AISHAH-SIDDIQAH 1 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com TUNASARWA/JAN HANKALI Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba. Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa. Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu. Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde. In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi Atqaakum”. Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna. Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada. –Takori Sumayyah AbdulQadir. SADAUKARWA Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki. KIYAYEWA Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali. GODIYA DA JINJINA Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa (editing) Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira. In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH. KAFIN MU FARA INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha Lame karshe ce wajen baiwa fata hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. -Takorinku SHIMFIDAR LABARIN WAIWAYE ADON TAFIYA (1) D r. Murjanatu, wadda kowa a gidansu da danginsu bakidaya da “Taiwo” yafi kiranta, kannenta kuma suce mata “Aunty Taiwo”, abokan karatu su ce Murjanatu Akanni. Murjanatu baka ce ba sidik ba, bakin da akewa lakabi da (chocolate beauty) sabida sanyin kyawunsa da haskensa, doguwar mace mai ‘yar kyakkyawar kiba ta jikin hutu, irin kibar da batayi munin da za’a ce mata lukuta ba. Saboda duk da kasancewar ingarman jiki keda Dr. Murjanatu to suffar jikinta mai tsari ce duk da kibarta, gata da doguwar fuska irinta fulani da dara-daran idanun yarbawa masu haske, Taiwo-Murjanatu, nada dogon hanci sambal irin na Kakarta ta wajen Uwa wadda ta kasance bafullatanar jihar Gombe da suke kira “NANI OUMMANA”. Sannan tsayin ta masha Allah shima bai wuce misali ba. Komai na Dr. Taiwo kamar ita ta aunawa kanta ta kuma zaba. Domin dai a fasalce baza’a kira Aunty Taiwo doguwa irin sambal ba, saidai ace kamar kwalbar nan ta coca-cola ga kauri ga tsayi da dirin jiki mai zati, tana a ma’aunin daidai na tsayin da akeso a tareda mace. Shekarun Murjanatu na haihuwa a wancan lokacin da muka waiwaya talatin cif. Murjanatu-Taiwo Akanni ga tsayi ga zati irin na mace mai aji da kasaitar nasaba, girman jikinta mai ban sha’awa ne don bai sa mata muni ba. A takaice komai na jikin Taiwo irin na matasan matan kabilar Yoruba ne, wato daga kabilar Yarbawa ta fito. Tafiyar Taiwo mai daukar hankalin mai kallonta ce, domin tana tafiya ne cas-cas akan tsinin dugaduganta, cikin rangaji na jan aji da kasaita sanna ga iya ado mara misaltuwa, kullum haka take cikin tsantsar gayu da yawan ado, duk yadda ta motsa ko tayi magana ko murmushi sai kaga wannan ajin na musamman irin na jinin sarautar gidansu ya nuna kansa a tareda ita. Kallo daya zaka yiwa Taiwo da dabi’unta da iya kasaitarta kasan ta hada jini da sarautar Yarbawa mai tushe, ko daga yanayin takun tafiyarta dinnan mai kayatar da idon mai kallonta kamar Dawisun da ya baza adon jikinsa yake tafiya. Tafiyar Murjanatu cikin kasaita da iya sarrafa jikinta da yake mul-mul irin na kosassun ‘ya’yan kabilar Yoruba da suka ci suka tada kai. A daidai wannan lokacin da Murjanatu ta shigo gidanta, yamma ce lis, hadari ya gangamo, sararin samaniya yayi duhu, sai cida da iska ke kadawa, gab ake da kecewa da ruwan sama mai karfi. Wannan na faruwa ne a cikin daya daga manyan biranen Najeriya mafi yawan al’umma da kabilu daban-daban, wato birnin Legas ko Ikko da aka fi sani da jihar Lagos. Gidan nata matsakaicin gidane kyakkyawan (Duplex Mansion) wanda anan Dr. Taiwo da iyalinta ke zaune tun dawowarsu Jihar Lagos da zama daga Ilorin, gidan yana nan a shiyyar babbar unguwa mai tsari ta masu hannu da shuni ‘Eko Atlantic’, gidan Murjanatu nada farin fenti mai dan duhu da ratsin ruwan madara-madara (off-white/milk), kuma gida ne da in ka gani ko daga nesa kasan masu shi sun jima da kama kasa. Zamu iya kimanta lokacin da misalin karfe shidda na yamma, daidai lokacin da Taiwo-Murjanatu, ta shigo da kan motarta kirar ‘Hyundai Creta’ harabar gidannata, bayan tasowarta daga asibitin da take (housemanship) acan, wato asibitin koyarwa na jihar Lagos. (Murjanatu-Taiwo Akanni, dalibar likitanci ce a Lagos State Teaching Hospital). A wannan lokacin duk tunaninta da hankalinta na kan karamar diyarta (Kiki) wadda ta baro a gida hannun sabuwar mai rainonta Bunmi, tun bayan data fara housemanship ta samo Bunmi ‘yar kabilar Ibira suke zaune tare. Kiki ‘yar kimanin shekaru uku wadda saboda son da dan uwanta yake mata, yasa a yawancin lokuta bata dauka cewa ita ta haifeta, tafi dangantata da ‘yarsa shi kadai, ko cewa zata yi Kiki sai ta hada da inkiyarshi, tace “Kikinshi” ko “Kikinsa”. A lokuta da yawa idan ana hirarsa, kasancewarsa ‘Polo Celebrity’ ne, ‘yar uwarsa Murjanatu data fi kowa kusanci dashi ta kan gayawa kawayenta daliban LUTH, musamman wadanda ke bibiyar kallon wasan shi a kafar talbijin ta “Global POLO TV, suke kuma mayatar son jin wani abu da ya shafeshi personally, Taiwo kan basu labarin irin son yaransa ne, ta kan ce da dai ace maza na haihuwa da kansu, ba mata ke haifa musu ba, da tasan shi zai yi nakudar Kiki ya haifeta, wato da bazai bar mata ta haifota ba, saidai shi da kansa, saboda sonda yake mata a matsayin karamar diyar ‘yar uwarsa, wadda duk duniya bashi da makusanci, amini, amar ita ‘yar uwarsa Taiwo. Ya sha gaya mata cewa ya raina adadin kulawar da take baiwa Kiki, tunda har ta zabi karatun likitanci akan zaman gida ta kula da kyautar ‘ya’ya biyun da Allah ya bata. Tana basu labarin irin yadda yake bata lokacinsa in yana gaban Kiki, don mayar da shekarunsa yake daidai da nata, su taru suyi ta zuba shirme na (Daddy and Daughters’ love). Wani lokacin Taiwo har addu’a take yi tace Allah ya bashi nashi ‘ya’yan shima. Saboda son yaran shi har yaso yayi yawa. Tana matukar marmarin ganin yaranshi, ko ba don komai ba don ta taya shi son su, irin dai yadda yake tayata son Kikin data haifa. Murjanatu kullum addu’arta kada Allah ya baiwa dan uwanta matar da zata raba soyayyar shinnan da ‘yarsa Kiki. Don ko ubanta Toafeeq albarka. “Kiki rigimammiya amanar Uncle dinta “Prince!”. Wakar da Aunty Taiwo ke yawan yi mata kenan, wadda ainahin sunan Kikin na yanka (Ruqayyat). To amma tana ji tana gani ala dole Prince ya mayar mata da sunan diya “Kiki”, wai a cewarsa saboda kibar ta, da kazarniyarta, da rikicinta irin dai na yara lukutaye ‘yan shekaru uku, yace Kiki ne ya dace da ita ba sunan Nanin Gombe ba. don kam ita Kakarsu Nani Oummana bata da rikici kona tsufa, balle irin na Kiki. Murjanatu na tafe ne tana tuki take wannan tunanin na dan uwan haihuwar nata, mafi soyuwa a ranta a duk cikin ‘yan uwanta da suke iyaye guda, kuma namiji daya tal a cikinsu. Gabadaya gidansu tafi shiri dashi watau shi Hussaininta, wanda suka zo duniya a tare, ta tuna ya hanata barin Kiki a gun masu raino, ba sau daya ba ba sau biyu ba, to amma yaya zata yi tunda ta saka ma ranta son zama likitar mata kota halin kaka? Shi, a matsayinsa na (lifetime) dan “Polo” ba zai taba gane hidimar aikin asibiti bata haduwa data kananan yara ba, dole sai da taimakon mai raino da raba hankali gida biyu, da kuma taimakon makarantar nursery ne kadai kowannensu zai samu isashshen lokacinta. Kuma dai tayi sa’ar samun Bunmi wato mai rainon Kiki yarinyar kirki ce, bata da matsalar komai sannan gata musulma don kuwa daga Ilorin ta taho da ita, tana kula mata da Kiki sosai. A yadda Prince yake son niece din nashi Kiki, wadda ainahi soyayyarsa da yarinyar ta samo asali ne daga sunan Kakarsu da taci wato Nanin Gombe Hajiya Ruqayya da suke kira (Nani Ummana), Taiwo ta tabbata da ace zata bashi ita ya rike a inda yake zaune, ta san tsaf zai karba babu musu, zai iya aje hidimomin Polo dinsa na wasu lokutan, ya zauna ya kula da Kiki da kansa sabanin ita, tunda gidansa babu mace har yau har gobe, amma kuma hakan bai hana shi kwadayin ta bashi rikon Ruqayyatu-Kiki ba. Fatanta dai yanzu shine Allah ya taimakesu iyayensu wato “Nenne” da “Dade” su amince da maganar marainiya Haseenah, dan uwanta ya samu abokiyar rayuwa, yayi settling rayuwar iyali hakanan (at the age of 30) kamar kowanne lafiyayyen matashi. Ita tasan ba wani uzuri da zata baima dan uwanta ya karba akan cewa kulawar da take yima Kiki tayi kadan, a wurinsa Kiki tafi karatun nata muhimmanci dari bisa dari don shi bai ga dalilin da Murjanatu zata ce sai tayi aikin likita ba. Watakila ko don yana ‘life-time’ dan Polo ne yasa yake ganin kowanne Profession na duniya wahala ne, sannan takurawa kai ne, kuma babu riba a cikinsa banda Polo Sport, don ko tabbataccen aikinsa na man fetur an shaida, baya baiwa muhimmancin da ya baima wasan Polo dinsa. A cewar Murjanatu ita kuma, karatun data zaba take yi na kishin kasa ne, bashi da alaqa da matsayin gidansu, reputation na gidansu ko na mijinta Toufeeq Adebayo. Sarauta bazata hanata yunkurin kokarin amfanar da al’umma ba ko neman abinci ta hanyar ilminta, don kuwa sun kere ma hakan. Taimakon kasarta takeso ta yi da nata dan effort din (with full patriotism) sabida karancin likitoci mata da ake dasu a kasarta, tunda kuwa gwamnati take da burin yiwa aiki da mata ‘yan uwanta ba private ba a ganinta aikinta mai hujja ne babba ba karama ba ko a cikin addini. Har ila yau, bazai hanata hidimar iyali ba. Bayan kasancewarsu ‘ya’yan sarauta mai suna sarauta data amsa sunanta, sarauta irin ta gado bata taka-haye ba, kuma jikokin manyan sarakuna gaba da baya, maigidanta Toufeeq Adebayo, har ila yau, ma’aikacin majalisar hadin kan turai ne (European Union) kuma yanada matsayi mai girma a cikinta. Don haka Toufeeq ba mazaunin gida Nigeria bane sosai. Karin dalilin da yasa Taiwo tayi amfani da damar wajen yin karatunta cikin nutsuwa a Ilorin, wanda ta tabbatar zai amfanar da al’ummar kasarta musamman mata ‘yan uwanta (Obstetrics & Gynaecology). Babban burinta mata su amfana daga ilmin likitancin data wahala tayi, a Public University ta Ilorin. Ta fara karatun ne da farko saboda rashin Taofeeq a kusa, madadin tayi ta zaman gida miji baya kusa, don a kalla Toufeeq sai yayi watanni uku ba tare da ya leko su ba ko meyasa? Nenne kance ita bazata iya zaman da Murjanatu ke yi ba na bin miji agindi-agindi akai-akai. Don itace tafi zuwa masa da yaran lokaci-lokaci inda yake, in ta samu hutu, wanda shi bai cika son haka ba. Toufeeq yafi son su zauna a gida inyaso duk sanda ya samu sarari shi ya zo, amma Aunty Murja bata yarda sai taje. Kenan zamu iya cewa Dr. Murjanatu da aka fi sani da (Taiwo), tana karatun aikin likita ne ba don albashin da zata samu ba, sai don dalilai guda biyu; debe kewar mijinta tun na auren saurayi da budurwa hutsun bature Dr. Toufeeq Adam Adebayo, da kuma burinta na amfanar da al’ummar kasar ta, musamman mata. Hassana (Taiwo da harshen Yoruba) wadda ainahin sunan ta na yanka (Murjanatu) da Hussaininta Prince Abdulrasheed (Kehinde da harshen Yoruba) tagwaye ne masu abin mamaki. Su din ‘yan biyu ne da aka haifa tare amma ta girmeshi da awanni biyu, suka kuma taso tare bisa doron tarbiyyar islama cikin shakuwa da kaunar juna mara misaltuwa, duk da kasancewarsu mace da namiji, sai suka maida kansu sune aminan junansu daga kuruciyarsu har girma basu da abokan shawarar da suka fi junansu. Taiwo (Morjanatou), da dan uwanta Abdulrasheed (Prince) wasu irin twins ne kebabbu a cikin kafatanin zuri’arsu saboda sune manyan jikoki kowa na girmamasu, amma a halayya da dabi’a basu da alaqa da juna don Taiwo mai wasu baudaddun halaye ce, wanda iyayenta ne kadai da shi dan uwanta kadai suke iya gane inda ta dosa, sune kuma kadai suke iya tafiyar da ita da baudadden halinta, amma ko Toufeeq wani lokacin haurawa suke su fado kasa saboda bashi da hakurin jurewa halin Mourja. Hadin kansu itada Prince shine kan gaba wajen nuna cewa su ‘yan biyu ne masu fahimtar juna, da tolerating each others’ attitude. Prince ne kadai in Taiwo tayi ba daidai ba zai zare ido ya gaya mata tayi ba daidai ba ba tare da yayi la’akari da girman awannin data bashi ba da cika idon ta ga al’umma, nan kusa babu irinsu a family dinsu ta fuskar closeness da sincerity ga juna. Su haka su rufe su binne sirrin juna ba wanda ya ji ba wanda ya gani, don haka wajen hadin kai da kaunar junansu basu da na biyu. Zumuncinsu ga juna mai burgewa ne, ban sha’awa da ban kaye, in kai mai nazarin ilmin mu’amala da zamantakewa ne har kaso yin rubutu a kansu, domin kuwa zumuncin su ya zarta normal irin wanda ke tsakanin ‘yan biyu na ciki daya, wadanda akasari kusan koyaushe zaka samu suna against junansu, ko yiwa juna cin diddige wato suke yin rivalry da junansu. Su kam nasu zumuncin na musamman ne, a kullum AbdulRasheed da Murja cigaban juna da farin cikin juna suke hangowa junansu. Abin hannunsa nata ne da ‘ya’yanta. A wasu lokutan har feelings na zukatan junansu suna iya ji a jikinsu, na farin ciki ko akasinsa, idan ya samu dayansu. A takaice tagwaitakarsu extraordinary tagwaitaka ce ta bada labari da bugawa a jarida. A wancan lokacin da na waiwaya na hasko muku su (flashback), Hassana Murjanatou da Hussaininta Prince, sun mallaki shekarun matasa ne talatin da haihuwa tana housemanship dinta a Lagos State Teaching Hospital. Ta iso gida kenan tana kokarin sanya motarta a ma’adanarta, wayar ta dake aje gefe ta hau ruri kiran Hasinahn Prince ya shigo mata. Da far’a sosai Aunty Murjanatu ta daga kiran Hasinah, duk kuwa da gajiyar dake tare da ita, ta kwana biyu bata ji ta ba dama, don kusan kullum sai sunyi waya tun barinta gidanta da fara karatun Digirinta a kusa dashi a birnin Tokyo. Taiwo ta daga wayar Hasinah (fiancée din Prince) tana tsokanarta da waka cikin yarbanci yadda ta saba koyaushe sukayi waya. “Hasinah ta Prince, Hasinah kanwar Taiwo, Hasinan Taiwo & Kehinde, ta Abdulrasheed PRINCE bada kanki a sare kije gida kawai kice ya fadi!”. A baya a duk lokacin da take mata irin wannan wakar mai kama da kirari kan Hasinah kumbura yake yi tayi ta blushing ita kadai kamar Aunty Taiwo na kallon ta, domin hakika tana jin dadin wakar gtana alfahari kwarai da son da Aunty Murja ke mata, amma a yau sabanin kullum sai tayi shiru tana kakarin magana amma maganar taki fita daga makogaronta tiryan-tiryan. Murjanatu ta fakamota ta kashe sai ta zauna a ciki ba tareda ta fito ba, ta ce. “Yaya akayi ne kanwata nake jin muryar ki a shaqe kamar mai fama da mura? Kin fadar min da gaba. Kwana biyunnan ban jiki ba dama, Dear Haseenah in ce ko lafiya?” Shiru Hasinah tayi bata ce komai ba ta daina kakarin maganar ma sai ciza lebe. Aunty Taiwo ta sake cewa “In ji dai lafiya kuke keda shi? I mean Prince din? Kuma yaya kuke coping da wheather din sanyinnan na winter da karatun naku ke da shi?” Amma ga mamakinta sai taji kamar Hasinah sheshshekar kuka take yi. Kukan ma irin na fitar rai da ta kasa dannewa, irin mai cin zuciyar mai yinsa, da dugunzuma zuciyar wanda ake yimawa. Murjanatu was shocked! Stunned daga zaunen da take a cikin mota, duk da ta kashe motar a ma’adaninta kukan Haseenah yasa ta kasa fitowa kuma. Da kyar taji muryar Haseenah na fita zuwa cikin kunnenta, cikin sauti mai nuna matsananciyar nadama. “Ki taimakeni ki bashi hakuri Aunty Taiwo, kaddara ce!!!” Murjanatu ta zaro ido, kafin tace komai Haseenah ta sake cewa “kema kin san ba halina bane, kullum kina gargadina akan hakan, kuma na dade ina kiyayewa, kun sani lafiya kuka dauko ni a ‘virgin’ daga Ambursa, wallahi kafin na zo school ban taba yi ba, sau daya ne, sai wannan na biyu, shima kuma wallahi da kudi Tokumbo yake jan ra’ayi na, na dade ina kaucewa fitinarsa, wannnan din ma akasi aka samu, tsautsayi ne. Nayi masa babban laifi Aunty Taiwo, kaddara ce ta fada mini. Zina ba hali bace afkawar kaddara ce da karfin sha’awar da ya gagari dan adam. Prince ya daina daga wayata yau kwana biyu kenan…. ya min iyaka da zuwa gidansa…. Ya ce kada in kara nuna masa mummunar fuskata ko a lahira! Laifina bai kai haka ba. I didn’t deserve such a severe punishment, zan jure kowanne hukunci banda na rabuwa da Prince. Na shiga uku Aunty Taiwo, yau kwana biyu ban saka Prince a idanuna ba… I am dying without him! Truly I am dying! Aunty Taiwo ki taimakeni! Ki cece ni ki ceci marainiya, ke kadai nake da yanzu, a duniya banda kamar ki, ki ceci soyayyar gaskiya da Prince yake yi mun, nasan Tokumbo ba aurena zai yi ba ya cuce ni ne kawai!”. (She screamed!!!). Irin ihunnan na girgiza zuciyar uwardaki. Har cikin kwakwalwar Murjanatu ihun nata ya ratsa ya kusa kurumta kunnuwan Murjanatu. Ta shiga afi da hurwa, tana tumami a kasa cikin hawaye da majina, kamar Murjanatu na kallonta, kalamai take na tuba da nuna nadama, amsar kaicon kai, da kuma daukar alkawarin bazata sake ba. Begging for “one more last chance”. Amma taki fadin hakikanin laifin nata, cikin matsanancin kuka na tashin hankali kawai take rokon Taiwo kamar itace Prince AbdulRasheed din da kansa. Ta kwana da sanin idan Aunty Murjanatu ta yafe mata, tamkar Abdulrasheed da kansa ya yafe mata ne. Kasancewar kowa dake tare dasu ya san Prince (AbdulRasheed) bai iya tsallake rarrashin Taiwo dinsa. Kamar yadda bai iya tsallake abinda ta umarceshi inta bullo masa da lallashi da banbaki ta bayan gida wanda ita kadai ta san lagonsa. Amma itama Hasinah duk da wannan tabbacin data ke dashi, ita da kanta wannan karon tana shakka. Ta yaya take da tabbacin laifin nata mai yafuwa ne ga Taiwo dinma? Since they sometimes share the same feelings itada kaninta Prince? Akan-karan kanta ta san laifinta ba mai yafuwa bane saboda girmansa. Musamman ga babban mutum, mai kishin kansa, dan babban gida da yasan ciwon kansa kamar PRINCE ABDULRASHEED. Wannan shine babban tashin hankalin Hasinah Bello, idan ta tuna lokaci yazo da Prince da zai barta (lokacin rabuwa da gatanta Prince Abdulrasheed yazo) ko taki ko ta so, duka wannan ihu ne take yi bayan hari Abdulrasheed bazai taba mantawa ba balle ya yafe mata, wanda shine komai nata kuma masoyin da suka kulla alkawurran soyayyar da bazasu lissafu ba, soyayya mai tsabta wadda ikon Allah ce kadai ta wanzar da ita don ta san bata kai nan ba, bata is aba, bata kai matsayin ba. Haba! Wannan tunanin yasa sai ihunta ya ninka na baya. Ta kuma kasa ambaton sunan Allah don tasan shima Ubangiji bata da uzuri a wurinsa don bata yi godiya da ni’imar da yayi mata ba ta bata sahihiyar soyayyar Abdulrasheed ba don isarta ba. Bata taba tunanin akwai abinda zai iya yin sanadin da Prince zai ce mata “You! The bastard WHORE! Don’t dare show me your ugly face again!!!”. Wadannan sune kalaman Prince na karshe a gareta, mafiya daga hankalinta, domin a sanda ya fadesu ta tabbata ya fadesu ne baka da zuci babu wata rana da zaiyi nadamar furtasu. Tunda abinda yayi Kehinde shi yayi Taiwo. And they often share the same feelings, kowa nasu ya san hakan. To idan har Aunty Taiwo ta ji laifinnata ma, anya zata kara kallonta da idanun rahma? Ko dubanta da aminci da kaunar da take mata wanda duk sanadin Prince dinne??? Kowa bai ishi Murjanatu kallo ba, in dai baida sarauta, mulki ko dukiya, itama din albarkacin Prince ta ci hawa-hawa a wurinta tunda har ta riketa na shekaru a hannunta, sai kuma jininsu yazo ya hadu daga bisani saboda dukkansu halayensu yazo daya masu son rayuwa ne sosai. Wannan tunani ya kara dugunzuma zuciyar Hasinah, ta kara kururuta kukan da take yima Dr. Taiwo a waya kamar zata fasa dodon kunnenta, fatan ta dai Murjanatu taji tausayinta. Ta kuma tuna ita marainiya ce, da bata da kowa sai su. Murja ta kasa gane komai akan kukan Hasinah da maganganunta, wadanda bata san ina suka dosa ba, ta bata su ne a lullube, a kudundune, amma hakika ta daga mata hankali fiyeda yadda Hasinan tayi zato, kasancewar Taiwo a very cool and reserved person, wadda ko kusa bata son iface-iface da hayaniya yasa ta sa hannu ta toshe kan wayar da hannunta, ita dai ta san daga ita Hasinah har ubandakinta AbdulRasheed son juna suke kamar su hadiye juna don soyayyah, AbdulRasheed na takun-saka da mahaifiyarsu Nenne akan taki yarda ya auri zabinsa Haseenah, wani cikinsu bai taba kawo karar dan uwansa gareta ba sai yau da Haseenah ta kawo karar Prince, don haka Taiwo ta kasance a uku, ta rasa bayan wa zata bi a cikinsu. Da kyar ta nisa tace da Hasinah cikin lallashi, da gajiyawa da jin kukan da ihun nata na marassa tawakkali, cikin nuna matukar concern ga damuwarta tace. “Hold on Hasinah, kina ji na ko? Ki bar kukannan haka take it easy Hasinahty, ki tsaya har in yi magana da shi yanzu, idan na samu ya daga kirana, I will get back to you ASAP. Nima yau kwana uku kenan ban ji shi ba, bai kira ni ba, nima kuma ban samu na kira shi ba, abin yana raina matuka amma yawan karatun dake gabana kuma bai barni na bi ba’asin long unusual silence dinnasa ba”. Irin kukan da Hasinah ke yi har zuwa lokacin yayi matukar daga hankalin Murja, duk kuwa da cewa Hasinah ta rage karfinsa sai sheshsheka da jan majina, maraicinta da rashin gatanta in babu su a tare da ita, ya fito karara ta cikinsa. Kamar ance karshenta yazo ne, idan Prince AbdulRasheed ya juya mata baya. Kamar zautatta sabon kamu haka sai ta hau sakin zance a kunnen Taiwo. Ni Hasinah da ba Uwa ba Uba ba dangi, ba asali ba nasaba ba tushe, sai Abdulrasheed da Taiwo dinsa, da suka karbeni a hakana, duk da rashin asalin nawa. I was ungrateful, selfish and greedy. Shine komai nawa, my life support and also a guardian, idan ya bar ni a dalilin kuskurena ina zan koma yanzu a karbeni banda GIDAN MARAYUN AMBURSA? Zancen zucinta kenan da har bata san yaushe ya fito ya subuce daga bakinta yake shiga kunnen Taiwo ba. Taiwo ta tabbatar al’amarin da ya saka Hasinah mai soyayyen idanu kuka da nadama irin haka akan AbdulRasheed, harta zauce haka, wanda kusan a baya sai abinda tace masa yake yi, saurayin kan-tace ne Abdul. Abdulrasheed din da ransa ne kawai bai fitar ya baima Hasinah ba don SO na gaskiya, ko meye wannan laifin zai kasance ba karamin laifi bane tayi masa da bazai iya yafewa ba. A takaice zamu ce Taiwo tafi kowa sanin irin son da Abdulrasheed ke yiwa Hasinah sabida itace confidant dinsa. Don haka ta katse wayarta da Hasinah ta dauko komatsanta ta fito daga motar zuwa ciki, tana shiga gida bata nemi su Kiki ba, da mai rainonta Bunmi, ta tadda babban danta Hakeem yayi dai-dai yana barci a falo, da alama ya kwaso gajiyar makaranta ne, a gigice take sosai da lamarin nasu, don haka sai ta wuce dakin barcinta kai tsaye ta rufo kofa jikake bamm! Kafin daga bisani ta zauna a bakin gado, tana warware mayafin laffayar jikinta, sannan ta ciro wayarta da gaggawa ta kira dan uwan nata. Wayar ta jima tana ringing har saida ta katse kanta, akalla Murjanatu ta kira ta kara kira ya kai sau uku kafin tayi sa’ar samun Prince ya daga, shima kuma ba tare da yace da ita komai ba. In da sabo ta saba da sarautarsa da ginshirarsa. Amma yau bayan jan aji na sarauta da ginshirar ma tabbas akwai wani abun. Tunda akalla duk jan ajinsa shi zai fara gaisheta. An dauki lokaci tana maimaita masa sallama cikin kwantar da murya da nema masa sassauci, tareda nema masa amincin Ubangiji ta hanyar cikakkiyar sallama, har saida ta kai ga jawo masa Hadisin daya yi umarni da wajabcin amsa sallama ga musulmi da mafi kyawunta ko mayar da martini da makamanciyarta. Kafin ta samu Engnr. AbdulRasheed (Kehinde) Idris Akanni, ya amsa mata da kyar. Kuma ciki-ciki. Ta hanyar cewa; “Wa’alaykumussalam-warahmatullah”. Bayan haka sai bai kara cewa ko uffan ba. Wannan wani abu ne weird daga Abdulrasheed zuwa gareta a wurin Murjanatu-Taiwo. Ko Prince zai ma kowa kyaliya irin wadda ya saba yiwa wanda ya bashi haushi banda ita Taiwo dinsa, amma me? He has his reason. Wato tuni ya riga ya san zancen da Taiwo tazo zata yi masa, bana komai bane na ‘yar dakinta Hasinah ne, ya riga ya san yadda soyayyarsa da Hasinah ta assasa aminci mai girma tsakaninta da ‘yar uwar tagwaitakarsa, Taiwo, sanadin zamanta tare da ita na wasu shekaru tana karatu a hannunta. Ya riga ya kwana da sanin cewa ta kanta Hasinah zata fara bi, da sunan a sulhuntasu, a bashi hakuri ko a lallashe shi. Yau ba Taiwo ba ko lallashin Nenne ne bazai ji ba, in dai akan matsiyaciya Hasinah ne. “Let her GO please! I will take her back to where I adopted her!”. Cikin murya ta lallashi da nuna kauna, irin tasu ta ‘yan biyun Nenne Sappa da kowa ya sani, wadanda ko a cikin tagwayen duniya bakidaya su twins ne na musamman ta fannin fahimtar juna da kaunarsu da juna, haka kulawarsu ga damuwar kowannensu mai girma ce, don ta zarta ta common Yaya da kaninta, saidai ace ta wadanda suka fito duniya daga mahaifa daya, sannan a lokaci guda. Ubangiji Subhana da kansa yaga damar ya dunkulesu ya haliccesu tare a mahaifa guda, don haka zukatansu sau tari suna aiki da bugawa tare ne. Taiwo ke yiwa (twin brother) din nata Prince Abdulrasheed magana cikin lallashi na hikima da taushin murya. “Kehinde, me ke faruwa tsakaninka da Hasinah haka? How can I let her back to orphanage a shekarun girmanta don kawai ta bata maka rai? A kowanne relationship, na soyayya ko mu’amala, dama ai akan samu sabani which is normal, amma a wannan lokacin hankali bata yake yi bat, sai ayi kokari asa hankali ya nemo shi. Dama ka daukota da niyyar watarana in ta bata maka rai zaka maidata ne? Ko kuwa ka daukota ne don ka aureta ba don tun asali ka taimaketa ba?” (Daga ita sai Kakansu Emir da Babansu Dade suke kiransa Kehinde, kowa PRINCE yake cewa) kannensu kuma suce masa HAMMA. Maimakon ya bata amsar tambayarta kamar yadda ta bukata sai taji muryarsa (in despair) cikin wani yanayi yana fadin. “Taiwo Please! Let that PIG go I said! (Ki bar wannan Aladen ta tafi nace), in kuma kin ki toh, ya rage naki. For now, ki hada ni da Kiki!”