MIN-QALB _Mamuhgee_ 1 Bismillahir-rahamanir Raheem. Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo ya zubar a babbar bolar bakin anguwar wadda za'a Kira da qaramar kasuwa sbd hargitsi da cunkushewar anguwar da manya da qananan kwatocinda suke cike taf da ruwa da ledoji tareda qananan abinci na wanke wanke dasuke biyowa, Daukar biredin tayi tana kakkabewa tareda kaiwa bakinta daya gama bushewa yayi fari fat harya Fara yayyankewa alamar ko yawun bakinta sun gama bushewa ta gutsura kadan ta Dan tauna taji zai shiga Da sauri ta qarasa turasa cikin bakin tana taunawa da sauri jikinta na rawa tareda hanjinta dasuke qugin jin wani abu ya saukar musu bayan kwanaki dasuka Dan dauka a na'de. Ganin wani almajiri yayo gurin Yana kallon biredin a yunwace Shima Dan ko gabansa baya kallo idonsa nakan biredin ko kyaftawa bayayi yasa tayi saurin miqewa tana qara tura biredin cikin bakinta da sauri sauri tana kallon almajirin karya iso gurinta Bata cinyeba ya kwace sbd wannan shine Abinda yake faruwa a bolar qwacewa daga marasa qarfi Wanda a duniyarma hakane duk me qarfi shike qwace Abinda yakeso gurin masashi, Batada uwa batada uba, Batasan kowa aduniyaba Wanda zata ce nata ne, Ita aduniyarma gaba daya batasan komaiba face yawon bola da tsince tsince. Almajirin na isowa gurinta yayi wuf da qarfi ya qwace biredin hannuwansa na rawa Shima yakai bakinsa yanaci da sauri sauri Yana hadiyewa ko taunawa bayayi sbd sauri yakai bakinsa. Kallonsa takeyi tana hawaye tana lashe sauran Dan gari garin biredin dake hannunta tareda uwar dau'dar dake tafin hannuwan nata dasuka sauya kala sbd dau'da. Tana kallo ya cinye biredin ya dago Yana kallon hannuwanta ko zaiga wani abin naci sbd yunwar dakeci hanjinsa yakai ko numfashi baya iyayi ko mushe yagani zai iya ci sbd qarfinsa daya gama qarewa gurin yawon bara. Ganin yanawa hannuwanta kallon yunwa yasa ta juya ta tafiyarta zuwa tsakiyar bolar tana bincikawa ko zata Kuma samun wani abin. Yarinyace qarama sosai Yar kimanin shekaru bakwai saidai yunwa da wahala Sunsa ta matse sosai kamar Yar shekaru shida, Dau'da tasa fatarta takoma baqiqirin ko tantance asalin kalar fatarta ba'ayi Ga gashin kanta daya gama tsinkewa sbd dau'da da zamansa a bude. Gangarawa tayi yafito cikin bolar tana qoqarin bude gwangwanin data samu cikin bolar fuskarta na nuna 'dokin son ganin me tasamo. Bakin shagon alhajiyat me abincin bakin titin ta zauna daga can gefe inda ake Mata wanke wanke ta faki idanuwansu ta dauki wata matacciyar butar tsarkinsu ta Dora baki tafara kwankwadar ruwan da sauri sauri wani sanyin rahama na sauka cikin hanjinta ita batamasan wani abu qazantar ruwanba burinta dai su sauka a cikinta. Fizge butar akayi da qarfi tareda jefarwa cikin masifa matar tasaka qafa ta tureta gefe tana cewa'" Wannan yarinya wlh anyi muguwar mayya, Yarinya saikace kafira ayita korarki Amma kullum saikin zo. Kallon matar takeyi tanason yin kuka Amma Sam takasa sbd tunda ta taso batasan wani abu waishi so,qauna,kulawa ba ko gata bare tasan zafin rashinsu hartayi kuka. Tunda tafara wayo daga ita sai kakarta kurma suke rayuwa a wani mataccen kangon shaguna wadda ita a wayonta batasan shin kakartace kokuma mahaifiyarta Itadai tasan itace komanta gashi kurma ce bataji Bata iya mgn ga tsufa ahaka suke rayuwar Bara da yawon bola neman rubabben abincinda zasuci idan dare yayi sukoma shagunan dasuke kwana su kwanta duk da Basu kadai bane shagunan duk mabaratane da nakasashshi, Koda iya tsohuwa tayi kwanaki kusan ashirin a kwance batada lfy tana gani tana kalla 'yarinyar ke fita yawon bola da bara tana ciyo abinci dame kyau da Mara kyau, Wani lokacin ma idan ta ciyo Mara lafiya tana gani zatazo tayita amai da zawo Amma ahaka take sake fitarta tasake samowa Koda a bolar ne taci abinta, Ciwo da yunwa da tausayin ganinsu ahaka yasa jikinta yin tsanani matuqa ahaka ta rasu batareda jamaa suna ankaraba ita Kuma batada wayon dazatasan meke faruwaba ahaka gawar tayi kwana biyu da yini take layin yafara daukar wani mugun wari wanda yasa sukasan akwai gawa. ahaka kullum da daddare itakam take zuwa ta kwanta gefen gawar tayi kwanciyarta tayi bacci gari ya waye ta fita. Koda aka gano gawar take suka Kira Yan sanda akazo aka bincika gawar suka tabbatarda rasuwa tayi ba wani alamar kasheta akayi suka kwashi gawar akai daji da ita acan aka binne a wata qaramar baqabarta. Tundaga lokacin rayuwarta tasake gararewa sbd ankorosu daga waincan shagunan yanxu duk inda dare yamata acan take kwana saidai kasancewar shagon abincin alhajiyat na sabuwar anguwar data fado masu dafa Mata abinci anan suke kwana shago yasa itama ta fake anan bayan shagon take kwanciyarta tayi baccinta. Bayan qawace butarda matar tayi komawa tayi gefen shagon daga inda suke watso ruwa ta zauna tafara qoqarin bude gwangwanin Amma Bata iyaba takasa. Kokuwa takeyi da gwangwanin tana saka farcenta tana budewa da qarfi Amma takasa sai jin tayi ankwace ta dago da sauri taga almajirin daya qwace Mata biredi ne da sauri ta miqe tana kallon gwangwanin hawaye na cikowa idonta tace" Abuna ne kabani inaso"ta qarasa tana Kai hannu zata karba ya tureta ya juya da gudu Yana qoqarin budewa Shima. Zaunawa tayi agurin tana hawaye daganan bacci yayi gaba da ita dama gashi yamma tafarayi. Cikin bacci tasaki fitsafinta Wanda tsumman kayan jikinta suka shanyesa ko gangarowa beyiba. Mangariba bayi ta farka tazo ta zauna gefen qofar shagon tana rarraba idanun samun Abinda zaa jeho waje. Ahaka har akayi ishai qarfe Tara tayi Bata samu komaiba ta miqe tana Sosa kanta dake danqare da dau'da Takoma bayan shagon tayi kwanciyarta. Gari ba wayewa ta miqe ta kama hanya neman Abinda zataci. Yauma duk Abinda tasamu almajirin jiyane ya qwace Mata ya cinye Kuma duk inda tayi kusan Yana biyeda ita sbd ga dukkan alamu shi sabon zuwa ne kamar baisan ko inaba kamarma baisan ya ake hakurin yunwaba sbd shi komaima yasamu ci yakeyi gashidai Shima zasuzo sa'a daya danshima bazai wuce shekaru bakwai dinba. Abun mamaki almajirin Nan saigashi gurinda take kwana Shima anan yake kwana idan gari ya waye tatafi duk inda tayi Yana biyeda ita. Ganin haka yasa yanxu tana samun Abu take rabawa biyu tabasa Rabin tun bai qwaceba ya cinye. Ahaka harsuka Saba sosai lokaci yaza sosai duk inda zasu tare suke zuwa harsuka samu wata roba a wata babbar bola da ita suke zuwa bara. Yau Kam ranar babu wata sa'a acikinta sbd ko ruwan dazasu sakawa cikinsu Basu samuba duk inda sukace korarsu da hantararsu akeyi sbd bayan wari da zarnin fitsarin tareda tsamin dau'da babu Abinda sukeyi. Kwanciya sukayi cikin bacci tafara jiyo sheshekar kukansa tayi saurin tashi zaune cikin tsoro ta kallesa tagansa zaune riqeda cikinsa. USMAN?????? takira sunansa cikin sanyin maryar dake bayyanarda itama a galabaice take sbd yunwa. Dagowa yayi ya kalleta da ido sharkaf da hawaye yace" Amah cikina ciwo sosai. Tashi tayi tareda kallonsa kafin ta juya tana cewa'" Zansamo ruwa saimu sha. Tana juyawa wasu manyan samari su biyu dake boye suka fito tareda toshe Masa baki suka dagasa cak suka wuce dashi suna zuwa motarsu suka bude da sauri suka jefasa da gudu suka bar gurin. Cikin sanda ta Isa qofarsu alhajiyat ta dauko butarsu dake cikeda ruwa ta sidado ta dawo da sauri saidai tana zuwa taga babu usaman din cikin sauri ta ajiye butar tafara duddubasa koina tana Kiran sunansa. Har kusan asuba Bata gansaba tadawo ta zauna shiru tareda qurawa robarsu ido, Akaro na farko arayuwarta bayan iya tsohuwarta data samu wani arayuwarta Wanda taji ayau tanason karya tafi koina ya tsaya gurinta suyita yawon neman abinci atare, Tasaba da usman sosai sbd a yanzu Koda Basu samu Abinda zasuciba sunada junansu damuwarsu kadance tunda suna debewa juna kewa. Har gari ya waye Rana ta fito Bata gansaba tayi yawon duk inda suke zuwa bara tare Amma Bata gansaba ga yunwa ga gajiya ga qishirwa ga Rana haka ta dawo agajiye da daddare ta kwanta bayan Tasha ruwan butarsu alhajiyat. Cikin bacci gaji motsin mutane tana bude ido taga wasu su biyu sunzo gefenta sun anjiye Usman din sun jiya da sauri sun tafiyarsu. Da sauri ta tashi tana cewa'' Usman Ina kaje?? Bai motsaba sbd ko numfashi baya fitarwa Ta juyoda fuskarsa tadan bubbuga tana sake Kiran sunansa har lokacin bai motsaba. Ganin kamar bacci yakeyi yasa ta gyara Masa kwanciya tareda juyawa ta kwanta tanajin Dadi akaroro na farko a rayuwarta sbd usaman yadawo. Koda gari yayi haske ta tashi har lokacin usman be tashiba ta dawo gabansa tana Kiran sunansa ya bude ido ya kalleta idanuwansa jawur jikinsa nata wani irin rawa atake taji tsoron ganinsa cikin yanayi da sauri tace' Usman menene? Kanajin yunwane haryanxu? Cikinka na ciwone haryanxu ma?? Ahankali ya nuna Mata duwawunsa Yana hawaye da dasasshiyar murya yace" Sunmin wani abu anan zafi yakemin sosai''sai kawai ya fashe da wani irin kuka Yana dafe gurin sbd tsananin azabar dayasha agurin dasuka dannesa sukai amfani dashi. Ganin irin kukan azabar daya keyi yasa itama tafashe da kukan ahankali musamman dataga jini a wandonsa tasan ciwone suka jimasa duk da basanma menene Abinda sukayiba. Wasa wasa sai zazzabi ya rufe usaman sosai har jikinsa na wani irin mazari duk saita rude takamasa suka kutsa cikin kasuwa neman bara. Suna shiga kasuwar taji wani me magani da lasifika Yana cewa' Idan duwawunka ba ciwo baka iya miqewa bayan bahaya to kazo Muna mafaninka, Idan kanajin fitsari baya fita sosai Shima kazo munada maganinka. Da sauri taja hannun Usman dake tafiya a duduqe sbd ciwo da zazzabi sukazo gaban mutumin ta kalli maganinsa tana nunawa tace'" Wannan zaka bawa Usman yaji ciwo a duwawu. Kallonta me maganin yayi kafin ya kalli Usman da kyau Yana tauna goro da jajayen haqoransa ya washe baki tace'" Ku kawo kudi' yana miqa musu hannu. Kallon hannunsa sukayi kafin ta dago ta kallesa ta girgiza Kai alamar ita batamasan meyene ba. Dari diyar ya fidda tareda nera dubu daya ya budesu ya nuna musu Yana cewa" Kuje ku samo wannan ko wannan ku kawo nabaku magani yanasha zai warke. Kallonsa tayi tana sake kallon kudin hannunsa kafin suka juya jikinsu a sanyaye sukabar kasuwar. Kwana biyu jikin Usman babu wani sauqi gashi itama qarfinta yafara qarewa dole ta fakaici idon mutane da daddare tashiga shagon alhajiyat ta sato irin kudinda me magani ya nuna musu har guda uku. Tana fitowa suka boye tunda safe suka shiga kasuwar neman me magani cikin saa suka Ganshi tabashi kudin duka tsabar zalinci saiya karbe duka dubu ukun yabasu canjin dari biyu tareda maganin Dan kanoma yafada musu su siya Koko susha dashi. Kokon duka Darin biyu tasiya musu Usman yasha maganin ta shanye sauran kokon jikinta na rawa. Dayake Shima Usman din harda yunwa dake cinsa yasa jikin tsananin Saigashi sun samu qarfin jiki bayan sun shanye kokon take suka kutsa kasuwa bara. Da daddare yauma batada zabi bayan sake sato kudin Tunda safe suka sake siyan Koko yau harda qosai. Sannu ahankali sata tashiga jikinsu Tun alhajiyat Bata ganewa ana Mata sata harta gane tafara saka ido sosai akan son kama barawon. Cikin saa takamasu aikuwa tasa akayi musu mugun dukanda Saida suka fita hayyacinsu Kuma tasa aka koresu daga anguwar gaba dayama. Wata sabuwar anguwa suka fada wadda tafi wadda suka baro hargitsi saidai wannan din 'yan ta'addane sukafi yawa acikinta sbd gasunan koina suna shaye shaye. Cikin saa nanma suka samu wata tsohuwar makaranta suna kwana aciki sauqinsu daya makarantar nada megadi shiyasa sukejin saukin kwana. Ranarda suka cika kwana shida a sabon gurin cikin dare suna dawowa wasu maza biyu suka taresu. Saurin riqe hannun juna sukayi suna ja da baya sbd yanzu sunfara wayo sosai. Damqo amatu dayan yayi da qarfi Yana cewa'" Kai saketa ka ware daga Nan gun. Dayan hannunsa yasa yaqara riqeta Yana girgiza Kai alamar aa. Wani wawan Mari dayan ya sakar Masa Wanda yasashi ihu. Suka toshe masa baki tareda matsesa Shikuma dayan ya fizge amatu tareda kwantarda ita qasa da qarfi. Kuka tasaki tana miqawa Usman hannu tana Kiran sunansa itama da sauri dayan ya rufe Mata baki Yana qoqarin cire wandonsa. Kuka sukeyi duk su duka musamman Usman dayaga irin Abinda akai masane zaayiwa amatu Kuma ya dandani tsananin azabar hakan bazai Bari amatu ta dandana ba. #mamuh. #Zafafa biyar# Saran boye Billyn Abdul Abin dake zuciyata Hafsat rano Kibiyar AJALI Miss xoxo Siradin rayuwa Safiyya huguma Min qalb mamuhgee Pay@ 09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:01 AM - ': *_MIN QALB 3_* _mamuhgee_ _Min qalb Na kudine_ Daki 'daya ya dauka iyami da amatu suka dauka daya Sabuwar rayuwa suka Fara a gidan inda ake zaman rashin nasiha da ragawa juna, Sam gidan kowa ta kansa yakeyi Babu Mai ta6uwa kowa ka taba Babu sauki sai masifa., Hakan yasa suma ahankali rayuwa ta koya musu yanda take, Sunaji suna gani itama amatu ta ajiye karatu suka fada gwagwarmayar neman abin rufawa Kai asiri, Amatu da iyami suka bazama neman ayuka Ita iyami tasamu aikin abincin wata makaranta amatu Kuma tasamu aiki bookshop din wata iyamura. Bata wani jima tana aiki gurinba saigashi Shima Usman aka kamasa aka rufe kusan wata biyu ga iyami ma tana fama da ciwon diabetes sai kawai tace Mata ta ajiye aikin abincin makarantar kada taji ciwo al'amarin yaqara lalace musu. Hakan yasa nauyi yahau kanta na kulada iyami damuma nauyin ci da shansu. Rayuwa da lokaci sune suka koyar da ita darussa da dama wanda ayanxu take musu kallon fahimta, Tunda lalurar nauyin ahalinsu tadawo kanta Bata taba samun Wanda yadubeta da fuskar taimakawaba kowa da wata mummunar manufa yakeson taimaka mata, Ansha niyar lalatar Mata da rayuwa tana tserata, Ansha wulaqantata akan ana Mata kallon fandararriya Mara asali, A ranarda wani yayi niyar lalatar Mata da rayuwa ta dole da niyar zai taimaka musu aranar ne zuciyarta ta gama qanqansewa da duk wani alamarin mutanen duniya Shiyasa take Kiran kanta da furen kan juji. Iyami ma hakan yasake busar Mata da zuciyar zata nemi kudi kota yayane Banda haram, Babban Abinda ke qara kawo tabarbarewar zaman lafiyarmu shine hukunci akan Wanda hukuncin laifinsa bai Kai ba shike kawo sauyawar tunani da zuciya, To kusan hakance tafaru da ahalin kawu, Bayan fitowar Usman tuni zuciyarsa ta gama kangarewa sbd rufesan da akayi suncire Masa tsoron gidan yari Kuma, Rayuwarsu tadawo sabuwa, Burinsu shine kudi, Farin cikinsu shine kudi, Mafarkinsu shine kudi, Mafarkinsu shine kudi Idan har kudi suke Hana Dan Adam wulaqanta da tozarta tareda azabta Irin wadda suka taso suka rayu acikinta to tabbas sun shirya samun kudi Koda na wani ne. Basu sake jinjinawa alamarin kudi ba Saida sukayi belin kawu da kudi naira dubu dari bayan yayi shekara daya da wata Tara gidan yari. Babban al'amarinda ya shallake tunanin abokan zamansu na gidan hayan shine qarmashewar da zuciyar kawu tayi fiyeda ta kowa acikinsu game da kudi, Yana fitowa gidan yari Abinda yafara fada afili shine'" Idan har kudi sune maganin wulaqanci da toxarci tareda maganin wani baqin ciki to tabbas burina yanxu shine kudi, Kudinma ba qananun ba manya nake buri. Shekaru sunja sosai alamura sunyi haske sosai a rayuwarsu sbd kowa yanada hanyoyin samun kudinsa, Acikin gidansu dake cike tab da 'yan haya to tabbas Babu me masifa da fitinar kawu, Bayada sauki ko kadan Dan babu ubanda yake ragarwa a gidan ciki kuwa harda alhaji mande me gidan, Duk masifaffun gidan suna shafawa kawu lafiya sbd fitinarsa Amma shikuma iyami ce kawai daidai dashi sbd ko atsakaninsu basawa juna nasiha ko sauqi. Damuwa,kuka,kunci,baqin ciki,takaici,tuna baya Wainnan duk wasu abubuwane dasuka binne a bayan rayuwarsu, Sun koya su ciyar da kansu tun basusan kan nasuba, Sun koya tsayawa da qafafunsu da junansu tun basusan meye duniyar ta qunsaba, Sunyi yaqi da wahala da yunwa tareda azabta su kadai batareda wani ya tallafesuba, Sun yakice tsoro tun basusan meye tsoronba Dan haka su aduk yanda rayuwa tazo musu yanzu basuda damuwa da ita sbd sunsan babu wata gwagwarmayar data fi wannan din. Wannan shine rayuwarsu, Rayuwar 'yancin Kai rayuwarda baduda burin komai cikinta saina suji Dadi su dawwama da juna acikinsa. AMATULLAH yanxu rayuwarta takeyi cikin jin Dadi da walwala, Babu Abinda ya dameta face taji dadin rayuwa tareda ahalinta data keda burin su samu duniya suji dadinsu, Duk inda tasamu aiki Bata jimawa ake watsewa sbd halayenta na Babu Abinda ya dameta bayan shiririta da yin duk Abinda taga dama Duk Wanda yayi gigin shiga huruminta kuwa Yara take sawa qanana su koyawa mutum hankali kokuma usi Wanda beda aikin yi yanxu sai yawon banza sai idan ansamu na sanfewa a sanfe. Amatu kyakkyawar cikakkiyar budurwace yanxu wadda tagama hada komai musamman kyawun jiki da fuska. Maza ko gigin zuwa nemanta basayi sbd a duniya idan akwai Abinda ta tsana fiyeda komai to mazane idan aka cire usi dinta da kawunta. Kana cewa kana sonta zata saka ahada maka jini da majina Wanda usi ne me aikin shida wasu abokanansa. Ayanxu Kam sunsan duniya sunkuma darassantu da iliminda tabasu shiyasa akoda yaushe ashirye suke da duk sabon darasinda zata kawo. AMATULLAH K SALEH shine cikakken sunanta Wanda kawu yabata aranar da yafara kaita makaranta, Usman K saleh 'dan uwantane da aduniya babu Abinda takeso da qauna sama dashi, Zata iya sadaukarda rayuwarta data Bari wani abu ya samesa, Hakama zata iya sadaukarda komai sbd shi sbd sunawa juna kallon uwa daya uba daya suke ko kawu baitaba sanin ba uwa daya uba dayane ya haifesuba duk da Shima bakowane yasan cewa bashine mahaifinsu ba musamman da kusan halayen amatu duk nasa ne na rashin hakuri ko kadan, Acikin su hudu kuwa baasan waye yafi wani son kudi da abun duniyaba shiyasa ake musu laqabi da dangin tsamiya. Arayuwarta tayi aiki kala dabam dabam zai Kai goma koma fiye Wanda takeyi yanxu a restaurant shine kusan na sha daya Hakama kawu yayi sanaoin harya gaji Amma yaqi kudi shiyasa ya tattara ya watsar yakoma zaman saka ido da jiran Wanda tsautsayi zaisa ya tabasa yaga masifa tareda siyan radio yakoma Shan waqe waqen gargajiya wanda kowa naji ba halin mgn sbd Shima ubanda zai tanka dinyake nema Amma haka kowa ke dannewa sbd azauna lfy duk da gidan kullum cikin fada da hayaniya ake. **** Qarar waqar sani sabulu ce ta _duniya wandon roba_ ta cika gidan ta karade wane daki da saqo na gidan sbd qarar muryar radio din da aka Kai qarshe gaba daya. Hankalinsa kwance yake yana Shan waqarsa Yana sakace haqoransa da tsinke Daka gansa zakasan babu Abinda ya damesa. Dukkanin mutanen gidan 'dai 'dai suka ringa fitowa rayukansu a 'bace da takaicinsa na kullum Wanda inda sabo sun Saba da dabi'arsa ta tayardasu kullum da sautin radionsa da muryarsa Bata qasa Gashi bamai ikon mgn 'yar gaban goshinsa da shaqiyin dansa suce ba Wanda ya isa Amma rshin arzikinsu babu kalar Wanda basa fafatawa dashi wanda kallo daya zakayi musu kasan su din abin mamaki ne, Rayuwarsu abin kallo ce sbd sudin abin mamakine. Yana ganin mutanen gidan sunfara fitowa ya sake dauke Kai sama Yana jiran yaji wani Mai shafaffun Mai akai ne zaiyi mgn ya sauke Masa masifar dake cinsa ta takaicin iyami daya kwana dashi na biya Masa bashin dabaiyi niyar biyaba yanzu da kudinda yaci burin canza radio dashi na AMATULLAH da USI. Cikin bacci qarar radio din ke shigarta Yana damunta, Juya kwanciyarta tayi tana toshe kunnuwanta da pillow Amma Sam qarar Bata daina shiga kunnuwanta ba. Tsoki tasaki ahankali tana cewa' Kawuuuu. Saidata sake rintsawa ta juya kwanciyarta tsawon minti goma Amma Sam baccin ya gagara sbd qarar radio din dole ta yaye lullubinta ta miqe zaune tana miqa tana cewa' Allah yasa yanda natashi yau cikin qoshin lfy yasa yau ranar sa'atace, Allah yasa yauma na hadu da irin hajiyar Dana hadu da ita jiya nayi mata kukan tausayi tabani kudinda zanyo...... Kasa qarasawa tayi tareda zaro ido sbd USI data tuno Da sauri ta dauki hularta dake kan katifarta ta sanya akai tareda zura silifas cikin sauri tana fitowa kota kan kawun batabi ba sbd daga yanayin waqar dayake sha a radio din ta fahimci yau ba sauqi a qule yake Wanda zai saukewa haushin yake nema shiyasa ba Wanda yace Masa uffan gudun masifa. Bokiti ta dauka ta nufi fanfon dake can kusada qofar shigowa cikin gidan Tana zuwa ta tararda wani bokitin yakusa cika Ta gefen ido ta kalli maman junior dake tsaye alamar natane take jiran yacika hancinta na asalin yorbawa sai cika yakeyi Yana fidda iska sbd ita kullum a shirye take da duk inda masifa zata fado ta hauyi. Shahada tayi ta rintse ido cikin ranta tace' Bayina bane Allah ne ya qaddaro bazanbi layin jiraba Ta sunkucesa da gudu ta fada bayin gidan daidai salamatu zata fito bayin tsoron ganin mutum a fujajan yayo ciki yasa ta zame ta Fadi qofar bayin Aikuwa itakam amah Bata tsaya wata wata ba ta rufo bayin tana cewa' Haka Allah yaso anty salamatu bayina bane Allah ne ya qaddaro zaki Fadi, Kema maman junior yi hkr Allah ne ya qaddara da ruwanki zanyi wanka bayina bane. Cikin wani irin tsananin baqin ciki da takaici salamatu ke kallon kanta zaune cikin ruwan qazantar qofar bayin bayan tayo wanka., Wani irin tiririn masifa zuciyarta keyi ta miqe amatuqar zuciye daidai isowar maman junior itama jikinta harwani mazarin masifa yakeyi tana cewa' Wlh yau gidan Nan saidai kowa alaji landlord yakore agidan Nan Amma sai anyi balain da ko kawu fatihu duk masifarsa bazai hanani yiwa yarinyar Nan dukan tashi Kisha ruwan gishiri ba. Kallonta salamatu tayi a harziqe tana cewa' Saiki sameta cikin bayin tunda akanki aka Fara sauke masifa duniya Kinzo kina qaramin haushi Idan ke duka zaki mata wlh ni yau saina dauko motar Yan Banga a gidan Nan kowa yaci ubansa tunda Nagano kowane shege a gidan Nan ya rainani tunda anga Ina zaman kaina. Kota kanta maman junior batabi ba tahau dukan qofar bayin tana fadin' Yau wlh zakisan halina dabaki saniba tun kafin kizo duniya nasan rashin arziki bazakizo ki rainawa kowa hankaliba kullum komai kikayi kina Kiran sunan qaddara ne daga Allah wlh yau Ina roqan Allah yahadaki da qaddarar Nan da kike kirawa mutane bayan nagama Miki dukan tuwon qasa. Alhaji mande dake jiyo yanda ake buga qofar bayin gidansa da qarfi ba arziki ya zubo babbar riga yafito ya zagayo gidan tun a soron gidan yake jiyo qarar radion kawu fatihu yaja tsokin takaici ko sallama baiyiba ya fado gidan Yana cewa' Uban waye zamansa ya qare a gidan Nan yau yake gyangyademin qofar bayi?? Maman junior najin haka tayo gurinsa tana masifa tana zayyane Masa Abinda yafaru bakinta ta kumfar masifar customers dinta nata jiranta ruwan dafa musu doyane tazo diba. Tanajinsu cikin bayin Amma ko ajikinta tayo wankan da sauri ta fito basuma ankaraba ta fada dakinta tahau shiri cikin sauri ta shirya cikin doguwar riga baqa mara Fadi sosai ta sanya hijab iya wuyanta ash ta dauki Jakarta qarama ta rataya a wuya ta fice. Gaban kawu tazo tana ciro qaramar wayarta jaka tace' Kawu sannu da tashi. Yi yayi kamar baijitaba Yana gyara zaman radionsa data ishi kowa gidan. Qofar dakinsu ta kalla inda iyami ke zaune tana sakawa Koko sugar tace' Iyami Ina kwana?? Lafiya kalau.''tace itama fuska a tsuke. Murmushi tayi Wanda yasa kumatunta lotsawa haqoranta suka bayyana Sbd tagano fadansune dai Wanda basa rabuwa dashi itada kawun Kuma ta tabbatarda akan kudi ne.. Dariya tayi tana juyawa tace' Allah kasa muyi kudi kawu da iyami su daina fada. Harta fito gidan alhaji mande da maman junior Basu daina fadaba sbd fadan tsakaninsu yakoma. Titi ta nufa da sauri tana adduar samun kudinda zata bailing usi. Tana isowa titin tasamu adaidaita ta tare ta fada cikin sauri tace' Blue fox zaka kaini. Tafiyar mintuna gomace takaisu gurin cikin sauri ta biyasa ta nufi harabar gurin dake tsareda security masu baqaqen uniform ta shiga tana kallon wasu motoci biyu dasuka dauki hankalinta sbd tsananin kyawunsu da sheqin dasukeyi Dan har kanka kake gani ta jikinsu ta kalli sama tace' Ya Allah kasa muyi kudinda zamu mallaki irinsu nida usi mu Hana su kawu fada. Ciki ta qarasa da sauri tana adduar Allah yasa yau tasamu sa'ar wani a cikin restaurant din. Tana shiga ta nufi dakinsu na staffs din gurin inda suke sauya Kaya zuwa uniform din aikinsu. Kayanta ta sauya izuwa uniform din aikin waitress dogon wando baqi da riga riga ash saita bar qaramin ash hijab dinta na iya wuya. So takeyi ta tafi da wuri yau sbd gabaki daya hankalinta nakan usi. Ta tabbatarda yanacan cikin wahala da damuwa duk da dai alqawarinsu ne bazasu taba saka kansu cikin damuwaba duk halinda zasu shiga sbd damuwa ciwo ce a ganinsu idan kasone zaka sakawa kanka damuwa a almarin duniya. Amah!!! Naam"ta karba tana juyowa daga jera drinks datakeyi a fridge. Manager dinsune sanye cikin black Suit da medical glass a fuskarsa cikin tsuke fuska yace" Ki hada black coffee dinda ake karbarwa _MD ZABEERA_ kullum ana kaimasa yau yazo da kansa zaisha anan, And ki tabbatarda kinyisa yanda koyaushe ake hadawa kar asamu matsala amah. Yaqe baki tayi da murmushin qarya tace'" Bazaa samu matsalab inshallah manager. Juyawa yayi ya fice Yana cewa' Allah yasa. Kamar yanda tasan ana hadawa haka tafara hadawa cikin sauri sauri tana gama zubawa Yana sake shigowa yace" Yawwa ki hada a tray ki Kai VIP 3 yagama Abinda zaiyi tafiya zaiyima. Babu Abinda ta tsana kamar kai abinci a aikinnan nasu tafison abarta a hadawa suna dauka suna kaiwa sbd idan tana ganin masu kudi burinta sake hauhawa yakeyi. Tsaki tasaki ta dauke baki ta dauka tana tafe tana qananun tsoki tana Harare harare. VIP dinsu Yana can sama Saida tagama tsinewa manager ko kafin takai saman daukeda tray din. Saida ta tsaya ta huta kafin ta nufi VIP 3 din tana isa security din dake gurin ya tura mata qofar gurin yana washe mata baki sbd mutuniyarsace ba ruwanta lafiyayyan takeaway take Masa idan zasu tashi shiyasa kowa gurin yake yinta Dan babu ruwanta bayarwa takeyi shiyasa lissafin nasu yanxu gurin kullum cikin rudarwa yake tunda aka dauketa aiki gurin. Tana shiga ta tsaya cak tareda lumshe ido tasaki wata irin ajiyar zuciya afili tace'" Hummmmm masu kudi turarensu ma qamshinsa na dabam ne, Ya Allah ga amah da usi. Bude ido tayi ahankali daidai wayarsa na daukar ringin batareda ya juyoba ya sanya dogon hannunsa da fatarsa ke sheqin hutu da haske ya dauki wayar tareda miqewa ya nufi window ya Dora wayar a kunne batareda yace komaiba. Zare idanuwanta dake neman rufewa su suma tayi tana girgiza kanta ahankali tace'" Ya Allah. Table ta nufa ta ajiye tray din idanuwanta suka sauka kan wallet dinsa dake ajiye da kudi acike acikinta batasan lokacinda tayi saurin dire tray din ta dauki wallet din ta bude taba zaro ido tace" Yau ranar sa'atace ya Allah nagode maka. Kudin ta zaro gabaki daya tana musu kallon qurilla fuskarta cikeda farin ciki tace' Kayi hakuri Dan balarabe Amma nafika buqatan kudin Nan. Aje wallet din tayi ta juya da sauri cikin farin ciki tana damqe kudin ta fice tana sauri Dan karya gama waya ya juyo yaga ba kudinsa ya biyota yace kudinsa zai qwata itakuma bazata bayarba. Ta glass din window dayake tsaye yake kallonta cikeda tsananin mamaki da qyamar halinta daya sanyashi kasa juyowa akaro na farko dayaga mace da irin wannan halin mafi Muni agaresa Wanda hakan yasahi kashe wayar wadda tunda ya daga baice komai sai sauraren zancen da ake Masa tacan Wanda kusan hakan dabi'arsa ce. #mamuh# #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:01 AM - ': _*MIN QALB*_ _Mamuhgee_ 2 Bazai iya ganiba sunaji suna gani qaton saurayin yake kokarin keta rayuwarta dabata gama sanin ciwon kantaba, Ita kukan datakeyi dannewar dayayi Mata akan duwatsu suna cin jikinta Shikuma Usman kukan zabar dayasha yake tunowa itace zaayiwa amatu Wanda sanadin hakan sunzama 6arayi dole da qarfi da yaji. Qoqrin bude qafafuwanta qaton keyi Usman yayi wani yunkuri tareda kama hannun Wanda ke maqure dashi ya sakar Masa mugun cizo Mai qarfi da haqoransa dasuka gama bushewa da dau'da. A gigice yasakesa Yana yarfe hannu sbd azabar cizon. Wani qaton dustsi Usman din yadauka baiyi wata wata ba ya buga akan qaton dake kan amatu Take ya sulale gefe kansa na tartsin jini sosai ko ihu daya beyiba ya zube agurin Yana wani irin Shure Shure. Suna ganin hakan wani irin tsoro yashigesu da gudu ya kamo hannun amatu Yana cewa'" Zo mu gudu amatu. A firgice dayan ya riqesu Yana cewa'" Kun kasheshi....a kidime yake fadar hakan cikin tsananin tsoron ganin abokinsa na Shure shuren mutuwa. Qoqarin jansu yakeyi Yana cewa'" Wlh police zan kaiku Kun kashesa, Bazaki guduba ku barni cikin masifa akamani. Jansu yakeyi da qarfi cikin firgici da tashin hankali suna kuka sosai suna rokonsa ya sakesu Amma Shima a rude yake kansa zai wanke kota halin Yaya. Irin kukan dasukeyi Basu taba yinsaba arayuwarsu sbd jin wani ya mutu sbd su Kuma Suma kashesu dayan sukaji yanacewa zaayi. Sosai suke kuka suna rokonsa ya sakesu Amma ko jinsu bayayi Dan Shima kusan kukan yakeyi na tsoro da firgici. Wata qatuwar gora daga bayansu aka kwadawa qaton a tsakiyar Kai Ya tsaya cak tareda sakin hannuwansu Yana qoqarin juyawa yaga ko waye ya yanke jiki yafadi jini nafita a qeyar kansa. Jikinsu na rawa cikin tsananin tsoro da firgici suka juyo suna qanqame hannuwan junansu tareda ja baya suna kallon qaton dashima yake Shure Shure. Cikin sauri megadin makarantar ya matso gabansu tareda riqo hannuwansu yasaka musu kudi Yana waige waige Yace" Kuyi gudu sosai kuje can qasan layin gaban kasuwar baya akwai makarantar almajirai ku shige cikinsu ku kwanta ku boye zanzo idan ankwana biyu Kuyi sauri karku taba dawowa tanan Kuyi sauri kuje.. Kallonsa sukeyi suna sake sakin sabon kuka sbd sunqara firgicewa da Abinda yake fada, Yaturasu Yana cewa'" Kuje kuje kuyi sauri karku dawo. Gudu suka Fara suna waiwayensa sbd akaro na farko da wani ya taimakesu arayuwarsu. Tun suna waiwayensa harsuka bace suna gudu cikin Daren gashi yace karsu hau titi subi kwana kwana. Koda suka Kai makarantar almajiran dare yayi sosai gashi karnika sai haushi suke musu duk inda sukabi. Suna kaiwa bakin makarantar suka tsaya suna rarraba idon Ina zasu boye sbd almajiran gasunan kwance birjik a fili kowa da matacciyar tabarmarsa wasu Kuma da kwalaye wasuma hakanan suke kwance a qasa ga cinnakai da qwari da komai Amma ba ruwansu kwance suke abinsu suna bacci. Hanunta usman yakama suka qarasa can qarshe yacire matacciyar rigar jikinsa data gama yagewa ta mutu ya shimfida musu suka kwanta kowannensu jikinsa na rawa numfashinsu na fita da sauri sbd tsananin tsoron dasuke ciki. Asubar fari dukkanin almajiran aka tadasu suyi sallah Wanda wannan shine karo na farko dasuka tabayin sallah Shima Suma dai sunyi yanda sukaga kowa nayi gurin bin Abinda malam yayi. Ana gama sallah kowa yadauko allonsa Yana bita. Gari yafara haske sai sukaga almajiran na kallon amatu cikin mamaki suna kallon kanta Wanda gashinta ke butu butu da dau'da da qazanta Wanda yake son nuna ita mace ce. Daga dama sukaji wani almajiri yace" Kai wallahi idan malam yazo yaga mace dukanku zaiyi wayace mace tana zuwa Nan?hmm Korarki ma malam zaiyi yanzu Yana fitowa. Usman najin kora ya kama hannunta suka miqe anabinsu da kallo suka fice a sanyaye. Harsunyi nisa kadan yatuno da maganar kawu megadi na cewa karsu koma yayi saurin juyawa da ita Yana kalle kallen inda zasu fake Kuma. Ganin har yamma tayi suna gararin gurin zuwa yasa ya lalubo kudinda kawun yabasu yaje shagon dake kallon inda suke yasiyo Rezar nera ashirin yadawo yajata suka zagaya bayan wani gida Yana cewa'" Amatu zo muyi aski irin nasu almajiran malam saimu koma cikinsu tunda bamuda wani gurin. Haka ta zauna yahau yimata aski Saida ya aske kan tas Wanda duk kusan Rabin kan ya yayyakenta sai jini ke fita kadan kadan Amma Sam Basu damuba Shima sama sama yayi nasa askin rabi yayi rabi beyiba suka dunkule Rezar sbd gaba suka koma makarantar dama kayan jikinsu duk riga da wandone dasuka gama yayyagewa suka sauya kamanni. Dayake makarantar ba qa'ida sukebi ba take malam ya kaebesu yaga sabbin alamjirai aka Basu tsoffin allon karatu take suka shiga sahun almajirai batareda kowa yasan cewa amatun mace ceba Koda malam ya tambayi sunayensu sukace Usman da amadu. Ahankali suka Saba da rayuwar almajiranci duk da akwai wuya Amma tafi musu rayuwarsu ta baya dansu yanzu ganin sukeyi sunyi gata. Akai akai Usman kemata aski sbd kar gashinta yafito musamman sbd tanada saurin tsirowar gashin, Sunsaba idan sungama ayyukan gidan malam akayi karatu aka gama su fita yawon bara sai yamma sudawo karatun yamma sannan sufita barar dare daga Nan Kuma dare nayi zuzo su kwanta. Yanzu suna samun yin wanka a sati ko so dayane shiyasa suka Dan Fara canzawa. Tun suna qirgen kwanakin zuwan kawu megadi harsuka daina suka koma qirgen kwanakin zuwansu har lissafi ya batar musu. Ko ayanxu dasuke cikin inuwar almajiranci abun dai 'dayane shine idan baka tsayawa kankaba Kaine a qasa ko yaushe, Sunsha gwagwarmaya zamansu makarantar malam din, Idan anyi sata su ake maqalawa, Barna sune, Laifi sune, Hatta laifin cikin gidan malam su ake maqalawa shiyasa sunfi kowa azabtuwa sbd irin dukan da malam da ya manyan yaransa suke musu, Shatin buloli ajikinsu yazama tamkar zanen fatarda aka haliccesu da itane, Tun suna kuka a almari harsun qame sun daina sbd ganin rayuwar ahaka take koina na sama ya danne na qasan. Duk hutunda akeyi sukam basa zuwa koina sbd basuda gurin zuwa shiyasa rashin tausayinsu yafi yawa sbd ansan ko an zalincesu basuda me tsaya musu. Ahaka dai rayuwa taja tsananin rayuwa Yana qara musu yawa musamman yanxu da amatu take Fara nonuwa kullum cikin boye boye suke gashi yanxu abubuwan naqara tsanantar musu ne gashi amatu ko mgn batayi sosai da qarfi da yaji suke boyon mganarta kar agano mace ce. Yanxu dasukayj wayo Usman shine me wahalar Abinda zasu ci duk da tare suke zuwa duk inda zasu gashi baqin jini tamkar a jininsu yake sbd duk inda sukaje tsanarsu da kyararsu akeyi shiyasa suka riqe aransu duniya kowa kansa kawai yasani basuda Abinda yafi musu junansu. Wani hutu da akayi kamar daga sama saiga kawu megadi Wanda tuni suka Fara mantawa da kamanninsa, Farin ciki da murnar dasukayi kamar shine danginsu da basuda musamman dasukaga yazo musu da gari kusan kwano buyi jikinsu har rawa yakeyi gurin yimasa godiya. Amatu ya qurawa ido musamman kanta dake aske tas Yana qyalli ga wasu qananun quraje a jikinsu zuciyarsa na susa yaji dukkanin kuzarinsa ya karye sbd tabbas duk da baitaba haihuwaba ita 'ya mace ce bazaa jima ana boyeta ba amatsayin namiji. Dazai tafi yasiya musu gwanjo kowannensu riga da wando masu Dan dama dama. Tun daga lokacin yake Dan zuwa akai akai Yana dubasu sai rayuwar tadan Fara yimusu sauqi. Awani zuwa da yayi Baizo da niyar tafiya dasuba Amma atake tunaninsa ya sauya akan amatu sbd girma daya Fara zuwar Mata gadan gadan Yana tsoron amatsayinta na mace ta abalage acikin maza. kallonsu yayi bayan sun zagayo bayan makarantar cikin karyewar zuciya Yana jinjina rabasun dazaiyi yace" Usman kaga amatu tafara girma akwai hadari abarta cikinku anan.. Kallonsa sukayi atare cikin rashin fahimta. Gyara tsayuwa yayi yace zantafi da ita zan kaita gurin me 'dakina idan yaso Kai saika riqa zuwa Mana hutu. Atare suka girgiza Kai itada Usman din suna kallon juna idanuwansu na cikowa da hawaye. Nasan zaa rina yafada cikin ransa Yana kallonsu zuciya a karye. Kamo hanun Usman yayi yajasa gefe ya fahimtar dashi sosai ta yanda zai gane Abinda yake nufi Harya gane Yakuma amince sbd har abada bazaiso Abinda zai samu amatu ba. Daga haka suka hakura sunaji suna gani suka rabu da juna kawu yatafi da su kafin daga baya Usman yadawo makarantar malam. Tunda amatu tadawo gidan kawu Bata taba haduwa da tsangwama ba saidai Kuma babuwa wani janta ajiki da iyami tayi. Basuda qarfi sai rufin asiri da haka malam yasakata primary school dinda yake gadi wadda tuni aka maidata 'yar maigadi. Usman shekara daya yayi batareda itaba ya tattara karatun yadawo gidan kawu Yana kwana a soro komai tsananin sanyi da zafi kuwa. A haka kawu yasamar Masa aikin tsaron gidan wanka da bahaya a Tasha har Shima yashiga primary 2 Yana shiga primary 5 ya tattara karatun ya ajiye sbd gwagwarmayar rayuwa. Kawu da iyami sune gatansu na farko, Kawu da iyami sune wainda suka cirosu daga bola suka basu sunanda ake kallonsu da daraja ayanzu. Shekakarda tashiga js 2 a shekarar suka shiga wata sabuwar masifar da akayiwa kawu sharrin satar cire winduna da qofofin makaranta ya siyar. Duk inda ake zuwa roqo da Kai kuka sunkai akan alamarin Amma Abu ya agagara qarshe dpo nunawa yayi sai idan ita amatu kokuma matar kawun zasu kwana dashi tukuna zai taimakesu. Akaro na farko da amatu ta tsani maza da taimakonsu. Ranar dukkaninsu kwana sukayi kukan baqin ciki sunaji suna gani akayi gidan yari da kawu hukuncin shekara biyu dama Kuma abin hadda gayya sbd Shima alqali yaso amatun tabasa hadin Kai sbd irin wankewa da jikinta yayi gashi fatarta Ashe me irin hasken Nan ce ga jikinta daya gama fitowa ana mace tsaf yanzu iyakaci qarasa balagewa ne dabatayiba a cikakkiyar mace. Tunda akayi gidan yari da kawu alamarin duniya yasakosu gaba ko abincinda zasuci ya gagaresu dole Usman ne yanaji Yana gani yake fita gwagwarmaya Amma sai ahankali. Wata bakwai da zuwan kawu gidan yari aka koresu daga gidan dasuke suka rasa gurin zuwa ga iyami Dan cikinsa take dauke dashi wahala tasaka ya bare ko kudin asibiti basuda. Akaro na farko da Usman yakoma sata kenan arayuwarsa ya kama musu daki buyi a wani gidan haya me dakuna goma reras a jere kamar shaguna, Gidanda ya hada mutane dabam dabam masu halaye dabam dabam. #mamuh# MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 4_* _Mamuhgee_ #ZAFAFA BIYAR#PAY@+234 903 234 5899 OR 09033181070 Tana fitowa dakin ta washe baki tareda daga kudin ta kallesu tana fitar fuskarta dasu tace" Hmmm amah zakiyi kudi ki mallaki uwayen wainnan kiyi rayuwa yanda kikeso ki juya Wanda kikeso hhhh. Kallon hashimu me tsaron qofar tayi tareda sakar Masa murmushin iko na nuna Masa itace agabansa tunda ita ke riqeda kudi, Sake juyasu tayi tareda zaro Yan naira dubu 'daya 'daya guda uku tabasa tana cewa'" Kana fadar Abinda yafaru yanxu to sunan aurenka matacce dan wlh sainaje nasa anhana. Damqar kudin yayi da sauri Yana turawa cikin aljihu tareda washe bakinsa har iyaka yace" Haba Hajiya amah kema kinsan hakan bazaitaba faruwaba, Ko bomb akamin belt dashi bazan fadaba. Dariya tasaki cikin girmama alamari da mutunci irin na kudi Wanda yasa hashimu fadar haka akan dubu uku kacal ma, Sake kallonsu tayi tana dagawa tace" Allah sarki kudi, Kudi muna sonku Bama gane kowane yare sai naku. Juyawa tayi tana cusasu cikin wandon jeans dinta dake cikin doguwar jallabiyarta tana cewa'" Hashimu bakinka qanin kafarka. Kallon tray din tea dinda takawo yayi yanason kallonsa amatsayin tsarkakken Abu Amma apatite dinsa yakasa dauka take yaji gurin gabaki daya yafita aransa ya kwashi wayoyinsa da wallet dinsa ya fito ya fice batareda ya kalli ko gefenda Hashimu ke Masa asauka lafiya ba. Tana saukowa ta sauya kayan aiki ta zari Jakarta ko sallama batayiwa manager ba sbd gabaki daya hankalinta yatafi a station sbd tasan usi nacan najiranta. Adaidaita ta tsayar ta fada tana cemasa' Central police station zaka kaini. Bayan ta zauna cikin napep din ta zaro kudin daga aljihun jeans dinta ta qirgasu dubu ashirin da bakwai ne kenan hadida dubu ukun data bawa hashimu dubu talatin kenan, Hmmm lallai wannan daga gani me kudine yau badan belin usi ba da kamawa kawu shago zatayi yafara Sanaa Koda ta awon su gero ne da gari. Daidai gate din central din aka ajiyeta ta sallami me adaidaita din ta kalli gate din station din tana Jan siririn tsaki cikin quluwa tace'" Tabbas da munada arziki da nafi qarfin zuwa gurin Nan Ina mace, Amma haka qaddara tazomin inaga stations din jahar Nan Babu Wanda bana zuwa sbd irin haka. Sauke numfashi ma qarfi tayi tareda Jan iska tana cewa'" Amah bakida Wanda yadamu da mutuncinki Dan haka ki daina kawo tunanin komai bayan na maida hankali ki Gina rayuwarki cikin jin Dadi batareda kinsa damuwar komai ko kowaba arai. Rataya qaramar Jakarta tayi tana nufar hanyar shiga tana karewa 'yan iskan kurtun police 'din dake binta da kallon qurulla saidai dayake sunfi kowa sanin waye ita yasa suka kama kansu sbd tsira da 'yan canjin dake aljihunansu sbd Suma a qone suke murus ba canji. Kamar daga sama insfector Garba ya ganta tashigo fuskarta a daure. Dan hadiye yawu yayi tareda shafa aljihunsa ya lalubo Yan kudadensa kusan dubu shida ya hadiye yawun qaqa nikayi sbd gskia yanason amah Amma Kuma duk lokacinda ya kusantota saita sanfesa tas har mamaki yakeyi yanda take zaresu bai saniba baikuma ganiba yanda kasan me aiki da aljanu haka take. Togewa tayi bakin kanta tana sake tsuke fuska ta kalli wainda suke incharge tace" Gurin USI nazo. 'Dayan dayake qule da ita tun wani zuwa datayi belin Dan uwanta ta samfe Masa dubu hudu yake haqe da ita Danma fitinanniyar Bata tabuwa sbd ogansu daya gama mutuwa kanta tana kassarasa Amma qaton banxan yakasa bude ido ya fahimci Babu Abinda amah keso arayuwarta idanba kudi da Dan uwanta usi ba sai kawu. Saida suka gama harare hararen juna kafin aka fiddo da Usi din aka Fara rubuce rubuce akace dubu gama sha biyar zata bayar. Bude jaka tayi taciro kudin batareda tace musu komaiba ta miqa musu tana yiwa kudin kallon bankwana cikin ranta tace'" Insfector Garba Kaine wlh zaka biya tunda kanaji kana gani suka kama usi akan sunyi fada da wani Dan masu kudi shine shi USI aka kamasa. Insfector Garba na ganin irin kallon datayi Masa ya fada office dinsa Yana zare dukkan kudadensa daga aljihunansa Yana turawa qarqashin lokar office dinsa Yana zazzare idanuwa sbd gskia yau bai shirya daukar asara ba. Kallon usi tayi zuciyarta na qunar ganin yanayinsa daga gani uban duka suka Mai suka cire haushinta Dan tasan kowannensu a qule yake da ita. Wata baqar €class0221 ce tashigo station din tayi parking atake duk suka ajiye Abinda sukeyi jikinsu na rawa suka miqe suna fadin' MD ZABEERA ya iso. insfector Garba ne yafito Yana cewa'" Sargent salisu kufito da yaron Nan Wanda MD ZABEERA yakira yayi mgn akai Wanda sukayi fada da USI. Yes sir" Da gudu suka fiddosa tsaf dashi ba alamar antabasa ko kayan jikinsa fes suke. Kallonsa tayi cikin mamaki jin shine abokin fadan usi atake taji haushinsu duk ya kamata ta kalli usi dayasha mugun duka tace'" Usi uban waye yayi maka wannan dukan? Ga abokin fadanka nan Babu alamar ko hararsa anyi bare duka., Wlh yau saina daukaka qara a kotu akan wannan abin...... Saurin katseta insfector Garba yayi sbd shigowar MD ZABEERA din Wanda qamshinsa yagama kame iskar gurin gabaki daya. Batareda tajuyoba tace" Bazanyi shiruba kodai abi Mana haqqinmu kokuma naje kotu wlh bazan yardaba... Murmushin yaqe insfector Garba yasaki Yana dan satar kallon gefen MD din yace" Kinga Dan uwanki shine baida gskia shiyasa Kuma Kinga...... Waro manyan idanuwanta tayi akansa cikeda mamaki tana cewa'" Ni kake fadawa usi ne baida gskia?? To wlh ma nafasa auren naka daga yau ko sunan anguwar mu kakira Garba Allah saina raba aurenka da matarka me kamada bokiti. Shiru dukkaninsu gurin sukayi musamman insfector Garba din sbd dai duk tagama bude Masa yawa agaban MD ZABEERA Wanda babban mutum da kowa ke matuqar respecting da matuqar karramawa sbd arzikinsa da mugun Jan girma da ajinsa bawai Kuma Dan shekarunsaba sbd duka duka shekarunsa bazasu fi talatin da buyar zuwa da shida ba aduniya, Yarone Wanda ake Kira da abokin manya sbd dukkanin abokanan hurdarsa manyane wainda wasu sun haifesa,wasu sunyi jika dashi wasuma sun kusa haihuwar tasa, A familyn daya fito su din wani babban family ne dasuke da girma da mutunci a idon duniya sbd kamannin kakaninsa da uwayensa Amma a yanzu kusan Rabin qarin girma da mutuntawar dasuke qara samu sbd shine shiyasa ko acikin familyn nasa wainda basa qaunarsa suka fi yawa. Kasancewarsa baida hayaniya da son shiga sabgoginda Basu shafi Abinda yake gabansaba yasa yake qara shiga ran abokanan harqallarsa Kuma hakan naqara Masa girma shiyasa koina yashiga ake matuqar mutuntasa musamman dayake yana mallakar wata irin tarin dukiyarda ta tsolewa mutane da yawa ido. Batareda yatsaya bi takan hayaniyarsuba ya kalli insfector Garba da idanuwansa dake cikeda da wani irin kwarjini Atake jiki na rawa insfector Garba yace" Ranka ya Dade Bismillah muje daga cikin office din" yaqarasa fada Yana basa hanyar shiga office din Su Sargent suka Mara masu baya tareda yaron dayazo belin. Wannan shine karo na farko arayuwarsa daya taba zuwa police station Dan haka bai tsaya Bata lokaciba ya kalli insfector Garba akaro na biyu cikin qosawa da zamansa cikin station din dayakejin kansa harya Fara juyawa ya bude baki cikin nutsuwarsa da kamewarsa datasasu Suma duk shiga nutsuwa yace" Meye procedures din???? Da sauri insfector Garba yace" Ba wani procedure sir just take him with u dama mun kamasane abisa rashin sani yanzu da safen Nan labari yazo Mana aishi din yaron amintaccen direbankane Wanda ka dauka kamar uba, Muma ai tamkar ubane agurinmu Ayi hakuri sir munsaka babban mutum kamarka zuwa Nan. Zuba Masa fararen idanuwansa masu sake rikitarda Insfector Garba yayi Yana nazartar yanda mutanen duniya suke, Wato Babu wata doka ko adalci shidai me kudi akoyaushe shine me gskia komai yayi daidai ne wat a life. Miqewa yayi tareda kallon mal aminu dayake kallon 'dansa cikin rauni da takaicin yau sune sukayi sanadin zuwan mutum me matuqar girma da mutunci kamar MAHMOUD DAHEER ZABEERA a irin nan, Shi mutum ne daya tsani mutanenda suka dauki kudi sune rayuwa Saigashi a hukuma ma kudin sune dai aka fifita. Ganin duk sun shige office din insfector Garba dayake shine DPO din Nan dama ana kiransane insfector sbd sunan yabisa tuntuni, Ta kalli usi da isonsa daya harya kusa liqewa sbd kumburin duka tace'" To da mutum ya mutu dai gwara yazama biri Dan haka da Babu gwara ba Dadi tunda sum ringa sun maka wannan dukan gurinsu zamu samu na siyan magani" ta qarasa fada tana zagayowa inda suka saka kudinda suka karba hannunta aikuwa cikin saa taga kudin aikin ranar gaba daya wani mugun murmushi tasaki tareda Kai hannu ta kwashe kudin gaba daya Wanda yayi daidai da fitowor MD zabeera cikin office din dpo Garba. #mamuh# Pay@ +234 903 234 5899 Or 09033181070 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 5_* _Mamuhgee_ ##Zafafa biyar#pay@ 09033181070 or 09032345899 Usi ne yafara ankarewa dashi yaga yanda qarara idanuwansa da fuskarsa suka nuna tsananin qyama da takaicin Abinda idanuwansa suka gane Masa Nan ya fahimci cewar yarigada ya ganta yayi saurin dauke idanuwansa dga kallonsa yayi sbd tsananin kwarjini da cika masa ido da yayi yai saurin yin qasa da murya Yana cewa'" Amah kiyi saurin barin Nan kokuma ki maida kudin. Batareda ta fahimci Abinda yafadaba ta kallesa tana cewa'' oya yi sauri mutafi nagama ramawa kura aniyarta anan, Insfector Garba Kuma zaizo yasameni a gida nasani acan zan fanshe wannan tozarcin dayamin agaban baqonsu da ko kallo bai isheniba bare na tsaya harsu gama kulasaba kafin su dawo kanmu. Gaba tayi tana zuge zip din Jakarta data saka kudin usi na biyeda ita Yana satar waiwayen baqon dake bayansu fuskarsa a hade ko inda suke bai kallaba ua nufi motarsa Yana duba agogonsa dake nuna Masa lokacin ganawarsa da mahaifinsu yayi gashi shi mutum ne dayake aiki da lokaci komai lokacinsa yake ware Masa sbd tsari dayayiwa rayuwarsa. Amah ko takan babbar motarsa batabi ba sbd gama quluwa datayi da Abinda Garba yayi Mata. Usman kuwa suna fitowa tafiya kadan sukayi yaja ya tsaya jikin wata bishiya Yana sauke ajiyar zuciya ya zauna Yana jingina kansa jikin icen ya sake sauke numfashi ya kalleta yana sakin 'yar dariya kamar Babu rauni da tsamin duka a jikinsa yace" Amah kina ganin akwai ranarda zamuyi rayuwa kamar sauran mutane masu daraja??? murmushi itama ta saki tana kallonsa cikin kulawa da rashin nuna damuwa kafin ta bude Jakarta ta shafo kudin dake ciki tana kallonsu tace" Bama buqatar wani rayuwa ko gatan daya wuce muyi rayuwarmu ayanda take, Karka saka wani Rai a wani rayuwan bayan kasan mu din asalin 'yayan bola ne, Bamuda wani rayuwa bayan Wanda muke ciki a yanxu. dariya Usi yayi hadi da miqewa tsaye yafara tafiya yana Dan dingyashi saboda raunin da akai masa a kafa sosai yake masa zugi cikin sake quluwa Amah tabi shi da idanuwa tana tunano irin kalar rashin arzikinda zatayiwa Garba. Tafiya sukeyi suna firarsu cikin nishadi sbd su Sam Babu Abinda suke ajiyewa arai ya damesu. Suna shiga gidan da Aunty Salamatu suka fara cin karo aikuwa ta soma sakin numfarfashin masifa dan Sam bata manta dibar albarkan da Aman tayi Mata ba kafin fitarta, Amah na ganin hakan ta fuske ko kallonta batayi ba ma tai wucewarta zuwa dakinsu jakarta ta ajiye hadi da cire karamin hijab dinta ta fito ta nufi qofar dakinsu kawu ta tararda Usi zaune tare da Kawu wanda ke tambayar Usin" wane shegen kurtun Dan sandan ne yayi maka wannan ta'asar??? Qwafa yayi Yana taba qafarsa dake Masa zogi yace" Ai kawu idona idon Sargent salisu saina saka anyi Masa zanen yarbawa har a goshi da qeya, Shikuma insfector Garba duk Yakuma zuwa gidan Nan gurin amah saina Masa askin kwalba. Cikin takaici kawu yace" Shi garban me kama da an sulala naman Kai shine yasa aka maka wannan dukan? Kokuwa shi Sargent salisu din dayafi kama da danyar alala yayi gaban kansa yayima wannan dukan kamar wanda yayi kisa¿ Maman basiru dake kusa dasu tana aikin wanke rishonta ta tabe baki tana cewa'" To meya raba dambe da fada¿ Tsuke fuska kawu yayi Yana kallon iyami dake fitowa daki daukeda robar garin tuwo dazata gyara yace" Iyami kinajin matar nan nafadamin mgn bazakiyi Mata dukanda mijinta ba mijintaba ko yayanta bazasu ganetaba, Waini iyami kodai auren dole ne mukayi?da kike wulaqantani ne kokuwa talauci haukane? Dariya usi yasaki Yana cewa'" Wlh kawu talauci haukane tunda gashinan duk bamuda hankali.... Butarda dake gefenda ya dauka a hasale Usin na ganin hakan ya tashi da sauri Kawun ya jefasa Masa Bata tsaya koina ba butar sai kan galan din kalanxir din maman basiru Wanda zata zubawa rishon take ya kwanta tana tsiyayewa dama kawun can yayi niyar jefawar ya tsuke fuska yahau masifar usi ya rainasa. Usu kuwa dariya yake Yana kallon maman basiru dake kallon kalanxir dinta cikin tuquqin zuciya Tama rasa Abinda zata ce musamman ganin fuskar kawun tasan yanxu tana mgn zai Kira mijinta yace suje police ayi musu iyaka Dan aikinsa kenan cewa aje police ayi Masa iyaka da mutum. Allah ya isana tace cikin ranta tana cewa bakinta yaja Mata saka baki cikin maganar Wanda Basu barin kowa da Allah. Amah dake kawowa ta kalli maman basiru da idanuwanta sukai rau kamar ta saki ihu sbd takaici ta saki dariya tana cewa' Iyami wlh karki Bari usi ya rainaki kaman yanda ya Rena kawu. Kallon Usin iyami tayi tace'" Kaje ka kimtsa idan kungama Abinda kukeyi kaida kawun, Wlh usman ka daina biyewa wata fitinar..... Iyami ki fito fili kice ni basai kin tsaya layi ba. Nidai yanxu bance kaiba.. Iyami Anya kinason shiga aljanna kuwa? Amah na ganin haka tasan fadan zasu Fara tayi saurin fiddo da kudin Jakarta take kalmar dake bakin kawu ta katse Yana qoqarin hadata. Iyami ma aje robar hannunta tayi tana matsowa Kawu ya bita da harara da qananun idanuwansa masu kama Dana 'yan Korea yace" Ke amatu maida kudin Nan jaka sai anjima zansan me zaayi dasu tashi tafi daki dasu ki aje. Kawu albashina ne na karba gurin aiki da niyar belin usi saigashi Basu karba ba sbd rawar jikin sunga wani baqonsu. Nasani ai dama kedai tashi dasu daga Nan kafin wani ya wafce su. Fizge jakar iyami tayi tareda cire kudin tana cewa'" Wlh