AISHA-SIDDIQAH 2 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com TUNASARWA/JAN HANKALI Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba. Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa. Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu. Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde. In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi Atqaakum”. Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna. Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada. –Takori Sumayyah AbdulQadir. SADAUKARWA Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki. KIYAYEWA Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali. GODIYA DA JINJINA Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira. In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH. KAFIN MU FARA LITTAFI NA BIYU INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. -Takorinku AISHA-INDO-SIDDIQAH 2 B ada jimawa ba binciken Malam Yunus da Yayansa Malam Barau ya bayyanar musu da duk abinda suke son sani game da ko waye Engnr. AbdulRasheed Idrees Akanni, ba kowa bane sai Polo Legend “The Latest Yoruba Demon” (inji abokin aikin Malam Yunus, wani bayerabe mai suna Abdulganiy musulmi da suke aiki tare a hukumar alhazai ta jihar Gombe wanda ya san zuri’ar Sarki Akanni kakaf sani na sosai da sosai, farin sani, kasancewar mahaifiyarsa ‘yar Ilorin ce kuma acan ya girma), mutuminnan ya gaya musu nasabar AbdulRasheed da iyayensa kaf dinta, a karshe ya gaya musu Prince din babban jikan Sarki AbdulRasheed Abdullateef ne (Emir of Ilorin) na yanzu, shine na fari cikin jikoki, sannan kuma jikan Sarkin Gombe ne na baya Sarki Ahmadu Jalloh Umar. Har ila yau, an tabbatar musu da cewa Prince din baida wani aibi takamaimi da za’a ce shi ya hanashi aure akan lokaci, maiyuwuwa shahararsa a wasan Polo ce da arzikin da yake samu a jikinta suka kwashe lokacin sa da sha’awarsa daga yin aure a sanda ya dace,Abdulganiy yace don 'Polo Celebrities' na duniya irinsa aure akan lokaci na musu wahala matuka, musamman da basa zama a wuri guda kullum a tafe suke, a takaice a bakin Abdulganiy suka ji kusan komai da ya shafi Prince, suka ji cewa duka lokutan rayuwarsa na wasan tseren Doki ne a kasar Polo ta Argentina, sannan ya kan fita tournaments a sauran kasashen da ake Polo a duniya. “Babu wanda yasan hakikanin abinda ya hanashi yin aure har tsayin wannan lokacin da yake cikin shekaru na 42”. Amma koma meye, a cewar mutumin mai bada shaida bazai zama hujja na a hanashi aure ba a wannan zamanin da masu auren wurin ma ba duka ne nagari ba, don iyayensa malamai ne, mutanen kwarai, kuma sarakuna nagari. Baban Aisha ya tsorata bayan jin wannan bayanin da kuma jin su waye Akanni’s, da matsayin ita kanta Haj. Nenne Sappa a Gombe, don haka ya tuntubi iyayen Ishaq akaro na uku kenan cewa Ishaq ya kawo sadaki ya aura masa Aisha a wuce wannan gabar don ya tsorata sosai. Domin koda suka yi tsammanin Nenne Sappa a matar mai kudi kawai suka tsammaceta, ba’a diyar sarkin Gombe, matar dan sarkin Ilorin, kuma uwar dan sarki mafi soyuwa a ran Kakansa ba. Ya tuna dadewar da Ishaq yayi tareda Aisha-Siddiqah, da karfin shakuwa da soyayyar dake tsakaninsu tun farkon balagar kowannensu, don haka ya yankewa kansa cewa Ishaq shi yafi kowa cancantar aurenta, yaro matashi kamarta, wanda zai rike masa ita da daraja da kima, kada ya kaita inda bazata yi daraja ba, shi baya son auren hadin iyaye irin wannan, yafi yarda da aure na na gani inaso daga namijin kansa ba daga iyayensa ko wani nasa ba. Ishaq kadai zai iya baiwa Aisha hakalinsa ya kwanta, don shi ya san asalinta ya san halinta ya san komai na iyayenta da ciwon asmarta mai dan tashi lokaci-lokaci. Malam Yunus mutum ne marar kwadayin abin duniya kamar matarsa Zaynaba. Tabbas duniya tayi musu wannan kyakkyawar shaidar akwai wadatar zuci. Shiyasa hankalinsu ya zo daya suke zaune lafiya shekaru aru-aru ba mai jin kansu. Hankalinsa a kwance ya kira dan uwansa Malam Barau ya gaya masa komai ya yanke, sai Barau yace su wuce gidan Malam Hassan din kawai a yi komai yau a gama wato mahaifin Ishaq a yita ta kare su aurar da Aisha su huta. Shima Baba Barau ya dade da sanin duk duniya ba mai son Aisha irin Ishaq Hassan, yaron ya jima yana hidimarta da dakon soyayyarta tun shigarta sakandire, ba wani mai mulki ko mai kudi da zai rude su su yi wa Aisha auren cushe. Auren da bazata yi daraja ba ko a maidata sadaka. Nan suka mike suka je har zauren gidan su Ishaq suka tadda mahaifinsa Malam Hassan kuma makwabcinsu, suka share wuri suka zauna suka gaya masa duk abinda ake ciki, a karshe Malam Yunus yace yana son aurar da Aisha a wannan gabar, yana tsoron al’amarinta, rana daya ne ba’a zuwa a sameshi akan maganarta da manyan mutane, Aisha manema gareta bila adadin ba tun yau ba, mafi yawansu kuma ‘ya’yan manya, sannan ‘ya’yan mutunci da iyayensu ke takowa da kansu har gidansa nema musu aurenta, wadanda mutuncinsu yake sawa bazai iya tula musu kasa a ido ba saidai yayi ta togaciya da Ishaq. Yace yau gashi ‘ya’yan Sarakuna sun fara zuwa neman aurenta. Gaba kadan bai san su waye kuma zasu zo neman auren Aishar da ya dade da ajiyewa Ishaq ba. Malam Yunus din yace farin jininta yana bashi tsoro a shekarar nan data shiga ajin karshe na sakandire. Budar bakin Malam Hassan kasancewarsa irin mutanen nan da basa tauna magana ko kadan kuma basu da kawaici akan ‘ya’yansu musamman in suka lura yaran nama mace mugun so, sai yace da Malam Yunus da dan uwansa Kawu Barau. “ku gafarce ni Barau da Yunusa, domin dai ni na dade da yiwa Ishaq mata a cikin dangin mahaifina dake kauyen Nafada, maganar gaskiya kawai kallonsu muke yi tuntuni (Aisha da Ishaq din) nida mahaifiyarsa, shiyasa tun da farko da ka tuntubeni watannin baya kan batun aurar da Aisha nayi shiru ban baka cikakkiyar amsa ba. Amma zuwa yanzu ba zan boye maka ba Ishaq ya jima da samun mata daidai da ra’ayinmu”. A karshe yace “bazai aura ma Ishaq (mai ciwon numfashi) ba, kamar aka ce mata sun kare a duniya, don Asthma ana gado, kuma (allergy) ne a cewarsa. Yace kuma shi za’ayiwa barazana da sarakuna da masu kudi don a takura shi tashi tsaye yin aure bai shirya ba dansa ma bai shirya ba sabida ka gaji da sayen inhaler da maganin Asma da yawon kwanciya a asibiti? Yace to ba sarakuna ba Barau da Yunusa, ko dan shugaban kasar Najeriya ne yazo neman aurenta na lamunce ka aurawa diyarka damuwarku ce. Ishaq yanzu yake kokarin hada hidimar kasa, baida halin aure a yanzu. Shiyasa na nema masa yarinya ‘yar shekara goma sha daya wadda zata yi daidai da zabinsa da namu”. Wannan magana ta fusata Malam Yunus da dan uwansa Kawu Barau, ta kuma bakanta ma Barau rai ba kadan ba, kasancewarsa mai saurin fushi da yawan harzukar zuciya a kusa, sukayi shiru shi da kaninsa Yunusa zaune akan tabarma a zaurensu Aisha. Barau tun fil azal mutum ne mai saurin daukar zafi akan ‘ya’yansu, sabida ko a cikin ‘ya’ya takwas maza da mata da shi yake dasu a gidansa manya da yara, tofa yana ji da Aisha-Siddiqa a cikin yaransa, kasancewarta daya tilo da Allah ya barwa dan uwansa, kuma duk rashin kwaramniyarta da kazarniyarta irin na sauran ‘yammata yana son dabi’unta. Bayan sun baro soron Malam Hassan Kawu Barau ya samu wuri ya zauna a zauren gidan su Aisha, ya dubi dan uwan nasa Yunusa da idonsa ya kada, yace “bayerabe ne kace dan ita Hajiyar Lagos din ko me? Kuma ya jima bai yi auren fari ba? Sannan ba’a kasar nan yake rayuwa ba gabadaya kuma dan wasan Polo ne shiyasa kake tababar bashi auren Indo ko?” Malam Yunusa ya gyada kai. Sai Kawu Barau yayi kuta yace. “To gara shi sau dubu akan zuri’ar wannan marar karar makwabcin naka daka kwallafawa rai, da bai san mutunci da kara ba, kamar ba bafullatanin mutum ba, na bi kabilanci da gudu na kamo shi na kawo cikin zuri’ata”. Nan take Kawu Barau ya shiga cikin gidan ya gayawa Haj. Zainab ta gayawa kawarta Haj. Sappa take ko Safiya? Duk sanda suka shirya su turo an basu auren “Aishatu-Siddiqah Yunus”. Kawu Barau yace cikin bacin rai, “ba Bayerabe ba ko dan sarkin Nufawa da Agalawa ne Dan nata, a gaya musu ya bashi Aisha. Tunda har uwarsa da kanta tazo ta durkusa a gabanka har da hawayenta tana rokon a basu auren Aisha sabida kauna, cikin darajawa da mutumtawa irin haka ba tareda la’akari da matsayinmu ba, alhalin ita ta san da Asmar Aisha, don haka shi ya basu Aisha-Siddiqah ko dan nata yayi saba’in a duniya ba arba’in da ‘yan kai ba, koda kansa fari fat ne yana dogara sanda don tsufa an bashi, in yaso Aisha ta yi zaman zuba ruwa a buta da kai masa ruwan wanka bayan gida, wato (tayi zaman kula da tsufansa ba zaman soyayyar miji da mata ba)”. **** **** **** R anar da Nenne Sappa ta koma Lagos tareda Aisha ta sauka a gidanta a Banana Island da tsakiyar marece, Aisha rike da ‘Handbag’ din Nenne tun daga Gombe ta riko mata, duk da bata son tafiyar kuma hakan ya kasa boyuwa a fuskarta duk yadda Nenne ta dinga kokarin daukar hakalinta da hira cikin fulatanci don dai ta saki jiki da ita, amma har suka sauka a Lagos kalaman Aisha a matsayin amsa basu fi biyar ga Nenne ba, haushin ta rabo ta da Ummanta ya ki barin ranta, tana dai kula ma Nenne da jakar hannunta da kan wayoyinta uku bata bari ta yi dakonsu ba, yadda take Ummanta in zasu unguwa ko ta rakata asibiti, suna isa gida ko hutawa Nenne bata yi ba ta kama hannun Siddiqa zuwa cikin gidan, babu kowa zaune a babban falon kasa sai talbijin dake ta aiki ita kadai cikin tashar kasar Yemen, barorin gidan dake giftawa kowa naaikinsa sunata russunawa sunama Nenne barka da sauka, tun daga fitowarsu a mota (Venza) da direba ya dauko su daga filin jirgin Murtala Mohammed har shigarsu ainahin kwaryar cikin gidan Engnr. Idris Akanni Aisha taga ma’aikata sun kawo gaisuwa sun kai su biyar, kai tsaye Nenne ta wuce rike da hannun Aisha-Siddiqah har dakin “Princesses” yadda take kiran (Firdausi da Fatima). Princess Fatima na kishingide a gado rike da wayar ta tana Magana da fiancé dinta Abdulganiyu Dasuki, yayinda Firdausi ke stretching gashin kanta da na’urar tazar gashi Nenne ta tayi sallama a kansu, Siddiqah na biye bayanta, Fatima ta kashe wayarta da sauri cikin murnar dawowar Nenne lafiya, Firdausi ta dago kai da murmushi suna amsa sallamar mahaifiyarsu da murna fal a fuskokinsu kafin su kula ba ita kadai bace, wata siririyar kyakkyawar yarinya mai ruwan ‘yan Gombe biye a bayanta, Nenne tace “shiga daga ciki ki huta kinji ko Siddiqah, Fatima a hada mata ruwan wanka, diyata ce na taho da ita daga gida (Gombe), ku kula min da ita da kyau, kamar yadda kuke kula da Ruqayyat (tana nufin Kiki), kafin a gyara dakin da zata sauka, zan shiga inga Dade, ina fitowa zuwa anjima”. Princess Firdausi da Princess Fatima suka dubi juna fuskar kowacce fal curiousity, sun sha mamakin inda Nenne ta samo ‘yar kyakkyawar bafullatanar yarinya haka. Kodayake tace daga gida Gombe take. Saidai basu santa cikin dangin Nenne ba kaf. Bata sauraresu ba da tarin tambayoyin data gani fal fuskokinsu ta wuce turakar mijin ta tana gaya musu cikin harhen yarbanci “su tabbatar Aisha-Siddiqah (feel at home) wato su tabbata ta saki jikinta dasu. Baba na faman aikin nasa na karatun jarida wanda ya zame masa lazim kullum tun bayan ritayarsa, Nenne ta zauna a kusa da shi cikin gajiyar tafiya bayan ya amsa sallamar ta ya kum a ajiye jaridarsa a gefe. Kallo daya Baba Engnr. Idris Akanni ya yi mata ya ga farin cikin da bai taba hangowa cikin idanunta ba. Tun kafin yaci abincin data shigo masa da shi ko suyi doguwar gaisuwa yadda suke yi idan dayansu yayi tafiya Nenne ta kasa jinkirta abinda ke bakinta. Ta gayawa Baba, ta samowa AbdulRasheed aure a Gombe. Engnr. Idris Akanni ya dago manyan idanunsa daga kan jaridar dake hannunsa yana duban matarsa Hajiya Sappa a hankali cikin nutsuwa, wato yana mata irin kallon nan na kodai tayi gamo ne? prince din zata ganowa mace? Shi baida idon gano matar data dace dashi a shekaru irin nasa sai an gano masa? Shi Engnr. Idris Akanni Waziri of Ilorin ya riga ya sakawa ransa Prince baida ra’ayin aure ne kawai shiyasa baya shiga sha’anin maganar auren da kowa ke yi a kansa kamar shikadai suka haifa, afterall sunada ‘ya’ya masu yawa a family dinsu da suka tara musu jikoki fal, maiyasa kowa zai damu kansa da Abdulrasheed shikadai? a rayuwar Idris Akanni shi bature ne baya shiga rayuwar kowa hatta ‘ya’yansa ya basu dama suyi abinda suka tsarawa kansu da wuya kaga ya shiga rayuwarsu daga lokacin da suka haura shekaru sha takwas. Don haka cikin yanayi na I don’t care attitude dinsa na halitta yace da Nenne “diyar wanene kika samo masa din? ‘Yar wace masarauta ce? Kinada tabbacin Abdulrasheed zai karbi zabin ki tunda ba wai mata ne baya gani ba a duniya? Me kika gano haka har ke da kanki yau kika zabi ki tafi nemo masa aure alhalin ina raye haka kannena maza? Amsar da Nenne ta bashi yai matukar saka shi bude ido sosai yana kallonta da mamaki don tace yarinyar bata da alaqa da sarauta. Har ila yau ya dauka ne zata ce a cikin danginta ta samowa Prince mata, tunda an zaga ta bayan fagge ance dashi Nenne ce ta daure gindin kada Abdulrasheed ya karbi mace a ‘ya’yan ‘yan uwansa wato jikokin Emir. Lokacin da akayi wancan zaman dashi yayi kuskuren cewa zai fadawa Nenne amsa ta zo ta fada musu. Daga lokacin ya gudu Qatar bai kara zuwa gida ba, sunata jira Nenne ta zo musu da gamsashshen bayani daga bakin Abdulrasheed akan zabin da suka bashi har gobe shiru. Baiwar Allah Nenne, bata ma san Abdulrasheed ya saka sunanta cikin maganarsa da kannen mahaifinsa ba a lokacin ta tafi aikin Hajji. Nenne ta kwantar da kai da murya a gaban Dade, ganin kamar cikin gatse yake mata magana. Mai bi masa wato Turaki ya masa famfo ba jimawa cewa Nenne ce ta hana danta Abdulrasheed karbar ‘ya’yansu. Sabida ta fi so ya auro daga nata dangin. Nenne bata san an yi haka ba. Tana zaune daidai kafafun maigidanta shikuma yana bisa kujera. Ta tankwashe kafafunta ta duka a gabansa (yadda take yi masa in zata yi masa magana mai muhimmanci), cikin girmamawa ta ce da shi. “Ba komai na gano ba Your Highness, ban ga sarauta ba, kuma ban ga tarin arziki ba. Na gano ma Abdulrasheed mace daya cikin dubu da na dade ina roka masa wurin Allah, irin wadda ta dace dashi ne, wadda zai matukar so fiye da komai na jin dadin rayuwarsa duk da gudun matan da yake yi. Yarinya karama wadda ta fito daga tsatson mutanen kwarai masu tarin halin kirki da nagarta. Na samo masa mace wadda ta samu tarbiyyar Uwa da Uba a tare, kwarai da gaske mai tarbiyya ce, wadda nake da yaqinin zata zauna da shi da zuciya daya ta taiamaka masa wajen gyara duniyarsa da lahirar sa. Zai zama cewa ta raba gardandamin auren zumunci da aketa so yayi daga kowanne bangare nawa da naka. Inada tabbacin Aisha Siddiqah ce kadai ta dace da zama (first wife) kuma uwar iyali ga Abdulrasheed ba tareda yawan shekarunsa ya dameta ko yayi sanadin kawo mishkila a aurensu ba. Sannan in akayi duba da kankantar nata shekarun sai naga cewa zata iya da halinsa da yi masa kowacce irin biyayya. Iyayen Siddiqah mutane ne dana dade banga irinsu ba, warin gudun duniya da tsoron Allah da tsayawa a matsayinsu. A takaice Dade naga duk abinda nake nema a suruka da surukai daga Siddiqah da iyayen da suka haifeta wanda shi yasanya ni kwadaitarwa Abdulrasheed aurenta, da fatan Barewa bazatayi gudu dan ta yayi rarrafe ba”. Nan ta kwashe komai na haduwarta da Haj. Zainab a filin Munna, da yadda ta tsinci Dollars din guzurinta ta kuma maido mata su cas a yadda ta tsince su, tace wanna shine babban abinda ya burge ni da mahaifiyarta, sannan kamanni na halitta da halayyar Siddiqah bakidaya yayi mata irin na mahaifiyarta, tana kwadaitarwa Prince samun wannan tsatson mai albarka. Sannan a surar Aisha ma bata jin AbdulRasheed zai kushe ta matsayin matarsa, tace saboda Aisha kyakkyawace shikuma aduniya yana son abu mai kyau. Duk da ake masa kallon wanda baya son mata tace zata gwada sa’arta akan Siddiqah. Tace saidai idan dansu Prince Abdulrasheed ba namiji banemai cikakkiyar lafiya. Nenne tace daga ganinta na farko da Siddiqah taji a jikinta ga matar Prince Abdulrasheed Allah ya nuna mata yau a zahiri, tace komai na yarinyar yayi mata shige dana yarinyar datake gani a istikhararta ta koyaushe, fuskar Siddiqah ta dade tana gani a cikin mafarkin ta, a matsayin matar Prince AbdulRasheed. Diyar dattaku da mutunci”. Haka dai Nenne tabi ko ta ina ta daddaure Babansu Taiwo, ya ji shi da kan shi yana son ahalin Haj. Zainab dinnan, wannan halin amana data nuna wa matarsa a wannan zamanin da muke ciki yayi matukar impressing dinsa. Ya dade bai ji hakan a kan mutanen arewa ba, kowa dai yaki halak-yaki haram saboda talauci. Dade Engnr. duk da haka bai amsa mata dari bisa dari ba, yace ne ta bashi lokaci yayi nazari sannan yayi shawara da Emir da sauran ‘yan uwansa. Ita kanta ta san Dade shikadai bai isa ya zartar da komai akan auren AbdulRasheed ba tareda amincewar Sarki da sauran ‘yan uwansa ba. ta gaya masa ta taho da yarinyar zata yi mata hutun sati daya, sai Dade yace da Nenne ta raka shi ya ga yarinyar da kansa. Baba da Nenne suka taho dakin Princess Fatima, inda Nenne ta baro Aisha-Siddiqah tun shigowarsu gidan. Siddiqah tayi tagumi a gefen gadon Princess Fatima (looking uneasy), cikin damuwa take sosai jin ‘yammatan gidan na Yarbanci, wani yare data tsana kuma bata son ji ko a makaranta, Yarbanci shine yaren data tsana fiyeda kowanne yaren al’ummar Najeriya sabida jinsa take a kunnenta kamar fada, ita kuma bata son fada da hayaniya ko kadan. Ko Ummanta ta sani Siddiqah bata shiri da bayeraben mutum a duk inda ta ganshi. Kai ita ko a makaranta bata kawance da ‘ya’yan yarbawa. A yau sai ta tuno da BISOLA! Akan kunnenta Princess Firdausi tace da Princess Fatima “Mi o mo ibi ti Nenne ti ri omo Fulani to rewa bayi. O ma’n fi oju kekere wo eyan”. (I don’t know where Nenne got this beautiful Fulani girl, she keeps looking at people with her small eyes - ma’ana; bansan ina Nenne ta samo wannan ‘yar kykkyawar bafulatanar ba, sai kallon mutane take da kananan idanunta masu kyau kamar almond)”. Princess Fatima ta dan saci kallon Siddiqah daga kwance, cikin ginshira irin ta ‘ya’yan sarakuna tana daga kwance akan gado tace “O jo ora oko ti ko ri itoju gidi (she looks local and unhealthy) wato da ganin ta mara lafiya ce kuma ‘yar kauye”. Aisha-Siddiqah taji hawaye ya surnano a idonta, tace a ranta “Oh ni Siddiqah! Umma ta san gidan Yarbawa ta turo ni? Ina zaune suna zazzagina da Yarbancinsu…… Wallahi bazan zauna ba sai an maida ni gida.” Sai hawaye data keta rikewa ya digo, dis-dis a saman kundukukinta tayi kasa da kai tana tsanewa da gefen mayafinta. Kyawun gidan, da alatun data gani cikinsa, da irin daular dake cikin sa wanda ko a talbijin bata taba gani balle a zahiri bai ko dadata da kasa ba, hasalima bata lura da komai ba hankalin ta yayi mugun tashi ya tattara ya koma gidansu a Jeka da Fari. Damuwarta yafi karkata ga yaren yarbanci da taji a bakin jama’ar gidan ba babba ba yaro, kowa da kowa, har ma'aikatan gidan, wanda tun farko ba shi ta ji a bakin mahaifiyarsu Haj. Sappa ba ai da kome Umma zatayi mata da bata yarda ta biyo Nenne Sappa ba Ga Siddiqah da dan banzan kabilanci a zuci. Ko bahaushen mutum bai cika mutum a idanun ta ba, balle Bayerabe, in dai kai ba bafullatani bane Siddiqah wani ganin daban take maka. Tun suna yara da ta ji ana waka ana cewa “Yarbawa masu kashi a kwano" to fa tun daga lokacin Siddiqah tasa a ranta duk Bayeraben mutum kazami ne. Ita a duniyarta da zuciyarta tana da kabilanci, data dade da gina zuciyar ta akai, na jin cewa kabilarta ta Fulani tafi kowacce kabila, tana ganin Bayeraben mutum kamar wani ‘alien’ ko wani na daban a cikin mutane sabida yarensa. Princess Firdausi ce ta lura da tsurewa da tsoron da ya samu Aisha a idanunta, amma bata san me ya kawo shi a tareda Siddiqa ba, sai taga jikinta na 'yar kyarma wanda bata ga dalilin sa ba. Ita kam Aisha-Siddiqah kawai yaren da suke yarawa ne ya tayar da hankalinta ya dugunzuma ta don ta gama sawa a ranta zaginta suke faman yi da yarbanci suna mata kallon raini wanda a zahiri ba haka bane yanayin kallon Firdausi da Fatima ne haka kaga suna kallonka daga kasan ido kamar suna harararka kasancewar sunada dara-daran idanu. Inda Allah ya taimaketa kafin su sake yin yarbancin dake barazanar saka ta ciwon kai, sai ga Nenne ta shigo tareda Babansu Taiwo wato da Dade Engnr. biye a bayanta. Nan Siddiqa ta ga ‘yan matannan biyu duk sun nutsu matuka, itama sai ta fara kokarin nutsar da kanta daga firgicewar ta. Amma idonta yayi kozai-kozai. Nenne da murmushin kaunar ta da Siddiqa tace “Aishan Nenne mutanen Lagos, yaya bakunta? Ga Babanku yazo don ya ganki”. Hawayen sabon tashin hankali ya kara digowa daga idon Siddiqah data gane Bayerabe ne mijin Hajiya Sappah shima. Kenan ita Nenne din kadai ce ba bayerabiyar ba a gidan? Haka zata zauna cikin Yarbawa kwana da kwanaki? Sai ta cije lebenta kamar 'yar goye, tana binsu da Ido ta kasa cewa komai. Amma tayi tunanin yakamata ta gaida Dade ko da ba zai gane nata yaren ba. Ta duka tana gaisheshi cikin Fulatanci, da matukar girmamawa cikin dari-dari don ta dauka baya jin ko alif a nata yaren, kamar yadda itama bata jin nasa ba kuma ta fatan ta koya. 'Yar dariya ta kama Engnr. Akanni. Kasancewar yana jin fulatanci suwayya-suwayya (kadan-kadan), ya kuma gane yanayin data ke ciki na kin sakin jiki dasu kamar ace kyat! Ta zuria da gudu zuwa Gombe, suka yi mata dariya gabadayansu ganin irin tsugunon data yi a gaban Dade ta kasa dagowa, dariyar su ta kara dugunzumata, don dai ita bata ga me ta fada abun dariya ba bayan gaisuwa. Ga mamakin Siddiqah sai taji Engnr. Idris Akanni yace “Calm down Aishah, feel at home kinji, zan hana su yin yare in kina zaune, ya kika sauka a Ikko kuma ya kika baro mutanen gida a Gombe?” Ya Karasa da Hausa. Wata wawuyar ajiyar zuciya Siddiqah ta ajiye, at least Uwar da Uban su sun iya Hausa. Kuma zasu hana a yi mata yaren oduduwa a kunne. Ta sakko daga gefen gadon tana gaida Baba da ‘yar karamar muryarta. Gaisuwa irin ta al'adar mutanen Gombe. Nenne ta dago ta daga gaisuwar “ina wuni?” Don ba haka ake gaisuwar al’adar Ilorin a gidan ba. tace a ranta coaching na musamman zata soma yiwa Siddiqah akan ala’adun gidan. Baba Engnr. na observing komai na Aisha a fakaice, sai ya tuna da sanda aka kawo masa Nenne Sappa gidan sa a matsayin matarsa, haka take ‘yar tsurut kamar Aishah duk ta rikice a cikin danginsa Yarbawa, lokacin itama bata wuce girman Aisha din ba sai tsantsar kyau irin wanda mazan Yarbawa ke matukar so daga matan Fulani (kyau da farar fata). Dade ya tambayeta makaranta, ajinta nawa? A hankali cikin nutsuwa da sanyin murya Siddiqah ta gaya masa aji shidda wato ajin karshe zata shiga da zarar an koma hutun nan. Dade bai jima tare dasu ba yayi musu sallama cewa zai fita kuma zai kai dare bai dawo ba kada su jira shi cin abincin dare. Waziri Idrisu ya fita da gamsuwa sosai da zabin da Nenne Sappa ta yiwa Prince Abdulrasheed. Zai iya cewa shigen nasa zabin ne da mahaifinsa Sarki Abdulrasheed yayi masa. Banbancin shine Siddiqa ba ‘yar sarauta bace ba ‘yar kowa ba. Bai san yaya akayi ba zuciyarsa dari bisa dari tayi na’am da zabin matarsa “Aishah-Siddiqah Yunus”, ta zamo musu suruka, mata ga tauraron zuciyar zuri’ar Akanni’s kuma tilon Dan sa namiji a duniya Prince Abdulrasheed (Kehinde). Firdausi ce tayi waya kitchen wa Femi, shugabar kukun gidan bakidaya, inda ta ce mata maza a shirya abinci yanzu, Nenne nada bakuwa daga Gombe tun zuwansu bata ci abinci ba, Nenne ta raka Dade har ma’adanar motocinsa ya fita, sannan ta dawo ta tarar Firdausi ta saka an shirya musu abincin rana a dining. Don haka ta hutar da ita wucewa kitchen wajen su Femi, ta dawo ta samesu a ‘dining area’. Princess Firdausi ita ta jagoranci Siddiqa zuwa ‘dining room’ dinsu. Bayan ta fito daga wankan data sata tayi. Ta bata sabuwar doguwar riga cikin kayan da niece dinsu Kiki ta bari a gidan tace ta saka kafin a wanko nata, ganin cewa Siddiqah bata fice sa'ar Kikin ba, tsayinsu ma zai zo daya da Kiki, kiba kawai Kiki Ruqayyat ta fita. A idon Firdaus sai taga kamar duk kayan Siddiqa masu datti ne. Don haka ta hada duk kayan da Siddiqah ta zo dasu tace Femi ta tafi dasu BQ ta wanke ta goge mata kayan bakidaya sannan ta dawo dasu, tace da ita da fulatanci “duka kayan naki ba guga ba saiti”. Wannan abu bai yiwa Aisha-Siddiqa dadi ba, don harda kayan sallahnta na bana a ciki, sauran kuwa duk kure adakarta ne atamfofine masu kyau da daraja daidai karfin Ummanta, cote d’voire ce da glitter da kuma atamfa ‘yar Ghana, amma sarkin fi'ilin gidan wato Princess Firdausi tace basu da saiti ba karin guga bayan sunfi wata uku a wanke a goge a kasan akwatinta na gida, tana makaranta shiyasa ba wani sawa take yi ba. Amma maganar da Firdausi tayi da fulatanci maimakon Yarbanci yasa taji dadi bat ace komai ba tunda Dade ya hana Firdausi da Fatima yin Yarbanci a gaban Siddiqah ganin yadda take muzanta in ana yi, sai suke yin turanci ko fulatanci, don da gaske Hausa bata wani zauna a bakinsu ba, don haka taji sanda Firdausi ta ce da Femi a kaisu BQ a wanke a goge, sai akayi sa'a ‘yan maganar Siddiqah basa kusa bata ce abar mata kayanta ba yadda taso fada tayi shiru, suka wuce zuwa dining tana bin bayan Firdausi. Nenne ta nuna mata kujerar gefen damanta tace ta zauna, haka ta zauna a dofane, ta ga ma’aikatan kitchen din wadanda duk mata ne dake kai kawo a gabansu suna aje akusan abinci duk tumatuman yarbawan Lagos ne, suna aje abubuwa suna juyawa suna kada bombom suna badeta da warin jikin yarbawa. Ko motsi wannan da kyar Aishah ke yinsa a ‘dining room’ din, don ita kam tasha jin ance jikin yarbawa body odour dinsu daban ne dana hausawa ba tun yau ba, ga Nenne ta cika gida dasu sune duka hadimanta ba bahaushe ko bafillace ko daya, ta riga ta saka ma ranta duk Bayerabe nada warin jiki daya banbanta dana hausawa da fulani, shiyasa har zuwa lokacin a darare take dasu kuma a kyankyame, ita dai a ranta kawai so take ta bude ido ta ganta a dakin Ummanta a lungun Jeka da fari, amma abu ya gagara, don haka ta zama rakumi da akala sai yadda Princess Firdausi tace tayi kawai take yi bata umh bata umh umh. Duk bakin nan na Aisha ya kama kansa a gidan Engnr. Idris Akanni musamman data lura babu hayaniya a gidan sam. Wannan abincin dai da aka zauna cinsa tare da Siddiqah, wadda a rashin saninta ta zauna ne a kujerar da Prince Abdulrasheed ke zama gefen a Nenne, kasancewar kujerun dining din a kirge suke iya jama’ar gidan kacal, sai ko ta Hakeem da Kiki ‘ya’yan