. A yadda Murjanatu taji muryarsa kadai ta fahimci yana cikin matsananciyar damuwa da kunar zuciya, kuma da gaske yake muryar Kiki kadai yake son ji da shirmen zantukanta ya fiye masa zacennan da take masa na wadda ya kira “karya” kuma “alade” Hasinah. Kiki kadai yake bukatar saurare a wannan lokacin, baya son wani zance bayan nata, koda ABCD dinta zata yi masa ya fiye masa wannan wa’azin na Taiwo mai kama da a kafa mata drum ta hau kai tayi ta yiwa wasu amma bas hi ba. Jiki sanyaye Murjanatu tabi umarninsa, ta fito da wayar a hannunta zuwa dakin da Kiki-Ruqayyat take wasa da mai rainonta. “Uncle AK wants to speak with you Kiki!” Taiwo ta fadama Kiki, tana mika mata kan wayar. Da zumudi mai yawa yarinyar ta dirgo daga dan gadonta ta amsa, tana dokin jin muryar Kawun nata, wanda koda take yarinya karama ta san girman kaunarsa gareta ko Daddynta Toufeeq albarka. Sabida yadda yake janta a jiki har ta saba dashi a waya. Balle kuma in ya zo gidansu, tayi ta sukuwa a jikinsa kenan. Taiwo ta koma gefen gado ta zauna cikin damuwa ta zuba tagumi tana kallon shirmen da Kiki ke masa a waya na sunayen dabbobi da suka fara da harafin “A” fuskarta fal annashuwa, shi kuma Uncle din ya dage yana biye mata cooly. Dama tone na muryarsa kullum is cool amma na yau is more than cool is despair. A tunaninsa a wannan yanayin da yake ciki muryar Kiki-Ruqayyat kadai da shirmenta ne zai mantar dashi ya debe masa kewa, ya rage masa zogin zuciya da radadinta kan abinda ya gani, wato ya mantar dashi abinda Hasinah tayi masa. Kiki his beloved little niece, amma ina! Ko Kiki ta gaza yau, domin ta kasa mantar da shi bacin ran Haseenah dake kasan ransa, still yana nan yana sakadar ruhinsa har zuwa lokacin. Kiki ‘yar lukuta yarinyar data shiga ran Engnr. Abdulrasheed matuka, itace diyar Taiwo ta biyu bayan Hakeem. Ganin sun ki gama shirmensu shi da Kiki, ita kuma an barta cikin ci da zuci, yaki ma ya saurareta balle ya gaya mata hakikanin abinda ya faru, sai Murjanatu ta karbi wayar daga hannun Kiki ta bar dakin, don ita tafi kowa sanin yanayin da Abdulrasheed zai iya kasancewa a wannan lokacin in har da gaske ya yanke shawarar rabuwa da Hasinah kwatakwata. Ta san Abdulrasheed bai iya sabo ba, sabo yana wahalar dashi, wholeheartedlhy yake sabawa da mutumin da ya kwanta masa, balle sabonsa da Haseenah na kusan shekaru biyar, kasancewar ta san ba karamin so yakewa Hasinan ba, kafin ya iya yakiceta daga ransa zai sha matukar wuya. Hausawa suka ce wai sabo akewa kuka ba mutuwa ba! sabon da yayi da Haseenah shi zai fi wahalar dashi fiyeda soyayyarta, wadda dama tausayi ne jigonta da wasu hujjoji nasu. Don haka ta bar dakinsu Kiki ta soma takawa zuwa dakin ta don kaucema kunnen Bunmi. Sai da ta zauna a gefen gado ta tattaro nutsuwarta sannan ta sake koro masa tambaya, (wannan karon sounding absolutely serious with seniority domin kuwa da sunansa na yanka ta kira shi, wanda da wuya kaji Taiwo tayi hakan. Itada Kakansu Emir (Kehinde) kawai suke kiransa wato sunan shi na al’ada wato (Hassan). “I said what’s happening ABDULRASHEED? Tell me! Nace me ya faru? Ko me ke faruwa tsakaninka da baiwar Allah Hasinah haka?” A shaqare (kamar wanda aka shaqe maganar a makogaronsa AbdulRasheed yace da ita. “Babu komai! Ki yarda babu komai! Amma ki sani KARYA ce kuma ALADE ce!!!” “Naji na kuma yarda, amma yanzunnan ta kira ni tana kuka, kuka fa as in screaming any how, tace ka daina daga wayarta yau kwana biyu kenan, kuma kayi mata iyaka da zuwa inda kake…. Kace kada ta kara nuna maka mummunar fuskarta. Me tayi maka haka da zafi? Bansan yaushe ka koyi wannan halin na saurin yanke hukunci da daukarsa a hannunka ba. Anya Kehinde, ba zaka dinga hakuri kana sassauta fushinka akan kananan abubuwa ba ga na kasa da kai alhalin kaida ita kuna shirin zama abu daya??? Mu fa mata duk inda muke sunanmu mata, daga lankwasashshen kashin hakarkarin kirjinku aka halicce mu, dole ayita hakuri damu, balle Hasinah da har gobe yarinya ce da bata kai ashirin da biyar ba, kuma marainiya… sannan…. sannan…kasan batada ko….”. Cikin karaji da nashi screaming din da ya firgita Murja. Wanda ya dame na Haseenah AbdulRasheed ya katse Taiwo, da iyakacin muryarsa yace. “Maraici nasa mace zama Alade ko dabba mai iya saduwa da shaqiqin mijin da zata aura, saduwar ma irin ta dabbobi? Irin…irin…”. Ya kasa karasawa sakamakon wani makoko da yazo ya tokare a makoshinsa, image din nasu ya kara gilma masa. “Hasbunallawu wani’imal wakeel”. Inji Taiwo “ko dai ka sha kwaya ne Kehinde?” Ya rintse ido da karfi. “Don Allah don Annabi daga yau sai yau…. Maman Kiki, na rokeki da darajar iyayenmu, ki manta da mun taba saninta, kada ki kara yi min maganar wata Hasinah daga yau na rufe babinta a rayuwata. Nenne ta fimu gaskiya, tsintacciyar mage bata mage, matsiyaci matsiyaci ne ko a tandun mai ka saka shi kandas dinsa zai fito ya nuna asalinsa na zina da halinsa na kwadayi, kada ki kara tuna min ita! I AM PURE AND I LOVE PURITY. Ni dan Sunnah ne cikin Uwa da Ubana, daga tsafta na fito ba najasa a jikina. Ki manta kin taba sanina da wata halitta wai ita Hasinah saboda Dabba ce…. karya ce! In dai a sanadina kika santa, kike kuma alaqar uwardaki da abota da ita, to daga yau na raba ku nasa almakashi na datse duk wata alaqa tsakanin ku, from thousand milestones. I hate them, I repeat I hate them! Har abada bani ba su!!!”. Murjanatu Taiwo, taji hankalin ta yafi nada matukar tashi, maganganun da yake yi are very dirty. Daga inda ya dauko Hasinah kadai, ya kawo ta kusa dashi, cikin rayuwarsa, zaka shaida girman son sa gareta. Tabbas ruwa baya tsami a banza inji Murjanatu, kalamansa kadai sun gama bayyana komai duk da cewa indirect ya fadesu. Taiwo sai nan da nan ta soma kuka don tana tsoron kada yayiwa kansa lahani. Gashi babu kowa a tare da shi a inda yake. “Abdulrasheed, my Kehinde, I am your only twin sister TAIWO! Gaya min me ya faru daku, ka ji Kehinde dina? As always, ka sani, zan rufe sirrinka, kuma ni zan fahimceka in karbi uzurinka, koda duk duniya bata fahimceka ba ni zan fahimta, zan kuma kasance a bayanka kamar kodayaushe, koda duk duniya bata bayan ka, be rest assured that your Taiwo will stand by you!”. Da irin wannan lallashi da ban bakin Taiwo take shawo kan Abdulrasheed, to yau ma da irin sa ta dage don ya gaya mata abinda ya faru tsakaninsa da Hasinah Ambursa exactly, ita da wa yake cewa ya tsane su haka babu ko sakayawa? Kalamansa dai, da wasu daga na Hasinah sun gama tona komai na kazantar da Hasinah din ta aikata, amma so take ya gaya mata abinda ya faru da bakinsa don tana shakka tana kuma tabaab Hasinan zata iya aikata hakan. Tunda dai a sanin ta da Abdulrasheed baida abokin fada balle masoyiyarsa, matar da yake burin zai aura yana kammala project na masters dinsa wanda Polo ya dauke masa hankali da tun shekaru biyun baya ya kammalashi? Inda wanda bazai taba boyewa damuwarsa a duniya ba komai girmanta ko muninta to Taiwo ce, abokiyar tagwaitakarsa, his very own twin, his confidant Murjanatu-Taiwo, duk abinda yake ciki a rayuwa ita yake fara fadamawa kafin kowa, komai zafinsa. Taiwo da Abdulrasheed sunada wani irin (twin bond) ga junansu da ko mahaifiyarsu Nenne Sappa, wani sa’in bata sanin girman sirrin amanar dake tsakaninsu. Itama kuma Taiwo hakan yake a gareta, Abdulrasheed shine confidant dinta, har sirrinta na mata wanda a matsayinsa na namiji bai kamata ya sani ba, amma Adulrasheed ya san komai na mata akan ‘yar uwarsa Taiwo, kamar lokacin da Taiwo ta samu girma wato lokacin data fara jinin al’ada lokacin suna ‘yan shekaru sha biyu shi ta fara sanarwa cikin tashin hankali da tsoron ko wani mummunar abu ta aikata, Abdulrasheed shi yaje chemist aka hado shi da always pad ba tare da Nenne ta sani ba, sai daga baya ne Nenne ta sani, bayan tuni Murjanatu ta iya kula da kanta da taimakon kaninta, akan Taiwo zai iya batawa da kowa itama haka, in yace kowa yana nufin KOWA! Itama din kuma haka yake a gareta, idan Taofeeq ya bata mata rai Abdulrasheed kadai take iya kira ta gayawa, domin a wurinsa ne kadai zata samu duk wani lallashi da shawarwari da kwarin guiwa da kuma goyon bayan da duk take nema cikin kowanne yanayi duk da kasancewarsa namiji. Abdulrasheed ne ya fara sani lokacin da ta samu cikin Hakeem, ko Toufeeq din bai sani ba yana can yawon duniyarsa, saida cikin ya girma. Abdulrasheed shi yayi ta kula da ita har ta haihu don gidanta ya koma da zama yana kaita asibiti da makaranta, don cikinta nata na Hakeem irin mai masifar laulayi ne kamar bazata kai ba, ga miji baya kusa. Taiwo da Kehinde kaunar ‘yan uwantaka sukewa juna irin wadda ba duk ‘yan biyu ba. A hankali Murjanatu taji numfarfashin Abdulrasheed a kunnenta, wani abu da bazata iya tuna (when last) ta ji shi ba, watakila tun farkon balagar su, lokacin da suna sakandire a kasar Japan idan Dade dinsu (mahaifinsu) ya hana shi hawa Doki ya janye shi daga bargar Dawakan Polo ya rankwasheshi yace ya tafi makaranta. Haka zai yi ta furzar da numfarfashin bacin rai kamar mai nakuda, don baya iya kuka a rayuwarsa. Wannan numfarfashin (is a replica) na kuka a wurin Prince AbdulRasheed, “her very own Kehinde”. Don haka lamarin ya daga hankalin Murjanatu fiyeda tsammaninsa. Kiris ya rage Taiwo ma ta fashe da nata kukan na zallar kaico, da taya dan uwanta bakin ciki da kishi da Allah wadai, he is totally heartbroken a baka da zuci, lokacin da yake yi mata bayanin abinda ya faru dasu kwana biyu da suka wuce tsakanin sa da fiancée dinnasa Hasinah, da dan uwansu cousin dinsu kuma amininsa guda daya a family da ya janyo jikinsa yake amfana dashi wato (Adetokumbo). Cewa yayi ya gansu suna irin sex din dabbobi akan gadonsa. “What a betrayal!” Taiwo kanta a karshe (could not control her own tears), ta barsu suka zubo a kundukukinta. Sabida feeling din Prince nata ne. And she feels the pain din har fiye da shi, don ita da hannunta ta rike masa Hasinah ba da sanin maahifiyarsu ba da farko, don sun san bazata amince ba, har sai bayan ta fara nisa sosai da karatun sakandire ma a hannun Murjanatu sannan Nenne ta san da zamanta wurinta. Zuciyar Murjanatu ta hau tafarfasa. Data tuna wacece Hasinah, da irin gatanta rayuwarta da Abdulrasheed yayi, kirjinta ya hau tururi kamar wuta ake hurawa. Ta tuna wanene kaninta Prince Abdulrasheed, gatan da yake dashi da girman nasaba da matakin rayuwar da yake kai, amma duk bai duba su ba, sabida halin tawali’unsa irin na Nenne, ya zabi Hasinah a matsayin life-partner din da yake burin mallaka, against the wishes na mahaifiyarsu, ita kuma a matsayinta na mai son duk abinda Kehinde dinta yake so sai ta mara masa baya, ta taya shi son Hasinah a haka da zuciyarta daya. Yau shekaru biyu kenan da suke ta takun saka da mahaifiyarsu a kan neman yardarta da amincewarta da aurensa da Haseenah, don Nenne ta kafa ta tsare bata boye ba, duk kirki irin nata da yawan taimakonta ga kowa kiri-kiri tace bata yarda Abdulrasheed ya aure ta ba, ba don komai ba sai don NASABA wani abu ce mai girma da muhimmanci a Aure. Amma a wannan lokacin, a wannan gabar, Taiwo ta san Prince support dinta kadai yake nema ba ingiza mai kantu da rura wuta ba. Idan bata karfafeshi ba yau, waye zai zama karfinsa??? Nenne me zata ce in taji? Banda Allah ya kara? Ta dade tana cewa dasu bata kin Hasinah, amma tsintacciyar mage bata mage. Shi garin banza duk kyawunsa a farau-farau din banza ne. Abin nufi wato mara tsarkin asali da kyawun nasaba ba duka keda tsarki ba. Shiyasa har gobe ba’a yi auren ba, ake ta jan lokaci. Don neman yarda da albarkar Nenne. Ashe da rabon zancen Nenne zai tabbata gaskiya tun tana raye kuma tun gabanin cikar alkawarin dake tsakaninshi da Haseenah? Taiwo ta kara fada a fili cikin girgiza kai “lallai tsintacciyar mage bata mage”. Kuma “Garin banza a farau-farau din banza yake karewa!”. A tunanin ta Hasinah zata dubi maraicinta da daga darajarta da Abdulrasheed yayi a tsakanin mata tsararrakinta, musamman fiddota da yayi daga gidan marayu na garin Ambursa ya dauketa cikin mutunci ya kaiwa ‘yar uwarsa, ta yi sakandire ta ‘ya’yan gata, kafin daga nan ya kawota kasar Japan, yasa a makaranta, cikin ire-iren marayun da yake ponsoring scholarship dinsu a kasashen waje ba wanda ya kawo jikinsa wato inda yake zaune sai Haseenah, a tunaninta ko wannan ya isa yasa Haseenah ta tsayar da soyayyarta da sha’awarta da hankalinta akan sa shikadai, ta zame masa matar rufin asiri, ba kamar sauran ‘yammatan da ke haukar son shi don wasu kyale-kyale nasa ba, kamar kasancewarsa “basarake” kuma “celebrity”. Sannan gashi “Handsome Yoruba Demon” da shaidanun matan Africa dake kasashen ketare ke rububi don son sheke aya dashi kawai ba. Ta dauka Hasinah zata barranta kanta daga masu neman soyayya ta watsewa bayan shigarta Jami’a, ta dauka Haseenah zata zama mai kamewa data iyawa maraicinta, ta dauka zata tsaya ga matsayin da Allah ya bata na fiancée din da Abdulrasheed ya yarda zai aura da zuciya daya cikin dimbin matan dake son shi da suka fita gata da kyawun nasaba, ko don kasancewarta musulma kuma bahaushiya, ashe kame kai ba daga yare ko kabila yake ba, saboda kyawun surar dan uwanta ma kadai ya ishi duk wata mace mai lafiya da dogon buri akan samun miji na nunawa sa’a tinkahon duk da zata yi a kan kowanne da namiji. Taiwo ta zabi su bar maganar nan a tsakaninsu. Suka binneta a ranar, ya zama wani sirri ne da ko iyayensu bazasu iya fadawa ba. Taji ta tsani Hasinah daga yau, da shima Toks din, wato dan uwansu (Tokumbo) fiye ma da yadda Abdulrasheed ke ikirarin ya tsanesu. Bata taba tsammanin akwai dan akuya cikin zuri’rsu ba sai yau. Shi ya san cewa (he has someone on his corner), all the time he need (a kowanne lokaci ya bukata), wata wadda zai iya kira (his own person) wato tashi, a duk sanda ya bida, wadda ba kowa bace sai ‘yar uwar tagwaitakarsa “Dr. Murjanatu-Taiwo Akanni”. Kafadar da zai jingina akai yayi kuka ko dariya a lokuta na bacin rai irin wadannan. ***** **** **** WAIWAYE ADON TAFIYA (2) (AMBURSA ORPHANAGE) A mbursa karamin gari ne a jihar Birnin Kebbi. Prince ya saba da irin wadannan tafiye-tafiyen cikin garuruwa da kauyukan Arewa a duk lokacin da yazo kasarshi ta haihuwa, kasancewar rayuwarshi tafi yawa a yankin Tokyo ta (Japan). Dabi’arsa ce kaunar marayu, don haka duk inda ya samu labarin akwai gidan marayu ya kan ziyarta, komai nisan garin daga inda yake, baya kasa a gwiwa zai je don kai tallafi. Idan yaje din kuma sai ya zaga ciki ya gansu, ya gaisa dasu, ya shafa kawunnansu, yana mai godewa Allah cikin zuciyarsa dashi yayi masa ni’imar iyaye, masu kykkyawan asali daga tsatso mai albarka, iyayen ma jajirtattu irin ‘Nenne’ da ‘Dade’ da ba duk duniya ake da irin su ba. Shi ba attajiri bane a lokacin dalibi ne, amma yanada attajirar zuciya, ‘philanthrophy’ musamman ga marayu a cikin jininsu ne na iyaye da kakanni. Kusan zamu iya cewa ya gaji wannan (positive attitude) din na son marayu da son inganta rayuwarsu ne daga Kakansa. Sarki Akanni mai ran karfe. A zuciyarsa yana tausayin maraya a duk inda ya ganshi, yana kuma jin maraicin da suke ji a ransa, ba don shi din maraya bane. Yana yawan kwatantawa a ransa inda ace shine su, yake rayuwar da suke yi a kange, babu Nenne da Dade a gefensa, a samansa da kasansa, ko yaya rayuwa zata kasance masa? Yana kan hanyarsa ta isa gidan marayun Ambursa ne daga Birni Kebbi, inda yaje halartar daurin auren abokin karatunsa Bello Dasuki. Bello D. abokinsa ne tuntuni da sukayi karatun sakandire tare a Japan a lokacin Baban Bello Jakada ne acan, dan asalin Birnin Kebbi. Don haka ne bai ji kiwar yin tattaki tun daga Lagos ya halarci daurin aurensa ba. Hira ce tayi hira tsakanin shi da Bello Dasuki bayan kammala reception na daurin aure, Dasukin na tsokanarsa da UBAN MARAYU! Inda sabo ya saba da wannan sunan daga bakin Dasukin, tun daga lokacin da ya nemi rakiyarsa zuwa wani gidan marayu a Bauchi. Dasuki yace dashi cikin hira ai kwanannan suma an bude musu sabon gidan marayu a garin iyayensa wato Ambursa. Zancen ya wuce, kamar bai ji ba ma, suka shiga wata hirar ta abubuwan da suka shafesu na POLO. Har sukayi sallama da Bello Dasuki zai wuce Airport, inda daga nan zai tashi zuwa gida Lagos, bai gaya masa zai ziyarci gidan marayun nan da ya bashi labari ba. Kawai tunaninsa na alkhairi ya gaya masa akwai bukatar yaje sabon gidan marayunnan ya gani, domin akwai wasu kudade tare dashi masu dan dama da yayi niyyar kaiwa gidan marayu na jihar Gombe, kuma ya tuna bazai samu zuwa Gombe ganin Kakarsa Oummana kafin ya wuce Japan ba lokaci zaya kure masa, tunda kuma daga Birnin Kebbin zuwa Ambursa babu nisa bari kawai ya karasa can, ya basu tallafin sannan su wuce Airport din Sokoto. Umarni yayiwa direban Bello Dasuki wanda ya dauko shi a motar Dasukin, da ya karkata kan motar ya juya dashi zuwa Ambursa. Ya ce dashi ko basu san wajen ba suyi ta tambaya. Don haka suka tasarma kauyen Ambursa, kuma koda suka shiga garin basu sha wahalar tambaya ba kasancewarsa kwararren direba kuma dan gari, suka samu sabon gidan marayun, wanda ba’a dade da kafashi a jihar Kebbi ba, sakamakon yawaitar tsintar ‘ya’ya da walagigin marayu a jihar. A saman gidan manyan rubutu ne da shudiyar kala an rubuta AMBURSA ORPHANAGE. Shugabar gidan marayun Mrs. Taibat ta karbeshi sosai, domin da gani babu tambaya; irin bakin da suke maraba-lale dasu ne, wato ‘ya’yan manyan kasa masu zuciyar taimako. Wato masu kawo tallafin kudi, ko na karatu ko na suttura ko abinci ga yaran, duk da bata san waye shi ba, amma ko daga yanayin tafiyarsa da kasaitarsa da maganarsa tasan dan manya ne, mai alaqa da sarauta. Don haka ita da kanta tayi masa jagora har wajen jarirai da ake kulawa dasu da madara, daga nan suka isa gun toddlers, ya gansu, ya shafa kansu harda yi musu wasa sosai kasancewarsa mai son yara. Sannan ta kaishi bangaren yara mata masu tashen balaga (teens) ‘yan makaranta. Anan idanunsa ya kyallo masa ita, bahaushiya ce, babu ko tantama mai kyau ce sosai, daga duba na farko zaka ga kyawun nata a zahiri, duk ‘yammatan sun lura da shigowar Madam tareda bakon, amma ita yarinyar bata lura ba, suka soma gaishe su duk hankalinta bai kai kansu ba, sai da Madam Taibat tace “Haseenah baki ga baki bane?” Da sauri yarinyar ta dago jin an ambaci sunanta, yayi mata murmushi ya karaso har gabanta yace “sannu da karatu Haseenah!” ta amsa, ta kuma gaishe shi sai ya karbi littafin hannunta yana dubawa. “Basic Science and Technology” ya ga an rubuta a jiki. (For junior secondary schools). Yarinyar zatayi sa’ar Hakeem dan abokiyar tagwaitakarsa Murjanatu. Don haka kawai babu shawara da Nenne yace bari ya dauketa daga nan ya kaiwa Murja in yaso ta hadata da Hakeem su cigaba da makaranta. Kyawunta ya fisgeshi sosai a matsayinsa na namiji, sannan jan ajinta. Dama ance irin wadannan ‘ya’yan kyau ne dasu. “Ajinki nawa Haseenah?” “Bana na gama JSS” (tana magana kai a sama, cikin ko’in kula) da gani ba wadatar tarbiyyah. “Kinada burin cigaba?” “Sosai ma kuwa, Enginiya nake so na zama”. Sosai yaji yarinyar ta bashi tausayi ko don yadda take magana kanta tsaye da boldness kamar ba marainiya a gidan marayu ba, don mostly yaran zaka same su basu da karsashi, basu da ko guts na karfin gwiwar kallon mutane ma cikin ido, sabida (inferiority complex) dake dabaibaye dasu, amma ita kar take kallonsa cikin ido, idanunta a tsaitsaye, ko kuma don kasancewar fanninsa kenan wanda ta zaba din a matsayin burinta yasa yaji ta burge shi? Don haka koda suka koma ofis shida Mrs Taibat yayi abinda bai taba yi ba tunda yake zuwa gidan marayu daban daban, watau yabi duk process din da ake bi na daukar yaro a gidan, na daga cike-ciken takardu ha a karshe yayi (adopting) dinta. Amma a ransa ya san ba dai ya kaiwa Nenne ba, yayi abunsa kai tsaye without a second thought, saidai ya kaiwa Murjanatu, it ace mai biyewa komai yake so mai kyau ko mara kyau, in yaso ya dinga daukar nauyin karatunta a makarantar kwana, shi dai yaji ransa na son kyakkyawar yarinyar, in yaso in akayi hutu ta zauna gidan Murjanatu har ta isa shiga jami’a ya nema mata admission a fannin Engineering din duk da take so. Ko iya haka aka tsaya ya gina rayuwarta, tunda in ta gama zata iya samun aikin da zai isheta kula da kanta har watarana ta tallafi gidan marayunsu da marayu ‘yan uwanta. ***** ***** **** Ya damka amanar yarinyar a hannun wato Aunty Murjanatu, ya kuma fara biyan komai na karatunta tareda Hakeem yaron Murja. Lokacin ba’a haifi Kiki ba. Murja ta kaisu makarantar kwana ta British int’l school a garin Lagos. Kasancewar duk abinda dan uwanta ke so bata opposing tana taya shi ne su cimma abinnan. Ta dade da sanin philanthrophic heart dinshi, na cikin dabi’un shi masu kyau, da suka banbanta shi da sauran matasan zuri’arsu kaf! Ta yarda ta amince babu mutum mai zuciyar halin girma da daukar girma tun bai girma ba cikin jikokin gidansu kamar Prince, duk wani hali irin na Kakansu Emir Abdulrasheed ya kwashe shi ya bar kowa da sudin kwano. A kafatanin zurri’ar gidansu ba mai kyakkyawar zuciya ta taimakon mara galihu irin ta dan uwanta Prince. Tun daga kan kannen mahaifin su, har zuwa tulin ‘ya’yan da suka haifa, ba wanda baya shan rabar taimakonsa (in one way or the other). Shi Da daya ne tamkar da goma ga iyayensu. Gidansu ba’a tara ‘ya’ya maza ba, shikadai ne namiji a cikinmata amma ya tarewa iyayensu gurbin misalin yara maza goma! **** **** **** Shekaru uku suka zo suka wuce da tarin cigaba ga yarinya Haseenah, bai yi kasa a guiwa ba yana biyan kudin karatunta tare dana Hakeem duk shekara, wadda da aka tashi bata permanent name a makaranta sai ya bata surname da sunan marigayin abokinsa Bello Ambursa, wanda ya rasu gaba kadan da daurin aurensa. Hakika Prince ya ji mutuwar Bello ba dan kadan ba, kullum ya ga Hasinah sai ya tuno shi har kaunarshi da Bello Ambursa ta shafi Haseenah Ambursa, ko bakomai sanadinsa yaje har inda take ya daukota. Daga kan Bello bai kara yin aboki ba sai Tokumbo wanda dama Cousin dinsa ne da suka taso tare. Duk sanda ya zo kasar Najeriya zai je wajenta a makaranta suyi ta tadi, in kuma suna hutu ne tana gidan Murjanatu acan yake ganinta har sabo mai tsanani ya gitta a tsakaninsu. A haka har Haseenah ta gama sakandire, a shekarar data kammala ya samar mata gurbi ya kuma yi sponsoring karatunta a wata jami’a a kasar da yake nasa karatun a lokacin, wato Tokyo. Wannan ne ya kawo kusanci na kamshin soyayya tsakanin sa da marainiyar da yake riko Haseenah, wanda (in no time) ya rikide musu zuwa soyayya. Har shi da Murjanatu suka yanke shawarar ya aureta kawai, don a zamanta a Japan duk da a hostel take rayuwa, tofa kullum tana like dashi a gidansa fiyeda sanda take hannun Murjanatu da gaisuwa da hirar makaranta kadai ke shiga tsakaninsu, acan kuwa bata san kowa ba sai shi, shiyasa koyaushe take like dashi a gidansa a lokutan da bata da karatu, musamman da idanunta suka fara budewa da maza ta san menene soyayya. Sun yanke shawarar shawo kan Nenne don ta yarda ya auri Haseenah shida Murjanatu gudun sharrin shaidan ya gifta tsakaninsu, to kullum suna tare a inda ba idon kowa nasu a kansu, yace da Murjanatu yana tsoron watarana ayi abinda ba shikenan ba duk da yana fin karfin zuciyarsa, amma Nenne ta kafe ta ki. Soyayyarsu shi da Hasinah tayi tsananin karfi a lokacin har suka soma sakin layi. Sun buga sun buga da Nenne ta bari ayi auren har lokacin ta ki, don zaman da take yi dasu ma Nenne bata so, tafi so kowanne irin taimako zata yi maka tayi maka shi daga nesa, ba tareda ta dauko ka ta saka cikin zuri’arta ba gudun kada a bata mata tarbiyyarsu. Wannan ne dalilin da yasa suka kawo har lokacin da Hasinah ta shiga mataki na uku a jami’a suna soyayya ba tareda sunyi aure ba. A irin hakane har ta saba da cousin dinsa mai zuwa gidansa lokaci-lokaci yana sauka a wurinsa wato Adetokumbo Akanni. Tokumbo a Japan yake harkokin kasuwancinsa, Automobile Business Mogul ne. A daya gefen shi da Murjanatu suna cigaba da fama da Nenne akan dai ta yarda ayi auren haka, amma Nenne tayi tsalle ta dire tace sai a bayan ranta danta zai auri adopted orphan. A girman nasaba irin tasu, wannan babban abin gori ne a gareta ko a wurin faccaloli, ace duk matan duniya da wadanda ke cikin family din mahaifinsa da nata ace wai Prince ya rasa matar aure sai akan Haseenah da take tsintacciya zai kare kamar wanda uwa tacewa jeka ka gani? Cikin wannan rikicin suke shi da Nenne har kawo yau, Murjanatu na taya shi fighting gun Nenne don shi Dade dinsu duniya ta shaida mijin tace din Nenne ne, shima da bakinsa yana fada “I obey her decisions because she leave no stone unturned”. Duk hukuncin da Nenne tayi bashi da ja, saboda tsabar yarda da sahihiyar soyayyarsa gareta. A ganinsu shi da Murjanatu babu wadda zai aura da zata girmama shi, ta kaunace shi saboda Allah irin Haseenah, ga Prince da son girma musamman daga matar da yakeso, kai duk bayeraben basarake akwai tsananin son respect daga mace, a ganinsu ita kadai zata aure shi ba don arzikin su ko don tarin “FAME” dinsa ba (shahararsa a idon duniya). Duk wata mace da zata aure shi a halin yanzu abubuwan da zata duba kenan (sarauta, kyau, arziki, da shahararsa), sun yi amanna banda ‘yar da ya raina ya ginawa rayuwa da kansa, har a yau take jera kafada da ‘yammata masu gata da ilmi ‘ya’yan manyan Najeriya a jami’ar da take wato Haseenah Bello Ambursa. Hasinah ta tsinci kanta rana daya a soyayyar