Babu dakinda zata kaisu Dan nasan ba albashinta bane, Amatu kifadamin gskia inda Kika samo kudin Nan?? Kallon kawu tayi daya qura Mata ido Yana jiran jin Abinda zata fada saidai yanda tayi da fuska yasa ya fahimci inda kudin suka fito ya gyara zama tareda murzawa idonsa toka ya matse fuska yace" Iyami so nawa nake fada Miki kidainawa yarinyar Nan haka? Addua akeyi Allah ya shiryamanasu yabasu abinyi, Kinga banason kina irin haka saiki tozarta gaban maqiya ga gida cikeda da maqiya komai muke ciki kunnuwan munafukai akanmu. Kallon takaici tamasa tareda tura kudin cikin zaninta tana cewa'" Allah yasa kugane yakuma shiryaku ku duka. Ganin maman junior shugaban munafukan gidan ta shigo yasa ya hadiye maganar dayayi niyyar yi tareda cewa amatu "jeki. Tana juyowa Ido biyu tayi da maman Junior wacce da alama daga kasuwa take ko dan jakar dake jikinta da uban mayafin data yafo daya gama miqewa da zufa ta dauke Kai ta wuce tana tsokanar junior dake gefen maman daukeda leda dayake yaron mutumintane suna dasawa sosai Ko kallon maman taqiyi sbd ganin irin kallon masifar datake binta dashi tareda harara. *** Bakin Babban gate din ZABEERA motarsa ta tsaya batareda yayi horn masu gadin suka bude Masa da sauri tsananin girmansa dasuke gani fiyeda kowa a gidan idan aka cire iyayen familyn. Da kansa ya tuqo motar sbd yabar malam take gida da yaronsa suyi sorting matsalar data kaisa hannun 'yansanda harya kwana station. Sake kallon agogonsa yayi bayan ya kashe motar kafin yafito a nitse ya rufe motar ya nufi doguwar hanyar dazata sadashi da sashen Modibbo wato mahaifinsu. Tafiyar mintuna hudu ce takaisa shashen Yana tura babbar qofar palon ummi na fitowa babbar 'yar gaban goshinta nuratu na gefenta kowannensu fuskarsa Babu alamar farin ciki Wanda daga gani ummin ce ke cikin baqin cikin nuratu ke tayata damuwa. Dattijuwace saidai hutu da tsananin jin Dadi da ilimi tareda gayu yasa shekarun nata sun dai 6oye sbd jikinta dayakeda kyau sosai. Kallon daya zakayi Mata kasan itace matar gaban goshin me mallakar gidan sbd tsananin Isa da ikon datake nunawa. Cak ta tsaya bayan ganinsa zuciyarta na qara tafasa da takaici saidai tayi controlling fitowar fushin nata ta kallesa da fararen idanuwanta Batareda ya kalli fuskartaba Yana kallon qofa cikin nutsuwar muryarsa data sanya nuratu Dan matsawa gefe tana kama kanta sbd tsananin kwarjininsa yace" Umme barka da yamma, Kina lafiya?? Kamalalliyar fuskarsa dake daukeda wani sirrin kyau ta kalla tana danne bacon ranta tace" KHALIL baya daukan maganata ka fahimtar dashi inason yayi aurene sbd lafiyarsa sbd mganarka kawai zai saurara sbd Kaine ubansa. Tana fadar hakan ta wuce Bata tsaya jiran Abinda zaice ba sbd tasan ba maganar zaiyiba ko zasu shekara ahaka tasan dai yaji Kuma ya fahimta. Wannan shine daya daga cikin Abinda ta tsana gamedashi shine tsabar miskilancinsa datake kallo amatsayin ji da Kai ganin yafi dukkanin 'yayan ZABEERA zama successful business tycoon Wanda yake muamala da manyan gwamnati da sarakuna. Kai tsaye yashiga cikin palon na Modibbo bakinsa na fitarda sallamarda modibbon ne kawai yaji ya amsa sbd sanin yanda mgn ke fitowa abakin 'dan nasa. Gaban Modibbo din ya zauna tareda dagowa cikin girmamawa yace" Barka da yamma modibbo, Ka yini lfy? Alhmdlh MAHMOUD Ya iyalin naka?? Alhmdlh"kawai yace tareda kallon 'dan uwansa dake gefensa zaune ya sakar Masa wani qayataccen murmushi Wanda duniya dashi kadaine zakaji yayi doguwar magana ta fira a kaf family haryayimasa murmushi Wanda ko mahaifinsu iyakacinsa dasu bin umarni da biyayya Amma Khalil ne kadai Wanda ke ganin sakewar Mahmud din ciki kuwa harda matarsa wadda iyakacinsa da ita zaman biyayyar aure da bin umarni tareda mutunta juna. Cikin murmushi Khalil ya kallesa Yana cewa'" Allah ya taimaki ZABEERA na hudu. Batareda ya kallesa ba ya murmusa har fararen haqoransa suka bayyana sbd wannan wata zolayace da Khalil din yake Masa tun suna Yara sbd ya tsokanesa musamman yanxu dayasan karban wata sarauta shine Abu na qarshe dazaiyi arayuwarsa sbd ya tsaneta indai akansa ce. Gyaran murya Modibbo yayi tareda kallonsu suka nutsu tareda maida hankalinsu akansa yasake gyara murya cikin bada umarni da hukuntarwa yace" Mahmud safiyar yau ZABEERA ya aiko da saqon a sanar dakai waadin mallakar kujerarka ta ZABEERA na hudu Dana bayarda sunanka yacika Zaka shirya komawa masarauta tareda iyalinka. A matsayin mummanan sako ya dauki zancen sbd zuciyarsa da Bata karbi abinba ko da a mafarki saidai Kuma Sam fuskarsa Bata nuna alamar gamsuwa ki rashinta Khalil kawai ne zai qarar da cewa wannan ba Abu bane me yiyuwa a rayuwar md zabeera din. Cikin girmamawa yace" Modibbo idan naje Naga ZABEERA akan wannan alamarin Ina fatan bazan 6ata maka ba??? Kallonsa Modibbo yayi na tsawon sakanni kafin yace" Idan har kana tunanin sanarda mahaifina ne cewa baka karba saqonsa ba tabbas zaka Sa6a ne. Cikin sake nuna biyayyarsa yace" Inshallah ba hakan bane. Karka damu zakaje Amma sai ranar tafiyarka gaba daya. Shiru yayi na Dan lokaci kafin ya miqe tareda cewa'" A yini lfy Modibbo. Ficewa yayi Khalil na biye dashi suna fitowa ganin yanayinsa yasa Khalil barinsa yaje yasamu nutsuwa tukuna duk da Babu Abinda ya nuna na damuwa ataredashi. Motarsa yaja ya qarasa sashen dayake can kusan qarshen babban gidan Wanda yake nasa yanayin parking yafito yashige. ZARAH dake zaune palon tareda me aikinta ta dago Kai tana ganinsa ta ajiye wuqar datake yanka gwaiba da ita ta miqe tareda qarasowa gabansa tana Masa sannu da zuwa cikin nutsuwa daidai shigewarsa hanyar dazata sadashi da zuwa sama inda dakinda yake ya amsa Mata da madaidaicin sauti sbd Bata iya wulaqanta ta sbd darajar sure dakuma biyayyarta tareda darajar Modibbo daya aura Masa ita. Ganin yanda ta taso din Dan kulawa yasa yadan tsaya tareda kallonta cikin Ido sosai Yana qoqarin Bata mahimmanci yace" Ina buqatan light abinci Mara nauyi. Murmushin qara ganin girmansa tasaki sbd yanda akoyaushe yake mutunta zamanta matarsa har kaqoranta suka bayyana ta matsosa sosai tareda kama hannun damansa ahankali ta riqe cikin nata ta dago ta kalli fuskarsa da ya juyo ya kalleta tace'" Thank you MD ZABEERA. Kallonta yayi yace" Ina jira""ya haye saman tana binsa da kallon kauna fuskarta cikeda murmushi kafin tajuya ta nufi hanyar kicin tana cewa'" Hafsat zo ki niqamun kayan Miya a blender. ** Umme tunda Takoma palonta ta zauna tana sauke numfashi tanason saukar da zuciyarta ga wannan al'amarinda yake faruwa da ita ako yaushe., 'yayanta kusan sune koma baya a cikin familyn ZABEERA, Dukkanin 'yayan Modibbo matane su goma sha shida Khalil da Mahmud ne kawai maza Kuma sune dukkanin wani burin Modibbo ya Dora akansu sai gashi ita nata 'dan shine wani iri Sam ko kyashin 'dan uwansa bayayi duk da Shima Barr ne babba me zaman kansa Kuma yanada nasa arzikin daya Tara bana mahaifinsu ba Amma Sam bai kamo MAHMOUD ba Wanda duniya shi kowa yafi sani a familyn ZABEERA yanzu. Burinta idan har MAHMOUD yafi Khalil ta wani bangaren to shi zai karbi zabeera na hudu ta yanda zai take MAHMOUD din ta fagen suna,arziki,mulki,dakuma martaba a idanun mutane saigashi Rana tsaka su Modibbo da zabeera sun zaba MAHMOUD Wanda Sam bazata yardaba. Kamar daga sama taji daga bayanta ance" Aisha wannan karon damar kice ta qarshe kisa Khalil yayi aure ko su Modibbo zasu sauya shawara su zabesa sbd shi wancan miskilin baya buqatar kujerar zabeera, Duk wani suna ko arziki ko girmanda ake buqata ya samu abinsa da kansa amatsayinsa na Architecture MD ZABEERA so yanzu zabi ya rage naki na kisan yanda zakiyi. MD bayada uwa a duniya bayada dangin uwa a duniya to kina tunanin idan yazamo zabeera na hudu waye zai nuna Miki iyakarki idanba zainab uwar matarsa ba wadda ko kadan kinsan Bata qaunarki. Rintse ido ummen tayi tana jinjina 'dacin da zuciyarta keyi da zafi tace'" Babu Abinda yakai ciwon hassada zafi a zuciya wlh Maryam, Tun kafin MAHMOUD yazo duniya bandamu da uwarsa ba harta haifesa ga bar duniya bantaba kulawa dashiba duk da tsananin biyayyar dayakemin Amma tunda yafara zama wani abu a rayuwa Abu yazo ya dameni wannan masifa dame tayi Kama wlh zuciyata takasa samun nutsuwa shawon shekarun cigabansa Amma wannan karon zanyi Abinda bantaba yiba. Dawowa gabanta haj Maryam tayi tareda zama kusada kejerar dake kallonta tace'" Me kenan??? Miqewa tayi tsaye tana takawa ahankali tace'" A duniya Babu Abinda Modibbo da zabeera suka tsana irin cin Amana da zubarda mutunci, Zansa su tsanesa tsana mafi Muni wadda zatasa sunansa yafita daga cikin zabeera bama zabeera kawaiba duk duniya ma saisunji yafita ransu sundaina ganin mutuncinsa. Murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana cewa'" Wane laifi? Wane cin Amana Kuma??? Laifin ciki Da laifin zubarda mutunci ta hanyar aikata 6anna. Wani murmushin haj Maryam tasaki tana cewa'" To waye yayiwa cikin ni ki fahimtar Dani yanda zangane. Baiyiwa kowa cikiba Amma kudi zasusa ace yayi cikin. Aisha kina tunanin akwai Wanda kudi zasusa tace MD yamata ciki karki manta MD mutuminda kowa ke mutuntawane wannan maganar bamai karbuwa bace mu canza shawara. Maryam kudi duk inda kike tunanin su sun wuce Nan, Akwai mutane birjik a duniyar Nan dazasuyi aikin komai sbd kudi musamman kudi irin wainda zan zubar akan wannan aikin. ##Mamuh## #ZAFAFABIYAR## 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 7_* _mamuhgee_ Kai tsaye change room dinsu ta nufa ta sauya kayanta zuwa na aiki ta fito tana gyara zaman qaramin Rolling dinta a wuya tana Dan yamutsa fuska tace, Ni wannan aikinma harya Fara isata sbd wannan kayan aikin kullum mutum atakure bazan iyaba aje aikin zanyi na huta kafin daga baya zanda usi yasamomin wani yanzu dai kafin na ajiye zansamu kudinda zasu riqemu kafin asamo wani. Tana isa reception dinsu manager dinsu na isowa Shigowarsa kenan Yana waya yayi Mata hannu cewar ta tsaya yagama wayar Wani harara tabisa dashi tana dauke Kai sbd manager dinnan nasu tafara gano take takensa akanta bazai shiga hankalinsaba sai ranar data sanfe duk wani arzikin dake aljihonsa, 'daga Masa qafa takeyi sbd kudaden datake sanfewa na restaurant Dan kullum saita diba son ranta take tafiya gida Bari tayi yaringa ji da 'daya Amma yakasa Kama kansa, Kullum sai ayi rikici gun lissafin yanda kudi ke ba'ta Amma ankasa ganewa har so biyu ana sauya cashiers din aje kudin Amma 'yanda kasan 6era ne me satar ko clue bata bari bare amayi zargin mutum ne me satar. Kallon qeyar kansa tayi tana sakin murmushin qeta tace" Manager tashi aiki zakayi kwanan Nan... Maganarsa ta kwasheta ta 'dago tana kallonsa tana 6oye murmushin gayyar datakeyi tace" Barka da zuwa manager, Kazo lafiya? Washe haqora yayi Yana gyara zaman medical glass dinsa cikin son nuna shi wani ne yace" Yawwa lfy klau amah Dama sbd matsalolin damuke fuskanta na 6acewar kudi a bangaren restaurant namu yasa na yanke shawarar maidaki gefen saloon sbd zamu dauki mummanan mataki akan maakatan restaurant din banason asaki acikin Abinda baima shafekiba, Dukkaninsu maganinsu zamuyi saisun fitar Mana da 6arawon cikinsu. Kallon Wawa taqare Masa kafin tayi fuskar marayu taredayin qasa da Kai cikin nuna maraicinta tace" Nagode da hakan Dan ni ko yanda alamarin kudi dake gudana agurin banma saniba, Banmasan meke faruwa a gunba da azo adauki alhakina abatamin suna kawuna ransa ya baci ciwonsama na hawan jini zai iya tashi idan yaji hadda ni acikin wainda zaa tuhuma da sata Kai Allah dai ya tsareni ya rabamu kalmar sunan satama batada Dadi. Sake washe baki yayi ganin kamar yayi Abinda ya burgeta taji Dadi ya sake gyara tsayuwa Yana katse Kiran dake shigowa wayarsa yace" Ai dama shiyasa naga yakamata a sauyaki saga gun sbd kada sunanki ya baci gashima Kinga Ashe kawunmu zai iya samun damuwa. Tana qaqalo murmushi tace' Eh dama gashi Muna fama dashi yau ciwo gobe lafiya ko tashi zaune baya iyayi" yaqarasa fada tana soke kanta kasa. Subhanallah Ashe dai alamarin sosai ne to Allah ya sawwaqa inshallah yau ko gobe idan nabar office zanje nadubasa. Zakasan me ake nufi da asalin sunan sata idan kaje duba kawo ka laluba kaji usi ya sanfeka tass""tafada qasa qasa tana Masa kallon sakarai.... Me kikace???? Eh cewa nayi akaini inda aka sauyamin din manager. Yawwa muje'' yafada yanayin gaba tana binsa abaya tana sake 6ata fuska sbd Sam ita Bata wani son wani canje canje ita dake Shirin barin aikin ake Mata wani yaje Jaye Amma dai bangaren saloon din idan taga yamata zata zata Dan jima Amma yanzu babbar damuwar shine kafin ta 'dan gama gane Nan bangaren harta Fara samun damar sanfesu za'a dauki lokaci qila gashi komai nasu yayi qasa na abinci iyami kasuwancinta na Saida garin 'dan wake baya tafiya da albashinta suka dogara yanzu sai Abinda tasamo ko usi yasamo..... Katsewa tunaninta yayi daidai lokacinda suka iso bakin qofar saloon din dake cikin blue fox din sbd wasu manyan hamshaqan Mata data hango ta cikin glass, Sake 'daga wuyanta tayi tana 'dan leqawa tasake hango wasu 'yan Mata daga dayan gefen take tasaki ranta tana cewa" Yauma ranar sa'atace kenan Nakusa zamowa shiyasa Allah yasa aka daukeni daga Inda mutane basa ajiye jakarsu Amma anan dole mutum ya ajiye jakarsa tunda aiki zaa Masa, Numfashi ta aje tana cewa" Inshallah usi nakusa samun kudin karatunka Dan Banda buri yanzu dayafi kayi karatu sbd Kaine namiji qarfinmu zaifi qarewa akan naka kawuma ga manyanci na rufarmasa. Tana cikin tunanin taji muryar manager na cewa" Shikenan amah kuje ga shugabarku Nan zata baki Abinda zaki ringa yi Sai akula please amah. Gyada Masa Kai kawai tayi sbd tuni hankalinta yayi ciki a matse takeda tashiga ai madam bell na cewa tazo sushiga tayi gaba Tana tura qofar glass din wani sanyin qamsh ya dameta ta lumshe ido tana qurewa gurin kallo daga sama taji madam bell na cewa" Oya amah kije gurin anny gatacan tana sawa wata Rolex ki riqe Mata tana sawa idan kungama saikizo kiyi kallon yanda zan gyarawa waincan baqin namu qafafu. To tace tana ajiye Jakarta a inda aka nuna Mata cikin haushi ta nufi anny din ta karbi robar Rolex din a karkace ta riqe tareda dauke Kai sbd yanda daga zuwanta ko Dan mutuntawar Nan Babu adai nuna maka Kai ba kowa bane face 'dan aiki. Yini tayi aiki ranar sbd kowane aiki madam bell sata takeyi ayi da ita sbd ta iya gabaki daya Bata zaunaba tundatashiga gashi aranar taga asalin ire iren Mata masu kudi wainda suke cikin kudi, Matane sai masu arziki da wainda suka fito gidan arzikin sune kawai ke shige da fice agurin wasu na fita wasu na shiga shiyasa gabaki daya taji yanxu zatayi kudi wato ma a restaurant bataga komaiba sbd can iyajacinsu Kai abinci su dawo. Sai yamma sosai Takoma gida a matuqar gajiye dan haka tana dawowa ta tarar ana fada hadda dambe da anty salamatu da maman basiru gasu maman junior a gefe anata qara zugawa kawu dai na zaune a shimfidarsa yaqi ko kallonsu bare ya matsa jira yake wani shegen ya fado Masa ya dauko musu motar yansanda ayi me kankat. Kota kansu batabi ba ta wucewarta daki tana cewa'" Allah yasa ayiwa maman basiru dukan sakwara muga qarshen qaryarta. Washe gari ma da wuri sukaje aikin bayan ta biya cafe din kusada layinsu tabada cikon kudin scratch card din usi dazai zana waec Wanda shi baima sani ba. Koda ta Isa gun aikin yauma Babu sauqi aiki tayi sosai ha lokacin tashi, Kwanaki kadan tayi a saloon din ta iya aikinsu ba laifi Dan dama daurewa takeyi tana aiki sbd samun sanin Yaya kan gurin yake kafin tafaracin ubansu da halinta musamman madam bell databi ta addebeta da aiki sai janta ajiki takeyi tana yabonta ita kuwa sai sake musu kwantan 6auna takeyi Amma dai abokan aikinta sunfara sanin halinta sbd ba sauqi a tsakaninsu qaniyarsu takeci har mamakinta sukeyi yanda madam ke yabonta sbd batasan waye amah din ba. Yau hakanan ta tashi da annashuwarta shiyasa batayi lattiba kamar yanda tasaba ta Isa blue fox din tana zuwa ta sauya cikin kayan aikinta suka hau aiki, Customers biyu yau ta tsamewa kudi a jaka Kuma dukkansu Babu Wanda ya lura bare yagane harsuka tafi ta qirge kudinta tsaf kusan dubu goma sha biyu ta maida jaka tana cewa' Saura dubu talatin da daya su cika kudin jarabawar usi ya Allah kabani ikon hadasu kan lokac...... Bata qarasaba wasu manyan hamshaqan Mata guda biyu suka shigo gurin tareda wata kyakkyawar budurwa tana biye dasu, Kallo 'daya tayi musu tasaki baki tana cewa' Masha Allah da ganin wainnan hajiyoyin da hutu ya bayyana ataredasu. Cikin gaggawa madam bell ta rude jiki na rawa take musu sannu da zuwa kamar zata kwanta su zauna akanta tsabar rawar jikin tarbonsu. Cikin girmamawa aka wuce can qurya dasu spa room dinsu madam bell nacewa" Welcome ma, Welcome ma I've arranged komai da Kika bugo zakuzo kuyi in no time za'a kammala. Suna shiga suka zauna tareda ajiye manyan jakunkunansu Haj Maryam dake waya har lokacin ta ajiye Tata akan kujerar bakin qofar shigowa tareda tsayawa jikin window tana sake bude muryarta gurin yiwa 'danta Salman fadan karya dawo yanxu sbd wani banzan nadin sarautar MAHMOUD dinda basuma wani San juna ba sbd ita din qanwace ga Modibbo ta Dade a gida sakamakon mijinta daya rasu shekaru goma kenan yabarta da manyan 'yaya biyu rak da nuratu da Salman din. Umme kawai aka farayiwa gyaran sbd sanin idan haj Maryam tafara waya saita share awanni tanayi itakuma nuratu dama gyaran Kai ne zaayi Mata so tanacan guri daban. Cikin nutsuwa anny keyiwa umme gyaran itakuma tana dudduba wayarta ahaka harsuka gama qafa daya Amah dake tsaye tana jiran haj Maryam tagama ita zatayiwa taja boyayyan tsoki yafi so ashirin harta gaji da tsayuwar ta Dan zauna gefe kan kujerar aikinsu kamar ance ta kalla saikuwa idanuwanta suka sauka kan jakar dake Kai wasu sabbin bunch na dubu dubu na leqota batasan sanda ta saki siriyar dariyar farin cikiba a boye tana sauke numfashin farin ciki tace" Sa'a sa'a wlh saina fanshe zaman jirana danayi akan jakarki. Fakaitan haj Maryam din tayi taga har lokacin waya takeyi tabada baya ta dawo da kallonta kan umme datayi nisa a taba wayarta ta 'dan matsa tana zirara hannunta ahankali sai akan kudin ta janyosu batareda tsoroba ta cusa cikin robar hannunta ta kayan aiki saita miqe tareda ficewa. Wani tsalle ta daka tareda kallon kudin tana washe baki tace' Hummm. Cikin Jakarta tasaka kudin tareda kaiwa ta boye cikin kayanta kafin tadawo sparoom din tana wani basarwa annashuwa na fita a fuskarta Takoma tana zaman jiranta tana cewa'" Ko darema kikai kina waya zanjiraki Dan nagama cire kudin zaman jirana. Anny nagama yiwa umme ta miqe ta ficewarta. Sai bayan fitar anny tagama wayar tazo ta zauna amah din tafara yimata har aka gama tas ta ficewarta. Tsabar zumudin kudin kasa Bari tayi atashi taje gurin madam nema alfarmar tafiya gida da wuri sbd uxuri ana Bata dama ko kayanta Bata sauyaba ta tattaro su ta fito zuwa gida tana tafe tana lissafi cikin ranta fal farin ciki. Wayarta ta fiddo tareda lalubo numbern usi taji switch off taja tsaki tana cewa'" Dama nasani tun ahekaranjiya na lura ka Saida wayarka sbd kudin daka bawa iyatu na garinta da jarin ya karye Karka damu kaida kawu duk saimun siya waya yau yaqarasa fada tana sakin murmushi itakadai a hanya. Ganin napep yaqi samuwa yasa tadan Fara takawa tana tafiya a gefen hanya Tayi nisa sosai wata qatuwar baqar mota Tasha gabanta tayi saurin matsawa tana qoqarin zubawa ko waye zagi. Parking motar tayi aikuwa itama cikin tsananin masifa ta matso taga uban waye yake neman kassarata adaidai gabar datake ganin tayi kudi. Cak ta tsaya lokacinda Glass din motar ya zuge tayi Ido hudu da matarda tabaro blue fox dinsu. 'dan hadiye fushinta tayi tareda 'dauke Kai zata tafiyarta tana damqe jakar kudinta. Kudin dakika dauka nabiyoki karba ko"""""kamar daga sama taji saikar zancen ta tsaya cak tareda rintse ido tana damqe Jakarta tace'"aiko wlh banyarda Naga samu Naga Rashi bazan bayarda kudin nanba kome zaayi. 'dan qaqalo sakin fuska tayi tareda juyowa tace'" Hajiya Dani kike??? Murmushin takaici umme tayi tareda cewa shigo muyi mgn idan bakyason Tarawa kanki abin kunya anan gurin. Murmushi tayi tareda Dan matsowa jikin motar tayi qasa da murya tace" Haj aini bana gudun abin kunya sbd acikinsa nake Banda kowa Dan haka Babu Wanda zanjawa abin kunyar yi mganarki hajiya. Kallonta umme tayi cikin tsananin qyama da mamakinta amatsayin mace ta yamutsa fuska tace" Kudin dakika dauka nakeson kidawo dasu kokuma na miqaki hannun Yan sanda su rufeki har sai anmanta da sunanki. Dariya amatu tasaki tareda dafe bakinta tace' Haj canza dai Amma amatu Bata tsoron 'yansanda ataqaice Babu station dinda basusan niba. Qarara mamakin umme ya fito tana sake kallon amatu din qyamarta na sake shigarta Dan tuni taji yarinyar ta sake fita ranta Sam Bata ko qaunar magana da ita Amma tun yanda ta lura tana kallon jakar haj Maryam cikin kwadaituwa da yanda ta dauki kudin cikin tsananin kwadaituwa dasu da yanda take kallon kudin ta fahimci soyayyarta da kudi ba 'yar kadan bace shiyasa taqi tonata Kuma ta mayarwa da haj Maryam kudin ta biyota sbd ganin qila itadin zata iya aikinsu. #mamuh# _____________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 6_* Wani 'dan murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye bayan ta ajiye qaramin pillow din kujera data dauka ta Dora a cinyarta bayan zamanta,ta tsaya gaban umme din ta kelleta tanason Bata qarfin gwiwa da Abinda take Shirin yi tace' Aisha Idan har wannan mafitar kike tunani zata bullar damu ga Abinda mukeso to haqiqa Ina taredake ako wane mataki dazamubi Wanda zai kaimu ga nasa, Saidai Abu daya anan shine abin dubawar,shi Mahmud din tayaya zai zauna yana kallo ya karbi wannan false accusations din Wanda zaiyi tarnishing image dinsa a idon duniya. Kallon haj Maryam umme tayi tareda sakin murmushin farko a ranar ta yau tace'" Mune zamuji Masa ciwo Kuma mune zamu zuba Masa gishiri a ciwon Kuma mune zamu hanasa sosawa, Abinda kenan wato shine Kinga Maryam narigada nasan weakness din MAHMOUD wato duk duniya rauninsa biyu ne wato mahaifinsa da Khalil, As long as Modibbo zai zuciya akan wannan alamarin to tabbas MAHMOUD yagama yawo sbd duk wani cigabansa rushewa zaiyi. To wani hanzari ba gudu ba ta Ina zamu Fara wannan Shirin? Ma'ana ta Ina zamu Fara neman me wannan aikin? musamman fa Kinga aikine me tsananin hadari sbd 6atawa mutum kamar MAHMOUD suna a duniyarnan babban risk ne ataqaice ma kamar mutuwace kake kirawa rayuwarka sbd kamar yanda yake dinnan a natse zuciyarsa a bushe take, Duk Wanda zaiyi Mana wannan aikin dole Muna buqatar Wanda zuciyarsa tagama mutuwa akan kudi. Karuwa,,,,,, Mene??? umme tafada da 'dan sauri tana kallon haj Maryam din sbd qyamar ma sunanda tafada. Yes karuwa nace sbd karuwace kawai zata iyayin komai akan kudi, Ita kadaice zata iya wasa da mutuwa akan kudin sbd sunanta matacciya daga lokacinda wannan alamarin ya lalace. Dafe goshi umme tayi tana cewa'" Maryam daina fadar sunan karuwa acikin zabeera sbd fadar sunanta kawai babban laifine a cikin ahalin Nan, Kawo karuwa acikin zabeera shine laifi mafi Muni dazamuyi Wanda yafi Abinda muke Shirin aikatawa. Aisha Idan har zamu iya qetare duk wata iyaka mu aikata irin wannan abin to inaga kawo karuwa ba komai bane, Wannan zancen ma bai kamataba munayinsa acikin zabeera ki shirya gobe muje gyaran qafa zamu tattauna acan kafin Nan kin yanke shawara. Ficewa tayi tana ayyanawa aranta dole Khalil yazama zabeera na hudu sbd 'yarta nuratu da ita su samu kyakkyawar gaba me kyau. Umme kuwa kasa zama tayi palon ta wuce dakinta tana dafe kanta dake sarawa sbd damuwar data sawa kanta ga mafita na neman gagararta Duk abinta bazata iya kawo karuwa ba a zabeera sbd sanin tsananin alada da Matsin dokoki irin nasu Wanda sune asalin zabeera da Abinda yasa suka fita dabam acikin mutane, Familyn ZABEERA family ne dasukeda wani irin tsatsauran raayi da dokoki Wanda suka zame musu tamkar addini, Basa auren bare,basa zama da bare,basa barin 'yayansu Mata suyi karatun jamiaa a qasar Nigeria saidai qasashen qetare na laraba sbd karsu barsu anan kowa yagama sanin 'yayansu wainda suke tamkar suna musu kulle ne sbd ko muamala basa barin yayansu suyi da mutane sosai, Asalinsu Hausa Fulani ne saidai yanayinsu yasa ake musu kallon Fulani sbd yawancinsu farare ne masu 'yar doguwar fuska kalar Fulani, Sarauta tasa dokokinsu da tsaurin raayinsu yin yawa saidai Kuma babban Abinda yasa suke buka mulki da iko shine Babu wani Dan ahalin daya taba karya doka ko qetareta, Suna tsananin tsoro da bin umarnin manyansu musamman ZABEERA na daya acikin 'dakinsu asalin dahir zabeeran farko MUHAMMAD USMAN ZABEERA wanda suke Kira da ANDI, Andi shine mahaifinsu Modibbo mahaifinsu MAHMOUD Wanda yake amatsayin zabeera na biyu Wanda yayi shekaru akai kafin yayi murabus ya sauka yabaro asalin zabeera dake cikin babban birninsu ya barwa qaninsa mulkin Wanda shine amatsayin zabeera na yanxu Kuma shine zabeera na uku Wanda ayanzu ne zaayi na hudu. Andi shine shugaba mafi tsanani da duk zabeera ake tsoro ake Kuma gudun bacin ransa dagashi dai Modibbo daya kusan zartashi fiyeda komaima na tsananin zafi da dokoki, Babu wani abu magi qyama agurinsu irin cin Amana da Abinda zai taba martabar ahalin, Duk babban attajiri tareda manyan Yan siyasa abokanan hurdar familyn ZABEERA ne shiyasa ake matuqar giramamasu da mutuntasu, Kaf familyn Babu wani sakewa atsakanin iyaye da 'yaya sai bin doka da oda sbd Sam basa Wasa ko sakewa 'yayansu shiyasa 'yayansu ke tsananin shakkar manyansu Dan kaf familyn Babu wani 'da dazaice yataba ganin dariyar manyansu iyaye maza saidai iyayensu Mata, Modibbo keda Mata uku kowacce tanada Yara hudu Mata Banda mahaifiyar MAHMOUD wadda keda shi shikadai ta Haifa ta rasu tun yanada shekaru bakwai a duniya sai umme datake da Khalil bayan 'yaya Mata hudu, Umme itace tafi kowacce mace zuba iko da Isa agurin Modibbo sbd zamanta uwargida itace Kuma uwar manyan 'yayansa da duk sunyi aure kusanma wasunsu sunkusa aurarwa Suma. Umme Bata qaunar 'dan daba nataba saidai Kuma bazata iya cutatar dashiba 'yayanta su kadaine 'yayanta bayansu ba ruwanta da 'dan kowa Koda kuwa zataga masifa ta tunkarosa ne, MAHMOUD shikadaine yataso a cikin iyalan Modibbo baida mahaifiya, Yataso ne acikin wani irin kadaici ya rayu acikin kadaicin, Tun Yana yaro baida Wanda yataba janza ajiki harya girma, Shi kadai yake komai nasa na rayuwarsa iyakacinsa da mahaifinsa gaisuwa da bin umarnin baitaba jansa ya tambayesa Yaya rayuwarsa take tafiyaba tunda mahaifiyarsa ta rasu bama shi kadaiba kaf duniya baida Wanda yataba jansa ajiki yaji ya yake ba, Baida kowa aganinsa, Baitaba shiga cikin 'yan uwansa ba sbd basayi dashi, Shi kadai yake kwana, Shi kadai take tashi, Ahaka yayi rayuwa ahaka harya girma, Da kansa ya koyi faduwa da yanda zai tashi kansa, Da kansa yasan yayiwa kansa fada ya tsaya ya nemi ilimi dan yin rayuwa dashi, KHALIL shikadaine 'dan uwansa dayake dashi Wanda yake tsananin qaunarsa duk da yanda umme ke hanasa muamala dashi saidai Sam qaunarsa Khalil ke Masa Babu Mai iya kwabarsa akan shifa alamuransa, Khalil na tsananin kaunarsa fiyeda wainda suke daki 'daya Wanda kowa yasan da hakan shiyasa tare sukai karatunsu tun primary har secondary saidai kasancewar Khalil din ba lafiyayye bane asthmatic ne Kuma irin chronic din Nan shiyasa daga secondary suka rabe MAHMOUD Modibbo ya turasa Sudan karatu shikuma umme taqi yarda yaje koina. A Sudan yaqara samun cikakkiyar rayuwar kadaici Wanda ta hade da rayuwar kadaicin daya baro sai hakan yazame Masa wata sababbiyar dabia wadda yazama rayuwarsa, Baya fira sbd baida abokan fira, Yayi gwagwarmayar karatun degree a Sudan na tsawon shekaru shikadai batareda yazo gida ba kokuma wani daga gidan yazo gurinsa, Babu wani Wanda yataba kiransa yajisa tsawon shekarun bayan khalil sai Modibbo Wanda shine yake kiransa badai shi yakirasaba, Baitaba damuwa da kadaicin rayuwarsaba da baida kowa sbd ahaka yataso Hakan shiya kashe duk wani walwala ko muamalarsa da mutane sai kadaici yafi Masa Dadi da nutsuwa fiyeda komai, Bayasan hayaniya ko shiga jamaa sosai sbd yafi samun nutsuwa a inda kadaici yake., Ahaka rayuwarsa ta nitsa inda yasamu nasarori bayan cikakkiyar gwagwarmayar rayuwa dayayi a cikin neman ilimi me zurfi, Gwagwarmayarsa tazo da nasarori da dama wanda yasa yayi fice cikin manyan mutane da qusoshin qasa, Zamtowarsa wani qusan Shima sai sunansa yaqarawa zabeera family suna da martaba sosai, Ya mallaki abubuwan arziki da dama wanda kaf zabeera yanzu Babu abokin karawarsa idan ba Modibbo ko Andi ba wainda sukafi kowa dukiya, Nasararsa tasa yanzu kusan kowa dangi binsa yakeyi saidai kasancewar bai Saba da a jasa ajikiba yasa baya sakewa da kowa ataqaicema baya iya rayuwa cikin mutane yafison zamansa a Sudan inda acan nasarorinsa suka Fara acan yafi samun nutsuwa idan ya kadaice abinsa Yana daukar lokaci baidawoba Dan yanafin shekara wani lokacin kafin yazo Wanda duk zuwansa sbd Khalil ne kawai yake zuwa sai Modibbo Wanda yake matuqar giramamawa fiyeda komai arayuwarsa, Ta bangaren 'yan uwansa kuwa sosai yake sake musu kudi duk da Babu wani sabo ko sakewa a tsakani Amma yakan Basu duk wani abu musamman umme dayake ganin qimarta sbd Khalil batareda yaduba yanda yataso ba sbd idan yace yaduba yanda yataso to zaitsani kowa arayuwarsa. Ganin kamar MAHMOUD din yayi musu nisa sosai Wanda yanzu suke alfahari dashi amatsayin Dan zabeera sbd mutunci da girma tareda qimarda yake sake kawowa zuriar sai suka yanke shawarar nemar Masa auren 'yar qanin Modibbon Wanda yake kan kujerar zabeera ayanxu ZARAH, Zarah ta auri MD ZABEERA cikeda alfahari da auren sbd samun miji yanxu kamarsa dibbin nasara ce arayuwa, Tana tsananin qaunarsa saidai sanin yafi karfinta yasa ko a mafarki Bata tunanin aurensa saigashi Allah yayi shidin mijintane Wanda taqara haukacewa a tsananin qaunarsa, Baya musu arayuwarsa sbd baisaba doguwar mgn ba ko ta fannin business dinsa ko deals dinsa Abune nayi ko bari bayasan dogon Bata lokaci shiyasa baibi wani dogon sawa Kai ciwon kaiba ya amince musamman da akayi saa zarah mace ce me tsananin nutsuwa da hkr ga biyayya da fahimtar Abu Sam Bata cusa kanta gurinsa tunda akayi auren Rayuwa suke ta mutunta juna da kiyaye gudun shiga haqqi., Shi mutum ne marason damuwa da hayaniyar mutane akusa dashi shiyasa idan har yananan ko volume din tv bata sawa sosai sbd karta damesa, Bata taba yin wani abu Dan damuwarsa ko sakasa ciwon Kai ba shiyasa yake respecting nutsuwarta musamman dayake dama baya shaawar mace arayuwarsa saidai sbd girman Modibbo da Andi dakuma qimarta yasa yake qoqarin bawa auren nasa haqqin. *** Yau amatu Bata fita aikiba Saida tagama hutawarta a gida kafin tayi Shirin aikin ta fito tareda usi Dan dama kullum tare suke zuwa aikin Suna Isa tun a harabar gurin suka fahimci da masu kudi a gurin saidai rashin saar dasukayi gefen VIP saloon dinsu sukaga motocin Wanda sunsan Babu rabonsu yau acikin aljihun masu wainnan motacin masu kama da tarwadar ruwa sbd sheqi. Direct gefen restaurant suka nufa usi na cewa" Juyawa zanyi amah zanje gurin insfector Garba naji uban me zaimin dayake nema na tun Daren jiya. Tana shigewa tace' idanma ni yakeson katayasa lallashi kafada Masa duk yabari nayi Ido biyu dashi Aina sace Masa shegen cikinsa me kama da tayar motar Mai. Juyawa yayi Yana cewa' nizan Fara nuna Masa kalar rashin mutuncina kawuma nacan Yana jiran ganinsa. #mamuh# ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 8_* _mamuhgee_ Kallon tsantsan mamaki da firgici yanzu takewa amatu din tana kallon qafafunta zuwa hannunwanta dasuka Saba dauka da zuwa stations takeyi mamakinta na qara girmama musamman shekarun amatun datake ganin bazasu haura ashirin da uku ba, Gyara zamanta tayi cikin motar tana 6oye mamakinta tareda 'dan kallon amatun datake qara damqe jakarta sbd kudin dake ciki alamar bakin Rai take da kudin ta saki wani guntun murmushi tana nazari wani abu kafin ta kalli fuskar amatun tana cewa'" Ta yaro Mai takeyi Bata qarko Idan har kinawa kudi wannan son ta tabbas zan baki kudinda kaf zuriarku bazaku iya qirgasuba, Sake kallon amtun tayi tareda sakar Mata murmushi kafin yace" Amatu idan da zaki bude idonki ki kalli Abinda nake qoqarin yi zaki fahimci Abinda nafada bashi nake nufiba sbd danaso kamaki da yanzu kin jima da sauya kammani a cell and banyi Miki Kama da wadda kike tunanin zaki fadawa bakya tsoron yansanda, Amatu akwai rayuwa me kyau danake Miki fatan samu Wanda zaki manta da yanda ake sata, Zaki samu rayuwarda ko a mafarki bakiyaba tunaninta, Zaki samu duk wani Jin Dadi da kudinda saikin rabawa 6arayi 'yan uwanki ta yanda Suma bazasu qara tuna sunan sataba. Wata siririyar dariya amatu tayi tareda sakin jakarta datayiwa riqon Gam Gam tana gyarawa jakar zama a kafadarta tareda gyara tsayuwarta tace" Hajiya mama Allah ne kawai zai iya cike gurbin kwadayin samu kudi danake dashi Dan gurbin me mugun zurfi ne cikesa ba qaramin aiki bane Kiyi hkr da wannan kudin Dana dauka tunda dai kinsan ba komai bane acikin arzikin da kike dashi to Allah ki barmin kawai sbd Nima dai bazan iya bayarwar ba. Bude jaka umme tayi tareda ciro wasu bunches din guda biyu ta miqa Mata tana cewa'" Ungo ki hada Dana hannunki ki hau abin hawa gobe zandawo spa dinku muyi mgn. Tana gama fadar haka tace'" Hafiz muje. Jan motar yayi suka bar gurin da speed me qarfi suka barta da baki a bude tana kallon kudin hannuwanta da qafafunta na rawa sbd wannan ne karo na farko data taba ganin kudi a fili haka irin Wainnan Kuma ma a hannunta da sauri ta turasu jaka tareda fadawa ckin napep dinda ya tsaya gabanta Yana tambayar Ina zuwa malama?¿ Tunda tashiga napep din take share zufan dayaqi tsaya Mata gaba 'daya kanta ya shiga lissafi Bata taba tunanin kudi irin wannan zasu rudataba duk tsananin samu kudinta dubu talatin ne zuwa qasa albashinta ma duka duka dubu goma sha uku be duk wata saina mutane idan ta sanfo Amma yau itace keda kudi dubu 'dari uku a hannunta amatsayin nata bama na sata ba""wayyo Allah" tafada tana dafe gashi. Kasa wucewa gida tayi direct ta kalla me a daidaita din tace yabiya da ita ta bakin Luna inda tasan usi na can. A daidaita din na tsayawa bakin Luna ko fitowa batayiba ta hango bakin gurin cike an taru Kuma daga gani rigima akeyi babba sbd har mitar 'yan sanda ta iso gurin. Da sauri ta fito tana cewa me napep din" Ina zuwa Ta qarasa gurin da sauri sbd hango usi da ake kokuwar sakawa cikin motar Yan sanda Yana cijewa su Kuma sai dukanda sukeyi. Tana isa ta qwacesa da qarfi tareda shiga gabansa tana karesa tace'" Lafiya meyake faruwa?? Cikin sa'a Allah yasa insfector falalu ne a shugaban tafiyar Wanda tunda dadewa yayi sonta Amma ganin batamasan meye rayuwa ba batada mahimmanci agareta yasa ya qayaleta Dan dole Amma Allah yagani yaso aurenta. Kallonta yayi Yana cewa'" Amatu kibari idan munje can office zamuyi magana saiki San Abinda yayi. Juyowa tayi ta kalla fuskar usi da harsun fasa gefen bakinsa taji wani mugun 'daci ya sauka zuciyarta ta juyo tana cewa'" Idan zaa kamasa meyasa sai andakesa? Laifin meyene da bazaku Bari sai anje can dinba kafin kufara hukuntasa? Kallonta yayi tareda matsowa yayi qasa da murya yace" Amatu karki Bata Mana aiki Kinga mutane na kallonmu kiduba can kiga kudin me gurin Luna din aka dauke daga tuhumarsa saiya Kama fada da yaran gurin gashinan yanzu an fasa kan 'daya acikin gurin Dole zamu tafi da usi. Akaro na farko dataji ta tsani falalun cikin fidda 6acin ranta tace" Duk cikin wainda akayi fada dasu usi ne kawai Wanda zaa Kama kokuwa Dan shi bashida kowane? Kinga ba anan zamuyi wannan zancen ba sbd wannan laifin babban laifine yanzu haka yaron Yana asibi antafi dashi Babu me tabbacin kozai tashi Dan haka matsa muyi aikinmu Ku kamasa mine. Kallonsa tayi da sauri zata tareda yayi saurin fitowa bayanta tareda miqa kansa sbd ganin idan bai miqa kansaba zasu iya ture amatun. Yana kallonta yashiga motarsu Yana cewa' amah kije gida ba Abinda zai faru. Tana kallo suka tafi dashi ta dafe Kai tana rintse ido cikin takaicinl ta juya takalla gurinda akayi fadan duk jini da kwalabai an faffasa ga kujerun gurin duk ayi jefa dasu. Adaidaita ta nufa ta fada da sauri tana cewa yabi bayan motar yansandan. Koda ta isa station din harsun cike Masa casefile da cewa yayi attemptin kisa take a qarfafa alamarin tini sukai masa mugun duka, Duk yanda taso ganinsa ba dama abin wannan karon yayi qamari gashi ankira asibiti yaron har lokacin bai farfadoba gashi ya rasa jini sosai haka tayita yawo tsakanin asibiti da station a yinin ranar har kusan qarfe goma Bata koma gidaba qarshe ma dai kawu yazo sukaita yawon fafutukar case din Amma 'yan sandan sun shafawa idonsu toka sunqi sauraronsu. Sai dare sosai suka dawo gida itada kawu ko abinci bataciba ta shige daki saidai iyami tabita daki da abincin ta takurata taci kadan. Washe gari tunda safe suka koma station din gaba dayansu harda iyami amma ko abincin dasuka kawo Masa anqi karba itada iyami suka kwasa sukaje asibiti gurin yaron sbd falalu ya tabbatar Mata da ko yaron yatashi sai iyayensa dashi sun janye qara zaa saki usi. Kwana uku suna Abu 'daya duk wani cin hanci tabawa shegun sunkasa sakin usi ga asibiti andaura musu nauyin lalurar qaton saurayin Wanda taci alwashin cin ubansa idan ya warke. Kwanansu biyar suna wahala kafin aka sallami kabiru din tun a asibiti taja ta tsaya ta kalli yayan kabirun da innarsu tace su janye qara tunda dai yasamu lafiya. Qiri qiri suka qi janye karar Dan wata sabuwar rigima ta qullu tsakaninsu dasu kabirun kawu tas Saida ya 'debe musu albarka Amma sukaqi. Station suka dawo tasamu falalu tayi Masa bayani ya kalleta bayan sun kebe kebe" Amatu ki dage su janye qarar Nan sbd kowane lokaci yanzu kotu zaa iya tura case din Kuma wlh ana zuwa kotu gidan yari usi zaije hakan qara tabarbarewar kawai zaiyi gwara ya tsaya a iya sata kar abin yamasa yawa. Oga falalu yanda kasan kafiran farko haka mutan Nan suke tsabar taurin Rai, Munyi munyi sunqi janyewa ni wlh banmasan ya zanyi musu ba Dan dai tabbas bazan bari akai usi gidan yari ba akan wannan Dan laifin da Babu tabbas din shine yayi. Amatu duniyarce ahaka Yanzu wainnan dakuke fama dasu Dan sunga duk kune marasa qarfi da ace case din da manya akeyinsa da yanzu case din ya mutu Kusamu wani abu kubawasu yaron Inshallah zasu janye. Numfashi ta sauke ahankali tace'' A rayuwa meyasa kudi sune masu mahimmanci, Meyasa kudi zaifi rayuwar 'dan Adam mahimmanci, Shin Dole masu kudi sune suke rayuwa yanda sukeso su huce takaicin komai a duk lokacinda sukeso. Kiyi hakuri amatu Babu yanda zanyi be Dana taimaki Miki akan case din Nan. Karka damu oga falalu Inshallah zasu janye badai kudine matsalar ba??daga yanzu kudi bazasu Kara zama matsalarmu ba arayuwa, Munga mummanan banbancin da akoyaushe ake nuna Mata fificin me kudi shine mutum mukuma muda dabba duk daya, Ako yaushe muna qoqarin taka matsayin mutane kamar kowa Amma koyaushe ana sake durqushemu Alan hakan, To idan hakane kudi sundaina zama matsalarmu zamu nemesu ta duka hanyar data dace matuqar hakan zaisa musamu daraja kamar kowa, Ada mun dauka maraici rashin kowa shine matsalarmu data saka bamada daraja agun mutane sai yanzu nake gano kudin dai sune komai, Idan bakada kowa matuqar kanada kudi ko bolace ta haifeka mutane zasu bika. Akaro na farko a rayuwarta tundata girma hawaye suka ciko idonta ta maidasu tana girgiza Kai tace" Karka tashi aiki oga falalu zanje nazo dasu ayau zasu janye qararsu a shirya takardun. Tana fitowa tace kawu ya jira zataje tazo da masu qarar. Gida tafara biyawa ta dauko kudin daya rage cikin kudaden ta qirga dubu dari da talatin da shida ta zuba jaka ta fito ta fice iyami ba batasan tashigoba. Gidansu kabirun ta nufa cikin sa'a har yayansa da innar duk sunanan suna ganinta kowanne ya tsuke fuska alamar bazasuyi Mata alfarmar datakesoba murmushin takaici tasaki tana qarasowa tsakar qaramin gidan ta zauna gaban innar tana cewa" Inna barka da yamma, Kabiru ya jikin? Ciki ciki innar ta amsa saidaima kabirun ne ya amsa da sakin fuska. Bata tsaya batawa kanta lokaciba ta ciro dubun dari ta ajiye gaban kabiri tana murmushi tace" Kabiru maganar janye qararku haryanxu bazaku janyeba kodan ana tare... 'dan washe baki kabirun yayi Yana kallon kudin kafin ya kalli innarsu da yayansa yaga yanda Suma suke yiwa kudin kallon qurulla suna zazzare idanuwa ya kalli amatun Yana qaqalo murmushin Shima yace" Nifa dama usi abokina ne su innane suka dage da qarfafa qarar ni dama ban riqesa ba na yafe Masa tun ranardana samu kaina. Cikeda mamaki innar tace" Au kabiru hakama zaka fada? Duk Abinda mukayi badan Kai mukayisaba shine yanzu tsabar rashin godiya zakace haka Shikenan tinda haka kace ai saimu cire kanmu muma a janye qarar tunda kaida mukeayi danka baka ganiba. Yayansa ma matsowa yayi Yana cewa'" Inna qyalesa yayi maganin gobe Babu shegen dazai qara shige Masa gaba idan haka takuma samunsa Nima nacire kaina zuwa zanyi yanzu na janye qarar tunda abin nasa yazama raini. Numfashi amatu ta sauke tareda rintse idanuwanta ta bude tana qara jinjina alamarin mutane. Miqewa tayi tana cewa to tunda dai can kayi gurin janye qarar Bari nabika muje tare Amma Bari na tafi da kudin idan ya janye saina basa yadawo muku dasu ko?? Tafada tana dauke kudin tana sakawa jaka ta zura takalmanta tana cewa'' Acikin minti biyar kudi yayi aikin dana fi sati inayi Amma sun kasa fahimtata. Adaidaita 'daya suka shiga suna Isa station din atake ya janye qarar tabiya kudin beli da tarar me shago dubu talatin kafin aka Basu usi din sukayo gida. Tun a hanya tafe suke cikin adaidaita Amma batace qalaba tayi nisa sosai cikin tunani, Ta gaji da wannan masifar ta kullum suna police ko gidan yari, Duk yanda taso Hana USI rigima takasa sbd da rigimar sukeci suke Sha suke rayuwa, Baya tunanin kansa sai nata danasu kawu, Dukkanin aikin datakeyi tana ajewa shine yake samo matasu shi ya gammaci rigimar Amma dai ita yafison tayi aiki, A iya saninta usi ya fison shi yayi satar a rufesa akan tayi shiyasa yaketa shiga rigingimu Yana kawowa gidan kafin lokacin albashinta Ga kawu maganarma ace yayi sanaa Bata tasoba sbd tsufa daya taso Masa bama zai iyaba musamman tun zamansa gidan yari wahala ta cinye Rabin qarfin qafafunsa shiyasa yanzu yake Dan fama dasu, Babban mafitar datake gano musu ayanzu itace usi dayake namiji yasamu yayi karatu yasamu damar daukar dawainiyarsu Nan gaba itadai karatu baya gabanta shiyasa duk burinsu itada kawu ya qare akan Usin yayi karatu Amma Abu ya gagara komai sai qara lalace musu yakeyi. Koda suka Isa gida jiki a sanyaye kowannensu yashigo ita dakinta ma ta wuce Kai tsaye Kawu ma haka Usin ne dai iyami ta zaunar tareda dauko ruwan zafin data Dora na jiran tsammanin Abinda zaa dafa suci ta gaggasa Masa fuskarsa da wuyansa da bayansa dasuka kukkunbura sbd duka da tsamin dasukayi. Haka suka kwana dukkaninsu Babu Wanda yaci abinci bayan usi da maman junior takawowa taiba yaci sbd lurada basuda abincin ci Dama Kuma dabi'ar jama'ar gidance taimakon juna duk da irin zaman fitinar dasuke yi idan sunga juna a matsi suna taimakawa junansu sai dai idan masifar ta tashi akwana a yini anayi. Washe gari sauran canjin hannunta dasuka rage dubu biyar da dari uku su ta bawa iyami dubu biyo aka siyo musu waina sukaci sauran Kuma ayi dubarar abinyi tayi Shirin fita aiki tasa Usin ya shirya tafadawa iyami idan kawu ya tashi asibiti zata Kai usi sbd dukkanin raunikansa sun kumbura sosai ga yankan kwalba a gefen cikinsa gwara suje asibiti tun wuri. Ganin kudin hannunta nada dama Dama yasa suka nufi wani babban private asibiti dake hanyar gurin aikinta ta baya cikin sa'a kuwa suna zuwa ba layi aka Basu izinin shiga. Usin ne a gaba tana bayansa fuskarta fayau ba wata walwala ayau sbd tunanin raunikan na Usin kada wata matsala ta biyo baya. Doguwar rigace a jikinta irin ta gwanjon indiyawa din Nan sbd tana doguwa sai sukai Mata kyau gashi Dan hijabinta na iya wuya ne na uniform din aikinta. Sanyin AC da qamshin office din yasa ta lumshe ido tareda sakin murmushi tana kallon Usi dashima dadin sanyin AC din yasashi sakin murmushi Yana kallonta qasa qasa tace" Usi karkayi saurin bashi amsa idan ya tambayeka Dan mu samu mu more sanyin AC dinnan na kwana biyu bansamesa ba sbd banje aikiba Kodan AC bazanyi saurin aje aikin blue fox ba. Gyaran murya doctor din yayi sukai saurin kallon inda yake zaune cikin fararen kaftans dasukayiwa kyakkyawar fatarsa kyau fuskarsa daukeda wani sahirtaccen murmushin dayasa amatu bude baki akaro na biyu dataga kyakkyawan namiji Mai wata irin Kamala da kwarjini saidai wancan din nasu insfector Garba ba murmushi a fuskarsa saima wani irin izza Mai bada tsoro sabanin wannan da kyakkyawan murmushinsa yaqara kyakkyawar fuskarsa kyau, Tasaba da ganin irinsu insfector Garba dasu Sargent salisu da manager dinsu dasukeda fuskoki kamar tuwon daya tashi shiyasa yanzu take ganin wannan amatsayin kyakkyawan dayafi kowa. Fadada murmushinsa yayi har haqoransa suka bayyana Yana kallon fuskarta sbd yaji Abinda suke fada yace" Bismillah to Nima bazan tambayeka da wuri dinba. Sosa Kai usi gayi Yana cewa'' Kyaleta Wasa takeyi likita. Kallonta yasakeyi akaro na hudu yana qara fadada murmushinsa yace" To kema Bismillah zoki zauna. Qarasowa tayi ta zauna tana kallon sunansa da aka maqala a table dinsa DR KHALIL ZABEERA. murmushi tasaki tana fadan sunan a hankali sbd hada kalmomin Dan karatun nata sai ahankali. #mamuh# _________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 9_* _mamuhgee_ Gabaki 'daya hankalinsa nakan fuskar amatu da ita Kuma hankalinta nakan usi da akewa dressing raunikansa bayan an wanke Masa hadda 'dinki Saida akai Masa a inda kwalba ta fasashi. Sakin murmushi ganin yanda takeyi kamar ciwon ne ajikinta tanata yamutsa fuska tana cewa" Usi daga yanxu ko sunan Luna nasake ji abakinka nice zanmaka dukanda ko kawu bazai iya ganekaba bare iyami, Yanxu duba kaga yanda kakejin azaba Shima wancan kabirun nasa Amin maganinsu Dan na aika buge katangar bayinsu ta bayan gidansu ta yanda duk kudin dasuka karba zai qare a gyara kaikuma.... Cikin 'yar qaramar dariya ya katseta Yana kallonta cikin burgewa yace" AMATULLAH antyn Usman ki kwantarda hankalinki Usman is perfectly fine,ba gashinan angama dressing ba shikenan kawai magani zai ringa Sha yanzu daganan raunikan zasu warke Suma. Kallonsa tayi tareda kallon Usi dake cewa'" Likita bafa antyna bace qanwatace. Duka takai Masa da Jakarta tana cewa" Kaine zakaita zama qani ako yaushe Dan haka kayi Mana shiru agurin Ina sake ganinka da kabiru nice zan dawo maka da duka raunikan nan sababbi. Dafe dinkinsa yayi da sauri Yana cewa'" Wayyo amah jini na fita dinkin ya warwa..... Da sauri ta durqusa cikin firgici tana qoqarin Kai hannu tana cewa" Dagaske? Mun shiga uku, Likita Zo ka duba Mana... Dariya Dr Khalil zabeera yayi Yana kallon firgicinta dayasa takasa tsayawa ta lura usi din tsokanarta yakeyi ya kalli usi Yana cewa'" Usman ka daina 'dagawa AMATULLAH hankali ko na saka a warware dinkin Nan ayi maka sabo yanzu. Dariya usi din kewa amatun Yana qoqarin miqewa sbd dukan datake Masa da Jakarta sbd sosai ya fifgitata Dan sanin Babu Abinda take tsananin tsoro kamar wani abu ya samu Usin. Takardar maganin daya rubuta musu ya miqawa amatun Yana cewa'" Ga maganin dazai ringa Sha Nan bayan sati daya saiku dawo mu warware dinkin ko?¿ Karba tayi tareda kallon fuskarsa dake yalwace da murmushin dake qayatar da ita tace" Mungode likita. Girgiza Mata Kai yayi Yana cewa'" Ki kula da kanki ba USI kawai ba AMATULLAH. Qoqarin fitowa sukeyi nurse dinda yayiwa usi dinki na shigowa ya miqa musu takarda yana cewa" Yawwa ga wannan zakuje ku biya kafin ku wuce. Karba amatu tayi suna kallon juna da USI ta duba ita batama gane Abinda ke rubuce ba ta miqawa Usin tana cewa" Duba kaga Abinda sukace aje abiya din. Karba yayi yana duba takardar Yana qoqarin hada kalmomin turancin Amma sunqi jaduwa ya duba gurin da akasa kudin yaga anyi 9 da zero hudu ya zato Ido da sauri Yana rawar murya yace" Dubu casa'innn.... Mene?????ta fada da qarfi tana fizge takardar da sauri ta duba gurin kudin taga 9000 ta hadiye mugun yawu tana cewa" Basuda hankaline?? Kuskure dai sukayi muje yayi Mana bayani Dubu casa'in saikace fatarka suka sauya maka gaba daya tsabar gyara raunika. Dr Khalil dake jinsu tun ayanda ya lura basuda wani ilimin bokon yasan ansamu rashin fahimta gurin duba kudin yaji sun sake burgesa ya taso yabi bayansu zuwa gurin biyan kudin. Suna Isa amatu ta ajiyewa cashier takardar tana cewa" Oga wannan dubu casa'in din da aka rubuto ta waye?? An Mana musayar takarda duba kagani. Yanda tayi maganar yasa saurayin dagowa ya kalleta a wulaqance yace" Malama takarda indai Kai aka bawa to Babu maganar kuskure idan biya zakuyi ku biya,idan kuna mamakin Abinda aka rubutane to wayace kuzo Nan da saiku tafi asibitin gwamnati. Yanda yayi Masu maganar yasasu quluwa dama amatun a qule take da kudin cikin takardar kallon walaqanci tamasa tana cewa' Kai Karen asibiti karkace zaka gaya Mana magana anan gurin Da kake maganar asibitin gwamnati idan har irinku zasuzo Nan suyi Karen asibiti mezaisa muma bazamu zoba??? Miqewa yayi tareda fitowa ya zagayo gabansu Yana nunata da yatsa Yana cewa'" Kisan Abinda zaki fada Nan bama tolerating 'yan iska irink..... Saukar mari yaji daga sama kafin yakai qarshen maganarsa A gigice ya dago usi ya cakumosa Yana cewa" Bayan wannan Marin har kamanni zan sauya maka duk bakinka yasake furtawa 'yar uwata wannan kalmar. Da sauri mutane dasuka Ankara sukayo kansu ana qoqarin rabasu Koda Dr Khalil ya iso gurin harya 'dan cika abin ya girmama da sauri ya qaraso gurin Yana zuwa ya kalli usi cikin tausasa murya yace" Usman sakeshi. Dakinda USI yayi Yana cewa'" Ka iya bakinka wannan tafi qarfin ko uwarka. A harzuqe saurayin ya taso Dr Khalil yayi Masa wani mugun kallon dayasashi dakatawa Yana huci yace" Dr wainnan 'yan iskan..... Shut up""Dr khalil yace da Dan fada Yana cewa'" Jafar koma gurin aikin and everyone should leave from here please. Da sauri kowa ya watse Yana mamakin Dr Khalil daya marawa wainnan baya maimakon staff dinsa. Bayan kowa ya watse ya kalle Usman da har lokacin ransa zafi yake da kalmar 'yar iskar da aka Kira amatu da ita yace" Usman this is not how to behave with people musamman wainda kasama gurin aikinsu, Meye abin fada anan infact meyema matsalar?? Kallon Usi amatu tayi tareda sakin murmushi danta saka ya sauko tace" Kai usi meye na wani fada tun bamu biya wannan kudin da ake fada akai ba zakayi wani fadan kaji rauni kasa kawu ya cinyeni 'danyata. Kallonta yayi a raunane zaiyi magana tasaki murmushi tana ce Masa" Karka damu ka manta bama saka maganar kowa aranmu sbd bamuda abin damuwa, Duk sunanda zai kirani dashi tunda dai banida Wanda hakan zai zubar Masa da mutunci to meyene aciki? Kawu ne Kuma Shima zagi da maganar kowa Bata tabasa Dan haka barsu su kirani da kowane suna baya damuna, Usi Kaine damuwata Dan Allah ka daina shiga rigimarda zata saka a hadari, Ka manta munada burin cikawa na zama alhazai" ta qarasa fada tana dariya sbd Shima ya sake. Sakin fuska yayi Yana cewa' Muje nidai. Tunda suka Fara magana yake kallonsu cikin wani irin yanayi yanason fahimtar zancensu dakeson nuni da su din marayune. Gyaran murya yayi tareda gyara tsayuwarsa Yana miqa Mata hannu yace'" Bani takardar kudin mugani. Miqa Masa tayi tana shafawa idonta toka tace" Dr mudai wannan kudin da aka rubuta mu biya bazamu iya biyansu ba sunyi yawa ni banma taba Kai qirqen casa'in ba a lissafin kudi Ni ko inadasu bazan bayarba wlh ba kawuba koni bazan iya barciba duk ranarda nabayar dasu. Murmushi yasaki sbd dama yasan za'a Rina ya kalleta yana cewa" Basaikin kasa bacci ba AMATULLAH dubu Tara ne a rubuce ba dubu casa'in ba. Kallonsa tayi da sauri tana karban takardan da sauri tana sake dubawa tana bin numbobin dakyau tace" Eh hakane kuwa.. Dagowa tayi tana kallon Usi cikin masifa zata Fara magana yayi saurin cewa'" Yi yi hakuri da masifar Inaga banduba daidai bane kokuma ban fahimta bane. Hadiye masifar tayi tana cewa'" Usi rashin karatun Nan saiyasa an dauremu wata Rana. Dariya sukayi atare kafin ta kalli Dr khalil tace" Dr ai maganar gskia ko dubu Taran Nan bazan iya biyaba zandai biya dubu biyu idan zaa karba. Kallonta ya shagala da yi tana sake burgesa yace" Usman kanada 'yar uwa anan, Kawun Nan Shima yanada 'ya anan. Murmushi tayi tana dauke ido daga wallet dinsa daya 'dan fito da aljihunsa daga gani Kuma tasan bazai rasa kudiba aciki Amma sbd kirkin Dr din tanata dauke ido akai sbd hakurinta yakusa qarewa takaiwa wallet din Hari. Zaro wallet din yayi ya bude yaciro ATM dinsa ya miqawa cashier ta window tareda takardarsu yace acire. Bayan ancire aka miqo Masa receipt ya miqawa amatu receipt din Yana cewa'" Shikenan har dubu biyunki anbar Miki AMATULLAH. Karba tayi ba wata kunya a idonta tace" Aikuwa ka kyauta Mana Dan akan dubu Taran Nan nafison na kwana 'daya a station da safe na fito nayi gida da dubu Tara ta. Girgiza Kai yayi Yana murmushi harsuka wuce Yana binta da kallo zuciyarsa na karban baqon yanayin dake shigarta akaro na farko da mace ta sauya bugun zuciyarsa a ganin farko. Suna fita ya koma office dinsa yasa Akira Masa daya daga cikin nurses dinsu dayaji Yana fadin yasansu amatun lokacinda ake fadan dazu Yana buqatar sanin inda suke. ##mamuh# _________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 10_* _mamuhgee_ Suna fitowa daga asibitin gurin aikinta suka nufa ya ajiyeta da adaidaita kafin shi yawuce gida, Babban Abinda yasa yau tazo aikin shine Jin ko hajiyar Nan tazo nemanta sbd yanzu dai Kam tana buqatar ganinta kodan Abinda yafaru yau na rashin ilimin dasukedashi sosai yasa taqarajin buqatar karatun nasu Amma dai yanzu na usi ne agaba. Da manager tafara haduwa a reception din blue fox din tana ganin ya washe Mata baki ta tsuke fuska tana cewa" Wannan Dan wahalar zai Fara damuna yanzu da surutansa wainda basuda amfani aguna,. Yana qarasowa itama ta washe Masa baki da gayya tana cewa'" Manager sannu da yawo. Washe baki yasake yi Yana shaga dogon kansa yace" Amah 'yan amata ya aikin?