Taiwo, wadanda suna cikin iyalin gidan, ko kwakkwarar loma uku Siddiqah bata yi ba, ta fada a ranta ita bazata iya cin abincin da tumatuman Yarbawan nan suka girka ba. dama dai Nenne ce tayi shine zata ci. Ta san yarbawa suna cin dodon Kodi da Qaguwa (shrimps). Duk yunwar data ke ji haka ta hadiye abarta, data tuno Dodon kodi da Qaguwar da yarbawa ke ci a cikin abincinsu, ta na juyawa kuwa ta yi ido biyu da Fatima ta cako katuwar shrimp da fork ta kai bakinta, tana shirin kurbar ruwa a tambulan don toshe yunwar dake addabarta wanda ba abinda yake mata sai kara kulle mata ciki, duk idanunta sun fada cikin lungu, Fatima na tauna ‘shrimps’ dinnan cikin taunarta ta gayu da yanga Siddiqah ta ji ta kware jikake “kat!” Da ruwan data ke sha, amai kuma ya zo mata gabagadi. Da sauri ta kai tafin hannunta ta toshe bakinta, idanunta fal! Kwallah! Dukkansu ba wanda ya lura cewa bata cin komai sai Nenne, ba kuma kowa ya lura da halin takura data ke ciki a a baka da zuci ba sai Nenne, wadda duk wani motsinta tana ankare ta gefen idonta har aman data kunso ta cika bakinta dashi. Kasancewarta Uwa mai tsananin kula da mood din ‘ya’yanta. Abincin da Siddiqah ta tsana a duniya (bakar Amala) ne aka yi da kuma lafiyayyar sakwara dakan hannu (pounded yam) da taji kirbin tabaryar Femi tayi laushi lubus da miyar ganyen Ugu da taji kaguwa da ganda zuqu-zuqu da naman Tolo-tolo wannan shine (favourite food din Dade) kuma don shi aka yi, in har yana gida to abincinsa kenan, duk da yace ba zai dawo da wuri ba a fitar da ya dan yi sun zuba a ma’adanan abinci (food warmers) sun ajiye masa nasa. Amma Siddiqah ko loma uku kwarara ta kasa, kuma ko sha'awa abincin bai bata ba, duk haduwar abincin da bajintar Femi wajen iya abincin yarbawa na alfarma, itafa komai na bayerabe bai burgeta, a wani bangarenma kyankyami abincin ya bata. Ba dadewa tun ba’aje ko’ina ba Nenne ta gama karanto matsalar Aisha-Siddiqah da zaman gidan (kabilanci) ne da ita, da belief din cewa kabilarta sama take data kowa, abinda masana zamantakewar dan adam ke kira ethnocentrism (feeling na cewa kabilarka tafi ta kowa daraja) irin wanda itama tayi fama da shi a farkon zuwanta cikin zuri'ar Emir Abdulrasheed Akanni, wato royal family na masarautar Ilorin. Banbancinta da Aisha-Siddiqah ita ko a lokacin data zo bata kyamaci abincin Yoruba ba, dagewa tayi ta koyi ci, kai komai nasu ma kokari take tayi adopting cikin dan lokaci with great passion, saboda soyayyar mijinta Engnr. Idris Akanni data yi wuf da ita lokaci daya, sabida karamcinsa da bala’in iya tattalin mace da nuna soyayyarsa karara gareta. Murmushi Nenne ta yi. Zuciyarta tayi tsalle ta tafi ga hasko mata ranar da za’a kai Siddiqah gidan Prince Abdulrasheed a matsayin matarsa. Ashe kuwa kallo na gaba, in dai haka Siddiqah ta dorawa kanta kabilancin kabilar Yoruba babu gaira babu dalili. Ko yaya Siddiqah zata ji ranar da aka sanar da ita Bayerabe dinne abokin rayuwarta na har abada toh? Bayeraben ma jikan sarkin Yarbawa, shi ne zai mallaki komai nata da take tinkaho na Fulani ne? Murmushi sosai Nenne tayi a lokacin, tana hangowa idanunta Siddiqah da Abdulrasheed a matsayin mata da miji. A cikin ranta tace “Aishatu-Indo Siddiqah! Ina jiye miki ranar karyata kai. Ai saidai Allah ya taroki tunda kin fado komar auren Bayeraben mutum. Tuni zaki mance da shirmenki da ethonocentrism dinki, domin su din maza ne na daban da suka fi kowacce kabilar Najeriya son matansu, iya soyayya da iya kula da bukatunsu da tattalin macen da suke aure. Ba jimawa na tabbata zaki manta da kabilancin, da zarar kin fada hannun Bayeraben miji. Nayi fin wanda kikayi a baya, kuma gashi na cika masa gida da zaratan ‘ya’ya na soyayya. Ta san dai nan bada jimawa ba komai zai kasance tsakaninsu cikin yardar Ubangiji wato tsakanin Prince da Aisha tunda har Dade yayi na’am da Siddiqah. Dama shikadai take fargabar amincewarsa. As long as ana tare da ita kuma, yau da gobe, koda bayan auren ta da Prince da kadan zai goge mata hadda, Siddiqa zata kai ga fahimtar babu mutane masu dadin mu’amalar aure da tsafta da gayu da son uniqueness da iya tafiyar da mace irin Bayeraben Najeriya! Don haka koda ta tsame hannu tace ta koshi, Nenne bata ce komai ba, ta tashi a hanzarce ta koma dakin da aka sauketa duk suka bita da kallo, kai tsaye toilet ta nufa ta tofar da aman da ya cika mata baki ta wanko bakinta ta fito, nan ta tarar an kawo mata kayanta da aka wanko aka gogo dukkansu, da wasu ma da a saninta ba nata bane, a rashin saninta dakin hutun Kiki ne dake daura dana su Fatima aka gyara mata. Nenne ko ta ji ba dadi da abinda Sidiqah take yi bazaka gane hakan a fuskarta ba, kasancewarta mai iya zama da mutum da duk wani halinsa da tafiyar dashi da halinsa, bin bayanta tayi bayan ta dauki madarar shanu (fresh milk) mai sanyi a firji da sinkin shawarma mai zafi da aka gama gasawa yanzu-yanzu ta bita dasu har dakin Kikin. Tun daga bakin kofa Nenne ta hangota ta shige cikin bargo ta takure ta kudundune, ta san yunwa take ji, yarinya sai kafirin kabilanci. Watakila kuma AC da aka kunna ce ta matsa mata ba kadan ba, don haka sai jijjiga take yi a ita kadai cikin bargo. Nenne ta tsorata, data tuna Siddiqah nada (Mild Asthma), da sauri ta karasa ta kashe iya kwandishin din, tana yi tana fada “wa ya ce a kunnama Indo AC?” Ta zauna a daidai kanta ta dora hannun ta saman goshin Aisha da har ya soma daukar zafi. Cikin dabara irin ta iuyaye da son nuna bata san halin da take ciki ba take magana. “Aisha lafiya kuwa? Meyasa baki ci abinci ba? Ina kula fa tun isowarmu baki ci komai ba sai ruwa, so kike in maida ke gida da ulcer kuma nida na dauko ki neman lafiya daga wata cutar?” Kasancewar Siddiqah frank, irin yarannan ne dasu ba za'a kirasu 'yan fari ba don wauta, sannan su ba auta ba sabida rashin iya rufe maganar dake cin ransu, a zahiri Siddiqa bata iya boyewa Ummanta abinda ke damunta komai girmansa, sai ta ke ma Nenne kyakkyawan zato na cewa in taji damuwarta zata fahimce ta, zata yi mata uzuri tunda ita `babba ce kuma bafullatana ‘yar uwarta, ta kuma lura Nenne nada kulawa a kanta, ga yunwa ta gama jigata ta don hanjin cikinta rawa yake amma bazata iya cin abinci mai qaguwa ba, don haka tsakaninta da Allah tace. “Umman Lagos wallahi bana iya cin abincin Yarbawa. Inada kyankyami, nayi kokari inci na kasa”. Wannan magana sai ta sauka a kunnen Princess Fatima data doso dakin neman Nenne, abin ya daure mata kai ya kuma bata mamaki sai ta dakata kadan don son ta fahimci me Aisha ke nufi, duk da ba halinsu bane labe, amma maganar ta doketa, me yarinyar ke nufi da abincin kabilar yarbawa din? Ita bata taba jin maganar da bata yi mata dadi makamanciyar wannan ba. Nenne tayi murmushi mai tafe da dariya tace “Siddiqah ho!” Duk da taji ba dadi a ranta musamman da burinta akan Siddiqah din na ta tallafi rayuwar Prince ya fado mata a rai, da irin alherin data keson kullawa a tsakaninsu, sai kuma gashi Siddiqah data zaba masa matsayin mata ta nuna kiri-kiri a matsayinta na Hausa-fulani kyamar kabilarsa take yi gabadaya, (which means) har shima bazai tsira ba daga wannan kyamar da kyankyamin ba kenan. Ta tuna yadda akayi ta kace-nace a danginsu lokacin da marigayi mahaifinta Sarki Ahmadu Umar Jalloh ya kawo batun aurar da ita ga Dan sarkin Ilorin, ba karamin opposition aka samu ba a lokacin don dai Sarki mai magana daya ne kuma ya isa da kowa dake karkashinsa amma hatta mahaifiyarta Nani Oummana bata so, bazata manta da statement din Oummana a lokacin ba “ka rasa wanda zaka baiwa Sappa sai Bayerabe?” ta rasa wane irin kabilanci bahaushe/bafullace ke da shi akan Yarbawa. Wanda su yarbawan a garesu ba haka bane suna girmama kabilar Hausa-fulani. Nenne sai ta wayance cikin lallashi da tsokanar Siddiqah tace, “Ha’an, kamar yaya ba kya iya cin abincin Yarbawa Aisha-Siddiqah?!” cikin hawaye dake tsatstsafowa tace “saboda qaguwa (shrimps) da aka zuba a miyar” “haka ya kamata kice, ba kya iya cin shrimps, amma ba bakya iya cin abincin yarbawa ba, this is sheer discrimination! Shin Siddiqah Bayerabe ba musulmi bane? To idan Allah yayi ikonsa kika auri Bayeraben mutum fa, kamar yadda nima na aura tun ina kankanuwa ba tare dana shirya kona zaba ba? Yaya zakiyi idan hakan ta faru dake tunda aure babu inda baya kai mace?” Saddiqah ta zaro ido cikin tsoro da firgicin maganar Nenne abin gwanin ban dariya ga wanda ya gani, sannan ta saki hawayen data ke maqalewa suka dirgo akan kuncinta tace “kuma kika yarda kina bafullata aka aura miki Bayerabe?” Wannan Magana ta kara rikita Princess Fatima dake tsaye tana jinsu. Aisha bata yi shiru daga wannan ba ta kara da cewa “Ni dai Umman Lagos ki tofar da miyaun bakinki, Umman Lagos kada kiyi min baki, indai akaina ne kinyi babban sabo kada Allah ya hada ni da miji bayerabe….. (iya abinda Princess Fatima ta iya jure ji kenan ta juya da sauri zuwa dakinta. Tun daga wannan ranar kiyayyar Siddiqah ta fara darsuwa a ran Fatimah. Aisha ta cigaba da gayawa Nenne cikin rufe ido da bayan hannnunta tana ‘yar dariya “Umman Lagos kada kice nayi rashin kunya. Allah ya riga ya bani miji bafulatani dan uwana fa ba tun yanzu ba, ki tambayi Ummana zata gaya miki Ishaq dan Gombe ne, haihuwar Nafada, tun ina karama muke tare yake riko na Umma tun ban san wani Kalmar so ba”. Nenne Sappa taji wani iri a ranta, Aisha wace irin yarinya ce haka mara kara da sakayawa akan abinda ta yardarwa kanta bata so? Ta dan yi murmushi cikin rashin jin dadi, sannan ta gyada kai tace. “naji Siddiqah, kuma Abbanki ma ya gaya min zancensa. Amma Siddiqah mace budurwa a addinance da al'adarmu ta Fulani musamman a zamaninmu na baya bata zabarwa kanta mijin aure, biyayya muke yi ga duk abinda iyayen mu suka zartar akanmu, sai muga alheri mai dimbin yawa ya biyo bayan hakan, ni da aka aura min Babansu Fatima ban ma ganshi ba har saida aka kaini Ilorin. Kuma a haka nayi biyayya yau na tashi da alkhairi da riba mai yawa. Ki dinga neman zabin Allah akan aurenki kin ji ko Aisha-Siddiqah? Ki yi kokari ki cire kabilanci daga ranki don bashi da kyau ga zuciyar mumini, shi din lahani ne ga Imani, tunda Allah da kansa yace “Innna akramakum indallahi atqakum”. Don haka (ethnocentrism) abu ne da bashi da amfani ko kadan a addinance, tunda dukkanninmu addinin musulunci muke bi, kuma mun yarda da Allah da Manzonsa to mun zama daya, dukkanmu musulmai ne da muka hadu akan kalmar LA’ILAHA ILLAH-MUHAMMADUR-RASULULLAH, wannan ce tsintsiyar data hada mu ta daure duka kabilun duniya ta mayar abu guda, ba iya ‘yan Najeriya kadai ba, mu duka al’ummar Annabi Muhammad SAW ne, dake kwadayin tashi karkashin inuwarsa ranar da babu inuwa sai tasa. In hakane kuwa ai kai bawa baka da ikon banbance kabilar da zata shiga karkashin wannan inuwar a cikin musulman duniya”. Haka Nenne tayi ta yiwa Siddiqah nasiha mai shiga jiki akan ta daina wariyar launin fata akankabilun da ba na arewa ba, tace ba Yarbawa kadai ba, dama kowanne yare in dai musulmi ne, har a karshe tacema Aisha cikin zolaya ganin ta kasa sakin ranta. “baki sani ba ko akansu ranar ki zata fadi Siddiqah?” Ta karasa da dariyar tsokanar Siddiqah, Aishah-Siddiqah ta sunkuyar da kai ta nutsu tana sauraren wa’azin Nenne kamar da gaske nasihar da take matan na shigarta. Sai tace a ranta ai tunda Babansu Firdausi Bayerabe ne, ko meye ma Nenne zata ce akan yarbawa din, dole kuma ta so su tunda har zuri’a mai yawa ta shiga tsakani amma ita meye nata, ita bata ga dalilin da zata yarda bayerabe da bafillace abune iri daya ba. A zuciyar Siddiqah tace “in Allah ya yarda a Nafada rana ta zata fadi, Ishaq Hassan Nafada, mijin da Allah ya zabar min tuni, baida alaqa da Yarbawa ko any yare, ta kowanne bangare shi hausa/Fulani ne ziryan”. Kenan nasihar Nenne ta shiga ta hagu, ta fita ta dama a kunnen Siddiqa, nan kusa bata ga me zai sa ta yarda bafullatani/bahaushe daya yake da bayerabe ba. Watakila dai Umman Siddiqah wato Haj. Zainab ta manta da halin Petel dinta ne na rashin wayewa da shiga jama’a da irin wautar ta na diyan fari ne ko auta za’a ce, wanda ta kan taba lokaci-lokaci, gashi ita ba ‘yar fari ba ita baza’a kirata auta ba. Aisha-Siddiqah a dabi’arta bata iya boye abinda ke ranta ga wanda ya girmeta musamman Ummanta da tafi kowa kula da abinda zai dameta, kuma kallon kawar Umma take kamar tata uwar. Shiyasa kai tsaye ta zayyano mata abinda ke ranta babu kwane-kwane, watakila Ummanta ta manta da hakan wato rashin sakaya damuwa irinna Siddiqah, da maiyuwuwa bata barta ta biyo Nenne Sappa ba, ba tare data sanar da ita Aisha nada tarin rashin wayewa ba. A rayuwar Aisha Siddiqah Yunus, ita batasan wani abu kara ba, ko fuska biyu, sannan bata san boye abinda bai yi mata daidai da ra’ayin taba, komai girmansa kiri-kiri zata nuna maka abin nan bai mata ba. Ita ’yar keke-da-keke ce. Ba sakayawa. Da kyar Nenne ta samu ta yarda ta sha fresh milk din data kawo mata, don tace mata a firjinta ta dauko, amma sam ta ki cin shawarmar. Tace a ranta mai yuwuwa da naman dodon kodi akayi shawarmar ma. Princess Fatima ta koma da baya zuwa dakinta da bacin ran maganganun Siddiqah fal ranta, taji bata son zaman Siddiqah a gidansu, nan da nan ta dauki waya ta dokawa aunty Taiwo, a mamakance tana labarta mata irin yarinyar da Nenne ta kawo musu gida daga Gombe wai kyamar Yoruba food take and Yoruba people. Taiwo tace “'yar waye haka?” Fatima ta labarta mata daga haduwa da uwarta a Saudiyya Nenne ta makale musu harda dauko 'yarta wai zata kaita asibiti”. Taiwo da yake ta san halin karamcin mahaifiyarsu sai bata yi mamaki ba, cewa Firdausi tayi “in kin bibiya hausawa ne, sune most attimes masu raina kabilar Yoruba. They are more ethnocentric. Kuyi hakuri ita da kanta zata maida ita inda ta daukota”. Princess Fatima har lokacin ranta bai gamsu ba, haka curiosity na son sanin dalilin Siddiqah na kyamarsu wai har abincinsu duk tsaftarsa ya ki ya barta. Sai ta kira Hamma (Prince). Tana so a bata karin bayani akan me Siddiqa ke nufi da hakan? She was like irin me aka fi su? Taiwo kuma kashe wayarta tayi bata yarda sun tattauna maganar ba don tana tareda Toufeeq a lokacin ya zo musu annual leave. "Hamma!" Daga daya bangaren, Prince ne ya amsa, a lokacin yana tsaye kan Pareto ana yiwa Dawakansa wanka, yaja gefe yana amsa wayar Fatima. "Bongel!” (Sunan da Prince yake kiran kanwarsa Fatima) wanda kalma ce ta harshen Fulatanci mai nufin “mai kyau”, ya kara da cewa “Bongel, yaya akayi ne?" A fusace Princess Fatima tace "Ka roki Nenne ta sallami yarinyar data kawo mana gida daga Gombe, kafin na yi mata ‘Ai lojuti’". Ta bashi dariya sosai don tana nufin (kafin tayi mata rashin mutunci) da harshensu na Yoruba. Da muryarshi ta girma da kasaita mai tafe da lallashi ga kanwar tasa Prince yace. "Wace yarinya ce haka? Bansan Bongel na da rashin mutunci ba". Nan Fatima ta gaya masa wata yarinya ce Nenne ta kawo bata fice sa'ar Kiki ba, sai mulki da fi’ili take zuba musu a gida da shan kamshi da kyankyami sabida taga Nenne na nan-nan da ita, wai bata iya cin abincin su sabida su Yarbawa ne". Abin ya bashi dariya sosai yace "Bongel, haka Hausa-Fulani ke ma Yoruba people kabilanci ai, tun iyaye da kakanninmu, tun muna yara munsan wannan irin kabilancin da hausawa ke mana, muma kuma Yoruba kada ki manta haka muke musu kallon wadanda basu waye ba, kauyawa, dakikai, muna ganinsu marasa ilmin boko da ko turanci basa ji duk ilminsu, kema ba sai ki rama ba? Hausawan da asalinsu maguzawa ne? Kice mata jikokin barbushe da tsimbirbira ‘yan kan dutse, in kuma bafullatana ce bakida halin ramawa fa Bongel, for Nenne’s sake, for Nani’s sake ki yafe mata. Saboda kema rabi itace, fullata, saidai kawai in kinje gidansu kema kada ki sha fura da nono kada ki ci tuwo da miyar kuka, inace shikenan kin rama?". Kasancewar da yarbanci suke maganar harshen da Princess Fatima tafi jin shi sosai fiyeda kowanne harshe da suke yi a junansu. Ganin Hamma yaki daukan zancen da muhimmanci ya kara tunzura Fatima. Gabadaya Hamma ya maida zancen wasa. Tace "Hamma I am serious, Nenne ta dauki yarinyar nan da muhimmanci wallahi, I am jealous of her, wata 'yar firit da ita, sai shegen kyau irin na aljannu". Wanna karon Hamman, couldn’t control his laughter akan wautar kanwar tasa, wadda daga murmushin kasaita da yake yi yanzu ta zarce zuwa dariya mai kima, yace "kada kice min kishin kyawun nata kuma kike yi Bongel? Shin Bongel akwai wanda ya kai tagwayen Nenne (Fatima da Firdausi) kyau ne a Najeriya? Kada ki manta sau biyu kuna dauko ‘beauty contest’ a makaranta in kin manta ni ban manta ba”. Fatima taji dadi, ta saki kasaitaccen murmushi (from ear to ear), ko ba komai Hamma Prince yasa kanta ya kumbura, ta rage jin haushin Siddiqah, amma ta rasa ta yaya zatayi dashi ya yarda bata son zaman Aisha-Siddiqah a gidansu, ganin ta kawai fadar mata da gaba yake yi, don jinta take kamar (part of the family), alhalin ba abinda ya hada su. Sai ta nisa tace "Hamma! Ni bana son zamanta damu kawai, Hamma bana son bare agidanmu, kai kadai zaka iya yiwa Nenne magana ta ji, to take her back to her home, har akwai wata kabila da zata aibata Yoruba a idanuna in so ta?" Yace "in kuma bafullata ce fa, tunda kince daga Gombe ta dauko ta? Ai kema Fulani ce idan anbi salsala, jinin Uwa ma da kaurinsa, don haka taci albarkacin ta fito daga tsatson kabilar Nenne, keda ita duk abu daya ne, kinji Bongel?!" Da haka Prince ya kashe bakinta ya lallasheta suka yi sallama a wayar, ko dama can haka yake da son kannensa da kula da al’amarinsu, kome yake ciki in suka kira zai tsaya ya sauraresu ya basu attention dinsa, amma duk da haka da Firdausi ta dawo saida ta gaya mata komai data ji tsakanin Nenne da Aisha-Siddiqah, don abin ya kasa barin ranta, da abinda Hamma Prince yace na hakan ba abunda zata damu bane, in dai akan hausawa da Fulani ne. Princess Firdausi tace “I once heard something like that fah, Hausawa na da kabilanci akan Yoruba food and Yoruba people in general, ba tun yau ba na sha jin wannan kisser ba, so ki manta da yarinyar nan har nawa take, kin faya mita da kambama karamin abu Fatima”. Nan suka hadu suna tattaunawa akan kabilancin da hausawa ke yi akan duk wani yare na cewa ko kai musulmi ne in dai wani yare ne kai ba hausa Fulani ba kallon wani arne-arne suke yi maka, basa maka kallon cikakken musulmi, meyasa? Kuma me ya janyo? Sannan saboda me hausawa ke yiwa yare haka? Haka Suka maida abin ‘topic of discussion’ dinsu na ranar, kamar masu yiwa juna (tutorial class). Su lallai suna son gano dalilin afkuwar hakan tun tali-tali. Fatima har da hada ‘Imo’ ta kira Yayarsu Taiwo. Suna shiga tattauna maganar tareda Aunty Taiwo dake Ilorin a lokacin. Amma Firdausi kare Aisha take tayi, tana cewa ai yarinya ce da bata wuce sa’ar Kiki ba, kuma bata da wayewar kan da har zata san sauran kabilu sun wuce haka yanzu a hannun hausa-fulani, tace ba wani exposure keda yarinyar ba tunda daga cikin Gombe take, su yi mata uzuri. Allah kadai yasan dalilin Nenne na son yarinyar alhalin bata da alaqa da su, kuma basu kai matsayin da Nenne zata yi alaqa ta jiki dasu ba irin haka a matsayin su na talakawan gari. Lafiyayyen dakin da aka baima Siddiqah ita kadai shimfide yake da sabon lafiyayyen zanin gado hade da duvet mahadinsa, amma Aisha-Siddiqah tasa hannu ta cire zanin gadon nan ta aje a gefe, ta yi kwanciyarta akan zanin atamfarta wai bata sani ba ko Yarbawa sun kwana a kanshi, ita bata son jin warin jikin Yarbawa. Duk fadan da Umma tayi mata kafin su taho na shan magungunanta, ta bayan kunnenta yabi ya fice. Tun saukarsu a Lagos bata kara shan maganinta ba, ta yi masa maboya cikin lokar jikin gado ta manta dashi. Dama dai Siddiqah ba dai kin kwayar magani ba. Cikin dare kuwa Asma ta tashi, sosai sosai, ita kadai tayi ta fama da inhaler ba wanda ya san me take ciki, ga yunwar data dorawa kanta don haka kafin garin Allah ya waye Aisha-Siddiqah ta ji jiki, tayi zuru-zuru a garin Ikko kamar ba gidan daula tazo ba. A tsarin rayuwa irin na Fatima da Firdausi, ba Siddiqah kadai ba ko wani wanda ya hada jini dasu ne ya zo gidansu da sunan kwana, misali daga Ilorin cikin dangin Dade, kota fannin dangin Nenne daga masarautar Gombe yarannan sam basa shiga sabgar bako, wasu irin ‘yammata ne masu halin ‘ya’yan sarakuna na halin girman kai da da wanda hali ne da ya sha bambam dana mahaifiyarsu da mahaifinsu kansa, balle Siddiqa da tazo musu da wani al'amari da ya bata ran su, wai kyamar Yorubawa take, Firdausi kadai ke mata uzuri, don haka Siddiqa da Nenne ta kawo gidan Engnr. Idris Akanni don ta nema mata magani ita kuma tana rarraba musu ido a tsorace wai tazo gidan Yarbawa in suna yarbanci, ita Siddiqah tsakaninta da Allah da gaske ko yarbanci ake yi bata son ji a kunnenta, damunta yake yi, don jin yaren take kamar fada-fada, ita kuma bata son fada da hayaniya, ta kuma kasa boyewa a ranta har ta kai ga Fatima ta fahimta, itama kuma ta kasa boye jin haushin hakan har ta fahimtar da sauran ‘yan uwanta, sai hakan yasa suka fara tsanar bakuntar Siddiqah, suka nesanta kansu da shiga sabgar ta, suka barta da Nennen data kawo ta kadai kuma basu nunawa Nenne hakan ba. Ga hudubar Aunty Taiwo na kada su sakar mata fuska ta samu damar zama dindindin a gidansu, ita bata son jaye-jayennan na Nenne, ko na ‘ya’yan yan uwanta da take kawowa hutu gidan Taiwo na yawan hanawa, musamman daga bangaren Gombe, Taiwo tafi son dangin Babanta ba tun yau ba don a cikinsu take rayuwa jefi jefi take zuwa Gombe, Oummana kanta ta sani Taiwo tafi son dangin Babansu, a cewar Taiwo bahaushe bashi da amana, gashi da butulci da rama khairan da sharran. Firdausi dai bata tsananta ba, cikin mu’amalarta da bakuwar Nenne Aishatu-Siddiqah, a kiyayyar da suka kafawa Siddiqah, ita tana yiwa Siddiqah uzuri da kuruciya da rashin wayewar kai. Fatima kuwa ta daina zaman gidan sabida Aisha-Siddiqah, ganinta kullum tareda Nenne cikin gidan yana bata mata rai, in ta fita tun safe sai yamma, dama service (NYSC) suke yi a wurare mabanbanta itada Firdausi. Don haka a kwana biyunnan asabar da Lahadi ba karamin shiga takura Siddiqa tayi a gidan Engnr. Idrees Akanni ba, na farko babu kawayenta na makaranta su Amintako, da Ramatu da sauran ‘yan gang dinta masu kara mata karsashi, ba Ummanta data ke zubawa shawagwaba kullum a gefe, sannan babu Babanta mai biyewa rikicinta sannan ba Ishaq masoyi mai sa ta dariya da murmushi sabida iya soyayyarsa, a wurin Aisha-Siddiqah duk wani farin cikinta yana tattare da kasantuwar wadannan mutanen data zayyano a sama a tare da ita. Don haka cikin kwana biyunnan Aishah duk ta birkice da dacin rai, duk kokarin Nenne nata saki jiki tayi feeling at home abun ya ci tura, Allah-Allah kawai take safiyar Litinin tazo, a kaita asibitin da aka ce don shi aka kawota Ikko, a gama a maida ita gidan su a Jeka da Fari. Don Nenne tace sai litinin zata kaita taga likitan Firdausi. Yau Lahadi da Nenne ta ga taki cin dinner ta kuwa ce mata komawa Gombe ba rana tazo gidan yarbawa kenan har abada. Musamman data lura da dabi’un Siddiqah na kabilanci basu canza ba, duk da nasihar data bata lokaci tayi mata, shiyasa take so ta saba dasu tun yanzu, tunda kuwa she is going to be part of them nan bada jimawa ba idan Allah ya so ya amince kuma ya yarda, tanaso ta cirewa Siddiqah ethnocentrism din data likawa zuciyarta akan kabilar Yarbawa. Don haka cikin serious ta gaya mata yau cewa komawarta Gombe fa ba rana in zata bude ciki taci abinci ta ci, ko ta dinga dafawa da kanta. Duk girman kulawar da Nenne ke baima Aishah-Siddiqah a gidanta, duk sonda take kokarin gwada mata, da daular da ta tsinci kanta ciki rana daya, sama A/C kasa A/C kai har a kitchen A/C ce da fitilu masu haske wadanda da dare sai ka dauka kamar rana ce a gidan Engnr. Idris Akanni, ga cima ta alfarma wadda bata ko taba gani ko mafarkin ci ba, ga motoci na zamani kullum a jere a parking lot suna jiran mai fita a gidan da direba, rayuwa ce irin wadda Siddiqah bata taba ji ko gani ko a mafarki ba a gidan Haj. Sappa dake a Banana Island, Lagos, amma duk wannan sabida kulafucin uwa irin na Siddiqah hankalinta bai taba kaiwa kansu ba balle tayi appreciating. Kacokam! hankalinta yana gidan su a Jeka da fari. A weekend dinnan kafin zuwan Litinin da zasu ganin likita, sau uku Aishah tana shiga toilet ta kulle tayi kukan makon uwarta da kewar Gang members dinta na Billiri, a karshe ta goge hawayenta ta fito, ita ba waya ba balle ta kira Umma ko Ishaq ta gaya musu kurkukun Yarbawa Umma ta kawo ta. Ishaq ya sha gaya mata cewa sabon data yi dashi yafi son da take masa yawa, yau ta yarda da cewar nan tasa it aba wani soyayyar namiji a ranta sai kauna da sabo na ‘yan uwantaka da shakuwa tsakaninta dashi, don a baya in ya fadi irin hakan fushi take yi sosai, ta ce ya raina son da take masa, ita ba wani sabo a ranta sai SO. Yau dai ta yarda Ishaq ya fita gaskiya ta saba da shine kamar Yayan da suka fito ciki daya shima wani irin kewarsa da take daban ce. Haka a daddafe Aisha Siddiqa Yunus ta kai safiyar Litinin a gidan Engnr. Idris Akanni, kafin kwana biyun nan duk ta kara ramewa kamar kudin guzurin da ake diba kullum, Umman Siddiqah ma tana can a Gombe amma hanakalinta yana Lagos, tana kewar Petel dinta duk da ta saba da hakan in ta tafi makarantar kwana amma wannan kewar bata san meyasa ba ta dabam ce, tasan dai Hajiya Sappa zata kula da ita har fiyeda kulawar da zata bata, don taga tsantsar kaunar Siddiqah cikin idanun ta rana ta farko data fara ganinta a kwance a jikin gado a asibitin FMC Gombe. Komai na gidan a darare Aishah-Siddiqah take dashi, ta sanyawa ranta son komawa Gombe a matsayin abinda zai bata kwanciyar hankali kadai. Nenne kuma tace ba rana. Ko jiya data baiwa Nenne tausayi ganin yadda ta maida kanta daddawar daka, saida tace da direban su Fatima in ya kaisu wajen saloon ya dawo ya dauki Siddiqah ya kaita yawo ta ga garin Lagos, ta bata kudi tace ta sayi duk abinda take so in sun fita, madadin zaman daki data ke tayi ta dankare a kuryar gado tun safe har yamma in har ba Nenne ta kirata falo ba. Amma Siddiqah taki, harda rokon Femi da Nenne ta aiko kiran nata. “Don Allah don Annabi a kyaleni kallo nake yi”. A ganinta gara ta zauna a gida tayi kallon talbijin da bata san ma me ake yi a ciki ba sabida hankalinta da baya jikinta yana Gombe ya fiye mata shiga cikin garin yarabawa, a ranta tace ta san duk garin Legas dinma Yarbawa ne, don haka ita bata ga abun kallo a garin Lagos ba. Nenne dai tana ta kara fahimtar (negative attitude) din Siddiqah akan kabilar da ba tata ba, duk wani motsinta a daki ne ko a falo akan idonta