*GIDANMU..*! _(Our House)_ *Book1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *All praise is for Allah the Lord of all being. I exalt him as is befitting to him and I bear witness That there is no deity except Allah Along. Having no Partners. I also Testified Muhammad is Allah"s Messanger and Servant May the peace of Almighty Allah be upon him,his Family,his Companion and these who follows on their Footstep untill the last Day.* *Once again I Thank Almighty Allah that give me Chance and Wisdom to start up my New Novel which is work Fiction.* *Any resemble to your life style was the nature of the story* *I ask Allah to guide,Protect me Throught and make it sucessufull till The end* *Warning:🚫* _Using Any Part of This book or making Audio Without the permission of the Author is prohibited_ *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *Gabadaya wannan Labarin Tun daga farko Har Karshensa mallakinsu ne* *🅿�1* *KANO STATE* _Area:Gadan kaya Da misalin karfe 8:30am na Safiyar Ranar Litini_ "Cikin Hanzarinta na koda yaushe ta Fito Daga Cikin Wani koridon Dake Yammah da wasu Jerun Dakuna guda uku,Ta bayyana a madaidaicin Falon Lokaci Daya Tana Daidaita zaman Daurin Dakwalinta na Zahra Buhari. Farar Budurwace Sosai kamar ka Tabata Jini ya fito Doguwa mai Jikin murjewa akallah a shekara bazata wuce ashirin da daya ba 21aduniya ba,yanayin Fuskarta da Zubinta In kayi mata kallo Daya zaka alakanta ta da ita din Jinin Fulani ne gaba da baya Balle ma Data sanya Hannu Tana kara gyara zaman Daurin Dankwalinta bisa kanta wanda yaZauna Daram saman Tilin gashinta wanda ta Daureshi da Band mai girma. Sanye take da Atamfa mai gold Blue da Milk dinkin Riga da Sikat ,kafarta Sanye cikin wani bakin Takalmi mai Saukakken Tudu sai karamar Jakarta,Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon ta Zube Jakar Lokaci Daya Tana Dafe kanta sai data Dago na Fahimci batayi kwalliya ba Domin in Hasashena ya zama gaskiya ko Hoda bata saka ba ammh Saboda Farin Fatarta da yanayinta yasa she is ok ko ahaka taTsaya ma. Sauri ta kwasa zuwa Cikin Koridon Kafin ta Shiga wani Daki bata jima ba sai gaahi ta Fito da waya a hannunta da wasu Tarin Littafai kamar wacce zata shiga wani Nazari,kan Kujeran ta Sake Zubesu Lokaci Daya tana Duba agogon Hannunta wanda ya kasance karami mai kyau na Fatar Damisa,siririn Tsaki Taja Kafin ta kara Daga kai Tana Hango Barayin Dinning Table din Dake chanta bangaran yammah Mikewa Tayi Da mamaki ganin bata gansa yana karyawa ba,Alhalin Tafi kowa sanin Daga ita sai shi sune masu Tashi da wuri acikin gidan Ita saboda Makaranta tana Shekararta ta Farko a BUK ne suna yawan Lacture din safe shi kuma YA YUSUF saboda Tafiya wajen aikinsa,sannan kuma shi ya kan Kaita ya ijiyeta kafin ya Karisa wajen aikin nashi sai dai in tagama abunda take yi ta hawo adaidaita zuwa Gida. Jikinta ne yayi sanyi Data karisa Saman Babban Teburin cin Abincin mai Daukan Mutum Biyar kachal,Ta Bubbude Kololin abincin Data tashi Tun asuba Tayi shi kafin ta Shirya Saboda Abbanta da yayyin nata Guda Biyu da Bayan su bata da kowa,Daman bata sako Abba ko YA IMU a lissafinta ba sanin basa karyawa da wuri har gwara ma Abba Tasan by Now yana nan Idanuwansa Biyu yana Fama da Tunanen Tunanen da suka zama abokansa ashekarun yanzu Ya Imu kuwa Sai Rana ta Take yake Fitowa,koma ya Fito ba Balle ya iyacin wani abu ba Sanin Halinsa mai Kaifi Daya da Muraddam Hali,bai cika Damuwa da abinci ba Barsa da Shan Tea da kayan marmari Sai kuwa Busar Tabarsa wacce Take Tunanin kila ita ke Cikamai Ciki wamda yasa bai cika Neman abinci To in ba ita ba me yake ci.? Abunda Tunda take dashi bata Taba ganin Lokacin da yayi kyakyawan Minti Biyar bai Busa Hayaki a abakinsa ba!Tun Tana mamakin Taya Rayuwar Mutum Zatatafi ahaka har ta bari ganin Rayuwar ahakam Tana tafiya Kuma Tana kam Tafiya yarda Kaddara ta Fado ma GIDANMU..! Jikinta a sanyaye ta bar wajen ta Nufi Jerin Dakunan Dake kallonta,Dakin Farko ta Fara Knooking kafin ta Tura jinta a Bude taShiga da karamar sallama abakinta Cikin Takun na na Natsuwa. Wani Farin Dattajo mai yalwar Gashin Kai Fari tas Har zuwa Gemunsa da Sajensa,dake Kishingide saman Gadon Dake Dakin yana sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara Kafafunsa suna Sambal Saman gadon Farare dasu duk gargasa,In ka kalleshi Zaka Fahimci ba Shekaru ko Tsufa ne suka sanyamai Farin gashi ba sai Hallitarsa ce haka Duba Daga yanayinsa a Tsarin Shekaru bai wuce 61 ba,Duk da ya kwana Biyu Hasken Fatansa bai DusaShe ba da kuma Tsabar kyan Fuska da Zati idanuwansa suna Lumshe ne Tamkar mai Barci Casbaha ne a hannunsa yana ja Lokaci bayan Lokaci Bakinsa na Motsi kamar mai mgana. Cak taTsaya agabansa ta Zubamai Ido Cikin wani yanayi idanuwanta sun ciko da kwallah suna gabda Zuba sai da na kara Dubawa Dakyau na Fahimci Tsananin kamar da suke da wannan Farin Dattijon ban gama Mamaki ba Naga ta Durkusa agabansa Tana Fadin"Abba ina kwana.."Tafada Lokaci Daya Tana Dafa Hannunsa Dake jan Casbaha. Cikin Natsuwa ya Bude Idanuwansa ya sauke akanta To daman in ba ita bace waye..?itace kadai wacce yake Fara ganin in garin Allah ya waye,Muskuta wa yayi ya gyara Zama yana Fadin"Lafiya lau MAIMUNATU..!yafada yana sakar mata Mirmishi Itama Mirmishin ta maida mai ta Mike Tsaye Tana Fadin"Kayi sallah Abba..? Kur yayi mata da ido kafin yace"Sallar mene Maimunari? Cikin Gyada kai tace"Eh Sallar asuba Abba.."Ido yadan Zaro kafin yace"Ke don Allah..An kira Sallar ne..?Maimuna Dataji kamar ta Fashe da Kuka saboda Tsausayin Abbanta ammh sai ta Dake Cikin Rawan baki tace"Anyi Abba..Yanzu fa Takwas ta wuce har nagama Abun karinmu yanzu haka nazo mu gaisa ne zan wuce makaranta.."Ta karishe Fada wasu Zafafan Hawaye suna Biyo Kuncinta. Abba Dayaji abunda Maimuna tace yasa yayi Saurin Dirowa Daga kan gado kamar zai Fadi har sai data Rikeshi Tana Fadin"Yi a hankali Abba..."Cikin Takaicinsa yace"Wlh Maimunari Bansan anyi sallah ba..Kinga zaman nan da kikaga nayi ina Jiram akira sallar ne fa..Ko dai agogon ki ne yaLalace Maimunari gari bai waye ba.."Yafada yanawuceta Zuwa Window dake Dakin ya Daga Labulen ya leka kafin Taji yana Fadin"Innalillahi...da gaske kike Munari gari yayi Tar.."Yafada kafin ya Juya da Sauri ya Nufi Hanyar Tiolet kamar zai kifa Maimuna kuwa Banda Shesshekam kuka Babu abunda take yi ganin zai Shiga Tiolet din ne yasa tace"Abba Magungunan ka sun kare ne..? Bai juyo ba yace"Basu kare ba..Likitan fa da Mugunta Wlh mgugunar dayawa ya Tulamin sai kace wani Jaki.."Daga haka ya Tura Kofar Tiolet din yaShiga Da Casbaha a Hannunsa ya Rufo Kofa Tana jinsa yanata mgana Shi kadai Nan maimuna ta Duke Tana kuka mai Cin rai da kuma Tsausayin Halin da Gidansu ke Ciki na kuncin Rayuwa Dana Zuciya bata iya Fita Daga Dakin ba Har Abba ya Fito Daga Tiolet dim yana Digan Ruwa da alamu alwala yayi da sauri ta Mike ta isa ga Cikin Makeken Wardrope dinsa Tabude ta Daukomai Darduma ta Shimfidamai Kallonta Yayi yana Mirmishi yace"Allah yayi miki albarka Munari.."Yafada Lokaci Daya yana Dafa kanta Hawaye ta Share tana amsawa da Ameen. Har ya Daidaita Sahu ya Dago yana kallonta Kafin yace"Kukan me kike Munari..? Da sauri ta Goge Hawayenta Tana Fadin"Bakomai Abba..wani abu ne ya Fadamin a ido.."Kai ya girgiza kafin yace"To kije Yayanki Yusuf ko Imram su cire miki mana..Ni kinga idanuwana duk sun Mutu ba wani gani nake yi ba sosai ba.."Yafada Lokaci Daya yana kara Damke Casbahan Dake Hanmunsa ya Tada Salla da Kallon Tsausayi ta bishi Dashi Tana Tuna Wasu Shekaru achan Baya Abbanta ba Haka yake ba ammh yanzu kalli yadda ya koma Depression ya sa ya koma kamar wani mai Tabin kwakwalwa ga Kuma hawan Jini Da suka Hadu sukamai yawa Wai ahakan ma Don Likitan Kwakwalwa na zuwa duk wata ya Dubashi da kila Abba yana Chan Gidan Mahaukata tasan ko zata Mutu Abba bazai ijiye Cashaban Dake hannunsa ba Shiyasa bata wani matsa ma Kanta ba ta Juya ta Fice Daga Dakin Bayan ta jawo Kofar. Tana Fitowa suka kusa cin karo dashi ya Fito Daga Dakinsa Zai Shiga Dakin Abba Baya taja Tana kallonsa Kafin tace"Gud Mrning ya Yusuf...! Kauda kansa yayi Saboda baya so ta Fahimci yayi kuka yace"Mrning Sisy how was ur Nite..?Yafada Cikin Sanyinsa kamar ko yaushe. Da kallo ta Bishi ganin yana ta kauda kai sama da kasa karemai kallo Dogo ne sosai mai Dan Jikin murjewa Sannan Shima Fari ne kamar ita sai dai ta Dan Fishi Haske suna Tsanananin kama da juna Kamanin Abba suka Debo kamar an Tsaga kara. Cikin Zargi da Tantama tace"Ya Yusuf Lafiya..? Domin bata ga yayi wani Shirin tafiya aiki ba kamar yadda aka saba ba,Kansa ya sosa yana Fadin"Lau..Me kike jira baki tafi school ba.."?Maimuna tace"Yaya kaifa nake jira..Har na gama Breakafast baka fito ba.."Hannu kawai ya saka a gaban Aljihun Jallabiyansa ya Dauko 1k ya Mika mata ta karba da mamaki kafin Tace wani abu ya Rigata da Fadin"Ki hau adaidaita kitafi makaranta yau ba zan je aiki ba ina gida.."Yafada Lokaci Daya Yana Kokarin Rabata ya Shige Dakin Abba da Sauri taRiko Hannunsa yakiya waigo sai ta koma ta gabansa ta Tsaya tana Kallon yadda Idanuwansa sukayi Jajir,alamun yayi kuka Cikin Tsausayinsa tace"Meya faru ya Yusuf..?kuka fa kayi..? Da sauri yace"Kuka kuma Sisy..? Ni ban yi kuka ba..' Yafada yana kokarin Sakin Mirmishi,itama Mirmishin ta Sakarmai Mai ciwo kafin tace"Kuka kayi ya yusuf..Ko baka Fadamin ba Nasani.."Ta karishe Fadai itama Hawayenta suna zubo mata Da Sauri ya Dafa Duka Kafadunta yana Fadin"Me ye na kuka Sisy..? Bafa kuka nayi ba kaina ne ke Ciwo Shiyasa kika ga kamar nayi kuka.."Kara saka mai kuka tayi Tana Fadin"Bari naje na kira Anty Safiya na gayamata kila ita Zaka gayamata meke damunka.."Tafada tana Kokarin wucewa da sauri ya Rikota yana Fadin"Kada ki kirata Munari Da sauri ta kallesa jin yadda yayi mgana sai taga kawai ya gyadaa mata kai yana fadin"Domin ko kin kirata bazata zo ba..Itama an Rabamu da ita Sisy.."Ya Karishe Fada Hawayen DayakeBoyewa suka Zubomai,Maimuna Dataji abun Daga sama Taji Jikinta yakarayin sanyi,Cikin wani yanayi tace"Itama din Yaya..? Itama din an gayamata Abban mu Mahaukaci ne,Sannan bamu da uwa bamu da kowa sannan itama an gayamata ya Imran bayajin mgama yana Shaye Shaye..? Itama din Am bata Labarin Gidanmu ko Yaya.. ?Ta ke Fada tana wani Gunjin kuka Da Sauri ya Rumgumeta kamkam Yana Fadin"An gayamata Sisy..An ce ma iyayanta irin kallon da Mutane suke mana Munari..Itama na rasata Munari.."Haka yake Fada yana kuka itama kukan take aka rasa mai Lallashin Daya acikinsu Sai da suka gaji kana suka saki Juna Maimunatu bata tsaya ba ta kwashi Gudu Zuwa Dakin ya Imran Dake gaba Kadan Da Dakin Abba da Ya Yusuf da kallo ya Bita Ita yafi Tsausayi gwarasu maza ne ammh itama fa mace ce,tafi su Rauni, Hawayensa ya Share da Sauri ya Tura Kofar Dakin Abba ya Shiga da Sallama. Bubbuga Kofar ta shiga yi Tana Kiran sunansa,Yana zaune akan Kujera kwara Daya Tal Dake Cikin Bedroom din nashi Yana Kishingide Taba ne a Hannunsa yana Busawa Hayaki ta baki ta Hanci Bai ma jinta Bugar Kofar Domin ya shigawata Duniya Sai zuwa Chan yaji Kiran sunansa Da Buga Kofar Bude Jajayen Idanuwansa yayi yana mamakin waye yazo zai Dameshi.?ko yace zai katse mai Jin Dadi Mikewa yayi a Fusace Dauke da Taban a Hannunsa ya isa ga Kofar ya Bude yana Fadin"Wai Wayeee...! Yafada Cikin kakkausan Muryansa Kallon kallon sukayi Tsakanin shi da Maimuna wacce ke Zubar kwallah Sama da kasa yake Kare mata kallo Lokaci Daya ya Karkata kansa gefe ya Saka Tabarsa abaki yayi mata wata Zuka,kafin ya Fesar Da Hayakin zuwa Fuskar maimuna Baya Taja Tana Toshe Hanci Saboda bata kaunar warin Taba. Kara Hade rai yayi ganin Tanawani Toshe Hanci Cikin Muryansa ta Kaushi ba Tausasawa yace"Ke...Ubam wa kike Toshe ma Hanci..?Ni sa"an ki ne..? Yafada yana Nunata da yatsa kafim ya Cigaba da Fadin"Cire hannun ki a saman hancinki..In ba Haka ba kika Tunzurani wlh zan kamaki na Danne ki sai na Karar da Hayakinta a cikin bakin ki.."Ya karishe fada yana Nuna mata Taban hannunsa Dake Kunne tana Fesar da Hayaki Lokaci Daya yana Zare mata Jajayen manyan Idanuwansa kamar na mace. Dagowa Tayi tana kallonsa Tana kukan Tsausayinsa da Tsausayin kansu shima sai Lokacin ya Lura da kuka take Da sauri ya kwara ware ido yana kallonta,Kamar yadda take kallonsa Dogo ne sosai Har yafi Yusuf Tsawo kuma Shi Faffada ne Da kuma Kirar Karfi da Zafi Jikinsa yana Cure ne Domin baya wasa da Motsa jiki Fari ne shi ammh ba sosai ba Sunfishi Haske,yana da manyan Idanuwa mai Dauke da Doguwar Fuska Sai Sajensa daya Zagaye Bakinsa,wanda ya fara koma baki baki saboda busa taba,kansa Nannade yake Da Askin nam na Dada,kuma ya Dace dashi Domin ya Tafi da bakin gashin Fulanin daya wani Nannade Bisa kansa Daga Shi sai Bakin Dogon wando Ko Riga bai Dashi Faffadan Kirjinsa mai Cike da gargasa duk yanawaje ne. Kukan da Maimuna take yi ya Dakatar dashi Domin shi bai ma Lura da kuka take ba Da sauri ya kariso gabanta yana Fadin"Ke..Kukan me kike yi ne.? Ya fada Cikin Daga murya da Bayyana Damuwa Domin Duk Iskancin Imu yasan Gidansu Baya kaunar yaga wani Daga Cikinsu Cikin Damuwa kasa mgana Tayi har sai da ya Harzuka ya Daka mata Tsawa yana Fadin"U better stop dis Nonsess ki gayamin abunda ke Faruwa...Tun kafin na jimi ki Rauni anan wajen.."Ya karishe Fada Lokaci Daya ya Dukan Bangon Wajen da Hannunsa mai Dauke da Taban Wacce ta Fadi kasa ya sa Kyakywan Farar kafarsa ya Take Wutan ko Zafi bai ji ba saboda Zuciya da Sauri Maimuna taja Baya sanin Halinsa in yayi wannan Bakar zuciya sai ya iya mata Targade ai tun kafin ya juyo tace"Ya imu..Dama..Daman ya Yusuf ne ke kuka.."Ido ya sakar mata Cikin wani yanayi kafin a Hankali ya Furta.."Kuka..? Cikin alamun Tambaya.." Kai ta gyadamai Cikin Kaushin Muryansa yace"Yana ina..! Da sauri tace"Yana Dakin Abba.."Bai ma Tsaya Sauraranta ba ya wuce Fuu kamar zai tashi Sama da Sauri ta maramai Baya zuwa Dakin Abba. Yusuf na Zaune gefen Abba yana Ballamai mgani yana bashi yana sha Daga Gefen Dirowam gado kuwa Mug ne na Tea da Bread wanda Yusuf din ya Dauko ma Abba yasha Saboda yasha mgani Suna Cikin wannan Halin Imran ya Bango Kofa ya Shigo Cikin Muryansa mai Cike da Amo da Sauti yace"Uban waye ya saka ka kuka Yusuf...! Ya fada Cikin Sauke Jajayen Idanuwansa kan Yusuf din wanda bai ma dago ya kallesa ba illah Mikama Abba mganin Daya Ballo masa ya karba ya saka abaki yabi da Ruwa Lokaci Daya Yusuf ya karbi Ruwan yana Fadin"Abba ka kwanta ka Huta don Allah.." Abba bai yi mgana ba illah yabi Yusuf da kallo yajuya yabi Imran da Munari da kallo kamar yana so ya Tantance su,Ganin haka yasa Yusuf ya kamashi ya kwantar Lokaci Daya yana Rufamai Bargo Daga kafarsa yana Fadin"Kayi barci..Wannan kuma Daya Shigo Imu ne Abba Mara Hankalin kanin nan nawa ne.."Yafada yana dan Mirmishi sai Shima Abba ya Murmusa yana kallon Imran wanda ke tsayr Kikam yana kallon Abba Yusuf ne ya waigo yana kallonsa kafin yace"Kai wai yaushe ne zakayi hankali ne..? Sai an ce ka gaida Abba zaka gaishe shi..? Imran ya wani Dage Hanci yana Fadin"Indai banyi hankali at age of 30 ba Kila sai age of 36.."Yafada lokaci Daya yana karisa ga Abba Hannu ya bashi Suka Tafa yana Fadin"Abba kana Hutawarka fa..!Kaji Dadinka Allah ya baka lafiya.."Ya karishe fada yana Shafa Gemunsa Abba yayi mai Dariya kafin yace"Allah yayi muku albarka.."Yana Fadin haka kuma sai duk sukayi wani iri Yusuf kuwa Hanyar fita ya kama Bazai iya tsayawa ba Fita yayi Daga Dakin Maimuna tabi Bayansa Imran kuwa Durkusawa yayi gaban Abba Idanuwansa ya kara Kadawa yace"Allah ya baka Lafiya Abba.."Yake Fada yana Rike da Hannunsa Kansa Abba ya Dafa Yana mai Mirmishi Cikin Muryan Barcin Daya Fara Fuzgan Abba yace""IMRAN.....! Bai karisa ba barci ya Tafidashi Dayake mgangunan akwai na Barci Imran Dake kallon Fuskar mahaifinsu yaji kamar ya Kurma Ihu Kai ya girgiza kafin ya mike Dakyar ya iya Sabule hannun Abba ya gyaramai kwanciya ya kuma Rage mai karfin Sanyin Dakin kafin ya Fice Zuwa Falo anan ya iske yusuf da Maimuna suna Zaune mgana suke suna ganinsa sukayi Shuru,bai damu ba yana zuwa gaban Yusuf ya tsaya yana Fadin"Kukan me kake yi ne kamar wani mace..?kasa wannan Shagwabbiyar kanwar naka itama tazo Tana Damuna da kuka.."Ya fada Lokaci Daya yana Tura Hannunsa Cikin aljihun wandonsa sai ga Taba ya Fito da ita da Lether ya saka abaki ya kunnata ya Zuka ya Fesa musu Hayakin yana Fadin"Ina Tambayarku kumin Shuru..Kada ku bari na Harzuka fa..Mahaukaci kuka maidani ko me..? Ya karishe Fada yana Fitar da Hayaki ta Hanci Dukkansu kallonsa suke ba wanda yayi mgana Daga kafa yayi ya Buga Jikin Kujera Cikin Tsananin Fushi yace"Nace waye ya saka ku kuka ne..?Yau yagane ba wanda ya isa ya saka wani Daga Gidanmu Zubda Hawaye.." Yusuf dai baice komai ba Maimuna ce ta Tsorata taja Baya Tana Fadin"Safiya ce..! Cak yaTsaya yana kallonta ganin haka yasa tace"Eh Anty Safiya Budurwan Ya yusuf...Itama..Itama.."ITAMA ME NE.! ya katseta Cikin Tsawa da Bala"i Yusuf ya kalleshi ganin yadda Munari kerawan Jiki yace"Kai fa Sakarai ne..Itafa macece kayi mata ahankali mana.."Jajayen Idanuwansa ya sakarmai kafin ya Bushi Hayakim Taba ya Fesamai yana Fadin"Ai tama fika Jarumta malam..'Yafadamai yama kallonsa karamin tsaki yaja ya Mike yana Fadin"Kada ka sake naji ka taka kaje gidansu Safiya kaji ma nagaya maka.."Daga hakaya juya zai tafi Imran ya Daki Kirjinsa Har sai da yayi kara Lokaci Daya yana Fadin"Itama sunce baazasu baka ba saboda muna Rayuwa agidamu bamu da Mace aciki..? Abban mu ya Haukace ni kuma ina Shaye Shaye ko..? Itama sun kara hanaka keman duk da Tarin Nasabarka Kafa fini Hankali Da Tunani meka rasa da zaka Dinga Neman aure ana hanaka..? Yusuf ya tsaya Cak yana Jin wani Kukan Zucci Cikin Sanyinsa yace"Bamu rasa komai ba Face KWARIN ZUCIYA.." Da mamaki Imran da Maimuna ke kallonsa bai waigo ba ya Cigaba da Fadin"Mun rasaa kwarin Zuciyan da zamu karbi kaddaranmu mu Cigaba da Rayuwarmu Tamkar kowa..Tunda Kaddaran nan ta Fadamana muka rasa komai Abba ya Koma haka Imran ka koma yadda kake ni kadai ne nake kokarin Tsayuwa da Kafafuna din ma na gaza Domin Kune kwarin gwiwata da komai nawa Domin ku kadai ne ahalina anan Duniya.."Ya karishe Fada Yana Sharan kwallah Imran ya Busa Taba mai tsawo Har sai da Hayakin ya Cushemai Zuciya ya Fara Tari da Sauri Yusuf ya Nufeshi yana Fadin"Kagani ko..?kaga irin Sakarcin ka ko..?baka da Lura ne ka rika Zuka a hankali mana Tunda ta zama ibadarka.."Da hannu ya Dakatar da Yusuf kafin ya Bude Manyan idanuwansa da suka kara zama Ja saboda Hayakin Daya taso mai Daga kai ya Nuna kansa yana Fadin"indai Ni IMRAN wanda ABUBAKAR MALAMI ya Diga kwansa ZUWAIRA Ta Haifeshi adoron Duniyanan sai na Aura maka Safiya..Ko Ubanta ya yarda ko bai yardda ba don Uwatai.."Yafada yana kara Nuna kansa da kuma Dukan Kirjinsa kafin ya Take Taban Hannunsa ya Murjeta da kafansa ya wuce yana wani Tafiyar Takama yusuf ya Shiga kwalamai kira yana Fadin"Imu..? Imu me zakayi kada ka kaje ka Karya mata Uba kamar yadda kayi ma Kawun Asmee fa..! Imran na jinsa Mirmishi kadai yayi a Hankali ya Furta"Ka bani Shawara ya yusuf Tanque.."Yafada Lokaci Daya yana Shigewa Dakinsa Yusuf ya Dafe kansa yana Fadin"Munari meyasa kika gayamai..? Kin fi kowa sanin zai je yayi act din sa Stupit kamar yadda ya saba..! Marairaicewa Tayi zatayi mgama ya Dakatar da ita da Fadin"Muje mu karya na kai School kin makara.."Da sauri ta Mike tana Fadin"Nayi missing din Lecture din Dr Sa"idu.." Dinning suka nufa ya zauna Tayi Serving dinsa Tea kadai ya sha da Soyayyan Dankali itama haka basu jima ba suka tashi Daki ya koma ya Dauki key din Mota Ita kuma ta kwashi Littafanta da Jakarta da mayafinta suka Fito Haraban gidan Sun Shiga Motar kenan Yusif zai yi Rivers sai ga Imram ya Fito ya Tsuke Cikin Riga da wando Duka bakake ya saka P.Cap ga wani Bakin katon Gilashi Daya kwafa fuskarnan ba Annuri Kafarsa Sanye Cikin wani Bakin Booth din Takalmi yana ganinsu yayi kamar bai gansu ba,Bakar mashin dinsa Roba roba Dake fake a Haraban gidan ya Hau Lokaci Daya yayi mata Key ya Tada ita yana Zuba Hon Iro megadi Dake Tsaye Daman Tuni ya wangale get din sanin Hali Yanzu sai yasha mari Imran bayason Jira sai da ya Fice Daga gidan kana suka Fita suma suna Tafe Yusuf na Tunanin kada Imran yaje gidansu Safiya yayi musu Haukanshi har ya sauke Munari bai da walwala Daga nan Gida ya Dawo saboda Abba,ammh Gabadaya Zuciyarsa bata Natsu da Fitar Imran ba yasan sa Kaifi Daya ne in yace Zai yi Abu sai yayi shi yaso kiran Safiyan yaji ko yaje..?Sai kuma ya fasa Domin Cin Zarafin Da babanta yayi mai Jiya bai fatan ta sake ma ganinsa Har Abada. *Ya kukaji salon wannan Mikakkiyar Tafiyar tamu..? Bamu ce komai ba bamu Fara Wannan Tafiyar ba har yanzu..Ku yi Kyakyawan Sharhi bayan kun yaba kun kuma danna min Kararrawar Voting ni kuma nayi alkawarin Sanya ku nishadi da wannan Labarin mai amon Sautin tafiya da Zuciyar mai karatu..*! *Comments* *Share* *Vote* *10/02/2022* *Shakira...* *IWA* 3/22/22, 23:02 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..*! _(Our House)_ *Book1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *🅿�2* "Daga gidansu gangarawa yayi Chan kasan Layinsu bai tsaya ko"ina ba sai Kofar wani Shago mai Dan girma inda aka Rubuta DA KUDI AKE NEMAN KUDI TAILORING CENTER ababban Allon Dake kafe a kofar Shagon. Yana Tsayawa ya zura hannu Cikin aljihun bakin Wando Dake Jikinsa ya zaro Tabarsa da makunninta ya kunnata ya Busa ya Fesar da Hayaki Cikin Shauki kafin ya Danna Hon din mashin din da karfi kamar Zai fasa ma Mutane Dodon kunni. Shigowarsa Shagon kenan yana Duba yaransa da kuma Sallahu wasu Dinkuna da zai basu yana da Lacture karfe 10am cikin makaranta zai shiga yana Cikin yima Babban yaransa Auwal mgana sukaji wannan Gigigitaccen hon din Imran ya cika musu kunni Dafe kai yayi Lokaci Daya ya juyo yana kallon Kofar wajen inda suka Hada ido suna kallon Juna. Karamin Tsaki yaja kafin ya juya yana kallon Auwal yace"Don Allah Auwal kuyi kokari ku gama Kafin Dare..Yau da Daddare Hajiya zata aiko Direbansu ya karba.."Auwal ya gyada kai Daidai lokacin da Imran ya kara Danna Hon din da karfi,kansa ya kara Dafewa Cikin Takaici ya Furta"Ya illahi.."Auwal Dake Dariya yace"Oga sai fa ka Fita..In ba Haka zai cigaba ne kasan Halin yan kayanka.."ya karishe Fada yana Dariya shi da Sauran yaran Shagon wani Daga chan yana kan keke yana Dinki yace"Imran kenan..Abokin Oga ko nace Amini ayi Fada aShirya hukuma sai da Lallashi..! Yana Jinsu bai yi mgana ba sai dan Mirmishi da yayi ya Taka ya Fice Daga Shagon yana Fitowa ya kallesa yana Fadin"Kai wai meyasa kake hakane..? Ko yaushe kazo waje sai ka bada alamun kazo.."Imran ya kalli Abokinsa SAGIR,ya zuki Tabansa ya Fesar da Hayakin kafin cikin Wata murya mai cike da gadara yace"Da kudi ake neman kudi Abokina..Taken ka kenan.."Karamin Tsaki Sagir Yaja kafin yace"Naji..Ya akayi ne..?Ya jikin Abba..? Imran ya Sauke Kafarsa Daya Dora Saman karfen Mashin kasa yana Fadin"Lafiya..Hau muje.."Sagir ya wani kallonsa ShekeSheke kafin yace"Na hau muje..? Ina kuma..? Idanuwansa ya sakarmai Kafin ya wana Mashin Din tayi Jinjin cikin Dakiyarsa yace"Malam ka Hau muje nace ko..'? Yafada Cikin alamun ya Fara Fusata Shima Sagir din Cikin Zafinsa yace"Ni kuma nace na hau muje ina..? Wani Wawan Harara ya Jefeshi Dashi kafin yace"Zan je na kai kanka ne Domin nayi Cininkinsa.."Karamar Dariya Sagir yayi kafin yace"Ina karyanka Wlh..Kaina yafi karfinka.."Wani mirmishin Rainin wayau Imran ya saki kafin yace"Naji..Ka hau Muje kafin Raina ya baci.."Sagir yace"Muje ina wai..?Nifa daga ganni nan Lacture gareni makaranta zan shiga.."Imran yaji kamar ya Kifamai mari Cikin Muryansa mai Cike da Amo da Zati ya kalli Sagir yana Fadin"Zaka hau ko bazaka Hau ba..? Yafada yana Tsareshi da Jajayen Idanuwansa Sanin Halinsa yasa Sagir din ya Taka ya Hau Bayan Mashin din Dariya Imran yayi kafin yace"Da kada ka hau kagani.."Sagir yace"me zaka iya..?Kai dai Nayi niyar Hawa kawai malam..! Imran bai yi mgana ya Taka Mashin suka Fara Tafiya Gefe Daya kuma yana Tuki yana Busan Tabansa da Dayan Hannunsa Sagir na Baya yama kasa mgana,ganin yana ta Tsula gudu yana neman kadasu yasa ya Tanka."Kai malam in ka Shirya mutuwa ne ni ban Shirya ba..fakani gefe ka saukeni sai kaje ka Tari Mutuwar kai kadai ba.." Dariya Imran ya saka kamar ta basawa kafin yace"Meyasa kake Tsoron Mutuwa abokina..? Ka manta Zaka Mutu Dolen ka..'Sagir yace"Nasan zan mutu..Ammh ina Burin kafin na Mutu na ijiye masu min addu"a kai daman bana ta kai Tunda ka Riga ka auri Taba gatanan ma ahannunka baka da mtsala.."Yana jinsa bai yi mai mgana ba ganin sun bar anguwansu yasa Sagir yace"Wai ina zaka kai ni ne..? Har ya Cire rai da zai yi mgana sai yaji yace"Gidansu Safiya zaka Kaini..! Sagir yace"Safiya..? Wata Safiyan kuma..? Imran yace"Safiya Buhari alhassan.."Sagir sai da ya Dafa Kafadan Imran saboda Razana Cikin Firgici yace"Budurwan ya yusuf fa kenan..? Yafada yana Bayyana Firgicinsa Dariya Imran yayi kafin yace"Sakeni Matsoraci kada kasa mu Fadi saboda Tsoron ka..! Sagir yace"Don Allah mu daina wasa me zai kaika gidansu..?ko Ya yusuf ya aike ka..? Imran ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Wazai aika ?Ni Imran..Kana shan kwaya ne..Ni zan aiki kaina malam.."Sagir yace"Me zakaje yi gidansu..? Imran yace"Ka Nuna min Hanyar Gidan mallam ba Tambayata zaka Tsaya kana yi ba.." Cikin Tsoro da Fargaba Sagir yace"Zoo road gidansu yake.."Batare da bata Lokaci ba Imran ya take mashin Har suka isa Zoo road ba wanda ya kara mgana Sagir ke nuna Hanyar gidan,Cikin Lokaci sai gasu Kofar Gidansu Safiya wanda ke Dauke da Katon Get mai Ruwan Madara Daga ganin Zubin gidan zaka Fahumci suna Rufin asiri eh mana suna Dashi Mahaifinta Alhaji Alhassan Buhari Lacture ne A BUK Dake nan Jahar kanon Dabo. Akofar gidan Imran ya Faka Mashin din nashi Sukasauka Gabadayansu Lokaci Daya ya Juya yana Bin Gidan da kallo yana Wani Shafa Sajensa ganin haka yasa Sagir yace"Imran Me zaka yi agidan su yarinyar nan..? Imran bai mai mgana ba Illah Tabansa daya Kara Fitowa da ita ya Kunna mata Wuta sai da ya Busa Hayakin ya Fesar kana ya Sauke kallonsa kan Sagir yana Fadin"Bafa wani abu ya kawoni ba..Kawai Kashedi zan mai da kuma Umarnin Yayi gaggawan bama Yayana auran yarsa in ba Haka ba.."Sagir Daya Zaro ido yace"in ba Haka ba mene Imu..? Don Allah ka bari kada ka Shiga gidan Mutane ka Tada wata Rigima so kake amaimaita abunda ya Faru a gidansu Asma"u..? Ka Karya ma kawunta Hannun Daga karshe ba Yaya yusuf ka bari da Shari"ar ba ina amfanin wannan Rayuwar da kaKe saka Kanka acikine..? Yana jinsa bai taka ba idanuwansa ma na Lumshe yana Zukan Taba yana Fesar da Hayaki,Sai chan yaBude Jajayen Idanuwansa yana kallon Sagir Lokaci Daya ya gyara Tsayuwa yana Fadin"Bazan karyamai Hannu ba..? GIDANMU fa ya zaga..? Ya kira Babana Mahaukaci..? Wlh Tallahi kowaye ya nunayatsa gareni ya zagi gidanmu ya kuma kira Babana Mahaukaci sai na Karyashi in ban Nakasaahi ba Sagir.." Ya karishe Fada Cikin Daga Murya Idanuwansa sun Sauya Launi Ganin haka yasa Sagir ya Sausauta Cikin Lallashi yace"Naji Bai kyauta ba..Ammh me ya jawo haka kuma yau..? Imran yace"Raba yayana yayi da yarsa..Can u juz imaging ya yusuf na kuka fa saboda yarsa kuma sai naje gida na kwamta ina Murna..? Ina so ya gane ya Tabani Wlh zan mai gargadi in yaji Ruwansa in bai jiba Jikinsa zai gayamai ne ba Ruwana fa.." Ya karishe Fada yana Zakuda kafadansa Lokaci Daya yana Fesar da Hayakin Taban Daya Zuka Harta Hanci ya Dumfari get din gidan Sagir ya Bisa yana mai magiya Cikin Takaicinsa ya waigo yana Fadin"Malam don Allah ka kara gaba..Haba nifa Gidan kawai na Bukata kuma ka Kawoni zaka iya karawa gaba Bai Dameni ba"Yafada kamar zai Dakeshi Sagir ya kallesa yana Fadin"Ammh ai har kofar Shagona kaje ka Dauko ni ko.? Imran ya juya yana Fadin"Kuma Da ka gama Biyamin Bukata nace U are Free to go ko..? Sagir yayi Kasake yana kallonsa Har ya Taka Jikin Get din yayi Knooking Sai gashi megadi ya Leko Domin ganin Waye Hayakin Taban da Imran ya Fesamai ya Faramai Maraba Baya yaja yana Fadin"Bawan Allah meye hakan..? Yafada ya kare ma Imran kallo wanda ya tsaya kyam Hannunsa Daya cikin aljihunsa Dayan kuma ya Rike da Tabarsa yana Busa sai da Lumshe ido ya Bude kana ya Sakarma Megadin wani kallo kafin yace"Alhassan Buhari yana Ciki..? Megadi ya zaro Ido Jin sunan Megidansa kai tsaye ya Tsorata ganin yanayin Imran din Shiyasa yayi saurin cewa"Eh..Eh..yana ciki bai riga ya Fita ba.." Imran yace"Gud..Shiga kace mai yana da Bako a waje.."da sauri megadin ya juya zai tafi Imran yace"Ji mana..! Cikin kaushin Murya Jiki na rawa ya juyo yana Fadin"Na"am yallabai.."Domim a Tsorace yake gani yayi kamar in yayiwani gardama Imran zai Fito da wuka Domin kallonsa yake kamar wani Dan Daba Duk da yayi Mishi kama da Yusuf Saurayin Daya Daga cikin yaran Gidan Jikinsa bai saki ba. Sai da Imran ya Busa Hayakin Tabansa kana yace'In yabukaci sanin waye kace mai IMRAN ABUBUKAR MALAMI ne...Kanin Yusuf Abubukar malami.."Ya karishe Fada yana wani Shafa Gemunsa,lokaci Daya yana Lailaya Taban Hannunsa,Da gudu megadi ya juya yana Fadin"To yallabai.."Sagir Dake gefe Tagumi kawai yayi aransa yana ta addu"an Allah ya kauda Fitina yaso ya kira Ya yusuf ya gayamai ko zai yi wani abu sai ya Tuna Lambarsa Tana Karamar wayarsa ne kuma ya manta da ita agida saboda Sauri. Megadi Har Falon gidan ya Shiga Daidai Lokacin Alhaji Alhassan ya Fito Zai Fita Matarsa Hajiya Mero ta rakosa Megadi ya Zube yana Fadin"Alhaji kana da Bako."Cikin mamaki yace"Bako..? Daga ina kenan..? Megadi ya Kaskastan dakai yana Fadin"Yace ace maka Imran Abubukar malami ne kanin yusuf.."Alhaji ya kalli Hajiya Mero Cikin Fushi yace"Kin ji ko..? Wannan kanin Shashan yaron chan ne da SAfiya ke ta kuka Tun jiya kan nace Bata bashi.."Hajiya Mero ta karkace kai Tana Fadin"Takadirin yaron nan dai kaninsa da muka samu Labari Alhaji..? Yana Saba Babbar Rigarsa yace"Shi mana..Bari naje Shima nayi mai Fata Fata kamar yadda nayi ma Yayansa Jiya..Ni ba karamin Mutum bane da inaji ina gani zan Hada jini da Dangin Mahaukata da yan iska.."Jakarsa ta Briefcase ta mikamai tana mai Allah ya kiyaye ya Fice yana Fada Megadi Daman Tuni ya Fice kada kai Tayi Ta koma Ciki Tana Ayyana abubuwa da Dama kan Al"amarin. Yana Fitowa Haraban Gidan ya mikama Direbansa Jakar yana Fadin"Ina yake..?Megadi yace"Yana Daga Wajen get Alhaji.."Karamin tsaki Yaja yana Fadin"To ya shigo mana..Ko ni zan Biyo sa ne..? Yafada da Dan karfi Har Imran da Sagir sai da sukaji Domin ya Taho gabda Get din ne balle ma Alhaji Alhassan irin Mutanen ne marasa mgana Cikin Natsuwa ga Sakin Murya. Megadi ya leko waje yana kallon Imran yace"Yace ka Shigo yallabai..'Mirmishi Imran ya saki kafin ya Saki Taban Hannunsa ta Fadi kasa ya saka kafa ya Murjeta Megadi ya wangalemai karamar Kofar ya Shige Sagir na ganin Haka ya bi bayansa Suna Shiga Haraban Gidan suka Hada ido da Alhaji Alhassan wanda ke Tsaye yana gyara Babban Rigan Jikinsa Lokaci Daya yana kare ma Imran kallo Daga sama Har Kasa Shi kuwa gidan yake Kare ma kallo afili ya Furta.."Nifa ba ganin kyale kyalen gidanka ya kawoni ba..Mgana nazo muyi kan Abunda ya Shafemu Alhaji.." Ya Karishe Fada yana Kafeshi da Jajayen Idanuwansa Lokaci Daya ya Zura Hannu cikin aljihu ya Dauko Tabarsa ya Kunnata hayaki ya Fara tashi Alhaji Alhassan Dake tsaye Bai yi mamaki ba Daman ya samu Labarai Dadama kan Imran din a Fusace ya Tako zuwa gabansa yana Fadin"Kai wannan wani irin Shashancin ne..? Kashigo Gidana kana Min Shaye Shaye..? Yafada Yana wani Kunfar Baki Domim ba Laifi Alhaji Alhassan akwai Fada. Ko Tak Imran bai ce mai ba sai ma Tabarsa Daya kara Zuka ya Daidaici Fuskar Alhaji Alhassan ya Sakarmai Hayakin da sai da yayi Baya Cikin Firgici yana kallon Imran wanda yayi Mirmishi ya Dagamai Gira yana Fadin"Ya akayi..? Ka tabbatar yanzu.? Ba Wani Dogon Surutu ya kawoni ba..Miye Dalilinka na Hana yayana Auran yarka..? Ya fada Cikin Tsuramasa Idanuwansa Kamar yana Bashi Umarnin yayi mgana Alhaji Alhassan mamaki ya kara kamashi Sagir kuwa yana Gefe bai yi mgana ba sai addu"a yake aransa kada Alhaji Alhassan ya Fadi wata mgana kan Gidansu ko Mahaifinsu yanzu ayi mara Dadi kamar yadda Kwanaki ya Faru da abokinsa KB a Shagonsa Suna Hira sai Imran yazo wajensa Bama dashi ake Hiran ba Cikin Labarin ne Kb ya sako mganar wani Mahaukaci su dai basu yi Aune ba sai Hakorin Kb da Jininsa suka gani a kasa Imran ya Naushemai Baki da sunan wai Dashi yake da Abbansa yake kwatance Fadan da yaso har Hukuma ta Shiga Ciki Shi yayi ta bama Kb Hakurin har ya Hakura ammh da Imran yaji cewa yayi Duk wanda ya bama Kb Hakuri ya Hakura Uwarsa taci Uwatai. Shiyasa yake ta Tsoron kada Hakan ta kara Faruwa yasan Imran kamar Yunwar Cikinsa zai iya komai ga Duk wanda ya aibata GiDANSU. Alhaji Alhassan da Ransa ya gama Baci ya Fara Fada da Bambami yana Fadin"An hanashi din..? Nace an hanashi din Zaka aura masa ita ne..?ko yarka ce.?Ina ce Ni na Haifeta kuma ba wani iko da ita ba.? Ko Uban wani ya Haifamin ita ?.."Ya Karishe Fada har kumfar Miyau na Biyo bakinsa. Imran Dake zukan Tabansa ya Dakata yana kallon Alhaji Alhassan kafin yace"Ammh dai Uban da ka zaga ba namu Uban ka zaga ba ko..? Yadda yayi mganar ne yasa Shakkarsa Ta Shiga Alhaji Alhasan ya juya kai Baiyi mgana ba Mirmishi ya saki kafin yace"Nagane..Ba Dogon Turanci nace kamin ba Malamin Kimiya da Fasaha Dalilinka kadai zaka Fadamin.."Alhaji Alhassan yace"In Kaji Dalilin sai kuma yaya..? Nace sai kuma Yaya..? Imran ya Zakuda Kafafa yana Fadin"Sai yaya kuwa..? Iyaka in Dalilin bai min ba na saka Ka Dole ka Kira yayana ka bashi Go Ahead kan ya Turo magabatansa.."Zaro ido Alhaji Alhassan yayi kafin yace"Ni..? In hada Zuru"u da irin Mahaukata Irin Tantiranci..uwa uba ga Rashin asali da Nasaba Gidanku ba Tarbiya ba kwaba Domin Tunda kuka zo garin nan Daga ku sai Mahaifinku albarkan zaman mace ma agidan baku samu ba kuna Zaune kara Zube sai ni Saboda bani da Tunani na Dauki yata na bakku.? Ai sai kimata da Mutumcina ya...! KAIIII...!Ihun da Imran ya Kwatsa kenan Lokaci Daya ya Daga Hannunsa sai Sauke ma Alhaji Alhassan wani Naushi wanda inda ya samesa sai ya Raunana Domin Tabbas Hakoransa na Gaba sai sun watse sai Dai Sagir ya Ceceshi Daga Hakan Ya Tare Imran Da Rikoshi da Karfinsa yana Fadin"Imran..Imu..Ka bari Don Allah..Kada ka Tabashi Don Allah.."Yake fada yana Rikesa da kyau ganin yadda yake wani Fizga Idanuwansa sun kala sun ji Jajir Tuni jijiyoyin kansa suka Daga haka yake sakin Hucin bakinciki da Hannu yake Nuna Alhaji Alhassan Dayayi gefe Tun Hargagin Imran yana maida Numfashi Cikin Muryansa mai Cike da Amo yake Fadin"Who is He da zai Fadi wata banzar mgana kan Gidanmu.? Shidin banza waye shi..? Wlh da barni da yanzu Bakinsa ya Cikada Hakoransa da Jini Kai har kana da Bakin mgana Kayi gaggawan bama Yayana Dama in ba Haka sai na Fallasaka agaban iyalanka gasunan suji su kuma Fahimci wani irin Uba ne Allah ya basu.."Ya karishe Fada yana Nuna su Safiya da sukaji Hayaniya Daga Haraban gidan suka Fito kuka kawai take Tunda Taga Imran duk bata taba ganunsa tasan sunan abakin yusuf kuma daga mganarsa ta Fahimci ko waye shi.. kanwarta Tasleem Tana Ta lallashinta Hajiya Mero kuwa Mahaifiyarsu kallon Imran take Tana kuma Kallon Alhaji Alhassan da Tunda yaji mganar Imran gabansa ya Fadi kardai yasan Sirrinsa na Neman matan Dayake yi..? In ko hakane ya Shiga uku Gwara ya basu auran Safiya daya Fallasa wannan Sirrin wanda Bayyanarsa zai yi Sanadiyar Kimarsa da Darajansa da Mutumcinsa da kuma aikinsa Dayake takama Dashi Yin wannan Tunanin yasa Jikinsa na rawa ya matsa kusa dasu Imran yana Fadin"Kaga ba sai an kai ga Haka ba..ku Turo mgabatanku Shikenan Tunda kun nace itama ta nace sai shi.."Yafada yanawani fiki Fiki da ido na marasa gaskiya Sagir Sai da Dariya ta kusa kamashi Imran kuwa Hannunsa ya Fizge Daga na Sagir ya Tura Hannu a aljihunsa ya Dauki kwalin Tabansa Har ya karar da ita Saura Daya ya Daukota ya Jefar da kwalin ya Jawo makunni ya kunnata ya Zuka ya Fesar da Hayaki kana ya kalli Alhaji Alhassan da Jajayen manyan Idanuwansa yace"Ka kira Yayana ka sanar dashi yanzu..NAN..! Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Sauri Alhaji Alhassan yace"Yanzu kuwa..Insha Allahu.."Yafada yana rawan Baki Imran bai Saki Fuska ba ya Taka Hargaban Safiya bai Taba ganinta ba sai sau Daya da Yusuf ya taba nuna masa hotonta duk da bai wani kalleta ba sosai ba,da Jajayen idanuwansa ya kare mata kallo Daga sama Har kasa Tasleem kuwa bayanta ta Labe Tana Toshe Hanci Daya lura da ita tsawa ya Daka mata yana Fadin"Ke....'jiki na rawa ta Dago kanta tana kalleshi cikin Dakiya yace"Ni sa"an ki ne da kike ganina kina Tushe Hanci..? Maza Bude Hancinki kafin ki Tunzurani na Targaki yanzu agaban Iyayenki..!"Da Sauri Tasleem ta saki Hancinta Tana rawan Jiki ta kamkame Bayan Safiya Da kanta ke Duke Tana kuka Hajiya Mero kuwa gum Tayi da bakinta batayi mgana ba Duk da itama warin Tabae ta isheta sai dai ba Halin mgana ganin yanayin Imran din ya Firgitata ta tabbata ko ita ba Shakkarta zai yi ba balle ma Dataga Shi kanshi Alhaji ya Saduda Safiya ya kallah kafin yace"Bhabi..Stop craying...Kin auri Yayana kin gama..See u sai mun Hadu a GIDANMU.."ya karishe Fada yana wani Mirmishi kafin ya Zuki Tabarsa ya Fesa musu Hayaki kana Lokaci Daya ya Juya yana wani taku Daya Bayan Daya yana wani Rangaji ya Fice Daga gidan Sagir ya maramai Baya Megadi ya Bisu da Allah ya Kiyaye sai da Alhaji Alhassan yaji tashin Mashin din Imran kana ya iya Motsi Juyawa yayi yana kallonsu Kafin ya Fara Bambamin kunya. "Tsayuwar mu kuke yi kukama..? Ai sai ku shiga Cikin gida...Ke Safiya ki kira shi yaron kicemai ya Turo manyansa Tunda irin Gidan da kika Zaba kiyi Rayuwa kenan ke kika sani.."Daga haka ya Saba Zaman babbar Rigarsa ya nufi Motarsa Direbansa ya Budemai Bayan Bakar prado dinsa ya Shige yana jin Zufa na ketomai Kafin Direba ya Shiga Bangaran Direba yayi Rivers Ya yi Hon megadi ya wangale get suka Fice sai alokacin Safiya ta Juya Cikin gida da Gudu Tana Dariya da kuka Tasleem ta Mara mata Baya kana Hajiya Mero da Jikinta ya gama yin sanyi da al"amarin Data gani. Imran kuwa Har ya maida Sagir bakin Shagonsa bai ce mai kanzil ba sai da ya ijiyesa kana Sagir ya kallesa yace"Mama Tana ta Cigiyarka.."Imran yayi Mirmishi kafin yace"Kace mata Zan shigo Gobe.."Daga haka ya Bama Mashin Dinsa wuta ya wuce ya bar Sagir da binsa da kallo har ya Bacema ganinsa bai koma Shagon ba ya Nufi Gidansu Dake Jikin Shagon nashi Domin ya Dauko wayarsa da Littafansa ya Shiga makaranta. Yana Shigowa Falon ya ci karo da Yusuf sai washe baki yake Cikin Murna ya Sarke Hannayensa yana Fadin"Bro..Wai me kayi ne..?Yanzu Safiya ta kirani tace Abbanta yaje na Turo Manya..Am so Suprise Mutumin Daya gama Rantsuwan jiyanan bazai taba bani Auran yarsa ba sai gashi yau da kanshi yace na Turo manyana.." Mirmishin Jin Dadi Imran ya saki ganin Dariya a Fuskarsa Dan"uwansa Hannunsa ya Zare kafin ya Dafa Kafadarsa yana Fadin"Imran kaifi Daya ne..Yana Cika Duk Abunda yace..So sai ka Fara Shirye Shirye ka kusa Zama ango akalla bayan Wasu Shekaru zamu samu wata mace zata karu acikin GIDANMU..! Yana gama Fadin haka ya Sauke Hannunshi ya Wuce zuwa Dakinsa ya Shige ya Turo Kofa,Yusuf ya Bishi da kallon Kauna da Tsausayin Dan"uwansa kafin ya Girgiza kai yana Fadin"Kana Matukar Burgeni IMRAN ABUBAKAR MALAMI.."daga haka ya juya zuwa Dakin Abba Cikin Farinciki Domin ya sanar dashi Allah yayi zai yi aure wannan karan. ****** *KADUNA..* _Area:Anguwan Sarki.._ Acikin anguwan Sarki acikin wani Tangamemen gida na Zamani Da misalin karfe 8pm na Dare wata yar Matashiyar Budurwa nagani wacce bata wuce Shekara 20 ba aduniya Doguwa ce sosai bata da Kiba Kirjinta kadai ne yake Tudu daga kasanta kuma ba wani abun kirki Sai Doguwar Fuskarta Kalar Fatarta baka ce ammh Ta samu Hutu da Jin Dadi,bata da Dogon Hanci Sai dai kana ganinta zaka Fahimci Ta Hada Jinsi da Fulani ko ta Uba ko ta Uwa tun bare ma yanayin Tsawonta da Idanuwanta Masu Dauke da gashin ido da kuma Gashinta Data Tufkeshi Har ya sauko Zuwa ga wuyanta. Sanye Take da wata karamar Riga kamar Shimi Doguwa kanta ba Dankwali Sai Faman loda kaya take cikin wata Trolley bayan wadanda Tagama Durawa akwatuna Hudu gasunan a jere asaman Dan madaidaicin gadonta. Har aka Bude Kofar aka Shigo Bata sani ba sai da taji Daga Bayanta ance"Auta wannan Uban kayan Duk na zuwa Kanon ne..? Muryan wani Namiji ya Fadi hakan da Sauri ta waigo Tana kallonsa Shima kamar ita yake sai dai abun mamaki Shi Fari ne kuma ya Fita Dogon Hanci da Jikin Maza saboda yana da Dam Kiba ammh da tsawon da yanayin komai iri Dayane,Shekarunsa kuwa baza su wuce 30 aduniya ba Zurawa Tayi da gudu zuwa gareshi ta Rumgumeshi Tana Fadin"Ya Bashir..Yaushe kazo..? Yana Mirmishi ya Shafa kanta yana Fadin"Autan Umma Kenan..Yanzu na Shigo nazo kawo su Abiden ne sun saka Rigiman wajen Umma yau zasu kwana.."Fuska Ta tabe kafin tace"Nifa ban gane musu bane..Suna so su kwacemin mtsayina wajen Umma da Da Daddy.."Yana Dariya yace"Wane su su kwace gwamnatin autan Umma da Daddy..Shalelen Ya Bashir da Anty Hauwa.."Tanajin wannan kirarin ta washe baki Tana Fadin"Shiyasa nake matukar sonka Ya Bashir..Zan yi kewarka in na tafi kano.." Ta karishe Fada Kamar tayi kuka irin na Shagwabbun yara bai samu Zarafin mgana ba wata Mata Baka mai Fadin Fuska wacce sai da ta Shigo na Fahimci inda ta Dibo Bakin Fatarta da Hancinta irin nata ne sak,Sai dai ita bata da Tsawo a Shekaru bazata gaza 40 ba Tana Shigowa ta gansu ahaka ta Tabe baki Tana Fadin"Kana nan kana Biye Shiriritar INTEESAR KO.? tun Dazu nake mata mganar ta Rage wadanan kayan taki jin mganata Ta kwashe Rabin kayanta kamar Chaj zata koma Har Abada..! Umma ta Fada Cikin kara Bayyana mamakinta Wacce aka kira da Intesar ta Fara Buga kafa na Shagwaba Tana Fadin"to ni Umma ba Karatu zan Tafi ba..Kuma ai ance yan Jami"a fa yan gayu ne sosai Dole nima naje da kayan gayuna kada wata ma ta Rainani.."Ya Bashir ya saka Dariya yana Fadin"Hakane fa Intin Umma..Gwara kije da Kayanki Jjc Student.."Ya karishe Fada yana Dariya jin Abunda yace ne yasa ta Nakwa nakwa kamar Zatayi kuka ta Kwashi Gudu Ta Fice Daga Dakin Tana Kukan Shagwabarta Tana Fadin"Sai na gayama Daddy..Kai da Umma kun hademin kai kuna min Dariya..! Umma ta Tabe baki ta kalle Bashir Dake Dariya tace"Kabiya ta Kitchen ka Karbi Dambun Wajen Talatu katafin ma Hauwa"u dashi.."Cikin Ladabi yace"To Umma..Angode.."Batayi mgana ta Fice Daga Dakin Shima ya Rufa mata Baya Jin Daddy na Kiran sunansa Topa Auta ta kai Sunansa yau shi da Daddy sai Allah Dariya kawai yake kasa kasa Har ya Kariso Falon. *Shakira...* 3/22/22, 23:02 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..*! _(Our House)_ *Book1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty*�� *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *🅿�3* "Da sallama ya Shigo Falon yana Danne Dariyansa ganin Inteesar dare Dare kan cinyar Daddy Tana ta Zubamai Shagwaba shi kuma yana ta Biye mata yana Lallashinta ga Abideen da Abida suna Tsaye gefe suna kallonta Daga duk alamu suna kan Jikin Daddy din ne tazo ta Turesu ta Haye Daman tace wajenta ne suke Neman su kwace mata. *ALHAJI MUSTAPHA HAMISU DUKKU* ya Dago kyakyawan Farar Fuskarsa Tar da ita kamar ataba Jini ya Fito,Hancinsa Har baka yake kana masa kallon Farko zaka Shaida Tabbas Bafullace ne,Akallah Shekara bazai gaza Shekaru 58 aduniya ba Fararsa ta goge da jin Dadi da Hutu In ka kara kallonsa zaka Fahinci inda suka Dauko Tsawo da Doguwar Fuska Daga Bashir din Har Inteesar din sai dai Bashir Hasken Mahaifinsa ya Debo wanda Gashin kansa da Gemunsa suka Fara Zama Fari bakin gashin kadan ne Daga ganin sa yana da yalwar gargasa ajikinsa. Cikin Muryansa ta Dattako ya kalli Bashir yana Fadin"Taho nan..Naji Meyasa kuka Tasa Autana agaba kuna mata Dariya kai da Mamarka..? Yafada yana dan Hade ransa ganin yadda Inti din ke kallonsa Bashir na kanne Dariyansa ya Zauna akasa Kusa da Kafar Daddy,Da gudu kuwa su Abiden suka Nufesa ya Daukesu ya aza kan jikinsa,Daga ganinsu yan Biyu ne saboda suna da Tsananin kama da juna Shekarasu bazai Wuce 3 aduniya ba yara ne kanana sai dai sun Debo Tsawon Babansu suna da Tsayi ba Laifi. Cikin Ladabi yace"Daddy ba Dariya muke mata bafa..Ita Da Umma ne tana mata Fadan Ta Dibi kaya dayawa Shine tace saboda kada taje yan Jami"a su Raina Sai fa kawai nace Jjc shikenan fa Daddy ta Fara Shagwabarta.."Ya karisa Fada Daidai Lokacin da Umma ta Fito Daga Bedroom din Dake Cikin Falon,Ta kariso kusa da Daddy ta Zauna Tana Kallon Intisar Lokaci Daya Tana Fadin"Ke miye haka..? Ko kunya baki ji ba Godai godai Dake kin Ture yara kasa ke Kin Hau Cinya ko.? Anya Inti kina so ki Girma kuwa.? Yarinya kina Girma kina kara Komawa baya koda yake ba Laifin ki bane na Alhaji ne duk ya Sangartaki.." Ko kafin tagama Mganarta Bakin Inti ya kusa Fadowa kasa Cikin Sangarta Ta kalli Daddy Tana Fadin"Daddy kaji Umma ko..? Shiyasa nake ta Murna zan Tafi na bar mata gidan.."Ta karishe Fada tana wani Tura baki. Umma ta tabe baki Tana Fadin"Ai chan bazaki samu Damar yin wannan Sangarta ba..Yaya Amina ba Irin Sakarkarun Matanan bane atsaye take..Ga kuma yayanki Sagir zan ce mai da kinyi wani Abu ya Zanemin ke.."Kawai ba sai Inti ta Saki kuka Kamar wata karamar yarinyar Bashir sai Dariya yake Umma ta kalleta Sororo kafin tace"Yau naga Sakalci Inti wai yaushe Zaki Girma ne..? Kin fa wuce Shekara ashirin Kina Shirin Shiga Jami"a kina Tabara Yau ko aurar dake mukayi Badi war haka kin Haihu.."Ai jin haka sai Inti ta kara Sautin kukanta Tanayi Tana Fadin"Ni ba zanyi aure ba..Kuma bazan Haihu ba.."Kai Dagajin kukan kasan na Sangarta ne Daddy ke Lallashinta yana Fadin"To daman yaushe Autana ta isa aure..!? Ai ba yanzu zaki aure ba sai kin kara girma...Shima sai naga Dacewar Mijin da Zaki aura wanda zai Rikemin ke ya Rika Lallabaki kamar yadda nake Lallabaki sai yayimin alkawarin kula da Hakan kana zan yarda na Bashi Autana.."Ya karishe Fada yana Shafa Kumatunta da Sauri ta Washe baki Lokaci Daya Tana Fadin"Shiyasa nafi sonka..Akan Umma Daddy..Kafi sona..Ita kuwa ssi ta cemin wai ni Shagwabbiyace.." Daddy yace"Rabu da ita...Duk yan Bakin ciki ne.."Ya Bashir na Dariya yace'Hardani Intin Umma..? Tana wani mele baki Tace"Ni ba Intin Umma bace..Intin Daddynta ne.."Umma na jinta Tayi tsaki Tana Fadin'Nabarmai yayi ta kaya..Ni ai Bashir ne D'ana..Ni Daman ba Mamanki bace Daga Gidan Marayu Alhaji ya Dauko ki.."Baki ta Bare zata kara sakin kuka Daddy ya Riketa yana Fadin"Au kukan zaki mata..? Daman ta Fadane don ta saki kuka..Haushin kinfi sona ne Autana Rabu dasu.." Washe baki Tayi tana Fadin"Yauwa Daddyna..Ammh zaka Kira Inna Amina kamata mgana ko..? Kaji fa umma nacewa Zata saka D'anta wai ya Rika Dukana.."Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Domin inti akwai Tsoron Duka. Kanta yake Shafawa yana Fadin"Waneshi ya Dakarmin Auta guda..? Sha kurumin ki ni Dakaina zan kai ki Har kano gaban Innan naki na Bada Amanarki kana naja ma D'an wajen nata kunni komai kikayi kada ya Dakeki ya Lallabaki ne Saboda ke Auta ce.."Murna Ta Farayi ta Rumgumeshi Tana Fadin"Ina Kaunarka Daddyna."Kanta yake Shafawa yana Fadin"Nima haka Auta Daga ke ba Kari Intin Babanta.."Umma Dake Goge ma Abidin Baki Daya bata da Madara tace"Uhm..Bashir tashi ka Tafi gidanka kada ka Biyema wannan Shirmen na Alhaji da yarsa..Kabar Hauwa ita kadai gashi kuma kasan Halin Datake Ciki.."Yana Kokarin mikewa yace"To Umma..." Yafada yana Mika mata Abida Data Fara Barci ta karbeta Lokaci Daya yana Fadin"Daddy zan tafi..Sai Allah ya kaimu.! Daddy yace"Shikenan Bashir.Ya ake Ciki kan mganar Tafiyar Inti din..? Kunyi mgana da yaron Wajen Innan naku..? Bashir yace"Eh Daddy munyi mgana..Lokaci fa ya tafi Tuni sun Fara Lacture ya kamata Cikin Satin nan Tatafi tayi Registration Sati na Sama ta Fara karatu gaskiya.." Daddy ya Jinjina kai yana Fadin"Shikenan Zuwa Jibi sai muje na kaita..Insha Allahu kafin Lokacin Komai ya kamallah ko Autana..? Inti ta gyada kai Tana Fadin"Daddy ai kagama Siyan min komai fa Abu Daya ya Rage f..? Yana kallonta yace"Menene shi Autana..? Cikin Daga kai tace"Sabuwar waya Daddy...Taya zan je da Wannan Tsohuwar wayar Jami"a ai sai su raina maka ni.."Ta karishe Fada tana wani Hura Hanci Umma ta saki Baki Tana kallonta kafin Tayi mgana Daddy yace"Hakane kuma fa..To kada ki Damu zuwa gobe Bashir zai je ya Dubo miki wata iri kike so.? Da sauri tace"Samsung Daddy..Ina sonta sosai.."Daddy yace"Shikenan Angama Intin Daddynta..! Dariya ta saki mai kayatarwa Tana Fadin"Nagode Daddyna..! Umma dake zaune tace"Ka biye mata kuma..? Wayata fa ko wata Biyar Batayi ba Daka Siya mata bafa..Haba Alhaji bai kamata kana Biye ma yarinyar nan ba..Yakamata ka Rika Duba Rayuwa in yau mune gobe bamu bane Haka koda yaushe Daada na Fadamaka in mukaje Gaishesu taga Inti na wannan Tabaran ko bakomai watarana Gidan wani Zataje.."Yana jinta bai yi mgana ba Illah kallon Inti Dayayi wacce ta batarai yace"Autana jeki ki kwanta kinji ko..? Sai da Safe.."Batayi Gaddama ba ta Mike Tana Fadin"Gud Night Daddy..Umma sai da Safe Ya Bashi ka gaida Anty Hauwa.."Dukkansu suka amsa mata Umma tace"Zo ki Dauki Abida wajen ki zasu kwana..'Baki ta Tura tana Fadin"Wajena kuma Umma..? Tab ni wlh A"a Shegun kukane dasu..Hanani barci fa suke Cikin Dare.."Ta fada kamar Zatayi kuka Umma tace"Allah..? Naga yadda zaki kare in kika Haifi naki..! Inti na Dariya tace"Daddy na zai Daukan min mai Reno.."da Filon Kujera Umma taRakata dashi Inti ta kwashi Gudu Zuwa Dakinta Tana Dariya Bashir ma Dariyan yake Shi da Daddy,sallama yayi musu ya Biya Kicthen ya Gaida Talatu daya Tarar tana wanke wanke Kafin yayi mgana ma Ta mikomai kulan Umma ta gayamata ya Fice Su Umma ya karama Sallama suka Rakashi da Allah ya kiyaye ya Fice Zuwa Haraban gidan ya Shiga Motar sa Kiran 4matic ya Zuba Hon megadi ya Bude mai get ya Fice Daga Gidan ya Dauki Titin anguwan Rimi inda gidansa yake. Sai da sukaji Tashin Motarsa kana Daddy ya juyo yana kallon Umma yana Fadin"Meyasa koda yaushe kike maimaita mgana Dayane Salaha..? So nawa zan gayamiki ki Daina Ganin abubuwan da Inti ke yi a wani abu kar ki manta fa yarinya ce fa In ta girma Zaki ga Duk ta Daina wadanan abubuwan kuma kada Ki manta Sai da Bashir ya Shekara Goma sha Biyu aduniya muka Sameta alokacin da muka Fidda rai da samunta ita kadai ce Mace awajenmu menene Laifin in mun bata kulawa da gata..? Ai hakan bai Hanata zama mai Tarbiya da ilimi ba ina alfahari da ita da kananun Shekarunta ta Sauke qur'ani yanzu kan Haddatanta take,Kuma kina gani Da kuruciyata gashi Zata shiga Jami"a Alhamdulillah bata Taba Jawo mana mgana ba Salaha ni banga abun Damuwa ba.." Ya karishe Fada yana kure ta da ido,Umma ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Uhm..Alhaji kenan wai kana Bani mamaki in kace Inti yarinyace..? Wacce ta Haura Shekara ashirin ce yarinya Alhaji..? Cikin Halin ko inkula yace mata"To in ba yarinya bace Babba ce..? Shekara ashirib Duka Duka nawa take..? Don Allah ki Daina wannan mganar..In bamu kula da yayanmu ba..Ai samun mu ya zama na banza sai mu Daina Fita Neman Salaha..! Sanin bazai Taba Fahimtarta ba yasa ta bar mganar ta Mike Dauke da Abida Tana Fadin"Bari na kai Abida Daki tayi Barci.."Daddy yace"Ga Abidin ma yayi barci ajikina.."Batayi mgana ba ta wuce Ciki Dakinta ta kai Abida ta kwantar kan gadonta kana ta Dawo ta Dauki Abeedin Shi ma takaishi ta kwantar ta Rufa musu bargo ta Rage musu Sanyin Ac ta kuma Rage Hasken Dakin kana ta Rufo musu kofa ta Fito Ta samu Daddy zaune in da Ta barshi ya maida Hankalinsa kan Talabijin yana kallon Labarai Kitchen ta wuce ta samu Talatu na Goge goge Sannu da aiki Tayi mata kai tsaye Fulas din Dake Kan Cabinet din kitchen din ta Nufa ta Dauki karamin mug ta Tsiyayo Ruwan lipton din Dayaji kayan Itatuwa da Ganyen Na"a Na"a ta Fice dashi Zuwa Falo Tana Zuwa Taja Center Table din Dake Tsakiyar falon ta ijiye Tana Fadin"Alhaji ga Ruwan Lipton din nan..! Dago kansa yayi yana Fadin"Yauwa Nagode..'Daukowa tayi ta mikamai ya karba ya Fara Kurba sau Biyu yayi ya Dauko yana kallonta yace"Wata anguwa Su Yaya Aminan suka koma ne Bayan Tashin su Daga zoo road..? Umma tace"Gadan kaya suka koma..Gidan Marigayi din da Sagir din yagada Ta koma Ciki suna zaune.."Daddy ya gyada kai yana Kurban Tea din yace"Sai nake ganin kamar Nauyi zamu kara mata Salaha..! Umma ta kalleshi a kaikace tace"Wani irin Nauyi kuma..? Sai da ya kara Kurban Tea din yana Fadin"Kai mata Inti da zamu yi ta zauna wajenta Tayi karatu..Ga Wahalan Rayuwa ga Kuma Rigiman Diyar taki..! Umma Tayi Mirmishi Tana Fadin"Wlh ko Daya Alhaji..Bakaji da na kirata na gayamata Intisar ta samu addmission anan BUK ba..Kafin na Furta mata ina son Inti ta zauna wajenta sai dai ta rika zuwa Tana Dawo in anyi Hutu sai Tazo mana nan tayi mana Hutu ita ta Fara Cemin ammh wajena Zata zauna ki..? Kasanta da son Diya mace kuma Allah bai Bata ba Danta kenan kwara Daya Sagir..Bayan mutuwar Mahaifinsa kuma tace bata Sha'awar kara aure ba yadda su Baba Bala basu yi da ita ba tace baxata kara aure ba Shiyasa taki Dawowa ta Fara sana"arta achan tana kula da Danta har gashi yana Karatu shima kuma yana Sana"ar dole suka sakamata ido.!. Daddy ya jinjina kai alamun gamsuwa yana Fadin"Hakan ma yayi. tunda wani Lokacin sai kiga karayin auran ma wani abu ne Dabam..Badai shi yaron Dangin Mahaifin nashi na waiwayansa ba..? Umma tace"Eh suna iya bakin kokarinsu..Ai kanin Babbansa Daya Wani Manu..Ko Yaya Aminan wh suna mata kokari..Ita Dayake bamai jira bace macece mai neman na kanta Ko Daga nan gida zaka ga ba kasafai take kira Tanemi wani abu ba.."Daddy yace"Allah sarki..Rabona da kano Tun Rasuwar Mahaifin yaron nata.."Umma tace"Sai gashi Dalilin yarka zai kai ka ko.? Yana Dariya yace"Zaki fara ko..! Kin san bana samun Zama ne..Allah ma ya Taimakeni Bashir yanzu yana kula da komai.."Umma tace"Gaskiya fa..! Daddy ya mika mata Mug din yana Fadin"Naji Dadi da Inti Tana da inda Zata zauna..Dama bana son zaman Hostel sam kinsanta Tana da Tsiwa kuma bata saba Zama cikin mutane ba..Uwa uba da kuma D'an wajen nata ko bakomai zai rika Taimakata awasu abubuwan Tunda Bashir ma yace shima nan yake Karatun nashi.."Umma tace"Eh Haka Yayan tacemin..Ya kusa gamawa tace shi.."Daddy ya Mike yana Mika yace"Shikenan dai..Zuwa gobe ki kamalla mata komai jibi zamu tafi insha Allahu.."Umma ta mike Itama Tana Fadin"Allah ya kaimu..Miya ce zan mata..Dambun namanta na Soya mata..Sai su Snaks Datace Tana so nayi ma kawata Mgana Gobe za"a kawo.."Hanyar Dakinsa ya Nufa yana Fadin"Ina jiranki aciki.."Hanyar Kitchen ta Nufa Dauke da Mug din Tana Fadin"Gani nan Tafe..Baban Inteesar.."Yana jinta yayi Mirmishi ya Shige Cikin Bedroom din Dayake mallakinsa,Umma Data fito Daga kitchen din Kashe Tibin Tayi Kafin ta Rufamasa Baya. ******* Yusuf ne ke Tallafe da Abba yana Bashi Tea abaki Munari na Gefensa Tana mikamai Buredi mai yanka yanka yana Bama Abba Imran na Tsaye Daga Jikin Wardrope din Dake Dakin Abba yana Sanye da Farar Singelet da Wani Bakin wando 3quater,Hannunsa sanye Duka Cikin aljihun wandonsa Allah ya Taimaka yau ba"a Busa abun Ransa ya Hade Tamau kamar bai Taba Dariya ba yanayin yadda yake Tsayen kiris yaje jira atabashi ya Fashe. Har Yusuf yagama Bama Abba Tea din ya bashi mgangunansa yana kokarin maidashi ya kwanta Imu Dake Tsaye yace"Ka barsa ma Ruwan zafi yabi Jikin nashi.."Yafada Cikin muryansa mai Cike da Amo da zati. .bai yi gaddama ba Munari ta sakamai Karamin Filo a bayansa suka Jinginshi ya Dago yana kallonsu yana Fadin"Allah yayi muku albarka.."Yusuf yayi Mirmishi ya amsa da Ameen Abba Allah ya baka Lafiya Dukkansu suka amsa da Ameen kafin Yuauf ya Zarce da Fadin"Na Fara Tunanin ko mu Sauya ma Abba Likita ne..? Imran Dake Duke da kansa yace"Saboda Mene..? Yusuf yace"Bana ganin wani Cigaba..Kullum Abba jiya iyau..Kamar ma Baya yafi akan yanzu.." Imran ya shafa Gashin kansa Dayayi Uban Dada yace"Ai ba Laifin Likitan bane.."Yusuf ya Kalleshi yana Fadin"Kake gani..? Imran yace"Kaima ka sani ko..? Yafada yana kallon Maimuna Dake kallonsa Cikin Hararanta yace"ke Lafiya kike kallona kamar Wata mayyah..? Da sauri ta kauda kanta karamin Tsaki yaja yana Fadin"Tashi ki Fita ma..Kinsan bana son yawan kallo ko..? Kwalkwal Tayi da ido kamar Zatayi kuka Zaburo mata yayi yana Fadin"Au bazaki tashi ba kin tsayane kina neman min kuka.? Fice anan kafin ki Tunzurani na Miki Dameji da Fuska.."Da Sauri tatashi Ta Fice Dauke da Mug din da Abba yasha Taa da Bread din. Yusuf ya kalleshi yana Fadin"Wai waya bata maka rai ne..Kazo ka sauke kan Munari.? Bai samu Zarafin mgana ba sukaji Muryan Abba yana Fadin"Kabi ahankali IMRAN...'Yafada ahankali Cikin Sanyin Murya duk sai Jikin Imran din yayi sanyi Kawai sai ya gyada kai yana Fadin'"Mubar Abba ya samu barci..Muje Dakina muyi mgana achan..! Daga Haka ya Fice yana Takunsa na Daya Bayan Daya. Sai da Yusuf ya ggyarama Abba kwanciya kana ya Baro Dakin Gidan Shuru kamar ko Yaushe Munari yassn ta kwanta Tunda Imu yayi mata jan ido. Dakin Imran din ya Shiga Cikin mamakinsa ya samesa yana Busa abar tashi Girgiza kai yayi yana Fadin"Wai kai baka gajiya da Busa Hayaki ne..? Kada ta maka illah Fa Imran..! Cikin Lumahe ido yace"Me yayi saura..? Ai ni Daman Tuni Illah ta gama illatani Hayakin Saura ya samu! Jin haka yasa Jikin Yusuf yayi sanyi kawai sai ya zauna Gefensa yana Fadin"Hakane..Ammh akallah muyi kokarin ganin mu Rayu Cikin Farinciki ko Saboda Abba.." Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace"Ya mganar Tura mgabatanka gidansu yarinyar nan..? Yusuf ya sauke ajiyar rai yana Fadin"Nima bansan ya za"ayi ba..Kuma Mahaifin nata niyake Sauraro.." Imran ya Busar Tabarsa yace"Wazaka Tura..? Yusuf ya kalleshi yace"Bansani ba..Ammh nafara Tunanin kiran gida na Sanar dasu inda muke da kuma abunda ke Faruwa akallah koda bamu koma wajensu ba zasu zo sukaga inda muke kuma Duniya Zata shaida bamu kadai bane AGIDANMU muma muna da Ahali.." Kamar wani Kumurci haka ya Mike yana Fadin"Kar ma ka Fara Ya Yusuf Kada ma fara nace....! Yafada da karfi yana Nuna yusuf din da Yatsa Mikewa yayi shima yana Fadin"Nima ba yadda zanyi ne hakan shine mafita..Domin aure ai ba wasa bane.."Imran yace"Ko ka kirasu sunzo babu Abunda zai Sauya su bazasu Taba Fahintarmu ba muma bazamu Fahimcesu ba..Zasu zo ne su kara Daukan Hauka su Dora ma Abba..Su Rika Bleeming dinsa kan Abubuwan da suke Faruwa..Muma ai ba Laifinmu bane Kaddaran Allah ne da Jarabawansa Saboda haka kada ka sake ka kira wani Ballatana a Fahimci inda muke gwara mu Cigaba da Rayuwar ahakan Tafiye mana zama inda baza"a Taba Fahimtar mu ba ballatana abamu Uzuri..! Ya karishe Fada Cikin kunar rai yana ji kamar alokacin ne abubuwa suke ta Faruwa. Dafasa Yusuf yayi yana Fadin"Na Fahimce kayanzu ina Mafita...? Kai Imran ya Shafa Lokaci Daya yana kai ma Gemunsa Wutan Taban Dake hannunsa da Sauri Yusuf ya Buge hannunsa Taban ta Fadi kasa Cikin Fada yace"miye haka..?Zaka yi ma kanka Lahani da kanka fa..! Mirmishi Imran ya saki yana Fadin"Common Bro..It's Normal fa.."Karamin Tsaki Yusuf Yaja yana yin baya Lokaci Daya yace"Kayi ma yi wanka yau kuwa..? Wlh duk warin Taban kake yi bakin ka kuwa kamar sokaye.." Imran bai Damu ba sai ma Dariya daya saki yabi Yusuf din yana Busamai iskan bakinsa Yusuf kuma yana mtsawa bayana Fadin"Don"t Come close..Imu Bari..Allah zan yi Amai.."Cikin Dariyan keta yace"Aman nake son na gani.."Da gudu ya Bisa shi kuma ya kwasa Zuwa Tiolet dinsa ya Rufo yana sauke Numfashi Dariya ta kama Imran ya Dinga kyakyatawa Cikin mamaki Domin ayanayinsa sai kace bai Taba Dariya ba. Kofar Tiolet din yaxo ya tsaya yana Fadin"Matsoraci Fito..Wasa ya kare..".daga ciki Yusuf yace"naki wayon...! Imran yace"Baka yarda dani ba..? Yusuf yace"Kace Wlh ka bari..! Imran na Danne Dariyansa yace"I swear na bari.."Sai alokacin Yusuf ya Bude kofar ya Leko da Sauri Imran ya Turo Kofar ya Jawosa suna Dariya gabadayansu kan gadon Imran din suka Fada Yusuf ya Mirgina gefe yana Fadin"Imu kazami..Matarka zata sha waharka..! Imran yace"Daman shi tazo yi..!. Yusuf yace"Wahalar..? Imran ya Zakuda kafada yace"Ofcourse..!. Tashi Zaune Yusuf yayi yana Fadib"To Allah ya shirye ka..! Imran yace"Ameen Shirin Allah bata Jigidan mata ba.." Yusuf dau sai dariya yake kafin yace"Tashi..What is d Solution.." Imran na kwance Rigingine yace"Baban Sagir zamu je muyi na mgana Shi zai nemi mutane su Shige maka gaba..! Yusuf yayi shuru kafin yace"Baba Manu..? Imran ya gyadamai kai Da sauri yace"Kana ganin zai yarda..? Imran ya Mike yana wani Tangadi kamar wanda yasha Giya yace"Kada ma yarda..Yagani..! Yafada daidai Lokacin Daya abude Kofar Tiolet dinsa Yusuf ya Kallesa yana Fadin"Naga kana layi..Anya Imu baka Fara Kora Giya ko Tabar wiwi ba..? Yana jinsa yamasa banza sai da ya Shiga Tiolet din kana ya leko yana Fadin'"Ban fara ba ammh Sai da Kafada naga ya kamata na Fara Tanque for ur Advice Bro..! Lokaci daya ya maida Kofar ya Rufe Yusuf yayi Dariya ya Jinjina kai yace"Imu...Imran...Ta bakin Abba yace Imran..Imran Rigima.."Daga haka ya Fice Daga Dakin zuwa nashi yasan Kila Safiya nata kiran wayarsa Daya barta adaki. *Tanque Masoyana naji dadin yadda kuka karbi wannan Labarin I promise u bazan baku kunya ba..* *Shakira...* 3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..!* _(Our House)_ *Book1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *🅿�4* "Ya fito Daga lacture din da suka shiga ta safe kenan yaji wayarsa Dake cikin Aljihun wandonsa na kara yana Fitowa da wayar yaga Sunan mai kiran nashi DAN ISKAN ABOKINA..! Sai da yayi mirmishi Daya ga sunan mai kiran Saboda ya Tuna sanda Abun ya faru,Ranar suna zaune ashagonsa ne Sai Wayar Sagir din ta Fada cikin kayan Dinkin mutane Dake kasa akayi ta Nema ba"a gani ba sai ya karbi Wayar Imran din da Niyyar ya kira Wayarshi yana saka Lambarsa yaga Sunansa ya Fito da BANZAN ABOKINA..! Galala yayi yana kallon Imran din Dayake kallon wani barayi Kamar ma baisan da Mutane a Shagon ba an ci Sa"a Ranar bai shigo yana zukan Taba nasa ba Daga dukkan alamu akwai abunda ke damunsa Ranar kuma bayaso Tattaunawa da kowa kuma baya son ya zauna agidan Shiyasa ya fito yazo shagon Sagir din ya zauna batare da ya Tankama Sagir din ba Duk da Tarin Tambayoyin daya rika Jefansa dashi. Cikin Jin haushi Sagir yace"Nine ma Banzan ko..? Batare da ya kalli Sagir din ba yace"Eh Ko kana da wani suna ne Bayan Banza..? Sagir ya kada kai yana Fadin"Wlh nima sai na Rama..! Yafada daidai Lokacin da ya kira Wayar tasa yaji kaaranta nan cikin kayan ya Tafi ya Dauko Yana Fadin"Kaima sunan banzan daka sakamin zan saka maka..Me ma zan saka maka ne..? Yafada da Sigar Tunani Batare da Sagir yayi aune ba Imran ya karbi Wayarsa Bayan ya taso Ya Goge sunansa da Sagir ya saka mai Ya maida masa da Da'n iskan Abokina kana ya mikamai yana Fadin"Gashi na Rama maka..! Ya karba yana gani kafin yace"Kai..! Dan iska ne kenan da gaske..? Imran ya Zakuda kafada Lokaci Daya yana Saka Duka Hannuwansa Cikin aljihun Wandonsa,ya Kama Hanyar Ficewa Daga Shagon yana Fadin"Eh ai Dan iska ne..! Daga haka ya fice Daga Shagon bai Damu da kallon da Sagir ke Jifansa dashi ba,Bai yi mamaki ba Sanin Halin Imran kai fi Dayane shi Gashi bashi da Tsoro,baya karya domin ka so shi ko ka yabeshi baya jin Nauyin gayamaka Gaskiya komai Dacinta baida Boye Boye ko Kumbiya Kumbiya shi Mutum ne Street Forword baya Munafunci Ballatana gulma baya jin kunya yace yana aikata wani abu koda Zaka Tsireahi ne,Wannan Hallayar nashi suna matukar Birge Sagir dashi shi kanshi ya san Imran Jajirtattace ne kuma Jarumi ne sai dai abu Dayane ya kasa ganewa game dashi..Menene Takamemmen Abunda ya Faru dashi..? Domin in bai manta ba Imran din da kansa ya Fadamai abaya ya Tsani mai Shan Taba ko Warinsa Baya son ji ammh Saboda kaddaran Rayuwa yanzu yafi kowa jin Dadin Shanta aduniya. Ko haduwarsu Allah ne ya Hadasu Tunda suka Dawo anguwarsu basu Taba Mu"amala da kowa ba sun kebe kansu iya su kadai Gidansu da suke zaune yanzu Babu Nisa da gidansu Sagir din gidaje kalilan ne Tsakani kuma ada asalin megidan Rasuwa yayi sai aka Siyar da gidan kila Lokacin ne su Imran suka mallaki gidan. Tun Dawowarsu anguwan Sagir yake ganin Imran da safe in ya Fito Jogging,shi kuma lokacin bai Dade da Bude shagon sa Dake kofar gidansu ba alokacin bashi da wani yaro shi kadai ne yake Dinkinsa da keke guda Daya. Akullum da safe yana ganin Imran Haka kuwa Allah ya Doramai kaunarsa Duk da basu Taba mgana ba ammh Shi kanshi Imran din in yazo wajen Shagon na Sagir sai ya tsaya sun ma juna kallo kallon kafin ya wuce. Watarana ne Imran din ya zauna yana Shan Taba abakin Shagon Sagir din Abunda ya kara bama Sagir mamaki bai Dace ace kamar Imran nashan Taba ba Daga ganinsa bai rasa komai na Rayuwa ba a kallon Farko ya Fahimci Imran yana da ilimi da Wayewar sanin Rayuwa haka kurum yaji yana so ya samu kusanci da Imran din Dalilin haka yasa Washegari da Safe da Imran din ya Fito Jogging Shima ya Fito har ya samu nasaran suka Bangaji juna kalma ta Farko da Imran ya Fara gayamai bayan sun gama karema Juna kallo "Kai baka ganina ina Tahowa ne..? Sai Sagir ya Ballamai Harara yana fadin"In na ganka sai me..? Hanyar ai bata gidanku bace..! Sai kalaman suka bama Imran Dariya Har sai da ya Murmusa ganin haka yasa Sagir ya bashi Hannu yana Fadin"Sunana Sagir kaifa abokina..? Kamar bazai bashi Hannun ba Saboda baya Bukatar wata mu"amala da kowa ko afarkon Rayuwarsa bai yi Abota ba ballatana yanzu da abubuwa suka Sauya sai dai ya kasa Kin bama Sagir din hannu Kamar Zuciyarsa na Jansa..Kaunarsu da abotarsu Daga Allah ne Mikamai hannu yayi yana Fadin"Imran..! Daga haka bai kara cewa komai ba Sagir ne ya Dingamai Zuba yana Nunamai gidansu,Har da gayamai wasu Tarihin Rayuwarsa na Rasuwar mahaifinsa da kuma Inda yakezaune shi da Mahaifiyarsa harda matakin karatunsa Shidai Imran Jinsa kawai yake yana mamakin Sagir daga Haduwa dashi sai ya fara gayamai wani abu a kansa..? Yana so yace ya kyaleshi ya Dameshi ammh ya kasa Haka kurum yaji bazai iya Wulakanta Sagir ba Duk iya kokarin Imran na kada Shakuwa ta Shiga tsakaninsa da Sagir sai da ta shiga,Shi sagir mutum ne mai barkwanci Da kuma Raha gashi bai da Zuciya da Fushi kome Imran zai Fadamai baya Damuwa Haka zasu Rabu Baram baram ammh Gobe zasu nemi junansu,Duk iya Kokarin Imran na kada Sagir ya shiga Gidansu sai da ya Shiga,Yaya yusuf ya sansa haka ma Maimuna da Abba,Sai dai har gobe Sagir bai san Asalin Labarinsu Koda ya Tambayi Imran baya Fadamai,Labarin da Sagir ya Dinga Bama Inna Amina Na su Imran yasa taji tana son ganinsa Ta shirya Sagir yakai ta har Gidan,Shi kuma Imran din Sagir ne ke jansa Gidansu da karfin Tsiya,Akwai wani al"amarin, da Allah ne kadai ya sani Duk da Imran na Zillewa ammh Sagir da Mahaifiyarsa basu Nuna sun gane ba sun Daukesu Tamkar yan"uwa Duk da Zamewarsa yana zuwa gidansu Sagir din in yajasa,Su shiga ya gaida Mama su kuma ci Abinci in Sagir ya matasamai barin ma in Tayi Abunda yafi so na Danwake. Ajiyar zuciya Sagir ya Sauke,Yana kokarin Daga kiran ta yanke sai yabi bayan kiran Shima Gabda zata Katse Imran din ya Daga kiran yana Fadin"Kai dai banza ne Wlh..Kana ina ina ta kiranka baka Dauka ba.? Yafada cikin Kaushin muryansa Wacce bata da Laushi Sagir yace"Dilla ina makaranta fa! Imran yace"Ok..Gani kofar Shagon ka..yanzu zaka dawo ne ko na Shigo School din na Same ka..? Da sauri Sagir yace"A"a gani nan Dawowa daman Lacture din Safe ce kadai garemu..Ka shiga ka gaida Mama kafim na Shigo..! Shuru Imran yayi bai yi mgana ba Jin haka yasa Sagir yace"Dom Allah ka shiga ku gaisa..Mama nata Tambayanka kwana Biyu bata ganka ba..! Imran yayi karamin Tsaki yana Fadin"Ba wani bata ganni ba kai ka mata wani Munafuncinka..! Sagir na Dariya yace"Ka tsargu ne..? Tsaki Yaja kafin ya yanke kiran Yana Fadin"Ina jiranka kawai mallam..! Imran bai yi Niyar shiga Gidansu Sagir ba sai dai bazai iya Juya alfarma da Kimar Mama ba Macece mai kirki da Dattako Yana Bala"in ganin kimarta Duk kuwa da irin yanayinsa. Cikin Takunsa na Sassarfa da Kazarkazar dinsa ya Nufi Gidansu Sagir din yaran Sagir Dake Shagon suna Nuna sa da baki,suna mamakin yadda Oga sagir ya iya abota dashi Tunda suke dashi bai taba Musu mgana ba kogaishesu sukayi baya amsawa sai dai ya kalli Mutum ya kauda kansa Ko da zai zoSagir baya nan bazai Tanka kowa ba Ko Sallama acikinsa yake,Suna ganin Miskilan maza ammh wannan nashi Miskilancin sun Dangantashi Harda Wulakanci Ya Dade tsaye a zauren gidansu Sagir din ya kasa Shiga yana Tunanin ya Shiga ne koya koma..? Sai dai yana Shirin juyawa ya koma yaji Muryan Maman Tana Fadin"A"a wanake gani kamar Imranu..? Tafada Daidai Lokacin Data karisowa Cikin Zaure Shara tazo Zubarwa Tunda Abun sharan nasu na Zaure ne in ya cika ne almajira ke zuwa ya Zubar ta Biyashi Fara ce sosai ba Yar gajeruwa bata da Tswo mai Fara"a Da Faramfaram da Mutane ba wata Babbace bace a shekaru iyakarta 45,,don ma Wahala da Rayuwa ce data samu jin Dadi datafi haka Yarinta Daga ganta kaga Sagir Saboda Fuskartane ya Debo Musamman ma karan Hancinta Sai dai Tsawon kila Dangin Mahaifinsa ya gado. Cak ya tsaya Tunda ta Riga tagansa juyowa yayi yana Sosa keya Dan ramkwafa Yayi yana gaisheta Mama ta amsa Cikin Sakin Fuska tana Fadin"Ikon Allah kake tsaye kuma a zaure Imrana kamar bako..? Meyasa baka Shigo ba Sagir din ya Fita makaranta Tun safe..! Kansa na kasa yace"Eh munyi mgana dashi..! Mama tace"Shine ka tsaya Daganan Imrana..?sai ya kasa mgana Kansa dai na kasa Mirmishi TayiHaka Allah ya Doramata kaunar yaron ba Domin abotar Dake tsskaninsu da Sagir ba Imran yana da Shiga rai Duk da Muradaddun Hallayarsa Juyawa Tayi tana Fadin"To shigo Daga Ciki ka jirashi ya Dawo..! Bai da yardazai yi Dole ya Cira kafa yabi bayansa Daki ta Shiga ta Daukomai Tabarma ta Shinfidamai a Karamin Tsakar gidan nasu da Maman tagama Shareshi yayi kal kal Dashi Zama yayi kansa na kasa yana jin kansa a Takure haka yake baya iya Sakin Jiki matukar ba a Gidansu ba. Mama ta kawomai Ruwan Purewater Tana Fadin"Ga Ruwa Imrana kasha..! Bai isa yace mata bazai sha ba Bai isa ya kauce ma Kararramawar ta ba,haka ya amsa ya Fasa ya sha kadan ya Rike Sauran A hannunshi yana Tunanin Sagir ya batamai Lokaci. Ganin yadda yayi Shuru ne yasa Maman tace"ya wajen Baban naku Kuma..? Ya su Yusuf da Maimuna kwana Biyu ban shiga na Duba baban naku ba..? Imran ya Saissauta Muryansa yace"Suna lafiya..! Daga haka bai kara mgana ba ya kauda kansa yana kallon wani barayin Mirmishi Mama tayi kafin tace"masha Allah..Allah ya kara lafiya Acigaba da kula kaji Imrana..Rayuwar nan duka sai Hakuri watarana sai Labari..! Kullum yazo sai tayimai wannan Nasihan Dakyar ya iya Bude baki yace"Insha Allahu Mama.." Taji Dadin haka tace"Allah yayi muku albarka.."Aciki ya amsa da Ameen Daidai Lokacin Data mike Daga Kan kujeran Tsugunon Data kai nan kofar dakinta Sai ga Sallaman Sagir ya Shigo Gidan Mama ce kadai ta Daga kai ta amsa banda Imran da kansa ke kasa bai Dago ba saboda ya Shaida Muryan Sagir din. Takalminsa ya Cire ya zauna kusa da Imran din yana gaida Mama ta amsa tana Fadin"Ga Imrana nan tun dazu yana ta jiranka..! Sagir na kallon Imran ganin yadda ya wani Hade rai yasa ya juya ya kalli Mama yana Fadin"Ai mama ni na Turo miki shi nace ya Shigo kina nemansa..! Mama tace"ai ka kyauta Sagir gashi yazomun gaisa..! Sagir na Dariya kasa kasa ganin wani uwar Harara da Imran yake Sakarmai kafin ya Mike yana kokarin saka Budadden Takalminsa na Fatar Damisa yana Fadin"Amobe in kagama munafuncin naka Muje waje ina son mgana Dakai..! Sagir ya mike kenan Mama Data shiga Karamin kitchen din da akayi shi da ginin Bulo an buga kwano ta sama harda kofar Katako Tana fadin"'A"a ina zaku kuma Ga Abinci na sauke Mutumin Imrana nayi Danwake..! Tafada da Fara"arta Sagir ne yayi Saurin cewa"Mama ba Nisa zamu yi ba..yanzu zamu dawo..! Kada kai Tayi tana Fadin"To shikenan ammh ku dawo da wuri kada ya huce kusan baya Dadi kaji Imrana..! Dole ya Bude baki yace'To mama..! Lokaci daya suna Ficewa Daga Gidan Imran na gaba Sagir na Binsa a Baya. Kai tsaye kofar shagon Sagir Imran yaje ya zauna Shima sai Sagir yazauna gefensa yana Fadin"wai menene kake nema na ne..?kayi kayi mganarka yunwa nake ji yau tun safe ko Ruwa bai Shiga Cikina ba mallam..! Kamar ba da Mutum yake mgana ba Shi Imran din ma Hankalinsa na kan Sandar dake hannunsa yana Ta Tada kasan Dake gabansa Sagir ya Kufula yace"kafa Shanyani ina da abunyi mallam..!. Kai tsaye Imran yace"Ni kuma gani wanda bai da nayi ko..? Yafada hankalinsa kwance batare dama ya kalleshi ba Sai kuma sagir din yaji Kamar bai kyauta ba kada kai yayi yana Fadin"Ni ba haka nake nufi b..! Bai gama Rufe baki ba Imran yace"What ever kai ya shafa..Zuwa nayi na gayamaka anjuma zaka rakani gidan Babanka Manu..! Sagir ya kalleshi Cikin mamaki yana Fadin"Wai Baba manu kake nufi..? Imran yace"Kana da wani Baban Bayan shi ne daka ke Tambayata..? Sagir yace"Bansani ba..Kai ne in zakayi ma mutane mgana Gatse gatse..! Mirmishi Imran ya saki kafin ya Gintse Fuskarsa yana Fadin"mutane sun fi gane irin haka ne shiyasa kake ganin ina amfani da hakan..! Sagir yace"Bama wannan ba Me zakaje yi gidan Baba Manu..? Har Sagir ya Cire rai da zai ce wani abu,sai kuma ya Mike Tsaye yana Tusa Dukka hannuwansa Cikin Aljihun bakin wandon Dake Jikinsa,Dayan hannu ya Zaro mai Dauke da kwalin aspen Taba sai kuma ya Zaro Lether bayan ya Zari Daya ya saka abaki ya Kyasta Lether din ya kunnata yayi mata kyakyawan zuka yana wani Lumshe ido Lokaci Daya yana Fesar da Hayakinta zuwa ga Fuskar Sagir wanda yayi Saurin Tashi yaja da Baya yana Fadin"Kaga wulakancin ka ko Imu..? Kafa san bana son warin Taba! Imran ya kallesa da Lumsassun idanuwansa kafin yace"Kuma gashi kana abota damai shanta sai yaya kenan..? Hararansa Sagir yayi yana Fadin"Mallam ka Fadamim me zakaje yi gidan Baba Manu..?Nidai nasan bama Haduwa kuke yi ba in yazo ballatana nace wani abu ya shiga Tsakaninku..! Imran yayi karamin Tsaki Lokaci Daya yana Zukar Tabarsa sai da ya Zuketa son ransa kana yasaketa a kasa ya saka kafa ya Taketa ya Murjeta yana Fadin"Kai banza...Zuwa zan yi nace ya shigema Ya yusuf gaba kan mganar auransa..! Sagir ya saki Hanci da baki kafin yace"Aure kuma? Zai yi aure ne..? Tafiya Imran ya farayi yana Fadin"Eh..Safiya wacce mukaje gidansu jiya ita zai aura Tsohonta yace ya Turo mgabantansa to Abba ne kuma kasan dai Halin Dayake ciki,shine na yanke Shawaran neman Baba manu sai ya Nemi ko abokansa ne suje ayi mganar auran..! Ya fada daidai Lokacin Dayake Tsayawa kofar Gidansu Sagir din Domin Tunda Mama tace Danwake take yi yaji bazai iya Tafiya ba sai yaci Duk Duniya bai ga Wanda yakai Mama iya Danwake ba ko Munari yasa tayi mai in tayi Bai iya ci sai yaji bai ka na Mama Dadi ba. Sagir ya tako ya Biyosa yana Fadin"Anya Baba manu zai yarda kuwa Imu..? Imran bai kallesa ba yace"Saboda mene bazai yarda ba..Aure fa akace ba wani Shashanci ba..! Sagir yace"Ba wannan ba Kasan dai ba mganar aure ba abun wasa bane..Ya kamata ace wannan karon kun Shigo da Danginku cikin mganar Imran..! Yafada yana Fatan Imran dinyace wani abu yau ko zai samu wata makama kan Abunda ya Shafi Imran din da bai sani ba har yau. Ammh sai me Ko kara mgana Imran bai yi mai ya Nufi Cikin Gidansu Sagir din yana Fadin"Mallam ni ban ce kamin Tsarinka ba..in baxaka Rakani ba nasan gidan..! Daga haka ya shige ya barsa Sagir ya Dade yana auna wasu abubuwa,Tunda yake da Imran bayan Abba da Maimuna da Ya yusuf bai taba ganin wani nasu ba ko wasu sun zo gidansu ba su kadai suke Rayuwarsu kuma Dukkansu basu yarda suyi mganar Wani nasu da kowa koshi Duk yadda yake ga Tambayan Imran bai Taba gayamai komai ba sai dai ya Taba Cemai Abba Bafullatanin Gombe ne, wanda Daman ba wanda zai kalle su yasan cewa su din ba masu Hali bane,Tabbas basu yi kama da wadanda Halin Rayuwa ta gasa ba kodaga Gidan da suka Siya suke Ciki Dankakeren gida ne,ammh bai karaya ba zaicigaba da Bin sa har ya gano Abunda yake son ganowa. Shima jikinsa a sanyaye yabi bayansa koda ya shiga ya iske Imran zaune kan Tabarmulan da suka tashi Dazu,yana cin Danwaken da Mama ta Zubamai itama Tana gefe kan kujeran Tsugguno Karisawa yayi shima ya Cire Takalminsa ya zauna kan Tabarman kusa da Imran ya saka Hannunsa cikin Filet din Dake gaban Imran din ya Dauki Cokali ya Debo Danwaken ya kai Bakinsa sai da ya Tauna ya Hadiye kana yace"Wato shine kazo kana ci ko ka jirani ko..? Ko kallonsa Imran bai yi ba yana Cin Danwakensa Mama ce tace"Inafa zaijiraka Tunda kai ka Shiga wata Sabgan.! Bakin Sagir cike da Danwake Yace"Wlh mama muna fa Tare ne muna mgana ya taho kawai ya barni..! Mama tace"Ai kunfi kusa ba Ruwana da shiga tsakaninku Sagir..! Tafada Tana Dariya Shidai Imran bai ce komai ba sai daya koshi ya sha Ruwa bayan ya Tashi yaje bakin makurara ya wanke bakinsa Daidai Lokacin da Sagir ke cewa"Mama Inna Salaha ta kiraki yau..? Mama tace"Eh munyi mgana da ita Dazu take gayamin gobe in Allah ya Kaimu Megidan nata zai kawo Inteesar din da kanta har nan gidan..! Sagir yace"nima Bashir ya kirani Dazu ina makaranta..Shi yake gayamin Baban nasu da kansa zai raka Inteesar cikin makaranta tayi Registration da wasu abubuwan domin akwai Abokansa sosai Laccharori abunda bata karisa ba yana Rokona dom Allah na Taimaka mata ta karisa..! Mama tace"Eh nima bayanin data min kenan ina Ruwan Inteesar.." Sagir yace"Mama gaskiya Suna ji da yarinyar nan kalli fa bama Bashir din ba Baban nasu xai bar komai nashi ya kawota..! Mama tace"Yar gatace sosai..Ita ce fa Autan Salaha har ta Fidda rai da samun Ciki ta samu Cikin Inteesar Tana ganin gata Mussmman wajen Uban.." Sagir na shan Ruwa baysn ya gama yace'"Ni kuwa ban santa ba..! Mama tace"Eh bazaka santa ba Kamar sau Daya Salaha ta taba zuwa Da ita tun tana karama Tun mahaifinka ma nada rai..Duk Zuwan Datakeyi Ita kadai take zuwa gaskiya kai kuma baka Zuwa gidan Salaha in kaje kaduna gaida su Inno Balle kasanta kafi sanin Bashir dim Tunda shi yafi kawota in zata zo..! Sagir ya Jinjina kai yana Mikewa Lokaci Daya yace"ina zuwa Mama in naje nida Muda ammh fa da Dadewa..! Mama tace"Ai abunda nake nuna maka kenan yaran zamanin nan bakwa son zumunci Shi kanshi Mudan yaushe Rabonsa da nam..Ammh nayi mai uzuri yana Taimaka ma Mallam Babba a kasuwa" Sagir yace'Mama nayi Tunanin a gyara Dakin nan sai ta zauna aciki.' yafada yana nuna wani Dakin da ke kusa da dakim mama inda take saka Tarkacenta. Mama tace"A"a duka duka nawa Inteesar take da zan raba wajen zama da ita..Tare zamu zauna da ita adakina ga gadona ta rika kwanciyarta ni kuma sai na kwanta a katifa ba Shikenan ba.." Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan yaji Imran na Fadin"Mama sai an juma ni zan wuce..,! Ashe Tun dazu yana Tsaye ba zai ce yana jinsu ba Sanin Halinsa ba komai yake bama muhimmanci ba abunda ma ya Shafesa bai cika Bashi Damuwa haka ba Mama ta rakaahi da Saka albarka da Sakon gaisuwa wajen Abba Sagir ya saka Takalmi yabi bayansa yana Fadin"bari na rakasa Mama..! Yana Fita yaga Imran har ya mika Hanya Dayake da kafarsa yau ya Fito bai Dauko mashin ba Da Gudu ya Cimmai yana Fadin"Kaifa baka da kirki..Sai ka Tafi ba Sallama..,! Imran na takunsa na Sassarfa Duka Hannuwansa na Cikin Aljihu bai ce ma Sagir kala ba suna dai ta Tafiyansu Sagir ne yace"Yanzu da Daddare zamu je gidan Baba Manun kenan..? Bai tankamai ba sai da suka iso Get din gidansu kana Imran yaja ya Tsaya yana Fadin"Karfe 8:00pm bayan an Fito Sallar Isha"i ka Fito kofar gida bana son ka batamin lokaci..! Daga haka kawai ya Kwankwasa Get din gidan nasu Iro megadi Da Daman yasan ko waye yazo ya Budemai karamar Kofar ya Shige shi kuma ya leko yana gaida Sagir din Daya amsamai Lokaci Daya ya juya ya Fara Tafiya yana Fadi a Fili"Imran akwai iko..kamar jinin Sarauta wannan inda Dan wani Sarki ne da anga Iko..! Bai koma gida ba Shima Shago ya Shiga yana Duba aikin Daya bar musu yau akwai masu karban Dinki da yawa da yayi ma alkawari,Ransa ya baci ganin basu ci karfin aikim ba Dayake Sagir ya sanu manya mata ke kawomai Dinki kuma akaci Sa"a ya iya Harda Dinkin Maza Shiyasa nan da nan Shagonsa ya Daukaka Har ya mallaki yaransa na kansa ganin haka yasa bai jira su ba Ballatana yaji Hakurin da suke bashi ya Haye keke ya Fara Rage wasu ayyukan Haka yake bai da Girman kai sam yana da Zuciya da Neman na kansa ko Domin Mahifiyarsa a koda yaushe yana so yayi ma Imran mgana kan yazo ya koyi Dinki zai Ragemai wani abun Tunda babu Abunda yake yi komai Yusuf ne ke Gudanar dashi. *Shakira...* 3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..!* _(Our House)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *🅿�5* *Da daddare* "Cikin Shirinsa na Fita ya Fito Daga Dakinsa Cikin Shigar riga da wando Black and white,na kamfanin Armani sai kafarsa sanye Cikin Bakin Rufaffen Takalmi na Fatar Damisa Sai hannunsa Dake daure da Bakin agogo na Fatar damisa mai kyau da yarari,Kwantacciyar suman kansa tasha gyara ta kwanta ta karama Fuskarsa kyau da Annuri Sai Bakinsa Wanda Bakin hayaki ya Fara mai dashi Duhu hakan sai ya karamai kyau da wani Haiba.. Fuskar nan nashi a Hade babu Fara"a ko kadan Key din Mashin Dinsa ne a Hannunsa yana Dakawa Sanda ya Fito Falon kamshin Turaransa na Man Daya saba amfani Dashi ya Fara ma Yusuf da Maimuna Sanar isowarsa Cikin Falon. Ya yusuf na Zaune kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Yana makale da waya a kunnensa yana mgana kasa kasa Cikin kwantar dakai Daga gani Da Safiya yake waya ko da wata Macen da Zuciyarsa ta gama yarda da ita. Maimuna kuma Tana Wajen Dinning area Tana jera Warmers da Filets din Data kwaso Daga Kitchen Tunda ya Fito ta Kuramai ido Ganinsa kamar kullum Ba Fara"a da Anuri yasa da Sauri Ta Daga murya Tana Fadin"Barka da Fitowa ya Imu..! Bai amsa mata ba Sai ma wani kallo Daya Bita dashi kafin ya Dauke kansa Ya Juya ya nufi Dakin Abba Bata damu ba sanin Halinsa baki ta tabe kawai ta juya zuwa Kichen ta Dauko Ruwa da Kofuna,Yusuf kuma Dake waya bai katse ba ya bishi da kallo Har ya Bude Dakin Abba ya Shiga da yar Karamar sallamarsa Ciki ciki kamar wanda akace yayi ta Dole. Har Gaban gadon da Abba ke kwance ya karisa cak ya Tsaya yana Kallon Abba Dake kwance Sambal akan gadon da ya zame masa Kamar wani Maginjini ko nace abun Dogaro ya kwana akai ya tashi akai ya kuma karishe wuninsa akai sanye yake da Farar Jallabiya a jikinsa Gashin Bakinsa da gemunsa ya cika alamun yana Bukatar a Rageshi Dogon Hancinsa ya kara Fitowa da Kyakyawan Fuskarsa ta Fulanin asali. Kuramasa ido Imran yayi yana jin Taruwar wasu Hawaye a kwarmin Idanuwansa Durkusawa yayi agaban gadon yana kallon Idanuwan Abba suna Lumshe alamun ya samu natsuwa Cikin Barcinsa. Hannunsa ya Riko Cikin Nashi yana Faman kokuwa da Numfashinsa Wasu al"amura da suka Shude suna kokarin Dawowamai Daki Daki yana Tuna Abba da Sadaukarwarn sa kan Iyalinsa da yan"uwansa ammh yau Dalilin Wata kaddara Kalli Halin Daya koma. Rauninsa ne ya Fara Bayyana Kamar zai yi kuka ammh kuma bai yin ba yayi maza ya Matse Hawayensa suka koma Lokaci Daya ya Mike Bayan ya saki Hannun Abba Yana Fadin"Allah ya Baka Lafiya Abba..! Daga Haka ya juya ya Fice Daga Dakin da Sauri Cikin Sassafarsa Daya saba akoda yaushe. Wannan karon Munari bata Falon Sai Yusuf kadai Dake kan Dinning yana cin Abinci Fitowar Imran Da kokarin Fita Dayake yasa ya Daga murya ya kirasa "Imu...! Tsayawa yayi Lokaci Daya ya waigo yana kallonsa abincin gabansa ya Nuna mai da ido kafin yace"Ina zaka kuma ga abinci Munari ta gama..? Yamutsa Fuska yayi kadan kafin yace"Am ok..! Ya juya zai Sake yunkurin Fita yaji Yusuf din na Fadin"Wai ina Zakane da Daran nan kake ta wannan Uban Saurin..? Kodai kodai..? Yafada Cikin Sigan Zolaya Jin haka yasa Imran ya juyo yana kara Hade Ransa yace"Kodai What..? Yusuf na kai loman Shinkafa da Miyar da Munari tayi yake Fadin"Ko dai Zence zaka ne..? Imran ya wani Kallesa Sheke sheke kafin yace"Menene kuma wani Zence..? Yusuf yace"Nufina Tadi zaka je wajen Budurwan ka Dakayi..Domin wannan gayun ina hasashen nata ne..! In ba domin ya yusuf bane Ashar yaso ya Dankara mai sai kuma ya Fasa ya karkace kai bayan ya Tusa Duka Hannuwansa Cikin Aljihun wandonsa yace"Abba nata barci ya ko tashi yayi Sallah..? Ya kauda Hiran Saboda bayaso Tayi tsawo Lokaci Daya kuma yana Fito da hannunsa agogon Dake Tsitsiyan Hannunsa yake Dubawa. Yusuf ya kada kai kawai yace"bai yi ba..Kasan Dr.Ya sauyamai mgani wannan karon so akwai masu saka Barci sosai..Zuwa 9 insha Allahu zai Tashi da kansa.Ammh fa bazan fasa Fadin Zence zaka ba..! Ya karishe Fada yana kunshe Dariyansa Lokaci Daya yana Tsiyaya Ruwa a glass Cup yasha ya koshi kana ya mike ya Zari Tissue yana goge bakinsa kafin ya Fara takowa Tsakiyar Falon. Yana kallon Fuskar Imran din wanda yayi shuru kawai yana Kallon Yusuf din kamar ya Makeshi haka yaje ji..? Shi Imran ne zai je Tadi ko menene ma yace..? Allah ya Tsareshi.. Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ni Imran ne zan je Zence kace ma kofar gidan wata yarinya..?Ni..Over my Death Body Wlh..! Yafada yana wani mele baki Yusuf ya karosa gabansa Lokaci Daya yana Fadin"Common Kada ka Cika baki..Sai dai in bazakayi aure ba in ko Zakayi Dole sai ka Sauke wannan Ra"ayin naka kaji..! Imran yace"Saboda me..? Nifa Shiyasa bana son Hada Shirgina da mata..Kasanni bana son Raini ko kadan su kuma da sunga kana Sakarmusu Fuska sai Raini ya Shigo Ciki..Ni aure bai Taba Zama Dole gareni ba sai don yana Sunnar ma"aiki in ma ya Zama Dolen zan yi auran sai na Ga wacce ita take sona zata iya Zama Dani tayi Hakuri dani kuma In har taji Tagani Shikenan Fine ammh ni kam bazan iya Lalacewa gaban Mace ina Rage Murya ba Allah ya tsari Imrana..! Tunda ya Fara mgana Yusuf ke Dariya har yana zama kan kujera Ganin haka yasa Imran ya juya kawai ya Fara Tafiya batare Dayace wani abu ba Gabda zai Fice Daga Falon Yusuf yace"Shikenan Imran Abubukar Malami We shall see..! Cikin son Tabbatarwa ya juyo ya saki wani Mirmishi kafin yace"We shall see..! Daga haka ya Fice Daga Falon yana sakin karamin Tsaki ganin Bata Lokacin Dayayi alhalin shi ba Mutum ne mai african Time ba. Mashin dinsa yaHau ya kunnata Lokaci Daya yayi Hon Iro megadi Dake kan Bencinsa zaune yana Dafa Shayinsa ya Tashi da Gudu ya Bude get din Imran ya Fice da Gudu Baki Iro ya Rike kafin yace"Nidai Allah ya kawoni gadi Wani Gida..Gidan da ban taba ganin kamar sa ba.! Yafada Lokaci Daya yana maida get din ya Rufe ya koma ya Cigaba da Fifita Rushin Dake Cikin karamin murhin gawayin Dake gabansa mai Dauke da Karamar Butar shayi yana Dafawa. Yana isowa kofar gidansu Sagir din yaji wayarsa na kuka,Kafin ya Cirota Daga Aljihu Sagir ya Bayyana gabansa Cikin Harara yace"Karfe Takwas din kenan..? Kasani na Fito ina jiranka kamar wani yaron aiken ka..! Karamin mirmishi Imran yayi yana Fadin"To da wanene..? Mallam Hau muje bana so mu yi Dare sosai..! Sagir na Hawa mashin din Lokaci Daya yana Fadin"Dare na nawa kuma..Ai mun gama yinsa..! Imran dai bai kara mgana ba suka Dauki Hanya Sagir ne ke ta maganarsa yana Fadama Imran din ya kira Baba Manun yace maizasu zo,Imran Yana Tuka mashin din yace"Waya aike ka..?. Sagir yace"Bangane ba..? In mukaje bai dawo daga gareji bafa..! Kai tsaye Imran yace"Mu bisa chan..! Sagir yace"Mganar bata kamata ayita achan ba.Agidan dai ya Dace..! Imran yace"Naji sarkin Tsari..Kamin shuru kasan na tsani ina Tafiya mutum na min Surutu a bayana..! Sagir ya Gimtse bakinsa bai kara mgana sai da suka isa anguwan su Baba manu dake mandawari Road,Daman Imran yasan gidan Domin In Sagir zashi Wani Lokacin Tare suke zuwa da Imran din sai dai bai taba Shiga Gidan ba sai dai ya Tsaya Daga waje Sagir din ya Shiga ya Fito Shima Baba Manun ya san Imran din Abokin Sagir ne sau Daya suka Taba Haduwa Har ya gaishesa shima Sagir ne ya Dinga Taka kafar Imran din yana mai in kiya Daya gaida Baba Manun. Akofar gidan suka Faka mashin din kafin Sagir ya kalli Imran Daya Coge gefen mashin dinsa yace"Shiga fa zamu yi..? Imran yace"Saboda mene.? Ya fito waje mganar bamai tsayi bace! Sagir yayi tsaki ya wuce yana Fadin"In kaga dama kazo mu shiga in kuma baka ga Dama ba ka koma! Daga haka ya saka kanshi Gidan ya bar Imran din nan Tsaye yana kallonsa Kamar bazai Bishi ba kuma komai ya Tuna sai ya Daga kafa ya Rufama Sagir din Baya. Da Siririyar Sallamarsa ya Shiga Sagir da Inna kaltume matar Baba Manu suka amsa,Wanda ke Zaune kan Tabarma kusa da Sagir din mgana yake a waya. Kamar Imran ya juya sai kuma ya Tuna Abunda ya kawosa yasa yayi karfin gwiwan karisawa ganin yadda Daga Baba Manun har Inna Kaltumen suka Sakarmai ido suna kallonsa Dayake akwai Wutan Lantarki Haske ya gauraye Tsakar gidan. Daga nesa ya Durkusa Kamar a Dofane yana Gaishesu sau Daya ina Wuni? Inna kaltume ne ta amsa mai Cikin Fara"a Tana Tambayashi Mutanen gidan Dakyar yace Lafiya lau yana kauda kai itama ganin haka bata mtsa ma kanta ba Ta juya kan Sagir Tana Tambayansa Mama yace Tana gaishesa Daidai Lokacin da Baba Manu ya gama waya ita kuma Inna Kaltume ta mike tana cema Sagir azubo Tuwo yace a koshe yake ta kalli Imran wanda kansa ke kallon gefe yana jinsa kamar a Takure tace koshi bazai ci ba..?.Sagir ya kallesa kafin ya girgizamata kai yace mata Ta barshi kawai bata ja da Nisa ba ta Shige Daki ta basu waje suyi mgana. Juyawa Sagir yayi yana gaida Baba Manu wanda da ga kanshi Zaka san sun Hada Jini da Sagir Saboda Zubinsu iri Dayane da kuma yanayin Dogon Fuskarsu Amsa mai yayi Cikin Fuska Lokaci Daya yana Fadin"Ina Ita Aminan..? Ina fatan lafiya kalau take..? Kan Sagir na kasa yace"Eh Baba Lafiyanta Kalau tace a gaisheka..? Yana kallon Imran yana Nazarinsa acikinsa Ransa yace"Ina amsawa Daman gobe nake cewa zan leka mu gaisa kwana Biyu! Sagir ya gyara zama yana Fadin"Baba ga abokin nawa danace maka zamu zo Tare..Imran yana so yayi mgana Dakai..! Baba Manu ya maida Hankalinsa kan Sagir kafin ya kalli Imran yana Fadin"Topha dan Saurayi in ce dai ko lafiya..?ba wani abu Sangirun yayi maka ba..? Imran da sai yanzu ya kallesa ya Girgiza kai yana Fadin"A'a ba mganar Sagir bane..! Baba manu yace"To to..Ina jinka..! Sagir ne ya kalli Imran din yana Fadin"Ka cire Takalminka ka Hawo kan Tabarman mana Imu..! Bai kallesa ba ya gyra Tsugunnonsa yana Fadin"Nan ma is ok..! Baba manu dai bai ce komai yana ta Tunanin wata mgana ce haka yaron da ba wani saninsa yayi ba yazo har gida saboda ita. Bai gama mamaki ba Yaji Muryan Imran din Ciki Kaushi kai tsaye yana Fadin"Dama kan mganar Auran yayana ne...Gidan Dayake son yarinyar sun nemi Daya Turo mgabantansa Shine nazo na sameka ina so ka Shige masa gaba a Bangaran Neman auran..! Ba wani Roko ko alfarma kai Tsaye ya Fadi mganarsa kuma bai Damu ba. Baba manu mamaki ya kamashi ya kalli Sagir,wanda ya Sunkuyar da kansa domin bai ta cewa Sanin Halin wanda ya kawon. Cikin mamaki yace"In shige masa gaba..? To ina iyayenku ko nace Waliyan ku..Ma"ana kanin Mahaifi ko Kanin Mahaifiya ko wani Daga Cikin Danginku..! Imran kamar bazai ce komai ba sai Chan yace"Bamu dasu..Gidanmu mu kadai ne Dagani sai yaya na sai kanwata sai Abbanmu..Kuma shi din bai da Lafiya ne shiyasa nazo wajenka..! Baba manu ya gyara Zama yana Fadin"To baku da yan"uwa ku din Daga sama kuka Fado..? Sai alokacin Imran ya kara Dago kai yana kallon Baba Manu Cikin wani yanayi kafin yace kai Tsaye"Eh..! Ba Baba Manu ba Harta Sagir sai da ya kalli Imran yana Auna masa Harara da ido Cikin Kufulwa da Rainin wayau Yaron Baba Manu yace"Kuma kace Min Eh..! Imran yace"Eh..Ai kaima kasan ba wanda ya Taba Fadowa Daga sama..Ballatana ka Tambayeni ko mu Daga sama muka Fado..! Hankalinsa kwance yayi mganar Zuwa Lokacin Ran Baba Manu ya Fara Baci Cikin Hargowa ya kalli Sagir yana Fadin"Au daman da saninka ka Kawomin wannan Tsagerin yaron har gidana zai Cimim Mutumci..? Sagir ya kwaso Rantsuwa Baba Manu ya Dakatar dashi da Fadin"Maza tashi ka Tarkatashi ku barmin gida kafin na Saba maka..ko ce maka akayi ni Mutumin banza ne..!? Sagir ya Sadda kai yana Fadin"Don Allah Baba kayi Hakuri..Ba Cin mutumci zai maka Shi haka yake don baka Sanshi bane..Imu ka bama Baba Hakuri don Allah..! Ya karishe Fada yana kallon Imran Din da har ya Mike daga Tsugunnon Cikin mamaki yace"Saboda mene zan bashi Hakuri..? Nayi mai wani Laifi ne..? Mgana na kawo mai ni kuma ya Tambayeni na bashi amsa do i do Something wrong..? Bana bada Hakuri a inda ban aikata komai ba Mganar aure ai Mganar alherice balle yace Mganar Shanshanci na kawomai..! Yafada Hankalinsa kwance yana Laluban Aljihunsa Cikin Takaicin ya manta bai Fito da Tabansa ba sai dai Lether din,Karamin Tsaki yaja ya juya zai Fice Daga gidan Baba Manu ya saka baki ya kira Sunansa Tsayawa yayi kafin ya juyo Da kai ya gyada mai kafin yace"Dawo ka zauna muyi mgana..Na Fahimceka! Yafada da Dan Sakin Fuska Domin a kalaman yaron ya gama Fahimtar sa irin yaran ne kaifi Daya marasa Tsoro,Gaba gadi basu karya ba Munafunci. Inda ya tashi ya koma ya Kara Durkusawa Cikin mamaki Sagir ke kallon Baba Manun sanin Halinsa na Fada ammh sai me sai yaji yace ma Imran din"Wani gida ne shi yayan naka yake neman auran..? Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace"Gidan Alhaji Alhassan Buhari..! Baba Manu yayi jim kafin yace"Kardai kace min gidan Alhassan malami a jami"ar Buk Dake Zaune a Zooroad..! Da Dauri Sagir yace"Shi Baba! Baba Manu yace"Ai ta kwana Gidan Sauki..Ai nasam sa makotan Marigayi yaya nane Mahaifin Sagir kafin Allah yamai Rasuwa a saida gidan suka Dawo nan gadan kaya da Zama..in hakane ba mtsala Zan nemi abokina Alh.sadi sai muje ayi mganar kada kadamu kaji..! Imran yace"Shikenan kamar me dame ake Bukata..? Baba Manu yace"To zuwan Farko dai Kudin gaisuwa ne za"a kai sai su Minti da goro ko Dabino da Tarbarmu ko Cafet na kayan na gani ina so..In kuma zamu kara komawa bayan mun yi mgana dasu Waliyan yarinyar sun yanke Sadaki sai muje dashi da kayan Saka Rana! Imran yayi shuru kafin yace"in naso aje gabadaya Sau Daya fa...? Baba Manu yace"Shi Alhaji Alhassan don ya Bukaci Haka..?. Kai tsaye Imran yace"Ko bai bukata ba..Ni haka nake so ayi.Kuma hakan za"ayi yanzu Duka da komai da komai har Sdakin ita yarinyar nawa zasu isa..? Abun sai ya bama Baba Manu Dariya Confident din yaron Cikin Dariyan yace"Ni kuwa ina zan san Sadakinta ni ba Ubanta ba..? Sai dai muje da kudin In sun yanke na Hannunmu sun kai mu basu in kuma da kari sai mu Dawo Mu kawo Daga baya..! Imran ya Mike Lokaci Daya yana Fadin"Gobe in Allah ya kaimu zan kawo maka 200k..Zuwa Jibi nake so kuje gidan..! Baba Manu yace"Wannan ba mtsala bace..Sai dai an sanar da megidan muna tafe jibin..? Imran kai tsaye yace"Yarshi zata sanar dashi..Nagode..sai ka ganni.! Daga haka ya juya Cikin Takunsa na Sarssarfa ya Fice Daga Gidan Baba Manu da Sagir suka Rakashi da Ido kafin Sagir shima ya mike yana Fadin"Baba sai da Safe..! Baba manu ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"ina ka sami wannan yaron..? Daga yanayinsa da mganarsa na gane akwai abunda yake Faruwa dashi koma ya Faru dashi Daya kara maidashi haka..? Sagir yace"A anguwar mu suke Baba.Sune wadanda suka siya gidan Marigayi Habibu Daya rasu kwanaki fa! Baba Manu yace"Au..Nan suke da Zama..! Sagir yace"Eh Baba..Nima haka na gansa har muka fara abota basu da kowa anan garin koma suna dashi ban taba gani ba basu Hulda da kowa daga su sai su kawai sai ni kuma da Allah ne kadai yasan Daliln Abotanmu..! Baba manu Dayaji Tsausayin su Imran ya kamashi yace"Allah Sarki Shi kuma Baban nasu Dayace bai da lafiya me ya same shi..? Kuma ina Mahaifiyarsu..? Sagir yace"Wlh nima Bansani ba Baba..Abbansu dai kullum yana Daki yana kwance likita ke zuwa gida yana Dubashi kuma agidan banta ba ganin wata mace ba Daga Imran din sai yayansa Yusuf wanda shine komai nasu sai Karamar kanwarsu Maimuna..! Baba manu na jinjina kai yace"Ikon Allah..! Zai sake mgana suka jin Hon din Imran da karfi da Sauri Sagir ya Duka yana Saka Takalminsa Lokaci Daya yana Fadin"bari naje Baba kada ya tafi ya Barni.Labarin yana da Tsawo zan Sake dawowa sai mu Tattauna..! Da toh kawai Baba Manu ya Bishi har ya Fice da gudu,Sai kuma ya Gyara zama yana Tunani da Nazarin Labarin da Sagir ya bashi game da Imran shidai yana ganin akwai wani abu mai Girma wanda yake cikin Zuciyar yaron kuma shike hanashi Sakin jiki Cikin mutane. Koda Sagir ya Fita Ran Imran ya gama Baci yana Hawa Mashin din ya Fizgeta sauran kadan Sagir din ya Fadi sai da ya Rike karfen Mashin din kana ya iya Zama Dakyau Cikin Tashin hankali Sagir yace"Yanzu daman Saboda ka yi sanadiyar da zan mutu ko na jikkata ka je har gidanmu ka Daukoni..? Imran ya saki Tsaki yana Fadin"Kamin shuru mallam..kafin na Sauya Shawara na Tsaya da Mashin din na Cikama baki da jini..! Sagir na jin haka yayi Shuru da bakinsa Domin yafi kowa sanin Zuciya irinta Imran bamai kyau bace Haka sukayi tafiyan ma wannan Karon Shiru har Imran din yakai Sagir din gida ko gama Sauka bai yi ba ya Figi mashin dinsa yayi Gaba Sagir ya Bisa da kallon kafin ya Girgiza kai kawai bai Shiga gida ba Shagonsa ya Shiga yana Duba agogon Hannunsa Tara ya wuce ya kamata su Rufe Shagon sai kuma gobe. ******* *Kaduna* Da Ihunta da Murnanta ta Shigo Falon Tana kwala kiran"Umma..! Umma..! Umma Dake Kitchen Tana Hadama Alhaji Tea dinsa taji Kakakin kiram suanta da Inteesar keyi ta Fito Tana gyara Daurin Zanin Atamfarta Golding Dake jikinta. Cikin Takaichi tace"Wai ke Inteesar yaushe zaki koyi Sallama ne ba ihu ba..? Tura Baki Inteesar din Tayi kafin ta Zube kayan Hannunta kan kujera Tana Fadin"Kai Umma ba nayi sallama ba..Ki Tambayi ma ya Bashir..! Tafada tana wani Diddira kafa na Shagwabbanun yara. Tabe baki Umma Tayi daidai Lokacin da Bashir yayi sallama ya Shigo,Umma ta amsa mai ya kariso Falon sai da ya Zauna ya Fara gaisheta ta amsa Tana Fadin"Ya ka baro su Hauwa"un..? Dazu yaranan sai kuka suke Shine da Babanku zai kai Inteesar gidan Inno nace ya biya da ita ta kaisu wajen Mamansu..! Yana yar Dariya yace"Umma Rigiman yaye ce kawai..Chan ma sai Rigiman suke mata..! Umma tace"Daman sai a Hankali..Tana ma kokari kai ne nace maka ka samo mata wacce zata rika taimaka mata..! Bashir yace"Umma itace fa taki..Ammh nima nayi mata mganar..! Umma tace'Ai shikenan Tunda bataso..Daman Wahala Renon yara ake jiyemata ga kuma Laulayin sabon Ciki..! Jin haka yasa bai yi mgana ya Sadda kansa kasa Domin Bashir akwai kunya. Sanin haka yasa Umma bata kara mgana ba ta maida Hankalinta kan Inteesar Dake ta Faman Bule Lodojin Data Shigo Dasu bakinta kamar gonar Auduga saboda Murna..! Umma tace"Ita kuma wannan ina ka samota..? Naga sai Murna take me ta samo ne? Bashir yace"Umma Daddy ne ya kirani yace naje na Daukota gidan Kawu Salisu na Daukota..! Umma ta Rike baki Tana Fadin"Au har chan sai taje kenan..Nifa Daga gidan ka naceta Hau adaidata ta karisa wajen Inno Tana min mitan kada Inte tatafi Batazo mata ssllama ba..Dama bai Dade da Dawowa ba sai Mitan yake Inte bata dawo ba yafa gaji wai zai kara Fita ya Daukota nace sai dai ya kiraka..! Kafin Bashir yayi mgana Inteesar ta Daga wani maroon dim Hijabi mai kyau ta kara ajikinta Cikin Murna tace"Umma ni fa yar gatace..Kalli kiga kayan da na samo..Wadanam Hijaban Anty Hauwa ta bani kala Biyar tace na Zuwa makaranta..Wadanan Gyale da Takamim kuwa Mamarsu Nasara ta bani Kawu Salisu kuma ya bani 10k Umma Inmo ta bani Gwarin da Kuli da yawa da yaji Data Dakamin,Mallam Babba kuma ya bani 5k Umma.." Ta karishe Fada Cikin Bayyana Farincikinta tana nuna ma Umma kayan da kudin Dake hannunta. Umma ta kariso tana Fadin"Nagani Kin gode..Ammh meyasa baki barma Mallam Babba kudinsa ba..? Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"Shifa ya bani sai naki karba..Kuma ance ma raina kadan..! Umma ta kaimata Dundu Tana Fadin"To uban nawa ne barawon..? Intesar na Dariya ta gaoce Bayan ta Tattara kayanta Tana Fadin"Nifa ba haka nake nufi ba.Ni bari ma naje na Nunma Daddy...Umma Daddy na Ciki! Umma tace"To mara Hankali yana Hutawa kya Bari da safe ko..? Inteesar tace"Umma da safe ba Tafiya zamu yi ba..,? Umma tace"Kafin ku taho..Tunda ba Sammako zamu yi ba ai ba yaki bane..Ba kuma kanki Farau jami"a ba..! Bashir ne Dake Dariyansu Tun Dazu yace"Umma Dake za"a Raka Autan Daddy ne..? Umma tace"eh.Da nace bazani ba Tunda tace ni ba uwarta bace..Sai nace bari dai naje ko na ga Yaya Amina mun dade bamu Haduba ni ban je ba kuma ita batazo ba ko zuwanta na karshe iyakarta gidan Inno,ni kasan Lokacin bama nan mun Tafi Dukku ni da Alhaji da Inte! Inteesar Dataji da Umma za"a je kaita kano ta Daka Tsalle Tana Fadin"Da gaske Umma Dake zamu Tafi..? Umma tace"Ba don Halin ki ba.?Ihu ta saki kafin tace"I love u Umma..! Ta kwashi gudu da kayanta Zuwa Dakinta Umma ta rakata da kallon kafin ta Girgiza kai tace"Kai bansan yaushe yarinyar nan zatayi hankali ba Allah ya Shirya..! Bashir ya amsa da Ameen yana Fadib"Zatayi Umma..Bari karatun ya kamkama..! Umma tace"Allah yasa..! Ya mike yana Fadin"Amern Umma bari na koma ki gaida Daddy Gobe da Safe kafin ku wucen zan biyo muyi ssllama da Auta..! Umma ta mike Tana Fadin"Shikenan ka gaida Hauwan da su Abiden..Allah ya Tashemu Lafiya..ya amsa da Ameen yana Ficewa Daga Falon Kitchen ta koma ta Sauke Ruwan Tea din Dayaji Na"a Na"a ta samu mug karami ta Zuba akai sai ta saka Siga kadan da Lemin Tssmi ta Dauka ta Fice zuwa Dakin Megidan nata. *Shakira* 3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *🅿�6* "Da misalin karfe 8:40am na Safiyar Ranar Laraba Daddy da Umma da Inteesar suka kama Hanyar Kano Booth din Daddy cike da Kayan Inteesar kamar wacce in tatafi sai bayan Wata Shekara zata Dawo saboda Uban kayan Data Diba akwatuna Biyar Shake da kayan sawa da Takalma sai kuma Sauran kayyakinta na Kwalama da kayan kwalliya. Inteesar na Gidan Baya Umma ce agaba Fushi take yi Sosai bakinta kamar ya Fado Fuskarta a Dakune saboda ta Shiga gaban Mota Da zasu Taho Umma ta Rankwasheta akai ta Fito da ita tace sai dai ta Shiga baya don Ubanta Daddy ransa ya sosu ya Fara Fada yana Fadin"Salaha kina fa min abunda bana so..? Ina wani abun Duka anan Menene abun Damuwa Domin inte ta shiga gaba..? Ba yarki bace ke sai ki koma Baya ki Zauna..! Kallonsa kawai Umma Tayi kafin ta kada kai Tana Fadin"Wlh Alhaji ba Domin agida na Haifi Inteesar fa Tsab zan ce ba yata bace An Sauyamin ita a asibiti ne..Kuma inda yau bani na Haifeta ba Kishiyar uwa nake gareta Tsab zan ce kana Fifita komai na Yarinyar akaina..! Tafada Tana bayyana irin Takaichinta game da abubuwan da Alhaji yake yi komai Inteesar Tayi daidai ne koda kuwa abun Fada ne da Sakarci. Shuru yayi bai ta amsa ba sai ma Juyawa da yayi bayan Motan yana Faman Lallashin Inteesar din wacce saboda Sangarta Harda kuka batayi Shuru ba sai da ya bata wayarsa Zata yi game Sabuwar Tata saboda Sauri bata Tsaya kwashe Apps din Datake da shi a acikin Tsohuwar ba Kuma ta manta ta agida Duk kuwa da yadda ta Shirya kayanta Duka. Umma na gaban Mota ta kallesu ta watsar Da karamin Tsaki Inteesar ta kalleta Tana Tura mata baki acikin Ranta Tana ta kunkuni. Bata kara bi ta kansu ba ta maida Hankalinta kan karamin azkar din Data Taho dashi Ba saboda komai tace zata Raka Inteesar ba din ba saboda Yaya Amina ne ta kwana Biyu bata leka ba kuma Tajata gefe ta bata Umarnin Da Zarar Inteesar tayi wani Rashin Ji ta rika saka Bulalane tana Jibganta kada ta Dauki wannan Sangartanta ta da Ubanta ne kadai zai iya da ita. ****** *GOMBE STATE..Dukku local goverment* _Area:Balikaje_ A karamar Hukumar Jahar Gombe,Wato Garin na Dukku, awata anguwa da ake kira BALIKAJE yau anta tashi da sanyi sanyi kadan na Wucewar Damina da Shigowar Sanyi Acikin anguwan daga farkon farkonta akwai wani Katafaran gida wanda kallo Daya zakayi mai ka Fahimci gidan ba fasalin ginin yanzu bane Tsohon gini ne Daya samu gyaran Masihan magina da kuma wadanda suka san Zanen Fasalta Gini yayi kyau har ya kawatu. Tana Daga Cikin kuryan Dakinta Tana Zaune kan Darduma Misalin 9:40am na Safiyar Ranar laraba Idar da Sallar Walhanta kenan Carbi ne a Hannunta Tana ja Lokaci Daya bakinta na Motsi Wata Farar Dattijuwa ce mai akallah Shekaru 82 a Duniya yanayin Jikinta Tana dan Kiba,da kuma Tsawo Kallo Daya zakayi mata ka Shaida kirar Fulanin Dukku ne duk da Tana daga Zaune ne, Duk da Shekarin sun ja ammh Farar Fuskarta da karan Hancinta basu Boye kansu ba..Da tsantsan kyau da Zati irin nata wanda in da zaka ka ganta Lokacin Kuruciya sai ka Tsaya Jinjina kyau da Zati irin na wannan Tsohuwar Lokacin Kuruciyarta. Gefe gefen Fuskarta Duk Karkasan Gashi ne gashin nan yayi Fari Fat hakama Gemunta akwai Tsirarrun Fitowar gashi Haka Halittar take mai yalwar Gargasa ne hatta Hannayenta gasu nan sun kwanta Duk da kuwa Ta kwana Biyu a Duniya uwa uba gashinta kanta Dake Dunkule shima ya koma Fari Saboda Shekaru. Sai dai aduban Farko in kayi mata sai ka Fahinci Tarin Jin Dadi da Hutu take Tattare da ita Duba da Dakin Datake Ciki da suka ji kayan alatun kawata Daki na Zamani kamar ba Dakin Tsohuwa ba Sai dai kuma yanayin Fuskarta da yadda ta kurama waje Daya ido Zaka Fahimci Duk da wannan Jin Dadin wani abu wanda Ya Dade yana Murkusanta yana Damunta acikin ranta wanda Har ya Bayyana kan Fuskarta. Tana Zaunen Tana Lazimi Taji Muryan Mai aikinta wacce Ta kasance kamar wata jininta kanwa gareta yanzu Wato Baba Asabe Tana Fadin"Maraba da Lauyan lauyoyi..Baban Sajida Sannu da Zuwa Lale marhaba..! Taji Tana Fade daga Falonta,Mirmishi ta saki kafin ta Girgiza kai bata san meyasa Asabe Tafi Damuwa da Lafiyarta Fiye da karan kanta ba, Sadaukarwan da matar tayi mata mai girma ne suna Tare tun Lokacin kuruciya har yau da Girma ya kamata bata yarda da ita ba Suna zaune tare Cikin Aminci da yarda kamar yadda suka Fara Tunchan Farko. Tasan Ko datace mata to bazata kira wani Daga cikin ya"yanta ta Daga musu Hankali ba tadai jita ne kawai tafi kowa sanin Halin Asabe..Asabe fa..Asabenta bazata Chanza ba tasan ita ta Kira KABIRUN. Tana cikin wannan Tunanin Taji sallamarsa Cikin Muryansa din nan mai Cike da Amo da Haiba kamar ta Dan"uwansa wanda yasa sai ta waigo da Sauri Tana kara ware idanuwanta akansa Cikin Bugun Zuciya ganin ya Duka Ya Cire Takalman kafarsa sau Ciki ya Fara tako laulausan Cafet din Daya malale Dakin da Safarsa yasa ta Tabbatar ma kanta Shi kadai ne Ba Hasashenta bane kanta ta maida kawai ta Cigaba da jan Casbahanta Lokaci Daya Tana amsa Sallaman nashi a saman Labbanta. Gabanta ya kariso ya Zauna yana Tankwashe Kafarsa Dogon Namiji ne ingarma mai Zati da Haiba,Akallah a Shakarunsa bazai wuce 65 haka ba,Fari ne Fatarsa mai Cike da Jin Dadi da Hutu kallon Farko zakamai kasan Jininta ne saboda yadda karan Hancinsa ya Fito Zur akan Fuskarsa. Yana sanye Cikin American Suit Ruwan Toka ya Daure Wuyansa da Tektie, *BARRISTER KABIR HAMISU DUKKU* kenan Babban D'a na farko Wajen Daada(Maryam) Mirmishi ya sakar mata kafin ya saka Hannunsa ya Riko Tattausan Hannunta da suke Tubus dasu Saboda Samun Hutu da kuma jin Dadi yace"Haba DAADA..taya baki da lafiya kuma ke baki kiramu ba kuma kika Hana Baba asabe kiranmu..? Yafada yana Kafeta da Kaifaffun Idanuwansa kamar na Mahaifinsu marigayi mallam Hamisu Dukku,gabadaya ya"yan nata Zaratan mazan Duka idanuwan mahaifinsu suka Dauko Gwara ma matan sun Dauko nata Idanuwan. Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin ta Zame hannunta Carbin Dake hannunta ta ijiyeshi nan Gefenta saman Darduman Datake kai Cikin Muryanta mai Cike da Amo da Tsufa adan shake tace"To kabiru ko na kiraku me zakumin..? Ina da mganguna nasha..Daman jiri ne fa kawai DanaTashi jiya da Daddare ya Kamani kuma zuwa yanzu kaganni Alhamdulillah..! Girgiza mata kai yayi yana Fadin"Ba shi kadai bane Daada..Akwai wani abu..Duk kin kara Ramewa Daadarmu taya ya kikeso mu kwantar da Hankalinmu achan inda muke Zaune muna aiki da iyalanmu Ahalin ke kuma kina nan kina ta Fama da Tunanin Dayake Haddasa miki Ciwo..? Haba Daada ya kamata ki Fahimci wani abu Tunani da Damuwa bashi bane mafita ki kuma sani Bayan Malami kina da wasu ya"yam da Jikokin da suke Bukatar ganinki a Raye Cikin Koshin Lafiya! Jin ya famo mata inda yake mata kaikayi yasa kawai ta Fashemai da kukan Data ke rikewa Tun Dazu Tuni ya Rikice Ya Rikota yana Fadin"Haba Daada.Don Allah ki Daina kuka..Kada nima ki sani kukan..! Yafada Daidai Lokacin da Baba Asabe ta yi sallama ta sawo kanta Dakin Dauke da Faranti Mai Dauke da Ruwa da Lemo itama Kamar Daadan take sai dai Daada Zata girmeta ba sai dai ita Baka ce mai Jiki ammh bata da Tsawo. Ganin Daaada na kuka yasa Bayan ta ijiye Farantin Hannunta gaban Alhaji Kabir ya Zauna tana Fuskantarsa tace"Lauya sai fa kunyi wani abu akwai..Kwanakin nan sam Daada bata samin Ishashen Barci..Koda yaushe sai dai ka ganta Cikin Damuwa ko wanchan Da Dr Madina tazo ta Dubata sai da tayi mata korafin Rage damuwa da Tunani..Kayi mata mgana kila ta Rage..Ka gayamata ta Taimakemu ta kwantar da Hankalinta muna Matukar Bukatarta..! Baba Asabe ta karishe Fada itama Tana matse kwallah Alhaji Kabir bai samu Zarafin Mgana ba Baba Asabe ta Fita da Sauri Tana kuka yau in suka rasa Daada ina Zata saka kanta matar da Tayi mata komai na Rayuwa ita da Iyalanta Tun zamanin kuruciyarta Tazo gida nan a matsayin yar aiki Daada ita da marigayi mijinta sun mata komai a Rayuwa,Duka ya"yann Daadan ita ta Renosu Domin ita Allah bai Taba bata Haihuwa ba Duk da Auran Wuri akayi mata auran ta Biyu,Dayake ita yar Minjibir ne Dake Jahar kano.Kuma ba wani Cikakkun Dangi Tunda uwa da Uba Duk sun Rasu Da Taimakon wata Hajiya Lanti mai kai mata aikatau gari gari ta Sadata da wannan gidan..Gidan Alheri da karamci kusan Shekaru Arba"in da wani abu Tana Tare da Daaada da iyalanta bata Taba kukan wanu abu ba sai dai Taje chan garinsu Minjibir takai musu alheri Daga Cikin Alheram Daada da Ahalinta Dole ta Rika Shiga Damuwa in taga Daada a wannan Halin. Bayan Fitan Baba Asabe Alhaji Kabir Cikin Jimami da Damuwa ya Jinjina Hannun Daada Dake cikin nashi yace"Daada menene mtsalan ne wai..? Kinga ni bama mu kadai ba Hatta Baba Asabe bata son rasaki ballatana mu ya"yanki da bayan Rasuwar Baffa kece komai namu mu da iyalanmu yau in kika Fadi kika Mutu ina kike so mu saka kanmu..? Kafin kiran Baba Asabe Dr.Madina ta kirani Tun satin chan Daya wuce ta fadamin yadda Jininki baya kasa Daada kullum sai kara Hauhawa yake yi Ta rasa Dalili Daman ina ta Shirin Tahowa aikine sukamin Yawa Cases gareni har uku Shiyasa baki ganni ba Sai jiya da Daddare da kiran Baba Asabe ya sani Dole na Biyo Jirgi Daganan na Hawo taxi zuwa nan..! Ya karishe Fada yana kallon Daada wacce ta ke sharan Hawaye kamar wata karamar yarinya kafin ta Dago Tana kallonsa tace"Bani da wata Damuwa sai ta Dan"uwanka Kabiru..Ace yau wajen Shekaru uku bashu ba Labarinsa Shi da iyalansa..? Anya an taba irin wannan Kuwa batan mutum ba Daya ba ba Biyu ba..Kabiru..? Ta karishe Fada Cikin Taruwar kwallar acikin Idanuwanta. Fesar da Numfashi yayi yana kara Nazarin yanayin Daada Daman yasan Tatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki..Damuwar Daada Gabadayanta ta Malami ce Shiyasani kowama ya sani. Cikin Lallami yace"Daaad kiyi Hakuri don Allah..ki kwantar da Hankali wannan Abunda kike yi bashi bane mafita..Ina so ki Sani Malami fa ba bacewa yayi ba..Ko kuma wani Mumman Abu bane ya same shi ba fa..? Daada da kansa ya Zabi yayi nisa Damu yaje inda Bazamu taba ganinsa ba koda Mun Nemesa..Kada ki manta Dani da Mustapha mun Taka Har Chan inda suka zauna Nemansa bamu san iyaka ba mun samo Miki labarin Da kansu suka bar komai nasu Daada..Gidanshi bai saida ba sai dai sun Rufeshi Jami"ar Dayake koyarwa munje Shima ba wani bayani haka Ma"aikatun da yaransa ke aiki munje sun Tabbatar mana da Cewa Sun ijiye aiki da kansu Daada..Kuma Har yau bamu Daina nemansu ba Saboda ke Daada..Na saka a saka ido saosai duk Randa akaga wani Cikinsu na Bada Lambar a wayata a kirani ammh Har yau babu Wani labari Daada..! Ya karishe Fada Cikin Bayyana Takaichinsa indai ya Tuna da Abunda Dan"uwan nasu ya aikata.. Cikin Sanyin Murya Daada tace"To ina zasu tafi..? Ina jin Tsoron kodai wani mumman abu ya same su..? Alhaji Kabir yace"Ina ji ajikina babu abunda ya Samesu..Ko Satin Daya gabata naje banki..Na saka an Bincikamin account din Malami an ga ana Cire kudi Lokaci Bayan Lokacin kinga kenan Duk inda suke suna chan suna Rayuwarsu Daada Sun manta Damu da komai nasu Batare da wani Tunani ba..! Daaada ta Girgiza kai Tana Fadin"Ban yarda Malami zai manta dani da ku yan"uwansa da asalin gabadaya ba..Kada ka manta Faruwar abunda ya Faru ya Taba kwakwalwar malami baya Cikin Hayyacinsa..Laifin na ya"yansa ne Musamman Babban..! Alhaji Kabir cikin jin Haushi yace"Bai fa Haukace ba Daada...Ciwon Damuwa ce kawai ai Bai fita Hayyacinsa ba yasan Daidai da Rashin Daidai..Na yarda ba da son Ransa suka tafi ba Sai dai ina da Tabbacin da saka Hannun wannan Yaron nashi mai Taurin kai da Zuciya wanda kaf cikin Dangin bansan ina ya kwaso wannan Hallayar ba shine zakka a acikin wannan zuru"ar namu Daada.! Duk Halin da Daada ke Ciki sai da ta Murmusa Cikin girgiza kai Tace'"Ba Zuciya bace Kabiru..Haka Hallitarsa yake mutum mai saurin Fushi da Fusata Akoda yaushe ina yi musu Uzuri da addu"an duk inda suke Allah ya karesu..Ni Karamar nake Tsausayi tunda itace Mace basu san kowa ba Duka Dangi suna nan Dukku,Dangin Uwarsu ai Nice nan Kabiru Tunda ni na yaye Zuwaira na Riketa har ta girma Mahaifinka ya aura ma Malami ita ina ji ajikina Duk inda suke suna chan su kadai Cikin kewa da kawa Zucci.! Ta karishe Fada tana Sharan kwallh yana kallonta bai ce komai ba sai da ya Numfasa kana yace"Kada ki damu Daada..Insha Allahu muna iya bakin kokarin mu da yardan Allah zamu dawo da Malami Cikin Ahalinsa..! Daada taji Dadi ta kara Damke Hannayen Kabir tana Fadin"Haka nake so naji Kabiru..Allah yayi muku albarka kaida Sauran yan"uwanka..Nasan ka kirasu duk ka shaida musu Tun Safe Bintalo da Maimunatu da Mustpaha ke kirana ban Daga ba Saboda nasan aikin Asabe ne..! Ta fada TanaFadada Mirmishinta,shima Mirmishin yayi ganin ta saki Ruwa ya Dauka ya Tsiyaya yasha ya ijiye Kofin kafin yace"Nida Mustapha kadai mukayi mgana Da Safe Daada..Nayi mai mganar tahowa mu hadu dashi muyi miki mgana kila zaki fi jin mu.Sai kuma yace min kano yake Shirin Tafiya shida mai Dakinsa zasu kai yar wajensa Zata fara karatu anan Buk kano,To yacemin yayi ta kiranki baki Daga in na iso na kirashi in bashi kuyi mgana..! Baki Daada ta saki kafin tace"Badai wannan Sangartattaciyar yarinyar nan Mustapha zai kai wata uwa Duniya da Niyar Karatu ba..? Alhaji Kabir na Dariya yace"Kai Daada..Takwarki ce fa...Kike Fada da ita..! Karamin Tsaki Daada taja kafin tace"ammh kuma bata Biyo Halina ba...ayi yarinyar sai Sangarta da Sokanci ta girma ita ba yarinya ba Duk Mustapha ya bata yarinyar nan Shiyasa sam bana Shiri da ita ko nan garin bata zuwa ko Uban ya matsa sunzo Tare bata ko yarda ta kwana tasan Halina Kaniyarta nake Ci ni ba"a zuwa gidana ace za"amin Sangarta da Sakarci..! Shidai yana ta Dariya kafin yace"Shiyasa Sajida tace Daada Rigima kamar me..! Daada tace"Ita ma kaji wata yar Tselan uwa nan..Ita bata da Sangarta sai dai Shigen kiyuwa da Son jiki..Duk Asma'u ta gama batasu dakai..Gwara ma Umaima tafi ta kazarkazar,ammh Duka nafison mai sunan megidana Hamisu! Alhaji Kabiru yace yana yar Dariya"Shima zaku fara fada in har yaji kina cemai Hamisun nan..! Daada tace"Ni rabani da Fi"ilinku na yan zamani..Hamisu shine sunan kwarai ba wani Feleke ba..Yana ma ina kwana Biyu ban jisa ba..? Yace"Yana chan Anambara inda yake aiki kila ya shiga Ruwa ne..Muma kwana Biyu bamu yi mgana dashi ba..Sajida kuma ta Fara karatu anan Base Universty ba Zama Umaima kuma kinsan Bana kinta da kulafuncin Uwa sannan itama ga makaranta ba Lokaci..! Daada ta gyada kai Tana Fadin"Allah ya rayasu...ya kuma bada sa"a da Rayuwa mai kyau ya kuma yi muku albarka ya kara arziki..! Ya rika amsawa da Ameen kafin ya Dora da Fadin"Nazo da kayan abinci da Dankalin Naga kamar naku yayi kasa ne..! Daada tace"Akwai sauranshi..Kai da yan"uwanka bakwa gajiya ko Sati Biyufa ba"ayi ba Bashir dan wajen Mustapha ya kawomin kayan Abinci da kudi hakama Itama Bintalo ta aiko Direbanta dashi..Babu abunda zence muku sai Allah yayi muku albarka ya Raya muku Zuru"arku suyi ta muku hidima kamar yadda kuke yi mini..! Alhaji kabir yace"Ameen Daada..In bamu yi miki ba wazamu yi mawa..? Ai bamu da kamarki Allah dai ya kara Tsawon rai..! Lokaci Daya yana Lalubo wayarsa daga cikin Aljihun wandonsa Daada ta amsa da Ameen daidai Lokacin da Alhaji kabir ya Kara wayar akunni yana Fadin"bari na kira Mustapha Daada..! Kai ta gyadamai kaunar ya"yan nata nakara Ratsata,tana fatan Allah ya cika mata Burinta na Hada ya"yanta waje Daya ***** Suna gabda da shiga garin Kanon Dabo Wayar Alhaji Mustpha Dukku Dake Hannun Inteesar ta Fara Neman dauki wayar ma ta Zame a hannunta saboda gajiyan Zaman Mota har barci ya kwasheta bata sani ba kiran wayar ya Tada ita Tayi Firgigit ta Farka Daidai Lokacin da Umma ke Fadin"Ke inte miko wayar Daddyn naki ana kiransa..! Cikin Alamun barci cike a idanuwanta ta Dauki wayar ta Mikama Umma batare data ma kalli mai kiran ba Umma ta karba Tana kallonta tace"Tsiyana Dake Raguwa ce Inte..Daga kaduna zuwa kanon ne Duk kikayi Laushi haka..?. Baki ta Zumbura wanda ya Zame mata jiki ta koma ta lafe Jikin kujeran Motan Tana Fadin"Allah Umma da Nisa sosai..! Daddy yana jinsu hankalinshi na wajen Tuki yace"Sahala Daukan min kiran kada ya katse..! Amsamai kiran Tayi tana Fadin"Barrister ne Mijin Asma"u..Baban Sajida..; Tafada tana Mirmishi Tunawa da kirarin da Daddy yake ma yayan nashi duk sanda ya kira waya ko suka Hadu. Gangarawa yayi gefen Titi yayi parking sanin mganar mai tsawo ce yace ya karbi wayar a Hannun Umma ya karata a kunni yana Fadin"Allah ya Taimaki Lauyan lauyoyi..Baban Sajida da Khamis Mijin Asma"u ma"u..! Dagachan Bangaran Alhaji Kabir ya Murmusa yana Fadin"Mustapha Mijin Sahala..Baban Bashir..Kuma Gatan Mai sunan Daada Inteesar..! Atare suka saki Dariya Harda Daada Dake zaune gefensa gaisawa sukayi kafin yace"Gani nan na kusa da Daada Tun dazu..Na samu na lallasheta Ammh kaima ka kara gata..! Yafada yana mikamata ta karba Cikin Fara"a cike da ladabi ya gaisheta ta amsa yayi mata ya jiki tace"Kaifa nifa na warke ba wani abunda ke damuna..Tadin Asabe ne da baya karewa..! Mirmishi yayi yana Fadin"Haba Daadanmu..Ai nasan ko baki da lafiya haka kike fadi..Don Allah Daaada ki kwantar da Hankali da yardan Allah Damuwarki ta kusa kwarewa Zamu dawo da Yaya Abun ki har gabanki Da yardan Allah..! Daada tace"masha Allah..Allah ya baku iko..Allah yayi muku albarka..Ina ita Mai Dakin naka..? Ina Babban mijina Basiru..? Ko dayake ko jiya ya kirani mun gaisa harda matarsa ma ina mijin dashi sosai..Banda wannan Sangartattaciyar yar taka mai shigen sangarta da Lalaci..! Mirmishi yayi ya juya yana kallon Inteesar data koma Barcinta yana Fadin"Kowa Lafiya Bashir yana kaduna shi na barma Harkokin namu yau..Ni da Sahala da Takwarki kuma Daada gamu mun kusa shiga kano Zamu kaita makaranta zata Fara karatun Jami"a da yardan Allah..! Daada ta kyabe baki kafin tace"Uhm ai yanzu Kabiru ke fadamin nayi ta Fada Mustapha..Bani dai Salahan ita na gayamata kila tafi Fahimtata in kaine kan wannan Diyar taka bajina zakayi ba.. Yana Dariya ya mikama Umma wayar yana Fadin"Daada ce..! Ko bai fada ba tasani Tunda suna Tare Da asuba sanda Baban Sajida ya kirasa yana Fadamasa Zencen kiran da Baba asabe tayi mai kuma bayan gama wayar tasu sun Dade suna Tattauna damuwar Daadan Dashi. Karba Tayi Cikin Ladabi Tana gaida Daadan Da Tambayanta Jikinta Daada ta amsa ta Cigaba da Fadin"ke yanzu Salaha da saninki Mustapha zai Dauki Yarinyar nan zuwa wata uwa Duniya da sunan karatu..? Tana gaban ki ma baki iya Tankwarata ba,saboda Ubanta ya Daure mata Gindi Chan din da zaku kaita kusan dasu wa zata fara Mu"amala..? Bafa irin su Maryam ake kaiwa makaranta inda ba kwabar iyaye ba sai ta kara Sangarcewa yarinya ta isa aure ammh Sai wani Sakarci take ko yarinyar yar shekara Biyar albarka..! Daada ta karishe Fada Cikin Fada Umma dai sai Dariya take kafin tace"Kema kya ce dai Daada..Kila ke yaji mganarki ya Daina Biyema Inte da sangantarta a kusan Koda yaushe ina gayamai aure zatayi watarana ya kamata ya Rage mata wasu abubuwan ammh daga ita har shi ba wanda ke Saurarata Daada..Mganar karatunta a kano kuwa abunda yasa na amince ba Cikin makaranta zata zauna ba Gidan Yaya Amina zata zauna Shiyasa..! Daada tace"Yayar nan taki ta kano da Mijinta ya rasu Shekarun Baya ko..? Umma tace"Eh ita Daada..Wajenta Zata zauna in ta samu Hutu sai ta rika dawowa kaduna Dayake ma Dan wajen Yaya Amina Sagir shima makarantar yake karatu zai rika kula da komai..' Daada tace"To koda naji..Yanzu hankalina yafi kwanciya Allah ya Tsare ya bada sa"a..Ina ita yar Tselen uwar take ne..? Umma tace"Gata nan tayi barci..Kinsanta Raguwa ce Daada..! Daada tace"Nasanta kuwa..To ki ce mata nace ayi karatu banda Sakarci da Sangarta. Umma na Dariya tace"To Daada..Allah ya kara girma..! Daga haka ta mikama Daddy wayar ya amsa suka cigaba da mgana da Daada yana kara kwantar mata da Hankali kafin abama Kabir din su Cigaba da mgana Cikin Lokaci Sukayi sallama Kana Daddy ya Tada Motar suka cigaba da Tafiya Jefi Jefi suna Taba Hira duk akan Abunda ke Damin Daadan na Batan Dan"uwansu da iyalansa. Karfe 11:34pm na Rana suka Shiga garin kano Daman Tun Daran Jiya Umma ta kira Yaya Amina ta sanar da ita gobe suna Tafe,To bayan Shigowarsu garin kano Daddy yayi waya da wani abokinsa Dake Lacture anan Buk din a Shashen Kimiya da Fasaha wato Computer Science Daman shi yayi ma Inteesar din Cuku Cukun samun Addmission din Shiyasa suna waya bayan sun Shigo yace su Fara shigowa cikin makarantar Inteesar din Ta fara Regisration din ganin Lokaci yana Tafiya har sun fara Karatu. Shiyasa kawai suka Fara wucewa Cikin makarantar sai dai Umma ta kira Yaya Aminan ta Fadamata sai sun gama abubuwan daya kawosu zasu kariso nan ammh kwana zasu yi sai Gobe zasu koma ganin Rana tayi kuma ko gama abunda ya kawosun basu yi ba. *Shakira..* 3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)*    *🅿�7* "Tunda suka shiga cikin makarantar ake ta Cuku cuku anan sukayi sallar azahar da La"asar suka kuma ci Abinci da Taimakon Abokin Daddy Inteesar ta kamallah registration dinta Sai abunda ba"a rasa ba,basu Fito Cikin makarantar ba sai wajen Biyar da Rabi na yammah 5:30pm Inteesar ta gaji Tubus,Sai raki take yi ita kuma ba yunwa take ji ba Domin taci abinci Kawai tagaji ne so take taji tayi wanka ta kwanta ta Huta abunda ke karamata Tashin Hankali Irin jin datayi gobe ma Zata koma ta karisa ita kadai ba Daddy yaushe zata iya wannan Wahalar ita kadai .? Ta iske Jami"ar Ta bayero ba yadda Tayi Tsammani ba ashe babbar makaranta ce mai Cike da Dalibai kala kala kabilu Dabam Dabam. Suna tafe amota bayan sun Fito Daga Cikin makarantar,Umma da Daddy suna Hira da yaba tsarin Jami"ar Inteesar na Baya tana Jinsu duk ta gaji so kawai take Tayi wanka Taji ta kwanta ko ta samu ta Huta ganin suna ta Tafiya har yanzu ba su iso ba yasa Ta Dago Dara Daran Idanuwanta Wadanda suka Cika da gajiya tace"Daddy bamu kawo gidan Inna Aminan bane..? Tafada Cikin Sangarta da gajiya a Muryanta. Cikin Tsausayamata ya juya Ammh Hankalinsa na wajen Tuki yace"Mun kusa Intee..Sannu nasan kin gaji anya zaki iya wannan Wahalan karatun ko mu koma gida na nema miki nan KASU ne..,? Ya karishe Fada cike da Tsausayawa jin Abunda yace ne yasa Inteesar tayi saurin Wartsake gajiyarta Tana Fadin"A"a Daddy..Ka barni anan Nafi son Jami"ar Bayero fiye da kowacce Jami"a..Kuma Tunda na taso Daddy ban taba Fita wani garin nayi Rayuwa ba Shiyasa na zabi karatu a garin kano Saboda na kara sanin wasu abubuwan! Daddy ya jinjina kai alamun jin Dadi Umma Dake jinsu Ta Tabe baki Tana Fadin"Ashe dai Kina da Hankali..? Hararanta Daddy yayi kafin yace"Me kika Dauke mu..? Umma na Dariya tace"Sangartattu mana Miye ku in ba hakan ba..? Tafada Tana kallon Inteesar da Bakinta ya kusa Fadowa kasa Cikin Kunkuni tace"Daddy kaji umma ko..? Wai nice Sangartattaciya..? Daddy yace"Manta da ita..Eh kin ji ke Sangartattaciyace wani kikayi ma Sangartanki ba Daddy ki ba..?kyaleta sai tafi kowa kewarki ko bakomai Gidan zai mata Shuru inta koma baki..! Sanda ya Fadi haka Dukkansu sai sukaji wani iri Tabbas Bai yi Karya sai taji Dabam ita ta Haifi Intee Tasan ta da Kulafucin Gida ko Wani waje bata yarda Taje ta kwana Bata jin ta taba takama Gidajen Baffaninta,sai dai in sun Hadu gidan Daada a Dukku Shima Din bata yarda ta kwana Kafarta kafar Daddynta Shiyasa Umma tayi matukar mamaki da Intee ta Zabi kano,Sai dai kuma batayi mamaki ba ganin yadda Ta Dora ma kanta yin Jami"ar Bayeron Tun ba yanzu ba Tasan Shi kadai ne Dalilin da zai saka Inteesar Tayi nesa da gida. Ba wanda ya kara mgana sai Umma Dake nuna ma Daddy Hanyar gidan Yaya Amina Tunda sun Shigo gadan kaya. Sai gasu a kofar gidansu Sagir wanda ke Cikin Shagonsa da yaransa suna ta faman Dinkin yau Tun safe bai zauna ba ya Shiga makaranta bai Dade ba ya Fito Mama ta hanashi Sukunu da Murnam zuwan Inna Salaha da yarta Tun asuba tatashi ta gyara Dakinta da gidan Gabadaya tasa yaje kasuwa yayi mata Cefenan Abunda Zata Dafa musu Duk ta kasa Sukuni Shima Daya Dawo makarantar ne Mama ke shaida mai Inna Salaha ta kirata tace suna Cikin makaranta sai sun gama Zasu Biyo nan zasu kwana sai Gobe zasu Juya zuwa kaduna. Dinki gareshi kacha kacha Shiyasa abinci kadai yaci ya Dawo Shago ya Hau keke ya Fara Dinki Sallah kadai ke tadashi Tundazu Dayaji karan Mota sai ya kalli bakin Shagon nashi ammh Sai yaga basu bane,Duk da Kofar gidan ba kwalta bane,ammh akwai Kasa mai kyau wanda Yawan Zirga zirgan Motoci da mashina ya Shimfideta kamar an saka kwalta. Lokacin Dayaji Dirin Motarsu yana Dagowa da Inna Salaha ya Fara Cim karo wacce ke gaban Mota itama kamar an ce ta waiga sai ta ganshi Cikin Murna ta Fara Kiciniyar Bude Murfin Motan Tana Fadin"Mun iso..Gama Sagir din Yaya Aminan chan Cikin Shagonsa yana Dinki..! Tafada Lokaci Daya tana balle Murfin Mota ta Fito Shima Daddy Fitowar yayi yana kallon Sagir daya taso Daga kan keken ya Fito Daga Cikin Shagon Cikin Fara"a Daddy bai wani Sanshi ba,Sanin da yayi mai bai yi Girma ba Haka ba. Sagir karisowa yayi ya rankwafa yana gaida Umma ta amsa mai Tana Fadin"Sagir idon ka kenan..? Rabona da ganinka tun zuwan da kayi gaida Inno Muda ya Kawomim kai..! Kansa na kasa yana Sosa keya yace"Inna ai Karatu ne ke Hanani Zuwa ko"ina ..Ammh Insha Allahu da mun kamallah sai kun gaji da ganinmu..! Umma na Dariya tace"Hakane kuma..Ga Shago nata Habaka Allah yasa albarka..! Tafada tana kallon Shagon Tama kara ganin Cigaba Domin zuwanta na karshe bai kai haka Cika da kekuna da yara ba. Sagir Daddy ya juya yana gaisawar ya amsa mai Cikin Sakin Fuska yana Tambayansa karatu yace Alhamdulillah Afizge Sagir ke kallonsa Haka kurum yaga kamar Fuskarsa da yanayinsa yana mai kama da wani sai dai kuma ya rasa ta ina zai kama..? Yana wannan Tunanin Yaga Daddy ya Bude Kofar Baya yana Fadin"Inteen Daddy Fito mana..Ai mun so gidan Innam taki..! Yafada yana Bude mata kofar Motar,Sagir ya Dago Idanuwansa yana kallon wata kafa mai kyau da Tsari Cikin Cover na kamfanin Gucci ta Zurosu waje kafin ita kanta ta Bayyana Masha Allah ya Furta akasan Ransa ganinta kamar Inna Salaha sai dai ta Dauko Tsawon Babanta da yanayin karam Hancinsa sai dai Fatanta irin ta Inna Sahala ce mai Duhuwa. Sanye take da Doguwar rigar Abaya Kirar Armani ta amsheta Tayi mata kyau sosai sai gyalen Abayan Datayi Rolling dinsa Daga Tsakiya tudun gashinta Data Tamkesa da Band,Hannunta kuma karamar Jakarta ne da wayarta sai takardunta wanda Tayi Cike cike a makaranta.. Lumsasun idanuwanta ta Lumshe Tana Bin yanayin wajen da kallo Lokaci Daya tana Shan iskar wajen kafin ta wani Dakuna Fuska Tana Fadin"Allah Daddy am Tired..! Umma ta Harareta Tana Fadin"Kedai Raguwa ce..Baki ga yayanki bane ba gaisuwa..? Tafada Tana nuna mata Sagir Daya gama kare mata kallo yana ganin ikon Allah katuwar Budurwa Tana Shagwaba kamar yarinya..Tabdijam wannan ne zata Zauna agidansu?akwai aiki..! Kallo Daya tayi mai ta kauda kanta kafin ta Rausayar da kanta Tace"Umma kinsan fa in nagaji bana gane kowa..Ina yini..? Ta fada Tana wani Yamutsa Fuska Kamar ta wurgar da kayan Hannunta Amsa mata Sagir yayi yana Fadin"Barka da zuwa kano kanwata..! Jin abunda yace ne yasa ta Sakarmai Mirmishi har Fararan Hakoranta suka Bayyana tace"Thanks yaya sagir..! Yaji Dadin haka Umma ce ta katse su da Fadin"Alhaji Bude Booth Sagir samu yara su shiga da kaya Ciki inteesar mu karisa Ciki nasan Yaya ta gaji da jiranmu..! Daga haka ta wuce gaba Inteesar ta Daga kafarta Dakyar dataji sun mata Nauyi tsskani ga Allah ta gaji inda wani zai karban mata kayan hannunta Datafi kowa Murna. Sagir ne yafito yaran Shagonsa da Hannu suka Fito suna Shiga da kayan da Daddy ya Bude Shake da Booth din Motarsa akwatunan da Kayan abinci Cike aciki haka suka dinga kwasa suna Bin bayansu Umma zuwa Cikin Gidansu Sagir. Sagir kuwa da Daddy basu Shigo ba sai da aka gama Shiga da komai kana Sagir yamai Jagora zuwa Cikin gidan. Suka iske su Umma a Falon Mama dan madaidaici mai Dauke da Saitin kujeru Sabbi wadanda Sagir ya saka akayi mata,Har da Cafet din ga Tibinta da Reseventa,Sai karamin Center Table a tsakiyar falon da karamin Fridge dinta Daman Daki Ciki da Falo ne sai Tiolet aciki Ko"ina Tsab Mama bata da Kazanta ko kadan. Tana ta ina ta saka da su Umma Inteesar kuma na kan kujera mai Zaman Mutum Daya ta lafe Tunda ta samu ta Zube kayan Hannunta tasha Ruwa taji ta fara Dawowa daidai. Mama ce ta cika gaban Daddy da Lemuka da ruwa sai Kololin Abinci kansa na kasa suna gaisawa Tana Tambayan Bashir da matarsa da yaransa duk yace mata suna gaisheta ta gangaro Kan Lafiyar Daada yace mata alhamdulillah. Mama ta juya tana kallon Inteesar da idanuwanta ke Lumshe Tana Fadin"Yata..Barci kike ji ne..? Tashi kici abinci ko wanka zaki fara ne..?naga alamar duk kin gaji..! Umma na Dariya tace"Baki ga alama ba..Dayake kun iya Haihuwa Raguwa y'a ba..! Mama na Dariya tace"Eh munji bakomai..Tashi ki Farayin wanka kafin kici Abinci.Kai kuma Sagir Tafi da Alhaji Dakin ka sai yaci Abincin a natse..! Daddy yaji Dadin haka Duk da ba wani yunwa yake ji ba Ammh zai fi Sakewa achan Sagir yamai Jagora Zuwa Dakinsa Dake kallon na Mama Shima yana Shimfide da Cafet da katifa Daya yada akasa sai littafan karatunsa na makaranta Dana addini sai Akwatin kayansa da Hanger Dayake Sagale kayansa na sawa sai wasu Drowers Daya kan ijiye wasu kayan Daya Dinka in yagama wadanda ba"a amsa da Wuri ba Komawa yayi ya Daukomai Abincin Ruwan yana kara mamakin Girman Inteesar ya Dade bai ganta ba Tun tana karamarta Kamar tun wani Zuwa da Inna Salahar tayi da ita,Bata kara zuwa ba sai yau Dayake yanzu wannan zamanin ba damuwa akai yi da Zumunci yara ba In manya sukayi Shikenan,Kuma ita bata cika Bin Umma anguwa ba basa Shiri bata Daukan Sangartata Tafi Tafiya da Daddyta Shi Dayake Biye mata. Wankan ta Shiga Daman Shi take da So,Mama da kanta ta Juyo mata Ruwan Zafin Data saka afulas,ta kai mata Har Tiolet kuma ta kwashi wayarta da Jakarta da Takardunta ta kaimata Ciki kan gadonta Sabo 6by7 na karfe wanda Sagir din yayi mata tare da kujerun Dakin nata,Sai katifa Lamba goma Sha Biyar sabuwa Dake jingine gefe sai karamin wardrope dinta mai Kofa Biyu,sai Ledan daki Sabuwa malale ga kayan Inteesar nan jere agefen gadon da akwatuna da wasu ledoji kayan abincin kuma Suna Falon Mama,Tunda Umma tace nata ne Tana ta Godiya Kamar bakinta zai Cire Umma na Fadin bakomai. Bayan Shigar inteesar wanka ne Umma da Mama suka zama Bayan sun gaisa Mama tace"Ya wajen su Inno..? Dazu da safe Muda ya kirani munyi waya da Mallam Babba nace musu kina Tafe sukace ai jiya Inteesar din tazo tayi musu sallama..! Umma tace"Eh Taje..Tare naso muje ammh ban samu zuwa ba..Taje har gidansu Nasara,! Mama tace"Allah sarki..Suma munyi mgana dasu Ranar Har Yaya Salisun Yake fadamin Nasaran zata Fara karatu itama anam kadunan..! Umma tace"Eh kasu zatayi ita..! Mama tace"Allah ya taimaka..! Umma ta amsa da Ameen Ameen suka Cigaba da Hiransu na Zumunci. Inteesar kuma taji Dadin wankan Datayi da ruwa mai Zafi Bayan ta Fito ta Fiddo kayan Shafanta ta Shafa ta Bude akwatinta ta Dauko wata Riga da Sikat mai gajeren hannu ta saka Saboda sune na zaman gidanta,atamfa ko wani leshi bai cika Damunta ba sai Umma ta matsa mata ko kuma taje gaida Inno ta isheta da Mita haka Daada Shiyasa bata marmarin zuwa Dukku har yau har gobe Shiyasa ba kowa ya santa ba sai dai sunanta da aka sani ba. Bata wani cin yunwa tunda sun ci abinci kan gadon ta kwanta Tana Sauke Numfashi Lokaci Daya Tana bin Dakin da kallo Tana Hura hanci tana Shakan kamshin Turaran Wutan da Mama ta Turara dakin dashi Masha Allah komai tsab Dashi Dakin ya Burge inteesar Duk da bai kama Kafar Dakinta na Gida ba sai dai ita Ba haka iyayenta suka bata Tarbiya ba,Bata da Dagawa ballatana Girman kai Kowa Daya ta Daukeshi Umma ta Koyamata iya zama Duk inda Rayuwa ta Fada mata ballatana ita kanta umman ba masu arziki bane Har yau har gobe Mallam Babba Hatsi yake saidawa akasuwa Itace sana'arsa Mahaifinta ne mai arzikin ammh bata da Halin kyama ko nuna tafi kowa barta da Sangarta da Tabara irin na yaran da iyayansu suka Shagwaba Shima bawai na Dolanci ba Domin tasan me take yi. Tana Daga kwwncen Taji Umma na gayama Mama ta rika Zaneta in Taga zata mata Sangarta ta tsawatar mata kamar yadda Zatayi ma Sagir Mama tace bakomai Insha Allahu Baza"a samu matsala ba,Tana da kwancen Take Tura baki,Sanin Halin Umma taso ta Fito Wajen Daddy suyi Hiran bakwana Gajiya ta Hanata Tun tana Jin Hiransu Umma har barcin yammah ya kwasheta sai dai Taji Umma ta Daga mata Duka Tana Kiran Sunanta. Bude Idanuwanta Tayi Cike da Barci Ta saukesu kan Umma Data Dauro alwala ga Ruwa nan na Diga,kan Fuskarta Hararanta Umma Tayi Tana Fadin"Kinga irin Halin naki ko..? Sai ki tashi kiyi Sallah..! Tafada lokaci Daya Tana kokarin Sanya Hijabi ta tada Salla kan Darduman da Mama ta Shinfida mata. Dakyar Inteesar ta iya mike Jikinta duk ya Mutu ga kasalan Data kamata ta Shiga Tiolet tayo alwala Tazo gefen Umma Ta Tada Sallah bayan ta Bude karamar akwatinta Data Jera Sabbin Hijabanta da mayafanta ta Dauki Daya cikin wanda Anty Hauwa ta bata ta saka ta tada Sallah. Nan itama Mama ta Shigo Tayi alwalan Tayi sallah Bayan ta idaar ne ta juya tana kallon Inteesar tace"Maryam bazaki ci abincin bane..? Inteesar taji abun wani bambarakwai Domin bamai kiranta da asalin sunanta sai Inteesar,Kai ta gyada kafin tace"Kila sai anjuma Inna Cikina ya cika..! Umma ta karbe da Fadin"gatanan sai kin mata da gaske..Bata son Cin Abinci shiyasa kullum Zaki ganta jiya iyau Sillen kara kamar a Hureta ta Fadi..! Umma ta karishe Fade Tana yar Dariya ganin yadda Inteesar din Ta Zumbura baki tana Dakuna Fuska ganin haka yasa Mama Jawota Jikinta ta Rumgume Tana Fadin"Kyale Sahala..In kika Tashi Zuwa Hutu na Tabbata bazasu ganeki ba..In ita bata son yar Dake ni ina so..Daman Daga Sagir sai ni agidanan naji matukar Dadin zuwan yata..! Tafada Cikin nuna Murnanta Sai Ta bama Inteesar Tsausayi Sai ta kara Lafewa ajikinta Tana Fadin"Yauwa Mamata..Daman Umma bata sona..Nima na samu Mamata yanzu..! Umma ta kyabe baki Tana Fadin"Kuje kuyi ta kaya..Indai wannan ne zaki dawo min ne..! Mama tace"Insha Allahu bazamu Taba Dawowa ba sai adawowar alkhairi..! Inteesar sai Mirmishi take Na jin Dadi Bazatace batasan Inna Amina ba,sai bata taba Zama da ita sosai haka ba wani lokacin in tazo tana makaranta sanda zata Dawo kuma Sai tatafi Gidan Inno ranar data kwana gidansu kuma Tana Dakin Umma ba wani Shakuwa Tsakaninsu sosai... Hira suka Cigaba da yi sama Sama Inteesar an samu Abunda ake so sai ta kara lafewa Jikin Mama Kamar wata mage har tana lumshe ido,Abunda bata samu wajen Umma ita bata yarda da wannan Sakarcin ba. Suna cikin Hiran ne sai ga Sagir ya Shigo bayan yayi sallama Suka amsa mai ya Shigo Ciki ya Duka yana gaishesu da yammah suka amsa mai sai yake fadamusu Daddy ne zai wuce masauki sai Gobe zai Dawo. Mama ta Mike Ita da Inteeaar Dataji Zencen Tafiyan Daddy. Umma ma ta mike,Mama ce tace"Bazai kwana anan ba Salaha..? Tunda ga Dakin Sagir zai Ishesu sai shi ya barmai katifar Shi kuma sai ya kwanta kasa..! Umma tace"Haka kawai Yaya Amina shi da Dakinsa yayi kwanan kasa..? Barshi yaje masauki Koma kinyi mgana bazai Zauna ba..! Mama bataji dadi ba tace Shikenan Dukkansu suka Fita Tsakar Gida Inda Daddy ke Tsaye da Gudu Inteesar ta isa gareshi ta Rungume Tana Fadin"Daddy na..! Shima riketa yayi yana Fadin"Intee ta..Uwata ta kaina..! Yafada Lokaci Daya yana Shafa kanta,Kara lafewa tayi ajikinsa kamar wata mage Sagir Dake gefe aransa yace"Yarinyar nan akwai Shagwaba..! Mama ce tace"Alhaji bazaka kwana anan ba..? Naga ai duk gida ne..? Daddy yace"A"a Yaya Amina bari naje masauku da safe zan dawo mu wuce in Allah ya yarda..! Bata da tacewa illah ta Bishi da Allah ya kiyayewa ya Fice Yana Rike da Inteesar Umma da Sagir suka Bi bayansu Har zaure Inteesar ta Raka Daddy tana ta mai Shagwaban gobe bazata iya Shiga makaranta ita kadai ba Wahala Umma tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Kada Allah yasa Ki iya..gobe da wuri Insha Allahu muna kaduna in zaki warware wannan Son Jikin naki da Rangwantanki kiyi karatu..Daman Daada ta kira waya tace abaki kina bacci tace na Fadamiki ki Dage da karatu banda Sangarta da Sakarci..! Kafin Umma ta gama mgana Inteesar ta kusa saka kuka Ta kalli Daddy tana Fadin"Daddy kaji Umma ko..? Daman Daada nan itama bata sona.Koda yaushe tayi ta min Fada..Taci ka Fadan Tsiya..! Umma tayi mata Dakuwa Tana Fadin"Kinga naki nan..? Wato Tacika Fada ko..? Ai Mai Biye mikin ma ta isa dashi kuma Fada take yi mai a zauna Lafiya ballatana ke..! Ai sai Inteesar tayi kokarin saka kuka Tana Dira Kafa Daddy ya Dafa kanta yana Fadin"Kada ki bata Hawayenki Inteen Daddy..Gobe da safe ki Shirya da Wuri in xamu Wuce sai mu Biya ta makaranta inkingama Komai kin Fara Shiga lacture sai mu wuce..Ga Dan"uwaki nan sai muje Dashi sai ki samo abokin Dawowa Tare..! Sai alokacin Ta saki Ranta Daddy ya kalli Umma yana Fadin"Sahala bana jin Dadin yadda kike Hantaran yarinyar nan fa..? Duka nawa Intee take da zaki bi ki Rika mata Fada kamar wata Babba..? Ba Umma bace take mamaki ba Domin ita saba gani Sagir ne yake kallon Inteesar yana auna mganar Daddy wai duka Duka nawa take..? Wannan gansamemiyar Budurwance yarinya..?lalle yau yana ganin Abu xai so Imran yana wajen nan ya Tabbata da ya kusa Mutuwa saboda Takaichi. Umma bata tsaya bata bakinta ba ta Juya tana Fadin sai Allah ya kaimu ta shige Cikin gidan Ta bar Daddy na Fadama Sagir gobe tare zasu shiga makaranta Dashi Sagir yace ba mtsala Dayake Shima yana da Lacran safe. Shidai yana gefe yana kallon Sangarta irin ta Inteesar Dakyar ta Saki Daddy ya Fita Sagir ya Rakashi Wajen Mota sukayi ssllama kana ya wuce Shagonsa yana kara mamakin Inteesar afili ya Furta.."Mama zata sha Fama..! Inteesar da Wuri Tayi barcin Tana idar da Sallar Isha"i Ta ci Danbun namanta da Umma Tayi mata,Ta hada da Lemo har mamana mganar bazai taso mata da Daddare ba..?Umma tace"Wannan ki kyaleta inda kika barta Shan zaki da kayan Kwadayi nan tafi auki babu abunda yake mata..! Mama tana Dariya tace muna da lafiya ne,Inta dai Intee Kayan Barcinta ta saka ta Bi Lafiyan gado sai barci,ta bar Umma da Inna Amina suna ta Hira Sama sama take jin suna waya da Inni da Mallam Babba,Sai kuma taji Ya Bashir ya kira ta wayarta Data Manta da ita saboda gajiya Umma ta Dauka sukayi mgana har tabama Inna Amina suka gaisa. Kusan Raba Dare sukayi suna Hira kafin su kwanta Umma kusa da Inteesar ta kwanta,Ita kuma Mama ta yada katifa ta kwanta. Da asuban Fari suka tashi..Mama ta Fita waje ta saka musu Ruwan wanka kana tazo tayi sallah Bayan ta idar suka gaiggaisa ta kara Fita Bayan Fitantane,Umma ta karayima Inteesar fada tana Nuna mata ta Rika Taimakon Mama da wasu ayyukan Inteesar tace Insha Allahu. Mama tayi musu abun karyawa bayan ta juyo musu Ruwan wanka Umma ta Farayi kana Inteesar,suna gama Shirya suka iske kayan Karyawansu tea da Buredi da Soyayyah kwai sai Umma datace Kosai take so da koko suka zauna suka karya atare,Suna Hira cikin Sha'awa Inteesar bata wani ci Abun kirki ba Bata iya cika Cikinta in Zata Fita wani waje ta Dade,Umma ta matsa mata sai da ta saka wata Sabuwar amtafa da Ummanta Ta Dinkamata Doguwar riga Chiganvi mai kalan green ssi tayi amfani da green din mayafi da Takalmi da Jaka. Sagir ma yayi wanka yana Dakinsa yana karyawa sanda Daddy ya karisowa shi ya Fita yayi mai Jagora zuwa Cikin gidan suka gaisa da Mama Da Umma lokacin sun gama suka Tashi suka Fara Shirin Tafiya. Daddy ya duka har kasa yana Damka Amanar Inteesar wajen Mama tace ta karba Tayi alkawarin Zata kula da ita kamar yadda Zata kula da Sagir. Yaji Dadin haka ya Dire mata kudi 30k tace bazata karba ba ya Fice bai Dauka ba. Umma ta Dauka ta bata bayan ta Hada mata da 10k tace ta Rike ahannunta Mama nata Godiya Inteesar kuma sai Hawaye kamar sallaman kenan bata Dauka haka abun yake ba da bata Zabi Karatu a Kano ba. Har waje Mama ta rakasu tana Godiya Tana Daga musu Hannu.Umma ta shiga Gaba Inteesar da Sagir abaya wacce ke ta Sharan kwallah Daddy na gaba yana Tuki hankalinsa na kanta kamar shima ya saki kukan. Daganan basu Dire ko"ina ba sai Cikin Jami"ar Bayero,Sagir bai Rabu dasu ba sai da komai na Inteesar ya kamallah Zata Fara Daukan karatu Daddy har bakin Hall din inda yan Department din su ke karatu suka Rakota Wato Itama Zata karanta Fanni Tsumi da Tanadi wato Economics. Inteesar Tayi kuka kamar Ranta zai Fita ta makalkale Daddy taki sakinsa Harta Umma sai da ta sakata kwallah,dalibai suna ta wucewa suna ganin abun mamaki kuka a jami"a..? Kamar wata yar sakandiri. Dakyar ta saki Daddy,bayan ya Share mata Hawaye,Ya lallasheta kana ta juya ta shiga Hall din Tana Daga musu hannu. Bayan ta Shige ne Sagir sukayi sallama yace shima zai Shiga karatu ne,Daddy ya kara Damka Amanar inteesar a hannunsa yace bakomai yanzu hakama Umma ta bashi Lambarta zai jirata su gama karatu su koma Gida Tare kafin ta saba Daddy yaji Dadin haka 10k ya bama Sagir ya karba yana ta Godiya Daganan sukayi sallama suka Shiga Mota suka kama Hanyar kaduna shi kuma ya wuce Department dinsu yana ta Sauri Tunda yasan an Shiga Tun Dazu! Wayarsa ya Fito da ita yana Dubawa yana tafiya,karamin tsaki yaja ganin har yanzu bai ga kiran Imran ba alhalin tun safe yake kiransa bai Daga wayarsa ba Jiya kwata kwata basu hadu ba yadai kirasa yace ya Turamai lambar Baba Manu ya tabbata ya kai mai kudin Da sukayi mgana ne,Yasan waye Imran in yace zai yi abu baya saba alkawari zai yi din ne yana so yaji yau su Baba Manun zasu je neman auran..? Ammh bai Daga kiransa ba Shiyasa har ya karisa cikin ajin yana ta sskin tsaki.! Abunda Sagir bai sani ba jiyan Banki Imran yaje ya Ciro kudi a Bankinsa wanda baya amfani DashivSai Lokaci bayan Lokaci,Sai kuma yaje Banki ya Cike Form yake iya Fidda kudi Gabadaya kudin bankin nashi Dubu Dari uki suka Rage bai yi mamaki ba yau da gobe bai bar komai ba yana Cire kudi Lokaci Bayan Lokaci yayi Hidimansa kanar siyan takalma,Kaya da Sauran abubuwan da baza"a rasa ba! Sauran dawaniyar Yusuf ke gudanarsu da albashinsa in ya gagara sai ya taba kudin Dake Bankin Abba ko na Marigayi Yayansu Nura saboda Dawaniyar Abba da Likitan Dake zuwa Gida Dubashi da kuma Dawaniyar mganguna,Ammh shi baya karba ko Naira Biyar wajen Yusuf da kudinsa Daya tara lokacin Daya fara aiki a inda suka zauna yake amfani. Bashi da Zabi Dubu dari Biyu 200k,ya ciro ya Dawo Gida a kuma Lokacin ya kira wayar Yusuf yace ya sanar ma Safiya ta Fadama Babanta mgabatansa suna tafe gobe,ya kashe nan take kuma ya kira Sagir yace ya bashi Lambar Baba Manu yana Turomai ya kirashi yafadamai sunansa yace ga kudin nan zai kawomai shi kuma yace ya bari zuwa anjuma yanzu yana gareji ne. Haka kuwa bayan Isha"i Imran yaje yakai ma Baba Manu kudin yau ko Rakiyar Sagir bai nema ba. Yusuf kuwa bai yi mamaki ba Sanin Halin kaninsa Duk Abunda yace zai aikata baya Runtsawa sai ya Tabbatar dashi..Safiya ya kira ya Fadamawa,Sai taji abun kamar wasa Cikin Tsoro Ta sanar ma da Mahaifiyarsu Hajiya Mero ita kuma ta sanar ma da Alhaji Alhassan bayan ya Dawo ya Cije a lebe a Fili ya Furta."Allah ya kawo su lafiya..! Domin ya gama Shirya abunda zai yi goben da Zarar sun zo..Shi da kimarsa da mutumcinsa agari bazai bari saboda Dalilin Safiya wannan Shegen yaron Mara kunya ya Zubarmai da Daraja ba.! *Ba na fara saka Lokacin Posting bane kamar yadda wasu ke Tunani ba,Ni bana Ware wasu ranakun Lokacin Posting,Ina yi duk rana alokacin da na samu dama da Lokaci sai dai in Rashin Lafiya ko ciwo ko wani Uzuri,Domin daman kana naka ne Allah yana nashi na Allah kuma shine Daidai Jiyan nan na wayi gari bani da Lafiya shiya kawo Tsaikun Rashin posting dina ajiyan..Ina ganin Comments dinku ina matukar godiya Yan Wattpaddian Voting dinku yayi kasa fa ya kamata ku kara kaimu nayi muku alkawarin Bazan baku kunya ba Insha Allahu* *Shakira..* 3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *🅿�08* "Asalin sunanta *MARYAM MUSTAPHA HAMISU DUKKU* ne Saboda taci sunan Mahaifiyar Babanta Daada yasa ake kiranta da INTEESAR. Alhaji Mustpaha Hamisu Dukku Haifaffan garin Dukku ne na Jahar Gombe,ya kasance d'a na uku a jerin ya"yan Daada Maryam da Mahaifinsu Alkalin Kotun Musulunci Alhaji Hamisu Dukku. Hajiya Maryam(Daada) Haifaffiyar garin Dukku ce ta uwa Data Uba Bafullatanan Dukku Ta gaba da Baya,Auran Zumunci ne tsakaninta da Megidanta marigayi Alkali Hamisu Dukku,Domin alokacin Makoci Tamkar Dan"uwa yake wajen makocinsa iyayen Daada da iyayen Hamisu Dukku sun yi Zaman makota shekaru masu yawa wanda Sanadin haka yasa suka Zama Tamkar yan"uwa wannan Dalilin ne yasa suka Hada auran ya"yansu Wato Maryam(Daada) da Alkali Hamisu Dukku. Maryam(Daada) bata yi Zurfi a Karatun Boko ba iyakarta Sencondary Alokacin ma agidan Mijinta Alkali Hamisu Dukku Tayi Candy,Tayi aure da kananan Shekarunta,Saboda Tana da Shekara Goma sha Shida ne alokacin. Alkali Hamisu Dukku,yayi karatun Zamani Dana Boko ya tafi Jami"ar Abu dake Zaria inda ya karanci Shari"a Low,Bayanan yayi Degree dinsa na Farko sai ya Dora bayan haka ya Hallaci Courses masu yawa akan Abunda ya Shafi karatunsa agidansu Shi kadai ne yayi karatun Boko mai Zurfi Duk da basu da yawa shi ne kuma Babba. Yayi aiki a mtsayinsa na Cikakken Lauya ya taka mataki mataki na Rayuwa sun Fara zama da Daada a garin Dukku agidan iyayensa inda ya gada Tunda Lokacin Allah yayi ma Mahafinssa Rasuwa kafin ya samu aiki a babbar katun Jahar Gombe ya mallaki gida da Motar Hawa ya Dauki matarsa suka koma Chan da Zama.. Sun koma ba Dadewa Daada ta samu Ciki,kuma yana bata Wahala sosai Dalilin dayasa Alkali yasa aka nema mata yar aiki kenan Allah ya Hadasu zama da Baba Asabe Tun tana da Danyen Shekarunta Ita take Taimakon Maryam(Daada)da abubuwan Cikin gida,Alkali Hamisu Dukku da Matarsa Maryam(Daada) suka Rike Asabe Tamkar wata jininsu ko nace Yar"uwansu.zuwa Lokacin duka sun rasa iyayensu saidai yan"uwa da abokan arzuka. Kabir shine Babban Dansu sai Abubakar,sai Mustpaha sai Fatima (Bintalo) sai auta Maimunatu,azuwa Lokacin da daya Tara ya"yansa Biyar ya samu Dukkan Cigaban Rayuwa,Asalin Komawarsu Dukku samun Alkalin alkalai na Babban Kotun musulunci Dake Dukku ne yasa yayi Ginin Zamani ya Tattaro Duka iyalansa suka Dawo nan da Zama Dindin Daman shi Alkali Hamisu yana da Kishim kansa yafi Sha"awar Zama a Kauyensu Fiye da Ko"ina To itama Maryam(Daada) domin duk inda zasu je basu da kamar Dukku. Alkali Hamisu Dukku bai bar Gidan Duniya ba sai da ya kwafa ya"yansa suka samu Wadattacen ilimin Zamani Dana Boko,Kabir Shine ya gado sa shi ya karanci Harkan Shariya,Abubakar kuma ya kasance Malamin makaranta ne kowa yasan Burinsa Tun yana karami Shiyasa Alkali Hamisu yake mai Lakabi da MALAMI..! Bai kuma bar gidan Duniya ba sai da ya aurar da duka ya"yansa Daga matan har mazan Bintalo Tana aure anan cikin garin Gombe,Tana auran wani ma"ikacin Fire service na Jahar Gombe kuma agidansa tacigaba da karatunta ayanzu haka Lacture ce itama anan Jami"ar Gombe Yayanta Uku Dayake bata cika yawan Haihuwa ba saboda Karatunta,Siyama da Hamida sai Hauwa"u Duka matane kuma Suna Gijajen mazajensu sunyi aure suma sun Haiyayyafa. Sai Maimunatu Tana chan Garin Bauchin yakubu Tana auran wani Soja ne,Ita tana da ya"ya sun kai bakwai,Manyan ya"yanta itama mata ne sai Mazan Sa"id da sadam. Sai kabir wanda ke Zaune a chan Birnin Tarayyah Abuja Yana mtsayin Cikakkem Lauyan gwannati ne,yana da mata Daya Asma"u wacce ta kasance Diyar Masu kudi ce Diya ce ga Alkalin akalai na kasa gabadaya,Sun hadu ne a wani Course Dayaje karanta a Washington,Itama taje Dukkansu Lauyoyi ne suka Fara Soyayah har takai su ga aure duk da Mtsayinta da Nasabarta Barrister Asma"u taga Barrister Kabir Hamisu Dukku kuma tayi na'am Dashi Mahaifinta bai hanata abunda take so ba Tunda su yan Boko ne abunda duk kake so Shi zakayi. Dagashi har matarsa Lauyoyi ne masu Zaman kansa,Tsarin Gidansu tsarin Gidan yan Boko ne gaba da Baya Gabadaya Haka suka Tsara Rayuwarsu Shiyasa ko a tsarin Haihuwa ya"yansu Uku ne Biyu mata daya Namiji Babba ne Namiji mai suna Hamisu wanda yaci sunan Marigayi Alkali Hamisu Dukku suna Kiransa Khamis,Yana Chan Anambra inda yake aiki a mtsayin Sojan Ruwa Navy. Sai kannensa Guda Biyu Sajida da Umaima wadanda Tazara ne mai Nisa a tsakaninsu dashi..Hakama Tsakanin Sajida da Umaima akwai Tazaran shekaru kamar Hudu haka. Sai Abubakar wanda Shima yayi aure kuma shima yana da ya"ya, Sai Lokaci Daya aka Nemehi aka Rasa Shi da iyalansa Wadanda suke a Rayuwa a lagos,Tunda Shi Abubakar din Malamin Philosopy ne a University of Lagos achan baya kafin wata kaddara ta Gitta musu wacce Tayi Sanadiyar Faruwar duk abunda ya Faru. sai Mustapah wanda ya kasance Dan kasuwa ne,kasuwanci ya karanta Domin Shine Burinsa,yana kasuwancin sai da kayan Mota,sai kuma yana Kiwo Harda gidan gona gareshi achan kaduna matarsa Salaha itama yar kaduna ce a Badarawa,Ita yar Talakawa ne ba masu Hali ba Inno da Mallam Babba,wanda yake sana"ar sai da Hatsi,su Biyar ne agidansu Yaya bala ne Babba,sai Yaya Salisu,sai yaya Amina sai Salaha(Umma)kenan sai karamin kaninsu Mudanssir. Auran Soyayya sukayi Tsakanin Shi da Salaha Allah ya Hada auransu yana Zaune anan garin kaduna anguwan Sarki inda ya Gina katon gida,Allah ya sakama Kasuwancinsa albarka Shima din za"a sakasa Cikin Jerin masu Dashi. Ya"yansa Biyu ne rak aduniya Basheer shine Babba wanda Bayan Haihuwarsa har sun Fidda rai da Haihuwa bayan Shekara Goma kana suka samu Haihuwan Inteesar wacce taci sunan Daada Maryam. Atsarin Rayuwarsu Suna da Hadin kai da Zumunci a tsakaninsu kuma suna Girmama junansu Bayan Rasuwar Alkali Hamisu dukku wanda Ciwon Hakoribyayi sanadin Mutuwarsa Daga Dare zuwa safe,Su suka Cigaba da kula da Daada da kuma Baba Asabe da suka Taso suka ganta agidansu,Kabir yaso ya Dauke Daada Daga Dukku ta koma Wajensa a Abuja ammh Taki yarda tace Yarda Alkali ya Mutu acikin gidanan itama nan Zata mutu Domin ya rasu bazata Ki Burinsa na son Ta Rayuwa ita da ya"yansu a garin na Dukku ba sai dai bata da yarda Zatayi ne Tunda aiki ya Raba kowannesu Inda yake ammh Ita kam ba inda Zataje Tana Tare da Baba Asabe a garin na Dukku agidan marigayi Alkali Muddum rai. Dole ya kyaleta Tunda ta kafe sai da yasa aka gyara gidan aka Maidashi na Zamani kowani Lokaci suna zuwa ganinta in suka samu dama. Kayan alatun More Rayuwa kuwa da jin Dadi Daada sai dai ta bama wasu Komai na Rayuwa ya"yanta sun Dauke mata shi Taje ta Sauke Farali bata san iyaka ba bayan wanda marigayi Alkali ya kaita kuma suka je Tare,Hatta Baba Asabe taje ta sauke Farali Sau Biyu Adalilin Daada da Yayanta Daada Tayi kokarin Hada kan ya"yanta da Jikokinta waje Daya suna zuwa mata Hutun karshen Shekara Duka matan da Mazan Domin kara Shakuwa tsakanin iyayen da kuma yaran sun san junansu da yan"uwansu gabadaya,ammh abun ya ki faskara sai da ya"yan nata su zo,ammh Ya"yansu basa zuwa sai Dai dai,in tayi mgana sai su kawo uzurin makaranta da aiki da sauransu. Barrister Asma"u matar Kabir itace bata Shiga Mutane,Tana da Dagawa da Takama sai dai Tana da Fara"a in ta saba da Mutum,Taso tazo Daya da Umma Salaha,Suna dasawa sosai Ko Saboda yadda wata kakkarfan Shakuwa ke tsakanin mazajen nasu ne oho Cikin ya"yanta Sajida ce kadai ta gado Duka Hallayarta Har ma ta fita sosai. Sajida akwai Dagawa ga Takama ga Raini,Tana ganin tafi kowa Domin iyayenta sun tsaya mata sun kuma taka wani abu a Rayuwa,Yar gatace ta gaba da baya,agidansu basu san suyi aiki ba komai yan aiki keyi musu hatta da Girki kuwa,Inda Asma"u tayi kuskure kenan ko ita batace ta iya wani Girki ba Tun farkom auransu ta sakarma yan aiki Duka Ragamar Gidanta Har yau har gobe Abincin yan aiki yake ci kuma bai Taba Korafi ba saboda sun Tsara hakan Daman tun Kafin suyi auran Khamis ne ya Debo kaf Hallayan Babansa,kuma ya Debo Hallayan Marigayi Alkali wanda yaci sunansa yaro ne matashi mai Hankali da natsuwa yana Bala"in son Tsohuwa Daada,Musamman Daga Anambara yake zuwa ganinta in ya samu Lokaci Waya kuwa Lokaci bayan Lokaci Tana jinsa kudi kuwa makudai haka yake Turomata,Duk Shekara sai ya Sauya mata Furniture din gidanta Shiyasa itama take matukar ji Dashi,Sai dai duk yadda take ji Dashi ba kai Soyayyar Datake ma kwara Daya Cikin Jikokinta ba Dukda ya kasance mai Budadden Hali da kowa baya jin Dadin mu"amala Dashi ita ahakan take matukar sonsa,sai dai Bata nunawa ba..Tunda bai Cika yawan Tako kafarsa Dukku ba sai da wani Babban Dalili Shima din sai Mahaifinsa ya Mtsamasa ne ya Tarosa suka Taho Tare,bawai bai Damu da kowa bane a"a yana Damu da Ahalinsa sai dai shiyanayin Rayuwarsa marasa son Doguwar mu"amala ce mara son Hayaniya da Zama Cikin Mutane, yana da Bambacin Ra"ayi da Mutame Koda kuwa yan"uwansa ne Shiyasa bai Cika Shiga Cikin yan"uwa ba,adangi ba wanda zai ce ya taba Doguwar mu'amala Dashi,ko da yan"uwansa da suka Fito Ciki Daya suna kuka da Hallayarsa masu Tsauri da Wuyar Fahimta. Wannan kaunar ta samo asali ne da kaunar Datake yi ma Mahaifinsa ne saboda ya kasance mai sanyi Rai ladabi Biyayyah ko baya son Abu indai Daaada ta Ce abu kaza ne sai yayi shi Biyayyarsa da wannan Sanyin nasa yasa Daada ke matukar sonsa uwa uba kuma ta wanke Diyar kanwaarta Data Zama kamar itace komai nata ta Riketa ta bashi kuma ya karbs ya aura ya Zauna da ita Har Mai Rabawa ta Rabawa Duk da Ya kawo mata wacce yake so. Shiyasa har Yau har gobe Daada bata daina kukan Rashinsa ba Ta kamu da Ciwom Hawan jini Saboda Damuwa ya"yanta suke Wahala kan lafiyarta Musamman Kabir ya Daukan mata Likita wacce take zuwa har Gida Tana kula da ita Dr.Zubaida Cikakkiyar Likita a babban asibiti dake garin na Dukku. Koda Daada ta tsufa Girma ya zo mata bata da Lalaci,kowa ya sani mace ce mai tsayawa akan kafarta Shiyasa bata Shiri da Sanganta da kiyuwa Sajida na yawan zuwa Hutu gidan Daada sai dai Rabuwa sukeyi ba Dadi Tun Kafin ma Hutun Sajidan ya kare. Umaima kanwarta ta fita sanin ya kamata gata bata kiyiwa in tazo Shara gyaran Daki har girki Take Taya Baba Asabe,gidan ta koyi wasu girken girken Data koma Abuja ta gwada Ranar Diyar Lauyoyi Taga Fada kamar su Daketa suna Fadin kada ta kara Wannan kwarambanin Hannunta bai yi kwarin da Zata yi Girki ba kada ta kone Itakuma Sajida Fadi take Tana Diyar Lauyoyin gwannati Jikar Alkalin akalai na kasa Duk da yayi Ritere,Kudi da jin Dadi sun gama Dabaibaye Rayuwa komai take kudi zasu yi mata Allah ya Tsareta da aganta tana aiki indai akwai yan aiki da kudi zasu yi mata komai Shiyasa basa Shiri da Yayanta Khamis Shima a tsaye yake a kullum yana tsawatar mata Da cewa ita macece Watarana Zatayi aure ammh Sai mahaifiyarsu da suke kira Mami ta Shiga mganar tana Fadin ya Daina Takura ma yarta yadda ta Samu jin Dadi agidan Mijinta itama Zata samu,Shidai kawai Shiru yake domin yasan Watan Watarana Zasu yi Nadaman wannan Rayuwar Bokom da Sakewan da suka Daukan ma kansu Shi Allah ya Taimakeshi Gombe yayi karatun Secondary Dinsa Bording in ya sami Hutu bai cika zuwa Abuja ba yana gaban Daada Shiyasa ya zama Dabam Yar tsamar Dake tsakanin Inteesar da Daada kuwa bawata maiyawa bane..Duk da tafi kowa Murna da Akayi mata takwara sai dai basa Shiri saboda irin gatan da Alhaji Mustpaha yayi ma Inteesar saboda Samunta Lokacin da suka Fidda rai. Inteesar ta shaku da Mahaifinta Fiye da kowa aduniya ko Mahaifiyarta bata Shaku da ita ba irinsa ba,Dalilin haka yasa bata da Sakin jiki da Mutane bata san kowa ba sai Daddynta sai Ummanta da yayanta Basheer sai kuwa Gidan kakaninta ta Bangaran Uwa gidan su Inno,Su da suke Biyema Sangartanta. Inteesar bata san kowa a Dangi ba Domin bata zuwa ko"ina gwara Dukku ma in Alhaji Mustapha zai je takan Biyosa suzo Tare,Bata yarda ta kwana Kafarsa kafarta Duk kuwa da Mitan da Daada ke yi na bata son Shiga Cikin yan"uwanta.ita kuwa bata son Rabuwa da Babanta ne kuma tafi sabawa dashi Fiye da kowa. Rabon Inteesar da Zuwa Dukku har ta manta saboda Korafin Daada akanta,Tayi ta cewa ta Cika Sangarta tayi ta ma Daddynta Fada kan ya Sangartata ita kuma abun Haushi yake bata yasa Daga Baya ta Daina Biyosa sai ta Fake saboda makaranta. Ko Duka gidan Za"aje sai dai taje gidan Inno ko gidan Kawu Salisu Saboda yarsa Nasara sa"ar Intee ce kuma tasu tazoDaya Shiyasa bata san kowa ba adangi su Inna Bintalo da Inna Maimuna sun gaji da mita sun Hakura Inteesar bata taba zuwa Gidan Daya Daga Cikinsu ba ko Za"aje bata zuwa bata son Abun mgana. Tuni ta Dauke kafa Daga Dukku Tun Tana karamarta har saida taGirma Lokacin Data gama Candy Tana jiran Sakamako Daada ta matsa Umma ta Ce sai taje tayi Kwana Biyu achan,Daddy shi ya Lallasheta yakai ta da kansa Aranar Dataje Washegari Sajida ta iso Daga Abuja. Inteesar bata ji Dadin Zaman Gidan Daada ba,Shiyasa Dukkun ta fita kanta Zaman da sukayi da Sajida Zama ne na kowa na Har kan gabansa Sajida girman kai da Dagawa..da nuna isa ita kuma Inteesar rashin Tsoro,itama tana ji Da gata sosai Shiyasa basu ga maciji,Daada ta Dinga Fada ita Sajida Kiyuwa da son jiki ita kuma Inteesar Da an fara mgana sai kuka Daada Tayi musu Fatata ta kira iyayansu suka zo suka Tarkasu,kowacce ta koma Gidansu da jin Haushin yar"uwanta,Sajida tana ganin kamar ita yar gata gaba da baya Diyar lauyoyi,yayanta Soja jikar Alkalin alkalai har wata adangi Zata Rainata Ina batazata yarda da wannan ba ita kuma Inteesar tana ganin ai Sajida bata fita gata ba bata isa ta taka ta ba. Haka kowacce ta koma Gida da Korafin yar"uwanta Umma dai ta tsawata ma Inteesar din Ta nuna mata yar"uwanta ce ayayinda Mami bata tsawatarma Sajida ba sai ma Nuna ma Datake tafi Inteesar din gata nesa ba kusa ba Duk kuwa da suna Dasawa da Umma sai dai ita akwai son kanta Tana so a ko"ina akomai Ita da ya"yanta su fi kowa a Dangi Ba kuma iya Zuru"ar Hamisu Dukku ba Harta Daga Bangaranta Tana da wannan Dagawan. Daga Lokacin kowacce ta ijiye yar"uwan nata awani muhalli na ban san kina Rayuwa ba,Basheer ne dan Dangi kowa ya sanshi kuma ba inda Kafarsa bai taka ba Tun yana Saurayinsa ma kafin yayi aure Dayake Jami"ar Bauchi yayi ya Zauna gidan Inna Maimuna Sosai yake da mu"amala mai kyau da kowa.. Inteesar kuwa bata taka kafarta Ko"ina ko Abuja gidansu Sajida Sau Daya taje Lokacin Tana karama da Tabi Daddy,daga wannan zuwan kuwa bata kara marmari ba,Lagos kuwa bata taba Zuwa ba tasan dai Tana da wani Uban achan lagos din inda yake Zaune shi da iyalansa ba kuma Tataba ganinsa ba sai Sau Daya sanda sukaje Dukku ita da Daddy Shima yazo shi da dansa bata dai san ko waye ba,Ta gansa alokacin ammh Tana karama bazata iya Shaidasa ba yanzu.Lokacin kuma da akayi Rasuwa anan Dukku aka Dawo aka karbi gaisuwa Lokacin Basu da Hutun makaranta Gidan Kawu Salisu tatafi abunta tayi Zamanta Saboda Nasara Domin aduniya Inteesar Bata da wata wacce ta Shaku da ita Kamar na Nasara kuma tasu tazo Daya daga ita sai Inno da Malam Babba Saboda yadda suke ji da ita sai kawunta Muda,shima akwai Biye ma Shiriritanta... Sajida Ta fara karatun Jami"a a Base University Abuja a wannan Shekara yar Jarida take son Zama,Journalist itama Inteesar Tana so ta karanci Fanni Tsumi da Tanadi Wato Economics,Ta lula kano Inda Zata Fara Sabuwar Rayuwa. ****** Baba Manu ne da abokinsa Alh.Sadi suka Faka Motarsu a kofar gidan Alhaji Alhassan, Da misalin karfe 11am na safe Daman yasan gidan Saboda Zama anguwa Daya da sukayi da yayansa marigayi Mahaifin Sagir. Motar ba tashi bace ta abokinsa ne Alhaji Sadi,ba kuma Domin kawu Manu ya rasa kudin da zai sai Mota ba sai dai shi Mutum ne da baya son yana Bayyana Samunsa kudi ne dashi sosai Donin gareji na kansa gareshi da yara kuma ba Laifi yana samun Rufin asiri,sai dai kuma yana da Zuciya mai kyau ko karatun Sagir Rabinsa shike Tallafe dashi kuma Lokaci bayan lokaci yana zuwa Gidan da kuma abun Arziki ko bakomai ba zai manta da Abunda Mahaifin Sagir yayi masa Ba Duk ya kasance Yaya garesa ya kafashi shine Sanadiyar daya mallaki Garejin Dayake Takama dashi. Shi ya kira Alh.Sadi abokinsa ya gayamai komai ya kuma nemi Daya Rakashi,Shine ya bada kudi aka saka mai suka Shiga kasuwa suka Siya Kwalayrn Minti da Dabino da goro,Kawu Manu ya Rike dubu dari da Hamsi Dubu Talatin kudin nagani ina so sauran kuma na Sadaki ne. Kawu Manu ne ya Fara Fitowa Daga Motan yana gyara Zaman Babban Rigar Shaddan Dake jikinsa Saboda zuwa neman auran nan bai Fita gareji ba haka kurum yake so ya Taimaki Imran bai san Dalili ba. Wajen megadi ya nufa Yayinda Alhaji Sadi ya tsaya kulle Mota shima ya Biyo bayansa yana gyara Babban Rigar yadin Boyel Dake jikinsa,kamar yau ne Daurin auran. Buga get din kawu Manu yayi yana kwada Sallama Megadi ya taso da gudu ya Bude karamar Kofar ya leko yana kallon su kawu Manu Cikin Alamun Rashin Sani. Ganin haka yasa kawu manu yace"Kai Megida nan yana nan..? Megadi yace"Eh yanzu ya shigo..! Kawu Manu yace"Alhamdulillah..Shiga ciki ka Sanar dashi magabata Ne masu Neman auran yarsa suka zo..! Yafada Cikin Tabbatarwa Megadi bai yi gaddama ba ya Juya Zuwa Cikin Gidan Cikin Sauri kamar zai kifa aransa kuma yana ayyana Daman Dalilin Dawowar Alhaji da wuri kenan..?Haba ko daga gani.! Yana wannan Zencen Zuccin ya Shiga Babban Falon gidan yana Rafka sallama Daidai Lokacin da Hajiya Mero ta Fito Daga Dakinta ta Chaba ado zata Haura sama wajen Alhaji. Sai ta Dakata jin sallaman megadi Har kasa ya Duka yana gaisheta ta amsa tana Fadin"buba ya akayi ne..? Kansa na kasa yace"Hajiya Alhaji ne yayi baki..Sunce ace mai masu neman auran yarsa ne..,!. Kuri Hajiya mero Tayi mai da ido kafin tace"Kenan daman da gaske zasu zo din..? Tafada cikin Bayyana mamakinta itafa ta Zata Kawai Fade sukeyi kuma data gayama Alhajin bai wani Damu ba ita azaton ta ya Shiryama hakan ne shiyasa bata Damu kanta ba. Megadi ne yaji Tana mgana yace"Na"am Hajiya me kikace..?. Kai ta girgiza kafin tace"Ka shigo Dasu Falon bakin Alhaji na waje..bari na Shiga na gayamai..! Da sauri ya mike kamar ya Kifa yana amsawa da Toh ya Fice ta Bishi da kallon kafin ta kada kai ta Fara Haura Steps tsakani ga Allah Auran Safiya da yaron nan bai kwanta mata,Ya za"ayi ace Mutum ba"asan danginsa ba kuma abashi Aure aka sani ko wani mugu ne..?bari dai ta samu Alhajin Tagayamai taji me zai ce..? Ta isa Falon nashi Cikin wani yanayi ta iskeshi Yana karantar Jaridar Dailytrust,ta yau da bai samu karantawa ba Hajiya Mero ta Shigo ganinta da yanayinta yaasa ya gane ba lafiya ya ijiye Jaridan yana kallonta Lokaci Daya yana Fadin"Mero...Meron Alhassan Me ya faru ne naganki wani iri..? Gefensa ta Zauna Tana Fadin"Uhm.megadi ne ya shigo yace kana da baki..! Cikin Sauri yace"Wasu baki ne..? Allah yasa dai bakin da nake zaman Dakon jira ne...? Hajiya Mero tace"Wai Magabatan yaron nan mara asali ne wanda Safiye ke so Kamar ta mutu.Ni ban Dauka da gaske bane zasu zo..! Da sauri ya mike yana Gyara Hulan kansa yace"Daman su nake jira..Saboda su yasa na dawo da Wuri..! Galala ta kallesa kafin tace"Alhaji yanzu da gaske auran yarmu zaka bama wanda bamu san komai game dashi ba? Ko kallomta bai yi ba ya Nufi Hanyar Fita yana Fadin"Nidai ba wannan mganar ba..Ina Fatan kin saka an Shiga da baki na ciki dai ko..? Cikin Daure Fuska tace"Eh nace ya kaisu Dakin bakin ka na waje..! Kada kai yayi yana Fadin"Dakyau ina ita Safiyan.? Hajiya Mero tace"Tana cikin Dakinta mana..! Bai kara cewa komai ba ya sakai ya Fice ta Bisa da kallon mamaki tana Tunanin me ya sauya Ra"ayin Alhajin..? Wanda ta sani da kansa ya kori yusuf kuma yamai iyaka da gidan nan sai dai kuma Ta hasaso Faruwan wani bu..Da kalaman da Imran yazo yayi Tun Lokacin ne taga Alhaji ya Sauya Ra"ayi..? Me ke Faruwa ne wanda Ita bata sani ba kuma Alhaji baya sota tasani din. Cikin saurinsa da Sassafar ya Fito Megadi na gaisheshi Hannu kawai ya Dagamai ya Nufi Falon bakinsa na Haraban gidan Lokaci Daya da sallama Kawu manu da Alh.sadi dake zaune suka mimmike tsaye da mamaki Alhaji Alhassan ya kariso yana kallon kawu Manu Domin yasansa,Farin sani Tunda Yawanci Gyaran Motarsa ko na yara garejinsa akeyimai kuma ya sanshi Dalilin yayan marigayi. Cikin mamaki ya mika musu Hannu sukayi musabaha kafin su koma su Zauna suka Fara gaisuwa Bayan sun gama gaisawa ne Alhaji Alhassan ya Fito da wayarsa Daga Cikin Aljihu ya kira Hajiya Mero tana Dagawa yace"Ki aiko da lemu da Ruwa na bakina..! Daga haka ya yanke kiran ya juya ga kawu Manu yana Fadin"Ikon Allah Mallam Manu..?kardai kace min kasan wannan yaron dake neman yata..? Kawu manu yayi Dariya Kafin yace"Eh to..Banace A"a ba..Sai dai kanin yaron mai neman auran ne abokin Dana Sagir dan wajem marigayi yayana Tasi"u da suka Zauna nan kusa daku..! Alhaji Alhassan yace"ikon Allah..Ko da naji..Domin yaron da kansa ya gayamin basu da kowa kuma nima nasaka am bincikamin..! Kawu manu ya gyara Zama yana Fadin"Alhaji Aure ba mgNar wasa bane..Shiyasa zan gayamaka gaskiya..maganar gaskiya yaron nan bazamu ce basu da kowa ba sai dai muce haka muka gansu Rana tsaka abunda na Fahimta akwai wani Boyayyen al"amari a Rayuwar gidansu,Bazan ce ka bashi Auran yarka ba sai dai kada ka Duba wannan ka Duba Nagartan shi yaron in har kana ganin ba mtsala to ni kuma na yarda na Shige gaba kan al"amarin auran nan da yardan Allah..! Alhaji Alhassan yayi Shuru kafin yace"Wannan bai Dameni ba..Ita taji ta gani Saboda haka Tunda nace mata A"a kuma ta Dage sai shi Zan aura mata wanda take so Taje Tunda ita ta gani ta kuma Zabi a gidan da bai Dace da ita ba..! Kawu manu zai yi mgana ya Dagamai hannu yana Fadin"kunzo da Sadaki ne..? Suka kalli juna shi da Alh.sadi kafin Kawu manu yace"Kwarai..Harda kudin nagani ina so da Mintin da Dabinom mu na Ganin iri..! Alhaji Alhassan yace"Gud..Yanzu abunda za"ayi ku Dauko Dabinom da Sauran kayan..Kawo Sadakin ai bazaku koma ba sai da Amaryarku..! Cikin mamaki suke kallonsa Alhaji Sadi ne yayi karfin Halin cewa"Amarya kuma? Yace"Eh to me zan jira..? Tunda kunzo da komai naku..Kuma ai da Shirin Auran kuka zo Tunda kuka ci Manyan Riguna..! Mamaki bai barsu sun kara mgana ba ganin ya mike ya Fita ya yafito megadi yana zuwa ya Tasa sa suka Dawo Cikin Falon mamaki bai barsu Kawu manu ba sai da suka ga ya zauna ya kalli megadinsa Dake durkushe yace"Zauna Dakyau Buba..Shaida Zakama Auran Safiya zan Daura yanzu..Ku miko sadakin kada ku damu ko nawa ne kuka zo dashi ku kawo..! Ba megadin ba hatta su kawu manu Sai da suka Daskare Jiki ba Laka Alh.sadi da kudin ke hannunsa ya mikama kawu Manu Shi kuma ya mikama Alhaji Alhassan ya karba yana Fadin"Na wa ne anan..? Kawu manu yace"Dubu dari da Hamsin ne..Sadaki da kudin gaisuwa..! Alhaji Alhassan bai tsaya sauraransu ba ya kirga Dubu Dari ya Cire ya maida ma Kawu Manu Dubu Hamsin yana Fadin"Sadaki kadai nake Bukata..Don shima ya zama Dole ne..Ku matso mu Daura auran Ni zan yi ma yata Walicci Megadina zai zama Shaida Cikin ku wazai Wakilci Yusuf din..? Nan da Kawu manu yaji ya muzanta Domin bai ma san Cikakken sunan Yusuf din ba,Sai ya Nemi adagamai kafa ya koma Gefe ya kira Sagir sai da yayi mai kira uku ya Daga Cikin Sauri ya Tambayesa Cikakken sunan Yayan Imu Batare da wani Tunani ba Sagir ya Fadamai Yusuf Abubakar Malami shi a Tunaninsa zasu tafi Neman auran ne.. Abun mamaki baya karewa Cikin Abunda bai fi Minti goma ba aka Tabbatar da Auran Safiyya Alhassan Buhari da angonta Yusuf Abubakar malami kan Sadaki mafi Daraja adaidai Lokacin ne yar aikin Hajiya Mero ta Shigo da Farantin Ruwa da Lemo ba wanda ma ya kalleshi Kowa yana ta mamakin wannan lamarin Alh.Sadi ne yaje waje Cikin Mota Megadi ya Taimaka suka Dauko Kwalayen Minti da Dabino suka Shigo Dasu. Alhaji Alhassan ya basu Hannu sukayi musabaha kafin ya Umarci megadi Daya Dauka zuwa Falon Cikin gida ya Rufamai Baya,bayan ya cema su kawu Manu su jira Amarya ta Fito su tafi da ita.. Kawu manu yaji kansa yayi Nauyi yace"Duk wannan gaggawar na menene Alhaji..? Mirmishi yayi yana ji kamar an sauke mai wani kaya Yana matukar Tsoron Furucin Tsegerun Yaron nan Daya barsa ya Tona mai asiri gwara yayi ya Sallama musu Safiyan ita taji ta gani.. Cikin Dariyan sa yace"To me zamu jira Tunda an Daura..? Kawai ku wuce da ita Daga baya zamu sauke hakkin mu na iyaye akanta zamu muyi mata kayan Daki Yanzu dai ta Farayin gaba Kafin komai ya Biyo Baya..! Daga haka ya Fice Daga Falon yana Rike da Sadakin a Hannunsa.. Kawu manu ya Cire Hula yana Fifita Alh.sadi ya kallesa yana Fadin"Manu wannan wani irin Auran kaddara ne..?meke damun Alhaji Alhassan ne..,? Shidai kawu manu bai samu zarafin mgana ba Tunanin ya tafi kan yanzu ina zai kai yarinyar mutane..? Shidai baisan gidansu Imran ba koma ya sani baya je musu kai tsaye ba Dole dai ta Inda aka Hau ta nan za"a sauka..! *Shakira..