sharen gyale ne Kiki ta yafa iya kafadunta da ‘yammata ke yayi, (chantily) kalar kayan jikinta ruwan zuma, a kafarta wani siririn (golden heel shoe) ne mai tsinin dunduniya sosai a santala-santalan kafafunta. Kiki ta danna kararrawa mai sanar da zuwan bako (door-bell) a kofar shiga sitting room, tana cike da dokin ganin Uncle din nata. Aisha na zaune a sitting room tana kallon bakaken larabawan Sudan na wakarsu ta Sudanese, shi kuma Prince yana daga can cikin Master bedroom dinsa. Kiri-kiri shi da falonsa Aisha ta gaje ta hanashi zama, ta maida shi zaman daki dole, don baya so su zauna tare na lokaci mai tsaho a falo ko mai yasa? Shima ya rasa dalili. Ya dai danganta hakan da baya so su saba, ta shiga jikinsa. Dadin wakar larabawa da akeyi a TV dinne yasa bata yi saurin mikewa domin taje ta bude ba, ai tasan zai ji yazo ya bude tunda gidansa ne, karewa ma bin wakar take yi tana kada ‘yan yatsunta a hankali da juya dogon wuyanta don tana matukar son wakar da akeyi din. Mai kiran bai hakura ba haka ya cigaba da danna door-bell din a nitse, sannan da zaquwar son azo a bude. Dole Aisha ta mike ganin Hamma bashi da niyyar fitowa da kansa ya karbi aiken, ta isa kofar dakin nasa tana masa knocking, don tana zaton Pareto ne, taji sanda ya kira shi ta waya ya aikeshi ya samo masa chamomile tea. Daga ciki Hamma ya amsa da. “Yes, I am coming”. Kafin ya bude ya fito daga shi sai farar bodycon da dogon bakin wandon Jeans, Aisha ta sunkuyar da kai don ta kasa kallon sa da suttura a jikinsa, ga (8 pack) dinsa duk ya bayyana ta cikin (bodycon) din da ke jikinsa, kanta a kasa tace, “Hamma anata sallama a kofa tun dazu”. Prince yace “kuma ke baki iya bude kofar bane ko yaya?” Ya fada yana binta da idanu daga sama har kasa, ita kenan kullum cikin dogayen riguna abinta, kamar ita tasa aka kera jallabiyyas, bata yin wani abu (to make him attracted to her) tsakanin ta da Allah ba kallon miji take masa ba, kallon babban Yaya ne. Ko kuma wani young kanin Babanta haka. Prince a ’yan dakikannan saida ya gama karewa kyakkyawar surar jikinta da fuskarta dake sunkuye kallo, sannan ya sauke wani boyayyen numfashi, ya ce, “to naji, kije kisa kallabi mana, bana son ganin ki a gabansa kai a bude babu dankwali, ga Pareto ba hankali ya isheshi ba, duk da yasan kina gidan amma kullum yana faman yi min Pareti a gida”. Kalmar tashi ta karshe “Pareto na faman yi min Pareti a gida” taso ta bata dariya. Daga haka ya wuce Aisha a wurin, tana tambayar kanta ko meye gamin Hamma da daura kallabi a kanta? Ita batama san lokacin da kallabin ya zame akan kujerar da take kwance a kai ba. Kodayake ko ba komai daura kallabi abu ne mai kyau musamman ga matar aure a gaban wanda ba muharraminta ba. Kenan Hamma bai fada don wata manufa ba. Tana kallo ya isa ga kofar cikin takunsa na kasaita ya bude, don da gaske ya dauka Pareto ne ya dawo daga aiken da yayi masa. Sai kawai ya ga Kiki ba zato tsammanin sa, kamar daga sama. Lallai kuwa Kiki tayi surprising Uncle din yadda tayi fata. Don can na ganeshi rike da bakin mamaki, har fuskarshi hakan ya nuna, wato mamakin ganinta, at the same time, yaji dadin ganinta. Kiki ta yi tsalle zata rungumeshi yadda ta saba, ga mamakinsa yau sai ya kasa rungumar Kiki gabadaya a jikinsa yadda ya saba, ko ba don Aisha dake bayansa ba, don ji yai girma ya karu masa akan nasa, (girman aure da haibar dake cikinsa). Itama kuma Kiki sai bata damu ba ko don ta san ta girma yanzu? Duk da cewa niece din shi ce sannan al’adarsu ta Yoruba bata hana hakan ba, dan side hug ya dan yi mata a kafadunta sannan ya kama hannunta yarike cikin nasa. "Kiki? Kece da gaske? How comes kika zo ba sanarwa, meyasa baki gayamin kin taho ba, inje in dauko ki bayan saukar ki?" Kafin Kiki ta bashi amsa ya sake cewa "ki daina zuwa ba sanarwa, tunda kin san ba nikadai bane a gidan yanzu". Da mamaki Kiki ta ce "Kai da waye toh a gidan Uncle AK?". Sai kawai ya matsa ya bata hanya ta shige cikin sitting room din. Zakin muryar Kiki mai amo kamar na marokiya da taji kamar cikin mafarki yasa ta juyowa da sauri daga gaban talbijin, sai idanunta suka sauka cikin na Kiki-Ruqayyat. Kiki saura kadan ta koma baya da gudu, don kuwa ba karamin tsorata tayi da ganin Aisha a gidan Uncle dinta Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni ba. How dare she came here? Ta ina tabi tazo har Argentina kuma gidan Uncle dinta? To me tazo yi? Me ye gaminsu? Kodai-kodai Aisha aljana ce bata sani ba, tukunnama meye hadinta da Uncle AK da zata dawo gidansa da zama? Iyakar tsorata da shiga rudani Kiki ta shigesu ta kuma firgita, mamaki ya kusan kasheta daga tsaye, sai ta koma daga bayan Prince ta dan rike rigarshi ta baya, tana buya tana lekowa kadan. “Uncle AK boyeni, kawata Aisha-Siddiqah ce take yi min fatalwa a gidanka ba don ta mutu ba”. Watakila tun zuwan Aisha gidan Prince batayi dariyar data fiddo fararen hakoranta waje ba sai yau. Da kyar Prince ya zaqulo Kiki daga bayan sa yana cewa “bana son shirme Kiki, kina nufin baki santa ba ko yaya ne? Mutuwa tayi da zata yi miki fatalwan?” Da gudu Aisha ta taho ta janyo Kiki ta karfi daga bayan Uncle ta rungumeta. Kiki na kokarin zamewa tana dojewa tana cewa. “Ba wani hugging dina da zakiyi. Ba wannan a tsakaninmu yanzu. Nayi fushi, nayi fushi sosai Siddiqah. Ki gayamin kawai saboda Allah me kike boye min haka tuntuni?” Kiki ta juya ga Baban nata cikin rudewa tace “Uncle AK, ku fiddani duhu, I am perplexed, that means Aisha-Siddiqah is your wife since?” Prince rasa amsar da zai baiwa Kiki yayi, don sosai yaji nauyin ‘yar tasa ta yadda zai ce mata kawar tata da basu fice shekaru daya ba matarshi ce ta sunnah, ba wani (age gap) ma tsakaninta da Kiki. Duk da haka yayi mamaki da bata sani din ba. Sai kawai ya zuba hannayenshi a aljihu yana kallon Kiki tana murje ido wai dai ta tabbatar ba mafarki take yi ba, Hamma ya samu hannun kujera ya zauna, ya mika mata hannu yace. “Come on my darling daughter, zo ki zauna kusa da ni, ki gayamin yaya hanya? Uncle missed you for long!”. Kiki taki zama, ta soma kukan dadi daga tsaye, tana bubbuga kafa a kasa na shagwaba don zuwa yanzu duk da bai furta ba ta gama gane komai. Cewa Kiki take daga inda take tsaye cikin kukan da ya wuce da dariya, “wayyo ni Kiki! Wayyo ni Ruqayyat! Uncle AK kawai kace min kayi aure, ashe inada rabon ganin wannan ranar? For how long akayi toh da har ni ban sani ba??? Auren ma kuma da Aishata! Itace na dade ina yi maka sha’awa fah!” Ta koma Yarbanci ziryan tana fadin “God so kind, yau da wace kalma zan godewa Ubangijina? Uncle dina yau da matar aure a cikin gidansa a Ranch dinsa?” Sai ga hawayen farin ciki na gudu daga idanun Kiki-Ruqayyat. Siddiqah ta kamota tana tirjewa ta zaunar da ita a gefenta, sai Kiki ta matsa can nesa da ita tana zumburo baki. “Daga yanzu ai nasan irin zaman da kike dani Aisha, baki daukeni aminiya yadda na daukeki ba, tunda har kika iya rufeni a bai-bai irin haka. Ni me aka dauke ni? Hayagaga rariya uwar Magana ko? Ko kuwa Aku-Kuturu sarkin zance ko? Shi yasa baza’a gaya min wannan abin alherin ‘officially’ ba aka yi ta yawo da hakalina? Aisha abokin kuka ba’a boye masa mutuwa”. Kiki mita da korafi da kyasci kamar ta ari baki, nan dai Aisha duk ta karbi laifin ta shiga baiwa Kiki hakuri itama kamar ta ari baki, tace “ai ba ni ya dace in gaya miki ba Kiki, nima kunya nake ji, a inda ya kamata a gaya miki daban Kiki ba’a nan ba. Kiyi hakuri kada ki ga laifina, to me zan ce miki ni a lokacin da kika zo Lagos? Bayan ni kaina bansan matsayina a gidan Nenne lokacin ba? Ina dai zaune ne kawai tareda Nenne. Ban kuma taba ganin Baban naki ba ko a hoto, saboda Allah me kike tsammanin zan iya ce miki akai a lokacin banyi azrbabi ba?” Kiki ta yarda da kariyar da Siddiqah ta baiwa kanta. Amma tace da Uncle dinta daga yau itama ta saka shi a bakin littafi. Tace itama daga yau ta daina masa zancen Tosin, tunda shima ya boye mata soyayyarsa da matarsa kawarta Aisha. Kiki ta ce “daga yau Aisha kece Uncle dita, kece kuma Aunty na, nayi fushi na daina Uncle da Uncle AK!”. Kai yau Hamma yaga boni da rigima iri-iri daga Kiki. Sai murmushi yake kansa a sunkuye yana latsa wayar hannunsa. Da ya gaji da mita da korafinta ya dago kai a hankali ya dubeta da manyan idanunsa tamkar ruwa ya kwanta a cikinsu. Don duk korafinnan da mitar nan da Kiki take yi kan Hamma Prince yana duke akan wayarsa ko dagowa bai yi ya kale su ba, amma tsaf yake jinta. Yana kuma murmusawa tarin kuruciyarta. Muryar Aisha dake ta kare kai kuma tana masa dadin saurare. Da kyar yace. “Kiki kinsan Uncle dinki care for you koh? Ba abinda zan boye miki wanda yakamata ki sani. Na aza kin sani. Yanzu dai duk kiyi mana uzuri, nida Uwar taki, ni banida say! Sannan banida uzurin baki”. Kuma har zuciyarsa har ga Allah hakane, ya zata ta sani, da gaske bashi da say akan lamarinsa da Aisha, tunda shima rana daya kawai ya ganta a Argentina. Bai san ta ina zai fara gayawa Kiki hakan ba, shiyasa ya kashe maganar da cewa baida abin cewa. Haka dai suka samu suka yi ta lallabata, har suka samu ta daina kuka da korafin an boye mata din. Ta koma kallon Aisha da Hamma tana ta murmushin farin ciki. Aisha ta dauki kayan Kiki zuwa dakinta, don Uncle yace ma Kiki ga mukullin nata dakin ta share kamarbata ji shi ba, tana tafiya zuwa dakinta da kayan Kiki yace “ko baki ji bane Aisha?” Aisha tace ba tareda ta juyo ba “a’ah, nawa dakin zai ishemu, a dakinta Kiki zata sauka”. Sai ya rabu dasu kawai. Da suka shiga dakin Aisha, Kiki ta kama kugu tana kallon ko’ina na dakin, taga ba’a canza masa komai ba daga yadda ta san shi, dakinda Mamanta da Nenne ke sauka a gidan ne, yana nan yadda yake sai kace ba sabuwar amarya aka kawo ba. Aishah bata lura da me Kiki ke sakawa a ranta ba a lokacin, wato dole ma Uncle ya saka ma Aisha sabbin furniture, ta tambayi Kiki ko me take son ci ta dafa mata sharp-sharp? Ko itama order din za’a yo mata irin wanda ake yiwa Babanta kullum?” Kiki ta kama baki tace “ban gane ba? order kamar yaya? Kina nufin ba ke kike dafa masa abinci ba tun da kika zo?” Aisha ta girgiza kai tace “Kiki to meye abin mamaki a ciki? Watakila ya riga ya saba dana inda yake sawa wannan Pareto din yake ko wa ya karbo masa nan kusa da mu. Maiyuwuwa ko yafi jin dadin wanda ya riga ya saba dashi dinne, bai fi sau uku ya taba cin abincina ba shima sama-sama, ko na dafa tare dashi na masa tayi cewa yake min “ya gode, he is okay!”. Kiki tace “tab! Ke kuma kika kyale shi yana cin abincin restaurant alhalin kina cikin gidansa? To zaman me kike? Meye amfaninki? Ai kawai Aisha tashi mu shiga kitchen in ma baki iya Yoruba cuisines ba daga yau ki fara koyo, don kuwa Uncle maso abinci ne baya wasa da cikinsa. Kinsan yana Polo. Duk mai Polo kuwa na bukatar abinci mai fa’idah. Daga yau kada ki kara bari a shigo miki da abincin sayarwa gida, haba Sidddiqah kada kiyi saken da Uncle zai raina min ke. Ko kin iya ko baki iya ba haka zai daure ya dinga ci har hannun ki ya fada”. “Balle ma Kiki na iya fa, duk yawancin abubuwan da ake sayo masa dinnan ba wanda Nenne bata koyamin ba”. Kiki tace “wallahi to da sake, sai mun gyarawa Uncle zama”. Sosai ta baiwa Aisha dariya. Kiki ko hutawa bata yi ba, sallah kawai tayi ta aje mayafi tace da Aisha suje su shiryama Uncle abincin dare. Wani nau’in abincin Yarbawa Kikin ta ce su yi mai suna Ewa Agoyin, da ake yi da wake, tace tasan Uncle AK na matukar son shi tun yana yaro, musamman idan yaje Ilorin sai yace Aunty Murja tayi masa shi. Kiki ce karfin aikin don Aisha bata san yadda ake yin Ewa Agoyin din ba, ta bude ido sosai tana koyo, don Aisha is a fast learner, sannan suka dora ‘Ofada rice’ da zasu hada ‘Ewa Agoyin’ din da ita. Suna girkin Kiki ta gaya mata da niyyar yin kwana biyu ta zo Argentina, amma saboda ita yanzu kwana bakwai zata yi sannan ta wuce makarantarsu a Los Angels. Siddiqa don murna kamar ta yi yaya, da jin cewa Kika zata yi mata sati. Suka kammala girkin suka kai suka jera a dining, suka gyara wajen abin gwanin ban sha’awa duk kamshin spices ya turare gidan, lokacin Uncle ya fita, ba su ci nasu ba duk da suna jin yunwa. Kiki ta ce su jira shi komai dadewar da zai yi, ta ce. Ta dinga cin abinci tare da Uncle zai zame musu hanyar samun karin shakuwa da fahimtar juna don ta fahimci dukkansu wani baya – baya suke da juna. Suna nan zaune a ‘sitting room’ suna jiran dawowar Prince har karfe takwas na dare bai dawo ba, Kiki ta soma hamma saboda gajiya, sai sannan suka jiyo motsin shigowar motarsa gidan. Prince ya shigo rike da ledar take-away dinsa na abincin dare, ga ‘Ice-Cream’ a wata ledar daban ya riko ma Kiki don ya santa da son Ice-Cream. Aka ce albarkacin kaza kadangare kan sha ruwan kasko, sai ya kasa sayo daya, ya sayo musu duk su biyun, a sannu ya isa ga dining ya dora ledojin hannunsa da ya shigo dasu. Nan ya ga abincin da aka shirya a wurin cikin tsari mai ban sha’awa. Ga kamshin turaren wuta na tashi a falon ya hade da kamshin girkin nasu. Kiki da Aisha har suna hada baki wajen yi masa barka da zuwa. Ya amsa yana cewa Kiki su dauki ledar can ice-cream ne a ciki kada ya narke. Ya samu waje kusa da Kiki ya zauna cikin gajiya, yace a ransa dashi wani maigidana ne na hakika tausa zai so ayi masa. Dan murmushi ya subuce masa, yana dago kai ya ga Aisha na satar kallonsa, yayi bala’in kyau cikin ‘casual wears’ marassa nauyi ruwan toka dake jikinsa. Kayan sun maida shi yaro mai tashen talatin da biyar. Kiki ta karya kai tace, “your dinner is ready Uncle, Ewa Egoyin and Ofada rice, tuntuni kai muke jira kazo mu ci”. A hankali ya dubi Aisha jin ta ki magana ita, yace “Kiki kun min jagwalgwalo dai”. “Wallahi ba jagwalgwalo bane, try us, sai an gwada akan san na kwarai”. Ta fada tana serving kowannensu a faranti daban, sai ta hada nashi dana Aisha a plate daya, tace “Uncle wannan ma ai ba yi bane, kana da mata a gida kana shigo da takeaway, me ka dauke mu ne?” Dariya Kiki ta bashi sosai, sai kace irin manyan matan nan, a hankali Hamma ya ce mata. “BABIES!” Wato jarirai ya daukesu. Alhalin idon shi na kan Aisha, wadda ta sunkuyar da kai, duk ta kasa sukuni sabida yawan kallon da Uncle ke mata yau. Sanda suke su biyu a gidan hardly ya daga ido ya dubeta sau biyu. Yanzu kuwa ta hada ido dashi a duk dagowarta ya kai sau takwas. Zuwan Kiki yasa ya sake sosai a gidansa abinsa. “Babies dinka sun girma Uncle. Duk sun isa aure. Don Allah ka bari. Aisha tace daga yau kada ka kara sayo abinci bata so, bata yarda ba, kuma bata jin dadi, ka bata damarta ta uwargida ta dinga baka daga tukunyarta”. Prince ya yi kyar da manyan idon shi akan Aisha din, ya ce, “ita bata da baki kece bakinta ko? Ai na taho da takeaway dina, ku ci abincinku ku kyaleni tunda bata magana ita”. Kiki sai ta je ta dauke ledar abincin da yazo da ita ta kaita firinji ta jefa ta rufe, ta ce, a shagwabe. “Uncle bansanka da gwaliya ba, ta yaya Aisha za ta sha wahala ta yi maka abinci da kanta, amma ka barta da shi ka ci na siyarwa na kafirai da basa sallah? Waya sani ma ko sun saka maka naman alade?” Shi da kansa sai ya kasa bata amsa. Ya kuma ji kyamar abincin takeaway din ya kama shi. Amma shirun nan na Aisha ya dameshi. Don in ba Kiki a gidan ai har wakarta takeyi ta ‘yan Sudan tun daga dakinsa yana jiyowa. Kuma ta kan kula shin in ya fito, har tayi masa tayin abincinta wani lokacin duk da tasan cewa zai yi ya gode, amma yau daga barka da zuwa bata kara komai ba. Kiki ta ja musu kujeru uku a dining din ta ce, “Aisha taso mu yi dinner”. Aisha bata musa mata ba, ta taso daga bisa kujera ta dawo gefensa na dama. Kiki na gefen hagu. Suka saka Hamma a tsakiyarsu duk kunya ta kama Aisha, ganin ta hada kafada da Hamma. Kiki ta yi serving dinsu tare a plate daya, sannan tasa nata daban. Tace “bisimillah”. Aisha ta kasa ci saboda kunya sai faman juya cokali cikin miyar Ewa Agoyin take. Yau Uncle na ganin iya shege a wurin Kiki, don cewa tayi, “Aisha ko sai Uncle ya baki a baki ne?”