ne ba tareda Siddiqah ta sani ba, ta fahimci irin kallon da Siddiqah ta ke yi jama’ar gidan bakidaya kallon (yare) bama musulmai ba, musamman kabilar yarbawa da sukayi kaurin suna (ridiculously) a idanun hausawa wanda a zahiri yake bukatar gyara, ta fahimci har zuwa lokacin Siddiqah ta kasa karbarsu a ranta. Nenne ta gama sawa a ranta ita kuma sai ta goge wannan negative perception din daga kwakwalwar Siddiqah koda ba a lokaci daya ba. Tace “Siddiqah na bukatar thearapy, counseling kai har da rehabilitation akan shin su waye kabilun Najeriya wadanda ba Hausa-Fulani ba??? Me yasa aka sanya mu karkashin tuta daya (gabas da yamma, kudu da arewa) muka amsa GREEN WHITE GREEN??? A ganin Hajiya Sappa kabilancin dake zuciyar Siddiqah da idanunta ya wuce kima ya kintace har ya zarce na musulunci ya zame mata wani abu daban kuma, domin kuwa yafi nata na can baya tsanani, a lokacin da take da shekaru irin na Siddiqa sanda ta tsinci kanta a gidan aure dumu-dumu a tsakiyar masarautar Ilorin, lokacin da aka kawota cikin dangin mijinta da babu bahaushe ko daya a matsayin mata ga daya daga cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni. Siddiqah ta yi wa kabilanci da banbancin yare da al’ada tsakanin ta da da kabilar da ba tata ba mummunar fassara wanda Nanne Sappa ke son ta rage ko bata yi nasarar cire mata shi duka ba. **** **** **** Ranar litinin da safe Nenne ta shirya tsaf cikin koriyar laffaya tayi sharr sai tashin sassanyar kamshin turarukan “Naseem” take, kyakkyawar bafullatana wadda bata kwalliyar fuska sam, amma fatarta sumul-sumul kamar ta shiga injin wankan fata, daka ganta ka ga daya daga irin matan manyan sarakuna ko masu arziki wanke hannu ka taba, kalarta harda jaja-jaja na samun kula da samun daular rayuwar da kowanne dan adam ke buri, hannunta cike da bangles na zinare hagu da dama ko yaya ta motsa sai sun motsa tamkar ba’indiya. Haka tasa Siddiqa a gaban motarta ita kuma tana hakimce a gidan baya direbanta Ojotu ya ja mota zuwa asibitin da zasu je. Tuntuni dama tayi (booking appointment) na ganin likitan nasu, tafiyar mintuna kalilan a manyan titunan garin Lagos daga Banana Island ta kawo su asibitin (Lagoon Hospital), da kanta ta kai Aisha har gaban likita Ayoade wanda shine likitan Firdausi, Dr. Ayoade Khalil. Dr Ayoade yayi mata kyakkyawan (check up) ya dorata akan sabon treatment da yafi wanda take kai a FMC Gombe, ya kuma canza mata magani mai kyau, da ya auna jininta yace sai yaga yadan hau, ga rashin nutsuwa a tare da ita da alamun akwana bukunnan data yi a Lagos ko sau daya bata ci abinci cikin nutsuwa ta koshi ba, likitan yace da Nenne zai riketa two days bed rest don ya ga jininta ya hau. Zai kuma sa mata drip. Nenne ta damu kwarai, yau tana ganin ikon Allah a gun Siddiqah wannan makon gida nata har ina! Ta ce ma Aisha bayan kaucewar likitan daga kusa dasu. “Yanzu saboda Allah Siddiqah me na raga miki? Me Umman take baki wanda bana baki? Na tabbata sabida baki son zama damu ne kika sawa ranki damuwa har ta kaiga bp?” Aisha-Siddiqah dai dai bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran yatsunta, amma gara mata zaman asibitin nan sau dubu akan gidansu Nenne, musamman data fahimci Princess Fatima ta sauya mata fuska yanzu. Wani kallo ma take mata mai zafi cikin ido. Nenne ta zuba madarar hollandia a tambulan mai tsaho ta mika mata, ba musu ta karba tana sha a urunce ji kake mukut-mukut, hadidiye madarar kawai take yi don yunwa, mamaki da haushin iskancin Aisha-Siddiqah ya ishi Nenne, ji dai yadda take shan madarar a yunwace mai nuna jiya bata ci abincin dare ba ta shige daki ta kudundune ta kwana da yunwarta, duk da ta ce da Femi abinda Aisha take so zata dafa, an kuma tambayeta tace tuwo, haka ta bar su da tuwon masara da miyar kubewarsu ya kwana a dining wanda akayi saboda ita ta yi barcin wuri duk don kada ta ci girkin Femi. Nenne Sappa ta nisa, sannan tayi kwafa tace. “Aishah, nace me yayi zafi na yiwa kai horon yunwa? To kwantar da hankalinki ki sauke jinin da kika dora a can sama, in sha Allah rana ita yau zan maida ke Gombe ince ko shikenan? Amma na rantse miki na sake rantsewa tafiya ce mai dawowa. Zaki yi dawowar da babu komawa sai dai da yawo in Allah ya yarda. In yaso in ga karshen kabilanci”. Siddiqah dai shan madararta take har da murmushi don hankalinta ya kwanta, tunda Nenne ta yarda zata maidata gida zance yak are, sauran zancen da tayi a karshe bata ji bama balle ta fassara shi da wata manufa don hankalinta ya kwanta yanzu. Shikuma Dade wato Engnr. Idris Akanni a ranar ya tashi zuwa Ilorin. Kafin Dade yaje Ilorin, saida yasa ‘yan uwan Nenne na Gombe suka yi masa duk wani bincike akan Malam Yunus da asalinsa, nasabarsa da sana’arsa, kuma duk abinda aka gaya masa din akan malam Yunusa Hamza na kwarai ne na sam barka. Malam Yunus ya samu duk kyakkyawar shaidar da ake nema ga mutumin kwarai mai kula da iyali da sadaukarwa akan su iyakar karfinsa. Haka matarsa ta samu kyakkyawan yabo na kula da hakkin makwabtaka da tarbiyyar Siddiqah kasancewar Allah bai bar mata ‘ya’yan da take ta Haifa ba sai Siddiqah din wadda suke tsaye kan jiki kan karfi wajen ilmin ta na addini dana boko. Siddiqah na cikin yaran kwarai da ake alfahari dasu a unguwar jeka da fari sannan tun tana shekaru 13 tayi haddar Alqur’ani a Tahfiz dinsu. Da wannan kyakkyawan albishir din Dade Engnr. yayi tattaki har Ilorin ya samu mahaifinsa Emir Abdulrasheed dan Abdullateef Akanni da maganar zabin da Nenne ta yiwa Abdulrasheed. Sarki da yake akan tsini shima, sai yaji kamar an masa allurar tuni da wani babban al’amari da duk suka zuba ido akai, yaji kamar an zaburar dashi ga wani muhimmin abu da ya saka shiririta a ciki, ya tuna cewa babban jikan nasa Prince Abdulrasheed ya wuce shekaru 40 a halin da ake ciki yanzu, burin sa a lokacin kowa ya san na Prince Abdulrasheed yayi aure yana raye ne, har in zai samu ganin ‘ya’yan jikan nasa zai yi farin ciki, amma meyasa ya biyewa gudun zuciyar Abdulrasheed har yau bai yi wannan yunkurin ba sai yanzu da mahaifiyarsa Sappa ta gaji da kawaicinta na fullata akan rashin auren dan nata tayi tattaki da kanta ta nemo masa aure da kanta? Shi kansa ya san son da yake yiwa Prince Abdulrasheed yayi yawa, shiyasa har baya iya tankwara shi akan duk abinda yace baya ra’ayi. Gaskiya ne duk wata kauna mara illah tabi bayan ta uwa gad anta. Ai sai nan da nan yace a kira meeting na gaggawa na duka ‘ya’yansa kamar yadda suka saba akan duk wani muhimmin al’amari da ya tunkaro iyalinsu. Kowanne cikin ‘ya’yan Emir of Ilorin su tara da ya haifa ya baro abinda yake yi a garin da yake zaune haka na cikin Ilorin duk sun baro ayyukansu sun taho fadar, har babban Yayansu Waziri wato Engnr. Idris mahaifin Prince su goma kenan duka sun samu halartar kiran mahaifin nasu na gaggawa, sarki mai ran karfe Emir Abdulrasheed Akanni na zaune a kan karagar mulkinsa sun saka shi a tsakiya hagu da dama, a gefen sa mutum biyar a hagu mutum biyar a damansa, kowa ya sunkuya ya kawo gaisuwa ta al’ada Sarki na amsawa daki-daki da harshen Yoruba, kafin ya yi musu addu’a ta hadin kai a tsakaninsu kamar yadda ya saba sannan ya shafa kan kowanne in ya sunkuya a gabansa kamar yadda suka saba, duk sanda akayi irin wannan zaman haka yake yi musu tare da nasiha akan su guji duk abinda zai raba kansu, yak an fadakar dasu akan cewa kada su taba bari ‘ya’ya su shiga tsakanin su, Sarki yace ‘ya’ya da daukiya fitina ne, sune manyan abubuwanda ke farraqa zumunci, a karshe ya shaida musu abinda yasa ya kirasu akan auren dan su Prince AbdulRasheed ne. Mahaifiyarsa Hajiya Sappa ta samo masa mata a Gombe, amma ba ‘yar sarauta ba. Shiru ya dan gifta. Kafin su balle da yarbanci a junansu na resentment. Kowa da irin abinda yake fadi a falon ganawar na Sarki, mafi yawan ‘yan uwan Dade sun ce ne ta yaya AbdulRasheed zai kasa samun mace a gidan sarautar Ilorin, dama duka masarautun kasar Najeriya sai a cikin ‘ya’yan talakawan garin Gombe? Uncle Abdulfatahi yace. “Kamar ance ‘ya’yan sarauta dana manyan attajirai da suke hada auratayyar abota (family friends’ marriage) da ‘ya’yansu sun kare?” Abu daya da zai burgeka a wannan zaman shine cikinsu babu wanda yayi magana akan banbancin yare dana al’ada dake tsakanin Yoruba da Fulani. Musulman Yarbawan Ilorin nada kyakkyawar alaqa da Fulanin Najeriya. Sun fi karkata sukar tasu da cewa iyayen Aisha basu da sarauta (ko ta mai unguwa). Kamar yadda na fada a baya, masarautar Ilorin (is a Yoruba-Speaking Fulani Emirate) hakan yasa ko kusa basa kin auren Fulani a tare dasu. Babban abinda ya kara wanke Fulanin Gombe a idon zuria’ar Sarki AbdulRasheed Akanni shine auren Gimbiyar Gombe wato Nenne Sappa da akayi da jimawa kuma aure na farko a zuri’ar Akannis, wadda har gobe alkhairinta kadai suke gani a tare da zuri’arsu, kodayake ita ta fito ne daga babban gida irin nasu, duk da haka baka rasa korafin matansu da ‘ya’yansu akan Hajiya Sappa din na cewa ta mallake Engnr. Idris da surkullensu na Fulani. Idris Akanni bai kara kallon kowacce mace ba da sunan kara aure har zuwa yanzu da ya fara tsufa bayan ita, yan uwansa kuwa daga mai uku sai mai hudu. Korafi dai da kananan maganganu irin na mata wanda baka rasa shi cikin kowanne gidan yawa, na talakawa ko na masu dashi ko na sarauta. Uncle din Abdulrasheed na hudu wato Mutawalle ya dage a kan bakansa na cewa a baiwa Abdulrasheed mace cikin ‘ya’yansu kawai, ko yana so ko baya so, a wuce maganar aurensa haka. Su basu yarda ya auri diyar talakkawa ba. Emir yace dashi cikin lallashi da harshen Yoruba (kasancewar Mutawalle baya jin kowanne yare sai harshensa na yoruba). “Oloruko mi o fe ni nkankan se pelu oye gege bi Baba e na. Mi o fe ke fi tipa je kanse nkanti won o ni ife si”. Ma’ana; ku cire takwarana a cikin lissafin sha’anin SARAUTA sabida shi da ubansa babu tunanin gadon sarauta a cikin rayuwarsu, to ku cire musu abinda basa ra’ayi daga zama dolen su”. Da kansa Emir ya mike ya taka da kyar ta hanyar dogara sandar girmansa zuwa kuryar turakarsa, ya dauko wata akwati ya kawo gabansu ya ajiye. Yace “Ga dukiyar aure da duk abinda za’a nema wajen gudanar da auren (Kehinde), na daukewa kowannenku wannan nauyin, a matsayinsa na jikana na farko, kuma wanda bai taba yin aure a cikin jikokina ba. na dauki nauyin komai da za’a kashe wurin aurensa. Na umarceku da ku amince da zabin da mahaifiyarsa tayi masa, ita kadai ta san dalilinta, a matsayin ta na wadda tafi kowa kusanci dashi, don haka ta fi ku sanin matar data yi masa daidai”. Da wannan magana ta karshe Sarki ya kashe korafin kowannensu akan auren Prince da diyar da bata sarauta ba, don a karshe bai ma kara bada wata dama ta wani cikin su ya kara fadin ra’ayin sa ba, yace umarni yayi musu su tafi su auro ma takwaransa zabin mahaifiyarsa, bai yarda ma a tuntube shi ba (Abdulrasheed din) sai bayan an daura auren. Abu idan Ubangiji ya rubuta faruwarsa shi shine sai kaga in lokacin faruwarsa ya zo ya faru nan da nan bagatatan, kodayake shi aure lokaci ne kuma kamar habo yake sai sanda Allah ya nufa kadai yake tabbata. Abu kamar wasa hausawa suka ce sai ga karamar magana ta zama babba. Aisha-Siddiqa da Nenne na ta zaryar ganin likita a Legas, a can Ilorin da Gombe kuma ana shirin daurin aure, shiri ake sosai babu kama hannun yaro daga dukkan bangarorin guda biyu ba tare da Siddiqah ko Prince dake can matatar man Fetur a birnin Qatar sun san ana yi ba. Akanni’s (‘ya’yan Emir) duka sun bi umarnin mahaifinsu babu wanda ya kira Prince ya gaya ma an karba masa aure. Dade yana Ilorin suka yi gangami da ‘yan ’uwansa da wakilan Sarki suka sauka a fadar Gombe ana sauran kwana biyu daurin aure wanda akasa za’ayi ranar Juma’ah bayan sakkowa sallahr juma’ah. Likitan su Nenne ya gama baiwa Siddiqah kyakkyawan treatment yadda ya kamata saida ta kwana uku a asibitin, ya sabunta mata inhaler. Yace da Nenne, Siddiqah tayi babbar sa’a asthma dinta ba mai tsanani bace kamar ta Firdausi (mild asthma) ce wadda in an guji allergy dinta zata dade bata tashi ba. Ita kanta Nenne Dade bai gaya mata me ake ciki akan maganar auren ba saida suka kama hanyar Gombe shi da sauran ‘yan uwansa daga Ilorin. Ya kuma ce ta kame bakinta har a daura baya so ko Taiwo ta samu labari. A ‘yan kwanakin nan da Aisha-Siddiqah Yunus ke tare da ahalin kawar mahaifiyarta Hajiya Nenne Sappa, tunaninta mara kyau akan Yarbawa sai ya fara canzawa gradually. Ta fasa bude zuciyarta tana gane su waye ‘yan kabilar Yoruba. Mutanene masu matukar tsafta a gidan ba kamar yadda take hasashe ba. Nenne kuma ta fahimci cewa Siddiqah a ‘yar kankanuwar rayuwarta mara exposure wadda iyakacinta kauyen Billiri da zagayen Kumo da Gombe, bata taba jin wani abu positive (mai kyau) akan Yarbawa ba, ko me take ji akan su is ridiculous (na habaici da ba’a) ne tun tana yarinya, shiyasa ta girma tana ma bayeraben mutum wani kallo na dabam da bahaushe ko bafillace. Aisha-Siddiqah bata san cewa su din, kabilar yarbawa wata babbar kabilar Najeriya bace mai martaba da daraja da kima da rikon addini (ga musulman cikinsu) kamar koma fiyeda kabilun hausa-fulani, sai da ta fara zama da ahalin Nenne Sappa ne ta soma gane hakan, ta fahimci ashe bayarabun ma suna suka tara. Dabi’un Nenne da ‘ya’yanta (Fatima da Firdausi) dana sauran jama’ar gidan, har ma da hadiman gidan su (Chief Cook Femi) da masu share-share da goge-goge kai har da masu kula da shukoki wadanda duk sun kasance kabilar Yarbawa ne, wasu ‘yan Lagos dinne wasu daga Ilorin aaka debo su, bakidaya suka taru suna narkar da wannan negative perception din na Aisha-Siddiqah wanda ta girma dashi a ranta akan kabilar Yoruba. Domin zuwa yanzu data saki ranta kadan a cikinsu, sai ta soma ganin abubuwa sabani ga tunaninta. Ta ga cewa Princess Firdausi da Princes Fatima ‘yan gayun ‘yammata ne na karshe masu ajin daya take nata, a bana suka kammala karatun jami’a, a irin tsarin kwalliyarsu ma kadai da tsaftarsu wadda ta take tata, Siddiqah ta gane ashe Bayeraben ma suna ya tara. Bayan an sallamosu sun dawo gida saboda ganin yadda yunwa ta kusan lahantata dole ta yarda take cin abinci, shima Nenne ta bata damar ta dinga fadin abinda take son ci, har tace ita da kanta zata dinga shiga kitchen ta girka mata, ba masu aikinta zata sa ba. Sanda Nenne ta fadi haka sai da Siddiqah taji kunya sosai, tayi duba ga girman shekarun Nenne da matsayinta da mukaminta a cikin gidanta, hadimai sai sun fadi kasa sunyi gaisuwa in zasu fadiwa Nenne sako. Dade da kansa yana girmama Nenne. Amma tace zata shiga kitchen saboda ita, alhalin mijinta kadai take yiwa girki da kanta, ta rasa wace irin kauna wannan baiwar Allah ke yi mata. A rashin saninta damshin son danta Prince ne ya nasheta. Siddiqah don kunya da nadamar abinda take yi sai ta sunkuyar da kai tace “Nenne ki bar ni in dinga yi da kaina, ko a gida nina ke yiwa Ummata girki”. “Lallai zaku shiryawa keda tawa Nanin (Nani Oummana) tana son mace mai yin girkin gidanta da kanta”. Ta shiga bata labarin Nani Oummana dake Gombe. Da yawan shekarunta amma bata fasa shiga kitchen ta yiwa iyalita girki ba musamman idan Prince Kehinde ya je wurinta. To kuwa har ya tafi Oummana da kanta take bashi abinci mai kyau na alfarma. Siddiqah tace “sunan mutum ne KEHINDE?” murmushi Nenne tayitana duban kyakkyawar fuskar Siddiqah with affection na Kehinde din akan fuskarta. Tace “shine Hammansu Firdausi. Amma shekaru masu yawa ya basu. Kehinde ba sunan yanka bane sunansu ne na yaren Yoruba me nufin Hassan da Hussaini ko Hassana da Hussaini. Sunansa na yanka Prince Abdulrasheed”. Da murmushi Siddiqah tace “Nenne shima ‘yan biyu ne kenan?” Nenne ta gyada mata kai “yes-yes. Shi da ‘yar uwarsa Taiwo”. Sai Siddiqah ta hau dariya tana cewa “Nenne uwar biyu sau biyu”. Suka fara hira tiryan-tiryan gwanin ban sha’awa. Ita kanta Siddiqah daga ranar ne ta fara sakewa da Nenne ta kuma fara jinta a ranta a kamar Ummanta. Nenne ta baiwa Femi Agbode Chief cook tagidan umarnin ta bar Siddiqah ta dinga girki da kanta, ta kuma dinga taimaka mata da duk abinda take bukata. Siddiqah aka shiga kitchen din Nenne aka sanya apron kamar gaske tafi awanni biyu tana aiki kuma ta sallami Femi. Kai saika rantse wani special abu take dafawa yadda ta tara hankalinta da nutsuwarta akan girkin. Can a jima sai ga kamshin suyar manja ya karade madafin Nenne. Daidai lokacin Nenne ta taso daga barcin rana tana mai jin yunwa sosai, ta zauna a karamin falonta kafarta daya kan daya ta kwalawa Femi kira. “Femi me kuke dashi mai sauki zan iya ci?” Femi ta amsa da yarbanci cikin damuwa cewa bata dora komi ba, bakuwar nan Aisha tana kitchen tun dazu ta hanata nata aikin komai, tace sai ta gama nata “Hausa food”. Dariya Nenne tayi tace “shine nake ta jiyo kaurin manja kuma maimakon kamshin girki? Siddiqah manya rigimammiya’yar Ummanta”. Ta dau waya ta kira Haj. Zainab suna gaisawa tana bata labarin cigaban da aka samu yau na cewa Siddiqah ta saki ranta har ta shiga kitchen tana girki da kanta kuma tana shan magungunanta. Suna cikin hirar nan Umma na cewa “ai na gaya miki zata ware, don bata saba zuwa ko’ina ta kwana bane bayan makaranta. Tace kuma dai dama Petel uwar makon gida ce ina tausayin ta ranar auren ta. in aka koma hutu koyaushe da kuka take komawa makarantar sai daga baya ne take warewa ta shiga sabgoginta”. Sun jima suna hirar Petel din kafin suyi sallama. Femi na tsaye Nenne na ce da ita tayi hakuri da Siddiqah. Amma ta sani ba bakuwa bace daga yau ba kuma ta zo ne don ta tafi ba a’ah ta zo kenan, ki kirata daya daga cikin yaran gidannan ki girmama sha’aninta kamar Firdausi da Fatima”. Sai ga Siddiqah an fito daga kitchen, da katoton tray a hannunta ta isa ga tebirin cin abinci ta dora. Da murmushi tace “Nene barka da tashi barci” Nenne tace “ba jiya naji na gyara miki ba? Nenne ne ba Nene ba?” Siddiqah tayi murmushi ta ja kujerar dining daya ta zauna a rashin saninta kujerar Prince Abdulrasheed ce har sai da Nenne taji gabanta ya fadi. Siddiqah tace “afuwan Nene, ni nafi so ince Nene” sai Nenne tayi dariya tace “Petel din Nene me aka dafa mana haka ya sha manja da yaji?” Femi ta leka tana son gane ko menene wannan abun da Siddiqah ta dafo amma ta kasa gane ko meye. Tana dariya don a zatonta Nenne bazata iya ko tabawa ba balle ta kai ga ci, tace da Nenne cikin yamutsa fuska “you are having delicious meal Ma”. Nenne ta kai idonta ga farantin Siddiqah taga ta shaqoshi ne da “danmalele” wanda akasari abincin ‘yammatan hausawa ne da yaji manja da uban yaji (borkono) tace “shagali wan dinner, to bari in zauna mu kwashi wannan garar tare”. Siddiqah na dariya daga tsaye ta dauka Nenne wasa take yi, bazata iya cin Danmalele ba, sai ga Nenne ta saka cokali tana kai loma cikin sukuni, ta zauna a kusa da ita suna ci tare suna hirar duniya abinda ya baiwa Femi mamaki. Ire-iren hakan da Nenne ke yi mata kullum, na janta a jiki da nuna mata cewa itama uwarta ce kuma kawarta ce kamar Haj. Zainab ya koya ma Siddiqah sakin jiki da ita, ya taimaka wajen da cire mata kabilancin dake damunta, yasa damuwar data ke ji a baya akan zaman gidan da kewar su Ummanta yanzu ya ragu hamsin cikin dari. Nenne da Siddiqah sun zama kamar uwa da autarta, kai sai ka dauka Gambon su Fatima ce. Tunda Dade ya tafi Ilorin kullum suna tare itada Aisha. Musamman da ya kasance Firdausi da Fatima basu cika zaman falon gidansu ba, ita Fatima bama ta dawowa gidan da wuri yanzu sabida haushin Siddiqah. Don haka Nenne da Siddiqa kadai take harkarta cikin gidan. Princesses koyaushe zaka samesu a daki suna waya da mazan da aka yi musu baiko wadanda duk family friends suke da zuri’ar Akanni, kuma ’ya’yan manyan sarakuna ne a yammacin kasar Najeriya, mijin Fatima Abdussalam Kayode dan Ohinoyi of Ebiraland ne, mijin Princess Firdausi kuma Prince Adesina, Da yake ga Oba of Ibadan. Ranar yau Firdausi ta dawo kasuwa ta tadda Aisha da Nenne a dakin Nennen, Aishah na kitse kan Nenne suna hirar kawayenta na makaranta wato ‘yan gang dinta su Amintako, Firdausi ta sha mamaki sabida a sanin ta Nenne ta yarda Nenne da bata son kitso, kai bata yarda ma kowa ya taba mata kai ita da kanta take gyara gashin kanta ta kitse ko ta fake shi, amma tun da ta fahimci Siddiqah ta iya kalba mai kyau don taga tana yiwa kanta yau tace ta yi mata. Princess Firdausi tace cikin tsokanar Aisha “Nenne I am jealous, kin yi auta kin ture ni gefe, yau tun safe baki neme ni ba sai Siddiqah” Saddiqah ta sunkuyar da kai tana murmushin jin nauyi. Nenne tace ma Firdausi “ai tuni na yaye ki kam!”. Aunty Taiwo ma tayi korafin Nenne bata kiranta a waya a dan tsakanin nan ko lafiya? Don in ta kira itama ba koyaushe take samun ta ba. Hankalin Nenne yanzu yana kan koyawa Siddiqah girkin data san shi Prince Abdulrasheed yake son ci, kullum suna kitchen tare. Ga Toufeeq yana gari ba damar ta zo Lagos har sai ya koma UK. Fatima sarkin korafi ta shiga tunawa Taiwo “Aunty Murja kin manta da zancen da nayi maki kwanaki na wata yarinya da Nenne tazo da ita wai Siddiqah?” Nan ta shiga labartawa Aunty Taiwo cikakken bayani cewa wata ‘yar farar yarinya da Nenne ta dauko daga Gombe a wannan zuwan data yi gida, tana nan mai ruwan fulanin kauye da rashin koshin lafiya kamar ba nutrition a jikinta, sai iyayi da kidifiri”, ta kara da cewa “amma kuma yarinyar mai kyauce fa, ko ni da bata yimin ba saboda abinda na gaya miki naji tana fadiwa Nenne kwanaki akan yorubas, na sallama kyawunta, daga haduwa da Mamanta a Saudi ta shige sukuf jikin Nenne. Nenne yanzu bata da lokacin kowa a gidannan sai nata, tunda Dade yayi tafiya”. Aunty Taiwo bata yi mamaki ba don tasan halin uwarsu da son kyautatawa mutanen dake kasa da ita, wadanda wata alaqa mai kyau ko yaya ta hadasu, amma bata daukosu ta ajiye a gidanta, don haka Siddiqah ma bazasu barta tare da uwarsu ba in taimako take son yi mata tayi mata daga nesa, amma ba’a cikin gidansu a dakin Kiki ba, duk wani taimako da Hajiya Nenne Sappa zata yi maka tana yi ne daga inda kake zaune, to why zata taho da Siddiqah? Taiwo tace “ha’an, na tuna zancenta”. Sun hada baki itada Fatima kan cewa duk yadda zasuyi su sa Nenne ta maida yarinyar Gombe zasu yi, a bisa dalilinsu na rashin son bare a cikin gidansu. Sun gama magana akan cewa su Taiwo zasu taho Lagos dinma in Toufeeq ya koma don ta kwana biyu bata zo ba, zata jira har ya koma, inyaso lokacin Kiki ta dawo daga Los-Angeles sai su taho gabadayansu (Kiki ta tafi yin wani gajeren kwas na ilmin na’ura mai kwakwalwa na watanni shidda a wata shahararriyar Institute dake Los Angeles) bayan kammala karatun sakandirenta a wannan shekarar. Ta shiga Institute dinne kafin ta fara jami’a. A lokacin Taiwo tana gidanta na Ilorin, an maida ta aiki asibitin koyarwa na jihar Kwara/Ilorin daga Lagos State Teaching Hospital da jimawa. A halin yanzu Taiwo Murjantu na matsayin Consultant a gyanaecology Kiki-Ruqayyat a lokacin ta gama sakandire ta nada shekaru goma sha takwas. Zamu iya kiran Kiki sa’ar Siddiqah amma ta bata wajen watanni tara, saidai Kiki tayi biyun Siddiqah a girman jiki. Ko don yadda Abdulrasheed ke sakar ma Kiki kudi tana wadaqa yasa ta zama irin (first class ‘yammatan nan), kaunar Kiki da Uncle dinta Prince har girmanta bata canza ba. Dade ya kira Nenne a daren ranar da suka sauka a Gombe yace da ita suna Gombe shi da ‘yan uwansa su Dan Iyan, Malami Uban Doma da Turaki da Mutawalli, gobe Juma’ah zasu daura auren Abdulrasheed da Aisha a garinsu mahaifinta wato (Kumo) in Allah yaso ya kuma yarda, bayan masallaci. Ya tabbatar mata komai na neman auren ya kankama Emir bai sa wasa cikin lamarin ba ranar da yaje masa da zancen, a take ya bada sadaki da dukiyar aure yace suje suyi komai da ya dace, ya gaya mata Baban Aisha-Siddiqah wato Malam Yunus da dan uwansa basu kawo kowanne uzuri ba don sun riga sun warware maganar aurenta da yaron da yake neman nata. Ya roketa kada ta gayawa su Taiwo komai don zata bata musu shiri. “Lets’ take all of them by surprise”. Inji Dade. Kunnen Taiwo na Abdulrasheed ne, baya so Abdulraheed ya kawo musu kowanne cikas ko da kuwa na cewa a dakata ne sai yazo ko makamancin haka, yace duk wata dama sun gama bashi ita yanzun hukunci yana hannunsu, don haka sai an daura ya ji daga baya, ya gaya mata cewa Emir yace kada a sanar dashi sai ranar da yazo gida dan kansa don a lokacin ma baya Qatar, ya halarci wani shahararren ‘tournament’ a yankin kasar Rasha. Nenne a wurin da take zaune ta fadi tayi sujjadah da wayar a kunnuwanta. Albishir ne irin wanda Dade bai taba yi mata mai dadinsa ba. Alas! Burinta yau ya cika, akan damuwarta ta rashin auren Prince Abdulrasheed (Kehinde), ko yau rayuwarta ta kare (wadda take da tabbacin ba mai tsayi bace) ta tafi cike da farin cikin cikar buri, ta tabbatar Aisha-Siddiqah data zaba masa bata yi masa zaben tumun dare ba, tana fatan ta zame masa matar rufin asiri kuma uwar ‘ya’yansa kamar ita da Dade, Nenne tace a fili “ko yau Allah ya katse tafiyar, ta gode masa. Don ta san Kehinde zai rike Siddiqah muddin ta bashi hujjarta ta hada su aure haka da gaggawa, zai riketa albarkacinta, koda baya son ta. Ita bata aura masa Siddiqah don ya so ta ba, ta aura masa ita ne don ya cika mutum! Mai kamala. Rayuwarsa ta zama cikakka kuma mai ma’ana kamar ta kowa, kuma ya samu zuri’a shima. Tana cikin damuwa da bakin cikin rayuwar da yake yi shikadai. duk da a yanzu bata zarginsa da rayuwar ashararanci face rashin auren wata jarrabawa ce a gareshi. Tana da yaqinin AbdulRasheed zai rike Aisha-Siddiqah a gidansa irin rikon da Dade yake mata don barewa bata gudu danta yayi rarrafe, zai shiga da ita duk inda ya shiga cikin duniya albarkacin cewa ita Nenne ce ta aura masa ita, ba don kasancewarta ‘yar wasu masu mulji ko dukiya ba sai don kasancewarta zabin Nennensa. Nenne ta kwana da sanin cewa babu gurbin soyayya a zuciyarAbdulrasheed dinta, ya dade da konewa kurmus daga kowanne sako na zuciyarsa, akan dalilin da har gobe ita bata sani ba. Amma ta shinshini cewa koma dai menene kin auren Kehinde yanada dalili in tayi la’akari da irin kalaman dake fita bakinsa akan mata. Koyaushe tayi masa maganar aure cewa yake “Nenne…they are nothing but gold-diggers… true love does naver exist. I am a hopeless romantic… And I want true love!” A ganin Nenne Sappa shi aure ba a yadda Abdulrasheed yake kallonsa yake ba a zahiri. Abdulrasheed yana kallon aure ne a matsayin wani abu mai girma wanda sai da sahihiyar soyayya yake yiwuwa (sai zukata biyu sun hadu akan son juna, sai yana son mace zai aure ta, itama sai tana matukar sonsa zai yarda da ita, alhalin kuma ya kasa son kowacce din balle ya