* 3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *Jiya 16/02/2020 muka wayi gari cikin Rashi..Rashi mai girma na Rasuwar Wanda yar"uwarmu zata Aura Wato Habieb din Sadiya Sidi Said wannan rashi babban rashi ne gareta garemu gabadakidaya Ya Allah muna rokon ka ka jikan Habieb din Sidiya Allah ya kyautata Zuwansa Allah ya sadasa da Mala"ikun Rahma Allah ya jikansa da Rahmarsa Allah ka bama baiwarka Sidiya ikon da Zuciyar karban wannan Kaddaran nata Allah ya tallafi Rauninta Allah ya bata Dangana da Hakuri Ameen ya Allah* *🅿�09* "Alhaji Alhassan Buhari Fagge Haka yake Tafiya cikin Sassarfa zuwa Shashen gidan nasa,hannunsa Rike da Sadakin Safiya,bayansa kuma Megadi ne ke Binsa Dauke da Kwalayen Cingam,da Minti da Dabino. Bai ji yayi Nadamar abunda ya aikata ba ko kadan ba sai ma Wani Saukayau Dayaji,aduniya Alhaji Alhassan ya tsani Mutane na ganinsa da Daraja da kima,wannan kimar ta Zube,Uwa uba ga Matarsa da ya"yansa Da basu san me yake aikatawa ba ya Tabbata matukar Boyayyen Zunubansa ya bayyana Hatta Jami"ar Bayero sai ta Koreshi,Asirinsa ya gama Tonuwa Mutanen gari Dana anguwa Da suke ganinsa da kima Duk zasu daina Dalilin Safiya gwara ya mika musu ita chan su karata Tunda itataji Ta gani Shi akan Kada kimarsa ta Zube zai iya yin komai. Bai damu ba wasu mutane ba,Inta Danginsa ne bai da Wata Damuwa ko kara ya saka a gidansu bamai Tsallaketa Saboda Shi kadai ne yayi karatun Boko agidan,Shi din Haifaffan garin Fagge ne na Jahar kano,Iyayensa Talakawa ne Futuk Mahaifinsa bashi cin yau ballatana na Gobe a baya Noma yake sai yazo ya samu Ciwon Baya ya kasa kuma Alhassan ne Babba Sauran kannen nashi Duka matane. Karatun da ya samuyi Da Taimakon wani malami ne inda aka kaisa Almajiranci a Dala,Sai Allah ya Hada jininsu da Mallam Iliya,Wanda Da Taimakonsa ya kawo wannan matakin ya Tabbata Da yana Raye shi kadai ne zai Tsawatamai yaji to Ya rasu Da Dadewa,Goggo ce kuma Matukar sonsa Datake yi komai yayi Daidai ne ballatana Sauran kannensa mata da shi ne komai nasu Shiyasa Basu da tacewa. Matsalan ma Daga wajen Hajiya mero ne da Danginta Yar nan cikin Kano din ne a Rijiyar Zaki. Itama Din bata isa ba shi ke da iko da ita da ya"yan da suka Haifa guda Biyu a Duniya Safiya da Tasleem.. Tundaga Falon kasa yake kwalama Hajiya Mero wacce ke Falon sama zaune tana jiran Tsammani Gabadaya yanayin Alhaji yasata Fargaba. Sai kuma taji yana kiranta kiran Daya sa har Safiya Dake Cikin Dakinta ta jiyo Daman tana kwance ne Tana game a wayarta,Sun gama waya da Yusuf kenan yana Tambayanta ko Bakin sun zo..? Tace bata sani ba Ammh kamar basu zo ba saboda har Abban nata ya Fita bata sani ba ta Shiga,wanka Dayake bata zuwa ko"ina Wanchan Shekara ta gama karatu Computer Sciencies ta karanta,Bata fara aiki ba sai dai Tana zuwa wani Cafe Dake nan bayansu Tana aiki dasu Duk ba wai tana musu aikin Parmanent bane,a hanyar zuwan ta ne ma suka Hadu da yusuf wata Bakwai da suka gabata. Abban nata bai yi Niyyar ta Fara aiki ba,Shiyasa bai neman mata ba Tasleem ne kadai ke zuwa makaranta sai wannan Shekaran zata gama Candy. Yusuf bai isa ya kira Imran ya Tambayeshi wani abu ba Domin shi bayason yawan Tambaya da Takura sai dai yafi kowa saninsa in yace Abu to ssai ya Tabbatar dashi ya Tabbata zasu zo din. To sun gama wayar kenan Tana kwance kan gadonta Tana Game taji kiran da yake ta kwalama Mommyn nasu shi ya sakata Zabura ta Sauko Daga kan gadon tazo bakin kofa sai kuma ta kasa Fita jin Saukowan Hajiya Mero Tana Fadin"Abban Tasleem irin wannan kiran fa..? Lafiya..? Hannunta ya Riko ya zaunar da ita kan Daya Daga cikin kujerun Falon kafin ya juya yana Fadin"Buba ijiye kayan hannunka..Kada ka tafi ban gama Dakai ba.! Jikin Buba Megadi na rawa ya ijiye kayan Hannunsa ya Zube kasa yana jiran Umarni. Hajiya Mero tabi kwalayen da kallo Cikin Faduwat gaba kafin ta maida kallonta kan Alhaji Alhassan Tana Fadin'"Nifa bangane komai ba..Wadanan kwalayen fa na miye.? Zama yayi gefenta Lokaci Daya ya kama Hannunta ya Damka mata kudin Dake hannunsa Lokaci Daya yana Fadin"Sadakin yarki ce Mero..Yanzu nan na Daura Mata aure da wanda ta kawo..Tare da Shaidun Waliyansa daya aiko Guda Biyu,da kuma Shaidata Data Buba megadi gashi azaune..! Yafada yana kallon Cikin Idanuwanta Cikin wani yanayi Buba megadi ya jinjina kai yana Fadin"Tabbas..Mun shaida Hajiya..Yanzu nan muka Tabbatar da auran..! Ai da wani Sauri Hajiya Mero ta Mike Lokaci Daya kudin suka Biyota suka watse a kasa kamar Saukan aradu haka taji mganar Safiya ma Dake kofar Dakinta Tana leken Falon bata ji me ya gayamata ba sai dai Yanayin yadda Ta miken ya Fadar mata da gaba sai ta kara Sako kanta Domin Taji meke Faruwa. Cikin wani Bacin rai ta kallesa daga Sama har kasa tana Fadin"Wani irin aure kuma..? Aure sai kace muna garin Gaba gaba Alhaji..? Juyawa yayi yayi ma Megadi inkiya da Hannu daga haka ya Mike ya Fice Domin zamansa baida Muhalli a wajen. Kafin ya maida kallonsa kanta Cikin Halin lko in kula yace"Auren gaske dai wanda kika sani..Miye amfanin jeka ka dawo..? Nayi mgana na Raba yarinyar nan ammh Taki jin mganata Ta rainani Ta turomin su kinga ai gwara na Aura mata shi Taje chan ta karata..! Yafada yana zakuda kafada Cikin Karaji Hajiya Mero tace"Wlh baka isa ba Alhaji..Yata bazata yi aure a wannan gidan ba..Gidan da kace ba gidan arziki bane..Gidan Yan shaye shaye..? Inace ba kanagani yaron nan yazo yaci Zarafin mu Ammh Duk da haka kace suzo zaka basu yarka..? Wlh ban yarda ba yata ba yar tsana bace Su Biyu kadai na Haifa bazan Taba bari ka Lalata musu Rayuwa ba Baka isa ba! Ta karishe Fada Cikin karaji wanda kaf mgangunta suka Fada kunnuwan Safiya wanda taji mganar Kamar Daga sama sai dai bata gama Fahimtar ina mganar ta Dosa ba. Alhaji Alhassan Babatun Hajiya Mero bai Dameshi ba ya kalleta yana Fadin"Ai na ma isa Mero..Tunda har na Daura auran..Kinga ki adana mgangunki Zuwa wani Lokaci Yanzu dai ki shiga ciki ki taya yarki Hada kayanta Waliyan Mijinta suna jiranta zasu wuce da ita..Daga baya in muka zauna muka Tattauna sai musan abunda Zamu yi mata a mtsayinmu na Iyayenta..! Yana Fada Lokaci Daya ya saka kai zai Haura sama Hajiya Mero da Zata out of Control bata san sadda ta isa garesa ba ta Chakume Rigarsa ta Baya lokaci Daya tana Fadin"Baka isa ba..Wlh Alhassan baka isa ba ba inda Safiya Zataje Domin ban yarda da wannan auran ba..!. Ta karishe Fada Tana Fashewa da kuka Mai tsanani Kwace Rigarsa yayi yana Fadin"Mero wannan wani irin Raini ne? Ina Mijimki Uban ya"yanki zaki Chakume min Rigata..? Kada ma ki Fara wannan mgana aure na Riga na Daura kuma Wlh kinji Rantsuwan Musulmai Yau zata tafi Gidan Da ta zaba sama da mu..! Yana karishe Fadar haka ya Tureta gefe sai da ta kusa Faduwa ya nufi Dakin Safiya wacce Rigiman iyayenta ya Tsorarata da kuma Abun ta fahimta yasa ta Bayyana atsakiyar Falon batare data sani ba Idanuwanta sun kala sunyi Jajir,kiris take jira ta Fashe da kuka aure abbanta ya Daura mata..?koda yusuf yake Zabinta ammh ai Tana so tayi auran gata da kowacce mace take yi. Kusa cin karo yayi da ita wanda yasa yayi Saurin ja Baya yana Hararanta Lokaci Daya yana Fadin"Au daman kina jin mu ko..? Toba sai naa maimaita ba ki Shiga Dakin ki ki Hada komai naki da kikasan zaki Bukaceshi Domin na Sallameki gabadaya kije Gidan da kika Zaba Fiye damu Farimcikin iyayenki na Daura Miki aure yanzu nan kuma Waliyan shi wanda kika Zaba suna waje suna Jiranki kada ki Fara Bata musu Lokaci..! Hawayenta ne suka zubo Sharr Cikin Rawan murya tace"Abbu aure..! Bata samu Damar karisawa ba ya Dakatar da ita yana Fadin"Aure nace don Ubanki bashi kike so ba..?har kina saba Umarni na..?Maza ki shiga ki Hado kayanki kizo ki ki wuce kafin na Ci Mutumcinki yanzu anan wajen..! Yafada Cikin Tsawa da Umarni Safiya ta Fashe da kuka Abunda Mahaifinta yayi mata kamar bai Taba ganinta ba taShiga Dakinta ya Bita yana ta Sababin Fada Tana Tusa kayanta Cikin karamar Trolley dinta yana Tsaye kanta yana Bala"insa ta Dauki mayafinta da wayarta ta Sakamayafi ya taso ta suka Fito suka iske Hajiya Mero na tsaye tana Kuka. Suna Fitowa ta Mike ko kallonta Alhaji Alhassan bai yi ba ya Nufi inda ta Zubar da kudin Sadakin yazo ya Tattara ya Sakama Safiya a Hannunta yana Fadin"Kije ni ba zan ce kije kiyi hakuri ba..Sai dai nace miki kada ki kuskura wani abu yasa kice zaki Dawomin gida Bazan karbeki ba Na riga na baki Zabi kuma kika Zabi Gidan da zaki yanzu sai nace Allah ya bada Zaman lafiya ga Sadakin ki nan Hakkin ki ne..Sauran abubuwan kuma Daga baya in muka Tattauna da mamarki Zaki jimu..Zan sauke hakkina na Uba gareki a karo na Biyu..Na cika na aure Tunda na aurar dake..! Daga haka yasaki Hannunta ta jimke kudin Tana jin wani irin Tsausayin kanta me ta aikata haka..? Daga tace Yusuf take so..?menene aibunsa Da har za"ayi mata wannan auran kamar wacce bata da gata..! Kukan ta ya Fito Sarari Hajiya Mero Ta mike Cikin kuka ta kasa Mgana,Alhaji Alhassan yace"Mero kiyi sallama da yarki..Suna waje suna jiranta..! Hajiya Mero taji wani Bakinciki Cikin azama tataho ta Rike Safiya Tana Fadin"Wlh baka isa ba..Ba inda yata zataje..! Tafada Cikim kuka jin haka yasa Safiya ta Fada Jikinta Tana Fadin"Mommy..! Lokaci Daya ta saka kuka mai Cin Rai,Karamin tsaki yaja yana Fadin"Don Allah ki saketa Mero..Miye na wani kuka sai kace anyi mutuwa..? Miye na ganin Laifina abunda yarki ta Zaba kenan kuma na bata..! Tana rike da Safiya tace"Baka isa ba..Bazan yarda ka Gurbata Rayuwar yata ba...Nima ina da iyaye da yan"uwa Zan kira su na gayamusu ina da hakki akan ya"yana Kamar yadda kake dashi..baka isa na Zura maka ido ka Lalata Rayuwar yata ba Alhassan..! Tafada Cikim kuka Wani Shekeke ya kalleta lafin ya saka Hannu ya Bambare Safiya ajikinta yana Fadin"Ai nafi son haka ma..Kije ki kira duk wanda zaki kira..Sai dai ina mai Tabbatar miki ba wanda ya isa ya Tada wannan auran koda kuwa Goggo ce..! Ai fadin haka da yayi yasa ta san yakai makura Tunda ya iyacewa Harta uwarsa bata isa ba to waye ya isa..? Babu shi Tana ji Tana gani ya tasa Safiya agaba Tana kuka Tana kiran sunanta ya Fice daita yana Fadin"Ga Shaidar Daurin aure nanki Raba Biyu..Kashi Daya na mutanen Fagge Daya kuma na Yan"uwanki..Kada wani yace bai sani ba Shaida ne..! Daga haka ya Tasa Safiya suka Fice Daga Falon Yana tafe yana mata Fadan ba ita ta Zaba ba to kukan Uban miye take yi..?ita kuwa Tafe take kawai Tana Jimke da kudin Sadakinta a hannunta da wayarta Dayam kuma tana Faman Jan Trolley dinta. Aharaban gidan suka iske Alh.sadi da Baba Manu su kansu sai da sukaji kamar suyi ma Safiya kuka ganin irin yadda take Shatatan Hawaye wanman wani irin Tozarci ne? Ace budurwa ba bazawara ba A daura mata aure ba wasu Mutane kuma za"a kaita ba wannan wanda zai rakata sai Waliyan Ango..?babu tsinke ballatama wani abun arziiki Gaskiya Alhaji Alhassan bai ji Dadin Rayuwarsa ba kuma Hakki da Kiwon ya"yansa sai ya kamashi. Suna isowa gabansu ya Tura Safiya gabansu yana Fadin"Ki Duka kigaishesu..Sune wanda kika Zaban yayo Haya suka zo Neman auranki..! Yafada kai tsaye yana kallonta kamar wacce aka Damkwafar a kasa haka ta Duka ita da kayan hannunta Tana Fadin"ina...ina..kwananku..! Cikin muryan kuka Da Rauni Tuni Tsausayinta ya kama Baba Manu da Alh.sadi yaji kamar yayi kwallah Bai san sadda ya isa gareta ba yasa Hannu ya Dagota Tsaye Lokaci Daya yana Rike da Duka Kafadunta yace"Yata ki Daina ki Share Hawayenki..Wlh ba Domin ganin idon ki ba..Ni ba wanda yyi Hayata kan nazo Neman auranki..Ra"ayin Kaina ya sani Zuwa da kuma Dalilin kanin Mijin da kika aura..Duk da ban Taba ganin wanda kika auran ba ammh ni naji ji ajikina kin Shiga Zuru"a mai kyau da Nasaba..Sannan kuma ina da Tabbacin suma kamar kowa ne sai dai wani al'amari wanda mu bamu sani ba..Sai dai ina da Tabbacin Zaki zama Sanadiyar Gyara Zamantakewar wannan Gidan ki Cika sa da farinciki Shigowarki ya zameusu Alheri Har karshen Rayuwarsu.!. Yau ta Taba ganinsa ammh mgangunsa sun yi matukar Tasiri acikin Zuciyarta wanda suka sakamata wani Dakewa da Juriya Bata ji ta karaya ba Tana kaunar Yusuf da Zuciya Daya kuma Tayi alkawarin sai tayi Sanadiyar dawomai da Farincikin Data lura yarasa Shi da Sauran yan"uwansa. Da wannan kwarin gwiwan ta Dago Tana kallon Baba Manu kafin tace"Insha Allahu..! Tafada Lokaci Daya Tana Share Hawayenta sai yaji Dadi ya Dafa kanta yana Fadin"Allah yayi miki albarka ya albarci Sabon Gidan daZaki..! Ita acikin Ranta ta amsa Alh.sadi ya amsa afili Alhaji Alhassan kuwa baki yaTabe kafin yace"Gata nan..Nagama nawa Saura naku..Safiya ki kula kada ki kuskura kice zaki Dawon gida da wani mgana kinji nagayamiki..! Kai ta girgiza Idanuwanta na Cika da kwallah Tace"Insha Allahu sai alheri zai kawo ni Abbu..! Daga haka ta Rike Trolley dinta Dakyau ta Fara Tafiya tana kuka Baba Manu ya mikama Alhaji Alhassan Hannu sukayi musabaha hakama Alh sadi kafin suyi mai sallama subi bayan Safiya Harta Megadi sai yaji kamar yayi kwallah Ballatana Hajiya Mero Dake kofar Falon da Haraban gidan Tana kallon Duk Abunda ke Faruwa,Hawaye na Zubo mata kamar famfo,Suna Ficewa Daga gidan Alhaji Alhassan ya Sauke ajiyar Zuciya acikin Ransa yace"Sai yanzu Hankalina ya kwanta..! Daga haka ya juya zuwa Cikin Falon Nan yaci karo da Hajiya Mero Tana kuka ya wuceta yana Fadin"Kina da aiki Mero..Waya isa ya Tada Hukuncin Allah.! Tana jinsa ta kasa mgana sai kuka acikin Ranta kuma Fadi take"Hukuncin Allah ko Hukuncin ka..? Daga haka ta juya zuwa Cikin Falon da gudu tana kuka ko Kwalayen Mintin Dake tsakar Falon bata bi takai ba ta Shige Dakinta ta Fada Kan gado Tana wani Gunjin kuka gabadaya ta rasa mafita ballatana ta kamo Zaren yadda Zatayi. **** Su Baba Manu suna Tafe a Mota Safiya na gidan Baya ta saka kanta tsakanin Cinyoyinta,tana ta kuka Baba Manu na gaba Alh.Sadi na Tuki ammh an rasa mai cewa komai gabadaya lamarin ya Daure musu kai uwa uba ga Tsausayin wannan Baiwar Allah Safiya,Shiyasa suka rasa bakin Zaren kamawa. Alh.Sadi ne ya juyo yana kallon Baba Manu kafin yace"Ina muka nufa yanzu Manu..? Baba Manu ya sauke Numfashi yana Fadin"Mu tafi Gadon kaya..! Alh.Sadi yace'Inda Matar marigayi Take zaune kenan..?.Baba manu ya Daga mai kai,nan da nan Alh.Sadi ya Take Mota Cikin Lokaci sai gasu a Kofar gidan su Sagir. Firfitowa sukayi Baba Manu ya umarci Safiya Data fito ta FitoJikinta a sanyaye gabadaya Idanuwanta sun koma Jawur sun Kumbura saboda kuka,Ganin tana layi kamar zata Fadi ne yasa Baba Manu ya karban mata Trolley din,lokaci Daya yana leka Shagon Sagir sai yaga Baya Ciki sai yaransa,Nufar gidan su Sagir din yayi Bayan yace ma Safiya ta Biyoshi Shi kuma Alh.Sadi ya jirasa a waje yanzu zai fito. Safiya dakyar take Daga kafarta hannunta Damke da Sadakinta da wayarta kamar ace kyat ta Zura da gudu sai bin ko"ina da kallo Takeyi Tana Tunanin bata taba Shigowa area din ba. Mama Tana zaune a kofar Falonta Tana gyaran wake Bata so Sagir da Inteesar su Dawo daga makaranta bata gama abinci ba Sama sama taji sallaman Baba manu ta Dago tana amsawa cikin Mamaki ganinsa jaye da akwati bata samu Damar mgana ba sai ga Safiya ta Shigo itama Da Hanzari Mama ta mike kafin ta samu Zarafin mgana Baba Manu yace"Amina miko Tabarma ina tare da bakuwa ne..! Batayi gaddama ba ta shiga Ciki ta Dauko Tabarma Lokaci Daya tana Sanya mayafi ta Fito ta Shimfida musu Baba Manu ya zauna Lokaci Daya yana kallon Safiya yace"Zauna..yata..! Jikinta a sanyaye ta Zauna agefe Kanta na kasa tana gaida Mama Ta amsa Cikin mamaki. Kafin ta Dawo da kallonta kan Baba Manu tana Fadin"Baban Sagir lafiya kuwa..? Wannan kuma wacece..? Baba manu yace"Sagir bai Dawo Daga makaranta bane..? Mama tace"Bai dawo ba gaskiya..Domin daya dawo ko zai Tsaya Shago sai ya shigo..! Baba manu yace"Bashi ma a shago Domin na leka ban gansa ba..! Mama tace"Allah yasa dai lafiya..? Kai ya girgiza kafin yace"Lafiya ba lafiya..Yanzu dai shi ga Yarinyar nan Ciki Amina kizo muyi mgana kana..! Mama batayi gaddama ba ta Mike ita ta Dauki Akwatin Safiya Ita kuma Baba Manu ya Umarceta data bi bayan Mama zuwa Ciki. Batayi musu ba tatashi ta Bita Sanan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta zauna Mama ta kawo mata Ruwa ta ijiye tayi Godiya aranta Tana Tunanin kodai nan ne gidansu Yusuf din..? Ammh ai ya Taba gayamata Mahaifiyarsu ta rasu Dagashi sai kanninsa da Kanwarsa da Mahaifinsu suke zaune agidan..? To in ba nan bane gidan su waye nan..? Mama duk ta kosa taji Abunda ke Faruwa Tana Fitowa ta Zauna Kafin ma Tayi mgana ya Rigata da Fadin"Wannan yarinyar dai da kike gani Yau mukaje Tambayan auranta Shine Ubanta ya Dauro auran kuma ya Hadomu da ita..! Cikin mamaki Mama tace"Topha..kamar ana yaki..?to matar waye..? Baba manu yace"Ina abokin Yaron nan Sagir..? Wayake da suna na manta..! Mama ta Zaro ido Tana Dafe Kirji Lokaci Daya tace"Aure Imran yayi..? Baba manu yace"Ba Imran din ba Yayansa..Na manta sunansa ko Wayake da suna ma..! Mama da al"ajabi yagama kamata tace"Yusuf sunansa..?nifa na shiga rudu garin ya haka ya Faru..? Baba manu ya gyara zama ya Shiga Rattabama Mama yadda komai ya wakana Tun daga farkon zuwansu Gidansa Sagir da Imran har yau da abunda ya Faru gidan Alhaji Alhassan. Mama ta saka Salati da Salallami ta Dire Tana Fadin'"Wlh baban Sagir bansan komai game da wannan mganar ba..Yaron nan Sagir bai gayamin komai Yau Tun Safe ya tafi makaranta salaha da sukazo da megidanta kawo autan ta karatu suka Daukesa shi da Inteesar din zuwa Cikin makarantan har yanzu bai Dawo ba! Baba manu yace"Wajen ki Zata zauna tayi karatun kenan..?. Mama tace"Eh Wlh..! Baba manu yace"Allah ya bada sa"a..Kin dai abunda ya faru yanzu ya zamu yi ne..?Me kika sani game da Gidansu yaron nan Amina..? Mama ta gyara Zama Tana Fadin"Wlh bana ce maka nasan komai ba..Ni dai na san Imran din abokin Sagir ne Allah ya Hada Jininsu..Sai kuma nasan basu da kowa Daga Mahaifinsu sai shi Imran sai kanwarsu sai Mahaifinsu Dake kwance ba lafiya Domin na Taba shiga Gidan Sau Biyu na gaidashi..! Baba manu yace"Ina mahaifiyarsu..?ina yan"uwansu da Sauran Danginsu..? Kuma laluran meye Mahaifin nasu ke Fama dashi..? Mama tace"Wlh nidai bansani ba..Sagir dai ya gayamin yace Daya Takurama Imran din ne da Tambaya ya gayamai mahaifiyarsu ta rasu mganar Danginsu kuma Wlh shi kanshi Sagir din bai sani ba Imran din baitaba yarda ya gayamai komai ba Laluran Mahaifinsu kuma Ni bansani ba ammh Tabbas Bashi da lafiya yana Cikin Daki kwance ko Falo baya Fitowa..! Baba manu yayi Shuru bai yi mgana ba illah Ajiyar rai Daya Sauke Lokaci Daya ya Zaro Wayarsa yana Fadin"Bari na Kira Sagir din yazo ya kira shi abokin nashi..! Mama ta kada kai Alamun hakane din ne. Baba manu ya kira Sagir,Shi kuma Lokacin yana cikin Makaranta ammh sun Dade da Fitowa daga Lacture,Inteesar yake jira saboda kada ya tafi ya barta bazata iya Dawo wa gida ba. Yana Dagawa Baba Manu ya Tambayeshi ko yana ina..? Yace yana cikin makaranta nan da nan Baba Manu yace in babu Abunda yake yi ya zo gidansu gsshi yana Jiranshi Hankalin Sagir ya tashi Dagajin muryan Baba Manu ba waasa acikinta,Gashi kuma Inteesar sun Fito Daga Lacture sun shiga wata kuma yana ma Department dinsu yana jiran Fitowar ta. Ya rasa ya zai yi sai Allah ya Taimakeshi sai gasu sun Fito yamike ya isa bakin Hall din nasu sai gashi Inteesar din ta Fito Dauke da Jakarta da Wayarta sai Takardun Dake hannunta. Tana ganinsa ta kariso gabansa Tana Fadin"La ya Sagir..? Badai kana nan Tun dazu kana jirana bane..? Sagir yayi Mirmishi yana Fadin"Eh mana..Kada ki Fito baki ganni ba ki fara kuka..! Abun sai ya bata Dariya Sai data Dara kafin tace"Sai kace wata yarinya ya sagir..! Yace"Eh mana ai yarinyar ce kada ki kira Babanki kice na barki ke kadai baki gane Hanyar gida ba.! Inteesar tace"Laa..Zan iya fa komawa Gida dakaina Allah..Kuma ai in ina gaban Daddyna ne nake Shgwabata in ya barni ni kadai Am Mature ya Sagir..! Mamakin Surutun yaji kafin yace"Wato Shagwabar ma Kinsan inda kike yinta ko..? Dariya kawai tayi Tana Sunne kai Agogon hannunsa ya kallah Daya na Rana ta kusa ya kalleta yana Fadin"Daman gida nake son Tafiya an kiranibshine nake Tunanin bazaki iya gane gida ba in an tashi Ki kirani sai nazo Mu Dawo Tare..Tunda ni na gama da makaranta sai kuma Jibi in Allah ya kaimu..! Da sauri tace"A'a kada na Wahalar dakai zan gane ba Gadon kaya ba..?in na samu mai adaidaita yana kawoni anguwan zan gane layin ina da Saurin Dauke abu akaina..! Cikin son Tabbatarwa yace"Kin Tabbata zaki gane..? Inteesar tace"Insha Allahu..!kai ya kada duk da haka bai yarda ba sai ya Fiddo wayarsa ya kirata sai ga wayarta na kuka acikin Jaka ganin tana kiciniyar Fitowa da wayar ne yasa yace mata"Nine na kiraki ga lambata nan ki kirani in baki gane ba..! Kai ta gyada mai Tana Fadin"Thanks..! Jinjina mata kai yayi kafin yace"In zaki yi sallah ki bi ayarin mata yan"uwanki zuwa masallacin Cikin makaranta in wani abu zaki siya ga Cafteria chan..Sai mgana karatu tunda an wuceki da yawa in kika Dawo sai mu Tattauna Dole sai mun samu Wani ko Wata Cikin Course mate dinki da zai mataimaka miki..! Cikin jin Dadi ta amsa mai da haka sukayi sallama ya kama Hanya. Minti Talatin ya bata saboda ya samu go.slow kafin ya kariso Gidan yana Shigowa ya iske Baba Manu har lokacin suna Tattaunawa da Mama Tuni ya Fita ya Sallami Alh.Sadi da Niyyar sau sun yi mgana ta waya ko sun hadu. Yana Shigowa ya Durkusa yana gaida Baba Manu Mama ta kallesa Tana Fadin"Ina ka baromin yata..? Sagir yace"Tana chan basu gama Lecture ba..Ammh ban barta ba sai da ta tabbartamin da zata iya Dawowa da kanta..Na dai bata lambata nace in bata gane ba ta kirani.! Mama ta kada kai kafin tace"Allah ya dawo da ita lafiya..! Ya amsa mata da Ameen kafin ya maida Hankalinsa kan Baba Manu Daya gyara zama yana Fadin"Ina abokin ka..? Sagir yace"imran baba..? Ban sani ba ammh ina kyautata Zaton yana gida Duk jiya bamu hadu dashi ba..! Baba manu yace"Kirasa a waya..Kace masa yazo nan gidan gani Ina tafe da Matar dan"uwansa..! Sagir ya zaro ido yana Fadin"Mata kuma Baba..? Mama ta karbe tana Fadin"Eh suna zuwa uban ya Daura auran.Kuma ya hado su da yarinyar tana nan cikin Dakina zaune..! Sagir yayi Sakace yana bin Mama da Baba Manu da Kallo Cikin mamaki kafin ya Zaro wayarsa a Fili ya Furta"Dankari...! _Masu cewa wai auran Safiya da Yusuf kamar yar tsana..? In kun bibiya labarin zaku iya Fahimtar Dalilin da yasa Auran ya faru cikin Lokaci Alhaji Alhassan yana matukar Daraja Mutumcinsa akan mutumcinsa kada ya zube zai iya yin komai,Kuma yarda yaga Imu ya tabbata zai iya bangala Sirrinsa yayi Tirere dashi acikin Farantin ya gama yawo dashi kowa yagani kuma ya saani bazai mai Wahala ba Shiyasa ya Daura auran ya yarda Kwallon mangwaro ya Huta da guda.._🤣 *Shakira..* 3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)* *Ina godiya masoyan GIDANMU Allah ya saka da alheri Allahu ya bar zumunci Ameen,Musamman yan gidan Gidanmu comments Section 1&2,Janaf Novella,Zauren Janafty Shakira da sauransu Tanque so much* *🅿�10* "Lokacin da kiran Sagir ya Shigo wayar Imran yana kwance akan gado acikin Dakinsa ya gama Busa Sigarinsa har yagaji ya koma ya kwanta. Gidan nasu ba kowa Yusuf ya tafi wajen aiki,Munari kuma Ta tafi makaranta shi kadai ne agidan,Daya tashi Dakin Abba ya leka ya sameshi yana zaune shuru Shi kadai shi ya taimakamai yayi wanka ya sauyamai kaya ya Hadamai Tea mai kauri da Soyayyan Dankalin da Munari ta soya kafin ta fita bayan ya bashi yaci ya koshi ya Doramai da mgungunansa,wanda ko Minti Goma bai yi ba ya Sulale yana Barci,wannan watan Chanjin mgungunan da Likita yayi mai kamar sun fi yimai amfani,Saboda ya na samu Ishashen Barci Kwakwalwarsa tana samun Hutu sosai Fiye da baya kuma suna ganin Chanji Sosai. Bayan yayi barcin ne ya Fito Falo nan kan Dinnig ya Hada Tea yasha da Soyayyan Buredi,yaci ya koma Daki ya Dora da Busa Hayaki bayan ya gama ne ya koma ya kwanta sai ga kiran Sagir ya shigo wayarsa karama Kirar Nokia ce Rakani inda Zani Domin Imran bai tabaa Damuwa da sai ya mallaki Babban waya,Shi dai a kira ya Daga kawai kuma Mutanen dayake kira Daga Sagir sai Yusuf ko Munari yana da lambarta ammh ba sosai yake kiranta ba. Cikin kasala ya Zura hannu ya Dauko wayar,ganin sunan mai kiran yasa yadan saki karamin Tsaki ya Daga kiran yana Fadin"Ya akayi ne Banzan Abokina..? Dagachan bangaran Sagir dake kallon Baba Manu yace"Kana ina ne..? Ga Baba Manu na gidanmu yana jiranka..! Imran ya lumshe idanuwansa kafin ya Bude su yace"Kaga mallam gajarta Zencen..Meya faru? Domin duk da yasan mganar Neman auran yusuf haka kurum yaji ajikinsa da wani abu. Baba manu ne yayi ma Sagir alamun Daya Fadamai Shi kuwa ya karkace kai yace"Kazo fa Domin Baban yarinyar nan Ya Daura auran Kuma ya Hado su Baba Manu da ita! Imran bai wani ji mamaki ba sai ma wani Mirmishi Daya saki Kafin yace"Dakyau..Yanzu ta na ina..? Sagir da mamaki ya cikasa yace"Tana Dakim Mama..! Imran ya mike Zaune yana Fadin"Gani nan zuwa..! Daga haka ya katse kiran,Cikin Sassarfa Ya Sauko Daga kan gadon afili yake wani Mirmishi kamar na mugunta aransa yace ya Rage ma kansa aiki..Shifa baisan komai akan Alhaji Alhassan ba Daga farko sai da ya Shiga Gonarsa kudi kalilan ya bada aka Zayyanemai Labarinsa bai sanshi bane shi kanshi a baya baisanhaka yake ba,Sai yanzu yake kara jin Tsoron kansa Sosai in yayi wani abun Wanka ya shiga a gurguje,ya fito ko Mai bai shafa ba ya Bude Wardrope dinsa Dake cike da kayansa ya Zari Riga da wando Ruwan madara da da bakin wando ya saka,bayan ya saka karamin Cum ya taje kansa ya Dauki Wayarsa bayan ya saka wani Budadden Takalminsa baki na Fatar Damisa. Dakin Abba ya leka ya iske har Lokacin bai tashi ba yana ta Barci yasa ya juya ya fice bai Nemi Hawa Mashin dinsa ba ya Taka da kafarsa ya Fice zuwa gidansu Sagir a kafarsa duk da dan Nisa bai damu ba,Kafin ya isa Gidan su Sagir ya Biya wani Shago ya siya kwalin Sigari da Lether ya manto nasu agida kuma yau yadda yake jin Nishadi ya kamata ya Busa Hayaki sosai. Acikin aljihun wandonsa ya saka kafin ya isa kofar gidansu Sagir. Waya ya Dauko ya kirashi yaceya Fito yana waje yana jiransa,Kafin Sagir ya Fito ya kira Yusuf sau Biyu bai Daga kiransa ba sai ya kyaleshi tunanin kila yana wani aikin ne Ba dadewa sai ga Sagir ya Fito Hannu ya bashi sukayi Musabaha kafin Sagir yace"Meyasa ka tsaya Daga waje baka Shigo ba..? Imran ya Dakuna Fuska yana Fadin"Kawai sai na kama Shiga Gidan Mutane kai na Tsaye..? Bar gani na D'an iska D'an iska nasan Abunda nake yi ina da Hankali..! Sagir ya kusa sakin Dariya sai dai ya kanne kafin yace"Aifa ga Hankalin nan nagani..! Kansa Imran ya Daka ya Duke yana Dariya kafin su Nufi Cikin Gidan. Sagir ne agaba Imran a baya Da yayi sallama iya sallaman Lebensa Mama na Kitchen Baba Manu ne ke zaune yana Shan Ruwa Sagir ne ya zauna gefensa shi kuma Imran din Daga chan gefe ya Durkusa yana gaida Baba Manu ya amsa mai,Daidai Lokacin da Mama ta fito itama ya Gaisheta ta amsa Cikin Fara"a tana Tambayansu Mutanen gidan ya amsa mata da Lafiya Baba Manu ya gyara Zama yana Fadin"kaji dai abunda ya faru ko..? Kamar yadda Sagir ya Fara gayamaka..Muna zuwa da niyyar Neman aure sai kawai aka Daura auran..Baisan me ya faru ba..Ammh naji ban ji Dadin Sanadiyar irin auran da yayi ma yarinyar ba haka ya Hadomu da ita ba Rakiyan kowa gwanin ban Tsausayi.! Baba manu ya karishe Fada yana Bayyana Jimamin Abun. Imran yayi Mirmishi kafin ya kada kai yana Fadin"Hakan yayi kyau..! Dukkansu sai da suka kallesa yayi kamar bashi yayi mganar ba,Baba Manu yazaro Sauran Kudin Imran ya Mikamai yana Fadin"Dubu Dari ya karba Sadaki sai dubu Ashirin da aka kashe na Siyan Minti da Sauransu Ga Ragowar Dubu tamanin dinka nan..! Kai kawai Imran ya Girzgiza kafin yace"Ka barshi kawai.! Baba manu ya zaro ido yana kallonsa hakama Mama da Sagir Cikin mamakinsa Baba Manu yace"bangane ba? Ni don Allah nayi muku komai karbi kudinka yaro..! Imran ya kara kada kai alamun bazai karba ba,Baba Manu yace"Ikon Allah..To in kabarmin wannan Zunzurutun kudin kai fa..? Imran ya kauda kai kafin yace"Ni ina da kudi..! Baba manu yace"Kana aiki ne.,? Ni a sanina Sagir ya Fadamin Yayanka kadai ke aiki..! Wani kallon ya Sakarma Sagir kafin yace"Ina da Sauran kudin Albashina dana ke Tarawa.! Gabadayansu mamaki ya Cikasu barin ma Sagir da bai taba jin Imran yayi mgana kan Abunda ya Shafeshi ba. Cikin karin mamakinsa Baba Manu yace"A ina kayi aikin..? Imran kamar bazai Tanka ba sai Chan yace"Ba anan bane..A lagos ne..! Gabadayansu suka Zuba musu ido,ganin haka yasa yayi Saurin Basarwa,Da sauri Sagir yace"Wai daman ku yan Lagos ne..? Da sauri Imran yace"A"a.. Daganan ya Tsuke bakinsa bai ce komai ba Sagir zai kara mgana Baba Manu ya Danne mai hannu ganin yadda Imran ya Hade kamar ya kuma matsa gefe kamar za"a ce wani abu ya tashi ya Fita. Cikin Basarwa Baba Manu yace"yanzu ina shi yayan naka..? Ina bukatar ganinsa..! Imran ya sauke ajiyar Zuciya kafin yace"Baya nan yana wajen aiki..! Baba manu yace"To ka kirashi..! Imran cikin kosawa yace"'Na kirashi bai Daga ba..! Baba manu ya jinjina kai kafin yace"Shikenam..Daman domin na Damkar amanar yarinyar nan ahannunshi..Duk da bamu hada komai daku ba naji ina kallon ku kamar kowa..Yanzu a ina zai ijiyeta..? Imran ya wani kallesa a karkace kafin yace"Yana da inda yafi GIDANMU ne..! Chan zai ijiyeta akwai Dakuna bazai gagaraba..! Baba manu ya jinjina kai yana Fadin"Shikenan Allah ya basu Zaman lafiya..Gata nan Dakin Amina ni zan wuce saboda zan fita gareji nagode kwarai..! Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Dukkansu suka Mike Imran ya kalli Baba Manu kafin yace"Nagode..! Kafadarsa ya Dafa kafin yace"Bakomai Kada ka Damu! Lokaci Daya ya Turamai kudinsa Cikin Aljihu yana Fadin"Kada kace wani abu..Bazan iya karban ko Sisi Daga wajen ka ba..! Dole Imran yayi shuru bai kara mgana ba Tare suka Fice Bayan Baba Manu yayi ma Mama Sallama Safiya na Daki tana jin mganganu sama sama,Tana Zaune afalon Mama bata fito ba. Suna Fitowa Bayan Baba manu ya tafi Imran ya kalli Sagir yana Fadin"Zan je gida na Dawo..Na bar Abba shi kadai..! Jinjina kai kawai Sagir yayi kafin yace"To ya za"ayi da amaryan ya Yusuf din? Imran yace"Ya kuwa.? Bari naje gida zan kirashi muyi mgana in ya Dawo yazo ya Dauki matarsa yanzu dai ta zauna wajen Mama pls..!Sagir yace"Kada ka damu ai an zama Daya..! Daga haka sukayi sallama,Sagir ya Dawo Cikin gida suna ta maida Zence da Mama. Imran kuwa har ya koma Gida Abba bai tashi ba sai yayi Zamansa afalo yana auna wasu abubuwa,Alhaji Alhassan mahaifin Safiya yana Tsoron Tonon asirinsa wanda wannan Dalilin ne yasa yayi gaggawar Dauran auran,ya kawo yarsa a Wulakance kamar bata da gata Hallacin da Safiya tayi ma Yusuf dasu kansu Shi zai sa su riketa Riko na gaskiya da Watarana sai Mahaifinta yayi Nadamar Abunda ya aikata ya Dawo yana bata Hakuri kuma ko bajima sai asirinsa ya Tonu Domin Shi Sharri ai Dan aikeni Inda ka aikashi sai ya Dawo. Sannan kuma Itace Mace ta Farko da Zata Shigo Gidansu a Lokacin da suka yanke tsammani da komai Ya Tabbata Yusuf ya Chanchanci yayi Farinciki Tun Bayan Afkuwar Kaddaran Data Fadamusu shi yake ta Wahala dasu ya Dauki Ragaman Abba Gabadaya akansa,Shiyasa zai Tsaya har sai ya ga ya samu abunda yake so koda shi zai rasa nashi Farincikin ne,Duk da daman Shi yariga yagama bamkwana da Farinciki. Yana nan zaune sai ga kiran Yusuf sai ya Dauka bayan ya Daga sun gaisa yace mai suna Meeting ne shiyasa bai Daga kiran ba. Nan Imran ya gajerce Mganar ya gayamai Abunda ke Faruwa Yusuf yana Zaune Cikin Officr dinsa sai da ya Mike Zaune Cikin mamaki da al"ajabi yace"An Daura auran kuma Imu..? Imran yace"Eh...To miye aciki ya saukaka ma kansa ne..! Yusuf na Sharan zufan Goshinsa yace"A"a Imran bamu shirya komai ba Infact ma ko Abba bamu Fadamawa ba..Ballatana Kanwarmu Munari ni bama wannan ba kai ina zan ijiye Safiya Imu..? Imran bai wani bama mganar Muhimmanci ba yace"In ka dawo sai ka Fadamai Abba bashi da Mtsala hakan ba abun alfarinsa ba ne..Mganar inda zaka ijiyeta kuma ai ba wani abun Damuwa bane..Sai ta fara zama adakin ka kafin mu gyara mata Falon nan da 2 bedroom din nan dake korido din Dakin Munari..! Yusuf yayi shuru kafin yace"Ok..Hakane Allah ya bani ikon Rike Safiya da Amana..! Imran yace"Ameen ya yusuf Domin She Loves u.! Yusuf ya saki Mirmishi kafin yace"I know..Zuciyata ta cika da Alherinta Imu..Ina ta kiranta Tun dazu bata daga ba yanzu tana gidan Maman Sagir din ne..? Imran yace"Bakajin Hausa kenan..? Yusuf yace"May be..! Imran bai tsayama Sauraransa ba ya Datse kiran ganin Yusuf zai fara Zolayansa da bakwarcinsa shi kuma Baya cikin Mood din. Dakinsa ya koma ya zauna kan kujera ya Shiga Busa Sigarinsa Hankalinsa kwance Sallar azahar ya tadashi yayi alwala yayi Sallah,sannan yazo ya adana Sauran kudin da Baba Manu ya maido masa,da niyyar zai bama Yusuf su ne yayi amfani dashi. ****** Bayan La"asar Yusuf ya baro wajen aikinsa zuwa gida,ko da ya Dawo ya iske Imran na Dakin Abba yana bashi Tea,Tunda Munari bata dawo Daga makaranta ba ballatana Tayi abinci. Yana Shigowa gidan Dakin Abba ya Fara shiga nan yake Imran ya Dago yana kallonsa Mirmishi ya sakarmai Ammh Shi Imran din sai ya kauda kansa Abba ne Cikin Fara"a yace"Yusuf...Ka dawo ashe..? kariso mana ka tsaya Daga bakin kofa..! Jin haka yasa ya shigo Dakin Yana Sabe da Jakarsa ta aiki a Kafadansa Gefen kafafun Abba ya Zauna Tunda Imran ya Zaunar dashi shi kuma yana Zaune gefensa. Yana zama yace"Abba ya jikin ka? Abba yace"Jikina da sauki Yusuf..Yau dan"uwanka yayi ta kula dani..Dukkan ku Allah yayi muku albarka,ya jikan yan uwanku da Mahaifiyarku..! Gabadayansu sai da sukayi mamakin kalamansa Domin ya Dade baya Fadar haka tun Farkon Lamarin,Kallon juna akayi Tsakanin Imran da Yusuf Mirmishi ya Bayyana Saman Fuskarsu da Sauri Imran ya mike Tsaye rike da Mug din Tea din yana Fadin"Da alamu dis Time around Abba ya fara samuwa..! Yusuf ma kusa da Abba ya Dawo ya Rike Hannayensa yana Fadin"Abba ka samu lafiya ne..? Abba Don Allah ka warke..Ka Dawo Abban mu da muka Saba Dashi..,! Abba ya saki Mirmishi kafin ya Dafa kan Yusuf yace"Na samu Sauki Yusuf..Dole na manta da komai na Fuskanci Rayuwar da Allah ya zabamim ko Saboda kai da Imran da kanwarku Maimunatu..! Dukkansu Bakinsu yaki Rufuwa Yusuf ya kara Jimke hannun Abba yana Fadin"Abba Daman na dawo ne na Fada maka wani Daddaan Labari..Abba nayi aure..Abba Imran ya Girma shi yabiyamin Sadaki shi yayimin komai na aure na Abba..! Abba yayi jim yana kallonsa kafin ya sauke Numfashi yana Fadin"Duk a yaushe akayi neman auran har akayi Auran ni bansani ba..?Kuma shi Imran din ne ya Shige maka gaba har aka baka auran.? Yusuf ya girgiza kai Kafin ya Fara Bama Abba Labari Kamar yadda Imran ya Bashi Labari da irin yadda Alhaji Alhassan ya hanashi Auran Safiya sai da Imran yaje kana..! Abba kafin yusuf ya gama Bada Labarinsa yaji Hawaye sun Fara kwaranya acikin idanuwansa Cikin Muryan kuka da Sarewa yace'Waye ya Gorantamuku Rashin asali..? Ku din yan asali ne ya"yan Dangi..Ba laifi na bane Bakuma ni na gayyaci Kaddran Data Fadamin cikin Rayuwata ba. Allah ne ya Doramin kuma Wlh ba Kamar yadda Sauran yan"uwana ke Fadi bane na yarda da Kaddara kuma na yarda da Allah da ya bani Zuwaira shi ya Karbi kayansa..Haka kuma Allah da ya azurtani da Haihuwan Nura da Asma"u da Salima shi ya karbi kayansa..Sai dai wannan Gagarumin rashi a lokaci Daya basan yadda zan iya Daukan Lamarim ba..Wlh ban sani ba..! Ya karishe Fada cikin gunjin kuka wanda ya kusa saka Yusuf kuka da Sauri ya Rumgume Abba Imran kuwa yana gefe tsaye ya Coge yana kallon kasa ba wanda ya iya Fahimtar wani Hali yake Ciki ba. Yusuf ya Dago Daga Jikin Abba ya Saka Hannu ya Sharemai Hawaye kafin yace"Ka daina kuka Abba...Don Allah kada muma ka sakamu..! Abba yayi Mirmishi Lokaci Daya yana Kara rike hannuwan Yusuf kafin ya Dago yana kallon Imran Lokaci Daya ya fara mgana"Yusuf..Imran..Babu abunda Zan ce muku sai godiya..Allah yayi muku albarka na baku Wahala akan Lalurata..Ga rikon kanwarku..ammh Duk da haka Ban ji Dadi da kuka yanke Shawaran neman auran yusuf Batare da kun nemi Daya Daga Cikin Iyayenku ba..Duk da ko Dawowarmu wannan gidan Ban ji Dadi ba..Ina jira ne na kara Samun Sauki Dole zamu koma Gida na nemi yan"uwana kuma ku nemi yan"uwanku Kowa Rayuwa ta koma mai yadda ya fara..! Wannan Karon Imran ne ya Motsa kafin yace"Abba Ka bar wanman mganar..Mutanen da sukayi ta Bleming din ka akan ka Zama mahaukaci saboda Rashin Daukan kaddara..Basu Tuna kai Dan"uwansu bane alokacin basu Duba Halin da kake ciki ba basu Duba irin rashin da mukayi ba su Rika Zargin ka suna ganin Rashin Hakuri ne da kaddara ne ya jefaka Cikin Halin dakake ciki..Ai gwara da mukayi nesa dasu muka dawo nan muma Rayuwa a inda ba wanda yasan Labarin Mu yafi yemama Zama inda ansan Laluranka ammh kuma baza"a Taimaka masa wajen ganin ya Rabu da Lalurarsa ba sai kara Doramai Cuta.Abba ka bar wannan mganar ni Na rantse ko Komawa zakayi sai dai Yusuf da Munari su Bika ni ina nan ba Inda Zani..! Ya karishe Fada Cikim kumfar baki Lokaci Daya kamar wani Kabubuwa ya Fice har yana Banko Kofar Dakin Daga Abba Har yusuf da kallo suka Bisa kafin su girgiza kai Abba ya Cije baki yace"Ashe har yanzu Imran bai Chanza ba Yusuf..? Yusuf yace"Sai ma abunda yayi gaba Abba..!Abba ya koma kawai ya kwanta kafin yace"Allah ya Shiryesa..Yanzu ita yarinyar tana ina..? Yusuf yace"Tana gidan Maman abokinsa Sagir yaron nan Dake zuwa Dubaka..! Abba ya gyada kai kafin yace"Allah ya bada zaman lafiya..! Daga haka bai kara cewa komai ba yayi dai Shuru ya Lumshe idaanuwansa kamar mai Barci ganin haka yasa Yusuf ya mike ya Fice Jiki a sanyaye sai da ya Fita ne kana Abba ya Bude idanuwansa yana Bin Kofar Dakin da kallo wasu Siraran Hawaye suna Biyo kunnuwansa a Fili ya Furta"Kiyi Hakuri Daada..Ki yafemin..! Yusuf Dakinsa ya wuce yayi wanka ya sauya kaya zuwa wata Farar Shadda Riga da wando da Hularsa Zanna Bukar,Yasa Bakin Takalminsa Rufaffe na Fatar Damisa. Ya fesa Turare yana Tashin Kamshi Dakin Imran ya Shiga ya Iskesa ya Turnike Dakin,da Hayaki sauri Yusuf ya karisa Shiga Dakin da Sauri ya Zage Labulyen Windows din Dake dakin ya Dage Glass din Yana Fadin"What Wrong with u ne Imu..? Kana zaune acikin Daki Hayaki ya Turnike ga na Cikin ka ga na Sarari illah Nawa kake so kayi ma kan ka ne.? Imran na Zaune yana jinsa bai tankasa ba sai ma kara Zukar Sigarinsa da yayi ya Fesar da Hayaki bai ko kalli barayin Yusuf din ba. Karamin tsaki ya saki kafin ya Tako gabansa ya saka Hannu ya karbe Sigarin yana sakata Cikin Farantin Dake gefen Imran din inda yake kashe sauran Sigaran nashi da wani Jajayen idanuwa Imran ya Dago yana Kallonsa Kafin yayi mgana Yusuf ya Rigashi da cewa'"Kafi kowa sanin Shan Taba tana da illah ga Lafiyar Dan'aman Imu..A baya Lokacin kana Banker Imran Abubakar malami na sani ko Warin taba baka so..Ammh Rana tsaka na tsinceka ka fi wadanda ma suka dade cikin shanta iya Zukanta da Shanta ma..Don Allah ka Rage shanta hakanan Tunda ba Abinci bane..! Saboda Bayason Hayaniya baya Cikin Mood mai Dadi yasa yace"Naji..! Da haka ya dauke Kwalim Sigari da bai fi Saura Daya ba Da Lether din ya Tusa cikin Aljihin wandon Dake jikinsa Yusuf yace"Yauwa..Tashi ka rakani gidansu Sagir din.! Imran ya wani Dakuna Fuska kafin yace"bazan je ba..Haka kurim sai kaje dani Daukan Amaryan taka..? Yusuf ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Ai ba cewa nayi ka Daukomin ita ba rakani kawai zakayi bazan gane gidan ba..! Yafada da Sigan Lallashi Imran kamar bai zai tashi ba sai da yaga Dama kana ya tashi ya Fice batare Dayace ma Yusuf din komai ba Shima sai yabi bayansa a Haraban gidan suka Hadu sai da Yusuf yayi Riverse da Motar yazo gaban Imran kana ya Bude gidan gaba ya shiga suka Fice Daga gidan Shi ya nunamai hanyar gidansu Sagir din sai gasu sun iso sun iske Sagir din a Shago ya Taso da Sauri yana gaida Yaya yusuf kana yamai Jagora zuwa Cikin Gida Domin Imran yace yana waje shi bazai Shiga ba,Dole Yusuf ya Shiga shi kadai Mama tayi ta ina ta saka dashi har Falonta Safiya na Ciki inda tayi Sallah Mama ta bata abinci taci kadan Tayi ta mata Nasiha harta Daina kuka Bayan sun gaisa ne Sagir yayi ma Mama bayanin Wanene Yusuf Ta washe baki suka kara gaisawa,kan yusuf na kasa yace"MAMA nazo tafiya da ita ne..! Mama ta mike tana Fadin"Masha Allah..Ammh ai bana barta ita kadai ba in ba Damuwa sai na Rakata gidan naku..! Yusif yaji Dadin haka da Sauri yace"Bakomai Mama mungode Batace komai ba ta Nufi Ciki ta iske Safiya tsaye tana kuka Rikota Tayi tana Lallashinta,Hijabinta ta saka ita Maman ta kuma Dauki akwatin Safiya suka Fito sun iske su Sagir sun Fice suna Waje suma Wajen suka Nufa Safiya ta Shige Cikin mayafimta Tana kuka Kukan bakkn ciki irin auran Wulakancin da Mahaifinta yayi mata. Mama ta rike da hannunta da alwatinta Imran na Waje tare dasu yusuf,Domin tunda yace Mama tace zata raka Safiya bai ce komai ba Mama ta Chanchanci komai. Yusuf kallo Daya yayi ma Safiya bai kara ba a jin kukanta yake har Cikin Ransa Mota ya Shige Tunda Imran suje shi zai taho Mama kuma ta juya tana barin ma Sagir Sallahu in Inteesar ta Dawo ya amsa mata Daga Maman har Safiyan gidan baya suka Shiga Yusuf na gaba Yajasu suka Tafi. Suna barin kofar gidan ba Dadewa Imran ya Zaro Sigarinsa ya kunna ya Cigaba da Fesar da Hayaki Sagir na gefensa Yana kallonsa kai kawai ya kada bai ce komai ba. Daidai Lokacin da mai adaidata ya ijiye Inteesar akofar gidansu Sagir din ta Fito Tana Duba Jakarta ta Daukoma mai Adaidaita kudinsa ta Mikamai ta Jiyo cikin Rangajinta Dauke da Jakarta da wasu Takardu a hannunta Idanuwanta sun kankamce saboda Gajiya Tunda ga Nesa Sagir yake washe mata baki Cikin mamakin gani ta gane Tunda Gashi har ta kawo kanta gida. *Shakira...* 3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..!* _(Our House)_ *Book1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*      *🅿�11* "Itama tundaga nesan ta Hangoshi Tsaye sai wanda suke taren ne bata Damu Data kalli ko waye ba ammh Tabbas tasan yanatare da wani ne a Tsaye. Kafin ma ta Kariso Sagir ya saki Mirmishi yana Fadin"Kai ashe kanwar tawa dai da gasken gasken Zata iya Dawo da kanta Gida kamar yadda tafada..? Ya karishe Cikin Zolaya,Cikin Hararan wasa lokaci Daya Tana Dakuna fuska Daya Zame mata jiki tace"Kaji fa Yaya Sagir ce maka akayi bazan iya Dawowa ba..? Ai daman na Fadamaka ina da saurin Dauke waje in dai naje koda Sau Daya ne..! Tafada Daidai Tana Gama Tsayuwa agabansu Cikin gyada kai yace"Ah Lalle naga alama kuwa..To ya makarantar..? Hop karatun ba wahala..! Inteesar ta yi naka naka da fuska kamar ta Saka kuka Tana Fadin"Wlh yau kamar na Dora hannu akai nayi ta Ihu..Karatu ai daman akwai Wahala ya Sagir ga bakunta ga rashin Sabo..gabadaya Jikina Ciwo yake kamar anyimin Dukan Tsiya..! Ta fada Lokaci Daya tana kara hura Kafofin Hancinta jin kamar Warin Data Tsana aduniya warin da in Ta Shaka yake Fitar da ita daga Hayyacinta Wato Warin SIGARI. Sagir bai Fahimta ba yace"Ke dai kawai kice ke Raguwa ce..! Inteesar najin Zuciyarta na tashi da Warin Taban Dataji kuma bata ga Sagir Dashi ba..Kuma Tunda tazo wajen Hankalinta bai bata tama kalli Barayin Imran ba kamar yadda Shima ko Sau Daya bai kalleta ba Karan Sigarin Dake hannunsa Tuni ta Kare sai ya Murjeta a kasa koda Inteesar tazo Warin kawai ta iske,Hankalinsa kwata kwata baya kansu yana kallon Gefe ne yana wani Tunani,Tunanin yadda komai na Rayuwarsu ke zuwa Daga wannan sai wannan. Inteesar Da tsayuwar wajen ya Fara Gagararta Ga tashin Zuciya Tana jin kamar Zatayi amai Tunaninta bai bata Sagir ke shan Sigari ba Sai tayi Tunanin kila wani ne yazo yasha a wajen Shiyasa taji wari. Cikin Dan Dauriya ta Harareshi kafin tace"Hakama yanzu Ya basheer ya gama Tsokana.munyi waya dasu sun kai gida tun dazu..Umma tace tana ta kiran Wayar Mama bata Daga ba.tacemin in na Dawo na Hadasu suyi mgana ni kuma 5:30pm muka Fito Lacture,sai na Tsaya na Tambaya aka Nunamin Classrep din mu na Karbi Lambarsa Saboda Shedules din makaranta Tunda bansan kowa ba kuma an wuceni Kafin nazo..! Sagir yace"Daz a very Gud Idea...Hakan nada kyau kinga sai ya nunami ki inda akayi kafin kizo..Mama kuma Wlh ta Fita nan Makota yanzu bada Dadewa ba tace in kin Dawo abinci na kitchen har ruwam Zafi ta saka miki a Falas yar gatan Mama..! Inteesar Tayi dariya tana Fadin"Eh din ko kaji Haushi ne nazo na kwace gwannatin ka..? Kamar mama ta sani na gaji wanka nake so..Ga yunwa duk wunin yau Cway ne kadai Acikina..! Sagir ya zaro ido kafin ya samu Zarafin mgana Hayakin Sigarin da Imran ya Zuka ya fesar har Wajen Fuskar Inteeaar wacce taji abun kamar Al"amara nan da nan Hankalinta ya tashi Taja Baya Jikinta na kyarma Lokaci Daya tana Jan Gefen mayafinta ta Rufe Hancinta Tana Fadin"A'UZUBILLAHI MINAL SHEDANIR RAJIM..' Haka ta fada jin yadda Zuciyarta ke tashi Cikinta na Hautsina ga Miyau ya Taru a bakinta tana gabda da Amai alokacin. Sai a wannan Lokacin gabadayansu suka Kalli Juna shi Imran Bai san Inteesar na wajen ba har Lokacin Shifa Tun sanda ta Nufosa yaga Sagir na mata mgana ya Shiga wani Sabgan Aduk a tunaninsa sun gama mganarsu ta Wuce Imran Mutum ne da bai Cika Damuwa da Mutane ba Shi d'an i Dont Care ne. Ta"awizin Data Sakarmai yasa yasan tana Wajen Har ya Dago yana so yaga wata Yarinya ce take Sakarmai ta"awizi haka Charaf kuwa Idanuwansu suka Hadu waje Daya wanda nan take Zuciyoyinsu suka buga atake tare da wani bakon Lamarin da basu gane ko na miye ba ammh dukkansu sun kurama juna ido Cikin Wani yanayin da suka,kasa Dauke Kallonsu Daga kan junanasu Tare da bugun Zuciyan da basu Gane ko na Miye ba,Ita Inteesar tana kallonsa zuciyarta nayi mata rawa sai take ji kamar ta sansa,yanayinsa bai yi mata kama da bakon data ta taba gani yau ba. Shi kuma Kallonta yake da mamakin Furucinta Shi bazai iya tuna Yaushe Rabon Daya tsaya yana kare ma Wata mace kallo ba,Ammh yau sai gashi yana Kallon Inteesar Dayaji ya kasa Daina kallonta,Sannan kuma Ransa ya gama Kuna da baci da jin ta kiramai Ta'awizi,uwa uba kuma Tana Faman Toshe Hanci kamar taga kashi. Ita kuwa Inteesar,Warin Sauran Sigarin Dake Hannun Imran ne ta isheta Gabadaya ta kasa Hadiye Miyan Bakinta ga Zuciyarta na Tashi Amai nataso mata,Yasa ta kauda kanta da Sauri ta Zubar da miyan Daya Taru a Bakinta sagir Dake Tsaye,Yaga abunda ya Faru,nan da nan ya juya yana kallon Imran yaga yanayinsa sai yaga ya Hade rai ransa Tamau kamar ma yafi koyaushe,Sai wani kallon Sama Da kasa yake Bin Inteesaer Dashi. Ganin haka yasa ya juya ga Inteesar yana Fadin"Inteesar lafiya kuwa.? Cikin kara Toshe Hanci tace"Ya Sagir Warin Sigari...Bana son Warinta sam..Amai yake Sakani Da Tashin Zuciya..." Daga haka bata ma tsaya kara mgana ta kwasa da gudu zuwa Cikin Gida Jin Aman yana Kokarin Fito da kansa ganin Haka yass ya bi bayanta yana kiran sunanta,sai bata tsaya ba Har zai Bita cikin gidan sai kuma ya Tuna da Imran sai ya fasa sai dai me yana Juyowa shima Imran Din yaga Bayanan,sai ya hangesa ya mika Hanyar Gida baki ya Rike aransa Yana Fadin Allah ya Huci Zuciyarka Inteesar ta tabo wanda bata sani ba. Sai ya koma Cikin Gidan nan ya iske Inteesar sai Sheka amai Take Duk Sai da Ta amayar da Cake din Dataji da Lemo Sagir Shi ya Taimakamata da Ruwa ta wanke bakinta,ya kuma kwasan mata Littafanta da Jakarta Zuwa Cikin Falon mama. Sai da ta Zauna Tana kana ta Shiga Sauke Numfashi Sama sama. Cikin Tsausayamata yace"Sannu..! Da kai ta amsa Kafin tace"Yauwa..Yaya Sagir ina ka samo Aboki D'an iska..? Sagir ya Zaro ido yana Fadin"Waye Dan iskan..? Wai Imran..? Inteesar ta Dakuna Fuska Kafin tace"Oho..Ni nasan ma sunansa..Eh mana..Sigari fa yake Sha agaban Mutane bako kunya..! Sagir yayi mirmishi Kafin yace"Ai Shan Sigari ba Iskaci bane Inteesar..Sai dai Kawai kice Tana Illah ga Lafiyan Dan"adam...! Inteesar ta saki karamin Tsaki Kafin tace"Duk Daya..Ni Wlh Tun ina karamata Daukan masu Shan Sigari nake yan iska..Ballatana Warinta bama Sonsa amai yake sakani da Tashin zuciya. Sagir yace"Sai don haka..Ammah shan Sigari ba Iskanci bane..Hakama Abokina ba yadda kike Tunani bane..! Tabe baki kawai Inteesar Tayi bata kara Mgana ba,ganin haka yasa Sagir ya mike Tsaye yana Fadin"Bari na Leka Shago..Komai kike Bukata ki Duba Kichen ko kina Bukatar wani Abun ne..? Inteesar ta girgiza kai kafin tace"Bana Bukatar komai..! Daga haka sagir yayi mata Sallama ya Fice Daga Gidan Inteesar ta kwashi Jakarta da Littafanta zuwa ciki Tana kunkuni ita kadai Tana Fadin"Allah ya isa..ya sani amai duk naji ma bana jin cin komai..Allah ya isana Wlh..! Haka take ta Mita ita Kadai kyan Jikinta ta Cire ta Duba Flas din Mama Taga Ruwan zafi ta Juye ta shiga wanka Dashi Ta Fito bayan ta Dauro Alwala jin ana kiran sallar mangariba Lokaci Daya Tana mamakin ina Mama taje haka..? Bata samu mai bata amsa ba,Ta Sauya kaya zuwa wasu Riga da Wando Marasa Nauyi ta Dauko Donut Din Da tazo Dashi Taci Kadan ta fito Falo ta Duba Fridge din Mama ta ga Lemon Cy,ta Dauka tasha Kadan ta Hada da Dunot din kana ta koma Ciki Ta tada Sallar Har ta idar ba"a Kawo Wuta ba Duhu ya Fara sai ta kunna Fitilar wayarta ta Fito Falo ta Dauki Tsintsiya ta Share Falon,Kana ta Dauki Littafanta da abunda akayi musu karatu yau ta Fito Falo Tana dubawa Lokaci bayan Lokaci Tana Duba Hanyar na ganin Dawowar Mama ba ita ba Sagir Kiran Daddy ya Dauke mata Hankali Daga Kadaicin Datake yi ita kadai. ****** Mama ita da kanta ta Shiga da Safiya Har Cikin Falon gidansu Imran,bayan ta Umarceta Data Shiga da kafar Dama Ta kuma yi addu"an Neman kariya da Zaman lafiya,Yusuf na Biye Dasu Dauke da akwatin Safiya yana Jinsa kamar yana Yawo a sararin Samaniya saboda Farinciki. Gefe Daya kuma kukan Safiya na Tayar mai da Hankali,Sai kuka take Cikin mayafi kukan da bai isa ya Hanata yinsa ba yanzu. Afalo yace su Zauna kafin yace bari ya Shiga Ciki ya gayama Abba Mama tace toh..Lokaci Daya Tana Zaunar da Safiya kan Kujera Itama ta Zauna Gefenta Tana kara Bin Falon da kallo Ko"ina Shuru da alamu babu kowa Babu dai abunda ya Sauya Daga yadda tasan Gidan Ba jimawa sai ga yusuf ya fito Fuskarsa Cikin Fara"a yace"Mama Abba yace ku shigo..! Mama ta mike Tana Fadin"Taso muje Safiya..! Tafada Lokaci Daya tana Rikota Mikewa Tayi Kanta Har Lokacin Yana Cikin mayafinta shi yayi musu jagora Har zuwa Dakin Abba. Yana Zaune gefen Makeken gadonsa,Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara ya Rame sosai gemunsa ya dan Taru Da Farin gashi,Yana Rike da Charbinsa yana ja Da alamu Alwala yayi Domin Fuskarsa akwai Dashin Ruwa. Yusuf ne akqn gaba Mama dake Rike da Safiya na Binsu a baya,Gefen Abba ya Zauna yana Fadin"Abba gasu nan..Mama ku zauna don Allah! Mama ta zaunar da Safiya saman Cafet a gaban Abba itama ta Zauna Gefenta Tana gaishe da Abba ya amsa mata cikin Sakin Fuska,Duk da bai da lafiya ammh yasan mai Gaisheshi Duk da bai taba Tsayawa ma ya kare ma Maman kallo ammh Tabbas yasan Maman Sagir abokin Imran Tazo Gaisheshi ba sau Daya ba Shiyasa ya amsata Cikin kulawa Duk dama Yusuf yamai Bayani komai. Mama ce ta Dafa kan Safiya Tana Fadin"Ga Safiya nan na rakota..gidana kanin Mahaifinshi Shi Sagir din da Sukaje suka sama da mganar Nema ma Yusuf din aure ya kawo ta Bayan Mahaifinta ya Riga ya Daura auran kuma ya Hadosu da ita..Shine nace bazan barta Tazo ita kadai ba bari na Rakota..! Abba ya jinjina kai Shuru kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Bakomai yusuf yamin bayanin komai..Mungode kwarai kiyi ma Kanin Shi Mahaifin yaron naki Godiya,Nagode kwarai Daya Tsaya ma Dana bawai Domin yq rasa masu Tsaya mai bane..A"a sai Domin wasu Mtsalaloli na Rayuwa..! Mama ta Murmusa kafin Tace"Ayya Bakomai..Ai ya"ya na kowa ne Alhaji..! Abba ya gyada kai yana Fadin"Hakane Duk da hakane Dole Zanyi Godiya Sabodq yayimin ni abunda ina da Rai na kasayi Saboda Rashin Lafiya ammh da Izinin Allah da Taimakon Ya"yana dana Likitan Dake Dubani na Fara Samun Lafiya na Dawo Cikin Hayyacina da Yardan Allah komai ya kusa Zuwa karshe..! Mama tace"Allah yasa..Allah ya kara Lafiya..! Yusuf ya amsa da Ameen Kafin Abba ya kalli Safiya Dake Duke kanta Cikin mayafinta Tana kuka Abba ya kalli yusuf kafin yace"Ya sunanta...? Yusuf na sosa keya yace"Sunanta Safiya Abba.. Abba ya maida kallonsa kan Safiya ya Daga baki ya kira Sunanta Har sau Biyu ta amsa Cikin Dattako yace"Dago kan ki nan yata..Dago kanki ki kalleni Dakyau ni ba Surukin ki bane..Daga yau ni UBA nake gareki Safiya kamar yadda nake Uba ga Yusuf da imran da Maimunatu..! Ba Safiya kadai ba Hatta Mama kalaman Abba sun kashe mata Jiki Cikin Sanyi Jiki Safiya ta Dago kanta ta yaye mayafinta Tana kallon Abba da Jajayen Idanuwanta,Lokaci Daya Tana ganin kamar Yusuf ne ya Tsufaa ga kuma Yuauf din a gefensa Tabbas wannan kamar har ta baci bazata iya Juran kallonsa ba sai ta Sadda kanta Dan Mirmishi Abba yayi kafin yace"Allah ya albarkaci Auranku..Dukkanku ya"ya na ne..Saboda Haka tare zanyi muku Faada..Ku Rike amanar Junanku Yusuf ka Riketa Amana Domin Tayi maka Hallaci,ni kuma nayi miki alkwarin Zan Tsaya Miki mtsayin Uba koda watarana Yusuf yayi miki Wani abu kada kiji komai kizo ki Fadamin Daga Rana mai kamata ta yau ni zan Dinga Tsaya miki Har karshen Numfashina..! Kawai sai Safiya ta Kara Rushewa da wani kukan,Kukan Farimciki da wani yanayi Domim kalaman Abba Dagaji Daga Cikin Zuciyarsa ne. Mama ne Tana Mirmishi tace"Ai kagama Mgana Alhaji..Allah ya basu ZAman lafiya..! Abba da yusuf suka amsa da Ameen Ameen. Abba ya kalli Yusuf yana Fadin"Yanzu ina Zaka sakata..?.dazu na Fita na Zaga ko"ina Gidan yana da Girma sai dai ba plan akan ginin.." Mirmishi Yusuf yayi kafin yace"Komai zai koma Daidai Abba..Zamu zauna da ita adakina..Kafin na gyara mata Falo da Bedroom din Dake kusa dana Munari..! Abba ya jinjina kai kafin yace"Hakan ma yayi kyau..Ammh dai Zaki Rakata Har Dakin Mijin nata ko..? Mama tace"Me zai hana..? Sai na mikata.."Abba ya Gyada kai kafin yayi ma Mama Godiya ta mike ta Riko Safiya suka Fice yusuf yabi bayansu Abba ya bisu da kallo yana kokarin Shanye Hawayen Dake kokarin kawo mai. Sun Fito kenan Falon Yusuf ya Dauki Akwatin Safiya yayi Musu Jagora Zuwa Dakin nashi Imran ya Shigo Kamar an jehoshi Ransa a bace yana Tafiya yana Wani Buda Jiki Daga Yusuf Har Mama ba wanda ya kallah Balanta su suka ran zai yi musu mgana,yusuf ne ma yake kiran Sunansa yayi kamar bai ji ba ya Tura Kofar Dakinsa ya Shige ya banko Kofa Baya ji,sai karan Ta"awizin Inteesar Dake mai amsa kuwwa cikin kunnuwannsa,Sai kuma ganinsa Gabadaya na Hasashomai Lokacin Data toshe Hanci ne da Lokacin Data Zubar da Miyar Ransa ya gama Baci. Bango ya Daka da Hannuwansa yana Fadi"Who is she..? Who is d Hell is Her...? Da har zata Toshemin Hanci ta kuma Zubarmin da miyau bayan ta Kirani Shadani..! Waye ita.? Haka yake Fada Zuciyarsa na Tafasa yana Daga Tsayen ya Zaro Sigari ya kunnata ya Yi mata kyakyawan Zukan da sai da yaji Ya kware da Hayaki kana ya Dakata ya koma yana Tari Idanuwansa sun kala sunyi Jajir,Kan kujeran Kwara Daya Dake Dakin ya Zauna ya Dora Kafa Daya kan Daya yana Girgiza ta Hannu Daya kuma yana ta Zukan Sigarinsa yana Fesae da Hayaki. Yana Tuna Ko Lokacin da yake amsa Sunansa na Natsattsen Imran Abubakar Malami ba wata macen Data Taba kallonsa Tayimai wadandan Abu uku da yarinyar tayimai ba..Tun ba yanzu ba ya Tsani Raini Shiyasa baya Hulda da mata Sannnan su da kafara Sakarmusu Fuska Zasu Samu Hanyar Rainaka..Ballatana da yanzu yake jin kansa na ya Ishi kowa Riga da wando..Ya ke jin kansa a Mtaayin roban Wando Daidai da kugun Kowani Shege bama shegiya ba..Shine wata Yarinyar karama Zata Kirashi Shedanu ta kallesa ta Tsitar da Miyau ta kuma Toshe mai Hanci ba bu Wanda ya taba cimai Zarafi irinta,Duk iya kokarimsa Na ya Cire Abun aransa ya kasa ji yake koda waasa abun bazai iya Wucewa a wajensa ba Har Abada. Sai da aka kira Salla ya tashi Bayan ya gama karar da kwalin Sigari Duka Ya Fada Tiolet aranshi Yana ji in Sagir ya bari suka Hadu Wlh sai ya Nausheshi a Bakin da sai Hakoransa na gaba sun kama gabansu Saboda ko yayane Shi yajawomai Raini wanchan wannan kwailar yarinyar inda bai Ganta yayi mata mgana ba ba yadda Zatayi ta Tsaya Har ta Cimai Zarafi ba. Yana wanka yana kwafa,ji yake kamar ya Daki kansa yana jin Haushin yadda ya iya kyaleta bai Tsinkamata marin Da Sai ta ga Taurarin Wuta Wanda nan gaba Ko bashi ba Bazata kara Kokarin Raina ma wani wayau ba ballatana taci Zarafinsa ba. Mama Har kan makeken Gadon Yusuf ta ZAunar da ita bayan Tayi mata addu"a da yar Nasiha ita da Yusuf kana Tayi musu Sallama Tace Zata tafi Yusuf yace zau kaita Gida tace ya Barshi, yayi Zamansa Sai dai yaki jinta Sai da ya rakata Har Bakin get yana mata Godiya kana ya koma Cikin Gida ita kuma ta gangara Zuwa Gida acikin Ranta Tana addu"am Allah yasa Sanadiyar Safiya Chanji mai Girma ya Faru a wannan Gidan Tafiyanta ba Dadewa sai ga Munari ta Dawo mai Napep ya Sauketa ta Sauka ta Bashi kudinsa ta Buga get Iro ya leko ganinta yasa ya Bude mata karamar Kofar ta ahigo yana mata Sannu da zuwa Bakinsa Cike da gulmar Shigarsu Mama da Safiya da Fotowarta ita kadai sai dai bai samu Fuska ba a gajiye take Ga yunwa ga Wahalan makaranta. Tana Shigowa Falon dakin Abba ta Wuce Direct ta iskeshi Yana Sallah Kanta ta Dafe ta fice Zuwa Dakinta tasan Ya Yuauf ya Dawo Tundaga Motarsa,Yau tayi Dare Tun Dazu suka Tashi Ta tsaya Amsan Note ne wajen Classrep dinsu,Sai kuma Data Fito Bata Samu Abun Hawa da Wuri ba. Dakinta ta yada Zango,Tiolet ta wuce Tayi alwala Tazo Tayi Sallar Tana Idar ta Fito Zuwa Kitchen ta Duba Flaak taga Da akwai Ruwwn Zafi sai ta Samu karamin Mug,ta Zuba ta Fito Zuwa Saman Dinning ta Fara Hada Tea sai ga Yusuf ya Fito Kamar zai Fita Cikin Hanzari da Sauri ta saka baki ta Kira sunansa ya Juyo yana kallonta Kafin yace"Munari yaushe kika Dawo..? Ta Dauko mug din ta Nufoshi Take Fadin"Yanzu..Na shiga wajem Abba naga yana Sallah..naga Motarka sai nayi Tunanin kana cikin Dakin ka ne..! Yusuf yace"Yauwa..Gwara ma da kika Dawo..Gama Shan Tea din nan ki Shiga ki Zauna da Safiya..! Munari ta kallesa Sakaka kafin tace"Wata Safiyan kuma Yaya..? Kansa ya Dafe kafin yace"Kash..Is a Long Story..Atakaiche dai Matatacce Dazu aka Dauramana aure...Ayanzu hakama Tana Dakima..Ki Zauna da ita Zan je na Dawo..! Munari mug din Hannunta ya kusa Subuce mata Cikin Mamaki tace"Anty Safiya ce matarka Ya yusuf..? Am so Comfused how Comes..? Kai ya gyada kafin yace"Lilsiy..Ki bar wannan mganar zamu yi ta Daga Baya..Yanzu dai juz go..! Munari tace"Oly..To dafa abinci zan Doramana kaga Tun Safe bana nan kuma Abba bai ci komai ba..! Yusuf Daya kosa da mganarta ya kama Hanyar ficewa yana Fadin"Who tell u..?Zan yo mana Takeaway in zan Dawo..! Munari tace"to ina shi Ya Imu..? Karamin Tsaki yaja ya fice yana Fadin"Check him..In his Room mana..! Daga Haka yafice Lokaci Daya yana Laluban key din Motarsa. Tsalle Munari ta Dakata bata ma Tsaya Shan tea din ba ta maidashi Saman Dining ta Fada Dakin Abba ta Iakeshi ya Idar da Sallah yana Azkar Rumgumesa Tayi ta baya tana Murna da Ihu yana jinta yasan ta samu Labari Allah Sarki. Shi Munari ta Tasa da Tambaya sai da ya gamayata yadda Yusuf ya gayamai da Abunda ya wakana,Munari Ta Washe baki ta Mike Tana Fadin"Wlh mu muna sonta Abba..Indai zata Zauna Damu..Zamu zameta komai da komai ko Abba..? Kai ya gyada mata yana Jan Cashaba Lokaci Daya yana Fadin"Da yardan Allah..! Ficewa Tayi tana Fadin"Abba Let me Met my Sister Inlow For d First time..! Tafice ya Bita da kaallon Tsausayi Munari mai son Mutane ne ya Tabbata Batajin Dadin Zaman da sukeyi Daga ita sai yan"uwanta acikin Gidan nan Safiya na Zaune inda Mama ta Zaunar da ita Har yusuf ya Fita ya barta bata Motsa ba Duk yace ga Tiolet nan ta Shiga Tayi Alwala Tazo tayi Sallah kafim ya Dawo ammh ta kasa Tashi Abubuea ne ke Dawomata Daki Daki.Na yarda auranta ya Faru kamar almara Allah Sarki mommy,ta Tuna Sadda take kuka tana Rike ta Tasan Laifin Abun su ne da Ta Mommy ce bazata bari ayi haka ba,Anfi karfinta ne Tuna Haka yasa ta Dauko Wayarta Dake Jikinta ZAta kira Mommy sai ta iske Missed call dinta ba adadi Jikinta na Rawa ta Bi bayan kiran,kira Daya taji an Daga kiran lokaci Daya Taji Muryan Tasleem da Mommy alokaci Daya suna Tambayanta ina ta Shige ne suna ta kiranta bata Daga ba. Safiya taji kuka ya kawo mata Cikin kuka tace"Ina Gidansu Yusuf Mommy..Wayata Tana Silent Banji ba..! Tasleem ta Saka kuka itama Tana Fadin"Anty Safiya..Nadawo naji Abunnda Abbu ya aikata Miki..Nayi kuka Mommy ma sai kuka take Kuma munso mu Boyoki Abu ya hana yace ba yanzu ba..! Safiya na Sharan majina tace"Kada ki Damu Ina nan lafiya Safiya..Kuma Zaki zo inda nake Abbu zai barki kizo Insha Allahu..! Tafada Tana Sharan kwallah kafin Tasleem din Tayi mgana Mommy ta karbe Wayan Tana Fadin"Safiya zan zo na Tafi Dake..Bazan yarda da wannan auran ba..! Safiya na Zubar kwallah tace"A"a Momny kada ki yi abunda Abu zai Yimiki Abunda mu bazamu mu manta ba ....Kinsan Halinsa fa kiyi Hakuri Insha Allahu ba Mtsala..Gidan Maman Abokin Kaninsa suka kaini Ba Dadewa yusuf dun yazo ya Daukeni zuwa Gidansu ita Maman abokin Ta Rakoni zuwa Gidansu Yusuf din..Mommy kada ki Damu ki barni nayi Zaman aurena Abba mahaifin Su Yusuf yace min kamar ya nake garesa zai rikeni kamar yar daya Haifa ta Cikinsa..! Mommy ta Sauke Numfashi kafin tace"Shikenan..Ammh bazan yarda ya aurar dake a wulakance ba..Sai na kwatan miki yancinki..Ki rika barin wayarki kusa Dake zamu Dinga kiranki..! Ta Bude baki Zatayi mgana kenan Munari ta Shigo Dakin Tana Fadin"Hello Bhabi..! *Shakira...* 3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*      *🅿�12* "Safiya tana ganin Shigowar Munari Ta Sanyaya Murya Tana Fadin"Mommy zan kira ku zuwa Gobe..Ki lallashi Tasleem Plz..! Hajiya Mero Dagachan bangaran ta share Hawayenta Tana Dafa Kan Tasleem Tace"Shikenan Ki kula da kanki Don Allah..! Safiya ta gyada kai Lokaci Daya ta katse kiran bayan ta dago Fuskarta Tana kare Munari kallo ko da bata Taba ganinta a Zahiri ba a kallo Daya zata gane Ita din Jinin Yusuf ce Ballatana Ta taba ganinta a Hoto a Wayar yusuf ya nuna Mata kuma Labarin Munari da Imu har Ta gaji da ji Ta Haddaceshi Saboda Karya ne Yuauf yazo wajenta ko ya kira Wayarta su gama Hira bai ambacesu ba ko bai Fada mata ba ta Tabbata su din sune Jinshkin Mijin nata. Shiyasa ta Saki Fuskarta kamar yadda Itama Munarin ta Washe mata baki Gefen gadon ta Zauna Tana Fadin"Anty Safiya Wlcm to Our House..Ina miki Fatan Alheri..Sunana Maimunatu Abubakar malami ni lilsister din Mijinki ne ya yusuf..Ina Farimcikin Zamowarki Daya Daga Cikin Ahalin gidanmu ayau..! Tafada Lokaci daya Tana mika mata Hannu alamun Musabaha. Safiya Tayi Mirmishi kafin ta mika mata nata Hannu suka Sarke lokaci Daya tana Fadin "Nagode Sosai Munari..Nima ina Farincikin Haduwata Dake sosai..! Munari ta Washe baki kafin tace"Waya Fada miki ana kirana Munari.? Safiya tace"Wazai Fadamin banda Yayanki..? Abakinsa naji Sunanki mai Dadi munarin Abba Auta ko.? Munari taji Dadi sosai Soyayyar Dan"uwanta na Ratsata tace"Yes..Haka kirarin yake..Ina jin Dadin sunan sosai Saboda Abba ne ya Sakamin Sai kakata wacce ta Haifi Abba na Daada Dayake Sunan Autanta su Abba naci Goggo Maimuna..! Safiya tace"Allah Sarki..Duk suna ina..? Ita kakar taku da goggon taku..? Sai Munari taki Cewa sanin ba Huruminta bane safiya na Nazarinta Sai ta Waske Kafin Tace"Yanzu dai ba wannan ba..Naga Abba Sauran Imu bangansa ba ko baya nan ne..?ko shi ne Dazu muna Falo ya Shigo a Fusace ya Shige Daki ya Bugo kofa..? Munari ta kalleta Har Lokacin Suna Rike da Hannun Juna tace"Bansani ba ko ya Dawo..Nima ai yanzu na Shigo Gidan Tun safe ina makaranta Buk nake Karatu Fanni Economics..! Safiya ta jinjina kai kafin Ta gyara Zama Tana Fadin"To dawa kuke barin Abba in kika Tafi Makaranta Yusuf ya Tafi wajen aiki..? Kuma meke Damun Abba ayadda na Fahimta a labarin da Yusuf yake bani kullum yana Daki baya Fita ko"ina ko Bai da Lafiyan Kafa ne..? Da Sauri Munari tace"Lafiyar Kafarsa Kalau..Bashi da lafiya ne Shiyasa Su Yaya yusuf basa yadda ya Fito ko Falo ne..! Safiya Tayi Shuru Tana kallon Munari Kamar Zatayi mgana sai ta fasa aranta Tace kada tace Na dameta da son jin kwakwaf,sai ta Share mganar Ta kara Damke Hannun Munari Tana Fadin"Amtsayina na Bakuwa bani Labarin Ya yusuf da Ya Imu..? Wanne yafi kula dake wa kuma kika Fiso..? Saura kuma Kice My Dear baya Kula Dake sosai sai na ciki Tara..! Munari ta samu abunda take so wanda ZAta ganta Gata tana Hira da Dariya ta saba Rayuwa ita kadai adukan Shekarun da suka Dawo kano da Zama Banda Yaya yusuf bata samun Sakewa da kowa sai kuwa Abba Shi kuma Bashi da lafiya in kwana Biyu ya samu Sauki Zuwa Chan sai abun nashi ya kara Rikicewa Dama Ya Imu bamai sakashi a lissafi ko abaya ba abokin Hirarta bane Shi,Ballatana yanzu da abubuwa suka Lalacemai sosai. Ko amakaranta ya Jamata kunni Kada ta kuskura ta yi wata kawa ko Wani Mutumcin da zai ka ga Har a san Gidansu,Sharudda ya kafamata Sosai kafin ya yarda ma Ya yusuf ya biya Kudi mata kudi a wata Makarantar Kudi ta Rubuta WAEC Da NECO,Da Jamb Har ta samu Gurbin Karatu a Jami"ar Bayero Tunda Lokacin da Suka Baro Lagos Tana SS2 ne,Duk somta da Mutane ta Ware kanta Tun yan ajinsu na Shigemata tana kauce musu Har sukayi banza da ita kowa ya kama kansa bata da Lambar Kowa Itama ba wanda ke da nata sai dai ta karbi Na Class Rep dinsu saboda In wani abu ya taso ta Rika sani Har Group dinsu na Department dinsu na Wasop ya sakata Tana gani ana Hira da Dariya bata da ikon cewa wani abu,sai da ta Shiga tagani in an bada Wani Assigment ko wani Infomartion mai amfani ta Duba Duk yadda taso Rayuwarta Tatafi yadda Hallitar take bazata iya Bijirema Umarnin Yayyinta ba itama Bazata zo ta Fuskanci Wulakaci da Tozarcin da Yayyinta ke Fuskanta kan Gidansu ba. Safiya ce ta Girgiza hannunta ganin Ta Shiga Dogon Tunani Da Sauri ta Dawo Hayyacinta Tayi Saurin Zare Hannunta Tana Goge Ruwan Hawayen da suka Fara kokarin Zubomata Cikin Dariya Dariya ta Fara Fadin"Ai baza ma ki Hada ba Anty Safiya..Abaya Ni yar gatace ta gaba da Baya..yar gatan Abba da Anni yar gata kowa agidanmu..ayanzu kuma Ni yar Gatan Abba ne Duk da bai da Lafiya Dagashi sai Ya yusuf,Bai Hadani da komai ba..Zai iya yin komai Saboda Farincikina Baya iya Runtsawa sai ya Tabbatar da naci Abinci na kwanta sannan zai iya barci..Ya yusuf Mutum ne mai Zuciyar Zinare,mai kirki mai Dattako mai Sanyin Zuciya Dana Hali bashi da Hayaniya ballatana Saurin fushi Zan iya ce Miki ban Taba ganin Fushinsa ba yana da Raunin Zuciya kamar mace Irin Zuciyar Abbanmu garesa suna da Bala"in Sanyin Hali da Dadin Zama ga waanda ya Zauna dasu..Zasu iya Sadaukar da komai Saboda Ahalinsu,ZAsu iya Sadaukar da Dariyansu da Farimcikinsu Saboda Ahalinsu,Anty Safiya bawai ina Kuranta Yaya yusuf bane Domin yana Yayana ba A"a sai Domin Halin Mutum ka Fadeshi bai taba ganina Cikin Damuwa ya barni ba sai ya Tabbatar da Fuskatata cika da Farinciki Shiyasa nake matukar sonsa acikin Zuciya naji Dadi da kika Kasance Abokin Rayuwarsa Anty Safiya Ki Rikemin Yayana Amana ina mai Tabbatar Miki Baza ki Taba yin Nadama ba Domin yana Sonki kuma Shi din Tamkar Misalin mijin Maraniya ce.! Ta karishe Fada Hawaye suna wanke mata Fuska Lokaci Daya tana Riko Hannuwan Safiya wacce itama kalaman Munari suka kara Raunana Nata Zuciyar Dayake Daman a Raunane. Safiya ta Saka Hannu Tana Share ma Munari Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Shii..Ki Daina kuka..Bayan Ya Yusuf yau nima gani Zan ninka Kulawar da yayanki yake Miki Fiye da Sau Goma Nayi Miki alkwarin Zaki Sameni mai kyautatawa da kulawa da abun da Mijina yafi so da kauna.! Sai ga Munari na Dariya da kuka Tace"Da gaske..?Zaki zame mana Haske a wannan gidan Anty Safiya..? Wlh Farinciki ya Dade da Kaura a wannan Gidan Don Allah kizama Sanadiyar Dawomana da Farincikin da muka rasa..! Sai kuka Jikin Safiya ya kara yin Sanyi ta kama Munari ta Rugume tana Lallashinta Lokaci Daya Tana Fadin"Da yardan Allah.ammh sai kin Bani Dukkan Hadin kai! Munari ta Dago Tana Fadin"Insha Allahu ina Tare Dake..! Safiya Tayi Mirmishi Tana Fadin"Yauwa..To maza Share Hawayenki Kuka ya Kare..Bani Labarin Ya imu..?Shi dai Duk da ban Zauna Dashi ba Yusuf na bani Labarinsa yafi ye Fushi da Zuciya ko..? Munari na Share Hawayen tace Cikin Dariya,"Rigimamme kenan.ai Ya imu Dabam yake acikin Gidanmu..Bamai irin Halinsa..Shifa Ya Imu bakomai ke Damunsa ba Baya Shiga Abunda ba Ruwansa Ko kuma yayi shisshigi kan Rayuwar wani yafi Damuwa da kamsa Fiye da kowa abaya..Ya Imu yana da Wuyar Sha"ani ko kema sai kinyi a hankali kin bi a Sannu Zaki iya gane wasu Daga Cikin Hallayarsa,Yana da Murdaddan Halin Da bamai iyamai sai Allah Daya Hallicesa ko Abba sai dai ya Kada kai ya Bisa da Allah ya Shirya Ballatana Ya Yusuf Shi din kaifi Daya ne In yace Abu to baya barci sai ya Tabbatar Dashi Baya Saba mganarsa Mutum ne Dabaya karya,Baya kuma shayi ko Tsoron Fadin mgana koda Za"a Kashesa ne yana Da Dakakkiyar Zuciya irin na Jaruman Maza,Bashi da Fara"a ballatana yawan Dariya Miskiline sosai na Bugawa a ajarida Bashi da Sakewa da Mutane infact ma Baya son Mutane ya Imu yafi jinDadin Rayuwa Shi kadai Fiye da Cikin Mutane ko da yan"uwansa ne Bashi da Sakewa da Mata koda kannensa ne Koda Nice Bashi da Sakewa dani..Tsakanina Dashi ke ina wasa Dake ni..?ni sa"anki ne..?kin Raina mutane ko..? Tashi ki tafi Dakinki ki ba Mutane waje kafin na Sauya Miki Kammani..! Ya tsani Raini Shiyasa Tun yana amsa sunan Imran dinsa Baya Harkan Mata Nifa ko Daidai da Rana Daya bantanajin Yayi Budurwa ba,Ammy nasan a Yadda yake Kyakyawan nan wannan bazai rasa masu Sonshi ba Ni kaina Wasu Hallayar nasa suna Burgeni Barin ma Kaifinsa yana da Zuciya Bakar Zuciyar da in Ta tasomai kowa sai ya Tsorata,bazan Tsaya Misalta Miki ya Imu ba sai dai nace Miki Shi din na Dabam ne da Duk yadda kika ga kai ga Hangenki baki isa ki iya Ganosa ba Duka ba sai dai ki San wanda kika sani Shidin kamar Wahainiya ce kullum Chanza Launi yake..Baya Lallashi sai dai Shi a Lallasheshi bashi da Rauni ko kadan Dakiya garesa da Kafiya In aka Taba wani nashi nan ne Za"a ga waye Ya Imu Bashi da Sakin jiki da Ahalinsa ammh Acikin Kirjinsa yafi kowa sonsu..Na Rantsw har ga Allah ba wanda ya isa ya Dagama Gidanmu yatsa kafin ya Saukr ya Imu bai karyasa ba Salon Soyayyarsa ba irin Takowa bace tashi Salon ta Nuna kwanji ne..! Munari ta karishe Fada Tana Sakin Mirmishi Safiya Tace"Ai nima nagani DAyazo Gidanmu Duk Fadan Abbu Sai da ya Sauraramai..! Munari tace"Haka yake..Bashi da abokai Rayuwar Duniya bata Damesa ba..Baruwansa da kowa Shi kawai Rayuwarsa ya sani shi kadai sai Abokinsa Daya Sagir wanda Mamansa Abba yace ta Rakoki..Shi ne kadai abokin Ya Imu..Shima din abotarsu Wani kaddararran Lamari me Daga Allah..Allah ya Riga ya Hada Jinsu Bayan Kaunar abota akwai Kauna wacce Allah ya Hadata a tsakaninsu Duk yadda Imu yakai ga yakice Sagir bai Yakican mai ba,Dole ya Rabu Dashi zasu hadau suyi Fada kuma Duka Fadan Ya Imu ne ke jansa Shi Mutum ne da in ba kansa ba ko Allah sa ba bamai iyamai ammh Kuma ahakan suke Tare ko Daya bai Nemi Daya Daya zai nemi Daya kuma Dashi da Mahaifiyarsa kadai Muke Mu"amala kuma sune suke Shigowa Gidan nan kai Tsaye Batare da wani Shamaki ba..! Safiya ta jinjina kai kafin Tace"Tabdijam..Wannan matar da zata aureshi nake Taausayamawa..! Munari ta kwashe da Dariya kafin tace"Ai ba Matar da Zata iya Zama Dashi.. Nifa aganina..Shifa bai Damu ba..Da ya Imu yayi aure mace ta Rainasa Ya kuma zama akwai wacce yake kula da ita bayan kansa gwara ya To ya Mutu bai yi auran ba bari ma Kiji na gayamiki..! Safiya ta Zaro ido tace'Bala"i..! Me Munari Zatayi ba Dariya ba sai itama Safiyan tabiye mata suka yi Dariya Sosai Har da Tafawa Hira Tayi Dadi. Safiya tace"Nidai bani Dan satan amsan yadda Zan zauna dashi..Kada watarana nayi mai Ba daidai ba ya Chanxamin kamani..!suka saka Dariya atare kafin Munari tace"Bazai Dake ba..Ai Baya Duka sai Ransa ya baci..Ko ni bai taba Dukana ba yasha Dai Fadan zai Dakenin a baki,Sai da mari ko tokari..kawai ki kiyaye baya son yawan gaisuwa,Baya son Hayaniya bayason ana Bugamai Kofar Daki ko kwana yayi bai Fito ba Kada wanda ya Nemeshi,Bai cika Cin Abinci ba yafi shan Fruit sai abu na Karshe Yana Shan Sigari kuma yana bata Muhimmaci..sannan koda baka son Warinta indai yana wajem Dole kayi Hakuri ka Shaketa ya tsani ka Toshemai Hanci Saboda gani yake Kamar shi kake kyama in kika Kiyaye wannan Babu wani abunda Zai Hadaku kila sai kuyi Sati Baku Hadu ba..Shi bamai Sakewa da mutane bane Yafi jin Dadin Rayuwarsa Shi kadai ko afalon nan baya Zama a koda yaushe in bai Fita ba yana Dakinsa ne..! Safiya ta jinjina kai kafin tace"Ai indai Wannan ne zan kiyayemai kada Watarana yace Min Safiya Kin rainani ko..? Gabadayansu suka Saka Dariya Suka Tafa jikake Tass..Har sai da kaji karan hannuwansu in ka kallesu alokacin kamar sun Shekara da sanin juna. Safiya ce tace batayi Sallah mangariba ba jin ana kiran Sallar Isha"i Ita kuma Munari tace Tayi mangariba Saura Isha"i su tashi suyi Sallah kafin Ya Yusuf ya Dawo. Nan suka Mike Safiya ta Fara Shiga Tayi alwala itama Munari Ta Shiga Tiolet din Yusuf tayi Alwala Dayake ita ke gyaran Dakin koda yaushe ba inda bata sani a ba adakin. Tare sukayi Sallar adakin Safiya tayi mangariban ta Ta Dora da Isha"i Ita kuma Munari Tayi Sallar Isha"i din da batayi ba,bayan sun idar suka Dasa kuma wata Sabuwar Hira Zuciyoyinsu ta Cika da Farinciki ita Munari ta Murnan Zuwan Safiya a Rayuwarsu Farincikin da suka rasa zai Dawo ta kuma Samu abokiyar Hira ita kuma Safiya Tana Murnan Ta samu kanwa Bayan Tasleem,Bazata yi kewa mai yawa ba,kuma nasan Ta Tabbata bazatayi nadaman Auran Yusuf ba. Suna tsaka da Hiran nasu Daidai Lokacin Yusuf ya Turo kofar ya Shigo da Sallama da Ledoji Guda Hudu a hannunsa na Tambarin kamfanin Gidan Abinci. Yadda ya gansu sai da yaji Zuciyarsa Tayi sanyi,Suna ganinsa suka Mike Ita Safiya Tana gyara Zaman mayafin kanta Ita kuma munari baki ta washe Tana fadin"Sannu da zuwa Ya yusuf..! Lokaci Daya tana karisa garesa da Niyarvkarban Kayan Hannunsa. Bakinsa Shima a washe ya amsa mata Lokaci daya yana kallon safiya yace"Babe kina samu akun Abba ko..? Nasan munari tayi keeping dinki Company..Nasan kanwata akwai son Hira..! Safiya kanta na Kasa ta Murmusa Tana wasa Da Gefen Mayafinta tace"Yes She so so Nice..I love her..! Munari najin Haka ta saka Tsalle Tana Dariya Shima Yusuf din sai da ya Dara Lokaci Daya yana Fadin"Ke kullum baki san kin girma ba Lilsis..? Above 20 fa..Kuma kina Yar jami"a Nan da Shekaru uku masu zuwa u are Going to become a Graduated in Ecocomics..! Sai ta Daina Tsallan Ta koma ta Natsu Tana Fadin"Wlh kuma hakane Yaya..Na bari..Yanzu ai am Mature ko..? Tafada Tana nuna masa kanta Dagashi Har Safiya sai da suka Dara Ledan Dake hannunsa Guda Uku ya mikama Munari Dayan kuma ya ijiyeta nan kasa sai dai ta karba yace mata"Ur Dinner..! Munari ta karba Tana Fadin"Allah yasa Fride rice ce Ya yusuf..! Yana Dariya yace"Mayar Fride Rice itace..Ki Dauki Dayan Ledan Is Urs..Daya kuma na Abba ne ki Tabbatar kin Bashi yaci yasha Mgani ya kwanta..Dayan kuma is for ur Brother Imran..! Munari tayi Narai Narai da ido Tace"Is He at Home..? Yusuf yace"Check his Room..! Munari ta Kara narke fuska Tana Fadin"Kasan He warning me kan Bugamai Room dinsa ko Ya yusuf..? In ba so kake ya Sauyamin dis My Beatifull Face ba is ok sai naje..! Yusuf ya kada kai yana Mirmishi yace"Shikenan ki aijiye Cikin Frigde din Kitchen if He Wanta Zai Shiga ya Dauka..Daman Choice dinsa ne Kayan Lambu! Munari tace"Tanque Ya yusuf..Sai da Safe..Anty Safiya see u Tomorrow..! Tafada tana Daga mata Hannu itama Safiyan Dagamata Hannu Tayi Tana Fadin"Ok see u Lilsis..! Daga haka ta Sa kai zata Fice yusuf ya Kirata ta waigo yace mata"U make Sure kin kwanta da Wuri..No Chart no Reading ko..? Kai ta gyadamai Tana Fadin"I promise u bazan yi ko Daya Daga ciki ba sai Barci..Basai kazo Dubani ba Ka zauna ka kula da Anty Safiya Dakyau asha Amarci Lafiya..! Tana Gama Fadar haka ta Fice da Gudu ta Rufo Musu kofar suka Bita da Dariya dukkansu. Sai alokacin Yusuf ya juyo zuwa ga Safiya ya Fara takawa Zuwa gabanta Idanuwansa kyam a kanta Ita kuma gabanta na Fadi kanta na kasa. Sai da ya iso gabanta bata Tsammaci Haka ba taji ya Rumgumeta Kamkame kamar wani Zai kwaceta sai kuma Taji ya saki kuka Cikij kukan yake Fadin"Tanque so Much Babe..Kin yimin Abunda Har na koma ga Allah bazan manta ba..Allah ya bani ikon Rike ki Cikin Aminci da kauna kamar yadda kika Nunamin..! Sai kuma ya kara Sakin mata kuka Tuni Taji ta Rude itama bata san Sadda Ta Saka hannu ta Rumgumeshi ba ta Saki nata kukan Tana Fadin"Basai kamin Godiya ba..Ka Chanchanta My Dear..Kaunarka gareni ce ta Sanya ka ganni Tsaye acikin Dakin nan a kuma Cikin Gidanku nidai Fatana ka Rike da Amana My Dear Ka soni Sosai Fiye da yadda nake sonki..! Yusuf na jan Majina yake Fadin"I do..Wlh I do..! Haka kurum yake Fada Kamkame Juna Sukayi kowannensu na kukan Fitar da Abunda ke Cikin Ransu Har sai da suka gaji suka koma suna Lallashin Juna gefen gado ya jata ya Zaunar da ita kan Jikinsa yana Fadin"Babe don Allah kiyi alfarman bazaki gayyatomin kowa Daga Barayinki ba Nan kusa Har sai na gama Gyara Miki Bangaranki na Saka miki komai na kuma yi miki kayan Lefen da kowani Namiji ke yi ma wacce yake matukar so ya ganta Zai Aura..! Safiya ta Sakarmai Ido Cike da kwallah Kafin tace"Ban yi maka wannan alfarman ba My Dear..!. Cikin mamaki ya Tambayeta"Saboda Mene Babe na..? Safiya ta Runtse ido ta bude kafin tave"Kayan Lefe na yafe maka su..Kayan Daki kuma ai ba Harumin ka bane na Iyayena ne..Ni ka kyaleni nan Dakin bai Ishemu Rayuwarmu bame Dagani sai kai..? Ga falo chan ga Kitchen ga komai na Bukatar Rayuwa..?me kuma nake nima Ni Safiya banda Kwanciyar Hankali da Zama Lafiya da Mijina da Sabon Gidan dana Tsinci kaina..! Ta karishe Fada Hawaye suna kwanroyomata Da Sauri Yusuf ya Rumgume tsam yana Fadin"Ba Saboda Ke zan yi kayan fa..Saboda kaina ne ki Rika sakawa kinamin kwalliya Dasu..Mganar Kayan Daki kuma ba Ruwanki Zamu koma wanchan bangaran nan da wani Lokaci ba Saboda ke saboda kyawawan Ya"yan da Zaki Haifamin nan gaba..Ni su Abbu sun gama min komai Tunda suka Bani ke bana Kuma Bukatar Komai Daga Wajensu! Ta Dago kanta ta Bude baki Zatayi mgana ya Hanata bayan ya Dora Hannunsa saman Lebenta yace"Shii...Zamu je mu gaishesu in muka Samu Natsuwa..Ammh all i say hakan ne Zai Faru..! Bata da ikob Sake mai gaddama sai ta koma Bisa Kirjinsa ta Lafe yana Rike da ita kamar wani zai kwaceta. Ahaka ya sauko Da ita saman Cafet ya jawo Ledan dan ya Fito musi da Takeway din Daya yi musu sai kaZa Gashashiya da yourghot,mai Sanyi Dakyar taci Shinkafar ya Hadamata da Kazan da Madaran sai da ta kusa amai ya kyaleta kana Shima yaci Sosai yasha Madaran Daga gani kila ya Wuni bai ci komai bane Kamar Tayimai Hawaye,bayan sun gama Tana Nokewa ya kwasheta zuwa Tiolet ya sakarmusu Shower Dole suka yi wanka Bayan sun gama Nanikan juna Duk da Yusuf din bai mata komai ba sai dai Rumguma da Kiss haka. Alwala suka Dauro,ya jasu Sallah Raka"a Shida Bayan sun Idar yayi musu addu'o"i sosai na Zaman lafiya kafon suyi Shirin Barci Shi ya Bude akwatin Safiya ya Dauko mata Wata Rigar barci guda Daya wacce wajen Tuso kayaneta Shigo ammh ko Barayin kayan Barcinta bata Bude ba Tana Nokewa Tana komai ya Dauketa ya aza kan gado ya Cire mata Doguwar rigar Data sakata yanzu Tunda kayanra sun Jike suna Tiolet Yusuf ya Shanya mata. Hakan nan ta Runtse ido ya sakamata Rigat barcin Shima ya Tube Dagashi sai Boxers ya Hayo gadon ya Ciccibita ya sakata Cikin Jikinsa ya Nadesu Cikin Blanker Bayan ya Rage Hasken Dakin yana jinta yadda Take Mutsu Mutsu da kuma yadda Zuciyarta ke Bugawa. Cikin Mirmishi ya Sunkuya kunnenta Yayi mara Rada yana Fadin"Relax babe Babu Abunda Zan yi miki ayau din nan..Ban kuma ce Gobe ma haka ba kawai dai kafin mu Zama Daya Dani Dake nake so na baki Labarin GIDANMU..labarin da kika so kiji ban Taba Fadamiki ba Labarin da ban Taba Gayama kowa ba sai ke yau din nan..Ba saboda komai ba sai Saboda Daga yau din mun Riga mun Zama Abu Daya Komai nawa naki ne Komai naki nawane haka Sirrina naki ne kamar yadda Sirrinki yake Nawa Babe na..! Safiya Dataji Abun kamar a Mafarki ta Dago da kanta bata ganin Fuskarsa Saboda Duhu sai dai tana iya ganin Shedar Fuskar tashi Cikin Tsananin Farinciki ta Damke hannunsa Tana Fadin"are u Serious..! Kai ya Gyada mata kafin yayi mata Kiss a goshinta cikin so da kauna Rumgumesa Tayi sosai Tana Fadin"Tanque Dear..Uhm...Am all Hears..! Yusuf ya kara Riketa ajikinsa Bayan ya zagayo da Hannyensa Bayanta zuwa Saman Cikinta lokaci Daya ya Sauke ajiyar rai Dana Zuciya Tuna abunda ya Faru dasu Shekaru uku Zuwa Hudu da suka gabata. *Shakira...* 3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)*      *🅿�13* *DR.ABUBAKAR HAMISU DUKKU* (Malami) shine Asalin sunan Mahaifinmu,Dr ne a bangaaran Ilimi kuma Malami ne Daya shafe fin shekaru Goma yana koyawar a Jami"ar Lagos, Wato a University of Lagos Fanni Sanin Hallayar Dan Adam Wato Phsychology Sunan Malami kuma da Abbanmu ke Amfani Dashi ya samu asali ne akan Tun yana karami yake kaunar Zama Malami Dalilin haka yasa Mahaifinsa Marigayi Alkali Hamisu Dukku ke kiransa da Malami Tun yana amsa Sunan Abubakar Hamisu Dukku Har Dukkun ya bace bat ya koma amfani da Abubakar Malaminsa Duk wanda ya sansa da wannan Fitattacen Sunansa ya sansa. Mahaifinmu asalin Bafullatanin Gombe ne ta Uwa ta Uba,Daada da Marigayi Alkali Dukkansu Haifaffun gombe ne,A karamar Hukumar Dukku Dake Jahar na Gombe. Awajen Mahaifinsu su Biyar ne Uku Maza Mata Biyu Abba ne D"a na Biyu awajensa,Akwai Baffa Kabir,sai Baffa Mustapha,sai Goggo Bintalo sai Karamarsu wacce Munari taci Sunanta Maimunatu. Abaya kafin Rayuwa ta Juyamana Gidanmu Gida ne na Soyayya da kaunar Juna da kuma Hadin kai. Mahaifiyarmu Hajiya Zuwaira auran Zumunci ne Tsakaninsu da Abbanmu,Domin Daada Mahaifiyarsu Diyar kanwartace ta Dauketa ta Riketa awajenta Har ta aura ma Abba ayadda Anni ta sanar Damu Lokacin Abba ya kawo wata tace da Niyyar ya aura Wata Shatu wacce suka Hadu da ita a Jami"ar Jos,inda yayi Karatu Sai Daada Ta nuna A"a ta kuma wanke Mahaifiyarmu Anni ta bashi bai Mata Gaddama ya saka Hannu Bibbiyu ya karba Domin Shi Mutum ne mai Sanyin Hali da Biyayyah. Da Farko ba a Lagos su Abba suka Fara Zama ba sai da suka zauna a nan Cikin garin Gombe,Lokacin yana Assistan Lacture ne a jami"ar Gombe Bayan Kamallah Degree dinsa na Biyu ne Ya samu aikin Bayan auransa da Anni kuma ya Daukota Zuwa Gombe. A garin Gombe aka Haifi Yaya Nura da Ni da kuma Imran Sai Zuwa Lokacin Abba ya gama Hada Phd dinsa Ya samu Sauyin aiki Daga Jami"ar Gombe da Tuni Daman ya koma mataayin Senior Lacture. Muka Tattara muka koma Lagos da zama acikin Tsakiyar garin Lagos A wata anguwa mai suna Vitoria Inland..! A lagos muka Dora Sabuwar Rayuwa,Daman Tun a gombe Ya Nura da ni mun Fara zuwa makaranta Dayake Dukkanmu Har Imu Haihuwa Kai kai ne Cikin Shekaru Hudu Anni ta Haifemu mun taso Gabadayanmu kanmu Daya ne,Da muka koma Lagos ne Abba ya Sanyamu a Wata makarantar kudi mai kyau mukaci Gaba da Zuwa,A kuma garin ne aka Haifi Asma"u da Salima sai Munari Itace Auta. Yusuf Daya kawo nan a Labarinsa Safiya Taji shuru Tana jinsa ta Muskuta ta Dago tana kallonsa jin yayi Shuru Duk da bata ganin Fuskarsa Tace"Ina jinka My Dear sai akayi yaya..? Ina Anni ina Ya Nura da Salima da Asma"u..? Ina kuma yan uwanku na Dukku Sauran Yan"uwan Abba..? Kuma wani Dalili ne ya Dawo Daku Rayuwa A kano Bayan komai naku yana Lagos..? Me kuma ya Faru da Abba Har ya samu wannan Rashin Lafiya..? Kuma meneme ainihi yake Damunsa..? Ta karishe Fada Cikin zumudi da son Jin karshen Labarin Gidansu Yusuf. Yusuf Da Jikinsa yayi sanyi Baya son Tuna Labarin nan ko kadan Ammh Ya Zama Dole ya Karishe ma Safiya Labarin nan ko Zata Fahimci ba Wai Da gangane ko Rashin asali ne ya Maidosu Rayuwa su kadai ba Wani Kadaddaran Al"amari ne da Allah ya Riga ya Rubuta sai ya Faru. kara kamkameta yayi ajikinsa Kafin ya Cigaba da mgana Cikin Sanyin Murya da Sarewa. Mun taso Cikin Soyayya da kauna ta Kowani Fanni Abba Mutum ne mai Dattako da Sanin ya kamata mai kula da Iyalansa da Danginsa Duk da muyi Nisa ammh kusan Duk wata yana Hanyar Gombe zuwa ganin Daada Bayan Rasuwar Mahaifinsu Alkali Hamisu Wani Lokacin Tare da Anni suke Tafiya wani Lokacin kuma Shi kadai mu kuma muna Zuwa makaranra Tun safe sai yammah in mun Dawo gida akwai malamin da Abba ya Daukar mana yana Koyamana Karatun addini Sakamakon ba Lokaci sai ya kasance sai mu Fi Shekara bamu Taka garin Gombe ba,gwarama ya Nura Dani mukam bi Abba Gombe in zai je Hutun Karshen Shekara sai abar Anni da su Asma"u a gida Kafin mu Dawo Shiyasa Duk Cikin mu muka Sanin Dangi Dangi ma suka fi Sanin mu. Lokacin gaskiya Zumunci yafi karfi ta Bangaran iyayanmu mu ya"ya bamu Damu dashi ba Kowanne ya"yansa na makaranta gashi ba"a zaune waje Daya,Ballatana arika Ziyarar juna akai akai Ballatana asan juna Sosai. Bamu san kowa ba sai Abba da Anni sune Duniyarmu Gaba da Baya Abba ya Sadaukar da komai nashi Saboda mu Anni kuma ta Sadaukar da Lokacinta da Lafiyanta Wajen Tarbiyantar damu da kula da mu,Lokacinta da komai namu ne Muna Matukar sonta da kaunarta Domin Duk Fadin garin Lagos Daga Anni sai Abba sai sauran yan Gidanmu kadai Muke Dashi Duka Dangi Basa kusa Baffa Kabiru yana Abuja Baffa Mustapha yana Kaduna Sai Goggo Bintalo tana aure a gombe ne Goggo Maimuna kuwa Tana aure a Bauchi ne Daada kuma Tana Asalin Gidansu na Dukku ne sai dai Aje Chan adubata. Duk Cikin mu Imran ne kadai yayi makarantar kwana acikin Garin Lagos yayi karatun Karamar Secondary Dinsa har Zuwa babba Primary ne Kadai yayi ta Jeka ka Dawo,Ba wanda Yayi mamakin Zabinsa Saninsa Shi bamai Son Sakewa da Mutane bane da Hayaniya Shiyasa yana garin Lagos ammh Sai an Samu Htu kamar Sauran Dalibai yake Zuwa Hutu Gida Shiyasa Gwara Kowa Dashi Ko Dukku Sai ya fi Shekara uku bai Taka ba,ko ya Dawo Hutu in Abba yace ya Shirya aje Dashi Sai yacFara Ciwon karya Saboda Bayason Zuwa Ballatana ya Shiga Mutane ko acikin Gida kowa yana Zaman Falo banda Imu Shi din Hallitarsace Miskilanci da Rashin Son Sakewa,Kowa Daya Fahimci halinsa ne sai kowa ya kiyayemai Ammah banda Asma"u itace Sakon sa Shiyasa Take Shan Wahalansa Kusan in ya Dawo Gida Hutu Kafin ya koma Sai ya Barta da Tabbai Akwai Lokacin da Ya Daketa Har sai da ya Sumar da ita Ran Anni ya Baci ta Mareshi Shine Imu yayi Fushi Lokacin yana Farkon Shiga SS3 NE daya Koma makaranta bai kara Waiwayan Gida ba sai da ya Zana Jarabawarsa Duka ya gama da makaranta ya Dawo Lokacin Ni da Nura Mun samu Gurbin Karatu a Jami"ar Lagos,Tsakanina Dashi Shekara Daya ne shiyasa Karatun namu yake Tafiya kai da kai. Abun bai bama Kowa mamaki ba Da Imran ya Cike Jami"ar Ibadan,Sanin Halinsa Chan ya Tattara ya Tafi karatu inda ya Zabi bangaran accounting,Wani Lokacin sai ayi Hutu Nawa bai zo Gida ba sai dai Abba Ko mu mu kai Ziyara Abba ma yafi Zuwa wani Lokacin in ya Dawo Daga Gombe yana Biyawa ta Wajensa Tunda Shi ya Haifi Abunsa yafi Kowa Sanin Halin kayansa Anni ce ke Damuwa Tayi ta Fadan Imran bayason yan"uwanshi Ballatana Danginsa Tunda bayason Zama Dasu,Abba ke Tausanta Lokacin yana Fadamata ta Cigaba damai addu"a Halinsa kenan,Tayi ta Korafin Dangi ba wanda yasan sa sai dai sunansa Tun yana karami Rabon Daya Taka Gombe Duk Zuwa sai Daada Tayi Mita da Korafi Sai dai Imu bai Damu ba yafi Damuwa da Abunda ya sakama Gaba Fiye da komai a Rayuwarasa. Haka Rayuwarmu ta Cigaba da Tafiya Ni da Nura muka kamallah Digree din mu na farko muka Dora na Biyu da Kwarin Gwiwan Abban mu Asma"u kuma ta Fara Karatu a Lagos state university Lasu Dake Lagos, Tana karantar phamarcy Salima kuma Tana Shekarar Karshe a matakin Secondary,Munari kuma Tana baya Saboda ita din Daga Karshen Anni ta Haifeta Bayaan Salima ta Shekara bakwai a Duniya. Zuwa Lokacin mun san Dadin Dangin mu da kanmu mukan Shirya mu Ziyarcesu ko da Abba baice ba Barin ma Nura yafi kowa son Zaman arewa Domin yace yana Burin ya samu aiki a arewa Yayi aure ya koma Chan da Zama,Shiyasa Duk bayan Wani Lokaci muna Ziyartsu Munje Har Gidan Baffa Kabiru da Baffa Mustapha da kuma Goggo Bintalo,Da goggo Maimuna kuma sun ji Dadi Sosai Daada kuwa Muna da Lambar ta Lokaci Bayan Lokaci muna kiranta muna gaisawa Sai dai Koda yaushe mukayi Waya da ita Zencen ta Daya kenan Imu,Shi kuma Yana Chan makaranta ba Sosai ma yake zuwa Gida ba. Sai Lokacin Daya gama Degree dinsa na Farko yazo Gida Hutu Lokacin ne Abba ya Rutsashi ya iza keyarsa Har Zuwa Dukku Gaban Daada Sai da suka kwana Biyu suka Dawo a wannan Zuwan ne Har su Baffa Kabiru sun zo Sun gansa Shima Lokacin yazo da' Wajensa Khamis Sa"an Imu din ne ammh Har suka Rabu Wata kyakyawan Mu"amala bata Hadasu ba imran bai da Sakin jiki Sam da Mutane Daada Tayi mai Nasiha yayi bakam Kamar yaji yana komawa gida ya yi Cuku cukun ya koma Ibadan ya Dora Degree dinsa na Biyu,ya manta Da Fadan Daada. Rayuwarmu Gidanmu Mun ginata Cikin Karatu Mai Zurfi ne Duka Dana Arabi Dana Bokon Harta Salima itama Tabi Sahu Ta Fadama Jami"ar Lagos ita Fanni Abba take karanta Wato Physchology Muna gama Hada Degree din mu na Biyu Muka Samu manyan ayyuka Nura ya samu aiki a Federal Inland Revenua Service(FIRS)Wato Hukumar Haraji ta kasa Dake Jahar Lagos,Yaso ya samu a arewa sai kuma Allah ya Rubuta nan ne wajen cin Abincinsa. Ni kuma na samu aiki a Hukumar INEC,rejen Jahar Lagos muka Fara aikin mu Cikin Lokaci kadan Cikin Naaara da Sa"a bamu Rufe Shekara Daya ba muka mallaki Motocin Hawa Dani da Nura,Da kudaden da muka Fara Ragema Abba Wasu Hidimdimun Ko Chan Dukku baya sanin muna turama Daada Sako Sai dai in ta Kirashi Tana Godiya ya sani. Asma"u ma Ta gama Karatunta Har ta Fara aiki a wani State Hospital na Lagos a phamarcy, Dake Garin Lagos Salima ita kuma Tana Karatun ne bata gama ba,ita Burinta so Take ta Zama Dr.Salima Watarana Ta gaji Abba Ashe Ashe Burinta bazai Cika ba Domin Lokacinta aduniya bamai yawa bane..! Yusuf ya Fada Hawaye masu Zafi suna kwaranyomasa Jikin Safiya yayi Sanyi Gabanta ya Fadi Cikin karyewar Murya tace"Innalillahi badai Rasuwa Tayi ba..? Yusuf yaji Rauninsa ya Bayyana Cikin Karyewan Zuciya Dana Murya yacCigaba Da fadin"Imran ma ya gama Karatunsa ya Fara aiki da Bankin GT reshen Jahar Lagos Shima ya mallaki Motar Hawansa,da kudaden Daya Tsaya kan Kafafunsa.. Faruwar al"amarin Daya Faru damu ko nace ya afku ga gidanmu kaddaran Da bamu isa mu guje mata ba,..Gaddaran Datayi Sanadin da muka Rasa komai namu Kaddaran Dayasa muka bar komai namu muka zo nan muna Rayuwa inda bamu da kowa.. Watarana ce da Zukata da gangar Jiki bazata Taba Mantawa Dashi ba,Baffa Kabiru ne ya samu Hatsari Daga Garin Abuja zai je Dukku bai ma yi Nisa ba saosai al"amarin ya Faru aka Dawo Dashi Specialist Dake Abuja aka Bashi Taimakon gaggawa Jikin nashi Da Sauki ba karaya sai dai Yaji Ciwo Kadan kadan Motarsa ne tayi Dameji bama Zata taahi ba Hankalu suka Tashi Kwarai Abba da Anni Ranar basu Iya barci ba Abba Sai Mtsawa yake a samu Buking din Jirgi Zuwa Abuja,Allahu akbar Allah Sarki Rayuwa Nura Shi yaje Filin Jirgi yayi Cuku Cukun komai,Allah ya Rubuta Lokacin Abba aduniya Bai kare ba wani Taron Malamai ya Tsaidashi,Ni kuma A wajen aiki ba"a barni ba Imran kuma Bama wanda yabi ta kansa Sanin Halinsa Ganin haka yasa Abba yace Nura da Anni da Salima da Asma"u su Farayin gaba Kafin mu muzo Daga Baya Tunda Lokacin Munari suna Jarabawa a makaranta,Abba kuma Zai Tsaya Taron su na Malamai sai Zuwa Gobe in sun gama Ni dashi Zamu Bi Jirgi zuwa Abuja muje mu Duba Baffa Kabiru Tunda Duka yan"uwa sun isa Chan Abuja. Har yau bazan manta da wannan Ranar ba Imran Tun bakwai na Safe ya Fita Zuwa Wajen aikinsa Munari na makaranta Ni Abba yasa na kai Su Anni da Nura da Asma"u da Salima Filin Jirgi na Murtala Muhammed ban kuma bar Wajen ba sai da Jirgin su ya Tashi ya Lula Sararin Samaniya. Na Dade tsaye Afilin jirgin bayan Tashinsy Na kasa Shiga Mota na koma Wajen aikina Haka kurum nake jin kaina wani iri kamar Wani abu Zai Faru Dani ashe ashe kuwa hakane Na koma Office na kasa Tabuka komai ko Cikakken Minti Talatin banyi ba Wayar Abba ta Shigomin ina Dagawa Naji Abba Cikij karaji yana Tambayana Jirgin su Anni ne ya tashi Minti Talatin da yawuce..!? Ni kaina na Rude bansan ina kaina yake ba Cikin Rudewa nace ma Abba Eh Sune Daganan ban ji komai ba sai karar Faduwar Abu naji Da Hayaniya Daganan naji Shuru Hankalina ya Tashi na Fito Jikina narawa anan naji Labarin Dayayi barazanar Tafiya da Numfashina Wai Jirgin Airic Daya Tashi Daga Filin Jirgin Murtala Muhammed Daga Lagos Zuwa Abuja Minti Talatin da suka Wuce ya Fadi a wani Daji Bayan ya bar Lagos. News na gani a Tv Dake ma"ikatan mu...! Yusuf yana kawo nan ya Saki kuka mai karfi Safiya ma Tuni Ta Fashe da kukan Cikin kukan Take Fadin"innalillahi Wa"inna Ilaihirraju"un..Daman yan Gidan ku na Cikin wannan Hadarin Jirgin Daya Cinye Rayuwanka Yan arewa Da yawa..!? Yusuf na Kuka yace"Da yan gidanmu Safiya..Da Anni da Nura da Salima da Asma"u Sun konee kurmus ko gawansu bamu gani ba kawai nidai na Farkane na ganni a asibiti Imran na Gefena yana ta kuka Kukan Da Tunda nake dashi ban Taba ganinsa yayi kuka ba,ina mikewa na Fara Tambayansa ina Abba sai dai bai min mgana ba ya Nunamin Abba Dake gefena Kwance Shima anamai karin Ruwa,Safiya bazan Tsaya baki Labaein Irin Tashin Hankalin da Muka Tsinci kanmu aciki,Abba ya Farka yana kuka yana Fizge Fizge yana Kiran sunan Anni da Nura da Asma"u da Salima Likitoci sun kasa Controlling dinsa Bamu da wani kwarin Gwiwa Domin Rashin da mukayi Babba ne wanda Babu Wani Abunda zai iya maida wannan Gibin. Ni da kaina na kira Wayar Baffa Mustpaha na Sanar dashi ina kuka Chan ma Hankula suka taahi Domin Gabadaya Hadarin Jirgi a Karade kasa Tunda Yawanci Duk yan arewa ne da Wasu manya a gwannati. Dagani Har Imran bamu kwana agidanmu ba Ni naje makaranrar su Munari na Daukota muka Koma asibiti muka Hada kai mu uku muna kuka Tun Munari bata gane Har ta Fahimta nan muka kwana da Abba asibiti,washegari kuma Baffa Mustpha da Baffa Kabiru Da ciwon da komai ya tashi ya Taho,sun same mu Cikin Wani Hali,Abbanmu kuma ya Fara Fita Daga Hayyacinsa Batare da Shawara damu ba suka Gama Cuku Cukunsu sukayimana Bukking din Flight Bayan sun karbi Report din Abba na asibiti din Abba Suka Tarkatamu Zuwa Gida muka Debo kayanmi Harda na Abba Dana munari Suka Tasamu agaba Sai Filin Jirgi Duk da Tsorata da Hawa Jirgi daya shiga Ranmu Hakanan muka Shiga bazan manta ba sai da Imran ya Suma Saboda Firgita. Daga Lagos Gombe muka Sauka Mijin Goggo Bintalo yazo ya kwashemu sai Dukku Gidan Daada koda muka isa Gida ya Cika da Dangi ana ta Koke koke Daada Tayi kuka kamar Idanuwanta Zasu Makamce,anan akayi karban Gaisuwa Har akayi Sadakan Bakwai Abba Baya Cikin Hankakinsa sai sambatu da Surutai,Mukan mu gamu nan kawai ammh Komai ya Fita kanmu da Rayuwarmu Gabadaya Bama da Wani Tunani sai abunda aka Fadamana Tunanin mu da komai ya Tsaya Cak.Har gwarani akan Imran da Munari ana ganin kamar bai Damu da Danginsa ba Ashe ashe abun sai yafi Tabasa Fiye da kowa. Saboda Halin da Abba yake Ciki yasa bamy koma Gida ba muna Dukku gaban Daada sai dai duk Sati Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha suna Hanyar Zuwa ganin Abba ya Kamu da Cutar nan ta Depression yasa Suka Daukesa suka kaisa asibiti aka Dubasa aka bashi mgunguna da Shawarwari da Farko Abun kamar yayi aiki Daga Baya sai Abba ya Kara Rikicewa Bawanda zai Fahimci Halin da Abbanmu ke Ciki sai mu da muka Dandanin Zafin Abun,Shiyasa cikin Yan"uwan Abba suka kasa mai Uzuri Ballatana su Fahimci Wani Hali yake Ciki basu Taba Dadanin Zafin Rashin Daya Dandana bane Shiyasa suka Fara ganin Laifinsa suna Fadin bai da Takwalli ne Dagashi har mu da kullum bamu da aiki sai mu tasaahi muna kuka ai ba kanmu Farau Mutuwa da Rashi ba Anni da Asma"u da Salima da Nura Sun Tafi kenan har Abada bazasu Taba Dawowa ba..Daada ce Kadai ta Fahimci Halin da Abbanmu da mu kanmu muke Ciki Baffa Kabiru yafi kowa Daukan Zafi Daga Karshe sai ya Zare hannunsa kan Abbanmu Tunda Likita yace Mgani baya aiki Tunda Abba bai Rage Damuwa ba kuma yaki ya manta da Abunda ya Faru Dashi..? taya zamu manta da wannan Rashin..? Ai har Abada Gidanmu ya Shiga kuncin da Bazamu Taba Fita acikinsa ba. Tun bamu gane ba Har muka gane irin Yadda yan"uwan Abba ke kallonsa a Saboda Rashin Takwalli Ya koma Mahaukaci bashi da aiki sai Sambatu,Mukuma ya"yansa mu Bar komai nami mun dawo muna Rayuwar kawai Saboda Baffa Kabiru yayi yayi Dani da Imran mu koma Lagos Saboda aikin mu muka ki..Imran ya Nunamai Aduniya Bamu da wani abunda ya Ragemana Bayan Abba Saboda Haka ba inda Zamu muna Tare Dashi Dalilin haka yasa muka kusa Wata Shidda a Dukku,ayyukan mu Duka sun Tsaya an gaji da kiranmu an kyalemu,Munari Tuni Karatunta ya Tsaya Cak itama Bata da wani Sauran abunda Zata Dora. Ni ban yi Tunanin Dauke Abba mu bar Dukku ba Imu ne ya kawo mana Wannan Tunanin Tun Lokacin Daya iske su Baffa Kabiru sun Tarun ma Abba suna ta mai Fadan yaki ya yarda da Kaddara ya Dawo Daidai ya Zauna yana Biyemana yana kwana kuka Mutuwa ce Dayace kuma wanda ya Mutu baya Dawowa Abba na kuka bayacewa komai Domin alokacin basu san Dacin Dayake ji ba Daada ma kukan Take ammh sun kasa Fahimtarsa,Suna cewa ya zama Mahaukacin karfi Dayaji kamar ba Musulmi ba,Baffa Mustapha baya mgana sai Baffa Kabiru yafi kowa Zakewa wannan Dalili yasa Imran ya mtsamin kan muce Zamu Tafi da Abba Lagos muje Chan muka Cigaba da aikin mu muna kula Dashi..Abun mamaki da muka Furta Daada ce kadai tayi musu ammh Banda Sauran yan"uwan Abba nan da suka amince acewarsu kila zai fi Samun Sauki batare da Rakiyan kowa ba Muka bar Dukku Zuwa Lagos,a mota muka Yi Tafiyar Domin Tun Abunda ya Faru Har Abada muka Tsani Jirgi. Mun Dawo Gidanmu na Lagos da Zama sai dai Babu abunda ya Sauya Nidai ban koma bakin aikina ba Hakama Imran,Ballatana mu kokarta mu maida Munari makaranta Duk wani Farincikin Gidanmu sai ya Gushe sai kunci da Bakinciki Abba koda yaushe yana Daki yana kuka yana Samabtu mu kanmu bamu da Wata natsuwa. Bayan Dawowarmu da Wata Daya Baffa Kabiru ya zo ganin mu Cikin Wannan Halin ya kara Bata ransa yayi ta Zaginmu yana mana Fada Abbanmu kuwa kamar ya Dakesa Daga karshe yace yaje yayi ta Haukansa In ya Haukace ni da Imran sai mu kaisa Gidan Mahaukata ko Zama bai yi ba ya Juya shima zuwan da yayi Daada ce ta matsamai yazo ya Dubamu. Awannan Ranar Ran Imu ya baci ya Fita,Fitan da bai Dawo ba sai da ya kwana Biyu yana Dawowa na gansa ya iya Busa Sigari,shi kuma ya ce Dole ne muyi Nisa da Komai namu in muna so mu Cigaba da Zama Lafiya Inda ba wanda yasan Labarin Gidanmu Ballatana akira Abbanmu da Mahaukaci muyi nisa da komai nanu asali,Nasaba Dukiya aiki da Komai na Rayuwa Ni kuma na amince Domin Lokacin na Fara Tsorata da komai kada Imu ya Fada wani Hanyar Banza. Bamu saida komai namu ba Gida Motoci Duka suna Lagos sai dai mun kai Takardan Barin aiki Daga Ma"aikatanmu da Muke aiki sai muka Tattara kudi Katin bankin mu Dana Abba dana Nura dana Asma"u da Takardun makarantarmu Dana Munari sai kayan sawanmu,muka Diba iya wanda Zamu iya muka Baro Lagos Bayan mun Sallami mai Gadi mun kulle Gidanmu bamu ma Tunanin Zamu Dwo Watarana ba sai Domin yin hakan Shine Mafitarmu Mun Taho da Abba Kano bai Cikin Hayyacinsa a Hotel muka Sauka Ni na Fita Na Bincikamana Gida Cikin kwana Biyu muka kara mallakan Wani gidan,Shine wanda muke Ciki,Muka Tattaro muka Dawo Domin Gina wata Sabuwar Rayuwa Bayan mun bar Duka Layukan mu da Wayoyim mu a Lagos Da komai inda Za"a Same mu saboda bama Bukatar Taimaakon kowa Tunda ankasa Fahimtar,Radadin Dake Cikin Babban Rashin da mukayi. Ganin in na Zauna Haka Rayuwar Gidanmu Zata kara Lalacewa Cikin kunci,Sai na yanke Shawaran Fita Neman aiki Duk da bamu rasa komai ba Muna da Kudi,ammh ban Zauna ba Cikin ikon Allah na samu aiki a hukumar Inec ta nan Reshen Jahar Kano,Ni ne na Zama Uwa da Uban Imran da Munari na Zama Garkuwan Abba na Daukan Mai likitan Dake Zuwa Gida yana Dubasa Duk Bayan Wata Daya,koda Abba ya Fara Dawowa Hayyacinsa ya Fahimci Abunda muka aikata yayi ta kuka sai dai Bai Da Cikakkiyar Lafiyar da Zai iyq Tambayanmu meyasa mukayi hakan..? Da albashina na Siya Motan Hawa na Siya ma Imran Mashin Tunda yace bai Bukatar Mota aiki ma yace bazai koma ba,Shi Baahi da Sauran wani Buri kuma,nayi nayi na Rabashi da Shan Sigari na kasa Saboda ya Riga ya Zama Jikinsa bazai iya Awa Daya bai Sha Sigari ba,duk Wasu Sabbin Halaye Rashi ne da Rayuwa suka maida Imran haka,Ni nayi Tunanin Inganta Rayuwar Munari Tunda ita Kadai take Ragemana na maidata makaranta.. Da farko ban Yi niyyar Fara Neman aure ba sai nayi Tunanin auran nawa Zai Tamaka ma Rayuwar Imran da Munari Sai dai kash Duk inda na Nemi aure sai mgana ta kamkama sai ta watse duk inda akayi Binciken Gidanmu aka gano wani abu duk da bama Hulda da kowa abun mamaki labarin komai sai ya fita, bamu da kowa kuma Abba bashi da lafiya yana Ciwon Hauka Dalilin haka Imran ya karya Hannun Kawun Wata Asma"u Dana Nema aka Hanashi Daga Karshe shi kawun nata yaci Zarafin Gidanmu Shari"a Dakyar na iya kasheta Na nemi aure kusan sau uku bana samu sai a kanki kema din da kokarin Imu na Sameki Tun kuma Bayan Tafiyarmu Har yau wani Daga Cikin Ahalin mu baisan inda muke ba bamu sani ba ko sun neme mu mudai bamu nemi kowa ba Har Rana mai kama ta yau..Ko naso mu nemi gida Imran ke Hanani Domin shi yafi Daukan Abubuwan da suka Faru Fiye dani Kaina. *Shakira...* 3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)*        *🅿�14* "Kinji irin kaddaran Data Fadama Gidanmu Babe..Tun bayan Faruwar Al"amarin Komai namu ya tsaya Cak Kawai Rayuwar muke gamu nan bawani Jin dadi ba Farinciki ba Walwala. Kinji Kuma Dalilin daya sa muka Baro komai namu kinji kuma irin Halin da muka Shiga da wanda Abba ya Shiga Da Dalilin mu na barin Komai namu muka Dawo muna Rayuwa inda ba"a Sanmu ba kuma kinji Irin Lalauran Data samu Abba Shi din ba Mahaukaci bane yanayin Rayuwa da kaddaran Allah ne suka Maidashi haka. Ya karishe Fada yana Tsiyayan Hawaye,Safiya ma Dake Jikinsa Hawayen Take,Cikin Sarkewar Murya tace"Allah ya jikansu Anni..Allah yayi musu Rahma Allah ya kyautata Makwancinsu.Hakika kunga Babban Rashi..Tabbas kun Hadu da Jarabawa Mai girma Mutuwar Rai har Guda Hudu a Lokaci Daya dole Zuciya Zata Raunana..Allah ya karbi Shahadarsu..! Yusuf na jan majina yake amsa mata da Ameen Ameen.. Safiya ta Cigaba da Fadin"Tabbas su Baffa suma basu kyauta ba..kamata yayi su ja ku ajiki da Lallashi da Nasiha da komai sai kuFara manta abunda ya Faru..Su Rika Nuna muku ku Fauwalama Allah komai su Nuna muku Hakan bashine Karshen Rayuwar ba akwai Wasu agaba..Ya kamata ace sun Zauna sunfi Kowa Fahimtar Halin da kuke Ciki..Abba kuma ya kasance koda yaushe Suna Lallashinsa da kokarin Nuna mai Komai Daya Faru da Sanin Allah kuma Mutuwa Dayace Muma Jiranta Muke,su da suka Tafi basu yi Sauri ba Muma da muke Duniyan Jiranta Muke na Tabbata da yanzu baku kai ga Daukan Wannan Matakin ba My Dear..! Yusuf Dake Sauraran Safiya yace"Gaskiya ne Babe..! Yafada Cikin Sanyin Murya mikewa Tayi Daga Jikinsa,Tana Fadin"My Dear Tashi muyi mgana..! Bai mata Musu ba ya Mike Zaune ya saka hannu ya kunna Hasken Dakin Suka Kurama juna ido Kan kirjinsa ta koma ta Lafe Tana Fadin"Ina da Wata Shawara My Dear game da Situation din Abba He Need a Help..ba na kai ka dai ba..Taimako yake Nema Awajenmu Dukkanmu matukar muna so ya samu Lafiya ya Daina Tuna Abunda ya Faru.! Da Sauri Yusuf yace"Wata Shawara ce Babe na..? Dagowa tayi Tana Kallonsa Hannunsa ta Riko Duka Biyun Tana Fadin"Bai Kamata ku bar Abba yana Fuskatar wannan Abun shi Kadai ba..Kada kuyi Treeting dinsa kamar su Baffa My Dear..Bai dace ace Abba yana Rayuwa acikin Daki ba ko Falo baya iya Fitowa Ahalin yana da lafiyar Kafarsa..Bai kuma Dace arika barinsa Shi kadai ba..Sai Tunanin Da ba"a so Sai yaRika Samun Matsugguni acikin Zuciyarsa ..Masu irin Laluransu suna Bukatar Wani a kusa Dashi a Koyaushe..Ba kamar yadda kuke Barinsa ya Wuni Shi kadai ba Hakan yakan Kara Haifar da Ruruwan Raunin Dayake Cikin Zuciyarsa..Abba yana Bukatar ya Riks Fitowa yana Sakewa yana Walwala,Ya Chanchanci yayi Farinciki..Duk Abunda Zai sakashi Farinciki Shi zAmu Rika Kokarin Yi agabansa muyi Keeping dinsa Yadda Tunani da Damuwa baza ma su samu Damar Nukurkusan sa ba..Kaga Ta hakane kadai Magungunan Likita Zai yi Amfani ajikinsa amfanin na Har Abada ba na dan Lokaci ba..! Tunda ta Fara mgana ya kafeta da Ido Zuciyarsa ta Cika da Farinciki Da Alfaharin Samun Macen Kirki kamar Safiya DAmam ance Duk Tunanin Namiji Ita mace Tamkar Garkuwa ce Garesa Gashi Cikin Lokaci Tana Warware Musu mtsalan da Shekara da Shekaru suka kasa mganceta. Girgizashi Tayi ganin yana ta Kallonta bai yi mgana ba tace"Bakace komai ba My Dear..? Yusuf ya Lumshe ido Kafin yace"Ina Jinki..Zuciyata ce ta Cika da Girma da alfaharin Zamowa Miji gareki Babe na..Ina jinki cigaba da Fadamin yadda komai Zai Tafi Wlh har na Fara Ganin Abba ya samu Lafiya na Har Abada..! Safiya tace"Insha Allahu Abba zai Samu Lafiya indai muka Taru muka Tallafamai..! Na farko Abba zai Daina Zaman Daki Zai kasance yana Wuni a Falo,sannan Zamu samo mai Abubuwan da zasu Debemai kewa kamar su Karatun azkar da karatun Karamin Qur"ani wanda Zai Rika Karantawa koda yaushe....Ko Jaridu Domin yarika karantawa yana Sanin Abunda Duniya take Ciki..Littafan Karatun Daya Shafi Fannin sa Wato Physchology,Abu na gaba kuma ya Daina Salla agida ya kasance yana Shiga Cikin mutane ko da bada Wata Mu"amala ba,Ya rika Sallar Cikin Jam"i hakan ma zai kara Taimakamai sosai Wajen Rage Damuwa da Tunani Sannan ya kamata Mu Rika Haduwa dukkanmu Da Daddare muyi Dinner Tare,Bayan mun gama kafin kowanne ya Shiga Barci mu Zauna dashi muyi Hira Labarai na ban Dariya wadanda Zasu Sanyashi Nishadi sannan kuma ya zama Dole ya rika ganin kowa Cikin Walwala ta hakane Shima zai yi kokarin manta komai sabi da ku..Masu irin Laluran Abba suna Bukatar taimakon Mutanen Dake kusa Dasu...! Bata gama mganarta ba tajita a Jikinsa Ya Rumgumeta Kamkam Kamae wani Zai kwaceta Cikin Farinciki yake Fadin"Tanque so Much Babe na..Allah yayi miki Albarka..U are a Bleesing From Allah..! Safiya itama ta saka Hannuwa ta Rumgumshi Tana Fadin"My Pleasure My Dear..Is My Duty Amtsayina na Matarka na Tallafeka a Dukkan Komai na al"amuranka Shine Zamantakewar..! Kamkameta Kawai ya karayi yana Fadin"Alhamdulillah..Allah ne Abun godiya..! Sun Dauki Tsawon Lokaci ahaka kafin ya Dagota yana Share Mata Guntun Hawayen Dake Idanunta Itama ta Saka Tattausan Hannunta ta Gogemai Nashi a Tare suka Sakarma Juna Mirmishi Hancinsu ya Hada Waje Daya yana Fadin"I love u Babe na..! Itama cikin Wani Shauki Tace"Love u More and More My Dear..! Komawa sukayi suka kwanta Bayan ya Dauketa Gabadayaanta ya Dorata Saman Jikinsa,Ya Kashe Musu Hasken Dakin Lokaci Daya ya ja musu Blanket yana Fadin"Oya Barci..Zamu karisa mganar dq Safe..! Tana Dariya tace"Ok..My Dear..! ***** Washegari Wasu Zukatan sun Tashi ba Dadi yayinda Wasu Zukatan suka Tashi Cikin Farincikin,Cikin Wadanda Suka kwana Cikin Bakinciki Imran ne Farko Kwata kwata Barci Barawo ne kadai ya iya sacesa Daya Runtse ido Sai ya rika ganin Inteesar Sanda Take Tofar da Miyau Lokaci Daya da. Toshe Hancinta In kuma ya yi Shuru kunnuwansa Amon Muryanta suke ji Inda Ta Kallesa Tana Kiramai Ta"awizi kamar Taga Shedan kwana Yayi Busa Sigari sai da ya karar da Kwalaye uku kana ya Saurara Gabadaya Bakincikin Yadda bai Sauyama Yarinyar nan kammani bane ya kamashi,Daya sani ko Mari ya Tsinketa Dashi ya Tattakata Wanda nan gaba bazata Kara Raina wani bama Shi ba,Ammh Takaichinsa Daya Da ya bari ta Subucemai ya Zama Dole ya Nemi Sagir ko wacece zai Santa Koma Daga ina take yana da Masaniyar komai ya Zama Dole ya Nemota ko domin yaci Ubanta ya Nuna Mata Karyanta Imran Ba wajen Wasanta bane. Bangaran Inteesar kuwa Tayi kwanan Farinciki Hankalinta kwance Tuni ta manta da wani Imran Ballatana Abunda ya Faru Daman koda Mama ta Dawo Ta gaji ta Fara jin Barci Sama Sama Sukayi mgana tace mata ta Shiga Makota ne,Daganan Ciki Ta Shige.Bayan Ta Tatarra Littafanta,Tayi Sallar Isha"i tabi Lafiyan Gado Barci ya Fara Daukanta Taji Mganar Sagir din nan Falon Mama Ita dai bata kara Samun kanta ba sai da asuba da Mama tasheta Sallah. Bayan ta idar da Sallar ne Tayi azkar ta Fita Tsakar gida Taga Mama na Shara ta gaisheta sai ta amshi Sharan Mama bata Hanata ba tunda Umma tace ta rika bata kowani aiki ne Saboda Ita Macece Domin amfanin kanta Watarana. Ita ta Share Tsakar gidan Tas ta koma ta Gyara Cikin Dakin da Falo ta Share ta Goge kafin ta gama Mama ta Dafa mata Ruwan Zafi sai ta Juye tayi Wanka Koda ta Fito 7:30am na Safe kuma ta Kira Classrep dinsu yace mata 8am suke da Lacture,Shiyasa Take Sauri Ko Tea da Buredin da mama ta Hadamata bata Tsaya Sha ba Complex Kadai ta sha..Sai Cake Data Diba ta saka ajaka ta Dauki Littafanta ta Fito Tana yima Mama Sallama ta Dauki Kudi ta bata taki amsa tace Tana da Kudi a Hanunta Jin Haka yasa Mama Ta kyaleta ammh Sai ta Buga ma Sagir Kofa tace ya Fito ya Raka Intee ta samu abun Hawa Zuwa makaranta. Haka kuwa akayi Shi ya Rakata Har Bakin Titi suna Tafe suna Hira sai da ta Samu Abun Hawa Zuwa Cikin makaranta Sannan ya Dawo yayi wanka ya karya ya Fita Zuwa Shago yau bai da Shiga makaranta sai Gobe. Bangaransu Yusuf da Amaryansa Safiya Lafiya kalau suka Tashi Cikin Farinciki ba domin ya Hanata Fitowa da Wuri ba da Tun Safe taso ta Fita Kitchen Ta Taya Munari Hada Breakfast,yusuf ya hanata sai dai ta Tayashi Shirya wa zai tafi Wajen aiki Domin ya Sanar da yayi aure ko Zai Samu koda Hutun Sati Daya ne..Dukkansu sunyi wanka Safiya ta Shirya Cikin Daya Daga Cikin kayanta na Gida,Shi kuma Yusuf yana Sanye da kananun kaya ne,Sun Fito Falon kenan Sukaci karo da Munari ta Fito Daga Dakin Abba itama Cikin Shirin Fita Tana ganinsu ta Washe baki Tana Fadin"Mr and Mrs Yusuf Abubakar Malami.. Gud Mrning..! Tafada Tana yar Dariya Yusuf ya Kalleta Lokaci Daya yana Lakuce mata yacw"Mrning How was ur Nite..? Safiya tace"Lilsisy kin Tashi Lafiya..? Munari tace"Lafiya Lau Anty Safiya..Ya yusuf Yanzu Abba ke Tambayanku..! Yusuf yace"yanzu Wajensa Zamu Shiga..ya karya..? Kai ta gyada mai kafin tace"Eh yau kunun Gyada nayi mana Sai na Soya Dankali..Yanzu na gama bashi yasha na bashi mgani Sauri nake tayi Yaya Zan Shiga makaranta 8am muke da Karatu..!. Yusuf yace"Sannu da kokari..Bazaki jirani na Sauke ki ba..? Agogon Fatan Dake Hannunta Ta Kallah Kafin tace"A"a Ya Yusuf bari na Tafi in na Tsaya jiranka Zan makara..! Bai mata Musu ba ya Ciro 1k Cikin Aljihun Wandonsa ya Mikamata yana Fadin"Take Care..! Ta karba Tana Fadin"Tanque Ya Yusuf..Anty Safiya Bye..!.Tafada Tana Daga mata Hannu,Hannun itama Safiyan ta Dagamata Tana Fadin"Sai kin Dawo ki kula da kanki..! Mirmishi Tayi musu kafin ta Fice su kuma suka Shiga Dakin Abba suka Iskeshi yana Zaune kan gado yana Tunani Kasa suka Zauna suka Gaisheshi ya amsa yana Saka musu albakar. Yusuf ya Kalli Abba yana Fadin"Ya karfin Jikin Abba..?Hope dai ba Wata Mtsala..! Abba ya Girgizq kai kafin yace"Ina Samun Sauki..!. Atare Shi da Safiya suka amsa da Allah ya kara Lafiya Kafin Yusuf ya Muskuta yana Fadama Abba Shawarwn da Safiya ta kawo Abba ya Dade kansa na Kasa kafin ya Dago ya Murmusa yana Fadin"Cikamakon Mutum Shine Samun Mace ta Gari...NAgode sosai yata..Kuma nayi Miki alkawarin Zan baki Kowani Hadin kai Domin Tamkar Munari nake kallonki..Sannan ni kaina Ina son na Warke Ko Domin na Koma ga Yan"uwana da Mahaifiyata..Itace araina Domin In har ina da Rai akwai Hakkinta Daya Rataya a Wuyana..! Yusuf ya kalli Safiya itama ta Kallesa suka Gyada kai atare Kan Safiya na kasa Tace"Insha Allahu Zaka Samu Lafiya Kamar baka Taba wannan Laluran ba. ! Abba yace"Allah ya amsa..!. Suka amsa da Ameen sun Dade Zaune Abba yana ta Tambayan Safiya matakin Karatunta Tana Fadamai sai ga Abba na Hirar Karatu da Safiya Data gayamai Fannin Data Karanta yake Fadamata abaya Daman yace in bai Zama Malami ba zai zama Masanin Na"ura ne . Sai ga Yusuf Farinciki yaki barinsa Ransa Har sukayi ma Abba Sallama suka Fice,Su Biyu Suka yi Breakfast Saman Dining sunayi suna Hira Bayan Sun gama Safiya ta Rakashi Har Haraban gidan bata koma ba sai da Taga Fitar sa Daga Gidan kana ta Koma Cikin Gidan. Dakin Barcinsu ta koma ta gyara Shi Tsaf kana ta koma ta Tatttara Abunda suka Bata Daga Dining zuwa Kitchen Tana ganin yanayin Kitchen din bai Wani Samun gyara Saboda Munari ce Ita kadai kuma Saboda makaranta Bata Samun Lokacin kanta Ballatana ta Tsabtace Kitchen din Ga kwanukan Wanke wanke nan Kamar sun fi na kwana Biyu Munari bata samu Damar wankewa ba,Nan Safiya ta Zage ta wanke komai ta maidaahi a Muhallinsa,Ta kuma Share Kitchen din ta Gogeshi Tas ya Fara Kyalli,Ta leka Store Taga akwai komai na Bukatar Girki na Gidan Masu Rufin asiri Ta gyara Store din Shima ta Duba Fridge Shima Shake da Abubuwan amfani bata san Sadda tace Masha Allah ba Domin Komai akwai Babu Abunda kuma Zata Nema Yusuf bai waasa da Cefane Duk Sati,Tasio tamai mganar Cefanen sai Kuma Ta fasa Domin bata san yasan Zata Fara Girki yau din ta tabbata Zai Hanatane.. Bayan ta gama da Kitchen din ta Fito Falo Shima ta gyarashi ta Dauko Abun Shara ta Share ta goge ko"ina Haushinta Daya ko Dan Turaran Wuta Bata Dashi,Sai taji kamar Tayi kuka Sai kuma ta Daure,Ammh Zata Fadama Mommy Abubuwan Data keso Ta Siyamata in sunje da yusuf Sai Ta Taho Daahi kafin Abubuwa su Daidaita. Daki ta koma ta Dauki Wayarta Da Niyar Kiran Mommy sai kuma Taga Kiranta sai Tabi Bayan kiran Har ta kusa Katsewa Kana Mommy ta Dauka Suka Gaisa Safiya tace"Mommy ina Falo ne na bar wayar a daki nazo Naga Kiran ki.. ! Mommy tace"Tasleem ce ta kiraki..Sai da na Hanata..Yanzu kuma Direba ya tafi kaita Makaranta..! Safiya tace"Allah Sarki Tasleem..! Mommy tace"Da kinga bazaki iya Zama ba Safiya ki kirani kinji ko Ni Dakaina Zan zo na Tafi Dake..! Safiya tace"Bafa komai Mommy..! Mommy ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Shikenan nima yau Zan je gida na Gayama su Baba abunda ya Faru Bazqn iya Kyale Mahaifinku ba Safiya Kada ya ga yayi yaji Dadi ya maimaita akan Tasleem kuma..! Safiya tayi Shuru kafin tace"Kiyi Hakuri Mommy..! Mommy tace"Sai na Dauki mataki..Kiyi ma Shuru Kawai..ya mganar Kayan Daki da abubuwan Da kike so ki Rubutomin komai ta Waya ki Turomin Fatana ya Tanadi Muhallin da Zamu saka Miki kayan Duk ga yadda Auran ya kasance..! Safiya sai ta Kasa cema Mommy Yusuf yace a barshi sai kawai tace Mata"Kibari nazo Mommy Zamu yi mgana..Domin yace in aka kwana Biyu Zamu zo mu Gaisheku..! Mommy tace"Shikenan..! Daga Haka sukayi Sallama Daganan bata zauna ba ta Fita Zuwa Falo Bayan ta Duba Lokaci 9am ta kusa ya kamata ta Shiga ta Duba Abba koda ta Shiga Sai Taga baya Dakin Data Saurara sai taji karar Ruwa yana Wanka kenan sai ta Fito Falo Ta Zauna tana jira Shuru ita Kadai ga Tv ammh kuma da alamu ma ba"a Taba Hadata ba,Batayi mamaki ba ammh Zata Saka Yusuf ya Hadata Saboda Shima kallon yana Rage Damuwa ko da Tashar Wa"azi ce tafi a rika Zama Shuru. Sai da ta Kwashe Minti Talatin Kana ta koma Dakin Abba ta iske shi tsaye yana Saka Botirin rigar Shaddar Dake Jikinsa Sai dai Bai saka Wandon Shaddar ba Wata ya saka yayi gamin Gambiza kenan. Tana Shigowa da Sallama ya Waigo yana amsa mata Cikin Sakin Fuska. Kanta na kasa Tace"Barka da Hutawa Abba..! Abba yace"Yauwa yata..Sai dai Gidan Duk ba kowa sub barki ke kadai ko..? Sai Imurana Kuma Dashi ba Babu Duk Daya na Tabbata har yanzu bai fiti ba..! Safiya tace"La bakomai Abba..Dama na Shigo na Dubaka ne..Nace ko Zaka Fito Falo yau ka Huta Kafin anjuma..!? Abba ya Murmusa Kafin Yace"Nagode yata..Naji Dadin hakan ni kaina Nagaji da Zama Waje Daya muje..! Kanta ta Sadda kasa kafin Tace"Amh..Abba Kayan ba iri Daya bane. ! Sai da ta Fada ya Duba ya ganu kai kawai ya Girgiza Kafin yace"Kinga ba Domin kin yi mgana ban Ma Lura ba..! Bata Damu ba tace"Bakomai Abba...In ba Damuwa bari na Duba maka wandon Rigar ko..! Yace"Yauwa to Dubomin ni Duk idona ma ya Cinye Saboda Rashin Ganin Hasken Waje..! Tana Bude Wardrope din Tace"Zai Washe Da yardan Allah Abba..! Cikin Farimciki yace Allah, yasa bata Wahala ba ta gano Wando ta Daukomai ya karba Sai ita kuma ta Fice Bayan ta Daukan mai Matashi,Falo ta koma ta Sakamai Matashin Saman kujera mai Cin Mutum Biyu,ta Shiga Kitchen ta Daukomai Ruwa da Kofi tazo ta Jawo Karamin Table zuwa gaban Kujera Ta rasa Ma Zata Dauko ma Abba ya Daukemai Hankali Sai ta Tuna Taga karamin Qur"ani acikin Dirowar Yuauf da Sauri taje ta Dauko Ta yanke Shawaran Zata kira Yusuf yazo da Jaridun Datayimai mgana Jiya. Tana Fitowa Abba Shima na Fitowa Mirmishi yayi mata itama ta maidamai Yau Rana Daya yana jin kansa Kamar bashi ba,Bai Taba Fitowa ya Zauna afalon nan ba Tun Dawowarsu Gidan koda yaushe yana Cikin Daki in baya kwance yana Zaune yana Tunani. Sai da ya Zauna kana ya Rika sakama Safiya albarka tana amsawa ta Tsiyayamai Ruwa ta mikamai yasha Kadan ya Miko mata Tana Karba Tana Fadim"Abba badai kajin Barci ko..? Abba yace"Gaskiya yau ban ji Barci ba..Ko Saboda na baro Katifar Dake Rinjayana Barcin ne..? Ya karishe Cikin Zolaya Kanta ta Sunkuyar Tana Mirmishi sai ta Mikamai karamin Qur"anin Tana Fadin"Kada ka Zauna Shuru Abba..Saboda Tunani marasa kyau..Ka karanta iya Abunda ya Sauwaka Zan kira Yusuf nacemai ya Taho Maka da Jaridu ka Rika karantawa kana Sanin Abunda Duniya take ciki..! Abba ya saka Hannu Biyu ya karba Hawaye sun kawo Idanuwansa yace"Barkallahu Fiki..Nagode..! Yafada yana jin Rauni ya bayyanamai Domin bazai iya Tuna Ranar Karshe Daya yi Karatu ba Lalle Mace agida Shine gida Matukar Bata kuwa sai a Hankali. Gefw ta koma ta Zauna akasan Cafet Abba yayi ta koma Kujera Taki sai ya Kyaleta Bude Qur"anin yayi ya Faraa Dubawa,Duk da Raunin Idanuwansa sukayi Qur"ani na Dabam ne,Ballatana ai yana da Hadda akansa nan da nan ya Bude Suratul Yusuf ya Fara Karantawa a Hankali Safiya na gefe Tana Kallonsa Cikin Tsausayi ganin Lokaci Bayan Lokaci yana Share Kwallar da suke Cikamai ido.. Acikin Wannan Halin Imran ya Fito Daga Dakinsa Sanye da Jallabiya baka,daga alamu kuma Tashinsa keman Sigarin sa ne ya kare,Sannan kuma Dole yaga Sagir Domin yagayamai Yar gidan Wacece Wannan Mara Mutumcin yarinyar,Sai kuma Fitowarsa yaci karo da Abun mamaki Abba ne Zaune afalo yana Karatu.? Gani yayi kamqr bai gani Daidai ba Sau ya kara Matsowa yana Mutsike Idanuwansa Still Dai Abu Daya yake gani Safiya ce ta Ganshi Da Sauri Tace"Ina kwana..! Sai alokacin ya ganta Kallo Daya yayi nata ya kauda kai Shi ai bacin Ran Daya Kwana Daahi Jiya yasa yama manta da Yusuf da wata Amaryansa ma,asaman Lebensa ya amsa mata da Lafiya lau,Kusa da Abba ya Karisa ya Zauna yana kallonsa ganin haka yasa Abba ya Dakata da Karatun ya Dago yana Kallonsa Imran Cikin Mamaki yace"Abba ...Abba Kai ne..!? Abba ya Murmusa kafin yace"Na"am..Nine Imran..! Yafada Lokaci Daya yana Dafa Kafadansa Saboda Murna Imran baisa Sadda ya Rumgumesa ba yana Fadin"Plz Abba..Come Back..We Need Dr.Abubukar Malami Back..Wanda Ke Tsaye Ga kafafunsa Saboda Ahalinsa ba Abubakar Malami ba Wanda Ya koma Yusud da Imran ne masu Kula Dashi ba..! Abba ya Murmusa kafin ya Buga Bayan Imran alamun Lallashi Lokaci Daya ya Dagosa yana Fadin"Insha Allahu..komai Zai Zama Tarihi Tunda My Son yayi Dacen Samun Mace Tagari..ita tace na Fito Falo na Huta ta kuma Bani Qur"ani tace nayi Karatu..! Abba ya Fada yana Nuna Safiya da kanta ke kasa..! Imran ya murmusa kafin ya Mike yana Fadin"She do alot to us..Tanque so Much..! Batace komai ba sai ta murmusa aranta Tana Tuna Hirarsu da Munari. Abba ya kallah Kafin yace"Abba ka Cigaba da Karatunka..Bari na Je nan kasa Wajen Sagir..! Abba ya gyada kai kafin yace"Sannan kuma Zaka Siyo Sigari ko..!? Imran ya Waigo yana kallon Abba Kamar bazai ce komai ba sai kuma yace"Eh Abba..Ammh Zan yi kokarin na Rage shanta Saboda kai..! Abba ya girgiza kai yace"Imran...Imran To Nagode..! Bai kara mgana ba ya sakai ya Fice Daga Safiya Har Abba suka Bisa da kallo Abba yana kallota yana Fadin"Ni na Haifeshi ammh Wani Lokacin yana Matukar min kwarjini..Rashin Tsoronsa da Gaskiyansa Wani Lokacin Suna kara Sakani naji yana Burgeni da shiga raina..! Safiya Batayi mamaki ba Tunda Munari ta gayamata Yusuf ma ya mata Bayani Abba bai nemi Jin ta bakinta ba yace"Allah ka kara Shiryamin ya"yana..! Safiya ta amsa da Ameen acikin Ranta Shi kuma Abba ya Cigaba da Karatunsa Yana jin Wata Natsuwa na Shigarsa Natsuwarsa da Tun Bayan Rasuwar su Anni bai kara Samun irinta ba sai yau. *Ina godiya Masoyana da Tarin kaunarku ga wannan Labarin Allah ya saka da alheri WhatApps fans dina Duka ina ganin Sharhinku ina kuma Godiya sai yan Wattpadian Kuma ina ganin Voting dinku da Comments dinku ina Matukar godiya Allah ya saka da alheri Allah kuma ya bar Zumunci Ameen..* *Shakira...* 3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*       *🅿�15* "Da kafarsa ya gangara zuwa Gidansu Sagir din Bai tsaya ma Daukan Mashin Din nashi ba domin kwana Biyu yafi jin dadin Tafiya da kafarsa fiye da ko yaushe,kwana Biyu bai Fita Jogging ba yana jin Jikinsa wani iri Shiyasa yake Treeking da kafarsa Wani Lokacin. Sai da yazo Kofar gidansu Sagir din yaja ya tsaya,Kuma ya leka Shagon ya Hangi Sagir kan keke yana ta Dinki Hankalinsa na kan Abunda yake yi,Bai ma Lura Da masu Shigowa da masu fita ba yau Dagashi sai Yaronsa Daya Sauran basu Riga sun zo ba shine ma yaga Lekowan Imran din ganin ya koma Shiyasa baima Sagir din mgana ba. Waya Imran ya Lalubo Cikin Aljihun Jallabiyansa ya Lalubo Lambar Sagir ya Dokamai kira yana Tsaka Da Dinki Wayarsa Dake ajiye gefensa ta Dauki Neman agaji Ta Wutsiyar ido ya Juya yaga mai kiran Imran ne bai Daga ba Sai da yakai karshen Inda ya Fara Dinkawa kana ya dakata ya Daga Kiran Yana Fadin"Ya akayi ne..? Imran Dake waje yace"Bansani ba..Mallam ka Fito gani a Kofar Shagon ka..! Sagir ya Dakuna Fuska kamar Imran na Ganinsa yace"To kai meye ya Hanaka Shigowa..? Ka Shigo mana Ina Dinki ne ba Zaune nake ba kamar kai..! Imran yace"Ban ga Daman Shigowa bane..Kuma Dake min Gorin Zaman banza Ka samo min aikin yin ne kaga nace bazan yi ba..? Sagir Dayaji Haka ya Mike yana Fadin"Ta kwana Gidan Sauki Indai aiki ne Ina dashi..Bari na Fito..! Yafada Lokaci daya yana Katse Kiran Yaronsa yayi ma mgana kafin ya Fita ya Iske Imran din Tsaye ya Tusa Duka Hannayensa Cikin Aljihun Jallabiyansa Yana Jiransa yayi mamakin ganinsa yau baya Busa Hayaki Shiyasa yana Zuwa yace"yau Watarana Abokina yazo baya Shan Sigari..? Imran ya kallesa kamar bazai yi mgana ba sai Chan yace"Zan Busata kuwa..Ta karemin ne jiya Cikin Dare..Yanzu kafin na Shiga Gida Zan Siya..! Sagir ya kada kai kafin yace"Don Allah Ka Daina Shan Sigari..Wlh Sam Shanta bai Dace Dakai ba ko alama..!. Batare Daya Kallesa ba yace"Daman masu Shanta din ta Dace dasu ne..? Sagir yace"Eh gsakiya Majority din masu Shanta Zaka ga sun Dace da Shanta Din ammh kai Fa kalleka Daga Sama Har kasa Duk da bansan komai akan ka ba na Tabbata kayi Ilimi mai Zurfi Tundaga na Zamani har na Boko Wanda bai ma Zauna Dakai ba Zai Fahimci U are a Luky Ballatana ni da na sanka Gaskiya Shan Sigari bata Dace Dakai ba Abokina Don Allah ka Daina Shanta Sam bana jin Dadi..Kalli bakin ka Har ya Fara Baki..! Imran yayi Shuru yana kallon Sagir Allah Sarki zai Rage shan Sigari ko Domin Abba da Sagir sun Damu Dashi kwarai Kuma Shi Mutun ne Da baya Juyama masu kaunarsa Baya Kota Halin Kaka sai ya Rama musu Alherinsu gareshi..! Ganin yayi Shuru yasa Sagir ya Dafa Kafadarsa yana Fadin'Kayi hakuri in mgana ta bata maka rai..Ina son Naga rayuwarka Ta Dawo Tamkar yadda kowa ke Rayuwa ne..Am sorry..! Imran ya Saki Mirmishinsa kafin yace"Bakamin komai ba..Zan yi kokari na Rage shanta ko Saboda kai da Abba..Ku din wasu Mutane ne masu Muhimmanci a Rayuwata bazan bari Rashin jina da Taurin kai na ya Bata Muku Rai ba..Ammh kasan sai a Hankali..Kamar yadda na Koyi Shanta Rana Tsaka Haka zan zo Rana Tsaka Kaga na Daina Shanta kwakwata..!. Cikin Farinciki Sagir yace"kai naji Dadi..Allah ya amsa..Ammh wai a ina ka Koyi iya Shanta ne..? Kwarewarka fa yasa na Fara Tunanin Any ba Kwalejin masu Shan Sigarin ka Shiga ka Samu Kwarewa ba..? Wannan karan Sai da Fararan Hakoransa suka Bayyana Saboda Dariya Wanda ba kasafai ake ganinsu ba Dukan Kafadan Sagir yayi yana Fadin"Ashe kai Dan iska ne..? Sagir na Dariya yace"Yaushe na Tashi Daga Banzan..? Imran yace"Duka kai ne...ga ka Banza ga ka D'an Iska Daman ai Telan Mata ai Dan iska ne..! Sagir ya Harareshi yace"Haka Dai Kace..Miya Hada Telan mata da Iskanci..! Imran yace"Baka na Gwadasu ba..Ranar fa ina ganinka Kasa Abun gwajinka kana gwada wata yarinya..! Ya karishe Fada Cikin Zolaya Lokaci Daya kuma Fadin yarinyar Dayayi sai ya Tuna da Abunda ya kawosa nan da nan ya Hade rai Shi Sagir bai ma Lura ba Dariya ya Kwashe Dashi yana Fadin"Ashe Shurun Shurun nan naka Mugun Dan saka ido ne kai a Fakaice..Wlh bana Gwada kowacce Mace sai dai ki kawo Measurement dinki,Wacce kaganta Yaro na ne yake Gwadata bani ba ta mtsa sai an gwadata ne ammh Ni kowa ya sani bana Gwada mace Saboda Kiyaye Addini da Mutumcina..! Imran bai cemai komai ganin haka yasa ya Dagi kafadansa yana Fadin"Yauwa kace na sama maka aiki ko..? Kai Tsaye Imran Daya Kagara mganar ta Kare yace"Eh..! Sagir yaji Dadi nan da nan yace"To kazo na samar maka aikin yi..Kazo zan Koyamaka Daukan Measurement Din Duk Macen Data Dake son sai an Gwadata ga Measurement Imran nan bata da Damuwa..! Wani Kallo ya Jefama Sagir kafin yace"Kutumar Uba ne..Wlh nafi karfin Wata mace ta Tsaya na gwadata..Baka Tashi bani aikin ba indai hakane..! Sagir na Dariya yace"Da gaske kake kenan..? To kazo Gobe sai muga da Abunda Zamu Fara Ni dai kaga Wajen Sana"ata Dinki ne kuma Alhamdulillah Dashi Nake Rufama Kaina asiri Da Mama..! Imran ya Kada kai kafin"Dakyau..! Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan Imran yace"Who is She..? Sagir yaji kamar bai jisa ba Cikin mamaki yace"She naji kace..wa..?ita wacce Zaka fara gwajin a kanta..!? Karamin Tsaki Imran Yaja kafin yace"Kai fa Banza ne..Wannan Yarinyar ta Jiya Data Kalleni ta Kiramin Tsarin Shedan sannan ta Toshemin Hanci ta Tofar da Miyau Don Ubanta Wari nake ko kuwa Tsabar Raini ne ko Wulakanci..!? Sagir daya Manta da Abunda ya Faru Tsakaninsu da Inteesar Jiya sai yanzu da Imran din ya Tunamai gabansa ya Fadi Cikin Mamaki yace"Wai Daman baka manta ba..? Imran ya kara Hade Ransa yana Fadin"Ta ina Zan manta..? Aini bana manta Cin fuska ko Raini..Ni Imran ba Wanda mace Karama irin wannan yarinyar Zata Raina bane..Ka Fadamin Wata Mara Mutumcin ce So nake na Koyamata Hankali in ta Takamarta Rashin kunya Nine Zan Gyara mata Zama..!Kila Cikin yan iskan matan nan ne masu Zuwa kawo Maka Dinki ko..? Sagir Yayi Saurin Cewa"A"a Wlh..Don Allah kayi Hakuri Bata sani bane..Kuma Bata san Warin Sigari ne baka gani ba..Wlh sai da Tayi amai fa..! Shekeke Imran yake kallonsa kafin yace"Oh Daman Duk kana Sane da Abunda ya Faru kenan..? Sagir yace"Eh Nidai Sorry on Behalf on Her..Kanwatace fa..Diyar kanwar Mama ce Inna Salaha ta Kaduna Shekaranjiya iyayenta suka Kawota Wajen Mama suka Damka Amanarta awajenta Karatu Ta Fara nan Jami"ar Bayero.! Kamar Imran bazai yi mgana ba sai Chan yace"Naji Dadin cewa ma kanwarka Ce..Zan fi Cimata Mutumci Dakyau..Ai ni Yayanta don Ubanta Kuma ka Fadamata Kada ta yarda mu Hadu Duk Ranar da muka Hadu sai na Toshe Bakinta na Dura mata Hayakin Sigarin sai na Tabbatar Daya Shiga Cikinta,In Aman kayan Cikinta Zatayi Sai dai Tayi..Hukuncin Toshe Hanci Agaban Imran kenan..! Yana Gama Fadin haka ya Wuce ya Fara Tafiya Cikin Sassafarsa Na koda Yaushe Sagir ya saki baki yana Kallonsa Kafin ya Sauke Numfashi yana Fadin"Inteesar Ta Taro ma kanta Macth bata da yan wasa..Kayyasa..! Daga haka ya juya ya koma Cikin Shagosa ya Tuna Yadda Imran ya Tsani yana Shan Sigari a toshemai Hanci ko Dashi ne sai sun Hau Sama sun Fado Koma miye bazai bari ma Su Kara Haduwa da Inteesar ba yasan Halin Imran bai da Mantuwa Akan Abunda akayimai. Koda Imran ya koma Gida ya Iske Abba ya Gama Karatun Qur"anin suna ta Hira da Safiya kamar sun Shekara da Haduwa yana ta Bata Labarin Yanayin Jami"ar Lagos da yanayin Karatunsa Dayake suna Hira ne kan Jami"o"i Bai ce musu komai ba ya Shige Dakinsa Ammh Tabbas yana Cikin Farimcikin ganin Abba ahaka kan gado ya zauna afili yana Fadin"Abba ba Mahaukaci bane..Abba da Hankalinsa Baffa Kabiru..! Yafada Lokaci Daya yanajin Suyan Tuna Wasu kalaman da akan Jefe Abbansu dashi na kalmar Mahaukaci. Wanka ya Shiga bayan ya Fito ya Shafamai Ya saka wani karamin Wando bai ko Saka riga ba,Ya Hau gado yan jin Zuciyarsa Ta Danyi Sanyi Tunda yabama Sagir Sako ya Tabbata kuma Zai gargadeta Bai damu da yadda suke ba Shi Raini ne baya so kuma Ko Munari ce tamai Haukan nan Sai ta gane bata da wayau ballatana Wata Chan Dabam Yayi alkawarin sai ya koyamata Hankali,Ya gama Lura Rashin kunya ce da Iyayi na yaran da suka Shiga Jami"a ba Bayero take ba Ko Duka Jami"ar Duniyace akanta Tunda ta Shiga Gonarsa He will Teach Her a Lesson a Big lesson din da Bazata manta ba. Saboda bacin rai ma yasa ya manta bai Siyo sigarin sa ba Tsaki kuwa yajasa yafi a kirga saboda Haushi. Safiya kuwa suna Cikin Hira da Abba Barci ya kwasheshi sai ta Kyaleshi ya Huta Daman barcin yana da kyau Sai ta Fada Kitchen taga Abunda Zata Dafa ta iske Nikakken kayan Miya a Cikin Fridge sai ta Dauko tace bari Tayi White rice da Miyar Kaza Tunda Taga akwai kazan Har da Ganyen Kabeji,nan da nan ta kunna Gas Din Duka Guda Biyu ta Dauko Tukunyar ta Fara aiki Cikin Natsuwa da Kwarewa aranta Tana Sakama Mommy Albarka Data Koyamata Aikim mata da yau Da aure ya kawota Wannan Ahalin da suke Bukatar Taimakonta bata san yadda Zatayi ba. Tana Cikin Aikin ne Taji Abba na kiranta da Sauri ta Dauraye Hannayenta ta Fito Tana amsawa Abba ya Kalleta Lokacin Daya mike Zaune yana Fadin"Barci ne ashe ya Kwasheni.? Safiya tace"Eh Abba..Nace ai gwara ka Huta Saboda mgungunka ne Akwai na Barci..! Abba ya kalleta kafin yace"Badai wani aikin kike ba Daugther...? Safiya ta Dukar Dakai tana Fadin"Ba wani aiki bane Abba abiincin da Za"aci nake Dafawa Munari taje makaranta In ta Dawo ta gaji kuma Ai Zaka ta zama da yunwa ne kai da kake Shan mgunguna..! Abba ya Girgiza kai yana Fadin"A"a gaskiya Dana sani bazan bari kiyi wani aiki ba..Jiya fa aka kawoki gida nan..Sam bai kamata ba Da baki Damu Dani ba ko Tea sai ki bani nasha..Nasan yusuf bazai shigo hakanan ba..! Mirmishi kawai tayi tace"Bakomai Abba..Miye amfanina na..? Indai ka Daukeni Tamkar Munari to ka samun Albaeka kawai..! Cikin kada kai yace"Shikenan Daugther Allah yayi miki Albarka Allah ya jikanki Kamar yadda kike jin kaina..! Cike da Farinciiki ta amsa da Ameen Kafin tace"Bari na koma na karisa Abba..! Ya amsa mata da To shikenan afito Lafiya,Cikin Sauri ta koma ta Cigaba da aikinta Cikin Kwarewa. Cikin Lokaci ta kamallah Daidai Lokacin Dataji ana ta kiran Sallar Azahar Aranta ta kudiri Niyyar Dawo da Farincikin wannan Ahalin,Ta Lura Daga Yusuf din Har Imran din ba wanda ke Zuwa Masallaci Bin Jam"i,Da sun Shigo Shikenan Ballatana su Rika Tafiya da Abba Gaskiya Hakan bai kamata ba,Suna Musulmai Ya zama Wajibi su Rika Sallar Cikin Jam"i Zata Gayama Yusuf Gasikiya su gyara Sallarsu. Sai da ta kamallah komai ta Juye komai a Flask,ta yanka Ganyen sai dai Bata Hada ba ta bari sai Zuwa anjuma,bata bar Kitchen din ba sai da Ta Goge komai sai Ta Fito Taga Abba Baya Falo Kila ya Shiga Ciki yayi alwala ne itama sai ta Shiga Daki ta Fada Tiolet Tayi wanka Saboda Girkin Datayi Tazo ta Sauya kaya Dole zata gayama Mommy A hada mata kayanta Waje Daya in sukaje ita da Yusuf Zata Taho da Abunta wata Doguwar Riga ta Samu ta saka Kirar Armani ta Saka Mayafinta Ta Tada Sallah Tana Cikin Sallar ne taji Abba na Knooking Din Kofa Lokaci Daya yana Kiran sunan Imran Tanaji yazo ya Bude Abba na Mgana bataji me yake Fade ba sai taji Abba na Buga mata Kofa Lokacin ta Sallame sai tazo ta Bude Abba ta Gani Harda Hulansa da Casbaha yayi mata Mirmishi yana Fadin"Daugther na taso Imran nace ya Rakani Massalaci Shima mu Fara Salla Cikin Jam"i Kamar yadda kikace..! Safiya ta Fadada Mirmishinta kafin Tace"Ka kyauta Abba..Adawo Lafiya..! Tafada Tana Hangen Imran Din Daya Sanya Wata riga sai dai ya Sauya Wando Dogo ya Sanyo karo na Farko da Abba zai Fita da Kafarsa Tun Bayan Dawowaarsu kano gwarama Imran yana Tsayawa masallacin kusa da Gidansu Sagir yayi Sallah in dai yana Waje in ya Shigo kuma Shikenan Ammh yau da Abba ya Bukaci Haka sai yaji Shima Zakwadin Abun Acikin Ransa ya kuma Kuduri Niyyar Daga yau Dagashi Har Abba da Yusuf indai suna Gida Masallacin Kusa da Gidan su Sagir zasu Rika zuwa Sallah acikon Ransa yana Kara Taya Yusuf Murna Na Samun mace irin Safiya aransa yana Ayyana Bata Dauko halin Tsohon najadun uban ta ba. Har suka Fice Bakin Safiya yaki rufuwa Waya ta Dauka zata Kira Yusuf Saima taga Kiransa Da yawa ya Kirata Kila Tana Kitchen ne,Nan da nan tabi bayan kiran sai dai bai Daga ba sai ta kyakeshi sai Zuwa Chan ya Kirata ta Daga Cikin Farinciki yana ma Tambayanta ina ta Shigene ita kuma Saboda Murna tana Fadamai Abba yau ya Fita masallaci Shi da Imran Yusuf Yana Office dinsa kenan Shima Dawowarsa Daga masallacin Ma"aikatansu kenan yakai goshinsa kasa yana Jeromaa Allah Godiya Farinciki Sai da yayi kwallah yama kasa Mgana Cikin Muryan Sanyi da Farinciki yake Fadin"Tanque...Tanque so Much Babe na..Allah yayi miki albarka Shigowarki Gidanmu Haske ne..Daga yau kin tashi Daga Babe na kin Koma Noor! Cikin jin Dadi tace"Nagode My Dear..In zaka Dawo ka Taho da Jaridun da Littafan da mukayi mgana..! Yace"Insha Allahu..Mai zan Taho Miki Dashi..? Da Sauri tace"Bana Bukatar komai Illah Son ganin ka Dawo Cikin Koshin Lafiya..! Cikin Annuri yace"Shikenan Sai na Dawo Take Care Of Ur Self..Zan Taho muku da Abinci..! Da Sauri Safiya tace"Daga jiya kagama Siyan Abinci My Dear. bai samu ce mata komai ba Farinciki ya Cika ransa Daganan sukayi Sallama. Banganran Abba kuwa kamar Sabon Mutum haka ya koma yau ya Fita Waje yaga anguwan Dayake Rayuwa,,Iro megadi yasha mamaki ganin Imran da wani mai kama dashi da Yusuf Baki ya sake kawai Domin bai Taba Zaton akwai wani agidan ba Sai dai ko ba"a Fadamai ba zai iya Cewa Mahaifinsu Imran ne Daman suna da Uba..? Shifa ya Dauka Daga su Sai su acikin Gidan,Dayake Yusuf ne ya daukosa Gadi,Shima din Security din Ma"aikatansu ya ma mgana Shine ya Samo mai Iro,ba Saboda komai ba sai Saboda Abba suna Fita su barsa Shi kadai ga kuma Gida watarana Ake ji Tunda yanzu Mutune bana Allah. Abba ya bama Iro Hannu suka Gaisa Cikin Fara"a Ganin kallon da yake ma Abba ne yasa Abba yamai Bayani da kansa Mamaki ya Cika Iro Cikin mamakin yace"Ammh Ranka ya Dade Alhaji ban taba ganin ka Fito ba Tunda Nake agidan nan..? Abba ya Murmusa kafin yace"Eh ai Tun Dawormu bani Da Lafiya Likita ke Zuwa Gida yana Dubani..! Iro yace"Kwarai kuwa anyi Haka..Likita kuwa na zuwa Lokaci Bayan Lokaci Ai bansani bane Sannu Alhaji Allah ya kara Lafiya..! Abba ya amsa da Ameen Imran kuwa Gaba yaci yana Fadin"Abba an fa Tada Sallah..! Abba yabi bayansa yana Fadin"Mu zamu Tafi Masallaci..! Iro yabi su da adawo Lafiya har suka Fice yana mamaki da Karin Al"ajabi A fili ya Furta"To wannan wani irin Cuta ce ashe Mutum Fin Shekarq bai Taba Fita ba..? Kuma naga Kafarsa Lafiya lau Oh..Ni iro..! Haka yayi ta Fadi mamaki dai yaki Barinsa. Haka achan masallaci ma Bayan an Idar da Sallah Sagir yaga Abba da Imran Daga Baya Dayake da suka Zo an Tada salla har anyi Raka"a Daya sai suka Tsaya Baya Tunda gaban ya Cika Bayan an idar suka Rama Sallar Farkon Abba na Zaume Bakinsa yaki Rufuwa sai da ya Share kwallah Mutane kuwa basu Damu ba Duk da basu Taba ganinsa ba suna Tunanin baki ne a anguwan Tunda ai Gari da Yawa Sagir ne har Zai Fice yaga Imran sai Chan yaga Abba Cikin mamaki yazo ya gaida Abba ya amsa mai Cikin Sakin Fuska Yana Fadin"Sagir ko..? Sagir ya gyada kai Abba yace"Mu je Wajen masallaci..! Mikewa sukayi suka Fice Abba kuma ya Tsaya gaisawa da wasu Daga Cikim Masallacin Sukuma suka Fita Waje Sagir ya kallesa yana Fadin"Abba ya samu Lafiya har ya Fara Zuwa masallaci..Na tayaku Murna Abokina..! Imran ya jinjina kai batare Da yayi mgana ba sai ga Abba ya Fito suka kara gaisawa da Sagir,yana Tambayan Mama yace ya gaisheta,Tare suka Jero har Zuwa Bakin gidansu Sagir din ganin ya Tsayane yasa Abba ya Tambayeshi nan ne gidansu yace Sagir din ya nuna mai Shagosa Abba ya saka albarka Daganan sukayi Sallama ya koma Shagonsa Cikin Mamaki acikin Ransa yaji Dadi Sosai. Safiya na Jera Flaks,kan Dinnig Su Abba suka Shigo da Fara"anta Tayi musu Maraba Imran dai Bai ko kalleta ba ya nufi Hanyar Dakinsa sai yaji Tace"Arm nace ba..! Ya juyo yana kallonta Tacigaba da Fadin"Nace ga abincin fa..! Imran ya kalleta kafin yace"ke kikayi Girki da kanki..? Mirmishi Tayi batace komai ba Abba Dake Zaune yace"Ni kaina sai da na Hanata ta Dage sai tayi..! Imran bai ce komai ba bayaso yayi mata gaddama Saboda karamcinta sai ya Kada kai yace"Later Zan ci..! Kai ta kada mai Shikuma ya Shige Dakinsa Shirya komai tayi kan Dinning din Harsu Filet sai da ta Jera Ta je gaban Abba ta Durkusa Tace mai ga Abinci chan Abba ya rasa bakin mgana sai saka mata albarka yake karon Farko Daya Taba Zaman Dinning,ba kan gadonsa yaci Abinci ba Ita Safiya ita ta Yi Serving Dinsa ta Hadamai Cowslow daidai wanda Zai ci,Ta Daukomai Ruwa da Lemo Zata Tafi yace ta Zauna itama ta Zuba taci Duk da tanajin kunya ta kasa ma Abba Gardama Dole ta Zauna itama taci Sosai Abba yaci Abincin Sosai acikin Ransa yana sakama Safiya albarka. Ranar Wuni yayi afalo Salla kadai ke Tadashi Safiya na Tare dashi suna Hira Kamar sun saba. Yana bata Labarin Kazar kazar dinta kamar Asma"u Safiya Taji Rauni ya kamata ganin Abba na kuka ita Tayi ta Lallashinsa Tana kara Numamai Mutuwa ta Allah ce addu"a kadai suke Bukata,Abba ya Share Hawaye yace"Hakane Daugther Allah yayi miki albarka..! Daga yau Addu"a ne Tsakanina da Matata da ya"yana Allah ya jikansu..! Safiya ta amsa da Ameen. Sai yamma Munari ta Dawo itama ganin Abba haka yasata Farinciki taRumgumesa Tana Murna ya gayamata yau Har Fita yayi Yaje masallaci,Kuma Duk Sanadin Safiya Munari ta Rumgume Safiya Tana Fadin"Thank u Bhabi..! Munari bakinta yaki rufuwa ganin Dinnig Da kololi Shake da Girki ta Buga Tsalle Saboda Murna Abba nata Dariya sai kuma tarufe baki Sanin Halin ya Imu kada ya jita kuma ya jitan bai dai Fito ba Tsaki yaja acikin Ransa yace"nonsesss..! Sai da taci ta Koshi Tana Santi Daganan Munari ta jata Dakinta,Suka Zauna suna ta Fira tana ta Bata Labarin Makaranta Sai da aka kira mangariba ta barta ta koma Dakinta ta Sake wanka,Ta fito Tana Sallah Yusuf ya Shigo Gidan Ya Tarar da Abba da Imran suna Masallaci. Bai gama mamaki ba sai da yaga Aikin da Safiya Tasha Da Labarin da Abba ya bashi na Safiya yadda suka Wuni Hira yau ya ma kasa mgana Saboda Farinciki. Yau agidan Rana ta Farko da suka Hadu Saman Dinning suka ci Abinci Munari da Safiya sun kara Shiga Kitchen sun yi Ferfesun kayan Ciki Imran Shima ya Fito Ferfesun Yaci kadan Yasha Ruwa ya koma Daki Abba Dai yaci Sosai,Da Yusuf da Munari bayan sun gama Suka koma Falo suka Dasa Hira Yusuf ya Dauko Jaridun Daya Siyoma Abba masu yawa Tundaga na Watan Daya gabata sai Littafan addini su azkar,Muwada Malik,Buhari da Musulim Da Qur"ani izifi Siitin Karami na Karatu Abba ya Karba yana ta Godiya Safiya tace Saura Medicated glass Wanda Abba zai Rika sakawa in zai yi karatu Saboda karamai karfin gani. Yusuf yayi na"am da Mganar Hatta Abban ma Saboda Zama Waje Daya Raunin Idanuwansa sun Ragu. Da Sallar Isha"i Abba da Yusuf da Imran Tare suka Fita Masllaci Sagir Sai da ya bama Mama Labari Bakinsa yaki Rufuwa ita kanta Mama tayi Farinciki,Inteesar na gefe Tana Latsa Wayarta bata Saka musu baki ba Tunda ba da ita suke mgana ba. Yusuf kuwa sun kwana Farantama juna Rai shida Safiya sun Riga sun zama Daya ya gama Gudartama Ransa Cikin Satin nan da anyi musu Albashi Zai Kwashe ya Dauketa suje ta Zabi Furture,da Zasu zuba ashashen da Zasu Zauna,Sai kayan sawanta Bayaso Wani nata yazo ya ganta tana Zaune a Dakinsa Hakan bazai mai Dadi ba Wlh Iyayenta sun gama mai komai da suka Kawo mai Haske acikin Gidansu. *Kalma Daya akan Safiya..?kalma Daya akan Oga Ranka ya Dade Imu🤣Kalma Daya ga Inteesar Inteen Daddy da Ya Basheer Maryama Takwaran Daadan Alkali Dukku..!* *Shakira....* 3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *DEDICATED TO:* *Aisha alto(Sisinah)* *Chubado muhammad(Uwar dakina)* *Yahanasu Soupnass(Qawalli1)* *Kausar salis(My jika)* *Rahma Ladingo(Dota)*     *🅿�16* *Bayan Sati Daya* Bayan kwana Bakwai da Auran Yusuf Da Safiya Abubuwa sun Fara Daidaita Gidansu Yusuf yanzu ya Fara Dawowa Daidai Tare da Mutanen Cikinta,kuma Duk a Dalilin Safiya Tuni ta Saka Yusuf ya kira mai gyara ya Saita Tv,Sai dai kaga Abba Zaune afalo yana Karatun Jarida Sanye da Gilashin sa mai karamai karfin gani ko kuma yana Karatun Littafin addini Safiya Dake kai kai da kawo Tsakanin Falon da Kitchen suna Taba Hira Sama Sama. Ya kasance Duk Safiya Tare suke Breakfast,kuma Duk Dare suna Dinner Tare sai dai Imran ne bai Cika Zama Cikinsu ba,Ba wanda kuma ya Damu Sanin Halinsa Tun suna Lagos Shi yafi jin Dadin gudanar da komai na Rayuwarshi shi kadai batare da kowa ba.Mutane suna da matukar Muhimmanci a Wajensa,Bai yason Ka takuramai Shima yana Girmama Rashin Takura ga wasu koda su din Ahalinsa ne sai dai Kowa ya gansa yasan yana Cikin Farinciki Gidansu ya Dawo Gida irin na Kowa Bayan sunyi bankwana da Farinciki Da Dadewa. Asatin Har Masallacin jumma"a Abba yaje Tare da Yusuf da Imran Cikin Farinciki kuma da Likita yazo Dubasa Yaji matukar Dadin ganinsa yace in Har Abba zai Cigaba da Tafiya haka Hakika Mgani bazai kara mai amfani ba Zai iya Dawowa Daidai insha Allahu,Farincikin Haka yasa Yusuf yayi Shawara da Abba da Imran kan yana so ya gyara Shashen Dake Koridon Dakin Munari Safiya ta Tare acikinsa tunda wanda suke Zaune yanzu Ciki Dayane,sai kuma yana son Siyamata kayan sawa,Abba yaji Dadin Haka Saboda Safiya ta Chanchanci komai na Rayuwa Shi ya bashi Umarnin Ya taba Kudin Dake bankin Nura marigayi,Tunda akwai kudi Har yanzu yayi amfani Dashi Imran ma ya yarda da Shawaran. Ranar Sati da auransu da Daddare suka Tafi Gidansu Safiya Shi da ita sai Tace Tare da Munari Zasu je Wanda Cikin Satin Daya sunyi matukar Shakuwa kamar yaya da kanwa In Munari bata je makaranta ba Suna Tare da Safiya aiki Tare suke yi Girki ma Haka wajenta tana ta kara koyin Abubuwa sosai Tunda ita Munari Da Karfi Da yaji ne ta iya girki,Lokacin Tana Karama Ba komai ta iya ba Sai dai ya Zaman mata Dole ne Tunda itace Macen Cikin yayyin nata da Taimakon Waya Online Clasess,Sai kuma Goggle yasa take kwaba Wasu abubuwan ammh Zuwan Safiya ya Kore mata komai,yasa ta gane ashe abaya Duk Shirme take yi. Koda suka je Alhaji Alhassan Baya nan Ya Tafi Fagge,Mommy Tayi Farincikin Ganin yarta Cikin Kwanciyar Hankali Tayi Fresh na Amarci,Tasleem Ta Rumgumeta Tana ta Murna ganinta,Mommy bata Taba ganin Yusuf ba sai Ranar ta yaba Sosai da Zabin Diyar tata Domin a Fuska yana da Kamala da Cikar Zati Tayi musu Nasiha Sosai,Tasleem Taja Munari Dakinta suna Hira Mommy Taja Yarta Ciki Suka bar Yusuf da Labarai da ake Nunawa a Nta,gabansa Cike da kayan makulashe da yar aikin Mommy ta Cika Gabansa Dashi Ruwa Kadai ya iya sha. Mommy take Fadama Safiya abunda yakai Abbun su Fagge kararsa ta kai Wajen Goggo,Bayan taje Gidansu ta Fadama Iyayenta Halin da ake Ciki Mahaifanta basu saka baki ba Sai dai sun Tausheta Datayi Hakuri Tunda aikin Gama ya Riya gamu,Yayartace ma Da ta ke binta Anty Saratu Dataji Ta Dinga Fada Dayake Tana da Fada sai Iyayensu suka Taka mata Burki Itace ta bata Shawaran su je Chan Fagge sun Fadama Goggo ko Yaya ne ai Mahaifiyarsace Zataji Rashin Jin Dadin Rashin Darajata da Yan'uwansa da Alhassan bai yi ba Shine sukaje ita da Anty Saratu suka Fadama Goggon komai sai da Tayi kuka Dataji Abunda ya aikata Shine ta Kirasa yaje yau Tun Dazu Kila Chan zai kwana Tunda Har Dare yayi bai Dawo ba,Daman Tun Bayan Faruwar abun Mommy ta Daukemai basu Dawo Daidai ba. Safiya bataji Dadin Rashin Jituwan Dake Tsakanin iyayenta ba Har yanzu yasa ta Sanyaya rai ta Dafa Kafadan Hajiya Mero Tana Fadin"Mommy Sam bana jin Dadin Rashin Jituwan Dake Tsakaninki da Abbu..Don Allah ki manta Komai indai Saboda ni ne Wlh Tallahi bana Cikin ko Wata Mtsala Mijina yana sona Abba kamar Diyarsa Munari ya Daukeni Bana Cikin Wata Damuwa baki ga alama ba..! Hajiya Mero ta kalleta ta Kada kai Tana Fadin"Ammh ai Da Farko shi da Kansa yace yayi Bincike basu da Kowa anan..Basa da wasu Dangi Anya Safiya Kina ganin hakan ba wata Mtsala bace...?kuma fa yacemin Mahaifin su Mahaukaci ne akacemai..,? Safiya ta Murmusa Tana Fadin"Mommy wa kika Taba ganin ya Fado Daga sama bashi Da Dangi? Suna da Ahali da Dangi irin na Kowa Mommy kawai yanayi ne yasa kika gansu kuma Mganar Abba..,karya ne Mahaukaci bane Wlh Sharri ne..!Nan da nan ta Fara bama Mommy Labarin da Yusuf ya bata ba Domin komai ba sai Domin Hankalin Mommy ya kwanta,Agurguje ta gayamata komai ta Karishe da Fadin"Mommy Kinsan Rashin Uwa a gida Babban Gibi ne..Su kuma Rashin Uwa sukayi da yan"uwa Har Uku yaya zasu Fuskanci Wannan Rashin..? Abba kuma Yayi Rashin Mata ce Uwar yayansa..Kuma yayi Rashin Ya"yansa Har guda uku alokaci Daya..Yaya kike ganin Haka Amtsayin in ya Faru Dake Mommy..? Sannan kuma yan"uwansa suka ki Fahimtarsa Ballataa su Taimakesa kan Halin Dayake Ciki..! Mommy ta Share kwallah Saboda Tsausayi tace"Allah Sarki ashe Hadarin Jirgin Daya kashe Mutane dayawa din na harda Mahaifiyarsu da yan"uwansu aciki..?Abun Tsausayi Allah ya jikanasu da Rahma..Wlh naga Kokarin yaran..Allah yayi miki albarka Safiya Yanzu Hankalina ya kwanta na Tabbata Mahaifinki bai kai Hannun banza kina Hannu nagari..! Ina alfahari Dake Ki Cigaba da Abubuwan Dakike,Insha Allah ke ce Haske acikin Gidansu da yardan Allah..! Rumgume Mommy tayi Tana Share mata Hawaye,Sun Dade aciki suna Tattaunawa sai da Yusuf ya kirata yace su Fito su tafi sun bar Abba Shi Kadai,nan ne ma Mommy ke mata Mganar Kayan Daki Take gayamta Yusuf yace shi Zai siya komai kawai abunda take Bukata Turaran TuraraGida sai na kaya,Sai abubuwan da ba"a rasa Mommy tace Insha Allahu zata kira Anty Saratu Zasu Shiga Kasuwa Zasu siyomata komai Sai Tajita,kafin suyi sallama sai ta bata leda guda Cike da kayan gyaran Jiki,Tace abunda bata gane ba ta Kirata Taji Takaichi yarda takai yarta Baatare da wani gyara ba Ammh ko Yanzu Lokaci bai kure mata ba Saratu Zata Hada mata komai Tunda itama Tana Taba Sana"ar kayan gyaran Mata.. Koda suka Fito Tasleem da Munari sun Gama Hadamata Duka kayanta Kadan suka bari akwati Uku suka Cikata Harda su Takalma da Takardunta na makaranta sai Littafan addu"o'inta,da Sauran littafanta na Karatu Novels na Turanci dana Hausa,Sakawa su kawai akayi a Mota Mommy da zasu Tafi Tayi ma Yusuf Gaisuwan Rashin da sukayi bai yi mamaki ba Sanin Safiya kila ta gayamata yaji Dadi sosai ya amsa yana Godiya Munari da Tasleen suka yi Sharing din Cantact din juna,Tace Sai tazo,Safiya tace ta na nan tana Jiranta suka Tafi suna Daga musu Hannu,Bayan Safiya ta bar Sallahun Agaidata mata Alhaji Alhassan in ya Dawo Mommy aranta taji bazata Fadamai ba Kuma Zata kwabi Tasleem So take sai ya Girbi Abunda ya aikata da kansa Tukunnah. Washegari Ta kama Lahadi ne Tun Safe Yusuf yace Safiya ta Shirya Zasu je ta zabi Funutures,da Kayan sawa,Bata iya cewa komai ba Domin Ta Lura Yusuf baya son gaddama,yau Munari ce tayi aikin Gidan,Tace Safiya Ta Huta Tun Safe tana Daki Gaida Abba kadai ta Fita,ta Dawo Daki ta Kwanta,Dole tatashi ta Shirya Bayan ta Shirya ne tace Tana so suje da Munari Ta tayata Zabe ya bata Rai yace Shima ai ya iya Zabe Dariya Kawai Tayi ta bar mganar,Doguwar Rigar Wata atamfarta ta Saka Mai kalan Green sai tayi amfani da Bakin Mayafi da bakar Jaka da Takalmi,Shima Yusuf din Shaddarsa Mai Duhu ce,Sun Fito Cikin Shirin Fita Suka iske Abba Falo suna Kallon Arewa24 shida Munari ganinsu sun Fito a Shirye yasa Munari take Tambayan ina Zasu je..? Abba ya kwabeta yace ina Ruwanta Tsakanin Miji da mata sai ta bata rai Tana Tura baki Abba da Yusuf suna Dariya Sanin shi yasan Inda zasu je. Sallama sukayi ma Abba ya Rakasu da adawo Lafiya, Wani Kamfanin saida Kayan Funuture suka Fara zuwa Tare da Safiya suka Zabi Kalan Bedroom da Falo,Dayan Bedroom din Dazai zama nasu Brwon and White sukace a Hada musu komai ,Dayan kuma da Zai Zama ko na Baki suka Hada Black and White,Sai Falo suka Hada Blue and Ash..Komai sai da aka Hada musu Harda su Cafet,kayan kallo,Sun siya Fridge Da wasu kanunun kayan Kitchen Tunda akwai karamin Kitchen a Ashashen,Ta Bank ya Tura Musu Kudinsu ya bada addreess Suka kuma Jadadda musu kayansu zai isa Kafin Su isa Gida Tare da Ma"aikatansu da zasu Hada komai sukayi musu godiya Daganan suka Shiga Kasuwa Safiya ta Zabi Kaya kama Daga less da atamfofi da Materials,Sai kayan Barci Da mayafi da Hijabi da Takalma bada yawa ya Siya mata saboda bai da kudi yace Sai sun kara Dawowa.. Suna Shagon Munari ta Kira Yusuf Take gayamai ga Masu kayan sun kawo nan yace Ta Nuna musu Shashen Dake kusa da Dakinta anan Zasu Jera Kayan Ta tayasu a Share Dakin,Munari tace ai Ta riga ta Share Dakin Bayan Fitansu Tayi Mopping Abba yace tagyara,Yusuf yace Shikenan ta Nuna musu su Jera komai suma gasunan zuwa.. Toh basu Dawo da Wuri ba Tunda sai da suka Biya suka kai Dinki Wajen Telan Da Safiya take kai Dinki Tun Tana Gida Kana suka Dawo sun Iske Tuni har kamfanin Tagama Hada komai sun Tafi.. Waje yayi matukar kyau sosai Munari ta Tayata dashi kanshi Yuauf din suka Kara gyara ko"ina Har Tv aranar aka Hadashi,Munari sai santi take Ita ta Tayata suka Kwaso kayansu Daga chan dakin suka Maidasu nan,Har Abba sai da yazo ya gani ya saka albaeka Imran ne dai bai Shigo ba,Daga bakin Koridin kawai ya Tsaya Daganan yayi Waje Shagon Sagir yaje Domin yanzu Chan yake Wuninsa,Tun Mganar nan da sukayi da Sagir na Zai bashi Sana"a Shikenan ya addabeshi Da kira wai yana Jiransa Dole yake zuwa ba Domin komai ba,Sai Saboda Sagir bai zai iya Ture alfarmansa ba, ammh ba wai Domin Ya koyi Dinki kamar yadda Sagir din yake Bukata Shi Aikinsa Daya ne aikin Banki ya Zauna kan kujera tana Juyawa dashi Lokaci Daya yana Sarrafa Computer shi aikinsa akwakwalwa yake,Bazai iya yima Sagir din gaddama ba Shiyasa yake Zuwa Sai dai Fara Zuwansa Shagon ya Takurama Yaran shagon basu da Damar Sakewa ko Hira ko Dariya in Har Imran na Shagon ba umh ba Umh ne ko Mganar Rada kayi sai yace ka Dameshi ka Fita yanzu yar Yar wakar ma da suke kunna Saboda Nishadin Dinki ba wannan Damar domin Ranar da suka Kunna Mp3 Din gabadaya Imran ya Rotsata da kasa ta Fashe,Tundaga lokacin Shagon ya Zama sai a Hankali,Yaran Sagir din Haushin Imran suke ji sai dai ba Halin su Furta Shi kanshi Ogan zai iya Bata Musu rai kuma ba komai yake yi ba Illah ya Zauna Kawai yana bin Wuri Daya da kallo in yaji Nishadinsa ya Busa Sigari ko baka san Warinta baka isa ka Fita ba kuma baka isa ka Toshe Hanci ba Dole ka Shaki Hayakinta. Shi Kanshi Sagir din yayi Nadaman Gayatton Imran din Domin ba yaransa Kadai ba Hatta shi ya Hana mai Rawan gaban hantsi ko Dinki Costumer suka kawomai Cinikayya sai dai su Fita Waje,Indai Imran na Shagon bayason Hayaniya da Takura,Sai dai ba yadda Zai yi Dashi Fada ne Kullum Kaca kaca suke Rabuwa,Bai kuma Hana gobe in Sagir yaji Imran din Shuru ya Kirasa Har kuma zuwa yau bai kara ganin Inteesar ba,Har ma ya manta da Babunta. ****** *Kaduna..* Da misalin karfe 8:00pm na Dare. Shigowarta Bedroom Din kenan Dauke da Karamin mug,Wanda Ruwan Shayin Na"aNa"a,Alhaji Mustapha ne Zaune gefen gado Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara,Ya Zabga Tagumi da Hannun Bibbiyu Har ta karisa kusa Dashi bai sani ba,Domin yayi Zurfi Cikin Tunanin Daya Tafi kan Side Drower din Jikin gado ta ijye mug Lokaci Daya ta Zauna Gefensa Tana Fadin"Abban Intee..! Ta fada Tana Ciremai Tagumin Sai Lokacin ya Dawo Cikin Hayyacinsa ya Fahimci Ta shigo Har tana Kusa Dashi. Ajiyar rai ya sauke kafin yace"Bansan kin Shigo ba..! Tace Tana Kallonsa"Ina fa Zaka sani kayi Nisa Cikin Tunani..kuma kasan yawan Tunanin illah ne ga Lafiyan Dan adam..! Sauke Dayan Hannunsa yayi Daga Tagumin yana Fadin"Umh..Tunani ya Zama Dole Sahala..Wlh na kasa Sukuni Tunanin Halin da muka baro Daada aciki ne ke Damuna..! Umma Ta yi shuru kafin itama Tace"Wlh nima Abban Intee..Daada ta kasa fa..Yaya malami kawai take son gani..Kaji fa Baba asabe Tana Fadin ko acikin Barcinta sunansa take kira..! Ta karishe Fada Cikin Bayyana Jimaminta. Alhaji Mustapha ya Sauke Twagayen Numfashi kafin yace"Ko achan Baya Soyayyar Daada ke ma Ya Malami ta Dabam ce shi din D'a ne masu Soyuwa gareta Duk yafi mu sanyin Hali Shiyasa yafi Shiga Ranta Dole Daada ta Shiga Damuwa Saboda Rashinsa Kusan kwanciyarta asibiti Biyu acikin Satin nan fa..! Umma tace"Ni Tsorana kada Hawan jinin nan ya Fadar da ita kasan fa Mugun Ciwo ne..Daman ta Amince ko ku saka baki kai da su Hajiya Bintalo ta yarda Tabi Baban Sajida Abuja In ma Baba asabe take ji Duka su tafi Tare nan Dukkun sai a Rufeshi In Allah yasa ta Samu Sauki sai su Dawo ni aganina Chan zai fiyemata ko kobamai akwai gilmawar Wani nata agabanta nan kuwa sai dai in an Taka an je..! Har tagama Mganarta bai ce mata komai ba sai Chan yace"Ai Daada alkwarin tayi ma kanta bazata bar gidanta Dukku Da Ranta ba..Sai dai in Gawartane ta yarda a Fitar da ita..! Umma tace"ai kaji kuma..Allah dai ya bata Lafiya Wlh jiyan nan da muka isa Naji Tsoro Hakama Basheer yace sai da nayi kwallah Lokacin Data Rike Hannuwanku kaida Baban Sajida Tana Rokon ku ku Sadata da Malami kafin ta bar Gidan Duniya..! Yayi kasake yana jinta Cikin wani yanayi kafin ya Mikamata Hannu yana Fadin"Bani Tea din..! Ba musu ta Dauko ta mikamai ya karba yakai baki Kurba Daya Zuwa Biyu ya Dakatana Yana Daidaita Zamansa Lokaci Daya yana Fadin"Baki san wani abu ba Salaha..Jiyan nan da Barrister ya kirani yana gayamin wai Dr.Zubaida Ta kirashi tace Daada na asibiti Wajenta Itama Tana gidan Baba asabe ta Kirata jikin Daadan ya tashi na Tsorata..Duka Duka ko fa kwana Hudu batayi da kwanciya asibitin ba ta Kwana Daya aka Dawo da ita gida..Ciwon Daada wlh yana Tadamin da Hankali akoda yaushe Ina Rokon Allah Duk inda ya Malami yake Allah ya bayyanashi Daada nada rai kada Sai ta Mutu Hakkinta ya kamamu..! Ya karishe Fada yana kara Kurban Tea din Hannunsa Umma Tayi Kasake kafin Tace"Hakki kuma..? Ai naga kuna iya bakin kokarin ku Wajen Nemansa bai kamata kace in Kun gaza Hakan Hakkin Daada zai kama kuba sai dai in shi Yaya Malami Tunda ko Yaya ka Lalace Uwa Uwace Har Abada kuma Tana da Nauyi da Hakki akansa.. Bai katseta ba sai da ta gama kana ya mikata mata Mug din ta karba ta Maidashi inda ta Daukosa,Shi kuma ya Mikar da kafarsa Saman Cafet din Dake malale a Bedroom din yana Fadin"Me kika sani Salaha..? Ai Duka Alhakin Barin Ya Malami Gida da Iyalansa yana Wuyanmu ne..Musamman Barrister Domin kinsan da Zafi sosai Alokacin da Abun ya Faru Ya Maalami ya Samu Depression kan Abunda ya Faru da su Yusuf suma ba wani Hop kansu sai yake ganin kamar Rashin Hakuri ne da rashin Yarda da kaddara yasa komai ya Lalace Har Laluran tasa tana ta gaba Kullum Likitoci suna cewa ba Cigaba..Dalilin haka yasa yayi ta Fada gaskiya munyi kuskure Domin naga wani Shiri,Tv Kwanaki Wani likita na mgana kan masu Fama da irin Lalurar Ya malami yace Ciwon Damuwa ne Ba Hantara ko Fada suke so ba ajashi ajiki Lallashi da ban baki a Zauna dasu adaina bari suna Tuna Abunda Zai sakasu Tunani,arika yin Abunda Zai sakasu Farinciki akoda yaushe kuma Tsakani ga Allah Bamu yi wannan kokarin ba Mun kawo su Dukku Gaban daada Mun koma Garuruwan mu,bamu yi La"akari da Daada ta Fara Manyata ba, bazata iya wani Kokari ba..Sannan iyalansa suma Raunin ya Tabasu da Har baza su iya Taimakon kansu ba Ballatana Shi Yaya Malami Ahaka suka nuna suna son Komawa Gida kuma na Tabbata Saboda Wannan Dalilin ne sukayi nesa Damu bayan sun koma Lagos Sun ga ba wanda ya Damu dasu..Na Tabbata Yusuf bazai yi Tunanin Yin nesa da Kowa ba Face mai muradden Halin nan Duk Cikin Dangin mu Imran yaron yana da Zafi Daman Chan Tun Farko Bai da Shiga Dangi Sosai sai da ya Girma ne ma Ya malami ke Tarosa in zai zo Dukku..Ina da Tabbacin Shi zai ba Yayan Shawaran Haka Shi kuma Bashi da Zabi sai ya Yarda da komai Suna ganin yin Nesa Damun din Shine mafita..Tabbas muma da laifin mu..! Ya Karishe Fada Lokaci Daya yana Saka yatsa ya Dauke kwallar Data gangaromai Umms Jikinta yagama yin Sanyi tace"Tabbas Hakane ba"a kyauta..Rashi ne sukayi Babba..Allah ya jikan Zuwaira Ya malami yayi Shuru Dole Ya Shiga Damuwa mace mai kirki Da Sanin yakamata Ga kuma Rashin ya"ya kai yaga Jarabawa Wanda bakowani bawa bane zai iya Tsallakewa Abban Intee in Wani ne sai ya kashe kansa..! Yayin Saurin katseta da Fadin"Wlh Abun Allah ya kare..Hakama likitan yace ,Wani babban Likitan kwakwalwa ne Daga asibitin ABU Zaria yace Tabbas suna kashe kansu To zasu ga basu da wani Sauran Amfani a Duniya..Wlh jikina yayi Sanyi sosai ina so na ganar da Barrister kuskuransa ammh kuma Ban samu Dama ina ganin kamar Shi Har yau Laifin Ya Malamin yake gani..! Umma tace"Wlh kuwa ai kaji Abunda yake Fada yau..Wai Malami ya Tafi Da gangan kuma gashi yanzu a Rashinsa zai kashe Daada..! Umh kawai ya iya Cewa ya kasa Mgana,Umma ta Mike tana Fadin"Allah ya kyauta ka Rage Tunani Don Allah mu Cigaba da gayama Allah..Insha Allahu Allah zai bayyanasa..! Ya amsa mata da Amen,Mug din Tea din ta Dauka Tana Shirin Ficewa yace"Bashir ya Tafi dasu Abiden ne..? Naji ban ji Motsin su bane..!? Umma ta Dakata Tana Fadin"Ai Rigima suka sakamai nace ya Tafi Dasu Wajen Uwarsu..Tun jiya basu ganta ba..! Ya jinjina kai kafin yace"Yaran ne akwai Rigima Irin Diyarki Intee..!. Umma ta Tabe baki Tana Fadin"Diyar ka Dai..Ni da Tunda tatafi ta yadani..Ta kira jiya muna Dukku Tana Min tsiyan ta samu Mamarta Mai sonta ba irina mai Hanata Sangartanta ba..! Mirmiahi yayi kafin yace"Ai gaskiya ta Fada..In wani yaki ka da wuni.Wani da kwana Dubu zai soka..ai zan bar ma Yaya Aminan ita kawai ta Aurar da ita achan mu namu gayyata ne Kadai..! Umma tace"Wa Kai din..? Dama Zaka iya ne Abba Intee..Da Ya Amina Taji Dadi..ammh Sai dai kulafuncinta bazai barka ka barmata ita ba Jifa Tafiyar ta fa sai da kafi kwana Biyu Baka Walwala in ka Dawo Gidan nan kaga bata nan..! Yana yar Dariya yace"Ai jiya Da Daddre na kira Inteen har tabani Ya Aminan muka gaisa Ta Tambayi Daada da Jiki..Sosai naga Inteer tana jin Dadin Zaman kano da Karatun na Gabadaya..! Umma tace"To tana samun Damar yin sagartatan son ranta mana..! Mirmishi ya sakarmata ita kuma ta Fice Tana Mita tana Fita ya Kwashe Kafafunsa zuwa kan gado ya gyara Kwanciyarsa Tunanin da baya so shi ya Shigayi Babban Tashin Hankalinsa Rashin sanin Inda Malami yake Domin har yau suna kan nema kuma ba wani Labari Daga kowani bangare Kuma an Tabbatar musu Tunda suka bar Lagos Har yau basu kara Takawa ba.. Ya illahi ina ya Malami ya Shiga Shida iyalansa ne..?Allahu ka bayyanashi ko Domin Damuwar Daada garesa..! *Shakira..* 3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*       *🅿�17* *Monday* 12:12pm BUK "Yau ta kama Monday ko"ina kabi Sai Hada Hada ke wakana Saboda Monday Tushen aiki ne,haka yake Gudana a Tsakiyar Jami"ar Bayero Dake kano. Dagachan Bangaran Economics Department na Hango Dandazon Jama"a Mata da Maza yan kwalisa Suna ta Tururuwan Fitowa Daga wani aji Daga Dukkan alamu Sun gama Daukan Lecture ne suka Fito,wasu Cikin makaranta suka Shiga wasu kuma Hanyar Cafteria suka Nufa Wasu kuma Masallacin Cikin makaranta suka Nufa Wasu kuma wucewa sukayi Suka Zauna Saman Kujerun Dake Zagaye da Department Din,wanda an Tanadanesu Ne Domin Zama da Huta gajiya ko kuma Karatu Irin haka dai. Acikin Masu Zaman Inteesar Tana Daga Cikinsu itama Waje ta Samu ita Kadai ta Zauna,Yau Datake kwana Goma da Fara Zuwa makarantar Bazatace ta Saba da komai ba Sai dai ta Fara Fahimtar abubuwa Dayawa Sai dai har yau batayi Wata kawa ba Ita Kadai Zakaa ganta Sai dai Tana Yada Sallama Duk inda Tajee ko Taga Gungun Jama"a Ita Haka take bata da Saurin Saki jiki da Mutane Ballatana Sabo. Yan ajinsu Da Dama suna Lura da ita Sai dai ba wanda ya Damu Kansa Jami"a Gidan kazo nazo ne,Akwai irin su Da yawa amakarantar Wadanda Basa Bukatar Alaqa da kowa cikin Masu Lura da Inteesar Tun Shigowarta Makarantar Harda Munari Sakamakon Department Dinsu Dayane Tun Ranar da Inteesar ta Fara zuwa Take Hankalce da ita..Sai Taga Itama kamar irin tace bata Hulda Da kowa kamar yadda Take ita Kadai haka Itama Inteesar take komai nata ita kadai,Tana ta so Tayi mata Mgana ammh Sai ta kasa sai yau Bayan sun Fito Daga Lecture din 10 to 12,Zasu yi Sallah suci Abinci 2pm suna da Wani Karatun. A idonta taganta ta Samu Waje ta Zauna ta Fito da Wani littafin Datayi Note game da abunda aka Koya musu Tana Dubawa Munari bata son Dalili ba kawai Taji Kafafunta najanta Zuwa Wajen da Inteesar Take Zaune,Sai da ta Kariso Gabanta kana ta yi mata Sallama. Inteesar Dake Tsaka da Karatu Hankalinta yana kan Karatunta ta Dago Suka Hada Ido da Munari Sai dai Ita Inteesar ta Toshe Idanuwanta da Wani Siririn Farin glass mai kyau da yarari yau Shigar Riga da wando Tayi Wandon Ja ne plazo mai Budewa Ta kasa,Sai Wata Riga Blue mai dogon Hannu Ta kama mata Jiki sai ta Dora Wata bakar Riga mai kama da kimoni a Saman kayan ta Zarge igiyarta Daga Wajen Jikinta,Sai Red din Vail Data yane kanta Dashi hakama Taklmin kafarta red mai Tudu sai Wata Karamar Jakarta Red Colour. Yayinda ita Munari take Sanye da Doguwar Riga Kirar Armani,Baka sai ta yane kanta da Gyalen Rigar Dayake Fara ce sai Fuskarta Tayi kyau itama Bakar Jakace ke Rataye a Kafadanta na Dama sai Wasu littafai Dake hannunta. Lokacin da suka Kalli juna suma basu san Dalili ba sai da gabansu ya Fadi a Lokaci Daya Kuma suka kasa Dauke Ido a Kallon Juna Cikin Sanyim Murya Inteesar ta amsa ma Munari Sallamanta Lokaci Daya Tana kara Kallonta da Nazarinta. Munari ta Murmusa kafin tace"Don Allah zan iya Zama..!? Tafada Tana nuna Gefen Inteesar din da Sauri ta Kwashe Jakarta da Littafanta Data ijiye a Wajen Tana Fadin"Haba sai ma kin Rokeni..Zauna mana..! Tafada Cikin Mirmishi itama Gefenta Munari ta Zauna tana Fadin"Nagode..! Mirmishi Inteesar Tayi mata kafin Tace"U are Wlcm! Daga haka ta maida kanta Kan Littafin Da Munari ta Sameta Tana karantawa. Sun Dade Shuru kowa na Nazarim Kowa Ita Inteesar Bata zata iya Gane Munari a ajinsu ba Tunda suna da yawa,Ba kamar Munari Datake ankare da ita Tun Fara Zuwanta makarantar ba. Cikin Son Takalo Mgana Munari ta Gyara Zama tana Fadin"Ammh baki Dade da Fara zuwa Makarantar nan ba ko..? Inteesar ta Dago kanta Tana Fadin"Eh..yau kwana na Goma da Fara Zuwa kefa..? Wani Course kike yi..? Munari tace"Course din mu Daya Economics nake karanta..! Inteesar ta dan Saki Fuskarta Tana Fadin"Allah Sarki..Ashe ma Tare muke Kema Kwananan kika Fara zuwa kenan..? Munari tace"Eh to ban 1 Month dana Fara zuwa..! Inteesar tace"Kice kin Rigani Fara zuwa..Aini koda na Fara zuwa Duk anyimin Nisa da karatu..Wajen ma Class Rep ne nake karban Wasu Note din ina rubutawa..! Munari tace"Ayyah..Ai baki da Shiga Mutane ne kamar ni da kin samu..! Inteesar tace"Kema haka kike kamar ni..? Kwata kwata bana da Sakin jiki da Mutanen da ban sani ba Haka nake Nafi sabawa da Yan gidanmu Fiye da kowa..! Munari tayi Mirmishi kafin Tace"Kamar Ni kenan..Ni kaina tunda nazo makarantar nan bani da wata kawa Ni kadai nake Rayuwata..sai yau Naji ina Sha"awar nayi miki mgana Duk da ina Lura Dake Duk Sanda kika Fara Zuwa Haka kurum naji kina Burgeni ina son nayi miki mgama mu gaisa..! Inteesar ta Fadada Fara"arta Tana Fadin"Allah sarki..Ni kaima Da kika min mgana sai naji ina son na gaisa Dake Haka kurum Daga ganin ki yau bansan Dalili ba..! Munari tace"Kila Allah ne ya Hada Jinimmu..Yana so mu yi kawance..! Atare suka saka Dariya gabadayansu Cikin Nishadi Shuru yadan Biyo Baya Kafin Munari ta mika mata Hannu Tana Fadin"My Name is Maimunatu Abubakar Malami ammh Agida Abbana da Brodas dina suna Kirana Munari ne..! Imata Inteesar din Hannu ta Mikamata suka Cafke Cikin Annuri Tace"Nice to Meet u Munari..ni kuma Sunana Maryam Mustpaha Dukku Nima Kamar ke Daddyna da kowa Agida Suna Kirana da Inteesar Saboda Sunan Mahaifiyar Daddy naci Daada..! Gaban Munari ya Fadi jin Inteesar ta ambaci Dukku Cikin mamaki Take Fadin"Ke yar Dukku ce..? Inteesar tace"No..Daddyna ne Dagachan.Ummata yar Kadunace..Nima a kaduna aka Haifeni Chan muke Zaune da Zama Karatu ne ya kawo ni kano ina Zaune Wajen Mama yayar Ummace..Kema Abban ku Dagachan yake...? Da Sauri Munari ta Girgiza kai Tana Fadin"A"a..Kawai na Tambayane..Ganin Daman kina Kama da Fulani..! Inteesar tace"Kema ai kina Kama Dasu ..Kalle ki fa Fara ni kuma Fatats mai Duhuwa ce..! Munari Tace"Ni kuma Nafi son irin Fatarki Wlh..! Inteesar tace"Kedai Fadi gaskiya..Farar mace alkyabban mata fa..Nima Ummata na Dauko Da Fatar Daddy ce kamar ke zan zama Saboda Farin Bafullatanin Dukkune Gaba da Baya..! Munari ta amshe da Fadin"Ni kuma Daga Abba Har Anni Duka Fulani ne kuma Fatarsu mai Haske ne Shiyasa..! Inteesar ta gyada kai kafin tace"Ke nan ke yar kano ce..? Munari tace"Eh..Gidanmu na Gadon kaya..kefa ina kike Zaune..? Inteesar tace Tana Dariya"Ikon Allah Nima ai Gidan Maman yana Gadon kayan ne..! Munari ta cafke Cikin Murna Tana Fadin"Shikeman Daman na Fadamiki..Haduwarmu Daga Allah ne..!.Inteesar tace"Na yarda da Mganarki..! Daganan ssi Hira ta Tsinke kamar sun Shekara da Sanin juna,Haka kowanensu ke jin wani Farincikin na yau Kadai da suka Hadu,karin Farincikin Inteesar ma Da suka Tabo bangaran Karatu ta Fahimci Munari Tasan Abunda take yi Sosai,nan tace zata ari Wasu Notes dinta ta Kwafa Daga baya sai Munarin ta Koyamata Inda Bata gane ba Sai gashi Tare sukaje masallaci sukayi Salla Daganan suka Shiga Shago Inteesar ta Siya musu Freshyo,tazo da Cake suka Koma Suka samu wani Waje suka Zauna suka ci suka kora da Madara,Kafin su Shiga Lacture suka Duba littafansu Munari na kara yima Inteesar Bayanin karatun da akayi musu a baya Inda bata gane ba,har Lokacin Shiga Lacture yayi suka Shiga Tare suka kuma Zauna Waje Daya yan ajinsu sai mamaki akeyi Wasu acikin Ransu sukace sun Dace da juna ganin dukkansu Daman basu da kowa acikin ajin. Ranar har suka gama Lecture dinsu na Ranar Suna Tare da juna 6pm suka Tashi,Tare suka Fita Bakin get suka Samu adaidaitan Gadon kaya Gidansu Sagir ne Farko kafin gidansu Munari ana Zuwa Inteesar tace zata Sauka Sai Munari itama ta Leko Cikin mamaki tace"Wai nan gidan kike Zaune..? Inteesar na Shirin Bama mai adaidaita Kudin ta juya tana Fadin"Eh kinsan Gidan ne..? Munari ta Fito Itama Tana Fadin"Sosai ma..Gidan su yaya Sagir..Ai abokin Yayana ne Ya Imu..! Inteesar ta Washe baki ta ba Munari Hannu suka Tafa Tana Fadin"Abun mu Chas Wlh..,!atare suka Saka Dariya Bayan Inteesar ta Hada duka ta Sallami mai adaidaitan suka Nufo Gidansu Sagir Munari na Fadin"Ai Ni gidamu yana gaba kadan ne..! Inteesar tace"Ayya Dayake Tunda nazo ban Taba Fita waje ba Daga makaranta sai gida..Bari mu Shiga mu Fito sai na Taka miki naga gidan naku..! Sun Kariso Kofar gidan kenan sai ga Sagir ya Fito Yana yarfe Ruwa Daga Fuskarsa Kamar a mafarki ya gansu Tare bai Daina mamaki ba Har suka Gaisheshi ya amsa yana Fadin"Inteesar ina kika Hadu kuma da Munari..? Inteesar na Mirmishi ta Kalli Munari sukayi Dariya kafin ta Kalleshi Tana Fadin"Makaranta yau muka Hadu..Ashe Course din mu Daya kuma ajin mu Daya..Ashe ma muna kusa sai da mukazo take cemin ai tasan nan Gidan kai abokin Yayanta ne..! Sagir yayi Mirmishi yana Fadin"Eh Wlh..Nasan itama ta Fara zuwa makaranta To ban yi Tunanin Abu Daya kuke karanta ba Abu yayi kyau kin ga ke Inteesar kin samu kawa kema Munari kin samu kawa,sai ku Dinga Taimakama juna amakaranta Tunda kuna kusa..! Suka Hada baki Wajen Fadin insha Allahu Sagir ya wuce yana Fadin"Ke Munari kada ki Zauna fa ki Fito ki tafi Gida..Yanzu ma muka Rabu da Yayanki ya koma Gida su Taho Salla Tare da Abba..! Inteesar ce Tayi Saurin Fadin'"Yanzu Zan Rakota Ya Sagir..! Ya wuce yana Fadin"Kuyi Sauri kunji an Fara Kiran Sallar mangariba..! Daga haka ya Shige Shagonsa su kuma suka Shiga Cikin Gidan suka Iske Mama a Tsakar gida Tana alwala ta Dago Tana amsa Sallamarsu itama Bakin ta Sake tana Kallonsu Daidai ta Idar da alwalan ta Mike Tana Fadin"Ikon Allah wa nake gani kamar Munari..? Dariya tayi Tana kallon Inteesar Tace"Nice Mama..! Mama ta Rike Haba Tana Fadin"Ikon Allah Maryam ina kika Samo ta..? Inteesar tace"Makaranta Mama ashe ajinmu Daya bamu san muma kusa ba..! Mama tace"Kaji wani ikon Allah..abu yayi Dadi ku shiga ciki ai nan kamar Gidane ga Munari gidansu na gaba Kadan,Imran yayanta ai Abokin Sagir ne na Sosai Ya kwana Biyu bai Shigo Gidan bane da kun Hadu..! Suna gaba tana Bayansu Zuwa cikin Dakin,Sai da suka Zauna kana Suka gaisa da Munari Inteesar Tana ma Mama Bayanin Haduwarsu da Sagir akofar Gida da abunda yace Mama tace"Ya fadi gaskiya..Munari ga Kawa nayi miki Diyar kanwatace Salaha kema Inteesar ga Kawa nan munari Makota muke dasu..! Suka Hada ido kafin su Hada baki Wajen Fadin insha Allahu Daganan Mama tatashi Bayan tacema Inteesar abincinta na Kitchen Itama kuma ta Shiga Ciki yin Sallah Inteesar Tayi ma Munari Tayin Cin Abinci sai ta Mike Tana Fadin"Nagode Kawas ki bari in na Sake Dawowa zanci..Yanzu Tafiya Zanyi in ya Imu yaga ban Dawo ba Wlh Zan ci kaniyata ne..! Jin haka yasa Inteesar tamike tace suje ta Rakata,Kayan Hannunta Kadai ta ijiye suka Fice Tunda Mama ta Tada Sallah Tafiya kadan sukayi sai gasu Kofar Gidansu Munari ta Kalli Inteesar Tana Fadin"To kin ga GIDANMU..! Inteesar ta Kalli Gidan Tana Fadin"Nagani Ai nasan Gidan yanzu..Da Zama ya Isheni in bamu Shiga Sch ba sai dai ki ganni..! Munari tace"Shikenan sai na ganki..Bye sai gobe in mun Hadu..! Inteesar tace"Gobe 10am muke da Lecture ki Biyomim mu Tafi tare..ko Kina da mai kai ki ne Kada na Takura Miki..? Munari tace"Yayana ne Daman ke ijiyine in muna Karatun 8am Daganan ya Wuce Office in kuma ya Wuce Haka Dan Sahu nake hawa..Kada ki Damu Zan zo sai mu Tafi Tare..! Inteesar tace"Yauwa..Kawo wayarki na Saka miki Lambata..! Ba Musu Munari ta Daukota Daga Cikon Jaka ta Mikamata ta Saka mata Tana Fadin"Wani Suna Zan saka miki..? Munari tace"Ki saka Besty Intee..! Inteesar Tayi Dariya Tana Fadin"Au..Nima kuwa Da kin je gida ki kirani Zan saka Besty Munira..! Dariya suka saka Gabadaya Daganan sukayi Sallama ganin Maza nata Haraman Zuwa Masallacin Inteesar ta Juya Zuwa Gida Tanajin Wani Farincikin in Tana Tare da Munari Sai take ji kamar Tana Tare da yar"uwanta na jini kamar Nasara,Dayake Daga Munari har Inteesar basu Taba gaanin juna ba Shiyasa bazasu Shaida juna ba sai dai Bond din Jini Dake Tsakaninsu ne yasa Sukejin kamar wani iri a Tsakaninsu hakama ta Bangaran Munari tana jin Intesar Sosai acikin Ranta. Tana Shiga Haraban Gidan suka ci karo da Abba da Imran Harda Ya Yusuf ya Dawo Ganin ya Imu sai da gabanta ya Fadi tana gaishesu Abba ne kadai da Ya Yusuf ya amsa bandashi Daya wani Hade rai yana kallon Gefe. Abba ne ya Kalleta yana Fadin'Munarin Abba ina kika Tsaya yau kin gota Lokacin Dawowarki..? Kafin Tayi mgana Ya yusuf ya Rigata Da Fadin"Ni kaina na Damu yanzu Safiya ke Fadin Shuru bata Dawo ba Har 6:30pm ta wuce..? Yafada Lokaci Daya yana Duba agogon Fata na kamfanin Rado Dake Daure a Tsitsiyan Hannunsa. Da Sauri Munari tace"Ban samu Adaidaita ne da Wuri ba Ya yusuf Shiyasa..! Jin haka yasa Dagashi Har Abba suka Kada kai Ya yusuf yace"Kawai Daga yanzu in na taso da Wuri Zan rika kiran ki naji in kun gama Sai na Biyo na Dauko ki..Kina mace bana so kina Yin Dare a waje..! Kai ta gyada batare da tayi mgana ba ta Mike ta Wuce Sum sum ta wuce Ba Saboda kowa taki Fadan inda ta Tsaya sai Saboda Ya Imu ko kowa zai Fahimeta ban dashi ta Tabbata sai yayi kwallo Da ita bayan ya Fara Sauya mata kammin Dayake ikirarin Tun a Haraban gidan kafin su Shiga Ciki Shiyasa ta Rufama kanta asiri. Cikin Gida ta Shiga su kuma suka Fice koda ta Shiga Safiya tana Shashnta Tana Sallah Domin ta Lekats sai kawai ta Wuce Dakinta Kafin ta Shiga wanka sai da ta Kira Inteesar sai taji bata Dauka ba sai ta Tura mata sako Salam Besty nice..Munari..! Daganan ta ijiye wayar ta Tube ta Shiga Tayi wanka,Ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Ta idar kenan Tana Saka kaya Safiya ta Shigo Tana yi mata Sannu da zuwa Sai da Tagama Saka Kayan suka Fita babban Falo su Abba basu Dawo ba sai da sukayi Isha"i Lokacin Munari taci Abincinta Saboda yunwa Tea kadai ta Kara sha tayi musu Sallama ta Shige Dakinta ta Kwanta tagaji,Ta bar Abba da Ya yuauf da Safiya a Falo Abba da Ya yusuf Hira suke Safiya kuma Tana kallon Imu dai yana Dakinsa yau ko Tea din bai Sha ba Tun bayan Dawowarsu ya Shige Ciki,Sigari Ta Riga ta gama Cikamai Ciki in ji Abba Suna Dariya Shida Yusuf. Washegari kamar yadda Inteesar Ta bukata Bayan Munari ta Shirya Gidansu Sagir ta Fara Biyawa Inda Allah ya Taimaketa Imran yana Gida bai Fito ba koda tazo Inteesar ta Shirya ita take jira basu Bata Lokaci ba Sukayi ma Mama sallama Suka Fito Ta bisu da addu"an Allah ya Tsare,Suna Fitowa suka Tsaya Bakin Shagon Sagir ya Fito suka gaisa Shi Kanshi ya godema Allah Imran baizo ba Kila da anyi wani karamin Shirin Film,500h ya basu suka ki karba yace sai dai in sin Raina Shiyasa Munari ta Karba Daganan basu Samu Abun Hawa ba sai da suka Taka da Kafarsu suna Hira Har bakin Titi kana suka Samu suka Hau zuwa Cikin makaranta,Koda sukaje ana Ta Shiga ajin Dole suka bi ayarin yan ajinsu suka Shige suma Domin yin Abunda ya kawosu. Ranar ma Tare suka wuni,Basu Je Cafteria ba sai da sunje Shago sun Siya Lemo Inteesar tazo musu da Biskit da,Donut sukaci suka Koshi Suka Tsinke da Hira Ranar Munari ta Sha Labarin Daddy da Umma da ya Basheer Har gaisawa sukayi da Daddy Daya kira yaji Inteesar Cikin Fara"a yake Tambayanta tace Besty ta samu Tabana Munari suka gaisa yana ta Saka mata albarka Munari Taji muryan Daddyn Intee kamar na Abbanta Sai dai bata yima Inteesar din mgana ba Shi kuwa Daddy Daga Barayin Yasan Munari ta Musamman ne Tunda Har Daga Haduwa Suka Kulle da Juna yana Fatan Allah yasa kawancensu ya Zama alheri ga juna. Ranar 4pm suka Tashi Daga makaranta Daganan gida suka Taho,Munari bata Sauka Daga gidan su Sagir ba,Saboda Tana Tsoron Haduwa da Imran illah kamar ta Sani yana Cikin Shagon Sagir,suka Rabu bayan Inteesar ta Karbi Wasu Note Hannun Munari Zata kwafe Tunda Gobe suna Gida bazasu Shiga makarantar ba. Lokacin Data Sauka Imran da Sagir na Fuskantar Kofar Shagon Sagir kadai ya ganta Shima bai Dade da Dawowa Daga cikim makarantar ba,kanta na kasa ne Tunda Shago ne na Dinki akwai Dandalin Maza awajen Har ta Wuce batama Dago Kanta ba,Imran kansa na gefe yana kallon Wani Atamfa da yaron Sagir ke yankawa Shi bawai yana son koya bane No sai dai yana Kallom komai Dake Gudana a Shagon kuma yana Dauke sa acikin Kwakwalwarsa Batare da ya bama Abun Muhimmanci ba. ****** *After 10Days..