ubangidanta kamar koma fiye dashi, bata kuma san daga wane lokaci shakuwarsu ta rikide zuwa soyayyah ba. Duk da banbancin yare dake tsakaninsu, ita Hasinah bata tuna cewa ma ita bahaushiya ce saboda cakuduwa dasu Aunty Murja dashi kansa Prince da ba hausar yake yi bama kwatakwata, ko ya iya ko bai iya ba Allah masani. Duk da ita Haseenah na ganin bata kai matsayin da Prince zai aure ta ba, amma kaninsa Tokumbo dake tare da shi kuma suke shiri itada shi irin sosai kullum yana yawan karfafata da cewa. “If she’s lucky…. Probably zata iya samun auren PRINCE!” A bakin Tokumbo Haseenah taji cewa Mamanshi ma bahaushiya aka auro musu ita, tazo ta haifesu shi da su Murja. Shiyasa taga shi da Prince duk da suke ‘yan maza zarr basa kama da juna. Yace su din surki ne na yare guda biyu; Fulani/Yoruba wato sun hada duka jinin yammaci da arewacin Najeriya, ba kamar sauran ‘ya’yan family dinsu ba da gabansu da bayansu Yarbawa ne. **** **** **** Taiwo tayi ajiyar zuciya data tuna asalin haduwar shi da Hasinah da kuma irin sakayyar da Hasinah tayi musu yau. Ita ba suruka ta dauki Haseenah bama face ’yarta ko kanwarta. Don haka taji ciwon lalacewarta duk da tayi iya kokarinta a kanta. Tafi ganin laifin Haseenah akan na Tokumbo. Ko maiyasa? Don itace mace, kuma ita ta bada kafa har ya sayi mutunci da martabarta daga ido da zuciyar Prince. Ta tabbatar Hasinah tayi rashi, rashin da duk duniya ya kamata ta taru ta jajanta mata, domin tabbas tayi rashin mai kaunarta da gaskiya sabida son duniya, kwadayi da biyewa zuciya da rashin sanin girman zina da illarta aikatata ga mai yinta a addinin musulunci. But who knows? Ko itama ta hanyar da aka sameta kenan? Sannan bata yi islamiyya ba. Dr. Taiwo, ‘yar uwa mai rike sirrin dan uwanta, ko bai roketa ba, ya san wannan magana zata cigaba da zama sirri ne a tsakaninsu su kadai, sai ko Allah da ya halicce su, da kuma Hasinan da Adetokumbon. Ko iyayensu tayi alkawarin bazasu ji wannan mummunar maganar daga bakinsu ba. Domin wani abu ne da zai kawo hargitsi mai girma ga zuri’ar Akanni gabadaya, watakila har ya jawo rarrabuwar kai, wanda basa fata. Jiharsu bakidaya ta shaida hadin kan zuri’ar Akanni da duniya bakidaya, na kasancewarsu tsintsiya madaurinki guda, don in wani ya yarda Adetokumbo zai aikata hakan a gareshi, duba da irin amintakar dake tsakaninsu, da irin taimakon da Abdulrasheed din keyi ga business din Tokumbo, wani bazai taba yarda ba, za’a ce sharri ne, ba don komai ba sai don kasancewar zuri’ar Sarki Akanni tsaftatacciyar zuri’ar kabilar Yoruba da basu yarda da ko bakar al’adar nan tasu ta a fara yin ciki a waje kafin aure ba, sannan bai da amini kaf zuri’arsu irin Adetokumbo Abdulfatahi Akanni. Adetokumbo shine (favourite cousin) dinsa a cikin tarin kannensa maza da suke ‘yan maza zar kaf a family din Emir Abdulrasheed Akanni, wanda ya kasance Da yake ga Dan Iyan of Ilorin, daya daga cikin kannen mahaifinsa. **** **** **** ASALINSU (ILORIN EMIRATE) B ari mu dauko tarihin tun daga tushe, wato asalin kafuwar masarautar Ilorin. Kamar yadda kowa ya riga ya sani Masarautar Ilorin da aka fi sani da ‘Ilorin Emirate’ tana nan a jihar Kwara a yammacin Najeriya, tana daya daga cikin manyan masarautun Najeriya masu dimbin arziki, Ilorin Emirate, wata babbar attajirar masarautar Musulman Yarbawa ce a kasarmu mai dimbin albarka, wadda kafuwar tarihinta ya faro ne daga rayuwar Shaihu Salih Janta, da aka fi sani da (Shehu Alimi). Kenan su din duk da kasancewarsu Sarakai, kuma manyan sarakunan kabilar Yoruba, to manyan Malamai ne, ma’abota sani na na addinin Musulunci da kyakkyawan riko dashi. Su din, har ila yau, sun kasance Shehunnan Yarbawa ne masu dauke da sani na Alqur’ani da Hadisi, wadanda sukayi gadon sahihiyar sarauta ta malunta da arziki mai dimbin yawa daga Kakan-Kakan su Shehu Alimi, sarautarsu sarauta ce mai asali da da kyakkyawar nasaba tun kafuwar kasar Ilorin. Ilorin Emirate, ta kasance (multiethnic Muslim Kingdom) wato cakude take da kabilu da yarurruka daban – daban na kasar Najeriya guda hudu, wadanda suka hadu suka samar da Ilorin Emirate din, sun hada da; Balogun Gambari (Hausa), Balogun Ajikobi (Yoruba), Balogun Fulani (Fulani), Balogun Alanamu (Yoruba). Kowanne bangare wato kowanne Balogun, nada (district head) wato sarkin dake wakiltar wannan bangaren/yankin, karkashin babban Sarki Emir of Ilorin, dattijo mai ran karfe Sarkin wannan zamanin da muke ciki a lokacin yanzu, wato Emir AbdulRasheed Dan Abdullateef Akanni. Engnr. Edrees Abdulrasheed Akanni, ya kasance Da na farko ga Sarkin Ilorin; Maimartaba Sarki AbdulRasheedu Akanni, (the 11th Yoruba-Speaking Fulani Emir) wato Sarkin Ilori na goma sha daya. Engnr. Idris shikadai ne Da a wurin mahaifiyarsa marigayiya Olori Murjanatu (Olori na nufin Queen bisa ga al’adar masarautar), tun Edrees yana yaro ta rasu sanadin cutar sankarar mahaifa. Sai bayan rasuwarta ne aka bawa Emir Abdulrasheed Sarautar mahaifinsa, aka kuma kawo masa mata har hudu daga garuruwan yammacin Najeriya daban-daban ya sake aure, sune suka haifa masa sauran ‘ya’yan sa maza guda tara, har Edrees da matarsa ta farko Morjanatu ta haifa in an hada su goma kenan gabadaya maza ‘ya’yan Sarkin na Ilorin. Emir Abdulrasheed da ya tashi yiwa dansa na fari aure wato Edrees Akanni, sai ya tsallaka ya auro masa Gimbiyar Gombe mai suna (Sappa) diyar abokinsa maimartaba Sarkin Gombe, Ahmadu Umar Jalloh (CFR) daga can cikin yankin jihar Gombe dake arewacin Najeriya. Engr. Idris Akanni tun lokacin da mahaifinsa ya aura masa Sappa Allah ya zuba masa matsananciyar soyayyarta, aure ne na gata irin na ‘ya’yan sarakuna don bai wuce shekaru 27 ba lokacin da aka aura masa Sappa, ita kuma bata fice 17 ba, tun daga lokacin yake kula da ita, don yana matukar son ta kamar ya hadiyeta. Sappa a hannun mijinta Engnr. Idris ta karasa girma ta kuma san rayuwa, ya shiga da ita duniya ta budi ido, wata irin soyayya Idris Akanni yake mata irin dai soyayyar Yarbawa ga kyawawan matan Fulani, (mazan Yarbawan Ilorin na matukar son matan Fulani) har dai in aka yi katari kyawawa ne masu farar fata da gashi yalalaa kamar dai ita Nenne Sappa din. Auren nan nasu ya kafa tarihi a cikin duka zuri’arsu daga bangarensa da nata, domin aure ne irin wanda ba'a taba yi a masarautar Ilorin da masarautar Gombe ba, wato aure tsakanin masarautar Ilorin data Fulanin Gombe, albarkacin amincin dake tsakanin Babansa Emir da mahaifinta Sarki Ahmadu Umar Jalloh (Uban Kasar Gombe). Sarki Ahmadu Jalloh Umar wato (Uban Kasar Gombe) da Sarki AbdulRasheed Abdullateef Akanni (Emir of Ilorin) sun hadu ne tun kafin su zama sarakuna magadan iyayensu, wato tun suna samari ‘yan bana bakwai a jami’a, sun hadu ne a yayin karatun digiri na farko da sukayi tare a can kasar Venezuela (South America) da iyayensu suka turasu inda dukkanninsu suka karanta siyasar duniya (International Politics). Kenan mahaifinsu Idris Akanni wato Emir of Ilorin (AbdulRasheed Abdullateef Akanni aboki ne na jiki tun na kuruciya ga Baban Nenne Sappa, sarkin Gombe Ahmadu Umar Jalloh. Kowa da ya sansu ya shaida Idrisu Akanni na ma Sappa wani irin mashahurin so, kamar babu wata mace a fadin duniya bayan ita. Banbancin harshe da yare bai zamo musu barrier ga soyayya ba. Da fari Nenne ta samu kanta cikin bakunta, kasancewar ta shigo cikin wata kabila da ba tata ba, al’adu da dabi’u sun banbanta, amma gradually tayi hobbasa ta koyi yarensa duk da wahalarsa cikin dan lokaci, shima kuma dama ya iya fulatanci, wannan ne ya taimaka mata sosai wajen zama a cikinsu. Sai ya zamanto Idris tun daga kanta bai kara marmarin auren kowacce mace ba har zuwa inda yau ke motsi da suka cimma shekarun girma shi da Nenne Sappa, da zaratan tagwayen ‘ya’yansu saiti biyu. Bayan aurenshi da Sappa da kadan ya samu aiki da wata masana’antar safarar jiragen ruwa a kasar Japan (Japanese shipping authority), sai ya dauketa da karamin ciki ya tafi da ita Japan, ya saka ta a makaranta tayi ilmin zamani mai zurfi a fannin aikin jinya (Nursing) ba don tayi aiki ba sai don ta samu ilmin kula masa da lafiyar yaransu a gida. Sappa ta fara da haihuwar ‘yan biyu mace da namiji a haihuwarta ta fari. Yaran da al’adar Yoruba ta riga ta basu suna “Taiwo” da “Kehinde” watau Hassana da Hussaini. Taiwo sunan Kakarsu ta wajen uba mai rasuwa taci wato “Olori Murjanatu”, Kehinde kuma kai tsaye ya samu sunan Kakansa Emir (Abdulrasheed) ake kiransa “Prince”, kenan Sarki aka yiwa takwara. Taiwo da Kehinde sun taso cikin koshin lafiya da samun kulawar iyaye wanda ya haifar musu da saurin girma, saidai kowannensu da irin halinsa da irin dabi’unsa. Kowa ya shaida Taiwo nada fitina, korafi, da mita tun tana karama, duk wani hali na matan yarbawa Taiwo nada shi musamma daukan tsegumi daga kannenta. Nenne Sappa bata shiri da Taiwo saboda kiriniyarta da wadannan halayen nata, gata da tsokanar yara ‘yan uwanta, Abdulrasheed kuwa gashi dai bas hi da aboki na jiki kamar Taiwo to kwatakwata halinsu ba daya bane, mahaifinsa na kiransa “Prince” Emir kuma yace masa “Kehinde”, a zahiri shi irin yaran nan ne kamammu, salihai, introvert, wadanda magana ma wuya take musu a zahiri saidai suyi action a gani, wato Abdulrasheed lumbu-lumbu ne da ake cema wutar kaikayi saidai yanada temper, babu mai sanin abinda ke zuciyarsa don fuskarsa bata bada expression na abinda yake ransa, wato kwarai ya iya waskewa da shanye expression, Nenne Sappa kadai ke iya karantarsa tana ganewa in abu yayi masa a fuskarsa ko bai masa ba. Babansu da suke kira “DADE” sanda suka fara budar baki shi da Taiwo, yaga yadda Prince yake saka Taiwo kuka ta ruwan sanyi, ba tareda iyayensu sun san me yayi mata ba, ya kance “Prince GREEN SNAKE ne”. Sun rayu tsayin shekaru kusan goma sha biyar shi da Sappa da ‘ya’yansu na fari a kasar Japan, domin saukar su a Japan da watanni kadan suka haifi ‘Prince Kehinde’ da ‘Princess Taiwo’. Abdulrasheed ya shiga ran Kakansa matuka, kasancewarsa namiji kuma jika na farko a gareshi, ya zama (favourite jika) ga Kakansa Emir of Ilorin, kuma babban aboki na jiki ga Kakansa Sarki Abdulrasheed. AbdulRashid (Kehinde) da Murjanatu (Taiwo) sunyi primary da secondary duk a Tokyo/Japan, ba tareda an yi masu kanwa ko kani ba, Taiwo na gama sakandire akayi mata aure da Toufeeq Adam Adebayo, wanda aure ne na (family friends) tsakanin iyayen su, Toufeeq Bayarabe ne dan abokin Engnr. Idrees ne, sun zauna a Ilorin da farko inda ta shiga Unilorin ta fara karatu, Taiwo ta jima tana karatu kafin ta fara haihuwa. Sau da yawa mahaifin Idris Akanni wato (Emir) yana yin tattaki har Japan in yana son ganawa da babban dan nasa Engnr. Idris Akanni, ko kuma in yana son ganin jikansa mafi soyuwa a ransa wato ‘Prince AdulRasheed’, sai da ya soma tsufa sosai ne ya daina yawon bin Idrisu kasar Japan inda yake zaune, don sauran ‘ya’yansa maza sun kawo karfi, sun taru sun hanashi fita daga Najeriya kwata-kwata, ko don kula da lafiyar sa data fara samun tasgaro da maida hankali ga hakkin talakawansa dake rataye a wuyansa. Daga baya Idrisu din yayi ritaya daga kamfanin safarar jiragen ruwan da yakewa aiki ya dawo gida Najeriya gabadaya da iyalinsa, amma still yaki zama a Ilorin, don gudun sarautar yake, baida sha’awar sarautar gidansu ko kadan, don ma kada watarana a kwadaita masa ita a matsayinsa na babban Da ga Emir, sai yai nesa da gida Ilorin. Inda ya zabi Jihar Lagos don zama na dindindin tareda iyalinsa bayan barinsa aiki da ‘Japanese Shipping Authority’. Kowannen su cikin ‘ya’yan Sarkin Ilorin (wadanda duk maza ne) su goma dinnan nada ‘title’ na sarauta da mahaifinsu ya nada musu da hannunsa. Suna kuma rike da ‘chieftaincy’ kala-kala na kasar Ilorin. Idris Akanni, a matsayinsa na babban Da, yanada ‘title’ na Waziri of Ilorin, sai mai bi masa Abdulyaqeen Akanni shine Turaki of Ilorin, sai Zanan of Ilorin mai binsa. Abdulganiyu Akanni ya biyo Zanan, sai Dan Iyan of Ilorin mai suna Abdulfatahi Akanni, sai Abdullateef Akanni wanda shine GrandMufti of Ilorin, sai Malami Ubandoma wato Abdulrazak Akanni. Biye dasu sune Madawaki, Tafida da Shettima da Mutawalli of Ilorin, duka kannensu ne dake binsu a haihuwa daga iyaye mata daban-daban guda hudu da sarki ke aure bayan rasuwar Olori Murjanatu wato matarsa ta lelle da suka rayu tare tun yana karatun jami’a, kowanne cikin ‘ya’yan sarkin sunansa ya fara da ‘Abdul’ wane (sunaye dai na manyan musulman Yarbawa). Wadannan gawurtattun ‘ya’yan na sarkin Ilorin, duk da ba dukkansu ne ciki daya ba zaka samu biyu a daki daya ‘ya’ya biyu ko uku dakinsu daya. Anyi sa’a dattijon mahaifinsu mai tsayuwar daka ne akan hadin kan ‘ya’yansa, ya dade da hade kawunansu wuri guda, duk da ba duka suke ciki daya ba suna kaunar juna da kula da zumuncin da mahaifinsu ya dorasu akai. Haka Idrisu da ya taso a shikadai a dakinsu baida dan uwa na ciki daya a cikinsu basa taba nuna ba uwa daya ta haifesu ba. ‘Ya’yan Sarki su goma maza sun zama tsintsiya madaurinki daya a jihar Ilorin, sunansu ya shahara yayi tambari, kowanne cikin ‘ya’yan Sarki ya rigada ya kama kasa yadda ya kamata, mahaifinsu ya wadatasu da ilmi daidai gwargwado na addini dana zamani, kowannensu yana bin rayuwar da addini ya tsara irin wadda ya zabawa kansa da iyalinsa babu mai shiga rayuwar dan uwansa da sunan hassada, suna kokarin hada kan ‘ya’yanu kuma maza da mata, sannan wasu daga cikin ‘ya’yan Sarkin suna auren mata fiye da daya, basa takurawa junansu da kyashi da ‘yan ubanci don ilmi da wayewa da alfarmomin rayuwa ya wadacesu, sannan babu rikicin gadar sarauta a tsakaninsu sai na competition na rayuwa, wato wannan na son ace ya kere wannan a cigaban rayuwa, musamman da Allah yayiwa tsohonsu tsahon rai, hakan ya rage rikicin neman gadon sarauta a tsakaninsu, sannan babban Yayansu Idrees Akanni da akewa ganin shi zai gaji gidan ya barranta kansa daga Sarautar gidansu kwatakwata, ta hanyar ficewa daga gida zuwa kasar Japan kusan shekaru ashirin acan ya zauna, inda yayi rabin rayuwarsa kacokam, har gobe Sarki Abdurrasheed Abdullateeef Akanni yana nan daram da ransa da lafiyarsa, yana gudanar da sha’anin mulkinsa cikin adalci ga talakawansa yana kuma kara hada kan mazan ‘ya’yansa da jikokinsa maza da mata da kullum suke karuwa. Mafi yawansu basa Ilorin yanzu, suna rayuwa ne a garuruwa daban daban a cikin kasar Najeriya, duk ayyuka da sana’o’I sun sun raba musu jihohin zama, kadan ne suke a Ilorin kusa da mahaifinsu. Sannan duk cikinsu, babbansu, wato Engnr. Idrees Akanni, shikadai ne ya taba ficewa daga gida, wato ya bar gida Ilorin tunda kuruciyarsa zuwa ketare ya jima sosai, shi da maidakinsa Hajiya Sappa da ‘ya’yanta ke kira “Nenne”. Saida Prince AbdulRashid da ‘yar uwarsa Taiwo suka cika shekaru sha tara a duniya, bayan Nenne Sappa da Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa bayan Nenne, AbdulRasheed shi ya saka mata suna (Nenne) har sauran kannensu suka kama. Kwatsam bayan fidda rai da sake haihuwa rana daya sai Allah ya kara baiwa Nenne Sappa haihuwa. Cikin ikon Allah wannan karonma Nenne Sappa ‘yan biyu mata ta sake haifa kyawawa son kowa, daya ta debo kalar dangin mahaifinsu Bayaraben usuli, dayar kuma ta debo kalar Nenne, fulanin usuli, sai suka cakuda, kamar yadda su Kehinde suke masu hasken kala amma bakake ne, amma fa ko kusa ‘yan biyu basu kama kafar Yayyunsu Prince AbdulRasheed da ‘yar uwar haihuwarsa Taiwo a kyau da farin jini gun iyaye da dangi ba. Sabida sunzo daga baya, bayan an fiddawa Nenne rai da sake haihuwa, su nasu kyawun ina nufin (Taiwo&Kehinde) surki ne na uwa da uba (Fulani da Yorubas); wato uwar da kuma uban suka debo duka suka hada gabadaya, don haka kamanninsu kamar na half-caste (ruwa biyu) suke don kyau da ban sha’awa wato Princess Taiwo da Prince Kehinde. Ranar suna aka kira jariran Nenne da suna Princess Fatima da Princess Firdausi. Daga kan ‘yan biyunnan ba’a kara ko batan wata a gidan su AbdulRasheed ba. Har kawo recently, da Princess Fatima da Princess Firdausi sukayi bikin cikar shekarun haihuwarsu ashirin da hudu a duniya a gidan iyayensu dake yankin Banana Island a jihar Lagos. Princess Fatima da Princess Firdausi sun kammala karatun jami’a a Jami’ar Nsukka, kuma kowacce da zancen aure a kanta wanda za’ayi shekara mai zuwa. Gidan Engnr. Idris Akanni, yana nan a Banana Island wani bangare na Ikoyi, waje ne da masu arzikin kasar Najeriya da masu sarauta ke buya su zabga gininnuka na hutu da garari, gidaje na gani na fada, su zauna suna cin arzikin da suka tara a ketare ta yaki-halak yaki-haram duk, tareda iyalansu a tsakiyar jihar Lagos. Banana Island, na nan a offshore din Ikoyi, inda acan aka haifi Princess Firdausi da Princess Fatima **** **** **** THE HORSE RIDER “ PRINCE” Ya taso da azabar son hawa Doki wanda ya budi ido yaga ana yi a gidan Kakansa Emir of Ilorin. Dadin abun shine, ko muce ludufin da Allah yayima iyayen Prince AbdulRasheed shine; duk sonsa da hawa Doki wanda ya kasance masa ‘hobby’ a tasowarsa, ya kuma zamar masa azababben ‘passion’ na rayuwa tun yana matashi, hakan bai hanashi tsayawa yayi karatun makaranta mai inganci ba. Ya kai cewa a yanzu ya taka mataki har na digirin digirgir, a fannin injiniyan mai (Petrochemical Engineering). Duk da haka Polo Sport ya zame masa hobby din da ya kasa bari tun tashen balagarsa. A can baya Prince yana yin wasan Polo ne (for fun) kadai, a matsayinsa na jinin Sarauta gaba da baya, ba don neman kudi ko neman suna ba, haka ba tareda tsammanin zai kawo mataki irin wanda yake kai a yanzu, a wasan tseren Dawakai ba. A kan karan-kansa ya san yana yin wasan Polo ne kawai don ransa yana so, yana yi ne don biyan bukatar sha’awarsa ga wasan, da nishadin da yake samu a cikinsa. Polo ne kadai ke mantar dashi damuwarsa, wanda ya fara koyo tun yana sakandire idan sunzo hutu Ilorin tareda yaran Baffanninsa su Adetokumbo. Later on in life, ya koma hawa Dawakan turawa da yara sa’anninsa a kasar Japan, wato kafin Dade yayi ritaya. Sai kuma Allah ya kaddareshi da samun duka abubuwan guda biyu dake cikin nasarar wasan Polo lokacin da ya soma girma, wato ya samu “kudi” ya kuma suna “suna” (wealth and reputation) a sanadin Polo Sport. Wadanda bai shigo wasan Polo domin nemansu ba, amma dare daya ya wayi gari dasu dumu-dumu a harkar Polo. A sa’ilin da ya cika shekaru talatin ya zama gawurtaccen dan Polo, wato ya zama ‘Polo Legend’ na Africa da Turai, don tun yana da shekaru ashirin da biyar ya fara fita (Polo Tournaments) a manyan kasashen da ake yin Polo a duniya. Kakansa ne ya fara saya masa Dokinsa na farko, kasancewar shikadai yake mara masa baya akan wannan ‘hobby’ din nasa na Polo, iyayensa duka biyu Uwa da Uba da Kakarsa ta wajen uwa Nani Ummana basa sonsa da Polo, sabida yadda yasa wasan a gaba ya mamaye lokutan rayuwarsa masu muhimmanci gabadaya, suna tunanin Polo ne ya hana shi maida hankali ga wajibinsa (yin aure) a lokacin da ya isa aure. Bayan kuma a wurinsa ba Polo bane, yana da dalilinsa, dalilin da su har yau basu sani ba banda aminiyarsa Taiwo. A can baya lokacin da mahaifin shi zai kai shi jami’a, sai Prince ya zabi tafiya kasar ‘Argentina’ yace ba inda zai je yin karatu sai acan. Hankalin Uban wato Waziri of Ilorin ya tashi kwarai, yaji tsoron kada ya kaishi can yaki yin karatu sai Polo, don haka ya kafe kan cewa bai yarda ba shima, zai saka shi a gaba ne su koma Lagos yayi acan tunda yayi ritaya a lokacin, kuma ba zai taba yarda Polo ya zame masa sana’a ba, saidai yayi karatun a gabansu, a lokacin basu kai ga dawowa Lagos ba. AbdulRasheed fafur yaki zabin Dade dinsa, na yin karatu a kusa dasu, ba don komai ba sai don tun a lokacin ya kwadaitu da komawa Argentina, yanada masaniyar cewa kasar Argentina itace kan gaba (lamba daya) a kan wasan Polo a duniya. Rigima shi da Babansa har gaban Emir Sarki Abdulrasheed. Shikuma kuma Kakannasa Sarkin Ilorin ya bi bayansa, yace akai shi duk inda yake so yayi karatu a duniya, a kuma barshi ya hau Doki son ransa har sai ranar da ya bari don radin kansa. A bashi freedom ya shiga ko’ina yake so a duniya yayi wasan Polo, da yarda da amincewa da albarkarsa da yawun bakinsa. Sannan ya zaunar da mahaifin yaron, wato dansa Engnr. Waziri Idrisu Akanni, yana masa nasiha mai shiga jiki irin ta manya inda ya nusar dashi cewa, duk abinda danka ke da ‘giftedness’ a kai, na karatu ko na sana’a ko ‘sport’, kada kayi ‘opposing’ dinsa, indai har ba sabon Allah bane. Yace dashi da harshen Yoruba “rather encourage him, support him and uplift him on it, baka san inda Allah zai kai shi akai ba, baka tunanin Allah ya sakama Kehinde nasibinsa da baiwarsa a cikin wasan Polo ne? Don haka kada ka tauyeshi akan nasibinsa. Barshi yayi tayi, shi da kansa watarana in girma ya haushi zai bari, kaidai ka bi shi da addu’ar kariya, fatan nasara da fatan alkhairi”. Wannan ne yasa Engnr. Edrees Akanni ya kyale AbdulRasheed ya tafi yin degree na farko a kasar Argentina, ya zagaya ya hade karatun da zuwa koyon Polo. Domin koda ya sauka a makaranta domin yin karatun digiri akan (Petrochemical Engineering) kwas din da mahaifinsa ya zabar masa a jami’a kenan, cikin babban birnin kasar wato ‘Buenos Aires’, tofa duk da cewa yana karatun amma sama-sama, rabin rayuwar Prince Abdulrasheed (Kehinde) a filin tseren Dawaki na kasar wato (Argentina Polo Ground) wanda akafi sani da (Cathedral of Polo), a can yake gudanar da rabin rayuwarsa. Ya gama first degree a Petroleum Engineering da matsakaicin sakamako (2.2) wanda hakan ya dan faranta ran Dade, sai ya wuce masters a Japan tsayin shekara daya ya dakatar da rubutun masters din na lokaci mai tsaho saboda Polo, kullum yanaso ya gama ko don ya farantawa Dade. Yadda wasan Polo ya rinjayeshi ne yasa Abulrasheed bai samu kammala masters da wuri ba har ya shiga cikin shekaru na talatin, bayan ya kammala at 33 da kyar da sudin ludayi, sai ya ajiye kwalayen a kasan gado ya rungumi Polo again, baya ko tunanin saurarawa Polo ko makamancin bari, har inda yau ke motsi. A daidai wannan lokacin fitar sunan AbdulRasheed Idris Akanni a wasan Polo, zamu iya kwatanta shi da hada kafada dana manyan ‘yan wasan Polo na duniya irin su Nacho Figueras, Mariano Aguerre, da Lia Salvo. A kasashen Africa kuma irin su Adolfo Cambiaso na South Africa, Bello Buba na kasar Najeriya, da matashin dan Polo mai tasowa a arewacin Najeriya wato Khalil Halilu, wanda bai kai su shuhura ba. A shekarun da suka gabata Abdulrasheed ya sha ciyowa Africa kofi a USPA Gold Cup, haka ya ci kofin World Polo Championship, Concacaf Gold Cup, Dubai Gold Cup, U.S Polo Championship, da Cartier Queen’s Cup. Duka wadanan siraran kofuna suna nan a jere akan makeken tebirin ofishinsa dake cikin (Qatar Petroleum Refinery) a birni mai tashen arziki (Qatar), inda ya samu muhimmin aikin yi irin wanda mahaifinsa yafi na’am dashi. Har zuwa lokacin cikarsa shekaru arba’in a duniya Prince bai kara sha’awar soyayya ba, bai kara sakawa ransa son yin aure ba, ya tattara maganar aure da mata ya tura su can wani gefe mara amfani na shafin rayuwarsa, ya zamo yana cigaba da playing Polo for fun and pleasure da kuma debe kewa kadai. Amma aikin da ya samu da (Qatar Petroleum Refinery) bayan kammala PhD dinsa akan (Oil and Gas Engineering) yasa dole ya bar kasar Polo ta Argentina ya tare a Qatar, sabida aikin refinery yafi cinye lokacinsa yanzu fiyeda wasan Polo. A halin yanzu da yake da shekaru arba’in da biyu a duniya, Engnr. AbdulRasheed Idris Akanni, zamu iya cewa ya gama accomplishing komai na daukakar aiki akan Oil and Gas, tunda yana kan matsayin ‘Star Engineer’ na ‘Qatar Refinery’, AbdulRasheed ya gama cika duk wasu burika na rayuwarsa, saura kaiwa makura a gasar Polo wato (10+ goal handicap). Kudi yake samu kawai daga kasashe daban-daban ta harkar Polo da kuma aikinsa, har bai san abinda zai yi dasu ba, babu Da, ba jika, balle matar da zata taya shi mora (babban tashin hankalin iyayensa kenan). Don haka AbdulRasheed ya himmatu wajen aikin alkhairi ga ‘yan uwansa mata guda uku musamman Taiwo, ya tsaya musu, ya tsayawa cigabansu, baya barin iyayensu su yi musu hidimar komai ta karatu kota yau da kullum, balle mijin Taiwo da yake da kankamo sai ya zamanto komai nata shine, har ila yau yana raba arzikinsa da iyaye da ‘yan uwansa na Uwa dana Uba (duk da kasancewarsu ba mabukata ba). A gefe kuma a boye, Prince Abdulrasheed ya dage wajen tallafawa gidajen marayu dana gajiyayyu a kasarshi Najeriya inda a irin haka ya samo HASEENAH. A halin da ake ciki yanzu (he mainly consults for the refinery) fiye da zama a ofis yayi aiki. Don haka ne yake samun lokacin da yake fita ‘tournaments’ kadan-kadan, to really play his passion which is ‘Polo’. Amma dai rayuwarsa yanzu tafi yawa a birnin Qatar. Wannan shine tarihinsu Prince AbdulRasheed da iyayensa, ‘yan uwansa, da komai da ya shafi rayuwarsa ta yau da kullum, rayuwar da kowa yake kallo masa a matsayin ‘incomplete’ wato wadda ba cikakkiya ba, mai wawakeken gibi, duk da tarin achievements din da ya cikata, da tarin arzikin dake cikinta musamman mahaifiyarsa, Kakarsa da mahaifinsa da ‘yan uwan haihuwarsa gabadaya suke cikin damuwa da rashin cikarta, domin kuwa har zuwa wannan lokacin da ya tasamma shiga shekaru 43 ba wanda ya san dalilin sa na kin yin aure ko yin budurwa in ka cire Murjanatu. Wanda ya zamo na jikinsa sosai ne kadai zai iya gane cewa, duka lokutansa na yanzu ya mallakawa wasan ‘POLO’ ne, da kuma aikinsa na matatar man fetur, sannan Prince yana ibadah musamman ta yawan azumi a gidansa, ba abinda duniya ke zarginsa dashi ne a gabansa ba. **** **** **** HEARTBREAK K wanaki uku kenan da