bata dama) har gashi yayi sallama da shekarun kuruciya. Bai kamata yayiwa matan duniya duka hukunci akan laifin mace daya ba. Ita Nenne ta yarda cewa ba lallai sai da soyayya ake yin aure ba; circumstances yana kawota (along the way) ga ma’aurata. Nenne tafi yarda da cewa ana yin aure ne don dalilai masu karfi na addini dana al’ada, muhimmi shine don raya sunnahr Annabi SAW da cikar kamala da addinin mutum, da neman zurri’a saliha. A al’adance kuma sai dashi kake cika mutum, kima da martabarka ke cika a idon al’ummar da kake tare dasu. Amma ba don soyayyahr da yake ikirarin shi bashi da ita akan diya mace ba. Nenne bata san cewa abinda ya hana shi sake soyayya tun daga incidence dinsa da Ex dinsa Haseenah ne, ya zama cewa he lacked his trust and feelings on women akan Haseenah Ambursa, al’amarin daya kwashe shekaru kusan goma sha biyu yana dawainiya da shi yana haunting dinsa, yana lalata yardarsa da bukatuwarshi akan mata bakidayansu. Shikuma ba aboki na jiki gareshi ba, tunda ya rasa Bello Birnin Kebbi, wanda zai zaunar da shi ya gaya masa gaskiyar cewa ba’a yiwa duka mata hukunci da laifin mutum daya. **** **** **** WAIWAYE “ Nenne Sappa has been battling with kidney stones for some years, ba tareda ita kanta ko wani cikin ‘ya’yanta ko mijinta Dade ya sani ba. Tana dai ‘yan ciwuwwukanta a tsaitsaye wadanda basu kwantar da ita ko sau daya ba, har zuwa shekarun baya da ya fara nuna alamu har ta kwanta a asibiti a Morocco. A shekarun baya tana yawan tafiya kasar Morocco da sunan ziyartar kaninta da iyalansa a rashin sanin kowa medical check-up take zuwa akan treatment din da ake mata don a lokacin kanana ne stones din likita na tunanin zai iya treatment dinsu ba tareda surgery ba. Daga baya ta manta da zancen don bata fama da kowanne ciwo ga yawan sabgogin iyali dana al’umma dake kanta. A check-up na karshe da Hajiya Sappa ta je Morocco aka tabbatar stones tana bukatar surgery don a ciresu gabadaya ta huta. Kaninta Abdulmajid baisa was aba yajaddada mata cewa da zarar ta dawo ta yi shiri ta sake dawowa ayi aikin. Amma Nenne tunda ta dawo kuma tanacikin koshi lafiyarta sai bata sake bi ta kan lalurarta ba. Daga ita sai Dr. Abdulmajeed Ahmadu Jalloh Omar, suka rike da wannan zancen na kidney stones dinta a tsakanin junansu, wato kaninta mai binta a haihuwa wanda likitan Koda ne dake aiki a babban asibitin Koda na kasar Morocco, su biyu kadai suka san da wannan al’amarin. A can baya da take yawan zuwa Morocco da sunan ziyarar Abdulmajid da iyalinsa a rashin sanin Dade da yaranta ana treating dinta ne, don samun lafiyarta. Daidai lokacin data dago daga sujjadarta, jikinta ya soma dan bari da karkarwa na shigar zazzafan zazzabi, bata taba jin zazzabi irin na wannan lokacin ba tun saninta da ciwon nata. Zafin jikin Nenne ya karu, har ta kai ga ta bar abinda take yi a kitchen ta koma dakin mijinta ta kwanta a gadon su na alfarma. Nenne ta dauki waya ta kira Abdulmajid, yana jin muryarta sanda suke gaisawa ya san jikin ya tashi sosai, yace “Adda kiyiwa Allah ki yarda ayi miki aikinnan kowa ya huta, ina amfanin zama da ciwo? Kuma kin hanai fadawa kowannensu har yau” Nenne tace “Abdul tsoron aikin nake ji, gara idan tafiya ce in tafi salin alin ba tare da an farke ni ba, ina rokon ka kara rike min sirri na, ban yarda Dade da Hammansu da Nani Oummana su ji wannan maganar ba…”. Abdulmajeed ya katseta cikin damuwa “Adda na gaji! Na gaji da wannan boye-boyen da muke yi, mara amfani, Adda boyewar nan bata da wani amfani, su dinnan duka musulmi ne Adda, musamman miji da mahaifiyarki, koba komai zasu yi miki addu’a ayi aikin nan a sa’a. shikuwa Abdul ai namiji ne shi yafi kowa dacewa ya san halin da kike ciki, ki sanar da ko Abdulrasheed da Murjanatu ne kadai su rako ki ayi aikin, in har bazaki bari Dade dinsu ya sani ba saboda hawan jininsa, su ya kamata su sani”. Nenne tace “ko zan sanar dasu ba yanzu ba sai na shirya, akwai abinda ke gabana yanzu, zan cigaba da shan magungunana da na bar sha kwana biyu. Tunda na samu cikar burina da raina akan Hammansu (Abdulrasheed) to Alhamdulillah!” Abdulmajeed Yace cikin damuwa da hukuncin ganganci na ‘yar uwarsa, “amma Adda idan kika mutu kina musu wannan boye-boyen ba tareda sun san jinyar da kika dade kina yi ba, suka kuma ji da hadin bakina, na rantse daga ni har ke bazasu taba yafe mana ba!”. Nenne tace “bazan taba saka sunanka cikin maganar nan ba Abdulmajeed, amma zan duba yuwuwar na sanar da Abdulrasheed shikadai, amma dai don Allah ka kara min lokaci Abdul, har Abdulrasheed ya karbi matar dana aura masa daga hannuna”. Abdulmajeed ya rasa me zai ce mata da zai sa ta dauki al’amarin lafiyarta da muhimmanci sama da zancen auren danta. Yace a hankali “Adda!” Nenne Sappa ta katse kanin nata cikin kulawa. “Abdul, Ko Allah hoddiri fe’an be tagu fe’an!”. (Abinda Allah ya riga ya rubuta zai faru ga bawa ba makawa sai ya faru)!” ***** **** ***** ROUQAYYAT-KIKI K iki (Ruqayyat) zuwa yanzu an zama manyan ‘yanmata, shekafun ta zasu kai sha bakwai da watanni tara. A bana ne ta kammala karatun sakandire. Can na hangota cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan gayu amma kuma wadda bata nuna tsiraici a tare da itaba, irin dai shiga ta yaran musulman Yoruba, rashin saka lullubi ko a kafada aka ya nuna ita din ba cikakkiyar bahaushiya bace, cikin wani hamshakin supermarket take shawagi a (Santa Monica) din birnin Los Angeles. Dana leka kwandon da Kiki take sayayya a ciki sai na ga cewa kanta take zabar ma ‘brazier’ da ‘panties’ da ‘undies’ da kuma ‘nighties’ ‘yan ubansu-ubansu, kasancewar a gobe ne zata koma hutu na farko gida Ilorin, tun bayan zuwanta kwas din Computing a Los- Angeles, sai wani tunani ya fado mata, kasancewar kome take yi Uncle AK baya barin ranta. Mai zai hana tayiwa Kawunnata gudunmuwa dasu shima idan aurensa ya tashi ya baiwa matarsa? Sabida a idanunta nighties dinnan da undies din duka unique ne, da kyawunsu da tsadarsu ya kai ya kawo. Kiki na nan ‘yar lukuta haka duma-duma kamar buloras, doguwa mai garin jiki kamar na mahaifiyarta, Taiwo. Da ‘yan yatsunta da suka sha adon bangles da zobban zinare ta latsa tsadaddiyar wayar hannunta wadda Uncle AK dinne ya mallaka mata (yadda take kiran Prince har inda yau ke motsi watau Uncle Abdulrasheed Kehinde) a ranar da yazo bikin graduation dinta na sakandire daga ‘Greensprings School’ dake jihar Lagos, alkawari ne da ya dade da yi mata cewa sai ta kammala secondary school da kyakkyawan sakamako sannan zai mallaka mata wayar hannu kuma a ranar ya samu ta cika shi. Musamman kasancewar Kiki tayi kokari sosai a jarrabawarta. Yana kwance cikin ‘sofa’ a ranch house dinsa atsakiyar babban birnin kasar Argentina, a jiya yazo kasar daga Qatar wani babban tournament. Dawowarsa kenan a matukar gajiye ko Polo Helmet din kansa da chukka boots din kafarsa da socks bai samu ya cire ba. Da chukka boots da safa da komai dake jikinsa ya fada akan Sofa-bed din, yana matukar son zuwan su Nenne a satinnan kafin lokacin tafiyarta aikin Hajjin bana yayi, don ya jima shi bai je ba. Idan kuwa har yayi irin wannan jimawar bai je gida ba irin haka Nenne kan tarkato kan kannensa Princess Fatima da Princess Firdausi, da ‘ya’yansa Hakeem da Kiki su zo su yi masa sati. Daidai lokacin yana tunanin mikewa don wucewa bedroom dinsa yayi sallah, ko ya samu yayi barci sosai, ya huta gajiya don rabonsa da barci tun daren shekaranjiya wato kafin su fara tournament din da ya kawo shi, wayar ‘yar rigimarsa Kiki ta shigo masa. Da kyar ya mika hannu ya daga idanunsa a lumshe saboda gajiya. Amsawar kawai yayi cikin dushewar murya ba tareda yace mata komai ba. Tace “Uncle AK size nawa zan daukar mata na backward da frontward?” Abdulrasheed ya yunkura ya mike zaune cikin yamutsa fuska yace “Kiki! Where are you now? What sheet are you talking about?” Kiki ta rangwadar da kai gefe irin na yaran da ke jin duniya akan tafin hannunsu tace “Uncle AK, lefe zan fara hada maka, in duba wata hadaddiyar Baby haka anan ajinmu in yi mata tallanka, Uncle nagaji da ganin ka kai kadai a gida, Uncle nagaji da ganin ka a cikin Dawakai ba ‘ya’yan ka ba”. Idanun Abdulrasheed suka dan bude kadan don mamaki, har an kawo wannan lokacin da ‘yar cikinsa ma ta damu da rayuwarsa har haka, da kyar ya iya ya hadiyi miyau, yace. “Kiki are you alright? Ko kin fara shaye-shayen zamani ne?” “Allah ya sani ban sha komai ba. Mamana ta hanani sauraron samari saboda kai, ina dalili? Akwai BF dina dana ke matukar so Mama ta hana ni ko magana dashi wai sai kayi aure, rannan fa cewa tayi wai bana jin kunya in shige gidan miji in barka a zaure?” Kiki ta karasa harda kirkiro ajiyar zuciyar damuwa, yadda take maganar kadai zaka san bilhaqqi take yinta cikin gabunta. Wata ajiyar zuciyata subucewa Prince, shikansa bazai iya tuna rabonsa da yin irinta ba, in ba yana magana da Kiki ba baya tuna yawan shekarunsa. Ita kadai ke iya saka shi dariya a kowanne lokaci koda bai shirya ba. “Idan na fahimceki daidai Kiki, kina so in yi aure ne don a baki dama kema kiyi aure?” Kiki tasa hannu daya ta rufe ido daya tana dariya don kunya, kamar Abdulrasheed na ganinta, shikuwa kallon mamaki yakewa kan wayarsa, har yaushe ‘yar cikinsa Kikin da yake sawa ‘diaper’ ta girma haka? “Alright Kiki, nina tsufa da aure, zan wa Taiwo magana kada ta kara fadin haka gareki. Ta baiwa mai kaunarki dama ya iso gida. Kiki har kayan dakinki na gama hadawa suna nan kulle a gidana na Qatar. Kuma ni zaki fara kawowa boyfriend dinki din kafin kowa. Sai nayi na’am dashi zaki kaishi ga Daddynki. Yaya sunanshi?” Don farin ciki Kiki kamar bakinta ya yage don murmushi tace “You know I love ko Uncle AK? Nayi alkawarin bazan taba sauraron saurayi ba sai kayi aure? Sunansa “Abdul-Nasir Oluwatosin”. A kwance Prince yake amma bai san yaushe ya tashi zaune ba. ya rike wayar hannunsa sosai yace “Tosin Abdulnasir, a footballer?” Kiki ta gyada kai tana jin kunya, kamar Uncle AK yana kallon idonta. Shi kuma yace “Kiki iyayenmu bazasu taba bari ki auri footballer ba, sai dan sarauta, ni nasan iyayenmu sarai, ki cire ni a gefe kan batun aure. Maybe your Uncle is not destined to marry in his life. Amma akwai mata fal a aljannah ai kin sani ko Kiki? They are called hurul’eeni, who knows ko mata na hudu suna cikinsu? Don haka ki daina damun kanki a kaina kinji. If you really-truly love this Guy, I will stand by you Kiki. AbdulNasir was a football celebrity. Me ya hada ki da dan ball? A ina kika hadu dashi?” Kiki ta labarta masa haduwarta Tosin AbdulNasir sun je kallon wasan da Inter-Miami tayi da LA Galaxy a California itada kawarta Badriyya. “Amma Kiki ban hanaki bin kawaye yawo ba? Ban ce daga makaranta sai makaranta ba? wato har kallon ball kike zuwa?” “Kayi hakuri Uncle AK, wallahi ba inda nake zuwa banda shopping, ranar ma Badriyyah ta matsa muje ne don taga AbdulNasir a fili, tana matukar son wasansa, na gaya mata ka hanani zuwa ko’ina, tace daga ranar bazasu kara zuwa yin wasa Los-Angeles ba, and she don’t want to miss seeing her favourite footballer in reality (bataso ta rasa ganin dan ball din data fi so a fili), sai na yarda muka je, tun a ranar ya nuna kaunarshi gareni muke waya, ban taba gayawa kowa ba sai Mama, shine ta bani waccan amsar cewa bazan taba sauraron kowa ba sai kayi aure”. Abdulrasheed yayi ajiyar zuciya ya ce “Kiki count me out kinji? Bani lambar yaron kuma ki bar ni da Taiwo”. Kiki ta dage itafa bata so itama, in Abdulrasheed naso tayi aure ko ta saurari maso sonta to ya barta ta hada masa lefe. Dariya yake yi a yanzu. Yace “Kiki! Daga hada lefe sai me? Na baki dama kiyi tayi. Kudi ne dake. Ki sayi kome kike son saya kiyita tarawa gaibu, amma bada kudina ba bana cikin shirme kinji?” “Yo dama Uncle ai ban ce ka turomin ko sisin kwabonka ba. Zai zama cewa tawa gudunmuwar kenan ta aurenka, saya maka akwatin (undies and night wears) dinta. Kawai cewa nayi ka gayamin frontward and backward size din matar ka”. Kan Abdulrasheed ya shiga duhu da shirmen Kiki, yace “meye kuma front and back?” Kiki ta hau dariyar shakiyanci sabida yadda Uncle Prince yayi maganar cikin yamutsa fuska dole ya baka dariya tace “brazier da panty dinta nake nufi, gani gaban wasu masu azabar kyau, amma bansan size dinta ba”. Da karfi Prince yace “Kiki! If I don catch you….” tayi maza ta kashe wayar don kamar zai fasa kunnenta da ihu. Itama ta san da a kusa suke yau ko Taiwo bata isa kwatarta hannun Uncle ba, in ya murde kunnenta. Ya kashe wayarsa yana fadin “Oh my God! Kiki ta girma, har ta fara raina shi, don ya maida kansa abokinta. Ya koma ya kishingida, amma barcin da yake so yayi yaki zuwa sam. Sai juyi yake gefeda gefe akan sofa-bed, maganar Kiki ta jefashi cikin wani yanayi na begen yayi auren don yasan yana missing wata rayuwa da bait aba shiga ba har shekarun girma suka riskeshi, sai kuma bacin rai ya biyo baya da wani tsohon tunani y gilma masa… A can baya shekaru masu dama da suka gabata ya taba sayawa Haseena brazier da Panty da hannunsa, itace da bakinta ta gaya masa size tace ya sayo mata, a lokacin ne ma ya taba sanin wani abu brazier, da wannan tunanin dana kadaitacciyar rayuwarsa wadda bai nemi komai ya rasa a cikinta ba sai macen aure kadai, alhalin yanada tabbacin cikakkiyar lafiya ta kowanne dan adam a tare dashi, idan kuma by now ya rasa mazantakarsa ne duk ba mamaki, watakila yawan shekarunsa yasa ya rasa feeling na manhood dinma gabadaya, har gashi ‘yar da ya haifa ta isa aure, da wannan tunanin mara dadi kuma mai sosa zuciya barci mai nauyi ya dauke shi. Yana fadawa ransa da zuciyarsa cikin barcin da ya debe shi mara dadi, mai wani irin nauyi; hatta matan aljannah (hurul eeni) in aka bashi zai ce baya so! Ko kuwa yace ya yafe!! He is not destined to experience that kind of life!! **** **** **** 1/RABI’UL THANI HIJRIYYAH P rince Abdurrasheed Idris Akanni, yana wannan barcin mara dadi agareshi kife da ciki (rub da ciki) akan ‘sofa-bed’, irin kwanciyar da bai san ma yayi ba don tun suna kanana Nenne ke gaya musu bata da kyau ga musulmi, mafarkai barkatai masu alaqa da aure da ‘ya’ya na ratsawa ta cikin barcin nasa mara dadi. Daidai lokacin da Turaki of Ilorin (mai bin mahaifinsa a haihuwa) ya mikawa Malam Barau Hamza (madaurin aure Aisha-Siddiqah) wato wan mahaifinta sadakin Abdurrasheed na dankwala-dankwalan sarkokin zinare a cikin battarsu, ga “Aisha-Siddiqah Yunus”. Aka daura auren nan da nan, bisa tsari da koyarwa irin na addinin musulunci, bayan an shafa fatiha, kalilan din shaidu kuma sun shaidah, masarautar Gombe data Ilorin da dangin Uwa da na Uban Siddiqah duk sun shaida domin kowanne bangare ya bada wakilai da suka shaida, aka fara musabiha a tsakanin iyayen wadanda suka kasance Yoruba da fulanis, daga kowanne bangare na farin ciki bayan kam]mala daurin auren mai albarka. Abinda zai baka mamaki shine ko a kafar sadarwa daya ba’a sanar da wannan daurin auren na Prince ba, wannan kuma ya faru ne bisa umarnin Emir, daga nan aka wuce fadar Uban kasar Gombe inda za’ayi reception na bayan daurin aure tsakanin dangin Siddiqah maza, dangin Nenne da kuma Akanni’s dake nan har lokacin. Sun kwashe akalla sati guda kenan a garin Gombe suna gudanar da komai cikin nutsuwa har alkawarin Allah ya tabbata a yau Juma’ah daya ga watan Rabi’ul Thaani da Siddiqah ta tabbata matar Abdurrasheed. **** **** **** “ An daura!”. Dade ya gayawa Nenne, fuskarsa fal murmushi kamar tana kallon shi, ya kara da cewa “sai ki daukota ki dawo da ita Gombe toh, kin kama musu ‘ya kin rike daga zuwa asibiti, at least tayi sallama da iyayenta ko, in yaso su kawo ta da kansu”. “Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Kawai Nenne ke maimaitawa a fili. Nenne ta shigo dakin da Siddiqah take da wani irin annuri a kyakkyawar fuskarta irin wanda Siddiqah ko wani dan adam ko ‘ya’yanta babu wanda ya taba gani a tare da ita, zuwa yanzu alamu na raunin ciwo sun dade da bayyana a tare da ita, tana dai daurewa ne tana kuma karfafa jikinta da son ayi biki a gama lafiya kafin ta tafi Morocco ayi mata surgery, sai ta tadda Siddiqah tana hada kayanta a trolley dinta hajaran majaran, fuskarta fal damuwa da ci da zuci. “Siddiqan Nenne yaya dai? Kayan menene haka aka dannawa a jaka ba ko ninki? Ko mun miki laifi ne za’a yi mana kaura?” Cikin damuwa Aisha-Siddiqah ta dago ta dubi Nenne tace “Gida nakeso zan tafi, baku yimin komai ba Nenne sai alkhairi, na duba date ne a kalanda naga gobe za’a koma makaranta shiyasa nake hada kaya na, kinga har na cinye hutun ma a nan, ban ma Ummana ko kadan ba”. Nenne ta karaso cikin dakin ta dafa kanta cikin tausayi da wata sabuwar kaunarta, tace “babu laifi Siddiqah munyi waya da Umman naki ma, tace goben dama zaki koma saboda makaranta”. Siddiqah ta hau murna. “Allah Nenne ba tsokanata kike ba gobe zan koma Gombe?” Sai ga Siddiqa tana far’a tana dariya kamar ba itace yanzunnan cikin damuwar data sameta ciki ba. Nenne tace “wannan ‘mood swing’ haka Aisha ai sai kisa inyi tunanin mu din ba kya jin dadin zama damu ne, ko nida ahalina bama kyautata miki a kan guiwa kike”. Siddiqah ta rufe ido tana jin kunya, sai ta kara fadada far’arta, tana “a’ah Nenne ba haka bane, nayi kewar Umma na ne da yawa, kin san ban taba zuwa ko’ina na kwana ba banda makaranta, sai nan, ko gidan ‘yan uwanmu na Kumo muka je da sallah bana yarda in kwana”. A washegarin ranar Nenne da kanta ta maida Aisha Gombe. Kai tsaye suka zarce zuwa gidansu Aisha kafin ko’ina. Nenne bata ko jima ba tasha kunun zaqi da cincin da aka sauketa dashi don basu samu Umman Siddiqah a gida ba sun fita da Baba Yunusa sayayyar wasu daga kayan auren Siddiqah duk kuwa da Emir yace a gaya musu yarinya kadai zasu dauka zuwa Ilorin. Sai ‘yan uwan Ummanta fal gidan. Ganin suna neman fallasawa a gabanta ta hanyar kiran Siddiqah da “amarya oyoyo!” Da ake tayi don haka suna gaisawa aka sauke kayan Siddiqah Nenne da direbanta suka juya a gurguje zuwa gidan Sarkin Gombe, suna tafe suna waya itada Haj. Zainab. Inda Nenne tace da ita a shirya amarya gobe-gobe zasu dauketa su wuce Ilorin bisa umarnin Maimartaba. Haj. Zainab ta kawo uzurin cewa a kara musu kwanakin tarewa su gama shirinsu a nitse, Siddiqah tayi sallama da danginta su kuma samu su lallasheta akai, tayi mata shirin aure kuma da ya dace. Nenne tace. “Kada ki damu da wannan Zaynaba nima Uwa ce, uwar kuma ta ‘yaya mata, nasan me kike nufi, in lokacin tarewar yayi zan yiwa Siddiqa abinda ko su Murjanatu ban yiwa lokacin aurar dasu ba. Zuwa yanzu dai Ilorin za’a isa da ita ga Emir da dangin mahaifin su. Kin gama mana alfarma ai tunda kin bamu diya kun gama komai, ku dai yi kokarin sanar da ita da lallashinta daga yau zuwa gobe”. Da haka sukayi sallama Haj. Zainab da Nenne, itada direba suka karasa fadar Gombe. Umman Siddiqah kuma ta gayawa Malam Yunus isowarsu bayan sun gama waya da Nenne, don haka a gurguje suka karasa sayayyar abinda suke yi suka koma gida. Kukan Petel tun daga soron farko shi ya fara bakuntar kunnuwansu. Daidai lokacin da suka sawo kai tsakar gidan, sai suka ji muryar Addar Kumo, sarkin kankanba wato kanwar Malam Yunus Magajiya da tazo daga Kumo tana ce da ita. “Shin wai laifi ne don su Hasssilo sun kira ki amarya? To ko kina nufin baki san an daura aurenki bane tun jiya, da Dan Sarkin Yarbawan Ilorin take ko Ibadan??” “Sun jika mana aiki!” Inji Umma cikin bacin rai, tana karasawa cikin gidan da sauri har zanin ta na kuncewa. Siddiqah na ganin shigowar Ummanta ta hau ja da baya a firgice, idonta cikin na Umma tana tambaya. “Umma wai da gaske ne?” Umman ta mika hannu zata rikota sai ta goce. Ido fal hawaye tace “ki gayamin Umma da gaske suke? Wai an yimin aure bada Ishaq ba? Umma wai da Bayerabe? Shiyasa kika kaini gidan Yarbawa na zauna dama Umma? To makarantata kuma fa Umma? Don Allah kada kuyi min haka!” Umma na isowa don ta rike Siddiqa dake kuka tana mazari sai gani tayi yiiip! Aisha-Siddiqah ta fadi kasa ta mimmike mata. Umma cewa take “ku bani inhaler”. Addar Kumo na fadin “ki nutsu Zaynaba, ki gane wannan ba tashin Asma bane, shidewa ce (suma) ne”. Malam Yunus na karasowa bai ce komai ba, sai kawai ya kinkimi Aisha a kafadarsa zuwa motarsa, sai asibitin da take da file wato FMC Gombe. **** **** **** A can gidan Sarkin Gombe kuma su Nani Oummana abin nema ya samu, shirin biki ya kacame ka’in da na’in, bikin jikan da aka jima ana jiran zuwan ranar aurensa a zuri’arsu Nenne Sappa, duk da Nenne tace bata son biki, sabida bata jin dadin jikinta. Uban kasa yaki amincewa, yace ta kwanta a daki ta huta ta barsu suyi. Abdulrasheed ne, dole su yi biki kona kwana uku ne, tunda dangin ubansa ma zasu yi irin nasu a Ilorin. Yayinda can gidansu amarya hankula ba’a kwance suke ba suna asibiti tun faduwar Aisha suke asibitin a hannun likita Umar. Ko a lokacin Haj. Zainab sunyi waya da Nenne ta gaya mata ga akori-kurar kayan abinci nan an taho saukewa sabida bakin da suka zo biki, komai na al’adar bikin gidan Sarkin gombe an hado musu dashi rankatakaf. Hajiya Zainab bata gaya mata Petel dinma tana asibiti ta rikice musu da sambatu ba. Don kada hankalinta ya rabu biyu, ko daga jin muryarta ta fahimci Nenne bata da lafiya, sai Haj Zainab ta roki alfaramar Nenne, tunda itama bata jin dadi kan cewa suna so a daga daukar amarya zuwa kwana uku don a samu a sanar da ita ko me ake ciki a kuma samu a lallasheta. Nenne ta amince da hakan inda ta sanar da ita matan ‘yan uwan mijinta masu daukar amarya zasu zo daga Ilorin, zasu hadu da nata ‘yan uwan su dauki amarya. Likita Umar shine likitan asmar da Petel take gani tuntuni shi suka samu nasarar gani a hannunsa Siddiqah take, kuma yana kula da ita yadda ya dace don dama sun saba sosai shi da ita, yace ba asma ce ta tashi ba, suma tayi dan firgici, ya bata (bed-rest) na kwana daya don yanaso yayi counseling dinta tunda Haj. Zainab ta gaya masa aure ne aka yi mata bagatatan. Koda ta farfado ma bin su Ummanta take da ido ta dauka asma ce ta kawo ta asibiti ta manta shaf da abinda ya faru din. Duk yadda Likitan ya iya lallashin Siddiqa don ta gaya masa abinda ya firgitata da bakinta yau Siddiqah shiru tayi masa, tace ya tambayi Umma don ita ta manta. Umma dake gefe tace. “Likita ba abinda aka yi mata rigima ce irin tata daga dawowarta bata ko ganmu ba, ta tsinci magana a wajen ‘yan uwanta shikenan ta fadi ta sume min. Umma ta kara da cewa “Petel dina, ai kinsan daga ni har Abbanki masu son farin cikinki ne, ba abinda zai daga miki hankali ba”. Sai a lokacin Siddiqah ta tuno exactly me ya faru daga shigowarta gidansu daga Lagos. Da sauri Siddiqa ta katse Umma hawaye nan da nan ya cika idonta. “Umma! Kuna son farin ciki na shine kuma aka aura min Bayerabe da ban ma san shi ba? Umma kinfi kowa sanin yadda bana son yarbawa”. Dr. Umar wanda mahaifiyarsa ‘yar kabilar Yoruba ce, bai san sanda ya kufula yace da Siddiqah. “shi Bayerabe ba mutum bane Aisha?” Ta yi maza ta sunkuyar da kai, hawaye ya zubo mata tace “amma ai inada miji, kuma ban gama makaranta ba”. Abban Siddiqah da Baba Barau tare suka shigo lokacin, suka ja kujera suka zauna ta gaban gadon Siddiqah aka cigaba da lallashin tare dasu. Muryar Abbanta abin tausayi yace “Aishah-Indo Siddiqah, to uban Ishaq din yace bazasu aureki ba tunda kinada cutar numfashi”. Aisha ta zaro ido daga kwance, Baba Barau ya gyada kai ya gyada mata kai cikin tabbatarwa, yace “to su kuma wadanda kikewa kabilancin son ki suke da asmar taki, da dukkan zuciyarsu sun karbeki cikinzuri’arsu, Ubanki kin ganshi sabida ya faranta miki ya kuma fita hakkinku don yasan kinason yaron nan shima yana sonki da gaske sai da ya yi tattaki ya isa ga mahaifin Ishaqa, amma bawan Alllahn nan ya wulakanta mu, don haka ya rage naki ki nemawa kanki mutunci kije inda ake son ki ko ki tsaya shirmen banza a inda ba’ayi dake saboda lalurarki. Hajiya Sappa Uwa ce da kowane Da zai so ta za uwarsa. Ke ya kamata ki bada wannan shaidar, kowadanne iyaye zasu so hada zurri’a da ita saboda karamcinta da girmama dana dam da halin tawali’u, ai dai kin dan zauna da su zuwa yanzu ya ci ace kin san ko su su waye. Inna kara jin Kalmar “Bayerabe” ta fito a bakin ki wallahi sai na kumbura miki shi, don dama yayi miki kadan”. Suka taru su duka har likita Umar suna tausarta, likita yace “Aisha kibi zabin mahaifinki nina gaya miki in sha Allah bazaki nadama ba, a cikin biyayyar iyaye babu nadama kin ji? I am a Yoruba man by maternal tribe, ina tabbatar miki mun iya rikon aure mun iya tattalin matanmu da girmama su”. Umma tace “wallahi wallahi bamu yi miki zaben tumun dare ba duk da ban san shi ba ban kuma ganshi ba ko a hoto, zuri’ar Hajiyar Lagos ba yarbawa ba ko inyamurai ne zan basu ke albarkacin ta da addu’ar da naji tana yi a filin Arfah, tunda dai kalmar shahada ta hada mu bakidaya. Ni bansan ina kika koyo wannan kabilancin naki ba, ni dai baki taba jin na ce wani da ba bahaushe ko bafillace ba daban yake da sauran mutane ba”. Ko ta ina sun rufu a kanta basa ko bari ta ce uffan, wannan ya koro nashi wannan ya cafe. Baba Barau yafi kowa zafi, shi baya hadawa da lallashin ma. Cewa yake ta kara fadin Kalmar yarbawa ko bayerabe yanzu ya kumbura mata baki. Malam Yunus shi ke lallashinta, yana gaya mata kaddadar kenan data hado Hajiya Zainab da Hajiya Sappa a aikin Hajji, wato kaddarar aure a tsakanin ‘ya’yansu. Kaddara mai kyau, wadda aka kullata a gaban Ubangiji a dakin Allah kan dutsen Arfah mai alfarma. Domin Umma ta gaya musu addu’ar data ji Haj. Sappa nayi a kan dutsen arfah. Ta ce tun a lokacin ta fada a ranta baiwar Allah inama zai amince da Petel dina! Ko ba komi addu’arta da tsarkin zuciya tayi ta, kuma sai ta riga ni furtawa kafin ni in furta nawa fatan. Ina kara fada miki cewa ban ganshi ba, ban taba ganinsa ba ko a hoto ban kuma taba jin muryarsa ba, amma shi na zaba miki a matsayin miji Petel”. Aisha ta saka kuka tana cewa “Umma karatuna, Umma makarantata shikenan bazan gama aji shidda ba?” Malam Yunus yace “Aishatu ni malamin makaranta ne kin fi kowa sani, na san muhimmancin ilmin diya mace, ko bana raye bazan bari a aurar dake a inda za’a tauye ki ta fannin ilmi ba. Ki bari ki samu lafiya ki barwa Allah komai, shi zai iya miki kinji ko?” Har dare suna kanta, kuka da sheshsheka har da jijjiga don kuka. Hawaye ya hade da majina. Saida likita Umar yayi mata allurar barci suka samu lafiyarta. Washegari da safe data tashi nurses suka bata maganin ciwon jiki da Panadol ta sha. Umma ta hada mata tea mai zafi da kauri shima ta sha. Wajejem karfe sha biyu na rana yace zasu iya tafiya gida sannan yace da Siddiqah ita kadai. “Babanki ya bani