* Bayan kwana Goma da Haduwar Inteesar da Munari Sosai kawancensu Yayi nisa wanda yasa Kowa bai iya Boyema Daya Labarinsa,Har takai Abba da ya Yusuf da Safiya sun san Sunan Inteesar Besty Munari a bakinta Abba yaji Dadin jin Diyar kanwar Mama ce Mahaifiyar Sagir Hakama Ya yusuf,Shima bai Hanata ba jin na Gidane Tunda yanzu suna Kokarin Daidaita komai nasu ya Dawo kamar Baya ne. Haka itama Inteesar din Daddy da Umma da Ya Basheer sun san da Zaman Munari Tunda In suka kira a makaranta indai suna Tare da Munari sai ta basu sun gaisa sun santa da Murya Sosai Harta da Nasara ma ta san Labarin Munari sun ma Taba gaisawa Watarana Datakira Inteesar din suna Tare da Munarin ta bata suka gaisa. Inteesar ta Taba Zuwa Gidansu Munari sau Biyu bata Hadu da Ya Yusuf ba Imu kuma yana Dakinsa Shi a labarin ma bai sani ba Domin Munari bata yarda ta Furta Indai Labarin Zai kaimai ba. Sai ta Hadu da Abba ita kanta Inteesar ganin Farko Datayi ma Abba sai da Tayi Shock Ta Dinga kallonsa Tana so Ta Tuna ina ta Taba ganinsa ta kasa Shekarun Dayawa Tana karama ne,Sannan kuma yanayin da Muryansa kamar ta Daddynta,Sai dai itama abun na Ranta bata iyama Furtama kowa ba,Sai ya Yusuf da suka Hadu Rana ta Biyu Data Dawo Shi kanshi Taso ta ganesa Domin da Girmanta Tataba Raka Daddynta Dukku suka Hadu dashi yazo Shida Marigayi Nura alokacin Sai dai kamaninsa ya bace mata Tunda ya Kara Girma aure yasa ya Zama wani Budede Sai kawai ta Watsar da Abun acikin Ranta ko Zencen batayi ma Munari ba. Tana jin Dadin zuwa gidansu Munari Sabida Abba da Anty Safiya Suna da Matukar kirki Haka Abba zai ta janta da Hira yana musu Fadan su maida Hankali ga Karatu,ita kuma Anty Safiya ta jasu Shashenta suyi ta Hiransu,Ta maida kanta Sa"arsu Ranar ma da Inteesar din tazo Suna Shashen Anty Safiya sai gasu mommy sun zo ita da Anty Saratu da Tasleem Dama Tun jiya Mommy tace Safiya tasa Idonsu Dayake ta Dade ta Tura musu Kwatancen Gidan basu sha Wahalan gane Gidan ba Tunda ba yana Lungu bane. A falo suka Fara ganin Abba yana Zaune yana kallo Suka Gaisa Dashi,Kafin Safiya ta Fito ganinsu Mommy yasa ta Murna ta Rumgumesu Cikin Farimciki nan take Fadama Abba Mamartace da yayarta da kanwarta suma ta gabatar musu da Uban Mijinta Suka kara gaisawa Sosai Abba ke ta Godiya sai da Mommy da Anty Sarati suka ji wani iri. Sun zo Da kaya sosai a manya Ledoji Safiya tajasu Zuwa Shashenta sun ga abun mamaki kayan arziki haka,Ba ko sisinsu,Nan inteesar da Munari suka gaishesu Tasleem ma suka gaisa da Munari ta gabatar mata da Inteesar,Nan suka barsu suka Koma Dakin Munari suka Cigaba da Hiransu Daga Baya nan Tasleem din ta Dawo suka Hade su uku suna Shan Hira Tasleem na Fadin itama Buk Zata Cike Taje chan su Hade tare. Safiya kuwa Ta Dinga ina zata saka da Iyayenta,Daman ta yi girki Dazu ita da Munari,Farar Shinkafa Miyar Kaza Sai Kunun aya da sukayi shi ta Zubo musu sukaci suka saka albarka suka Leka ko"ina suna yabawa Anty Saratu ta Kada baki tace"Ni kam ai banga aibun da Alhassan ke Fada akan wannan Gidan ba..Ga Baban Mijinta Dattijon yasan Karamci ji yadda yake mana Godiya mu da muka kawo musu ya ba komai ....Ji Abun arziki Mero..Ji Safiya tayi kiba kamar ba ita ba ai wannan gida..Tabbas Gidan Aure ne Wlh..Allah ya Zaunar Lariya..! Hajiya Mero Tana ta Dariyan Farnciki,Sun zo mata da kayan Kitchen,da Turarun ka Daki Dana Jiki sai Speciess na girki da Garin kunu da Zogale Bushashiya,da su Kubewa,kuka Da Sauran abubuwa sai Kayan gyara,Da kayan gara irin su Mangyada da manja da Kwalayen Indome da Taliya da Macaroni suka Gyara Kitchen din suka Jera komai gwanin Sha"awa Basu Tafi ba sai yamma da Yusuf ya Dawo suka gaisa,Lokacin Inteesar tatafi Gida Tasleem da Munari suka Rakata Gida suka Dawo suna Dawowa Suka Tafi su kansu suna ta yima Yusuf Godiya Shi kuwa aransa yana Fadin ai Shi ke da Godiya Safiya ai Kamar Zinare ce a wajensa Bayan sun Tafi ta Nunamai kayan da suka kawo mata ya gani ya saka albarka har Abba ta Fadamawa Shi ma ya saka albarka Sun Tafi sun barta Cikin Farinciki Suma sun koma Cikin Farinciki suna Yabon Irin Gidan da Safiya tayi aure aciki. *Shakira.. * 3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*       *🅿�18*  Yau din Takama Ranar Sati ne Wato Asabar ce Tun Safe Inteesar tatashi da ayyuka,Da wankin kananun Kayanta ta Fara Iners dinta da bata ba dasu Wanki,Daman Tun tana gida ta iya kowani aiki banda wankin kaya sai Dai tana wanke Inners Dinta Sauran kayanta kuma Wanki a ke kai musu Nataa da na Umma sai dai a dawo Dasu a goge tas dasu. Hakama Datazo Gidan Mama Tana Kowani aiki in Tana Gida banda Wanki,Itama Maman bada kanta Take Wankin nata ba kaiwa akeyi Sai da Inteesar din tazo ake Hadawa da kayanta Sagir ke kai musu Suma sai dai adawo dashi agoge. Tana yin girki Duk Ranar Datake Gida kamar asabar da Lahadi,In bata nan Tana makaranta sai Mama tayi. Yau ma hakan ce ta Faru bayan ta gama Wankin Kayan nata ta Share Daki ta gyara tayi mopping ta kuma Wanke Bayin Daki Da kuma na Waje ta Share Tsakar gidan ko"ina Tayi Tsaf, Da Mama tace ta bar Girkin ta Dora sai tace Maman ta barshi Ita Zatayi Shinkafa da Miya da wake ta Dafa musu,Da Salat Bayan ta gama tayi wankanta ta Saka Wata Doguwar Rigar atamfarta Gold mai kalan ja da Brown Anty Hauwa Matar Ya Basheer ta Dinkamata shi,Ta kashe Daurinta na Zara Buhari Fuakarta Tayi kyau Sosai Duk ita ba ma"abociya Kwalliya bace. Sallaya ta Shimfida ta Tada Sallar Azahar Daman Daga Tiolet ta Dauro alwala,Bayan ta Idar da Sallar ne taje Kitchen ta Dibo ma Mama Abinci Ta kawomata Zobon da Tayi Jiya da Daddare Bata Taba gwadawa ba Ko tana gida sai dai Tana ganin Talatuwa mai aikin Umma nayi Shine jiya Dataga Mama nada kayan Hadin Zobon Tace bari ta gwada sai gashi kuma Yayi Dadi,ammh Sai da Munari Tazo ta Taimakamata. Sannu da aiki Mama Tayi mata Tana Daga kan Darduma bayan ta Idar da Sallah Tana Lazimi. Inteesar ta amsa mata Cikin Jin Dadi Domin Tana bala"in jin dadin Zama da Mama Tana ganinta kamar Umma abaya ta Zata tafi Kowa Kewar Gida sai gashi Tana jin Dadin Zaman Gidan Mama,Sai dai kewa ta iyaye kuma gashi Suna mgana ta waya Kusan kullun sai sunyi Waya Daddy Fiye da Sau Uku Rana Umma ce ma sai Bayan an kwana Zata kirata taji ya Karatun ko Bata kirata ba Takan kira Maman su gaisa. Ganin Zata Koma Cikin Uwar Dakin ne yasa Mama ta Daga baki Tana Fadin"Inteesar ina zaki kuma..? Ke banga kin Debo abincin Kinci ba kuma kin gama Dafa Abinci da kanki..! Inteesar ta Juyo Tana Fadin"Mama ba yanzu Zanci ba sai anjuma..Dambun Namam da naci da Safe ya Cikamin Ciki..! Mama tace"Ina Dai Lura Dake baki san cin abinci sai kayan kwalama da Shan Zaki Shiyasa gaki nan Har yau bakya Kiba..! Dariya Inteesar Tayi kafin Tace"Kai Mama Allah ina ci..Rashin kibata kuma wlh ina jin Dadin kaina ahaka Sam bana son kiba..! Mama tace"ai shikenan nayi Shuru..! Yar Dariya Inteesar Tayi kafin Tace"Mama zan Dan kwanta In ya Sagir ya Shigo Abincinsa na Kitchen..!.da kai Mama ta amsa mata Tana cigaba da Laziminta ita kuma Inteesar ta Juya ta koma Ciki kan gadon Datake kwana ta yada kanta Lokaci Daya Ta Dauki Wayarta Ta kira Munari har Sau Biyu bata Dauka ba Lokaci ta Duba taga Har 1:30pm Tayi,Sai tayi mamaki Rashin Zuwan Munari alhalin sun Rabu ajiyan kan cewa yau Zata zo da Wuri suyi Karatu Tare suna Taimakon juna inda Daya bai gane ba in Daya ya gane sai ya Tada Dan"uwansa haka suke yi Duk Karshen Sati basa yarda su Zauna haka ko suce sai Test yazo ko Jarabawa Zasu Fara karatu a"a su Tuni suke Karatun Duka Course dinsu Saboda Karatun Shi suka sakama gaba ba Shirmen da wasu ke yi ba.. Har Barci ya kwasheta Munari bata Biyo Bayan kiran nata ba,Karfe 2:30pm ta Farka ta sake Duba Wayarta Ganin Ba Missedcall din Munari yasa ta Kara Kiranta Nan ma bata Daga sai Hankalinta ya tashi tasan ba Lafiya ko Bata kusa da wayar in tazo ta gani Zata kirata. Saukowa Tayi Daga kan gado Tana gyara Daurinta Daya Warware gabam Madubin Dake Dakin ta Tsaya taga Fuskarta ganin batayi komai ba yasa ta Bude Akwatinta ta Dauko Jan Mayafinta ta Yafa ajikinta Ta Nufi Wajen da tayi Domin Ma"ajiyar Takalmaanta,Ta Dauko wani Flat Shoe red Colour Shima ta Saka ta Dauki Wayarta ta Fito falo ta Samu Mama na Zaune ta gama cin Abinci Tana gyanyandi Cikin Dariya tace"Mama kina jin Barci basai ki Shiga Ciki ki kwanta ba..? Kina ta gyangyadi a azaune kamar yadda Inno take yi..? Mama ta Farka Cikin Muryan Barci Tace"Kaniyarki Innon Kike cewa Tana gyangyadi a zaune..! Inteesar na Dariya tace"Kai Mama keda Umma bakwa so kuji an Taba Inno..mallam Babba yafi ku ji da wannan yar Tsohuwar matar tasa..! Mama ta yunkura ta mike tana Fadin"Kinga Laifinsa..? Mutum da matarsa kuna sakamai ido..! Inteesar Tace"Tsofai Tsofai dasu Mama..! Mama ta harareta Tana Fadin"Bana son Shakiyanci Iyayen namu ne Tsofai Tsofai Ai Soyayya bata Tsufa sai dai Masoyan su Tsufa Ballatana Irin Soyayyarsu su na Mutan Da..! Inteesar Dariya kadai ta saka Kafin Tayi mgana Mama ta Rigata da cewa"Ina Zaki kuma..? Ni ina nan Zaune bayan na gama cin Abinci gyangyadi ya kwasheni ban sani ba..Asama sama nake jin mganarki..! Inteesar tace"ki shiga ki kwanta Mama ahakan ai sai Kanki ya Sage..! Mama tace"To bari na dan Mike Saman kujeran nan..! Inteesar tace"Yauwa ko kefa Mama..Bari in leka Munari Tace yau Zata zo muyi Karatu kuma najita Shuru,Na kirata bata Dauka ba.! Mama na ZAma kan kujera Tace"Eh Leka Ki gani ko Lafiya..in Lafiya take ai da yanzu ta Shigo Gidan nan..! Inteesar ta Duka Tana Kwashe Filet din da Mama taci Abinci ta Fice dasu Mama ta Bita da adawo Lafiya. Sai da ta Biya Kitchen ta ijiye abun Hannunta Nan taga Sagir bai ma ci Abincin ba kenan bai Shigo ba Shima Ficewa Tayi Daga Gidan Cikin Takun na Natsuwa Zuwa Gidansu Munari. Sun gaisa da Iro Megadi Kamar yaushe In tazo gidan kana ta Nufi Cikin Gidan Cikin Sanyinta Iska na kadata kamar Zata Fadi. Sallama Tayi Daga Kofar Babban Falon Gidan nasu Munari Abba Dake Zaune Shiyajita sai ya Amsa mata Duk da bai san ko wacece ba. Turo Kofar Tayi ta Shigo Lokaci Daya tana kara yin wata Sallamar. Wannan karon Harda Safiya Da Yusuf a masu amsa mata Tana daga gefe Wajen Dining Tana goge goge Abba na Zaune Kan Daya Daga Cikim kujerun Falon Center Table na gabansa Dauke da Ruwa da karamin Kofin Tangaran,Sai karamin Qur"anin Dake Hannunsa,an Dauke wuta Shiyasa yau babu karan Tv. Abba yana Sanye da Shadda mai Ruwan madara Riga da wando kansa ba Hula ammh Yana sanye da Farin glass dinsa. Imran ne agefensa kansa da Idanuwansa na Duke ne yana kallon Zanen cafet din Dake Falo,sanye yake da Vest Fara Wacce ta kama jikinsa Sosai Har ta bayyana Karfinsa Domin gabadaya Muscles dinsa sun Bayyana sai Wando Baki 3Quaters,Tun Shigar Da yayi da Safe ce yaje jogging,Karan Sigari ce a Hannunsa Tana kunne Hayakinta na Fita sai sai ba Sha yake ba Gabadaya kansa na kasa ne ba wanda ma ya Fahimci wani Hali yake Ciki,Sai yusuf Dake gefen Imran din Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara. Abba ne ke mai Fadan Shan Sigarin Dayake yi ganin,Tun Safe bai ci komai ba bayan ya Dawo Daga Jogging Dinsa suna Breakfast Safiya tayi mai Tayi yace ya koshi Da Rana Tayi Lonching ma bai ci ba ammh Yusuf ya Shiga Dakinsa ya Tarar sai Busa ma Cikinsa Hayaki yake yi Shine ya kawo kararsa Wajen Abba For d First Time ganin yanzu Abba Alhandulillahi ya Dawo Hayyacinsa. Jikinta a sanyaye kanta na kasa ta kariso Falon Tunda taga da Mutane afalon,Gaban Abba ta Zube kanta na kasa Tana gaishesa ya juyo yana Kallonta Cikin Fara"a yace"Daugther Kin Tashi Lafiya..? Inteesar ta amsa kanta na kasa Ta Gefen Idon ta Hango Yusuf Zaune da Sauri Tace"Ina yini ya Yusuf..? Ina Yini Anty Safiya? Tafada bayan ta Daga kanta sun Hada ido da Anty Safiyan Dake goge Saman Dining Din da wani karamin Towel. Shima Cikin Sakin Fuska ya amsa mata da Cewa"Lafiya Lau Inteesar Hala kin ji kawar taki Shuri kika Biyo Sawunta ko..? Kai ta gyada Lokaci Daya Hancinta na Shako mata Warin Sigari Tunda ta Shigo Yayi mata Maraba sai bata kawo hakan ba aranta tace bamai Shan Sigari agidansu Munari sai ta Lakanta hakan da Yadda bata son Warin Sigarin Shiyasa take jin kamar Tana Jin Warinta sai dai zuwa yanzu Data dan jima afalon ta Fara gasgatan Hancinta. Safiya ce Dagachan Tace"Ai kawar taki yau Tatashi Batajin Dadi Shiyasa Baki ganta ba..Ki tashi ki SHiga Tana Cikin Dakinta..! Da Sauri Inteesar ta Mike kamar Tana kan kaya Zuciyarta ce ta Fara Tashi Miyanta ya tsinke,Sai kawai ta Saka Gefen mayafinta ta Toshe Hancinta Daidai Lokacin Data kai Dubanta kan Inda Taga Hayakin Sigarin na Fita Zuwa Saman Fuskar ma mallakin Hannun Dake Rike da Sigari Bata ga Fuskarsa sosai ba ammh ta Cika da Mamakin ganinsa Domin bata Taba ganinsa ba Sai dai tasan Munari na Fadamata Bayan Ya yusuf Tana da Wani yayan kuma yarda ta Lura Tana Matukar Tsoronsa. Abba ne ya Lura da yadda take Toshe Hanci Cikin kulawa ya kalleta yana Fadin"Inteesar Lafiya kuwa..? Da Sauri Inteesar tace"Abba..Warin Sigari bana so..Yana samin Tashin Zuciya da Amai..! Adaidai Lokacin Dayaji Muryanta kamar Saukan aradu acikin kunnuwansa tun Shigowarta bai maida Hankali Wajenta ba Yana Fama da Dacin Ran Fadan da Abba kemai,Sai yanzu yaji mganarta Sai kuma ya gane Muryanta Da Sauri ya Dago Idanuwansa ya Sauke a nata Karaf wannan lokacin a karo na Biyu Suka kara Hada Idanuwansu Lokaci Daya kuma Zuciyoyinsu suka Kara Bugawa atare kamar wanchan Lokacin. Imran kara Girman Idanuwansa yayi yana kallonta Tabbas itace ammh miye kawota Gidansu? Mganar Abba ce ta katse mai Tunaninsa Inda yace"Yi Hakuri..Maza shige Wajen Munari..Yanzu nake mai Fadan yawan Shan Sigarin Dayake tana Illah ga Lafiya Ke gashi ma Warinta amai yake sakaki shi kuma Hayakin itace abincinsa..! Kamar Abba ya Watsamai Gwarwashin Wuta haka yaji mganar Abba aransa ya ayyana Dama Marinsa Abba yayi wlh Daya fiyemai wannan Tozarcin gaban wannan Mara Mutumcin yarinyar nan za"a Tasashi ana mai Fada Lalle me ya Zama Dole yaci Ubanta Ko Zata gane Shi din ba"asanta bane,Duk da Abba ya riga yagama Sakawa yarinyar ta kara Rainasa Yana mata Fada agabanta. Mikewa yayi a Fusace kamar wani Damisa Daidai Lokacin da Inteesar ta Fara Tafiya Zuwa Dakin Munari yace"Ke..! Cikin Kakkausan Muryansa Cikin Tsawa da Bacin Rai Cak ta Tsaya Lokaci Daya ta Juyo Tana Kallonsa ai Ransa bai kara baci ba sai Da yaga yadda Take kara Toshe Hancinta da Mayafinta Sai yaji kamar yayi Tsalle ya gansa a gabanta yana Kwallo Da ita Har sai ya Rakata Waje da Duka. Abba da Yusuf suka Saki baki suna Kallon Ikon Allah Safiya bata Wajen Tana Kitchen sai dai har chan Taji Tsawan Shiyasa ta Fito da Sauri. Cikim Takunsa na Takama da Sassarfa ya Fara Taku zuwa gabanta yana Fadin"Ni sa"an wasan ki ne..? Ni Tsaran wasan ki ne kina kallona kina Toshemin Hanci..? Ya Karishe Fada yana Nuna kansa Cikin Dakuna Fuska Inteesar kuma jada baya take yi acikin Ranta kuma Tana ayyana Lalle ne ma wannan Mutumin bai da Mutumci Dukanta Zai yi ko menene Nufinsa..!? Fadi take Munari batayi Sa"an Yaya bane..Mara Mutumci Tsageri Kuma Dan iska Saboda Tsabar Tacewa Shi a gaban Abba ma Shaye Shayensa yake Baya ko Shakkar Boye Mummunan Laifinsa kamar yadda Sauran masu aikata Laifi irin nashi suke yi. Yusuf ne ya Mike yana Fadin"Kai Imu Lafiyan ka kuwa..? Abba kuma yana Zaune ne kawai yana Kallon Ikon Allah. Inteesar Tana da Tsoro ammh kuma Bata bari a Takata ko Yayane Juya Manyan Idanuwanta tayi Lokaci Daya Tana Tura bakinta ta Cikin Mayafin Hannunta tace"To nifa bana son Warinta..Amai take sakani..! Tafada Lokaci Daya tana kallon karan Sigari da Har Lokacin Take Rike Tsakanin yatsunsa manya Guda Biyu na hannunsa Cikin kwarewa Inteesar tace acikin Ranta"Jar uba..Lalle wannan ya kware a Harkan ji wani Rike Sigari..! Bata gama Mganar Zucinta ba Taji yace"Ashe kuwa yau Zaki Aman kayan Hanjin ki..Maza ki Cire Abunda kika Sama Hancin ki..Zan gani yau ko Zaki mutu ne...! Yafada Lokaci Daya kawai Ransa na kara kuna ganin yadda yarinya kamar Wannan da bai Wuce ya saka Hannu ya Damketa ya Murjeta ba itace Zata Tsaya yana Fada Tana Fada..? Kai bata isa ba Dole ya koyamata Hankali ayadda yake ji kamar yayi ta Dukanta Har ta suma Ta Daina Numfashi. Kallon Anya kana da Hankali Inteesar Tayi mai kafin ta Nuna kanta Tana Fadin"Wai ni...!!? Kai Imran yaji kamar Wuta ne acikim Zuciyarsa Saboda yadda ta Fara Tafasa Tuni Jiyoyinsa sun Tashi na Saman kansa Radau Tuni ya Fara Fitar da wani Huci Kirjinsa na Sama yana kasa. Kamar kiftawar Wani abu sai gashi a gabanta so yayi ya saka kafa ya Tadiyeta ta Fadi sai ya fasa ya Daga Hannu zai kai mata wani Dukan da Kila sai tayi Sati acikin Coma bata Farfado ba,Inteesar Da Tsoro ya kamata ganin yanayinsa ta Falfala da Gudu Zuwa Bayan Safiya Cikin Alamun kukan Shagwabanta Tace"Wayyo Allah na..Abba ka gansa ko..? Tafada Tana kara Boyewa Bayan Safiya Jikinta na Rawa ganin yadda ya Rikide ya Sauya Lokaci Daya Ganin haka yasa Abba yace"Yusufa Rikomin shi kada ya Illata yar Mutane..! Da Sauri Yusuf ya Mike ya Rikosa sai ya Fizge,Kallon Inteesar kawai yake da Rinannun Idanuwansa yana Tunanin Ko Kasheta ma zai yi ya Huta da Yadda yaji Zuciyarsa na Fitar da Wani Zafi. Abba ne ganin haka ya Mike da kansa ya isa ga Imran ya Rikosa Da yaso ya Bangaje Yusuf din sai ga Abba sai ya Dakata yana Sakin Huci. Sigarin Hannunsa Abba ya amsa ya Mikama Yusuf yana Fadin"Fita da ita..! Amsa yayi ya Nufi Hanyar Fita da ita Shi kuma Abba ya Riko Hannunsa ya Zaunar dashi kan kujera yana Fadin"Imran wannan bakar Zuciyar taka ina Rokom maka Allah ya Rabaka da ita..Tun Zuwaira nada rai Tasha maka kukan wannan bakar Zuciyar taka..Tasha Fadamim Tayaya kana irin wannan abubuwan Za'a Dauki mace abaka..? Wanda bai iya Kula da Rayuwarasa bane zai kula da na wata..? Ko Dago kansa bai yi ba kansa na kasa Shi Abba wai baisan kara ma wutar Abun yake ba yana Mai fada gaban wannan Mara mutumcin yarinyar bane,Shiyasa kawai ya Mike saboda in yacigaba da Zama komai zai iya Faruwa ba Cikin Sassarfarsa ya Wuce Dakinsa ya Shige Lokaci Daya yana Bango kofa Bumm! Abba ya Bisa da kallo Kafin ya Kada kai yana Fadin Allah ya Shirya. Inteesar ya kallata Da Tayi Tsuru Tsuru Yace"Inteesar kiyi Hakuri kin ji ko..? Yi tafiyarki Wajen Munari haka yayan naku yake sai Hakuri..! Kamta ta Sadda kafin tace"Bakomai Abba.." Ta juya zuwa Dakin Munari sai ma ta ganta akofar Dakinta Ashe Tun Tsawan Farko ta Fito ganin Abunda ke Faruwa ya bata Tsoro yasa ko Fitowa ta kasayi kada ganin Wajenta tazo itama ahada da ita. Hararanta Inteesar taja Tana Fadim"Ashe kina Tsaye kina ganin wannan Mahaukacin yayan naki Zai Dake ni..? Munari batayi mata mgana ba Tayi Saurin jan Hannunta suka fada Dakinta ta maida Kofa ta Rufe Tana Waigre Waige,sai abun ya bama Inteesar Dariya ta Zauna Bakin gado Tana Fadin"Dillah bsshi fa anan Dakin..Naga kina ta Waige Waige ne..! Munari ta Zauna kusa da ita Tana Sauke Numfashi tace"Baki san wanene ya Imu ba..Da baki Fara yana mgana kina maidamai ba Besty..! Inteesar ta Saki karamin Tsaki Tana Fadin"Munari Daman wannan Dan iskan ne yayan ki..? Tabdijam gaskiya baida Mutumci Wlh...! Kallon da Munari tayi mata ne yasa ta Fahimci barnan Datayi da Sauri ta Wayance Tana Fadin"Yi hakuri ba Haka nake nufi ba..Ammh kawai sai ya Dakeni..? Kuma fa Shaye Shaye yake har acikin gida agaban Abba..? Ranar da na Fara ganinshi Tare da Sagir yana Shan Taba sai da nayi amai yanzu ma haka Zuciyata tashi Take yi Wlh..! Ta karishe Fada tana wani Dakuna Fuska. Munari ta karkace kai gefe tace"Ya Imu baya Shaye Shaye Besty..! Inteesar ta Kalleta tace"Ita Sigarin kin Cireta a Ciki ne..!? Munari Tace"Kefa wani Lokacin kina jin kanki kamar Wata bagwariya..Sigari ai ba Bugarwa kuma Bata saka maye bata Cikin kayan Shaye Shaye..! Inteesar ta Bugamata Harara Tana Fadin"Kare mai Tunda Yayanki Ne besty..Ammh ni kam kiyi hakuri bazan fasa Fadin gaskiya ba Itama Sigarin ai Duk Mayen ne miye maraban Dambe da Fada..? Nifa Tun ina karamata Na daukan mai Shan Sigari nake Dan iska..! Munari Tayi Mirmishi Tana Fadin"Ko Daya..Ba ina karema Ya imu bane sai Don yana Dan"uwana ba A"a Sai dan Gaskiya nake Fadamiki baya Shan kowani kayan maye banda Sigari..Ita kam Ta Zama addict atare tsshi Dashi..Zai iya Shanta Daga Safe Har Dare bai Nemi wani abinci ba ko Ruwa ba..! Inteesar ta Zaro ido Tana Fadin"Kuma Lafiyarsa Kalau..? Munari tace"Ba gashi kingani ba..Ai da kim Tsaya daya Nuna miki Lafiyarsa kalau..! Inteesar tace"Tabdijam wa ni..? Na Tsaya ya Karyani..? Naga yadda yake Huci kamar Zakin Daya Kwana Biyu bai Samu Nama ba..tsoro ya kamani badomin su Abba ba yau da na gama Yawo wannan Mara mutumcin yayan naki! Kallon ta kawai munari tayi batayi mgana da Sauri tace"au na manta Sorry..! Munari ta kada kai kafin Tace"ke mai Sa'a ce Besty..! Inteesar ta Kalleta Tana Fadin"Sa"ar me..? Munari tace"Banta ba ganin ya Imu ya Tsaya yana mgana da mace Haka kamar yadda kukayi ba..ko mu da muke kanmensa baya mgana Damu Mu maida masa martani Daga kusa kusa..Baya som ka Rainashi ko alama Yana Daga Cikin Abunda ya Tsana Kazo wucewa ko kazo gabansa yana Shan Sigari ka Toshe Hanci..! Wlh ni nan ya Taba kamani na Toshe Hancina Domin Nima bana son Warinta Wlh Tallahi Daya Kama Bakina ya Damke Ya Rika Fesamin Hayakin Sigarin acikim Hancina sai da kara Daya ta kare Hayaki na Shiga Cikina da ace ina da Asthma na Tabbata da sai na Mutu Har Lahira aranar..! Inteesar ta Kwalalo ido Cikin mamaki da Tsorata tace"Kai Besty..Kuma kika Tsaya..? Meyasa baki gudu ba..! Munari ta saka Dariya Tana Fadin"Dana Gudu da kila Har da Duka Zai Hadamin..Ai shi bakayi mai Laifi Ya Kiraka ka Gudu..Zai ga ka Rainashi Saboda Zuciyarsa In ya kama Dukan Mutum sai ya Sumar dashi..! Zuwa Lokacin Inteesar ta gama Tsorata Cikin Kwalkwal da ido Tace"Na Shiga uku Besty..Ya Zanyi na koma Gidan Mama yau..!Me munari Zatayi in ba Dariya ba Harda Dukawa Inteesar ta Daka mata Duka abaya Tana Fadin"Shegiya Daman Ciwon karya kike yi ko..?Domin ni ban ga alamun patient anan ba..! Munari ta Dago Tana Lamgwabe Wuya Tana Fadin"Wlh bani Lahiya Zazzabi yau na Tashi Dashi..Taba Jkina ma kiji..!ta fada Tana Daukan Hannun Inteesar ta Dora Saman Wuyanta. Inteesar taji da Dumi tace"Eh gaskiya kina Fever to kin sha mgani..? Kai ta gyada mata Tana Fadim"Tashin na kenan tunda nssha Mgani..Sai naga Kiranki a waya ina Shirin kiran ki naji Tsawan ya Imu Shine na Leka sai na ganki Kina ta Zare ido nace yau Besty ta Fada inda bai Dace ba..! Inteesar tace"Umh bari kawai..Ai Insha Allahu bazamu kara Haduwa ba.Na tsorata da Labarin da kikabani im na Auna yadda naga Lokaci Daya ya koma..Ammh dai ke bai taba Dukkan ki ba ko..? Munari tace"ya taba Kamar sau Biyu ko...Inaganin. shima mari ne da Tokari.Ni ai ina Kiyayemai Anty Asma"u ce Tasha Wahalan sa sosai Har Sumar da ita ya taba yi Dayake ita ke Binsa..! Inteesar taji Gabanta ya Fadi ta Dafe Kirji tace"Innalillahi Anya bai da Aljanu..! Munari tace"ke Lafiyansa kalau fa..! Ta karishe Fada Tana Dariya Inteesar Tace"Ai naji abun nasa ne bana Hankali bane..Allah Sarki Yanzu ina ina Anty Asma"u? Hala tayi aure ne..naji baki taba bani Labarinta ba..! Munari Tayi Shuru batace komai ba Inteesar ta Kalleta kafin Tace"Ko Ta Rasu ne..? Munari ta Kalleta da Sauri tace"Ya akayi kika sani..?Inteesar Cikin jimami Tace"Yadda naga kin yi ne Besty..Am sorry bansani bane da Ban Tambaya ba Allah ya jikansu da Rahma Kice Bayan Rashin Anni Harda ta Asma"u ma kunyi..So Sad..! Dayake inteesar din ta Taba Tambayanta Ina Mahaifiyarsu tace mata ta Rasu. Cikin Wani yanayi Munari ta amsa da Ameen. Daganan suka bar mganar suka Shiga Wata,Suna ta Hira makaranta suna Dariya,Sai ga Anty Safiya ta Shigo Itama ta Shige Cikinsu suna ta Hira,Sai bayan La"asar Inteesar Tayi Shirin Tafiya bayan Tayi Salla,Basu yi karatun ba sai gobe lokacin Munari ta kara jin Sauki, Sun Fito Falo Munari taji Sauki ta Rakota suka Iske Anty Safiya tana Kallo Munari ta Tambayeta Abba tace Yusuf ya Dauketa sun Shiga Cikin gari zama Wuri Daya ba Dadi Munari ta kada kai Tace hakan nada kyau sosai. Daganan Sallama Inteesar Tayi mata Suka Fice Haraban Gidan suna Tafe suna Hirarsu basu ma Lura da Wanda ke Tsaye a Haraban gidan ba jikin Mashin Dinsa,da Tun Fitowarsu Idanuwansa Gabadaya yana kansu..! *Nidai ba ruwana na Falla a guje���kada Oga Imu ya Hada dani..* *Shakira..* 3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*      *🅿�19* Lokacin Daya koma D'akinsa yana Sakin Huci yaji kamar yayi Bindiga Shi kadai,Saboda Zuciya sai da yasaka Hannunsa ya Naushi Dayan Hannunsa,Kafin ya Zube kan gado yana maida Numfashi,Yaso ya Busa Sigari ko ya Daina jin radadin Abunda yarinyar nan tayimai,Sai dai kuma ya kasa Saboda Abba Yana ganin kamar in yasha bai ji mganarsa ba kenan,Kawai sai ya Matse bai sha ba,sai dai Saboda Zuciyarsa tayi sanyi yasa ya kira Sagir kan yazo su Fita suje Kallan kwallo,Ko ya ji Sanyi a ransa yana kallon Kwallo Tun a Abaya sai dai da suka Dawo kano ba kasafai yake zuwa kallon ba Saboda Hayaniyar Dake Wajen,Ko yaje baya ma iya Zama yau din Yana so yayi nisa da Bacin rai Shiyaasa zai Fita Daga Gidan kada Takaichin Rashin kunyar Inteesar yasa Zuciyarsa ta Buga. Abunda yake karamai Takaichi da Mamaki Tun abaya Dayake amsa Sunansa na Imran ba macen Data Taba yimai Abunda Mara Mutumcin yarinyar nan Tayi mai ballatana Yanzu Dayake jin kanshi yana Daidai da Kugun kowa Bai jin zai iya Daukan wannan iskancin kuma ba Kowa yajamai ba Sai Sagir da Munari su su ka Fara Gayyatota Cikin Rayuwarsa ba Domin Sagir ba bazai Taba Haduwa da ita ba Tun Farko ba kuma Domin Taurin kan Munari ba Da bata Jawota Cikin Gidan nan sun Sake Haduwa ba.. Tun Dazu ya Fito da Niyyar Tafiya ammh ya kasa bai san mai ya Tsaidashi ba Yana Tsaye Jikin Mashin Dinsa kawai Zuciyarsa ta Tsaya Waje Daya Tana Wani Tunani na Dabam. Koda su Abba zasu Fita sai da Yusuf yamai Tayin Fitan yace shi ba zai je ba Haka kurum saboda ya rasa aikin yi sai ya kama Hawa Mota ana Zagayen gari dashi..? Yusuf yace"Nagode Nida Abba ne Marasa aikin yin kenan..!? Imran ya Dakuna Fuska yace"Ni dai ban ce ba..! Yusuf bai kara bi ta kansa ba,Haka ma Abba Daya kada kai kawai yana ma Imran din addu"an Shiriya. Har bayan Tafiyarsu yana nan Tsaye shi bai koma Cikin Gida ba Shi kuma bai Hau Mashin din ya Tafin ba ana Cikin Hakane sai ga Munari da Inteesar sun Fito Inteesar Zata koma Gida Munari Zata taka mata Tun Daga Nesa ya Gansu bai tsaya kurama Munari ido ba Sai dai baisan Ta ina kuma wani Lokaci ko kuma Sanda Idanuwansa suka Raja"a a kallon Tsarin Hallitar Inteesar din Tun Daga nesa,Zuciyarsa ce take Turasa shi kuma yana so ya kaucema hakan sai dai ita Daman Zuciya ita ke Sarrafa gangar Jikin Dan adam Wannan karon Duk yadda Imran yaso ya kaucema Bin Umarnin Zuciyarsa abun ya gagara Tundaga nesa yake kare mata Kallo Har suka Kariso gabda shi basu gansa ba Hankalinsu na Wajen Hiran da Sukeyi suna Dariya Cikin Nishadi Tundaga Kallon Sama da Kasa yake Bin Inteesar Dashi Mamakin Sirita kanta yake yi yana mamakin Daman mace ce wannan..? Abu kamar Kara ai wannan inda ma ya Damketa ya Tabbata Babu abunda Zai dauka ajikinta sai dai ya Kasheta Tabe baki yayi a Fili acikin Ransa yaji sam Tsarinta bai Burgesa ba a tsarin dai Mace,ko abaya bai cika karema Mata kallo ba Tsakaninsa da mace Kallo Dayane Na Addini Shima in ya Zama Dole aiki ya Hadasa ko Mu"amalan Data Zama Dole a wajensa. Sai dai Duk bai Maida Zabinsa a wani abu mai Girma ba,Bashi da Burin auran karamar Mace irinsu Munari kayan Raini da Lalaci maimaikon Ita Zata kula dakai Kaine ZAka koma kana Bin Bayanta kamar Wani Sakarai Yafi son auran Babbar Mace Wacce Ta san Ciwon kanta Wacce Zata iya Kula da kanta wacce ta san komai ba sai an zauna ana Fama da ita ba. Yana wannan Tunanin Daidai Lokacin da Inteesar ta Dago idanuwanta Daga Mganar Datakeyi ma Munari Karo na Uku Suka kara Hada Idanuwansu Kuma Alokaci Daya Suka ji Bugun Zuciyarsu Kamar yadda yasha Faruwa in suka Kalli Juna Cikin ido. Inteesar Taji Jikinta ya Fara rawa da Sauri ta kauda kanta Lokaci Daya Tana Damke Hannun Munari Tana Fadin"Na shiga uku na Munari..Ga Yayan ki chan zai Dake ni ko..? Wayyo Gashi Abba baya nan yanzu ya Zanyi..? Sai Alokacin Munari ta gansa yana Tsaye Jikin Mashin dinsa Sanye da Riga da wando na Kirar Armani Rigar Farace mai Dogon Hannu Tana da Layin Zanen Ash ajikinta Sai Wandon Jikinsa Ash Colour ne,Kafarsa Sanye Cikin Wani Bakin Takalmi mai Igiya Booth,Na Fatar Damisa,Kansa yasha Gyara sosai yana kyalli Key din Mashin Dinsa na Hannunsa yana Kadawa Ayayinda yayi Tsayuwar Nauyin Kafa Daya kan Daya yana Binsu da Wani kallon da suka kasa Gane Manufarsa. Ita kanta Munari Jikinta ya DAuki Rawa Cikin Dauriya ta kara Rike Hannun Inteesar din Tana Fadin"Kada mu nuna mu gansa..Lallaba Besty ki Tafi Kada wata mtsalan ta kara Faruwa..! Jin haka yasa suka Fara Taku Sadaf Sadaf kamar wadanda sukayi Sata,Ganin haka yasa ya Daka Musu Tsawa Cikkn Dakakkiyar Murya yace"Kai ina Zaku..? Cak suka Tsaya sun kasa gaba Ballatana Baya,Cikin Daure fuska da Yanayinsa yace"Tsayuwar Uban me kuke yi anan..? Ku zo nan..! Yafada Cikin Kaushin Muryansa na koyaushe ba waasa. Inteesar tazaro Ido Tana kallon Munari itama ita take kallo Kafin Tace"Sai muje wai Besty..!? Munari tace"Tafiyarmu karin wani Babban Laifi ne..Wato Raini gwara Muje kawai Insha Allahu bazai mana Komai ba..! Inteesar tace acikin Ranta"Tabdijam wazai je..?ya sumar dani..Dole ne na Sama ma kaina Mafita. Da wannan Tunanin taji Munari ta Fara Janta suna Nufarsa Sai da suka kusa kawowa garesa Inteesar ta Kara Rike wayarta sosai a Hannunta Ta Danke Takalminta Dakyau Munari ba Zato kawai taji Inteesar ta Warce Hannunta ta Kwasa da Gudu Kamar Walkiya sai gata Bakin get Ta Tsaya Tana Haki Munari da Imran suka Bita da kallon Mamaki. Kallon Imran Tayi ta Juyamai ido Kafin ta Rike kunnuwanta ta Marairaice Fuska Alamun ban Hakuri kana ta Juya da Sauri ta Fice Har da Gudunta Gudun kada ya Biyota.. Munari ta Tsure Tana Tunanin Kila yau Kafin su Abba su Dawo Ya Imu ya kusa Kasheta Ga Laifin Fitowa ga Laifin Inteesar Da zai hau kanta. Ammh sai mai Data saci kallonsa Karo na Farko Tun Bayan Dawowarsu Kano Dataga mirmishi Saman Fuskar Imran sai abun ya bata mamaki Inda yake Kallo tabi da kallo Bakin get ne inda Inteesar ta Wuce. Sai abun ya kara bata mamaki Matuka ganinsa yana kada kai yana Mirmishi Haka kurum yaji Wani Nishadi da abunda Inteesar din Tayi duk da ba Komai ke basa Nishadi ba. Munari ne taga kamar ya manta da ita yasa Cikin Rawan Murya tace"Ya Imu g..Gani..! Sai alokacin ya kalleta Cikin Daka mata Tsawa yace"Da kika Fito ina Zaki..? Munari taja Baya Jikinta na Rawa tace"Dama..Da..man ina so Zan Rakata ne..! Wani kallo ya watsa mata kafin yace"Shiga Ciki kafin nayi kwallo Dake..! Ai da gudu Munari ta Nufi Cikin Gida aranta Tana ayyana ai ta isa Barka da ya Kyaleta bai Tabata ba itama da Gudun ta Shiga Cikin Falon suka yi Kicibis da Anty Safiya ganinta haka yasa ta Tambayeta Lafiya nan take Labartamata Abunda ya Faru Safiya Tayi Dariya batace komai ba Illah Allah ya kyauta Domin Lamarin Imran Sai dai Allah ya kyauta kawai. Haka Itama Inteesar ta Shiga Gida a Tsorace,Sagir da Mama suna Falo Sagir ke Cin Abinci suna Hira SAma sama da Mama ganinta yadda ta Shigo Duk a tsorace Yasa Sagir da Mama suka Hada bakin Wajen Tambayanta Ko Lafiya..! Sai da Ta Zauna ta Sauke Tagwayen Numfashi kafin tace"Ya Sagir Ashe Abokin naka mai Shan Sigari Yayan Munari ne..? Tab ayau Allah ne ya Kwaceni ba Domin Abbansu da ya Sumar dani nima Domin na Lura Shaye Shayensa ya Fara Tabamai Kwakwalwa..! Sagir ya Zaro ido Kafin ya ijiye Spoon din Hannunsa yana Fadin"Kai badai Imran ba..! Tabe Baki Inteesar Tayi Tana Fadin"Oho ni ina nama nasan Sunansa Inga shi..! Nan ta Fara basu Labarin Abunda ya Faru ta karishr da Fadin"Ina zan je Ina jin Besty Muna tana Labarin in ya Fara Duka sai ya Sumar da Mutum aiko na Gudo chan na barsa da Munari Allah Sarki Allah ya kareta Kada ya Huce akanta gashi su Abba sun Fita..! Sagir Da Mama suka Kalli juna Cikin Mamaki kafin Sagir ya kada kai yana Fadin"Imran baya Shan komai sai Taba Inteesar..Kuma Lafiyarsa Kalau haka Hallitarsa yake yana da Zuciya ce sosai wanda Wani Lokaci Baya iya Contolling din Fushinsa..! Mama ta Jinjina Kai tace"Koda ga Alamunsa..Yata ki Daina cemai yana Shaye Shaye kin ji ko..? Inteesar ta Gyada kai alamun Taji Sagir ya Mike yana Fadin"Ita kanta Taban da kika ga yana Shanta abaya bai ma Santa ba..Kawai yanzu din waniYanayi ne na Rayuwa ya kawosa Haka..Zaman da kikaga nayi kiransa nake jira ya Kirani yau zamu je kwallon Ball Daganan na gane Ransa yana bace ne zai Shiga Mutane in Ransa ya baci baya Kadaice kansa Saboda Kada Zuciyarsa ta Buga ya Gwammace ya Shiga Cikin Hayaniyar Daya Tsana Daya Zauna Takaichin Abun ya illatashi..! Inteesar ta Jinjina kai kafin Tace"Kai Shi dai Matarsa ta Shiga uku..Allah yasa ma ya Samu mai auransa Mama..! Daga mama Har Sagir sai da sukayi Dariya Mama Tace"In bai samu mai Auransa ba sai na bashi ke..! Inteesar ta Kwalolo ido kamar Taga Wani abun Tsoro Lokaci Daya Ta Dafe Kirji Tace"Ni kuma Mama..?wlh ko Narasa mai sona Sai dai na Mutu ba aure bazan Taba auran wannan ba Tabdijam. Allah na Tuba Mama bari wannan mganar kada yan Ameen su Amsa..! Ta karishe Fada Tana wani Dakuna Fuska Mama Dariya ta sakamata Shima Sagir din Dariyan yake ya Fice yana Fadin sai ya Dawo Mama ta Bisa da adawo Lafiya. Wannan mganar da Mama Tayi duk sai ta Damu Inteesar Bini Bini ta Tuna ta yanka tsaki afili Tana Fadin Allah ya Tsareni da auran wannan Mara Mutumcin..! Har tayi wanka Tayi Sallar mganriba ta Dibo Abinci tazo Tana ci Tana Tsaki Mama na lura da ita batace mata komai ba sai Dariyan Wauta irin ta Inteesar take Daga wasa sai ta Dauki abun da Gaske kadan taci Abinci sai ta Sha Tea kawai Saboda Zata kwanta ne. Washagari da Daddy ya kirata da Safe Abun na Ranta sai da ta bashi Labari Komai Daya Faru Harda mganar Mama ta Karishe da Fadin"Daddy wai kaji fa Mama..Dan iskan zan aura mai Shan Sigari gashi Daddy Mahaukaci ne Wlh Duka fa wai yake har sai ya Sumar ni Wlh yanzu ma Tsoron Zuwa Gidansu Munari nake Daddy..! Daddy na Dariya yace"Intee Daddynta..Ki daina Cemai Dan iska kin ji ko..?ko bakomai Ai Yayan Kawarki ce kinga ai yayanki ne kuma ba kyau Raina na gaba dakai ki Daina Saboda in ita Munarin taji kina cewa haka bazata ji Dadi kina Zagin Yayanta kamar yadda kema Bazaki ji Dadin azagar miki Yaya Basheer din ki ba..! Inteesar ta Tura baki Kamar Yana ganinta Tace"Allah ya Tsare Ya Basheer dina ba D'an isk..! Umma Dake Tsaye gefen Daddy Tana Hadamai Tea a Saman Dining yake Zaune Tashin su kenan zasu yi Breakfasat ya Kira Yar Lelen tasa Wayar Tana Handfree ne Umma Tana jin komai ita ta Katse Inteesar bata karisa ba Tace"Inteesar meyasa bakya jin mgana ne..? Ana miki Fada kina kara Sakarci..Ki kiyayi kanki fa Kina cemai D'An iska Tsaranki ne..Kince Yayan kawarki ce..Kuma kince Abokin Sagir ne Shine zaki Zauna kina Kiransan Dan iska mara Mutumci..? Haka muka Koya miki kiyi ma na gaba Dake..? Ta Karishe Fada Cikin Bacin rai Daddy bai ce komai ba Sanin gaskiya ne gwara arika Gyarama Inteesar din in Tayi wani abu. Sai dai kallonta yayi yana Fadin"Salaha ki mata a Hankali don Allah..! Ko kallonsa Batayi ba ta Cigaba da Fadin"Ki Daina wannan Sakarcin ke ba yarinya bace yanzu..Ina so ki Sani kada mu rika Zargin mutane in bamu san komai akansu ba kada mu yanke musu Hukunci..! Inteesar da Jikinta yayi sanyi Karo na Farko tace"Bazan Kara ba Umma..Kiyi Hakuri..! Jin haka yasa Umma ta Sasaauta Tana Fadin"Yauwa ko kefa Yar Umma da Mamanta..Daga yau in kika gansa ki Rika gaishesa kin ji ko..? Duk wanda ya Girmeka yayanka ne Balle ma Yayan Kawarkice munari kikace..! Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"ni fa Umma tsoro nake ji kada ya Dakeni..kin jifa Munari tace yana Duka Har yana fa Sumar da Mutum..! Ba Umma ba Harda Daddy sai da yayi Dariya Cikin Dariyan ne Daddy ke Fadin"Bazai miki komai ba..Daga gaisheshi sai duka..? Kada ki Damu kin ji Intee Daddy kedai ki Zama mai Ladabi da Natsuwa a Duk inda kika je..! Inteesar tace"Insha Allahu Umma..! Umma Tayi mirmishi Tana kallon Daddy tace"Allah yayi miki albarka ya Karatun..? Ina maman taki..!? Inteesar tace"Alhamdulillah Umma..Mama kuma Tana Lafiya Tana Tsakar gida..! Umma tace"Badai aiki take yi ba kina kwance.? Da Sauri tace"A"a Wlh Nagama Duka ayyukan tana dai Zaune ne Tana Shan Hantsi suna Hira da Ya Sagir..! Umma ta kadai kai Tana Fadin"Naji Dadin haka Allah ya bada Sa"an karatu Sai a kula Sosai kin ji ko..? Inteesar tace"To Umma..Bama Daddyna Wayar..! Daddy Dake gefe yace"Gani nan Inteen Daddynta..! Inteesar Tayi Dariya kafin Tace"Daddy ina ya Basheer ya manta Dani kwana Biyu ko..? Daddy tace"Injiwa..? Aiki ne yayi masa yawa ammh Zaki jisa da kuma Rashin Lafiyar Matarsa...Su Abiden ma Jiya suka koma suna nan Tare Damu.." Inteesar tace"Wayyo Har yanzu Jikin nata..? Allah ya bata Lafiya Daddy wai Ciki ne da ita..!? Umma Dake Turama Daddy Mug Din Tea gabansa ta Rike baki Daddy na Rike Dariyansa yace"Eh haka akace waya gayamiki..!? Inteesar tace"Ya Basheer ya gayamin..! Umma tayi karaf tace"bana son Shiga mganar manya Intee..! Daddy shima ya karbe yana Fadin"To itadin me kika maida ita..? My Intee is Not a Small Bby kamar yadda kike Tunani..! Umma tace"Yau kuma..? Ka manta kai ke Fadamin Kullum Intee yarinya ce..! Daddy yace"Eh ina nan akan bakana Sai dai ba yarinyar da kike Tunani ba..She know wht she is Doing..! Baki Umma ta tabe tace"Allah ya kyauta..! Lokaci Daya jan Daya Daga Cikin kujerun Dinng din Dake kusa da Daddy ta zauna ,Inteesar Dake Jinsu a Waya aranta ta Murmusa tana Fadin Daddy bazai Saki ba ita kuma Umma bazata Daina Jayayyaba. Cigaba da mgana sukayi da Daddy gabda Zasu yanke kiran Take Taambaysaa Daada ya jikinta..? Daddy yace"Ta samu Sauki Sosai Last Week naje na Kara Dubata..! Inteesar Tace"Allah ya kara Lafiya..Ka gaisheta Daddy..! Yace"Zataji ki kirata Da kanki mana..Tana Tambayanki indai naje Dukku..! Inteesar tace"bani da lambarta a wannan Wayar ka Turomin Daddy..! Cikin jin Dadi yace"Ok zan Turo miki..Bye zamu Breakfast ne sai Zuwa anjuma zan kiraki..! Inteesar ta Shagwabe Tana Fadin"Wait Daddy..Yaushe zaka zo..! ? Tunda kuka kawoni Almost 4 to 5 weeka ba wanda ya kara Zuwa ya Dubani..? Daddy yace"Sorry My Angle..Rashin Lafiyan Daada yasa baki ganni ba..Ammh ki saka Ganina Next week in ban samu Zuwa ba Basheer zai zo in kuma Munzo Tare shikenan..Akwai wasu Karafan da Zamu zo mu siya anan kanon..! Tsalle Intee ta Daka Kafin tace"Plz Come Daddy Don Allah..! Cikin Farinciki yace"Insha Allahu.." Daga haka suka yanke kiran Bayan sunyi Sallama Umma na Jinsu Tana ta Kurban Tea dinta Lokaci Daya tana Hadawa da Soyayyan Dankali da Kwai Kala batace ba Shima suna gama Wayar ya Fara karyawa Cikinsu ba wanda ya kara mgana Har sai da suka Kamallah. Inteesar na gama Wayar ta Fita Tsakar Gida Tana Gayama Mama Mganar zuwan su Daddy Mama na kan kujera yar Tsugunno ta Fadada Fara"arta Tana Fadin"Kai masha Allah..Allah ya kaimu Allah ya kawosu Lafiya..! Intee ta amsa da Ameen Tana Fadin"Mama ya Sagir ya Fita ne..? Mama tace"Eh yanzu ya Fita Kamar an Kirasa a waya ne..! Kai ta kada mata Kafin ta Koma Cikin Dakin. Ba Dadewa sai ga Munari Tazo Dauke da Tarin littafai nan Waje ta Fara Tsaayawa suka Fara gaisawa da Mama kafin ta karisa Ciki,Rumgume juna sukayi da Inteesar suna Murna kafin su Zube kan gado suna Dariya Abun na Ran Inteeaar Cikin Zolaya tace"Besty ya kika kare da wannan yayan naki..?yama sunansa..? Munari tace"Au yau kuma Sunansa kike Tambaya..? Ai da D"aniska mara Mutumci kike kiransa..! Inteesar sai taji kunya Cikin Sanyin Murya tace"am sorry Besty..Nasan ban kyauta ban kara kiransa da wadanan sunayen Gayamin sunansa Allah dashi zan Rika kiransa..! Munari tace"Imran muna kiransa Ya Imu..! Da Sauri Inteesar tace"Yauwa Ya IMRANN..ya kuka yi Dashi..?na dawo gida ina ta Tunanin ko Kila jiyan ya Sumar Dake da duka..!ta Karishe Faada Tana Dariya Duka Munari ta Dakamata Abaya Tana Fadin"Muguwa ba Mutuwa bace kin manta ne ba Suma da kika gudu kika barni SAi yanzu ne zaki Tuna dani..! Inteesar na Dariya tace"To sai na Tsaya..? Wlh ban tsayawa Gudu ya Zama Dole Besty nidai gayamin Allah yasa bai Dake ki ba..? Munari Tace"Baimin komai ba Wlh..Sai yace na Wuce Cikin gida kafin yayi Kwallo Dani..! Atare suka saka Dariya Har da Tafawa nan suka Cigaba da Hiransu Munari na kara bata Wasu Labaran Halin Imran Inteesar taji ai yama Wuce yadda Take Tunaninsa A Tsegaranci Shi lamba Dayane. Ba su Fara karatun ba sai da Inteesar ta Zubo musi Dambun Nama ta Dauko musu Lemo suna Ci suna Korawa da Lemu suna Karatu ganin haka yasa Mama tace suyi Karatunta ita Zat Dafa abincin Ranar. Haka kuwa akayi mama Tayi musu Danwake da mai da yaji da salad,Sukaci sosai Harda Santi Munari tace"Ya Imu nasan Danwake sosai ammh in nayi agida sai yace ban iya ba..Mama tafi ni iyawa..! Mama na gefe tace"Ai yanzu ma Sagir yazo ya Daukan musu suna Shago zasu ci..Ni kaina Saboda shi nake yawnn yin Danwaken..Kuna Cikin Daki Dazu ya Shigo muka gaisa yake Cemin Mama ina Danwake kwana Biyu..? Shine nace yasha Kuruminsa yau Saboda shi Zan yi Danwaken..! Munari ta Zaro ido Tana Fadin"Ammh baisan muna nan ba ko mama..? Mama tace'A"a ina ma ya wani Damu da ku..Bai ma san kuna nan ba inaga..! Ajiyar zuciya Munari ta Sauke Inteesar na mata Dariya Sanda ta Fito Gida Bata gansa ba Abba Kadai Tayi ma Sallama Anty Safiya ma da Ya yusuf suna Shashensu basu Fito ba. Munari na Tare da Inteesar har yammah,Kana Tayi Shirin Tafiya Inteesar ta Sako Dogon Hijabinta Maroon wanda Anty Hauwa ta Dinkamata Mai Hannu sai Fuskarta Tayi kyau sosai. Munari tayi Sallama Da Mama Suka Fito Tare da Inteesar Bayan ta Diban mata Dambun Nama dasu Cake da Donot,Dambun naman ya kare Cake din na Sauran kadan Dayake ba ita Kadai take ci ba,Mama bata cika ci ba ita da Sagir ne sai Munari Da takan Diba su tafi Dashi makaranta. Koda suka Fito basu ga kowa akofar Gidan ba,Suna Daga Chan Cikin Shago su kuma suka yi gaba zuwa Hanyar Gidansu Munarin Har gida Inteesar ta Raka Munari ta Shiga suka gaisa da Abba munari ta Nunamai Abunda Intee ta bata yana ta Godiya da Saka albarka Wanda Inteesar ke jin Dadin hakam Har ga Allah in ta gansa sai Taji kamar Tana Tare da Daddynta ne Tana ganin a mgana da wasu abubuwan suna mata kamanceceniya da Juna sai dai shi Abba yafi kama da Alkali Hamisu ne su kuma su Daddy sun Dauko Fuskar Daada ne. shashen Anty Safiya suka Shiga intee ta gaisheta tadan Zauna a Shashen Antyn Safiya suna Hira kafin ta Fito Munari ta Rakota Har Bakin get Taci Sa'a Imran baya Gida. *Ina godiya Masoyana na Nesa dana kusa Masoyan Imu da Intee Suma sunce suna Godiya sosai Allah ya saka da alheri..* *Shakira...* 3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*       *🅿�20* Inteesar da Munari na wucewa Imran ya Fito daga cikin Shagon Sagir ya Tsaya a kofar Shagon ya Fito da Sigari Guda Daya ya kunnata ya Cigaba da Zuka yana Fesar da Hayaki. Sagir ne ya Fito Daga Cikin Shagon Nashi Ya isa kusa da Imran yana Kallonsa Cikin Wani yanayi kafin ya Rausayar da kansa yana Fadin"Yau Kuma a waje ake son Busa Hayakin..? Imran bai ma nuna yasan da Wanzuwar Sagir a wajen ba Ya cigaba da Busa Hayakinsa,Sagir ya kara Kallonsa yana Gyada kai kawai. Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace"Kawai yau naji ina son na Busata a waje ne..! Sagir yace"Dahaka kake yi da baka Takurama yaran Shago na ba..kasan dai Tun Fara zuwanka Shagon nan Kake Takura musu ko..? Imran ya wani Mele baki Lokaci Daya yana Sauyama Sigarin nasa Hannun Zama kafin yace"I know..! Sagir ya kallesa Cikin mamaki kafin yace"Ka sani kace..? Imran sai da ya Fesar da Hayakin Daya Busa kana ya Bude baki yace"To ni zan Hana Zuciyarsu yin Abunda Tagama Da Gangaar jikinsu ne..Ban isa na sa su soni ba..Ban isa na Saka musu Ra"ayina ba sai dai na Isa na Hana su yin Abunda ni zai zama Takura gareni..! Sagir na Shirin mgana Imran ya Katseshi da Fadin"Har da kaima ai na Lura kamar na Takura maka ko..? Sagir yace"Ai ni ba tun yanzu ba ka Dade kana Takura ma Rayuwata..! Imran ya tsaki karamin Tsaki yana Fadin"Halin Dan adam kenan yanzu da ban rika zuwa ba sai kace naki Karban mganarka yanzu kuma ina Zuwa kana neman gayamin mgana..! Yafada Cikin nuna jin Haushinsa Da Sauri Sagir yace"To daka karbi mganata Ka fara koyan Sana"an ne. ? Tunda ka Fara zuwa baka komai sai dai ka Zauna kana bin kowa da kallo in ka gaji ka Busa Hayaki gayamin me ka Koya..? Imran ya saki kayattacen Mirmishin da yakan Dade bai yisa ba Kafin ya bude baki yace"Waya Fadamaka ban fara koya ba..? Tun yaushe ai ma nayi nisa da Fara koyon Dinki! Sagir ya wani kalleshi a karkace kafin yace"Bangane ba..? Ta ina ka Fara Koyon..?me kuma ka Fara Koyan..? Imran yace"Abunda Kake koyama Mutane mana Inace ba yanka Dinki bane da Hawa keke da Dinkawa bane..? Sagir yayi Dariya yana Fadin"Sannu Mallam Riga maasllaci To ai ba Haka kaga kowa na Koyon Dinkim ba balle kace..! Imran yace"Ai ni sunana Imran..Kuma Dabam nake da kowa..Kaganni nan da Kwakwalwata nake Koyon Abu bana da Bukatar Rubutawa ko Gwaji..! Sagir ya kallesa kafin yace"Uhm..wai me ma ka karanta ne a makaranta..? Imran na kallon Sagir Cikin ido kafin yace"Daman na taba Fada maka nayi Karatu ne..? Sagir yace"Ko baka Fadamin ba yanayinka da Tsarinka na Masu Ilimi ne sai dai in baka son Fadamin..Dama nine na Daukeka Abokina kuma Dan"uwana kai baka Daukeni ba Imran..! Sagir ya Fada Cikin Wani yanayi Da Imran yaji wani iri,Baki ya Mele kafin ya Saki karan Sigarin Dake hannunsa Data kare,Ya saka Rufaffan Takalminsa ya Take ta Kafin ya Laluba Aljihun wandonsa ya Dauko Wata ya saka Lether ya kunnata Sagir Duk yana kallonsa Kai ya Girgiza kafin yace"Don Allah ka Rika Dagama Shan Sigarin nan kafa..Ba Saboda Komai ba sai Saboda Lafiyarka Imu.! Imran yayi kamar bai jisa ba sai da ya Busa Hayakin yaji sa ya ji Daidai kana ya Fesar da Hayakin har zuwa Fuskar Sagir wanda ya kauda kai yana Fadin"Bana son Wulakanci fa..kan Fuskatane wajen Fesa Hayakin Sigarin naka..? Imran ya karkace kai yana Fadin"Kila..! Daga haka ya Tsuke Bakinsa Sagir ya Bata Fuska yana Fadin"Au kila ko...?Nagode ai ba sai ka ganni ba ballatana kamin Wulakanci..! Ya juya zai koma Shagonsa yaji Muryan Imran din yana Fadin"Ka Tambayeni Mena karanta a makaranta ko..? To Accounting na Karanta Nayi Degree na Farko Har zuwa Master..! Sagir Daya Dawo da Sauri lokaci Daya yana Zaro Ido Cikin Mamaki yace"Are u Serious..!? Imran bai bama Tambayarsa Muhimmanci ba yace"A University of Ibadan IU,nayi duka Karatuna..! Sagir da mamaki bai gama Sakinsa ba yace"To meyasa kake Zaune baka Nemi aiki ba..? Ko baka samu bane..? Imran ya wani kallo Sagir a Dakune kafin yace"Nayi aiki da Gt Bank Reshen Jahar Lagos a baya..! Sagir ya kara Sandarewa da mamaki Baki ya Bude Kafin yace"Kai din nan Ashe ma"aikacin banki ne Ban taba Sani ba Imran..! Imran yace"Bagashi ka sani ba yanzu..Sai me..? Sagir ya Dafasa yana Fadin"To meyasa ka bar aikin ka..?kenan in Hasashena ya Zama gaskiya ku a Lagos kuke kuka Dawo nan da Zama..! Imran ya kalli Cikin Idanuwan Sagir kafin yace"Eh..! Daganan bai kara cewa komai ba ya Cigaba da Shan Sigarinsa yana Fesar da Hayaki Sagir da ke Tsaye yana kallonsa Cike da mamakinsa Sosai akan Fuskarsa Kafin ya kara Gyara Tsayuwa yana Fadin"Ammh Tambayar Data Dade tana DAmuna ban samu amsarta ba..Shin Meya Baro ku Dachan Lagos din kuka Dawo nan..? Kuma meyasa kabar aikin kazo nan ka Zauna baka da aiki sai Shan Sigari..! Imran kamar bazai ce komai ba sai chan yace"Is a long Story..!Kila zaka san Dalilin Watarana Ammh Not Now..! Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan ya hango Inteesar Tana Tahowa Cikin Natsuwarta Kura mata ido Yayi yana Tunanin kila Daga gidansu Imran Take ganin inda Sagir ya Shagala da Kallo ne yasa Imran Shima ya Waiga yana kallon inda yake kallo,Daidai Lokacin da Inteesar din ta Iso kofar gidan Tana Dago kanta sai Cikin na Imran kamar ko yaushe alokaci Daya Zuciyoyinsu suka Buga alokaci Daya gaban Inteesar ya Fadi Ras Data ganshi,Abun kuma Daya kara Bata mamaki ganinsa Dauke da Sigari yana kallon Cikin Idanuwanta yana Zukan Hayakin yana Fitar da Hayakin ta Hanci ta baki sai ta kara Jinjina al"amarin Tana Shirin Saka Hijabintata Toshe hancinta Ta Tuna da Abunda ya Faru sai tayi Saurin Maida Hannunta da Gudu gudu ta Shige Cikin Zauren Gidansu Sagir Tana maida Numfashi. Imran ya Bita da kallo Cikin mamaki kafin ya Saki karan Sigarin Hannunsa Zuwa kasa ya saka Takalminsa ya Take ya murjeta Lokaci Daya yake Fadin"kalli yarinyar chan saboda Ta Rainani..In ta ganni tana guduna...Kamar Taga wani Dodo. ? Sagir Dayake Lura da abunda ya Faru yace"Ba Dole ta rika Gudunka ba..Taji Labarin kana Sumar da Mutun indai ya Shiga Hannunka..!. Imran yayi Tsai da idanuwansa da suka Kamkance suka Sauya Launi Saboda Busa Hayaki yace"Ina sumar wa..? Uban wa na taba Duka Har na Sumar dashi..? Sagir yace"To ni ina zan sani..?Nima ita ke Fadamim..! Imran da Ransa ya Fara Baci yace"Mganar banza..! Daga haka kawai ya juya cikin Takunsa na Sassarfa da Jarumta ya Fara Tafiya Haka kurum yaji Zuciyarsa na tafasa Sagir ya Bisa da Kallon Haka kurum yake Tunanin Hanyar da Zai Taimakama abokinsa wajen Dawo da Rayuwarsa ta Baya ta Inganta yabar wannan Rayuwar Dayake Ciki. Shikuwa Imran koda ya karisa Gida ko Gani Dakyau bayayi saboda Tsabar Bacin rai,Yana Shigowa Falon ya Fara Kwalama Munari kira Cikin Tsawa da Hargowa. Abba na Tsaye a Falon yana gyara Zaman Hulan kansa da Casbaha a Hannunsa,Fitowarsa Daga Dakinsa kenan ya Dauro alwala yana Jiran Yusuf zasu tafi masallaci Imran ya Shigo Cikin Fushi shiyasa bai ma lura da Wanzuwar Abba a falon ba. Yusuf ya Fito Daga Shashensu Safiya na Bayansa Cikin mamakin wannan Gigitattaciyar Tsawan da Imran ke amfani da ita Wajen Kiran Sunan Munari Daman shima yana Shirin Fitowa ne su tafi masallaci da Abba. Ya yusuf ne Da suka Bayyana a Falon ya Kalli Imran yana Fadin"Lafiyanka..? Me Munarin Tayi maka kake mata wannan kiran..? Ko Kallonsa bai yi ba illah Daga Murya Da yayi yana Kallon Safiya yace"Where is She..? Cikin Launin Bacin Ransa da Tuni Muryansa ta Sauya Cikin Sanyinta Tace Tana Kallon Yusuf"Tana Dakinta..! Bai Tsaya ma Mgana ba ya Fara Taku Zuwa Kofar Dakin Munarin yana Fadin"Wlh kinjin Rantsuwa Daya ko..Kika bari na Taka kafata Daga Inda Nake baki Fito ba.. sai na Tabbata da na Miki Dukan da Ba suma zaki yi ba sai kin ji Kamshin Lahira yadda Zaki ji Dadin ba wata Labarin ina Sumar da Mutane..! Yafada Cikin Fushi Lokaci Daya Jijiyoyin Kansa suna Tashi Radau Kirjinsa na wani Tashi yana komawa Yusuf ya Kallesa ya koma yana kallon Abba Da yayi Tsaye kawai yana kallon Ikon Allah. Munari Da Tun Fitowarta Daga Tiolet Taji kiran da Imran yake mata Tasan Yau Kashin taya Bushe Tsoro ne ya Hanata Fitowa,Tana Tsaye Tana Rawan Jiki dana Zuciya Jin abunda yace ne yasa ta Ta Sadakar ta Fito Domin ta Tabbata Zai aikata Abunda yace Ba wanda ya Isa ya Hanashi Mganar sa kamar Kaifi Tokobi ne in yasara sai tayi yanka.. Cikin karkarwan Jiki ta Fito Daman Kofar tana Bude ne tun Shigar ta bata Rufe ba Haka ta Hade Hannayenta Saman Cikinta Tana Fiki Fiki da ido Har sun Fara kawo Ruwa Saboda Tsoro Tana Hango Kanta Bayan ta Shiga Hannu Ya Imu yana Kwallo da ita kamar Yadda yake Fadi. Bata gama Karisowa gabansa ba ya Daka mata tsawa Cikin Kakkausan Murya yana Fadin"Kina jina ina kiranki Kina banza Dani Don Ubanki..?kin Raina ni ko..?Ko ni Sa"an Wasan ki ne.? Ya Karishe Fada yana Nuna ta da yatsa Lokaci Daya yana jin kamar yasaka Kafa ya bata wani Bugun da sai ta Suma nan take.. Munari Data Rude ai sai ta Zube gabansa ta Fashe da kuka tana yi tana Kamkame jikinta Waje Daya. Abba Dake Tsaye ya Daga Baki yace"Imran kada ka Daketa Nace..!. Ammh Imran bai ma san Abba na Mgana ba Bacin rai ya Rufemai ganinsa da Jinsa. Cikin Kufuluwa ya Kalleta yana Fadin"Wannan kukan naki bazai Hanani Sauya miki kammani yau acikin Gidan nan ba..Wane ne ya Baki Izinin kawo wannan yarinyar Gidan nan..? Kuma Waya baki Izinin da Zaki Kulla kawance da ita Da Har Zaki Rika bata Labarai akan Gidanmu..? Iskancin naki ma bazai tsaya kan Wanda kika Raina ba sai kin Tsallako kaina ko..? Saboda ban taba Yima Fuskarki Dameji ba Shiyasa Har kike da Bakin Fada ma Wata Mara Kunyar yarinyar Chan ina Duka Har sai na Sumar da Mutum ko..? Ya Karishe Fada da Tsawar data Gigita Munari Ta Fara mgana Cikin kuka."Ni..Ni...Wlh..Ban..Fada..mata ko..! Ai bata kai karshen mganarta ba ya Daga Hannu ya Wanketa da wani Lafiyayyan marin da sai da ta Kife ya kuma saka Kafa yayi kwallo da ita ta Fadi chan gefe sai da kanta ya Bugu da kujera ji kake kum,Wanda ta saka Dole Munari ta saki marayan kuka Tana Fadin"Wayyo Allah na Ya Imu don Allah kayi Hakuri..Abba..Ya yusuf Ku Taimakamin..! Take Fadi Tana kuka Abba bai Motsa ba Shima Ransa ya Baci Yusuf ne ya Riko Imran din Cikin bacin rai ganin yana Shirin kara Bin Munari ya Taka da Takalmin kafarsa,Safiya kuma Baya taja Tsoro ya kamata gashi Tana son Isa Wajen Munari Tana Tsoron kada Itama ya Illatata. Ya Rikesa Sosai yana Fadin"Imran Wht is your Problem ne..Abba na maka Mgana ka maidashi Banza..? Me tayi maka kake Dukanta kai baka jin kunyar Dukan mace..? Macen ma Kanwarka Wacce baka da kamarta..? Imran ya Kallesa Idanuwansa Jajir kafin ya Kwace Jikinsa yana Fadin"Ina mgana tana cemin baa Haka ba..?Zan mata karya kenan ko..! Ni ina Wasa da ita ne zata Rika bama Wannan yarinyar Labarin ina Sumar da Mutane..? Yusuf Let me Tell ur wani Abu bana son na Bata ma wani Rai Shiyasa bana shiga Shirgin da ba nawa ba..Nima na Tsani ka batamin Raina Saboda BANA SON RAINA YANA BACI..! Yafada Cikin hargowa Lokaci Daya yana Wani Buga Kafarsa ya Cigaba da Fadin"Zan Cigaba da Dukanta Har sai ta Suma sai taji dadin bada Labarin ina Sumar da Mutane..ina na kara ganinki da wannan Yarinyar sai na Illataki..Nonsesses kawai..! Daga haka kawai ya Daga Kafa ya wuce Fuu zuwa Dakinsa ya Shiga ya Banko Kofa ji kake Bam! Kamar zai Ballata Abba ya Jinjina kai kawai ya kasa cewa komai Yusuf ya Kallah wanda ya Daga Munari Dake ta kuka ya kalli Safiya yana Fadin"Kamata Don Allah..! Da Sauri ta Riketa Tana mata Sannu Cikin Tsausayawa Abba ya Juya yana Fadin"Mu tafi masallaci Yusuf..! Ba Musu yabi bayan Abba suka Fice ita kuma Safiya ta kama Munari zuwa Dakinta sai da suka Shiga ta Rufo Kofar take Fadin"Kema munari me ya aike ki bama Intee wannan Labarin gashinan yaje kunnunsa yanzu..! Munari na kuka Tana Dafe da goshinta Inda Har ya Sumtuma tace"Wlh bansani Ba Anty Safiya..Bansan zai ji Labari ba da ban Fada mata ba..! Safiya tace"To ita ya akayi ma ta gansa Har ta Fadamai..? Munari na Sharan Majina tace"Bazai zama ita ta Fadamai ba..Sai dai in Tayi Zencen da Ya SAgir ne shi kuma Cikin mgana ya Fadamai kuma zai kawo nice..Daman ga Haushin Abunda Intee tamai Duka ya Hada ya Huce akaina Da kuma Haushin kawancen da muka Fara da ita Saboda yamin kashedin kada na yarda nayi kawa da kowa..Anty Safiya Taya zai ce kada nayi kawa ni ba Mutum bace da bana son Farinciki..?ko kuwa shi ba Abokin garesa ba Shi wa ya Takuramai..? Ta Karishe Fada Cikin kuka da Tsausayinta ya kama Safiya ta Rumgumeta ta bata baki DAkyar ta Lallasheta Tayi Shuru,Ta Dauko man Zafi ta Shafa mata agoshinta Bayan ta Sake alwala ta Fice ta barta Tana Kokarin Tada Sallah Itama Shashenta ta Shiga Domin ta gabatar da Sallah aranta Tana Tunanin Duk iya Hasashenta kan Imran ya Wuce Yadda Take Tunani ko take Tsammani. Su Abba basu Dawo ba sai Bayan Sallar Isha"i suna Fitowa Daga masallaci suka ga Imran ya Fito yana Saka Takalmi ya Sauya Kaya Daga Riga da Wando Zuwa Wata Bakar Jallabiya Sagir ne ke mai mgana yayi banza Dashi ya wuce kamar zai Tashi Sama Dashi akayi sallar mangariba Duk da Raka"a Daya ya samu sai ya Rama Sauran ya Tsaya Har akayi Sallar Isha"i yana Sahun baya ne Shiyasa su Abba basu Lura dashi ba. Sagir ne ya gaisa dasu Abba. Abba ya Dafa Kafadansa yana Fadin"Ka Rabu dashi Yau Zuciyar tasa ne tatashi Har gobe da wannan bakar Zuciyar sai wayi gari..! Sagir ya Kada kai yana Fadin Allah ya kyauta da haka sukayi Sallama ya Nufi Cikin gida Duk da ya Damu yana Tunanin kan mganar Daya Fadamai n in bai Kuskure ba komai zai Dawo kan Munari ne Domin zai ce ita ta gayama Inteesar Tuna Haka da yayi ne ya Dafe kansa yana Fadin ya Illahi me na aikata ne..? Nafi kowa sanin Imran in Ransa ya baci kamar Mahaukaci yake..Kada yaje ya Duke yar Mutane fa..! Abba bai Tada mganar ba har bayan sun Dawo sai da suka gama Dinner kana ya Taka da kansa Har Dakin Munari Domin taki Fitowa tace ma Safiya ta Koshi kan gado ya ganta Dukunkune Cikin Bargo Tana kuka bata ma san ya Shigo ba sai da ya kira Sunanta kana ta Dago Tana Kallonsa Cikin Dattakonsa ya Zauna Gefenta yana Fadin"Tashi Zaune mgana zamu yi..! Ba musu ta yaye Bargon Data lulluba Dashi Lokaci Daya tana Sharan Hawaye. Goshinta ya Shafa ganin ya Kumbura yace"Yana Zafi ne Munarin Abba..? Kai ta gyadamai sai ga Hawaye Sharr Rumgumeta yayi yana Fadin"Kiyi Hakuri..Shii.Daina kuka kin ji ko..? Kai ta gyada mai shi kuma ya saka Hannu yana Share mata Hawaye Lokaci Daya ya Dagota yana Fadin"Kalleni nan Maimunatu..! Kallonsa Tayi shi kuma ya Tallafe Fuskarta yana Fadin"Menene Matsayin Imran a wajen ki..? Cikin Sanyin Murya tace"Yayane Abba..! Abba ya jinjina kai kafin yace"Duk abunda zai yi miki bai isa yace baya Sonki ba. kema baki isa ki Cire wannan Jinin daya Hadaku ba Munari..Imran baya Shiga Shirgin da bana nasa ba..Kuma baya Duka ko Fada Indai ba"a Tabasa ba. Ko..? Kai ta gyada mai Sai ya Cigaba da Fadin"Ba ina Shigarmai bane A"a Sai don ina so na Nuna miki Laifinki D'aya a wannan abun..Shine kin yi Rashin Wayau Munari..Imran Dan'uwanki ne na Jini da kuke Zaune Gida Daya..Inteesar kuma Kawarki ce da kuka Hadu ba da Dadewa ba..Bai kamata ki gayamata abunda ya Shafi Imran ba Munari..Menene naki na Labarin yana Duka har ya Sumar..? Waya taba sumarwa..? Marigayiya Asma"u?itama Lokacin Harkansa ta Shiga ta batamai rai ya Zuciya ya Nausheta aciki sai abun yazo da Tsautsayi ta Fadi ta suma..bayan ita kin karajin ya Sumar da wani ne..? sai dai Hargowansa in aka batamai rai..Nasan bai da kyau yana da Bakar Zuciya irin ta Fulanin Da suka Fito Daga Dukku ammh duk da haka bai kamata ki Zubar da kimar Dan"uwanki Data gidanku ba Munari..Wannan Labarin sam bai Dace kuma baki kyauta ba..Inteesar Zata Raina Yayanki Duk da nasan bazata aikata haka ba na yarda da Tarbiyanta ina mata kallon Kamar kice Munari..Ammh Duk da Haka abunda kika aikata bai yi Daidai ba sam..! Ya kariahe Fada Cikin Taushin Murya Munari Data gano Laifinta tace"Hakane Abba ban kyauta ba..Nima ba da wata Manufa na gayamata haka ba..Insha Allahu naji mganarka bazan Kara ba..! Abba yaji Dadi ya jinjina mata kai kafin ya Saketa yana Fadin"gud Munarin Abbanta..Yanzu kimin alkwarin da Safe in ya Huce zaki Bashi Hakuri..! Da Sauri tace"Insha Allahu Abba zan bashi Hakuri..! Abba ya Dafa kanta yana Fadin"Allah yayi miki albarka..Dake da Yayyinki Gabadaya..! Munari ta amsa da Ameen Kafin ya Mike ya Fice ta Rakasa da Kallon Kauna Har ya Fice kafin ta koma ta Kwanta Shiyasa take son Abba yana da Saukin kai sosai bazai maka Fada ba sai dai cikin Sauki zai ganar Dakai Kuskuranka ta gano Laifinta kuma da yardan Allah Zata bama Ya Imran Hakuri da Safe kafin tatafi makaranta. ***** Washegari ta kama Monday ne Karfe 7:30am na safe su Munari keda Lacture,Shiyasa ta Shirya da Wuri Safiya ta Hada Breakfast,Tea kadai tasha da Bread,Yusuf ma ya Shirya Cikin Suit Baki da Fari na Tafiya Wajen aiki Dukkansu a tare sukayi Breakfast banda Imran wanda Tun Jiya Daya Dawo Masallaci ya Shige Dakinsa ba wanda yaji Motsinsa. Munari ta Fara Tunanin ta Bugamai kofa ne sai kuma ta Fasa sanin Halinsa kar ta kara wani Laifin Suna Shirin Tafiya yau Ya yusuf Zata Bi ya Ijiyeta makaranta sai ga Imran din ya Fito Sanye da Wando 3Quater Ba Riga ajikinsa bai ma kowa mgana ba Abba kadai yace ma Ina kwana Anty Safiya ma na gaisheshi yayi kamar bai jita ba ya Wuce Kitchen. Yusuf Dake Tsaye ya Mika mata Hannu ta bashi Briefcase dinsa ya karba yana Fadin"Kada ki kara gaisheshi..Kanina yake ba Yaya yake gareni ba yadda Zai girmamani haka kema zai girmamaki Anty Kike a wajensa..!Safiya taji abun wani iri batace komai ba ammh aranta tace ban matsama kaina ba da sai ya kirani Anty ba Imran Daya Fito Daga Kitchen Dauke da Goran Ruwa ,yaji Duk Abunda Yusuf yace bai nuna ma yaji ba sai ma kara Dakuna Fuska da yayi zai Wuce Munari Dake gefe Cikin Shirin Fita tace"Ya Imran gud mrning..! Cikin Dari dari..Bai ma ko Sanda da ita ba ya Rike marikin kofarsa kana ya Juyo yana kallonta Da Sauri ta rike kunnuwanta Kafin tace"Am Sorry Y Imu..Bazan karaba Plz..! Yadda tayi ne yasa sai yaji kuma Zuciyarsa Tayi sanyi dan Fuska ya saki kafin yace''Is ok..! Daga haka ya bude Kofarsa ya Shige ya Rufe Abba Dake saman Dinning yana Karisa karyawa yace"Hallayarsu suna min kamanceciniya da juna..! Yusuf yace"Abba da wane..? Abba sai da ya Dade bai yi mgana ba kafin ya kada kai yana Fadin"Baffanku..Ya Kabiru..Barrister Baban Khamis da Sajida..! Daga Yusuf har Munari ba wanda ya iya mgana saboda yadda Jikinsu yayi Sanyi balle Safiya Dake gefe aranta Tana Tunanin yanzu Abunda ya Rage ma wannan gidan kenan su Koma ga Ahalinsu kuma tayi wannan alkawarin sai ta cikashi da yardan Allah. Sallama sukayi ma Abba suka Fice,Safiya ta Rakasu har Haraba suna Fita Daga Gidan Inteesar ta Kira Munari tace tana Kofar gidansu Sagir Tana Jiranta su Wuce sai ta Rasa me Zata ce mata tana jin kunyar tace mata ta Wuce alhalin kwanakin nan Duk Tare suke Tafiya. Yusuf ne Dayake jin mganar Inteesar din ta Cikin wayar Domon Volume din wayar yana Cike ne yace"Ki gayamata gamu nan zuwa zamu Dauketa..!. Cikin mamaki ta kallesa sai ya Gyada mata Kai Lokaci Daya yana Sakar mata Mirmishi da Sauri ta Fadama Inteesar din ga sunan zuwa ita da Ya Yusuf zai kaisu makaranta kafin ya Wuce Office. Haka kuwa Akayi suna zuwa Kofar Gidan suka ganta Cikin Shirinta yau kamar sun Hada baki dukkansu Hijabai suka saka Inteesar ta Bude Bayan Motar ta Shiga sai da suka Fara Tafiya kana ta gaida Ya yusuf ya amsa mata Cikin Sakin Fuska,yana tambayanta Karatu ta amsa da Alhandulillah nan yace su Dake Allah ya basu sa"a suka amsa da Ameen Inteesar nata kallonsa Itafa Har yanayi yake mata da Ya Basheer in yana mgana. Har bakin Department dinsu yakai su kana Ya basu 1k yace su siya abinci suka amsa suna Godiya kafin yayi Riverse ya juya ya Fice Daga makaranta ya Dauki Hanyar Ma"aikatansu Lokaci Daya yana Duba agogon Silban Dake Daure a Tsitsiyan Hannunsa. Intee bata lura da Kolin goshin Munari ba sai da suka Fito daga Lacture Data Tambayeta sai tace mata kume wa tayi da Kofar Tiolet dinta Inteesar ta nuna Tsausayawa sosai har tana ce mata ko zasu je asibiti ne.Munari ta nuna bakomai ammh bata yarda ta gayama Intee komai ba Sai ma Intee din take bata Labarin jiya Bayan ta Dawo Daga Rakata ta ga Ya Imran da Sagir ta Shige gida da Gudu Munari Mirmishi kadai Tayi batace komai ba. Ranar sai 5pm na yammah suka gama da Makaranta suka Dawo gida,Daga Bakin Titi suka Sauka suka gangaro Inteesar ta Fara Shigewa ita kuma munari ta karisa gida Bayan tasha Labarin zuwan Daddyn Inteesar din a Bakin Inteesar din yau a makaranta Itama sai taji tana son ganinsa ko Domin Tasan Yana Son Inteesar Shiyasa yake Shagwabata. *Shakira..* 3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*        *🅿�21* Cikin satin kaf Ya yusuf ke kaisu Makaranta kafin ya wuce wajen aikinsa Dayake kuma an ci Sa"a duk Lacture din safe garesu,ranar jumma"a ne kadai suka tafi da Kansu saboda sai 10am suka shiga makaranta na Safe. Wannan karamcin na Gidansu Munari Inteesar na matukar jin Dadinsa Har Daddy da Umma sai da ta bama Labarin Yayan Munari ke kaisu makaranta Kullum Duk yadda kaji wani na son naka ko yana Hidima Dashi kaima Dadin haka kake ji Abunda ya Faru da Umma da Daddy kenan Shiyasa yayi alkawarin Tabbas in yazo Inteesar zata Rakashi Gidansu Munari yayi musu Godiya. Ranar asabar ba makaranta Tun Jiya da Daddare Daman yusuf yace Safiya ta Shirya ita da Munari zasu je anguwa Shiyasa Tun Safe suka gama Duka ayyukansu bayan sun gama Breakfast suka yi Luch suka Zuba a Kula suka Rufe Kafin su dawo. Karfe 11am na Safe suka Fita Suka bar Abba da Imran agida wanda Gudu kadai ya Fita yayi ya Dawo gida ya Shige Dakinsa Abba kuma na Falo yana kallo Yana Debema kansa kewa. Ashe gidansu Safiya zasu je sai da suka Dauki Hanya yake gayamata Farinciki ya cikata Duk da Tana waya da Mommy da Tasleem ammh Tana Bukatar zuwa ta gansu Duk da Tasleem din na zuwa wajenta Lokaci Bayan Lokaci in Mommy ta aikota da Wani Sakon,Bata da Mtsala da su Abbu ne mtsalanta Domin Tunda tayi aure basu Taba Haduwa ba Ta taba Kiransa Sau Daya a waya yace Kada ta Kara Kiransa ta Zauna Gidan auranta Tayi ma Mijinta Biyayyah. Sun ko ci Sa"a Alhaji Alhassan yana Gida yana Sama yana Hutawa suka iso Mommy da Tasleem suka kasa Zama Saboda Murna suna ta ina suka Saka da Yusuf da Munari Mommy kuwa Bakinta kamar zai Tsage saboda murnan ganin yarta Tayu cikar Daki wanda ganin Farko zakayi mata ka Shaida Bata cikin Wata wahala ballatana Damuwa. Kafin kace kwabo an cika Gabansu da abinci da abunsha,Tasleem Taja Munari Dakinta Safiya kuma Tana Dakin Mommy sai aka bar Yusuf kadai afalo. Safiya ta kalli Mommy Daidai Lokacin Datake Zama gefen Kayattacen Gadon Daya Malale Dakin tana Fadin"Mommy Abbu baya gida ne..? Naga motarsa a parking space..! Mommy ta tabe baki Tana Fadin"Yana Nan..Bai fito bane yana sama yana Hutawa..! Ta Bude baki Zatayi mgana Hajiya Mero ta yanketa tana Fadin"Kin mai mganar zuwa gidan kakanin naki Rijiyar Zaki da gidan Yaya Saratu..? Safiya tace"Eh na gayamai Mommy yace Zamu je to bansani ba ko duka Tafiyar yau ta yuyu Tunda kinga Rana mai kama ta yau yake samun Hutu..Tunda Sauran ranakun sun siyar ma gwannati Lokacin su..! Mommy tace"Hakane kam..Kudai yi kokari kuje Alhaji da Hajiya suna ta mganarki..! Safiya tace"Tom Mommy ai Dayake ma muna mgana dasu ta waya..! Mommy ta Mike tana Fadin"Haka Hajiya tace min..Ki je Falo wajen Mijinki kada ki barsa Shi kadai..! Safiya tace"Mommy Abbu fa..? Bazai Fito su gaisa da Yusuf ba..? Mommy ta bata rai kafin tace"Shi ya ma Taba Tunawa Dake ne..?ki Rabani da mganar Mahaifin da baisan Darajan Ya"yansa da Hakkinsu Dake kansa ba..Ni kuka zo Dubawa kuma nagode ku gama abunda zaku yi ku wuce ku tafi bana son ma ya Fito ya ganku..! Safiya bata samu Zarafin mgama ba sukaji Muryan Alhaji Alhassan yana Kwalama Hajiya Mero kira atare suka Kalli juna kafin dukkansu su Kama Hanyar Fita Daga Dakin. Suna Fitowa Falo suka iske Yusuf duke a kasa ya sauko Daga kan kujera kansa na kasa Alhaji Alhassan kuma yana Tsaye da Jallabiya yana Mazurai.. Hajiya Mero ta Hade rai Tamau ta Nufeshi Tana Fadin"Gani Allah yasa Lafiya..? Yabude baki zai yi mgana sai Lokacin yaga Safiya Dake bayan Mommy Baki ya Saki yana Kallonta ita kuma kanta ta Sadda ta karisa kusa da Mijinta ta Durkusa Tana Fadin"Ina kwana Abbu..! Kada kai yayi sai Lokacin ya gane Yusuf ne yaron nan don da Farko Daya Sauko Yusuf din ya Duka yana Gaishessa bai wani ganesa ba, Tunda ba wani Tsayawa yake yana Kallonsa ba Koda yazo wajen Safiyar a baya. Maida mganarsa yayi Cikin Cikinsa ganin Haka yasa Hajiya Mero ta karisa kusa Dashi kasa kasa Tana Fadin'"Yanzu ai kagane ko waye ko..? mijin yarkace Safiya da kayi ma Auran Kaskasci Ma"ana Surukinka yazo yayi maka Godiyan Aura masa Safiya da kayi ne..Sai ka Natsu..! Tafada Lokaci Daya tana Hararansa Tana kuma Dagowa sai ta Murmusa Tana Fadin"Ku tashi ku zauna kan kujera mana..Yusuf ai nan din ma Duk gida ne ko Alhaji..? Alhaji Alhassan bai da yadda Zai yi Dole ya saki Fuska yana Fadin"Hakane..Ku tashi ku zauna Sannunku Mero sai ki gayamin yau muna da baki agidan nan Safiya Sannu da zuwa..! Ba mommy ba Hatta Safiya da Yusuf Mamaki ya hanasu Motsi gefensu ya samu kan kujera ya Zauna Yusuf ya kara Ramkwafawa yana Gaisheshi ya amsa mai Cikin Sakin Fuska yana kara Nazarinsa ita Mero bata gane wani abu ba Shifa koda yayi ma Safiya wannan auran yasan me ya aura mata yayi Binciken kan Yusuf Yaro neNagari mai Neman na kansa Sannan kuma Dalilin wannan Tsagerin Kanin nashi ne komai ya Lalace Domin yayi Hannun Riga da duk abunda zai tabamai kimarsa Sai da Ya tattara Safiya ya mikamusu ya ke iya Barci Harda Minshari,bawai Domin baya son yarsa ba Taya Mutum zai Haifi ya yakita sai domin Zuwanta wannan Gidan Shine Rufin asirinsa kuma bazai iya Fitowa yayi ma wani wannan Bayanin ba Shiyasa ko Dayaje Fagge Goggo Tayi Fada kamar ta ari Baki kamar ta Dakesa shi dai sai ban Hakuri yake bata bai da tacewa Tunda aikin gama ya gama ya riga ya gamaba Goggo ba Ya riga yaShiryama Daukan Kowacce mgana kan abunda ya aikata yana Shiryen da hakan indai Boyayeyen Laifinsa bazai Fito a idanuwan yan"uwansa da Matarsa da ya"yansa ba Dama Sauran Mutanen Dake ganinsa da kima ba Kallon Safiya yayi yana Fadin"Safiya ya Sabon Wuri..?kina Bukatar wani abu ne..?Ki Fadamin komai kike Bukata zan yi miki mishi.! Cikin Mirmishi ta kalli Yusuf Shima ya kalleta kafin tace"Bana Bukatar komai Abbu..Komai Mijina ya Siyamin ina Cikin Farinciki a Sabon Gidan da nike yanzu..Ina Rayuwa ne Tmkar yadda nake Rayuwa a gabanku..! Hajiya Mero Dake gefe taji Dadin amsansa sai da ta aikamai da kallon ba Haka kaso ji ba ko..? Shi kuma sai yayi kamar bai ganta ba ya Shiga Saka musu albarka ita da Yusuf wanda yayi musu Matukar Dadi Ita da Yusuf din har ya kasa Boyuwa Saman Fuskarsu ita kanta Hajiya Mero Jin Haushinsa ya Ragu acikin Ranta. Suma cikin hakane sai ga Munari da Tasleem sun Fito ta Duka ta gaida Alhaji Alhassan ya amsa yana wani kallonta Cikin kwarewa kasa kasa Tuni yarinyar tatafi da Imaninsa irin Kayan Harkan Dayake so kenan sai dai Tunaninsa ya Tsaya ne sanda Safiya ke Fadin kanwar Mijinta ne. Miyau ya Hadiye mukut..Ya maida Kwadayinsa ko Ya haukace bazai yi wannan ganganci ba Ko bama Safiya ba ya Tabbata wannan Kanin na Yusuf yaji Labari sai ya Tabbatar da ya Kwaye mai Rigar Mutumcin Dayake yaudaran Mutane dashi..Da Mannau gara Hanau. Da sauri ya gyara Natsuwarsa ya amsa gaisuwarta Cikin Fara"a da Dattako yana saka mata albarka basu Dade ba sukayi Haraman Tafiya,Yusuf ya Ijiyema Mommy 10k Abbu 10k Safiya kuma tace Abbu ya bar Tasleem ta Rakasu Rijiyar Zaki gidansu Hajiya Mero yanzu yake Fadamata Daga nan chan zasu je ba gaddama yace sai sun Dawo Hajiya Mero bakinta yaki Rufuwa ta shiga Ta Dauko ma Munari Turmin atamfa da Turare sai Turaran Wuta ta Diban ma Safiya da Humra,Sauran kuma tace takai ma Hajiya Har Haraban gidan suka Rakasu ita da Alhaji Alhassan Ita kuma Tasleem nata Murna suna Daga musu Hannsu suka fice Daga Haraban Gidan Sai da suka Fice kana Hajiya Mero Ta Daga Hannu Sama tace"Alhamdulillah..Allah nagode maka da Allah bai ma wani Damar Tozarta Rayuwar yata ba..Allah nake Roko ya Kareta yasa ta Zama a Haske ga Mijinta da Ahalinsa gabadaya..! Tafada Lokaci Daya tana Nufar Hanyar Cikin gidan ko kara Kallon Barayin Alhaji Alhassan batayi ba Shi kuma da kallo ya Bita yana Mirmishi Gefen Bakinsa aransa yana Fadin kayi ki gama ne. Suna Fita Daga zooroad basu Tsaya ko"ina ba sai kofar gidan su Hajiya Mero Rijiyar Zaki sun ci sa'a nan suka Hade da Anty Saratu tazo gaida su Hajiya sun ji Dadi sosai sukayi ta saka musu albarka basu wani jima ba suka Tafi Bayan Yusuf yayi musu alheri,Safiya kuma ta bama Hajiya Sakon Mommy Anty Saratu kuma tace Tunda sun Hadu anan tana Binsu bashi Yusuf yayi mata alkwarin Insha Allahi suna nan zuwa. Daga Rijiyar zaki kuma Gidansu Sagir suka Sauka Yusuf Ya shiga Har ciki suka gaisa da Mama kana yace in Sagir na nan zai rakasu Gidan Baba Manu yamai Godiya,Mama taji Dadin haka Tana saka albarka Koda suka zo Inteesar na kwance tana Barci Tayi aiki Ta gaji yau har yan kayan Mama kala Biyu da Hijabai ta wanke ta Hada da nata Inears din ta wanke Shiyasa take kwance sai da Munari ta Shiga Har kurya ta Taddota Ta Daka mata Duka kana tatashi a gigice ganin Munari ya sa tatashi nan take Fadamata Tare da Ya yusuf suke da Anty Safiya Hijabinta ta Dauka suka fita ta gaishesu suka amsa mata Cikin Sakin Fuska. Mama a waya ta Kira Sagir tace mai yana ina ne..? Yace mata yaje banki ne ammh gashi nan zuwa,ba Dadewa sai gashi ya shigo har gabansa ya Fadi ganinsu yusuf ya Zata wani abu ne ya Faru da Imran domin Tun Ranar da sukayi mgana basu kara Haduwa sun yi Wata mgana da Imran din ba ya Dauke Kafa da zuwa Shagonsa sai dai su Hadu a masallaci su gaisa Sama Sama ya Raasa me yasa Imran ya Dauke masa Kwana Biyun nan sun saba Fadansu su Shirya sai dai wannan karon Abun yasha Bambam Sai da suka gaisa kana Mama ke Fadamai Dalilin sai lokacin yaji Hankalinsa ya kwanta. Gabadaya suka tafi Harda Inteesar Tasleem Dayake chan Rijiyar Zaki suka barta Anty Saratu zata Leka Mommy Zasu koma Tare Mama kadai suka bari gidan Wannan karon duka Matan suka Hade a Bayan Motan Sagir na gaba yana Nuna Hanyar gidan Baba Manu. Yusuf ya kallesa yana Fadin"Sagir ina Mutumin ka..? Sagir ya Juyo yana Kallon Yaya Yusuf kafin yace"Kai zan Tambaya Ya yusuf...Imran na Fushi Dani ko mgana nayi mai sama sama yake amsani..,! Yusuf ya Murmusa kafin yace"Babu abunda kayi mai kuma badakai yake Fushi ba..Sai dai shi haka yake duk Lokacin da wani ya batamai rai..Yana Hada bacin Ransa na Tsawon Lokaci sai kuma Hakan ya Horasa Shi kadai..Ni kaina sai na Bisa Dakinsa nake ganinsa baya ma son Fitowa ko Falo balle a mtsamai da mgana Abba kadai Daya zamemai Dole yake gaisawar..! Gabadaya Tayi shuru suna Sauraransu Sagir ya jinjina kai yana Fadin"na gane..Sai dai Imran nada Wahalaf Sha"ani ina Matukar Tsausayama matarsa in bata sanshi ba Zata sha Wahalansa..! Yusuf yace"Ko ni da nike Dan"uwansa Ciki Daya yana min Wahalar Mu"amala ballatana Mace..! Sai dai kasan soyayyar Kila sai ta Sauya shi Watarana..! Kai Tsaye Sagir yace"Imran bai yi Beleive kan Soyayyah ba bana Tunanin hakan zai iya Faruwa..! Yusuf yayi Dariya yana Fadin"Ai karya yake yi..Nifa ina da yakinin Mace sai ta Sauyashi Shi din banza..! Dariya Sagir ya saka kafin yace"Shikenan mu jira mu gani..! Ammh ina da Shakku har yanzu..! Yusuf yace"Kajira Lokaci kawai Sagir zaka ce na Taba Fadamaka..! Su safiya na bayan Mota suna jinsu Tabe baki inteesar tayi aranta Tana Tsausayama mai Tsautsayin data yarda ta Auri wannan ta gama kashe Rayuwarta Gabadaya Mutum na Rayuwa kamar ba Mutum ba sai Kace wani Aljani. Suna isa gida suka kuma Taki Sa"a Baba Manu na gida Lokacin da Sagir kemai bayanin yusuf sai yaji Dadi da Sauri ya Mike sukayi Musabaha Daman Wlh Safiya na Ransa Saboda yana Tunanin shine fa yayi jagaba kan Auransu in wani abu ya Faru Allah bazAi barshi ba sai dai ganin yusuf da ita Kanta Safiyar ya Ciremai kowani Shakku Kaltume nata ina ta saka dasu Ruwa kadai suka sha Yusuf ya Ijiyemai 5k suka Fito Har waje ya Rakosu yana Godiya Lokaci Daya yana Musu addu"a har sun Shiga Mota Baba Manu ya Duka Saitin Yusuf yana Fadin"ina Murdadden kanin nan naka..? Yusuf yayi Mirmishi kafin yace"Imran..Yana gida Baba yace a gaisheka..! Baba Manu yayi Dariya kafin yace"Kai dai ka ari bakinsa kacimai albasa..Nasan bazai ce ba..Ganin Biyu nayi mai zuwa uku ammh na Nazarcesa kamar na Shekara da Saninsa..Ku rika Sakashi yana yawan Shan Ruwan Zamzam hakan zai Taimaka wajen Saukakamai al'amuransa..In ka koma Gida kace Baban Sagir na gaishesa..Manu nake..,! Yusuf ya gyada kai yana ta Godiya kafin su tafi acikin Ranshi yana Kara auna wasu abubuwan shifa ba Domin Abba ya Rantse mai Imran baida Aljanu ba shi kansa da Farko kallon mai Bugawar Junnu yake mai ammh yanzu kam da Baba Manu yayi mgana zai Tsaya tayin daka wajen ganin Rayuwar Imran ta Inganta kamar baya bazai zuramai ido yana da Komai na Rayuwa,ammah ya Kare rayuwarsa Cikin Wani Hali ba. Daganan Sagir da Inteesar suka ijiye agida suka karisa suma. Suna Dawowa abinci suka ci suka yi Sallar La"asar Abba da Yusuf kuma Daman masallaci suka tafi,Imran kuma yana Cikin Dakinsa ba wanda yaji Motsinsa kuma ba wanda ya Neme sa yaji sanin Halinsa. ***** Washegari ta kama Lahadi ne Tun Safe Inteesar ta tashi da Murna Domin Tayi mgana da Daddy yace suna Hanya shi da Ya Basheer ammh sai sun gama abunda ya kawosu zasu zo nan gidan Maman,Gabadaya ta kasa Zama Saboda Murna Mama natayi mata Dariya Ya Basheer na son Alala shi tayi mai Abba kuma Tuwon Semo Tayi mai miyar Kubewa Bushashiya Sai wajen 1pm ta Gama komai ta shiga wanka ta Shirya ta Zauna zaman jiransu Ko abinci ta kasa ci,Mama sai Fada Take mata kan ta Rika cin Abinci ammh ta kasa ita Haka in tana Zakwadin Abu abinci ma Baya gabanta. Duk bayan Mintina sai ta Kira Daddy taji ko sun gama abunda ya kawosu suna Hanyar zuwa Gidan Mama sai yace Mata A""a har ta gaji da kira ta Hakura tana ganin kamar bazasu zo bane Har Munari ta Kirata Tana Tamnayanta ko Daddy ya iso tace eh Yana cikin kamo sai dai basu kariso ba Tace to bara tayi wanka gatanan zuwa,Da haka suka rabu kuma sai ta Jita Shuru karfe 3:00pm na rana Daddy da Ya Basheer suka iso ho zo kuga Murna wajen Inteesar ta makale Daddy gamgam Tana Fadin tayi kewarsa Hakama Ya Basheer ta Rumgumesa shima ya Riketa Cikin Farinciki Mama itama Murna Duk ya kamata ta rssa ina Zata sakasu haka take akwai son Yan"uwanta sosai. Bayan sun zauna sun sha Ruwa da Inteesar ta gama jera musu aka Fara gaisawa Sagir na gefe Daman yana Shago yaga Isowarsu shi yayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan. Mama da Sagir suka basu Waje su gana Da Inteesar nan ta zauna tana Zubamai Shagwaba da Tambayoyin ina Umma..!? Talatuwa..? Anty Hauwa ina su Abiden ya Basheer gajiya yayi da amsa mata yayi Shuru yana cin Alalansa Dakyar ta bar Daddy yaci Tuwonsa yaci sosai jin Intee tayi mai,bayan ya gama ya Kira Umma ya bata sukayi mgana inda tace ta bama Dadynta sakon Dambun nama da Kayan Snkas,Roba Biyu ne Daya nata Daya na Mama nan tace ma ta kaima Mama Wayar suyi mgana nan ta Fice Tsakar gida ta Mikama Mama Wayar sukayi mgana da yar"uwanta sun Dade suna mgana barin ma mganar Kan auran Yarinyar Wajen kaw Bala ne nan da Wata Biyu. Daddy sai da sukayi Sallar La"asar sukayi Shirin Tafiya bayan ya cika Mama da kudi Tana ta godiya kuma sun sauke mata kayan abinci Inteesar harda Lemonta Freshyo,Katan uku Daddy ya Taho mata dashi ya bata 20k a Hannunta Ya Basheer 10k ya bata Kuma ko Sati ba"ayi ba Daddy ya Turamata 20k ta bankinta ko Tabata batayi ba. Sam ta manta da Munari sai da Su Daddy suka fito ta Rakosu ita da Sagir Daddy ya Kalleta yana Fadin"Banga Kawarki da muke jin Labarinta ba Intee..Ko bata nan ne..?wanda kikace yayanta na kai ku makaranta..? Sai alokacin Inteesar ta Tuna da Munari ta Bude baki Tana Fadin"Laa..Daddy kaga zuwanku ya sa na manta..Munyi mgana da ita Tun dazu tace zatayi wanka tazo bari na kirata naji plz Daddy..! Daddy ya Murmusa kafin yace"Anything For my Angel..! Ya Basherr na gefe yana waya da Anty Hauwa Tana Tambayansa suna Hanya ne yace yanzu dai zasu taso. Inteesar Tana ta Kiran Munari Tana Ringing bata Dauka ba ganin yadda ta Dakuna Fuska ne yasa Daddy ya kalleta yana Fadin"Baki same ta bane..? Inteesar tace"Na sameta bata Dauka ne Daddy..! Tafada cikin Shagwaba ya Basheer Daya kamalla wayarsa ya Kalleta yana Fadin"Sai ki bari Next time in muka Dawo..Yanzu pass4 kuma kinsam Kaduna muka Nufa..! Inteesar ta Marairaice Tana Fadin"Kai ya Basheer..Tafa ce zata zo wlh..Gidansu nan nan kusa Daddy naje na Kirata..?Itama tana so Taga Daddyna ne fa..,! Kafin Daddy yayi Mgana Basheer yace"No Daddy..Lokaci na tafiya in ka Biyema Shirmen Intee zamu yi Dare a Hanya..! Sagir yayi Saurin cewa"Ai gidan ba Nisa..Nan fa kusa ne..! Daddy ya kallesa yana Fadin"Ai mun Riga mun yi Daran Basheer barta taje ta Kirata..!.. Basheer bai ce komai ba kada kai kaawai yayi,Inteesar taji Dadi ta Fara Tafiya Tana Fadin"Tanque Daddy..! Gudu Gudu Sauri Sauri Take Tafiya Har ta isa Gidansu Munari Saboda Saurin Datake yi ne yasa bata Tsaya kula mganar Iro ba shi kuma yana so ya gayamata ba kowa agidan sun Fita Har da Abba Amotar Yusuf. Tana ta Sallama Bayan ta Turo kofar Falon ta Shigo ba"a amsata ba Tayi mamakin rashin ganin Abba zaune yana Kallo ko yana Karatu Falon tabi da Kallo alamun Shuru ba kowa Tayi Tsam kafin aranta tace ko basa nan ne..! Tuna haka yasa kawai ta Juya Zata koma sai taji Karan Bude kofa Tana Juyowa suka Hada ido Hudu dashi. Imran ne yana Tsaye yana kallomta Yana Sanye da Dogon Wando baki da Wata Farar riga amles,Hannunsa Daya Cikin Aljihun wandonsa Dayan kuma Karan Sigari ce tana kunne Hayakinta na Turiri. Gabanta sai da ya Fadi Data gansa Haka Duk gabar jikinsa tana waje sai ta gansa wani Kato dashi. Baya taja cikin Rawan jiki zata kara Juyawa Taji yace Cikin Kaushin murya"Wa kike nema..? Yafada Lokaci Daya yana wuceta zuwa Saman Dining. Ruwa ya Dauko a wani Jug ya samu karamin Kofi ya Tsiyaya ya Dago yana kallonta Daga sama Har kasa Lokaci yana Kurban Ruwannsa Hade kuma da zukan Hayakin Sigarinsa.. Inteesar Dataji gabanta na Dukan Tara Tara bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana. Shi kuma Ransa ne ya Fara baci da Yarinyar lokaci Daya cikin Dakiyarsa yace"Ke kurma ce..? Ina mgana kina min banza..I Hate it..Ya zama Dole in nayi mgana abani Amsataaa..! Yafada cikin Tsawa da Daga Muryan Dayasa da Sauri ta Dago Tana kallosa Itama Mamakinsa take ji yadda yake Zukan Taba Kuma yana Kurban Ruwa anya wannan yasan abunda yake yi kuwa..! Itafa duk sadda zata gana yana Shan Taba ne ko Lafiyarsa ma Bayaji..? Ganin kamar ya fara Takowa ne yasa da Sauri tace"Ina yini..Wajen Munari nazo..kuma inta kiranta a waya bata Dauka ba..! Kwayar idonta yake kallo yaso ne ya isa gabanta yayi kwallo da ita sai kuma yaji ya kasa Muryanta da Idanuwanta kamar wani Kaifin Dafi ne garesa sai yaji ya kasa komai. Dakyar ya iya kauda kai yace"Bata nan..! Kallonsa Tayi ta gefen ido kafin tace"Ina taje..? Abba fa da Anty Safiya..!? Yaso ne ya Daka mata Tsawa sai kuma ya kasa Cikin kosawa yace"Suma..! Daga haka ya tsuke bakinsa Cikin mamaki take kallonsa tace"Suma basa nan..? Kai ya gyada mata Domin ta Fara Takuramai da mgana. Abun sai ya bata mamaki tace"Ina sukaje haka..? Yana jinta yayi kamar bai jita ba Har ta Juya sai taji yace"I don"t know..Kamar dai sun shiga cikin gari ne..yama sunan wajen wasannin nan.? Da sauri Inteesar ta waigo tace"Shoprite..,! Kofin Hannunsa ya Ijiye bai yi mgana ba Inteesar an samu waje sai ta karkace tace"Wato Family Outing sukaje yau kenan..? To kai me ya Hanaka Zuwa..? Da sauri ya Dago Jajayen Idanuwansa yana Kallonta Sauri ja da baya Tayi Domin Warin taban ya Isheta zuciyarta ta Tafara tashi kuma ba Halin Toshe Hanci. Cikin kallon kin Rainamin wayau yace"Ni nayi miki kama da yaro ne Dan goyeko mai Tatata..?am not a Boy kin gane..? Yadda yayi mganar kamar ta saka Dariya sai ta kanne nan kan Dinning din ya Mutseki Sigarin ya wuce zai shiga Dakinsa,bayansa tabi da kallo Haka kurum taji Tsausayinsa itafa har ga Allaj kallon mara Lafiya take mai. Cikin gwarin gwaiwa tace"Don Allah ka Daina shan Sigari bata dace dakai ba Sam..! Cak ya Tsaya Daga Dora Hannunsa kan Handle din bedroom dinsa ya Waigo yana kallonta Sagir da yusuf suna Fadamai shan Sigari bata dace dashi ba bai taba jin mganar ta shigesa ba sai yau. Ba karamin Juriya tayi ba wajen Kallon kwayan idanuwansa ba ta Cigaba da Fadin"Ba domim Iyalanka ba..Ko Domin Lafiyanka Don Allah kabari..nasan ka sani sai dai zan kara Sanar dakai a likitance Shan Sigari Tana Illah ga Lafiyar Dan"adam..Domin Lokaci Daya take yima Huhun Mutum illah..! Tana Gama Fadin haka ta Juya da Sauri ta Fice jin wayarta na Vibration kuma ta Tabbata ko Daddy ko ya Basheer ne suna jiranta. Ficewa Tayi Daga Falon tana Sauke Numfashi Miyau ta Zubar Jin Hancinta na Budewa Tana so ta Shaki iskar Haraban gidan ne ko Hancinta zai Daina Shako mata Warin Sigarin Dake Neman sakata amai. *Ina godiya masoyana na WhaApps da yan Wattpadian ina ganin Sharhinku Allah ya saka da alheri sai dai ina so nadan yi wani Tsokaci ne kan mganganun wasu masu Sharhi kan Suna Tantama Anya Imu kansa Daya..?wai ko yana da Aljanune..?ko kuma yana da mental problem..?Amsa itace Imran Lafiyayyan Mutum ne kamar kowa,Bai da wata Cuta ko Nakasu in kun Duba Labarin Tun abaya ba inda na saka yana da wani mtaala sai Mtsalansa D'aya na Rashin Controling kansa in Ransa ya baci,Kuma akwai mutane irin haka yana da zuciyar Fulani ne ajikinsa,in kun lura Saboda Sanin Halinsa yasa bai shiga Harkan kowa kuma baisan batama mutane rai koda ahalinsa ne,in kun karanta ko da yan gidansu bai Doguwar mu"amala saboda gujema bacin Ransa,Baya kaunar a batamai rai shiyasa yake gujema bacin ran Wadanda ke Zagayo dashi a labarina ban nuna inda Imran yayi wani abu haka kurum batare da an shiga Harkansa ba,Yana da zuciya mai kyau kuma ka in kiyayemai zaka ji Dadin Zama Dashi mganar ko Imran baida Lafiya to Lafiyarsa Kalau Tsarin Hallitarsa ne haka Team Imran da Team Inteesar duka sun ce suna Godiya Son so Fisabilillah* *Shakira..* 3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *🅿�22* Tun bayan fitan ta bai motsa Daga inda yake ba Mganganunta sun kashe mai Jiki duk ba wannan ne Karo na Farko da aka sha gayamai shan Taba bai dace dashi ba kuma ba yau ya Fara sanin Smooking yana da Matukar illah ga Lafiya ba sai dai karon Farko ne ya Farajin Tasirin mganar acikin kansa da kwalkwalwarsa. Kofar data Ficen ya kurama Ido Lokaci Daya Zuciyarsa na Bugawa da karfi da karfi a duk Lokacin Daya ganta ko yaji mganarta wani abun mamaki mganarta Tana da matukar Tasiri acikin Zuciyarsa. Cikin kasala da Sanyin jikin da Kalaman Inteesar suka Sanyasa ya Tura Kofar Dakin nasa ya Shiga Kafin Fitar sa Yayi Niyyar Daya dawo zai Dora Daga inda ya tsaya na Busan Hayakinsa Tunda Kishirruwa ne ya Fitar dashi sai dai kuma Ya kasa Daukan karan Sigarin ballatana ya kunnata Haka kurum yake jin amsa Kuwwar mganar Inteesar tarika Tasiri acikin Jikinsa da Zuciyarsa yasa yana ji yana gani bai kunna karan Sigarin ba sai ma Tattarasu da yayi ya Tura Cikin Side Drower din gadonsa ya koma ya kwanta Ringigine yama Rasa wani Tunani zai yi ko zai kama. Inteesar kuwa Tana Fita taci karo da Daddy da Ya Basheer da Sagir ya Rakosu a Mota sun gaji da Jiranta Tana Fitowa suna isowa kofar gidan Fitowa Daddy yayi yana Fadin"Bata nan ne..? Kai Inteesar ta Daga kafin tace"Eh Daddy sun fita..! Daddy ya Bi gidan da kallo Haka kurum yake jin wani irin yanayi Tare Dashi Kafin yace"Harda shima Yayan nata Dake kaiku makaranta..? Inteesar tace"Harda Abba da Anty Safiya suka fita..Ya Imran kadai na Tarar a gidan..! Daddy zai yi mgana Ya Basheer Dake Bangaran Direba ya Leko yana Fadin"Plz Daddy..Lokaci fa yatafi..! Daddy yayi ajiyar Zuciya kafin ya Kalli Inteesar yana Fadin"Shikenan ki gaishesu in sun dawo..Shiga Mota sai mu sauke ku mu wuce..! Yafada yana kara Bin gidan da kallo kamar kada ya tafi Zuciyarsa Tana jansa Tana jin kamar akwai wani abu mai Muhimmanci da in ya Tafi Daga Wajen zai rasa,Sai dai bai da wata Masaniya kan haka,Komawa Gidan gaba yayi ya Zauna yayinda Inteesar ta shiga Gidan baya inda Sagir yake. Ba wanda ya kara mgana har suka kariso kofar Gidansu Sagir aka sauke su Inteesar sai da Idanuwanta suka cika da kwallah Lokacin Datake Dagama su Daddy Hannu har sai da Motarsu ta Kule ta Daina ganinta kana ta Juya Zata koma Cikin gida. Sagir ya Kirata ta Juyo Tana kallonsa Kai Tsaye yace"Kinga Imu..? Kai ta gyadamai batare da tayi mgana ba ganin yanayinta yasa bai kara magana ba Har ta Juya ta Shige gida. Koda ta Shiga Mama ta Zagaya Makewayi Daki ta shige ta Fada Kan gado Cike da kewar gida Tana nan kwance Mama ta Shigo Tana Tambayanta lafiya ta ganta Kwance tace Lafiyalau nan take Fadama Maman bataji Dadi ba Daddy basu hadu da Munari sun gaisa ba Har gidan Taje basa nan.. Mama tace kada ta Damu akwai wani Lokacin zasu hadu su gaisa Tunda ana tare da juna. Sai bayan Mangriba Munari ta Kira Inteesar tana bata Hakuri Dawowarsu kenan Salla kadai tayi ta Duba wayarta Sai taga Kiranta nan Inteesar ke gayamata Har gidan tazo bata Isketa ba Daddy ne yazo zai Wuce yace a Kirata su gaisa Munari ta Ciji yatsa tace ta zata bazasu Dade bane,Sai gasu sune Har gidan Zoo Shiyasa suka Dade basu Dawo ba Inteesar tace bakomai akwai gaba Kamar yadda Mama tace Daganan sukayi Sallama Akan sai Gobe In Munarin ta Biyo mata Tafiya makaranta. Washegari Monday da Safe 8am suke da Lecture 7:30am suka shirya Ya Yusuf ya ijiyesu Kafin ya wuce Wajen aiki Har shi sai da Inteesar ta Fadamai Zuwan Daddy su gaisa jiya basa nan Shima bai ji Dadi ba yace sai dai Wani Lokacin da yardan Allah zasu Hadu su gaisa. Ranar da Wuri suka Fito Daga Cikin makarantar,Shiyasa Inteesar taja Munari zuwa Gida ta Diban mata Dambun nama da kayan Snaks din tace ita dasu Abba Munari nata Godiya sai da Tayi Sallar La"asar suka ci abinci kana Inteesar ta Fito Zata Rakata Zuwa Gida sukayi Kicibis da Imran da Sagir akofar gidansu Imran din suna mgana,Da suka gansu Munari tafi Tsorata Domin jikinta sai Rawa yake yi Inteesar kuma mamaki take na yau Kadai da Tataba ganinsa baya Shan Sigari. Yana Sanye Cikin Riga da wando,Rigar mai ruwan kasa Mai gajeren hannu sai Wandon baki ne Wanda yadan Kamasa ta kasa Kafarsa Sanye Cikin Wani Tattausan Takalmi,Kamar Koda Yaushe Hannayensa Zube cikin Aljihunsa. Sagir kuma yana Gefensa Har Kafadunsu na Dukan na Juna duk da Imran din ya Fisa Girman jiki da Tsawo. Tundaga Nesa ya hangesu sai da gabansa ya Fadi Daya ganta yarinyar nan Kamar Aljanna Jiya wuni yayi Tunaninta Haka kurum baisan Dalili ba Fuskarta na yawan Gilmamai acikin Idanuwansa. Yau a tsarinsa bai ma yi niyyar Leko waje ba,ko Sallah acikin Dakinsa ya Dinga yi shi kadai yau din yana Son ya Zauna shi kadai baya son yaga wani Wanin kuma bazai gansa ba sai da Zuwan Sagir yasa Dole ya Fito,Har ciki ya shiga suka gaisa da Abba da Anty Safiya bayan ya Kirasa har ya gaji bai Daga ba Shi ya Bisa Har cikin Dakinsa ya jawosa nan waje yana Tambayansa Laifin me yayi mai ya Daukemai kafa..? Bai ma kai ga bashi amsan bane ya Hangi Tahowar Munari da Inteesar. Ganin inda ya Raja"a Kallo ne yasa Sagir maida Hankalinsa wajen sai ya Ci Karo da Munari da Inteesar. Karisowa sukayi gabansu Munari ce Cikin Rawar murya ta fara Fadin"Sannun ku..Ina yini Ya Imran..?Ya sagir ina yini..? Tafada Cikin rawar Baki Tana kara Damke Jakarta Dakyau tana Jiran Imran yace kyat ta Zura da gudu Daman Ledan da Inteesar ta sakamata Su Dambun Naman yana Hannunta ne. Imran kallo Daya yayi ma Munari ya gauda kai bai kara Kallonta ba kansa na kasa ya Kurama yan Yatsun kafar Inteesar Kallo da sukayi kyau Cikin wani Falt din jan Takalmi yatsun Dogaye ne suna da Haske sai jan Lallen data Cike Fararan kumbunanta dasu bai Taba Tsayama ya Kare ma Fuskar Mace kallo ba Ballatana Kafarta sai gashi yau ya shagala da Kallon Kyakyawan yatsun kafafun Inteesar Batare daya sani ba sai dai yaji Zuciyarsa na son Kallonsu Sun Burgesa sosai. Sagir ne kadai ya amsa yana Tambayansu Karatu sukace Alhamdulillah Inteesar kuwa Ina yini Ya Sagir..! kadai tace aranta tace bazan gaisheka ba ka Dizgani Kanwarka ma bata Isheka kallo ba Ballatana ni Maras Mutumci mai shan Taba kawai Duk aranta take wannan Zencen cikin Takaicinsa. Ita ta kama Hannun Munari suka Buga Kofar get din Iro ya leko ganin sune ya Bude musu suka Shiga Da Karamin kallon Gefen Fuska Imran ya Bisu dashi kafin ya Sauke ajiyar rai yana cije baki yace"Yarinyar nan bata kunya naga alama..! Sagir ya Kallesa Cikin mamaki Kafin yace"Wata Yarinya..? Ido nacikin ido Imran ya Kallesa kafin yace"Wata yarinya kake Tambaya..?kanwaka din nan wacce take zaune agidanku mana..! Sagir ya karbe da cewa"Da tayi maka mene..!? Imran yace"Bata gaisheni ba.ko kana Nufin Abunda tayi mai kyau ne. ? Sagir ya saki karamin Tsaki kafin yace"Eh mai kyau ne..Saboda Halinka...Agabanta Munari ta gaishemu kaki amsawa kayi kamar ma baka ganta ba..kana Tunanin ko Nice zan gaisheka bayan agaban idona naga abunda kayi ma kanwarka..? Imran ya Dakuna Fuska kafin yace"Wannan ba Hujja bane..Gaisuwanta Dabam na Munari Dabam..!. Sagir yace"Duka Dayane Mallam..Kai dai kawai kace ka Tsani yarinyar nan Shiyasa naga ba tun yau ba kake Neman kowani Laifi ka goga mata..! Tsaki Imran ya Saki kafin yace"Eh na Tsaneta ko zaka Daukan mata mataki ne Ubanta..? Yafada yana Jefan Sagir da kallon kada ka karamin wannan mganar Banzar.. Sagir yace"Inafa..Ai Allah ne yakadai zai iya mganinka bani ba..! Imran ya Murmusa kafin yace"Bettter Daka Fahinci hakan..Mallam zan shiga Ciki in baka da tacewa..? Sagir yace"Yaushe zaka Dawo shago..?ko kuwa gabar da kake yi dani baka Saki bane...? Imran ya Dakuna Fuska kafin yace"Gaba..? Ni Imran bana gaba da Wani ko wata..Sai dai in nagaji da Zama da Mutum nayi nesa dashi..Kai im zan yi gaba dakai Gaba da gaba Zan Tareka nace maka baka bani..Tunda kai ba Ubangijina bane Bana Fatan Watarana naji tsorom wata Hallita ba Allah na ba..! Ya cigaba da Fadin"Kuma ba Daina zuwa shagon ka nayi ba saboda kamun wani abu ba..Kawai ina Bukatar Kadaici ne..In na Dawo Daidai zaka ganni kai dai ka Girma ammh kullum kana Dawowa kamar wani yaro..saboda cin kasa! Ya karishe Fada yana Kara Hade rai Baki Sagir ya saki kafin yace"Nine wanda ke cin kasan..? Imran ya juya ya fara Tafiya yana Fadin"To da waye..? Ya fada yana yar Dariya Kafin ya shige gida ya bar Sagir nan tsaye yana Binsa da kallo Tsaki yaja yana Fadin ba Laifinka bane nawa ne da nake binka kana gayamin mganar banza..daganan ya Juya Fuu ya Fara Tafiya aransa yana Fadin bazai Kara Neman Imran ba In ya Nemesa Shikenan in kuma bai Nemesa ba He don"t Care. Imran na Sawo kansa Cikin Falon suka Ci mummunar karo da Inteesar Da Sai da Kafadarsa ta Daki kanta Tunda ya Fita Tsawo,bata san dashi ba da Karfinta ta Jefa jikinta Munari na Binta zata Rakata Haraban gidan,Kafadarsa ba kadan bace kuma Shima da Sakin jikinsa ya Sawo kansa Falon baisan da ita ba Shiyasa ya Bangajeta Bangazan da ta kasa Tsayuwa da Kafafunta tatafi Luu zata Fadi ta Gefenta da Wani Zafin Nama ya Saka Lallausan Igarman Hannayensa ya Tarairayota ta Fado kan Kirjinsa da karfinsa Har Karan Hancinta da Kirjinta suna Dukan Faffadan Kirjinsa. Munari Dake tsaye har ta Sadakar Inteesar ta gama shan kasa,sai kuma ta kame gefe Daya tana kallon Inteesar Rike hannun Ya Imran hannayensa Zagaye da Kugunta Yayi mata Riko sosai. Inteesar abun ya Faru cikin Lokaci kadan ne shiyasa bazata iya Tantance komai ba,sai da taji wani Ingarman Namiji mai Zatin jarumta yayi Saurin Tareta kuma ya Tallafota zuwa jikinsa Maida Nunfashi take sama sama Inteesar akwai tsoro ta Tsorata da Fadin da Zatayi yasa ta Saka Hannayenta Guda Biyu ta Rike Rigar Imran dashi Idanuwanta a Lumshe Tana maida Numfashi. Imran kuwa wani Sanyi yaji yana Shiga Jikinsa da Zuciyarsa wanda Tunda yazo Duniya bai taba jiba ba..Kirjinsa Duka kawai yake yana Fat..! Fat..! Da karfi kamar wanda yaga wani abu tsoro.. Fuskar Inteesar ya Kurama ido Wacce ke kan kirjinsa Tana Rirrike dashi Da karfi,Kallonta yake kamar yana son ya Haddacr komai na Fuskarta Kada ta bacemai,Yana jin kamar Rikonta wani Salama ne da Farinciki awajensa kamar in ya Saketa zai Tagayyara ko zai Lalace yana jinta acikin jikinsa kamar Wani gafara ne Daga Allah. Abba ya Bude Kofar Dakinsa ya Fito Dauke da karamin Littafin azkar Jikinsa Sanye da Wata Farar shadda Dinkin Riga da wando har da Hula. Ganin Imran da Inteesar a wannan yanayin sai da gabansa ya Fadi Cikin Azama ya Karisa Cikin Falon yana Fadin"Kai Imran Lafiyar kuwa ka Rike Diyar mutane..,? Yafada da dan Karfi wanda ya Dawo dasu Dukkansu Cikin Hankalinsu. Inteesar jin muryan Abba asama yasa ta Dago Tana kallon Fuskar wanda ke Rike da ita ai Tana ganin Imran taji wani Yam! acikin jikinta da Sauri ta Kwace Jikinta Ta mtsa baya tana Maida Numfashi Shi kuwa Daman jikinsa ba Karfi ga Kasalan data Rufeshi shiyasa Inteesar ta iya kwace Jikinta.. Da Lumsassun idanuwansa ya Kalleta Kafin ya juya ya kalli Abba batare da yayi mgana ba ya Fara tafiya zai shiga Dakinsa,Abba ya Daga baki yace"Kai IMRAN ya ka nan ya ina maka mgana kana wucewa..? Yafada cikin bacin rai baya Fatan ace Ya Doke yar Mutane ne Juyowa yayi yana jin mganar tamai nauyin ya Fada Munari ce tayi Saurin cewa"Abba Karo sukayi da Intee...Basu ga juna ba Shine zata Fado ya Rikota..!. Ajiyar rai Abba ya Sauke Kafin ya Maida kallonsa kan Inteesar Dake Jin wani iri acikin jikinta yace"Sannu Baki dai ji ciwo ba ko..? Inteesar Dakyar ta iya Bude baki tace"A"a Abba..Sai da safe..! Tafada tana Juyawa,ta gefen ido Take kallon Imran yana Shiga Dakinsa Abba yanata ta gaida Mama,Ta fice Munari ta Bita abaya suna Fitowa Munari ta Riko Inteesar tana Fadin"Kai Besty kinga yadda kikayi ajikin Ya Imu..? Na Rantse har ga Allah kunmin kyau kamar a Indian Film din nan irin Jarumar zata Fadi Jarumin yayi AzAman rikota ta Fadomai..! Ta Kariashe Fada tana Dariya Inteesar ta Harareta Lokaci Daya tana Tuno yanayin data Fada kan kirjinsa sai da jikinta ya amsa domin Bayan Muharramanta wani namiji bai Taba koda taba Hannunta ba sai yau wanda Komai ya Faru bisa Rashin sani. Ganin taki mgana yasa Munari ta Cigaba da Fadin"Nayi mamakin Ya Imu yau..? Kun bala"in dacewa kamar ace ku din Couple ne..! Da sauri Inteesar tace"Da wa..?Allah ya Tsareni baki man fatan kwarai ba..Indai na auran wannan Muradadden yayan naki ne..! Munari zata kara mgana Inteesar ta Dakatar da ita da Fadin"Kinga ni kyaleni..Nagode Daya Taimakeni Daga Faduwa kawai..Sai da safe ki koma gida malama..! Munari ta kada kai Tana Fadin"Daga waasa..? Allah baki Hakuri..! Inteesar ko kulata batayi ba ta wuce Munari ta Bita da kallon Cikin Rashin jin Dadin yadda ta Bata mata rai ita Har ga Allah waasa take mata kada kai Tayi ta koma Cikin gida Tana Fadin gobe zata bama Inteesar hakuri banda Abunta Ya Imu ai ba Aure ma yake da Ra"ayin yi ba Ballatana wannan mganar ta Dameta. Inteesar har takai gida ta rasa yanayinta Kowani Dakika abunda ya Faru ne yake Dawowa mata Kuryan Daki ta Shige ta Fada kan gado ko Hijabin Jikinta bata iya Cirewa ba,gabanta sai Fadi yake Data Runtse ido sai ta ganta Rike da Imran Kirjinta yana Saman kirjinsa Runtse ido Tayi a Fili ta Furta"Shikenan Mara Mutuncin nan ya gama dani..! Take fada tana kara jin wani Takaici Da ta Tuna abun sai ta Saki Tsaki kuma abun yaki bace mata acikin Ranta da Zuciyarta Har Mama Sai da ta Tambayeta ko Lafiya jin yadda Lokaci Bayan Lokaci take sakin Tsaki Sai ta sanu kanta da Boye abunda ya Faru tace bakomai. Bangaran Imran kuwa ya kasa Gane Yanayinsa In ya Runtse ido Sai yaji Fadowar Inteesar a Kirjinsa sai gabansa ya amsa Yana jin alokacin Yanayinsa ya sauya kamar bashi ba yana Tuna yadda ya Saka Hannayensa ya Zagaye kugunta dashi,yana kwance da Silasin Dare ya kasa barci Ya Busa Sigarin nasa Ammh duk a banza Yana kwance yana Tunani kafin ya Murmusa afili ya Furta"Kugun nata ma D'An karami ne kamar yadda take karama da ita..! Yafada yana Bin hannuwansa Daya Daga da kallo. Kafin ya kara Juyawa yana Yin Filo da Hannayensa yace"Sai Rashin kunya kuma..! Yafada shi kadai kuma yayi Mirmishi kamar wanda ya zare,Rufe Manyan Idanuwansa yayi Yana Fatan barci ya Daukesa sai mai gabadaya Fuskar Inteesar ne take mai Hazo da Gilmawa acikin Rufewar idanuwansa,Sai Mirgina yake yi yakasa Barci in ya Bude Idanun nasa ba Fuskarta yake gani,Mikewa Zaune yayi Cikin Duhun Dakin Sai dan Hasken Dake shigowa ta Labulan Dakin Dayake Dagawa ta Window. Kansa ya Dafe yana Fadin"meke Shirin Faruwa dani ne..?taya ya ko ina nake ganin Fuskarta..? Kodai ba Mutum bace Aljanna ce..!? Wata zuciya tace"Mutum ce ba Dazu kaga Kafarta ba..Bata da Kofato..! Sai kuma ya Saki Mirmishi kafin ya koma ya kwanta Ringingine yana mai Dora kansa saman Hannayensa acikin Ransa yace"Koma aljannace...Ni Imran nafi karfinta..! Daga haka barci ya kwasheshi Dakyar ammh Abun mamaki masu cike da mafarkin Inteesar Washegari sai 10am suka shiga makaranta Shiyasa Ya Yusuf ya tafi ya barsu sai da suka fito Daga Lecture suna Hanya zasu masallaci Munari ta Kalli Inteesar data ganta Yau wanu iri bata da Kuzari kamar ko yaushe tace"Besty wai duk fushin ne... ? Am Sorry..Wlh am just kidding..! Inteesar ta kalleta kawai batace komai ba Sai Munari Taji wani iri Riko Hannun Inteesar tayi yasa suka Dakata da Tafiya Munari ta kalleta Tana Fadin"Meke damun ki ne..? Inteesar ta Saki Mirmishi kafin tace"Bafa komai..Kece wai kika bani mamaki kina wani ban hakuri..? To miye na ban hakuri..? Munari tace"Ai naga jiya baki ji Dadin nganata bace kuma..! Manta kawai..! Inteesar ta Katseta Lokaci Daya tana jan Hannunta suka Cigaba da Tafiya Munari dai sai kallonta take tana Naxarinta ta Tabbata wani abu na Damun Inteesar Ta san ta Tana da Sakin jiki da wanda suka saba kuma Tana da Kuzari da kazar kazar ba kamar yau data ganta sai a Hankali ba Ganin yadda Tayi ne yasa bata kara Tambayanta ba ammh Haka suka Wuni acikin makaranta Inteesar bata da Kuzari sai chan ne na ta Dan saki suka Fara Hira, Abunda Munari bata gane bane Inteesar Tunanin Abunda ya Faru jiya yaki wucewa acikin Ranta,itama Har mafarkin abun ta Sake yi,wai gata Rumgume ajikin Imran sai abun ya Dameta sosai Tana ganin ya gama da ita ne Tunda ya Rumgumeta kuma abun da bata saba dashi ba Shiyaasa duk ya Sakarmata Jiki da kwarin zuciya. Sai dai ta saka aranta bazata Kara yarda su hadu da Imran ba Domin ai Tunda ya Rungumeta yaji Tudun Nonuwanta ya gama da ita Har Abada. Tun kuma Daga Ranar Inteesar ta Yanke duk wani Hanyar Haduwarta da Imran ta Rage shiga gidansu in zata Shiga kuma sai ta Tabbatar da Baya gida,In kuma ta Hangesa sai ta Boye kanta saboda Bata so ya ganta. Imran daya Daina ganinta bai Damu ba Sai Daga baya sai ya fara jin ya Damu Saboda ya daina ganinta agidan kuma bazai tambayan Munari ba,Yana Tsoron kada ace ta Koma Gidansu ne,Ya ma rasa Dalilinsa na Wannan tsorom Ranar har kiran Sagir yayi yana Tambayansa Wannan yarinyar fa..? Daman Sagir na jin Haushinsa a Gadarance yace mai"Wata yarinya kuma..!Rainin Wayau ne baya so Shiyasa ya Datse Kiran yana kara jin Haushin kansa me ye hadin da ita..! Da zai ji ya Damu Domin ya Daina ganinta da wannan Tunanin ya Watsar da komai shi kuma Sagir bai maida kai kan mganar Imran ba yana Tunanin wani Wulakancin nashi ne ya Tashi kan Inteesar shiyasa ya Nunamai bai ma Fahimcesa ba. Sai dai mai Imran yaji Duk Duniya Fuskar Inteesar yake son gani Duk da ya gama Haddace Fuskarta Inda ya Iya zane zai iya Zama ya zana sai dai Haka nan yake son kara Kallon Fuskarta Kamar za"ayi mai gafara Dalilin haka ya koma Zuwa Shagon Sagir,wanda yaransa Har sun Fara Sakewa suna Murnan Takurarre ya Daina zuwa sai gashi Ranar kwatsam ya Dawo,Ai Ranar ba wani wanda yayi Wani Motsi mai Karfin Sanin Halinsa Mganarsa kamar yankan Takobi ne in yace Dole sai takai Sara ne. Ba domin kowa ya dawo ba sai Domin Inteesar ya gama yanke ma kansa mganar Cewa Inteesar ba haka ta barsa ba indai ita ba Aljannah bace to Akwai wani abu akasa. Taya ya haka kurum rana Tsaka Zai Dawo ba Wacce yake son gani sai ita a Baya yadda da ana cewa Ana ma Mutum asiri sai yanzu ya Fara Tunanin asiri tamai ya Zama Dole ya ganta ko yatambayeta Me yasa tamai asiri sai dai bai samu ganinta ba,Ko makaranta suka Dawo bata yarda ta Sauka ta Kofar Shagon Sagir sai takara Chan gaba in kuma a kafa suka Tako da Sauri take wuce wajen bata ma ko kallon Barayin Duk da tana ganin Imran din ammh shi baya ganinta,sai sau Daya kuma kafin ya yi wani yunkuri ta Shige shi kuma bazai iya Binta ba. Ana cikin haka suka Fara Test basa Samun Lokaci domin suna gabda Fara Exams din Farkon Zangon Karatunsu. Daddy yazo ya ganta Sau Daya shima amakaranta ya Bita bai gayamata zai zo ba,Kawai ya Kirata yace ta ina..?murna kamar Inteesar zata Shida aka kuma yi Rashin Sa"a Munari ta Shiga Masallacin yin Sallah ita kuma Inteesar sai bataje ba ta Zauna anan Department dinsu tana Duba littafanta Daddy ya kirata. Ashe ma ya shigo Cikin makarantar yana Office din abokinsa Wani Daurin auran Yar abokin su da sukayi karatu Tare ya kawosa,chan taje ta samesa suka ga juna,bai wani Dade ba yace zai tafi Har Department dinsu suka Dawo Neman Munari bata ganta ba Ta Kira wayarta sai ta Tuna ai jakar na Munarin gata a Hannunta,Kuma har Masallacin taje akace mata ta Fito,Karshenta Dai Daddy tafiya yayi basu hadu da Munari ba sai bayan tafiyarsa ne ta ganta ashe itama Nemanta Takeyi kuma ba waya ballatana ta Kirata Cikin Rashin jin Dadin Inteesar ta Fadamata Zuwan Daddy da Tafiyarsa ta bata 5k din Dayace ta bata Ita kuma 15k ya bata 10k yace takai ma Mama Munari ta karba Tana ta Godiya Tare da Cizon Yatsan Rashin Ganin Daddy a Karo na Biyu. Sati biyu da gama Test dinsu suka Fara Jarawabawarsu Cikin Kwarewa Dama Tuni sun shiryamata basu sha Wahalanta ba,Inteesar nata Murnan Zuwa Gida Kaduna yayinda Munari ke alhinin kewar Inteesar din. Sai uku sukayi suna Jarabawa kafin su gama sun samu Hutun Sati uku kafin su Dawo su Dora a Karatun Zango na Biyun aji Daya Aranar da suka gama Inteesar Kamar Zata Suma saboda Murna ta gama Hada kayanta Ya Basheer da Safe zai zo ya Tafi da ita. Munari duk ta shiga Damuwa Saboda Tafiyan Inteesar din itama Tana jin Zatayi matukar kewar Munarin. Bayan sun Rabu aranar Inteesar Tayi Tunamin ta bama Munari wani abun Da Zata Rika Tunawa da ita sai ta Dauki wani Dankunnen gold dinta mai Sarka da Zobe da awarwaro ta saka ajaka zata kaima Munari ba Domin bata dashi ba sai Domin Wani abun da Zata Rika Tunawa da ita in ta koma Kaduna itama Zataje Munarin ta bata wani abun da In ta koma Kaduna ta Kallah Zata rika ganinsa kamar Munarin. Karfe 5pm tayi ma mama sallama ta Fito tana Sanye Cikin bakin Wando plazo da wata Riga Mai Dogon Hannu ammh Tana da dan Tsawo,sai ta Sanya Farin hijabinta mai Hannu wanda yakai mata Har Gwiwa. Karamar Jakar data saka Dan kunnen aciki sai Kafarta Sanye cikin Takalmi Sahu Ciki Fari kalan na mata. Tun fitowarta Gidan ya ganta Lokacin ya Fito Daga Shagon Sagir Karan Sigari rike a Hannunsa yana sha Gida Zai tafi Domin yagaji da Zaman sai ya ganta Tanufi Hanyar gidansu Gabansa sai da yya fadi,Tun bayan mganar Data Fadamai na ya Daina shan Taba Kowa yasan ya Rage shanta sai dai Yanayin Dayake ciki na bukatuwan son ganinta ya kara maidashi Ruwa.. Jikinsa har wani mazari yake Zuciyarsa na Ingizasa yabi bayanta Cikin Takunsa na Sasasarfa ya Taka mata Baya Kowani Dakika na Takunta Sai Zuciyarsa ta Buga,kawai ya gama Sakama Ransa yarinyar nan asiri tayimai kuma yau sai ya Shaketa ta gayamai inda ta Binne koma Menene taje ta Hakosa Imran yafi karfinta bama Itaba yafi karfin matan da suka Fita komai da komai da duk Abunda suke Takama. *Janafty* 3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *🅿�23* Inteesar Tafiyarta take cikin Natsuwa Kwata kwata bata ji takun Sawun Imran ba Ballatana ta Fahimci He is after Her,Saboda Shi Yana tafiyarsa Cikin Sassarfa da mazantaka irin na Jaruman Maza sai dai yana komai Cikin Natsuwa ne da baka isa yana Tafiya kaji takun Sawunsa ba Shiyasa bata jiba har ta iso gidansu Munari,Karamar kofar tana Bude ne Ta saka Hannu da Niyyar Bugawa sai Kofar ta dan Bude shiyasa ta saka kanta kai Tsaye ta Shiga gidan Imran Shima alokacin ya Mara mata baya. Iro megadi bashi a Haraban gidan ya Kewaya. Hankalinta yayi gaba kawai taji ansha Gabanta da Sauri Cikin Tsoro taja baya Jikinta ya fara rawa da ganin wanda ke gabanta ya Kafe ta da Idanuwansa yana More Kallonta Da dukkan zuciyarsa Sai alokacin yaji Salamar Daya Dade bai samu irinta ba wani Natsuwa da Farinciki suna kara Kwaraya acikin Ransa wanda ada yake jinsa kamar yana yawo asaman Gajimare,Duk adalilin rashin ganin fuskar Inteesar wanda ya kara Tabbarar mai da Asiri Inteesar tayi mai kuma yau sai ya Tabbatar da koma Miye,sai ta Hako shi Duk inda ta Binnesa. Inteesar da gabanta ke Fadi saboda Ganin Imran taja baya tana Kara Rike Jakar Hannunta Dakyau Wuri Wuri Take da ido Tana Neman Hanyar Gudu Har ga Allah bata son ta Hadu Dashi gani take kamar yana mata kallon na riga nagama Dake. Imran ya Lura da yadda take Neman Zurawa da gudu da Sauri yace"Don"t Ever Try it..Ranki zai baci in kika Gudu ban yi mgana Dake ba..! Yafada Cikin Dakuna Fuska da Kakkusan Muryansa. Miyau ta Hadiye da Sauri Kafin ta Sadda kanta kasa Tana Fadin"Ba..ba guduwa zan yi ba..Ina yini..? Tafada Tana kallon kasa bata so ta Dago su kara Hada ido Jikinta wani iri yake mata kamar ba nata ba. Karkace kai yayi yana Kallonta Cikin Nazari kafin taji yace cikin Kaushin Murya"Ina kika Binne asirin..? Da sauri ta Dago Tana kallonsa Cikin mamakin kalamansa tace"Asiri kuma..? Tafada Lokaci Daya tana Zaro mai ido Kai ya gyada mata kafin yace"Eh asirin da kikamin wanda yasa nake son ganin Fuskarki koda yaushe..! Yafada kai Tsaye domin shi daman Dan kai Tsaye ne Baya karya Domin ka so shi. Inteesar ta saka Hannunta Guda a Kirji ta Dafe Lokaci Daya Tana Fadin"Ni nayi maka asiri..? Ransa ne ya fara baci Cikin Dakuna Fuska yace"Eh kefa..Kina Nufin zam miki karya ne..? Inteesar datsoro ya kamata sai Idanuwanta suka Tara kwallah Cikin kwalkwal take fadin"Wlh..Wlh..Allah ni ban yi maka asiri ba..Ni ban taba sanin ma a ina ake asiri ba..Kayi Hakuri..! Sai hawaye Sharr duka Idanuwan Biyu Lokaci Tana Jan majina,Mamakinta ya kamashi ganin Daga mgana sai kuka yasa ya kasa ce mata komai. Kanta na kasa ta shiga Furta"Ban yi maka komai ba..Wlh bansani bane..Bansani ba..! Tafada cikin kuka Har tana Shan majina da Shessheka. Sai jikinsa yayi sanyi ganin yadda take kuka da Sauri yace"Ke daga mgana sai kuka..? Stop it kada wani ya fito yace ni na Dake ki..! Jin haka yasa ta fara share Hawayenta Tana Kara jam majina Kafin ta Dago Tana Fadin"Ka yarda ban maka asiri ba..? Wlh ban san ma inane ake asirin ba..In Umma taji wannan mganar Gobe in na koma Gida Zata min Fada ni kuma bana son Fada..! Tana kallon kwayan Idanuwansa Tana mgana Sai kuka kuma Sharr ta Kara Rike Jakarta Tana kuka,jikinsa sai ya Saki ya kasa Dauke ido Daga kanta Haka kurum yau karo na Farko yaji bai kyauta ba yasa wani kuka,Yau yaji Bai kyauta ba Daya Tareta da wannan mganar gashi tayi kuka ko Daga ganin yanayin mganarta bata san komai ba. Cikin Sanyin murya yace"Bazata ji ba..Kuma bazata miki fada ba..! Yafada karo na Farko Cikin Sigar Lallashi Jin haka yasa ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Ka yarda ban yi maka komai ba..!? Tafada Tana Kallonsa Kallon Dayajisa Cikin wani yanayi,Kai ya dan kauda kafin yace"Eh..Share Hawayen ki .! Yafada yana Kokarin Saisaita kansa Domin yanajin kamar ya Fara Fita Daga asalin Imran din sa yana komawa kamar bashi ba. Jin abunda ya Fada yasa tayi Saurin Saka Hannu ta Share Hawayenta Shi kuma yana ta kallonta tana Dagowa suka Hada ido da Sauri ta Sadda kanta Kafafunta na rawa. Aransa kuwa ayyana Shagwaban yarinyar kawai yake Daga mgana sai kuka..? Baisan Dalili ba kawai yaji yana ce mata"Gobe..ina zaki..? Bata Dago ba tace"Gida..yau mun gama Exams..! Cikin wani yanayi yace"Ina ne gidan naku..? Kanta na kasa Sitll tace"Kaduna..! Tsam yayi yana Kallonta jin Zuciyarsana so taji Rashin jin Dadin Tafiyarta bai san sadda Bakin sa ya Subuce ya Furta"In kin tafi sai yaushe Zaki Dawo..? inteesar ta Dago cikin mamakinsa Tana Kallonsa sai kuma ya Hade rai yana Tunanin meke Damunsa .? Kai ta Rausaya Kafin tace"Hutun Sati uku garemu..So kila bai fi na kara 1 week ba kafin na dawo..! Har tagama mgana bai ce komai ba Idanuwansa na kallon Gefe yana Tunanin yadda zai iya Zama har na Tsawon wata Daya kafin ta Dawo Cikin Idanuwansa yake kallonta Kafin yace"Ki dawo alokacin da kukayi Resuming..? Promise..? Yafada kai Tsaye yana Sakarmata Duka Idanuwansa wadanda suka Sake Rikita taji bazata iyamai gaddama ba. Da sauri tace"Tom..! Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya Bata Hanya batare da yayi mgana ba Kanta na kasa ta fara Tafiya shi kuma yana Gefe ya Harde Duka Hannunsa a Kirjinsa yana Binta da kallo yana ji kamar in tatafi shikenan kamar an Daukemai wani gafara,kamar ya Hanata Tafiya baisan yaushe ne ba..? Sai dai kallonta na mantar dashi Dukkan wani kuncin Duniya. Kamar ance ta Waiwayowa tana Juyowa suka Hada ido,Da sauri ya Dauke kansa ita kuma sai ta Murmusa kawai ta Tura Kofar da zai sadata da Falon Gidan tana jinta Cikin yanayin Data ke Tsintar kanta indai Tana gaban Imran. Sai da ta shige kana ya Sauke Idanunsa ya koma Kan Mashinsa Dinsa Dake Fake a haraban Gidan ya Haye Samanta Aljihun wandonsa ya saka Hannu ya Dauko kwalin aspen da Lether ya Kunnata ya shiga Zuka so yake yaji baya Tunanin Inteesar ballatana Gilmawar Fuskarta ko son ganinta so yake ji He don"t care in Tatafi sai dai ina Hayakin na Shiga Cikinsa Kamar baya saka Komai gabadaya komai ya Tsayamai Cak Mood dinsa ya sauya yana so yayi Tunanin kan karan kanshi ammh ya kasa Kowani Dakika yana jin Tsorom Tafiyarta na Tsawon kwanaki bazai ga Fuskarta ba. Bai san adadin Lokacin Daya Dauka yana Zaune yana Busa Hayakinsa ba Har sai da Ya Yusuf ya Dawo Daga Wajen aiki,Har mgana yayi mishi Imran din ya Daakuna Fuska ya Kaida kai ganin haka yasa ya Girgiza kai kawai ya Rataya Jakar Briefcase dinsa ya Nufi Cikin Gida aransa yana Tunanin zai samu Abba da Mgana ya Lura Imran abubuwansa basa Raguwa sai ma Karuwa da sukeyi. Afalon yaci karo da Inteesar Munari ta Rakota Da ita da Anty Safiya sai Abba Dake zaune Sallama Tayi Musu Abba nata saka mata albarka. Kallonta yayi yana Fadin"Me sunanki na gaskiya..? Inteesar na Mirmishi Cikin Ladabi tace"Sunana MARYAM Abba sunan Kakata naci wacce ta Haifi Daddy na shiyasa yake kirana da Intee har sunan ya Bini..! Abba ya Kalleta Cikin Dattakonsa yana Fadib"Masha Allah ai nima sunan Mahaifiyata Gareki..Daga yau kin tashi Daga yata kin koma Uwata..Allah yayi albarka..! Inteesae bakinta Har kunne tace"Na zama Maman Daddy da Abba kenan..! Su Munari nata Dariya ta gaida ya Yusuf ya amsa yana Kallon Safiya yace"Naga kamar kuna Sallama ne..? Da sauri Munari tace"Gobe zata koma Gida Hutu ya Yusuf.! Tafada Cikin nuna Rashin jin Dadinta Kada kai yayi yana Fadin"Ayyah..Munarin Abba zaki bari da kewa...Anywhy..Allah ya Kiyaye Hanya muna gaida kowa da kowa..! Abba ma ya Karbe da cewa"Kice ina gaida Daddyn naki..In Allah ya Nufa zamu hadu..! Inteesar tace"Zaiji Abba..Ka manta bakace agaida Umma ba..Umma Sarkin Fada..! Tafada Tana Tura baki Munari ta Zungureta tana Fadin"Ke kuma Sarkin Shagwaba da Laifi ko..?Dariya suka sakamata Anty Safiya ta Mikamata Leda Hannunta Tace takai ma Umma Turaruka ne Dana Daki da Humra Inteesar ta Karba Bakinta Har Kunne Sallama sukayi ta karbi Jakar Hannun Ya Yusuf suka Nufi bangaransu Itama Daganan tayi ma Abba Sallama ya Bita da Allah ya Kiyaye hanya Ana gabda da kiran mganariba yasa ya tashi ya Shiga ciki Domin ya Dauro alwala,ita kuma Munari ta koma Bedroom dinta ta Dauko Mayafinta ganin ba kowa afalon yasa Inteesar ta Fice zuwa Haraban gidan ta jirata Hannunta Dauke da Ledoji guda Biyu Daya Sakon Anty Safiya ne Daya kuma na Munari ne kaya ta bata Da Hijabi Sabo ne bata taba sawa ba ya yusuf ya Dinkamatashi itama ta bama Inteesar in ta koma Kaduna in ta gansu ta Tuna da ita. Tana Tsaye tana Mirmishi Gefe Daya Tana ayyana gobe i uwar haka tana Jikin Daddynta tana Zubamai Shagwaba kamar an ce ta Waiga sai taci karo da Imran zaune kan Mashin dinsa karan sigari a hannunsa idanuwansa suna Lumshe yana Busawa Hayakin yana Fita ta Hanci ta baki. Tsam tayi tana kallonsa,tsausayinsa ya kamata ganin yanayinsa wanda yasa bata san sadda ta taka zuwa gabansa ta Tsaya ba ganin har ta Tsaya bai Lura da ita ba yasa ta san yayi nisa Cikin yanayin Dayake ciki. Kawai sai ta saka Hannunta guda Daya ta Zare Karan Sigarin Dake hannunsa Daidai Lokacin daya Ware Idanuwansa akanta. Dam! Gabansu ya Buga atare, Suka kurana juna ido Cikin Bugawar Numfashi da Muradi mai girma, Ita ce tayi Saurin Janyen idanuwanta Saboda tana ji kamar Kafafuwanta bazasu iya Daukanta ba Cikin Sanyinta tace"Ka manta na Fada maka Ita shan Taba Illah take ga Lafiyar Dan adam..? Ko ka manta na taba Fada maka Shan Taba bata dace dakai ba..? Har tagama mgana yana kallon Dan bakinta ko Kiftawa bayayi ita bata ma Kara Kallonsa ba ta Saki Taban a kasa ta Mutsuketa Tana Fadin"Bazan barka da ita ba..Bani na aljihunka i know akwai wasu aciki..? Tafada Cikin Kamewa Lokaci Daya Tana Mikomai Zararan Hannayenta.. Galala yake Bin Hannun nata da Kallon Mamakinta na kamashi Cikin Dakiya ta kara Fadin"bani na aljihunka nace...Kadai san nasan ba wannan bace ita kadai ba ko..!? Dariyarta ma yake yi acikin Ransa yana mamakin yau rana ta Farko da Mace ta Tsaya gabansa Tana bashi Unarni haka. Yaji bama zai iya yimata gaddama ba Ya saka Hannu a aljihu ya Dauko Kwalin Taban ya saka mata a Hannu Harda Letthe din gabadaya. Kwalin tabi da kallo kamar tana kyamkyami nan da nan Zuciyarta ta Fara tashi Daman Daurewa take,Da Sauri ta Bude ledan hannunta ta Watsashi aciki Tana yamutsa Fuska tace"Kamar itace abincinka..? Bantaba Ganinka baka shan Taba ba sai sau Daya..Plz ka bari In ba so kake Huhunka ya samu mtsala ba .!. Tafada Tana kallon Gefe domin bata so ya Fahimci bakinta ya Cika da Miyau.. Mirmishi ya Sakarmata mai kara Har sai da ta Dago Tana kallonsa Cikin mamakinsa Saukowa yayi Daga Mashin din yana Fadin"Ban ce miki Daman zan daina sha ba..! Inteesar ta gyara Bakinta tace"To yanzu kayi min alkwarin zaka Daina shan Taba..! Kallonta yayi kafin yace"No..Ni bana haka ba. bazan yi miki alkwarin da bazan cika ba..Zan daina shanta Duk Ranar da Allah yace..! Mamaki ya kamata ta Kada ido Tana kallonsa yace"Yes bana yima Mutum alkwarin da na san bazan cika ba..kuma bana so nima ayimin alkwarin da baza"a cikamin ba..Kuma ni bana karya agaban mutum saboda ya soni..Ina Fadin gaskiyatane gaban ko Waye Allah ne kadai nake jin Tsoro ba Mutum ba..! Daga haka kawai ya wuce ta yana Tafiya Cikin Sarsassafa kafin taji yace"Kada ki sake ki mana Amai Gida..! Da kallo ta Bisa Har ya shige cikin Gida Mirmishi ya kamata Miyau ta Zubar Daya cika bakinta afili ta Furta..'He is nice..ashe ya Lura ta kusa amai..! Bata san da zuwan Munari ba sai taji kawai ta Dafa ta har ta Tsorata sai da ta Waiga ta ganta ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Har kin bani Tsoro..! Munari tace"Hala Ya Imran kika gani..? Yanzu na gansa ya shiga gida yana Cika yana batsewa..! Inteesar tace"Kamar wani kabewa..! Dariya suka saka Harda tafawa kafin su kama tafiya suka Fice wa Daga gidan. Suna tafe suna Hira har gidan Mama akofar gidan sukayi sallama da Munari akan Gobe zata zo kafin Intee din ta wuce,Sai dai Inteesar ta Boyema Munari abunda ya Faru tsakaninta da Imran haka kurum taji bazata iya fadamata ba Haka Inteesar ta shiga cikin Gida Tana nuna ma Mama Abunda Anty Safiya ta bada akai ma Umma ta Karba tagani Tana ta Godiya. Ranar barci barawo ne ya sace Intee Saboda Murna asuban Fari tatashi Tayi ma Mama sharan Daki ta Share Tsakar gida,Ta zo ta saka Kettle daya Tafasa ta Juye tayi wanka Kafin ta Fito Mama ta Hada mata abun kari Saboda Murna ko Yunwa ma bataji sai da Mama ta Mtsamata ne tasha Tea kadan da Buredi. Koda karfe 11am na safe Basheer na Falon Mama shi da su Abiden yazo,Shi daman dan akida ne baya son Tafiyar Dare kuma bayason bata Lokaci shiyasa suna gaisawa da Mama yace Intee ta Fito su Dauki Hanya Sagir ne ya Fitar mata da kayanta akwati Daya zata koma dashi,sai Sakon Mama na Umma da nasu Inno,sai na Anty safiya,bawasu kaya me da yawa ba. Tun tana cikin gida ta Kira Munari ta Fadamata ya basheer yazo zasu tafi Munari tace gatanan zuwa sai dai Shuru Har Ya Basheer din da Sagir suka Fita waje aka gama Saka kaya a Booth Munari bata zo ba,Ita kuma Har ta kawo Falo Taga Imran ya Fita Haraban gida sai ta Labe ta Leka taga ko ya Fita sai taga yana Jingine jikin Mashinsa yana Danna Wayarsa karama bashi ma da Niyar tashi,Ballatana ta samu ta Fita kuma ta Tabbata in ya ganta bazai barta ta Fita ba.,Sai ta tsaya nan falon tana Lekonsa Gashi ta bar Wayarta acikin Bedroom dinta Inteesar nata Kira Bata Dauka ba. Ga ya basheer nata mata Fadan su tafi bayason Tafiyar dare ga yara yazo dasu,Dole tana ji Tana gani ta Fada Gidan Gaba Tana Tura baki Domin tasan ko giyan wake tasha bata isa tace su jira zuwan Munari ba ko kuma su Biya gidansu ba Dama Daddy ne yauwa tasan shi zai mtsamai ammh yau ba Daddy bata isa ba. Saboda Haushi ma Abiden na Hawa Jikinta ta Harareshi ta Mtsa jikin Kofa Tana Tura baki Basheer bai Damu ba Kallonta kawai yayi ya kada kai,Abida Tana Jikinsa Ta lafe ita akwai son jiki ne Abiden din ne Sarkin wasa. Haka suka tafi Sagir na Daga musu Hannu da Mama na Daga Zaure Itama Tana Daga musu hannu Allah Sarki Sabo Turken wawa. Munari dai Dole Daki ta koma tana Cijon yatsa,Wayarta ta Daga taga Kiran Inteesar sai tabi baya,Inteesar na ganin kiran Munari taki Dauka sai da ya Katse ta Turamata Sako. *Muna hanya..Nayi ta Jiranki baki zo ba..* Munari na ganin Sakon sai da taji wani iri da sauri ta Rubuta mata da Amsa. Am sorry Besty..Naso na Fito Ya Imran na gani aharaba shiyasa..Allah ya kiyaye Hanya ki gaida Daddy da Umma..! Ta turama Inteesar wanda Tana gani sai da ta Murmusa da ta Tuna da Imran cikin Dariya ta Turama Munari.. Is ok..Ameen zasu ji..Ki kula da kanki da kowa da kowa Expecially Muradaden yayanki IMRAN..! Tana gama Tura mata ta maida wayarta jaka tana Mirmishi Basheer na kallonta bai ce mata komai ba sanin ko yayi mgana bazata Tankasa ba Yau yasan Karansa Wajen Daddy Fada sai ya Toshe kunne. Munari kuwa Tana ganin sakon ta Zaro ido a fili ta Furta."ni ai bazan iya Kula da Ya Imran ba Tabdijam..! ***** Koda Inteesar ta Dawo Daddy baya gida,Umma ce Kadai sai Anty Hauwa Inteesar ta makale Umma Tana Murnan ganinta,Haka ta Rumgume Anty Hauwa Tana Murna ya basheer ta bari da Shigo mata da kayanta Murna ya mantar da ita,Shiyasa akace No place Like Home Inteesar ta Fahinci hakan Umma ta yi mata Shinkafa da Miyar Kaza,sai kunun Aya,Inteesar ta Zauna taci ta koshi sosai,Daddy bai Dawo gidan ba sai Dare Intee ta Rumgumesa Tana Murna ganinsa shi kansa Bakinsa yaki rufuwa Saboda Dawowar yar Lelen nashi. Ranar kusan raba Dare sukayi suna Hira,Daddy yasha Hirar Makaranta da ta Mama data Ya Sagir sai Hirar Munari da yan gidansu da sakon Gaisuwan Abba zuwa garesa. Ta kuma bama Umma sakon Anty Safiya Umma ta Karba tana ta Godiya da Sakon Mama na Garin Dan wake,da Yaji sai Daddawa Dakakkiya da kuka da Kubewa,Haka ma Wanda ta aiko ma su Inno harda Garin Kunu Umma sai Murna take.. Inteesar sai da ta Duba ledan Kayan da Munari ta bata taci karo da sigarin data Karba Hannun Imran da Lether dinsa Saurin Dauka Tayi ta Jefa Cikin Tiolet tayi flooshing kada wani ya gani ta Shiga uku. Inteesar Tana matukar jin dadin Hutunta agida,kwananta Hudu da Dawowa taje gidan su Nasara Ta wuni Daga gidan ta Biya badarawa ta gaida Inno da Mallam Babba sai Dare Muda ya Rakota ta Dawo gida aranar ne da Daddare Munari ta kira Suka gaisa da Umma Harda Anty Safiya bayan sun gama mgana ne Inteesar ta Nuna ma Umma Hotonsu ita da Munari da suke Dauka a makaranta Umma ta kurama Munari ido a Fili tace Kuna kama da kawarki taki Inteesar. Inteesar tace mata haka kowa ke Fadi Umma kinsan ance kawayen juna wani Lokacin kamarsu na Rikidewa Umma na Dariya batace komai ba Suna Cikin hakane sai ga Daddy ya Shigo Daya Tambayi me suke ma Dariya Umma ta Fadamai bai ga Hoton ba Umma tace ya bari ya Huta Daganan ya manta itama Inteeesar din sai ta sha"afa. Har gidan Ya Basheer taje ta kwana Biyu Dakyar kamar tana kan kaya ta Mtsa sai da ta koma Gida,Suna Waya da Mama Da Sagir Lokaci bayan Lokaci suna gayamata sunyi kewarta.. Munari kuma kusan kullum sai sunyi mgana da juna ta waya ko ta WathApps. Kwanan Inteesar goma da dawowa Daga kano ta fara Zazzabi mai Zafi Wanda sai da ya kwantar da ita a asibiti. Maleria ce ta mata mugun kamu,Sauron kano sun Debi Rabonsu Daddy nata Fadan meyasa ba"a saka mgani agidan Mama tunda akwai sauro Inteesar ta dawo da Maleria. A dakin da aka kwantar da Inteesar din ne a kebantattacen Daki na Musamman,Asibitin kudi ne,Ya Basheer da Umma da Anty Hauwa da ya"yansu su Abiden din adakin Daddy ke ta Fada Tunda Likita yace Maleria ce ta kama Inteesar mai Zafi. Ran Umma ya baci ta Dubu Daddy Tana Fadin"Haba Abban Intee kadaina Fadin haka fa kamar baka yarda da kaddara ba? Kuma daka ke Fadin an barta Sauro ya Cijeta Ita Ya Aminan zata zauna tana kula ita kada Sauro ya Cijeta ko..? Kuma ita da Sagir Da suke gidan Su ba Mutane bane Inteesar ce kadai Mutum Tunda yar so ce..! Tafada Tana Bayyana Bacin Ranta Har Daddy zai yi mgana Basheer ya Girgiza mai kai ganin kada su Fara Fadansu na Fama gaban Suruka.Dole tasa Daddy ya bar mganar Ammh Umma sai Huci take ranta yagama baci. Wasa wasa dai sai da inteesar ta Kusa Share Sati a asibiti,Saboda da taji Sauki Likita yace zai Sallameta Daddy ya Hana yace sai ta kara Hutawa kwana Shida tayi ta koma Gida Munari ta sani Tunda Data Kira Wayar Inteesar din Umma ta Dauka Ta gayamata Tana asibiti bata da Lafiya Hankalin Munari ya tashi Ta kuma tashi Hankalin su Abba bata Kwantar da Hankalinta ba sai da Taji Inteesar Ta samu Sauki har an sallamo su Daga asibiti ta Dawo gida..! *Shakira* 3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *🅿�24* Duk abunda ya faru Imran bai sani ba Kowani Dakika da kuma Wayewar gari Inteesar na cikin ransa yana kuma Kirga kwanaki da Ranar da Hutunsu zai kare,Domin tun yana Daukan Lamarin wasa har ya fara ganinsa da gaske ne,Domin baisan wani yanayi yake ciki ba ammh Tabbas da Tunaninta yake kwana dashi yake tashi yana jinsa kamar ba Daidai ba in bai ganta ba yana jinsa kamar ya rasa wani kuzarinsa ne da Tatafi. ya zauna yayi Tunanin meye Hadinsa da ita da Har Tunaninta yake Hanashi Sukunu ya kasa gano bakin Zaren yanzu ya daina Tunanin Tayi mai asiri sai dai yafi Tunanin kila shine Aljanun suka shigeshi Shiyasa ya kasa Gane kansa Kwata kwana. Afarke yake ko cikin Barcinsa Inteesar ce take giftamai abum kamar almara Ko yana zaune ne yana Kallon wani Waje Fuskarta yake gani Mganarta kuma namai amsa kuwwa acikin kunnuwansa Saboda ita yanzu ya Rage shan Sigari koda ya Daukota zai kunnata sai ya Tuna da mganarta yaji kawai bazai iya Saba mganarta ba Duk da bai mata alkawari ba sai da yaji yana son ya Daraja mganarta akalla ko bata Dawo ta gansa ya Daina sha ba ta Gansa ya Rage shanta Fiye da baya ba kuma domin yana Tsoron kada Tamai Lahani ga Lafiyarsa ba wannan baya gabansa Ya sani Shi Tuni Lafiyarsa ta Samu Tawaya. Ko alama baisan bata da Lafiya ba Saboda ko Sagir bai taba mai Zencenta ba kuma Saboda ita yake zuwa Shagon akai akai Koda Hirarta ne yaji Sagir din yayi mganarta shi kuma ko Sau daya bai taba mai ba Shi kuma Ego dinsa bazai taba barinsa ya Tambayeshi ba. Ko agida bai taba jin Mganarta ba Saboda baya zama cikin su Munari ce Ke da Labarinta kuma baya Sakarmata Fuska ba,ballatana yaji wani Zencenta kuma bashi da Lambarta ballatana ya Kirata Ko da ma yana Dashi bazai iya Kiranta ba Saboda yana ganin ai bashi da wata alaqa da ita Abun na Dauremai kai Ko Lokacin dayake amsa sunansa na Imran Wata mace bata taba Burgesa ba Ballatana yanzu Daya Juyama Rayuwar jin Dadi baya,Abun kunya ne babba agareahi wani ya Fahimci Halin Dayake ciki Dalilin haka yasa ya Rage yawan Walwalwarsa Fuskarsa kullum tana Hade ba Fara"a koda bai da yawan mgana ballatana Yawan Dariya Ya yusuf da Abba sun Fahimci wani abu na Damunsa sai dai sun sani koda sun Tambayesa bazai taba Fada Musu ba Imran yana da Ego gayama wani abunda ke Damunsa koda Damuwar abun zai kasheshi ne ya Gwammace ya bar abun shi kadai baya son yadda Ransa ya baci kan al"amarin ya Raba Bacin ran da wani nashi. Shiyasa yake ta Kokarin yakice abun acikin ransa,Bayason Tunanin Inteesar din tarabi Tunaninshi Sai dai ya kasa Controlling kansa da Tunaninsa Kowani Tunaninsa da Motsinsa Tana makale acikin Ransa da Zuciyarsa Kamanninta da mganganunta sun kasa bacemai acikin Idanuwansa da Kwakwalwarsa. *** Sunday. 10:03am na safiyar Ranar Lahadi. Abba ne da Ya yusuf sai Anty Safiya da Munari zaune kan Dining suna Breakfast,tunda yau din Lahadin karshen mako ne,Ya yusuf na Gida cin abinci Sukeyi batare da kowa yayi mgana ba bakajin komai sai karam Cokula da karan Mug din Tea. Ya yusuf ne ya Kurbi Tea kafin ya maida Mug ya ijiye yana kallon Abba Dayake cin Soyayyan kwai ahankali ammh Rabinsa Hankalinsa baya kan abunda yake yi ya tafi wani Tunanin nadabam. Ya yusuf ya gyara Zama yana Fadin"Abba badai Tunanin zaka Dawo dashi ba..? Yafada yana kallonsa Abba Daya Sauke ajiyar Zuciya ya ijiye Fork din Hannunsa yana Fadin"Kunyi mgana da Dr..? Yusuf yace"Eh jiya na kirashi yace...! "Wannan watan da kaina zan je asibitin..Kuma ina Fatan ya zama na Karshe Tunda alhamdulillah na Warke da yardan Allah..! Abba ya katesshi yana fadin hakan Yusuf ya kalli Safiya itama ta Kalleshi Kafin ya maida kallonsa kan Abba yana Fadin"Alhamdulillah Abba haka nake son ji..Allah ya kara Lafiya Gobe Kafin na wuce wajen aiki sai muje Tare In Allah ya kaimu..! Abba ya gyada kai bai yi mgana ba Munari Dake gefe ta Tusa Dankali da kwai bakinta tace"Abba Am so Happy..! Kamta ya shafa yana Fadin"Ki daina mgana hakan kada ki kware Munarin Abbanta..! Kada kai tayi tana Kokarin Daukan Mug din Ruwan tea din Dake gabanta ta kurba ko abunta ta saka abakinta yawuce mata. Abba ya Dauki Tissue yana Share Bakinsa Lokaci Daya yana Fadin"Yanzu ai nafi kowa sanin Illar Damuwa da Tunani Tunda Sanadinta yasa nayi nesa da komai nawa Ciki Harda yan"uwana da Mahaifiyata..Nasan Zafin Rashin naka sosai na kuma san Zafin Mutuwa Wanda cikin Zafinta nake har yau har gobe..Sai dai na Dauki kaddaranta nasan Mutuwa ta Allah ce kuma Kaddara Musulmi takaci..Mu kanmu Watarana zamu mutu duka munbar Duniyar muje mu Tarar dasu..Ni yanzu Addu"ata garesu Allah ya jikansu da Rahma Allah yasa sun Huta..! Gabadayansu suka amsa da Ameen Cikin wani yanayi Abba na Shirin mikewa Yusuf yace"Abba Daman Ina son mgana Dakai..Kan Imu ne..! Abba ya koma ya zauna yana Fadin"Meya samu shi Imran din..? Yusuf yace"Abba kafi kowa sanin Imran na Bukatar Taimakon mu sosai..bazamu zura ido Rayuwarsa ta tafi a banza a Shan Taba ba Abba We hv to do Something..! Abba yayi Shuru yana wani Tunani kafin ya kada kai yana Fadin"Kamar wani mataki kake ganin zamu iya Dauka kan Hana Imran Shan Sigari Yusuf...? Kafin ya bashi Amsa Safiya ta Mike Zata bar wajen Abba ya Kirata ta Dawo Cikin Dattakonsa yace"Koma ki Zauna ina zaki..? Cikin Ladabi tace"Abba zan koma Daki ne..Naga kuna mgana ne..! Abba yace"A"a koma ki Zauna..Meye baki sani ba..?wannan gidan kema Kamar Gidanku ne zauna mganar Dukkanmu ta Shafemu..! Bazata iya ma Abba gaddama ba, yasa ta Koma ta Zauna tana gyara Zaman Vail din Data yane kanta dashi. Abba ne ya maida Hankalinsa kan Yusuf yana fadin"Umh ina jinka Wata Hanya kake ganin zata Bullemana..? Bayan Nasihan Dakemai nima kuma inamai ita bai Daina ba..? Yusuf yace"Eh to kamar mu nema mai Taimako wajen Malaman addini na addu"a Abba..Ko da bana shan sigari ba..Na bakar zuciyar nan Abba da rashin son zama cikin Mutane..! Abba ya kalli Yusuf sosai Kafin ya dan Murmusa Cikin Dattakkonsa yace"Ba wani Taimakon da zamu nema mai Yusuf..Kafi kowa sanin Imran kamar yadda nasanshi bazai bamu hadin kai ba..Taimako Dayane kawai ya Ragemin agareshi zan koma cikin Ahalina Ina da Mahaifiya Hakkin Daada yana kai na matukar ina da rai da Lafiyata In na koma gareta Cikin yan"uwana zan basu dama su Zartar da Hukunci kan Rayuwarsa na Tabbata bazasu barsa haka ba..! Yusuf ya kada kai kafin yace"Abba Inran din zai yarda wani bakai ba ya Zartar da wani abu akan Rayuwarsa..?bama haka ba Abba Bana jin Imran zai yarda ya koma cikin Yan"uwanmu Domin kullum ikirarinsa kenan..! Abba yace"Shi ne zai bani Umarni ko nine zan basa..? Ya yusuf ya kada kai kafin yace"Kai ne zaka bashi Abba..! Abba ya Cije baki kafin yace"To bai isa na bashi Umarni ya Tsallake ba..Koda kaga ina Dagamai kafa na Dan Lokaci ne..Zamu koma Cikin yan"uwana Lokaci kadan da yardan Allah In yaga Zai iya Binmu ya kyauta ma kansa in kuma Taurin kansa ya Hanashi sai yayi Ta zama ni baruwana dashi..! Yana gama Fadin haka ya Mike Da sauri Munari tace"Abba Lagos zamu koma ko Dukku..? Ya waigo yana Kallonta kafin yace"A"a ba inda zamu ai nam din shine GIDANMU munari..Lagos kuma Zaman achan ya kare bazan iya Zaman garin ba..Dukku kuma Zamu jene ganin Daada da Sauran yan"uwana In Allah ya yarda..! Munari tace"Abba kenan nan zamu Cigaba da Zama har Abada..!? Gyada mai kai kafin yace"Da yardan Allah..Shine gidanmu..! Washe baki tayi tana Murna kanta Abba ya Dafe kafin ya wuce bai Tsaya afalo ba ya shige Daki Daga gani mganar Imran ta Dameshi Sosai. Yusuf ya Sauke Numfashi batare da yayi mgana ba ya Mike shima ya Wuce Shashensu Itama Safiya ta Mike tabi bayansa bayan ta bar ma munari Sallahun in ta gama ta Kwashe komai takai Kitchen tace mata Toh Chan taje ta bama Yusuf baki Domin Taga Shima duk ya Damu,Abunda ta Dade Tana Nusar dashi kenan kan Neman Danginsu sai gashi yau Abba ya Furta da kansa sai mganar Imran shi kuma Wata mganace ta Dabam baka isa fa ka Chanxa Abunda Allah ya Hallicesa ahaka ba sai dai kayi iya Bakin kokarinka ka barshi yadda yake. Sai dai kila Mace zata iya Sauyashi Watarana Indai yana sonta. Haka Safiya ta Fadama Yusuf mganar Dariya ta bashi sai da ya Murmusa kafin ya Kalleta yana Fadin"Wata Macen ne zata juya Imu..?ban jin akwai wannan macen Baby..! Bata iyamai gaddama ba Tunda ko ta Fada bazai yarda ba su suna ganin bamai iya Lamkwasa sa ita kuwa Tana Hange Imu Wani Lokaci anan gaba da Mace zata Zama tanajan Ragamar Rayuwarsa. ***** *Dukku local goverment* Area:Balikaje. Kamar yadda take Ranar Lahadi a garin kano haka take Lahadin karshen Satin agarin na Dukku. Yau gidan na Daada yana Cike da Mutane ne kama Daga ya"ya zuwa Jikoki,Tun jiya asabar Wasu suka sauka kamar su Inna Maimunatu da Inna Bintalo su da gayyar ya"yansu da marasa auran da masu auran duka suna Gidan Daada,Tun safe kuma Baffa Kabir ya sauka shima Tare da Mami Asma"u da ya"yansu duka Uku Wato Sajida da Umaima da Khamis wanda wannan karon Dolensa ya bar Aikinsa ya Taho Saboda Kiran Daada. Baffa Mustpha ne karshen Zuwa Misalin karfe 11am na Safiya suka iso Bashir ne ke jan motar Umma da Inteesar da Hauwa suna Baya sai su Abiden Dake jikin Umma. Inteeesar tun da suka Dauko Hanya bata iya cewa kala ba Bakinta kuwa ta gaji da Turasa ma ta Hakura ne bata so zuwa Dukku ba har ga Allah hakan baya Cikin Adanjanta Gobe ne suke Komawa Makaranta ta Fara Shirya kayanta Zata dawo ko Laraba ko alhamis Domin har mgana sunyi da Munari Zata dawo haka Kurum taji bata Kyauta ba in ta sabama Ya Imu alkwarinsa kuma ya gayamata Baya alkawari in yasan bazai cika ba kuma Shima bayaso ayimai in har baza"a cika ba.. Bata so ta karyamai Zuciya da Saba alkawarinta shiyasa ta Fadama Daddy zata koma Ranar Alhamis ko Laraba kuma ya amince mata har yayi mata alkawarin zai maidata kano da kansa Har Umma ta fara mata Shirin komawa Tunda har Mama ta kano sun yi mgana tace mata Intee na tafe Cikin Satin nan mai shiga kawai Rana Tsaka Ranar jumma"a Sai ga Kiran Baffa Kabir yana Fadama Daddy Daada Tana chan tana kuka Baba Asabe ta Kirashi ta gayamai shine yace abama Daada Wayar yana Tambayanta me ya faru nan take fadin Tana son ganinsu dukkansu kwansu da Kwarkwatansu Bata son ace mata wani baya nan ko yana makaranta ko yana Wajen aiki Dasu da duka ya"yansu take son gani kafin gobe a Dukku Domin Tana so ta Hada kansu ne kafin Ajali ya Risketa. Ba Lallashin da bai mata ba ta Kafe kan mganarta Dole ya Kira Daddy ya Fadamai bayan ya Kira Su Inna Bintalo ya Shaida musu Halin da ake ciki Shine nan fa Kowa ya Tarkato Iyakansa ya Yada Zango adukku Gidan Tsohon Marigayi Alkalin Alkalai Hamisu Dukku. Baffa Kabir Daman Khamis yazo Gida a Ranar zai yi kwana Biyu ya koma sai ga Kiran Daada Sajida kuma suna Hutu Tana gida Umaimace Take makaranta ba Halin adauje ma Tafiyar Duk yadda ko suke Girmama Karatun ya"yansu wannan karon basu da Tacewa Dole suka Tarkato har su sai sun Rasa aikinsu Gobe Monday Tun ba lalle bane su koma aranar sai takai su Gobe Tunda basu san Dalilin Taruwar da Daada ta Hada Lokaci Daya ba Tun suna Hanya Mami ke ta Fada Tana Fadama Baffa Kabir Tana san bai wuce kan malami ba,tasa sukabar Komai nasu suka taho Mutumin Daya Gujeta da kansa kuma Miye abun Damun kai,Shidai yana Jinta bai ce komai ba sai Korafi take zata Rasa aikinta Gobe kadai Sajida ma Ranta bace saboda bata son Wahala ballatana Hayaniya gidan Daada kuwa komai da kanka Zakayi ba yan aikin da zaka saka suyi maka Khamis kuwa Da Umaima Ransu Fes Suna Farincikin zasu mahaifarsu suga Daada Daman Shima yana da Niyyar Zuwa sai ya bari sai wata watan in ya samu Huti bazai ma je Abuja ba Direct Dukku zai wuce yayi Hutunsa na Karshen Wata awajen Daada tunda Har ta gama Shan jinya bai Zo ba sai da ya Tura mata sako kuma Sunyi mganata ta waya.. Aharaban Gidan Basheer Ya faka Motar kusa da Tsala tsalan Motocin Ya"yan na Daada,Sai da kowa ya Fito Daga Motar kana Inteesar ta Fito Tana Tura baki Fuskarta ba Fara"a ko kadan Sanye da wani Riga da wando,Rigar Top ce Baka mai Dogon Hannu sai Wandon nata ja ne mai Tsuke ta kasa ya kamata ba sosai ba Sai kafarta Cikin Red Talkami Sawu Ciki Ta sanya After Dreess Baka Ta Saka Red din Vail din Mayafi ta yane kanta dashi haka kuma karamar Jakar Bayanta,Mai ratsin ja ce itama wacce ta ke goye abayanta kayanta ne ke Ciki Kala Daya da sauran kayan amfaninta. Inteesar Tana bala"in son Best clour dinta Shiyasa yawancin kayanta Red ne. Daddy ne akan gaba Sai Ya Basheer Dake Dauke da Abiden sai Umma Dake bayansu Dauke da Abida,Anty Hauwa ce ke baya Tana Tafiya a Hankali Saboda bata jin Dadin jikinta sosai,Laulayi Inteesar na bayanta kamar Tana Kirga takunta Gabda zasu Shiga Falon gidan ne Umma ta Waigo Tana kallon Hauwa Dake tafiya Sannu sannu ga Jaka ahannunta Inteesar na Bayanta bata karban mata Jakar ba. Dakatawa tayi su Daddy suka Shige Shi da Basheer sai da Hauwa ta Kariso kana Umma tace"Hauwa basai ki bama Wannan Sangartattaciyar Rikon Jakar naki ba? Kina tafiya Dakyar Dakyar Dauke da Kayan Nauyi kuma ga yanayinki..! Anty Hauwa ta Murmusa tana Fadin"Bakomai Umma zan iya..! Tafada Tana Sadda kanta kasa Domin ita akwai kunya. Umma ta kalli Inteesar Data ke Tafiya kamar kwai ya fashemata acikin Ciki ta Aikatamata da Harara kafin tace"Abun da kika iya kenan..Kina ganin ta tana Tafiya Dakyar bazaki karban mata Jakan hannunta ba..? Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"Nima fa Umma ina Fama da tawa Jakar ba wanda ya karban mun..! Umma ta aikamata da Dakuwa Tana Fadin"kin ga naki nan mara Mutumci..Ni ko Ubanki ko yayanki ne Zamu karban miki jakan..? Kinga Inteesar ki kama jikinki ina gayamiki nan dai Dukku ne ba Kaduna ba..ki kama Jikinki Dangi sun Hadu kada atafi Dake a baki..! Daga haka ta mikama Hauwa Hannu Tana Fadin"Bani jakar ni na Rike Miki Hauwa..! Anty Hauwa ta Girgiza kai Tana Fadin"Umma don Allah ki barshi Zan iya..Kina fa Dauke da Abida nauyin zai Miki yawa..! Umma ta Mika hannu ta karba jakar Tana Fadin"Bakomai bani ai ni bana Dauke da Lalurar dakike Dauke da ita..! Dole ta sakarmata Jakar ta Dauka Daman ta kayansu Abiden ne da Madaransu sai ruwa jakar nasu kayan Tana Booth din Mota tare da nasu Umma.. Ko bi ta kanta Umma batayi ba ta Wuce zuwa Kofar da Zata Sadaka da Babbam Falon na Tsohuwa Daada. Anty Hauwa ce ta Juya tana Kallon Inteesar data kusa Sakin kuka Saboda Haushi ta Murmusa kafin tace"Intee Daddy kawo jakar taki na Rike miki..! Kunya ta kama Inteeaar sai ta sunne kai Tana Dariya Anty Hauwa ta kamo Hannunta Tana Fadin"Ai sai na Daukan Miki yar kanwata..! Inteesar tace"A"a barmin abata kafin Umma ta ganki ta kusa tsireni gaban yan Uba..! Dariya suka saka gabadayansu kafin su fara taku zuwa Cikin falon Anty Hauwa ce agaba ita kuma tana Binta abaya Tun daga Wajen kake jin Hayaniya nata tashi da kananun kukan yara yamutsa Fuska Inteesar Tayi aranta tana jin Zata Takura Tsakani ga Allah bata son Hayaniya wani Lokaci. Ta Saka kanta Cikin Falon kenan Shima ya Sako kansa zai Fito wayace a makale a kunnensa yana mgana Basu san Da junansu ba yasa Inteesar ta Bige hannunsa Wayar dake hannunsa ta fadi kasa ta Watse Da Sauri gabadaya Jama"ar Dake Falon na Daada suka Dago kansu zuwa Bakin Kofar Falon. Inteesar Dake Tsaye ta Dago Dara Daram Idanuwanta ta Sauke su kan na Dan"uwanta Khamis Kabir Hamisu Dukku Dogon Namiji kakkarfa mai Cikar ZAti da kamala Fari ne ba sosai ba yana da Duhu akallon Farko in kayi mai kamar Baffa Kabir yayi kaki ne ya Tofar saboda yadda suke kama kwata Kwata kamar ba Mami ta Haifesa ba ko alama baya kama da ita kamaminsa ta asalin Fulanin Dukku ne. Yana sanye da Rigar Fara sai Wandon Sojiji Dake jikinsa,Kamar yadda Take karemai kallo itama haka yake kallonta sama da kasa wani irin Kallo wanda lokaci Daya Inteesar taji kallon bai mata ba da Sauri ta kauda kanta bata sanahi ba sai dai tana ganinsa bata Bukatar karin bayani Dan Baffa Kabir ne. Kauda kanta Tayi kafin ta Duka kasa ta Fara Tattaramai wayarsa da Sauri ta Dago tana mikamai Cikin Sanyin Muryanta tace"Sorry..! Tafada Lokaci Daya tana Mikamai Sake baki yayi yana kallonta da Duka Tunaninsa Inteesar taji Haushi ya kamata kamar ta kara Wurgi da Wayar nashi a kasa,wannan kallon har ina..? Sam bai dace ba yanayin yadda yake kallonta. Kamar Daga sama wata Murya Daga Cikin Falon ta ratsosu Tana Fadin"Khamis karbi phone dinka mana..! Kamar an Dawo dashi Daga Duniyar daya shiga ya saka Hannu ya karba Tare da Shafa Gefen hannun Inteesar din wacce tayi saurin janye hannunta Tana kallomta Lokaci Daya ta ballamai Harara asaman lebenta tace"Allah ya isana Dan iska..! Shi yaji Sauttin Allah ya isan sai dai bai ji karshen ba ta kauceshi Zuwa Cikin Falon yabi bayanta da kallo Cikin mamakinta. Kafin ya kada kai yafice Wayarsa Dauke a Hannunsa Sawu cikin kafarta ta Cire kafin ta Fara Taka Lallausan cafet din Falon da Kyawawan kafafunta Gabadaya a Tsarge take ganin yadda kowa ya Zubo mata ido gabadaya Falon yana Cike Dakyar ta iya Daga ido ta Hango Inna Bintalo kusa da ita Inna Maimunatu ne suna Zagaye da yara da alamu jikokinsu ne Tuna Huduban Umma Tun kafin su Fito yasa bata Tsaya ba ta karisa gabansu ta durkusa Tana Gaishesu Inna Maimunatu ta Dafa kanta Cikin Fara"a Tana fadin"Allah mai iko..Mai sunan Daada ce ta koma haka Ya Mustapha? Yana Daga chan gefen Kan Daya Daga Cikin kujerun falon. Kusa da Baffa Kabir ya Dagamata kai yana Fadin"Ga tan fa MAimunatu..! Masha Allah take ta Fada Inna Bintalo ce ta tabe baki Tana Fadin"Basu son zumunci Salaha bata nuna mata Darajan mu ba..har gwarama Basheer yasan Hanyan gidajenmu..Ammh ita kam bata sani ba ni Rabo na da ita ma Tun batakai haka ba Wlh.! Yarta Hamida Dake aure a Katsina Dake gefe tace"Mama ko mu ta ganmu ahanya bazata gane mu ba..Bata kuma je gidanki ba ina ga mu namu gidajen..? Yar"uwanta Siyama Dake gefe Tana Shayar da Jaririyanta ta Karbe da cewa"Gaskiya akwai mtsala..Nifa sai wannan Haduwar ne ma nake ganin wasu..Har gwarama Ya"yan Barrister Baffa kabiru ana ganinsu..!. Kamar an tsokane su haka suke ta Tofa albarkacin bakinsu Inteesar Haushi kamar ya Kasheta Umma Dake Kusa da Mami Asma"u ta kada baki tace"Kayya Bintalo bai ko kamata ki ga Laifina ba..Intee ai taku ce Dukku Tun Tana karama take zuwanta In Babanta zai taho Data Girma ne saboda Karatu ta Dauke kafarta..! Inna Bintalo baki ta tabe batayi mgana Domin ita daman in ta Raina Kurarka akwai Wulakanci basu yima Mami saboda bata Raga musu sun santa Sarai kan ya"yanta sai ajita Dakai Shiyasa tana Zaune ko Tankasu batayi ba Farin gilashi ne a idonta Tana Kallon Wayarta bama ta Lura da Abunda ke Faruwa ba,Tun bayan Shigowar Inteesar da Karon da sukayi da Babban Dan"ta Taga irin mayen kallon Dayake Binta tayimai mgana Domin Ita bazata taba bari Wani abu ya Shiga kansa ba yarinyar sam ba ajinsa bace. Sajida ce zaune gefenta Ta Dota kanta Saman kafadarta Idanuwanta suna Lumshe kamar mai barci Alhalin Idonta Biyu ta gaji ne kwanciya Take so yi bata son Damu da Takura. Inteesar dai Dataga Cin Mutumcin bazai kare ba sai ta mike Fuskarta ba Fara"a ko kadan ta Wuce Inna Bintalo ta Bita da kallo kafin ta Rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..ji yadda take Kumburi Yi hakuri yar nan kada ki Dakemu don munyi mgana..! Baffa Kabiru ne ya Dakatar da mganar yana Fadin"Binta kibar mganar nan hakanan..Taruwarmu anan Saboda Daada ne bawai zaman kace nace ba..mu bari Daada tatashi Daga Barci muji Dalilin Dayasa tayi mana wannan Kiran gaggawan..! Inna Maimuna ta kada kai Tana Fadin"Baban Sajida..Ai itama Uwace ko bata zo ba ita ai sai taje ko..? Ammh itama Shekarar ta nawa Rabonta da gidan Ya Mustpha..? Bafa yaranmu nee keda mtsala ba abun Daga Wajen mu ya Samo asali bama Ziyartar junanmu sai dai in Mun hadu anan Wajen Daada imu imu fa to ta yaya ya"yanmu zasu san muhimmancin nasu Tunda basa ganinmu muna Ziyartasu lokaci Bayan Lokaci..! Kowa falon sai da ya Natsu da mganarta. Sa"id Dake gefen Basheer zaune ya jinjina kai yana Fadin"True Talk Mommy..Kin fadi gaskiya ni kaina naji Dadin wannan Kiran na Daada ina so nima na fadi wanna mtsalan su Kawu su Duba su gani ataru a gyara Shiyasa nazo da Iyalaina suma suga yan"uwana..! Sadam Dake gefensa yace"Nikaina Kana kirana ka gayamin na Tattaro Anisa muka taho dasu Waleed Domin sau Daya muka taba zuwa Dukku dasu..! Ya"yan Inna Maimunatu kenan suke mgana Mazan na ta fari Tuni sun Girma sun zama magidanta Sadam din likitan Ido ne a kano yake Zaune anan asibitin Makka yake aiki yana Zaune da Matar Anisa da ya"yansu Waleed da Waleeda shi kuma Sa"id yana Zaune ne a garin Dutse yana aiki da Hukunar Wutar lantarki ta Jahar gabadaya,Ammh basu san suje gidan kowa ba sai Bauchi,sai kuwa in sun Leko Dukku shima yana da Mata da Ya"ya uku sunan Matarsa Fareesatu suna zaune da kanwarsu Wacce batayi aure ba Hafsatu,Karima da Zainabu sun yi aure anan cikin garin Bauchi kuma suma sun samu zuwa.. Kowa yaji mgangansu kuma yasan kan gaskiya ne,Baffa Mustpaha yayi Shuru yana Tunani yayinda Baffa Kabir bai ma Damu da mganarsu ba Mgana suke kasa kasa Shi da Diyarsa Umaima Dake gefensa. Ganin haka yasa Itama Inteesar ta Nufi Wajen Dadynta ganin Anty Hauwa tana Tare da Matan su Sa"id Umma kuma na kusa da Mami ita kuma bata ma kaunar kallon barayin Jikin Daddynta ta Raba tana gaida Baffa Kabir ya amsa mata hankalinsa nakan wayarsa kafin ta maida kanta kan Daddy tana Fadin"Daddy am so tired..Ina Daadan take ne..? Kanta ya Shafa ya Mike yana Fadin"Tana barci tasha mgungunanta sai tatashi Inteen Daddy..Ko zaki je ki kwanta ne..? Bata samu Zarafin mgana suka Hada ido da Umaimai sai Tayi mata Mirmishi itama Tayi mata Daidai Lokacin da Baba asabe ta Fito Daga wani Daki Dauke da Manyan Dardume Tana ta Maraba kafin ta Shimfade su nan Tsakar Falon ta koma Kitchen tana Jido wasu manyan Flaks da Kayan tea da Sauran Kololi Inna Maimunatu ce ta Kalli Autarta Hafsatu tana Fadin"Sannu da aiko Baba Asabe..Ke Hafsa tashi ki Taya Baba asabe jigilan kayan nan ai da yawa gayyar..! Tsam ta Mike bayan ta Sauke Yarinyar Hamida Abul Dake ke Jikinta Tun Dazu itama kamar sa"ar Inteesar ce,Umma na jin haka ta Kallo Inteesar Tana Fadin"ai bama ita kadai ba Maimuna Ga sauran yan"uwanta nan tashi..Intee kema ki kama mata..! Inteesar batayi gaddama ba ta Mike tana Ciro jakarta ta baya ta Mikama Daddy Baba Asabe tace"Da kun kyalesu ai na gama komai..Nasan kun sha Hanya ku samu ku karya ku watsake kafin Daada ta tashi..ga Dakunan fa Hajiya Mami da Umman kaduna Tunda ko zuwan yau ne ku shiga ku samu Hutu..! Umma ce kadai tace"Kada ki Damu Baba asabe..Gasu nan su Tayaki miye amfaninsu..! Ganin haka yasa Umaimai ta Mike Tana Fadin"Nima zan tayaki Baba asabe..! Mirmishi Tayi tana Fadin"To yar gidan Baba asabe..! Daidai Lokacin da Khamis ya Dawo Falon bayansu kawai ya gani sun shiga Kitchen Mami ya kalla yana Fadin"Mami wadanchan fa ina zasu..? Yafada yana Zama gefen Sajida Lokaci Daya yana kallonta Mami Tace cikin ko in kula"Zasu taya Baba Asabe Dauko Breakfast ne..! Kamis ya kalli Sajida yana Fadin"And ita kima wannan Zaman me take yi..!? Mami tayi kamar bata jisa ba Cikin Bada Umarni ya Zungureta da Kafada yana Fadin"Oya Comon Mike kema kije yayi aikin Dake mai shegen son jikin Tsiya..! Sajida ta Fara Kokarin kuka Tana kara Lafewa Jikin Mami tana Fadin"Mami kingansa ko..? Mami ta Dago ranta bace Tana Fadin"Khamis zan fa bata maka Rai..Meyasa kakeson Takuramata ne..?ko agida kaga ina sakata aiki ne ballatana ka mtsa mata sai tayi aiki anan..? *Shakira..* 3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *Soyayyar da masoyana ke nuna min kan wannan labarin sai godiya kawai..Domin bani da kalmar da Zan Biyasu da Tarin Alkhairansu zuwa gareni sai dai kalmar Godiya ya Biyo baya Hakika ina ganin duka Sharhinku Sosai nake jin Dadi Nagode kwarai Allah ya bar Zumunci Wannan Shafin kacokam sadaukarwa ne ga Masoyan Oga Imu da Inteen Daddy sunce suna Godiya Khamis ma yace ace muku Hy Sajidan Mami tace nace muku ita fa tagani Tana so🤣* *🅿�25* Kowa afalon sai da ya juyo yana kallon Mami Asma"u cike da mamakin kalamanta ba ga yaran Dake Zaune ba har ga manya irin su Inna Maimunatu dasu Umma,ammh ba suyi wani mamaki ba sanin Halinta daga ita Har Mijinta da yarda suke gudanar da Tarbiyan ya"yansu. Ko ayanzu din ma yana gefe yana ji ammh kanzil bai ce ba Sai Khamis din ne da kunyar kalaman Mamin suka Rufeshi ya kasa mgana illah kada kai da yayi ya tashi ya koma Kan kujeran Dake Fuskanta Hanyar Kitchen din Dake Falon Daada so yake ya kara Kallonta Domin tagama Tafiya da Duka Tunaninsa. Mami Asma"u ta yatsina Fuska Hannunta kan Fuskar Sajida tana Shafawa tana fadin"Am sorry dota..Kada ki damu kwanta abunki bamai Takura miki indai ina Raye..? Tafada Tana kara Kwantar da Jikinta a gefen kafadanta Cikin bayyana Soyayya da kauna da Sangarta Da suka nuna mata.. Kowa kauda kai yayi bai yi mgana ba Sajida kuwa ta kara nanikewa Jikin Uwarta Bata da Niyar tashi Inna Maimuna taga Abun ya wuce Misali Ta kalli Mami Asma"u Da hankalinta ke kan wayarta tace"Hajiya Mami ai gaskiya Khamis ya fada..Da kike fadin ko agida bamai sakata aiki ba kanshi yake ji ba sai ita yau Sajida mace ce tana gabanki gobe gidan auranta Zataje in yau kin tsaya mata Zaki gidan Mijin nata ne ki ZAuna mata ki bar naki Gidan...? Tsakani ga Allah fa Mu Tuna ya"yan nan Amana ne agaremu ko ba gaskiya ba..?in na Fadi ba Daidai ba ayi hakuri..! Tafada kanta Tsaye Ran Mami Asma"u ya baci ta Dago Tana kallon Baffa Kabiru itama ita yake kallo Zatayi mgana ya Girgiza mata kai sai shine ya Kalli Inna Maimuna yana Fadin"Maimuna kina Nufin ban bama Ya"yana Tarbiya mai kyau ba kenan..? Yafada Cikin Bacin rai da Sauri tace"A"a ko Daya ni ba kai nake nufi..! "Ok bashi kike Nufi ba sai ni..Tunda nice Bare shi kuma Dan"uwanki ne ko..? Mami Asma"u ta katseta Cikin Fushin mganarta Daman ga Takaichin Zuwa ba Shiri,Inna Maimunatu ta Kalleta Cikin mamaki ta Bude baki Zatayi mgana Sa"id Dake gefe yace"Mommy plz..! Yamaata alamun hannu a saman bakinsa ganin haka yasa ta kada kai kawai tayi shuru,Inna Bintalo Dake gefe Tayi Yar dariya kafin tace"Nifa ina mamakin wasu mutanen Shikenan da Zarar ka bama yayanka Jin Dadin Rayuwa sai ace ka batasu to waya ki jin Dadi da Rayuwar Hutu..Ke Maimuna da kike Fadin Watarana Aure Zatayi in da kudi Yan aiki zasu bika Duk inda kake Sai dai ka sa ayi maka kana Bada Umarni..! Jin Haka yasa Mami Asma"u ta samu bakin mgana Cikin gatse tace"gayamata dai Binta..Naga alamar kin fita saurin gane abubuwa..Shikenan in kana Bama ya"yanka Duka Tarbiyan daya kamata Kana basu jin Dadi duk sai ido ya koma kanka..? Domin wa muke aiki Koda yaushe..? Saboda ya"yanmu ne kuma Dadin abun nima ina aiki Ballatana ace da jikin wani na Dogara ko bana aiki mu yan gidan na gada ne ba na Haya ba..kuma Alhamdulillah ko acikin Dangi ya"yana sun fita Dabam dana kowa..! Tafada lokaci Daya tana Sakin Siririn Tsaki Lokaci Daya ta maida kanta bisa Wayarta Umma Dake gefe ta kada kai kawai domin aHalin Mami Asma"u wanne ne bakonta..?. Ba wanda ya kara cewa komai sai Falon yayi Shuru,Sai ya"yan Inna Bintalo ne keta mgana kasa kasa Baffa Mustapha kuwa maamakin yayan nashi ya kamashi ganin ko Sau Daya bai Tsawarta mata sai Fadin mgana Take son ranta. Inna Maimunatu dai tunda Sa"id yayi mata mgana bata ma nuna tana Wajen ba jikanta ne a Hannunta yaron wajen Karima An yayeshi Daman Wajen sati biyu kenan Uban da uwar suka kawosa Bauchi yana Wajemta,Madara take bashi Ta Toshe kunnenta Bata ma nuna taji ba ballatana tace wani abu ba. Falon ya dau shuru na wani Lokaci Sai su Sa"id ne ke mgana da Basheer sama sama sai Inna Bintalo da ya"yanta Sai ga dawowar Baba Asabe Falon Dauke da manyan Kololi,Bayanta Hafsat ne Dauke da Filtes da Cokula,Sai Umaimah Dake Dauke da Mug din Kofuna a hannunta Daga baya kuma Inteesar ce Dauke da Kananun Vowl a hannunta Tana Tafe Cikin Sanyinta da Natsuwarta Gefen hannunta kuma Dauke da Katon Kwalin Tissue. Tunda suka fito Idanuwansa ke kanta Ita ajikinta taji ana kallonta ta Duka Zata ijiye abunda ke hannunta Ta Dago suka Hada ido sai ya Daga mata Gira,Ganin haka yasa ran Inteesar ya baci tayi saurin kauda kai Tana Mikewa Lokaci Daya Tana gyara Zaman After drees din Dake jikinta Sam bata yarda da Khamis ba kallon Dayake mata ya Sabama irin kallon da addini ya amince ya shiga Tsakanin Namiji da mace shiyasa duk ta Tsargu kanta,ita ana ta Tunamin bai dace yana kallonta kamar zai Cinyeta Danya ba. Wajen Daddy ta karisa ta Karbi Jakarta Hafsah ce ta kariso wajenta Tana Fadin"Kawo jakar muje Dakin da muka sauka..! Kamar Inteesar zatayi mata Musu sai suka Hada ido da Umma ta gyada mata kai Shiyasa ta sakarmata Jakar Umaima ma na ganin haka ta kalli Mami Tana Fadin"Mami ina kayan mu..?nima Dakin su Inteesar zan sauka..! Wani Harara ta Sakarmata kafin ta saki karamin Tsaki Tana Fadin"Kibari Ki sauka inda zan sauka keda Sajida..! Baba Asabe Dake duke tana Bude kololin Da ta kawosu take fadin"Ai bamu da mtsalan Masauki kun sani..Daada tasan tana da Zuru"a kowani Daki ta sa an gyara mata shi..Ke Umaima ki sauka inda Hajiya Zata sauka ita da Sajida ke kuma Inteesar sai ki sauka Dakin da Hafsat ta sauka Umman kaduna ta sauka Dakin Daada,Wadanan surukan namu kuma sai su sauka Daki daya,Inna Bintalo da ya"yanta Daman suna Daki Dayane Inna Maimunatu ne jiya ta kwana Dakin Daada,Mazan kuma suna Wanchan Flat din na korido Daman chan su Sa"id suka sauka Jiya da suka iso..! Ba wanda yayi gaddama da Hukuncin Baba Asabe saboda duk abunda tace kamar Daada ne ta Fadeshi. Umarni da ta basu kan su sauko suyi Breakfast,rana tayi ba musu Iyayan suka Fara Saukowa Kafin Matansu sai ya"yan Daga baya Khamis duk yadda Zai yi sai da ya Zauna Facing din Inteesar saboda ya rika Morema Kallonta ita kuwa duk sai ta Takura ta Kasa Sakewa duk Dagowan da Zatayi sai sun Hada ido yana Binta da wani Mayattacen kallonsa Dataji kallon bai Burgeta. Ganin haka yasa Tea kadai tasha sai Soyayyah Dankali tatashi bayan tace ma Hafsah wani Daki takai mata Jaka na nuna mata Dakin Dake kusa da Dakin Daada Tayi,Daddy ne ya Kalleta Tana Shirin wucewa"Intee Daddy badai har kin koshi ba..? Kai ta gyadamai Tana Fadin"Eh Daddy nasha Complex kafin mu fito Daga Gida..! Kai ya gyadamata bai ce komai ba Gabadaya da kallo aka Bita,Inna Bintalo Harda tabe baki,Umma na Lura da ita aranta tace kya yi dai ki gama Binta. Sai da ta Fara Lekawa Dakin Daada taga kan gadon ba Kowa alamun Zubar ruwa a bandaki yasa Tayi Tunanin tatashi Tana Tiolet ne sai ta Fice ta isa Dakin da Hafsah ta nuna mata komai Neat akwai gado sai Katifa babba Dake kasa Dakin bakomai sai Cafet din Daya mamaye Dakin sai Tiolet Dake gefe wajen jakarta ta Nufa Da Hafsah ta ijiye mata nan kan gado,Zama Tayi agefen gadon Tana Tunanin yadda Zata iya kwana agidan Daada yau tagama Fahimta akwai abunda badai dai ba..Dazu fa sun fara karyawa Suka Hada ido da Sajida ita har ga Allah bata ma lura da ita akazo ba sai alokacin kallon kallon sukayi ma Juna kafin kowacce Ta dauke kanta Inteesar mamakin Sajida ya kamata ganin yadda Kowa ya Zauna a Matsayinsa ammh ita Tana Nanike da Mami Asma"u kamar wata yarinya ganin Haka yasa ta saki karamin Tsaki abun ba tsari kwata kwata tasan Tana da Shagwaba ammh nata na masu aji ne ba na irin nata ba.Shiyasa duk zaman wajen ya Gundureta da kuma Kallon da Kamis yake Binta dashi ita haka Kurum taji kallon bai mata kama da kallon Mutanen kwarai ba Daga ganin idanuwansa Ya saba kallon mata koda ga yadda yake wani Kashe mata ido. Karamin tsaki taja acikin Ranta tace Dan"iska kawai. Daganan Wayarta ta Ciro a jaka tadan Kishingida Munari ta Kira sukayi mgana ta Fada mata suna Dukku in sun Dawo gobe kila Jibi ta Tadawo in kuma basu dawo ba Dole sai Saturday ko sunday ne dawowarta. Sun dade suna mgana kafin suyi sallama Daganan game ta farayi da wayarta sai barcin gajiya ya kwasheta ta Bingire ta fara barci batasan tayi barci da yawa ba sai da Taji Hayaniya akanta kana Taji Ana kiran sunanta Tana Bude ido Taga Anty Hauwa Tsaye akanta Mikewa tayi tana Mutseke ido,Tana kallom Anty Hauwa Kafin tayi mgana sai taga wasu na Sallah Ido ta Zaro tana Fadin"Anyi Sallar Azahar ne Anty Hauwa..? Anty Hauwa na saka Hijabi jikinta tace"Eh mana gajiyan Hanya ne yasa baki san kinyi barci mai yawa haka ba..! Mikewa tayi tana Mika saboda Bayanta ya Sage,Hafsah ce ta Fito Daga Tiolet tana kallon Inteesar tace"Kin tashi..? Inteesar tace"Eh wlh..ashe nayi barci da yawa haka..! Hafsah tace"Nima na shigo na ganki kina ta barcin nace gajiya..Nima jiya da muka iso haka nasha Barci na Har sai da nagaji..! Mika Inteesar tayi kafin tace"Daada tatashi Daga Barcin..? Ta daga mata kai Tana Fadin"Tun dazu..Tana Ma Falo ana ta Hira da ita ta Shige cikin ya"ya da Jikoki..! Inteesar ta kalli Hafsah kafin tace"Wai Kiran menene Daada ke ma kowa ne..? Hafsah tace"Wlh bansani ba..Ko muma da muka iso Tun jiya taki cewa komai tace sai gabadaya an gama Haduwa Zatayi mgana..! Inteesar kai kawai ta jinjina ta Tura Kofar Tiolet ta shiga Domin ta Dauro alwala,Yadda taga Tiolet din Tsab a wanke yasa ta kwabe tayi wanka Saboda Jikinta ya saki Daganan ta Dauro alwala koda ta Fito su Anty Hauwa sun idar da Sallah da Aneesa Matar sa"id da Faree matar Sadam suna Hira sama sama,Hafsah kuma na Gefe kan Darduma. Wajen jakarta ta Nufa ta Bude ta Dauko Wata Doguwar riga Ja da gyalenta,ta koma cikin Tiolet din ta saka kana ta Fito ta maida kayan Nata Data Cire cikin jaka. Hijabinta kwara Daya da tazo dashi ta Dauko ta sanya ta Tada Salla nan gefen da Hafsah ta matsa mata. Bayan ta idar da Sallar Tana Zaune shuru Hafsah ce ke mata mgana Sama Sama take bata amsa saboda Ita bata da Sakin jiki Tana Tambayanta kan Karatunta ne,tace mata Buk kano take ita kuma Hafsah tace Dutse take Karatu Federal Univesity Dutse Tana ZAune agidan ya Sadam. Umma ce ta shigo Dauke da Abida sai kuka take ta mikama Anty Hauwa tana Fadin"Uwarta take son gani..! Dariya tayi ta sunne kai kafin ta Karbeta sai ko yarinya tayi shuru ta Lafe jikin Uwarta Umma ta Rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..Yaran Zamani ita anan ta san uwarta..! Inteesar tace"Umma kema ai kene kiyi ta Wahala dasu bafa ya"yanki bane..Ni ce nan ya kamata ki rika Wahala dani ni da nake Autanki..! Ta Karishe fada Tana Tura baki Umma ta Aikamata da Dakuwa tana Fadin"Damam nasan zaki yi mgana ai Kishiyoyinki ne dasu kike Kishi..Inteesar Allah ya Shiryaki..! Dariya su Anty Hauwa suka saka Daidai Lokacin da Baba Asabe ta Shigo Tana Fadin"Nam kuma Wata Hira ake yi ana Dariya shine ba"a Kirani ba..? Umma ta Waiga tana Fadin"Ni da jikar nan takice Baba Asabe..Kishi take da ya"yan Wajen Basheer! Baba Asabe ta Kada baki tace"Aiko nice nayi Kishi..Tunda fa kikazo kike Dauke dasu ita kuwa ko kadan baki kulataba..Jika dai bai fi D"a ba atoh..! Jin haka Yasa da Sauri Intee tace"Yauwa Baba Asabe kema kin gani ko..? Tace"Kwarai na gani kuwa mai sunan Uwar Dakina..! Umma tace"Kidai na kama mganar yarinyar nan..Shigen son jiki ne da ita Tana Gamsamemiyar Budurwa da ita Zan kama Dauka ina Sakama jikina..?indai jika bai fi ba D"a ba to ai D"a bazai fi jika ba..! Dariya aka saka gabadaya ganin Inteesar ta Tura baki Baba Asabe tajuya tana Fadin"Gaskiya dai mune bamu yarda ba..Kufito Falo Daada Tayi kira fa..! Jin haka yasa Dukkansu suka mike Suka Fice Inteesar ne Karshen Fita da kamar zata Cire Hijabin datayi sallah sai ta Tuna kallon kurillan da Khamis ke Binta dashi sai ta fasa ta Dauki Wayarta ta Zura Hannayenta Cikin Hannun Hijabin ta Fice zuwa Falon. Daada na zaune saman kujera Tana Sanye da Hijabinta Fari,wanda yakai mata Har gwiwa Casbaha ne a Hannunta tana ja,Daada duk ta Rame ta kara Fari Tsufanta ya kara Bayyana Daga gani bata da Cikakkiyar Lafiya. Daga kasanta kuma Baffa Kabir ne da Daddy sai Chan gefe kuma Inna Bintalo da gayar ya"yanta Inna Maimuna na kusa da Umma,sai su Any Hauwa da matan su Sa"id,Su Ya Basheer na Daga gefe suma a kasan Cafet din suke zAune su hudu harda Khamis Sai Hamshakiya Mami Asma"u Tana Zaune ya"yanta Guda Biyu Umaima da Sajida sun sakata a Tsakiya ganin haka yasa Inteesar taNufi Kusa da Inna maimuna inda su Karima ke zaune gefe Hafsha ne nan ta Zauna Abiden na ganinta ya baro Wajen Umma ya Rarrafo wajenta Ganin haka yasa ta Dagosa Tana Fadin"Nifa ba Daukan kaba Shegen Karfi ne Dakai..! Daada Dake zaune tana Nazarin kowa sai da Murmusa tace"Ba"a dai san mai sunan Maryama da Rangwanta ba..! Dago kanta Inteesar tayi tana kallon Daada Cikkn Tura baki tace"Daada kada mu fara fadan nan dake..kinga dai baki da Lafiya ki samu dai mu Rabu Lafiya muzo muci gunban Mutuwarki..! Daddy ne ya juyo yana Fadin"Intee..! Ya kirata alamun tayi Shuru sai ta Dukar dakai Daada Tayi Mirmishi Tana Fadin"Kyaleta Mustapha..Daman ai wasan jika da kakan nake so nayi da Jikokina bana samun Daman..Dukkanku kuna wata uwa Duniya..Bana ganin ya"yanku sai dai ku..Kusan yadda nake jin Farincikin in na ganku kunzo Tare da ya"yanku..? Baku sani ba Shiyasa baku Damu da ku kawosu wajena ba sai dai wanda ya Girma ya kawo kansa kamar su Basheer sai Megidana Akali sai su Sa"idu sauran yaran kuwa bana ganin kowa..! Ta karishe Fada Muryanta ta Fara kamar ta saka kuka Baffa Kabir ya Dago kansa yana Fadin"Daada don Allah ki daina saka wannan aranki..Mune fa Ahalinki Duk Duniya baki da kamarmu..Mganar yara kuma Daada kin sani ba domin karatu ba Da zaki rika ganinsu akoda yaushe..! Daada tamai wani kallo kafin tace"Kayya Kabiru kullum mganar kenan Karatu..Naji karatu..Ba sa samun Hutu ne..?suna samu meyasa alokacin baza ku kawosu ba yanzu anan Wajen ba Domin kiran da nayi muku ba na Tabbata ku kadai zaku zo..Matayen ku ma ba Sosai suke zuwa ba sai wani abu ya taso..Na tabbata Wasu anan Rabonsu da Dukku sun manta wasu kuma kila yau suka fara ganin junansu a Mtsayinsu na yan"uwa ina amfaninshi...?kunga hakan ya Dace kai ne Babba Kabiru kafi kowa sanin yadda Mahaifinku marigayi Alkali yake da Riko kan Zumunci sai gashi yau bashi da rai Daga Gidansa ma Cikin ya"yansa Zumunci ya Lalace kuma yayi Rauni..! Kowa afalon yayi Shuru yana Sauraran Daada mgangunta sun kashe ma kowa Jiki Inna Maimuna ta Kada kai tana Fadin"mganarki gaskiya ne Daada..Ni kaina Rashin Zumuncin nan namu na cimin Tuwo a kwarya Daada..Ace muna da yawa fa gamu da ya"ya ga jikoki zmunci duk mun Sakeshi kuma Laifin yana Wuyanmu ne muke da alhakin Nuna ma ya"yanmu gidajen yan"uwanmu Domin susan kowa..Koda muka yi Nisa muna da Rufin asiri daidai Gwargwardo Muna da abun hawa zamu iya Tashi muje duk inda muka ga Dama..Allah na Tuba cikin mu ba wanda yabar kasar nan Baban Sajida yana Abuja in anso arika Ziyartar juna Abuja ai kamar zuwa Dukku ne sai Ya Mustapha yana Kaduna ina Kaduna ina Abuja,Sai ya binta Dake gombe nan da Gombe ma Allah na Tuba Menene aciki Tsakani ga Allah..? Ammh bamu yi wwnnan kokarin ba..Daada ce kadai muke zuwa Dubata mu da ta zame ma Dole bamu yi Tunanin suma ya"yanmu Dolensu ce ko banza nan din Tushensu ne Sai kiga ammh suna Ziyatar sauran Dangin nasu na uba ko na uwa mu bamu damu da susan kowa ba gaskiya akwai gyara ban Cire kaina ba Har ni ina Da Laifi kuma ko Daada batayi wannan mganar ba ni zan yita ko Saboda Mganar Barin Ya Malami Dashi Da iyalansa Daga cikin mu wani Abun Takaichi ne da Abun mu Zauna musanta ina zamu bulloma Al"amarin..? Nasani kun sani Wlh ko Kaffara bazan yi ba Rashin Lafiyan Daada Tana da alaqa da rashin Sanin Takaimaiman Wani Hali ya malami ke Ciki da Iyalansa ne ko nayi Karya Daada..? Takarishe Fada tana kallon Daada wacce Har hawayr ya fara wanke ma Fuska Cikin Muryan kuka Daada tace"Kin yi gaskiya Maimunatu..Wani Lokacin in kikayi mgana kamar yayanki Malami haka yake da Sanyin Hali da Hangen nesa..Hakika abunda ke Cikin zuciyata kenan kuma Dalilin kiran danayi muku shine kan gaba sai yadda Zamu taru mu gyara Kuskuran da muka Bullo dashi acikin Ahalin mu Tukafin mu Kara yawa abubuwa suzo suki gyaruwarmana yadda muke so..Ko kuma na Fadi na bar Duniya ku Watsar da Zumuncinku Gabadaya..! Ta karishe Fada tana Sharan Hawaye da Gefen Hijabinta Daddy Cikin Sanyin Jiki ya Dafa Kafafuwan Daada Yana Fadin"Don girma Allah Daada ki Daina kuka..Mun gane kuskuranmu kuma mun miki alkwarin zamu gyara..Mganar Ya Malami kuma Na Rantse miki har ga Allah Dagani har Barrister bamu zauna ba muna ta Cigiya kuma da yardan Allah za"a dace ina ji ajikina Ya Malami ya kusa Dawowa garemu..! Daada ta Kwace jikinta Cikin Bacin rai tace"karya kakeyi Mustapha..! Gabadaya falon sai da aka juyo ana Kallon Daada yadda Tayi mgana Cikin Fushi Daddy ya Dukar dakai Yana Fadin"Allah ya huci zuciyar Daada..! Daada bata tsaya Sauraransa ba ta Cigaba da Fadin"Koda yaushe kalaman ku kenan kaida Dan"uwanka In nayi mgana sai kuce kuna iya bakin Kokarin ku..?yau ne ya bar gida..? Yanzu fa Kimamin Shekaru uku har da wani abu da Bacewarsa shi da Iyalansa Ammh ba wani Labari sai Faman Fadamim kike yi kuna iya bakin kokarinku..Ina Kokarin yake..?ba wani Kokarin da kukeyi kowannenku yana chan yana Harkan gabansa Kawai Shi ya Dameshi baku Damu da Dan"uwnku Daya bar gida Cikin Lalura da Raunin Rashin Daya Fuskata ba..To bari kuji na Fada muki ba iya Kokari nake so kuyi ba Sama da Kokarinku zaku yi ku dawo min da Dan"uwanku gida in ba Haka ba Nima Zaku wayi gari kunyi Sanadiyar Rasani Kamar yadda kukayi Sanadiyar Barin Dan"uwanki Cikin Ahalinsa yabar komai nashi yayi Nesa Damu saboda yadda kukayi ta Tafiyar dashi..! Ta karishe fada Tana kara Goge kwallarta da Haban Hijabinta Kowa afalon ya kasa Motsi saboda Shesshekan kukan Daada,Baffa Kabiru da tunda aka fara mgana bai ce komai ba sai alokacin ya gyara Zama yana kallon Daddy Lokaci Daya ya maida Hankalinsa wajen Daada yana Fadin"Haba Daada wannan wani irin mgana ce ya zaki dora mana Alhakin baarin Malami gida..? Wannan ai ba mgama bace ya bar gida ba saboda komai bane sai baya son a Fadamai gaskiya sannan ya Biyema Mganar ya"yansa Har ya iya Tafiya har yau bai nemi kowa ba..Daada ki Dora duka Laifin akan karansa shi da ya"yansa ba akanmu ba..! Mami Asma"u dake gefe tace"Nima abunda Zan ce kenan Baban Sajida What all d Bleming akan ku kuma..? Wanda ya tafi batare dayayi Shawara da kowa ba..Shi ya kamata a Dora ma Duka Laifin ai Daada..! Inna mainunatu ta Kalleta Tana Fadin"Sam bai kamata ba abunda kuma kikayi ba Daidai bane..Bai dace Manya na mgana ba kina saka baki ba..Koda kike Matar ya kabir wannan ba Hurumin ki bane mganace ta Tsakaninsu bai kamata ki saka baki ba gaskiya...ko kuwa nayi Laifi Jama"a..? Tafada tana kallon Daddy kai ya gyada mata kafin yace"baki Laifin komai ba Maimunatu..! Daada ta Dago daga Sharan kwallar Tana Fadin"Kabiru ka tsawartama Matarka..Kada ta kara sakamin baki in ina mgana da Ya"yana..! Bai da yadda zai yi Dole ya juya wajen Mami Asma"u data gama cika Da mganganun Inna Maimuna sai Harare Harare take bai mata mgana ba da ido kadai ya Kalleta alamun kada ta kara Mgana sai ta koma tayi Laushi Lokaci Daya Tana kara Rumgume Sajida Dake jikinta Inteesar Dake rumgume da Abiden tayi Tsaki acikin Ranta kafin ta Juyar da kanta Karaf suka Hada ido da Khamis ya Kureta da ido Saurin Kauda kanta tayi acikin Ranta tana Ayyana wannan kodai Maye ne wlh kurwanta kur indai itane. Daada ta kara Gyara Zama cikin Shakewar murya tacigaba da Fadin"Zakace min kada na Dora alhakin barin Malami gida akanku Kabiru..? Musamman ma kai Domin Mustapha In yana da Laifi Kadan ne na Biye maka da yayi bai fadamaka gaskiya ba. ni kuma har ga Allah bana sanin abubuwan Dake Faruwa wani Lokacin.' Ran Baffa Kabiru ya baci cikin Fushi ya kalli Daada yana Fadin"Daada Kifa Daina dora alhakin komai akaina ki Dorashi kan Malami Da ya"yansa Musamman yaron nan nashi Kanin Yusuf Mara jin mgana ga shi yana ganin yana Daidai da kowa Tun kafin hakan ta Faru daman baya son Zama Cikin Danginsa Bazan ga Laifi in sun Tattara sun tafi wata uwa Duniya ba..! Daada cikin tsawa tace"Yimin shuru anan wajen Kabiru kada ka kara cewa Tak..in ba haka ba sai na saba maka..! Kowa afalon sai da yaji wani iri Baffa Kabiru kuwa kamar ya yi Bindiga haka yake ji saboda Fushi Ita kuma Mami Asma"u Sai cika take itacda yarta Don me Daada Zata Tara Mutane tana cima Mijinta Zarafin Bazata Dauki wannan Rainin ba. Daman Tun malami nan nan Tasu bata zo Daya ba Tana ganin kamar shi ne yake so ya goga Kafada Daya da Mijinta akomai kuma alokacin Anni itama tana sakawa tana Cirewa Mai Tsada Su Asma"u ma badai ka gansu Cikin wani yanayi ba Daka gansu Zaka Fahimci suma din sun Tara kodaga Kayattacen Gidansu na Lagos Mami Asma"u tasan da Anni Zata goga acikin Dangi,saboda bata kaunar wani ya fita ita da Mijinta da ya"yanta ako"ina ne shiyasa bayan Faruwar abun Take da Zuga Barrister kan meyasa Daada take Wahalar dasu ne kan Nemo wanda basu san ina Ya shiga ba ko alokacin Dayake Ma Abba Fadan ya haukace duk itace ke Kitsamai wai yaki Daukan kaddaransa Tayaya kuma zai zo shi ya Zame musu Lalura Allah ya yita Mace mai son kanta da yawa shi kuma Baffa Kabiru yana Matukar sonta ya gama bata Dukkan Amana. Daada ce cikin Muryan kuka Tace"In bazasu yi nesa damu ba wani mataki kake so su dauka..?Suma ya"ya ne Tamkar ya"yanku Bazasu taba Jure Zama kana kiran Mahaifinsu da Mahaukaci ba Kabiru alhalin kasan Rayuwace da Rashi ta maida Malami haka da Kaddaran da bawa bai isa ya kaucemata ba..Rashin Rai yayi matarsa Zuwaira da ya"yansa Har guda Uku Kabiru ka Fadamin ko kai ne Wani Hali Zaka tsinci kanka..? Na tabbata yadda kake son matar nan naka da ya"yanka in wani abu irin wannan ya samesu na Tabbata kai kila Sai ka Rataye kanka ma Saboda Tashin Hankali..! Gabadaya falon sai ya Kaurevda Mganganu kasa kasa na Tuna abunda ya wuce a Shekaru uku da suka gabata Jikin kowa yayi sanyi Mami Asma"u kuwa Kallon Daada Take ta cikin Glass dinta aranta Tana Fadin"Bakin ki ya sari Danyan kashi mai Doyi Daada. ! Take fada Acikin ranta Domin Gani take kamar Daada na yi musu Mugun baki ne.. Daada kuka take harda Shasheka ganin haka yasa Daddy ya Matsa gareta yana Fadin"Don Allah Daada ki bar kuka kina Karyamana Zuciya..Ga Matayen mu ga ya"yanmu harda Jikoki bai kamata ba don Allah ki bar kukan nan ki Share Hawayenki..! Batayi gaddama ba ta Share Hawayenta Tana jan majina tace"Naji zan Share Hawayena ayanzu..Ammh ku sani har in dai ba Dan"uwanku kuka Dawomin dashi ba bazan Daina Zubar da Hawayaena ina kuka ba..Kuma In har baka gayama Kabiru Cewa Laifinku bane game da Barin Malami gida ba Shima baZai sai na Fasa Fadin kune Sanadin Barinsa Gida Dashi Iyalansa agaban ko waye ba..! Daddy ya dukar dakai yana Fadin"Gaskiya ne Daada..Ni ban Musa ba Muna da Laifin Tabbas Wajen Ya"yan Ya Malami su Daukesa Daga Cikin mu..! Da sauri Baffa Kabiru ya Dago yana kallonsa kafin yace"Au kaima ka yarda Laifin mu ne..? Daddy ya dago yana kallon Baffa Kabiru yace"Gaskiya ce Dole a Fadeta Baban Sajida..Na Dade ina son na Gayamaka wannan gaskiya..Alokacin da abun ya faru ba haka ya kamata mu Tafiyar da Ya Malami ba..Yana Bukatar Lallashi da jansa ajiki da kuma Nunamai Soyayyah,alokacin bai Bukatar fada ko Hayaniya domin amasu irin Laluransu Fada yana kara Karfin Tasirin Cutar acikin jikin mutum sai ya rika ganin kamar shi kadai ne,Tabbas alokacin muna da kaso mafi yawa Tunda bamu Jasa ajiki ba bamu nunamai kulawa ba sai ma Kokarin numamai ko ta Halin kakane sai ya koma yadda yake afarko kuma abun ba haka yake ba ita Cuta ce take Shiga Farat Daya Waraka sai a Hankali kuma bamu yi la"akari da Raunin Daada ba da ya"yansa kansu da suma Raunin ya Tabasu ba..bayan haka suka nemi komawa Lagos ka Amince musu bakayi Tunanin Tayaya Zasu iya wannan Rayuwar su kadai ba bayan Tafiyarsu Kaje har Gidan ka Samesu cikin Wani hali bakayi wani yunkuri domin Dawo da Rayuwarsu Daidai ba ka taho ka barsu bayan wani Lokaci aka nemesu aka Rasa tayaya bazamu dora alhakin Faruwar hakan a wuyan mu ba..? Daada uwa take garemu Hakkinta na kanmu ya Zama Dole mu yi abunda zamu yi mu Daina Sakata kuka..! Gabadaya kalamansa ya Kashema kowa Jiki shi kanshi,Baffa Kabiru ya kasa Cewa komai Domin yasan gaskiya aka fada. Daada kuwa Mirmishin ta saki irin na Manya kafin tace"Irin wannan Ranar nake jira....yau in ku bazaku iya ba Zan Raba aikin harda ya"yanku wasu ku nan kusan Baffan ku Malami shi yake Bima Kabiru bayan Hatsarin Jirgi ya Rutsa da iyalansa abubuwa sun Faru marasa Dadi har yayi Sanadiyar barin sa Gida shi da ya"yansa guda uku wadanda basu san sa ba Yanzu Asabe zata Dauko Hotonsu ku karba Daya bayan Daya ku duba wanda Allah yasa yayi katarin Ganin Daya Daga Cikin su Sai ya sanar damu..! Asabe Shiga Dakina cikin Sip ki Daukomin Hoton nan..! Ta Karishe fada ta Kallon Asabe Dake gefe da Sauri ta Mike tana Fadin"To Daada..! *Shakira..