¿ Sai yanzu Kika shigo? Eh sai yanzu nashigo na yagi robana daya wuceni kwana biyu. Me Kika?? Aa cewa nayi nayi latti Bari naje kafin a nemeni. Tana fadar haka ta wuce tana cewa'' Kuje kuga gayu da wayewa gurin Dr Amma kunzo kaida insfector Garba bansan Waye haqoransa sukafi na wani dafewa ba. Tana shiga saloon madam bell ta kalleta cikeda mamaki tana cewa" Amah sai yau kikaga Daman zuwa aikin??? Ta gefen ido ta watsawa madam din mugun kallo kafin tace" Madam lalurace ta hanani zuwa ba ganin dama ba. Bude Ido madam tayi tana cewa" Ni kike wa magana haka? Dauke Kai tayi tai qasa qasa da murya tace" Ke din uwatace? Me kike cewa amahhh? 'dan washe baki tayi cikin gatse tace" Cewa nayi sorry madam. Qwafa tayi sbd taji Abinda amatun tafada da farko tace" To ki tafiyarki kawai Dan anyi replacing dinki da wata. Kallon baibai tayi Mata tana cewa" Madam korata kikayi ne? Eh" madam din tafada Kai tsaye tana cigabada da aikin datakeyi. To Ina tayaki murna madam bansan an maidake manager ba da bana nan. Aje Abinda takeyi tayi tana yiwa amatun kallon mamaki sbd tasan baqar Magana ce ta jeho Mata wato tunda ba itace manager ba bazata iya korarta ba. Amatu na ganin ta kunnata ta gyara tsayuwarta zata sake wata maganar aka bude qofar shigowa ana cewa" welcome ma. Madam ce tayi saurin aje towel din hannunta tana nufar qofar bakinta a washe tana cewa' Welcome ma. Gyara tsayuwa amatu tayi batareda ta juyaba Kuma batada alamar juyawar Taji ankira sunanta Da sauri ta juyo sbd ta 'dau muryar Aikuwa ita din ce ta qarasa gabanta tana kallon madam bell tasaki yaqen tura haushi tace" Madam dama bankwana nazo Miki tareda tayaki murnar samun matsayin manager Dan haka Allah ya sanya alkairi. Kallon hajiya aisha tayi tana qaqalo murmushi tace" Haj Mama Ina kwana??? Murmushin mamakinta umme tasaki tareda kallon madam bell tace" Dama ita nazo nema sai dai next time idan nadawo,amah muje ko??? Gaba amah tayi tana murmushin farin cikin daga yau rayuwarsu zata canja idan har hajiya mama tabata sabon aikin datake cewa. Motar haj Aisha din suka shiga wani sanyin AC da qamshin ya ratsata ta lumshe ido tareda shafa kujerar motar datajita da wani irin laushi da santsi, Yaune karo na farko a rayuwarta data taba shiga motar Dana taxi ba ko taxi din tafi shekara goma rabonta datashiga. Kallon motar takeyi tako Ina tana tabawa ta kasa 6oye farin cikin datake ciki a fili tace" Hajiya mama ko ahaka Kika barni kincikamin qaramin burina.... Dauke Kai haj Aisha tayi cikin gundura da amatun tun yanzu tace" Motarma gaba daya zata iya zama mallakinki ko 'dan uwanki usi da Wanda ma ya tsinceku idan har zakiyi Abinda nakeso Wanda a wata biyar kingama aikinki Kuma kin mallaki Abinda zakiyi hannun riga da talauci. Parking motar tayi daidai kwanar gidansu amatun Wanda yasata juyowa ta kalleta ta yanda tasan gidansu zatayi magana hajiya aishan ta katseta Kai tsaye da cewa" Zan baki naira miliyan uku tareda makaranta me tsada wa 'dan uwanki harya gama sai gidan zama me kyau ga kawunki da jarin sana'a me kyau ga matar kawunki idan har zakimin Abinda nakeso. Suman zaune amatu tayi tareda sakin baki gaba daya ta daga hannu tana lissafa abubuwan da hajiyar tace har lissafinta ya 6ata tayi saurin girgiza Kai tana 'dan dukan kanta tace" Amatu amatu amatu dawo kanki... Dawo kanki..... Hajiya mama duka abubuwan Nan dakika fada saidai naji kokuwa kunnuwanane???? Qaramin tsoki umme tasaki tareda bude wata 'yar jaka dake daukeda kudi dubu 'dari uku ta miqa Mata tana cewa" Kije kibawa su kawunki wannan idan kingama aikin zanbaki dukannin Abinda nace Qaninki kuwa zanbaki takardun makarantarsa ki riqe a hannunki. Da sauri ta karba kudin ta shafa cikin zaquwa take cewa" Wannan yanxu duk nawane halak malak?? Hajiya mama na amince zanmiki aikinki koma wane iri ne na shekara biyarma zanmiki bana wata biyar ba. Kallon takaici umme tai Mata tana mamakinta saidai duba da 'yar tashace Kuma 'yar bola hakan ba wane abin mamaki bane Dan duka tarihinsu tasamu agurin binciken datasa akai Mata akansu Wanda alhaji mande ne yabada bayajin Shiyasa tasan tsaf amatun zatayi wannan aikin ba gashi indai akan kudi ne. Zanje dake gidana zaki gabatarda kanki a matsayin wadda akayiwa fyade harda ciki ajikinki, Ba shaidu, Duk wasu manyan shaidu na tanadar Miki su tun daga Kan likitoci harzuwa Abinda zai biyo baya, Aikinki na kammala na tanadar muku gida da sanaar yi a wani guri can nesa da Nan bazaku sake dawowa Nan ba shikenan kunyi bankwana da talauci da damuwa zaku samu damar Fara sabuwar rayuwa. Duk iya yanda ta rude da Jin abubuwan dazata samu Bata taba kawo hajiyar batada isashiyar lafiya ba sai yanxu datai wannan maganar Amma Kuma bataga alamar hauka atareda ita ba, Itadai yanxu matsalar dayace ko haj nada lafiya ko batada bazata mayar Mata da kudin nanba. Yanda amatun ke kallonta yasa ta fahimci tunaninta ta 'dan qaqalo sakin fuska tace" 'dana ne nice na haifesa Nasa kimin hakan ne sbd banason abawa 'yayana mulkinda zasu cutu Kuma Allah ya tambayesu ranar qiyama, Mulkin zabeera akwai hadari, Za'a iya hallakarmin da 'yaya sbd kwadayin mulki shiyasa nakeson kije amatsayin hakan Dan kada abawa 'yayana mulkin da zarar an nada wanda yakamata a nada zan kaiku inda zakuyi rayuwa cikin farin ciki da walwala. Shiru amatu tayi tareda gyada Kai sbd soyayyarta da kudi yasa Kai tsaye tayi na'am da hakan Kai tsaye tunda daima ceton Rai ne zatayi koba komai Babu ruwansu da wani abin kunya tunda dai bayi tayiba tasan dai kawu ne bazai yadda da wannan tsarin ba bare iyami. Kallon kudin tayi ta kalla hajiya aishan tace" Kinada tsarin fadawa kawuna ya amince??? Dan nidai nariga na amince. Murmushi umme tasaki tareda tayarda mota suka qarasa shiga layin gidansu amatun tace" Kawunki bazaisan gskia ba sbd gudun samun matsala agaba, Kidai saka aranki aikin kudine zakiyi domin samun ingantacciyar rayuwarsu kawai zan aiko a sanar dashi kinsamu aiki a zabeera tareda albashi me kyau zaki ringa zuwa duk sati kina ganinsu har tsawon wata biyar. Kawu bazai yadda ba"tafada tana tunanin mafita. Karki damu zai yadda idan wadda zanturo tazo saiki qara da dubarunki ta yadda zai yarda. Kallonta amatu tayi kafin ta kalli kudin tsawon daqiqu tana nazari zuciyarta na son yin rawa a alamarin Amma burinta na hana hakan. Rintse idanuwa tayi tareda sauke ajiyar zuciya me qarfi ta furta na amince saitazo nikuma Ina fatan wannan alqawarin yacika. Gyada Kai kawai hajiya aishan tayi tareda nuna Mata qofa. Fita tayi tareda kudin tabi motar hajiya aishan da kallo harta bace mata ta sauke ajiyar zuciya tana cewa' Amatu wannan sa'a ce ko rashin sa'a??? Tana shiga gida Kai tsaye gurinsu kawu taje Allah yasa duk suna dakinsu kawun harda USI dayashigo yanashan magani kawu Kuma na gefe yanashan waqar 'dan indo,ta qaraso ciki tana sallama tareda qarasawa ta zauna gefen iyami dake ballowa usi magani ta ajiye Daurin kudaden tareda sauke boyayyan numfashin zancen dazata qirqiro. Idon kawu na sauka kan kudin yatashi zaune da sauri daga kishingiden dayake Yana qarar radionsa Dan kada aji Abinda zai fada yace""kudi" Yana sake bude idonsa akansu. Iyami ma dakatawa tayi daga bude maganin ta kalli amatu da sauri, USI ma kallon amatun yakeyi zaiyi magana ta rigasu da cewa" Duk nasan tunani kukeyi dabam dabam Iyami wlh tallahi ba kudin wasu bane na dauko, Kawu aiki aka koreni sbd nayi kwanaki banje ba to, to ,to shine dama inawa wata babbar hajiya mama aiki a saloon dinmu shine tace ita zata daukeni aiki zata budemin gurin aiki irin fire fox me sassa dabam dabam wanda nice zanzama managan gurin Amma.... Amma me????iyami ta tambaya da sauri zuciyarta naqin gasgatuwa da zancen.. Amma Wai sai nashiga training dinda zaayiwa manyan ma'aikatansu a can inda aka kebe na tsawon wata biyar zuwa shida. Tsit sukayi a dakin duka kowa na qoqarin fahimtar zancen saidai ta Yaya?? Kallonta USI yayi dakyau yaga itama shi take kallo yace" Amah idan har cigabanki ne me kikeso yanxu to. Kallon kawu da iyami tayi Shima kawun kallonta yake yace" To wannan kudin fa??? Kai tsaye tace kudin albashinane aka bani na watannin Dan daukar nauyin Kai kafin mu fito training din. Iyami ta kalla tace" Wlh iyami aiki zanje Yi ba qarya nakeyiba na rantse Miki... Duk shiru sukayi kafin kawu yace" Naji kuje zanyi tunani akai. Miqewa tayi ta fito usi ya biyo bayanta suna fitowa yafara watso Mata tambayoyi tajasa zuwa dakinta da sauri Dan kar kawu yajisu suka zauna tafara yimasa bayani komai Kai tsaye yace wlh bai amince ba. Hayaniya suka Fara tayi saurin rufe qofa tana cewa" Idan baka gaji da yawon cell ba ana maka dukan wulaqanci to ni nagaji da ganin hakan, Rayuwa me kyau nakeson muyi kamar kowa Usman, Idan har kanason farin cikina danasu kawu wannan maganar mungamata, Banyi Dan Jin dadinaba sai Dan wainnan bayin Allan dasuka sadaukar da komai saboda mu, Babu uqubar dabasu shigaba amma suka riqemu da Amana, Kaima inason ganin kasamu ingantacciyar rayuwar sbd ka tallafesu a gaba Dan ni nasan rayuwata acikiku taqaitacciyace kobanaso nasan Dole wata Rana kawu saiyamin aure.. Usman mubar maganar Nan kawai qwarin gwiwarka nake nema. Kallonta yayi idanuwansa na cikowa da hawaye yanajin inama ya mutu ya rage Mata 'dawaimiyar datake ganin itace akai, Maimakon yazama jagora Amma yazama wani irin koma baya itace jagorar. Ficewa yayi Yana share hawayen fuskarsa dasuka saka jikinta yayi sanyi matuqa Amma batajin zata fasa sbd tariga takai qarshe zasu bar Nan din sbd karatun Usman din. Kwana biyu ana rigima sosai a tsakaninsu kafin iyami da Usin suka amince akan aikin nata bayan dattijuwar da aka aiko tayi zuwa kusan hudu tukuna., Kwana uku masu zuwa zata tafi Amma duk sai jikinsu su hudun hakanan ya mutu sosai suka shiga damuwar tafiyarta duk da dai Basu fadaba sai hakan yataba 'yan gidan Suma sbd su kawun dadu amah sune hayaniyar gidan dake qara Raya gidan shiyasa Suma duk sai sukaji ba Dadi, Amatun ma hakanan takejin kamar zata rabu dasu kawun ne rabuwar har abada Wanda usi ne ma tadawo Yana qoqarin cire Mata damuwa, Iyami da kantace ta hada mata duk wani abin buqata a 'yar Jakarta ta goyawa ranarda akazo tafiya da ita iyami duk hakurinta saidatayi hawayen rabuwa da amatun sbd zuciyarta takasa samun nutsuwa da tafiyar, Kawuma kasa rakiyarta waje yayi saidai Usman ne aka tafi dashi Dan yaje yaga inda take. Su maman junior hadda rungumeta sukayi sunajin kewarta tun Bata tafiba. **** Wayarta data gamayi ta kalla tareda kallon haj Maryam dasuke zaune a palon tace" Su amah ne gasunan a hanya isowa zasukai mintuna ashirin kafin su iso zuwa lokacin an halarta gurin meeting din familyn ZABEERA daza'ayi yau Yau komai zai qarewa MD ZABEERA. Murmushi haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye tace" 'yan jaridar Dana gayyatoma suna daga baya suna jiran kirana suzo ya sakarwa duniya wannan labarin da dumi duminsa. Dariyar farin ciki suka saki atare daidai lokacinda nuratu tashiga cikin kyakkyawar adonta na wata Kuwait jallabiya datayiwa fatarta kyau sai qamshi takeyi tace" Momy kusan kowa fa ya halarto dan gasu anty bahijja nacan sun iso taredasu anty juwairiyya dasu baba qarami. MD ZABEERA ma Naga shigowarsa yanxu tareda ZARAH. Kallon juna sukayi tareda cewa" Shikenan muje. *** _40 min later_ A bakin babban qaton gate din ZABEERA motarsu ta Parker Wanda akayi juyensu da ita zuwa wata matacciyar golf baqa., Akaro na farko ta 'dago hoton MAHMOUD ZABEERA da aka Bata bayan anmusu bayani wasu abubuwa akansa ta kalli hoton zuciyarta tayi wata irin bugawa akaro na farko... Rintse ido tayi zuciyarta na wani irin tsalle tayi saurin rufe hoton tana dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi tace" Ya Salam.. Meyasa zuciyarta ke bugawa da ganinsa a hoto??? Kallon Babar dasuka Zo tare tayi tana qoqarin Hana zuciyarta bugawa Amma sai qara bugawa tayi tayi saurin miqa Mata hoton tana cewa'" Ki riqe a hannunki nariga Naga hotonsa zan ganesa da kaina. Kallonta baba Jamila tayi tana cewa'" Ki nutsu fa. Gyada Kai tayi tana yiwa qatoton gate din zabeeran kallon kwadayi da qauyanci. Shima usi kalle kallen yakeyi baki abude sbd tsananin girma da kyan gate din kafin suka nufo gate din Babu dogon musu sbd babban security in charge yasan da zuwansu yasa aka Bari suka shigo suna kalle kallen baki asake Amatu tace" Usi kana ganin Abinda nake gani kuwa???? Kasa magana yayi yafarabin manyan motacindake harabar gidan da kallo Yana cewa'" Wlh amatu wannan gidan aljannar duniya ce muka shigo. Itama motacin tahau shafawa tana cewa'" Aikuwa sa'a takawoni Nan ni amatu. ##mamuh## ______________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 12_* _Mamuhgee_ Kasa riqe hawayenta umme tayi suka gangaro Kan fuskarta ta shafa cikin firgici ta dago hannunta ta kalla taga tabbas hawayene, Yau ni Aisha mezan gani ne?? Wace masiface wannan yarinyar na gayyatowa kaina ranar farko data sako kafarta gidana hawayenda na manta ya akeyinsu tun quruciya yau sune a fuskata, Wlh shirina bazai lalace ba Koda kowama zai rasa saidai kowa ya rasa... Juyawa tayi Kan khalil cikin tashin hankali da rudewa tace" Khalil karkayiwa kanka haka ka 6ata rayuwarka kafada gaskia wannan yarinyar bakada alaqar komai da ita, Rintse ido yayi Yana danne tsananin 'dacin da zuciyarsa ke Masa Ummin ta girgizasa da qarfi tana sake Marin fuskarsa tace" Kafada gaskia Khalil wlh bazan yadda a maqala maka cikin qaryaba wannan yarinyar 6arauni..... Katseta Modibbo yayi da cewa" Aishatu ki nutsu kisan a inda kike, Shiru yayi Yana nazari cikin tsananin baqin cikin da takaicin Abinda ke faruwa ya dago ya kalli khalil Khalil din yayi saurin sauke kansa Yace" Khalilu Abinda kayi a tunaninka meye shi?? Modibbo a musulunce shi aure idan har an daurashi Akan yanda sharuddan aure sukace to banyi laifi ba, A tsakanina daku iyayena Kuma laifi ne sbd na boye Muku nayi bada izininku ba saidai nayine sbd girmamaku Dan inajin tsoron kawo muku zancen sbd tsoron bazaku Bari, Dan haka na aikata laifi babba Kuma Ina neman yafiyarku dakuma amincewarku da amatun kodan Abindake cikinta baida laifin komai kada a hukuntasa ko mahaifiyarsa nine me laifin Kuma na dauka a shirye nake da dukkanin wani hukunci saidai Allah ya huci ran Modibbo ina fatan itama amatu abata adalcin datazo nema duk yanda akayi hukuncin zamu dauka. Tsit sukayi suna kallon bakin Khalil din cikin girgizuwa da kalamansa, Dukkanin Abinda yafada jin sukayi kalmomin na son tabasu, Shi cikin babu ruwansa to meye mafita ga wannan alamarin? Kallon mahaifiyar amatun Modibbo yayi yace" Ina mahaifin yarinyar?? Ya rasu tun tana yarinya qarama. Ina danginsa? Daga maiduguri mukayo Nan munrasa kowa bamuda kowa nanma amatsayin 'yan gudun hijira muke har mahaifinta yasamu aikin sanaar Saida kayan Miya harya rasu daga Nan ne muka hadu da......sai tayi shiru tana satar kallon hajiya aisha sbd Abinda zata fada itama ba yanda ta iya Dole tabi tsarin yanda al'amarin ya juya kodan fita da ranta tace" Daga Nan ne muka haduda likita shine yake taimaka Mana harya sanyata makaranta shine yakawo maganar son aurenta nikuma na amince saidai bai fada Mana cewar iyayensa Basu aminceba yakawo Mana wani amatsayin mahaifinsa aka daura auren yanzu shekara daya kenan, Mu Kuma kusan wata biyu kenan bamu sake ganinsa ba munyita zuwa asibiti bama samun ganinsa saigashi ciki ya bayyana atareda ita mutane harsun Fara binmu da gori da maganganu marasa Dadi shiyasa mukazo... Faduwa ummi tayi Kan kujera tayi zaman 'yan bori tana kallon baba Jamila tayi wani kukan kura tayi kanta tana cewa'' Qarya takeyi Modibbo wlh taron maqaryata ne.... Saurin riqeta hajiya Maryam tayi cikin tashin hankali take itama tace" Modibbo Sam wannan matar qarya takeyi wlh daga gani sharri ne zuke qullawa sbd kudi......kallonda Modibbo yayi Mata yasata yin shiru baqin cikin future din 'yarta dake Shirin lalacewa na cinta kamar ta rufe amatu da bugun mutuwa. Khalilu duk Abinda tafada gskia ne kokuwa? Gyada Kai yayi kansa na qasa Dan duk duniya bai ta6a Jin tsanar wani lokaci 'daya ba kamar baba Jamila. Bsyan dogon nazari da tunanin irin rashin 'da'a da wulaqanta zabeera da Khalil din yayi take yafita ran Modibbo da kusan kowama a gurin kai tsaye cikin nuna qyamarsa ga khalil din da halayyarsa Modibbo yace" Ban karbi wannan auren naka ba likita haka Kuma kaima na cireka daga iyalina ka dauki matarka kuje kibar Nan karka sake Kiran kanka da zabeera har abada, Kuma kuje ga adalcin dakuke nema Nan anbaku, Anbarwa 'yarki mijinta har abada duk ranarda qafarku ta tako zabeera aranar ne zakusan asalin hukunci da zafin Zabeera......... Kuka ne qarfi umme ta fashe dashi tareda riqe Khalil din da idanuwansa suka qarasa rinewa jajir Yana Mata kallon kece Kika jawo.. Girgizasa tahauyi tana kuka Mai qarfi tace" Dan Allah Khalil kafada musu gskia bakai bane Wlh bazan yardaba nizan fada gskia.. Girgiza Mata Kai yayi tareda zamewa daga hannuwanta yayi qasa da murya cikin qunci Yana cewa'" Ummi kema kisani idan har kina Sona da 'dan sauran farin cikin daya ragemin bazaki taba fadar gskia ba sbd zata saki keda amatu cikin hadari Wanda bazan iya daukaba, Umme kece rayuwata gabaki 'daya amatu kuwa itace zuciyata Meyasa zakiyi haka ummi....?? Mutuwar tsaye tayi tana kallonsa cikin tsananin tsoro da tashin hankalin Abinda yafada, Me Khalil ke nufi? Amatu zuciyarsa, Dama sunsan juna da gske kokuwa ita yakeson rainawa hankali, Amatu dama tasan 'danta shine ta karbi aikinta kenan ita take rainawa hankali tabbas zatasan tayi Wasa da wuta. Gangarowa wasu sabbin hawayenta sukayi ta girgiza Kai tana cewa'" Khalil wlh bazan iya gani na rabu dakaiba, Ka saketa saki uku, Cikin ma a zubar kabawa Modibbo hkr Amma Dan Allah Khalil kada katafi yaqarasa cikin kuka tana sake riqesa..... Cikin tsawa wannan karon Modibbo yakira sunanta Yana kallon Khalil yace" Ko bayan kabar Nan duk ranardaka saketa daga ranar zakasan ainihin fushin mahifinka, Haka cikin dake jikinta. Zubewa qasa umme tayi da sauri Yana cewa'" Na roki Modibbo daya taimaka ya sassautawa Khalil wannan hukuncin. Miqewa Modibbon yayi Yana cewa'" Taro yaqare kowa ya tafi. Kamar daga sama sukaji security din bakin qofar shigowa na bada sanarwar isowar Andi Wanda yasa kowa miqewa cikin tsananin firgici sbd Abinda andin yafi shekaru ashirin beyiba wato zuwa meeting palon. Hajiya Maryam data yiwa amatu text din takira andin tafada Masa halinda ake ciki ta saki ajiyar zuciya tana riqo umme data miqe da sauri itama ganin Andi yau da kansa take ta shiga taitayinta tana shanye kukanta saidai hawayenta dasukaqi tsayawa ta kalli hajiya Maryam tace" Kin kyautamin Maryam sbd Andi ne kawai zai iya ceton Khalil Dina yanxu. Modibbo da kansa ya miqe yabawa mahaifinsa dake tattareda wata irin izzar mulki da cika Ido tareda razanarda mutane da kallo 'daya idan yayi maka Wanda kaf cikin zuriar zabeera mutum biyu ne suka 'daukosa sak alqasim zabeera mijin haj Maryam daya rasu sai MAHMOUD ZABEERA wanda beyi mulki ba Amma Yama wucesa a mugun miskilancin da kwarjini me ban tsoro. Shigowar Andi tasake saka kowa cikin tsoro da firgici Saida yayi zaman minti biyar tsit bayan gama amsa gaisuwar kowa kafin ya bude muryarsa me amsa amo yace" Khalilu da kanka zakayi bayanin abindake faruwa daga farko. Ba inda inda Khalil yasake koro Masa bayanin komai tareda hukuncinda Modibbo ya yanke Masa ya 'dora da fadin" Na aikata babban kuskure Kuma na amsa laifina nakuma karbi hukuncina Andi, Zanyi nesa da Nan Kuma bazan taba Bari maganar ta fitaba bare sunan zabeera ya baci, Nayi alqawarin daga lokacinda zan fita Nan zan aje sunan zabeera Dan kada gaba nayi Abinda zan kawo batanci gareku ba da...... Cikin firgici ummi tayi saurin zubewa qasa tana cewa'" Allah ya taimaki Andi Dan Allah Andi ya tausaya a sauqaqawa Khalil tsaurin hukuncinsa kada arabasa da sunansa da zuriarsa indai akan laifin wannan yarinyar ne Andi abasa dama yayi Mata saki uku bayan ancire cikin....... Maganar ummin yasa Andi dagowa ya kalli Modibbo Modibbon yayi saurin qasa da Kai Yana cewa'" Ayi Mata afuwa Andi uwa ce dake cikin firgicin rabuwa da 'danta. Kallonsa andin yasake hakan yasashi yin shiru Yana cewa" Allah ya huci zuciyar Andi da Abinda aishatu tafada. Kallonta Andi yayi tareda kallon baba Jamila yace" Aishatu matsayinki na mahaifiya kikeson a cutatarda 'yar wata sbd naki 'dan wannan ba adalcin Andi bane. Kallon baba Jamila yayi cikin sautin dayasata rudewa qafafunta suka hau rawa yace" Kinxo neman adalci anbaki adalci Kin aminta da auren 'yarki Dan haka 'yarki zatayi zaman sure bayan munyi bincike akan auren, Zaki bar 'yarki anan Kuma zata zauna cikin gata da aminci Zata raini cikinta a hannun matar 'dan uwansa MAHMOUD ZABEERA bayan haihuwarta anbawa mahaifiyarsa halak malak saimu sake daura musu aure, Aishatu kinason kashe abindake cikin tun baizo duniyaba to kece zaki rainesa har girmansa bayan zuwansa duniya an mallaka Miki shi halak malak. MUHAMMAD""fada sunan Yana 'daga sautinsa. Sai alokacin MAHMOUD ya dauke idanuwansa daga Kan Khalil da amatu sbd jin a hannunsa yarinyar zatayi rainon cikinda bai gama yadda da akwaisaba sbd aduniya shine yafi kowa sanin wannan ba halin Khalil din bane ya kalli inda Andi yakira sunansa ya taso cikin nutsuwarsa dake qarawa Andi ganin kwarjininsa ya qaraso ya tsaya gaban andin tareda sauke kansa cikin girmamawa yace" Allah yaqarawa Andi tsawon Rai. Matar 'dan uwanka zata zauna a hannun matarka har tsawon lokacinda zata haihu, Cinta da Shanta duk na hannunka, Ciwonta da maganinta na damqasu hannunka Dana matarka, Na damqa maka tsaron lafiyarta Dana Abindake cikinta sbd aishatu ta tabbatar Mana da AMATULLAH da abundake cikinta na cikin hadari a hannunsu Dan haka Kaine kawai Wanda na yarda dashi nabaka amanarsu a hannunka. Shiru yayi bai motsaba sbd Abinda andin yafada yaxo da wani al'amarine da kansa yake kasa dauka, 6arauniya a gidansa?ta Yaya zai iya Bari wannan yarinyar ta zauna acikin inda yake rayuwa Khalil dinma haryanxu yakasa yarda da shidin ne uban cikin wannan yarinyar ahankali yadan dago ya kalli gefen datake tsaye riqeda rigar Khalil sbd zuwa lokacin tafara firgita da abindake faruwa Jin hukuncin da aka yankewa Khalil daga farko taji bazata iya Bari tazama sanadin batawarsa da rabuwa da iyayensaba saiga zuwan wannan Andin Wanda ganinsa kawai yasa taji tsoro da firgici ya kamata gashi ana maganar riqeta ta haihu Ta Ina dakuma ta Yaya zata haihu Kasa riqeta qafafunta sukayi tsabar rawa shiyasa ta boye bayan Khalil din. Taro ya tashi kowa ya watse nagama magana abubukar a aika mahaifiyarsa gida tareda kayan abinci da jarin sana'a me kyau sbd itace kakar Zabeera na shida Inshallah. Modibbo a qarqashinka zaa kula sosai matuqa da AMATULLAH Ina fatar Nanda watanni kadan za'a bani zabeera na shida a hannuna. Kallon amatu yayi akaro na farko data saki fuska dukkaninsu Saida suka bude Ido sbd ganin murmushi akan fuskar tasa yace" AMATULLAH ni Andi nine gatanki keda Abinda yake cikinki acikin zabeera nayi Miki alqawarin baki kyakkyawar rayuwa keda Abindake cikinki sbd zalincin da khalil yayi miki da Wanda mahaifiyarsa ke shirin Yi na cutatar dake da Abinda ke cikinki Dan haka na Miki alqawarin idan har Ina Raye Kika haihu indai namiji sai yayi mulkin zabeera wannan shine babban adalcin dazan baki, Kece mace ta farko Kuma mutum ta farko data shigo zuriar zabeera a tarihi ki riqe wannan a ranki Dan haka karki Bari har abada Nasameki da illa ko laifin dazai sakani takaicin hukuncina sbd cin Amana,yaudara da qarya ba abubuwan da Andi ke yagewa bane. Kai Kuma Khalil hukuncinka na ranardazan daura maka aure da ita. Kowa yatafi nagama mgn. Hannu umme take Shirin dorawa akai tasaki kukan baqin cikin wannan alamarin Modibbo ya aiko Mata da mugun kallo Haj maryam ma dake Shirin fasa ihu Andi ya nuna musu qofa sunaji suna gani suka hadiye cikinsu bame iya Jan wani suka fito Babu me ganin gabanta tsabar tashin hankali. MAHMOUD ma ficewa yayi batareda yaqara ko second dayaba. Baba Jamila da Sha Taranta ta arziki aka kaita gidanta inda suka tsara komai Koda anxo bincike. ZARAH aka kirawo ita tazo aka damqa amatu hannunta wadda atake alokacin amatun tashiga ranta ta kalli amatun dake qara damqe rigar Khalil sbd hankalinta daya tashi gaba daya da alamarin sbd ita yanzu Tama rasa Ina aikin data zoyi yaje Sam sun rikita 'yar qaramar qwaqwalwarta. Kallon Khalil tayi tana sake matsesa tana girgiza Kai tace" Dr gida zani nafasa bana...... Hannu ya Dora a bakinta tareda girgiza Mata Kai Ya bude bakinsa daya gama nauyi muryarsa na nauyi a karye yace" Kije kibi ZARAH komai zai daidaita bazan Bari komai ya sameki ba na Miki alqawari, Kuma zansamu kawu nayi mgn dashi zan Masa bayani yanda zai fahimta Inshallah. Qura Masa Ido sosai take kallonsa sbd yadda dashi datayi dari bisa dari kafin ta daga Masa Kai tasakesa ahankali tareda kallon zarah dake Mata murmushi suka wuce. Bayan fitarsu Kai tsaye motar zarah din suka nufa suka shiga ta jazu sukabi ta bayan gefens Modibbo zuwa part dinsu dakeda nisa cikin zabeera din sbd kusan sune na qarshe. Umme nashiga palonta ta zube qasa tareda Dora hannu akai zata saki ihu juwairiyya tayi saurin rungumeta tana Kiran sunanta itama muryarta na karyewa dason yin kuka. Haj maryam ma kuka takeyi wiwiwi itada nuratu dake wani irin kuka tana kwantawa jikin momyn Tata sukam yau wace irin baqar ranace agaresu. ##mamuh# ______________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 13_* _mamuhgee_ ANNUR PERFUMES ANNUR PERFUMES!!!!!! JAMA'A MA'ABOTA SON QAMSHI DAN SANYAYA ZUCIYA Ina kuke kuzo ga sabuwar duniyar turare sabon tashe ANNUR PERFUMES sunkawo muku, Turarensu qarshene, Qamshinsu na daban, Kayansu tabbataccine, Aikinsu ingantacce ne shin kataba/kintaba amfani da ANNUR PERFUMES kuwa? To maza qarzayo karki Bari ayi badakeba dankuwa kayansu lamba dayane Kuma amintaccine masu guarantee domin kuwa mun tabbatar. ANNUR PERFUMES donjindadin customers munkawo muku dadadan turaruka na musamman masu nishadan tarda Amarya da uwar gida harma da angonta kamar haka turaren wuta humra kala daban daban kwalaccha Dana matsi na infection biki ko suna dyadya ko sari ina kano gaida layin massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka 07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo. ANNUR PERFUMES TURAREN WUTA KHUMRAH. KULACCAM MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI) DECORATIONS .. KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING) TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK! Koda zarah tayi parking bakin flat dinsu motat MD na gurin tabbacin Yana ciki, Fitowa tayi tareda zagayowa ta budewa amatu qofa tana murmushi tace" Muje ko amatu. Kallon flat din takeyi tana zaro Ido sbd tsarinsa da kyansa tun daga wajen, Fitowa tayi motar tana zare idanuwanta Kan kusan motaci biyar dake gurin a jere kowacce sai daukar Ido takeyi ta nufesu zata shafa zarah ta riqota tana cewa'" Muje ciki ki huta kina buqatan hutawa sbd hayaniyar da akayi gashi kinta kuka zai iya taba lafiyan babyn kinji Dan haka please ki kula. Kallon zarah din tayi tareda shafa cikinta tana cewa'' Wannan cikin zaki kula Dani ne har qarshen rayuwarki idan kina Kiran na haifesa Dan Babu uban komai aciki sai wainar iyami ta safiyar yau danaci. Magana kike?"zarah ta tambaya tana juyowa daga tura qofar babban palonsu. Qaqalo murmushi tayi taba cewa" Cewa nayi harna Fara kewar babata. Riqo hannunta zarah tayi suka shigo cikin palon tana cewa" Karki damu Inshallah zakiga jimawa sosai zakiga kin haihu lfy saiki koma gurin babah kafin daga baya saimu sake daukoki kidawo Nan shikenan kinzama ta Dr khalil dinmu. Dan sunkuyar dakai tayi tana qaqalo kunyar Dole tana Dan murmusawa saidai suna shigowa cikin palon ta fiddo idanuwanta gaba daya tareda Fara jujjuyawa tana sakin baki tace" Wayyo USI Zo kaga aljannar duniya a gidan Nan. Kallonta zarah tayi tareda sakin murmushi tana qarasawa ta ajiye gyalenta da keys din motarta tana nufar kicin da kanta ta dauko ruwa Mara sanyi tadawo ta dube robar ruwan ta zuba a cup ta jawo amatun data zage tana taba duk Abinda ya burgeta tana fiddo idanuwa tana Kiran sunan usi. Zaunar da ita zarah tayi tana miqa Mata ruwan tace" Sha ruwa amatu Kuma ki zauna kada ki Fadi da wannan zagayen da kikeyi idan kin huta zakiga komai ahankali tunda anan zaki zauna kibari ki huta tukuna. Kwankwade ruwan tayi ta miqawa Zara cup din idanuwanta nakan dining dataga me aikin zarah din na jere wasu irin manyan kulolin abinci masu daukar Ido da fresh fruits daga fridge sai hayaqin sanyi suke ta hadiye yawu tana satar kallon zarah dake sake zubo Mata ruwan fuskarta na bayyanarda annashuwar datake ciki ta Basu amatun da akayi. Ganin yanda take kallon gefen dining yasa zarah juyawa ta kalli dining din saita fahimci kamar yunwa amatun keji ta juyo tasaki murmushi tana cewa' Muje nakaiki kifara watsa ruwa zakifi Jin dadin cin abinci. Bedroom 'din dake kusa da nata takaita da kanta tasake gyara Mata shi ta sauya Mata zanin gado tareda kunna AC ta sauyo Mata room fresheners tana cewa' Duk Wanda kikaji bakyason qamshinsa kifadamin sai a cire Miki shi kada ya sameki. Toilet ta 'dan wanke Mata sama sama Dan baida dattin komai sbd babuma Wanda yataba amfani dashi dandai ita dana bedroom dinta take amfani batama shigowa Nan dakin gaba daya bare MD dako nata bedroom din baitaba shigaba bare yashigo wannan. Towel tabata sabo fil tareda kawo Mata shower gel din jaggins da sabbin undies da wata doguwar jallabiya Mara nauyi me dogon hannu ta fice tana cewa' idan kingama zankawo Miki abincinki har daki kibi ahankali a toilet karki Fadi Dan Allah. Gaba daya hankalinta nakan dakin da ake nufin ciki zata zauna batamaji me zarah din ke fada ba ta fada Kan gadon da qarfi Yana jujjuyawa tace" Wayyo amatu ko daga Nan aka tsaya qaramin burinki yacika kinshiga cikin Masa kudi. Sai data gama juye juyenta akan gadon AC na shigarta tareda qamshi masu sanyin Dadi kafin ta miqe ta cire kayanta ta shiga toilet din Wanda tuni Shima ta rude da haduwarsa Wanda badan tayi aiki agureren masu girma ba kamar irinsu blue fox da bazata San ya ake amfani da irin wannan toilet din ba. A toilet din tsayawa tayi gaban tangamemen madubin tana duba kanta tana shafa cikinta sai alokacin ta dawo hayyacinta gameda abinda yake faruwa ta lumshe ido tana tunano Khalil da halin dayake ciki, Ita Sam Abinda Bata ganeba shine Haj Mama data aikosu wannan aikin kukan datakeyi na qarya ne kokuwa? Idan har kamar yanda tace MAHMOUD da KHALIL yayantane to meye banbanci Dan ance Khalil ne ba MAHMOUD ba? Shin wannan abindaya faru yau din menene ainihin Abinda yake nufi sbd saitake ganin kamar yanda aka tsaro abin kamar ya sauya taku me matuqar hadarin gaske, Ta Yaya zata haihu bayan batada ciki, Ta Yaya zata auri Khalil bayan ba ranar haihuwa tunda ba ciki, Shogowarta fa anan kamar tashigo wani mugun keji ne ta rufe kanta sbd tunda Babu ciki Babu ranar haihuwa, Babu ranar haihuwa Babu ranar tafiyarta.. Shiru tayi tana jinjina Kai tace" Ina buqatan ganin Haj Mama naji ni meye matsayina a yanxu. Wankan tayi tana shaqar gel din me qamshin Dadi tafito ba wani shiririta ta shirya cikin kayanda zarah din takawo Mata tana cikin saka hula akanta zarah din tashigo daukeda tray din kayan fruits hafsatu me aikinta na bayansa daukeda tray din abinci. Washe baki tayi tana zama qasa Kan qaramar carpet din dake gefen gado tana cewa" Anty sannu da aiki kinata fama tunda nazo. Aje tray din zarah tayi tana murmushi tace" Amatu tunda aka banike nasan hidimarkice yanzu nafara harsai kin haifarmana me kama da Dr dinmu kokuma gwara dai ki haifar Mana me kama da MD dinmu dagani har Dr din saimunfi sonsa sbd MD shine 'dan uwanda Dr yafiso acikin familynsa gaba daya, As for me nikuma MD shine rayuwata. Apple amatu tayiwa babbar gutsura tana ci tace" Anty Dr Yana ina yanzu? Yar dariya zarah tayi tana zuba Mata Salad Kan dafaffen dankalin da aka dafa matashi da zallar Naman kaza da cabbage tace" Dr Yana bangarensa Amma nasan tunda matarsa da babynsa na Nan bazamu Kai dare batareda yazoba Dan haka ki kwantarda hankalinki Dr nanan zuwa idanma baizoba zankirasa yazo. To kawai tace tana cika bakinta da dankali da nama sbd 'dadin da abincin take Mata tace" Anty idan nagama cin abinci mezanyi Kuma?? Bacci zakiyi ki huta amatu kafin zuwa gobe zanfadawa MD saimu kirawo Dr dina yazo afara dubaki da lafiyar baby. Sarqewa tayi da qarfi tasaki tari Jin Abinda zaran tace. Da sauri Zara ta dauki ruwa tana miqa Mata tana Mata sannu tace" Amatu kodai abincin be Miki bane?? Girgiza Kai tayi da sauri har lokacin tana tari tace" Ba Dr ne zai ringa dubani ba tunda shine Mijina?? Aje cup zarah tayi tana cewa'' Aa Dr bashi zai ringa dubaki ba munada Dr dinda zai ringa dubaki wato gynecologist Dr likitan Mata Wanda Nima shi nake gani sbd matsalar rashin haihuwarta. Shiru amatu tayi tana tura abincin kawai sbd tasan ba jimawa asirinta zai tonu duk aka kawo wani likita yadubata zaisan batada ciki Andi sakawa zaiyi a harbeta da kibiya sbd da gaskia ta fito. Tana gamawa zarah tasata kwanciya bayan tayi sallah ta rage Mata sanyin AC ta fice bayan tasa hafsatu ta gyara gurin suka ja Mata qofa. Shiru tayi tsawon mintuna tana tunanin goben idan likita yazo Miqewa zaune tayi tana cewa'' Dole Naga Dr khalil yau nafada Masa kafin goben Amma dai yanzu inason Fara magana dasu usi. Jakarta da aka saka cikin wardrobe ta bude ta dauko matacciyar wayarta ta lalulo numbrn USI ta Danna Masa Kira. ##mamuh## ______________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins hudu golden and red sbd girmansa ga kalar dasuka qara qawata palon, Shine palon da dukkanin familyn ZABEERA ke meeting acikinsa qarshen kowane wata to wannan watan ma hakan ce tafaru dukkanin daukacin zabeeras dake jahar suna cikin palon kusan su sama da arbain kowanne yasamu guri ya zauna ana tsimayin fitowar me kankat wato Modibbo Wanda fitowarsa tayi daidai da tsit da gurin ya dauka sai gaisuwa kawai dake tashi Yana amsawa ta hanyar 'daga Kai batareda ya bude baki ba. Zama yayi Yana bin kowa da kallon jinjinawa na riqe wannan al'adar dasukayi har idanuwansa suka sauka akan MD ZABEERA wanda ke zaune can bayani iyayensu dukkanin hankalinsa gabaki daya Yana Kan waya dayake karanta email din saqo daya shigosa, Kallon zamansa Modibbo yayi har zuwa fuskarsa dake daukeda wani irin kwarjini da haiba ya jinjina Kai Yana cewa' Tabbas Babu wani zabi daya wuce akan mulkin zabeera ayau taron naka ne. ZARAH kuwa duk da ta shige cikin 'yan uwa da qawayenta 'yan uwanta Amma hankalinta na kansa akai akai take satar kallon gefen dayake sbd ganin yauma dai kamar ko yaushe arayuwarsa ya kebe ne daban duk da yanzu duk Wanda yashigo cikin qanne da tsaransa ma harma da wainda suka girmesa zuwa sukeyi suna gaidashi Wanda Shima yawanci daga Kai ne kawai bai cika bude bakinba Yana amsawa musamman sbd rashin sabo da Yan uwan duk wasu da dama baisansuba. Khalil ne abokin zamansa akowane meeting tun quruciya Amma yau Khalil din baishigo da wuri ba Abinda baitabayiba ranar meeting wato latti. Khalil kuwa yanacan ne hanyar gidansu amatu data Hana rayuwarsa da zuciyarsa sukuni, Tsawon kwanakin Nan bayan haduwarsu da ita bincike yayi me kyau akanta sbd shigo da ita a rayuwarsa Dan sauya musu ingantacciyar rayuwa dakuma tunaninta daya kasa fita ransa da kansa, Tabbas yasan babban laifine a zabeera neman aure a waje wanda bama ataba yiba asai yanzu dazai Fara shigo da tsarin karya dokar manya sbd bayajin zai iya hkr da maganar amatun a shirye yake daya tallefi yarinyarda zuciyarsa ta riqe a gani na farko Koda hakan na nufin barin zabeera ne barema yasan zai shawo kansu da taimakon MD. Babban rashin sa'ar dayaci shine bayan isarsa kawu yayi Masa bayanin aiki tasamu ta tafi training Amma dai yabasa numbernta Dana usi din duk da shi Usin Rakata kawai yayi dawowa zaiyi. Koda ya karba lambar agogo ya duba yaga yayi lattin meeting ga umme Bata gansa ba sai kiransa takeyi sai bai tsaya Kiran numbrn ba yayi saving tareda dawowa zabeera cikin sauri sbd yasan zuwa yanzu anfara meeting din. Yana qoqarin shiga gate din zabeera yaga motar 'yan jarida na tsayawa ta gate suna qoqarin gyara cameras dinsu ya Dan tsaya Yana kallonsu cikin mamakin meya kawosu musamman ma da zabeera basa muamala da duk Abinda zai hadasu da 'yan jarida sbd tsira da mutuncinsu da sunans ahalin, Ganin yayi latti sauri yakeyi yasa bai tsayaba yashigowarsa, Yanayin parking harabar gidan Kiran nuratu nashigowa wayarsa ya saki siririn tasaki Yana dafe kansa dake Masa ciwo sbd rashin bacci kwana biyun yayi rejecting kiran ko Ina bai tsayaba Kai tsaye ya nufi palonsu na meeting dasuke Kira da zabeera hall. Yana shiga yaga har anyi nisa yayi saurin yin gefenda ya hango md zaune Ya lumshe fararen idanuwansa ya kwantarda kansa ta baya jikin kujerar dayake Yana sauraron Abinda ake fada cikin nutsuwa. Qoqarin miqewa alhaji qarami yakeyi zaiyi mgn suka Fara jiyo hayaniya me 'dan qarfi tana tashi daga wajen qofa, Sharewa sukayi alhaji qaramin yafara bayani Amma sai gaba hayaniyar keyi Alhaji qarami ya kalli yakub babban 'dan alhaji qaramin yace" Yakub dubo meke faruwa ne. Miqewa yayi ya fita Dan dubowar sukuma suka cigaba da meeting din. Mintuna biyu da fitar yakub sai gashi yadawo da sauri yazo gefen babansa yayi qasa da murya yafada Masa abin dake faruwa da sauri ya kallesa Yana cewa'" Mene? Kowa najin haka yayi tsit suna jiran jin abindake faruwa. Je kashigo dasu""alhaji qarami yace Yana qoqarin cigaba da bayanin dayakeyi. Sallama sukayi wadda tasa kowa juyawa hadda Shima dazaiyi maganar duk suka kalli qofar wadda ke seti tana kallon center inda Modibbo yake zaune Shima sbd ba'a taba barin wani shigowa ba idan suna taron yasashi dakowa ya kalli qofar. Baba Jamila ce agaba amatu na bayanta fuskarta rufe da doguwar hijab dinda tasaka fuskarta da idanuwanta a kumbure sosai sunyi jajir tsabar aboniki dasuka Sha kamar wadda tayi wata biyu tana kuka. Tsit sukayi kowa palon na aika musu da kallon mamaki da jiran bayani Amma sai qif qif baba Jamila keyi da idanuwanta tana sunkuyar da Kai. Alhaji qarami ne ya kalleta tareda kallon amatun dake bayanta kafin ya kalli qafafunsu har zuwa zamansu ya gyara murya yace" Malama Yaya dai?? Lafiya?? Daga Ina?? Saurin zubewa qasa tayi tareda sauke kanta qasa cikin rawar murya tanason fashewa da kuka tace" Ranka ya Dade adalci nazo nemarwa 'yata..., Kowa kallonta yayi wasu Kam Kai tsaye kallon mahaukaciya suke Mata mamakinsuma yanda akayi tashigo zabeera harta iso Nan din. Cikin mamaki alhaji qarami ya miqe ya qaraso gurinta ya tsaya Yana cewa'" Malama adalci kike nema ai banan ake zuwaba, Mu Nan Kinga Muna wani taro ne me mahimmanci kinyi batan hanyane kije security zasu nuna Miki qofar fita...... Girgiza Kai tayi wannan karon tana fashewa da kuka Mai shiga zuciya tana bubbuga kanta. Yanxu Kam mamakinsu yafara cirewa sai fargaba Kamar daga sama taji saukar muryar dattijo me ran qarfe, Muryar data saka 'yan hanjinta kadawa Dan tsoro da firgita da wani irin amo yace" Idan da kanki a hayyacinki kikazo Nan kifadi Abinda yakawoki kokuma ki hadu da hukuncin kutse da datse mahimmin Abu acikin zabeera. Jan hanci tayi tana shage hawayenta dasukaqi tsayawa murya na rawa tace" Ranka ya dade 'yatace gatanan cikine a jikinta...... Cikin tsawa me qarfi alhaji qarami ya e" To Nan asibitine ko gidan aurenta dazaki...... Uban cikin Yana Nan"""ta katsesa cikin rawar murya tana sake bulbulo da ruwan hawaye. Atake gurin yayi tsit kamar ruwa ya cinyesu musamman Modibbo daya gyara zama Yana kallon matar da kyau kafin ya dago ya kalli amatu dake tsaye har lokacin tana matso hawaye cikin hijab. Kallon amatu yayi cikin wani irin amo yace" Ke yarinya bude fuskarki kiyi bayaninda mahaifiyarki keson fada saidai duk Abinda zaki fada kifara tunanin a inda kike. Qarar wayar Dr khalil ce ta katse maganar Modibbo wadda tasa kowa juyowa ya kallesa da sauri ya Danna wayar tareda miqewa ya fita da sauri Yana magana qasa qasa sbd daga asibitinsane ake Kiran wasu takardune da ake buqata emergency yace suzo su karba Nan gida. Harabar gidan ya nufa gurin motarsa yana tareda budewa ya dauko takardun cikin Burnet din motar ya nufi bakin gate ya fita Dan miqawa Dr ashir. Sama sama yayi Masa bayanin takardun sbd hankalinsa dake Kan 'yan jaridar da har lokacin suna gurin take yaji yakasa samun nutsuwa da hakan, Meke Shirin faruwane? 'yan jarida a qofar zabeera, Ga Kuma wasu baqi aciki suna maganar anyiwa 'yarta ciki..... Da matsala yafada Yana sallamar Dr ashir ya juya ciki da sauri Yana tunanin Dole da akwai inda matsala take, Me zaisa wannan matar su gayyato 'yan jarida??anshirya hakan ne Dan idan baa karbi cikin bane kokuma me?? Something is definitely fishy mezaisa tazo da masu jarida ita Bata damu da mutuncin 'yarta bane idan Yan jaridar suka watsa to kodai tanada wani manufa be??? Oh no.." yafada da sauri tareda yin ciki da sauri haryana hadawa da gudu gudu... Karo yayi da mutum Wanda yasashi yin baya zai Fadi USI yayi saurin rikosa Yana cewa'" Dr. Da sauri Dr khalil din ya dago Ya kalli Usin mamakinsa a bayyane Dan komai nasa ya nuna mamakin cikin sauri yace" Usman? Kaine anan? Me kakeyi anan?? Kallonsa Usman yayi Yace" Aiki amatu tasamu anan...... Saurin gintse bakinsa yayi sbd shaf ya manta Abinda ya kawosun., Ya shafo kansa Yana waskewa yace" Dr kaima me kakeyi anan din??? Kafa Masa Ido Dr khalil yayi ba Wasa a fuskarsa yace" Wane aiki ne amatu tasamu anan din?? Ina amatun take???? Shiru yayi Yana shafa Kai Yana qoqarin hado qarya Dr khalil ya katsesa da cewa" Ina amatun? Rasa yanda zaiyi yayi yace" Tana ciki tashiga da wata Mata..... Wattt??? Yafada da qarfi cikin firgici da tashin hankali yace" Meke faruwa? Me sukaje yi? Infact meya kawoku Nan din nakeson ji""zuwa lokacin yafara hasala yace" Kuma wlh karka kuskura kamin qarya. Kame kame usi yafara Yana neman yanda zaiyi saidai gskia zai fadawa Dr khalil idan yaso qila shi zai taimakesa ya shawo Masa Kan amatun kar tayi Abinda zatayin Kallonsa yayi tareda jansa gefe yace" Dr Dan Allah kayi alqawarin zaka taimaki amatu bazakayi Abinda zai jefata hadariba Dan Allah kayi wannan alqawarin. Cikin zaquwa Dr khalil din yace" Koba Dan alqawarinka ba bazan taba Bari amatu tashiga hadariba zan tsaya Mata ako Inane just tell me. Cikin fargaba Usin yafada Masa yanda amatun tayi da hajiya aisha saidai ya boye Masa da yardar amatun nuna masa yayi kamar tursasata hajiyar tayi sbd amatun ta daukar Mata kudi. Tsit yayi kamar ruwa ya cinyesa Har wani duhu duhu idanuwansa ke gani sbd tsananin tsoro da firgicin zancen, Ita umme ko tunanin hadarinda zata jefa 'yar mutane batayi da kantama tunda komai jimawa dai wataran gaskia zata fito, Idan ita amatu hankalinta bai Kai ba ita meyasa zatayi hakan?? Qarin tashin hankalinsa MAHMOUD za'ayiwa wannan mummunar 6ata sunan Haqqinsa bazai bar umme ba hattasu yayanta sai haqqin MAHMOUD ya shafesu Dan haka bazai Bari tadau wannan alhakinba dazai ja Mata azaba gaban Allah hakama bazai Bari rayuwar 'dan uwansa ta lalace ba hakama amatu rayuwarta nacikin mugun hadari..... Da sauri ya kalli usi yace" Usman Yi sauri kabar Nan katafi gida namaka alqawarin dawo da amatu Babu Abinda zai sameta maza katafi karka fadawa kawu komai.. Da gudu ya nufi ciki yayi hanyar palon Yana adduar Allah yasa amatun Bata bude fuskartaba Yana Isa ya fada palon da qarfi daidai lokacinda amatun tariga ta bayyana fuskarta akace ta fada cikin waye ajikinta,meye alaqarsu dame cikin?¿ Bude baki tayi hannuwanta da qafafunta na rawa zuciyarta na harbawa da qarfi zatayi magana tana kallon inda MAHMOUD ke zaune har lokacin idanuwansa lumshe Kuma duk yana jin abindake faruwa kawai dai ba huruminsa bane shiyasa ko hankali bai badaba, cikin wani irin sauri Dr khalil ya dako tsalle ya fado tsakiyar palon tareda cewa" Allah ya taimaki Modibbo nine. Wattttt????umme tafada da sauri tareda miqewa tsaye tareda haj Maryam Nuratu ma da antynsa juwairiyya duk miqewa sukayi cikin tsananin firgici Take palon yadauki hayaniya cikin rasa abin fada alhaji qarami yace kowa yatafi antashi meeting. Hayaniya aka Fara saidai yanayin Modibbo yasa kowa yin tsit suka Fara sulalewa suna ficewa. Kaf kowa ya fice Banda uwayensu maza da 'yannansu maza sai iyaye mata hatta MAHMOUD na gurin bai fitaba lokacinda yaji muryar khalil amatsayin me cikin yasashi bude Ido ahankali ya sauke Kan amatu dake gefen Khalil din tana kallonsa cikeda mamakin daga Inda ya fado. Kallonsa takeyi tanason Kiran sunansa Amma ganin yanayinsa ta tana hango tsananin 6acin Rai da takaicinda yake ciki, Idan har da khalil da MAHMOUD yayan hajiya mama ne kamar yanda tafada mata to acikinsu duk Wanda tace shine me cikin ta cecesa daga hawa mulkinda zaa salwantar da rayuwarsa to kenan duk dayane koba komai zatafi farin cikin kubutarda Dr khalil sbd kurkinsa akansu. Da hanzari umme ta qaraso gabansa ta kalli cikin idanuwansa cikin 6acin Rai tace" Me kake fada? Maza maza fice wannan ba Abinda ya shafeka bane...ba magana nake maka ba""ta fada cikin tsawa da firgici. Gyaran murya Modibbo yayi akaron farko bayan shock din daya samu na daqiqu ya kalli khalil tareda kallon amatu dake kallon Khalil din cikin rashin Jin Dadi qunci da bacin ran datake hangowa cikin idonsa. Khalilu ta Yaya kazama uban cikin jikin yarinyar na??? Hadiye wani yawu me mugun daci yayi sbd dai gskia bazata faduba Dan idan yafada gski umminsa da amatu duk suna cikin hadari Dan umminsa har zamanta cikin zabeera saiya ware. Rintse ido yayi ya budesu suna kadawa jajir take jijiyoyin kansa suka firfito sbd qarya ba halinsa bane bare wannan qaryar datafi kowace muni. Muna sauraronka Khalil kafin fushinmu ya sauka akanka kayi bayani"cewar alhaji qarami. Sauke Kai yayi daga kallonda Modibbo ya tsaresa dashi me girgiza jarumtarsa yace" Mun jima muna qaunar juna tsawon shekaru uku Nasan bazaa Bari na aurotaba shine mukaje wani guri aka daura Mana aure.....tassssssss Umme tasakar Masa wani gigitaccen Marinda Saida ya zube Kan gwiwoyinsa tareda sauke Kai. Cakumo amatu tayi cikin tsananin 6acin Rai tace" Modibbo ba gskia yake fadaba Khalil bazai taba aikata wannan qazamin aikinba wannan ita zata fada ubanda ya Mata ciki Amma badai Khalil ba....hannu ta daga zata kaiwa amatun Modibbo ya daka Mata tsawa da cewa" Aishatu ki dawo hankalinki ciki ne ajikinta kada hannunki ya sauka jikinta.. Ke matso fili ki fada Mana Abinda yafada gskia ne kokuwa?? Fitowa tayi daga bayan Khalil din tana kallon idanuwan umme dake fitowa da ruwa tace" Eh gskia ya fada. A Ina kuka hadu?? A asibitinsa. Shekara nawa yanxu da auren?? Rawar murya tafara tana neman dufewa tace" Daya. Aikuwa take kowa yaqarin tsit cikin tashin hankali. ##mamuh# ______________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.     Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku Æ´an biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 14_* _mamuhgee_ ANNUR PERFUMES ANNUR PERFUMES!!!!!! JAMA'A MA'ABOTA SON QAMSHI DAN SANYAYA ZUCIYA Ina kuke kuzo ga sabuwar duniyar turare sabon tashe ANNUR PERFUMES sunkawo muku, Turarensu qarshene, Qamshinsu na daban, Kayansu tabbataccine, Aikinsu ingantacce ne shin kataba/kintaba amfani da ANNUR PERFUMES kuwa? To maza qarzayo karki Bari ayi badakeba dankuwa kayansu lamba dayane Kuma amintaccine masu guarantee domin kuwa mun tabbatar. ANNUR PERFUMES donjindadin customers munkawo muku dadadan turaruka na musamman masu nishadan tarda Amarya da uwar gida harma da angonta kamar haka turaren wuta humra kala daban daban kwalaccha Dana matsi na infection biki ko suna dyadya ko sari ina kano gaida layin massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka 07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo. ANNUR PERFUMES TURAREN WUTA KHUMRAH. KULACCAM MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI) DECORATIONS .. KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING) TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK! ************** Ringin numbern usi din keyi harta katse bai daga ba tasake Danna Kiran tana cewa' Usi idan muka hadu saina fasa maka baki da kai tunda har zaka iya bacci baka kirani kaji Yaya ta kasancemin ba a wannan zabeerar da kallo daya Andi da Modibbo sukewa mutum sai cikinsa ya mur'da, Uwa uba arasa gurin ajeni sai anan cikin wannan me bada tsoron da matarsa. Kira biyar tayi Masa Amma baa daukaba takira wayar iyami cikin sa'a kuwa ta dauka Nan suka jima suna mgn iyamin na maimaita Mata karta taba duk Abinda zata gani na kowa karkuma ta jawowa kanta fitina ko rigima ta jawo musu kafin aka miqawa kawu wayar Shima dai yayi Mata maganar karta taba abun kowa sbd kada 'yan kudin Nan dasuka samu su qare a gun kashe rigima Shima usi sunfada Masa kada ya kuskura ya janyo rigima sbd tanadin kudin Nan zasuyi sbd abinci dakuma qarasa hada takardun komawarsa karatu. Fadawa lafiyayyan gadon tayi ta kwanta tana lumshe ido bayan tagama wayar Tai wani juyi tana lulluba da bargon me shegen laushi sbd sanyin AC dake ratsata ta lumshe ido tana cewa'" Masu kudi wato ko a gurin bacci sunfi talaka samun nutsuwa Da agidanmu ne da yanxu radion kawu da qarar dakan turmin maman junior da qarar bude tukunyar maman basiru sun Hana mutum bacci, Rufe idanu tayi tana sake gyara kwanciya take bacci me dadi yayi gaba da ita ga gajiya ga lafiyyan abinci dataci ga lafiyayyan gurin kwanciyar dakuma sanyin AC ga ba hayaniya ai Dole baccinta yau yayi dadi. Saida garin ya hantse ta tashi tana wata irin miqa me Dadi fuskarta a sake da farin cikin irin baccin data samu tana qoqarin saukowa gadon ne zarah tashigo daukeda sababbin brushes da toothpaste masu kyau tana kallonta tace" Amatu Yaya? kintashi lfy? Ya babyn dr? Qarasa saukowa gadon tayi tana sake yin wata doguwar miqar datasa zarah saurin ajiye kayan hannunta tana riqeta tace" Amatu zakiwa kanki illa idan kina irin wannan miqar Idan kinajin gajiya ne za'asa ayi Miki tausa ahankali Amma Dan Allah ki daina kinji?? Kallon sakarai amatu ta Mata Jin hadda miqar ma yanxu wani tsurku zaa kawo sbd ciki... Amma dai ko yayane bazata Bari banxa ta wucetaba tubda damace tasamu gwara ta dama kafin Takoma inda tafito Dan haka sai ta 'dan yamutsa fuska tana 'dan dafe bayanta tace" Anty zarah ko Ina jikina ciwo yakeyi na gajiya shiyasa nake 'yar miqar ko zanji jikin ya sake Amma tunda kince za'amin tausa inaga idan anyi zanji jikin ya saki. Murmushi zaran tasaki tana sakinta Takoma gaban mirror ta dauko toothpastes din different flavors kusan kala biyar tace" Ga Macleans ki bude kowanne kiji Wanda qamshinsa ya Miki Wanda bazai tayar Miki da zuciyab saiki ringa amfani dashi. Karba tayi tana washe baki tana duddubasu tace" Duka ma sunmin abarminsu kowanne ma qamshinsa zaimin sauran gida zanje dasu idan zantafi. 