tausayi Aisha, ki duba yadda ya damu da halin da kike ciki, jiya ya sameni a ofis ya gayamin yafiso yayimiki abinda kikeso amma yana ganin kimar wannan baiwar Allah, kiyi hakuri kiyi masa biyayya kinji bazaki tabe ba”. Ya kara da cewa “one more albishir, Yarbawa fa sun fi Fulani iya soyayya Siddiqah”. Siddiqah ta harareshi sannan ta gyada kai, tana tsane hawayen idonta, Umma kuma na can tana tattara ‘yan kayansu batasan me Dr. Umar ke fadawa Siddiqah ba wanda shi fisabilillahi an yi masa riga malam masallaci ne tuntuni yana matukar son Siddiqah, amma da yaji ko sakandire bata gama ba shiyasa ya dakata, don shi kadai take gani a matsayin likita duk sanda tazo FMC. Umma tazo inda suke sukayi sallama da likita ta kamata ta sakko daga gadon suka wuce zuwa mota inda malam Yunus ke zaune cikin motar shi Toyota Corolla yana jiransu. Ko kafin su iso gida, an sauke buhunhuna da katon katon na kayan abinci daga gidan Sarkin Gombe. Siddiqah ta wuce uwar dakin Ummanta ta kule a karshen gadon Umma bata ko kula kannen iyayenta dake tsokanarta ba, wai ciwon aure take yi ai normal ne. Addar Kumo da yake mijinta bai jima da rasuwa ba, tabi Siddiqah har dakin Umma tace da ita, “to ni ki bar min Bayeraben mana? Shashasha jikan uban kasar Gombe ne ta fannin uwa, ni inasonsa tunda ba wani tsufa nayi ba”. ta kara da cewa (cikin jin takaicinta) “Su Indo! An tako arziki ana kokarin fatali da shi da gangan”. Siddiqah kasa shiru tayi tace “Adda wallahi Allah na bar miki bayeraben dari bisa dari kuma da zuciya daya, koda Ishaq ba zai aureni ba ai na fi karfin auren bayerabe jikan oduduwa”. Sai jikake gab! Umma data shigo ta gabje bakin nata. “Inace dazunnan Babanki Barau yace kada a kara jin kalmar nan ta kabilanci daga bakinki?” Siddiqah kuka ya koma sabo, bazata iya tuna (when last) Umma ta kai hannu jikinta ba sai yau. Itace ta fari itace auta tsakanin ta da Umma sai soyayya. Sai yau akan Bayerabe dan kawarta. Tayi kuka-tayi kuka ta gode Allah bata kara tankawa kowa a gidan ba. Daga bisani kuma barci ya dauketa. Data farka da la’asar da kyar Addar Kumo tasa ta tayi wanka shima duk rabi ita ta cuda mata baya Siddiqah na rufe kirjinta wai kada Adda ta gani. Wannan abu ya kara kular da Siddiqah don tayi tayi Addar ta fita ta bata wuri tayi wankan da kanta taki, tace na san biji-biji zaki yi, gara in cuda ki da kaina, da aka haife ki ma ni dinnan nina cude ki, har yaushe kika yi girman? Ina abin yake da zan gani wai maye ya ci jinjiri kirji kamar ‘ya’yan goriba? Haka in kin haifo mana jikan Uban Kasa ni zani har kasar Yarbawa in sake wanke ki fes da runhu da ganyen darbejiya”. Kabakin abinci iri-iri aka dinga fiddawa daga gidan su Siddiqah da soyayyen naman Sa zuqu-zuqu akai, wanda aka saka cikin abincin ya wadata. Lemuka (soft drinks) kamar a wanke tsakar gidansu Aisha dasu. Surutu iri-iri a Jeka da fari, don basu bayyana neman auren ba sai bayan daurin auren aka bayyana kowa yaji. Wasu ma sun ce Uban kasa ne da kansa wato Yayan Nenne Sarki mai ci a yanzu Abdul Yasar Jalloh Umar ya auri Aisha-Siddiqah. Duk kuwa da cewa ana kishin-kishin wai sarkin Ilorin ne da kansa ko babban dansa. Shaci fadi iri iri musamman daga gidansu Ishaq. A lokacin shi Ishaq yana can Abia state yana bautar kasa babu wanda ya sanar dashi daga gidan su. A kwana biyun Aisha ta dan kwantar da hankalinta, amma bata fitowa daga daki. Adda tayi mata kwalliya amma iyakata uwar dakin Umma. Ko falo bata zama. Musamman da Malam Yunus jiya da daddare yazo har dakin Umma ya sameta, ya bata kunshin balangun da ya shigo mata dashi mai zafi da ruwa-ruwa, don yasan ko abinci ba sosai take iya ci ba, sai Umma ta zauna ta bata a baki, shima loma uku take yi tace ta ko shi. Malam Yunus ya zauna a gefen gadon da Aishah take kwance, yace da ita “kwantar da hankankalin ki kin ji Indo? Dazu nayi Magana da Hajiya Sappa kan makarantarki, ko zasu mana alfarma su bari ki karasa kafin ki tare, tunda term biyu kadai ya rage miki? Tace kada in damu, gtana sane da wannan, zasu wuce dake gidanta a Lagos ne daga Ilorin, in an kai ki kin ga dangin mahaifinsa, Kakansa ya ganki yasa albarka, amma a gidanta zaki zauna har sai kin zana WAEC da NECO zaki bari ki tare a gidan mijinki”. Wannan albishir ya dan faranta ran Siddiqah. Ba’a tashi drama da Siddiqah ba sai a washegari da ‘yan daukar amarya suka iso da hantsi ido na ganin ido daga masarautar Gombe, tareda hamshakan dangin Abdulrasheed mata daga Ilorin. Matan Baffanninsa ne su duka tara da dangin marigayiya kakarsa Olori Murjanatu, wadda ta haifi Waziri Idrisu, su uku suka zo daban, suka hade da mutanen Ilorin suka taho Jeka da fari a manyan motoci Hummer Jeep bakake wuluk masu tinted. Raba Aisha da Ummanta kadai abin kallo ne domin wani ‘show’ ya koma, don saida aka boye Umman aka iya fitarda Aisha daga gidansu zuwa fadar Gombe, tare da Goggonninta su Addar Kumo, da Baba Barau da kansa a gidan gaban motar a matsayin uban aurenta kamar yadda yake a al’adar su dole a yi mata uban aure. Nasiha iri iri babu wadda iyaye da ‘yan uwa da baba Barau basu yiwa Aisha-Siddiqah tun daren jiya ba. ko ta dauka ko bata dauka ba dai ta ji su. A gidan Sarkin Gombe a dakin Nani Ummana wato Kakar Abdulrasheed data haifi Nenne Sappa aka kai amarya da iyayenta, Nani duk da ta tsufa sosai amma kasancewar 'ya'ya na kula da ita ga rike ibadah tsufa baisa ta rikice ba, tsaf take, cikin nutsuwarta, ita ta amshi amarya da iyayenta inda aka wadatasu da nau’I nau’I na kayan abinci na alfarma da abin sha gwargwado. Daga bangaren matan Sarki na yanzu wato Yayan Nenne Uban Kasa Abdulyassar wanda shi ya gaji mahaifinsu duk an kawo kabakin abinci iri-iri na sarauta. Da daddare ne aka kai Aisha har turakar uban kasa yayi musu addu’a mai tsayi, inda yace da ita suna mata maraba da shigowa masarautar Gombe. Suna mata fatan alkhairi mai yawa da fatan bada jimawa ba ta cika musu gida da 'ya'ya. Sun kwana a gidan Sarki karkashin kulawar Nani Ummana da hadimanta sai washegari Nenne da wasu daga ‘yan uwanta da iyayen Abdulrasheed mata da suka zo daga ilorin suka dauki amarya suka wuce Ilorin da ita ta jirgin sama, don a kaita ga Emir, da kuma dangin mahaifin sa da da yawa basu ma san da zancen auren ba. Abinda zai baka mamaki hatta Taiwo bata san komai ba. Nenne da Dade suna ta boyewa, Taiwo itace kunnen Abdulrasheed shiyasa suka boye mata kada su bata musu shiri, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya kira ta a kan maganar don ta tafi UK tare da mijinta bayan y agama hutunsa. Da yawa cikin family din su ma basu sani ba, banda matan baffaninnsu da suka je Gombe dauko amarya. Princess Fatima da Princess Firdausi kuwa suna can gida Lagos, basu san meke gudana ba, sun dauka Nenne ta tafi mayar da Aisha wajen iyayenta ne kawai, daga nan zata ga gida ta dawo, basu san ana can ana bidirin auren Hamma (Prince) da Aisha a Gombe ba tare dasu ba. Duk abubuwa na al’adar su na karbar amarya an yi wa Aisha-Siddiqah a Ilorin, aka kuma kaita ga Emir. Sarki Abdulrasheed dan Abdullataeef Akanni, ya dade yana musu addu’a itada Kehinde ya kuma baiwa Aisha kyautar zoben zinare mai daraja a cikin battarsa, kyauta ce ta bajinta da sarki ya dade baiyiwa kowa ba. domin kuwa zoben na marigayiya Olori Murjanatu ne da ya gada. A kofar fitowarsu daga turakar Emir ne mayafin Siddiqah ya dan zame, fuskarta ta bayyana sai a idon Bisola. Bisola ta cika da mamaki, wannan kamar abokiyar fadanta Siddiqah Yunus. Ta tambayi ta kusa da ita aka tabbatar mata daga Gombe aka aurota. Bisola sai da ta san yadda tayi ta kutsa cikin mutane ta isa har jikin Siddiqah wadda ke rike cikin hannun Adda Magajiya, ta sunkuya daidai kunnenta ta ce “an fadi ba nauyi. Aisha Sadiqqah! Kece kuma kika bige da auren dan sarkin yarabawa?” A firgice Siddiqah ta dago sai taga Bisola Akanbi. Bisola ta kyabe baki ta ce “dama an ce mutum bai san inda ranarsa zata fadi ba. Sai a koyi kiyaye harshe acan gaba”. Ta murguda baki ta kada ido ta wuce cikin ‘yan kallo. Kafin su wuce Lagos kusan duk masarautar Ilorin sun samu labarin auren. Masu mamaki nayi masu jin haushi da takaicin an rasa wadda za’a baiwa Prince duk cika da batsewar masarautarsu sai diyar fulanin arewa na yi, kuma wai ba ‘yar sarauta bace diyar malamin sakandire ce, ko daga nan Aisha Siddiqah bata samu wani maraba sosai daga dangin mahaifin Prince ba. Musamman da ba wani shahararren biki aka yi mata ba irin wanda aka saba yi a gidan, ba kuma angon, kuma babu danginta masu yawa da suka nuna ita mai yawan dangi ce, sannan kowa ya tabbata Prince Kehinde, bai san ma ana yi ba. Rabonshi da kasar shi an doshi watanni uku kwarara yanzu. Sai bayan sun koma gida Lagos ne an kai Aisha dakinta na da, an kai mata duk abinda zata bukata sannan Nenne ta samu nutsuwar zama ta kira babbar diyarta Taiwo a waya, dake Lancashire a lokacin tare da maigidanta. Bata san cewa kafin ta kira ta tuni Fatima ta kira Aunty Taiwo din cikin tsegumi da mamaki, wai Anti Bisi (matar Uncle dinsu Malami Uban Doma) ta gaya mata sunje Gombe dauko amaryar Hamma Prince, amma meyasa Nenne bata saka su a ciki ba. Me hakan ke nufi?” Taiwo (was like) irin bata yard aba wasa ake yi, hakan ba mai yuwuwa bane a yiwa Kehinde dinta aure babu saninta. Wane irin aure ga Prince haka bagatatan kamar wasan yara? Ita din ai daga mahaifiyarsu wato Nenne, sai ita a mutane masu matsayi cikin rayuwar Prince, kuma ta ya za’ayi masa aure babu sani da amincewarsa sai kace wai saurayi ko karamin yaro? Don ko jiya sunyi waya dashi lafiya-lafiyar Allah sukayi sallama bai ce mata komai ba, mai nuna ya san zancen. Tana kashe wayar Fatima don tsananin haushi ta kasa cewa komai, sai ga kiran Nenne na shigowa, kamar jira take Fatima ta gama tseguminta sannan ita kuma ta kira. Taiwo ta amsa wayar mahaifiyarsu ba tareda ta nuna jin haushinta na tsameta da tayi daga al’amarin ba. Nenne ta kwashe komai ta gayawa Taiwo, tun haduwarta da Hajiya Zainab a tafiyar filin Munna, da yadda taji sha’awar karbawa Abulrasheed auren diyarta bai ko sani ba, ba don komai ba sai don ita kadai taga ta dace dashi. Yarinya ‘yar masu mutunci sannan mai addini da tsarkin nasaba. Amma ina! Hankalin Taiwo yana kan Haseenah da labarin data zo har UK ta bata akan abinda ya faru tsakanin ta da Tokumbo, cewa daga baya ta gane magani Tokumbo yasa mata a lemo a gidan Prince, yayi raping dinta a dakinsa shine har Prince ya zo ya gansu basu sani ba. Da sauran maganganu very sensitive na kare kai, da yasa ta daina ganin laifin Haseenah kwatakwata. Ai daga jin Nenne tace daga Gombe ne ta karbawa Hamma aure, nan take Taiwo ta tuna da zancen yarinyar nan ‘yar siririya da Fatima ke bata labari kullum, wadda tace Nenne ta dauko a Jeka da fari tana zuba musu fi’ili a gida har da kyamar abincinsu. Babban abinda ya bata ran Taiwo da aka yi abinnan babu sanin ta, ba kuma ita ta tsara komai ba. ba karamin buri ta ciwa auren Kehinde dinta ba duk ranar da yazo. Amma wai an yi an gama babu ko saninta. Taiwo nada son girma, wannan halin a ciki jininta ne, wanda ta tashi dashi a matsayinta na babbar Yayarsu tun suna yara tanada son seniority. Hakannan tanada son duk wani sha’ani in dai ya shafi Prince Kehinde ya kasance kacokam a hannunta. Kuma wai yarinyar da aka ce kyamar kabilarshi ma take yi, koba itace akace wai bata iya cin abincin gidansu ba. Me Kehinde zai yi da karamar yarinya haka (teen) mara exposure? Ai ko Haseenah da ya so ta baiwa shekaru 22 baya a lokacin, kuma tana ajina uku a jami’a a turai, duk da shi ya saka ta. Ta tabbata Prince ba zai taba yarda da wannan zabin ba ita kuma har kullum tana bayan abinda yake so ne. Ita a wurinta Prince har gobe yana son Haseena bacin rai ne da kishi, wanda tayi alkawarin sulhunta su. Nenne bata taba yin wani hukunci da ya bata ran Taiwo irin na wannan lokacin ba. Don ta katse duk wani hanzarinta na shirin sulhunta Haseenah da Kehinde. Kafin Taiwo tace komai, Nenne ta soma gargadinta kan cewa bata yarda Hammansu Fatima ya ji komai akan maganar auren shi daga bakinta ba, ta kyaleshi har zuwa ranar da yayi niyyar zuwa don kansa, bata yi mishi aure don ta takura shi ba, ita da kanta zata sanar dashi ta hanyar da zai fahimceta, don yanzu makaranta ma zata mayar da Aisha abin bana gaggawa bane, zata ta zana WAEC da NECO kafin lokacin da yaga damar zuwa don radin kansa. Taiwo was speechless. Har suka gama magana da Nenne, bata yarda ta ce uffan ba don bacin rai, ita bata yarda bama ba’a mafarki taji zancennan ba. Wasa kawai ake yi hakan ba mai yuwuwa bane Haseenah da Kehinde zasu komawa juna da taimakonta. Don a halin yanzu ma suna tare da Haseenah a UK, wadda tayi tattaki ta sameta har gidanta a Lancashire ta gaya mata komai na hanyoyin da Tokumbo yabi ya yaudareta ya rabata da Prince. Ita kuma kamar wata Rakumi da Akala duk tabi ta hau kai ta zauna. Ita ta san zuciyar Prince har gobe Haseenah take so, don soyayyar da yayi mata irinta ce ake kira soyayya ta gaskiya da babu material attachement, tunda kuwa a kanta ne ya guji dukkan ‘ya’ya mata. Haseenah ta gaya mata cewa ta dade da barin kasar Japan, wato bayan kammala karatun digirinta, tana aiki da bankin Barclays a yanzu haka a garin Leicester. Har gobe aure ya gagareta, ba don batada masoya ba, a cewarta sai don Prince kadai take jira ya huce. Yadda Nenne ta sanar da Taiwo haka ta gayawa Firdausi da Fatima, cewa kada su sake su sanar da shi sai ya zo don gigin kansa. Taiwo ta rasa me yasa ta yarda da duk abinda Haseenah ta gaya mata, har hakan yasa kwanannan take jin kewar rashin Haseenah cikinsu a ranta, ji take babu macen da ta kwanta mata a matsayin partner ga dan uwan nata irin rainonta HASEENAH AMBURSA! Yo waye yake sama da aikata kuskure ma? Haseenah ‘yar adam ce kamar kowa, mai sexual feeling at her very age a lokacin, Nenne kuma ta hanasu aure itada Prince, don haka ta dauko uzuri saba’in ta yiwa Haseenah tun sanda ta sanar da ita asalin komai da ya faru ta daina tsangwamarta a ranta. Sai ma ta koma ganin beken dan uwanta kan ya fiya kullata. Abu baya taba barin zuciyarsa ya wuce. Shi Kehinde din zai ce a tsayin rayuwarsa bai taba kusantar kowacce mace bane? Musamman in akayi la’akari da inda yake zaune, a matsayinsa na namiji mai cikakkiyar lafiya da arzikin rayuwa mai albarka irin wannan?? Saidai idan da gaske ne da ake kishin – kishin din cewa, bashi da lafiya ta auratayya ko aljana ta shafeshi. A ganinta Haseenah ce kadai ta dace da bukatun Prince, ita kadai zata iya baiwa Prince kulawar aure da ya dade yana bukata daga mace, ba wannan yarinyar kamar ‘yan tallan nono ba. Fatima ta tura mata hoton Aisha Siddiqah ta waya ba tareda Aisha ta san lokacin data dauketa ba, tun ranar da sukayi discussion a kanta, kyau kam akwai shi tareda Aisha-Siddiqah Yunus itama ta shaida, ko makiyin Aisha zai shaida wannan farat daya, gashinan har neman zuba yake inji zuciyar Aunty Murjanatu, ga cikar sumar kai, ta gira data ido masha Allah, amma kuma nakasunta shine ba exposure (ba wayayyen kai) da zata jera da Prince matsayin matarsa. Har ila yau kamannin Siddiqah sun nuna innocent looks dinta, babu sanin me duniya take ciki ko dabarun zama da namijin duniya irin Prince Kehinde. Uwa Uba babu dressing a tareda Aisha-Siddiqah irin wanda zai dauki hankalinsa a matsayinsa na celebrity, ba cikar kirji balle na mazauna kamar ma yanzu ne ta soma balaga, Ya Ilahi ga mazansu na Yoruba da son mata masu manyan abubuwa, gatanan dai a hoton irin (typical Fulani girls) na garin Gombe. Wadda babu abinda take da shi da zai dauki hankalin namiji irin dan uwanta (Prince). Wannan din dai tunaninta ne amma, bata ce lallai kowa ya yarda da ita ba. Yanzun damuwarta shine ya zatayi da Haseenah in taji Prince yayi aure? **** **** **** Yau kwanan Siddiqah uku kenan a gidan iyayen mijinta. Mijin da ko a hoto bata taba ganinsa ba, ko a sauti, bata ji muryarsa ba. haka ko a mafarkai bata taba yin na ta ga kamanninsa ba. Saidai kuma karamcin iyayensa ya danne komai. Tsakanin Nenne Sappa da magidanta Dade wato Engnr. Idris Akanni, sai ka rasa waya fi damuwa da son a kyautatawa Siddiqah a cikin gidan. Suna kula da ita su duka biyun daidai gwargwadon iyawarsu. Duk abinda aka san zai kwantar mata da hankali shi ake mata. Ba’a yare a gabanta tunda Dade ya hana, don muzanta take sosai in ana yin yarbanci ana kallonta. Iyayen Abdulrasheed mutane ne maso son ‘ya’yan su kamar larabawa suke wurin son ‘ya’ya shiyasa soyayyar su da Abdulrasheed duk ta dawo kan Siddiqah ganinta suke kamar Prince da kansa a gefensu, ko wani bangare na jikinsa. Don ya jima rabonsa da gida, shi da kowa nasa yanzu sai dai waya. Don haka zamu iya cewa matsayin kaunar Prince a zuciyarsu ya shafi kaunarsu da Aisha-Siddiqah. Duk yadda zuciyarta ta kai da kin auren, da kuma kabilancinta garesu, wanda har kawo lokacin yake kwance lambam a kasan ranta wanda zuwa yanzu zaka iya fahimtar cewa kabilancin Siddiqah ga yare (in born character) dinta ne, wato kabilanci a jininta yake ba ga kabilar Yoruba kadai ba har ma ga Inyamurai, ‘yan Kudu da duk ma wata bakuwar kabila da ba tata ba kuma suna yin yare, in dai ba Hausa ba ko Fulani, ba wai da gangan take yinsa ba, a’ah, da gaske zuciyarta ta raina Yarbawa, ta riga tayi underestimating dinsu a ranta. Saidai kuma zuwa yanzu ta gane cewa kabilar yarbawan ma wajen tsafta akwai (exception). In general ma ai Yarbawa yanzu sun fi gaban irin kallon data ke musu. Wannan din da ya samu muhalli a tareda Siddiqah wani abu ne da ke faruwa tun zamanin iyayenmu da Kakanninmu akan Yorubawa amma ba a wannan zamanin ba. Sannan kuma rainin da zuciyarta ke musu a yanzu baida alaqa da rashin tsafta, ko warin jiki (kamar yadda take fadi) ko makamancinsu, kawai dai perception dinta ya riga ya ginu akan cewa Bayerabe bai kai malam bahaushe ko bafullace daraja da martaba ba a duniya. Don haka har zuwa lokacin kabilancin Siddiqah yana nan a ranta ba tafiya yayi ba, tana jin kiyayya da kyamar aurenta a ranta, musamman in ta tuno maiyuwuwa mijin nata ma Bayerabe ne, abin ba wai ya bar ranta bane gabadaya amma ya ragu kadan data gane cewa Yorubas ba yadda take jinsu (in theory) suke (in practice) ba. Zamu iya cewa kaso hamsin cikin dari ya russuna ne sabida abinda take ta cin karo da shi akan yarbawa ya saba da tunaninta. Yawanci duka mockery ne na hausawa sabida kabilancinsu garesu Adadin yawan kyautatawar iyayen Prince a gareta, wato kulawar da (Nenne da Dade) suke mata yasa dole zuciyarta ta sanyaya da zaman gidan, ta ragewa kanta damuwa da takurar zuciya ta ragewa kanta kewar Ummanta. Ta dauko ‘yar walwala dai – dai misali ta sakawa fuskarta a gidan, in ka ganta kadaran-kadahan bata fushi kuma bata far’a, ko don Nenne ta san cewa tana appreciating kyautatawar da suke yi mata taga ya kamata ta saki ranta. Ina laifinsu don sun kawota don ta zauna a cikin family dinsu? Ai ba mai kawo ka cikin iyalinsa a wannan zamanin sai mai kaunar ka da gaskiya duba da ajin rayuwarta dana iyayenta akan nasu. Yau Nenne taje ta ga Likitanta na Lagos ta dawo, jikin nata dai da sauki, ta samu Siddiqah da Firdausi suna shirya abincin rana, maimakon abincin da Nenne ta bada order ayi a gidan wato (Oka/Amala and Ewedu Soup) sai ta samu suna shirya shinkafa da wake da salad da mai da yaji (daga gani ta gane bisa zabin Aisha ne) Firdausi kuma ta biye mata aka yi. Ire-iren abubuwanda ke bata ran Princess Fatima kenan, don haka bata ce musu don me ba kada Siddiqah taji ba dadi, amma sai tasa Femi ta dafa mata indomie da sardines ta jajjaga mata attaruhu da albasa a ciki, ba zata iya cin wannnan abincin na hausawa mara ban sha’awa ba. Firdausi ta yarda ayi wake da shinkafa dinne matsayin abincin gida duka, duk don tasa Siddiqa ta yi (feeling at home) daga yadda ta kasa far’a a gidan tun dawowarta, zuwa yanzu ita Firdausi da yake psychology ta karanta, ta fahimci Siddiqah sosai har fiyeda kowa a gidan, duk da ba janta a jiki take ba, ba kuma daki daya suke kwana ba, ta gane ba da gangan Aisha-Siddiqah take yin kabilancin da take yi musu ba, tsakaninta da Allah da ya halicceta bata taba samun kanta a wata kabila daban ko shiga wata al’ada ba bayan tata, kuma bata taba jin wani abu ‘positive’ akan kabilar Yoruba ba sai ‘negative’, so adopting komai nasu gareta farat daya a matsayin sabuwar al’ada zai mata matukar wahala, saidai ace zata iya with time, idan sun jata a jiki su basa nuna mata kabilancin, gradually (a hankali) nata ma zai tafi, musamman in tana tare da Hammansu Prince. A wurin Firdausi ba mutum mai kirki irinsa a duniya. Sannan shi baida al’adunsu sosai a tare dashi, yawanci dabi’unsa na western societies ne, wato inda ya rayu tun haihuwarsa ya kuma girma cikinsu. Nenne ta isa dining tana duba abincin cikin a manyan food warmers na alfarma da suka shirya shi ciki, sai ta zauna a kujerar dining daya a gajiye, ta ce su zuba mata taci ta kwaso yunwa da gajiya, amma kada su saka mata barkono (yaji), ta tambayesu ko ina Princess Fatima? Bata jin dadin yadda Fatima bata zama tare dasu. Firdausi ta gayawa Nenne cewa Fatima ta fita tareda Seun (Direba) yanzunnan bayan taci abincin rana, wai zai kaita wankin kafa, daga nan zata kitso amma tace bazata jima ba. Aisha-Siddiqa ta ga Nenne ta rame mata a idonta, amma ko ya akayi ‘ya’yanta basu kula da cewa a kwanakin nan karfin hali kawai take yi ba amma cikin ciwo take? Siddiqah ta samu kanta da jin tausayin Nenne, ta dauko gorar ruwan swan mara sanyi ta kawowa Nenne ba tareda ta bukace shi ba, bayan Firdausi ta cika mata abincin a plate, Nenne ta karba da murmushin godiya ga dukkansu, har tana tsokanar Aisha duk da muryarta ba karsashi. “ka ga min Indo amaren Lagos! Kaga min amaren bana masu abin mamaki sai kyallin goshi suke amma ba tsoka”. Siddiqah ta kyalkyale da dariya, itama ta san bata da tsoka irin ta jama’ar gidan, dukkasu bulbul suke, Nenne ce kawai har yau jikinta na Fulani bai canza ba, kamar bata haife su ba dika-dika dasu. Ganin yau ta sake tana dariya sai Nenne taji dadi, ta kara da cewa. “Yo daman kina faman cin abinci da mai da yaji kullum Aisha ina zakiyi wani kumari? Bari dai insa Femi ta barzamin garin gero dana farar shinkafa, sai a hada da garin Aya na dabino da na cukui, in samu lokaci daga gobe in fara hada miki abinda zai sa ki murmure nan da nan”. Dariya Siddiqa ta kara yi, zata so kwarai taga ta murmure din itama, ta zama cif-cif kamar Aunty Princess Firdausi, wajen kwalliya kuwa da iya taku na class Princess Fatima wadda kullum cikin kalkale jikin ta take a shagunan beauty make up, saidai ina! Tasan ita bazata taba iyawa ba don bata taso cikin hakan ba. Nenne ta shagala cikin kallon Aisha-Siddiqah tana dariyar, tayi mata kyau sosai a idonta, sai tayi kama da furen fulawar nan rose don kyau. Dariyar data keyi har ranta, ta kawata ‘yar karamar kyakkyawar fuskarta sosai. Nenne ta soma tunanin ko yaay Prince zai karbi zancensa da Siddiqah ranar da ya ganta? Ta sani ba komai ke burgeshi ba, amma ko hasidin iza hassada bazai kushe Siddiqah ba sai don kawai ace bata da wayewa irin tasu, Nenne ta kara cewa cikin mamakinta, “anya Indo! Ba kya ko tambayar wani cikinmu wanene angonki? Yau kwananki uku gidannan babu shi babu alamarsa, amma ko a jikinki, sai cin wakenki da shinkafa kike hankalin ki kwance, kamar ba aure aka yi miki ba, ya dai kamata zuwa yanzu ki kauda kawaicin kice “Nenne, ku nuna min shi haka mana?” Kunya sosai ta kama Siddiqah. Da sauri ta bar wurin zuwa dakinta cikin sassarfa, don ji tayi kamar ta nitse a gun don kunyar da Nenne ta bata, ba tareda ta cewa Nenne komai ba ta gudu dakinta. A ranta ta san idan tana marmarin ganin mijin nan nata, kada Allah ya bata abinda take so. Bata san shi ba, bata fatan tasan shi ko a hoto ko a mafarki. Namiji daya take so har gobe a ranta da ruhinta, wato Ishaq Hassan Nafada, wani kwayan mutum guda daya da ya nuna mata yadda zata so shi tun bata balaga ba, kuma tunda ta rasa shi shikenan. Ita kawai gata nan ne a gidannan bata san me tazo yi ba. an dai yi mata yankan kauna an rabota da Umma. Amma Nenne da Dade na kokari matuka a kanta, bazata taba kushe kulawarsu da soyayyarsu gareta ba. Ko don hakan zata cigaba da zama a gidan Engnr. Idris Akanni, har Allah yayi hukuncin da ya dace akanta. Ita dai ta san tayi biyayya kuma falalar biyayyar take jira. Princess Firdausi na dariya tace ma Nenne. “Har fa album na hotunan Hamma na dauko mata fa, tuna yana yaro dana dokunansa, na ce ta ganshi takuma ga SAHEEB dinsa kafin yazo, amma kememe Siddiqah ta ki yarda ta kalla sai ma ta tashi ta bar min wurin”. Zuwa yanzu Aisha- Siddiqah ta kara fahimtar cewa, shi din, wato mijin nata da bata sani ba wato Hamma Prince AbdulRasheed, dan gata ne a wajen mahaifiyarsa da ‘yan uwansa mata, haka a wajen mahaifinsa Dade bashi da na biyu, ko don shikadai ne namji a cikinsu? Ko daga yadda take yawan jin zancensa a bakin su kowa “HAMMAH”. Komai zasu yi sai sun tuno shi “HAMMAH” dai. Akalla sai tace babu ranar Allah da bata ji sun ambace shi ba tun dawowarsu daga Ilorin. Haka shiga goma fita goma kowaccen su sai ta ambaci Hamma yayi kaza ko yana son kaza, ko tana kewarsa, Siddiqah uma ta sha jin Ummanta na cewa yawana adadin ambaton ka da mutum yawan adadin kaunarka gareshi, hakan kuma ya nuna mata cewa akwai kyakkyawar alaqa tsakaninsa da twin sisters din shi Princess Fatima da Princess Firdausi. Itama mahaifiyarsu Nenne a cikin gidan nan kullum sai ta ambace shi cikin hira. Sannan ko cikin maganar wasa sai ta tunawa Siddiqah cewa zaman shi take yi bana kowa ba, sannan ta kan ce yana gab da zuwa Lagos, nan bada jimawa ba. Amma har sati biyu da tarewar Aisha Siddiqah wato har ya koma Qatar daga aikin da yaje yi babu Hamma Prince ba labarin zuwansa. **** **** **** Jikin Nenne kwana biyunnan da sauki sosai, don an hadata da wasu magunguna masu tsada da zasu taimaka wurin kwantar da ciwon nata har zuwa lokacin da zata bukaci a yi mata surgery din. Nenne ko magungunanta zata sha bata sha a gaban su, tana dai yawan ce musu bata jin dadi zata shiga daga ciki ta kwanta. Sai ta shige uwardakinta, ta rufo ta barsu tayi ta murkususun ciwon cikinta har ta samu ya lafa. Idan kuma tana jin kwarin jikin to koyaushe zaka samesu a kitchen itada Siddiqah, suna hada girkin Dade tare. Siddiqah ta like ma Nenne a gidan don ita kadai take gani a matsayin yarenta (Bafullatana) suyi fulatanci tare taji dadi. Saddiqah ga makon Uwa, ko Ummanta haka take like mata a kitchen in tana girki, koda kuwa bazata tayata da komai ba to zata zauna a gefenta tana girkin ita kuma tana cika ta da dumin zance. Ta kan manta cewa Nenne uwar mijinta