* 3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*      *🅿�26* Ba bata Lokaci sai ga Baba Asabe da Wani Hoto a hannunta an yi Elagement dinsa ta mika ma Daada,ta karba Lokaci Daya tana Kallon Hoton Cikin Raunin zuciya sai ga Hawaye Sharr sun Zubo mata hannun da Casbaha ke hannunta ta sanya tana Shafa Hoton Tana Fadin"Allah sarki Rayuwa...Zuwan da Zuwaira tayi na Karshe ne da bata kara zuwa ba Allah yayi mata rasuwa,bayan wata Karamar Sallar azumi ta kawomin wannan Hoton tace Daaada saboda ke na saka aka wanke shi aka Gyara miki shi Gamu nan dukkanmu Harda Marajin jikan ki an samu Dakyar ya Shiga Hoton watarana in kinyi kewar ganinmu sai ki Dauko ki Duba..! Tabbas ta fadi gaskiya ashe Watarana Zan yi kewa kewa kuwa ta har Abada..! Daada ta Karishe fada cikin karyewan Murya kafin tace"ALLAH yajikan ki Zuwaira ya Kyautata makwancinki..Ya"yanki da kuka Amsa kiran Mahallicinku atare suma Allah ya Karbi Shahadarsu Allah ya Hadamu a aljannah Firdausi..! Gabadaya Falon aka amsa da Ameen Jikin kowa yayi sanyi kamar yau ce akayi wannan Babban Rashin Inna Maimuna sai sharan kwallah take Saboda Tana ganin kamar yau ne komai ya faru. Share Hawaye Daada tayi kafin ta Mikama Baffa Kabiru Hoton tana Fadin"Ku bama Matan ku da ya"yanku su gani..! Daga haka bata kara mgana ba ta Cigaba da Jan Cashabanta Cikin Rauni da Rashin Lafiyar Jikin Tsufa. Bai ma Tsaya kallon Hoton ba ya mikama Daddy ya karba Shine ma ya Tsaya yana kallon Hoton,Malami ya Kurama ido yana kallonsa sai yaji wata Kwallar ta tarumai a kwarmin Idanuwansa Dukkansu ne da Sallah ne suka Dauki Hoton da Ya"yan da Uban Duka Farar shadda suka saka da Hula Anni kuma dasu Asma"u suna Sanye da wani Leshi mai kyau iri Daya sai Auta Munari Dake sanye da Shadda Fara irin ta su Abba an mata aikin mata Imran ne kadai a Hoton bai saka Shaddan ba,lokacin Ya dawo Daga makaranta Ibadan Ba"a son ranshi ma yayi Hoton ba sai da Anni tace in bai Tsaya ba sai ta Sabamai Shi Sanye yake da Bakin wando da Farar riga mai Kauri Gajeren hannu Gareta,kirar Armani Yadda ya hade rai ya kalli Gefe Fuskarsa ma bata Fito DAkyau ba Zaka Fahimci baiyi niyyar Daukan Hoton nan ba Dole aka sakashi Imran kenan. Daddy saboda Raunin Dayaji zuciyarsa tayi yasa ya mikama Inna Maimuna Hoton suka Taru ita da ya"yanta suna gani tana Fada musu Sunayensu Sai da tazo kan Imran ne ta Dago Tana kallon Daddy Lokaci Daya Tana Nunamai shi Tace"Ya Mustapha wannan banganeshi ba. ? Me sunansa na kusa da Yusuf..!? Kafin ya bata Amsa Daada Dake ZAune tace"IMRAN kenan Miskili kafin mahaukaci ban Haushi..! Gaban inteesar sai da ya Fadi Dataji an ambaci sunan Imran haka take Fama da Faduwar gaba Tunda ta Dawo ko sunansa ta Tuna sai gabanta ya Fadi ballatana ta Tunashi ta rasa Dalilin haka.. Haka Hoton ya Dinga Zagaya Falon Daya bayan Daya,Inna Maimunace take nuna Wadanda suka Rasu da wadanda aka nema aka Rasa Daidai Lokacin da Hoton yazo hannun su Anty Hauwa ita kuma Inteesar tatashi Zuwa Cikin Dakin da Anty Hauwa ta Sauka ta Dauko Madaran Abiden Dake Cikin Fidarsa yana Hannunta sai ya Fara Kuka Umma tace taje ta Dauko to Dataje sai ta zauna achan ta Hadamai ta Bashi yasha koda ta Dawo Hoton ya bar Hannunsu yana Hannun Mami Asma"u wacce ta mikama Umaima ita kuma ta mikama Sajida wacce ta Dade Tana kallon Hoton Imran Take kallo duk da ba sosai Fuskarsa ta Fito ba sai da akallo Daya zakamai ka Fahimci yana da wasu abubuwan da bakowani Namiji ke dashi ba ta Shagala da kallon Hoton har sai da Khamis ya taso da kansa ya karba ya Koma Wajen zamansa suna Kallo su da su Sa"id dasu Ya basheer suna kara Jimanin Mutuwar su Anni da su Asma"u Allah Sarki da yau sunan nan anan Wajen da duk abunda ya Faru bai Faru ba. Duk da Inteesar taso ganin Hoton ammh Ganinsa Hannun Khamis yasa bata ma ce Zata gani ba,Da Umma ta TAmbayeta ko ta gani sai tace Eh tagani Saboda bataso ace taje ta karbo hannun wannan mai Mayen Kallo. Bayan kowa ya gama ganin Hoton aka Maida ma Daada abunta ta karba Ta ijiye gefenta irin su Sa"id dasu Ya Basheer harda Snaping din Hoton a Wayarsu. Daada tayi gyaran Murya Tana Fadin"Ina Fatan kowa ya ga Hoton nan ko..? Gabadaya aka jinjinamata kai kafin ta Cigaba da Fadin"Ina neman Taimakon ku..Ba Taimakon Dai dai kun ba..kowa Dake wannan wajen ban Dauke mai ba Mazan ku da matanku ina ji ajikina Malami bai yi Nisa sosai ba yana nan kusa Damu don Allah ku saka Ido ku nuna ma abokan aikin ku Da Wadanda kuke mu"amala dasu ko Kila wasu daga cikin su sun Taba ganin Daya Daga cikinsu,na tabbata baza"a rasa wanda wata Mu"amala ya Taba Hadasu dasu ba koda Bayan barin su gida ne..! Gabadaya aka amsa mata da Insha Allahu Sa"id ne ya Daga hannu yana Fadin"Daada in kin bani Dama Ina so zan yi mgana. ! Daada ta gyadamai kai Tana Fadin"An baka Dama Sa"idu! Mikewa yayi Lokaci Daya yana gyara Zaman Rigar jikinsa Data Tattare saboda Zama yana Fadin. "Assalamu alaikum da farko dai Kamar yadda wasu suka sani ni Sunana Sa"id Sulaiman ni D"a nake wajen Inna Maimunatu da Farko wani dan Shawara zan kawo mana game da Riko da Zumuncin da Daada Tayi mgama..Gaskiyan mgana akwai gyara a Tafiyar nan tamu kamar yadda Mommy ta kawo mgana ne kan cewa Dukkanmu bamu yi nisan da zamu ki Ziyartar gidajen yan"uwanmu da iyayenmu ba,Sannan da yawanmu anan Wajen bamu san juna ba Akwai Kadan da na sani ammh da yawa wasu duk ban sansu ba sai dai kawai kasan kana da wan Mahaifiya yana da Mata yana da y"ya ammh kuma bakasan matar ba bakasan ya"yan ba kuma sunan an Fito Daga Tsatso Daya,Shine na yanke wani Tunani me Zai hana Tunda nasan kowa acikin mu Daga mu yaran Har iyayan namu muna da wayar Zamanin nan Data Zama ruwan Dare ko bamu Samu takawa munyi Zumunci ba ta kafa ba akallah kowa nada Lambar kowa bayan kowani kwana Biyu Zamu rika Kiran juna awaya muna Sanin Lafiyar junamu da kuma Sanin in wani abu ya Faru..sannan abu na gaba Zan Bude mana Group a manhajar nan ta Zamani Wato WhatApps Da sunan IYALIN MARIGAYI ALKALI DUKKU Zan karbi lambar kowa zamu yi adding dinsa acikin wannan Group Kama Daga mu har iyayanmu Inda Zamu Rika Sada Zumunci a Tsakanimu in wani abun karuwa ya samemu za"a sanar Domin mu Taya wanda abun ya sama Murna in Rashi ne ma kowa zai sani Tunda duka ana Chure waje Daya sannan in ma wane bai sani ba Wane ya sani zai sanar dashi..Mganata ta Karshe shine ya kamata bayan kowani Wata Biyu a samu Ranakun karshen Sati a Dunga Haduwa ana Tattauna wasu Batutuwan da suka Shafemu ta hakane Zamu san mtsalolin junanmu sannan Shakuwa mai Karfi Zata Shiga Tsakaninmu kuma hakan zai Sanyayama Daada rai Baza tayi Fargaban ko Bayan Ranta Rabuwar kai ZAta Shigo wannan gidan ba Daga karshe ina mai Sanar da Daada ta Kwantar da Hankalinta tunda ta Shigo Damu Cikin wannan Al"amarin sai inda Karfinmu ya Kare Indai Kawu Malami na Cikin kasar nan zamu nemosa Duk inda yake mu Dawo miki Dashi Gida shida iyalansa da yardan Allah..Wssalam..! Ya karishe Fada yana komawa ya Zauna ba Daada kadai ba Kowa Dake Wajen yaji Dadin kalamansa kuma yayi Na"am dasu Daada na Mirmishi tace"Mustapah da Kabiru kunji Abunda D"anku yace ko..?kune Manya ku Zartar da Abunda ya kamata Duk abunda yace yayi Daidai yayi tunani mai kyau kuma naji Dadi..Allahu yayi muku albarka Gabadayanku daku da ya"yanku da Zuru"arku gabadaya Allah yasa yadda muka Hadu ayau anan Wajen haduwa ta gaba ace Ga Dan"uwanku agefeDaya Allah ya Bayyanasu Allah yasa suna Cikin Koshin Lafiya kamar yadda nake Fata..! Gabadaya aka amsa mata da Ameen Jin an Fara kiran Sallar La"asar kana Daada tace"Kowa ya tashi yaje yayi Sallah..Daman Dalilin kiram nawa kenan ko ba Domin haka ba ina Bukatar ganin Ya"yana da Jikokina a kusa Dani yau gashi na ganku naji Dadi kwarai Allah ya maida ku Gidajenku Lafiya bazan zaunar daku ba Saboda akwai masu Ayyuka da yara Masu Karatu zuwa Gobe na Sallami kowa zaku iya Komawa Gidajenku Allah yayi albarka...! Aka Shiga amsa mata da Ameen ta Mike Bayan Daddy ya Mike ya Taimakamata ta Kalleshi Shi da Baffa Kabiru Daya Mike Tsaye yana Duba agogon FAtan Dake hannunsa yana auna Lokaci ne in zai isheshi yau din Zasu juya abuja Daada ta gama batamai rai bayason ma ya kara Kwana agarin yaji tace"Mustapha kai da Kabiru in kun Idar da Sallah kuzo ina Neman ku..Asabe In kin idar da Sallah ayi Haraman Dora abinci mun cinye Lokaci anan wajen..! Daga haka ta Juya tana Tafiya a Hankali Zuwa Cikin Dakinta Daddy ya Kalli Baffa Kabiru kafin su kada kai su Fice Baba Asabe kuwa Tuni ta amsa ta Shiga Dakinta Domin ta gabatar da Sallah Mazan ma sun bi iyayansu Waje Matan kuma Kowa ya kama Inda ya Sauka. Bayan sun idar da Sallar ne Umma Tace Inteesar da Hafsah suje Kitchen su kamama Baba Asabe aiki Inna Maimatu harda karima da Zainabu tace suje suyi aikin gabadaya,Haka kuwa suka shiga Kitchen suka Zage suna Taya Baba Asabe aiki suna Hira Duk Rashin Sakin jikin Inteesar ta Fahimci ya"yan inna Maimunatu Dabam suke suna da matukar Kirki Shiyasa ta dan Saki jiki da su suna ta Hira Ita Karimam a Bauchi Take aure ita kuma Zainab tana auran Dan Wazirin Azare ne achan take da Zama duk adan Hiran da sukeyi ne ta ji hakan Daganan suka gangaro Hirar Inna Bintalo da ya"yanta yadda suke Fadan Halinta sam Inteesar batayi mamaki ba ko Daga ganin yanayinta,Daganan Hirar Mami Asma"u ya Shigo itama da ya"yanta Sai Hankali suna mgana sukace duka Laifin na Baffa Kabiru ne Shine ya Sakarmata Komai da kuma da Fifita Boko Fiye da al"adunn Addinin Musulunci,Suna labarin Halayyar Sajida kaf na Uwarta ne ta kwaso gwarama Umaima sau Dubu Sajida ga Rashin kunya ga ba kwaba sai Sangarta da Sakarci kamar wata yarinya Duk Inteesar na jinsu ita dai bata Tofa ba sai dai kawai ta Murmusa aranta Tana fadin ita Taga Rashin kunyar Sajida tun lokacin ta Gama Sanin Halinta kaf ta kuma san inda ta ijiyeta.. Sai gabda mangariba suka gama aikin white rice ne sukayi da Miyar Naman Rago sai Ferfesun kaji da Daddy ya bada kudi su Basheer suka Fita suka Siyo sai Salat da Lemon Aya da na Kankana suka Hada,Daganan kowa ya tafi yayi sallah Su Umma da su Inna Maimuna daman suna Falo suna kallo suna Taba Hira Mami kuwa da ya"yanta suna Daki basu Fito ba koda Umaima tace zata je Kitchen hanata Tayi. Inteesar dai bata iya Sallah ba Sai da ta Watsa Ruwa kana ta gabatar da Sallah Tana Kan darduman har aka Kira Insha"i tatasshi ta gabatar ta Idar ba Dadewa taji Hayaniya afalo kenan Mazan sun Dawo daga masallaci sun Shigo kenan,Tana nan zaune bata tashi ba Hafsah tazo tayi Sallar Isha"i tace tazo su je su Taya Baba Asabe kawo su abinci Karima na Wajen tace Su Anty Aneesa gasu chan suna kwasowa jin haka yasa bata yi yunkurin Fita ba sai da Hafsah tace ta Fito suci abinci kana ta Fito duk da bama ci Zatayi ba ita abu mai Ruwa Ruwa Zata sha Shiyasa tana Fitowa Kitchen ta Nufa ta Tsiyayo Ruwan Zafi a Flaks ta Hada tea a wani karamin Mug ta Fito dashi da Cokali Tana Juyawa Daki tayi niyyar komawa Domin yau cin abincin basu Daddy suna Dakin Daada suna mgana Matan ne sai Ya"ya sai jikoki sai Tattaban kunnen Daada Dake Tsalle Tsallemsu afalon. Har takai Kofar Dakin taji an ce"Ina Zaki..?badai bazaki ci abinci ba Inteesarr..! Yadda ya fadi mganar ne Cikin Wata Murya yasa ta waigo Khamis ne ko ya Kureta da Mayen kallonsa kauda kai Tayi Tana Fadin"Eh am ok..! Sai da ya wani kalletaa kasa kasa kafin yace"U are ok dame..? Me kikaci..? Takaichi da Haushi suka kama Inteesar ba ita kadai ba Hadda da Mami Asma"u da Sajida da basu ga Dalilinsa nayi ma Inteesar mgana ba. Rausayar dakai tayi Cikin Kosawa Tana Fadin"zan sha Tea..! Tafada tana Dagamai Mug din Dake hannunta Zai sake mgana Mami Ta Kallesa Kafin tace"Khamis plz kaci abincinka Tace She is ok ko Dole ne..? Tafada Cikin Halin ko in kula Umma naji batace komai ba sai chan Tace"Intee bamai cin abinci bane..Tafi daman shan Ruwan zafi in Zata kwanta.! Mami Ta tabe baki Kafin tace"Plz Help me.. tell Him..! Daga haka ta Tsuke bakinsa Shima bai kara mgana ba sai Binta yake yi da kallo Itama Juyawarta Tayi ta zata Shigo Dakin Sa"id ya Kirata ta waigo Cikin Girmansa yace"Ya Zaki tafi..? Da fa mun gama cin abinci zam karbi lambar kowa..Kowa kuma zai yi Sharing Cantact dinsa da Dan"uwansa..! Yake Inteesar Tayi kafin tace"Ya Basheer plz ka bashi Cantact dina..! Harara ya Dago ya Sakarmata yana Fadin"Ni dan aikin ki ne..? Shagwabe mai Tayi tana Fadin"Plz Bro..plz Mana..! Kallonta yayi kafin yace"Ok..Naji kafin ki samin kuka..! Dariya tayi har sai da Fararan Hakoranta suka Bayyana tace"Tanque Bhaya..! Sa"id ne yace"To in an bamu taki na Sauran fa yaushe zaki karba..? Da sauri tace"In d mrming kafin mu tafi Insha Allahu..! Kai ya jinjina kafin yace"Is ok..Buh ki karba kisan Is very Important..! Kai ta gyadamai kafin ta Juya ta Shiga Cikin Dakin tana Sakin Sirrin Tsaki Aranta Tana Zagin Khamis kallo kamar Wani maye yayi ta Kallonta Haba ita fa ta kosa Gobe Tayi subar Gidan nan ta koma Tayi Shirin komawa makaranta Munari tace itama bazata Shiga School ba sai in ta Dawo su Shiga gabadaya. Tana gama Shan Tea dinta ta Haye gado Ta gaji Barcine a Idonta Lokaci Kadan baeci ya kwasheta Sama Sama Tana jin Tashin mgangansu Daga Falon Daada. Su kuwa sai wajen 11pm Taron ya tashi Adaran Sa"id ya Bude group din ya Karbi Lambar Kowa ya sakashi,Daga kan iyaye har kan Kanne da yayyi irinsu,Ya kuma Umarci Kowa ya Karbi Lambar kowa,haka akayi sukayi ta Sharing din Cantact din juna da alkawarin Kiran juna Lokaci bayan Lokaci,Umma daman Tana da Mami sai dai su yi Wata Biyar ba wacce ta kira Kowa acikinsu Sai ta karbi ta Inna Maimuna da Inna Bintalo yaran yaran kuma suka Karbi da junansu,Umaima ce ke bata Lambarta Cikin Dadin rai banda Sajida har gwarama Mami ta bata nuna wani abu ba Ba wanda na yabi ta kanta Ballatama ya Damu da ita banda Hafsah ba wanda ya karbi Lambarta,Sai ya"yan Inna Bintalo Daman Hadeje ce da kano,Lambar Inteesar kuwa Umma ce tayi ta badawa Mazan kuma Basheer ya basu Wannan abun yafi yima Khamis Dadi Domin Hanya mafi Sauki kenan Wajen Cimma Burinsa kan Inteesar da Tunda ya Fara ganinta Tunaninta da Soyayyarta suka yi mai mugun kamu basu barshi yayi barcin Kirki ba.,Love at first sight kenan Su Daddy kuwa sai Wajen 12pm suka Fito Daga Wajen Daada suka ci Abinci suka Nemi makwanci Nasihohi ne Tayi musu sosai mai Shiga jiki wanda Har sai da shi kanshi Baffa Kabiru ya yarda da Kuskuransa kuma yayi ma Daada alkawarin Inshu Allahu zai gyara Daganan suka Shiga Hira da Tsara yadda Zasu Hada hannu dasu da ya"yansu su zama Zuru"a Daya ba Wariyar Launanin Fata shi ya bata musu Lokaci basu Fito da wuri ba. Ranar Daada Tayi barcin Farincikin Data Dade batayi ba. Washegari Tun 4am na asuba Kowa ya Tashi saboda Sammakon Tafiya,ko kafin karfe bakwai na Safe Masu Shirin Tafiya duk sun Shirya Baffa Kabiru suka Fara Tafiya Sadam wanda Zai je kano Inteesar ta karbi Lambar Matarsa Aneesa tayi mata alkwarin in ta koma kano ZAta zo Gidansu tunda tace suna Sharada Phase3 ne da Zama. Daga sune sai Sa"id da zasu je Dutse Tare suka Tafi da Hafsah tunda Tana Wajensa ne itama sun karbi Lambar juna ita da Inteesar,karfe tara na Safe su Inteesar suka Mika Hanya sun bar Inna Maimuna na Shirin Tafiya ita da ya"yanta sai sun Biya ta Bauchi Inna Bintalo kuwa sai gobe Zata koma,gida duk yayi Shuru tunda Baki sun Watse Daada ta Bisu da addu"an Allah ya kaisu Gidajensu Lafiya kamar yadda suka zo hankalinta bai kwanta ba sai da Kowa ya Kira yace ya sauka Lafiya Har Inna Maimunatu da suka Tafi Daga baya suma sun sauka Bauchi lafiya sai dai kuma wani Haduwar In Allah ya nufa. ****** *Kaduna.* Tunda suka dawo Daga Dukku Inteesar ke shirin komawa makaranta Taso tafiyar nata ya Zama Alhamis Sai Daddy yace bari Asabar ko Lahadi sai ta Koma,bata so ba ammh bata da yarda Zatayi Ganin zaman gidan ya Isheta yasa taje gidan Nasara ta Kwana Daya gidan Ya Basheer ma ta Kwana Daya gidan su Inno ma Tayi kwana Daya Ranar Jumma"a tadawo Saboda Shirin Tafiya Umma ta mata Miya da Dambun kaji sai kayan Snkas Sai sauran Tarkace irin su madara Indomie da Complez wanda Zata tafi dashi sai kuma Dinkuna da Daddy ya Sake Dinkamata umma ma ta Dinka mata Kala Biyu duka guda Biyu iri Daya Munari tace takai ma Kala kala Daya sai ta bar wasu kayan nata agida ta Kara Dibam wasu kayan ta Hada da Sabbin Zata koma Dashi. Suna waya da Hafsah tunda suka koma ita ke kiranta mai sonka ka soshi itama Tana kiranta Har ta bata Anty Fareesa su gaisa Ya Sa"ad kuwa shima ya Kirata sau Daya suka gaisa Tayi Saving din Lambarsa ya Sadam kuwa Kusan Kullum sai sun kirata shi da Anty Aneesa wai ko ta Shigo kano ne tace a"a Shi Ya Sadam din har kiran Daddy yayi yana Rokonsa Inteesar ta Dawo Gidansa da Zama Daddy ya basa Hakuri yace bazai yuyu inda take ma Duk gida ne ammh yayi mai Alkawarin Zai gayamata ta Rika Zuwa Weekend gidansa in ta Samu Dama da sukaji haka sukace ba komai. Da Umma taji tace ai bakomai Tunda suna Garin Inteesar zata Rika zuwa Ita kanta Umma suna waya da Inna Maimunatu da ya"yanta Mami ce Sau Daya ta Kirata suka gaisa Sama Sama tace Tana Kotu ne Daganan basu kara mgana ba group kuwa su Ya Basheer suna Kokarin ingatansa Inteesar dai bata taba mgana ba Tana dai Shiga ta Karanta Sakoninsu,Ba Laifi su ya Sa"id suna Hira da dadddre haka in sun Dawo daga aiki Daddy ma yana mgan ba Sosai ba,Baffa Kabiru ne sai dai Turo Mrning Text da Gudnigjt ba wanda bai Ciki Harda Sajida ammh itama bata Taba mgana ba Sai Khamis ya taba mgana da Umaimah Shi khamis taji Ya Sa"id na mganar ya koma Wajen aikinsa Shiyasa aka jisa Shuru. Inteesar Tafiyarta bai samu Asabar ba Sai Lahadi Da Sassafe Ya Basheer ya Tafi kaita banda Daddy ya tashi da Ciwon Kafafu sai kawai Yace Basheer ya kaita wannan karon ma sai da Inteesar Tayi kuka sai dai suna Daukan Hanya ta Warware suna Hira da Ya Basheer har suka iso Misalin Karfe 11am na Safe suka isa Lokacin ko Shago Sagir bai Bude ba Tunda Daman Ranakun hutun mako bada Wuri yake Bude Shagon ba. Sai dai Mama Taga almajirai na Shigowa da kaya sai ga Sallamar Inteesar Mama ta Fito Daga Daki ita da Sagir tana mata Maraba Rumgumeta Tayi Inteesar tana Cewa Mama nayi kewarki sosai. Mama tace"Nima haka yata..ai tun jiya da Salaha tace zaki taho nake ta Zura ido..Tafiya bata yuyu ba sai yau..! Ya Basheer Dake baya Dauke da akwatin Inteesar yace"Wlh Mama sai yau Allah yayi..! Maraba ta shiga musu Sagir ya bashi Hannu suka gaisa suka Rankaya zuwa Falon Mama. Bayan gaisawa da Tambayan Mutanen Gida Mama ta kawo musu Kunu da kosan Datayi yau da Safe Ya Basheer yasha kunun sosai Inteesar nema taci Kosan kawai. Ya Basheer ya bama Mama 20k in ji Daddy sai Kayan abinci da suka zo mata Dashi Tana ta Godiya Inteesar kuma ana Ciki tana gyara kayanta Sai da Ya Basheer yayi Sallar Azahar yayi Shirin Tafiya Mama tayi tayi ya Ci abinci yaki wai bayaso yayi Dare Ahanya Hakanan sukayi sallama Har Bakin Mota Inteesar da Sagir suka Rakashi Sukayi sallama suna Dagamai Hannu har ya Fice Daga Layin sagir Shagonsa ya Shiga Tunda Yaransa Har sunzo sun Bude shagon sunyi Shara,ita kuma sai ta koma Cikin Gida. Ashe Ya Basheer ba Gida ya dau hanya ba Gidan Ya Sadam yaje Daman ya gayamai zai shago kano Dawo da Inteesar makaramta da kwantance sai gashi agidan Chan suka Hade suna Hira Aneesa Tamusu lunch sukaci Sai Karfe 4pm ya bar gidan yadau Hanyar kaduna Sai da Inteesar din ta Kira Anty Aneesa ta gayamata yau ta Dawo Shine take Fadamata Yanzu Ya Basheer ya bar gidansu Inteesar taji Haushi tace bai Fadamata zai biya ba data Bisa Aneesa tace haka yace ma Sadam dayace meyasa bai Dauko ki ya kawo ki kin ga Gidan ba Sai yace baya son ki batamai Lokaci ne. Inteesar bataji Dadi ba ammh sun Rabu kan Insha Allahu Zata zo ko Cikin Weekend din da zai kama ne. Suna gama Waya ta Kira Munari tace mata Ta iso Munari sai murna Kamar Zata Tsinkama Inteesar dodon kunne ta Kashe wayar Tana Mata Dariya Munari kuwa Daman Tana Dakintane itama tana gyara Kayanta da mai wanki da guga ya kawo ne Sai gata ta Fito da gudu Tana Murna Abba Dake Falo Shi da Ya Yusuf suna Hira kan Yadda Harkan Tsaro ya Tabarbare a kasar nan Gefe daya kuma suna kallon NTA news na Karfe 4pm.Anty Safiya kuma na Kitchen Ta fito tana Tsalle. Abba ya Kalleta yana Fadin"Munarin Abba meyafaru ne..? Jikin Abba ta Fada Tana Fadin"Abba Intee ta tadawo..! Tafada tana Washe baki karaf sai a kunnen Imran Daya Fito Daga Dakinsa sanye da wani 3Quater wando mai Ruwan madara Jikinsa ba Riga da Farko Daya fito yaso ne ya isa ga Munari ya bata wani Kyakyawan mari da sai ta kusa suma kan Ihun banzan Datake musu acikin gida sai dai sunan dayaji ne ta ambata ne yasa ya Tsaya Cak ya kasa Karisawa,Saboda yadda gabadaya Kirjinsa ya amsa Harda gangan jikinsa.. Abba dake Mirmishi ya shafa kan Munari yana Fadin"Ah Dole kiyi murna..Aminiya ta dawo ko..?ai sai tashi aje ayi mata sanu da zuwa..Nima kice ina mata barka da Dawowa..! Da sauri Munari ta Mike tana Fadin"Yanzu kuwa Abba..Ya Yusuf ina Anty Safiya..? Yace"Tana Kitchen..! Gudu ta kwasa Zuwa Kitchen din tana Kiran sunan Anty Safiyan Abba da Ya Yusuf suka Bita da Kallo Abba yace"Allah ne ya Hada kauna Tsakanin Munari da yarinyar nan yadda suke son juna Kamar wasu yan"uwa.! Ya yusuf yace"Sosai Abba Daman haka Rayuwa ta gada..Wani abokin ko kawa sai ya koma maka kamar wani Dan"uwanka..! Abba ya jinjina kai yana Fadin"Gaskiya ne..tashi muje masallacin naji ana ta kira tun Dazu..! Atare suka mike Daidai Lokacin da Imran ya koma Ciki da kallo suka Bisa Kafin su girgiza kai suna mai addu"a cikinsu ransu fita sukayi Daman sunyi Alwalarsu sun Fito da Niyar tafiya Masallaci ne labarin wani Hari da yan kiddaping suka kai kauyan Zamfara yaja Hankalinsu. Sun Fita ba Dadewa Imran ma ya fito Bayan ya saka Jallabiya ya Nufi Masallacin Zuciyarsa sai Zafi take yi maimakon yaji sanyi Tunda wacce yake jiran da neman ganin ta Dawo sai dai ta sabamai alkawari Shiyasa yaji bama yasan ganinta. Tasan Wahalar Daya sha Saboda rashin ganinta..? Tunda Lokacin komawarsu makaranta yayi yake Duban Hanya saboda ita a Shagon Sagir yake wuni ko zai ga Dawowarmata ammh Shuru Sai ranar yaji Munari na Fadin ba Satin zata Dawo ba Tundaga Ranar yaji Ransa ya gama baci ya tsani ayi mai alkawari a kasa cikamai baisan Dalili ba Yaji baya son ganinta kwatakwata Duk da kuwa yadda Zuciyarsa ta azalzalu da son ganinta din. Suna Dawowa masallaci Munari ta Shirya tatafi Gidan su Sagir chan suka Hade Inteesar da sai Murna chan ta Shantare sai bayan mganariba Inteesar ta Rakota dauke da Sakon Umma Munari nata Godiya suka rabu kan sai gobe da safe Munari zata Biyo ma Inteesar su shiga makaranta. *Shakira...* 3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *🅿�27* Washegari Monday tun Karfe 7:40am Munari ta biyo ma Inteesar suka Shiga makaranta basu jira Ya yusuf ba Tunda shi sai 8am zai fita BUK old Site suka nufa anan suke lectures dinsu a wannan Zangon karatun na Biyu,Zangon karatunsu na farko Gabadaya sun yishi ne a New site,sai jifa Jifa suna shiga Old site din yin wani lectures din. Sai 5pm na yammah suka Dawo gida Daga bakin Titi mai adaidaita ya ijiyesu suka Tako da Kafarsu zuwa Cikin anguwa Inteesar ce ta Roki Munari ta shigo Ta diban mata Dambun nama da kayan Snaks din Data zo dashi Munari bata da yadda zatayi Dole ta bita suka Shiga gidan Tare ta gaida Mama kafin su Shiga Ciki,Bata wani Dade ba Saboda mangariba ta kawo jiki Abinci sukaci Tuwon Shinkafa Miyar Zogale Mama tayi Sai Inteesar ta Diban mata Dambun naman da yawa dasu Samosan da Cincin da Springrool,da Donot Tace ita dasu Abba Munari ta rasa bakin godiya Domin alkharin Inteesar gareta mai fadi ne haka Jiya Data nuna ma Abba kaya yana ta Saka albarka,Basu baro gidan ba sai da Inteesar ta kira ma Munari Umma suka gaisa Tayi mata godiya. Da inteesar taje raka Munari ta mtsamata sai da ta shiga suka gaisa da Abba da Anty Safiya Ta nuna musu Abunda ta kara bata Abba nata Saka mata albarka Har taji kunya,Itama bata Zauna ba tayi musu Sallama Zata tafi ta Fito Falon kenan Munari ta Rakota taga Imran zaune gefen Abba Yana mai mgana ya kauda kai yana kallon wani gefe Daga alamun dai Fada Abba kemai Shiyasa Fuskarnan ba Annuri.. Lokacin Dayaji Muryanta sai da gabansa ya amsa haka Itama Tana ganinsa taji wani Sanyi ya Shigeta acikin Jikinta Lokaci Daya Duk yadda yaso kada ya Dago ya Kalleta ya kasa sai da Zuciyarsa ta Rinjayi gangar Jikinsa ya Dago yana kallonta Daidai Lokacin itama Shi take kallo,Yanzu adakin Munari ta gama Tambayansa Munari tace ita duk yau bata gansa ba yana Dakinsa sai gashi sun hadu. Lokacin da suka Hada ido sai yaji kamar Zuciyarsa tayi Tsalle waje Daya ta Daina aiki Da Sauri ya kauda kai ya Hade rai Yana wani Dakuna Fuska ganin shi yasa Munari ta fasa Rakon da Zatayi ma Inteesar zuwa Haraban Gidan. Ita kuma Inteesar sai ta kallesa kafin tace"Ina yini Ya Imran..! Haka muryanta a bazata cikin Sanyinta akoda yaushe yi yayi kamar bai jita ba,Sai da Abba yace mai bai ji ana gaisheshi bane kana ya amsa yana wani Tattare giransa Waje Daya..ita dai bata bi ta kansa ba Tayi ma Abba Sallama Daganan suka Rabu da Munari duk da daman ta san Munari ta na matukar Tsorom Imran kamar Ranta bazatayi wani kwakwaran Motsi agabansa ba.. Duk da yana Fushi da ita kan taki cika alkwarin datayi mai bai Fasa ganin ta Rame ba,Kuma Zuciyarsa bata Fasa jin Dadin ganinta ba,muryanta kuwa Dayaji kamar wani Waraka ne Daga Garesa haka yake jin kansa ya rasa gane Meke Damunsa Ballatana ya Dora hakan kan wani Mizani. Cikin Satin kaf su Inteesar basu samu Zama ba Saboda Karatu kullum in suka Shiga makaranta sai yammah Suke dawowa,Saboda sun Fara Karatu ne Gadan gadan ba zama Ga kuma assigment da suketayi akwai wadanda aka bada lokacin basu Dawo ba Shiyasa basu da Lokacin kansu sam. Ranar jumma"a Karfe 7:30am suke da Lecture tun 7:20am Inteesar ta gama Shiryawa ta Fito kofar gida Tana Jiran Munari sun yi mgana tace mata gatanan Fitowa Tana Sanye cikin Doguwar riga atamfa Gold,mai kalan Brown sai da ta saka Karamin mayafinta Sikiws,sai bakar jaka da Bakin Takalminta mai dan Dudu sai wasu littafai a hannunta. Sakamakon Lokacin yayi Safe ne da yawa ba Mutane sosai sai Daidai ku ne ke Wucewa sai yara masu Haraman zuwa makaranta. Tana nan Zaune Tana kallon Shashen da Munari Zata bullo Lokaci Daya Tana Kuma Duba agogon Fatan Dake Hannunta na kamfanin gucci. Sai dai me..? Maimaikon Taga Munari sai taga yayan Munari yana Tahowa Cikin Kayan jugging Riga da karamin Wando duka Farare,sai Takalmin Kafarsa Booth shima Fari ne Tafe yake yana Jogging a Hankali ko'ina na Jikinsa na amsawa gabadaya Muscles dinsa sun bayyana alamun Karfi da Mazantaka. Inteesar tunda ga Nesa ta Kuramai ido bata san ta Shagala da kallonsa ba,bata son haka yake da kyau da Zati ba Shan taba bai dace da Kamili mai Daraja irinsa ba,bakinta ta Saki da Hanci Tana kallonsa batare Datasan me take yi ba Shi kuma Tundaga nesa Daman ya Hangeta sai yayi kamar bai ganta ba sai dai Kallonta Datake Binsa Dashi ne yasa ya kasa Wuceta sai kuma Karamin gyalen Dake jikinta Haka kurum yaji Haushin yadda Zata Tafi makaranta Cikin Duban maza da wannan mayafin da bai Rufe mata jiki ba,,Har ya Tsaya sai wata Zuciya tace menene naka..? Sai kawai ya Kada kai ya wuce Kuma sai ya kasa Zuciyarsa sai ta Fara Zafi da kuna wanda yasa ya Juyo zuwa gareta batare da wani Tunani ba.... Shagalan Datayi da kallonsa yasa bata san ma yazo gabanta ba,Sai dai kawai taji Hucin Numfashinsa agabanta Da Sauri taja baya Tana Rarraba ido Binta yake da kallo Daga Sama Har kasa Bakinta ma yayi Nauyi ta kasa mai mgana sai kallon Zufar Goshiinsa Take wanda ke gangarowa zuwa saman Fuskarsa. Sai da ya Kalleta ido Cikin ido kafin yace"Koma ki Cire wannan Mayafin ki Sako Hijabi..! Yafada kai tsaye cikin bata Umarni a karkashin Zuciyarsa kuma yana Fadin ko bakomai kamar kanwa take gareni Tunda Kanwar Sagir ne,Zai kula da ita kamar yadda zai kula da Tarbiyan Munari duk da ta batamai rai ta yi mai alkawari kuma ta Sabamai. Ita kuwa mamakin kalamansa Taji,sai dai kuma Kaifin Idanuwansa yasa bazata iyamai Musu ba Sai ta Rausayar dakai tana fadin"Ban fa da kalan Hijabin nan..! Tafada Tana nuna mai Kalan Brown din Dake jikin Atamfan,Dan Hade rai yayi kafin yadan Mtsa baya yana fadin"bai zama Dole in an bani Umarni nabi..Ammh ya Zama Dole in na bada Umarni ni abi..! Yafada kai tsaye Cikin Dakewarsa Bata isa ta kara cewa wani abu ba,Ganin yadda Girman Jikinsa duk ya Babbage ko"ina sai kawai ta Juya ta koma Cikin Gida yana Bin kowani Takunta da kallo Zuciyarsa na amsawa. Sai dai Mama ta ganta ta Dawo Data Tambayeta sai tace Zata Sauya Mayafi ne,Wani Farin Hijabinta ta Dauko ta Sakamai hannu wanda iyakarsa Gwiwanta,Ta sagala Hannun ta Dauko Jakarta da Littafanta ta sake yi ma Mama Sallama ta Fice. Yana nan Tsaye inda ta barsa Tana Fitowa Kaifin Idanuwansa yasa ta Fara Jin kamar Zata Harde Jikinta Duk sai ya Fara sanyi bata iya Jure Kallon nan nashi,Kanta na kasa ta Kariso gabansa Kafin tace"Kagani..! Na chanzo..! Tafada Cikin Shagwababbiyar Murya,bai ce mata komai ba ganin Munari Tana Tahowa kawai sai ya Kada kai yayi gaba abinsa Inteesar ta Bita da kallo har ya bace ma ganinta afili ta Furta"Komai nashi na Dabam ne..! Daidai Lokacin Munari ta iso Wajen Cikin mamaki take kallon Inda Imran ya bi ya wuce ta Kalli Inteesar Tana Fadin"Kamar Ya Imran na gani..? Inteesar ta Kalli Munari kafin ta Waske mganar tana Fadin"A ina..? Munari tace"Tsaye anan wajen kuna mgana ko bashi bane..? Da Sauri Inteesar tace"Anya..? Baki lura badai..Wani dai ya wuce ta nan wajen ammh ba shi bane..! Munari tayi Shuru tana Tunanin itafa Taga wani kamar Ya Imran,sai dai kuma Inteesar tace bashi bane,Ganin kamar Ta shiga Nazari ne yasa Inteeasr ta Duba agogon Hannunta Tana Fadin"Muje kin Sakamu makara..In kuma zaki zauna Dogon Nazarin ki ne shikenan..! Munari ta Sauke Numfashi kafin tace"Shikenan Muje..! Daga haka Suka bar mganar suka Fara Takawa zuwa Bakin titi Domin su Samu adaidaita sun kai Titin kenan suna Jiran abun hawa sai ga Ya Yusuf yazo da mota zai tafi Wajen aiki ya Daukesu zuwa Makaranta sai da ya ijiyesu har cikin makaranta kana yayi Kwana ya Dauki Hanyar ma'aikatan su. Basu samu zama ba sai da weekend ta Zagayo,Ranar asabar suna gida Inteesar sunyi mgana da Ya Sadam kan in ta Shirya tamai mgana zai zo ya Dauketa saboda tafi Saurin gane gidan to tayi ma Munari Mgana Kan Zata Rakata ayau din Har Abba ta Tambaya ya barsu sai kuma Bayan ta Shirya Tana jiran Munari Ya Sadam din ya Kirata yace wani Emergency ya taso mai zai shiga cikin asibitin ko Zata Bari sai gobe ne ko kuma da yammah in ya gama abunda yake yi acikin asibitin sai yazo ya Dauketa sai ta kwana agidan sa Gobe sai ya Dawo da ita. Ganin bata Shirya kwana ba kuma bata Gayama Mama ba,sai tace mai kawai ya bari sai gobe sai yazo ya Dauketa Da haka suka Rabu ganin haka yasa tace Ma mama bari ta je gidan su Munari tunda sun fasa Tafiyar sai gobe Mama tace sai ta Dawo Tana Fita suka Hade da Sagir ya Dawo Daga kasuwa ya siyo kayan Dinki Zai shiga tamai sannu da zuwa ya amsa yana Tambayanta ina Zata tace Gidansu Munari yace ta gaida su. Daganan suka Rabu shi ya Shiga gida ita kuma ta kama Hanyar Gidansu Munari. Yana Zaune Saman Motan Yusuf ya Dauko karan Sigari acikin Aljihun wandonsa ya sakata abaki ya Dauko Lether ya kunnata kenan Yana Shirin Maida Lether, Aljihun wandonsa yaji an Dauke Taban Dake Bakinsa Da Sauri ya ware idanuwansa akanta Cikin Mamakin ganinta Domin bai ga Shigowarta ba kuma yana dan jima awajen,Ya fito ya Busa Hayakinsa ne Saboda Abba ya Hanashi shan Taba,Shi kuma bazai iya bari ba sannan baya so ya zama Sillar Sabama Abba Shiyasa ya koyi shanta aboye. Duk da ya Rage shanta ba kamar baya ba Daya maida ita cinsa da shansa ba Batare da yayi mata mgana ba ya mika mata Hannun alamun ta bashi Noke Hannunta Tayi Da kafadarta Lokaci Daya.! Waro mata ido yayi Lokaci Daya Yana Mamakin Karfin Halinta Dakyar ya Bude baki yace mata"Bani..! Kawai ya iya Fada Cikin Dakewa.. Kara Nokemai kafada Tayi alamun A"a Dan Dakuna Fuska yayi acikin Ransa yana Fadin yarinyar nan akwai Shagwaba. Saukowa yayi Daga kan Motan wanda yasa Inteesar tayi baya Da Sauri Tana Fadin"Plz kada ka Dakeni..ga abunka..! Ta fada tana Mikamai Cikin Tsoro wanda ya bayyana acikin Idanuwanta. Sai yaki karba ya gyara Tsayuwa Lokaci Daya yana Saka Duka Hannuwansa Cikin Aljihun Bakin Wandon Dake jikinsa yace"Bazan karba sai kin Fadamin meyasa kika karba Daga Farko..? Kuma yanzu kina so ki bani..? Bayan da farko nace ki bani kince A"a..! Narai narai tayi da ido kafin tace"To bakai bane naga kamar Zaka Dukeni ba..? Sai da Mirmishi ya Subuce Cikin Kaushin Muryansa yace"Kawai sai na Dake ki..?Me kikamin...? Aini bana Duka Haka kurum sai mutum ya batamin rai ya kuma Shiga Hurumina..! Gyada kai tayi Tsoron ya Saketa Kafin ta Sauke ajiyar Zuciya tace"Ai kamin alkawarin ka daina sha ko..? Meyasa ka Saba..? Kai Tsaye yace mata"Ni ban miki alkwari ba..Saboda nasan zan Saba miki. ni kuma bana Daga cikin mutanen Dake saba alkawari..Ina Matukar girmama alkawari sannan kuma bana Shiri da wanda bai daraja Girman Alkawari..! Yafada yana kallonta ido Cikin ido Da Sauri ta Janye idanuwanta Kafin tace"Kana Jin Haushina Saboda na Saba maka alkawari ko..? Daga Kafadarsa yayi kafin yace"Kinsani kema..! Kanta na kasa Tace"Naso na dawo..Sai dai bani da Lafiya koda na koma Gida Hutun Ciwo nayi..! Kura mata ido yayi kafin yace"Shiyasa kika Rame..? Da mamaki ta Kallesan kafin tace"Daman na Rame ne..? Cikin idonta ya kallah kafin yace"Eh..Ciwon me kikayi..?kuma meyasa baki gayamin ba..! Sai da ya fadi hakane sai yaji kuma Mai ya kaisa cewa haka..? Itama cikin Mamakinsa tace"Maleria ce Sauron kano ne da suka Cijeni..Kuma ai bansan ta ina Zan fada maka ba Sai dai Munari tasani dasu Abba.Lokacin ina asibiti ta Kirani muka gaisa da Abba ya gaisheni..! Da sauri yace"Asibiti..? Kai ta gyada mai kafin tace"Eh kwana na Shida a asibiti kafin na Dawo gida..Naso na dawo sai Daddy yace na Zauna sai na kara Warwarewa..! Kallonta kawai yake yi yana jin Zafin Ciwon datayi baisan sadda yace"Kin ji Zafin Allura..?kinyi kuka..?nasan ki da Shagwaba..! Yar dariya tayi kafin tace"Eh mana nayi ta kuka Daddy ne mai lallashina Umma Tayi ta fadan wai na cika Rangwanta..! Imran ya Kalleta afili ya Furta"Eh mana ke raguwa ce..! Ido ta waro kafin tace"Ni..? Bai mata mgana ba inda ya Tashi ya koma ya Hau kafin ya zaro Wata karan Sigarin yana Fadin"Tafi ki barni..Kada kice zakiman amai..! Daga haka ya saka Lether ya kunna abarsa Inteesar sai ta Tsaya tana Binsa da kallo Lokaci Daya tana kallon Karan Sigarin Dake hannunta kai kawai ta Kada kafin ta juya Ta nufi Cikin Gidan gaskiyansa ne Zuciyarta har ya fara tashi,Kada tayi mai amai kamar yadda yace. Acikin Fulawoyin Dake Haraban Gidan ta Cillar da Taban kafin ta Shiga Cikin Falon. Dukkansu suna Falon Sun gama Cin Abinci ne suke Zaune suna kallo suna Hira Abba ke kusa da Ya Yusuf suna mganarsu kasa kasa Anty Safiya da Munari suna Gefe suna kallon Tashar Mbc2,Munari ta shirya Domin taci Gayunta tana ganin Shigowar Inteesar ta mike Tana Dariya Haranta Tayi kafin ta Duka tana gaida Abba da Ya Yusuf. Abba ya amsa mata yana Fadin"Mamana..Har kin gaji kin biyo kawar naki yanzi nake cemata ba yau kika ce min Zata rakaki gidan yayan naki ba take zaune..Tacemin yanzu zata tashi Sai gaki kin shigo..! Inteesar ta kalli Munari wacce ke Dariya Tana Fadin"Kyaleta Abba..Ai ma mun fasa tafiyan sai gobe..! Abba yace"To..Allah yasa Lafiya dai..? Inteesar tace"Lafiya lau Abba..YaSadam din da zai zo ya Daukemu Tunda banta zuwa Gidan ba Ya kirani Aiki ya tasomai a asibiti Shine kawai nace ya bari sai gobe..! Abba yace"Eh hakane sai goben kuje da Wuri yadda zaku yi musu Wuni..! Inteesar tace"Insha Allahu Abba..! Daga haka ta Mike kusa da Anty Safiya ta Karisa suka gaisa Tana Tambayanta Tasleem. Anty Safiya tace tana gidan Anty Saratu ammh tace mata ta nan zuwa Tunda yanzu jarabawa zata zana na Fita,ba sosai take zuwa makaranta ba. Nan Inteesar ta zauna suna Hiransu suna Kallo Sama Sama Abba kuma suna Gefe da Ya yusuf suna mganarsu Duk akan samun Lafiyar Abba ne Domin Lokacin da sukaje asibitin da Abba an yi mai gwaje gwaje kuma Alhamdulillah komai Normal Likita ya Tabbatar da Samun Lafiyar Abba, hakan wani karin abun Farimciki ne Duk mganar Abba na Shiryann su Tafiya Dukku ne Yusuf yace ya bashi Lokaci ya Dauki Excuse a wajen aiki koda na Sati Daya ne sai su Shirya Tafiya Zuwa Lokacin itama Munari tayi Covering din Semester ta Kada su Tafi ta dawo ta samu wata mtsala kuma ba yadda zasu iya tafiya su barta. Suna nan Zaune sai ga Imran ya Shigo zai wuce Dakinsa Abba ya Saka baki ya Kirashi ya Juyo yazo ya Durkusa gaban Abba,ta gefen ido yake Satan kallon Inteesar yana Fatan kada Abba ya mai Dizgi gaban yaran nan. Sama da kasa Abba ya Kallesa Kafin yace"Kaje ka sha Sigarin kenan..?.ga mamakin Inteesar ta zata zai yi Karya ne sai taji yace"Eh Abba....! Zaro ido Tayi tana kallonsa Abba ya Girgiza kai yana Fadin"Yayi maka kyau..! Cikin Sadda kai yace"Saboda bana so in sha kagani ne Ranka ya baci..Am Sorry Abba..! Daga haka ya Mike ya wuce saboda baya so mganar tafi haka,Baya son Rainin yara Yana Kallon Inteesar ta gefen ido Tana kallonsa. Da kallo suka bisa dashi Har ya Shige Daki,Abba ya Girgiza kai kafin yace"Bazai taba maka karya ba ko da Kashe shi zaka yi..!. Yusuf yace"Daya daga cikin Tsautsauran Ra"ayinsa kenan Abba..! Abba ya gyada kai kafin yace"Allah ya Shiryesa..! Ya amsa da Ameen Inteesar Dake gefe aranta Tana ayyana bata Taba ganin Mutun irin Imran ba komai nashi Dabam ne. Kiran Sallar La"asar ya tadasu Daga Falon su Abba sukayi alwala suka Fice zuwa Masallaci Anty Safiya ta Shige Shashenta Ita kuma Munari da Inteesar suka nufi Dakinta sukayi Salla suka Cigaba da Hira Rabinta duk na Karatu ne. Suna cikin hakane Hafsah ta Kira Inteesar suka gaisa,ta bama Anty Faree itama suka gaisa kana Hafsah ta kara Karba Tana Tambayan Inteesar meyasa bata mgana a Famiy Group..? Inteesar tace haka kurum Hafsah tace ko Zasu Bude nasu isu isu Yan"mata..? Inteesar tacemata Shikenan daga haka sukayi sallama.. Bayan sun gama wayar ne Munari ke Tambayanta take gayamata Munari sai taji Tsausayin kansu aranta Tana Tunanin da itama Yau tana cikin Dangin da yan"uwa kanar Inteesar ganin Kamar munarin Fuskarta ta Sauya ne yasa Inteesar ta Tambayeta ko Lafiya..? Munari tayi Saurin Waskewa Tana Cemata bakmai ita kuma bata matsa mata sai taji ko menene ba,sai dai ita duk atunaninta Yan"uwansu Munari basa nan garin suna chan garinsu ne shiyasa bata taba Damuwa ta Tambayeta ba. Inteesar nan ta shantake Munari na bata Labarin Tayi wani Saurayi a Sahad Store Ranar data Raka Anty Safiya da Ya Yusuf siyayyah ya nace nata sai da ta bashi Lambarta Yayi ta Damunta da kira da mgana ta Chart Munari ta nuna ma Inteesar Hotonsa tana mata Dariyan Budurwan gajere Tunda gajere ne Munari na jin Haushi Tana Kai mata Dundu..! Basu an kara ba sai da Anty Safiya ta Leko tana fada musu ana Kiran sallar mangriba,Suka Mike cike da mamaki,suka Dauro alwala suka zo sukayi Sallah kana Inteesar tayi Shirin Tafiya Munari ta Rakota. Sun kawo Haraban gidan sai ga Abba da Ya yusuf sun dawo Daga Masallaci Abba nata Fadan meyasa tabari Dare yayi mata yace tayi Sauri ta koma Gida Munari bata yi nisa ba Inteesar tace mata ta koma sai gobe zata Karisa Sukayi sallama Ta koma ita kuma Inteesar ta cigaba da Tafiya Ganin akwai Duhu Lokacin Wata bata Raba ba kuma yanayi ne ya Sauya ana mganriba Duhu ke shiga sai ta Fiddo Wayarta Tana Haskawa. Wasu maza biyu ne dake Biye da ita Tunda suka Rabu da Munari irin yan iskan Gari ne masu kwacen waya Tunda suka ganta ta Fito da waya suka Fara Bin Bayanta Dayake Hanyar bata da yawann Mutane ba wanda ya Lura dasu,ga kuma Mangariba tayi Kowa yayi Salla ya shige gida. Bata san suna Binta ba sai Daga baya Dataji Takun Sawunsu Daga bayanta Tana waigawa sai suka Tsaya Tundaga Lokacin sai Tsoro ya kamata bata yarda Dasu ba ta Fara Sauri sai da suka ga Hanyar ba kowa kana suka Fara Sauri suna so su cin mata ganin haka yasa Inteesar ta Fara gudu batayi nisa ba Daya yasha gabanta Dayan kuma yana Bayanta. Gabadaya Inteesar ta Tsure Jikinta Sai rawa yake abunga gamai Tsoro tsayawa Tayi tana kamkame jikinta Cikin Muryan Tsoro tace"Su waye ku..? Lafiya kuke bina..? Tafada Hawaye na cikamata Kwarmin ido... Dayan ne wanda yasha gabanta ya Kece da Dariya kafin ya Mikamata Hannu yana fadin"Ba Dole bane kinsan ko suwa ye mu..? Ki bamu wayar Dake hannunki Salim Alim..Sai mu Rabu Lafiya in kuma kin ki..! Ya fada yana nuna ta da Hannu kafin ya kara Sakawa Dariya na Bayan ne ya zuro Hannu zai karbi Wayar Inteesar ta Tsorata Ta kamkame jikinta da wayarta ta Fashe da kuka Tana fadin"don Allah ku kyaleni..Wayarnan wayatace bata ku bace..! Tafada Tana waigen waigen ko Allah Zai kawo wani sai dai ba kowa.. Na gaban ne yace"Jika aiki Taurin kai Zata nuna mana jika mata aiki..!Hannu ya Daga Daga gefen Wandonsa ya Zaro Wuka Inteesar na ganin Wukan ta Kara Tsoracewa ta Zaro ido ba Inda Jikinta bai Rawa Cikin Rawan jiki Tana kuka Ta mikamusu wayar Tana Fadin"Ga..Gashi...Don...Allh kada ku tabani..! Take Fada take gabadaya Zufa ya gama wankemata Hijabin Dake jikinta. Dariya suka kwashe dashi a tare kafin na gaban ya karbi Wayar yana Juyata yace"Kin san da hakane kika faramana gaddama..? Jika aiki bata Mari koda guda uku ne ladan batamana Lokacin Datayi..! Bai gama mgana ba ya Daga hannu Zai wanke Inteesar da mari wacce Har ta Runtse ido Tana makyarkyata tsoro Taji shuru Lokaci Daya Da tsayawan Wata inuwa agabanta Da Sauri ta Bude idanuwanta Duk da Bayansa Tagani jikinta da yadda Zuciyarta ta amsa ya Tabbatar mata da Imran ne Bayan sun idar da Sallah ya Tsaya Kofar Shagon Sagir suna mgana Duk da Hirar duk Sagir keyinta sai dai gabadaya Zuciyarsa ta kasa Natsuwa yana jin Wani abu na Faruwa Domin gabansa ne ke Bugawa Fat..! Fat! Wanda ya Rasa Dalili ganin haka yasa kawai yama Sagir Sallama ya biyo Hanya Tunda Daga nesa ya Hangosu,Da fitilan Wayarsa yayi amfani ya Haska kasa Da Zai wuce sun Shagala da aikata barnan su basu lura dashi ba. Zuciyarsa ta kusa Bugawa Daya Fahimci Inteesar ce Maza Biyu suka Zagayeta Daya na Shirin kaimata Duka Cikin Zafin nama ya Dira gabansu Lokaci Daya yana Rike Hannun wanda zai kaimata Dukam Cikin Bacin rai da Zafin Zuciya. Cikin mamaki suke Binsa da kallo na Gaban ne yace"Mallam lafiya..? Kada ka shiga abunda ba ruwanka ka barmu muyi aikinmu mu gama in ba so kake yanzu Jikin ka yayi Lahani ba..! Bai ma tsaya Sauraransa ba ya yarfar da Hannunsa Cikin Fushi wanda sai da ya Ja baya kamar zai fadi cikin mamaki suka Dago suna kara Kallonsa. Inteesar Data ga haka cikin Sauri ta Taso ta Rumgume Imran ta baya tana Mkarkyartan Tsoro da kuka Tana Fadin"Ya Imran sun karbemun waya..Sun fito da wuka zasu kasheni..! Gabaadaya ta Rukumkumesa Kukanta kuwa ji yake kamar wani Dalma na Shiga Cikin kwakwalwarsa. Ransa na baci Zuciyarsa na Zafi kamar Zata kama da Wuta Jijiyoyin kansa sun tashi Radau. Mai Wukan ne yace"kai jika aikin zaka Ma haka..?lalle ka kira Ajalinka yau..! Yafada Lokaci Daya yana Ciro wuka dake jikinsa ya Nufi Imran da ita yana zuwa ya daga zai Chakamai ya Damke hannunsa da Karfi Har sai da Wukar ta Fadi kasa ya murde hanun ka ya Saka Gwiwan kafarsa ya Daki bayansa sai da ya Fadi kasa,Dayan na ganin haka ya ja baya Cikin mamaki. Imran ya Mika masa Hannu yana Fadin"Bani Wayar da ka amsa..! Cikin Kaushin murya Tsoro ya kamashi ammh ya Dake yana Fadin"Wata Waya kuma mallam..!kai Waye..? Imran ya kara Mikamasa Hannu yana Fadin"Bani nace..Kada ka bari na Sake maimaita mganata bazaka ji da dadi ba.Kuma ni ba wanda ya isa yamin Tambaya sai dai ni na isa nayi Tambaya kuma Dole abani amsataaa .! Ya karishe Fada Cikin Tsawan da gayen da Sauri ya mikamasa Wayar yana Fadin"Baba mu gudu..Ina jin Soja ne..! Yana fadamin haka ya taketa Shima Wanda aka Daka din ya Mike nan yabar wukar nashi yabi bayan Dan"uwansa suka Ari na kare basu Tsaya ba sai da suka bar Layin.. Ajiyar Zuciya ya Sauke ganin sun Tafi ita kuwa Inteesar kuka Kadai Take yi Tana kamkame dashi Tsoro ya Riga ya kamata.. Dan Raba jikinsu yayi Saboda Gabadaya wani Iri yake jin kansa Ammh taki sakinsa sai ma kara Rikesa datake yi Tana Shasshekan kuka Ganin bata cikin Natsuwarta yasa ya Saka Hannunsa Guda Daya ya Dafa kanta yana Fadin"Shiii...Sun tafi fa..! Yake fada yana dan Buga kanta alamun Lallashi. Sai da yaji ta dawo cikin Natsuwarta ta Daina kuka ta koma ajiyar Zuciya. Kana ya Dagota yana kallonta Fuskarta Tayi kace kace da Hawaye da Majina..Cikin Kaushin murya yace"Me yasa kika kai Dare..?baki da Hankali ne..?yanzu da ban zo ba Allah kadai yasan me xasu yi miki..? Ila ma su Illataki..! Yafada cikin Tsawa da Takaichi yana jin Zafi acikin Ransa yana auna da Wani abu ya sameta vaisan yadda Zai yi ba. Kuka ta kara sakamai tana Rike da Hannunsa tana Fadin"Wlh bansani ba..bansani bane..! Take fada kamar ranta Zai fita ganin Mutane sun fara wucewa suna Kallonsu ne yasa yace"Naji is ok..Share Hawayenki ki wuce kije gida..! Yafada yana Mika mata Hanky din Dake Hannunsa tana Kallonsa ta Karba ta Goge Hawayenta ta mikamai ya girgizamata kai Lokaci Daya ya Mikamata Wayarta yana Fadin"Ga wayarki..! Karba Tayi hannunta na rawa tana Waigo Waigo ganin haka yasa yace mata"muje ko..! Tafiya ta farayi tana Waige waige Cikin Tsoro ganin yana Binta abaya ne yasa Taji dan Sanyi suna cikin Tafiya Ledan Pure water da aka sha aka wurgar iska ya kadasa ya Hau kafarta ta Saka ihu ta Dawo baya ta Rirrike Imran cikin Tsoro. Kallonta yayi yana Fadin"Ki bar rike in ba Haka ba zan koma na barki ke kadai..! Tana jin haka ta sake shi ammh taki sakin hannunsa Cikin mamaki yace"Leave my Hand..! Tana shan majina tace"Don Allah ka barni na rike..Ina jin tsoro ne kamar Zan mutu..! Take fada Tana tsiyayan kwallah sai ta bashi Tsaiusayi bai kara mgana ba Har suka zo kofar gidan har Zaure ya Rakata Kafin ya Kalli Hannunsa yadda ta kamkame yace"To sakeni ki shiga gida..! Sai alokacin ta Sakeshi kwallah na Zubomata tace"Tanque so much For Saving my Life Ya Imra..Nagode..! Tafada Tana kuka kai ya Girgizamata kafin yace"Bana son kuka nan..Ki share Hawayenki ki shiga gida..Kada ki Fadama kowa abunda ya Faru kin ji ko.? Kamar yadda yace haka tayi Tana Share Hawayenta tana Dagamai kai kafin ta Fara Tafiya zuwa Cikin Gidan Tama yi tana Waigensa Har ta shige sai da yaga Shigarta kana ya Juya yabi hanyar gida cike da Tunane tunane Inteesar Allah ya Taimaketa Mama na Bayi shiyasa ta Lallabata ta shige kurya ta Haye gado ta Dunkule tana kuka Data Runtse ido Wukanan take gani Gabadaya Taakasa Natsuwa sai kuka Takeyi dataji motsin mama ne sai ta yi Shuru ta koma Ta Lafe. *Shakira..* 3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *🅿�28* Shigowar Mama cikin dakin yasa Inteesar ta kara nokewa kamar tayi barci ganin yanayin kwanciyar nata ne yasa Mama ta kalleta tana Fadin"Inteesar lafiya kuwa..? Yaushe kika shigo.? Bata da yadda zatayi Dole tayi saurin goge Fuskarta ta Dago kanta Lokaci Daya da mikewa Zaune tana Fadin"Yanzu na shigo kina Bayi Mama..! Mama tace"Eh ammh Lafiya naganki wani iri..? Tafada Tana kallon Kwayan idanuwanta da Sauri tace"Bakomai Mama ina tafiya a Hanyane wani karo ya Shigarmin ido ammh ya fita..! Mama tace"Ayyah hala mai Shegen yajinan Ido yayi ta Hawaye..Sannu in bai bari ba ina da wani mganin ciwon ido sai na Diga miki..! Inteesar ta gyada kai Ita kuma Mana ta Nufi kwabarta ta Dauko hajibi ta Tada Salla bayan ta Shimfida Darduma Komawa Inteesar tayi ta Kwanta Lokaci Daya tana kamkame Kirjinta da Hannayenta,Tsoron ya Fara Sakinta sai dai yanayin Data Rumgume Imran yaki barin Tunaninta Data Runtse ido Shi take gani,Jikinta yana amsawa ko"ina ya Saki Kasala ya kamata. Lumshe idanuwanta Tayi kamar mai barci nan kuwa ba barci take ba Fuskar Imran ke Gitta mata Cikin kowani yanayinsa,ba domin yau ya Ceceta ba kila da sai Buzunta ammh ya Sadaukar da Rayuwarsa saboda ita Bazata taba mantawa dashi ba. Ta tuna sanda ta Rikeshi da cewar da yayi ta sakeshi,da yanayin kallonsa Sai da Tsigar jikinta tatashi afili sai da ta Murmusa ta Furta"He is so nice..Yana da Kirki sai dai kirkinsa Boyayye ne bakowa ke sanin haka ba..! Tafada tana jin wani nishadi acikin ranta tama manta da Mama acikin Dakin sai da ta juyo tana Fadin mgana kike ne Inteesar. ? Kana ta tadawo Cikin Hayyacinta tace A"a Mikewa Tayi Daga kan gadon bayan ta Sauko a kasalance ta Fita zuwa Kitchen ta Duba Flaks taga ba ruwa sai ta kunna Gas ta saka So take yi tayi wanka ko taji Dadin jikinta. Kan kujeran Tsugguno ta Zauna acikin Kitchen din Ta Zafga Tagumi Tana Tunanin Abunda ya Faru awanni kadan da suka Gabata Tsoro duk ya cikata ammh da Ta tuna Imran sai taji wani irin Sanyi aranta. Ya nemi alfarman kada ta Fadama kowa kuma tayi mai wannan alfarman bawanda zai ji koda Daddy ne,sai dai tana ganin kamar Godiyar Datayimai yayi kadan ya kamata ta Fara Tunamin Hanyar da Zata kara Godiya Saboda yadda ya Ceceta Daga Mutuwa. Sai da Ruwan ya tafasa ta Diba sauran ta Juye a Flaks,ta Dauka takai Tiolet ta saka Ruwan sanyi ta surka Daidai tayi wanka Dashi,Bayan ta gama ta Dauro alwala ta Fito ta shafa Lotion dinta ta saka Kayan barcinta Riga da wando masu Ruwan madara masu Taushi, Lokacin ana ta Kiran Sallar Isha"i a wasu maaallatan sai ta Shinfida Darduma ta Tada salla,ta idar kenan Lokacin Mama na Falo Kiran Umma ya Shigo wayarta Daman tana kan gado ta jawota ta Daga suka gaisa Ta Tambayeta Daddy tace bai riga ya Shigo ba bayan Tambayan Karatu sai ta bama mama Wayar daman ita Ummn ke nema bai wuce kan mganar Bikin Yar wajen Kawu bala Domin yazo tana ma Tunanin wannan Satin ne Anty Jamila,Inteesar suna Chart Sama sama suna gaisawa ba Sa"arta su bane ta Girmesu sosai ita da Nasara da ace Tana kaduna ne Zataje Bikin ammh yanzu kam datake Makaranta sai dai in sun samu Hutu ta koma suje suga Daki ita Nasara Tunda nan cikin Kaduna Zata zauna.. Mama da Umma sun Dade suna mgana suka rabu kan Maman Zata taho Kaduna Tun Ranar alhamis sai kuma Bayan Biki in Allah ya yarda da Zata dawo,bayan sun gama Wayar Umma ke fadama inteesar wacce ta Hada Complex tana sha Inteesar ta bata Fuska wai bazata iya Zama ita Kadai ba.. Mama tace ba Damuwa in bazata iya ba sai ta koma Gidan su Munari har ta dawo Sagir ne kuma Tana Tunanin Shima Ranat asabar zai shigo Kaduna Daurin auran sai ya Jirata su dawo Tare Sai da Inteesar taji haka kana Hankalinta ya kwanta. Da wuri ta kwanta Saboda bata Cikin Natsuwarta ta Dade barci bai kwasheta ba Tana Tunanin Abunda ya Faru kuma koda barcin ya kwasheta Cike da mafarkinsa Kala kala Abun har ya soma bata mamaki. Da safe har ta ma manta da Zencen zuwa Gidan Ya Sadam wayar sa ya tasheta Daga Barci yace ta shirya zai Shiga asibiti in yagama abunda yake yi Zai Taho ya Dauketa Dole ta Mike ta yi Sharan Daki ta gyara ta wanke Tiolet ta gyara Tsakar gida,Mama kuma ta gama Abun Karyawa kunu da kosai sa ta sha kunun da Buredi ita,kana ta Juye ruwan Zafin da Mama ta Cika Flaks dashi tayi wanka Bayan ta Fito ne ta Dokama Munari kira Lokacin ma barci take bata tashi ba Sai da ta mata Kira Biyu ana ukun ne ta Dauka Tana Muryan barcin Inteesar ta Auna mata Zagi tana Fadin tatashi ta Shirya Ya Sadam ya Kirata jin haka yasa Dole Munari ta Mike. Falo ta Fita taga ba kowa yau Lahadi Ya Yusuf suna ciki Dakin Abba ta Shiga ta Iskeshi yana ta Karatun Qur"ani sai bata kateshu ba ta Fito ta Shiga Kitchen ta fere Dankali ta Dora Ruwan Zafi kana ta Fito ta dan gyara Falon itama ta Share ta goge ko"ina kana ta koma ta Soya Dankalin ta soya kwai sai ta Dafa Ruwan Tea,ta jera saman Dining ta shige Dakinta ta fada wanka a gurguje ta Shirya,Daman Inteesar tace su saka Kayan da Umma ta Dinkamusu shi ta saka ta Sagalo Mayafin kayan Sea green. Har zuwa Lokacin ba wanda ya Tashi,Tea ta Hada ta sha ta Hada da Dankalin kana ta koma Dakin Abba ta Iskeshi ya gama Karatun yana Zaune kan Darduma yana jan Cashaba ta Duka ta gaisheshi ya amsa mata yana Shafa kanta Nan take yagamai Zata je gidan Mama Inteesar ta Kirata Abba yayi mata Fatan Dawowa lafiya ta Fice Tana Fadamai Ta Hada Breakfast tun dazu yace mata Allah yayi mata albarka ta amsa da Ameen bayan tace mai in Anty Safiya ta fito ya gayamata ta tafi yace tom. Koda ta Fito Daga Gidan nasu 10 ne da wani abu na Safe,batayi wani Tafiya sosai ba ta iso Gidansu Sagir a kofar gida ma ta Ganshi yana mgana da wani suka gaisa ta shiga Ciki ta iske Mama na gyaran Wake a Tsakar gida ta Rankwafa ta gaisheta Ta amsa mata Cikin Fara"a Tana Tambayanta Mutanen gidan nan ne mama take Fada mata Zataje bikin Diyar yayanta kaduna Kafin ta tafi zata zo tama Abba Mgana Inteesar zata zauna dasu kafin ta Dawo Munari baki kamar ya Tsinke saboda Murna... Haka ta shiga ta iske Inteesar ta Shirya itama cikin irin kayanta tayi kyau sosai. Zama gefen gado Munari tayi Tana Fadin"Ke Mama tace zaki dawo gidanmu kafin ta dawo Daga kaduna..! Inteesar na Saka Sarka a wuyanta Tace"Eh nima jiya take fadamin..Bazan iya zama ni kadai ba,Ya Sagir ma Ranar asabar zai tafi Daurin aure..! Munari tace"Wai bikin waye za"ayi a kaduna..?. Inteesae tace"Bikin Anty Jamila Diyar Kawu Bala shine babba a Dakin su Mama..! Munari tace"Allah Sarki Shine ke bazaki ba ko..! Hararanta Inteesar tayi kafin tace"Sai na bar miki karatun nawa kenan ko..? Munari batace komai ba Tana Dariya,Suna Hiransu Sama sama har Inteeaar ta gama Shiryawa,Tana so ta Tambayi Munari Imran sai ta kasa sai chan wata Dubara ta Taso mata ta Kalli Munari tana Fadin"ya su Abba..? Ina Anty Safiya da Ya Yusuf ina Dan Rigiman gidan ku Ya Imran..? Munari tace"Ban hadu da kowa ba yau sai Abba..Kinsan yau Lahadi su Anty Safiya basa Fitowa da Wuri..Ya Imran kuma ina Tunanin ya Fita Jogging Tun dazu har ya Dawo..! Inteesar tayi shuru Tana Tunanin tama manta yana Fita Da Safe Motsa Jiki,Data fita ko kofar gida da Safe ne taga ko Zata gansa..? Wata zuciya tace ki gansa a saboda mene..? Da sauri ta ba kanta amsa saboda in karamai Godiya ya Ceci Rayuwata. Daganan bata kara cema Munari komai ba ganin sun gama Shiryawa yasa ta daga waya ta Kira Ya Sadam sai dai wajen kira Hudu bai Dauka ba Sai ta Kira Anty Aneesa take Fadamata Tana jin haka tasan aiki yayimai yawa a asibiti in tace su jirasa zasu kai wani Lokaci kawai sai tace su Fito su samu mai adaidaita su Kirata su bashi tamai kwantace in suka zo Zata Biyasa Haka kuwa sukayi bayan sun ma Mama Sallama suka Fice wajen 11am naSafe suna Fita Kofar gidan bakin Shagon Sagir suka ci karo da Imran yana Tsaye sanye cikin Riga da wando na Jc Mai ruwan ganye ya Tusa duka Hannuwansa cikin Aljihun wandon,Kafarsa sanye cikin wani Takalmi mai kama da Silifas Gefensa Sagir ne kamar suna mgana ne Munari ce ta Fara ganinsu ita Inteesar nachan tana Kokarin gyara Zaman Karamar Jakar Dake hannunta Yafito Inteesar tayi tana nuna mata Imran Lokaci Daya Tana fadin"Mun shiga uku Intee Ya Imran..! Da sauri ta Dago Tana kallonsa Shima Daidai Lokacin Daya juyo suka Hada ido Dukkansu sai da sukaji Zukatansu sun amsa Ajiyar rai Imran ya Sauke na Samun Natsuwar zuciya daya ganta haka Tun jiya Daya koma Gida ya kasa Barci Saboda Tunanin Halin da Inteesar ke ciki Tun da Safe ya Fito Joging har Kofar gidan nan ya zo ya Tsaya ko zai ganta Shuru,bai ganta ba ya kasa Natsuwa yana so ya ganta ya Tabbatar da baatayi ta kuka ba kuma Lafiyanta kalau ya koma Gida ya kasa Natsuwa,Abakin Abba yake jin Munari bata gida tazo wajen Inteesar zasu anguwa yana Fadama Ya Yusuf da Matarsa Shiyasa ya Fito Domin ya ganta ya samu Sukuni yana ganinta yaji kamar anyimai gafara. Itama anata Barayin hakane wani Sanyi Sanyi taji yana Shiga Jikinta Basar da su yayi ya Dauke kai kamar bai gansu ba Sagir ne ya gansu ya Saki Fuska Inteesar ta kamo Hannun Munari suka karisa gabansu Dukkansu suka gaisheshi Sagir ne kadai ya amsa su Gogan kuwa sai ma Dauke kai kansa da yayi kamar bai gansu ba nan kuwa,ya gansu yana ma ta Satan kallon Inteesar ne ta Gefen ido. Har suka wuce suka Fara Tafiya zuwa Bakin Titi yana Kallon Gefensa baya so Sagir ya Fahimci ya Bisu da kallo sai da suka dan Dade da wucewa kana ya Hangesu Daga chan suna Tafiya Kadafa da kafada da Munari sun rike hannun juna acikin ransa sai da yaMurmusa yace"Ji besu kamar wasu yara..Kaya iri Daya kuma sun wani rike hannun juna..! Shikadai abun ke bashi Nishadi,ganin ya Riga ya ga abunda yazo nema yasa Sagir namai Hira sama sama yake jinsa Daga Karshema yace mai Zai je gida sukayi sallama Daganan Sagir ya Koma Cikin Gida shi kuma ya Nufi Hanyar gida. Suna zuwa bakin Titi suka Samu mai adaidaita suna Shiga Anty Aneesan na kira bayan ta dauka take Tambayanta suna ina ne..? Tace suna cikin adaidaita sai tace ta bashi wayar ta mikamai ta mai kwantace yace ya gane wajen gasunan yanzu zai kawosu,nan ya mikama Inteesar tace mata sai sun iso. Sun dauki Hanya kenan Wayar Inteesar tashiga kara tana Hannunta ne Tana Dagowa taga lambar mai Kiran ta Saki wani Siririn Tsaki batayi Sarving din Lambar ba ammh nacin Kiran Dayake mata yasa ta Haddaceta Saboda bata so ya Kira ta Daga.. Haka ake ta Kira bata Dauka ba Munari Dake gefenta tace"Wai hala baki ganin ana ta Kiranki ne..? Inteesar ta tabe baki kafin tace'Ina gani bazan dauka bane..! Munari tace"Eyye ko an yi sabon gaye ne Shine ba"a son Daga wayar agabana..! Inteesar ta Harareta tana Fadin"Allah ya kyauta wannan ya Zama Saurayina..Ya khamis ne Dan Baffa Kabiru na Abuja Tunda mukaje Dukku lokacin nan ya nace min ya Samu Lambata ban huta ba yayi ta Kirana ni kuma Wlh bai min ba sam..! Munari tace"To miye aciki Don ya Kiraki ku gaisa..!?ai ba cewa yayi yana sonki ba Besty..! Inteesar tace"In na bashi Dama haka zai ce..Ni kuma bai burgeni ba Asalima Haushi yake bani..! Munari tace"Kedai kowa ma sai kice yana Baki Haushi..Naga mijin ki kuwa..kilama Gajere ne baki mai Katon kai da..! Inteesar ta katseta da Fadin"Ba Ameen ba Muguwa insha Allahu Mijina Ba kamarsa yarinya..! Dariya Munari ke ta mata ita kuma ta sha mata kunu gashi Khamis din yaki Daina Kiranta sai kawai ta Kashe wayar In sun isa ta kunna Kila in yaji Tana Kashe ya Hakura. Cikin Lokaci sai gasu sun iso,layin Ashe su Anty Aneesa suna Farko Farko ne,Tun da suka taso ta Fito bakin Get din Tana jiransu Suna ma Cikin Tafiya Inteesar ta Hangeta Ita da Waleeda sabe a Kafadanta tace ma mai adaidaita ya Tsaya sun kawo. Sai dai ta gansu kawai agabanta suka Fito Daga Cikin adaidaita Cikin murna sika Rumgume juna ita da Inteesar suna Murna ganin juna ta Karbi Waleeda Dake hannunta ita kuma ta Karisa ta bama adadaita kudinsa,ta nufosu Inteesar tana musu maraba tayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan sai alokacin ta Lura da Munari sai da gabanta ya Fadi ta Kuramata ido Tana kallonta wannan tayi kama da na Hoton nan da Daada ta nuna musu a Dukku karamar ciki ammh in hakane meyasa Inteesar bata ganeta ba Ammh Tabbas wannan tayi kama da ita.. Tana ta kallon Munari,Har Munarin ta Tsargu ganin haka yasa sai ta Waske,gidan dan madaidaici mai kyau da tsari sai gasu acikin Falon gidan Anty Aneesa tace su Zazzauna Tatafi Kicthen ta kawo musu Ruwa da Abun shq kana ta Zauna suna Kara gaisawa. Anty Aneesa ta Kalli Inteesar Tana Fadin"Itace kawar naki da kikamin zaku zo tare..? Tafada tana kara Kallon Fuskar Munati wacce ke wasa da Waleda dake hannunta. Inteesar tace"Eh itace sunanta Maimunat..Munari ga Anty Aneesa matar Ya sadam yaron autansu Daddy ne.inna Maimunatu. ! Munari ta Dago tana Fadin"Allah Sarki..Ina yini..? Anty Aneesa ta amsa tana kara kallonta sai dai tana yi da taku kada Munarin taga kamar tana ta kallonta. Inteesar tace"ina su waleed hala..? Aneesa tace tana Mikewa"Ya bi Abbansa Asibiti..ai nasan in ya Shiga asibitin nan sai Allah Shiyasa nace ku Taho kawai..! Inteesar tace"Gaskiya kam..gwara da muka Taho ba gashi mun zo ba..! Aneesan tace"Wlh kuwa..Allah sa dai ya dawo kafin ku tafi..! Inteesar tace Amin daganan ta koma Kitchen ta barsu nan Tana Hada musu Brekfast Tana ta Tunanin Munari itama in bata manta ba Kamar Fuskar ne tagani a Hoton nan sai dai hoton yana Wayar Baban Waleed ne Daya nan ne data Dauka ta Kara Dubawa ba kodai ba ita bace..?in da itace da Tabbas Inteesar zata fara sani kafin ita ammh in ko hakane kamar har ta baci. Ferfesun kayan ciki ta kawo musu da Waina da Miya datayi da Safe,sai kunun Aya,da Soyayyan Naman kaza,Tazo ta zauna suna ta Hira da Inteesar ta rika jan Munari da Hira har itama ta Saki jikinta suka Zauna sukaci Wainan sosai da Ferfesun nan,suka kara komawa saman kujeru suna Hira sai da aka kira azahar kana suka Tashi zuwa Sallah Dakinta takai su tace suyi sallah ita kuma ta shiga Dakin Baban Waleed,waleeda Tana Manne dasu musamman ma Munari kamar ta santa. Bayan ta idar da Sallah Kitchen ta Shiga ta Dora musu Dambun Cuscus na Zogala Cikin Lokaci ta gama shi suna Cikin Dakin suna Hira sai dai tazo tace su Fito suci suna ta mamaki. Dambun yayi Dadi sukaci suna ta Santi,Sukace basu iya ba zasu dawo ta Koya musu Tace sai sun zo. Bayan sun gama cin Abinci ne suka Dora da Zobon mai Dadi Data Hadamusu cikin su ya cika ammh Dadin Zobon yasa sai da sukaji ba Wajen Shiga kana suka Hakura. Inteesar ta kunna Wayarta ta Kira Daddy tana Fadamai gata gidan Ya Sadam sai dai baya Gida sai Anty Aneesa Har ta bata suka gaisa Harda Umma,Daganan Ita Anty Aneesan ta Kira Anty Hauwa suka yi mgana da Inteesar ashe suna waya sosai Zumunci ya kullu Masha Allah. Sai da sukayi Sallar La"asar kana sukayi Shirin Tafiya Tunda Ya Sadam shuru bai dawo ba,Aneesa nata Kiransa yace mata cikin wadanda suka ma aikin ido ne ya samu mtsala sai da suka kara komawa dashi su jiransa nan da Minti Talatin. Sai dai har Ta wuce bai Dawo ba sai Inteesar tace bari su tafi Ranar Dayake gida Zata dawo ba yadda Aneesa ta iya sai dai taso yazo yaga Munari kila shima yaga abunda tagani ganin zasu tafi yasa tace su Tsaya suyi Hoto in ya Dawo Zata Nunamai haka kuwa akayi sukayi ta Daukan Hoto ta Daukesu Munari da Inteesar da yawa ta Dauka na Munari ita kadai itama Aneesan Inteesar ta Daukesu itada Munarin da Waleeda.. Kana ta Rakasu bakin Hanya suka Hau adaidaita zuwa gida ta basu 2k tace su biya mai adaidaita suka karba suna ta Godiya. Gidan Mama suka yada Zango da suka Dawo sun gaji gashi Cikin su ya cika sun kasa Tafiya Munari bata koma Gida ba sai da Cikinta ya Sarara kana Inteesar ta rakata Gida,Koda suka je Abba ne kadai agidan Ya Yusuf da Anty Safiya basa nan Bata da Lafiya ashe Tun Safe take amai ya tafi ya kaita asibiti. Jin haka yasa Inteesar ta zauna Har sai gabda mangariba suka Dawo Jikin nata da Sauki sai da Labari mai Dadi Tana Dauke da juna Biyu na kimanin Wata Uku Ba kunya Yusuf sai murna yake da bakinsa kuma ya Fada ma Abba. Ana cikin Murnan sai ga Imran ya Fito Daga Dakinsa Da Sauri Yusuf ya Rumgumesa yana fadamai ya kusa Zama Baba sai alokacin Inteesar ta ga yayi Dariya Harwasu Daga Cikin Hakoransa sun Bayyana waje ya Bubbuga bayansa alamun Farincikin. Su suka Rike Anty Safiya zuwa Shashenta suna mata Sannu Abunda yasa Inteesar ta manta da Abunda ya Faru da ita Jiya har ta kaiwa Bayan Mangariba. Sai da su Abba suka dawo masallaci ta Tsorata ta tashi tace zata tafi Gida,Yana Dakinsa yaji Tana ma Abba Sallama Daman itace aransa yana Tunanin ta koma gida ko bata koma ba...?.sai yaji mganarta agogon Fatan Dake hannunsa ya kallah 7pm tayi Duhu ya fara Shiga Ransa ya baci ya Fito Lokacin har ta Fice Daga Falon Munari taso ta rakota tace mata ta Zauna Wajen Anty Safiya yau ma ba wayar nata agida ta barta. Ta fito Gabanta sai fadi take tana ta Waige waige,Taji Tafiya a bayanta da Sauri ta Juya suka Hada ido dashi Sai taji wani Sanyi kamar an yi mata Gafara Tsayawa tayi tana Kallonsa yana Sanye da Riga da wando Baki da Fari,Ta lura blck and White kalansa ne Domin yawancin kayansa kalansu kenan sanan bata taba ganinsa da Manyan kaya ba Tunda ta Fara ganinsa bayan Jallabiya. Ganin ta Shagala da kallonsa ne yasa ya Tsaya Hannayensa Cikin Aljihunsa yace"In kin gama Kallon nawa sai muje na Rakaki tunda ke baki jin mgana..! Daga sama taji mganar sa Sai taji kunya ta Sadda kanta kasa Tana Fadin"Bansan Dare yayi bane..! Da sauri yace"Oya muje..Bana son wata mgana kafin ki fashemin da kuka Shagwabbiya kawai..! Yafada yana Kauda kansa dan Dariya Tayi kafin ta wuce yabi bayanta Sahu Sahu kafa kafa kamar wani mai tsa ranta Har Kofar gidan su Sagir Ita kuwa Gabadaya ta saka gane yanayinta jinta take kamar tana yawo Saman gajimare sai da suka iso kana yaja ya Tsaya ita kuma ta Waigo Tana kallonsa,Shima ya kallentan sai da ya Dauke kansa Mirmishi tayimai kafin tace"Nagode..! Dahaka ta juya ta shiga Gida,dan Bakinsa yadan Cija kafin ya Juya zuwa Gida Aransa yana Fadin"Batajin mgana yanzu ba ban rakota ba wani abu ya Kara faruwa fa..? Da sauri ya Kauda wannan Tunanin jin har Zuciyarsa ta fara rawa. Tana Shiga gida tama Mama sannu da gida ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan ta Idar ne ta Duba wayarta Taga Kiran Ya Sadam da Anty Aneesa,Da Mayen nan Khamis karamin Tsaki taja kaawai Ya Sadam ta Fara Kira ya dauka bayan sun gaisa ya Fara bata Hakurin rashin Dawowarsa tace bakomai kana ya bama Anty Aneesa ta yi mata ban gajiya Tana Tambayan Munari tace Yanzu ta Dawo daga Rakata Daga haka suka yanke kiran bayan Ya Sadam din yayi ma Inteesar Alkawarin sunan nan zuwa. Aneesa Tayi ma Sadam mganar Munari tace"Honey ni kuwa naso ka Dawo dazu kaga wani abun mamaki..? Yana kai Lomar abinci bakinsa ya Dakata yana Fadin"Mamakin me..? Gyara Zama Inteesae tayi Tana Fadin"Kawar Inteesar da suka zo Tare take min kama da karamar yarinyar nan ta Hoton nan da Daada ta nuna mana adukku..! Kallomta yayi kur kafin yace"Kina Nufin Hoton iyalan Kawu Malami..? Aneesa ta Daga mai kai sai taga yayi Dariya yana Fadin"Daga ganin..Hoto sai kiga yarinyar mutane kice itace..?Ai da itane da Inteesar din ta Fara sanin hakan..! Aneesa tace"To in ba itabace kamar har ta baci Wlh..Saboda haka nace muyi Hoto bari ka ganta..! Cikin Halin ko in kula yace"Yauwa muga Hoton..! Ta Lalubo Hoton Munarin kenan zata mikamai Waleeda Dake jikinta ta kwabe hannunta Wayar ta Fadi kasa ta Watse Ran Aneesa ya baci ta Maketa Ya sadam ya fara fada yana Fadin"Saboda Wayar banza zaki Daki yarinya..! Cikin Kufulawa tace"in ta Lalatamin fa..? Banza yayi da ita ya Dauketa yana Lallashi ita kuma Aneesa ta Duka Tana Tattara Wayarta bayan ta Hadata Tayi tayi ta ki kawowa sai Ranta ya baci ta Shige Dakinta ta Jefa Wayar Cikin Wardrope shikenan ganin Hoto bai samu ba. Tafiyar Mama ya tashi Ana gobe Zata tafi Taje gidansu Munari da kanta Inteesar ta Rakata ta gaida Anty Safiya wacce ke fama da kasala,da Amai kana ta gayama Abba Zataje Biki Zata bar Inteesar Wajensu Abba yace bakomai bama sai tazo ta Taambaya ba,Inteesar kamar ya take a wajensa,Munari da Inteesar sun fi kowa Murnan hakan,Washegari Tun Safe Sagir ya Raka Mama tasha tahau Motan Kaduna,Inteesar kuma sun Tafi makaranta sai da suka Dawo Munari ts Tayata Debo kayan da Zatayi amfani Dashi kafin Mama ta Dawo,Sagir daman baya Zaman gida yana Shago Abinci kuma Siya zai rika yi Shima Ranar asabar zai tafi kadunan. Imran baisan Inteesar ta Dawo Gidansu ba sai da Sassafe ya Fito zai Tafi jogging ya ganta Tana goge Dining Abun ya bashi mamaki har tsayawa yayi yana Kallonta baki sake Data gaisheshi Abun sai ya kusa saka Inteesar Dariya ta Rufe bakinta ta Shige Kitchen da gudu Munari Dake Feran Dankali ta bita da kallo. Daman saboda ta gansa tace ma Munari bari ita ta gyara Falon ta Goge,Ita kuma ta Soya Dankali da kwai Kada su makara Karfe 8:30am suke da Karatu,Anty Safiya kuma Lafiyan sai Hankali bata Girki a asibiti ance ta Huta sosai kafin ta fara aiki. Kuma ta gansa Taji sanyi acikin Ranta ita kanta akwanakin nan ta rasa meke Damunta jinta da ganinta Imran ne in bata gansa ba ta rika Shiga Damuwa kenan sai ta gansa take jin Sanyi,Sabida ta gansa tazo gidan ta Wuni bata tafiya sai duhu yayi Saboda ya Rakata tasan bazai taba barinta tabi Hanya ita kadai ba Kamar ma Dakonta yake yi Data Fito zata gansa yana Binta abaya koda bazai ce mata komai ba har sai ta Shiga gida zai koma ya Lura batajin mgana ga Tsoro ga Taurin kai bayason yayi mgana ta sakamai kuka ya Lura ta Fiye shagwaba Shiyasa Ya gwammace ya Rika gadinta Kullum in tazo takai yammah agidansu. Har ya Dawo Daga Jogging yana Mamakinta Yana Shigowa Haraban Gidan ya gansu Yusuf ya daukesu zuwa makaranta Sai da ya Shiga Gidan ne ya Shiga wajen Abba yana so ya Tambayeshi ammh ya kasa sai ya bar Abun aranshi. Sai dai ya samu amsar Tambayarsa Wajen Sagir Tunda ya fadamai Gobe Zai tafi kaduna Daurin aure Mama ma tana chan Tun jiya Shiyasa Inteesar ta koma Gidanku maimakon ada da bayason wani ya Rabesu,sai yaji Salama da wani Natsuwar da bai taba jiba. Washegari Asabar da kanshi ya Raka Sagir tasha akan Mashin dinsa ya Daukesa Sagir yamai Tayin zuwa yace bazai jeba bai bar wajen ba sai da Motarsu tatashi kana ya koma Gida. Kamar yadda suka saba kwana Biyun nan Suna Falo ita da Munari suna Kallo suna Hiramsu Anty Safiya na Barayinta ita da Ya Yusuf Abba ne Kuma yanzu yana cikin Dakinsa In suka gansa sai su Natsu suna Raba ido Da ya shiga Daki sai su Fara Dariya. Hakaman yake jin Dadin ganinta a kusa Dashi koda bazai mata mgana bane baya ma son Mama ta Dawo ace ta koma Gida,Ranar asabar da yammh Tasleem tazo ita da Mommy da Anty Saratu suka zo Duba Safiyar basu jima ba Mommy da Anty Sarati suka tafi suka bar Tasleem Datace nan zata Kwana sai Monday Zata koma Taga su Inteesar. Suka Hade su uku suna ta Bidrinsu Inteesar ne ke jansu zaman Falo Saboda Taga Giftawan Imran Munari kuwa bata so saboda Imran bayasom Hayaniya tafi son su zauna Shashen Anty Safiya yafi susha Hiransu kala kala bamai Takuta musu. Adakin Munari suka Kwama Dukkansu Harda Tasleem Dataki kwana Shashen Anty Safiya. Washegari Lahadi suka zage suka gyara Gidan Inteesar ta matsa ma Munari su Zauna afalo su kunna Kallo,bayan sun Karya Abba na Samam Dining shi da Ya Yusuf suna Cin Abinci suna Hira su su kuma suna saman kujerin falom Sun kunna Arewa24,lokacin ana Maimaicin kwana Cha"asin suna ta Hayaniya Munari da Tasleem nata bama Inteesar Labarin Film din Tunda ita ba wani Kallo take sosai ba Daman Saboda Taga Imran ne yasa ta Mtsa musu su Zauna. Yana cikin Dakinsa Hayaniyarsu duk ta Cikamai kunni Tun yana Sharewa Har Ransa ya baci ya tashi ya Fito a Fusace Jikinsa ko Riga babu Daga shi sai 3Quater,kamar Walkiya suka gansa gaban Kayan kallon ya Zare Soket din gabadaya ya yar a kasa ai kafin ya juyo Munari tayi ta kanta Tasleem ma ta mara mata baya Inteesar ne ta Tsaya tana Raba ido Hararanta yayi kafin yace"Bar nan Wajen..! Da sauri ta Mike tana Kokarin Hana kanta Dariya yana kallonta aransa yace"Shikenan ta gama Rainani.! Abba suna gefe suna kallobsu Abba ya Sa baki ya Kirashi ya Juyo yana kallonsa Cikin Mirmishi yace"kai da idon sani da bako Duk Dayane awajen ka ko Imran..? Dakuna Fuska yayi kafin yace"Abba Hayaniya suke min akaina..! Yusuf yace"Ai ba Dakinka suka shiga ba Ishasshe..! Bata rai yayi ko mgana bai kara ba Ya shige daki har yana Bango Kofa Yusuf yayi Dariya yana Fadin"Na tabo Yaron Abba..! Mirmishi kadai Abba yayi bai kara mgana ba. Su kuwa Shashen Anty Safiya suka koma suna Sauke Numfashi Munari Ba bakin mgana Inteesar na Dariya ta Daka mata Duka tana fadin yau daya Daketa kanta zata rama ta kusa jamata masifarsa Ita dai Dariya kawai takeyi Burinta ya Cika Tunda ta gansa,sai da yanayin Data gansa ayau din ba Riga Gabadaya yasa ta jin wani iri Imran yana da Cikar Zatin da kowacce Lafiyayyiyar mace in ta gansa ahaka Taji wani iri hakan ne ya Faru da Inteesar wacce ta Wuni Tunaninsa bai bace mata ba. *Shakira* 3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book 1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��*        *🅿�29* Har garin Allah ya waye Inteesar bata kara saka Imran a idonta ba duk da kuwa yadda taso ta kara ganinsa,Gashi yau din ta kama Monday ne suna Class da safe shiyasa suka Shirya da wuri Ya yusuf ya daukesu yakaisu kafin ya wuce wajen aiki basu kuma dawo ba sai yammah Tun suna makaranta Inteesar sukayi Mgana da Umma ta fadamata Su Mama sun kamo Hanya tun dazu shiyasa da suka dawo nan ta Tsaya tunda sun dawo gama Sagir nan a kofar Shagonsa shida Imran suna mgana. Sun gaisheshi Sagir ya amsa cikin Fara"a yana Tambayansu karatu sukace Alhamdulillah,Inteesar na Tambayansa ya Kaduna yana Fadamata Hargidansu yaje Imran na Gefe ya Kauda kansa yau din ko sau Daya bai kalleta ba bayaso Zuciyarsa ta Saba da kallonta alhalin yau zata koma Wajen Mama,lokacin da Sagir ya Kirasa ya gayamai sun dawo bai ji dadi ba ko baya ganinta yana Samun Natsuwar Sanin Tabbas Numfashinta yana Kusa da nashi,yanzu din ma ita yake son gani yasa da Sagir ya kirasa yace sun dawo ya Fito suka Hadu Tunda yaga Munari bata dawo ba ya tabatar da suna makaranta in ma kuma sun dawo suna gidan su Sagir ya Tabbatar ma kansa zai ganta.. Har suka wuce cikin gida kansa na kallon wani waje,Duk da Satan kallonsa da Inteesar din Tayi tayi bata Samu Nasara Hada ido dashi ba. Sagir na lura dasu acikin Ransa ya Dade yana mamakin wani abu Shi dai bazai ce soyayya suke yi aboye ba..?sai dai ya Fara Lura da wani abu ko Rakotan da Imran yake yi Sagir na ganinsu bai dai taba ma Imran din mgana bane sai shi kadai yayi ta mamaki yasan waye Imran ya Tabbata Baya abunda Ransa bai so ba Bamai sakashi yayi abu Dole duk abunda yayi ko ya aikata yayi Niyya ne kuma Ra"ayinsa ne Sai dai in ya Tuna Kaifin Imran sai yaga da kamar Wuya ace Soyayya suke shi da Inteesar sai dai yabar abun acikin Ranshi ya zura musu ido yana Bin Duka Takunsu itama ya Lura da kallon Data dinga bin Imram din dashi kallo ne na samun Salama da sukuni ya shiga Rudani shiyasa ya kasa Dora komai a inda ya dace ya bar Lokaci ya bayyana komai. Tare da Munari suka shiga gidan tayi ma Mama sannu da zuwa,bata wani jima ba Inteesar ta Rakota Kofar gida,Sukayi sallama da cewa sai gobe Inteesar zata zo ta kwaso kayanta Leda baka karama a hannunta cike da Goriba da gyada Tsaraban Mama ce ta bata ta kai gida,Lokacin da ta rako Munari Daga Sagir din Har Imran din sun tashi Daga wajen har Leke tayi bata Hangosu ba ajiyar zuciya ta Sauke Ranta duk ba Dadi yau data bar Gidan su munari batasan meke damunta ba ita kanta abunda ta sani Shine Imran yana cikin Ranta da Tunanin wanda komai take sai ya Fado mata arai ganinsa kuma Tamkar karin kuzari ne da Farimciki agareta Rashin ganinsa kuma sai taji gabadaya batajin Dadin jikinta da Zuciyarta tarasa Dalili sai dai ta Danganta haka damai kula dakai kaima ka Kula dashi ko bakomai Imran ya mata komai arayuwa Tunda ya ceci Rayuwarta. Sai washegari da suka dawo makaranta taje ta kwaso yan kayanta ta Dade agidan saboda Tasleem na nan Har yanzu bata koma ba,Anty Safiya Taji sauki sosai Sai dai Rashin cin Abinci komai taci sai ta dawo dashi Sai dai zuwa in an kwana Biyu Laulayin yabi jikinta. Tasleem da Munari suka rakata Har gida da kayanta,tayi ta waige waige agidan su Munari bata ga Imran ba Shi kuma ya ganta Saboda yana Haraban Gidan Lokacin da suka Fito bayaso su Fahimci ya tsayane kallon Inteesar yasa Lokacin datake waige waige ya Boye jikin Motar Yusuf har suka Fice daga gidan yana Kallonta,yana jin kamar yaje ya Riketa Kada tatafi karamin Tsaki yaja acikin Ransa ya rasa Meke damunsa..? Abubuwansa bama raguwa sukeyi ba sai ma Karuwa kan baya. Haka suka cigaba da Karatunsu cikin maida Hankali Tasleem Sati Daya tayi ta Koma gida Tunda Anty Safiyan ta Warke sosai har tana aiki ma da kanta,Munari kuma basa zama sai Weekend tun safe in suka Tafi makaranta sai yammah basu da wani Ishashen Lokaci. ****** *Bayan sati daya..*! Yau Alhamis tunda sai 6pm suka Dawo Daga makaranta tun safe sun Wahala daga Newsite suka tafi Class Oldsite,gabadayansu sun dawo jikinsu na Ciwo shiyasa yau kowa ta wuce gida. Inteesar sai dai tayi wanka ta gasa Jikinta kana ta iya shan Ruwan Tea domin Karatu bai barsu sun Tsayama cin wani abu yau a makaranta ba. Kwance take kan gado Tun bayan data idar da Sallar Isha"i take nan Zube kamar kayan wanki tagaji kafafuwanta Ciwo suke mata sosai inda zata samu mai mata Tausa da taji Dadi sosai ido kawai take Lumshewa ga barci Tana ji ga gajiya data Lullubeta ta Saukar mata da kasala. Wayarta ta Dauko Data Tuna da wani abu Dazu suna makaranta ta Dauki Wayar Munari ta saci Lambar wayar Imran Bata sani ba Kwanakin nan bata ganinsa koda gidan taje ballatana ta Rage zuwa saboda Wuni suke Zungur acikin makaranta.. Haka kurum take son ta adana Lambarsa acikin Wayarta ko bazata Taba Kiransa ba Zuciyarta ta aminta da Hakan sai dai me..! Yadda ta kurama Lambar ido haka take ganin Gilmawar Fuskarsa ta cikin Wayarta,Kurama Fuskar wayar ido Tayi kowani Dakika jikinta na kara Saki Cikin yanayin kasala..? Meke Faruwa dani ne..? Bata samo amsar tambayanta ba Hannunta ya kubce ta Danna ma Imran kira batare data ankara ba da Sauri ta Mike tana Shirin kashewa sai dai me...? Kiran Tuni ya shiga har ta fara Ringing gabanta ya yanke ya kanta ta Dafe kanta Dayake Saramata Jikinta ya Fara rawa bata da kwanan Amin taji ya Daga Kiran duk da kuwa Bai Taba Daga Bakuwar Lamba ba. Yadda take kwance Tana Tunaninsa Haka shima yake kwance yana Tunaninta Sai dai shi yana Rage ma kansa wasu abubuwan in ya Busa Sigarinsa yanzu ma Tabance a Hannunsa yana Busawa cikin kwarewa yana Kwance ya Kishingida da Filo,Dagashi sai bakin dogon Wandojikinsa bako Riga kwantancen Gashin Kirjinsa mai Santsi ya kwanta Sai kyalli yake.. Yayi mamakin ganin bakuwar Lamba Tana Kiransa shi ba wanda ya sani masu Kiransa Daga Sagir sai Yusuf acikin Contact din nashi ma Kwaya uku kadai garesa Daga ta Yusuf sai ta Sagir sai ta Munari ita da bai cika Kiranta ba sai Lambar Baba Manu kuma ya Dade da gogeta Tun sanda ya gama amfani da ita. Da farko kamar bazai Daga ba sai Zuciyarsa taki bashi Daman haka haka Kurum yaji ta Rinjayesa ya Daga Kiran sai dai bai yi mgana ba yayi Shuru yana Sauraran Bugun zuciyar Inteesar da yadda ta Dafe Kirji Tana Ajiyar Zuciya. Mamaki ya kamashi jin an ki mgana kuma yana jin Saukan Numfashi acikin kunnuwansa Ransa ne ya baci ya kashe wayar batare da yayi mgana ba Inteesar ta Rumgume wayarta Tana jin kamar Imran ta Rumgume saboda yadda Saukan Numfashinsa yasa Taji ta kasa Controling kanta. Zama ta gyara ta sake Kiransa bai Dauka ba Sai da ta kara Kira kana ya Daga Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Ko waye ke kirana yafadamin kai Tsaye.. kada ya bari Raina ya baci na Bincikosa da kaina..! Yafada Cikin Kaushinsa kamar yadda ya Saba maimakon tace wani abu sai taki ta Damke bakinta Tana Dariya Farinciki ya cikata dataji Muryansa ganin an ki mgana yasa ya Dago Wayarsa yana Bin Lambobin da kallo acikin Ranshi yana Tunanin wanene? Bai samu amsar ba yaja karamin Tsaki ya datse kiran Lokaci Daya Da kashe wayar nashi gabadaya Zai iya Zuwa Mtn office kan wannan lambar ya Tsani arainamai wayau,kuma abun da ba"a tabamai ba Dole wani wanda yashanshi ne ko dai Sagir ne...? Anya shine kuwa..? To in bashi bane Waye? Yusuf dai basa irin wannn Dashi Kodai Munari ce..?ai ita yana da Lambarta To kodai kodai yarinyar nan ne Mara jin mgana..? Zai iya Zama itace saboda yaga ta fara Rainasa Mirmishin Saman lebe yayi ransa ya tabbatar da itace ba wata ba zai bita a sannu zai kamata. Ita kuwa yana kashewa ta saka Dariyan jin dadi acikin ranta tace ko bazai daga ba zata kirasa sai dai ta kara kira wayar tana kashe,ta kasa Samun shi,sai ta Hakura zuwa Gobe ta maida wayarta ta ijiye ta koma ta Kwanta Hannunta Rumgume akirjinta,Bata Dade da ijiye wayar ba sai kira ya shigo wayarta da Sauri ta dauko da Murnan ko Imran ne sai taga Khamis ne karamin tsaki taja Lokaci daya tana ijiye wayar Wani Takaichi yana kara kamata bata san Dalili ba ta tsani Khamis din,Sau daya ta taba Daga wayarsa bata Kara ba data Fahimci shine achart kuwa ya Tura mata sako ba adadi bata taba Budewa ba. Messages kuwa ta waya ya turo ba adadi bata taba Budewa ba Bashi ke gabanta ba ita Mu"amala da ya"yan Mami Asma"u kwata kwata bazata iya ba Saboda basu da hali mai kyau har gwarama Umaima,ammh Sajidan nan ai tafi kowa Iskanci tama fi Uwarta Komai ta Damata ta Shanye,haka shekaranjiya Hafsah ta Kirata tana Fadamata Wulakancin data kirata ta mata saboda ta yi adding dinta a group din data Bude musu na mata Zallah Shine ta Fita ita kuma ta sake adding dinta shine ta fita ta Kira Hafsah a waya ta fada mgangun marasa Dadi kan kada ta kara adding dinta saboda ita bata da wannan Lokacin kuma ita ba sa"arta bace da zata Zauna tana wannan Shirmen kada ta kara mata haka bataso Daga haka ta kashe Wayarta ta kuma Sake Fita Daga group din Hafsah na gayama Inteesar taji Takaichin ba ita Sajida ta Kira ba da ta gane bata da wayau da sai ta Raina kanta ta rika ma Hafsah Fadan meyasa ma ta Sakata aciki..? Abu ne na Zumunci ba Dole aciki wanda ya dama ya shiga ayi dashi wanda bai ga Dama shi ya sani,ba wanda ya kara bi ta kanta su Anty Hauwa dasu Aneesa suna cikin Group suna Haduwa ayi ta Hiran Zumunci Inteesar ta kan Jefa mgana Daya biyu ba sosai ba. Tana cikin wannan Tunanin ne taji karan Shigowar sako Bata ma yi kokarin Dubawa ba,saboda tasan ko waye sai da asuba ta duba Khamis ne Yana magiya ta Daga Kiransa Tsaki Taja ta Share duka Sakonninsa bata ma Tsaya karanta su ba. Allah yasa basu da Class din safe shiyasa tasha barcinta ta Huta sosai sai 12pm suka shiga cikin makaranta ita da Munari,achan ma makaranta Haka Khamis yayi ta Kiranta taki Dauka Har yabama Munari tsausayi ta Roki Inteesar data Dauka tace mata Wlh bazata Daga ba sai ta Kyaleta.. Tundaga Ranar Inteesar ta samun Abun yi duk dare sai ta Kira Imran ko da bazai dauka ba sai dai yana Dagawa Dukkansu suyi shuru suna jin Numfashin juna,Har ya gaji ya katse Kiran sai ya kashe kiran Tayi da Dariya ita kuma batasan ya ganota ba Ya karbi Wayar Sagir ya saka lambar ya yana Danna kira sai ga Sunan Inteesar sai ga Lambarta ta bayyana Mirmishin Saman baki yayi shi ya sani itace ba wata ba.. Yarinyar nan ta rainashi wlh ammh zai yi mganinta Sai da sukayi wajen Sati Daya tana kiransa Ranar tana Kira ya daga tayi Shuru taki mgana shi kuma cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Yarinyar nan kin rainani ko..?! Ni sa"an wasanki ne da zaki rika kirana kina kin mgana..? Cartoom kika maidani ko karamin yaro irinki..? Yafada mata Cikin Kaushinsa Koda yaushe Tsoro ya kamata ya akayi yasan itace sai ta fara Kifta ido ta rasa abun cewa Mirmishi yayi kafin yace"Kina mamakin ya akayi na gano ki ko..? Duk abunda Imran yaci alwashin sani sai ya sani..! Kifta ido take yi kamar yana gabanta ta kuma kasa cewa komai Yasan daaman bazata iya mgana ba Ganin haka yasa yace"Oya jeki kwanta Tunda baki da abun fada..Ki daina Kirana kiyi Shuru bakya iya mgana Am not a Child kamar ki ok..! Daga haka ya datse kiran Yana Mirmishi har cikin Ransa baisan meyass ransa bai baci da duk Abunda take yi mai ba sai ma Nishadi Dayake jinsa Ciki. Ita kuwa yana Kashewa ta Fada kan gado tana Sauke Numfashi kamar wacce Tayi gudun Tsira,afili ta Furta"ya akayi ya gano ni..? Na bani..! Take fada tana Dariyan Nishadi. Tunda ga ranar bata kara Kiransa ba ya dauka ba sai dai ta Kira data shiga sai ta Katse kiran,ko kuma Daya Dauka sai ta kashe Imran baisan meyasa ba baya damuwa da abubuwan da Inteesar keyi da wani ne kemai Rainin wayau nan bazai Dauka ba sai gashi ita tana yimai bai taba Daukan wani mataki ba in ta Dameshi sai ya Kirata sai ta Dauka taki mgana Shi kuma sai yace"Kin raina ni ko..? Oya ki je kiyi karatu ki kwanta bana son wannan Shirmen.!.daga haka zai yanke kiran ko ahakan aka Tsaya He make her Night sosai,shima ana shi barayin hakane. Ta dubasa a Wsop taga bayayi saita koma Turamai sako ta Messages sai tana Zaune ta Turamai sakon"Ya Imu kaina na ciwo..? Ya imu ina jin yunwa..? Ya imu kana ina..?kaci abinci..? Allah yasa yau baka sha sigari ba..? Na dawo makaranta nagaji Ya Imu..? Yarinta kala kala take Zubamai mai shi kuma ya kasa Dakatar da ita in ta Turomai sakon zai karanta baya ce mata komai sai tace mai ta dawo makaranta ta gaji kanta na Ciwo sai yace mata tayi wanka tasha mgani ta kwanta,in ta Tambayeshi yasha Taba..?sai yace mata Eh yasha Koda Ranta zai baci sai ya gayamata Gaskiyansa Shiyasa yake kara Burgeta Dukkansu sun Shiga Tarkon son juna batare da sun sani ba. Ranar asabar basu da makaranta Tunjiya data dawo daga makaranta Taji Cikinta na ciwo kadan kadan sai dai bata maida kai ba bata taba Tunanin Period pain dinta bane yadawo mata wanda abaya Tana Fama Dashi sosai in zatayi kamar ta Mutu to Tana karban mgunguna sai abun yayi mata Sauki sanda Tana Kaduna sai ta shafe wata Uku Tana Period batayi mugun ciwon maran nan ba sai dai kadan kadan wanda bai Shahara ba Shiyasa ko Mama bata taba sani ba kuma ganin Tunda tazo bata Taba yi ba ko sau daya ba sai Mgungunanta wannan Hutun data koma gida ta maidasu. Abun yana mata Kadan kadan ne yasa bata Dauka zai yi Tsanani ba Ranar ita tayi duka aikin gidan,Tace Mama ta Huta Jinin bai zo ba sai Zuwa Dare,Munari bata zo ba yau itama bataje ba tasan gajiya ne na makaranta sai dai zuwa gobe zasu Hadu.. Tana ganinsa tayi wanka ta gyara Jikinta tazo ta saka kayan Barci ta kwanta sai dai mai Tun tana ganin abun wasa wasa har ya Fice Tunaninta ta Fara rike ciki tana wayo Wayyo Allanta Tun tana ciki a Hankali har ya fito Fili Mama Dake falo taji Da Sauri ta shigo Ciki ganin Inteesar kan gado ahannunta kan cikinta Tana Birgima tana kuka Lokaci Daya sai ta Rude ta isa gareta ta Tarairayota Tana Sallami Cikin Kaduwa take fadin"Na shiga ni Amina Maryama meke damumki..? Meya sameki..? Inteesar na kuka Hannunta kan cikinta Tace"Mama ci..Cikina..marana ciwo..! Hankalin Mama ya tashi ta Rude Tana Fadin"Daman kina ciwon mara ne in zaki jini..! Kai Inteesar ta Dagamata Bata samu bakin mgana ba.. Mama ta rasa yadda zatayi Fita falo tayi ta Kira Sagir a waya Tana Fadamai Halin da ake ciki shi kuma Lokacin suna Tare da Imran awaje sai da yagama wayar ne yake fadamai Inteesar ce ba Lafiya Tuni yaji Hankalinsa ya tashi kamar yabi bayan Sagir din sai kuma ya kasa,Ya fara Safa da marwa a waje yana Jiran Fitowarsa shi kuma Sagir yana Shiga ganin Halin da Inteesar ke ciki yasa yace Mama ta sakamata Hijabi bari ya Sami adaidaita su tafi asibiti ta amsa mai da Sauri ta Bude Akwatin Inteesar ta dauko mata Wani jan hijabinta ta kamata ta sakamata. Shi kuma Sagir yadda yaga Imran ya Rude ne ya kara bashi mamaki bai ma Tsaya yaji wata mgana ba ya fara Tambayansa ya jikinta..?shi kuma ya Fadamai tana jin jiki Adaidaita zai sami su tafi asibiti da Mama kai Tsaye Imran yace basai Mama taje ba Bari su samo adaidaitan sai su kaita bai iya cewa komai ba Sagir sukaje bakin Titi suka sami mai Adaidaita zuwa Kofar gidansu Sagir din kana ya shiga cikin gidan ya Iske Mama ta shirya tana Jiransa Lokacin Inteesar din taji Sauki ta Daina Rike cikin,Nan ya fadama Mama ya samo mai adaidatan yana Waje ammh Imran yace basai taje ba Shi zai rakata su kaita tare . Mama tace taya zata barta su tafi da ita dukkansu fa Maza ne sai dai suje tare,Inteesar na jin haka tace ma Mama ta zauna saboda Dare zata iya Zuwa Insha Allahu jin haka yasa Mama bataso ba ta barsu suka tafi har Waje ta Rako Inteesar tana Rike da Hannunta,Mama dai taga Dare yayi kuma Inteesar mace ce Sagir Namiji ne Imran ma haka sai kawai ta ce bari ta Rufe gidan tare zasu tafi ba wanda yace mata wani abu.. Tunda Mama ta Rikota yake kallonta Bata ma iya Tsayuwa sai da ta Jingina da Bango Tana Halin ciwo ne ammh Ganinsa yasa taji wani Sanyi Mama ta kulle gidan ta Kamata suka Nufi adaidaita,Mama da Inteesar suka Shiga Baya Sagir da zai shiga bayan sai Imran yayi Sauri ya Shige shi kuma sai ya zauna agaban adaidaita Wani asibitin kudi Sagir yace mai adaidaitan yakaisu. Inteesar tana kan Kafafun Mama ne da Farko ammh da Ciwo yayi ciwo ta fara Mirginawa tana Rike da Cikinta Tana kuka tana Fadin wayyo Allah zata Mutu Tsausayinta ya kamasu Mama ta kamata ta fashe da kuka Tana fadin mai adaidaita ya yi sauri Imran kuwa yana Zaune ne kamar ya Ciro ciwon jikinta ya maida akansa Rabin jikinta yana jikinsa ne,domin ta kasa Zama waje Daya Hannunta Guda ya Rike gam yana mata addu"an samun Sauki acikin Ransa. Tana Halin ciwo ammh Rikons na Dabam ne Idanuwanta cike da Hawaye take kallonsa Cikin so da kauna mai Zafin data shigets bata sani ba... Koda suka karisa asibitin ta galabaita Suna zuwa aka amsheta ganin yanayinta Direct gado aka bata ma,aka sakamata Drip da allurai sai barci Lokacin ta samu sauki ba kamar yadda suka zoba,Likitan yace sai dai ta kwana sai zuwa gobe sai su sallameta agaban Mama da Sagir da Imran yayi ma Mama bayanin ciwon Mara ne ya Sarketa mai Tsanani In Jinin ya Zuba sosai zuwa gobe zataji Dama,ammh ya mata alluran zuwa Gobe in ta Farka zata wartsake. Dole Mama ta zauna ta kwana da ita Sagir da Imran sai 11pm suka koma Gida,Sagir ya Tsaya gidansu Imran ya wuce gida koda yakoma Abba da Ya yusuf basu iya Runtsawa ba Saboda susan baya taba kaiwa Dare kuma suna ta Kiran wayarsa bai Dauka ba Shi kuma yaga Kiran sai dai lokacin suna asibiti ne. Yana Dawowa Yusuf ya faramai Tambayan ina yaje..? Bai iya karya ba kai tsaye ya fada musu Inteesar suka kai asibiti bata Lafiya sai jikinsu yayi sanyi sosai Suka Tambayesa ya Jikinta..? Yace taji sauki tana chan asibitin Daganan ya shige daki Baida wata Natsuwa bai yi wani barcin Kirki ba sosai saboda Zullumi. Washegari Munari taji labari Hankalinta ya tashi ita da Anty Safiya suka tafi asibitin Da ya yusuf harda Abba koda sukaje Inteesar ta farka Taji Sauki sun iske Sagir yazo da ruwan da Zafi da kayan Tea Mama ta taimaka Inteesar ta wanke baki tana bata Tea. Hankalin Munari ya kwanta saboda Taga Inteesar tasamu sauki Mama tace likita yace anjuma zasu koma gida tunda taji Sauki,Imran yaki zuwa asibitin tunda yaji suna chan,to suna ma asibitin aka sallameta sai Yusuf ya kawosu zuwa Gida kana ya koma ya Dauko Abba da Sagir. Munari nan ta wuni gidan Mama tana kula da inteesar wacce taji Sauki Sosai Shiyasa tace ma mama kada ta Fadama su Daddy tasan Halinsa yanzu Hankalinsa zai tashi,Tana asibiti yana ta Kira mama ta Dauka Tace mai sun shiga makaranta ta bar Wayar agida,Sai davta dawo ta Kirashi Jin Lafiyanta kalau yasa Hankalinsa ya kwanta. Imran Tunda yaji an sallamo Inteesar sai hankalinsa ya kwanta bai Je ya Dubata ba sai dai ya kirata a waya yayi mata sannu da jiki yace ta Rika shan ngani ita duk kunya ya kamata Saboda kowa yasan Mtsalanta.. Monday bata samu zuwa makaranta ba sai Munari ne ta leka sai Ranar Talata data samu sauki sosai ta shirya suka Tafi tare. Ranar alhamis da suka tashi makaranta basu dawo gida ba gidan Ya Sadam suka sauka gaida Waleeda Data ke ta Zazzabi sunyi waya da Aneesan take fadamata sun iske taji Sauki waleedan har tana wasanta. Sunyi sallar la"asar sunci Abinci Daman koda suka zo Sadam baya Gida suna Shirin Tafiya sai gashi yazo Aneesa ta dinga Kiransa ta mtsamai sai yazo yaga Munari. Yau ta kara tabbatar ma kanta Munari ce ta Hoton nan saboda ta kara Duba Hoton wayar Sadam,Shine dai bai ganta ba saboda wayar nan tata bata tashi ba wata ya siya mata Shiyasa bai samu ganin Hoton ba,Daman Waleedan taji sauki ita Aneesan abun na Ranta ne yasa ta mtsa sai Inteesar din tazo ita da munarin don Sadam ya ganta da idanuwansa. Tabbas Shima daya ganta Sai da yayi Shock,ita kanta Munarin taji wani iri Data gansa,Sama sama suka gaisa dasu yaja Hannun Aneesa zuwa Cikin Dakinsu. Sai da suka Turo kofa kana ya Saketa Cikin Sauri tace"Kaima ka ga..! Bai bari ta karisa ba ya Fiddo da wayarsa yana Fadin"Aneesa kila Wahala ce tazo karshe..Tabbas wannan yarinyar jininmu ce..!. Yafada yana Binciko Hoton sai gashi ya gani Daidai Munari yayi Zooming yana nuna ma Aneesa lokaci Daya yana Fadin"Indai kuwa ba itace bace suna mugun kama..! Aneesa tace"nifa inaji ajikina itace..Ka duba kaga kammaninta duk da bata kai haka alokacin ba kamminta bai bace ba..! Sadam ya gyada kai yana Fadin"Meye sunanta..? Aneesa tace"Maimunatu..Suna Kiranta Munari..! Ido ya waro yana Fadin"kai..Kin manta Daman Daada tace Karamarsu ita ce taci sunan Mommy..Ina da kyakyawan Zato yarinyar Diyar Kawu Malami ne..! Aneesa tace"Nima ina da wannan Tabbacin Tun ranar dana fara ganinta..! Kansa ya dafe yana Fadin"Ina ne gidansu..? Kenan suna garin kano ba wanda ya sani..! Aneesa tace"Bansan gidan ba Inteesaar tace kusa da inda take zaune ne..! Wayarsa na Hannunsa yace"jeki falo ki Tsaida mun su bari na kira Sa"id a waya muyi mgana..! Tana Kokarin Fita tace"Shi kadai zaka Kirafa..Ka mu kira mu fada yazo ba Haka bane..! Kai ya gyada mata yana Fadin"Nasan Abunda nake yi Aneesa..! Daga haka ta Fice ta barsa yana Kiran Wayar Sa"id kira Daya cikin na Biyu ya Daga kiran ko sallamsa Sadam bai amsa ba ya Shiga Rattafamai abunda ke Faruwa. Yana zaune a office ne sai da ya Mike Zaune cikin Firgici yace"Sadam kada ku bari ta subuce muku.Tunda kuka Tabbatar da kammaninta da sunanta am Very sure itace.! Sadam yace"Nima ina Tunanin haka..ammh yanzu ya kake ganin za"ayi..? Sa"id yace"Ka kira su Kawu ne..? Sadam yace"Ba wanda na kira sai kai..! Da sauri yace"Yauwa..kada ka fadama kowa yanzu kada kabari su tafi su kadai ka Tsaida komai ka kaisu kada kayi sanya kasan yadda Zakayi ka Shiga Har cikin gidan nasu domin ka Tabbatar da abunda muke zato..! Sadam yace"Shikenan yanzu daman koda Aneesa ta Kirani zasu tafi..Bari na fita nace zan kaisu gida..! Sa"id yace"Good..Yadda ake ciki ina Jiranka sai ka kirani..! Daga haka suka yanke kiram Jikinsa na rawa ya Fice Saboda Rudewa Cikin Bedroom din ya manta da key din Motar sai da Aneesa ta shiga ta Daukomai nan yace shi da Aneensa da yara zasu kai su domin suga inda Inteesar ke zaune. Ba wani bata Lokaci Aneesa ta Sako mayafinta,waleeda na Hannun Munari Inteesar ta riko ma Waleed hannun suka Fice ta kulle kofar Falonta. Inteesar da Munari da yaran suna Baya su kuma suna gaba Sadam yana Driving yana kara kallon Hoton nan na wayarsa yana kara Kallon Munari ta Madubin Motarsa Har sai da ta Fara tsarguwa Tasbihi kawai yake acikin Ransa domin ya gama Tabbatarwa wannan itace Maimunatu diyar kawu Malami. Sa"id sai kiransa yake bai dauka ba Sai dai ya Turamai sakon suna Hanya ne basu isa ba,In sun isa komai kenan zai kirasa. Sun shigo gadan kaya Sadam ya Juya yana kallon Inteesar yana Fadin"Bari mu fara kai kawarki gida mu shiga mu gaisa da mahaifinta sai mudawo mu shiga inda kike zaune agaisa kafin mu wuce..! Inteesar tace"To ya Sadam..! Munari kuwa haka kurum taji gabanta na Faduwa kwata kwata bata yarda da zuwa gidansu ba sai dai ta kasa cewa komai. Tafe tafe Inteesar na nuna Hanyar har Kofar gidansu Munari ya Sadam ya Zuba Hon Iro megadi ya leko cikin mamakin ganin Mota ganin bata Yusuf bane Har ya Bude musu suka Sulala cikin Haraban gidan bai Daina mamaki ba. Imran dake duke a gaban mashin dinsa d yana gyara Wani Abu ne Daga kasa yaji Shigowar mota bai Damu Daya Dago ba azatonsa Yusuf ne shiyasa ya cigaba da Abunda yakeyi. A parking space sadam ya faka Motarsa suka Firfito koda ya Fito idanuwansa na kan Imran dake Duke so yake ya Dago da kansa yaga ko waye..!? Ita kuma Munari duk ta Tsure yau mai kwatanta Hannun Ya Imran sai Allah tunda ta gayyato wasu gidansu abunda ya tsana. Imran mganar Waleed yaji yana kiran Daaddy,yasa ya Dago da kansa Lokaci Daya yana Mikewa gabadaya Daidai Lokacin Sadam nata saitinsa suka Hada ido Hudu atare gabansu ya Fadi,lokaci Daya suka Zura ma juna ido Aneesa ma ta Juya tana kallonsa duk da ahoton ya kauda kansa hakan bai hanata ganesa ba. Imran ya taba Haduwa da Sadam Lokacin gaisuwan rasuwan su Anni a Dukku sau daya domin da suka zo gaisuwa basu kwana ba Shida Sa"id..!Yusuf ne ya sansu sosai Tunda suna waya lokacin sannan suna Haduwa in yaje Dukku duba Daada. Imran mamaki ne ya kamasa yana so ya Tuna Fuskar Sadam ya kasa..?sai dai yaji wani yanayi ajikinsa. Sadam kuma sunan Imran ne ya bace masa ya kasa kamawa sai kuma gwiwansa dayayi sanyi ganin yadda Imran din ya Hade rai bamai ma Nuna ya Taba ganinsa ba. Inteesar da Munari basu Fahimci komai ba yaran sukaja zuwa cikin Gidan Aneesa ta bara musu baya ta Kosa ta shiga gidan ta kara Tabbatarwa ko gaskiya ne duk da Shaidu Biyu sun nuna kansu. Wayar Sadam ce ta yi kara yana Dubawa Sa"id ne shima ya kasa Natsuwa Kashe kiran yayi ya Turamai sako..! *Sa'id ina kyautata Zaton Farincikin Daada zai dawo..Gamu aharaban gidan naga ma karin wani Shedan na Mutum daya sai dai ba Yusuf bane na manta sunansa..kada ka kirani sai na kiraka.* Daga haka ya Turamai kafin ya Dago Imran ya koma ya Cigaba da abunda yake yi. Ganin haka yasa ya Nufi cikin gidan yana Waigen Imran wanda ke Hangensa ta Jikin Mashin dinsa Haka kurum jikinsa ya basa wannan Dan"uwane duk yadda akayi. Sadam na shigewa Motar Yusuf na Shigowa Haraban gidan shima yayi matukar mamakin ganin bakuwar Mota Imran dake Tsaye ya rasa abun cewa da Yusuf ya Tambayesa Kallonsa yayi bai cemai komai ba bai Damu ba ya Dauki ledan Yalon daya siyoma Safiya zuwa Cikin Gida ya bar Imran na Tunanin kila yau komai zai Zama Tarihi. Sadam na shiga Falon ya iske su Aneesa da Inteesar zaune a Bisa kujerun falon da su waleed. Kallon Aneesa yayi kafin yayi mgna Aneesa ta Rigasa da cewa"Munari taje kiran Abbanta mu gaisa..! Jin haka yasa ya ja ya Tsaya yama kasa Zama Daidai Lokacin da Yusuf ya sawo kansa Falon da Sallama abakinsa. Sadam na Facing din kofar Shigowa ya Zurama Yusuf ido shima yana Shigowa Idanuwansa ya fada kansa. Atare suka Zaro ido Lokaci Daya kowa na nuna kowa cikin mamaki da al"ajabi suka ambaci sunan juna..! "Yusuf...! "Sadamm..! Suka Fada atare adaidai Lokacin Munari ta Fito Daga dakin Data shiga Bayanta Abba ne yana gyara Hulan kansa jin Munari tacemai yan"uwan Inteesar suka zo su gaisheshi. Sai dai ya Dakata da gyaran Hulan nashi Sanda Idanuwan Sadam suka kusa Fadowa akansa Saboda mamaki Aneesa ma ta Mike Tana kama baki Inteesar ma haka Kanta ya Kulle ita da Munari suna kallon kallon. Cikin Rawan baki Sadam ke nuna Abba yana Fadin"K...ka..kawuu..! Yafada cikin Rawan Murya dana baki Abba yayi jagale yana Bin Sadam da kallo Hawaye sun cikamai kwarmin ido kamar yadda na Yusuf suka cikamai Cikin wani yanayi Yusuf yace"Abba ka ganeshi..? Sadam ne Dan Wajen Inna Maimunatu..! Yafadi haka Daidai a kunnin Imran Daya bayyana afalon bayan kasa Natsuwan da yayi a Haraban gidan. *Janafty* 3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!* _(Our House)_ *Book1* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty��* *Bazan Rufe wannan Shafin Batare dana ambaceki ba,Godiya ta tayi kad'an na Furta miki Sisina Aisha alto da Hidimar da kikeyi dani da Rubutuna kin yi jimarin Posting din wannan Littafin Daga farko har zuwa yau din nan da muka kawo karshen littafi na Farko Nagode kwarai Allah ya saka miki da gidan Aljannah Firdausi Ameen*        *🅿�30* Abba da jikinsa ke rawa idanuwansa sun cika da kwallah suna shirin zubowa Lokaci Daya ya fara takowa Tsakiyar falon duka Idanuwansa suna Kafe kan Sadam kamar wanda ya warke makanta.. Cikin wata irin Murya kewa da Farinciki da kuka Abba ya kalli Sadam yana Fadin"Sadam...! Ya kira sunansa cikin wani yanayi Sadam da Hawayensa suka gangaro saman Fuskarsa yace"Na"am kawu malami..! Yafada yana wani kada kai Abba Hannayensa ya Budemai yana Fadin"Taho nan Sadam Taho naji Dumin ka..Taho na ji dumin wani Daga Cikin Ahalina yau..! Da gudu kamar karamin yaro ya Karisa ga Abba suka Rumgume juna Lokaci Daya yana Fadin"Kawu ina ka shiga muna ta neman ka..? Kowa ya shiga damuwa saboda kai..Daada kowa yaushe kuka take yi yau lafiya gobe babu duk saboda Rashinka..! Abba yaji Hawayen dayake ta Tarewa sun zobomai yayi Saurin Sharewa Lokaci Daya ya dago Sadam yana Fadin"Ban je ko"ina ba ina nan a kasata..Nayi nesa da gida ne saboda Wasu Dalilai ko bamu hadu ba daman Lokacin da Zan koma cikin Dangina yayi ba saboda kowa ba ko Saboda Daada da nike kwana ina tashi da ita..! Kada kai Sadam yayi Lokaci Daya yana Dauke kwallarsa Dagowa yayi suka Hada ido da Yusuf dayake sharan Kwallah Wajensa ya nufa yana Fadin"Dan"uwa Yusuf..! Lokaci Daya suna Rumgume juna Inran na gefe yana Binsu da kallo Fuskarsa bata bayyana Wani Hali yakeciki ba na Farinciki ne ko na bakinciki. Inteesar da Munari gabadaya sun Shiga Rudani sai bin kowa da kallo sukeyi ita dai Munari ta Fahimci Yau boye boyensu ya kare ne Dangin sun san inda suke ita kuma Inteesar ta Shiga Rudanin kada dai ace Munari yar"uwanta ce..?Abba shine Baffa Malamin da su Daddy ke wahalan nema Daada na Rashin Lafiya Saboda shi ammh take zaune dasu tsawon Lokaci bata taba Sani ba. Aneesa na gefe farinciki ya cikata Harta su Waleed sun natsu ganin yadda Abbansu ke kuka yana Rumgume da Yusuf,sun dau tsawon Lokaci kafin su saki juna Sadam ya Bubbuga kafadarsa yana Fadin"Shekaru uku ba kwana bane..Duk ka Sauya Yusuf..! Yusuf na Dariya yace"Kaima haka duk ka Sauya..! Dariya suka saka gabadayansu Abba na Gefe yana kallonsu Lokaci Daya yana karama Allah godiya daya sa Daada bata bar gidan Duniya ba Tana da Rayuwarta zai koma mata.. Sadam ne ya juya yana kallon Imran Lokaci Daya ya Karisa gabansa yana Fadin"Imran ko .? Yusuf ne ya bashi amsa ammh Imran Sai ya wani basar Kallon ma wani barayin yayi kamar ba dashi yake ba ganin haka yasa sadam bai Rumgumesa ba illah ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Dan"uwa kai bamu san ka sosai ba..Ko a da chan Yusuf ya fika son zumunci .! Kamar yana mgana da gunki haka Imran yayi mai Abba ya Kalleshi yana Fadin"Imran sadam ne dan Wajen Goggon ku Maimunatu ta Bauchi..! Dakyar ya iya bude baki yace"Na ganshi..!. Daga haka ya dauke kansa Sama Sadam bai damu ba ya jinjina kai aransa yana ayyana abubuwa Dadama kan Imran din . Inteesar ne data gama Shiga Rudani ta Kalli ya Sadam Tana Fadin"Ya sadam...Abba..!. Tafada Tana kallonsu dukkansu da Sauri Sadam ya Karisa gabanta ya Riko Hannunta yana Fadin"Inteesar baki gane su ba ko..? Baki ga Hoton da Daada tace a nuna ma kowa lokacin da mukaje dukku ba..? Inteesar cikin kosawa tace"Bangani ba meya faru..?kamin bayani ka sani a duhu naji kana cema Abba Kawu..Kawu malami kardai kacemin Baffa Malami ne..! Ta karishe fada cikin wani yanayi gabadaya sai kallo ya koma kansu harda Imran daya natsu yana so ya Fahimci wani Abu.. Abba ya Kallesu cikin mamaki yana fadin"Sadam..! Lokaci daya yana nuna Inteesar da Hannunsa,Sadam ya kamo Inteesar zuwa gaban Abba yana fadin"Kawu baku gane juna ba..Abba Inteesar itama yarka ce..! Cikin mamaki yace"Yata kuma..? Imran ya waro ido yana so ya Fassara mganar hakama Yusuf Munari kuwa Hawaye take yi na Farinciki koda ba"a Fadi komai ba ita ta san kaunar dake Tsakaninta da Inteesar ta jini ce. Sadam ya dauki hannun Inteesar ya saka cikin na Abba yana Fadin"Kawu Inteesar ce Diyar Kawu Mustpaha na kaduna..! Abba yaji wani sanyi jiki ya kamashi Lokaci daya da Sauri ya damke hannunta yana Fadin"karamar yarinyarsa..Wacce taci sunan Daada..! Sadam ya dagamai kai yana fadin"Itace kawu..Inteesar ce kana Tare da jininka ammh baka sani ba..! Abba ya Ji hawayensa suna Kokarin kara Zubowa ya Rike Duka Hannuwan Inteesar yana fadin"bamu rike zumunci ba sosai ba...Ace yau na hadu da Diyar Mustpaha na wani Lokaci Tana Tare damu ban ganeta ba..Sai dai Wlh har ga Allah Tun ganin Farko da nayi mata naji wani abu acikin Raina ban taba mata kallon bare ba Daya na Dauketa ita da Munari Ashe Ashe itama Diyata ce..! Yafada cikin Raunin Murya da Sauri Inteesar da itama ta fara Hawaye tace"Baffa....! Tafada kafin ta fada jikin Abba tana fadin"Nima ina jin haka duk sadda na kanga sai naga kamar Daddy na..Yanayin mganarku da komai iri Dayace..In nazo gidan nan ji nake kamar ina Gidanmu in ina tare da Munari kamar ina Tare da yar"uwata uwa daya uba Daya..Ashe Gidanmu ne ku din Jinina ne Wayyo Dadi Abba..! Take Fada tana kuka Shima Abba Hawayen yake yi Shi da Sadam da Yusuf Da Aneesa da Kukan Farinciki ya Kamasu Lokaci Daya,Imran ne kadai ke Tsaye idanuwansa ba alamun Fitar kwallah sai dai yadda abubuwan suka Juye ne suka sakashi Tsintar kansa a wani Hali Tabbas Jini yafi Ruwa kauri,ko shi yasa Yafi damu da Inteesar fiye da kowa..? Ashe ita din jininsa ce..! Anty Safiya Dake gefe tana sharan kwallah Tun dazu ta fito ba wanda ya Lura da ita Hayaniya taji ta Fito tana Kwance afalo acikin Shashenta sai ta iske Abun Farincikin daya samu wannan Gidan ayau na cikon Abu Dayan da ya Rage gidan ya cika ya zama Gida irin kowani gida. Yusuf ne ya hangota da sauri ya isa gareta ya Rumgomta yana fadin"Noor Boye boye ya kare..Danginmu sun same mu..!. Tana rike dashi Tana Fadin"Alhamdulillah..Duka Burikana sun cika my dear..!. Take fada cikin Farinciki. Inteesar na kuka ta dago kanta tana Kallon Munari cikin kuka tace"Dilla ke baki zo muyi kukan tare ba. ? Tafada Lokaci Daya Hawaye da Dariya da sauri Munari ta wani taho da Sauri ta Fada Jikin Abba dukkansu ya Hada ya Rumgume sai ga Hawayen Farinciki sharr. Sadam Wayarsa ya zaro Tun dazu Sa"id ke kiransa bai dauka ba cikin Farinciki ya kirasa yana kiransa Ringing daya ya daga da Sauri yana Fadin"Sadam ya ake ciki..? An dace kuwa. !? Sadam na kallon Abba yana fadin"Sa"id an dace gani ga Kawu Malami..Alhamdulillah gani cikin gidansu Zagaye da iyalansa..! Sa"id ya mike da Sauri yana Fadin"Finally Alhamdulillah..! Bai ma jira cewar Sadam ba ya Katse kiran Murta ta sa ya rasa nayi,Komawa yayi ya zauna yana Hamdala afili kafin kuma ya Fara Tattara kayansa yau komai Dare sai ya Shiga kano Sadam ya kara Kira yana Dauka yacemai kada ya bar gidan nan yanzu zai tashi daga Office yana zuwa Gida zai taho kano ayau din nan bai iya cemai kada ya Taho ba domin ya kamata yazo din. Abba kuma yana Rike dasu Inteesar Hawayensa yaki tsayawa yana Kaicon wannan Zumuncin na wannan Zamanin da har yakai mu ga Lalacewar da jininka na tare dakai ammh baka sani ba. Waje aka samu aka zazzauna Saman kujerun falon Abba ya fara Tambayan Sadam sauran yan"uwa yana Fadamai kowa Lafiya Imran na gefe bai Zauna ba ya Harde Hannayensa saman Kirjinsa yana jin duk abunda ake fada sai dai kalma Daya Tun bayan na Dazu bai kara Furtawa ba bama wanda ya Damu dashi sanin Hali Sadam ne ke yawan kallonsa Lokaci bayan Lokaci yana mamakin shi wannan Haka yake.? Abba ne ya kalli Aneesa yana Fadin"Wannan mai Dakin ka ce..? Sadam yace"Eh Abba..ga yara na nan Waleed da waleeda. ! Abba ya mikama su hannu yana Fadin"Ku taho nan wajen kakan ku da baku sansh ba..! Basu da bakunta suka karisa Wajensa ya Daukesu asaman jikinsa. Munari da Inteesar na gefe sun rike hannun juna baki yaki Rufuwa Safiya na Cikin su da Yusuf cikin Farincikin da bazasu misalta ba,Shiyasa tunda ya Fara ganin Inteesar wlh jininsa ya bashi Intadin kamar jininsu ce,bai taba mata Wani kallo ba ashe jini jini ba na waaasa ba. Abba na kallon Waleed yace"Nasan sanda aka Haifi babban..Lokacin Maimunatu ta Kirani take fadamin Matarka ta Haihu wacce muka je cikin garin Azare muka karbo Auranta..! Sadam na dariyan Farinciki yace"Anyi haka kawu tabbas baka manta ba..! Abba na Mirmishi jin dadi yace"Ina Yayanka Sa"id da sauran kannen ku mata..? Kayya zumunci sai a hankali duk ban sansu ba..! Sadam yace"Sa"id na Garin Dutse Abba chan yake aiki yana zaune da matarsa da ya"yansu uku..Karamar kanwarmu Hafsah tana Wajensa saboda Tana karatu nan Federal Univestiy dutse. ! Abba ya jinjina kai yana Fadin"Ku kiramin yan"uwana inaso na Hada dasu yau..Gobe ina so naje ni da duka Iyalaina naga Daada na Roketa gafara..!. Imran na gefe ya kalli Abba irin Kallon nan nasan za"azo wajen bai dai ce komai ba Sadam ne yace"Kawu saboda Murna ban ma kira kowa ba Sa"id ne kadai shima yace yana Tafe yau din nan bari na fara Kiran Mommy na Fadamata..! Inteesar dake gefe tace""Ni kuma bari na Kira Daddy na fadamai..!. Dukkansu atare suka Kira wayar Sadam na Kira Mommy ta Daga Cikin Murna tana Fadin"Sadam yanzu nake shirin kiranka gama wayata kenan da Dan"uwanka yana gayamin wani Labari mai dadi kaga Yaya Malami da iyalansa..? Tafada cikin wani Shauki Saukewa wayar yayi daga kunnensa ya saka Speaker yana Fadin"Wlh Mommy gani ga kawu ga yusuf ga Imran ga Inteesar Mommy ga Matar yusuf din dan wajen kawu malamin har yayi Aure .! Inna maimunatu tana kwallah tace"Hadani da dan"uwana naji muryansa..!Sadam bai yi gaddama ba ya mikama Abba wayar ya Karba yana Fadin"Maimunatu Autan Daada..! Tana jin muryansa sai kuka tana Fadin"Ya ya Malami ashe kana da Ranka..? Ka samu lafiya Allah abun godiya..! Cikin wani yanayi yace mata"Na warke Maimunatu..Na samu Lafiya da ikon Allah..!. Inna maimunatu tace"Allah mun gode maka da kakaddara Haduwa Tsakanin daada da Ya malami..Nima bazan iya zama ba bari Alhaji ya shigo na gayamai yau din zan taho kano..! Da sauri Abba yace"A"a Maimunatu kada ma ki fara Dare yayi..Ki bari insha Allahu gobe bazan kara kwana agarin nan ba sai a dukku gaban Daadarmu sai mu hadu achan.! Inna Maimunatu na sharan kwallah Tace"Shikenan Ya malami daman Sa"id yace min ya kira Kawunshi kabiru na Abuja yafadamai shima yace zai kamo Hanya in ya Samu jirgi shikenan in kuma bai samu ba zai yi Tafiyar Mota..! Abba na Dauke Hawayensa bai so su kara zuba yace"Barrister..Yaya kabiru ashe baya Fushi dani..! Da Abba ya Fadi haka kamar Imran ya Mutu haka yake ji,baima san sadda Abba ya gama Wayar ba sai da ya tsinci Muryan Inteesar tana mgana da Daddynta. Alhaji Mustpha shigowarsa Gida kenan Shida Basheer Inteesar ta Kirashi Kokari ma yake ya shiga gida yayi alwala ya samu Sallar mangariba Domin yaji ana ta Kira Basheer kuma ya Biyosa gida ne saboda akwai Lissafin da zasu yi yaji kiran Inteesar. Suma shiga Falon ya Daga Kiran irin yadda yaji yanayinta cikin Murna yasa yace"Inteen Daddynta me ya Faru ne najiki cikin Annshuwa..? Inteesar na kallon Abba tace"Daddy Albishirinka..! Yana zama kan Daya daga cikin kujerun falon yana Fadin"komai Intee na take so shine goron albishir dinta..! Yafada Daidai Lokacin da Umma ta iso Falon dauke da Ruwa da Kofuna Basheer na gefe zaune yana Latsa waya a Hannunsa.. Inteesar tace"Daddy gani ga..Baffa Malami gani kusa dashi..! Daddy yaji mganar asama adaidai Lokacin kuma Ana ta Kiransa a waya Call Waiting,. Cikin Dan daburcewa yace"Wane kikace Intee Daddy..!? Da sauri ta kara Fadin"Baffa malami Daddy gashi ma kuyi mgana..! Tafada tana mikama Abba wanda ya karbi Wayar yasa a kunni lokaci Daya yana Fadin"Mustapha Baban Basheer Mijin Salaha..! Kamar a mafarki haka yaji muryansa da Sauri ya mike jikinsa ba inda baya rawa,har yana Ture Umma Dake duke gabansa Tana Tsiyayamai ruwa. Suka Mike atare suna binsa da kallon mamaki. Cikin In ina yace"Yaya Abbakar..? Kai ne da gaske..! Abba na Mirmishin jin dadi yace"Nine Mustapha..Abun kunya Inteesar na tare damu na tsawon Lokaci ban gane yata bace..! ? Yafada abun na karamai ciwo Daddy daya yi mutuwar Tsaye yace cikin son Tabbatarwa "kai..kai ne Baban Munari kawarta..!? Abba yace"Ni baban Mai sunan Daada ne..sai dai in kaine Baban Mai sunan Autan Daada..! Sai ga Daddy na Hawayen Farinciki cikin murna yake kallonsu Umma yana Fadin"Wlh shine Salaha Basheer..Babanka ne ya Malami ne fa muke mgana dashi..Ya malami fa Alhamdulillah Alhamdullilah..! Su Abba suna ji daga alamu ma ya manta yana waya ne ya Gama Rudewa Inteesar ta karbi wayarta ta kashe nan take ta Kira Mama tace ita da Sagir suzo gidansu Munari hankalin Mama ya tashi ta Zata wani abu ya samu Abba Sagir na Kofar gida Yana kokarin Daura alwala ya shiga Sallah Tunda an kira Mama ta Fito da Hijabi a Rude tana Fadamai Halin da ake ciki Sallar da bai shiga ba kenan ya Rufa mata baya zuwa gidansu Imran. Su Umma mamaki ya cikasu da Daddy ke maida Zencen ya kasa Zama Umma tana ta maimaita Allah gagara Misali Daman Munari yar"uwan Inteesar ce..? Koda tace ramar data fara ganin Hotonsu tare sai da taga kamarsu Data fada kuma ba wanda yabi ta kanta. Suna cikin haka Baffa Kabiru ya kira Daddy ashe shi yake ta Kiransa yana waya da Inteesar yana Dagawa Cikin Farinciki ya gayamai labari mai Dadi sai yaji yana Fadamai Cikin Farinciki Daddy yace"Wlh nima har mgana ma munyi da ya malami Barrister...Inteesar ta Hadani dashi Allah sarki Rayuwa..! Baffa Kabiru Daga chan bangaran yace"Yanzu haka ina hanyane ban sanu jirgi ba Tafiyar mota ce ni da Ma"u ce,kaima kayi kokari ka Tashi yau din bana so mu kuskure ya sake bace mana kuma ka da ka kira Daada so nake mu bata mamaki har Bintalo na gayamawa yanzu muka gama mgana da ita..chan zamu kwana Gobe in Allah ya kaimu sai mu hadu da kowa da kowa a Dukku..! Daddy yace"Yanzu kuwa zamu kamo Hanya..! Daga haka suka yanke kiran Daddy na Kallon Umma yana Fadin"Salaha Shirya..Ko kuma ke Salaha ki bari gobe Direba ya taho daku keda Hauwa da yara mu a hadu a dukku..Kai Bashir kira matarka ka Fadamata bari na shiga ciki na fito yanzu zamu dauki Hanyat kano ba sai gobe ba..! Baima Tsaya Sauraransu ba ya Shige ciki kamar zai kifa saboda Sauri. Umma ta Kalli Basheer tana Fadin"Kai duk tare zamu tafi..Nima bazan iya Zama sai gobe ba kira matarka mu biya mu daukesu ayi tafiyar gabadaya..! Basheer yace"Umma anya Zata iya..? Kunsan yanayinta ko zamu Kyaleta kawai mu muje..! Umma ta kada kai tana Fadin"Kuma fa hakame..Shikenan kirata ka Fadamata sai muje din..! Daga haka ta bi bayan Daddy shi kuma ya Dauko wayarsa Domin ya Kira Hauwa ya fadamata Halin da ake ciki. Mami Asma"u ta kalli Baffa Kabiru bayan ya gama mgana da Daddy Tana Fadin"Yanzu daman duk wannan uban Wahalan neman da kuke ma wannan bawan Allah yana kano zaune abunshi bbu abunda ya Dameshi..!. Take fada Lokaci Daya tana kara gyara zaman gilashin dake idonta suna Kishingide a bayan Motarsu Kirar prado Direba na gaba yana jansu. Cikin wani yanayi ya kalleta yana Fadin"Bari kawai. Ni kaina naji abun haka..Ace yana nan kusa ammh ya kasa neman kowa..? Kuma daga alamu he is Fine now..! Mami Asma"u ta tabe baki Tana Fadin"This is Selfish yana chan yana Jin dadinsa ya manta da ku..Alhalin kuna nan baku huta ba wajen nemansa..! Baffa Kabiru yace"Saboda Daada nake komai kuma kinga all the blemming akaina Daada ta maidashi so yanzu zan yi amfani da wannan damar na Daukesa na maida mata..! Da sauri tace"Shikenan kuwa..Ammh sam bai kyauta muku ba..! Shidai bai kara ce mata ba sai Dannan Wayarsa yake yi Khamis ya Tura ma Sako ya kira Wayarsa bai Dauka ba.. Umaima da Sajida suna gida suka barsu Umaima ce ma taso zuwa Uwar ta Hana Sajida kuma bata manuna Concern dinta ba she is telling cewa Test zasu fara karatu take bata da Lokaci. Mami Asma"u ita da kanta tayi Ra"ayin zuwa saboda tana so taje taga komai kuma Komai za"ayi so take ayi shi agabanta bayan ikonta da izzanta na akwaita da son gulma da kure Mutane. ***** Gidan Abba cike da Mutane sai godiyar Allah haka Mama da Sagir suka zo sukaji Abun al"ajabi Sagir yace Wlh ranar daya fara ganin Daddyn Intee sai da ya ga yamai kama da wani sai dai ya rasa ta ina zai kama kamannin,Ashe ashe suna kusa da Danginsu basu sani ba Mama sai mamaki take ashe Abba yaya yake wajen Mijin kanwarta Salaha Allah ne abun godiya,duk da Sun shiga rudanin Dalilin wannan lamarin sai dai basu ce komai ba suna da Tabbacin yadda wannan ya fallasa to sauran Dalilan ma Zasu jisu in Lokaci yayi. Sai murna ake da Farinciki ana maida Zence,Sadam kuma Tuni ya Hau WhatApps ya shiga Group din Marigayi Alkali Dukku ya bada Sanarwa da gargadin kada wanda ya Kira Daada ya fadamata sai Gobe kowa da kowa za"a hadu a Dukku. Basu an kara ba sai dai sukaji kiran Sallar Isha"i kana zaman ya tashi Matan suka Shiga ciki domin gabatar da Sallolin da suka Subuce musu mazan kuma suka Dauro alwala suka Ja Sahu anan Falon Yusuf yayi musu limanci Abba da Sadam da Sagir da Imu suna Binsa abaya wanda Har zuwa wanna lokacin bai ce komai ba yana so ne sai an zo gabar da zai tanka yanzu ba Lokacin mgana bane. Bayan sun idar ne aka sake Fitowa aka Hadu afalo ana jiran sauran Baki,saboda Murna ba wanda ya Nemi abinci sai Imu daya Shige daki ya Busa abarsa,abu daya ke sashi Farinciki zuwa Biyu ayau dinan Shine na Farko yaga Inteesar Cikin Farincikin da bai Taba gani ba na Biyu yau din Ranace da zai Rama wasu abubuwa da suka Shude shekarun baya yana Fitar da Hayakin Taba yana Mirmishinsa na saman Lebe Lalle ya yi Shuru shekaru uku da suka gabata ammh awannan gabar ba wanda ya isa ya hanashi mgana koda Abba ne da kansa. Safiya ta Kira Mommynta tana Fadamata abunda ke faruwa jin haka yasa Hajiya Mero murna tana farinciki ko banza Alhaji Alhassan zai ji kunya Daga yadda Safiya ta bata Labari Dangin yusuf din ba mutaenan banza bane suma wasu ne Ita ta roki Hajiya Mero da ta saka yan aiki suyi musu abinci mai yawa saboda baki abama Direba ya kawo da Sauri Hajiya Mero ta amsa mata suna Sallama ta Fita zuwa Kitchen tana bama masu aiki Umarni kafin ta afito Ta Nufi Dakin Tasleem ta Fadamata wannan abun Farincikin. Sa"id shi ya fara iso Tunda shi yafi kusa,yana Shigowa ya Kira Sadam shi yamai kwantace cikin Lokaci sai gashi ya ya iso shi da Yusuf suka Fita Tarbansu. Sa"id ya Rumgume Yusuf suna Murnan ganin juna,da iyalansa yake tafe Harda Hafsah dataji Labari tace sai tazo itama. Dukkansu suka Dumguma zuwa Cikin gidan sai ga Sa"id sun Rumgume da Abba suna murnan ganin juna Fareesaatu ma ta gaisheshi ya amsa yana Daukan ya'yansu na Karshe ne Abubukar takwaranshi kafin ita faresan ta Karisa Wajen matan ana ta gaisawa Hafsat suka Rumgume juna da Inteesar,bayan ta gabatar da junansu da Munari suka Rumgume suna Murnan Haduwa da juna Anty Safiya Tana ta ina ta sakasa dasu,mama da Sagir suna nan zaune suna ganin ikon Allah.. Sa"id kam shi sai da ya Rumgume Imran ammh yaki tabasa shi baima Tsaya Wani lura da lamarinsa ba. Akwai salloli agabansu yasa Safiya taja Fareesan zuwa Shashenta Sa"id kuma Da Sadaam Yusuf ya sauke su Tsohon Bedroom dinsa Ba Dadewa sai ga Direban gidansu Safiya da kololin Abinci manya manya Daman Tun tasowarsa Mommy ta Kira ta fadamata to da iro ya shigo yana Fadin an kawo sako tasan kwanan zencen iro kuwa sai Raba ido yake tun sanda Bakin Motoci da Mutane keta shigowa gidan nan Abunda bai taba gani ba so yake yaji ina ba"asin Lamarin..! Anty Safiya dasu Inteesar suka Taimaka mata suka Shishigo da kololin Abinci zuwa Kitchen da suka ce a zo aci abinci ba wanda yabi takai ana Jiran isowar su Daddy. Karfe tara da rabi na Dare goma Saura su Daddy suka shigo Anguwan gadon kaya,Dayake susan gidan Zuwan bai musu Wahala ba. Abba najin Dan"uwansa ya iso baima Tsaya ba ya fice zuwa Haraban gidan Tunda ya fito Daddy dake gaban Mota ya kyalla ido ya gansa ya balle Murfin Mota ya futo suka Nufi juna suka Rumgume sai kuka,Sauran duk suka Biyosa abaya banda Imran daya na chan Dagachan gefe... Yusuf da Basheer suka Rumgume juna suna Murna Inteesar ta Rumgume Umma cikin Murna kafin suka Rankaya zuwa cikin gida.. Abba da Daddy suna Rike da Hannun juna ganin kamar mafarki ne nan aka Shiga gaisawa da juna Umma ta Rike Mama suna kara mamakin wannan al"amarin ta Rumgume Munari tana jinta kamar Inteesar,suka gaggaisa da Su Sadam da matansu da Ya yusuf da Anty Safiya Imu na gefe chan Saman Dining ya Harde Hannayensa saman Kirjinsa yana kallon kowa Daya bayan Daya ba ma wanda ya Damu dashi. Sai da Daddy ya tambayesa ne kana aka fara Waigen waigen nemansa chan aka gansa Zaune Daddy bai jirasa ba ya Mike ya isa garesa yana Fadin"Asshe ashe..Imran din da Inteesar ke bamu labari ashe jininta ne yayanta ne Salaha..! Gabadays kowa sai mamaki daman Inteesar na basu Labarin Imran ne Ita kuma sai kunya ya kamata ta Noke bayan Umma Tana Leken Imran da Daddy ya Rumgume abun mamaki yadan Saki Ransa kadan sai dai suna Hada ido da Inteesar ya Hade rai bayan ya Harareta aranshi yana ayyana Rainin da yarinyar nan tamai. Daddy ko awa daya basu yi da isowa ba Baffa Kabiru suka iso suma da kwantancen suka iso Gidan Abba. Tundaga Haraban gidan Mami Asma"u ke karema komai na Gidan kallo acikin ranta Tana fadin ashe yama samu wani jin dadin Rayuwar duk da yabar komai nashi abaya. Shima Abba da Daddy da sauran Mazan suka Fito Tarbansu Baffa Kabiru yayi mamakin ganin Abba Shar dashi Cikin Koshin Lafiya ya Zata zai gansa duk ya lalace ne saboda Halin Rayuwa hakama Mami Asma"u take kallonsa kamar bashi ba ya kara Kiba ya samu jin dadi ya bar Mijinta na Wahalan nemansa. Duka suka Dunguma zuwa cikin Falon a karo na ba adadi. Baffa Kabiru yayi mamakin ganin Yusuf da Munari da Imran dey look so nice daga gani basu da Wahala ko daga Gidan da suke ciki Dukkansu sun gaisheshi banda Imu dayayi kamar ma bai ganesa ba Yana daga chan inda yake Zaune Hannayensa a Harde yana Kallon kowa sama da kasa. Mami Asma"u sai bin kowa take da kallo Mamaki bai kasheta ba sai taga Matar Yusuf Safiya abun ya kara bata Haushi Bata Damu da yaran dake Wajen ba ta Bude tace"Ba shakka..Abban Sajida kuke chan kuna Wahalan nemansa bakwa barcin kirki Daada kuma na chan Hawan jini ya kamata tana kwana kuka Saboda Tunanin dan"uwanka Shi kuma yana nan ya samu Sabuwar Rayuwa da Sabon gida.ba shakka..! Take fada kanta Tsaye tana gyara Zaman gilashin idanuwanta Kowa sai da ya Kalleta Abba ya Murmusa yana kallonta yace"Barrister Asma"u Tafida kina nan da Halin nan naki kenan..! Kallonsa Tayi cikin ido kafin tace"Dr.Abubakar Hamisu Malami ashe baka manceni ba..! Tafada Lokaci Daya tana dan Sakin Dariya ganincyadda aka Sako mata Ido Mirmishi ya saki Cikin natsuwarsa yana Fadin"Ban manta dake ba..! Yafada Lokaci Daya Daddy da Baffa Kabiru suka Bisa da kallo komai nashi bai sauya ba Hatta mganar Abba da Tafiyarsa kana gani zaka san baida Hayaniya Ballatana Fada. Imu na gefe yana jin Abunda Mami Asma"u tace aransa yace anzo wajen ya ganeta Sarai duk cikin matan Baffaninsa yafi saninta da kowa saboda Lokacin da Su Anni suka Rasu suna Dukku duk zuwa da ita ake zuwa ta kuma Taya Mijinta aibata Abba agabansu abaya in sunyi sunci riba wannan karon sai ya Tabbatar musu da ba wanda zai kai Labari.. Kafin suci abinci sai da su mami Asma"u suka gabatar da Salollin dake kansu aka baje afalo aka ci Abincin da Hajiya Mero ta aiko dashi Abinci kala kala sai wanda ka Zaba. Bayan sun gama ne yara yaran suka Kwashe komai zuwa Kitchen aka kara zaman Hira Abunda yabama Mami Asma"u mamaki Imu ne ganin kowa yaci abinci bandashi da Daddy yayi mgana sai Abba yace haka yake bayason cin Abinci Tana gani daya tashi Zai shiga Dakinsa kamar Hararanta ma yayi kafin ya shige. Tasan yaron abaya da Tsaurin ido bata Taba Zaton Abunsa yakai haka ba. Isu isu ne zaune afalon Mama da Sagir tun zuwansu Daddy ba Dadewa sukayi musu sallama zuwa gida mama tace sai da safe. Ana ta Hiran yaushe gamo Inna Bintalo ta kira har sunyi mgana da Abba ita da megidanta suka Rabu kan sai gobe in sun hadu a Dukku. Baffa Kabiru ya gyara Zama yana Fadin"Malami ka samu Lafiya sosai..? Abba na Mirmishi yace"Alhamdulillah..! Baffa Kabiru ya jinjina kai yana Fadin"Alhamdulillah duk da akwai mganganu da yawa a bakina ba Lokacin Fadansu bane yanzu sai In allah ya kaimu gobe mun isa gaban Daada..! Abba ya gyada kai baice komai ba Baffa Kabiru ya cigaba da Fadin"Gobe sai ka shirya kaida iyalanka..Damu gabadayanmu zamu isa Dukku da yardan Allah..! Kamar daga sama sukaji Muryansa cikin Amo da Cikar Kaushin kamar yadda ya saba. "Ba inda Abba zai je..Kuma muma bazamu mu biku ko"ina ba..! Gabadaya falon aka juyo ana Kallon Barayin Inda mganar ta Fito. Imran ne tsaye a kofar dakinsa ya Sanya Hannunsa guda daya cikin Aljihun bakin wando dake jikinsa Hannu Daya kuma Tana kan bakinsa yana Rike da Karan Sigarinsa. Bai damu da yadda ido ya dawo kansa ba ya lumshe manyan idanuwansa kafin ya Bude su tas kan Baffa Kabiru Lokaci daya Hayakin daya zuga ya Fesar dashi ta Hanci ta baki zuwa Saitin Fuskar Baffa Kabiru. Gabadaya Falon jikin kowa yayi sanyi,ido kowa ya Fiddo waje cikin mamakinsa da ganinsa acikin wannan Halin Banda Abba da ya yusuf da suka Dafe kai cikin Tsantsan Takaichi da bacin rai. *Alhamdulillah Godiya ta Tabbata ga Allah Subuhanu Wata"ala daya bani ikon Fara wannan labarin kashi na Farko gashi yau yazo karshe Ina godiya ga duka Masoyana da suka Taru suka nunamin Soyayyarsu kan wannan Labarin nawa Nagode kwarai Allah ya bar zumunci ina godiya ga Tarin Zaurinka da suke jimarin Bin wannan Labarin da kayattacen Sharhin su nagode kwarai Allah ya Biyaku da aljannah Firdausi Ameen* _Nayi muku labarin Gidanmu Kashi na Farko kyauta sai dai kashi na Biyu na kudi ne kuyi hakuri kila hakan bazai yi ma wasu daga cikin ku Dadi ba sai dai daman chan bai kamata Labarin Imu yazo duka a kyauta ba,Acikin wannan Labarin ko Rabinsa ma bamu yi ba,kuma bama muce komai ba akwai Sauran Rina akaba Kina Bukatar son ganin wani al"amari ne zai Faru a Falon gidan su Yusuf..?Imu zai yarda su bi su Daddy zuwa Dukku..?in sun isa mezai Faru..?Mami Asma"u tana gefe ga Sajidan wacce ta kyasa Imu batare datasan ba wanda ya Tsana sama da iyayenta ba,Kun Hango Badakala da Chakwakiya a falon Daada..?yaya mtsayin makauniyar soyayyar Intee da Imu..?Imu zai gane yana sonta..? Zai sauya saboda ita..?Na Tabbata Imu kuka sani ayanzu baku san shi a anihin BANKER IMRAN ABUBAKAR MALAMI ba,na Tabbata zaku so ganin Imu ya Juya Harshensa Cikin Tsaddacen Turancinsa kuna kuma son gani yadda Soyayya zata kai su shida Intee in sunyi aure ya zasu yi Zaman auransu..?kada ku manta akwai Khamis fa agefe Daya gashi Daada Tayi alkawarin Daidaita kan Zuru"arta kafin ta bar Duniya kada na Cika ku da Surutu Akwai abubuwa Dadama da Zasu Faru mai bukatar cigaban wannan Tafiyar Saboda Ku masoyana da kuma yanayin Rayuwar da muke ciki zaku biya Kudin karatu akan #300 Kachal zaku turo kudin karatu ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB,,Sai aturo shedar biya ta wannan Lambar 09069067488,masu katin waya kuma zaku iya Turo hoton katin ku ta wannan Lambar 090690674488,Zan Fara posting din Book2 da Zarar Mutane 100 sun yi payment Insha Allahu ina godiya Masoyana kuma ina Maraba da ko akoda yaushe._ *Tanque* *08/03/2022* *Janafty* *Intelligent writer"s asso* 3/22/22, 23:13 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�1* *Ki biya ki karanta cikin Salama da Aminci,Ki sani ki kara sani Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata wannan Littafin na kudi ne kan Naira 300 kachal ki biya ta wannan asusun bankin 0552179550 gtb ko kuma a Tuntubi wannan Lambar kai Tsaye 09069067488* Bai damu da yanayin kallon da ilahirin falon suke binsa dashi na mamaki ba banda Yusuf da Abba da su munari wadanda suka sansa suka san zai iya aikata abunda yafi haka. Mami Asma"u cikin mamaki da al"ajabi ta juya tana kallon Baffa Kabiru bata samu bakin mgana ba,Imran ya kara gyara tsayuwa Hannunsa guda daya na cikin aljihun bakin wandon dake jikinsa dayan hannunsa kuma yana rike da karan sigari kansa Tsaye idanuwansa basu Rusuna ba yake bin Fuskar kowa da kallo kai Tsaye Fuskarsa bata bayyana Fara"a ko sakewa ba,ya hade ran ya dakuna Fuska kamar an aikomai mala'ikun mutuwa. Daddy ya kalli Baffa Kabiru cikin mamaki shima ya kallesa,Kafin su maida kallonsu kan Abba wanda ya Dafe kai cikin Takaichi. Imran ya kara Kausasa Muryansa yana Fadin"Eh da gaske nake yi..ba inda Zamu je bama bukatar zuwa ko"ina wannan shine gidanmu..! Yafada yana Kai sigarin bakinsa ya zuka ya sake Fesar da Hayakinta Cikin kwarewa. Yusuf ne ya mike da Hanzari ya isa garesa Lokaci daya yana Fadin"Imu..Imu saurareni..! Kallonsa yayi ido cikin ido ganin haka ya sa Yusuf yace"Ka koma Dakin ka wannan ba mganarka bace..Mganar Abba ne da yan"uwansa bakai bama ko mu da muke gaba dakai bai dace mu ce wani abu ba..So ka koma cikin dakinka don Allah..! Yana mganar ne Imran namai kallon Tara saura kwata gira daya ya Dagamai cikin Salon rainin wayau kafin yace"Oh Really..Sai yanzu ne su sakansa shi dan"uwansu ne..? Meyasa lokacin dayake bukatar Taimakonsu suka Juyamai baya..?meyasa alokacin basu nuna ma Duniya su din Ahalinsa bane suka yasar dashi,suka Kyalesa suka Rika aibatasa da kaddaran da bashi ya Dora ma kansa ba wani kokari ko Himma sukayi wajen Sauya wannan al"amarin nace ka Fadamin wani kokari sukayi..? Yafada cikin Tsawa Ransa ya fara baci Idanuwansa sun sauya Launi Tuni jijiyoyin kansa suka Mike Radau suna Harbawa. Gabadaya kowa shi ya zuba ido yama kallonsa yana Sauraransa,Daddy ya sunkuyar da kansa aransa yana Fadin anzo wajen dayake ta gudu Tuntuni Baffa Kabiru kuwa mamakin Rashin kunya irinta Imran kadai yake,Matan kuwa kowa sai mamaki Mami Asma"u kuwa bawai ta kasa mgane bane mamakin al"amarin ne ya isheta Abba Take kallo Tana ayyana Abuubuwa da dama ganin yadda ya zauna yayi Shuru Yaronsa na Diban albarka ya kasa mgana. Yusuf dayasan Imran in ransa ya baci zai iya Fadar komai yasa ya Rikesa Gam yana Fadin"Is ok muje ciki don Allah Imran..! Kwace jikinsa Imran yayi yana Fadin"Wlh ba inda zan je..ai da Farko bam ce komai ba saboda ba"a kawo gabar da zan yi mgana ba yanzu ne Lokacin da zan ce wani abu..Daman Tuni ina jiran wannan Ranar da wani Daga cikinsu zai zo yace Mu koma Gida to bazamu koma ba..Naji dadin da kuka zo kuka ga Abba ya warke yasamu Lafiya yanzu kun Tabbatar da Ko da ku ko bako zamu iya Rayuwa..?kun tabbatar da Abbanmu ba Mahaukaci bane kaddarace ta Fadaamai kuma cin jarabawa da Daukan kaddara duk na Allah ne wanene acikin ku zai iya jure daukan Girman Raunin da muka Dauka? Abba ya rasa Anni mata take garesa Uwar ya"yansa ta rasu ko gawanta bai gani ba Ya rasa ya"yansa uku aLokaci daya acikin ku waye zai iya daukan girman wannan Raunin..?waye zai iya Tsayuwa da kafafunsa in wannan Jarabawan ta Fadamai ehe?Masu cewa Abba yaki yarda da kaddara su in haka ta faru dasu zasu iya daukan..? Masu cewa Abba ya zama Mahaukaci su in haka ya faru dasu waya sani ko zasu kashe kansu ne..? Masu ce mana muma bamu da amfani muna kara Raunana Abba su din sun manta Muma Uwa muka rasa da Ginshikin Ahali har uku..?sun manta muma muna sonsu ko sun manta muma muna da Zuciya da kwanjin in muka rasa namu mu nuna?ko shikenan mu ba Mutane bane Dabobbine da zamu yi wannan Babban Rashi kuma mu dawo muna Dariya Lokaci daya..?meyasa baku jamu ajiki kun Lallashemu ba..? meyasa baku nuna mana gata da soyayyah ba..? Meyasa baku rika nuna maana amfani Hakuri ta Lallashi da nasiha da ban baki ba..? Wlh har yau har gobe ina jin kunar kalmar Mahaukaci da wannan Mutumin ya Kira Abba dashi ina jin zafin hakan zafin daya kan kusa kona Kirjina in na Tuna Nayi ma Daada Uzuri yafi sau saba"in saboda Raunin Tsufanta ya bayyana kuma kamar yadda muke da Rauni haka take dashi itama Tana neman Mai Tallafamata ne in nayi ma Baffa Mustapha uzuri bai wuce Uzurin ya kasance mai Sanyi Hali kamar Abba kuma bai taba aibatamu saboda Kaddaran data Fadamana sai dai ina ganin Laifinsa na Hana Baffa Kabiru Aibata kaddaranmu na Hana sa Zagin Abbanmu da kiransa Mahaukaci Laifinsa na kin gayamsa gaskiyan kan Abunda yake Aikatawa abunda baitaba Tunanin yaya mu ya"yansa zamu ji acikin kirjinmu ba Ko ka manta Cewa Yadda ya"yanka suke awajenka Haka na kowa suke..?ka taba Tunanin ya ya Nauyin mganarka zata Kuntatamana..? Ka taba Tunanin yaya ya'yan Dan"uwanka zasu iya juran wannan Tozarcin naka..?baka taba Tunani ba Shiyasa kake komai naka kanka Tsaye shine yau zaka zo kace Abba ya bika ka kaima Daada shi Saboda tace ka dawo mata shi..? To ba inda Abba zai je Gari na wayewa kowa ya watse ya kama gabansa nan ne Gidanmu yanzu duk wanda ke son ganinmu sai dai ya tako yazo kamar yadda kuma kuka zo..! Ya karishe Fada yana Sauke Numfarfashi Cikin zuciya Idanuwansa sun kara sauya kala har sun cika da kwallah Saboda Tuna Abunda ya faru Baya,Gabadaya Falon kowa jikinsa yayi sanyi masu Saurin kuka Irin su Munari har ta Fara Inteesar na Lallashinta itama kwallar take ganin yadda Duk kafiyar zuciya iri nta Ya Imu yau Rauninsa ya bayyana Su kansu su Sadam jikinsu yayi sanyi basu da sani kan Abunda ya Faru Lokacin ammh indai Hakane Tabbas ba"a kyauta musu ba kuma suna da Ikon suce wani abu a wannan gabar. Baffa Kabiru ransa ya baci saboda kara kara Imran ya ambaci sunansa ya Nuna dashi yake cikin bacin rai ya mike yana kallon Abba Lokaci Daya yana fadin"Malami a gaban idonka kama ji kana gani D"an daka Haifa yana neman cin Zarafina ka kasa ceewa komai..? Yafada cikin mamaki yana kallon Abba Kafin Abba yayi mgana Daddy ya Rigasa cikin Kwantar dakai Yace"Barrister mganar gaskiya Imran gaskiya ya fada..Daman Ranar da nake ta Tsoron zuwanta kenan Ranar da wani Daga cikin ya"yan Yaya Malami zasu Tuhume mu da Laifi da kuskuran Gudumuwarmu wajen Nesanta kansa da yayi damu ina ta jin Tsoron wannan Ranar..Kada ka manta ko Zuwan mu dukku na Karshe kiran Daada kenan kuma ta fada ta kara Laifinmu ne laifin mu ne Ya Kabiru kaima ka sani..! Yafada cikin wani yanayi Umma ta Jinjina kai Batayi mgana ba,Sanin duk abubuwan da suka Faru,Baffa Kabiru yana da kaso mai tsoka kan Faruwar komai bai daukan abu da Muhimmanci indai bai Shafi matarsa da ya"yansa ba bazatace dai komi baa Saboda ba Huruminta bane bata taba mgana Kan Lamarinsu Daddy indai bashi ya tace wani abu ba. Mami Asma"u da mamakin kalaman Imran suka Daskaran da ita ta kasa wani Motsi tafa san gaskiyane saboda ai Da ita ake komai da gudummuwarta a Lokacin tana gayamai bai kamata ya zauna yayi ta Wahala da Abban ba ai ba yaro bane kuma baida ilimin sanin Mutuwa ce da zai zauna yana wani abu kamar mara Hankali Tana nunai ai da gangane saboda su ya rika Hanasu Harkokin gabansu da irem iren wasu maganganu alokacin koma meya faru da saka Hannunta ammh Dayake ita Macece mai son kanta bata iya ganin hakan ba sai take ganin kawai ana neman cin Zarafinsu ne. Mikewa tayi Tana Tafa hannu Cikin mamaki kafin tace"Au har dakai Baban Basheer..?Yau da bakin ka kake Bude baki kana Fadin Abban Sajid bai kyauta ba shi keda laifi kai ka cire kanka..? To Tunda shi keda alhakin komai meyasa alokacin daka Fahimci haka kai bakayi kokarin gyara komai ba tunda kai ka Fahimci shi ya bata komai..? Tafada tana kallonsa bai yi kaurin baki ba yace"Kin ji sanda na ce shi kadai keda Laifi Barrister Asma"u..? Cewa nayi dukkanmu munyi laifi ya sani na sani Kowa ma ya sani Tunda Daada gaban duka ya"yanmu ta fadi haka..! Mami Asma"u ta dagamai hannu Cikin Fusata tana Fadin"Bana son jin komai Mustapha..ai ka riga ka gama mganarka Abban Sajida kaga abunda nake Fada maka ko..?ai daman na fadamaka kune kuka damu dashi shi kam bai damu ba yana nan yana Rayuwarsa Kama gani Harda dan Shaye shaye ma ya samu cikin ya"yansa..Baya bukatar kowa..Ka taso mu tafi Abuja batamana Nisa ba bayadda zan zauna ina ji ina gani ana Tozarka ba..! Tafada Tana isa garesa Lokaci Daya ta kamo Hannunsa Shi dake tsaye ya kasa mgana saboda baida ta cewa,shi kanshi ai yasan bai kyauta ba to shima Selfish bazai barsa ya iya Daukan haka ba da kuma Ego irin nashi Daman dagashi har matar tashi They are d same. Maimakon ya nuna mata hakan datace bai dace ba sai ya kada kai yana Fadin"Yes hakane abunda ta Fada..Daman duk abunda nake yi saboda Daada ne..Tunda kuma shima Malamin ya nuna yana bayan mganar Da"nsa bani da tacewa..Ma"u muje..! Yafada suna Kokarin barin Falon kowa ya Bisu da kallo baki sake Abba Dai na Zaune duke da dakai bai cekomai ba Har wannan Lokacin. Daddy ne ya mike yana Fadin"Haba Barrister ya zaka Biye mata..? Itafa macece ya kamata ka zauma mu Fahimci juna..! Ko juyowa basu yi ba suna Shirin barin Falon Imran ya saki wata Dariyan Basawa Cikin Kaushin Muryansa yace"Ka kyake su tafi Baffa..Daman ai ba komai ya kawosu ba sai son kai irin nasu abunda kuma suka zo dominsa sun ga ba Nasara Abba bazai je ko"ina ba..! kalamansa yasa gabadayansu Juyowa kowa sai da ya jinjina mganar Umma ta kada kai aranta tana fadin yau an samu mai daidai da Asma"u Sa"id da Sadam suka kalli juna,hakama Matansu suna ayyana Tabbas Tsaurin Idanuwan Imran sun wuce Tunaninsu. Mami Asma"u ce ta nuna kansu tana Fadin"Mume kake kira masu son kansu..? Lalle shaye shayen ka yayi maka Rana..Tunda har kakiramu masu son kai.kuma kake Tunanin Daada ta tako kafarta ta Biyoku lalle Kwayarka bata Fadamaka daidai ba mara kunya..! Imran ya Dakuna Fuska yana kallonta ido cikin ido Tabarsa ya zuka Hayakim ya sakesa ta Hancinsa harta Kunni cikin kallon sama da kasa yace"Ni kin ji sanda nace Daada tazo nan..? Ai ni ina girmama Daada..Ko bakomai Daada ta nuna Rauninta kan abunda ya same mu,nifa da ku nake bada Daada ba, kada kuma ki kara Kirana Mara kunya bake kika Haifeni ba mganar kwaya kuma in ma na sha ai ba da kudin Lauyoyi na siya ba ko..? Kowa ido ya zaro da jin kalamansa Yusuf ya Dafe kansa cikin Takaichi Mami Asma"u taji ta Muzanta ta kalli Baffa Kabiru wanda yake bin Imran da kallo yana Tunanin Tsegerancin yaron zai saka ma ya iya Zaginsu kila ma Har malamin ya gagaresa Tunda gashi ya kasa mgana. Yana neman hanata mgana ta Kwace hannunta ta fara taku zuwan gaban Imran tana nuna kanta Lokaci Daya Tana Fadin"Ni kake fadama wannan mganar..? Kasan wacece ni..? Irin kallon sama da kasa na Rainin nan yayi mata Irin to ke din wacece cikin Gadaransa yace"To ke din Wacece..? Ai b..! Bai karisa ba ya yaji tsawar Abba ta karade Falon cikin bacin rai yace "Kai IMRAN...! yafada yana Huci Huci mai zafi Tun dazu ya kasa cewa komai saboda Yasan tankwasa Imran ba abu bane mai Sauki Daman yasan tabbas sai haka ta Faru,sai dai an kawo gabar da Dole yayi mgana yana da Tabbacin da bai Tare Imran ba cemata zai yi kedin ai ba uwata bace..Zai iya Zaginta Duk mganarta yana da amsarta shi ya Haifi Imran yafi kowa sanin baya da Shayi ko Tsoro ba Asma"u ba ko Baffa Kabiru zai iya kallah yace mai ai ba Ubansa bane shi ballatana ita. Imran ya wani kalli Abba a karkace kafin yace"Abba daka koma ka Zauna..Na dade ina sauraran mganarka ammh yau kam bazan saurareka ba..! Yana Fadar haka ya juya wajen Mami Asma"u Lokaci daya ya saka Hannunsa ya Murje Sauran Taban Hannunsa Data rage da Wutar da komai ya saki Sauranta a kasa Hannunsa duka Biyu ya maida cikin Aljuhun wandonsa yana Fadin"Arm kika ce ma me..? Yauwa na tuna bansan ko wacece ke ba ko..? To ni ina ruwana da saninki Tunda ke ba Uw....! Abba ya kara Dakamai Tsawa yana Fadin"Wlh in ka kara cewa Tak anan Wajen sai naci Mutumcinka imran kaji ma na Fadamaka..! Yafada cikin kakkausan Murya yana nuna shi da yatsa. Imran ya dago yana kallon Abba Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska. Mami Asma"u tayi wiki wiki kamar mara Gaskiya Dariya kowa ke kunshewa aciki ganin yadda tayi,Basheer da Sadam suka kalli juna suna Mirmishi Inteesar kuwa sai da ta Dara Tana Rufe bakinta aranta tana godema Ya Imu yau taga mai mganin iskancin Mami Asma"u saura Diyarta Tsagera mara kunya,Hatta Umma abun yayi mata dadi kanta na kasa tana Dariya kasa kasa wato mganin Mami Asma"u sai tsageru irin su Imran Daddy na gefe bai ce tak aransa yana fadin in bata kama girmanta ba ai yaron zamani zai tayata kamawa. Abba ya karisa wajen su Baffa Kabiru yana Fadin"Ya kabiru don Allah kuyi hakuri ku dawo..Bai kamata ka Dauki wannan abun da zafi ba..wajena kuka zo ba Wajen Imran ba kuma Imran bai isa ya hanani Abunda nayi Niyya ba..Kuma bai isa ya Raba jinin dake Tsakaninmu ba Ya kabiru..! Baffa Kabiru ya kada kai yana Fadin"Ammh kana ji yana neman Zaginmu ni da iyalina..! Baka iya dakatar dashi ba..? Abba yace"Ai na Dakatar dashi Baban Sajida..kuyi hakuri..! Kafin ma Baffa ya samu bakin mgana ta tareshi da cewa"Ka tareshi lokacin Daya gama Tozarta mu ba? Wannan gabar Daddy ne yayi magana yana fadin"Yaya ya kamata ka Dakatar da Asma"u kan saka baki cikin mganar nan ba Huruminta bane..nan wajen fa akwai mutane kuma bataji kowa ya tanka ba..Mganace Tsakanimu iya mu nan manya bai kamata matarka tana Sako baki ba..! Su Sa"id dake gefe suka kada kai alamun gaskiya ne. Mami Asma"u tabi Daddy da Harara Tana Fadin"Sai nayi shuru ana cin Zarafin Mijina ko..? Ni Asma"u nasan Ciwon kaina kan Mijina da ya"yana zan iya yin komai domin sune iyalaina anan duniya..! Daddy yace"Musan wannan kowa anan ai Ya"yan nasa da matarsa sune iyalansa kuma don su ma muke fita nema ammh bai kamata kina Tsallake in da ba Huruminki ba..! Ta bude baki zatayi mgana Baffa ya Rike mata Hannu ammh duk da haka sai da ta Furta cikin bacin rai tace"Ammh shi Tsagerun yaron naku daya Tsoma baki sako cikin mganar kukayi..? Daddy zai yi mgama Abba ya Hanashi ta Hanyar tareshi yana Fadin"Mustapha ba girman kabane..Kyaleta don Allah Yaya kabiru Asma"u don Allah kuyi hakuri ku dawo ku zauna ba domin kowa ba saboda girman Allah da kuma Girman zumunci..! Yafada yana Hada Hannayensa alaman Roko Imran Dake Tsaye yaji Haushi ya kamashi Karamin tsaki yaja kawai bai ce komai ba. Jin haka yasa Baffa Kabiru ya kalli Mami Asma"u yana Fadin"Muje mu zauna..! Zatayi mgana ya hanata bayan ya Girgizamata kai dole ta Bishi ya koma in da ya tashi ya zauna itama Haka sai Harare harere take yi tana waige waige,kowa yayi kamar bai ganta ba. Suna Zama Abba ya koma ya Zauna Kafin yayi mgana Baffa Kabiru ya Rigasa da cewa"Malami Imran Shaye Shaye yake yi..? Yafada yana kallon Abban Imran Dake gefe kamar yace"Eh ko zaka iya Daukan mataki ne..? Sai dai ba Halin mgana saboda Abba ya hanasa ammh Kallon kafa fara cikani yake ma Baffa kasa kasa Yusuf na gefensa bayaso ya bar Wajen domin Imran bazai damu da ya Zubar da Halin nashi ba. Abba ya dan Murmusa Kafin yace"Imran baya Shaye Shaye Yaya..Taba kadai nasan yana sha..! Baffa Kabiru yace"Taba..? Kaidai ita kagani ammh daga ganin yanayinsa bazai rasa shan kayan maye ba Allah ma ya kyauta bayashan giya..! Yafada yana kallon Imran din daya ji kamar ya Durama Baffan Ashariya. Abba yace"Eh bazan yi shaidansa ba..Sai dai nafi kowa sanin Imran duk cikin Ya"yana shi kadai ne bayamin karya..Yana fadin gaskiya komai Dacinta Inda yana shan wani kayan Maye bilahil azim kaji Rantsuwan musulaimai sai na fara sani..! Baffa Kabiru ya jinjina kai bai kara mgana ba Abba ya gyara zama yana Fadin"Yanzu dai ya mganar zuwan mu Dukku gobe..Ina so naje naga Daada na roketa gafara..! Yafada cikin wani yanayi Baffa Kabiru ya dan zakuda kafada kafin yace"Aini na gama mganata..Gobe nace daga nan mu isa Dukku bana so kowa ya Fadama Daada sai dai ta ganka kawai ammh naji Yaron ka yace bazaka je ba kila ita Daadan kake so tazo ta sameka..! Abba ya girgiza kai yana fadin"Ban isa nace haka ba Yaya..! Baffa Kabiru yace"D"an ka ya yanke maka Hukunci kuma baka iya cewa komai ba..! Imran da ransa ya gama baci ya Budi baki yace"Ba Hukunci bame haka ce zata Faru ba inda zamu je..! Abba ya Mike ransa yana Fadin"Imran..Imran me na gayamaka..? Cikin Dakuna fuska yayi yana Fadin"Kace kada na sake mgana..! Abba yace"Shine kuma saboda ka Rainani ka sake yin din ko..? Imran yace"Ammh Abb..! Rufemin baki kafin Raina ya baci na tsinke ka da mari..! Abba ya katseshi cikin Fusata kafin ya Cigaba da fadin"Ina Ruwanka da mganarmu.?kana sako baki cikin mganar manya yaya fa Yayana ne Uba yake gareka ya isa dani Ubanka bama kai ba..! Imran ma kunkuni acikin ransa yana fadin Tab ni dai ba Ubana bane wlh. Kowa yaga Motsin bakinsa Hatta Abba sai dai bai bi takai kada ya Matsa ya fada da karfi kowa yaji ya kuma san ba abu bane mai kyau ya fada ba. Cikin Kaushin Murya Abba ya Nunashi da yatsa yana Fadin"To kul na sake jin kayi mgana anan wajen..Mganar Tafiya Dukku kuma da yardan Allah Gobe zamu tafi dukkanmu dani da kai da Yusuf da Munari da Matarsa In kaga dama kabiyomu in kaga dama kada kaje..! Yafada cikin Fushi Imran yabudi baki yace"Fine..ni tunda bakace Dole naje ba Allah ya kiyaye hanya..! Yana fadar haka ya juya zai koma Dakinsa Abba ya rike baki cikin mamaki kafin yace"To na fasa..Wlh sai kaje! Imran ya Juyo cikin mamaki yana fadin"Abba..! Yace"Eh sai ka je Umarni ne Daga ni Mahaifinka in kuma ka Sauya wani Uban ne zan gani..! Yana gama Fadar haka ya koma Wajen Zamansa Ransa na baci. Imran kamar zai yi mgana Ya dago ido keman suka Hada Ido Hudu da Inteesar kai ta girgizamai tana Lamgwabe kai alamun kada yace komai batajin dadin Fadan da Abba kemai yana sata jin wani iri. Shi kuma Saboda ita bazai iya cewa komai ba Idanuwanta suna da kaifi a gareshi yasa ya juya kawai ya Shige Dakinsa ya bango kofa. Abba ya jinjina kai kawai bai ce komai ba ya juya yana kallon Baffa Kabiru da Daddy yana Fadin"Kuyi hakuri dashi..Haka yake sai fatan Allah ya shirya..! Ameen kawai sukce ba wanda ya kara mgana Abba ne ya mike yace su Daddy su tashi su shiga Dakinsa sa tattauna achan sauran matan kuma Safiya ta kwashi gayya zuwa Shashenta Inteesar da Munari da Hafsah suka tafi Dakinta Yusuf kuma yayi ma su Basheer jagora zuwa Dakinsa na baya. Shi kuma sai ya yanke Shawaran kwana Dakin Imran tunda yana da Tabbacin ko giyan wake yasha bazai Tura wani Dakin Imran ba. Shashensa ya koma ya iske Safiya ta bama Kowa wajen kwanciya Bedroom dinta ta sauke su Aneesa. Dayan kuma ta Sauke Umma da Mami Asma"u wacce ke ta wani shan kamshi Umma dai sai dariya acikin ranta to shan kamshi me ke da yaro ya gama Tsage miki gaskiyarsa. Imran na Kwance yana fama da Nauyin Umranin Abba bashi kuma da yarda zai yi ya Tsalleke mganar sai Mami Asma"u dayake Tunanin sai yayi mata kyakyawan zuwan da zata gane Waye shi zata kiyayesa dauka take ita wata ce..? Shi ko Baffan mijin nata ba ganinsa yake da wata kima ba ballatana ita karan kada Miya. Yaja tsaki yafi sau ba adadi shi kadai kafin yaji Shigowar,Yusuf dago kai yaga waye zai shogomai daki sai yaga Yusuf da kayan barcinsa da Blanket da Safiya ta kawomai Kallon Irin lafiya yabi shi dashi Shi kuma Yusuf yana ganin irin kallo yayi Fuska ya ijiye bargonsa ya shiga Tiolet ya sauya kaya ya fito ya isa gaban Madubi ya Fesa Turaran Imu yazo gefensa ya Kwanta yana fadin"Wash..Nagaji..! Kallon mamaki Imran yabishi dashi kafin ya Mike Zaune yana Fadin"Miye haka..!? Ina dakin matarka..? Yusuf na kwance yace"Da baki aciki..Ko cikinsu kake so na shiga na kwanta..! Karamin Tsaki Imran yaja kafin ya tashi ya Haye saman kujeran Dake Besdroom din ko mgama bai kara ba. Yusuf yayi dariya ya kara Ware kafa da Jiki yana fadin'Yauwa zan sakata na Wala wlh..,! Ya fada yana satan kallon Imu dayaji kamar ya fitar da yusuf Daga dakin shi baya kwana da wani akan gado takura yake yi juya baya yayi kawai baice komai ba Yusuf na kallonsa yana Dariya kasa kasa. *11/03/2022* *Janafty..* 3/22/22, 23:13 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�2* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Da asuba gabadaya mazan suka tafi sallar asuba a masallaci,Imran yayi ta nuku nuku har sai da suka tafi suka barsa kana ya taho daga baya daman dasu ne bayasan jerawa yusuf daya san Halin dan kayansa bai ko bi ta kansa ba ganin jiyan bai yi wani barcin kirki ba Farkawa Goma sai yaji motsin Imran yana sakin Tsaki shidai bai bi ta kansa ba ya bararraje yana ta kwasan barcinsa Hankalinsa kwance. Da suka Hadu da Sagir a masallaci Yayi mamakin ganin Imran bai hada Sahu da Ahalinsa ba Layin baya yaje abunsa,kuma ana idar da Sallar shi ya Riga kowa ya fita,Fuskar nan a Hade kamar wanda aka aikomai da wani mumman sako da asuban Fari. Sagir ya tsaya sun gaisa da su Abba yaga Baffa Kabiru ya kara Jinjinama kansa Lalle su Imran din yan Dangine gaba da baya. Koda suka koma Gida Imran ya Shige Dakinsa ya kulle ya Haye gadonsa Yusuf dariya ta kamasa Daman duk Saurinsa kenan bai damu ba ya Shige Dakinsu Sadam suna Hira Abba ma Dakinsa suka Shige suka cigaba da Tattaunawa Tsakanin yan"uwan da suka Fito Daga Jini Daya sai Allah. Mata matan kuma suma suna Sallar asuba basu koma barci ba suka Fito zuwa Kitchen Safiya da Tawagar yan matanta Inteesar,Munari da Hafsah,Sai su Aneesa da Fareesatu da suka ce suma bazasu zauna ba,sai suka mikama Mazan nasu yaran nasu su kuma suka Fada Kitchen suka Fara Kokarin samar da abun karin safe da Wuri tunda akwai Tafiya agabansu. Ruwan Tea suka Fara Dafawa wanda yaji Citta da kayan kamshin Shayi sai Suka Fere dankali suka soya da kwai suka kuma yi pancake,Safiya ta bada Shawaran suyi kunu da kosai Saboda su Abba nan da nan kuwa daman Tana da garin kunun da Mommy ta aiko mata dashi,suna da Sauran Nama a Fridge da kayan ciki suka Hade su sukayi Ferfesu kada su bar gidan zuwa Dukku kafin su dawo ya Lalace. Soyan kosan ya zama na Karshe ne bayan sun gaggama komai,Safiya Da Aneesa suna tajera komai Cikin kololi ita kuma Fareesatu tana ta Jera Mug,da Filet filet da Fork iya adadin mutanen da zasu yi Amfani dashi. Inteesar da Munari da Hafsah sune ke wajen soyan kosan,inteesar na dagachan gefe saman Cabinet din kitchen din ta Haye daga Sama Sanye take da Rigar barcin munari doguwa mai Ruwan madara,mai taushi sai dai saboda Munari tafi ta kiba sai Rigar tayi mata yawa kadan karamin mayafi ne a saman kanta ta dan Ratayeshi. Hafsah ce ke gaban Kaskon Suya ita kuma Munari na ta faman buga Kullim kosan suna yi suna Hira Jefi Jefi. Ba wanda yaji Shigowarsa Saboda gabadayansu Hankalinsu nakan aiyukan da sukeyi ne kuma suna Hira kuma Dayake Sallamar nashi iya Saman lebensa ne ba wanda ya Jisa. Anty Safiya ce ta ganshi Lokacin Dayake Bude Fridge ya Dauko goran Ruwa mai Sanyi yana sanye da Jallabiya mai ruwan madara,wacce bata kai kasa ba sosai Fararan kafafuwansa masu cike da gargasa suna Waje ne. Ganin sun Hada ido da ita yasa yace mata"Ina kwana..! Yafada yana dan Daga idanuwansa yana Karema wadanda ke Kitchen din kallo ta kasan Idanuwansa. Safiya tayi mirmishi Lokaci Daya Tana Fadim"Lafiya lau Imran mun tashi Lafiya..? A saman lebensa ya amsa daidai Lokacin da suka Hada ido da Inteesar wacce ta Kuramai ido tana kallonsa cike da wani Shaukin da bata san dashi ba,Kowa ya juyo yana kallonsa ganin haka yasa Munari ta gaisheshi Hafsah ma haka su Aneesa ma suka gaisheshi ba domin ya isa ba sai Domin yana da kwarjini da cika Fuska uwa uba kuma Oga Imu ne da kansa ai baza ka jira sai ya gaisheka ba.. Tundaga gaisuwar Farko bai kara amaawa kowa ba ganin haka Inteesar taki gaisheshi,Sai ma wani lamgwabe kai datake yi tana kallonsa Shi kuma Gabansa ne ya Fadi ganin saman kirjinta yana waje ne,Kuma Rigar bata da wani kauri ga Shatin saman Nonuwanta nan ta waje Jikinsa ne yaji ya fara rawa yasa ya juya zai Bar Kitchen din dauke da goran Ruwan a Hannunsa. Daman Inteesar tana ta gefensa ta bangaran Fita ne,ita bata sani ba yazo fita sai ta zuro kafarta ta taba mai Cinyarsa da sauri ta janye tana kallonsa kankance idanuwansa yayi yana kallonta kafin yace cikin Sanyin Murya."Ke kin raina ni ko..?kowa ya gaisheni ammh ban dake ko..? Noke kai tayi tana yar dariya kafin tace"Ina kwana..!Mirmishi kadai yayi na gefen baki yana Ficewa Daga Kitchen din bai ce komai ba. Yana Fita Munari da Hafsah da suka ga komai suka Juyo suna kallon Inteesar dake Dariya kasa kasa suka kalli juna suna rike baki tana juyowa suka Hada ido da ita,Ganin yadda suke kallonta yasa ta bata rai ta wani Hura Hanci Dariya suka saka Harda Tafawa ita da Munari Hafsah tayi ma Munari Rada a kunni tana Fadin"Yarinyar nan akwai munafuncin datake Boye mana..! Hafsah tace"Barta..Kuma zasu dace da Masoya..! Suka kara Kyalkyacewa da Dariya Inteesae ta tsargu ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"Anty Safiya ga su Munari nan basa aikin da kika saka su suna ta Gulmana..! Anty Safiya ta waigo Tana Fadin"Kuyi dai ku gama lokaci yana tafiya..! Da toh suka amsa ita kuma Inteesar tana yi musu gwalo,su kuma suna ta Hararanta tana Dariya sama sama. Cikin Lokaci suka gama komai su Inteesar suka je sukayi wanka Domin sunce bazasu iya Karyawa basu yi wanka ba,jin haka yasa suma suka Shiga Domin yin wanka suyi ma yaransu kafin su Abba su fito. Karfe 9:00am na Safe kowa ya Hallara a Falon saboda Breakfast,An shimfida Katuwar Darduma anan Tsarkar falon su ka jera komai asamanta. Sai da kowa ya Hallara banda Imu,Har an fara karyawan Daddy ya Dago yana kallon Yusuf kafin yace"Ina Dan"uwa yake Yusuf..? Yusuf na Kurban Tea dinsa yace"Baffa yana Cikin dakinsa..! Ya kada kai yana Fadin"Meyasa bai fito ya karya ba..? Yusuf yace"Bai cika cin wani abu da Safe haka ba kila sai chan da Rana..! Kada kai kawai yayi bai ce komai ba Mami Asma"u na gefe aranta tace gwara hakan ma Domin Tun abunda ya faru jiya Tsagerancin yaron yayi mata Tsaye a saman kanta. Inteeesar dake gefen Hafsah zaune ta Dauko Wayarta ta Shiga Messages ta Turama Imu sako. "Ya imu kafito kayi breakfast..! Ba dadewa ya maido mata da amasa. "Bana jin yunwa..am ok..! Inteesar na ganin haka ta Turamai da Sauri. "Saboda ka cika cikinka da Hayakin Sigari ko Ya Imu..!? Sai da yadan jima kafin ya bata amsarta,Tama kasa cin kosan dake gabanta Hankalinta na kan wayarta. "Eh..! Kawai yace mata Mirmishi tayi tasan bazai mata karya ba Tunda yace Eh to yasha ne,sai ta Rubutamai. "Kana so ka mutu ne Ya Imu..? Da sauri ya maido mata amsa wannan karon. "Eh in na mutu Who care..!? Tana ganin haka sai da gabanta ya Fadi da Sauri ta Rubutamai. "Ni mana..Zan ta kuka nadaina cin abinci har nima na mutu..! Yana kwance ne yaga sakonta sai da ya Mike zaune yana sosa goshinsa afili ya Furta yarinyar nan akwai Rigima. Amsa ya bata da cewa"bazaki mutu ba..! Tana ganin haka da sauri ta maidamai da amsa. "Zan mutu mana indai kai ma ka Mutu na daina ganinka Ya Imu..! Sai da ya dade bai Bata amsa mata ba har ta Fara sarewa sai ga sakonsa ya Shigo "Wayace miki zan mutu yanzu..? Oya eat ur Food bana son shagwaba am not in d mood..! Tana ganin haka sai da tayi Mirmishi akallah dai tasakashi yayi mgana batayi kokarin kara Turamai komai ba sanin Tunda yace baya cikin Mood din bazai kara cemata komai ba Tana kallon Wayarta Tana Mirmishi ita kadai Hafsah data Tabo Munari Tun dazu suna ta kallonta ta dago suka Hada ido Hararansu tayi kafin ta Boye Wayarta cikin karamin Hijabin Dake Jikinta,Su kuwa me zasu yi in ba Dariya ba Har sai da kowa ya Juyo yana kallonsu Daddy dake lura da Inteesar tun dazu bataci komai ba sai Danna waya take yace"Intee ijiye wayar nan ki Karya..! Kanta a kasa tace"To Daddy..! Lokaci daya Tana Hararan su Hafdah dake mata Dariya kasa kasa. Basu wani bata Lokaci wajen Breakfast din ba,kowa ya tashi su Hafsah suka Tattara komai zuwa Kitchen suka fara wankewa,Su kuma su Anty Safiya suna ciki suna Shirya Tunda ance kowa ya shirya nan da 11am zasu dauki Hanya. Suna gama wanke wanken suka Gyara Kitchen din suka koma Daki Domin Shiryawa Munari ta kalli Inteesar Tana Fadin"Intee ya zamu yi da School yau..! Inteesar tace"Ya kuwa..? in mun dawo zamu yi covering din inda aka wucemu..!. Munari ta gyada kai alamun gamsuwa Inteesar ta kalleta tana fadin"Sai naje gidan Mama na Dauko kayana..! Munari tace"Basai ki saka nawa ba..!. Inteesar tace"A"a bazan iya ba sun min yawa salon na Dinga yawo aciki..! Hafsah ta saka Dariya ita da Munari Inteesar ta Hararesu bata kara cewa komai ba. Sai da ta jira su Munari suka Shirya tsab Munari ta Hada kayanta cikin karamar akwati kala Biyu da kayan barci Tunda basu san yaushe zasu dawo ba Inteesar tace su hada kayansu Waje daya Shiyasa suka Dauki akwatin kayan zuwa gidan su Mama su dauko na Inteesar su tsaya ta Shirya achan Tare da Umma suka Tafi zata leka yar"uwanta. Suna zuwa gidan Abun mamaki suka Iske Sagir shima cikin Shirinsa na Tafiya basu Shiga mamaki ba sai da sukaji Mama na fada musu Imran ne ya Kira Sagir yace su Shirya su tafi Dukku Tare. Umma dariya kawai tayi bata da tace akan Lamarin Imran ballatana Mama. A gurguje Inteeesar ta Shirya Cikin Riga da Sikat na wata atamfarta Codedubuwa mai kalan Blue da Fari sai tayi amfani da bakar jaka da Takalmi da mayafi baki ta Dauko Kayanta itama kala Biyu da kayan baeci sai kananun kayan da zata Bukata suka Hada kayansu Waje Daya suna Shirin fitowa Daddy ya Kira Umma yace su dawo ana Jiransu. Dole suka Fito da Sauri Sagir ya Tsaya Shagonsa yana sallama da yaransa,Su kuma suka tafi har da Mama data Yo musu Rakiya bakin kofar gida Tana ta addu"an Allah ya Kiyaye Hanya. Koda suka iso duk suna Haraban gidan ne,kowa cikin Shirin Tafiya Bangaram su Ya Basheer su Inteesar suka karisa suka gaishesu kana suka karisa inda su Abba ke tsaye suka gaishesu suka amsa cikin Sakin Fuska. Sannan suka juya suna gaida Mami Asma"u dake gefe tsaye tana Latsa wayarta tana kallon Mutane ta Cikin Siririn Gilashinta,Sama sama ta amsa musu ba wanda ya Damu da ita sanin Halinta. Aka Fara saka kaya acikin Mota Yusuf yayi Riverse da Motarsa,zuwa Inda Abba ke Tsaye yaci Shadda Fara Tazarce yayi shar dashi,Sadam daman Da safe yaje gida ya Dauko musu kaya nashi dana Aneesa da yara dukkansu sun Dauki Uzuri a wajen aikinsu yau sai Dukku. Awajen kowa ya hallara Imran ne kadai bai fito ba Abba ya yafito Yusuf da Hannu yana zuwa yace mai"Kira min Imran..! Yataka kenan zai koma cikin Gidan sai ga Imran ya fito Sanye cikin Riga da Wando baki da Fari na kamfanin DKNY,wandon baki ne yadan kamasa ta kasa sai wani katon bakin Booth din Takakmi sai Farar rigaraa mai kauri mai gajeren hannu Tana da Rubutu baki agaban rigan an saka GENTLY. kansa kuma yasha gyara Dadan nan ya Zauna Daram yana Sheki Fuskarsa ba Fara"a ko kadan kamar an aiko mai da sakon mutuwa Hannunsa sanye da agogon Fata,Bayansa Rataye da wata Jaka baka irin ta matafiya inda ya saka kayansa da Abunda zai bukata Tunda Umarnin Abba ne bai isa ya Taallake ba ammh ba domin shi ba ya Rantse har ga Allah bamai sakashi zuwa Dukku yau. Yusuf ya kalli Abba yana Fadin"Gama Imu din nan Abba..! Kai Abba ya gyada kafin ya juya yana kallonsa yana Tahowa Hannunsa Daya Cikin aljihun wandonsa Dayan kuma karamar wayarsace a hannu yana Dannawa ba Abba kadai dayake Dansa ba kowa awajen sai da ya tsaya yana kallon Imran koda yanayin Tafiyarsa zaka Fahimci shi din Namiji ne ballatana Cikar Zatinsa da Kwarjinsa na dabam ne. Inteesar dake tare da su Ya Basheer tana Rokonshi suna son zama amota Daya ita da Munari da Hafsah, bata san ta shagala da kallonsa ba sai da taji Basheer na fadamata to su shiga Motar Sadam shi zai tuka su Umma. Kana ta iya dawowa cikin Hayyacinta Tana Sauke Nunfashi. Imran kuwa gaban Abba ya karisa Ya gaishesu ina kwananku yace sau daya bai kara cewa komai ba ya Dauke kansa sama Daddy ne kadai ya amsa sai Abba ammh Baffa kabiru na gefe yana Waya.. Abba ya dafa kafadansa yana Fadin"me ka tsaya yi kaifa kadai muke jira..!? Imran yace"Abba Sagir nake jira..! Abba da Yusuf suka kallesa cikin mamakinsa Kafin Abba yace"Sagir kuma..? Kai ya gyada batare da yayi mgana ba suma basu ce komai ba sai Yusuf dayace"Ka kirasa zamu wuce ne..! Bai yi musu ba ya koma Gefe yana Kiran Sagir ta waya. Su kuma su yusuf suka fara tsara yadda Zaman Motan zai gudana. Abba da Daddy da Baffa Kabiru zasu shiga Motarsa Direbansa yajasu wanda ya kwana nan wajen Iro megadi. Sai Umma da Mami Asma"u zasu hau Motar Sa"id. Yusuf kuma zai Dauki Imran da Sagir,Sadam kuma zai Dauki Fareesatu da Aneesa da Safiya da yaransu sai Basheer zai dauki Su Inteesar. Kowa ya yarda da Tsarin banda Mami Asma"u data bata rai tafiso tayi tafiya Mota Daya da Mijinta sai dai bata samu Fuska ba Wajen Baffa Kabiru ko yaya naka yake ai naka ne tuni sun shige Mota shi da yan"uwansa Dole itama ta shiga Motar Sa"id gidan Baya Umma ta shiga gaba abunta. Imran bai shiga Mota ba sai da Sagir yazo kana ya yarda ya shiga gidan gaba Sagir ya shiga baya. Motan su Abba ce ta fara fita Daga gidan sai Motar su Umma sai ta Sadam sai ta Basheer sai ta Yusuf ta Karshe,Iro nata daga musu hannu da Fatan Allah ya kai lafiya. Da suka dawo sallar asuba Yusuf ke fadamai zasu yi tafiya na kwana Biyu kafin su dawo ya kula da gida yace bakomai Cikin gida kuwa daman sun kulle kulle ko"ina kafin su tafi. Sai da suka Dauki Hanya kana Baffa Kabiru ya kalli Abba yana Fadin"wanchan da naganshi Tare da Imran waye..? Abba yace"Sagir..?abokinsa ne..! Baffa Kabiru yace"Tafiyar ta Shafesa ne..!? Abba yace"Imran yace yazo yamai Rakiya..D'a na kowa ne ballatana Sagir ba bare bane na gida ne yaron wajen Yayar Salaha ne matar Mustapha Dalilinsune ma kuka san inda muke zaune..! Baffa Kabiru bai kara mgana ba Daga gani zuwan Sagir din bai mai Dadi ba Daddy dai da Abba suka cigaba da Tattauna mganarsu. Suna Hanya sun kusa shiga Gombe Inna Maimunatu ta Kira waya tace gasu fa a dukku koda ta iso ta iske Inna Bintalo da ya"yanta sun iso sun gama Gayama Daada Komai ga Daadan nan sai kuka take tana cewa Ta kosa taga Malami ko Hankalinta zai kwanta. Daddy yace ai gasu nan sun kusa isowa da yardan Allah har aka bama Daadan ya kara Lallashinta bai dai bama Abba Wayar ba yafiso suga juna Ido na ganin ido. Sun tsaya a Gombe sunyi Sallar azahar wajen karfe Biyu na rana kana suka Dauki Hanyar Dukku ba Dadewa suka iso Cikin Haraban gidansu na Dukku Abba na kallon Haraban gidan yana ganin komai kamar baya babu abunda ya Sauya sai ma sauye Sauye da aka samu,Idanuwansa suka ciko da kwallah na kewar Gida da Ahalinsa gabadaya da Daada dayake matukar jin kunyar Hada ido da ita. Sai da kowa ya fito daga Mota kana Imu ya fito yana cin mgani Sagir sai bin Gidan da kallo yake yi yana Auna wasu abubuwa acikin ransa,Da Inteesar suka Hada ido suna Shirin Shiga Cikin gidan gira ta Dagamai Kafin ta dagamai hannu kau ya kauda kai kamar bai ganta ba,nan kuwa sun yi ma juna sako ta waya Inteesar sai mai Tabara take wai ta gaji da Zaman Mota shi kuma yace ta ce a sauketa in ta gama Hutawa sai ta hayo wata Motar ta samesu achan tunda bayan Shagwaba da Rigima ita din Raguwa ce sai Dariya take dayacemata haka. Daddy ya Riko Hannun Abba gaba gaba zuwa Babban Falon Daada. Wanda tunda sukaji isowarsu suka Firfito falo Daada da kafarta ta Fito Tarban Abba su Inteesar suka Fara shigowa sai su Aneesa da su Umma Mazan suna Baya ya"yan Inna Mainunatu su zainab natayi musu maraba su kuma suna ta Neman inda zasu ga Dan"uwansu,sai gashi Sun shigo shi da Daddy Baffa Kabiru na Binsu ta baya,Su Basheer na takemai baya Imu da Sagir ne abaya shi yana Tafiyama kamar bazai taka kasa ba. Inna Maimunatu ce ta fara isa wajen Abba ta Rikeshi da Murna tana kwallah ita da Inna Bintalo,Daada na Bayansu Baba Asabe na Riketa Cikin Mika Hannu take fadin"Ina Malami..Taho nan naji Duminka na Tabbatar da yau Allah ya amshi addu"ata..! Tafada cikin murya Tsufa Dakyar ya saki Hannunyensu inna Bintalo ya Nufi Daada cikin karayan zuciya,Hannayenta ya Riko yana Fadin"Daada...Daada..ki yafemi...! Sai Hawaye Daada ta Rumgumesa tana Shafa bayansa Lokaci Daya Tana Fadin"Har Abada banta rike ka acikin Raina ba Malami..Addu"q da Fatan alheri ne tsakanina dakai naji dadi nagodema Allah dana ganka ka dawo Cikin Koshin lafiyarka Abubakar..! Daada ta fada Cikon muryan kuka Duka suna Tsaye cikin Tsasayawa da Fuskar farinciki. Ta dagosa Tana kallonsa kafin ta Shafa kanshi Tana Fadin"Allah na gode maka..Zan hada kan iyalaina kafin nabar gidan Duniya..Ina yaran nan Yusuf da Maimunatu..! Abba ya juya yana Kiran Yusuf ya Taho da Sauri Munari ma haka Abba yakira Safiya itama ta kariso zuwa gaban Daada. Daada na Hawaye ta Rike yusuf Tana Fadin"Yanzu wannan Yusufa ne..? Kamkame hannunta yayi yana Fadin"Nine Daada..! Idonsa ya ciko da Hawaye Ta dafa kansa Tana fadin"Masha Allah naji Dadin ganinku cikin Koshin lafiya..! Tafada kafin ta maida Dubanta kan Munari dake Hawaye Daada ta Dafa kanta Tana fadin"Mai sunan Auta ta zama Budurwa itama Maimunatu kin ganeni..? Nice karki Daada..! Tafada cikin karaya da tsufa jin haka yasa Munari ta Rumgumeta Tana Fadin"Eh na ganeki mana Daada..Daadam Dukku..Daadan Anni..! Jin haka yasa kukan Daada ya Karu ta Rike Maimunatu tana fadin"Allah ya jikan Zuwaira da gafara..Allah ya jikansu ita da ya"yanta da suka rigamu gidan gaskiya..! Gabadaya aka amsa da Ameem jikin kowa a sanyaye. Daada ta dago da Munari daga jikinta Tana fadin"Ina yar tselen uwar nan Maryama da akace kun hadu Tuntuni baku gane juna ba..? Munari na Dariya ganin Inteesar ta Hade rai tana fadin"Kai Daada bama kiji Dadi ba sanadina kin hadu da Baffa ba..! Daada na Dariya tace"Naji dadi kwarai sai dai abu dayane bai min dadi ba..Yadda kika hadu da yan"uwanki baki sani ba wannan Dalilin ya kara Zaburar dani gyara wanu Gibi dna barsa a Bude insha Allahu..! Baffa Kabiru ne yace kowa ya zauna Kada Daada ta gaji da Tsayuwa kowa ya samu waje ya zauna,Munari ta makale kusa da Daada Abba kasa ya zauna saman Cafet kusa da kafufuwan Daada shi da Yusuf. Daada Mirmishi yaki barin Fuskarta sai Hamdala take acikin Ranta haka Yusuf da Munari bakinsu yaki Rufuwa Safiya sai waige waige takeyi Tana kallon kowa aranta Tna fadin ina Abbu yazo yaga Asali da kyakyawan Ahalin irin ahalin su Yusuf wadanda suka fisu komai na Rayuwa. Daada ce ta ganta bata santa ba ta Kalli Abba Tana fadin"Malami wacece wannan..! Badai aure ka kara ba bamu sani ba..? Mirmishi yayi Safiya sai taji kunya ta Sadda kanta Abba yakalli Daada yana Fadin"Yaushe na Warken ne Daada da zan kara aure..? Matar Yusuf ce wattani Baya ya aureta..! Daada ta washe baki Tana fadin"Masha Allah taho nan Yata bana Jikar dake ni..! Safiya ta Rarrafa wajen Daada ta Shafa kanta tana tasaka albarka. Daada ta fara Wurga wurga ido tana neman wanda take son gani Sai dai bata gansa ba yana ta bayanta Shi da Sagir suna Tsaye kamar wasu sojoji sagir na son zama Imran saboda Mugunta ya hanashi. Cikin dan Rage fara"a Daada tace"Malami ina cikon Dayan..? Ina jikana Imrana..! Abba ya dago shima yana Wurga Idanuwansa cikin Falon hakama kowa afalon ke wurgawa sai gashi an Tsintosa chan baya kamar wani bare Baba Asabe ne Dake gefe tace"Daada gashi nan a bayanki..! Duk da bata wani sanshi ba ammh yanayinsa yasa tasanshine Imran din ballatana ai tana jin Labarinsa Wajen Daada. Abba ya kalli Baba Asabe yana Fadin"Baba Asabe ya bayan rabuwa..? Baba Asabe na Dariya tace"Sai alherin Malamin Daada Tunda gaka ka dawo Ciwon Daada ya Kare..! Yana Mirmishi yace"Da yardan Allah. !Daada kuwa Juyowa tayi Tana fadin"Ina imranan yake ne..?ko nima baya son ganin nawa ne kamar yadda yace baya son ganin Baffaninsa..! Kowa sai ya fara mamakin ina Daada ta samu labarin abunda ya faru a Kano Mami Asma"u ce ta labartama Inna Bintalo yau da safe data Kirata ita kuma Tana zuwa ta Saukema Daada da ya"yanta. Abba ya kalli Imran dayake Tsaye ko Motsi yana Fadin"Kai baka ji Daada na mgana bane..? taho mana..! Ba yadda Imran ya iya Dole ya Jawo Hannun Sagir yana Tirjewa yana wani balle mai Harara Dole ya Biyosa suka Zagayo zuwa gaban Daada a Dofane Imran ya Durkusa kusa da Abba Sagir dai zama yayi domin Tsakani ga Allah ya gaji. Kansa na kasa yake gaida Daada Mirmishi tayi kafin tace"Bazan amsa wannan gaisuwan ba Imrana..Matso kusa na jika kusa dani..! Bayadda ya iya Abba ya mtsamai ya Karisa Kusa da Daada ya Durkusa kasan na kasa ta shafa kanshi Tana Fadin"Imrana..Har yau baka Sauya ba kana nan a yadda na sanka ko..! Imran ya Dago yana kallon Daada Kafin yace"Asan ka da Hallayarka Shine Cikakken Mutum Tsohuwa Daada..! Daada ta Murmusa Tana Fadin"ina nan ina ta ciwon rashin sanin inda kuke..Kai kuma Ahakan har kana cewa Babanka bazai zo inda nake ba ko Imrana..? Kai Tsaye ya rike Hannunta Guda Daya yana fadin"Ban isa na Hana Abba zuwa ganinki ba Daada..Ban kai wannan mtsayin da zan raba Uwa da Danta ba ai nasan Radadin rashin Uwa Daada..Kuma ko ina ganin Laifin kowa bana ganin naki Daada Lokaci bayan Lokaci ina Tunaki har nayi miki addu"a acikin Raina..! Daada taji Dadi ta Washe baki Tana fadin"Allah yayi muku albarka Naji Dadin ganinku haka..Kun kula da Mahaifinku da Kanwarku Allah ya saka albarka..! Gabadaya aka amsa da Ameen Sagir ya gaisheta ta amsa cikin rashin Sanin Abba ne yayi mata bayani ta jinjina kai Tana fadin"Oh yaron wajen Amina kenan Yayar Salaha dake kano wanda Maryama ke wajenta ko..! Abba yace mata Eh ai abokin Imran ne Daada tace"Masha Allah sannunku..Allah yayi muku albarka ina Maman naka take..? Kansa na kasa yace tana gaisheta tace tana amsawa.. Baffa Kabiru ya Duba agogon Azurfan Dake hannunsa yana Fadin"An kusa Kiran Sallar la"asar mu bari muyi salla sai muci abinci sai mu zauna ko ya kika gani Daada..? Daada tace"bazamu zauna batare da kowa ya Hallara anan wajen ba..! Kowa ya kalleta da Mamaki kai ta gyada Tana fadin"Binta ki kira su karima su iso suma kaima Kabiru ka Kira me sunan megidana Hamisu Da sauran yaranka Sajida da Umaima suma sai sun zo sannan zamu taru muyi wannan Zaman da yardan Allah.! Bai da tacewa illah Shikenan Daada Mami Asma"u tamai kallon ya zakace haka kasan yaran na makaranta Shi kuma yayi mata kallon ba Mafita sai Bin Umarnin Daada. *Janafty..