yin wayarsa da ‘yar uwarsa Murjanatu. Kwatanta halin da Abdulrasheed yake ciki a kwanaki ukunnan bazai yuwu ba, he is frustrated and heartbroken, kasancewar babu kowa a tare dashi shikadai ne a gidansa sai mai yi masa hidimar share-share da goge-goge da girkin abinci, daga shi sai zuciya da kwakwalwarsa suke aiki a kwanaki ukunnan, don haka suka taru suke ta kitsa masa duk abinda suka ga dama akan mata da al’amarinsu. Mai kyau da maras kyau. Shaidan ma yana taka rawarsa wajen gaya masa mata duka mazinata ne ya fita harkarsu. Babu wata soyayyar gaskiya in existence. Hakan yasa tunaninsa mafi rinjaye duk ya gurbace akan diya mace. Abdulrasheed ya kullaci mata da soyayyarsu kowace iri ce, ta aure kota watsewa duk ya barranta kansa daga ciki, daga yau ya nesanta kansa da kowacce iri. Ya tsani taimako, duk da in tunanin hakan yazo masa yana cewa (astagfirullah). Ya zo ya tsani yarda da duk wata mace. Shaidan ya cigaba da ribatar sa yana gaya masa ai duk mata irin Hasinah ne marasa godiya, maciya amanar kauna, kuma marasa tsarki na jiki dana zuciya. Saboda shi mahaifiyarsa ta dade tana cusa masa wani irin tsoron zina, tun sanda ya fara balaga, ta taso dashi da upbringing mai kyau cikin hikima da lallami take cusa masa kin zina, sau tari tana yawan gaya masa cewa ko mata nawa yake so kuma ko ‘ya’yan wa yake so a sarauta da arziki, haka kona talakawa ne yakeso zasu aura masa indai akwai nagarta da kykkyawar nasaba. Amma ya taimaki kansa da su kada ya kusanci zina a rayuwarsa, sabida ita zina bashi ce wato dattinta naso yake yi a cikin zurri’a, da wannan belief din ya girma a ransa, duk da Haseenah taso ta wargaza wannan tufkar da Nenne ta dade tana yi a zuwanta Japan. Amma yau Hasinah tasa abin ya shafi har mu’amalarshi da kowa, don gani yake duk ‘yan uwansa na wajen Uba ma irin Tokumbo ne wato mazinata ne (subhanallah), marasa la’akari da girman ‘yan uwantaka da abokantaka da yarda da aminci in dai akan mace ne, idan babu tsoron Allah ai ana barin halas don kunya. Watakila shiyasa iyayensu maza (musamman Dan Iyan of Ilorin, Babansu Tokumbo) ya damu sai yayi aure cikin ‘ya’yansa mata kuma yafii kowa damuwa a takura masa yayi auren cikin gida, ashe ya san ‘ya’yan nasa watsatstsu ne marasa tarbiya. Hakika Tokumbo yaci amanar tarbiyyar gidansu. Ya saka a ransa ba shi ba aure a duniya balle cikin zuri’arsu, kai duka matan duniya daga yau ya yafe su koda diamond aka kerasu, zai rufe ido ya kauda kai daga kansu in dai tawali’unsa wajen zaben macen aure (did not yield a positive result), wato indai kaskantacciyar hanyar da yabi wajen zaben macen aure bata sa ya samu abinda yake tsammanin samu na macen da zata so shi ta girmama shi, ta kaunace shi domin Allah ba. Ya yardarwa kansa a can baya ‘ya’yan marayun sune zasu fi zama nagari saboda rashin gatansu zasu iyawa maraicinsu, fiyeda ‘ya’yan masu arziki dana sarauta, wadanda yake ganin baza’a samu masu tarbiyyar da yake so a cikinsu ba, da irin yadda yakeso matarshi ta kasance ta so shi tsakani da Allah, sune yafi tunanin a cikinsu babu nagari, to ashe matan daga kowanne tushe suka fito ba kwarya bane balle ya kwankwasa cikinsu ya zabi ta kwarai. Babu wadda zaka ci wa alwashi akan soyayya, haka babu macen da zaka iya baiwa amanar zuciyarka da soyayyarka a wannan zamanin ba tareda ta ci don abin duniya ba, a karshe zata kekketa zuciyarka tabi ta kai ta tattake ba tareda tayi la’akari da tarin alkhairorinka gareta ba. Da daddare Prince Abdulrasheed yana zaune a karamin falon gidansa da na’ura mai kwakwalwa a gabansa da sunan aikin project dinsa zai cigaba, wanda ya dade da jinginarwa saboda harkokinsa na Polo. Yau bacin zuciya da rashin abinda zai debe masa kewa yasa ya dauko project dinsa yana son karasawa ko ya samu ya bar kasar Japan bakidaya, ko ya samu ya huta da binbinin da Haseenah ke masa kullum na neman sulhu. Amma abin takaici ya kasa tabuka komai daga aikin da yake son yi. Har zuwa lokacin zuciyarsa bata koma daidai ba, amma dai ta rage tafarfasar da take yi. Gidan Prince Abdulrasheed na Japan wanda ya kasance karamin ‘Penthouse Apartment’ ne cikin birnin Tokyo, Kakansa Emir ne ya kama masa hayar gidan shikadai don kawai ya zauna yayi karatu babu takura, baya son duka abunda zai takura takwaransa kuma jikansa na farko da yake kira “Kehinde” wato Hussaini, don haka ne ya gwammace ya kama masa wannan tsadadden gidan ya zauna a cikinsa shikadai yayi karatunsa cikin nutsuwa, maimakon ya zauna cikin gidajen dalibai yana manejin rayuwa irin wanda galiban kowanne dalibi da yazo kasar ke yi. Shi da kansa ya san ko cikin zuri’arsu ta Sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni shi dan gata ne, yafi kowa gata da samun kulawa da soyayyar Sarki. Prince yayi amanna da cewa, Sarki Abdulrasheed na masa son da baya yiwa kowa cikin ‘ya’ya da jikokinsa, cikin zuri’ar Sarki Abdulrasheed kaf dinsu shine na gaban goshin Kakan nasu. Hatta Taiwo da aka haifesu tare saidai ta biyo bayansa a gun Emir duk da taci sunan mata mafi soyuwa a gareshi Olori Murjanatu. Kai Sarki baima cika shiri da Taiwo ba don yakan ce halinta irin na Babanta ne bata son shiga cikin dangi. A kokarinsa na neman abinda zai kwashe masa damuwar da yake ciki, sai ya sake kunna na’u’rar ya budo aikin ‘final project’ dinsa na kammala digiri na biyu, wanda shi ya rage masa, in ya gama ya mika aka bashi certificate zai bar kasar Japan. Wayarsa a kasha take tun jiya bayan sun gama magana da Taiwo, ya kasheta gabadaya ne don tsira daga azababben kiran Hasinah, wanda take jefo masa shi a jejjere babu kakkautawa sanda ya bar wayar a kunne, haka na Tokumbo ma yake shigo masa duk bayan minti, wani zubin kiran nasu har turereniya suke yi da juna, amma ko kusa ya kasa dagawa dayansu, don ya san maganar guda daya ce (hakuri zasu bashi) wanda bashi da amfani gareshi a halin yanzu, me zasu ce masa bayan wannan? Ya riga ya gama (making mind) dinsa kan cewa babu shi babu soyayyar mace bayan mahaifiyarsa! Babu shi babu soyayya da kowacce mace kuma. Don haka tunda har zuwa lokacin zuciyarsa bata saki ba sai ya kasa tabuka aikin komai na (project) din nasa, wanda daga shi ya hada masters dinsa a (Petro Chemical Engineering). Har ila yau, Abdulrasheed yayi wani kuskure domin kasa furta addu’ar yayewar bakin ciki, kamar yadda Nenne ta dade tana nuna masa cewa a duk hali makamancin wannan ya dimanci addu’ar yayewar kunci da damuwa da Annabi SAW ya koyar, amma a yanzu bayan bakin ciki har da shaidan ke jagorantar ragamar fushin zuciyarsa, yana controlling emotion dinsa da grievance dinsa, yana gaya masa saboda abinda Hasinah tayi masa to daga yanzu bashi babu kallon wata diya mace, koda da jan yaqutu (emerald) aka kerata, daga nan har gaban abada. Daidai lokacin, kararrawar kofa (door bell) ta sanar dashi yanada bako a bakin kofa. Kamar bazai tashi ba, don kafafunsa kansu sun yi masa nauyi, sabida dadewarsa a zaune, kamar yadda zuciyarsa ma tayi nauyi mai yawa a cikin kirjinsa, ya dade gaban allon kwamfuta (doing nothing). Baya tsammanin zuwan kowa a dai-dai wannan lokacin don a saninsa bashi da appointment da kowa, amma ko mai yasa? Sai ya ji ya kasa kyale kiran kararrawar, don mai dannawa ya ki tsagaitawa da dannawa, ya tashi ya taka a hankali cikin basarakiyar tafiyarsa, yana tafe cikin nutsuwa kamar bai son taka kasa, wadda tafiyarsa ce wannan ta halitta. Abdulrasheed ya bude kofar falon fuskarsa ba yabo ba fallasa. Ga mamakin sa sai ya ga ‘yar uwarsa rabin ransa da bait aba kawo zuwanta a yanzu ba. Doguwa kakkaura Murjanatu-Taiwo ce a tsaye, cikin bakar abayat, ta nade kanta da dankwalin a bayar ta saka face-mask, wanda ya rufe fiyeda rabin fuskarta, Taiwo na rungume da diyarsa (Kiki) Ruqayyat. Kiki ta sha ado da ribbons mai kalar pink da yellow kamar ka sace ka tafi da yarinyar don kyau. Taiwo a Tokyo, unexpected, don kawai hankalinta ya gaza kwanciya da halin da yake ciki. Hakika kamar yadda tayi tunani yana bukatar wani nasa kamar ta a gefensa, a dai wannan lokacin, wanda zai tunasar da shi ALLAH! Da karbar kaddara. Ko Nenne da Dade basu san da tahowar Taiwo Japan yau ba. Daga ita sai Toufeeq wato mijinta suka shirya maganar tahowar tata da gaggawa don ta lallashi Abdulrasheed don ta san shi bai iya daukan frustration da sauki ba musamman in yana ganin ka masa unfair treatment da bai cancanta ba. Hannu yasa kawai ya karbi Kiki daga kafadunta ya sumbaceta bayan ya bude kofar, ya dan yiwa Taiwo (side hug), amma ya kasa boye feeling din dake kasan zuciyarsa na hakika ya ji dadin ganin su a wannan lokacin akan basarakiyar fuskarsa. Taiwo ta kama hannunsa ta rike cikin nata, a haka suka karasa tsakiyar madaidaicin hadadden falon nasa, tana mamakin fadawar da Kehinde yayi, cikin ranta tana korafin duk neatness din dan uwan nata da kullum zaka ga komai na gidansa tsaf-tsaf yana kyalli, yau falonsa kaca-kaca, gabadaya ya canza daga dan gayun Kehinde din data sani cikin kwanaki biyar kacal. Ta tabbata da kyar idan a duka kwanakin nan ya ci abinci kuma yayi wanka yadda ya saba, balle akai ga zancen gyaran fuskar da bai bari da kasumba. Ta yarda soyayya masifa ce (ga wanda bai yi sa’arta ba) sannan cin amana daga wanda kake so, ka kuma yarda dashi da zuciya daya, ka wahaltawa rayuwarsa a lokacin da yake tsananin bukatar taimako kamar Haseenah da Adetokumbo yafi komai lahanta zuciyar dan adam wato (butulci). Balle Abdulrasheed da zata rantse bai taba cin amanar kowa a rayuwarsa ba, mai kirkine mai alkhairi ne shi, zuciyarsa mai kyau ce kuma mai tsafta ce akan kowa da komai, komai zai yi ma mutum yana yi ne saboda Allah ba don ya rama masa ba. Taiwo ko kafin ta ko huta kicin ta shiga ta samar masa abinda zaya ci mai zafi da nauyi wato Amalar bawon doya miyar Ewedu data ji naman turkey da smoked fish zuku-zuku. Saida ta tabbatar ta masa favourite food dinsa ya ci sosai ya sha tea na nescafe mai zafi, sannan ya kishingida akan sofa da Kiki a gabansa yana wasa da ita. Ko a kwayar idonsa ta lura yunwa tayi masa lahani a kwana biyar ba kadan ba, kasancewarsa mutum mai yawan cin abinci, kullum Nenne na cewa “his best friend is food”. Idan akwai abinda yafi karyawa namiji zuciya toh Hasinah ta karya maza, ta karya zuciyarsa raga-raga. A daren shi da Taiwo sun zauna sun kara tattaunawa kan al’amarin da ya faru dashi da Hasinah, kuma Taiwo bata barshi da mummunan tunanin da ya riga ya tsirga ya samu muhalli a zuciyarsa ba na cewa duk mata haka suke, tayi ta bashi baki da kwantar masa da hankali da bashi kyawawan misalai iri daban – daban na halin lalacewar da al’umma ke ciki a wannan zamanin, tace don haka wannan bazai zamo wani abin mamaki daga halayyar dan adam ba. Taiwo ta kara da cewa “ka yarda ba kuma duka mata muka taru muka zama daya ba a halayya da dabi’a, ta kara da nuna masa cewa Hasinah ba itace karshen rayuwarsa ba, sannan ba itace autar mata ba, wasu matan ma nagari ko haihuwarsu ba’a yi ba, tace kada hakan yasa ya fidda kyakkyawan fata akan mata tagari. A cewar Taiwo, “mata nigari yanzu aka fara haifarsu”. Shirmen Kiki ma ya taimaka kwarai wajen cheering dinsa up. Ya fara murmushi, murmushinnan nasa mai matukar kyau da aji, da Kiki ta hau jan kasumbar daya bari a fuska wadda bata saba gani a tareda shi ba, ya dan fara sakin ransa da mantawa da damuwar Hasinah Ambursa don ita tafi bashi mamaki fiye da Adetokumbo wanda dama su maza ai kunyarsu ragagga ce akan macen da zuciyarsu ta kwadaita musu. Shikuwa Tokumbo Akanni a ranar bai kara kwana a Tokyo/Japan ba, yana jin karshen shigarsa kasar Japan din kenan gabadaya, har dai in Abdulrasheed yana cikinta, duk da a can ne harkokin kasuwancinsa suka fi yawa. Taiwo da Kiki, basu baro Tokyo ba saida suka kwashe sati tare da Prince Abdulrasheed (Kehinde), har sai da ta tabbatar Prince din ya manta da damuwar da Hasinah ta haddasa masa, ya koma harkokinsa da rubutun project dinsa amma ko sunanta yace kada ta kara ambata masa. A zahiri Prince Abdulrasheed ya saki ransa sosai yadda Taiwo keso, har ya koma harkokinsa na baya ya soma duba schedules na tournaments, yayi kokarin da ya kammala project dinsa kaf tun kafin barin su Taiwo gidansa. Musamman da komai Taiwo ke masa cikin gidan na kula da abincinsa da tsaftar gidansa da lallashinsa shi kawai aiki yake wuni yi akan kwamfuta. Amma abinda Taiwo bata sani ba shine mummunar illar da incidence din yayi a zuciya da tunaninsa, ya riga ya gurbata psyche na tunanin sa akan mata da soyayyar dukkan diya mace in general. Ranar da suka kwana bakwai tare dashi Taiwo da ‘yarta suka juyo gida Lagos cike da kewarsa. Da alkawarin sai sun zo bikin kammala karatunsa nan da ‘yan watanni masu zuwa. ***** ***** **** WACECE NENNE SAPPA? N enne (na nufin ‘Uwa’ kenan), da harshen fulatancin Arewacin Najeriya na sassan Gombe, Adamawa da Taraba, wanda Hajiya Sappa ta fito daga cikinsu, kuma da shi yaranta ke kiranta, Nenne Sappa, irin iyayen mun nan ne na zamanin da, masu halin zuhudu (gudun duniya), taqawa, da tsananin yawan ibadah wadanda duk halaye ne na NANI OUMMANA. Mahaifiyar ta Nani Ummana ta kasance mace mai yawan kaskantar da kai, da gudun rudin duniya, wadannan sai suka zamo halaye ne wadanda dasu ta raini Sappa, duk wani halin tawali’u wato humbleness (a down to earth personality) Nenne Sappa ta hada shi cikin kyawawan halayenta. Nenne Sappa ta kasance kyakkyawar dattijiya, fara ce kal, jazur da ita mai yalwar sumar kai, gira data idanu, mahaifiyarta Nani bafullatanar garin Gombe ce don haka kusan zamu ce kamanninta Sappa ta debo, wadda yawan shekaru baisa kyawunta ya gushe ba sabida hutun da take ciki kuma jikinta mai boye shekaru ne, yanayin jikinta ya nuna cewa an zuba kyau da farin jinin manyan sarakuna a zamanin kuruciya. Kai kace Sappa ita ta zabarwa kanta duk wata kankanuwar halittar dake jikinta don kyawun fasali, har zuwa yanzu data baiwa sittin da biyar baya, Nenne Sappa, na nan da extra added beauty dinta (zallar kyawunta). Kenan a takaice sai mu ce Nenne, (Hajiya Sappa) ta samo personality dinta na (Down to Earthiness) ne daga mahaifiyarta Nani Oummana, wadda ta kasance uwargida a cikin duka matan Maimartaba Uban Kasar Gombe, Sarkin Gombe na goma, wanda duk da kasancewarsa basarake to gawurtaccen Shaihun malami ne shima. Nenne itace ‘ya ta biyu cikin ‘ya’yan da ya haifa masu tarin yawa da matansa na aure hudu. Cikinsu duka yafison Oummana da suke kira Nani wadda ta kasance mahaifiya ga Haj. Sappa. Bayan rasuwar Sarkin Gombe wato mahaifinsu Nenne a dakinsu ne aka gaji sarautar. A halin yanzu Yayanta da suka fito ciki daya ne akan karagar mulkin Gombe wato Maimartaba Sarki AbdulYassar Jalloh Umar (CFR). Tsohuwa Oummana ta cigaba da zama ne a dakinta bayan rasuwar sarkin Gombe Ahmadu Jalloh Umar, yayinda sauran matan da yake da sauran kuruciyarsu duk suka fita suka sake aurarraki. Don haka ta zama uwa ga ‘ya’yan sarkin Gombe bakidaya wadanda ta haifa da wadanda bata haifa ba wato diyan kishiyoyinta duk ta hada ta rike ta mayar nata don yanzu babu iyayensu mata a gidan. Sarki AbdulYassar babban dan Nani Oummana shi Hajiya Sappa ke bi haihuwa, sai autan Nani Abdulmajid wanda ke kasar Morocco da iyalinsa, sukenan ‘ya’yan da Nani ta haifawa uban kasa, sauran ‘ya’yansa maza da mata guda goma sha biyu duk na kishiyoyinta ne amma bazaka taba iya banbance wadanne ne wanda Nani Oummana ta haifa da wadanda take rikewa marigayin mijinta ba, saboda adalci da halin dattaku irin na mutanen da. Da irin wadannan kyawawan halaye Nani Oummana ta raini diyarta Sappa mace daya (Nenne Sappa) cikin maza har itama ta girma suka aurar da ta ga zuri’ar Akanni’s tun mahaifinta yana raye, har itama a yanzu gashi ta tara nata bataliyar iyalin. A yadda Hajiya Nenne take gudanar da rayuwarta wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yanta hudu dake gabanta, sak halin mahaifiyarta Nani Oummana, ba bazaka taba cewa ita din ‘yar Sarki kuma jikar Sarki, sannan matar babban dan Sarki, uwa ga jikan Sarki na farko bace. Sabida yadda take nuna musu gudun duniya da mantawa da madaukakiyar nasabarsu, ita dai burinta shine su bi Allah, su kasance masu tausayawa mara karfi, su kiyaye sallah akan lokaci, su nisanci zinah kowacce iri kowanne nau’I ce, wannan itace tarbiyyar Nenne kullum ga yaranta hudu, duk wani burinta a yanzu shine ya zamo cewa halinta suke kwaikwayo, halin kankan da kai da tawali’u, shi takeso Taiwo da Kehinde da kannensu twins mata guda biyu wato Firdausi da Fatima su siffantu dashi. Amma me? Cikin ‘ya’yan nan nata guda hudu kowa halinsa daban da nata, babu mai irin halinta na kaskantar da kai. Suna gudanar da rayuwarsu ne bisa tsari na ‘ya’yan manyan sarakuna da irin tarbiyyar gidansu na Akanni’s wato yadda suka taso suka tarar a masarautarsu ta Ilorin. Kakansu Sarki Abdulrasheed da kansa ya taba cewa Nenne ta haifo masa jikoki masu halaye daban-daban da yake tinkaho da dabi’unsu na sarauta. Abdulrasheed baya rayuwa irin wadda take so, baya zama a kasarshi, rayuwa ce yake yi daidai data ‘ya’yan gata kamarsa, domin Kakansa ya tsaya masa. Taiwo kuma miji ya tsaya mata don ba karamin dukiya Toufeeq ya mallaka a turai ba. Sannan Fatima da Firdausi Yayansu Abdulrasheed da suke kira Hamma wato (Prince) ya dade da tsayawa rayuwarsu matuka, tun shigarsu jami’a yake dawainiya dasu, bai yarda Dade (mahaifinsu) ya kashe komai akan karatunsu da bukatunsu ko dawainiyarsu tayau da kullum ba, shine komai nasu, baya so su kannen sa su nemi wani abu komai tsadarshi su rasa tunda shi ba iyali ya ajiye ba, so kusan zamu iya cewa komai na Prince na ‘yan uwansa ne baida wani buri bayan walwalarsu da wadatuwarsu. Princess Fatima da Princess Firdausi nada albashi mai tsoka duk wata kai tsaye daga account dinsa zuwa nasu. Haka Kiki da Hakeem ‘ya’yan Taiwo. Hajiya Sappa kullum tsaye take a kansu da addu’a, shine kadai saukinta. Musamman shi da yayi nisa da ita, kullum ko a waya bata fasa tunasar da shi bin Allah, kaunar musulunci da kiyaye sallah, ko yana dauka ko baya dauka ita dai Nenne bata fasawa kuma bata fasa yi masa addu’a ta musaman a duk inda yake cikin duniya Allah ya kare mata shi daga rudin zamani dana kuruciya, kasancewarsa namiji daya tal a cikin mata uku da Allah ya bata. A yadda Hajiya Sappa take rayuwa cikin yawan ibadah kullum, da kula da bautar aure da mijinta uban ‘ya’yanta, kai sai kayi tsammanin ita din wata waliyya ce. Shigarta kullum cikin hijabai (jilbabs) kala-kala kamar bata da alaqa da kowacce sarauta. Duk shekara Hajj da umarah basa wuce Nenne Sappah, bata azumin Ramadhan a gidanta dake Lagos sai a birnin Makkah da Madinah duk shekara, wani abun burgewa da Nenne in zata je Hajji bata bin International saidai Pilgrims duk cikin halinta na (down to earthiness) da kaskantar da kai, wanda take bi duk shekara daga hukumar alhazai ta jihar Lagos zuwa Saudiyyah. Shekarun Nenne Sappa a halin yanzu sun kai kusan sittin da biyar a duniya. Yayin da mahaifiyarta Nani tayi tsufa mai inganci saboda ibadah, har yanzu cikin koshin lafiya Nani Oummana take rayuwa a Gombe da jinta da kuma ganinta garau. Tun Nene Sappa nada shekaru akalla sha biyar take gidan aure, kamar yadda na fada a baya mahaifinta Uban Kasar Gombe Ahmadu Umar Jallo, ya bada aurenta da hannunsa ga dan abokinsa kuma babban amininsa wanda ya kasance Bayeraben Ilorin (dan kabilar Yoruba). Saida Prince AbdulRashid ya cika shekaru ashirin a duniya, bayan Nenne Sappa da Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa saboda son da yake ma Nennen Prince Hajiya Sappa, AbdulRasheed shi ya saka mata suna (Nenne). Kwatsam bayan fidda rai rana daya sai Allah ya kara baiwa Nenne Sappa haihuwa. Cikin ikon Allah wannan karon Nenne Sappa ‘yan biyu mata ta haifa kyawawa son kowa fara da baka, wato daya ta debo kalar dangin mahaifinsu Bayeraben usuli, dayar kuma ta debo Nenne, amma fa ko kusa ‘yan biyu basu kama kafar Yayansu Prince AbdulRasheed a kyau da farin jini gun iyaye da dangi ba, sabida shi nasa kyawun surki ne na ruwa biyu; wato duk uwar da kuma uban ya debo ya hada, don haka kamanninsa kamar na half-caste (ruwa biyu) suke. Aka kira su Princess Fatima da Princess Firdausi (Princess na nufin Gimbiya da harshen hausa). Daga kan ‘yan biyunnan ba’a kara ko batan wata a gidan su AbdulRasheed ba. Har kawo recently, da Princess Fatima da Princess Firdausi sukayi bikin cikar shekarun haihuwarsu ashirin da hudu a duniya a gidan iyayensu dake yankin Banana Island a jihar Lagos. Daga Princess Fatima har Princess Firdausi sun kammala karatun jami’a a Jami’ar Nsukka, kuma kowacce da zancen aurenta a kanta. Gidan Engnr. Idris Akanni, yana nan a Banana Island wani bangare na (offshore) din Ikoyi, waje ne da masu arzikin kasar Najeriya da masu sarauta ke buya su zabga gininnuka na gidaje, su zauna suna cikin arzikin da suka tara ta yaki-halak yaki-haram tareda iyalansu tsakiyar a jihar Lagos. Banana Island, na nan a Ikoyi, inda acan aka haifi ‘yan biyun; Princess Firdausi da Princess Fatima. **** **** **** BAYAN SHEKARU GOMA SHA HUDU Y a zama cewa a halin yanzu Engnr. AbdulRasheed (Prince) ya cika shekaru 44 na rayuwarsa, shekaru ne da suka zo suka wuce kamar kiftawar ido cikin tarin nasarori masu dimbin yawa da budi da falala a gareshi da bazasu lissafu ba. Wace duniya Haseenah take bai sani ba, don bayan kammala Masters dinsa sai ya bar Japan kwatakwata. Ya koma Argentina yayi PhD a jami’ar da ayayi karatun digiri na farko. Daga baya ya koma Qatar inda ya samu aiki da ‘Qatar Refinery’. Bayan wancan incidence din da ya faru dashi shekaru goma sha hudu a baya still yana nan akan ra’ayinsa na tafiyar da rayuwarsa yadda yake yinta ba tare da tunanin aje iyali ba, sannan ba wani aikin ashsha ne a gabansa ba sabida hardly Prince ya zauna baya komai in ba lokacin barci ba, bashi ma da lokacin kansa kona tunanin abinda ya dace a gareshi don koyaushe baka raba shi da yawon fita tournaments kasashen duniya da ake ji da wasan Polo. Polo a kasashen da ta karbu babbar sana’a ce mai matukar farin jini kuma ta manyan ‘ya’ya, Prince Abdulrasheed ya samu duk abinda ake nema a cikin Polo zuwa yanzu saura taki daya ya rage masa. Polo na jika shi yadda ba’a zato har fiye da aikinsa na matatar mai, domin yana cigaba da dauko kofin zinare a yawancin tournaments dinsa, sunansa da shararsa na kara harbawa yana shawagi a sararin samaniyar duniyar wasan Polo na duniya. Saidai kuma duk dan adam mai lafiya ai baka raba shi da feelings. Ya yarda shi dan adam ne ajizi kamar kowa, amma kuma mai iya controlling feelings dinsa, by making himself always busy da harkar Dawakansa a cikin gida, da aikinsa na matatar man fetur idan yana birnin Qatar, da kuma tseren doki idan ya fita tournaments sauran kasashe. Yafi rayuwarsa a kasar Argentina inda acan yafi yin wasan Polo, kasar data zame masa uwardaki bayan kasar haihuwarsa, Argentina. A yau tana zaune a ranch house dinsa cikin wata kujera sakar kaba ta hannu, yana kallon ingarman dokinsa da ya kira da suna ‘SEHEEB` wato ‘ABOKI’ daga can nesa dashi. A tsaya fadin cewa Dokinsa Saheeb mai muhimmanci ne da tsohon tarihi a cikin rayuwarsa bata baki ne, kasancewar shine dokin da ya fara mallaka a rayuwarsa, kuma wanda yafi so cikin duka sababbin Dawakansa. Dokin na cin korran ciyayin da suka mamaye gidan daga korran shuke-shuke masu ban sha’awa da kayatar da idanun wanda duk ya kusanto su. Daga can gefe yana iya hangen duk wani motsi na hadiminsa Pareto wanda ya dukufa aiki, saurayin dake kula masa da Doki Saheeb da sauran Dawakan dake cikin stable din gidansa. Saurayin yana rage tsayin ciyayin gidan ne da inji, yana daidaita tsayinsu da cutlass, yadda zasu fi bada sha’awa. Sannan yana kwashe kashin Doki a abin shara na musamman. A sa’ilin ba komai Prince Abdulrasheed ke yi ba sai kurbar sassanyar ruwan Inibi a tambulan na glass mai garai-garai, yana cikin tunanin yadda tournament dinsa na gobe zai kasance. Wani wasan tseren Doki ne wanda ya jima yana jiran zuwan lokacinsa, da yi masa kyakkyawan shiri. Ba don komai ba sai don kasancewar wasa ne da zai gama daga darajar sa a duniyar wasan tseren Doki, da shahararsa a Polo a kasar da yake yiwa Polo tana biyansa (Argentina). A wannan wasan ne yake saka ran kaiwa sauran taki kadan din daya rage masa…. In Allah yasa yayi nasara, zai samu ya kai matakin karshe na kwarewa a wasan Polo da ya dade yana harin kaiwa wato (10+ goal Polo Handicap). Shi kansa Saheeb kamar ya san shirin da ubangidansa keyi akan fitarsu ta gobe, da burinsa akan tournament din gobe, don haka in ka ganshi sai kayi mamakin yadda yake annashuwa, sai harbin iska yake da haniniya cikin sabo da yanayin da koshin lafiya a tare dashi. Hausawa suka ce wai rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya, kome aka sawa rana cikin yardar Allah zai iso kamar kiftawar ido, gobe ne wannan ranar da Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni ke ta dakon zuwanta wadda yake yiwa wannan babban shirin da kyakkyawan fatan, wato ranar tseren Dawaki na duniya da Argentina ta shirya tsakaninta da sauran kasashen Polo na duniya. Amma shin ba masu azancin magana ta tsinkaye sunce mafarkai kamar dan da ba’a haifa bane? Wani a haife shi a raye, wani kuwa a mace ake haifarsa. Ba kowanne fata, ba kowanne buri ne yake tabbatuwa a lokacin da mukeso, ko muka tsara yuwuwar tabbatuwarsa ba! Sai lokacin da Allah ya so, ko ya ga damar tabbatuwarsa. **** **** **** RANAR GASAR KOFIN TSEREN DAWAKI NA DUNIYA A KASAR AJANTINA (ARGENTINIAN INTERNATIONAL OPEN POLO TOURNAMENT) S ahu biyu ne na mahaya Dawakai zaka iya hange, suna masu kallon juna sashe-sashe sun jeru reras akan layi. Duka Dawakai goma ne a kawanne sahu, nashi dokin yana tsakiyar sahun farko, Dawakan sun tsaya car da kafafuwansu, suna kartar kasa da kofatonsu gwanin ban sha’awa cikin koshin lafiya sai faman ragaji da harbin iska suke tsabar koshi, sai sheki suke kamar zasu fashe sabida tsaftar da suke samu, ‘Polo Riders’ din (mahayan) sun yi irin tsayuwar nan ta jiran umarni daga ‘umpire’ bisa ingarmomin Dawakan tseren Doki na musamman wadanda ake kira (Polo Horses). Dawakan duka murdaddu ne kuma kosassu, sannan dogaye sambal, kalolinsu sun hada da farare, bakake da ruwan kasa, ga gashi yala-yala a kansu, da ka gansu kaga lafiyayyun Dawakai rainon gidan gona saboda koshinsu da cikar tsokar naman jikkunansu. Wadannan Dawakai ana rainonsu ne musamman don wasan tseren doki (Polo Tournament) na kwatankwacin irin wannan da ake yi yau, ko kuma don mallakar manyan Sarakuna da masu kudin gaske, dake da sha’awar wasan tseren Doki a matsayin ‘hobby’ dinsu ko ‘sport’ dinsu. Irin wadannan Dawakan zaka samu ba’a ko’ina ake kiwata su ba, kuma ba’a sayar dasu a ko’ina kamar yadda ake sayar da sauran normal Dawakai na kasar Hausa. Su din Dawakai ne na musamman, da sai a wannan babbar kasa kuma hamshakiya a sha’anin wasan Polo (Argentina) kadai ake kiwata su, wadda sanin kowa ne ta shahara fiyeda kowacce kasa a duniya in dai akan sha’anin wasan Polo ne, wato birnin Buenos Aires (Capital of Argentina). Ana kiran wadannan Dawakan da suna; ‘Thoroughbred Argentinian Horses’. Gabadaya mahayan nan suna sanye da kaya iri daya, wanda ya zame musu (uniform) na wasan tseren dawaki wato; fararen riguna masu kwala da farin wando (Polo t-shirts and white Trousers). Kamar yadda na fada a sama ‘team’ din mahaya Dawakan guda biyu ne, sukayi sahu-sahu suna masu fuskantar juna cikin jiran a kada kararrawa, su fara. Kawunansu sanye da ‘polo helmets’ wadda itama fara ce kal da ratsin shudi kamar kalar kayan jikin su. Yayinda kafafunsu ke sunke cikin fararen takalmannan tsadaddu da ake kira ‘Brogues’ da 'Chukka boots' da kuma ‘loafers’. Umarnin ‘umpire’ kawai suke jira ya kada kararrawar bada umarnin farawa, su kuma su fafari dawakansu ta hanyar baiwa Dawakan umarnin tafiya, wato daga nan za’a fara ‘match’ din. ‘Umpire’ (mai bada umarni/alkalin wasa) ya duba lokaci a agogonsa, yaga lallai lokacin da aka saka domin farawa ya cika, karfe hudu na yamma ta cika daidai (agogon kasar Argentina). Sai kawai ya kada kararrawa… and the match begins marvellously (wasan ya fara da matukar ban sha’awa, da burge idanun dubban masu kallo matuka gaya), masu gani physically cikin ‘yan kallo da masu gani virtually. Abin takaici Dokin kowa ya tafi, amma nasa Dokin bai ko motsa ba, sai ya tsaya yana kartar kasa cikin ‘yan mutsu-mutsu da alamu na kin son tafiya, babu gaira babu dalili kuma, hasali ma dai Doki Saheeb bai taba yin irin haka ga ubangidansa ba tunda ya mallakeshi. Wanda hakan ya bashi mamaki, at the same time ya kuma fusata shi matuka. Da kakkausar muryarsa ta ‘yan Polo, wadda ta fito very harsh and unpleasant (raspy voice) yace da dokin nasa; “SAHEEB!!!” Saheeb din yayi haniniya cikin amsawa, amma bai tafi ba. Ya kara cewa da sauti mai karfi fiyeda na farko “SAHEEB, Go!”