ce sam ko don babu mijin tare dasu ne? Nenne sai tayi amfani da wannan damar ta like mata da Siddiqah keyi a kitchen ta soma koyawa Siddiqa ‘Traditional Yoruba Dishes’ musamman wadanda ta san AbdulRasheed naso. Tana yawan gaya mata Hamman nasu Firdausi nada son cin abincin gargajiyarsu, in yazo ba abinda yake so irin ayi ta jere masa su, ‘traditional Yoruba food’ kala-kala, yana diban wanda ransa yake so da kansa, saboda baya samun irinsu a can inda yake rayuwarsa, Nenne tace “his best friend is food”. Abin nufi. “Abinci shine babban abokinsa (tana nufin Prince nada yawan cin abinci mai maida ruwan jiki). “Don haka Siddiqah ki dage ki koyi wadannan girke-girken na Veggies dana ke yiwa Dade dinku kullum. Su Abdulrasheed ke ci. Saboda yana yawan kona ruwan jikinsa ta hanyar exercise mai matukar wahala kullum safe da yamma. Ta fada mata yanada son cin “WARA” wani abincinsu ne na Yoruba da ake yi da nono, mostly Yarbawa ke yin shi da kansu (deep fry na Nono). Sannan Nenne ta kan ce mata “Abdulrasheed yana da son neatness na muhallinsa, musamman toilet, in kina so ku haura, to ki bata masa toilet, ko ki hargitsa masa daki, ko ki bar masa shirgi akan gadonsa, yanzunnan zaku bata dashi a jiku duk shirin da kuke yi. Ta kara da ce mata kuma shi mahayin Doki ne. A bakin Nenne taji cewa Hamma din, Polo Legend ne, a tsakanin kasashen Africa dana Turai. Tace "yana da Dawakai, yana son Dawakan shi yana kula da su matuka, kada kiyi mamaki innace miki kamar yadda mutum ke kula da ‘ya’yan da ya haifa. Kullum cikin dawainiyarsu da hidimarsu yake rayuwa. Ki taya shi son su, musamman wani tsohon dokinshi Saheeb, sai ki ribaci zuciyarsa da wurwuri. Nenne kan samu lokaci again tana koyawa Siddiqah yadda ake hosting baki a family dinsu. Hatta dressing dinta na yanzu bata barta da irin wanda take yi a Gombe ba, ta kan gyara mata kadan-kadan. Misali ta kan ce ta rage jambaki yayi yawa, ta rage kaurin gazal, ko tace tasa mascara a girarta maimakon jagira, tace powder mai duhu ya dace da ita ba mai haske ba tunda ita mai hasken fata ce, don haka powders mai duhu ta saya mata cikin sayayyar data yi mata tunda su basa lefe. A satinnan an dinka mata sittiru iri-iri sun kai hamsin daidai jikinta, sittiru masu daraja da zata dade tana mora. Firdausi kuma tana tare da Aisha koyaushe tana kara koyar da ita tsaftar jiki yadda ya kamata da matar aure, don ta raina tsaftar Aisha. A gidan Nenne ne Siddiqah ta san cewa in za’a kwanta sai an yi wanka da brush na barci. Don a Gombe bata yinsu take barcinta abinta. Princess Firdausi Ta koyar da ita yin shaving akai-akai. Tace duk sati biyu ya kamat tayi ba sai gashi ya taru ba. Hatta manner din cin abinci tareda jama’ar gida bisa tebir, Nenne bata yin shiru in ta ga Aisha tayi wani abu ba daidai da su ba, wanda a wurinsu kauyanci ne ko Arewanci, sai ta gyara mata (in a nice way) yadda bazata ji ta muzanta ba, mostly in suna girki a kitchen suna hira, bata yimata gyara a gaban su Firdausi. Ta wannan hanyar tunani na farko da ya dade da samun muhalli a tareda Siddiqa ya goge na cewa duka Yarbawa kazamai ne. Ya Ilahy, ashe a rashin saninta, wasu yarbawan dai har sun fi wasu hausawa da Fulanin tsafta, kudin goro hausawa ke musu na isgilanci da iya shege da suke kiransu masu kashi a kwano ko masu tukin tuwo da Duwawu. A hutun karshen makonnan baki suke tayi a gidan yawanci danginsu ne dake zaune a Lagos da family friends, masu zuwa ganin amaryar Prince, manyan mutane sosai ke zuwa suna tafiya, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da ‘yan sarauta da manyan ma’aikatan gwamnati dake da alaqa dasu Nenne. A zahiri suna mamaki in suka ga ‘yar ficikar yarinyar da aka aurawa Prince Abdulrasheed da bata ko kai shekaru ashirin ba, in suka fita sai sun gulmanta, Bayerabe da son tsegumi, kuma babu wayewa irinta kabilu ko ‘yan bokon arewa a tareda ita, (typical Gombe Fulani girl). Wasu basa iya shiru ko a gaban Nenne sai sun tanka, cewa “Prince shi ya zabi little fulani girl haka?” Nenne saidai tayi murmushi tayi shiru bata cewa komai. Jikin Aisha da ake yawan yiwa ba’ar siranta a wurinta harda sakacin Haj. Zainab ga irin abincin da ta bar Siddiqah tana ci. Ire-iren abincin da Aisha ke ci duk na kwalam ne, tafi ganewa mai da yaji da kayan kwalam su agwaluma, dinya, kanya, magarya wanda babu wani sinadarin gina jiki a cikinsu. In kuma abinci zata ci sai ta shirbineshi da barkono yayi jajir Nenne kan ce Allah ya so ta bata da ulcer, suma Yoruba na son yaji amma na Aisha is over ace ko abinci aka yi da miya da nama ita sai ta dibi fara ta sa mata mai da yaji zata ci. Duk wannan enne na kokarin rabata dasu yanzu. Kai hatta yadda zata dinga dukawa ta gaida Emir da sauran Baffanninsa in taje Ilorin ko sun hadu Nenne bata barta haka ba sai da ta koya mata dukawar gaisuwarsu ta al’ada, ta maida kanta TUTOR ga Siddiqah ba Uwar miji ba. Duk da dai Siddiqah bata nuna wani interest akan abubuwan al’adar Yoruba da Nenne kullum ke kokarin dorata a kai. A wurin Nenne aure abu ne mai broad perspectives, wanda cikinsu ya hada da rungumar al’adun juna (embracing each others’ cultures and traditions) don samun karuwar soyayyar juna, wanda ita Siddiqa a tunaninta bai zame mata dole ba ai, since she has her own culture data riga ta girma cikinta. Nenne kuwa ta yarda da cewa in ka auri mutum ka aure shi ne da shi da danginsa da kabilarsa da iyayensa da dabi’unsa bakidaya, wato dai ba shikadai ka aura ba. shiyasa ta dage wajen koyar da ita abubuwanda watarana su zasu taimaketa a zama da Prince da danginsa. Duk da haka Aisha na jin dadin girke-girkennan data ke koyo daga Nenne, don wani ilmi ne na daban yazo mata, sannan yana keeping dinta busy a gidan har bata zama tunanin gida. Nenne ta gaya mata in zata maida kai ta dinga cin abincinsu ta maida, shine zai gina mata jiki ta zama mace. Ta gaya mata cewa Yoruba na amfani da komai na abincinsu (fresh veggies) ne masu kara lafiya, duka abincinsu kyakkyawan vegetables ne da protein, basa cin abinci saida isashshen nama da kifi da korran ganyayyaki iri-iri, shiyasa take ganinsu healthy cike da kuzari, ga su Firdausi nan masha Allah dasu, bul-bul, cif-cif, kamar ka taba jini yayi tsartuwa. Siddiqa gani take jikinsu Fatima kamar da an soka tsinke zai bule don laushi da kyau. Kirjinsu tantsan da dukiyar Fulani, bayansu cike da mazauna kamar balan-balan, har bata son kallon kanta a mudubi a gidan don sai taga kanta kamar kwancen yunwa, har bata son duba mudubi. Ta maida hankali ga cin ire-iren girke-girken da Nenne yiwa Dade kullum, musamman da yake tare suke yi ba Femi ke yi ba. Nenne tace mata Hammansu Fatima ma abinda yake ci kenan mostly wato Brown Amala da Ewedu Soup. Ta taba gaya mata Hamma baya cin Igbin saboda snails da ake sakawa a ciki. Inda abincin Yoruba guda daya da baya so a duniya to Igbin ne, don baya cin snails tun yana yaro. Amma Gbegiri ma yana sonta sosai. Ta gaya mata shi din ne ma’abocin cin korran ganyayyaki ne a cikin abinci, sannan yana matukar son WARA. In ka gansu a kitchen sun hada kai itada Nenne suna hada girke-girke akan cooker kamar kanwarta dake mata zaman daki, don jikin Nenne baya nuna shekarunta sam. Kullum tana nan fit and healthy don akan ce jikinta na Fulani Prince ya samu mai boye shekaru da rashin mummunar kiba. Bata da kiba, kuma sannan bata da rama sam. Jikinta daidai ita kamar ita ta zabawa kanta. Da farkon zuwanta tana dan jin kunyar Nenne, daga baya da taga bata da wadda ta fita a gidan ga sakewar fuska irin na Nenne Sappa sai ta ware ta maida ita kamar Yayarta. Kai bazaka ce wai danta ne aka aura mata ba kwanaki kadan da suka gabata, ko watakila don ita kanta Siddiqar bata shaida hakan bane a zahiri, wato bata yarda tana auren dan Nenne ba, tunda kuwa da idonta bata ganshi ba, sannan da kunnenta bata taba jin muryarsa ba ko inuwarsa bata sani ba. Don har gayawa Nenne take tanaso tayi kiba da cika irinna su Firdausi. Nenne tace “good, ai siranta ba abin so bace, haka itama kiba, amma taki kam akwai rashin ‘good nutrition’, to daga yau sai ki cire kabilancinki ki dage da cin su Gbegiri, Oka/Amala, yam flour/ponded yam, da miyar Ewedu. Ga kuma kunun farar shinkafa, garin gero, cukwi da aya da dabino dana sa aka niko, zan ke dama miki kullum kiyi ta sha. Nina gaya miki har sai kinfi Firdausi cikar ido da cikar kirji, wadannan ‘yan kirgen dangin naki da aka rasa size din braziyar da zata yi musu daidai, suma su cicciko suyi gwanin ban sha’awa, gasu dama ‘yan kanana da basa bukatar rigar mama”. Kunya sosai ta kama Aisha ta kare fuska da tafukan hannunta tana dariya, hakan da Nenne ta fada ya tuna mata wani abu da ya faru da jimawa sanda Ummanta ta sa muciya ta buge kirgen dangin data soma, wato ta mayar da nonon, lokacin da ya fara fitowa cikin wata hikima ta iyayen da. Nan ta hau dariya ita kadai, tace. “Nenne, ni fa na san dalilin da yasa har gobe ni banida manyan nono, zan baki labari, amma kada ki gayawa Ummana na gaya miki”. Nenne tace “umh, I am all ears, amma ‘yar shekaru kusan sha takwas haka bata saka ‘bra’ ai da mamaki, to ina jinki” ta dakata da abinda take yi ta bada hankalinta tana sauraron Aisha. Rufe ido Siddiqah tayi da fararen tafin hannunta tana kyalkyala dariyar maganar da Nenne ta gama yanzunnan, kafin tace. “Ai wato Nenne sun fito fa da farko, tun ina 13 years, Ummace ta bige su da muciya, lokacin da suka fara fitowa ta samu muciya ta karanta addu’ar da bansan me ta karanta ba tace "Ya Allah ba yanzu ba, sai ta kara girma", sai ta buge su da bakin muciyar, daga lokacin suka koma”. Nenne ta kasa rike dariyarta, don ita bata taba jin inda akai haka ba, kai Hajiya Zainab sai a barta, saida ta gama dariya mai isarta kafin tace. “to ita kuwa Umma meyasa tayi hakan ai girma dole ne ga diya mace, fatan dai shine Allah ya taya mu akan tarbiyyarku, har mu mika ku gidan mazajenku. Fara kirgen dangi da wuri ba abinda zaisa ba abinda zai hana in lokacin aure ya zo wa mace. Sabida shi aure lokaci ne dashi ga kowacce mace ba sai sanda ta shirya ba”. Siddiqah tace “ai Ummana bata so ayi min aure da wuri, ga Babana yayi alkawarin da wuri zai min aure, saboda ya samu jikoki da wuri tuda shi bashi da’ya’ya da yawa, ita kuma Umma tunda nikadai ke gareta, sai bata son auren wuri gareni, shine dalilin data komar da kirgen dangin lokacin da ya soma fitowa, tace itama Goggonta Allah ya jikan rai haka tayi mata kuma suka koma, don in Abbana ya gani zai ce ai kawai na isa aure”. Kai yau cikin Nenne har kullewa yayi don dariyar da Aisha ke bata, tace “kuma sai gashi hakan bai hana auren yazo miki da wuri ba, Allah kenan! Mai yin yadda yaso a lokacin da yaso”. Ita kuwa Siddiqah sai yanzu take jin takaicin abinnan da Umma tayi mata, da yanzu tana cancada gayu kamar su Fatima, don gani take ko kwalliya tayi bata kyau kamar yadda su Firdausi ke cika idon mai kallonsu, suna juya jikinsu yadda ransu yake so. Tun daga ranar Siddiqah ta cire kyankyamin abincin yarbawa, ta bude ciki tana cin ire-iren abincin da akeyi a gidan, irinsu ‘Afang Soup’ da ‘Ewedu Soup’ da ‘Oka (brown amala), ga Iyan (yam flour/pounded yam) da 'ékuru' da akeyi da wake’. Duka abinciccika ne masu gina jiki da kara kuzari. A gefe kuma ga kamun da Nenne ke yi mata da kanta kullum da yamma bata mantawa har cikin dan lokaci ya fara bin jikin Siddiqah. **** ***** **** THE PRINCE Bayan ya koma Qatar baifi da sati biyu ba aka turashi consultation na aiki a Abu-Dhabi Kamfaninsu ‘Qatar Refinery’ ne ya tura Engnr. Abdulrasheed consulting wani aiki na sati biyu a (Abu-Dhabee National Oil Company) don haka yau da safe ya kira Nenne a waya, don ya sanar da ita, yaso kwarai a satin da za’a shiga suzo masa hutu Qatar yadda ya riga ya tsara tunda farko, lokacin da Abdulrasheed ya kirata ko fitowa Nenne bata kai ga yi daga dakin barcinta ba don safiya ce sosai a wurinsu Dade kuma ya jima da fita jogging. Bayan sun gaisa yadda suka saba shi da mahaifiyarsa, kasancewar baya yiwa Nenne kowanne yare sai fulatanci, don yasan shi tafi so su dinga yi mata musamman in shi da ita ne, yarbanci wannan saisu Fatima, sam basu cika yin fulatanci ba sai harshensu na gado. Aunty Taiwo kuwa dama maganarta duka rabi turanci ne ita saboda mijinta Toufeeq da yaranta su Kiki shi suka fi yi a junansu. Yace da Nenne cikin fulatanci “Nenne inata dokin son ku zo wannan watan gabadayanku keda twins, har Hakeem, muyi hutun Easter dinnan tare duk da babu Kiki. Itama naso ince ta samemu anan don ta kusa Hutu. Amma tafiyar aiki ta sameni unexpextedly zuwa Abu-Dhabee sai suka rushe min plan, sai idan na dawo in sha Allah sai kuzo”. Nenne tace “to sarkin kanne Uban Hakeem da Kiki. Sune kawai ababen kulawarka iyali ko oho. ‘Allah hokku sa’a ko ayahi dabbutugo Albarka Annabijo" wato (Allah ya bada sa’ar abinda aka je nema albarkar Annabi), Ya kuma dafa muku”, sannan ta nisa tace. “Hammansu bazamu zo ba wannan Easter Holiday din, saidai kai kazo. Am not feeling fine da zan iya hawa jirgi nan kusa”. Amma Prince ya riga ya sakawa ransa nan kusa shikam nan kusa bai zuwa Lagos ko Ilorin, ba don komai ba sai don gujewa fushin Baffanninsa. Yayiwa Nenne alkawarin zai zo amma sai bayan wani lokaci. Yayi mamaki da bata yi masa korafin Baffanninsa sun bude mata wuta akan rashin zuwansa ba yadda ta saba. Sunyi waya da Aunty Murja ma duka a ranar, wadda ke can cikin bacin ran Nenne ta hanata sanar dashi maganar aurensa har yanzu, balle ta san yadda ya karbi al’amarin ta bangarensa. Da yake bakinta nata kaikayi saida tace masa “Kehinde!” Yace “Na’am” ta sake cewa “Prince! Sau nawa na kiraka?” Yana dariya yace “Taiwo! Kin kirani sau biyu, wani abu?”. “Ka daure kaje gida immediately daka gama aikin da zaka je dinnan”. Ya nemi karin bayani dalilin kalmar immediately din, don yaji seriousness sosai a kan muryarta, sai kawai ta kashe wayarta ba tare data bashi amsa ba. To haka su Fatima ma baki nata kaikayi, kamar sun ci bawon Doya, musamman Princess Fatima uwar tsegumin gidan bakidaya, komai a bakinta Taiwo ke ji. Har hotunan Siddiqah ta tura mata. Amma wane mutum a gidannan Nenne tayi umarni yayi fatali dashi? Ko tasa kara mutum ya tsallaka? Ko basa so zasu bi. Don kowa na gudun bacin ran Nenne Sappa. Da wuya tayi bacin rai a cikin iyalinta amma in tayi shi basa ji da dadi, don bata sauka ta sauki sai kowa yaji a jikinsa. Yau da ba don Nenne uwarsu bace kuma itace da kanta ta hada auren nan na Prince da Aisha, da Murjanatu tace an kwari Kehinde dinta, an zubar masa da class a inda bazai kwasu ba, da aka aura masa Aisha. Ta fadi hakan ne lokacin data ga hoton Aisha Siddiqa a wayarta. Ba wai Siddiqah din ba kyakkyawa bace, a'ah don kyau Masha Allah ko makiyinta ya san ta kere sa'o'inta a kyawun sura. Amma a ganin Aunty Murja kyawun ba shi Prince yake bukata a halin yanzu ba da shekarun girma suka riskeshi. A yadda Prince ya kwashe shekarun kuruciyarsa babu aure a ganin ta cikakkiyar mace kuma kilalliya wayayya preferably ‘yar kabilar Yoruba ce ta dace dashi in har ba Haseenah ba, mace 'yar shekaru akalla Talatin wadda zata kula da komai nasa, ta tarairayeshi ba hijabin kunya, sannan ta jiyar dashi dadin aure da ya jima bai sani ba, amma ba dai shi Prince a halin yanzu yayi zaman rainon ‘teen’ ba. A yadda Fatima ke fasalta mata abubuwan da Siddiqa keyi a gidansu na kauyanci da kuma hotonta data gani ba maraba da ‘yan tallan nono a kasuwar Gombe. Don haka zamu iya cewa, from Day 1, Aunty Taiwo bata yi na’am da dacewar Siddiqah da Prince ba a matsayinta na mafi kusanci dashi data fi kowa sanin likes and dislikes dinsa. Ko dalilinta ya isa dalili? Ko kuma na son zuciyarta ne bazan iya cewa ba. Dan adam din kenan, har kullum halinsa sai shi. Marar godiyar Allah marar tuna baya. In banda haka sai muce ko dai Aunty Murjanatu ta mance yawan shekarun dan uwanta Prince Abdulrasheed dinne? Da dadewarshi yana Polo babu aure, kuma har gobe bashi da niyyar yi? Maimakon Taiwo tace dan uwanta ya tsinci dami akala, na samun yarinya danya sharaf (in her teens) wadda bazai sha wahalar tankwarawa zuwa duk yadda yake so ba. A ganina, Aisha-Siddiqah ce za’a ce ta kwaru da auren Prince Kehinde, wanda a haife sai mu ce ya haifeta, ko mu ce ya kusa haifarta da yayi aure a farkon samartakarsa, amma ba Prince za’a ce an kwara ba a logical reasoning. Taiwo-Murjanatu, bata duba duk wannan ba, ji tayi kamar ta fashe don haushi da taji cewa matar da aka aurawa Prince ma wai ko sakandire bata gama ba, sannan ba ‘yar kowa bace a Gombe, kawai haduwar kan titi ne ita da Nenne. Sai taji fit! Matar Prince bata da muhallin kima a gunta. Wani abunda zai baka mamaki a lokacin ma sai Haseenah ta dawo ranta. Wadda a lokacin suna tare a gidanta ta kawo mata ziyara har Lancashire. Wannan ba shine zuwan Haseenah na farko gun Aunty Murja ba. Don haka a wurin Aunty Taiwo ma kamar danginsu na Ilorin, zamu iya cewa Siddiqah bata samu maraba ba, amma ba yadda zasu yi tunda zabin iyayensu ce. Taso kwarai ace da Prince bai auri Haseenah ba, to zama ya auri wadda zata iya kula dashi, wadda ta fi Haseenah komai na kyau, ilmi da wayewa, Uwa Uba babbar nasaba ta sarauta da da zasuyi tinkaho da ita a cikin dangi tunda akan nasaba ne Nenne taki Haseenah, kuma mace mai cikar halitta da Kehinde zai iya jerawa da ita a ko’ina, amma ba wadda ko a shekaru da matakin ilmi bata kai ya jera da ita ba. A cikin watanninta na uku tareda iyalin Abdulrasheed, sai ga Siddiqah ta fara cikowa, jikinta na faman murmurewa a hankali yana glowing, fatar jikinta tayi lukui-lukui, ta zama wata danya (fresh) wanke hanu ka taba sakamakon zaman waje daya, sanyin iya kwandishan da shan fruits (kayan marmari) da ake yi a gidan kala-kala ya fara huda fatar jikin Siddiqah, hatta farcenta na kafa da hannu wani irin jazur ya koma, kumatunta luwai-luwai sumul-sumul dasu fatar bakinta ta koma wani irin soft, pinkish da ita. Kugunta ya shiga wani irin budewa a hankali ta zama kamar kwalbar nan ta coca-cola daga kasa. Siddiqah zuwa yanzu ta zama kamar an barota daga cikin kwai don kyau da kyawun fasali, sulbin jikinta har daukar ido yake. Madallah da kulawar uwar miji irin Nenne Sappa, madallah da kyawun abincin yarbawa mai inganci da gina jiki (freshy Yoruba food), ga kamun gero da cukwi din Nenne, tabbas yana aiki ba kakkautawa a jikin Aisha-Siddiqah. **** **** **** CIKA ALKAWARI Yau dai Nenne ta cika alkawarin data daukarwa mahaifin Siddiqah, domin kuwa ta shigo dakinnta ta sameta ne tana gyaran kumba, sai ta mika mata littafai da uniform harda takalmi da jakar makaranta, ta gaya mata gobe in Allah ya kaimu zata fara zuwa makarantar da Kiki tayi. Har ila yau, ta sanar da Siddiqah cewa ta shirya an daukar mata malama da zata dinga yi mata lesson Asabar da Lahadi akan jarrabawar WAEC din dake gabanta. Hakan yasa Siddiqah ta kwana cikin zullumin wayewar garin, maimakon farin ciki, wanda shi ya kamata ace tayi, don samun damar karasa karatunta data yi cikin sauki kamar yadda Nenne ta dauki alkawari tuntuni ga iyayenta, ba kuma don komai ta shiga zullumin ba sai wani tunani daya tsirga mata babu gaira babu dalili. Wai gata dai yanzu ta tsinci kanta dumu-dumu a garin Yarbawa ta dalilin auren da bata shiryawa ba, duk wannan bai isa ba, yanzu gashi gobe zata fara cudanya da dalibai suma yarbawa, ta tabbata duka daliban makarantar Yarbawa ne tunda su suka fi yawa a garin Lagos, kuma cikinsu za’a kaita tsundum a barota suyi tayi mata yaren da bata son ji dinnan, in a gida ana ragewa sabida ita. Shin ko yaushe hakkin Bisola Akanbi zai barta ta huta? Ta tabbata shiyake ta bibiyarta har yau. Kabilanci yaki sakin ranta ta sarara, kullum tana tunanin ko ta koma Gombe. Gabadaya rayuwarta ta dawo cikin yarbawan data raina matukar rainawa, takewa shagube da mockery yadda ranta yake so, Allah kenan. Yau dai gata tsundum a cikinsu da sunan zama na dindindin har inda bata taba mafarkin shigowa koda ziyara ba (masarautar yarbawa). Babu ko shakka alhakin Bisola ne ya tsundumota cikin kabilar yarbawa, ya hanata samun rayuwar fulani yadda ta yi mafarkin samu, ta kuma yi burin samu tareda wanda takeso, saurayin bafillace dan uwanta, wanda ya san ciwonta da darajarta, suke harshe da yare guda (Ishaq Nafada). Sai Allah ya jefo ta duniyar yarbawa data ke yiwa wani kallo-kallo da shagube. Yanzu idan taje makarantar itama daliban suka yi mata irin abinda take yiwa Bisola fa a matsayinta na bahaushiya ita kadai? Duk sai taji zancen karasa makaranta ya fice mata aka, gara ta cigaba da zamanta a gidan tunda su suna raga mata, Fatima ce kadai bata raga mata in taga ba iyayensu a wuri ma da gayya ma take suburbuda yarbanci, da zata iya da tace da Nenne bata so kawai a kyaleta. Ta hakura da zana WAEC din don dam aba wani jami’a take son zuwa ba. Dan ilmin data samu na karatu da rubutun hausa ya isheta ya wadaceta Allah ya amfana. Don ko turanci ba wani iyawa tayi can acan ba, tana dai ji in an yi mai sauki amma ko na su Fatima ba duka take ganewa ba. Da wannan damuwar Aisha-Siddiqa ta kwana yau, wadda ta saka mata kewar FGC Billiri, ta hadu da kewar Umma data gang members dinta su Amintako, Ramatu da sauransu. Ga Ishaq dinta masoyi na hakika data kwallafawa burin rayuwa tare dashi ya mata nisa yanzu, ta tambayi kanta ko zuwa yanzu Ishaq ya gama NYSC? Rabon ta dashi har ta manta. Kowa nada wayar hannu a gidan nan banda ita, don Nenne tace makaranta zata fara, nan kuwa bata so Siddiqah ta dinga yiwa Ummanta kuka a waya ne, don kusan kullum ta hada su waya a gabanta sai Siddiqah tayi kuka da ta ji muryar Umma, saidai ta kai yanzu Nenne ta dade bata hadasu gaisawa da Haj. Zainab ba. Yau kam da yake cikin tension da takurar zuciya take, saita nutsu, tana sauraron zuciyarta, shiga tunane-tunanen abubuwan da suka dace suka kuma shafeta, ciki har da tunanin wai shin ma wanene shi wannan Hammansu Firdausi din da ake kira Hamma Prince??? Ko meye matching dinta dashi da har yasa iyayensa suka ga kamatar su katse mata rayuwa a kansa, ta hanyar hadasu wannan makalallen aure haka bagatatan bata shirya ba, kawai daga haduwar Umma da Nenne a hanyar Munna, alhalin sun san ba sonta yake yi ba shanyata zai yi a garin yarbawa? Ai ko ba'a fada ba zuwa yanzu ta gane kamar ma baisan da auren ba, don kusan duk wayarshi da Nenne dasu Firdausi ta kan ji jefi-jefi, bata taba jin wani cikinsu yayi masa zancenta koda da subutar baki ne ba. Kamar ma boye masa suke, me hakan ke nufi? Anya Umma ta san zaman kashe wando da take yi a Lagos ba a gidan Prince din takde ba? Haka kawai an raba ta da mai sonta bayan shi ba son ta yake ba baima da lokacin zuwa kasar Nigeria, me yasa iyayenta zasu takurata a yi aurennan don kawai su farantawa Nenne dake cikin damuwa akan danta. Ita ba'a damu da nata feeling din akan kabilar yarbawa ba. da gaske take tanada kabilanci da ethnocentrism ba da gangan gtake yi ba. amma aka tashi aka aura mata Bayerabe da bata ko taba gai ba shima kuma baya sonta. Ta tabbata da yana son ta, da tuni ya zo, ko bai zo ba, da wani cikinsu ya gaya masa batun auren su da zaman jiransa data ke yi. Gashi har ana neman fita watanni uku. Shi wanda aka ce zaman shi take yi a gidannan bai zo ba, bazai wuce shima bakin bayerabe bane kamar kowanne bayeraben mutum data sani, kuma irin katoto dinnan ya tsa tsagu ba kamar Ishaq ba. Kodayake taga cewa Dade baida tsagu, kuma indai irin kalar su Fatima ne kuma Nenne ce ta haife shi da gaske to ba lallai yayi muni ba. Ai kawai data rasa takamaimai tunanin daya dace tayi, ta kuma ga cewa tunaninta ya fara fita daga saiti, sannan ta kuma ji ta na dokin ganin Prince Abdulrasheed (just to quench her curiousity about him) sai ta karkace ta cusa kai a kasan pillow ta tsinke da kuka ita kadai, irin kukannan na banida tsumi bani da dabara. Ba tareda ta san mawuyacin halin da al’ummar gidan suka kwana a ciki ba. Ashe ita kukan samun wuri takeyi. Kwana sukayi Nenne na suma tana farfadowa cikin murmukususu na azabar ciwon ciki. Don haka cikin daren akayi asibiti da ita. Sai da asubahi taji ana buga mata kofa, dama barcin nata ba wani nisa yayi ba, ba kuma dadinsa take ji bat un bayan daya sureta, tana dai kwance ne kawai, nan da nan ta bude ido tana mutstsika shi sai taji ya kumbure suntum. Ta mike ta bude, sai taga Femi tsaye cikin damuwa. “Aisha ki sauko falo Dade na kiranki”. Gabanta saida ya tsinke ya fadi, amma bata tambayi Femi komai ba ta dauko hijab ta dora akan kayan barcin ta cikin kidimewa tabi bayanta zuwa downstairs. A falon kasa ta tadda Dade a tsaye yana jiranta, Fatima da Firdausi basa gidan suna Ilorin bikin cousin sister dinsu ‘yar wajen Malami Uban Doma. Da girmamawa ta hau kokarin gaisar da shi, amma ko daga fuskarsa ta ga damuwa, Dade yace mata cikin Hausa “Aisha biyoni, Nennenku ce babu lafiya tun cikin dare muna asibiti, and she’s calling you”. Iyakar firgita da rudewa Siddiqa ta shigesu. Ta bi bayan Dade zuwa mota a sukwane, Seun direba ya ja suka tafi asibitin da Nenne ke zuwa wato Lagoon. Suna tafe a hanya Siddiqah na jan hasbunallahu wani’imal wakeel saboda ko daga damuwar da Dade ya nuna a fuskarsa ka san jikin na Nnnne ya matsa, ta na jin sa yana waya da Hammansu Firdausi, akan hanyarsu ta isa Lagoon Hospital. Dade na magana kamar cikin hassala yana cewa. “Kehinde na rantse maka zaka hadu da fushi na, na ga alama baka san zuru ba, na rantse in ban ganka gobe ko jibi ba zaka sha mamaki na, aiki da hawa doki yafi ahalinka ko? Yau watan ka nawa rabon ka da gida saboda Baffanninka? To in kaga dama yanzu ai ka zo, in kana da rabon ganawa da mahaifiyarka dake kwance rai kwakwai, mutu kwakwai tun jiya. Gata nan kwance rai a hannun Allah amma da yake har kullum kana ranta bata fasa kiran sunanka ba. Ka tabbatar ka bar duk abinda kake yi ka nemi jirgi mafi kusa ka taho Lagos”. Ya danyi shiru, da alama rokonsa Prince yake ta daya bangaren, kan ya fadi masa ko me ya faru da mahaifiyarsu Nenne? Dade sai da ya nisa kafin yace. “Wai ashe Hajiya Sappa ta jima da 'renal stones' har 'cyst' ya fito a ‘kidney’ dinta, tana treating ni ban taba sani ba saboda zurfin ciki irinnata?” Da haka Dade ya kashe wayarsa, ba tareda ya jira amsar Hamma Abdulrasheed Prince ba, ya koma ya jingina da allon kujerar motar, ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali yana kiran sunan Allah As-Sattaru, yana rokonsa ya tashi kafadar matarsa abar son sa uwar ‘ya’yansa Nenne Sappa. Itama Siddiqah ta tsorata sosai da jin halin da Nenne ke ciki. Tuni ta fara mata addu’ar duk da tazo bakinta. Sanda suka isa asibitin Nenne ta sha allurai ta samu barci mai nauyi amma bata san wanda ke kanta ba, motsin