* 3/22/22, 23:13 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�3* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Daganan aka tashi zuwa sallah,Mazan gabadaya masallacin kusa da gidan Daada sukayi sallah wanda Tsohon masallaci ne Tun marigayi Alkali Hamisu dukku nada rai. Bayan sun dawo aka Hadu a falon zaman cin abincin da Baba Asabe ta girka da Taimakon su Zainab, suka kamallah komai,Daada da ya"yanta suna cikin Dakinta sun kule kansu,suna Hirar yaushe gamo Daada Tana Zaune su Abba sun Zagayeta Farinciki ya cikata yau Allah ya cika mata Burinta malami ya dawo cikin Ahalinsa,Tana kallonsu tana Sharan Kwallah ta gefen Hannunta Cikin bayyana Farincikinta,ko abinci ma nan ciki Baba Asabe ta kawo musu yara yaran ne ke Falo suna cin Abinci. matasan mazan kuma Haraban gidan suka Fita Baba Asabe ta Kawo musu babbar Darduma suka Shimfida suka Zauna suna cin Abinci banda Imran Wanda yake gefe zaune kamar Dole jakarsa Har Lokacin Tana Sagale a bayansa yaki yarda ya ijiyeta. Lokacin da aka kawo abincin da Yusuf yamai mgana sai yace bazai ci ba su Sadam mamakinsa ya ishesu ganin Tun suna Kano basu ga Imran yaci komai ba Ta yaya mutum zai Rayu ba abinci. Haka Sadam yayi ma Yusuf wannan Tambayar Lokacin da suke cin Abincin Mirmishi kawai yayi yana kallon Imran dake chan gefe kan wani Dakalin gini da aka yi domin Zagaye Fulawowin haraban gidan kafin ya Daga ido yana kallon Sadam yace"Abinci bai damesa ba..Sai ya kwana ya Wuni haka bai damu ba..! Sa"id na kai Lomar Shinkafa yace"Tab..Kuma lafiyarsa kalau..? Wannan karon Sagir ne ya kada kai yana fadin"Shi yafi bama Ruwa Muhimmanci fiye da abinci..Sai kuwa Busa Hayaki..Abu na karshe Fruit da kila dasu daya ci ko bada yawa ba..! Kowa kai ya jinjina suna kara mamakin Imran na wani Lokaci daya suna Juyawa suna kallonsa shi kuma Tunda yaga haka jikinsa ya basa Mganarsa akeyi,Daman Haushin Sagir yake ji yadda ya wani Sharesa ya shige cikin su Sadam suna Hira kamar sun Shekara tare,Sai faman aikamai da Harara yake yi shi kuwa baima bi ta kansa ba cin abincinsa kadai yake yi suna Hira Sama sama. Imran da ya gaji da zaman hakan nan ba wani abun tabawa ya Dauko Karan Sigarinsa dake cikin Aljihun wandonsa ya kunnata ya shiga Zuka yana Fesar da Hayaki Ya Basheer ya kallesa yana Fadin"Ikon Allah shi kuma nashi Abincin kenan..? Gabadayansu suka juya suna kallonsa shi baima san sunayi ba Idanuwansa suna Lumshe ne yana jin Dadin yanayin Dayake ciki. Sadam ne yace"Gaskiya ya kamata Yusuf ayi wani abun da zai sa ya rage shan wannan Hayakin ko saboda Lafiyarsa..! Yusuf yace"Ina ta rokon Allah ya yayemai shanta kamar yadda Allah ya Doramai shanta Lokaci Daya..! Jin ya Fadi haka yasa suka amsa da Ameen Tunda ya ambaci Allah ai ya gama komai. Gefe kowa ya koma ya Fiddo wayarsa Lokaci daya suna Taba Hira,Yusuf dashi da Sadam ne suke ta Hiransu Yana bashi Labarin group dinsu na WhaApps nan da nan yace ga Lambarsa ya sakasa shi kuma Basheer dashi da Sagir suke Hiransu Sa"id yana saka musu baki Lokaci bayan Lokaci. Sun juma suna Hiransu kafin Hauwa ta kira Basheer a waya ya tashi zuwa Gefe suna mgana sai Hiran ta Koma kadan saboda Shima Sa"id ya maida Hankalinsa kan wayarsa ne ganin haka yasa Sagir ya mike ya isa Inda Imran ke Zaune ya gama Busa Hayakin ga Sauran Sigarin nan a kasa Daya gama ya Taketa,gefensa ya Zauna yana Fadin"Abokina ka dinga shiga Mutane don Allah..! Kamar ma baisan yana Wajen ba kansa na kallon gefensa sai chan yace"Ai shiyasa naga kai ka shiga Cikin su ka manta dani..! Sagir yace"Ah to tunda kai baka san shiga mutane ni sai naki shiga..!? Imran ya waigo yana kallonsa yace"Eh saboda ni na gayyatoka..! Yafada Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska Sagir yace"Eh ai ban ce bakai ka gayyatoni ba ammh su Ya yusuf ne fa ba wasu ba balle kace..! Imran yace"Ya yusuf din shi kadai ne..? Wadanchan ba wasu bane..?Sagir ya saki baki kafin yace"Su waye wasun..? Chan fa duk yan"uwanka ne Imu..! Baki ya tabe kafin yace"Eh ammh ai ban saba dasu ba..! Sagir yace"To ta ina zaka saba dasu baka Shiga cikin su ba..! Imran yace"Ashe kuwa bazamu taba Sabawa ba indai sai na Shiga cikinsu..Kai ni ko Ya Yusuf a wasu Lukutan ban son zama dashi nafi son zama ni kadai..! Sagir yace"Allah ko ya rabamu da zaman kadaici..Sai kayi ta zama ni dai sai na shiga cikin mutane..! Yafada yana Shirin mikewa Imran ya dago kansa yana Fadin"Baka isa ba..Dawo ka zauna..! Sagir ya kallesa kallon Mamaki kafin ya Girgiza kai yana Fadin"To Ubana Tasiu..Ko Uwata Amina..! Yafada yana komawa ya zauna cikin dan bata Fuska yadda Sagir ya Fadi mganar ne ya bama Imran Dariya Har sai da ya washe fararan Hakoransa a waje wadanda bakasaifai ake cika ganinsu ba Sai ga dariya Lokaci Daya mai Sautin da Har sai da ta bayyana Su Sadam dake gefe suka Juyo suna kallon Abun mamaki Sadam ya kalli Sa"id shima ya kallesa Kafin su kalli Yusuf Sadam yace"Kai ashe yana Dariya..Tun haduwarmu ko Mirmishinsa ban gani ba sai yanzu naga yana Dariya..! Yusuf na Dariya yace"Yana Dariya mana..Ammh Tana da Wahala kaga yayi irin wannan Dariya bakomai ke Burge imu ba ballatana ya sakashi Dariya haka..Yafi yin Mirmishin Fatar Bakinsa in hakan ya zama kamar in muma mgana dashi haka..Irin wannan Dariya kuwa da Sagir kadai yake yinta ko dani in na Tsokaneshi..! Gabadaya kai suka Jinjina Basheer ya kada baki yace"Allah mai iko..! Sadam yace"Kuma mai Mutane kala kala..! Dariya suka saka gabadayansu Sa"id yace"Tunda munsan Halinsa sai mu ci mganin zama dashi..Azauna Lafiya In ji Sadam daya Karishemai suna mganar suna kallonsa yadda yake Dukan Kafadar Sagir yana Dariya shi kuma ya saka Kafa ya Taka takalminsa yana Hararansa. Lura da yayi suna kallonsa yasa Dif ya Dinke Dariyan tasa ya koma ya Hade rai kamar yaga Mala"ikan Daukan Rai su abun ma sai ya basu Dariya suka koma suka cigaba da abunda sukeyi Lokaci Daya suna Hira sama sama Shima din Hirarsu da abokai suke shida Sagir wanda Rabin Hirar Sagir ne Sauran mganar Imran din duk Gatse Gatse ne cikin yanayin mganarsa. Sai da aka Kira mangariba suka tashi Daga wajen nan zuwa masallaci shima sai da su Abba suka Fito ne suka Tasasu zuwa masallacin basu koma Dawo gidan ba sai da sukayi Sallar Isha"i abunda yakara bama su Daddy mamaki Imran da Jakarsa yaje masallCi ya ijiye ta agefensa da zasu Fito ya Dauko kayansa mamakin hakan Yasa sai da Daddy ya maganta suna Hanyar Dawowa ya cema Abba"Shi Imran bai yarda da kowa bane..? Abba yace"Saboda me kace haka..? Daddy yace"Duba fa kagani Tunda muka iso bai sauke Jakar nan ba Duk inda zashi da ita yake zuwa..! Abba yayi yar Dariya yana Fadin"Kyalesa in ya gaji zai samu waje ya ijiyeta..! Yafada yana bayyana Dariyansa Shima Daddy dariyan yayi kafin su Wuce suna cigaba da mganarsu Baffa Kabiru kuwa yana baya yana ta gwada Kiran Khamis bai samesa ba sai ya Turamai sako. Bayan sun dawo Mazan da iyayen nasu Falon Daada suka yada Zango Imran dai wani Daki ya samu ya Shiga ya ijiye Jakarsa yayi wanka ya saka Jallabiya ya kwanta yana Hutawa achan Falo kuma Baba Asabe Tuwon Shinkafa Tayi da Miyar Zogale yan matan suka Tayata dasu Anty Safiya aikuwa kowa yaji Dadin Tuwon nan sosai Daada Farinciki ya cikata ganin Ahalinta Zaune Waje Daya sai dai bata ga Imran ba yasa ta juya tana kallon Sagir Tunda ta gansa shi ya saki Jikinsa Cikin su Sadam tunda damab ba Bare bane Tace"Sangiru ina Abokin ka Imrana Shi kadai ne yayi saura bangani ba..? Sagir ya kalli Daada yana Fadin"Daada yana cikin Daki ya kwanta..! Daada tace"To baka fadamai ya Fito yaci Abinci ba..! Yusuf ya karbe mganar da cewa"Daada ki kyalesa in yana Bukata da kansa zaki ga ya fito..! Daada Tayi Shuru Tana Tunani Inteesar dake gefe itama ta Damu Tun dazu bata gansa ba Har sako Ta Turamai yana ina..? Yace mata gashi goye a bayanta ya saka mata bakar mgana Daganan ta kyalesa sanin bazai Biyemata ba. Kokarin Mikewa Daada Take Tana Fadin"Ai baza"a kyalesa ba Yusufa ni bari naje da kaina na Fito dashi..! Ba yusuf kadai ba Kowa da kallo ya Bita na mamaki,Da Sauri Inteesar ta Mike ta isa kusa da Daada ta Riketa ta Mike Tsaye dakyau Inna Maimunace tace"Yauwa jeki Daada..Kila in ya ganki ko kila ya Fito ya zauna cikin yan"uwansa..! Sadam yayi karaf yace"Mom Wlh Tsausayi yake bani Duk da haka Allah yayi sa ammh akwai ciwo fa rashin Shiga Mutane..! Kafin Inna Maimuna tace wani Abu Inna Bintalo ta tabe baki Tana Fadin"Sai kace Wani yaro Daada da sai kin je kin Lallaso yaci abinci..? Ai yunwa bata da sabo da yajita Zaki ga ya Fito..! Kamar Mami Asma"u na Jira ta kada kai Tana fadin"Umh ai nama kasa mgana Binta..Gardin Namiji ba yaro ba Ana damuwa dashi sai wani Lallabashi akeyi kamar shi kadai ne jika kwara Daya Tal..! Tafada Cikin jin HUshinta wanda sai da Abba ya Dago yana kallonta ya Kada kai baice komai ba Hakama Daddy yana Jin Takaichin Yadda Mami take Shiga mganar da ba nata ba,kuma Yaya Kabiru na zaune bazai Tsawarta mata ba. Daada bata ce komai ba ta kalli Sagir Tana Fadin"Sangiru wani Daki Kaga ya Shiga..? Mikewa yayi yana Nuna mata Wani koridi Lokaci Daya yana Fadin"Dakin farko Daada..Muje na rakaki..! Da sauri Inteesar tace"A"ah Zauna abunka Ya Sagir zan rakata da kaina..! Jin haka yasa ya koma ya Zauna ita kuma Inteesar ta rike hannun Daada suka Nufi Koridon Kowa ya Bita da kallo Mami Asma"u harda Hararan kasan ido aranta tana Fadin Tsohuwar nan akwai rigima ba wanda ya kara mgana kowa ya cigaba da cin Abinncinsa. Yana kwance Ringingine yana kallon Rufin Dakin ya saka Duka Hannuwansa Biyu yayi Filo dasu idanuwansa sun kankance kamar mai jin Barci Su Inteesar suka Shigo Dakin bayan sun kwankwasa Lokaci Daya da Sallama. Bawai bai ji bane yaji Mamaki ne ya kamashi na waye zai zo ya Damesa bai kawo ma su bane duk a Tunaninsa Sagir ne yasa ya Juya baya kawai bai ko Dago kansa ba. Daada ta Murmusa tana Fadin"Nine baka san gani Imrana..! Jin muryan Daada yasa ya Dago kanta yana kallonta karaf suka Hada ido da Inteesar dake kallonsa Ido Cikin ido. Lamgwabe kanta tayi kamar zatayimai kuka Saurin dauke kansa yayi Lokaci Daya yana Mike Zaune yana Fadin"Daada..! Kafin Daada Tace wani abu Inteesar Tayi Saurin cewa"Daada ta damu baka ci komai ba Shine tazo da kanta..! Kura mata ido yayi yana kallonta Daga sama Har kasa sanye take da Doguwar riga mai Ruwan kasa Kirar Armani mai Roba ta dan manne mata ajiki sai ta saka Vail din Rigar ta yane kanta dashi Zuciyarsa taji tana Bugawa yasa yayi Saurin kauda kansa Kafin ya Zuro fararan kafafuwansa kasa ya Sauko Daga kan gadon ya isa ga Daada yana Fadin"Daada ai ba sai kin taso ba..bana jin cin komai shiyasa..! Daada tace"a"a kana jin yunwa sai dai in bazaka ci ba..Ko Tuwon ne baka so sai Maryama gatanan ta dafa maka wani abu ammh ai zama da yunwa bai da wani amfani Imrana..! Imran yasa mezai ce Inteesar ya kallah ta Dagamai gira Hararanta yayi kafin yace"Daada..! Bata bari yace wani abu ba tace"In baka son zama cikin mu sai ta kawo maka nan Dakin ba shikenan Damuwar ba..! Kansa ya shafa kafin yace"Zan ci muje Saboda ke Daada..! Taji dadin haka ta shafa kanshi Tana Fadin"Allah yayi maka albarka..! Ya amsa da Ameen yana kallon Inteesar dake danne Dariyarta Hade rai yayi yana Fadin"Ke..Dariya kikemin ko..? Yarinyar nan kin rainani saboda banta Sauya miki kamanni bane shiyasa..! Daada Tayi gaba bata jisu ba Inteesar tayi Raurau da ido kafin tace"Am sorry badakai nake yi ba..! Bai tsaya ce mata wani abu ba ya Nuna mata Hanya da Hannunsa Dole ta wuce sum sum shi kuma yabiyo bayanta Duk Takunta yana Kallonta kamar kuma da Zuciyarsa take Tafiya Har zuwa Falon Daada. Suna Fitowa kowa ya Dago yana kallonsa Shifa ya Tsani kallo wani Lokaci Fuskar nan ya Hade ba Fara"a su Abba kadai yace ma sannunku sai Inna Maimunatu Inna Bintalo baima Lura da ita ba yasa bai gaisheta ba Yana Shirin karisawa Kusa da Daada ya Zauna yaji Tana Fadin"Ni kuma Kashi nayi maka agado da ko sannun bansamu ba..! Shifa bai ma zata dashi take ba yazauna kusa Daada yana dan Wurga Idanuwansa,Yaji Abba yace"Imran ka gaida Goggonka Binta gatanan..! Yafada yana nunata Sai Lokacin ya Dago yama kalleta Wani Kallo ta sakarmai shi kuma yayo mata kallon Kyahuwa..,? Irin to me ya Hadasu da zata mai wannan kallon Dakyar ya iya ce mata Sannu goggo..! Ta Bude baki zatayi mgana Daddy ya Dakatar da ita da Fadin"Badai ya gaisheki ba..? Ku rika kama Girmamku Binta wadanan yaran fa Kamar ya"yanku suke..!. Jim haka yasa tayi Shuru bata da tacewa Shiko Imran ko ajikinsa. Daada tace munari ta sakamai Tuwon bai yi mgana ba ya Nannade Hannun Jallabiyan Jikinsa ya saka Hannun a Filet din Daada ya Debo Tuwon yakai Bakinsa da Bismillah kowa da mamaki yake kallonsa barin ma Abba da Ya Yusuf da Sagir da Munari da Inteesar sai dai bamai San sunayi ba Ya hade ransa ya cigaba da cin Tuwonsa Daada Ranta Fes tana kallonsa Tana Sakin Mirmishi Aranta Imran in ya Gutsiro Tuwon sai ya Tura gaban Daada kamar wata yarinya haka ya dinga mata sai dai ta Dauka tace cikin Taruwar Hawaye tace"Allah yayi maka albarka Allah ya jikan Zuwaira..Kullum kukanta Daada Yaushe Imu zai sauyane..? Yayi kaza yayi kaza Baya son zama cikin yan"uwa yau data na Raye data zo ta ga Imranu yana cin Abinci kwano Daya Dani yana Gutsiromin Tuwo saboda yasan na Tsufa baya so na Wahala..,! Da karfi Tayi mganan dayasa kowa yajita sai aka koma ana kallonsu Cike da mamaki Abba Farinciki ya cikasa shi da Ya Yusuf Imran kuma baima Kalli kowa ba bai wani ci mai yawa ba ya Zare Hannunsa ya Mike Daada ta Kallesa Tana fadin"Har ka koshi kenan..? Kai ya gyada mata bai yi mgana ba ya Wuce zuwa Kitchen ya wanke hannu ya Dauko Ruwa Gora guda Daya yazo ya wuce ya koma Daki abunsa batare Dayace ma Kowa komai ba Daada sai Mirmishi take ita Kadai Mami Asma"u na Binta da Harara kasa kasa itafa bata Kaunar taga Daada na nuna ma wani Jika so da kulawa in ba ya"yanta ba akomai tafi so su kasance sune kan gaba da kowa. ***** Washegari ma haka gidan ya tashi acike da yan"uwan Munari Farincikinta yaki Boyewa tana cikin Danginta ta kwana cikinsu ana Hira Imran dai Daki daya suka kwana Da Sagir,Wanda Imran kasan Cafet ya kwana ya barma Sagir gadon domin bazai iya barci da wani akan gado ba. Basheeer kuma dasu Sadam dukkansu Daki daya sukayi kwanciyarsu ko ajikinsu suka kusa Raba Dare suna Hira. Su Abba ma Daki daya suka kwana Abunsu hakama su Inteesar da Hafsah da Munari su Aneesa ne da Safiya da Fareesatu da su Zainab daki Daya Mami Asma"u dai ita da Umma suka Kwana Daki Daya Inna Maimunatu Dakin Daada tayi kwanciyarta. Kamar koyaushe ma yau din Baba Asabe sukace ta Huta su sukayi Breakafast kowa ya Fito banda Imran Daada tace ahada kayan karyawansa akai mai Daki Munari ta Zare Jikinta Inteesar da Hafsah suka Dauka sai gashi sun dawo dashi sunyi ta Knooking bai bude ba Hankalin Daada ya tashi ta fara Tunanin ko wani abu ne ya sameshi Abba yace mata kada ta damu lafiyansa Kalau kana ta koma ta Zauna ammh duk ta Shiga Damuwa Bata kai Inteesar shiga Damuwa ba. Daki ta koma ta Dauki wayarta ta Kirasa bai Dauka ba Har sau uku,sai na Hudu ya danna mata Busy sai ga Sakonsa. "Kada ki dameni da Rigimarki da safan nan..Am not in d Mood..Barci nake yi..Kuma an sure kece kika zo kina min knooking ko..? Don't let me Catch u bazaki ji da dadi ba..! Data ga sakon sai da ta tintsire da Dariya kafin ta maida amsa. "Daada zaka kama ko..? Domim ita ta aikoni na kawo maka Breakfast dinka.." Amsa ya bata da cewa"Nidai ke nace ba Daada ba..! Dariya tayi sosai tana Jin Dadin tsokanansa Kyaleshi tayi jin yace baya cikin Mood din. Falo ta dawo domin bata gama shan Tea dinta ba ta zauna kenan taji Daada na Fadin"Kabiru ya mganar zuwan su Hamisu ne..? Binta kefa kin kirasu Hamidan..? Baffa Kabiru ne yafa fadin"Eh Daada na Kirasa ban samesa ba sai dai na Turamai sako nasan yan gani zai Dauki Excuse wajen aiki ya taho..Su Sajida kuma Asma"u nace tayi mgama Dasu..! Kai Daada ta jinjina batace komai ba. Inna Bintalo tace"Su Hamida suna Hanya na Kirasu..! Daada tace"Yayi kyau..Asma"u Su Sajidan kinyi mgana dasu..! Cikin Mganarta Tace"Eh Daada. Nayi mgana da Sajida duk da sun kusa Fara Text nace Direbansu ya kawo su yau ita da Umaima..! Tafada cikin jin Haushi Tsakani ga Allah an takurama ya"yanta. Daada tace"Ai ba Dadewa bane abun Asm'u zuwa gobe ko jibi in mun gama Abunda ya taramu kowa zai koma bakin aikinsa Tunda ai kowa ma yana da ayyukan ya Saukesu ya Taho..! Cikin hikima Daada ta maida mata mganarta Inteesar kuwa Farincikinta Duk ya tsaya Lokacin dataji ance Khamis zai zo acikin Ranta Tana ta addu"an kada Allah yasa yaga ma Sakon na Baffa Kabiru ballatana ya Taho. Bayan sun gama Karyawan su Inteesar suka Tattara komai zuwa Kitchen ita da Munari suka Fara wankewa Hafsah taje yima yaran su Anty Aneesa wanka su Waleeda. Su Abba kuma suna nan afalon Tare da Daada Mami Asma"u daki ta koma ta Kira Sajida tana Dagawa tace"Mami ko mu yi zaman mu ne..?. Mami Asma"u tace"A"a ku taho kawai yanzu Sajida..Daada ta matsa sai kun zo..! Sajida ta bata rai Tana Fadin"Mami to me zamu zo muyi..? Nifa i hv alot to do Mami kinsani Test zamu fara Next Upper week..Ina son kadaici na samu nayi karatu..! Mami Asma"u tace"Nasani buh ai zuwa Gobe ne zamu dawo kada ki Damu bzai shafi karatunki ba ni kaina ban so ba To kinsan Daada rigimarta Tayi yawa kuma Dad din ku bazai ce komai ba ammh banga Abunda zata ce sai yara sun bar karatunsu sun taho ba..! Sajida ta Tabe baki kafin tace"Wai to ba Baffan ya dawo ba? Ta gansa Inace ba Shikenan ba..? Mami Asma"u tace"Uhm kya fada kema..Ina Umai..! Sajida ta juya tana kallon Umaima Data Fito wanka tana shafa Lotion sai Murna take tace"Gatan nan tayi wanka..Sai murna take Mami kinsanta..! Mami Asma"u tace"Bata da.wayau ne bata san ciwon kanta ba..Ku taso yanzu kada kuyi dare..Make sure kun dauko duk abunda zaku nema kuma kizo da komai na Karatunki harda Laptop dinki kinji..! Sajida tace"Ok Mami see you..! Daga haka suka yanke kiran Umma na gefe ta kishingida Tana jinta batace mata komai ba itama bata mata mgana ba Sanin Halinta yasa Umma ke cin mganin zaama da ita. Imran bai fito ba sai azahar da zashi Msallaci Sagir ko ta kansa bai bi yana cikin su Basheer abunsa,bayan ya Dawo a masallaci Aharaban gidan ya Tsaya ya sha Sigarinsa Baffa Kabiru ma ya Fito ya gansa yayi kamar bai gansa Baffa Kabiru kuma bai nuna ma ya gansa saboda yadda Imran yake Tabbas zai iya zaginsa in ya cika Shigema yaron. Bayan ya gama shan kayansa ne ya Shigo Cikin gidan ba kuma wai domin yana jin Tsoron Shanta acikin Gidan ne,A"a saboda Abba ne shi kadai ne yake Gudun bacin ransa sai Daada Dake yake ganin Girman Tsohuwan da kuma Kaunarta Dayake yi ko domin kaunarta ga Abba da Anni dasu Gabadaya. Yana Shigowa Falon su ka kusa cin karo da Inteesar da Suke wasan banzan Ita da Munari da Hafsah Daga gyaran Falo suka Fara Wurgama Juna Cussion din kujerun falon. Batama san ya kawo ba ta taho bata ganin gabanta,Kawai ta Fadamai da yayi baya sai tatafi luu zata Fadi ya saka Hannunsa ya Tallafota ta Fada kan Kirjinsa male male ta Rikesa gam tana Sauke Numfashi. Munari da Hafsah suka Tsure kowacce ta Tsaya tana Raba ido Sai Alokacin Inteesar ta dago Tana ganinsa ta Saki baki Shima kallonta yake da dukkan Tunaninsa da Zuciyarsa. Sakinta yayi kafin yadan matsa Baya jin jikinsa ya fara saki,kallonsu yayi Daya bayan daya kafin yace"Are u a kid..?manya daku kuzo kuna wasan banza..!? Kowacce ta koma ta natsu kafin nayi kwallo da yarinya..! Ai kafin ya gama mgana Munari da Hafsah sun bace afalon Inteesar ce ta Tsaya taki tafiya Kallonta yayi kafin yace" kin rainani ko..?Ok daman nace zan rike ki..? Kina son duka ne ko..? Ai jin haka yasa ta Zaro ido kafin tayi narai narai da ido tace"Duka kuma Ya Imu..? Kai ya gyada mata kafin yayi mgana ta wuce sum sum tana waigensa Dariya ta kamasa,sai kawai ya Murmusa ya wuce itama tana lekensa tana Dariya. Cikin Ikon Allah Sai ga Khamis ya Riga su Sajida isowa ashe yana ganin Sakon ya nemi Uzurin Rashin Lafiyar kakarsa aka bashi kwana Biyu Jirgi ya shigo zuwa Gombe daganan ya Hayo Taxi zuwa Dukku sai dai aka gansa Kwatsan Mami Asma"u sai Murna Yaronta yazo ta saka Baba Asabe ta cikamai gabansa da Abun sha da ci. Har kasa ya duka yana gaida Abba ya Dagosa ya Rumgumesa yana sakamai albarka haka suka Rumgume da Yusuf Cikin jin Dadin ganin juna haka suka Gaisa da Munri cikin Fara"a acikin Ransa yana Fadin She is Beautifull. Imran ne bai gani ba yana cikin Daki Inteesar kuma Tunda taji Zuwan Khamis ta shige daki taki Fitowa bata Kaunar su hadu shi kuma ita yake tason gani karfin ma zuwansa Saboda itace yana so su hadu suga juna Ya gayamata Sirrin zuciyarsa Soyayyarta yana sakasa cikin wani yanayi gashi bata Daga Kiransa Ita kuwa Taki Fitowa gashi sai kiranta yake yi taki Dagawa. Ya iso ba Dadewa sai ga Su Sajida sun iso,Umaima ce ta shigo Da Murnanta da Farincikinta banda Sajida Datake Tavwani Hura Hanci Mami Asma"u sai kai da kawo take kan ya"yanta Umaima ce taxo inda su Inteesar suka ta gaisa da Munari cikin Murnan Haduwa da ita banda Sajida wacce sai da Baffa Kabiru yayi mata mgana ta gaida Abba tana kallinsa tana Tuna kamanninsa. Sanin Halinta yasa ba wanda ya Nemeta Cikin su Inteesar itama bata Neme kowa ba. Imran kuma da Khamis basu Hadu ba sai da suka dawo masallaci Sallar Mangariba,ya gansa tare da Sagir yake Tambayan Sadam yamai bayani mamaki ya kamashi ganin ya mikamai hannu suyi musabaha Imran yaki bashi Hannu,sai kawai ya maida Hannuwansa Baya Sagir ne ya mikamai suka gaisa,shi kuwa Imran Kallo Daya yayi ma Khamis bai kara ba Saboda yaji bai kwantamai arai ba Shima Khamis din ransa ya baci da Wulakancin da Imran din yayi mai Da Farko yana Tunanin bai ganesa ba Ammh sai da yamai bayani sai yaga bai nuna ma wata alaman sani ba Sai Ransa ya baci Haka kurum yaji bai ji Dadin wannan Tozarcin ba sai dai bai nuna ba. Haka suka Dawo gida suka Shigo Cikin Falon a Tare,Lokacin su Sajida da Mami Asma"u suna Zaune a Falon kowa ya samu waje ya zauna Su Abba Dakin Daada suka shige abunsu. Kowa waje ya samu ya zauna kusa da wanda sukafi dasawa Sagir kusa da Basheer ya zauna Imran ne kadai ya Coge a tsaye Daga kofar Shigowa ya Harde duka Hannuwansa saman kirjinsa da kafarsa yana kadata Yana sanye da Riga mai Ruwan madara mai Dogon Hannu sai bakin Wandonsa wanda ya Tsukesa ta kasa Kansa yasha gyara Dadan nan ya kara yawa Fuskarssa a tamke yana Bin kowa da kallo Cikin Nazari. Sajida dake Duba wayarta Sanye take da Riga da sikat na yan kanti pink colour kanta da Kitson galaba,mayafin data yane kanta Dashi ya dan zamo ta bayanta Kafarta Daya kan Dayane Tana gefen Mami Asma"u ne. Daidai Lokacin data Dago kanta Shima Imran idanuwansa sun kai Kan ita Sajidan suka Hada Ido Hudu da ita Gaban Sajida ya yanke ya Fadi,yayinda ta Zurama Imran ido Tun daga sama Har kasa Tana karemai kallo cikin yanayin data kasa Fassarawa Yayinda Imran yaji Haushin Kallonta garesa ya Sake Hade rai ya Dauke kansa sama yana wani Dakuna Fuska kamar yaga Kashi. *Janafty..* 3/22/22, 23:13 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�4* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Ta kasa dauke idanuwanta akansa Haka kurum bata san Dalili ba Zuciyarta ta fara Bugawa Fat!Fat!yanayinsa da komai ya tafi da Tunaninta wanda ya Haifarmata da kuramai ido ta kasa Dauke idanunta akansa. Shi kuwa Tunda ga wannan kallon bai karama kallon Inda take ba ammh yanaji ajikinsa Tana kallonsa Tattare Naman goshinsa yayi waje daya cikin Takaichi ammh yaki yarda ya Kara kallon barayinta Akallon Farko yaji Kwata kwata yarinyar batamai ba Daga yanayinta da komai Tun kafin yasa itadin wacece Tunda shi dai Tunda yazo bai taba ganinta ba sai yau. Ita kuwa kallonsa take Tana so Tayi Tunanin waye shi..?Domin bata taba ganinsa ba ko yana daga cikin Ya"yan Baffa Malamin ne bata sani ba..?koma waye ajinsa da yanayinsa sun mata a irin yadda take son ganin cikakken Namiji mai cikar Zati da Haiba. Basheer ne ya Daga ido ya kalli Imran Daya ke Tsaye kikam aransa yana mamakinsa Shi ko gajiya ma bayayi Gyaran Murya yayi yana Fadin"Imran zo ka zauna mana..Kana ta Tsayuwa..! Yafada yana kallonsa Shi kuma dan yamutsa Fuska yayi kamar yace A"a sai yaji bazai iya Ture alfarmansa ba Haka kurum Sagir kuwa yana Shirin cema Basheer ya kyalesa bazai zauna ba sai gashi ya bashi kunya ya Fara Takawa Cikin Takunsa na isa da Sassarfa ya isa kusa da Basheer din ya Zauna Lokaci Daya yana Harde Hannayensa saman kirjinsa yana Jingina da Jikin kujera Bai saki Fuskarsa ba sai ma kara wani Hade rai da yayi,su Sadam suna gefe suna kallon komai Mirmishi kawai sukayi akallah dai ya Fara shiga Cikinsu. Dago idon da Imran zai yi suka kara Hada Ido da Sajida dan Waro manyan Idanuwansa yayi akanta irin Lafiya..?sai lokacim ta sunne kanta A kafadan Mami Asma"u dake gefenta sai alokacin Taji kunya ta kamata Imran kuwa Dama ya Fahimci Sajida ita waye karamin Tsaki yaja Har sai da su Basheer suka Juyo suna kallonsa bai basu daman mgana ba ya Kirne Ran nan ya Kauda kansa Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska. Khamis ne Dake kusa da Sa"id ya taso yazo ya zauna Kusa da Mami Asma"u suka sakata a Tsakiya kenan Kallonsa Tayi Tana Fadin"My son ya wajen aikin naka..? Hop ba wata mtsala ko..? Tafada Cikin Kulawa da Annurinta na son ya"yanta. Kansa ya Dora saman Kafadanta yana Fadin"Komai Normal Mami na..I miss u..,! Sumar kansa ta shafa tana Fadin"Muma muna kewarka Our Son..! Sajida dake gefe ta Tura baki Tana Fadin"Wai Mamina..? Sai kace Maminka ne kai kadai..? Kallonta yayi kafin ya Dago kansa yana Fadin"Yarinyar nan baki da kunya kin Rainani ko..?Shegen son jiko kamar mage ga Umai ce ta Shiga Cikin yan"uwa ke kuma kina nan Wajen Mami kina Sakale da ita Kamar Zaki koma ciki..! Yafada Cikin jin Haushinta Sajida ta kara Nanikema Mami Asma"u Tana Fadin"Mami kin gansa ko..? Mami Asma"u tace"Zaka fara ko..? Kaifa babba ne..Namiji kuma Ita kuma Macece ko aure tayi a wajenmu She is a kid..! Bai ce komai ba Sanin wacece Mami Asma"u kai kawai ya Rausayar Daidai Lokacin da idanuwansa yakai kan Imran wanda shima yake kallonsu Duk da ba suna Kusa bane sosai sai dai Yana jin duk Abunda suke Fada Haushi duk ya kamasa Matar nan yar Renin Hankali ne daga ita Har ya"yanta da Mijinta They are all Selfish. Bawai fa bai gane Khamis bane ya gane sa Sarai domin ya tuna gabda Rasuwar su Anni da Abba ya matsamai suka zo suka kwana Biyu Khamis din ma yazo Tare da Baffa Kabiru kawai dai Shi bai son mu"amala da Khamis ne,Haka nan yaji yaron bai mai ba yana ganinsa Kamar Mahaifinsa ne,kuma shi baya Doguwar Mu"amala da wanda Ra"ayinsa da Zuciyarsa bai kwanta Dashi ba,Bakinsa ya Mele Lokaci Daya yana wani Yamutsa Fuska kamar yaga Kashi ya wani Dauke kansa Khamis shima ya kallesa a Saukaken kafin shima ya Kauda kansa Mikewa yayi ya koma cikin su Sa"id da Yusuf Sajida kuwa Tana jikin Mami ammh gabadaya Hankalinta da Tunaninta na kan Imran wanda bai ma kara Kallon Barayinta ba Sajida ko Wayar nata bata kara Dannawa ba Saboda Kallon Imran gabadaya ya Dauke mata Hankali. Waige waige ya farayi acikin Falon ko zai ganta saboda yaga ga su Munari na Taya Baba Asabe jera abinci ammh bai ganta ba sai yaji ya Damu,Falon Dayake isu isu ne kadai su Abba suna Dakin Daada,Kamar ya share sai kuma ya kasa Kuma bayason ya Tambayi Munari ta Rainashi sai kawai ya Fito da karamar Wayarsa Ya Shiga Wajen Tura sako. "Kina ina..? Ban gan ki ba..? Haka kawai ya Rubuta mata ya Tura mata Sai dai Har tsawon wani Lokaci yana Duba wayarsa bai ji sakonta ya Shigo ba alhalin yana da Tabbacin Inda Lafiya da Tuni ta bashi amsa sake Turamata yayi. "Ki amsani mana..! Sai dai shima Shuru sai ya kasa Natsuwa zuciyarsa ta fara Bugawa baisan Dalili ba,Ganin ya kasa Daurewa ne yasa ya Mike kawai zai Fice Daga Falon da Sauri Yusuf Dake gefe yace"Imu ina zaka..!? Yana Tsoron Kada Zarginsa ya Tabbata Sigari zai fita yasha Ya tsaya ammh bai juyo ba yace"Zan yi kiran Waya ne..,! Ya fada Cikin jin Haushin Tambayar da Yusuf din yayimai ajiyar Zuciya ya Sauke jin abunda yace Saboda ya Tabbata da ita zai sha sai ya Fadamai gabadaya kowa hankalinsa ya koma kan Imran Daman Tun Lokacin da Yusuf yayi mgana kowa Hankalinsa ya koma kan Imran din Har ya Fice Daga Falon. Sajida acikin Ranta ta maimata sunansa"IMRAN..! Nice Name..! Take Fada tana dan Mirmishi Shi kuwa Sagir mamaki ya Kasheshi Dawa Imran zai yi waya..,? Wanda ya sani Dagashi sai ya yusuf yake da Lambarsu sai munari kuma Duka gasu tare,Mamakin hakan ya kamashi Sai dai bai isa ya karyata shi ba Sanin Halinsa Kaifi Daya baya karya Duk Abunda kaji ya fada to iya gaaskiyansa kenan bai mtsama kansa da Tunanin dawa Imran zai yi waya ba ya watsar da komai suka Cigaba da Hirarsu Sama sama da Basheer. Imran kuwa yana Fita Haraban Gidan Jikin Motar Yusuf ya Jingina yayi Shuru yana wani Tunani gabadaya yaji bai da Natsuwa In kuma bata da Lafiya fa..? Tuna haka yasa da Sauri ya Lalubo lambarta ya Kirata sai dai Har ta gama Ringing bata Daga ba Ransa sai ya Fara baci ga Zuciyarsa na masa Zafi ya kara Danna mata kira Gbda zata katse Inteesar dake kwance ta Daga Kiran cikin Kasala da Sanyin Murya tace"Hello..! Muryan ta Dakesa sosai har sai da yaji Hakan acikin Ransa sai dai Cikin Dakewarsa yace"Meyasa nayi miki Sako baki bani amsata ba..? Sai da yayi mgana ta Zabura ta Mike Cikin Kasala Lokaci Daya Tana Dafe kanta Dake saramata ta kara Bin wayar ta da kallo Ta kara Tabbatar da mai Kiran nata Tunda Cikin dan Barcin Dayafara Daukanta Taji kiran Wayar Idanuwanta sun mata Nauyi bata Tsaya ma Duba mai kira ba ta Daga. Jin tayi Shuru yasa yace mata"Kina jina ina mgana Shine kike banza Dani..?kinsanni kuwa..? Bana mgana ayi banza Dani kuma bana Tambaya aki bani amsata ya zama Dole duk Abunda nake son sani na Sani din..! Yafada mata Cikin Zafinsa bai Tsaya Jiranta ba ya Datse kiran yana Jin kansa kawai yana Daukan Zafi haka Kurum baisan Dalili ba. Inteesar Daga chan bangaran kanta ta Dafe Cikin yanayin dan Jin jiki kamar wasa suna Kitchen suna Taya Baba Asabe aiki suda su Munari,Kanta ya Fara saramata shine ta dawo Daki ta Kwanta Dakyar tayi sallar mangariba Taje ta Fadama Umma,ita ta bata panadol tasha tadan kwanta Shine taji Kiran Wayarta da Imran yayi mata. Bin bayan Kiran nashi tayi kamar bazai Dauka ba sai daga chan ya Dauka bai yi mgana ba yana cin mgani. Cikin muryanta Sanyi Sanyi tace"Am sorry Ya Imu..Bani da lafiya ne..! Sai datace haka yaji ya kara Shiga Damuwa Cikin Dakewarsa yace"meke Damunki..? Meyasa baki Fadamin ba..? Kara Lafewa Tayi kan gado Tana Fadin"Ciwon kai ne..nasha mgani..! Kara gyara Tsayuwa yayi yana Fadin"Kinci Abinci..? Kamar tana ganinsa ta Girgizamai kai Kafin tace"Ban ci ba..! Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Ki fito kici wani abu kada ki zauna da yunwa..Ok..! Da sauri tace"Tom..! Daga bangaransa yace"Ki rike wayarki a kusa dake kada na Kiraki baki Dauka ba..! Da tom ta kara amsamai Kafin ya Datse Kiran asaman lebenta tayi dan Mirmishi,Ko minti Daya bai ba da Katse Kiran Ya sake Kiranta Da Sauri ta Daga Tun Kafin tayi mgana Taji yace"Ki duba Sako na ki bani amsa..! Yafada Cikin Kaushin Murya Cikin Shagwaba tace"Ya imu to ba munyi mgana ba..! Cikin dan waro ido kamar tana ganinsa kafin yace"Ki bani amsata..ni ne kadai nake da ikon kimin sako naki baki amsarki ammh ni ya zama Dole ki kulani kuma ki bani amsata Lokacin da nake Bukata..! Abun nasa ma sai ya bata Yar Dariya Har sai da yajita da Sauri yace"Au dariya ma kike yi ko..? Ashe kina son Duka kenan ko..? Da Sauri tace"Ban fa da lafiya..! Tafada Cikin Shagwaba Har sai da yaji Hakan acikin Ransa Mirmishin Saman Lebe yayi kafin yace"Do as i say..! Yes sir..! Tacemai tana yar Dariya shima Dariyan yaso yi sai dai bai bari taji ba ya Datse wayan ya koma ya Jingina jikin Motar Wani Nishadi na kara Shigarsa baisan Dalili ba In yana mgana da yarinyar yana jinsa kamar bashi ba Ya kasa Fassara hakan sai dai ya barsa ne a karfin jinin yan"uwantaka atare dasu,Shiyasa yanan nan Tsaye yaji Shigowar Sakonta,Da sauri ya Duba. "Ban je ko"ina ba Ya imu..Ina Daki ina kwance ban lahiya..! Sai kuma Dayan"Ehyyee..Ya imu ya Damu dani..! Haka ta Rubutomai Dariya yayi afili ya Furta"Shagwabbiyar yarinya kawai..! Yafada sanda Sagir ya kariso wajen yana Fadin"Kai kuma kai da Waye kake Dariya kai kadai..? Dagowa yayi yana kallonsa Lokaci Daya ya maida Wayarsa aljihu yana Fadin"Ina Ruwanka banza Dan saka Ido kawai..! Sagir yayi dariya daidai Lokacin da Sauran mazan suka Fito Harda su Abba domin zuwa masallaci an Kira Sallah da Sagir yama Imran mgana su Tafi cemai yayi shi Yaron sane da sai ya Tasa agaba...? Yaje yasan Hanya zai zo Daga baya Sagir bai damu ba ya wuce,haka ma su Yusuf suka Fice abunsu sanin Halinsa kamai gwaninta ya Dizgaka Ganin su Abba ne yasa ya wuce da Sauri bayaso ya gaida Baffa Kabiru shiyasa yayi saurin wucewa Abba yana kallonsa kuma ya Fahimcesa Sarai Mirmishi kadai yayi suma suka Rufa Musu baya zuwa Masallacin Dake kusa da gidan Bayan an gama Sallah gabadaya suka Dungumo suka Dawo Gidan Imran ne abaya Shi kadai yaki ma yarda ya Jera da Kowa ko Sagir daya so ya Jirasa Cemai yayi yayi gaba basai ya Jirasa ba. Bai damu ba ya Taka ya bi su Basheer ya kyaleshi yana Tafiya kamar bazai taka kasa ba. Gabadayansu afalon suka yada Zango Domin cin Abinci Har da su Abba Daada ma ta Fito nan falon Imran yaso ya gudu ya koma Daki Daada ta Hanashi ta Kirasa tace yazo ya Zauna Kusa da ita bai da yarda zai yi Dole yaje kusa da ita ya Zauna,Yana cim mgani Irin su Mami Asma"u sai cika take tana batsewa,Ya"yanta na Gefenta Sajida da Umai,Sajida sai Satan kallon Imran take yi shi baima san Tanayi ba. Tuwon Semo ne da Miyar kubewa Danya Dataji Naman Rago da Manshanu,sai Ci suke suna Sakin Santin su Anty Safeya dasu Aneesa suna Gefe suma cin na su suna Hira haka suma Mazajen nasu suna Waje Dayane,Haka ma su Abba suna Zaune dasu Daddy waje daya duka dai duk suna kan Katuwar Dardumam da Baba Asabe ta shimfidamusu ne. Daada ne ta kalli Umma Dake gefen Inna Maimuna tana Fadin"Salaha ina Maryama..? Banganta ba..! Tafada tana kallonta kafin Umma tace wani abu da Sauri Munari tace"Tana Daki batajin Dadi Daada..! Daada ta jinjina kai kafin tace"Ayya..Meke damunta..? Taci abinci?tasha mgani..? Tayi Tambayar Duka Lokaci Daya,Munari tace"Eh Daada tasha Tea dazu kafin na Fito..! Daddy ya ijiye Spoon yana Fadin"Tun yaushe ne bata da lafiyar..! Umma tayi Saurin Taresa Tana Fadin"Yanzu da yamman ne fa Abban Intee..Ni na bata mgani kasanta Raguwa ce gajiyan Hanya ne..,! Kai ya kada bai ce komai ba Saboda Yasan meyasa Umma ta katsesa. Khamis kuwa Hankalinsa ya tashi jin Inteesar bata da Lafiya Daman Tunda yazo ita yake songani Cikin nuna Alhini ya kalli Munari yana Fadin"Mai sunan Goggo jikin Inteesar din da Sauki ko..? Kai ta gyadamai kafin tace"Eh Kamar ta samu barci ne..! Kai ya jinjina duk ya Damu yama kasa Cigaba da cin Abinci,Mami Asma"u na Lura dashi Ranta ya baci ta kallesa Tana Fadin"Kacigaba da cin Abincika Tuwo ne fa nasan kuma Kan sonsa sosai..! Dan Mirmishi yayi ya cigaba da cin Abinsa Imran kuma Cokali Daya yayi bai kara ba,wayarsa ya Fiddo ya Turama Inteesar sako. "Ki fito falo kici Abinci..,! Ya turamata ya ijiye wayar a gabansa Daada Dake kallonsa Tace"Imrana kaci abincin mana..ko Baka cin Tuwon ne a sama maka wani abu..? Da sauri ya Girgizamata kai kafin yace"Wannan ma is ok Daada Zan ci.! Kai ta gyadamai Lokaci Daya Tana kara Nazarinsa Juya Cokalin yake yi Sai ya Dauki Lokaci kafin ya karaci yanayi yana kallon Wayarsa Zuciyarsa ta fara Zafin ganin bai ga sakonta ba,atsawon Mintina Hudu kafin yaji Sakonta ya shigo da Sauri ya Dauka ya Duba. "Nasha Tea Ya imu..! Da Sauri ya Rubuta mata Amsa da cewa"No..Do as i say Inteesar!!!..Kinsan bana son gaddama ko..? Ya turamata kafin ya ijiye wayar Yana Sauke Numfashi. Daga bangaran Inteeear kuma ganin Sakon Imu yasa Dole ta mike sanin Halinsa kada tayi laifi Dogon Hijabin Hafsah ta saka Ja,mai hannu Dama karamar Rigace ajikinta mai kama da Shimi shiyasa ta saka Dogon Hijabi,Allah yasa Munari ta tasheta Tayi sallar Isha"i ta matsa mata ta sha Tea. Cikin Tafiyar kasala ta fito daga Cikin Dakin zuwa Falo lokacin data Fito ma Wasu sun gama cin abinci wasu ne basu gama ba Tukunnah,Tana yin sallama acikin Falon idanuwan Khamis ya fada kanta ya wani Kuramata Ido kamar zai lasheta,Imran ma ganinta yasa yaji sanyi shi kallo Daya yayi mata bai kara ba ya waske yaji dadi tanajin mganarsa,Bai ma lura da kallon da Khamis ke Binta dashi ba. Ta gansa sai dai tayi kamar bata gansa ba ko barayinsa bata kallah ba Wajen su Abba ta nufa ta duka ta gaishesu suka amsa mata suna Tambayanta ya jiki ta amsa musu da sauki,Daddy ya Dafa kanta yana Tambayanta ya jikinta ta amsa mai cikin Shagwaba kamar ta Kwanta ajikinsa sai dai ba Hali tashi tayi ta koma wajensu Umma Tana gaida su goggo Maimunatu,ita kadai ta amsa mata cikin Sakin Fuska banda Goggo Bintalo Sama sama dai bata damu ba ta Lafe jikin Umma,Umma ta Tureta tana Fadin ta dagata Shagwabe afuska Tayi goggo Maimunatu nayi musu Dariya Daga Khamis har Imran kallonsa na kanta shi khamis irin kallon nan ne ma marasa aji yayinda Imran yake kallonta ta kasan Idanuwansa wanda ba wanda zai Fahimci yana kallonta ne. Tashi tayi ta koma Wajen su Anty Safiya inda suke Hira dasu Munari Kafin taje ta gaida Daada Wanda Imran ke gefenta,Lamgwabe tayi jikin Daada Tana mata Shagwaba Daada na tambayanta jikinta ta amsa tana kallon Imran wamda ya Dauke kansa kamar bai ganta ba. Daada ta Umarce da akwashe kwanunka da aka gama cin Abinci nan da nan kuwa su Munari suka Mike dasu Anty Safiya suka Tattara komai suka maida Kitchen Munari da Hafsah da Umaima suka Share Wajen suka Goge. Daada ta Umarce ya"yanta su Matso kusa da"ita Inteesar tatashi ta koma Cikin su Munari yayinda Imran ya koma Chan karshen kusa da Sagir bai da yarda zai yi ya gudu saboda Daada bayaso yayi abunda zai bata mata rai. Sai da kowa ya natsu kana Daada ta fara da Sallama ta Umarci Sadam daya Bude Taron da addu"a ya Bude aka Shafa Daada ba wani Dogon bayani tayi ba Abba ta bama Daada ya bama Kowa Labarin inda suka Shiga bayan barinsu Lagos. Abba bai yi Nauyin baki ba ya gyara Zama ya shiga bada Labarin Abunda ya sani na Komawarsu kano daga Bakin ya"yansa dayasha ji da kuma Wanda ya sani ya Karishe da Fadin"Ya"yana sune garkuwata sune Duniyata..Musamman ma Yusuf gashi nan dan albarka ya Dauki Ragama da Nauyin daya kamata ni zan dauka ya kula dani..Ya kula da Kannensa Munari da Imran,ya Dauke komai a Wuyansa Imran ma ba"a barsa abaya ba Yana da kwanjin Kula da Ahalinsa Babu Abunda Zance musu sai Godiya da Fatan Allah ya basu masu Rama musu..! Yafada cikin sadda kai Lokaci Daya aka amsa da Ameen. Kafin Abba ya Dago ya cigaba da Fadin"Daada kiyi hakuri ki yafemin keda Sauran yan'uwana..Har ga Allah ba"a san raina Suka yanke wannan Hukuncin ba Lokacin bani da lafiya Sanda na Dawo Cikin hayyacina babu abunda zan iyayi saboda Ina neman Lafiyata ne kafin komai..! Daada ta jinjina kai Tana Fadin"Bakomi Malami ban taba Rikon ka acikin Raina ba Tsakanina Dakai sai addu"a da Fatan Alheri..Ba kuma Laifinka bane ba kuma Laifin su Imrama bane Laifin Yan"uwanka ne da suka kasa Fahimtarka Musamman ma Kabiru..! Tafada Tana nuna Baffa Kabiru Wanda ya Dago yana kallonta Hakama Ya"yansa da Matarsa suka Dago suma kallon Daada. Cikin Muryan Tsufa ta Cigaba da Fadin"Da basu rika ganin Laifinka ba..da duk haka bata faru ba..Da sun jaka ajiki da duk haka bata faru ba..Ammh tunda kaga ka dawo Alhamdulillah kuma sun gane kuskuransu..Yanzu kai kabiru da Mustpaha ku juya ku bama Dan"uwanku Hakuri..! Abba zai yi mgana Daada ta Hanashi Tana Fadin"Ku bashi Hakuri..nace..! Daddy ne ya fara mgana inda ya kalli Abba yana bashi Hakuri Abba ya girgiza kai yana Fadin"Bakomai Mustpaha Wlh bantaba Kullatanku ba..! Baffa Kabiru kamar bazai yi mgana ba Mami Asma"u sai Hararan Daada take yi Sajida ma ranta duk ya baci gani take kamar Daada ta Dizga Dad dinsu gaban Mutane bai isa ya Tsallake Umarnin Daada ba ya juya yana bama Abba Hakuri ya girgizamai kai yana Fadin"Wlh ko daya ban taba Rike hakan Araina ba..! Daada ta murmusa Tana Fadin"Naji dadin jin haka..Daman fa"idan haka ku hada kanku Waje daya ne..Naji dadi sosai Allah ya kara Hada kanku..yayi muku albarka Gabadayanku ku da Zuru"anku..! Dukkansu suka amsa da Ameen Abba ya gyara Zama yana Fadin"Daada ina son na gayamiki wani abu kada ki gani kice ban Fadamiki ba..! Da mamaki Daada ke fadin"Meya faru Malami..!? Abba juyawa yayi yana kallon Imran Wanda kamsa ke kasa kamar baya jin Abunda ke Faruwa nan kuwa yana jin komai,Maida kallonsa yayi kan Daada kafin yace"Faruwar abunda ya Faru ya Sauya Imran sosai..har Sigari ma yana sha..Sai dai nasan Tunda komai ya Daidaita zai daina sha da Izinin Lahi..! Shuru falon yayi Imran kuwa ko Dago kai baima yi ba,Kamar ma bai ji ba Haka ya nuna,Mami Asma"u ta tabe baki tace"Ai wanda ya fara ShayeShaye..Da wahala kaga ya iya barinta..! Tafada kai Atsaye ba wanda yabi ta kanta Sajida kuwa Gabanta ne ya Fadi Imran ke Shaye shaye..? Gabanta ya kara Faduwa ta fara Wurga idnuwansa nemansa Cikin Falon sai chan ta Hangosa kansa na kasa ta na kara Nazarinsa taga Yayi mata kama da mai Shaye shaye ko A"a..? Sai dai bata ga wata alama ba. Inteesar kuwa Mami Asma"u ta kallan Tana Mamakinta ita meyasa bata kama Girmanta ne..! Daada kuwa Mirmishi tayi kafin tace"Ai ya gayamin ma Malami Dazu da safe..! Gabadaya kowa ya Kalleta Cikin mamaki kai ta gyada tana kallon Imran kafin yace"Eh da kansa ya Fadamin..Halinsa iri dayane da na Mahaifinku Alkali baya karya komai zai Fada iya gaskiyansa kenan..Bakomai Allah yayi mana mganin komai..! Suka amsa da Ameen Tabe baki Mami Asma"u tayi ba Haka taso ba taso ne Daada tayi fada sosai.ta zageshi sosai ta kuma ji ta tsaneshi sai dai hakan bai samu ba Daada ta nuna ko ajikinta ma. Imran kuwa yana Duke dan Mirmishi kawai yayi bai ce komai ba acikin Ransa yana auna wasu abubuwa. Kwatsan yaji Daada tace"bayan haka akwai wani abu da nike son gabatarwa..Wanda na zauna na yanke Hukunci ni kadai da Zuciyata Kuma ba Shawara bace Umarni nake so na baku koda shi kadai ne abu na Karshe da zan gudanar ina da Rayuwa..! Kowa Hankalinsa ya maida kanta Domin karin bayani. Daada ta gyara Zama Kafin ta Cigaba da fadin"Mustpha,Malami da kai Kabiru kune Maza manya..Ina son ku Hada Auran Imran Dan wajen Malami Da Sajida yar Wajen Baffa Kabiru Saboda Dalilina na kara Hada kanku ya"yana da Jikokina waje daya..! Gabadaya Falon sai da kowa yaji mganar Daada kamar Daga sama Baffa Kabiru ya zaro ido yana kallon Daada Abba kuwa Daddy ya juya ya kallah Shima shi yake kallo cike da mamaki. Zuciyoyi uku kuma sun Buga Lokaci Daya Zuciyar Imran data Sajida sai ta Inteesar wacce ta kwalalo ido Tana kallon Imran wanda ya Dago kansa Cikin mamaki yana kallon Daada yayinda Sajida ta rasa gane yanayinta Farinciki ko bakinciki. Munari da Hafsah suka kalli juna cikin mamaki haka su Yusuf su kansu mganar tazo musu a bazata. Inna Maimuna kuwa jinjina abun take ita da Umma suna Hango Tashin Tashina kan wannan mganar. Mami Asma"u kuwa kamar ma bataji Daidai ba Idanuwanta kan Daada kafin tace"Sajida fa kikace Daada..? Wata Sajidan..? Daada kai Tsaye ta kalleta Tana Fadin"Wata Sajida kika sani..? Sajida dai Yar wajenki Asma"u..! Ai da sauri Mami Asma"u ta Zabura ta Mike Cikin Hargowa take fadin"Na Rantse da Allah Daada bazai sabu ba..Arasa wa za"a bama Dan Shaye Shaye Tsageri fitsararre mara kunya sai Ya"ta..? Ina wannan mganar bama mai yuyuwa bace Sajida bazata taba auran Dan iska ba wanda baida Sana"a sai Shaye Shaye..! Tafada Cikin bacin rai Lokaci Daya tana Tada Jijiyan Wuya da nuna Rashin yardanta kan mganar. *Kuyi Hakuri Don Allah yau nayi Fama Da rashin Chaji ne,Bamu da wuta nakai wayata Chaji ban karbo akan Lokaci ba afuwan..* *Shakira* 3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�5* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Mamakin Mami Asma"u ya kama Ilahiran wadanda ke cikin Falon,Barin ma Abba da Daddy da suka ga yadda Mami Asma"u take nuna Hannu tana so taja da mganar Daada wanda ko su basu isa su ja da Umarninta ba. Imran manyan Idanuwansa ya Zubamata da suka Fara Chanza Launi Saboda bacin rai bai ce komai ba sai dai ya kara Ware idanuwansa kan Yarinyar da Daada takira da Sajida Duk da bai san ko itace ba a mganar Mami Asma"u ya tabbatar da Zarginsa sai akaci sa"a itama Sajidan shi take kallo da dukkan Tunaninta Shima sai Lokacin yake kare mata kallo Cikin kaskanci da bacin rai Billahil Azim Ko Dauramai wannan yarinyar akayi a Kafarsa sai ya kwance ko mata sun kare a Duniya babu abunda zai yi da ita ballatana Har Uwarta ta Nemi gayamai mganar Banza Daada kamar Tayi kuskure ne Wajen Fadan suna. Sagir kuwa Tsabar mamaki ya kasa mgana Shi da Yuauf Imran kadai suke kallo suna Fatan kada wani Hargitsi ya Faru a wannan zaman sun sansa sun san Halinsa bayason ka Shiga Harkansa ka batamai rai yanzu zaku samu mtsala. Khamis kuwa bai ce komai ba Ammh Shi kansa Hadin ai bai yi ba ina Sajida ina wannan Muradadden Mutumin wanda baisan yan"uwansa ba sai dai yana da Tarbiya bai saka baki cikin mganar da ba nasa ba. Inteesar gabadaya Jikinta taji yana Rawa Zuciyarta na Bugawa Fat!Fat.Kamar wacce tayi Gudun Fanfalaki Kanta ya Fara wani Sarawa da Karfi Har Jikinta na kasa Daukanta Daga inda take Zaune Hannun Munari ta Damke Lokaci Daya tana Runtse Idanuwanta ta sauke kan Imran wanda ya Kauda kansa Daga kallon Sajida yana maidawa wani barayin yana Kokuwa da bacin Ransa ne bayaso Ransa ya baci ya Hargitsa wajen Wanda kuma ya Tabbata bazai ma kowa Dadi ba. Munari da Hafsah cike da mamaki suke Bin Inteesar da kallo wacce ke Hada Uban gumi duk da Sanyin Fanka da A.c dake cikin Falon ammh bai isheta ba Lokaci daya Jikinta sai karkawa yake yi Har suna jin haka a Hannuwansu data Damke cikin nata. Cikin Firgicin da suke ciki Munari tace"Intee meya faru..?Ciwon kan ne ya tashi..? Haka suka Shiga Jera mata Tambaya Ita da Hafsah sai dai ita kanta Baxata iya Fasaara Halin data Shiga ba Tun Lokacin da Taji Daada tana Fadin Umarninta ne Imran ya auri Sajida Taji komai nata ya Tsaya Cak ta kasa gane gaba ballatana baya. Cikin wannan Halin ne Muryan Inna Maimunatu ya Karade falon Inda ta Mike Cikin bacin rai Tana Fadin"Haba Asma"u ai banzata Tsaurin Idanuwanki yakai Har Daada tayi mgana ko gama Sauke Numfashi batayi ba ki mike kice bazai sabu ba..In kin manta bari na Tuna Miki Daada Uwa take ga Yaya Kabiru kuma Kaka take wajen Sajida kamar yadda kike da Iko da ita muma muna dashi..kuma Dangin Uba sune Kan gaba Wajen zaba ma ya"yansu Mazajen da suka Dace dasu ba ke ba..! Ta Karishe Fada Cikin bayyana bacin Ranta da yadda Daman take Cike da Mami Asma"u da Raininta. Mami Asma"u da idanuwanta suka Rufe ta Fara Tafa Hannu Tana Fadin"Eyye Ahhye..Wato saboda ba yarki bace shiyasa kikacewa haka..?in adalci ne meyasa sai yata..! Ba yar Muatpaha ba yar wajenki..Ko ba yar Wajen Binta Dole sai yata.?oh saboda kowannenku anan yasan Zafin nashi kuma Ko Mahaukaci nasan abu mai kyau da Nagarta,Shiyasa ba wacce Zataso a Dauki yarta a Hadata da Mai Shaye Shaye kuma Dan iska..! Daddy ne yaji abun ya isheshi yana Daga Zaune ya Daka ma Mami Asma"u yana Fadin"Ya isa haka Asma"u..! Jin haka yasa ta tasomai Tana Fadin"Ba zan yi shrun ba..?Saboda kada na Fadi gaskiya ko..?To wlh ba wanda ya isa ya Dinkemin baki sai nayi mgana In adalci ne ka Dauki Inteesar ka basa mana Sai ka Shiga maganar in kana so na Rufe bakina nasan kuma adalci ne za"ayi anan Wajen ba son kai ba..! Tafada Tana kallon Daada Datake kallonta batayi mamaki ba Sai dai Tana kara Nazarin Wasu Hallayar Asma"u da ta dade da karantarsu,sai dai bata taba Nuna mata agabanta ba sai yau. Kowa mamakinta ya cikasa da mamakin yadda take Fadar mgana son Ranta Baffa Kabiru ya kasa Dakatar da ita Daddy ya kallesa Cikin Takaichin ganin yayi Shuru ko Uffan baice ba Ballatana ya Dakatar da ita Cikin bacin rai ya Maida kallonsa kan Mami Asma"u yana Fadin"Wlh Tallahi ba Domin Umarnin Daada bane da yau na Nuna Miki iyakarki Asma"u Da yau na Nuna Miki Da Imran da Inteesar duka Dayane awajena anan Wajen ba sai gobe ba zan Biyamai Sadaki a daura musu aure..sai ki jika Taki yar kisha..Domin ba ita kadai bace ya"a ki duba Fadin Falon nan Cike yake da ya"ya da jikoki Saboda ya"yanki kadai Daada bazata ji Tayi wani Maraicin Rasa Jika ba..! Yafada cikin Bayyana Bacin Ransa Imran kuwa jin Abunda Daddy yace ne yasa dago kansa ya Kalli Barayin da Inteesar take zaune karaf kuwa suka Hada ido Itama kallonsa take Cikin zuciyarta Tana jin Wani Rauni na shigarta,Hawayenta Datake ta Tarewa suka samu nasaran Zubomata Sharr saman Kuncinta shi kuma Imran sai yaji Ransa na Suya ganin tana kuka Wato itama saboda taji ance Zata aureshi ne take kuka..? Har haka ya zama abun kyama bai sani ba..? Shi fa Imran shine Inteesar take kuka Saboda mganar Daddy..! Tuni zuciyarsa ta bayyana Rauninsa Wanda ya Dade bai bayyana ba Abun yamai Ciwo kwarai shi bai damu ba don Mami Asma"u tayi wasu mgangu akansa Daman bata ishesa kallo ba ammh Yafi jin zafin ganin Inteesar na Hawaye bai sani ba Baisan yadda Inteesar take ji bane da bai yarda ya Zargeta kan Halin da ita kanta bata san Dalilin Shigarta ba. Mami Asma"u da kalaman Daddy suka bata Dariya ta Murmusa tana Fadin"In ka Burgeni ka Daura mai Daure da Inteesar yanzu Mustpaha..! Daddy ya yunkura zai mike Abba ya Rikeshi ya Dago yana kallonsa sai ya Girgiza mai kai shiyasa ya koma ya Zauna yana Huci Umma Kuwa na gefe Ranta duk ya gama baci tana ganin Sakacin Barrister sai yau ta Kara Tabbatar ma kanta ya Dade da Zama Mijin tace sai abunda Asma"u ta yanke. Inna Bintalo ne ta Tabe baki Tana Fadin"Mganar gaskiya aduba mganar Asma"u..Ko yayane..Gwara abu mai kyau da Lalala..! Mami Asma"u na jin haka Ta ce"Yauwa Binta daman nasan ko kowa bai Fahimceni ba ke zaki Fahimceni..Ki fa Duba Sajida fa kalleta ace Rana Daya za"a Illata Rayuwarta a aura mata Mashayi Rayuwarta ta Dauwama cikin kunci da bakinciki na Har Abada..Ina bazan bari a Cuceki ba Sajida bar kuka..! Tafada Tana kallon Sajida dake kuka Wanda ita atunaninta kukan Mganar Daada take nan kuwa bata sani ba Sajida tana kukan yadda Lokaci Daya Zuciyarta ta kamu da son Imran sai dai Tana Hango wani al'amari nan gaba. Daada da sai yanzu Tayi mgana Baffa Kabiru ta kalla cikin Takaichi kafin tace"To sallammmane ka Dakatar da Matarka hakanan tayi iya abunda zamu iya dauka ya kuma isa haka..Ko Tayi shuru ta koma ta zauna ko ta Ficemin daga Falo bana son ganinta! Daada ta Fada Cikin bayyana bacin Ranta Mami Asma"u ta saki baki Tana kallonta ta Bude baki Zatayi mgana Khamis ya mike yana Fadin"Mami plz..! Yace mata yana Riko hannunta Dole ta koma ta zauna kana ya koma Wajen zamansa Baffa Kabiru kuma bai ce komai ba,Kansa ma yamaida kasa,kamar bashi a falon saboda Yasan bazai iya Dakatar da Asma"u ba Yasan tabbas tana kan gaskiyanta ne sho kanshi bai yarda da mganar Daada ba banda Rikicin Tsufa Ina Sajida ina Imran ai Tazaran akwai Nisa kamar Tazaran sama da kasa ne. Daada ta kada kai tana Fadin"Nayi matukar mamakin yadda na bada Umarni wanda ko ya"yana basu isa suce A"a ba sai ke Asma"u kika Mike agaban ya"yana kika ce ban isa ba kuma nayi son kai banda adalci..! Ta karishe Fada Tana Kallon Mami Asma"u datake cika tana Batsewa. Kafin ta Cigaba da fadin"Kuma agabanka Kabiru baka iya cewa komai ba saboda abunda tayi a wajenka Daidai ne ko..? Dagowa yayu yana Shirin mgana ta Dagamai Hannu Tana Fadin"Ba sai kace komai ba na Riga nagama Fahimtarka..Ka nuna ban isa dakai ba Matarka ita keda iko dakai..Sai dai ina so ka sani Sajida bata fi karfin Imran ba sai ma shine yafi karfinta ba Domin Rayuwa ba ita bata isa ta taka Inda ya taka ba duk takamarta kuwa..Imran yafi karfinta da Duk Abunda Uwarta take takama dashi..! Ta karishe Fada Tana bayyana Bacin Ranta. Mami Asma"u tasan da ita Daada take wannan mganar Khamis sai girgizamata kai yake mganar Daada tayi ma Daddy da Inna Maimunatu Da da Munari da Safiya da Yusuf da Sagir Dadi Domin Ransu kuna yake data ke jifan Imran da kalmar dan Shaye Shaye Umma ma taji Dadi sai sakin Mirmishi take yi,Inteesar kuwa Ranta kuna yake ga Cin Fuskar Mami Asma"u ga Imu ga kuma mganar Daada. Baffa Kabiru dayaji kunya ganin Daada ta ganosa ya muskuta yana Fadin"Ba haka bane Daada..! Da sauri Tace"In ba Haka bane meyasa kayi shuru..?in kana so na yarda Matarka ba ita keda iko dakai ba..Ka Amince da wannan Hadin nawa..Sannan ina son a Daura auran nan Kafin kowannen ku ya koma Bakin aikinsa Gobe kenan in Allah ya kaimu..! Gabadaya aka Zurama Daada ido Gaban Baffa Kabiru ya yanke ya Fadi ya Dago yana kallon Daada ta Hade rai ba Fara"a,kansa ya maida Wajen Mami Asma"u wacce ta Girgizmai kai da Sauri Rauninta ya bayyana bazata Jure ganin an Ruguzamata Rayuwar yarta ba. Imran kuwa kansa na kasa bai Dago ba,yana Tunanin shi yaro ne da za"ayi mai irin wannan auran..? Me Daada take daukesa ne..?mara amfani ko wanda baisan inda kasan ke mai Ciwo bane?Kamar shi Imran ba wanda ya isa ya Wulakanta shi ko yakaskastan dashi bai nunamai kuakuransa ba Karyansa zai nuna ma Mami Asma"u tayi kuakure bazai taba Auran yarta ba Har Abada. Baffa Kabiru bai da wata Manufa bai isa ya Bijerema Umarnin Daada ba Sai da ya Sadda kasa kafin yace"Shikenan Daada..Na Amince Allah ya kaimu goben lafiya..! Da sauri Daada ta Saki Mirmishin Farinciki Tana Fadin'Masha Allah.Kai fa Malami me kace kan mganata..? Abba bai da tacewa kansa ya Gyada yana Fadin"Duk yadda kikayi daidai ne ni da Imran masu Bin Umarnin ki ne..! Mami Asma"u ta Mike Cikin Hargagi tace"To wlh in shi ya amince..Ni ban Amince ba..In dai ina Numfashi bamai Aura ma Ya"ta Dan iska Dan Shaye wanda baida Sana"ar fari ballatana na baki sai shaye shaye..! Tafada da karfi Tana Zaro idanuwanta Waje. Imran daya gama jin iya Abunda zai ji yakai wani limit din da Bazai iya Jurewa ba ya Mike da Sauri jikinsa na Rawa Cikin Dakakkiyar Muryansa mai Cike Amo da Zati yace"Kada ki kara Kirana Dan"iska..Ko Da'n Shaye..Shaye..Don"t Try it again..Don"t Ever Try it...! Ya karishe Fada Jijiyoyin kansa sun Mike Radau har ana ganinsu Naman Kirjinsa na sama da kasa Lokaci Daya yan Sakin Huci mai Zafi tare da Zafin Zuciya kamar yayi Bindiga haka yake jin kansa,Hannunsa Manuniya ya Daga yana nuna Mami Asma"u dashi Cikin Alamun gargadi. Gabadaya kowa sai ya koma kallon Imran cikin Mamaki,Umma aranta tace ai gwara yayi mganinta Haka ma Inna maimunatu taji acikin Ranta. Mami Asma"u da Ta tsaya tana kallonsa Cikin dan shakarsa Tace"In na kara fa? Me zaka iya Mara kunya Fitsararre..? Tafada Cikin Ingili tana Jifansa da Harara,Imran dayaji ya Fara rasa Duka Controling dinsa ya Fara Takawa zuwa gaban Mami Asma"u Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Sai na nuna miki Halin Dan Shaye shaye..Na kuma gwada miki Halin Yan iskan da kike Fada..! Yafada yana kallonta Ido Cikin ido babu Wani tsoro ko Shakkarta. Taji Tsoro saboda ganin yanayinsa sai dai kasawa ba nata bane Cikin Dari dari tace"An ce maka Dan shaye shaye..? Karya akayi ba Dan Shaye Shayen bane..? Tafada Cikin Nuna iya gaskiyarta ai batama gama Sauke Numfashi ba taji Hucin Imran gabda Fuskarta kamar Walkiya ya kariso gabanta Idanuwansa Sun Rufe baima gani Dakyau Zuciyarsa ta gama Rufewa da wani Duhu har yana Hango kansa yayi Ball da Mami Asma"u da sai ta Gamu da Bango kanta ya shafe ya Tabbata bazata taba manta dashi ba. Sai dai ya Daga hannunsa da Niyar Tureta Abba ya Mike da Sauri Cikin Abunda bai fi kiftawan ido ba ya Dakamai Tsawa"Imran...kada ka Fara..! Yafada cikin Tsawa da Hargagi wanda ya Firgita kowa,Mami Asma"u tayi bayan Baffa Kabiru da suka Mimmikewa Cikin mamakin Imran,Imran kuwa Cak ya Tsaya yana Sakin Huci mai Zafi idanuwansa sun Juye kamar yana cikin maye,Inteesar da Munari suka kamkame juna suka Fashe da kuka Su Sadam kuwa suma Mimmikewa sukayi cikin mamaki. Abba cikin Sauri yace"Yusuf da Sagir ku Rukemin shi..! Yafada a Taushashe Daada Dake Zaune bata Motsa ba Illah dan Mirmishi Data saki In Asma"u ta tabata Kabiru yayi shuru ta tabbata In tayi ma Imran bazai kyaleta ba yaron Zamani ne mai ji da kuruciya Shine Daidai da ita. Da sauri Yusuf da Sagir suka Karisa suka Rikesa daman suna Ta tsoron kada ya balle musu,Kokarin Fizge kansa yake yi suka mai Riko sosai Yusuf ya Kallesa yana Fadin"Imu..Imran kalleni..!natsu Nace maka..! Yafada Cikin Daga Murya,kallon Yusuf din yayi yana Budemai idanuwansa Cikin Muryansa mai cike da amo yace"Na natsu fa kace..?Kake fadamin na Natsu..? To bazan natsun ba..ka sakeni nayi mganin matar nan..Nace bana son ana batamin rai Bana so...BANA SO..! Tunda nazo na shiga Harkan wani..? Ina kebe kaina ne saboda ina Girmama yanayina..Bana so na bata ma wani rai nima bana son wani ya batamin Tayi ta mganganu akaina Cikin son ranta..Waya Dakatar da ita..?ko wayace mata ta bari bai kamata ba? Sai ni domin nagaji nayi mgana..? Wlh billahill Azim bata san Waye Imran ba yau bazan ji mganar kowa ba indai matar nan ta kara Bude baki ta Fadi wata mganar banza akaina sai na Nuna mata Kalata sai na Nuna mata ita din ba kowan kowa bace a Wajena..! Ya karishe Fada Cikin Tabbatar da mganarsa Khamis ne ya Isa gaban Inran Cikin Fushi daman Tun dazu yana Tsaye so yake yaga Karshen Rashin kunyar Imran din in zai iya Dukan Maminsu..? Lalle da yau yagane Shayi Ruwa ne..! Kikam ya Tsaya gaban Imran yana Fadin"Yanzu kai in aka barka sai ka Daketa..?kasan wacece ita agareni.?mahaifiya kasan kuwa mtsayin uwa a wajen D'anta..!?da zai iya zama ya Jure Cin Zarafinta Daga wani bangara..? Yafada Lokaci Daya yana Dukan Kirjin Imran wanda ya tsaya Kikam Shima yana kallon Khamis Cikin wani Kallo na Takaichi Karamin Tsaki yaja kafin ya kwace hannunsa a wajensu Yusuf ya Saka Hannunsa ya bambare Hannun Khamis akan kirjinsa yayi irin Wurgi da Hannunsa da Zafi sai da Yayi baya kamar zai fadi kana ya Tsaya da Kafafunsa. Cikin Nuna sa da yatsa Imran yace"Kai yaro kauce badai kai zan yi ba..Ita din wacece..?ni ba kowa bace a wajena..Ko Baffa Kabiru dake mtsayin Yayan Mahafina bai isa ya tsaya yana gayamin mganar da wanchan matan take Fadamin ba ballatama ita ba kowan kowa ba..In kai kasan Darajan Mahaifiyarka ni kuma da bani da uwa ai nasan Darajan kaina...Kauce kabani Wuri kafin ranka ya baci..! Ya Karishe fada Lokaci daya ya bangaje Khamis dake tsaye sai da yayi gefe kamar Zai Fadi Sagir ya Rikosa gaban Sajida dake makale jikin Umaimah ya Karisa Cikin kallon Kaskanci Tare da kare mata kallo Daga sama Har kasa kafin ya Nunata da Yatsa yana Fadin"Wannan abar ne kike Rigima akanta..? Ai ni ban ga mace anan wajen ba..Na Rantse ga Allah ni Imran Abubakar Malami Wannan yar taki a cikin yanmatan da zan iya maneji dasu bata aciki ko acikin Tsakiyan Shinkafa ta shiga zan saka Hannu na Tsinceta na Wurgar..Nafi Karfin yarki da Duk Abunda ta mallaka..! Yafada yana karkato da kansa Wajen Daada kana cikkn Kaushin murya yace"Daada ki janye mganarki..Ni ban amince da wannan Hadin naki ba Ko matan Duniya zasu kare Bazan iya Auran Diyar masu som kai da son zuciya ba. infact ma batamin ba..Bana sonta bazan taba sonta ba..! Yafada kai Tsaye Zaro ido Kowa yayi yana kallonsa Mami Asma"'u taji Tsoro yasa ta kasa wani Motsi tana Bayan Baffa Kabiru da shima ya kasa Cewa kala ballatana Fadan datafi karfinka sai ka maidashi wasa. Ballatana Khamis da Mamakin karfin Imran ya kamasa Sagir dake rike dashi ganin yana Kokarin kwacewa yasa ya Girgizamai kai yana Fadin"Kada ka shiga wannan Fadan..Abba ne kadai ya isa ya Dakatar da Imu ammh wlh kai bazaka iya ba..! Zallar gaskiya ya gani acikin Idanuwan Sagir yasa ya kasa Motsi. Sajida kuwa Kukanta ne ya Karu jin Abunda Imran yace ita kuma alokacin ji take Imran yayi mata Dari Bisa Dari. Inna Bintalo ce ta Saka Salati tana Fadib"La"ila Ha'illahu Ni Bintalo yau ina ganin Abun mamaki kai Imran Matar yayan Mahaifinka ka Daga hannu Zaka Daka..? Ashe baka da kunya da Tarbiya bansani ba..? Kai Tsaye Imu ya kalleta Ido Cikin ido kafin yace"Eh..Ai ba uwata bace..?ko Ita din U..!!! Bai kai Karshen mganarsa ba Yaji Abba ya Sauke mai kyakyawan mari Guda Biyu Dama da Hagu da sai da Kansa ya koma gefe yana jin Wani Radadi daga kasan Ransa Idanuwansa ya Runtse ko Dagowa bai yi ba. Abba ya Nunasa da Yatsa Cikin Takaochi da Bacin rai yace"In ka kara cewa Tak anan wajen..Ni ba Mahaifinka bane..! Da sauri ya Bude idanuwansa Jajir ya Sauke kan Abba zai yi mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin"Kace Tak zan ci maka Mutumci Imran..Kaji ma na Fadamaka..!.dole Imran yayi shuru Ya koma yana kokuwa da Bacin Ransa ji yake kamar ya Naushi kansa saboda Bakinciki da tozarci. Abba ya sauke Hannunsa Cikin bacin rai yana Fadin"Ni kaina ban isa na take mganar Daada ba ballatana kai..To bari kaji na Fadamaka ba wanda ya isa ya Tada Umarninta Za"a Daura wannan auran agobe da yardan Allah kamar yadda tace sai dai in zaka Rataye kanka ne ko kuma ka sha Fiya Fiya ka Mutu karewar rashin So kenan..! Yafada cikin Tabbatar da mganarsa kafin ya cigaba da Fadin"Kuma na Rantse in ka kara cewa wani abu kan wannan mganar sai naci maka Mutumci..Duka ka bama Asma"u da Yaya Kabiru Hakuri kafin na Saba maka..! Yafada cikin bada Umarni Imran ya Dago ido yana kallon Abba,kai lalle uba ma wani abu ne Da ace yau ba Abba bane waya isa..? Ganin ya tsaya kallonsa ne da Jajayen Idanuwansa yasa ya Dakamai Tsawa Har Jikinsa na rawa yace"Ko bazaka Duka bane ni na Duka da kaina na basu Hakurin Rashin kunyarka..? Yafada yana Nunasa da Yatsa,Yusuf ganin yadda Abba ke rawan jiki yasa ya Isa kusa dashi ya Riko sa yana Fadin"Abba koma ka zauna zai yi Abunda kace..! Yafada yana Rikosa,Yusuf ya kallah kafin yace"Kyaleni kawai Yusuf..! Yafada cikin Tabbatarwa da nuna Bacin Ransa jin haka yasa ya Kyalesa ya Karisa Wajen Imran ya Dafa Kafadansa yana Fadin"Kayi Abunda Abba yace Imu..Plz..! Bai yi gaddama ba ya saka Gwiwiyinsa a kasa Kirjinsa na kuna Cikin Dashashewar Murya yace"Ku...yi hakuri..! Lokaci Daya yana Sadda kai Cikin Takaichi yanajin kansa kamar ma yayi Bindiga saboda Zuciya. Mami Asma"u ganin an bata Hakuri yasa Ta fito daga bayan Baffa Kabiru Tana wanu tabe baki ganin haka Yasa Abba ya juya yana Fadin"Ina kara baku hakuri a madadinsa..Yaya Kabiru dake Asma"u ku yi hakuri ku yafe masa..! Yafada yana Hada Hannuwansa alamun Roko Baffa Kabiru ne ya Jinjina kai Lokaci Daya yana Sauke ajiyar Zuciya Kafin yace"Is ok..! Da haka bai kara cewa komai ba,Mami Asma"u baki ta tabe kafin tace"Uhm..Shikenan..! Abba ya gyada kai yana Fadin"Nagode..! Lokaci daya ya juya wajen Imran yana Fadin"Tashi ka koma Wajen zamanka..Kuma ba cewa nayi ka Fita ba..! Yafada kafin ya kalli Sagir yana Fadin"Sagir kamasa kuje..! Sagir na jin haka ya Rikosa yana Fadin"Tashi Imu..! Bai yi gaddama ba ya Mike ammh Idanuwansa ma basa ganin gabansa Saboda bacin rai nan idanuwansa yakai kan Inteesar dake kuka Sai Yakara Rikicewa Kujeran dake Kusa dasu ya saka Kafa ya Daketa sai da tayi baya ta Wuntsula suka tashi a Firgece su uku ita da Hafsah da Munari suna Makyarkyata da kallo Kowa ya Bisa Abba kai ya Girgiza Shi da Yusuf. Sagir yayi ya zauna yaki a Tsaye ya tsaya ya Harde duka Hannuwansa saman Kirjinsa ya Lamkwashe kafafunsa yana Girgizawa. Daddy ne yace kowa ya koma ya Zauna kana Falon ya natsu bayan kowa ya Zauna Abba zai yi mgana da Daada ta Dakatar dashi da Fadin"Ba sai kace komai ba Malami..Abunda kayi daidai ne ka nuna mana Rauninka baisa ka Daina bama ya"yanka Tarbiya ba,Duk da itama Asma"u bata kyauta ba ta shiga mganar da ba nata ba sai dai Duk inda karami da babba ke Fada to Karamin ne za"a Hukunta ko da shi keda gaskiya naji Dadin Hukuncinka..! Ta karishe fada Cikin Dattako kafin ta Dora da fadin"Dalilina na Hada wannan auran don Dinken wannan Barakan dana Hanga Tuntuni ne..Za"ayi wannan auran gobe insha Aallahu kamar yadda nace..Ke Asma"u Allah yasa kiyi Hankali..Yanzu Imran suruki yake wajenki in baki Daukesa Danki ba..Kai ma Imranu Asma"u Suruka take gareka in baka Dauketa Uwa ba..Ku koyi girmama juna saboda haka..Dare yayi kowa yaje ya kwanta ya"yana kuma zamu kara Tattaunawa acikin Daki..Allah yayi muku albarka Gabadayanku..! Wasu ne suka samu amsa ma Daada da Ameen Mikewa tayi Daddy da Abba da suka mike tsaye suka Taimaka mata zuwa Dakinta,Inna Maimunatu da Inna Bintalo da Baffa Kabiru suka mara musu baya. Imran kuwa shi ya Fara Fita Waje Haraban gidan kansa sarawa yake yana jin kamar ma yayi Bindiga saboda Bacin rai wato sun Dage sai anyi ko..? Lalle zasuv samu karamar bazawara kamar yadda suka Dauramai bada son ransa ba Wlh Tallahi sai ya aikata abunda bazai ma kowa Dadi ba. Yafada Lokaci Daya yana Zaro karan Sigarinsa ya kunnata ya Haye saman Motan Yusuf ya shiga busa Hayaki ta Hanci ta baki itace kadai zata saka yaji Bacin ransa ya Ragu in ba Haka yau ba zaman lafiyaa Achan Falo kuwa kowa ya Watse Munari ta kama Inteesar suka Shige tana Waigen Inda Imran yabi ya Fita Mami kuwa ya"yanta ta Rumgume tana jin wani Radadi acikin Ranta Yayinda Khamis yazo yana bata Hakurin ganin Harda kukanta. Su Anty Safiya Daki suka shige Kowa zuciya ba Dadi Umma ma Dakin ta Shige Domin barci ne a idonta itafa bata ji wani damuwa ba mganin mai Son kansa kenan Su Yusuf kowa wajen kwanciya suka Nema kowa ba Fara"a ammh kai tsaye Sadam yace yaji Dadin abunda Imran yayi ma Mami Asma"u kila ta Daina abunda takeyi. Badai wanda yace komai Yusuf da Sagir Tunaninsu na wajen Imu basu san Halin Dayake ciki ba sai dai Dole su kyalesa sun san ko giyan Wake suka sha Karyansu suje wajensa ahalin Dayake ciki Kadaicinsa Shine mafita da wani yaje ya Damesa sai dai suna Fatan Allah ya Huci zuciyar Mazaje...! *Sai hakuri Team IMSAR�� kuyi Hakuri..ku kara Hakuri kila Burinku zai cika agaba ammh a wannan gabar Daada ke da Filin Dagar�🤣* *Shakira* 3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�6* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Mami Asma"u ta Rumgume Sajida ajikinta Tana Lallashinta ganin tana ta kuka,Dago kanta tayi tana Share mata Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Kalleni nan Sajida..In dai kin yarda ni Mahaifiyarki ce bazan taba bari a Rusa miki Rayuwa ta Hanyar aura Miki wannan Dan iskan ba..Ki daina kuka kinji ko My Sajida..! Tafada Cikin son Tabbatar da mganarta ga yar Tata. Khamis da Umaimai Dake zagaye da ita Tun bayan Ficewar kowa Daga Falon shine ya budi baki yana Fadin"Mami plz.Bana jin Dadin Abunda kike yi..Umarnin Daada ne kuma Kin Tabbata ko Dad bazai Tsallake mganarta ba ban ji dadin abun kikayi ba..Kamar yadda Dad zai bi Umarnin Daada kema Dolenki ne mganar wannan Yaron kuma am Begging u Mami ki daina Shiga Shirginsa zai iya miki komai domin baisan Darajanki ba..! Yana mgana Mami Asma"u na Hararansa Sai da yakai Aya kana ta Saki Wani Dogon Tsaki kafin tace"Sai kawai nayi shuru a cutar dani da Rayuwar ya"ta to bazan yi Shurun ba..Mganar Dan iskan chan kuwa bazan fasa Fadin gaskiya ba duk abunda zai yi ya Dade bai yi Uban da ya fasa yaci Ubansa..! Tafada cikin bacin rai jin haka yasa bai kara mgana ba ya Fice Daga Falon zuwa Dakunan da suke kwana Mami Asma"u ta Tada Sajida suka kamata Ita da Umaima zuwa Dakin da ta sauka ita da Umma,koda suka Shiga sun samu Umma na Sallar Shafa"i da Wuturi kan gadon dake Dakin ta Ssuke Sajida dake faman ajiyar rai Tana Lallashinta tare da mata alkawarin auran nan bazai Tabbata ba Umaima na gefe batace komai ba ita karama ce ta Tabbata ta Fadi wani abu wanda ya saba Ra"ayin Mami Sai Ranta ya baci Sajida kuwa tana kwance lamo acikinta Ranta Tana Fatan Allah yasa a Daura auran nan Tunda take bata taba jin bugun zuciya kamar yadda take jin kan Imran ba Daman saboda shi ne yasa Har kawo Lokacin bata ga wanda yayi mata ba sai da ta gansa ta Tabbatar da yayi Daidai da Ra"ayinta Rashin Tsoronsa da Zuciyarsa ke kara Tsumata akansa Taji gabadaya ya gama Burgeta bata Damu da mganar Mami na Shaye Shayensa ba Ta tabbata in suka yi aureta Zata gyarasa ya Daina shan komai,Tasan in ta Bude baki tace wani abu Yau Mami Asma"u sai ta kwana tan Fada kamar ta ari baki Shiyasa tayi bakam kamar Itama tana cikin Damuwa da Umarnin Daadan ne nan kuwa bata sani ba Ranta Fes yake. Umma na gefe Kanzil batace ba sanin itama Mamin ba Ragamata Zatayi ba Tunda Har Daddyn Intee Bata Ragamai ba Umaimai Dakin da su Munari suke ta koma Zata kwana Mami Asma"u na cikin Damuwa yasa bata ma bita kanta ba. Bangaran Inteesar kuwa Kukanta gabadaya yaki Tsayawa tana kwance kan gado tana kuka,Munari da Hafsah na Zaune gefenta sun Saka Tagumi sunyi Tambayan Duniyan nan Taki ce musu komai. Hafsah ce ta kalli Munari tana Fadin"Ko ciwon kan nata ne ya matsa mata..!? Munari ta Sauke Taguminta tana Fadin"Ni bansani ta kuma ta ki tayi mgana..! Tafada daidai Lokacin da Umaimah ta Shigo ganinsu haka yasa take Tambayansu ko lafiya Hafsah suka nunamata Inteesar dake kuka Har yanzu tana Dukunkune kanta Cikin Hijabinta tana Shesshekan kuka. Umaima ta Zauna gefen gadon Tana Fadin"Ko mu kira Umma ne..? Munari ta mike tana Fadin"Yauwa bari nayi mata mgana..! Jin haka yasa Inteesar ta Dago kanta Cikin Shakewar Muryan data gaji da kuka Tace"Kada ki kirata Muna..! Munari ta jiyo tana Fadin"Saboda Mene..? Kin ki gayamana meke Damunki ammh kin zauna kina ta kuka ba Dole Hankalin mu ya tashi ba..! Inteesar ta Koma ta kwanta Tana Juya Idanuwanta da suka koma jawur saboda kuka wani suya take ji acikin Kirjunta da wani Nauyi,kamar an Dora mata wani Dutse mai girma,Cikin Dauriya tace"Ciwon kaina ne fa zai bari in na samu Barci kada ku damu dani ku kwanta abunku..! Tafada tana kara Dunkule jikinta Waje Daya gabadaya kallonta sukayi Cikin wani yanayi batare da sun kara mgana ba suka koma suka Zauna Jugum jugum ganin haka ne yasa Inteesar din ta Mike ta Zare Hijabin jikinta Idanuwanta na Rufewa Ta Wuce cikin Sanyi sanyi ta Fada Tiolet Domin tayi wanka ko ta Daina jin Abunda take ji acikin Zuciyarta ita Damuwarta Daya Imran bata san Wani Hali yake ciki ba,Tasan Halinsa da bakar Zuciya yana Wajen nan bai dawwo cikin Gida ba,Gashi Har 11pm ta wuce Dare ya fara Nisa. Ganin ta shiga Tiolet ne yasa sukayi Shirin kwanciya Hafsah ta Dauki Filo da blanket ta yada saman Cafet ta kwanta Munari ta saka kayan Barci ta kwanta saman gado ita da Umaima kowa na sake sake acikin Ransa. Bangaran Imran kuwa bai san iya adadin Lokacin Daya dauka yana Busa Hayaki ba har sai da duka Sigarin ta kare gabadaya kana ya Hakura wani irin Turiri yake ji acikin Ransa sai yau ya kara jin Radadin Rashin Uwa ya tabbata da yau Anni na Raye da zama bango garesa ammh Saboda bai da Uwa yau ga abunda ya Faru dashi domin ya Daukesa ne a mtsayin Tozarci Abunda Mami Asma"u tayi mai Abba ba"a sakashi a Lissafi sanyinsa yayi yawa,agaban Daada da yan"uwansa Baya Daga Murya Tun farko saboda haka yasan bazai ce komai ba ammh shi Dole ne yayi mgana. Kafafunsa ya Hade waje daya ya Saka kansa Tsakanin Cinyoyinsa ya Fashe da wani kukan Dayaji yana Tasomai Daga kasan Ransa,Rabonsa da kuka Tun Lokacin Rasuwar su Anni sai yau Zuciyarsa nada Taurin da kuka ba kasafai yake iya yinsa ba sai dai Zuciyata tayi ta kuna ammh yau yaji yana son yayi kuka kukan Rashin Mahaifiya agaresa,Kukan Rasa Anni yana Tuna Sanda Tana Raye mai kula dashi,Tana fadin Imran ka dinga shiga Mutane ka Rage wannan zuciyar taka Saboda Rayuwa in yau mune watarana bamu bane Imrana ina jiyemaka Ranar da zakayi kukan Rashina Rashin mai fadamaka gaskiya... Haka yake jin Amon muryanta acikin kunnuwansa kamar alokacin take Fadamai sai ya kara Fashewa da kuka ammh Abun mamaki babu ko Digon Hawaye sai dai idanuwansa sun kala sun yi Jajir,Haraban gidan Tar yake da Hasken Wutar lantarki,Shiyasa Megadi dake zaune bakin get kan bencinsa yake Hangensa,Tun Lokacin Daya Fito ya gansa yana shan Tabarsa kada kai yayi kawai bai ce komai ba ya Cigaba da jin Radion sa. Inteesar ta bata Lokaci kafin ta Fito Daga Tiolet din wanka Tayo ta Dauro alwala Domin taji barcin ya Fita Daga Idanuwanta kanta nata Sara mata ga Nauyin kirjin datake ji wanda ta rasa Dalili ta iske dukkansu sunyi barci. Wata Rigar barcinta ta saka Riga da wando masu Taushi ta saka Hijabinta ta Daidaici gabas ta tada Salla Shafa"i da Wuturi tayi Kafin ta zauna nan inda Tayi sallar ta jingina da gado Ranta namata Daci ita ba wai wani abu ba Bata son Ya Imu ya auri wannan marar mutumcin bata Dace dashi ba sannan Cin Zarafin da Mami Asma"u tayimai yau ya bala"in sosa mata rai Bacin ran Imran bacin ranta ne in wani abu ya samesa sai taji duk ta Damu wayarta ta jawo Dake saman gado ta Duba Lokaci 12:12am na Dare jikinta yayi sanyi Tana Tunanin Ya Imran ya Dawo cikin gida ko yana Waje..!? Wajen sako ta shiga ta Turamai "Kana ina ne..? Plz ka dawo cikin gida Dare yayi..'!! Tunda ta Turamai take jiran amsarsa ammh Wajen Fin Minti goma bata gani ba,Sai ta kara shiga damuwa Kiransa tayi Har sau uku bai Dauka ba Hankalinta taji ya kara tashi ta Mike Tsaye tana Tunanin ta Fita ne tagani ko kuwa A"a..? Imran yana Cikin kukan Zuccinsa dana Sarari yaji Shigowar sako acikin Wayarsa kamar ya Share sai yaji ya kasa ya Dago kansa bayan ya Zaro wayar daga aljihun wandonsa ya Duba sai yaci karo da Sakon Inteesar wani Dum yaji acikin Zuciyar sa Ransa ya kara kuna yana Tunanin me Zata fadamai ita datake kuka Saboda Mganar Daddy..? Karamin Tsaki yaja ya goge ma sakon nata wanda ta Turo ammh ya kasa goge duka Sakonninta Haka kurum yaji bazai iya ba.. Wayar na Hannunsa take ta kira yaki Dauka sai da ta gaji da kira ta Hakura kana yaji Kamar bai kyauta ba ita Kadai ta damu dashi da Halin dayake ciki Shiyasa ya Turamata sako. "Ki daina Damuna plz ki kyaleni..' Haka ya Rubuta mata tana Daga Tsayen Taji shigowar sakonsa Hannunta Har rawa yake wajen ta Duba Tana ganin Abunda yace taji Hankalinta ya kara tashi a Fili ta Furta"Yana cikin damuwa Ransa ya baci.Kuma shi kadai a waje..! Tafada Wasu Zafafan Hawaye na Biyo kuncinta batasan meke damunta Taaudsyin Imran da wani abu acikin Kirjinta da batasan ko na miye ba suka Rinjayeta ta Fito Daga Dakin Tana Sanda,Falo ba kowa shiru Duk an kashe Haske,dakuna ko"ina akulle Su Abba Tuni sun gama Tattaunawa Da Daada ta Sallamesu sun nemi makwanci Ba motsin kowa,Ahankali ta Fara takawa bayan ta Dan Taba Wayarta Haske ya kawo saboda ta rika ganin gabanta Har ta samu nasaran Ficewa Daga Falon Tunda kofar a Bude take ba"a Rufeta ba. Tana Fitowa Haraban gidan ta Fara waige waige Karaf kuwa ta Hangosa kan Mota ya Cusa kansa Tsakanin kafafunsa Allah sarki kalleshi shi kadai Haka ta fadi acikin Ranta tanajin wani Feeling dake taso mata Daga kasan ranta kan Imran da har yau ta kasa Tantance Menene hakan..? Jikinta a sanyaye ta Fara takawa zuwa Gabansa bai ji tahowarta ba sai dai mganarta kawai yaji. "Ya imran..! Tafada Cikin karyewan muryan Data Shake a kuka da Sauri ya Dago shima Rinannun idanuwansa ya Sauke Cikin nata gabadaya sai da Jikinsu ya amsa Hade da Bugawar Zuciyarsu,mamakin ganinta ya kamashi Saurin Dirowa yayi Daga saman Mota yana Fadin"Ke meya Fito dake yanzu da Tsohon daran nan..? Yafada Lokaci daya yana Duba Agogon Fatan dake hannunsa yaga 1 saura na Dare ido ya sakamata ganin Ta faramai Hawaye Cikin Bacin ran data karaman ganin kukan ta ya Daga Murya yana Fadin"Wayace ki Fito..? Nace wayace ki fito..?.. Yafada Cikin Tsawan data Fashemai da kuka Tana fadin"Wajen..ka..nazo..! Tafada Cikin muryan kuka Zuciyarsa ZAfi take da kukanta shiyasa Ransa ke kara baci Cikin Tsawan ya kara cemata"Ban ce ki kyaleni ba..Ni bana Bukatar kowa I don"t Need Anybody..Ki wuce ki koma Cikin Gida Tun kafin Raina ya baci na saka miki Hannu anan Wajen..! Ya karishe fada yana so ya Danne Abunda yake ji yana Tasomai Daga kasan Ransa. Ita kuwa kuka kawai take Ta saka Hannunta taja Hijabinta ta Toshe Bakinta ganin in ta Cigaba da Tsayiwa yana jin kukanta Zuciyarsa Zata Tsawartse saboda Bacin rai yasa ya nuna mata Hanya yana Fadin"Oya your way here..Kije chan ki cigaba da kukan naki ba sai kin zo kin fadamin ba..Nima bazan ce a auran mik...! Bai gama Mgana ba yajita kikam ta Fadomai jikinsa da wani irin karfi Ta Rumgumesa kamkam kamar wani zai kwace mata shi Lokaci Daya tana kara Fashemai da kuka. Jinta Cikin jikinsa da yadda ta kamkamesa sai ya sauya komai yaji sa Cikin yanayin dayake shiga duk sanda Jikinsu ya Hadu waje Daya kukanta ya sakamai Rauni jin Dumin jikinta ya sakashi jin wani yar acikin jikinsa Tuni Zuciyarsa ta Bude ya Farajinsa kamar bashi ba,Zuciyarsa ce ta Rinjayesa yajisa ya saka Duka Hannayensa ya Rumgumeta kamkam shima atare suka ja Numfashi Cikin Bugawar Zuciyarsu alokaci Daya. Shima indaizai Fitar da Hawayen Dayaji Dadi ya fita tsawo shiyasa kanta ya tsaya saman Faffadan kirjinsa Shi kuma ya nannadeta da Hannanyensa a saman kanta ya aza kansa ya sauke Numfashi. Cikin muryan kuka Inteesar ke Fadin"Kada ka kara fadin haka ya Imu..!Ni bazan taba gudunka ba Har Abada..! Kalamanta Daki daki ke shiga Cikin kunnuwansa,Yana Rike da ita cikin Wata irin Raunanniyar murya yace"A"a..Bana so naga ina sakaki kuka..Kiyi Hakuri Daady bazai aura Miki Dan iska kuma dan Shaye shaye ba..! Yafada yana kara jinta ya Riketa kamar itace Salama acikin Rayuwarsa,Rikon yayi mata Zafin Dayasa sai da ta saki yar kara sai kuma Lolacin ya Farga da abunda ya aikata da Sauri ya Saketa ya mtsa baya yana Kokarin Daidaita kansa Inteesar kallonsa take Cikin wani yanayin Da takasa gane ma kanta ta Bude baki Zatayi mgana kawai ya Ja Hannunta Lokaci Daya suka Fara Tafiya zuwa Cikin Falon Daada. Ta kara yunkurin mgana ya waigo yana jan Bakinsa"Shiiii...! Alamun tayi Shuru Dole ta maida bakinta ta kulle sai dai idanuwanta suna kan Hannunwansu da suke Hade Waje Daya tana jin wani irin Babban al"amari acikin zuciyarta Idanuwanta ta maida kansa yanayin Tafiyarsa kadai Zaka Fahimci maza na inda suke.. Tunaninta ya katse ne sanda suka Shigo Falon,sun shigo kenan Sajida Data Fito Daga Kitchen ki shi ya Fito da ita Daukan Ruwa kuma ta Kunna Hasken Falon idanuwanta Kur akan Hannun Inteesar dake cikin na Imran Cikin Faduwar gaba take Binsu da kallo. Imran kallo Daya yayi mata bai kara ba Ita kuma Inteesar gabanta ne ya Fadi,tuna yanayin data gansu kada ta Zargesu da aikata wani abu. Ta bude baki zatayi mgana kenan ya Saki Hannunta yana Fadin"Ki kwanta..And Stop craying ok..! Yafada yana Tsareta da Idanuwansa masu cike da bacin rai. Tana kallon Sajida dake kallonsu tama kasa gaba ballatana Baya bakinta ya kasa Motsi ganin haka yasa kawai ya Juya ya nufi Koridon da zai sadashi da Dakin da ya ssuka cikin Tafiyarsa ta Sassarfa da Jarumta Daga Intee Har Sajida ba wacce ya kara kallah,Bakinciki ne fal acikin Ransa,Yana jin wannan yarinyar ayadda yake jin Zuciyarsa Zai iya Kasheta bai Huce ba baima san kallonta Shiyasa yayi wucewarsa kada ma ya kara ma kansa Bacin rai. Sagir kadai ya iske a Dakin Yayi barci Ashe sama sama ne karan Bude Kofa ya Farkar dashi da mamaki yake kallon Imran wanda ko kallonsa bai yi ba ya Tura Kofar Tiolet ya shige ya Bango kofa. Sagir ya Sauke Numfashi kafin ya koma ya kwanta bai jima a Tiolet din ba ya Fito Dagashi sai Gajeron wando Jikinsa na Digan Ruwa Daga gani Wamka yayi,ko mai bai shafa ba ya Watsa kayan daya Cire nan kan gadon yaja Filo ya yada kan Cafet ya kwanta Ringine Ruwan jikinsa na Diga a inda yake bai Damu ba saima Hannayensa Daya goya saman Kirjinsa yana Sauke Numfashi Sama sama. Sagir Harda Tashi Zaune yana Lekensa yana kallonsa yayi kamar bai gansa ba sai ma ya juya bayansa Kawai yana kara Hade ransa kamar bai taba Dariya ba. Afalo kuwa Inteesar ce ta fara wucewa Dakinsu batare data kara Kalln gefen da Sajida take Tsaye ba,Sai da ta shige ta Rufo kofa kana ta Sauke ajiyar Zuciya tana goge Busasun Hawayen dake idanuwanta,Jikinta yayi wani irin sanyi haka ta karisa gefen Hafsah ta koma kwanta Tana jin wani yanayi a tare da ita Runtse ido tayi Ba domin tanajin Barci ba sai Domin Tana Fatan ya Dauketa,Hankalinta ya kwanta Tunda ta gansa kuma ya Dawo Cikin Gida Sai dai Hankalinta ya tashi da kalamansa, Shi a zatonsa tana kuka ne Saboda Abunda Daddy yace..?Baisan tana kuka bame saboda Tsausayinsa da wani Lamarin data kasa gane Wani yanayi ne? Menene yasa Kirjinta ke Nauyi kan Imran..? Meyasa bata son bacin ransa? Zuciyarta na Zafi in ta gansa Cikin damuwa Bata san Dalili ba sai dai ta Danganta haka da Dan"uwanta ne sannan akwai sanin juna Tsakaninsu tun kafin su gane su din Ahali Dayane. Sajida kuwa Har Inteesar ta Shige ta barta Zuciyarta bata gama Dokawa ba,Idanuwanta na hango mata gilmawar magijin Hannaun Inteesar Cikin na Imran dinta Zuciyarta taji tana Dokawa da karfi datayi Tunanin kodai soyayya suke yi..? Kai ina badai so ba sai dai in wani abun to kodai kodai..!.da sauri ta yanke wannan Tunanin domin ya kusa sakata ganin Jiri to ammh in ba ko Daya meye sukeyi Cikin Dare ko wa yayi barci Hannayensu Cikin na juna..? Bata damai bata wannan amsar Shiyasa cikin Sanyi jiki ta karisa Cikin Dakin Data Fito,Dauke da goran ruwan Data Dauko Daga Kitchen Mami Tayi barci duk da Kila bataso ma Tayi barcin ba sai dai ai shi ba"acin bashinsa Umma ma kan Darduman data gama sallah Tayi barcinta Ita da Mami ne suka Hau kan gadon.... Lallabawa tayi ta Haye gado ta kwanta Tana kokarin Daidaita Tunaninta kada Zargi ya shiga Cikin Zuciyarta ya Dagulamata komai.. ******* *Washegari* Kano. 10:00am Hajiya Mero ce da Alhaji Ahasaan da Tasleem zaune kan Dining din Dake Falon gidan,Suna Breakfast kowa na cin Abincinsa bakajin karar komai sai Cokali da bugawar Filet da Kofuna. Hajiya Mero bata wani ci da yawa ba ta Share bakinta da Tissue tana kallon Tasleem tace"Tasleem tashi ki Daukomin wayata acikin Bedroom dina..! Alhaji Alhassan dake Zaune yana Tura Dankali soyayye Cikin bakinsa,Cikin muryan Abu na Cikin bakin mutum yace"Haba Mero kina gani fa Breakfast take yi ai kya bari ta gama ko kuma ke tunda kin gama ki tashi ki Dauko Da kanki..! Wani kallo tamai batace komai ba Tasleem ta mike tana fadin"Bakomai Abbu bari na Dauko mata..! Shima bai yi mgana ba ya cigaba da Tusa dankalinsa yana Hadawa da Kurban Ruwan tea a wani karamin mug mai kyau da yarari. Ba jimawa sai ga Tasleem ta Dawo da Wayar Hajiya Mero a hannunta sai da ta Zauna ta mikamata Tana fadin"Gashi Mommy..! Karba Tayi tana Yar dariya da sai da suka Kalleta gabadayansu Lambar Safiya ta Lalubo ta doka mata Kira ta saka Wayar a Speaker ta ijiyeta nan kusa da Hajiya Alhassan saman Tebir din. Kira Daya biyu uku Safiya Daga Chan bangaran da suke Kitchen suna aikin Abincin da su Abba sukace ayi mai yawa Saboda bayan Salar azahar in in aka gama Daura auran za"a Fito da Abincin arabama Mutane. Gefe ta koma kafin ta Dauki Wayar Tunda gabadayansu suke Kitchen din Har da Inna Maimunatu dasu Zainab dasu Aneesa da su Munari Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba tace kanta na Sara mata. Sallama ta Ragada kafin tace"Mommy ina kwana..! Momny ta amsa Tana Fadin"Lafiya lau Daugher ya kuke..? Ya Dukkun..? Tafada tana kallon Alhaji Alhassan Daya ijiye cin abinsa yana Sauraransu Da mamakin jin ta ambaci Dukku. Safiya Dagachan bangaran tace"Lafiya lau Mommy gamu cikin sha"anin biki kin ji Hayaniya ko..? Mommy tace"Eh fa bikin waye..? Safiya tace"Mommy Imran za"a Daura ma aure yau da yar"uwansa Diyar wanda Abba kebi Baffa Kabiru Barrister Dake Zaune A Abuja..,! Mommy ta Rike baki tana Fadin"Ikon Allah kice Tuwon a maina Za"ayi..Ammh abu cikin gaggawa haka..? Safiya tace"Daurin auran kadai za"ayi Mommy Tarewa inaga sai daga Baya..Daada ta hada abun saboda kara Hada kansu Waje Daya..Mommy kinga Danginsu gabadayansu kowa yazo da ya"yansu gidansu Babban Gida ne Mommy a Dukku su din Dangin Manyan Mutane ne Duk garin Dukku ba wanda baisan Iyalan Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku ba..! Mommy Dake sakin Dariya Tana kallon Alhaji Alhassan ta gfen ido kafin tace"Masha Allah..Naji Dadi sosai Safiya..Allah bai barin Zalunci Daman Nagodema Allah yadda wani yaso ki tozarta Allah bai bari haka ya Faru ba gaki yanzu cikin Ahalin mijinki Cikin nasaba da Karamcin da Tushe da asali in arzikin ne suma sun Taka Allah ma godemaka da kika Tsallaken Siradin Tozarci sai dai Mutum ya Tozarta..! Ta Karishe Fada da karfi kuma da gayyah ba Alhaji Alhassan ba Hatta Tasleem da Safiya susan da wanda suke. Safiya tace"Plz Mommy..! Tafada Cikin shagwaba Hajiya Mero Tace"Ki gaidamin da Yusuf sai kun dawo zamu zo da Saratu da Tasleem Insha Allahu..! Safiya tace"Tom Mommy ki gaida Abu da Tasleem sai na Kiraki..! Daga haka ta katse kiran Mommy ta Mike Dauke da wayar tana yar waka Lokaci Daya tana Fadin"Allah ba azzalumin bawa bane..Allah kana gani..! Haka take fada Cikin Salon waka ta wuce zuwa Falon tana Hararan Alhaji Alhassan Ta gefen ido samin baida gaskiya ko Dagowa ma bai yi ba kansa na kasa gabadaya Jikinsa ya gamayin Sanyi Tsoro ya Shigesa yana Tsoron kada Hakkin Safiya ya kamasa a sirinsa ya Tonu,Domin bai fa Daina Dabi"arsa ba sai dai kalaman Hajiya Mero sun bashi Tsoro,Ashe yaron nan Yusuf dan asali ne,Lalle ne kada ka shiga Hurumin Ubangiji gabadaya ya kasa Tashi ma Har Tasleem ta gama tabi bayan Hajiya Mero zuwa Falo kunya ya hanasa wani Motsi. **** Imran cika kawai yake yana batsewa kamar yayi Bindiga sai kunkuni yake Fuskar nan ba Fara"a ya Hade ran nan kamar bai taba Dariya ba. Zaune yake gefen gadon dakin da suka sauka,Sagir da Yusuf na Tsaye kansa,Wasu Fararan kayane Riga da wando na Wata Shadda mai kyau da yarari,kayan Yusuf ne Abba yace ya bama Imran ya saka saboda Daurin aure,Da farko so yayi ma ya Gudu ya bar anguwa sai Abba ya Ritsashi yace mai in yasake ya Fita sai ya sabamai baida yarda zai yi Dole ya koma yayi lakwas,Sha biyu ta wuce sun fara Haraman Daurin auran tunda Har sun Daddy ya baama su Basheer kudi sun siyo goro da Minti Umarnin Daada ne Gida kuma ana ta Girki Kayattace,Mami Asma"u na Cikin Daki ta kasa Zama sai kiran Baffa Kabiru take tana so su kebe bai bata Dama ba Saboda baisan me zai ce mata bai isa yabi mgnarta ba yabar Umarnin Daada ba Shiyasa yaki yarda su Hadu hankalinta ya shi sosai,Khamis ma ta kirasa tana Fadamai yaje ya gayama Baffa Kabiru kada ya yarda a Daura wannan auran bata amince ba Da ya fita bai Dawo ba bayason Mami Tana irin wannan sai abu yazo ya Lalace Daga baya. Sajida kuwa Daada ta saka Inna Maimunatu da Da Inna Bintalo suka Daukota nan Dakinta Mami Asma"u tana ji tana gani bata da tacewa,Ta Kira Chan gidansu ta Fadama Tsohon Alkalin Alkalai Justice Tafida tana kuka bai biye mata ba yace Baffa Kabiru nada Hurumi da iko kan yarsa ganin ba Sa"a yasa ta Kira Hajiyarsu Hajiya Turai itacre ta Dauki ZAfi ta Kira Baffa Kabiru,bayan sun yi mgana ya nuna mata Umarnin Daada ne shi kuma bai isa ya kauce ma Umarninta ba Dole tayi Shuru ta kira Mami tana bata Hakuri Mami Asma"u ta Cika kamar ta Fashe ga ya"yanta basa Goyon bayanta Umaima ta shige cikin Danginta Ita da khamis suna ta Shirin Daurin auran Sagir ne ya kalli Yusuf yana Fadin"Ya Yusuf inaga fa sai mun Dannesa mun sakamai kayan nan zai saka su..! Ya yusuf yace"Naga alama..Imu tashi ka saka kayan nan kafin mu danne ka mu Maka Sintir mu shiryaka..! Bai ko kallesu ba yana Daga Zaunen yace"Ni ba kayan da zan saka..Kayan Jikina sun isheni..Kuma infact ma ni manyn kaya ba Kayan sawa na bane zan iya kirga sakasu ma da nayi a Duniya..! Yafada Cikin Dakuna Fuska yanajin an gama Kashe Rayuwarsa wlh. Ya yusuf yace"zaka sa ko kuwa sai mun Danneka..,,? Kallon irin lallene ma yayi musu kafin ya Tabe baki yace,"Uban Daya Fasa..! Zaro ido sukayi dukkansu suna kallon Imran din wanda ya kara Hade ransa Sanye yake cikin Shigar riga da wando 3Quater,duka bakake ya gyara Gashin kansa Daadan nasa ya kara Fitowa tas dashi ahaka zai je Daurin auran domin ya gama Tsarinsa bamai sakashi Sauyawa. Ya yusuf ya kada kai yana Fadin"Bari na Kira Abba na gayamai kace Uban da ya fasa..! Yafada yana Fito da wayarsa ya Farra Dannawa Imran na jin haka ya Mike Cikin kunkuni yana Wani Dakuna Fuska yana Fadin"Tsakani ga Allah an Takuramin..An Takuramin an gama dani ni dai an cuceni Wlh..,! Haka yake fada kamar yayi kuka Dukkansu dariyansu suka kanne Yusuf yace"Abba ya gode..Tunda ya Cuceka Imu..! Yana Daukan kayan yace"Ni ban ce ba..kuma afita abani waje ko agabanku zan Tube na saka kayan masu gadi..? Yafada Cikin bacin rai da Takaichi Dariya suka saka Imran ya Saka Kafa ya Shuru Sagir Yana Fadin"Munafuki..Shidai gefe ya matsa yana Dariya Yusuf yajasa suka fice suka Rufomai kofa abakin kofan suka Tsaya suna gadinsa sanin Halinsa zai iya Fitowa ya kara gaba. Sun bashi Minti Talatin suka koma Dakin Wow mssha Allah haka suka Hada Baki wajen fada. Sagir ya Kalli Imran da yayi wani irin kyau cikin mayan kayan,Ya yusuf ya azamai Hula zanna Bukar Dake hannunsa,mai zanen bakin zaren aikin Dake jikin shaddan yana Fadin"Rufe wannan Tozom gashin naka..Kada ango ya zama abun nunawa..! Imran ya yamutssa Fuska yana Fadin"Asan Mutum dai asan cinikinsa Shine Rayuwa ba Karya da munafunci ba..Ni ban damu ba ko Duniya zata nunani am Remain Who i am..! Ba su tankasa ba sanin yana neman Hanya ne,Sagir kuwa Hoto kawai yake Daukan Imran yana Fadin"Da kasan yadda manya kaya ke maka kyau da daga yau baka kara saka kananun kaya ba..,! Wata uwar Harara Imran ya Aunamai yasa ya kama bakinsa yana Dariya suna cikin haka sai ga su Sadam sun shigo da Sa"id da Basheer suna ganin Imran suka Fara ihu suna yaba kyansa Suka Firfito da wayoyinsu suna ta Hotuna dashi,Suma kowanne yaci kayansa sabi duk da abun ba Shiri ammh sun shirya ba Laifi. Duk Hoton da akayi Imran bai saki Fuska ba Sa"id ne ya Daki Kafadansa yana Fadin"Haba Angon Sajida Smile..! Daya fadi haka Sai da Imran yaji kamar ya yarfamai mari Saboda sunan Daya ambata daga saman lebensa yace"Har Abada bazn taba zaman angonta ba ko na zama na yan a wanni ne a suna..! Dakyar yadan saki ransa aka gama Hotunan kamar wani Rakumi da akala haka Sagir da ya yusuf suka Riko Hannunsa zuwa Falo,Sai da wayar sagir yaji ana kira ne kana ya sakesa Mama ce ke kira Domin Umma ta Kirata ta shaida mata komai tace ace ma Imran tanamai murna. Su Aneesa da su Abida kefadin ga Ango ya Fito Inna Maimunatu ta Fito tana Guda,Gudan Daya Fadar ma da Mutane guda uku gaba na Farko Inteesar dake kwance cikin Daki na Biyu Mami Asma"u na uku Sajida dake Dakin Daada Inna Bintalo ta gama Shirya ita da ya"yanta Hamdiya ta mata kwaliya Saukakkiya suka Dauko Cikin kayan data zo dashi wani less suka sakamata bayan sun azamata Daurin Zahra Buhari sai gashi ta Fito duka Daada ta bada Umarnin hakan. Inteesar na jin haka ta sauko Daga kan gado ta Leko Falo karaf kuwa ta Hangosa duka Mazan dake falon shi Zatinsa na musamman ne Manyan kayan Dake jikinsa sun kara Bayyana kyakyawan Zatinsa da Haibasan yayimata kyau din da bai taba mata ba. Idanuwa shima yake Wulgawa Yana nemanta bai ganta ba kamar ance ya Kalli Kofar dakin suka hada ido wanda da Sauri tayi baya batasan ya ganta ba Wani Dum yaji acikin Ransa yana jinsa kamar bashi ba. Daada har Falon ta Fito bakinta yaki Rufuwa Dafasa tayi tana Fadin"Allah yayi maka albrka Imrana kamar yadda Ka Bi Umarnina Allah ya baka y"yan da zasu bika kaima! Su yusuf ne suka amsa da Ameen banda Imran da acikin Ransa yace"Ba Ameen ba kar allah ya bani da'n da zan Tursasamai yin abu yayi ba don son ransa ba..kuma ki daina Saurin jin Dadi Bacin rai zai gauraye wannan Dariyar taki.keba Uwata ba kin Rikitomin bala"i cikin Rayuwata..,! Yana Tunanin yana wani Dakuna Fuska Daidai Lokacin da Mami Asma"u ta Fito suka Hada ido kallon kallon suke ma juna ganin yadda duk ta ZAbge ne tayi wani wuri wuri yasa Imran yaji Dadi harda Dan Taune lebensa na kasa kafin ya Daga mata Babban yatsanshi yayi kasa dashi alamun kin Fado. Takaichi da bakinciki suka kamata bata iya yin komai ba Har suka Tarkasa suka fice Daga Falon,Sagir da Yusuf na Rike dashi kamar zai gudu. *Shakira...* 3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�7* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* A haraban gidan suka iske su Abba Shida Daddy suna mgana suma sunci manya kayansu sun sha kyau sai Baffa Kabiru dake gefe yana amsa waya Khamis na kusa dashi shima wayar ce a Hannunsa yana ta Latsawa Suma sun yi Shiga mai kyau da Tsari. Tunda suka Fito Hankalinsu Abba ya koma kansu Zaratan SAmarin ya"yan nasu Imran duk ya Cinyesu akomai Kallo Daya zakayi mai kaga Tsabar Zati Haiba da kamala Uwa uba Kwarjini da wani baiwar Kyau da Allah yayi mai. Abba da Daddy baki suka Washe azuciyarsu suna Fadin Masha Allah ballatana Baffa Kabiru da Khamis da suka Saki baki suna kallon Imran Duk da bai saki Fuskarsa ba ko kadan ammh Kana kallonsa Zaka Tabbatar da wannan cikakken Namiji ne inda ake Kiran Maza masu sunan Maza. In bace maka akayi yana Busa Sigari ba akallo Farko bazaka taba yarda ba Saboda yadda kyansa ya Fito da kyakyawan Zati sukansu sun shaida Karyansu suce Sajida tafi karfin Imran Sai dai shi yafi karfinta ma sai dai in Akayi duba da abunda suke Dubawa din ba Domin wani abu ba. Har gaban Abba da Daddy Yusuf da Sagir suka Kaisa yana ta wani Fadin Rai Abba ya Dafa Kansa yana Sakn Mirmishin Farinciki Cikin Annushuwa yace"Allah Sarki Zuwaira Allah ya jikanki da Rahma ina ma Kina Raye yau kikazo kiga Imran din ki Zai zama Babban Mutum..! Gabadaya sai jikin kowa yayi sanyi jin kalaman Abba da kuma yadda Hawaye suka ciko Idanuwansa yayi Saurin maida su yana Jijjiga Kafadan Imran Lokaci Daya yana Fadin"Allah yayi maka albarka..! Daga saman Lebensa ya amsa da Ameen Hakama Daddy ya sakamai albarka ya amsa Kamar mai Ciwon baki. Sai Lokacin Khamis ya Kariso wajen ya bama Duka su Basheer hannu sukayi musabaha Daya Miko ma Imran sai ya Karkace kansa gefe kamar bai gansa ba Khamis ya karajin ya muzanta Da Sauri ya maida Hannunsa Bayaso wani Cikin su yaga wannan Tozarci da Imran ke nuna mai duk sanda ya Nemi wani Huldar Arziki ta Shiga Tsakaninsu. Koda Baffa Kabiru ya kariso Wajen Imran Saboda kada ya gaisheshi baya ya koma,kawai ya Saka Hannayensa Cikin Aljihun wandon Shaddar Dake jikinshi yana kallon kowa Daya bayan Daya yana jinsa yau din nan kamar bashi ba,Ga wadanan kayan Dake Jikinsa ba karamin Takuramai sukayi ba. Ganin Lokacin Sallah ya kusa ya saka duk sukayi alwala anan Haraban Gidan,Inna Maimunatu ta Fito musu da Botoci sukayi amfani dasu kana suka Rankaya zuwa masallacin Dake kusa dasu,Basheer da Sadam na Dauke da Dabino da goron da za"a Raba Kafin Daurin auran Imran kuwa Yusuf da Sagir na rike dashi kamar wani mai Laifi ransa ya baci da hakan ya Kallesu yana Fadin"Wai meye haka kuke wani Rirrikeni kamar wani Barawo..? Yafada yana kara Dakuna Fuska Sagir ne yace"Saboda munsan Halinka Za"a iya nemanka awajen Daurin auran nan a rasa..! Wani Mirmishin Takaichi ya saki kafin yace"Rubbish..Dilla Malamai ku Sakeni na Rantse da Allah in nayi niyyar Tafiya ba wanda ya isa ya Hanani..Daman bazan je ko"ina Saboda Abba Shi kadai ne yake iya Takama Ra"ayi Burki..So please let me go.Nasan abunda nakeyi.! Yafada Cikin bacin rai jin haka yasa Yusuf yace su sakeshi Tunda ya Fadi haka ba inda zashi sun sakeshi yana ta Hararansu kamar ya Dakesu haka yake ji ba karamin Cutar Rayuwarsa akayi ba wlh ayadda yake fama da kansa Din nan ace za"a kara Dauramai wani Nauyi..? Ina Wlh bazai Dauka ba su dai Daura auran ai Alhakin komai yana Hannunsa ne yaga ta yadda Zai zauna da wannan Shegiyar yarinyar mai kama da uwarta. Sai da aka idar da Sallar azahar kana aka kara Sanar da Daurin auran Daman kuma Tun safe Daddy yazo ya sanar da limamin masallacin akwai Daurin auran Jikokin Marigayi Alkali Hamisu Dukku. Mutane duk basu Tafi ba Daman masallacin ana cika sosai nan su Basheer suka tsshi suka Fara Rabon Dabino da Goro,suna gamawa aka Fara Gabatar da Neman aure Daddy shi ya Biya Sadakin Imran Naira Dubu Dari Cif,Baffa Kabiru ya Umarci Liman Daya bada auran Daddy shi ne Uban ango shi ya karbi Auran Sajida Kabir Hamisu Dukku Yayinda Daddy ya Karban ma D'ansa Imran Abubakar Malami auranta kan Sadaki Dubu Dari lagadan ba ajalan ba. Lokacin da aka Tabbatar da Daurin Auran sai da Imran yaji kansa ya Saramai Bakinciki kamar yayi kuka Babban Ci bayane ma ace an Taba Daura mai aure da wannan Yarinyar Har Abada bazai manta da wannan Ranar a Sahun Ranakun bakincikinsa ba. Bazai iya Zama acikin masallacin ba Shiyasa ya Fito ya saka Takalmi kenan sai ga Sagir ya Fito rikosa yayi ganin Mutane Tundaga Ciki suna ta gaisawa dasu Abba kowa na Wurga idon ganin Ango Yusuf ne ya Hangosu Daga Waje ya nunasa nan fa Mutane ke ta zuwa da sun zo suna kokarin mikama Imran Hannu sai ya Kara Hade rai ya Kauda kai Hannayensa na Goye a bayansa ko Fito dsu bai yi ba Sagir ya bari da karban Musaban yana kuma amsa Fatan Alherin dinsu. Da kafarsa yake zungurin Imran Wanda ya wani Dauke kai kamar ma baisan me ya aikata ba Mutane sun zata ma Sagir ne ango Imran abokinsa wasu Da dama sun tafi da Fadin kai Abokin angon nan bai da Fara"a Ko kadan shi kuma ko ajikinsa Domin tsayuwarsa a wajen ma ba karamin Takura bane ga Rayuwarsa yau Darajan Abba kadai akaci da ko Sama da kasa zasu hade bai ga Uban Daya isa yayi mai abunda akayimai yau ba. Gajiya da Zungurinsa da Sagir yake yayi ya Wurgamai Harara yana Fadin"Mallan Lafiya..? Kafa isheni ka mtsamin Kafin na Sauke bacin Raina akanka Wlh yanzu ka tsinci kanka cikin wannan Kwalbatin Dake gefenmu..! Imran ya Fada yana Nunamai kwalbatin da baki Sagir ya juya yana kallon Kwalbatin cike da kwata da Sauri ya matsa Yabar Kusa da Imran din Saninsa Wlh zai iya aikata Abunda ya Fada Mirmishin Fatan baki Imran ya saki Kafin murya kasa kasa yace"Better for u..! Hararansa Sagir yayi saboda yajisa Kafin yace"Kaifa baka da Mutumci Daman na sani..Kana ta wani cin mgani Gata Daada tayi maka ta aura maka wannan Santaleliyar Budurwa batare da ko sisinka ba ya kamata ma ka Gode mata ne ba wai kazo kana wani Daure Fuska kana wani yamutsa Fuska kamar kaga kashi ba..! Imran ya kallesa galala irin kallon Are u Mad..? Karkace kai yayi yana Fadin"Nace tamin gatan ne..?Ko Daadan Uwata ce..? Yafada yana Tsatsare Sagir da Mayun Idanuwansa Cikin mamaki Sagir yace"Ikon Allah Ita Daadan..? Cikin Takaichi ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Eh ita ai ba uwata bace..Bani ta Haifa ba bata da wani iko akaina..Abba ne Da'nta meyassa shi batayimai gatan ba..? Ai naga shima bai da mata dashi tama wannan gatan bani ba..Kuma Duk Cikin Tarin Jikokinta sai ni ta Zaba..!Wato nine Maraya Uwata ta mutu Dole a Dinga Walagigi da Rayuwata to ban Dauka ba Wlh..Koda nayi Rashin Uwa baisa na Rasa kimata ba nasan Darajan kaina da Mutumcina saboda Haka ni Daada batamin gata ba wlh sai ma Kokarin Takurama Rayuwata Datayi kada ka kara cewa wai Daada tamin gata ni ban gani ba kai koma gatan tamin ban gode ba domin ban ce ina Bukata ba..! Ya Karishe Fada a Fusace kafin ya Tada Iska ya wuce Fuu kamar zai Bangaji Sagir yayi Saurin mtsawa yana Binsa da kallo kafin ya Girgiza kai yana Fadin"Kin auri aiki yarinya..Imram..Imran ba kanwar Lasa bane..! Fitowa kawai su Abba sukayi basu ga Imran ba Sagir yace ya wuce gida suma Daganan gidan suka Wuce Tare da wasu Mutane saboda Walimar da sukace zasu suyi. Suna zuwa Haraban gidan suka iske Imran na saman Motan Yusuf yana ta Busa Sigarinsa ya Cire Rigar jikinsa Daga shi sai Vest ya kwabe Hula wai ta Damesa,Sai da yaga Abba ne yaji kunyar Ya Saki Taban ta Fadi kasa ammh ko ganin Baffa Kabiru da Khamis ba sa ya Fasa Abunda yake yi ba,Baffa Kabiru da Khamis Takaichi Duk ya Cikasu na ganin irin Mijin da Sajida ta aura Mutum Har Mutum ammh ba kyan Hali haka Khamis ke Fada acikin Ranshi. Abba ne ya mikama Imran din hannunsa yace ya bashi Kwalin Sigarin da makunninta kafin ya Sabamai Dole baida yarda zai yi ya saka Hannu acikin Aljihun wandon Dake Jikinsa ya Dauko Duka ya Mikama Abba ya karba yana nuna ma Daddy,Kai kawai suka Kada acikin Ransu suna Fatan Allah ya gyara Kayanshi Domin shiriya tana wajen Allah ne. Ganin haka yasa Imran bai Tsaya ba ya Kwashi Rigarsa da Hulansa ya wuce Cikin Gida yana wannan Takun nasa na Sassarfa afalo yaci karo Dasu Basheer su Sagir gasu Inna Maimunatu suna ta Hayaniya jin an Daura auran Sadaf sadaf ya wuce kafin a gansa ya shige Dakin da suka Sauka shida Sagir ya Rufo kafa Gabadaya ya Kwabe wandon Jikinsa Da Vest din ya Rage dagashi sai Boxers ya haye gado ya kwanta bayan ya kunna Fanka Zafi duk ya ishesa Yana jin karkashin Zuciyarsa na wani kuna Bini Bini ya saki Tsaki kamar wani Tsaka. Achan Falo kuwa Tunda Labarin Daurin auran yazo Cikin Gida Mami Asma"u ta shige Daki tana ta Rizgan kuka yanzu Shikenan Tsagerin yaron nan yayi nasara akanta ina bazai yuyu ba Tunda aka nuna mata iyakarta itama sai ta nunama kowa nata iyakar Sai a Dauki Sajidan akaimai Tagani Indai Tana Raye ba wanda ya isa. Sai da taji kukanta ta gaji kana taje tayi wanka ta Shirya Fuskarnan duk ta Kumbura ba wanda yabi ta kanta su Umma duk suna Falo ana ta Hidima Bata ga ko Daya Daga Cikin ya"yanta ba,Sajida Tana Dakin Daada Umaima tana Tare dasu Munari Khamis kuma suna Haraban Gidan inda suke Walimar su nacin Abinci isu isu da sauran Mutane an Shimfida manyan Dardume suna zaune suna cin Abinci ga ababen sha nan Birjit sai wanda ka Zaba Imran ne kadai bashi a wajen kuma ba wanda ya Damu Dashi Sanin Halinsa. Bangaran Amarya Sajida kuwa tana jin Gudan Inna Maimunatu Tana Fadin an Daura aure taji wani sukuni Tare da Salama ya Shigeta,abaya kafin Taga Imran tasha Mafarkin yadda Kayattacen Bikinta zai bar Tarihi a Nageria sai dai ganin Imran da Faruwar komai ya Sauya mata Duka Tunaninta Abunda ya Faru bai Dameta ba sai ma wani Salama Dataji na Zamo warta Mata ga Imran Ya"yan Inna Bintalo ne suka zo suna ta Daukan Hoto da Sajida su Hamida,anan ciki aka kawo mata Abinci Tunda Daada ta hanata Fitowa Daga Dakin ballatana su Hadu da Mami Asma"u Alokacin ma ita kanta Sajidan bata kaunar ma taga Mamin Saboda tasan har yanzu da aka Daura bazata Daina adawa da wannan auran ba ita kuma ayadda Lokaci Daya Soyayyar Imran tayi mata kamun kazan kuku Tana Daidai da tayi Fito na Fito da wanda yace zai Rabata da Abunda take so..! Bangaran Inteesar kuwa tun Safe tana Kwance gabadaya ayyukan da akayi da Ifacen ifacen da akayi ta yi acikin Gidan baisa ta Fito ba kanta Nauyi yayi mata Kirjinta na mata Zfi duk sanda ta Tuna da Imran zai auri Sajida ba yadda su Munari basu yi ba kam Tatashi Tayi wanka taci abinci tayi banza Dasu,gajiya sukayi suka kyaleta,su dai bayan sun gama aiki suka shaba wanka da kwalliya Har da Umaima Data shige Cikinsu suna ta Daukan Hotuna Munari ita ko ajikinta Domin ba wani Sanin Sajidan tayi ba,sai dai ta Tsausayamata Domin har ga Allah an bata aiki babba na Aura mata Ya Imu. Inteesar tana daga kwancen Munari tazo tana Fadamata an Daura aure gasu Ya Basheer chan sun dawo Sai Inteeser taji kamar Zata Mutu sai Hawaye Sharr Hankalin Munari ya tashi ita taje ta Kira Umma Duk ta Rikice ta Rikita Umma itama ganin tana kuka yasa ta zata Jikin ne basusan Hakikamin me ke Damunta ba ita kanta bata sani ba Ballatana ta Fada musu sai dai Kirjinta nayi mata wani Zafi kukan datake yi shine kadai Salamanta. Umma ce ta Lallabata tarakata Tiolet tace tayi wanka ta saka Munari ta Hado mata Tea saboda tasha Cikinta ya Warware,Inteesar na Shiga Tiolet din ta Zauna saman sit din Cikin Tiolet din ta Fashe da kuka yi take ba kakkautawa kamar wacce akace wani nata ya Mutu kanta yana Sara mata ga Nauyin Kirji,tana cikin kukan Wata Zuciya tace mata"To ke Inteesar kukan me kike yi..? Ina ruwanki Domin yayi auransa bai kamata kizo kina saka kanki acikin Damuwa ba Har kina kuka ba Tunda ba sonshi take ba..,! Sai wata Zuciyar tace mata"Ko bana son shi ai dan"uwana ne bazan so mai abunda baida kyau ba..Sajida bata Dace dashi ba Shiyasa nake Damuwa..! Tafada acikin Ranta tana jin yes wannan ne Dalilinta,Da wannan Tunanun ta Lallashin kanta ta yi wanka ta Dauro alwala ta Fito Umma da Munari na Jiranta,mai ta shafa kafin ta saka Doguwar Rigarta baka Kirar Armani,Munari ta mika mata Tea din tasha Umma ta balla mata mgani ta bata tasha ta Dora Tea din Daman tana jin yunwa Cikinta sai kuka yake,Tagama sha sai Zufa alamun dai ta Fara samuwa ganin haka yasa Umma ta Fita ta barsu,Munari ta Shimfida mata Darduma ta Fita ta barta Bayan ta Tada Sallah. Tana Fitowa Falon Lokacin su Abba na Shigowa nan suka gaggaisa dasu Inna Maimunatu suna ma juna Fatan Alheri da Fatan an kulla alheri kafin su Dunguma Zuwa Dakin Daada dake Cikin Dakinta taci kwalliya bakinta Har kunne Casbaha na Hannunta tana ta Lazimi ranta Fes Koyau ta Mutu Burinta ya cika. Ganin Shigowar ya"yanta nata yasa ta Kira Hamida tace tazo ta kai Sajida wajen Mahaifiyarta haka kuwa akayi ita ta rike Hannunta zuwa Dakin da Mami Asma"u wacce bakin ciki kamar ya kasheta. Saboda Takaichi takasa ma cema Sajidan komai kallonta kawai take tana kyafci tana Girgiza jiki da kafa,Wayace a Hannunta tana ta Kiran Baffa Kabiru bai Dauka ba suna Gaban Daada,bazai iya Daukan Wayanta ba yasan Rigima ce kwance a wajen Mami Asma"u. Inteesar Dole yasa ta Fito Falo Tunda Munari sun mtsa mata sai ta Fito,ita kuma Ranta baya mata Dadi,sannan bata son ta Hadu da Khamis yana ta Damunta da waya da Sako ko ta kansa batabi ba.. Koda ta Fito duka an hadu a falon Mazan da matan su inna maimunatu dai suna Dakin Daada su Aneesa ne dasu Anty Safiya kowacce tana Tare da mijinta sai su Munari dake Hotuna,Khamis na Dakin Mami yana bata baki har ya gama mgana kanzil batace ba,har yagaji ya Fito nan yayi Tozali da Inteesar ya kafeta da ido yana kallonta Yarinyar nan tana bashi Wahala sosai gabadaya soyayyarta ya gama kasarashi sai dai tanayin wani abu kamar bata gane ina ya Dosa ba.. Suna Hada ido ta Hada rai ta kauda kanta kamar bata ganshi ba ta Dauko wayarta tana Dannawa ba Domin tana wanu abu ba Imran take Tunani bata gansa ba wata Zuciya tace"Ina Ruwan ki kumi dashi..Yanzu ai baida Lokacinki Tunda yayi aure. ! Tuna haka yasa taji zaman Wajen ya gagareta tatashi tana Shirin Tafiya Zainab din Inna Maimunatu ta jawo tace suyi Hoto bata da yarda zatayi Dole ta tsaya Khamis kuma yana binta da kallon Sha"awa da kauna ya Nufi wajen su Basheer dake zaune suna Hira gefe kuma Matayensu Sa"id ne sun ci gayu suna ta Hira gwanin Sha"awa. Suna ta Hotuna Kada Munari da Hafsah suji Labari,Munari ce uwar kankaba tace afito musu da Amarya suyi hoto Hafsah tasan Hali bata je ba Umaima ce taje ita dasu Hamida suka Fito da Sajidan Daga Wajen Mami Asma"u wacce ke cika tana batsewa kala bata kara Furtama kowa ba Bata so tayi mgana saboda in ta Bude baki tace wani abu zata iya Fashewa da kuka kuma Faruwar hakan kamar Imran yaci nasara akanta kenan Baffa Kabiru take jira shine Zata saukema gabadaya Bala"in Dake Cinta. Sun Fito da Sajida nan Falo waje ya Kaure da Gudan ga Amarya su Sa"id na Dariya Yusuf da Sagir suna kallon Sajida sukace masha Allah tayi kyau matuka,Inda Imran mai Wayau ne basu ga aibun Sajida ba mace duk inda ake neman takai,Khamis yazo ya Rumgumeta ganin Inteesar a wajen Har dashi ya Dinga shiga Hoton Bakinciki ya cika Inteesar tana so ta gudu Munari ta Hanata,Ga Waleedan Anty Aneesa ta makalemata sai ta Dauketa Kallon Sajida take tana mamakin ganin ta ko Damuwa acikin Idanuwanta Fuskarta bayyana wani Damuwa ba,sun kalli juna ido Cikin ido kafin kowa ya Dauke kansa,Abunda ke bama su Inteesar da Hafsah mamaki ganin Sajida tana mgana da Munari har da mata Dariya Inteesar Ranta wani kuna yake yi wato Saboda ta auri Dan"uwanta Ita tasan Darajanta,Inda ma mutane zasu Lura Hawaye ya cika kwarmin idanuwanta Tayi saurin Sharewa kada wani ya gani. Sun cigaba da yin Hotuna har Da su Sa"id da suka taso ana ta Family Picture,Khamis sai da yasan yadda yayi ya dawo kusa da Inteesar ya Riko Hannunta bata zata ba da Sauri ta Dago tana kallonsa Gira ya Dagamata Lokaci Daya yana marairaicemata kamar zai yi kuka kwace hannunta tayi tana Hararansa Haushi Rike mata Hannun da yayi taji Har Cikin zuciyarta. Mtsawa tayi daga kusa dashi ta koma Kusa da Hafsah ganin munari na kusa da Sajida,wacce ke ta wurga ido tana Neman inda zata ga Imran bata gansa ba bata so kuma tayi mgana aga Zakewarta sai tayi shuru da bakinta. Kiran Sallar La"asar da Fitowarsu Abba ya Dakatar da Hotunan suka ce mazan su fito su tafi masallaci matan kuma suma suyi sallar acikin gida. Baffa Kabiru sai Lokacin ya Shiga Inda Mami Asma"u take tana ganin Shigowarsa Rauninta ya bayyana ta Mike ta isa gabansa Tana Fadin"Yanzu Kabir kana gani aka Daura ma yarka aure da wannan Dan iskan yaron.?Kana ji kana gani aka yi ma yarka auran kaskanci ammh ka kasa cewa komai ko Kabiru..? Tafada tana Fashewa da kukan Takaichin Dake Cinta acikin Zuciyarta Saman kirjinsa ta fada Tana Dukansa Riketa yayi yana jin pain din Datake ji Cikin Lallashi yace"Ma"u ya zan yi..?Ni ban isa na Tsallake Umarnin Daada ba..Kada kuma ki manta Abubakar Dan"uwana ne Dana saki Nono ya kama Taya zan nuna ina gudin hada jininsa da nawa..?ya zai ji acikin Ransa..? Ammh wlh ni kaina Ma"u banso wannan Hadin ba Tunda kikaga ban yi mgana ba bani da Mafita ne acikim al"amarin..! Ya karishe Fada yana riketa acikin jikinsa bata iya cewa komai ba sai kuka Bakimciki ya cika ta gani take Cika bakinta ya zama na banza Daada ta gama Cutar da ita cutar da bazata manta ba Har Abada. Dakyar ya iya Lallashinta Tayi shuru da cewa bari yaje suyi salla su dawo zasu yi mgana kana ta yarda ta sakeshi ya Fice ta koma ta zauna tana Sharan kwallah jira take yazo suyi mgana Gobe goben nan bata kaunar ta kara Kwana agarin Dukku Har Daadan bata kaunar gani Zata Tarkata ya"yanta ta tafi dasu Sai taji kuma ta gani wanda ya isa yazo ya Dauki Sajidan Wlh sai dai ya gaji da auran ya Saketa tana Fatan Tsautsayi ya sa ya kwaso kafafunsa zuwa Abuja A nan ne Zata nuna mai ikon Barrister Asma"u..! Imran sai bayan da kayi sallar La"asar kana ya Farka Daga Barcin Daya kwasheshi cikin kasala ya Mike ya Fada Tiolet ya Dauro alwala yazo ya saka Riga da wando baki da Fari,kana yayi Sallarsa acikin gida tunda an riga anyi Sallar,sai Lokacin ya Fito Daga Dakin Falon ba kowa duk suna Dakuna suna Sallah Hafsah kadai ya gani Data gaishesa Sai da ya juyo yana kallinta asaman Lebensa ya amsa kafin ya kada kai ya Fita Haraban gidan Inteesar yake son gani bai ganta ba Tun dazu din nan Daya hangota ta Boye kanta. Yana Duba wayarsa su Basheer suka shigo gidan sun dawo Daga masaalaci Ganin su yasa ya koma Chan gefe yayi kamar yana waya saboda bayason mgana da wani suna ba wanda yabi ta kansa Harta kuwa da Sagir suka Shiigewarsu cikin Gida sai da yaga Shigarsu kana ya Sauke Wayar Daga kunnensa ya Lalubo lambar Inteesar ya Tura mata sako. "Kina ina ne..? Ki fito na ganki..! Ya tura mata Ya koma ya Coge yana Jiranta,Inteesar kuwa Ta idar da Sallar kenan tana zaune kan Sallaya taji Shigowr sako Ta zata Khamis ne yasa batabi takai ba sai da mike Daga Kan Sallaya ta karisa bakin gado ta Zauna ta Dauki wayar kana taga sunan Imran har jikinta na rawa wajen Budewa abunda tagani ne ya Kara bata mata rai Baki ta Tura kamar Yana ganinta afili tace"Ina ruwanka dani..Kaje kaga matarka..! Haka tafada Har sai da Munari Dake Zaune ta waigo tana kallonta ganin haka yasa Inteesar din ta Mike ta koma chan kusa da Tiolet ta turama Imran Sako. "Ina daki ban ji dadi.." Daman jiran sakonta yake yi yasa Yana Shigowa ya Duba Shuru yayi yana wani Tunani Jikinsa yayi sanyi bata da lafiya Har yanzu..!? Haka ya Tambayi kansa da Sauri ya Tura mata sako. "Ki fito naga yanayin jikin naki yanzu..Bana son gaddama do as i say malama..! Ya tura mata Dataga sakonsa Sai da tayi yar dariya Imran bazai taba Sauyama ba. Tura baki tayi kamar yana kallonta ta Turamai. "Kana ina ne..? Kamar yana jiranta ya Turomata. "Ina Waje..ina jiranki..! Ganin sakon sa yasa ta Dauki Mayafinta ta yafa Munari ta kalleta Tana Fadin"Ina zaki Kuma? Tana yamutsa Fuska tace"Nan waje zani yanzu zan dawo..! Hafsah da Munari suka kalli juna kafin su tafa suna fadin"In tayi wari zamu ji..! Kallonsu tayi taja karamin Tsaki ta Fice,suka Bita da kallo suna Dariya su azaton su da Khamis suke mgana ta Messages kuma Wajensa Zataje shiyasa suke mata Dariyan sunsan komai. Bata bi ta kansu ba ta Fice Taso ba wanda zai ga Fitarta sai dai duka suna Zaune acikin Falon Har dasu Abba Baffa Kabiru ne baya nan yana Dakin Da Mami Ta Sauka Sajida kuma tana Dakin Daada. Wajen Daddy da Abba ta nufa ta Rankwafa ta gaida su,suka amsa mata Cikib Fara"a Abba ya Dafa kanta yana saka mata albarka Duk Khamis na Lura da ita Tun Fitowarta Mikewa Tayu tace Abba da Daddy bari ta zo yanzu zata dawo basu damu ba sanin ina Zata ba ta fice Daga Falon zuwa Haraban gidan. Tafara Waige waigen Neman Imran kenan Khamis yasha gabanta da Sauri Har yana neman gugan Jikinta da Sauri Taja baya tana Binsa da kallo mai kama da Harara Cikin sanyinta tace"Lafiya? Lamgwabe kai yayi yana Fadin"Kinsan ai me ya kawo ni wajen ki ko..? Look inteesar na gaji da Horan da kike min na Tabbata ke ba yarinya bace kinsan Abunda nake nufi kada mu bama junanmu Wahala..I love u Tun Ranar dana Fara ganinki sonki yana bani Wahala kuma da aure nake sonki ina so ki bani Dama mu Fahimci juna kafin iyayanmu suji mganar Daga Baya Plz.! Ya karishe Fada yana narka mata wani irin kallo na Kauna Taso ta Yi mai Tsaki ne sai kuma ta fasa Tsuke bakinta tayi kafin tace"Ni ba yanzu zan yi Aure ba am sorry Karatu nake yi..! Tana gama Fadin haka ta juya Zata wuce Caraf ya saka Hannunsa ya Damki Hannunta Wajen ta Waigo da Sauri gyalenta ya Zame daga saman kanta zuwa Kafadanta Gashin kanta ya bayyana wanda ke Tsife sai dai ta Nannadeshi Cikin band dinta Juyowar da zatayi suka Hada Ido Hudu da Imran Dake Tsaye ta gefen Khamis Hannayensa goge a kirjinsa Zuciyarsa tana wani bugawa Tun Lokacin da Inteesar ta Fito ya ganta ya taka zuwa Wajenta ne sai ga Khamis yana bayansa Duk abunda ya Fada a kunnensa Bai taba jin Bakinciki ba irin na yau da Khamis yace wai yana son Inteesar yana kokarin Controling din bacin Ransa ne yaga ta juya shi kuma ya Riko mata Hannu gyalenta ya Zame gashin kanta ya Bayyana Agaban Wani katon Namijin yana kallon Hannunta Daya Rike ga kuma Mayatacen kallon Dayake Bin Inteesar dashi Kamar Zai Lasheta Tuni Imran yaji kirjinsa na Harbawa Jijiyoyin kansa sun mike Idanuwansa sun Rufe radadi ya cika Ransa na ganin wani rike da hannun Inteesar kuma yana kallon surar jikinta. *Shakira..* 3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�8* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Khamis da baisan da wanzuwar Imran Daga bayansa ba ya shagala da kallon kyakyawan Surar Inteesar da gashin daya kwanto ta saman Goshinta ya tafi dashi har baisan Sadda ya Furta"Wow..Beatifully.! Yafada Cikin wata Murya mai cike da Muradi mai girma. Imran Dake bayansa wani Takaici ne ya kara kamasa Tuni naman Goshinsa ya Tattare ya koma Waje Daya Inteesar yake kallo wace ke kallonsa Cikin Wani yanayi Dayake kara Wutar bacin Ransa. Kokarin Daidaita kansa yake shi yasa bai yi mgana ba Hannu kawai ya Saka Cak ya Dauke hannun Khamis dake Rike da Inteesar Cikin ZAfinsa har sai Da wajen yarfar da hannun Khamis yayi baya Ya fadi kasa Dabas Saboda Imran din da karfi ya Wanchakalar da Hannun nashi,Shi kuma ya saki Jikinsa ne saboda baisan Haka Zata Faru ba Shiyasa ya kasa Rike kansa Har Sai da yakai kasa. Da mamaki ya Dago suka Hada ido da Imran Dakemai wani kallo na rainin Wayau da kaskasci. Saurin Mikewa yayi shima Ransa ya baci Cikin Bacin rai yace"Mallam Lafiya kazo ka Tureni na Fadi kasa..? Imran ya Kara Hade rai bai yi mgana ba Ganin haka sai Ran khamis ya Fara Tafasa yana ganin Karshen Rainin Hankali Imran ya gama Rainasa shiyasa yakarisa gabansa ya saka Hannu ya Daki Kirjinsa yana Fadin"Mallam ina mgana ka kyaleni..? Wa ya baka izinin Tabamin hannu Har kana Tureni..? Yafada Shima Fararan Idanuwansa sun Fara Juyewa zuwa Jajaye Alluran Sojojin shima sun Fara aiki ajikinsa. Imran Dayake Cije baki Yana kokarin Daidaita Bacin ransa yaki cewa komai illah Inteesar ya kalla wacce Ta Fara Fiki Fiki da ido tana neman yin kuka ganin Abunda ke faruwa. Cikin Dakiyarsa yace"Ki koma Cikin Gida..! Tsayawa tayi tana kallonsa bata tafi ba Khamis ya kalleta yana Fadin"Tatafi ina..?Ina Ruwanka da ita ai bakai ka Kirata ba..Inteesar ba inda Zaki ok..? Yafada shima yana bata Umarni Sai kawai ta Tsaya ta kasa gaba Ballatana Baya,Ran Imran sai ya kara Baci Zuciyarsa ta Fara Tafarfasa Cikin Daka mata Tsawa yace"Nace ki bar nan..! Yafada Cikin Dakakkiyar Muryansa Cikin Fushi Daya Tsorata Inteesar ta Juya Zata Koma Cikin Gida tana Kokarin Boye kukanta da Hannunta Bayan ta saka Mayafin jikinta Ta Rufe bakinta dashi saboda kada kukanta ya Fito Khamis na ganin haka yayi Saurin Riko Hannunta again yana Fadin"Ba inda Zataje..Zan gani in kai ka Kirata in kuma Zaman ka takeyi Acikin gidanan..Haba rainin wayau ka ya Isa haka..Kana ganin cewa tsoron ka Kowa yake ji shiyasa kake yin Abu ba"a Tanka maka..? Wlh ina Daidai da Duk Abunda kake takama dashi Inteesar ba inda Zataje sai kayi abunda Zakayi in ka Isa..! Ya Karishe Fada Cikin Bacin Rai yana kuma Rike da Hannun Inteesar wacce take kokarin kwacewa ganin yadda Imran yake kallon Hannun nata kamar Zuciyarsa Zata Buga ya mutu gabadaya Cikin Kokarin Daidaita kansa yake fadin"Sakar mata Hannu..! Khamis ya kallesa yana Fadin"In naki fa..?Ko kana Tsammamin zaka Dakeni ne..? Imran ya Taune Lebensa na kasa Kafin Cikin Tsawa yace"Nace ka Sake mata Hannu Kafin Raina ya baci..Nayi maka Biji Biji anan wajen..! Khamis ya taresa Shima Cikin Tsawa yana Fadin"Naki na saketa din kayi Abuda zakayi..Ina Ruwanka in narike mata Hannun..?Au sonta kake yi..? Lalle baka da Tunani Shaye shayenka sun gayamaka karya in ka manta bari na Tuna maka Yau aka Daura maka aure da Sajida kanwata Ko agarin gaba gaba muke ana barin Halas ko don kunya..Ko kana so baka so Inteesar mallakina ne ina sonta kuma Zan aureta ita din Tawace..! Ya karishe Fada yana kara Riketa wannan karon harda Kafadunta duka Biyu. Ai Imran sai yaji wani Tukikin Takaichi acikin Raina Duhu ya mamaye idanuwansa na ganin yadda Khamis ya Rike Inteesar baisan Sadda ya isa gabansa ba ya saka Hannu ya Daki Kirjinsa da Hannunsa ya Kara Bangajesa da Karfin da sai da Ya kara Faduwa duk yadda ya kara saka Karfinsa Sai da Imran yadin ya kaisa Kasa Inteesar ta ja gefe ta fashe da kuka Jikinta ya fara Imran Cikin Dakakkiyar Muryansa Ya na nuna Khamis daya yatsa yake fadin"In ka kara Saka kazamin hannun nan naka ka Tabata wlh sai ka Raina kanka..?ubanta ne kai da zaka rika Tabata duk sanda kaga Dama..?Kuma daka ke fadin Shaye shaye bai fadamin gaskiya ba da kudin tsoho ko da na Tsohuwa nake shaye shayen..? Auran kanwarka kuma ninace ina sonta..? Nace ni nace ina sonta balle kazo kana gayamin mganar banza..Har Abada wannan yarinyar bata isa Imran ya sota ba Domin bata kai wannan mtsayin ba..Kuma na Rantse da Allah daya Halliceni in ka kara Cewa Inteesar taka ce sai nayi maka Dukan Mutuwa acikin gidan nan..Bazata taba zama taka ba Har Abada..! Ya karishe Fada yana Kumfar baki,Khamis da shima idonsa ya Rufe ya Mike jikinsa na mazari ya Fara Ture Imran yana Fadin"Kaima sonta kake yi kenan..?mallan sai ka Fadamin kishi kake yi domin na Tabata? To baka isa ba Inteesar da kamilalle ta dace ba Dan iska Sauran Shaye. shaye ba..Gashi na Riketa in baka Min Duka ba wlh baka Haifu Cikin uwa da u.! Bai gama Rufe baki ba Yaji Saukar Naushi a bakinsa yana kokarin rike hannun inteesar yaji wannan Dukan Daya sa sai da ya Duke yana Dagowa Bakinsa ya fashe sai jini Ya duba ya gani Hankalinsa ya tashi ya mike shima yakai ma Imran duka shima abaki shima nan da nan bakinsa ya fashe ganin yadda suka Fitar ma da kansu Jini yasa Zuciyar zaratan maza ta Fara Zalzal akan kishi Batare da bata Lokaci ba suka Sarke da Mumman Dambe Kowanne yana Dukan Dan"uwansa duk inda ya Samu da Karfin da Allah ya basu.. Inteeasar ta Dora hannu asaman kanta ta kwarara ihu dayaja Hankalin Megadi Dake bakin get ya Zuro da gudu ganin abunda ke Faruwa,yana kokarin Rabasu ammh ya kasa Inteesar ganin haka yasa ta Nufi Cikin Falon gidan tana Ihun Kiran sunan Daddy da Abba. Wanda daman duk suna zaune afalon suka fara jin Hayaniya sai ga Inteesar ta shigo tana kuka tana Haki Lokaci Daya tana Kiran sunan Abba da Daddy gabadayansu suka Mike Har wadanda ke Daki sai da suka Fito,Cikin Tashin Hankali Abba da Daddy suka Isa ga Inteesar suna Tambayanta meke faruwa Cikin Tashin Hankali.. Tana kuka Tana nuna musu waje Cikin Rawan baki take fadin"Abba...Abb..Imran..! Hankalin Abba ya tashi ya Riketa yana Fadin"Ki natsu Inteesar Ki Fadamana me ya faru da Imran din..? Inteesar ta girgiza kai Cikin Muryan kuka tana fadin"Abba Imran suna Fada da Khamis a waje..! Ido kowa ya zaro Cikin kidima kafin kowa yayi waje da sauri Abba kamar zai Fadi harta su Munari ba"a barsu abaya ba Baffa Kabiru da Mami Asma"u dake cikin Daki tanamai Rigiman gobe su koma Abuja sukaji kukan Inteesar suka Fito agabansu ta Fadi suna Dambe da Khamis ai Mami Asma"u kamar ta Kife Glass din Idonta na neman ya Fadi ta Fita Haraban Gida kamar ta Kifa Saboda Razama Harta Daada sai da ta Fito Falo jin wannan al"amarin Jikokinta Guda Biyu suna Fada da junansu. Yadda suka Fita suka iske wannan Fadan ya tashi Hankalinsu Cikin Lokaci sun jigata junansu,Khamis yana da karfnsu na Sojoji Shi ma Imran yana da karfi ga Zuciya Duka Idanuwansu sun Rufe basaaji basa gani. Abba da kansa ya Rike Imran da karfi Shida Yusuf da Sagir da Basheer Daddy kuma da Su Sa"id suka Rirrike Khamis suna sun hada ma kansu jini da majina,Matan masu Rauni sai kuka Irinsu Munari dasu Hafsah Mami Asma"u hannu ta Dora akanta tana Ihu Tana kururuwan Fadin Imran zai kashe mata yaronta Harta Sajida sai ta Fito sai kuka Baffa Kabiru Shima yana Cikin masu rike Khamis ganin yadda yake Zillo yana neman kwace kansa. Imram ma haka yake cida yana zillo kamar wani kadan Ruwa ammh su Abba suka Dannesa. Daddy ne ya Daka musu tsawa yana Fadin"Kai meye haka.?Meke Damun ku ne..? Kuzo kuna Dambe kamar Wasu yara abunda kannenku zasu yi ku yi musu fada ammh ku da kanku Zaku Zauna kuna Fada da junanku..ku Sake su naga wanda ya kara Taba Dan"uwansa in ya isa..! Ya fada Cikin Bacin Rai Sakinsu akayi suka koma suna maida Numfashi Imran ya Lakato jinin Dake gefen Bakinsa yana kallon Khamis yace Cikin Muryansa"Ba shikenan ba..Tabbas in ka kara maimaita kuskuran da kayi Wlh..Sai na Maka abunda yafi wannan..! Yafada yana Haki Khamis din Shima Yana Hakin yana Lakatan jikin Dake gefen bakinsa yana Fadin"In kafasa..Ai basai na kara ba..Mu Cigaba mana Uban wa kike tsoronka..! Yafada Cikin bacin rai kokarin kara Hadewa suke Mami Asma"u ta shiga Tsakaninsu Tana Fadin"Khamis zan ci Ubanka in baka bari ba..In shi bai da Tarbiya kai baka dashi ne..? Tafada Cikin kuka Sai ya koma ya tsaya yana Maida Numfashi,Imran kuma kallon Mami Asma"u yake kamar yayi ta Dukanta sai dai ya Taushi kansa,shima Numfashin yake Saukewa. Inteesar da Munari sun kamkame juna suna ta kuka Kowa abun baimai Dadi ba Mami Asma"u taja Hannun Khamis suka Nufi Falo Yusuf da Sagir suka kama Imran zuwa Cikin Falon Su Abba suka mara musu baya sauran ma Haka Daada na Falon tana Jiransu Ranta Duk ya baci Umarni ta bata Kowa ya nemi waje ya Zauna ya"yanta suka matsa gabanta. Ta shiga Fada ta Inda take shiga bata nan take Fita ba Ta nemi jin ba"asin me yafaru Khamis ne ya iya maida mganar Imran kuwa kala bai ce ba yana Gefen Sagir yana Sauke Numfashin Alamun Fushin bai gama Sauka ba. Khamis ko kunya yana Fadin Saboda ya Rike ma Inteesar hannu yasa Imran yace zai mai Duka Mami Asma"u Cikin bacin rai tace"Ya zata kaima Kanwar lasa ne da zai Latsa ka yaga Jini..D"ana Soja ne yasan Me yake yi..Kuma Daya rike mata hannu ina Ruwansa Wht is dey a taba hannu ai yar"uwansa ne bai kamata ya shiga ba Kowa anan Wajen yasan Imran bai da Gaskiya adauki mataki ko ni na Dauka bazam yarda adakeni kuma ahanani kuka ba..! Take Fada Cikin Bacin rai ba Zato ba Tsammani Imran ya Dago Jajayen Idanuwansa yana kallonta kafin yace"Waht is dey a taba Hannunta..?Shi Ubanta ne ko Muharraminta da zai Rika taba ta duk sanda yaga Dama.?ba Soja yake ba ko Shugaban Sojojin Duniya ne in ya kara Tabata sai namai Abunda yafi wannan Sakarai kawai..! Yafada yana cije bakinsa Cikin bayyana yadda Ransa ke kuna. Sai kowa ya koma Binsa da kallo Umma Tayi kasake tana kallonsa Ranta yayi mata Fari domin da Farko Ranta ya baci yadda Mami Asma"u take nuna bakomai bane Abunda Khamis din ya aikata Hakama Daddy sai da ya Murmusa Abba zai yi mgana Daddy ya hanasa Domin kalaman Imran mganace mai kyau kuma yaji Dadinta Inteeear y'ace mafi soyuwa gareta Bazai so wani yaci Zarafinta ba ya Tabbata Indai Tana da Dan"uwa irin Imran bai mai iya cin Zarafinta bai Rama mata ba Hakama Ya Basheer aransa yana Mamakin Wasu Mutane meye na rike mata hannu? Har yana nuna ba wani abu ai koda take yar"uwansa hakan bai dace ba. Sajida kuwa kallon Imran take shi baima san da ita ba,Tana Fadin acikin Zuciyarta Meyasa shi ya Rike ma Inteesar hannu jiya..?Shi din Muharraminta ne inda zata iya da sai Tayi mai wannan Tambayar sai dai bata da wannan kwarin gwiwan. Daada ita kanta taji Dadin mganar Imran Dole ta hana Mami Asma"u mgana Tayi ma Khamis fadan Abunda yayi bai kamata ba kansa na kasa yace"Daada nifa bada wata Manufa nayi hakan ba..Ina son Inteesar..Kuma neman Damarta nakeyi ta amince na gabatar da mganarmu wajenku A tsaida mana Lokacin Aure..! Gabadaya sai Falon ya Dau Shuru Mami Asma"u baki ta saki Cikin Takaichi Tana kallon Khamis Baffa Kabiru baice komai ba Domin kansa ya Kulle,Abba ya kalli Daddy shima ya kallesa Umma ma ta Dago Tana kallon Daddy domin taga yaya ya karbi mganar sai dai Inteesar ta bata amsa Domin Cikin kuka ta Bude baki tace bata son Khamis kuma bazata auresa ba Daddy ne ya tsawarta mata abunda bai Taba mata ba Tsawa Dole tayi shuru ta koma Tana sheshhekan kuka. Daada ta Dade batace komai ba Sai Daga Karshe tace Khamis ya Nemi so wajen Inteesar in ta amince su basu da Mtsala saboda acikin Ranta Taana Tunanin kada ta karayin kuskuran da tayi yau dinnan na Hada Auran Imran da Sajida Saboda a abubuwa su Daidaita sai dai Tun Daga jiya zuwa yau abubuwa suna Faruwa marasa Dadi wanda suka sata ta Fara Tunanin anya batayi kuskuran Hada wannan auran ba..?Tana ganin kamar wasu abubuwan marasa Dadi zasu kara Faruwa nan gaba Shiyasa ta ce Khamis ya nemi Yarda Daga Wajen Inteesar in haka ta Faru zata fi kowa jin Dadin Jikokinta sun hada kansu. Baffa Kabiru ya mike ya nemi Izinin Daada na komawa bakin aiki gobe tace ta bama Kowa Damar tafiya gobe in Allah ya kaimu sannan mganar Sajida da Imran kuma wannan yana Wuyan Imran din. Mami Asma"u ta Bude baki tayi mganar Karatun yarta Tana Fadin bamai yanke ma yarta Karatu Daada tace Ai ba wanda yace zai yankemata Duka wadannan Tsaran Tsaran za"ayisu Daga baya. Daddy ya mike yace Sati mai zuwa sun yi mgana da Daddy zasu je Lagos chan gidan da suka baro dashi da Yusuf da Imran din sannan zai Tura Cv dinsa anan Jami"ar Bayero Ko Allah zai sa za"a Dace Tunda Abba ya Nuna yafi son Zaman kano Fiye da Lagos.kowa yayi na"am da mganar Daddy saboda Abba da Sauransa Tabbas Jami"a zata amfana da iliminsa Ita da Dalibai. Kana Daga Karshe Daddy yace Imram ma ya kawo Takardunsa yana da wani aboki Dake aiki a First bank nan Resshen kano kuma Manager ne insha Allahu komai zai yi Daidai agaban kowa da kowa nan take Imran yace shi bayaso bazai yi aiki kuma baya Bukatar Taimakom kowa Sai da Abba ya Daka mai Tsawa yace kada ya kara Mgana Dole yayi shuru. Daada taji Dadin mganar Daddy ta Dinga sakamai albarka Mami Asma"u sai Hararansa take gani take duk wannan abubuwan Dayake yi na Munafunci ne,Ta kalli mijinta Dayayi Shuru bai ce komai ba ita hakan yayi mata Daidai Kada ya ce komai Suje su karata,Gabadaya zuwansu Dukku ba Alheri bane a wajenta Gabadaya Ranta yana bace ne,Allah Allah take Su bar Dukku kamar tana kan kaya. Daada bata yarda Taron nan ya Watse ba sai da Ta Saka Khamis da Imran suka Nemi yafiyan juna Bayan tayi ma Imran Fadan Kai ma Khamis hannu Da yayi har suka Fara kokawa ta saka Sunyi musabaha da junansu Azuciyar khamis yaji komai ya wuce ammh banda Imran Da abun ke cikin Ransa. Koda Taron ya tashi Zuciyar kowa ba Dadi,Inteesar da su munari suka Kule Cikin Dakin duk Tambayan duniyan nan sunyi ma Inteesar taki yadda ta Fada musu komai Dole suka kyaleta. Mami Asma"u kuwa ita da ya"yanta Tayi ta ma Khamis Fada kamar ta Dakesa sai da Baffa Kabiru ya tsawarta mata kana tyi shuru Sajida na gefe ita da Umaima Mami Asma"u ta Umarce su da su hada kayansu gobe da Sassafe zasu Dauki Hanyar Abuja Har garin Allah ya waye Zuciyiyon kowa ba Dadi suna ta shirin komawa Inda suka Fito,Mami Asma"u da ya"yanta kamar suna kan kaya ko Breakafsat bata yarda sun Tsaya sunyi ba Ta mtsama Baffa Kabiru yayi sallama da Daada da Sauran yan"uwansa suka mika Hanya ko Sajida da Daada tace ta bari su gana da Imran bata bari ba ta Tarata suka Shige Mota sai da suka bar Dukku Taji ta Samu natsuwa kadan. Daga Su Mami Asma"u Sai Inna Maimunatu ita da ya"yanta suka Wuce Bauchi,Sai Hamidan Inna Bintalo itama ta wuce katsina Sai Sa"id mutanen Dutse suma suka Dauki Hanya da Hafsah da suka yi kamar suyi kuka ita da Munari da inteesar Su Abba ne kusan karshen Tafiya Domin sai da Daddy daya Basheer da Umma suka mika bayan sun bar musu Inteesar zasu koma kano da ita saboda makaranta. Suna wucewa suma sukayi Shirin Tafiya Imran dai Tun Abunda ya Faru jiya bai kara ma kowa mgana ba kamar Wanda aka Dinkemai baki Sagir har gaya gaji damai mgana ya kyalesa Kowa yayi sallama da yan"uwa banda shi,Ko Daada bai ma Sallama ba gani yake duk itace ta jamai wannan Bacin rai baima son ganinta Haraban gidan ya Fita yana Rataye da Jakarsa yana cika yana batsewa. Abba tare da Sadam Zasu mika Tunda duka kano zasu nufa,Sadam da Imran Dake gefensa agaba Matarsa Aneesa da ya"yansu Waleed da Waleeda sai Sagir suka Fara Mikawa sai Yusuf Dake driving Abba na Gidan gaba,Sai Munari da Inteesar da Anty Safiya Dake gidan baya Imran yana ganinsu yace bazai shiga Motar ba ya gwammace ya shiga ta Sadam ba ya son ya Zauna kusa da Inteeaar Baya son ganin kwanyan idanuwanta kallonta kadai kasala yake sakamar so yake yayi yaki da koma meke Damunsa bazai bari a Fahimci Rauninsa ba. Su Imran su suka fara yin gaba kuma sun Riga su Abba isa kano,Har Gida Sadam yakai sa har sai da yadan Jira su Abba suka kariso kana sukayi sallama ya kama Hanyar gidansa Dauke da matarsa da ya"yansa. Tuni imran ya shige Cikin Gida ya Fada Dakinsa ya maida koda Sagir bai shiga ba Daganan yayi ma su Abba Sallama ya wuce gida Domin ya Shaida Mama, Dawowarsu Inteesar bata Bisa ba Tunda itama yanzu Gidan su Munari kamar gidansu yake Munari tabi Zuwa Dakinta gabadayansu duk sun gaji ammh Inteesar Rabin Hankakinta na kan Imran Data gansa wani iri Har Sako ta Turamai kuma yagani bai bata amsa ba gabanta Fadi yake tana Fatan Allah yasa Fushin Khamis bai shafe ta ba. Sai da sukayi wanka suka yi salla suka Huta kana munari da Inteesar suka shiga suka sama musi Abunda zasu ci. Zuwa Dare kuma Kowa ya isa Gidansa Lafiya. Ta wayar Yusuf Abba ya Kira Baffa Kabiru da Daddy yayi musu ban gajiya Harda Inna Maimunatu itama ta isa gida Lafiya Inna Bintalo Tana Dukku sai gobe zata koma ita. Daddy da Abba sun Dade suna Tattaunawa kan Tafiya Lagos Sati mai Zuwa da yardan Allah Rayuwa Zata Inganta Ranar da Daddare Mama Sagir ya Rakota tazo ma Abba Murna da ban gajiya,Taga kowa banda Imran wanda tunda ya shiga Dakinsa bai Fito ba ko Sallah aciki yayi abunsa Da Mama Zata tafi ta Dunga ma Inteesar tsiyan Taga Gidan Abbanta Ta gujeta Inteesar na Dariya tace gobe Zata dawo Munari ta Daka Tsalle tace kafarta kafarta Abba yace ko"ina suka zauna Duka Gida ne shi bai da mtsala. Washegari da Safe Yusuf ya Tafi aiki Munari da Inteesar suka shiga makaranta saboda ana ta Karatu an Wucesu Safiya kadai ce agida Tana aiki sai Abba Imran na Daki sau Daya ya Fito da Safe ya Hada Tea yasha yagaida Abba ya Dauki Ruwa ya koma Cikin Daki. Da wuri Yusuf ya Dawo Daga Wajen aiki ya Siyoma Abba Sabuwar waya Saboda ya fara amfani da ita Abba yaji Dadi ya Dinga sakama Yusuf albarka suma su Munari sai yammah suka Dawo Daganan wajen Mama suka Sauka Munari ta Kira Ya Yusuf ta Fadamai yace bakomai. *Janafty* 3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�9* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* *After 1 week* Kimanin Sati Daya kenan da zuwansu Dukku,Imran har zuwa wannan Lokacin bai warware ba Ya daina ma kowa mgana Abba ne kadai daya zama Dolensa yake Fitowa ya gaishesa da Safe,duk da kowa ya sanshi da Rashin son shiga jama"a ammh wannan karon abun nashi ya Taba zuciyar wadanda ke tare dashi,ganin ko Masallaci ya daina zuwa na kusa da Gidan su Sagir sai ya koma zuwa wani karamin masallaci na chan gaban gidansu Tunda suka Dawo Daga Dukku ba wanda yaji kalma Daya Daga Bakinsa bayan gaisuwa. Abun ya damu Yusuf har sai da yayi ma Abba mgana Domin har ga Allah shima yaga baiken Daada akan wannan Hadin a yadda Imran yake Gudanar da Rayuwarsa auran Hadi bai Dace dashi ba kuma bai Chanchanta dashi ba. Kamata yayi ya samu wacce yake so tana sonsa ahakan Za"a samu Riba kan Riban abunda ake nema ammh a yanzu da kunci ya kara Dabaibaye Rayuwarsa zai iya koma Fiye ma Imran din da suka sani abaya,Shan Taba kila Har ya Fara kora wasu kayan Mayen in ya Damuwa tayimai yawa Har acikin Ransa bai da yadda Zai yi ne ammh Tabbas Hadin nan na Daada ko alama bai kwantamai ba Duk da Sajidan bata da wani aibu sai dai A kallo Daya da yayi mata yasan bazata iya Zama da Imran ba bata dace dashi ba. Abba Dayaji bayanan Yusuf shi kanshi ya gamsu kuma Daman yana Cikin Damuwar haka din ne sai dai bai bari Yusuf din ya Fahimceshi ba Sai ya nunamai ya kyalesa babu Abunda zai faru dashi Fushi yake na wani Lokaci in Abun ya sakesa zai Wartsake,Ya nuna ma Yusuf kada ya sake ya Tari Imran da wata mgana Saboda bayaso kuma abubuwa su Dawo baya Yasan Halin Imran ciki da Waje shi ya Haifesa ya kuma Tabbata shine kadai weekness din Imran in ba shi ba bai ga wanda ya isa ya Rika Lamkwasasa yadda yaga Dama ba Shi kanshi yana jin Tsausayinsa sai dai Abun nan da Hausawa kan Fadi kaki naka Duniya tasoshi hakan da yake yi Shine Daidai in Imran ya gane yana Tsausayinshi to zai yi amfani da wannam Damar yayi abunda yake so Shi kuma bazai barsa ba Yana da Sanyin Hali yana son Mahaifiyarsa da ya kwashe Fin shekaru uku bai sata a ido ba karon Farko bayan sun Hadu ta bada Unarni kan Abunda ya Haifa bai isa ya Taka wannan Umarnin ba ko shi baya Taka Umarnin Daada ballatana Abunda ya Haifa Shiyasa Daga shi Har yusuf suka Zura Mai ido Bawanda yace mai kala kamar yadda Shima bai damu yace dasu wani abu ba.. Ammh acikin Ransu suna Fata damai addu"an Allah ya sassautamai koma Miye ke Damunsa acikin Zuciyarsa. Bayan Abba da Ya yusuf Inteesar ma tana Cikin Damuwa wannan yanayin da Imran ke Ciki Tunda suka Dawo bai kara yarda sun hadu ba Tayi ta Turamai sako zai gani zai karanta bazai bata amsa ba,Datagaji sai ta Fara Kiransa nan ma sai ta gaji da Ringing bazai dauka ba Daga karshe sai ya Kashe wayarsa Inteesar ta shiga Damuwa sosai na Rashin Sanin Halin Dayake ciki ga Karatun makaranta yayi Zafi sai ta fara Rama atsaye gata Daman ba wani kauri ba,Duk yadda taso su hadu hakan bai samu ba Zasu kwana su Wuni acikin Gidan nan ko Gilmawarsa bata isa ta gani ba Tunda suna Raba Raba ne,Yau su kwana a nan gidan Gobe gidan Mama saboda ta Saba da Inteesar tafiyarta zai saka ta ji Kadaici ya Dameta shiyasa suke Raba Raba ita da Munari da suka kara Shakuwa kamar wasu yan Biyu Daya bai iya Boyema Daya abu sai dai Inteesar ta Boyena Munari Damuwarta kan Imran ko dataga Tana ta Ramewa Data mata mgana sai ta ce saboda Stress din Karatu ne. Inteesar Zuciyarta Zafi take tana da Raunin Data kasa Daukan Lamarin Imran yana bata Wahala batare data san Dalili ba Zuciyarta na Zafi Wani Lokaci Jikinta ya Dauki Dumi Zata iya Jure komai banda Fushin Imran Dafi ne gareta Ta zauna Tayi ta kuka ita Kadai in abun ya Dameta sai kuma Daga baya tayi wani Tunanin Kila ya Daina kula tane saboda Sajida yayi auransa me zai yi da ita yanzu..? Inteesar batasan Soyayya ba Domin bata taba yi ba ballatana ta gane itace ta mata Mugun kamu sannan bata karance karance Social median ma Bata wani Dameta ba,shiyasa ta gaza Fahimtar wani Hali take Ciki kamar yadda Ego din Imran yaki bari ya Fahimci Inteesar ta gama Mamaye Zuciyarsa da gangan Jikinsa ta yadda bazai iya Gudanar da komai acikin wannan Rayuwar ba sai da ita. Abunda Inteesar bata sani ba Imran yafi ta Shiga Damuwa ya fita Wahala akanta,Sai dai shi Namiji ne kuma Shi din bamai Rauni ne bane ko Rauninsa ya bayyana baya yadda wani na Kusa Dashi ya Fahimta. Atsakanin nan yadda yake azabtuwa da Rashin ganin Inteesar ko Abunda Daada tayimai baya Damunsa Saboda yagama da wannan Shafin Tuni Ransa ne yake bace tun Dawowarsu Daga yaji bayason kowa kusa dashi yafi son ya zauna shi kadai Daga shi sai Busa Hayakinsa,Bai taba Tunanin Rashin ganin Inteesar zai zama Cuta garesa ba sai alokacin,Fushi yake da ita Fushi mai Tsanani Saboda In ya Runtse idonsa ganinta yake Khamis rike a Hannunta sannan kuma yana Tuna kalamansa na ita din tashi ce in ya Tuna Hakan sai yaji har ita bayason gani kwata kwata.. Yana ganin Sakonta kuma yana karantawa Domin sune suka Zamemai Tamkar Rigakafin Samun Saukin Wutar da Zuciyarsa ke ciki,In bata Turo ba Wuni zai yi yana Duba Wayarsa yana sakin Tsaki in bata Turo ba Haka zai ta maimata sakonta na Baya wani yayi Mirmishi wani yaji Haushi,in kuma ta Turo ya Dinga maimaitawa kenan kamar yadda yarinyar ta damu dashi matuka Sakonta Duka iri Daya ne. "Ya imu kana lafiya ko..? "Kaci abinci..? Don allah ka Rika cin Abinci bana so ka zauna da yunwa.." "Fatana dai ba rashin Walwalarka Laifi nayi maka ba ko? "Ya imu plz am sorry in wani Laifi nayi maka kada ka Hora kanka da Zaman kadaici.." "Ok..Naji..Plz kada rika shan Sigari..bana son watarana na Rasaka I miss u.." Iraren sakonta kenan sakon da sukasa Nishadi,Suke Debemai kewa Cikin Satin Dayan da yayi yana Boye mata kanshi,Ko Sagir bai kara yarda sun Hadu ba Tun bayan Dawowarsu ya Kirasa a waya yaki Dagaewa Kila Shima Fushi yayi bai kara Kiransa ba kuma bai nemesa ba Shima yafi son haka,Yafi so ya gama Da Kansa Tukunna kafim yazo kuma yaji da Damuwar wasu kuma. ****** *Abuja* Labarin mutanen Abuja Hajiya Mami da ya"yanta wanda tunda suka koma bata barsu sun zauna Lafiya ba haka take ta fada Tana fadin Baffa Kabiru yayi Shuru Danginsa sun ci Zarafinta ita da ya"yanta tayi ikirarin wlh Sai ta Raba auran Sajida da Imran yarta bazata taba zama da Dan"iska ba. Baffa Kabiru dai bai ce mata komai ba Khamis ne ke bata baki shima ta Hada dashi ta Balbale tare da Gargadi mai Girma kada ta karajin mganar Inteesar a bakinsa bata kaunar wannan Hadin kwata kwata,Ita ce nan Mahaifiyarsa ita Zata zabamai da matar Daya dace da shi. Anan gabar kan Baffa Kabiru yayi mgana yace mata kada ta shiga Hurumin da banata ya yadda Imran bai Dace da Sajida ba,Ammh Inteesar bata da wani aibun da Zatace Khamis bazai aureta ba Kuma Diyar Mustapha ce suna da kyakyawan alaqan Jini da yan"uwanta da bazai ji Kyashin Hada Zuru"a dashi ba. Mami Asma"u na jin haka ta Daka Tsalle tace bazai sabu ba bazata bari su hade mata kai shi da Danginsa ba,Sajida an mata auran kaskascin Auran da bazata iya Daga baki ta Fadeshi Cikin Dangi ba Ta tabbata masu mata Dariya suna da yawa sannan kuma shima Khamis din sai ya kara Zama nasu ta gama Wahala Dashi ya kawo yanzu sai ya zama Surikin Mustpaha da Salaha ita ta Zama yar kallo kenan bata yarda ba bata Amince ba kuma ba wai tace yarinyar nada Illah bane kawai Hadin ne bai mataba bata Ra"ayi kuma Tunda aka mata fim Karfi kan Sajida wannan karon bazata kara yarda ba. Baffa Kabiru dai bai biye mata ba Sanin Halinta sai ya kyaleta,Sai ta koma kan Khamis tajamai kunne sosai na kada ya sake taji wata mgana kan Inteesar ta kara tashi Daliln Dayasa yaji Zaman Abujan ya isheshi kwana Biyu yayi ya koma Anambara Sai dai kafin Tafiyarsa sun yi mgana da Baffa Kabiru sosai ya bashi Daman Indai yana son Inteesar ya Nemi soyayya da yardanta yayi mai alkwarkn zai shigemai gaba sai ya aureta da wannan kwarin gwiwan ya koma Bakin aikinsa da yakinin zai samo kan Inteesar da yardanta Tunda Dad ya shigemai gaba Mami ba Damuwarsa bane in ta gama bambaminta shikenan. Bangaran Sajida Mami Asma"u ta dawo kanta ganin Khamis ya koma bakin aikinsa,Ta riga ta kudura ma Ranta Tsarwatsa auran nan kuma ta Lashi Tokobin sai ta Wulakanta Imran Tana Fatan ya tako kafarsa zuwa Gidanta sai ya Raina kansa. Tattara Sajida tayi tace ta koma makaranta Zasu fara Test,Daman A Hostel take zaune sai dai bayan 2 weeks take Dawowa Gida tayi weekend wani Lokacin har Sati ma Tana Dawowa Gida sai in Sun Fara Test ne ko jarabawa take zama acikin makaranta sosai wannan karon Mami bata ma barta tayi Tunanin makomarta ba ta Tarkatata makaranta da kanta ta kaita ta maidata bayan ta mata Fadan ta Cire komai acikin Ranta tayi Facing din Karatunta kamar wani abu bai Faru ba Sannan ta Gargade ta kada ta Sake ta fadama wani an mata aurre..Domin kaskanci ne sosai wani yaji wannan Labarin Sai ayi mata Dariya. Sajida a makaranta bazatace ga Halin Datake ciki ba,Zuciyarta da Duka Tunaninta suna wajen Mijinta Imran ne bata San ta wata Hanya zata bi ta samesa ba,Ba mgana take da kowa ba Acikin Dangi ballatana ta saka ran Zata samu ko wajen wata ne,Bata kuma da lambar Munari Umaima ce ke dashi kuma tana gida bata san kuma ta Kirata Mami taji Labari ita ko bata Dama ta gana da Mijin nata ba"ayi ba abubuwa suka zo suka Faru ba Dadi ita dai koma Menene bazata yarda Mami ta rabata da Imran ba Tana son shi tana Kaunarsa ya Dace da Duka Zabinta bata damu da Hallayarsa ba shi take so kuma bata Damu da Rashin Jituwansu da Mami ba Ballatana Ya Khamis ba yare Daya take Fahimta Shine Son Imran mijinta Har wani alfahari take da hakan kuma bazata jura ko Ganin wani ya Shiga Tsakaninta da abunda take so ba, koda Mamin ne da kanta. Haka take Sukuku bata da wani Karkashi Allah ne ma ya Taimaketa Kwakwalwarta naja shiyasa ta iya Tabuka wani abu a Test din da sukeyi ammh Rabin Hankalinta da komai nata suna ga Imran ne duka Mafarkinta nashi ne. Ta bari ne su gama Test ta dawo gida Sai ta san yadda tayi ta mallaki lambarsa su rika mgana Kila jin Muryansa zai Rage mata wani Radadin ba ruwanta dashi bai Nemeta ba,ita din zata Nemesa saboda Shi din Mijinta ne nata ita kadai. ******* *Kano..* Yau ta kama Jumma"a ne a masallacin Jumma"a suka Hade tsakanin Sagir da Imran,Daman nan suke Sallar Jumma"a Shida Sagir,Abba kuma na chan Tsallaken Gadon kaya yake zuwa ,Tun ana Huduba Imran ya iso masallacin,shiyasa ya samu Shiga Cikin masallacin aka gama Huduba aka Tada Sallar sai da aka idar irin Tururuwan Fitowana nan sukaci karo da juna. Tsayawa sukayi suna kallon kallon juna Sagir na sanye Cikin Sabuwar Shaddansa Fara Dinkin zamnii na Riga da wando Da Hulansa Zanna Bukar,sai Dardumansa Dake hannunsa yayi kyau sosai kuruciyarsa ta kara Bayyana da Samartakansa.. Yayinda Imran ke sanye da Jallabiya mai Ruwan madara,bata da tsawo sosai sai ya Hada da wani bakin Wando kafarsa Cikin Takalminsa Sawu Ciki na Fatar damisa,kansa ba Hula sai dai yasha gyara Hannunsa kuma Agogon Fata ne baki na Fatar Damisa fuskarnan ko kadan ba Fara"a Ya wani Kara Dakuna Fuska da suka Hadu da Sagir. Sagir bai damu ba Mirmishi yayi mai Lokaci Daya yana bashi Hannu alamun Musabaha bai yi gaddama ba ya mikamai suka gaisa Daganan suka jera har Wajen masallacin Mutane nata Xirga Zirga tafiya masu ababan Hawa nayi masu Tafiyar kasa nayi. Sagir ya kalli Imran yana Fadin"Kazo da Mashin ne..? Ko tankasa Imran bai yi ba Hanyarsa ya Dauka ya Fara Tafiya wanda hakan da yayi shi ya bama Sagir amsa sa bai Hakura ba ya taka ya Bisa suka Fara Jerawa Suna Tafiya Kafada da kafada ammh ba wanda ya kara ma wani mgana sai Sagir ne ya kallesa yana Fadin"Na kiraka baka Dauka ba..Hala wayarka Ta lalace ne..?domin naga baka Biyo baya ba..? Imran ya wani kara Tamke Fuska Hannuns Daya Cikin Aljihun Jallabiyansa kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Bata lalace ba..Kawai bana Ra"ayin mgana Dakai ne..! Sagir na Dariya yace"Nagane..Daman mai Amarya Danyan Sharaf irin Sajida ina zai yi ra"ayin mgana Damu..! Kamar ya watsamai Wuta haka yaji mganarsa Da ace ba domin suna Bakin Titi bane da sai ya Daki bakin Sagir ya Fitar da jini sai dai yaci Daraja Daya suna Cikin Mutane ne da yau ya gane Kuransa na gayamai wannan mganar. Kala bai kara cemai ba Sai ma kara Hade Rai da yayi yana wani Bude Hanci ganin ya kunnosa yasa Sagir bai kara mgana ba sai Kunshe Dariyansa yake yi. Haka suka rika Tafiya kamar kurame har suka kariso kofar Gidan su Sagir din wanda yayi ya shiga ya gaida Mama yace bazai shiga ba kuma Shima Sagir din bazai shiga Gidan ba yanzu Sagir ya Tsaya yana kallon Ikon Allah ga Shagonsa yaronsa Auwal ya Rufe sun tafi masallaci Da alamun ya Rigasu dawowa. Bai ce komai ba ya gyara Tsayuwa suna Tsaye kafada da kafada suna Bin Hanya da kallo kamar masu kirga wani Abu. Ta bangaran Imran ba haka abun yake yau yaji ya gaza Inteesar kadai yake son gani,in bai ganta ba ji yake kamar zai iya Mutuwa gashi ta Daina Kiransa kwana Biyi bai ga Sakonta ba Ko ta Daina Damuwa dashi ne..? Juyawa yayi yana kallon Kofar gidan Mama Tun jiya bai ji Motsinta ita da Munari agidan ba,kila Gidan Mama suka kwana kuma yau har yabar Gida bai gansu ba Abba da Anty Safiya ya bari agida Yusuf na wajen aiki. Kallon Kofar gidan yake kamar yana so yaga Inteesar din ta Fito Sagir Dake Lura dashi Tun dazu ya Juyo yana kallonsa Cikin Nazarinsa kafin yace"wai wakake nema ne sai kallon Waje Daya kake yi..?Nace kuma kazo mu shiga kace A"a..! Imran bai ce komai ba sai ma Mtsawa Da yayi gefe ya Fito da wayarsa Dake Cikin Aljihu Sagir na gefe Hannunsa Saman Kirjinsa yana kallon ikon Allah Cike da Nazarin Imran din. Sako ya Tura mata saboda yana son yaji ko Tana ina ne..? '"Kina ina ne.."