'yar dariya zarah tayi tana girgiza Kai rashin damuwar amatun na sake burgeta musamman data 'dan Fara lura tun jiya inda amatun tafito tana tareda yunwa gskia Dr be kyautaba barinsu su wahala haka tana matsayin matarsa bayan duk arzikin dayakedashi. Fita tayi Takoma kicin ita Kuma amatu toilet tashiga tafara yin brush da kusan toothpaste kala hudu kowanne saidata fasa ta 'dan lakata tayi dashi take bakinta suka ringa bada wani qamshi masu Dadi dasuka sakata yin wanka cikin nutsuwa da annashuwa. Tana fitowa saidatayi sallah kafin ta shirya cikin doguwar rigar jallabiya Mara nauyi Wanda duk zaran ce takawo Mata daga gani duk nata ne Amma suka sabbi ne Babu Wanda ta taba sakawa. Tana cikin fesa turare tana lumshe ido cikin jin Dadi tace" wainnan turaren dasu zankoma gida idan zankoma ma komai saina dauka naje dashi bazanga irin wannan Batinba nabariba. Turarukan ta kwashe duka tabude wardrobe tazubasu cikin Jakarta daga can qasa ta rufe zip din tadawo gaban mudubin tana gyara zaman rigarta a jikinta saiga zarah tashigo tana kallonta Jin dakin yacika da qamshin turaruka yasata Dan 'yin tari tana cewa'" Amatu wannan turarukan bazasu cutatar dakeba kuwa¿ Qamshin yayi yawa Zo muje dining muci breakfast idan Kuma akwai Abinda kike buqata ba Wanda akayi ba sai hafsatu ta Dora miki ga Dr khalil ma yazo Yana palon MD suna Magana. Ba qaramin Jin Dadin zuwan Dr khalil tayi ba sbd sanar dashi Abinda su zarah din ke shirin Yi na Kiran wani Dr shiyasa ta farayin gaba tana cewa'' Ni komaima aka dafa yamin zanci Amma Dr nakeson Fara gani anty zarah Dan Allah kinji. Biyota tayi tana cewa'' Wannan rashin hkr haka amatu bazaki jira yagama yazo yasameki har dakin ba. A palon ganin Dr khalil baida lokacin fitowa daga gurin MD yasa ta marairaicewa zarah fuska tana taba cikinta Take zarah ta tashi da kanta ta hado Mata nata abincin a tray sbd kada yinwa tai Mata illa sbd cikin dake jikinta bazata iya jiransu ba. Dakinta Takoma acan tayi zaman Yan bori akan carpet tafara cin lafiyayyan breakfast din tana bude plate din farfesun kifin da akayi kawai sbd ita dayaji kayan qamshi da 'dan yaji batasan lokacinda tasaki dariyar farin cikiba tana diba takai bakinta saiga Dr khalil yayi knocking yashigo fuskarsa tayi wani iri na yanayin damuwar dake tattare da ita. Tsayawa yayi daga bakin qofar ya qura Mata ido yanda take cin abincin sosai cikin Jin dadinsa dakuma bayyanarda baqone agareta sai yaji jikinsa yasake yin sanyi ya rintse ido Yana Jin zafin zuciyarsa na qaruwa sbd baisan ta Ina zaifara da wannan qaqqarfar rigimarba sbd Nan ana Magana ne akan ciki da aure Wanda baa Wasa dasu sbd komai dadewa gskia zata fito idan akwai idan Babu, Ta Yaya zaifara neman mafita? Ta Yaya zaifara neman inda mafitar cikin amatu zata fito? Gasu usi yanxu da Dole nauyinsu zai dawo kansa sbd inganta rayuwarsu su duka din ta yanda har abada komai zai faru bazasu Yi shaawar sake komawa rayuwar dasuka fito ba, Idan har amatu zata iya saka kanta acikin irin wannan masifar me hadari akan kudi to tabbas zaiyi amfani da kudi da qarfinsa ya wadatasu da dukkanin abin buqata har sai amatu ta cire kwadayin kudi a ranta, For now Abindake gabansa shine mafitar cikin jikinta da ake zaton akwai Amma bazai Yi rushing abubuwan ba tunda tana Nan hannun MD yasan Babu abin dazai sameta she's morethan safe anan Dan haka zata cigaba da zama anan zaije gurinsu kawu zaifara aikin kulawa dasu daga yanzu. Gyaran murya yayi Yana sake gyara tsayuwa tayi saurin dagowa tana ganinsa ta miqe tana qarasa kwankwade sauran kakkauran tea din dake hannunta cikin cup tace" Dr tun jiya kaina ke neman bugawa da son ganinka na..... Quite amatu""yafada cikin 'yar tsawa ransa a 'dan bace. Cak ta tsaya tana kallonsa ganin yanda bacin Rai ya bayyana a fuskarsa sosai sai hakan yasa jikinta yin sanyi tayi qasa da Kai tana kallonsa fuska a marairaice. Ya dauke Kai sbd ganin zata sa zuciyarsa saukowa yace" Kinsan zaman da kikeyi acikin zabeera? Saurin matsowa tayi tareda katsesa da cewa" Wlh dr aiki Na.... Amatu just keep quiet please, Wane qarya kike tunanin zakimin bayan duk abin daya faru jiya gaban kowa and yanxu Ina tambayanki kinason kawo min wani different story Ki saurara kiji usi yafadamun komai Wanda yasa nake mamakinki har yanzu Amatu har kudi yayi mahimmancin dazaki 6ata sunan wani akansu, Rayuwarsa kike neman batawafa gaba daya Shin kinsan shi Wanda kikaso batawa rayuwar shine Wanda nafiso a rayuwata fiyeda kowa bayan iyayen dasuka haifeni??? Tsit tayi tana sake yin qasa da kanta cikin rashin Jin dadin yanda yake maganar cikin tsananin 'daci da bacin Rai akaro na farko a rayuwarta dataji nauyin wani mutum. Juyowa yayi Yana kallonta yacigaba fa cewa" Amatu wannan duk Abinda kike tunani ya wuce Nan Wannan alamarin babbane bazaki ganeba sbd tunaninki kawai ya ta'allaqa ne kawai akan kudin dazaki samu Meyasa kudine kawai Abinda kike gani amatu wannan alamarin babbane meyasa bazaki ganeba, Umme mahaifiyatace duk Abinda tasaki kizo kiyi tayine sbd rashin mafitar datake gani tana ciki Gashi yanzu kunsani a tsaka me wahala bansan yazanyi da kowannenku ba, ku duka bazan iya barin wani Abu ya sameku ba kokuma wani mummunan hukunci ya hau kanku sbd kowaccenku nada matsayi me girma agurina gashi yanzu ta kowane bangaren nine zansan Yaya zanyi. Kuna tunanin MD sakarai ne daza'a Zo Kai tsaye afadi wannan alamarin ace shine ya zauna ya dauka kawai sai sunansa ya baci? Tabbas dakun aikata babban kuskure sbd ilimi da matsayin MD yawuce inda umme ke tunanin ke bakyama ciki sbd komai ma qaramin kanki bazai ganeba gameda waye MD Dan haka ki saurareni da kyau kiji, Daga yanzu dakike cikin zabeera duk Abinda zakiyi da Wanda yake faruwa ki tabbatarda kina sanar Dani, Karki kuskura Koda Wasa kiyi maganar Abinda yake ainihin gskiyar maganar Nan da kowa Koda kuwa zarah ce ko a waya karkiyi maganar da USI sbd kadama wani yaji, Kince kinada ciki Dan haka zakici gaba da zama a me cikin harsai na samu mafitar fita cikin wannan shirmen da kuka faro, And bayan zarah karkiyi muamala da kowa acikin zabeera batareda izininaba lastly Kuma karki yarda kiyi Abinda za'a zauna meeting akanki kokuma asan asalin waye ke acikin zabeerar Nan hakama karki yadda kiyi Abinda zaisa a fahimci bakida ciki idan nace karki kuskura I mean kada Koda Wasa ki kuskura Duk Abinda kike so kifadamin zan kawo Miki shi Kuma kullum zan ringa zuwa Nan dubaki kafin na wuce office da idan nadawo and you better behave yourself duk da MD baida lokacin batawa agurin matarsa bare ke to yanada lura sosai zai iya ganoki a lokaci daya hakan Kuma na nufin samun matsalarmu.. Kin fahimci dukkanin abubuwan Dana fada right?? Gyada Masa Kai tayi ahankali tana Dan satar kallonsa sbd ganin yadauka zafi yanda yaketa fadan. Ajiyar zuciya ya sauke tareda kallonta Yana sassauta fushinsa yace" Shikenan karki saka damuwa ko tsoron komai aranki Ina Nan Babu Abinda zai sameki, Usman ma tun jiya ninace kada ya dauka wayanki Koda kinkira sbd nasan zakuyi Magana Kuma wani zai iya jinku idan nafita zan Masa Magana yadauki wayarki tun jiya nasan labari Yana bakinki Wanda zaki basa. Sai alokacin ta saki murmushi tana kallonsa Jin ya sauko gaba daya ta washe baki tana cewa" Duk da haka saina fasa Masa baki idan nagansa tunda yaqi daga wayar. Kallon fuskarta yayi Yana sauke wata ajiyar zuciya sbd gaba daya tagama sauke fushin dayazo dashi ya sakar Mata murmushi Yana cewa' Shikenan basai idan kingansa ba zaki fada bakin Makaranta zai tafi Kuma hostel zai zauna infact idan yatafi bazai dawoba saiya Gama karatun Amma dai zai dawo Daurin aure inaga. Kallonsa tayi baki sake tace' USI zaije makaranta? Haj Mama ta biya ne??? Batareda ya kalletaba yana duba Kiran dake shigowa wayarsa yace" Duk wani deal ko aiki ko kwangilane ma dake tsakaninki da umme babusa yaqare so ki cire zancensa completely a kanki Babu wannan zancen. USI zaije school ne sbd shine burinki nikuma nauyine Dana dorawa kaina na cika dukkanin burinki. Wani tsallen murna tayi tana Kiran sunansa daidai shigowar zarah tayi saurin kallon amatun tana cewa' Amatu wannan tsallen fa Zaki yiwa kanki illa. Kansa ta mayarda kallonta zatayi Magana ya rigata da cewa" Zarah amatu sai kinyi da gske she's stubborn.. Cikin tsananin farin cikinta daya kasa boyuwa tace" Anty zarah Dr jarumi ne Babu kamarsa..... Tsit sukayi zarah na dariya cikin Jin nauyin Abinda amatun ta fada shikuma idanuwansa ya zuba Mata jikinsa na mutuwa da qaunar yarinyar. Atakam batama kawo tunanin komai gameda maganar yataba sai sake sako maganganunta takeyi ganin haka yasa zarah ficewa da sauri shikuma ya fito sbd yayi lattin zuwa asibiti itama biyosa tayi tayi Masa rakiya zuwa mota suna tafe tana Masa sambatun irin farin cikin datake ciki har suka Isa motarsa dayazo da ita har qofar part din nasu zarah ta kallesa tana sake cewa idan kaje Dr Dan Allah Ina sake gaidasu kawu Iyami ma kace Mata Inshallah bazan jawo rigimar kowaba. Harya zauna cikin motar yace" To nikuma fa Abinda nace? Dariya tasaki kafin tace'" Kai duk Abinda kafada narigama nafara aiki dashi tun lokacin. Murmushi yasaki tareda gyada Kai Yana cewa" Good AMATULLAH. Juyawa tayi zata tafi cikin taushin murya yace" Me zan kawo Miki idan zandawo. Kallonsa tayi Wanda yasashi Jin wani iri kafin tana 'dan tunani tace" Duk Abinda masu ciki keci shi zaka siyomin naci Kona rage zafin sunan me cikin da ake Kirana dashi. Girgiza Kai yayi Yana cewa" Shikenan koma ciki ki kula Kuma. Sam yau farin cikinta yakasa boyuwa tana shigowa ciki Palo ta zauna tareda miqewa akan doguwar kujera tana kallon zarah data fito hanyar zuwa saman mijinta tasake bajewa tana cewa' Anty zarah qafafuwana tsami sukemin sosai Kuma. Qoqarin kawar da damuwar data sauko da ita daga Daman tayi tana qaqalo murmushi tace' Bari na dauko man massaging sai a Dan mammatsa Miki qafar. Dauko oil din tayi takirawo hafsatu Nan suka zauna tana yankawa amatun manyan gwaiban datace tanaso tana Mata fira ita Kuma hafsatu na mammatsa Mata qafafunta dake miqe Kan glass table din da aka Fara Dora Mata pillow me laushi kafin tadora qafafun. Sunyi nisa zarah ta Dan 'dago tareda juyawa ta kalli hanyar saukowarsa sbd qamshin turarensa na IMPERIAL MAJESTY data Fara shaqowa Yana doso palon. Jin zarah tayi shiru daga labarin datake Bata tana yanka Mata gwaibar yasata dagowa ta kalleta saitaga tana kallon wani gefe fuskarta kamar da damuwa ahankali itama ta juya ta kalli inda take kallon Wanda yayi daidai da saukowarsa gaba daya Yana sanye cikin suit din _Alexander vanquish 11 bespoke_ ash kala dasukaiwa fatarsa kyau sosai sai wani irin kwarjini da sirrin kyau dake fita daga fuskarsa da Babu sakewa acikinta. ##mamuh# #MIN QALB❤️ Mamuhgee ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MIN QALB 15_* _mamuhgee_ Jin idanuwa ajikinsa yasashi 'dan dagowa ya kalli inda suke Yana qarasa fitowa palon gaba daya Su kuwa duk su biyun idanuwansu zube suke akansa Babu ko qyaftawa musamman amatu dake qare Masa kallon tsaf zuciyarta na harbawa sbd yaune karo na farko a rayuwarta datake kallon wani namijin data kasa dauke idanuwanta a kansa. Ko inda suke bai qara kallaba ya dauke Kai fuskarsa na sake fitar musu da annuri ya nufi qofa zai fice zarah tayi saurin ajiye wuqa da gwaibar hannunta tana miqewa ta nufesa tana cikin kulawa tace" Fita zakayine gashi har an jere maka komai na breakfast a dining, Ko zaka daure kaci ko ka..... Zanyi a office idan naje I'm late already excuse me" Rabata yayi ya wuce Yana daukar wayarsa datai ringin batareda yasake waiwayartaba ya fice. Shiru tayi agurin tareda bin qofar daya fice din da kallo jikinta a matuqar sanyaye sbd a zaman aure kulawa da lokacinsa ne tasan bazai taba Bata ba gashi abin Yana damunta matuqa musamman idan a gaban mutane ne. Qaqalo murmushi tayi tareda boye damuwarta ta juyo tadawo gefen amatun ta zauna tana kawo wani labarin daban sbd wancan datake Bata na farko ta manta Abinda take cewa. Tsura Mata ido amatu tayi tana kallon hannunwanta dake yanka gwaibar duk sai taji bataji dadiba Sbd me zai dizga anty zarah din bayan ita kulawa ta nuna Masa¿ Dafa hannunta tayi tareda karban wuqar da gwaibar ta aje cikin plate dake Kan table tana qoqarin kawar Mata da damuwa ta saki murmushi tana cewa" Anty zarah gwaibar Nan ta isheni haka babyb harya Fara zama qato daga zuwanmu jiya sbd ciye ciyen da kike basa. Sai alokacin tasaki fuskarta sosai cikin Jin dadin Abinda amatun ta kalla tace" Ai dama so nakeyi yayi qatoto cikin qoshin lfy ta yanda iyayensa da kakanninsa zasu bani lambar yabo ta musamman. Hmm anty zarah waye zai baki lambar yabo acikinsu Dan kin kula da renon cikinda ba'a so? Dr ne kawai ke sonmu sai ke Dan haka Kona haihu ke zanbarwa babyn har sai kema kinsamu nai. Dariya sosai anty zarah tayi tana cewa'' Waye yake kyautar ciki tun baa haifesaba amatu, Kuma ki daina cewa ba'a son abin dake cikinki sbd idan har ana maganar gata to na tabbata abin dazaki Haifa gata yagama yimasa yawa, MD ZABEERA Dr ne Wanda yafi kowa qauna fiyeda komai da duk abin daya mallaka Dan haka Ina tabbatar Miki da Babu wani uba bayan Dr dazaifi MD qaunar abindake cikinki musamman sbd ni ba haihuwar nakeba Kinga kuwa Dole zai qaunaci 'dan Dan uwansa uwa uba Kuma Dr khalil shi yanzu ai bashida kamarku keda cikin Dan hakama ki daina cewa ba'a sonku mu Muna sonku Andi ma Yana sonku hakama Modibbo. Gyada Kai kawai tayi tana daukar sauran fruits din dake gabanta tana cinyewa tana lumshe ido Dan dai tunda tazo idanba da daddare data kwanta ba bakinta bai zauna a rufeba komaima cin cire haushi take Masa sbd ganinsa kamar ba kudi aka saka aka siyoba komai akwai kamar a banza. ****** Zaune take tana sauraren 'yar guntuwar da nasiha tareda lallashi da 'yarta juwairiyya ke Mata cikin kulawa da tausasa harshe Amma ita Sam hankalinta baya kanta tayi nisa gurin tunanin abindake damunta, Ganin hankalinta baya kanta yasa juwairiyya yin shiru tareda miqewa tana cewa" Umme tafiya zanyi ga dadynsu Fatima na kirana Kuma gobene tafiyarmu Lagos sai gaf da azumi zamu dawo Inshallah. Dagowa tayi ahankali ta kalleta batareda tace komaiba ta gyada Mata Kai tana shafa Kan Ahmad 'dan qaramin 'danta tace" Allah yakaiku lfy. Amin tace suka shiga bedroom din umme suna qarasa dauko sauran kayansu suka fice. Shiru tacigaba dayi tana saqa da warwara, Yarinya qarama kamar amatu itace tayi Wasa da tunaninta tasakata cikin wannan tunani da halin na baqin ciki har ana cewa itace Zara raini cikinda Babu ubanda yayishi, Wlh bazata yarda ba tunda shirinta ya lalace na kowama saiya lalace Dan kuwa sai ansan wa aka taba, Idanma MD ne ya ninkawa wannan makwadaiciyar kudi datake iya komai akan kudi ta kuwa kowa sai yaji ajikinsa wlh, Amatu cikin dayayi sanadin baki Jin Dadi da gata acikin zabeera shine zaizama mugun sanadin barinki zabeera da mummunan hukunci tareda wulaqancin da sai Yan jarida sun buga, Zanga yanda za'a haifi cikin da Babu. Shigowar Haj maryam ce tasata kallon qofa tana sake ajiyar zuciya ganin yanda itama haj Maryam din duk ta hargitse sbd burinsu na shekara da shekaru ya lalace cikin mintuna goma a hannun yarinya qarama. Zama tayi ummen nace mata' Yaya nuratu? Nuratu na can haryanxu kuka takeyi Wlh Nima aishatu nakasa yadda da khalil wata yake aure ba nuratu ba, Yarinyar Nan fiyeda shekara goma take fama da son Khalil sai yanxu da ake maganar aure kwatsam wannan mugun labarin ya fada, Labarin da mune muka qirqiresa Amma sai asamu wani juyin Masa a zancen Ni dai wlh Kam wannan Abu ban amince dashi ba nabawa nuratu wuqa da nama nace ta qetare duk wata iyaka ta qwato Khalil dinta mukuma maji da sauran. Cikin quluwa itama ummen tace" Dukkansu zasu raina kansu ne harshi Khalil din saiyaga bacin raina. ***Da Rana lafiyyan faten dankali da Naman kaza da carrot akayi sbd ita kawai Haka ta zauna tacinye Wanda aka kawo Mata tas ta kora da ruwan roba masu sanyi Danma lemu masu sanyi taso Sha anty zarah din ta hanata da cewa saidai Tasha fruits drinks ba lallai su bawa baby lafiya ba Haka ta hkr badan taso ba Dan ita wannan cikin badan Shiba da duk abindake gidan saita ringa cinsa ba kakkautawa. Baccin Rana tayi bayan tayi sallah sai yamma sosai ta tashi bayan tayi la'asar suka Fara waya da USI Nan yake fada Mata Dr yazo gida yafadawa su kawo shine 'dan wadda ta daukeki aiki Kuma zai ringa zuwa Yana dubamu kafin kidawo hakama ya tafi dashi anyi cike ciken makarantar dazashi har ilorin. Saidatayi sallar magrib tukuna ta fito Palo ya zauna tareda miqe qafafu hafsatu na matsa Mata tana kallo cikin ranta tana cewa" Amatu kinfa zamo hajiya Irin wannan Jin Dadi haka Gashi dama ba wani ciwo da qafafunta keyi tsaban son Jin Dadi da wuce wurine yasa take cewa ciwo suke Mata Dan a matsa Mata. Wata tashar turawa take kallo ana wani film na adventure sai washe baki takeyi tana cin cake din data sa anty zarah tasa hafsatu tayi mata na inibi me laushi yaji butter sai ci take tana lumshe ido tana kallo tana Jan hafsatu da labari itama hafsatun na tayata fassarar qanxon kurege na turancin da akeyi Dan itama ba wani iyawa tayiba Amma ta dage tana fassara Mata. Anty zarah ce ta fito daga dakinta ta nufosu cikin ado da kwalliya me kyau sai qamshi me Dadi take fitarwa amatu tabita da kallo cikin farin ciki tace'' Anty zarah kinyi kyau sosai Amma meyasa zakiyi kwalliya yanxu da dare tunda kwantawa zakiyi? Zama tayi kusa da ita tana murmushi tace" Amatu MD na hanyar dawowa shiyasa. Ohhh ohhh nagane anty zarah" Taqarasa fada tana dariya. Miqa Mata plate din cake din tayi tana cewa'' Anty zarah kici kiji yayi Dadi sosai. Har takai hannu zata dauka saita fasa tana cewa" Idan naji cikina zai cika bazan iya cin wani abincin ba kada MD yadawo nakasa tayasa cin abinci a dining. Kallonta tana cewa' kici ko kadan anty zarah tunda kinaso. Girgiza Kai tayi tana gyarawa amatun pillon data jingina dashi tana jawo Mata wani labarin take amatun tahau dariyar labarin datake Bata anty zaran na tayata sunyi nisa sunata nishadinsu saiga bude qofar palon aka shigo Dr ne hannunsa daukeda qatuwar ledoji da amatu ta ajiye plate din cake din hannunta ta taso kenan saigashi a bayansa Shima ya shigo fuskarsa kawai ta kalla ta janye daga gefen Takoma gefen Dr ta tsaya tana Masa murmushi zatai Magana yace" Baki gaida MD ba amatu. Kallonsa tayi kafin ta kalli inda MD din yake Yana qarasa shigowa palon tayi qasa da murya tace" Ina wuni sannu da dawowa. Hannu kawai ya daga Mata ya nufi hanyar samansa anty zarah dake zaune ta miqe itama tana Masa sannu da dawowa to ita ya bude baki ya amsa Mata tareda Dan tsayawa ya kalleta kafin ya dauke Kai Yana cewa' Karki jirani dinner nariga nayi dinner agurin Modibbo. Kallonsa tayi Yana qoqarin wucewa tace" Akawo maka ko fruits ne? No thank you. Wucewa yayi ya barta a tsaye tana binsa da kallo fuskarta na 'dan canzawa Amma Jin duk idanuwansu akanta yasa ta washe fuska tareda juyowa tadawo inda suke tana cewa" Dr ko zakayi dinner tareda mu ne to? Kallonta duk su duka sukeyi girmanta na qaruwa a idon Dr Tausayinta da qaunarta na shiga a zuciyar amatu tareda takaicin MD din ta yanda anty zarah ta Hana kanta cin komai sai yadawo Amma ya take hakan ya wucewarsa ko kwalliyar datayi danshi bai tsaya yayi Mata kallon ko mintu biyu ba ko me ya dauki kansa Dan ma yasamu mace me kirki da kyau kamar anty zarah tana sonsa wlh da itace koya Masa hankali zatayi taga qarshen kyau da Jan ajin banzansa. Kamo hannun anty zarah din tayi suna zama palon tace" Anty zarah Zo kici cake din Nan kiji Allah yayi Dadi sosai. Ledojin hannunsa Dr ya miqawa amatu Yana cewa" Nima a gajiye nake kamar MD shima yau a gajiye yake sosai Nima tunda muka hadu baicemin ko qala ba sbd gajiyar dayake tareda ita zanje na kwanta Saida safenku Amatu ki kula ok?¿ Gyada Masa Kai tayi tana cewa'' Nagode Saida safe. Yana fita zarah tasaki murmushi tana cewa" Dr kayaushe kanason gyara Abinda MD yakeyi Dan kada aga laifinsa Kadaina damuwa Dan Nima Babu ranar dazanga laifin nasa. Takaicin MD din yasake Kama amatun tasake dagewa Saida anty zarah din taci cake din sosai Tasha apple drink suka cigaba da firarsu Ganin hankalin zarah din na Kan hanyar sama yasa amatu sakin tsaki qarami tana miqewa tace" Bacci zanyi Saida safe anty zarah. Tana shigewa zaran tasa hafsatu ta kashe komai itama tashige Suna shigewa taje dakinta ta shirya ta nufi dakin MD. Ahankali amatu tasaba da zarah da hafsatu sosai kamar sunyi shekaru atare, Kulawar dasuke Bata da gatan datake samu daga garesu yasa hankalinta ya kwanta sosai acikinsu musamman ma da kullum tana waya dasu kawu dasuketa sawa Dr khalil albarkar yanda yake kula dasu sosai Dan yanzu ranakun matsuwarsu sun qare ga USI anata shirye shiryen zuwa makaranta, A duniya yanzu mutanen datake so a rayuwarta fiyeda komai da kowa sune USI,kawu,iyami,Dr da anty zarah sbd sune mutanenda tasan tabbas qaunarta sukeyi Babu wani qyama ko munafurci. Dr ya Gina qaunarsa cikin ranta danasu kawu sbd Suma shine mutum daya qwal daya fito ya tsaya musu a rayuwa yake qaunarsu batareda qyama ba ko buqatan wani Abu daga garesu shiyasa dukkaninsu kowannensu ya bude baki Dr ne abakinsa sai anty zarah dinta. Qaunar data kewa anty zarah din yasa take Jin tsanar MD matuqa cikin ranta sbd yanda tagama lurada Sam baya damuwa da alamarin zarah din kullum shine damuwarta shine kukanta shine jimaminta ko tausaya Mata bayayi da yanda take matuqar qaunarsa/sonsa da ganin girmansa, Duk yanda zarah din take qoqarin boyewa hakan baya boyuwa ga Wanda yake zama taredasu shiyasama Sam ta tsani ko ganinsa matuqar Yana gida Bata fitowa sbd kar wataran tayi amsa zagin maguzawa akan Abinda yakewa antyn saidai duk Abinda zai faru yafaru ba ruwanta. A bangaren Jin Dadi kuwa zatace itakam gwara da akayi Dan kuwa rayuwa ta sauya Mata sosai Dan ko jikinta da fatarta sum nuna suna cikin hutu sbd lafiyayyar rayuwar datake ciki, Banza ta Fadi" kaman yanda take fada Dadinta takeci ba qaqqautawa duk wani Abu me Dadi cewa takeyi tanaso ba Bata lokaci kuwa Zarah zatasa akawo Mata shi, Hafsatu kanta ta qararda 'yar ta'addace a gidan Dan kuwa tunda amatu tazo Bata zaman awa biyu batai aikin hada mata wani abuba, Itace ayi Mata gullisuwa, Tuwon Madara, Kwakwameti, Cake, Dambun nama, Dambun kaza, Furar Madara da Milo Komaima ci takeyi ita Bata taba ganin me ciki irin wannan na amatu ba da baya tadar komai Komai ci takeyi hadda Wanda masu ciki baya shafa musu lafiya Gashi ko ciwon Kan Nan na banza da masu ciki keyi ita batayi kullum daram dam take Ga Dr ya Hana asa kowane likita ya duba matarsa yace shine zai ringa dubata musamman da kwanakin umme tasaka fitinar sai Modibbo yasa anyi scanning Dan asan ranar haihuwar cikin su Fara shiri. Hankalinta bai wani tashiba sbd tasan Dr na Nan shine zaisan yanda za'ayi da Maganar scanning din itadai damuwarta 'dayace shine anty zarah data Fara maganar cikin baya girma sbd ta shanye kusan wata biyu a gidan gashi Koda tazo tace ciki wata biyu wata hudu kenan Amma Babu alamar tasowar cikin shine anty zaran ta daga hankalinta cewar cikin baida lafiya itama tanason ayi scanning. ##mamuh## ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:02 AM - ': *_MQ 16_* Zaune take gaban madubin dakin daya zama Mata tana kallon fuskarta datayi haske sosai tareda duka fatar jikinta har wani qyallin samun hutu da kayan gyara masu tsada da mutunci zuwa qirjinta daya ciko shima yayi daram dam sabanin dah banbancinsa da shafe idan tasaka brazier ne push up. Mayarda kallonta tayi Kan cikinta tana miqewa tsaye ta Dan matse rigarta tana shafa cikin sai tasamu kanta da sakin murmushi karon farko datai shaawar dama ace cikin gasken ne da ita da zaiyi mata kyau Kuma da duk wahala da dawainiyar anty zarah baza taje a banxa ba, Dan sake dafe cikin tayi tana cewa'' To idan ace cikin gske ne to waye zai zama babansa? Dr?? Girgiza Kai tayi tana cewa'' Ummen sa bazata Bari ba. Amma dai duk da haka shine zaifi iya bawa babyna kulawa Amma dai kamanninsa kuwa anty zarah nakeson ya dauko sak sai Kuma...... Shiru tayi takasa qarasawa Daga bayanta taji ance' sai Kuma me maman bby? Juyowa tayi tana kallon ZARAH din kafin ta juya ta qurawa cikinta ido ta cikin madubin ahankali tace' Sai Kuma inason ya dauko hancin MD. Zarah dake qoqarin zama bakin gado tsayawa tayi ta kalli amatun tana karban zancen a baibai saidai kawai tasan duk irin shirme shirmen Amatun sai kawai tasaki murmushi tana janye Amatun daga gaban madubi tana cewa" Zoki zauna zaki gaji da tsayuwa gashi yau zamuje scanning anjima kadan MD nake jira ya kirani na sanar Masa zamu fita nayita Kira baya dauka tun safe bayan fitarsa. Ki qyalesa anty zarah mu tafiyarmu kawai tunda Dr na can Yana jiranmu a asibitin tun dazu yake Kira bamu fitoba. Bazaki gane bane Amatu dokar MD ce baya barina fita Babu wani babban dalili me qarfi sbd shi mutum ne me buqatar sirrintacciyar rayuwa Mara hayaniya shiyasa bayason ko iyalinsa ace kowa ya sansu a haka dai zance MD mutum ne me tsananin kishi. Dibar zancen na anty zarah tayi ta watsar da baki tana cewa" Anty zarah to nidai gskia muje karki tsaya jira tunda yaga Kiran naki fa na tabbata, Kuma nidai bazan Bari Dr yayita jiraba tunda Modibbo da Andi sunsan da zancen fitar muje kawai Dan Allah. Miqewa anty zarah tayi tana nufar qofa tana cewa' Amatun 6acin ran MD ba kyau bazan iya take dokarsaba Zan iya fita yanxu wani Abu yafaru wlh bazan iya daukar fushinsaba kiyi hkr Bari nasake gwada kiransa kozai dauka.... Takaici yasa Amatun dafe ciki ta durqushe tana cewa'' Wayyo Allah anty zarah cikina marata ciwo sosai Dan Allah anty ki taimakeni kada cikina ya samu matsala Ina sonsa banason ya zube..... Da gudu anty zarah ta dawo tana Kiran sunanta cikin tashin hankali tana riqota Ita kuwa Amatu sai wani murqususu takeyi tana sako hawayen qarya tana Daman cewa'' Anty ki taimakeni banaso cikina ya zube. Tsabar tashin hankali da firgici tareda tausayin Amatun me tsanani ZARAH batasan lokacin data fashe da kuka ba tana kamota jikinta tana qoqarin muqar da ita tana kwalawa hafsatu Kira Dan tazo su kamata suyi asibiti. Kamata sukayi suka saka mota a gigice anty zarah ta yafo gyalen jallabiyar dake jikinta ta fada motar ta jasu suka fice tana cewa hafsatu" Hafsatu maza Yi sauri ki Kira Dr khalil ki sanar Masa Abinda yake faruwa gamunan zuwa. Shiru Amatu tayi daga kukan qaryan datakeyi jikinta na yin sanyi da yanda anty zarah ta daga hankalinta sai hawaye takeyi tana Mata sannu Amma Babu yanda ta iyane itama sbd Dr yace Mata komai zatayi ta tabbatarda sunxo asibitin sbd yabasu scanning din daya shirya Dan ita din idan basuxo asibitin ba to tabbas wani likita ummensa zatasa akawo har zabeera din Dan kawai ayi komai yafito fili A bangare daya Kuma ga USI da shima zasu hadu duk a asibitin shiyasa tayi hakan, Ahankali ta kamo hannun anty zarah din bayan har sun iso asibiti Khalil ya karbeta sun shige yayi duk yanda zaiyi ya hado scanning din aka kwantar da ita office dinsa tareda 'yan magungunan vitamins sai alokacin hankalin zarah yadawo jikinta ganin Amatun tadawo daidai ciwon ya daina. tana kallon anty zarah din bayan ta riqe hannunta ganin har lokacin da sauran damuwa a fuskarta itama cikin sanyin murya furta" Nagode anty zarah, Nagode da matsayin da Kika bani na qanwa tamkar wadda kuka fito ciki daya, Anty zarah wlh kece mutum ta uku da Kika taba qaunata tsakani da Allah ba qyamata ko wulaqantawa Dan haka kinada babban matsayi a zuciyata da har abada bazan mantaki ba. Kasa cewa komai anty zarah tayi sbd har lokacin Bata Gama fitowa cikin shock din halinda Amatun tashigaba Dan wato da ace wani Abu yasamu cikin bazata taba yafewa kanta ba. Shigowar Dr da USI a bayansa yasata miqewa zaune da sauri tana washe dukkanin haqoranta cikin tsananin farin ciki takira sunansa tana qoqarin saukowa gadon Dr khalil yayi Mata gyara murya Yana kallonta Take ta kallesa tana dawowa nutsuwarta saita waske ta hanyar cewa" Anty zarah ga qanina usman. Kallonta anty zarah tayi irin da gasken Nan kike? Daga Mata Kai tayi murnarta na sake bayyanuwa ta jawo Usman din gaban anty zarah tana cewa" Usi ka gaida anty zarah. Da sauri cikin girmamawa yace" Anty mun wuni lafiya? Ya gida Yakuma qoqari? Mungode sosai sosai fa anty Allah ya saka Miki da alheri Ya biya Miki buqatunki na alkairi. Murmushi anty zarah tayi tana kallon yanda jikinsa har mazari yakeyi gurin gaidata Yana fiddo dukkanin girmamawar dayake ji akanta sbd duk yanda take qaunar Amatunsa tafada Masa shiyasa shima tun baigantaba yake Jin qaunar halayenta da ganin girmanta. Kallon Amatu dake cikin dokin ganin usman din tayi tana cewa'' Amatu me Kika fada Masa yaketa wannan addua haka? Usman karka ji komai ba komai Amatu tamkar qanwar da kuka fito ciki daya nake jinta Saidai kayi Mata nasiha ko zataji Amatu Bata zama kurum kodan halin datake ciki gashi yauma sbd tasa damuwar fitowa Dole yasa akaso samun matsala har muka qare kwance a asibiti. Anty zarah ki ringa doketa kokuma ki Fara hanata kayan Dadi zata dawo hankalinta. Dariya sosai anty zarah tareda Dr suka saki harda ita Amatun tana kaiwa usi mugun duka a baya tace" Ni zakayiwa baqin ciki usi? Zakasan dawa kayi sai nasa kawu ya aura maka qanwar maman junior data maqale maka. Cab wannan ai koni tafi iya sanin yanda ake sanfewa Dan wlh koke duk qwarewarki saita sanfeki Kisa ranarda aka kawota ta sanfe Dan cinikin iyami da kawu kejin yanzu yafara zamowa sahun masu abun Kai kawu ya kwana ya debewa auren albarka. Dariya suka saki gaba dayansu hadda anty zarah da batasan meye sanfewarba dagasu sai Dr ne kawai suka sani shima sbd yayi bincike sosai akansu ne Kuma sun zauna dashi su kawu da USI din Basu boye Masa komaiba gameba rayuwarsu sbd sunriga sun daukesa kamar jininsu. Ta Dan saci kallon Dr da ita yake kallo shima zuciyarsa na samun nutsuwa da yanda yake ganinsu cikin nishadi zuciyarsa na sake samun nutsuwa Ta juya ta harari usi tareda take Masa qafa da qarfi har Saida ya zabura tayi saurin dafesa Dan kada anty zarah tagane qasa qasa tace" A gaban Dr baban babyn nawa kake tayarda maganar qwarewata a sata ka shirya kwanciya a asibitin Nan Dan saina fasa maka baki da haqora idan anty zarah ta fita. Kallon Dr yayi da Ido Yana cewa'' Ka ceceni matarka zata fasa bakina Wai. Kamar zaiyi Magana sai ya fasa Yana sakar Mata murmushi sbd idanun data zuba Masa tana jiran jin Abinda zai ce ta mayarda rigimar kansa. Ikon Allah anty zarah tayita kallo a tsakaninsu sunata raha da nishadinsu cikin tsananin qaunar junansu ga Dr da tuni dama yazama 'daya daga cikinsu gabanta harsu iyami aka Kira da kawu a wayar Dr Nan aka Dora wata sabuwar hayaniyar sbd labarin fadanda kawu yayi dasu maman basiru ya dauko motar yan sanda biyu aka kwashe gidan kaf harda alhaji mande daya iya shigar sani infika. Dariya sukeyi sosai musamman da iyami ke fadawa Amatu kawunta ya zabure yanzu tunda yaga ya 'dan tsayu hakama insfector Garba na Nan Yana bibiyar kawun akan maganar aurenta. Nishadi sosai suke saka anty zarah tayi zugum tana kallonsu suna burgeta hakanan taji inama acikinsu take itama data samu farin ciki kamarsu, Abu daya tasani shine Koda take cikin wadata ta taso cikin tun tana gidansu Basu San wani Abu Wai sakewa cikin nishadi kayi rayuwarka ba, Tun a gida sun Saba bin umarni ne kawai da oda suka sani Iyayensu basa jansu ajiki Wai da sunan tarbiya da kadasu lalace Shiyasa yawancinsu Basu wani cikin walwala saidai kawai suyi rayuwa cikin daular Amma Babu wani walwala saigashi wainnan bayin Allan sunada duk wani nishadi da walwala suna rayuwarsu hankali kwance, Tabbas shi nishadi da farin ciki ba siyansa akeyiba Allah ne yake baka Gashi ayau duk da tarin daular datake ciki rayuwar wainnan talakawan tana burgeta harma tanajin inama acikinsu take. Anan sukai kusan Rabin yinin sai yamma suka fito gabaki dayansa tana Jin kewar usi dasu kawu tun Usin be tafi Amma hakanan suka rabu shida Dr suke tafi a motar Dr sbd yakaisa gida itakuma suka tafi a motar anty zarah da hafsatu. Suna tafe suna tana kallon titi cikin nishadi sbd tunda tashiga zabeera tsawon wata biyu sai yau tafito, Gskia dai ma Ashe wani lokacin masu kudin rayuwar takura kawai sukeyi kullum a killace Wai sbd kar mutane su dameka, Ita Sam batason akoma gidan yanzu yawo takeso tadan sakata ta Wala. Qaramin tsoki taja a fili Wanda yasa anty zarah kallonta tana cewa'' Yaya dai Amatu? Bata fuska tayi tana yamutsawa tace" Anty zarah Dan Allah muje blue fox na taba yin aiki acan Muje kibiya madam dinmu kudi yau da kanta zata wanke min Kai da qafafu tasan Nima bayan ta koreni aiki nayi gaba ba bataba. Murmushi tayi tana cewa'' Amatu ba dama. A blue fox wani shaqiyanci ta dinga yiwa madam bell din tana cewa ga Abinda da Abinda takeso Haka dai suka ringa yimata Abinda tace sbd ganin wadda sukazo tareda ita din she's from zabeeras. Gyaran Kai akai musu itada anty zarah din tareda kyan qafa da gyaran fuska take suka koma tamkar wasu amare musamman amatun da Bata taba irin wannan gyaran ba take suka hau wani irin sheqi. Daga nan restaurant din blue fox din ta matsawa anty zarah suka shiga Nan tayi odar kayan dadin dataci harta Bar saura sbd sunfi qarfin cikinta suka fito nanma matsawa anty zarah tayi suka nufi wani qatoton shopping mall datace tanada kwadayin son shigarsa. Suna shiga mall din me hawa biyu batasan lokacin data saki tsallen murna ba tana rarraba idanu cikin gurin farin cikinta a bayyane. Sama suka hau gurin kayan babies antyn na cewa kayan baby kawai zasu siya Nan anty zarah tadan zaba kayan babies suka sauko Amatun nata zare Ido tarasa abin dauka sbd duk kayan Dadi da maqulashen dake gurin akwaisa a gida hakama sutura Bata buqata sbd Dr kusan kullum cikin kawo Mata su yake hakama anty zarah Idan turarukane duk tanadasu a gidan hakama takalma, Ita Kam da a dah ne tazo wannan gurin da saita sace kusan kayan dubu dark saidai suje station Amma ko yanxu ba damuwa Dan saita yiwa Dr tsarabar dazai ringa tunata. Wani tsadadden agogon Rolex tagani Yana qyalli take ta hango kyanda zaiyi a hannun Dr tasaki murmushi tana kallon anty zarah dake qoqarin Ciro card dinta tabayar gurin payment ta faki idanuwansu ta zaresa tareda sakawa cikin aljihun doguwar English gown din dake jikinta tana waskewa tahau 'yan juye juye tana latsa wayar anty zarah dake hannunta. Suna Gama payment din suka fito har zasu shiga mota aka tsayar dasu da sauri ana cewa su dawo ciki anason ganinsu. Tsayawa anty zarah tayi tana kallonsu cikin mamaki kafin ta kalli time har anfara Kiran sallar magrib tace" Lafiya? Sauri mukeyi munyi dare fa. Dayan ne me sanyeda suit kamar ma shine babbnsu yace" Haj wani Abu mukeson kugani da idanuwanku kafin muyi mgn please. Qaramin tsoki tasaki tana cewa'' Amatu ku jira a mota Ina zuwa. Aa hajiya da ita zakuzo duka muke buqatar ganinku. Ba musu suka koma ciki har office din managern gurin suka zauna take aka kunna musu Abinda footage na CCTV camera Mutuwar zaune anty zarah tayi cikin mamaki da kunya Amatun ma cikeda kunyar anty zarah ta dago ta kalleta kafin tayiwa manager kallon takaici Bataji kunyarsa ba ko kadan ita anty zarah ce kawai abin Jin nauyinta itama dandai na farkone datayi a gabanta. Bude baki anty zarah tayi Yana Mata nauyi zatayi Magana kenan saiga Yan sandan da aka Kira mota guda har sun iso Nan take aka gargadosu zuwa mota anty zarah tsabar rudewa da tashin hankali ko magana ma takasa Yi. Wata baqar Mercedes-Benz beymach30745 2020 ce tashigo harabar gurin tayi parking Tareda wasu motoci guda biyu manya na asalin me mall din dasukazo Dan duba gurin zai siye tareda estate din dake bayan mall din. saidaya dauki lokaci Yana qarasa wayar dayakeyi kafin yafito Lokacin su alhaji bayo din yafito tareda P.A dinsa dukkanin ma'aikatan gurin sunyo gurinsa suna Masa barka da zuwa hakama ganin MD ZABEERA taredashi yasasu qara bada girmamawa suna Masa barka da zuwa barema daman sunji shine zai siye gurin. ##mamuh# ZAFAFA BIAYAR SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee YANKAN BAYA billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:03 AM - ': *_MQ 17_* _Mg_ Ana qoqarin turata motar Yan sandan ta hangosa tareda mutane Yana waya har lokacin kamalarsa na sake fita dabam acikinsu batasan lokacin data washe baki ba tana cewa'' Anty zarah bazan Bari kije station ba da mutuncinki, Fizge hannunta tayi daga hannun 'yar sandar mace ta maraice da fuska kamar zatayi kuka tace" Officer madam Dena riqeni da qarfi cikine Dani Kuma.... Kallonta anty zarah tayi duk da tsananin baqin ciki da kunyar datake ciki Bata fatan Abinda zai samu Amatun sbd cikin jikinta Zatai Magana idonta ya sauka kan MD dasuke qarasowa daf dasu zasu shiga mall din Wani mummunan tashin hankali ya shigeta tai saurin fadawa motar Dan kada ya ganta bazataso mutuncinsa ya zube agurin ba da zarar angano ita matarsa ce Barema sanin dokarsa da Abinda yafi tsana shine iyalinsa suzo budadden gurinda za'a Gama ganesu kamar wasu marasa daraja. Amatu na ganin haka ta 'dan daga murya tace" Ku bamu damar Kiran wani daga gida Sbd daga babban gida muka fito wato ZABEERAS. Cak ta 'dan tsaya bai juyoba saidata qara Kiran sunan zabeeras din tana sake Dan daga murya sbd ganin ya tsaya Kai tsaye ya juyo idanuwansa suka sauka kanta a bakin motar 'yan sandan Babu alamar kunya ko Jin nauyi atare da ita Kai kawai ya dauke zai tafiyarsa saikuma ya tsaya cak sbd kamar matarsa ya hango cikin motar Saiya kasa juyowa tsawon seconds kafin ya juyo cikin nutsuwa ya kalli cikin motar Zarah dince kuwa a zaune tana sunkuyar da kanta take wani irin dacin Rai me mugun tsanani ya rufesa Amma idanba Wanda yasansa ba bazai iya ganewaba Rintse idanuwansa yayi dasuka sauya atake yana controlling nutsuwarsa ta sakan hudu kafin ya budesu ya sauke Kan managern gurin cikin muryarsa me taushi da nutsuwa yace" Meyake faruwa anan? Bayani tsaf manager ya koro Masa Yana qarawa da cewar" Ranka ya Dade wannan itace asalin wadda tayi satar inaga ita waccan me ajewa ce wato shugabarta Kuma......... Hannu ya dagawa managern Yana qara controlling fushinsa da idan yasakesa agurin fasa gurin zaiyi gaba daya Dan bazai iya daukar fushinsaba. Yana daga wayarsa dake ringing yace" Ku sakesu suje Abar zancen daganan Zanyi handling komai da kaina. Okay ranka ya Dade angama Officer ku sakesu su tafi Ke hajiya fito Allah ya taimakeku MD yasa baki ku wuce karku sake zuwa Nan sbd next time bazaku samu wannan damarba ta kubuta Dan munsan yanda muke dealing da qananun barayi irinku.. Zuwa lokacin kuka anty zarah keyi sbd maganganun dayake jefa musu dakuma sanin yau taqare Mata tsakaninta da MD Dan ita kawai ke iya hango _rage_ din dake fuskarsa gasu tafito bada izininsa ba, Takai dare a waje ga wani irin bacin suna da aka ja Masa Danma ba'a gano ita matarsa bace. Daqyar take Jan qafa jikinta na mugun rawa ga hawayen datake sosai ta nufi mota Amatu na binta jikinta a macen itama sbd ganin halinda anty zarah din ke ciki Wanda Bata taba ganinta acikinsaba. Suna shiga mota daqyar anty zarah din ta iya tayarwa suka bar gurin Babu me iya ko dogon motsi a motar har suka Isa Kuma har lokacin hawayen anty zarah Basu tsayaba. Suna barin gurin ya daga wayarsa daketa ringin Kai tsaye yace" Dr duk Abinda kakeyi ka tabbatarda matarka tabar gidana acikin Daren Nan. Kashe wayarsa yayi Yana Gama fadar hakan kafin yajuyo ya kalli P.A dinsa yace" Faruk handle this for now Gida zanje gobe zaka bani details din yanda akayi. Juyawa yayi Kai tsaye ya nufi motarsa ya fada tareda janta da kansa yabar gurin sai alokacin suka fahimci da matsala sbd yanda yaja motar yabar gurin. Suna shiga Palo tayi saurin Shan gaban anty zarah tareda zubewa qasa da qarfi Kan gwiwoyinta tana sunkuyar dakai cikin tsananin nadama tace" Anty zarah kalmar hakurina bazata canza komaiba gameda tozarcin Dana janyo Miki yau din Dan Allah anty zarah kiyi hkr wallahi bantaba Jin kunya da takaicin halinaba sai ayau, wlh sbd ke yau naji na tsani wannan halin nawa Dan Allah anty zarah kiyi hkr wlh banyi Dan tozarta..... Saukar wani lafiyayyan Mari taji a fuskarta Wanda yasata qarasa zubewa zaune tana taba fuskarta amatuqar gigice ta dago a zuciye zatai Magana idonta ya sauka cikin nasa idanun dasuka kada sukai jajir.... Da sauri zarah ta zube qasa itama zatai Magana ya daga Mata hannu batareda ya kalletaba yace" For first time ayau naji nayi takaicin amincewa da aurenki, Hw cud you zarah, Bakisan mutuncin kanki da Wanda ya ajiyeki bane dazaki fita in the first place batareda izini ba Ever this stupid being came here nasan zaayi haka wata Rana sbd wannan ba mace bane she is just a shame, Sata rayuwarta ne Shi aka reneta dashi sbd Abinda tasani shine kawai sata da yawo cikin maza with no shame, A hausance banma san sunan dazan kirataba sbd idanma ankirata da abin kunya an Bata sunan mutunci Amma ke this is the last thing I expected from you... Banason hayaniya I prefer rayuwata ni kadai yafi nutsuwa da kwanciyan hankali so please ku duka just park ur things kubar Nan Ni kadai nakeson zama anan just I think kowannenmu need a break....... Wani irin kuka Mai taba zuciya anty zarah tasaki tana qoqarin basa hkr ya juyawarsa zai haye sama Amatu ta miqe da saurin Tasha gabansa tareda sake zubewa tana tsiyayo hawaye masu tsananin 'dacin kalaman daya furta akanta saidai komai 'dacinsu zata hade bazata Bari laifinta ya lalata auren anty zarah ba kodan yanda tasan shine rayuwar anty zarah din. Akaro na farko a rayuwarta datake qwallan cin zarafi da akai Mata sabanin da ko ajikinta Dan ko damuwa batayi barema ada Babu Wanda ya Isa ya tsareta ya iya fada Mata haka Bata saka an Masa zanen yorbawa a fuskar ba. Sabbin hawaye suka gangaro Kan fuskarta ta bude baki muryarta a matuqar sanyaye tace" Dan Allah kayi hakuri anty zarah batada lai... Ko kallon inda take baiyiba ya wuce tayi saurin rarrafawa zatasha gabansa cikin tsananin 6acin Rai ya daga qafa zai wuce da ita aka saka hannuwa biyu aka tare qafar Ya tsaya cak kallon Dr daya riqe qafar tasa cikin tsananin mamaki da sabon takaici. Dr daya jima tsaye Yana sauraran duk Abinda MD din ya fada suna dukan zuciyarsa duka me tsananin daya karya gwarin gwiwarsa. Baice komaiba sai kawai ya sauke gwiwoyinsa qasa gaban MD din tareda sunkuyar da Kai cikin tsananin rauni da damuwa me nauyi murya a sanyaye yace" MAHMOUD karka hukunta zarah akan laifin amatu na roqeka da sunan Allah, Itama Amatu Ina roqonka daka yafe Mata Koda hakan zai zama alfarmar qarshe dazakamin arayuwata to Dan Allah ka yafe Mata ba laifinta bane laifina ne Dana kasa bar Mata duk Abinda yakamata nabar Mata...... What???Khalil Kama San waye wannan yarinyar kuwa? Tun farko bansan me kagani na hankali atareda wannan yarinyarba harka iya sabawa iyayenka ka aureta, And now kana durqushe a gabana duk sbd ita Khalil Kama ganin daidaine hakan? Rintse idanu Dr yayi a sanyaye Yace" Abinda nasani yanxu arayuwata shine indai sbd itane zanyi har Abinda yafi durqusawa sbd tsirar Mata da mutuncinta, Kai Dan uwanane mafi kusanci agareni Wanda kalmomin batanci mafi Muni suka fito daga bakinka kan macen danafi so da qaunar Kare martabarta shiyasa na durqusa gaban nake neman afuwarka sbd ita, Cikin sake kunnasa da Khalil din yayi da maganganunsa hakanan kawai yaji mugun zafinsu Yau Khalil ne ke fadar kariya da martabarta Rintse ido yayi suna qara rinewa ya kalleta Sautin kukanta na fita ahankali sbd maganganun Dr sungama sanyata cikin nadama me tsanani Take zafin zuciyarsa yafara loosing control ya juya zai wuce Khalil ya miqe tareda Shan gabansa yace" MD matuqar haryanxu matsayina na Nan a zuciyarka da rayuwarka inason ka tabashi biyu kabani nida Amatu sbd wlh ni itace tawa rayuwar, Zakaimin alqawarin yafe Mata tareda Bata mutunci amatsayinta tawa, Idan bakayi Dan ni ba kayi kodan jinina dayake jikinta Wanda yake shima naka jinin, MD Ina fatan zakamin wannan alfarma ko bayan idona. Kasa kallon Khalil din yayi sbd baqin ciki da takaicin duk akan mace ya zare haka macen ma ba kamar matan mutunci ba haryana kirarin idan yana qaunarsa saiya qaunaceta Ra'besa kawai yayi ya haye sama tun kafin shida Khalil din ta 6aci akan yarinyar. Bayansa Khalil yabi da kallon harya shige kafin ya saki numfashi a sanyaye tareda juyowa ahankali ya zauna gefen amatu dake kuka qasa qasa takasa ko motsi. Kallon zarah dake nata kukan yayi zaiyi mgn ta miqe tabar gurin tayi dakinta ta rufo sbd itama kukan takeso tayi sosai ko nauyin zuciyarta zai ragu. Cikin sanyin jiki ya maido da kallonsa Kan amatu yafara lallashinta Yana Mata nasiha hartayi shiru da kansa ya dauko ruwa a fridge yabata Tasha ya rakata har dakinta kafin ya wuce zuwa nasa part din jiki da zuciyarsa amatuqar sanyaye. Sallolinta tayi ta zame ta kwanta Kan dadduma a inda tayi sallar yau ba Maganar cin Dadi Amma datayi awanni a kwance taga bacci ba zuwa zaiyiba sbd yunwa hakanan ta miqe ta fito taje kicin taci fruits dinta da yoghurts ta qoshi tazo ta kwanta tunanin Dr na dawo Mata bangare daya Kuma damuwar da anty zarah take ciki. Washe gari tunda safe Dr khalil yazo sbd yasan shikenan MD zai Fara rashin 'dan zaman dayakeyi a gidan fita tinda safe dawowa sai dare qarshema yasan zai iya tafiya yabar qasar yakoma wata qasa sai yaga dama ya dawo. MD na ganinsa ya kallesa Yana watsar da tunanin abubuwan jiya din sbd shi ba mutum ne me aje hargitsi cikin kansa ba Sam ko maganar batason a tayar sbd kar asashi cuwon Kai. Kallonsa Dr khalil yayi Yana qaqalo murmushi yace" Good morning MD ZABEERA. 'dan kallonsa MD din yayi Yana maida kallonsa Kan agogon hannunsa cikin miskilanci yace" Morning Dr khalil zabeera. Murmushi Khalil din yayi Yana cewa'' Sorry MD. Kallonsa ya 'danyi kafin yaci gaba da duba wayarsa. Bai kamata nama Magana irin yanda nayi maka a jiyan kayi hkr. Karka damu I can't even recall Abinda yafaru a jiyan. Numfashi Khalil ya sauke Yana gyara tsayuwa kafin yace" Amma akan Amatu inakan duk Abinda nafada Dan haka Ina riqon alfarmarka sbd abin dake cikinta please kabata damar dazan gyarata kodan 'yayana su samu uwa ta gari. Gaba daya MD din ya dago ya kallesa wannan karon tareda 'dan lumshe fararen idanuwansa yasaki wani sahirtaccen numfashi kafin yace" I hope you know wat u're doing. Motarsa ya fada tareda cewa'' Mu yini lfy Dr. Murmushi Khalil yayi Yana cewa'' Zan dauki wannan amatsayin amincewa da roqona thank you. Ciki ya qarasa gurinsu sbd Suma yanason mgn dasu musamman zarah bayason tasamu matsala da Amatu akan wannan alamarin sbd ita kadaice yasan Amatu is safe a gurinta. Cikin sa'a kuwa Zarah din na dining tana qoqarin jera breakfast tayi 'dan adonta duk da ba walwala sosai a fuskarta duk sbd taqara bawa MD hakuri. Cikin sakin fuska yakira sunanta Ta juyo tana yaqen Dole suka gaisa Suna cikin mgn saiga Amatu ta fito jiyo muryarsa A sidade ta qaraso tana kallon fuskar zarah a raunane. Ganin yanda tayi din sai anty zarah din taji rashin Dadi ta saki 'dan guntun murmushi tana cewa'' Amatu Zo Kinci abinci jiya da daddare kuwa?da maganinki ma kinsha?? Wani sabon girma da qaunar anty zarah dinne suka rufeta batasan lokacinda ta qarasa gurinta da sauri ba ta rungumeta tareda sakin wani siririn kuka tana cewa'' Anty zarah Dan Allah ki yafemun wlh nayi nadama me tsanani akan Abinda na ja miki. Karki damu Amatu qaddarane Kuma yariga ya wuce tunda kince bazaki sake ba. Zama tayi gefen anty zarah din ta share hawayenta tana sunkuyar da Kai tace" Anty zarah kunyarki nakeji haryanxu sbd tun yanxu nafara saka Miki da Abu Mara kyau akan alkairi da qaunar da kike mini, Ayau naji gida nakeson komawa inda nafito, Cikin mutanenda nafito, Cikin rayuwar damuka saba da qanqancin da muka Saba dauka sbd nafara gane ban cancanci zama cikin mutane masu mutunci da daraja kamarku ba, Anty zarah daukar abin wani yazama tamkar qaddaratace sbd saimun dauki abin wani muke iya ciyar da cikinmu abinci wata Rana, Rayuwa da mutanen cikintane suke tilastamu ga aikata wasu laifukan wata Rana, Nida usi muntaso cikin bola muka rayu acikinta mukayi wayo, Acikin bola muka Fara sanin yanda zamuyi fafutuka mu gudanar da rayuwarmu, Bayan Tasha shine gurin kwananmu Shine muhallinmu a lokacin, Tun munada shekarun da bamu Gama sanin bambamcin jinsuba aka lalatawa usi rayuwa ta hanyar Masa fyade, Fyaden da shine sanadin farko na qarin tabarbarewar rayuwarmu, Alokacin mukasan ba tausayi atareda mutanen cikin duniya, Munkoyi data Danmu ci mu tsira mu rayu, Anty zarah bamu qara fuskantar qasqancin halin rayuwa da mutanen cikintaba sai alokacin da nida USI aka kamamu a gaban idonsa aka yaga tsumman sutura dake jikina za'ayi mini fyade Wanda yayi sanadin haduwarmu da mutum na farko daya Fara yima kallon muma 'yayane Kuma mutane 'yan Adam, Kawu ya gabatar Mana da sabuwar rayuwar almajiranci wadda nayita acikin maza da siffar maza ta hanyar rayuwa usman namin aski, Munyi almajiranci na wahala Wanda yasamu baqin jini acikin almajirai Yan uwanmu, Munyi kukan sarari munyi na fili saidai bamuda tudun dafawa har Saida rayuwar wahala da garari ta aure mu kafin kawu yasake kallonmu da idanuwansa na rahama da jin qai ya zamo uba garemu, Ya bamu uwa me qaunarmu tamkar 'yayanta iyami, Mezamu ce arayuwar Nan bayan wahala da rayuwar garari a jininmu take shiyasa ko a gidan kawu tsanani da Matsin rayuwa be qare Mana, Muna kwana da yunwa mutashi da ita Kuma muyi rayuwarmu, Munshiga masifu iri iri da rayuwa ta jefamu aciki saidai Babu wani mahaluki 'daya daya taba kallonmu da zuciya me kyau Kowa nada buri Mara kyau akanmu Wanda ya dangantamu da irin wannan rayuwar da ake qyamarmu sbd ita, Rayuwa ta zabar Mana gwagwarmayar samun Abinda zamucu kota halin Yaya alokacinda 'yaya kamarmu suke makaranta suna karatu shin anty zarah bawa shi yake zabarwa kansa qaddarane?? A tsawon shekarun ban bantaba Jin nadamar daukar abin waniba sai a jiya Dana jawa macen data Soni tsakaninta da Allah batareda ta hada komai daniba, Anty zarah a shirye nake Dana bar Nan sbd zamana anan masifa zai janyo Miki ba alhe....... Rungumeta anty zarah tayi da sauri Yana sakin sheshekar kukan datakeyi na tausayin Amatun da usman tareda su kawu dasuka taimakesu bayan Suma taimakon suke nema. Tabbas Amatu sbd Allah nakesonki tun ranar da kikazo Nan, Kinmin laifi Amma ban riqeki a raiba sbd sanin ajizanci irin na 'dan Adam, A da Ina zaune dake amatsayin matar Dr dakuma Amana da aka bani Amma daga yanxu zan zauna dakene amatsayin qanwa da muka fito ciki 'daya. Zamewa Amatun tayi da sauri tana share hawayenta ta saki qaramar dariya tanason kawar da kukan anty zarah din tace" Anty da gaske? 