da bakinta ke yi ya nuna salati take yi da hailala wanda daman baya rabo da bakinta koyaushe. Gari na kara wayewa likitoci sun gama shirinsu na shigar da Nenne tiyata. Dade yayi shahada kan ba yadda zai yi yasa hannu, aka wuce da ita dakin tiyata. Shi da Siddiqah suka koma suka zauna a dakin da aka bata, kowannensu yayi tagumi da hannu bibbiyu yana kissima irin girman rashin da zaiyi, it will be (irreplaceable loss) rashin Nenne a tare dasu. Idan Nenne bata fito da rai ba, dukkansu rayuwarsu ta durkushe suna addu’a suna kuma hawaye, Siddiqah har da kuka wiwi amma Dade ko umh bai iya yace mat aba balle ya lallasheta shima fama yake da kansa, da zai iya shima fashewa da nasa kukan zaiyi yadda ta yi ba kananan hawaye ba amma dai ya jure yanata hailala da carbinsa yana tsane ruwan ido. **** **** **** Koda Dade ya kashe masa waya. The Prince was shocked, hankali a tashe ya zubar da komai da yake yi a lokacin, yanada tournament din da zai halarta swannan satin a Argentina amma ya kansile shi nan take, haka yayi ta kansile duka scheules dinsa na sati yana bada excuse, ya soma neman jirgin da zai kawo shi Lagos ido rufe. **** **** **** Sosai Siddiqah kewa Nenne addu’a kafin fitowarta dakin tiyata da carbin da da Dade ya ciro a aljihunsa ya mika mata, yace tayi masa shiru haka, kafin isowar Femi da kayan karin kumallon su. Amma ko kallon kwandon abincin babu wanda ya iya yi a cikinsu, kuma Dade ya ki kiran kowa nashi daga Ilorin ko nata daga Gombe don ya sanar da su, don yasan da ya fada za azo a cika asibitin. Ya dai kira Fatima da Firdausi yace su bar bikin su dawo gida maza-maza. Bai kuma basu damar tambayar ba’asi ba ya kashe wayarsa amma sun tsinkayi damuwa a muryarsa. Wajen karfe sha biyu na rana aka fito da Nenne daga theatre room. Cikin ikon Allah an yi aikin lafiya, an cire stones and cyst, aka kawo abubuwanda aka ciro din aka nuna wa Dade, Dade sai hamdala yake yana godewa Allah, Siddiqah ta rungume hannu a gefe tana hamdallah, aka fito da ita tana barci akan gado aka gungurata zuwa dakin hutu. Sai lokacin Dade ya samu ya fita ya tafi gida don ya dan kintsa, ya bar Siddiqah tana jiran farkawar Nenne. Ta sakata a gaba, motsi kadan ta gyara mata rufa. Amma an tabbatar musu komai lafiya lau, nan da mintuna talatin zata iya farkawa. Kona minti daya Siddiqah bata dauke ido akan Nenne, fatanta dai Nenne Sappa uwar alkhairi ga al’umma ta farka cikin koshin lafiya don ita tafi yarda zaman Nenne take a gidan, ba zaman kowa ba. Wato ta fi yarda cewa ta zowa Nenne hutu ne gidan ta a Lagos, kamar yadda aka fara tun farko. Ita kadai ta sani, da ita kadai ta saba a cikinsu. Bata san wani Hamma, bata addu’ar ta san shi nan gaba. Ta kuma yarda cewa Nenne Sappa mai kaunarta ce, ba saboda dan ta ba sai saboda amincinta da mahaifiyarta. Ita da Haj. Zainab Allah ne kawai yaga dama ya hadasu zumunci a dakinsa mai alfarma, don su abokantaki juna ba don ajin rayuwarsu ya zo day aba, sai don halayensu da suke kusan daya, na kaskantar da kai, tsoron Allah da yawan tawali’u (down to earthiness). Don haka lokaci-lokaci inta kalli Nenne ta tuno abubuwanda aka ciro a cikinta wadanda aka ce sun dade suna wahalar da ita har share hawaye take sake yi da gefen hijabinta. Aka turo kofar cikin wata irin nutsuwa kamar ansan mara lafiyar barcin allurar anaesthesia take yi. Wani dogon ingarman mutum ya bayyana a gaban Siddiqah. Shi ba fari bane ba kuma za’a kira shi baki ba. In fact, kalar fatar jikinsa rarely kaga mai irinta a kusa, domin mai wuyar samu ce a cikin al’ummar Afrika ta yamma. Gashinan dai ingarman gaske, ma’abocin fadin kirji da kasaitar tafiya. Sannan akwai kamala da nutuwa ta ban mamaki. Sallamarsa cikin wani accent mai dadin ji da zakin sauraro. Kai tsaye bazaka iya gane ko wane yare ne hakikanin harshensa ba. Domin accent din sallamar yafi kama dana Fulanin da basu kware da Hausa ba tsantsa. Yana sanye da ‘casual wears’ na wani tsadadden yadin Filtex ruwan makuba, wadanda da gani babu tambaya zaka fahimci masu matukar daraja ne a inda ake amfani dasu. A kafarsa bakin takalmi ne sau ciki samfurin Raul Burgundy (Black Italian Leather Loafers). Idan kana neman perfection na rayuwa to ka gama samunsa a wannan mutum mai shigowa, dauke da sassanyar sallama a siririyar fatar bakinshi, wadda gashin bakin nan na (man’s pride) yabi ya zagaye har kasan habarsa inda ya kwanta sosai akan habarsa. **** **** **** Siddiqah bata dauke ido a kansa ba har ya zo daidai kan Nenne ya tsaya, hancin ta ya shako mata wani ni'imtaccen turaren maza na “Boss Intense” har bata san lokacin da ta ja numfashi ta aje ba. Ko lura da ita bai yi ba, don gabadaya hankalinsa yana kan Mamansa. “Here comes THE PRINCE!” Zuciyar Siddiqah ta ta gaya mata cikin whisper. Alhalin har yatsun kafarta kakkauran takalminsa ya dan taka mata kuma ta ji zafi da radadi, amma da yake hankalinsa baya jikinsa bai lura ba, kacokam hankalinsa ya dauku kan mahaifiyarsa dake kwance saman gado, baima kula da ya dan taka yatsun mutum ba, yama dauka inuwar daya cikin twins ce a zaune gaban Nenne. Sai ga Nenne ta bude ido a hankali bayan ta shaki turarensa, kamar tana jiran isowarsa kafin ta bude ido, sai idanunta cikin na Abdulrasheed. Prince yasa tausasan yatsunshi ya damke hannun Nennensa sosai, yana fadin "Nenne please don’t leave us..... gani nazo. My Nenne get well soon I beg you, duk abinda kikeso zan yi, koda barin Polo ne dungurungum, na rantse in har yanzu ba kya so daga yau na daina! Na kuma dawo gida kenan!!". Nenne ta lumshe ido ta bude, ta tabbatar Abdulrasheed ne a gabanta, ba cikin mafarkinsa take ba, yadda yayi ya zo haka cikin gaggawa shikadai ya sani. Ta damke hannunsa itama cikin nata, ta nemi ciwon da take ji ta rasa, tana kokarin juyawa idanunta suka fada kan Aisha-Siddiqah. Wadda ta ja can gefe ta tsaya duk ta sha jinin jikinta cewa Prince Abdulrasheed ne. Siddiqah ta sunkuyar da kai, lokacin da Nenne ke yafitota da hannunta da Prince bai rike ba, ko dagowa kasa yi tayi, don jikinta ya gama bata. Hamman gidan ne ya iso. In ka lura zaka ga yadda jikin Aisha ya dan dauki rawa da ‘yar karkarwa. Nenne ta juyo saitin da take tace Siddiqah matso nan kusa dani. Ga Hammanku kingan shi ya zo!" Da hanzari Siddiqah ta dago, anyi sa’a shima Prince ya dan cira ido ya dubeta. Suka hada ido. Siddiqah taji gabanta ya fadi, shima kuma Prince haka yaji. Saboda nauyin igiyar aure ba wasa bane. Amma dai Prince ya dake ya cije faduwar gaban data sameshi a lokacin tunda baima santa ba. Da kailula Siddiqah ta iya cira kafa ta isa ga Nenne, ta tsaya a gefen Prince suka jeru gaban Nenne, jikinta har lokacin bai daina bari ba. Abdulrasheed ya juyo gefensa a hankali yana kallon bakuwar fuskar mai jinyar mahaifiyarsa wadda Nenne ta kira da suna Siddiqah. Wadda da farko sabida rudun da yazo a ciki, tun dazu ya dauka Firdausi ce a zaune a gefensa. Sai ya juyo gareta sosai, ya bude manyan maganansa masu salki da haske da wani irin sheki na musamman a cikinsu, yana kallon bafullatanar yarinyar. A idonsa bata fice sa'ar Kiki ba. Idonsa ya gano masa tarin kuruciya da innocent looks irinna Kiki a fuskarta. Amma cikin dangin Nenne kaf bai santa ba. Nenne bata bashi damar gama tunanin inda ta samo yarinyar ba ta soma shaquwar dake bukatar ruwan Sha, irin na wadanda aka yiwa CS. Don haka da hanzari da zafin nama Prince ya durfafi firjin dakin da saurinsa. Amma ko kafin ya juyo... Siddiqa sarkin zafin nama ta rigashi da nata irin zafin naman, ta dauko robar ruwan Faro akan lokar gado ta bude ta kafa ma Nennne a baki. Saida ta sha sosai ta koshi shakuwar ta lafa mata sannan ta dauke robar daga bakinta, Nenne ta koma ta kwanta ta rufe idanunta a hankali ta barsu. Dade ya murdo kofa ya shigo dakin. Ya tadda Prince da Aisha sun kafa ma Nenne ido, kowanne da gorar ruwan Faro a hannu. Siddiqah ta manta yadda ake gaisuwa sakamakon nauyin igiyar aure na wannan bafillacen sardidin bayerabe dake tsaye gefenta da yazo nan take yayi mata dabaibayi, ta san dai ana gaida babba a ko’ina aka ganshi, Ummanta tayi mata wannan tarbiyyar, amma ta rasa dalilinta na kasa gaida Hamma Prince. Shigowar Dade dakin ne ya ceceta domin ya bata damar shaqar numfashin da ya kasa ratsa huhunta yadda ya kamata tun dazu, sakamakon inner feelings na wanzuwar Prince a wurin da take ji a ilahirin jikinta. Aisha tayi ta maza ta amsa sallamar Dade idonta a kasa, muryarta na dan shakewa. Sai taga kawai bari tayi amfani da wannan damar ta fice daga dakin, zai fi mata sauki fiyeda cigaba da tsayuwar rashin sakewa kusa da Prince, ta kama tafiya ta nufi kofa da zummar fita reception na asibitin ta zauna, ko ta samu damar jan numfashi ta koshi, kuma ta basu dama su gaisa sosai shi da mahaifansa. Amma sai Dade yace “yaki Aisha, zo nan ki gaida Yayanku Abdulrasheed kinji, sai kije Seun yana waje ya kaiki gida ki yi wanka da sallah ki huta, ki ci abinci don nasan rabonki da abinci tun jiya, tunda ga Abdulrasheed ya zo, shi sai ya karbe ki jinyar. Zuwa dare sai Seun ya dawo dake ki kwana shi ya koma. In kuma su Fatima ma sun iso kan magariba kina iya zamanki a gida sai gobe da safe kya dawo”. Daga bakin kofar da take tsaye ta russuna da irin durkuson yarbawa ga manya ta soma gaisheshi, wani irin innocently bewildered, ba tareda ta dawo cikin dakin ba, muryarta na fita a nitse, a ladabce, tana kuma dan shaking haka, cikin fadin, “Barka da zuwa HAMMA ABDUL. Yaya hanya? Allah ya huta gajiya ya baima Nenne lafiya”. Prince AbdulRasheed dai ya rasa a yanayin da gaisuwar tata ta riskeshi, yana cikin wani hali ne na juyayin halin da mahaifiyarsa ke ciki, tunanin halin da Nenne ke ciki yasa baya fahimtar komai sosai yanzu. A halin da yake ciki yanzu bashi dako muhallin da zai iya amsa wata gaisuwa daga kowa in har ba ya ga Nenne ta mike akan kafafunta ba. Don haka bai amsawa Aisha ba. Ya bita da kallo kawai da manyan maganansa da suka dan kada. Sai Aisha tayi amfani da shirun nasa tayi ficewarta. Kallon idanun Prince kadai ya nuna mata bai santa ba sai yau, kamar yadda itama yau ne ta ganshi gani na farko, bayan auren watanni akalla hudu, kuma ganin nasa ya hargitsa nutsuwarta da tunaninta, don yadda ta zace shi ba haka ta ganshi ba. Tayi tsammanin ganin irin katon bakin bayerabe. Sai taga ba haka ba, wani sardidin matashi ta gani tsaye a gabanta mai wadatar lafiyar jinin jiki da koshin lafiya da kuzari, ingarman jiki gareshi irin dai na ‘ya’yan sarakunan Najeriya. Amma me? Bata ga wani gurbi a fuskarshi na ya santa a matsayin matar shi ba. Gashinan dai emotionless. Ba wani reaction da ya nuna mai nuna ya santa ko sanayyar miji zuwa ga matarsa, wani abu data dade tana tambayar kanta “anya Hamma dinma ya santa?” yau dai ta yarda ko a fuska bai santa ba shima. Itama bata ji komai game dashi a ranta ba bayan ‘yar faduwar gaban data samu daga ganinsa na farko yana shigowa, Hamma ya bayyana sabani ga tunaninta. Fuskarsa kadaran – kadahan, wato ba yabo ba fallasa a lokacin da suka hada ido, wato dai kallon da kake yiwa wani da ka fara gani yau aka nuna maka ya sanka kafin ka ganshi, amma bayan wannan babu abinda Siddiqah ta iya ta fahimta a tare da facial expression dinsa. Dade kuwa binsu yayi da kallo a sace su duka biyun yana kokarin karantarsu, har Aisha ta fice daga dakin asibitin da ‘yar sassarfa, dogon maroon kala hijabinta, yana binta yana jan kasa. Seun, ya daukota sai gida. Ta bude ta shige dakinta har da tuntube, ta kulle kanta ta fada toilet ta sakarwa kanta shawa mai dumi tayi wanka sosai, daga bisani ta daura alwallah ta dauro towel a kirjinta wanda ya sauko har saman cinyoyinta ta fito. Tana idar da sallah Princess Fatima da Princess Firdausi suka shigo dakinta a tare, suna tambayarta ina Nenne. Saukarsu kenan daga filin jirgi suka biyo taxi suka iso gida. Siddiqah ta gaya musu Nenne na asibiti babu lafiya yanzu ta dawo daga can, Seun yana waje ai, shi ya dawo da ita, tace su je ya kai su ya san dakin da Nenne take. Don ita Dade yace ta dawo gida tayi wanka sai dare zata koma in ta girka abincin Nenne. A firgice Fatima ta dubi ‘yar uwarta Firdausi, itama ta dubeta, sai suka juya da gudu cikin razani, da sauri suka fice. Saddiqah ta cewa ranta tunda dai duk ‘ya’yan Nenne sun hallara akanta, to komawarta asibitin a daren yau bashi da amfani kada ta takura musu, musamman zasu so su sake da Yayansu da ya jima baya nan, a ganinta presence dinta a wurin zai iya rage musu jin dadin haduwa da juna ko ta hanasu sakewa yadda suka saba. Don haka bata koma asibitin a daren ba. Seun ta shiryawa abinda Nenne zata iya ci ya tafi dashi, faten dankalin turawa ne tayi mata mara yawa da yaji ganyen alayyahu da hanta da koda. Sai washegari da safe ta sake shirya karin kumallon mara lafiya, ta yi wanka ta shirya tsaf cikin ruwan goron atamfa mai glitter din silver da ratsin baki ta dauki abincin a Kwando ta tafiwa da Nenne. Seun ya dauketa sai asibitin. Lokacin Fatima da Firdausi kadai ta tarar a dakin. Prince ya je gida yin wanka shima don anan asibitin ya kwana. Don haka sosai ta sake cikinsu Fatima suka gaisa ta tambayi mai jikin da gajiyarsu ta biki a Ilorin, daga nan ta karbi komai a hannunta na kula da Nenne. Su kuma suka sakar mata suka fara shirin tahowa gida, dama Nenne tafison Aisha tayi mata komai, ta kan ce ai ta fisu zafin nama. Aunty Murjanatu ma daren ranar ta baro UK zuwa Lagos don duba jikin Nanne. Ko don taron dangin da iyalin Engnr. sukayi a asibitin yasa dole likita ya baiwa Nenne sallama a washegari, musamman da ya kasance surgery din da aka yi mata na zamani ne kuma yayi kyau sosai baya bukatar doguwar jinya, in yaso ta cigaba da shan magani da ganin likitanta a gida. Sun dawo gidan dukkansu a tare, a mota guda, in ka cire Prince da ya biyo motar Dade. Nan gida ya kacame da hidima, masu aiki sai shige da fice suke yi suna kaiwa da komowa don wadata al’ummar gidan da abinci da abubuwan bukata da tsaftace shi. Prince tun daren jiya ya zama curious sosai akan bafullatanar yarinyar dake jinyar Nenne a asibiti, yana hankalce da duk irin kyakkyawar kulawar da take baima Nennensa da dukkan nutsuwarta da attention dinta in tana gaban Nenne itace kawai a gabanta, ko uwarta ce sai haka, kuma yaji dadi sosai a ransa. Ya cika da son sanin ko wacece yarinyar. Kwana biyu kacal da dawowarsu Nenne ta kara warwarewa, duk da bata bar gado ba amma tana iya cin komai da Siddiqah ta sarrafa musamman don ita. Yau da kansa ya tambayi Nenne bayan fitar Aisha daga dakinta, bayan ta gama bata maganin safe. Tana kokarin fitowa shikuma yana shigowa. Sai ta rabe cikin ladabi ta bashi hanya ya wuce ciki, ta gaisheshi a gajarce yana amsawa yana karasawa ciki. Prince ya zauna a gefen kafafun Nenne, suka gaisa yadda suka saba, ya tambayeta ina ke mata ciwo yanzu Nenne tace babu sai bayanta, shima din saboda yawan kwanciya ne. Yau dai Prince ya kasa shiru har ta kai da ya tambayeta. “Ni Nenne ‘yar waye wannan kika samu haka mai kokari a kanki da nutsuwa, sannan ga hankali da ladabi haka?” Nenne taji dadin furucinsa, a lokaci taga ya kamata tayi masa bayanin kome ke akwai, don a yanzu taji karfin jikinta zata iya daukar reaction dinsa. Tayi sassanyar ajiyar zuciya tace. "Abdulrasheed Aisha matar ka ce fa. Itace matar dana zabar maka a duniya da lahira. Cikakken sunanta “Aishah-Siddiqah Yunus”. Ita muka zaba maka nida mahaifinka da albarkar Kakanka Emir. Itace matar da muka aura maka baka nan, kusan watanni hudu kenan tana tare dani tana jiran zuwanka. Kayi min biyayya yadda Aisha-Siddiqa ta yiwa iyayenta, ka zauna da ita cikin kauna da amana ko bayan raina". Nan Nenne ta koro masa labarin asalin haduwarta da Haj Zainab da yadda komai ya wakana. Abdulrasheed ya rasa tsakanin mafarki da ido biyu wanne yake ciki. Don jin abinda Nenne ke fadi yake kamar almara mara yuwuwa. Prince Abdulrashheed ya yi shiru yana jin bugun zuciya na wani lokaci kamar ruwa ya cinyeshi. “Aure? Aure? Aure? Mata? Gareshi shi Abdulrasheed Idris Akanni Kehinde din? Ko kuwa dai wani ne daban da ya sani mai irin sunansa Nenne ke nufi?” amma a yadda tayi maganar nan she seriously mean it. Ba shiri ya yiwa Nenne sallama yace zai je yayi sallahr walha, ba tareda ya tofa komai akan muhimmin zancen Aisha data gama yi masa yanzu ba. Ai kuwa tun daga lokacin Prince ya daukewa Aisha wuta, 'yar gaisuwar ta da yake amsawa a mutumce da karsashi in ya zo ya tadda ta tare da Nenne ya koma baya amsawa ma. A kwanaki biyun nan kullum zaka samu ‘ya’yanta sun zagayeta amma Siddiqah taki zama a cikinsu musamman bayan zuwan Aunty Murjanatu (Taiwo), da irin tarbar data samu a wurin ta, sannan da dauke mata wuta da Hamma yayi lokaci guda, ba tare data san ba’asin abin ba. Don wani sabon daure fuska ya koma yi mata. in kuwa ta shigo dakin Nenne yana ciki to zai fita yace ma Nenne yana zuwa. Hakan yasa duk ta takura, ta fara killace kanta a dakin ta zuciya babu dadi. Amma hakan baisa ta fasa zuwa ta yiwa Nenne hidimar data saba yi mata ba, ta bata magungunan ta, ta gyara mata gado ta bata abinci ta killace mata daki. In ta gama sai ta bar musu dakin, ta daina zama sam a dakin ko a falo ta koma nata dakin kawai, ko ka sameta a kitchen tana taya Femi da sauran masu girkin gidan shirya abinci. Nenne ta fiso Siddiqa ta dinga zama a cikinsu, bata son ware kanta dinnan data soma yi wanda ta lura saboda Prince ne, amma taga yaran nata kamar sunfi gamsuwa da hakan da take yi musamman Aunty Taiwo wadda ko bude ido bata son yi taga Aisha a cikinsu, ba kuma ta son yiwa kowannensu korafi akan Aisha don tserar da martabar Aisha din a idanun su kada su rainata, amma dai ta gane babu wanda ya damu da zamanta cikin gidan banda Firdausi, musamman bayan zuwan Aunty Murja duk sun kara ja baya da Aisha. Kannenta sunata murnar zuwanta kamar me don Aunty Murjanatu ta dade batazo Lagos ba. AbdulRasheed, Murjanatu, Fatima da Firdausi sun hadu yau sun saka Nenne a tsakiya kowa na bata labaran da suka shafe shi da harshen da yafi so, masu yarbanci na yi haka masu turanci, amma Nenne da fulatanci take mayar musu. Can na hango Prince AbdulRasheed a gefe yana cin “WARA” akan wani ‘royal plate’ mai ruwan gold, wadda yasa Femi tayi masa, ya takaitawa kansa yawan magana a cikinsu yanzu, ba don komai ba sai don tunanin yarinyar da aka kira matarsa ko tana inama? Baya son wani dan adam ya shiga takura saboda shi, ya kuma lura zamansa a gidan ya takura Siddiqah din, don haka ya sakawa ransa komawa da gaggawa ba tareda ya batawa kowa rai ba. A rashin sanin dukkansu su suna hira ne, Prince kuwa yana danna waya yana yiwa kansa booking flight tunda dai jikin Nenne masha Allah Alhamdulillah, bai ga zaman me zai yi ba kuma. Kwatakwata saboda shaukin haduwa da juna sun manta da wata Aisha kamar ma babu ita in existence a gidansu, to basu saba da shigowar bare cikisu ba. Hatta Princess Firdausi mai dan damuwa da Siddiqah yau ta manta cewa tana gidan sabida murnar zuwan Aunty Murjanatu da tarin tsarabobin data kawo musu daga UK. Wannan abu ya damu Nenne, kuma ta lura itama Aisha din tafi son zaman dakinta yanzu ko meyasa? Ko dai Hamma yace mata wani abu ne? Bata yarda ta zauna a cikinsu in Hamma da Murja suna falo, tun dawowarsu gidan daga asibiti. Nenne ta kasa shiru ganin sun gama rabon tsaraba a junansu ba wanda yace ga ta Aisha-Siddiqah. Maganar Asoebi ma suka koma yi wanda zasu yi na bikin kawar Fatima yar Sarkin Ibadan, suna rokon Hamma ya kawo kudi masu kauri. Ko kula su bai yi ba domin hankalinsa ya dauku ga abinda yake yi a wayarsa yanata danne-dannen da basu san me yake yi ba a ciki, ya samu jirgi mai tashi zuwa Qatar a gobe, don haka yayi maza ya yi booking, ya san dai Nenne bazata hanashi komawa bakin aikinsa ba tunda ta san yanke komai yayi ya taho sabida lafiyarta ba don yana cikin hutu ba. Nenne ta juya tayiwa Murjanatu kallon disappointment, tace a sanyaye “Maman Kiki, ina tsarabar ‘yar uwarki kika baiwa kowa banda ita?”. Aunty Murja ta juyo tana kallon Nenne, idonta na bidar tambaya, Nenne tace cikin lallashi “Kada ku manta she is now part of the family, in zakuyi irin wannan zaman na zumunci a gabanmu da rabon kaya kona menene ku dinga hadawa da ita”. Har suna hada baki wajen cewa “toh Nenne ai bamu ce kada tazo nan ta zauna ba?” Nenne tace “kun kirata cikin sakewa ta ki zuwa? Aishatu-Siddiqah bata da saurin sabo sai a hankali nikaina ta saba dani, ita kadai ce ‘ya a gidansu da mahaifiyarta kadai ta saba, zata saba daku idan kuna janta a jiki!”. Ta fada a hankali cikin lallamin ‘ya’yan nata idonta na kallon reaction dinsa. Prince, wanda har lokacin fuskarsa take expressionless, kansa na bisa wayarsa. Mikewa ma yayi daga bisani fuskarsa a sake yana fadin “I booked my flight back tomorrow Nenne, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka, ina son ganin ku hakannan complete family, I am missing this!”. Nenne ta bishi da ido tana mamaki, kamar bai yi noticing maganar aurensa ba? Kamar bata gaya masa zancen aurensa da Siddiqah ba? Ko kuwa iya shege ne abun irin na su na diyan yarbawa? Zai kuwa ga iya shege albarka Annabijo (da albarkar Annabi). Sai kawai ta bi shi da adduar data saba yi masa wato. “Allah hokku sa’a Hammansu ko a yahi dabuttugo albarka Annabijo”. Kuma ko a fuskarta babu bacin rai. Watakila Prince harda auren aljana a tare da shi ta ke gayawa kanta. Namijin da zai ga mace tamkar Aisha-Siddiqah a matsayin halalinsa amma zuciyarsa bata ko motsa ba, manhood bai motsa masa ba. Sannan bai yi wani action ko kankani da zai nuna cewa ya san da wanzuwarta ba, alhalin ko jiya tana jin yadda Dade ya zaunar da shi kusan awanni uku yana labarta masa yadda aurensa da Siddiqah ya wakana, tun daga haduwar Nenne da Hajiya Zainab a filin Munna ya dauko masa labarin har kawo zuwa yau. Har Dade yayi yagama tana jin su daga kwancen da take uffan wannan Prince Abdulrasheed Kehinde bai ce ba. Dade da saurin hassala a lokacin taji yace da shi “ka samu lalurar ji ne ko Kehinde?” Dan murmushi ya yi cikin kasaitarsa yace “Dade, kunnena ras suke. Banida abin cewa ne, banda Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a gareni daku da yarinyar bakidaya”. Wannan ne yasa Nenne bata kara yi masa zancen Aisha ba ita, koba komai he is now aware of it. His I don’t care attitude ne ya bata mata rai ta fasa ce masa ya tafi tare da Aisha. Aisha tafi karfin ta cusa ta wajen namiji, ta barwa Allah wannan ikon nasa. Su dai sun sauke nauyin dake kansu da addini da al’ada suka dora musu sauran ya rage nasa. Yarinya dai data dauko daga gaban uwarta da ubanta zata kula da ita kamar koma fiyeda tana gabansu. Don haka bayan barin sa wurin Nenne ta cigaba da yiwa Aunty Taiwo ciwon bakin tayi rabon tsaraba ta manta da ‘yar uwarta. Murjanatu-Taiwo, nan ta hau babbaka dariyar shakiyanci nan ta maida Nenne Kakarta, tana cewa “Nenne mai ‘yar fingi-fingi, kamar kazar mayu, ina ganin sai kin hada da addu’a fa, naga Kehinde yarinyar nan bata masa ba”. Ta kara babbako dariya tace. “Allah na tuba Nenne, wadanne irin matane Kehinde bai gani a kasashen duniya? Wadanne irin mata ne basa bibiyarsa kamar su bashi ransu har gida da ofis, Kehinde da in mata dari yakeso a rana zai aura, sai kece mai idon gano masa macen aure Nennenmu? Nenne a shawarce ki maida yarinyar nan ga iyayenta, ki basu hakuri kawai. An daina irin wannan auren yanzu”. Nenne tace da kakkausan lafazi, “Murjanatu! Shin ke kika haifa min yaron nan ko ni na haife shi? To in har ba ke kika haife shi ba, baki kuma shayar dashi ba, sannan baki tayani jegonsa da rainon cikinsa ba daga yau na cire ki daga sha’anin auren sa. Shiyasa dama tun farko ni ban saka ki ba don nasan dama tunaninki akan Abdulrasheed ragagge ne sai abinda yakeso kike bi, ba abinda zaifi masa alkhairi ba. Shiyasa tun farko kika biye masa akan waccan yarinyar. Na yarda har yanzu da sauranki Murjanatu a sanin baiwar da Allah yayiwa 'ya'ya mata, yawan shekaru da zurfin ilmi ko cikar jiki basu ne ba. Haka naki shekarun basu yi miki amfani ba, tunda har kike tunani akwai namijin da yafi karfin wata bafullatar mace don kawai bata da wayewa irin ta kabilunku. Murjanatu ta rage dariya ganin Nenne ta hassala sosai, gashi bata da lafiya, tace “Nenne ni dai ba ruwana fa kiyi hakuri, I rest my case akan maganar nan, shawara ce dama na bayar sabida saninda na yiwa Kehinde, amma kiyi hakuri ga ku ga Kehinde”. Nenne tace "ki yi fatan alkhairi ko ki fita daga sabgar da ba'a saka ki ba tun farko". Ai kuwa a washegari tunda asubah Prince ya tashi zuwa Qatar ko Dade sai a masallaci sukayi sallama da shi. Dade yaso yace dashi Siddiqah fa? Yaga cewa wannan ba wurin da ya dace suyi maganarta bane, amma ya sha mamaki da cikin daren Nenne tace masa gobe AbdulRasheed zai koma har yayi mata Sallama, ta rokeshi kada ya takura masa kan tafiya da Aisha wato yace sai sun koma tare, ya zuba masa Ido, ita bazata cusa masa ita ba don saya mata martaba a wurinsa don ta lura kawai shida Taiwo basuyi na'am da zabinsu ba. Dama kullum bakinsu daya. Kasancewar bata da koshin lafiya sai bai cikata da magana ba kawai ya gyada kai. Sukayi sallama da Dan nasa yadda suka saba yasa masa albarka ya kuma yi masa addu’ar da ya saba yi masa. Seun, ya wuce dashi zuwa filin jirgi. Kwanansa daya da tafiya itama Murjanatu ta koma gidanta a Ilorin. Gidan ya koma yadda yake wato su ya su. Sai lokacin da Firdausi ta tabbatar mata Hamma ya koma, Auntynsu Murja ma ta wuce gidan mijinta, sannan Siddiqah ta soma fitowa falo cikin su yadda ta saba ta sake. Nenne ta yankewa kanta shawarar bazata sawa ranta damuwar komai ba, cututtukan nan na zamani na zuciya da hawan jini ba karya bane. Ta samu ta sha da kyar daga cyst and renal stones. Bari ta maida hakali kan abinda zai fishsheta da ibadarta ta gama da damuwar Abdulrasheed kuma. Ya rage nasa ya gama da yazo ya dauki matarsa a sanda ya shirya ko ya cigaba da rayuwarsa a jirkice yadda yake yinta. Ita dai ta san ba zata kwari yarinya ba idan ya shekara bai dauketa ba, zata mayarwa iyayenta dake ganin mutuncinta ta ce musu ta gane bashi da lafiyar iya yin aure, wanda mutuncin ne yasa aka bashi ba wani abu nasa ba. Bazata yi sanadin da zumuncin ta da Haj. Zainab wanda sun ginashi ne saboda Allah zai lalace akan ‘ya’ya ba. Allah ya gani wahalar da ta sha a baya akan damuwar rashin auren Abdulrasheed, bazata kara maimaitata a yanzu ba. Ta cimma shekaru na girma da take bukatar tattalin lafiyarta. Kehinde ba shikadai ta haifa ba. Amma shikadai matsalarsa ke wahalar da ita, bazata taba lafiyarta dake reto saboda shi ba, alhalin shi yana can cikin jin dadin rayuwarsa. Tunda ta wanke masa ‘labelling’ na