? Haka kurum ya Turamata ya koma yana Jiran Tsammanin amsarta Sai dai Har wajen Shudewar Mintina Goma bai jita ba sai kallon Wayar yake yana Sakin Siririn Tsaki wata Zuciyar na Fadamai kila Fushi Take yi Dakai tana Kiranka baka Dauka Ransa ya kara baci Wato ita ce ma Zatayi Fushi ita bata ga abunda tayimai ba ko? Kwafa yayi kawai yana kokarin Daidaita kansa Sagir Dake lura dashi ya matso kusa dashi yana Fadin"Wa kake ta kira ne haka..? Ko yaki Dauka ne naga sai Tsaki kake ja kai kadai..ko Amarya ce taki Dauka tana ja ma Ango aji..! Ya karisa Fada yana yar Dariya wani banzan Kallo Imran ya Bisa Dashi kafin ya maida wayarsa aljihun Jallbiyan Dake jikinsa Kokarin Dunkule hannu yake yakai ma Sagir din Wani Naushin da Kila sai Bakinsa ya Zubda Hakora Lura da Hakan da yayi ne yasa yamtsa da Sauri yana Fadin"Daga mgana..? Allah ya Huci Ran angon Sajida ya Dade..! Yake Fada yana Dariyan ganin yadda Fuskar Imran din tayi saboda Haushi Kwafa yaja kafin yace"Banza Dan saka ido..Ai daka Tssya Daka gane Ango yau..! Yafada yana kara Sakin wani Tsakin ya koma gefe wayarsa ya kara Fiddowa Shuru bai ga Sakon Inteesar ba Ransa sai ya kara baci,Ga Sagir Sai Dariya yake yi mai Banza Dashi yayi bai bi ta kansa ba Duk da Sunan Sajidan Dayake ambata kamar ya Juya ya Watsamai mari da ashariya haka yake ji. Sagir ganin Imran din bai kula sa ba sai ya Daina ya Matso kusa dashi ganinsa sai Bini Bini ya Duba Waya yana Sakin Tsaki ya Fahimco wani abu na Damunsa Cikin Lallami yace"Meke Damunka Imu..?na lura dakai kamar Miskilancin naka yau yafi na koyaushe..! Imran yayi kamar bai jisa ba Sai chan yace"Ina Ruwanka..? Sagir ya kada kai yana Fadin"Au Daga Tambaya..? Nima Allah karamin da nake kokarin jin Damuwarka kaga Tafiyama ka Dade damuwar bata Kashe ka ba Tunda kai baka son Abun Arziki ba..! Yafada Lokaci Daya yana wucewa Shagonsa ya shige Daman Tun dazu suna Tsaye su Auwal din suka Dawo suka zo suka Bude shagon da kallo ya Bisa shifa bama Sagir ne agabansa ba..Damuwar Dayake ciki tafi karfin ya Tsaya yana bi ta kansa wanda yasan anjuma nan zasu Shirya kansu. Ganin Shuru Shuru bai jita ba yasa ya yanke Shawaran Kiranta Duk da baya son Kiran nata ammh Zuciyarsa ta Rinjayi gangar Jikinsa Daya kasa Hana kanshi Sai dai ya gansa kawai yana Kiranta,Zuciyarsa Bugawa take da Sauri da Sauri so yake ji Muryanta ko ya Samu Salama,Sai dai me yana Kiran nata ta shiga yaji Call Waiting ma"ana Tana amfani da wayar kenan Wani Rugugin bala"i Imran yaji sun Saukomai acikin kansa Har wani Jiri Jiri yake gani bai Katse Kiran ba Sai da ta yanke da kanta,Kansa ya Dafe yana jin wani Daci Daga kasan Ransa Wato ma Tana ganin Sakonsa Tayi banza Dashi..? Da ganga taki kulasa..?kan Bala"i bata san Waye Imran ba Ya zama Dole Abunda yake so ayimai in kuma akaki yimai ba Zaman Lafiya. Wani Tunanine ya shiga kansa Kodai da wannan Banzan gayen take waya ne..? Domin ai yaji Daada ta bashi Umarnin ya Nemi yardanta in ta Amince shikenan Tuna Haka da yayi sai da Idanuwansa suka Sauya Launi Kirjinsa ya Fara tashi yana komawa da wani bakin Kishi da shi kanshi baisan yana da shi ba Tana Waya dashi Shine tayi banza Dani..Ina Bata isa ba..Shima khamis din bai isa ba Inteesar bazata taba Zama nashi ba Har Abada. Abunda bai sani ba Sakon Daya Turama Inteesar ba ita ta gani ba Munari ce,Domin yau din da Safe suka Shiga School shima Assigment suka yi Submitting,suka Dawo gidan Mama suka kwana Daman bayan sun Dawo kuma suka yi Girki,Da Niyyar da sun gama zasu je gidan su Munari,To bayan sun gama ne Duka aikin su ne Mama tana Falo ta samu Barci Saman kujera ita kuma Inteesar ta shiga wanka Munari tace bazatayi wanka ba sai anjuma Tunda Tayi da Safe Inteesar tace sai ta karayi bazata iya Fita hakanan ba Tayi kaurin Kitchen Munari ta tabe mata baki ta shiga wanka tana mata Dariyan kazama Tana jinta bata tanka mata ba.. Tsakar gida Munari ta Fita ta Dauro alwala tazo ta shimfida Darduma tayi Salla Ta idar kenan tana kan Sallahya Tana Lazimi taji shigowar sako Daga wayar Inteesar wayar tana kusa da ita ne Daga bakin gado sai ta saka Hannu ta Dauko Tasan Passaword din Inteesar yasa ta saka ta Bude Tana Budewa ita bama da Niyar ganin wanda ya Turo sakon ba sai dai ganin Sunan YA IMU�� Da Love agaba alamun Shi ya Turo Sakon ya bata mamakon da batasan Sadda ta shiga Sakon ta karanta ba Mamaki ya kara kamata ita dai Ya Imu Daya ta sani..Kuma in shine yaushe suka Fara haka da Inteesar bama haka ba Shi yana da Lokacin Tura ma mace Sako ne..?kodai wani ne bashi ba..? Bata gasgasta ba sai da ta jawo wayarta ta Kwafe lambar Imran ta Saka awayar wata Tana Danna Wajen Kiran Sunan Daya Fito ya kara bayyanar mata da komai Batasan Sadda Dariya ta kamata ba Ya Imu da Inteesar What a pecfect martch,Bata Tsaya sanya ba ta koma Cikin Masages din ta Rika karantawa Tunda Daga Farko Tana karantawa Tana Tsintsiran Dariya ita kadai Ganin irin yadda Imran din ke Rubutoma Inteesae sako kamar Dole?Wannan wani irin Soyyyace..! Lalle ta yardan ma kanta Ya Imu ne na Dabam ne taga duka Sakonnin da Inteesar ke Turamai yaki bata amsa Duk Sai taji bataji Dadi ba Har ga Allah Zata Fi kowa Jin Dadin wannan Lamarin Sai dai Tana Tsausayama Inteesar Zata Sha Wahalan Soyayya da Imu saboda Baya bama Masu zama dashi Damar Saninsa in yau yazo da wannan kalan gobe wani ne,Ta fara Tuna duk Abubuwan da suka Faru da yawan mganarsa da Inteesar ke mata da yawan Damuwa dashi dashi kanshi Yadda yayi Fada da Khamis a Dukku Saboda ita Allah Sarki su kuma irin su haka Salon Soyayyarsu take mai Wuyar Sha"ani Tana da Tabbacin sun kamu da son juna basu sani ba,Soyayyar da ake Kira Makauniyar soyayya ta Tabbata Inteesar bata Fahimci Feeling dinta ba Shiyasa bata taba gayamata ba Gabadaya sai Tsausayinsu ya kamata Tuna ga Sajida ta shiga Tsakiyarsu,Ta Tabbata Duk da ya Hallata ya Hadasu Dukkansu ya aura ammh Hakan bamai yuyu bame Saboda Kishi kuma sannan su yan"uwan juna ne hakan zai kawo Tarin mtsaloli masu yawa Barinsa shine mafi Alheri. Tana cikin wannan Halin ne taji Kiciniyar Bude Kofar Tiolet din yasa tayi Saurin maida mata wayar ta ijiye sai ta Dauki Tata tayi kamar Tana Latswa. Inteesar na Fitowa bata Zargi komai ba Ta tambayi Munari ko Tayi sallah ne tace mata eh itama ta Dauro alwala tana gama Shafa Lotion dinta ta saka Dogowar rigarta baka ta Zurma Hijabi Ta Tada Sallah bata idar ba Daddy ya Kira Wayar Inteesar,Munari ta Dauka Jin ita ne yasa suka Fara gaisawa kafin ya bama Umma su tsinke da Hira,Umma ita yanzu ta zama mai ya"ya Biyu Inteesar da Munari suna wayar ne Imran yayi ta kira ita ko ji ma batayi ba,Har Inteesar ta idar da sallah suka zo suka Hadu suna ta wayar Har Umma ta gaji tace subama Mama wayar Lokacin har tatashi tayi Sallah suka Mikamata wayar ta cigaba da mgana da Ita. Imran yana Tsaye ne ammh ya kasa Taka kafarsa Saboda Nauyin Datayimai cikin wannan Halin Sagir ya Fito Daga Shagonsa,Har da zai Shiga Gida,sai yaga Imran din yana nan Tsaye sai ya fasa ya Dawo yazo ya Tsaya agefensa yana Fadin"Mu shiga wajen Mama mu ci Abinci..Tunda bazaka Fadamin meke damiunka ba..! Yafada Cikin kulawa Jin haka yasa Imran ya Dago Jajayen Idannuwansa yana kallonsa Cikin jin yadda Zuciyarsa ke suya Sagir daya ga Idanuwansa sun yi ja yace"Subhanallah me ke damunka Imu..? Kan mganata ce..? Am sorry bazan kara maka wannan wasan ba indai hakane..! Yafada Cikin bayyana Damuwarsa Imran Ya Cije bakinsa kafin yace"Ni da wannan yarinyar ne.! Ya fada kai tsaye saboda bai da wata Munafa Cikin mamaki Sagir ya Kallesa Kafin yace"Wata yarinya..? Sajida..? Yafada Cikin Dariya Imran ya Saki katon Tsaki kafin yace"wacece kuma Sajida..? Nifa na manta da ita Saboda na Shafe shafinta Tun a dukku..Inteesar nake mgana kanwarka..! Yafada yana kara jin wani Haushi ya kumesa Sagir yace"Kanwarmu dai ai kaima Takace ko..? Imran ya kallesa Cikin ido kafin yace"Ta Raina ni ina Kiranta bata Dagawa kuma in na Tura mata sako bata bani amsana ba..? Wai kuma kasan Abunda yasa naji Raina na kuna..? Sagir kamar gaula ya Girgizamai kai Cikin Bayyana Bacin Ransa Imran yace"Na kirata Call Waiting tun dazu..Kaga kenan tana gani..Ni ne ta Raina bazata Dauki wayataba ammh Tana chan tana mgana da wannan Dan"iskan yaron..! Yafada yana Cizan Lebensa na kasa da karfi. Sagir Daya gama yin galala yana Sauraran Imran cikin son Tabbatar da Zarginsa yace"Kara kiranta mu gani..! Imran ba Musu ya kara Doka ma Inteesar wayar har lau lokacin Call Waiting Cikin Hargagi ya nuna ma Sagir yana Fadin"U see..Na sani Dashi take waya..Ji na nake kamar yanzu na Bude ido na gansa agabana wlh in na Fara Dukansa sai ya Mutu uban wa yace ya Kirata..? Inteesar bazata taba Zama nashi ba Har Abada Ni Imran zuciyata bazata Jure ganinta da wani ba..! Yafada Cikin Fitar Hayyaci da Bacin rai wanda yasa baima san me yake Fada ba. Sagir Daya sake baki kawai yana jinsa Baisan Sadda ya saki wani kayattacen Mirmishi ba Kafin ya kalli Imran Ido Cikin Ido yace "Imu U are in Love...KANA SON INTERSAR..! da wani mamaki da Razana Imran ya ware idanuwansa masu girma akan Sagir Kalamansa suna mai yawa amsa kuwwa a kunnuwansa. KANA SON INTEESAR..Wannan So ne..? Yana sonta ne Daman..? Tambayan Daya Runtse ido yana yi ma kansa kenan. *Janafty* 3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�10* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Kallonsa Sagir ya cigaba da yi yana Fadin"Ko ka yarda ko karka yarda Kana son Inteesar Dama ni Tuntuni naga alamun haka sai dai nayi Shuru ne Tuntuni ganin kai kanka ma baka san Ka kamu da soyayyarta ba..! Ya karishe fada cikin son Tabbatar da mganarsa ganin yadda Imran din ke Girgiza kai cikin alamun zai musa mganarsa. Imran kuwa mamaki ne ya cika shi yasa ya kasa mgana sai Girgiza kai kawai yake yi yana Tambayan kansa Daman haka so yake..? Shi yana sonta ne Daman..? Kai ina wannan ba Soyayya bane shi bai taba soyayya ba kuma bai santa ba kuma baya so ya santa ya Dauki Soyayya a mtsayin Shirme da bata Lokaci Da Takura shi kuma baya ciki da duka Daga ciki. Kenan Saboda yana sonta yasa yake son ganinta..? Baya son kukanta..? Baya son tayi mgana da kowa yana jin Zafi acikin zuciyarsa Duk Sanda ya Tuna da Lokacin da Khamis ya Rike mata Hannu wannan ma So ne Imran..? Acikin Zuciyarsa yake Tambayan kansa yaki yarda ya bama Zuciyarsa Daman karban Rauninsa da Feeling dinsa ya karyata kansa da cewa Imran wannan ba so bane,Kawai dai kana Tsausayamata ne saboda ita din yar"uwanka ce kuma mai kula dakai kaima ka kulasa to Khamis fa meyasa yake jin Haushinsa akanta..?Shima So ne..? Kai ina a"ah yana jin Haushin sa ne Saboda Son kai irin na Baffa Kabiru da Mami Asma"u sannan bai Dace da Inteesar ba ammh shi ba Sonta yake ba Sagir bai Fahimce shi Daidai ba. Sai da yaga Duka nazarinsa kana ya Bude Dararan Idanuwansa da suka kala sukayi Jajir Saboda Halin Dayake ciki Sagir na kallonsa yana Nazarinsa Cikin Taunan Lips dinsa yace"A"a ba gaskiya bane..Baka Fahinceni ba..Ni ba Sonta nake yi ba..Ban taba son kowa ba..Ni ban yarda da Soyayya ba Abunda kake Tunani bashi bane..! Yafada yana wani Dakuna Fuska Lokaci Daya yana kara Hade rai kada ma Sagir ya kara Fadin wata mgana. Sagir yayi Mirmishi Sanin Daman mawuyacin Abu ne Imran ya yarda da Feeling dinsa da Zuciyarsa saboda Sanin Halinsa yasa yayi Mirmishi mai kayatarwa kafin yace"Nasan daman zaka ce haka..Bazaka taba yarda da Zuciyarka ba..Ammh ko kaki ko kaso kana son Inteesar Imu..!. Yafada Wit Full Confident Imran ya kallesa ido cikin ido kafin yace"Wannan ma ai mganar banza ce..Taya ya zan fara son wannan karamar yarinyar..?Ai nayi mata Girma na tabbata Ko Rabin Kirjina na Dora mata sai ta suma ballatana Duka Mazantakana infact ma ni bana son Soyayya da yara kanana ni da nake Fama da kaina na dawo ina fama da wata..Ina ban yarda da mganarka ba kama Daina Fada Raina yana baci ne..! Ya karishe Fada yana saka Hannunsa Saman sumar kansa Sagir yace"Naji baka sonta meyasa kake jin haushi in Tana waya da wani..? Meyasa kayi Fada da Khamis a Dukku Saboda ita..? Meyasa kake da lambarta ni a Tunani baka taba ijiye lambar wata mace a wayarka ba sai ita kagani kuwa ita din ta Dabam ne Kana Sonta ne ammh kai kanka baka sani ba kaki kuma yarda da mganata ballatana ka bata Damar fahimtar Feeling dinka..! Tsaki Imran ya saki bai yi mgana ba kallon Sagir kadai yake yi yana Auna mganganunsa Sagir kuma ganin Imran bazai yarda dashi ba sai ya Sauya mganarsa Cikin Danne Dariyarsa yace"To naji ba sonta kake yi ba..Ammh kai sai ka bari Khamis din yayi nasara akanka..? Imran yamai kallon bangane ba Sagir yace"Eh ina Nufin Cewa fa yayi yana sonta da aure kuma Daada ta bashi Dama ya nemi yardanta yanzu in ta amince fa ya nuna kai ne baka yi nasara ba shi yayi nasara akanka kuma Rashin Nasara ba Dabi"arka bace Imran..! Ya karishe Fada yana kokarin Hana Dariyarsa bayyana ganin yadda Imran ya gama yadda da duka mganarsa Zuciyarsa da soyayyar Inteesar suna ta Rinjayansa bai sani ba. Imran ya jinjina kai yana Tuna Sanda Khamis ke fadin Inteesar sai ta Zama nashi shi kuma ya Tabbatar mai da karyansa baza ta zama nashi ba kenan Gaskiyan Sagir ne In yayi shuru To Khamis yayi Nasara akansa Dole ne yayi wani abu akai ya zama Dole ya Dakarar dashi,In yama Tuna Sunansa Ransa Har wani Tafasa yake saboda Bacin rai da Kishi. Cikin Bacin ran ya kalli Sagir yana Fadin"Ka Fadi gaskiya Sagir..Baka Taba mgana mai kyau ba sai yau..Lalle Dole na nuna ma mara kunyar yaron nan mganata kamar Saran Takobi take in na Sara sai tayi yanka..kuma Nine Imran wanda in nace Abu bana Barci kirki sai na aiwatar da gudurina..,! Sagir ya kada kai yana Fadin"Yauwa Abokina..nuna masa Bakin Rijiya ba wajen wasan makaho bane..! Yafada yana Bubbuga Kafadan Imran Lokaci Daya yana Danne Dariyarsa. Imran ya wani Cije bakinsa yana Fadin"Na tsani yaron nan ban san Dalili ba..ga mata da yawa ammh yace sai ita..? Sagir yace"Shi nagani..yanzu to ina Mafita ta ina zaka Fara..? Imran ya kallesa kai Tsaye yana Fadin"Ta inda aka Hau ta nan za"a sauka...! Sagir yace"Auranta zaka nema..? Yafada yana kallon Imran ido Cikin Ido. Imran yayi Tsam yana kallonsa Zuciyarsa na Bugawa ammh ta natsu da mganar Sagir Cikin wani yanayi yace"Nima ban sani ba..Ammh in dai ina Raye acikin Duniyar nan yaron nan bai isa ya sameta ba Har Abada..! Sagir yace"Ita Sajidan fa..?ya zakayi da ita..? Imran ya saki Tsaki yana Fadin"Tuni na gama da Shafin wannan yarinyar..Ni ba ajinta bane..ba ita ba Harta iyayanta sun sani nafi Karfin su..! Sagir dai kallonsa yake yi bai ce komai ba Tsausayi kawai Imran ke basa ganin yana cikin Halin Soyayya ammh bai sani ba irin makauniyar soyayyar nan mai Wahalar da mai yinta. Yana cikin wannan Tunanin yaji Imran na Fadin"Yara nan suna cikin gidan nan ne..? Yafada yana Nuna Gidan su Sagir da Hannunsa. Sagir yace"Eh basu dade da Dawowa Daga makaranta ba suna ciki indai ba bayan Tafiyata masallaci suka Fita ba..! Imran kai kawai ya Daga kafin yace"Bari na shiga gida..! Ya bama Sagir hannu sukayi musabaha kafin suyi sallama Sagir ya shiga gida Imran kuma ya kama Hanyar gida yana Tafe yana Tsara wasu abubuwa Daki Daki. Gobe Baffa Mustapha yace Zai zo zasu Tafi Lagos jibi Lahadi su dawo da Farko yace bazai je ba ammh Daddy yace sai yaje Haka kurum yaji bazai iya mai Musu ba ko don yana Baban Inteesar ne..? A"a Saboda shi bai kullace shi kamar yadda ya Kullaci Baffa Kabiru ba Shiyasa Ya riga ya gama Tsara komai suna Dawowa Ranar Litini Dukku zai je Zaima Daada Diran Mikiya Duk da yana jin Haushinta ammh Yanzu zatamai amfani Dole ya Danne komai yaje suyi mgana,ammh kafin nan sai ya bata ma Inteesar Rai ta fara Rainashi,kamar shi ya Kirata tana waya Ta sagale shi a Call waiting ya Tura mata sako ta karanta tayi banza Dashi..? Tana chan tana waya da wannan Khamis din ko..?lalle sai ta gane bata da wayau ranta sai ya baci. Har ya isa gida yana Huci shi kadai yana Cika yana batsewa Shiyasa bai ma Lura da Bakuwar Motar Dake Haraban gidan ba,sai da ya shiga ciki ne ya iske Sadam ne yazo gaida Abba Daga masallacin jumma"a yake. Bai da yarda zai yi Dole ya Tsaya suka yi musabaha yadan Saki Ransa kadan ba Sosai ba Har yana Tambayan Sadam din ya yara..?bashi ba hatta Abba yayi mamaki sai da yayi Dariya yana kallon Imran Daya kara Dakuna Fuska. Daki ya shige baisan Tafiyar Sadam ba sai La"asar ya Fito Daure da alwala na Tafiya masallaci,ya riga ya gama Tsara Komai Tare da Abba suka Tafi masallaci suka kuma Dawo tare,Jin gidan Shuru yasa yasan suna Gidam Mama har yanzu,Yusuf ne ya dawo alokacin Yana jin yunwa ya Fita Chan Bakin Titi ya siyo kankana da Lemo daya dawo bai shiga gida ba aharaban gidan ya ci Burki saman Motan Yusuf ya Haye ya wani karkace kamar Wani Saraki yana shan kayan Lambunsa Hankalinsa kwance ya samo Mafita,Abu Dayane yanzu agabansa yaga Inteesar so yake yaji Dalilinta na yimai abunda tayi mai kuma yana so yaji shin dawa take mgana awaya Data sharesa... ? Zuciyarsa zAfi take duk sanda ya Tuna da wani Khamis Shiyasa ya Kasa ya Tsare yaga shigowarsu yau in bai ganta ba zai taka Har Cikin gidan Mama yaji Dalilinta na maida shi Abokin wasanta saboda Taga yana mata Dariya. Yana gama Shanye kayan Lambunsa ya Zaro karan Sigarinsa ya kunna ya Cigaba da Fesa Hayaki iro megadi na Daga gefe kan bencinsa yana kallonsa aransa yana ayyana ga Mutum har Mutum ammh ya bata kansa da shan Sigari. Yayi Nisa Cikin Duniyar Hayakinsa Kamar Daga sama yaji Dariyansu Sama sama da Sauri ya Bude Idanuwansa da suka Fara Lumshewa ya sauke su akansu suna Tafe Hannayensu cikin na juna ita da Munari daga alamu ma basu Lura dashi ba Munari ce ke nuna mata wani abu acikin Wayarta yasa suke Dariya Shagala yayi da kallonta ganin yadda Fararan kananun Hakoranta suka Bayyana.. Kara Ware ido yayi akanta Cikin Bugawar Zuciya gabadaya ta gama Tafiya dashi acikin Ransa ya Furta"Tana da kyau in tayi Dariya..! Ganin bama su san da wanzuwarsa ba a wajen yasa yayi saurin Wurgar da Taban Dake hannunsa a kasa haka kurum yaji karo na Farko baya so Inteesar ta kara ganinsa yana shan Taba tunda yake bai taba ganin wani yaji kunyar shan tabansa ba Karo na Farko a Rayuwarsa ba sai yau. Saukowa yayi Daga saman Mota yama gyara Farar Rigarsa data Tattare Saboda Zama ya sauya kaya Daga Jallabiya zuwa bakin wando da Farar Riga. Daga Inda yake Tsaye ya Kausasa Murya yana Fadin"Kai ina zaku..? Gabadayansu sun ji Faduwar gaba atare suka juyo suna kallonsa Munari ta Fara rawan jiki banda Inteesar data Kuramai ido wami sanyi na Shigarta Farinciki ya Cikata data gansa kamar Wacce ta warke makanta Shima ita yake kallo kai Tsaye sai dai ya san Takunsa Kauda kai yayi ya kara Daure Fuska Cikin Daga Murya yace"Da kuka Tsaya anan ni kuke so nazo na Same ku..? Yafada yana kara Hade rai,Ai da Sauri sum sum suka kariso gabansa Suna Dukar da kai kamar Munafukai,Inteesar tace kadai taga bazata iya jurewa ba ta Dago Karaf suka Hada ido daman ashe ita yake kallo,Kallon juna suke Daga karkashin zuciyarsu suna jin wani Salama da Farinciki Imran Har boyayyiyar ajiyar Zuciya ya sauke saboda ganinta kamar an ce mai an gafartamai Zunubansa sai da yana kallonta yaga ta Ramemai ta idaanuwansa itama Salama take ji da Farincikin ganinsa Idanuwanta suka cika da kwallar ganinsa sai dai itama taga yayi mata Rama acikin Idanuwanta Dukkansu sun Jigata matuka da Rashin ganin juna sai dai Raunin Intee yafi bayyana Imran kuma yana Kokarin Boye Rauninsa ne. Munari da kanta yagaji da Dukewa ta Dago ai sai ta ga an kure juna da kallon Soyayya sai ta Ware ido kawai ta na kallon Ikon Allah Dadi da Farimciki Lokaci Daya da matsanancin Tsausayinsu na Ratsata Har batasan ta shagala da kallonsu ba sai da taji Imran ya Daka mata Tsawa Domin ya ganta sanda ta kafe su da ido Da Sauri ta sadda kanta tana Kokarin Daidaita kanta Hade rai yayi saboda kada taga Fuskar Rainasa cikin bada Umarni da Dakiyarsa yace"Tsayuwar Uban me kike yi..?Bace min dagani kafin na Sauya Miki kammani Nonsess..,! Ai bai ma Rufe baki ba Munari ta bace da Sauri aranta Tana Fadin"basai takai ga Haka ba..! Kamar ta Kifa wajen shigewa Cikin Falon Har Inteesar da ta bita da kallo ta Kusa Dariya yana kallonta Tana Juyowa suka Hada ido Harara ya sakarmata yana wani Kara Dakuna Fuska Tasan Laifinta Narai narai tayi mai da ido kafin ta saka Duka Hannuwanta biyu,ta Rike kunnuwanta Dake Cikin Farin Hijabin Dake jikinta Cikin wata irin Sanyin Murya tace"Am sorry..Sorry..! Tafada Idanuwanta na cika da kwallah Fuskarta yake bi da kallo yanayinta na Ratsashi cikin Dan kauda kai yace"Ashe kinsan kinyi Laifi ko..? Haka kika Raina ni ko..? Saboda kin ga ban taba kwallo Dake ba ko..? Da Sauri ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"To bana baka Hakuri ba..! Tafada Tana Turo bakinta gaba Sha"awa ta bashi ya Tsaya yana kallonta ji yayi kamar ya kama Bakinta yayi ta tsotsa Shawaran da zuciyarsa ke basa kenan ammh yayi Saurin kauda wannan Cikin dan Hade rai yace"Ni kike Turama baki..? Shagwaba ko...?shagwaban ki zai Dawo kuka yarinya..! Yafada kai Tsaye yana Tusa Duka Hannayensa Cikin Aljihun wandonsa yana More mata kallonta ji yake yana Cikin Farinciki gsshi ga Inteesar kamar bai taba jin kansa Cikin wannan Halin ba indai suna Tare sai yaji sa kamar yana yawo saman Gajimare saboda Farinciki. Jin Abunda yace yasa ta Rufe bakinta Tana yar Dariya kallonta kawai yake kamar ya kamata ya Rumgumeta haka yake jin wani yanayi yana Shigarsa Tuna abunda ke Cinsa araina neyasa ya Hade ransa kafin yace"Shine na Turo sako kika gani kika ki kulani ko..? Kuma na Kiraki baki Dauka ba Saboda kina chan kina Waya da wannan D'an iskan yaron ko..? Yafada yana bayyana Bacin Ransa Lokaci Daya yana kara Hade Girar sama data kasa Inteesar ta waro ido Lokaci Daya Tana Fadin"Yaushe..!? Hararanta yayi kafin yace"Ok nayi karya kenan ko..? Da Sauri tace"Ni ban ce ba..! Shima Cikin Saurin yace"U mean dat..! Inteesar ta marairai ce kafin tace"Allah ban gani ba Ya Imu da yaushe..? Nima ai ina ta kiraka baka Dauka ba nayi ta Tura maka sako Shiru na Damu har kuka nayi ta yi..! Tafada Cikin Damuwa Idanuwanta sun cika da kwallah Kasake yayi yana kallonta baya so yayi mgana baisan me zai ce mata ba yasa ya kalleta Cikin Idanuwanta kafin yace"Meyasa kikayi kuka..? kai Tsayen tace"Saboda kaki kulani ni kuma bansan Halin Dake ciki ba Shiyasa na Damu ina ta kuka..! Tsigar Jikinsa Sai da ta tashi Haka yarinyar ta Damu dashi bai sani ba Wayyo Allah shima Data san irin Wahalan Daya sha Saboda ita da batace haka ba. Kai ya Kauda kafin yace"Kada ki Sake kuka Saboda ni..kukan ki zai Hurting dina..! Kallonsa Takeyi kai Tsaye kamar yadda Shima yake Kallonta kamar an ce su Haddace kamannin juna. So yake yaji bada yaron nan take Waya ba yasa yace mata"Dawa kike ta waya Tun dazu..? Inteesar ta Dago wayarta Dake hsnnunta Kafin tace"Daddy ne fa ya Kirani muna ta mgana ya bama Umma mukayi ta mgana dani da Munari Har Umms tace na bama Mama sun Dade suna mgana ni ban ma san ka kira ba..! Tafada sai Lokacin data Bude wayar taga Misssed calls dinsa ido ta Zaro kafin yace"Ai kuwa gashi..Allah ban gani ba ya Imu ka yarda dani..,! Shi dai ya riga ya samu Salama Jin ba da shi take mgana ba Har sai da ya Sauke Numfashin Salama. Kallonsa Tayi lokaci Daya tana kallon Taban Data gani a kasa Cikin mamaki Tace"Miye wannan..? Tafada Tana nuna mai kasan yasan ko miye bai kallah ba ya Dauke kansa kafin yace"Meye..? Nima bansani ba..! Dariya ta kusa kama Inteesar har sai ta Murmusa Tana kallonsa Dakuna Fuska yayi kafin yace"Kina son Duka ne..? Dariyan nata sai da ta Fito da Sauri ta saka Gefen Hijabinta Tana Danne Dariyanta Hannunsa Daya ya Fito dashi Yana shafa kansa yana Mirmishi Cikin Dariyan kansa Inteesar ganin Fararan Hakoransa a waje ya Shagaltarta da ita tana ta kallonsa Tana auna irin kyan Imran He so nice. Ganin Taki Tsayawa da Dariyan ne yasa ya Tallabi kanta ahankali Cikin Nishadi yace"yarinyar nan kin Rainani ko..?kinga gadon barci na..! Yake Fada yana Kokarin Daidaita kansa. Kanta ta sosa tana yar Dariya kallonta yake Cikin Sha"awa kafin yace"Yana kiran ki..? Tsayawa tayi tana kallon cikin mamaki kafin tace"Waye shi din..? Yana Dakuna Fuska yace"Yaron nan mana..Wanda yace yana sonki..A Dukku..! Fara"arta ta Rage kafin tace"Yana kirana bana Dauka ko ya Turomin sako bana Dubawa..Tunda muka Dawo Daga Dukku yake Damuna..! Tafada cikin bayyana Jin Haushinta Ransa yayi fari jin bata kulasa Sai dai bai kamata ya sakankance ba Hannu ya mikamata yana Fadin"Muga lambarsa..! Batayi musu ba ta lalubo ta Daga Sama Saboda ya Kirata ma da Safe,Ta Haddaceta Duk da batayi Sarving ba Mikamai tayi ya karba wayar ya shiga ya Sakata Cikin Blook ya shiga bangaran Sakon nin yayi musu Delete all ya mikamata wayar yana Fadin"Ko kina son shi ne..? Karban Wayar ta tayi kafin tace"Ni bana son shi..! Tafada Tana Tura baki wani sanyi yaji acikin Ransa kafin ya kalleta yana Fadin"Gobe zamu tafi Lagos..! Ido ta sakarmai kafin tace"Lagos..?ku da suwa..? Imran yace"Ni da babanki da Abba da Ya Yusuf..,! Baki ta Washe kafin tace"Daddy zai zo nan..Eyeee..,! Tafada Tana bayyana Murnanta. Kallomta yake yi yana jin Farincikin ganinta haka cikin dan Hade rai yace"Kina Murna saboda zan tafi..! Bata rai tayi kafin tace"Ah"a nifa ina Murnan zan ga Daddy na ne ai kuma ba Dadewa zaku yi ba ko..? Kai ya gyada mata kafin yace"Jibi zamu dawo..,! Kai Tsaye yace"Chan zaka koma da aikin ka..? Yana kallomta yace"Wayace miki aiki zan koma..?Gidanmu dake chan zamu je mu gani..! Ajiyar Zuciya ta sauke kafin tace"Har naji Dadi..Bama so kayi nisa na Daina ganinka in ma zaka fara Aik plz Ya Imu ka yi shi anan garin kaji..! Kamar wani gaula haka ya gyada mata kai Dariya tayi kafin tace"Zamu dinga mgana ta waya in kun je ko..? Dauke kansa yayi kafin yace"A"ah..,! Bata rai tayi kafin tace"A"ah kuma..? Tafada Kamar Zatayi kuka Karo Farko Dataji Sautin Dariyansa yana Fadin"Shikenan zamu rika waya..Kada kimin kuka Shagwabbiya kawai..! Yafada yana kallonta da Dukkan Zuciyarta sai Lokacin ta saki Fuska Tana Buga Kafarta Tana Fadin"Kai Ya imu kaima zaka Biye ma Umma ne..Nice ma Shagwabbiyar..? Kallonta kawai yake yi bai yi mata mgana ba,Yanayinsa ne ke Sauyawa ganinta ahaka yasa ya kauda kai yana Fadin"Shiga gida..! Kai ta gyada mai kafin ta wuce Tana Waigensa,tana Dariya ta zata bai ga abunda tayi ba Sigarin nan Daya Wurgar ta saka kafa tatafi dashi Tana ja ya ganta yayi kamar bai ganta baa ya Kauda kai yana mirmishi Lokaci Daya yana shafa sumar kansa jinsa Cikin Farincikin da suka yi mai kaura Tun bayan Rasuwar su Anni sai da ya Hadu da Inteesar yake jinsa kamar ba shi ba. Koda ta shiga ciki Abba ne kadai afalo nan ta Zauna suka gaisa suka Shiga Hira anan ma shima ya gayamata zasu je kaduna gobezasu tafi Lagos tayi musi Fatan Sauka Lafiya da Dawowa Lafiya,kafin tatashi ta nufi kitchen inda Taji mganar Anty Safiya da Munari Tana Shigowa Munari ta Fara Dariya saboda ta ga Ya Inteesar din Zatayi ta Kalleta Tana Fadin"Allah yasa ba wani Laifi kikayi mai ba..? Ta fada Cikin Damuwa Inteear tace"Fada kawai yayimin..! Munari ta Kwashe da Dariya a Fili ta Furta su Fada manja Inteesar bata gane ba tana Dariya Anty Safiya ma bata gane komai ba sai itama Dariyan take ta Zata Shakiyancin Munari ne. Tare suka kama Girkin sai gabda mangriba suka gama kana suka shiga Domin yin wanka da Sallah. Bayan sun idar ne Inteesae tace Munari tatashi ta Rakata Gidan Mommy ta Dauko mganinta na Ciwom mara Data zo dashi Daga Gida Jin maranta ta dan Fara mata Ciwo kadan kadan,Munari ta sako Hijabi suka Fito a Falo suka bar Abba da Ya Yusuf shima sai da yayi musu Fadan Fita duhu ya Shiga Jin Mgani zasu Dauko yasa yace suyi sauri ko kuma su Tsaya wajen Maman su kwana. Sum sum suka Fice suna zuwa Haraban gidan zasu Fita suka kusa Cin karo da Imu ya dawo Daga masallaci ba Wutan Nepa sai dai Wata ta Raba gari Tar. Lokacin da suka Fahimci shine Sai da jikinsu ya Dau rawa kallonsu yake Cikin mamaki kafin yace"Ina zaku yanzu da Daddaran nan..? Yafada yana kallonsu Cikin Dakiyarsa Cikin In ina Munari tace"Gidan..Ma...ma zamu je..! Inteesar dai batayi mgana ba sai Morema kallonsa take yi yana Lura da ita sai dai bai bata Damar ma ta Fahimci ya ganta ba. Hade rai yayi kafin yace"Yanzu da Daddaran nan..? Yafada yana kara Duba agogon Fatan Dake daure a tsitsiyan Hannunsa. Kafin ya Cigaba da Fadin"Ammh baku da Hankali ko..? In akace ku Fita iyanzu sai ku fita..? Munari kanta na kasa tace"inteesar ce zata Dauko mganinta..! Tafada tana Zungurin Intee datayi mgana ita kuma taki cewa komai. Kallonta yake cikin Mamaki yace"Mgani bata da lafiya ne..? Da Sauri Munari ta gyadamai kai Inteesar din yake kallo ita kuma taki yarda su Hada ido cikin Dakiyarsa yace"Oya ku koma gida in dai kunsan ba Chan zaku kwanaa ba....! Munari tace"ai yau anan zamu kwana..! Cikin gajiya da mgana yace mata"to bazaku fita ba..Ku koma ke gayamin Inda mganin yake naje na amso miki..! Imteesar tq Fara Wiki wiki da ido kafin tace"Barshi ma gobe da safe sai muje na Dauko..! Tabe baki yayi kafin yace"Better..! Sum sum suka wuce yana Bin bayansu Har Falo ganin su haka yasa su Abba sukasan ya Korosu ne Dariya sukayi kawai su kuma suka wuce Daki suna Tura baki. Washegari Daddy bai samu Biyowa ta nan Kano ba,Saboda zai yi baya Ya yusuf da Abba da Imran suka Samesa a kaduna,Su Munari suna ta Barci koda suka tashi Tuni sun kusa isa kaduna Domin 6:30am suka Fita Suna Dawowa Sallar asuba Tunda Tafiyan Motace zasuyi Dukkansu sun Tsani hawa jirgi Tun Faruwar Lamarin Daya Faru. Da kwatace da komai sai ga Abba agidan Daddy farinciki kamar me Wajen Daddy ya kama Abba da su Yusuf ya Rumgume Umma kuma Tana ta ina ta saka dasu,Basheer ma yazo Dayake Har dashi Za"ayi Tafiya za"a Tafiyu iya Tafiya shiyasa Dole su nemi Wanda zai taimaka ma Yusuf da Driving Tunda Imu dai ya Dade bai Taka Mota ba. Sai da suka karya kana suka Mika Hanya,Wajen 10am na Safe Umma ta Bisu da Allah ya Kiyaye Hanya Yusuf ke Tuki Imram na Gidan gaba Basheer da Abba da Daddy na Gidan Baya sai da suka Tsaya suka cika Tankinsu da mai suka Dau Hanya Da guzurin Abinci su da kayan Snak a bayan Booth Wanda Umma tayi musu tunda Tafiyace ba kadan ba kila su da isa sai Cikin Dare ko da asuban Gobe. *Shakira* 3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�11* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Basu isa cikin garin Lagos ba sai Misalin 3:30am na Dare suka isa,Saboda Shigar Dare sukayi ga Gajiya yasa suka kama Hotel suka kwana suka warware gajiya sai da garin Allah ya waye bayan sun yi wanka sun yi breakfast kana suka Dauko Hanya zuwa Ainihin gidan su Imran wanda suka barsa Shekaru uku da wani abu. Abba da Yusuf Rauninsu yafi bayyana ammh banda Imran wanda ba wanda ya isa ya bayyana wani Hali yake ciki. Duk da sauye sauye ya karu a Birnin na Ikko basu manta kayattaciyar anguwan masu hannu da shunin da sukayi Rayuwa ba wato Victory inland ba. Gidansu na nan yadda suka Barshi Katon get garkame da katon kwado Sai dai saboda Dadewa get din duk yayi kura yana sun Rufe wajen alamun dai ma mallaka Gidan sun Dade basa rayuwa acikinsa. Ba wanda ma zai iya Tuna ina key din kwadon yake Lokacin da suka Rufe gidan suka Tafi suna cikin yanayin da ba baza su iya su iya gane komai ba. Sai da Yusuf ya shiga Cikin gari ya samo mai yanke kwado aka zo aka yanke shi aka Bude gidan suka Shiga Ciki. Allh Sarki Rayuwa Duk mai Imani Dole ya koka ma wannan Ahalin Gabadaya Haraban gidan ya Cika da Kura kyakyawan Marbels din Dake Shinfide a Haraban gidan ya cika da Ciyayi duk sun bushe Flowers duk sun bushe sun mutu murus Yana duk ya Lullube ko"ina ga Motocin su na Zamani guda Hudu reras,Na Abba dana Imran dana Nura sai na Yusuf gabadaya sun Lalace sun yi kasa Saboda ajiya Tayoyinsu sun Faffashe ba kyan gani sun yi kura Har sun gaji sun Fara Kokewa saboda Zama Waje Daya,Domin kana ganinsu Zaka Fara Tunanin da wahala su tashi Har su iya Moruwa koma sun Morin sai sun Dade a gareji suna cin uban kudi. Kuka Abba keyi Reras sanda suka Shiga Ainihin Falon gidan ba Kurar Daya bata gidan bane Damuwar ba yana Tuna each and Single Moment da suka gudanar acikin wannan kayattacen Gidan shi da iyalansa da Matarsa sai gashi komai ya Zama Tarihi. Abubuwa Dadama agidan nan sun Lalace kama Daga kayan kallo Frigde da Sauransu kujeru ne sai gadaje basu yi komai ba ammh duk wani kayan Wuta ya gama aiki gidan yayi kura yana Duk ya Rufe ko"ina sai da Basheer da Yusuf suka rika saka Sanda suna Cire inda Zasu Taka. Wasu Kofofin Dakunan ma Sun ki Budewa sun kame sai an kira masu Cire Kofa Imran ya shiga Dakinsa yana Kallon kowani kusuwar Ya Duba Cikin Wardrope dinsa da Gabadaya kura suka mamaye ka'ina kyawawan Suit dinsa na kamfanoni Dabam Dabam da ke shake Cikin Wardrope din Duk sun gama sauya kala Kama Daga Takalmansa na Kowani kamfani masu Tsada da yarari duk sun sauya kamanni da Dadewa da kura komai nashi acikin Perfect ne Lokacin yana amsa sunansa Banker Imran Abubakar malami ba yanzu da komai ya sauya ba shi kanshi yaji Tahowar kwalla yayi saurin kauda kai bai bari Hawayen ya Zubo ba yasa Hannu ya Dauke kwallarsa. Haka bangaransu Yusuf da Abba Suna Bin ko"ina da kallo suna Hawaye Daddy da Basheer suna ta basu baki,Basu iya ko zama ba saboda ba Wajen zama suna dai Tsaye suna Zagaya Ko"ina na Gidan suna kallo Suna Tunawa da Rayuwar baya. Daddy ya fara kawo shawaran bazasu Tafi su bar gidan nan hakan nan ba Zai kara Lalacewa Tunda ba su da Sha"waar kara Rayuwa aciki sai dashi Abba yace bazai Taba saida wannan Gidan ba Har Abada Ko ya Mutu ga Yusuf ga Imran ga Munari gidane mai Dimbin Tarihi zai barsa Kila ko watan Watarana Su rika zuwa Hutu ko kuma Yanayin Rayuwa zai iya maido da Daya Daga Cikin su Imran nan garin Tunda suna da Muhallin Abubuwan bazasu yi wahala ba Kowa yayi na"am da mganar Abba ammh sai aka Fara Tunanin yadda za"ayi Daddy yace Dole kafin su koma a samu wadanda zasu Zauna agidan nan da sunan gadi su kuma Rika gyarashi suna kula Dashi Domin barinsa ahaka shine Jidali. Suna cikin Hakane sukaji Sallama Daga Kofar Falon gabadayansu sun ji mamaki Abba ne da Daddy suka Fita Haraban Gidan Ikon Allah Abba kawai ke Fadi na ganin Abokinsa Amininsa Dr.Isa Ali Argungun Abokin aikinsa ne shima Lecture ne a nan Lagos Universty,Sai dai shi yana Shashen Kimiya da Fasaha ne Wato Computer Science sannan kuma Makota suke da juna Domin gidansa da Gidansu Gida Dayane Tsakani sun yi Zaman Amana sosai da Amintaka Duk garin Lagos Abba bai da aboki kamar Dr Ali argungu Matarsa Hajiya Barira Kawar Anni ce Lokacin tana Raye,Sannan karamin Dansa Ibrahim Khalil,ma"ikacin Banki ne shima Tun alokacin da shi kadai Imran ke gaisawa Sama sama abota dai wacce bata Zama Takura ba yayinda shi Khalil ke aiki da Firstbank nan Reshen Jahar Lagos shi kuma Imran yana aiki da GT bank suna Haduwa Lokaci bayan Lokaci in Bankunansu ta Tura su wata Seminar Tunda dukkansu Zakwakurai ne abangaran da suka karanta ma"aikatan su na matukar ji dasu,yanzu ma Tare da Khalil suka shigo Abba suka Rumgume juna da Dr.Ali Argungun suna masu Hawayen Farincikin ganin juna jin shuru ne yasa su Yusuf suma suka Fito Haraban gidan nan suma suka ga Abun mamaki nan fa aka Shiga gaisawa Cikin Tambayan juna bayan Saduwa Dr.Ali argungun yaja su zuwa Gidansa Tunda nan yayi kura ba wajen Zama basu yi gaddama ba Sanin sa ai shakiki ne ga Abba ko su Daddy sun san Tunda Lokacin Rasuwar su Anni Har Dukku ya Taka Daga baya daya samu Labari shi da Iyalansa. Alokacin da Abun ya Faru bai sani ba Har Suka zo suka tafi da Abba chan Dukku sai daga baya yaji Labari kuma garin Dukku ba boyayye bane sannan Gidan Marigayi Alkali Dukku ma haka da Tambaya da komai suka isa Dukku Lokacin Abba yana Halin Rashin Lafiya baya gane komai sai sambatu Dr.Ali argungu ya Dawo da Tsausayin Abokinsa matuka acikin Ransa kuma yasha zuwa Dubasa Har Dukku kusan Sau Uku Daga baya da suka Dawo Lagos kuma basu Dade ba aka nemesu aka Rasa ya Zata sun kara komawa Dukku ne sai da yaji Shiru ba waya ba komai Achan Jami"a ma ba wani Labari yasa yaje Dukku da kansa nan ya iske Labari mara Dadi an nemi Dr.Abubakar malami ko sama ko kasa Shi da Sauran yaransa ba'a gansu ba Lokacin ya gana Daada Tana ta kuka Tana Bayyanamai Damuwarta ya Dawo Lagos shima da Damuwar Abun kuma shima yayi ta Bincikensa ba wani Labari sai dai ba Cire rai ba Suna da Lambar juna shi da Daddy yana Kiransa Lokaci bayan Lokaci yaji ko an ji Labarin Malami sai dai Shuru ne,Shima Daddy yakan kirasa yaji ko da wani Labari Lokacin da Abba ya Dawo Wasu abubuwan sun Doke wasu Shiyasa bai samu Damar Sanar da Abba komai ba. Dr.Is Ali Argungun Koda yaushe zai shiga gida ko zai Fita sai ya kalli get din gidan nan ko zai ga an Budesa Shekaru uku da wani abu bai Taba ganinsa a Bude ba sai yau daya Dawo Daga Wajen aiki yaga Gida a Bude mamaki ya kamasa haka ya Shiga Cikin Gida yana Fadama Hajiya Barira Ita ma tayi mamaki suna cikin mganar ne sai ga Khalil ya shigo shima Dai zencen yake musu shine Dai Hajiya Barira tace su leka su gani ko yan"uwanshi Daga Dukku ne kila zasu samu wani labarin suna zuwa kuma sai suga Abba sai Sabon Labari ya tashi anan Falon gidan Dr.Isa Ali Argungun Abba nata bashi Labaran bayan Rabuwa shima yana gayamai Faculty dinsu tayi rashinsa Wlh kuma yana mai Tabbatarmai ko yau ya koma Zai koma da aiki Jami"ar Lagos bazata yi sakacin rasa Zakwakurin Malami kamarsa ba,Nan sukayi Lunch Cikin Farincikin kara Saduwa da juna Hajiya Barira ta Fito suka gaisa Jin cewa su Abba kano suka koma da Zama yasa Dr.Isa Ali argungun yace ma Abba ai kano gida ce Hajiya Barira yar Fagge ce dake kano ne suna zuwa kano Sosai Rashin Sani sun gaisa ta karamai gaisuwan su Anni ya Amsamata Cikin Jin Dadin karamincinsu yana ta godiya. Hajiya barira bata da wani D"a gabanta sai Khalil shi kadai ne bai yi auree ba kuma shi kadai ne Namiji Sauran duk matane suna gidajen Auransu,Shiyasa Gidan Daga ita sai yan aikinta da Mijinta da Danta Khalil. Sai da suka yi Sallar Azahar anan cikin Gidan Yusuf yayi musu Limanci,bayan sun idar ne kuma suka kara Tsinkewa da Hira Khalil ma da Imran Cikin Ikon Allah suna ta mgana kan abunda yashafi aikinsu Yusuf da Basheer suna ta mamaki duk da Daga Khalil din Har yusuf din Daya ne bama su son Hayaniya bane da yawan mgana ba. Daddy shi yayi ma Dr.Isa Ali Argungu mgana kan wanda za"a Samu ya rika gadin gidan Abba,Dr.Isa Ali argungu yace Faduwa tazo Daidai da Zama Megadinsa Buba Dan BAuchi ne Bahaushe ne nan suke Xaune dashi Shi da iyalansa suna BQauters,Daman kaninsa yazo kwanakin nan Wajensa yake yana ta neman Aikin gadi bai samu ba in hakane sai ya koma Gida ya Dauko iyalansa su zauna a BQuatre suna Kula da gidan Allah barshi Duk wata sai arika Biyansa Abunda ya Sauwaka Duk da yaso Abba ya baro Kano ya Dawo Lagos kamar baya su Cigaba da aiki Tare Abba ya nuna a"a Shi Zaman Lagos ta Fitarmai arai kwata kwata bai mtsamai ba Tunda Daddy yace A Buk kano zasu neman ma Abba aikin su gani ko Za"a Dace Tunda Lokacin aikinsa bai Wuce ba.. Ba bata Lokaci akayi ma Buba Megadi mgana Shida kaninsa Lurwanu sun ji Dadi Matuka Abba yace yaje ya Dauko iyalansa su zauna agidan su Rike Amana su kula da gidan sannan Yusuf ya Dau alkawarin Biyansa Kudi mai Tsoka Duk wata wannan abun yayi Musu Dadi suna ta Godiya. Aranar basai da aka kwana ba aka Fitar da komai na Gidan Daya Lalace aka Zubar Motocin kuma aka Saida su aka Karbi kudadensu kalilan ba masu yawa ba Aranar basu koma Hotel ba agidan Dr.Isa Argungu suka kwana Washegari da Safe Lurwanu ya dau Hanyar gida zai je ya Dauko Iyalansa Kudin Motan da komai Dr.Isa Argungun ya basa,Yana Tafiya shida Abba da Daddy da Ya Yusuf da Basherr suka tafi Jami"ar Lagos inda Abba yayi aiki Shekaru ashirin abaya Abba yaga Tarin Sauye sauye yaga wadansu wanda sukayi aiki Tare Lokacin wasu kuma sun bar Wajen wasu kuma sun Rasu,Shugaban Jami"ar da kansa ya Nemi Abba ya dawo ya Cigaba da aiki da inda ya Kwarewa Ammh ya nuna ya Gode bai kara Sha"awar Zama a Lagos,Basu damu ba sun mai Fatan Alheri sanin duk inda yaje Takardunsa da kwarewarsa sun isa yasa a kowata jami"a ta Daukesa ma Bama Buk ba. Koda suka Dawo gida Imran da Khalil basa Gida kuma basu gayama kowa Zasu Fita ba,ba wanda ya Damu Sanin kila sun Fita Zaga gari ne. Ashe abun ba haka bane Bankin da Imran yayi aiki Khalil ya Daukesa yakaisa Kafin ma Imran ya yarda Zai shiga sai da aka kai Ruwa Rana da Lallashi da ban baki Khalil ya nuna mai Hakan nada Muhimmanci sosai. Tare suka shiga Har Ciki shima din yaga Tarin Sauye Sauye a wajen yaga wadanda sukayi aiki tare wasu kuma da yawa an sauya su wasu kuma Rai yayi Halinsa,wadanda suka sansa sai Turruwa suke wajen gaisawa dashi To alokacin Waye baisan Imran Abubakar malami ba kan kwarewa a aikinsa da Miskilancinsa iya Daukan wanka bama aiki Muhimmaci gabadaya Dokokin bankin shi nashi Dokar ma ya Take nasu shiyasa ba Ma"ikacin da Manaja ke ji dashi Alokacin Irinsa Saboda yadda ya maida kansa kamar wani bawa gwannati na amfana da Tarin baiwarsa da lafiyarsa. Manajan Wajen ba"a Sauyashi ba wani Bayarbe ne Mr Tunde Abdulwasi yana ganin Imran sai da yayi wani ihu ya Rumgumesa Tsakani ga Allah sun yi Rashin Zakaran ma"aikaci kamar sa haka yake ta Fadama Imran da Khalil sun nemesa har sun gaji sun Nemi Wayarsa shuru sun ta Turamai Sako ta Email dinsa ma Shuru shi ko Imran yama manta yana da wani Email Tin bayan Faruwar abunda ya Faru ya Daina Mu"amala da Duk Abunda ya Shafi Socoal media ya koma Rayuwarsa yadda yake yanzu sai dai ammh yana ji ajikinsa kila Lokacin da Wannan Imran din zai sauya ne zai Dawo ainihin Imran Abubakar Malami A Banker,Manaja yamai Tayin Dawowa aiki kan Mstaayin da yafi na Baya Imran ya nuna mai A"a Baya Bukata Duk mganar da suke yi Cikin Rantsantsan Turacin kasar Amurka ne in kaga bakin Imran yadda yake Tsara mgana Cikin Harshen Turanci sai mamaki ya kusa sumar dakai ka Fara Tunanin Anya wannan Imran din ne mai Shan Taba..? Khalil ne yayi ma Manaja Tunde Abdulwasi bayanin a takaice na Komawarsu Imran kano da Rasuwar Mahaifiyarsu da yan"uwansu bai ji Dadi ba ya Tsausaya musu,Ya kuma Dage Imran sai fa ya Dawo aiki ko ba anan Lagos ba zai yi waya da Manajansu na Gtbank din su Dake Reshen kano,zai Turamai Duka Bayanan Imran da Takardunsa ta Email Zasu kirashi da Zarar ya koma Zai Cigaba da aiki kamar baya bazai Taba barin wanda aikinsa ke da Mutumci Fiye da komai a idonsa ya Zauna haka ba ballatana tun abaya suna da kyakyawan alaqa da Imran din Hallayarsa na Burgesa rashin Shiga Mutane,baya da shiShishig baya Shiga Harkan kowa baya Hulda da mata sai yazo aiki ya Wuni har yammah ya tafi bai tanka ma kowa ba sai ya Zama Dole aiki ya Hadaku Mutane da yawa acikin bankin suna jin Haushinsa sai dai basu da yarda zasu yi dashi,Ko ya sani bai Damu ba Tunda bai isa yaasa su so ra"ayinsa ba Shidin Kaifi Daya ne. Bashi da yarda zai yi ya karbi mganar sukayi Sharing din Lambar juna shida Manaja Tunde Abdulwasi,kuma bazai iya Turo Alfarma Khalil ba yana nuna Kulawa akansa.Daganan bakin Ruwa suka je suka dan Huta duk da ba wata Hira suke ba ammh yanayin yayi ma Imran Dadi yana gefe yana kallon Khalil Dake waya yana wani Narke Murya Kila da Budurwansa yake mgana Tsakani ga Allah Tsausayi ya bashi Namiji har Namiji ya Zauna Mace na Juyashi har yana neman mata kuka Duk da abaya yasan Khalil din kamar shine yana da Miskilanci Ammh jisa ya zauna yana wani marairacewa kamar zai yi kuka karamin Tsaki yaja yana kallon Daidaikun Mutanen Dake wucewa Idanuwansa yakai inda yaga wasu Beatifull Couple Duk da bai sani ba Zuciyarsa ta basa Ma"aurata ne,suna Rike da hannun juna suna Tafe Cikin Soyayya da kauna yana kallonsu yana jin wani yanayi kansu kawai yake Hangowa shi da Inteesar Tuna ta yayi sai da yaji wani Sanyi a fili ya Furta"Shababbiyar yarinya..Na kawota nan ai shagwabarta zata yi tamin..! Yafada yana jin wani Annuri na Shigarsa Wayarsa ya Dauko ya Tura mata sakon "Kin manta dani ko..? Alhalin fa ko jiya ta Kirashi sun yi da Daddare data kirassa yaki Dauka Saboda suna Tare da Khalil sai da ya Turamata sakon. "Oya ki kwanta ki barci..Bana son Damu..! Shine ne wai yau ta manta dashi so yake yajata da Zence. Bata kai ga Turomai amsa ba Kiran Sagir ya shigomai ya Dauka suna mgana yana Tambayansa yaushe Zasu dawo yace bai sani ba,basu wani dade suna mgana ba ya katse kiran Saboda Hankalinsa baya kansa yana Wajen Inteeaar ne. Illah kuwa yaga Sakonta Cikin Shagwabarta Duk da baya ganinta tace. "Laaaa...Kai ya Imu nice ma na manta Dakai kai da kaje Lagos ka manta Dani kaga yanmatan Birni..Au koda yake ai kana da Matar Abuja Sajida.." Sai da ma yaga Sakonta ya Tuna da Wata Sajida Tsaki yaja jin tama batamai Mood dinsa Raini yagani Kirkiri Tsaakaninsa da Inteesar Wato Shine ma ya samu yanmata ko..?kiranta yayi kai tsaye tana Dauka ya Fara Fadin"Kin raina ni ko..?Wato nine ma na samu yanmata ko..?Ni sa"anki ne Intee..? Yafada Cikin wani Salon daya gama Kashe mata Jiki Gabadaya sai ta Fara mganarta Cikin Shagwaba Tana kanunun kuka Maimakon ya Dakamata Tsaawa yace ta Daina sai ya kasa ya samu kansa da jin Dadin Duk Abunda tayimai shi kanshi baisan Yaushe ba yadai samu kansa yana Biye ma Duk wata Tabaranta Wai kukan Shagwaba take yi basu dawo ba alhalin yace mata kwana Daya Zasu yi sai ga Imran yana mata Rantsuwan Wlh ba Laifinsa bane Daga su Daddy ne. Soyayya mai sauya Mutum ta Sauya Imran bai sani ba ko aikin Daya amince zai koma Saboda Inteesar ne,yasan Zataji Dadi sosai,Kamar ya gayamata sai ya fasa yafi so ya bata Mamaki ne suna cikin Wayar Khalil ya zo Inda yake yana ganin haka ya katse kiran,Sai gashi ta kara Kira Bai Dauka ba sai da ta katse ya Tura mata Sakon "Kije kiyi karatu...We tok Later bana Gida ne.." Haka ya Rubuta kafin yabi Khalil wani dan Cafe inda suka Siya Coffea da lemu Anan Imran ya siya Sigari Khalil yaji mamakin ganin Imran na shan Sigari har sai da ya Furtamai Bai ce komai ba amsa Daya ya basa da cewa Life kenan. Imran yasha Sigarinsa sosai,Saboda Tunda sukazo bai shafa ba,Har da Guzurinta yayi Khalil sai mamaki yake da Tsausayin Domin ya Tabbata Rayuwace ta maidasa haka abaya ko Kusa da ita baya zuwa. Da suka koma gida basu ma Kowa bayanin inda sukaje ba Suma ba wanda ya Tambaeyesu.. Sai gashi bakin da zasu yi kwana daya sai gashi sai da suka kwana Hudu Tunda sai da suka jira Lurwanu ya Dawo da Iyalansa,Matan sa Biyu da yaya Bakwai irin auran Wuri ne ayi ta Tara ya"ya suka shige BQuaters Matar Buba da ya"yansu suka Tayasu gyara Komai har Cikin Gidan ma suka share suka Goge suka gyara kayan wasa kuma nasu Imran dasu Anni duk afito dasu wadanda bazasu Mori ba aka Zubar masu kyan suka Dauka sauran kuma zasu Sadakar dsshi ga Mabukata ana Gobe zasu tafi acikin Gidan suka kwana Saboda an gyara komai,Daga Gidan Dr.Isa Ali Argungun ake kawo musu Abinci Washegari Tun Safe suka Dauki Hanya bayan Abba da Dr Isa sun karbi Lambar juna haka ma Khalil da Imran sun Rabu kan in an nemesa zai gayamsa Insha Allahu. Sai Cikin Dare suka iso kaduna anan suka kara kwana Sai Ranar Alhamis suka Dawo Kano,abun da ya bama Abba Da Daddy mamaki Har sukayi wannan Tafiyar Baffa Kabiru bai kira yaji Ya akayi ba sai dai sune suka Kirasa Daada kuwa Hankalinta kwance Koda yaushe Tana Waya da Malami Jininta ya Daina Hawa sai Dai ma yana ta kara Sauka ne. Abba ya wakilta Yusuf ya Turama Daddy duka CV sa na Takardunsa Shi kuma ya Tuttura ma abokansa na nan Jami"ar Buk suka kuma Tabbatar da za"a dace Daman ana neman Wadanda suka kware kan Abubda Malamin ya karanta ya jira Lokaci kawai za"a kirasa. Intee tafi kowa Murnan Dawowarsu daman Rashin ganin Imu duk ya Ramar da ita da kuma Gidan ba Dadi basu Abba Mama bata nan Taje Kaduna Bayan Tafiyan su Daddy Lagos jikin Inno ya Motsa sai sukayi mgana da Umma Maman ta Shirya tatafi Wajen kwananta uku kenan Daman Tun kafin tatafi suka dawo nan Gabadaya Saboda Taya Anty Safiya Zama. Har ya dawo basu Hadu sunyi dogowar mgana ba sai dai sukan Hadu su kalli juna tayi mai Dariya shi kuma ya Hde rai ya Harareta,Sun Dawo Alhamis Ranar asabar da Daddare bayan sun gama Dinner gabadayansu Imran daman ba Zaman Dinner yake yi ba Tea kadai yasha sai gashi ya Fito Daga Daki ya Duka gaban Abba yana Fadamai Gobe yana so yaje Dukku. Sun ji mamakinsa sosai Abba cikin mamaki ya kallesa yana Fadin"Dukku..?. Kai ya gyada batare da yayi mgana ba Ya Yusuf dake Zaune gefen Abba ya kada kai yana Fadin"Dukku..? kodai Abuja mallam gayamana gaskiya..Kana son ganin Sajida ka Fake da Dukku..,,! Kamar ya watsamai Ruwan Zafi haka yaji kallon Ya Yusuf yake yana auna in ba Domin shi bane wlh sai ya Duramai Ashariya Saboda Haushin mganarsa. Inteesar ya kallah Dake gefen Munari da Anty Safiya itama kallonsa take Gabadaya Sai taji Ranta ya baci da aka ambaci Sajida kenan da gaske wajenta Zai je. Kauda kansa yayi bai ce komai ba Abba na Dariya yace"Ai kamar tana makaranta bata dawo ba..Barsa kila ganin Kakarsa ne ya tasomai in yaje ya Dawo sai ya shirya yaje yaga matar tashi Lokacin ta dawo gida Tunda Ya Kabirun yace min suna Test ne..! Har Abba ya gama mgana bai Dago ba. Abba ya kallesa yana Nazarinsa kafin yace"Kwana zakayi in ka tafi goben..? Dakyar yace"In Dare yayimin sai jibi zan Dawo..! Abba ya kada kai yana Fadin"Allah ya kaika Lafiya Daada nada manyan Baki..! Imran yaji Dadi da Abba bai kara Cewa komai ba ballatana ya Tambayessa me zai je yi wajen Daada yana Haararan Yusuf Dake Dariya ya Shige Dakinsa da Haushin Inteesar ta Kauda kai taki yarda su hada ido wai itana nan taji Haushi ne ko..? Karamin Tsaki yaja yana jin Takaichi ya Riga yagama Shirinsa gobe sai Dukku waya ya Dauka ya Turama Intee Sako. "Yayi miki kyau Tunda nine kike Turama baki kina kauda kai baki san ganina..! Ba Dadewa ta bashi amsa da Cewa "Eh din..Gobe zakaje kaga Amaryanka ina Ruwanka dani..! Sai da ya waro ido Daya ga mganarta Dariya ta kamsa Yarinyar nan ta gama Rainasa cikin gatse yace mta "Kamar kin sami ta Abuja zan sauka ko kina da sako wajen Amaryan tawa..? Ya tura mata Sakon yana ta Dariya Har yana jin Sautinta yasan ya gama Kunno yar shagwaban kamar ya sani Dataga sakonsa sai da Zuciyarta ta Buga Saboda Takaichi da Kishi Cikin Tura Haushi ta Turamai. "Ka gaisheta..Ango mijin Amarya..In kaga Nawa Mijin ka isar mai da Sakon i Miss Him Khamis Kabir Dukku nake nufi.." Ai sai nata yafi Zafi Daya sakon nan kamar yayi Bindiga kiranta yayi taki Dauka sai yaji kamar Zuciyarsa Zata Fito Saboda Kishi Wai Mijinta..? Lalle nema to ba sai ya zama mijin nata ya gani ba haka yake ta Fada yana Sakin Tsaki. Itama chan bangaranta haka tayi ta jan Tsaki tana kunkuni ita kadai Daga Karshe ma barin Falon Tayi,Ta shige Ba wanda ya Lura da yanayinta sai Munari ga Dariya ga Tsausayi.. Tana shiga Daki Ta Fada kan gadi ta saka kuka ranta na kuna Afili ta Furta"To ni ina ruwana ya ma je su Tare tare achan babu Abunda ya Dameni..! Take Fada Cikin tura Haushi Lokaci Daya ga Hawaye Munari shigowarta kenan taji Abunda Intee ke fada Ssi ta bata Tsausayi bata nuna mata taji ba ta Basar ammh Tana Lura da ita bata wani samu barci ba Bini bini ta juya ta saki Tsaki shi kanshi Imran din Rabi da Rabi ne barcin nasa kowa ya kwana da Takaicin kowa. *Shakira* 3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�12* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Da garin Allah ya waye saboda ita da Safe yazo ya Tsaya a Haraban gidan Saboda yasan suna da makaranta yau da safe so yake ya ganta kafin ya tafi. Sai dai duk yadda yaso Inteesar da suka Fito ya yusuf zai kai su kafin ya wuce wajen aiki bata yarda ta Hada ido dashi ba,Duk yadda yayi kokarin haka yaga Idanuwanta sun tasa alamun Tasha kuka jiya da Dadaddre.. Munari ce kadai ta gaisheshi Inteesar kuwa Mota ta shige Fuskarta ba Fara"a ko kadan ta maida ma kanta wani gefe Ran Imu ya sosu yaji ba Dadi yau shine Intee bata son ganin Fuskarsa abun is so painfull acikin Ransa. Ya yusuf ne Daya fito ya gansa Tsaye Jikin Mashin dinsa ya Hade Hannuwansa Saman Kirjinsa kamar ko yaushe Kallonsa yayi yana Fadin"Yaushe zaka wuce ne..? Kai Tsaye Imran yace"Yanzu..! Yafada Kan Sa tsaye Kuma Duka Kallonsa naga Inteesar wacce ta maida kanta gefe batama yarda ta Dago ba ballatana su hada ido ba duk da ta Lura ita yake kallo kuma jikinta ya bata Wadandan Kafaffun Idanuwansa suna kanta ne. Ya yusuf yayi sakake yana kallonsa Kafin yace"Yanzu..?kuma kake Tsaye anan ba wani Shirin Tafiya..? Imran gajiya ma yayi da mganar Yusuf ya barsa yaji da abunda ke gabansa mana bai ce mai komai ba ya Taka zuwa Cikin Falon ko waige Yusuf ya Bisa da kallo kafin ya Tabe bakinsa sai alokacin Inteesar tabi bayansa da kallo Cikin Samun Sukuni da Salamar Dake Tattare da ganinsa din Munari na Gefenta Tana Lura da Komai acikin Ranta tace Allah Sarki Soyayyah.. Yusuf shima Shigowa Motar yayi ya Kunnata yayi Riverse suka Fice Daga Haraban gidan. Suna Tafiya ba Dadewa Imran ya Fito Cikin Shirin Tafiya yayi shigar Riga da Wando Rigar Fara ce mai Dogon Hannu Tana da Layin Baki ajikinta Sai Wandon Jikinsa baki ya kamasa daga kasa Kadan kafarsa sanye Cikin Bakin Takalmi Sawu Ciki na Fatar Damisa,Ahannunsa na Hagu sanye da bakin agogon Fata na Kamfanin Rado Kan nashi yasha gyara,Bayansa ya Rataye da Jakarsa baka ta baya kamar ta yan makaranta Bawani Kure adaka yayi ba ammh ko sau Daya ka kallesa sai ka kara kallonsa Cikar Zatinsa baiwa ce Daga Allah kwarjinsa da Kyansa kuma Hallitace ta Ubangiji Duk Takamar mace da Kudinta da Iliminta in Imran ya Tsaya a gabanta ya Kalleta ido Cikin ido sai taji ta Raina kanta da Duk Abunda ta mallaka Maza kuma yan"uwansa Dole in suka kallesa sai sun kara kallansa sun kuma Tabbatar ma kansu Babban Goro sai magogin karfe. Ko afitowar da yayi Abba Dake kan Dining yana karyawa Sai da ya Dago ya kallesa acikin ransa yana Kirari ga Allah mai gagara Misali da ya Hallici Imran a yadda yake,Safiya ma Dake Zaune afalo bayan ta Rako Yusuf ne ta Jabe anan tana Hutawa ta kasa karisawa Shashenta Cikinta har ya Fito Domin ya Shiga watansa na Biyar,Itama Dake Zaune sai da ta kallesa ta kuma Jinjina Kwarjinsa Ya gaisheta ta amsa mai Cikin Sakin Fuska yana gaisheta Wani Lokacin In suka Hadu Gab da gab ammh fa baya Binta ya gaisheta in sun hadu shima din yana Cikin Mood mai Dadi in Ransa na bace kuwa baya bi ma ta kan kowa. Wajen Abba ya karisa ya dan Rankwafa ya gaisheshi Abba ya amsa Cikin Sakin Fuska yana Fadin'Bakon Daada..badai har an fito ba..? Imran na Shafa keyarsa yace"Na fito Abba..! Abba yace"To haka zaka tafi baka ci komai ba..? Imran ya Girgiza kansa yana Fadin"A"a Abba bana cin wani abu in zan yi doguwar Tafiya..! Abba ya jinjina kai kafin ya kallesa yana Fadin"To kana da kudi a Hannunka ne..,? Imran yadan yi Mirmishi kafin yace"Kada ka damu Abba..! Abba yace"Dole na Damu mana..Zaka gane gidan kuwa..?kadai kula da kanka kaji ko in baka gane ba ka kirani! Imran da ya Murmusa sai da kyakyawan Fararan Hakoransa suka Bayyana ya Mike yana Fadin"Abba am not a Boy fa..?Nasan abunda nake yi..Zan kiraka da Zarar na isa Dukku ku gaisa da Daada..! Abba yace"Shikenan Allah ya kaika Lafiya Daman mun yi mgana da ita da Safe bam ma gayamata zaka zo ba..Nasan Zataji Dadin ganinka..! Kai Imran ya Kada bai yi mgana ba suka kara yin Sallama da Abba ya Fice bayan ya Fadaamai Sagir zai kaisa Tasha da mashin dinsa Zai bar mai Mashin din a wajensa har ya Dawo Abba yace hakan yayi nan ya fice Abba da Safiya suka bisa da Faten isa Lafiya. Yana Fitowa ya Hau mashinsa ya Fice Daga Gidan Iro megadi ya bisa da Allah ya Kiyaye Daman sunyi Waya da Sagir Tun jiya da Daddare,kuma da Safan nan sun yi mgana yana Kofar gida yana Jiransa,yana zuwa Sagir ya Karbi Tukin Mashin din Imran ya Dawo baya ya zauna suka tafi Tasha koda da sukaje Motar Gombe suka Tarar ta kusa cika Sai Imran yace bari ya Hauta in yaje Gombe sai ya Hau Mota ta karisa dashi Dukku. Akwai kudi a Hannunsa Sauran kudinsa Bankinsa ya Ciresu Saboda Tafiyar nan,20k ya Cire ya bar 10k agida Saboda akwai abunda zai yi dasu in ya dawo 10k ya Sako a Aljihu Saboda Tafiyar nan Kafin Motan ta karisa cika suka Tsaya nan Gaban Motan suna Mgana Sagir ya kallesa yana Fadin"To ita Inteesar din tasan zaka tafi Dukku Saboda ita..? Imran ya bata rai Cikin bayyanar Bacin Ransa yana Fadin"Ita Datake Fushi Dani..!. Sagir ya kallesa cikin Mamaki kafin yace"Fushi to me kayi mata..? Imran ya mele baki ya fara bama Sagir Labarin abunda ya Faru ya Karishe da Fadin"Kaji fa wai yarinyar nan ni zata Rubuto ma wai khamis Mijinta..?ni fa ta rainani yarinyar nan Naji dama sanda take fadin haka tana kusa dani na Daki bakinta sai yayi Jini nan gaba zatasan me zata rika gayamin Tunda ni ba sa"an wasanta bane..! Yafada Cikin bayyana jin Haushinsa Sagir kuwa Dariya ta kamashi Har da Dukawa Imran ya Bisa da kallon Takaichi yana fadin"Kai fa Banza ne..! Sagir ya Dago Daga Dariyan Dayake yi yana Fadin"Ban ga Laifinta bafa..wayace kace Sajida Amaryarka..? Ashe ba Dade ai kuma ta baka amsarka Daidai da mganarka..Wow..wannan Salom Soyayyar taku ta fara Burgeni kuna son juna ammh Dukkan ku baku sani ba,Inteesar Tana sonka Shiyasa take Kishin Sajida kamar yadda kake Kishin Khamis..! Yafada yana kara Sakin Dariya kallonsa Imran yake Cikin Nazarin mganarsa Cikin mamaki yace"Itama Tana Sona..? Sagir ya gyada kai yana Fadin"Am Very Sure..Itama Tana sonka kamar yadda kake sonta..! Shuru Imran yayi bai yi mgana ba yana Jujjya mganar Sagir Cikin Dakuna Fuska yace"Ni ai ba sonta nake yi ba! Sagir ya kallesa yana Dariya yace"Allah ko..? Imran ya Hararesa yana Fadin"Kai wai a ina kasan Soyayya ma haka Daka ke fadin cewa ina sonta tana sona da karfin Gwiwanka ko ka taba Soyayya ne ban sani ba.,? Sagir yace"Ni ba irin ka bace..ina shiga Social media ina Hulda da abokai ina Karance karance nasan abubuwa da yawa kan soyayyah ammh ni ban Taba soyayyah ba sai dai irin na yarinta..! Imran ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Shirme kenan..Ni ko na yarinta ma ban yi ba..! Sagir zai yi mgana kenan akace Mota ta Cika a Hado kudin Mota Dole ya Dakata Imran ya bada Kudim Mota ya Shiga Gidan gaba Key din mashin din Daman yana Hannun Sagir nan yace ma ya riketa a wajensa Har ya Dawo Sagir bai bar tashan ba,Sai da Motar su Imran tatashi Kana ya bar Wajen Cikin kewar Imran din. Sai da suka Dauki Hanya kana ya Lalubo Wayarsa ya Danna ma Inteesar Kira ammh bata Dauka ba Koda baya son nuna Damuwarsa Dole Damuwar ta bayyana Sako ya Tura mata. "Zan yi doguwar Tafiya ba Allah ya Kiyaye Hanya..? Haka ya Tura mata bai saka Ran Zata bshi amsa ba san sai ga Sakonta daman Lokacin Daya Kira suna Lecture ne. "Allah ya kiyaye Hanya..' Daga haka bata kara ba,Sai da ya Murmusa daya ga Sakonta ganinsa kawai yayi yana Rubuta mata. "I miss u....! Ya tura mata bai kuma damu daman Data bashi amsa ba kamar yadda itama Data gani kamar yana gabanta ta Turamai baki tana fadin"Ba wani nam..Kai da zakaje wajen Wata..! Ranta kuna yake in ta tuna haka sai dai bata isa ta kankare kalmar Sajida matar Imran bane. Tunda suka Fara Tafiyar har suka kai bai yi mgana da kowa ba amotar duk da na kusa dashi da Direba da wasu a baya sai Hiran yadda Harkan Tsaro ya Tabarbare sukeyi a kasar nan namu ya Takura matuka da Hayaniyarsu sai dai ba yadda Zai yi bai Tofa bakinsa ba an Tsaya wasu sun siya Ruwa da abubuwan ci na saman Hanya ammh ko Shi ko abunda ba"a so bai siya ba,Har na Kusa dashi ya Siya Buredi da Ruwa yamai Tayi ya Girgiza kai Sunyi Gudu soaai koda 12pm na Rana tayi suna garin Gombe Daganan ya Hau Mota zuwa Dukku Goro kadai ya Tsaya a gombe ya siyama Daada Tunda tana ci sama sama. Daya saura na Rana ya iso Dukku Daada na cikin Dakinta taji Baba Asabe nayi ma Imran maraba mamaki ya kamata lokacin Dataji sunansa Bata yarda ba ta Zata bataji Daidai bane Alwala ta Dauro tana Kokarin Tada Salla Imran ya shigo Dakinta da Sallamarsa Cikin Kaushunsa Koda yaushe. Takalmin kafarsa ya Tsaya ya Cire nan Kofar Dakinta kafin ya kariso baki ta Saki Tana kallonsa Cikin mamakin ganinsa Shi kuma gabanta ya karisa Fuskarsa bata bayyana Fara"a Sosai ba sai dai ya Saki Ransa ba kamar yadda ya Saba ba,Har gabanta ya karisa cikin Dan yakensa yace"Daada..! Daada data kasa mgana ta shafa kansa Daya dan rankwafa agabanta yana gaisheta tace"Kai nake gani ko kuwa Idanuwana ne suka Fara Rauni ne..! Mirmishi yayi kafin yace"Nine Daada..! Daada Farinciki ya kamata ta kamasa suka Zauna saman Darduman Data Shimfida bakinta Har kunne Tana Fadin"Masha Allah Sannu da zuwa yanzu kake tafe Imrana? Ya wajen Malami da sauran yan"uwamka ko ba daga gida kake ba domin munyi mgana da Mahaifin naka da Safe bai ce min kana Tafe ba..! Yana Sauke Jakar Bayansa yake Fadin"Daga gida nake Daada..Wannan Tafiyar ta takanas ta kano Taki ce Daada..! Yafada yana Kallonta Cikin Jin Dadin yadda yaga Tana Murna da ganinsa Cikin Jin Dadinta tace"Kai..Aikuwa naji Dadi sosai ka kyauta..Yau ina Zuwaira Allah ya jikanta tazo taga yau da kafarka ka tako zuwa Dukku Domin ka Dubani..,! Kai ya kada yayi kafin yace"Allah ya jikansu da Rahma..! Daada ta amsa da Ameen daidai Lokacin Baba aasabe ta shigo mai da Faranti shake da Ruwa da ababen sha,Suka gaisa sama sama ta Fice Ruwa kadai ya Tsiyaya yasha,Kafin ya Ciro goron Daya siyama Daada a aljihunsa ya mika mata ta Karba Tana ta Godiya da saka albarka kamar ya bata Duniya Duk sai yaji Tsausayinta ya kara kamashi ba,tun yau ba yasan Daada Tana matukar kaunarsa Soyayyar Datake yi ma Abba ne ya Shafesa. Mikewa yayi Dauke da Jakarsa yana Fadin"Daada yi sallar ki..Nima bari naje nayi wanka nayi Sallar na Dawo wajenki nazo akwai mganar da nikeso mu Tattauna..! Daada na Mirmishin Farinciki Tace"Shikenan ina jiranka..! Daga haka ya Fice Dakin da suka Sauka shi da Sagir wanchan karon nan ya sauka yayi wanka ya Sauya kaya Saboda duk yaji kayan sun Damesa Karamin Wando ya saka 3Quater,da Wata karamar riga yayi Sallah kafin ya Dawo dakin Daada Baba asabe ta jera abinci mai Rai da lafiyan nan ya Zauna gaban Daada Tare sukaci abinci White rice da Miyar kaza Bai wani ci da yawa ba Daadan ma haka Kunun aya dai yasha da yawa suna yi suna Hira sama sama Sai da suka gama Imran ya Kira Abba ya Bama Daada sukayi mgana. Sai da suka Natsu Daada nacin goron da Imran ya kawo mata ta kalleshi yana Zaune gabanta yadan Kishigida Daga Jikin gadonta tace"To ina Sauraranka Jikana..Allah yasa kan mganar Tarewar Sajida ne adakinta yau da nayi Farincikin da ban taba yi ba..! Imran kallonta kawai yayi bai yi mgana sai chan ya Mike Zaune Dakyau ya gyara Zama yana kallon Daada kafin yace"Ita ai Tun Washegarin Ranar da aka Dauramna Aure na gama da babinta..,! Daada ta Kalleshi Cikin Tsoro kafin tace"Bangane ba..? Dan Mirmishin Saman lebe yayi kafin yace"Manta da wannan mganar Zamu yita Daga baya..Yanzu dai kan mganar yarinyar nan ne ta kawo ni Daada...plz zan Roke ki kada ki aura mata wannan yaron basu dace da juna ba Infact ma bata sonshi kada ki kware ta kamar yadda kika kwareni..! Yafada kai Tsaye yana Kallonta Daada Tayi Sagale tana Bin Imran da kallo Tana auna Wasu abuubuwa acikin Ranta, Cikin Karin Haske data ke so Daga Wajensa tace"Wata yarinya kenan..?kuma dame na kwareka..? Imran kai Tsaye yace"Inteesar mana Daada..Da yaron nan na wajen Baffa Kabiru wachan zuwan namu kina cewa ya nemi yardanta..,! Daada tana kara Nazarinsa tace"To menene mtsalan Imrana..! Imran ya Dakuna Fuska yana Fadin"Mtsala Daya Daada bata son sa kuma bai dace da ita ba..! Daada ta dade shuru batayi mgana ba ganin haka yasa Imran ya Rike duka Hannayenta yana Fadin"Daada kada ki yarda da mganarsa..Wlh inteesar bata sonsa koda yazo yace miki wani abu karya yake yi..kada ki Saurareshi..,! Daada ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Naji bata sonshi..To wa take so..,? Imran ya tabe baki yana Fadin"Ni bansani ba abunda kawai na sani bata sonshi kuma amtsayina na Dan"uwanta bazan so hakan ya kwareta ba..! Daada ta Kallesa ido Cikin ido kafon tace"Kai kake sonta kenan shiyasa kace kada na yarda da mganar mai sunan megidana Hamisu..? Abazata yaji mganar da Sauri ya Kalleta yana Nazarin mganarta meyasa Daada itama tace ko yana son Inteesar ne Hade rai yayi yana Fadin"Nifa ba sonta nake yi ba..Ni fa ban ma sani ba ko ina sonta ko bana sonta..! Daada Tayi mirmishin su na manya akallah dai a shekarunta Zata iya gano Inda Imran ya dosa domin ta ma Lura Shi kanshi baisan yana son Inteesar din ba Zuciyartsa ke jansa yana aikata wasu abubuwan baisani ba. Saboda ta kara Tabbatar da Zarginta ta gyara Zama Tana fadin"Naji bata son Khamis kai ma baka sonta..To na yarda da mganarka ature mganar khamis daman akwai wani yaro dan kawata Aina"u tuni take son mu Hada Zuru"a da ita sai nayi mata mgana yaje ya ganta su Sasanta nasan Zasu Daidaita..,! Ai kamar Daada ta Zubamai Wuta haka yaji mganar nata,Kallonta yake kai tsaye yana jin Zuciyarsa na suya Daada na Lura dashi Tana Dariya acikin Ranta. Bata rai yayi yana Fadin"A"a daada baza"ayi haka ba gaskiya..! Kai Tsaye tace"To ya za"ayi.?ko kana da wanda za"a hadasun ne nifa bana son na Mutu ban aurar da duka jikokina ba Daga Mazan har matan..! Imran yayi shuru yana wani Tunani Kafin kai Tsaye ya kalli Daada yana Fadin"Ni zan aureta Daada shikenan..! Daada ta saki Dariya aranta tace Dan kwal uba kama Dawo Hanya ne.. Kai Tsaye tacemai"Sajidan fa..?kasan bazaka Hada jini Daya kishi ba ko..!? Tabe baki yayi yana Fadin"Daada matso kiji..! Kunnenta ta kawo ya rada mata mganar da baisan kome yace mata ba Naga dai Daada ta Zaro ido Tana kallonsa kafin tace"Innalillahi wa"inna Ilaihirraju"un Imrana meyasa kayi hakan..? Batare da Shakka ba yace"Saboda Hakan kadai ne mafita Daada..Kiyi Hakuri ban iya cika Miki Burinki ba..Ammh ki bani Auran Inteesar na miki alkawarin bazan baki kunya ba..! Daada Cikin jimami tace"A"a itama ai baka sonta bazan baka ita a maimaita abunda ya Faru ba..! Da Sauri yace"Bazai faru ba Daada..Nifa ina son ganinta kusa dani ban Tsaneta ba..Kinga ai zan iya Zama da ita ko..!? Yafada batare ma Daya sani ba Daada Tayi Shuru batayi mgana ta shiga wani Tunani,acikin Ranta bata isa tace ma Imran A",a ba kodomin ta gyara Kuskuranta na baya na Auramai Sajida Domin gyara Zumunci sai dai abubuwa sun Faru marasa Dadi.maimakon Zumuncin ya gyaru sai abubuwa suka Lalace a mganganun Imran ta Lura yana son Inteesar wannan ne karo na Farko Daya nemi wami abu a wajenta bazata hansa ba Tunda ya kasa Rike abunda ke Ransa yazo ya gayamata kuma Tabbas Zatayi amfani da wannan Damar ta nuna ma Mami Asma"u kuskuranta ta kuma Nuna ma Kabiri sakacin da ya aikata, Duk da abunda Imran ya aikata bataji Dadinsa ba Da Sajida da Inteeaar duka nata ne,Sai dai gwara hakan gwara ayi abunda za"ace gwara da akayi da Abunda Daga baya za"a zo ana nadama ita kanta Daga wannan Datayi bazata kara aikata irin wannan Kuskuran ba. Daada na chan na Nazarinta ita kadai Imran ma nayin nasa shi fa a Tunaninsa zai yi Taimako ne Tunda Inteesar bata son khamis bazai bari a aura mata shi ba,Kuma bazai yarda Daada ta kawo wani ba Shiyasa yace Zai aureta ba domin ya yarda da mganarsu na cewa ko yana sonta bane baiyi Beleving kan wannan abun ba. Daada ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Zan yi mgana kan auranka da Inteesar kuma bamai Tada mgana ta..Sai dai kaima ina so kamin wani abu Guda Daya..! Kallonta yake yi bai yi mgana ba Daada ta gyara ZAma Tana Fadin"Da Farko Dole zaka Dawo Imran din ka Dana sani..Ka daina shan Taba ka koma aiki ka zama Mutum wanda zai iya Rike mace saboda Nauyi ne zai Hau kanka Ina so don Allah ka Dawo Rayuwarka ta baya komai yayi Tsanani Saukin sa na wajen Allah indai zakamin wannan alfarman nayi maka alkawarin Karshen Wata Zan kira kowa da kowa kuma baza"a Watse ba sai da auranka da Inteesar da yardan Allah..! Kamar Daada tayimai gafara haka yaji Cikin Farimcikinsa Daya kasa Boyuwa yace"Insha Allahu Daada..! Daada taji Dadi sosai ta Rika sakamai albarka Kiran La"asar ya tadasu ya tafi yayi sallah Daya dawo ya shiga ya kwanta yana Barcin gajiya bai tashi ba sai gabda mangariba Ya tashi yaje yayi salla ya Dawo barcin yammah Cikin kunci ya tashi ga kuma Fushin Inteesar bata Kirasa ba sai shima ya Shareta. Da Daddare sun sha Hira Daada Shi kanshi yana ta mamakin kansa ko Saboda Rabi Hirar Daada ke yinsa kuma Duka Labarkn Anni ce shiyasa yake jin Dadin Hirar kuma bama Haka ba Zuwansa Dukku yazomai da Sauyi sosai yaji Dadin zuwansa Wajen Kakarsa sai alokacin yake jin Dadin da Sauran mutane ke ji in suka zo wajen kakkaninsu bai taba Samun kusanci da Daada ba sai wannan karon. Washegari daya tashi da Safe yaga Kiran waya da bakuwar lamba ba adadi,ga Sako yayi mamakin wanda ya Kirasa,sai dai sakon Daya gani ya bashi amsa Sajida ce. Tsaki yaja yayi Bloking dinta ya Share Sakon nata Domin baya Bukatar Wata mu'amala da ita bashi da akala da ita Ita kuma Daman Umaima ta saka Ta Tambayan mata Munari ita kuma ta Turo ma Umaiman ta Tura mata,Shine ta Dinga Kiransa bai Dauka ba ta Turamai sako Daga baya ta Dinga Kira bai shiga ba ta Fahimci ya Kulleta ne Tayi kuka sosai kamar Ranta Zai Fita kuma ta Dora Bleeminng din komai kam Mami Tama ganin koma menene ya Faru itace Sila,Shiyasa bayan sun gama Test tayi zamanta a Hostel bata Dawo gida ba saboda Haushin Mami Asma"u take ji. Sai ga Imran dayaje Dukku da Niyyar kwana Daya ya shantake har kwana Biyu sai dai Ranar Lahadi da Safe Bankin GTB, Reshen Jahar kano suka Turomai sakon suna son ganinsa Karfe 8:00am na safe tayimai a Office din Manaja Ranar Monday abaya bai Damu ba da aikin ba,ammh yanzu ya Damu ko Saboda mganar Daada,Khalil ya kira ya gayamai sun Dade suna mgana yana bashi Shawarwari da Kwarin gwiwa kafin suyi sallama alokacin yayi shirin Tafiya Kano da shirnsa ma ya shiga Dakin Daada yayi mata sallama Tana ta mamakin Tafiya ba Shiri yace mata wani abu ne ya taso. Kamar kar yatafi haka Daada taji shima haka sai dai ba yarda zatayi haka sukayi sallama karfe 12, yana gombe,Daganan ya Hau Motar kano sun samu Goslow a hanya da kuma Wahalan Mai yasa basu shigo da Wuri ba sai bayan mangariba suka Shigo kano.sai dai su Abba suka gansa kamar Daga sama. *Naji Sauki Sosai...Nagode da addu"o'inku..Allah ya bar Zumunci Ameen..* *Shakira* 3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�13* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Ganinsa Kamar daga sama bai sa wani ya Tambayesa Dalilinsa ba,Sanin halinsa shiyasa ba wanda ya Damu daya cemai wani abu ko Abba ya saka ma Ransa ya gaji da zaman Dukkun ne Shiyasa Lokaci Daya yaji dawowa gida,ba wanda ya kawo Tunanin wani abu,Shima baice ma kowa komai ba so yake sai komai ya tabbata ya bama Abba da Yaya Yusuf a big Suprise. Inteesar da Munari suna gidan Tunda Mama bata dawo ba,Bai bi ma ta kanta ba saboda Ransa ya baci da abunda tayimai Yayi Doguwar Tafiya ko ta Kirashi Taji lafiya ya sauka Shiyasa yayi shigewarsa Daki bayan ya barsu afalo tare da su Abba Ko kallonta ma bai yarda yayi ba ita kuwa Tana kallonsa Cikin wani Shaukin Dake Fitowa daga kasan Ranta. Wanka yayi ya sauya kaya yayi Sallar mangariba,sannan ya fita yaje Kitchen ya Hada Tea ya Fito Dauke da Mug din kan Dinning ya zauna yasha Abunsa Inteesar da duke zaune afalon Tana ta satar kallonsa sai kuma Taga ko kallonta ma bai yi ba yana shan Tea dinsa yana Nazarin abubuwan da zai Faru gobe shiyasa yana gamawa ya mike ya Fice Daga Falon Inteesar ta Bisa da kallon kauna. Masallaci ya nufa,Saboda yaji kamar an Tada sallah Su Abba ma sun tafi tun Dazu,koda yaje Raka"a Biyu ya samu Sauran sai da ya Rama yana cikin Masallacin Abba da Ya yusuf suka Fice Sai Sagir ne ya Jirasa ya idar suka Fito tare. Akofar gidan su Sagir din suka Tsaya Sagir na Tambayansa ya sukayi da Daada bai gayamai ba yadai cemai komai lafiyalau Key din mashinsa ya amsa,yace ma Sagir gobe da Safe akwai inda Zashi ganin Imran din bai gayamai inda zashi ba yasa Shima bai Tambaya ba,Ba Dadewa sukayi Sallama Sagir ya Fada shagonsa Shima Imran din ya wuce gida. Da wuri ya kwanta Saboda akwai Gajiya ajikinsa Har ya kwanta ya Tuna da Inteesar karamin Tsaki yaja kawai Mikewa zaune yayi ya Dauko Wayarsa ya Kirata alokacin bai da Riga Dagashi sai Boxer Imran ko ana Sanyi baya shiri da Zafi kwatakwata Wayar ta shiga sai dai bata Dade Tana Ringing ba yaji ta danna mai Nomba busy,ido ya waro yana bin wayar da kallo Zuciyarsa na Zafi kamar Shine Inteesar Zata kashe ma Waya..?Shi Imran..?ko abaya ba wacce ta isa ballatana ma yanzu Dayake jin kansa Daidai da kugun kowani Dan iska Shiyasa Tun Farko baya harkan mata Saboda Raini,Inteesar ta gama Rainasa Wato saboda taga yana mata Dariya Shine Zata Kashemai waya ga Dan iska ta samu ko..? Ko ma ace yaje Wajen Sajidan ne da gaske ta isa ta Hanashi zuwa ne?Shifa Namiji ne kuma yaya yake gareta ya bata Shekaru ba iyaka in Haihuwar kaji ne zai iya Haifarta Wlh shi Namiji ne Mijin Mace Hudu wata mace bata isa ta Zauna tana Raina mai wayau ba Ko Wacece ita kuwa,Ahaka ne Sagir ke cewa yana sonta..?aikin banza in taji ma wannan mganar sai Rainin nata ma yayi yawa shifa ba macen da Zata Zauna yana bata Hakuri yana Lallashinta yana da abubuwan yi masu Tarin muhimmanci da suka fi bata Lokacinsa kan Shirme Duk yadda Ransa ke Tafasa haka ya kanne ya Cije yayi ma kansa alkawarin Fita Sabgarta Domin Tsira da Mutuncinsa sai dai yadda yake ji game da ita ya Kasheshi daya zauna yana Fuskarta Raini da wannan Wulakanci a wajen yarinyar da bata wuce yar Cikinsa ba badai shi tama haka ba ko..? uhm Fushi Ta Cigaba da yi daga yau har Mahadi ya bayyana yafita Taurin kai da Zuciya. Duk yadda yaso barci ya Kwasheshi a wannan Daran ya kasa,sai da ya tashi Sauran Sigarinsa Daya siya a Dukku,Tun Da yaje bai wuce sau biyu yasha Sigari ba yana da Sauranta ita ya Dauko ya Dinga ban kama Cikinsa Har sai da yaji Zuciyarsa ta Cunkushe Kirjinsa da Kansa sun yi masa Nauyi kana ya Hakura ya koma ya kwanta yana Sauke Numfashi Daya bayan Daya. Ya Dade bai yi barci ba sai chan Dayayi Ruf da ciki duk da ba kyau ammh bai da Zabi,yayi Filo da Hannayensa saman Fuska sai Lokacin ya samu barci yaso ma ya makara ba Domin Abba ya Bugamai Kofa ba sanda Zasu masallaci shi da Yusuf Dakyar ya iya tashi da jan kafa ya shiga Tiolet,in ya Tsaya yin wanka zai Rasa Salla Shiyasa ya dauro alwala yabi bayan su Abba zuwa masallaci Allah ya Taimakesa an Tada Sallar ammh ba"a kai ga Ruku"u ba,Bayan an Idar da Sallar ya Dade yana addu"an Nasara a Rayuwarsa yana addu"an Samun wannan aikin Duk da Manaja Tunde ya bashi Tabbacin ammh bazai kwanta da hakan ba ayanzu yana Bukatar aikin Ko domin cikama Daada alkawarinta,Uwa uba kuma Lokaci Yayi da komai zai Sauya ko domin ya maida ma wasu martani irin su Mami Asma"u. Sai Bakwai Saura ya baro Masallacin zuwa Gida yana zuwa wanka yayi a gurguje baya so yayi african Time Daman chan ba Tsarinsa bane bayan ya Fito ya shafa lotion dinsa ya Taje Sumar kansa bayan ya shafamata Mai gyaran gashi,Wardrope dinsa ya Bude yana Duba Jerin suit dinsa Dayake dasu wanda ya Taho dasu Daga Lagos bai Taba sakasu anan garin ba barshi da Saka Saukakun kaya. Suit din na kamfanin DKNY ne sai na kamfanin Armani suna da kyau da Quality shiyasa Har Lokacin basu yi komai ba suna Sagale cikin Hanger wasu ma Sabbi ne suna da Leda ajikinsu bai Taba sakawa ba. Daya Daga Ciki ya ciro na kamfanin Armani Kalan Black and White ya Dauko Daya Daga Tektie dinsa Baki,Lokacin yana Lagos gabadaya kayansa Suit ne saboda yanayin aikinsa Wlh bamai nuna mai iya saka kaya a Tsuke wannan yana ma Daga Cikin Tsarin aikinsu Cikin Lokaci yayi shirinsa Woww..Nace Lokacin da ya Tsaya gaban Madubi yana Daura Tek tie dinsa,ya Hade har ya gaji da Haduwa Cikar Zatinsa ya kara bayyana kamar wani babban Mutum,baza kayi mai kallo Daya kace Imran ne mai Busa Hayaki ba sai ka karemai kallo kafin ka iya Tantace shine ko ba shi bane.? Agogon Azurfa ya sanya atsitsiyan Hannunsa na Hagu,silba ne yana Kyalli,Yana da irin su Dadama sai dai baya amfani dasu,bai cika damuwa da sai Rayuwarsa ta dawo kamar baya ba ammh a yau kam gabar ta bayyana Dolene ya Dawo Imran dinsa in yana son Cimma Burinsa. Takalminsa Rufaffa ne na Fatar Daminsa baki shima suit din baka ce haka ma wandon baki ne sai Rigar Ciki ne Fara,Imran mai kyau ne kuma shidin Dan baiwa ne Tuni ya Fito a ma"aikacin bankinsa da ba wanda ya isa ya Kallesa da kallon Raini Karamar Wayarsa ya Dauka ya Saka Cikin Aljihu yanzu bashi da komai sai dai in yaje komai ya kamkama akwai Bukatar ya mallaki wasu abubuwa kamar su Laptop,da waya saboda aikinsu baya Tafiya sai da haka Lokacin Laptop dinsa ma bazai iya Tuna ina isalinta ba,ana ta Rai wake ta abun Duniya alokacin. Key din Mashin dinsa ya Dauka saboda shi yake dashi alokacin ya Fito bayan ya Fesa Saukkan Turaransa mai Dadin kamshi na azzaro Visit. Dukkansu suna kan Dinning suna Breakfast,ya Fito Cikin Shirinsa Gabadayansu baki suka saki da Hanci suna kallonsa. Inteesar kuwa kamar Idanuwanta Zasu Fado Tunani take yi anya wannan Imran ne ko mai kama dashi..?gabadaya zuciyarta wani Tsalle take yi waje Daya dashi ta kwana acikin Ranta Kiran da yayi mata Jiya tazo Dauka sai bata sani ba ta kashe Kiran batayi Tunanin bazai kara Kira ba Domin har Ga Allah ta Saki Fushin taga alamar ita ce Zata sha Wahala daga baya daga ga Shuru bai Kara Kira ba sai ta Kirashi Sharrin Network yasa bata Sameshi ba. Yadda ta kafeshi da ido sai da gabansa ya Fadi ammh ya Kauda kai bai yarda ma ya kara kallonta,Daga tsayen bai karisa ba ya kalli Abba Dake kallonsa Cikin Mirmishi da Alfahari yace"Gud mrning Abba..Zan je wani waje bazan Dade ba zan dawo..! Abba kai kawai ya gyada Farinciki yasa ya kasa mgana ganin Imran cikin wannan Shigar ya Tunamai da abubuwa da dama ashekarun baya Lokacin yana ainihin Imran dinsa mai ci da guminsa,Yana Fatan wannan Fitar ta saka na alheri ne yasa Addu'arsa ne Allah ya amsa Imran zai sauya zai dawo Imran din Dayake so kuma yake Fata. Ya Yusuf ne ya ijiye mug din Tea din Dake Hannunaa yana Fadin"Woww..Long Time Imran Abubakar Malami..! Yafada yana bayyana Mirmishinsa da kuma bayyana irin kyan Zatin da kanin nasa yayi yau daya Dade bai yi wannan Shigar ba. Safiya da Munari suma ayyanawa kawai suke acikin ransu ko cikin Dubbam Maza Imran na Musamman ne banda Inteesar data riga ta zama gatanan ne azaune saboda wani Rauni Dataji ya kamata ganin yadda Imran din ya nuna bama ya son ganinta din Daga Yusuf har Abba basu matsa da sai sun ji Ina zai je ba Tunda suka ga bai Fada musu ba bayanzu yake son su sani ba Har ya fice suna binsa da Allah ya kiyaye da Fatan Nasara da Sa"a,yana Fita Daga Haraban gidan Wayar Khalil ta shigomai Dakatawa yayi Daga Hawa mashin din nasa ya amsa kiran mgana dai sukayi kan aikinsu Inda Imran din ya Fadamai yanzu ya fito zai isa Bankin sun Rabu kan Duk abunda ke nan Imran din zai Kirasa ya Fadamai haka ya Hau mashin dinsa ya fice Daga Haraban Gida acikin Ransa yana jin ya Zama Dole ya sauya ko saboda Mutanen da suka Damu da ganin Cigabarsa irin su Khalil da Sagir. Karfe 8:00am tayi ma Imran a office din Manager Turanci ne kadai ke tashi acikin wajen su biyu ne kadai Sai karan iskan AC,Manager din Bahaushe ne Sulaiman Ishaq Dawanau,Sai Imran Dake zaune kan wata Kujera Dake kallonsa gabansu wani katon Tebur ne baki mai Sheke sai ruwa da lemo,Dake gaban Kowanensu. Tattauna sukayi sosai Duk ba Interview bane sai dai Sulaiman Ishaq ya Karu da abubuwa sosai da D'an karamin Tattaunar da sukayi da Imran ta Tsawon awa Daya,ya Fahimci Abubuwa Dadama,ciki harda Sanin Tarin Ilimin Imran da baiwarsa da Sanin Abunda ya karanta din ba Shakka Lokacin da yayi aiki an samu Zakaran ma"aikaci ya Duba Duka bayanansa da Mr Tunde ya Turo musu ta Email dinsu mganace Daga Sama ba wani bata Lokaci Bayan sun gama Tattaunawa Sulaiman ya Mike yana bama Imran hamnu sukayi musabaha bayan ya Zana sunansa a Mtsayin assistan Manager na Branch din Gt bank din Dayake ciki Suna maraba dashi da ko a gobe ne zai iya Fara aiki Office dinsa yana Ready. Imran Dayaji haka cikin karfin gwiwa ya basa Hannu suka jinjina bakinsa nata Fadin"Thank u sir..Thank Very Much..! Sulaiman na Mirmishi yace"U are Most Wlcm Mr Imran..! Imran bai Tsaya bata ma kansa Lokaci ba yace ko yau zai iya Fara aikinsa Sulaiman Ishaq yaji Dadin haka yayi mai Jagora zuwa Cikin bankin yana nunamai ko"ina bayan ya sanar da Taron meeting lokacin da aka tashi break na Lunsh da masu yin Sallah yana so ya gabatar da Imran a Mtsayin mataimakinsa a wannan wajen mai kula da duka Shashen Dake Cikin Bankin. Kayattacen Office din Imran na Hawa na Uku ne Tunda Buliding din bankin Babba ne sosai,Office ne babba mai Dauke da glass Daya Zagaye wajen,ana ganin na ciki na ciki ma yana ganin na Waje sai Tebur baki daya kusa Cika Office din,sai kujerarsa Baka mai mukami sai wasu Dake Fuskarta guda biyu wannan na karban baki ne akwai Laptop na aiki Sabuwa awajen komai ma sabo ne Tunda assitan din Dake Wajen karin girma ya samu zuwa Manager na Brarch din su Dake Abuja Shiyasa aka Daukesa adaidai Lokacin kuma sai ga Imran shiyasa Faduwa taxo Daidai da Zama,harda karamin Frige akwai da kuma Tibin bango karami sai AC masu sanyaya Waje guda uku Daga gaban Teburin an Dora wani karamin Katako mai kyalli Wato IMRAN ABUBAKAR MALAMI(assitance Manager) da sunansa makale ajiki kamar yadda suka sanya komai an Riga an Tsara kuma an gamashi. Nan Sulaiman ya barsa bayan sun kara shan Hannu da juna Cike da Farimcikin da Imran ya Dade bai jisa a Ciki ba ya tsinci kansa Lokacin Daya ambaci sunan Allah ya Zauna saman kujerarsa Idanuwansa suka cika da kwallah aikin Banki Burinsa ne kuma Muradinsa Shiyasa wani Rauni ya bayyanamai da kewa mai Tsananin Dayaji kamar ya Fitar da kwallah. Bai Fara komai ba sai da ya Fito da Wayarsa Abba ya fara Turama Sako.. *Alhamdullillah Imran is back..Am now a Assitance Manager GTB branch Kano..* Bayan Abba haka yayi Copying ya Turama Sagir da khalil sune ma Masoyansa ne kafin ya kashe Wayar gabadaya yasan zasu kirasa shi kuma ayau Dayake jin kansa wani iri so yake yayi aikin Daya Dade yana kewa ko Hakan zai Ragemai jin Dadin Dayake Ciki,Har ya kashe wayar sai ya Tuna da Mr Tunde da Sauri ya kunna kamar yana Jira sai ga Kiransa yana Dagaawa ya faramai Congratulation, Yana Tayashi Murna ya amsa mai Cikin Sakin Fuska lokaci Daya yana mai Godiya,basu wani jima suna mgana ba suka yanke kiran suna gama Wayar ya kara kashe wayar ya maida ita aljihu yajawo Computer gabansa ya kunnata komai da komai da Duk wasu bayanai da zai Bukata yana Ciki Tuni ya fara aiki ba kama Hannun yaro yanayi wani Annuri yana Fita daga Cikin Ransa Har zuwa Saman kyakyawan Fuskarsa. Abba ne ya fara ganin Sakon na Imran Lokacin yana Falo Inteesar da Munari sun fito suna shirin Tafiya makaranta yau bada Safe suke da Lectures ba. Abba daya ga sakon Sai da ya Daidai Gabansa ya Duka yayi Sujjada ya yi ma Allah godiya da Kirari sai da ya Dago Farinciki yasa sai da yayi kwalla nan yake Fadama su Inteesar abunda ya Faru Munari ta Daka Tsalle da Ihu Lokaci Daya ta Rumgume Abba ihun ne ya Fito da Anty Safiya Inteesar baki har kunne,zuciyarta Dake Cikin Damuwa tayi Fal da Farincikin jin Imran dinta ya Zama kamar yadda Kowa ke Bukata Allah Sarki Munari ta Rumgume Inteesar da Anty Safiya Tana Murna ita kanta Safiyar tayi murna kwarai Tana ta saka albarka Lalle Imran wato shi dai na Dabam ne Komai sai dai aji kawai,Yusuf ne ya kira Abba ya Dauka yana Murnan gayamai Sakon da Imran ya Turomai Abba yace mai shima ya Turomai Farincikin su yaki Boyuwa Abba nata Fadin Allah nagode maka Allah ka kara Shiryamin wannan yaron ka kara Mishi Natsuwa Allah ka yayemai wannan Zuciyar dayake Fama da ita. Haka chan ma Khalil da Sagir suke Cikin wannan Farincikin sannan dukkansu sun kirashi wayarsa tana Kashe aiki gamai kareka kenan Sagir haka ya kira Mama yana Fadamata itama tana ta saka albarka Inteesar suna Hanyar zuwa makaranta ta Kira Daddy ta Fadamai yace yanzu suka gama waya da Abba ya Fadamai sun dan jima suna mgana inda yake Fadamata shima Abba Saura Kadan a kirashi Domin Manya Daga sama a gwannati suna Duba lamarin. Bayan nan ta Kira wayar Imran a kashe sai ta Turamai Sako. *You had the passion, and you had an ambition. You truly deserved every bit of the success you have achieved. Congratulations Ya Imu..* Ta turamai Tana Mirmishi ita kadai Munari na Lura da ita sai Mirmishi take yi bata dai ce mata komai ba Tana jiran Wata rana ranar da mganar Zata shigo ko kuma ita Inteesar din ta tareta da mganar Zata Fito ta gayamata cewa Son ya imu take yi bata sani ba. Imran bai tashi daga wajen aiki ba sai 6pm,Da suka Fita lunch da karfe 1pm Sulaiman Ishaq ya hada karamin Taro inda ya gabatar da sabon Assistan Manger wato mataimakinsa a wannan Reshen bankin ya bada kadan Daga Cikin Tarihin Imran da yarda yazo yayi aiki a Branch din su na Lagos da irin kokarin da yayi Domin duk sanda Banki Zata je Seminar shi ake Turawa kuma zai je yayi kamar yadda ya kamata Cikin Shekaru da yayi yana aiki ya jawo ma Bankin Gt Daukaka da Cigaba sosai jin Dadin haka yake wannam Mtsayin ko ba"a Fada ba Daga ganin Imran bazai yi wasa ba Yanayinsa da Cikar Zatinsa kadai ya Isa Shaida kuma Daga ganinsa He is Ready abunda ake Fada akansa duka ba karya bane,Ya gaggaisa da ma"ikata mazan dake karkashinsa,mata kuma bai yarda yayi hannu da kowata Mace ba bai ma Saki Fuska ba Fuskarnsn dai gatanan ne kadahan kadahan. Da aka tashi Kowa na shiga Tsararriyar Motarsa ammh Mataimakin Manager ya Hau Mashinsa bai ji Wani kunya ba ya Wuce gida Sulaiman Ishaq ya gansa yayi Wani Tunani acikin Ransa Kafin ya Shiga Motarsa ya Fice Daga Bulding din bank din. Koda ya koma gida irin Murnan Da Abba da yusuf sukayi bazai misaltu ba,Dukkansu suka Rumgumeshi suna Murna Anty Safiya da Inteesar da Munari da Sagir suna gefe suna Tafi Lokaci Daya suna Fadin Congaratulation Dear. Mamaki ya kamasa ganin party fa suka Shirya kwarya kwarya wannan kuma Shawaran Intee ne suna makaranta Tunanin ya Fado mata ta Gayama Munari itama tayi na"am Basu Dade a makaranta ba,lecture daya sukayi suka Dawo gida suka Fadama Anty Safiya ita kuma ta shige gaba ita ta Kira Yusuf ta tafadamai yce Tabbas wannan al"amarin ya Chanchanci ayi mai Party,Abba ma Dayaji bai hana ba,Inteesar ita ta Kira Sagir ta gayamai sunyi Girke girke da Lemuka Ya Yusuf kuma bayan ya tashi Daga wajen aiki ya biya Shoprite ya siyo Sweet ba adadi,Safiya kuma da Taimakon su Intee suka Hada Tsararran cake din Dake Dauke da CONGRATULATION IMRAN..! Basu barsa ya shiga Dakinsa ba suka jasa Saman Dining inda suka Jera komai,Duk da bai saki Fuska sosai ba ammh kana kallonsa Zaka san yaji Dadi matuka Da Hannun Abba dana Yusuf ya hada ya yanka Cake din ya Gutsira ya bama Abba,Abba ya karba bai ci ba ya sakamai a baki Sai ga Taruwar Hawaye Imran yaji Rauninsa ya bayyana ya Rumgume Abba,Abba ya Rikesa cikin Farinciki yana Fadin"Congatulatiom My son..U Deserve everthing..Allah ya bada sa"a Allah yayi maka albarka..! Su Anty Safiya nata amsawa da Ameen Ameen Yusuf ma ya Debo zai kai bakinsa sai ya rike hannunsa suka Hada Hannu suka kai bakin Yusuf atare kafin su dawo dashi bakin Imran Kafadansa Yusuf yadan Bubbuga yana Fadin"Bravo alaika...Allah yayi jagora dan kanina.! Dakuna Fuska yayi yama kallon Abba yce"Abba Abeg tell him bafa wani Shekaru ya bani ba..! Gabadaya Dariya aka saka kafin Sagir ya Yanko katon cake ya Dunfari bakin Imran baya yaja yana dan Fiddo ido waje bai gama mamaki ba Sagir ya Turamai abaki har wajen Hanci Da kumatunsa dama dama da cake Dariya aka sanya gabadaya ganin yadda ya wani Tattare Fuska kamar an yabamai Kashi. Sagir yace"Congratulation Abokina..Allah ya tayaka riko am so Happy for u..! Wata uwar Harara ya Wurgamai yana Fadin"Kaifa banza ne tsiyana Dakai kana Girma kana cin kasa..Ya kamata ka Rika gane bambamcin Boy and Man dis abunda kayi is a Childness..! Yafada yana nuna Bakinsa cikin kyamkyama shifa bai son Abu ya Cika Zak'i shiyasa baya mu"alama da Chaculate sai Dariya su Abba kemai Munari da Safiya suka cemai Congaratilation ya amsa banda Inteeaar da kallo Daya yayi mata ya Kauda kai duk da tayimai kyau a ido Bai Hanashi nuna mata kwanjinsa ba Tayi Shigar bakar abaya ne sai tayi Rolling da karamin Vail fari Fuskarta ba kwalliya sai dai ta shafa ma karamin Bakinta Jan jan baki,Tayi kyau matuka a acikin Idanuwansa ammh bai bayyana mata ba,Dayake ana ta Murna ne ba wanda ya kula da bai amsa mata ba,ya sulale ya shige Dakinsa sukuma suka Cigaba da Shagalinsu Inteesar duk sai taji Gwiwanta yayi sanyi itafa ta Saki wannan Fushin nata Tuni Munari ce ta katse mata Tunani bayan ta Tura mata Cake a baki Har akan Hancinta Sai ta Bita itama ta gutsiro Cake din ta Bita dashi suka Fara guje gujen suna Dariya Abba na gefe yana kallonsu Cikin Jin Dadi da godiyar Allah. Sagir dai Daki yabi Imran yaga ya shiga wanka sai da ya jirasa ya Fito ya Dinga mai hira yana amsa mai Sama sama Saukakkun kaya ya saka karamin Wando da Riga Fita Falo yayi yaga Inteesar da munari nata Hotuna Harda Anty Safiya baima bi ta kansu ba,ya fada Kitchen ya Dauko Ruwa ya Hado Tea a karamin Mug wajen Abba da Ya yusuf ya nufa suna zaune kan Dining din Sagir ma nan ya Fito ya samesa suka fara Hira ahankali yake bama su Abba Labarin yadda komai ya Fara Sanadin khalil ne Abba nata Godiya yana saka albarka nan yace ma Dr.Ali isa ya kirasa yana mai murna kila khalil ya fadamai.. Sun dade suna ta Hira sai chan Dare suka watse Sagir ranar anan ya kwana Tunda gidan ba kowa mama Tana Kaduna. Kamar koda yaushe Imran kan kujera ya kwana ya bar ma Sagir gado,Sagir yasha mamakin ganin Imran na Busan Sigari Cikin mamaki yace"Tab kai yanzu daman baka Hakura da shan Taban nan ba..? Ko kallonsa Imran bai yi ba,Ya cigaba da Busa Hayakinsa,kamar bazai ce komai ba Har Sagir din ya koma ya kwanta yaji Imran yace"Ka Dauka na Daina sha ne saboda na fara aiki..? Bai ma Sagir damar mgana ba ya cigaba da Fadin"Ma'aikacin banki baya shan Sigari ne..? Sagir yadan Saki Tsaki yana Fadin"Wlh dai in kaje kana Busawa achan bankin kasan Sauran..! Dariya Imran yayi har ana jin Sautinta. Washegari tun Safe ya amsa Kiran wayoyin mutane ba dama Daddy ne Farko har Umma sai da ya bamawa tayimai Murna Kimarsa ta kara Karuwa acikin Idanuwansa,Khalil ya kira sa sun Dade suna mgana Har Mahaifinsa Dr.Ali isa argungun ya Kirasa yayimai Murna Basheer dasu Sadam duk sun kirasa kuma an bada Sanarwan a Group din marigayi Alkali Dukku ammh Baffa Kabiru bai kira Ko Abba ba ballatana Imran wanda Lambarsa ya Zaga ko"ina acikin Dangi kalilan ne ya adana Lambarsu kamar Daddy da Su basheer. Yaga Sakon Inteesar Daya kunna Wayarsa har da ma da Kiranta ammh bai bi ta kanta in ita Nata wasa ne shi da Gaske yske yi saboda aikinsa yasa baima da Lokacin wani banzan Tunani,da tagaji da kiransa ta Hakura ta Turamai sakon ban Hakuri har tagaji,Bai taba maida kai ba ya shareta ya nuna mata Shi Namiji ne kuma Har yanzu yana nan a Imran dinsa bai sauya ba Ranar data Damesa Sai yaTura mata Sakon cewa "Kin gama Fushin ne..? Da sauri tace "Eh nagaji na tuba nabi Allah na bika Ya imu..! Mirmishi yayi kafin yace mata "In kin Gama ni yanzi zan fara nawa..! Aikuwa ya fara nashi Domin Dif ya Dauke mata ya Rataye ta bata ma ganinsa tun 7:30am na safe yake Fita sai 6pm na yamma yake dawowa in kuma ya dawo yana Daki yana aiki Tunda ya siya karamar Laptop Apple Saboda aiknsa kudin nan ne lokacin Bikin Yusuf da Baba Manu ya dawo mai Dasu,Yusuf bai karba ba ya cika ya siya Computer,Sannan Abba yasa Yusuf ya basa kudi ya siya kaya da Takalma tunda har lokacin Akwai kudi a Bankin Nura sannan akwai kudin da suka saida Motocinsu da su ya kara ya siya Suit masu yawa da Takalma da agoguna Saboda yanayin aikinsa. Mganar aikin Imran har Daada sai da taji Daddy ya Kirata ya Fadamata Tayi ta Saka albarka,Da sukayi ma waya da Abba Tayi ta addu"a Imran din basu samu mgana ba Tunda baya barin Wayarsa a Bude sai ya dawo gida. Sati Daya da Fara aikinsa Bankin Gt ta mallakamai Gida Mai 2bedroom madaidaicin Falt,da Sabuwar Motar hawa Kirar 4matics kyauta Halak malak,saboda Sadaukarwarsa da da jajircewarsa Sulaiman Ishaq ne ya shigar da Korafin a Chan Sama Board of Directors kuma sanin Waye Imran Abubakar malami yasa akayi approving din mganar aka kuma Tabbatar. *Shakira* 3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�14* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Da wannan Labarin Farincikin Imran ya dawo gida Ranar Cikin Sabuwar Motarsa baka 4matic da makullin gidan da suka mallakamai Sulaiman ya kaisa yaga gidan dake Anguwar Alu Venue. Abba Hamdala kawai yake ma Sarki gagara Misali Sai da yayi hawayen Farinciki,haka ya yusuf daya dawo yaga Sabuwar Mota aharaban gidan shi kam ya kasa Boye murnansa sai Faman cema Imran yake Congratulation u deserve everthing Brother,Safiya ma ta tayashi Murna su Munari suna makaranta sai da suka dawo sukaji abun arziki,Ba kamar Inteesar a Farinciki duk da gogan nata yana Fushi da ita Sagir yazo yaga Mota ya shiga ya zauna baki yaki Rufuwa ashe ashe akaai Ranar da zai ga Imu zaune cikin Mota yana Driving ba shakka Rayuwa ta gaji haka kada kuma Kaga Mutum a wani yanayi ka Raina masa Domin bakasan Baiwar da Allah yayi mai ba kuma Dan Hakin daka Raina Watarana shi zai Tsole maka ido. Imran ya Fadama Khalil wannan kyautar Girma shima ya tayashi Murna matuka da kansa ya Kira Mr Tunde ya Fadamai Duk ya sani shima ya Tayasa murna tare da karin wasu Shawarwari. Duk wanda ke tare da Imran sai da ya tayashi Murna saboda ya Chanchanta Inteesar ta Test messages ta Turamai Sakonta kuma yagani ammh bai nuna mata ya gani ba wannan Shariyan nasa tana matukar Damunta har ta fara rama barci kuwa sai ta kusa Raba Dare ya kasa Daukanta ammh gogan nata baisan tanayi ba komawarsa aiki yasa ya kara zama Rashin Tabbas Fiye da baya. Ko sati ba"a Rufe ba Sai ga sunan Abba Jami"ar BUK ta Zana a mtsayin DEEN na Department din Daya fi kwarewa Akai wato Psychology Proffesor ne suka zauna da Daktoci da Deen na Faculty da Deens na Department da shuganni masu rike da madakin ikon Jami"ar Turanci ne kawai akayi ta Zabgawa kamar ba a kasar Nageria ba,ilimi ne da manya Kwalaye yayi aiki,Abba ma sun gayyaceshi yaje sun zauna Cikin manya manyan Proffesor,bai Razana ba ko kadan Tuni tsohon Dr.Abubakar Malami Dukku ya dawo,Tattaunawa Data kwashi awanni goma kafin agamata washegarin Ranar ne aka Fadi sunan Abba A mtsayin Deen na Departarment din Psychology. Wannan abun wani Budi ne da Ni"ima Daga Ubangijin mai Rahma mai jinkai In wata Kaddara ta sameka ka Dogara ga Allah shi din Yana mganin kowani Tsanani da Sauki In ka Yi hakuri Zaka ga sakamakon ka a wajen Allah to hakan ne ta Faru da wannan ahalin da sukayi hakuri suka Dauki Kaddaransu Hannu Bibbiyu sai gashi Allah yana Dawo musu da Ninkin ba Ninkin Abunda suka Rasa. Wannan Nasaran da Abba ya samu Daddy ne kan Tsani Duk da ba aikin Gwamnati yake yi ba yasan manya sosai acikin gwammati masu manya Mukamai da Taimakon su da Chachantar Abba ne ya kaisa wannan Mtsayin. Tsayawa Fadar irin Farincikin wannan Gidan ma bata Lokaci ne sun yi Murna kuma sun godema Allah Duk da bazasu iya dawo da Ran Yan"uwansu da suka rasu ba akallah dai Zasu iya Dawo da Fiye da Farincikin da suka rasa abaya Dr.Abubakar Malami ya kara Tabbatar ma kansa mai Hakuri Shine keda riba wata Rana kuma Komai Tsanani mganinsa na Wajen Allah in kaddaran sa ta Faru dakai to akasin Farinciki da samu zasu Faru dakai in kayi Hakuri abaya ya riga ya Gama Fitar da rai da Rayuwa ballatana Har ya Cigaba da amfana da Iliminsa sai dai shi Allah mai kyauta kuma mai kari ne. Wannan Sabon mukamin na Abba ba wanda bai jisa ba yan"uwa Sai kira suke suna Tayashi Murna Daddy da Umma Takanas ta Kaduna sukazo kano Taya Abba Murna Suka kwana Daya suka koma Tare da Mama suka Dawo Tunda Jikin Inno yayi Sauki ta Warware,Inna Bintalo da ya"yanta duk sun kira Abba haka Inna Maimunatu Sadam kuwa kullum Shida Aneesa in yau basu zo ba gobe suna gidan,Hatta Mutanen Ikko Dr.Ali isa Argugun ya Kira Abba yace a Jarida ya gani a Big Congratulation ya Chanchanta da wannan mukamin. Banda Baffa Kabiru shi kam sai da kowa ya Kira kusan shine na Karshe ya Kira ya Tayashi Murna Abba Mutum ne bamai Riko ba sannan yana yima wadanda yake Tare dasu Uzuri ballatana Baffa Kabiru da shi ya Fita Dabam acikinsu. Bai nuna mai wani abu ba ballatana yaga alamun ya Fahimci bai kyauta ba Shima Sai yayi amfani da kalmominsu na Lauyoyi ya Irin nuna ma Abba Hidimomi ne suka sha kansa shima Abba sai yayi amfani da Iliminsa na Sanin Hallayar dan adam ya nuna bakomai ya Tabbata daya samu Lokaci Har gida zai zo mai murna da Haka suka Rabu Labarin da Har Cikin Family Group din su sai da Sadam ya Sanar kowa ya gani Hatta Sajida wacce Take chan makaranta Bakinciki da soyayyar Mijinta sun kusa illatata Tana da Labarin samun aikinsa Ta Kirasa sai dai har Lokacin bai Sauketa Daga Sagale tan da yayi ba,Ta Riga ta gama Sarewa ta Tabbata da Mami Tayi mata mummaan Ramin da kafin ta iya Cikesa sai ta sha Wahala Tana son Imran kuma zata tabbatar da hakan bazata jura rasashi ba,shiyasa ta yanke shawaran Dukku Zata tafi wajen Daada ko kuma taje Gidan Baffa Malamin Imran din in ya ganta Dole zai karbeta tunda dai ita Matarsa ce,Sai dai kafin nan Zataje Dukku ta Fadama Daada tana son ta Tare a Dakinta Mijinta ta Tabbata in ta Cigaba da yin shuru Mami Zata kashe mata aure in kuma hakan ta Faru ta gama shiga uku ba wanda take ji take gani a farke ko acikin Mafarki irin Imran Rayuwa babu shi bata san yaya zata kasance ba ta bari ne su gama Covering semester su sai ta Shirya zuwa Dukkun koda makaranta ne batare da Mami Asma"u ko Dad sun sani ba ta Tabbata Sukaji Labari bazasu taba barinta ba. Khamis ma yana Cikin Damuwa ganin Yadda Inteesar taki bashi Dama aiki ne yayi mai yawa bai samu Lokaci ba ammh ya Kuduri niyyar karshen Wata Zai je Har kanon zai kira Baffa Mustapha ya bashi Full Addrres din inda Zai sameta Zai je domin neman yardanta Bai ma Fahimci haka sonta yamamaye mai Ransa da Zuciyarsa ba sai da ya koma Anambara Tunaninsa duk itace tayi Daidai da Zabinsa da irin kalan matan dayake so. Khamis bai Taba Zina ba Sai dai Bazawarin Kan Titi ne ya Fige mata da yawa asha baki yayi Romancing na Fitar Hayyaci aji Dadi da juna ammh bai Taba Tsallake iyaka ba ko kuma ya Tsallake Gonar da bata tasa ba ya riga yayi ma kansa alkawrin bazai tsallke Gonar kowa ba sai tasa. Mami Asma"u Dataji Labari mamaki ya kamata ta Dinga maimaita lamarin a Fili,Tasani kuma ta kara Sanin Malami da iyalansa sun musu nisa ita kuma abunda da bata kauna kenan wani ya Fita ko ya fi mijinta da ya"yanta tana da Labarin samun aikin Imran Harda kyautar da aka bashi da Mota da Gida Zuciyarta tayi Sauki kan Auransa da Sajida sai dai kafin ta bashi yarta sai ta Gindaya wasu Sharruda kuma sai ya tako gidan nan ta Wulakantasa son ranta. Ko awaya bata Kira Abba ba kuma a group da ake ta Fatan Alheri Tana gani batace komai ba Kuma Baffa Kabiru bai iya gayamata abunda ya kamata ba abunda taga Dama shi take yi shi bai isa yace wani abu Saboda Tun Farko haka suka Gina Rayuwar Zaman auran nasu. Safiya ta Kira Hajiya Mero ta Fadamata Abun Alherin Daya samu Abba bakinta yaki Rufuwa daman wannan Ranar take jira da gayya Taje tana Fadama Alhaji Alhasan wanda Ya Razana kuma yaji mamaki Daman Sabon Deen da Jami"ar Bayero ta Fitar da sunansa Mahaifin Yusuf ne,Bai taba Tsamnani ba kuma bai Taba kawowa ba,Hajiya Mero tace ya Shirya yau Har dashi zasu tafi Gidan Taya su Murna ya Fara Kifta Ido,Wanne shi ake kira Inda ka Raina in da zaka na Ran maka ya Raina Yusuf ya Ci Zarafin gidansu sai gashi In bai yi hankali ba Kunya da Nadama zasu kamasa Lokacin hakan bai yi ba. Ya Tabbata yasan Labarin yadda ya Basu Safiya a wulakance da yadda ya Tozarta Yusuf din Tabbas bai zo so su Fara Haduwa Cikin wannan yanayin ba Duk yadda yaso ya Zillema Tafiyar bai Samu ba Domin Hajiya Mero ta Tsaya sai yaje ita da kanwarta Anty Saratu da ta zo su tafi Tare. Bashi da Mafita illah ya shirya Da Daddare suka tafi dukkansu har da Tasleem Masu Karatu zan so ku Hango Fuskar Alhaji Alhassan agaban Abba kamar yayi mai sujjada ya kaskastan da kansa baya iya Hada ido da Abba ballatana Yusuf har ita kanta yarsa tasa Safiya,Gani yakevkamar Abba ya na kallonsa da abunda ya aikata Cikin Rashin sani yo cikin Rashin Sani mana in da ya san Akwai irin wannan Ranar wlh da bai fara wannan Tozarcin ba. Sai dai ta bangaran Abba ba haka bane ya ma manta da wannan mganar Tunda akace mai ga iyayen Safiya Har da Mahafinta sun zo mai Murna Farinciki ya Kamasa Alhaji Alhassan na neman ya Dukamai ya Tarosa yana bashi hannu Cikin Fara"a Lokaci daya da godiya Domin iyayen Safiya abun karramawarsu ne Safiya Haske a Gidansu itace Sanadiyar da suka kawo yau a wannan Rayuwar Dole ne ya Godema iyayenta da ahalinta. Lokacin da Abba ke godiya kan Alhaji Alhassan na kasa ya kasa ma Dagowa bai Taba nadamar Hallayarsa ba sai yau Ji Abba dai Daga ganinsa kaga Tsabar Ilimi da Wayewa tare da shi Wanda ko saman kafarsa bai kama ba godiya yake yimai Saboda ya aura ma Da'nsa auran Safiya a kaskaace bai Tuna da Cin Zarafim da yayi ba to shi kuma a wa..? Tabbas a wannan Gidan yaci sunansa gidan karamcin Kunya da Nadama sunki barinsa ya Saki jikinsa Su Mommy tun bayan da suka gaisa da Abba suka Rankaya shashensu Safiya Tasleem kuma Tana Tare da su Munari. Abba da Alhaji Alhassan Suna Falo Abba ne ke tamai Hira Cikin Faram Faram da wayewa shifa sai dai Zugum da gyada kai,a Hiran Abba ne yaji Labarin Abba yayi Koyarwa a Jami"ar Lagos kusan shekaru ashirin ya Hallaci kwasa kwasa ba adadi kan abunda ya Shafi karatunsa Dr ne shi a bangaran Ilimi Babansa Marigayi Hamisu Dukku har ya rasu alkalin alkalai ne na Kotun musulunci to shi Waye..? Alhassan ne fa wanda ubansa ba kowan kowa ba almajiranci yazo yi garin Kano Allah ya taimake sa Da Taimakon Mallam yayi karatu da kuma alfarmansa ne har yau yake kan wannam mtsayin shi ko Rabin Dr bai kai a iliminsa ba,Karamin alhaki ne in kazo matakin rayuwa a kan Abba da Zuru"arsa. Yusuf ya Fita Haraban gidan yayi waya sai ga su Baba Manu da Matarsa Kaltume da Mama da Sagir sun kawosa daman Tuni yaji Labarin komai a bakin Mama Shiyasa Dayaji wannan abun Faricikin yace ta kawosa yayi musu murna da Yusuf suka Fara jin karo yaji Dadin ganin Baba Manu saboda bazai manta dashi ba,Yayi musu jagora zuwa Falon gidan su inda su Abba ke zaune bayan sun gaisa Daga Waje Abba ya mike Cikin girmamawa Sanda Yusuf ya sanar dashi Baba Manu ne baban Sagir wanda ya karbomai Auran Safiya Alhaji Alhassan dake Zaune yana ganin Manu aransa yace Shikenan na Mutu Daman yana zaune ne yana Allah Allah kada tsagerin yaron nan ya Shigo Kada ya yagemai Sauran Rigan Mutumcinsa Dayeta ita a wajen Abba. Sun gaggaisa Cikin Aminci da Farinciki Abba yayi ta ba Baba Manu Hakuri Da baisamu zuwa yayi mai Godiya ba Baba Manu yace Haba ba komai Shi kanshi yasan Wani kaya fa sai Amale Yusuf sun wuce Raini da Wulakanci Tunda yaji ance Yaya yake Wajen mijin Salaha kanwar Amina yasan Babban goro sai magogin karfe. Sai da aka Natsu yama Lura da Alhaji Alhassan nan take ya Kira sunansa ya basa Hannu yana Dukar da kai da Kifta ido ya amsa mai shi bai ma Lura dashi ba sai acikin Ransa yaji Dadin Da Alhaji Alhasan din ya gane cewa Safiya batayi ma kanta Zaben Tumin Dare ba ta shiga Ahali irin Ahalin da kowa Ke Burin nashi ya kasance. Munari da Inteesar keta Hidiman kawo ma baki abun sha da kayan Motsa baki Sagir dai Dakin Imran ya shiga ya samesa zaune kan Tsakiyar gadonsa yana ta aiki Bisa karamar Laptop dinsa nan ya Zauna suna gaisawa jin cewa da Baba Manu suke Imu ya mike ya Zira Jallabiya ko bakomai yana ganin kimar Baban Sagur din ba Dan"uwa bane ba kowa ba ammh yayi musu Ranar da wani nasu bai musu ba. Ai yana Fitowa Falon Alhaji Alhassan yaji kamar kasa ta Tsage ya Fice ga Sanyin AC ga komai ammh Sai zufa yake yi,Imran bai ma gansa ba da Baba Manu suka gaisa sai su Mama da suka Fito Daga Shashen Anty Safiya Zasu tafi ne ma,Kawai yaji Alhaji Alhasan na gaisheshi kowa awajen sai da yayi mamaki sai alokacin Imu ya gansa yako hade rai ya amsa lokaci Daya yana Bashi Hannu sukayi Musabaha yana jin Sadda Hannunsa ya Jike da Zufa sai rawa jikinsa yake yi Dariya ta kamasa aransa yace kowa ya Tuba don Wuya ba lada Saboda Safiya bazai so asirin Mahafinta ya Tonu a Bainar nasi ba sai dai zai so ace ya Tuba kuma Allah ya Shiryesa ya Dawo uba nagari kamar kowaa yasan dai shi Imran bai jin mgana ammh Wlh bazai iya Fallasa asirin da wani ya Rufe ba har ga Allah yana mai Fatan Shiriya. Su Baba Manu suka Fara Tafiya sai gashi Har da Ya Imu a yan Rakiya,sun Tafi kenan Ba Dadewa suma su Alhaji Alhassan suka wuce bayan yayi ta Dokama Mommy kira ta fito su tafi kunya yakeji gani yake kamar Kowa yasan abunda yake aikatawa Abba Har Bakin Mota ya rakasu Mutum mai Saukin kai inji Mommy Anty Saratu tace Dagani ya Gado Dattako da Mutumci shidai yana jinsu Tak bai ce kunyar duk ta gama kamasa sai da suka isa gida ya iya Ssuke Numfashi Anty Saratu nan zata kwana sai Gobe Zata koma Gidanta nan suka baje afalo suna labarin Karamcin Gidansu Yusuf anan me yake jin Labarin Safiya nada Ciki sai yaji Dadi ko bakomai zai yi Farinciki in ya Hada zuru"a da Abba Shi kanshi ya sani Babban Goro ai sai magogin karfe. ****** Washegari ta kama Labara ne,basu da Lecture sai 10am na safe shiyasa ma basu Shirya ba,yau basu tashi da wuri ba,Anty Safiya tayi Breakfast Tunda dai basu tashi ba suna ta barci Inteesar 7:20am na safe ta Farka Daga kan Darduman Data idar da Sallar asuba Munari na saman gado tayi Daidai tana Sharan barci tana Fashin Sallah ita kadai tatashi da asuba Tama makara saboda bsu yi barci da wuri ba sun Tsaya yin Browsing din wani assigment da aka basu kuma yau din za"a karba Agogon Wayarta ta Duba Taga Lokaci in taci sa"a Ya Imu bai ga Fita ba kenan,Yau za"ayi ta kare tagaji da wannan Fushin nasa In Horata yake son yi Wlh ta Horu har tayi Laushi,Da Dogon Hijabin Datayi Sallah ash mai Hannu ta Fito Daga Dakin,Ba kowa afalon sai karan Tafakeken Talabijin din Dayake tayi shi kadai Falon sai tashin Kamshin Girki yake da na Turaran Wuta aikin Anty Safiya ne ta gama Jera komai asaman Dining ta koma ta Taya Ya Yusuf shirya kafin su Fito tare domin yin Breakfast. Bata Tsaya wani Tunani ba ta Fice Daga Falon zuwa Haraban gidan illah kuwa Ta hangosa Tsaye ya Bude bayan Motarsa ya saka Karamar bakar Jakar Briefcase dinsa kafin ya Rufe ya Zagaya ya shiga bangaran Direba sanye yake da American Suit masu Ruwan Toka na kamfanin Armani ya yi amfani da Tek tie ash ya Daure wuyansa dashi kafarsa sawu Ciki ne Bakake,na Fatar damisa sai agogon Hannunsa Shima mai kyau da yarari kirar golden kansa ya sha gyara yana Sheki ko kadan bai Rage Dadan Daya Tara a kansa ba sai hakan yayi mai kyau a kallon Farko in kayi mai sai yayi maka kama da jaruman Kasar Waje na Bolloywood. Ganin ya shiga Motarsa ne yana Neman Tada ita ya Fice Daga Gidan yasa ta tattara Hijabinta ta Zura da gudu bai da Tsammani kawai yaji Mutum a kusa da Kujeran mai Zaman banza,Kukan ta kawai yaji da Shesshekanta ya Dago daga saka ma Motar key ya sakarmata Dara Daram Idanuwansa masu cike da Sheki yana kallonta itama shi take kallo Tana mtse ido tana jan Hanci alamun kuka Duk da ba hawaye adonta nata sai Tsabar Shagwaba. Kallonta yake Cikin Salama da wani Sukuni Idanuwansa na bayyana yarda yayi kewarta sosai ammh Saboda kada ta Fahimci haka ya Hade rai yana Fadin"Ke miye haka..? Baki ga zan tafi wajen aiki bane kika zo kika tasani kina min kananun kukan ki na Fama ko..? Jin haka yasa ta kara Wage Murya ya saka kukamai kuka Harda Dora hannu a saman kanta Ido ya Waro yana kallonta Cikin mamakinta ganin fa sai kara Volume take yi yasa yace"Kin rainani ko..?Tukuna ma me akayi miki na kuka..? Jin haka yasa ta Dago Tana kallonsa Tana Sharan idon da ba Hawaye tace Cikin Tura baki tace"Ba kai bane....! Tafada Cikin Tabara da Sangarta Shagala da yayi da kallon Dan bakinta kafin ya kada kai yana Fadin"Uhm yarinyar nan kin cika Shagwaba Umma da Baffa Sun bataki..ni me ye namiki da zaki ce wani nine..? Inteesar najan majina kamar gaske tace"To ba kai bane..Kana Ta Fushi dani nayi ta kiranka baka Dauka ba na Tura maka sako ba adadi kaki kulani kuma..kuma! Tafada fada tana wani kara Goge Hanci kamar kuka Dariya ta kamasa ya kanne kafin yace"Ina jinki..kuma me..? Imran sarkin Laifi..? Inteesar Da ta Fakaici idonta ta Debi Miyau ta goga i donta saboda yaga da gaske take tunda na gasken yaki zuwa batasan yana kallonta ba Dariya ta kusa Subucemai acikin Ransa yace"Yaro yaro ne..Yaro man kaza..! Cikin Shagwabbiyar Muryanta tace"Kuma baka bari ina ganinka kafin na fito ka tafi aiki in kuma ka dawo da Daddare ne kana cikin Dakinka ni fa kuma na baka Hakuri kaki Hakura..? Yana Mirmishin Saman baki yace"Au ai kin gama naki Fushin ne ni na Dauka ba shikenan ba..? Fito da idonta yaga Hawayenta Tace"Ai nace kayi Hakuri fa..! Tafada Tana kara Tura baki Yana Danne Dariyansa yace"Ok naji..Yanzu kin Hakuran ne na Rika zuwa Wajen Sajidan..? Kallonsa Tayi kyam Ranta Tuni ya Baci Mood dinta ya Sauya kanta ta Kauda gefe ta Murgudamai baki ya ganta Sarai shiyasa ya Hade rai yana Fadin"In kika kara Juyamin baki sai na Bike Bakin yayi jini..? Am i ur Mate..? Saboda kinga ina Miki Dariya shiyasa Kika Rainani ko..? Tana shirin mgana ya Dakatar da ita da cewa"bana son jin Wata mgana..Bana son Raini ni bana daga Ciki yayyinki wadanda kike rainawa kina ma Sangarta yadda kikaga Dama Ina nan a Imran din da kika sani Wlh ban Sauya ba u better Behave ur Self kuma ma naje wajen Sajidan ke kin isa ki Hanani ne..!ke ce zaki bani Umarni ko ni ne zan baki..? Baibata Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin"Ni namiji ne Mijin Mace Hudu..Zan iya auran mata uku nan gaba Bayan Sajida kuma infact ma ke Matatace da zaki hanani zuwa wajen wata..? Yafada yana kallonta Saurin Sadda kanta tayi kafin Cikin cikin Sanyinta Idanuwwnta sun ciko da Hawayen gaskiya"Kayi hakuri bazan kara ba..! Sai ta bashi Tsausayi wani abu na yawo acikin Ransa kai ya kauda yana Fadin"Is ok..Tunda kin bani Hakuri nima na Janye Fushin..! Kallonsa ta dago tanayi ido Cikin ido Hawayen kishin Sajida suka Zubo mata Karamar Dariya yana Duba agogon Dake Daure a tsitsiyan Hannunsa yace'"Sai yanzu kukan gasken yazo..?bakya Bukatar saka Miyau bakin kii ko..? Kunya ta kamata ta Rufe Baki Tana yar Dariya Cikin shagwaba tace"Duk ba kai bane..! Nishadinsa ya kasa Boyuwa yace"Ni kuma..?laifi na baya karewa..Kedai Kazama ce kawai..! Yafada yana yar Dariya ganin Zata faramai shagwabanta ne ya nuna mata agogon Hannunsa yana Fadin"8am na kusa..Kada ki sakani na Fara abunda ban saba ba plz ki goge wannan Hawayen naki ki koma gida Zamu hadu in na Dawo wajen aiki..! Kallonsa Tayi kafin tace"alkawari..! Tare da Mikamai karamin yatsaanta bai Rike ba yadai murmusa yace"Cikawa..! Sai Lokacin Hankalinta ya kwanta ta Share Hawayenta ta Bude Motar ta Fito Lokaci Daya tana Rufomai Murfin Motar,Tana Tsaye a wajen Tana Dagamai Hannu har yayi Hon iro megadi ya Budemai get ya Sulala Waje,sannan ta koma Cikin Gida Cike da Wani Farinciki Tana shiga Falon Taga Ya yusuf da Anty Safiya suna karyawa Gaishesu tayi kafin ta shige ciki Anty Safiya na mata mganar Karyawa tace sai tayi wanka Lokacin Munari ta Farka Daga Barci in bata Farka ba ita zata tasheta. ***** Shikenan Fada tsakanin Inteesar da Imu ya kare suka koma kamar baya Yawancin sunfi mgana ta Test Messages,Tunda bai da wani ishashen Lokaci,waya sai Lokaci bayan Lokaci in Bukatar hakan ta taso. Suna Haduwa yawanci a Haraban gidan ko kuma aa kitchen in yaje Daukan Ruwa ko Zai Hada Tea ko Zai Dibi abinci Wani Lokacin kuma yanzu in yana Daki yana Bukatar wani Abu ita yake kira takaimai. Koda basu yi wata mgana ba They are ok Tunda suna ganin juna Koda yaushe sun dai yima Mama yaji sai dai suje da wuni badai da kwana ba Tuni Inteesar ta kusa kwshe kayanta Duka Zuwa Gidan Abba Mama bata isa ta Raba Kaunar Munari da Inteesar ba,Shiyasa bata Damu ba Tunda suna kusa kuma nan din ma Gida ne ba wanda ya kawo wani abu sai Munari Domin ita tasan komai Abba bai Fara zuwa Offife ba sai Farkon Wata Lokacin komai ya Daidata Harta Motar da sukayi Shawara da Imu zasu siya ma Abba da Sauran kudinsa da na Marigayi Nura zasu siyama Abba Mota mai rai da lafiya da Direban da zai Rika jansa batare da sun Fadamai ba sun fi so yaga komai kwatsam Karshen Wata nayi Daada ta Kira Duka ya"yanta ta Fada musu tana son ganinsu bazata mtsa sai da ya"yansu ba ammh wanda ke da Hali yazo,ta kuma ce Mami Tazo da Sajida Khamis yazo,Imran Daman suna Waya daya Kirata ta gayamai daman Wannan Lokacin yake jira ya shirya ma Hakan Mami Asma"u dataji labarin Ta Dauka mganar Khamis ne da Tarewar Sajida Lalle Lokaci yayi da zata Tauna aya Domin tsakuwa taji Tsoro sai Imran ya Raina kansa Sajida na makaranta Baffa ya Kirata yace in ba mtsala tazo Gida zasu da ita Dukku ne Daada tace taje,Tana jin haka bata tsaya wasa ba Ta Tattaro ta dawo gida Daman Damar nan take jira Tunaninta itama ya Tafi kan mganarta da Imran Allah yasa mganar Biki ne da Tarewa da sai tafi kowa Murna. Su Inteesar dai zasu fara Test Monday sukace bassu je ba,su aka bari agida Da Anty Safiya su Sadam su kadai suka Tafi sun bar iyalansu agida. Ranar Jumma"a Abba da Ya Yusuf da Sadam suka tafi a Motar yusuf din Imu yana Wajen aiki yace sai asabar da Safe zai taho Baffa Kabiru ma sai Ranar asabar yace zasu zo su Daddy ne chan su Abba suka iske su shi da Umma da Basheer Inna Bintalo ta iso ita da Inna Maimunatu wannan karan ba yaran kowacce ita kadai tazo,Sa"id ma Aranar da Daddare ya iso Daga Dutse. Imran sai Ranar asabar da Safe shida Sagir suka hau Motar Haya zuwa Dukku agida ya bar Motarsa *Shakira* 3/23/22, 12:02 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�15* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Basu isa da wuri ba,Sai wajen 12pm na rana duk da sun fito da wuri,Sagir dai nashi dan bi ne domin baima san da Tafiyar ba,ana gobe Tafiyar ya kirasa a waya yace mai ya shirya gobe Zasu tafi Dukku ya zata ma amotarsa Zasu tafi Imran din yace A"a saboda bai wani san hanya ba Yusuf ne yasan Hanyar sosai,infact ma bai yi niyyar zuwa da Motar tasa ba. Sagir kallon Imran kawai yake Ko da bai gayamai komai irin Mirmishin Dayake ta saki na kasan Lebe yasan na mugunta ne irin Mirmishin Imran naci Nasara shifa Bai taba ganin mutum mai sa"a kamar Imran ba Komai ya sama gaba sai yaga bayansa komai yace zai yi to tabbas Zai yi ne yana da kyawawan Halayya da ba kowa ke sanin haka ba sai kana Tare dashi,Mashin dinsa Halak malak ya mallakamai Sagir din Saboda ai ya Chanchanta shi Sagir din ma yaki amsa Daga Farko Imran din ya wurgeshi da key din yace in bayaso to ya Bada ita yadai san In Imran ya Fadi mgana baya sauya mgana Mashin dai ta Zama nashi sai dai shi yayi abunda yaga Dama da ita. Koda suka isa Tuni bakin Abuja sun iso,Hatta Khamis ya iso,Daman jiya da Daddare ya sauka a Abuja da Safe suka kamo Hanya Harda Sajida Umaima Tana gida Saboda makaranta. Imran bai yi wata Shiga ba kamar yadda ya saba haka yayi sanye yake da Riga da wando,Rigar mai ruwan kasa ce Mai Hasken wandon kuma Shima mai ruwan kasa ne sai dai yana Duhu sosai,Wando daga kasa ya Tsuke kadan Ya kamasa. Sun shigo Har falon Daada inda su Umma ke Zaune ita da Mami Asma"u da su Sajida dasu Sa"id da Basheer,Su Abba suna Dakin Daada tun da suka Shigo Sajida idanuwanta suka Kafe akanshi shi Wlh bai ma ganta ba yaga dai Uwarta wacce ko kallo bata isheshi ba Umma kadai ya gaisar Kadahan kadahan,Sai ya karisa wajen su Ya Yusuf suka gaisawa ta Hanyar yin Musabaha,Abun mamaki Da kansa yau ya mikama Khamis hannu suka Gaisa suna kallon Juna ido Cikin ido. Imran kallon kayi kadan yake yi ma Imran irin na Riga na gama Dakai shi kuma Khamis Kallon Au ka Tuba ne..?Irin dai dole dai ka dawo Hanya yaro. Daganan Dakin Daada ya Shiga ya gaida su Abba,Da Daddy sai Inna Maimunatu,Yana kallon Goggo Bintalo da Baffa Kabiru yaki gaishesu da Abba yayi mgana sai yayi Shuru ciki Ciki ya gaishesu kamar bai ganesu ba,Abun yayi ma Inna Bintalo Ciwo sai dai bata mgantu ba Kada yaron ya Zageta tasan Tsab zai iya Tunda bai da kunya,Baffa Kabiru kam bai Damu ba Domin yasan Daman yaron baya Darajasa kuma bai Dauke sa a Uba ba. Dakin da suka sauka wanchan karon nan suka kara sauka shi da Sagir wanka Imu yayi ya sauya kaya saboda yana jin Zafi,yazo da karamar Laptop dinsa saboda aiki akwai aikin da Wani Ma"ikacin su zai turo mai Daga gyagyadi branch yau din so yana Bukatar ya Duba shiyasa yazo dashi Wayarsa ya Dauko domin yaji karan Shigowar sako Kamar yadda Ya zata Intee ce. Tana Tambayansa ko sun issa Lafiya ya Tura mata da cewa eh suna Dukku,Daga haka ya maida wayarsa aljihu,agogon Tsitsiyan hannunsa ya Duba yaga lokacin Sallah ya kusa Daman ya Dauro alwala cema Sagir yayi alwala su tafi masallaci ba Musu ya tashi yaje yayi alwala suka Fita Tare koda suka fita duka mazan suna Waje suna alwala har da su Abba ya Hadu da Mami Asma"u a Falo bai ko kalli barayinta ba,Dariya yake cikin Ransa Domin har yana Hango irin yadda Zatayi in taji Hukunci da ya yanke akanta da ita da yarta. Gabadayansu suka Dumguma zuwa masallaci sai da suka Tsaya aka Tada sallar tunda sunje da wuri bayan sun idar suka nufo gida. Imran da shi da Sagir suna Baya sai Daga baya suka Shigo gidan Tun Daga Nesa ya Hango Sajida Tana Tsaye ko da bai sani ba yana da Tabbaci shi take jira zatayi mgana dashi Sanye take da wani material mai Santsi Dingin Doguwar riga ta yane kanta da karamin Bakim Vail kafarta Cikin takalmi baki sawu ciki a Fuskarta ta Rame sosai Idanuwanta duk sun Sauya Launi Sagir na ganinta ya Zunguri Imran yana Fadin"Ga Amaryan ka nan..! Ko kallonsa Imran bai yi ba sai ma kara Tamke Fuska da yayi kamar bai Taba Dariya ba Har suka kariso kusa da ita Sagir na Shirin Dakatawa Imran ya wuce Kamar ma bai ganta ba ganin haka yasa Sajidan da gabanta ke Fadi Saboda yadda Imran din yayi mata Kwarjini tace"ina yini..! Imran yajita ammh yayi kamar bai jita ba ya cigaba da Tafiyarsa Sagir Daya ga haka ya Daga Murya yana Fadin"Imu tana gaisheka fa..Don Allah ka Tssya..! Da kamar bazai Tsaya sai Wata Zuciyar tace ka Tsaya ai ba wani Sauran Rina Dake Tsakaninku. Cak ya Tsaya Lokaci Daya yana juyowa Hannuwansa ya Haarde Saman Kirjinsa yana kallon Sagir irin gashi na Tsaya sai yaya..? Sagir ne ganin haka yasa ya Kalli Sajida da kanta ke kasa jikinta ma ya fara rawa tana ta wasa da Kwalliyar Jikin Rigarta. Ya sanyaya Murya yarinyar ta bashi Tsausayi saboda yasan wacce Zata iya gaba da gaba da Imu ba karamar Jaruma bace Yace"Ki je ki sameshi in ba haka ba zai Tafi abunsa..! Daga haka ya wuceta da sauri kusa da Imran ya karisa daidai kunnensa yayi mai Rada"Plz ka saki Ranka She is ur Wife..! Sanda Sagir ya fadi haka sai yaji kamar ya Mangaresa da mari,sai kuma yayi Fuska kawai ya kara Hade rai ko kadan ba annuri ballatana Samun sukuni agame dashi Sagir dai Ciki ya shige yana Fatan kada Allah yasa Imran ya zabgama yarinyar nan Rashin Mutumcinsa. Gajiya yayi da tsayuwa ganin Ta na nan Tsaye bata ma tako ba,juyawa yayi niyyar tafiya sai gata ta kariso Salau Salau kamar mara kuzari aransa yace ji ta kamar wata ta Allah. Kanta na kasa bata son Hada ido dashi Tace"Ina yini..! Tafada Lokaci Daya gabanta na Faduwa,Saboda bata son kallonsa kwayan idonsa yana bata tsoro matuka yana saka taji duk wani Comfident dinta ya tafi indai tana gabansa gabanta sai Fadi yake in da Zai lura har rawan jiki dana Baki take yi alokaci Daya. Kallonta yake Daga sama Har kasa so yayi ya sakin mata Tsaki sai kuma ya fasa cikin Dauke kai da Dakuna Fuska yace"Lafiya..! Yafada yana kallon Fuskarta acikin Ransa yace irin Fuskar uwarta ya"yan nagada ba na haya ba. Gajiya yayi da tsayuwa yasa yace"Ammh kinsan dai ba wasa tsakanina Dake da zaki Tsaidani ki tasani agaba kuma kiki mgana ko..? Yafada cikin Kaushinsa kamar ko yaushe. Jim haka yasa ta kara Sadda kanta Tana Fadin"Dama..Dama! Wani Haushi ya kamashi yace"Dama What..?ke kinga ni ina da abunyi yanzuma Da kika ga na Tsaya Wlh ba wai domin darajanki bane ke har kin Isa..? Ba macen data isa ta sani ni Imran nayi abunda ban yi niyya ba Darajan Abokina kikaci..So in baki da Fada on my..! Bata bari ya karisa ba,Tunda taji mganarsa Cikin Kaushinsa kafin tace"Dama ina ta Kiranka a waya ne baka Dauka ba Daga baya kuma sai na Daina Samun ka..! Karamin Tsaki yaja kai Tsaye yace"Nayi Blooking dinki ne..! Batasan Sadda ta Dago rinannun Idanuwanta Tana kallonsa ba Cikin mamakin kalamansa Duk da tasan dai Ya kulleta ne ammh bata Zata zai iya gayamata haka ido Cikin ido ba. Ganin irin kallon Datake yimai ne yasa ya Daga mata gira guda Daya yana Fadin"Yes..Saboda bana son Wata mu"amala ta shiga Tsakanina Dake Infact ma bamu da wata alaqa..! Bai bata Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin"Nasan zuciyarki na Fada miki ba an Daura mana aure ba..? Auran Dan iska dan Shaye shaye bai Dace da Sajida Kabir Dukku ba Diyar Lauyoyi jikar Lauyoyi Diyar na gada ba na Haya ba..To u better wake up..kinga kuwa ni ban Dace dake ba..Ke ba Matata bace bamu da wata akala! Gabadaya kalamansa sun rikitata Bata san Sadda ta dago kanta Tana kallonsa ba sanda yace ita ba Matarsa bace Kara Dakuna Fuska yayi kafin yace"Eh nace bamu da akala ko muna Dashi ne? Nasan zaki ce to ko ba aure ai ni yar"uwarka ce u ara mad in kikayi Tunanin haka akaina ni Imran Wlh wanda keyi dani sai ma naga Dama Zanyi Dashi acikin Dangi ballatana Wanda basan da wanzuwarsu ba So plz and plz ki Rabu dani kada ki kara Kirana am not ur mate kada ki kara Kirana In baka ba Haka zaki san Oder Side dina! Tsaki yaja mai karfi yana Fadin"Rubbiish kawai..! Daga haka ya juya ya shige cikin Gida,da kallo ta Bisa Hawayen da suka cika mata ido suka zubo mata masu Zafi da Tsananin kaunar Imran Kuka Take so ta fashe dashi ammh Zuciyarta ta Chuse waje Daya Meyasa yace ita ba Matarsa bace ko ya saketa ne? Saurin dafe kanta Tayi jin ya sara mata da wannan Karamin Tunanin a Fili ta Furta"A"a bazai taba sakina ba..Bazai sakeni ba bazai sabama mganar Baffa data Daada ba..Wlh ina sonsa inajin kamar in na Rasashi Zam iya Mutuwa..! Take Fada tana Sharan Hawayenta kamar Wata Tattabiya soyyaya Ta sakata Zatayi hauka kafin ta Dibi Sauri Zuwa Cikin Gida. Tana shiga Taga ana ta cin Abinci Mami Asma"u dake Faman nemanta ta Tsareta da ido Cikin Tuhuma Tana fadin"Ina kika shiga Tun dazu..!? Cikin kame kame tace"Na fita amsa waya ne Mami..! Tafada Tana kallon Imran Dake kusa da Yusuf suna cin Alalan da Baba asabe Tayi a Filet Daya,Ko barayin Datake bai kallah ba kansa na kasa ya bada natsuwasan kan abun ke gabansa. Hararanta Mami Asma"u tayi Tana Fadin"Waya ko..? Ita kuma wannan ta waye..? Tafada Tana Daga mata wayarta da ta barta gefen Mami Asma"u din bata sani ba. Kanta ta Sadda kasa batace komai ba Hankalin kowa baya kansu Ba wanda ma yabi ta kansu su Abba suna Dakin Daada achan suke cin nasu abincin. Mami Asma"u kure Sajida da ido take yi,Tana Nazarin wani abu acikin Ranta Taga shigowar Imran kuma ba Dadewa Taga Sajida ta shigo Allah yasa ba ajinta ta Zubar taje tayi mai mgana ba in ko hakane da sai taci Uban Sajida in ta kuskura tayi mata wannan Shirmen. Abinci tace tazo taci bata cikin good Mood yasa tace bazata ci ba wucewarta Tayi Dakin da suka Sauka ita da Mami Asma"u ranta duk ba Dadi Mami Asma"u ta bita da wani kallon yarinyar nan Tana Hauka ne..? Ba a dauki Lokaci ba kowa ya gama cin Abincinsa nan mazan suka Zauna suna Hirarsu Imu ma na cikin su sai dai baya mgana Sai dai yana jinsu kawai in abun mgana ce aka Sako sa sai da ya gyada kai ko ya Rage Daure Fuskar Wayace a hannunsa Mgana suke da Intee Tana mai shagwaban gida ba kowa duk ba Dadi tana Missing dinsa,Sakar mai da kasala Take duk da ba Waya suke ba Massages ne bai biye mata yace ta wuce taje ta Dauki Littafanta Tafara Karatu baya son Shirme. Suna nan Zaune sai ga su Abba sun Fito Dukkansu sun taso Tsohuwa Daada agaba Tana Tafe sanye da Hijabi mai ruwan kasa,Bai da Tsawo sosai Carbi ne a Hannunta tana ja Inna Bintalo da Inna Maimuna suna Kafada kafada da ita sun sakata a Tsakiya. Kan kujera suka Taimaka mata ta Zauna Gabadayansu suka Zauna a kasa Umma Dake saman kujera ta Sauko ta zauna akasa,Daman Mazan duk suna Malale zaune ne saman Cafet din Daya malale Falon. Mami Asma"u dai Bata sauko ba sai ma kara gyara Zama datayi akan kujeran ta kara gyara Zaman Siririn Gilashin Dake idanuwamta Khamis na gefenta a kasa yazauna wajen Kafafunta. Tuni Falom yayi Tsit sai Sautim Muryoyin su Sa"id da suke ma Daada Barka da Fitowa amsawa take cikin kulawa,Tana Bin Kowa da kallo Daya bayan Daya sai ta sauke kallonta kan Mami Asma"u wani abu na cin Ranta Uhm Lokaci yayi da Asma"u zata gane Kuskuranta Juyawa tayi Tana kallon Baffa Kabiru kafin tace"Ina Sajida..?banganta ba ko bada ita kuka zo ba..? Kai ya girgiza mata kafin ma yace Wani abu Mami Asma"u ta yi Caraf tace"Da ita muka zo mana Daada..Yanzu ta shiga ciki..! Daada ta gyada kai kafin tace"Jeki kirata..Domin wannan Haduwar ta Shafeta sosai..! Mirmishin Saman baki Mami Tayi Damam ai tasan mganar Sajidan da wannan Tsagerin yaron nan Lalle kuwa yau Zata nuna ikonta a Mtsayinta na uwa,Sai ta ja Imran a kasan Kafarta bai isa yaja da ita ba. Tana shiga Dakin ta iske Sajida kwance Tana Hawaye jin muryanta a saman kanta ne yasa tayi Saurin Share Hawayenta ta mike Zaune tana kokarin Kauda idonta kada Mamin Ta gano Halin Datake ciki. Kallon Tsab Mami Tayi mata kafin Tace"Wai Sajida kukan Uban me kike yi ne Tun dazu..? Sajida tace"Kuka kuma..? Ni ban yi kuka ba Mami..? Tafada tana kokarin mikewa ta kaucema Kaifaffun Idanuwan Mami Asma'u Daga gano yanayinta. Mami Ta wani kalleta a karkace kafin tace"Kina Zaton ban san kukam me kike yi bane..? Uhm yaro man kaza..Dazu fitan da kikayi wajen Dan iskan yaron nan kikaje..! Sajida ta Dago kanta cikin mamaki ta Bude baki Zatayi mgana Mami Ta Dakatar da ita lokaci Daya Tana Daga mata Hannu tana Fadin"To bari kiji na Fada miki in ma Kina kokarin Saukowa ne ki yarda da auransa Cikin Sauki ni Asma"u uwarki ban yarda ba ko Zan amince da wannan auran ba yanzu ba sai na ja Yaron nan akasan Kafata ya duka yana kuka yana Bani Hakurin Rashin Da"ar da yayi min sannan kuma yana kuka yana Rokon na bashi ke sannan zan iya yarda ma ki Zauna dashi ammh in ba haka ba Duk wacce Za"ayi sai dai ayi bazan bari ki Zauna da wannan Dan iskan yaron ba.!. Tafada cikin son Tabbatar da mganarta bata damu da yanayin Sajidan ba ta Fice Tana Fadin"Ki fito Daada na kiranki..! Sajida Kuka ya kwace mata Mami bata son Imu shine Rayuwarta ba Wani irin so mai Tsanani ne ya kamata alokaci Daya tana jin kamar Zata Mutu in ta rasashi Wata Zuciyar tace to ke sai ki bari ki rasashi..Ina bazata taba bari haka ya Faru ba Imran mijinta ne kuma Dole tayikomai Saboda ta Dauwama Dashi Wannan karon zata Dakatar da Mami Zata Fadamata gaskiya She Love Imran Tana matukar sonshi kuma Zata Zauna dashi a duk yadda yake so ta kyaleta don Allah kada ta Shiga Rayuwarta ta lalata mata Tiolet ta shiga ta wanko Fuskarts tazo ta Tsane da mayafinta kana ta Fito Falom ita ake ta jira ba"a Fara Taron ba Tana Zama gefen Dan"uwanta Daada ta kalli Yusuf Tana Fadin"Yusufa Bude mana Taron da addu"a.." Ba musu ya gyara zama ya Bude Taron da addu"a aka shafa sannan Daada tayi gyaran murya ta Fara mgana..! "Da farko dai ina yi ma Duka ya"yana da jikokina da suka Taru anan wajen barka da zuwa..nasan kun baro duka Tarun ayyukan ku ka amsa kirana Naji Dadin haka Allah ya saka Muku da mafificin Alheri ya raya muku Zuru"a ya baku ya"ya wadanda zasu ji kan ku kamar yadda kuke jin kaina..! Gabadaya aka amsa mata da Ameen Ameen. Kafin ta dan yi shiru kafin ta Cigaba Cikin muryan tsufa"Dalilin Dayasa nace ina son ganinku duka da wasu Daga cikin yayenku Mgana ce Daya zuwa Biyu..na farko mgana ne kan Imranu gashi chan Dan Wajen Malami sai Sajida Yar wajen Kabiru..Kafin naje gaba a mganata kowa anan wajen ya Shaida Auran dana saka aka daura shi Wata Daya Daya gabata a garin nan tsakanin Imranu da ita Sajidan ko..? Kowa ya gyada kai alamun hakane Daada tana Jan Casbahanta tacigaba da Fadin"Alhamdulillah kuma kowa anan yasan abubuwan da suka yi ta Faruwa bayan an Daura auran da kafin a Daura Inda Asma"u gatanan matar Kabiru ta rika nuna rashin Amincewarta tare da Diban albarka kala kala ammh duk na kauda kai bam ce komai ba Saboda bai kamata nayi mgana alokacin ba Kuma ni miye nawa..?ko me zan ce tunda agaban Mijinta ne Gashi nan kabiru bai Tsawarta mata ba kenan shima ya yarda da duka abunda ta Zauna akai bai so hadin Zumunci Tsakanin jininsa da jinin Abubakar ba..! Tafada Tana dan Sauke Numfashi Kowa afalon yayi shiru yana Sauraranta Baffa Kabiru ya dago kansa ya kare kansa Daada ta wurgamai wani kallon Da Dole yayi Shuru da bakinsa Mami Asma"u kuwa na gefe Kafa Daya kan Daya tana karkadawa alamun tana jiran kowa wanda yace kule sai tacemai Chass..! Daada ta cigaba da Fadin"a lokacin da nayi Tunanin wannan Hadin har ga Allah Zuciyata Daya ina ganin cewa hakan shi Zai kara mana Dangom Zumunci da son junanmu sai Daga baya na gane nayi kuskure kuma nayo Hadi inda bai kamata ba na manta Asma"u ita ke jan Ragamar Rayuwar gidan Kabiru tamkar itace mijin shine Matar baya iya Zartar da mgana sai abunda tace,Sannan ko mganace ta Dangi bazai iya mgana ba sai da yawunta ko da amincewarta Shiyasa data nuna bata amince ba shima ya Goyi bayanta..To Alhamdulillah na Taraku ne anan saboda na gyara Kuskurena..Mustapha ina son ka bama Danka Imranu auran Diyarka Maryama mai sunana ba sai gobe ba yau din nake son adaura wannan auran indai kaima ka amince saboda ina Tsoron nuna isata akan ku Alhalin ban isa ba! Gabadaya Falon sai kallo ya koma Wajen Daada ita kuma ko ajikinta Sagir ya kalli Imran alamun How comes,shi kuma ya Dagamai gira Khamis da yayi mutuwar Zaune ya Dago yana kallon Daada lokaci Daya ya koma yana kallon Imran wanda ya Cije mai baki ya Dagamai girarsa Duka Biyu irin kaga nawa ikon..?to yaya Zata zama takan ne..? Gabadaya kowa sai mamakin Daada yake yi,Yusuf ya kalli Imran ganin ko ajikinsa ya juya yana kallon Abba da Daddy da suma suke kallon Daada aransu suna Tunanin Riikicin Tsufa ya Fara Taba Daada. Daddy ne ya bude baki zai yi mgana Abba ya girgizamai kai,Baffa Kabiru kuwa bai ce komai ba Domin ya kasa Dora komai akan Mizani.. Sajida kuwa allah ne kadai yasan Halin da Zuciyarta take ciki gani take kamar ta Kurmance bataji Da kyau ba Mami Asma"u kuma mamakin yadda Zaton ta ya sauya take yi anya Daada nada Hankali kuwa..? Abba ne ya Dago yana kallon Daada Cikin Sanyin murya yace"Daada bawai ina ja da mganarki bane..ko kin manta cewa Imran ya auri Sajida kuma Inteesar Shakikiya ce ga Sajida Daada duk da ba Haram bane ammh ana barin Halas ko dom kunya..! Karamin Mirmishi Daada ta saki kafin Tace"Na sani..Ina sane da komai..Ai ba aure Tsakanin Imranu da Sajida a yanzu..! Gabadaya mamaki ya hana kowa Mgana Inna Maimunatu ce tace a wannan karon"Daada bamu gane kan mganarki ba..! Daada ta Dago ido Tana Fadin"Ku juya amsarku Wajen Imranu..Kai Imranu gayamusu abunda kazo ka Fadamin..! Imran ba wani Tsoro ko Fargaba ya Dago kansa yana kallon yadda gabadaya Idanuwa suka koma kansa Ya gyara Zama yana kallon Idanuwan Mami Asma"u da Sajida da ya kusa Fadowa saboda Firgici da Tsoro. Cikin Kaushin sa yace"Na saki Sajida Tun Washegarin Ranar da aka Daura mana Aure da ita..! Ya fada kai tsaye Lokaci Daya yana Fito da wata Takardan a Aljihun Wandonsa ya mikama Yusuf Dake kusa Dashi Wanda yayi Jagale yana Bin Imran din da kallon mamaki. Kalamansa sun Daki kowa afalon banda Daada Data san mganar. Ammh Firgicin yafi bayyana kan Fuskar Baffa Kabiru,Mami Asma"u da Sajida wadanda Tsabar Rudani ko Motsi sun kasa. Daada ta Umarci Yusuf ya Warware Takardan ya karanta afili kowa yaji Cikin Sanyi jiki ya Bude Takarda ga Hand Writting din Imran nan ya Rattaba Rubutun kamar haka. *Ni imran Abubakar Malami na Saki Matata Sajida kabir Saki Daya Saboda bana sonta kuma bana som na cigaba da Zama da auranta na kwari kaina Daman chan Nayi Biyayya ne kan Mganar Abba Daya Gindayamin Umarni Sai dai Umarnin Auran kadai ya bani ba Umarnin kada nayi Sakin ba..Allah ya bata wani mijin Agaba wanda baya Shaye shaye daidai da ita..* Kowa sai Shuru ba bakin mgana Musamman Abba da Daddy da suke kallon juna cikin Tarradadi,Abba Imran yake kallo Ransa na kuna da Baci sai dai ya Tabbata ko kashesa zai yi bazai Taba Sauya Ra"ayi ba sai yanzu ya gane cewa Shurun da Imran din yayi Lalle ya shammacesa. Daada ta Umarci Yusuf daya miko mata Tadardan ya mike ya kaimata ta karba Lokaci Daya tana Mikama Baffa Kabiru da gabadaya Bacin Ran wannan Tozarcin da Imran yayi mai ya Lullubesa. Mikamai Tayi Ya karba Cikin wani yanayi kafin yayi mgana ta Rigasa da cewa"karbi Takardan Sakin Sajida..Ka mikama Matarka..Tayi hakuri Bisa Rashin Daidai da muka mata tun Farko Daman tace indai Tana Raye ba wanda ya isa ya Tabbatar da wannan auran to gashinan Imranu din ya Yanke komai shiyasa dayazo ya gayamin ban damu ba Duk da naji Ciwon Abun sai dai hakan yayimin Daidai Tunda dai an yi muku abunda kuke so Ba Damuwa in wani yaki ka da wuni wani da kwana Zai soka Ga Mustapha nan na Roki alfarman ya aura masa yarsa in shima kuma bai Amince ba Wlh bazan ce Dole sai an Bi Umarni na ba..! Tafada Idanuwanta na kawo kwallah Gabadaya sai jikin kowa sanyi Wato Daada Ranta ya baci da Baffa Kabiru da Matarsa sai yau take Dafasu Cikin Ruwan sanyi. Baffa Kabiru ya ji bakinsa yayi nauyi yama kasa mgana Kamar zai yi mgana sai ya kasa Daada ta kalli Daddy tana Fadin"ka amince ko baka Amince ba..?Salaha kema kina da Hakki kan wannan mganar..? Khamis Da yaga Wankin Hula zai kaisa ga Dare yayi Zaraf zai yi mgana Daada ta Dakatar dashi da Fadin"Kada kace komai..Inteesar tace bata sonka agaban kowa da kowa saboda haka baxan mata Dole ba..Ni Maryama na Riga na Cire bakina kan ya"yam Kabiru Duk Abunda iyayenku suka Zaba muku Daidai ne..! Kansa ya Sadda Hawaye sun cikamai ido ya kasa mgana Daada ta Dawo da kallonta kan Daddy tana Fadon"Ko kaima bazaka bashin ba..? Da Sauri Daddy yace"Ni na isa Daada..? Na amince Dari bisa Dari Imrana kamar Da yake a wajena Dashi da Basheer da Inteesar Wlh basu da maraba..Mganar Salaha kuma bata da Mtsala Daada ita din mai Umarni da duka Mganata ce ko mganarki..! Yafada aransa yana jin Dadi duk da Sakin da imran yayi ma Sajida bai ji Dadi ba ammh yau kadai zai Rama mganar Mami Asma"u Datace Daada Tayi sonkai Dayake mgana shi Zai iya bashi yarsa ce to yau Zata gani kuma Za"ayi agaban idonta. Umma ma baki ta Bude Tana Fadin"Daada ni ban taba ja da mganarki ba..Imran Mutun ne kamar Kowa Ina Taya autata Murnan Samun Gwarzon Namiji kamarsa..! Tafada cikin som Turama Mami Asma"u Haushi Wacce take Zaune ita da yarta kamar Mutum mutum. Daada ta saki kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Masha Allah naji Dadin haka..! Baffa Kabiru ta kallah kafin tace"Bayan Sallar La"asar nake son ku Daura auran..! Khamis ya zaraf Cikin kunar rai yace"Daada kiyi Adalci mana..Taya Zaki aura mata wanda baya sonta kuma Da kikace tace bata sona shi tace Tana sonsa ne..! Daada bata nuna Damuwa ba tace"Mustapha Kiramim Maryama ka Tambayeta Zaka aura mata Dan"uwanta Imran abunda muka ji Daga gareta dashi Zanyi Amfani..So nake na goge kalmar Rashin aldacin da ya"yan Baffa Kabiru ke jifana dashi su da iyayensu. Ba wanda yayi motsi Daddy ya Dauko Waya ya Kira Inteesar ta shiga ta Fara Ringing da Bugawar zuciyar wasu Sajida Mami da Khamis Imran kuwa ko ajikinsa bai Damu ba yasan ko Intee ta amsa ko bata amsa ba shike da Nasara yau din nan. *Shakira* 3/23/22, 21:51 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�16* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Inteesar da Munari suna baje a Falo a kan Cafet din Daya yi ma Falon kwanya Littafansu suka baje suna karatu Saboda test din da zasu fara Ranar Monday da farko Hirar su suke sha Da Anty Safiya bama su fara karatun ba sai da Imran yace mata Taje tayi karatu kana ta mtsama Munari ta Dauko musu Littafan suka Fara Hankalinsu ya tafi kan abunda ke gabansu bama su ji kiran Wayar Inteesar da Daddy ke yi ba sai da ta katse ya sake kira kana Munari taji ta Dauko Wayar tana Fadin"Besty kinga Daddy nata kira bamu ji ba..! Inteesar na Duke da Biro a Hannunta Tana Rubutu cikin wani karamin Littafi kai Tsaye tace"Dauka Sakata a Speaker! Ba musu munari ta Daga Kiran ta sakata a amsa kuwwa ta ijiyeta anan Tsakiyarsu dukkansu suka Hada baki Wajen gaida Daddy bayan yayi Sallama. Daddy ya amsa cikin Sauri yana kallon Daada Data kafesa da ido Cikin Gyara Zama da mgana mai muhimmanci Daddy yace"Intee kina jina Dakyau..? Cikin Mirmishi tace"Yes My Hero Dad !Tafada cikin barkwancin da suka Saba Daddy bai biye mata ba yace"Tambayarki zan yi kuma ina so ki Fadamin gaskiya kin ji Intee..! Daga ita Har Munari sai da suka Dakata da Abunda suke yi suna sauraran Daddy Intee cikin Wani yanayi Lokaci Daya gabanta na Faduwa tace"Insha Allahu Daddy..! Kai Tsaye yace mata"Daada ce ta Umarceni da bama Dan"uwanki Imran auranki..Ammh na Tambayeki ko kin Amince da hakan..? Daga ita Har Munari ido suka Fiddo Waje Cikin mamakin kalaman Daddy Intee Sai taji kamar bataji da kyau ba Tana Kifta ido kamar yana gabanta Tace"Daddy me kace...? Wani Dan"uwan nawa..? Ya imu..? Tafada cikin rawan baki Lokaci Daya Tana kallon Munari Data Washe baki Tsantsan Farinciki ya Cika mata Zuciya na ganin wannan Ranar Intee da Ya Imu as a couple Boyayyiyar Soyayya Zata bayyana kanta don Ubanta ko taki ko ta so. Inteesar kuwa yanayin Datake ciki Allah ne kadai zai iya Fassara yanayin Sai kuma Ma"abota soyayya yayinda sukaji Labarin mallakan Abun da suke so Zuciyarta ta cika da Haske Farincikin da bata Taba Zato ba ko Tsammani Ya Imu fa shi zai zama Mijinta kai Daada ta Biyasheta Mijinta fa Ya imu..? Gabadaya bata son idanuwanta ya cika da kwallah ba sai da suka Zubo Munari ta zungureta alamun Tayi mgana Daddy naji,Domin kowa yayi Shuru Daga chan bangaran ana jiran amaar Inteesar Daada kuwa bata Damu ba Tana da kyakyawan yakinin ba Macen data kai Macen da Zataki Imranu karyanta shi kuwa Imu sai da aka Kirata ya samu Faduwar gaba To yanzu in tace bata son sa fa? Sai Daada ta aura ma Khamis ita Tuni yaji Duhu ya mamayemai ganinsa Wata Zuciyar tace ka manta Sagir yace Tana sonka,Kuma in bata sonka meyasa take Fushi Dakai saboda kace zakaje Wajen Sajida? Daddy ne dayaji Shurun yayi yawa yayi gyaran Murya shima acikin Ransa yana da Full Confident Intee Tana Ra"ayin Imran kodaga yadda Take yawan yin Zencensa Lokaci Bayan Lokaci Umma ma addu"a take acikin Ranta Allah yasa Inteesar ta amsa Domin wannan Hanyar ne kadai Zasu maidama Mami Asma"u martani Sannan ita ai tayi ma Intee sha"awar Yaron Tsayayyen Namiji dazai iya Rike gidansa a kowani Hali Sannan ta Hango Dacewarsu Tun ba yau ba kowa sai addu"an ta amsa yake yi barim ma Yaya Yusuf Sagir dai yasan Komai ma zai tafi kamar yadda yake Fata Inna Bintalo ne kadai Ranta a Hade Tunda yar Fadan Mami Asma"u ce wacce Ke Zaune kawai kamar kankara ya Daskarar da ita Sajida na gefenta Tana Rafzan kuka Khamis kuma kansa na kasa Idanuwansa sun yi jajir ya rasa ma a wata Duniya yake. Munari nata Zungurin Intee tayi mgana Taki yi tama kasa cewa komai kunya da Farimciki sun Lullubeta Dadday yace"Inteesar ke fa muke jira da Abunda kika ce zamu yi amfani..,! Inteesar ta kasa mgana kunya take ji Munari na ganin haka tayi Zaraf tace"Daddy bazata iya mgana ba Wai tana jin kunya gatanan Tana ta Rufe ido Tana Dariya Wlh tana son shi Daddy shima fa Ya Imu yana sonta soyayyar munafunci suke yi ba wanda yasani suna waya kuma su yi ta turama juna Messages na kalaman soyayya I miss u ina son ganinka don Allah Daddy iz not a Love? Daddy da Dariyan Farinciki dana kalaman Munari suka sakasa ya amsa da cewa"Na love Daugther...! Gabadaya su Sadam sai da suka Dara Imu mamaki ya cikashi Lalle yarinyar ta Rainasa wato munari ta na nan Tana Lura da duka Motsinsa Tana Sakamai ido har cewa ma take suna Munafunci ko Lalle jikinta na mata kyaikyayi ne kuma shi kowa sai yace Yana sonta shi yaushe yace yana wani Sonta? Intee Dagachan bangaran ta fizge wayar Daga Hannun Munari ta kashe Tana Hararanta Lokaci Daya Tana Fadin"Munafuka..! Munari na Dariyan Farinciki ta Mike Tana Rawa Lokaci Daya ta na Bude shokki tana Fadin"Intee Amarya oga Imu da kansa kai Ranar akwai shagali! Hararanta Inteesar ta karayi Tana mamakin yadda tasan suna waya da Ya imu Munari tayi Dariya kafin tace"Uhm ai na Dade da gane komai yarinya..Kuna son juna ammh ku kan ku baku sani ba..yanzu ai sai ku bayyana ma juna Tunda zaku zama ma"aurata ni bari naje na Fadama Anty Safiya ta fara shi ZAmu sallama ya Imu kowa ya Huta..! Da gudu ta kwasa zuwa Shashen Anty Safiya Tana kwalamata Kira Daga jin yadda take mgana Zaka hango Tsantsan Farinciki a tare da ita ta bar Intee zaune ta kasa tashi Jikinta yayi mata wani sanyi In ta tuna Imran kadai sai Tsigar jikinta ya tashi Wata Xuciyar tace me ya faru a Dukku da Daada tayi wannan Tunanin? Ko dai Ya Imun ne yace yana sona..?kai Ya Imu bazai ce ba Tunda nima bai Taba Fadamin ba keman gaskiyan Munari ne muna son juna This is a Love bamu sani ba..? Wata zuciyar tace mata to ya aureki ya makomarsa shi da Sajida..!? Tuni taji komai ya Tsaya mata Farincikinta ya gushe Allah na gani Tana matukar Kishin Sajida ko Sunanta ta Tuna amtsayin Matar Imran sai taji kamar ta saka kuka. Achan Dukku kuwa Wayar na katsewa Daddy ya Dago yana kallon Daada kafin ma ya samu Zarafin mgana ta rigasa da cewa"Me muke son ji..? Ta bakinta ai mun ji komai Daga bakin mai sunan Autana..Sannan ita amsar mace Daman Shuru ne Mganar suna son juna Gaskiya ne Domin nima na Dade da ganin Alamun haka.! Tafada Tana kallon Imran daya Dakuna Fuska aransa yana fadin"Lalle nema Daadan nan to Datake kallo na dawa take? Falon yayi shuru Daada ta cigaba da mgana"Mustapha ku fara shiri..Malami baka ce komai ba..?kuma bana son naji kayi ma Imran Fadan abunda yayi duk da ba bamai kyau bane ammh Allah ya Hallata Saki kuma yayi shi a gabar Daya dace gabar da muka samu Masalaha..! Abba kansa na kasa yace"Shikenan Daada mu masu bin Umarninki ne Da dukkan Abunda kikace..Allah yasa mu Kulla alheri..! Yafada yana kauda kai Daga kallon da Baffa Kabiru ke binsa dashi kunya yake ji Wlh Imran ya basa kunya sosai da abunda ya aikata ammh bashi da ta cewa Daada ta mara mai baya. Daada ta gyara zama Tana Fadin"Yau fa nake son a Daura auran nan ga ya"yanku nan zasu Taya ku shirya komai kuma bana son bata Lokaci nan da Wata Daya nake son ayi Taron Tarewarta Ayi komai a gama cikin Lokaci..! Daddy ne ya karkace Kansa yace"Daada sai naga ko abar Daurin auran zuwa gobe ne..! Kinga yamma Tayi kuma ko Goro da dabino bamu siya ba da zaki mana lamini zuwa gobe da safe karfe Tara na safe sai a Daura auran zuwa 10 ko 11am na safe kowa ya Dauki Hanyar inda ya fito ko ya kukace.? Yafada yana kallon su Abba da Baffa Kabiru wanda yake kallonsu kawai a bai ce ba,Inna Maimunatu tace"Eh hakan yayi Daidai daada..kiyi Hakurin Goben sai a Daura da yau kuma da goben duk Daya ne a wajen Allah..! Daada ta jinjina kai Tana Fadin"Shikenan...Kai Kabiru..? Tajuya bangaransa Dago kansa yayi yana Fadin"Na"am Daada..! Daada tayi Mirmishin su na manya kafin tace"Naji tunda muka fara wannan zaman bakace komai ba..? Kai zaka biya ma Danka Imranu Sadaki ko..? Tafada Tana tsareshi da ido Cikin Rauni da wani Takaichi ma yake kallon Daada Bai samu ma Zarafin mgana ba Mami Asma"u ta Mike da karfi kamar wata mahaukaciya Sabon kamu,Shock din Daya Riketa sai alokacin ya Saketa ta kara Tabbatar ma kanta Daada ta gama Tozarta ta Imran ya gama Tozarta yarta ya gama Wulakantata Saki..?ko Tareewa batayi ba auran da ko wata Daya bai cika ba Shine za"a yi ma yarta wannan Sakin Tozarcin da wulakancin. Daada ta kallah Ido na cikin ido tafara Fadin"Wlh ba"a isa ba..Ba wanda ya isa..Ni Asma"u aka shirya a Tozarta..Asaki ya'ta ko wata batayi da aure ba sakin Tozarci da wulakanci Sannnan agaban idon mu Daada kike cewa Baban Sajida ya sake biyama Wanchan mara Mutumcin yaron Sadaki..? Kai mustapha harda kai Ashe haka zaka ma Dan"uwanka ko Daada tace zata aurama yaron chan Yarka saboda Baban Sajida bazaka hanata ba? Kai kuma Malami Daman au nasani D'anka ai ya gagareka Duk Abunda yaga Dama shi yake yi ba kuma wanda ya isa yace don me to Wlh bazata sabu ba Bazan yarda akan Wannan al"amarin sai na shigar da ku kara akotu Wlh sai an bima ya'ta Hakkinta..! Ta Karishe Fada Rauninta na Bayyana sai kuma ta fashe da kuka Tana kara Fadin"Wlh bazan yarda ba..Wlh bazan yarda ba..! Take Fada Tana kuka har Gilashinta na Fadi kasa bata sani ba. Daddy ya dago yana kallonta Cikin mamaki yace"wazaki kai kotu..Asmaa'u.? Mami Asma"u ido na cikin ido take kallon Daddy da Jajayen idanuwanta Tace"Daada zan kai kara Kotu..Sai kuma wannan Tsagerin yaron.Duk Abunda ya Faru saboda ita ne Tsohuwa mai sonta kanta kawai ai ba Malami da Mustpaha kika Haifa ba Harda Baban Sajida meyasa baki nuna adalaci a kansa..? Kin cika som kai kuma baki da adal.! "ASMA"U.......!! Bata karisa ba Baffa Kabiru ya Dakatar da ita da karfin amon Murya yana Tsaye ne Ransa na Tafasa da abunda ya Faru da kuma kalaman da Ma"u take jifan Daada dashi ai duk Lalacewar Uwa ai uwa ce Mami Asma"u bata Dagata ba ta Cigaba Da Fadin"Bazan yi shuru ba..Wlh bazan bari rashin adalci wannan Tsohuwar ya Rugamin gida da Farincikina ba..! Wannan karon Daddy ne ya Mike cikin Fushi yana Fadin"Kar ki kara kiran mana sunan uwa kice bata da adalci..Uban waye mara adalcin in bake ba? Adalci me kike so Daada Tayi miki banda wanda tayi miki..! Inace anan wajen agaban kowa da kowa kikace sai bayan ranki wannan auran zai Tabbata kuma yau an cika Miki Burinki ga yar naki nan a gabanki an warware komai sai me..!? Nace sai me ? Bayan wannan adalcin kuma wani adalci kike so..? Da kike Fadin Na yarda zan aura ma Imran Inteesar saboda ke sai naki yarda..? Miye aibunsa..? Jini nane dan Yayana Malami sai na gujeshi Saboda Rudin Duniya..? Ko kin manta Zaman mu na karshe da nayi mgana kan Hukuncin Daada cewa kikayi in adalci ne ni na bashi yata mana..?kin manta..? To ni ban manta ba shine yau na nuna miki adalci nan In kin Hanashi yarki bashi zai hana wani Uban ya Dauki tashi y'ar ya bashi ba nama Sauya mganata yau ba sai gobe ba zan biyama Imran sadaki na Dauramasa y'ata in kin isa Asma"u muga Barikin sojoji gabadaya ko kuma muga Duka kungiyar Lauyoyi acikin Gidan nan mara Mutumcin mata wacce batasan ana Raga mata ba..! Ya karishe Fada yana Sauke Numfashi Daga gani Ransa ya riga ya gama Baci Umma ta saki karamin Tsaki a Fidi ta Furta Allah ya waddan naka ya Lalace. Mami Asma"u idanuwanta sun Rufe Da kalaman Daddy cikin Fusata tace"Au haka kace..?to bismillah shege ka Fasa..kuma kada ka kara cemin mara Mutimci ai mara Mutumcin kun santa gata na...! Bata kai ga karisa mganarta ba Baffa Kabiru ya karisa gabanta ya Daga hannu Zai kai mata mari cikin karaji yana Fadin"ASMA"U...! Daddy ma ya yunkuro da Inna Maimunatu Ransu ya gama baci sai dai Daada ta Dakatar dasu Cikin Daga Murya tace"Kul..Kada wanda ya Tabata..Asma"u bata da Laifi ai ban Haifeta ba Laifin na wajen Kabiru shi da na Haifa bai nuna mata Ina da Wata Daraja ba duk Abunda Tayi shi ya bata Dama..! Daada ta Fada sai ga Hawaye kuka Shabe Shabe. Ran ya"yanta ya baci Hatta da Abba Harda jikokinta irin su Basheer da Sadam suna ta fadin wannan ai rashin Mutimcine gasikiya Baffa Kabiru ya gyara Rayuwarsa.. Inna Maimunatu na Huci tace"Gaskiya Yaya kabiru ka saki wannan matar taka ba matar kwarai bace ban ga Dalilin da zai saka igiyar auranka ta Cigaba da Zama kan wacce ta Zagi Daada ba kuma ta sakata kuka ba! Khamis Dake duke yana ganin an kawo wannan gabar ya Mike da Sauri ya isa gaban Daada ya Duka yana Fadin"Don Allah Daada kiyi Hakuri ki Yafe ma Mami..! Daada na Hawaye ta Kallesa tana Girgiza kai Lokaci Daya Tana Fadin"Batamin komai ba..Wlh ban Taba Rike Asma"u ba ko Zagina Datayi ai Tayi Daidai kabiiru na Haifa ba ita ba..In iyayenta ne ai bazata Zagesu ba..Daman ance dan kuka ke jama Uwarsa Zagi ni Ubanku yajamin da duk Abunda ya Faru..! Ta karishe Fada tana kara Saka Kuka Daddy jikinsa Har rawa yake yana Fadin"Yaya kana gani fa? Agaban i don ka Ta Zagi Daada ta sakata kuka Kana Tsaye baka Dauki wani mataki ba..? Baffa Kabiru ya Runtse ido yama rasa Madafa bayan Asma"u zai bi ko bayan Daada Tabbas an bata ma Asma"u sai dai bata kyauta ba abundaa Tayi Idanuwansa ya Bude yana Kallon Mami Asma"u cikin Kaushin murya yace"Ma"u ki Duka ki bama Daada Hakuri..! Mami Asma"u ta tsaya kyam taki Dukawa Tana kallonsa Cikin Hawaye tace"Wlh bazan bata Hakuri ba ai ba wani Laifi nayi mata ba gaskiya na Fada..Saboda Hakkina sai nayi mgana Wlh..Na fada na kara fada bazan yarda ba..! Ya sake yunkurawa Daada ta Daka mai Tsawa Tana Fadim"Kada ka Sake kamin Duka agabana gaban Sauran ya"yana da jikokina kabiru..Ranka zai baci..! Tafada cikin bacin Rai kafin ta Mike Da karfi Ta kusa Faduwa ma sai da Inna Bintalo ta riketa. Cikin Tsananin Fushin da ba wanda ya Taba ganin Daada dashi Tace"kaji kunya Kabiru yau na ce maka Kaji kunya..Yau ina ma Mahaifinka nada Rai Wlh shima sai yayi Tir da Haihuwanka..Komai ya Faru kai ne Sila banda kana Shashasha Sakarai ko Mahaukaci ne Imran na Tabbata zaka iya bashi yarka Saboda jini yafi Ruwa Kauri Malami fa Dan"uwanka ne Daka Saki nono ya kama ammh yau saboda Macen macen ma wacce kuka Hadu bayan ka samu iyaye da yan"uwa Saboda Bata Nuna amincewarta ba yasa kaima ka nuna ka kyamaci jininka Wlh ka bani kunya Tir da kai Tir da Hallayarka Ficemin agabana kafin Raina ya baci na Daga Maka NONO...! Ta karishe Fada Cikin Tsawa da bacin Rai Lokaci Daya hawayenta na Zuba Baffa Kabiru jikinsa ya Fara rawa ya Zube gaban Daada yana Fadin"Don Allah Daa "KA FITA NACE...KA FITA KABIRU BANA SON GANINKA AGABANA." Tafada cikin Tsawan da sai da kowa ya tsorata Jiri ke Dibanta Tayi luu Zata Fadi Ya"yanta suka Tallbeta da Sauri suna Kiran sunanta kowa ya Mike harda Imran Dake tsaye yana jin Dadin Abunda ya Faru yau karyan Sonkai kuma ai ta kare Daada Idanuwanta na Zubar kwallah Tana jikin Abba tace"Malami Ku fadama Kabiru ya ficemin Daga gida..Ya ficemin Daga gabana Dashi da matarsa Da Duka ya"yansa na Cire Hannuna akanshi da duka iyalansa Allah nagodemaka ina da wasu ya"yan kamar ku da yau bakinciki sai ya kasheni..! Daada ta fada Tana kuka Shabe Shabe gwanin ban Tsausayi,Daddy ya kalli Baffa Kabiru dake duke yace"Yaya kuje kawai Tunda Daada tace kuje..Ku tafi din Kada ciwonta ya tashi Sakacin ya jawo mana Rasata gwara ka tafi kawai..! Yafada shima kamar zai yi kuka,Baffa Kabiru ya kasa Mikewa saboda yadda Jikinsa yayi Nauyi,Sai khamis ne ya kamasa ya Daga sa Mami Asma"u kuma batayi Nadama ba ko ajikinta Wajen Sajida ta Nufa wacce Kanta ke kan Kafafunta Tana ta kuka ta Dago ta Tana Fadin"Ki daina kuka taso muje...Indai ni Asma"u na cika Mahaifiyarki sai na Daukan miki Matakin wannan Tozarcin da akayi miki Taso mu tafi da yau bamu da Muhalli da mun shiga uku..! Tafada Cikin gatsali ba wanda dai ya Tankamata,Sajida kuwa taki yarda ta bita Tana Mikewa ta Turje taki Tafiya Mami ta juyo tana kallonta Cikin mamakin take kallonta kafin ta Samu Zarafin mgana Sajida ta Kwace hannunta Ta isa gaban Imran ta Zube Gabadaya shi baya ma yaja yana kallonta gabadaya sai kallo ya koma kansu. Cikin kukan Fitar Hayyaci Sajida ta Hada Hannayenta Waje Daya alamun Roko Tana Fadin"kada kamin haka..Kada Laifin da ba ni na aikata ba ya Shafeni Laifin Mami da Dad bai kamata ya Shafeni ba..Kayi hakuri kada kace Zaka Rabu dani don Allah..! Kowa sai ya saki baki yana kallonta Mami Asma"u da taji gabadaya Duniyar nan na Juyi da ita Cikin Fusata ta isa gaban Sajida ta Dagota Tana Fadin"sai me..? Nace sai me don ya Rabu Dake..? Wlh bai isa ya Tozarmu ba..Ke baki isa ki duka kina Bashi Hakuri ba sai dai ke ya Duka yana baki Hakuri..! Dariyan Saman Lebe yayi na Kalaman Mami Asma"u Sajida kuwa Hannunta ta Fizge Tana Fadin"Ya isa Mami ya isa..! Tafada Cikin Tsawa Lokaci Daya Hawaye na Shatatan mata. Mami Asma"u ta Sandare Tana kallon Sajida cikin mamakinta. Sajida ta Daga Ma Mami Hannu Tana Fadin"This is Enough Mami Enough..Ya isheki kin gama Lalata komai ammh duk da haka bazaki kama bakin ki ba..? Kin Kashemin aurena auran da nake mafarkinsa..Kin Rabani da Mijina ne kuma kina kokarin Dora Laifin kan Daada Wlh duk Abunda ya Faru kece Silan komai to in baki sani ba bara na Fada miki Wani abu Wannan Da kike aibatawa kina Kiransa da sunanyen Banza Shine MAFARKIN YARKI..SHINE MURADINTA GINSHIKINTA..Eh Mafarkina Domin Ina SON SA..KUMA na shirya Mutuwa saboda shi kin taba Tambayanta Sajida kina son wannan auran..?ko kin Taba tambayata Sajida zaki iya zama dashi?kin taba jin Ra"ayina..?gaskiya ne kina da son kai..Baki son kowa sai kanki baki Damu da abunda Dad yake so ba ko yana so sai Ra"ayinki zai bi Baki Damu yayi biyayya ga Daada ba Kema zAi yi biyayya da Duka Dokarki Haka kike son adalci..? Ahalin kema bakya ma kanki adalci Wlh Tallahi kafin ki kai Daada kotu ni zan shigar Dake kara..Karar kan Uwa kamar Ki Barrister Asma"u Tafida ta kashema yarta aure Saboda Selfish dinki Ke din Wata irin uwace..?Nace ke din Wata irim Uwa c..! Ai bata kai karshen mganarta ba Khamis ya Dauketa da wani Lafiyayyan marin da sai da ta Dukae Ta kara Fashewa da kuka. Khamis Cikin Rawan jiki Alluran Soja ta tashi yace"Mamin kike Fadama Haka Saboda wani Sarakan Namiji..?ke wata irin Dabba ce acikin Dabobbi.? Sajida da Idanuwanta suka Rufe ta Dago Tana Fadin"Eh naji ni Dabba ce..Indai akan Son Imran ne naji ni din Dabba ne kuma bazan Fasa fadin Mami Mai sonkai bace..! Ya daga hannu ya kara kaimata wani Wawaan duka Mami Ta Taresa Da jikinta ke rawa Kuka take Kamar Idanuwanta zasu Fado yau bama Gilashin tuni yayi ta kansa Mami jiri Take gani Cikin Karfin Hali tace"Kyaleta Khamis...Kyaleta..! Take Fada Jikinta na rawa Rikota yayi Daya Lura da Zata iya Faduwa yana kiran sunanta Cikin Duhu duhun Datake gani tace"Muje Mota..Muje Khamis jiri nake gani..! Ai bai Tsaya ba ya Tallafeta suka fice bayan ya Bi Sajida da wani mtsayacin kallo,wacce ta Duke kawai Tana Kuka. Ba wanda bai ji Tsausayinta ba afalon nan Hatta kuwa Daddy banda Imu da hakan yayi mai Daidai. Dukawa yayi agabanta yana Fadin"Sorry fa..Ba Laifina bane..Gani nayi Dan Shaye shaye bai Dace da auran Diyar Lauyan lauyoyi ba..Ai hausawa sukace Babban goro sai magogin karfe,karamin goro sai ya nemi Daidaishi ke din matar Manya ce Diyar Barrister Asma"u sai Diyar Masu rike da madafin ikon gwamnati ba Imran da bai da komai ba Irina..! Yafada Cikin Kwanciyar Hankali kafin ya Mike Tsaye Sajida kuwa kuka take kamar Zata Shida Baffa Kabiru ya kada kai shima Kwallar sun taru acikin idonsa ya Fice yana zuwa Mota gidan gaba ya shiga Mami Asma"u da Khamis suna gidan baya Tana ta kuka yana Lallashinta Fadi take Shikenan Nagama Tozarta ni Asma"u na gama Yawo..! Baffa na jinta yayi kamar baya Motar Umarni ya bama Direeba kafin ya kwana yayi hon megadi ya wangale get suka Fice Daga Haraban gidan cikin su ba wanda iya Bude baki yace Ina Sajida domin ai idonsu ya Tabbatar musu da abunda ta aikata bata Bukatar bin su. Suna Fita Dada jikinta ya Rikice Dole Daddy yayi ma Dr.Zubaida waya tace Gatanan zuwa Gabadaya Taron ya tashi Zucicyi ba Dadi banda Imran da Ransa Fes ko ajikinsa. Sajida Inna Maimunatu ta kamata zuwa Daki Tana ta lallashinta da bata Nasiha ammh bata Daina kuka ba Su Abba basu samu natsuwa ba sai da Dr Tazo ta Duba Daada Jininta ne ya Hau ta bata mgunguna Tace data samu Barci Shikenan kuma adaina Tuna mata da abunda zai sakata Damuwa,jininta ya hau sosai su Abba suka amsa da ba komai zasu kiyaye dukkansu suna Dakin Daada sai da ta Samu barci suka Fito sukayi Sallar La"asar data Subuce musu, kowa ka gani ba Fara"a Saboda Halin da Taron ya tashi da abubuwan da suka Faru ba masu Dadi bane. Banda Imran Dake cikin Daki yana aiki Bisa Laptop dinsa Ransa Fes ko ajikinsa Sagir na kallonsa yana ayyana Imu karshe ne Shi ko ajikinsa Daga gani ma Dadi yake ji to me zai Damesa...? Abunda suka aikata ne suke Girba. *Shakira..* 3/24/22, 14:21 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�17* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Aranar dai ba"a samu Daura Auran Inteeasar da Imu ba kamar yadda Daada taso,saboda yanayin Motsawar Jikinta da yadda Zukata suke babu Dadi,Allah ya taimaka da Daada ta Farka taji Sauki sosai shi ya kwantar ma dasu Abba Hankali. Ranar gidan na Daada kowa kadaha kadaham banda Imran Daya kusa Raba Dare yana aiki Saman Laptop dinsa ko irin agefen Kwalan Rigarsa. Sajida kwana Tayi kuka kafin Safe Zazzabi ya Rufeta duk mai Tsausayi ya ganta sai ya Jimanta mata Umma da Inna Maimunatu ne ke ta kula da ita Ita Taje ta Fada ma su Abba Hankali Tashe suka Rankayo Dakin suka ga Halin Datake ciki,Sajida ai tasu ce koda Daada tace ta cire Hannunta akansu Bacin rai ne ammh Hanunka baya taba Rubewa ka yankeshi ka yar Daddy ne bai Damu ba gwara Da Daada Tayi ma Yaya kabirun haka ko ya dawo Cikin Hayyacinsa ammh har ga Allah yana Takaice da Mami Asma"u kuma da jin zafin yadda ta Ci ma Daada Mutumci bata gama ganin komai bama yanzu ta fara gani. Abba kuwa Daman Dan Sanyi ne gabadaya ya shiga Damuwa bai so yayi ma Daada mgana ne ta Birkice mai ga kuma Dokar Likita Lura da hakan da Daddy yayi ne yace ya bar mganar kwana Biyu sai su dawo su samu Daadan su zauna su Lallasheta ta yafe ma Yaya Kabiru,Kada Fushinta ya Shafesa a mtsayinta na Uwa a garesa ammh awannan Lokacin sun fi Bukatar Natsuwar Daada da kwanciyar Hankalinta. Da wannan mganar Abba yayi shuru bai ce ma Daada komai ba ammh Hakika Lamarin ya Tabasa yana ganin kamar shine Silan komai da Imran bai Saki Sajida ba da haka duk bata Faru ba sai dai abun nan da Hausawa kan ce Ka Haifi yaro ne baka Haifi Halinsa ba. Da Dr.zubaida tazo duba Daada da Safe Daddy yace ta Duba Sajida ta Wahala Zazzabin ya narkemata Jiki ga Ciwon kai ga Nauyin kirji Allura Tayi mata ta Rubuta Drip da mganguna ABBA ya Umarci su yusuf da Basheer sukaje suka siyo suka kawo tayi mata amfani Dashi ta Dora mata Drip din bayan ta saka wasu Allurai aciki ba Dadewa Sajida ta samu Barci Duk ta jeme ta Lalace Fuskarta sai Sauran Bushewae Hawayen kukan Data kwana Tanayi dukkansu suna Dakin gwanin ban Tsausayin Halin da Mami Asma"u ta saka yarta. Daada ta aiko kiran Abba da Daddy suna zuwa tace maza suje a Daura auram nan da Abba ya kawo mganar Rashin Lafiyar Sajida sai Daada ta Saka Musu kuka,kan cewa in suma baza su yi mata Biyayya bane Sai su gayamata jin haka yasa suka Fice Daman Allah yasa da suka je Sallar asuba Daddy ya sanar da Liman akwai Daurin aure karfe 11am na Safe. Haraban gidan suka Fice Daddy ya Kira Basheer da Yusuf ya basu kudi sukaje suka siyo Goro da dabino,Sha Dayan bata cika bama suka isa masalllacin Imran na Gida bai zo ba da Sagir yamai mgana kallonsa yayi kai Tsaye kafin yace"Ko naje ko ban je Inteesar Zata Zama matata so plz ka kyaleni..! Sagir ya kada kansa yana Fadin"Kai dai Wlh baka da Tsausayi nan fa nazo Dazu ina Fadamaka Halin da yarinyar nan take ciki ammh kana ta jin Dadi anya kana da Zuciya a kirjinka..? Imran ya kara Murmusawa kafin yace"In baka yarda bane ko Zamu saka Wuka ka fasa Kirjin nawa sai ka Duba kagani ina da Zuciyar ko bani da ita..! Tunda ya Fadamai haka bai kara bi ta kansa ba to duk kowa bai da Natsuwa haka aka Daura auran Inteesar da Imran kan Sadaki Dubu Dari Daddy shi yayi ma Imran Waliyi Abba kuma ya bada Auran Inteeaar Mutanen anguwan suna ta yabon Ahalin Alkali Dukku marigayi suna Fadim bayan Ransa basu ya da Zumunci ba,Suna ta Hada ya"yansu auratayya Cikin Aminci,Kuma Daurin auran yayi jama"a matuka Domin kaf Anguwan ba wanda bai shaida karamici irin na Marigayi Hamisu dukku ba. Daada bata ji Zuciyarta ta kwanta ba sai da Abba da Daddy suka dawo suka zube mata sadakin Inteesar da Goro da Dabino suka Tabbatar da sun cika mata Wannan Umarnin. Daada na Sharan Hawaye tana saka musu albarka Tana fadin kamar yadda suke bin Umarninta Insha Allahu bazasu taba samu ya"ya wadanda Zasu bijiremusu ba Daada ta Bala"in basu Tsausayi Rauninsu ya bayyana sukaji suma kamar suyi ta kukan nan suka Taru suna Lallashinta Kafin ta Daina kuka ta koma Fara"a Da Dariya Lokaci Daya Tana Saka musu albarka. Lokacin da Sagir ya shigo Dakin da Imu yake yana fadin an Daura mai aure Shi da Inteesar sai da ya Tsaya da aikin da yake yi gabadaya Jikinsa ya Saki yaji Wani irin Feeling mai karfi yana Tasomai yanzu Intee Matarsa ce ita din mallakinsa ne. Baisan Sadda ya Furta"Alhamdullillah..! Afili har Sagir ya jisa ba sai dai bi bi ta kansa ba Ya gama batamai rai ya kuma bashi Haushi Dauke kansa yayi kamar bai gansa ba ya Fara Shirya jakarsa Tunda yau zasu koma Imran na Kallonsa aransa yace kayi ka gama. Umma kuwa Daman Tun jiya ta Kira Chan su Inno ta gayamusu komai suka Saka albarka da Fatan alheri,dukka yayyinta ta Kira su su Kawu Bala da kawu Salisu ta Fada musu sukace ba Domin bata gayamusu tun da Rana ba da sun samu Daurin aure tace bakomai suyi Zamansu Tunda anan kaduna za"ayi Bikin Tariyan Inteesar din. Mama kuwa Daman ita ta Fara Kira ta fadamata Mama ta Saki Guda a waya Tana Bayyana Murnanta ta Tuna da Sanda tace ma Intee zata aurama Imran ita a wasa ashe dai Allah ya Hada al"amarin sai fatan Allah yasa su zauna Lafiya,Gari na Waye ana kuma Daura aura ta Kirkkira su Kawu Salisu ta shaida musu Nasara Kawar Inteesar sai da taji Labari kamar Daga Sama wai an Daura ma Intee Aure ita ta Fara Kiranta a waya tana Fata kwakwazon bata gayamata ba Inteesar tasha mamaki bata Taba Zaaton Auran zai zama cikin gaggawa haka ba tama kasa mgana Jikinta ya Mutu duk da kwanan Farincikin Datayi Zata Zama matar Imran jinta a Mtsayin Matarsa bayan a wanni kadan yasa komai ya Tsaya mata tama kasa gane wani yanayi take ciki. Munari ta bari da wayar Tana ma Nasara Bayani har ta Fahimta Tana jinsu Suna Tsara yadda zasu gwangwaje alokacin Tarewar Bikin su Intee na Jinsu aranta tace badai da ba Ya Imu na aura ba shine zamu gwangwaje ammh wannam Dan ka"idan Allah yasa ma ya bari ayi Bikin. Koda Anty Safiya ta shigo ta Fada musu Abun Farinciki sai ta iske ma Munari na waya da Nasara suna mgana Itama Yanzu Yusuf ya Kirata Rumgume Inteesar Tayi Lokaci Daya Tana Rangada guda,Munari na ganin haka tayi Saurin katse wayar Nasara bayan tace Zata Kirata Daga baya suka Hadu da Anty Safiya suna tayima Inteesar guda Da Wakar. "Ke Kikace kina so..da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba..! "Ta zama ta zama ta zama Dauko Riga ta zama Dauko wando..Ta zama Dauko Kofi...Ta zama..Ta zama..! Kawai sai Inteesar ta saka musu kuka Hawaye Shabe Shabe Anty Safiya ce taci Girma ta koma Tana aikin Lallashi Tana fadin"yi shuru abunki..Amarya guda da kuka..?matar Imu guda a"a bar kuka Kada yazo yaga nasaka matarsa kuka yace zai Sauyamin kammanni..! Gabadaya suka saka Dariya Harda ita Tana Hawaye,nan suka zauna da Anty Safiya da Munari suna Tsara yadda komai Zai tafi harda kirga ankon da Zasu yi lokacin Bikin Tariyar domin zasu Famshe Bikin yaya yusuf da ba"ayi Taro ba zasu yi gayya na kece Raini Taro sunan Taro ita dai Tana gefe Tana kallonsu Gabadaya Hankalinta da Tunaninta na kan Imran yana ina..? Wani Hali yake ciki..? Kafin kace kwabo Labarin Daurin Auran Inteesar da Imran ya Zaga kunnen kowa a Dangi Ya Basheer ya Hau Whatapps ya sanar a Group Cikin Fahari da Farinciki a Mtsayinsa na Dan"uwan Intee yasan ta Gama Dacen Miji irn Imran irin su ne ake kira One in Million,Matan kuma su Anty Hauwa su Aneesa duka mazajensu suka kirasu suka Sanar dasu Inna Maimunatu ma ta kira su Zainab ta Shaida musu kowa yaji Sai yayi Murna yana Fadin Wlh Imran sun Dace da Inteesar Hadin yayi matuka. Hafsah ma Dataji Labari ta Daka Tsalle ta Rangada guda Tana juyi Tana Fadin kano akwai Shagali Fareesatu namata Dariya,Kiran wayar Inteesar Tayi munari ta Dauka suka Dinga mata ihu suna Tsokananta da Amarya Amarya,ita dai tana jinsu bata mgana yau aure ya kashe bakin Intee Hafsah Har tafi Munari Zumudi Tana Fadin Taga wani less ko shi Zasu yi Ranar Dinner..? Intee Dariya suke bata da Tsausayi Sun manta wai Waye Imran ne Ta Rantse har ga Allah sai yayi Ra"ayi Duk abunda bai yi Ra"ayi ba ba wanda ya isa. Hatta Baffa Kabiru Dake Abuja ya samu Labari inna Bintalo Gulma na cinta bayan ta gama Kiran ya"yanta su Siyama ta Tseguminta musu Duk Abunda ya Faru sukayi ta Zagin Imran suna Kuma cewa Daada bata kyauta ba tayi ta Kiran Mami Asma"u a waya ammh Wayar na Ringing bata Daga ba sai ta Kira Baffa Kabiru Lokacin ma yana Office Suna da wata Sharia mai Zafi ga Damuwa ga Abunda ya Faru jiya Wanda har suka iso Abuja bai ko kalli Barayin da Mami take ba har kuma yau din nan basu kara Haduwa ba Domin Tun bayan Dawowarsu kowa ya Shige Dakinsa Bai nemeta ba itama bata Nemesa ba Khamis ma yana cikin dakinsa yana Faaman da Raunin Zuciya na Rasa Inteesar gefe Daya ga Mtsalan da Mami da Dad,Umaima ce kadai ta Leka Mamin Sai tace mata batajin Dadi ta fita ta bata waje bata kawo wani abu ba,Ta koma Dakin Dad sai ta iske ya Fita bata Damu da Rashin Ganin Sajida ba atunaninta ta Wuce makaranta chan suka Fara maidata ita kafin su dawo gida batabi ta kan Khamis ba itama Tun Safe Direba ya kaita makaranta yan aiki kadai aka Bari suna ta Bidirinsu acikin Gida. Lokacin da Binta ta Fadamai an Daura aure bai wani Damu ba Saboda ba Shakka Jiya ya kwana bai yi barci ba yana Nazarin Rayuwarsa Tun Daga Farkon yarintarsa Har Girmansa Haduwarsa da Asma"u zuwa auransu da yadda yake sonta ya kuma nuna mata Ya Tabbata Soyayyar Dayake ma Asma"u ce Weekness dinsa itace Silar Faruwar duk abunda ya Faru,ya sakar ma Asma"u komai nashi Rayuwarsa Rayuwar ya'yansu itace Take Tafiyar da komai Rayuwarsa ma shi da yan"uwansa shi ya bata Damar Tafiyar da komai saboda baya iya yin wani abu acikin Dangi sai ya Bata Labari kuma in tace kada yayi kaza ga yadda take so ayi haka ne zai Faru ne,Tana amfani da wannan Weeknees din nashi Tana yadda Ta gama Dama a Rayuwarsa gaskiyan Daada ne shi ya bata Komai da Tun farko bai bata Damar saka baki Cikin abunda ya Shafi Ahalinsa sa ba ita bata isa ta Ja da mganar Daada ba da Tun Farko bata Nuna Jajayarta kan auran imran da Sajida ba da Imran bai Saketa ba,da ya nuna mata bacin Ransa ya Nuna mata bata isa ba da haka bata Faru ba ammh Sai ya goyi bayanta yana ganin eh Daada batayi Daidai ba Yau ga abunda ya Faru Asma"u ta Ci Zarafin Daada bataji kunya ba..Itafa Ta Haifeshi Itace Uwa garesa ammh Asma"u bata Duba wannan ba kanta Kadai ta sani Shima son kansa Shi yajamai komai da ace bai da son kai da bai kyamaci Jinin Malami ba.Da Abunda ya Faru bai Faru ba,Da Daada batayi Fushi Dashi ba da Sajida ta Samu Abunda take so take Buri. Fatan Alheri yayi Yana kokarin Dauke Hawayen da suka acikin Idanuwansa,Sai dai ya shiga Damuwa Sanda yaji Sajida na kwance ba Lafiya Batama san an Daura auran ba Baffa Kabiru yaji Takaichi Asma"u zata Kashemai ya saboda son kanta Wlh Shi Zai kaita kara Kotu in har wani abu ya samu Sajiya ya gane kuskuransa zai nemi Daada gafara zai kuma gyara Tsakaninsa da yan"uwansa Zai gayama Asma"u ta Shiga Hankalinta in kuma ba Haka ba Komai zai iya Faruwa. Khamis ma ya Samu Labari ta waya Daya gani a group haka ya kwanta Saman gado yana kuka kamar karamin yaro ba Soja ba Mami Ta Riga ta Ruguza komai ba,Ta yi Sanadiyar shiga Tsakaninsa da abunda yake so Sai dai bazai yi Fushi da ita ba,uwa take garesa Sai dai Dole zai yi nesa da gida in ya Tafi baxai Dawo nan kusa ba so yake yayi nesa da Duk wata Hayaniya ko Damuwa ya yarda Imran yayi nasara shi kuma He is a Loser. ***** Abba da Daddy shiryen Shiryen Tafiya suke yi sun yi mgana da Inna Bintalo da Inna Maimunatu zasu zauna su kara kwana Biyu har Daada ta Watseke Mganar Sajida kuwa sai da Abba da Daddy suka duka suna Rokon Daada Ta amince Sajida ta zauna in ta ji Sauki sai ta koma Abuja Kana Daada ta amince ammh da Farko cewa Tayi Sajida bazata zauna mata agida ba bata da Alaqa da ita ta koma Abuja gaban Iyayenta. Kafim su Wuce sai da Daada ta kara Jadadda musu cewa Tarewar Inteesar kada ta wuce Wata Daya bata son jan Lokaci Tana son Ta dauki dan Imran da Inteesar da hannunta Jikan Mustapha da malami kafin ta bar Duniya Daddy ya tabbatar mata da Insha Allahu bazai Dauki Lokaci ba Da Daddy yace ma Daada ko nan Dukku Za"a dawo ayi Taron Bikin Daada tace a"a bata Bukatar ganin kowa su yi Taronsu chan wannan Tsakaninsu ne sai yadda suka Tsara. Sai dai a turo mata Inteesar tana son ganinta kafin Lokaci sannan ayi al"ada kada ace baza"ayi wannan ba saboda na gida ne A"a Aure irin auren kowa ne abama Imran Wahala sosai yayi Duka al'adu kafin Abashi Inteesar su Abba nata Dariya Imran na wajen ya Hade rai yana cema Daada nima sai ta Wahala zan yarda na Tare Dariya su Sagir harda rike ciki,sai da suka sanya Daada Farinciki kana suka Wuce Motar yusuf su Sadam da Abba suka shiga sai Sa"id wanda ya Dauke su Imran zai ijiye su kano kafin ya wuce Jigawa,Umma kuma da Daddy ya Basheer ya Tuka su,a gombe suka Tsaya sukayi Sallar Azahar kana suka Dauki Hanya. Allah Sarki suka baro Dukku Cike da Tsausayin Sajida da ita kanta Daada,Sai bayan Tafiyar su ta Farka Ta dan samu karfin jiki kuma Zazzabin ya sauka,Inna Maimunatu ta Taimakamata tayi wanka tadan Tsakuri abinci Inna Maimunatu ne ke ta Kula da ita Inna Bintalo kuwa Gulma kadai ta iya da Munafunci ta Girma bata san ta Girma ba ita ta Lallabo bayan Fitam Inna Maimunatu Zuwa Dakin Daada tazo tana gayama Sajida an Daura auran Imran da Inteesar nan da nan ta sake Rikicewa da kuka da Inna Maimunatu tazo ta ganta Cikin Wannan Halin Tasan Dalili Bintalo ce ai bata da Girma sai na Jikinta Kullum tana Girma Tana cin kasa Ko ta kanta bata bi ba,Ta koma Tana Ta Lallashin Sajida,wacce ke kuka kamar Ranta zai Fita Idanuwanta Jajir take kallon Inna Maimunatu Lokaci Daya Tana Fadin"Goggo Shikenan Ya Imran ya sakeni..Shikenan Mami Ta Rabani da Mijina..! Take Fada Tana kuka Rumgumeta Inna Maimunatu tayi kamar tayi kukan itama Tace"A"a ba shikenan ba Sajida kin ji ko..? Kiyi hakuri ki Daina kuka da yardan Allah zaki samu wani Mijin Dayafi Imran komai da komai..! Girgiza kai take yi Tana Fadin"ko na samu bazan so shi ba..Imran nake so shi zuciyata ke Zafi saboda soyayyarsa..! Tafada Tana Dagowa Hannun Inna Maimunatu ta kama ta Dora Saman Kirjinta Tana Fadin"Kin ji yadda take Bugawa ko..?to da soyayyar Imran take Bugawa kuma Tana gabda Daina Bugawa Saboda shi..! Ta karishe Fada Hawaye na wanke mata Fuska Inna Maimunati sai ta kasa mgana Hawaye take share mata Acikin Ranta Tana fadin anya Asma"u zata ga Daidai kuwa..? Hakkin yarta Sajida ta tabbata bazai barta ba Dakyar ta samu Sajidan Tayi shuru ta koma ta kwanta Tana Shesshekan kuka,Ta fice zuciyarta Cike da Tsausayin Sajida ga Daada Tayi Fushi Sosai da Yaya kabirun da duk abunda ya Shafe shi ballatana taje ta gayamata Halin da Sajidan ke ciki Lamarin sai gyaran Allah kawai. Su Imran suna Cikin Tafiya sun kusa isa kano,sai mirmishi yake shi kadai in ya Tuna shi fa yanzu Mijin Inteesar ne sai Nishadi yake ji in ya Tuna hakan,Yana ayyana yadda zai Rika Zuba Mulkinsa son rai,Kamar zai Tura mata sako sai wata zuciyar ta Hanashi da Cewa kul Imran wlh Ka kiyayi kanka Yanzu taji labarin komai sai ta Zata kana sonta ne Raini ya Fara shiga Tsakaninku abunda bazai taba yarda ya Faru ba Har Abada Balle da Munari Ta fara cewa wai suna Munafunci Yarinyar taci abinci in suka Hadu sai yayi kwallo da ita Tuna haka yasa kawai ya Share duk da har suka iso Tunaninta yake yi shi bai yarda yana sonta ba Imran naso ya rika karyata Feeling dinsa. Tun da suka Taho Yusuf ya Kira Safiya ya Fadamata ta sanar dasu Munari,Munarin ta tayata suka Dora abinci Inteesar dai bata ma da Wani Kuzari bata san da wani ido Zata iya Kallon Imu ba wani Haduwa zasu yi akaron Farkon su na mata da miji..? Ga Abba ga ya yusuf gaskiya Tana jin kunya sosai bazata iya Hada ido dasu ba. Tuna Haka yasa ta Lallaba ta Kwashi Littafan karatunta na gobe ta Gudu Gidan Mama koda Munari ta Laluba bata Gidan ta Gudu Data Kirata a waya sai tace Tana gidan Mama chan zata kwana Munari ta Rike baki Tana mata Tsiya. Chan din Mama ta sakata gaba da Tsokanan Abaya Lokacin Datace Allah ya Tsareta ta Zama matar Imran yanzu kuma gata mtsayin matarsa yake nan..? Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"ai bani nace ina sonsa ba..! Mai mama zatayi ba Dariya ba Dawowar Sagir Bayan mangariba yasa Tasan su Imu sun iso kenan Shima ai yana shigowa gidan ya Ganta yahau Tsokananta da Matar Abokina Dan iska ko mai Shaye Shaye..? Intee Tayi kwal kwal da ido kafin Tace"Kai ya Sagir..Mama kin gansa ko..,? Cikin Shagwabarta kamar Zatayi kuka mama tace"Kyaleta Mana kada ka sata kuka..Ta gudu ne bata son Hada ido da Abba tana Surukanta dashi ba Uba ba..! Dariya suka saakamata yasa ta Shige Ciki Tana Kukan shagwaba wanda bai da Hawaye Sagir yace ai su Abba sun Rigasu isowa su Sa'id ya Daukosu Ya kuma wuce jigawa Sadam kuma sai da su Abba suka ijiyesa agida kana suka Wuto nan. Dakinsa ya shiga ya ijiye jakarsa ya Fito ya Dauki Buta ya Zagaya. Yana Fitowa yayi alwala ya shiga Daki yayi Sallah Mama ta gabatar da abinci yaci yasha Ruwa yana bama Mama labarin kadan Daga abunda ya Faru a Dukku Harda Sakin da Imran yayi ma Sajida Mama ta nuna jimami sosai ammh fa akasan Ranta tasan Inteesar tafi Dacewa da imran. Inteesar na Daki Taji komai Duk da bataji Dadin Haka ba sai dai Taji Sakayau Nauyin Kirjinta ya Ragu da Kishin Sajida sannan taji Haushi wai Da Sagir ke bama Mama Labarin Sajida tace tana son Imran Ranta ya Baci ta Tura baki tana Fadin"Ai sai ta yi ta sonsa..mara zuciya ba ya saketa ba..! Ita kadai tayi ta Bata rai Sai dai taji Dadin yadda Mami Asma"u Taga Karshenta sai dai Baffa Kabiru ne ya bata Tsaisayi aranta tace Allah ya kara shima. Mama bataji Dadi ba Salallami take,ko kadan abun bai mata Dadi ba Kiran Sallar Isha"i ya Fitar dashi chan masallaci suka hadu dasu Abba da Imran sai da suka idar suka fito Waje Sagir ya yafito Imran yana Fadin"Amaryanka na gidanmu ko zaka shiga ne ka rage Dare..? Imran yayimai wani kallo kafin yace"Kaifa Dan iska ne a ina kasan ana Rage Dare Sangiru..La"ilahaillalah..Ka lalace na bani.. Dariya Sagir ke yi shima imran Dariyan yake yi kafin yace"Abun mata da miji fa..Allah ya shirye ka zan Tashi Tsaye na nemo maka matar aure kada ka Fara Leke gidajen Jama"a cikin Dare Yafada yana Dariyan keta Duka Sagir yakai mai a Gefen Cikinsa ya kuwa Samesa shima Imran din ya Hambaresa yana Fadin"Dan iska karya nayi maka..! Sai Dariya suke cike da Nishadi Daga ganin Dariyan da Imran yake yi na Tsantsan Farinciiki ne bai sani ba. Ba yadda Sagir bai yi ba Daya shiga yaki shiga Cikin Dakuna Fuska yace"Bazan shiga ba Uban me zan mata..? Ai tasan muna Hanya ta Tafi gidan Mama kuma Dataga ganka meyasa batazo tamin Sannu da zuwa ba sai nine zan Bita Allah ya Tsari Imran..! Daga haka ya wuce Sagir yabi sa da kallon Hum ka kusa zuwa Hannu. Shi kuwa Haushi ta bashi,Koda suka Dawo idanuwansa ita suke son gani ammh bai ganta ba kuma bazai iya Tambaya ba sai da Abba ya Tambaya Munari na Dariya tace Abba ta Fara Suriki Dakai shiyasa ta Gudu gidan Mama. Abba Dariya kawai yayi shi da Ya yusuf Imran naji Ransa ya baci Wato ta Gudu saboda kada ta gansa ko..? Ba wani Saboda Abba karya take yi. Da wannan Haushin ya koma Gida kunun Ayan da Anty Safiya tayi kadai ya sha ya shiga ya kwanta saboda Fita aiki da wuri gobe ammh yana ayyana yadda in suka Hadu da Inteesar zai nuna mata shi ba sa"an wasanta bane ta bar ganin suna mata da miji yanzu bashi zai hana ta kawomai Raini ya Tattaka ta ba. *Shakira...* 3/24/22, 23:22 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�18* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Washegari da safe Tun karfe 7:30am na Safe Inteesar ta gama shirinta saboda suna da Test karfe 8am daidai na Safe ne ta Kira Munari tace mata ta jirata kofar gidan Mama gatanan Fitowa. Ta fito tana Tsaye sanye da shigar riga da wando,wandon plazo ne red sai Rigar top ce mai Dogon Hannu,baka ta sanya bakar abaya tayi Rolling da bakin Vail kafarta sanye cikin Takalmi mai tsini baki mai igiya Ta sanya karamin Farin glass ta zagaye idonta dashi,Karamar jakace a Hannunta da wayarta Lokaci bayan Lokoci Tana Duba Agogon Gucci Dake Daure a Tsitsiyan Hannunta bata so su makara Dr Mahadi bai da Mutumci ko Minti Daya ka kara bazaka shiga Test dinsa ba. Rumgume Wayarta tayi Saman Kirjinta Tana kallon Hanya ba Kowa sai Wucewar Daidaikun Mutane Tunaninsa take yi mamaki take yanzu wai suna Mtsayin mata da miji..?har yanzu bata Daina mamakin haka ba komai ya Faru Cikin Lokaci,Lokacin da basu yi Zato ba. Tundaga Nesa ya hangota Tana Tsaye ita kadai Fitowarsa daga gida kenan Zai tafi wajen aiki Sanye yake cikin American Suit na kamfanin Armani,mai Ruwan kasa ya Matse Wuyansa da Tie,Mamakinta ganinta tsaye ya fara Daga farko har yana Duba Agogon Fatan Dake hannunsa sai kuma ya Tuna makaranta Zasu Tafi. Dan Tsagaida Gudun Motar yayi Daga nesa yana kare mata kallo Daga Sama Har kasa Wando..?Haka kurum Dresing din bai kwantamai ba Duk da ta saka Bakar abaya Daga Sama yarinyar nan bata da Hankali ne..?batasan ita matarsa bace da Zatayi wannan Bazan Shigar tatafi Cikin Dubban maza?Wato ta Rainasa ma kenan..?daman jiya ta gudu bata ma Tsaya ta gaisheshi ba Hakan ya sosamai rai kwarai da bacin Ranta ya kwanta kara gudun Motar yayi bata ankara ba Kawai taji Tsayuwar Mota a gabanta Dago Dara daran Idanuwanta Tayi ta Sauke akansa Daidai Lokacin Daya Sauke Glass din Barayinsa Suka Hada ido hudu Lokaci Daya kuma atare gabansu ya amsa Ras! Yadda yazo da Masifarsa kallonta kawai Da yayi sai yaji komai yana Sauka ita kuma karon Farko dataji wani irin yam acikin Jikinta da suka Hada ido Lamgwabe kai Tayi idanuwanta ya ciko da kwallah Ware ido yayi akanta ya kasa ma ce mata Komai jira yake yaga Zata gaishesa ballatana ta amsa Laifinta..? Ita kuma Jikinta ne ya fara rawa bata Shirya Fuskartan Ya Imu a Mtsayin Mijinta ba yanzu kwata kwata ta Rasa Ina Zata tsoma kanta wani irin Feeling neyake Fito mata Daga karkashin Zuciyarta wanda yasa Hawayen idnta suka zubo Saman Fuskarta Dakuna Fuska yayi yana kallonta Kuka..? Ni take ma kuka ko auran da aka Daura mana? Ya kasa gano ma Dalilinta ya Bude baki yayi mata mgana yaga ta Juya da Sauri Gudu gudu Ta shige Zauren Gidansu Sagir Baki da Hanci ya Saki kawai yana kallonta Tuni yaji Bacin Ransa ya kara Ninkuwa. Wata zuciyar tace mai Imran kagani ko..?Duk abunda ka Hada da mace sai kaga ba Daidai ba,Macen ma karamar yarinya Raini sai abunda kagani Shi yarinyar nan zata Sakama kuka ko mgana fa bai mata ba, Afili ya Furta"Shagwabbiya ce..Mtsawww..! Tsaki yaja kafim ya Tada Motarsa ya Wuce da Gudu a Fili yake Fadim"Imran be a Man..Kada ka bari Yarinta yarinyar nan ya bata maka rai juz ka kyaleta zata gane bata da wayau ne inaga ta manta Wanene Imran ne ban Sauya ba ina nan a yadda nake Mace bata isa ta zauna ina Lallashinta ba banda wannan Lokacin.! Haka yake ta Fada yana so ya Kure baacin Ran abunda acikin Ransa Ahaka ya isa Titi ya Dau Babbar Titin da zai Sadashi da Brach din Bankin Dayake aiki yana kokarin manta komai da Lamarin Inteesar sai ta nemesa da kanta Zata gane bata da wayau. Sanda ya isa Ma"aikata sun Fara zuwa ya Fito Daga Motarsa Cikin Takunsa na Sassarfa da Zati,Rike da Karamar Briefcase dinsa,Suna ta gaisheshi hannu kadai yake Daga musu har ya karisa Office dinsa Dayake Tsaf kamar bai Taba Datti ba ya zauna yana kokarin yakice Inteesar acikin Ransa ya Fara aikinsa gadan gadan sai dai duk Motsinsa Inteesar Tana makale acikin Ransa Ta Riga ta samu matsungunnin da bazata iya Fita Cikin Sauri haka ba. Inteesar kuwa a zauren Mama ta Labe Tana lekensa Sai da Taga ya wuce kana ta Sauke ajiyar zuciya Tana maida Numfashi kanta ta Dafe Lokaci Daya Tana fadin"Kash..Meke Damuna ne Inteesar..?Me na aikata ne..? Tafada tana Dangwalo Hawayenta Tana kallo Dariya Tayi afili ta Furta"Wawiya Inteesar..! Sai kuma tace"Ai ya Imu ne yana da Kwarjini gabadaya kallonsa Daburta Mutum yake yi..! Kiran Wayar Munari ne ya Katseta Fuskarta ta goge da Sauri taci karo da Munari tana kokrin shiga gidan,ganinta yasa ta Dakata Tana kallonta Cikin Nazarinta Ganin haka yasa Inteesar tayi gaba Tana Fadin"Allah ya taimakeki ki Tsaya kallona har ya hanamu shiga..! Munari agogon Fatan Dake Tsitsiyan Hannunta takai Duba kafin tabi bayan Inteesar din Tana Fadin"Ina ganin Amarya ce..Amarya tasha Kamshi..! Mirmishi kawai Inteesar Tayi batayi mgana ba sun Fara Tafiya zuwa Titi Munari ta Kalleta Tana Fadin"Kinsan Cewa fa yanzu kin tashi Daga yan mata kin koma matar aure..Taku Daya in kika yi batare da Izinin mijinki ba Kina Cikin Tsinuwan Mala"iku..Ina Fatan kin Tambayi Mijinki kafin ki Fito..? Munari ta Karishe Fada Tana yar Dariya Inteesar ta juyo ta Harareta Tana Fadin"Ban Tambaya ba..Kuma bazan Tambaya din ba..! Munari ta Zakuda kafadarta Tana Fadin"Daga mgana.?gaskiya fa na Fadamiki..? Ke kika sani koda yake ai Jiki Magayi matar Ya imu..! Tafada Tana Dariya Inteesar na jinta tasha kunu Tayi mata banza ammh jikinta yayi sanyi sosai yanzu ita din Komai Zatayi sai da iznin miji..!? Harda ma makarantar..? Tura baki tayi acikin Ranta tana Fadin ai ba sai na Tambaya yasan ina zuwa makaranta! Munari na kallonta Tana Danne Dariyarta Har suka kai Titi suka Samu adaidaita suka Hau zuwa New site. ****** *Abuja..