. Wanda hakan ya zama fusataccen umarni na biyu ga Dokin da aka kira da suna “SAHEEB” abinda bai taba faruwa ga Dokin ba (ubangidansa yayi masa umarni sau biyu). Shi kansa dokin sai ya rikice. (Thoroughbred Horse) ne wato haihuwar Argentina kuma acan aka raine shi har ya girma, mamallakin nasa ya kwashe shekaru yana kiwata shi cikin gata da kula da lafiyarsa da tsaftar jikinsa da akaifarsa, kasancewarsa (favourite horse) dinsa cikin duka Dawakan da ya mallaka a (stable) din dake Ranch House dinsa (wajen kiwon Dawakai a jere cikin gidan gona). Ba Saheeb ne kadai Dokinsa ba, Dawakan hawansa sun kai shida, amma shine na gaban goshinsa, babu mai ganin soyayya da gatan da Saheeb ke samu. A ka’ida duk bayan shekaru biyu sai ya sake lafiyayyen Doki, amma shi wannan da ya kira “Saheeb” abokinsa ne da bai taba sake shi ba, kula yake da shi kamar dan cikinsa, kasacewar ya fito daga hannun daraja, wato hannun Kakansa da yake matukar so (dattijo mai ran karfe), tun lokacin da Kakan nasa yayi masa kyautar sa har kawo yau yake son Dokin sosai. Kakansa ya saya masa Dokin ne a wani zuwa da yayi musamman har kasar Argentina da kansa, don ganewa idonsa yadda babban jikan nasa yake gudanar da wasan nasa na Polo, a lokacin gasar ‘World Polo Championship’, wanda shima an gudanar dashi ne anan kasar Argentina. Haka yake bata lokacinsa da aljihunsa wajen kula dashi da lafiyarsa, kamar yadda yake kula da tasa lafiyar. Abincin da ake masa cusa dashi daban dana sauran Dawakai ‘yan uwansa, haka yanada kwararren Vetrenary Doctor dinsa (likitan dabbobi), wurin kwanan Saheeb na musamman ne cikin duka Dawakansa. Saheeb yana kwana ne a cikin korran ciyayi masu taushi (pitch grass) dake cikin (stable) dinsa. Mai kula da taje gashinsa da rage shi da gyara shi da yankan kumbarsa zaman Dokin yake a gidansa dindindin, ma’aikaci ne specialist akan raino da kula da Dawakai yake zaman albashi domin kula da Doki “SAHEEB” a (ranch house) din mamallakinsa shine Pareto. Albashi na musamman Pareto yake lamushewa daga aljihun maigidansa don kula da hamshakin Dokin nan nasa (Saheeb). Shi wannan saurayin Ba’ajantine (Pareto) wani kwararren ‘Horse Breeder’ ne, wanda yayi karatunsa da kwarewa musamman akan kiwon Dawakai da kula dasu. **** **** **** Umarni na biyu wanda ya fito cikin matukar fusata daga Ubangidansa, da dukan da yayi masa da sandar Polon dake hannunsa (polo mallet), shi ya sanya Doki SAHEEB yin fitar kibiya don bin umarnin ubangidansa, ya daddage ya taka a guje, yabi bayan sauran Dawakan har nan da nan kamar kiftawar ido ya cimmasu. Daganan mahayan suka saki ragamar Dawakan a guje, da wani irin gudu mai gigitarwa. ‘Helmet’ din dake kan kowannensu, wadda ta rufe rabin fuskokinsu ta bar rabi a waje, shi zai sa ka gane cewa Abdulrasheed (Kehinde) shikadai ne bakar fata dan Africa a cikin su, kuma dan kasarmu ta “Najeriya” mai wakiltar hadakar kasashen Africa ta yamma a ‘tournament’ din. Baka jin komai na tashi daga bangaren ‘yan kallo (sashen ‘yan Africa) sai ‘applause’ na kiran sunansa da fito da usur, cikin ambaton “…. PRINCE!!! PRINCE! PRINCE!” Suna masu daga masa hannu cikin tarin kauna da bada karfin guiwa…. As he started to lead the match now…. wato ya zamo shine akan gaba, dokinsa ya yiwa sauran fintinkau, duk da kasancewar dokinsa yayi jinkiri da farko, amma daga bisani dokin gudu yake baya ko sassautawa kamar ma ya fita a hayyacinsa sabida sabo da yayi jinkiri, gudu kawai SAHEEB yake zubawa kamar zai tashi sama dashi, har shi da kansa ya sha jinin jikinsa cewa gudun da Saheeb yake yi yau ya zarta kima. Gab da zasu isa ‘goal’ ne mummunan tsautsayin mara dadin ji da gani mai muni sosai ya afku. Taki kadan kafin isar su ga ‘goal’, PRINCE ya fado kasa daga dokinsa ji kake timmm! Sakamakon faduwar bazata da dokin nasa Saheeb yayi, alhalin yana gab da isa ‘goal’. Nan da nan hankula suka tashi, ‘yan kallo suka mike tsaye cikin alhini, Alkalan gasa ma haka suka dakata, aka kawo gado nan da nan aka dauke shi daga wajen zuwa asibiti, bayan an fara bashi duk wani taimakon gaggawa tun a hanya kafin a isa asibitin dashi. Karo na sau ba adadi da faduwarsa a Doki, a duka tarihin hawa dokinsa tun na kuruciya, bai taba faduwa yaji rauni irin na wannan karon ba, Saheeb ya raunata shi sosai, bayan kwashe kusan shekaru masa dan dama yana wasan Polo dashi a wurare daban daban cikin kasar Argentina. Duk da bashi kadai yake hawa ba, wato wani zubin yana hawa wasu Dawakan bayan Saheeb kuma lafiyayyu kamarsa, amma ya camfa cewa yafi jin kaimi da sakewa da nishadi idan ya hau shi don yin wasan Polo, kuma yafi samu nasara idan Saheeb ya hau. Ko babu komai ya fito ne daga hannu mai albarka, hannun Kakansa Sarki AbdulRasheed Akanni. Playing Polo has been the hobby of his life. Ya sha cin kofin zinare a wasan ‘polo’ a ciki da waje, a garuruwa daban-daban na kasashen duniya. Don haka wannan faduwar bazata da ta faru yau da Prince, ba ‘yan Africa kadai masoya Prince ta dagawa hankali ba, har dasu Turawan na Ajantina, wato (host country) na wasan da ake gudanarwa, da mahukunta gasar na kasar ta Argentina. Wani hamshakin asibiti mai zaman kansa aka kai Prince AbdulRasheed yake zaman jinya a can ba nisa da gidansa. Zaka yi mamaki in kaji cewa, duka raununnukan nan da yaji a jikin sa, har da karaya a kafa da hannu, sabida ba karamin faduwa yayi ba, domin Dokinnan sai da ya wulwula shi a sama sannan ya tika shi da kasa, amma raunukan nan basu dame shi ba, haka zugin ciwon su bai dami Prince Abdulrasheed ba, kamar subucewar kofin gasar nan, na ‘champion’ din duniya a POLO daga hannunsa.…. Wanda da wannan tsautsayin bai faru ba, ya saka ran zai kai shi ga attaining 10+ goal polo handicap (highest rank of the world’s polo player). **** **** **** BANANA ISLAND, LAGOS P rincess Fatima, ta shigo da dan saurinta tana cewa da mahaifiyarsu Hajiya Sappa. “Ni me ya faru da kunnen Nenne na ne? Anata kiran ki a waya tun dazu kina kallonta ido hudu amma dagawa ta gagara, halan baki ji kiraye-kirayen bama Nenne? Tun daga falo nake jiyo ringing din wayarki ba kakkautawa. Nenne meke damunki haka yau? Tun safe nake ganinki haka sukuku (moody) cikin tagumi da damuwarnan, duk kin birkice”. Princess Fatima, ta karasa shigowa dakin na mahaifiyar su cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan manyan sarakuna, ta fadawa mahaifiyarta Nenne Sappa kalaman cikin taushin murya, Nenne dake gyangyadi akan dardumar data yi sallahr walha ta dago tana duban Fatima fuskarta fal damuwa. A hankali ta bude ido sosai daga lumshewar data yi musu ta dubi doguwar diyarta Gimbiya Fatima, kyakkyawa ta karshe, wadda ke tsaye a kanta da wayar Nenne din a hannunta data sunkuya ta dauka a gabanta, har zuwa lokacin anata kira ba'a daina ba. Da sauri Nenne tace “Miko min wayar, Allah yasa shine, bana cikin nutsuwa Fatima, saboda yau kwana biyu bai kira ni ba, gyangyadinnan da kika ga nake yi mafarkinsa nakeyi a cikinsa, wai bashi da lafiya, dadin dadawa tun shekaranjiya rabon da ya kira ni, abinda bai taba yi ba, jinkirta kira na a duk yanayin da yake ciki (koda kuwa ace yana kan Doki ne)”. Fatima ta mika mata wayar, sannan ta zauna a gefe tana bata labarai. “Nenne jiya ne ‘Championship Tournament’ din su Hammah fa, a can Argentina, bashi da lokacin kansa kin sani. Na so inje kallo physically Dade (Baba) ya hanani, tun dazu kuma na kunna ‘PoloLine.TV’ ba’a nuno gasar ba. “I am worried too”. Ta karasa fada da harshen yarbanci. Wato itama cikin damuwar take kwatankwacin ta mahaifiyarsu. Ba tareda ta amsawa Fatima maganarta ba Nenne ta amsa wayar da ake tayi mata ba kakkautawa da sallama cikakkiya irin tata ta nutsuwa, ta hanyar nemawa wanda ya kirata amincin Ubangiji ba tare da ta san cewa katon Bayahude bane ke kiranta ba musulmi bane ba kuma Dan nata ba, duk kuwa da cewa da lambarsa aka kira ta. A wayar aka shiga yiwa Nenne bayani da harshen da ba ganewa take yi ba, wato yaren “Araucano” na Argentina. “Sunana Pareto Danny, ina magana daga wayar ubangidana, ya samu tsautsayi ne… muna asibiti, inason magana da Mother dinsa…”. Don haka sai kawai ta mikawa Princess Fatima wayar cikin yamutsa fuska tace “ungo nan Fatima, kiji me wannan yake fadi haka?”. Ba don ma taga lambar ta Ajantina bace da bazata amsa kiran ba, a ka’idarta Nenne Sappa bata amsa bakuwar lamba, amma kasancewar ta san cewa AbdulRasheed yana can, kuma yau kwanaki biyu kenan tana alhinin rashin kiran wayarsa da bata samu ba kamar kullum, domin duk halin da yake ciki baya kasa kiranta kona minti uku ne, shine yasa ta amsa wannan kiran da gaggawa don jikinta ya bata ya shafe shi. Maganar mintuna kusan uku Princess Fatima tayi da Pareto a wayar, ta fahimci me yake kokarin sanar dasu, wato Prince ya fado daga Doki, ya jikkata fiyeda koyaushe, yana asibiti a kwance da karaya a hannunsa, don haka Fatima sarkin raki sai kawai ta saki wayar a kasa ta dora hannuwa aka ta sakawa Nenne kuka. Kasancewar Fatima mai tsananin so ga Yayan nata kuma mai saurin kuka. Suna son junansu suna kula da juna shigowar bare cikinsu ne dai karbarsa sai a hankali. Nenne nata tambayarta ta gaya mata me aka ce mata? Da kyar, kafin Fatima tace cikin hawaye “Nenne Hammanmu wai, ya fado daga Doki yaji raunuka a jikinsa, yana asibiti can a kwance, an kira Dade a gaya masa ba’a sameshi ba shine aka kira ki”. “Subhanallah!” Inji Nenne, cikin kidimewa da mikewa tsaye, tana cewa “wannan DOKI!” Nan dai ta nemi fulatancin da take gwadawa akan AbdulRasheed sau tari yau ta rasa, Nenne bata jure rashin lafiyarsa ko kadan, duk da yana jimawa bai fadi a doki ba amma ko ya fadi baya jin wani ciwo na azo a gani, yaushe rabon ace yana kwance a asibiti ma ta manta koda ya fado daga Doki bai taba kwanciya asibiti ba sai dai ya sha maganin ciwon jiki yakwanat zuwa wayewar gari ya shiga harkokinsa, bait aba samun mummunan wani rauni ba. Cikin damuwa ta ce da Fatima tayi mata ‘booking flight’ mafi kusa, tace da kanta zata tafi har can ta yi jinyarsa, tunda dama duk suna da Visa na shiga Argentina sun saba zuwar masa koyaushe suke so. Kasancewar a kasar Argentina Prince AlbdulRasheed ya mallaki gidan kansa (Ranch House) mai ‘field’ na ‘Polo’ a cikinsa. Iyayensa, Taiwo da danta na fari Hakeem (kafin a haifi Kiki) da kannensa mata ‘yan biyu Firdausi da Fatima, na yawan kai masa ziyara gidan, kafin ya samu aiki a Qatar refinery y araba rayuwarsa gida biyu tsakanin Qatar da Argentina. A Qatar Penthouse gareshi wanda bai kai girman gidansa na Argentina ba kuma babu Dawakansa acan. Sai Princess Fatima tace itama don Allah zata bi Nenne gun Hamma suyi jinyar tasa tare, tace bazata iya zama a gida ba, alhalin bata san halin da Hamma ke ciki ba, damuwa zata isheta, don haka suka fara shirin tafiya itada Nenne. Princess Firdausi kadai da masu aikinsu aka bari a gidan, don ta jira dawowar Dade ta kuma kula da gida wato ta jira mahaifinsu da zai dawo a satin, kada ya dawo gidan babu kowa kuma agidansa kawai yake cin abinci, wanda shima ya tafi nasa ‘medical check up’ din ne na lalurar sugar dinsa a Egypt. Wani abun burgewa da wannan gidan nasu Prince Abdulrasheed shine tringualism dinsu; Babu irin yaren da bazaka ji anayi a gidan su AbdulRasheed ba cikin manyan yarukan nan uku su da iyayensu biyu da kannensa mata, tsakanin Hausa, Fulatanci da ‘native language’ na Babansu wato Yoruba, duk babu wanda basa ji, kuma babu wanda basa yi, wato babu wanda basa yarawa a junansu. **** **** **** THE PRINCE N enne Sappa da Princess Fatima sun sauka lafiya a kasar Argentina a wani marece na tsakiyar winter season, ana tsaka da tsuga yayyafin kankara. Nenne Sappa sanye da Hijab dinta ruwan kasa-kasa daga samanta har kasa, yayinda Princess Fatima ke sanye cikin wasu ‘Blue Royal Outfits’ masu kauri. Kamar yadda aka riga aka tsara hakan ce ta kasance; yaronsa Pareto shi yazo ya daukesu da wata kankanuwar motar Abdulrasheed din (Alfa Romeo), daga filin jirgi zuwa asibitin da yake, Pareto yayi musu jagora har dakin da Prince yake a kwance yana jinya a asibitin kashi. Sanda suka shiga dakin barci yake yi sadidan, don zugin hadewar kashi ya ishe shi, hakan yasa aka yi masa allurar barci don ya samu sa’ida ya kuma huta azabar. Nenne da Princess Fatima, suka taka suka isa gareshi suka tsaya a kansa suka kura masa ido, suna kallon kyakkyawar fuskarsa (with great affection) da alhini cikin idanunsu, daga bisani duk suka aje mayafansu akan kujera don yin alwallah su sauke sallolin da suka riskesu a hanya. Har suka yi sallah suka idar duk AbdulRasheed yana barci na karfin allura baima san da zuwan nasu ba. Pareto wanda shi yake kula dashi a asibitin kafin isowar ‘yan gidansu, shi ya kawo musu abinci na alfarma daga ‘restaurant’ din asibitin, daga cikin provisions din da aka yiwa Engnr. AbdulRasheed, duk irin abincin da yake so shi asibitin zai bashi, haka wadanda ke tare dashi don kula dashi. Sai magriba ya farka, yana bude ido a hankali, ya yi tozali da Nenne a gefensa tana sallah, Nennensa, daidai lokacin data sallame sallahr, wani kyakkyawan murmushi Prince ya saki yana fadin, “welcome my Nenne, saukar yaushe haka babu zato? What a surprise!” Sannan ya yunkura ya tashi zaune da kyar, ta mike daga kan dardumar ta gyara masa filo a bayansa yadda zaiji dadin jingina sannan taja kujera daidai kansa ta zauna, shikuma ya gaisheta cikin harshen Yoruba. Ita kuma sai ta mayar masa cikin fulatanci, haka sukeyi daman, in sun yi mata tana ji amma bata mayarwa, don har gobe Nenne jefi-jefi take yin yaren mijinta da ‘ya’yanta, tafi rike nata da kyau. Bata son yadda yaranta suka fi yin na Babansu suke kin yin nata, ba kuma don basu iya ba saidon sun fi girmama nasu. Nenne ta koma kujerar daidai kanshi ta zauna, ta dubi yadda ya sha daurin bandeji waje-waje, hannu da kafa duk karaya, tayi kwafa cikin damuwa da takaici ta ce. “Isn’t this enough Hammansu? Ni na tabbata yadda ka dauki hawa Dokinnan da muhimmanci bana jin ko aikinka kana maida hankali haka a kansa. Balle kuma sallah da ibadar Allah, na tabbatar suna wuceka, alhalin kana bisa sabgar Dawakai, wadanda su kadai zasu tserar da dan adam ranar lahira ba wasan tseren Doki ba”. Sai kuma Nenne ta dakata kadan sannan ta sassauta murya ta koma yin magana wannan karon cikin lallashi da lumana, ganin yadda Prince ke wani irin yamutsa fuska akan zantukanta, baya so take cewa baya ibadah sai hawa Doki. A ganinsa yana baiwa kowanne lokacinsa yana kokari kwarai wajen kiyaye sallah a duk inda ya samu kansa. In akayi la’akari da irin schedules dinsa. Yana irin nasa kokarin a ganinsa. “Magana ta domin Allah, Hammansu, ka maida kan ka kamar wani tsuntsu mai tashi sama kan fiffike, yau baka nan gobe baka can duk don hawa Doki?? Ni menene a cikin hawa doki ne? Ka ki tsugunnawa a wuri guda ka fuskanci rayuwa ta reality. Saboda Allah yaushe rabon ka da zuwa aikin Hajj don sauke farali balle umarah da take sunnah? A tunanina duk wata daukaka, ko suna da kake nema cikin wannan sana’ar ina ganin zuwa yanzu daka mallaki kofunan Zinare sau ba adadi a sanadinta, in ban yi kuskure ba kofunanka sun kai biyar, ko shidda, ina ganin ai ka gama samun daukakar Polo kuma Hammansu. Ko tunanin aure da aje iyali baka yi wanda shine wajibinka a rayuwa ta hakika kuma mai ma’ana ga dan adam, ba don komai ba sai don saboda hawa doki ne kadai a ranka, ka manta cewa harka fita shekarun kuruciya da jimawa ka shiga na girma, don ma dai bakayi kama da shekarun ka ba; you are still looking fit and healthy”. Nenne ta kara kwantar da murya yadda dole dan nata ya tausaya mata, tace “Abdulrasheed ko tausayina baka ji, duk faccalolina sun ajiye jikokin ‘ya’yansu maza ni ko daya babu, ba don Taiwo ta bani ba, jikoki ba da saidai kowa ya riga ni tarawa, har wadanda sukazo a bayana, ga maganganun nan marassa dadi da duniya ke yi akan ka suna dawowa kunnenmu, haka ‘yan uwan ubanka suma suke yimin irin tasu tijarar a kanka, suna ganin ni na hana Ubanka kara aure har tsufansa, haka zai mutu da mace daya kamar rai sai kace auren zobe, kai kuma dana haifa mun daure maka gindi kana yawon tambada da lalata a duniya ka ki cika Sunnah, kana gudun aure wanda yake sunnar Annabi SAW. Ka ki ko tsayawa kayi tunanin ya kamata ace a wannan matakin na rayuwarka kana da yara lafiyayyu har guda uku ko hudu. Yau dai tunda Doki ya kusa hallaka ka kana ji kana gani, ina ganin ya kamata ka hakura dashi haka Kehinde! Babu sauran alfanu kuma a cikin hawansa”. Prince AbdulRasheed ya muskuta ya gyara kwanciyar sa cikin jin azabar zafin ciwo irin na hadewar kashi, yace. “Nenne bana so ko kadan kike sakawa kanki damuwa akan abinda at least kin riga kin san bazan iya bari da sauki ba. Polo ya zama wani bangare na jikina Nenne, ina yi ne kawai don jin dadina da biyan bukatar sha’awata ga wasan Polo, amma ba don tara kofuna ba, yana debe min kewa yana hanani tunani yana kuma hana ni damuwa da komai, ba don neman wani abu kuma nake Polo ba ko da can balle yanzu da nake da aikin yi kwakkwara, don haka banaso kina damuwa da ance-ance din mutane wadanda basu da gadonka. Su mutane ai al’adarsu ne damuwa da abinda bai shafesu ba. Abinda ka kwashe rabin shekarun rayuwarka kana yi yana da wuyar bari a dare daya kuma farat daya Nenne. Kimin addu’a, idan inada rabon barin hawa Doki in bari a hankali. Nenne nifa zan iya ajiye aikina na refinery dungurungum! In rungumi wasan Polo shikadai. Idan Doki shine ajalina haka Allah ya kaddara min Nenne”. Yayi dan shiru yana dan haki, na zafi da zogin ciwon karaya, kafin yace “Nenne tun shigowarki bakiyi duba da halin ciwo da nake ciki ba, sannan ko jajen raunin da SAHEEB yaji baki yimin ba kin hau ni da fadan rashin aure anya Nenne? Ki godewa Allah da ban zarce ba, na barki da ciwon rashina bana rashin aurena ba. Kimin addu’ar samun sauki da gaggawa kinji Nenne na, ki daina damun kanki akan abinda banida rabo a cikinsa, ki roka min tsahon rai da lafiya mai amfani mu rayu tare, yafi min rayuwa da wata mace, tunda ba wani abun kunya na ke yi a yawon hawa Dokin nawa ba, sha’awa ce kawai, hobby na ne kawai yin wasan Polo. Amma ba haka kawai rana daya kice lallai in bar abinda nafi so a rayuwata ba, wai don tsautsayi ya gitta min wand aba yau farau ba, kuma mutane suna maganar banza a kaina da ke, ina ruwana da maganar mutane? Ko an gaya musu inada business da mutane su yabe ni ko su zage ni? Aure ra’ayi ne, kuma banida ra’ayin yinsa a yanzu, tunda dai auren nan Sunnah ne ba farillah ba”. Nanne sai ta zama speechless, ta rasa me zata ce masa kuma, duk ta inda tabi don Kehinde ya gane damuwarta da ciwon ranta akan rashin aurensa bazai gane ba, ta yarda kuma babu abinda zai sa AbdulRasheed barin Polo, idan wannan karairayewar da ta sameshi yanzu, basu saka ya barta hakannan ba. Ta kuma yarda bashi da niyyar yin aure nan kusa, aure baya ransa kwata-kwata, baya cikin burikansa da fatansa na gaba, burinta na samun jikoki daga jikinsa, bata san ranar da Allah zai dubeta ya cika mata shi ba. Wayar Murjanatu ce ta katse tunanin Nenne, ta boye dan guntun hawayen da ya tsatstsafo mata. Hankalin sa kacokam ya koma kan waya da Aunty Taiwo dake ta koka jin abinda ya sameshi ta waya tana zata taho itama yana ta zauna ai ya ji sauki, yana lallashinta da taushin murya, yana gaya mata ta san dai ba yau ya fara faduwa a Doki ba, shi nasa ciwon bai daga hankalinsa ba kamar lafiyar SAHEEB dinsa. **** **** **** Zaman jinyar Nenne da Fatima tare da AbdulRasheed a asibiti, ya taimaka matuka gaya wajen samun lafiyarsa da wuri, sakamakon addu’o’I na (Ayatushshifa) da Nenne takeyi kullum a ruwa tana bashi yana sha dare da rana, da kuma dorewar lafiya da take roka masa a duk bayan kowacce sallahr farillarta. Ya fara jin sauki sosai cikin ‘yan kwanaki kalilan, har yana tashi ya zauna yayi sallah daga zaune, bakin Nenne baya hutawa da yi masa nasiha akan bin Allah da tunasar dashi soyayyar Manzonsa, saidai in basu kadaice a dakin jinyar ba. Har ila yau Nenne bata gushe ba da nasiha sannan bata fasa ba. A kullum bata gajiya wajen nuna masa muhimmancin aure da ajiye iyali ga faein ciki da cigaban rayuwarshi, cikin nasiha da lumana, ta kan ce masa ‘ya’ya sune gatan bawa duk arzikinsa, tunda su zasu dinga yi masa addu’a a bayan ransa. Kuma su tsaya masa a sanda yake bukatar su. Auren kuma da yakewa kallo na daban Nenne tana kokari wajen nuna masa cewa ibadah ne ba son rai bane. Koma meye dalilinsa na gudun yinsa bai isa dalili a wurin Ubangiji ba, tunda dai ya bashi lafiya da abinda lafiya zata amfana. Tace ana yinsa ko ba’a so domin katange kai daga sabon Allah da tsarkake kai daga daudar zinah da katange zuciya daga sha’awar aikata sabo kowanne iri ne. Wadannan sune ire-iren kalaman Nenne Sappa ga danta Prince Abdulrasheed lokacin jinyarshi. Princess Fatima kuma ita ke bashi abinci a baki da cokali. Yau daya gama cin abincin rana, Princess Fatima tana gyara masa filon da zai kishingida ta bayansa, a cikin tarin sumar kansa sai ta hango tsillin ‘furfura’ a cikin gashin kansa. Ta kai waje guda 20 a cikin lallausar sumar kansa, ta kuwa ce me zata yi ba sakin shakiyyar dariya ba. Princess Fatima tasa hannu ta tsigo furfura guda daya daga saman kansa, tana dariya tana kanne ido ta nunawa Nenne, tana fadi cikin yanayi na (banter) harda neman sikewa don dariya, “someone has finished, ooh my Dear! Getting white hair before even getting a first wife… Nenne furfura ce fal! A kan Hamma!”. (Ta kara gishiri). To ma yanzu sabida Allah Nenne, wacece zata yarda ta auri mutum over 40 kansa duk yaci furfura? Ai saidai kwantan ‘yammata kamarsa dan (mid forties), irin bazawara mai ‘ya’ya biyu haka, ko widow (wadda miji ya mutu ya barta) haka dai, amma ba dai (sweet 16) ba!”