. Aisha ta bude idanuwa da baki da hanci tana kallon Kiki, shi kuma Hamma yayi kamar bai ji su ba, yayi bisimillah ya fara cin abincinsa, yana cewa a ransa “Kiki shakiyyar duniya, zaiyi maganinta aure zaiyi mata”. Shi kansa Prince ya ji banbanci mai yawa tsakanin girkin da yake ci yau, dana African Cuisine dinsa. Abincin Aisha da yaci kadan a baya, da wannan da yake ci yanzu, dandanonsa yana yin arashi daidai dana girkin Nennensa. Bai san me ya sa yake ganin attributes din girkin Nenne a tare da girkin Aisha ba. Don hatta yadda Nenne ke yankan albasa slices haka Aisha take yi tsabar kwas da tayi na shiga kicin tareda Nenne. Aisha ta ci abinci yau plate daya da Hamma, duk hirar su shi da Kiki suke yi, kuma da harshen yarbanci, batasan meyasa shi yarbancinsa is cool ba, baya kama da fada-fada, a tsanake yake furta abunsa. Kiki tace ma Hamma akwai bukatar sabbin furniture a dakin Aisha, “haba Uncle AK! Amarya fa komai sabo dal ake saka mata”. Zuwa yanzu kam Aisha ta soma tsintar yaren yarbanci sosai fiyeda baya, in anayi ta kan ji, mayarwa ke bata wahala. Uncle ya baima Kiki amsar da ba sosai ta fahimta ba. Da suka kammala Hamma ya koma daki don yayi wanka, bai kara leko su ba kuma. Wajen karfe tara sun gama komai na shirin kwanciya, Kiki bata ga Aisha na shirin tafiya ‘master-bedroom’ din Prince ba, tayi wankanta tasa kayan barci sai ta jefa filo akan ‘sofa bed’. Kiki ta kasa shiru ta ce. “Aisha, ba dai anan zaki kwana ba?” Da mamaki mai yawa Aisha tace “da a ina nake kwana? Ai tunda nazo nan ne dakina”. Kiki ta kama baki, “me ya sa ba za ki tafi dakin Uncle ki kwana ba wai? Kina nufin ba daki daya ku ke kwana ba kenan? As in daban – daban ko yaya? To a wanne dalili kuke raba daki a matsayinku na sabbin aure?”. Aisha ta fiddo ido, ta ce, “Kaiii! In kwana a dakinsa fa ki ka ce Kiki? A’uzubillahi….!!! Subhanallahi!”. Kiki ta ce, “Me ye haka Aisha? Daga maganar gaskiya ki ke min korar shaidan?” Aisha ta ce, “Yo ai ni ji na yi kamar kin yi sabo. In kwana dakinsa fa kika ce, Hamma Abdul din? Ni don Allah kada ki kara fadin haka kada ma wani ya ji ki. Wallahi tunda na zo ni ko kofar dakinsa ban taba takawa ba. Ai sai ki sa ma na fara jin kunyar Uncle AK ina zaman zamana lafiya dashi”. Kiki ta ce, “Au da ba kya jin kunyar tasa? Ba mijinki ba ne ko ba soyayya ce tsakaninku ba?” Da sauri Siddiqa ta ce, “ba sai ana son mutum ake jin kunyarsa ba, ni wallahi kallon wani ‘Young Uncle’ dina nake masa, ko irin babban Yayana dinnan, ko kuwa ma, in miki mai gabadaya kamar kanin Babana nake kallonsa. Yadda dai ke diyarsa kike kallonsa, to nima haka nake kallonsa”. Kiki ta kasa rike takaicinta, ta harareta sama da kasa kamar manyan idanunta zasu fado kasa, tana cewa. “Lallai ma Aisha, wannan ‘Hot Uncle’ dinnawa ki ke yi wa RM? (Rashin mutunci) amma kina missing!”. Aisha ta kyalkyale da dariya tana nuna Kiki, “Look at you, wai Hot Uncle, Old Uncle dai, ba an ce 52 years Hamma yake nema ba? Ni kuwa baby girl dani sweet 18 malam, ai yadda ki ka dauke shi Babanki, haka ni ma na dauke shi Babana”. Kiki ta kule, ta ci magani sosai tana hararar Aisha. Ita kuma Aisha ta ci gaba da kyalkyala mata dariyar shakiyanci. ‘Yan tsokanar na Billiri sun motsa. Kiki ta ce. “Banda sharri kuma, Uncle 42 ne fa ba 52 ba, ke wai wannan Uncle din nawa yadda ya hadu ya hade kike ma shegantaka haka a gabana? Wallahi Aisha sai na naushe ki”. Kiki ta bi ta da gudu, Aisha ta falla a guje. Suka yi ta zagaye dakin kamar yaran goye, Aisha na cewa, “Wasa nake miki Kiki, kwantas ‘yar Uncle AK!”. Kiki ba ta fasa binta da gudu ba, tayi rantsuwa sai ta nausheta, sai Aisha ta kwasa a guje tayi hanyar waje don neman mafaka. Wato kofar da za ta fiddata ainahin sitting room din gidan. Tana bude kofar ba tare da ta lura ba don tsoron kada Kiki ta kamata, daidai za ta fita da gudu ta yi mugun karo da mutum. “Uncle AK in all his glory”. Sanye Hamma yake da ‘lounge wears’ da suka yi matukar fiddo zahirin surarsa ta ingarman basarake kuma namijin duniya in his forties, ga (8 pack) dinnan ta fito cikin bodycon din da ya saka, ya fito da niyyar magana da Kiki ne daganan ya wuce gun Saheeb ya jiyo tashin dariyarsu da karadinsu tun daga sitting room, kofarsu kuma a bude. Kawai ya samu kansa da tsayawa a bakin kofar yana kallon yarinta da kurucci zallahrsu, sunata guje-guje, yana kuma sauraron su kalma bayan kalma. Duk maganganunsu ya gama ji tsaf. Ya sa hannu ya taro Siddiqah don saura kadan ta yi mugun faduwa a gabansa, Kiki kuma na gab da kama ta. Da matsananciyar faduwar gaba Siddiqa ta dago suka yi ido hudu da Hamma Prince, gata kuma cikin hanunsa gabadayanta, ya samu kansa da kara riketa sosai saboda laushin jikinta, wai yau shine da mace cikin hannunsa! Wani irin kallo ya yi mata mai wuyar fassarawa, ya ce a hankali. “Old Uncle ko? Kuma Babanki dan 52 years kike aure ko Ayshah?” Ya cikata, ya juya ya wuce ya barsu a wurin yayi hanyar fita, wajen Saheeb ya tafi domin ya yi masa sai da safe. Aisha komawa ta yi kamar jikakken tsumma saboda mutuwar jiki, tayi tsaye jingine jikin kofa bayan wucewar Hamma. Kiki ko ta ce me zata yi ba dariyar Allah kasheni in huta ba? Ta dinga sheka mata dariya ta ce, “Ai gara da ya ji da kunnensa irin tsufan da kike kallonsa da shi”. Aisha ta dawo gefen Kiki ta zauna. Jikinta ya mutu, bata yi zaton Uncle na jinsu ba, don data ji shi shiru tun dazu ta dauka ya fita ko ya jima da yin barci, da ko kusa bazata fara wannan tabargazar ba, ita tsokanar Kiki take yi, ta kama hannun Kiki cikin sanyin murya tace. “Gaskiyar magana Kiki, auren nan namu fa babu wanda ya gaya miki me ya kunsa ne, don ba auren na-gani-ina so bane. Ba wata soyayya tsakanina da Babanki, sai ganin girmansa da nake yi saboda ya girmeni sosai, da albarkacin Nenne ce ta haife shi nake zaune gidannan, shikuma yake mutuntani saboda iyayensa sun karrama ni a idanunsa. Kin-ji kin-ji yadda komai ya wakana”. Nan ta shiga labarta wa Kiki komai, tun haduwar Ummanta da Nenne a Saudiyya. Har zuwa ranar da Dade ya sako ta a jirgi ta taho Argentina. “To kin gani Kiki ni da Uncle dinki duk biyayya muka yi ma iyaye shi ya sa tunda na zo nan I feel like Hamma kamar Yayana ne ko wani karamin Uncle dina nake tare da shi. No any other strange feeling bayan wannan”. Yanzu kam Kiki ta fahimta sosai, ta ce, “Amma Pretty, kin taba yin saurayin da ki ke so ko? Kina mi kama da wadda tayi rashin masoyin dake matukar sonta” Nan ma Aisha ta baiwa Kiki labarinta da Ishaq Hassan Nafada, daga A har Z, da irin rawar da ya taka a rayuwarta, rabuwar da suka yi ba tareda ko sallama ba bayan tafiyarsa NYSC a Ibadan, tace rabuwar kenan, har yau ba su kara ganin juna ba. Duka wannan ma a rashin saninsu a kunnen Prince Abdulrasheed, domin ya kasa nisa da dakin Aisha, bayan jin maganarta ta dazu, sai ya zama glued ga son jin me zata ce kuma, bayan data fahimci ya ji kallon Babanta take masa, don haka a jikin tagar dakin Aisha wadda kuma take a bude yake tsaye yana jiran isowar Pareto inda yake, domin su karasa su zaga cikin ‘Ranch’ don tabbatar da lafiyar Dawakan, don Pareto ya gaya masa a waya cewa Saheeb ba ya jin dadi. Shiyasa ma ya kasa kwanciya ba tare da ya zo ya duba lafiyarshi ba. Hasken fitilun lantarki na alfarma manya da kanana sun taimaka sun maida daren kamar tsakar rana a hamshakin ‘Ranch House’ din na Prince Abdurrasheed (Kehinde) Idris Akanni. Ga dukkan mamakin Abdurrasheed, sai ya ji ransa ya sosu matuka, yana kuma cigaba da sosuwa da wannan labarin da Aisha take baiwa Kiki a kan ‘Ex’ dinta Ishaq Nafada. A ransa ya ce, ashe ma tana tsaka a kogin soyayya da wani banza can aka tsigota ni aka ba ni? Saboda cewa nayi na rasa matar aure ko? Bayan an san bata da gurbin saka kowa a zuciyarta shine ni aka bani? Irin wannan soyayyar ta kuruciya wuyar mantawa ne da ita a zuciyar mace. Ga shi nan da aurensa ma kuma a gidansa take ci gaba da bada labarin tsohon saurayinta cikin bege mai tsanani. Abdurrasheed ya ji wani irin bacinrai na taso masa, kafin haushin kansa mai tsanani ya kama shi, ina ruwansa da yarinyar nan nema? Balle Ex BF dinta ya dame shi? Ya girgiza kai yana ce da kansa, to tun farkoma meye nasa na jin haushi don yayi musu laben da shi yasa kansa? Allah ma ai ya hana labe. A take Prince ya baima kansa amsa da cewa, ai ko babu komai shine mijinta a yanzu, akwai igiyar aurensa har ukku rus a kanta, wadda ko babu So, tabbas akwai ta. Aure kuma girman matsayinsa da martabarsa ya wuce duk yadda za’a kwatantashi. Darajarsa dole a jita a rai ko da So ko ba So. Ba wai don wani abu daban ba yaji haushin maganar saurayin Aisha sai don cewa shine mijinta yanzu short and simple. Kwarai kalmar nan ta Aisha “Babanta/Babban Yayanta/Uncle dinta” ta zafafe shi a rai. Wato shi ga shi tsoho ko? Irin sa’an Babanta dinnan, don haka yaro sabon jini can shi ta ke tunawa da bege da soyayya a matsayin daidai ita. To shi yanzu in ma ba ya fada da bakinsa ba wa zai ce shekarunsa 42? Yau da babu Kiki a gidannan sai Aisha ta farraqe banbancin aya da tsakuwa, don sai ta gaya masa da bakinta yaushe ya haifeta, don kawar da komai zaiyi a tsakaninsu na rashin sabo da rashin soyayya ya nemi hakkinsa na aure, ta hakanne zai nuna mata miji ko dogara sanda yake yi don tsufa sunansa miji ne ba “Uncle” ba a gun matarsa koda kuwa ace ita matar jaririya ce don yarinta. Isowar Pareto ne ya katse masa zazzafan tunanin, amma yaji dadin isowar tasa koba komai ya ceceshi daga sauraron Kiki da Aisha, don baya son cigaba da jin muryar Aisha, kasancewar ta jefashi a tunani da bacin rai, kuma tunaninta da Ex dinta zafi yake masa a rai, don bai saba da irinsa ba. Karfi da yaji maganganun Aisha da sanyin muryar tannan so suke yi su jefa shi a wani hali na jin radadin kishi wanda bai saba da shi ba. Da Pareto ya iso inda yake sai Prince ya taka ya wuce gaba. Pareto na binsa a baya, suka karasa stable din Saheeb, don abinda ya fito da shi cikin daren kenan, wato ya duba lafiyarsa sosai don shima ya tabbatar Dokin ya rage walwala a satinnan. Yace da Pareto dole da safe yayi gaggawar kiran Vetrenary Doctor din Saheeb ya bashi allura da magani. Daga nan ya rufe ko’ina na gidan ya kashe wutar falon ya sa kai zuwa dakin barcinsa, yana shiga ya maida kofa ya rufe kansa. Lokacin kusan karfe goma na dare. A dakinma Prince kasa barci yayi akan lokacin da ya saba, Aisha’s low tone voice mai nuna tayi rashin abinda bazata iya mayarwa ba wato soyayyarta da Ishaq Nafada, ya tsaya masa a rai. Bai so aka hado shi da wadda zuciyarta na tareda waninsa ba. Amma yanata sharewa da baiwa kansa tabbacin ba kishi bane ke damunsa, it’s just normal ai aure ne, tunda koma meye aurenta yake yi shiyasa yaji ba dadi, ya kuma ji tana zancen waninsa a gidansa ko wanene dole zuciyarsa ta motsa. Duk yadda Kiki ta yi kokarin wai Aisha ta tafi ‘master-bedroom’ din Hamma ta tayashi kwana, har tana gaya mata cewa ta dinga kokarin yi masa tausa da kanta zata samu lada, don ta ga da injin tausa yakewa kansa messege, dan Polo ne dole zai bukaci yawan tausa kullum, tace ta tafi don Allah ta samu ladansa ta bar mata dakin ita kadai, Aisha tayi fumfurus ta ki amincewa, ta ce, “Kiki ki rage karambani, da kaini inda Allah bai kai ni ba, ki bar mu yadda ki ka same mu kin ji ko malama, har gobe zamu cigaba da zamanmu ne irin wanda kika zo kika taras, a matsayin ‘Diya da Ubanta”. Sai Kiki ta kule, dama tana da saurin shaka, ta jefa pillow a kan gado ta haye can karshen gadon, ta ja duvet din bisa gadon ta rufe rabin jikinta ta juyawa Aisha baya, tana cewa. “Zauna nan wayiya, ki ci gaba da maida shi Baba, in kinso ma kice masa Kaka, har ranar da zai samo wadda za ta dauke shi Darling, duk girman nasa. A gefe guda kuma mala’ikun rahma sunata kwashe miki albarka!”. Aisha ta zaro ido tace, “Kiki!”