* 7:40am Cikin shirin Tafiyarsa ya Fito Daga Dakinsa jikinsa sanye da kayansu na Sojijin Sama Ruwa Navy,Bayansa goye da wata Jaka irinta Sojojin,Kafarsa ma Cikin Wani katon Booth din Takalmi,Yan aiki ne kadai ke ta Kara kaina Atsakar Falon suna ganinsa suka Fara gaisheshi hannu kawai ya Daga musu yana Kokarin Haurawa Sama Inda jerin Dakunan Dad yake Hade da na Mami. Suka ci karo da Umaima ta FitoCikin Shirin Tafiya makaranta Sanye Cikin Uniforman dinta,Jiya Hadda ta tafi Tun safe Sai s yammah ta dawo yau kuma makarantar boko Zata tafi Rumgumesa Tayi tana gaishesa ya amsa mata cikin dan yake da Rinanun Idanuwansa da suka Rine Saboda Damuwa. Cikin Mararaice Murya tace"Ya Khamis Me ya Faru a Dukku ne..?Tunda kuka dawo na kasa gane kan Dad da Mami,Kuma ina Anty Sajida..? Ban ganta ba nazata ta wuce makaranta ne inta kiranta bata Dauki Wayata ba..! Kallonta yake yi kur yana wani Tunani Umai tayi kankantar Sanin Wani abu Shiyasa yadan yi mata yake yana Fadin"Don"t worry kin ji ko Umai..Bafa komai kinsan Halin Mami da Rigima Dad kuma da kyaluwa ko..? Zasu Daidaita kansu Sajida kuma Tana makaranta she is ok..Kila karatu ne yayi mata zafi yasa baki jita ba! Yafada yana Shafa Kumatunta kallonsa kawai tayi tafa gani a group na Daurin auran Imran da Inteesar jiya da Daddare ma ta Kira Hafsah ta kara Tabbatar mata Tana da Tabbacin komai ya Faru to yana da nasaba da hakan. Bataso ta kara cewa wani abu,Shiyasa Tayi mai mirmishi Tana Fadin"Nasan Tafiya Zakayi..So safe landed bro..! Kai ya gyada mata yana Fadin"Tanque Lil sisy..! Daga haka ta wuce saman Dining ta Nufa Domin tayi Breakfast shi kuma ya Cigaba da Haura Stairs din Dakin Baffa Kabiru ne afarko yasa nan ya Fara Shiga yana Shiga ya iskesa cikin Shirin Fita shima Sanye cikin Suit ya Matse ga Rigarsu da Hulansu ta Lauyoyinan saman gado shi kuma yana daga Tsaye yana Duba wasu Takardu Khamis yayi knooking Lokaci Daya yana Turo kofa ya shigo. Baffa Kabiru ya dago kansa Daga Duba Takardun Dayake yi yana kallon Dan nashi Cikin Dan bayyana Damuwa kadan asamar Fuskarsa. Khamis ne yadan Ramkwafa yana Fadin"Gud mrning Dad..! Ya ijiye Takardun hannunsa yana Fadin"Mrning Son How was ur Night..!? Khamis a saman lebensa yace Fine ba Domin haka din bane Kallon Tsab yayi mai Kafin yace"Na ganka da Jaka are u going..? Khamis na Duba agogon Farin Azurfan Dake hannunsa Lokaci Daya Yana fadin"Eh Dad..jirgin 8:30pm zan bi Zuwa Anambra Insha Allahu..! Kai ya gyada yana Fadin"Allah ya Kiyaye..Allah ya bada Sa"a..Be a Man kaji.! Yafada Lokaci daya yana Dafa Kafadarsa Cikin Alamun Lallashi Domin ya karanci Tarin Damuwa da Rashin wani abu Acikin kwayan Idonsa Mirmishi kawai Khamis yayi kafin yace"bakomai Dad..Kai ne ma Zan bama Hakuri akan Abubuwan da suka Faru plz ka yafema Mami ku Daidata kanku Dad..! Kallonsa yake yi ko Kiftawa bayayi wani abu nayi mai ciwo acikin Ransa Dan Mirmishi saman lebe yayi kafin yace"Ai bani nayi mata Laifi ba ita tayimin..Kuma kana dai ganin abubuwan da suka Faru son..Ya Dace na kyale Asma"u taci Zarafin Daada a banza kuma na koma ina bata Hakuri..?in nayi haka kai kanka bazakayi Tunanin wani irin Uba ne ni ba..? Ko kuma wani irin D'a ne ni..? Khamis ya Girgiza kai yana Fadin"A"a dad ba haka nake nufi ba..Ina Nufin ka Nuna mata kuskuranta abunda tayi gaskiya bata kyauta ba ka nuna mata Bata yi Daidai ba ku Daidaita kanku Taje ta bama Daada Hakuri is better in mu ya'yanku indai kuka Shiryan kanku..! Kai ya kada mai kafin yace"Shikenan..! Khamis ya Rusuna yana Fadin"Zan ga Mami kafin na wuce Dad..! Yana Daukan Takardunsa yake Fadin"In bazaka Dade ba sai mu ijiyeka Airport kafin na wuce Office..! Khamis ya juya yana Fadin"Yanzu zan Fito Dad..! Yafice Uban ya Bisa da kallon Tsausayi ya Tabbata karfin Hali kawai yake yi ammh abun ya tabasa Asma"u batasan ta Ruguje Farincikin ya"yanta alokaci Daya bane,Sakarya kawai. Takardun Hannunsa ya ke sakawa cikin Karamin Briefcase dinsa. Knooking ya farayi yaji Shuru jin Kofar tana Bude yasa ya Tura ya shiga Lokaci Daya da Sallama. Tana zaune kan kujeran Dreesing Mirror Tana waya shiyasa bata ma ji knooking din ba. "Ka shirya komai..Yau nake so na shigar da Complain din Brr.Zailani..! Iya abunda yaji kenan ya Kira Sunanta da dan karfi. "Mami..! Da sauri ta waigo cikin dan Tsoro jin kira Daga sama ganin shine yasa ta Sauke ajiyar Zuciya ta Mike Lokaci Daya Tana Fadin"Zan Sake kiran ka Brr.Zailani..! Daga haka ta Datse kiran Tana kallonsa lokaci Daya Tana Fadin"Son badai har zaka wuce ba..? Tafada tana kokarin Zama gefen gadonta. Kallonta yake yi cikin Tsaisayinta ganin yadda tayi wani Figai Figai Cikin kwana Biyu ba gayun nan sam kamar wacce ta tashi Daga Cuta Idanuwanta duk sun kode saboda kuka da Damuwa. Ajiyar zuciya ya Sauke kafin yace"Why Mami..? Meyasa bazaki bar mganar nan ba..? Daad zaki kai kara ko Daada ko su Baffa..? Karamin Tsaki taja Kafin tace"Yancina Zan kwata son..Rayuwar yata suka Lalace Wlh bazan bar wannnan abu ya Tafi a banza ba ka duba ka gani Sajida Tana gayamin mgana ni Mahaifiyarta gaban kowa da kowa..? Wlh Bazan Lamunci su Rabani da y'ata ba Dukkansu zan maka su a Kotu Dad dinka naga alamun yana so ya manta da ku ya"yansa ne zai Biyema yan"uwansa to bai isa ba ko ya amince ko bai amince ba sai na shigar da Complain..! Tafada cikin son Tabbatar da mganarta. Khamis ya Dafe kansa yana Fadin"Mami why nace.? Inace ke kikace baki son Auran Sajida da Imran kuma yanzu komai ya kare Why kike hakane.? Inace abunda kike so aka yi miki..?me yayi Saura..! Don Allah ki bar mganar nan ki Je ki samu Dad kuyi mgana ki basa Hakuri sannan kije har Dukku ki bama Daada Hakuri Saboda mganar Gaskiya baki kyauta ba Uwa uwace kuma ana Sauya mata ammh Mami Ki Sani ba"a Sauya uwa kamar yadda Muma kome kika mana kome kika Zama kina nan a Mtsayin Mahaifiyarmu bamu isa mu sauya ma Tuwo suna ba kuma sai in da karfin mu ya kare in muka ga wani zai Tozartaki..! Mami Asma"u baki ta saki da Hanci Tana kallonsa kafin ta Mike Tsaye da Sauri Tana Fadin"Au Shi Kabirun ne ya aiko ka ka gayamin haka..? Yana kokarin mgana ta Dakatar dashi da Hannu Tana Fadin"Ya isa..Basai ka kara cemin wani abu ba..Bana Bukatar jin komai Daga gareka ai ka Riga ka Fadi sakon ka Shikenan sai ka bari nima nayi mgana.! Shuru kawai yayi yana mamakin Taurin kanta Cikin bacin rai ta Cigaba da Fadin"To in aiko ka yayi kaje ka Fadamai bazan je na bama kowa Hakuri ba Domin ban Batama kowa ba Ni ya kamata ba abama Hakuri ni da aka Lalatama Yata Future dinta Bazawara zan kirata ko Sakin Wawa..?wannan ai Cutar ma tana da yawa in shi yayi shuru ni sai nayi Shuru..? Wlh basa kaunarsa sunan yana Dan"uwansu ne da basu yi mai haka ba In shi bazai iya cewa komai ba Ni zan iya kan wannan mganar sai inda Karfina ya kare..Ni ina da kudi kuma na gaji kudi da asali Zan iya shari"a Dasu har Mahadi ya bayyana Shege ka Fasa..! Kai ya gyada kawai kafin ya Juya yana Fadin"Mami kiyi Tunani..Ki kara Tunani abunda kika aikata bai Dace ba..kuma wanda ma zaki aikata bai Dace ba..Ina Tsoron abubuwa suxo su Lalace..! Tsaki taja Tana Fadin"Komai ya Dade bai Lalace ba..Bazan ja da baya kan mganata ba..! Ficewa kawai yayi ransa na kara Kunci In Mami ta aikata abunda tayi Niyya komai fa Zai Lalace wazai Dakatar da ita..? Dad bafa bazai iya Dakatar da ita ba,Ta gama Rainasa sai dai in Justice Tafida zai kira ya Fadamawa Mahaifinta Kila in ya mata mgana Taji Hajiyarsu kuwa bama zai kirata ba Domin kamar gadon Hallayanta ne Mamin ta Dauki bama zata Dakatar da ita ba sai ma kara mata Karfin gwiwan da zatayi. Koda ya Fito Dad na Jiransa ya shiga Mota suka Fice Umai ta Dade da wucewa makaranta a Airport suka ijiyesa kafin Baffa Kabiru ya wuce Wajen aiki Kafin Jirgin su ya tashi Khamis ya Kira Kakansa Tsohon Alkalin Alkalai na kasa Gabadaya Justice Tafida bayan sun gaisa ya Kwashe komai in Brief ya Fadamai sannan ya karishe da rikonsa kan ya Dakatar da Mami kan shigar da wannan Complain din..! Justice Tafida ya Fahimci jikan nashi kuma yayi mai alkawarin Zai kira Mami Tazo gida ta samesa zai mata mgana Daga haka suka Rabu Lokacin ma Jirgin su ya kusa tashi sai kiran suna akeyi kashe Wayarsa yayi ya Hau kan Layi yana Tunanin in ya tafi zai Dade bai Waiwayi gida ba sai ya manta da Bacin Ransa ba zai kara Dawowa kuma wani Bacin ran ya kara adding kan nashi ba. Koda karfe 9am na Safe yayi jirgin su ya Lula Sararin Samaniya yana Fatan Allah yasa Kakan nasa yayi wani abu In kuma bai yi ba to abubuwa fa zasu Kwabe ne,Domin yadda yaga Dad ya Shirya aikata komai kamar yadda Mami Tace baja da baya. Ashe duk wayar nan da Justice Tafida yayi Hajiya Turai Mahaifiyar Asma"u Tana Zaune ta gama jin komai suna gama mgana ta fara Bala"i tana Fada Tana Fadin"Wlh kada kace Zaka Hanata Kwatan yancinta..Wannan ai Ya saba Sharia..auran kaskasci sukayi mata da Farko ni nan na Taushi Asma"u ta yi Hakuri da mganar kuma Shikenan yanzu sai a sakar mata yar da ko Gidan auran ma bataje ba? Ai ko Kabiru bai Taki gaskiya ba Shi din banza waye shi?Takala dan talaka Asma"u ai ba Kalar sa bace Soyayya ce kawai da Allah ya Dora mata ammh ai Wlh ko Daya Kalan Zaren ai ba Kalan yadin bane in shi yana Tsoron yan"uwansa bazai iya mgana ba a kyalemin ya'ta ta kwaci Hakkinta amfanin Ilimin kenan! Justice Tafida ya Murmusa kafin yace"Hajiya Turai kubi komai a Sannu..Kada kimanta Kabiru ke auranta..Sannan wannam mganace ta Danginsa fa da Mahaifiyarsa..Anya Asma"u ta taki gaskiya?Daman ai tace bata son Auran yar taata da shi yaron Dan uwwn mijin nata ba ya Saketa ba ba shikenan an muku abunda kuke so ba kuma mganar shigar da kara For What Turai..?Wlh ki shiga Hankalinki kema ki Fadama yarki Kada ta Sake ta shigar da wata kara in kuma taki ji bataki gani ba..! Daga haka ya Dauki Farin Glass dinsa ya sanya ya Cigaba da karatun Jaridarsa yana jinta Tana ta Masifa Tana Zagin Kabiru wai dan Talaka bai da komai Mirmishin gefen baki yayi aransa yace"A"a fa Kabiru fa ba Talaka bane...Shi wani ne Mahaifinsa Har ya bar Gidan Duniya Alkali alkalai ne na Kotun musulunci kuma Talaka bai Taka wannan Mtsayin..! Hajiya Turai Daki ta koma ta Kira Yarta Tana Fada Tana Fadin ita ta bata goyon baya Shari"a zuwa Kotun koli su bazasu ji tsoronta ba Mami Asma"u ta Fashe da kuka tana ta Fadamata irin yadda yan"uwan Baffa Kabiru suka Tozarta tare da Mahaifiyarsu Ta kare da Fadin"Hajiya Sun Rabani Da Sajida..Wlh neman zagina take saboda wannan Tsinannen yaron..! Hajiya Turai tace"Rabu dasu duk zasu gane basu da wayau..Saki ne dai Matakin da Kabiru zai dauka na karshe ko..? To in ya fasa ya sake kin yagani in baki samu wani Babban goron Daya Takasa ba..! Dayake Idanuwanta ya Rufe bata Fahimci Zata Tafka kuskure ba Mami Asma"u na Fadin"Wlh Hajiya..Ai daman ance Babban goro sai magogim karfe..! Sun dade suna mgana Hajiya Turai bata Taushi Yarta ba ko Daya sai ma kara zugata Da tayi shi ya kara mata Kwarin gwiwa suna gama waya tayi wanka ta Fice a gurguje ko Karyawa batayi ba Ta fita taje Office suka Hadu da Brr. Zailani kan Tana so Ashigar da karar kai Tsaye ne Daga Kotu ta Cike Complain Form kuma ta na karan Daada ne da ya"yanta Guda Biyu Mustapha Hamisu Dukku da Abubakar Hamisu dukku..! Abunda bata sani ba suna gama mgana da Brr.Zailani ya zagaya ya Kira Baffa Kabiru ya sanar dashi komai,Daman tun sanda Mamin Ta Kirashi kan Complain din yaji mamakin wai zata shigar da kara kan Mahaifiyar Brr. kabiru da Yan"uwansa Shiyasa ya Kirasa ya Fadamai shi kuma yace da Zarar ta Cike Complain Form ya fadamai Lokacin ne zai yi mganin Asma"u Zata ga True Colour dinsa da bata taba gani ba sai ya Koyamata Hankali Zai nuna mata ana Sauya mata ammh ba"a Sauya Uwa da yan"uwa. Gabadaya Ransa ya gama baci yau Za"ayi ta kare Baya so ya yanke Hukunci cikin Fushi shiyasa bai Dawo Gidan ba yana son ya yanke komai a Saukake. Yana Office Sajida ta Kirasa Tana Fadamai ta Dawo makaranta yau daga Dukku yana ta mamaki Tsausayinta ya kamashi Data gayamai a Motar Haya ta dawo ya sani itama ta Guji Gidan ne saboda Mahaifiyarsu ta gama Illata Zuciyarsu,Yaji kamar yayi mata Kwallah Fatan alheri yayi mata da kuma Nasihan ta Cire Damuwa tayi Facing din karatunta ta amsa mai da Insha Allahu. Dukkansu sun kashe Wayar kowa Zuciyarsa ba Dadi,Baffa Kabiru kamar yayi kwallah,Kudi ya Tura mata 30k yace ta siya abunda bata dsshi Lokacin Dataga Sakon nasa Tana libary ne tazo Karatu ba Domin Tana Fahimta ba sai domin shine Mafitanta. Yau da Safe goggo Maimunatu ta koma Bauchi Mijinta yazo duba Daada Daganan ya wuce da ita Daman itace ke Kula da ita goggo Bintalo ba Ruwanta Ballatana Daada da Fushin Mami da Dad ya shafeta Ta riga tasan tayi rashin Rashim Masoyin da bazata taba maida kafarsa ba,Mami Ta riga ta gama Lalatamata Farincikinta gani tayi Zaman bai da wani amfani yasa ta fara shirin Tafiya Duk bata wani jin Dadi ga Sakewar jikiga na zuciya. Sai da tagama Shiryawa kana taje Dakin Daada Tayi mata sallama Daada Tsausayin Sajida ya kamata ta Rumgumeta tana Lallashinta da ban baki Sajida na kuka tana Rokon Daada ta yafema Dad dinta Daada tace bata Rikesa ba in ya gano kuskuransa ita Tafi kowa Murna da haka. Ita ta bama Sajida 5k duk da tace tana da kudi tace ta kara Tunda makaranta Zata koma Bayan Tafiyar Sajida Daada tayi kuka,Yarinyar abar Tsausayi ce Dama Dama haka bai Faru ba data Hakura da Cin Mutumcin Asma"u sai dai ai ba ita auran ke hannunta ba Wanda Auran ke hannunsa ya warware kuma bazata Tursasamai kan sai ya maida Sajidan ba, tayi alkawarin ta bar kara Tursasa kowa koda ya"yanta na Cikinta ne. *Shakira..* 3/25/22, 22:52 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�19* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Karfe 8:30pm na Dare ya shigo Gidansa,Mami Asma"u ma bata Dade da shigowa ba gidansu ta wuce Mahaifinta ya kirata awaya yace Tazo yana son ganinta Justice Tafida. Duk da Justice Tafida yace mata ta Janye Ra"ayinta ammh bata ji ba shi kuma Dan Boko ne mai akidar Dabaya mtsama ya"yansa kan Ra"ayinsu zai gayamaka gaskiya Ruwan ka ne kayi aiki Dashi ko kar kayi aiki dashi Shi dai bazai Tursasaka Dole ba kayi Karatu kasan Daidai da akasinsa. Hajiya Turai ce ta rika Zuga yarta ta batayi Tunanin abunda kan je ya dawo ba Mami Asma"u saboda Tana ganin kamar abun kunya ne aji wannan abun ya Faru da yarta yasa ta Roki mahaifiyarta karta Fadama kowa cikin yan'uwanta Asma"u basu da yan Uba Hajiya Turai ce kadai Matar Juctice Tafida tun auran Saurayi da Budurwa. Da wannan Famfon Asma"u ta Dawo Gida Allah Sarki Umai ce kadai agida Daga ita sai yan aiki,shiyasa saboda Kada kadaici yayi mata yawa data yi wanka Ta sauya kaya ta Sauko kasa ta Zauna Wajen Umaima Wacce take assigmemt din da aka basu a makaranta ta Hanyar Browsing a wayarta. Bata ce ma Mamin komai ba bayan gaisuwa saboda ba Huruminta bane Ammh Tabbas akwai Mtsala Tsakanin Mami da Dad din,Suna nan Zaune ya shigo Kallo Kallon sukayi ma juna Shida Mami Asma"u shi ya Fara Dauke kansa Umaima ce tataso Ta Rumgumesa tana yimai Welcome lokaci Daya tana karban yar karamar briefcase din Dake hannunsa ya Haura Sama tabi bayansa Mami Asma"u ta bisa da Hararan kasan ido gobe goben nan Zata je ta shigar da kara taga mai hanata Har Dakinsa Umaima takai masa Jakar ta Fito ta barsa zai yi wanka bayan ta Fadamai tana Jiransa ya Sauko su yi Dinner. Saboda Umaima yasa bayan yayi wanka ya saka Jallabiya ya Sauko kasa Direct Saman Dining ya Nufa Umaima na ganin haka tace ma Mami itama Ta taso,suci abinci Saboda Umai yasa ta Mike Tana wani Takun isa ta karisa Saman Dining din ta Zauna gabadayansu haka sukaci Abincin kowa na saka abunda zai Fishasheshi acikin Ransa Umaima ce kadai ke karadinta ita Kadai duka iyayen Daga Uhm sai Uhm ne Har suka gama cin Abincin kowa ya Watse Umaima Dai Dakinta ta Shige Ta karisa assigment dinta ta kwanta daman ka"idan Gidan da Wuri kowa ke shigewa ya kwanta taji ta samu natsuwa Dazu da sukayi mgana da Sajida bayan ta Dawo makranta Ita Sajidan ta Kirata sai dai yanayinta a Sanyaye yasa tasan Zarginta ya Tabbata wani abu ya Faru ko yana kan Faruwa Sun rabu da Sajida kan Umaima din zata zo ta ganta Ranar Sati a makaranta Tunda ita Sajidan tace ba zata samu Dawowa Gida Weekend ba wannan Satin. Akallah ta samu natsuwa bada yawa ba. Misalin Sha Daya na Dare Baffa Kabiru ya gama Duba wasu Tarkadu kan Shari"ar da suke kai ne Kana ya Mike ya Fice Daga Dakin nashi Sai da ya Fara Leka Umaima yaga tayi barci kana ya Rufomata kofa Direct Dakin Mami Asma"u ya Nufa Daman Saboda Kada Umaima taji Sa"insan da ita ne yasa ya bari sai ta kwanta barci. Bai Tsaya ma mata Knooking ba kawai ya Tura kansa Lokaci Daya da Sallama Fitowarta Daga wanka kenan ta Saka wata doguwar Riga mai Taushi Ta barci shirin kwanciya Take yi ya shigo. Dakata tayi da kokarin Zama kan gadon ta gyara tsayuwarta Tana kallinsa shima kallonta yake yi Cikin Wani yanayi sai dai bai Hango Nadama a Tare da ita ba yasanta Tana da Kafiya da Taurin kai,Ko a Sharia in ta samata naci bata sukuni sai Tayi Nasara. Gyara Tsayuwa yayi Lokaci Daya yana Harde Hannunsa ya goya a bayansa Cikin Kallonta ido na ganin ido ya Fara takowa zuwa gabanta suna Tsaya suna Nazarin juna na wani Lokaci ita ta Fara kauda idonta a Kansa saboda ai Namiji ne bazata iya Juran kallon Cikin Idanuwansa ba. Cikin dan Sanyin Murya yace"Asma"u Meyasa kika cike complain Form..? Kai Tsaye yayi mata Tambayar yana kallonta Tana kallonsa Dan mele baki tayi Tace"Kafini Sani..! Yana kokarin Boye bacin Ransa yace"Wa zaki kai kara..? Mahaifiyata ko yan"uwana..? Mami Asma"u bataji wani ko Dar ba Tace"Dukkansu..Zan yi kara Domin da saka Hannunsu Rayuwar y'ata ta ragu,je in kai kayi shiru ni bazan yi Shuru ba sai na kwaci yancina..! Bata gama Rufe baki ba ya Tare ta da Fadin"Yanci ko..?ina yancin..? Ke kisan wani abu wai shi yanci ne..?In yancin kike nema shi aka baki kin nuna bakisan auran Sajida da Alokacin na mara Miki baya saboda son da nike miki yanzu kuma an yi miki Abunda kike so kuma ya Zama abun Tozarci a wajenki..?ke wata irin macece mai son kanta Asma"u..? Baki Tunanin kowa sai kanki.?tunda mukayi aure na Sakar miki Duka wani Dama hatta da Damar dangina Duka na baki ina bin Duka Dokokin ki kamar kice Mijin nice matar..Ina jin mganarki ina Danne Ra"ayi na Saboda na Fitata naki Ra"ayin Duka wannan abun bai isa yasa ki gane ke mai son kanki bane..?ki duba irin abunda kika aikata a Dukku Saboda na baki Dama kika cima Daada Zarafi kika Hada da yan"uwana ke baki ji kunya ba..?in nayi ma iyayanki Haka zakiji Dadi..?nace ki Duka ki bata Hakuri gaban Duka Kowa da kowa kika Nuna ban Isa Dake ba Nima ba kowan kowa bane a Wajenki,Sanadinki Daada tayi Fushi Dani kinsan Dafin Fushin Uwa kuwa Asma"u..? Kuma Duk da Hakan bai isheki ba Sai kuma kika Bullo da wata mganar banza na zaki kai uwata da yan"uwana kotu ke gaki Ubanki Tsohon Alkali kuma ga ki Lauyar gwannati ko..? To Shege ka Fasa Asma"u ni kuma zan nuna miki Jini yafi Ruwa kauri Uwa da yan"uwa suna gaba da kowa a wannan Duniyanan nagodema Allah Dayasa na gane kuskure tunda wuri kuma da yardan Allah Duk Zan gyara inda na kuskure ba kyalekin da nake yi bane yasa kike Wasu iskancin ba To kiyi yanzu nagani nace kiyi yanzu na gani din in ban yi mganinki ba..! Har ya gama mgana Mami Asma"u bakinta a Bude Tana Binsa da kallon Mamaki Kafin tace"Ni yau kake Zagin Ubana Kabiru kan gaskiyata..? Kai Tsaye yace mata"Eh an Zaga din Ashe Uba yafi Uwa ko..! Naki iyayan yan Daraja ne kuma yan gold ne ashe kina Sane nawa uwar kika Raina..! Cikin Bacin Rai tace"Iyayena sunsan Abunda sukeyi bazasu taba aikata abunda Taka Uwar ta aikata ba...Mai son kanta kawai..! Cikin Shima Bacin rai da Hargowa ya nunata da yatsa yana Fadin"In kika kara Fadin kalma Daya na batanci kan Daada sai na Bata Miki rai..! Azatonta Burga yake mata sai ta gyara Tsayuwa Cikin Gatsali da Hargowa tace"In nace fa..? Me zaka iya Kabiru..?Na Fada na kara Fada Daada Tsohuwa ce mai son kanta Mara adalc..!bata gama kai karshen mganarta ba wasu Tagwayen Maruka Dama da Hauni suka Ziyarci kuncinta Saboda Zafin marin Da Sai ta Kife saman gado Cikin Zafin zuciya jikinsa na Rawa yake Nuna ta da yatsa yana Fadin"Kadan kika gani in har bakin ki bazai yi linzami ba..Na Rantse har ga Kika Kara fadin Tak kan Daada sai nayi miki Abunda baki Taba Tsammani ba..! Yafada Jijiyon kansa suna tashi Saboda Bacin rai Mami Asma"u da mamaki ya Sandarvda ita Gefe Daya ga Zafin marin Daya gigita Daga zaunen Hannanunta saman kuncinta Cikin Zubar Hawaye tace"Ni ka Da ga Hannu ka mara yau Kabiru..!? Kai ya gyada Mata yana Fadin"Wannan ma kadan nayi miki In baki iya bakin ki ba Sakarya kawai wacce bata san inda ke mata ciwo ba..! Mami da kukan Bakinciki ya Ciyota ta Mike Cikin Hargowa da kuka taci Kwalan Baffa Kabiru Tana Fadin"Wlh baka isa ba Tunda ka mareni baka mari banza ba..Kan gaskiyata..? Ance Daada ta cika sonka Tsohuwar banZa ce i...! Bazai iya jin Duka kalamanta ba Saboda in ya gama ji Bacin rai zai sa yayi mata Dukan Mutuwa Watsar da ita yayi a kasa cikin Fushi da Tsananin kamar ya bita ya Tattakata yake ji bai Taba Nadamar auran Wayewa da Boko ba sai yau Cikin Fitar kwallar Cin Zarafin Dayajama Daada Uwa garesa yace"Kije na SAKE KI Saki Daya Asma"u..Kibar min gida yanzu nan..kuma mganar Complain kada ki Fasa shigar da kara ni kuma Ina nan ina Jiranki Yar iskar mata kawai mara lissafi..! Bai Tsaya Jiran Kwakwzonta ba ya Fice Daga Dakin Saboda bacin rai har Bangaje Umaima yayi bai sani ba wacce Rigiman iyayan nata ya Tada ita kuma taci kalmae Sakin da Dad ya Fadama Mami ai sai ta kasa Gaba ballatana baya,Balle taga yadda ya Fito ta Fusace sai Hawaye da kuka kafin ta Kwashu gudu zuwa Dakin Mamin nan ta ganta inda ya yasar da ita kamar irin ta shiga Shock haka Domin tayi kuri ne Hawaye suna Zubomata Shar kamar an Bude Famfo. Gani take kamar waasa wai ita Kabiru ya ce ya saketa?Duk Abunda take yi Tana Takama da Son da yake mata baata Taba Tunanin Akwai Watarana da Kabiru zai Furta mata Kalmar Saki ba ba Burga kawai take yi Tana Tunanin bazai iya ba,Tana ganin Soyayyar Dayake mata bazai barsa ya iya Sakinta ba yanzu Daya Furtamata Sai Duniya ta Fara juyawa da ita. Umaima ta Rungumeta Tana kuka Tana Fadin"Mami What all dis..?Dad fa naji yana Fadin ya Sake ki plz ki Fadamin wasa ne ba gaskiya bane.! Mami Asma"u ta Zura mata ido Tana Fadin"Kema kin ji ko Umai..?Daddy ku yace wai ya Sakeni..Da gaske ya Sakeni ne..? Umaima na Kuka tace"Mami Haka yace kema kin ji nima naji da kunnena yace ya Sakeki ki bar mai gidansa Why Mami..?meyasa kika azagi Daada.?kamar uwata take fa kema a wajenki Kada ki manta Ita ta Haifi Dad bazai Taba Jure cin Zarafinta Daga Bakin kowa ba Koda Kece kuwa! Sai alokacin Mami Asma"u ta tabbatar da kanta komai fa daya Faru gaskiya ne Kabiru ya saketa kuma yace ta barmai Gidansa ai sai ta Rukumkume Umaima ta fashe da kuka Innalillahi me ta aikata..? Saki Gotai gotai da ita da manya Ya"ya ta koma gida Zawarci bata Taba Dauka Haka abun yake ba Lokaci Daya Nadama ta Isketa,Mikewa Tayi Da Karfi kamar Wata Zararriya ta Rarumi Wayarta ta Doka ma Hajiyarsu Waya Umaima na gefe Tana kallonta Tana Sharan Hawaye Lokacin da Mami ke kuka Tana Sanar da Hajiya Turai Brr.Kabiru ya Saketa Ashar ta Lailayo ta Sakar mai Dashi da Daadan gabadaya Ta Fara fadin"Yau naga aikin Fulani Daman ance Fulani akwai bakinciki da Hassada da son kai da Wauta da Rashin Lissafi eh lalle naga aikin Fulani kuwa ni Turai..Da Tsohon Daran nan zai sakar mana ke ,gotai Gotai Dake ko kunya Kabiru bai ji ba..? Ai ko bai Darajaki ya Ragamiki don Soyayyar da kika Nunamai ba ya Duba Wadanan Zaratan ya'yan da kuka Haifa in mu bazai ga Girman mu ba..! Tafada Tana kumfar baki Mami ma sai kuka take abun ya Daketa ita kanta Hajiya Turan fa Fada ne kawai ammh Ina Zakaso D'anka da girmansa Shekaru sun ja a kore maka shi awannan Lokacin ai abun kunya ne sosai kuma ba wasu iyaye da zasu so haka ita kanta Kabirun Wlh ya bata Mamaki bata Taba Zaton zai iya Furta kalmar Saki Ga Ma"u ba Tun Daga yanayin Zamantakewarsu da yanayin Zaman auran nasu. Justice Tafida ta Fadama Halin da ake Ciki Daman yana Zaune ne yana kallon Labarai A tashar CNN,kai kawai ya gyada kafin yace"Ki Fadamata ta shirya Direba zai zo ya Dauketa..Tunda bataji mganata ba Har takai su ga haka Is ok..Kowa yayi yadda yake so..! Daga haka ya cigaba da Kallonsa Kafin Lokaci Daya yana Danna Wayarsa zai Kira Direban da zai Dauko Asma"u. Hajiya Turai ta Kallesa kafin tace"Ranka ya Dade ayi haka..?Gotai gotai da Ma"u sai ta dawo gida Zaman Miji ya saketa..? Bai mata mgana ba sai da ya gama Waya Da Direban kana ya Dago kansa bayan ya ijiye wayar yana Fadin"Sai ta zauna bayan yace tabarmai gidansa Turai..?Abunda ta Zabama kanta kenan bazan hanata ba ai ba yarinya bace She know What is Right and Wrong..Katon gidane ina dashi akwai Dakuna Kowa ya yanke ma kansa Irin Abunda ta Zamar ma kanta bazan hanasa Zama agidana ba kowa nada Righat dinsa so banga abun Damuwa ba..! Daga haka ya dauke kansa ya Cigaba da kallonsa Ai bata kara mgana ba ta Daga Waya ta Kira Mami Asma"u tace ta Shirya ga Justice nan ya Turo Direba ya Dauketa daga haka ka Katse Kiran. Mami Asma"u na kuka Umaima nayi Baffa Kabiru bai san sunayi ba yana Cikin Dakinsa Bai kuma yi Nadamar Abunda ya aikata ba.. Yana Daga Tsaye wajen Window yana kallon Haraban gidan Daga waje Mota ta Shigo Daga lambar Motar ya gane Daga Gidan Justice ne karamin Tsaki yaja yana jin karin wani Takaichi Sam dai ba Tsari ace kana Babba da iliminka da komai kace Bazaka Tsawata ma yaranka ba sai dai kace su ba yara bane suna da Rigaht din da Zasuyi abunda suka ga Dama,Daman fa In Boko yayi yawa wani Lokacin Har Kafirta Mutun yana yi. Agaban Idonsa Mami Ta Fito Umaima na Riketa Tana kuka itama kukan take Tana Dauke da Karamar akwatinta,Yana Tsaye yana jiran yaga koda Umaiman zata tafi sai yaga ta shiga Mota Direba yaja sun Fice Daga Gidan Umaima ta Durkushe nan tana kuka,Sai ta bashi Tsausayi Dalilinta yasa ya Sauko kasa ya Fita ya Rarrasota ya Riko Hannunta yakai ta Har Dakinta Fadi take "Plz Dad ka Dawo da Mami kada bari tatafi..! Kai kawai ya gyadamata ammh acikin Ransa ya Kudira in har Asma"u bata gyara ba To ya yarda su Rabu Rabuwa Ta Har Abada. Sai da yaga ta Daina kuka kana ya bar Dakin ya koma Dakinsa yana Fita ta Mike wayarta ta Kunna ta shiga Neman Layin Khamis ammh bata Samesa ba Wayarsa tana kashe. Abunda bata sani ba Khamis ya Sauke Layinsa da kowa ya san sa dashi ya Siya wani ya Dora Tun bayan da isa wajen aiki ya Kira Mami da Dad ya Fada musu ya sauka Daganan ya Sauke Layin ya bama yanmata gari da ma"abota son Holewa kara shiga Rayuwarsa ya Bude ma Club da Mashaya Bakin Aljihunsa aranar Daya koma Duk Saboda ya manta Da Inteesar Har Giya yanzu yana sha da kayan Maye wanda ke matar dashi komai Na Duniya da Duk wani bacin rai. Ganin bata Samesa ba sai ta Kira Sajida itama Dayake ba barcin Wuri take ba kuka ma take kwance Tanayi Dayake su biyu ne Adakin ita da Wata Jenefer ba musulma bace itama iyayanta Wasu ne,Ta Girgiza sanda Taji mganar Umaima wai Dad ya Saki Mami har ta tafi gida duk da abun ya Shigeta ammh tafi Tsausayama Dad akan Mami ita ai ta Chanchanci koma Menene. Jin tace mata bata samu Khamis a waya ba yasa tace ta Kira Baffa Mustapaha ta Fadamai in tana da Lambarsa Umaiman tace tana dashi bari ta Kirasa,Sajida na son tace mata ta bari sai gobe da Safe Dare yayi sai dai bata Saurareta ba Ta kashe Wayar Saboda Hankalinta ba yana Kwance bane. Sajida taji Rauninta ya Karu Tashi Tayi ta Shiga Tiolet chan ta Saki Kukanta son Ranta tanayi Tana Rufe bakinta kada tatashi Jennefer Dake Barcinta Bata da wata Damuwa,Mami Duk ita ce Silan komai yanzu kuma ta kara Bullo da wata Rigima har takai ga Dad ya Saketa ai Allah ya kara mata Ita sonkanta komai Mami zatayi sai ta Fara Duba kanta kafin ta Fara Duba wani Shiyasa taki komawa Gida bata so taga Bakinciki Sai gashi Abunda ta Guda ya Faru Abunda basu Taba gani ba ko Fada ne na Chachar Baki Tsakanin Mami da Dad har Fata take in Tayi aure Zata gina Gidan auranta yadda Mami da Dad suka gina nasu gashi yanzu komai ya kare. Sai da tayi kukan ya isheta kana ta Hakura jin kirjinta na mata suya kanta ya Fara sara mata yasa ta Wamko Fuskarta ta Fito Tana Dafa Bango Jiri take gani saboda Tsabar Tashin Hankalin Datake ciki Tazo ta Fada kan katifarta yaraf kamar kayan Wanki Umaima kuwa ta samu Daddy a waya Dayaga Kiran sai da gabansa ya Fadi bai da lambartaa ammh kiran Waya da Daddare haka yana Fadar ma Da Mutane gaba,Umma Tayi barci Tun Dazu Shima Wani lissafi ya Tsaidashi yasa bai yi barci da wuri ba. Koda ya Daga Kiran Kukan Umaima ya Faramai Maraba Dakyar ta Tsagaita Tamai bayanin Abunda ke Faruwa Salati ya saka Cikin Rashin jin Dadin Abunda ya Faru ya lallahi Umaiman yace mata da Safe zai kira Abba in ta kama ma zasu zo nan Abuja Haba ai bazasu bari haka ta Faru ba,da kalaman Daddy Umaima taji Sanyi tasan Zasu ja Hankalin Dad ya Dawo da Mami gida. Salatin Daddy ya tada Umma Daga Barci,Cikin muryan barci Take Tambayansa ko Lafiya cikin Damuwa yake Fadamata abunda ke Faruwa ita kanta Sai ta Dafe Kirji Tana Fadin"Saki..? Abun har yakai ga Saki ne Abban Inttee..? Cikin jimami yace"Gashi kuwa..Allah dai ya kyauta bari na kira Ya malami muji yadda zamu yi yariyar tana ta kuka ko Saboda yaran..Da kuma an Riga an girma bai kamata ba..,! Umma ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Karamar ce ta kira ko Sajidar..! Daddy yace"Karamar ce Umaima..! Umma tace"Allah ya kyauta..Da ka bari sai gobe da safe ka Kirasa yanzu Dare fa yayi sai ka Tayar mai da hankali..! Kansa ya jinjina alamun Ya yarda da mganarta,Barin kiran Wayar yayi ammh Lissafin da bai karisa ba kenan abun ya Damesa da asuban Fari ya Kira Abba ya Fadaamai yana ma Hanya ne zasu dawo daga masallaci su Yusuf sukayi gaba suka barsa suna mgana shi kanshi bai ji Dadi ba suka Tsaida mganar dashi da Daddy zasu Tafi Abujan su samu Baffa Kabiru Ranar Alhamis,Saboda Abba zai Fara aiki Ranar Monday ne da haka suka Rabu Zukata duk ba Dadi. Abba bai yi Zencen da kowa ba Shima Daddy bayan Umma bai Sanar ma Kowa ba Baffa Kabiru bai kirasu ba kuma suma basu kirasa ba suna Jira ne kawai ya gansu kwatsam Aranar da yammah Yusuf yakai Abba Wajen Siyan Mota yace ya Zabi Wacce yake so Abba ya Zabi prado babbar ta Imran baka mai kyau miliyan 6 Sabuwarta nan take yusuf ya Biya kudin bai kai ba Sai da ya Hada Sauran kudin acct dinsa. Tare da Motar suka isa gida atare Yusuf ya Sallami Wanda ya Rakosu da Motar. Zuwan Motar ne yasa da Munari ata fadama Inteesar yasa ta jawota Dole tazo taga Mota tayima Abba Murna,Tana ta wani Sunne kai Abba ya jawota Jikinsa yana Fadin shi baya Suruka da ita yarsace ita Ya yusuf kuwa ta Daina Hada ido dashi gogan kuwa Tunda ga Ranar bata kara ganinsa bai nemeta ba itama bata nemesa ba. Ranar Laraba sun fito daga Lecture din Safe ita da Munari Cafteria suka je suka siyo Lemo da Biscuit,suka Samu wani Inuwa bakin wani Department suka Zauna sun fara shan Lemon kenan suna Hira Wayar Munari tayi kara Tana Dubawa Taga Hafsah ne ta Dauka suna mgana Inteesar na kallonsu duk kan Shagalin da zasu yi da Bikin su ne Suna Fadin zasu bude Bride group za"a Saka ango da abokansa suma zasu sako kawayen Bride. Munari na Dariya tace"Ke ango bai da Babbar Waya sai Rakani Kashi..! Gabadaya ita da Hafsah suka saka Dariya Inteesar ta Hade rai Tana Hararanta. Daga chan bangaran Hafsah tace"To sai mu kyalesa Daman ko yana dashi ke zan jona ki sako manashi..! Munari ta waro ido Tana Fadin"Wa ni..?Rufamin asiri waya aikeni ballatana yaga na Dade..? Wlh badani ba yaga ni Sakashi ki auna yadda zaizo ya sauyamin kammani..! Dariya Hafsah ta Saka mata Munari ta Cigaba da Fadin"Abokai kuma Daya na Sani Ya Sagir..Kuma bamu da Mtsala Dashi..Kawaye kuma Imu imu ne daga ke sai Nasara sai ni sai Tasleen kanwar Anty Safiya Bana jin Intee nada wasu kawaye..! Hafsah tace"Shikenan ma hakan yayi wai yanzu yaushe Date din Bikin..?Naji ya Sa"id na cema Anty Faree Daada tace wannan na Hannunsu Baffa kuma yace sun yi mgana da Sadam yace Baffa Mustapha yace Date din Biki Sai ya Imu ya Saka Rana da kansa Tunda shine mai gayya da aiki..! Munari tayi Sakai sakai kafin Tace"Topha ya Imu muke jira kenan..? Dankari..! Hafsah tace"Nima abunda nace kenan..Ita ai maatarsa in mu muna jin tsoro ita Ta tambayan mana shi mana Muna so muji Lokacin ne yadda zamu Tsara abubuwanmu..! Da wannan Shawaran suka Rabu Tsakanin Munari da Hafsah. Inteesar Tayi bakan tana jinsu batace komai ba.. Munari ta Zungureta Tana Fadin"Nasan kina jina da Hafsah ko..? Mganar Tarewarki ce..Ance fa su Daddy sunce mganar Sanin Hakikanin Date na wajen Ya Imu..! Yamutsa Fuska Inteesar Tayi kafin Tace"Sai akayi yaya..! Munari ta Kalleta Cikin mamaki kafin Tace"Kamar ya..?Tambayo mana shi Zakiyi yaushe ne ya Tsaida Lokaci saboda Shirye shirye.! Inteesar ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"Abunda ni ko kulani ma bayayi..Tunda aka Daura mana aure ko dan irin Text messages babu ballatana Kira..Nima kuwa na Sharesa bai nemeni ba nima ban nemesa ba Tun Ranar Monday da muka Hadu kofar gidansu Mama.! Shakeke Munari ke kallonta kafin Tace"Au ke daman kina Jiran ya Nemeki ne...? Kin manta Waye ya Imu..?Dankari na Rantse har ga Allah ko Tarewar kukayi ke za ki sha Wahala in har kina Tsammanin ya Sauke wannan Egon nashi ya Nemeki u are mad ma Wlh Ya Imu fa..Kai ai kina ma Cikin Masifarsa zai ce kin gama Rainasa Intee..! *Shakira..* 3/25/22, 22:52 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�20* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Inteesar ta kalli Munari cikin wani yanayi tace"Na shiga uku Munari ya Zan yi yanzu..? Tafada tana kwalkwal da Idanuwa kamar Zatayi kuka Munari ta gyara Zama Tana Fadin"Ya kuwa..?kin fa san Halin ya Imu mijinki ba irin na kowa bane Inteesar..Kuna son junanku ammh Soyayyar tana Wahalar daku baku Sani ba..! Inteesar ta Harareta Kafin tace"Ya akayi kikasan muna son juna..?in ni na yarda Yes ina son ya imu shifa kinga alamun Sona a tare dashi..? Tafada Cikin bayyana Damuwarta. Munari ta Dan yi mirmishi kafin tace"Wlh Ya Imu yana sonki..So mai Zafin da bai isa ya iya Guje miki ba..soyayyar Data shigesa batare Daya sani ba,Kema kuma kina sonsa soyayya mai Zurfin da baki san yaushe ta Fara ba Intee..! Inteesar ta kalleta kafin tace"Duk ya akayi kika san haka..?ke da ba Soyayyah kike yi ba..? Munari tace"Ni ina son soyayya ina son naga Masoya suna Kwasan Soyayya Raba Raba na Dade da Fahintar ku keda Ya Imu kyaleki kawai nayi Naga gudun Ruwanki,Sai kuma gashi komai ya zo karshe kun zama Miji da mata to ai zama bai ganki ba yarinya ba yanzu bane zaki kwanta kice zaki ja ajin nan ba Sai mun kamasa a Hannu in Tafiya tayi tafiya sai muja Zaran mu son ranmu yadda Zai zo ya fara ban baki da Lallashinmu batare da ya sani ba..! Inteesar ta Sauke ajiyar zuciya kafin tace"Munari Wlh ni kaina sai Daga baya na Fahimci na kamu da Son Yaya Imu ban Fahimci haka ba sai da aka Daura mai aure da Sajida kamar na Mutu haka naji alokacin..Ammh ni yanzu Damuwata Daya ne Shin ya karbi Aurena saboda yana sona ko Saboda ba yadda zai yi ne kamar na Sajida..? Munari tace"Saboda soyayyar dayake miki yasa ya aureki ba komai ba..Wlh Ya Imu yana sonki zaki ce na Fada miki Inteesar..! Inteesar tace"In hakane meyasa bai Taba Fadamin ba..?bai taba nunamin alama ba..? Munari tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Shi Ya Imun ne zai Fada miki Yana sonki a wannan gabar ko..?U are not Serious Ai shi kanshi yana karyata kansa ne bai gama yarda yana sonki ba kece zaki sakasa ya Furta alokacin da bai sani ba..! Inteesar Tayi shiru kafin tace"Ta yaya..?ta wacce Hanya zan bi hakan ta Faru..? Munari ta Rike mata Hannu Tana Fadin"Ai kin Riga kin kama Zuciyarsa..Ya Imu bai taba bama Wata Mace dama a Rayuwarsa kamar yadda ya baki ba..Kin ga kenan kina da Babban Mtsayin da ba kowa ke dashi ba..yanzu gyarawa zaki yi ki Sani Ya Imu ya TSani Raini shiyasa bazai Taba Nemanki ba yana ganin in yayi Haka Zaki Rainasa,Ammh ke in kika Rika Nemansa ya zaki saka ya Fahinci kina basa Girmansa a mtsayinshi na Mijinki ko bai kiraki ba ki kirashi dan Text din ba Fasawa Zaki yi ba ki cigaba da yayi a wannan gabar Lokacin sa ne Ki bari namu Lokacin na gaba..Lokacin da zaki ja ajinki son Ranki kuma Dole ya Biyoki ya Lallasheki Saboda ya riga ya Fada Komarki Alokacin bazai iya Karyata Kansa ba bazai iya karyata Soyayyar Da yake Miki ba..! Inteesar ta gyada kafin tace"Yanzu me zan yi..? Munari ta gyara Zama kafin tace"Kiransa Zaki yi kice kin Kirashi ne ki gaishesa da aiki..In mun Tashi Daga School mu wuce gidanmu ki Dagaci dawowarsa Daya shiga Daki ki Dauki Ruwa ki bisa dashi In kika kai mai ke Macece kinsan yadda Zaki yi ki Tambayesa Yaushe yake ganin Za"ayi Bikin Tarewarku muji mai Zai ce..! Inteeesar ta jinjina kafin Tace"Allah yasa kada ya gwasale ni..! Munari tace"Dillah ke ce fa..?wlh baya gwasaleki..! Inteesar batayi mgana ba ta Fiddo da Wayarta acikin jaka ta lalubo Lambar Imran ta Kirasa wajen Kira Biyu tayimai bai Dauka ba ana uku sai ya Latsa mata Busy ta Dago kamar Tayi kuka Tana kallon Munari tace"Ya fa kashemin Kira..! Munari tace"Kara kira me nema ai yana tare da Hakuri..! Batayi musu ba ta kara Kira wannan karom bata Dade Tana Ringing ba ya Daga cikin Kaushin Muryansa na Koyaushe ya katseta Daga Sallaman Datake yi mai yana Fadin"Tunda kika ga kina ta Kira ban daga ba meyasa bazaki Fahimci ina aiki bane Inteesar....!!!! Yadda yaja sunansa sai da Jikinta ya amsa wani yarr Lumshe ido tayi kafin ta Bude,Munari na gefenta tanajin komai Duk da ba a amsa kuwwa aka Saka wayar ba Tanajin abunda yake Fadi Tunda suna Zaune ne kafada da kafada Zungurin Inteesar tayi ganin tayi Shuru Ta kasa mgana Sai ta Kalleta sai ta Fara mata alamun tayi mgana da idonta ganin tayi Shuru yasa yace"Kin Tsaidani ina aiki kuma kin yi shuru..?meyasa kika kirani..?any problem..? Da Sauri Inteesar Tace"Am..Ba..Bakomai..Daman na Kiraka na gaisheka ne ya aiki..? Yana Daga zaune saman kujeran sa Hannunsa Daya saman Laptop din Dake gabansa Dayan ne ya Sagala Wayar a kunnensa kafin yace"Kin kirani ne ki gaisheni..?yaushe kika Fara Kirana ki gaisheni..,? Bai bata Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Bakisan inda nake kwana bane..?Yarinyar nan Tsabar kin Rainani ma ni kike gani kina Guduwa kamar kin ga wani Sakarai ko..?na Kyaleki ne naga iya inda Zaki Tsaya ni ba Shashasha bane da zan saki aikin gabana na koma ina Lalacewa wajen Lallashin ki me akayi miki..?ko auran ne baki so..? Inteesar da idonta ya Fara cika da kwallah Tace"Yi hakuri.! Da sauri yace"No ba zencen yi Hakuri bane ko baki son auran ne kin fi so a warware kije ki auri wanchan Yaron..? Inteesar da Sauri Tace"Ban ce ba..! Tafada Tana Tura baki Sanyi yaji acikin Ransa kafin yace"To meyasa da kika gani kika gudu kina kuka..?na Dake ki ne..?kada fa ki manta ko ba Mtsayin Girman Miji ba ni yayanki ne so kinga ina da Girma Biyu a wajenki ammh na Lura baki kiyaye ko Daya ina Mijinki ammh Sai ki tashi ki Kwana ki Wunu baki neme ni ba irin U don"t care din ko..? Uhm ai yayi miki kyau zan kula Dakai na bana Bukatar komai Daga Wajenki sai dai bazan yarda ki Taremin agida da nayi mgana ki Faramin kuka ba..! Yafada kai Tsaye cikin kokarin Fadin Abunda ya Dade yana Damunsa acikin Rai. Kasa mgana Tayi jin tayi Shuru yasa yace"Is ok..ina aiki ne we tok later..Ko kuma in na dawo..! Da Sauri Tace"Am sorry..! Kansa ya shafa yana jin bacin Ransa na Sakinsa yace"Ya zan yi Dake..?ai dole na Hakura kada nace ban hakura ba ki Fara kuka Har sai Daddy daga Kaduna yaji Labari Tunda an Hadani da Shagwabbiyar kamarki ai an Hadani da aiki ni kuma gashi ban iya Lallashi ba ban da Taushi ko kadan Kananun kuka suna batamin rai Wani Lokacin ya za"ayi kenan..,? Dariya tayi batayi mgana Munari na gefe tana jinsu tana kallon Inteesar Wato Love kenan mai saka ko Sarki ne ya Rusuna. Jin Tana Dariya yasa yace"Au dariya ma na baki..?zaki yi bayani ne in muka Hadu..Later..! Yana Shirin katsewar wayarsa Munari na mata Rada tana Fadin"Banza kice i Miss u Allah ya dawo min dakai Lafiya Mijina..! Inteesar ta kalleta tana Kyafta ido Munari ta kara Fada tana wani kare Bakinta kada yaji batasan shi Tuni yaji ba har zai kashe Wayar yaji ana mgana Kasa kasa kunnensa kamar na Maciji yake yana da karfin ji sosai shiyasa ya Dakata mamaki ya kamasa Wato ma mara kunyar yarinyar nan Tana kusa kenan..? Ai shi fa ya gama Shiga Ciki Tunda ya auri Irin su Munari ammh Dole ya Tsare Giransa ya Tauna Tsakuwa Domin aya taji Tsoro. Bai yi mgana ba sai da Inteesar tace"Hello Ya Imu kana jina..? Idonsa ya Lumshe kamar Tana ganinsa yace"Uhmm..! Sai da ta Runtse ido kafin tace"Allah ya dawo min dakai gida Lafiya..And...! Ta kasa fada ta Fara Raba ido Munari na Zungurinta cikin Danne yanayinsa yace"And What..?Umh..!? Da sauri tace"I miss u...! Da sauri ta Datse kiran Tana Fadin"Ina jin kunya Munari..Ya Imu ne fa..! Munari tace"dillah sai me shi ba Namji bane..?ana koya miki yadda Zaki kamsa a Hannu kina wani Shirme ke kika sani Wlh ya ta baki Wahala..! Inteesar na shirin mgana wayarta ta Dauki kara Tana Dubawa ta Zaro ido Tana Fadin"Munari na Higesu Ya Imu ne ya Sake kira..! Munari tace"Shine me..?ki Dake ki Dauka kefa yanzu Matarsa ce kina da Damamarki da yawa ba kamar irin mu bace..! Jin haka yasa Hannunta na rawa Tana Dauka kafin tayi mgana yace"Saka wayar a amsa kuwa..! Cikin Zaro ido tace"Eh me kace..? Dakuna Fuska yayi kafin yace"Abunda kikaji a Farko..! Dagowa tayi tana kallon Munari itama Tana kallonsta kafin ta Sauke Wayar a Kunnenta ta sakata a amsa kuwwa. Cikin Nauyin baki tace"Na saka..! Gyara zama yayi yana Fadin"Sannu da aiki Jullet Uwar soyayya..?har ke ce kika tsara ace min i miss u ko..?Mara kunya yaushe kike..?da har kikasan ana kiran I miss u..?daman ba Karatu kike Tsayawa yi ba abunda kike koya kenan ko..? Munari ta kwaso Rantsuwa ya Dakatar da ita yana Fadin"Stop..Stupit ni sa"anki da zaki rika karanta mata abunda Zata ce min don Kaniyarki..?Jikin ki na kaikayi ko..? tsaya Tsaya ma waya baki Izinin miji da mata suna mgana ki shiga Tsakiya..?ke Matar aure ce ko uwar mata...? Munari da bata rai kafin tace"A"a..! Cigaba yayi da Fadin"Oh ko ni kuka maida abokin Wasanku..? wlh as from to Day in muna Mgana ki rika Tsshi Daga wajen ko Tarinki na kara ji sai na Tattaki kina so ki koyi Rashin kunya ko..?sai ki bari in kin kawo wanda kike so muka aurar Dake sai ki koyi gayamai U miss u..Bush gril kawai kuma ki bari mu Hadu Dake ki gani sai nayi kwallo Dake..! Bai jira cewarsu ba ya Datse kiran yana Jin Aransa na baci Inteesar din ce ta Rainasa ba wata ba itama zai koma Gidan sai ta Raina kanta. Munari kamar tay kuka Take Fadin"Daga Taimako..?ai shikenan..! Inteesar mai Zatayi banda Dariya Munari na Kallonta batace komai ba Ta sha kunu ta Dauki Lemonta ta Suri Jakarta ta wuce Inteesar ta Rakata da Dariya Lalle ne ma Ya Imu Wato munarin ce nawa take..? Bata san I miss u ba..Ita kadai in Ta Tuna Sai tayi Dariya sai da tagama shan Lemunta kana ta tashi tatafi Neman Munari Cikin Ajin Da suke Lecture ta ganta Tana karatu Tana ganunta ta Hade Rai Inteeaar na Danne Dariyanta ta isa kusa da ita Zauna ta Fara bata Hakuri Dakyar Munari ta Hakura ammh ta Dauki alkwarin bazata Taba yarda su hadu ba Ballatana Har yayi kwallo Da ita. Sai 6pm Suka Tashi Daga makaranta Direct Gidan su Munari suka Wuce,Sun iske Abba baya nan sun Fita gari shida Yusuf a Sabuwar Motar Abba din Anty Safiya ce agidan ita kadai agajiye suke abinci sukaji Sukayi wanka Lokaci Daya da Dauro alwala Tunda an Kira Sallar mangariba. Shashen Anty Safiya sukaje suna Hira Cikinta Har ya Fito sosai yana cikin Watansa na shida Suna nan har aka Kira Sallar Isha"i suka tashi sukayi Sallar sai lokacin sukaji Dawowar su Abba Falo suka Fita suka gaishesu ya amsa yana Tambayansu makaranta Suka ce Alhamdulillah. Nan falo suka Zauna Tunda Ya yusuf ya Dawo yana Tare da Anty Safiya Abba kuma ya shiga Ciki. Inteesar ta kalli Munari Lokaci Daya Tana kallon Kofar Dakin Imran tace"Ya imu ya dawo kuwa..? Munari na Dannar wayarta tace"Ki Dubasa mana..! Tafada cikin gatsali Inteesar Sai da tayi Dariya tashi tayi ta Leke Haraban Gidan Taga Motarsa ta Dawo Tana cema Munari"Ya dawo fa ga Motar sa chan..! Munari bata ma kara kallonta ba Inteesar ta koma Ta Zauna kenan Imran ya shigo cikin Sallama karama iya Saman Lebensa. Gabadayansu suka Dago suna kallonsa Munari sai da gabanta ya Fadi Da Sauri ta Mike tana gaisheshi ya amsa bai ko kalleta ba Inteesar ya kalla Wacce tayi Saurin Sadda kanta kasa bai ma Tsaya bi ta kan Munari Data Kwashi Sauri zuwa Dakinta ba Hannunsa Cikin Jallabiyansa ya Tura Kofar Dakinsa ya shige. Inteesar ta Sauke ajiyar Zuciya tshi tayi ta shiga Kitchen ta Dauko Ruwa mai Sanyi da Nutri milk ta Dora saman wani Tire da Karamin Kofin glass guda Daya sai da ta tabbatar Abba bai fito ba kana Tayi Sadaf Sadaf ta Kwankwansa Dakin Imu yana jinta jikinsa ya bashi itace shiyasa yace mata ta Shigo. Shigowa Tayi Lokaci Daya da Sallama,Ya amsa mata iya saman Lebe yana Zaune gefen gado yana Duba Wayarsa Kiran Khalil ya gani kila Lokacin Daya tafi masallaci ne ya bar Wayar agida. Daburcewa Tayi ganin yadda ya Dauke kansa Kamar bai san da Wanzuwarta acikin Dakin ba ganin ta Tsaya mai kikam a saman kansa yasa ya Dago yana kallonta Cikin Dan Hade Rai yace"In bazaki ajiye ba ki koma Dashi mana..! Yafada Kai Tsaye yana kallonta Da Sauri ta ijiye nan saman Drower din gadon,Ta koma gefe Tana Fadin"Ruwa na kawo maka sannu da zuwa..! Yana kallonta baya so ya gwasaleta Yasa yace"Is ok..Nagode..! Da haka ya mike Laptop dinsa ya Dauko Cikin Briefcase dinsa ya Dawo ganinta nan Tsaye tana waasa da Zoben hannunta Daga sama har kasa Tana Sanye cikin Riga da Sikat na wani leshi kayan sun mata Das ajiki gabadaya Sturcute dinta ya bayyana Saurin Dauke kansa yayi jin yanayinsa na Sauyawa,Karamin kugunta yake kallo ta gefen ido kan gadon ya zauna yana Bude Laptop din gabansa Lokaci Daya yana Fadin"Kina Bukatar wani abu ne..? Yafada yana kokarin Daidaita kansa Cikin Shagwaba ta Dago Tana Fadin"Bakai bane kana ta Fushi Dani ba..! Waro ido yayi yana kallonta kafin yace"Ni..?yaushe..nace ina Fushi Dake ai kin bani hakuri kuma na Hakura..me kuma nayi Ni Imrana bawan Allah Sarkin Laifi..! Yafada yana Tattara Duka Hankalinsa akanta Cikin Sha"awar kallonta. Lamgwabe kai Tayi tana Fadin"To naga sai Fushi kake dani kaki Sakin Fuskarka..! Kai ya gyada kafin ya Mike Lokaci Daya yana Ture Laptop din gabansa yace"kinsan yanayina..Ni bakimin komai ba..! Sake Bata Fuska tayi Zatayi mgana yayi Saurin cewa"Kada kimin kuka..Plz am not in d mood..Kuma ni ban iya Lallashi ba sai duka..! Baki ta Tura kafin tace"Yanzu sai ka Dakeni..!? Gira ya Dagamata yana Fadin"Yes of course kina ganin bazan iya bane..! Zaneki Zan yi Tsab yadda baki da wani kiba nan..! Yafada yana yar Dariya Lokaci Daya yana kallonta kasa kasa. Cikin Tura baki tace"Laala..Matar taka Zaka Daka..? Tafada Tana kallonsa ido na cikin ido,irin yadda yake kallonta yasa tayi Saurin Sadda kanta kasa Imran ya Dage giransa yana Fadin"Really..?Hakane fa ke Matatace! Yafada yana shafa Sajensa kafin yace"Zo...! Da sauri ta Dago Tana kallonsa kafin tace"Ni..? Daure Fuska yayi kafin yace"A"a Ni..! Yafada yana kauda kansa jin haka yasa ta Fara takawa zuwa gabansa Kanta na kasa sai da taji Tana jin Hucin Numfashinss kana ta Tsaya Tana Fadin"Gani..! Yana kokarin Daidaita kansa yace"Ai na ganki..! Yafada yana kallon kirjinta da suke mai Maraba,jikinsa ya Fara Shaking bai san yaushe ne ba kawai ya jisa ya Saka Hanmu ya jawota jikinsa ya Rumgumeta kamkam kamar wani zai Kwace masa ita atare suka saki ajiyar Zuciya Cikin Salama Inteesar kara gyara Kwanciya tayi a Faffadan Kirjin Imu Tana shakan kamshin Turaransa mai Dadi da Tafiya da zuciya Har Lumshe ido take yi shima kansa ya Dora Saman kanta Lokaci Daya yana Zagaye bayanta da Faffadan Hannunsa Jinsa yake kamar yana yawo a gajimare saboda Farinciki da Salama. Dankwalin kanta ya Sabule ya Fadi kasa,Inteesar ta kara Rikesa sosai Ta saka Hannunta ta Zagaye kugunsa cikin yanayin da batasan ma Tayi ba Wani irin yarr Imran yaji wanda yasaa ya Tusa kansa cikin Kitson galaban Dake kan Inteesar Neman rasa Control dinsa yake yi yasa Cikin Wata Murya yace"Waya miki wannan kitson..? Inteesar Dataji kamar tayi ta barci Har Abada a jikin Imran tace cikin Wata irin murya"Munari ce..! Hannunsa Daya yasa yana shafa kan nata gabadaya sai inteesar taji Tsigar Jikinta na tashi Wuyanta ya Shafo Takara Rikesa da karfi jin wani Zirr acikin jikinta Lokaci Daya Tana Fadin"Washh..!!! Tafada cikin wata kasallaciyar muryan da bata san tana dashi ba Wannan Muryan datayi amfani da Rikon Datayimai yasa gabadaya yaji yana neman rasa Controlling dinsa yasa yayi Saurin Sakinta ya koma ya Zauna gefen gado da sauri Saboda kada taga Girmansa yadda ta Mike Tsaye Sambal ta bayyana kanta. Kansa ya Dafe ya kasa ma Dagowa saboda yana so yayi kokuwa da yanayin Dayake ciki. Inteesar sai Lokacin taji kunya ya kamata tayi Saurin Daukan Dankwalinta ta Daura Ta juya Cikin Rawan jiki dana Kafa Zata bar Dakin taji yace"Baki fadamin abunda yasa kika shigomin daki ba..? Yafada cikin Sanyin muryan Datake cike da sha"awa. Cak ta Tsaya bata waigo ba tace"Dama..Dama.! "Dama me.?Malama ki juyo kimin mgana ni yaro ne da zaki juyamin baya kina min mgana..! Bata da yadda Zatayi gabanta na Duka ta Juyo Bata yadda ta Kallesa ba shi kuma Duka Shanyayyun idanuwansa ya Zuba mata. Cikin Dakewa tace"Dama na Tambayeka yaushe ne Ka Tsaida Bikin Tarewar mu..? Kallonta yake cikin mamaki kafin yace"Kin kosa ne..? Da Sauri ta Dago kamar tayi kuka Tace"Wlh A,a..Su munari ne suka mtsa suna so suji saboda Shirye shiryen fa..Ni yaushe nace na kosa..! Tafada Tana Tura baki. Kansa ya shafa yana Fadin"Yaran nan sun cika azarbabi..To da suke Tambaya Kayan Daki zasu hada miki ko su zasu min akwatin auran ne da suke Tambaya..? Inteesar ta marairaice Tace"Sufa Saboda Events din da zasu shirya ne..! Kasan kuma hakan na Bukatar Tsare Tsare..! Imran ya Hade Fuska yana Fadin"Event..? A bikin waye zasu yi Event din..? Yafada yana wani Kara Dakuna Fuska. Inteesar tayi narai narai kafin tace"Bikin Tarewar fa..! Tabe baki yayi yana Fadin"an gama mai wuyar Tunda aka Daura auran..Ba wani shanshanci kuma dazai biyo baya in nagama Shirina ni da kaina zan Daukeki mu tafi bana son Hayaniya da wata mgana Ok..! Inteesar ai mamaki ya Kasheta bata samu Damar mgana ba ya cigaba da Fadin"Kuma ma Wa yace a zo a Tambayeni..?meyasa baku kira Daada ko su Daddy ko Abba ba..Kun Rainani ko..?ke kuma mara wayau kece yar aike ko..?da sun sani sun Tare ni da kansu..! Inteesar tace"Ai Daddy ne yace kai zaka Tsaida Date din Imran na Dariya yace"Nagodema Daddy..Ki Fada musu nan da Next year lokacin nima na Tara kudi sosai Kema kinga Lokacin kin Shirya tunda ai yanzu kin ce baki kosa ba..? Inteesar takallesa Kafin ta kauda kai Lokaci Daya Tana Tura Baki yana Danne Dariyansa yace"Eyye ni kike Tura ma baki..? Ai bata ma bari ya kara mgana ba ta Fice da Sauri ya Rakata da Dariya aransa yana Fadin"Yaran fa basu da Hankali so suke su min bidia a bikina...Ashe kuwa zan karya yarinya..! Daki ta koma ta iske Munari na Charting nan ta zauna ta Fadamata Abunda Ya Imu yace Munari tace"Bari zan kira Ya Sagir muyi mgana..yasin Bazamu yardaba sai munyi Bidian da baya so..In yaki ma Daada zamu hadasa ko da su Abba..! Inteesar tace"Gaskiya..Shifa yarda yake so dagani sai shi ba biki ba komai fa..Kamar wata mara Galihu..! Munari tace"Bafa zai sabu ba yadda mukaci Burin bikin nan sai fa an sha Hidima iya Hidima Amaryan Oga Imu..! Dariya suka saka gabadayansu kafin su cigaba da Hiransu sama sama. **** Washegari Abba ya wuce Kaduna Motar Haya yabi,Ba"a riga an samomai Direban da zai rika Tukasa ba Tunda shi Tuki yanzu ai sai dai su Yusuf,Ya"yan nashi basu so ya hau Motar Haya ba yace ba komai Bai kuma yadda ya Fadamusu zasu je Abuja ba Yusif Daya tambayesa yace Zai je Wajen Baffa Mustpaha ne Imran kuma bayanan sun dai yi sallama da Abba Kafin ya wuce wajen aiki. Yusuf da su Munari suka kai Abba Tasha sai da Motarsu ta tashi Daganan ya Biya ya kaisu makaranta Shikuma ya wuce wajen aiki. Wajen karfe 11am na Safe Abba ya isa Daddy yazo ya Dauke anan Tashar kawo Daman yasan da zuwansa. Suna zuwa gida Umma ta gabatar musu da Breakfast suka karya already daman Basheer ya siya musu tiket din Jirgi gobe karfe 6am na Safe zasu Wuce Abuja Gidan Baffa Kabiru.. Bayan sun gama karyawan Daddy yaja Abba suka Fice yakaisa Shagunansa ya gani ya saka albarka Har gidan su Umma sai da sukaje suka gaida Inno da Mallam Babba. Sai La"aar suka Dawo gida sun iske Anty Hauwa tazo ta kawo musu Dambun Shinkafa Dayaji Zogala da gyada sukayi ta ci suna Saka mata albarka,Ga Lafiyayyan Zobon Data Hade musu dashi da Sanyayyan kayan Marmari,Tunda Basheer ya Fadamata Abba yazo shine tazo gaisheshi ita dasu Abidin. Bayan sun gama suka baje afalo suna hira kan Abunda ya shafesu har kan mganar Tarewar Inteesar Da Abba yayi mgana Daddy yace Mgana tana Wurin Imran ko gobe yace Inteesar ta Tare bai da Damuwa Abba yace to in ya koma zai kirasa yaji saboda kada su Dauki Lokaci Daada tace sun yi Watsai da mganarta. Nan Abba ya kwana shida Dan"uwansa Daki Daya suka kusa Raba Dare suna Hira irin tasu ta yan"uwa gari na Waye suka shiga Jirgin kasa sai Abuja Karfe 9am na Safe suka sauka Daganan suka Nemi Tashar Taxi sai gidan Baffa Kabiru Dake Maitama Abuja. *Shakira..* 3/26/22, 22:59 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�21* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Gida ba kowa sai yan aiki Mami Asma"u Tana gidansu tun Ranar Umaima ta tafi makaranta Baffa Kabiru kuma ya tafi Office. Dayake yan aikin sun sansu gama kama nan,Kuma Daddy na yawan suwa Abba ne ya Dade bai zo ba Tun kafin barinsu gida yasa nan da nan suka shiga dasu babban Falon gidan Kafin kace kwabo sun cika gabansu da kayan Ciye Ciye da Shaye shaye. Daddy ne ya Kira Baffa Kabiru a waya ya sanar dashi gasu acikin Gidansa yayi matukar mamaki sai dai bai Tsaya bata Lokaci ba ya Hado ina inasa ya taho gida. Lokacin Daya shigo Falon Yaga yan"uwansa Zaune suna Jiransa bai kawo cewa sun ji Labarin Rabuwarsu da Asma"u ba ya zata sun jisa Shuru ne suka Biyo Sahunsa da kuma Tattauna abunda ya Faru a Dukku. Kunya ta Hana Baffa Kabiru iya kallon Cikin Idanuwansu sanda ya kariso Gabansu ya basu hannu Dukkansu suka Sarke Musabaha. Sai ga Baffa Kabiru ya Duka gaban yan"uwansa yana Hawaye yana Sharan kwallah yana Rokonsu Gafara yana Fadin"Ku yafemin yan"uwana..Ku yafemin Duk da nasan Ni din mai Tarin Laifi ne..Bai chanchanta ku yafemin ba na Zama babban Banza wanda bai rike yan"uwansa da Amana ba,ku yafemin Wlh kunya da Nadama ne suka Hanani nemanku ammh na yanke Shawaran ko baku zo ba gobe na Shirya Tafiya Dukku na Duka na Roki Daada gafara kan Laifin dana aikata mata ko ta yafemin Allah ya Duba Lamarina..! Yafada yana Goge kwallah Abba da Daddy jikinsu yayi Sanyi sosai suka Mike atare suka Rikosa Suka Hadu suka Rumgume shi suma Kamar su yi Kwallar Saboda Tsausayinsa Jini jini ne duk inda naka yake komai Lalacewarsa naka ne. Daddy ke fadin"Haba ya kabiru ka Daina kuka..Bai kamata ba..Wlh mu bamu Taba Rikon ka ba..Daada ma bata Rike ka ba Fushi ne na Dan Lokaci kuma Zata sauko da yardan Allah..Muma kafarka kafarmu zuwa Dukku Bazamu samu Salama ba sai Dan"uwanmu ya Daidaita da Mahaifiyarmu ko ba Haka ba Ya Malami..? Abba ya gyada kai yana Fadin"Tabbas hakane..Duk da akwai Dalilin daya kawomu ammh shima wannan yana daga Cikin Babban Dalilin zuwan mu..! Baffa Kabiru ya Dago yana kallonsu kafin yace"Nagode muku sosai..Malami musammann kai ka yafemin nafi kowa sabamaka..Ammh Insha Allahu na gane inda na Kuskure Da yardan Allah zan gyara ZAmu je gaban Daada Zan Roketa gafara na kuma mata alkawarin ko Bayan Ranta Bazan bari Zumuncin mu ya Rabe ba mun Zama Tsintsiya Daya madaurinta Daya..! Yafada cikin son Tabbatar da mganarsa,Daddy da Abba suka Rike Hannunsa Cikin Jin Dadi suka Hada baki Wajen Fadin"Insha Allahu..! Daganan suka koma suka Zazzauna,Daganan suka yi Breakfast Harda Baffa Kabiru domin shima bai karyan ba ya Fita duk ya zama wani iri kamar bashi ba Daurewa kawai yake ammh Tabbas Rabuwa da Asma"un ya Tabasa. Sai da suka Natsa kana Daddy ya gyara Zama yana kallon Baffa Kabiru lokaci Daya yana Fadin"Wani Labari mukaji mara dadin ji Ya kabiru..? Ya kallesa Cikin mamaki kafin yace"Wani Labari kuma Kuka ji Mustapha..? Daddy yace"Shekaranjiya Da Daddare Yar Wajenka Umaima ta Kirani a waya Tana kuka Take fadin kun yi yar Hatsaniya da Asma"u Karshe dai Har da Saki..! Baffa Kabiru ya sauke ajiyar Zuciya yace"Eh..Ashe ta Kiraka..! Daddy yace"Eh Data kirani Gaskiya Hankalina ya tashi..Sai na Kira ya Malami mukayi mgana,muka Tsaida mgana kan cewa yau zamu zo mu ji Ta yaya haka ya Faru..? Mu kuma baka Hakuri komai ya Faru ya wuce Zuciya bata da kashi kayi Hakuri ka maidata Dakinta Ko Domin Darajan ya"yanku bazasu ji Dadin hakan ta Faru a Tsakaninku ba..! Abba ya karbe da cewa"Kuma in Rai ya baci ai Hankali ke Nemosa Mustapha..Duk in akayi Hakuri sai komai ya wuce Watarana sai Labari..Kuma ku ba yara bane kun Girma bai kamata hakan na Shiga Tsakanimku ba ya kabiru..! Baffa Kabiru na jinsu kansa na kasa Sai da suka gama kana ya Dago Kansa yana Fadin"Duk naji bayanan ku..Buh kuyi Hakuri Zama Tsakanina da Asma"u ya kare in har bata gyara Halinta ta gane tayi ba Daidai ba..! Daddy yace"Ai ya Kabiru hakuri zakayi a Hankali kana nuna mata Har Ta gane..! Baffa Kabiru yace"Kayya ai bazata taba ganewa ba..Da kuke cewa na maidata kunsan abunda ta aikata..?bayan cin Zarafin Datayi ma Daada a Dukku a gaban i...! Daddy ya Dakatar Dashi Da Fadin"Kayi Shuru Kawai Ya Kabiru ba sai ka Fadamana abunda ya Faru ba wannan Sirrinka ne Tsakaninka da matarka kuma Sulhu muka zo nema ba Tada mgana ba Don Allah kayi hakuri ka maidata ita kanta Daada in taji haka bazataji Dadi ba ga ya"yanku Taya zasu Fuskanci wannan Raunin..?kuma an riga an zama Daya Ku da zaku yi ma wasu Fada Yaya..! Bai kamata ba don Allah kayi Hakuri ka Maida komai ba komai ba ka Maidata Dakinta ko Saboda Darajan Daada da ya"yanku da alfarman da mu yan"uwanka muka Nema don Allah..! Abba ya jinjina kai yana Fadin"Kuma zama ba Mata haka ai bai Dace ba..Ko ni Saboda Mutuwa ce da kuma Rashin Kwanciyar Hankali ammh ai cikar Namiji Shine Matarsa don Allah kabar Tuna baya ka yi Hakuri ka maidata Dakinta..! Baffa Kabiru ya Sauke Numfashi kafin yace"Zan maidata ne saboda Darajan Daada da kuma Kimarku da kuka baro Ayyukanku kuka zo har Gida Domin nuna Damuwarku akaina..Nagode kwarai Allah ya bar Zumunci..! Suka amsa da Ameen Cikin Jin Dadi Daddy yace"To baka ce ka maidata ba..? Baffa Kabiru yace"Ni kabiru na maida Matata Asma"u na janye Sakin Dake Tsakaninmu.Ba Shikenan ba..! Abba da Daddy suka yi Dariya suna Fadin"Alhamdulillah..! Baffa Kabiru ya ce"Na maidata ammh da Sharadin bazan Gayamata na maidata ba Har sai ita da kanta tayi Nadaman abunda ta aikata na Nemi mu Daidaita sai na Fadamata na Maidata ammh ko nan da shekara nawa ne in bata yi Nadama ba ni kuma bazan nemeta ba..! Suka jinjuna kai atare kafin Daddy yace"Insha Allahu ba Matsala ai Barrister ta barrister ne Zaku nemi juna in kuka Huce..! Ya karishe Fada yana Dariya Abba na Tayashi Baffa Kabiru Mirmishi kadai yayi bai ce komai ba. Abba ne yace"Ina Sajida take ne..?munyi mgana da Daada tace min ta Dawo Daga Dukku..? Baffa Kabiru ya Muskusta yana Fadin"Daga Dukkun bata dawo gida ba Makaranta ta wuce Direct,ba kowa agidan nan Asma'u Tun Ranar da abun ya Faru Mahaifinta Juctice Tafida ya aiko da Direba aka Tafi da ita Khamis ma Ranar Monday yabi Jirgi ya koma bakin aikinsa..! Cikin Tsausayawa suke Kallonsa Abubuwa sun Taru sun yimai yawa sosai. Daddy ne ya fara baki bshi Tare da Lallashi Abba dai ya kasa mgana Sabida yana jin kunyar abunda Imran ya aikata na Sakin Sajida sai dai bawa bai isa ya ja da Hukuncin Allah ba. Daddy ya kada kai yana Fadin"Nadade ina jin Labarin Rikewar Boko Da akidan Banzan Justice Tafida ban kara yarda ba sai yau Sabani ya Shiga Tsakanin Yarka da Mijinta ammh bai Kira yaji Neman ba"asi ba kawai ya Turo Direba an Dauketa me hakan ke Nufi..? Baffa Kabiru yace"Ai bazai Taba kirana ba..Shi a kidansa bazai Turasasani na maidata kan Ra"ayina ba itama bazai mtsa mata kan hakan ba acewarsa sanda muka Hadu muka Kulla Soyayya muka Aminta da juna bai Sani ba kuma muka yadda da Ra"ayin auran junanmu yanzu kuma da Hakan ta Faru Ra"ayinmu ne Justice Tafida yana da akidan Bin Ra"ayin Kowa baya kutse Cikin Ra"ayin Wani ko da Ya"yansa ne na Cikin shine suna da wannan Right din..! Daddy da Abba suka jinjina kai,ba su ce komai ba Domin abun ya wuce suyi mgana Aran Abba yana Fadin Dole Asma"u Ta zama yar gaban kanta ta Hadu da Uban mai Bin Ra"ayin kowa da Ra"ayi mai kyau da mara kyau Daddy kuwa Tir da Tarin Ilimi yake Ilimin da bazai amfani Mutum ba. Nan fa suka Bude Hira Kala Kala su tabo Chan su Tabo chan,Har mganar Samun aikin Abba sai da sukayi Baffa Kabiru yana nuna jin Dadinsa sosai Sallar Azahar ya tadasu bayan sun je sun Dawo su ka kara zaman Hira yaushe gamo suna ta Tabo Labarin baya Tun Lokacin Gwarzon Mahaifinsu nada rai suna Tuna abubuwan da suka Faru alokacin Tuni Baffa Kabiru ya saki Jiki Cikin yan"uwansa Kamar bai da wata Damuwa. Sai da Umaima ta Dawo makaranta Daga su Abba taji Dadi sosai ta Dinga Murnan Mami Zata dawo. Allah Sarki Mami Asma"u tana chan Cikin Damuwa da abun kunya Domin Gotai gotai da ita Sakin aure a gareta abun kunya ne in wani yaji Labari zai zama abun Dariya a gareta. Koda yan"uwanta suka zo gidan suka ganta bata yarda ta Furta Kalmar Sakinta akayi ba nuna musu tayi Tazo ta Huta ne ba wanda ya yarda da ita Taya ya Zata baro Gidan Mijinta Tace Tazo Gida Hutu da wani dai mgana,Hajiya Turai ma taki ce musu komai ballatana Justice da ba Ruwansa da Shiga abunda ba"a Saka sa ba,Indai ba Asma"u ta Fada ba shi baza"aji komai Daga Bakinsa ba. Batare da Shawara da kowa ba Hajiya Turai tace ma Asma"u ta Dakatar da Shigar da karan nan Saboda ceton Auranta ita kanta Barazanace ammh Asma"u fa ba yarinya bace akwai Tarin Kalubale ta Zauna gabanta Tana Zawarci ba gaddama ba Musu Mami ta Kira Brr.Zailani tace a Dakatar da komai Shi kuma bai kawo abun har takai ga Rabuwa ba ya Zata Brr Kabiru yayi ma abun Tufkan Hanci ne bai san ya bama Mami Red card ne wanda ya Girgixata da Girmanta an Saketa abunda Tun Lokaci Tana da kuruciya bai Faru da ita ba,Ta tsinema Daada acikin Ranta yafi a Kirga Domin har lokacin bata Fahimci bata kyauta ba gani Take Duk Daada ce ta ja komai kuma itace silan Mutuwar auranta,Ego dinta da son kanta yasa ta kasa Zama ta Fahimci matsalan Daga Wajenta yake,Sakin ya Dameta gani take kamar Abun kunya Aji kamarta ace Mijinta ya Saketa ko kawayenta sai sun Rainata Sajidan ma Datake Fada akanta ta Gujeta ta Zabi Dangin Ubanta akanta bayan Sakin Wulakancin da Kabiru yayi mata tayi ta Kiran Sajidan bata Dauki Wayanta ba daga Karshe ma Sai ta Ratayeta kwata kwata ma ta Daina Samunta Khamis ma bata samunsa Kwata kwata a waya Umaima ce kadai take Kiranta Umaima kuma yarinya ce bata san komai ba,gabadaya taji kamar ta Rasa komai ya"yanta da bata da kamarsu batasa tare da ita Ta kara jin Ta Tsani Daada tana ganin Duk itace Silan komai. Sai da Umaima ta Fadamata Sajida na School kana Hankalinta ya kwanta,Sannan ta Gudura aranta Bazata nemeta ba ai ita Uwa take gareta komai lalacewarta Tana nan a Mtsayinta na Uwa Zata Tsaya tagani Shin Sajidan ta Sauya wata Uwar ce Bayan ita.. Umaiman duk sanda sukayi Waya ta Dinga Fadin Plz Mami Come Back itama Sai tace ba Laifina bane Umaima a kunnenki kikaji Ubanku ya Sakeni yace nabarmai Gida,Har Fadama Daddy da Umaima Tayi ta Sanar da Mami Asma"u aranta tace Dole yazo ya bani Hakuri Haka Umaima na Dawo makaranta ta gansu ta Kira Mamin ta Fadamata kanta ya Fashe ta Fadama Hajiya Turai wacce tace"Ai daman na sani Kabiru baazai iya Rayuwa baki ba..Allah yasa su kwaso Kafafuwansu nan gida sai nayi musu Fata fata kafin na yarda ki koma mu Zaimaida Kananun mutane..! Ita kuma Mami Sai Mirmishin Mugunta take yi Tana Tunanin yadda Mustapaha da Malami da shi kanshi Kabirun zasu Duka suna bata Hakurin ta koma ma Dan"uwansu sai Ta Rama Wulakanci da Tozarcin da suka mata Musamman ma Mustapha Daya Dauki yarsa ya aurama Imran bai ma Tsaya Jimamin Sakin kaskascin da akayi ma yarta ba Da Umma data bata mamaki Wlh ita taga Kalar kowa a wannan Dangin Bata taba Tsammanin Umma Zata yarda a bama Imran auran yarta ba ta Dauka saboda ita da Sajida ita ta mike tace A"a in ta kama sai dai Imran din ya Maida Sajidan ko kuma ya Fita Waje ya auri wata badai acikin Dangi ba. Sai dai tayi ta Zaman Jiran gawan Shanu Har Washegari Shuru bata ga Kowa ba ta ta kiran Umaima bata Samu ba Tatafi makaranta Sai da ta Dawo Dataga Kiran Mamin Dayawa Bayan ta Kirata take Tambayanta ina Baffaninta..? Umaima ta Tabbatar mata tun da Safe suka kama Hanyar Dukku Harda Dad dinsu Mami Asma"u sai taji jikinta sanyi Jin Tunaninta bai zama Daidai ba Ko Hajiya Turai dataji sun Tafi Dukku Jikinta yayi sanyi ada ta Hango Daidatawar Komai,Taso ne itama ta Wulakanta Kabiru kamar yadda ya Tozarta mata y'a sai dai hakan bai samu ba ba Baffa Kabiru ba su Abba sai Mami Asma"u ta koma Tana neman ma kanta Mafita ammh Har Lokacin batayi nadama ba Tana ganin koma meya faru ita aka Cuta..! ***** Daada sai da tayi kwallah da Taga Zaratan ya"yanta nata agabanta Bata Zata ba sai dai ta gansu kwatsam Baffa Kabiru ya zube gabanta yana kuka yana Rokonta gafara Daman Wlh Aranar ta yafemai komai ita bata Rikesa ba Bacinrai ne ta Rumgume sa Tana Fadin ta yafemai Duniya da Lahira. Da kansa ya Fadama Daada Hukuncin Daya Dauka kan Asma"u bai Fadamata Sa"insansu ba yadai Fadamata ta shigar da Complain Zatayi kararsu,Shiyasa ya Saketa Daada bata ji Dadi ba sosai tayi mai Fada ta kuma ce Maza maza ya maida Matarsa Dakinta nan yake Fada mata Zuwansu Abba da jiya da Abunda ya kawosu da yadda suka Shawo kansa ya Maidata Dakinta da Sharadin Daya Saka mata. Daada taji Dadi Farinciki ya Cikata ya"yanta sun Hada kansu ta Dinga Saka Musu albarka su da Zuru"ansu Ta ce kuma Sharadin Baffa Kabiru yayi Daidai gwara ya Rabu da Asma"u Tayi Hankali da kanta ammh in yayi Saurin Dawowa da ita Zata ga ta isa ne kuma Mtsayinta yakaine. Daada Ranar Tare da ya"yanta taci Abinci Cikin Soyayya da kauna Tana Sharan Kwallar Tunawa da Marigayi Hamisu Dukku Allah ya jikan Maza Domin Tabbas Mazaje sun kwanta Dama. Kiran Sallar azahar ya tadasu Daga gaban Daada suka tafi masallaci su kai Sallah suka Dawo suka iske Daada na Sallah bata idar ba nan suka Zazzauna suna cigaba da Hiransu Cikin Hiran ne Baffa Kabiru ya kalli su Abba yana Fadin"Malami Mustpaha nace ba..?ina mganar Tarewan ya"yana ya aka kwana ne Imran da mai sunan Daada..!? Ya fada yana kallonsu Daddy da Abba suka Kalli juna cikin jin Dadi Lalle Ya Kabiru ya Sauya..! Abba yace"Mustpaha yacemin wai Mganata tana Hannun Imran..Ammh ai naga Daada ce Zata yanke Lokacin ko..? Daada Data Shafa adduarta bayan ta idar da Sallah ta juyo Cikin Fara"a Tana Fadin"A"a mgana bata Hannuna ai na gama nawa Tun a wanchan karon na Sanar daku ku zaku Tsara Komai nace dai ayi Biki na al"ada na Fulani ku bama Kowani bangare Dama ni ina nan Dukku bana bukatar kowa sai dai aturomin ita Mai sunan Tawa kafin Tarewar ina son ganinta..! Suka Jinjina kai Dukkansu kafin Daddy yace"Insha Allahu Daada Zata zo..Dayake Text suke yi a makaranta kuma ina jin da sun gama sai Jarabawar Second Semester..! Abba yace"Eh hakane ma naji suna Fada ita da mai sunan Autan Daada Munari..! Baffa Kabiru yace"To ai sai mu Tsaida Lokaci ko .?me ake jira ai anyi mai Wahalar tunda aka Daura auran gwara ayi komai Cikin Lokaci Ta tare Dakin Mijinta mun gama Dasu sai muji da Sauran yaran namu gama Babbansu nan Malami kaima aure Zan maka..! Gabadayansu Dariya su ka saka Harda Daada Abba na shafa kansa yace""Haba dai Yaya ina ni ina aure Tsofai Tsofai dani ko Daada.? Ai ma barma yaranmu..! Baffa Kabiru yace"Ban yarda ba..Daada ki Zama Shaida in akwai Wacce Daga barayinki kika ga ta Dace muyi mgana zan Biya Sadaki da komai kabar cewa ka Tsufa yadda kake din nan sai ka auri yarinya Danya Sharaf da ita Wlh..! Dariya suka kara sawa Gabadayansu Abba na Fadin"A"a Allah ya Rabani da abun kunyar auro Sa"ar Munari..! Daada dai Dariya Kawai take yi Ranta Kamar Farar Takarda Saboda Farinciki. Baffa Kabiru ne ya kauda mganar da Cewa"Ina jinku..Ya kuke ganin Za"ayi..? Daddy yace"Ni mun yi mgana da Ya Malami nace mgana tana Hannun Imran ya tambayesa yaushe yake son Tarewar? Tunda shine Mijin kuma Dukkan Hakki na kansa ne ni ina da a Shawaratace da an Bari nan da Wata Hudu zuwa Biyar Tunda bai dade da Fara aiki ba yanzu kan Lokacin komai ya Daidaita sai a Shirya Bikin Tariya ga Ya Malami ma Monday zai Fara shiga office shima kan Lokaci abubuwa sun Daidaita itama Inteesar sun gama Jarabawa sun shiga Level 2..! Daada Nadaga gefe tace"Mustapah yayi Tsawo..nifa so nake kafin na Mutu na Fara goyan ya"yan Jikokina abayana..! Baffa Kabiru yace"Zaki goya da yardan Allah Daada ba Mtsala indai kan Kudi kake wannan mganar Mustapha ba Ruwanka kaida Malami ni nine nan Uban ango kuma Uban Amarya na Daukin Nauyin Siyama Imran Gidan da zai zauna da Kayan lefe ita kuma Inteesar Kamfanin Marhaba Zata zo ta kawata mata Gidanta da yardan Allah ni nawa Bangaran kenan a Mtsayina na Uba..! Ai Abba da Daddy sun kasa mgana Daada ce tace"Allahu akbar..Allah ya jikan Mahaifinku..Allah yasa ya Huta..Ka kyauta kabiru..Sai yau ka Nuna min ko bayan Raina kai Uba ne ga Duka kannenka da ya"yansu Allah yayi muku albarka..! Suka amsa da Ameen dukkansu. Abba yace"Imran nada gida Bankin Daya Fara aiki dasu sun basa Gida Da Mota Kyauta..Ya kabiru Abubuwan zasu maka yawa..! Baffa Kabiru yace"Bakomai kada na karajin wani cikin ku yace wai Abun zai min yawa don Uba yayi ma ya"yansa Wani abu Laifi ne..? Ko kuwa ku in kumma Sajida ko Umaima wani abu a Mtsayinku na Iyayensu zan ce wani abu ne..? Gabadayansu suka girgizamai kai. Shi kuma sai ya Kada kai yana Fadin"To kada ku kara Cewa komai..Yanzu abunda Za"ayi kai Malami kiramana Imran din muji yaushe yake son Tarewar..? Abba bai yi gaddama ya Fito da Wayarsa ya Lalubo Lambar Imran ya Kirasa sai da ta gama Ringing bai Dauka ba kana ya Biyo bayan Kiran Abba din.. Abba ya saka a wayar a amsa kuwwa Suka gaisa da Imran Dake Cikin Office dinsa yana Tsaka da aiki duk da ya Kusa tashi Karfe 3pm na Rana zai koma Gida. Abba yace"Imran yaushe ne kake Tunanin ya kamata Inteesar ta tare a Dakinta..? Imran ya Dakata da Latsa Computer Dake gabansa kafin yace"Abba meyasa kowa ke Tambayana ne..?Haka itama yaran nan su Munari suka Turo ta Tana min mgana na Dauka ku zaku yanke Lokacin..! Abba yace"Eh duk da haka kaima aji Ra"ayinka da Lokacin Daka ke so..! Imran yayi Shuru yana wani Tunani kafin yace"Abba Kuna Tare da Daddy ne..? Abba yace"Eh Harda Baffanka Kabiru muna Dukku gaban Daada..! Imran ya karkace kai aransa yace na gano komai wato su Abba sun je Daidaita Daada da Baffa Kabiru ne Yamutsa Fuska yayi kafin yace"Ni fa Abba bani da ta cewa..I think ba wani abu ko duk abunda kuka yanke is ok..! Abba yace"Kada ka damu ka Dai Fadi Lokacin..Ga ma Baffanku nan yace shine Uban ango da Amarya Hatta Lefe ya Dauke maka..! Imran ya Zaro ido Cikin Mamaki kafin yace"Ni din..! Abba yace"Kwarai da gaske Haka yace..! Imran bai samu Zarafin mgana ba Baffa Kabiru ya karbi wayar Hannun Abba yana Fadin"Son..Baffan ka ne Time kawai zaka Fadi Lokacin da ka ga yayi maka daidai..Baka da Mtsala ko Katin gayyata ban ce ka Bugo ba ni Dakaina zan yi komai Lokacin kawai muke son ji..! Imran yayi kasake yana ganin abun mamaki kamar a mafarki sai dai bai yi Saurin Saki ba Saboda bai gama Tabbatar da abunda Zuciyarsa ke Fadamasa ba. Cikin Dan Kaushinsa yace"Da ka barshi Zan yi komai da kaina Insha Allahu..! Baffa Kabiru bai Damu ba Daman yasan Za"ayi haka shiyasa yayi Mirmishi kafin yace"Ba ruwanka Nauyin Uba Daya Rataya akaina zan Sauke Lokaci kawai nake so naji..! Imran bai da ta tace illah ya Muskuta yana Fadin"Karshen wannan Watan a Think is ok..! Baffa Kabiru yace"Is ok..Allah ya kaimu ya nuna mana Allah ya bada Zaman lafiya..! A saman lebe Imran ya amsa kafin ya Katse wayar. Shuru yayi yana wani Tunani kafin yace a fili"Su Baffa Kabiru an ji wuya..! Yafada yana yar Dariya afili,Ko Dazu Sagir sai da yayi mai mgana da Safe kan mganar Lokacin Tarewar bai bashi amsa ba,Sagir din kuma Daman Munari ce tamai mgana ta Fadamai yadda Imu sukayi da Inteesar Sagir yace ai mganar banza ce zai mai mgana Dayayi mai sai bai wani bashi Amsa mai kyau ba. Abba Kwana Daya sukayi a Dukku Ranar asabar kowa ya kamo Hanyar Gida,Baffa Kabiru Direbansa Daya kawosa ya Daukesa zuwa Abuja Bayan sun Tsaida lokacin da Imran din ya Fada nan da kwana Ashirin da Biyar Abba da Daddy Motar Haya suka Shiga suka koma Gidajensu,Su ka tafi suka bar Daada Cikin jin Dadi Tana saka musu albatka. Zuwa Washegarin Ranar dasu Abba suka Dawo Mganar Lokacin Tarewar Inteesar da Imran ta yada Dangi da Abunda Baffa Kabiru yace Zai Dauki Nauyi,Kowa yaji sai yaji Dadi ana ta Fadin ai da haka yake yi da Ba asamu waniFada acikin Dangi ba. Daddy ya Fadama Umma ita kuma ta Sanar da yan"uwanta su Munari abakin Anty Safiya sukaji Shima Abba ne ya Fadamai Ya yusuf Imran dai bai ce mai komai ba,Sagir kuma Mama ta Fadamai shima Imran bai Fadamai ba Shiyasa ya Sharesa. Ranar Monday Abba ya Fara Shiga Office An samo mai Direba Musa wani Dan kasan Layinsu su Sagir ne Matashi ne mai mata Daya da yara Biyu,Zaratan Ya"yansa suka Rakasa Yusuf da Imran da Munari da Inteesar Harda Anty Safiya suka Raka Abba Har zuwa Babban Office dinsa na Department of Physhology. Sukayi addu"a suka saka albarka kana Kowa ya wuce Wajen aikinsu Munari da Inteesar kuma Daman Gida suka zo suka wuce Department dinsu suka wuce suna da Test,Munari sai Rawan jiki take suna ta waya dasu Hafsah suna ta Tsara Event din da zasu gudanar tun jiya Munari ta Bude group a Manhajar WhatApps mai Suna *IMSAR*��💫 ta saka Hafsah,Da Nasara da Tasleem da Sagir. Inteesar bata ce komai ba Gabadaya zullumi ya isheta Tana Tunanin Saura kwanaki kadan su Zama Miji da mata na Hakika Tsakaninta da Imran su Zauna agida Daya su kadai a mtsayin miji da mata. *Shakira..* 3/26/22, 22:59 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�22* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* *After 1 week* Bayan Sati Daya da Tsaida Lokacin Bikin Tarewar Inteesar da Imran ta kowani bangare Shirye shirye yana ta Gudana,Domin Baffa Kabiru yace Umma Zatayi Taron Bikinta a Kaduna ne,Yayinda Inteesar zata koma Wajenta Angawaye zasu Dauko Tawagan Amarya zuwa kano Gidan Abba inda Suma zasu shirya nasu Taron Bikin. Imran Dayaji haka mamaki ya kamashi yace shi kuwa ba zai je kaduna ba,Wannan ai Wahala ce Abba yace sai dai kada yaje ammh Tabbas Inteesar zata koma gaban Iyayenta achan zasu yi Taron Bikinsu,Shuru kawai yayi ammh acikin Ransa yace ba Inda zai je kafar Daya kaita sai ya Daukota ya Dawo da ita. Baffa Kabiru shi ya karbi Ragaman komai gabadaya Tsarin komai sshi ya Tsara shi da Daddy sun zo har Kano sun ga Sabon Office din Abba sun saka albarka suka kwana Daya suka koma a kuma zuwan ne Baffa Kabiru bai Duba Girma da Shekarunsa ba ya nemi Gafaran Imu saboda yasan yaKullace shi kuma shima yasan bai kyauta ba. Imran bai isa yace bazai yafe ma Baffa Kabiru ba Tunda ya gano kuskuransa,Daman kuma Mami Asma"u duk ita ke kara sakashi aikata Wasu abubuwan,Yanzu kuma bata nan Yusuf ya kyankyasamai Rabuwar Baffa Kabirun da Mami Asma"u Dalilin Zuwan Abba Kaduna suka Tafi Tare da Daddy a Abuja har acikin Ransa Dadi yaji kuma acikin Ransa yana addu"an Allah yasa Kada su Daidaita sai Daga baya ya Fahimci itace kan Macijin Shi kuma Baffa Kabiru ne gangar jiki kuma kai Shike Sarrafa Dukan jiki. Inteesar Amarya kuma ba Lokaci Saboda suna ta Test da sun gama kuma Zasu Fara Jarabawa da suka Lissafa zata tare Ranar Lahadi,Ranar Monday da Safe zasu Fara jarabawa basu da Lokaci Zamansu kadan ne shima na Karatu ne ga kuma Shirye Shirye. Basu cika Haduwa da Imran ba Saboda Sanda zasu Tafi makaranta Shi ya Tsufa a wajen aiki in suka Dawo kuma wani Lokacin suna Gidan Mama,In kuma suna gidan Abba Shi kuma yana ciki yana aiki Bisa System dinsa. Sai dai kamar yadda Munari ta bata Shawara bata yar ba Tana Turamai Sako Kullum da Safe na Gud Mrning da kuma na Gud Night Tana Kiransa bayan kwana Biyu Taji Lafiyarsa,Kuma hakan yana ma Imran Dadi sosai yayi mata Uzuri Domin yasan Karatu ne yayi Zafi ga Test kuma yasan sun kusa Fara Jarabawa abakin Sagir yaji Tunda shi Sagir din suna ma Jarabawar ne ta shiga aji Hudu Shiyasa basu cika Haduwa ba Dukkansu basa Zama. Akallah dai yana jin Dadin ta basa Girmansa kuma ta Daraja Mtsayin Miji Dayake awajenta shima in yajita Shuru yana Kiranta yaji Lafiyarta Bai isa ya karyanta yana son Inteeaar ba Domin Duka Motsinsa Tana cikin Ransa ne Ko wajen aiki yaje itace makale acikin Ransa,Tayi kane kane Zaman da bazata iya Fita da karfi da yaji ba Domin ta shiga a Hankali ne Batare Daya sani ba. Batare da Sanin Imran ba Sagir Ya Dauki Lambar Khalil a Wayarsa ya Kirasa ya Fadamai Halin da ake Ciki Saboda Imran yaki yarda ya basu Halin kai ga su Munari sun Dage sai sunyi Shagali a taron Bikin nan. Khalil bai yi mamaki ba Domin Lokacin yaji labarin Auran Imran din ammh a bakin Abbansu Dr.Isa Ali Argungu shima Abba ya Fadamai ammh Shi da Imran bai Fadamai ba,kuma alokacin Auran Sajida ne so bai san an samu wani Sauyi ba kuma shima Sagir din bai Tsaya mai Bayani ba. Khalil yace kada ya Damu,ya bada Lambarsa a sakasa cikin Group din sai su Tattauna,Daya fadamai abunda Imran yace bamai mai Bidi'a abikinsa khalil yace wannan mganar Banza ce sai anyi Bidia ko yana so ko baya so Ai ba Jiransa zasu yi ba su zasu Shirya komai. Haka kuwa akayi Sagir ya baama Munari Lambarsa ta saka cikin IMSAR Together,Sun ji Dadin Tattaunawa da Khalil She is Very Friendly,Duk da shima yana da Miskilanci Sai dai bai kai Imran ba,Dashi da Sagir kadai ne abokan ango Su kuma suka Dauki Ragamar Tsara komai,Sum bama su Munari Damar su Rubuto Abunda Zasu Shirya na Event su kuma su Duba su ga abunda zai yuyu din Munari da Tasleem da Hafsah Da Nasara suka Zauna suka Tsara abubuwan da zasu yi,Sunce zasu yi Bridal Shower sai kuma Lonching,Da suka Fada musu Khalil yace su kuma Zasu Shirya Dinner da Walima mata Ranar Lahadi in an kawo Amarya da kuma addu"an Bude Sabon Gida da wannan Shawaran suka Tsaya Kuma duk wannan Tsara Tsaran Imran bai san anayin su ba Daga Sagir din Har Khalil din ballatana Inteesar da sai sun Tattauna Take jin mganar a bakin su Munari. Umma ta shirya ma wannan Bikin na Autarta ita da Daddy shima ya Sakarmata kudi sosai,Inna Maimunatu ita ta fito da ankon yinin Biki,Less ne Rantsattse mai kyau Daga Bangaran Umma Tunda ita Zatayi Tarinta Ranar Jumma"a ne asabar da Safe Zata taho da Inteesar Kano Akuma Ranar ne Anty Safiya Zata Gudanar da Taronta itama Wanda ya Yusuf da Abba suka bata goyon baya Itama ta Fidda ankon Material Mai kyau mai yarari na yinin Bikinta Shiri suke sosai Domin Yusuf yace suma Harda Taron Bikin da basu yi ba nasu Zasu Hada suyi Tare zasu gayyaci Mutane Dabam Dabam domin suzo su tayasu Murna. Baffa Kabiru Inna Maimunatu ya bama Kwangila Hada kayan Lefen Inteesar Kudi kawai ya Tura mata Lokaci Daya sai dai ta Kira Intee ta Tambayeta Size din abubuwan amfaninnta,Ita da ya"yanta suke Hada kayan Zainab da karima Tsadaddun kaya na gani na Fada sai Wanda ya gani ba Ha"inci ba zamba cikin Aminci. Mganar kayan Gida kuwa sun gama mgana da Kamfanin Marhaba Kudi kawai suke jira ya Tura musu zasu zo su Kawata gidan sai wanda ya gani Dagachan bangaran Umma kuma Tana Siyayyan yan abunda ba"a rasa ba,Mama taje ma tayi Sati a Wajenta suka gama Shawara bayan ta dawo ta Dawo da kayan wanka na Lalle da su margaya ta jikama Inteesar aka Zuba Ruwan Turaruka Kala kala Inteesar tana wanka Dashi Safe da Rana sannan ga mgungunan Infection na Gargajiya shima Maman ta Dake ma Inteesar din tana amfani Dashi. Yan"uwa kowa yana ta zumudin Bikin banda Inna Bintalo da abun bai Dadata da kasa ba Dataji Labarin Abun Alherin Baffa Kabiru cewa Tayi bai da zuciya Tunda har za"ayi ma yarsa wannan Sakin Wulakanci kuma yazo yana Rawan jiki,Ba wanda yasan Tanayi bama abi ta kanta ba Itace ta Fara Kiran Mami Asma"u ta Labartamata komai,Jikinta yayi Sanyi ta kuma kara Tabbatar ma kanta Kabiru dai da gaske yake ya Rabu da ita Tunda gashi ya Shareta har yau bai nemeta ba kuma gashi ya Daidaita da yan"uwansa Har yaje yana Kashe kashen Dukiya saboda wanda ya Lalatama yarsa Rayuwa ya maidata Bazawara duk da Taji mganar Tarewar abakin Umaima bata Zata Lokaci kadan aka Saka ba Mami Asma"u da Inna Bintalo kadai take waya a Dangin Baffa Kabiru kowa ya kamasa kansa da ita da yawa ma basu san abunda ya Faru ba itama Inna Bintalo Ta Kira Mamin ne tana mata Tsegumin da Saninta Baffa Kabiru ke Kashe kudi haka Sai kuma taji Labari mara Dadi ita kuma ta Fadama Inna Maimunatu wacce ta Tabe baki afili ta Furta Ya kabiru yayi min Daidai Wlh..Allah ya kara mganinta kenan! Ganin Bata samu Fuskar da Zata kawo Wata mgana ba yasa ta kama kanta Musamman ta Shirya taje Dukku Tana yima Daada mganar ita azatonta bata Sani ba Daada ta nuna mata Babba babba ne bata nuna mata ba Taji ba Sai ta Nuna mata abakinta ma take ji ballatana ta Fadamata yadda sukayi da ya"yanta nata taja bakinta ta Tsuke sanin Halin Bintalo akwai Daukan mgana sannan suna Dasawa da Mami Asma"u tana kuma da Tabbacin Mamin Asma"un ne ta gayamata yadda akayi ammh tasan Kabiru Ko Mustapha ko Malami ba wanda Zai kira Binta Domin ya Fadamata wata mgama shiyasa tayi mata abun nan da ake cewa ta yaro kyau take bata Karfo. ******* Sajida Tana makaranta bata san Abunda ke Faruwa ba saboda ta yanke alaqa da duk wani abunda zai Karamata Mikin Dake cikin Ranta Da Umaima kadai sai Dad take mgana ta Sauke Duka Kafar sada zumuntar Dake Wayarta sun gama Test suna gabda Fara Jarabawa ammh bazasan Hakikanin Abunda ta Rubuta ba,Gadai Tanan nan kaawai Ta Rame Duk ta lalace kamar ba Sajida yar gayu bai ji da kanta da Takama da komai ba. Ita kanta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Har ta koma ga Allah Bazata Daina son Imran ba ba ita ta Dora ma kamta ba Allah ne ya Dora mata kuma bata isa tace Zata yaye ma kanta ba,Sai dai ta Dauki alhakin komai ta Dorama Mami itace Silar komai Sannan Daya Daga Cikin Ayyukan Mamin ne ita ta Girban mata Sakamako ne take gani ta Dauki hakan a Mtsayin kaddaranta Tunda Duk Zuwan da Dad zai yi wajenta ko ya Kirata a waya Nasihar shi da ita kenan yana Shiga Damuwa in ya ganta Ta Rame duk ta saki Ta Zama wata iri kamar ba Sajida ba Bata da kuzari kamar mara Ishashen jini ajikinta ko Ruwa bata Farinciki Koda yaushe Cikin kunci in Ta gaji da Boye abun acikin Ranta tayi ta kuka Karatun ma bata Fahimtar sa kawai yinsa Take yi ba wai tasan ina Take ba ko ina Zata ba..!Jenefer kamta da suke Zaune Daki Daya tasan Sajida Ta Sauya haka ma abokan Karatunta da kawayenta Kowa Sajida What Wring..?me zata ce..!nayi aure ban Tare ba Mijin ba ya Sakeni..?kuma Duka Uwata Data Haifeni ta Ja Faruwar haka?bata da karfin Gwiwan bada wannan labarin amsarta Dayane bakomai ba abunda ke Damunta alhalin ita kanta ta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Cutar da Sanadinta Mami Asma"u indai ta Fara Bin Ra"ayinta Tun Farko da ta Tabbata abunda ya Faru bazai Taba Faruwa ba. Abakin Umaima take jin mganar Tarewar Inteesar din da Imran alokacin Sauran kwana Goma Sha Biyar,Ta zo Dubata tayo mata abinci da Miya Direba ya kawota Ranar asabar,ita kanta Umaima tayi ta ma Sajidan Korafin Ramarta Sai tace mata Stress din Karatu ne anan nema Umaima ke Nuna mata ankon da Munari ta Turo mata Guda Uku Less,na Dinner sai Wani Material na Bridal Shower sai Atamfa na Yinin Biki shi kuma za"a saka aje Lonching ta Nuna ma Dad yace ta zo ta nuna mata In tana Bukata sai a Daukan mata Sajida tace Bata Bukata bazata samu zuwa taron Bikin ba Saboda Lokacin sun Fara jarabawa Umaima bata Mtsa mata ba nan ta wuni Tare da ita akallah dai ta Debe mata kewa Umaima ta Tambayeta ko suna mgana da Khamis tace mata basa mgana Tun Dawowarta makaranta Cikin Damuwa Take sanar da ita basa samunsa ta waya Harta kuwa da Baffa Kabiru baya samun Khamis din Waya Sajida ta ce kila yanayin aikinsa ne kamar yadda Umaima ta Tambayeta Baffa Kabiru ma ya Kirata ya Tambayeta tace basa mgana bata Duba ammh Tana da Tabbacin shima yana chan yana Fama da Zuciyarsa kamar yadda itama take Fama anya Mami ZAta gama da Duniya Lafiya kuwa..?Tabar ganin Tana da Mtsayin Uwa a wajensu kamar yadda Take da Hakki a kansu suma suna da Hakki a kanta Sai dai bata Duba wannan ba Daga ita Har Khamis batayi musu adalci ba. Umaima Tazo asabar Mami Asma"u ta shigo Cikin makarantar Ranar Lahadi,Daga Office take taje Duba Wasu Takardu shine ta Biyo ta makarantar su Sajidan Tunda ta Rufe Duk Hanyar da Zata sameta suyi mgana Mami Asma"u ta yanke Shawaran ta zo ta samu Sajidan suyi mgana Taji menene Nufinta..?ta sauya taa ne a Mtsayinta na uwa ko yaya..? Har Hostel din ta shigo Dakin da su Sajidan suke Sajida na kwance Tana Fama da Tunanin Data Saba a koda yaushe Karatu take yi ammh bata Fahimta Sai da ijiye ta koma Tana Tunani Zuciyarta na mata suya Hawaye suna Zubomata in ta Tuna da kalaman Imran akanta Son maso wani Take yi Domin a gabanta a gaban Kowa da kowa ya Tabbatar mata da baya sonta kuma bazai Taba Sonta ba Har Abada. Duk Sadda Ta Tuna da Wadandan kalaman sai ta kwana kuka Kirjinta yayi mata Nauyi yana Suya yanzu din ma kukan take ita kadai acikin Daki Jenefer ta tafi gida Weekend bata nan Sai ga Mami Asma"u ta shigo. Dukkansu sunyi Shock da ganin junansu Sajida tana kallon Mami yadda Ta koma duk ta wani Fige kamar ba ita ba,Idanuwa sun Zurma Daga gani bata Samun Cikakken Barci Ballatana Kwanciyar Hankali ita kuma Mami Asma"u ta Firgita sosai na ganin yadda Sajida ta Rame tayi baki ta koma kamar Wacce take cikin Wani Cuta. Sajida ta gabatar ma da Mami Ruwa da Lemo Tunda suna da Fridge acikin Dakin,Mami bata iya ko shan ruwa ba Ta Fara Tambayan Sajida me ke Damunta..? bata da lafiya ne..?meya sameta..? Sajida kallonta kawai take yi Lalle ne ma Mami Tambayanta ma take yi me ke Damunta..?ita bata sani bane..? Ai tafi kowa sanin Damuwarta Tunda itace Silar Shigarta Cikin Wannan Halin batacemata komai ba illah Shuru Da tayi mata tana Binta da ido. Ta Zata Sakin da Dad yayi mata zai saka ta Sauki ta gane kuskuranta Sai dai a kalaman Mamin Gabadaya ba Nadama Illah kara Kaucema Hanya. Tunda tazo take Zagin Daada Tana Dora alhakin komai akanta Sajida Tagumi Ta Zabga Tana kallon Mamin Sadda take Fadin"Sajida kema kin Gujeni ko..?kema Daada ta Rabani Dake kamar yadda ta Rabani da Babanku..Ga Yayanku shima Tunda ya Tafi ban kara Samunsa a waya ba..Sajida nasan kina jin Haushina ko.?miye Laifina na..?miye Laifina Domin na so ya"yana na Nuna ma Duniya kune Duniyata..? Sajida wannan yakin saboda ke nake yinshi Kalleki yadda kika koma da Kuruciyarki da komai an Bata Miki Rayuwa an maidake Bazawara da karfi Da yaji wannan wani irin Abun kunya ne..?in na Tuna wannan abun sai naji kamar na Kashe kaina Saboda Takaichi kuma na mike Zan kwatar Miki Yancinki Dad din ku ya Sakeni Sajida kuma kun juyamin baya,Nasan kan wannan yaron kike Rama Sajida ki Kwantar da Hankali kefa Diyar Asma"u ce da Kabiru Gangariyan Miji yana nan zuwa Miki wanda yafi wannan yaron komai da komai ki cireko aranki Domin bakya gabansa Bikin Tarewarsu ma da yar Wajen Salahan ya kusa Babanku na chan yana Kashe Kudi Kinga fa Bintalo ta gayamin Shi zai yima Mara Mutumcin yaron nan Kaayan Lefe Ita kuma Inteesar din shi zai yi mata kayan Gida Gabadaya shi bama ta ya"yansa yake ba yana chan yana Kashe kudin Inda aka ci Zarafinsa aka Sauke Darajan yarsa Sajida ina Cikin Damuwa bana iya barci Babanku bai Nemeni ba bai Nemeni ba Yana Nufin ya Rabu dani gabadaya kenan..?Umhm..Shikenan ai Barrister Asma"u bazatayi kwantamai ba Zan samu Mijin Dayafisa komai da komai Tunda shi Daada ta shiga Tsakanina dashi ita da su Mustapaha..! Take fada Tana Hawaye kallo Daya Zakayi mata kasan bata cikin Hayyacinta Surutai kadai take yi bata san me take fada ba Damuwar take cinta ne take Furta batare Data sani ba Ance Uwa uwace ko da kuwa Mahaukaciya ce,Tuni Tsausayinta ya Sarke Sajida duk da kuwa Tana Fushi da ita Tun bayan Faruwar Lamarin ammh ganinta Cikin Wannan Halin Tana kuka ya karya mata Zuciya Rauninta ya bayyana ta Rungume Mamin Tana Fadin"Mami u are not Well..Bakya samun barci muje asibiti a Dubaki plz..! Mami Asma"u na kuka Share Share kukan da Tuntuni take son tayi bata samu Kafadan da Zata Kwanta Tayi kukanta ba,Tabbas Tayi Rauni ta kuma gaza Duk kuwa da Taurin kanta wannan karon ta gaza ta yardan ma kanta Mijinta da ya"yanta ne Duniyarta Da kuma su take Takama yau da basu Tare da ita Rayuwarta ta Zama cikin Wani Hali Halin kakanikanin da bata Taba Tsammanin Zata shigesa ba batama Dauka abubuwan zasu Dakule mata haka ba. Sajida kuka Mami Asma"u nayi Kafin Sajida ta Tsagaita da kukan ta ta Share Hawayenta Mamin na Bukatarta a wannan Lokacin,Fiye da yadda ita take Bukatarta. Mikewa Tayi Tana Fadin"Mami Tashi muje asibiti a dubaki..Bakya barci Idanuwanki sun kumbara..! Mami Asma"u batayi gaddama ba bata Barci,Ga ciwon kai Datake kwana Dashi batayi ma Sajidan Musu ba ta Jirata ta sako Mayafinta Ta Riko Hannunta bayan ta Rufe Dakin... Specialist Hop suka je inda suke da Fayel Dr.Barau ya Duba Mami Asma"u ya Tabbatar mata da jininta ya Hau Saboda Damuwa da Rashin Barci ya Rubuta mganguna sosai da Shawarwari ga Mamin,Bayan an dubata ta Mtsa Sajidan ta Zauna itama a Dubata ta ki yarta tace ma Mamin itafa bakomai Strees ne na Karatu kawai ba Domin Mamin ta yarda ba ta kyaleta sai da Mamin ta koma ta Maida Sajida makaranta Kana ta Tuka kanta zuwa Gida. Da hajiya Turai ta ganta ta Dawo Cikin wani yanayi shine take Tambayanta tace mata Wajen Sajida Taje Daganan ta Rakata asibiti taga Likita Jininta ya hau. Hajiya Turai ya kyabe baki Tana Fadin"Uhmm..Asma"u kenan kaza mai ya"ya..Ai kulafacin Kabiru da ya"yansa Kadai aka barki ba Jininki ne bane zai Hau ba har Bugawar Zuciya Zaki iya samu..yarinya kina Wahala kanta bata sani ba..Ta Debeke ta Watsar ke kuma kin kwashi jiki kin Bita kamar itace Uwar..Wannan Bakin Halin na Fulanin Dukku sun kwasoshi Wajen Ubansu shi kuma ya kwaso wajen wannan Kafaffiyar Tsohuwar..! Mamin dai na jinta bata Tanka mata ba ta Shige Ciki gabobinta sungaji so take ta kwanta Maltina ta Dauko ta sha ta Sha mgani ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi sai kuka Allah Sarki Rayuwa yau ina Brr Kabiru..?ina Khamis..?ina Sajida..?ina Umaima..? Basa Tare da ita Sai ita kadai Tayaya ko Zuciyar Karfe ce da Barrister Asma"u bazata Raunana ba Ya"yanta da Mijinta fa sune Duniyarta. ******* Kwanci Tashi babu Wuya a Wajen Allah duk kuma abunda aka Sanyama Lokaci sai yazo,gashi yau Bikin Tarewar Inteesar da Imran Saura Kwana Shida a kuma Ranar ne Inteesar da Munari suka Sauka a Dukku Daganan zasu wuce Kaduna sai kuma an gama Taron Bikin. Tuni Inna Maimunatu ta gama Hada kaya sai da aka kawoma Daada ta gani Ta saka Albarka Baffa Kabiru yayi kokari kuma ya Cika Uba wajen Imran akwatina Goma sha Biyu Tsala Tsala Cike da kayan Alfarma,Inna Bintalo da Inna Maimunatu ta Kira suka Hadu Gidan Daada Tunda Daganan Kaduna zasu kai kayan,Da Farko Baffa Kabiru yace afara kai su Kano Abba yace Dawainiya Zata yi yawa akai su kaduna Gidan Daddy. Ganin irin Uban Dukiya sai da Taji Tsoro,Gulma na cinta Harda Vidoe tayi ma Mami Asma"u Ta Turamata Wacce Datagani Sai jiri ya Kwasheta ai ko Khamis Dansa Daya Haifa da Cikinsa sai haka Hawan Ruwa ne ya kusa kamata Data ga kayan. Daga Inna Maimunatu sai Inna Bintalo sai Baba Asabe suka kai kayan nan Kaduna Dangin Umma suka karba su Mama da matan Bala da Salisu da su Anty Hauwa kowa yaga kaya sai barka ana ta ma Baffa kabiru Fatan gamawa da Duniya Lafiya Inteesar ma suna kano basu ga ko Kalar kayan ba sai dai ta Waya da su Zainab suka Dauka suka Dinga Turama Mutane Har Imran ya gani Yusuf ya Nunamai ya saka albarka Hae acikin Ransa ya yaba da Kokarin Baffa Kabiru a kansu. Gida kuwa Tuni Anty Safiya da Mama da Matar Baba Manu Kaltume da Anty Saratu da Mommy da Anty Aneesa sukaje suka Tsabtace ko"ina washegari kamfanin Marhaba tazo ta jera kaya,2 Bedroom ne sai Falo guda Daya da Kitchen kowani Daki akwai Bandaki.. Falon Har Bedroom din Kalan Red and Black ne Zabin Amarya Inteesar,Bedroom din Imran kuma Kalan Baki da Fari ne kowa da Zabinsa Gida sai wanda ya gani. Katin Biki kuwa kayattace Hadadde mai kyau na Zamani irin na ya"yan masu kudi Baffa Kabir ya Bugashi Copy 300,ya aiko ma da Abba 50,Inteesar da Imran 100,Yusuf 50,Daddy kuma y 50,Duk da Umma ma ta Buga nata Katin Anty Safiyama Ta Buga nata Katin Safiya Yusuf Hamisu Malami na gayyatan Kowa da kowa zuwa wajen Daurin auran kanin Mijinta Imran Abubakar Malami da amaryansa Maryam Mustapha Dukku(Inteesar) gayyata Har Gidan Radio sai da Anty Saratu takai Safiya tayi gayyah Makota da yan"uwa da abokan arzuka Mama ma tayi nata gayyan Domin tace ita Uwar ango ce Tana Kaduna,Saboda komai Anty Safiya ita take sakawa a gaba ita da Anty Saratu. Sagir ya sa an Buga Katin Waya wanda su Munari sukace suna so saboda Turama Kawayensu dake nesa yan Makarantar su,Sannan kati nan da Baffa Kabiru ya aiko Dashi Imran Ya Kirasa Inteesar ya bata bayan ya Tura mata 100k na gyaran Jiki Cikin kudin Albashinsa na Farko. Sauran Katin kuma ya bama Sagir Tunda dai ba wanda zai bama wa Sagir kuma Daman sun Buga wani Shida Khalil na Events. Imran bai sani ba bai da Labari sai dai yaga Kati Da programme of Event Daya so yayi ma Sagir hauka sai ya Hasada sa da Abba shi kuma yace kul Imran din ya Kyalesu suyi abunda suka Shirya Tunda shi bai da kara Dole yaja Bakinsa yayi Shuru. Sagir yayi kokari sosai ya D'inka musu Shadda Kala Daya da Boyel Kala Daya shi da Imran da Khalil Duka kuma shi ya Dinka sannan su suka Shirya Dinner,Lonching da Bridal Shower a Kaduna za"ayi Dinner ne za"ayi a Kano Ranar asabar in aka kawo Amarya,Ranar Lahadi kuma agidan Inteesar Za"ayi Walima Tunda Ranar Jumma"a Umma Zatayi nata Taron Nan kano kuma Ranar asabar gabadaya Dangi kaduna zasu je Daganan ne zasu Dawo kano,Aneesa ce kadai take Kano suna ta Shirye Shirye ita da Anty Safiya,Anty Fareesatu kaduna zasu Sauka dasu Inna Maimunatu kuma Duk kowa yayi ankon Fitar Bikin na Kaduna dana Kano,Su Sadam ba"a barsu a baya suma duk zasu ce kaduna Daganan su kwaso Tawagan Amarya Zuwa Kano. Imran bai sani ba Duk Sagir ya gama Satan Lambobin su Mr Tunde da su Mr Sulaiman duk ya Tura musu Progrmme of Event da Code din Dinner maza deep Blue din Shadda Mata kuma Deep blue din Head Leess din kuma Sky blue ne,Sai code din Bridal Shower material ne Red,Sai Atamfan Yinin Bikinsu itace ta Lonching. Kwana Biyu sukayi a Dukku Suka Wuce Kaduna bayan Inteesar tasha Nasihu Wajen Daada,Sannan Baba Asabe ta Dafa mata Zabbin Amare da gumba mai yawa wanda Daada tace ta Rika sha da Nono,jaka guda suka Tafi dashi Kaduna na Nono,sun gama Test amakaranta sai jiran Jarabawa. *Shakira..* 3/28/22, 18:34 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�23* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Ranar talata da yammah suka Dira a Kaduna sun iske gida acike da yan"uwa da abokan arziki,Inna Maimunatu da ya"yanta Tun Ranar Monday suka iso,Inna Bintalo ne bata Riga ta iso ba ammh Dangin Umma sun Cika gida ana ta Hidima Nasara Daman already sun yi mgana ta waya tasan da zuwansu,Dayake gabadaya Dinkunansu na ankon da suka Fitar Kudin suka Turama Anty Hauwa gabadaya ta siya musu Nasara tazo ta karba ta kaimusu Dinki Gabadayansu Harda Umaima da Daddy ya siyamata itama Munarin da Hafsah Daddy ya siya musu Tasleem kuma Ya yusuf ya Tura nata kudin Duka ankon,Kayan Lefen Inteesar kuma Umma ta Diba ta Bama Nasara ta Hada da kayan su takai Dinkin Shagon Telan da suke kai Dinkunansu ita da Inteesar tun Tana Kaduna kafin ta tafi kano Karatu. Washagari Laraba Hafsah da Tasleem Suka Dira a kaduna,Hafsah jiya Da Daddare suka iso kano ita da Anty Fareesatu da yara gidan Abba suka kwana nan ita zata Tsaya tayi Bikinta Ita da Anty Aneesa a kano ita kuma Hafsah Damansun yi mgana da Tasleem In tazo zasu wuce Tare haka kuwa akayi,Tare da Tasleem suka Dira Kaduna Alhaji Alhassan bai da tacewa Saboda duk abunda ya Hada da iyalan Gidan su Imran bai da Karfin Gwiwan yin wani Motsi mai karfi Gabadaya ma Sha"anin Biki,Hajiya Mero da Danginta ne suke ta kaida kawo da gayya ma Hajiya Mero ke basa Labarin Wasu abubuwan Saboda ya Shaka. Umaima bata samu zuwa ba sai Ranar Alhamis Ranar da zasu yi Bridal Shower dinsu,Ta jirgin kasa ta zo Baffa Kabiru yayi yayi Ta bari yasa Direba ya kawota tace ya siyamata Tiket na Jirgin kasa Zata iya kai kanta Har Kaduna Bazata gane gidan ba Zata Kira Munari a waya haka kuwa akayi Tana isowa kafin ma ta Kira Munari Baffa Kabiru ya Kira Basheer ya Fadamai yaje ya Daukota in ta Sauka. Daman Tana da Lambar Ya Basheer din ta Kirasa ta Fadamai ta Sauka Daman yana Kusa shi yazo ya kawota Har Gidansa Inda su Inteesar din suke nan fa suka Hade suka Rungume juna Cikin Farincikin ganin Juna Umaima Babu Ruwanta Tana da kyakyawan Zuciya bata taba Duban Inteesar da Duba Ta auri mijin yar"uwanta ba,Tasani komai ya Faru Daga Allah ne SannanTa sani Mami bata san auran Shiyasa ita bata ga abun nuna Wata Damuwa ba ta shigo Cikin yan"uwanta wanda daman Tare suke Shirya komai.. Agidan Ya Basheer suka Shirya kayattacen Bridal Shower dinsu,Nasara ta gayyato Kawayen Inteesar sosai da suka yi makaranta Tare,sun kira mai Decoration yazo ya kawata Haraban gidan komai dai sun yishi Cikin Tsari da Wayewa Khalil da Sagir sun yi kokari Su suka basu 100k bayan Dinner da zasu Shirya Sagir fa gabadaya albarkar Dinki ya Fito Dashi Ana ta Hidima Indai akan Imran ne ko nawa ya Kashe bai Fadi ba. Sun Kira mai Makeup Tazo ta Tsantsarama Amarya Kwalliya mai kyau ita da Zaratan yan"uwan nata Munari da Umaima da Hafsah da Nasara suna Zagaye da ita Kawayen su sunzo sun mata kara sosai Sun Kira Dj yazo sun Chase iya Chasewa Anty Hauwa da yan"uwanta duk sun zo Da kannenta dasu akayi komai Ga Cikinta ya Fito sai Fama Take yi ita da Anty Safiya ga Hidima suna Fama da Ciki agabansu Tiri tiri,Sun sha Hotuna sosai Inteesar tayi kyau matuka Sanye Cikin Red din Yadi Daman kusan Ja kalanta ne sai akayi mata Head da Bakin wani yadi mai kyau yana Daukan Ido Fitted ce Rigar ta kamata Daga kasa an Saki baza Rigar da wani Bakin Tazaran wani yadi mai Raga Raga,An Salaga mata Wani Yadin Fari mai Dauke da Rubutun BRIDE..! Su Munari suma Haka akayi musu Dinkin Sai dai nasu ba"a Sake sa Daga kasa ba ammh su nasu Kalan Lemon Green ne sai akayi musu Kwalliya da Jan Flower suka Sirka suma sun sha Kyau Masha Allah,barin ma Amarya kamar ka saceta ka gudu Saboda yadda Inteesar tayi kyau sosai Sai dai ta Rame kadan Saboda Stress din Maakaranta da Zirga zirga da kuma Fargaban wannan Tarewar. Sai 7pm na Dare suka tashi Daga Shagalin Tuni Hotuna suka Fara yawo a Social media barin ma Group din Marigayi Hamisu Dukku nan suka Turasu Kala Kala yan"uwana saiDauka suke suna sakawa a Status Intergram,Da sauransu suna Tayasu Murna sai dai Ba Ango ba wanda ma yaga Kyallinsa sai dai Sagir sai da ya Nuna mai Hotunan,yafa ga yadda Inteesar tayi kyau matuka sai dai ya kauda kansa bai nuna ma Kwalliyar nata sun Dakesa Har yaji yana son kallonta bai ko son Kiftawa. Basu yi waya ba Tunda suka je Kaduna sun dai yi mgana Lokacin Tana Dukku Har tabama Daada sukayi mgana Inteesar din bama ta san ina Isalin Wayarta take ba Tana Hannun Munari Shi kuma Imran aiki yayi mai yawa ga Gida ya Fara cika da Jama"a Jiya ma Dakin Sagir ya kwana saboda baya son Hayaniya Mama ta na chan Gidan itama suna ta Hidima ya Kirata Sau Daya Munari ta Dauka yana jin Muryanta ya Kashe bai kara Kira ba ita kuma bata Nemesa ba sai da yaga Hotunan nan ya gane ga Shanshancin da suka Tsaya yi kenan Inteesar ta manta Dashi,Harda Videon da sukayi Rawa suka saka Inteesar a Tsakiya suna ta Rawa su Munari ita dai batayi Rawa ba Tana Tsakiya Tana Mirmishi Hade rai yayi yana mamakin yara kanana sun iya Iskanci haka..? Shiyasa yace baya son Bidia a Bikinsa bazai Dauki wannan Shanshancin ba. Washegari kuma Jumma"a A Kaduna aka tashi da Yinin Biki,yinin Bikin Gabadaya a Gidan Daddy zasu gudanar Harda Lonching din wanda Za"a Fara da karfe Biyu na Rana a tashi Shida na yammah kuma a Haraban Gidan zasuGudanar da komai. Imran bai so yazo kaduna ba Daman yayi niyyar ba zo ba din Sagir yace saiyaje Ya Yusuf ma Haka Sadam da Sa"id ma sun iso sukayi mai Chaa suma Kadunanan zasu su Dagachan ne Gobe zasu Dauko Amarya da Tawaganta Imran yaso ya Zille sai dai bai isa ba Abba ya saka baki kuma Daga Wajen aikinsa Mr.Sulaiman ya bashi Hutu na Ranar yace yaje bakomai ya kuma Hada damai Fatan Alheri bai yi mamakin a ina yaji ba Tunda yana Tare da Katon Ameobe Sagir kenan. Ai bai gama mamaki ba sai da Khalil ya Kirasa yace mai yanzu zai Hawo Jirgi ammh ta kaduna zai Sauka su Hade ta chan Tun jiya yaso tahowa bai Samu Dama ba Dr.Ali isa Argungu ne suka Taho jiya Hajiya Barira tazo Duba Innarta Dake Fagge bata jin Dadi Daganan zasu zo suyima Abba Allah sanya alheri kafin su koma. Imran ya kasa mgana Lokacin da Sagir ya Fitomai da Sabuwar Bugaggiyar Shadda Gezner wanda taji Dinkin Hannu na Zamani Dinkin Riga Sharashara da Babbar Riga,Aikin jikin Shaddan Baki ne Haka ma Hula kansa baka ya sanya da Bakin Takalmi Rufaffe na Matar Damisa Agogon Hannunsa ma Baki ne shima na Fata ne mai kyau da yarari duka aikin Sagir ne shima Irinta ya saka sai dai Tashi ba Babban Riga Imran yayi kyau Har gaji da kyau kamar Wani Wata Dan Daran Goma sha Biyu yadda yake Walwalin Daga Kallon Farko zaka Fahimci Yana cikin farinciki duk da Fuskarsa bata wani Saki ba sosai. Lokacin da sukaje yima Abba Sallama sai da yaja Dogon Tasbihi ga Allah Domin yadda Imran ya zama kamar Wata acikin Taurari ya Dafasa ya yi mai addu"aTare da sakamai albarka Daga Karshe ya Bisu da Allah ya kaisu Lafiya Sagir da Imran Motar Yusuf suka Shiga Sa"id da Sadam suka tafi a Motocinsu tunda suna tare da abokansu ne suma,Karfe, 1pm suna cikin Garin kaduna a masallacin Sultan bello sukayi Sallar Jumma"a kana suka karisa gidan Daddy wanda dashi da Ya Basheer din duk sun gansu nan a Masallacin Tare sukayi Salla bayan sun idar suka Dumguma gabadaya Koda suka isa an kawata Haraban Gidan da ado mai kyau an saka Kanofi da kujeru duka aharaban Gidan Masha Allah ga masu abinci nan kala kala Daga mabambamta Gidan abinci ga Moticin Ababen sha nan sai Wanda ka Zaba Falon Bakin Dake kofar Waje Daddy ya shigar da ya"yan nashi kana ya Kira Umma ya Fadama ta gasu Imran sun iso,Lokacin su Inteesar basa nan suna Shagon Sallon in da za"ayi musu wankin Kafa da Kwalliya Kunshi sunyi jiya da Safe,achan zasu Shirya ga kawayensu nata zuwa basu Dawo ba.. Sagir Hafsah ya Kira ya Fadamata sun iso tace basa gida ammh gasu nan Zuwa su an gama musu Amaryace kadai ta Rage ana karisa Shiryata,Anty Hauwa ce da kannenta suka yi ta Hidima da su Imran ta Bangaran Abinci da ababen sha,Sai Wurga ido yake yaga ta inda zai Hango Inteesar bai ganta ba Sagir ne ya Fadamai basa Gida ga Inda suke Dakuna Fuska yayi yana Fadin Shirme. To bama su Dawo ba Khalil ya Kira Waya yace ya Sauka,Sagir yayi yayi ya Tsaya azo a Daukesa yace su bashi address zai hawo Mota haka kuwa akayi Ya Basherr ya bashi Kwatancen Cikin Lokaci sai gashi nan suka Rumgume juna da Imran da Sagir da suka Riga suka Saba ta waya nan da nan Sagir ya gabatar mai da Nasa kayan ya Kwabe Shaddar Jikinsa shima ya Chakare Masha Allah abokan ango suma sun Fito Ras dasu Masha Allah. Su Inteesar sai wajen uku saura suka Dawo Gidan,Anata jiransu Lokaci ya Tafi suna shigowa Cikin Gida Goggo Maimunatu ta Dauki Gudan ga Amarya nan saboda kyan da Inteeear tayi,Sanye Cikin Wani Ubansu Less cikin na Lefenta ne mai kalan Blue da Golden Dinkin Riga da Zani Ciki da alaku anyi mata Nadin Golden din Head a saman kanta kafarta Cikin Wani Takalmi mai igiya mai Tsini shima Golden haka Karamar pos din Dake hannunta,Tasha Kwalliya Tayi kyau Har tagaji da kyau su Munari kuma suna Sanye da Atamfar yinin Biki ne suma sunyi kyau har sun gaji da kyau. Maman Nasara ta ta ja Hannun Inteesar din zuwa Dakin Umma,su kuma suka Nufi Falon Baki inda su Sagir suke suna Shigowa Kallo ya Dawo kansu Khalil na gefe ne yana kyalla ido yaga Munari ya Rude baki Bude yace Wow...Shima Sagir Hafsah kadai yake Kallo Domin ta gama Tafiya da Imaninsa. Imran na gefe Kunya duk ta kamsa yadda Sagir da Khalil ke wani Rawan jiki kan kannen bayansu Hade rai yayi ya kauda kai,gabadaya suka gaida kowa da kowa har da su Ya yusuf Imran dai ta saman Lebensa ya amsa yana dan duba duben ta ina zai ga Inteeesar din..? Waje Sagir da Khalil suka ja yanmatan suna mgana ganin Tuni mutane sun Fito an Fara Lonching din ba Amarya ba ango Tunda Lonching din Harda Manya su Umma kenan da gayyar Kawayenta. Maman Nasara ta Fito da Inteeear ta Zaunar da ita inda aka Tanada Domin Amarya da ango guda na tashi da Kida mai Taken Aure ya Dauri sannan su Sagir suka shiga suka Fito da Imran Dakyar kamar Dole alhalin shima yana so ya Fito yaga Inteesar Rashin ganinta fa agaresa kamar Cuta ne. Wow..Kawai Mutane ke Fadi sai tashin Flash din masu Hotunan da aka Kira Lokacin da Imran ya daidaita Zamansa kusa da Inteesar Khalil ya Harde Hannu a Kirji yana kallon Munari lokaci Daya yana Fadin"Wow...Wow..What a Perfect March...! Haka yake fadi ita kuma Tana ta Daukansu Hoto Tana Fadin"Kai Ya Imu yayi kyau..Wow..Intee na Besty Wlh They are made for Each Other..! Khalil kallonta kawai yake yi ammh Beb din ai ta gama Tafiya dashi Kowa Masha Allahu kawai yake Fada Na ganin Tsabar kyau Zati da Haiba Wajen Imran da wani Kwarjini Duk da Fuakarsa bata saki ba ammh yayi kyau matuka Inteesar bata iya Hada ido Dashi ba kanta na kasa tana Wasa da Zobon Dake hannunta na Gwal yana kyalli. Imran dai yagama Hade Ransa Dole ya Karkace kai yana kallon Inteesar Baisan ya Kafeta da ido ba sai da ta Dagosuka Hada ido gabayansu sai sukaji kamar mayen karfe ya makalesu su Sagir dasu Munari suna ta Ihun Dariya suna Fadin kallon Love an kashe Hotuna cikin wannan yanayin ba adadi kafin Imran ya Fara Farga ya kauda kansa da Sauri yana wani Dakuna Fuska Inteesar ma kanta Ta maida kasa Tana Dariya. Anci an sha a wannan Wajen anyi Rawa an Taba Bidi"a Umma ma tazo Tajawo Amarya da ango cikin Fili Ta Rika Sakar musu Mannin yan Dubu Dubu ita da Maman Nasara da Goggo Maimunatu da ya"yanta ganin haka yasa su Sa'id ma suka shige suna Rawa suna Manni Har da Ya yusuf da su Munari gabadaya Iyalan Daada ne sun Shige suna rawa suna Liki Imran na Tsaye kikam kamar Gunki ba Domin Umma bace da kanta da sai yace Umma abarma yara mana yana nan Tsaye yana Bin Inteesar da kallo kamar ya Lasheta haka yakeji ga wani Kamshi na tashi ajikinta Inteesar taji gyara soaai Umma ma bata Tsaya kunya ba ta gyara Diyar ta Ciki da baya. Sagir ne yazo ya Hada hannunsa da nashi ya yafito su Ya yusuf suka zo suna ta Jansa da Rawa Hararansu yake yi ammh basu san yana ma yi ba Hayaniya ya ishi Imran ammh sai Mangariba aka Tashi Daga wannan Taron sai kuma Gobe in an isa Kano. Gabadayan sun gaji Saboda Zirga Zirga,Ya Basheer gidansa ya kaisu Imran suka kwana Tunda gabadaya Matan suna Gidan Umma saboda Shiryan Shiryan Tafiya da Safe. Sagir da Khalil dai sai chan dare suka Dawo suna gidan Umma Tare dasu Munari suna kara shirya Dinner Gobe Imran Harara kadai yake maka musu in suka Hada ido su kuma suyi tamai Dariya Allah kadai yaaan me suka Shiryamai gobe. Garin Allah na Wayewa Daddy yace su Fara Harama Domin su tafi da Wuri,Masu Karatu zan so ku hangomin kukan da Inteesar tasha na Rabuwa da Umma da Daddy tana Sanye Cikin Nadin Lifaya,Gaban Umma Tana ta kuka Umma ma sai Hawaye tana ta sakama Inteesar albarka. Ta Rumgumeta Tana Fadin"Umma ki yafemin..! Umma na Sharan kwallah Tace"Na yafemiki Duniya da Lahira..Allah ya Zaunar daku lafiya..! Dakyar Maman Nasara ta iya Raba Umma da Intee su Munari basasu iya gani ba Tuni suna Haraban gidan Tare dasu Sagir inda suka sanya kayansu Amota ai kuka sai Agaban Daddy ita da Imran ya Hadasu yayi musu nasiha sosai ya Hada hannayensu yace su Zama Bangon junansu Daga Karshe ya Bisu da addu"an Zaman Lafiya yadda Inteesar ta kamkame Daddy tana kuka ko shi Imran din sai da ya Taausayamata ya Rikota acikin Jikinsa yana Lallashinta Daddy kuma baya ya Juya yana Dauke kukansa. Maman Nasara tazo ta kamata zasu Fara biyawa ta badarawa gidan su Inno Kafin su wuce inda Kawunanta ke chan zasu mata Nasiha. Ya Yusuf shi zai Dauko Amarya a Motarsa Imran Motar Sadam ya shiga shida Goggo Maimunatu dasu Zainab,Suka Farayin gaba Su Sagir suna Tare da su Munari shi kuma baya son Harka da yara Shiyasa ya kama kansa akwai Motoci Tunda ga na Daddy da na Ya Basheer,sai nasu Goggo Bintalo itama da Mota tazo da Direba ita da ya"yanta Har Gidan Inno da ita aka je bata yarda ba sai taga Komai Saboda taji Dadin Kyankyasama Mami Asma"u gulma. Achan gidan Inno ma Inteesar tasha kuka su Kawu bala sun mata Nasiha sosai da Inno da Mallam Babba Muda Yana makaranta chan ya koma sun Fara Jarabawa shiyasa bai Taho ba Basu jima ba achan ba suka Dauko Hanya Maman Nasara na Rike da ita da Anty Hauwa Yusuf na Driving Anty Jamila Diyar Kawu Bala Tana gidan Gaba. Basu yi gudu Bisa Hanya ba sai 12 suka iso kano tuni su Imran sun Dade da isowa kuma Gidan Sadam din suka yada Zango,Ya Damu yana so yaji ko Inteesar ta iso yana ta Kiran wayarta Bata Dauka ba sai daga baya aka Dauka yaji Muryan Sagir na Fadamai sufa suna Hanya kuma wayar Amarya Tana Wajen su Munari Tsaki yaja ya Datse kiran wai meyasa bata Rike wayanta ne sai ta Rika bama Shashanshan yaran nan Ya ja Tsaki yafi a Kirga kafin ya Kira Ya Yusuf shi yake Fadamai sun iso har su Maman sun zo Taran Amarya zuwa Cikin Gidansu Gida ya Cika Makil suma Haraban Gidan Cike da Mutane an saka Kanofi da kujeru Hajiya Anty Safiya yayar Ango mai Masaukin baki Taci Gayunta kamar Wata Amarya. Taro Ta Hada itama gagrumi sai wanda ya gani Hajiya Mero da Danginta sun yi kara soaai Mama itace Uwar ango ita da Kaltume Matar Baba Manu,Abba dai Dole ya bar Gidan zuwa Cikin makaranta Saboda Gida ya Cika ba Mtsaka Tsinke.. A Shashen Anty Safiya aka Sauki Amarya Inteesar Wacce ke ta kuka Cikin lifaya Gefe da gefenta Maman Nasara da Antya Uwani matar kawu bala,Anty Hauwa Tuni ta shige Cikin su Aneensa an hadu ana ta Shewa da Hiran yaushe gamo bata ga su Munari ba Tadai san tun a gidan Daddy ta barsu kila suna Hanya gashi ba Waya a Hannunta Ballatana ta Kirasu. Sai 2pm na Rana suka iso wai Mai ne ya Tsaya musu a Hanya Motar Sa"id suka Shigo matan mazam kuma Motar Basheer Gidansu Imran suka ijiyesu tunda nan ma akwai yinin Biki suka wuce gidan Sadam koda sukaje Tuni su Imran har sun yi Sallah sun Wuta sun ci Abinci suma Sallar sukayi suka ci binci suka Zauna Zaman Hira da Labarin yadda Dinner anjuma Zata kaya. Imran na gefe yana jinsu to me zai ce..?bai isa yace komai ba yadda Khalil da Sagir suka Hada kai ai sun fi karfinsa sai dai ya Bisu da ido Gidan su Imran kuwa Biki fa yayi Biki Anty Safiya ta Kira dan Asharalle yazo Yayi kida Mata sun chase Har da ita ga Ciki ga komai ita dasu Anty Hauwa Ko Nauyin Jikinsu basa ji,Harda Inteesar duk sun Fito Haraban gidan suna kallon Rawan manya mata Goggo Mainunatu tayi rawa itama ta Kira Bidi"a Sosai kowa kagani yayi anko Tabbas Anty Safiya ta yi gayyah kuma an Mata kara sosai Tunda Shagali ne Wanda ba"a taba yi ba Duk Tsawon Shekarun da suka Shude Dole abiya bashi. Chan na hango yan Dandalin GMB2BANDGROUP,Suma sun cakare cikin ankonsu sun sha kyau har sun koshi sai hotuna suke da Amarya Inteesar bakinsu yaki Rufuwa Yau gasu ga inteen Imu duk da basu samu ganin Imun ba sun Rage Zafi. Sai yammah aka tashi Wannan Rawar Makota da yan"uwa wadanda baazasu kwana ba sukayi Haraman Tafiya masu Shirin Tafiya Dinner kuma suka Fara Shirya Daman already Munari sun Dauko mai Kwalliya wacce Zatayi musu na Tafiya Dinner kawayensu na Buk abokan arziki suma duk zasu je Wajen Dinner maza da mata. Pass dinka shine Code din Dressing din Dinner din shine pass din Shigarka. Amarya ko kafin 8:00pm Tayi an gama Shiryata kuma 9pm za"a Fara Dinner din,an Shiryata Cikin Less mai kyau Skya Blue itama an mata Nadin Head Deep blue,sai Daga baya an yafa mata Wani yadi mai Santsi Sya blue yana da Kwalliyan Deep blue na Duwatsu yana Daukan Ido Har kasa yanasharan kasa haka Jakarta ma Deep blue pos sai Takalmin kafarta ma Haka mai Tsini Shima Deep Blue Wata Kwalliya akayi mai mai kyau da Yarari Cikin Lokaci kamar ba ita ba kafin a Fara Shirya Sauran kawaye Tunda Sagir ya kira suma Kadan ya Rage su karisa Shiryawa zasu zo su Dauke su. Ango Imran yasha Shadda Deep Blue da Babbar Riga da Hulansa Zanna Bukar mai Zanen aikin jikin Shaddan Skya blue sai Takalmin Kafarsa Baki ne Rufaffe na Matar Damisa sai Agogon Hannunsa na Kamfanin DKNY,yayi kyau har ya gaji da kyau Kayan Dinkakku ne,,aikin Ya Yusuf ne suma sun Cakare da nasu Kalan Shigar na deep Blue din Shadda ammh su ba Babbar Riga,Har da su Ya Sa"id domin fa sun ce suma matansu Zasu je suma bamai barinsu a baya Ballatana Ya Yusuf da kafarsa kafar Matarsa Anty Safiya,Wacce Har Hajiya Mero zata Hallaci Wannan Dinner ita da kawayenta Da yan'uwanta irin su Anty Saratu. Karfe 9 da wasu Mintina su Sagir suka Kariso a Motar Abba Ango da Amarya zasu Shiga Abba ya Dawo saboda Mutane yana Gidan Sadam shima. Sai sauran Motocin kuma zasu Dauki Sauran Mutane. Sai Kiran su ake yi Hall din mai suna Mina Event Center fa ya Cika Damkam da Mutane su kadai ake jira,Imran na bayan Mota ya Hakimce yana jiran yaga ta ina Inteesar zata Bullo..? Ai kuwa yayi kyakyawan gani Domin Sanda yaga su munari sun Fito da ita baki ya saki yana kallonnta baisan Sadda ya Furta masha Allah ba Saboda yaga tayi sanyayyan kyau mai Cike da sakama zuciya Natsuwa. Har Cikin Motan suka Rakata suka Sanyata Kusa da oga Imu wanda suna karisowa ya Dauke kai kamar baya kallonsu Munari ce da Hafsah suka gaisheshi da Dakyar ya amsa. Aransu sukace kamar Dole..? Sai da Motar su Sa"id ta Fara yin gaba da Ta Basheer da ta Sadam kana Motar Ango da Amarya ta Daga Khalil da Sagir na gefe Khalil ke tuka motar. Suna Kallon Imran ta Madubi suna Danne Dariya shi baima Lura dasu ba Tsabar Haduwar Intee da kamshinta ya gama Rudasa har bai san ya Riko Hannunta ba Sai ji yayi ta Dago Tana kallonsa Cikin Narkakun Idanuwanta. Lamgwabe mata kai yayi a Hankali yace"Meyasa baki bar wayarki a Hannunki ba Ahalin kinsan zan kiraki..? Tana Kokarin Daidaita kanta jin Yadda yake Faman shafa Hannunta Tace"Ni ban ma san inda take ba..Kamar Tana Hannun Mu..! Dakuna Fuska yayi zai yi mgana suka Hada ido da Sagir ya Ballamai Harara yana Fadin"Munafuki i donsa na kan miji da mata Watarana sai idonka ya Tsiyaye..! Sagir da Khalil Sai Dariya suke kwasa koda suka isa Wajen su Munari sun kariso suna Waje suna Jiransu ba Bata Lokaci Imran ya Fito Shida Inteesar ba wanda ya bashi Shawara shi yaga Dacewar ya Damke Hannun Amaryan Tasa gam Ransa na kuna in ya Tuna ahaka maza dadama zasu kallemai adon mata. Sune kan gaba da su Waleeda da akayi ma Kayattacen shiga suna kan gaba tawagan su Munari na baya dasu Sagir da sauran gayyar suna Shigowa wajen ya Dau Sanyayyan Kidan Aure ya Dauru ga Kyali kyali na Sauka ta Ko"ina Waje ya Cika Damkam da Jama"a Imran bai saki baki ba sai da yaga Dimibin Abokan aikinsa A Wajen Har Mr Sulaiman da Mr Tunde,mamaki ya Kamashi su kuma sai dai suka Dagamai Hannu Suna Zama Inda aka Tadanar musu MC ya Fara Jawabi,Saboda Dare yayi kuma Imran ya bada Sharadin in aka Wuce 11pm Wlh zasu Nemesa su Rasa Susan Halinsa Shiyasa suka Gayana Mc ayi komai Cikin Lokaci. Game aka Fara gabatarwa Irin dai na Mc,Tun alokacin Imran yaji ya Fara gajiya,sannan aka Umarci abokan Ango ya bada Tarihin ango Sagir da Khalil suka Fito Sagir ya Fara Bada Takaitattacen Tarihin Imran Daya Sani.Khalil ma ya karba ya bada Nashi Wanda ya sani Tun suna Lagos. Kafin Sagir ya karbi Abun mgana yana Fadin "Wato Soyayya Tsakanin Inteesar da Imran Wata soyayyace da Bantaba ganin irin ta ba..Makauniyar Soyayya ce da su kansu basu san sun Fadama juna ba in ance yana sonta yace Shi ba sonta yake ba ammh Kusan me..? Baya son kukanta..?baya son bacin Ranta bayason ganinta da wani kun Taba ganin Damben maza..?ku Fadamin soyayyahce ko yan"uwataka ke sawa Namiji yayi Fada kam mace yaji yana Kishin ya ganta da wani Ku Fadamin da karfi Soyayyah ce ko Yan"uwanta ka..? Gabadaya Hall yadau Ihun Soyayyace Wlh na Love Sai Dariya da ihu da Tafi Imran Hararan Sagir kawai yake yi yakasa mgana Sagir na Dariya yace"Uhm...Harfa Rakata yana yi.. Gadin ta ma yake Wato Mr imran ya Dade dai yana Son Inteesar Daga Karshe Dayaga za"ayimai Kafa sai ya Zabura ya mike ya bayyana kansa ammh fa shi adole bai yarda yana Sonta ba Cewa yake..! Yakasa karisawa Saboda yadda Imran ke aunamai Harara ga Ihu ya Kaure a Hall din Sagir na Dariya yana Fadin"Ammh fa soyayyar tasu ta Musamman ce..Ina wasa Dake ne..? ni Sa"anki ne..?kin Raina ni ko..? Zan Sauya miki kammani Zan yi kwallo Dake..?To Amarya Inteesar Shaawaran da zan baki a mtsayinki na kanwata Sai kin yi Hakuri kin Dage da Ninka Biyayya ga Girman Miji ga na Yaya in baki yi a Hankali ba Angon naki cikin Kwanakin nan na Amarci zai iya Sauya miki kamanni Ko kuma Gidan ku ya koma Gidan Kwallo da Mutane.! Gabadaya aka kara Saka Tafi da ihu Imran kallon Sagir kadai yake ya auna yadda zai Yi kasa kasa dashi in suka Kebe Inteesar sai Dariya take kasa kasa yana kallonta. Sagir ya cigaba da Fadin"To kai kuma abokina sai fa ka yi hakuri..Mata fa yan Lallashi ne duk da kace kai Allah ya kyauta ka Zauna kana Lallashin Mace..! Khalil ya Karbe abun mganar yana Fadin"Sagir nace Ranar Lallashin bata zo bane..Nace Jama"a ku Fadama Mr Imran Ranar Lallashin bata zo bane..Sanda zai shige Dimuwa yana Fadin Baby Plz mana kiyi Hakuri..! Ya Karishe Fada yana kwaiwayon mganar Imran ai gabadaya aka Saka Dariya wasu Harda Rike ciki Kai in aka Biyema Khalil da Sagir zasu Kullan ma da Mutane Cikinsu kuma ga ba Lokaci Imran Kamar ya Fashe Sagir da Khalil sun gama Dashi Gaban yara. Su Yusuf Dariya kamar su kwanta yana kallon Fuskar Imran yana Dariya Nasara aka Kira tazo ta bada Tarihin Amarya Daganan aka bada Lokaci akaci akasha kana aka Fito Filin Rawa Imran duk yadda yaso ya Zille sai da su Sagir suka Fito dashi suka Rika mai barin kudi shi da Inteesar da sauran Dangi aka kuma barsu su kadai su Rausaya Imran dai ko Gyada bai yi ba sai ma Inteesar data dan juya shima bai bari ba ya Rikota yana mata wani kallo Dayasa ta Dataka sai Hall ya Dau sowa da ihu Wajen yanka Cake ma abun kallo ne Imran ai Oga ne Komai nashi na Dabam ne. Awajen Dinner ma chan na kara Hango gayyar yan GMB2BANDGROUP,da nasu Hadadden ankon Dinner din masha Allah sai Washe baki suke Daga nesa suna Daukan Intee da imu Hoto saboda suna Tsoron su karisa wajen Imu ya Fahimci Hoto suke Daukansu zasu bazama duniya yace baisan Raini zai Sauya musu kammani suna Daga gefe sun kame suna Kallo kowa Daya bayan Daya suna masu Farincikin ganin wannan Ranar da su munari da Sagir kadai suka samu Damar gaisawa sosai. Anci an sha an sha Rawa an yi barin kudi su Inna Bintalo ana gefe atana Daukan ma Mami Asma"u Video Tana Turamata tana kara Tada mata da Hankali Sai 11pm aka taahi Imran suka Fara Tafiya sai da suka kai Inteeear gidan Abba kana suka wuce Gidan Sadam,Suka ijiyesa Khalil da Sagir suka juya zasu Dauko su Munari ko mgana bai musu ba ganin suna Rawan kafa kan yaran zai Fada musu gaskiya su kama kansu baya son Raini. *Shakira...* 3/28/22, 18:34 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�24* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Karfe 10:00am na safe aka Sada Inteesar da kayattacen dan madaidaicin Gidanta Dake Alu Venue anan cikin garin kano,Ta samu Rakiyan Mama da Maman Nasara da Anty Uwani sai su Inna Maimunatu da su Inna Bintalo da Sauran Tawagan Matan su Basheer da na Anty Safiya da ita kanta suka Sada Inteesar har saman Kayattacen Dakin Barcinta Kan gadonta na Royal bed mai kyau da yarari wanda yaji Shimfidun alfarma sai wanda ya gani bayan sun Umarceta da Tun kafin ta shiga Gidan ta Dafa Ginin Gidan ta karanto addu"an kariya da Zaman Lafiya Acikinsa da Dukkan alherai na Har Abada. Kafin a wuce da ita Abba yayi mata Nasiha sosai da kuma Fatan Zama Lafiya Tsakaninta da Imran ya kuma Horeta da sai tayi Hakuri Sosai sanin Halin wanda Zata Zauna dashi An kaita da Wuri ne saboda Za"ayi Walima,Atashi karfe Biyu na Rana akwai Wadanda zasu koma Gida yau Saboda ayyukansu kamar su Khalil da su Sa"id yau zasu koma Gida. Duk wanda yaga irin Uban Dukiyan da aka Narka a wannan gidan sai kaji yana Sakama Baffa Kabiru albarka ana Fatan Allah ya bar wannan Zumuncin Har gaban Abada,Kowa sai Santin gidan yake Kitchen kuwa shima ya kawatu matuka Umma ce ta Roki alfarman a bar mata Kitchen din Ta gyara a Mtsayinta na Uwa sai aka Barmata Lalle ta Aurar da Autarta Sai wanda ya gani Kayan abinci cike da Store wannan aikin Duka na Daddy ne Ba abincin da Babu aciki Fridge kuwa Cike da kayan Cefene wannan kuma aikin Yusuf ne yasan Waye kaninsa Careless ne sosai kan Abunda ya Shafi Cin Abinci Shiyasa ya gama da Wannan Barayin ya Tabbata Cefanen zai matukar basa Wahala. Irin su Anty Aneesa da su Fareesatu sai Daukan Hoton Gidan suke su Munari kuwa sai Faaman Daukan Hotuna suke yi ko gajiya basa yi Kowa yana Nuna Murnansa a Fili banda yan Bakinciki irin su Inna Bintalo Har Video gidan sai da ta Dauka ta Turama Mami Asma"u Tana nuna mata Irin Kudin da Baffa Kabiru ya bar nartar kan wanda ya Saki yarsa da Inteesar din da aka yi mishi auran Tura Haushi da ita. Mami Asma"u Tun Jiya Take kwance bata da lafiya ta gama Sarewa da al"amarin Baffa Kabiru ta gama yarda ya Juyamata baya kuma bai da Niyyar Dawowa gareta,Daada da yan"uwansa sun yi musu Farraku lokacin Dataga Hoton Imran da Inteesar Awajen Dinner sai da kwalla ta kawo mata A zahirin gaskiya Imran bai da makusa ko D'anta Khamis Wlh bazai jera kafada Dashi ba Cikin Maza Dubu Sai an Tona za"a samu kamarsa anya anya ba Gaskiya bane Tana da Sonkai.?ta so kanta da yawa yasa bata Fahimci Babban goron da Allah ya Kashe yabama yarta ba sai Rudin Duniya da hujjarta mara Tushe Ballatana makama ta Ruguza komai ta Bata komai Karshenta itace tayi Biyu babu An Saki yarta Sajida Tana chan Tana Ramewa Saboda Damuwa itama Gatanan Gotai Gotai Da ita Miji ya Saketa ta dawo Gida Zawarci Itafa bata yarda ma ta Fara Kirga kwanakin Iddarta ba gani take kamar Wasa Kabiru yake zai zo ya Dauketa su koma Gida bai Saketa ba. Da Bintalo ta Turo mata Video gidan Tagani Batace mata komai ba ta Fara Jin Haushinta Taya zata Rika Turo Mata Abunda zai Dagamata Hankali Ita kuma ba wani mganin Matsalarta Zatayi mata ba Shiyasa ta Kashe Wayarta bata son ta Dameta da Tseguminta wanda ta Saba kuma ya Zame mata jiki gwara ita Tana Gidan Mijinta kuma ya"yanta ba wacce aka Taba Saka ta zama karamar bazawara irin y'arta Sajida,kuma duk fa aje a dawo Daada uwa take ga Bintalo kuma kabiru da su Mustapaha Shakikan yan"uwa ne gareta Duk inda akaje ita ce ke cikin Bala"i ba Bintalo ba Shiyasa ta Kashe Wayarta abunda Taji ya Isheta bata Kaunar kuma ta kara jin wani abunda zai yi barazar Tafiya da Numfashinta. Karfe 12:00pm aka Fara Walima Malama Juwairiya Anty Safiya ta gayyato an saka Kanofi a Haraban Gidan Duk da bai da Girma sosai an Fito da Amarya Saboda Wa"azin Walimar Aure,Masha Allah Malama ta yi Wa"azi sosai kan Hakkokin mata ga Mijinta da Hakkin miji kan mata da yadda Mu mata zamu gyara Jikinmu Tare da Shawarwari ga Amarya an Raba Snks da Key Holder da Kofuna da Memo karamin Choter,Hanky da Riguna da Jaka Duka Dauke da Tambarin IMSAR FOREVER��🤩 Duk wannan aikin su Munari ne Snks din kuma aikin Umma ne,naga Tarin Mutane sosai a wajen Har da gayyar GMB2BAND GROUP suma sun Hallaci Wannan Walimar Domin Tabbatar da su Team din Imsar Forever ne. Sai Karfe 2pm aka tashi Walimar sai aka Fara shirin gyara gidan da kuma Haraman Tafiya abar Amarya a Muhallinta. Dr Isa Ali argungu sun zo shi da Matarsa Hajiya Barira yima Abba Allah sanya alheri aure da kuma aikin Daya samu yau zasu bi Jirgin Karfe 4pm zuwa Lagos tare da D'ansu Khalil Daga Fagge Suke daman Tunda suka iso suna chan gidan Dan"uwanta Taje Dake nan Zoo Raod ta iske Duka Gidan basa nan yayan nata kadai ta gani suka gaisa duk sun Tafi Biki. Koda suka zo Gidan Abba ma ba Kowa sai su Imran da shi kanshi Abba Duka suna Chan gidan Amarya. Bayan sun gaisa da Abba tayimai Allah sanya Alheri tace akaita Ta Leka Gidan Amarya kafin ta wuce Yusuf ya Dauketa Amota zuwa Gidan Tana zuwa suka Hade da Anty Safiya sai suka Tsaya suna kallon juna Baki Sake Anty Safiya Tace"Goggo Barira..! Hjiya Mero ma ta Kira sunanta itama Cikin mamaki tace"Hajiya Mero..Ikon Allah yanzu nan Da muka Fito Daga Fagge gidanku muka Fara zuwa bakwa nan sai Alhassan kadai muka iske shine muka kariso chan Gidan Dr.Malami ai makotan mu ne,abokin aikin Dr.Ne tare sukayi koyarwa nan Jami"ar Lagos kuma mun zauna ga gida ga gida a Lagos..! Sai kallo ya koma Sama Hajiya Mero Cikin Fara"a tace"Ikon Allah..Ai Safiya Yusuf take aure..! Hajiya Barira ta rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..Wato auran da Goggo Tace yayima yarsa a Wulakance batare daya Fadama kowa ba ashe ma D'an Gida ta aura Yusuf Duk Tare da ya"yanmu suka tashi. Iyalan Dr.Malami nasu Nagarta ne ni nan munyi Zaman Amana da Mahaifiyarsu Marigayiya zuwaira Allah ya jikanta Khalil kuma Hala baku Hadu bane ai abokin Imran ne yana nan Tun Ranar jumma"a Hajiya Mero tace"Hajiya yaushe zasu Shaidasa ko ni nan ai na Dade ban gansa ba ko yazo iyakarsa Fagge baya karisowa kece dai in kika zo sai kin kariso..! Nan fa Hira ta Sarke Hajiya Barira Tace"Ai Dayake ga Karatu ga yanayin aikinsa Banki ne ba Lokacin sun gama Sayarma gwannati..! Nan fa Aka Tsinke da Hira Anty Safiya sai Nuna Hajiya Barira take kanwar Alhaji Alhassan ce Da goggo da Wacce ta Haifeta Inna Furare Uwarsu Daya Ubansu Daya Zumunci sosai kowa da yaji yayi mamaki matuka Har Bedroom din Inteesar Mommy ta kaita ta saka Amarya albarka Sauri Take yasa Datace Zata koma Mommy tace su tafi Gabadaya suma Daman yanzusuke Shirin Tafiya yusuf na Haraban Gidan yana Jiranta sai gasu sun Fito nan yake jin Sabon Labari yana ta mamaki haka ma su Abba sukaji Wannan mamakin da suka koma Hajiya Mero kam sai jin Dadi take irin wannan Ranar take jiyema Alhaji Alhassan Ranar da zai ji kunya,Hajiya Barira da Dr.Isa Ali argugu suna bada Labarin karamccin da Mutunci irin na Abba da Duka Iyalansa suna Fadin har suka Zauna dasu na Tsawon Shekaru basu Taba Samun Mtsala ba Shiyasa ko yanzu Megadin Dake Tsaron Gidan nasu da Iyalansa DR.Isa Ali argungu ke Biyansa Duk Wata yace ma Yusuf kada ya Damu shi ya Dauke wannan,Tsakaninsa da Abba sai Godiya anyi Zaman Amana da Mutumci Hajiya Barira da kanta ta Kira Alhaji Alhassan tana Fadamai,Dayake Daganan Filin Jirgi zasu wuce kunya da Nadama suka kara Lullube Alhaji Alhassan ya Godema Allah baya Wajen da wani idozai kalli Yusuf da Abba..?ballatana Imran Daya gama Sanin Duka Sirrinsa. Yaji kunya sanda Hajiya Barira ke Fadamasa Marigayiya Hajiya Zuwaira Kawartace sosai har Allah ya Dauki Ranta Daga Karshe ta Sanar dashi AhalinDaya bada yarsa kyakyawan Ahali ne mai Cike da Nagarta Alhaji Alhassan dai ba baki Zufa kadai ke Ketomai har suka gama mgana yana Tunanin Allah na son shi Dayake ta Nuna mai Ishara kala kala alamace Ta ya Tubarma Allah kafin Lokaci ya Kuremai in ba Haka ba ya Gujema Ranar da Duniya zata san Halinsa na Boye sai ga Alhaji Alhassan na kuka da Idanuwansa kukan Nadama da danasani Ba shakka Imran ya Cika Mutumin Kirki mai kyaakyawan Zuciya a yadda yake kallonsa bai taba Zata Har yanzu bazai iya Tona mummmunan aikinsa ba sai gashi ko alama yaron ya nuna masa yasan Abunda yake yi alokacin Alhaji Alhassan yaji komai ya Fita kansa Nadama ta Shigesa yadaukan ma kansa Alkawarin ya Daina neman mata Har Abada yana me yin Nadama ga abunda ya aikata a baya. Khalil kuwa baisan Wainar da ake Toyawa ba sai da ya Dawo Shima Kiransa Babansa ke tayi Lokaci ya Kusa kada su Rasa Jirgi suna chan Gidan Amarya Shi da Sagir kowa yaja Wacce ta shiga Ransa yana Fadamata Sirrin Zuciyarsa Saboda Dama Daya Take zuwa a Rayuwa. Sagir ya gama gabatar da kansa Wajen Hafsah kuma ya samu shiga kwarai da Gaske sun karbi Lambar juna khalil ma ya gama Sace zuciyar Munari Tuni itama tayi Na"am da mganar na Khalil saboda ai ya gama Haduwa Shima,Tuni suka karbi Lambar juna Duk da kowa nadashi Imran nachan sai Kiran su yake su Hajiya Barira na Jiransa Ya Yusuf zai kai su Filin Jirgi sai da suka gama Kafa Zuciyarsu sai gasu sun Dawo sai Alokacin Hajiya Barira ke nuna mai Hajiya Mero da Anty Safiya,Tasleem ma ashe kanwarsa ce Shiyasa yaga kamar ya santa Tunda shi yama Dade Rabonsa da kano yafi Shekara Bakwai. Imran sai Hararansu yake yi Shi da Sagir saboda wani Hade kai da yaga sunayi Da yayi mgana Sai su yi mai Chaaa,A gurguje akayi sallama gabadaya acikin masu Rakiyan Har da Imran da Sagir suka shiga Motar Imran din suka Rakasu Filin Jirgi basu Baro ba sai da Jirgin su ya tashi suka Dawo a Mota Imran ya wani Hade rai Sagir ko ta kansa bai bi ballatana ma ya Tsaya Tambayansa. Bayan La"asar su Inna Maimunatu duk suka dawo Gidan Abba sai gobe zasu Tafi su Maman Nasara kuma Gidan Mama suka yada Zango suna sai gobe zasu tafi Su Munari suka bari agidan dsu Anty Aneesa itama Anty Safiya ta koma Data Raka Mommy da Anty Saratu Tasleem dai Tana Gidan Amarya sai an juma Zata dawo. Su suka Hadu suka kara gyara Gidan suka Share suka Turare gidan Turaran Wuta masu kamshi da Sanyaya rai Wanda Maman Nasara tazo ma da Inteesar da yawa kala kala bayan na Jiki harda na Daki dana Turara gida.. Sai gabda mangariba suka yi Shirin Tafiya Fareesatu sun fasa Tafiya suma sai Gobe Mazajen nasu suka zo Daukansu zuwa Gidan Abba abar Amarya Ta Huta kafin Ango ya Shigo. Inteesar da Farko bata Damu ba sai da Taga Tafiyar zasu yi da gaske kana ta Fara Kuka Tana Rike Munari Duk Dauriyan Munari Sai da tayi kukan Sabo hawaye shabe shabe aka Bambare su Daga Jikin juna aka yo Waje da Munari Hafsah ma da Tasleem da Nasara sai kuka, Harda Umaima itama Haka suka Shiga Mota suna Sharan Hawaye Inteesar kuma Ta Kudundune kan Gadonta Tana ta kuka kukan da kowacce mace take yinsa Ranar da aka Kaita Gidan Mijinta Za"a Tafi a barta. Gashi kuma suna da Jarabawa Allah yasa Munari ta Dauko mata Wasu Li ttafai da Zata Bukata Ba mganar Amarci mganace ta Karatu kawai ba kama Hannun yaro,Sagir ma yazo Daukan su Hafsah aMotan Imran din Tunda ya iya Tuki Imran ya koya masa,Dukkansu agidan Abba sukayi Sallar mangariba aka Zauna anata Labarin Biki da maida yadda abubuwa suka Kasance Imran na Cikin Dakinsa ya kasa Tabuka komai Kewa yake jin kewa zai yi nesa da Abba da Ya Yusuf da Gidansu Daya Saba Dashi Fiye da ko"ina zai Tafi yau ya Kwana ainda bazai ji Motsin Abba ba Rauninsa yaso ya Tabasa Raunin Tuna Anni a wajensa Yau yayi aure zai Tare a Gidansa ammh Anni bata Wannan Duniya yana Tuna kalamanta Imran Duk Ranar da kayi aure ni da kaina Zan Rakaka Dakin Matarka ba Kai ne Zan bama Hakurin Zama da ita ba kai zan bata amanarka na kumace Tayi Hakuri Domin ba karamar Jaruma bace Macen da ta yadda ta aureka.. Alokacin Tabe baki kadai yake yi baya Mgana ammh yau sai da Zafafan Hawaye suka Zubomai acikin Kwarmin Idanuwansa ya Hade kansa da Gwiwa yana ta kuka kukan mai Cinrai da kewa da kaunar Uwa acikin Ransa. Abba ne yake ta Cigiyansa kan abar Inteesar ita kadai achan Gida Sagir aka Kira kosuna Tare yace shima Nemansa yake yana ta Kiransa bai Dauka ba Yusuf ne yasan ba inda Za"a Gansa sai Cikin Dakinsa Halin Daya Samesa ne yasa ya Kira Abba Shi kanshi Abba sai da ya Fitar da kwallah Shima yayi kuka a irin wannan Ranar Allah ya jikan Zuwaira da Sauran ya"yanta Allah yasa suna Cikin Aljannah Haka Abba ya Rungume Zaratan ya"yan nashi yana Sharan kwallah yana Lallashinsu sun yi ma yan"uwansu da Mahaifiyarsu addu"an Dacewa da Fatan Allah ya jikansu da Rahma. Yusuf shi ya Hadama Imran Kayansa da Zai Bukata Tunda bai Dauki Hutu ba Mr Tunde da Mr Sulaiman sun yi Dashi ya Dauki Hutu yace bazai Dauka ba Duka Duka yaushe ya Fara aikin Da wannan kuma don wannan Dole suka kyalesa Har Khalil ma yamai mgana shima wannan Hujjar ya kawomai kuma shima ya yarda yace ya bari sai nan gaba sai ya Dauka sai susha Honey moon Cikin Natsuwa Lokacin itama Intee ta gama Jarabawarta ba Streess na makaranta. Duk yadda Imran yaso kada Rauninsa ya bayyana kasawa yayi yau Rana ta Farko da kowa yaga yana kuka Ya Rumgume Abba kamar Wata Mace ba wanda bai Tsausayamai ba Abba ya Buga Kafadarsa yana Fadin"Ka Daina kuka..Jarumai kamar ka da Juriya aka sansu ba kuka ba..Kaje Ga.Matarka Allah yayi maka albarka ka Riketa Amana Kanwa take gareka Ta Kowani bangare ta Chanchanci Kulawarka..Sannan Rokona na Karshe ka Rage Zafin Rai don Allah Imran kuma ina Rokon Allah yasa wannan auran ne Sanadiyar Dukkan Wasu alherai Allah ya Zaunar daku Lafiya! Gabadaya aka amsa da Ameen Ameen Sagir ne zai Tukasa zuwa Gidan bayan an gama Saka kayan nashi a Mota ya Shiga Gidan Gaba Sagir yayi Riverse ya Fice Daga gidan su Abba na Dagamai Hannu Yusuf bai san yana Kwallah ba sai da yaji Abba ya Saka Hannu ya Sharemai ko da Imu ya kasance bamai Hayaniya da shiga Mutane ba Akwai Shakuwa Tsakaninsu Sosai Kuma shi Sabo ai ake yima kuka Su Sa"id suna ta bama Yusuf baki suna Fadin suma fa Tare koda yaushe suka so zasu ga juna ba"a Rabu ba Har Abada. Shi kanshi Sagir Jikinsa ya Mutu da yanayin Imran din kuma shima wannan kewar na Damunsa Bai fi Shekara uku Dayasan Imran ba Ammh Sun yi Sharing din kauna da Shakuwa a Tsakaninsu suyi Fada su Shirya ammh kuma basa iya Rabuwa da juna Ammh yau aure yakai Imran wani Mtsyin da zai bar anguwan Gabadaya sai dai Waya ko kuma in ya Lekosu shima Tuni jikinsa yayi sanyi Har suka kai Gidan ba wanda yayi ma Dan"uwansa mgana.. Gidan bamai gadi Imran ya Sauka ya Bude Get din Sagir ya Shigo Ciki Shi ya Tayasa suka Kwashe kayan zuwa Cikin Gidan Har Cikin Dayan Bedroom din da zai zama mallakin na Imran ne. Sagir ya zauna Saman Daya Daga Cikin kujeran Falon yana Fadin"Ango ba Kazan Amarci haka zaka shigarma Amaryan taka Hannun Rabbana..! Imran na Tsaye yana kallon Wani Barayin ya Karkace kai Idanuwansa sun kala yace"Uhm..! Daga haka bai kara cewa komai ba Sagir ma sai bai kara cewa komai ba yana Bin Falon da kallo yace"Baffa Kabiru yayi Kokari..Allah ya Biyasa..! Imran na Jinsa bai ce komai ba Tunaninsa ya Tafi yadda Rayuwa Zata Juyamai na Rayuwa shi da Inteesar a Inuwa Daya a mtsayin mata da Miji. Anya zai iya Daukan wannan Nauyin..?shifa ba Daya yake da kowa ba Kansa ma bai Damu dashi ba ballatana Nauyin wata..?wata zuciyar tace mai ai ita Zatta kula Dakai kaima ai Zaka kula da ita Tunda itace kadai Zuciyarka bata manta da ita ba..! Yana Cikin wannan Tunanin Sagir yace"kamar Tashin kuka fa nake ji aciki..?ko Inteesar ne bata Daina kukan Rabuwa dasu Munarin ba..? Sai alokacin Imran yaji dan Tashin kuka Kofar Bedroom din Dayake Kyautata Zaton tana ciki ya sakama Ido Itama Tana kuka ne..? Shi tasan meya sa yake kuka..?saboda yau zai kwana inda ba Yusuf ba Abba ba Munari wadanan sune Ahalinsa da baida Kamarsu duk Duniya ko"ina Yaje ya dawo Su din kamar wasu Garkuwa ne a garesa yana kukan yau ya bar Gidansu Wata Rayuwa ta kawosa Wata gabar da bai Taba Hasashe ba ko Fatanta nan kusa ba bai Taba ji aransa zai iya aure nan kusa ba sai gashi shigowar Inteesar Rayuwarsa ta sauya komai. Sagir ne ya Katsesa Yana Fadin"Bari na Tafi..Tunda naga anko kuka kai da Amaryan taka kai kuka ita kuka..Kawai ka shiga Ciki ne ku Hada kai kuyi ta Rafzan kuka sai gobe da asuba sai ku Dakata..! Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Tsaye Imran ya Murmusa Lokaci Daya ya saka Kafa ya Daki Kafar Sagir yayi Gaba da Sauri yana Fadin"Bakomai na yafe Maka duk cikin Nishadin Ango ne..! Yafada yana jin wani kewa na kamaaa sa bayaso ya waigo Hawayen Dayake ta Rikewa ya bayyana Imran ya Taka ya Bisa yana Fadin"bazaka Tsaya mu yi Sallama ba..!? Sagir na Ficewa yana Fadin"Wani Sallama.?bayan wacce mukayi..Sai da Safe a gaida Amarya sai an kwana Biyu indawo cin Girkinta ka Fadamata tayi Hakuri haka auran yake kaima Allah ya baka Hakuri Imran Allah ya baku Zaman lafiya..! Yafada Lokaci Daya yana Dauke Hawayen da suka Cikomai ido Imran ya Tsaya Cak yana kallonsa juyowa yayi yana Mikamai key din Motarsa yana Fadin"Sai da safe..! Imran ya saka Hannu ya karba yana Fadin"Zaka Samu abun hawa kuwa..? Sagir ya Gyada kai yana Fadin"Insha Allahu..! Imran yayi gaba yana Fadin"Muje na Taka maka! Yafada yana Tusa Key din Motar Cikin Aljihun yadin Boyel din da Sagir yayi musu wanda suka sanya yau din Yana jin Wani abu Daga Karkashin Ransa Sagir yabiyosa suka jera kowa na Sauke Ajiyar rai Imran acikin Ransa yana Fadin Waye Sagir a wajena..? Sagir Dan"uwa ne kuma Abokina aminina wanda bani da kamarsa acikin Wannan Duniyan ya Zauna Dani Da Dadi ba Dadi duk abunda na Zama yau ko na Taka da Gudummuwarsa Abokina Wanda Samun Irinsa sai an Tona Inda Haka abokai suke kamar Sagir da Mutane da Dadama sun ji Dadin abota bazai Kirasa aboki ba ya Zama Bangaran Dan"uwansa da Kokarinsa akaina bazan Taba mantawa ba. Sagir kuma Tuna Alheran Imran yake a garesa Duk da yana da Murdaddun Halaye ammh shi ya Fi kowa Fahimtarsa yana da kyakyawan Zuciya da Tunani mai kyau mai Kirki ne kuma mai Nagarta ne bai Taba Haduwa da aboki kamarsa ba ya wuce aboki ya wuce amini Shi din Dan"uwane a Wajensa Suna wannan Sake saken suka isa Bakin Titi Cikin Sa"a Sagir ya samu mai adaidaita sai ya juya ya mikama Imran hannu sukayi musabaha yana Fadin"Ka koma ka bar Min kanwata ita kadai..Kuma Mallam ka Sauke wannan Ego din naka da wani Kukan ka agefe in ka koma ka Lallasheta Ta Daina kuka Haka ango kema kowacce Amarya sannan Tell Her sorry Kazanta Tabini Bashi Khalil gabadaya Nauyin ni ya Doramawa kuma yana kaina Zan Biya bashi..! Imran kallonsa kawai yake bai ce komai ba sai da ya gama yace"Shirme..! Yafada yana wani Dakuna Fuska,Sagir ya Daki Kafadarsa yana Fadin"Ko da yake na Tuna..Ranar Lallashin bata zo bane ko Imran..? Yafada cikin Dariya Shima Imran din Dariya yake suka Rumgume juna Kowa na Dauke Hawayensa Imran ya Dago yana Jinjina Hannun Sagir lokaci Daya yana Fadin"Tanque....Nagode kwarai..Bansan da wani baki Zan gode maka ba..! Sagir yace"Ni bana Bukatar Godiyarka mallam abu Daya zakamin..? Imran ya Kallesa yana Fadin'menene shi..? Sagir yace"Ka so kanwata..Ka bata Kulawa kuma don Allah kada ka bari wannan Girman kan naka ya Bata Wahala..! Yafada yana Dunguremai kai Dariya suka saka gabadaya yana Fadin"Insha Allahu zan taimaka muku.! Mai adaidaita ne ya gaji da jira yayi hon kana suka kara Sallama Sagir ya shiga Imram na Dagamai hannu suka Wuce kowa na Dauke kwallarsa. Jiki ba Laka Imran ya Taka ya dawo Gidan sa yana Kallo da nazarin anguwan da kansa ya Rufe get din Kana ya taka zuwa Cikin gidan ya Kulle Kofar Falom a aransa yana Fadib"Lalle na yarda nabar gida..Imran na kulle gida..? Sai da ya Murmusa Har zai shiga Dakinsa ya fasa ya Tunkari Dakin Da Inteesar take ya Tura a Hankali sai ta Bude bai Shiga ba kansa ya Leka ya Hangota Tsakiyar gado Cikin mayafi ta Dungule Tana Ta kuka sai ta Bashi Tsausayi sai ya Bude Kofar gabadaya ya Shigo Kafafunsa suna Taka Italian Cafet din Daya malale Bedroom din Bataji Takun sa ba ballatana Bude Kofarsa,Tadaiji mganar su Shida Sagir a Falo da Farko har Tsorata ma tayi kafin ta gane sune kawai taji Muryansa a saman kanta. "Kinsan bana son yaawan kuka ko..!? Haka ya fada yana Tsaye Gaban gadon hannayensa Zube Cikin Aljihun Wandon Kayan Dake jikinsa ya Zuba Mata Idanuwansa yana kallonta da Duk Zuciyarsa. Dagowa tayi ahankali jajayen Idanuwanta da suka tasa saboda kuka suka Shiga Cikin nasa gabadayansu sai da Zuciyarsu ta amsa Shi yayi Saurin kauda kai yana Fadin"Subahanallah Maryam kuka haka..? Mamakin yadda ya Kira sunanta taji yasa Hawayenta suka karo ta Runtse ido kafin ta Bude akansa Karisowa yayi gabanta yana Fadin"Look nifa kinga ban iya Lallashi ba..Kuma kowa yace na Kula Dake ban iya da wannan Shagwabar taki Intee kiyima Girman Allah ki Daina kukan nan kin ji ko..? Kallonsa Take yi Cikin so da kaunarsa Mganarsa tana kara sakata Dariya Sai dai bata Daran ba Idanuwansa ta kallah Taga sun sauya shima kamar yayi kuka yasa tace"Kai ma kayi kuka ne..? Tafada Tana lamgwabe mai kai Cikin Dabi"arta Daya zame mata jiki Saurin Kauda kai yayi yana Fadin"Kuka..! Ni ban yi kuka ba..! Yafada Lokaci Daya yana Dakuna Fuska Mirmishi Tayi tana Hawaye tace"Nasani..Kayi kukan Rabuwa da Abba da ya yusuf da Munari ko..? Nafada tana kallonsa Shima kallonta yake da Dukkan Zuciyarsa Kai ya girgizamata yana Fadin"Anni..Anni na Tuna..! Inteesar taji kaunarsa ya kara kamata da Tsausayinsa Bataasan Sadda tace"Allah ya jikanta da gafara..da Sauran duka musulmai nima ina jin Zafin Dakake ji Ya Imran..! Nima ina ta kuka da zan Rabu da Umma da Daddy na da Ya basheer..Ina ta kuka..,! Ta fada Lokaci Daya Tana Fashewa da kuka Imran ya Dafe kai yarasa Mafita ganin Tana ta kuka yasa ya Zauna gefenta batare da Tunanin komai ba ya jata Jikinsa ya Rumgumeta kamkam yana Fadin"Intee plz..Ki bar wannan kukan ni ban iya Lallashi ba..Bansan ta ina zan fara ba..! Ya Fada Muryansa na karyewa kamar Zai yi kuka shi ya karama Inteesar Rauni Ta kamkamesa shima suka Hade Waje Daya suna Jin Bugun Zyciyar Juna Imran yana Shakan kamshinta yana jinsa kamar yana Wata Duniya kanta yake ta Shafawa alamun Lallashi. Yana Fadin"kiyi Shuru..! Dole tayi Shuru Dolenta ta karbi Wannan Lallashin da Imran ya Tattaro Duka Karfin Halinsa yanayi mata Sai daga yaga Tayi shuru kana ya Rabata da Jikinsa yana kallon Fuskarta yace"Kin yi sallah..? Kai ta girgizamai kafin tace"La"asar kadai nayi..Ban yi mangariba da isha"i ba..! Tafada Tana kallonsa Shima kallomta yake yi kafin yace"Ni kuma nayi mangariba Tare da su Abba Isha"i ne ban yi ba..bari najr nayi wannka In Dauro alwala kema ki tashi kiyi wanka kiyi alwala kiyi mangariba sai nazo mu yi jam"i muyi Sallar Isha"i Tare ko baki so..? Inteesar tace"Ina so mana..Ai bamu da kowa anan sai mu kadai ko.? Mirmishi yayi yana Lakuce mata Hanci bai ce komai ba ya Mike ya Fice ta Bisa da kallon Kauna yana Fita ta Mike Daman Less din Jikinta ya Dameta Tiolet ta Fada daman Tun kafin Fitan su Anty Safiya sukace tayi wanka Kukan data Fara ne ya mantar da ita komai. Tayo wanka tazo ta Shafa lotion da Turare,kayan barcin ta acikin na Gida ta saka wata riga doguwa mai Taushi Saboda kayan suna cikin akwati kuma bazata iya Bude su ba Allah yasa Munari Duk ta Hado mata kayanta Taji Dadin ganin Harda Littafan Karatunta gobe karfe 8:00am na Safe suke da Jarabawa ga Gajiyan Biki Da Zirga Zirga bata gama Sakinta ba Ta idar da Sallar mangariban kenan sai ga shi ya shigo Cikin Jallabiya Sabuwa mai Ruwan Madara Ruwa na Diga ajikinsa Mikewa tayi Hijabi ne ajikinta suna kallon junansu kamar wasu masu warkewar makanta. Ganin Ruwa na Diga Daga wuyansa ne Tace"Ya Imu baka Shafa mai bane..? Yana yin gaba Wajen Darduman yace"Ni bai Dameni ba..Taho muyi Sallar..! Yana gaba tana bayansa ya Tada Salla Sai da sukayi isha"in suka idar kana Sukayi Sallar Raka"a Hudu na Godiya ga Allah bayan sun Idar Imran ya Daga Hannu yayi ta addu"a Duka Rabin addu"ansa na Allah ya Jikansu Anni ne har Sai da ya kusa kara saka Inteeesar kuka,Sannan ya Rufe da addu"an zaman lafiya a tsakaninsu. Sanda suka Shafa addu"an ya juyo yana kallonta Wayarsa yadan Danna yana so yaga Lokaci 10 ta wuce na Dare yana kallonta yace"Kina jin yunwa..? Kai ta girgirzamai alamun A"a ajiyar rai ya sauke yana fadin"Kinsan me..?ni fa imran na Dabam ne shiyasa ko Irin kazan nan da ake siyoma amare bansani ba Sagir ne ya san irin abubuwanan ni Shirme na Daukesu yace a gayamiki zai kawo miki..! Kanta na kasa tace"Bakomai..Ni na yafe..! Imran kallonta kawai yake yi yana jin wani Salama kafin yace"Gobe zaku Fara Jarabawa ko..? Ta gyadamai kai kafin ya cigaba da Fadin"Nima gobe zani wajen aiki Karfe nawa ne sai na Fara ijiyeki kafin na wuce..! Tana kallonsa tace"8:00am na Safe ne..! Kansa ya gyada kafin ya Mike yana Fadin"Is ok..Ki kwanta Kiyi Barci and Don"t Stress ur self kice zaki karatu kin ji ko..?nasan ai baki da wasa Insha Allahu komai zai zo da sauki..! Gyadamai kai Tayi tana Mikewa Idonta yayi Raurai ita kadai Zata kwana.!? Bata samu bakin mgana ba Har ya Fice Lokaci Daya yana Fadin"Kiyi addu"a...! Daga haka ya jawomata Kofar ya Nufi Dakinsa yana Sauke Numfashi. Shifa bai iya kwana da Mutum a Daki ba Ko Namji ne ballatana Mace baisan ta ina zai fara ba..! Bama haka ba ai in taga yanayin kwanciyarsa sai ta Rainasa. Inteesar kuwa haka ta kwanta a Darare tana jin Tsoro ba batajin Motsin kowa ko agida Watarana Ita da Umma Take kwana,yau dai taji kewa sosai haka ta Dungule ita kadai Tana Jin Tsoro gata a sabon Wajen da bata Saba ba ita kadai Saboda gajiyan Biki Da suka sha yasa Barci ya kwasheta bata sani ba barci mai nauyi kamar yadda ya sace Imran yana Tsaka da Duba wani aikin da zai bama Manager Mr Sulaiman gobe. *Shakira..* 3/28/22, 18:35 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�25* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Barci ne suka yi na gajiya Wanda yasa suka makara basu sani ba Kuma Dayake Kusa da gidan ba Masallaci Sai Dagachan nesa ne,Shiyasa har akayi Sallar asuba aka idar Imran bai ji ballatana Inteesar Datake baje Tana Barcinta Bilhakki da gaskiya.. Allah ne ya Tada Imran da Misalin Karfe 6:30am na Safe Koda ya Farka ya Duba agogon Wayarsa sai ya Zaro ido ya Mike Zaune da Sauri Lokaci Daya yana Dirowa Daga kan gadon laptop dinsa ya Tattara wacce barci ya Kwasheshi yana aiki akanta ya Fada Tiolet ya makara shiyasa bai Fara yin wanka ba ya Dauro alwala ya Fito Tunani yake yi ko Inteesar ta tashi..? Ko Itama bata tashi ba..! Agurguje ya Saka Jallabiya ya Fita Zuwa Dakin Inteesar Knoking ya fara yi mata yana Kiran sunanta a Hankali bai ji ta amsa ba yasa ya Tura Kofar ya Shiga.. Yanayin Kwanciyarta Kadai ya tabbatar mai da itama Barcin Gajiya n e ajikinta yadda ta Karkace kai gefe ko Filo bata Nema ba ko kuma Zamewa yayi bai sani ba. Kusa da ita ya isa yana Kokarin Tashinta din Gefen katifar yake Duka Kadan kadan yana kiran sunanta Kamar a mafarki haka taji Kiran nata Sama sama yasa ta Bude Idanuwanta Cike da Barci akansa Da Sauri yace Mata"Ki tashi mun makara fa..! Mikewa Tayi Zaune a Hankali Tana gyara Wuyan Rigarta Daya Zame Imran kansa ya kauda yana Kokarin Daidaita Natsuwarsa baya so idonsa ya kara kaiwa kanta Zata Sa ya rasa Duka Natsuwarsa da Jarumtarsa. Da Sauri yace mata"Ki tashi kiyo alwala muyi sallah ina Jiran ki..! Cikin Kasala da alamun Barcin a Idonta ta mike Tana Fadin"Karfe nawa ne Ya Imu..?naga kamar gari ya waye..? Tafada Tana kallonsa shi kuma yana Kokarin Daidaita Darduma bai kalleta ba yace"zaki wuce kiyo alwala ne ko Zaki Tsaya Tambayan Lokaci..? Lokaci Daya yana Sakarmata Manyan Idanuwansa,Tura baki Tayi Lokaci Daya Tana yin mika da Sauri ya kalli Gabansa yana Kokarin gyara Tsayuwarsa ganin yadda ta bangaro Kirjinta Sama in ya cigaba da kallonta Wlh alwalarsa sai ta samu Rauni Cikin Dakewarsa yace"Wlh zan yi Sallata in yaso sai kiyi Taki..Bana son Shanshancin banza..! Ya karishe Fada yana Hade rai jin Haka yasa ta Zagayasa ta Shige Tiolet ya Bita da kallo ta kasan ido Gwara ya Rika mata jan ido kada ta Rainasa Daman ta Fara Rainansa. Agurguje tayo alwala ta Fito Hijabinta ta Sanya Dake kan gado kafarta ya gani a waje yasa yace"Ke ahaka zaki Sallar..? Kallon kanta Tayi kafin tace"Rigar fa Doguwa ce Ya Imu..! Tafada Cikin Shagwaba Dauke kai yayi yana Fadin"U are not Serious..Oya Dauko Wani Zani ki Rufe wannan Siraran Kafafuwan naki kafin Ranki ya baci..! Yafada Cikin Kaushinsa Kamar ko yaushe kallonsa Tayi sai ta kama kanta Kada tasha mari ganin ya koma mata Imu dinsa Sak. Wardrope din Dakin Ta Bude ta Dauki Zanin Wani less dinta ta saka tazo Ta Bisa suka yi Sallar suna Idarwa ya Mike da Hanzari yana wani cin mgani ya Fice yana Cemata"Make sure kin Shirya da wuri..Bana son Jira..In kika batamin Lokacin kin san Sauran..Ni ba irin Ya Yusuf bane yana Jiranku kamar wani Direbanku..! Ai Tana jin haka ta Mike ta Fada Tiolet Tayo wanka Sai da ta Fito ta Duba agogon Wayarta da Munari ta bata Jiya da Zasu tafi 7 ma Tayi a Gaggauce ta Shirya Cikinta ke kugin Yunwa Daman Tun Fara Shagalin nan bata wani ci abincin Kirki ba. Riga da Sikat ta saka na atamfa Cikin Kayanta ne na Gida da Munari ta Hado mata,Kayan sun kamata sun mata Das. falo ta Fito sai alokacin ta Samu Damar karema Gidan kallo Tana kara Jinjina ma Baffa Kabiru yayi kokari Sosai Kitchen ta Fada Domin samo musu abunda zasu karya Tayi mamakin ganin Harda Cefene sai dai ba Lokacin da Zata Sarrafa wani abu Gas ta kunna ta samu karamar Tukunya ta Dora Ruwan Zafi Tana kara Duba Kitchen din Tana Godema Umma da Daddy dinta da Kokarinsu akanta. Ta Duba Taga Harda da kayan Tea,Mirmishi Tayi Munari ta Fadamata aikin Ya Yusuf ne ai kuwa yayi Taimako don inta Ya Imu ne yau da yunwa zasu Fita. Ruwan Zafi ta Juye acikin Flaks ta Dauko Mug din Kofuna Guda Biyu ta Wanke ta Zubo Ruwan Zafi ta Kwaso kayan Tea din zuwa Falo Saman Dan Madaidaicin Dining din Dake yamma da Falon Komawa Tayi ta Bude Store ta samu Karamin Filte ta Dibo Snak din da Umma ta saka akayi mata su Donot su Cincin su Cake da sauransu ta debo su kadan bada yawa ba Tana Fitowa Imran na Fitowa Daga Dakinsa Lokaci Daya yana gyara Zaman Net Tie din Dake Wuyansa Shigar Suit Green yayi yau Dayan Hannunsa na Dauke da Jakar Briefcase dinsa da Key din Motarsa. Ido suka Hada Dashi Shagala Tayi da kallonsa Shi kuma bai bari ta gane Kallinta na kayatar dashi ba Sai ya Kauda kai Daidai Lokacin Data kariso gaban Dining din Tana Fadin"Gud Mrning..! Yana Duba agogon Radon Dake Hannunsa yace"Mrning..Kin gama Shiryawa..? Kai ta gyada Tana Fadin"Yes..Ammh ga Tea bazamu sha kafin mu Fita ba..? Yamutsa Fuska yayi kafin yace wani abu da Sauri Tace"Nidai plz ka bari nasha Kada naje Exams ina Zare idon Yunwa..! Dariya taso kamasa sai ya Dake ganin yadda Tayi mgana kai ya gyada mata yana Fadin"Ok.5Mn..! Da Sauri Taja Kujeran ta Zauna Tana Fadin"Bazan ma kai ba..Ya Imu kazo sha faa ba wani abu bane mai Nauyi ba..! Bazai iya mata gaddama ba yasa ya ijiye kayan Hannunta ya Isa Kusa da ita ita tajamai kujeran Dining din ya Zauna Ta Turamai Mug din gabansa da Flaks Zata Zubamai ya Dakatar da ita yana Fadin"Barshi sha..Kada ki batamin Lokaci..! Yar Dariya Tayi ta sakarmai ya Tsiyaya Kadan ya Zuba Madara da Bonvita da Siga kadan ya Fara kurba Filet din gabanta ta Turamai Tana Fadin"Madadin Bread..! Kallonsa yayi kafin ya Dgo yana Fadin"what is dis..? Inteesar ta waro ido Tana Fadin"Baka sansu ba..?tab ka bar Dadi..Ci wannan kaji..! Ta Dauko Cake ta Mikamai Bazai iya Ture Mganar Inteesar ba yasa ya Karba ya Gutsira Da Sauri Tace"Ya kaji..?Cake ne ana shansa da Tea..! Bai ce mata komai ba,sai da yakara Cake din Guda Biyu ya Hada da Tea din kadan ya Mike Duk Saurin Inteesar yana kallonta Tana Turawa cikin Bakin ganin ya Mike Dariya Ta basa yasa yace"Kici a Hankali kada ki tura da yawa kije kina Amai kuma..Ba Ruwana..! Yafada yana Wucewa Jakarsa ya Dauka yana Fadin"ki Tafi dashi ma in kin Fito Exams din sai kici..! Mikewa Tayi Tana Fadin"Am ok..Bari na Dauko mayafina da Jaka da wayata..! Bai mata mgana ba ta kwashi Gudu Zuwa Cikin Daki da kallo ya Bita Kafin ya Girgiza kai Bata Dade ba sai gata ta Fito da bakin Mayafi da bakar Jakar sai Takalminta mai Tudu Duk Cikin kayanta na Gida ne. Kallon Sama da kasa yayi mata Lokacin Data Tsaya agabansa Tana Fadin"Am Ready..! Hararanta yayi Ransa na Bacin yadda Zataje Cikin maza da Gyale kuma Sikat din ya kamata Cikin Dakewarsa yace"ba hijabi ne sai wannan Mayafin..? Inteesar tace"Wlh babu..Duka suna Kaduna Guda biyu ne kuma suna Cikin kayama na gidan mama Duka Goggo Maimunatu Gyale ta sakamin..! Tafada Cikin Muryan Shagwabar da ya Zame mata jiki. Karamin Tsaki yaja Kafin yace"Sako sa saman kanki..Da kika saka sa a Kafada kin manta ke da da yanzu ba Daya bane..? Yafada yana Sakarmata ido Zatayi mgana yace"Bana son gaddama Do as I say..! Bata da yadda Zatayi ta Warware ta Saka saman kai Allah yasa Babba ne,Makullaye ya mika mata ta saka Hannu ta karba ya Fice yana Fadin"Key din duka Doors din Gidanan ne.in kin dawo ki Rika amfani Dashi Wajen Bude get din zuwa Kofar Cikin Falo..! Da Toh ta Bisa kafin ta Bi bayansa Shi ya Rufe Kofar Falon Tana gani kana suka Taka,wajen Mota ita yace ta shiga Shi kuma ya isa ya Bude Get din Kana yazo ya shiga Motar sai da ya Fito kana ya kara Fitowa Daga Motan ya Kulle Get din da makullin Dake Hannunsa Tunda guda Biyu ne Daya ya bata ne a Hannunta Saboda ba Lokaci Daya Zasu Dinga Dawowa ba. Sun Fara Tafiya ya Dauki Hanyar Buk Ba wanda ya kara mgana Wayarta Tana Cikin Jaka Munari nata Kiranta bataji ba suna gabda isa ya kalleta yana Fadin"Ina za"a samu Hijabai..? Yafada Lokaci Daya Hankalinsa na Wajen Tuki Inteesar kai Tsaye tace"Kasuwa mana..! Acikin Ransa ya maimata kasuwa Tabdijam to ina ma yasan kasuwan..? Ganin bai kara cemata komai ba yasa itama bata kara mgana ba har suka Shigo Cikin makaranta Har Kofar Department dinsu ya kawota Ta kallesa Tana Fadin"Daman kasan Department din mu Ya Imu..? Bai kalleta ba yace"kina so na makara ne..! Da Sauri ta Bude Motar tana Fadin"Allah ya Kiyaye ya bada Sa"a..! A saman lebe ya amsa da Ameen yana Fadin"Good luck..! Ta Kada mai kai Har zata Rufomai Motar ta Tuna da Sauri ta Dawo Ta Zauna Tana Fadin"Ya Imu plz in mun gama Exam din yau nabi Munari naje Gidan Abba..?kaga duk yau baki zasu koma muyi sallama..! Kallonta yake yi kawai bai ce komai ba Ganin haka yasa ta marairaice Tana Fadin"Plz Ya imu don"t say No..Please..! Tafada Cikin Shagwabarta Baisan Sadda yace"Ok..! Da Sauri ta Yada kanta Saman kafadansa Cikin Murna Tana Fadin"Tanque..So much..In ka Tashi Daga Wajen aiki sai ka Biyo mu koma Gidanmu ko..! Kamar wani Gaula haka ya gyada mata kai Hannunsa Guda Dayan Dake saman Cinyarsa ta kama ta Sumbata Tana Fadin"Ya Imu na..See u later..! Tafada Lokaci Daya tana Ficewa Daga Motar ta Rufemai ta Dago Tana Dagamai Hannu Baki Sake yake kallonta Gabadaya ta gama Sakamai kasala Dakyar ya Daga mata Hannu Lokaci Daya ya Tada Motar yayi kwana ya Fice Daga Wajen. Sai da ya Dauki Hanyar Bankinsu ne ya Tuna bai bata kudin Mota ba..?kansa ya shafa yana Fadin"Su Imran miji manya..?miji ya bar Matarsa ba kudin Mota..! Yafada yana Dariya to me ya sani na Daukan Nauyi shifa Nauyinsa kansa ba Duka yake Dauka ba Har yakai Cikon Bankinsu yana Dariyan kansa . Intee kuma Tana waigen Neman Munari bata ganta ba ta karisa Cikin Department dinsu ta Fara gaisawa da Course mate dinsu Da suke ta mata Fatan Alheri Wayarta Take Kokarin Cirowa taji an Riketa ta baya tana Juyawa Taga Munari suka Saka Ihu atare suka Rumgume juna. Kafin Munari taja Hannunta su samu Waje su zauna Tunda da Sauran Lokaci.. Nan fa Hira ta Tsinke Munari sai Tsiya Take mata tana kallonta Tana Fadin"Uhm..Amarsu ta angonta..ai na ganku..Aure mai Daraja wai yau Ya Imu ne da kawoki makaranta..! Duka Inteesar ta Dagaamata suna Dariya Munari na Cemata ta Kira wayarta tace bata gani ba yana Jaka Munari sai Faman kallon Inteesar Take Tana Dariya Lokaci Daya Tace"Allah kadai yasan irin Romin amarcin da Ya Imu ya kwasa yau ya kawoki makaranta..Muma mun kusa shiga wannan karnin domin Khalil yace yana komawa zai gabatar da mganarmu..! Inteesar na Dariya tace"Munari ana son Aure..Wai daman yace yana sonki ne..?kun dace fa..! Tafada Bayan ta boyema Munari Wani abu bai Faru Tsakaninta da Imu ba. Munari tace"lalle Tun yaushe...Sagir ma ya kafa Gwannatinsa Wajen Hafsah..! Inteesar ta Zaro ido Tana Fadin"Ki bari don Allah..! Munari tace"Ki zauna mima mun kusa Shiga Daga Ciki yarinya..! Dariya suka saka Inteesar ta nuna jin Dadinta sosai aman take Fadama Munari in sun gama jarabawar yau Tare zasu tafi gida ya Imu ya barta Munari tace aiko kin ji Dadi kya yi Sallama da yan"uwa. Tsaida Hiran sukayi Suka Fara Bitan Jarabawar da zasu yau duk da basu da Mtsala suna Karatin Jarabawa tun Lokacinta batayi ba Karfe 8am na Safe Daidai suka Shiga Paper 1 sai 11am suka Fito basu Zauna wani hira ba suka koma Wacce zasu shiga karfe 12am na Rana Har zuwa Lokacin. Karfe 2pm na Rana suka Fito Shikenan sai kuma Gobe Suke da Guda Daya Daganan Inteesar da Munari suka samu adaidaita zuwa Gidan Inteesar sai Murna take kamar Wacce ta Shekara Kamar ba Jiya bane,Tabar gidan. Koda suka isa Ya Basheer da Anty Hauwa da Anty Uwani da Maman Nasara da ita kanta Nasara sun kusa isa kaduna Harda Umaima Data Bisu Zata kwana anan Kaduna Ya Basheer zai siyan mata Tiket Tabi Jirgin kasa zuwa Abuja. Inteesar bataji Dadi ba Domin ai tasan Daman bazai Tsaya ba Ya Basheer baya son Tafiyar Dare,Inna Maimunatu ma Ta mika Hanya ita dasu Zainab,Inna Bintalo ma ta wuce ita sai ta Biya wajen Daada Dukku. Sa"id ne kadai ya Rage basu Tafi ba sai Sadam su yan Gida ne. Kowa mamaki Dayaga Inteesar Munari ce ke azarbabin cewa Ya Imu yace ta Biyo ta nan in ya baro Wajen aiki zai Biyo ya Dauketa Shiyasa Abba yayi Shuru Sai Gabda La"asar su Sa"id suka Tafi da Hafsah bayan sun gama Sallama da su Munari da suka Hada kai suna ta ma Inteesar Tsiya Harda Tasleem da itana Sallar La"asar kadai sukayi Ita tatafi Gida,Bayan La"asar kuma Ya Sadam da Tawagar Matarsa da ya"yansa suka Wuce gida,Gida ya Rage Daga Anty Safiya sai Abba Dashi ma bai jima da dawowa Daga Office ba. Ya Yusuf bai je aiki ba Ranar yana Gida Sai da suka ci Abinci suka koshi kana Inteesar ta Tambayi Abba zuwa Gidan Mama ta kwaso sauran kayanta ya barta Munari ta Rakata Mama Taji Dadi Itama Gajiyan Biki bai Saketa ba Ta kara yima Inteesar Nasiha sosai kafin ta Dauki Sauran kayanta Saura kuma Tace Mama ta bada su kawai basu wani jima ba Saboda Abba yace Kada su zauna suka Dawo gida. Gyaran Gidan suka Taya Anty Safiya Kafin su Shiga Kitchen suka Dora Girki,Farar shinkafa da Miya Sukayi da Nama Sai mangariba suka gama bayan sun Jera komai Saman Dining kowa yaje yin Sallah kafin su Fito su Abba suka shigo Harda Imran Daya Dawo da Sagir a masallaci suka Hadu Nishadi yake ji kamar ya Shekara baya Gidan.. Ranar Gabadaya suka Hadu Saman Dining Harda Imran da Sagir sukaci Abinci Cikin Farinciki,Bayan sun gama Abba bai yi kasa a gwiwa ba ga kara Yi Musu Nasiha sosai mai Shiga Jiki basu sukabar Gidan ba sai Wajen 9pm bayan Hankaluna sun kwanta Baki sun koma Gidajensu Lafiya.. Suna komawa Gida sun gaji sai Barci Kowa ya Nemi makwancinsa. ******* *After 10 days* Haka Rayuwar Auran Imu da Inteesar ya Cigaba da Gudana Kullum da Safe in Tare zasu fita Zata Dafa musu Ruwan Zafi su sha Tea kafin su Fita in kuma Batare zasu fita bata da Jarabawa da Safe shi kadai yake Fita Inteesar na kwance ma sai ya tasheta Wani Lokacin Har Yau da suke kwana Goma da aure Inteesar bata Fara Girki ba sai dai Tasha Tea taci kayan Snak,in Tana Gida domin in Ta shiga makaranta Munari take bi zuwa Gidan Chan take Wuni sai yammah Tayi in Imran ya Dawo shima nan yake Sauka sai Dare suke Dawowa Gida da sun Dawo sai barci kuma Har alokacin kowa Dakinsa yake kwana babu abunda ya Sauya. In basu Fita tare ba Yana bar mata Kudi in Lokaci yayi sai ta Kulle Gidan ta Fita ta Hau adaidaita da Farko Har Biyama Munari Take yi Abba ya Hana yace Kada ya kara gani Imran bai ma Sani ba yana Wajem aikinsa. Shi cin Abinci bai Damesa ba Barsa da Shan Tea da kayan Marmari Abinci sai yaga Dama yake ci shiyasa har yau bai Damu da rashin Fara Girkin Inteesar baisama san wai Ta Fara Girkin ba Ballatana yayi mata mgana Shi yana ganin akwai komai in Tana jin yunwa tasan yadda Zatayi Shiyasa bai Taba Damuwa da Rashin Fara Girkinta ba. Kuma ba wanda ya kawo musu Ziyara ballatana yaga aikin da suke yi Daga Imran din Har Intee sai addu"a bamai Sauke Hakkin Dake kansa. Ita bata komai sai Kwanciya in bataje makaranta sai Ciye ciye kayan snka da Shan Tea sai Tayi karatu in Tagaji Ta Danna Waya kayan kallonsu ba a Hada ba gogan Kallo bai Damesa ba...shidai barsa in ya Dawo aiki Tayi mai Sannu da zuwa ya amsa ya Shiga yayi wanka ya Sauya kaya zai Fito Falo ya zauna yana aiki Bisa Laptop aiki Dayasa yake sa ka Inteesar Wanke kayan Marmarin Dayakan Shigo dasu ta sakomai afilet da Fork karama yana aiki yana cin abunsa Hankalinsa kwance ita kuma Tana Gefe Tana Danna Waya tana Hadawa da Ciye Ciyenta ko ajikinta In Tagaji Tamai Sallama Ta Kwashi littafanta Zuwa Ciki,ko kuma Tayi waya dasu Umma wannan Kullum ta Dinga Kira kenan tana Musu Shagwaban sun ki zuwa ita da Daddy Umma tace Gotai Gotai da ita agidan yarta Daddy kuma yace Intees tasha Kuruminta in zai zo Tare zasu zo,Umma fa har hana Daddy take kiran Inteeear ammh shi ba Ruwansa Wani Lokacin suna Waje Daya da Imran in yace ina Mijinki sai ta mikamai su gaisa da Daddy Har su Taba Hira Umma sai dai ta Rike baki Tana kallon Wannan aikin. Shidai Imran tunda dai Inteesar bata Rainasa ba Alhamdullilah..Kowa yayi abunda yaga Dama ba Takura. Shiyasa bai Taba kallon hakan da sunan Wani abu ba yana ganin hakan Shine Daidai. Inteesar bata Taba Zaton Imran bai daina shan Taba ba,Sai ranar Dataga yana shanta bayan ya Dawo yana Zaune yana aiki Bisa laptop dinsa Shi yama manta da ita Kakarinta yaji kawai ya Juyo yana kallonta yaga Tana Toshe Hanci Gira ya Dage mata yana Fadin"Ke nama manta Dake fa..a falon nan..Bari na bari sai na koma Ciki na kunna..,! Yafada yana Kasheta saman Farantin Daya gama shan kayan Marmari.. Inteesar tace"nifa na Dauka ka Daina sha Kwatakwata Har ina Celerabration..! Imran sai da yayi Dariya kafin yace"Su Celebration Manya.Haka Sagir yace min jiya daya ga ina sha..Daman ai bamu yi Dake Zan Daina Shafa ba Kuma ita shanta ai Lokaci ne kuma yanzu Lokacina Duka na gwannati ne Kalilan ne nawa.. Bata Fuska Tayi bata samu Damar Mgana ba ya Katseta da Fadin"Na Rage sha sosai..Fiye da baya..Kuma in kinsan kina jin Amai u better go to ur Room..Allah in ki kayi min amai anan Wajen kinsan Sauran..! Tura baki Tayi batayi mgana ba Shi kuma sai ya kauda kai yana Danne Dariyansa yarinyar nan in ya biyemata Tabaranta Zata Rika yimai kala kala. Ranar da suka Cika Sati Biyu da Tarewa Baffa Kabiru yazo Kano, Saboda Imran da Inteesar bai Kwana ba Aranar ya Juya bayan ya Taka har Gidan ya Cikasu da Tarin Nasihu da Fatan Alheri Imran bai Taba jin Nadamar abunda ya aikata ba Sai Ranar yaji kunya Baffa Kabiru Rana ta Farko ta kamasa anya ya Chanchanci Wannan Kyautatawar ga Baffa Kabiru..?shida ya Sakarmai ya..? Bai Rikeka ba sai m karin kyautatawa Daya Biyo ba Imran yaji kunya saai Dai Ya yi Fuska kamar babu Abunda ya Faru Tare da Abba suka zo suka kara ganin Waje suka saka albarka. Baffa Kabiru duk ya Rame yayi wani Iri kawai Karfin Hali ke tafe Dashi,Ga Damuwar Dayake Ciki ba Asma"u Tare dshi,Ga Khamis ba"a Samun Wayaarsa kwata kwata Ga Sajida Tana makaranta cikin Damuwa duk da bata Fito ta Fadamai ba shi ya sani wannan Raunin nata bamai Cike mata shi Sai Imran shi kuma ya Riga Yayi mata Nisa har Abada. Wadandan Damuwan suna Ransa Kawai Karfin Hali ne da Tsabar Jaruma ke tafe Dashi yake kuma Tsaye da Kafafunsa alkawari ya Daukar ma Kansa bazai nemi Asma"u ba sai in itace ta Nemesa ba shima din Sai ya yarda da Nadamarta,ko yace bai azabtu da rashinta ba yayi karya Asma"u ai Soyayyah Ta Hadasu ba Kiyayyah ba kuma basu Taba Samun Irin wannan Babban Mtsalan ba sai wannan karom ya sani kamar yadda yake Cikin Wani Hali itama Tana Cikinsa Har kuma zuwa Lokacin bai ji Daga Justice Tafida ba Daman yasan bazai Nemesa ba Ko shi ya Nemess zai ce abunda suka yanke ma kansu Daidai ne shi bazai ce komai ba Tunda Ra"ayinsa ne. Daga shi sai Umaima sai yan aiki suke Rayuwa Sajida basu gama Exam ba ammh yace mata da Zarar sun gama Ta dawo gida kada ma Tace Zata Zauna a makaranta ita kuma taso ta Cigaba da Zamanta a makaranta Tana Jinyar kanta ba wanda yasan Halin Datake Ciki.suna Waya da Mami Lokaci Bayan Lokaci itama Hawan ajini Duk ya Fadar da ita Karfin Halinta kawai an fa ta Fara Sarewa an Kwarari Wata na Biyu bataji Daga Kabiru ba ta Fara Saki ta Fara Zama Tana yima kanta Tunanin Ina Mafita.?shin ta ina ta Kuskure..? Shin Tana da Son kai kamar yadda aka Fada..?tana so ta Fahimci kanta da kanta kafin ta yanke ma kanta Hakunci. Washegarin Ranar da Baffa Kabiru yazo Ranar Monday Daga makaranta Munari ta matsama Inteesar suka Dawo Gidanta Munari ta yi mamaki Data shiga Kitchen din Inteesar ta Bude Fridge Taga Nama da Kifi har sun kankare ga abubuwan amfani nan duk bata taba amfani Dashi ba ai Batama gama mamaki ba sai da inteesar tace mata bata Fara aiki ba Daga dafa Tea shikenan take yi Munari ta Rike baki Tana Fadin"Baki Fara Girki ba..? Inteesar ta gyadamata kai Tana Fadin"Eh ya imu bai ce na Fara ba kinsan baya cin abinci..Ni kuma kinga Gida muke wuni..,! Munari ta Girgizakai Tana Fadin"Wlh sai yau na kara yarda kina son ya Imu ammh bakisan Halinsa ba..Shine zai ce ki Fara girki sannan ki Fara..? Inteesar ta daga mata Kai Tana Fadin"Eh mana kawai bai ba in na Fara ina asara ga bansan kowa anguwan ba Shuru ko almajirai babu kuma Kinsan ba kyau Zubar da abinci..! Munari ta Saki baki kawai kafin Tace"Uhm..Baki san Waye ya Imu ba..Zaki Shekara shekaruma ahaka Indai shi kike jira yace ki Fara Girki..?shi ina Ruwansa zai ma Taba Tunanin ya kamata ki Faran ne..! Inteesar tace"Kingane..Allah kinsan bai cika Damuwa da abinci ba im na Dafa na Dinga asaransa kenan..! Munari bata kara mgana ba Indomie ta Dafa da Hanta taci Ta hada da Lemo Bata yarda Takai Dare ba sanin Halin Imu Wlh bazai maidata Gida ba Dama Ya Yusuf ne zai ce kafarta Data kawota Ta maidata.. Munari na komawa Gida ta Kira Umma ta Fadamata Komai na Halin da Inter ke ciki Domin tasan Umma ce kadai Zata iya mata mgana taji. Umma ta saka Salati ta Dire Wato Dai Inteesar ta auri miji Daidai da ita in Iskancin ne ya fita zaune kawai suke bamai ma wani Fada. Ai bata bari Daddy yaji ba ta Kira Inteesar aranar ta mata Fada kaca Kaca Inteesar na Tura baki Tace ma Umma"Shifa Umma baya cin abinci Fruit yake sha kullum sai Tea kuma ai ina Dafamana..kuma bai ce min na Fara Girki ba ni..! Umma kamar Inteesar na Kusa da ita ta kamata da Duka Zaginta Tayi kamar Tana ganinta Kafin tace"Ji Sakarci Jira Kike sai yace ki Fara..?ai kinsan Wanda kika aura Shine kike Zaune ya Kiraki yace ki Fara Girki kin Taba Dafamai kika mai Tayi yace A"a..!? Ta girgizamata kai Tana Turl Baki Umma Tace"To banda Wawanci wai kina Zaune bakya girki ko to me kuke ci ko nace ke me kike ci..,? Inteesar tace"Munari na ke bi zuwa Gida in mukaje Exams..Da Daddare ya Imu yaje ya Daukoni..! Umma ta kara Saka Salati kafin ta koma Lallashi da ban baki Tana Fadin"Ki Daina zama haka Kin ji Intee yanzu kin Girma Nauyin Ciyar da Mijinki yana kanki..Duk da bayason cin Abinci in kika Girka kika Matsamai ko Saboda ke ai zai ci ko..? Inteesar tace"Eh zai ci Umma in yaga Dama..! Umma tace"Ki Fara Girkin ki bakomai Watarana sai Labari ai kina da komai na Cefane ko..!? Inteesar tace akwai komai Ya Yusuf ya cika mata Fridge da Cefane,Umma aranta tace shima yasan halin kaninsa Inteesar taji Fadan Umma ta kuma Kiraa Mama tace Mata tazo ta kara jan kunnen Inteesar to bata zo ba ammh Ta mata Waya itama ta Kara mata Fada tace Insha Allahu Zata gyara sai dai ta Kira Munari ta Zageta ta ce mata Munafuka Tunda tasan ita ta Hadata da Umma Munari dai tana ta Dariya. Washegari ta Fara Girki Ranar basu da Exams ana Saka musu Interval Sosai,Sai da Imran ya Dawo Wajen aiki ya iske tayi abinci jalop din Shinkafa da Kifi. Mamaki ya kamashi yace waya sata girki Tana Shagwaba tace ba Umma bace ta Kirata tana mata Fadan wai bata fara Girki ba kuma ai shine bai ce ta Fara ba..! Dariya yasha sosai ranar agaban Intee Wai Daman shi Take jira..!ai in ta barsa shifa ya manta da ma wani Girki bai kuma Taba Tunanin yace ta Fara ba sai da yaji Dadin mganar Umma ko Bakomai ai ita Macece Ranar yaci kadan dai Tunda ta Girka sai da yace ta Rika Girkawa Kadan iya Cikinta Tunda ba Lalle bane ya Rika ci kullum Haka kuwa takeyi kadan Take Dafawa shima Ranar Datake gida in kuma ta shiga makaranta Munari take bi Gida Bata Girki Ranar Umma da kanta ta Kira Abba tace mai ya Faffataki Imran da Inteeear su daina Taremai a Gida ta kawomai Misalai Rashin Dacewar haka Harda na Rashin Girkinta tace Koda Imran yazo shi Namiji ne ita fa Mace ce kuma matarsa Saboda Haka Ta Zauna a Dakin Mijinta wannan Gantalin ta Daina shi Abba kuma ya Fahimceta yace yasan mganinsu ko Daady bata bari yaji Labarin ba tasan Halinsa ba Fahimtar komai zai yi ba Aikuwa Abba shi da kanshi Ya gaji Daman da Ganin Inteeear da Imran suna Raba Dare a Gidansa kullum Ta dawo makaranta Chan take yada Zango shima in ya Dawo aiki yana nan Abba ya Kirasu yace su Zauna gidansu Inteesar kada ta kara Biyowa in sungama Exam ta Koma Gida shima in ya tashi aiki ya wuce Gida Imran ya Dinga Kumburi wai Abba na Koransa Abba yace Eh ya Koresa in yaji Haushi kda ya kara Dawowa Imran yaji Haushi Tunda ga Ranar yace ma Inteeesar in taje makaranta Ta Rika Dawowa Gida,Inteesar sai Kumburi Take Imran mamaki ya kamasa Lalle yarinyar nan wato saboda ya sakarmata da Farko Tana yadda Tagama Dama shine ta Fara Rainasa ai kuwa yaFita Butunta bama Tunanin Ya Tsaya ya Lallasheta bai da wannan Lokacin. *Shakira* 3/28/22, 21:16 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�26* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Inteesar kwana Biyu ta Dauka Tana Fushi da Imran kan Hanata zuwa Gidan Abba shi kuwa baima san Tanayi ba in ma Fushi ne tayi ta gama Shi baima nuna ya gane hakan ba Ballatana ta saka ran zai Lallasheta. Kwana Biyun ko mgana batayi mai Daga gaisuwa shikenan kuma bataje Makaranta ba basu da jarabawa daman Guda biyu ya Rage musu su gama. Abun ma nata sai ya koma basa Dariya ko Falo ta Fito da Daddare ta gansa Zaune yana aiki sai ta wani Dauke kanta ta zauna chan nesa Tana Taba wayarta ko Tana karatu Duk yana Lura da ita,bai kuma Taba nuna mata yana ma Fahimceta ba. Bata san wani abu ba Shi ko basu yi mgana ba Ganinta kawai da Tabbacin Ita din matarsa ce wani Sinadiri ne na Farimciki da Samun Salama da Sukuni a Rayuwarsa. Data gaji ne da kanta ta Hakura Sanin bazai Taba Sauya mgana ba Ballatana Ya Imu dai baisan ka bata rai kan yayi wani abu ya baka Hakuri ko ya Lallasheka ba. Imran bai taba jin Labarin Soyayyar Sagir da Hafsah data Khalil Data Munari ba shi ya Dauka da aka gama Biki sun kama kansu da rawan Jikin da suka Dinga yi kan yaran sai Ranar Yaji Inteesar na mgana da Hafsah ta Waya suna Zencen mamaki ya gama kamasa aransa yana Tunanin meke Damun Sagir da Khalil ne..? Banda Tsabar jama kai Raini ina su ina Wadanan yaran..? Yana Zaune ne saman Kujera Sanye da karamin Wando 3Quater da Karamar Riga mai Gajeren Hannu Laptop dinsa ne a gabansa yana wani aikin da gobe Manager din Branch din Gyadi gyadi zai karba yaji suna mgana ita duk azatonta yana aikinsa baya jinta bata sani ba Duka Motsinta a idonsa ne sai dai yana komai da Taku ne kuma yana da Karfin ji kamar Maciji Daga cikin Wayar ma yana jin Abunda Hafsah take Fadi Har suka gama waya bai yi mgana ba Inteesar Complex take sha batayi Girki ba Gogan bai Damu ba Daya Dawo Tea kadai yasha Cikinsa ya Cika. Sai da suka gama kana ya Dago yana kallon Inteesar Dake sanye cikin Wata Riga mai Taushi tashan Iska sai dai Tana da dan Kauri kadan sai dai bata da Dogom Hannu kanta Hula ce ta Zamani ta yanmata ta Rufe kanta Dashi Kafarta Daya kan Daya ta Dora Tana shan Complex dinta. Suna Hada ido ta Turamai baki Har da Murgudawa Ido ya Ware yana Fadin"Ni kike Harara kuma kike Turamin baki harda Murgudamin Baki Duka ni kadai..!? Cikin Tabara tace"Ni fa badakai nake ba..! Yana Sosa Gemunsa yace"Uhn..Kin rainani..?to bada ni kike ba dawa kike..?akwai wani agidan ne bayan ni dake..,? Yafada yana Tsareta da Kaifaffun Idanuwansa bazata jure ba yasa ta Kauda Kai batayi mgana ba sai Chan Tace"To ba kai bane..Sai kazo ka zauna ko fa Hira bakamin ni in nayi mgana kace zan dameka da Hayaniya kana aiki ne..! Imran na Cigaba da aikinsa yace"Yes..Ko ba aikin nake yi ba..?in na Biye miki zaki hanani aiki na ne..! Jin haka yasa bata kara mgana ba Ta Cigaba da shan abun Dake Hannunta Shima haka sai chan yace"Wai wasu yara ne Sagir da Khalil ke soyayya dasu..? Yafada yana Cigaba da aikinsa bai Dago ba,Inteesar Taji Hira ai sai ta Gyara Zama tana Fadin"Sagir yana son Hafsah..Shi kuma Khalil Munari..Don Allah basu Dace b..?munari tace min yace soon iyayansaa zasu zo ayi mgana Hakama Sagir..! Mamaki ya Cikashi Cikin karin mamakin ya Dago yana Fadin"Wacece Hafsah..!? Inteesar tace"Laa..Hafsah Autan Goggo Maimuna,wacce ke karatu nan Dutse tana zaune tare da su Ya Sa"id..! Kai ya gyada yana Fadin"Su yaranan suke so..?yaran da yaushe aka gama Share musu majina..Khalil da Sagir sun ji Haushi basu da Girma sai na Jikinsu..! Inteesar ta Rike baki Tana Fadin"Munarin da Hafsah ne yara Ya Imu..!,? A karkace yace"Eh in ba yara ba manya ne..? Inteesar tace"Tab..Age mate dina ne fa Nima kenan yarinya ce..? Imran ya Dage gira yana Fadin"To ai kema Duka Kina Layinsu yarinya ce Baki san abunda kike yi ba..! Yafada kai Tsaye Inteesar ta Mike Tsaye Har tana neman Ture Mug din Dake Hannunta Kan Centet Table din Dake gabansa ta Dankwar dashi Tana Fadin"Ni ce ma yarinya..?ni ce bansan Abunda nake yi ba..? Tafada kamar zatayi kuka Imran ya Hade rai yana Kokarin Danne Dariyansa yace"Eh mana..! Ai sai Inteesar ta Fara Buga Kafa tana Tsallen Shagwaba da kukan karya Tana Fadin"Ni Wlh ba yarinya bace..Babba ce Tunda nayi aure..! Mirmishi yayi yana Kokarin Boye Dariyansa yana kallonta yace'"Ai wannan aikin ma da kike yi na yaran ne..Kuma kin ce ke Babba ce Tunda kin yi aure ko..? Kai ta gyadamai Tana Jan Hanci kamar mai kukan gaske,Kansa yake Shafawa yana Fadin"Ai fa ga Babba nan..Sannu Babba..! Yake Fada yana Dariya Inteesar an samu Waje kawai sai ta koma ta Zauna Dirshan saman Cafet ta saka kuka Baki ya saki yana kallonta Kafin ya Gimtse Fuska yana Fadin'"Lalle ma yarinyar nan Duka kike so inaganin ba Lallashi ba ko..!? tsayawa Tayi da kukan Tana kallonsa kafin Ta waro ido Tana Fadin"Duka..? Kai ya gyada mata yana Fadin"Eh mana nan fa ba Umma ba Daddy..Wlh kika Dameni Zanemiki jiki Zan yi.U..! Ai bai gama mgana ba Ta Mike da Sauri ta Dauki Wayarta da Mug din Datake shan Complez suma sum Ta Shige Kitchen bata Dade ba ta Fito ko Gud Night din ma batacemai ta Shige Dakinta Dariya yayi yana Fadin"Better..! Domin bai Shiryama Rigimarta ba a wannan Lokacin Ita batasan Tana Dagulamai lissafi bane Shiyasa take kara yin wasu abubuwan. Abun na Ransa bai manta ba Washegari Daya Fita aiki Bayan sun tashi Lunch ya Kira Sagir yana Cemai yanzu banda Tsabar Raini da Zubar da Girma ina su ina soyayya da yaran da ko Hankalin kansu basu gama mallaka ba..? Ga mata nan manya masu Hankali acikin Gari sai su yarda Girman ku kuna Biyema yara..! Sagir yayi Dariya kamar me kafin yace eh sun ji shi ba yarinyar ya aura ba..?Sanda yake makale Murya yana Fadin don Allah Baby in d'an kara suna ina..? Imran ya Rike baki yana Dariya yace"Sangiru ka zama Dan iska In kara uwar me..? Sagir na Dariya yace"Koma miye ka sani in kuma kana son na Fada ne to..! Imran yace"Basai ka Fadama ba kada Kasa Kunnena ya Toshe..Sangiru Allah ya Shirya ka Zama D'an iska har kana san Abunda miji da mata suke yi.. Gabadayamsu Dariya suke yi Sagir yace"Bamu sani ba sai kai Tunda kayi aure .! Imran yace"Kai dallah..Ni fa bana son Raini sam.Kagani nan ko zan amshi Hakkina umarni zan bada kawai..Allah ya kyauta in zauna ina Wani Rage murya kamar wani Sakarai..! Sagir yace"Uhm..Lokaci na zuwa..Lokacin da zaka gane Karuwa ba yar iska bace..! Imran yace"Wlh yar iska ce..! Sagir yace"A"ah fa Sana"arta take yi kada kace haka..! Gabadayansu Dariya suke yi Daga Karshe Imu yace Wlh su nemi mai musu Best friend Allah ya kyauta yaje Cikin yara yana Bude baki da Girmansa,da komai. Sagir yace bakomai sun ji gari da yawa maye ai baya ci kansa ba kuma ko bai zama Best friend ba ai ya Zama Babban yaya..! Haka ya Kira Khalil yana gayamai Shima cewa yayi ai karamar yarinyar ya aura Daga Wajensa suka koya shiyasa Haka shima yace mai Bazai je Cikin yara yana mgana ba in sun neni manyan mata shikenan yana Tsausaya musu ga kayan Raini ga Dawainiya maimakon Ta Kula Dakai kai ne Zaka koma kana kula da ita Dukkansu sukace mai sun ji kuma sun gani sun gode da Shawara ji ya Zama Dole yadda ne ba Dole ba. Khalil sai da ya bama Munari Labari batayi mamaki ba Sanin Halin Ya Imu Tace ai ita kanta Inteesar Wahalar sa Take sha Kafin ta Samu Lagonsa sai Ta yi kamar tanayi irin su kana yi ne kamar Baka yi ba irin Mazan da suke Laushi bane lokaci Daya,Ammh Zai yi Laushin In Tafiya Tayi Tafiya In ji Khalil. Ranar Friday ta kama Zasu yi Second to d the Last Paper dinsu Sai Tafiya Hutun da zasu dawo su shiga Aji Biyu sai karfe 12pm suke da Exam gida Imran ya Barta In Lokaci yayi Zata Kulle Gida ta Hau adaidaita Tatafi makaranta Bata Tambayashi Zuwa Gidan Abba ba sai da ya Tafi Wajen aiki ta Kirashi bai Dauka ba sai ta Turamai Sako Don Allah ya barta Tabi Munari zuwa Gidan Abba. Daya gani sai ya Shareta Aiki yayi mai yawa sai da ta kara Kiransa Sannan Mganar ta dawomai Sako ya Tura mata Cikin Gatsensa "Bana ce kada ki kara Zuwa ba..? To ki Tafi din..! Haka ya Tura mata ita kuma Tana ganin haka sai ta Zata ya barta ne suna gama Jarabawa tace Zata bi Munari zuwa gida Munari tace Ya Imun ya barta ne..?saboda ai aganbansu Abba yace kada su kara zuwa nan kusa Har Imran din yayi Fushi Daman Haka Abba yake so su Dauke Kafa na kwana Biyu su Zauna agidansu su kara Fahintar juna. Sai Inteeaar tace eh ya barta Munari bata kara mgana suka tafi Abba baya nan yana cikin makaranta sai da ya dawo ya ganta Dayayi mgana Tace Imu yace tazo in ya taso aiki Zai Zo ya Dauketa Abba yayi mamaki yafa san Halin Imu bazai Huce nan kusa ba ammh dai bai ce komai ba. Har bayan Isha"i Shuru ba Imran ba Dalilinsa kuma a ka"idarsa yana Tashi aiki Hudu zuwa Biyar na yammah in ya Tsaya wani abun ne Shida na yammah Kafin mangariba ya iso ammh Yau shuru Inteesar Tayi ta Kiransa bai Dauka ba sai idonta ya Raina Fata Munari ta Kalleta Tana Fadin"Wai Daman bai barki ba kika Taho..! Inteesar na ta Fito da Wayarta Tana Dubo Test din da yayi mata ta Nuna ma Munari Tana Fadin"Shifa yace naje kalli ma ki gani..! Munari ta amsa ta karanta Cikin Mamaki ta kalli Inteesar Tana Fadin"uhm..ni ban ma san me zan ce miki ba..?Kalli fa abunda yace Keji din..?shine kuma kika je din..?Allah ne kadai yasan yadda Kika Batamai rai kila don ma kene Da yau wani ne ko Wata da ya Raina kansa..! Inteesar Idonta ya Raina Fata Tayi Shuru ta kasa mgana Munari na Kallonta sai ta bata Tsausayi ya Imu naWahalar da Inteesar ta rasa ta yadda Zata gayamata ta gane komai itama Ta Dauki Hanyar Ramawa bata karance karance bata damu davSocial media ba ballatana ta san wasu abubuwan gata kadai ta sani ita Tana Karance karancen Littafan Hausa Dana Turanci Tana kuma Mu"amala da Social media Tafi Inteesar Bude ido sosai kuma ta Fita Shiga Mutane.. Ganin ta Damu yasa Munari taje ta Fadama Abba yadda akayi Abba bai ce komai ba Daman yasan Za"a Rina Ya Yusuf na gefe yana Fadin"Shi yama yi Auran Har yau bai yi Hankali ba..? Abba ya Daga waya ya Kirashi bai Daga Kiran ba sai da ta Katse kana ya Kira Daga baya Abba bai ma Tsaya amsa Gaisuwarsa ba yafara Fadin"kana ina..? Imran ya Dakuna Fuska yana Tsaye a Falon gidansa Roban Ruwa Hannunsa Guda Dayan kuma yana Rike da Waya yace"Ina Gida Abba..! Abbba yace"Ka manta da Matarka ne ka wuce gida baka zo ka Dauketa ba..? Imran yace"kafar da ya kawota sai ya Maidota Abba..ni ai ban aikota ba..! Abba yace"Ni kake Fadama haka Imran..?wato Kafarta ta maidota ko..!Nagode..! Imran yadan Bude ido yana Fadin "Abba kada ka Dauki mganar nan da Zafi..Ba dakai nake ba..Ni ban ce tazo ba ta Raina ni ne Dole ne sai abunda Take so zan yi akoda yaushe..?nace mata Kada taje bataji mgana ta ba ta Tafi ai tunda ta iya gaban kanta sai ta Dawo da kanta..! Abba yace"Kayi mata hankali Ita yarinya ce..! Ran Imran ya kara baci yace"In ita yarinya ne sai ni kuma Shikenan sai na Lalace akanta..?Ni Bata mata Rai zan yi bana son wasa meyasa batajin mgana ne..! Abba yace"Kayi Hakuri kazo ka Dauketa..Yaushe Zata rika Fahimtar ka kana mata mgana Gatse gatsen ka Kwata Kwata kai Imran baka Laushi..! Imran yace"Abba nayi Laushi Saboda ita..Bata Samu Compt Imran ba Half Ta samu..kuma na riga na Rantse ni ban Zo na Dauketa ba kuma bata isa ta Sani Kaffara ba..! Abba ya Bude baki kafin yace"Har nima ko..! Cikin Dakuna Fuska yace"Ni fa Abba ban ce kai ba..! Abba ya gyada kai yana Fadin"Ka dinga dai Hakuri kai Babba ne ka Girmeta..Ka Rika Tunawa sai ka Sadda kan ka wani Lokaci ita yarinya ce akwai kuruciya Tare da ita..! Imu Hade rai aransa yana Fadin Wato ya Sadda kai ya Zama Sakarai Allah ya Tsareshi..! Abba yace"Yusuf zai kawota..Zan mata Fada kada ka mata wannan Hargagin naka nasan Halinka..! Imran ok kawai yace ya Katse Kiran Ransa na baci kokarin ma Daidaita kansa yake In yace abu baya so kuma ana Damunsa akai Abba fa da kansa yace kada su dawomai Gida nan kusa Shi mutum ne Dake Daraja Kalaman mutane masu Daraja awajensa Musamman Abba Shi bama da Wata Manufa yace mata kada taje ba ya bari ne sai Abba ya nemesu da kansu suma su Rama bacin Ransa Daya daya Dawo bai ganta ba wato ke je din Taje din Sai Taga abunda zai Faru..! Abba Fada yayi ma Inteesar Sosai Tayi Narai Narai kana Abba ya Umarci Ya Yusuf Daya maidata Gida Tace Munari Tazota Rakata Munari tace Allah ya Tsareta Ta Rakata Ya Imu ya Hada da ita,Tana ma Rokonta Kada ma a bayaninta ta Kira sunanta Inteesar dai Tasan yau sai ta sani da Fada Ya Yusuf ya Dauketa ya kaita Gidan ya kulle gidan ta Ciki sai da Ya Yusuf ya Kirasa a waya kana ya Fito ya Bude mata bai Shigo da Motar ba Daganan yayi musu Sallama ya Juya Imran yana wani Cin mgani aransa yace Yau Inteesar ta Zama nama kenan.. Shi ya Tsaya Rufe Gidan ita kuma Tayi Sadaf Sadaf ta Shige Cikin Gidan Tana Kokarin Shiga Dakinta ya Shigo Falon Cikin Dakiyarsa yace"Zo nan..! Cak ta Tsaya gabanta na Fadi kafin ta Juyo bata iya Dagowa ba kanta na kasa Tana wasa da adon Gyalen dake Jikinta Daga sama Har Kasa ya Kalleta Kafin yace"Sagir bai baki Sako ba..? Kai ta girgizamai Cikin Dakuna Fuska ya Danna ma Sagir Kira ta Wayar Dake Hannunsa Buga Daya ana Biyu ya Daga Yana Fadin"Ango kasha Kamshi..! Imran yayi Tsaki yana Fadin"mallan ina Aikin da na baka..? Sagir yace"Wani aiki kuma da Daddaran nan..? Imran yace"Hijabin da na baka kudi a Dinkama MARYAM..! Sagir yace"Au na manta kasan bani ke yi ba Kasuwa nakai Wajen wani abokina yana Dinkasu kala kala bari gobe zan Tabosa naji ko ya gama Hala Baka son Tana saka Mayafi ne..? Banga Laifinka ba kada Maxa su kalle ma yar babynka..! Imran Tsaki yaja ya Datse Kiran Yabar Sagir da Dariya Inteesar na Gefe Tana Sauraransa Zama yayi saman Kujera ya Dora Kafa Daya kan Daya yana Sanye da Riga da Wando Fari da baki. Kallonta yake yi yana Kokarin Daidaita kansa Cikin Kaushinsa yace"Yaushe kika Fara rainani da Har Zan ce kiyi abu kiki yi..Sai abunda kika ga Dama Zakiyi..? Yauahe muka Fara wannan Dake..? Ya Fada Cikin Tsawa da Daga Murya Inteesar da Tuni Idonta ya Ciko da Hawaye ta ce"Kai fa..kai fa kace naje..! Cikin Hararanta yace"Yaushe nace kije..?cewa nayi ki je din Shine kuma Saboda Tsabar kin Raina ni sai kika je din ko..? Inteesar na Sosan Idonta tace"Naji to kace naje kuma...! Ransa ne ya kara baci ya daka Mata Tsawa yana Fadin"Shup up anan Wajen in kika kara mgana Kika Harzukani Zan tashi nayi kasa kasa Dake anan Wajen..!. Jin haka yasa ta Toshe bakinta da Mayafinta Tana Hawaye bata son Fada a Rayuwarta. Cikin Fushi yace"Bana so..Bana so..Ina mgana kina mgana Raini ne..Zaki cemin ke bakisan gatse bane..?da zaki kwashi Kafafu ki Tafi..?Kina Biyema wannan yarinyar ko..?munari Daya kuke da ita..?ke fa matar aure ce nan ne gidanki itama Chan ne gidansu Ammh baki da aiki sai Biyemata sai anyi mgana Kice Munari Munari kaza kaza..Munarin Daya kuke da ita nace..? Yafada Cikim Tsawa ai Sai Inteesar ta Saki kukanta cikin kukan Tace"Ni bansani ba..Wlh bansan Gatse kamin ba..kana ta min Fada..Ni bana son Fada..! Take Fada kafin ta Shige Daki da Gudu Tana kuka Baki ya Saki yana kallonta Wato ita batasan Fada..?to ya barta ta Cigaba da iskanci kenan bai Mata Fada ba,daya Daga Cikin Illan Auran yara kenan Yanzu in babba ce Taya ya Zaka Xauna ma kana mgana..?ai tasan abunda ya Dace da ita Soyayya batayimai adalci ba Data saka ya Fada soyayyar yarinya karama Datake Neman ta Sauya shi Daga Imran dinsa Zuwa Wani Imran din na Dabam Yana Jinta Tana kuka yayi banza da ita In bai rika mata haka ba Watarana Da mganarsa Zata Rika ja tana yarda taga Dama Kwanjinsa bai Hana in Anyi ba Daidai ba ya magantu Soyayyat taci kaza kazanta alokacin in Komai ya Dawo Daidai sai a Tuna. Yana Aiki Bisa Laptop dinsa yaji Har Tana jiniyan kuka kamar Wata karamar Yarinya. Da Sauri ya Mike Ransa na Baci ya Shiga Dakin afusace kan gado ya ganta ta Dunkule Tana kuka kamar ya Daketa Cikin Fusata yace"Na Dake ki ne..?Kukan Dadi kikeyi kinsan Allah in baki min Shuru anan Wajen ba Na Tako Inda kike sai nayi kwallo Dake Nagani kukan Jini Zaki yanzu ko na Hawaye..! Ai jin haka yasa Kaji Inteen Daddy Tsit Tasan zai aikata Kyafci yayi ya Fice Daga Dakin Ta rakasa da Harara Damam kukan Tabara ne afili Tace"Ko ma ya Lallasheni ina kuka.!.tafada Tana Tura baki Ranar Bai kara ganinta ba da Safe mahar ya Fita bata Fito ba aransa yace in na Nemeta zata Rainani ne gwara na Kyaleta ai itace Tamin Laifi da Wannan Tunanin ya Fita Batunta mai Dade a Office Dayake asabar ne wani aiki ma ya karisa Daganan Shagon Sagir yaje suka sha Hira bai bar Sagir yayi Salama ba sai da sukaje suka karbo Dinkin Hijaban Inteesar matar mallam Imu ce yadi Hudu Hudu ne Har yana jan kasa Mama Tayi Danwake ya Shiga Har Ciki Suka gaisa suka ci Danwake shida Sagir yana ganin Gidansu yaso kamar ya Shiga sai kuma ya fasa kada Intee taji tace Ita ya Hanata Shiyasa ya Fasa shiga ammh sun Hadu dasu Abba a Masallaci Ya Yusuf nata yimai Tsiyan mai Yaji ya Daka Borkunu Imun Abba.. Bai ce komai ba ya Kara Hade rai kamar an aikomai da Sako mara Dadi a an anguwar yayi sallar Isha"i kafin ya Koma Gida Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba ya Damu Yana so yaji Lafiyarta ya barta itaa kadai agida Tun Safe. Ya Kirata bata Dauka ba ya Turamata sako. "Kina lafiya..?. Ta karanta Ta Sharesa Wata Zuciya Tace ka kama kanka Imran da Girmakka Yarinya na neman janka a kasa da wannan Tunanin ya Fita Batunta ammh fa Tana Ransa Ranar Lahadi ba aiki yana Gida yana Daki yaji Fitowarta da Safe ta Shiga Kitchen yana jin haka ya Fito Falo ya Zauna Saboda yaji kamar Girki take yi Sai da Ta gama ta Fito Dauke da Filet Shake da Indomie,Ko Gaisheshi batayi ba Bakinta agaba ta Shige Daki Dauke da Goran Ruwa ta kasan ido ya Kalleta Dariya ta kamsa afili ya Furta"Imu ka Tabo Autar Daddy sai Allah..! Kitchen din ya shiga yaga iya Cikinta ta Dafa,Cikinsa ya Shafa ya Lafe sosai yana jin yunwa Inteesar Muguwa ce ko Ta Dafa dashi in bazatayi mai mgana ba ko acikin Kitchen din ta ijiyemai yazo yaci bakomai. Hakanan ya Dafa Ruwan zafi yasha Tea sama sama ya Dawo Falo Laptop dinsa ya Dauko ya Fara aiki Domin ya Daukemai Hankali. Ranar haka suka Wuni Inteesar Har Kai take kaudawa bata son kallonsa Imran shima ya Mazaye baya bari Ta gane ya ganta shima ya nuna mata ya Fita Zafin kai. Washagari Monday Ranar ne Last Paper dinsu,Karfe 10:00am suke da Jarabawan Zai Rigata Fita Shiyasa da Safen ya Taka Har Dakinta tana Kudundune Cikin Bargo ta Rufe ido kamar mai barci batasan ya ganta ba Tana Danna Waya tana jin Sallamarssa Ta Tusa wayar Cikin Bargo Tana Barcin karya. Bai bi ta kanta ba ya Ijiye mata Ledan Hijaban yana Fadin"Ki yi amfani dasu..Bana son na kara ganinki da Mayafan nan..! Yafada Lokaci Daya yana Dora mata Dari Biyar saman ledan Ya kama Hanyar Fita yana gyaran Zaman Briefcase din Dake hannunsa. Yana Fadin"Kiyi maneji ba kudi a Hannuna..! Daga haka ya Fice ya Turo mata Kofar sai da Ta Tabbatar da ya bar Gidan kana ta Mike Zaune ta jawo Ledan Tana Dubawa ai data Gwada sai da ta Rike baki Tana Fadin"Tabdijam..Ni ce Zan saka wannan kamar wata Malama..! Tafada Tana kallonta ta Madubi,Wata Zuciyar tace"Kuma ki ki sawa..Abu ya Zama Bala"i..Kila ma wannan karon Har da duka! Tuna Haka yasa ta bata rai Hijabin kala Goma ne kala kala gashi an yi musu Dinkin Zamani. Bata bar gidan ba sai ta Soya kwai tasha Da Tea da Buredi wanda sai da ma suna Hanyar dawowa Gida Ranar tagani tace su Tsaya su siya kana ya Tsaya ya siyan musu shi ba ci yake yi ba ballatana Yayi Tunanin siyowa. Dakyar ta samu Daya daga Cikin Hijaban ta saka Kalan pick Zanen Material din Jikinta Har kasa ya kaimata ya Rufemata Diga digi ya ta iya Matar Imu take in batajin mgana Mganinta Zai yi a Dake ka kuma a hanaka kuka kuma aki Lallashinka sai dai ka gaji kabama kanka Hakuri..! Lokacin da Munari taganta a makaranta Sai da ta Kusa Kaiwa kasa Saboda Dariya Inteesar sai kwal kwal kuka Cikin Shagwaba tace"Duk ban yi kyau ba ko..? Ba yaya Imran bane ya kawomin wai kada ya kara ganina da mayafi..! Munari na Dariya tace"Tab..Mrs Imran Abubakar Malami..! Take Fada Tana Dariya wayarta ta Fito da ita Tana Fadin"Bari nayi miki Hoto naji Dadin Bama su Nasara Labari..! Daman Kiris take jira sai ta sakamata kuka ganin haka yasa Munari ta Daina Dariyan afili Sai da Taga Inteesar din Idanuwanta duk sun kumbura alamun tasha kukabata Tambayeta ba sai da suka Fito Paper Course mate din su suna ta Murna Final Suka samu Waje suka Zauna Munari ta kalli Inteesar Dake Fama da Hajibi Tana Fadin"wai ya imun dukan ki yayi ne naga Idanuwanki sun Sauya..?in dai kuwa ya Dakeki Wlh Tashi muje office din Abba ki Fadamai kan me..?aure ai ya wuce wasa..! Inteesar ta Dago tana kallonta kafin Tace"Wlh bai Taba Dukana ba..! Munari tace"To me ya yi miki..?daga ganinki kin sha kuka wannan i don naki..! Inteesar ta kauda kai batayi mgana ba Munari tace"Shikenan Tunda baki san Gayamin ammh Zan Fada miki gaskiya in baki Mike Tsaye ba Wlh Ya Imu Wahala Zai ta baki kafin ki gano kansa Kingama Jigata..! Inteesar ta Juyo tana kallonta Kafin tace"Uhm..Naga alama..Ranar da naje gidan nan..!., Nan ta shiga bama Munari Labarin abunda ya Faru ta Karishe da Fadin"Haka ya dinga min tsawa da Fada ina kuka bai Lallasheni ba yace ma in na kara Damunsa yazo nan sai yayi kwallo Dani..Ni ba ance Miji na Lallashin matarsa ba ni Wlh Ya Imu bai Taba Lallashina ba Munari in ma Fushi zan yi baisan inayi ba sai don in nagaji na Hakura dakaina anya Yana Sona..? Munari ta gyara Zama anzo Wajen Data ke son zuwa Cikin Hikima tace"Wlh yana sonki..So mai Tsanani ma Daya kai ku wannan Mtsayin in da baya Sonki ko sama da kasa Zasu Hade bazai Aure ki har ya Zauna dake ba Baki ga Sajida da baya sonta ba ya Saketa.ba..?haka Ya Imu yake Dan kafiya Dan Ra"ayi bamai Turasasa yayu abu Dole sai Abba ammh ko shi baya yarda yasakashi ya Zauna da abunda baya Ra"ayi..! Inteesar ta jinjina kai alamun gamsuwa kafin tace"Ai bai taba Cemin yana sona ba..! Munari tace"Ai bazai fada ba..Ke ce Zaki Sakashi ya Fada ma bai sani ba..! Inteesar tace"Ta yaya..? Munari tace"Baki gane ba..?tsaya ma wai Kun Fara amarcin ne ko kuwa Dai kina nan kina Jiransa..! Inteesar ta Rausayar da ido Tana Fadin"Bama mu taba fa kwana Daki Daya ba Tunda muka yi aure..! Munari ta Zare ido Tana Fadin"No Wonder shiyasa bai yi Laushi ba Har yanzu..ke kuma kika yarda..?baki cemai kina jin tsoro ba..! Imteesar tace"To ya zanyi..?dakinsa yake Shigewa fa sai na Bishi..!? Munari tace"Sosai ma.irinsu ya Imu sai da Tarko..Ki bisa ki Danamai Tarkon da zai kawo kansa da kansa yana Magiya..! Inteesar tace"Ta yaya hakan zai Faru..?kamar fa baya son abun ne ni ko irin Romance din nan bamu taba ba..! Tafada Abun na fitowa Daga Karkashin Ranta Munari tama kasa mgana Inteesar ta Cigaba da Fadin"Ina Fadamiki sirrina ne saboda Ke Kawatace kuma yar"uwata wacce banda kamarki..ki bani Shawaran ya Zanyi..? Munari tace"Insha Allahu Inteesar Zan baki Shawara kamar yadda Zan bama kaina..! Nan Munari ta Zauna Tana ta karanta mata Yadda Zatayi da Dubarin mata Inteesar tayi Kasake tana ji kafin tace"Kina ganin...kin fa san Ya Imu..! Munari tace"Ai shima Mutum ne kamar Kowa kuma Namiji mai Lafiya Wlh karyansa ya Ture Kiran wannan Majalisar Dinkin Duniyan in kuma ya Fara Dandanarta To zai so kullum ya Dinga Ninkaya aciii ina nan Zaune Zamu gani Ya Imu yayi Laushi sai yadda kikayi Dashi..! Inteesar tace"Allah yar"uwata..! Munari tace kina wasa ne Dariya sukayi lokaci daya suna Tafawa Inteesar na Fadin"Khalil ya Shiga uku..,! Munari na Fadib"Ai yama shiga Goma ne..!. Dariya suka saka gabadayansu sun dan jima acikin makaranta bayan sun gama Sallama da Course mate dinsu suka Tafi Office din Abba suka gaisheshi bayan sun gama shan A.c da Lemo suka Mai Sallama suka Tafi Daga Bakin Get suka Rabu kowacce ta hau adaidaitan da zai kaita inda zata suka Rabu Da Inteesar kan Zata gwada Shawarwarinta. *Shakira..