. Nenne an sosa mata inda yake mata kaikai, sai ta gyada kai tace “in ya samu sweet 16 din sai ki hana ruwa gudu! Furfura baiwa ce ‘yar nan, ba itace tsufan namiji ba, wani ma sai ya fara ta yake fara jin mazantaka da karfin samartaka, rashin aure haka kawai babu dalili shine mishkilarsa, domin tamkar izgili ne ga rahamomin da Ubangiji yayi maka Abdulrasheed. Saidai kuma bansani ba ko abinda mutane suke fadi marar dadi a kanka din, ko gaskiyane Abdulrasheed?” Yanayin fitar sautin muryar Nenne, a halin yanzu ya nuna helplessness din da take ciki akan situation din, wanda hakan yayi matukar karya zuciyarsa, jikinsa yayi sanyi matuka, amma dai bai yi magana ba. Princess Fatima, ganin yanayin da suka shiga na damuwa su duka, sai ta dauki ipad dinta ta bar musu dakin, ta koma can reception na asibitin ta samu kujera ta zauna tayi tagumi itama, don taga zancen na Uwa da Danta ne, kuma yau raunin Nenne da bakin cikin ta na shekara da shekaru akan rashin aurensa yafi na kowacce rana bayyana a tare da ita da nauyin shekarunta da suka bayyana kan kyakkyawar fuskarta yau saboda damuwa. Wai AbdulRasheed ya fara furfura ba aure!!! Wannan al’amari ya tsorata Hajiya Sappa matukar tsoratawa. Fitar Princess Fatima keda wuya, sai ga hawaye mai kauri ya tsinke a fuskar Nenne Sappa. Kamar jira take Fatima ta gusa. Hankalin AbdulRasheed yayi tashin da bai taba yi ba yau, ba yau Nenne ta soma korafi da kuka akan rashin aurensa ba, amma na yau yafi na kullum daga hankalinsa ko mai yasa? Don ya ga bakin cikinta muraran a idanunta. Abdulrasheed ya shiga rokon Nenne cikin kaskantar da kai, akan ta gaya masa menene exactly damuwarta har haka akan rashin aurensa, take irin wannan zafafan hawayen dalilinsa, masu barazanar tarwatsa rayuwarsa? “Zubar hawayenki a kaina Nenne masifa ne a gareni kin sani”. Nenne Sappa saida ta yi sharbe son ranta, tana gogewa da habar hijab dinta. Kafin ta soma Magana cikin rauni da karaya. “Na soma zama cikin zargi mai girma a kanka nima! Na soma yarda da zargin da duniya ke maka, na cewa neman maza ‘yan uwanka kake yi (you are gay) shine abinda yasa ka juyawa auren Sunnahr Ma’aiki SAW baya. Haka ne ko ba haka bane Kehinde?” Nenne ta tsatstsareshi da jikakkun manyan idannunta da suka rine kamar garwashi suke jike shatab da hawaye mai yawa. Ko kadan babu firgita kan kalamanta a tare da shi, ko don ba yau ya fara jin ana zarginsa da hakan ba? Jin maganar yau daga bakin mahaifiyarsa shine babban abinda yafi tada hankalinsa. Amma ko kadan babu tashin hankalin maganar akan fuskarsa sai tsantsar damuwa da yanayin da mahaifiyarsa ke ciki. Abdulrasheed yace (cikin despair). “Nenne in kowa zai min wannan mummunan zargin ke UWATA (mahaifiya) ya kamata ki kyautata min zato. Ban taba zaton Nenne ranki zai yi bacin da zakiyi duba da wannan banzan zargin na mutane marar tushe da hujja ba, tunda kin san irin tarbiyyar da kika yi mun da hannunki, ba wani ya tarbiyyantar miki ni ba, kuma kinada tabbaci a kan ingancinta, na cewa ko bayan ranki bazan zubar da ita ba, balle da ranki da lafiyarki in yi wannan mummunan aiki. Anyway, bazan musa ko daya ba, cikin abubuwan da ake zargina dasu din. Allah ne kadai ya san zahiri da badinin zuciyar bayinSa, da abinda suke aikatawa na fili dana boye, kuma shaidarsa nake nema bata mutane ba Nenne, tunda ke kanki da kika haifeni kin kasa shaidata….…”. Yayi shiru, ya koma ya kwanta yana maida numfarfashi da sauri da sauri kamar mai ciwon asthma. A hankali AbdulRasheed ya rufe idanunsa…. Mummunan ‘scene’ din na Hasinah da dan uwansa kuma wanda ya rika a matsayin “amini” duk cikin family dinsu Adetokumbo akan gadonsa na gilma masa. Abinda ya faru kusan shekaru goma sha hudu a baya, amma har yau yake ‘haunting’ dinsa… ‘trauma’ din abun ya kasa barin ransa ya huta, zuciyarsa ta sake da mata. Cousin dinsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni da fiancée dinsa Hasinah Ambursa turmi da tabarya, kuma a kan gadonsa sannan a dakinsa mallakinsa a gidansa dake kasar Japan. Wani ‘incidence’ ne da kullum yake komawa ‘GREEN’ a idanunsa… ya kasa barin duhun idanunsa su huta ko hasken wata mace ya ratsa ta cikinsu. Shikuwa me zaiyi da mata yanzu? Ai ya dade da rufe babinsu daga kan Hasinah Bello Ambursa. A cewarsa dukkansu are nothing but ‘Gold-Diggers’, wadanda in dai namiji zai basu kudi to ya gama samun mutuncinsu, kowanne kare da kowanne doki ma yazo ya fanshi mutuncinsu da diyaucinsu in dai yana da kudi. A tasa mummunar fahimtar da ya dade da yiwa mata daga kan Hasinah, wadda ta dade da yin babakere a zuciyarsa ya gama yardarwa kansa duk matan yanzu irin Hasinah ne, masu son holewa ta jiki data aljihu, ya yarda mafi akasarinsu namiji daya ba zai taba isarsu ba, batare da sun zagaya sun ci amanarsa ba ko me zai musu na halacci kuwa, ko me zai basu iya karfinsa don kula da lalurorinsu, kuma koda zai yagi naman jikinsa ya basu bazai hana su hango wanda ya fishi samu ba, they are totally greedy, rashin wadatar zuci ya yiwa zakatan ‘yammatan yanzu katutu, babu soyayya ta saboda Allah a zuciyarsu yanzu. Shiyasa yake ganin bashida mata a duniya, ba’a haifi macen da zai kara gangancin so ba, bazai kara yarda da mace a duniya da sunan soyayya ba in ka cire soyayyar da yake yiwa Nennensa da ‘yan uwansa mata. Bai ki ba dai a gidan aljannah in yana da rabo. Me yasa mostly kyawawan mata kamar Hasinah ne kullum suke yin dage, domin hango wani wanda bai kama kafar mijin da Allah ya basu a komai ba? Marasa shararren kyau zaka samu basu cika dage ba. Me ya rasa da Da namiji ya rasa daya cancanci abinda Hasinah tayi masa? Me Tokumbo zai nuna masa banda cikar aljihu a lokacin? Idan har aljihun wani namiji dan uwansa ne zai sa Hasinah yi masa haka, to kuwa duk matan duniya ya dade da yi musu jimilla da ‘gold-diggers’, kwadayayyu, hadamammu, ma’abota manta halaccin mai halacci, wadanda burinsu kawai namijin da zai basu kudi suyi bushasha, ba wanda zai so su saboda Allah ba, kuma wanda zai kwatanta irin soyayyar da suke so ta banza da da sunan itace soyayyar da zata bulle dasu, koda kuwa ace babu abinda Allah ya rage ka dashi a rayuwa. Ya rasa wane irin jin dadi mata ke nema a wurin namiji fiyeda daya. Shi kuma Allah da ya halicceshi yayi shi mai matukar kishin kansa da kishin macen da yake so, watakila shine dalilin da yasa daga kan Hasinah ya daina sha’awar kowacce mace sai Polo dinsa, yanada kishin kansa fiyeda yadda harshe zai iya bayyanawa! Nenne ta rainesu akan turbar tsoron Ubangiji, tana tare dasu ko bata tare dasu suna tuna Allah, ta rigada ta dorasu akan turbar gujema ketare iyakokinSa. In aka duba kuma, a rayuwa ba abinda bai yiwa Hasinah ba, a matsayinta na wadda yaso aure da dukkan zuciyarsa ba tareda tunanin banbancin nasabarsa da tata ba, kuma marainiyar da ya fiddo daga gidan marayu, ya maidata daliba mai ‘yancin higher education, ta hanyar sponsoring karatunta daga gidan marayu zuwa Lagos eventually zuwa kasar Japan ba tareda sanin kowa nasa ba bayan Taiwo. Bayana fara karatunta na jami’a ya zama shine uwarta shine ubanta a Tokyo, shine cinta shine shanta, shine sutturarta da duk wani shopping dinta duk don ya katangeta daga neman wani abu ta rasa a rayuwarta duk da shima a lokacin ya dogara ne da abinda Kakanshi ke turo masa duk wata, da na mahaifinsa, a matsayinsa na dalibin postgraduate, soyayya ta gaskiya ba irin wadda bai yi mata ba, har da ta kauce hanya, domin ta saka shi ya danyi deviating daga tarbiyyar da Nennensa ta bashi, duk don ya faranta ma fiancée dinsa Hasinah ya kuma katangeta daga sha’war wasu mazan ba don yana so ba. A dalilin ganewa da yayi cewa ta soma wayewa da irin wannan rayuwar da tazo ta tarar ‘yammata da samari kamarta nayi a jami’a, lokacin da ya fahimci ita din mai son wannan rayuwar ce sai ya biye mata, bisa dalilai guda biyu; na farko son da yake mata, na biyu tsoron shi na kada ta kwadaici wani, idan shi din yaki biye mata. Da wannan Hasinah ta dulmiyar dashi a baya cikin rayuwar soyayyar shan minti, kazamar rayuwar da ’yammata irinta ke yi a turai, rayuwa ta rashin tarbiyya da baya ko son tunawa yayi da Hasinah yanzu. Duk da haka a kullum yana godewa Allah da bai taba sanin Haseenah diya mace ba (as in having sex) bai taba ba. Sai abinda ba’a rasa ba bisa jagorancinta. Amma duk da soyayyar shan mintin da ya biye mata suka soma ba don yana jin dadin afkuwar hakan ba, saboda a irin son da yake ma Hasinah yafi so ko meye zai shiga tsakanin su sai ya mallaketa ta hanyar aure, amma ta nuna ita bazata iya jira har zuwa wannan lokacin da Nenne zata amince da maganarta ba, dole ya biye mata suke kananan abubuwan da har ransa baya so. Don kuwa mace duk inda take komai kankantarta shaidaniya ce, balle shaidancin Hasinah mai license ne tunda ‘yar kwararo ce, amma duk da hakan biyemata din domin ya katangeta bai sa ya iya ya rike sha’awarta da hangenta da kwadayinta na abinda shi har lokacin ya kasa yi mata ba, saboda addu’ar Uwa ta dare da rana dake tasiri a kansa, ya kasa rike sha’awar Hasinah daga sauran mazan da basu kaishi komai ba. Amma a bukatun rayuwarta kam na yau da gobe baya jin ya gaza, sai dai don ta kasance mai son bushasha da sha’awar rayuwar kere sa’a. By Allah! Yayi duk wata bajinta da namiji kamarsa mai gata da asali da nasaba tsarkakakkiya ta sarauta da ilmi mai zurfi da malanta bazai yi akan matar da ya tsinto a kwararon gidan marayu ba! Bayan duk wannan wane irin sakamako ya samu a mahaukacin son nan kuma gurbatacce da yayiwa Hasinah??? Prince ya runtse ido da karfi, yana tuna Hasinah a ranar, da kazantaccen yanayin da yazo ya samesu ba zato, mantuwa yayi ya dawo, abin mamaki tareda kaninsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni, the worst part dinma kuma a dakinsa sannan a kan gadonsa. Saboda kawai Abdulfatahi ya fishi kudi, ya fishi iya shege ya fishi rashin tsoron Allah, uwa uba yanada ra’ayin yin bushashar arzikinsa ga matan banzan duk da zasu bashi jikinsu, don a lokacin shi Abdulfatahi wani babban Automobile Business Mogul ne, kasancewar a tsakanin Japan da Spain yake harkar shigo da motocinsa, to duk sanda ya shigo Tokyo a wajen dan uwansa Prince Abdulrasheed yake sauka, baya sauka a hotel, kuma ta haka ne ya san Hasinah a matsayin fiancée din dan uwansa, har suka saba shi da ita suna tsokanar juna irin dai wasan nan na kanin miji da wadda Yayansa zai aura. Yaya akayi-yaya akayi suka sarke a bayan idonsa kuma bai taba gane komai a tsakaninsu ba banda sani da yayi tun fila azal Hasinah mai dogon buri ce, mai kwadayi ce, mai son kyale-kyalen mata na fita tsara ce wato (Hasinah is a designer baby) sannan yana ankare da cewa tana son wannan harkar, a hakan kuma yana iya bakin kokarinsa akanta, don ganin bata rasa komai take bukata ba, kusan duk abinda iyayensa ke aiko masa a matsayinsa na dalibi a lokacin akan bukatun Hasinah masu dan Karen tsada yake karar dasu da kwalliyarta na sittiru tsadaddu, da kayan kawa da khyale-khyale ba tareda Nenne ta sani ba. Ko dama ita Nenne from day one, Hasinan bata kwanta mata ba tunda aka ce a gidan marayu aka daukota, tun a lokacin Nenne tace “NASABA” wato tsatso, wani abu ce mai girma da muhimmanci a neman aure to amma Hasinah fa? Suwa zata bugi kirji ta kira Kakannin jikokinta na wajen uwa na jikin Abdulrasheed Kehinde? Shikuma har a lokacin lallaba Nenne yake yi akan ta yarda ta karbi Hasinah a matsayin surukarta, ita kadai zuciyarsa keso, ita yake yiwa kauna ta saboda Allah ba zai iya auren kowacce mace in ba itaba. Shi ya bata surname da Bello Ambursa lokacin da zai shigar da ita makaranta, sunan abokinsa Bello da ya rasu. Sakamakon da ya samu a duk wannan sadaukarwar da yayiwa Hasinah shine Hasinah ta bige da cin amanarsa, itada dan uwansa mafi kusanci dashi, mafi kazantar cin amana har a gadon barcinsa kuma a gidansa. A cire maganar girman zina wadda lahani ce mai girma ga martabar diya mace. Abin ya kara dawo masa sabo. Kamar yanzu-yanzu ya faru. Shekaru goma sha hudu kenan da faruwar al’amarin a can baya, amma kullum sabo scene din yake koma masa a idanu da zuciyarsa, in ya tuna ko aka yi masa fadan yin aure ko ya kamata ya zabi matar aure a family dinshi. Nan da nan jikin sa ya hau tsuma, zazzabi mai zafi ya rufe shi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, zuciyarsa kamar ta hudo kirjinsa ta fito sabida yadda take hawa da sauka don bacin rai….. Ya dade bai shiga bacin rai irin na yau ba sakamakon wannan dogon tunanin da yayi. Ita da kanta Nenne ta lura da halin canjin mood da kalamanta suka jefa dan ta Prince AbdulRasheed, sai taji wani irin babu dadi a zuciyarta da kasan ranta. Ita ta san Abdulrashid dinta is always bold and smart fiyeda Taiwo, kasancewarta mace tanada saurin nuna rauni (sai karambani da rawar kai da shiga sharo ba shanu), but today he looks pale har fiyeda Taiwo uwar kankanba idan ta raunana. A ganinsa tunda har uwar data haifeshi ma ta fara yarda da zargin da duniya ke masa na cewa wai (he is gay), don kawai yana rayuwa a cikin turawan yamma, kuma yana practicing wasansu na tseren Doki a matsayin sha’awar ransa kuma sana’a mai girma, hujjar kowa ta makala masa wannan zargin shine kawai don ya ki yarda yayi aure ko kawo mace gidansa da sunan matarsa? Zargi wani abu ne mai girma da muni a musulunci balle zargi irin wanda duniya ke masa. Auren ai Sunnah ne ba farillah ba tunda Alhamdulillah yana iya rike kansa ta hanyoyin da addini ya koyar. Kusan kullum baka Abdulrasheed da azumin litinin da alhamis a bakinsa, baya kallon haramun, balle kai kansa inda ake aikatata, he is always busy planning and scheduling his Polo time-tables across the globe da tsara ayyukansa na Consultation a matatar man fetur a (Qatar refinery). Zina ai sai mutum ya bata kafa take shigowa rayuwarsa. Ga kuma addu’ar tsayayyyar Uwa irin Nenne Sappa a kansa kullum wadda zamu iya cewa itace babban makamin dake katange Abdulrasheed ga ayyukan sabo in akayi la’akari da yanayin rayuwar ‘yan Polo. Duk da cewa Nenne ta yi dana sanin furta masa damuwarta, amma kuma hakan ya taimakawa zuciyarta, yanayin da ya shiga kadai yasa ta rage tasirin zargin na mutane daga ranta akan dan nata, ko daga irin halin rudu da damuwar da ya shiga akan maganar kadai ta gane ba haka bane, zargi ne mai muni ake masa da shaci-fadin mutane da basu da gadon ka sai gadon magana akan ka. Ita kawai tayi la’akari ne da fadar nan ta hausawa dake cewa “ka haifi Da, amma baka haifi halinshi ba” kuma akace wai “ba’a shaidar ‘ya’yan yau”, da kuma yadda kana tufka a matsayinka na uwa; modern society da influence na ilmin zamani na warware maka tufkar ta baya, musamman shi AbdulRasheed da in akayi la’akari da irin ‘life-style’ dinsa, wato yanayin rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita gabadaya kome aka ce akansa al’umma bazata musa ba. “To me ya hanaka aure har yau Kehinde? Na roke ka da girman Allah yau ka gayamin. Ni mahaifiyarka ce da baka da wanda ya fini ba kuma wadda zata rufa asirinka a duniya irina. Shin idan baka sanar dani hakikanin matsalarka ba, wa zaka sanarwa a duniyarnan?” Zuwa lokacin ya soma dawowa cikin hayyacinsa, amma maimakon ya baiwa Nenne amsar data dace da tambayar data yi masa, wato menene hakikanin abinda yasa ko zancen aure baya kaunar a yi masa? Sai ya bige da maida zancen wani kala daban, don Nenne ta bar zancen, don har gobe babu wanda ya san abinda Adetokumbo yayi masa kaf cikin zuri’ar su, daga shi sai shi Tokumbon, sai kuma Taiwo, sai ita shaidaniyar HASINAH! Da bai san a wace duniyar take yanzu ba. Sai kuma Allah da ya haliccesu. Zai kuma cigaba da barin wannan zancen a ransa yana haunting dinsa shikadai ba tareda ya gayawa wani a danginsu ko iyayensu ba bayan Taiwo, albarkacin zumuncin Akanni’s da hadin kan gidansu. Yau ace wani cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni yana zina da macen da ba tasa bama abu ne da zai taba mutuncin su bakidaya, abun kunya ne ba karami ba, ga zuri’ar sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni a idon talakawansu dake ganin martabarsu da girman nasabarsu, wanda zai iya lalata hadin kan gidansu gabadaya wanda gida ne ko kuwa zuri’a ce data zamo abun buga misali a ciki da wajen jihar Ilorin. Sai ya maida abun zolaya ga Nenne, bayan ya maida murmushi mai sanyi akan fuskarsa, Prince ya soma magana cikin lallashin mahaifiyarsa. “To yanzu Nenne, ki gayamin saboda Allah, duk fadin Najeriya wacece kike ganin zata aureni da tsillin furfura kamar yadda Fatima tace, umh? Ta kuma kaunace ni da furfurar nikadai ba tare data hada soyayyata data wani na ba? Ba kuma don abin duniya da reputation dina (shaharata) a kan wasan Polo ba, soyayya pure nake nufi tsarkakakkiya ta saboda Allah! A dai yawan shekaru irin nawa, wadanda babu sauran kuruciya a cikinsu yanzu? Believe me Nenne, duk matan zamanin nan, ina fade ina karawa kullum (are nothing but gold-diggers) sannan karnukane babu daraja a tare dasu. Daga kan HASINAH AMBURSA… na gama rufe babin mata Nenne, (they just want money over pure LOVE), don haka basa gabana gabadayansu Nenne, har abada babu ni babu ‘ya’ya mata”. Nenne sai ta bishi da ido zuruuu! Ta kasa gane inda zantukansa suka dosa. Me Hasinan da ta san yanaso kamar ya cire ransa ya bata tayi masa da ya karya zuciyarsa haka? Ashe a kanta ne yake gudun mata tun zamanin samartakarsa? Ta dade bata kara jin komai game da Hasinah din ba. Ko daga bakin aminiyarta uwar dakinta (Taiwo) bata kara jin zancenta ba. Wacce a baya kullum suka hadu bata da aiki sai lallashin Nenne ta barshi ya auri Haseenah. A lokacin AbdulRasheed ya koma ya jingina da filo a jikin gadon jinyarsa, ya runtse idonsa a hankali yana motsa hannunsa na dama kadan da aka kwance daga daurin karaya. A can kasan zuciyarsa magana yake shikadai wadda baisan tana fita a fatar bakinsa ba, tana shiga kunnen mahaifiyarsa. “I am now a hopeless romantic. I want an idealist (true love)”. Wanda ya riga yayi amanna da cewa babu shi sam-sam a zamanin yanzu. Babu irin soyayyar da yake burin samu! Domin y agama yardarwa kansa a wannan qarnin da muke ciki, wani qarni ne da mafi yawan mata suka daina soyayya irin wadda yake buri ta domin Allah, ba don komai ba sai don zukatansu sun zarme da kwadayi da son rayuwar duniya da ta wuce kima, hakan yasa suka zama insatiable ga mazan da Allah ya basu masu yi musu kauna ta gaskiya, suka maida kawunansu sex slaves to rich men (sun zamar da kansu bayin biyan bukatar gangar jikin maza masu kudi ko mulki, soyayya ta hakika ta gushe a zukatan mata. Engnr. Abdurasheed ya kara kishingida sosai yana cigaba da cewa da kansa da kansa. “I am a hopeless romantic. I want true love!”. (Karin haske). “Prince AbdulRasheed (Kehinde) Idrees Akanni, yana nufin ya riga ya yardarwa kansa cewa babu soyayya ta gaskiya, true love is hard to find, or does not exist at all, matan yanzu duka are incapable of that...!”. **** **** **** Ba jimawa saboda irin kulawar da yake samu ya karasa warwarewa, aka sallamesu. Suka koma gidansa. A wannan dan zaman jinyar da Nenne Sappa tayi na dan ta Prince AbdulRasheed Kehinde, a kasar Argentina, ya basu damar samun shakuwa da wani irin kusanci da juna na uwa da data wada y agama mallakar hnkalinsa amma still yana bukatar kulawar Nenne da zamanta a gefensa, shekaru da yawa basu samu damar zama tare na lokaci mai tsaho irin haka ba, saboda yawace-yawacensa na Polo a duniya. Nenne ce ke dafa masa duk abinda zaya ci da kanta kullum, wanda shi da kansa yake zabar abinda zata dafa masa, haka take saka shi a gaba sai ya ci sosai, sannan ta tabbatar da ya sha magungunansa akan kari, wanda take barowa da hannunta akan farin tafin hannunta ta zuba ruwa a tambulan mai garai-garai ta bashi ya hadiya akan idonta don Abdurasheed baya son kwayar magani sai akan idon Nenne don baya son abinda zai bata mata rai tun yana yaro. Saida AbulRashid ya warke ragas har ya fara shirin komawa wajen aikinsa a Qatar sannan sukayi sallama shi da Nenne da ‘yar uwarsa Fatima, Taiwo ta tabbatar masa zata sameshi a Qatar in ta samu leave ta ga jikin nasa. Sun kwana hira shi da Nenne yau, zancen da baya so ko kankani a yi masa wato zancen aure itama tana avoiding dinsa yanzu, don bata son ganin yanayin tashin hankalin da yake fadawa a duk lokacin da tayi subutar bakin yi masa zancen aure. Su Nenne zasu koma Lagos a washegari, don lokacin tafiyar Nenne aikin Hajj na wannan shekarar ya kusa. Sun tashi zuwa Lagos da kwanaki biyu, shikuma ya tashi zuwa Qatar inda ya koma bakin aikinsa cikin koshin lafiya. **** **** **** FGC BILLIRI, GOMBE “ Yarbawa masu kwalo-kwalo, da Duwawu kuke tukin tuwo!!!”. Bisola ta kauda kai bata kula ta ba, ta ci gaba da tukin Teba da take yi da ludayin karfe a cikin robar cin abincinta mai fadi. Wannan duk bai ishi siririyar yarinyar ba mai siririn hanci da manyan idanu masu walainiya, hakoranta yiri-yiri farare kal kamar kankara, ta sake leka fuskar Bisola cikin matukar tsokana da iblisanci irin na ‘yammata ‘yan makarantar kwana da aka fi sani da teenagers. “Nace ko ba ku bane? Yarbawa masu kashi a kwano?!” Jikake kyal-kyal-kyal. Yaran dakin da duka ‘yammata ne masu tashen balaga wadanda a shekaru basu fice shekaru 15 zuwa 16 ba, in sun yi da yawa 17, dukkansu sun kara kyalkyalewa da dariyar shakiyanci da shegantaka (mockery). Karo na sau ba adadi da AISHATU-SIDDIQAH YUNUS tasa Bisola Akanbi kuka, sanadin wannan wakar da irin wannan cin zarafin da take mata a gaban sauran yara tsararrakinsu da suke kwana daki daya. Ko a aji ko a filin wasa ko a hostel kai har a masallaci in taga Bisola sai ta mata irin wannan tsokanar. Sauran daliban kuma, wadanda suke gang din Aisha duk sanda Aisha ta fara yima Bisola wannan wakar ta shakiyanci wadda take yi tana juya siririn kwankwasonta (irin dai na yadda yarbawa ke juya mazaunansu) wanda baya wani motsawa sabida sirantarta sai sun daddage sun barke da dariya. Ba Bisola ce take basu dariya ba, karewa ma tausayi take basu, sabida yadda Aisha ta matsa mata, ita Aishar ce take basu dariya yadda take daddagewa tana juya kwankwaso da ‘yan mazaunanta da sunan kwaikwayon tukin tuwo ko Tebar Yarbawa, alhalin kwankwason nata duka bai fi girman a hada tafin hannu biyu ba. Farin jininta a wurin tsararrakinta kuwa sabida kiriniyarta da kyawunta da kaifin bakinta, ga wauta da gwalangwaso abin ba’a magana. Bisola Akanbi kullum Aisha ta fara mata waka saita koma gefe cikin muzanta kamar mujiya a cikinsu, don yadda Aisha tasa ‘yan dakinsu suke nuna mata wariya da kyama wai don kasancewarta bayarabiya daya tal a hostel dinsu, cikin dalibai masu yawa hausawa da fulanin Gombe da suka fi yawa a FGC Billiri, wadda aka kawo daga jihar Ibadan, aikin asibitin federal government ne ya kawo iyayenta garin Gombe, har yayi sanadin da aka yi mata transfer zuwa FGC Billiri. Bisola Akanbi musulma ce gaba da baya. Yarinya mai hakuri da rashin sakewa da hausawa. Har ya zamnto daga zuwanta Billiri zuwa yanzu su Aisha da gang dinta su Amintako, Ramatu da Zannura suna neman jaza mata ciwon damuwa, sabida yadda Aisha ke nuna kamar itaba cikakkar mutum bace, ko kuma ba daya take da sauran dalibai ba, wai tunda ita bayarabiya ce. Kabilanci muraran a wurin Aisha abin ba’a cewa komai. Yau dai abinna Aishatu-Siddiqah Yunus, ya kai Bisola Akanbi bango, duk hakurinta Aisha ta kaita karshe, don ta sa an wareta daga cin abinci tare dasu a dakin, sabida itace gang leader ta dakin gabadaya, ‘yan dakin tun kan a kawo Bisola suna yin ciyayyar abinci a dakinsu. Da aka kawo Bisola daga baya suna ci har ita, yau Aisha tace idan har basu cire Bisola daga ciyayya ba ita zata daina ci tareda su, don ita bata son cin abincin yarbawa ko ci tare dasu, alhalin taji ana fadin suna kashi a kwano, don haka Bisola ita kadai aka zuba mata nata a plate, aka tura mata gefe wai don ita bayerabiya ce. A cewar Aisha Yunus, gang leader ta ‘yan aji hudu (SS 1) bazata ci abinci da Yarbawa masu cin dodon kodi da hannunsu ba. Wannan abu yaima Bisola ciwo. Kasancewar ta dade tana shaqa daga Aisha, ta yi hakuri mai yawa da Aisha, hakurin da ya hada da dan tsoro-tsoro, kasancewar Aisha nada wasu ilhamomi, watau kwarjininta da kyawunta da kaifin harshenta dake sawa aji ana shakkarta, sannan duk ‘yan gang dinta su Amintako halinsu daya da ita na tsokana da fin karfin wanda bashi da baki kamar Bisola. Amma yau? Dama aka ce mai hakuri bai iya fushi ba. Da kuka Bisola taje (staff room) ta gayawa Discipline Master duk abinda Aisha ke yi mata a hostel, a aji, a library, a wajen wasa ne dama duk inda ta ganta tun zuwanta FGC Billiri. “This is Mockery! Derision!” Inji Malamin cikin bacin rai. Discipline Master Uncle Sayyadi ya cika da mamaki, ransa kuma dana sauran malamai ya baci sosai, ace a makaranta ta gwamnatin tarayya (unity school) ta Najeriya ake irin wannan abin Allah wadai su malaman basu sani ba? Nan ya aika Head Girl Hasiya Mato, yace maza-maza ta kawo masa Aisha-Siddiqah Yunus ofishin malamai (dead or alive), sannan yace Bisola ta zauna a gefe, yau sai ya ga uban Aisha. Bisola ta koma gefen Teacher din tana sharar hawaye domin hakika Aisha Yunus, ta zame mata matsala cikin makarantar, ta dade tana cutar da feeling dinta. Head girl Hasiya din taje har dakinsu ta sako Aisha a gaba har ofishin malamai, duka malaman sun hada kai a ofishin suna tattauanawa akan al’amarin da Bisola ta kawo kara tana neman ayi mata iyaka da Siddiqah Yunus. Discipline Master yafi Bisola jin bacin rai, koda yace a kawo masa ita, kafin sui so ya shirbinawa dorinarsa man shanu sau uku kuma dama gashi lokacin san yi ne, yace a ransa yau zai ga karshen kabilancinta, zai gani idan ubanta ne ya wanzar da hausa bakwai da banza bakwai. Malaman kowa na tofa albarkacin bakinsa akan kabilancin ‘yan arewa ga ‘yan kabilar Yoruba, da yawa ana samun hakan, wanda ko kadan bashi da amfani musamman ga yara masu tasowa ana saka musu wani nagetive tunani daban a ransu akan kabilar Yarbawa. Kamar su din wata halitta ne daban da hausawa da Fulani. Ko Hausa/Fulani din sun fisu wata martaba ne. Aisha ta iso sumui-sumui da ita don tasan kiran Malam Sayyadi ba alheri bane, ganin Bisola a gefensa tana kuka yasa ta gane kwabarta tayi ruwa yau, wato yau Bisola ta kai kararta, ai kuwa nan da