. Kikin tace daga kwance, tana kara jan duvet ta rufe har saman kanta, “Yess, gaskiyar maganar kenan. Mala’iku nata tsine miki. Kina kwarar Babana Aisha me yayi miki? Baki duba shekarun da ya kwashe babu aure ba haba, yayi auren ma bada son ransa ba amma kina raba daki da shi ba wata kulawa ba tarairaya. Ina gani fa ko magana ba kya son yi masa shikuma duk ya damu da rashin kula shi da kike yi Am sure ba haka Nenne ta zata zaki yi ba”. Daga haka Kiki bata kara magana ba ta soma jan rago (minshari) ta bar Aisha a zaune dungurgur, tana tunani da jin ba dadin hakan a zuciyarta. Musamman data ambato Nenne. Ta kuma tuna amanar da Nennen ta bata akansa na ta yi kokari ta canza shi daga yadda ta same shi. Amma ba abinda zata iya a cikin abinda Kiki ke so tayi wato tafiya (master bedroom) da sunan ta biyo miji turaka. Ko wanda Nenne ke so tayi, wato ta dinga shiga rayuwarsa tana motsi, alhalin shi da yake namiji bai nemi faruwar hakan ba in one way or the other. “Kiki kuma sai in tafi uninvited? Walk before you run Dear. Komai dan a hankali ne, kuma komai da lokacinsa, amma ni bazan je ba tareda ya nemi zuwana ba”. Kiki da farko ta yi mata shiru, don minsharin karya take yi, tasan ta hada mata zafi, amma don Aisha ta san ta jita kulata ne bazata yi ba, sai ta kware bargon ta mike ta dauko wayarta a caji, ta kunna ta zauna gefen ta soma kiran layin Tosin AbdulNaseer, ta murguda baki tana cewa, “ni in ki ka kara kula ni Allah ya isa, tunda ba kya son Babana”. Kiki sai ta koma bata dariya rigimarta da giringidishinta Allah yayi yawa dasu, kamar ‘yar fari ba uata ba, ta kuma yarda kaunarta da Uncle dinnata mai girma ce don tsakaninta da Allah tayi Allah ya isan. Washegari da safe ma sun sha gardama ita da Kiki, don Kiki ta dage sai ta bi Uncle daki ta gaishe shi da safiya. Aisha ta ce, “Kiki ki bari sai ya fito (sitting room), ki fahimceni bana son wuce gona da iri, tukunnama kan ki zo kin san ya muke zaune da yanzu za ki bi ki dame ni a kan abinda bazan iya ba, ba kuma zai taba yiwuwa tsakaninmu ba?” Kiki ta shaka, ta yi kwafa ta kyale ta, ko girkin safe da Aisha ta fara Kiki wanka ta shige ta ki taya ta, ta ce tunda ba ta je ta gaida Babanta ba bazata kuma taya ta girki ba. Da misalin karfe goma na safe Prince Abdulrasheed ya fito (sitting raoom) din. Yana sanye da kayan barci farare sol. Daren yau ne zai tashi zuwa kasar France wasan tseren Doki na Concacap Polo Championship. Aisha ya hango a kitchennette ita kadai, tana kai da komowa, don kokarin hada musu karin kumallo. Motsin Uncle da kamshin turarensa ta ji a bayanta yana shigowa madafin. Da hanzari ta juyo sai ta ga Uncle ne cikin kayan barcinsa, da alama ko wankan safe bai kai ga yi ba. Aisha sai ta tsugunna ta gaishe shi, ya amsa a dake yana cewa, “Ina bakuwar taki ta barki da aiki ke kadai?” Aisha ta amsa da cewa, “Kiki ta shiga wanka”. Ya ce, “Yau zan yi tafiya zuwa tournament, zan yi akalla sati guda kafin na juyo. Kiki ta gaya min ta fasa tafiya gobe za ta zauna dake har sai na dawo. Sai ki kula da gidan, da komai, kada ki manta ban da zuwa wajen Horses don suna harbi da kafafunsu. Musamman Saheeb, ba ya so kowa ya je inda yake in ba ni ko Pareto ba, he is very Anti Social”. Kafin Aishata bashi amsa Kiki ta fito ta sha gayunta kamar koyaushe, ta tadda su suna maganar tafiyar tasa. Ta ce, “Uncle sai ka bamu kudi, kudi sosai fa, muna da activities masu yawa nida Pretty. Kama daga Shopping, zuwa su Hiking da Camel Riding. Tunda Aisha ta zo na tabbata ko sau daya ba ka fita da ita ta ga kasar nan ba”. “Ke ba sai ki fito da itan ba, uwar ‘yan kankanba da kilbibi, baki kamar na Aku-kuturu, halan ba’a gasa bakinki yayin omogwu ba?”. Kiki tasa dariya tace, “ka tambayi Maman Hakeem (Aunty Taiwo). Nidai kawai Uncle ka yi mana izini muna da wuraren zuwa mu mike kafa tunda baka nan”. Katin cirar kudinshi na daya daga cikin bankunan da yake ajiya ya ciro ya mika ma Kiki, ya ce, su sayi ko me suke so har ya dawo. Sannan zai bar masu mukullin mota daya Kiki ta kai su ‘tour round the city’. “Banda kai wa dare Kiki, kin ji na gaya miki”. Kiki ta amshi credit card din ta yi godiya, ta ce, “Insha Allahu Uncle ba za mu dinga yin dare ba”. Aisha dai tana gefe tana jera abincin da ta gama bisa tebir ba ta saka musu baki ba. Kiki ta ce, “Aisha ki yi mana godiya mana, an bamu dama mu je shopping, kuma in kai ki tour cikin gari”. Dan murmushin gefen baki Aisha ta yi ta ce, “Kiki ni ba abinda zan saya, sannan kuma bana son yawo, gajiya zan yi”. Kiki ta ce, “Ai da ma ban tambaye ki ko za ki sai wani abu ba, ni na san duk abin da ki ke bukata kuma ni zan dauko miki”. Hamma bai saurare su ba, ya ja kujerar dining daya ya zauna, yau ma a tsakiya suka saka shi, Aisha na dama Kiki na hagu, suka soma cin abincin. Bayan Kiki ta yi serving dinsu kamar jiya. Jefi-jefi Kiki da Uncle dinta na magana cikin yarbanci akan abin da ya shafe su. Maganar Kiki kullum guda daya ce, ‘yasa baki Maman Hakeem ta yarda Tosin ya iso gida, tunda dai shi da take kafa hujja da shi din yanzu ya kama Dahir”. Aisha ta kudire a ranta zata kara zagewa wajen koyon harshen yarbanci da gaske daga ranar yau, don ta lura Prince ba ya so ta ji ko me suke tattaunawa, shi ya sa ma ya koma magana cikin kasaitaccen yarbancinsa. Kiki ta ce, “Uncle AK da ban zo ba kenan haka za ka tafi ka bar Aisha a gidan nan ita kadai?” Prince ya harare ta, ya ce, “Kiki ke ce uban ne ko ni ne?” Dariya ta yi, Aishama saida ta murmusa, ta ce, “Amma dai Uncle amarya ba’a barinta ita kadai a gida, son samu a ce tafiyar nan France tare ku ka yi ta, (as in honeymoon a tsakiyar birnin masoya irin Paris) koh?”. Kunya ta nuna a fuskar Uban Kiki. Yayi maza yace “na gaya miki amma tournament za ni je ko? Kiki why are you disturbing me?” Kiki ta bar zancen don bata son bata masa rai, ta ce, “Shi ke nan Uncle, Allah ya kiyaye hanya. ‘yar ka zata kula maka da Aisharka har sai ka dawo!”. Prince ya tashi da daddare, Kiki ta tsara musu duk abubuwan da za su gudanar yadda za su mori satin sosai, kafin ya dawo. Tana so Aisha ta san gari, ta kuma daina bakunta da rashin sakewa a gidanta. Washegari suka shirya ko break fast ba su yi a gida ba, suka tafi shopping. Kiki ita ce mai diban kaya Aisha mai tarawa. Kiki ta daukar wa Aisha lingeries, English wears da nighties kala-kala data lura bata dasu, ta ce, “Daga yau bake ba kara saka atamfa a cikin gida, musamman in yana gidan, sai wadannan da na zabar miki in dai kinason zaman lafiya da ni”. Aisha tayi dariya tace “wasa kike yi Kiki, kema kinsan bazan iya ba”. Kiki tace “to ki ajiye ki boye, can gaba in kin yi kilin zasu yi miki amfani”. Sosai Kiki ta bata dariya. Suka koma bangaren kayan wanka ta daukar mata su feminine wash, deosprays da su body scrub, daga nan suka je ‘sight seeing’. Ba su dawo gida ba sai yamma lis. Haka washegari suka sake ficewa zuwa ganin Penguins, waterfalls da wajen Camel Riding. Ana saura kwana uku Prince zai dawo kiki ta kai ta aka yi mata SPA da Moroccan Hammam (wajen gyaran jiki na mata na Moroccan Hammam). Nan aka wanke Aisha tas, aka yi mata spa, body scrubing, pedicure da manicure, har da gyaran gashi, aka wanke gashin Aisha aka yi steaming dinsa, sai ga fatar Aisha har sheki ta ke yi abin gwanin ban sha’awa, dama ga ta fara tas, to sai ta koma pinkish, har wani jaja-jaja fatarta ke yi. Kiki da aka kammala gyaran Aisha ta saita camera ta kashe ta da kyawawan hotuna, kuma bada saninta ba kawai Kiki ta tura su wayar Uncle dinta, ta (whatsapp application) dinshi. Saura kwana biyu Prince ya dawo da yammaci suka ga wani guri ana YOGA. Don haka washegari tun da safe suka shirya suka tafi YOGA. A can suka wuni sur! Aisha ta ji dadin session din nasu a can, waje ne na motsa jikin mata zallah, sai yamma lis suka dawo gida. A YOGA ma sun yi hotuna masu kyau, kawai Kiki ta hau turawa babanta hotunan da suka dauka na charming lady dinsa AISHA-SIDDIQAH ba tare da Aisha ta sani ba. **** **** **** Prince yana reception na hotel din da ya sauka a kasar France yana hutawa kafin ya haura sama zuwa dakinsa, kawai sakon Kiki ya cimmasa. Yana budewa kyakkyawar surar ta bayyana kamar da an tabata jini zai yi tsartuwa. Gabadaya fatar jikin Aisha ta canza daga yadda ya santa. ‘Moroccan Hammam’ din da ta sha da SPA sun karbeta, gashin kanta ya sha steaming da gyara na musamman ya kwanta a dokin wuyanta, gashi bakikkirin da shi, sai sheki yake yi. Wani bala’in murmushi da ta sakarwa Kiki a hoton, sai daya kusa kashe idon Prince Abdulrasheed Kehinde. Bai taba yi mata kallon da har zai ga natural features dinta a fili ba, sai yau a hoton nan. He was dumb founded, domin bai taba ganin abu mai kyau irin Aisha-Siddiqah ba. Ga naivity ga innocence appearance dinta wadanda sune attributes dinta da ya fi so. Prince jinsa ya yi duk ya zama wani upset, a karshe ya kasa zaman reception din domin ji yake tamkar bafaranshan da ke bayanshi yana taya shi kallon hotunan matar tasa, sai kawai ya rufe ya tashi ya bar reception din, ya bi lift zuwa dakinsa. Kyawun wadannan hotunan ka kallesu daga kwance kuma bada alwallah ba. Kwanciya yayi rigingine a gadon hotel din ya dora kafa daya a kan daya, ya ci gaba da bankado hotunan nan na Aisha da Kiki ta antayo masa, yayi ta kallo yana admiring kowacce kankanuwar halittar da ke tare da matarsa “Aisha Siddiqah Yunus”. Alama ya gani na cewa Kiki ta saka sabon status, a kan whatsapps dinta. Yana budewa ya ci karo again da zafafan hotunan nasu da suka fi wadanda ta turo masa haduwa da nuna natural beauty din Aisha. Prince har da zooming iya fuskar Aisha, yana kara kare mata kallo, wani irin abu na motsawa a zuciyarsa da illahirin gangar jikinsa, kawai sai ya samu kansa da kiran Kiki a waya ransa a mugun bace, da wani abu mai kama da allura da nan take ya soki zuciyarsa, (KISHI). Ko mintuna biyar Kiki ba ta yi da dora status din nan ba ta ga kiran Uncle AK yana shigowa cikin wayarta kamar kiran kansa a fusace yake shiga wayarta. Da murnarta ta daga zata soma yi masa karadinta da korafi da mita na rashin kiransu akai-akai tun tafiyarsa, Hamma yace a fusace. “Kiki wait, ina so ki cire hotunan Aisha da ki ka dora a status yanzu, idan abokanki da samarinki maza suka gani fa? Ke ba ki san matar aure ba ce ne? Ko an ce miki daya kuke ke da ita?” Kiki ta hau danne dariya, don bata taba jin Uncle AK na fada haka har da tada jijiyar wuya ba sai yau, fada sosai yake yi kamar ya ari baki ya kara akan nasa, bai ma dace dashi ba tunda sparking irin wannan ba halinsa bane. “Na baki minti daya maza-maza ki sauke su duka”. Kiki ta ce cikin kokarin boye dariyar da ta taho mata. “Uncle I’am sorry zan sauke su yanzu”. Hamma ya koma da baya ya kwanta, ya kasa ajiye wayar ya ci gaba da kallon matarsa Aisha-Siddiqah, wani kallo na kurillah da bai taba yi mata ba sai yau. A zuciyarsa har tasbihi, yake domin Ubangiji ya yi halitta. Har gaya wa kansa yake wai wannan beautiful sweet 16 din matarsa ce, wane kyakkyawan aiki ya yi wa Ubangiji haka, da ya cancanci wannan kyautar da bai taba tsammanin samu ba?”. Komawa ya yi kan status din Kiki yana saving kowanne cikin wayarsa. Sai kuma ya ga Kiki na sauke wa din. Uncle ya kasa karashe sauran kwana biyunsa a France, a kwanansa na shidda ya canza booking. Gara ya koma gida haka, kafin Kiki ta koyawa Aisha bariki. Don yaga gabadaya ta canza masa mata, fatar jikinta da tsarin kwalliyarta duk ya canza. Ranar da Uncle zai dawo Argentina bai gaya musu ba, kuma ranar Kiki ta tuna ba su je ‘Hiking’ ba. Don haka ta kwashe su a motar Prince suka tafi Hiking (long walks na hawa duwatsu). Ranar daga Kiki har Aisha ‘sport wears’ suka saka na mata, cikin wasu kayan Kiki ne, shaf Kiki ta manta da gargadin Uncle na dawowa da wuri, kuma dai bata da masaniyar yau Uncle zai shigo Argentina ta aza sai jibi. Aisha da Kiki suka sha ‘sport wear’ abinsu riga da wando sakakku, suka zama tamkar tagwaye don kayan iri daya ne sai kala da ta bambanta, gasu tsaho daya, saidai kasancewar Kiki baka ce mai jiki, Aisha fara siririya maia mugun shape. Kodayake yanzu Aisha ba ta a layin siraran mata, tunda bazamu kirata mai kiba ba, haka ba za mu kira ta siririya ba, saboda samun diet na kabilar Yoruba mai kyau. Suna can suna ‘hiking’ Uncle AK ya dawo gidan tun azahar. Bai taddasu ba. Har zuwa la’asar shiru ba su dawo ba, kuma bai ga sun shirya masa wani abu da zai iya ci ba. gashi sun koya masa kyankyamin takeaway. Ya kuma ki kiran Kiki a waya don ya ga iya gudun ruwansu. Ashe dama dare suke kaiwa haka a gantalin nasu? Aisha dama bai taba gwada kiranta ba, tun tafiyarsa, sai dai ya ce da Kiki ta gaishe ta. Ya zauna a ‘sitting room’ ko kayan da ya dawo da su a jikinsa da ‘socks’ din kafarsa bai cire ba, don ba ya son ya tashi su shigo, so yake su shigo a kan idanunsa ya kare musu tanadi tas. Ashe lasisin gantali ya baiwa Kiki tayi da matarsa da ya bata mukullin mota shi bai sani ba? Bai zaci ko fitar da suke yi din suna wuce azahar din da yace musu ba, amma ga shi har magriba Kiki na waje da matar aure don rashin hankali da rashin mafadi. Wayarsa ya kunna yana amsa sakonni da kiraye-kiraye, don dai ya rage bacin ransu, nan ya jiyo dirin motar da ya tabbata su ne suka dawo gidan. A tare suka shigo sitting room din suna hirar wata zamowa da Aisha ta kusan yi daga kan dutse, ana dariya ana maida yadda aka yi, idon Aisha ne ya fara fadawa cikin na Uncle da ke zaune a three sitter, ya dora kafa daya kan daya rike da waya, yana kallon shigowarsu rai a matukar bace. Ransa ya kara baci da ganin kayan ‘sport wear’ din da ke jikin Aisha, duk da ta dora mini hijab, kuma kayan ba masu kama jiki sosai bane, amma sun fiddo kirar jiki da kugun Aisha sosai. Wani abu ya huda zuciyar Hamma Prince, wanda bana ko tantama kishi ne kamar yadda Kiki tace, amma sai yayi fadan nasa a jumlace, ya ce. “Kiki am? Uban wa ya ce ku saka wannan kayan ku fita? Kwatakwata kin manta da matar aure ki ke tare ko? Sannan kin san tun yaushe na dawo gidan nan ba ku dawo ba? alkawarin da kuka yi min kenan?” Fada sosai Hamma yake yi yau, fiyeda wanda yayi mata a waya kafin ya dawo. Yana fadan yana kallon Aisha ta gefen idonsa, wadda ta yi tsumu-tsumu, ta kuma rikice duk a lokaci guda. A nature dinta bata son fada ko daga waye, balle daga babban mutum irin Hamma. Kiki