'daga Mata Kai tayi tana share hawayenta itama. Anty zarah karfa wata Rana kice aa alqawari kikamin munzama kamar ciki daya muka fiyo. Dariya antyn tayi har lokacin hawayenta Basu Gama tsayawaba tace" Amatu nayi alqawari ba canzawa Amma kema kinsan kinyi alqawari zakiban babynki idan kin haihu"" tafada cikin tsokanar Amatun. Da sauri ta kalla Dr dayayi mutuwar zaune da tsananin so,qauna, tausayi tareda ganin girman Amatun Ta dafe cikinta tana cewa'' Dr kaji anty zarah Wai zamu Bata babyn. Yana kallonta cikin tsananin shauqi yace" Idan har kin amince zaki Bata ni Kuma idan har nine dadynsa nayi alqawari da hannuna zanbatashi. Murmushi yasaki tana shafa cikinta ahankali tace" Inama inada cikin wlh Dana baki anty zarah. Qasa yayi da murya daidai kunnenta yace" Karki damu watanni kadan ne yarage mufita wannan dilemma din zamu bawa antynki da MD baby. Kallonsa tayi da sauri tana boye dariyarta Dan batasan yajitaba ganin yakasa daina murmushi yasata miqewa da sauri tayi hanyar dining tana cewa'' Anty zarah mijinki yagama ci muzo muyi namu party din a dining Dan wlh har yunwar jiya saina fanshe abuta. Murmushi sukeyi suna Mamakinta ganin tabbas Bata aje al'amarin duniya a ranta sbd karta wahalar da kanta a banza sbd me gatane ke tsayawa kuka da damuwa Dan a lallashesa suda basuda ko daya sunyi futo na fito da kuka da damuwa tareda abin kunya Sam baya damunsu. ##Mamuh# ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 18_* _Mg_ Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya Mata qwarin gwiwaba amma Dole yace Mata MD yariga yafice tun dazu so karma su jirasa suyi abinsu shima bai tsayaba sbd yau umme tace taredashi zatayi breakfast ya fice ya nufi can tun kafin rashin zuwansa ya shafi Amatu Dan Babu ranarda Bata tsinewa ranar data Fara haduwa da amatun. Shiru anty zarah din tayi a sanyaye Jin MD baya gidan ya fice. Dafa hannunta dake zuba chips Amatu tayi tana murmushi tace" Anty karki damu zai hakura inshallah, Nice nayi laifin Kuma nice zan gyara Inshallah Allah saina sa Rabin ranki ya yafe Miki Dan haka ki daina damuwa Amatu zatai Miki handling komai. Qasa tayi da murya Yana cewa'' Saina Fara sashi yasan dawa yakeyi kafin Nan, Shine jiya haddasa Dr ya durqusa agabansa Yana wani daddaure fuska Yana Shan qamshi to zaisan yasa Dr da anty zarah damuwa indai nice Amatu saiya sani. Me kike cewa Amahh. Cika baki tayi da chips da kwai tana cewa'' Bance komaiba anty zarah Zauna kici abincinki karki Hana kanki abinci sbd soyayya. Zama tayi tana murmushi tace" Amah samun Wanda kakeso yanada Dadi hardai idan shima Yana sinks, Kinga kamar ke da Dr. Tea ta kwankwada tana cewa'' Yanxu ni da Dr son juna muke?? Eh Mana gashinan a fili Muna gani musamman Dr bayada damuwa sai Taki, Farin cikinki da walwalarki sune nasa Kina gani yanda baya iya dauke Ido a kanki koyaushe kece first priority dinsa. To ni anty banajin wainnan abubuwan da Kika fada nadai San acikin maza banida kamar su uku shi da kawu da usi, Yanda kakejin usi hakan nakejin Dr zan iya komai Dan farin cikinsa da kula dashi. Bakyajin faduwar gaba duk lokacinda Kika jiyo muryarsa kafin ya iso gareki?? Sake cika bakinta da soyayyan qwai tayi tana cewa'' Banaji Amma Kinga Rabin ranki Dana jiyo ko qamshin turaran Nan Masa me qarfi gabana faduwa yake sbd masifarsa. Tsit anty zarah tayi tana kallonta kafin tasaki murmushi tana cewa'' Shikenan karki damu zankoya Miki yanda zakiso Dr matuqa kamar yanda yake sonki. Anty zarah inason nazama wacce zata bawa Dr farin ciki da dukkanin wata soyayya.. Bazaki iya basa farin ciki ba sai kin basa dukkanin zuciyarki da soyayyarki. Zanbasa sbd shine kadai a duniya cikin maza ya cancanci zuciyata Koda zuciyata batasan meye so ba zanbada ita saiya koyar da ita da kansa. Taso bawa maganganun amatu nutsuwa Amma ta watsar sbd Amatun kanta batasan abubuwan datake fadaba Dan haka ba amfanin nazarinsu. Suna Gama cin abincin Palo suka dawo anty zarah ta zauna tana waya da ummanta ita Kuma Amatu dakinta Takoma Dan watsa ruwa. Wanka tayi ta sanya riga da skirt na atampa coffee kala ta tsaya gaban madubi Yana duba kanta tana sauke ajiyar zuciya sbd ganin Masha Allah yanxu ita da kanta sha'awar kanta takeyi sbd mulmulewa da jikinta yayi da hutu da kayan gyara jiki da fata. Akan cikinta dake shafe kamar bashi yake daukar uban kayan Dadi da abincin datake zuba Masa ba ta shafa ahankali tana gyara tsayuwa Hakanan kawai yanxu tsananin son cikinta ya shigeta duk da tasan ana Magana ne akan Abinda Babu kwata kwata saidai ita zancen yashigeta musamman idan tayi tunanin ganin babyn a hannunta tana Masa Wasa Yana murmushi irin na Dr. Dankwalin kayan jikinta ta zare tareda nadawa ta saka cikin rigarta daidai cikinta saita saki rigarta cikin yataso ya zauna daidai tareda qarawa tsayinta kyau sai tayi kamar sabuwar amarya me qaramin ciki Batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana shafa cikin saiga anty zarah tashiga tana cewa'' Amatu baki gama Shirin bane gurin Modibbo zamuje gaisuwa tunda kikazo bakije kin gaishesaba hakama umme sune fa iyayen mijinki.... Tsayawa tayi da maganar lokacinda idonta ya sauka kan 'dan matashin cikin na jikin Amatun take dukkanin farin ciki da Jin Dadinta ya fito fili ta qaraso da sauri tana cewa'' Kinga Amatu yanxu cikinki yafito sbd kinsaka riga da skirt dogayen rigunan Nan boye cikin sukeyi gaba daya.. Kallonta Amatu keyi tana murmushin ganin yanda ganin fitowar cikin kawai yasaka anty zarah wannan farin cikin to ranar da aka haifesa fa ta daukesa a hannunta. Anty zarah Inshallah kema zaki dauki ciki ki haifi 'yayan kanki Dana Rabin ranki. Allah yasa Amatu Sbd babbar adduata a yanxu shine samun haihuwa tareda MD sbd haihuwa ce kawai zanyi na tabbatarda MD ZABEERA yazama nawa,nasamu muhalli acikin zuciyarsa da rayuwarsa. Gyale coffee ta yafa akanta suka fito zuwa sashen Modibbo, Kamar Wasa saigasu sun 'dan jima agurinsa sbd yanda Amatun ta zage tana basa labarin qanxon kurege na aurensu da Dr daya sake tambayarta, Hakanan sai ta 'dan shiga ransa sbd Jin yanda sukayi gwagwarmaya itada mahaifiyata baba Jamila. Daganan sashen umme suka nufa Kai tsaye Amatu nata sake bude idanuwanta da zabeera din koina kallo takeyi cikin burgewa tana sake tantance asalin girma da wadatar Zabeera din. Kwankwasa qatuwar qofar shiga palon umme sukayi Tsawon mintuna hudu kafin me aikinta tazo ta bude musu suka shigo Amatu na santin kallon qayataccen palon da qamshi tareda sanyin AC suka cikasa. Zama zukayi jiran saukowarta saidai shiru shiru Bata saukoba Nan Zarah da aka Kira tayi baquwa ta tafi tabar Amatu na zaman jira. Saidata shafe awa kusan biyu a zaune kafin ummen ta fito cikin shigar alfarma tana waya Kuma dagaji da Dr take wayar sbd yanda take amsawa da Dan sauran haushinsa dabai Gama sakinta ba Saidata shigo tsakiyar palon ta lurada Amatu dake zaune tana kallo tana Kira ruwan lemu da aka kawo Mata hankalinta kwance Dan wuce guri da volume bai ishetaba ta dauko remote taqara tana shigaba da kallonta remote din a hannunta sai murmushin Abinda take kalla takeyi. Ko sallama da Khalil din batayi ba a wayar ta kashe tana cewa" Uban waye zaune har cikin palona? Juyowa Amatu tayi tana aje cup din hannunta da murmushi Kan fuskarta tace" Haj Mama nice Amatu matar khalil nasan zuwa yanzu kinmantani. Cikin quluwa ta daka Mata tsawa tana cewa" Uwar matar khalil din ce ba matarsa ba Zoki fice kafin nasa kiyi nadamar zuwa Nan. Matsowa Amatu tayi da sauri gabanta tana cewa'' Umme Dan Allah kiyi hkr da Abinda yafaru ba laifina bane bakuma laifin Dr bane qaddarane Kuma nidai na karba qaddarar nan da hannu biyu ta zama matar Dr wlh inaso..... Ganin tafara loosing patience dinta batason tayiwa Amatun komai yanzu sbd tanadin datai Mata tukuna shiyasata fixgota a wulaqance ta jeho ta waje daidai isowar Nuratu wajen ta tareta daga faduwar dazatai saidata dago taga Amatu ce aikuwa ta saketa amatun tayi muguwar faduwa akan hannunta na dama take ta samu kurdewar qashi tasaki wani razanannen ihu tana qoqarin tashi Amma takasa dafawa sbd azaba take wani zufa ya karyo Mata ta kalli Nuratu a masife tace" Ita waccan data jeho ni nasan dalilinta kekuwa da kikaimin haka meye naki dalilin?? Dalilina shine cikin jikinki""tafada cikin tsananin tsana da takaicin ganin cikin jikin Amatun. Miqewa tayi da qyar tana dafe hannun cikin azaba tace" To ke meye ruwanki da cikina kokuwa kema cikin 'yan koren uwar Mijina ce sbd dai bakida alama da 'yan zabeera daga Ina malama??? Baqin ciki maganar Amatun tai Mata tana sake quluwa tace" Ni ba matsiyaciya bace kamar ki wadda Babu Wanda yakeda tabbacin ba karuwa bace Khalil ya fada tarkonta ta auresa sbd kudi Wama yakeda tabbacin wannan cikin nasane Kona wani qa........ Wani gigitaccen Mari ya sauka akan fuskar Nuratun dayasa gefen bakinta 'dan fashewa Ta dago da sauri tace" Ni Kika Mara??? Zuciya data gama ciyota kukan kura tayi tai Kan Amatun zata mareta aka riqe hannunta ta bayanta ta fizge zata Kuma Yi Kan Amatun ya sake riqe hannunta tareda zagayo gabanta kyakkyawar fuskarsa ta jinin zabeera tana fidda sheqi Tace" SALMAN???? Sakeni, wlh saina koyawa wannan mummunar karuwar hankali.. Saukar wani Marin ne a fuskarta yasata qarasa zaucewa tana qwacewa tace" Wlh yau sainaga ubanda ya tsaya wannan tinkiyar... Sakinta Salman din yayi tareda kallon Amatu da mamakinta yagama kashesa yana cewa" Lallai Nima zanso ganin Wanda take dashi daya Bata wannan qwarin gwiwar me ban mamaki da burgewa Ina buqatar saninsa Dan basa jinjinawa ta musamman. Kallonsa Amatu tayi ganin Yana qarawa wutar masifar fetur tace" Amatu itace tsayayyiyar kanta Bata buqatar tsayawar wani gurin nunawa kowa matsayinsa, Ki zauna ki nanatawa tosashiyar qwaqwalwarki ni Amatu nariga Masha gabanki Idan har akwai Amatu har abada Dr khalil zabeera bazai taba kallonki ba Kai da kake Dan uwanta saika taimaka Mata gurin fahimtar hakan Amatu ba tsarar yinki bace. Tana Gama fadar hakan ta wuce Yana shafa cikinta Dan qara qular da Nuratun Cikin mugun baqin ciki da takaici nuratu ta juya a zuciye tabar gurin tana fidda huci kamar zuciyarta zata tarwatse idanuwanta har wani cikowa da hawayen baqin ciki suke Dama can Kuma halinta ce saurin fusata. The great ORTHOPEDIC Dr Salman zabeera kuwa gabaki daya Amatu tagama basa mamaki lokaci daya da burgesa sbd sanin darajar kanta datayi takuma nuna batareda tsoro ba, Koma wacece Amatu shi tagama burgesa shiyasa yakasa dauke Ido daga kanta harta bace. ##Mamuh# ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 19_* *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_* *KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?* *wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya* *magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*ğŸ’†ğŸ¾â€â™€ï¸ğŸ™ŽğŸ½â€â™€ï¸? *magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽‍♀️👯🏽‍♀ï¸? *karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke* *garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac* *ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz* *_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_* *_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ ********** Doguwar tafiya tayi har zuwa sashensu tana Jin tsananin azabar radadin da hannunta keyi ta daure ta iso tana rintse ido cikin uwar azaba ga zufa sai karyo Mata yake shiyasa tana isowa tun a Palo ta zube Kan kujera tana kallon hannun da harya Fara kumbura Sanin anty zarah na dayar palon tareda baquwarta yasa ta sulala tayi dakinta ta kwanta Dan kada ta dagawa anty zarah din hankali saidai ita kadai tasan uwar azabar datake ciki shiyasama takira usi Yana daga wayar sai alokacin taji hawaye sun ciko idanuwanta sai Kuma takasa mgn ta kashe wayar ta ajiye tana gani yanata Kira takasa dauka sbd karta daga Masa hankali kawai. Duk yanda take tunanin zata iya riqe ciwon takasa sbd sosaine tasamu gocewar qashin hannun sai kumbura yakeyi har takai tafara kasa motsasa sbd tsamin daya dauko. Har dare tana dakin Taki fitowa sai bayan magrib baquwar anty zarah ta tafi Itama anty zaran dakinta ta nufa sai datayi sallar magrib da ishai tukuna ta fito palon saidai rashin ganin amatu a palon yasa ko zama batayiba ta nufi dakinta. A kwance ta taddata Idanuwanta a rufe tanajin anty zarah din ta tashi zaune tana rintse ido alamar ciwo Nan anty zarah din ta qarasa bakin gadon da sauri tana dafa Hannun me azabar Bata saniba Wani irin zabura Amatu tayi cikin tsananin radadin dataji tana tana cewa'' Anty hannuna ya karye. Da sauri anty zarah ta kalli hannun batasan lokacin data zaro ido ba ganin ya kumbure sul a rude tace" Amatu meye wannan nake gani? Garin Yaya hakan yasame ki?? Sai alokacin hawayenta suka gangaro tace" Anty wannan me son Dr din ce ta tureni na Fadi a hannun..... Mene??""anty zarah tafada da qarfi tana maida kallonta Kan cikin Amatun da har lokacin Bata cire cikonba tace" Ta ture ki batada hankaline bataga Abinda ke jikinki bane ko so hauka ne Bari nakira Dr yanxun Nan yazo Ita Kuma Nuratun I will deal with her later wannan ai ganganci ne. Dr najin Abinda yafaru hankalinsa ya tashi gashi wani mahimmin meeting sukeyi sbd gobe shida wasu manyan likitocin asibitinsu zasuyi tafiya zuwa china gurin wani program na sati biyu. Tunda zarah takirasa tafada Masa hankalinsa ya rabu biyu Meeting din kawai suke Amma Rabin hankalinsa na gidan sanyi daya dayakeji aransa shine SALMAN yananan yadawo kwararren likitan qashi ne yasan basa buqatar zuwa koina. Sai guraren 8:40 suka fito gashi Kuma yanada wani Wanda yayiwa alqawarin ganinsa idan yafito hakanan yakoma office dinsa Koda ya Isa office din mutumin na kiransa Nan suka Fara mgnar dazasuyi ahankali yanayi Yana shafa qirjinsa da numfashinsa ke Dan sauyawa tun safe yakejin hakan Kuma yasan alamace ta ciwonsa zai iya tashi ko wane lokaci Amma meeting din yasa baisamu damar amfani da inhaler gashi idan yataso duka Dole saidai oxygen Wanda duk lokacinda aka saka Masa oxygen rayuwarsa tana cikin mugun hadari ne sbd oxygen din nabawa lungs dinsa matsala sbd dama can basuda qarfi lungs din tun haihuwarsa shiyasa shida likitocinsa sunriga sunkai qarshe akan karya taba Bari ciwonsa natashi gaba daya harya tafi qarfin inhaler ta riqesa. Qoqarin Kama numfashinsa dake son qwace Masa yakeyi Yana dagawa mutumin Kai sbd Magana tafara son gabatarda ya dago daqyar ya kallesa Yana dannewa yace Masa yaje zai nemesa idan yadawo daga tafiya zasuyi Magana. Mutumin na fita ya dafe qirjinsa cikin tsananin azabar rashin fitar numfashi idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa sunfito sosai Hannunsa na rawa ya jawo drawer office din nasa ya Fara laluba baiji inhaler dinsa ba, Firfito da duka kayan ciki yayi Yana watsowa cikin sauri da tsananin azabar dayake ciki baiganta ba gashi yafara loosing control din kansa sbd idanuwansa sun Fara gani dishi dishi Da sauri ya miqe ya dauki wayarsa da keys din motarsa ya fito Yana riqeda kurkinsa ya nufi motarsa ya fada Yana tayarwa yafito asibiti saidai abin yaci qarfinsa gaba daya zuwa lokacin sbd numfashinsa daya dawo gaba daya bakinsa tuni motar tafara qwace Masa. Daga government house yafito daga wani guntun meeting dayayi da deputy governor akan investing dasuke sonyi a sabon ZABEERA LTD dinsa dake Bangkok, Shida malam Umar ne a motar shike tukasa Gaba daya hankalinsa nakan wayarsa dayake duba tarin misscalls din da akaita Masa Wanda duk yawanci daga mutanen hurdarsa ne sai sauran daga family wainda yasan dukansu bazai wuce buqatar kudi daga garesaba Wanda Sam shi ko mamakinsu baida lokacin tsayawa yayi Misscal din zarah guda hudu ne ya kalla numbernta dayayi saving da ZB wato zarah zabeera, Sam Bata gajiya da Kira ita duk da tasan bako yaushe yake dagawa Amma Sam taqi sabawa da hakan Wasu mutanen suke aikata Abinda zai 6ata ransu, Abinda tasani ya koya a rayuwarsa shine kayi rayuwa akan mizanin dazai baka nutsuwa da ease Baya tunanin har abada zai iya jefawa ko Kai kansa ga Abinda zai baqanta ransa ya Bata Masa Rai yayi iya qunci da baqin cikin dazaiyi tun Yanada quciya Dan haka wannan babin na damuwa akan alamarinda wani zaisaka ya Dade da wucewa agurinsa MD ga wannan kamar motar Dr khalil ce Kuma kamar dai ba lafiya ba Dan..... Bai qarasa yayi saurin over taking motar Dr din sbd wani junction dazata nufa ta buga. MD din ne da kansa yafito ya nufi motar Yana budewa idanuwan Khalil din na qoqarin rufewa da zafin nama ya fizgosa daga cikin motar tareda taimakon malam Umar suka kamasa zuwa motarsa da kansa ya qara sanyin AC din motar tareda fitowa cikin sauri ya zagaya ya bude gaba cikin sauri yabude can qarqashin sit din driver saigashi yaciro inhaler da sauri ya zagayo ya dago Kan Khalil din Yana shaqa Masa Amma Ina Sam ko Shiga batayi sbd numfashinsa ya tsaya gaba daya. Kasa mgana yayi yafito idanuwansa na sauya ya karbi mukulli hannun malam Umar ya zagaya ya figi motar cikin mugun speed din dayasa Mutanen gurin watsewa da sauri sbd gudun tsautsayi shikuma Mal Umar yashiga motar Dr din yaja yabi bayansu. Zabeera ya nufa Kai tsaye Securities suna hango motarsa da yanayin da yake tahowar cikin speed yasasu saurin wangale Masa makeken gate din da mutum uku ne ke iya rufesa Yana isowa yashige gate din Yana qara gudun motarsa yabi bangaren dama inda tacan gefen hanyar zuwa part din Khalil din yake. Yanayin parking bakin part dinsa yafito ya nufi wata qatuwar flower vase dake bakin qofar shiga palonsa inda anan yasan Khalil din na aje keys dinsa. Ya a budewa da bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye sbd yasan inda allurar take Tun daga cikin dakin ya hadota yadawo motar Yana shiga ya daga hannun Khalil din ya soka Masa tareda dannata da sauri ruwan suka shige jikinsa take yayi wani irin yunquri tareda Jan numfashi me qarfi da qara kafin jikinsa yakoma yasaki. Sai alokacin MAHMOUD ya sauke ajiyar zuciya Yana 'dan dafe goshinsa tareda lumshe fararen idanuwansa dasuka sauya kala., A duniya idan akwai mutum daya dazai iya sadaukarwa Koda rayuwarsace to shine Khalil, Khalil ne kawai weakness dinsa a duniyar Nan sbd shikadai ne yake shiga tashin hankali akansa aduk lokacinda yaga ciwonsa yatashi sbd hakan na razana jarumtarsa Dan Khalil shine mutum na qarshe dayake baya iya tunanin ma rasawa, A rayuwarsa he has only two dear ones, Na farko mahaifiyarsa da har yanzu take cikin qasan ransa daya kasa cire kewarta, Sai na biyun shine khlail,Wanda bayada wani Dan uwa dayake gani amatsayin jininsa kamarsa. Tsananin mataki da kulawar daya daukarwa ciwon Khalil din yasa dukkanin motocinsa da office dinsa yanada ajiyayyar inhaler dayake ajewa sbd Khalil din Dan Koda ta kwana irin haka. Ahankali yaji an dafa hannunsa Saida yaqara rinste idanuwansa yasaki qaramin numfashi kafin yabudesu akan hannunsa da khalil din ya dafa a wahalce. Kallon fuskarsa Khalil yayi tareda sakin wani wahalallen numfashi ganin duk duniya idanba ubangiji daya halacci MAHMOUD din ba Babu me iya gane kowane yanayi na MAHMOUD da Abinda yake ciki sbd fuskarsa Bata taba nunawa,farin ciki ko akasin hakan. Kallonsa yayi da jajirtaccin idanuwansa cikin nutsuwa yace" Koma me kake tunanin kanayi zaifi idan kadawo kanka, You know this is stupidity right?? Menene amfanin aiki da gwagwarmayar idan Babu lafiya you better come back to your damn senses. Girgiza Masa Kai Khalil yayi tareda qoqarin fitowa motar Amma bazai iyaba sbd jikinsa ba qwari Dole MAHMOUD din yakamasa suka fito yakaisa har cikin bedroom dinsa kafin yayi amfani da wayar khalil din yayiwa umme txt akan bayajin Dadi. Harzai juya ya fice Khalil din ya riqo hannunsa Saida ya fidda numfashi ahankali na marasa lafiya kafin ahankali ya furta" Thank you. If you want to thank me be careful about your health, Next time idan kayi Wasa irin haka yafaru ka shirya rabuwa Dani sbd i can't take this stupidity, U're unbelievable Khalil Kana likita Amma Kaine kake Wasa da lafiyarka har kake tunanin yin tukin mota cikin wancan yanayin, Menene cikin kanka dayafi kula da lafiyarka mahimmanci???? Amatu. Tsit MAHMOUD yayi sbd Jin zancen na Khalil a bazata. Kallonsa yayi cikin zallar mamakin irin like seriously?? Lumshe ido yayi Yana sake maimata sunan Amatun a gajiye Yadora da fadin" MAHMOUD wallahi Amatu itace tunanin kulawa da ita yafimin lafiyata, Acikin yanayin danake ciki Babu Abinda nake tunanin cimmawa kamar na iso gida gareta sbd tana cikin halin buqatata akusa, Banajin yanayina kawai Abinda nakeso na iso gida alokacin. Zame hannunsa MD yayi tareda miqewa Yana qoqarin barin gurin sbd idan baiyi nesa da Khalil ba tsaf zaisa a binciko Masa the best psychiatrist Dr taduba Masa shi. Tashi zaune Khalil din yayi cikin dasasshiyar murya yace" Amatu amanata ce idan kana qaunar 'dan uwanka zaka kulamin da ita aduk lokacin da bana kusa Shine kawai Abinda nake roqanka a matsayin alfarma ta har iya rayuwa. Cak ya tsaya tareda kasa juyowa zuciyarsa na juya Abinda Khalil din yafada Wanda yasashi Jin wani iri saidai kawai ya wuce batareda ya juyoba Kuma baice kala ba ya ficewarsa daidai isowarsu umme tareda Nuratu da tuni hankalinta yayi mugun tashi Jin Khalil dinta bayajin Dadi. Zaune zarah take a Palo tana jiran isowar Khalil din sbd tayita kira daga bayan nan wayarsa a kashe Allah ma yasa Amatun tasamu bacci ya 'dan dauketa. Yana shigowa ta dauka Khalil dinne tayi saurin miqewa zatai Magana saitaga MAHMOUD ne fuskarsa daukeda wani yanayi na kasala da sauri ta qaraso gabansa tana cewa" Sannu da dawowa¿ Kallonta yayi tareda kallon agogon dake palon yasake maido da idanuwansa kanta yayi Mata kallon minti biyu cif ahankali ya daga Mata Kai alamar amsawa cikin sautinsa me sanyi yace" Haryanxu kina zaune a Palo Akwai matsala ne? Kallonsa tayi wani irin sanyin Dadi na kwaranya cikin zuciyarta harsaida murmushinta ya bayyana ta kalli cikin idanuwansa ya dauke Kai sbd Sam bayason ana kallon cikin idanunsa ahankali tace" Dr nake jira nakirasa tuntuni yanzu Kuma wayarsa akashe Amatu ce ba lafiya taji ciwo sosai a hannunta..... Cak ya tsaya daga tafiyar dayakeyi batareda ya juyoba saikuma ya tafiyarsa Yana cewa'" Shima bayajin Dadi bazaiso damuwa ba yanzu shima Kuma gobe tunda safe zaiyi tafiya so just handle her situation for him. Wucewa yayi yabarta tsaye dafe da goshin tunanin mafita da abin Yi. Ganin Amatun tasamu bacci haka ta lallaba itama taje ta shirya tayi dakin MD din saidai duk Rabin hankalinta na qasa gurin Amatu. Dr Khalil kuwa asubar farko lafiya kalau yatashi da qarfinsa kamar baisamu attack din ba ajiyan, Qarfe Bakwai na safe jirginsu zaitashi Dan haka qarfe shida da rabi yafito a shirye driver din umme zai kaisa airport Yaso ganin Amatu Amma yasan lokacin Basu tashi ba hakanan ya hakura ya wuce bayan yayiwa zarah text tareda transfer din kudi masu kauri na kulada duk Abinda amatun ke so kafin sati biyun yadawo, Hakama bai wuceba Saida yayi Magana da Salman akan zaije yaduba Amatu yasan matsalarta da Abinda za'ayi Mata. Tun qarfe hudun asuba ta tashi tayita juye juyen azaba tun tana daurewa harta kasa tafara hawayen azaba tana juye juye Dan haka Koda gari ya waye anty zarah tashigo tuni idanuwanta da fuskarta sungama kunburewa sbd kukan azaba aikuwa tana ganin anty zarah din ta sake sabon kuka Da sauri zarah ta rungumeta tana rarrashinta da Mata sannu kamar zatayi kuka. Hannun har wani qyallin kumburi yakeyi shiya qara daga hankalin zarah ta kamota suka fito Palo tana cewa'' Dr yayi tafiya Bari nafadawa MD zamuje asibiti. Tana qoqarin juyawa saiga qwanqwasa qofar Salman tareda usi bayansa Wanda Dr khalil ya roqesa akan yadaukosa aje dashi yaduba Amatu sbd tun jiyan data kirasa taqi Magana hankalinsa yake atashe. Aikuwa amatu na ganinsa tasaki sabon kuka Da gudunsa yayo gurinta hankalinsa a mugun tashe Yana cewa'' Amatu?? Zama yayi kusa da ita Yana kallon hannunta sai kawai yaji shima idanuwansa sun ciko da hawaye kamar mace saigasu suna gangarowa. Dr salman zabeera sai suka basa dariya ya zauna Yana duba hannun Yana cewa" Zarah kina ganin mutuniyarki tasa oga Usman kuka saikace ba namiji ba, Usman dama jarumtar taka a baki take kenan. Matsa hannun nata yayi da qarfi take tasaki wani razanannen ihu tana damqe hannun dataji akusa da hannunta dake Kan hannun kujera Shikuma da saukowarsa kenan basusan dashiba ba yazo wucewa yaji an damqe hannunsa ya tsaya cak batareda ya juyoba sbd ko bai juyoba yasan itace sbd zafin ciwo ta riqesa batareda tasani ba Saidai Kuma samun kansa yayi da tsayawa batareda ya qwace hannunba yana gane radadin datake ji ta hanyar yanda ta mugun matse hannunsa. ##mamuh# ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 21_* *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_* *KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?* *wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya* *magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*ğŸ’†ğŸ¾â€â™€ï¸ğŸ™ŽğŸ½â€â™€ï¸? *magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽‍♀️👯🏽‍♀ï¸? *karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke* *garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac* *ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz* *_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_* *_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ ********** Seat din gaba yasakata ciki tareda 'dan kwantar da seat din ya rufe ya zagaya yashiga motar ya tayar yabar gurin cikin gudu sosai, Cikin mamaki securities suka firfito Amma suna ganinsa sukai saurin bude Masa gate din suna Masa adawo lfy kota kansu baibiba ya fice. Anty zarah sai alokacin ta tsaya sake da idanuwa tana cewa" To Ina zai iya da ita shi kadai daya Bari nabiyosu, Kiran khalil ne yashigo wayarta cikin sauri ta dauka tana fada Masa MD ne yatafi Kai Amatun asibiti..... What????""""yafada da sauri cikin firgici Yana cewa'" Me umme tace? Yaushe suka tafi?? Umme Bata daga wayarba gashi jini yafara balle Mata shine yatafi kaita da kansa, Dr Ina fatan kada wani Abu yasamu cikin Nan Dan Allah ka Kira asibiti tun kafin su Isa kafada musu suyi duk iya qoqarinsu Dan Allah karsu Bari cikin Nan yasamu matsala. kasa Magana yayi ya kashe wayar tareda Kiran Dr Fatima dayasan asibitin na hannunta yanzu tunda bayanan cikin tsananin damuwa da tashin hankali yayi Mata bayanin abindake faruwa. Cikin sauke numfashi tace" Karka damu Bari su iso Ina asibitin yau zanyi call(night) ne Inshallah za'ayi yanda aka Saba Mata duk wata, Problem din dai shine sunriga sunga cewa tafara bleeding ya zamuyi da wannan? Just handle everything please Dr Fatima Nabar Miki komai ki kula dashi nidai kawai please Dr Fatima Amatu azaban datake ciki nakeson kifara bi takai Inaji ajikina tana cikin azaba sosai Dan Allah Dr Fatima ki kularmin da ita gobe zan biyo jirgin Rana nadawo bazan iya daukaba Tafiyan kwana daya harta Fara shiga abubuwa iri iri..... Calm down please Dr khalil komai zai zama daidai Inshallah Babu Abinda zai samu Amatun zanyi iya dukkanin qoqarina gurin ganin Babu Abinda zai sameta. Thank you Dr""yace Yana kashe wayar sbd Jin ana buga office din datake. Tun kafin ta aje wayar nurse Abida tashigo tana cewa'' Dr Fatima ga MD ZABEERA nan matar Dr Khalil ya kawo it's emergency mun karbeta ke ake jira. Medical glass dinta kawai ta dauka ta miqe suka fito sister Abida nasake Mata bayanin taimakon gaggawar dasuka Bata. Tana zuwa taga halinda Amatun take ciki take tasaki wani guntun murmushi sbd ganin yanda Dr khalil ya daga hankalinsa akan alamarin ba haka bane menstrual pains ne kawai. Nan tahau dubata tareda Bata allurai Dan samu 'dan relief tareda qarin ruwa sai paracetamol data Bata. Tana fitowa daga cikin emergency din sister Abida ta biyota tana cewa'' Dr Fatima zamuyi shifting nata ne zuwa Amenity ko kuwa? Yes u can shift her Amma kafin Nan kufara taimaka Mata ta gyara so that kar jinin ya qarasa Bata Mata jiki, Ok zamu Bata pad ne kokuwa abata cotton tayi amfani dashi, And dose na injection dinta after 2 hours ne zamu sake Bata parainject din?? Yes after 2 hours ko Kuma 3 hours tunda menstrual pains ne kawai. Ok. Sister Abida na barin gurin Kiran Dr khalil ne yashigo wayarta saidata saki numfashi kafin ta dauka tana cewa'' Kafin kace komai Dr khalil please listen to me Maganar gskia Dr yarinyar Nan tunda har kasan kowane wata irin wannan matsalar ta al'ada na damunta Kaine kawai zaka iya magance Mata matsalar sbd kada wata Rana abin ya zarce ya zamar Mata matsala babba, Mu'amalar aure ne kawai zai kawo Mata qarshen wannan monthly pains din. Zata sake Magana ya katseta da cewa" Dr Fatima lafiyanta kalau yanzu dai ko?? Eh komai ya daidaita zuwa asuba zasu iya tafiya gida.. Ok thank you Fatima Sauran maganar please mubarta idan nadawo zamuyita. To kawai tace tareda kashe wayar ta wuce tabar gurin batareda ta juya taga MD dake zaune a bayantaba idanuwansa ne kawai ba'a kanta ba Amma hankalinsa gabaki daya akan zancen datayine tunda nurse Abida har Khalil dasuka Gama Magana yanzu, Shiru yayi Yana qoqarin nazarin fahimtar zancen sbd idan har yayi amfani da iliminsa na 'dan Adam Koda baitaba haihuwaba ko samun ciki da amatarsa yasan dai Mai ciki Bata period, Hakama Mai aure harda ciki baza'a ce Yana buqatar rayuwar auratayyaba kafin yasamu saukin cramps, Bude idanuwansa dake lumshe yayi ahankali Yana tunanin Khalil na boye wani Abu gameda yarinyar Nan wanda yake da matuqar mahimmanci ko hadari, Koma dai menene ba huruminsa bane Abu dayane zai fadawa Khalil yasan Abinda yakeyi. Dakin da aka maidata ya qarasa yashiga lokacin ta bude idanuwanta daidai shigowar tasa sai idanuwansu suka shiga cikin na juna Ita tayi saurin yin qasa da idanuwanta sai kawai idon nata ya sauka kan farar jallabiyarsa da jini ya Bata daga gaba gurin cikinsa take tayi saurin rintse ido akaro na farko wata irin kunya me tsanani ta kamata saita samu kanta da kasa bude Ido ta kallesa. Shi kuwa dauke Kai yayi tareda kallon inda yaga ta kalla din kafin ta rintse ido Idonsa ya sauka kan abindake rigarsa Saurin dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi take kallo tana jiran reaction dinsa Sai kawai shima yaji abin wani iri sbd shi ko so daya Koda Wasa baimasan ya kalar jinin Mata yakeba Dan ko amafarki baitaba ganin na matarsa ba bare gashi yanzu Yana ganin wannan ajikinsa ma...... Fuskewa yayi tareda juyawa yabar dakin tanajin wani irin yanayi kamar yanajin kunyar kansa. Itama Jin tayi kamar qasa ta tsage ta shige har batasan lokacinda ta Dan daki kantaba tana cewa'' Wannan abun kunya yayi Miki yawa amatu. Daga shi har ita kowannensu kasa hada fuska yayi da Dan uwansa sosai ya hade fuska har aka sallamesu suka dawo gida zuwa lokacin Tama fisa Jin kunya ganin yanda ya fuske ko nuna yanani baiyiba. Har suka Isa bame motsi cikinsu ita tafara fita tayi ciki da sauri tana gyara zaman hijabin da Dr Fatima ta Bata ta sanyo. Anty zarah dake safa da marwa a Palo sbd rashin sanin ya ake ciki gashi yabar wayoyinsa gida Tana ganin Amatu tayo kanta da sauri tana riqota zatai Magana kenan sai gashi shima yashigo fuskarsa na Kan agogo zatayi Masa gamana idanuwanta suka sauka akan rigarsa dake daukeda stain din jinin Amatu Wanda ta tabbatarda daga jikinta ya fito sai ta dago ta kalli fuskarsa dayake qoqarin rabata ya wuce Sai kawai taji wani irin yanayin kishinsa ya Dan shigeta Ta juyo ta kalli amatu da kunya qarara ta bayyana Kan fuskarta har tana sauke Kai sai ta watsar kawai da tunanin komai cikin kulawa tana Jan Amatun zuwa daki tace" Amatu ya babynki? Ina fatan Babu Abinda ya samesa?? Daga Mata Kai Amatun tayi zata sake mgn Kiran Dr khalil yashigo wayarta data Bari gida Kan gadonta. ##Mamuh# Please Dan Allah kuyi manage inada uzuri ne yau🙏🙏🙏 ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 20_* *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_* *KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?* *wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya* *magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*ğŸ’†ğŸ¾â€â™€ï¸ğŸ™ŽğŸ½â€â™€ï¸? *magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽‍♀️👯🏽‍♀ï¸? *karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke* *garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac* *ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz* *_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_* *_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ ************* Jin mutum ta bayansu a tsaye yasa anty zarah Dan dagowa tana qoqarin juyawa Amatu tasaki wani sabon ihu dayasata dawo da kallonta Kan Salman cikin damuwa da tausayin Amatun tace" Salman please ka danyi Mata ahankali kodan juna biyun jikinta..... Daga salman din har MD cak tunanin kowannensu ya tsaya da maganar da Zarah din tafada, Zame hannunsa yayi da sauri tareda barin gurin kansa na Dan sarawa sbd ihunta daya cika part din gaba daya, Yana fita qofar gym dinsa dake maqale data shigowa palonsu yashiga Yana qoqarin clearing mind dinsa da cewa'' Khalil wane irin shirme kasani aciki¿¿ Matarka ce and she's pregnant.... MAHMOUD just stay out of this. Geamin din dayazo Yi yafara Yana komawa asalin MD ZABEERA dinsa. Salman kuwa shiru yayi Yana nazarin kalmar a cikin kansa duk da dai ba yanzu ne yasani ba tun kafin yadawo Nuratu ta sanar dashi komai Kawai abin rudewar anan shine shedan dake saka Masa wasi wasin hakan sbd Amatun data shiga kansa hakan kawai yake jin bazai Bari Nuratu ta cutatar da itaba Koda Bata ciki, Abu daya daya sake tsaya Masa arai shine Sam idanuwansa da iliminsa na likitanci duk da bana mata ba sun kasa gasgatar Masa da akwai ciki a jikin Amatun. Kallon fuskarta yayi ahankali yasaki murmushi ganin hawaye shabe shabe a fuskarsu su duka ukun,ita da usi harda anty zarah din ma. Handkerchief dinsa dayake daukeda tambarin asibitinsa da sunansa ajiki yaciro daga aljihunansa ya miqawa usi yace" Usman share Mata hawayenta. Daqyar da fitina da koke koke ta ihu da komai aka dubata yasa Usman yaje motarsa ya dauko wasu magunguna da allurai yayi Mata da kansa yabata maganin Yana Mata sannu tareda tsokar yanda idanuwanta suka kumbura sbd kukan raki. Saidata ci abinci da sauran maganin yaga anty zarah takaita daki ta kwanta tafito tace Masa tayi bacci kafin yatashi suka fito tareda usi dakejin kamar karya tafi yabarta ta bangare daya Kuma kallon koina yakeyi Yana jaddada daula da dukiya irinta wannan ahalin zabeera. Sashen Salman din suka nufa cikin motarsa sbd kowane sashe zuwa sashen akwai 'yar tafiya shiyasa duka yawancinsu da motacinsu suke zuwa sashen juna sai dai idan kaso motsa jiki kaje da qafa. A palon Salman din suka zauna Nan USI yaqara ware Ido Yana kalle kalle badan yayiwa Dr khalil alqawarin bashi ba abin wani har abada ba da yau Allah ne kadai yasan abubuwan dazai sanfe daga cikin zabeera dinnan Dan tun a part dinsu anty zarah yaga abubuwan dauka Amma hakanan ya hadiye ya dauke Kai sbd karya kunyatar da Dr khalil. Abinci lafiyayye aka aiko daga part din mahaifiyarsa Haj Maryam aka jera Masa a dining suka zauna ci shida usi dasukai sabo cikin qanqanin lokaci sbd gano tsananin qauna da kulawa dake tsakaninsu shida Yar uwarsa Amatu. USI na Ido biyu da kayan Dadin dake jere a dining din take yaji hakurinsa na Kama mutuncin Kai ya qare take ya washe baki Yana cewa'' Allah ya taimakeni saura kadan yau nadauki azumin alhamis da Dr ya doramu akai nidasu kawu Kawuma yau dayaji Dr yayi tafiya wlh win dauka yayi yace mu huta kwana biyu kafin Dr din yadawo sbd duk litinin da alhamis taredamu yakeshan ruwa acan gida. Dariya sosai Salman yayi Yana sakejin Usin na burgesa sbd baya boye boye yace" Kace yau dai akwai ciye ciye sai ciki yakasa dauka. Lumshe ido USI yayi bayan yazuba kakkauran soyayyan kwai cikin bakinsa dayaji kayan qamshi da albasa take yasaki murmushi Yana sakawa Dr khalil da adduar samun nasara a rayuwa Dan komai suke samu a rayuwa sbd shine Yagama Basu duk wani Abu da suka kasa samu a rayuwarsu ta kadaici, talauci,garari da rashin sanin daraja. Sosai salman yaji tausayi da qaunarsu tareda son samun Lada da adduar da Dr khalil ke samu daga garesu sbd kyautatawa da kulawar dayake Basu amatsayinsu na wainda basuda shi, A iya firar da yayi da USI ya fahimci su din talakawane masu tsananin buqatar taimako Wanda yasa Dr Khalil shigowa rayuwarsu ya taimakesu har suke ganinsa a Wanda yafi musu kowa da komai, Idan baiyi kuskuren tunaninba yanasa ran sbd tallafawa rayuwarsune yasa ya auri Amatun batareda sanin iyayensu ba, To Amma Kuma a yanda labari yazo a zuwan Amatu zabeera ance batada mahaifi ita din marainiyace, To shi kawu waye tunda ba'a ce sunada kawun ba a takaice cewa akayi basuda kowa, Gashi yanzu yanatajin sunan kawu a bakunansu, Da akwai inda wani Abu ya maqale to, Akwai Abinda dagasu sai Dr ne suka San abinsu koma dai menene yasan Dr khalil ya boye ne sbd wani dalili me kyau. To gashi shima Amatu da USI sunshiga ransa alokaci daya, Yaji yanason kasancewa acikin farin ciki da walwalar da Amatu da ahalinta zasu samu. Bayan sun Gama cin abinci shigewa yayi ya kwanta yabar USI yanata faman kallon wani action film Yana cin wani lafiyyan dabino me laushi daya Gama daukan sanyi a fridge. Sai azabar salman din yatashi bacci zuwa lokacin shima usi ya Dan miqe a kujera yayi baccinsa sanyin AC na hudasa hankali kwance. Tayar dashi salman yayi tareda nuna Masa dayan bedroom dinsa yace yaje yayi wanka zai kawo Masa Kaya. Dakinsa yakoma ya hadowa usi din manyan kayansa designers masu kyau da tsada kusan kala shida da takalma na alfarma da agogai ya hado Masa tareda wata qaramar akwati yasa aciki yakawo Masa saiga usi yayi wanka ya shirya tsaf cikin qananan kayan dasuka fiddo da ma'anarsa da kyawun dayake dashi shima hardasu feso turaren da duk ya shaqa a jikinsa saiya saki murmushi abinsa Yana sake godewa Salman da yiwa Dr khalil addua. Dasuka fito Saida suka koma yasake dubo Amatu zuwa lokacin har ta tashi bacci itama tayi wanka taci abinci tasha magani tana zaune Palo anty zarah na gefenta tana miqo Mata yam balls datasa akai Mata tana ci tana tunanin Dr Khalil da har lokacin basuyi Magana ba. Kwankwasa qofa akayi hafsatu tazo daga kicin tabude suka shigo suna yar fira kamar wainda sukai shekaru atare duk da Dr salman ne me jan usi din da firar sbd yasake sosai dashi Dan dama can shi Dr Salman yanada Magana sosai da son raha da Wasa. Tunda taga USI da kayan dake jikinsa ta sake baki tana kallonsa cikeda mamaki tana cewa'' Usi a Ina ka...... Da sauri yace" Dr Salman ne ya...... Katsesa shima Salman din yayi da cewa" Wai Kai itace yayarka ko Kaine yayanta da kake Jin shakkarta ne., Sosai Kai usi yayi Yana murmushi yace" Dr bakasan Amatu bane da zafin Rai yanzu Nan saitace zata fasamin Kai ko baki. Dariya Dr da anty zarah suka sake Anty zarah tace" To lallai Nima naji tace zata fasa maka Kai da baki yafi so goma Amma bantaba ganin anyi ba. Kallon Amatun usi yayi Yana cewa' Anty zarah dafa tanayi yanxune anan batama ganni ba bare tayi Amma ada tsaf zata saka wata Jakarta me kama data wanzamai ta kwadamin akai ko baki Jakar Nan yanda kikasan da qarfe akayita tsabar qarfi. Dariya duk su duka suka sake sosai hadda hafsatu dake jera abincin Rana a dining Itama Amatu dariyar tayi tana cewa'' Usi tashi kabar Nan kafin na fasa maka baki wlh... Kinji ko anty zarah tasake fada Ai a yini tana cewa zata fasa bakina da kaina yafi so ashirin Kawu ne duk ta fada sai yayi sadakar ruwa wa qadangaru su Sha Wai yana fidda Mata baki kada fada Babu cikawa ya fado Mata. Filon kujerar datake ta dauka ta jefa Masa da qarfi tana cewa'' Kamar anyi a kunnen kawu Kuma Allah saina fadawa Dr yau bakayi azumi ba dan Banga alamarsa atare dakaiba yanda nasanka kamar mace da mugun Jin azumi. Kallonta yayi da sauri kafin ya kalli Dr Salman yana Dan nutsuwa yace" Idan Kika fada Masa to kisani banine kawai banyiba Kawuma ya ajiye yace wlh saiya huta. Zaro Ido tayi itada anty zarah tace" Kawu ma ya ajiye? Eh Mana iyami ce kawai ta dauka abinta sai kwadayayyun gidan dasuka Saba duk akayi ana raba musu abubuwan abinci basusan yayi tafiya ba sunacan duk sun dauka. Shiru Amatu tayi tana sakin murmushi kewa da tsananin qaunar Dr khalil da girmansa na sake cikata sbd ya kawowa gidansu rayuwa me inganci da samun tsira, Duk litinin da alhamis yakeyin azumi harya koyawa su kawu Suma sauran Yan gidan tuni suka dauka sbd duk litinin da alhamis din Yana kawo kayan abinci a raba gidan Dan Shan ruwa Wanda wasu suna musu kwana biyu Basu qareba, Da farko sbd samun kayan dayake kawowa suke azumin Amma yanzu kusan dukkaninsu abin yafara zama jikinsu Kuma kowannensu yasha ruwa takanas sukewa Dr khalil adduarsa ta daban sbd yakawo sauyi da walwala a rahuwarsu gidan gaba daya. Anty zarah ma cikin jinjinawa Dr khalil tace" Allah ya biyawa dr buqatocinsa na alkhairi sbd wannnan aikin ladar dayayi. Amin Amatu tace tana kallon Dr Salman dashima yaji yana sake ganin girman Dr khalil zabeera tareda yiwa kansa kwadayin Lada da kyautawa su Amatun. Anan sukaci abincin Rana taredasu Amatu kafin suka fito suka wuce Salman zai maida usi gida. Bayan tafiyarsu cikin kulawa anty zarah tace" Nagode Amatu. Juyowa Amatu tayi ta kalleta cikin rashin fahimta tace" Anty zarah me akayi? Murmushi tayi tana kallon Amatun gaba daya tace" Amatu kinkawo dariya da walwala acikin rayuwar kadaicin Dana samu kaina acikin gidan nan, Tsawon shekarun aurena Banda ranar Dana taba zaunawa acikin gidan nayi fira nayi dariya harda qyaqyatawa saida Kika shigo cikinsa, Banda abokin fira,abokin nishadi acikin gidana, Maimakon nakawo sauyi da walwala acikin gidan Nan da rayuwar MD sai Nima kadaici da rashin walwala da rashin farin ciki suka aureni sai gidan yaqarasa zama cikin duhun dayake ciki tuntuni., Amma zuwanki amatu yakawo walwala da annushuwa acikin gidan Nan Wanda ko hafsatu datake amatsayin me aiki na hango walwala atareda ita bayan zuwanki cikinmu Shiyasa nake Miki godiya sbd ko ahaka kin shayar damu yanda walwala da nishadi sukeda Dadi a rayuwa. Murmushi tasaki tana gyara zama tace" Anty zarah banbaki kwatan Abinda kikamin arayuba, Kin qaunaceni a yanda nake Kika Kuma karbeni hannu biyu bayan kingama sanin waceceni, Kinbani matsayin qanwa kamar ta jini bayan baki hada komai Dani wannan shine babbar kyautar Dana samu a rayuwata ta samunki keda Dr khalil, Dr khalil shi yariga yazama wani jigo atare Dani da bazan iya Babu Shiba Wanda nake fatar dagake harshi mutuwace kawai zata rabamu, Farin ciki Kuma Babu Wanda yake bawa wani farin ciki a rayuwa sai Allah saikuma Kai da kanka idan ka ture komai ka bawa kanka mahimmanci, Anty zarah kece da kanki zaki kawo walwala da sauyi a gidan aurenki idan kinso, Bansan meye zaman aureba tunda banzauna da Dr ba saidai ni nawa tunanin daga lokacinda Kika auri mutum to duk mulkinsa da dukiyarsa da muqaminsa da duk wani Jin kansa to fa anzama daya Idan bai aje Dan kansa ba ke zaki aje masa, Anty zarah kinsa tsoro da shakkun mijinki fiyeda sonsa acikin ranki Wanda shike sa kiga an tsufa da jikoki da 'yaya da komai saikiga mace mijinta na Mata fada ko dixgawa a gabansu Wanda ita ta daukar Masa hakan tun anada kuriciyar aurensu., Mijinki mijinkine baida wani suna bayan wannan hakama kema bakida wani suna bayan na matarsa ko bayaso Dan haka anty zarah ki aje tsoro da shakka ki gyara rayuwar aurenki sbd bazan zauna Nan dakuba dazanta kawo dariya a fuskarki kece zaki kawo dariya a fuskarki data mijinki, Dan haka Dan Allah anty zarah ki gyara sbd kada lokaci ya qure Miki. Zugum tayi tana sauraren Abinda Amatun ke fada tanajin kamar da wuya al'amarin. Murmushi Amatu ta sake tana cewa'' Anty zarah tunanin me kikeyi? Miqewa tayi tana cewa'' Sam ni Banga abin tsoro ko shakku ba agun Rabin ranki a takaice ma ni tsaf zan gyare Miki zamansa matsalar da aka samu itace ni ko qamshinsa na jiyo gabana faduwa yakeyi sai naji zuciyata tana bugawa da sauri kamar zata fito daga qirgina, Idan na kalli fuskarsa kuwa rasa nutsuwata nakeyi, Bansan meyasaba shikadaine nakejin hakan akansa, Shi kadaine bana iya yiwa fuskarsa kallo biyu sbd dukan da zuciyata takeyi, Meyasa idan......... AMATULLAH"""yakira sunanta gaba daya batareda yasan yayi hakan ba sbd zantukanta dake juya kansa da tunaninsa.... Juyowa sukayi su duka hadda anty zarah datai qaramin suman zaune Jin abubuwan da Amatu ke fada akan MD Wanda idan shedan ya Rudi fahimtarta to zata ce ne wannan so ne me zafi..... Saurin girgiza kanta tayi tana Dan bugawa tace" Tunani ne Amatu matar Dan uwan MD ce Tanama daukeda cikinsa Bazata taba son wani ba bayan Dr khalil bare Dan uwansa MAHMOUD tunanin banxana ne kawai. Ganin Dr Salman ne yakira sunanta yasa anty zarah sakin ajiyar zuciya a boye Ita Kuma Amatun murmushi ta sakar Masa tana cewa'' Harka dawo¿ Gabaki daya kansa juyawa yakeyi Wanda hakan har akan fuskarsa ya nuna confusion sai kawai ya miqa Mata ledar hannunsa daya siyo Mata tarikicen kayan chocolates dasu cookies ya juya baice ko kala ba. Yana fita Saida ya zauna cikin motarsa ya yamutsa kansa Yana cewa'' Amatu MD ZABEERA takeso bayan tana matsayin matar khalil zabeera kokuwa kansa ne bai fahimci yanda abin yakeba???? Kasa yadda yayi yaja motarsa yana qoqarin yakice tunanin dama duk Abinda kunnuwansa sukajiyo Masa. Bayan fitarsa kuwa cikin farin cikin abubuwan daya kawo Mata din tazauna gefen anty zarah suna bubbudewa suna cin wasu suna dauko wata firar tasu maman junior tana bawa anty zarah din labari suna dariya hankalinsu kwance. Sasai Tasha chocolates din Wanda har Saida anty zarah tace ta daina sbd ciwon Mara Amma haka ta share tunda tasan ba wani ciki ajikinta sasha kayan zakinta harsai dataji cikinta kamar zai Yi ciwo ta aje sauran cikin fridge. Da daddare tana qoqarin zama bayan futowarta daga wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci masu Dan akuri ta saka wularsu sai qamshin turaren Dr khalil takeyi Wanda yabata datace tanason qamshinsa saiga kiransa yashiga saidatai wani wuntsilawa sbd farin cikin ganin kiransa sbd dazu yakira da numbernsa tacan tayi saving. Tana dauka tafara zuba Masa qirafin da batai Masa dazu ba sbd gaban anty zarah ne tace" Nifa ban daina fushiba katafi kabarni zabeera ni kadai. Murmushi me sauri yayi Yana qara Jin sonta har cikin ransa a natse yace" Baga zarah Nan ba. Shiru tayi kafin ahankali tace" A cikin zabeera da wajenta a yanzu Babu inda nakejina cikin tsaro da kulawa idan har bakanan, Dr kariga ka koyar Dani Jin rashin tsaro idan baka kusa Dan Allah kadawo da wuri tsoro da fargaba nakeji idan baka kusa. Nutsuwa maganarta ta qara Masa yaji sanyi Yana qara samun nutsuwa yace Mata" Inshallah Amatu idan Ina Nan kina cikin tsarona Babu Abinda zanbari yasameki sai qaddara. Nasani Dr""""tafada tana Dan yamutsa fuska sbd mararta data Fara murdawa gashi dama ita qa'idane duk wata saitayita baqar wahala idan zatayi period, Tunda tazo zabeera Dr khalil sbd cikin da akace tanadashi Yana gano tana ciwon period yake kaita asibiti duk wata tana ganin Dr Fatima ana Yan dubaru har tagama period din tukuna. Fira sukeyi tana daddaurewa ahankali sbd ciwon marar gadan gadan yakeson taso Mata sai alokacin tagane Abinda anty zarah ke nufi data daina cin zaqi. Jin kamar tanajin bacci yasa yayi Mata addua kamar yanda ya Saba duk dare kafin ya kashe wayar saidai hakanan yakejin kamar ba lafiya takeba. Lallabawa tayi ta kwanta tana juye juye hardai abin yataso Mata sosai Nan tafara hawaye tana Kiran sunan Allah. Bayan kusan awa biyu da Gama wayarsu ya yakasa samun nutsuwa ya kalli agogo yaga yanzu su can a Nigerian dare yayi sosai sai ya janyo wayarsa yashiga massage yayiwa zarah text yasan tana tareda MD Amma dai idan har tagani zataje ta dubo Amatu tagano masa. Anty zarah na dakinta yau bataje dakinsaba sbd yanda yadawo tasan a gajiye yake bazaiso a takurasaba shiyasa tayi kwanciyarta dakinta tanata juye juye cikin tunanin daukar shawarar Amatu Amma tanajin shakku, Saiga massage dinsa yashigo tana karantawa ta miqe sanyeda kayan baccinta riga da wando irin na Amatun sak ta nufi dakin da sauri. Salati tasaki me qarfi tana Shiga dakin cikin tashin hankali tayi kanta ganin tanata juye juye riqeda ciki tana wani irin numfashi da kukan azaba. A rude takira Dr tana fada Masa cikin tashin hankali yake dama daya duba yaga yaune date din period dinta da sauri yace" Kira umme Dan Allah ta taimaka Mata takira Mata Dr Fatima. Umme Kuma""" Anty zarah tafada cikin mamaki sbd sanin kowa yasan umme Bata qaunar Amatu da Abinda yake cikinta. Shikuma sanin umme ce kawai tasan Amatu batada ciki yasa yace aje gurinta sbd yasandai bazata tonaba yanzu. Eh Zarah Kira umme Dan Allah Yi sauri. Jiki na rawa ta Danna Kiran numbrn umme Saida tayita ringin kusan Kira biyar sai ana shida ta daga cikin bacci. Umme zarah ce Gamunan Amatu batajin Dadi zaki Kira Mana Dr Fatima ne Wai. Wani qaton ashar ummen ta gundumo tana cewa'' Uban Dr Fatima zankira muku, Zarah Kika sake kirana cikin Daren Nan saina mugun Bata miki wlh. Kallon wayar da ummen ta kashe Mata tayi cikin mamaki da tsoron Ina mafita gashi idanba idonta yayi Mata qaryaba saitaga kamar jini a jikin dogon wandon Amatu din. Wani razanannen qaramin ihu tasaki tareda jefar da wayarta tana fitowa da gudu tayi sama dakin MAHMOUD cikin sa'a Yana zaune yana aiki a laptop da cikin tashin hankali da rudewa tace" Amatu ce ba lafiya kamarma jini cikinta zai lalace..... Cak ya tsaya tareda dagowa ya kalleta ta daga Kai cikin rudewa tana kasa Magana. Kallon agogo yayi batareda ya motsa yaga dare be Zata sake Magana ya aje laptop din gefe tareda miqewa ya zura jallabiya Fara qal Kan singlets da short dake jikinsa ya dauki keys ya sauko zarah din na bayansa. Kamar bazai Shiga dakinba saikuma ya Shiga daidai tayi wani juyin azaba zata fado qasan gado ya tareta da hannunwansa biyu Unfortunately sai idanuwansa suka sauka kan stain din jinin dake jikinta Ya rintse ido da sauri tareda dauke Kai Yana shawarar daukanta saikuma ganin halinda take ciki yasashi daukarta cak gaba daya yafito Yana cewa'' Zarah ki Kira zamu dawo zuwa da safe. ##mamuh# ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 22_* *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_* *KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?