nan cikinta ya duri ruwa. Aisha da Bisola suka gurfana gaban Discipline Master, kan Aisha a sadde da ganinta kaga maras gaskiya. Discipline Master ya daka mata tsawa yace “maimaita tsokanar da kike mata kullum a kunnen mu muji, isashshiya diyar barbushe da tsimbirbira”. Aisha tayi narai-narai da sexy eyes dinta akan malamin bafillacen, wadannan idanun na Aisha masu kama da hawaye ne fal ya taru a cikinsu, shi kansa Discipline Master din sai da ya kauda kai sabida kwarjinin idanun Siddiqah, ya taba cewa wani Teacher dan uwansa mai suna Malam Tafida ya daina kallonta, Malam Tafida yace shima bai san meyasa yake yawan kallonta ba, Uncle Sayyadi yace da Malam Tafida cikin takaici, “yarinyar nan in ka cika kallon ta musamman wadannan maganadisun idanun nata alwala bazata zauna a jikinka ba”. Bai manta dariyar da malam Tafida yayi ta yi ba a ranar, to yau ma hakan ce ta kasance. Discipline Master da Aisha tayi masa narai-narai da ido cikin rokon ta tuba bai san sanda ya zabura don kwato kansa daga tasirin idanun Aishah ba, ya buga dorinarsa a kasa cikin barazana. “Zaki fada muji ko ba zaki fada kowa ya ji me kike yi mata ba?” Maimakon Aisha ta bada amsa sai ta soma tumami a kasa tana kuka tana shura kafafu. “Malam in ka dake ni Asma ta tashi zata yi, Malam ni asthmatic ce. Ummana kafin a kawo ni tace ayi mata alkawarin ko me zan yi za’a bani punishment, na aiki ko kneel down kowanne irine a bani, amma kar a taba mata lafiyar jiki na. Wallahi Malam nima a bakin yaran unguwarmu naji”. Discipline Master da sauran malamai duk suka saki baki da ido galala! Suna kallon Aisha-ikon Allah, irin kukan da take yi da tumami a kasa na shagwaba kamar karamar yarinya alhalin tayi 15, bayan ko dukan nata ma bai yi ba ya hanasu sake ce mata komai. Ta sake sakin kuka tana cewa Bisola ta mata sharri. Ai kuwa Disdipline Master ya fusata ya zuba mata dorinar a gadon bayanta guda daya, kafin ta farfado ya daddage ya sake zuba mata wata akan siraran kafafunta, yace “bari in saki kukan shagwaba da hujja, ko kinga Umman naki anan da zaki mana shagwabar banza da wofi? Tukunnama makarantar nan ta Babanki ce da zaki uzzurawa ‘yar mutane?” Aisha suma ne kawai bata yi ba, don bulalar ta shigeta yadda ya kamata, muryarta fal kuka tana mutsu-mutsu tace “Na tuba Uncle, na tuba nabi Allah na bi ka, na daina wallahi Uncle, daga yau bazan kara yi mata ba, kuma na daina cewa Yarbawa masu kwalo-kwalo ne”. Malam Sayyadi ya kara shimfida mata lafiyayya wadda tafi ta baya shiga tsokar jikinta, Aisha tayi flat a kasa wannan karon sabida yadda bulalar ta shigeta har wani dan karamin fitsari ta saki ta cikin uniform dinta. A wahale ta ce tayi “na maida kalamai na, Bisola ki yi hakuri, Yarbawa basa tukin tuwo da duwawu, Yarbawa basa kashi a kwano, ke ba bayerabiya bace mutum ce ‘yar najeriya kamar mu, na tuba na bi Allah na maida kalamai na Uncle”. Daga malaman dake gefe har Discipline Master din saida Aisha ta basu muguwar dariya amma suka hadiye don so suke sata a saiti. Suka rufu wajen yi mata fada da nasiha cewa abinda take yiwa Bisola ba daidai bane ko a addini, Bisola musulma ce kamarta, ‘yar kasa cikakka kamarta, abinda takeyi din kabilanci ne da wariyar launin fata. Sannan a matsayinmu na ‘yan Najeriya dole mu kaunaci juna, mu cire banbancin yare da na al’ada har ma dana addini inta kama, in har ana son a samun cigaba da hadin kai a tsakanin al’ummar Najeriya. Bisola ta dinga basu labarin irin uzzurawar da Aisha ta dade tana yi mata, ta ce komai tayi sai Aisha ta kushe, tana jin dadin kiranta “bayerabiya” a cikin yara ‘yan uwansu, kai sai ka rantse da Allah kiran bayerabe da Aisha ke yi cikin ‘mockery’ na nufin bayeraben mutum ba cikakken mutum bane wani abu ne daban, (kusan haka yake a idon Aisha-Siddiqah) a kabilancin data dade da sawa ranta akan Yarbawa. Ita a tunaninta Bayerabe wani kalar mutum ne daban wand bashi da katabus a cikin hausawa da Fulani, kamar wani alien take kallonsa. Ko kuma ka dauka wani ‘yanci bahaushe ko bafillacen mutum yafi bayarabe in dai a idon rigimammiya… ‘yar Ummanta, Aisha-Siddiqah Yunus ne. **** **** **** Labarin jinyar da AbdulRasheed yayi bayan fadowa a Doki ta kai kunnen Kakansa Emir of Ilorin, ai kuwa ya tubure sai an shirya masa tafiya har Qatar don gano jikin Kehinde. Inda su Turaki da Mutawalle da Shettima har ma da Waziri mahaifin Kehinde din suka taru suka ki amincewa da hawansa jirgi a yanzu, don a lokacin jikin girma ya fara motsawa ba lafiya ce ta isheshi ba, in ya sa rikici kan yana son yayi abu, su duka goman damuwa suke shiga saboda basa iyawa rikicin tsufansa. Daga baya suka yanke shawarar su kira Abdulrasheed din yazo kawai sai dai Kakan ya ganshi ba tare da an gaya masa zai zo ba. Turaki shi ya kira dan nasu Engnr. AbdulRasheed a waya, yace lallai yazo cikin satinnan Emir ya ganshi hankalinsa ya kwanta ko suma nasu ya kwanta da rikicinsa. Bai jima da komawa Qatar ba, yanada tarin ayyuka a gabansa amma kuma, baya hada lamarin Kakansa da komai, don haka Abdulrasheed ya ajiye komai dake gabansa ya shirya zuwa Ilorin a sati mai zuwa don ya ga Kakansa. **** **** **** Sarki Abdulrashid ya rika ina yaka-saka-ina-yaka-aje da jikansa mafi soyuwa a gareshi Prince AbdulRasheed (Kehinde) ta bakinsa, lokacin da ya sauka a Ilorin, tarba ta girma aka shirya ma babban jikan na Sarki Prince AbdulRasheed, kuma takwaransa. Basu samu kebewa ba shida Sarki sai da daddare kasancewar saukar safe yayi, ya gaya masa raunin da dokinsa mai tarihi wato SAHEEB yaji sosai sanadin tsautsayin da ya samesu shida dokin. Yanzu haka ya daina wasan Polo dashi sai sauran dawakansa. Sarki da karawa aya zaki wajen taya jikan nasa son Polo da duk abinda yake so nan take yayi alkawarin sayawa AbdulRasheed sabon yaron Doki (Criollo Horse), a karshe yace. “Baka hau doki ba kayi me jikana? Ride it with passion the great Prince of the Ilorin Emirate!!! Tsautsayi na Allah ne don ka fadi doki sai ace ka daina Polo kwata-kwata? To wa tsautsayi ya bari inace abu ne da baya wuce ranarsa? Rabu dasu takwara duk jinsu nake kawai ina biye musu don a zauna lafiya, amma ba mai hanaka yin abinda kake so kaji. Don duk sun hada baki wai na hanaka hawa Doki daga yau, fau-fau. Allah na tuba “Prince” din duk da bai hau doki ba ai bai cika “Prince” din ba”. Shiyasa fa AbdulRasheed ke matukar son Kakan nasa, yake kuma amsa kiransa a duk lokacin da ya bukaci ganinsa a ko’ina yake kuma kome yake komai muhimmancin abun zai bari yazo. Sabida a duniya ba mai son farin cikinsa irin Sarki. A daren ranar sunyi hirarraki iri-iri wadda ta shafi lafiyar Kakan nasa, da cigaban rayuwar AbdulRasheed kacokam. Wani abu da yasa Abdulrasheed yake sakewa da Kakansa yake kuma yin doguwar hira dashi saboda shi baya matsa masa akan maganar aure, kullum addu’a yake masa don ya yarda rashin auren AbdulRasheed har zuwa yanzu ba haka kawai bane, akwai dai abinda Allah ya boye a ciki, ko dai aljana ta aureshi, ko kuma akwai wani boyayyen dalili da kowa bai sani ba. Bayan sunyi sallama da Kakan kan zai je ya kwanta, kafin AbdulRasheed ya kai ga isa turakarsa dake gidan sarautar Ilorin, Kawunsa Turaki, wato mai bin mahaifinsa a haihuwa ya aiko ace dashi lallai suna son ganin shi su duka gobe (kannen mahaifinsa Akanni’s gabadayansu) kafin ya koma Qatar. Tun daga nan AbdulRasheed ya sha jinin jikinsa, cewa ganawa ce ta musamman iyayen nasa maza zasu hada a kansa, ayi masa taron dangi a titsiyeshi kuma ba’a kan komai ba sai akan maganar aure da baya ko son jin an alaqanta shi da ita. Ya so ya gudu cikin daren kafin wayewar garin, to ‘booking’ dinsa sai akayi rashin sa’a na jibi talata ne. Haka yayi ta kokarin canza ‘booking’ don dai ya samu ya kubucewa wannan haduwar wadda yasan bazata yi masa dadi ba, Akannis sun gama zura masa ido da bata yawun bakinsu akan maganar aurensa, duk yadda yayi kokarin barin Ilorin a daren don gujewa fushin iyayensa maza bai samu damar hakan ba. A washegari mahaifin Prince wato Engnr. Idrees Akanni da shima suka gayyato don ayi zaman tare dashi ya iso Ilorin, a ranar taron ya iso don ta jirgin sama ya taho daga Lagos. **** **** **** THE TEN AKANNIS’ S u goma dinnan, wato kannen mahaifinsa da mahaifin nasa haka suka saka shi a tsakiya yau suka zagayeshi a fadar Maimartaba Sarkin Ilorin, akan yau ba inda zaije sai ya gaya musu ‘exactly’ me ya hana shi aure a rayuwarsa? Duk kannensa na cikin family dinsu sunyi aure, ga albarkar ‘ya’ya, daga mai yara hudu sai mai biyar. Wannan masifa a cewar Akanni’s, sun kasa gane mata. Yo masifa mana?! Rashin aure babu dalili wanda addini ya yarda dashi ga mai shekaru sama da 40 ya zama masifa a cikin zuri’arsu. Suka hada baki wajen cewa “bazasu amince ya bata musu ‘image’ na gidansu da maluntarsu ba, don kawai ya ga Sarki yana daure masa gindi yana abinda yaga dama, ba don komai ba sai don yana gudun bacin ransa. Suka ce Sarki yafi kowa damuwa da son yayi aure ya dauki ’ya’yansa yana raye, kawai baya nuna masa ne don ya ga baya so, amma su sun sani, Sarki baida damuwa a halin yanzu sai ta rashin aurensa, suka taru akan cewa bazai kashe musu tsoho da damuwa ba dole ya bashi tattaba kunne ya dauka yana raye. Mutawalle Abdulfatahi ya ce “idan macece bai samu ba, su iyayensa maza zasu bashi ko guda nawa yakeso a cikin ‘ya’yansu mata matasa da basu kai ga yin aure ba. Idan kuma baya son auren gida, ya fadi duk diyar Sarkin da yake so a masarautun Najeriya, na kudu dana arewa, su kuma za suje su auro masa. In kuma lafiyar yin aure ce bashi da ita, itama yau dai sunaso su sani, zasu shiga ko’ina su fita daga nan har birnin Sin, su nema masa magani, su iyayensa ne da suka haifeshi, ya yarda cewa babu boye-boye yau a tsakaninsu. Tunda ya nuna Ubansa wato Waziri bai isa dashi ba, saboda Polo da abunda yake samu cikinta dake rudarsa, suka ce to Waziri Idreesu ya basu dama su yanke masa duk hukuncin da suka ga ya dace da shi yanzu. Su kuma a adalci irin nasu da Allah yace musu su yiwa ‘ya’yan su, bazasu yanke masa kowanne hukunci ba, sai sun bashi dama sun ji ta bakinsa tukunna, wato sai sun ji hujjarsa ta kin yin aure daga bakinsa. Alhalin mahaifinsa nada shekaru 25 mahaifiyarsa Sappa nada 15 aka yi musu aure, wanda albarkar hakan ne har suka sameshi cikin kuruciyarsu suka girma tare dashi. Shi yau Abdulrasheed shekaru 43 yake nema, me kuma ya rasa a rayuwarsa? The Akannis’ suka kara da cewa; wannan rashin auren nasa masifa ce babba a garesu da zuri’arsu. Suka kuma rufe zancen da cewa, “idan har bashi da hujjar kin yin aure, bashi kuma da wadda ta kwanta masa da yake ganin zai iya aure, gobe-goben nan zasu aura masa mata hudu, akai masa su gidan sa, kuma sun yi rantsuwa da Allah dole ya zauna dasu gabadaya in yana son albarkarsu, bijirewa wannan umarnin na nufin zasu cireshi cikin ‘ya’yansu tunda dai Allah yasa ba shikadai suka haifa ba. Shine babba cikin family duka, amma yafi duk kannensa basu wahala akan maganar aure da janyo musu magana daban-daban daga al’ummarsu duk akan rashin aurensa”. Prince AbdulRasheed Idris Akanni, tunda iyayensa suka fara wannan cece ku ce din yake sauraronsu, ya rasa irin amsar da zai bayar da zata gamsar da iyayensa maza hujjarsa ta gudun aure a yau. Cewa mata sun dade da sire masa, bashi da wani buri a kan diya mace yanzu, ba macen da zai kara so a rayuwarsa. Shin shi mai maganar cewa yazo ga kannensa nan a gida ya bashi wato, Abdulfatahi Akanni, yanada masaniyar cewa dansa ne ya raba shi da mata bakidayansu??? Ko yanada masaniyar cewa dansa Adetokumbo ne yayi masa cin amanar data sa ya tsani mata koda gold aka kerasu tun daga kan Hasinah Ambursa??? He is speechless a lokacin, sai zufa, jibi, da gumi da yake ta yankawa daga zaune cikin kurkukun idanun iyayensa da suke zazzare masa su daya bayan daya irin nasu na jiga-jigan yarbawa. Da suka takura da jin ta bakinsa sai yace musu yana jin nauyin dukkanninsu, su yi masa alfarma ya gayawa Nenne amsarsa in yaso ta gaya musu. Ganin irin halin da ya shiga ne na rudu mai yawa da gigita yasa suka kyaleshi, domin sun tado masa kwantaccen bacin ransa, aka yi addu’a aka rufe taron a haka. Suka ce lallai a gobe suna jiran jin amsa daga bakin Nennensa, in ba haka ba, zasu dauki matakin da ya dace ne kawai wanda shine aura masa kannensa mata hudu kuma a rana daya daga cikin ‘ya’yansu mata. Ita kanta Nenne din zille mata yayi ta yi basu hadu ba har ya koma Qatar. Ya san kuma bazata jira zuwansa ba don a ranar da asubah zata tashi zuwa pilgrimage (aikin hajji) daga hukumar alhazai ta jihar Lagos, kuma in ta tafi Hajj sai tayi kwanaki arba’in wato jirgin karshe sannan take dawowa gida. Kafinnan ya samu ya yanke mai fishsheshi, su kuwa kannen Ubansa yasa a ransa bazasu kara ganinshi nan kusa ba. Bayan tashin Nenne zuwa Hajj, ya koma Qatar, ya cigaba da fuskantar aikin sa na (Oil Refinery), wata irin rayuwa Prince Abdulrasheed keyi ta cikawa kai aiki a gida da ofis da daukewa kai kewa a ‘stable’ din dawakansa a kowanne yammaci ta hanyar bankawa cikinsa Nescafe (coffee) alhalin likita yayi limiting shan (coffee) dinsa, a cewarsa in ya sha yana jinsa fresh babu damuwa ko kankani a cikin ransa, shan coffee yana kara masa kuzari, kwana biyu dai bai hau Doki ba don har zuwa lokacin hadewar karayar jikin sa bata bar dan motsa masa lokaci zuwa lokaci ba. **** **** **** ZAMAN HEMAR ALHAZAI A MINNA N enne Sappa, ta sauka a kasar Saudiyyah domin sauke farali na wannan shekarar tare da diyarta autarta Princess Firdausi. A zaman Hema ne na kwana uku da ake yi a Minna, ana zuwa jifan shaidan ana dawowa Hema a huta ko ayi kwanan ibada, Nenne ta hadu da Haj. Zainab. Wadda tazo daga jihar Gombe, maigidanta Malam Yunus ma’aikacin hukumar alhazai na jihar Gombe. Ba Hemar su daya ba, don kamar yadda kowa ya sani ne Hema din (is state by state), Haj. Zainab na Hemar Alhazan Gombe, Nenne tana Hemar Alhazai Yarbawa na jihar Lagos. Wajen tafiya jifan Shaidan ne suka tafi tare, tafiya ce da alhazai ke yi mikakka wadda bata karewa kamar bata da karshe, zuwa inda za’a jefi la’anannen Allah. Suna tafiya suna Hailala, Princess Firdausi bata biyo su ba yau, tana kwance a Hema domin rashin tsarki da ya sameta a ranar. Jiki na girma, tafiya tayi tafiya sai Haj. Zainab taga Nenne na neman faduwa, domin ba karamin jigata tayi ba. Sai ta kama hannun Nenne, ta karfafeta, tace “baiwar Allah don Allah mu dan tsaya mu sha zam-zam ko ma samu karfin cigaba da tafiya.” Nenne tace “kin kyauta diyata, ni fitsari ma nake ji”. Suka sha zam-zam suka koshi, suka zagaya bayan wata Hema don shiga bayan gida. Nenne Sappa ita ta fara shiga ta fito ta gama zata wuce ba tareda ta jira Haj. Zainab ta shiga ba, don dama ba wai tare suke tafiyar ba a’ah, hanya ce kawai mai hadin zumuntar dole. Da ta fito, bayan sun yi sallama ta kuma gode mata bisa kulawar data nuna mata. Har ta gaya mata ita daga Lagos tazo, ita kuma tace mata daga Gombe tazo. “Ashe ‘yar kasata ce, madallah dake. Nima asalina ‘yar Gombe ne, aure ne ya kaini jihar Lagos”. Sukayi sallama, Nenne ta wuce ta cigaba da tafiyar ibadah, Haj. Zainab kuma ta shiga toilet din. Har ta gama abinda zatayi ta fito, ta lura da bakar jakar nan ta guzurin mahajjata ta matar can ‘yar Lagos rataye a jikin kofar bandakin. Wato ta manta guzurinta gabadaya. Ta dauka ta bude, yawan dalolin data gani ‘yan dari-dari a ciki ya firgitata, domin ya zarce normal dalolin guzurin mahajjata da ake basu, daloli ne tsura abin tsoro da firgitarwa, domin ita dai da idonta bata taba ganin irin wadannan takardun kudin a zahiri ba. Da sauri Haj. Zainab ta fito ta duba hagu da dama, gabas da yamma, kudu da arewa babu Hajiyar lagos babu alamarta, ta bace a cikin dubunnan mahajjata masu sanye da fararen kaya da bakake kusan bakidayansu, kalar kayan jikin maza fari, na mata baki ne tako kasa gane ko mai kama da ita. Haka ta daure jakar nan a cikin jikinta taje ta karasa jifanta ta dawo Hemarsu, tana ta addu’ar Allah Ubangiji ya hada fuskarta da Hajiyar Lagos kafin su gama zaman Minna su koma Makkah. Dadin abun ma ba’a sayen abinci a Minna, da bata san yaya Hajiyar zatayi ‘coping’ a wannan lokacin ba. Duk inda ta ga ‘yar Najeriya sai tayi kokarin ganin fuskarta, ko Allah yasa ta dace da ganin wannan kyakkyawar bafullatanar baiwar Allah, wadda haka kawai ta shiga ranta domin ta ga tsantsar mutunci da kamala a tareda ita. Washegari Haj. Zainab din tayi wani tunani, me zai hana taje Hemar alhazan Lagos ta duba ta a can? Sai ta kira maigidanta wanda tare sukazo kasancewarsa ma’aikacin hukumar alhazan jihar Gombe, sun samu kujerar Hajji ne ma sanadin aikin nasa ba karfine dasu cancan ba. Maigidan nata Malam Yunus, tsohon malamin (federal government) ne da ya jima yana koyarwa a makarantar sakandiren ‘yammata ta Bajoga, shekaru biyu baya Allah ya tarfawa garinsa nono aka dauke shi aiki a Gombe State Pilgrims Board (ma’aikatar alhazai ta jihar Gombe). Tun daga lokacin ne kuma suka samu damar da duk shekara yake samun kujerar hajji biyu, karkashin hukumar alhazai don su zo su kula da mahajjatan Gombe a Saudi. Shine yake baiwa maidakinnasa. Da kyar ta samo Hemar ‘yan Lagos, bayan ta ci tafiya da zagaye a cikin Minna har ta gode Allah. Haka Haj. Zainab tayi ta bin fuskokin mata Yarabawa daya bayan daya tana dubawa amma ko mai kama da wannan kyakkyawar dattijiyar bafullatanar bata gani ba, ita gashi ko sunanta bata sani ba balle ta tambaya, amma tabbas ta rike kamannin fuskarta da kyau. Ita gani take ma fuskar na mata yanayi da wata popular fuska data sani ko a hoto ne ko a zahiri, amma ta kasa gane inda ta san fuskar Hajiyar Lagos. (A rashin saninta, fuskar Haj. Sappa na mata yanayin kama ne data Sarkinsu na Gombe, wato Uban Kasar Gombe na wannan lokacin, wanda suke kamar an tsaga kara da Nenne Sappa, don shi ya sha nono ya saki ta kama. Allah bai tashi hada su ba sai ranar hawan Arfah a kan dutsen ARFAH. Bayan Haj. Zainab ta fidda ran ganin Nenne Sappa don damka mata dukiyarta. Har ta fara tunanin kaiwa hukumar kasar Najeriya ta Saudiyyah kudin tayi musu bayani. Haduwar tasu a filin Arfah ya zo ne indirectly ba tareda zaton kowaccensu ba. Addu’ar data ji matar bayanta ta daga hannu sama tana yi a fili ne ya ja hankalinta gareta. Hannayenta biyu matar ta daga cikin kaskantar da kai ga Ubangiji da tsananin ikhlasi da tawali’u cikin addu’arta, sannan cikin zubar da hawaye mai yawa a kan dutse mai alfarma na Arfah, ranar da Ubangiji yayi alkawarin baya juyar da addu’ar bayinsa akan wannan tsarkakakken dutse, taji matar tana yin addu’a ga haularta (abinda ta haifa) a fili cikin harshen fulatancin Gombe ziryan. “Ya Ubangiji ga Dana ABDURRASHEED dan IDRIS ABDURRASHEED (Kehinde), managarcin bawanka mai kyautatawa iyaye da kula dasu, mai tsantseni wajen ibadarka da kulawa ga ‘yan uwasa mata, mai yawan alheri ga danginsa da kyakkyawar zuciya ga kowa, mai tarin halayen kwarai na kyautata zumunci. Na roke Ka, Ka dubi halin da Kehinde yake ciki na rashin aure. Ya Ubangiji ka yanke masa, kasa yana da rabon yin aure a rayuwarsa, ka kare min shi daga duk wani nau’I na aikin sabon ka a dalilin rashin aure, Ya Allah”. Ta shafa addu’arta a daidai lokacin da take ji a zuciyarta Allah ya amsa mata, Mala’iku sun ce Ameen Abdurrasheed zai yi aure, kamar yadda Hajiya Zainab dake bayanta ma tace “Ameen” a fili, ta kuma tayata da shafa addu’ar itama zuwa tata fuskar cikin tausayawa, ganin yadda Nenne ke kuka tana addu’ar. Sai Nenne taji an dafa kafadarta a hankali ta baya, anyi mata sallama cikin nema mata amincin Ubangiji. Da far’a ta juya ta amsa tana share ido, kuma nan da nan suka gane juna. Suka rungume juna suka sauko daga kan dutsen Arfah tare rike da hannun juna. Hajiya Zainab ta kwanto lalitarta daga cikin jikinta, ta damkawa Nenne Jakarta hannu da hannu. “ga nan kudinki ne masu yawa da kika manta nake ta nemanki in baki. A bandakin da muka shiga a Munna kika mantasu, na nemeki kamar ba gobe, har Hemar ku ta ‘yan Lagos naje nemanki Allah baiyi haduwarmu ba, inata addu’a dai da rokon Allah ya hada mu cikin sauki in baki, don in aka shiga Makkah bansan halin da zaki fada wajen sayen abinci ba idan babu guzuri a tare dake, don kamar dukkan guzurinki yana cikin jakar nan.” Baki Nenne ta saki tana mamaki. Ta tuna zunzurutun dalolin dake cikin jakar. Sai ta kara rike hannun Haj. Zainab gam. Tare suka zauna akan kananun katifunnan na filin Arfah Haj. Sappa ta rasa da bakin da zata godewa wannan baiwar Allah. Abinda ya bata mamaki shine na farko da ganin matar ba wata wadata ce irin tasu a tareda ita ba, amma ta iya wannan halin na mutanen kwarai, mai wuyar samu a wannan zamanin. Dala na gugar dala da har dala dubu biyar ne a cikin battar, data kirga suna nan cif yadda ta lankwasasu ta ajiye a cikin zip ko guda daya bata yi ciwon kai ba. Ashe dama har yanzu akwai mutane masu wadatar zuci da gudun abun duniya irin haka? Nenne Sappa, ta tambayi kanta domin kwarai Haj. Zainab ta burgeta. Kudine da Abdulrasheed Kehinde ya bata domin tayi guzurin aikin Hajjinta dasu kamar yadda ya saba bata duk shekara. Da ta tabbatar ta yar da su taji babu dadi amma bata yi mamaki ba sabida irin gajiyar datayi da tafiya a lokacin a Munna, ji take kamar ta yanke kafafunta bakidaya ta yar, don suma sun mata nauyi da kyar take iya cirasu, balle jakar guzuri. Nenne da Hajiya Zainab basu rabu ba daga filin arfah ba sai da suka karbi adireshin junansu na hotel din da kowacce take zaune a cikin Makkah. Bayan sun koma Makkah Nenne ta soma tunanin me zata baiwa wannan matar a matsayin kyauta ta jinjinawa, sabida taji dadin wannan halin kwarai data gwada mata har fiye da kudin data maido mata. Nenne Sappa na matukar son mutum mai tsoron gamuwa da Allah, mai gudun duniya mai cin halal. Don haka da taje sayawa Princess Fatima warawaran zinaren data bata sautu a kasuwar Jiddah, sai ta sayi wasu warawaran (bracelet) again, sak irin na ‘yan biyunta Firdausi da Fatima wadanda kudinsu mai kima ne da daraja sosai. Data dawo daga Jiddah shagon zinaren kai tsaye ta wuce gidan ‘yan Gombe wato masaukin ‘yan jihar Gombe a Makkah. Da yake ta rike lambar dakin da haj. Zainab ta gaya mata, sai ta hau lifta (elevator) ta isa har kofar dakin, ta danna ‘door-bell’ daga ciki akayi mata iznin shiga sannan tasa kai ta shiga dakin da sallama abakinta. Nan ta tadda Haj. Zainab ita kadai a dakin dawowarta kenan daga Dawafi. Haj. Zainab tana ganinta nan da nan ta shaidata, ta kuwa shiga lale marhabin da hidima da ita da duk abinda take dashi a dakin na sakawa a baka, itace kawo Laban(Al-mara’i) itace kawo ‘Aseer’ wato jus mai sanyi. Kai har Gahwah data koyi sha a kasar ta hada mata wadda ake kira (Gahwah Al-Arabiyyah) ta zuba musu a kananan kofunan karau suka zauna a gefen gadon Haj. Zainab suna sha sai suka balle da hira. Ko daga yadda Nenne Sappa take magana kadai cikin yanayi na kasaita Haj. Zainab ta alakantata da Sarauta mai girma cikin zuciyarta, in kuma ba sarauta ba to da arzikin da ya zauna a muhallinsa, komai na jikinta kadai dake walwali cikin zobban zinare ya fallasa hakan. Sun dade suna hira kafin Nenne ta ce zata koma hotel dinta, don ta baro autarta Firdausi a daki kwance bata jin dadi tun dawowarsu Arfah a nasu Fundaq (hotel) din. Ta ciro warwaron data zo dasu a cikin battarsu ta damkawa Haj. Zainab a cikin hannunta. Ta ce kyauta ce tayi mata don su rinka tuna juna in su koma garuruwansu mabanbanta. Tana son mutane masu irin halinta na gaskiya da rikon amana. Sama da komai tsoron abin duniya. Haj Zainab ta ce “ba’a maida hannun kyauta baya, don hakata gode”. Kuma duk da bata san darajar wadannan warawaran ba, amma ko ba komai aka ce ido ba mudu ba ya san kima. Tayi godiya mai yawa sosai ga Nenne, tanakokarin gwada warawaran, cikin ‘yar dariyar jin dadin alkhairin da aka yi mata Haj. Zainab tace da Nenne. “Yo ni wannan ai bazasu shiga hannu na ba, sun min kankanta na yara ne, sai dai in kaiwa PETEL (AISHAH-SIDDIQAH), yafi kama da na ‘yan mata”. Nenne ta ce “har nawa kike da bazakiyi kwalliya da awarwaro ba?” Nan ta daga nata hannun tana nuna mata nata warwaron guda shidda tace “bana rabo dasu a hannayena don su din adon diya mace ne. suna karawa kwalliyar mace kima su da zobuna, wacece Petel-Aisha-Siddiqah kuma? Halan kinada ‘ya budurwa ne kema kamar su Fatima? ‘Yan biyuna (Firdausi da Fatima) na sayawa, shine kema nayi miki sha’awarsu”. Cike da far’a Haj. Zainab tace “eh, inada Petel-Siddiqah a gida, itama ‘yan biyu ce, su biyu aka haifa tun lokacin Hassanar ta rasu a wurin haihuwa, ita kadai ta saura mana. Allah ya dora min iftila’in WABI, domin kuwa haihuwata goma amma AISHA-SIDDIQAH ce kadai Allah ya bar mana a raye”. “Allahu akbar!” Inji Nenne, “lallai dole ki so AISHAH-SIDDIQAH. Har nima yanzu zan tayaki son nata, naji a raina ina son SIDDIQAH. Ajinta nawa yanzun?” Murmushi sosai Haj. Zainab tayi tace “Petel na ajinta na biyar a makarantar gwamnatin tarayya ta Billiri Gombe”. Sun dade a bakin kofar suna hirar Aishah, kafin Nenne ta karbi lambar wayar Haj. Zainab ta gida Najeriya, da alkawarin duk ranar da Allah yayi mata shigowa Gombe (kasancewar tana yin shekaru kusan biyu bata zo ganin gida ba), zata nemi Haj. Zainab har unguwarsu su gaisa. Kafin dan lokaci kakkarfan kawance ya kullu tsakanin matan biyu a aikin Hajjin bana. Sati daya bayan nan Alhazai suka soma shirin komawa gida. Ranar Asabar Nenne da Princess Firdausi suka koma gida Lagos. Yayinda Haj. Zainab jirgin kusan karshe suka bi suka koma gida Gombe don saida aka gama kwashe ‘yan jihar su kaf. **** **** **** Tunda Haj Zainab ta koma Gombe Kusan kullum sai ta