* 3/29/22, 14:31 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�27* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Inteesar ta koma gida da Kudiri Tare da Niyyar gwada Shawarwarin Munari da kuma amfani dasu. Tana komawa Gida bata Zauna ba Bayan ta sha Complex tayi alwala Tayi Sallar la"asar Domin sunyi Sallar Azahar a makaranta ita da Munari. Daganan ta Fara gyaran Gidan bata gyarasa Koda yaushe sai Ranar Datake Gida shima Daga Falo sai Kitchen sai Dakinta ko Hanyar Bedroom din Imran bata Taba kallah ba. Sai da ta kal kale ko"ina Har Bedroom din nashi ta shiga ta gyaramai Duk da ba wani gyara saosai bai da kazanta Duk Abunda yayi amfani Dashi yana Kokarin Maidashi Muhallinsa Har Tiolet sai da ta wankemai Tas yana Tashin Kamshin Turaran Dakunan Data Turara Gidan dashi a Burner. Tana gamawa Ta Fada Kitchen ta Fara Sarrafa abunda Zata Dafa Saukkan Abinci Tayi Farar shinkafa da Miyar ganye Da Kifi sai ta Soya kaza Tayi mata Pepe Chicken da yaji albasa da kayan Kamshi,akwai Fruit a dayawa a acikin Fridge Saboda Imran baya bari ma ya yankemai Wani Lokacin da yawa yake siyowa Tana sha ammh ita dai barta Da Cin kayan Fulawa da Zak'i. Kayan Lambun ta yayyanka tayi Fruit Salt ta saka afrige Lokacin Data gama an Fara Kiran Sallar mangariba Bata Shiga Daki ba sai da ta Jera komai Saman Dining kana ta shiga Ciki. Wanka Ta Farayin kafin ta Dauro alwala ta Fito Sallar ta Farayi kafin ta Shafa Man shafawarta na Olive Ta Fara kokarin neman kayan da zata saka Wadanda zasu ja Hankalin ogan akanta. Cikin akwatin kayanta na Gida Wanda Nasara ta Hadamata,gabda Biki ta Bude Tasan Tana da wanduna da Riguna Lokacin Tana Gida da Zata Taho kano ne Umma ta Hanata Tafiya Dasu Taji Dadin ganinsu aciki Batasan Umma ce ta saka su ba,Domin ai Tasan Zasu yi mata amfani Tunda Gidan Miji Zataje Daman ko Gidan Maman abunda yasa Umma ta Hanata Zuwa Dashi Saboda ba kamar nan bane Da ba Kowa Daga ita sai ita sai Daddy Ya Basheer na Gidansa ba Kullum yake zuwa ba,gidan Mama kuma akwai Sagir kuma shi ba Muharraminta bane Shiyasa ta Hanata tafiya da Wandunan datake Sakawa su Lameta sosai suna Fitar da Surar Jikinta. Wani Wando ta Samu Red Colour Daga Kasa ya Tsuke sosai iyakarsa kuma daga gwiwanta Kadan ya Wuce sai Wata karamar Riga mara Hannu Itama Ja ce sai dai Tana da Zanen Baki a Jikinta an yi Rubutu kanana daga gaban Riga Data Sanya kayan Ta Tsaya gaban Madubi sai ta Fara Tunanin Anya Zata iya Fita gaban Ya Imu haka..?kayan Tun Tana gida bata cika sakasu ba sun kamata sosai Wandon ma Dakyar ta saka Gabadaya Shafaffan kugunta ya Bayyana Kirjinta ya Cika rigar ta kamata sosai da Har Shatin Cibiyarta ana gani sannan kuma Da kadan ta Wuce Cibiyarta Data Daga Hannu Lafaffan Cikinta Zai Bayyana Waje ne. Sumar kanta Da bata Kitse ba Ta Tattara ta Daure Daga kasa ta Sakamai Band kafin ta Samu Wata Hula red itama mai adon kamar Love ta gaba ta saka bayan ta Saka wani Saukakkan Dan kunnen da bazai Dameta ba kara kallonta Take ta Madubi kafin Wata zuciya tace mata"To ke Intee keda zaki burge Miji ai bakya Bukatar wannan Hular..! Tafada Tana Cire Hular kanta Sake Sauya yanayin Band din Tayi ta maidashi ta Tsakiya duk da ba wata Doguwar suma gareta ba Tana da Cika da na Zaman Falo. Karan Bude get taji Tasan ya Dawo kenan Tanaji ya Shigo da Motarsa ya koma ya Rufe get din Wanka Ta Fara ma kanta da Hunra da Turaruka masu Kamshi Da Fitar ma da Duk wanda ya Shake su Hankali yau akwai jan mgana. Kugu ta Rike Tana Sauke ajiyar rai a Fili ta Furta"Zan Burgesa..? Allah yasa ma ya Kalleni Nasan Halin Wanda na aura ba komai ke Burgesa ba..Zan so Tarkon na ya kamashi Can"t Wait naji Ya Imu ya Kalleni yana Fadin I Love u Inteesar..Bazan iya Rayuwa bki ba..! Tafada Hartana Kwakwaiyon Salon mganarsa Kafin ta Tsintire da Dariyan Farinciki Bakinta Ta Rufe jin Motsin Shigowarsa ya shiga Dakinsa kana ta Sauke ajiyar Zuciya gefen gado ta Zauna Tana Kara jiran Fitowarsa kamar yadda ta Tsara sai ta Fita Ta ja Fada daman ai basa mgana suna Fada ne. Yayi matukar mamakin ganin Dakinsa Tsab yana Tashin Kamshi Sai dai yasan Intee ce ta gyaramai Daki Mirmishi yayi yana Fadin"Allah Sarki..Yarinyar Tana da Hankali..Allah yayi miki albarka..! Yafada kafin ya ijiye Briefcase din Hannunsa ya Sabule kayan Jikinsa ya Shiga Wanka Har ga Allah yaji Dadin Ganin ko"ina na Tashin kamshi Sosai yayi wanka cikin jin Dadin Da Annushuwa aransa yana Fadin Ta Daina Fushin kenan..? Bayan ya Fito bai Tsaya Shafa mai ba Ya Saka Karamin Wandonsa baki 3Quater da vest wacce ta Dan kamasa Ya Tsaya a Hanya yayi Sallar mangariba Kishi yake ji sosai Gefe Daya yana jin yunwa kuma yau din ba Na Shan kayan Marmari bane na ya samu Abinci mai Rai da Lafiya yaci ne. Laptop dinsa ya Dauka akwai wani aikin da Manaja zai karba Ya fito Falo yana Takunsa Wayarsa Rike a Hannunsa kamar Dole yaki Sauya waya,Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya zauna Lokaci Daya yana Ijiye Laptop dinsa saman Center Table din glass din Dake Tsakar Falon Kamshin Girkin da kamshin Turaran Wutan Daya Gauraye Falon bai sa ya Zauna ba yanufi kicthen ya Dauko Ruwa a Fridge kafin ya Nufi Dining kai Tsaye ganinJerarrun kololi masu kyau da yarari a jeri Cikin Sha"awa da Burgewa Yana Daga Tsayen ya Bude Ruwan ya Kwankwada Rabi kana ya Sauke yana Sauke Numfashi kan Dining din ya ijiye Goran Hannunsa Lokaci Daya yana Bubbude Warmers din Da Pepe Chicken ya Fara cin karo Kamshi ya Dakesa Tuni Miyansa ya,tsinke sai kuma ya ci karo da Fruit Salt yana Turirin Sanyi ai Imran baima Tsaya ba yaja Kujera ya Zauna ya Zari Filet ya Diba Wannan Naman kazan Ya samu karamin Mug ya Diba Fruit Salt din Bata saka siga ba Shi ya saka ya Fara Lodama Cikinsa aransa yana Fadin"Yau Intee an sauko ba Mugunta..! Acikin Ransa yana Dariya yana Tsaka da CinNamansa ta Fito Daga Cikin Dakinta Cikin yanayin Takun Wahainiya Kowani Taku Daya Kirjinta na Shaking Tare da Kugunta Dayake karyawa duk inda tabi bai ji Fitowarta ba sai dai Kamshinta ne yamai Maraba ya Dago kansa yana kallonta Daidai Lokacin Dayakai Cinyar kaza bakinsa itama Shi Take kallo Direct suka Hada ido Gabadayansu sai da sukaji wani yam acikin Jikinsu Imran da gabadaya ya Kafeta da manyan Idanuwansa yana Kallomta Daga sama har kasa Ita kuma ganin haka yasa ta Kauda kanta Ta Kara Kaimin Takunta da dan Sauri Ta wucesa zuwa Kitchen Galala kamar Wani Sakarai haka ya Juya yana Binta da kallo Har ta bacema ganinsa. Nannauyar ajiyar rai ya Sauke sai Lokacin ya iya Tura Naman Daya Dauko Bakinsa yana jin wani Dum Dum a Tsakar kansa gabadaya Wani iri yake ji Inteesar ta Taimaki kanta Data Bacema ganinsa Domin ya kusa sume mata cikin yanayin Daya kasa gane Meyake Faruwa dashi. Bata jima ba sai gata ta kara Fitowa Dauke da Filet da Cokali nan ma ya Sake Binta da kallo yana mamakinta Yasha ganinta ba Hijabi ammh bai Taba ganinta da kayan da suka bayyana Surarta ba irin haka. Bai Taba Tsammaninhaka take ba yasha ganin mata Masu Cikar Hallita suna Mu'amala da mata a banki kuma yanayin Shigarsu mai bayyana Komai ne bai Taba ganin Macen da Cikar Hallita ta Dace da ita ba irin Inteesar ba Duk da bata da wani kiba kallon Kitse yake ma Rogo Tsab Ta mallaki mayan kayan da Kallon awajen Manya mata yake Tunanin Samu ashe Ashe Yana mata kallon yarinya ta Wuce da Duka Tunaninsa. Tasan yana kallonta shiyasa ta kariso Har Dinning cikin Tafiyarta ta yanga Bata yarda ta kallesa ba ta Duka Har Tana dan Bege Cinyarsa da Zata Diba Shinkafar da Miyar ganye ta Duka Sosai har Matsatsun na Shanunta suka Bayyana Daga sama Imran ya Hadu dasu sai kaji Mukut Sautin Wucewar Abu a makwogwaronsa Batare daya Shirya ba Inteesar na Jinsa Da ba domin ta Daure ba babu abunda zai hana bata Kwafsa ma kanta Wajen Kwashewa da Dariya ba Saboda yadda yayi Lokaci Daya yana Wani Zare ido kamar yayi karya. Fruit Salat din ta diba cikin karamin Mug ta saka Siga da yawa saboda Tana son Zaki sosai. Tana Shirin wucewa Dauke da Filet din da Mug din batare data Kallesa ba ya Daga baki yana Fadin"Inteen Daddy ba gaisuwa..! Yafada yana kallonta Cike da karim mamaki. Kai ta Dan kadai kafin ta Juyo Tana kallonsa irin sai ma yanzu na ganga ta Wani Tabe baki kafin tace"Oh..Sannu da zuwa..ai bansan ka shigo ba..! Tafada tana wucewa kan Daya Daga Cikin Falom ta Zauna yadda Zai Rika Fuskartata Galala yayi yana kallonta yadda ta Dora abincin Saman kujera batama kara kallonsa ba. Aranta ya Furta"Lalle yarinyar ta karo Wulakanci..! Kai ya Kada kafin ya sha Fruit Salat din Daya debo bai ma Cinyen Naman Dayasa ba ya goge Bakinsa da Tissue ya taso zuwa inda ya zama Wajen Zamansa Duk Dare ya Zauna suna Fuskarta,juna shi da ita Cikin Kufuluwa ganin yadda tayi wani kamar Bata gansa ba yace"Inteesar kin Rainani ko..?kina abu kamar baki ganni ba..? Dagowa tayi Tana kallonsa Lokaci Daya Tana saka Mug din bakinta ta Kurbi Abun Zuuu..kamar irin na yara Tana Tande Lebe batayi mgana Karkace kai yayi yau yaga Karshensa yarinya karama Zata Birkitasa Gabadaya ya kasa Daina Kallonta Duk abunda take yau Direct yake kare mata Kallo kamar Wani Maganadisu. Kansa ya shafa yana Fadin"Uhmm..Saboda kawai nayi miki Fada..Shine kike Fushi Dani..?shikenan ke baza"ayi miki Fada ba kenan..? Yafada yana Sakarmata Idanuwansa da suka Shanye saboda kallomta Cikin Bakkm yanayin da bai Taba Riskan kansa ba. Sai da takai abinci bakinta ta Hadiye Kana ta Dago Kanta Tana kallonsa Cikin Basarwa tace"Fushi kuma.?ni ba Fushi nake yi ba Fushi kuma ai sai manyan mata da suka san Ciwon kansu Ni karamar yarinya Dani bansan komai ba..Maganar Fada kuma ai ka Isa kamin Fada ko baka da Mtsayin Mijina kai din Yayana ne..! Tafada Lokaci Daya Tana wani Far da idonta kafim ta Dauke kanta. Burauba Imran ya Fada Aransa sanda yaji kamar ya tashi ya Riketa acikin Jikinsa a yadda yake ji Wato yarinyarnan mgana ta gasa mai ko..?illar auran yara kanana kenan wani Lokacin kai da ya kamata ka Zama dan Lallashi kai ne zaka koma kana Lallashinsu suna maka Iskanci Kiri kiri. Ballatana yadda yaga Intee na wannan abun in yace zai Sakarmata Fuska Tsab zata ci Ubansa Hankalinta Kwance shiyasa ya Hade rai aransa yana Fadin Imran ka kama Girmaka ka Daina kallomta hakanan. Da sauri ya Janye idonsa yana wani Dakuna Fuska Lokaci Daya yana Fadin"Better..! Laptop dinsa ya jawo ya Budeta ya Kunna bari ya Fara aikinsa ko Zai Daukemai Hankali Dakai kansa Inda Sauran Girmansa zai Zube Inteesar tabi ta Tattaka. Yana aikin yana Satar kallonta yarinya kamar yar Tsana sai ka Taba katabo ma kanka Duk Tana kallonsa sai dai bata nuna tasan yanayi ba. Saboda Takalan mgana yasa kalleta yana Fadin"Ammh dai kinsan Cin Abinci akan Kujera ba Ladubban cin Abinci bane..Ga Dining in baki son ci anan sai ki Sauka kasa ki ci saman Cafet is ok..! Mikewa tayi Dauke da Filet da Kofi Tayi mika Cibiyarta da Cikinta suka Bayyana Waje kafin tace"Alhamdulillah..Ai nama Koshi..! Tafada tana wani kara bankaro Kirji Ta wuce Ta gabansa kamar Zata Fadomai Saura kadan Laptop din hanmunsa ta Subuce ta Fadi kasa yayi Saurin Tallabowa da Kallo ya bita kafin ya Fitar da Numfashin Daya Sakesa..! Umh....! Yafada afili yana jinjina kai baisan me ya Shiga kan yarinyar nan so take yau ta Kuresa..! Bata jima ba ta Dawo ta Zauna inda Ta tashi Hade rai yayi yana Dakuna Fuska wai kada taga Fuska ta Rainasa ammh gabadaya Hankalinsa baya kan aikinsa yana kan Intee ita kuma ta Lafe Kan kujera Tana ta Muskuce muskuce Tana mikar karya Datake kara Kwancemai kai bata sani ba Gabadaya ya Rasa Natsuwarsa Kuzarinsa na neman Kwacewa Daga Hannunsa dukkan wani Juriyansa da Kaifinsa yana Neman Bashi kunya ayau dinnan. Inteesar Tana so ta Tsokane sa yasa ta gyara Zama Tana Fadin"Ya Imu plz ka kira mai hada Kayan kallo nan su Hada mana ni ina so fa..! Kallonta yayi cikin Dakuna Fuska yace"Anki salon ya Dauke miki Hankali Daga Karatu ko..? Tura baki Tayi Cikin Shagwaba Tana Fadin"To ba mun yi Hutu ba yau..! Yana Kokarin Daidaita kansa yace"Uhmmm!!!! Kamar wanda aka Shake ta Wutsiyar ido ta kallesa aranta tace kadan ka gani baka Rainani ba zaka sha mamaki. Mikewa tayi zumbur kamar wacce aka Tsira Tana Wani Tsalle tsalle Komai na Jikinta na Motsawa Kirjinta suna Shaking suna Dukan juna Imran ya gaji gabadaya Inteesar Zata Tina mai asiri in ya tashi Domin gaban Wandonsa ta Cika Tana Harbin Iska in har Intee taga Girmansa ai ya gama yawo. Cikin Kaushin Muryan Data Shake yace"Miye kuma haka..!? Cikin Shagwaba tace"Wani abu naji kamar yana min yawo ajikina..! Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Mtswww..! Yafada yana Kokarin Daidata kansa Zata koma ta Zauna yace"Kinga koma Daki ki sauya wannan kayan.baki da Hankali ne..?kina mace kina yawo da wannan kayan acikin gida..! Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"To ai gidan Mijina ne ba Haramun bane..! Idanuwansa ya kankance yana Fadin"Eh ba Haramin bane Shedanu ake gudu..Ki rika Suturta Jikinki..,! Inteesar Dariya ke cinta ganin yadda ya Fittike yana Fada kamar wani Laifi Tayi so take ta samu Sarari ta Saki Dariyanta Son Ranta yasa ta Mike batare da tayi mgana ba ta Wuce Zuwa Dakinta Da kallo ya Bita Cikin Kokarin Matse Kafarsa Dayajin wani abu na Shirin Zubomai kamar ma Fa yana jin wani Zur zur ne ya rasa ma gane kansa. Ai yana ganin ta shige ya Mike yana duba kansa Ajiyar rai ya Sauke ganin yadda gaban Wandonsa ya Kumbura kansa ya Dafe yana Fadin"Meke shirin Faruwa Dani ne..? Yake Fada kafin yayi karamin Tsaki ya Kwashi kayansa zuwa Cikin Daki Alwala ya sake Domin ta Baci ta Farkon Sallar Isha"i yayi aransa yana Fadin Zaman falo ya Haramta garesa in yana son ya Tsira da Mutumcinsa in ba so yake Inteesar tayi Wansharere da adekon Mutumcin nashi ba. Ita kuwa Inteesar tana Shiga Dakinta ta Zauna sai Dariya take kwasa sai da ta Duka harda rike Ciki a Fili tace"Yau ina ma Munari na nan..?taga Mazuran idon da yayanta yake yi gaya Manyan kaya a wajen karamar yarinya..! Sai da ta ci Dariyanta ta Koshi kana ta Tashi Da alwalanta baki ta Kuskure ta zo Tayi Sallah da Hijabin Sallar ta Fita Falo Taga Wayam a Ranta tace"Zan Biyo ka har Dakin ne Mijina..! Kayan Dining din ta kwashe zuwa Kitchen ta Daureye wanda suka bata Kwanukan Sauran Naman ta Saka Cikin fridge da duka sauran abincin Kafin ta baro Kitchen din. Daki ta koma ta Sake shiga wanka Tana Fitowa ta Tsane jikinta ta Fara Bin Kowani Kusurwa na Jikinta da Turaren Humran da Umma ta bada na Musamman ne aka Hadamata Inteesar ta Shirya kara Rikita imran Saboda Wata arniyar Rigar barci ta Dauko Cikin Wanda Goggo Maimuna ta Hado mata ne acikin Lefe. Rigar pick ce mai Haske Shara Shara ce,daga gabanta kuma Tana Bude ne sai dan Kokon Breziya Daga Sama yadan Tare hannun Vest ne gareta kuma da kadan ta Rufe mata Cibiyarta. Pant kadai ta saka bata ma Saka Bra din ba,ta juya ta kara Juyawa Tana kallon kanta ta Mudubi Gaskiya Da kunya Taje haka sai ta Dauki Zani ta Daura Saman Rigan ta Cire band din kanta Ta dan baza gashinta,Sai kuma Tayi wani Tunanin Zanin ta Cire Sai da Ta gama Daidaita kanta Kafin ta Fito Tana Sanda ganin baya Falon yasa ta Danyi Tsalle tana Fadin"Yes...! Kofar Dakinsa taje ta kara kunnenta sai taji kamar yana Waya komawa Tayi Kofar Bedroom dinta Ta Kwso Gudu da karfi Tana Fadin"Ya Imu..Wayyo Allah Dodo..Mai Buzuzu..! Take Fada Har da kukanta kafin taTura Dakin nasa ta shige da Sauri Lokaci Daya tana Waige waige Cikin Tsoro da Firgici Imran Dake Zaune yana Waya yayi Saurin mikewa Cikin Tashin Hankali da Khalil suke mgana yasa yayi Saurin Datse kiran ai bai gama Daidaita Tunaninsa ba yaji ta Kikam ta Fado Jikinsa tabi ta kanannyesa Tana kuka Tana Fadin"Wayyo Ya Imu..Wlh Dodo a Dakina..ya biyoni..! Tafada Tana Fashewa da kuka kamar Gaske acikin Kirjinsa Shima kara Riketa yayi yana jin yadda Gabadaya na Shanunta suka mai Rumfa a saman Kirjinsa. Cikin Mganarsa yace"Dodo kuma..? Inteesar na kukanta tace"Eh Wlh yana chan adakina ta Wajen madubi mai Buzu buzu..wayyo..!ka Boyeni..! Take Fada Tana kara Shigewa Jikinsa da karfi Kokarin Rabasa da Jikinsa yake yi taki yarda sai kuka Take tana Fadin ta shiga uku mai Buzu buzu zai kamata. Kanta yake Shafawa yana Fadin"Shii...Daina kuka muje na ga Mai Buzu buzun..! Ya fada yana kokarin Dagota Dakyar ya Samu nasaran Dagota ba Hawaye ammh Tana ta bare baki Riketa yayi yana Fadin"Bakomai fa..Muje mu nagani..! Yafada yana kama hannunta kamar gaske tabisa sun Fara Tafiya ta Daka Tsalle ta Dane Jikinsa da karfi Tana Fadin"Wayyo Ya Imu ga yi nan..Ga shi nan..! Take Fada Lokaci Daya suna Fadawa Saman gadon Tunda bai saka ma kansa karfi ba baisan Zata fadomai ba Sai gasu Malale kan gado Inteesar na Kwance Dare Dare kan Jikin ya Imu Gashinta ya Rufe mai Fuska yana kokarin Dagota tana kara Kamkamesa Tana Fadin"ka Boyeni ina jin Tsoron kada ya kamani..! Take Fada Cikin Shagwabarta,Gabadaya ta gama Jikamai aiki duk wani Dauriyansa da Tanadinsa ya rasa jinta acikin Jikinsa Tana Kara Dagulamai Lissafi. Duk yadda yaso ta Sakesa taki sai ma kara Rikesa da take yi Nonuwanta sun gama Mai maraban Tattausan Fatanta ta gama Kadasa Kamshinta ya gama Birkitasa duk da A"a da wata Zuciyar ke Fadamai bai Sauraresa ta ba ya Saka Duka Hannuwansa ya Rumgume Inteesasar kamkam Lokaci Daya yana Fitar da Sautin Numfashi Waje. Wani yanayi ne da bai Taba Tsintar kansa ba ya samu kansa aciki Hannunsa yasa yana shafa gadon bayanta zuwa Tudun Hip dinta yana dan Murzwa kafin yayi sama da Hannunsa yana Wasa da gashin kanta Lokaci Daya yana Tusa kansa Tsakanin Wuyanta yana Sakin mata nishi da karfi Tsorata Tayi da Rikon da yayi mata ta fara Kokarin Tashi Daga Jikinsa yace baisan wannan ba Tana Dagowa ya Samu Bakinta ya Cafke Daga saman Lebunan yake ma Wani Tsotsa da zafi Zafi kamar ya Samu wani Tom Tom. Da karfi yake mata Shiyasa take jin Zafi Zafi Tana kokarin Kwatar bakinta ya samu nasaran Tusa Harhensa da karfin Tsiya ya fara Juya Harshenta Cikin Kwarewa da Muradi mai Girma. Gefe Daya yana rike da ita da karfi yana Shafa duk inda Hannunsa yakai a Gaggauce kamar wani mayimwacin Zaki Lokacin da Hannunsa yakai Kirjinta Sai da yaji yace"U...mmmmmmm....! Acikin Bakinta bai sani ba Saboda yadda Yake Shafasu ta Cikin Rigar basu Gamsheshi ba yaja Hannun Rigar ta Sabule lokacin da Fatan Hannunsa ya shafi Fatan na Shanun nata Gabadayansu sai da sukaja Nunfashi kamar wasu wadanda Shooking ya kama."Hmmmmmmmm...!!!! Kokarin Kwace bakinta take yi ya kara Riketa ya Matseta cikin Jikinsa ji yake kamar in ya Saketa zai Mutu Daga kasan sa kuwa wani abu ne kamar Sandar rake ke ta Harbin Cinyoyinta Inteesar ta fara Raina kanta da inda ta kawo kanta yau Dadi dadi take ji Jin yadda yake Murza Kirjinta Cikin kwarewa da batasan Sadda ya Juyata ba ta dawo kansa ba Sai ji Tayi kawai ya Zare bakinsa cikin bakinta Da ya bata Damar Sakim Nishinta"Hhmmm...Shi kuma yana wani Karkar da jikinsa na rawa ya Kafa Bakinsa a nononta Guda Dayan kuma Kifa Tafin Hannunsa yana Murzasa Inteesar ta Fara Mutsu Mutsun jinta a wata Duniya kanta take Girgizawa kamar Mahaukaciya Tana Fadin"Uhmm...Uhm..Ya...Imraaaannnn...ka...ba..ri...! Take Fada kamar Fitan Hayyaci shi kamar ma karamai kaimi Take jikinsa Rawa yake yi lokacin Dayakai hannunsa kasanta yana shafawa Pant din ya Zame mata bata sani ba,shi ma Da Sauri ya Cire Bakinsa kan Nononta Lokaci Daya ya Cire Rigar da Wandon Dake Jikinsa Duka Sandar Girmansa Data gaji da Hayaniya ta bayyana Tsaye kamar taci Babu Inteesar bata Gama Fita Daga Dadin sucking din Da yayi mata ba taji ya Daga Kafafunta sama kan Wuyansa kafin ta dawo Hayyacinta ya Tusa kansa ya Kafa kansa a wajen yana Tsotsa yana Zukowa kamar yana Zuko wani abu aai sai taji kamar Zata Mutu Ihu ta Kwala Tana Fadin"Ummmmma....! Tana Harba Kafafunta ammh ya Riketa sosai gashin kanta Ta Rike gam Tana Fitar da Numfashi sama sama kamar mai asma. Sai da yaga Ta gama Saki gabadaya Wajen yayi Danshi Sosai yana Aman ruwa yasa ya Ssketa ta koma Sharaf kamar kayan Wanki bata da wani karfi Daidaita Girmansa yayi ya Saita goga mata ya Farayi kafin ya Fara Laluban Hanya Lokaci Daya yana addu"a wannan Zafin Laluban ya Dawo da ita Daga Cikin Hayyacinta ta Zabura Zata Mike ya maidata ya Danneta yana gurnani ta Firgita ta tsorata da jin Iccen dake Zungurinta kamar Za'a gayamata gaba Dagowa tayi da karfi Ta Sakarmai Cizon Azaban Dataji a Damtsen hanmunsa da karfin dayasa ya Saketa da karfi yana Fadin"ouchhh...! Ai Da tana jan jiki ta Turesa Daga kanta ta Diro Daga kan gadon da karfi Har sai da Kafarta ta amsa bata Tsaya ma Jiran wani abu Tana kokarin rike Rigar barcin Dake neman Faduwa a Tamamin ta bar Dakin zuwa nata Dakin Tana shiga ta Murza key Tana Maida Numfashi kan gadonta ta Hau ta Kwanta tana Fashewa da kuka jin yadda gabanta ke Radadi kamar Reza ya yankata. Shi kuwa Imran baya Cikin Hayyacinsa Lokacin Da Inteesar ta Fice Shiyasa ya Mike ba kaya ajikinsa yana Rangaji ya Rufamata baya Koda yaje ta garkame Dakinta Bugawa yahau yi kamar Zautattace yana Fadin"Inteesar kiyi wa Girman Allah ki Bude..Zan Mutu..Ki Bude ki Taimakamin ko sau Daya kada na Mutu..! Yake Fada yana mata magiya Batare Daya sani ba kuka yake yi Yana Rike Girman nasa Dake neman tsinke kanta ga Maransa Daya Tamke Waje Daya. Inteesaer tsit tayi tana jin Abun da ya bata Tsoro kuka fa..?wai ita Imran kema ma kuka yana magiya..?innalillahi..? Haka take Fada Tana Toshe Bakinta Kada yajita,Imran Kuka yake yana magiyan Inteesar ta Taimakesa Tayi mai Biris ita kanta ga Tsoro ga azaban Da kasanta ke yi yasa ta kasa ma wani Motsin Kirki. Nan ya Sulale kofar Dakinta yana Kiran sunanta Maransa ta kara Turnikesa ya koma yana Fama da kansa Mikewa yayi sai alokacin ya Fara Dawo Hayyacinsa ganin ayyada ya Fito Saurin komawa Daki yayi yana jan Kafa Kai Allah ya Taimakesa yau daya Tafka abun kunya inda Inteesar ta Fito ta gansa ahaka da Girma ya Fadi. Tiolet ya Shige yayi wanka ko Zai Samu Salama shima ba Sauki Taune Lips dinsa kawai yake yi shi kadai yasan Halin Dayake Ciki ya Dade yana Danne Abubuwanan ba Saboda komai ba sai Saboda bai Shiryama zuwan wannan Ranar nan kusa ba sai gashi Inteesar ta bata komai ta kuma saka komai ya Faru a alokacin da bai shirma hakam ba. Yana Fitowa a Daddafe ya saka Boxer ya koma ya Kwanta jin maransa ta Cire Waje Daya in ba Fitarwa yayi ba bazai samu sukini ba yana Kwanciya sai Zazzabi nan da nan ya Fara Rawan sanyi yana Hada Hakora imran ya Dandana Gudarsa a wannan Daran Barci sai dai Barawo ne ya Sacesa da kuma ya Sacesa azaban Ciwon mara Zai Farkar dashi ga bamai Mataimaki sai Allah yanaji ana Sallar asuba ya kasa Tashi ballatana ya Taimaki kansa sai Da gari ya waye ya iya Rarrafawa Zuwa Tiolet yayi wanka ya Dauro alwala ya Saka Jallabiya a Zaune yayi Sallah Yana yi yana Dukewa kafin ya Sake Cire Jallabiyan Dagashi Sai Boxer ya koma ya kwanta yana Rike da maransa yana Birgima Bisa gadon. Inteesar batasan Halin dayake Ciki ba ita kanta sai ta gasa kanta ya Fara Ji mata Rauni Itama din Dakyar barcin ya Kwasheta ga Raki ga Tsoro. Itama ta makara batayi Salla kan Lokaci ba Ta koma ta Kwanta abubuwwn da suka faru suna Dawomata Daki Daki Ya Imran na kuka yana Rokomta Tabdijam..Daman abun akwai Zafi Wlh inda tasan hakane Da bata Fara ba Ta gwammace su zauna haka har Abada ta Zata iya Dadin Tabe Tabe ne Dan Romancing din da yayi mata Jiya Ashe akwai babbar harka..?ita kam baza ta koma ya Kasheta ba. Yunwa ce ta Fito da ita Daga Daki Ta Zata ya Fita aiki Kitchen ta Shiga Ta Dafa Ruwan Zafi tasha Tea kadan Jikinta Duk ba Dadi. Tazo Shigewa Dakinta taji kamar Nishinsa Daga Ciki sai ta Dawo da baya ta kasa kunni sai ta karajin Nishi Sosai Tsorata tayi da batasan ta afka Dakin ba yanayin Data gansa Kwance kan gado yana ta Mirgina Rike da maransa yana Gurnani da Nishi Da gudu ta karisa gabansa Tana Fadin"Innalillahi ya Imu..?meke Damunka na shiga uku..,! Take Fada Tana Rikosa Muryanta Dayaji kamar abun yama karu ne Tana Rikesa kamar ta karamai Ciwon nema ya wani Mirgino Gabadaya Lokaci Daya da ita Jikinsa bai Tsaya Jirantaba yayi mata Rumfa Cikin Azaba yake Fadin"Ke kika Fara..Kuma ke zaki Karisa..! Tana so tayi mgana ya hanata ya Kannayeta da Bakinsa gefe Daya da Girman Jikiinsa ba Hanyar Tsira Duk iya Kokarinta ta kasa kwataan kanta ta Riga ta Sadakar Yau ba Hanyar Tsira Domin yau din ba Imran bane wani ne Dabam ya juyemata kamar wani Zakin Daya yi kwanaki bai samu abinci ba.haka yake juyata yana Sarrafata cikin Sauri da Gaggawa Cikim Kosawa da Fitar da rai Cikin Rauni da Fitowar wani abu Daya Gallabesa. Inteesar batasan aWata Duniya Take ba Sama Sama taji yana karanto addu"ar Saduwa da iyali bata da Wani tsumi Ballatana Dubara shima bai isa ya Dakatar da kansa Fadamata ba ssi dai ya samu Turjiya sosai kafin ya Samu Shiga bayan ya sakamata Karfin da in Cikin Hankalinsa ne bazai sak mata shi ba. Lokacin Dayajisa ya shiga Cikin Tsudum Ya salam kawai ya Furta Zufa na karyomai,sanda ya Fara kai da komo aciki kadan ya Rage bai Zare ba Sai kuka Hawaye Share share Inteesar ma kukanta Take Na zucci Tunda Bakinta ma ya Rufe Saboda azaba Imran kuwa Tun yana iya Gurnani da kukan Boye Har baisan sanda ya Wage Murya yana Kukan Gaske ba Ihu sosai yake kwararamata da guranina da sumbatun da ita bazata iya gane ma kowani yare bane illah yaran Murza da uban Wahalan Datake ci hannun Maza,Domin gabadaya sai da ya juyemata wannan nauyin maran nasa da Duka Ruwan da ya Tara Shekaru Talatin da suka gabata ya Share Mintina Talatin da wani Abu yana kai komo kafin Komai ya Tsaya Lokacin Daya Jisa ya Samu Cikakken Natsuwar da bai Taba Samu ba Tunda yazo Duniya ba.. Kanta yafada Yaraf kamar wani kayan Wanki Numfashinsa ne kadai ya Tabbatar da Ransa Bata iya Motsa ko Hannunta kan Nauyin daya Sakarmata Ya Toshe mata Hanci da baki yasa Cikin Muryan da bata Fita Tace"NUMFA...SHIIII...Na...!!!!! Take Fada da Dishashiyar Muryanta Data sha kuka ta Dishe Saboda azaba da karban bakon Lamarin da ya Girmeta alokacin da bata Shirya ba. *Shakira..* 3/30/22, 08:48 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�28* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Kwata kwata bai jita ba Saboda har zuwa lokacin bai gama Fita Daga Cikin Duniyar da Inteesar ta kaisa ba,Duniyan nan da bai Taba Tunanin akwai Wata Duniya bayan Duniyan da suke ciki ba Yana jinsa kamar yana yawo acikin gajimare ne Dadin na Ratsasa har alokacin bai Dawo Cikin Hayyacinsa ba Shiyasa bai ji sanda Inteesar ke faman kokuwa da Numfashinta ba. Mutsun mutsun kwatar kanta Take yi Saboda Numfashinta Dake barazanar Fita Daga Jikinta,yasa ta kara Fadin"Numfashi na...!!!! Cikin Dashashiyar Murya, Data sha Wahala,kamar acikin mafarki haka yajita Daga sama,sai da yadan kara Saurarawa sannan ya kara jin muryanta Cikin galabaita da Fuzgar Numfashi Tana Kara fadin"Numfashi na...! Da Sauri ya Dago Rikitattun Idanuwansa ya sauke akanta Lokaci Daya yana kamota zuwa Jikinsa Cikin Kasala da Muryan kuka yake Fadin"Inteen..Inteesar..! Yafada Cikin wani yanayin Fitar Hayyaci,gabadaya sai taji kamar barkonu Daga kasanta Sanda ya Dagota shiyasa ta saki Karamin kuka Cikin Muryanta da bata Fita Saboda Azaba sai alokacin ya Fahimci A inda yake Kwance Dare dare kan Jikinta Da Sauri ya Dagata yana Rawan jiki,bai ma Cikin Natsuwarsa yasa ya Diro Daga kan gadon yana Binta da kallo Daga Samanta Har kasanta ganin yadda gadon gabadaya yaHargitse kamar an yi wasan kura akai Ita kanta Inteesar din Imran sai da yaji Faduwar gaba yadda yaga ta Koma kamar bata da Rai Numfashin ma a Wahale take Fitarwa Saboda azaban Datake ji Tana so tayi kuka ammh kuma Muryanta ta Dishe sai da na Zucci Hawaye na Bin Gefe da Gefen Idanuwanta. Boxer dinsa ya Raruma ya saka Jikinsa na Rawa Cikin Rashin Natsuwa Dukawa yayi a gaban gadon yana kallon Inteesar sai alokacin ya Fara Fahimtar aika aikan daya aikata Cikin Fitan Hayyaci Da Rashin Sani. Hannunta ya Riko Shi kanshi Jikinsa ma Rawa yake yi Ganin yadda Hannun yayi Sanyi kuma ya saki kamar gawa yasa ya Firgita ya Tallabo Fuskarta da Duka Tafukan Hannunsa Cikin Rawan Murya yake Fadin"Inteesar..Inteesar..MARYAMA..! Yake Fada Cikin Rawan Jiki da na Zuciya Dakyar ta Bude Kumburarrun Idanuwanta tana kallonsa kafin ta koma Ta Lumshe Tana jin Kirjinta na Suya K'ishi Take ji kamar wacce ta Shekara bata sha Ruwa ba Ganin ta maida idon ta kulle ne yasa ya Fara Bubbuga Kumatunta Cikin Rudani yana Fadin"Kinga..Bude idonki..Plz ki Taimakeni..Kinsan fa bansan komai ba ban Shiryama wannan Ranar ba Wlh bansan haka Zata Faru ba Ki Taimakamin Maryama ki Bude idonki ki Fadamin Wani Abu zanyi..?ta ina zan Fara..?Taya Zan Taimake ki..? Yake Fada Cikin Fitan Hayyaci Lokaci Daya yana Bubbbuga Kumatunta Inteesar Ga Raki ga Shagwaba ga Ragwanta Duk da Imran ya Farmaketa Lokacin da bata Shirya ba yaji mata Rauni Rauni irin wanda kowani Cikakken Namiji yake Jima Matarsa ta Sunna Datakai Budurcinta Dakinta. Sai dai ita abubuwan sun Hade mata ne yasa take kwance yaraf kamar Wacce aka Ciroma ya"ya Biyu,ko kuma Wacce Ta kwana Goma Tana Naguda Lokaci Daya ta Fita kammininta Jin abunda yake fada ne yasa ta Bude ido Tana Fadin"Ruwa..Ruwa..! Tana Cije Bakinta Daya Bushe jin Abunda tace ne yasa ya Kwashi Gudu ya Fice Daga Dakin kamar zai Kifa,Da Idanuwanta da sukayi mata Nauyi ta Bisa da kallo,Tana so ta tashi Ta Taimaki kanta ta kasa saboda Tasan Inran bai san komai ba kuma ta Tabbata baisan ta yadda zai iya Taimaka mata ba. Duk da bata Taba Zato ko Tsammanin haka Daran Farkon yake ba,Tadai san Mata suna shan Wahala ammh bata Taba Kawo ma kanta Wahalan Har takai irin wanda taci yanzu hannun Imran ba Duk da bata karance karance ammh Lokacin suna Islamiya Tasan Abubuwan addini sosai takuma san yadda Mace Zata Taimaki kanta in Miji ya Risketa adaran Farkonta Shima din irin adan Labarin kawaye Sama sama tasan haka. Dakyar ta iya Mike Zaune Tana Cije Baki Tana Wayyo Wayyo Hawaye na Zubomata ji take kamar an Saka mata Barkonu a kasanta Tsoro Taji da taga Jini jini Duk ya bata zanin gadon Har ya Fara Bushewa a wajen Kafafunta Inteesar Ta Fashe da kuka kamar wata karamar yarinya Daidai Lokacin da Imran ya dawo Dakin Cikin Hanzari kamar zai Kifa Dauke da Goran Ruwa mai Sanyi da Karamin Cup. Yana Daga Tsayen ya Bude Goran Ruwan yana Tsiyayamata Cikin Fitar Hayyaci yake Fadin"Plz Stop Craying.ya zan yi in kina wannan kukan..? Yake Fada shima kamar zai yi kukan gabanta ya Dauke yana Riko kanta Da hannu Daya Hannun Dayan kuma yana bata Ruwan da Sauri ta Karbe ta Shanye ya Kalleta yana Fadin"More..? Kai ta gyadamai da Sauri ya Tsiyayamata again ya bata sai da Shanye Duka Sannan ta koma tana Sauke Numfashin Wahala da azaba sai Kuka kuma Imran Zaman Dirshan yayi agabanta ya Dafe kumatunsa Cikin Tagumi yana Fadin"Ya zan yi..?kina wannan kukan duk Rudani kike yi Inteesar..Ki Fadamin dame zan Taimaka miki ni bansan komai ba..! Yake Fada yana kallonta Inteesar ta Kauda kanta Cikin wani yanayin da ita Kadai ta san yadda take ji. Ta rasa ta ina zatayi mai bayani ma ya Fahimceta Shi kuma Sai yau Rana ta Farko Daya Fara jin Haushin kansa da bai Damu da sanin wasu abubuwan ba,Gashi yau Rana tazo mai Rana mafi Muhimmamci da Tarihi a Rayuwarsa baisan komai akanta ba Yau din yaji Takaichin kansa Takaichin yadda ya Zama Careless akan komai Wazai kira da zai Taimaka mata..?shi Mutum ne mai Sirri bayaso wannan al"amarin ya Fallasa ba Domin kowa ba sai Domin wannaan abun wani Sirri daga Cikin Manyan Sirrikan Rayuwarsa Kukan Inteesar ne ya Damesa baisan Sadda ya Mike ya Zauna Gefenta ba ya Tarairayota Jikinsa Tana Wash da Kuka ya Rumgumeta kamkam kamar Zai maidata jikinsa cikin Farinciki da Annushuwa Suna bayyana Saman Fuskarsa bazai taba mantawa da wannan Duniyar da Inteesar ta kaisa ba shiyasa ya Zage yana ta Saka mata albarka da Kalmar Godiya sai ga Imran Abubakar Malami bai sani ba bai kuma san ma kila yanayi ba ya Tarkakare yana ta Lallashin Inteesar da ban baki da ban Hakuri Tunda yasan shi ne yayi Laifin Hadawa yake da Duka Baiwarsa da Kalamansa Wajen Lallashinta abaya yana Fadin bai iya Lallashi ba sai gashi kalaman na Fitowa Daki Daki kamar Daga Kwanyansa batare Daya sani ba Daman ai Sagir da Khalil sun ce Ranar Lallashin batazo bane Imran daman wannan ne Ranar..?tabbas in dai Domin wannan Koramar Dadin ce ba Lallashi ba ko Kwanciya Inteesar Tace ya Rikayi Tana Takasa sai ya Kwanta Indai Zata Cigaba da Kaisa wannan Duniyan komai take so a wannan Duniyan indai bai fi karfinsa ba ta Samu ta gama. Dakyar ya samu ta Daina kuka da ban baki da komai ya samu ta Fadamai yadda zai Taimakamata Tana kuka Tana Turamai baki da kunkuni Duk yaji kuma ya Dauka,Da kansa ya Shiga Tiolet ya Hadamata Ruwa mai Zafi kana ya zo ya Dauketa Ya kaita har Cikin Jaccuzi din Inteesar Dataji Ruwan Zafi na Shigarta ai sai ta yanka Ihu Zata Fita ya Riketa sosai ya Dannata yana Shafa kanta Cikin Rarrashin da ya iyashi yanzu nan kuma ya Haddaceshi Har yana waniHura mata iskan bakinsa ganin yadda Take Zufa. Da Kuka da majina da Ihu Harda Duka Haka Imran ya Jure kafin ya gama Taimaka mata ta gasa kanta inteesar bata lura da Naked take ba sai da tadawo Cikin Hayyacinta Dafe Kirjinta Tayi da Hannayenta Tana Kallonsa da Jajayen Idanuwansa Tace"Ka Fita zan yi wankan Tsarki..! Imran ya Kalleta Cikin Rinannun Idanuwansa,cikin Sha"awa da Burgewa da soyayyarta Data gama Tsumasa bai ce mata komai ba Tunani yake yi Tunanin abunda ya Faru Mintina kalan da suka Shude yajisa Sakyau kamar an saukemai Nauyin Daya Dade asaman kansa wani Sakayau yake jin kansa kamar Jaririn Da aka Haifa yau. Yasan in yace bazai Fita ba Rigima ce kawai da Kuka to ya ya iya..?shi ya Tabo ma kansa Inteen Daddy yar Rigima yar Shagwaba Dole yayi Hakuri Fita yayi Daga Tiolet din yana Dariyan Nishadi aransa yana Fadin Daga baya kenan ganin yadda take Danne Kirjinta saboda kada yagani Yo shi da yagama ganin komai Har suka sha Tsotsa da Murza son Ransa To ita kanta ai ta Karbi Murzan Daga Hannunsa. Shi kanshi ya Firgita da Jinin Daya ga ya bata Zanin gadon Saurin yayeshi yayi ya Dungule wai Saboda kada Ta gani baisan Tana gani ba yama raasa Mafita saboda baisan komai ba Bata jima ba sai gata ta Fito Daure da Towel Tana Bin bango kanta ya jike da Ruwa yana Diga da Sauri ya Kariso Gareta Zai Riketa ta Shagwabe kamar Zatayi kuka Tana Fadin""Ni ka kyaleni..! Tafada sai Hawaye baya yaja yana Daga Hannunsa alamun yayi Saranda yace"Na kyaleki..! Yafada yana kallonta baki ta Tura Tana Jan Hanci da Tale kafa kamar Wata yar kaciya ta wucesa Batama Tsaya Daukan Rigarta Dake yashe a kasa ba wacce Imran yayi Gumurzu da ita,neman Hanyar Fita Take Daga Dakin yayi Kasake yana Binta da kallo Tafiyarta Kadai abar Dariya ne dayasa baisan Dariyansa Har ta Fito ba Tana gabda Fita Taji Sautinta Dariyansa ta Waigo Tana Kuka Hawaye Shabe Shabe tace"Eh ai kayi min Dariya..Tunda kamin mugunta..Ji yadda nake Tafiya dna Taka Kafata sai naji Zafi kamar Zan Mutu..! Kawai sai ta Fashe da kuka da Sauri ya Karisa gareta Ya Rumgumota jikinsa Tana Dukan Kirjinsa cikin Shagwaba da Raki Tana Fadin"Ni ka kyaleni..bayan kamin mugunta..! Take Fada Tana Tsiyayan Hawaye,Shidai bai da ta cewa Ya Matseta acikin Jikinsa bai bata Damar kara wani Motsi ba yana Fadin"Am so Sorry..Kanwata. Ba Laifina bane ba ke kika ja ba..! Yafada shima cikin Muryan Shagwaba da wani Sanyi Inteesar bata isa ta bijirema wannan Lallashin ba Dole ta Lafe ta Cigaba da amsan Sabon Karatun Imran da acikin Ranta Take Mamakin Daman ya iya..?Ko yanzu ya Koya..! Duk yadda taso ta Zille Hanata yayi,Dakinta suka koma ya kanannadeta,shi ya shafamata mai ya Saka mata Wata Riga iyakarta Gwiwa mara Nauyi,Sannan ya kwantar da ita Har Lokacin sai jan majinan kuka Take ba Hawaye Agurguje yaje yayi wankan Tsarki,Zanin gadon kuma ya Jefa Cikin kwandon wanki,Ya bude Wardrope dinsa ya Dauki wani Zanin Gadon ya Shimfida sama sama a karkace shi kuma ya saka riga da wando Yana Sauri gabadaya Hankalinsa na kan Inteesar Koda ya koma Dakinta Barcin ya Fara Fizganta Wayarta ya Dauka ya Shiga Goggle yayi Research din yadda Zaka kula da Macen da akayi Disvirging dinta nan yaga Mataki mataki na yadda ake Basu Taimakon gaggawa bai Tsaya ya koma Dakinsa ya Dau key din Mota ya Fice Daga gidan phamarcy yaje ya siyo mata maganin Rage Radadi,Koda ya Dawo ta Farka Bata gansa ba Sai kuka Zaman Lallashi ya karayi Dakyar tayi Shiru daya nuna mata Mganin Dayaje siyomata,Tea ya je ya Hado mata mai Kauri ta sha ta Hada da mganinta da panadol ta koma ta Kwanta Tana Murza ido.. Ba Jimawa Barci ya kwasheta,Sai alokacin Imran ya samu Natsuwa ammh fa kanta na kan Cinyarsa shi yana Zaune yana Shafa kanta ai shi Ko alaman barci bayaji Farinciki Da Annushuwa sun gama Cikamai Ciki Uhm tuna yanayin kadai in yayi sai Tsikar Jikinsa ta tashi yana jin kansa ya tashi Daga Imran ya koma Cikakken Imran babban Mutum Daya Tanadi Duka jin Dadin Duniya Inteesar yar albarka ya rainata yana ganin bazata iya dashi ba sai gashi ta bashi mamaki Ta Daukesa Tsab Ta kima Shayar da shi Zumar da bai Taba Tsammanin akwaita acikin wannan Duniyan ba Wlh inda yasan haka auran yake in ya Zubamata ido Shege yake da Tuni ya Dade da Shiga koraman nan yana Ninkaya Irin wannan Ni"ima haka ai ba"abun ya Tsaya wasa bane. Inteesar ta sha barci sai Chan da Rana Ta tashi bayan Sallar azahar,Shima Imran barci ya kwashesa alokacin Kukanta ya Farkar dashi taji Sauki fa Ammh Inteesar sai Bullo da Tabara Take Kala kala Ranar Imran Ko Sau Daya bata barsa ya Huta ba Daga tace wannan sai tace wannan tace ya Dafa mata Taliya ita Zataci bai iya komai ba ya rasa ya zai yi kuma tace bata son na Siya Imu kamar zai yi Hauka Ba Halin korafi Tunda shi yaja kuma Har ga Allah in yanzu ta bashi Dama fa komawa zai yi. Dakyar ya Lallasheta ta yarda ya Fita yaje yayi mata Takeaway din Jallop din Taliyan da Kifi sai Ferfesun Kayan Ciki Da kuma ya kawo mata kadan Taci ta Ture Kayan cikin ne ma taci kadan ta koma ta Kwanta ajikinsa in kuma ya Tabata ta Fara Kukan Shagwaba wai ya Daina Ta bata Hakuri yake bata ya Maida Hannunaa Saman Kirjinsa ya Harde. Ranar bai je aiki ba,Sako ya Turama Mr Sulaiman cewa bai da lafiya to ai kamar shi ne bai da lafiya Tunda shine mai jinyar Wuni Zungur guda Imran na Faman jinya da Lallashi ita kuwa da gayyar take kara Narkewa Tana jin Dadin yadda gabadaya ya Susuce akanta su Mrs Imran manya Ashe dai an iya Lallashi da ban baki. Rana Ta Farko Tun bayan Tarewarsu suka kwana Daki Daya Saboda Jinyar Inteesar Tana da kwance sai ta Shagwabe tace Ruwa sai ya Dauki mata tasha ya koma ya zauna sai tace kaza kaza..Gajiya yayi ya kamata ya Rumgume kamkam Duk da Rigiman Datake yi yasaketa ya Kashe musu Hasken Dakin yace ta Kwanta Tayi barci hakanan shima tayi ma wa Allah ta barsa ya Huta kana ta yarda Domin har ga Allah tasan ya Wahala Kwata kwata Wahala da ita bai barsa ya Zauna ba ballatana ya Huta. Washegarima bai je aiki ba Domin Dayace ko zai tafi ne Tunda yaga Inteesar din Taji Sauki Ai sai ta Fashemai da kuka Har su Birgima Dole ya Fasa zuwa ya Zauna yana Faman Lallashinta sai ya koma bata Tsausayi bai iya ba komai yake yi karfin Hali kawai yake yi bawai Domin shi din ya saba ba ko kuma ya iya din ba Shiyasa Tunda taji Sauki sai ta Sassautamai Tunda Tana Shiga Ruwan Zafi,Radadin ya Ragu sai dan Abunda ba"a Rasa ba,Kwana Biyu baya Zuwa aiki Yana Faman Jinyar Yar Rigima Inteesar ya yarda ma kansa Ranar da zai yi Lallashin bai zo bane yanzu Daya zo ai baimasan yanayi ba. Arana ta Uku ne ya Fita aiki Tunda Inteesar din ta Warware ita tace yaje Ganin Har Tsausayinsa Take ji wani sonsa na kara Shigarta komai tace mai da Gudu jikinsa na rawa bawan Allah Ko Ihun Taji yanzu Zai Fara"Am Sorry nine ko..?plz kada kiyi kuka kinji..! Haka yake fada Saboda bayason kukanta Tagama Lura shi kanshi Lallanshin bai Saba ba Wahala Hakan ke basa ganin ta Ji sauki yasa tace ya tafi aiki ammh Tunda ya Tafi baida Natsuwa Bini Bini ya Kirata"Intee...Yaya kike ji..?kin Tabbata u are ok..? In kina jin wani abu ki Fadamin am so sorry ba Laifina bane..! Haka yake ta Fada sai da Ta kwantar mai da Hankali Bayan ta Tabbatar da Tana Lafiya kana ya Samu Natsuwar yin aiki. Sai aranar Inteesar ta samu Daman Kiran Munari sukayi mgana Inteesar bata Bude mata Duka ba Tunda Sirrinsu ne kuma yayanta ne akallah Zata kallesa da wani abun Munari Taci Dariya mamaki ya kamata jin Ya Imu ya iya Lallashi Har da su Rashin zuwa aiki kwana Biyu yana jinya Lall aiki ya samu inda ake Nemansa Shakiyanci Ta Dingaa ma Inteesar wai Daman anyi Hutu sai suci Amarci son Ransu Inteesar ta Kashe Wayarta Tana Durama Amarcin Ashariya ina Zata yarda ya kara..?irin wannan azabar Daya Gana mata ai an gama Har Abada ni ko nace kin yi Kadan Domin Tunda Mr Imran ya Dandani wannan Gardin na Tabbata Mutuwa ce kadai Zatayi iya mai katanga da wannan Wajen. Ta Kira Umma suka gaisa Umma ta kara yimata Nasiha,kana ta Kira Daddy suka gaisa,bayan shi ta Kira Yaya Basheer suka gaisa da yara da Anty Hauwa Ranar Zumunci Tayi ta yi Ta Kira Har su Ya Sadam da ya Sa"id suka gaisa. Wuni Tayi barci Tunda Imran yace kada tayi wani aiki Shi ya siyi musu abinci da zai dawo Daga aiki sukaci Tare Salloli ma Tare suke jan jam'i acikin Gida,Inteesar ta Riga ta Firgita da al"amarin Shiyasa ko Tabata Imran yayi zata Fara kuka Ranar yaso yadan Koma ai batabari ba ya Fara Wasannani da ita ta Fara kuka Da ga baya Ta saki jiki itama Tana Karban Sakon,Da Tafiya ta mika ne ta Fahimci inda ya Dosa ta Tuburemai Dole ya Kyaleta ammah a Rana ta Hudu bai Daga mata haka fa kamar Ranar Farko Haka ya Ritsata bata zata ba ya Kara Kaisu Wata Duniyar Duniyar Dabaya Fatan Wata Rana wani abu yamai Gatanka da shiga wannan Duniya mai Cike da duk wani jin Dadi. Tadan Jigata ammh ba kamar na Farko ba ai Ranar yasha Harara da murguda baki da Shagwaba da Safe shi ko ajikinsa Data Murgudamai Baki ta Harareshi sai yace"Au kina son na kara ne..,? Ai da taji haka Zata sakamai kukan Shagwaba Harda hawaye sai taga kamar da gaske yake ya taso ya Riketa ya Rumgumeta sai kukan gaske ta Faramai magiya ashe Daga mata Kafa kawai yake Tunda ya Fahimci Rakinta yayi yawa ya Fita Batunta Ya koma sai ya Lalubeta Tas sun gama jin Dadin sai ya koma Lallashi Lallashin da yanzu ya Kware akai wanda Ko Sagir da Khalil sai dai ya basu Satan amsa. ****** Cikin Sati Biyu da sukayi suna Gurzan juna da Amarcin da basu ci ba abaya Imran Har wani kiba ya kara da Kyau ita kanta Inteesar din ta kara Kiba da Cika da Kumatu Imran bai yi kasa a gwiwa ba,Ba mganar Girma bata Indai Zai Samu abunda yake so Girman yaci Batan Ubansa..! haka yake Marairaicema Inteesar yana Fadin"Plz Intee na kara Ko sau Daya fa..?sau Daya fa..! Ita kuma Tana jamai aji Duk da yadda Jikinta ya Riga ya saba ita kanta Tana Bukatar Bakuncin nashi Sosai sai ta Gama jamai aji da yanga sannan tace"To Wlh sau daya..Kuma in ka kara Har na gobenka..! Dariya kadai yake yi Saboda yasan Lagonta da zai saka tayi mukau Har sai ta jigata kana yake kyaleta sai Daga baya ta koma Tana Fushin Ba Gaira ba Dalili Alhalin Tana ji kuma ammh Tayi Lamo acikin Jikinsa Da ita sukaji Dadin Duk yana an kare da ita bai Hana anjuma ko Gobe ya kara Lallabowa yana magiya.. Haka Rayuwarsu ta Cigaba da Cikin Tsafattaciyar Soyayya Basu da Lokacin Kowa sai kansu ko Waya Indai Yana Gidan Inteeasar bata ta kanta tunda suna nane da juna Shi kanshi bai Taba Nadamar aikin Banki ba sai a lokacin yaso irin kasuwancin yake yi Kullun yana Gida Tare da Inteesar yana Lallabata yana amfana da Romon damokuradiya. Ko Gidan Abba ba wanda yaji Duriyansu ba kuma wanda ya Nemesu Shiru ke sa aji Shuru Sagir ma Haka yajisa Shuru aransa yace Shege ya samu Wajen Hutu ganinsa zai Fara mana Wahala haka ya Kira Khalil sukayi ta Gulma suna Dariya shi baima san sunayi ba sai da Sagir ya Kirasa yana mai Tsiya Tsaki yaja yana Fadin"Ina Tsausaya maka Sagir..Ka Kokarta kayi aure Ko Zaka samu wannan Rabauta da jin Dadin da muke samu..! Bai jira amsar sa ba ya Kashe Wayar yana Dariya Sagir yayi ta Kiransa bai Dauka ba daya gayama Khalil cewa yayi ya Kyalesa kwana nawa ne suma Zasu je Sahunsa Domin shifa har ya gabatar da mganar Munari ga iyayensa kuma yana nan zuwa Kano Domin su kara Fahimtar juna shima Sagir yace ya Fadama Mama komai tace Bakomai yaje ya samu Baba Manu su Tattauna Tunda shine Ubansa yanzu. Sun ta Gulman Imran suna Fadin ya samu yarinya karama ya Tsote mataa albarkatu ammh yana cewa baya son Raini Oho dai shi baima san sunayi ba yana Chan yana Hango su yara basu san Dadin da shi yake ji ba Ko nace yake kwasa ba Dadin Daya fi karfin yara sai dai Manya irinsa Shi wani Lokacin Har mamakin Jarumtar Inteesar yake abaya yana ganin Tayi mai kankanta sai gashi Tsab Take Dauke Dukkan wani Bukatunsa Bai Taba Zaton Zatayi ba sai dai ya kara yardan ma kansa Dan Hakin Daka Raina Shike tsole maka ido Watarana gadai Inteesar nan tana Daukesa Tsab Dinsa Dashi da Duka Bukatunsa. Sati uku da Dinkewarsu Ranar Lahadi Tun Safe suka sTaho Gida sai dai su Abba su ka gansu Kwatsan Shima Din Inteesar ce ta Matsa sai kuma Abba Daman da Ya Yusuf sun Kira suna Tambayansa Lafiya suka jisu Shuru yace suna neman sune bayan an Koresu Shine Abba yace suna Biko.. Nan suka Wuni Har Gidan Mama sun je,Imran dai sai kafa kafa yake da Inteesar yana wani Tsare Giransa bai barsu ma sun kebe da Munari ba Saboda gani yake kamar Zata gayamata wani abu ai in Munari taji ya gama yawo abunda bai sani ba Yana mata Kallon Biri ne tana yi mishi na Ayaba. Ranar imran har gidan Baba Manu Sagir ya Rakasa Kuma Yaji Dadi sosai chan sukayi Sallar Isha"i kana suka je Gidan Ya Sadam sudan jima Daganan suka Dawo Gida sukayi ma su Abba Sallama suka koma Gidansu yaji da Rigiman Inteesar na sai taje Kaduna Kafin su koma makaranta da wannan Damar Imran ya samu yana ta Shagalinsa Domin yace adadin Kwanakin da zatayi in taje kaduna adadin yadda Zata basa Dama yasha Budurinsa ita kuwa Tana son zuwa ta Sakar mai Ragamar Rayuwarta yana ja Sanda yaga Dama. Sun yi mgana da Abba kan zasu Tafi Kaduna Ranar Jumma su Dawo Lahadi shi da Inteesar Domin bazai iya Jimarin Rashin wannan Wajen ba Har na Kwana Biyi ba kuma ya Saba da ita in Tatafi ta barsa zai Tagyara Jin haka yasa Abba ya Bashi Shawaran su kwana daya Kaduna Su wuce Abuja su kwanan ma Baffa Kabiru Daya Imran bai yi gaddama ba Saboda Baffa Kabiru kam yanzu ai Tsakaninsu sai Mutumtawa.. Haka kuwa akayi Farko Inteesar ta gayyato Munari a Tafiyar Imu yace Sai dai Ta Zabi Daya ko su tafi su biyu da ita Dashi ko kuma Afasa Tafiyar Dole Inteesar ta bama Munari Hakuri daman Batayi Ra"ayin zuwa ba Inteesar ta matsa mata sai taje.. Kaduna suka Fara zuwa Umma da Daddy suka rasa ina zasu sakasu Saboda Farimciki,baki yaki Rufuwa Umma Farimciki ya Cikata ganin Inteesar taki Kiba sannan ta Rage rawan kai ba kamar baya ba. Ya Basheer najin zuwansu Ya kawosu Anty Hauwa da cikinta ya Tsufa da yara suka Dira Gidan nan fa aka Hadu murna Inteesar tazo Ganin gida ta kira Nasara ta Fadamata gata Kaduna Nasara tace bata yarda ba sai da ta bama Umma Taji Muryanta kana ta yarda sai mamaki take yi ya akayi ya Imu ya Barta tazo..?uhm basu san yadda ta Saki Jiki bane Oga yaji Dadi shiyasa. Nan suka kwana Imran Daki na Musamman aka Saukesa Inteesar ta Gudu Wajen Umma ta kwana suka kusa Raba Dare suna Hira Washegari Imran ya Fadama Daddy Abuja zasu je gaida Baffa Daddy yaji Dadin haka yace hakan yayi kyau ammh Kafin su Tafi Daddy yace Imran yayi Hakuri Inteesar takai sa Gidan su Inno da gidan Kawu bala da gidan su Nasara ai kuwa sai da suka lelleka kafin su Wuce Nasara ga Gulma abakinta ba Halin mgana Oga Imu na Wajen ya Tsare Gira Dole suka bar mganar sai sun Hadu ta waya. Baffa Kabiru bai san da zuwansu ba Ranar yana Gida Dashi da Umaima Sai Sajida Da Baffa Kabiru yace maza ta Dawo gida tayi Hutunta bata da yarda Zatayi ammh Da Farko Taso tayi Zamanta a Hostel ne Su suka kasance su kadai suke Rayuwa agidan sai yan aiki sukaga Imu kwatsam da Intee Umaima ta Rumgume Inteesar Tana ta Murna Baffa Kabiru ya Rumgume Imran yaji Dadi sasai har ya kasa Boye Murnansa Sai zuwan da sukayi ne Inteesar tasan Mami sun Rabu da Baffa Itama Umaima ke Fadamata Sajida kuwa Gwanin ban Tsausayi ta Rame Duk Ta Lalace kamar ba ita ba Duk Rashin Jituwarsu da Inteesar data ganta sai da ta Firgita ta Fara Tambayan Umaima ko Sajidan Tayi Ciwo ne Umaima tace bata sani ba Sajidan bata Dade da dawowa Daga makaranta ba Baffa Kabiru ma ya Zaunar da ita yayi Tambayan Duniyanan Tace lafiyanta Kalau sai ya Kyaleta ammh kowa ya ganta yasan Bata da Ishashiyar Lafiya. Harta Imu Daya ganta ya Dade yana kallonta kamar wacce ta Shekara Tana Ciwo Ita kanta Sajidan bata so Fitowa ba Baffa Kabiru ne yace Umaima Ta Kirata tazo ta gaisa dasu Imran wanda Tunda taji zuwansu ta ki Fitowa Domin ganinsu kamar Fami ne acikin Zuciyarta. Ta dade tana kallon Imran kallon iri na so da kauna da kuma Kallon Yanzu Shikenan na rasaka..? Shikuma Har ga Allah ya Tsausayamata Uwarta ta sakata Cikin Bala"i Shiyasa yake kara Godema Allah Daya sa Baffa Kabiru ya Saketa ya Tabbata Zuwa yanzu ta Fara Karban Sakamakomta Daki Daki Tunda suka gaisa Sama sama ta Koma Daki Tana ta kuka Zuciyarta na Suya Tari ya Sarketa ta yi Saurin Shigewa Tioler sanin in dai Tayi Tari Har da Jini Jini yake Biyowa. Imran ne suna Zaune da Baffa suna Hira ya Tambayesa Khamis Cikin Jimami Baffa Ke fadamai Kwata Kwata Tunda ya Tafi basu kara Samunsa a waya ba ba Labarinsa Imran yayi Shuru kafin ya bama Baffa Kabiru Shawaran zuwan chan Anambara ya gani ko Lafiya..? Baffa Kabiru yaji Dadin Shawaran Imran Da Tuntuni bai kawo Tunanin ba.. Ya Tabbatar mai da cewa da aiki yayimai Sarari zai je chan din yagani Insha Allahu. Sun sha Hira sosai Hira ta Tsakanin d'a da Uba Hirar da suka Dade basu yi kamarsa ba. Washegari da wuri suka kama Hanyar har suka tafi Basu kara ganin Sajida ba,suna Hanya Sai da tayima Imran Zencen ya Hade rai yace ko kin bar mata ne..? Harara ta sakarmai Tana Juyamai Baki Dariya kawai yayi yana Fadin"Juya Dakyau akwai Biyan Bashi Duk zan fashe..! Jin haka yasa ta Daidaita Natsuwarta Tana Fadin"Bafa haka mukayi dakai ba..Ba kayi har da na tafiyar nan ba..!? Yana Danne Dariyan sa yace"Ni yaushe..?bamu yi haka Dake ba Malama bana son Runto..! Inteesar harda kukan Shagwabanta duk don ya Kyaleta yayi mata Fuska suna Isa Kano duk wannan Gajiya sai da ya karamata wani Da ta Fara Shagwaba yace zai Fanshe Har da Na Zuwansu Abuja Dole ta ke kama bakinta Tayi Shuru Fadan Dayafi karfinka sai ka maidashi wasa. *Sannunku da kokari wannan Sannun Na wadanda na bama Amanatace suka Rikemin Hannu bibbiyu Nagode kwarai naga GMB2 Nata gantali Agari ba shi chan gidan bashi chan gidan Da inda ya kamata da inda ma bai kamata ba Duk yana shiga Dole na gode muku Allah ya Saka muku da alheri in kun sakamin da naku Alherin in kuma akasinsa ne Allah mai ji ne kuma mai gani ne kuma shi ya Hanemu da zalunci kuma yana Kwatar ma wanda aka Zalunta Hakkinsa..Nagode kwarai..!* *Shakira* 3/30/22, 16:27 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�29* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Duk da wannan Garan da Imran ke kwasa bai hana In Inteeear tayi mai laifi ya Fitttike ya Dakuna Fuska ya Hade rai kamar bai Taba Dariya ba,yayi mata Fada ita kuma ga Shagwaba bata san Fada Daya Fara zata faramai kuka shi kuma bayason kukanta in yayi mata Tsawa sai ta shige Daki Tana Kuka Wuni zatayi batamai mgana Tana Fushi Dashi,bai hana kuma Dare nayi ya Lallaba wajenta yayi ta aikin Lallashin daya kware sosai akai ita kuma Inteesar ga son jiki ga kuma Karban Lallashi ballatana Lallashi irin Lallashi Mazaje irin Imran bata Sanin ma Ta bada kai Bori ya hau sai komai ya kamallah sai ta dawo Tana Tura baki Tana mai kukan Shagwaba shi kuma yana Biyemata. Rayuwarsu suke Cike da so da kauna mai Hade da Sadaukarwa Kallo Daya Zakayi musu ka Fahimci Ma"aurata ne da suka Auri juna bisa yardan Zukatansu Zama ne sukayi na Yanci da Yadda suka Tsarama kansu Imran nada kyawawan Hallayar da sai da Suke Zaune waje Daya Inteesar take kara saninsa Yana da Hankali Da Sanin ya kamata yana da Sanyin Hali wanda ba kowa ke sanin haka ba sai Wanda ya Zauna dashi ya Rabu Dashi Sosai ammh ahaka sai arikamai kallo mai Wani hali mara kyau da Muguwar Zuciya wanda in ka Fahimcesa zasu Zauna Lafiya har ku Rabu wani abu bai Taba Hadaku ba. Abu Dayane baya so Raini Inteesar tasan Halin kayanta Tsab Shiyasa take Kokarin Kiyayemai na wani Lokacin Yasan Lagonta kamar yadda itama Tasan nashi sai zaman nasu ya bada wani Sha"awa da Burgewa. In yana Gida Tare suke Salla ya ja musu Jam"i Tana binsa abaya in kuma baya gida Sai tayi nata ita kadai shi kuma sai yayi a masallaci in kuma ya Dawo suna Manne da juna Tana Zubamai Shagwaba yana Biyemata Saboda yasan Daga Karshe shi ke da Riba. Duk kuma wannan Soyayyar da suke kwasa Imran bai taba cema Inteesar yana sonta ba,Gashi Tana son taji kalmar Daga bakinsa Duk da a Duka ayyukansa sun Riga sun gama Nuna Itace Mahadin Rayuwarsa,ko bai Furta mata ba Tana gani a aikace Irin yadda yake nuna mata Salo Salo na Soyayya wanda take ta mamaki a ina ya sansu..?ko daman ya sani ne..?batasan wani Karatun baka saninsa sai Lokaci Daya in Lokacin abun yayi baka sanin sadda kake yin wasu abubuwan ballatana in suka Kebance yadda yake Zubamata Sambatu Kamar zai zauce kalmar itace Rayuwarsa kam Tagama Haddaceta wannan sai dai bata kama mganar Sanin baya Cikin Natsuwarsa ne lokacin kuma shi Imran yana Daga Cikin Mutanen da basa iya Boye jin Dadinsu sai fa ta Rika Toshemai Baki da nata take samun Rufe bakinsa. Ita kanta ai Shiga wata Duniyar take Ogan nata ai Karshe ne ya iya Tafiyar da mace ta manta da komai nata sai shi kawai take gani ya iya Sarrafa Mace iya Sarrafawan da Zata Fita Daga Cikin Hayyacinta Shiyasa ahankali Wani Shakuwa da Soyayya mai Zafi Datake kara shiga Tsakaninsu basu sani ba...! Basa jin Duriyar kowa sai dai a waya,kamar an san suna cin Armaci Shiyasa aka kyalesu su samu Natsuwa Tsakaninta da Munari sai dai Tana Waya in sun yi mgana ko kuma in sun Hadu a Chart in kuma Imran na Gida Batama da Lokacin Waya gabadaya Lokacin nashi ne ko aiki yake A laptop suna Manne da juna Tana Zubamai Shagwaba yana Biyemata Agantale yana aiki in Shagwaban nata ya Rinjayi aiki sai a Bige da Neman Lada. Yau ma din haka ta kasance Bayan sunyi Sallar Isha"i suka dawo falo suka yada Zango shi yana Faman aiki a laptop dinsa yaana zaune saman Kujera mai Zaman Mutum Daya Dagashi sai Boxers Ko Riga bai dashi,Inteesar na kwance Dare Dare kan Jikinsa,tana wasa da gashin Kirjinsa Tana Sanye da karamin Mini Sikat da Karamar riga mai kama da Half Vest,Jan gashin take yi yadda sai yaji Zafi in ya Dago ya Harareta sai ta Kwashe Da Dariyan Shakiyanci kallonta kawai yake yi so yake yagama aikin da yake yi wannan Dariyan nata zai koma kuka in ta Shiga Hannunsaa Inteesar Taba chan ja chan,Taja Hancinsa ta Mele bakinsa ta Gwalemai ido ya Dago ya kalleta Da Iduwansa da suka sauya Launi da yanayin Datasashi aciki yace"Bana ce ki bari ba..? Meyasa kin cika Rigima ne Maryama..? Tura baki Tayi kafin tace",Daga ina wasa Da Mijina..! Imran ya Murmusa yana Fadin"Yaron Wasa ne ko Teddy..? Inteesar na Danne Dariyanta Tace"Teddy ne..! Ahankali yadda bazai ji ba,Ashe ya jita Cikin Kallon Sha"awa ya kalleta kafin yace"Uh.m..Teddy ko..? Da Sauri Inteesar ta Sunne kai kan Kirjinsa Tana Dariya bai kara Tankamata ba illah gyara mata Kwanciya da yayi sosai a jikinsa Lokaci Daya yana Mikewa Tsaye da ita jikinsa,Inteesar ta Zaro ido ganin ya Tsallake aikin Dake gabansa ya Nufi Cikin Daki da ita Tana Zare ido Tace"Ya Imu ka gama aikin ne..? Imran yace"Ban gama ba..wannan aikin yasha gabansa...! Inteesar bata samu Zarafin mgana ba ya saka Kafa ya Tura Kofar Bedroom din sa ya shiga bai Dirreta ko"ina ba sai kan Tsakiyar gadonsu,Inteesar ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"Me zamu yi anan..! Imran na Danne Dariyanss yace"Wasa da Teeddy mana..! Inteesar ta Zaro ido Tana Fadin"Teddy..? Cikin alamun Sangarta Domin a kallon Dayake mata TuniTa gane karatun,kafin ma ta kara mgana ya Rufe bakinta da nashi Intesar bata isa ta Kauda kai ga Imran ba Itama Cikin Zumudi ta Tarbesa Lokaci Daya ta Tallafesa Tana kara Taimakamai Wajen Samun Natsuwa Cikin so da kauna da Muradi mai girma Shudewar Mintina Talatin kafin su Samu Natsuwa suna Manne Cikin Bargo Dukkansu ba kaya ajikinsu Inteesar ta yunkura Tana Fadin"Ya Imu mu je muyi wanka..! Tafada Tana shafa Sumar kansa Daya Kara Taruwa ita tace kada ya aske Sumar tana yimai kyau kuma Tana jin Dadin wasa da ita. Yana jinta bai ce komai ba Tana Cikin Jikisa ne ya Tusa kansa Tsakanin Wuyanta kamar mai Barci nan kuwa yana ta Sauke Numfashi ne Inteesar bata Isarsa bai Koshi ba Kari yake so..! Jin sa yayi Dif yasa ta Motsa Tana Lekansa Ta kara Fadin"Ya Imran..! Tafada Cikin Shagwaba dan Motsawa yayi kafin yace"Uhmmmm...! Baki ta Tura Tana Fadin"Ka tashi muyi wanka kaifa kake min Fadan ba kyau Zama da Najasa..! Ta karishe Fada tana Mintsininsa a Gefen Cikinsa D'an Kaucewa yayi Yana Rikota sosai Cikin Jikinsa yana Sauke Tagwayen Numfashi Tunda taji haka tasan Kwanan Zencen sai ta Fara Kokarin Zillewa Ta Mike Zaune shima ya Mike ya Rumgumeta ta baya yana Fadin"Uhm...Uhm...I need More Mah..! Inteesar ta Kallesa Tana Fadin"Nidai A"a ka kyaleni..! Imran ya Shagwabe mata Fuska yana Fadin"Ta ya zan kyaleki..?kin Taba jin inda Masoyi ya kyale masoyiyarsa..?kedin ce kin cika Dadi Dadin baya isata Anty Inteesarr...! Yafada Har yana wani Juya mata Ido Dariya tayi kafin tace"Ni yaushe na Zama Masoyiyarka..?kuma wato Tunda Zakamin wayau Kai ne yau kake cemin Anty..! Karan Hancinta yaja yana Fadin"To ke din in ba Masoyiyata ba macece ke..? Duk Duniya ban da kamarki Kece Matata kuma Sirrina in ban miki Wayau ba..Wazai miki..? Yafada yana mata Dariya Shagala Tayi da kallonsa Kafin tace"Ya Imran kana SONA..!? abazata yaji mganarta sai kawai ya Tsaya yana kallonta Idonsa take kallo Kafin tacigaba da Fadin"Ban taba jin kace kana sona ba..! Imran ya Lumshe ido kafin Yace"Nima ai baki Taba cewa Kina Sona ba..! Inteesar tace"Ai ba sai na Fada ba Tun afarkon Fara mganarmu Na Fara Sonka..! Imran yace"Nima ai ba sai na Fada ba..Na Fara sonki ne Tun Ranar dana Fara ganinki ban sani ba Inteesar..Sonki yayi min kamun da ni kaina bansani ba..Sagir ya Dade yana Fadamin ina sonki naki yarda da Hakan sai dai abu Daya na sani na Tsani naga wani Namiji Tare Dake bana so kowa ya Rabeki sai ni..Bana son kukanki ballatana Fushinki Rashin ganinnki Azaba ne a wajena Inteesar kin bani Wahala sosai kafin ki Zama mallakina..! Ya Karishe Fada idonta na Cikin nashi Inteesar da gabadaya kalamansa ya Sanyayamata rai ta kasa mgana sai Binsa take da kallon Kauna kafin tace"meyasa baka Taba Fadamin ba..! Imran yace"Kauyanci ne na Tsaya Ina I Love u..Kawai ayyuka na akanki Zai sa Ki Fahimci haka kuma ni kinsan ban wani san ya kamata ba abubuwa masu Muhimmamci Ina ganinsu a Shirme sam ban kawo Tunanin ya kamata na Sanar dake ba..! Inteesar ta Fada Kirjinsa ta Rumgumesa kamkam Cikin Farinciki Tana Fadin"Nima Ina Matukar Sonka Ya Imu..Nima na Fara sonka Tun Farkon Haduwarmu banfara yarda ina sonka ba sai da ka kwaceni hannun yan iskan nan masu Kwacen Waya Nima ka bani Wahala..! Take Fada tana Dukan Kirjinsa Riketa yayi yana Dariya yace"Naji An buga wasan daidai duka min bama juna Wahala..Ni dai yanzu ki bari na kara..? Ido ta waro Tana Fadin"Ka kara me..? Cikin Karya wuya ya shafo Kirjinta da suke kallonsa yace"Allah sau Daya zan kara..! Inteesar tayi mai wani kallo Kafin tace"Kai fa sai kace sau Daya kana min Wayau in na yarda Allah wajen sau Uku kake karawa kayi ta yi..! Tafada Tana Tura baki Rumgumota yayi yana Fadin"Yanzu Daya zan kara My Sweeeet Intteee..Na kara..!? Yafada yana kallonta Kai ta Dagamai kafin yace"Kayi alkawarin D'aya..? Kai ya daga kafin yace"Kai Intee meya kawo mganar alkawari..? Tana Dariya tace"Ai nasan sai ka Zarce ne..! Shima Dariyan yake yana Fadin"Ai nasan Matata mai adalci ne in na kara ma Zata yafemin..! Da wannan Dadin bakin Imran ya Samu suka kara Komawa Ruwa Sai da ta Hada da kuka da magiya kana ya Sauraramata sukaje sukayi wanka Tare achan ma Tiolet din Tabara kawai sukayi tayi Kafin su Fito tare suka Shafa ma juna Mai suka ka kuma koma suka Kwanta suna Nane da juna Adaran dai bai kara ba ammh da Asuba bayan sun gama Sallar asuba sai da Imran ya kara kafi Siga Dadi. Haka Rayuwarsu ta Cigaba da Tafiya Imran shi haka Salon nashi Soyayyar take mai Zafi ce sosai,bai iya Fadinta abaki sai dai a aikace Inteesar Tana ganin Abu Salo Salo A aikace ta Zama yar gata Wajen Imran ta kuma kara yardan ma kanta Shi din na Dabam kamar yadda yake na Dabam acikin Ranta.. Inteesar Ta ji Dadin Hutun Makarantar da suka samu Saboda yadda suka samu Ishashen Lokacin da suka Murje amarcinsu Imran bai so ma suka koma ba Hutun Wajen Wata Daya da kwanaki kana suka koma makaranta,Kudin Rigistration din su Ita da munari duka shi ya Biya musu na Shiga Aji Biyu,ba yadda ya iya ne kamar yace abar karatun Tunda da suka koma Lectures sosai sukeyi sai Yammah suke dawowa shi yake zuwa Watarana ya Daukosu ita da Munari ya Fara kai Munari gida kafin su wuce Wani Lokacin kuma kusan atare suke Dawowa Gabadaya dan kiban datayi na amarci Duk ta fara ramewa Ga gajiyan makaranta in ta dawo ga Girki da Laluran Miji Imran ba Daga kafa ya Saukar da gajiyan Dare ya Saukar da ta asuba to yata iya yasan Lagonta ko Ta Hanasa sai ya Lallabata ya ji Dadinsa ba ruwansa. ***** *After 2 Month* Bayan Wata Biyu da Daidatawar abubuwa Tsakanin Inteesar da Munari Daada ta Zame a bandaki Tayi Gocewar Kashi da sai da aka Dangantata da asibiti,Hankalin iyalanta ya tashi sosai da duka Jikokinta,gabadaya kowa da kowa sai fa sa yaje saboda jin Halin da Daada ke Ciki,ga Jikin Tsufa ga Kashi ya Tabu Baffa Kabiru da Abba da Daddy tun da abun ya Faru suka bar komai nasu suka Tafi Chan An gyara Kafar Kwananta Hudu aka Sallamota su Goggo Maimunatu ne tare da ita,Jikokinta duk sun zo su Sadam da su Sa"id ya su ya Basheer Ya Yusuf ma yaje Imran dai sai Weekend suka Tafi da Inteeear lokacin Harta su Abba sun koma Goggo Bintalo ne ke Zaune da ita Har Lokacin. Daada kamar bakinta zai yge Saboda Murnan ganin Inteesar da Imran Cikin Farimciki da annushuwa Daman abunda take Fata kenan tayima Allah godiya ta kuma kara Godemai da ya Hada kan Iyalanta Waje Daya Kwana Daya sukayi suka Juya Inna Bintalo kam ga Gulma abakinta ba wajen Fada Tunda Mami Asma"u da Rayuwa ta gama ma kullin Goro ta Daina Daukan Wayanta Tun bayan Bikin Imran da Inteesar Data Kirata Tayi mata Tas tace kada ta kara Nemanta indai ba Alheri Zata Fadamata ba in kuma ba Daidaita abubuwa Zatayi ba ta barta da Halin Datake Ciki Tundaga Lokacin bata kara Sauraran Inna Bintalo ba. Mami Asma"u ta gama ganin Rayuwa ta kuma Sarewa da al"amarin ta Tabbatar ma kanta ta riga ta rasa komai,ita ba Miji ba ya"ya ba Khamis ma bata samunsa kwata kwata awaya Sajida kuma ta Zama sauran Cutar Namiji Baffa Kabiru ya gama Toshe duk Wata Hanyar da zasu hadu ballatana ta saka ran in suka Hadu yaga Yadda ta koma zai Tsausayamata ta Rame ta Fige kamar ba Mami Asma"u in lissafinta yayi Daidai Tama Fita Iddanta Kenan Aure ya Haramta Tsakaninta da Kabiru sai in har ya Sake yarda an Daura musu aure gashi Tun tana Boye abun har ya bayyana yan"uwanta sun gane Sakinta Mijinta yayi mgana har wajen abokan aikinta ana ganinta ana Gulmaanta a kawayenta ma duka sun samu Labari Harda wadanda suka Tareta suka mata mgana Mami Asma"u Wlh ta yarda Duka Kuskuranta ne ammh bata san ya Zata gyara abunda ta Riga Ta gama batawa ba. Bata da wata Hanya Hatta Hajiya Turai ta Sare tace Mami ta Kira Baffa Kabiru ta basa Hakuri Mami kunya ya Sata kasa Kiransa sai dai ta bama Umaima Sako ita kuma Data Fadamai bai ce komai ba Saboda ai bata gama Nadama ba In ta yi Nadaman da gaske Tasan yadda Zata gyara komai,Shi kanshi baya Cikin Natsuwarsa kan Rashin Sanin Halin da Khamis yake ciki,Yaso yaje tun sanda sukayi mgana da Imran sai dai wani Case ne ya Rikesa yasa ya kasa Tafiya yana so sai sun yi Covering din komai Tukunnah ya Shirya yaje Har Chan Anambara ya gani ko Lafiya..?shiyasa ya Share Mamin Asma"u yasani akwai Watarana da Zata gane Duka abubuawn Data aikata kanta suka Dawo,Shiyasa ya Kyaleta sai Ta Fahimci Kuskuranta da kanta. Su Inteesar na Tsaka da Karatu Anty Hauwan Ya Basheer ya Ta Haihu Ya mace Murna wajen Inteesar ba"a gama sai dai Murnanta ta koma Ciki Tunda sai ana gobe suna Imran ya bari suka tafi Tare da Anty Safiya da itama Cikinta Haihuwa ko yau ko gobe da Munari da Anty Aneesa da Fareesatu da Hafsa,suka Tafi Kaduna suna shima din Inteesar sai da Abba ya Saka baki ya barta tayi kwana Biyu,Yarinya Takwaran Inteesar ne Domin taci sunan Maryama ne kuma Itama Inteesar za"a rika Kiranta ai ko Auta Tayi bajinta ita Goganta Imran sun Siyama Mejego da Baby kaya na alfarma,Domin duk wacce taci sunan Inteesar abar karramawarsa ce a zuwan su suna ne kowa yake jin Labarin Soyayyar Hafsah da Sagir da na Munari da Khalil kuma kowa yayi Na"am Tunda Sagir yaje Dutse sau Biyu,kuma ya Sa"id yayi Na"am Dashi Shi Sagir din bai gayama Imran ba Shi Sa"id din shi ya Kira Imran din sukayi mgana Anan ne yaji Sagir din yaje har Dutse Imran aransa yace Uhm da gaske Yaron nan yake Shiyasa yadda bai Gayamai yaje ba Shima bai Numamai ba Kowa yaji Abun sai yace Hadin ya kayatar Ita ma Munari Khalil din yana nan tafe Kafin Iyayensa su suzo shima ya gabatar da mganar awajensu Dr.Isa Ali Argungu A kuma Lokacin ne aka kara Tattauna Lamarin Mami Asma"u da Baffa Kabiru,Tunda Labari ya bayyana acikin Dangi Auransu ya Mutu kowa sai Fadi yake ai mganinta keman Taga Karshenta goggo maimunatu bata zo ba ammh ya"yanta su Zainab da Karima sun je Daga Kwana Biyu sai ga yan suna da kwana Hudu Imran ransa ya Baci Inteesar sai ta Saki jiki ta Rama mai Kwanakin da bata nan ya Kwashi Dadinsa Shine yasa ya Dan Hakura Kadan Daga baya kuma sai da yayi mata Fadan nan nasa ta gama Tura Bakinta ta Hakura tunda itace bata da gaskiya. Tsakanin Haihuwan Anty Hauwa da Anty Safiya Kwana Hamsin ne Itama Allah ya Sauketa Lafiya a asibitim Murtala,Danta Namiji kyakyawa mai kama da Imran kamar shine Ubansa yana Kama na Jini da Mahaifinsa da Mahaifiyarsa. Haihuwan nan Kamar wani karin Haske ne a wannan Gidan Tun a asibiti Yusuf yayi mai Huduba da Imran,Masha Allah Imran baki yaki Rufuwa Ya Yusuf yamai Takwara Yaji Dadin har yakasa Boye Murnansa Inteesar sai rawan kafa Take Takwaran Gwarzonta Anty Saratu ke Tare da Anty Safiyan har suka Dawo Gida Mama Ya yusuf ya kira Tazo sukaje asibiti tare,Suna Dawowa Gida ta Saka Ruwan Zafi tayima Maijego wanka Ta kuma Gyara mai sunan Imran,nan da man gida ya Cika da Dangin Anty Safiya Abba kuma baki yaki Rufuwa Anyi jika Daddy da Baffa Kabiru sun kira sun yi barka da Fatan Alheri. Tunda akayi Haihuwan Inteesar chan take wuni Sai Dare Imran ke Daukanta su koma Gida,da sun Dawo Makaranta nan suke yada Zango,Alhaji Alhassan da kansa yazo Har gida yayi barka ya bama mejego 50k Amtsayinsa na Uba bayan kuma akwatin Kayan Daya shako Cike da kayan Bby da Na uwar,Alhaji Alhassan ya Riga ya gama yin Nadama ya Zama Mutumin kwarai yana so ya gyara Halinsa ya Roki Hajiya Mero Gafara ita da Danginta da nashi Dangin. Inteesar Taci Darajan mai sunan Imran da kuma Darajan Ya Yusuf yasa Imran ya Sakarmata kafa sosai tana Wuninta agidan,Shima amtsayinsa na Wanda Jariri yaci sunansa yayi rawan gani Shima akwati guda yayi na kayan yaro Inteesar kuma ta siya mai Jego atamfofi. Anyi suna Taro sosai an tashi Lafiya Mama ita ke zuwa Tana ma Safiya wanka da Imran junior safe da yammah Mommy Taji Dadin haka Daman ta Fara Tunanin wacce zata Zauna da Safiyan sai ga Mama Abba ma Kyautar Dubu 100ya yi ma Jikansa na Farko Duniya kuma mai sunan Dansa Gabadaya Ahalin Daada sun Hadu Hatta da inna maimunatu sunzo sunan da su Inna Bintalo,kuma sai da sukayi kwana Biyu kana suka koma,Raguna uku Yusuf ya yanka ma takwaran Imran an sha Shagali sosai kam sai Fatan Allah ya Raya Imran karami. Bayan suna kuwa Inteesar ta Gayama Aya Zakinta Domin Imran sai da ya Famshe kwanakinsa Inteeear ta Jigata sosai a Hannunsa Sai ta Fara Hadamai da kuka da magiya yake kyaleta Tunda yanzu ta Fara Zama Raguwa Tun Sunan Anty Hauwa bata jinta Daidaita Tunda suka Tare bata Taba Jini agidan ba sai dai Kafin Tarewar ne tayi period,Bata Dauka komai ba Saboda yana mata haka Shiyasa bata Damu ba,sai bayan sunan ne na Anty Safiya ta Fara Zazzabi da Amai Ta Rame duk ta Tsurr har da kwanciya asibiti lokacin da aka Tabbatar da Inteesar nada Cikin Wattani biyu da wani abu Murna wajen Imran kamar Zai Shide bai Taba Zaton Watarana zai Zama Baba ba sai gashi da kanshi ya Kira Sagir da Khalil ya Fada musu ya Kusa Zama Baba suna nan a yara Su kuma sukacemai Suna kan Hanya da yardan Allah Samuwar Cikin Inteesar ya Zaga Dangi Har kunnen Daada,Sai Jin Dadi Take Tana saka albarka,Inteesar kuma Cikimta mai Laulayi ne ga makaranta Dole Munari ta koma Gidan Tana Taimakamata Tana ganin Abu Su Ya Imu asan ya"ya Wato na wasu ne bai Damu dasu ba ya Damu da nashi Tana kallon Rayuwa yadda Inteesar ke Zuba Shagwabanta Dama gata mai Raki Baban Urborn kuma na Tarairayanta,kuma bai jin kunyar Munari Ko ajikinsa ammh da sun Hadu ya Hade rai yana Hura Hanci Munari tace aranta Daman ai nasan Watarana Mace Zata sauya ya Imu ko bai gama Dawowa Daidai ba Watarana in ya zama uba zai dawo Daidai yanzu ma Shan Taba ya Ragesa Saboda Intee abun ya Zame mai jiki ne yasa yake sha asati sau Daya wani Lokacin balle yanzu Data samu wannan Cikin Inteesar ta kara Lalacewa Tsurfa kala kala batacin komai Daga Goriba sai tuwo sai su Fante da sauransu Imran shine da baisan Hanyar kasuwa ba ya sani yanzu Tunda zai zama Baba Munari kuma ke ta Wahala da tsurfan Inteesar Umma Daman dataji Labari tace Imran ya shiga Uku Daddy na Dariya yace ai Daman sun Hadu da sun Dace ne Dagashi har Inteesar din. Allah ya Taimaki Inteesar basu Fara Test da wuri ba sai da tadan samu kanta Kana Munari ta koma Gida Bayan sun gama Test suka fara Jarabwwa Lokacin Laulayin yayi Sauki aman ya Tsaya suka samu hutu na Sati uku Imran yaji Dadin haka ta koma Gida tana Hutawa. ****** Baffa Kabiru ya samu zuwa Anambara Har gidan Khamis inda yake Zaune gidansa Daya mallaka Halak malak,Halin da Baffa yaga Khamis sai ya Dawo Abuja yana kuka da Idanuwansa yana Durama Mami Asma"u Allah ya isa. Yaje yaga Khamis ya Kazance ya koma Cikin Wata Rayuwa,Shaye shaye ga Shan Giya shi yaci Uban Taba,harda Wiwi yana sha,ga Harkan mata Koda Baffa Kabiru ya isa gidan cikin maye ya iskesa ya Tara Kasumaba Duk yayi kazanta Harda mace ya gani agidan,Baffa Kabiru kuka Shabe Shabe Bai iya kwana agarim ba,Har ya baro garin Khamis baya Cikin Hayyacinsa bai san ma yazo ba tun a Garin ya Daga Waya ya Kira Mami Lokacin Tana Hanya Zata Dawo makaranar su Sajida da aka Kirata Bata da Lafiya har an kwantar da ita a Clinic din makaranta Tayi kuka sosai Data ga Halin da Sajida Take Ciki sai dai Sajidan ta nuna ma Mamin Ulcer ce ke Damunta Saboda Tana Zama da yunwa ba komai ba ta Boyemata yadda Take Tarin jini wani Lokacin Achan makaranta ta wuni sai da Taga Sajida ta koma Hostel Tayi Tayi ta Bita Gida Taki ta Fake da Sun kusa Fara Jarabawa Bata so tayi Loosing abunda bata sani ba Mami Taje ta Duba result din Sajidam sai da taji Tsoro ta kuma Tabbatar ma kamta Sajidan Rabuwanta da Imran ya tabata Gabadaya Tayi kasa sosai G dinta Low,Kowa kuma yasan Sajida da Kokari ammh Yanzu Har an yi mata Warning din Kora Daga Deparmnt Mami Asma'u ta baro makaranta cikin wannan Damuwar Tana Tafe tana Driving Tana kuka Har ta kusa Bugama wani Mota ya leko yana ta Zagimta Dayasan Halin Datake ciki Da bai Tsayama bi ta kanta ba Da yayi mata Uzuri. Bata kai ga isa gida ba Kiran Baffa Kabiru ya shigo wayarta karo na Farko Bayan Abunda ya Faru Wata Shida Cikin na bakwai. Da farko ta Zata gizo idonta ke mata Har ta katse bata Dauka ba sai da ya kara Kira kana ta Zabura Tana Dauka Tana Sharan Hawaye sai Fuskarta ta Cika da Alhini da Kuka Data barke da shi bayan jin Abunda Baffa Kabiru yake Fadamata Cikin Kaushin Murya"Asma"u me zan ce miki..?in nace na barki da Allah Kamar nayi miki adalci Gwara na Miki Allah ya Isa Allah ya isa Asma"u ko naji Sanyi a Raina Kin Zama Silar Tsarwata Rayuwar ya"yana da bani da kowa sai su..kin ta aibanta Imran kina Kiransa Mai Shaye Shaye Dan iska To Shi Taba Kadai yake sha D'anki gashi chan yana Kora Giya da Wiwi yana Budema Mata Rayuwarss gabadaya kinga Illah aibata D'an wani da Mugun bakin ki ya kamaki me zaki ce..?Kin Ruguzama Sajida Duka Rayuwarta Kin saka Tayi Sallama da Farincikinta In ban yi miki Allah ya isa ba Me zan ce miki..? Wlh bazan yafe miki ba Asma"u yadda Kika sani kuka Insha Allahu kema sai kinyi mafiyin nawa..! Ko Cewarta bai jira ba ya Datse Kiransa yabar Mami da kuka Allah yasa Kafin ta amsa Wayar sai da Ta Faka Motar agefen Hanya da Allah kadai yasan Irin Hadarin da Xata Hada kanta ta Hade da Sitiyarin Motar Tana kuka kukan Wurjajan kamar Mahaukaciya afili Take Fadin"Ai nama Fara Kuka Kabiru..Na Dade ina kuka kai ne baka sani ba..Kaicona Ni Asma"u na Kashe Kaina da kaina na Illata Duka Rayuwar ya"yana ba Auran ba Farincikina ya"yana Innalillahi Wa"inna Ilaihirraju"un haka ta Ke Fada Tana Dafe kanta Datake jin yana Barazanar Fashewa Lokaci Daya Tana gunjin kuka. Dakyar ta iya Rarrafawa Ta Tada Motar Zuwa gida aharaban gidan Da tasamu ta isa Dakyar bata iya Fitowa Da kanta acikin Mota ba sai dai Fito da ita akayi Jiri Take gani Hajiya Turai ta Firgita da ganin Mamin Aranar sai da Likitansu yazo ya Dubata ya Dauramata Drip tana kwance Tana Fadin"Kaico na..Kaico na ni Asma"u..Ya"yana mijina..! Haka take ta Fada tana Kuka Hajiya Turai Jikinta ya gama yin Sanyin Ta Fita Taje wajen Justice tace ya Kira Kabiru ya Rokeshi yazo su Daidaita da Asma"u yace bazai Kirasa ya Tursasa ba Sanda yake bama Asma"u baki ai bata Jisa ba Shi ba Ruwansa abunda ta Zabama kanta kenan. *Shakira...* 3/30/22, 20:57 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�30* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Asma"u ta rasa ta ina Zata farama Hajiyarsu bayanin abunda ya Faru Kunya take ji ita kanta in ta Tuna Kabiru yayi mata Allah ya isa ya Fada ya kara Fada Allah ya isa bai yafe mata ba Ta ina Zata Fara wazata Tunkara da zai saurareta Ballatana ya Fahimceta duk inda taje itace akasa Bata da gaskiya tabi son Ranta da son kanta Eh mana gaskiya ne Tana da son kamta mana in ba Domin haka ba da ta Duba Ya"yanta da Mijinta ta ijiye son Ranta da Tabi Ra"ayi da duka Muradan Mijinta da ya"yanta Kaiconta haka take ta Fada Tana kuka kamar Zatayi hauka. Hajiya Turai ta Damu kwarai da gaske ganin haka yasa ta samu Mami Asma"u tana kwance bayan kwana Biyu Da kiran da Kabiru yayi mata Gabadaya ta Fige ta rame Ita kanta tasan bata da lafiya Jiri take gani in ta Mike duk da mgungunar Likita ammh Saboda bata cikin Kwamciyar Hankali ko sau Daya mganin bai mata amfani ba Batama sha sai Hajiya tazo ta mtsamata to gani take ko ta sha bai da amfanin Halin Datake ciki Mgani bazai Lafar da komai ba bazai Hana Wutar Nadama da kuskuran Data aikata ci acikin Zuciyarta ba. Kwance ta sameta yaraf kamar ko yaushe kamar kayan wanki gabadaya Jikinta ya gama saki kamar mai Cutar Shanyewar barin jiki ba na barin Jiki bane na Mutuwar Zuciya ne Kuka Take na Boye dana Sarari hawaye sun riga sun gama Samun Matsungguni akan Fuskarta Kukan Zucci kuwa Shi take kwana Tana wuni Tanayi,batare da tasan Hanyar da Zata Dakatar da hakan ba Har Hajiya Turai ta shigo ta Zauna gefen gado kusa da Mami Asma"u bata sani ba ta Riga tayi Zurfi Cikin Tunanin Daya Zameta abun yi akoda yaushe Zafafan Hawaye suna Kwaranyomata. Hajiya Turai Ta Kira sunanta Har yafi sau uku bata jita ba sai da ta Tabata kadan Tare da Girgizata Lokaci Daya Kafin tayi Firgigit ta dawo Cikin Hayyacinta daga Zurfaffan Tunanin Data Fada idonta ya sauka akan Hajiyarsu Saurin Share kwallah Tayi kafin ta yunkura ta mike Tana Fadin"Hajiyarmu yaushe kika shigo..? Hajiya Turai tace"Ina Zaki san na Shigo kin Shiga Cikin Tunanin ki na Fama..?sau nawa zan Fada miki wannan Tunanin da kike yi da kukan nan bashi bane Mafita ba,Likita ya Fada miki ki Daina yawan Tunani da Damuwa saboda Jininki ya Hau sosai..! Mami batace komai ba illah kanta Data sadda kasa Hawayenta na Diga har kan Cinyarta,Kafin tace"Ya zan yi Hajiya..?kukan shi kadai ne mafita na Na Rasa komai na Rasa aurena na Rasa Ya"yana da Duka Martabana Hajiya ya zan yi..! tafada tana Kara Sautin kukanta Hajiya Turai kai Tsaye tace"Akwai mafita ki nemi Kabiru ki basa Hakuri ku Daidaita kanku..In ya"yanku suka ga haka suma Hankulansu zai kwanta..Nasan nima nayi kuskurre a Mtsayina ta uwa gareki ban Fadamiki Gaskiya ba sai na rika Zugaki Har Kika Tafkan wannan Kuskuran nima sai Daga baya na Fahimci Bamu kyauta ba Dagani har ke shiyasa nake so ki gyara Kuskuran ki ki same sa ki basa Hakuri ya maidake Dakin ki Daga baya sai komai ya Biyo baya..! Mami Tasaki Mirmishin Dayafi kuka Ciwo kafin tace"Ai bazai Saurareni ba Hajiya..Gabadaya Tun bayan Faruwar lamarin Ya yanke duk wata Hanya da zai sa mu hadu..Bazai taba Saurarata ba Hajiya na Rantse..! Hajiya Tayi shuru kafin tace"To ya za"ayi kenan..? Gashi kuma Justice yace bazai Kira sa ba..! Mami Asma"u batace komai ba ta koma Ta kwanta Tana jan majinan kuka,Hajiya Turai ta girgiza kai kafin Ta tashi ta Fice Cikin Nadaman Gudummuwar Data bata Wajen Kashe ma yarta aure da Lalata gabadaya Mafarkinta Tabbas itace sila in da a mtsayin ta na Uwa ga Asma"u ta bi Hanyar daya Dace da duk haka bai Faru ba Mami kuwa kuka kawai take Tana Tunanin mafita haka take Wuni ta Kwana cikin Daki bata Fita Tana Tunanin mafita da yadda Zata gyara Abunda ta bata.... Tayi ta Kiran Lambar khamis bata Samesa ba Ta Kira Wayar Sajida ta shiga ammh bata Dauka ba,sai Daga baya ta Kirata Daga yanayin Muryanta tasan bata da lafiya ammh sai tace mata taji Sauki Mami batabari Sajidan ta gane bata da Lafiya ba sai ta Boye mata adaran Jiya Ta samoma kanta mafita Batare da ta Yi shawara da kowa ba ita kadai ta Bata kuma ita kadai Zata gyara. Bata cikin karfin jiki Jiri ma take gani Ta Riga Tama Direban da zai Tukata mgana Tun Safe ta Shirya ba wani Shiri Tayi ba Kamar ba Asma"u yar gayu ba Tuni Gilashin idonta ya kama gabansa ma bata san isalinsa ba Tana ta kanta ne Figai Figai da ita ta Fito Ta Samu Hajiya Turai ta Fadamata Zata je wani Waje sai yammah Zata dawo. Hajiya Turai ta kalleta sai dai batayi mgana ba ta mata Fatan Dawowa Lafiya. Daganan ta Fice Direba ya Tukata suna Fita tace mai Dukku Zataje ba Musu ya Take Mota suka Dau Hanya ta Riga ta gama Neman ma kanta Mafita Zuwa dukku shine Mafitanta zataje ta Duka har kasa Ta bama Daada Hakuri ba domin Kabiru ya maidata Dakinta ba ko Zata ga Haske a Rayuwarta Sajida tana Halin cutar da taki barin Ma a Dubata ballatana agane meke Damunta ga Khamis ya koma Wani iri,Irin yadda take aibata ya"yan wasu Kai innalillahi rayuwa ta Juya mata baya bazata iya ita Kadai ba Wlh bazata iya ba wannan Nauyin yayi mata yawa Tabbas bazata iya ba. Har suka isa Dukku Mami Asma"u na kuka Hawayenta basu Tsaya ba lokacin da Baba Asabe ta shigo Dakin Daada Tana Fada mata zuwan Mami Asma"u din bata gama mamaki ba sai da Taga Mami Asma"u din Tsoron Allah ya kara kama Daada da Tsoron Duniya ganin yadda Mami ta koma Daada Sai Tayi kwallah Lokacin da Mami Asma"u ta Zube agabanta ta duka ta Dafa kafarta tana kuka Tana bata Hakuri Tana Fadamata irin Halin Datake ciki da Halin da Sajida ke Ciki da Halin da Baffa Kabiru yaje yaga Khamis aciki Mami Asma"u na Kuka hawayenta na Diga saman Kafafun Daada Dake Zaune take Fadin"Ki yafemin Daaada..Wlh nayi Nadama..Na Fahimci Abunda na aikatane duka suka Dawo kaina Daada Wlh bazan iya ba nayi Rauni nayi Laushin da bazan iya Daukan abubuwanan ba ni kadai Daada Kabiru ya Kirani yamin Allah yasa isa kan Ya"yansa Daada ina zan Saka kaina..?Wlh hakkin ku ne keda Imran da Malami da su Mustapaha da kukan da na Sakaki shine yake Bibiyata ban yi Tunanun kema kamar Uwa kike gareni ba ko Tsinemin kikayi sai na Bi Duniya..Don Allah da Zatin Allah Daada Kiyi Hakuri ki yafemin..! Daada Kwallah sai da ta Cikamata ido Ta saka Hannu ta Dago Mami Asma"u Data Durkushe gabanta Tana kuka Hawaye Shabe shabe hannu Daada ta Saka Ta Share mata Hawaye Tana Fadin"Wlh ban ta ba Rike ki araina ba Asma"u na yafe miki..Kuma suma zasu yafe miki..Ai tunda kin gane Kuskuranki bawanda zai ki karban Tubanki..Kabiru bai Fadamin Halin Daya je ya Samu Khamis ba Bansani ba..Ammh Zan Kirasa baza"a Zura ido ba su hadu shi da yan"uwansa suje su Taho Dashi Damuwace tasa ya shiga Halin Daya shiga ammh da Izinin Lahi Komai zai koma Daidai ki Daina kuka bakomai Insha Allahu..! Mami Asma"u na goge kwallarta Tana Fadin"Bayan Damuwa harda Silar Bakina Daada nayi ta aibata Imrana Ina Kiransa da sunayej banza..yau gashi Duka sun Tabbata kan Da"ana Daada Sakayyace Allah ne ya kamani Kaico na..! Tafada Tana Kara Saka Kuka Daada na Lallashinta Cikin Zuciyarta Tana Tsausayin Kabiru Lokaci Daya Kaddara ta Fadamai Allah Sarki yana chan cikin wannan kunar ga Asma"u Yadda ta koma Ko da wannan ka kallah Zaka Gane Allah shine gagara Misali. Bata yadda ta Fadama Mami Har Lokacin ita Matar Baffa bane sai dai ta Lallasheta ta kuma mata alkawarin Zatayi magana da Baffa Kabiru Sajida kuma zata dawo gida Domin asan meke Damunta Mami Asma"u bata jima sosai a Dukku ba Hankalinta ya kwanta jin Daada bata Riketa aranta ba Dakyar ta Tsaya taci abinci Sama Sama Tayi ma Daada sallama Direba ya Juya da ita,Daada ta bita da kallon Tsausayi. Tana Tafiya ta saka Baba Asabe ta Kira mata Baffa Kabiru Dake chan yana Faman Kokuwa da Zuciyarsa shi kanshi Tun bayan Dawowarsa Anambara Da ganin Halin da Tilon Dansa ke ciki bai da Cikakken Lafiya yayi kuka har ya Gode Allah kwakwalwarsa Ta toshe yarasa Tunanin ma me zai yi..?ballatana ya Samu Mafita Lokacin Daada ke Fadamai zuwan Asma"u bai ji mamaki ba sai dai bai Zata Zata karaya haka Cikin Sauki ba ya Dauka Bata gama ganin komai ba yanzu ta Fara gani nuna ma Daada yayi karya Take duka kukan Munafunci ne Daga baya kenan bayan ta gama Lalata komai..?shi yanzu yadda zai Dawo da Rayuwar Khamis kamar baya yake Tunani Tunda Taje ta Fadama Daada komai,Daada tace maza ya Kira yan"uwansa aje a taho da Khamis Gida yafi a barsa chan inda bai da kowa abakin Daada yaji Labarin Rashin Lafiyar Sajida shi kanshi in da Zai kwanta adubasa Wlh Jininsa ya Hau har suka gama mgana Da Daada baya Cikin Hayyacinsa Hawaye da kuka sun Rufemai jinsa da ganinsa Allah yasa yana gida kwana Biyun bai je ko"ina ba. Sai da ya Samu Natsuwa ya Kira Abba da Daddy ya gayamusu komai suma Hankalinsu ya tashi Daddy yace Da kansa zai hau jirgi zuwa Anambara Gobe zaiTaho da Khamis Basai Abba da Baffa Kabiru sun taho ba Yace Baffa Kabiru ya turamai Address din nan da nan kuwa ya Turamai sun Rabu kan Gobe zai tafi Sajida kuma Zai je Har makaranta ya Taho da ita Gida. Ashe abunda basu sani ba Khamis bayan ya Dawo Daga Hayyacinsa budurwansa abokiyar Watsewarsa Tasa mai suna Suzana,Ta sanar dashi Zuwan Mahaifinsa da Halin Daya Tarar dashi,Batasan Baffa Kabiru ba ammh Kamarsu da Khamis da kuma cemata da yayi shi babansa ne aranar Dayazo bayan ta Budemai kofar Falon Gidan. Gabadaya Jikin Khamis ya gama yin Sanyi Tsoron Allah ya kamashi da wani ido zai kalli Dad dinsa..?wata amsa zai bai bashi in ya Tambayesa meyasa ya koma haka..?yace Saboda Rasa Mace..?ya koma Sabama Allah..?wannan duka ba Hujja bane ya karya Zuciyar uban Daya Dora yakini akansa Tir da Rayuwar Daya Zabama kansa Tundaga Ranar ya Tattara komai ya Watsar Tare da alkawarin Har Abada bazai kara ko Busa Sigari ba ballatana Har ya Daga wata kwalba ya Rufe babin mata da komai na Harkan Shanshanci Har Abada ya Fara Shirin Tahowa gida Domin ya Nemi Gafaran Daad ya yafemai Laifin Daya aikata. Aranar da Baffa Kabiru sukayi mgana da su Abba da asuba Khamis ya Sauka a Filin Jirgin Abuja Taxi ya samu zuwa Gida sai dai Baffa Kabiru da Umaima suka gansa Kwatsam Allah Sarki Rayuwa Khamis yayi kuka sosai Dayaga yadda ya tafi ya bar Baya da Kura Mami Ta Dade bata gida sun Rabu da Daad Sajida Tana makaranta Cikin Halin Ciwo shi kuma yana chan yana Shanshanci Kai consa,Abakin Umaima yake jin komai Domin Sanda ya iso Dad na cikin Dakinsa sai da ya Fito ya gansa.. Haka Khamis ya Duka ya Rike Kafafun Baffa Kabiru yana kuka yana Rokonsa Gafara Tare da alkawarin ya Daina Duka Abunda yake yi Har Abada bazai koma ga aikin Daya baro ba Me ya kamata Baffa Kabiru yayi banda ya Tallafi D"ansa da Allah ya Dubesa ya Karkatomai da Hankalinsa kan Hanya Madaidaiciya ya Rumgumesa yana Godiya ga Allah Hawaye na Ziraromai bai bari Khamis din ya gani ba yayi Saurin Dauke hawayen.. Nan da nan Baffa Kabiru ya Kira Daddy ya Fadamai ya Dakata da Tafiya Anambara ga Khamis ya Dawo gida da kansa jin haka yasa yayi Hamdala Daddy ya Kira Abba ya Fadamai Khamis ya Dawo gida Abba ma Nata Hamdala sun isa Barka. Aranar ma Baffa Kabiru bai Fita ba yana Tare da ya"yansa Khamis da Umaima Domin ya Dauki Daraman Gyaran Duk inda ya Kuskure Domin Dawo da walwalan ya"yansa sun yanke Shawaran gobe da safe dashi da Khamis zasu je makarantan su Sajida su Taho da ita sai dai Misalin karfe Daya na Dare Sai ga wayar Mami Asma"u ta Kira Baffa Kabiru karo na Farko Bayan Lalacewar abubuwan Daya ga Kiran bai Dauka ba Tunda Idonsa Biyu Har Lokacin bai yi barci ba Mugun Haushinta yake ji Gani yake Munfuncine ba Tuban Allah da Annabi bane gani tayi ba Sarki sai Allah ta kuma Rasa komai Shiyasa ta Dawo Tana Rabe Rabe Macijiya. Sai da yaga Kiran yaki ya kare kana ya Daga afusace ya auna mata ashariya ko Ta kyalesa sai da jinta Cikin kuka Tana Fadamai gasu a asibitin Specialist Hospital inda aka kawo Sajida bata da Lafiya Tana ta Tari da Jini Jin haka yasa Hankalin Baffa Kabiru ya kara tashi Cikin Tsananin Tashin Hankali ya Zura Jallabiya ya Fice Dakin Khamis ya shiga ya tasosa hankali Tashe yake Fadamai Halin da ake Ciki,Shima Hankalinsa ya Tashi Umaima ma Muryansu ya tasheta Daga Barcin Daya kwasheta itama jin Abunda ya Faru da yar"uwanta sai kuka Gabadayansu suka Dunguma suka Tafi. Koda suka je sun Iske Mami Asma"u da Hajiya Turai da Justice Tafida yarkace yarkace sai kuka Take TanaTuma kamar Mahaukaciya Idanuwanta sun Kole saboda kuka Ita jenefer ta Kira saboda itace Lambar Karshe da Sajidan Tayi mgana da ita suna Kwance adaki Sanda Tarin ya Sarke Sajidan da Zafi Har ta Fita Daga Hankalinta Jenefer ita taje ta Fadama Maman Hostel dinsu ita kuma ta Sanar da kuma Hukumar makaranta aka Kwaso su zuwa asibiti bayan an Shiga Da Sajida Emergency ne Ta samu Wayar Sajidan ta Kira Mamin Ta Fadamata wanda Kurruwanta ya Fito da Justice da Hajiya Turai jin Abunda ke Faruwa yasa suka Rankayo Gabadayansu Cikin Tashin Hankali. Ita uwa uwace ko ya ta Zama Haka Umaima da Khamis suka isa ga Mami Asma"u suka Dagota suka Rumgumeta suna Lallashinta Data kyalla ido Taga Khamis sai Rauninta ya bayyana ta Fada Jikinsa Tana Fadin"kaima ka Gujeni Khamis..Dad dinku ya sakeni Sajida Zata Mutu ta barmu Aman jini fa take..an shiga da ita Likotoci basu Fito ba Har yanzu na shiga ukuna na Lalace..! Haka take fada Cikin kuka tana Rike Jikin Khamis da shima yake jin kamar ya Fashe da kuka Idanuwansa sun yi Jajir kukan Mami kuka ne da zai Kassara Duk zuciyar mai Sauraranta Ammh banda ta Baffa Kabiru bayan gaisawa da Justice Tafida da Hajiya Turai bai kara mgana ba sai gaisuwan abokiyar Karatun Sajida Jenefer Daya amsa ko Barayin Mamin bai kallah ba Ballatana ta saka Ran wani Rahma Daga bangaransa. Gabadaya Hankula basa kwance Fin Mintina arba"in kafin Likitocin da suka Rufu kan Sajida su Fito basu tsaya amsa ma su Baffa Kabiru Tambayansu ba sukace jictice Tafida ya Biyosu Office shi da Baffa Kabiru Matan su Tsaya a waje. Baffa Kabiru ya Razana Dayaji bayanin Likita kan Abunda ke Damun Sajida ta Hadu da Heart problem Ciwon Zuciya Wanda har ta Fara Tabuwa saboda matsanancin Halin Datake Ciki Ta fara ganin jini in tana Tari bata zo asibiti ba har abun yayi yawa,Ammh dai yanzu ta Fita Daga Cikin Hatsarin Datake ciki sai dai Duk Abunda akasan Tana son gani ko Tana so a kawo matashi gabanta da Zarar ta Farfado in ba Haka ba zata samu Heart Attack arasa ta gabadaya. Baffa Kabiru Haka yake sharan kwallah Da Gaske Sajida take Tana son Imran Asma"u ta rabata dashi Gashi Soyayyarsa zai Zama ajalinta Shi kanshi Justice yaji Mganar sosai Jikinsa yayi sanyi shine ya iya Fita yayi ma su Khamis Bayanin da Likita yayi musu ai sai Wajen ya kara Rikicewa Mamin Har wani Suu Tayi Zata Fadi Hajiya Turai da Khamis suka Tarota kasa takai hannunta Saman kanta ta manta asibiti suke ta Kwarara Ihu Tana Fadin"Na shiga Uku..Na Shiga uku Ni Asma"u na lalace..! Baffa Kabiru da Ransa ya baci Tana Neman Tara musu jama"a Allah yasa ma Dare da sanin su manyan Mutane ai da ba haka ba wata Gigitattaciyar kara ya Daka mata Cikin Kaushin Murya ya fara fadin"Dillah kima Mutane Shuru..Kukan Uban me kuma Zaki mana..?kukan karya da munafunci..?ko na nadaman Dole..?duk abunda ya Faru da Sajida kece Sila...ke kika Rabata da abunda take so kika yi Sanadiyar Shigarta wannan Halin sannan kizo ki Damemu da kukanki na Banza Baki bani kin Lalace ba Asma"u Sai Y'ata ta Rasa Ranta ta Dalilinki na Rantse da wanda Raina ke Hannunsa sai nayi Shari"a dake sai kin Biyani Diyar kashemin yata da kikay Muguwa kawai azzalumuma mai Zuciyar Zalunci wacce batasan komai ba sai kanta.! Ya karishe Fada Cikin Sakarmata Jajayen Idanuwansa da suka Rine Saboda kuka Ba wanda iya mgana sanin ai gaskiya ya Fada Mami Asma"u jikinta na rawa da bakinta ta kasa mgana Jikin Khamis ta koma ta Lafe Umaima ta Kwantomata Tana kuka ai ita kukan natama ya Tsaya ta shiga wani yanayin da bawa bai isa ya Fassara ba. Hajiya Turai ne cikin Damuwa tace"Haba Kabiru don Allah ka Ragama yarinyar nan mana..Tafuskanci abubuwa da yawa ko baka Ragamata ba Saboda Zaman tare ba ai ka Ragamata saboda Daranjanmu iyayenta Dake Tsaye da su kansu Yayanku gasu nan da kuma Wacce ke kwance cikin nan Cikin Kokawaa da Numfashinta..! Ai in ma ya Bude baki yace wani abu Allah Zagin Hajiya Turai zai yi shiyasa yayi Shuru ya Dauke kansa yana ajiyar Zuciya Sai Wurin yayi Tsit sai Jan majinan Umaima ake ji Mamin kamar ai Wutarta ta Dauke justice kala bai ce Daman ba kuma zai ce ba Wanda bai ji bari ba bazai ji Hoho ba Dukkansu Zaman jiran Farfadowam Sajida suke Gabadayansu suna asibitin aka Kira sallar asuba kana Mazan suka tafi masallaci cikin Asibitin Harda matan sukayi Sallah Kowa Zuciyarsa ba Natsuwa Jenefer sai alokacin Tayi musu sallama ta koma Cikin makaranta su kuma tunda suka Dawo Sallah ba wanda ya Mtsa suna Fatan Sajida ta Farfado Cikin Hankalinta. Saboda Tashin Hankali yasa Baffa Kabiru ya mamta da Kiran kowa Sai da Sajida ta Farfado Daman Tana Emagency din har alokacin Likitoci sun Rufu kanta ammh ba sunan Datake Kira sai sunan Imran kuma Rashin Ganinsa Cikin Lokaci Mtsala ne haka Likita ke sanar dasu Baffa Kabiru Hankulansu ya kara tashi an basu Izimin Shiga su ganta Mami ce kan gaba Kamar Zata Kifa Tana Shiga Tafada jikin Sajida dake kwance Rai kwakwa Duk ta Rame tana mai Fashewa da kuka Tana Fadin"Ki yafemin Sajida..Dom Allah ki yafemin..! Sajida Tana kuka Tana Rike Saitin Zuciyarta Tana Fadin"Mami Ku kiramin Imran in ban gansa ba Mutuwa Zan yi..! Take Fada Tana kuka Gabadayansu Sun Zagayeta masu Saurin kuka irin su Hajiya Turai da Umaima suna ta Faman Sharbawa Justice Tafida ne ke Fadan Mami Ta Daga Sajida bata ga bata da Lafiya bane kuma ta Danneta Tana kuka Khamis kuwa Gefen Gadon ya Durkushe yana kokuwa da Numfashinsa. Baffa Kabiru waje ya Fita yana Dauke kwallarsa bazai iya Juran ganin Sajida ahaka ba ba ita ya kamata ta Fuskanci wannan ba Asma"u ita ya kamata ta karbi wannan Hukunci. Kai Tsaye Abba ya Kira da Daddy ya Sanar dasu abunda ke Faruwa Hankalinsu ya tashi Kwarai Tare da Tsausayin Dan"uwansu dukkansu sun Tabbatar mai gasunan zuwa yanzu zasu kamo Hanya. Daga su sai Imran Baffa Kabiru ya Kirasa Lokacin ya bar Gida zuwa Wajen aiki ne Jiya gidan Abba suka kusa Raba Dare Khalil ne jiya ya zo Daga Lagos wajen Munari mgana har Taje kunnensu Abba Tunda Dr.Ali argungun ya Kira Abba sun yi mgana,Wajensa ya Tsaya suna Hira da kuma Rigiman Inteesar na da sai ya barta ta Kwanan anan ya Tubure mata ya dawo Mata a Imran dinsa da baya Daukan Raini ballatana Wargi Dole ta biyosa suka Dawo Ko yau da Safe ya Fita ya barta Tana ta Fushi ya Fita Batunta daya dawo ya Fara Lallashinsa Zata mamta komai ta bada kai Bori ya hau. Lokacin da Baffa Kabiru ke Fadamai Halin da ake ciki jikinsa yayi Sanyi sai bai kara yin sanyi ba sai da yaji Baffa Kabiru na Rokonsa Allah da Annabi kan yazo yaga Sajida kafin ta bar Gidan Duniya yana mgana Daga jinsa kuka yakeyi Imran bai taba Jin Tsausayin Baffa Kabiru ba irin na Wannan Ranar ba har baisan Sanda ya Tabbatarmai da Insha Allahu yana Tafe yanzu da yardan Allah.. Jikinsa a sanyaye ya Tattara kayansa ya Biya Office din Manaja ya Fadamai Uxurin Rashin Lafiya ne yamai Izinin Tafiya ya Fito Daga Bankin kenan yaji Kiran Abba ya Dauka sukayi mgana Abba yana Fadamai Halin da ake Ciki yace Yanzu Baffa ya Kirashi shima Abujan zai tafi yanzu Abba yace yaje ya Dauko Inteesar gabadayansu Zasu Tafi da haka suka Rabu. Gida ya koma Inteesar na Kwance da Matashin Cikinta yace ta tashi ta sa Hijabi su tafi shi ya Zata gidan Abba zata zauna kafin su dawo jin Tafiyace ta Mike da Murna ta saka Hijabi suka Tafi koda sukaje sun iske har Ya yusuf shima dashi Za"a tafin bai je aiki ba Khalil ma yace dashi Za"aje Kowa yace sai yaje harda Munari Anty Safiya ce kadai aka bari agida Tana jego Saboda Yadda Labarin ya same su sun matukar Tsausayamata da Halin Datake ciki,ganin haka yasa Itama Inteesar tace sai taje itama Imran bai da yadda zai yi ya Hanata zuwa ammh bai so bayaso gudan Jininsa ya Wahala sosai ammh baida yarda zai yi. Ashe Labari Tuni ya Zaga Dangi suna Shirin Tafiya sai ga Wayar Sadam shima zai je basheer ya Kirasa ya Fadamasa yace ya Kira sa"id shima ya Tabbatarmai da yana Hanya Duk wanda yaji Halin da Sajida Take Ciki Sai ya Tsausayamata. Sadam suka Tsaya jira ba Dadewa sai gashi Shi kadai ne Aneesa na Gida da Yara Imran ya Kira Sagir yace ya Shirya su tafi Daman jiya su ukun suna Tare sun Hade shi da Khalil suna ta Caccakasan yayi musu banza. Imran a Motarsa ya Dauki Khalil da Sagir Ya Hada matan chan Motar Yusuf,Abba dagashi sai Direbansa hakama Ya Sadam suka Dauki Hanyar Abuja,suka bar Anty Safiya Dayake Tasleem na Tare da ita ga kuma Mama Achan kaduna ma Daddy Da Umma sai Ya Basheer Dake Tukasu suma din duka Hankalinsu ya tashi goggo Bintali da goggo Maimunatu suma sun ji labari Daddy ya Kirasu ya Fadamusu,Daada ce kadai basu Fadamawa ba Gudun Tashin Hankalinta,Dukkansu sun kamo Hanya basu zauna ba Domin Haka suna da kara iin wani abu ya Faru da nasu kwansu da kwakwartansu. Daddy su suka fara isa Abuja waya kadai yayi ma Baffa Kabiru ya basu kwatancen Inda suke,Daman yasan asibitin nan take sai gasu sun iso Lokacin an kai Sajida ma Daki na Musamman kebabbantacce. Koda suka iso an mata Alluran barci Ta samu barci ganinta Tana ta kuka da Sambatun Kiran sunan Imran Umma ta kara jin jikinta yayi Sanyi ganin yadda Mami Asma"u ta koma Kunya Ya hanata ta iya Daga ido ta kalli kowa Kukan ma ya Daina zuwar mata sai ajiyar zuciya kawai ta Jeme kamar ba ita ba Shi kanshi Daddy sai da ya Jinjina. Gudu sosai sukayi a Hanya kafin su iso,wajen azahar suma Direct asibitin suka iso,Mami Asma"u ta kasa Iya Hada ido da su Abba ballatana Imran Kusan Lokaci Daya suka iso da Inna Maimunatu da Mijinta ,Inna Bintalo ma ta iso Daddy da Abba Dan"uwansu suka Rumgume cikin Damuwa da ganin yadda shima Duk ya Jeme Saboda Damuwa su Sadam suka isa ga Khamis shima abun Tsausayi Umaima ta Rumgume Munari Tana ta kuka,ba Dadewa sai ga Sa"id ya iso Shi da Fareesatu da Hafsah da yara Inteesar dai na makale da Umma itama Duk jikinta yayi Sanyi,Khamis kuwa Sau Daya ya kalli Inteesar bai kara ba haka itama Imran na Tare da abokansa Sagir da Khalil,Sai dai Kuma karo na Farko da yaji Taausayin Mami ya Darsun mai ganinta a rakube Duk ta Fige ta Rame kamar ba ita ba Rayuwa kenan Dayake Justice da Hajiya Turai sun Koma Gida Dazu bada Dadewa ba Kamar Sajidan ta sani suna isowa ta Farka ta Fara Kiran sunan Imran,gabadayansu suka Nausa Cikin Dakin Baffa Kabiru ya bangaje Mami yana Hararanta wacce ta isa ga Sajidan Tana Riko hannunta Mami kanta na kasa ta kasa dagowa ma ta kalli kowa sai Hawaye dake bin Kumatunta Kowa adakin sai da ta bashi Tsausayi Umma ce ta Rikota zuwa gefenta ganin Tana neman Faduwa. Baffa Kabiru ya isa ga Sajida ya Riko Hannunta yana Fadin"Sajida ga Imran nan yana jinki..Gashi nan kin gansa..? Yafada yana Nuna mata Imran wanda Abba ya jawosa Gefen da Baffa Kabiru ke Zaune daga ido Tayi tana kallonsa Shima kallonta yake yi cikin Kallon Kuduran ubangiji ganin yadda Sajidan ta koma Lokaci Daya.. Idanuwanta na Zubar kwallah ta Kira Sunansa..! Imran..! Sai Hawaye sharr..Baffa Kabiru ya tashi Daga kujeran Dake gefen Sajida ya nunama Imran alamun ya zauna ba Musa yaja ya zauna Cikin bayyana Jimaminsa sai dai bai nuna afuska ba,inteesar na gefen Munari duk sai taji Kishi ya kamata kada fa ace Mijinta ya sake auran Sajida..?domin bazata iya zaman Kishi da ita ba..! Sajida ce ta kara kiran sunan Imran yasa ya amsa mata Cikin Muryansa mai Cike da Zati tana kallomsa Tace"Imran nasan ka Tsane ni ko..? Sai kuka wiwi sai tari mai Hade da Jini Imran yaji wani iri acikin Ransa Hannun Sajidan da ba"a sakama Drip ba ya Rike gam yana Fadin"Wlh ban Taba Tsanarki ba Sajida..! Yafada yana jin Rauni da Taausayinta sai dai ba wai don yayi Nadaman Sakinta ba A"a baya sonta bazai aureta ya Cutar da ita ba. Sajida tace cikin muryan kuka.."Meyasa ka sakeni..?meyasa baka sona..! Imran ya Runtse ido kafin ya Bude yace"Na sakeki ne saboda bana sonki na aure ki in na Zauna Dake zan kwareki..Inteesar nake so..Kinga bai kamata na Zauna Dake ahalin ina son Wata ba..Kuma ni zuciyata Tana Girmama Ra"ayina mganar na Tsaneki bata taso ba..Ina sonki Soyayya irin ta yar"uwa da Dan"uwanta..! kafesa Tayi da ido kafin tace"Kana sona Kamar kanwarka Munari.?ko haka na samu ma na gode..! Take Fada Tana Hawaye Hannu ya saka yana Dauke mata Hawayen Lokaci Daya yana Fadin"Ki Daina kuka..Munari ta zama Old kece sabuwar kanwar tawa Tilo....! Tana Dariyan DAuriya tace"Ko yau na Mutu naji Dadi..! Imran yace"Ba mutuwa yanzu kamwata..Maza kitashi Aure ma zan yi miki da yardan Allah..! Cikin Rinanun idanunta tace"Wazai aureni...? Bai amsa mata ba ya Dago kansa yana kallon Khalil Dake kallonsa Shida Sagir Gabadaya ma Dakin Hankalunsu na kansu Banda Inteesar da Kishi ya Turnike tun sadda ya Rike hannun Sajida ta kauda kanta. Tashi yayi Tsam yaje ya Riko Hannun Khalil wanda ya saki baki yana kallonsa Munari ma haka dasu Abba Har gaban Sajida ya Zaunar dashi inda ya tashi ya Dauki Hannunsa danata ya Hada yana kallonta yace"Ga Mijin dana Zaba miki kanwata ina Fatan bazaki bama yayanki kunya ba..! Yafada yana kallomta kafesa Tayi da ido kafin tace"yana sona ne..? Imran ya kalli Khalil dayayi sunan Zaune Kafin yace"Sosai ma..Tambayesa kiji..Wazai ki Zangadediyar yarinya kamarki Diyar Lauyoyi jikar Lauyoyi..! Ya karishe Fada da Sigar Zolaya. Sajida ta kada kai Tana dariya da Hawaye Lokaci Daya Tana kallon Khalil da jikinsa ya gamayin Sanyi ya Imran zai mai haka ya manta da Munri ne kamar yadda Itama Munarin ke Tambayan kanta haka suna kallon juna ita dasu Hafsah da inteesar. Sajida na kallon Khalil tana Fadin"Kana sona da gaske..? Tafada Cikin karyayyiyar murya Cikin Rauni da saka rai Imran ya Daki Kafadan Khalil bayan ya Dago ya kallesa Kallon ya zakamin haka.? Bazai iya watsamai kasa a ido ba yasa ya Gyadamata kai yana Fadin"Indai kin amince ko gobe ne A Daura mana aure..! Sajida Sai Farinciki ya kamata ko bata auri Imran ba ko bai sota ba ya Fadamata bai Tsaneta ba sannan itama Zatayi aure kamar kowa sannan Zata auri abokinsa Daman haka Rayuwa ta gada ba Lalle ne sai mun samu abunda muke so ba.. Ido ta Runtse sai Hawaye gabadaya Kowa sai jikinsa yayi sanyi Khalil ya Kasa Hada ido da Munari Lokacin Datake kallonsa na yaya Zakayi Dani..? Imran ya isa gaban Baffa Kabiru yana Fadin"Baffa Khalil abokina ne..Zaka bashi Auran Sajida..? Baffa bai san me zai ce ba iya Kafadan Imran Daya Dan Daka yana Fadin"Allah ya sanya alheri..! Abun fa na Imran ba wasa bane kamar yadda wasu suka Dauka. Gaban Mami ya isa kafin yace"Mami Zaki bama abokina Khalil yarki..Kin gansa ko Sigari Bai taba Shaba..Sai dai Ma"ikancin banki ne kamata babansa kuma Malamim Jami"a ne kamar Mahaifina ba Lauya bane kuma ba Jikan Lauyoyi bane..! Yafada yana kallonta Mami kuka ya Kamata batasan Sadda ta Durkushe kasa ba Tana Fadin"Ku yafemin don Allah ku yafemin.! Yadda Take kukan sai ta bama kowa Tsausayi Imran ya Saka Hannu ya Dagota yana Fadin"Haba Mami..Bai kamata ki Dukamin ba..Nima ya kamata na Duka miki nima ai nayi Miki Rashin kunya ki yafemin.? Mami na Kuka Tana Fadin"Wlh bakamin komai ba Ni nayi muku..Maimunatu Malami da Mustapha ku yafemin Kabiru kaima ka yafemin da duka sauran wadanda na Batawamawa ku yafemin.! Kuka take jiri neman gadata Imran ya Riketa da Sauri Khamis yazo ya Taimakamata Daddy yadauko mata Kujera ta Zauna Abba ya Miko Ruwa suka Bata ta karba tasha Tana Dauke kwallarta Tana Musu Godiya Abba da Daddy sukace su bata musu komai ba sun yafe mata. Inna Maimunatu ma haka Inna Bintalo ma sai Hawaye ganin yadda Mami ke kuka itama ta Roki yan"uwanta gafaran Abunda Tayi ta yi na Gulma da Bin bayan karya sukace sun yafemata. Munari dai ta kasa mgana kanta na kasa Khamis ya bama Imran hannu suka yi Musabaha bayan sun ma juna Sallama Khamis ya Kalli Munari kafin ya kalli Imran yana Fadin"Babban yaya Tunda dai am min kafa awajen Inteesar sai ka bani Dayan kanwar Taka Tunda naga kana ta badasu ka manta Dani..! Gabadaya sai da kowa ya Murmusa Har Sajida dake kwance. Imran ya shafa kansa yana Fadin"Wacce Daga ciki..!? Hafsah dai Na Riga na bama Abokina Sagir..Sai Autar Abba Daman ta ishemu na baka ita..! Ya juya wajen Munari Dake Hawayen wannan Karfin Halin na an rabata da masoyinta za"a likamata wani. Yace"Ke..Ga Khamis nan shine mijinki bana son gaddama..Saura ki rainasa yayanki ne kuma sojane kinsan sauran..kai kuma in tayi maka ba Daidaita ba ka sauya mata kammani ni na baka Umarni..! Khamis ya Ramkwafa yana Fadin"An gama Babban yaya..! Imran ya Dafa kansa yana Fadin"Yauwa dan abarka..Kafi sauran ladabi..! Yafada yana Hararansu Khalil Gabadaya Wajen sai da aka Saka Dariya ganin yadda Imran yayi Harda Mami da Murna da kunya suka kamata Ita taki Imran saboda yana shan Taba yau ga Malami zai bama D'anta Yarsa wanda har da mata yayi mu"amala Mami ta ji kunya Nadama Ta kara shigarta. Khamis gefen Munari ya koma yana mata mgana Sagir na gefen Hafsah Hakama Khalil yana gefen Sajida ya Duka yama mata mgana Domin Lamarin Tsarin Ubangiji ne matar Mutum kabirinsa. Imran ma Wajen Inteesar ya koma ganinta Tana Tura baki Ido ya kanne mata yana Fadin"Sorry..! Tura baki Tayi ta kauda kai yana Dariya ya rikota su Abba kam suna ta kara bama Baffa Kabiru baki kan ya saurari Mami Asma"u su yusuf kam komai yayi daidai suna ta mgana dasu Sadam Umma na Tare dasu Inna Maimatu kafin Lokaci kadan gabadaya an samu Fahimtar juna gaban kowa da kowa Mami ta Duka ta bama Mijinta Hakuri ya Dagota yace ya yafemata kuma yashaida mata ita din Matarsace tun sadda ya Saketa yan"uwansa suka saka ya maidata Mami ta karajin kunya ashe haka su Abba suke..?yadda taci ma Daada Zarafi basu Riketa aransu ba da sun Riketa da basu ceci auranta ba Hakan ba karamin Dadi yayi ma Khamis da Umaima ba suka Hadu suka Rumgume Mamin da Baffa Kabiru Sajida na kwance Tana Miko hannu suka Tafi gareta suka Rumgumeta Mami nata kuka tana share ma yarta Hawaye Kowa sai Dauke kwallar Farnciki yake yi Munari ma Tuni ta Daina kuka suna ta mgana da Khamis Domin ta ma Cire Khalil Daga Lissafinta Lokaci Daya Taji Khamis din ya kwanta mata kamar yadda Shima anashi Barayin yaji Sajida tayi mai daidai dashi Duk tun a hanya sagir ya bashi Labarin abunda ya Faru da komai da komai. Likita ne yazo ya Korasu waje suka Duba Sajida suka mata allura Barci Likita ya Fito da Murnan ganin Chanji Tare da tabbatar musu indai Sajida Zata kasance Cikin Farinciki Zata Samu kanta dayardan Allah Sai da suka baro Dakin ne Imran ya Radama Yusuf wata mgana akunne shi kuma yaja Daddy da Baffa Kabiru ya Fada musu suna Dawowa suka kalli Abba Daya Tsargu Baffa Kabiru yace"Malami kaima aure zam maka nagaji da ganin ka ahaka..! Abba ya Zaro ido gabadaya wajen aka Saka Dariya Daddy yace"Eh musan zaka ce baka da wacce ka Tsaida mu muma dashi..Imran da Yusuf sun ga Chanchantar Amina yayar Salaha..Maman Sagir Saboda haka ita muka Zaba maka itama musan bazataki ba..! Abba zai yi mgana kenan Imran yayi Zaraf yace"Kuma saboda Daada..Allah ta kusa Mutuwa gwara dai ta Fara Daukan sauran ya"yanku kafin namu! Abba ya kaimai Duka yana Hararansa ya Goce jikin Yusuf gabadaya aka saka Dariya Yusuf ya Daga hannu sama yana Fadin"Ba ruwana Abba Imran ne..! Yadda yayin ne Zaka gane bai da gaskiya Dariya aka kara sakawa Sagir ma Farinciki ya Cikasa Abba ai Mutum kwarai ne kowacce mace Zata so ya Zama bangonta. Inna Maimunatu ta Kira Daada ta Labarmata komai Daada nata Kukan Farinciki akabama su Abba Tayi ta saka musu albarka Tana jin hadin da Imran yayi da kuma mganar Abba Daada ta Roki alfarman Azo Dukku duka a Dauran auran da Shagalin Bikin Tana Bukatar ganin Ahalinta Waje Daya Cikin Farimcikin da bata Taba gani ba nan da man kuwa su Abba suka amince Umma kuwa har ta Kira Mama ta Tsegunta mata mama kunya ta kamata in ita ina kin Abba..?Umma ta fesa Labari har kaduna Wajensu kawu Bala sukace ai wannan Labarin ya gama yi musu Dadi ba Dukku ba ko"ina ne sun yarje sun bada Dama Ko Daddy ya isa ya zama Waliyin Mama Gabadayansu Gidan Daddy suka kwana Harda Mami Data Kira Hajiya Turai ta gayamata Komai nan da nan Tayi hamdala da jin wannan Labarin Tana gayama Justice bakinta kamar ya Tsage shima ya jinjina kai afili ya Furta Alhamdulillah! Sajida kadai suka baro a asibitin saboda basa Bukaatar masu jinya An kwana cikin Farimciki matuka imran da Sagir da Khalil da Khamis sun Hade waje Daya suma su Inteesar suna Tare da Umaima Washegari Kafin suwuce sai da suka Biya ta asibiti suka Duba Sajida taji Sauki sosai kamar ba ita ba Gabadaya bakin suka koma saboda ayyuka Khalil kadai suka bari sai gobe zai bi Jirgin Abuja zuwa lagos Khamis kuwa kafin Su Munari su tafi sai da ya Tabbatar da cikin Kwana Daya shima ya kafa nashi Ginin. Su Daddy sun Rabu kan in An sallami Sajida Daga asibiti zasu hadu a Dukku su Tattauna mganar gagarimin Bikin da zasu gudanar na Yan mata uku Zaratan Samari Uku da Daurin auran Iyayen nasu Mama da Abba..! *Janafty* 3/31/22, 15:36 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�31* *Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488* Sai da Sajida ta shafe Sati Biyu a asibiti kafin a sallameta ta dawo gida bayan taji Sauki sosai ta fara maida Jikinta ganin Rayuwa tayi kyau Mami Asma'u Ta gyara Halinta ta Rumgumi ya"yanta ta Fahimci inda ta Gaza yanzu da Ra"ayin Baffa Kabiru da duka Umarninsa take aiki. Abba da Daddy da Baffa Kabiru sun je Dukku sun zauna da Daada mganar auran dake gabansu Daada tace ita nata Fatan alheri ne da addu"a Mgana da Zartarwa Duka nasu ne sun Taru sun Tsaida Lokacin Bikin gabadaya nan da Wata Hudu kuma Duka a Dukku Za"ayi in an gama Biki araka Amare Gidan zasu zauna da Mazajensu. Mganar Abba da Mama kuma Daddy yaje Har gida yasamu Inno da Mallam Babba kan mganar su kuma suka bashi Wuka da Nama kan lamarin Kawu Salisu yace ko shi ya isa ya Zama Waliyin Mama saboda Haka sun Amince Dari Bisa Dari indai Mama ta Amince Daddy ya Kira Abba yace yaje su gama da Mama. Abba bai iya watsama ya"yansa da yan"uwansa kasa a ido ba yaje Har Gida ya Samu Mama suka Tattauna Mama bata isa taki Abba ba Domin wani Bango ne Allah ya Aiko mata dashi Tun bayan Rasuwar Mahaifin Sagir bata karbi Sadakinta ba sai da ta Samu Baba manu ta Fadamai komai Domin ya Chanchanta kanin Mijinta ne na baya ammh bayan kasa ta Rufe idon Tasiu ya kula da Rayuwarta ita da Sagir Shima Lokacin Dayaji Abba amtsayin Wanda zai auereta sai yafi Mama Nuna Murnansa da Amincewarsa Dari Bisa Dari Mama Taji Dadin haka Daman game da yan"uwanta bata da Damuwa Umma Tafi kowa Murna da wannan Hadin. Baffa Kabiru shi ya biyama Abba Sadaki kamar yadda yayi alkawari Naira Dubu 100,Dakyar Mama ta yarda ta amsa da tace yayi yawa sai dai an Rage Zata karba sai da Baffa Kabiru yayi mgana da ita a waya kana ta yarda ta amsa An Fara Daura auran Mama da Abba anan masallacin Kusa dasu inda suke Salla a wata ranar Jumma sai aka bar Tarewar Lokaci Daya dana su Munari Baffa Kabiru ya karban ma Abba Aure Kawu Salisu ya zama Waliyin Mama Aranar Bakin Imran da Sagir Dana Yusuf yaki Rufuwa Allah Sarki Rayuwa Allah ya jikan Anni da Gafara Mama tana Tare dasu Umma da Maman Nasara, Da Mami Asma"u da suka zo Tare da Baffa Kabiru da Khamis sai Mommy maman Anty Safiya duk ba Taro bane ammh Mama taci gayunta an kuma yi abinci suma chan gidan su Inteesar nata nasu Shagalin da su Anty Safiya da Munari da Hafsah da Tasleem da Nasara duk sunsamu zuwa suma sun yi kayattacen Girke girke da Ababen sha su Abba da yan"uwansa suna Haraban gidan suna cin Abinci suna ta Fira su kuma matansa suna Falo suna ta cin Abinci suna Hira Harda Sadam yazo Aneesa da yara suna Cikin Shashen Anty Safiya yan matan ba wacce ta Leko Tun bayan da suka Cika gabansu da abinci suka bace duk kuwa da yarda Samarin nasu suke ta Tura musu sakon su fito suna son ganinsu ba wacce ta Leke sanin Halin Wanda ke wajen Imu Domin Tun suna Kawo abinci yake ta Hararansu yace suyu su gama su bar nan Wajen. Khamis ne yaje ya Duka ya Nemi Izinin Babban Yaya na yana son ganin Munari Imran ya Hura hanci kafin yace an bashi,izini ya tashi yana Dariya ya Kira Munari ta Fito suka Kebe Sagir ne yace wlh bazai nemi Izinin ba Imran yace ba kuwa zai ga Hafsah ba yace bai isa ba Imran yace To sai ya gani. Duk da Sagir ya Kirata Tana Fitowa kallo Daya gogan yayi mata ta Koma Ciki da Gudu Sagir ya Saki baki su Yusuf na Dariya Imran ko ya Hade Rai Zaginsa yayi bai damu ba sanin ai Sagir ba Girmansa yake gani ba Khalil ya Kira ya Fadamawa shi kuma yace ya Kyalesa na Lokaci in suka yi Ciki da kannin nashi ya isa ya kafa musu Wata Doka ne,Dole ya Kyalesu suyi yadda suka ga dama. Imran bai yi magana ba Sanin Halin Khalil in suka Hade da Sagir sai Allah,Shi da yake da Sauran mai Cutar Xuciya Kafin auran Jinya zai tayi ko nacema yana kanyi Tunda Sajida Har yanzu Tana agida Karkashin Kulawar Likita Gefe Daya Khalil na bata Kyakyawan Kulawan Datake kra Taimaka mata batare data sani ba ta Shaku dashi sosai Kamar sun Dade da Sanin juna. Washegari kowa zai koma Inda ya Fito Da Daddare Da Imran yace Intee ta Fito su tafi sai ta yo mai gayyar su Munari da Hafsah da Nasara zasu Bita su kwana agidansu da Imran yaga haka Ransa ya bace har Intee ta koma su kwana Tare Ita bata gane ba Tana ta Murna batasan Talala yayi mata ba Washegari da baki suka Watse suka koma Gida sai da ta Raina kanta Daya Damketa sai da ta koma magiya da Ban baki kana ya Ragamata Hukuncin ta kenan na Hanasa Shagali Daran Jiya. Inteesar sai dai Tura baki bata ta tacewa Daman haka yake mata yace Tunda bata son Fada to Hukuncin Daya Dace da ita kenan ba Duka ba Zagi zai ladabtar da ita Hankalinsa kwance. Ta kowani Bangare sun Fara Shirin wannan Gagrumin Bikin Duk da basu yi wani Wahala ba ko Daura ma kai Nauyi ba Dukkansu Sadaki Kadai Baffa Kabiru ya Zartar Domin shine kamar makwafin Alkali Dukku marigayi Allah ya basa Girman kuma ya karba,Mami Asma"u ba Zama Zata aurar da manyan ya"yanta Guda Biyu sun Hade kai da Umma Kamar yadda kawunan Mazajensu yake a Hade Mami duk ta Zubar kawayenta ta kama Umma Hannun Bibbiyu ta Fahimci zama da Mutanen kwarai yafi Zaman da Mutanen Banza. Wannan Karon an Raba Daddy shi ya Dauki Nauyin yima Amare Jeren Daki Baffa Kabiru kuma Baban angwaye shi ya Dauki Nauyin yima Duka Zaratan Mazan akwatuna aure Da Sagir da Khalil da Khamis Harda Abba Wannan karamincin yasa Dr.Ali Argugu ya taso Tun Daga Lagos Har Kano yayi ma su Abba Godiya Domin koda Khalil yaje musu da Labarin Chanji Daga Munari zuwa Sajida basu ce komai ba Sanin Daman ai Matar Mutun kabarinsa kuma wani baya auran Matar wani daman chan Allah ya Rubuta Sajidan da ita Za"ayi... Mama ma Tana ta Godiya Baffa Kabiru yace bayason Godiya Da Khamis da Khalil da Sagir Duka Dayane a Wajensa. Imran dai na gefe bai Zake ba ya Kama Girmansa na Babban Yaya Khamis ne kadai ke basa Girma yana Shawara dashi banda Sagir Daya gama Rainasa gwara ma Khalil yana Ragamai Tunda dai yana Kularmai da yar kanwarsa Sajida wacce kusan koda Yaushe yana Kiranta yaji Lafiyanta ya Dauki alkwarin Kula da ita na Musamman acikin kannensa ba Domin in ya aureta bazai yi adalci ba Daya Aurota ya Hadata da Inteesar to ya kwana da sanin baza"a zauna Lafiya ba,Rigimar Inteeear ba Ko yanzu ma Bata kaunar Taga yana Mganar Sajida ko Taga ya Kirata a waya yanzu Zata Chanzamai fuska sai ya koma yana Lallashinta Tana da Kishi sosai,shi kuma bai iya Hayaniya ba Ballatana ya jawo ma kansa aiki Masu Shirin Shagali su Intee ce ana gaba gaba sune manya. Sajida a Lagos Zata zauna Gidan Khalil,Hafsah kuma agidansu Zata Zauna Inda Sagir yasa aka Fara Bugesa za"a Sauyamai Samfarin Ginin Zamani Falt mai kyau da Tsari Tunda Mama Gidan Abba Zata koma Shima Abba yasa an Fara Gina wani kayattacen Shashi Daga gefe nan Shashen Gabadaya zai barma Yusuf ne. Khamis kuma porthercourt Zasu Zauna Domin ya samu Transfer Daga Anambara zuwa Porthercourt,chan zai Tafi da ita ammh sai sun yi Sati Biyu a Abuja,Ta kowani bangare Shirin Bikin ake Gudanarwa,ba kama Hannun yaro Dayake Allah ya Rufa asiri sai komai yayi Daidai ba wata Mtsala sun Tsara zasu yi Events dinsu a Dukku zasu yi Fulani Day,sai Lonching,sai Matan da zasuyi Walima. Inteesar duk ta Fara Damuwa Munari Zata tafi ta barta ita kadai a makaranta da garin gabadaya,Saboda Chan Khamis zai nema mata makaranta in tasamu Transfer ta Cigaba Saboda Shirye Shiryen Bikin Har sun Fara wasa da karatun nasu Dayake suna Second Semester ne na aji Biyu sai da Imran yayi musu Fata Fata kana suka maida Hankalinsu. Bangaran gyaran Amare kuma Inna Maimatu da Inna Bintalo suka Karbi Mangaran suka aika da Jarkunan mganin Sanyi da Gumbar mata Abuja da kano Da Dutse Munari da Hafsah da Sajida duk sukace su fara amfani Dashi Umma ma ta Dakema Mama kan sai ta gyara itama Tana ta Korafin wai Ta girma wannan aikin yara ne Umma tace sai fa ta gyara ita da Maman Nasara suka Hade mata kai suna Fadin ai ko Manyan ma suna son agyara musu suji Dadi Dukkansu Dole ta Fara karban gyara Daga garesu Domin kaunace ta kawo Haka. Sagir da Taimakon Filinsa daya Gada ya Saida ya Fara aikin Ginin an Sauya Fasalin Gidan Gabadaya an Fitar da kayattacen Falt mai Dauke da 2Bedroom da falo da Kitchen sai wani karamin Shashe mai Falo Daya da Bedroom Daya,Sai Haraban Gidan da Get domin Shiga da Mota Tunda ai Cigaban Rayuwa ake nema sai Daga Shagonsa ya Bigeshibaka kara Fili aka Bude Babban Shago mai girma ya Bude Kofa ta Waje data Cikin Gida Saboda yana so nan gaba ya kara Kekuna Da ma"ikata Tunda dinkin nan Dashi Yake Rufama kansa asiri yau ko ya gama Makaranta ba Lalle ne ya Samu aiki da Wuri ba Imran ya Bashi wannan Shawaran Domin shima yayi ma Sagir alkawarin Hada Hannu Dashi Wajen Bunkusa Kasuwancinsa sosai. Wasa wasa Biki nata Matsowa Dama kuma Hausawa sunce Duk Abunda aka Sakama Lokaci sai yazo gashi yau Bikin ya Rage Saura Wata Daya Tuni Ginin Abba Shima ya kamallah Gabadaya an sauya Fasalin Gidan An Hade Shashen gabadaya An kara Fadada Bangaran Yusuf da Anty Safiya Sannan anyi bangaran Baki Daga Ciki Daga Chan Gefec kuma Kayattacen Falt din Abba ne mai Dauke da 3bedroom Da Falo Guda Biyu Daga Bakin get kuma an Fitar ma Iro megadi Dakuna Biyu Ciki da Falo Shida Direban Abba Tunda duk nan suke kwana an Sauya Fenti Har da Duka Sabbi kayan Cikin Gidan Abba yace baya Bukatar komai sai Mama Gabadaya Kamfanin Marhaba suka zo suka kawata Bangaran sai wanda ya gani. Wannan Karon Mami Asma"u da Umma Baffa Kabiru ya bama Kwangilan Hadama Zaratan Mazan kayan Lefe,Mami Asma"u ta bada Shawaran su tafi Dubai su Hado komai haka kuwa akayi Dubai suka Tafi Harda Maman Nasara Saboda Tasan Wajen Tana zuwa Saro kaya Sati Daya sukayi suka jiyo da akwatuna Saiti Biyar cike da kayan alfarma,Dayake kafin su Tafi sun karbi Size din Ya"yan nasu A Abuja suka Sauka nan suka Fara baje kayan Baffa Kabiru yace nan Za"a Barsu Dasu Za"a Tafi Dukku Zai Dinka musu wasu kayan Fitan Bikin na Dabam Abun fa nayi ne Bakin Aljihu kadai ya Saki su Umma na amsa suna ta Shirinsu Daga Mazan har matan kala Biyar Biyar yayi musu na kayan Fitar Biki,Harda Abba da Mama suma Baffa Kabiru bai barsu abaya ba. Ana Saura Sati Biyu Biki Inna Maimautu tazo ta Hada kan Amaran Waje Daya ta tafi dasu Bauchi ta gyara su Inteesar harda kukanta taso taje Imran yace Ya Hakura da gyaran iya wanda ke Jikinta ma ya Ishesa jin Dadin in tatafi shi kuma ya Zauna da wa..? Dole ta Hakura Tunda Oga ya Hana ammh Kullum suna waya dasu suna Fadamata yadda suke shan gyara Ana ta Musu Dilka da kayan gyara na Da"a Daga Sokoto Inna Maimunatu ta bada Sako aka Kawo mata tana ta gyaran Ya"yanta. Mazan suma suna nan suna ta Shirinsu na kece Raini Imran dai Na Gefe bai Zakewa yace shi Babban Yaya ne sai dai Shawara ko bada Umarni sun Dinka angon Fitar Bika Kala Hudu Hudu wannan kuma Gudummuwar Yusuf ce yayi musu Gabadayansu har dasu Ya Basheer dasu Abba Ranar Daurin auran gabadaya ankon Farar shadda Zasu saka,,Manyansu da yaransu Matan ma sun Fitar da wani less shima mai kyau na Yinin Biki Hatta Daada ba"a bari a baya ba ya"yanta sun Dinka mata ita da Baba asabe.. Ana Saura Sati Daya Bikin Hajiya Barira da Sairan ya"yanta suka Sauka akano Fagge ta sauka agidansu Chan itama Zasu yi Taronta Dr.Ali argungu sai Saura kwana Uku zasu iso da Khalil sai bayan Biki zasu Tattara su koma Lagos har da Amarya Sajida. Da yanzu taji Sauki sosai kamar bata Taba Wata Cuta ta bar makaranta Saboda Daman ta rasa Shekararta ta Biyu Dole baya Zata dawo in taje Chan Lagos tace ma Khalil in Ta koma Cjan Zata Dora Daga Farko ne Tunda Lokacin ya gabato suna ta Shirin Tafiya Dukku ne bayan an gama Jerin Dakunan Amaram Daman kamfani ne suka zo suka jera komai sai abun da ba"a rasa ba Matan suka shiga Kasuwa suka kara musu Sajida ita sai sun isa Lagos din za"a siyamata komai Munari kuma bata Bukatar komai Saboda Gidan da aka bama Khamis achan Porthercourt akwai komai na More Rayuwa sai abunda ba"a Rasa ba Hafsah ce aka kawatama ta Shashenta Balle ya Hadu da Sabon Tsararran Ginin da Sagir ya Narka Dukiya aka narka mata Mama Tana Sabon Shashen mai Dauke da Bedroom guda Daya Kafin itama ta Tashi Zuwa Gidanta Inda Abba ya gama kawata mata. Tun ana Saura Kwana Uku Taron Bikin Matan suka Fara Sauka Adukku Inna Bintalo da Tawagan ya"yanta Inna Maimunatu itace ta iso da Tawaagan Amaran da suka Sauya Saboda gyara ko"ina suka Gitta sai Tashin Kamshin Fatarsu na Santsi da yarari,Ranar al"amis Sauran suka Iso Umma da Mama da Tawangansu Maman nasara da Anty Uwani sai Mami Asma"u da Umaima da suka Taho Daga Abuja. Inteesar Tawagan su Anty Safiya ta Biyo Ita dasu Anty Aneesa da Anty Faresatu da Tasleem sai Inna Kaltume matar Baba Manu, Nasara tana chan Daga Kaduna tabi su Umma,Mommy Tana Fagge su ke da Taron Bikin Bangaran Uwar ango Khalil Hajiya Barira. Tawagan angayen kuma Sai Ranar Jumma"a suka iso gabadayansu Yaransu da Iyayen Ciki Harda Kawu Manu da Alhaji Alhassan da Dr.Ali Argungun da suka iso kano Tun Ranar Laraba a Kaduna suka Hadu gabadayansu suka Dunguma suka kamo Hanya gabadaya sai dai aka Rufe Gidajen. Aranar da Yammah sukayi Fulani Day a Aharaban Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku,Shigar Fulani gabadayansu sukayi matan su da Mazansu sun siya kayan banda su Abba Da suke gefe suna Kallon yayan nasu Cikin Alfahari Harda Daada sai da Ta Fito Bakinta yaki Rufuwa bata taba ganin Ahalinta sun Hadu waje Daya ba Tashin Hankali ba sai yau Ga Mami Asma"u da Yan"uwanta duk sun zo sai Shiga da Fita suke yi suna Raba Damammiyar Nono da Fura mai kyau da Aka siyo da yawa saboda irin wannan Ranar kowa kagani yana Cikin Farinciki,Amaren suna Waje Daya suma sun Cakare Cikin kayan Fulanin Kamar yadda Inteesar ma ta saka nata sai dai ta kara kiba Ciki ya Budata Kana ganinta Zaka Fahimci Tana da Shigar Juna Biyu Imran na Tare da ita yace ta kama Girmanta Duka wajen itace yayarsu har su Sagir da Khamis sudai Dariyansa kawai suke shi ala Dole sai an basa Girma ko ana so ko ba"a so Inteesar kuma Tana so ta samu Sake cikin Yan"uwanta susha Firansu Dukkansu achan akayi musu Kunshi da gyaran kai Sajida data maida Jikinta sai Walwali Take Bini bini kadan Tazo ta kawo karar Khalil wajen Babban yaya in yayi mata wani abu Shi kuma yaja kunnensa in kaga wannan ahalin Aranar sai sun baka Sha"awa kayi Musu Fatan zama cikin Farincikin nan Har karshen Rayuwarsu Sai wajen goma Dare suka Tashi Taron suka koma Cikin Gida Mazan Matasa da Su Abba duk suna BoyQuaters da aka Riga aga gyarashi Tsab. Gari na Wayewa suka Tasshi da Hidiman Biki da Daurin auran suka Tashi Gabdaya Girke Girken duka su suka Zage sukayi kayansu Kala kala sai wanda ka Zaba ballatana ga Dangin Uban Hafsah suma da Safen suka iso Harda Mijin nata da yan"uwansa hakama Mijin Inna Bintalo Gida dai ya Cika Sosai Gwanin ban Sha"awa. Da wuri gabadaya akayi wanka Kowa ya Cakare gabadaya matan Shigar iri Daya sukayi na Less din nan Amaran suma Shigar iri Daya sukayi suma na Less ammh kalar nasu dabam Harda Inteesar itama kamar amarya Domin tasha Kwalliya an Kashe mata Dauri kamar Amarya sai dai ana ganinta anga mai Matashin ciki. Mai kwalliya suka Kira tazo Tayi musu Daada ma ta Ci Wakanta Itama su Inna Maimunatu sun kashemata Dauri sai Hoto suke Daukanta Bakinta yaki Rufuwa. Mazan suma suna chan duk sun Shirya Cikin Fararan Shadda Kowa kuma da Babban Riga da bakar Hula da bakin Takalmi da bakin Agogo,Harda iyayen suma Shigar sukayi Harda yara irin su Waleed da Abidin Daurin auran karfe 12pm na Rana ne da an Daura za"ayi Walimar maza a Wani Restauranta inda zasu ci Abinci Matan kuma nasu sai gobe ne Lonching zasu Gudanar. Daddy shi ya bada auran Duka ya"yan nasu Hafsah da Sajida da Munari Saboda Dangin Mahaifin Hafsah sun yi musu kara sosai,Dr Isa Argungun Yayi ma Alhaji Alhassan kara shi ya Nemar ma Khalil auran Sajida yayinda Baba Manu ya karban ma Sagir auran Cikin Kankanin Lokaci Aure ya kamallah yayinda Baffa Kabiru Shi ya Biyama Duka Zaratan Mazan Sadakin Dubu 200 ne. Nan da nan Masallacin ya Kaure da Hayaniyar fatan Alheri ana ta gaisawa da Mutane da angwayen da ba"a gane su Tunda Duka Shiga iri Daya sukayi Daganan Reception sukaje sukayi koda suka dawo har an Fara Lonching din Daman mata da Maza ne nan da nan kowa yaja Amaryansa Gefe,Imran mamaki Yaran ma suke bashi sai Wani Rawan kafa suke Saboda sun yi aure ba su Munarin ba Su Sagir din ba Shima Inteeear yaja Gefe suka kame afili ya Furta suma ai angwayen ne Dole suma su Cakare. Anci an sha an yi Rawa sosai Sagir da Khalil da Khamis sun kwaso Shoki Abunsu da matansu Imran na Gefe yana kallon Abun mamaki ko kunya Cikin yara Inteesar sai Fushi Take yi Tana so Ta shige aammh Imran yayi mata Jam ido Yace bai son Iskanci da Cikin nashi ne Zataje Tana Girgiza kuma sannan baya son Shirme ta barma yara Dole ta Hakura Tana Gefe Tana kallo sai dai sunje a manya yayyi kamar yadda Imran yake so sun yi manni kudi an sha Hotuna kamar ba Gobe Kowani Hoto Sai an gawayen sun Rike Imran anyi dashi dasu Amaran sai Dai Fuskarnan ba Fara"a ko kadan su Ya yusuf suna Gefe a Mtsayinsu na manya yayyi. Washegari Aka yi Walimar aure anan Haraban Gidan da Yammah,Ranar Litini kuma akayi Shirin mika Amarre Hafsah Kano Za"a kawota ita da Sajida Munari kuma Abuja zasu wuce ita da Khamis dasu Mami. Inna Bintalo Zata Bisu Abuja Inna Maimunatu zata je kano su Da su Umma Domin mikama Mama itama Gidan Auranta. Daganan Dukku Iyayen mazan sukayi Sallama da juna bayan Daada ta tarasu tayi ma Duka Ma"auratan Nasiha da zasu tafi harda Kukanta Domin Tana ganin kamar Kara Haduwarsu na Mutuwarta ne. Masu Tafiya Kano Duk Tare suka Dauki Hanya Wajen Motoci Goma Sajida Tayi kuka wajen Rabuwa da Mami da Baffa Kabiru da sauran yan"uwanta Munari ma Tasha kuka ita da Inteesar haka ta kamkame Abba Da ya Yusuf Harta da Imran sai da idonsa ya Sauya ya Rumgumeta yana Shafa kanta Daga Dukku Jirgi suka Hau zuwa Abuja Ita da Inna Bintalo dasu Mami. Suna isowa kano Mama aka Fara Rakawa Gidanta Shashenta Sai son barka Rakiyan Umma da maman nasara da Anty Uwani da Inna Kaltume Sajida kuma Mommy da Anty Saratu suka Tarbesu,Aranar suka Tafi Fagge ita da Khalil da Umma,sai Gobe zasu bi Jirgi zuwa Lagos Inteesar bata raka Ko Dayansu ba sai Hafsah,Ita da aka kaita Kusa Inna Maimunatu ta mikata Dakinta Tana ta kuka ba wanda suka kwana Kowa ya watse sauran baki suka koma gidan Abba wasu kuma Gidan ya Sadam suka koma suka kwana. Washegari Talata Kafin su Khalil su wuce sai da suka Biyo Tanan sukayi Sallama da yan"uwa Kafin su Dunguma Gabadaya aka Rakasu Filin Jirgi Zuwa Lagos Umma da inna Maimunatu ne zasu Raka Sajida sai yayar Mami Asma"u Guda Daya. Inteesar Tasha kuka Data Waiga ba Munari tana chan Abuja Allah Sarki Rayuwa Imran ne da suka koma Gida Yayi ta Lallashinta Tun aranar gabadaya Kowa ya watse aka bar Amaran da angwayen su samu Natsuwa,barin ma Abba da Mama,Sagir da Hafsh suma su kadai agida sun Fara Cin Amarcinsu Umma da Inna Maimunatu kwana Daya sukayi a lagos suka Jiyo Zuwa Kano Domin ai Dr.Ali argungun ya gama komai gabadaya Gidan shi ya kawatashi yace Sajida ya'tace garesa Saboda Malami kuma Shi da Iyaalan Daada ai sun Zama Daya haka suka dawo da Labarin mai Dadi sai Fatan Allah ya basu Zaman lafiya Daga Kano Inna Maimunatu ta wuce Bauchi ya"yanta suma kowacce ta koma Gidanta Umma kuma bata Kwana ba ta koma kaduna Tunda Daddy da ya Basheer sun koma Shi da Anty Hauwa da Little Inteesar Anty Safiyama Da Imran karami Daya Fara Wayau duk sai sukaji Gidan Shiru ba Gilmawar Abba yana Barayinsa ba Munari sai su kadai Allah yasa ma ga Kirniyar imran karami. Munari kuma Dagachan Abuja Inna Bintalo kwana Biyu tayi ta so tayi ta Koma Baffa Kabiru yace taa Tsaya ta Raka Munari Dakinta haka kuwa akayi kwanansu Uku a Abuja suka wuce Porthercourt da Rakiyan Inna Bintalo kwananta Biyu suka Hadota da sha Tara na arziki suka Sakota ajirgi sai Gombe Ta koma Gidanta Domin ta Sauke gajiyan bayan ta Kira Duka yan"uwanta tasanar dasu ta Dawo Lafiya ta Raka yarta Munari Dakinta. Sai da suka Shafe wajen Sati Biyu suna Sauke Gajiya Domin fa an sha Zirga Zirga Munari suna waya da Inteesar da sauran yan"uwanta Inteesat tasha Korafin irin Wahalan da Abokan Mijinta suka gana ma kawayenta Harda Sajida ma suna mgana Ita tabama Imran Labari yayi ta Dariya To Daman Tunda suka auri wadanan Tazuran ai sun gama yawo sai Fatan Allah ya basu Zaaman lafiya ita kanta Inteesar din ai ta gayama aya Zaginta Domin kwanakin nan kaf sai da Imran ya Famshe ita Duk Sauke gajiyan da Kowa yayi bata samu wannan Damar ba. Allah Sarki Inteesar ita kadai ta Cigaba da zuwa makaranta kafin Transfer din Hafsah ya samu ta dawo nan da Karatu Gidansu Imran ya kara Zama Gida Saboda Mama ta kama su Imran ta Rike gam kamar ya"yanta Abba kuma yahada kan Iyalansa Waje Daya Sagir Daya kasance Dan Gida ne bai da wata Mtsala Anty Safiya na jin Dadin Zama da Mama sosai Gabadaya Renon Imran karami ya koma Hannunta ashashenta yake wuni Ta Tabbatar ita da Abba zasu kwaceshi ne Ita kanta Anty Safiyan in ba Abba ko Ya yusuf ne ya dawo ba tana Wajen Maman. Sagir ma shi da Hafsah suna Gidan kusan kullum sai da Abba yayi musu irin na Imran yace su zauna Gidansu kada su kara zuwa kana akaji Shiru Gabadaya Imran Dayaji Labari yana ta Dariya Harda gwalo. Munari ta Bude musu Group isu isu Ita Hafsah,Inteesar, sajida Nasara da Tasleem Nasara itama an saka Ranarta anan Kaduna Zatayi aure wani ma"aikacin NNPC zata Aura Saura Tasleem da itama Zata Fara Karatu anan jami"ar Bayaron Inteesar nata Murnan ta samu yan uwa sunan Group din SISTER"S FOREVER��,Chan suke Haduwa suna Baza Iskancin su son Ransu suna Tadin mazajensu da yarda zasu kara Zama Taurari a Wajensu da bama Juna Shawara Kowa Tana Fadin in Mijinta na kwararamata Ihun Dadi Inteesar taki cewa komai suna ta Tambayanta To ai in Ta Fada ta gama Tona asirin Ya Imu Daya Dade a Lullunbe bazata so kannensa su ji wannan mganar ba ganin Taki Fada suka Zageta suka Kyaleta ita sai dai Dariya kawai. Ba Dadewa Hafsah ta samu Transfer ta Fara zuwa makaranta ba Depatment daya suke da Inteesar ba haka ma Tasleem data Fara zuwa sai dai kusan Kullum suna Haduwa Tasleem Direba ke zuwa Daukanta ita kuma Inteesar watarana Imran in yazo suna Tare da Hafsah ya Daukesu Dukkamsu in kuma sun tashi da Wuri kowacce Tayi gidanta Domin sun Fara Biya biyen Gidajen kansu ko na Abba Imran ya Tsawatar yace kowa ta Zauni Gidanta. Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai a Dade ba"a je ba Gashi har Cikin Inteesar ya isa Haihuwa, Tana zuwa awo a wani asibitin kudi Ciki yayi Kato yayi Girman da bata iyama kanta Komai Allah yasa sun samu Hutun shiga aji Uku Daada Dataji Labarin Halin da Inteesar ke Ciki ta Kira Umma Tace tazo ta Dauke yarta ta Haihu agabanta Imran yaso ya Hana sai dai Abba yayi mai mgana Dole ya Kyaleta Daman ta Zama abun Tsausayi Ciki ya hana komai.. Umma tazo ta tafi da Inteesar ta Dawo gabanta ko kwana Goma batayi da dawowa ba ta Haihu a asibitin Barau Dukku Dake kaduna Yan Biyu ta Haifa mace da Namiji masu kama da Imran Murna Wajen Wannan Ahalin sai wanda ya gani Imran kamar ya Zuba ruwa akasa yasha a Kaduna akayi Shagalin suna Yara sukaci sunan Abba da Anni Wato Abubakar da Zuwaira kuma da Abba da Anni Za"a Rika Kiransu,Hafsace kadai tazo suna Sajida da Munari ba wacce tazo duk da sun so zuwa Munari Laulayi ne ya Hanata Sajida kuma Suna Jarabawa Domin ta Fara Karatunta Hafsah kuma Daman Tana da Karamin Cikinta.. Imran yayi bajinta sosai a Haihuwar Inteesar ya siyamata kyauta Mota karama 206na Murnan Haihuwan yan Biyu nan tayi jegonta Cikin Kulawar Umma da Daddy Kamar ya maidata Intee Ciki su Anni kuwa suna ganin gata Bayan Tayi arba"in bata koma Kano ba sai da ta Zaga Dangi sune har Abuja,Gidan Baffa Kabiru sai da suka Kwana Biyu suka Dawo Taje Bauchi Wajen Inna Maimunatu taje Gombe Daganan ta Karisa Dukku Burin Daada ya Cika ta Dauki Ya"yan imran da Inteesar jikokin Malami da Abubakar Sauran Jikokin Malami da Kabiru. Har Dutse sai da Inteesar taje gidan ya Sa"id bayan dawowarta Daga Kadunna ammh shi ita da Imran sukaje suka kwana Daya suka Dawo Ta Dawo da Kwana ashirin ta koma Bikin Nasara sai a wannan karom Sajida da Munari suka zo murna ba"a mgana da suka Hadu sai Tashin Hira Gabadayansu suna da ciki banda Sajida Da suke mata Tsiyan ko Tana planing ne tace musu AllaH ne bai kawo ba Dukkansu da mazajensu suka zo bayan Biki kuma kowa ya tasa abarsa suka koma Amarya nasara ta tare agidan Mijinta Dake Malali kaduna. Inteesar mai Taya Reno aka Daukan mata Wata yar yarinya saboda makaranta Mama ta samo mata nan kasansu take kwana wajen Inteesar din sai Weekend take zuwa Gida sunanta Hanne,Inteesar Tana Wahala sosai ga makaranta ga Renon yaran har Biyu ga Ubansu bai iya Komai ba sai fadan in anyi ba Daidai ba. Sagir ya gama Karatunsa ya Cigaba da Dinkinsa Tunda aikin bai Samu ba suna dai Cigaba da nema. Ashekaran suka je Lagos ita da Imran da yaran su an Turasu Seminar Gidan Abba suka sauka ba Hotel ba,Tunda Matan Lurwani maigadi suna kula da gidan ko"ina Tsab,Sati Daya sukayi kafin su gama Seminar,Su Inteesar taje Gidan Sajida suma sun zo musu Har Gidan Dr Ali argungun sunje,Bayan sun dawo Sukaje Parthecourt,Harda Sagir da Hafsah suka gano Munari suka Dawo. ****** *MURFI...*!!! _AFTER 7 YERARS BACK..._ Bayan Shudewar wasu Shekaru Bakwai da suka gabata Ahalin Marigayi Alkali Dukku ayau ya Zama abun kwantance Baffa Kabiru girma ya kara kamasa Tun bayan Rasuwar Daada Shekaru Biyar da suka gabata ammu bata bar Gidan Duniya ba sai da Ta Dauki Jikokin Malami da Kabiru ta kuma Hada kan Zuru"arta Waje daya kafin ta bar Duniya. Rashinta ya Girgiza ya"yanta sun yi kuka sosai sai dai kuma sun Dauki Girma da Ragamar komai akansu. Ashekarun da suka gabata an samu Cigaba sosai ta bangaran Haiyayyafa da Karin Girma ayyukan wasu. Imran ya samu karin Girma daga Assistan Manaja zuwa Manajan Gt brach Dake Lagos inda ya Taba aiki basu da Mtsalan gida ga Gidansu nan suka gyara ya Kwashi Matarsa da ya"yansu suka koma chan da Zama Sajida tafi kowa murna sun dawo kusa da juna duk da shima Khalil din ya samu karin girma, Shekaru Biyu da suka gabata Tunda Inteesar Ta gama makarantar ta,Su da kano sai in sunzo ganin gida ga gidansu suna da Wajen sauka in sunzo garin. Bayan Haihuwar su Anni haihuwanta Biyar acikin Shekara bakwai Saboda Gwarne Takeyi Data yaye shikenan sai wani Cikin taso ta fara tsarin Ilyali Imu yace sai ya gani Allah ya Taimaketa Hanne na Tare da ita tana kara Taimaakamata. Daga su Abba karami tazo Tayi mai sunan ya Yusuf suna Kiransa Boy,Sai mai sunan Daddy Mustapha,sai mai sunan Baffa Kabiru,Sai Sagir da Imran yayi mai Takwara yana Kiransa Friend sai Karamarsu mai sunan Daada kuma mai sunan Inteesar suna Kiranta Afiya. Ya yusuf ya samu karin Girma shima iyalai sun cika Gida,Abba tuni ya gida wani Gaton gida a sharadi phase 1 sun koma da Mama tare da Imran karami da Khadija diyarsu da suka kwace musu, an kara gyara wannan Gidan Sagir ya dawo suna zaune Tare,gidansu kuma sun bama Baba Manu ya dawo nan da Zama Sagir ya samu aiki sai dai har yau har gobe bai bar Dinkin ba domin kome ya Zama Dinkin ne Sila shida Imran suka Hada Hannu suka kara Fadada harka yanzu Manyan Shaguna sun fi goma Cike da kekekuna da ma"ikata yara sai dai Sagir ya Daina Dinkin sai dai yaransa shi kuma Oga sama oga kasa. Shima sun tara ya"ya shima yayi ma Imran,takwara sai mai sunan Mama Amina da mai sunan Babansa Tasiu. Munari ma ya"yanta Hudu itama Tayi ma Anni da Abba duka Takwara da Mami Asma"u da Baffa Kabiru Sajida kuma ya"yanta uku ita kuma sai Tayi ma su Inna Maimunatu kara da Inna Bintalo Daada kuwa mai sunanta Kusan kowa nada Daada agidansa. Nasara ma da ya"yanta Biyu su ya Basheer dasu Sadam duk sun zama magidanta Girma ya kamasu Tasleem ma Tayi aure sai dai kafin haka sai da Kaddara ta Fadamata wani Lecture ya Ribace ya Lalata mata Rayuwa. Sai daga baya ya aureta bayan ta Tsarkaka Alhaji Alhassan yayi ta kuka Saboda yasan Ishara ne Allah ya Nuna mai Koda ya Tuba. Gabadayansu Mazan sun Hade kansu Matan ma haka Imran ya Daina shan Taba Kwata Kwata saboda Shekara Uku da suka wuce ya Kusa Mutuwa Hayakin Dayayi ta bankama Cikinsa ya Taba Huhunsa sai da Abba ya Fita Dashi Kasar Amurka Ya kusan Wata Shida akayi mai aiki kana ya warke ya Dawo Gida Inteesar har ta Fara kukan rasa Namijun Duniya sai gashi ya Warke sai dai Tundaga Lokacin ko Warin Taba bayaso shi da ita har Abada. Su Inna Maimunatu kam sun Zama Goggon gaske Yanzu Baba Asabe suka kama Suka Rike itace makwafin Daada Gidansu na Dukku na nan da Ransa bai Mutu ba Baba asabe na Cikinsa Tare da yan aiki masu Taimaka mata Suna zuwa yin Hutu ko Sallah Duk shekara gabdaya kwansu da kwarkwatansu Baba asabe me Zata ga Iyaalan Daada..?illah dai Fatan su gama da Duniya Lafiya da Fatan Allah ya Jikan Daada da Alkali Hamisu Ameen. Umaima tayi aure anan Kaduna Wani Dan kasuwa take aure mai kudi sosai har da Danta Daya. ***** Lagos.. Yau din Ranar Lahadin Karshen mako ne Inteesar na kwance Tana Barci acikin Bedroom dinsu Ta Ninkaye Cikin Bargo Tana barcinta Cikin kwanciyar Hankali Da Salama Daga gani kuma barcin Sauke gajiya ne Domin jiya da Daddaran Ranka shi Dade Imran bai barta ta Huta ba. Da asuba ma sai da ya kara kafi Siga kafin ya barta ta Kwanta Shiyasa ta baro Dakinta Tunda chan suka kwana Zuwa Dakin Imran saboda bata son yaran su tashi su Dameta. Suna Tare da Hanne domin Tare da ita suka Taho Duk da ba reno take yi ba yanzu Allah ne ya Hada Jininta Dana Inteesar Da zasu dawo lagos ita da Imran suka Nemi yardan iyayanta suka basu ita suka dawo da ita nan tare da duka yaran suka Hada suka sanya makaranta In baka sani ba sai kace Kanwar Inteesar ce Duk inda Tabi yaran Anty Hanne sama Anty Hanne kasa. Matan Lurwanu ne megadinsu Dasuke Tare dasu anan Boyquater ke Taimakamata da aiki in yaran sun Tafi makaranta Inteesar bata aiki Tunda Imran bayaso sai dai Tana alfahari da Kwalin karatunta. Tayi nisa acikin barcinta Taji Kiran Wayarta Dakyar ta iya Zuro Hannu Tana daga kwancen bata iya tashi ba ta Dauko Wayar Daga Side drower din gadon bata Tsaya Duba mai Kiran ba ta Daga wayar Cikin Muryan Barci Take mgana. Dagachan BAngaran Sajida Mata agidan Khalil tace"Au barci ma kike yi..?kin manta mun ce zamu shiga Kasuwa..?kinfa san Salla ta Kusa ZAmu Tafi Dukku in bamu yi wannan Siyaytar ba sai yaushe..? Inteesar ta yamutsa Fuska Tana Fadin"Wlh nagaji ne Sajida..Gani nan kwance ammh yanzu zan tashi..Ina Zaki kai yara..? Sajida tace"Gidan Baba Dr mana..Kema ki kawo su nan Tunda Ubaninsu ba Yadda zasu yarda mu bar musu su ba..! Imteesar tace"Uhm..aini sai ma na kara Tambayan da nayi mganar bai ce komai ba..! Sajida na Dariya tace"To ai sai kije kiji da Yayana kuma Saura acre Dole sai an Fita abarsa ya Huta sosai a kula Dashi..! Inteesar tace"Uhm..Ai wannan yayanki naki sai shi..Gabadaya ya Fara Gajiyar dani..Wnnan ma gajiyar Duk tasa ce..! Sajida na Dariya tace"Banga Laifinsa ba..! Inteesae tace"Muguwa Allah yasa Daran yau Khalil yayi miki mugun kamu da sai kin samu Ciiki..! Sajida Tayi Saurin Cewa"Ba Ameen ba Gwarne ai sai Inteen Ya Imun mu..! Inteesar ta bata rai kafin Tace"wlh ina nan a Inteen Daddyna..! Dariya suka saka gabadaya kafin su yanke Kiran Muskutawa Tayi ta gyara Kwanciyarta Inteeear din kamar ba ita ta Haifi Zaratan ya"yan nan ba. Bata kai ga komawa barcin nata ba Ta sake jin kiran Wayarta Idanuwanta suna Rufewa saboda barci ta Daga Kiran Tana amsawa cikin Shakewar Murya. Hajiya Munari mata agidan Khamis Kabir Dukku tace"Ke lafiyanki kike min mgana kamar me maye..? Inteesar tace"Ai gwara me mayen a kaina..Yayanki zai kasheni Mu..! Munari ta Kwashe da Dariya Tana Fadin"Su Ya Imu manya..Ina zai Daga kafa ai wajen akwai danko..! Zagi Inteesar ta Dora mata kafin Tace"Allah nifa ina jin ku ne gwara Kowa da Mijina..! Munari tace"Uhm naki dai kika sani..Kowa ma nashi ya sani..Nifa da samun cikin nawa kamar Ya Khamis zai Haukacemin Wlh Watarana Har Tsausayi yake bani..! Inteesar tace"Kidai ji tsoron Allah..Kuma naji Sajida tana Fadamin kin ma Yaya Zainab din goggo Maimunatu mgana zata zo mana da kayan Da"a A dukku..?anya Munari zan karba kada na dawo ina Kuka Ina Rokon ya Imu zai kasheni..! Munari ta Kwashe da Dariya Tana Fadin"Banza kizauna shine auran aie..Wlh wannan nanikewar matarba ce Intee..Gwara mu sha ance in kana da kyau ka kara da wanka..Gwara mu gyara dA haka zamu katange mazan mu Daga matan Bariki..! Su Hafsah ma duk sun ce suna so fa Ya Sagir ai shima ba Dama..! Inteesar ta sauke Numfashi Tana Fadin"Ke dai yi a hankali kina da ciki..Ba kyau kina wannan banke banken..! Munari tace"Ke ni kyaleni Gwara na banka..Domin na kara Rikitashi Ina nan cikin arna da yare ina Kwato mijina suna Lasan Lebe daga waje..! Inteesar tayi Dariya Kafin tace"Ina yarana..? Munari tace"Sun fita da babansu yawon gari tun dazu..! Inteesar tace"Nima yanzu zan tashi kasuwa zamushiga da Sajida..! Munari tace"Ta Fadamin dazu da mukayi waya..Yanzu har kasuwa Ya Imu ke barinki..! Inteesar tace"Kada ma ya barin ya gani..! Munari tace"Allah..?wato ki matse Cinya ko..?Allah Sarki Zan sauya Miki kammani an yi Laushi Ya Imu Duniya..! Ta Fada Tana Fashewa da Dariya Zagi Inteesar ta Dankara mata kafin ta yanke Kiran Tana Dariya Munari sai Allah ya shirya Khamis ai na ganin Duniya. Ta koma kenan Taji kuka da Haniya a saman kanta kafin ta ankara sun Hawo Gadon da Gudu Afiya ce mai kukan Tana Fadin"Ummi..Ummi.. Kinga ya Abba ko..? Take Fada Tana kuka Mai sunan Baffa Kabiru da suke kira Baba ya rika Jaye bargon yana Fadin"Ummi ki tashi ga Ya Abba chan na Dukan Ya Boy a Falo..! Ai jin Haka yasa ta Mike bata Shirya ba Tana kallon ya"yanta kansu Daya Afiya Dake kuka ta saka ajikinta,Sai Baba Data Dafa kansa Ta juya tana kallon musty mai sunan Daddy Dake gefenta yayi kwal kwal da ido Shi akwai Tsoro kamar Farar Kura Cikin bacin rai Tace"Me yayi mishi Dayake dukansa..? Kawai sai ya saka mata kuka yana Fadin"nima bansani ba Ummi..! Sai suma Sauran su saka mata kuka Daga ganinsu a Tsorace suke suna Bala"in Tsoron ya Abba baya Musu Dakyau in ya Fara Dukan Mutum bayaji baya gani yari dan Shekara Takwaas sai Bakar Zuciya irin ta gado. Ranta ne ya baci ta kallesu Tana Fadin"Kumin shuru..Ina Anty Hanne..? Baba yace"Tana Tiolet Ummi..! Karamim Tsaki taja Tana Sauki Daga kan gadon Dauke da Afiya Take fadin"Ina Abi..,? Wannan karon Musty ne yace"Yana Study Room yace kada wanda ya Damesa..! Inteesar ta zura Bedroom Shoe dinta ta Fice tana Fada yaran sukabi bayanta Tafe take Tana Fadin"Wato kada a damesa ni kuma azo a Dameni kenan..? Take Fada har suka iso Tafkeken Falon suna zuwa Daidai Lokacin da karamin yaro ya saka kafa zai Taka wani yaro Dake kasa kwance bazai wuce shekara Shida ba yana kuka Anni yar Shekara Takwas Tana gefe Zaune ta Ragume Idanuwanta sun Fito Saboda Tsoro Itama Tsoronsa Take ji Duk da abokin Tagwayenta ne Tsawa Inteesar ta Daka mai Hade da Kiran sunansa. "Abubakar...! Da karfi Har sai da Imran Dayake Study Room yana aiki ya Jita Hanne Dake Tiolet itama Ta Jita da Hanzari ta Fito samin Halinta ta kuma san yanzu Zai ci Duka bari taje ta Kwaceshi bakar Zuciya garesa ko Kashess za"ayi bazai mtsa Daga Inda yake ba. Jin kiran sunansa yasa ya Tsaya Cak yana Sauke Numfashi kamar wani Zaki Boy ganin Ummi yasa ya Tashi ya Nufeta yana kuka Jikinta ya Fada ta Rikesa Sauke Afiya Tayi Daga Jikinta ta Tarbi Danta Anni ma wajenta Tazo Tana Kifta ido tana Fadin"Ummi Aljanun Ya Abba sun tashi..! Kamar ta maketa haka take ji yarinya sai Tsoro da Shagwaba kamar Abba Dukanta yake ya gama Raina ta wanda suka Fito Duniya Rana Daya. Rankwashi ta bata saman kamta Tana Fadin"Matsa ki bani Wuri babban banza wawiya kawai..! Gefe ta koma Tana Hawaye Dafe da kanta Dake Cike da suma. Mikewa Tayi a Fusace ta Nufesa Ta saka Hannu ta Juyosa yana Cika yana Batsrewa Mari mai kyau ta sakarmai kafin tace"Don Ubanka me yayi maka Daka ke Dukansa kamar Zaka Kashehi..? Tafada cikin Fushi da bacin rai,Yana Tsaye kikam yaki mgana sai Faman Huci yake abunda ke kara mata Bacin Rai kenan ta kara kaimasa Duka Tana Fadin"Ni zaka nuna min Zuciya..?Sai na maka Dukan Tsiya acikin Gidan nan naga mai kwatanka..! Tafada Cikin Fusata Sagir ne yayi mgana yace"Ummi fa takan muna wasan Buya shine Ya Boy ya Boye adakin Ya Abba shine shine fa ya Fara Dukansa wai yayimai ihu akai..! Baki ta Rike kafin tace"Eh Lalle sannu..waye kai da baza ayi maka Ihu ba..?Abubakar imran Abubakar ko..!?To ko Ubanka yanzu ya Hakura da Hayaniyar yana sonta wlh in baka Daina Tada Bakar zuciyar nan ta gado kan ya"yana ba sai naci Ubanka acikin Gidan nan..! Ta fada Tana Murdemai kunni Daidai Lokacin Imran ya Shigo Falon bayan ya gama jin Abunda ya Faru gabanta ya Tsaya ya Riko Abba Dake Fama da Zuciya yace"Basai kin sha Wahala ba au ga Uban nasa sai kici da Hujja..! Yafada yana Jefa mata Harara Dagowa Tayi Tana kallonsa batace komai ba ta kauda kanta Yaran suna ganinsa suka Rufesa gabadaya Fada ya fara yi musu yace su bama Abba Hakuri Kunne suka kama suna Fadin"We are Sorry Ya Abba...! Ko kallonsu bai yi ba Imran ya Dafa kansa yana Fadin"Sun ce kayi Hakuri ok..?kai gyada Fuskarnan ba Fara"a Kumatunsa ya Shafa yana Fadin"Kadaina Sauke wannan Fushin naka kan kannen ka kaji ko..?ko ni da ake ma Gorin kayo Gadona bana Duka haka Kurum sai an Shiga Sabgata yara ne ka rika Musu Uzuri babban yaya kaji ko..? ko kuma ku daina Mai abunda baya so kunji ko..? Gabadaya suka gyada kai suka ce "Yes Abi..! Kansu dukkansu ya shafa yana saka musu albarka Hanne ce ta Fito suka Nufeta suna Kiran sunanta Abba ya juya yana wani Taku kamar Imran ya shige Dakinsa Imran ya Bisa da kallo yana Mirmishi. Hanne ta gaisheshi ya amsa mata cewa yayi ta shirya su Gidan Baba Dr. Zasu je yanzu jim haka yasa suka Fara Murna suka kwashi Gidu zuwa Dakinsu Hanne ta mara musu baya Dauke da Afiya Inteesar Tuni ta koma Dakinta Domin ta Shirya. Imran ya mara mata baya Inteesar ta Rainasa batajin mganarsa Yana wannan Takun nasa Hannayensa Cikin Jallabiyan Jikinsa bai sauya ba sai ma kara Zama wani Matashi mai ji da Komai na Rayuwaa daya zama. Yana shiga Dakin yaganta Daure da Towel iya Cinyarta Zata Shiga wanka Taji Shigowarsa ammh bata Dago ba Kokarin Nannade gashinta take Waje adaya bata san Jikashi. Agabanta ya Tsaya yana Fadin"Kin kyauta..Na kuma gode da rashin jin mganata..! Ido ta sakarmai kafin tace"Uhmm..Ina jinka me kuma nayi Sarkin Laifi..! Yana Hade rai yace"Ni kuma Sarkin Fada ba..Wlh sai nayi mgana in naga anyi ba Daidai ba..! baki tabe batayi mgana ba Cikin Bacin rai ya Cigaba da Fadin"sau nawa zan Miki Fadan ki Daina ZAgin yaran nan agabansu..?in ranki ya baci zaki Hukunci kina gunduma Ubansu Zagi suna jinki kinsan yaro da Daukan abu kuwa..!sai ya Zata mai kyau ne ya Dauka na Fadamiki ki Daina Bana so bana so ammh Kin Rainani kin maida mganata banza Bansan yaushe kika koyi irin wadandan manya manyan ashariyan ba.! Batadai ce komai ba ganin haka yasa yace"baki son fada...Kuma nikam naga an yi ba daidai sai nayi mgana Kinsan Halina..! Sai da ta gama jinsa sannan Tace"Naji Zan kiyaye ina so nayi wanka. kasuwar da na gayamaka zamu je da Sajida..! Tafada Tana kokarin juyawa ya Fizgota sai gata kan Kirjinsa riko Kugunta yayi yana Kallon Fuskarta Cikin Wani irin Murya yace"wanka..?aai baki ga ta wanka ba..Bakin ce Zaki ci Ubansu ba gani nazo ki cini..Basai kin Wahala ba na kawo miki kaina.. Ido ta waro kafin ta Tura baki Tana Fadin"Ni fa ba ce ba..! Yace"Me kikace..!? Yana zagaye bakinta da Yatsunsa Hannunsa Dayan hannun nasa na Wasa da Tudun Hip dinta gabadaya ya Fara Rikitata dayasa itama ta Fada Jikinsa ta kamkamesa shima Riketa yayi yana Fadin"Ki bari ki gama cin Ubansu din kafin ki Fita Kin ji Matata..! Inteesar na Dariya Tana sunne kanta Tace"Ni fa ba haka nake nufi ba..! Imran yace"Uhmm to yane..?ai ko baki Fada haka din ne..! Dariya ta saki kawai batayi mgana ba Janta yayi suka Fada kan gado Cikin Bargo suka Shige kafin ya Rabata da Towel din Jikinta yana Fadin"Mu ci Uban juna Kin ji Inteen Imu..!Babu mai ce ma meyasa..! Yafada yana dariya Kara Nanikarsa Tayi Tana Farincikin Lokaci Daya Tana Fadin"I Love u so Much..Imun Intee..! tafada tana Kokarin Rabasa da kayan jikinsa Shima yana Kokarin Tayata yace"Love u so much..So Much Much Inteen Imran Shi kadai Yar albarkata yar Aljannata uwar ya"yana Matata wacce ita kadai ce Burina wacce ta iya zama Dani A yadda nake Tun ina Dan jagaliyana mai shan Taab...! Bata bari yaKarisa ba Ta Hade bakinsu Waje daya sai da sukayi sumba mai Tsawo kafin ta Saki bakin Ta Lafe Bisa Kirjinsa Tana Fadin"Ka Daina Fada..Ni nafi kowacce Mace a sa"a Duk wacce ta samu kamar Gwarzon mijina kawai tayi irin nawa Tace ALHAMDULILLAH..! IMRAN na kallon Cikin idonta yace"Nima ko ina Fatan duk Namijin Daya samu Mace kamarki mai Shagwaba mara son Fada mai Kishin Mijinta Kawai yayi irin nawa yace ALHAMDULILLAH..! Atare suka saki Dariya suka Rumgume juna Bakinsu suka Hade Waje Daya lokaci Daya ya Mirginata ta Dawo kasansa. Daganan na juya ya sakayo musu Kofar na Sauke alkalamina na Sha Ruwa na Sauke Numfashi nima nace ALHAMDULILLAH...! *Tammat bihamdullahi Godiyata Ta tabbata ga Allah Subanahu wata"ala daya bani ikon Fara wannan Littafin Lafiya na kuma gamashi yau Lafiya Allah ne abun godiya Tsira da aminci su kara Tabbata kan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi wasallam,Tare da Iyalansa da Sahabansa gabadaya Ameen summah Ameen..* _Bazan Rufe wannan Littafin ba sai na Mika Dukkan Godiyata da jinjina kan Masoyana masu son cigabana Masoyana da suka Taru suka nuna min kauna Wajen siyan wannan Labarin Da kuma yadda suka yi jimarin Bin Rubutuna Tun daga kashi na Farko Har gashi yau mun kamallah kashi na Biyu Wato GMB2BANDGROUP Hakika naji Dadi kwarai Allah ya saka Muku da alheri Allah ya Biyaku Allah ya bar Zumunci Allah ya kara Hada Fuskokinmu da alheri,Sannan ina Neman afuwarku Kusan Dukkan Dan Adam Tara yake bai cika goma ba Allah ne Kadai Dari Bisa Dari ni Mutum ce kuma yar adam ce mai Rauni mai Kuskure in har a wannan Rubutun na bata ma wani ko wata don Allah ku yafemin kila akwai inda na Kuskure muku ko inda baku so haka ba to kuyi hakuri Ajizanci ne na Dan Adam ni ban isa nayi shi Dari bisa Dari ba Ina Fatan Sakon da kuka karanta zaku amfani da Darasin Dake Ciki akasinsa kuma ku Watsar Dashi Allah ya yafemana Kurakuran da mukayi Cikin wannan Rubutun ya bamu Ladan Dake Cikinsa Nagode kwarai da gaske sai Allah ya kaimu bayan Sallah da Rai da lafiya akwai Alkawarin Goron Sallah da nayi muku Da yardan Allah zan cikashi Zamu Fada Labarin SUNAIMA da MIJIN KANWARTA daya zama kaddaranta Shin wata irin kaddara ce..?kada ku Damu zamu fara wannan Tafiyar in muka gama azumi Lafiya Allah ya bamu Dacewa da Yantuwa acikin wannan Watan Allah ya Sa muna Cikin Salihan Bayi Ameen ya Allah Tanque all..._ *Janaftyshakira* *31/03/2022* *Intelligent writer"s ass* *GMB2ONELOVE*