kuma ko a jikinta, sai faman rike dariya a cikinta take don fadan ma Uncle bai iya ba, bai yi masa kyau ba, musamman da bai saba ba, ta fahimci kawai dai kishin an fitar masa da mata titi da ‘sport wear’ ne ya birkita mata Babanta. Amma a zahiri shima a nasa idanun Prince yasan Aisha ba karamin kyau tayi ba, kamar a sace ta a gudu (looking takeaway). Hamma ya kasa danne zuciyar sa da fushinsa ganin sun masa shiru, ya sake kankance ido yana kallon Aisha. Wadda take jin idanun Hamma na zaneta tamkar saukar bulala a jikinta, da wannan kallon kankance ido da yake mata. “A irin hankalinki yakamata ku rika saka irin wadannan kayan ku fita ko, in Kiki bata da hankali sai ki biye mata? Kin manta matar aure ce ke Kuma Uwarta ce ba kawarta ba da zaki maida kanki kamarta. Duba agogo ki gayamin karfe nawa kuna waje don rashin mafadi da rashin sanin darajar aure ko Aisha?” Wannan karon kai tsaye da Aisha yake kuma ita ya jefawa tambayarsa. Aisha ta sunkuyar da kai, tayi tsumu-tsumu, idonta fal kwallah, karo na farko da taji Hamma ya ambaci sunanta kai tsaye. Kasa cigaba da tsayuwar ma tayi kada taje Baban Kiki ya hada da duka. Sum-sum-sum ta wuce dakinta, domin Uncle fada yake sosai, sai da ya surfe su tas. Sai da y agama ya zauna a kujera yana maida fushi Kiki ta ce, “Uncle kai fa da hannunka ka saya min wadannan kayan a wancan zuwan naka Ilorin, ka manta ne?” Shi da kansa sai da ya ji kunya, tabbas shi ya sayawa Kiki kayan, bai san ba ya so a saka din ba ya sayo mata sai da matarshi ta saka, Kiki da bai saba da yi mata fada akan sanya suttura ba itama wannan karon ta shaka, don shi da kansa ya sayo mata kayan ya kai mata har gidansu. Aisha ta shiga daki ta zumbulo katon hijabin sallarta ta fito ta wuce su a falon har yanzu suna wajen suna kaftawa ta wuce zuwa kitchenette don ta samar musu abin da za su ci, bata ga alamar ya ci komai ba sai fada, gashi daga tafiya ya dawo. Jikinta har bari yake da fadan Hamma. Kiki kuwa daga baya ganin da gaske yake ta daina boye dariyar ta koma sai hakuri ta ke bashi, duk da ranta ya sosu. Sai ga Aisha ta fito Hijabi yana binta yana jan kasa ta wuce ta gabansu zuwa kicin, Prince bai san sanda dariya ta kufce masa ba. Wai hausawa suka ce ta baya ta rago. Ita dai fatanta ya kyalesu haka da fadan nasa don har ga Allah ya kidimata. Itama Kiki dariya ta saka da ganin hijabin da Aisha ta zumbudo, don Hamma ya daina fada. Bayanta ya bi tana firar dankali tana share hawaye, because she hates to offend someone, balle babban mutum kamar Uncle AK. Daga bayanta ta ji motsin mutum da kamshin turaren Uncle AK, ba ta juyo ba ta ci gaba da fere dankalinta jikinta da hannunta yana rawa, space din da ke tsakaninsu bai fi taku biyu ba. Ya kuma fahimci hawaye Aisha ta ke yi kadan kadan saboda yadda fadansu ya rikitata. "bar firar nan, baiwa Kiki tayi, kiyi a hankali kada ki yanke". Inji Hamma. “Haba Aisha, am, ni ban ce ki je ki sako hijabi a cikin gidanki ba. Bayan kin gama nuna wa mazan waje abubuwan da ni kadai addinin musulunci ya yarda in gansu. Sai kuma ni a zo a zumbuda min hijabi me kenan akayi? Fita ce nace bai dace a yi da wadannan kayan ga matar aure ba. Amma ba a cikin gida ba. Ba ki ga yadda kayan suka yi miki kyau ba ne, looking ravishing!”. Da sauri Aisha ta juyo don ta tabbatar wa kanta Uncle ne yake wannan maganar a kunnenta? Kuma a tausashe? Shi ma kuma cikin borin kunya sai ya juya ya bar wurin don kamar subutar bakin ba-zata ne ya same shi. Ko da Prince ya koma dakinsa ya rasa me ya sa duk ya koma upset saboda Aisha, wani irin emotional ya tsinci kansa. Sai da ya nutsu ne ya gane kukan da ya sa Aisha ne ba komai ba ya birkita nutsuwarsa. Kiki kuma a daren ta hau hada kayanta, da ma a gobe ne za ta wuce makaranta. Ga haushin fadan da Uncle ya yi mata don kawai tana kokarin maida Aisha ‘yar gari, ta daina tsangwamar zaman kadaicinta. Ai dai yasan ba za ta kai Aisha inda za ta cutu ba ko a cutar masa da ita. Tana cikin hada kayan Aisha ta shigo dauke da tray din abinci da ta gama girka musu, bayan ta ajiye na Uncle a kan dining, express ne tayi musu chips ne da agada (plantain). Ta ajiye tray din a gaban Kiki, hankalinta duk ya tashi da ta fahimci Kiki tafiya za ta yi. “Amma Kiki ya kamata ko sati daya ne ki kara, kin ga ni ban saba da Hamma ba har gobe, zuwanki ne ya sa muka dan saba har muke cin abinci tare, ni in ki ka tafi ki ka bar ni daga ni sai shi takura zan yi”. Kiki ta harare ta tana cewa, “Aisha da sauranki, nikam ban iya zama daku alhalin kuna wannan rayuwar mara ma'ana, sannan taurin kaine dake bakya jin shawara, alhalin kuna matsayin ma'aurata amma kin kasa jan mijiki a jikinki. Sabida wauta da rashin wayo kin zauna Uncle ya maida ke hoto a gidansa ba matar gida ba. Na farko kin barshi yana kwana shi kadai a dakinsa, ke ya ware ki a nan kamar kanwarsa Fatima. Yana tafiya wata tournaments yana barinki gadin gidan gona, halan maigadi aka kawo masa daga Gomben? Dan night dressing din nan na gayu da gyaran gashinki yadda za ki bada kala ki dimauta uban nawa duk ba kya son yi, kullum sai uwar atamfa da leshi da jallabiyya a cikin gida, haba Aisha shi ya sa fa ‘Yoruba Demons’ ke raina matan Hausawa. Dazu kuma saboda Uncle na fada kika wani je kika sungumo hijabi kina asarar hawaye, in ni ce ke wallahi shigar da tafi ta farkon fitsara zan yi in kara fitowa in yi juyi a gabansa, in kada masa bombom, ke in makaleshi ma in masa kyakkyawar sumba, in yaso ya yi gunduwa-gunduwa da ni karewar fada. Don abin haushi har da wani kuka-kukan ki ke ga ki mai Uba ko? Na ce Babanki ne shi da za ki tsaya kina kuka don yana fada? Ko ni ‘yar sa kin ga na yi kuka? Haba mana kada ki bada Aishoshi. A sanina duk Aishoshi ba matsorata bane, ba wawaye bane. Duk inda na san Aisha na san mace ce mai karfin zuciya da kwatar kanta wurin miji ta hanyar kissa da iya kisisina. Sannan ta bada misali ga sauran mata saboda iya tarairayar miji, ta riga ta sha gaban mijinta duk shekaru da sarautarsa. Kada ki manta kannen Nana Aisha kuke. Wadda kankantar shekarunta basu hanata zamowa tauraruwa a idon Ma'aiki SAW ba, ke saboda kankantar shekarun nataa ne ma yasa yafi biye mata". Haka Kiki ta yi ta kwankwadawa kwakwalwar Aisha hudubarta, irin ta wayayyun ‘yammatan yarbawa. Wani abun ma in ta fada Aishar ta ke bari da jin kunya, wato sai ta barta da ji mata kunyar duniyancin da ta ke so Aishan ta koma yi wa Hamma, da cirewa kanta rauni da tsoro a zamanta da Prince Kahinde, musamman in yana fada. Ta ce, “Baban nan nawa sai kin yi da gaske Aisha, don zuma ne ga zaki ga harbi, sannan ya kwashe shekarun kuruciyarsa babu aure, yanzu da ya samu bazai rike shi da wasa ba kishinsa akan matarsa yanzu ya fara. Ki yi duk abin da ki ka san zai sayo miki martaba da kima da soyayya a idanunsa”. Aisha ta zumburo baki, ta ce, “Kiki, ni na ce miki ina son soyayya daga Babanki Hamma Abdul? Ai ki bar mu yadda ki ka zo ki ka same mu kawai, ba abinda zai iya canzawa a tsakaninmu don duk zaman biyayya muke yi ba neman canji muke ba”. Kiki ta ce, “Taurin kanki shi yake ba ni haushi dake, amma na tabbata Uncle ya fara kamuwa da sonki. Ko daga kishinki muraran da ya soma nunawa ba tare da ya san yana yi bama. Tunda nake Uncle bai taba yi min jan ido ba sai yau a kanki. Wanda ke nuna zuciyarsa ta fara sauyawa positively a kanki”. Aisha bata ce komai ba, rokon Kiki ta ke a kan ta kara kwanaki, Kiki na cewa lokacin komawa makarantarta ya yi. Zadai ta Kara kwana daya saboda gobe akwai wani surprise data keson yiwa Uncle AK. Tsabar fadan sa na yau yasa ya manta (tomorrow is his 43rd birthday). Washegari tunda safe Kiki ta soma shirye shiryenta a boye na shiryawa Hamma Candle Lit Dinner. Na farko ta bada order din birthday cake mai kyau da tsada ta kuma sa Chef a kusa dasu su shirya mata dinner na abinci da abin sha na alfarma, na iya mutum biyu zuwa uku, tun kafin karfe bakwai na magariba aka kawo mata komai. Ta sa Pareto ya kai mata karamin dining table na farar roba da kujerunsa zagaye dashi a wani bangare na korran ciyayi dake cikin Ranch din. Aisha na fitowa daga wanka Kiki ta zabo mata wata gown ta wani jan material da ratsin baki, budaddiya sosai daga kasa amma ta kama kirjinta sosai, cikin kayanta da tazo dasu daga Lagos, tace tayiwa Allah su zata saka yanzu, sannan ta zaunar da ita bisa stool din mudubi tanaso zata yi mata kwalliya. Kiki ta fara zizara mata sassanyar make-up, wato irin light make-up dinnan ba mai daukar ido ba. A isha dai tana kallon ikon Allah don Kiki bata gaya mata ko me take shiryawa ba. A can kuma Pareto ya gama shirya table din da kwalliya ta ban kaye bisa umarnin uwardakinsa Kiki-Ruqayyat. Ya shirya abincin da ya karbo order, ya aje katon cake a tsakiyar table din. A jikin cake din Kiki tasa an rubuta “Happy 43rd Birthday Uncle AK”. Kiki ta fara zuwa wajen ta tabbatar komai yayi yadda take so ya kuma tafi yadda ta tsara. Sai tasa Pareto ya kashe mata wutar harabar wajen gabadaya. Sai wata 'yar kankanuwar ‘dim light’ ya bari. Ta dawo daki tana cewa Aisha “Pretty biyo ni muje cikin Ranch, amma don Alah kada ki tambayeni komai”. “Kiki ho!” In ji Aisha, da alama dramomin Kiki ba masu karewa bane. Haka tabi bayan Kiki zuwa cikin gidan gonar. Kiki ta kama hannun Aisha ta zaunar da ita a kujera ta kuma karbe wayar Aisha ta rike don ma kada Aisha ta haska wajen da wayartata. Komawa tayi neman Uncle cikin gidan har dakinsa, acan ta samoshi idar da sallahr isha’insa kenan yaji knocking din Kiki. Saida ya kwashi mintuna kafin ya taso ya bude don yasan bazai wuce ita din ce ba. Casual wears dinsa ne a jikinsa kamar kullum wato shirt da dogon wandona Mark Jacobs. Harda farin karamin cazbaha a hannunsa. Yana bude kofar Kiki na kamo hannunsa. “Uncle don Allah biyo ni, amma kada ka tambayeni komai”. Inda sabo Prince ya saba da rigimar Kiki da dramarta kala-kala, haka ya yarda ya bi bayan Kiki zuwa bangaren data keso suje na gidan. Bai kuma tambayeta din ba har shima ta zaunar dashi a kusa da Aisha yana cewa, "me ya faru aka kashe wutar wajen nan haka? Ina Pareto?" Kiki tasa lighter tana kukkunna candles din cake din, sannan ta kunna fitilar wajen haske mai ni’ima ya wadata ya gauraye wajen. Kiki na dariya tana clapping hannayenta. Ta soma wakar. “Happy birthday Uncle AK!”. Sai lokacin duk suka fahimci me take nufi. Da abinda ta shirya. Wato sai lokacin ma Hamma ya tuna yaune zagayowar ranar haihuwarsa shekaru 43 a duniya. Excitement dinsa ya kasa boyuwa, domin ko ba komai Kiki ta bashi babban surprise din da ya sashi dariya, diyar nan tashi Ruqayyat tana matukar kaunarshi, ko bai haifi da ba a duniya ya godewaTaiwo data haifa masa Kiki. Kiki tana kula tana kuma sane da komai nasa, don shi ya manta ma. Duk da ba wai yana celebrating ranar haihuwarsa bane a baya a kowacce shekara, amma idan ranar ta zagayo, Nenne da Dade su kan kirashi suyi masa fatan alkhairi da addu’a, shikuma ya kan kara ninka sadaqarsa ga gidan marayu, a kowacce ranar birthday dinsa. To yau wayarsa tana kashe, domin ya baiwa kwakwalwarsa hutu. Ta cikin hasken candle lit din ya juya yana duban Aisha dake gefensa, sai ya ga ta koma masa tamkar furen fulawa don kyau. Kamar an kara wanketa an canza mata launin fata, sakamakon wannan sassanyar kwalliya mai tsari da Kiki tayi mata, serene make-up din ya amsheta sosai. At long last! Yau shi Abdulrasheed ya cika shekaru arba’in da uku tare da matar aure by his side (a gefensa). Auren da bai taba zaton yiwuwarsa gareshi a gidan duniya ba. Tabbas aure lokaci ne dashi ga kowanne dan adam, komin tsarin daka yi masa, idan lokacinsa ya zo daga Allah ko mutum yanaso ko baya so zai tabba dashi. Prince ya sakarwa Aisha kyakkyawan murmushinsa, wanda bai san lokacin da ya subuto masa daga zuciya zuwa fatar bakinsa ba, ganin itama kallon shi take yi yau da dukkan admiration na mace ga miji cikin idanunta. Ta kasa ce masa “happy birthday” din ita sabida kunya, amma a cikin zuciyarta ta fada ta kuma maimaita, har ta kara da cewa, “Allah ya karawa rayuwarka albarka the Great Prince of the Ilorin Emirate”. Kiki ta hau hure candles din dake bisa kan cake tana cewa. “Bari toh in huresu, a madadinka Uncle!”. Ta hure candles din duka. Tace sai Uncle AK ya yanka cake dinnan nasa da kansa. Nan ma dai Hamma dariya ce ta kama shi, da girmansa gemai-gemai za’a ce ya yanka cake! Yace Aisha ta yanka a madadinsa. “Lets the wife represents the husband”. Kunya ce sosai ta kama Aisha irin wadda bata taba ji ta Hamma Prince ba, a yau da ya dangantata da matarsa. A karshe sai Aisha da Kiki ne suka hada hannu suka yanka cake din tare. Aisha ta zaftaro katoto tayi bakin Kiki dashi, sai Kiki tayi kwana da hannun Aisha zuwa bakin Hamma Abdulrasheed (Prince). Ta kuma yi maza ta daukesu hoto. Aisha tayi dumu-dumu da bakin Hamma da cake. Daga Aisha har Prince kunya ce ta kamasu da wannan hoton da Kiki ta dauka don idonsa yana kan Aisha, babu irin wannan shaquwa da sakewar a tsakaninsu kafin zuwan Kiki. Don haka Kiki ta zama rahma ga auren ma’auratan nan. Kiki ta cigaba da waka a wurin tana musu hotuna tana wakar. “Happy Birthday Uncle Abdulrasheed Kehinde!”. Daga nan ta bubbude foil paper da aka rurrufe abincin dashi, ta zauna itama tana fuskantarsu suka soma cin dinner din tare. Suna ci suna hira gwani ban sha’awa, Kiki nata basu dariya da hirarrakinta na wauta, suna gamawa Prince ya kunna wayarsa ya zagayo hannunsa ta gaban Siddiqah, yace da Aisha, “dan matso nan Siddiqah muyi selfie nida ke, cikin wayata saboda tarihi!”