baiwa Maigidanta Mal. Yunus labarin kawarta mai karamci Hajiya Sappa ta Lagos da suka hadu a Minnah, kawar da tayiwa Petel dinta kyautar warawaran zinare ta yaya zata manta ta? In ana haddace labarin mutanen kirki Malam Yunus ya dade da haddace wannan labarin na Haj. Sappa daga bakin matarsa. Shima kuma ya yaba da kirkin nata duk da bai ganta ba. Domin ya san matarsa sarai shishshigi gun masu kudi ko dukiya ba halinta bane, sannan ya shaideta kan ita din ba mai kwadayi bace, kuma mai wadatar zuci ce. Allah – Allah take Aisha-Siddiqah wadda take kira (Petel) dinta tazo hutu, ta gwada mata warawarannan da suka fito daga hannun Haj. Sappah, Baban Petel ya tabbatar mata na danyen farin zinare ne (white gold) kirar kasar Saudiyyah. Ta san Patel da son warwaro, kusan kullum baka raba hannunta da awarwaro, kamar wata ba’indiya haka zata yi ta rawa ita kadai tana juyasu tana kadasu idan tana cikin farin cikin wani abu, an sha ‘seezing’ dinsu a makaranta amma hakan bazai hana gobe ta sake rokon Ummanta ta sai mata wasu ta sake sakawa ba. Ranar hutun 'yan makaranta Aisha - Siddiqa Yunus, siririyar budurwa ‘yar shekaru goma sha shidda, Aisha mai sassanyan kyau, ma’abociyar yalwar suma (gargasa) a gira da saman idonta, wadda kaurinsu ya fallasa adadin yawan wadda zaka tarar a gashin kanta, da tsakar rana ta dawo gidan su daga Billiri. Motar haya ta biyo yadda ta saba ta dawo gida, ba tareda anje daukota ba. Data shigo dakin ta wata irin mika Aisha tayi ta gajiya da farin cikin dawawo gida, tana fadin "Oh no place like home!". Sannan ta ajiye jakar goyonta da bacconta ta fada wanka. Bata samu Ummanta a gida ba ta shiga makwabta gidansu Umman Abdul dubiya, don haka Aisha take ta kissima kome da me Ummanta ta sayo mata daga Saudiyyah a hajjin bana? Ta san dai tsarabarta tafi ta kowa yawa a wurin Umma. Allah dai yasa bata manta da sakonninta na Abaya da dogayen riguna ba. Umman Siddiqah (yadda ake kiranta a unguwar su ta Jeka da Fari) ta dawo gida gefen la’asar daga dubiyar data shiga a makwabtansu, ta tadda Aisha-Siddiqah ta fito daga wanka kenan har ta saka kayan sallahrta koren jilbaab ta tada sallah. Don haka ta wuce ta hada mata abinci, sannan ta koma dakinta ta janyo jakar tsarabarta ta soma fidda tsarabar Aisha din a gefe. Musamman (bracelet) din wajen Nenne, ta san sai Aisha tafi murna da shi fiye da duk tarkacen abayoyin data kwaso mata. Aisha na idar da sallah ta ma kasa tsayawa ta shafa addu’a tsabar dokin ganin Umma, sai ta wuce dakin Umma da gudu ta fada jikinta cike da farin cikin dawowarta lafiya, rabon ta da Umma yau wata uku kwarara tun komawarta hutun farkon zango. Lokacin visiting dinsu duk tana Saudiyyah. Umma ta rungume ta itama tana dariya tana fadin. “Petel am miyelwi ma (Petel dina nayi kewarki)”. Bada bata lokaci ba ta shiga fiddo warawaran na na wajen Haj. Sappa, guda shidda rus ta shiga zurasu a hannun Aishah daya bayan daya. Kasancewar Petel ‘yar karama mai karamin jiki kuma ‘yar siririya, komai na halittar Siddiqah karami ne, hanci ido da baki, sai suka shige hannun nata sukuf babu gargada, kuma basa zamewa sun zauna cif-cif kamar saida ta gwadasu tun farko. Rashin kumari irin na Petel yana matukar damun mahaifiyarta, don sam bata da jiki kuma bata da kauri hakanan bata da cika ido, wasu lokutan Aisha bata da kuzari idan Asma dinta ya motsa. Tana da Asma kadan (Mild Asthma), a gida ne ko a makaranta koyaushe baka rabata da inhaler a tare da ita. Bakin Aisha ya fadada har kunne, don murna, warawaran sun burgeta wadanda bata san ina Ummanta ta samo su ba, ta san dai Umma ko tana da kudin sayensu bazata saye su haka kawai ba, Petel (Siddiqah) ta kasa boye mamakinta da farin cikinta, don ta san ko guzurin Ummanta gabadaya aka hada bazai sayi bracelet dinnan ba, in dai na danyen zinare ne kamar yadda suke zagin idonta. (Bayeraben mutum nada son ajiye kadarar zinare, don haka shine kadara abin ajiyewa a wurin Nenne Sappa da ‘ya’yan ta mata, Taiwo, Firdaus da Fatima). Aisha-Siddiqah tace da Umma cikin mamaki “Umma ina kika samo awarwaro mai kyau da tsada haka?” Nan Umma kamar jira take don har zuwa lokacin shaukin haduwarta da Hajiya Sappa da karamcinta na makale a ranta, kullum da tunanin sake haduwa da ita take kwana take tashi, nan ta kwashe labarin haduwarsu da Haj. Sappa a filin Muna ta labartawa Aisha, yadda ta tsinci jakar kudinta da yadda ta maida mata, irin amincin da ya shiga tsakanin su sanadin hakan. Ta ce ta dai lura matar Basarakiya ce ko matar Basarake. Sannan kuma bafullatanar Gombe ce itama. Aisha ta koyi wasu abubuwa guda biyu cikin labarinnan da Ummanta ta gama bata yanzu, wato “gaskiya da amana su ke sawa a so mutum!” tace a ranta “na shaida Ummana mai gaskiyace, amana da rashin kwadayi halin Umma na ne, nima daga yau zan koye su don kowa ya so ni. A karshe hirarsu Aisha ta yarda idan ka rike gaskiya, amana da rashin kwadayi suka zama symbol dinka watarana zasu samo maka abinda baka taba zaton samu a rayuwarka ba, da kauna da amincewar mutanen da kake zagaye dasu”. A yinin ranar bakidaya har dare labarin da suke yi kenan itada Umma wato na Hajiyar Lagos, tsakanin Aisha da Ummanta aka rasa wanda yafi wani dokin son sake haduwa da Nenne Sappa, Aisha ta ji itama tana son matar har cikin ranta duk da kuwa labarin kirkinta kawai Umma ta bata. Kwanan Aisha-Siddiqah uku da dawowa hutu Asthma dinta ya tashi haikan, tun asali (she’s asthmatic) wato mai fama da ciwon Asthma ce (mild asthma) da sai ta dade bata motsa ba. Wannan karon tashin da yayi yafi karfin a kwantar dashi da (inhaler) dinta don a karshe har sai da ta kai su ga kwanciya hajaran majaran a babban asibitin Gombe wato (FMC Gombe) ake ta treating Aisha. **** **** **** Maimartaba Uban Kasar Gombe wato Yayan Nenne (Sarkin Gombe na lokacin) ya aika mata sammacin kira yana son ganawa da ita a gida Gombe, ido da ido, ba maganar waya bace. A ganin Uban kasa har da daurin gindinta a rashin auren da Prince Abdulrasheed ya ki yi har shekarun kuruciya suka fice masa, domin in tayi masa umarni a matsayin ta na uwa in har yana son albarka dole yayi ko yana so ko baya so. Ya gaji da maganganu akan Abdulrasheed, ko’ina ka shiga sunan Abdulrasheed Idrees Akanni ne a bakin samari ‘yan bana bakwai a kasar Najeriya, har wani lakabi suke binsa da shi “The Latest Yoruba Demon (Prince). Ita kuwa Nenne ta fannin ta Allah ya gani bata san ya zata yi da Abdulrasheed ba kuma, tunda har hawayenta ta zubar masa, hakan kuma bai sa ya amsa cewa ya yarda zai yi aure ba. Iyayensa maza ma sunyi iya bakin kokarinsu duk a banza, bai amsa musu da komaiba har gobe, bazata dorawa kanta ciwon da baida magani ba akan abinda bata da maganinsa. Duk da cewa tafi kowa damuwa da al’amarin idan ta tuna yawan shekarun Abdulrasheed na yanzu. Watakila baida rabon auren ne a gidan duniya, in haka ne tana masa fatan samun masu albarka a lahira, ba kowa ke samun rabon aure a rayuwarsa ba, ta yarda da danta dari bisa dari ba lalata ce ta hana shi aure ba. amma mafarkin data ke ta yi a ‘yan kwanakinnan fa? Don haka Nenne ta taho Gombe ranar wata Lahadi da nufin zata yi kwana uku a gida, ta ga ‘yan uwa da dangi ta kuma gana da dan uwanta Uban kasa da ya kira ta officially, don ta jima rabonta da Gombe, ko bai kirata ba tayi niyyar zuwa a wannan watan. Nenne na shigowa garin Gombe tana kwance a bayan mota ‘Ford’ direba na sharara gudu da ita, babu wanda ya fado mata a rai sai kawarta ta filin Arfah da Filin Munnah wato Haj. Zainab Yunus. Don haka ta yunkura tun a cikin motar kafin su isa fadar Gombe, ta dubi direban Uban Kasa daya daukota dake ta aikin sa na tuki tace “tsaya a gefen titi!”, sannan ta ciro wayarta a jaka ta kira layin Haj. Zainab da tayi saving da (Zaynaba mai gaskiya). Haj. Zainab na dagawa da sallama taji muryar Haj. Sappan Lagos kamar a mafarki, tana fadin “Zaynaba gani a Gombe, maza turomin adireshin ki, in fara tsayawa wajenku yanzu in ga Aisha-Siddiqah kafin na isa cikin gida in kasa samun lokacin sake fitowa kuma”. Ta kara da cewa “ina fatan na sameku lafiya cikin alkhairi keda malam Yunus da diyata Petel Siddiqah?”. Haj. Zainab cikin ‘yar damuwa take amma kuma taji dadin ji daga Nenne Sappa ta ce “barka da zuwa Haj. Sappa, Jabbama-jabbama da Hajiyar Lagos maraba da isowa gida jewel in the savannah (Gombe kenan) inji ‘yan boko” duk suka yi dariya. “Sai dai kash! Bama gida, kin ganmu nan a FMC tareda Petel din babu lafiya, asthma dinta ya tashi, tashin da ya jima bai yi irin sa ba. Ina cikin damuwa da asmar nan tata Haj. Sappa domin Siddiqah itace ‘ya ta goma sha daya dana samu a duniya kafin Allah ya bar min, ban sani ba ko itama a shekarun girma Allah bazai bar min ita ba”. “Ashsha Zaynaba, daina fadin haka, da yardarm Allah Petel zata ji sauki, kada ki girgiza imaninki akan ciwon ’ya’ya, ciwo ba mutuwa bane kin ji? Diyata Firdausi ma tana da (brittle asthma) haka muke ta fama. Allah zai bata lafiya da yardarSa”. “Nagode da karfafawa Hajiya Sappa kuma ma dai yau din alhamdulillahi tana warwarewa ba kamar jiya ba, don har ta karbi shayi ta sha sosai”. Nenne ta ce “to bari kawai in karaso asibitin in sameku can, ai bani ita zakiyi in tafi da ita Lagos kawai ko na sati biyu ne taga likitan Firdausi, tunda an yi hutun makaranta, Dr. Femi ya kware sosai akan treating asthma”. Umman Siddiqah ta kwatanta mata inda zata same su a female ward. Tana fadi aranta “ba inda zata iya bari Petel taje inba cikin dakinta ba, in ka san soyayya ta rabin rai ta Aisha-Siddiqah da Ummanta ne”. Mintuna ashirin ta kawo su har kofar dakin da Aisha Siddiqah take kwance, sai Nenne ta kira Haj. Zainab ta sanar da ita suna bakin kofa. Hajiya Zainab ta fito ta yiwa Nenne jagora zuwa cikin dakin har gaban gadon Aisha-Siddiqah. Wanda daki ne na mutum daya (sideroom) a sashen kwanciya na bangaren mata. Nenne ta sa kai a dakin bakita dauke da sallama. Kallo daya Nenne Sappah ta yiwa “AISHA-SIDDIQAH YUNUS” dake kishingide a gadon marassa lafiya da karin ruwa a hannun ta taji wani bakon yanayi a tare da ita. Idanun Nenne basu sauka a ko’ina ba sai akan warawaran zinaren dake hannun ta wadanda suka kawata halittar fatar hannunta fara sol. Ga yarinyar ‘yar karama da ita (mai karamin ruwa) wato irin amsu karamin jikin nan ce siririya sosai kamar in ta sunkuya karyewa zata yi. Idanunta kamar na kwan zabo, masu haske da kyau. Nenne tayi birki a gaban gadon Siddiqah ta kama hannunta mara allurar a jiki tana kallonta da murmushi, Siddiqah wadda ke kishingide akan filo, rike da dan littafin addu’o’I na hisnul muslim a hannunta ta daga fararen idanunta a hankali tana kallon Nenne Sappa. Umma bata lura da yanayin kallon kaunar uwa da Haj. Sappa ta fada akan Siddiqah ba, tana ta faman lale-maraba da Hajiyar Lagos, (jabbama-jabbama), ta bata farar kujerar roba ta ‘yan dubiya don ta zauna amma ina! Hankalin Nenne Sappa ya tafi ga wani tunani daban. Ya bar jikin ta gabadaya. Domin dai yau ji take a jikin ta ga uwar jikokin ta, wato ga matar Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni, yau Allah ya nuna mata da sauran numfashinta, wadda ta dade tana ganin surarta a cikin mafarki duk ranar data yi istikhara akan sha’anin auren Prince Kehinde. Ta dade, ta jima tana ganin wannan kyakkyawar fuskar a cikin barcin ta, bata taba sanin alaqar yarinyar da mafarkan istikhararta ba. Taji a ranta bata iya barin Gombe ba tareda Aisha-Siddiqah ba. Lokacin da Aisha-Siddiqah ta bude baki tana gaida Nenne da sassanyar muryarta ta mai jinya Nenne kasa amasawa tayi, domin Aisha da komai nata ya shiga ran Nenne farat daya (daga gani na farko). Ji tayi kamar ta sace ta kawai ta gudu da ita Ikko, in yaso ta aurawa Prince Abdulrasheed Kehinde. Ta san dai ko zaiki kowacce mace banda wannan kyakkyawar halittar dake gabanta. Da kyar ta iya amsa gaisuwar Siddiqah da wani kyakkyawan (maternal feeling) akan fuskarta. Kafin su zauna su bude babin hirar Saudiyyah tsakanin Hajiyar Lagos da kawarta Hajiya Zainab irinta wadanda suka aminta da juna, tabbas kawancensu hadin Allah ne kawai, domin ajin rayuwarsu ko kusa ba daya bane. Allah shi yake hada mutum da mutum su kaunaci juna saboda Allah. Nenne tace da Haj. Zainab ta nema mata iznin Baban Aisha tana so ta tafi da ita Lagos taga likitansu Firdausi, kwararre ne sosai akan lalurar huhu da numfashi, wanda shi yake duba Princess Firdausi (itama asthmatic ce), daga nan tana so Aisha ta karasa hutun wannan zangon a hannun ta. Hajiya Zainab tayi dan jimmm! Kafin tace “Babanta yana wajen aikinsa amma na san ba zai ki baki Petel ba, don ba tun yau yake da labarinki ba, zan masa bayani idan ya dawo kafin ki gama abinda ya kawo ki Gombe, kwarai nice dai zanyi kewarta, don bama raba gari tun haihuwarta sai da ta fara makaranta a Billiri. Akwai yaron da ke rikon neman aurenta Ishaqa dan makwabtanmu, yana jami’a a Ibadan, yanada da hakki shima a sanar dashi kafin ku tafi din”. Nenne tace cikin jin faduwar gaban ta sameta a take “an yi musu baiko ne?” Kafin Haj. Zainab ta bata amsa Nenne ta kira sunan Allah sau ba adadi tana neman daukinsa akan Allah yasa Aisha rabon su ce. Wani ikon Allah sai Haj. Zaina tace “A’ah tukunna, Ishaqa dalibi ne a jami’a, mahaifinsa yace sai ya kammala ya fara aiki koda zai masa aure, suna dai matukar kaunar juna shi da Petel kowa ya sani, sabida shi Aisha bata sauraron kowa. Gida biyu ne a tsakanin mu dasu, tare suka taso tun suna kanana soyayyar ba ta yau bace, kuma dai Ishaq yana da hankali da nasaba mai kyau, ya dade yana hidima da ita don haka dukkanmu mun yi na’am da shi tuntuni sai fatan Allah ya nuna mana lokacin”. Aisha na jin su, kunya kamar tayi yaya! Sai ‘yan mutsu-mutsu take kamar tace kasar ta tsage ta shige. A karshe Haj. Zainab da Haj. Sappa sunyi sallama kan sai jibi zata zo ta gana da Baban Aisha, in ya amince ta wuce da ita Lagos ganin kwararren likitan numfashi da huhu. Da Nenne zata tafi ne ta matsa gaban gadon Siddiqah. Tana murmushi tasa hannu ta shafa gashin kanta cike da damuwar ganin yadda take ta kokawa da inhaler ita kadai, tace “get well soon my dear, Allah ya baki lafiya kinji ko Siddiqah? Sai na dawo”. Har bakin mota Haj. Zainab ta raka Nenne. Suka sake kafa sabuwar hira kafin suyi sallama da kyar. Nenne Sappa ta samu dan uwanta Uban kasar Gombe da iyalinsa lafiya, suka sha hirar zumunci irin wadda suka dade basu sha ba. Kafin ya gaya mata maqasudin abinda yasa shi kiran da yayi mata, wanda dama ta tsammace shi tun ma kafin ta ji shi. Maganar dai guda day ace. Gabadaya danginta da iyayenta da dangin mahaifinsa da nasa mahaifin basu da damuwa yanzu sai ta auren Prince. “Ki turo AbdulRasheed ya zo ya ga ‘yar uwarsa Naziha, malaman fada sun gayamin idan har ba auren muka yi masa da kanmu ba, a haka zai kare rayuwarsa bazai taba kawo mace yace yana so ba don sunce aljana ta aure shi. Sannan ance dani akwai aguminsu na maketan Yarbawa makiya Kakansa, akwai kuma sihiri irinna magauta gidansu duk a jikin sa, bazai taba ganin mace yace yana so ya aura ba”. Nenne tayi ajiyar zuciya cikin damuwa, bata son irin wannan false beliefs din ita sam, gasgata malaman tsubbu da Yayanta Uban kasa ke yi a rayuwarsa yana damunta, ita tafi yarda da cewa auren Abdulrasheed LOKACI ne bai yi ba, kuma koda yayi din, duk da za’a kira shi ‘LATE MARRIAGE’ tofa ba zai wanke masa tarihin cewa ya jima bai yi aure ba, don haka ba kowacce mace zata yarda ya aura ba musamman cikin ‘ya’yan ‘yan uwa don kada abata zumunci in ya jingine musu ‘ya’ya saboda Polo. Ta rasa abinda zata ce da Uban kasa, a karshe ta samu bakinta yana bashi hakuri, tana fadin ta yi wa AbdulRasheed mata, kuma anan Gombe, sannan cikakkar bafullatana diyar dattijai. In sha Allahu data koma Lagos zata gabatar da maganar ga mahaifinsa. Uban kasa bai ce a’a ba, duk da yafi matukar son Abdulrasheed yayi aure a cikin gidansa, saidai ya nemi jin su waye iyayen yarinyar data ke ikirarin ta samar masa ta kuma fada masa, yace zai yi bincike akan Malam Yunus din da sana’arsa da gaggawa. Ba’a kwana ba, ba’a yini ba saida komai na Malam Yunus ma’aikacin hukumar Alhazai tsohon malamin federal government na jihar Gombe ya zo kunnen Uban kasa har asalinsa, duk wata shaidar arziki da kyakkyawar nasaba malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Hamza sun gama samun ta a unguwarsu Jeka da fari. Sunyi waya da Haj. Zainab a ranar da zata wuce Lagos bayan an sallamesu daga FMC cewa tana tafe a hanya zuwa gidan Malam Yunus. Yau ko fita Abba bai yi ba, yana jiran zuwan Haj. Zainab. Bakuwar da matarsa take ambata da alkhairi kamar tafi kowa kirki da darajta dan adam a duniya. Nenne ta iso wajejen karfe goma na safe don taredasu ma ta karya kumallo da kunun gyada da kosai mai zafi a falon Haj. Zainab. Aisha na daki tana ta kumburi, Ummah tace wai zata bi kawarta Lagos tayi hutu kuma taga likita. Tunda Aisha take a duniya bata taba barin garin Gombe ba, kai ko Azare bata taba shiga ba banda Billiri makaranta, balle akai ga kwana da wani wuri da ba makaranta ko dakin ta ko na Ummanta ba. Aisha akwai makon UWA, irin yaran nan ne da gasu dai sun girma, amma kamar yaran goye suke agaban iyayensu mata, ko kusa bata son gusawa daga jikin Ummanta. Amma yanzu maganar zata je tayi sati biyu a Lagos ake yi. Tun jiya da taki hada kayanta Umma da kanta ta hada mata. Tana ta lallashin ta da cewa Haj. Zainab bazata roki alfarma ta kasa yi mata ba. Kuma dai lafiyarta ake son ingantawa. Budar bakin Aisha sai cewa tayi (cikin alamu na karyewar zuciya da damuwar cewa yau Umma tace zata tafi wani gari ta kwana ba tare da ita ba). “Amma dai Umma kinsan ba yau na fara ciwona ba ko, wane irin likita ne ban gani ba? Kuma Umma kin dai san Asthma bata da wani magani bayan inhaler ta da wadanda nake sha yanzu ko?” Umma ta girgiza kai itama ranta a dame da damuwar Aisha tace “babu ciwon da bashi da magani sai tsufa sai mutuwa kinji ko Petel, shi magani dace ne, shin Siddiqah in baki koyi shiga mutane yanzu ba sai yaushe ne? Ko wajen yan uwana ko na Abban ki ba kya yarda ki je ki kwana, kada ki manta watarana aure ne zai raba mu gabadaya”. Ai kuwa Aisha ta balle da kuka tana fadin “Umma in kika sake cewa zamu rabu in nayi aure to bazan yi auren ba har abada”. Umma na dariya tace “to ai Ishaq din bazai yarda ya daukemu mu biyu ba, mun yi yawa a gidan Ishaqa”. Aisha ta hau rantsuwa, kan cewa sun dade suna kulla alkawari itada Ishaq cewa in yayi kudi ya tashi ginin gida zai ginawa Umma daki a gidan sa, in ba haka ba bazata yi auren ba”. Umma abin ya bata dariya sosai, da yake lallabata take don ta yarda ta bi Hajiya Sappa sai tace toh ya isa haka ta ji, ta kuma amince ita din itace ‘yar zaman dakin Petel (Siddiqah)”. Suna daki suna dambarwa ita da Aishah Haj. Zainab na can gaban Malam Yunus a falonsa tana gabatar masa da uzurinta na nemawa tilon dan ta wanda a cewarta ya manyanta auren Aisha-Siddiqah daga mahaifin ta Malam Yunusa Hamza. Tace masa in ya amince da ta koma Lagos zata sanar da mahaifin Abdulrasheed, cewa tayi masa matar aure a Gombe, ba jimawa iyayen Abdulrasheed maza zasu zo da komai na dukiyar aure, basa bukatar komai, amarya kawai za’a basu su dauka. Malam Yunus ya hau zufa nan take, sabida kwarjinin da Nenne Sappa tayi masa sai ya kasa cewa kai tsaye bazai bayar ba, yasa habar taguwarsa yana share zufa daga goshin sa daya tuno irin soyayya da shaquwar dake tsakanin Ishaq da Aisha, ya kauda idonsa daga kwarjinin Nenne yana fadin “akwai wanda ke neman aurenta tun tana kankanuwa, amma ban tari hanzarin ki ba inna tambayi cewa shi Abdulrasheed dinne ya ga Aisha yace yana so? Ko kuwa shi Abdulrasheed ne yace a nemo masa matar aure? Ke kuma hakannan kika ga dacewar zaba masa Aisha-Siddiqarmu? Nenne Sappa ta saka habar mayafinta tana share hawayen da suka kawo mata a idon ta, ta kwashe labarin su kaf ta baiwa Malam Yunus, da yawan shekarun AbdulRasheed a duniya amma bai taba aure ba. A karshe ta gaya masa halin tsangwamar da take fuskanta daga dangin mijinta akan rashin auren Prince, kowa ya bude baki laifinta yake gani, sabida mijinta baya son laifinta, da yadda take raba dare bata barci saboda damuwa da addu’ar Allah ya yanke masa, in yana da rabon aure a rayuwarsa Allah ya nuna mata, don ita bata yarda da wai aljana ta aure shi ba, tafi yarda in za’a ce yawan sabgogin Polo da ya saka a gabansa ne suka cire masa tunani da sha’awar aure kwatakwata. Har mafarkin fuskar Petel data sha yi sai da ta gaya masa a duk ranar data yi istikhara, Malam Yunus ya tausaya ma damuwar da Nenne ke ciki akan dan nata, ya kuma dan tsorata duk da bai gaya mata ba, shima fa yanata mafarkin mutum akan doki a ‘yan kwanakinnan, gashi tace dan nata mai hawa Doki ne. Nenne Sappa ta katse masa tunani da cewa, “na yarda Ubangiji ya aiko ni Gombe ne wannan karon don lokacin da nake ta addu’ar zuwan sa ya zo ga AbdulRasheed, kada ka juyawa wannan alkhairin da nake nufin mu kulla nida ku baya. Ka yiwa Allah malam Yunus mu taru mu taimaki juna ta hanyar kulla aure mai albarka tsakanin ‘ya’yanmu. Wanda zai mikar da zumunci na daku har illa ma sha Allahu. Na amince daku dari bisa dari ba tun yau ba, haka na amince da Siddiqah ce kadai zata zama surukata a cikin duk matan dake garinnan, da wadanda ke garinsu mijina (Ilorin) dama kasar Najeriya gabadaya Siddiqah nake fata da addu’ar ta zame min suruka. Malam Yunus ya nisa, duk da yayi na’am da komai da Haj. Sappa ke furtawa amma yace tayi hakuri, ba zai yi gaggawar amsawa ba sai yayi shawara da na gaba da shi, kuma sai ya san hakikanin abinda ya hana Abdulrasheed yin aure har zuwa wannan lokacin sannan zai yarda ya bashi Aisha, shima kuma sai idan Ishaq bai tashi aure yanzu ba. Yace ya gaji da yawan maneman auren Aisha, kullum masu zuwa yau daban dana gobe, yace gara ya aurar da ita haka ya huta, kowa ya huta, dama bai mata alkawarin samun ilmin gaba da sakandire ba. Amma shi baya ra’ayin karatun boko mai zurfi sam a gareta. Burinsa shine tayi aure da wuri ta haifa masa jikokin da zai kalla a matsayin ‘ya’yan da shi Allah bai yi nasa sun zauna a raye ba, don mahaifiyarta ma iyakacin ta firamare ya aure ta. A karshe yace ya ji bukatar ta na son tafiya da Aisha taga likitan Asthma, sai kuma yace bai yarda ta zauna a Lagos har sai hutu ya kare ba, saboda tana zuwa Tahfiz yin haddar Al’qur’ani a kowanne hutu anan kusa dasu a unguwar Dawaki, da ta gama ganin likitan don Allah a dawo da ita gida ta karasa hutunta tare da su don suma sun jima basa tare da ita tun tafiyarsu aikin Hajji. Nenne Sappa tayi ta mamakin wannan soyayya ta iyayen Aisha ga diyarsu Aisha, ta dauka Haj. Zainab ce kawai ke mummuken Siddiqah ahe har baban nata, ta amince da yadda Malam Yunus ya zaba cewa Aisha zata yi sati daya a Lagos ta dawo musu da ita gida. Malam Yunus ya bukaci sanin waye mahaifin AbdulRasheed da kuma asalin ita Nenne anan Gombe. Nenne ta bashi damar yayi duk wani bincike da addini ya bashi dama akan Prince AbdulRasheed dasu iyayensa. Sun rabu akan cewa zai yi bincike zai kuma yi shawara da maidakinsa da Yayansa, sannan zai sa Zainaba ta sanar da ita abinda suka hadu suka yanke. An samu shawo kan Aisha da kyar da sudin ludayi ta yarda zata bi Hajiya Sappa Lagos bayan ta ci kuka ta koshi ta gode Allah a toilet don kada Hajiya Sappa ta ga kukanta, wai sati guda! Sati guda babu Umma yaya rayuwa zata yi dadi ga PETEL?! Sati gudan da a cikinsa dukkkan kundin kaddarar rayuwar Aisha take, tareda dan kabilar Yarbawa. Nenne da Aisha suka kama hanyar Lagos ta jirgin sama, domin daga Gombe kai tsaye suka tashi a jirgin Azman mai zuwa Ikko. **** ***** **** MURFIN LITTAFI NA DAYA Ga dai Aisha-Siddiqah a hanyar zuwa Lagos gidansu Prince ABDULRASHEED IDRIS (KEHINDE) AKANNI, gidan da ga dukkan alamu zai zame mata fadar rayuwar aure da surukuntaka, ga dai Aisha da Prince (Fullatana da Bayarabe) na shirin zama mata da miji kamar yadda manyan alamu suka nuna, alhalin Aisha ga hasashenta da alkiblarta da take-takenta akan kabilar Yarbawa. Mu biyo Siddiqah Petel ‘yar Ummanta, don jin cikakken labarinta, yadda zata kaya tsakanin ta da Polo Legend na Africa da turai, wato Yariman Ilorin PRINCE ABDULRASHEED (KEHINDE) IDREES AKANNI, mijin da kaddara ta zabar mata su fafata har su baiwa hammata iska a fagen soyayya, wanda ya kasance dan asalin kabilar Yarbawa. Yanzu ne zamu shiga cikin gundarin labarin Aisha da Prince. Har yanzu a himfidar labarin muke. Abinda zamu so sani a gaba shine; Shin ko Aisha-Siddiqah zata barranta kanta daga matan da Prince Abdulrasheed ya riga yayiwa kudin goron maha’inta, mayaudara, masu saka khairan da sharran, sannan (gold-diggers&insatiable)? A cewarsa dai “duk mata marassa godiya ne, da yawansu mazinata ne, marassa tsoron Allah ne, sannan basa yin soyayya ta fisabilillah! Ta yaya Aisha zata goge wannan perception din daya ya riga ya ginu tun kuruciya daga kwanya da zuciyar Prince Abdulrasheed Kehinde? Shin ko Prince zai samu irin soyayyar da yake fata, yake kwadayi, yake mafarki, yake kuma burin samu shekara da shekaru daga Aisha? Mun ji dai sanda yace “He’s a hopeless romantic, in search of true LOVE! Wanda ya riga ya amince babu shi a duniya”. Shin ko Aisha-Siddiqah zata so kabilar Yarbawa tunda ga dukkan alamu kaddarar rayuwarta na cikinsu? Mu karasa a littafi na biyu wanda tare suke da dan uwansa. Taku har abada SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORIN TAKORITES) 07030137870 WHATSAPP ONLY. 10/4/2024 (PAID BOOK) (INA TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa fata hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. -Takorinku