* *wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya* *magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*ğŸ’†ğŸ¾â€â™€ï¸ğŸ™ŽğŸ½â€â™€ï¸? *magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽‍♀️👯🏽‍♀ï¸? *karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke* *garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac* *ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz* *_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_* *_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ ************ Cikin kulawa yake tambayarta ya jikin nata itama cikin kulawar take amsawa tanason fada Masa komai na Abinda yafaru tun zuwansu asibiti tanajin nauyin anty zarah Ganin hakan yasa anty zarah miqewa tayi toilet Dan taimakawa ta hada Mata ruwan wanka tana hamdalar cikin dayake lafiya kalau Babu Abinda ya samesa. Tun tanayin wayar a zaune harta Dan jingina da Kan gadon tana rufe idanuwanta tana sauraran abubuwan da Dr ke fada Mata tana murmushi sbd sbd girmqn mahimmancinta a rayuwarsa yake fada Mata Yana Mata fadan ta rage ciye ciyen kayan shiririta. Ganin ba gamawa zasuyiba yasa anty zarah karbe wayar tareda kashewa Tana cewa'' Tashi kije kiyo wanka yanda jikinki zai qara warwarewa, Miqewa tayi tana murmushi har lokacin ta cire kayanta tareda daura towel ta fada toilet din. Ahankali take wanka tana tunanin Rabin ran Anty zarah ta yanda zai iya wanke jinin daba na matarsa ba, A yanda yakeda tsafta da Shan qamshin Nan Bata tunanin zai iya taba rigar bare ya wanke da kansa, Duk yanda za'ayi ita zata karbo rigar ta wanke da kanta tunda jinin natane koba komai abin kunya ne gareta wani ya taba jinin al'adarta Wanda ba mijintaba. Kodata fito wanka anty zarah na dakin tana sauke abincin da hafsatu tashigo dashi Wanda akayi domin Amatun kawai. Tasamu qarfin jiki matuqa sosai datayi wankan shiyasa cikin walwala ta shirya bayan tafara shafa Mai kadan ta sanya doguwar riga me Fadi sbd ganin anty zarah nata kallon cikinta cikin kulawa itadai lafiyar cikin ce a gabanta. Zama tayi suka hau breakfast tareda anty zarah din suna 'dan taba firar Dr daya damu da haryana cewa zai dawo yau daqyar ta hanasa. Suna gamawa ta hau gadonta ta mimmiqe Anty zarah takira hafsatu tana Mata tausa ahankali ahankali har bacci ya dauketa sai alokacin Anty zarah tasaki ajiyar zuciya tareda miqewa tabar dakin. Dakinta tafara zuwa ta sauya kayan jikinta tareda qara shafawa jikinta body mist ta fito tana gyara zaman qaramin qyalen dake daure akanta Wanda yaqarawa kyakkyawar fuskarta kyau ta nufi dakin mijinta. So daya tayi knocking tareda bude qofar bedroom dinsa tashiga bakinta daukeda sallama Mai sanyi. Tsaye yake gaban mirror daureda brown towel iya qugunsa Yana shafawa jikinsa spray din Hugo boss fuskarsa a fuske kamar dai koyaushe. Kallon budadden bayansa tayi dayake fari tas Babu tambon sai qyalli yakeyi kamar na mace har zuwa wuyansa da faffadan qirjinsa datake gani ta jikin mudubi Wanda tuni yaji ajikinsa shi take kallo saiya juyo ahankali yayi Mata kallo daya yaga yanda take kallonsa cikeda so da qaunarsa saiyaji zuciyarsa ta danyi sanyi sbd yasan zarah mace ce me tsananin hakuri da juriya Wanda yasa yake matuqar respecting dinta akan hakan,. Gabanta ya qaraso ahankali ya tsaya Yana kallon fuskarta itama shi take kallo tana jin sabuwar soyayyarsa na shigarta ahankali ta matsa ta shige jikinsa tareda zura hannuwanta bayansa ta rungumesa ahankali tana kwantarda kanta akan qirjinsa tareda lumshe ido tana sauke boyayyar ajiya zuciya. Sai daya jima shiru Yana sauraran bugun zuciyarta dake dukan qirjinsa kafin ya daga hannuwansa ya rungumeta ahankali tareda lumshe ido ya sauke numfashi, Sun dauki kusan mintuna biyar ahaka shiru Babu me motsi kafin ahankali ya dagota daga jikinsa ya dauketa gaba dayanta ya nufi gadonsa da ita Yana kallon fuskarta data soke cikin qirjinsa, Yana kwantar da ita Kan gadon yayi Mata rumfa da fadadden qirjinsa Yana Kai hannu Kan zib din gaban jallabiyarta. Bayan wasu lokuta haryayi sabon wanka ya fito ita alokacin take qoqarin saukowa daga gadon tayi saurin daukar fadawa toilet din nasa duk da shi mutum ne dabai cikason wani na amfani da toilet dinsaba Amma kasancewar yanzu Basu kadai bane Dole bazata iya fita ahakaba kamar da wani zai iya ganinta. Wanka tayo tafito lokacin harya shirya cikin farin filtex transparent da hular qube coffee brown Yana fesawa jikinsa turarensa na IMPERIAL MAJESTY. Kayanta ta maida bayan tagama goge jikinta ta shafa oil kadan tareda turarensa. Sai alokacin ta tunoda Abinda yakawota ta kallesa Yana qoqarin daukar wayarsa dake Kan bedside cikin taushin murya tace" Am...amm dama rigar dazu ta jikinka nace ko zaka kawo na bayar a wanke sbd Naga ta samu lalacewa.... Cak ya tsaya daga Abinda yayi niyar Yi hakanan yaji maganar Tata kamar ta ciza ransa, Idan tunaninsa na aiki daidai yasan me wankin zarah din namiji ne Wanda kusan duka familyn shike yiwa wasu da yawa daga ciki wanki, Tana nufin shi gardin zata bawa jinin dayake sirrin Amatune ga wani gardin ya wanke??? sake 'dan tamke fuska yayi tareda juyowa ahankali kamar zai kalleta saiya fasa ya juya ya dauka wayarsa batareda yabata amsaba yafara qoqarin barin dakin. Saurin biyosa tayi tana cewa'' Nace bakajiba rigarka ta yau da safe nakeso kabani zanbawa wa.... Kallon daya dago yayi Mata yasata matsawa baya kadan tana sauke Kai zuciyarta na bugawa da sauri. Kamar zai wuce baiyi Magana ba saikuma ya tsaya batareda ya juyo ya kalletaba cikin sautinsa me daukan hankali yace" Karki sake kawo maganan riga da Abinda yasamu riga agabana ok???? Kallonsa tayi tana son sake maganar Amma ganin yanayinsa na Babu Wasa ko sakin fuskarsa yasa ta 'daga Masa Kai tana cewa'' Adawo lfy. Can qasan maqoshinsa yace" Thank you"tareda wucewa ya sauko qasa tareda ficewa zuwa office. ##Mamuh# Gashinan please yauma kuyi manage gobe Inshallah zamu koma pages dinmu masu tsawo yauma uzurine ya riqeni kuyi hkr da wannan din🙏🙏🙏 ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 23_* *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_* *KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?* *wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya* *magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*ğŸ’†ğŸ¾â€â™€ï¸ğŸ™ŽğŸ½â€â™€ï¸? *magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽‍♀️👯🏽‍♀ï¸? *karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke* *garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac* *ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz* *_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_* *_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ğŸ¤žğŸ¾ ********** Yinin ranar cikin farin ciki dukkaninsu sukayisa sbd musamman Andi da Modibbo suka aiko akaje da Amatu gurinsu suka duba lafiyarta qarima Dr Fatima Dr khalil yaturo ita taduba musu lafiyarta taqara Basu tabbacin komai lafiya daga ita har cikin, Musamman Andi yayowa Amatu kyauta ta musamman Wanda tasake qara Mata baqin jini da qiyayya gurinsu umme da Haj maryam wadda taga Salman dinta na wani rawar Kai akan Amatun tun agabansu Modibbo ta buga tsalle tace" Wlh Salman karka kuskura kace zakamin kwashe kwashen bacin Rai Dan ni ba dauka zanyi ba. Ganin basusan akan me take Magana ba yasa kowa tayi watsi da ita saishi uban gayyar datake Magana akansa yafahimci Abinda take nufi sai anty zarah da Amatun dake aika musu da kallon hadarin kaji sbd yanxu daidai takeda kowa kaf cikin zabeera sbd Andi daya tsaya Mata. Koda suka fito a hanyarsu ta komawa suka hadu da Nuratu tana ganinsu tahau yada maganganu in marasa Dadi Har Amatu zata tankata anty zarah tayi saurin riqo hannunta tajata sukabar gurin sunaji tana cewa zarah din munafuka Amma Basu kulataba suka wucewarsu. Da yamma Salman da kansa yazo ya maidata asibiti tasake ganin Dr Fatima suna baro asibitin kamar a mafarki sai kawai tagansu qofar gidansu yayi parking mota Da sauri ta juyo ta kallesa bakinta da fuskarta daukeda tsananin mamaki da farin cikin dayasa takasa mgn sai kawai ta bude motar ta fito da gudu tayi ciki. Da iyami tafara cin karo a tsaye tana kwashe shanya cikin tsananin farin cikin ganinta ta rungumeta tana cewa'' Iyami wlh bansan haka nayi kewarkuba sai yau Dana ganni a qofar gida Ina kawu da usi??? Kawu dake fitowa daga daki Yana jinta dama ya fito Yana ganin yanda Amatunsa ta koma take ya washe baki Yana cewa'' Maza kuzo mu shige daki kada Ido da baki suyi Miki yawa kinsan gidan harda qarin 'yan bani na iya aka samu. Dariya tayi tana sakin iyami tace" Yanzu nasan Ina gaban kawuna. Kallonta iyami takeyi itama cikin Jin Dadi da farin cikin ganin yanda ta sauya tayi kyau kamar 'yar masu kudi har wani qyallin haske fatarta keyi ga suturar alfarma ajikinta sai annushuwa takeyi. Dakin suka nufa suka zazzauna Nan aka nude sabuwar fira saiga shima usi dake shirye shiryen tafiya jibi yashigo Nan aka Dora firar ga fankasu da iyami tayi aranar dayaji miyar Naman rago da Ganda Nan aka kawo musu suka hau ci suna Santi musamman Salman dan shima yamasa Dadi matuqa. Suna Nan saiga Kiran Dr khalil yashigo wayar kawu dauka yayi suka gaisa ckin sakewa kamar 'dansa na cikinsa yakejin khalil sbd shiga ransu da yayi iyami ce madai takejin nauyinsa na sirikantaka sbd tuntuni sunsan Amatu yakeso Dan Yama fada musu Kuma sunyi na'am da hakan jira kawai suke tadawo asa ranar aure, Sabuwar Hira suka Dora da Dr din a waya su Amatu na fada Masa Abinda suke ci Yana cewa'' Umma iyami idan nadawo Nima shi zakibani wandama yafi nasu Dadi. Murmushi iyamin tayi cikin Jin nauyinsa tace" Khalilu duk Abinda kakeso idan kadawo Inshallah duk sainamaka su. Yawwa nagode umma. Kawu ke tambayarsa ya aikin dayaje yi dafatar akwai nasara?? Eh yace Masa Yana qarawa da alhmdlh Inshallah muna gamawa zan juyoma. To Allah yakawo ku lfy. Amin Basu bar gidanba sai kusan yamma sosai Wanda anty zarah tayi musu Kira yafi a qirga Itama Saida iyami ta hado Mata fankasu suka je Mata dashi. Kamar kada su tafi hakanan ta fito suka tafi tana sake dagawa Yan gidan hannu kowa nasakejin kamar kadata koma. Saida suka biya sahad yayi Mata soyayya sosai har abin na Bata mamaki Amma ganin yanda ya dauketa kamar 'yar uwarsa ya nuna bayason godiyarta da mamakinta itama saita daukesa kamar usi Nan suka sake shiriricewa sai magriba suka kamo hanyar gida. Suna tafe suna fira harda qyaqyata dariyarsu sukeyi Yana tuqi da gudu gudunsa aikuwa Basu ankaraba wata mota tayo Aron hannu a guje itama me motar yake tahowa, Cikin wani razanannen firgici yaso kaucewa Amma ganin akwai express dayan gefen sai kawai yayi dayan gefen sukai Kan wata bishiya suka daketa Amatu da tuni ta saki ihun sadaqarwa kanta ya daki qofar motar tsananin tsoro da firgici yasata somewa agurin. Cikin sauri ya juyo Yana qoqarin dagota Yana Kiran sunanta da qarfi cikin damuwa sbd yasan suman tsoroce kawai tayi gashi Babu wani abindama yafaru din sbd bai daki bishiyarba sosai. Ruwan dayasha ya rage kafin alamarin ya dauka ya shafa Mata saigata tasaki nannauyan ajiyar zuciya a rude tana cewa'' Wlh banason na mutu yanzu saina cikawa Dr khalil burinsa na aurena. Dariya maganarta ta basa duk da ta daki zuciyarsa Kuma. Cikin kulawa yace" Nima banason ki mutu sainaga rabon wace ke a qarshe. Kallonsa ta juyo tayi cikin rashin fahimta tana qoqarin sake dawowa nutsuwarta. Murmushi yayi tareda tayarda motar yayi ribas sukabar gurin Yana cewa'' AMATULLAH ki dinga tuna sauran bayin Allah yayin yiwa mijinki na baa dauraba addua. Sake rudata yayi tasake juyowa gabaki daya tana kallonsa saidai ganin kamar reaction dinta nasake basa damar yadda da hasashensa koma dai yardarsa sai kawai ta basar da zancen tana dariyar tsoron dataji da sumanta tana cewa'' Dan Allah Dr Salman kada anty zarah tasani Tana sani zata Fara daga hankali ta fadawa Dr banaso ta daga Masa hankali. Sai alokacin ya Dan juyo ya kalleta zuciyarsa na wani sarawa Yana maida hankalinsa Kan titi cikin sautin nutsuwa yace" Idan zuciyarki na tsananin kulawa da qaunar Khalil haka Meyesa zata so MD ZABEERA??? Cak ta tsaya gabanta yayi mummunan faduwa Amma sbd Bata fahimci zancen nasaba saita saki wani yaqen dolen Dole tana kasa juyowa ta kallesa tace" Meye hadina da Rabin ran Anty zarah kuma? Ko gaisuwa Bata hadani dashi bama ya cikin mutanen danake qauna gaba daya sbd halayensa na wulaqanta antyna..... Baya cikin wainda kike qauna sbd shi sonsa kikeyi Amatu., Amatu bansan meyasa shedan yake yawo atsakaninmu ba dayake haifar Mana da wani tunanin dabai kamataba bayan sanin cewa ke amatsayin matar khalil kike, Amatu nafada Miki hakane Dan kije kiyi tunani kada ki auri Wanda farin ciki ya cancanta a rayuwarsa ba dakon son maso wani ba, Dr Khalil zabeera shine duk duniya cikin maza ayanzu yafi cancanta daya asameki gaba dayanki daga zuciya har ruhi da ganganr jiki Dan haka kada ki azabtar da rayauwarsa ta basa gangar jiki da qauna kawai Yana buqatar dukkanki gaba daya har soyayyarki da zuciyarki sbd koba komai shi din Asthmatic patient Wanda yakeda alaqa da zuciya Dan haka AMATULLAH kije ki zauna ki nutsu kiyi tunani ki Fara koyawa zuciyarki soyayyar khalil ba qaunarsa ba soyayyarki yake buqata. Kallonsa takeyi sosai kanta na neman bugawa da maganganunsa ta girgiza Kai Yana rintse ido cikin rudewa take cewa'' Mezaisa naso Rabin ran Anty zarah ni Dr nakeso, shikadai nake qauna, shikadai nake tunani shikadai nake gani, shikadai nake....... Mafarki fa??? Tsit tayi tareda kasa qwaqqwaran motsi sbd Jin tambayarsa, Idan har ba qarya zatayi Masa ba to tabbas 'daidaikun ranakune Bata kwantawa batayi mafarkin Rabin ran antynta ba. Cikin firgici ta dago idanuwanta na cikowa da hawaye zatayi Magana yayi parking Yana cewa'' Mun iso gida. Da sauri ta juya ta kalla waje tagansu qofar part dinsu anty zarah din Ta sake juyowa gurinsa zatayi Magana cikin rawar murya da sarkewar tunani Ya katseta da sakar Mata murmushi me sanyi sbd jikinsa da zuciyarsa dasukai sanyi idanuwansa na Dan sauyawa sbd yanayinta ya Gama tabbatar Masa da hasashensa katseta yayi cikin sanyi da cewa'' Kije ki zauna kiyi tunanin Abinda yakamata. Shiru tayi tana kallonsa kamar bazata fito motarba saigashi kuwa motar MD ZABEERA ta iso gurin yayi parking Dan da kansa yayo tuqin yadawo gida. Motarsa ta qurawa ido zuciyarta na bugawa da sauri da sauri kamar zata bullo qirjinta ta fito, Saida yadauki mintuna biyu zuwa uku kafin yafito motar Yana amsa waya fuskarsa a 'dan sake Wanda yasata kusan suman zaune da sauri ta rintse idanuwanta tanaji kamar yanzu ne da Salman yayi maganar ya zuba Mata son MD din me tsanani cikin ranta ta girgiza Kai da qarfi Yana cewa'' Bazan taba son Rabin ran Anty zarah ba. Bude motar tayi da sauri ta fito batareda ta sake waiwayo Salman ba Wanda tunda motar MD tashigo fuskarta ya tsurawa ido Jan motarsa yayi yabar gurin Yana sauke numfashi me zafi ya nufi gurin mum dinsa da tun rana take kiransa duk tabi ta hargitse ta daga hankalinta akan alaqarsa da Amatu Wanda yakejin da akwai matsala Dan kuwa kome zatayi bazai iya rabuwa dasu Amatu da familyntaba. A sukwane tashigo ba cikin hayyacintaba tayi nisa cikin tunani da fargaba tareda tsoro taji andafa ta tayi saurin dagowa sukai Ido biyu da anty zarah tana sakar Mata murmushi tace" Amatu Yaya dai? Sai yanzu kuke dawowa tundazu nakira Usman yace kunbaro. Qaqalo murmushi tayi tana qarasa shigowa palon tace" Wani guri mukaje Salman yayi min siyayyar kayan babies da kayan dadi" ta qarasa fada tana qaqalo dariya sbd kawar da banzan tunanin dayake yawo cikin kanta. Siyayyar ta miqawa anty zarah tareda fankasu din dasuka Zo Mata dashi Cikin farin ciki ta karba tabawa hafsatu tace ta zubo Mata a plate Ita Kuma dakinta ta nufa Dan yin wanka ta gyara jikinta Amma cewa anty zaran tayi zatayi sallah ne. Wankanta tayo tareda shiryowa cikin riga da wandon bacci masu Dan kauri ta sanyo qatuwar rigar sanyi akai sbd ana Dan sanyi gashi gidan Sam komai sanyi sunsaba da rayuwar AC ta sanyo hula tareda slippers ta fito tana waya da Dr khalil Wanda yanzu take tsananin Jin kunya da tausayinsa. Cikin annashuwarta ta fito suna wayar harda 'yar dariyarta sosai sbd labarin abincin dasuka ce na 'yan Chinese yake Bata kamar zaiyi kuka da amai Ganin yanda labarin ke sakata nishadi yasa yaketa Jan labarin Yana sake fada Mata yanda kalar abincin yake da yanda ake cinsa sbd walwalarta na basa farin ciki da nutsuwa. Dining ta nufa tana sake qyaqyata dariyarta datasashi tsayawa cak daga cin abincin dayakeyi akan dining din tareda zarah wadda yau duk farin cikinta a bayyane yake sbd gata ga Rabin ranta suna cin abinci tare. Qoqarin zamata takeyi a dining din idanuwanta suka sauka cikin nasa daidai dagowarsa ya kalleta da idanuwansa dasuka narketa gaba dayanta saita samu kanta da kasa dauke idonta daga kansa zuciyarta na harbawa ahankali. Sarqewa yayi sbd wani dalili daya kasa sani yafara tari ahankali Yana Kare bakinsa da tissue Anty zarah dake Shirin Magana tayi saurin daukar ruwan sanyi zata miqa Masa daidain Amatun ita Kuma ta miqa Masa juice cikin cup. Kallon juna sukayi itada anty zarah din tayi saurin dire cup din tana barin gurin da sauri ya 'dan bi bayanta da kallo qasa qasa ahankali kafin ya karbi ruwan hannun zarah din yakai bakinsa ya kurba kadan ya ajiye yakai hannunsa ya dauki cup din juice din yakai bakinsa yasha kadan sai kawai ya miqe Yana cewa'' Alhmdlh I'm full. Binsa anty zarah tayi da kallo harya haye stairs din zuwa samansa tana karantar yanayinsa Idan nazarinta yabata daidai MD na wasu abubuwan dabata ganewa kwanakin Nan duk da dai dama can Bata ganewa MD Amma dai yanzu kamar tana nazartan wasu abubuwan nasa. Bin bayan Amatu tayi tana kawar da tunanin komai tana zuwa dakinta ta sameta Dr khalil na qoqarin cigaba da sata nishadi itama tana qoqarin nuna Masa nishadantuwarta sbd kada ta sace Masa gwiwa. Palo suka dawo da anty zarah tasata gaba akan saitaci abinci ga cake din datakeso koyaushe Wanda ake Mata duk Bayan kwana biyu Amma ta kasaci komai ko ruwa ta kasa Sha sbd kanta dake daure tamau har wani sarawa yake Mata takasa cire tunanin komai cikin ranta saima wani irin tunanin MD din dayake neman zauta kanta bangare daya ga tunanin Dr da koma me zaije yadawo shi tayiwa alqawarin kanta matuqar suna raye saidai tunanin MD dakuma yake sake rikitata. Miqewa tayi ahankali tace" Anty kaina Yana ciwo sosai zanje na kwanta kozai rage. Kallonta anty zarah din tayi tace" Dakin daure kinci abinci ko kadan ne Kinga pasta ce aka dafa Kuma me ruwa ruwa ce zuwa anjima kadan lalacewa zatayi kada yunwar dare ta tayar dake ki rasa abincin ci yau ko fruits Babu a gidan Nan baa siyoba gashi rabonki da abinci tun rana da Kika ciyo a can gidanku. Girgiza Kai tayi tana Dan dafesa tace" Wlh banajin cin abinci saidai zuwa da safe idan ya warware zanci harda biyan bashin na yanzun din. Miqewa anty Zaran tayi itama tareda wucewa gaba tana cewa'' Shikenan Allah ya tashemu lafiya Kisha magani kafin ki kwanta Dan Allah. Hanyar dakin MD ta nufa tana gyara zaman rigarta a jikinta Wanda yasa Amatun binta da kallo idanuwanta na qoqarin cikowa da hawayenda suka sata saurin dawowa hayyacinta tayi dakinta da sauri tareda fadawa Kan gadonta tana rintse ido. Tunda ta kwanta takasa bacci tana kwance ta qurawa Dan qaramin hoton Dr khalil dinta Ido dake cikin qaramin frame gefen gadonta Wanda anty zarah ce ta kawo Mata. Dr Dan Allah kayi gaggawar dawowa sbd Ina buqatar kayi saurin aureni na zamo mallakinka Bazan iya jira cikin Nan yakai wata taraba kadawo kasan yanda zakayi dashi nidai aurenka kawai nakeso yanzu fiyeda komai tun kafin zuciyata tafi qarfina. Har qarfe goma sha biyu da arbain batayi bacci ba gashi zuwa lokacin yunwa tafara hanata sukuni sbd jikinta harya Fara 'yar makarkata Ta tashi zaune tana kallon agogo. Saukowa Kan gadon tayi tareda mayarda qatuwar rigar sanyinta me kaiwa har gwiwa ta zura hula tareda sanyo slippers ta fito tana adduar Allah yasa abincin bai buga ba Dan wlh bazata iya kwana haka ba. Tana fitowa ta nufi dining Kai tsaye daidai shima yafito daga dining din sbd abincin daya sauko ci Dan duk yinin ranar baici abinci ba sai Daren Kuma spoon biyu kawai yaci yatashi sbd Abinda yafaru gashi yanzu yasauko abincin ya buga. Kallonsa tayi bayan itama ta bude abincin batasan lokacin datace wlh yunwa nakeji ni bazan iya kwana ahaka ba. Palo yadawo Yana tunanin zancenta koba komai tunda tanada juna biyu ayanda sukace Dole tana buqatan abinci akai akai. Shima Dole Yana buqatan abinci bazai iya kwana a hakan ba ya juya zuwa dakinsa ita Kuma tayi kicin ta hau dube dube Babu Abincin ci ta dauko ruwa Tasha taji cikinta na neman qullewa ta fito tana riqe cikin daidai ya sauko sanyeda riga da wando masu Dan kauri kamar na sanyi hannuwansa daukeda mukullan mota da wayarsa batareda ya kalli fuskartaba kamar bada ita yake maganarba yace" Muje. Tsayawa tayi binsa da kallo harya fice kafin tabi bayansa da sauri. ##mamuh# ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': *_MQ 24_* Tafiya sukeyi ahankali cikin motarsa Babu me Magana sai sanyin AC da qamshin turarensa daya Gama Kama motar dama can yake ratsata Yana Bata wani sabon yanayi cikin zuciyarta Wanda yasata fadawa tunani., Tuqinsa yakeyi cikin nutsuwa shima Yana jiyo siririn sahirtaccen qamshin jkinta na Shiga hancinsa ahankali Wanda kusan shima yasashi Shiga tunanin banbanta yanayin qamshinta Dana zarah., Istigfari yayi saurin Yi cikin ransa Yana Dan tsuke fuska tareda 'dan qarawa motar gudu. Ganin sun kamo hanyar blue fox yasata saurin kallonsa murmushi na sauka Kan fuskarta tace" Rabin ran Anty Dan Allah muje blue fox akwai abinci me kyau da dadi acan....... Wani irin kallo ya juyo ya aika Mata Jin sunan data kirasa dashi Wanda yasashi qurawa cikin Idanuwanta Ido Yana son sake tabbatarda Abinda takirasa dashi _Rabin ran anty_ yanda tafada sunan batareda kulawar komaiba yasashi yimata wannan kallon itama Jin idanuwansa akanta yasata kasa juyowa ta qurawa waje Ido Yana damqe hannunwanta dake rawa zuciyarta na harbawa. Jin shiru yasata Dan dagowa tareda juyowa ahankali ta kallesa hankalinsa na Kan hanya saita qurawa fuskarsa da fararen hannuwansa dake tuqin motar cikin nutsuwa da qwarewa, Kan fuskarsa ta tsayarda kallonta tana yaba kyawu da tsarin fuskarda ubangiji yayi Masa me daukeda da tarin kwarjini da Kamala, Dogon hancinsa ta kalla zuwa manyan idanuwansa batasan lokacinda ta lumshe ido ba hawaye na gangarowa daga cikinsu batareda ta gogesuba cikin ranta tace" Meyasa zuciyata ta zabi wahalar da rayuwata data Dr ta hanyar son Dan uwa mafi soyuwa agaresa? Dukkanin kyawu da Abinda MD yakedashi Dr khalil dinta nadasu harma yafi MD din kyawawan halaye masu sanyaya Rai hasalima kusan kamanninsu daya sbd duk mahaifinsu Modibbo suka dauko har Khalil dinta ma yagi MD din hasken fata saidai MD ya nuna Masa gogewa da hutu irin na Boko da yawan qasashe suka hudasa sai kalar fatar mahaifiyarsa daya dauko me sheqi. A harabar blue fox din yayi parking tareda Dan juyowa ya kalli gefenta tayi saurin share hawayenta tana bude motar ta fito tana washe baki cikin tsananin farin ciki ta juyo daidai ya zagayo tace" Yau duk abindake restaurant dinnan saina cire kwadayinsa na tsawon aikin danayi anan din. Bai kalletaba yayi gaba ta biyosa tana sake bayyanar da murnarta ta zuwa gurin. VIP direct suka nufa inda tuni aka hau sintirin attending dinsu ga mamakinta kusan Rabin ma'aikatan gurin an sauyasu Nan ta bada odar abinci kusan kala hudu da tarkacen su fruit salad harda ice cream da furar blue fox din me shegiyar Madara da Laban yoghurts. Table dinsu kusan kasa daukan abubuwan yayi sai kawai yayi odar noodles with veggies salad da power drink yafara ci cikin nutsuwa Yana kallonta tana cin abincin cikin tsananin Jin Dadi Dan harwani lumshe ido takeyi tana cika bakinta da Naman kazar chicken rings dataji carrot da spices. Yana kallo ta Gama yagalgala kazar ta janye gefe ta jawo shawarma tafara ci itama ta ajiye ta janyo soyayyan dankalin dayaji egg source Furarta ta janyo ta kurba ta lumshe ido tana cewa'' Wayyo Dadi" kafin ta aje tacigaba da cin noodles Kuma. Jingina yayi da Bayan kujera Yana zuba Mata iduwansa masu karya kuzarinta tareda dukkanin nutsuwarsa Yana kallonta kamar ya baby a gabansa. Saida tayiwa komai ci rabi aje rabi kafin ta qoshi ta dauki ice cream dinta ta bude ta diba tana hadiye yawun matsuwa taji sanyinsa ya sauka a bakinta taji anrike ice cream din Da sauri ta dago idanuwansu suka shiga cikin na juna ahankali ya girgiza Mata cikin qaramin sauti yace" This is not good for your health...... Kasa motsi tayi ta harya zare ice cream din daga hannunta ya ajiye idanuwansu na cikin na juna Saida waiter din dake tsaye yayi gyaran murya da qarfi Yana sake miqawa MD din bill dinsu. Fuskewa yayi Yana Dan tamke fuskarsa ya juyo ya Ciro ATM card dinsa ya miqawa waiter din batareda ya karba bill dinba. Bayan andawo Masa da atm din anyi clearing bill dinsu suka fito suka Shiga mota sukabar gurin. A mota shiru tayi tana sauraron karatun Qur'an din dayasa a motar Yana fita ahankali saitaji tana sake samun nutsuwa da yanayin da suke ciki na kasancewa da juna ahaka. Koda suka dawo zabeera har bacci yafara daukarta cikin motar shiyasa da yayi parking sai bai tayarda itaba hakama bai kashe motarba sbd AC ya zauna ya fiddo wayarsa Yana duba saqon dayaji shigowarsa sunacin abinci. Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda bacci ta zuba akansa tana lumshe ido ahankali ta furta" Tabbas Ina cikin tsananin son MAHMOUD ZABEERA Kuma so me qarfi Wanda nakejin kamar ruhina zai rabu da gangar jikina idan nayi nesa dashi, Lumshe ido takuma Yi tareda budesu akansa cikin sauti me taushi dazai iya jinta tace" Nagode. A natse ya juyo ya kalleta da nasa idanuwan dasuka nuna sunfara Jin bacci taji zuciyarta na qara narkewa da sonshi tayi saurin dawowa hayyacinta tareda tashi zaune tabude motar da sauri ta fice hartana hadawa da Dan gudu tayi ciki. Kai tsaye bedroom dinta ta nufa ta fada Kan gadon tana sakin hawayen dataketa riqewa tace" Amatu kidawo hankalinki Mana, Kidawo Amatunki da kowa yasani, Amatun Dr khalil matar Dr khalil, Babu kowa a zuciyarki sai Dr khalil sbd shine Wanda zuciya da ruhinki keson aure. Ta jima ahaka kafin ta miqe tafada toilet ta wanko fuskarta tayi fitsari tazo ta kwanta tareda lullubewa tana qudurtawa ranta gobe zata amayarwa Salman abindake zuciyarta kafin ta rufe zuciyar gaba daya ta mallakawa Dr khalil dinta Wanda idan har tana Raye Inshallah batada miji sai Dr khalil. Washe gari tunda wuri ta tashi yau da kanta ita tafara Kiran Dr Meeting zasu shiga Amma ganin kiranta Saida ya tsaya ya dauka yaji lafiyarta kafin yace idan yafito zaikirata. Wankanta tayi ta shirya cikin riga da skirt na atampa kalar blue tayi Mata kyau sosai ta yafo gyalen akanta sbd Bata dauro dankwalin kayanba. Palo ta fito ta nufi kicin da kanta yau ta dafawa kanta indomie da dafaffen kwai guda biyu sai custard data hado Wanda yaji uwar Madara takoma dakinta acan tayi breakfast dinta tana gamawa ta fitoda kayan ta maida kicin Takoma daki ta sake kwantawa tana tunanin Dr da irin dibbin soyayya da qaunar daya Bata, Ya juyawa iyayensa baya akanta alokacinda aka koresa ya amince zaibar komai da komai ciki hadda iyayensa da 'yan uwansa da rayuwar daya taso ciki duk sbd ita To menene Dan itama ta danne zuciyarta ta tauyeta daga Abinda takeso ta bashi koba komai Al'amarin da zuciyarta ta dauko me girma ne sbd mijin anty zarah ta haramtawa kantashi Koda sonsa zai kasheta har abada su biyun Nan anty zarah da Dr bazata taba barin susan halinda zuciyarta ta Shiga akan mutuminda sukafi qauna da komai arayuwarsu..... Kiran Salman ne yashigo wayarta cikin nutsuwa ta daga tana qoqarin kawar da damuwarta tace" Likitan qashi na duk Nigeria""ta qarasa tana Yar dariya. Shima 'yar dariyar yayi Yana gyara zama cikin motarsa yace" Zakije mukai usi airport kokuwa na tafiyata? Wuntsilowa tayi bakin gado tana janyo dankwalinta da gyalenta ta fito tana cewa'' Ai karma kamin haka idan ban takasa a matsayin 'yar uwarsa da bamu taba rabuwaba arayuwa sai yanzu to zan takasa amatsayin matar Dr khalil tunda bayanan Dan shine yafi kowa cancantar ganin wucewar usi Dan shine yakawo wannan murmushin akan fuskarsu na samun cikar buri su samu ilimi kamar sauran 'yaya. Ganinta kawai yayi tana bude gaban motar ta shigo ta zauna tana kashe wayar tace" Muje ko¿ Dariya tabasa ya girgiza Kai Yana cewa' Amatun likita bokan turai. Kallonsa tayi tana cewa'' Nidai muje tun kafin na huce da zafi zafina nafito Dan yiwa USI huduba. Jan motar yayi suka fice suna Dan taba fira ahankali har suka Isa gida inda su kadai ake jira suzo dauki usin., Tunda tashigo gidan idanuwanta suka sauka Kan 'yan gidan kaf a tsaye cirko cirko tsakar gidan kowanne fuskarsa cikeda yanayin damuwar rabuwa da USI din ta juya ta kalli kawu dake zaune radionsa a kunne Amma yanayin fuskarsa yasa taji idanuwanta suna qoqarin cikowa da hawaye tana kallon iyami sai kawai ta qaraso da sauri Yana sake hawayenta ganin yanda Usin yake tsaye riqeda hannun iyami Yana Bata qwarin gwiwa. Usman din ta kalla tana share hawayenta tasaki murmushi Dan cirewa kowa damuwa takai Masa duka a baya tana cewa" Ki yanda kasa kowa cikin damuwar tafiyarka bayan duk hutawa zamuyi da rashin Jin ka musamman maman junior da anty salamatu ko???""tafada tana kallon maman junior da anty salamatun dake qarasowa da jakarsa data fito Masa da ita. Murmushi maman junior tayi tana cewa'' Usi Allah yabaka sa'a kamaida hankali kayi karatu ko zaka tallafa Mana wata Rana idan lokacin cin amfanin karatun yazo sbd Kaine kasan wahala da gwagwarmayar rayuwa damukeyi anan gwamnati batamasan da ire irenmuba. Maman junior kada ki damu daya bayan daya dukkaninmu sai usi yakaimu Hajj da umrah da albarkar wannan karatun dazaije Amma idan kuka tsaya Kuna Masa wannan fuskar ta marayu ta Yaya zaije da gwarin gwiwarsa ai kawai ki Masa tashin hankali da hayaniyar da kuka Saba shizaisa yaje Yana tuno kowa ayanda halayyarsa take.... Dariya dukkaninsu suka dauka Nan aka hau hayaniya ana Masa Allah ya kiyayaye shima sai hakan yasashi Jin Dadi ya saki fuska Yana amsa musu kowa ana Masa alqawarin Abinda za'ayi Masa idan akai kudi. Kawu da iyami dasu akeje har airport inda suka taru su duka da hayaniyarsu suka cikawa Salman motar da hayaniya sai suke qara burgesa musamman Amatun dake qoqarin Hana kowa shiga damuwar tafiyar Usin bayan ita Yana iya hango tsananin damuwa da fargabar rabuwa da Usin a idanuwanta tana daurewa ne kawai. Suna Isa ko zama basuyiba aka Kira jirginsu Salman ya kallesa Yana basa sauran dukkanin bayanan da Dr yace yayi Masa tareda basa takardun komai Dana atm card na account din da aka bude Masa tareda wadataccin kudi aciki ya miqa Masa tareda Dan rungumesa Yana cewa'' Zaka ringa ganina akai akai inshallah har sai kagama sanin komai da komai just take care brother, Kuma Ina fatar zaka saka mijin 'yar uwarka alfahari dakai wata Rana. Kallonsa yayi ya kalla Amatu Yana qirqiro murmushin qwarin gwiwa yace" Inshallah Dr khalil saiyayi murmushi ga wannan aikin alkhairin nasa. Gyada Masa Kai tayi tana qoqarin maida hawayen dake subuce Mata Suka rungume suna tana sakin hawayenta gaba daya suna zubowa ba tsayawa. Cikin kunnenta yace" Amatu Ina Miki fatar samun Abinda kikeso arayuwa Wanda zaisaki farin ciki, Inaso Kuma kimin alqawarin Babu wani Abu dazai sauya matsayin Dr acikin rayuwarki kimin alqawarin da ke da kanki zaki kirani Dan sanar Dani aurenki da Dr Khalil idan lokacin yayi. Rintse ido tayi hawayenta na sake gudu ta janye jikinta tana kallon qasa tace" Usi zuciyata takamu da son wani Wanda ba Dr khalil ba so me girma Amma wlh shima son Dr khalil bai sauyaba a zuciya da rayuwata, Ba laifina bane sbd bansan yaushe hakan yafaru ba, Bansan ta Yaya zan kankare wannan son daga zuciyata ba Amma nasan ta yanda zan dannesa dannewar da har abada bazai tasoba bare wani yasan dashi zanbarshi cikin Raina har mutuwata, Jan kuka tayi ahankali tana cigaba da cewa'' Usman ayau ni Amatu nayi maka alqawarin bazan taba auren kowaba sai Dr khalil, Nayi alqawarin Dr bazai taba fuskantar sauyawa daga gareniba sbd shi kadai na zaba amatsayin mijina Inshallah...."wani siririn kuka taqarasa maganar dashi zuciyarta na wani irin nauyi. Baiyi mgn ba ya juya gurinsu kawu yayi musu bankwana ya wuce Yana danne zuciyarsa dake Jin tsananin damuwa da tsoron Abinda Amatu ta fada, Shin yayi Mata adalci satayin alqawarin auren Dr Bayan tafada Masa akwai Wanda zuciyarta ke tsananin so??? Baya tunanin baimata adalciba sbd a nasa gani da sanin Babu Wanda zata aura ya sota ya qaunaceta yabata farin ciki da kulawa fiyeda Dr khalil zabeera Dan haka koma waye zuciyarta keso farin cikinta da kulawar dazata samu daga Dr yafi matasu ahankali zata manta sonta zuciyarta ta koya son KHALIL din. Ahanyarsu ta komawa Babu me mgn acikinsu kowa yayi shiru Yana tunani kamar basune suketa hayaniya ba a hanyar zuwa. Su kawu tunanin rahuwarsu dasu Usin sukeyi sbd dukansu basa gabansu yanzu sai sukejin kamar rabuwa sukayi dasu gaba daya musamman iyami datakejinsu kamar itace ta haifesu gashi yanxu ta tashi Babu ko daya a gabanta. Shikuma Dr Salman yasan irin ciwo da radadin datake ciki na zabar danne sonta tabi Abinda rayuwarta da 'yan uwanta keso. Ajiye su kawu sukayi suka nufi gida har lokacin Babu me Magana acikinsu Saida yayi parking qofar part dinsu anty zarah sai ga MD ZABEERA yafito Yana amsa waya fuskarsa sai sheqin kwarjini takeyi ya nufi motarsa ya bude ya shige drivernsa na ciki yaja sukabar gurin idanuwanta na binsa da kallo har motar ta bace Salman na lure da ita ya saki numfashi ahankali yace" Duk zabin dazakiyi Amatu kisani ni Salman zabeera Ina bayanki dari bisa dari saidai bazanso ki zabi Abinda zai kawo damuwa da qunci cikin rayuwarkiba, Soyayyar MD ZABEERA Babu Abinda zata baki sai damuwa sbd bazai baki soyayya da kulawar da kike nemaba infact baimasan kinayi ba Koda yasani Babu so agabansa sbd keda idonki Kinga hakurinda matarsa keyi akansa Wanda mu bazamu iya ganinki kina irin wannan rayuwarba so please AMATULLAH for our sake kadaki saka kanki cikin quncin dazaki sakamu muma. Share hawayenta tayi tasaki murmushi me ciwo tace" Dr Salman zabeera daga yanxu anan munrufe maganar MD ZABEERA sbd soyayyarsa ba Abu bane Dani Amatu zansamu, Soyayyarsa wani bangarene me girma a zuciyata da bazan iya cirewa ba saidai Kuma illace ga mutane da dama Dan haka na zabi azabtuwa da ita ni kadai acikin Raina bazan Bari ta azabtarda masoyanaba dan haka daga yanxu Babu mgnar MD ZABEERA da AMATULLAH, Zuwa yanzu nasan kagama sanin Abinda yake faruwa kasan banida aure da Dr Khalil dan haka idan har ka daukeni kamar Yar uwa wadda kake tsananin qauna to ka nesantani duk Abinda zai cigaba da zurafaf soyayyar MD ZABEERA ka tayani nitsawa da kutsawa cikin son KHALIL ZABEERA sbd na riga na yanke shi na zabarwa kaina. Kallonta ya tsaya Yi zaiyi Magana tayi saurin girgiza Masa Kai tana share fuskarta da tissue din motar tana murmushi tace" Zancen ya wuce Kuma ai"" dan sake batarda zancen ta Dora da fadin" ni yanzuma so nakeyi kafara koyamin wannan turancin naka na turawa idan Dr yadawo so nakeyi nabasa mamaki. Dariya yayi Yana jinjinawa gwarin gwiwarta na kawo dariya Kan fuskarta da boye abindake zuciyarta Wanda hakan na daya daga cikin Abinda yake burgesa gameda ita. Fitowa sukayi suna fira sama sama suna dariya kamar Babu Abinda yafaru. Anty zarah na ganinsu ta daga wayar hannunta tana cewa'' Cikinku fa daya zankira sbd Ina ganin bangantaba nasan Kaine kawai zaka fita da ita. Ko zama beyiba suka gaisa da anty zarah din ya juya ya fice sbd mum dinsa daketa qwalo Masa Kira. Fes ta sakewarta Takoma Amatun ta me rayuwarta cikin Raha da Jin Dadi, Duk wani Abu ko inda tasan zata hadu da MD ZABEERA ta tosheta gaba daya data fahimci lokacin dawowarsa yayi take komawa daki takira Dr ko USI ko Salman suyita firarsu cikin nishadi. Kulawa kuwa da qaunar da anty zarah take Mata sai ninkuwa sukeyi sbd yanzu kwata kwata ta daina cire cikon datakeyi sbd umarnin Dr khalil ne Dan shima yanzu so yakeyi daya dawo Susan dubarar Yi maganar cikin Nan yaqare su fuskanci reality itakuma anty zarah data qwallafawa cikin Rai har MD ZABEERA yiwa zancen takeyi idan tasamu fuska sai hakan yafara basa tunanin Dole daman Suma wata ran suyi sha'awar samun 'da ko 'ya. Sannu ahankali sabo da shaquwarta da Dr Salman yayi qarfi Dan shima saitakejinsa kamar usi da baya kusa duk wani gurbi na 'dan uwa me kulawa ya cike matashi Dan dukkanin shawararta da sirrinta dashi takeyi ta yanda shima baya boye Mata komai sai suka zama tamkar wasu best friends kokuma Yan uwan dasukafi kusanci da kowa. A bangare daya Kuma yanzu su umme sun Dakota gaba itada Haj maryam sbd ganin dukkanin yayansu sun qare da rawar qafa agunta sai suka sanyota gaba ba itaba ba anty zarah ba tun abin baya damunsu harya Fara damunsu zancen yajewa ummah mahaifiyar anty zarah tazo tayi musu mgn sai abin yazama fitina akayi tashin hankali tun abin na dagasu sai yayi tsanani akai kusan qaramin yaqi a familyn Wanda yasa akayi taro na musamman Amma duk da haka sai abin yaqara jawowa Amatu baqin jini sbd ganin kamar itace takawo fitina cikin familyn ZABEERA sai aka Fara camfata ga nuratu data sanyota gaba sosai tafara bincike a kanta sbd gano haqiqanin gaskia Dan bazata taba Bari Dr khalil ya auri wata banzar karuwa ba yabarta. Zuwa yanzu satin Dr khalil uku cikin na hudu da tafiya suna saka ran dawowarsa gobe shiyasa take cikin farin cikin data kwana biyu batayiba sbd tashin hankali sbd wannan fitinar da akayi yasa Andi saka doka me tsanani akanta akan kullum taje ta gaida uwar mijinta Wanda duk taje da bacin Rai take dawowa. Blue fox sukaje akayo musu gyaran Kai da qafafu akaiwa Amatun Jan lalle a hannuwa Basu bar gurinba sai yamma sosai sukayo gida Salman ne ma ya daukosu suna yin parking motar MD ZABEERA nayin parking akusa dasu ita tafara juyowa daidai shima ya juyo idanuwansa suka sarqe cikin na juna ##mamuh# ZAFAFA BIYAR👇👇👇 SIRADIN RAYUWA safiyya huguma MIN QALB mamuhgee SARAN BOYE billyn Abdul KIBIYAR AJALI Miss xoxo ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA hafsat rano Pay @09033181070 Or 09032345899 6/17/21, 8:04 AM - ': _*MQ 25*_ Saurin dauke idanuwanta tayi tana juyar da kanta zuwa wani gefen tana cigaba da dariyarta ta firar dasukeyi da Salman Wanda shima ya lura da yanayinda Amatun tashiga sai ya basar kamar yanda itama ta basar suka fito suna cigaba da zancensu. Gurin MD din ya nufa ya bude Masa mota ya fito Yana gaidashi tareda fada Masa saqon Dr khalil daya basa sbd yakasa samun wayoyin MD din duka. Itadai gaba tayi tashigewarta ko Palo Bata tsayaba sbd sanin ciki sukayo Anty zarah ce ta tsaya tai Masa sannu da zuwa ganin Salman yasata itama wucewa sbd yanda ya amsa kamar bazai amsa ba karya kwafsa Mata gaban Salman din itama bedroom dinta ta wuce Kai tsaye sbd dukkaninsu suna buqatar wankene kawai Dan ko yunwa basa ji Dan Babu kalar cimar dasuke buqata wadda Salman be siya musu ba Wanda kusan hakan yasa tafarajin qaiqayin ciwon Abinda rayuwarta take ciki na rashin kulawa daga kowa musamman mijinta Wanda shine yakamata ace ya jiyar da ita dadi da nushadin rayuwa amma Bata samu hakan daga kowa ba sai yanzu sanadin Wanda batamasan meye ake Kira gata da arziki ba a rayuwa gashi ta sanadinta suna nishadantuwa da rayuwarsu da Basu San komaiba sai bin umarni da oda. Wanka tayo ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya dogon hijab tayi sallah tana idarwa taje ta dauko yoghurts a fridge ta zuba cikin cup ta qara Masa madarar gari sosai ta juya sosai tadawo daki tana Sha tana daukarwa Dr khalil hotunan lallenta tana tura Masa saigashi yakira. Daukar wayar tayi tana murmushi qasa qasa tace" Kai Dr baka shanye rada ba. Wani siririn numfashi ya sauke Wanda yasata aje spoon din hannunta cikin kulawa tace" Yadai??? Lafiya najika kamar kana bacci? Murmushi me sauti yasako Mata Yana gyara kwanciyarsa da lullubinsa yace" Lafiya kalau kawai sanyin garin Nan ne yafara tabani tun satin daya gabata garin qasar ta daina shafamin lafiya Amma ai alhmdlh tunda gobe zamu dawo. Ajiyar zuciya ta sauke tana cigaba da Shan yoghurts din tace" To Meyesa zaka zauna harka Dade haka a inda baya shafa maka lfy??? Gwara da gobe zaka dawo da yau saina daga maka hankali kabaro. Murmushin qarfin hali yayi Yana cewa'' Gobe idan nadawo me Kika ajemin? Wani juyi tayi tareda kifewa kan carpet tace" Saika dawo zaka gani. Fira sukeyi ahankali sbd yanayin yanda yakejin jikin nasa sbd sanyi ya shigesa sosai Wanda yafara yiwa lafiyarsa barazana Dan yanaji ciwonsa yafara tashi ahankali. ****Miqewa Nuratu zabeera tayi daga zaunen datake a cikin restaurant din blue fox tana juya envelope din data karba tana sakin wani irin qyayataccen murmushi tace" Manager kayimin Abinda zai juya rayuwata nasamu Abinda nakeso kaima kasamu wadda kakeso, Wannan taimakon naka yabani farin cikin danayi shekaru bansamu ba sbd Dr khalil zabeera shine farin cikina,burina dakuma zuciyata... Kallonta yayi tareda miqewa tsaye yace" Ina fatar zan mallaki Amatu kamar yanda kikaimin alqawari?? Karka damu idan ka iya takunka zakayi amfani da damarka ka sameta daga lokacinda aka watsota daga rayuwar farin cikina da zabeera ma gabaki daya. Barin gurin tayi tana sake riqe envelope din farin cikinta na qaruwa ta nufi motarta tashiga ta rufe.. Bayan ta zauna cikin motar kallon envelope din tayi tana cewa" AMATULLAH K SALEH wannan shine asalinki tun kina Yar bolarki har zuwa yanzu, rayuwar alfaharinki tazo qarshe, Kinyi kutse a tsakanin masoyanda ba'a iya rabawa sbd son danakewa khalil hankalinkima bazai daukaba bare ki iya rabamu, Kina alfahari da kanki dakuma gatan da Kika samu daga Khalil, Modibbo da Andi ma gaba daya Zan ruguza rayuwarki gabaki daya sai nasaka kowa ya tsaneki fiyeda yanda tunaninki zai dauka, Ki shirya komawa rayuwar sata da dauke dauken da Kika fito bayan kinyi shari'a da familyn ZABEERA na Bata sunan da kikaso yimusu. Cikin handbag dinta ta sakashi ta ajiye jekar gefenta tareda tayarda motar tabar gurin cikin mugun speed Dan amatse take data Isa zabeera sbd so takeyi kafin Dr khalil zabeera ya iso an dade da korar Amatun daga rayuwarsu, Agogon motar ta kalla taga qarfe biyar ta yamma takusa gashi guraren yamma jirginsu Khalil ake sakaran zai sauka,gudu taqarawa motarta tana kallon titi. ***Cikin riga da skirt na lace maroon tayi adonta tareda daura dankwalin lace din ta sanya Yan kunne marasa tsawo sosai kalli agogo tana zama bakin gado da wayarta a hannu tana daukar hoto tace" Kowane lokaci yanzu Salman yace Dr zasu iya saukowa Meyesa yau nakejin wani iri cikin raina kamar inajin kunyarsa ne kokuwa wani abin daban. Shiru tayi gabanta na 'dan faduwa taji duk batajin sukuni ta miqe tana ajiye wayarta gefen gadon ta miqe tareda fitowa zuwa Palo gurin anty zarah ko zata debe Mata yanayin da fira. Tana fitowa anty zarah na fitowa daga nata bedroom din sanye da doguwar Turkish abaya red itama tayi kyau sosai sai qamshi takeyi kamar Amatun sai abin yabasu Daria kusan atare suka saki dariyar Zarah na cewa'' Wannan da kishiyoyi muke bansan wa mijin zai Fara kalla ba sbd kalar duk jajaye ne Kuma kalar ja idan ba mantawa nayiba tana cikin kalar da MD ke tsananin so sbd ance kalar kayan mahaifiyarsa kenan kafin ta rasu sbd sarautar da mahaifinta yataba Yi. Kallonta Amatu tayi tanayin shiru cikin tunanin kalamanta aranta tace" Anty zarah Allah yasa kada 'yan Amin na kusa su karba Miki zancenki sbd ita Magana ana fadarta ne da fatar 'yan Amin su amsa shiyasa ake cewa kafada alkhairi ko Kayi shiru. Wucewa gaba anty zarah din tayi Amatu naci gaba da binta da kallo zuciyarta na sake shiga fargaba saita kuma komawa daki zata zauna kenan saiga Kiran wayar Salman da sauri ta dauka Dan dama shi zata Kira ya debe Mata kewar tunaninta.. Salman ka...... Muryan Dr khalil taji yace" AMATULLAH. Wani irin sanyi da farin ciki taji ya kwaranya cikin ranta batasan lokacinda tasaki wani irin qaya taccen murmushi ba tana furta" Alhamdulillah ya Allah. Har cikin ransa yaji dadin hakan ya kashe wayar tareda miqawa Salman batareda yace komaiba suka kamo hanyar gida. Koda suka iso gida a gurin ummensa ya sauka Dan itama a matse take da ganin Dan nata musamman sbd kwanakin wata sabuwar qauna da kewar danta ke kamata shiyasa itama a matse take da taga abinta Nan aka hau hidimarsa kayan abinci da snacks kala kala anyi Masa taredasu fruits dasu fura duk dai wasu kayan marmarin kewar gida anyi Masa Nan yaci abinci tareda ita da Haj maryam da salman da Nuratu wadda koda ta iso gida kusan ataredasu Khalil din ta shigo Dan motarsu na gaba kafin Tata Ganinsa yasa takasa riqe farin cikinta da zumudinta tama manta da Abinda tadawo dashi Nan ta zauna cikinsu anacin abincin tana faman kula da duk motsinsa da Abinda yake so iyayensu kuwa sai washe baki sukeyi sbd dama shine burinsu hada Khalil din da Nuratu. Bai bar gurin umme ba sai magriba ya wuce gurin Modibbo acan sukai sallah taredashi da salman da MD ma Wanda ya shigo ana magribar. Bayan sungama sallah anan suka zauna tareda Modibbo Yana tambayar MD Amatu sbd duk yau da jiya Bata Zo ta gaidashiba kamar yanda ta Saba shiru MD din yayi Yana Dan sauke Kai yace" Inshallah duk suna lfy sbd Nima na kwana biyu bana zama gobe ma insha Allah Nima zanyi tafiya zuwa Germany. Allah ya taimaka ya tsare yabada sa'a Kuma. Amin dukkaninsu sukace suna qoqarin miqewa cikin sautinsa me saka nutsuwa yace" Khalilu matarka Ina saka ran a lissafi saura wata uku haihuwarta ko??? Tsit sukayi dukkaninsu su ukun Take zufa tafara Dan tsatsafowa Khalil din MD kuwa fararen idanuwansa ya zuba Masa Yana jiran jin amsar da Khalil din zai bada sbd shidai wadda ake maganar cikin akanta tana zaune gidansa Amma baitaba ganin ciki a jikinta ba gashi ana maganar saura wata uku haihuwa. Dan gyara murya Khalil yayi cikin girmamawa yace'' Inshallah haka ake saka Rai saidai cikin yazo da tangarda ne sbd rashin girmansa ya bayyana cikin baida lfy inasaka ran ma gobe zanje da ita asibiti musake dubawa. Cikin watanni da dama baa fada baida lfy ba sai yanxu? Sarqewa Dr khalil din yayi Yana Dan gyara murya yace" Ayi mini afuwa Modibbo nayi kuskuren rashin sanarwar. Shikenan ba damuwa kuje Allah ya Bata lfy. Amin"Khalil din yace suka miqe suka fito tare suna tafiya zuwa hanyar sashensu dayake direction guda. Tafiya sukeyi su biyu Banda salman daya wuce ya nufi motarsa yafita zabeera ahankali kowannensu shiru Babu me mgn dama sun Saba haka suke koyaushe idan suna tare saisun jima shiru kafin su Fara mgn Wanda MD ne me wannan halayyar shikuma Dr khalil Yana girmama kowane irin Hali da MD ya zabawa kansa da rayuwarsa. Tsayawa yayi ahankali batareda ya juyo ya kalli khalil dinba yace" Bansan wane mataki ka dauki wannan alamarin ba Amma ya kamata kasan kana saka kanka cikin hadari along with her.. 