. Ba karamar kunya ce ta lullube Aisha ba, lokacin da Hamma ya kashe kyawawan fuskokinsu shi da Aisha da flash din dalleliyar camarar wayarsa Idan da Kiki zata yi duba da duk abubuwan da ke faruwa yau, da wadanda suka faru tun zuwanta, sai ta godewa Allah, domin kuwa ta samu ladan wadannan ma’auratan. Zuwanta yayi riba. Tayi silar abubuwa na farin ciki da yawa a gare su, da cigaba cikin irin zaman da ta tarar suna yi. Don kafin zuwanta wani irin zama suke yi kamar na ‘jahiliyya period’. Don yafi gaban a kira shi na doya da manja don baza’a kira shi zaman aure ba. don kuwa alhakin juna suke dauka. Zuwan Kiki ya haska gidan. Ya hurawa zukatan ma’auratan ruhi. Sai mu ce madallah da Kiki-Ruqayyat, madallah da zuwanta gidan a wannan lokacin. Kiki zamewa tayi ta bar su a wurin da cewa zata je ta dawo. Ganin Prince duk hankalinsa na kan Aisha. Yau Prince da Aisha ne zaune dab da juna, har ya samu kansa da janta da hira. “Siddiqah bani labarinki mana? Tunda kikazo kin kunshe min baki, bansan kina walwala haka ba sai bayan kawarki tazo ko?” Aisha ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran ‘yan yatsunta tace “Uncle me kake son sani a kaina?” A takaice Prince ya ce da ita. “Komai! Tun daga labarin iyayenki, ‘yan gidanku, samarinki, kawayenki da makarantar ku. Yadda kika tsinci kanki a auren Bayerabe alhalin kina bafullatana mai kin yarbawa da sauransu. Kin ga ni na tabbata kinsan komai a kaina a gidanmu, amma ni har yau bansan da wa nake zaune ba, banda cewa ina tare da matar aure na kawai”. Aisha ta rufe fuska da zara-zaran yatsunta tana cewa cikin murmushi. “Hamma Abdul, banida labari ne ni, gidan mu ba kanne ba yayye, nikadai ce ‘ya a gidanmu. Nice yar kaina nice kanwar kaina. Samari kuma bana sauraron kowa sai Ishaq Nafada. Kawayena na makaranta kuwa sunada yawa, babbar aminiyata a cikinsu Amintako ce, sai Ramatu da Ruma, don ni dinnan da kake ganina shiru-shiru a gidan ka ‘gang leader’ ce dake shugabantar fitinannun yara a makaranta. Sunan makarantarmu FGC Billiri Gombe. Yadda nayi na samu kaina da auren bayeraben miji bazan iya cewa ba, illah ince wata addu’a ce ta Ummanka ta filin Arfah, ta fado a kaina ni Siddiqah, kamar yadda Ummata ta bani labari nima”. Prince ya soma dariya kamar bashi ba, bai zaci Aisha haka take da baki ba, yace “wato Nenne addu’a tayi akaina, sai ta fado a kanki ko Aishahh?” Ta sake rufe fuska tana dariya ta ce “exactly, sosai kuwa, wata irin zazzafar addu’a tayi a inda Allah baya juyarda addu’a, don Ummana ta ce da ta ji Nenne tana addu’ar nan a lokacin, a take a zuciyarta tace inama zata ganshi ko waye shi ta bashi PETEL dinta! Sai Allah yayi ta tsara abubuwan daki-daki yadda ya ga dama, suka yi ta faruwa subsequently (wani na bin wani). A rayuwata ban taba jin wani abu mai kyau game da kabilar Yarbawa ba, sai bayan da Nenne ta dauke ni zuwa gidanku a birnin Ikko. A nan ne Yarbawa iri-iri suka goge min hadda, tun daga kan ma’aikata da masu girkin gidan, na fahimci cewa Yoruba kabila ce mai matukar daraja a Nigeria, kamar Hausa/Fulani. Dana zo Argentina na tadda Prince of the Ilorin Emirate, sai ya karasa wanke duk wata negative hadda dake cikin kaina akan Yarbawa, don na gane cewa Prince din Bayerabene na gaske, mai alfahari da kabilarsa. Da bakinsa ma ya fada min; he’s a proud Yoruba man. Don haka ni yanzu duk inda naga Yarbawa tsakanina dasu girmamawa ce da karya hula, sanadin kaunata dasu”. Prince ya lumshe ido cikin murmushi, kowacce kalma dake fita daga bakianaata tana masa dadi, ya budesu a kanta yana cewa. “Aisha frank kenan! Naji wannan, na kuma taya yarbawa bakidayansu murna da kika cire musu kabilanci daga dictionary dinki. Bayan wannan zan so in san wane irin so kike yiwa Ishaq? Ina nufin yaya kike jinsa a ranki kafin auren ki da Bayerabe da yanzu bayan auren?” Aisha ta hau ‘yar dariya tana cewa. “Uncle me yasa ka tambayeni wannan? Babu kyau binciken abinda yaa riga ya wuce”. Kai tsaye Hamma ya saka idonsa cikin na Aisha ya dan budesu cikin nata. yace “because I am extremely jealous of him!”. Aisha ta sunkuyar da kai tana jin wani irin dadi a zuciyarta, amma tana so ta baiwa Prince wannan amsar koda zai ji babu dadi. Ba don ta goge kishin da yace yana yi akan Ishaq ba, sai don ita ‘yar keke da keke ce tun asalinta, bata da rufa-rufa (frank). “Ina son shi sabida he is caring. Kullum muke tare sai ya gaya min how much he cares and loves me. Baya gajiya da gayamin muhimmancina cikin rayuwarsa duk da kankantar shekaruna. Na taso na san shi a matsayin fiancé dina shikadai na saba da shi na kuma shaku da shi. Rana daya aka ce an bada ni ga waninsa kuma Bayerabe da ban ko taba gani ba. Ka gayamin in kaine ni yaya zaka yi? Ai dole ka yi dan protest ko? Musamman daka gane cewa shi wannan da aka mallakaka gareshi din bai ma san da kai ba, bai damu da kai ba, bai san kana existing ba, kuma baka cikin lissafinsa a rayuwa”. Hawaye suka digo mata tace “it’s not easy, ina gaya maka Hamma, it’s not easy, don ma na roki Allah juriyane, da danganar karbar rayuwa a duk yadda ta riske ni”. Amma bayan nan ina dadewa ban tuna Ishaq ba, na yarda “he is my past, I don’t have a present”. Ba don komai nace haka ba Uncle sai don kasancewar Uncle AK da aka aurar dani gareshi rana daya bana cikin lissafinsa. Ya karbeni a gidansa ne kawai kan ba yadda zaiyi da umarnin mahaifinsa”. Hamma yace cikin karfafawa. “Prince Abdulrasheed yanada past mara dadi akan mata, kin zo rayuwarsa a lokacin da ya tsani mata, bashi da sauran hope akansu. Amma duk da haka Prince zai yi kokari ya komar da hannun agogo baya, wato ya yi kokarin manta past dinsa, ya karbeki a gidansa da rayuwarsa a matsayin present dinsa, don radin kansa ba don tursasawar iyayensa ba, hakan zai faru ne only ranar da kika daina yi masa kallon BABANKI!” Da sauri Aisha ta rufe ido da tafukanta cikin jin kunya daidai lokacin da Kiki ke tahowa garesu. Tana karasowa tace “Uncle AK zan dauki Uwata haka, lokacin barcinmu yayi, in ya so ka kawo kayan zance sai in barka zuwa tadi!” Hamma ya zaro ido yace “Kiki, kina maida ni Kakanki koh? Zan yi maganinki aure zan yi miki soon”. Koda suka koma cikin sitting room Aisha da Kiki kallo suka kunna a falon, suna kallon girke-girke a Netflix. Hamma dakinsa ya wuce cikin wani yanayi. Domin maganganun Aisha bakidaya na yau sun zame masa food for thought. Ya kasa barci a daren nan ya samu kansa da kallon selfie dinsu shi na birthday shida Aisha, da tuna hirarrakin da suka gudana a tsakaninsu. A daren yau Prince yayi abinda bai taba yi ba, wato yin rubutu a shafukansa na social media. Domin bayan ya kasa daina kallon selfie din, sai ya budo status dinsa na whatsapp, yayi wani rubutu mai matukar jan hankali da shikadai yasan ma’anar kayansa, a kasan hotonsu shi da Aisha, bayan yayi covering fuskar Aisha, amma gangar jikinta ta fita gaban candle lit cake. “Happenings at 43rd Birthday ….. !!! The wife that is slowly becoming the centre of my universe”. **** **** **** Wani ikon Allah Taiwo ce ta fara ganin status din brothernta. Ta sha mamaki ganin yau Kehinde ya dora status don baya yi sam. Don haka da doki da zaquwa ta bude don taga me Kehinde zai daura? Ta kuwa ci karo da wannan magana da hotonsa shida Aisha, da suka yi matukar daure mata kai. Me Kehinde ke nufi? Ya folawa wannan yarinyar ko yaya ne? Nan take tayi screenshot cike da takaici da tsegumi ta turawa Haseenah. Washegarin ranar Kiki tayi musu sallama ta wuce makaranta bayan Kawun nata ya cikata da duk abinda zata bukata, har ma da wanda yafi karfin bukatunta. Bayan wucewar Kiki Aisha duk ta canza wa rayuwar gidan, dan fitowa falo da take yi duk ta daina. Aisha ta maida kanta daddawar daka, gabadaya walwalar nan da ta ke yi sanda Kiki ta ke nan ta dauke daga fuskarta ta komar da kanta yadda suka saba zama ita da Hamma tun kafin zuwan Kiki. Duk inda miji yake sunansa miji, da soyayya ko babu, to hakan ce ta faru Prince Kehinde, bayan tafiyar Kiki da canzawar yanayin Aisha, duk sai ya ji ya damu. Ya shiga takura da canzawarta da rashin fitowarta falo yadda suka saba. Ko da ma can shi Aisha tausayi ta ke ba shi, balle yanzu daya fara sanin wacece AISHA-SIDDIQAH. Zaman Kiki ya haifar mata da walwala mai yawa, ya fara bankado masa asirin dake kunshe a zuciyar Aisha, ya ga excitement a tare da ita, irin wanda bai taba gani a tare da ita ba, kafin zuwan Kiki. Sai Hamma yaga cewa zai yi kokari ya maye mata gurbin Kiki, wato ya zame mata babban aboki kuma dan uwa, wanda zata iya yin dariya da walwala tare da shi idan har zata yarda da hakan. It’s not easy a rabo ka da iyaye, dangi, kasarka da kowa naka sannan a barka cikin damuwa. Yau kwanan Kiki hudu da wucewa, kuma tun lokacin ganinsa da Aisha sau daya ne tak! Ya zauna a falon har ba adadi domin ya ga gilmawarta ko don ya tabbatar da lafiyarta amma ko kamshinta bai ji ba. Aisha wadda ta koma daddawar daka tun bayan tafiyar Kiki Ruqayyyat, ko kiraye-kirayen waya data ke wuni tana yi da jama’ar gidansu dana gidan Nenne yanzu ta rage. Ta fi yin tilawar Alkur’ani da nafilfili a cikin dakinta, sai ta tabbatar Hamma ya fita ‘Ranch’ ta hanyar hango shi cikin stable din dawakansa ta tagar dakinta take fita kitchen ta dafa taliyar indomie da bakin ruwan tea, tayi maza ta juye a flask ta shige daki shikenan. Dama Kiki ce ta matsa suke cin abinci tare dashi. A rashin Kiki kuwa, sai ta maida musu rayuwarsu ta tun asali irin yadda suka fara ta. Duk iya juriyar Prince da dakewa da jin sarauta, ya kasa yin biris da wannan silence din na Aisha. Da canjin data kawo musu. Because it’s killing him inside. A can dakinta ita kuma a kwanakin nan guda hudu, Aisha babu abin da ta ke yi sai sauraron zuciyarta, tana ‘digesting’ maganganun Kiki na hankalin dana wautar. Tana daukar na hankalin, tana watsar da na shirmen. A ciki Kiki ta ce da ita kada ta kara yarda Hamma ya barta jiran gida. Ta dinga saka su lingeries a cikin gida da sauransu. Kiki ta manta duka wannan ana yi ne a inda akwai soyayya da kaunar juna. Ba ta haufin yau da a ce Ishaq ta aura za ta iya yin fin abubuwan da Kiki ke koyar da ita. Ita ba bagidajiya ba ce irin yadda kowa ke daukanta, ta san duk abin da ya kamata macen kwarai ta yi a dakin aurenta, uzurinta kawai shi ne Prince ba sonta yake ba, ita ma kuma haka, sannan ba ta hango musu wani canji a zamantakewarsu nan kusa ba, domin ita da shi duka danjuma ne da Danjummai. Wato babu wanda ya damu da wani abu wai soyayya, ita a kan Ishaq duk wani tsuntsun soyayyarta ya gama tashi. Tana wannan tunanin mara adadi a zuciyarta ta ji motsin ana knocking kofarta kadan-kadan. Kafin a shiga kwankwasawa sosai, a nitse Aisha ta tashi zaune daga kwanciyar da ta ke, ta isa ga kofar ta bude don ta san babu mai yi mata knocking har kofar dakin barci a gidannan a kuma daidai wannan lokacin da dare ya fara nisa in ba shi Hamma Prince din ba. Aisha ta taso ta bude wa Hamma kofa, ta rabe jikin kofar ta ba shi damar shigowa don alamu sun nuna shigowar yake so zai yi dakin. Sai da ya baza manyan idanunsa yana nazarin tsaftar dakin. Ba laifi Aisha ba ta watsar da shirgi, komai nata neat. Don haka ya zabi sofa-bed guda daya dake dakin ya zauna, kafin ya dago a hankali idanunshi a lumshe ya fuskanci inda take tsaye tana gaisheshi, bai amsa gaisuwar ba yace, “Are you alright? Kwana biyu bana ganin wulgawarki a sitting room, baki ko gaisheni, ina fatan dai lafiya?”. Kan Aisha a sadde ta bada amsa, “Wallahi lafiya kalau Uncle, kawai ina kewar Kiki-Rukayyat ne”. Prince ya yi murmushi ya ce, “Ni kuma da kika daina fitowa kinsan ya nayi kewar ki? Na ga alama jininki ya hadu da na Kiki, ga shi ba ki san ita yarinya ce mai kiriniya da rawar kai ba. Kawancenku ba zai yi daidai ba, considering cewa ke din Uwa ce a gare ta. Ba komai za ki dinga tattaunawa da Kiki ba akaina please, zan kai ki makaranta insha Allah idan nagama hutuna mun koma inda nake aiki a Qatar, domin ki samu abin debe kewa”. Godiya sosai Aisha ta hau yi, tana jin kamar Hamma ya mata bushara da kujerar makkah, kwarai ta ke son komawa makaranta, ta dauka karshen karatunta a rayuwa kenan sakandire, amma ta san wannan shekarar dai ta shige mata, sai ko shekara ta gaba. Prince yace yana mikewa tsaye, hannunwansa biyu zube cikin aljihu, “ina fatan gobe da safe zan samu breakfast daga hannun Ayshah? Tunda Kiki ta tafi kika daina bani, bayan kwana biyu kun shagwabani da kyawawan girke-girken nan naku”. Ya fada yana kokarin saka idanunsa cikin na Aisha, ita kuma tana kokarin sunkuyar da kai ga barin kallonsa. Prince ya kai bakin kofa yana cewa “Good night Ayshah!”. Amma kuma ya kasa ficewa daga dakin gabadaya, rabin jikinsa har lokacin yana cikin dakin. Wani bakon yanayi yana ziyartarsa. Da kyar da dakiya da jan kafa da karfafa giyar mulkinsa kada ta gudu ta barshi, da maintaining class dinsa kada ya bada kansa da yawa gaban little Aisha, Prince ya samu ya fidda gangar jikinsa data makale a dakin, amma har washegari zuciyarsa na reto tsakanin dakinsa zuwa na Aisha. Ji yake kamar ya dawo ya kwana a dakin tareda ita. A washegari kuma ya samu waya daga Ilorin cewa, Emir babu lafiya, ko fada baya iya fitowa, yau kwana uku yana kwance saidai a kwantas a tayar. Bai yi niyyar zuwa gida nan kusa ba, ko sake yin tafiya cikin hutunsa, amma sanin kowa ne sha’ani in ya hada da Kakansa Emir daban yake a gare shi, balle magana ake ta lafiyar Kakansa Maimartaba Sarki, ba zai iya kara wasu kwanaki bai je ya ganshi ba, a take Prince ya soma neman jirgi mafi kusa domin tafiya Ilorin. Ya tuna Siddiqah, yaya zai yi da ita idan ya tafi? Wancan lokacin da Kiki, wannan kuma babu. A karshe ya ga gara ta zauna ita kadai din maimakon ya dauke ta yanzu zuwa Ilorin, ya yi wuri ma ta je gida nan kusa, gara ma tun yanzu Aishah ta koyi zama ita kadai, don kuwa tafiye-tafiyensa ba masu karewa ba ne. Banda sauyukan dake faruwa dashi a ‘yan kwanakinnan a kanta, wato yanzu da ya fara sabawa da ita, ya kuma fara fuskantar dadin mu’amalar da yarinyar keda shi, da ba zai damu don ya tafi ya barta ita kadai cikin gidannan ba. Zuwa yanzu Prince da kansa ya fara tantama a kan cikar lafiyarsa, don duk da tabbacin da yake da shi na cewa Siddiqa matarsa ce, bai taba jin darsuwar wani abu game da ita a ransa ba da ya danganci ‘sexual urge’. Ya dai fara jinta a ransa, ta manne a zuciyarsa. Watakila kuma ko don ya riga da ya saba da yadda yake rayuwarsa ne tuntuni daga shi sai shi, sai ibadar addininsa, sai lafiyar Dawakansa sai kuma zuwa Polo tournament sai aikinsa na ‘Qatar Petroleum Refinery?’