rashin aure (tambari) wanda addini da al'ada ya dora musu sauran hukuncin na rayuwa da matar ko a'ah nasa ne ba nata ba. Nenne ta sha mamaki da Aisha Siddiqah ta koma rayuwar walwalarta cikin gidan bayan barin Taiwo da Kehinde gidan. Wato itama ta gane Taiwo bata yin ta kenan. Allah sarki! Yo aka ce shimfidar fuska tafi ta tabarma, sannan ido ba mudu ba amma ya san mai maraba dashi, kai tsaye Aunty Murjanatu bata boyewa kowa ba matar Kehinde bata yi mata ba, including iyayennasu da suka hada auren bata yi musu alkunya ko Karar ganin ido ba wajen nuna musu basu yi zabin da ya dace ba. A wurin Siddiqah gidan har wani fili ya kara da iska mai dadi da Hamman su Firdausi ya bar shi. Wanda iya hangenta na kushe dan adam ko kabilan da ba nata ba data saba kushewa ta kasa hango ta ina zata iya kushe Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni. He's perfect, duk da ana cewa duk mutum tara yake bai cika goma ba. Gani uku ko hudu ta yi masa cikin gidan kuma ba wai ta masa kallon kurilla bane ko a asibitin. Amma tashin farko ta gane shi din ko cikin mazan Yoruba kyakkyawa ne na gaske ashe. Classique. Jinin fulanin Gombe ya wanke shi tas! Akwai abinda ya burgeta guda daya a tare dashi wanda shi kadai ta rike a kamanninsa, “Tabon Sallah_shaidar Sujjadah” wanda ke shimfide can farkon saman goshinsa. He didn’t give her a second look either… Iya abinda ta hango a tare dashi kenan, bata hango maraba ko rashin maraba da ita a tare Abdulrasheed ba. Kai ko kai ne Sigmund Freud ko Wilhelm Wundt wurin karantar dan adam bazaka karanci komai akan Siddiqah a tare da shi ba. Nenne na kara jin karfin jikinta, ta koma harkokinta na cikin gida, aka maida Aisha makarantar su Kiki ta jeka ka dawo. ***** **** **** Malamar da aka daukowa Siddiqa ma Bayerabiya ce mai suna Mrs Yemisi. Ana saura kwana biyu ta fara zuwa makaranta wato asabar malamar ta fara zuwa suka soma karatun bita. Muhimmin abinda zata koya mata shine Lissafi da Ingilishi. Siddiqah ta fara karatu daga takardar transfer da Babanta ya karbo mata daga FGC Billiri, ya aikowa Dade, ta fara ne daga (first term) na aji shidda inda daga shi sai zango na biyu sai zana jarrabawa Ranar data fara zuwa a darare take, ba abinda take tsammani a makarantar sai yaran yarabawa zasu yi mata “Atule bahaushiya!” Irin wanda take yiwa Bisola. Tunda ta gama saddaqarwa alhaki kwikwiyo na Bisola keta walagigi da ita a cikin Yarbawa. Amma akasi ga tunaninta daliban kowacce harkar gabanta take yi babu wadda ta lura da ita balle su kula cewa ita din bahaushiya ce, har saida form master din ajin ya gabatar da ita ga sauran dalibai a matsayin sabuwar daliba daga Gombe suka ji sunanta na hausawa ne. Tun yinin rana ta farko a makaranta Siddiqah ta san cewa makaranta tazo, wadda ta amsa sunan makaranta, ta ko’ina ta zarta Billiri zafin karatu, ba hadi ko kusa. Turancin makarantar har yaso yafi karfinta. Don haka Siddiqah ta dan ture kabilancin nata a gefe ta soma karatu tareda ‘yammata Yarabawa da sauran kabilu, amma yorubawa sun fi yawa. Har bada jimawa ba ta soma tsinttar wasu kalmomi na yarbanci irin su “Zo” (Wa) “Jeka” “bari” “good morning” (Ekaaro) da sauransu. Ta ga cewa ma akwai hausawa tsilli-tsilli a ajinnasu, wadanda galiban aiki ya kawo iyayensu jihar Lagos, don taji ana kiran jakadiyar ajin (class monitress) din da suna Maijidda Sulaiman Yabo. Cikin sati daya Aisha Siddiqah ta saki jikin ta a makaranta. Mrs Yemisi kuma na kokari da ita a gida, don ganin cewa ta haye Ingilishi daa Lissafi a yayin zana jarrabawarta ta kammala sakandire. **** ***** **** KIKI A karshen wannan watan da ake ciki ne Kiki ta kusa kammala course din da take yi a LA tazo Lagos hutu don gaida Kakanninta. Da shigowarta babban falon gidan ba wanda idonta yayi tozali da shi sai Aisha-Siddiqah, a lokacin tana zanawa Firdausi lalle a kafafunta. Sha’awar abun ya kama Kiki ba kadan ba, don Kiki akwai son abubuwan hausawa amma bata da kawaye hausawa, Aisha sai kallon Kiki take tana admiring komai na Kiki a ranta; ga tsayi, ga kiba kamar Aunty Murja, don ita Siddiqah duk wani mutum mai cikakken jiki sha’awa yake bata, ta kasa gane cewa jikin ta ma abinso ne musamman ga wadanda ke neman weight loss. A shirye suke dasu biya makudan kudade in zasu samu irin jikin ta. A ganinta Kiki komai ta hada, ga iya ado sannan ga kibar, ga hutu yabi jikinta, ya hadu da iyayi da rawar kan wayewar 'yammatan zamani masu yawo a duniya, duk wannan ya nuna a tare da Kiki. Ita kadai amma duk ta ishi gidan da karadi. “Nenne bakuwa kukayi ne, halan daga Gombe? So Pretty and Georgeous!” Nenne ta sha mamaki da Taiwo bata gayawa Kiki maganar Siddiqah ba, sannan shima duk yadda yake da Kikin ace bai mata zancen ba. wannan kadai zai nuna maka (how uncared they are) da zancen Aisha daga Taiwo din har Kehinde dinnata. “Umh!” in ji Nenne cikin takaicin Murjanatu, tafi takaicinta fiye da Kehinde saboda da ace ta karbi Aisha 100% da kyakkyawar fahimta akan zabin da ita Nenne tayi da komai zai zo da sauki, don ita kadai ce zata iya convincing din shi ya kalli Aisha da idanun rahma, har ya fahimci alkhairin dake tare da ita don da farko shi da bakinsa ya yabe ta kafin yaji maganar aure a tsakaninsu, Taiwo da taga dama zata iya taimakawa kwarai Kehinde ya bude zuciyarsa ya samar ma Aisha gurbi ko yaya, ya manta da komai da ya jima da sakawa ransa a kan mata. Amma har gobe tana kan bakanta na bazata cusa Aisha ga Prince ba, ta ma fara tunanin da Aisha ta gama karatun data sa aka katse mata a garinsu ta karbi sakamakonta na WAEC sai ta maida ita Gombe hannun iyayenta cikin salama. Ta san Aisha akan dole take zaune tare dasu don ba yadda zata yi ne amma zuciyarta tun fil azal bata son mu’amala da yarbawa balle alaqa mai girma ta aure. Fin karfinta iyayenta suka yi, sai kuma kirki da karamcinsu iyayen Abdulrasheed din a gareta ya taimaka wajen kwantar mata da hankali ta zauna. Amma Prince da al’amarinshi basa gabanta. Har Nenne ta soma ganin laifin kanta ta dinga tunanin anya bata dauki alhakin Aisha ba, data hada wannan auren? Ita dai tasan manufarta kyakkyawa ce akai, ta kwadaitu da hada tsatso da kyakkyawan iri ne, mai addini mai albarka, sauran kuma Allah shine shaida amma bata da wata manufa cikin hada auren Siddiqah da Prince. Bata san ya zata yi ta fahimtar da Taiwo da Kehide hakan ba. Idan Taiwo bata yi na’am ba, mawuyaci ne ya zama Kehinde zai taba yin na’am, because they share each others’ feelings. A tunanin Nenne Taiwo da Kehinde sun hada baki ne akan su yi wa Aisha kora da hali, wanda aka ce yafi kora da sanda, akan wannnan gallafirar Haseenah din rainon Taiwo. Ita kuma zata kyale su suyi abinda suka ga dama. A rayuwarta bata matsawa kowa yayi abinda ba ra’ayinsa ba, ta dauka farat daya Murjanatu in taga Aisha zata karbeta da hannu bibbiyu da zuciya daya, ta zamar mata uwar daki a cikin su, shikenan ta Kehinde zai zamo mai sauki, amma har gara shi din, bai kushe ba amma bai ce komai ba. Ita kuwa Taiwo muraran ta kushe Aisha har tace a mayar da ita ga iyayenta kai tsaye. ‘Ya’yan yanzu ne ba’a tuka su, musamman a shekaru irin nasu shida Murjanatun, babu karamin yaro a cikin su da zata tankwara ta karfi akan dole yayi abunda take so, musamman Abdulrasheed yadda yake gudun bacin ranta da gudun zuciyarta yake iya kokarinsa wajen kyautata mata da ‘yan uwansa, itama bazata yi abinda zai takura shi ba, duk da cewa in ta takura din zai bi, tunda ta lura da gaske bashi da lafiyar yin aure duk da ya musanta hakan ita yanzu ta yarda da hakan, ta kuma barwa Allah ikonsa, tana addu’ar Allah ya bata ladan kyakkyawar niyyarta na dabbaqa Sunnah a tsakanin Siddiqah da Prince, ya bata karfin zuciyar fuskantar iyayen Siddiqah ranar ta mayar da ita su yarda da hujjarta na Prince baida lafiyar auratayya koda bai fadi ba. Amma namijin duk da za’a baiwa lafiyayyar mace kamar Siddiqah a gaya masa matarsa ce ta Sunnah ba tareda ya kashe ko kwabonsa ba, zuciyarsa ta kasa motsuwa to ba namiji bane mai lafiyar mazantaka. Don in babu SO to akwai SHA’AWA a tareda kowanne Da namiji. Ita bata kin Haseenah din da Taiwo take so dashi, kawai tsatsonta ne tace bata yarda ya gauraya a cikin tsabtataccen jininta ba, ba kuma don komai ba sai don babu tabbacin halaccin haihuwarta. Amma tunda daga Taiwo har Kehinde su suna ganin abinda a wurinsu ita bata gani kalas! Yaje ya auri Haseenan dama duk matan gidan marayun Ambursa masu wayewar kai da iya rangwada in har yanada lafiya, don yanzu ita uwarsa ma tana tababa akan ingancin lafiyarsa. Sai suyi mai fishshesu ta maida Siddiqah ga iyayenta ko ba takardar saki, don bazata iya cewa ayi abinda Allah ya halatta amma baya so ba (saki). Dama Siddiqah din ba kwantai tayi ba kuma ba wani girma tayi da iyayenta suka gaji dashi ba. Mutunci ne da sanin yakamata da alkhairi yasa aka bashi ita. To amma ina mafita? Aisha zata dauwama ne da auren Kehinde da bashi da gurbin ajiyeta cikin rayuwarsa ko lafiyar da zai iya ijjema bukatar aurenta. A rayuwarta kuma bata ko son jin kalmar “saki” balle gittawarsa a aure, watakila ko don babu ita a kamus din gidan sarauta gabadaya daga nasu gidan sarautar har na mijinta. Sai taji ta kasa ce da Kiki Aisha matar Uncle dinta ce, in tayi hakan tamkar ta cusa Aisha ne a inda bata da kwarjini, tace da Kiki Aisha diyar kawarta ne kawai ta zo mata hutu daga Gombe. Ai kuwa tashin farko Kiki ta makalewa Siddiqah tana rokon itama tayi mata lallen, Firdausi tace “na kudi ne malama?” Kiki tace “Ke kudin kika biya Aunty Feedy? Imma na kudin ne kinsan Uncle dina zai biya mun ayi mun” Ta fada cikin tsananin shagwaba irin tata, Aisha na dariyar shagwabar Kiki katuwa da ita sai sokonci, tace. “Wasa Anti Feedy take miki kinji Kiki, zan miki lalle wanda yafi na Aunty kyau kin ji?” Kiki ta hau murna tace “kuma zaki na koya min hausa?” (kasancewar maganar Kiki duk rabi yarbanci ne sai kuma turanci da yafi yawa), Siddiqah ta ce “zan koya miki hausa har sai kin ce ta isheki”. To dama a dakin Kikin Aisha Siddiqah take zaune, sai ga Kiki na shigo da jakunkunanta jikake keeeyyy! Tana jansu a kasa cikin dakin cikin dokin zama tareda Aisha. “Pretty, tare zamu dinga kwana har in koma gida, yaushe zaki koma Gombe zan biki in ga gidanku?” Aisha ta rasa me zata cewa kiki, ita kanta batasan sunan zamanta a gidan Engnr. Idris Akanni ba, haka bata san matsayinta ba. Don haka a karshe sai tayi kundumbala kamar tasan shirin da Nenne ke yi tace, “Sai na gama WAEC zan koma gida”. A daren Kiki bata bar Aisha tayi barci da wuri ba sabida hira, Nenne taji dadin irin reception din da Aisha ta samu a gurin Kiki, ko dama bata jin ta, indai wajen son mutane ne da saukin kai a gaskiya Kiki ba’ayi halin Anti Murja ba. Ita daga nata sai nata, sai kuma wanda zuciyarta taga damar so, kamar Haseenah Ambursa kenan da suka dade tare. Kiki akwai surutu, sa'annan akwai kirki da manyance, sannan ga hannun kyauta. A take ta hau daukan kayan kwalliyarta tsadaddu tana baiwa Aisha, don taga bata da kayan gyaran jiki, wadanda ta sayo tun daga Santa Monica din Los Angeles. Ta kwana tana zuba mata labarin da ya shafeta ko wakafi Kiki bata sakawa. “Ni dinnan da kike gani nice ‘yar gatan Hamma, I mean Hamma Prince na gidannan, ai kin san shi ko?” Murmushi Aisha tayi, tace “naga alama Kiki, ko daga wannan uwar sayayya da kika jido, kamar zaki kwaso kasar da kika dawo bakidaya ai sai dan gatan”. Kiki ta kyalkyale da dariya tace “ai Uncle dina bashi da wayau in dai a kaina ne, ya manta da canjinsa a wurina basu kare ba, da nace zan yi shopping a “Santa Monica” sai kawai ya karo min. Har sayayyar matar shi mai zuwa nan gaba a kudinsa nayi mishi ya dauka kudi nane, to wa yake bani kudi in bashi ba? Mum (Taiwo) ba’a cin kudinta ko zaka yi yaya. Kinsan likitoci akwai rowa, Dad kuwa ina na ganshi ma ko abu zai turo mana saidai ita ya tura mata yace ta saya mana. Allah ya gani ina yiwa Uncle dina sha’awar kyakkyawar yarinya kamar ki. Inama zai yarda da an yi ‘yar gida tunda Nenne tace Mamanki kawarta ce”. Kiki ta dan yi shiru kafin cikin damuwa tace “to bazai yiwu ba, don naji ance aljana ta auri Uncle dinane shiyasa yake gudun mata, ko zancen aure baya so ayi masa. Yanzu gashi lamarinsa ya shafeni, Mum ta saka min takunkumin kin kula BoyFriend dina, tace sai ranar da Uncle yayi aure don bazata yarda yayi jika bai yi aure ba. Sabida Allah Aisha Uncle AK fa har furfura ya fara (clicking to 43 years), jiran gawon shanu Mama take yi, da zai yi aure da tuni yayi, don ba irin matan da baya tare dasu a kasashen ketare”. Aisha taji ta kara tsorata da lamarin Prince Abdulrasheed, jin abinda Kiki ke cewa a kansa, har a cikin idanunta da Kiki ta lura da taga tsagwaron tsoro tsantsa, wai har ya fara furfura, sai ta tuno Ishaq din ta dan shekaru 28 National Youth Cervice Corp Member (dan hidimar kasa). "Banza bata kai zomo kasuwa tabbas", inji hausawa, akwai dai abinda ya hana Hamman su Firdausi yin aure ba haka kawai ba, har sai da aka zabo masa aka kuma yi masa bada saninsa ba. Komai kuma yazo ya kare a kanta, poor her! Saboda anga iyayenta masu karamin karfi ne aka bata tsoho. Can anjima kuma Kiki ta saki zancen Prince ta koma bata labarin footballer dinta, apple of her eyes; TosinAbdulNasir. Labarin soyayyar Kiki da dan ball gwanin burgewa da ban kaye, domin soyayya ce suke yi mai tsafta ba tareda suna ganin juna ba sai a hoto da vedio call da Imo. Har lokacin sau daya Tosin ya ganta, itama sau daya ta ganshi a LA (Los Angeles). Kiki ko shafa labari shuni ce ita sai haka wurin bada labari. Ga saurin sabo. Koda yake zamu iya kiran al’amarinta da Aisha da haduwar jini na farat daya. Haka itama Siddiqah Kiki ta shiga ranta from day 1 ta ji ta kamar kanwarta ciki daya. Don Kiki irin yarannan ne frank da basu da munafurci ko nunkufurci. In tana son mutum kawai tana fara son shi ne daga sanda ta fara ganinsa ba tareda wani dalili ba. Kiki is innocent, kwatakwata bata dauko tsauraran halayen yarbawa na Aunty Murja ba. Washegari Kiki har makaranta ta raka Aisha suka dawo tare da Seun, tace “Aisha kiyi karatu da kyau kinji, ki fito da 9 credits, in kika yi wannan kokarin, ni kuma zan sa Uncle dina ya kai ki makarantarmu kiyi irin course dina. Yayi sponsoring karatun ‘ya’yan marayu ma balle ke diyar kawar Nenne? Uncle AK is a philanthropher. Yana daukar nauyin karatun marayu da yawa a wurare da dama a ciki da wajen kasar nan. Kinsan hatta Ex-dinshi Haseenah Mum ta taba bani labarin cewa a irin yawon shi na a gidan marayu ya daukota”. Aisha dai haka take ta biyewa surutun Kiki, da murmushi da gyada kai, ba don duka take ganewa ba. In fact, tana yi tana hadawa da yarbanci ko turanci. Daga jiya zuwa yau Kiki ta ambaci Uncle dinta yakai sau malala gashin tunkiya. Wannan kadai ya nuna (how close) karfin kusancin da take dashi da Hamma din. Wani mutum da tun bayan komawarshi, ko na minti daya Aishah, bata taba zama ta ware muhimmin lokaci ta zauna tayi tunaninshi ba. Da shi da wanzuwarshi da rashin wanzuwarshi cikin rayuwarta duka sammakal. Karshen yankan kauna an gama mata itakam tunda an rabota da mai sonta da ya san darajar soyayyarta (Ishaq Nafada). Amma tasa a ranta komai ma zai zo ya wuce ne kamar ba’ayi ba cikin hukuncin Ubangiji, don bata ga ta ina rayuwarta data Prince ta zo daya ba. Iyayenta zasu hakura su maidata ga Ishaq komai daren dadewa, ranar da suka gaji da jiran gawon shanun basarake Hamman da baya da tabbas. Ta jinjinawa (down to earthiness) din Nenne (halin tawali’un Nenne) da har tayi tunanin mace kamarta marar zurfin ilmi, mara nasabar sarauta, marar ajin rayuwa irin nasu zata iya zama mata ga Hammansu Fatima. Ya Allah kanwarsa Fatima da ‘yar uwarsa Taiwo ma ya aka cika dasu wajen kasaita balle kuma shi kansa? Ita sau dubu gara mata Ishaq da yake bahaushe/bafillace ba dan kowa ba akan Bayeraben Prince din. Darajar idon Nenne kadai ya hanata cewa don Allah in ya tafi kada ya kara dawowa. Tafi jin dadin rayuwa cikinsu da ya bar gidan. Don a dan zuwan Prince gidan hatta numfashi wuyar shaqa ya koma yi mata. Kwarjininsa ya bi ya cika kowanne sako na gidan Engnr. Idris Akanni. Dade kadai ne ya san cewa Siddiqah murna take da komawar Prince, don yafi kowa lura da reactions dinsu ita da shi, don lokacin Nenne bata gama samun kanta ba, so bata ta tasu ta lafiyarta take, amma shi yana hankalce da motsin kowannensu, shi kansa Prince ya takaitawa kansa magana cikin ‘yan uwansa a wannan zuwan da yayi ba kamar yadda ya saba ba. Daga irin kalaman bakin Nenne na yanzu Dade ya fahimci ta fidda rai akan al’amarin, wato ta fidda ranta akan auren Prince da Aisha. Jira take, Allah-Allah take Siddiqah ta gama WAEC ta maidata Gombe, akalla zata cigaba da rayuwa da mahaifiyarta a gefenta. Ita kuma ta fita zargin kanta na cewa bata kyautawa Siddiqah ba. Don haka Dade ya fara nasa shirin shima don ruguza na Nenne. A wurinsa Aisha tazo cikin ahalinsa kenan. Aure tsakaninta da Abdulrasheed anyi kenan, ko yace yanzu aka fara daga nan har gaban abada, bazai yi saken da Siddiqah zata bar Abdulrasheed ba no matter ho worst things are becoming. Hasalima bada sanin ita Nenne ba shi da mahaifinsa maimartaba sarki sun riga sun yi shawara, ji da Emir yayi Abdulrasheed yazo har ya tafi bai nuna bukatar daukar Siddiqah ba yace lallai jikan nasa sai an fito masa ta bayan gida, Emir ya gayawa dansa Engnr. Idris yadda za’ayi da Prince, yace in ma aljanar ce tare dashi da macen aure ta shiga gidansa alkadarinta ya gama karyewa, wato sunada yadda zasuyi maganinta cikin sauki. Don haka yasa Dade ya fara shirin abinda ya dace akan Prince da Siddiqah. Satin Kiki biyu tare dasu ta koma gidan iyayenta a Ilorin, bata tafi ba sai da tayiwa Nenne dadin bakin da yasa ta baiwa Aisha kan waya don a baya tace sai ta gama WAEC zata bata. A cewar Kiki ta yaba da hankalin Aisha tana so zata dinga kiranta akai-akai don neman shawara. Kuma bai dace a dinga hadata waya da Ummanta ta wayar Nenne ba a barta ta dinga kwana tana hira da Ummanta tunda yanzu bata kukan. Kuma dai Aisha bata da `BF’ a cewar Kiki da zai ke distracting karatunta da zancen soyayya. Nenne ta kalli Kiki tana hararar ta wai bata da kunya, amma maganganun Kiki suka sa dole ta baiwa Aisha waya tsadadda, ta yarda Kiki na son Aisha. Su Siddiqah sun fara jarrabawar gwaji wato mock kusan kullum suna waya da Ummanta da Abbanta suna binta da addu’ar samun nasara (albarkar Annabi). **** **** **** Watarana Kiki ta kirata tsakar dare daga Ilorin. “Siddiqah ko kin san addu’ar rufe bakin mutum ya kasa magantuwa akan wani abu?” Dariya sosai Aisha tayi tace “Kiki wa kuma za’a rufewa baki dungurungum? Wane mai tsautsayinne ya shiga komar yar gatan Uncle dinta?” Kai tsaye Kiki tace “Mamana! My Mum. Oh! My Mum is annoying. Aisha tayi maza tace “akul! Kiki daina fadin haka gareta tun kafin mala’iku su rubuta” Kiki tace “To ya zanyi da Mum dina? Tosin yace zai zo Ilorin, musamman don ya gabatar da kansa gareta ya gaisheta ya kuma gaida Emir, amma ina tsoron gaya mata, don nasan bazata yarda ba, yanzu zata hau cewa sai Uncle AK yayi aure, bayan Uncle da kansa ya bani go ahead, har Tosin yaje ya sameshi a Qatar ya ganshi ya kuma amince da shi. Amma ita sarkin tagwaitaka ta nace sai yayi aure zanyi, sabida Allah Aisha Mum bata kwareni ba idan ta janyomin na rasa Tosin? Abinda na sani ina son AbdulNasir sosai. Kuma Uncle din nawa ya amince dashi. Haka kawai Mum zata yimin sakiyar da babu ruwa. Bata san yawan ‘yammatan dake son Tosin bane”. Muryar ta yanzu gwanin ban tausayi cikin damuwa. Aisha ta san bayan wauta da gata da suka yiwa Kiki yawa, still da gaske tana neman shawara da mai hankalin da zai sa ta a hanya. Ta san ko ta girmi Kiki to da kadan ne, amma hankalinsu da wayonsu ba iri daya bane. She’s so much infatuated akan Tosin AbdulNasir. Har tana ganin laifin mahaifiyarta akan saurayi. Irin Kiki duk abinda wada suka yarda dashi ya fada musu dashi zasu yi amfani ba tareda wani dogon tunani ba. Siddiqah ta nisa, a hankali tace da Kiki cikin kwantar da murya. “Kiki ki dinga addu’ar neman zabin Allah kin ji? Don’t be obsessed with him, ki bi mahaifiyarki akan duk abinda takeso wallahi zaki ga alfanu a gaba. Kuma ko a kan son da kika ce min Uncle dinki na yi miki zaki iya yi masa solidarity ki jikirta baiwa zuciyarki abinda take so kamar yadda Mum take so sabida shi, da gaske baza taso ki yi aure ki haihu alhalin shi bai yi ba, baki son soyayyar twins ga junansu bane musamman in opposite sex ne (mace da namiji). Nima bana son zaman gidannan, bana son zaman Lagos at all, amma yana iya? Dole na yiwa iyayena biyayya kuma ina kan yi. Na san ko bajima ko ba dade zan tsinci wannan biyayyar dana yi musu a gaba ko a kan ‘ya’yana ne. Ke kinji dadi ma kina tare da ita har gobe (mahaifiyarki) an kuma barki kin gama karatu kafin ayi miki aure kuma ga dukkan alamu wanda kikeso za’a barki ki aura …..”. Sai bayan ta fadi hakan ta tuno cewa ta saki layi. Kiki bata san wacece itaba har yau a gidannan. Bai kamata Kiki taji daga gareta cewa tana da auren Uncle dinta daga bakin ta ba, idan har Nenne da Aunties dinta babu wanda ya ga dacewar ta sani din ita akan me zata fada? Amma ina! Aka ce magana zarar bunu ce ta riga ta fita, ta kuma shiga kunnen Kiki-Ruqayyat. Kiki tayi dan jim, kafin tace. “Kina nufin kina da aure? Ko kin taba yi kenan sister Aisha?” Ta girgiza kai da sauri tana cewa “Kiki chapter closed, kiyi ta istikhara kina addu’a idan Tosin rabonki ne, kuma akwai alkhairi a tarayyarku, Allah ya kawo auren Uncle dinki kurkusa kamar yadda Mum keso, idan hakan ne kwanciyar hankalinta. Kada kimanta kullum tafi Tosin muhimmanci agareki”. Kiki ta ja numfashi tace “Sister Aisha, my Mum is annoying, wadda take so Uncle ya aura fa ba wata bace Aunty Haseenah ce, his ex Haseenah Ambursa, koda yake ya so ta acan baya, amma wallahi yanzu baya sonta, ban dai san abinda ya raba su ba amma anfi ten years da rabuwarsu, rana daya naga ta dawo jikin Mum dina sun koma shiri, ni nafi Mum sanin Uncle dina, bakina da nasa yace min shi matansa Hurul eeni ne suna aljannah, me Uncle zai yi da Haseenah yanzu? Don kawai ya taimaketa? Tsintacciya ce fa as in ‘yar gidan marayu bata da iyaye shiyasa Nenne bata so. “Ho Kiki! Shafa labari Shuni!” Duk da Kiki bata san me kalmar shafa labari shuni ke nufi ba, ta san yana nufin dai kamar ta faye surutu ko fadi ba’a tambayeki ba. Ta hau dariya tana cewa “da gaske nake duk abinda na gaya miki ni bana karya, ke nafi ganin dacewar Uncle ya aura kuma zan je har Qatar in sameshi akan hakan”. Siddiqah tace da karfi “Kiki! Ni nace miki banida wanda nake so toh? Ba kyau cin naman mutane ki daina zancen wata budurwarsu. Is better you mind your business Kiki, ki rabu da sa damuwar kowa a ranki. In Allah yayi matarsa ce tunda Mum naso, sai kiga anyi”. Kiki tayi maza tace “ba amin ba! Because my Uncle has a pure heart, I assure you he’s pure and clean, with a golden heart! Allah bazai bashi mace wadda ba mai tsarkin nasaba ba. Bazai taba auren mara asali ko lalatacciya ba in sha Allah”. Amma ko bayan gama wayar su da Kiki, Aisha sai tayi jimm! Tana jin maganganun a ranta. Ashe shiyasa bata samu reception a wurin Aunty Taiwo ba, akwai wadda ta dade da yiwa dan uwanta tanadi. Banda haka bata ga me tayi mata ba da ko gaisuwarta sama-sama ta amsa kuma a shaqare. “Umh! Su suka sani” inji Aisha. Babu wani Bayerabe data saka a ranta balle damuwarsu ta dameta. Sati biyu bayan nan su Aisha suka fara zana WAEC, wadda zata dauke su tsayi sati hudu suna zanawa. Watarana Siddiqah ta fito dakin jarrabawa ta tadda Seun yana jiranta zai dauketa zuwa gida, suka kamo hanyar gida, sai taga Seun ya karkace kan motarsa ya tafi wani wurin da ita. Saida suka isa wurin ta fahimci ko’ina ne, wata ma’aikata ce ta shige da fice a jihar Lagos (immigration office). Da ta tambayeshi ko’ina zasu je yace “tayi hakuri Dade zai dauka. Suna isa ta hango dade a nesa yana jiransu, sai ya karaso jikin motar tana kokarin fitowa cikin girmamawa don ta gayar dashi, yace ta biyoshi zuwa ciki. Tare suka shiga ciki yasa aka mata hoto da finger-print. Seun ya dauko su zuwa gida gabadaya. A kan hanya Dade na tambayarta yaya jarrabawar tana gaya masa ita bata da matsala har suka iso gida. **** **** **** BAYAN SATI HUDU MURFIN LITTAFI NA BIYU “Dade har ka kwanta ne?” Nenne dake karasowa gabansa ta tambaya, ganin shi a kwance, ido a lumshe kamar baya jin dadi, sai ta zauna gefensa ta dora hannu akan goshinsa, zafi rau. Dade ya bude ido da suka kada yayi mata murmushi, kafin yace “masassara ke son rufe ni tun dazu” “sannu Dade, to tashi ka sha magani”. Ya yunkura ya mike zaune akan gadon ita kuma jiki na rawa ta doshi (first aid box) dinsu don dauko maganin. Dattijan biyu na matukar kula da junansu, kullum kamar sabon aure haka suke mu’amalarsu, ta ballo maganin kan hannayenta ta bashi ya kora da ruwa sai ya koma ya sake kishingida. Nenne ta yi amfani da wannan damar ta zauna a jikinshi ta soma magana. “Dade nace dama gobe ne Aisha zata zana final paper, ina so jibi in maida ita Gombe in Allah ya kaimu”. A kishingide Dade yake, amma bai san lokacin da ya taso zaune ba, yace “zata je ganin gida ne? Har yaushe aka yi auren Hajiya Sappa? Ko dai Nani Ummana zaku je ganowa?” Girgiza kai Nenne tayi, tace “Dade, in ta tafi ta tafi kenan, Allah ya gani na yi nadamar hada wannan auren, na bata muhimmin lokacina a kansa, don zuwa yanzu na yarda da gaske Abdulrasheed baya bukatar mace a rayuwarsa. Na yi nadamar rabo yarinya da iyayenta. Da na san in ya ganta bazai karbeta ba da koda wasa ban fara ba”. “Dama ana nadamar aikata alkhairi ne ga haularka Hajiya Sappa?” Dade ya tambaya idonsa a kanta. Ba tareda ya jira amsarta ba ya cigaba. “Kada ki karaya, kada ki sare tun yanzu kada ki maida alkhairinki baya. Wanda zashi sama ya taka tsauni ai yayi kokarin azo a yaba. You truly made it my dear. Tunda har kin aura masa ya san da zancenta ya kuma ganta ganin idanunsa, ya kuma san tana zamansa. To kin gama naki, ki barni inyi nawa nikuma. Da wannan Dade ya lallashi Nenne kan kada ta mayar da Aisha gida, ya soma yi mata bayanin abinda ya dade yana shiryawa wanda shima Emir ne ya bashi idea din hakan. “Yana hutun karshen shekara (Annual Leave) a gidan sa na kasar Argentina currently”. Mu karasa a littafi na uku. Tare suke. Taku har abada SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORIN TAKORITES). 10/04/2024 (MASOYA LITTAFAN TAKORI INA FARIN CIKIN TALLATA MUKU JAKADIYAR KAYAN KAMSHI NA ORIGLAME HAJIYA AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. -Takori Sumayyah Abdulkadir April, 2024