. Bai gaya wa Siddiqah maganar tafiyarsa Ilorin ba sai bayan ya gama duk wani shiri yayi (booking flight) dinsa na tafiyar, wato ana i-gobe zai tashi zuwa Ilorin. Siddiqah tana kitchennett tana tana dauraye kofin Mug din data sha tea, ta ji motsin Prince ya shigo inda take. Kai tsaye firij ya nufa, ya bude ya dauki gorar ruwa ya rufe. Ta gama wankin kofin tana kife shi a wurinsa taji motsinsa dab da gefenta. Siddiqa ta rusuna tana gaishe shi da irin gaisuwarsu ta ce, “Ekaaro Uncle” (wato ina kwana)”. Wannan Uncle da Siddiqah ke lanqaya masa ba ya son jin shi, har gara masa Hamma Abdul din da take kiransa dashi da fari kafin zuwan Kiki. A kan me za ta dinga ce masa Uncle sai ka ce wata Kiki? Uncle din nan da ta ke ce masa na sawa ya ji kansa tsoho sosai a kanta sosai. Amma wannan ba shi ne abin da ya kawo shi yanzu ba da yayi korafi, ya zo ne ya gaya mata batun tafiyarshi duba Emir gobe. Tun shekaranjiya rabon shi da ganin Siddiqah. Jiyan da shekaranjiyan duk bai karya kumallo a gidan ba, ya wuni ne a ‘Cathedral of Polo’, shi ya sa bai ga gilmawarta ba, don ko babu komai koda bazata saki jiki dashi yadda yakeso ba yanzu, yana son ganin gilmawarta a kitchen don dai ya tabbatar da lafiyarta. Murya a tausashe ya ce, “Siddiqah, in baki ganni ba ba kya nemana cikin gidannan ko? In ma mutuwa nayi cikin daki ko bani da lafiya duk ba damuwarki bane ba ko Ayshah?”. Kiran sunan nata da ya yi har sau biyu yasa ta bashi hankalinta, don yau ne karo na biyu da Prince ya ambaci sunanta. Ya kara matsowa dab da ita, ita kuma ta dan ja baya. Ya ce, "daina ja da baya ba rike ki zan yi ba Pretty, so nake na gaya miki zan je Ilorin, zan dubo jikin Kakana. Ba na fatan in wuce kwanaki bakwai ban dawo ba, ko akwai abubuwan da ki ke bukata?” Siddiqah kamar ta ce masa za ta bi shi, to amma ita ma tasan ya yi wuri su Nenne su ganta yanzu, duk da cewa ba abin da ke hada su cikin gidan ta san akwai mutum, idan yana nan. Don haka ta samu kanta da rashin jin dadin zancen tafiyarsa, haka ta daure ta ce, “Bana bukatar komai Uncle, ka saya mana komai, ina maka addu’a Allah ya kiyaye hanya ya bawa Emir lafiya, ina duba shi da jiki, in ka karasa wajen su Nenne, ina gaishe su bakidaya, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”. Prince ya ji kamar ya riko hannayenta ya sumbata, ganin damuwa karara a kyakkyawar bafullatar fuskarta. Ashe haka mutum yake ji idan iyalinsa sun masa addu’a? A zuciyarta kuwa hudubar Kiki ke ta mata aiki, na ta daina yarda yana tafiya yana barinta gadin gidan gona, to amma kwarjinin Hamma da girmansa da ta ke gani cikin idanunta ya sa kowanne hukunci ya yi ba ta da ja a kai, musamman a kan zuwansa Ilorin dinnan itama ta san ya yi wuri a ce ta bi shi yanzu. Ta kalle shi a raunane, shi ma kallonta din yake yi da wani sabon yanayi cikin idanun Hamma Abdulrasheed Prince, ya zuba dukkan hannayensa cikin aljihun wandonshi ya juya ya bar kitchen din, yana kokarin maida wani abu da ke neman fita daga bakinsa, wato kalmar ‘I will miss you’ da yake ganin bata dace ya furtawa Aisha ita ba. Amma tabbas zai yi kewar tata, gashi yana son ya zauna tare da Kakansa a wannan lokacin ya kula da shi da kansa. Prince ya tashi a washegarin ranar litinin Siddiqah ta tashi da azumin tadauwa’I a bakinta, wajejen karfe sha daya na rana ta kammala shiryawa ta fito zuwa falo. Ta kunna TV da taimakon remote tana kunnawa din kuma tashar Polo ta ‘PoloLine TV’ ce ta kama, ga dukkan alamu ita ce tashar da ya fi kalla. Ta tarar ana gudanar da wasan tseren Doki. Ta sha jin Nenne na ce mata Hamma yana polo, bata taba ganinsa a profession din ba sai yau, gashinan tsaf ya fito cikin kayansa na polo. A lokacin ana gudanar da wasan ‘Concacap World Polo Championship’. Kasancewar Helmet din kansa budaddiya ce ya bata damar gane fuskarshi sosai cikin mahaya dawakan. Dokin da yake kai wani farin kosasshen doki ne mai fatsi-fatsi, wanda a halin yanzu Prince baya wasan Polo da shi, tun wancan lokacin da suka fadi tare shi da dokin nasa. Siddiqah aka gyara zama ana kallon duk wani motsi na Prince Abdulrasheed Kehinde . Gudu yake da doki cikin kwarewa da iyawa, kamar zai yi fiffike ya tashi sama. “Wannan shi ne ake kira Polo kenan!” Inji Siddiqah. Kuma a koyaushe ta kalli wasan da aka nuno zata ga cewa kusan Prince shi ne jagaban wasan, wato shi ne a sahun gaba na wadanda ke neman isa goal. Abin ya burge Siddiqa matuka don kuwa a wannan daren kusan kwana ta yi tana mafarkin Prince Abdulrasheed a kan doki, yana mata murmushi da helmelt dinsa mai ban sha'awa a a kansa. Shi kuma Hamma tunda ya sauka a Ilorin bai samu sukunin da zai tuna kowa da komai bama don jikin Emir ya yi tsanani, ko wayarsa bai iya ya bude ba. A washegarin ranar ne Aisha ta fara fitowa ainahin kwaryar ‘Ranch house’ din, sabida kadaici daya dameta, kallo sosai Siddiqah take na dabbobi kala-kala masu daraja, harda wadanda ko a talabijin bata taba ganin irinsu ba. Tana tafe a sannu itace har wurin stable din dawakai. Daga ganin farin doki mai fatsi-fatsi “Saheeb” Siddiqah ta gane shi saboda irin kebewa da killacewar da aka yi masa. Wato an ware shi daga ragowar. Ba wanda ya isa ya je inda yake ba tare da Saheeb ya harbe shi ba, daga Prince sai Pareto. Amma daga nesa Pareto ya hango wani abin mamaki, wato Siddiqah ta isa har gaban Saheeb bai harbe ta ba. The beautiful royal horse “Saheeb”, duk ya fi sauran dawakan girma da mulmulallen jiki mai kyau. Ga tsafta ta kama jikinsa saboda kulawar Pareto. Farcensa kansa tsaf-tsaf yake, sannan yana zaune cikin korran ciyayi masu taushi da tsabta. Nan Siddiqah ta shashance har lokacin sallar azahar tare da doki Saheeb a stable dinsa. Pareto sai komawa ya yi da baya don ya ga tana jin dadin zaman wajen, sauran ma’aikatan gidan gona kuwa kowa yana bisa aikinsa babu wanda ya ba ta hankalinsa. Sai ya zamana daga ranar kullum da safe sai Siddiqah ta je stable din Saheeb, har dokin na Prince ya fara gane ta. Da ya ga tahowarta zai fara haniniya yana daga kafafu sama irin yadda yake yi idan ya ga Prince. Ba da sanin kowa ba cikin kwanaki hudu kacal da tafiyar Prince Ilorin Aisha da Saheeb suka yi developing good bond. Har wajen shanun Prince ta ke shiga inda ake tatsa (milking) mai kula da shanun yana mata bayanin madarar sayarwa kamfanonin sarrafa madara suke yi. Pareto ya sha mamakin sabon da ya ga ya shiga tsakanin Siddiqag da Saheeb cikin dan lokaci. Sosai abin ya burge shi. A rashin abin yi Siddiqah ta mayar da Ranch din dawakan wajen shakatawarta da debe kewa da shan iskarta. Wani zubin kuma ta tsaya kallon dramarsu shi da Pareto. Daga irin dramar da ake bugawa tsakanin Saheeb da Breeder din nasa Pareto Siddiqa ta ji doki Saheeb ya kara shiga ranta. Koyaushe ta zo gun Saheeb sukan gaisa da Pareto ta zauna a kujera a gefe tana kallon yadda al’amuransu ke gudana tsakanin Saheeb da mai kula da shi, tamkar saheeb wani dabba ne mai tarin hikima da baiwa, duk mai kula da shi ya sanshi farin sani. Kadan-kadan Saheeb ya fara gane fuskar Siddiqah, watarana cikin dari-dari ta kai hannu ta fara shafa jikinsa da kyakkyawan gashin wuyansa, har Pareto ya tsorata ya zo da sauri zai hanata, sanin halin Saheeb da yayi, na ba ya barin kowa ya zo inda yake bai yi harbi ba. Amma abin mamaki sai ya ga Saheeb ya kwantar mata da kai kasa tana shafa shi yana dada kwantar da kai. A haka a haka har karambani ya sa rannan ta ce da Pareto tana so ta hau bayan dokin. Pareto ya gaya mata cewa ba ya bari a hau bayanshi in ba mamallakinshi ba. zaiyi tutsu a ita. Aisha ta dage cewa she wants to give it a try. Dole Pareto ya kyale ta ya saka mata sirdi ta hau Saheeb, ya rike mata linzami suka shiga zagayawa cikin Ranch din. Sune har kofar fita ‘ranch’ da wajen BQ din Pareto, daga nan suka juyo suka dawo stable dinsa. Siddiqah ta sauko lafiya. Sai hakan yasa ta kara sabawa da Saheeb sosai, kullum nan ne wajen wuninta. Kusan ba ta da damuwa a yanzu, don Saheeb ya debe mata kewar kowa da komai. Siddiqah na nan tana fama da Saheeb, Prince yana Ilorin jikin Kakansa Sarki Abdulrashed Akanni ya rikice. Likitoci har uku ne ke tsaye a kansa a gidansa na masarautar Ilorin, tare da ‘ya’yansa (Ten Akannis). Ciwon cikin wuni uku daya firgita zuri’ar Sarki Abdurrasheed gabadaya. Prince kwana yake tare da Kakansa a turakarsa don ko matansa na aure basa bari dashi. Yau da dare jikin nasa da sauki sosai, don an masa allurar barci, amma cikin dare ya farka ya ga Prince a zaune a gefen kansa yana gyangyadi, lokacin kowa ya je ya kwanta. Sarki Abdurrasheed Dan Abdullateef Akanni, ya ce da jikan nasa Prince. “Kehinde! Barci kake yi a zaune?” Kamar cikin mafarki ya ji muryar Kakan na kiran sunansa, tuni ya wartsake ya matso daidai kansa. Sarkin ya kamo hannunsa ya rike cikin nasa, ya ce cikin harshen yarbanci, “Kehinde Jikan Sarkin Ilorin, jika mafi soyuwa a gareni, me yasa baka zo min tare da matarka na hada ku na sa muku albarka ba? Ina fatan zuwa yanzu komai ya daidaita tsakaninku yadda muke fata? Ka karbi zabin mahaifiyarka da hannu bibbiyu? Nan bada jimawa ba zaka ajiye min mai sunana? Wanda zai gaji gidannan tunda ba kwa son gadona kai da Ubanka?” Prince rasa amsar da zai baiwa Emir ya yi, sai cewa yayi cikin yarbanci “tana lafiya Allah ya ja zamaninka, na baro ta lafiya cikin koshin lafiya, kuma maimartaba na dade da karbar matar nan da kuka zaba min da godiya da yabawa. Tana da attributes na matan kwarai da ban san su a tare da ‘yammatan wannan zamanin ba”. Sarki Abdulrasheed ya gyada kai cikin gamsuwa da jin dadi, sai kuma yace. “A yadda nasan ka kullaci mata, da yadda giyar mulki ke hanaka sakewa, ina da yakinin har zuwa yanzu ba ka dora mata idda ba. Ko Qur’ani zan dafa akan ba ka dabbaqa sunnarka ba har yau, me yasa? Donni in za’a shekara ana cewa ba ka da lafiyar aure ba zan taba yarda ba, na san lafiyarka kalau, baka samu wadda kake so bane, kuma bazaka iya hada jiki da matar da baka so ba shine babban dalili, tunda na san yaya halittar sarakuna take a kan matan da suke so. Kada ka manta na so Kakarku Murjanatu kamar raina. A lokacin da take raye ban taba zaton zan tsufa ba, kullum sabuwar samartaka take kara min saboda soyayya, ina gaya maka kayi gaggawar dabbaqa sunnarka kafin ranar da wankin hula zai kaika dare, wato ranar da zata gane tana son ka tayi maka bore ta hana ka kanta”. Prince ya hau zufa daga goshi, ga kunya da ta kama shi. Ya kasa cewa komai. Amma da zai iya da yace da Kakansa sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba, amma ya fara jin sauyi a zuciyarsa da gangar jikinsa sosai a kan Siddiqah. Sun kwana suna hira shi da Kakansa abin gwanin sha’awa, inda ya sa shi yi masa alkawarin zai kula da aurensa, zai kuma kula da Siddiqah kwatankwacin yadda Dade yake kula da Nenne. Ya kuma tabbatarwa Kakan nashi cewa shi lafiyarsa kalau ba kamar yadda mutane ke kuskuren fahimta ba. Yana jiran ya ga yadda Allah zai yi dasu ne shi da Siddiqah. Emir kuma ya ce masa “ka yi amfani da dama a lokacin da ta ke hannunka”. Har aka kira asubahi idonsu biyu, Kawunsa Malami Ubandoma, da mai bi masa Mufti of Ilorin suna daga shigifar farko a nan suka kwana, Prince ne kadai ya kwana tare dashi da asubah yayi masa alwallah yayi sallar asubahi daga kwance, sai ya ce da Prince yasa masa bargo sanyi yake ji. Kuma ya kunna masa Suratul Mulk a radiyonsa. Prince yayi duk yadda Kakan ya ce cike da kauna da kulawa, sannan shi kuma ya tada tashi sallar. A nan inda ya yi sallah kasancewar ya yi kwanan zaune barci mai nauyi ya yi awon gaba da shi. Har gari ya soma haske Abdurrasheed bai farka ba. Ashe sallamarshi kenan da Kakan nasa Emir Abdurrasheed Akanni. Abinda ya faru yana barci shine Kawunsa Mufti ya shigo kawo karin kumallon Sarki, a lokacin da aka kawo daga cikin gida, shi ya gane cewa ran Emir ya yi kaura zuwa ga mahaliccinsa. Sai ya tashi Prince daga barci ya yi masa nuni da abin dake faruwa. Prince ya isa ga Emir ya tallafo kansa ya tabbatar wannan ruhin da ya rayu shekaru sama da shekaru arba’in da biyu yana lelensa yana kula dashi yana kyautatawa rayuwarsa yau babu shi. He is more than shocked. Don ko kusa bai kawo wa Emir mutuwa yanzu ba, don ya saba ciwo fiye da wannan ma ya girgije ya tashi. Shi ya san ya yi rashin da ko iyayensa ne suka fadi yau suka mutu suka barshi iyakar kukan da zai yi kenan. A wayewar garin ranar labarin mutuwar sarkin Ilorin, Sarki Abdulrasheed Akanni, ta riski al’ummar kasar Najeriya, labarin yayi tambari ya riski duk wani jininsa, kafin kace meye wannan kafatanin zuri’arsa na garuruwan Najeriya da wajenta sau bubbugowa suke yi Ilorin. Akannis sun gigice sun dimauce baki daya, amma babu wanda ya kai Prince AbdulRasheed gigicewa, su Nenne ma da su Princess Fatima, duk a ranar suka taho Ilorin, Taiwo da ke nan Ilorin kuma akan idonta aka yi wa sarki suttura, duk a ranar suka taho masarautar, haka dukkan ‘ya’ya da jikoki na nesa da na kusa suka hallara. Sun dade basu shiga halin dimauta da gigita irin na wannan lokacin ba. **** **** **** Tun Siddiqah na zuba idon ganin Prince ya dawo a satinsa na biyu da tafiya har ya zamanto ta fara damuwa da rashin dawowar tasa, duk da ba wai shiri suke yi ba, ba kuma shakuwa ce ta sosai a tsakaninsu ba, amma mutum a cikin gida rahma ne. Kai ita yanzu ta fara jin tsoron zaman gidan ma, daga ita sai Dawakai da dabbobi. Ta yi da na sanin rashin yin bore na sai ta bishi kamar yadda Kiki ta ke so ta dinga yi, wato ko’ina Hamma za shi ya tafi tare da Aisha. Amma cikin hudubobin Kiki na arzikin wanne ta dauka? Kusan a inda ta bata su, tun tafiyarta a nan ta ajiye mata su saboda taurin kanta. Yanzu ga shi rashin Hamma a gidan ya dame ta, musamman da ko sau daya bai kirata ba. Sati biyu kenan da tafiyar Hamma Ilorin, ranar da aka yi rasuwar Nenne ta kirata, nan ta gaya mata rasuwar Kakan nasu Fatima. Sai kuma Kiki ma ta kirata suna gama magana da Nenne. Kiki tana cikin damuwa domin makarantarsu ba za ta bata excuse din zuwa gida ba kasancewar ba ta jima da dawowa ba. Nenne again a washegarin ranar rasuwar ta sake kiranta, ta ce, ta kira Abdulrasheed ta yi masa ta’aziyya. Domin kuwa shi aka yiwa mutuwa a kafatanin zuri’ar Akanni, ta gaya mata babu wanda ya kaishi kusanci da shakuwa da Sarkin. Kuma babu wanda Emir yake girmama sha’aninsa da kaunarsa cikin jikokinsa kamar Prince din, wadanda a kiyasce jikokin na Emir Abdulrasheed Akanni sun tasar ma (82). Nan fa ake yinta! Don Siddiqah da Prince ya kirata bayan saukarsa a Ilorin, ya gaya mata saukarsa lafiya ya kuma tambayi yadda take coping tace masa batada matsala, ashe lokacin ko lambar Prince din bata yi saving cikin wayarta ba, tsabar yadda bata daukeshi matsayin mijinta ba face Yayanta/Babanta, wannan abun kunya da me yayi kama? Taji kunya sosai yau, sannan da kunya ta tambayi Nenne wai lambar mijin da suke kwana gida daya. Har suka yi sallama da Nenne jikinta a salube yake, bayan ta sake yi mata tata ta’aziyyar, Nenne kuma ta kuma hadata da Dade shima tayi masa, da Princess Firdausi da Princess Fatima, ba ta iya ta tambaye ta lambar Hamma ba. Me Nenne za ta dauke ta? A yau sai ta ga cewa ma a gabadaya zamansu wanda ya ki samun daidaito da fahimtar juna har lokacin ba laifin Hamma Prince bane, laifin ta ne. Saboda Hamma yayi iya kokarinsa da ya karbeta a matsayinsa na wanda aka yiwa auren dole, ita da take mace ita ya kamata ta canza shi zuwa yadda iyayensa sukayi fata, suka kuma dora burin hakan a wuyanta saboda kyakkyawan zaton da suke dashi a kanta. Amma me ta tsinanawa Hamma na kyautatawa tun zuwanta? Hasalima bata dauki auren nasu a matsayin aure ba sai zaman biyayya. Bata shiga sha’aninsa yadda ya dace tayi, ba abinda Kiki bata ce mata ba wanda shi zai sa ta kusance shi su shaku da juna, ba abinda bata koya mata ba cikin dabarun abinda Bayeraben miji yake so daga matarsa, wanda zai sa ta kama zuciyar Hamma nan da nan, haka mahaifiyarsa ta dade tana bata training akan zama da shi. Amma a ciki wanne ta aikata baka da zuci? A zahirin gaskiya bata cika expectations din iyayenshi a kanta ba, da yardar da suka bata dari bisa dari na zata iya, zata kawo kyakkyawan canji a cikin bahaguwar rayuwarsa. Cikin watannin data yi tare da Hamma Abdulrasheed wane abun ku zo ku gani ta kulla a zaman nasu, wanda in aka tambayeta progress na zaman su zata iya adarwa da babbar murya? Idan da ta bi shawarwarin da Kiki ta bata, duk da ake cewa Kiki bata da nutsuwa, in aka dauka a tsanake aka dubasu za’a ga cewa shawarwari ne masu kyau da za su taimaka a rayuwar aurenta. Tunda auren nan ya riga ya zama rubutacce daga Allah! Wanda babu yadda za ta yi ta guje wa kaddarar kasancewarta mata ga Prince Abdulrasheed jikan marigayin sarkin na yarbawa. **** **** **** Daga wannan lokacin Siddiqah ta yi kyakkyawan kudiri a zuciyarta na in Prince ya dawo daga ranar zata canza irin zaman da suke yi, zuwa zama mai armashi da ma’ana koda bazai bata hadin kai ba. ta fannin ta zata yi kokarin sauke nauyin duk da iyayensa suka dora mata, sama da komai Ubangiji ma ya dora mata. Zata koma kyautata aurenta dashi iyakar kyautatawa. Kiki ta kira a lokacin da take tsaka da wannan juyayin, Kiki na cikin alhinin babban rashin da suka yi don itama Emir yana sonta albarkacin son da Abdulrasheed ke mata. Yau sai ta ji hatta Kiki din abin kunya ne babba ta tambaye ta lambar Hamma. Amma har gara ta murje ido ta tambayi Kiki, a kan dai ta tambayi Nenne. “Kiki am, nace ba, ko zaki ba ni lambar Hamma don Allah, ina cikin damuwa, tunda ya tafi ya kirani sau daya bai kara kira na ba, ni ma kuma nayi wani kuskure da ban kira shi ba, na dauka nayi saving no. din tun a lokacin, ai yanzu na duba ban ganta ba, a tsammanina zai kira again, sai inyi saving to amma yanayin da yake ciki nasan shi ya hana bai kira din ba”. Kiki was shocked da wannan ganganci zata ce ko childishness na Aisha. Ta ce, “Aisha me ki ke cewa? Sati biyu ba ki ji motsin mijinki ba, kuma ba ki kira shi ba ke? Sannan ba ki da digits dinshi a wayarki? To kenan ashe duk shawarwarin da na bata lokacina na baki ma babu wanda ki ka dauka kika gudanar kenan? Aisha me ke damunki har haka na tabbata ba kiyayya bace. To menene? Kin san girman hakkin Uncle AK da ke wuyanki kuwa? Haba Aisha, kankantar shekaru da rashin soyayya ba hauka ba ne, domin bayan dukkansu akwai abin da ya kamata mace ta yi la’akari da shi a zaman aure, shine sanin yakamata da sanin girman hakkin mijin duk da Allah ya rubuta shi ne mijinta”. Jikin Aisha duk ya idasa macewa, dama kuma ko kafin ta kira Kiki Rukayyat, duk ta yi wadannan hasashen itama, Kiki ta ce, “Lallai ne yanzu Uncle ke bukatar kulawarki da soyayyarki Aisha. Ya yi rashin masoyin da bai da kamarsa”. Nan Kiki ta shiga bai wa Aisha labarin irin kaunar da ke tsakanin Sarki da Hamma. Ta gaya mata hatta dokinsa Saheeb data gani yana matukar so, da daya matashin ‘Criollo Horse’ din, duk kyauta ce ta musamman daga Emir zuwa gare shi. Abubuwa da yawa da bata sani ba a kan rayuwar Prince, a ranar yau duk ta ji su a bakin Kiki. Aisha daga karshe kashe wayar tayi tun kafin suyi sallama da Kiki, saboda zuciyarta tayi rauni, tausayin Hamma Abdulrasheed Prince, hade da wani sabon ni’imtaccen feeling da ke sauka a kasan ranta a kansa. Kiki ta turo mata lambobin ta hanyar text message, ta kara da turo mata sakon text. “Text him. And call him tonight’. A take ta rubuta sakon text ta tura wa Prince. Sakon ya kunshi ta’aziyyah zallah a kan rashin da ya yi, da fatan Allah ya bashi hakuri da danganar musulunci, ya kuma jikan Maimartaba Sarki. A kasan sakonta ta rubuta sunanta; “Aisha-Siddiqah Yunus”. Prince bai bude wayarsa ba sai da ya zo kwanciya barci, bayan fitar Taiwo kenan daga masaukinsa, yau ne aka yi sadakar bakwai, kuma har ya soma shirin komawa Argentina. Yanzu Taiwo ta bar masaukinsa tana masa wasu maganganu da suka ba shi haushi da mamaki, ko dai Taiwo ta manta irin rashin da yayi ne da ta zo tana masa wannan shirmen? “Kehinde, yanzu saboda Allah don zubar da aji da barar da kima, yarinyar nan mai kama da kazar mayu ka dau hoto da ita ka dora a status? Ka san iya mutanen da zasu bude? Me kake nufi da kalaman daka rubuta a kanta? Abu daya ma yanzu ni nake son sani, tunda aka tura maka ita ‘have you ever touched her?” Dan bude idanu ya yi a hankali wadanda duk sun kankance, yana kallon ‘yar uwar tagwaitakarsa Taiwo Akanni, his very own twin sister Taiwo. Sai ya rasa amsar da zai bata, domin tambayarta ta fi kama da crossing limit da shiga personal marital affair dinsa. Taiwo ta ce, “Don in baka tabata ba in ba ka shawarar amfani da kwararon roba, tunda naga alama ta fara samo kanka, na san it will not be easy for you to be using condoms, yadda ka dauki lokacin nan ba aure, ace ka daure ka iya hakan. Amma Kahinde ka sani ba ta isa mu hada zuri’a da ita ba, make her your sex slave kawai, Allah ya gani ba zan taba son yaran da za ta haifa ba”. Abdulrasheed sai ya bude idanunsa gaba daya yana kallon ‘yar uwar tasa da mamaki da tsoro. Da kyar ya iya motsa bakinsa da yayi masa nauyi, don magana ma wahala ta ke masa tun bayan rashin Emir, yace, “Maman Kiki, bana son yadda ki ke min maganarta. Alaqata da ke daban, wadda ke tsakanina da ita daban”. Ya hadiyi wani abu da kyar da ya tsaya masa a makoshi, a dalilin dacin da ke zuciyarsa na rashin Kakansa, ya dubi Taiwo sosai ya kauda kunya yadda itama ta iya kauda kunya ta yi masa wannan zancen. Yace. “Shin Maman Kiki in tambayeki please. Zaman zina nake yi da ita da zan yi amfani da kwararon roba a kanta? Ko Concubine (kwarkwara) aka kawo min itaba matar aure uwargida ba I will never do this. Kamar na wofintar da umarnin Nenne da Dade ne. Kin ce bazaki taba son ‘ya’yan dana haifa da ita ba don kawai diyar talakawa ce. Ni kuwa kin ga ko da ‘Kare’ ki ka haifi su Kiki bama mutum dan Adam mai kima ba, banida kamar su, ba zan taba kin son ‘ya’yan da na tabbatar daga jikinki suka fito ba”. Da wannan Prince ya maida bakinshi ya dinke. Ya ki kara kallonta. Ya maida hankali ga kunna wayarsa dake kashe tun safe. Taiwo sai ta ji kamar bakar magana ce Kehinde yau ya gaya mata a kan mace. Macenma wannan mara aji irin Siddiqah, wadda ba diyar kowa ba. Wato Kehinde ya fara sanin dadin mace har ya dube ta yau ya gaya mata baqar magana irin haka akan Siddiqah? A take Taiwo taji ta kara tsanar matar dan uwanta. Kwafa ta yi ta mike tana cewa, “Kehinde maida wukar I came in peace in dai akan ‘yar Malam Shehu ne. Abinda ya kawo ni gareka ma ba zancenta bane rabon in samu rabon bakar magana ne. Inata so in gaya maka tuntuni cewa I met Hasina coincidently. She explained to me all what happened between she and Tukumbo. She made a mistake and she realized it. She is haunted. How much she hurt you had been haunting her. Tana ta neman yadda za ta ba ka hakuri but to no avail. Daga baya ta yi aure har sau biyu a UK ta fito, ta ce min ta tabbata alhakinka ne ya hana ta zaman aure. Ina rokonka ka yafe mata, ta ci albarkacina”. Prince ya ce a dan hassale, “Maman Kiki ba ni da say a kan wannan batun da ki ka zo da shi, sai dai in ce, please! Please!! Don’t mention that bitch again to me, idan kin yafe mata is okay ni ma na yafe, domin kada ki manta abin da ya yi Kehinde shi ya yi Taiwo”. Da sauri Taiwo ta ce, “A da ba… kafin ka samu abun hutawa, amma a yanzu kana neman canzawa ne completely daga Kehinde dina”. Kehinde din sai ya yi shiru har Taiwo ta yi tsaki ta wuce yana mamaki. Me ya shiga kan Taiwo dinsa ne? Tunda aka yi masa auren nan ta ke acting kamar ta samu tabin hankali a kan matarsa. Ya yi nafila raka’a biyu ya sha zazzafan chamomile tea, ya kunna wayarsa kenan sai ga sakon Siddiqah ya shigo. Ya karanta ya maimaita, sai ya samu kansa da tura mata reply da kalmar, ‘thank you’, a fili kuma ita ma haushi ta bashi. Ko da ya san ba auren so aka yi musu ba amma fisabilillah yana iya kokarinsa wajen kyautata mata a gidansa. Bai tsangwame ta ba, bai kuma rage ta da komai ba. Amma ace ya yi tafiya irin haka har tsahon sati biyu Siddiqah ko sau daya ba ta kira shi ba, sai da ta ji ya rasa Emir? Saboda shi Prince a mulki irin nasa matarsa ce ya kamata ta dinga kiransa don yana son respect mai yawa daga matarsa. Kusan wannan dabi’a ce ta mazan Yoruba, suna da tsananin son respect, musamman daga matan su. Musamman a wannan lokacin da yake ganin jinyar Kakansa ya zo, ita ya kamata ta dinga kiransa don jin ya jikin Maimartaba. Amma ba ta yi hakan ba sai yanzu? Bai san cewa ita Siddiqah ko digits dinsa bata yi saving a wayarta ba, saboda bata dauki auren nasu da wani alkibla a baya ba. Bayan zama na biyayya. Amsar da Hamma ya bata nan take, duk da a gajarce ne, showing nothing, shi ya ba ta kwarin gwiwar kiransa. Kirjinta da zuciyarta baki daya suna harbawa a cikin kirjinta, don yau ji ta ke Hamma na samun wani special reception a gunta, data dangata shi da tausayinsa. Yana kallon lambobin Siddiqah suna shigowa da mamakin kiran kamar ta san me yake sakawa a ransa, shi yana da lambobinta ai, kasancewar layin da wayar duka nashi ne a baya. Kuma daya bata din, sai ya yi saving da sunanta, sunan da zuciyarsa ta ga damar bata a lokacin, wato “Baby”, don a wurinsa Siddiqah jaririya ce kamar yadda Kiki take a idanunsa. Sai da kiran ya yi dab da katsewa Prince ya amsa, Aisha ta tausasa murya tace. “Assalamu alaikum!”. Sai kuma ta yi shiru tana shirya abin fadi, don duk wata hikima da ta ke da ita a lokacin subucewa ta yi. Prince ya ciccibe ta, ta hanyar amsa sallamarta. Sai ta samu kwarin gwiwa ta yi masa ta’aziyya ta fatar baki. Hamma ya yi godiya sannan ta ce a raunane, “Uncle yaushe za ka dawo?” Shi kuma ya amsa, “Ranar dana tashi daga Uncle dinki!”. Siddiqah sai ta yi wani murmushi mai kyau kamar Hamma yana ganinta. Yace “Ko ba haka kika ce ba, kallon kamar Babanki kike min ko Aishah?” Girgiza kai kawai tayi kamar yana kallonta amma ta kasa amsawa. Prince yace “To yaya gidan ince ko babu matsala?” “Babu matsala Hamma, gidan kawai yayi tsit da baka nan babu dadi”. “To ko in aiko miki ticket ki taho duk da gashi ina shirin komowa?” “Tunda zaka dawo soon ai bai kamata kuma in taho ba, zan yi hakuri harka dawo”. “Yaushe har kika damu da presence dina ai ba wani banbanci da ina nan da bana nan a gunki Aisha, ba kya sakin jiki dani tunda Kiki ta koma”. Aisha taji wani irin dadi a ranta, (something more of excitement). Hamma ashe yana yinta, koda ita bata damu dashi ba. Murmushi Aisha tayi ta sake rike kan wayarta sosai a kunnenta, tace “ina kara yi maka ta’aziyya Hamma Abdul. A gaidasu Maman Kiki”. Prince ya amsa da cewa, “Za ta ji, yanzu ta bar nan, ina fatan idan na dawo inga canji, kuma duk abin da kike so Pareto was there to help, he is always at your service”. A tare suka ajiye wayar, Prince na ajiyar zuciya ya ce a ransa, ita Aunty Murja din tana nan tana binki da mummunan kulli, ke kina cewa a gaishe ta Aisha. Tana fatan kada a hada zuri’a da ke, ‘yar mallam shehu. Tana neman kariya daga hada jini da ni, don matata bata yi daidai da ra’ayinta ba. In ya ce bai ji zafin abin da Taiwo ta fada ba ya yi karya, amma ya zai yi? Dole ya hadiye tunda Taiwo ce. His very own twin, his one and only Taiwo. Ranar lahadi Prince Abdulrasheed ya dawo gidansa, Siddiqah tana can wajen Doki Saheeb, bata da masaniyar dawowarsa. Ta kama sirdi ta haye, shi kuma ya soma tafiya da ita a hankali, tana tafe kan Saheeb tana rangaji irin na tafiyar doki a hankali zuwa karshen ranch. Kawai sai Saheeb ya hango shi daga nesa ya harde hannuwa a kirji yana kallonsu. Saheeb ya fara kokarin gudu da haniniya har yana neman jefo Siddiqah, da karfi ta ce, “Saheeb!” Dan saura kadan ya jefo ta kasa, amma tsawar nan da ta yi masa ya sa ya koma cikin nutsuwarsa, ya fasa fudun ya kuma daina haniniyar. Abun ya kashe Prince da mamaki daga tsaye, ta yaya Siddiqah ta yi ta samo kan Saheeb cikin sati biyu haka, har da bashi umarni kuma ya bi? The Prince was dumb-founded. At the same time, abin ya burge shi matuka gaya. Sai lokacin Siddiqah ta ankara da Hamma, fuskarta ta haskaka da ganinsa, Hamma ya rame sosai a idonta, ta jefa masa murmushi (full of innocence), a idonsa she looks pure and angelic, ta kada linzamin Saheeb suna tahowa inda yake tsaye. Murmushinta na kara fadada, domin harr anta taji dadin ganinsa, tace “Uncle shine baka gayamin yau zaka dawo ba? Sannu da zuwa Hamma Abdul! Sannu da hanya Uncle!” Cikin dan lokacin nan zuciyar Prince ta shiga wani yanayi na raguwar radadi, ya dan mance da zugin da zuciyarsa keyi na gajeren lokaci, ganinta kawai kuma akan Saheeb ya zama tamkar haske maganin duhun da zuciyarsa ke ciki, ya samu kansa da takowa domin ya cimmasu. Suka game a tsakiyar filin wajen, hamma yace “ashe haka kike da karambani? Idan kika fado fa?” Aisha tayi murmushi kawai tace “sannu da dawowa” tana kokarin saukowa daga bayan Saheeb, Hamma ya shagala da kallonta ya mika mata hannu ta kama cikin jin nauyi ya kama kugunta ta sauko, sai lokacin yaga takalmin sa na hawa Doki ne a kafarta (chukka boots) duk da ya mata yawa. Bayan ta sauko Hamma ya tsaya yana kallonta tana dan manne a jikinsa, Siddiqah ta sunkuyar da kai duk ta rikice ta kasa kallon idon Prince, haka ta kasa gasgata abubuwanda ke faruwa yau. Ganin rikicewar data yi dinne yasa Hamma ya cikata, yana dan tsokanarta da cewa. “Inye Siddiqah, yaushe na baki takalmin da kika dauka mun, haaa!” Siddiqah na murmushi kamar ta nitse a haka suka jera a tare yana rike da hannunta suka shige cikin gidan. A sitting room ya zauna yana nazarin yadda Siddiqah ta gyara shi, ta canza zaman kujerun zuwa yadda ya fi yi mata daidai, ga kamshin turaren wuta na tashi mai dadin kamshi. Siddiqah ta tsugunna tana masa barka da zuwa tare da sake yi masa ta’aziyya, ya tambaye ta ko ina Pareto? Ta ce, ta aike shi cefane. Daga haka ya shige dakinsa bai kara fitowa ba har la’asar. Siddiqa ita kadai a kitchen tana girki duk ta bi ta damu da rashin jin motsinsa. Ganin Hamma yau ko abinci bai nema ba, sannan ba ta kara jin motsinsa ba har yamma. Don sai yanzu ne ma bayan ya dawo ya kadaice a dakinsa. Mutuwar Kakan ta soma taba shi, rayuwarsa da Emir ta dinga dawo masa filla-filla tun lokacin da yake yaro, da moments dinsu tare, da karfin soyayyar Emir a gare shi. Ya tabbata ya yi rashi irin wanda ba zai taba mayar da shi ba. Prince sai yau yake kuka da hawayensa tun bayan rasuwar Sarki Abdulrasheed. Domin sai yau ne ya samu kadaici, a can gida Ilorin koyaushe yana tare da jama’a, ga Dade da Uncles dinsa da basa bari ya bar kusa da su sai lokacin barci. Idan ma ya shiga barci Taiwo na biyo shi ne ta taya shi hira, kasancewar tunda aka yi rasuwar tana nan main house dinsu ba ta koma gidanta ba. Toufeeq ma ya zo ya musu gaisuwa ya koma UK. Da taji shirun nasa yayi yawa ta kasa daurewa ta isa ga kofar bedroom din nasa tana knocking a hankali. Prince ya share hawayensa da hankacif yace “Yes!” Sai Siddiqah ta bude kofar ta shiga a hankali, karonta na farko da shigowa masterbedroom din na Prince, dakin ya tsaru iya tsaruwa, komai ya zauna a muhallinsa cikin tsari mai ban sha’awa, ga kamshin turarukan Prince da suka hadu suka cakude dana room freshner. Aisha taji wata irin nutsuwa na shigarta karo na farko da shigarta turakar mijinta, shima kuma Hamma ganin Siddiqa yau a dakinsa sai wani bangare na zuciyarsa yaji contentment na cewa yau gashi ga macen Sunnah a dakin barcinsa, lallai da gaske yanzu ya yarda yanzu an masa aure. Kallo daya Aisha tayi masa ta gane kuka Hamma yake yi, taji wani irin damuwa ya tsirga a ranta, da kyar ta daure tace dashi cike da kulawa. “Uncle na ji ka shiru ne, are you okay?” Ya sunkuyar da kai, jin wasu sabbin hawayen na kara fito masa bayan wadanda ya share kafin shigowarta, amma yayi kokarin hadiyesu. Yace “No Aisha. But Alhamdulillah!”. Aisha ta sake yiwa Hamma sabuwar ta’aziyya, ta bashi hakuri, Prince yana mai yabawa da hankalin Aisha a ransa yace “ya gode”. Aisha tace “don Allah ka dai na kuka haka Uncle, in babba na kuka abun yana tada mun hankali sosai”, itama tayi narai-narai da ido nata hawayen na shirin zubowa. Abin ma sai yasa shi dariya, yace “to na dena, jeki cigaba da abinda kikeyi”. Tace “tau abinci ne nake maka dama, bansan yau zaka dawo ba, ai zaka ci don Allah ko?” Aisha tayi maganar a shagwabe da zuciyarta daya, bata ma san tayi ba. Hamma yace “tohh!”. Sai ta fita ta saka karatun Al’qurani a falon Suratul Noor, tana girkinta tana sauraron karatun har ta gama. Lokacin taji ana kiran Magriba, shiru har lokacin Hamma bai fito ba, ta sake isa ga kofarsa ta sake yin knocking, sai taji shiru, ta bude a hankali ta shiga sai ta ganshi akan sallaya yana barci. Aisha tayi tsaye a kansa yau tana karema Uncle kallo. “A beautiful man, with a beautiful heart” ta fada a ranta. Bata san lokacin da Hamma ya bude ido ba, sai muryarsa taji yana fadin “Aisha, yaya dai kiketa kallona?” Taji kunya sosai ta juya masa baya, tace “anyi maghrib ne, na jika shiru nazo in ga ko lafiya?” Yace “subhanallah!” sai yace mata “bari nayi wanka nayi sallah ina zuwa”. Aisha tace “toh, na gama abinci ma, inyi setting table yanzu?” Hamma yace “no, jeki yi sallah ki gama, nima wanka zanyi inyi sallah tukunna”. To sai ta koma dakinta ta shiga wanka, ta fito ta saka ‘lounge wear pink and white’ wando da riga sakakku da basu kama jikinta ba, wandon kamar pallazo amma mai taushi, samfurin ‘duvet days collection’ sunbi jikinta sun kwanta, Aisha ta saka ‘plush slipper’ na cikin gida shima pink ta zama tamkar angel don kyau, ta shafa turare mai sanyin kamshi, daman tayi jan lalle a yan yatsunta, ga gashinnan bata dade da wanke shi da steaming dinsa ba, Aisha ta jima tana shan SABAYA da Ummanta ta bata lokacin da taje gida Gombe sallama so Aisha ta kara cikowa sosai. Saida tayi sallah magrib da isha da shaf’I da wutr sannan ta fito falon, taje ta shirya table ta sake kunna oil burner na turare. Ga sanyin AC ya hade dana turaren, taje ta zauna akan 3 seater tana kallon PoloLine TV. Nenne kamar ta san halin da Prince ke ciki a daidai wannan lokacin sai ta kira Siddiqa. Siddiqah ta amsa kiran Nenne alhalin ta saka wayar a handsfree. Da damuwa a muryarta Nenne ta ce, “Aisha ya kuke? Ya Hamma din?” “Nenne yana kokari ba laifi” “yaci abinci?” “na dai gama masa pounded yam (Iyan) da Afang Soup shinake jira ya idar da sallah ya fito” Nenne tasa mata albarka, tace “ki kasance tare da Hammanku a wannan lokacin kin ji, yana bukatar mai karfafa shi da ba shi kwarin gwiwa. Na san halinsa sai yanzu ne zai soma nashi ‘mourning’ din. Ki tausashe shi, kin san yadda yake da Kakan nasa”. Aisha cikin jin kunya ta amsawa Nenne da cewa “Insha Allah Nenne zan kula da Hamma”. Bayan da idonta har lokacin bata ga Hamma din yanada alamar fitowa ba, yau dai Hamma tunda ya sauka ko Ranch dinsa bai shiga ba, ko kula Dawakan nasa bai yi ba tunda ya kama mata ta sauko daga Saheeb, komai ya fita kansa saboda rashin Sarki. Aisha bata kula da fitowarsa ba harma yana jinsu itada Nenne, daidai sanda Nenne ke fadin, “to ko zaki bishi da abincin daki? Kamar kinsan yana son Afang Soup, ki ta lallaba shi a haka har ya ware ya koma sha’anoninsa kin ji ko Aisha-Siddiqah?”. Sukayi sallama da Nenne tana ta saka mata albarka. Sai taji Hamma daga bayanta yana cewa. “toh ni baby ne da Nenne ke checking up on me haka, kuma through another baby din like you za’ayi checking up din? Lallai!” Maganarsa ta baiwa Aisha dariya sosai. Ta yi ‘yar dariya tace “saboda ta damu ne ai, nima dazu ai ka bani tsoro da naga kana kukan” Prince yace “Oh! So you are genuinely worried about me, not because of Nenne?” Aisha bata bashi amsar wannan ba, tayi murmushi ta karasa tashi tace “muje kaci abinci toh Hamma”. Ashe dankwalinta ya zame ta baya akan kujerar data tashi bata sani ba. Nan Prince yaga wani zallar bakin gashi mai laushi da sheki yana zagin idonsa. Wani abu Hamma ya hadiye a makogaronsa, kafin yayi ta maza ya zauna ya fara kwasar daddadan girkin amaryarshi Aisha. Koda suka gama cin abincin ma haka tayi ta lallabashi. Da taga ya zauna shiru zata fara yi masa hira. Har lokacin kwanciyar Prince yayi, ya mike ya na ce da Aisha. “Ko zan samu ‘yar tayin kwana? Banason kadaici yana dawo da damuwata baya, please Aisha”. Sunkuyar da kai Aisha tayi, kamar mai tunanin taje ko a’ah? Hamma ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye yana fadi cikin lallashi, “I only need your presence, ba abunda zan miki Aysha. In baki son jina ma a kusa dake ba sai na kwana akan gadon ba”. Don haka da Prince ya saka hannun shi cikin nata suka soma tafiya, sai ta kasa resisting offer dinsa. Hamma ya cika alkawari, domin kuwa Pillow ya jefa akan kilishi ya bar mata ni’imtaccen gadonsa, ba jimawa da kashe wutar da yayi barci ya daukeshi dama ga gajiya ya tara. Saida Aisha taji numfashin Uncle na sauka a nitse ta tabbatar yayi barci sannan ta samu sakuni a ranta, daga wata irin fargaba data shiga ranta a dalilin kwananta a yau master bedroom tareda Prince. Washegari tare sukayi sallar asubahi. Prince ya koma barci Aisha ta fita zuwa dakinta tayi wanka ta shirya ta koma kitchen tana hada musu abin kari. Da hantsi ya daga ma suna tare a parlor amma har zuwa lokacin fuskarsa da damuwa. Duk dai don ya daina damuwar Aisha tace “Hamma please, yau zaka fara koya min Polo”. Ya juyo with attention ya kalleta. Magana in ta Polo ce dama Hamma na sonta, don haka gladly ya amince su fara. Amma yace ‘riding’ zai fara koya mata kafin Polo. Dama kuma itada Saheeb sun riga sun saba sosai. A haka Prince ya fara koyawa Aisha ‘horse riding’, yana ajiye damuwarsa a gefe. Rana ta farko data biyu tare suka hau bayan Saheeb, don yanata koya mata amma ta kasa ganewa, saida ya hau tareda ita ya saka ta a gabansa. Rana ta biyu suna cikin yi Aisha ta kusa fadowa, Prince yayi saurin tarota da hannu daya, inda unintentionally hannunsa akan dukiyar Fulani ya sauka. Da sauri ya saki, itama kuma haka ta saki linzamin, duk suka daburce suka zamo tare daga bayan dokin. To da yake ba gudu Saheeb din yake yi ba, ga uban tausasan grass carpet sai basu ji ciwo ba. Saida suka fado ne Prince ya tuna abinda ya cafko, sai ya fashe da dariya, itama kuma haka. Ya fuske yace “to daga yau an gama, tunda fadowa zaki dinga samu muna yi”. Ya dinga tsokanarta don yayi shaking off the awkwardness. Sai bayan ya kwanta ne a daren, kafin shigowar Aisha, duk sanda ya tuno irin laushin da yaji sai hankalinsa ya tashi. Lokacin ne ya tabbatarwa kansa ashe dai lafiyarsa kalau, bai zama abinda shima yake tababar ko ya zama ba. Something strange deep down inside him is working like ignition or arousal. Sha’awa tace salamu alaykum, shiyasa koda Aisha bata zo taya shi kwana yau ba itama saboda kunyar abinda ya faru yau, shima bai je bikonta ba. A rana ta uku ma da kyar suka yi one hour ana koyon Polon, gabadaya ya zama aware of her body, da son taba ta da gangan, a wajen rike linzami da sukuwa da hawa da sauka daga doki jikinsa a gugar nata yana kara birkita shi, kamshin jikinta da laushin fatar jikinta inda duk yayi kuskuren kai hannunsa sai ya kidima shi, gabadaya Prince ya kasa gane kansa a wannan koya Polon da Aisha ta saka shi. A haka a daddafe aka yi kwana biyar ana yi. Suna kuma kwana a daki guda, amma Prince na kan pillow da kilishi rufe da duvet, ya sallama mata gadon, Aisha bata san irin faman da yake da kansa ba kafin wayewar kowanne gari. Sai ya zama Prince na Allah-Allah hantsi ya dubi ludayi wato lokacin Polo lesson din su yayi, just to have that closeness da Aisha akan Doki. Sarai ya gane zata iya riding da kanta itama kuma ta fada masa yanzu ta iya, amma yace sammm, bai yarda ba fadowa zatayi in ya barta ta hau ita kadai. Duk dai don ya samu wannan kusancin da Aisha, da dan body contact dinnan mai hargitsa duk wata nutsuwa da Prince din ya mallaka cikin dare da ido biyunsa. A sati guda da akayi ana koyon Polo Prince ya samu duk wata sha’awarsa ta da namiji ta dawo jikinsa. Aisha bata san haka ba ta koma saka lingeries da nighties din da Kiki ta sai mata. shakuwarsu kullum daduwa take yi, they have build a good bond of friendship, a satin da ya biyo baya Prince ya soma kai Aisha yawo da shopping, ita kuma ta saki jiki da shi sosai ta sake dashi kullum tana zuba masa hirar gidansu da nasu gidan, ta fito a real Aisha dinta ta Billiri mai baki zauu. Unknown to her, komi tayi kashe shi take yi da soyayyarta cikin ransa. A wadannan satittikan Prince Abdulrasheed ya gama sanin komai game da matarsa Aisha-Siddiqah. Itama kuma ta kara sanin abubuwa da yawa game da shi da rayuwarsa da zuri’arsu ta Akanni gabadaya. Ya soma kiran iyayenta a waya akai-akai yana gaishesu. Ya kuma gayawa Aisha shi ya kaisu airport ya saka su a jirgin da zai maidasu arewa lokacin da suka zo Ilorin yi musu ta’aziyyar Emir kafin dawowarsa. Dade ya gabatar dashi ga Ummanta da malam Yunus. Ba karamin jin dadin wannan labarin Aisha tayi ba. Suna cikin wannan yanayin da yafi gaban biro ya rubuta don dadinsa garesu, suka wayi gari da bakuwa a gidansu. Aisha dai Pareto ya zo ya gaya mata sunada bakuwa. Tayi mamaki. Amma tace kawai ya shigo da ita jin cewa mace ce. Prince na dakinsa yana shiryawa zasu fita lokacin da Haseenah ta shigo falon. Aisha tayi mata sannu da zuwa fuskarta ba yabo ba fallasa. Ita kuma Haseenah sai karewa Aisha kallo take, small beautiful girl, wadda ganinta yafi jinta! Irin kallon da Haseenah ke mata, da irin shigar dake jikinta duk basu yiwa Aisha ba. suka zauna shiru a falon, Haseenah bata ce mata ga wanda tazo nema ba, ita kuma taga bai yi daidai tace mata wa take nema ba. sai suka zauna zaman kurame a falon. Haseenah na kallonta da budadden ido Aisha na neman inda zata boye kanta kada wannann bakuwa da bata san ko mayya bace ta cinyeta. Sai ga Prince ya fito daga dakin sa cikin shirin fita, yana cewa “Aisha ina kika saka mukullin Lamborghini?” sauran maganar makalewa tayi a makwallatonsa, da yayi arba da Haseenah Ambursa zaune a falon gidansa. Mu karasa a littafi na hudu (4) (INA MAI TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.