'dan shiru yayi kafin ya juyo ya kalli khalil din cikin wani irin yanayi yace" Atleast kayi tunanin Hali da Abinda zata fuskanta kafin kasata a irin wannan tight spot din sbd yanxu ku duka Kuna situation dinda only God can help so kafin komai ya fita hannunka kasan Abinda kakeyi ka dawo daidai,the truth doesn't cost anything but a lie could cost you everything. Kallonsa Khalil yayi tareda sauke ajiyar zuciya cikin damuwa yace" Bansaniba ko kasan Abinda nake qoqarin boyewa Amma bazaka iya fahimtar dalilina nayin hakan ba sbd komai yazone alokacinda banyi tsammaninsaba Babu mafita bayan wadda na dauka a wancan lokacin da yanzu ma.. Denying the truth doesn't change the fact cewa ka dauki hanya Mara bullewa, Ka zauna kayi tunani zaka samu wata mafitar wannan batayi ba. Yana Gama fadar haka ya wuce gaba batareda ya juyoba yayi hanyar sashensa. Shiru Dr khalil zabeera yayi yana tunanin maganganun MAHMOUD din wainda suka sakashi zurfin tunanin sbd tabbas qaryarsu takusa qarewa wadda idan bai nemo mfitaba asiri ya tonu to daga Ummensa har Amatu dashima suna cikin matsalarne, Babban burinsa daya dawo dashi shine maganar auren Amatun tukuna sbd duk wasu kayayakin aure na akwati ya siyosu yazo dasu saitin akwatinsa cif ya hado kayan aurensa Wanda ko gidan bai kawosu ba daga airport gidansu kawu suka Fara ajiyesu kafin su qaraso gida. Ajiyar zuciya ya sauke kafin shima yabi Bayan MD din zuwa ganin Amatu da tun Yana gurin umme take kiransa yaqi dauka sbd kada farin cikin ummen ya gushe. ##Mamuh# Kuyi hkr kuyi manage da wannan hutun weekend naje dakuma mura dake damuna🤦🤦🙏🙏 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 26_* Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi ganin duk tazama so serious Wanda Sam kowa yasan ba halinta bane tafi sabawa da hayaniya shiyasa duk inda take to hayaniya na gurin., Ana bude qofar palon atare dukkaninsu suka kalla qofar shigowar kowacce fuskarta daukeda murmushin yiwa Dr khalil din maraba Musamman Amatun da murmushinta na yau ya banbanta Dana kullum sbd yau sauran zuciyar Khalil takeson qarasa sacewa sbd ta zamo Tata ita kadai shiyasa yau komai nasa na musamman ne agareta saidai sabanin ganin fuskar Dr khalil zabeera a cikin idanuwan MAHMOUD ZABEERA idanuwanta suka sauka murmushinta me sanyi da tsada akan fuskarsa yafara sauka gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauya cikeda mamaki da fargaba da sanyin jiki.. Tsayawa yayi kallonsu fuskar na bayyanarda mamakinsa daba'a cika ganewaba ganin yanda dukkansu suka waiwayo suka zuba Masa Ido kowacce fuskarta daukeda murmushin daya mugun daukar hankalinsa da sakashi wasi wasin mamakinsu musamman Amatu datafi bayyanarda murmushinta da dukkanin farin cikinta dabai taba ganiba, Ganin Ahankali Amatu ta dauke idanuwanta dake cikin nasa tana kallon bayansa murmushinta da farin cikinta fiyeda na farko Yana dawowa yasashi dawowa MD dinsa ya sauke boyayyan numfashinda Babu Wanda yaji ya Fara takowa ahankali idanuwansa na sauyawa cikin wani boyayyan yanayin dayake ciki sbd sai alokacin ya fahimci Khalil ne keda wannan murmushi da farin cikin, Zama yayi Kan couch din dakinsa Yana rintse idanuwansa tareda yamutsa kansa yanajin wani irin zafi na ratsa dukkanin jikinsa Take kuwa zufa ya kakkaryo Masa Tako ina bayan ga kukan AC Nan yanaji yasan a kunne yake.... Zarah ya tuno da itama taketa washe baki tana murmushi to idan ita waccar tayi Dan Yana sunan mijinta to itafa??? Jin kansa ya dauki zafi Yana neman saukewa zarah laifin sai kawai ya miqe ya fada toilet yayo wanka yayi clearing mind dinsa ya shirya cikin kayan bacci ya dauki laptop yafara wani aiki Yana basar da tunanin komai da kowama. Dr khalil kuwa duk yanda yake tunanin Amatu takai cikin ransa sai yanzu yake gane ta wuce Nan sbd wannan murmushin datake jifarsa dashi yagama hargitsa Masa Kai da tunani., Zama yayi bayan sungama gaisawa da zarah ta wuce tabasu guri ya juyo suna fuskantar juna Yana kallonta cikin kulawa yace" Hw are you AMATULLAH??? Zuba Masa idanuwanta tayi har lokacin murmushinta bai daina fitaba tace" Nayi fushi ka koma na barwa Nuratu. Wani irin Dadi yaji ya kamasa me sanyi cikin nutsuwarsa yace" Kishi kikeyi ita tafara tarbona??? Harara ta sakar Masa tana cewa'' Zanyi maka kuka idan kasakemin maganarta. Kallonta yayi Yana cewa'' Ok tom yanzu duk wannan adon sbd zandawo akayisa? To Meyesa baki shafamin Dan lipstick dinnan naku danaga ana sakawaba Nuratu tasaka ita...... Miqewa tayi a fusace tayi dakinta Yana kiranta ko waiwayosa batayiba tana shiga gaban mudubi ta wuce Kai tsaye Ta dauki janbaki hot red tashafa a bakinta tana kallon madubin saikuma taga tayi kyau saita dauki turare taqara fesawa tadawo palon tana kallon yanayin dayake kallonta fuskarsa na bayyanarda farin ciki sosai sai taji farin ciki yakamata sbd ganin ta kyautata Masa shiyasama take nuna kishin Nuratu sbd ganin hakan na sanyasa farin ciki. Cake din datayi da fruit drink dominsa taje ta dauko takawo Masa Nan suka Fara fira cikin nutsuwarsa yake cin cake din duk da a qoshe yake Amma sbd itace tayi da kanta yakeci cikin alfahari. Sai guraren qarfe goma yabar part din ta rakosa har waje kafin tadawo ciki ta wuce dakinta tanajin farin ciki kamar bazata iya bacci ba yau din. Washe gari ataredasu Dr khalil din yayi breakfast kafin suka fita tare harda Dr Salman daya Fara aiki asibitin Dr khalil kafin ya kammala shirye shiryen sa danshi ba anan qasar yakeson aikiba. Gidansu kawu suka Fara zuwa tunda ta Isa gidan kowa ke Mata wani irin kallon burgewa suna tayata murna Wanda yasata sakin baki tana kallonsu cikin mamaki. bakin dakin iyami tagan akwatina a jere tsaf su maman junior sai washe baki sukeyi suna budewa iyami ma yau bakin Nan har kunne sai annashuwarta takeyi tana sake bubbudewa su maman junior kayan suna gani suna shewa. tsayawa tayi tana kallonsu cikeda mamaki kafin ta juyo ta kalli su Dr khalil dasuka tsaya qofar shigowa suna Magana da kawu Wanda shima yau harda saka babbar rigar farar shadda wadda itama Dr khalil ne ya dinko mishi su kusan kala bakwai. Sake juyowa tayi gurinsu iyami da suke Mata barka da zuwa Maman junior kuwa rawa tahau Yi tana janyota tana waqarsu ta yarbawa tana cewa'' Amatunmu tasamu mijinda zai Bata farin ciki da suna me girma na mutunci. Kallon rashin fahimta tayi Mata gabanta na mummunan faduwa ta qwace da sauri zatayi Magana iyami datasan Abinda zata iya fada tayi saurin cewa'' Kayan Dr khalil ne jiya da daddare aka kawo. Kallon iyamin tayi da sauri tareda juyawa ta kalli inda suke Magana da kawu Yana Dan sato kallon inda suke Dan yaga reaction dinta.. Wani irin farin ciki Mara misaltuwa ya shigeta da sauri ta rungume maman junior tana cewa'' Alhamdulillah ya Allah. Dariyar farin ciki iyami ta sake tana sake sakawa Khalil din albarka sbd duk iya bincike kawu yayi akansa Kuma sun Dade da yaba nutsuwarsa da halayensa sbd a wannan zamanin basu taba haduwa da yaro me nutsuwa ba kamar Khalil din, Shiyasa Babu wani dogon janye janye na al'adu kawu yabasa auren Amatun kawai waliyan Khalil din yake jira idan sun daidaice da khalil din sbd Khalil ya sanar dashi akwai Yar hayaniya a zuriar tasu idan ta lafa zasu zo idan Kuma akasin hakan ne ya amince asamu waliyai a daura musu aure. Zama tayi gefen iyami ta bude kayan tsaf taga abinta tana sake Jin inama gobene ranar auren ayi kowama ya huta. Ciki su Dr khalil din suka qaraso suka gaida iyami tareda gaisawa da sauran mutanen gidan suka koma waje suna jiran Amatun tagama ganin kayan su fito. Kusan awa biyu ta Bata kafin ta fito suka wuce asibiti inda ya ajiyeta a office dinsa suka Shiga meeting tayi zamanta tareda miqewa a kujerarsa tana game a wayarsa daya barmata wadda kyakkyawan hotonta yake shimfide lock screen dinsa na ummensa Kuma a main screen dinsa sai hakan yasaka jikinta yin sanyi sbd a rayuwar Khalil yanzu duk Wanda yasansa yasan itada ummensa sune sanyin zuciyarsa da idaniyarsa Amma Kuma gashi Sam ko inuwa daya basa zama a taqaicema ummen Babu Wanda ta tsana a rayuwa kamarta ita Kuma Babu wadda take ganin ta rainawa wayo kamarta sai kawai taji Bata girmama soyayyar Dr khalil dinba. Sai qarfe uku suka baro asibiti sai kawai suka wuce gurin cin abinci a 5star daganan ma gurin shopping suka wuce sai gab da magrib suka shigo zabeera Kai tsaye sashen ummensa ya nufa tana ganin sunyi parking bakin flat din tayi saurin kallonsa shima ita ya kalla Yana cewa'' Inason ganin Mata biyu masu mahimmanci gareni sun zama daya wannan shine babban fatana, Amatu please kiyi hkr da duk Abinda umme ke Miki ki Bata dama kigani tanada zuciya me kyau, Abinda nasani shine duk Abinda nakeso ummina na sonshi bare ke datasan Ina Miki tsaftatacciyar so Wanda bazan iya dainawaba Dan haka nasan zata soki wata Rana ko Ina Raye ko bana Raye nasan wata Rana saita soki kamar yanda takesona,so please AMATULLAH ki qaunaceta ki kulamin da ita I promise you wata Rana zata daina tsangwamanki zata qaunaceki kamar yanda take qaunata. Wani irin sanyi jikinta yayi sosai saitaji kunyarsa ta kamata ta dago a sanyaye ta kallesa ya da yayi saitaji kamar Bata girmama soyayyarsa ba tunda takasa girmama mahaifiyarsa., Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikin sanyi tace" Inshallah Zan kiyaye zancenka daga yanxu zanyi iya qoqarina gurin kyautata Mata. Numfashi ya sauke ahankali yace" Thank you AMATULLAH. Fitowa sukayi suka nufi ciki Yana gaba tana gefensa jiki a sanyaye take tafiyar sbd yanayinsa duk ya Gama sanyayata ga wani irin damuwa daya shigeta ga faduwar gaban yanda zasuyi da ummen Amma koma menene tayi alqawarin jurewa sbd shi. A palon farko dasuka shigo take qoqarin zama ya tsaya tareda juyowa ya kalleta yana girgiza Mata Kai tareda cewa'' Follow me. Falonta na qurya suka nufa Wanda dagashi sai bedroom dinta Yana gaba tana bayansa. Zaune take tana kallon wani Shirin girke girken larabawa da akeyi a mazzika taji shigowarsa tareda sallamarsa ta juyo fuskarta daukeda murmushin dake bayyanarda girman son datakewa Dan nata sai idanuwanta suka sauka akan wadda ke bayansa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauyawa zuwa bacin Rai da fushin ganinta ta tsuke fuska sosai tana dauke Kai daga bakin qofar. Tsayawa Amatu tayi daga Inda take tana sauke Kai ganin irin kallon qyama da tsanar da ummen ke Yi Mata, Qarasowa yayi gefen ummen ya zauna Yana kallon fuskarta data canza yaji ransa yaqara jagulewa ya sauke wani irin numfashi Mara Dadi Yana dafa hannun ummen cikin kulawa da sanyin jiki tareda sautin daya sakasu kallonsa duk su duka biyun yace" Umme Meyesa Zaki dauki halayyar daba naki ba¿ Shin Amatu tanada wani banbanci ne da sauran mutane da Kika zabi qyamarta ita kadai? Umme Amatu matar dazan aurace sbd Ina sonta da dukkanin zuciyata Shin umme kodan son datakewa dan naki bazaki qaunacetaba kodan hakan? Girgiza Kai tayi tana danne 6acin ranta ta kallesa tace" Khalil kadaina cewa tana sonka wannan bayan kudi duk duniya Babu yaren datake ganewa, Wannan Babu wani buri a rayuwarsu Bayan samun kudi ta ko wane halin Yaya, Kudine kawai agabanta ta yanda zata iya yin komai akan kudi ciki ina fada maka harda mutuncinta zata iya siyarwa akan kudi, Wlh khalil kaima sbd kudinka take sonka da bakada kudi bazata taba sonkaba Irin wannan matar kakeson nabari ka aura Khalil??? Dagowa yayi ya kalli Inda Amatun ke tsaye cikin wani irin yanayi na damuwa ya sauke ajiyar zuciya tareda cewa'' Zo AMATULLAH, Zo Nan kusada umme. Kallon ummen tayi taga ko kallon inda take Bata qaunar Yi sbd qiyayya ta tako ahankali tazo gefensa ta zauna ahankali Kan carpet din dake gurin tana sauke kai maganganun ummen na sake jujjuyawa cikin kanta. Numfashi ya Kuma saukewa cikin wani irin yanayi na damuwarsa dake bayyane wadda tasa dukansu su biyun kallonsa yasake riqo hannun ummen cikin sanyin murya yace" Ummen banfara son AMATULLAH ba Sai danasan asalin wacece ita, Nafara sonta ne bayan nasan batada kowa aduniya, Banfara sonta ba saidanasan a bola ta tashi acan tayi wayo ta koyi gwagwarmayar rayuwa, Banfara tsananin sonta ba saidanasan irin wahalalliyar rayuwar datayi amatsayin almajiri Mara yanci Wanda ta rayu cikinsu amatsayin namiji bayan tana matsayin mace, Amatu bakowa mace face yarinyarda wasu bayin Allah suka taimaka suka daukesu Bayan sungama wahalalliyar rayuwa acikin bola da mataccin gidaje da shagunan daba'a gamaba, Babu Wanda yataba kallonsu da idon Rahama, Babu Wanda yataba duba yanayin shekaru da jinsinta amatsayin mace ya taimakesu, Sun kwana da yunwa suntashi da ita, Sunyi sata dan suci suyi rayuwa, Maza da yawa sunyi yunqurin lalata rayuwarsu da sunan taimakawa shin umme Wanda yake ciki irin wannan qaddarar Dan yayi sata dan yaci ya Hana kansa Zina illa ne dahar za'a gujesa?????? Umme wallahi tallahi ina tsananin son AMATULLAH da dukkanin zuciyata bansan ta Yaya zanyi Miki bayani ki qaunaci Amatu ba, Na shirya auren AMATULLAH na zamo gatanta itada zuriarta Wanda Babu wani Abu dazai sauya niyata akan hakan, Shin umme kintaba zaunawa kinyi tunanin irin tarin Lada da farin cikin dazaki samu aduk lokacinda Kika kawo murmushi da farin ciki a rayuwar marayu? Umme tarin ladace me yawa wadda zata iya gyara Miki ko wanke kurakurenki Kuma yabaki nutsuwar zuciya da ruhi.... Zuwa lokacin Amatu kuka takeyi sosai sbd Bata taba sanin khalil yasan asalinta ba daduk halinda suka Shiga arayuwa Kuma ahakan yake sonta tabbas yagama bawa rayuwarta girgizar data sauya zuciyarta akansa gabaki daya. Umme ma hawaye takeyi sosai tsananin so da qaunar danta na ratsata... Ahankali ya zamo qasa ya durqusa gabanta tareda riqo hannuwanta idanuwansa dasukai laushi na kallonta a karye yace" Umme ayau gani na durqusa a gabanki Ina roqonki daki ajiye dukkanin wani burin rayuwa ko komawa Allah kodan samun nustuwar zuciya, Umme Ina roqonki da ki qaunaci Amatu ki da zuciya daya sbd bazan iya ganinku acikin halinda kuke cikiba, Umme...... Bata Bari ya qarasa ba tayi saurin dagosa tana rungumesa hawayenta na qara tsiyayowa tace" Nayi maka alqawari Khalil wlh Babu wani al'amarin duniya dazan sake Bari na 6ata akansa, Idan dai Amatu ce Kuma wlh na amince maka bazan qara qintaba idan har na tabbatarda har zuciyarta itama take sonka.... Rungumeta yayi da sauri Yana cewa'' Thank you ya umme. Share Mata hawayenta yafarayi tareda juyowa ya kalli Amatu dake kuka sosai ahankali tanajin Sam Bata cancanci soyayyar khalil ba, Zuciyarta batayi Mata adalci ba son wani 'da namiji a zuciyarta Wanda ba khalil ba... Ahankali yakamo hannunta ya dawo da ita gefen umme dake kallonta cikin wani irin sabon yanayi ya zaunar da ita ahankali yace" Amatu ga amanar ummi na ki kular min da ita amatsayinki na matar 'danta. Dago jajayen idanuwanta tayi ta kallesa kafin ta kalli ummen ta daga Kai ahankali takasa cewa komai sai binsa takeyi da Ido zuciyarta na karban zazzafan baqon yanayi akansa Wanda ta tabbatarda sone me zafi. Murmushi umme tasaki ahankali tareda kallon Amatun tana nuna Mata gefenta tace" Kimin alqawarin zaki so shi fiyeda yanda yake sonki?? Murmushinsa me nutsuwa ya saki Yana kawar da zancen da cewa" Umme wannan son Kaine zakice ta Soni fiyeda yanda nake sonta sbd bazata iya Sona yanda nake sontaba nawa me girma ne. Murmushi sukayi Banda Amatu dake Jin wani babban al'amari me girma atareda ita hakanan taji gabaki daya nutsuwarta na barinta. Haj maryam da Nuratu dasuka jima Bakin qofar palon suna jin dukkanin Abinda yafaru baqin ciki me girma yarufe zukatansu da idanuwansu musamman nuratu data gama zaucewa a fusace ta juya tana qoqarin sakin ihun baqin ciki da zuciyarta dake neman tarwatsewa da gudu Haj maryam tabi bayanta tana cewa'' Yau tunda Kika juyamin baya Aisha akan danki kowa ya shirya tashin hankalin dazai biyo daren Nan Dan wlh yau sai takardun asalin Amatu sun kwana a hannun Modibbo da Andi. ##mamuh# 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 27_* Ko gabanta Bata gani ta qarasa sashensu tana qoqarin dafe qirjinta dake mugun zafi da radadi kamar zai tarwatse Tana shiga palonsu ta zube qasa Kan gwiwowinta tareda fashewa da wani irin kuka me tsanani da zafin Rai, Da sauri momynta ta qaraso ciki tana rikota tana Kiran sunanta cikin nata ciwon ran me tsanani da tausayin 'yarta tana sake kamota tace" Nuratu please kada kiyi irin wannan kukan wlh karyamin zuciya zakiyi bazan iya ganinki cikin irin wannan halin ba Dan Allah kidaina kuka zamu samu mafita, Bazan taba Bari Khalil ya auri wadda bake ba musamman wannan barauniyar karuwar yarinyar Dana Gama alwashin bazata taba aurensaba kodan yanda ya fifita sonta akanki. Tsananta kukanta yayi tana girgiza Kai tana cewa'' Momy wlh inoson Khalil fiyeda yanda 'dan Adam zai iya lissafawa, Zuciyata zafi takeyi sosai bazan iya kallonsa ya auri wata ba, Gwara na mutu danaga wannan ranar..... Da sauri momyn ta rufe Mata baki tana girgiza Mata Kai cikin tashin hankali tace" Dan Allah Nuratu kidawo hayyacinki ki daina wainnan maganganun Zan zamo Mana mafitarda zamu Kori Amatun daga rayuwarmu gaba daya da duk ahalin zabeera ma bama Khalil kadai ba..... Dagowa nuratu tayi da idanuwanta dasukai jajir suna tsiyayo hawaye tana qoqarin fahimtar zancen momyn ta zabura da sauri tana tunowa da takardun data karbo hannun manager na kaf asalin Amatun harma da qarin rayuwar karuwanci datasa aka qara Mata akai, Dakinta ta nufa kamar mahaukaciya ta nufi inda handbags dinta suke tahau wargazasu tana neman jakar da tasaka envelope cikin hauka, Ganin yanda take wargaza Kaya yasa momyn saurin qarasowa tana sake riqota saigashi ta zaqulo jakar Jikinta har rawa yakeyi ta bude ta dauko envelope din gaba cewa'' Momy yau Babu Abinda zai Hanani wulaqanta wulaqantacciyar rayuwarta, Saina sakata kuka ninkin Wanda ta sakani tun zuwanta zabeera, Ayau zata San asalin irin girman soyayyar Dana kewa Khalil. Juyawa tayi ta fice tana share hawayenta dasuke sake bulbulowa cikin tsananin zafi da baqin cikin da zuciyarta ke ciki Da gudu momy tabi bayanta tana Kiran sunanta sbd ayanda take yanzu ba acikin hayyacintaba komai lalacewa zaiyi Bata haka zasu tona asirin Amatun ba so takeyi harda umme ta fito cikin zancen.... A firgice ta biyo bayan Nuratun tana Kiran sunanta Amma tuni nuratun ta hada da gudu gudu tana sake sakin sabon kuka ta nufi sashen Andi inda tasan Modibbo nacan taredashi a daidai lokacin. Ganin takasa cimma Nuratun data nufi hanyar sashen Andi yasa hankalinta mummunan tashi tuni ta firgice sbd wlh tasan Kwana zasuyi aciki Suma sbd zancen ba qaramin tashin hankali da masifu zai janyo ba,,, Salman dake qoqarin parking yaga wucewar Nuratu da gudu gudu kamar tana kuka Yana qoqarin kashe motar ya fito saiga momynsu cikin sauri itama tanabin bayan Nuratun hankalinta amatuqar tashe daga ganinsu yasan ba lafiya ba bare ganin sunkama hanyar sashen Andi koma meyene to ya girmama dan duk Abinda yasa aka wuce Modibbo aka nufi Andi to da matsala babba. Kashe motar yayi da sauri ya fito yana qoqarin bin bayansu saiga Dr khalil ya fito daga sashen ummen tareda Amatu da ummen zasu mayarda Amatu Da sauri Khalil ya taresa ganin Yana Shirin gudu yace" Lafiya likitan qashi??? Kallon hanyar Sashen Andin yayi cikin sauri sauri yace" Inaga akwai matsala ne Naga Nuratu da momy sun nufi sashen Andi kowannensu Babu nutsuwa atare dashi Nuratu ma kamar kuka takeyi... Juyowa yayi ya kalli khalil din cikin fargaba yace" Ina Jin tsoron Abinda zaisa suje gurin anty musamman Nuratu nasan halinta da tsananin fushi da rashin tunani Wanda kowa yasan yawancin fushinta akan Abinda ya shafeka ne Akwai Abinda yafaru yanzu a tsakaninku ne???? Dukkaninsu su ukun da sauri suka kallesa cikin wasi wasi da shakku Da sauri umme ta kalli me aikinta dake fitowa dan kawo Mata wayarta dake ringin cikin sauri tace" Shafa'atu Maryam da Nuratu sun shigo sashena bayan shigowar su Khalil???? Da sauri cikin tashin hankali duk suka zubawa shafar Ido jiran amsarta Tace" Eh da Kuna ciki sun shigo Amma....... Bata qarasaba Salman ya juya da mugun gudu Yana cewa'" Innalillahi-wainna ilaihirrajiun..... Da sauri Dr khalil ya juyo ya kalli umme da zufa ya katse Mata ya kalli Amatu da tuni qafafunta suka Fara daukar rawar tashin hankali ya riqo hannuwansu duka su biyun cikin qoqarin bawa kansa nutsuwa Dan kwantar musu da hankali yace" Umme duk tsanani karku Fadi asalin abinda yafaru na gskiar Abinda yafaru tsakaninku Kika kawo Amatu zabeera, Amatu komai zai faru karki bude baki kiyi magana nine zanyi Magana ok??? Kallonsa umme tayi da sauri tana cewa'' Ta yaya Zan tsaya Ina kallonka ka dauki hukuncin Abinda bakaine kayiba... Umme please kuyi kawai Abinda nace ku koma ciki Bari nabi bayansu tun kafin su Isa. Da sauri yabi bayan su Yana share zufan goshinsa akaro na farko dayaji yanawa wani fatar faduwa ya Suma sbd Jin yake inama Nuratu kafin takai tafadi ta suma a hanya.. Kasa hakuri ummi tayi takasa komawa ciki ta tsaya gurin tana zarya cikin tsoro da fargabar Abinda zai biyo baya.... Bakin qofar shiga momy tayi nasarar damqe Nuratu da sauri tana sauke numfashin wahala da tashin hankali tace" Nuratu kidawo hayyacinki kada kiyi Abinda masifarsa zata qare kanmu sbd wannan alamarin ba Abune me sauqi ba dazamu Bari Modibbo yaji daga garemu ba bare Andi Maza kawo takardun Nan mukoma muyi Magana a nitse...... Qwacewa tayi tareda tura qofar palon zata shiga har lokacin kuka takeyi sosai tace" Momy yau idan ban tona asirintaba duniya tasan ko ita wacece ba hankalina bazai taba kwanciyaba So nake ta dandani 'dacin rabuwa da Abinda kakeso.... Fixgota Salman yayi da qarfi Yana qoqarin kwace envelope din ta fizge da qarfi tana cewa'' Kaima bayanta zakabi aci gaba da barin karuwa tana rayuwa acikin zabeera? Me take Baku da duk mazan zabeera kuka haukace akanta?? Abinda take bawa sauran mazan waje........ Wani wawan Mari salman ya sauke Mata Wanda yasata haukacewa cikin tsananin firgici da masifa tace" Wlh ka sake dasamin tsanarta me tsanani Koda Zan rasa Raina saina tabbatarda Andi da Modibbo sunsan karuwace ita, Barauniya ce, Yar bola ce, Me aikin karuwanci a gidan abinci....... Ba zata Marin dayafi na farko zafi da qara ya sauka akan inda Salman ya mareta Wannan karon radadin yayi tsananin data kasa riqewa saidata zube a qasa ta dago ta kallesa idanuwanta na qarasa rinewa hawaye masu tsananin zafi da baqin ciki suna gangaro Mata murya na rawa tace" Khalil duk akan wannan karuwar ce?? Cikin tsananin bacin Ran dabasu taba ganinsa aciki ba ya bude baki zaiyi Magana akai gyaran murya daga bakin qofar Shiga palon kusan duk atare suka juya cikin firgici da tashin hankali sukaga Andi ne da kansa a tsaye Modibbo na gefensa kowannensu kallo daya zakayi Masa kasan dukkanin fushi da bacin ransu a bayyane yake Cikin nutsuwa Modibbo ya qaraso gaban Nuratu da itama tashiga firgici ya sanya hannu ya zari envelope din hannunta batareda yace qala ba ya juya yadawo gefen Andi Yana bude envelope din Wanda yasa tuni kowannensu ya shiga rawar jiki musamman momyn tuni ta durqushe qasa tan neman sakin kuka Andi yayi wa gefenta kallo daya take ta hadiye kukan batareda yafitoba yakoma tana rawar jiki. Duk inda tashin hankali da sanyin jiki yake Yana tareda Amatu da umme sbd kowannensu yakasa samun nutsuwa ta ja qafafunta dasukai nauyi ta nufi hanyar sashensu idanuwanta na sake kadawa bayan kumburin dasukayi na kukan data gama sha, Tana shiga palon da anty zarah dake zaune tana qoqarin kiranta tayi saurin miqewa ta qaraso gabanta cikin tashin hankali da tsoro take Kiran sunanta tana tambayarta lafiya. Kasa motsi tayi bare Magana sai kawai ta fashe da sabon kuka me shiga Rai tana zubewa qasa... Innalillahi-wainna ilaihirrajiun" anty zarah ke maimaitawa tana zubewa qasan itama cikin tashin hankalin ganin irin kukan da Amatun keyi cikin rudu muryarta na rawa tace" Amatu meya sameki kifadamin tun kafin kisa zuciyata fashewa itama Dan Allah, Kukanki na bani tsoro tareda sani cikin tsananin firgici Dan Allah kiyimin mgn..... Dagowa tayi ta kalli anty zarah din jajayen idanuwanta na tsiyayo da hawaye masu zafi tanajin tausayin kanta Dana zarah din sbd tasan lokacin rabuwarsu ne yazo, Abinda Bata saniba shine zarah din zata tsaneta idan taji Abindake faruwa? Koda zata tafi zatayiwa anty zarah adalcin fada Mata gskia da bakinta ko Dan zallar qaunarta gareta. Wasu hawayen ne suka Kuma tsayayo Mata ta rintse ido zuciyarta na radadin Abinda zata fada ahankali tace" Anty zarah ki gafarceni na zamo babbar butulu me mayarda alkhairi da cin Amana, Na cutatar dake ta hanyar wahala akan Abinda Kika saka Rai da burika akansa, Na hanaki bacci da sukuni gurin dawainiya Dani akan qarya yaudara... Anty zarah banida ciki ajikina, Bantaba daukar cikiba, Bantaba sanin namijiba bare nayi Abinda zaisa nasamu ciki, Dr khalil ba Mijina bane......... Sakinta anty zarah din tayi cikin tsananin firgici da mamaki tayi baya tana zaman 'yan bori idanuwanta na silalo hawayen tsoro da karyewar zuciya ta Fara girgiza Kai tana son yin Magana takasa sai hawaye.... Anty zarah bantaba sanin a duniya akwai masu irin tsarkakakkiyar zuciya irin tasu kawu ba sai Dana hadu da Dr khalil dake da salman kuka kawo wani irin farin ciki da sanin mutuncin Kai arayuwata Amma Babu Abinda nakawo Muku sai yaudara da damuwa..... Cikin rawar murya anty zarah dake rawar jiki gaba daya cikin firgici tace" Idan duk Abinda Kika fada hakan ne to meya kawoki cikin rayuwarmu???? KUDI"""""tafada Kai tsaye tana sauke Kai hawayenta na qaruwa.. Son kudi da burin samunsu kota halin Yaya yasani shigowa rayuwarku Saidai bayan haduwata daku na fahimci samun mutanen dake sonka da son farin cikinka tareda zama acikinsu shine asalin farin ciki da walwala Wanda kudi baya siya maka suba, Anty zarah girmanki da qaunarki alqawarine da bazai taba gogewa azuciya da rayuwataba, Anty zarah idan lokaci yayi Zan fada Miki gaskiyar duka Amma ayanzu iya Abinda Zan fada Miki kenan. Miqewa tayi da sauri ganin irin hawayenda anty zarah din keyi tana bin cikinta da kallo burirrikanta akan cikin suna tarwatsewa daya Bayan daya, Cikinda akai alqawarin Bata Abinda za'a Haifa Wanda tuni tafara kallon kanta amatsayin uwa Nanda lokacin qanqani. Buga kofar da akayi da qarfine yasasu kallon kofar tun kafin su motsa aka sanarda saqone Andi nayiwa Amatu Kiran gaggawa. Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro ta juya ta nufi qofa. A tsaitsaye suke Babu Wanda yasamu damar motsawa daga Inda yake sbd tashin hankali kusan mintuna suka share ahakan sbd shock dinda su Andi suka Shiga Bayan Gama sanin wacece Amatu dakuma irin qazamtacciyar rayuwar karuwancin datayi qarshe ta qare acikin zuria mafi tsafta da mutunci, Umme da sauran manyan yaran Andi da Modibbo da tuni aka kirasu suka qaraso Babu wanda ya zauna duk tsaye suke cikin tashin hankali da jimanin abinda zai biyo Andi kawai ake jira yayi Magana. Dagowa yayi cikin wani irin yanayi na tsanani yayiwa Khalil kallon dayasa kowa sake Shiga firgici cikin amo me firgitarwa yace" Kowace tambay amsa daya nakeso, Ka auri wannan yarinyar?? Aa, Acikin takardan Nan anrubuta cewa Ita din Mara asali ce, Yar bola ce, Karuwa ce, Barauniya ce, Gidajen abinci,hotels da gidan rawa take aiki, Babu police station dinda batayi zamaba har gidan yari Gaskia ne ko qaryane??????? Cikin tsananin firgici da tashin hankali muryarsa na rawa yace" Gskia ne Amma Banda....... Hannu Andi din ya daga Masa fuskarsa na nuna dukkanin fushinsa da bacin ransa. Take yace kowa ya watse ya sallamesu ya juya yayi ciki 'yayansa na binsa abaya. Kasa motsi kowa yayi sbd sanin abin bazaiyi kyauba. Daga ciki kuwa kallon alhaji qarami yayi Kai tsaye yace" Yarinyar da mariqanta a daukesu a rufe a central station dinda Khalil zaifi shekaru goma Yana nemansu baigansu ba a sanarda commissioner laifin datayi ta yanda zasusan girman laifin Bata sunan zabeera. ##Mamuh# 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 28_* Cikin nutsuwa da girmamawa Modibbo ya kalli Andi a natse yace" Kama yarinyar da mariqanta kamar su ba'a musu adalci ba sbd da yiyuwar qila bada masaniyarsu ta aikata hakanba kamar yanda shima Khalil Babu saninmu yaje ya kwaso Mana ita.. Tsit Sukayi kowa na kallon Andi da yanayinsa sbd maganar da Modibbon yayi ana jiran jin me andin zaice. Zama batareda ya dagoba ya kallesu yace" Alhaji qarami na damqa case din a hannunka a shigar da qara me qarfi akan yarinyar da mariqanta idan ka Gama binciko zancen gaskia ne ko aa akan laifin qage da shirin batawa zabeera suna ta hanyar qage akan cikin qarya, Hakama asaka likitoci masu kyau suyi bincikenta aduba idan da akwai ciki a jikinta ko Babu, Kada abari Khalil yasan inda aka Kai case din duk tsanani hakama MAHMOUD ZABEERA kada abari ko kadan yasan Abinda yake faruwa tunda baya Nan sbd acikin minti biyu zai iya saka agano wa Dan uwansa inda yarinyar take. Cikin biyayya alhaji qaramin yace" Angama Inshallah Andi. Sahirtaccen numfashi Modibbo ya sauke zuciyarsa na daci da alamarin sbd baiso komai ya lalaceba. Amatu na isowa sashen motar civil defense din na fakawa bakin qaton gate din ZABEERA Alhaji qarami ne yafito daga palon ya kalli khalil yace" Ka shiga ciki Andi na zaiyi magana da Kai. Kasa motsawa yayi ya juya ya kalli Inda Amatu ke tsaye yanajin kunyar kansa daya Bari har suka tsintsi kansu a irin wannan Matsin dabai samo mafita ba tuna farko sukai aure tun kafin zuwan wannan ranar. Kallonsa itama takeyi zuciyarta na sake karyewa da wannan masifar Itadai komai tsananin hukunci da zafinsa zata dauka matuqar ba rabata za'ayi da Khalil din ba. Sake maimata Masa alhaji qarami yayi Yana kallonsa cikin fushi Wanda yasashi dauke idanuwansa daga Kan Amatun yafara takawa ahankali ya nufi qofar palon yashige. Yana shigewa alhaji qarami ya kalli Amatu dake tsayayo hawaye masu ciwo tanajin zuciyarta na sake karyewa ya nuna Mata hanya alamar suje. Da sauri umme tayi gurinta tana qoqarin riqeta anty zarah data biyota tayi saurin rungumeta ta baya tana sake sabon kuka sbd su duka sun San matuqar aka tafi da Amatu ba lallai su Kuma ganinta arayuwarsu ba. Daga umme har anty zarah din da Amatu kuka sukeyi sosai musamman umme datasan idan Amatu ta tafi rayuwar Khalil dinta na cikin hadarin rasata. Haj maryam ma a katse take har lokacin sbd Basu Gama sanin inda Rana zata Fadi ba gashi dai Nuratun ma kuka takeyi sosai sbd wannan fitinar tasan shikenan Khalil bazai taba sonta ba yanda take fata komai yagama lalace Mata. Matane su biyu da uniform dinsu na civil defense manya manya dasu kowacce tanaji qarfi da rashin Imani sbd Babu kalar bahaushiya acikinsu bare ace musulmai suna qarasowa alhaji qarami ya nuna musu Amatu sukayi kanta suka kana hannuwanta biyu suka Fara janta umme da anty zarah suka bisu abaya suna roqonsu cikin tsananin kuka Amma tuni suka wuce da ita, Salman kuwa cikin palon yayi da sauri ko sallama baiyiba ya tsaya gabansu Andi ya kalli khalil dake sunkuye da Kai yace" Dan Allah Andi a sassauta Amatu a tsaya a fahimci zancen ta hanyar nutsuwa mace ce ita wlh rayuwarta zasu lalata idan aka Bari suka tafi da ita aka kulleta Dan Allah.... Da sauri Khalil ya juyo ya kalli Salman din cikin tsananin firgici bai tsaya gama sauraren Abinda yake fadaba ya turesa ya fice da gudu ko gabansa baya gani..... Ba Andi kadaiba hatta Modibbo Saida ya kidima da wannan alamarin, Yaransu da Basu taba dago Kai sun kallesuba idan suna musu Magana, Yaransu da Babu Abinda suka sani arayuwa bayan yimusu biyayya da bin umarninsu Koda baiyi musu daidaiba Amma ayau akan mace kamar abinda sukai shekaru suna Dora 'yayansu akai na neman rushewa, Yau Andi da kansa Yana zaune ake tafiya abarsa yana magana hakama shima wannan yau shi Andi da kansa yake kalla Yana cewa ba'ayi Abinda yakamata ba....da matsala,da matsala babba ma kuwa. Juyawa Salman yayi yabi bayan Khalil Yana fasa maganar da yayi niya cikin 'dacin Rai idanuwansa na sake sauyawa. Koda suka Isa bakin qofar zabeera tuni aka wuce da Amatun motar alhaji qarami nabin bayansu. Cikin tsananin tashin hankali Khalil ke qoqarin bin motar da gudu da qafafunsa Salman yayi saurin riqesa Amma ya fizge yabi motar da gudu Salman da umme na kiransa cikin tashin hankali umme ke cewa'' Salman dauko mota da sauri kabisa idan yayi gudu ciwonsa zai tashi Dan Allah kabisa kada kabari komai yasamu Khalil shikadai nakedashi. Ciki yakoma cikin sauri jikinsa har rawa yakeyi yafada mota yajawo da gudu yabi Bayan Khalil din. Koda ya cimmasa harya Fara galabaita numfashinsa yafara sarqewa. Da sauri ya tsayar da motar ya fito yakamasa yasaka motar ya zagayo ya shiga Yana qara Masa sanyin AC din motar Yana janyo tissue da yawa ya miqa Masa yana qoqarin daidaita muryarsa yace" Dr kada kayi Abinda zai kaika kwance sbd kana buqatar tsayuwa da qafafunka gurin fitarda Amatu cikin wannan matsalar. Kasa Magana Dr khalil din yayi Yana fitarda numfashi cikin yanayi na azaba ya lumshe idanuwansa dasukayi jajir ahankali yace" Muje gidansu kawu Ina buqatan daukesu daga gidan yanzu. Hanyar gidan suka kama Yana tuqi Yana kallon Khalil din daketa fama da numfashinsa Dan daidaitawa kada yabari yaci qarfinsa. Koda suka Isa Salman ne ya bude Masa motar yafito Yana sake qoqarin daidaita numfashinsa ya share zufansa suka nufi cikin gidan. Zaune kawu yake Yana sauraron radio iyami na zaune gefensa tana shafawa qafarta daya Jan lalle sai gasu sunshigo da qaramar sallama suka qaraso iyami na ganinsu ta ajiye lallen datake qoqarin sawa dayar qafar tana musu maraba da zuwa duk da dai yanayinsu yasata fargaba musamman sbd zufan da kowannensu yaketa sharewa bama kamar Dr daketa fama da numfashinsa Yana dannewa sbd kada agane halinda yake ciki. Kallo daya kawu yayi musu yasan ba lafiya ba Ya tashi zaune daga kishingiden dayake ya janyo radionsa kusa ya qure murya sbd kada aji zancen dazasuyi ya kalli khalil daya zauna gefensa yace" Likita lafiya naganku kamar 'yan saqon mutuwa??? Salmanu lafiya kuwa?? Numfashi Dr ya sauke Yana lumshe ido sbd azabar dayake ji ya kalli kawun cikin taushin murya yace" Kawu zanyi maka bayanin abindake faruwa Amma Dan Allah yanzu inason ku biyoni muje wani guri muyi maganar. Kallon juna kawu da iyami sukayi suka sake maido da kallonsu kansa cikin rawar murya iyami tace" Akwai Abinda yasamu Amatu ne? Meya faru ne kafara fada Mana mu musulmaine zamu dauki qaddara koma menene. Ajiyar zuciya salman ya sauke cikin sake bawa kansa nutsuwa yace" Ba Abinda kike tunani bane iyami Amma dai yanzu muna buqatar barin Nan ne tukuna. Kallon Dr khalil kawu yayi da kyau kafin ya miqe Yana cewa' Iyami sanyo hijabinki muje na yarda da Khalil fiyeda kowa arayuwata Dan haka koma menene Yana mahimmanci barin Nan din tun sun fada. Jiki mace iyami ta miqe ta wanke qafa dayar dakeda lalle ta fada daki ta sanyo hijabi hannuwanta na rawa sbd hakanan takejin tashin hankali tun kafin suji koma menene yake faruwa. Babu Wanda suka fadawa suka rufe dakunansu suka fice. A mota Dr khalil yakira babban yaronsa na asibiti Ibrahim ya sanar dashi Yana buqatar gidansa daya Gama be tare ba na kwana biyu, Cikin sauri yace angama likita. Anguwar can take nesa kusan hanyar wajen gari duk da akwai mutane da yawa a anguwar Amma kasancewar dukkaninsu sun Saba da anguwannin cikin gari sai sukaji anguwar wani iri. Gidane qarami me daki biyu sai bayi da kicin a qaramin tsakar gidan sai daki 'daya a hanyar shigowa. Zaune suke akan qatuwar tabarmar da Ibrahim din yakawo suka shimfida kowannensu shiru sunkasa qwaqqwaran motsi alokacinda Dr khalil yagama yimusu bayanin dukkanin Abinda yafaru. Wasu irin hawayen baqin ciki iyami keyi tana sauke kanta sbd tsananin kunyarsu Khalil din ahankali Tace" Bantaba tunanin son kudi da rashin hankalin Amatu yakai har haka ba, Yanzu wace irin masiface wannan ta dauko wadda bamusan ta Yaya zamu fuskancetaba. Shiru kawu yayi sbd nisa da yayi a tunani Yana Dora dukkanin laifin akansa sbd shine yafara daukar rayuwa da rashin mahimmanci har su Amatun suka dauka shiyasa tayi irin wannan alamarin me girman gaske Wanda ba mutuncin Zabeera ba kawai shi kansa idan zancen ya fita da wane Ido zai kalla mutane duk rashin kunyarsa kuwa. Ganin yakasa magan yasa Salman yashiga basa Magana Dan rage Masa nauyin zuciya Amma sam ko kadan yau bayajin komai bayan qunci. Da zasu tafi Dole yace sutafi dashi gurin neman ofishin da aka Kai Amatun. Yawon ofishin Yan sanda da civil defense suka Fara tun abin na aikin hkr har suka sake Shiga tashin hankali sbd duk inda sukaje ba anan aka kawota ba tuni suka fahimci Alamarin Babu sauqi acikinsa Babu Wanda baishiga cikin mummunan tashin hankali acikinsuba musamman kawu dayake ganin kamar kasheta za'ayi. Wasa Wasa har dare Babu labarin komai daganan suka nufi wata local government din dake kusa canma baa kaitaba. Dawowa sukayi suka ajiye kawun anan gidan Ibrahim gurin iyami suka nufi zabeera cikin sabon tashin hankali. Koda suka Isa Kai tsaye gurin Andi suka nufa inda suka tararda Modibbo acan anan suka zube qasa Khalil din na roqo da ban hakuri abisaga laifin Amma Sam Babu wani sauqi sbd atake Andi yabata umarnin ya rufe maganar case din daga ranar kada Wanda Yakuma tayarda zancen. Kasa komawa ciki Khalil yayi yafice daga zabeera din yaje ya siyo abinci da kayan buqata ya nufi gurinsu kawu. Zaune suke tsakar gidan zaune sunyi shiru Babu me Magana acikinsu kowanne da tunanin dayakeyi yashigo da sallama suka dago suka kallesa cikin sanyi da mutuwar jiki. Qarasowa yayi ya zaune gefen kawu tareda ajiye musu abincin Yana qaqalo qwarin gwiwa yadan Basu Magana kafin ya miqe ya fita yadawo motarsa ya zauna tareda rintse ido sai kawai hawaye suka gangaro Masa Yana dafe kansa yace" Allahumma ajirni fi musibati.. Zaune ya kwana cikin mota a qofar gidan kamar yanda Suma ciki su kawu Basu rintsiba iyami kwana tayi sallah. Gari na wayewa ciki yashigo anan yayi sallah dakin farko yafito yaje yasiyo musu abinci yakawo haka suka takurasa shima yadan ci kadan yafice zuwa zabeera. Duk yanda yaso ganin Andi ma abin ya gagara sbd hanyar sashensa anrufe ga Modibbo ma yaqi ganinsa sai alamarin yaqara daukar zafi Yana fitowa daga zabeera Salman yakirasa yake sanar dashi anshigarda qarar maganar sbd gashinan 'yan jaridu harsun buga zancen ya Basu koina alamarin yayi Muni sbd dukkanin inda amatu tayi aiki anbinciko kowa yabada shefar qwararriyar barauniya ce Dan haka yanaga suyi qoqarin sanin inda take ayi belinta kafin case din yashiga Court akwai matsala sbd itada umme ne zasu kwana ciki musamman idan sunan MD ZABEERA yafito amaganar Andi da Modibbo bazasu dauka da saukiba. Cikin tsananin tashin hankalin dayafi na farko Dr khalil yasake bazama yawon neman inda aka rufeta ga bangare daya su kawu sun matsa Saida ya maidasu gida saidai tunda suka dawo ake nunasu da Abinda Amatun tayi inda aketa cewa Ashe shiyasa khalil zabeera ya tsaya musu yaketa kashe musu kudi tarewa tayi a gidansu Yana muamala da ita. Duk masifa da fadan kawu yakoma ko zaman waje ya dainayi sbd maganganun hadda qari da cin zarafi sawa akeyi wainda suke cikin gida dayane kawai suke ganin mutuncinsu har lokacin suna Kuma tayasu baqin cikin wannan alamarin. Kwanaki kusan shida kenan Yana bulayi yakasa samunta, Duk iya inda alamarin yake ya girmama, Ko abinci baya iyaci sai ruwa idan ummensa ta takura Masa yasha, Ya rame cikin kwanki shidan yakoma kamar bashiba, Ya daina zuwa asibiti gabaki daya sai sakin kudi yakeyi koina ana bincika Masa kowace station da office din civil defense Amma Babu haske. Zaune yake gaban kujerar dake kallon insfector Garba acikin office dinsa Yana kallonsa da idanuwansa dasuka shige sbd damuwa ahankali yace" Zanbaka dubu dari biyar kamar yanda ka buqata cikin awa biyar zaka bincikamin dukkanin ofishinku na cikin gari da qauyuka. Murmushi insfector Garba yayi tareda kallon Dr khalil din yace" Mutum me mutunci da girma dai kamar wace irin qaddarace zata kaika batarda kudade masu yawa irin haka akan Amatu da kowa yasan dabadan kudinkaba wlh ko kallo bazaka ishetaba sbd Ina fada maka yarinyar terror ce tasan siririn iya sata...... Miqewa yayi Yana katsesa da cewa'' Mungama Magana Ina jiranka Nanda awa biyar din. Ficewa yayi ransa abace yabar station din Yana sakejin kamar zuciyarsa zata fashe babu me bude baki yafadi alkhairi akan Amatu duk station 'dinda yaje. ##Mamuh# 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 29_* Zaune yake gefen kawu Yana Shan furarda iyami ta matsa Masa yasha Kiran Insfector Garba yashigo wayarsa cikin sauri ya daga Yana aje ludayin hannunsa Su kawuma duk shi suka tsurawa ido suna jiran jin Abinda za'a fada Masa. Ahankali ya lumshe ido tareda sakin boyayyan numfashi jin Abinda garban yafada Masa ya katse wayar tareda kallon kawu dayayi zuru zuru cikin farin cikinsa daya kasa boyuwa yace" Tana central ta hanyar zaggen. Ajiyar zuciya kawu yasaki tareda Dan rufe Ido batareda yace komaiba hakama iyami numfashi ta sauke sbd harta yanke hukuncin yau dai zata fadawa usi yasan halinda ake ciki. Miqewa Dr khalil yayi Yana zura takalminsa yana cewa'' Kawu muje inshallah yau Amatu agida zata kwana. Zabura kawun yayi dama jira yake ace yatashi din. A mota Dr khalil kasa nutsuwa yayi wani irin yanayi yakeji na tsananin kewar Amatun Inama ace Amatu mallakinsa ce da tabbas ayau rungumeta zaiyi ajikinsa saiyaji dukkanin kewarta ta sakesa,Amma ko yanzu wannan alamarin daya faru bai barsa da zabin komaiba face na aurenta cikin qanqanin lokaci sbd samun Bata kariya daga kowanne irin barazana. Doguwar tafiya sukayi Mai Dan tsayi takaisu central din inda daqyar aka barsu suka Shiga sbd tsaro. Yana yin parking suka fito kawu na qarewa gurin kallo cikin tsananin tashin hankali ace anan Amatu take zaune akan qanqanin laifi irin wannan Wanda ko zagi da bannar suna da gorin da mutane suke musu aka barsu dashi sun hukuntu, Amma ace ankawota irin gurin Nan dasai masu laifin babbar kisar gilla ake kawowa sbd kawai tayi Abinda ba laifinta bane, Wani irin kunci da bacin Raine ya cika zuciyarsa yanajin ba'a taba yimusu rashin adalci ba tun takaicinsu irin wannan, Yarinya qarama mace budurwa za'a kawo irin gurin Nan?¿ Yanda yakejin tsananin bacin Rai wallahi daba mahaifiyar Khalil ce tasata a wannan halinba wlh dasai yayi shari'a da duk Wanda yake cikin zuriar zabeera sbd arziki ba hauka bane hakama talaka ba dabba bane. Shi kansa Dr khalil Jin yayi dukkanin gwiwoyinsa na sanyi zuciyarsa na cika da baqin ciki da bacin ran ganin anan Amatu take,anan aka kawota cikin masu manyan laifuka sbd kawai tayi qaramin laifinsa baifi ayisa agama cikin gidaba... Babu Wanda ya iya yiwa wani Magana acikinsu sbd halin tsananin baqin cikin dasuka Shiga na ganin irin cin zarafi da wulaqantawarda akayiwa Amatu. Koda suka Isa bakin office din commissioner Saida aka Shiga aka isarda zuwansu shima sbd Khalil din 'dan Zabeera ne da Babu wanda zai Bari ko hanyar office din su Isa. Daga cikin office din commissioner kuwa Bayan anzo ansanar Masa da zuwansu waya ya dauka ya dannawa alhaji qarami Kira Wanda akaci sa'a a lokacin Yana gurin Andi. Shiru alhaji qarami yayi bayan yagama sauraran Abinda commissioner ke fada Masa cikin mamaki yace" Ya akayi yayi saurin ganowa Bayan kabada tabbacin aqalla har maganar taje court bazai gano inda takeba.?? Yanzu dai Bari na sanarda Andi saina kiraka kafin ka gansu. Aje wayar yayi ya kalli Modibbo kafin ya kalli Andi cikin nutsuwa da girmamawa yace" Andi khalilu ne yasamu gano inda take Yana bakin office din commissioner ma yanzu haka. Dagowa yayi ya kalli alhaji qarami din da mamaki a fuskarsa kafin ya kalli Modibbo cikin bayyanarda mamakinsa yace" Me Khalilu yakeson komawa ne akan mace???? Shiru Modibbo yayi Yana sauke Kai cikin takaici da mamakin Khalil din. Sake bayyanarda mamaki da takaici Andi yayi Yana cewa'' Tabbas khalilu Yana buqatar hukuncindazai dawo dashi hankalinsa tunda yazabi wulaqanta hukuncina akan mace.. Dan gyara zama Modibbo yayi tareda gyaran murya cikin girmamawa yace" Allah ya huci ranka Andi Amma sai Inaga tunda yariga yayi nisa duk wani hukunci sake tsaurara abin zaiyi tunda Babu wani a zabeera daya taba take hukuncin Manya sai akansa gashi yanzu kowa yafara ankarewa da hakan da azo ayi Abinda zaisa agano bijiewa yayi yayi watsi da hukuncinka asamu masu Goya Masa baya abun yayi yawa. Shiru Andi yayi Yana sauraronsa cikin qoqarin son fahimtar zancensa Ya dago ya kalli alhaji qarami dakeson Magana shima yace" Kaikuma meye naka hasashen? Gyara zama yayi Yana tausasa murya yace" Inaga akashe maganar a idon duniya ma'ana a janye qarar amatsayin munduba maraicinta mun qyaleta idan yaso sai commissioner su saka kudin belin da Khalil din bazai iya biyaba idan yayi yayi Dole zai hkr kokuma ace za'a biya kudin belin Amma saiyayi alqawarin rabuwa da yarinyar Hakan shine mafita a yanayin da ake yanzu sbd Khalil idan baa janye qararba zai iya dagewa qarshe ya aikata Abinda zai saka zabeera kunya. Jinjina Kai Andi yayi Yana na'am da bayanin alhaji qaramin yace" A aikata hakan Amma kafin Nan ayau nakeson Modibbo dukkanin Abinda Khalil ya mallaka na zabeera a karbe. Kallonsa Modibbo yayi da sauri saikuma ya sauke Kai Yana jinjina hukuncin sbd kaf 'yayansa bama shikadaiba kusan duk yayan zabeera da arzikin Zabeera suke tinqaho MAHMOUD ZABEERA ne kawai Babu qwandalar zabeera acikin dukiyarsa da guminsa da wahalarsa yatara arzikinsa, Idan akace akwace komai na Khalil to motarsa ta hawa da kudaden account dinsane kawai zai tsira dasu Dan kuwa ko asibitinsa dayake tinqaho da ita MAHMOUD ne ya Gina Masa ita amatsayin tayasa murnar zama cikakken likita. Koda commissioner yabasu izinin shiga bai nuna musu komaiba suka gaisa kafin Khalil yafara Masa bayanin Abinda yakawosu Babu dogo musu yacewa Khalil din an janye qara belinta kawai zasuyi akan kudi naira miliyan daya sai kudin tarar bacin suna miliyan daya da rabi duba da yanayin gidan da akayiwa bacin sunan. What?????"""Khalil yafada cikin tsananin mamaki da yiwa commissioner din kallon rashin hankali yace" Beli ne wannan kokuwa hukuncin Rai da Raine wannan??? Murmushi commissioner yayi Yana gyara zama yace" Dr khalil zabeera zaka iya Kiran lawyer dinka zamu basa komai a rubuce sbd samun qarin fahimta. Kallon bakinsa kawu keyi cikin yanayin tsoron dayafi mamakinsa miliyan biyu kudin beli?gwarama su fito su fada musu bada itane bazasuyiba. Koda lawyer din Dr khalil ya iso aka miqa Masa takardun belin da aka bugo cikin qanqanin lokaci ya karanta yasake karantawa zuciyarsa na tafasa ko ba'a fada yasan shirine akayi Dan quntata Masa shida su Amatun, Koma menene akayi Dan a cimma bazai taba rabuwa da Amatu ba, Idan anyi ne Dan aga gazawarsa tabbas bazai taba gazawaba zaiyi komai iya iyawarsa zaikuma qwatar Mata mutuncinta da yancinta. Dagowa yayi ya kalli kawu da idanuwansa sukai jajir sbd tashin hankali saiyaji zuciyarsa ta sake karyewa ya waiwayo ya kalli commissioner cikin yanayin na nuna rashin gazawa yace" Ahada takardun belin su zama ready zuwa gobe zankawo kudin. Kallonsa sukayi da sauri duk su duka commissioner na boye mamakinsa akan Khalil din yace" Shikenan Dr khalil zabeera muna jiranka goben. Miqewa yayi ya fice kawu da Barr Bashir na bayansa kowannensu cikin damuwa Yana Isa bakin mota ya tsaya ya juyo ya kalli Barr Bashir da idanuwansa dasukai jajir yabude busashen bakinsa yace" Barr zankiraka gobe muhadu anan abasu kudin inshallah. Kallonsa Barr yayi cikin kulawa da jimami Yana cewa'' Dr khalil kana ganin zamu karbi belin Nan ahaka? Inaga muje can zabeera aroqi maganar tarar ajanye Mana ita zaifi.... Girgiza Kai yayi Yana qoqarin boye rauninsa yace" Ba buqatar hakan zanhada kudin zuwa goben Inshallah. Shikenan tunda zaka iya biya ba damuwa Allah yakaimu goben. Suna Shiga mota yayi shiru cikin tsananin damuwa da tashin hankalin ta inda zai Fara hada kudin sbd dukkanin kudin account dinsa ya rabesu gurin case dinnan cikin kwanaki kadan Duka duka abindake account dinsa baifi dubu dari bakwaiba Kuma gidan haya yayi niyar kamawa dasu ya ajiye Amatun. Bayan kudin account dinsa da motarsa baida wata babbar kadara sai tsadaddun agogunansa da wayoyinsa, Asibitin dayake tinqaho da ita bata cikin lissafi sbd tamkar alamar qaunarssuce me qarfi dake tsakaninsa da 'dan uwansa. Kallonsa kawu yayi cikin tsananin damuwa da sarewa yace" Khalilu kada ka takura kanka da hada wainnan kudaden daba haduwa zasuyiba, Qaddarace wannan me girma ta samemu wadda Allah zai fitar damu inshallah., Zamuje muyita addua Allah yabamu ikon cinye jarabawa sbd koba komai munqara bambamce halaye irin na wasu masu arzikin Wanda bayan suna Babu Abinda suka damu dashi, Farin cikin yayansu da walwalarsu bai damesuba kamar yanda sunansu da girman kansu ya damesu. Ahankali yaja motar suka bar gurin suka kamo hanyar gida har lokacin bai iya cewa ko qala ba sbd nisa da yayi a tunani. Koda suka Isa ajiye kawu yayi ya wuce zuwa zabeera. Parking yayi daidai sashen Modibbo yafito ya nufi ciki jikinsa da zuciyarsa amatuqar sanyaye. Sallama yayi palon yashiga cikin sa'a Modibbon na zaune shikadai Yana kallon labarai Koda yaga khalil din Saida yaji tausayinsa Amma bai nunaba sbd ya dauke Kai Yana cigaba da kallon labaransa. Gabansa ya zube tareda sunkuyar dakai wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanuwansa akaro na farko daya nuna gazawa cikin wani irin sauti Mai tsananin sanyi yace" Modibbo Ina roqon yafiyarku akan dukkanin Abinda yafaru Dan Allah ku sassautawa Amatu wlh batada laifi akan hakan kuskure ne da rashin sanin ciwon Kai wlh batayi Dan wata manufar Bata suna ko wani Abu ba dabam tayine kawai sbd kudi Wanda tsananin rayuwa yakaita ga hakan., Modibbo Dan Allah Ina roqon gafara da yafiyarku Dan Allah ku duba maraicinta kada ku tsaurara Mata. Juyowa Modibbo yayi ya kallesa sosai ganin yanda babban namiji jajirtacce kamarsa ke kuka ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa" Khalilu zancenka ba'a hannuna yakeba Amma amtsayina na mahaifinka zanfada maka Abu daya, Kada kayi Abinda zai kawo maka matsalarda bazaka iya tsayawa kaga wucewartaba, Idan kanason yarinyar Nan tsakani da Allah Dan tallafawa maraicinta to tabbas na amince maka ka aureta sbd aurenta ne kawai zaisa Andi ya iya sassautowa tunda tariga tazama Zabeera Amma idan kasan tsakani da Allah yarinyar Nan batada nasaba to Ina baka shawara kayi gaggawar cireta daga rayuwarka shine kawai sauqi da mafita agareka.. Da jajayen idanuwansa ya dago ya kalli Modibbon Yana nazartar zancensa wani irin sanyin sassauci na shiga zuciyarsa sbd ya fahimci zancen mahaifin nasa take sabon qwarin gwiwa yasake shigarsa ya sunkuyar dakai cikin sanyi yace" Nagode Modibbo Allah yaqara tsawon Rai. Yana fitowa sashen ummensa ya nufa inda ya tararda ita zaune tayi tagumi kamar koyaushe cikin kwanakin tana ganinsa tayi saurin miqewa ya hanata ta hanyar mayarda ita zaune yana girgiza Mata Kai murya a mace yace" Umme zanbar zabeera...... A firgice ta kallesa idonta na cikowa da hawaye zata fashe da kuka yace" No umme karki manta kinmin alqawarin bazakiyi kukaba Kuma kinyi alqawarin bani support adukkanin Abinda Zan yanke., Umme albarkanki nake nema a rayuwar dazanyi wajen zabeera dan Allah umme kimin alqawarin bazaki saka kanki cikin damuwar dazata cutatar dakeba. Kasa riqe kukanta tayi ta fashe dashi tana cewa'' Khalil Dan Allah kada kabar zabeera kabarni katafi Dani Nima Wlh bazan iya zama baka nanba, Katafi Dani duk inda zakaje zanzauna acikinku, Zan zauna taredaku zanyi renon 'yayan dazaku haifa........ Kasa hkr yayi ya rungumeta Yana girgiza Mata Kai Yana cewa'' Umme Zaki zauna anan gidan aurenki sai mutuwace kawai zata fiddaki zabeera. Aa khalil zanbika Dan Allah kada ka tafi kabarni. Ganin yanda ta daga hankalinta yasashi zamewa da sauri ya fice Yana danne zuciyarsa dake neman fashewa yayi hanyar sashensa. Kayansa ya diba a akwati tareda kwashe agogunansa da takalmansa masu tsada sosai da duk abubuwan dazai buqata ya saka cikin mota tareda dukkanin takardunsa yafito yaja motarsa yabar zabeera. Daga zabeera gidan Ibrahim yaje yafara ajiye kayansa acikin dakin farkon Shiga ya rufe dakin da mukulli ya fito yarufe gidan ya wuce. Tareda Ibrahim din sukaje gurin masu Saida agogo akayiwa agogunansa kudi kaf aka shiye suka hada kusan dubu dari uku daganan gurin Wanda zai siye motarsa suka nufa aka Fara cinikin saidai abin son Rai yayiwa mutane yawa Dan siyan wulaqanci sukaiwa motar har kusan mutum shida sukaiwa motar siyan wulaqanci qarshe Dole ya saidata miliyan daya da dubu dari suka karba ya hada hadda kudin account dinsa suka tashi 2.6. Mashin yahau Abinda baitaba hawaba a rayuwarsa ya nufi gidansu kawu anan yafadawa kawu ya hada kudin daga iyami har kawu basusan lokacinda suka fashe da kuka ba. Murmushi me ciwo kawai yasaki batareda yace komaiba anan yayi sallar ishai iyami tasashin tuwon Dole kafin yatashi yatafi. Mashin yasake hawa yakoma gidan Ibrahim Yana Shiga Allah ya taimakesa ana kawo nepa Nan ya tube yayi wanka da ruwan rijiyar gidan da Ibrahim yacika Masa durum da kansa masu shegen tsananin sanyi Wanda Saida suka saka numfashinsa kusan daukewa daya watsasu. Boxer da singlet kawai yasaka yadawo ya kwanta Kan sabuwar katifar da Ibrahim din yasiyo yau yakawo Masa. Kiran salman ne keta shigowa wayarsa Yana qin dagawa sbd duk kwanakin ya tashe duk banyarda salaman zaishigo cikin Al'amarin sbd bazaiso laifin ko wani Abu yasamesaba kodan yanda Amatu ta daukesa kamar usinta. Kiran MD ZABEERA ne yashigo wayar ya qurawa wayar Ido tsawon sakanni kafin ya dauka Yana boye damuwarsa Nan suka hau Maganar shi cikin sanyi MAHMOUD Kuma cikin nutsuwa da miskilanci. Koda asuba tayi daqyar ya iya dafawa ya tashi zaune sbd tsananin sanyin daya Gama shigewa ya Kama dukkanin qasusuwansa. Daqyar yayi sallah ya jingina da bango Yana makure jikinsa guri daya sbd kaf gidan gaba daya koina sanyi yake fitarwa sbd gaf suke kusada ruwa. Daqyar yaga qarfe Tara na safe tayi ya miqe yasake zuwa bayi ya watso ruwan sanyin yafito jikinsa na Dan rawa yashigo daki ya shirya cikin qananan kaya masu Dan kauri ya bar gidan sbd Jin kamar zai iya suma da ciwonsa dake gaf da tashi. A gidansu kawu yaci biredi da kunun tsamiya tareda waina da iyami tasiyo Masa me kyau ta shinkafa. Kobai fadaba sungama gano halinda yake ciki sbd kada su qara Masa damuwa sukaqi yimasa maganar sai tattalinsa dasukeyi. Qarfe goma da rabi a central tayi musu shida kawu suka zauna zaman jira har qarfe goma sha biyu commissioner bai buqaci ganinsuba sai daya da rabi Bayan anyi sallah anfito tukuna aka kirasu suka Shiga. Barr Bashir ne yacire kudin beli da Tara ya bayar akayi rubuce rubucen daza'ayi aka gama kafin akace afiddo Amatun. Lokacinda aka kawota suna ganinta kowannensu idanuwansa suka ciko da hawayen baqin cikin ganin halinda take ciki Amma ita ganinsu yasata qaqalo qarfin hali tana danne azabar cizon sauri da galabaituwar yunwa da dau'dar datake ciki Danma tunda tazo koda Wasa ba'a taba dukantaba Wanda umarnin Andi ne kada a daketa ko so daya. Babu Wanda ya iya mgn acikinsu aka Bata gyalanta da takalmanta suka fito tana tafiya daqyar a galabaice. Suna fitowa titi taga suna qoqarin taron adaidaita ta kalli Dr khalil din da mamaki Kan fuskarta saidai batayi maganaba suka tare adaidaita biyu ita dashi suka shiga daya kawu yashiga daya. Ahankali ya juyo ya kalleta cikin tsananin kulawa da damuwa akan fuskarsa yace" Are you ok? Kallonsa takeyi tana mamakin sauyawar dayayi Yayi duhu tayi Rama hakama kamar Wanda baida lafiya sai Nishi Nishi yakeyi kamar Wanda yayi aikin wahala. Kai ta daga Masa ahankali tana lumshe ido a wahalce. Koda suka iso gida tuni mutanen gidan suka rude da murna da yiwa Allah godiya take aka hada ruwan wanka masu zafi aka Kai Mata Maman junior hadda tayata wanka kamar me haihuwa haka aka gasata tasamu 'dan qarfin jiki aka Bata abinci taci tareda magungunan da Dr Khalil din yasiyo Mata ta kwanta take baccin wahala ya dauketa. Da daddare kafin ya wuce Bayan yaci tuwon iyami cikin nutsuwa ya zayyanewa kawu duk halinda yake ciki yanxu tareda gabatarda buqatarsa na auren Amatun Kawu ya sauke numfashi me sanyi yace" Khalilu ko bakayi mgn ba nayi niyyar aura maka Amatu kobabu danginka ko daya sbd aduniya Babu Wanda ya cancanta yazama Dole yazama mijin Amatu idan bakaiba Dan haka wlh khalilu nabaka Amatu amatsayin Mata ka shirya nida kaina zanje masallacin juma'a nayi sanarwa ranar juma'ar Nan Inshallah za'a daura muku aure. ##Mamuh# 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 30_* Wani irin sanyin farin cikine ya Shiga zuciyarsa Wanda ya manta rabonsa dashi ya kalli kawun cikin girmamawa yace" Nagode sosai kawu Allah yaqara girma da Nisan kwana. Amin Amin" yace Yana cigaba da yimasa nasiha akan hakuri da rayuwa komai lokacine dashi wata Rana komai zai wuce. Bai jira sake ganin Amatunba yanayin sallar ishai a masallaci taredasu kawu yayi Masa Saida safe ya wuce. Ahanya ya tsaya ya siya cardigan me kauri da sabon bargo me laushi kafin ya wuce gida. Sbd sanyi hatta qafaguwansa da hannuwansa Saida ya sakawa socks bayan yasaka rigar sanyin ya dunqule cikin bargo Amma har lokacin yanajin sanyi na shigarsa hakanan ya daure har wahalallen barci ya daukesa. Washe gari da safe ba laifi da kuzarinta ta tashi saidai kawai sauyi sosai data gani daga iyami har kawu Wanda ya tabbatar Mata da fushi sukeyi sosai da ita sai taji hankalinta ya tashi duk yanda taso Basu hakuri ko fuska taqi samu Saida Dr khalil yashigo ne taga sakewar fuskarsu ta kallesa da Ido ta nuna Masa fushi sukeyi da ita yasakar Mata kyakkyawan murmushi Yana nuna Mata Babu ruwansa Suna Nan zaune saiga salman zabeera yazo Yana ganin Amatu cikin tsananin farin ciki yaqaraso Nan aka hau sabuwar fira inda anan ne takejin dukkanin Abinda yafaru hadda komai da Khalil din ya rasa bayan aikinsa da asibitinsa baida komai yanxu. Jitayi sabuwar soyayyarsa tasake shigarta hartanajin ko bayada komai zata auresa ta zauna dashi Kuma alqawarine ta dauka saita shiryasa da familynsa ta maidasa cikinsu. Koda maganar aurensu sati me zuwa ta bayyana tuni kowa yahau murna Nan aka Fara shirye shirye musamman iyami data bada himma gurin gyaran Amatun ga umminsa ma kusan kullum saitazo gurin duba Amatun taso taimakawa sosai Amma Khalil ya nuna kada tayi Masa komai zai iya iya qarfinsa shiyasa Dole tabari sai itama ta maida hankali gurin gyaran Amatun sbd 'danta yaji Dadi. Sauran kudaden dasuka rage Masa yaso Kama wani gidan hayar dasu Amma duk gidajen babu Wanda zasu iya zama saiya aje kudin da niyar bayan daura auren Koda da sati biyune zaiyi qoqarin hada kudaden dazasu Samar musu gida me Dan kyau. A bangare daya sanyi yayiwa jijiyoyinsa da qashinsa muguwar shiga a 'yan kwanakin sbd yanxu takai kowane dare Baya iya bacci daurewa kawai yakeyi cikin mutane baya nunawa Amma ciwonsa yatashi matuqa yanajin yanda lungs dinsa sukai mugun laushi baya iya Jan numfashi yanda ya kamata duk iya qiqarinsa yanayi Dan ganin ba'a fahimci halinda yake cikiba. _GERMANY_ Kallon hoton katin Daurin auren da Khalil yaturo masa yakumayi da fararen idanuwansa dasukai wani irin laushi lokaci daya ya lumshe ido Yana sake kallon hoton katin ya ajiye ahankali tareda miqewa ya nufi gaban qaton window din dakinsa dake kallon swimming pool din gidan ya zuba hannuwansa cikin aljihun three quarter din dake jikinsa Yana qurawa waje Ido zuciyarsa na sanyi. Tunani zuciyarsa keyi Amma ya yakuce hakan Yana lumshe ido Tabbas zai halarta sbd ranar farin cikin Dan uwansa ce. Juyowa yayi ahankali tareda dawowa yadauki wayarsa daya kashe sbd rashin son damuwa ya dannawa PA dinsa Kira Yana dauka Kai tsaye cikin muryarsa me sautin girma yace" Ka shirya Mana komawa gida jibi akwai Daurin auren dazan halarta. Done sir. Kashe wayar yayi ya ajiye Yana sake karanta sunan dake rubuce 6aro 6aro akan hoton katin KHALIL DAHEER ZABEERA da AMATULLAH K SALEH. sake dauke Kai yayi yana lumshe ido tareda sauke ajiyar zuciya ya juya yabar gaban labtop din. _NIGERIA_ da kanta ta shirya tsaf Babu Wanda yasani ta fito suka fita da salman zuwa zabeera mansion. A sashen Andi sukai parking tafito ahankali tana kallon koina komai na dawo Mata sabo tana tuno yanda tabar anty zarah dinta cikin kuka da damuwa take taji idanuwanta sun ciko da hawaye Bata damu da tsaidaduba Saida suka gangaro tasaka hannu ta gogesu ta nufi qofar shiga palon Andi din ta tura tashiga da sallama dama Salman ya tabbatar Mata da a irin wannan lokacin Modibbo na gurin Andi. Modibbo ne yafara gabeta ya zuba Mata idanuwansa masu kwarjini da Khalil da MD suka dauko ta qaraso ahankali ta zube qasa gabansu sai alokacin Andi ya dago ya lura da waye. Cikin tsananin biyayya da nuna damuwarta a fili tace" Ina miqo gaisuwata ga Andi da Modibbo tareda neman afuwar babban kuskuren Dana aikata Wanda ya shafi 'da mafi biyayya da gujewa zuciyarku. Kallon mamakin rashin tsoronta da gwarin gwiwarta suke Mata su duka din ta sauke Kai cikin nutsuwa da girmamawa tace" Wallahi tallahi Dr khalil zabeera baitaba aikata laifin da kuke tunanin ya aikataba koma wane irine, Taimako ya hadani da Dr khalil Kuma shine yasa yayita ajiyata acikin zabeera, Ni marainiya ce kuma Yar bola kamar yanda kowa ke fada Amma Kuma banice nakai kaina bolarba harnayi rayuwa acikinta na tashi acikin Rayuwa da jarabawar rayuwace takaini wadda itace tabaku girma da matsayi tareda sunan dakuke ganin yafi Dan Adam daraja, Nayi rayuwar maraici da tozarci irinku masu arziki Baku dubemu ba kuka taimaka Mana saidai maigadin makarantane Wanda yake karban dubu bakwai a wata ya taimakemu, Nayi rayuwar almajiranci Ina matsayin mace sbd kawai na rayu, Nayi rayuwar wahala da qasqanci duk Dan sbd na rayu, Munkwana da yunwa muntashi acikinta, Lokacinda yaranku da jikokinku suke karatu mu bara mukeyi alokacin sbd muci, Da kaina na koyi yanda zanyi yaqi da maza na qwaci kaina daga sharrinsu tun inada qananun shekaru Shin nayi dukkanin wannan ne sbd nazama karuwa a rayuwa???? Nice na zabarwa kaina yin sata amaimakon karuwanci Dan kawai na rayu sbd sata Zan iya rokon me Abu ya yafemun wata Rana Amma Zina fa??? Dr khalil zabeera shine mutum me arziki na farko daya shigo rayuwarmu, Yakawo Mana walwala da farin ciki a zukatanmu, Talakawan bangarenmu wainda Dr khalil zabeera yakawo farin ciki akan fuskokinmu da rayuwarmu basa qirguwa, Meyasa mutum me zuciya irinta Khalil maimakon ayi alfahari dashi za'ayi fushi dashi? Shin Kuna tunanin ladar aikin Khalil kawai Bata Isa takawo qarin haske da walwala acikin zabeera ba?? 'yayan da Allah yabaku dukkaninsu amanace agurinku Allah zaitambayeku alaqarku dasu idan da akwai cutatarwa, 'yayanku ne Amma Kuna gudanar da rayuwarsu kamarta dabbobinku kokuma bayinku, Wasunsu da dama a tauye suke basa rayuwar farin ciki, Zaman auren Dole da qunci sukeyi duk sbd bin umarni da qaidojinku, Shin haramun ne neman farin ciki a wani gurin kokuwa musulunci ne ya hana? Shi mutunci da girma Allah ne yake badawa Kuma shiya Baku Idan Allah yabaku suna duk Abinda wani Dan Adam zaiyi bazai Bata hakanba Koda kuwa me zaiyi., Nazo zabeera ne sbd son kudina dakuma rashin sanin ciwon kaina Amma sbd tseratar da mutuncinku yasa ya karbi laifi da bacin sunan da baisan lokacinda aka hadosaba, Wallahi niba karuwa bace, Bantaba aikata zinaba, Bansan ta Yaya ake aikataba, Aikin gidajen abinci danayi nayine Dan neman halak Dina Wanda haryanxu Ina alfahari da hakan sbd Allah bai bani matacciyar zuciya ba. Dagowa tayi da idanuwanta dasukai jajir ta ajiye katin Daurin aurensu cikin sanyin jiki tace" Babban burinsa shine aurena yakawoni gabanku Dan neman yafiyarku da gafararku nikuma babban burin danakeson cika masa shine bashi kaina amatsayin mata dakuma sasantawarsa daku iyayensa, Hawaye masu tsananin zafi suka gangaro Mata cikin daci da damuwa tace" Dan Allah Ina roqan gafarar ku yafe Masa kodan kasancewarsa 'da me biyayya da gudun zuciyarku a baya, Ku basa farin cikin dabai taba samu daga garekuba tun haihuwarsa.... Umme dake bayanta tuntuni a tsaye batasan lokacinda tafashe da kukaba tana sake Jin qaunar Amatu ta qaraso gabansu Modibbon ta zube itama cikin kuka tace" Andi Dan Allah ku yafewa khalil kubarsa ya aureta wlh dukkaninsu ba laifinsu bane nice me laifin sbd nice na kawo Amatu zabeera da wata manufarda rashin wadataccen ilimina yabani. Zayyane musu komai tayi sukai tsit Babu me motsi musamman Andi dashi maganganunsa Amatu ne sukafi shigarsa, Shin dukkanin yawancin 'yayansu rayuwar kunci sukeyi sbd gudun zuciyarsu??? Tabbas tunda yake tsawon rayuwarsa Babu Wanda yataba kallonsa yafada Masa haqiqanin gaskia sai yau yaringa qanqanuwa daya Isa haihuwar ubanta koma kakanta ta kallesa tafada Masa quncin dayake saka 'yaya da jikokinsa shekaru wa shekaru. Modibbo Kam dama tuni Amatu ta Dade dashiga ransa bazai iya nunawa bane sbd bacin ran Andi Amma tuni yajima da sanin yarinyace me fadar gskia batareda tsoro ko shakkaba. Miqewa tayi ahankali ta juya ta fice tana share hawayenta daketa fita da gudu ta fada mota suka bar zabeera. Kwance yake yau kwana biyu kenan ciwonsa nacinsa harya Fara cin qarfinsa ko fita daqyar yakeyi sai dare cikin duhu yake zuwa gidansu kawu sbd kada agano halinda yake ciki magungunsa yasiyo dasu inhaler Amma Sam kamar basa Masa aiki sbd kullum sanyi sake shigarsa yakeyi a gidan. Yau laraba saura kwana daya Daurin aurensu Amma abin yaci qarfinsa tuni aka gano baida lafiya sosai sbd Koda Ibrahim yaje gidan tuni ya Dade da fita hayyacinsa hankali tashe ya kwashesa sai asibiti. A asibiti Koda aka karbesa numfashinsa yayi nisa sosai cikin gaggawa akai emergency dashi ana qoqarin saka Masa oxygen. Su kawu Ibrahim din yafara fadawa kafin yakira salman yafada Masa cikin qanqanin lokaci duk suka halarto asibitin hankalinsu duk atashe. Kallo daya Amatu tayi Masa hankalinta yayi mummunan tashi sbd lokaci daya sanyi ya kumburasa Numfashinsa Sam kwata kwata Babu saidai oxygen dinne ke janyo Masa ahankali idanuwansa a rufe fuskarsa tayi haske hakama bakinsa yayi haske sosai ya bushe. Hawaye ne suka kufce Mata ta saki siririn kuka ahankali tana cewa'' Meyasa zaka boye bakada lafiya harsaida abin yayi tsanani haka? Zaman rashin hankalin kurame sukeyi a asibitin daga ita har kawu da iyami duk suna asibitin da salman sai ummensa dasu Nuratu dasuka iso kowa cikin tashin hankali bama kamar umme datasha kuka idanuwanta sukai jajir. Sunanan zaune har magriba saiga anty zarah da MD ZABEERA sun iso tana ganin anty zarah suka tsaya kallon juna cikin tsananin kewa da qaunar juna tazo da gudu tafada jikinta tana fashewa da sabon kukan datake ta riqewa tuntuni na ganin har lokacin sai Abinda yayi gaba ajikin nasa. MD ne dakansa yaje yayi mgn da likitocin suka sake yimasa bayanin sanyine yayi mugun shigarsa Wanda yasa gaba daya jijiyoyin huhun Jan numfashinsa sun daskare ya tayarda ciwonsa gaba daya harya basa attack Sam numfashinsa yaqi dawowa ta oxygen dinma alamarin sai ahankali. Tsorone yashigesa akaro na farko rayuwarsa Dawowa yayi dakinda Khalil din yake ya tsaya akansa Yana kallonsa yaji zuciyarsa na neman karyewa da sauri ya juya fice. Anan ta kwana asibitin itada ummensa da iyami har gari ya waye be farkaba zuwa lokacin Kam ko mgn basa iyayi da junansu sbd damuwa zazzaune kawai suke suna rarraba idanuwansu dasuka kode sukai zuru zuru. Da yamma tayo alwalar magriba tazo gefensa ta tayarda sallah tayi tagama tana cikin addua taga kamar ya motsa hannunsa kadan ko shafa adduar batayiba ta zabura ta miqe sai taga idanuwansa a bude sunyi fari tas dasu cikin tsananin farin ciki ta fada kansa ta rungumesa tana sakin hawayen farin ciki. Umme data fito toilet din dakin tana ganin haka tayo kansu da gudu har sanyin ruwan qafarta na zameta itama fadawa tayi kansa ta rungumesa Ya lumshe ido ganinsu su biyun ba qaramin farin ciki yasashi ba yasake lumshe ido cikin azabar ciwo yanason motsawa Amma sun dannesa MD daya shigo yayi gyaran murya itace tafara juyowa sukai Ido biyu tayi saurin dauke Kai tana maido da kallonta Kan Khalil cikin tsananin farin ciki tace" Dr Dan Allah karka sake rufe idonka. Qarasowa yayi ahankali Yana kallon fuskar Khalil din yau farin cikinsa dai Kam ya bayyana Shima Khalil din shi yake kallo fuskarsa nason bayyana farin cikin ganinsa Amma azabar ciwo ya hana. Cikin sautin murya me taushi yace" Kun sakar Masa nauyi da yawa inaga. Da sauri dukkaninsu suka dagasa kafin suyi wata Magana saiga Andi da Modibbo tareda alhaji qarami sun shigo salman yakawosu take umme da amatun suka saki hawayen farin ciki suna kallon fuskar Khalil din da idanuwansa suka nuna zallar farin ciki ganinsa hawaye masu dumi suka gangaro ta gefen idonsa Andi da kansa ya matso gefen gadon ya dafa kansa yasaka tissue ya share Masa Yana jinjina Masa Kai. Salman da MD ne suka tayar dashi zaune amatu ta hado ruwan zafi da towel suka gyara Masa jikinsa tareda Sanya masa shirt Mara nauyi aka basa tea yasha kadan har lokacin da oxygen a hancinsa Kuma har lokacin bai iya mgn sbd bai iya jan dogon numfashi. Kafin dare yadan warware ba laifi sbd Yana Dan magana ahankali tareda zuwa toilet idan ankamasa. Da kawu yaso daga Daurin auren a gobe Amma Andi yace abarshi kada a daga tunda anriga anyi sanarwa. Da daddaren ranar duk yanda ta nace hanata kwana asibitin akayi akace Takoma gida Salman zai kwana dashi tunda washe garine Daurin auren Dole ta koma bayan tayi Masa bankwana yabiya da Ido cikin kewarta tun Bata wuce dinba. A gida duk wani hidimar al'ada sunyi abinsu hatta lalle anyi Mata a blue fox anty zarah takaita akayo Mata tareda gyaran Kai dana jiki Daurin auren kawai suke jira a goben akaita zabeera. Tunda ta kwanta mafarkin Dr kawai takeyi sai kawai ta tashi tayo alwala tazo ta tayarda sallar nafila. Tunda gari ya waye takejinta batada qarfin jiki sbd barin gida dazatayi., Qarfe daya da rabi dubban JAMA'A suka shaida Daurin auren KHALIL ZABEERA da AMATULLAH SALEH Wanda ya bayarda tarihi me girma sbd itace mace ta farko da aka auro daga waje. A asibiti dagashi sai MD ZABEERA ne Wanda yace zai zauna dashi tunda kowa na gurin Daurin auren. Bacci yakeyi sbd alluran da akai Masa bada jimawaba sbd jikin daya dawo Masa sosai., Bayan Daurin auren JAMA'A duk asibiti sukaita zuwa dubasa sai yamma lilis ya farka cikin ikon Allah saiya tashi da qarfin jiki haryana iya Magana tana Kuma fita sosai. Wanka MD ya taimaka Masa yayi ya sanya farar jallabiyar datai Masa kyau matuqa yayi sallolin da ake binsa yazauna kenan saigasu umme da Nuratu wadda idanuwanta sukai luhu luhu sbd kukan data kwana tanayi. Abinci ta zuba Masa ta zauna gefensa ta miqa Masa kanta a sunkuye batareda ta kallesaba. Karba yayi tareda sauke numfashi cikin sanyin muryarsa dake fita ahankali yace" Nuratu inshallah zaki samu Wanda zai wadata rayuwarki da farin cikin Dana kasa baki. Kallonsa tayi idanuwanta na cikowa da hawaye murya na rawa tace" Meyasa kakeson Amatu??? Lumshe idanuwansa dasuke a 'dan galabaice ahankali yace" Allah ne yasamin sonta fiyeda komai Kuma Ina fatar zaki qaunaceta kodan sbd ni. Murmushi me ciwo tasaki hawayenta na sake gudu tace" Zangwada. Murmushi shima ya sakar Mata tareda juyowa ya kalli MD dake amfani da wayarsa yace" Kaifa MAHMOUD??? Zaka gwada qaunar matata ko Dan sbd ni? Juyowa yayi ya zuba Masa idanuwansa batareda yace qala ba. Abinci umme ta matsa Masa ahankali yaci kadan Tasha tea me zafi har zufa yadan karyo Masa aka kunna Masa AC kadan. Ganin yanayin jikin nasa dakuma shi kansa daya nema sallama yasa suka sallamesa bayan sallar magriba zuwa ishai Koda suka Isa zabeera daidai isowar motacin dasuka je dauko amarya Amatu. A gurin Andi aka kaisu duk su duka yayi musu nasiha sosai kafin aka wuce da ita gurin zamanta wato sashen Khalil din Wanda aka sauyawa komai sabo. Iyami da kanta taredasu maman junior suka kawota har cikin dakinta suna jinjina arzikin duniya irin na familyn ZABEERA kafin aka maidasu gida. Ahankali yashigo dakin datake zaune zugum bakin gado tana tunanin da batamasan tanayiba... Ji tayi anzauna kusada ita ahankali ta juyo sukai Ido biyu dashi gabanta taji yafafi ahankali ta dauke Kai zata sunkuyar ya riqo fuskarta ahankali tareda girgiza Mata Kai ya rungumeta cikin jikinsa ahankali tareda sauke ajiyar zuciya batareda yace komaiba. Sunjima ahaka kafin ya saketa tareda cewa ta tashi suyi nafila. Tashi tayi Babu musu sukaje toilet din tare sukayo alwala suka fito yakama hannunta suka nufi dakinsa. Bayan sungama sallar hannunta ya riqo cikin nasa ahankali yace" Zakici abinci ko wani Abu? Akwai abinci da umme da antynki suka kawo gashi can a dining. Dagowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta girgiza kai. Murmushi yasake ganin yau itama tazama kurma kamarsa tunda yafara ciwon baya iya doguwar Magana. Miqewa yayi tareda tayarda ita tsaye Yana zame Mata mayafinta kyakkyawar fuskarta ta bayyana da kyau cikin qarfin hali yace" Alhamdulillah. Sunkuyar dakai tayi tana qaqalo murmushi ya janyota ya sanya cikin jikinsa ya rungumeta Yana lalubar zib din goguwar rigar Julius Holland din dake jikinta me laushi ya bude rigar ta Fadi qasa tabarta daga ita sai farar bra din dake jikinta da farin under. Saurin rintse ido tayi zata durqushe ya tareda tareda rungumeta cikin jikinsa baida qarfin jiki sbd ciwo Amma hakanan ya cirata tana qanqamesa ya kwantar da ita Kan lafiyayyan gadonsa tareda rage hasken wutar dakin ya zare jallabiyarsa ya hau gadon ahankali tareda jawota jikinsa Yana kallon fuskarta ya Dora bakinsa akan nata tareda 6alle hook din bra dinta Yana cillowa qasa. Qarfe ukun dare taringa Jin wani irin Nishi sama sama cikin kunnuwanta ta bude idanuwanta ahankali tana kallon inda take saita tashi zaune da sauri tana kallon gefenta a firgice tagansa numfashinsa na qoqarin daukewa cikin tsananin firgici ta diro gadon ta zagayo gabansa tana Kiran sunansa cikin tashin hankali Amma Sam tayi nisa a kidime ta janyo jallabiyarsa ta zura sbd itakadaice zata shigeta alokacin sbd firgici Sam Bata damu da tsakiyar darene ba ta fito da gudu tayi hanyar sashensu anty zarah dake kusa da nasu a kidime tahau buga musu kofa tana Kiran sunan anty zarah da qarfi. MAHMOUD dake zaune daram acikin Daren yakasa ko rintsawa sbd tsananin ciwon Kai yafara jiyo bugun qofar ya sauko daidai itama zarah tafito daga dakinta Dan taji bugun qofar itama. Shine yafara cewa" Waye??? ta jikin qofar Cikin sauri da tashin hankali tace" Nice Amatu Dan Allah kuzo Dr ne...... Tun kafin ta qarasa ya bude qofar yanayin datake ciki yasashi Kama hanyar sashen nasu batareda tagama fadar Abinda zata fada din ba. Koda suka iso tuni Dr khalil zabeera yayi nisa shima yau gigitar yashiga ya janyo wata jallabiyar da sauri ya sanya Masa ya daukesa da dukkanin qarfinsa yafito dashi suka biyosa Zuwa lokacin Amatu kukanma takasa Yi suka fada mota Banda zarah dayace taje hafsatu ta Rakata ta fadawasu umme. Koda suka Isa asibiti cikin gaggawa aka karbesa akai ciki dashi zuwa lokacin Amatu idanuwanta neman qanqancewa sukeyi kamar wainda ke bayansu saiga umme da Modibbo harma da Salman sun qaraso asibitin Babu me nutsuwa Hakanan yau ciwon nasa yasasu cikin wata irin rashin nutsuwa da firgici. Dr ashir ne da Dr Fatima suka fito daga dakin emergency din idanuwansu kowanne jajir Dr Fatima tuni idanuwanta suka kawo hawaye rauninta na bayyana Dr ashir ya sauke Kai gaban Modibbo yace" Saidai hakuri Allah ya karbi Dr khalil zabeera. Wuta kowannensu ya dauke musamman Amatu da umme Amatu qyafta idanuwa tayi kusan so biyu kamar zata makance sbd duhu dake mamaye idanuwanta suka yanke jiki a some kusan atare itada umme wadda Modibbo ya tare ita kuwa MD ne ya tareta ta zube jikinsa dukkanin jikinta ba saki. ##Mamuh# 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 31_* MAHMOUD ZABEERA ma yau dukkanin jarumta da qarfin ransa ji yayi Yana kakkaryewa daga zuciya har gangar jikinsa, tarota kawai yayi Amma shima Jin yake kamar faduwar zaiyi, Dr Fatima tayo gurinsa da sauri tana hawaye ta tattaro Amatun jikinta tana Kiran nurses da duk asibitin jikin kowa da zuciyarsa tayi sanyi da rasuwar Dr khalil zabeera Wanda ya zamto cikakken mutum sbd kyawawan halayensa dasukeda wuyar samu acikin mutanen yanzu. Dr ashir kuwa ganin dukkaninsu kowa neman zauce musu sbd tsananin tashin hankali da sauri ya dauko kujera yakawo wa Modibbo daya tare ummen data Suma, Kiran wasu nurses yayi aka Kama umme itama akai ciki da ita aka kwantar gadan dake gefen Wanda aka kwantarda Amatu cikin sauri aka Fara Basu taimakon gaggawa dansu farfado tinda suma. Su Modibbo kuwa zaunar dashi MAHMOUD yayi dukkanin jikinsa na rawa idanuwansa sunyi jajir ko mahaifin nasu yakasa kalla Jin yanda jikinsa ke rawa sosai yasa Modibbo dagowa da jajayen idanuwansa ya kallesa tareda dange hannunsa Yana rintse ido tareda jinjina Masa Kai alamar sai hkr. Dr salman zabeera kuwa kuka yakeyi sosai kamar mace sbd rasuwar Khalil din tamkar saukar tsawa sukajita kwatsam Babu Wanda yakawo tunani ko zancen mutuwa yanzu ba'a kansaba kosu Andi dasuke tsofi Basu kawo tunanin mutuwa akansuba. MAHMOUD ne yayi qarfin hali da jarumtar karban wayar Modibbo yakira Andi dake zaune cikin tsakiyar Daren Yana salati sbd baccin dayaji haka kawai ya dauke daga idanuwansa Kiran farko na asuba dayaji anyi yasashi miqewa zaiyo alwala yafara ko nafilfili wayarsa tadauki haske alamar Kira. Juyowa yayi ya kalli wayar yana mamakin Wanda ke iya kiransa a wannan lokacin saiyaga sunan Modibbo ya sake shiga mamaki ya dauki wayar tareda dauka cikin nutsuwa yayi sallama. Daga can asibiti Saida MAHMOUD ya tattaro qarfin halin iya bude bakinsa cikin rawar muryar dabai taba ba arayuwarsa yace" Muna asibine taredasu Modibbo da umme Allah yakarbi Khalil cikin Daren Nan. Tsit Andi yayi tsawon mintuna Yana qoqarin kakkamo zancen dazai fada yafara da Kiran" Innalillahi-wainna ilaihirrajiun. Kashe wayar yayi tareda ajiyewa yakoma bakin gadonsa ya zauna Yana sake maimata taslima Yana jinjinawa al'amarin ubangiji dayakeyin yanda yaso alokacin da yaso, Ya dauke Khalil bayan cika masa burinsa na kwana daya tal, Wannan shine cikakkiyar ikon ubangiji da Babu Wanda ya Isa ya sauya sbd yau da ace dukiya da mulkinsu nada iko meya hada Khalil da mutuwa a ranar yau da ko awa ashirin da hudu aurensa baiyiba. Astaghfirllah" yafara maimaita tawa Yana rintse idanuwansa ya sunkuyar dakai cikin tsananin jimamin rasa yaro me tsaftatacciyar zuciya da tausayi tareda tawakkali irin Khalil. Allah yayi maka rahama yabaka hasken kabari da sakamakon gidan aljanna KHALIL. Koda asuba tayi akai sallar asuba tuni rasuwar Khalil ta yada zabeera da familynta nako Ina da ko Ina tuni kuku ya sauka a zabeera sbd mutuwar ta girgiza kowa sbd Babu Wanda yayi tunanin mutuwa Kuma tasa adaren, Koda gari yayi waye sosai tuni family suka Fara halarta zabeera tafara cika tun kafin akawo gawar tasa gida dama wainda sukazo biki Kuma dama Basu tafiba tunda a Daren jiyan aka kawo amarya Ashe basasu koma daga bikinsa ba saisunyi zaman makokinsa, Duk Wanda ya iso saiyayi kukan wannan babban rashin na khalil zabeera sbd kowa Yana shaida kyawawan halayensa da nutsuwarsa wadda tasa yakeda jamaa ciki da wajen zabeera. Ahankali tabude idanuwanta ta rufe tasake budewa tana qyaftasu Da fuskar usi dake rungume da kanta tafaracin karo ta rufe idon ta bude taga shi din daine ta zabura da sauri ta tashi zaune har tana zamewa saura kadan ta fado qasan gadon iyami da maman junior da idanuwansu sukai jajir musamman iyami da har lokacin hawaye Basu dauke daga idanuwanta ba sukayi saurin tarota ta kallesu da manyan idanuwanta dasuka firfito sun bushe sai wani irin ja dasukayi tafara qoqarin miqewa qafafunta da hannunwanta tareda muryarta dasuke wata irin rawa tana cewa'' Ina...ina..Ina khalillll???? Sunkuyar dakai sukayi Banda iyami datayo kanta tana neman rungumeta tayi saurin qwacewa tana nufar qofar dakin asibitin USI dake kuka sosai yayi saurin tarota Yana kuka yace" Amatu Ina zakije antafi dashi gida muke jira ki farko muma muke gidan....... Zamewa tayi ta zube qasa tareda sakin wani irin gigitaccen kuka me qarfi dayasa asibitin suka qara daukar shiru kowa na sake rafka tagumin rashin Khalil din dakuma kuka da tashin hankali dazata shiga idan ta farka Wanda suka shirywa Sha dama. Tsayawa sukayi kowannensu na nasa kukan me tsananin cikin tausayinta da Kuma zafin rashinsa Suma daya bugesu Babu Wanda yayi yunqurin hanata sbd kuka Kam yariga ya sameta abarta tayisa ko zataji sassucin radadin ZUCIYA. Irin kukan datakeyi ne yasaka hankalin duk Wanda ke asibitin tashi sbd kukan nata taba zuciyoyinsu yakeyi Yana sake tuno musu da Dr khalil sbd rashinsa ne kawai yasa take wannan kukan Dan kuwa da Yana Raye Amatunsa bazatayi irin wannan kukan ba matuqar ba al'amari yafi qarfinsa bane. MAHMOUD ne da kansa Modibbo yasashi yadawo asibiti yadaukosu Amatun tunda yashigo asibitin yaji tsit Yana Kama hanyar dakin datake yafara jiyo kukanta dayasashi tsayawa cak qafafunsa da zuciyarsa na qara daukar nauyin rashin Dan uwa mafi soyuwa garesa. Jin kukan na kakkaryasa yasa yayi jarumtar qarasawa dakin ya tura ahankali yaci karo da ita zube bakin qofar tana kukan idanuwanta kamar zasu zazzago qasa. Saurin juyawa yayi yacewa su iyami su kamota sutafi gida. Daqyar suka tattarota suka saka mota suka nufi zabeera inda take cike tundaga farkon layin anguwar talakawane tako Ina bulbulowa sukeyi dukkaninsu yawanci mutanensa ne da taimako ya hadasu. Ko a anguwarsu kawu jama'ar dasuka halarto dan jana'izarsa basa qirguwa Hakama ko anguwar gidan Ibrahim daya zauna Saida yayi mutane sbd ko acikin rashin Saida ya taimaki mutane da dama. Sashen Modibbo akayi da ita inda gawarsa take shimfide an lullubeta su Modibbo da Andi taredasu alhaji qarami da kawu dake gefe zaune Yana tsiayayar hawayen dasuka kasa tsaya masa,wallahi ayau ki yakeyi tamkar 'dan daya fito daga tsotsonsa ne ya rasa sbd Khalil yarone daya shiga ransa Wanda yakejin inama ace haddashi ya tsinta lokacinda ya tsinto su Amatu da Usman. Kukan umme ne dake zaune gaban gawar ta daga qafafunsa tana addua tana kukan da bayama fita sbd disashewa da muryarta tayi hakama ko gani batayi sosai ayanzu sbd kumburin da idanuwanta da fuskarta sukayi. Tun kafin ta iso gaban gawar tasa qafafunta suka kasa daukarta ta zube tana sake sabon kukan dake taba dukkanin mutanen dake palon tafara rarrafowa tanajan jikinta ta matso gaban gawar tana kallon fuskarsa dake bude tayi fari fes Yana sheqi kamar zaiyi murmushi. Qoqarin daukewa numfashinta yafarayi Salman da USI sukayi kanta suna Kiran sunanta anty juwairiyya dake palon itama tayi saurin tarota tana shafa Mata fuskarta zuwa bayanta numfashin na Dan daidaituwa. Cewa akayi su fita za'a yiwa Khalil din wanka sbd lokacin jana'izar yayi sabon kuka Amatu tafashe dashi tana kallonsa tana Kiran sunansa ganin zata karya musu zuciya yasa Andi yace juwairiyya tayi cikin gida dasu itada umme wadda sai anriqeta sbd sosai Bata gani komai sai dishi dishi. MAHMOUD ne yabiyo bayansu bayan sun fito Yana rintse idon damuwar tambayar dasu Andi suka turosa yayiwa Amatun ya tsaya bayansu kadan yayi Dan gyaran murya kadan yakira juwairiyya ta tsaya tareda juyowa tana kallonsa da jajayen idanuwanta Ya Dan kalli Amatu da umme dake hawaye Babu me lakkar qwaqqwaran motsi acikinsu a taqaicema baya tunanin zasu fahimci Abinda zai fada ya Dan dauke Kai cikin qaqalo nutsuwa yace" Zaki tambayetane ko da akwai janaba atare dashi. Dummm taji itama juwairiyyar tareda sauke Kai ta gyada Kai tareda matsawa gurin Amatun dake tafiya tanajan qafa jiki a sake ta riqota tana kallon fuskarta datai ja ahankali tace" Amatu wanka za'a yi Masa anason sanin idan da akwai janaba ataredashi¿ Cak Amatu ta tsaya tareda juyowa ta kalli anty juwairiyya da jajayen idanuwanta dasuka Fara bushewa taji sabon kuka na zuwar Mata sbd tun yanzu taqara tabbatarda mutuwa tonon asiri ce, Amma tunda tariga ta rasashi meya rage Mata tun yanzu tafara ganin tonon asiri ahankali ta juyar dakai tana qoqarin wucewa ta 'dagawa anty juwairiyya din Kai Wanda yasa MAHMOUD ZABEERA dayaga amsar data bayar juyawa ya koma Yana qoqarin Hana mutuwar jikinsa bayyana, cikin sanyin jiki ya sanardasu Andi Nan aka Fara yimasa wanka, Suna gamawa aka shiryasa cikin farin likafaninsa aka shimfidesa tsaf aka sake aikawa matarsa da mahaifiyarsa sukazo sukai masa adduar data Kuma Kai Amatu ga Suma akai ciki da ita aka dauki gawarsa aka fito da ita inda dubban mutane ke jira Wanda yasa iyayensa da Yan uwansa mamakin lokacinda yayi wainnan jama'ar a waje wanda yawancinsu talakawane da marasa lafiyarsa Wanda yasa Andi Jin kunyar kansa alokacin dasuke zaune suna zuba mulki da oda alokacin 'yayansu nacan suna taimakawa talakawa da marasa qarfi, Ya tabbata koshi ya mutu yanzu bazaiyi jama'ar Khalil ba Wanda sukewa fatan ya dace tun anan. Anyi jana'izar Dr khalil zabeera ankaisa kwancinsa na qarshe andawo anci gaba da karban gaisuwar da aketa ganin mutane kala kala a zabeera Wanda yaketa saka iyayensa da Yan uwansa alfahari da Jin sasssaucin zafin rashinsa sbd ganin Inshallah ya dace tunda kowa yazo da alkhairin dayake fada akansa. Acan cikin gida kuwa a sashen umme ake karban gaisuwar Umme ko Magana Bata iyawa idan anmata gaisuwa saidai daga Kai kawai Dan ko mutanen Bata ganewa sosai, Amatu kuwa zazzabine me qarfi ya rufeta bayan anty juwairiyya da anty zarah sun taimaka Mata tayi wanka ta gyara jikinta tareda sallar asuba aka kwantar da ita a quryar bedroom din umme anty zarah ta zauna tareda ita tana shafa kanta sbd irin ajiyar zuciyar datakeyi Babu qaqqautawa kuka tuni idanuwanta suka bushe ko zuwa bayayi sai ajiyar zuciya da idanuwan datake zarewa. Nuratu kuwa hajiya Maryam tafi kowa shiga tashin hankali bayan iyayen Khalil din da matarsa sbd Nuratu da abin ya buga sosai sai zabura takeyi tana somewa qarshe dai ankira likita yace saisun tafi da ita asibiti fatarsu alamarin bai taba qwaqwalwartaba. Da daddare Amatu sashenta aka maidata tareda iyami da da anty salamatun gidansu da zasu zauna da ita kafin agama zaman gaisuwar asan abin yi. Bedroom dinsa tashiga ahankali ta kunna wutar dakin tana juyowa ahankali da jikinta da Babu qarfi ko kadan idanuwanta suka tsaya akan shimfidar dasuka kwana a Daren jiyan ta qurawa jinin dayake Kan shimfidar ido tafara takawa ahankali ta Isa bakin gadon ta zube qasa tareda jawo zanin gadon ta qanqame tana sake kuka ahankali tana tuno Daren na jiya wanda yayisa a cikin yanayi na ciwo da rashin qarfin jiki sosai kamar Wanda rabo ke cizo Kuma kaman yasan rabuwa zasuyi, gwara da Bata hanasa kantaba Ashe datafi kukan datakeyi ayanzun. Cukuikuye zanin gadon tayi cikin jikinta tana shaqar qamshin jikinsa dake jikin zanin cikin kuka tace" Jiya kana taredani Dr meyasa zaka tafi?????? Kuka take fitarwa me qaramin sauti a bakin gadon har wahalallen bacci ya dauketa zaune a qasan. Sai asuba ta bude idanuwanta dasukai nauyi sbd kumburi ta tashi tana gyara zamanta kafin ta miqe ahankali tana kallon zanin gadon dake jikinta ta sake kallonsa kafin ta nannadesa ta nufi cikin wardrobe din dakin tayi Masa kyakkyawan boyo ta fito dakin takoma dakinta inda su iyami suke sanyin AC yasa wani irin dogon bacci ya daukesu, ta shiga toilet tayo alwala tana fitowa iyami na farkawa ganin alamar alwala atareda ita dakuma Jin ana sallah a masallacin cikin zabeera yasa tasan asuba ce ta tashi zaune tana qoqarin saukowa gadon ta nufi bayin itama. Sallah Amatun ta tayar kanta na tsananin ciwo kamar zai tsage qarshe dai a zaune tayi sallar. Guraren qarfe Tara na safiya aka kawo abincin safe aka jere musu a dining tareda sabuwar me aikin da aka iko ma Amatun. Anty zarah ma tunda safe ta iso sashen ta gaidasu iyami dake zaune Palo jigum sbd Amatun ta rufe kanta a dakin Khalil din tanata kuka ita kadai taqi fitowa. Duk yanda anty zarah tayi qin fitowa Amatun tayi salman da USI ma sunxo sunyi sunyi taqi bude dakin Saida akaje aka sanarwa umme. Ummen na zuwa qofar bedroom din nasa kasa Magana tayi itama sai kawai ta fashe da sabon kukan daya daga musu hankali Amatu dataji kukan ummen hankalinta yaqara tashi ta rarrafo ta bude qofar tareda fadawa jikin ummen tanajin kukan ummen har cikin ranta kamar yanda idan Dr na Nan tasan zaiji kukan ummensa. Daqyar juwairiyya dasu anty zarah suka sallashesu aka fadowa su Modibbo saiga Andi dakansa ya zauna yayi musu nasihu masu karya zuciya da saka tawakkali Nan suka dauki qaddara suka dangana. Anty zarah ce da iyami suka Bata abinci Dan Dole Tasha tea kawai sai guntun slicebread anty zarah takaita ta watsa ruwa ta sanya doguwar riga da hijab suka dawo Palo ta zauna cikin mutane. Dukkanin kulawa da cinta da yanayinta anty zarah ce takeyi sai su iyami dasuke kwana yimata addua suna tofa Mata sbd yanda take firgita cikin bacci idan ya dauketa. Anyi adduar uku anyi ta bakwai an watse kowa yakoma inda yafito sai anty salamatu da sabuwar me aikinta da aka bar Mata tayi zaman takaba Wanda taso takoma gidansu tayi umme ta ringa roqonta kada ta tafi tabarta Dole akace ta zauna anan tayi takaba tukuna. **** Rayuwa me sauyawa kamar yanda mutuwa take Dole hakama dangana daci gaba da rayuwa yake Dole., Kusan sati hudu kenan yanzu da rasuwar Dr khalil zabeera Wanda tuni wasu suka manta suka koma harkokinsu Banda Amatu da mahaifiyarsa da har abada mutuwarsa bazata taba sakinsuba, USI yakoma makaranta daqyar sbd kasa tafiya yayi yabar Yar uwarsa alokacin datafi buqatarsa Amma itace da kanta ta tuna Masa cewa burin Dr khalil ne yayi karatu me zurfi Dan ya tsayu da kansa ya tsaya musu wataran kamar irin yanzu da basuda Khalil din tabbas sunyi Rashi Dan yanzu zasu koma Matsin rayuwarsu ne na dah. Sosai anty zarah da anty salamatu ke kula da ita hakama kullum umme saitazo da kanta ta dubata musamman saka mutuwar arai datayi arai sosai sai lafiya take neman gagararta sbd kullum cikin zafin jiki da zazzabin dare take, Modibbo da kansa kullum yake Kira yaji lafiyarta da kansa ba saqo ba shikuwa Andi kullum saiyayi musu aikin idan da Abinda Amatun ke buqata saidai Kuma MD ZABEERA baibar ko wace irin qofa dazasu buqaci wani abinba koyaushe buqatarsu cikakkiyace daga garesa duk da baitaba zuwa inda takeba rabon daya kalli ko inda sashen yake tun ranarda ta dawo. Rasuwar 'dan uwansa ta dakesa sosai harsaida hakan ya taba himmarsa da jajircewarsa a aiki shiyasa take dukkanin iya qoqarinsa gurin cire tunanin wanzuwarta a zabeera yariga ya damqawa zarah komai na buqatar Amatun harta fita takaba Dan haka yagama komai baida sauran tunani akanta saima busy daya qara saka kansa zama Dan yanzu tafiye tafiyensa sundawo dama sbd Khalil ne dake takura Masa yasa yarage tafiye tafiyensa Amma yanzu Kam sai ya qarawa kansa yawan tafiye tafiyen. ##Mamuh# *_'yan uwa inaga anan zamu tsaya sbd duba da azumi daya riga yazo inshallah saimu Bari idan Allah yabamu yawancin ran kaiwa bayan sallah saimu qarasa Inshallah._* _NAGODE_ 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 32_* Gyara zama anty zarah tayi tana sake qurawa fuskar Amatun datayi haske sosai Ido tana maida kallonta zuwa hannuwanta dasukai haske sosai har wani yellow yellow sukayi taji hankalinta nason tashi gabanta na faduwa ta maida kallonta Kan fuskarta tanabinta da kallo ko Ina har zuwa qasanta ta ajiye cup din furar da Amatun tasa aka kawo Mata tana cewa'' Amatu yanayinki na bani tsoro da rashin nutsuwa sbd yanayinki na nuna kamar bakida jini, Ruwa idanuwanta ke qoqarin kawowa tana kallon fuskarta Amatun dake zaune ka kwantarda kanta jikin sofa idanuwanta a lumshe Wanda yanzu hakan yazama tamkar dabia gareta sbd aduk lokacinda ta zauna tayi shiru idanuwanta take lumshewa sbd tunanin rayuwarta data juya Mata kamar upside down Dan kuwa sai yanzu take sake tabbatarda rashin Dr khalil zabeera arayuwarta babbar gibi ce ga rayuwarta sbd shine farin cikinta, walwalarta,gatanta,burinta,alfaharinta, nutsuwarta gatanta dama asalinta gaba daya... Hawayen datake riqewane suka gangaro daga cikin rufaffun idanuwanta Wanda yasa hankalin Anty zarah sake tashi tunanin qilan eh da gasken Amatun batada jinin tunaninta ya zama gaskia ta dafe goshi tana rintse ido cikin tsananin damuwa da firgici tace" Amatu Dan Allah ki bude Ido kiyi magana wannan kukan naki na zuci Yana wahalardamu masu qaunarki, A zabeera kaf gaba daya yanzu Babu Wanda akeji dashi ake tsananin qaunarsa fiyeda kowa kamarki sbd kece Abinda duniya gaba daya ta shaida Dr khalil zabeera naso fiyeda komai har rayuwarsa, Damuwarki damuwar kowa ce, Kukanki baqin cikin mune, Amatu Dan Allah kiyi hkr ki dauki dangana tareda daukar qaddarar rashin Dr Khalil sbd ganinki ahaka na karya dukkanin qwarin gwiwar ummen khalil, Yanzu Amatu bansan yazanyiba gaki da rashin lafiya ajikinki ta zazzabin dare kullum Amma kinki ko karban magani gashi yanzu Ina sakaran ko jini na neman gagararki Amatu meyasa,meyasa......hawaye ne suka katse Mata takasa qarasa maganar ta miqe da sauri zata bar gurin Amatu ta riqo hannunta ahankali tana bude idanuwanta dasukai jajir ta zubawa fuskar anty zarah din dake hawaye tanajin qaunarta tako Ina tana shigarta tareda tausayinsu su duka. Jawota tayi ta maidata zaune tana kallon fuskarta ta tashi zaune ahankali tareda sake hannun anty zarah din tana dauke idanuwanta daga kallonta ahankali ta bude baki cikin yanayi na karyewar zuciya tace" Anty zarah meyasa kike qaunata har haka? Meyasa keda Dr kuke min irin wannan son haka? Anty zarah kinsan arayuwata bantaba samun soyayya irinta Dr khalil zabeera ba, Shine ya koyamin sonsa alokacinda zuciyata batasan wata soyayya ba saita kudi, Shine yabani sunan mutunci da martabar mace, Dr khalil zabeera yazabi soyayyata fiyeda komai da kowa, Yasa zuciyata takamu da zazzafar soyayyarsa me wuyar Bari bare mantawa Amma yatafi ya barni a daidai lokacin da zuciyata batasan komai da kowaba bayanshi, Meyasa yatafi yabarni anty zarah Ina tsananin buqatarsa....... Rufe Mata baki anty zarah tayi tana girgiza Mata Kai hawayenta itama suna gudu tace" Amatu kada kiyi sa6o ki dauki dangana shima da ana bada zabin mutuwa da bazai taba zabin barinki ba sbd bazaiso ganinki cikin irin wannan halin dakike cikiba yanzu.. Kiyi hkr ki rungumi hukuncin ubangiji akanku hakan da yayi shine daidai kizama me godewa ubangiji aduk halinda Kika tsintsi kanki. Sauke Kai Amatun tayi hawayenta suka Gama gangarowa ta dago tana sharewa ta kalli anty zarah datake kallonta cikin tsananin damuwa ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda lumshe ido ta bude ta miqawa anty zarah din hannu tana kallon cup din furar data kawo Mata. Da sauri anty zarah din ta dauki cup din ta Bata tana bayyanarda Jin Dadinta na sassautowa da Amatun tayi cikin guntun zumudi tace" Thank you AMATULLAH. Da sauri Amatun ta kalleta tana fasa Kai cup din bakinta sbd duk duniya Dr khalil dinta ne kawai ke Kiranta da cikakken sunanta AMATULLAH. Fuskewa anty zarah tayi tana qaqalo murmushi ganin tana neman dawo da gaba baya tace" Banma iya fadar sunan yayi Dadi ba kaman yanda ake fada. Ganin tashiga kame kamen fadar sunan datayi yasa Amatu sake sauke ajiyar zuciya tana Kai cup din bakinta tana kurba ahankali ta lumshe ido tana gyara jinginawarta sbd dadi dakuma karbuwa dataji bakinta da cikinta sunayi da furar saita saki jiki tanasha ahankali furan na sake sanyata lumshe ido. Anty zarah ganin yanda furan tasamu karbuwa sosai agun Amatun yasata miqewa da sauri ta nufi fridge ta dauko gaba daya jug din furan ta dawo dashi ta ajiye gaban Amatun tana cewa'' Kawo cup din aqara zubawa Kisha Dama nasan zakiji Dadinta sbd har sabuwar Madara na zuba Miki aciki. Qara Mata tayi takuma shanyewa Saida ta shanye kusan cup uku kafin tace ta Isa abarta haka. Cikin Jin Dadi anty zarah tagyara zama tana Mata fira ahankali tana matsa Mata qafafunta dasuka Dan kumbura sbd zama guri daya Ahaka har bacci ya dauketa cikin nutsuwa Wanda rabonta da irinsa tun kafin rasuwar mijinta sai yau. Gyara Mata kwanciya zarah tayi kafin ta zame ta fice daga part din gaba daya takoma nasu Nan ma wani aikin tahau sbd MAHMOUD datake saka ran dawowarsa ayau din duk da gaba daya yinin ranar basuyi wayaba dama itace tafi Kira to itakuma yau ganin yanayin sauyin jikin Amatu yasa hankalinta yadan dauku ko yanzu tana ganin kamar hasashenta gaskia ne Amatu na buqatar ganin likita jikinta bai nuna tana lafiyaba Dole zata fadawa umme kokuma MD idan yadawo yau asan nayi kada wani ciwo ya kamata basuda masaniya. Aikin gyare gyare da girki suka hau Yi itada hafsatu sbd tuntuni ta zauna tayi nazari zata dauki shawarar Amatu ta kawo gyara arayuwar aurenta da tsakaninta da mijinta, Zata cire shakku da tsoron mijinta ta fuskanci reality rayuwar aure sukeyi ba zaman darasiba Dan haka zata sauya kanta ta sauya zamantakewarta da MAHMOUD ZABEERA kada tayi sake lokaci ya qure Mata. Sai yamma suka Gama komai tayi wanka ta sanya doguwar riga ta atampa tareda yafa qaramin qyale akanta ta hada abincin data dibarwa amatu ta jera a tray hafsatu ta dauka suka nufi can. Koda suka shiga futowarta wanka kenan itama ta sanyo riga da skirt na atampa ta sanya., Abin mamaki maimakon taji kayan sun Mata yawa sbd Rama saitaji kamar skirt din ya kamata hakama rigar. Kallon anty zarah dake kallonta cikin yanayi na tunanin dabasanma na menene ba haka kawai idan tana kallon Amatu wani lokacin saita Shiga tunanin yanzu saime Kuma zaizo gaba a rayuwar Amatun. Anty zarah kina ganin na qara jiki ne kokuwa nece naji hakan? Numfashi anty zarah din ta sauke tana matsowa gaban Amatun ta Dan ja rigarta daga gefe gefe taji ba wani space tasaki murmushi tana cewa'' Gskia baki wani qara ba inaga sbd dai kin Dade baki sakasu bane shiyasa gashi bakida wasu tsofin kayan bare kisaka Amma kiyi hkr kiyi manage tunda ba abin ado bane Kuma ba fita zakiyi ba bare kice Zaki takura. Gyada kanta tayi tana sanyawa kanta hula Mara nauyi ta Dan saki fuska ta qaqalo murmushin yaqe sbd faranta ran Anty ZARAn tace" Anty zarah wannan qamshin na Rabin ranki ne? Sbd nasan shi kadaine akewa wannan Shirin na musamman. Kasa boyuwa farin cikin anty zarah yayi ta saki annushuwa sosai tana cewa'' Amatun kin bawa MAHMOUD sunan Dole Wanda harya zauna cikin kaina Nima RABIN RAN ANTY ZARAH. Falo suka fito suna cigaba da Dan fira sama sama sbd karta zaqe da yawa ganin Amatun tafara sakewa. Suna zama tace" Anty zarah kokinsan meyasa idon mutum ke nauyi wani lokacin kamar zasu juye ga ciwon Kai me tsanani??? Kallonta da kyau zarah tayi kafin tace" Kinajin hakan ne? Gyada Kai tayi ahankali tana cewa" Qila sbd kukan danakeyi ne koyaushe. Aa Amatu ba lallai hakan bane ni nafi zargin rashin ishashen jini atare dake kibari Akira likiti ya dubaki. Ba buqatan hakan anty kawai daima yanzu Kwan biyun Nan nadainajin nauyin idon ciwon Kai me tsanani yafi damuna idan akwai maganin ciwon Kai kawai kiban danasha shikenan zanji sauqinsa Inshallah. Akwai ibuprofen agurina Yana maganin ciwon Kai sosai yanxu idan na koma xan aiko hafsatu takawo Miki kisha kafin ki kwant kafin safe zakiji wasai. Nagode anty zarah Allah yabarki da Rabin ranki yabaki zuciyarsa. Wata Yar dariyar farin ciki tasaki tana qoqarin dasawa zuciyarta zancen ta hanyar cewa amin saidai Kuma wani sashen na zuciyar na ganin kamar da wuya samun zuciyar MD ZABEERA koba agurinta ba ko agurin kowama. Salman ne yashigo palon daukeda babbar ledar fresh fruits da ledar gasassun kifin dasuka gasu cikin source din veg chips sai qamshi sukeyi. Da kallo dukkaninsu suke binsa har su hafsatu suka karbi kayan hannunsa sukai kicin dasu Dan zubowa a tray ya qaraso ya zauna gefen anty zarah Yana kujerar dake kallon ta Amatu Yana kallonta cikin yanayi na tsananin kulawa Yana tambayarta Yaya take Ta amsa Masa cikin yanayin sake bawa kanta qwarin gwiwa sbd su masoyanta dasuka damu kansu akan damuwarta. Maida kallonsa yayi Kan anty zarah dake yankawa Amatu kankana cikin fruits dinda su hafsatu suka kawo bayam sun sake wankowa yasaki murmushi Yana cewa'' ZARAH Ashe MD yadawo yau. Dagowa tayi tana Masa kallon mamaki da tambaya tana miqawa Amatu kankana a qaramin plate da fork. Ganin alamar batasaniba akan fuskarta yasashi karban plate din dashima take miqo Masa ya gyara zama yafara Sha kafin yace" Kafin nafita da yamman Nan Naga shigowar motarsa an daukosa daga airport Amma sashen Modibbo Naga motar ta nufa Kuma acan mukayi sallar magrib tare agun Modibbon Amma dai by now inaga yabar sashen Modibbo. Kallonta Amatu tayi tana sake murmushi ahankali cikin nutsuwa tace" Barka anty zarah. Itama murmushi ta mayar musu tana gatsa apple ahankali zuciyarta na shiga yanayi na 'yar damuwa tana basarwa sbd qilan yakirata bayan dawowarsa din Dan tabar wayar acan sashensu tana charging. Ganin hankalinta bai Kan Yar qaramar firar dasukeyi yasata miqewa tareda Yi musu Saida safe daidai fitowar anty salamatu daga dakin dayake zaman nata a zaman dazatai agidan kafin sukoma inda suka fito. Qarosowa tayi suka gaisa da zarah dazata fice kafin ya qaraso ta zauna gefen Dr salman suna gaisawa Yana janta da Yar firar dasuka Saba tun amatu nasaka musu baki hartayi shiru ta lumshe ido tana saurarensu sbd kanta dake sarawa. Shigowar hafsatu ce data dawo tasata bude idanuwanta ahankali ta saukesu akan hafsatun tareda karban maganinda anty zarah din ta aikota takawo Mata ta juya ta fice. Miqewa tayi da kanta ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko ruwa ta bude tareda ballo maganin Tasha ta maida sauran ruwan tareda fitowa tayiwa salman Saida safe ta wuce daki direct tayi sallar ishai ta kwanta sbd tsanani dataji kamar Kan nata nayi Dan har jiri jiri take gani. Zarah kuwa bayan tabawa hafsatu maganin takaiwa Amatu direct sama ta nufa dakin MD bayan tasake fesa turare ta daura dankwalin kayan jikinta tana sake gyara zaman curves din rigar taje ta hado Masa abincin sukai Masa marasa nauyi a tray ta Isa qofarsa tayi knocking so daya kafin ta tura qofar tashiga bakinta daukeda sallama cikin yanayi na nutsuwa. Fitowarsa wanka kenan Yana tsaye gaban mirror Yana goge ruwan jikinsa ahankali ya dago ya kallota ta jikin madubi da fararen idanuwansa ya amsa sallamar ahankali cikin muryarsa data kashe jikinta Nan take. Kallonsa takeyi da dukkanin idanuwanta da bakinta da hancinta da nutsuwarta da komaima nata sbd wani sheqi da jikinsa yakeyi na hutu dayake samu. Jin shiru yasashi juyowa ahankali ya kalleta yaga yanda duk ta sake gurin kallonsa ya dauke Kai ahankali tareda bude wardrobe ya janyo jallabiya Mai tsantsi da taushi brown ya saka tareda fesa spray dinsa na imperial majesty ya nufa kujera ya zauna Yana daukar wayarsa dake kashe ya kunna tareda dagowa ya zuba Mata manyan idanuwansa ya bude baki ahankali yace" Nasameku lafiya? Dan firgita tayi da tareda dauke idonta akansa cikin tsananin Jin nauyin mayen kallon datazo ta tsaresa dashi batareda yimasa ko sannu da zuwaba bare gaidashi. Cikin Dan Jin kunya ta qaraso gefensa ta zauna ahankali ta ajiye tray din akan table tana saita kanta cikin Jan mutuncinta a natse tace" Barka da dawowa,ya hanya? Ajiye wayarsa yafarayi bayan ya saka silent ya Dan juyo ya kalleta cikin nutsuwa har zuwa adon datayi dominsa ya sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ya dauke Kai Yana Dan sakin fuska yace" Alhamdulillah, Ya kuke? Sake kallonsa tayi sbd yanda gabaki daya ko awaya yawanci tambayoyinsa suka koma Mata kalmar KU. Jin shiru yasashi dagowa ya kalleta ya sake maimaita tambayarsa da cewa'' Kuna lafiya??? Zuba Mata Ido yayi sbd amsa yakeson ji. Akwai matsalane acan gefen?? Sai alokacin ta kallesa cikin Ido sbd sai alokacin ta fahimci Amatu yake nufi ta saki ajiyar zuciya tareda sake murmushi tana gyada Kai tace" lafiya kalau Nake su Amatu ma lafiya kalau suke saidai duk da Bata fadaminba inaga kamar batada lafiya sbd sauyawar datayi ga ciwon Kai me tsanani datace tana........ Tari me qarfi ya sarqesa na abincin dake bakinsa, Spoon din faten dankalin daya maida cikin plate batareda yakai bakinsaba kamar yanda yayi Niya yasata kasa qarasa fadar Abinda take fada tana kallonsa ta kalli abincin cikin mamaki da fargaba tace" Ya salam, Sorry, Lafiya? Akwai wani Abu ne tareda abincin? Dan lumshe ido yayi tareda budewa batareda ya kalletaba yace" I lost my appetite. Cikin damuwa ta matsosa da sauri Yana dafasa cikin kulawa tace" Bakada lafiya ne? Ko akawo wani abincin? Numfashi ya sauke Yana sake kallonta yace" No I just lost the need to eat karki damu. Kasa hakura tayi ta zubo Masa coconut drink dinda tafi awa biyu tana hada Masa sbd sanin Yana qaunarsa ta zubo a cup ta miqa Masa cikin sauri da kulawa daidai kiran Salman zabeera nashigowa hannun dayayi niyyar karban drink din datake basa shi ya wuce dashi ya dauki wayar Kai tsaye Abinda bayayi Kiran farko ya daga waya, Yanaji a rayuwarsa daga Modibbo sai Khalil ne kawai ke Masa Kira daya ya dauka. MD Amatu ce ba lafiya sosai she's ko numfashi batayi and she is bleeding ba kakkautawa am taking her to hospital... Aje wayar yayi Yana qoqarin saita nutsuwarsa Saikuma kawai ya miqe tareda daukar wayarsa da key din mota yafice. Bayansa zarah tabi da kallo kafin tabi hannunta dake sangale da cup din data miqa Masa bai karba ba tanaji wani nauyi na danne zuciyarta Wanda yasa idanuwanta cikowa da hawayen dabatasan Kona menene ba. #Mamuh# 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 33_* Ahankali ta sulale zaune hawayen datake qoqarin maidawa suka gangaro,haka kawai zuciyarta kejin zafin Abinda yayi Mata din a yanxu Aqalla koma menene tunda ba mutuwa akace Amatun tayi ba ya kamata yayi Mata mgn kokuma ya karba Abinda take miqa Masa din, Share hawayen tayi tareda ajiye cup ahankali ta miqe ta fice tana qoqarin cire damuwar abin kwata kwata cikin ranta sbd idanma ta barshi cikin ranta itace zata fi kowa wahala. Bedroom dinta ta nufa tareda sanyo gyale ta dauko wayarta ta fito tana latsa Kiran anty salamatu. Cikin sanyin jiki da kulawa tace" Anty salamatu menene yasamu Amatun? Kuna Nan kokuwa anwuce asibitin? Numfashin damuwa anty salamatu ta sauke cikin tsananin damuwa tace" Wlh haka kawai muka dinga Jin nishinta da salati Koda mukazo harta some ga jini ba qaqqautawa sai zuba yakeyi gamu dai muna isowa asibiti yanzu tareda MD da Dr salman. Katse wayar tayi ahankali tareda sauke numfashi tana sake bawa kanta qwarin gwiwa da hkr ta nufi sashen umme tana amsa Kiran mominta data Kira tana Mata barkar dawowar mijinta lfy. Tana shiga umme na fitowa da jaka a hannunta Nuratu na biye da ita hankalinsu a matuqar tashe musamman umme dako lulluba gyalenta daidai takasa tadai ratayosa a wuya ta gyara cikin mota idan tashiga. Fadawa motar tayi itama tace zata bisu zuwa asibitin suka wuce sbd zumudi ma Nuratu ce ta tuqa motar sbd bazasu jira shigowar driver ba daga main gate tunda akwai tafiya daga gate din farkon zuwa ciki. A mota umme ta kalli zarah datai sanyi tana cewa'' Zarah menene yafaru ne? ko bayan magriba dinnan nayi waya da ita najita lafiya kalau har Ina godewa Allah danaji muryarta tafara sakewa da walwala, Shin da akwai matsala ne tuntuni daban saniba kokuwa yanxune kawai abin yasameta? Numfashin damuwa anty zarah ta sauke ta kalli ummen cikin sanyi tace" Lafiya kalau nabarta bayan magriba dinnan tadaice tanata fama da ciwon Kai me tsanani sai jiri hakama gskia ta sauya sosai Dan saima ni nakega kaman batada jini sbd yanda tayi fayau fayau, Kallonta umme tajuyo tayi gaba daya zuciyarta na bugawa daidai isowarsu asibitin suka fito suka nufi hanyar dakin dasukasan Dole tanacan sbd asibitin mijintane aka kawota, Cikin tsananin damuwa da firgici umme ta kalli anty zarah bayan sun iso qofar dakin sun tarardasu salman a tsaye suna jira cikin rashin sukuni Tace" Zarah meyasa baki fadamin dukka wannan ba sai yanxu? Shin Bayan jiri da ciwon Kan metace Miki tanaji? Dan jujjuyawa tayi ta kallesu ganin kowa ya juyo ya zuba Mata ido Yana jiran amsarta Jin tamvayar da ummen tayi Mata MD ma dawowarsa kenan daga amsa wayar Modibbo ya qaraso Yana kallon yanda sukai cirko cirko. Cikin kulawa tace" No Kan ne kawai da jiri take min complain to saina Bata Ibuprofen maganin ciwon Kai........ What?????? Dr Fatima data fito dakin tafada cikin tsananin firgici tana qarasowa tace" Ibuprofen? Wayace kibata Magana batareda taga likitaba ya rubuta Mata? Shin kinsan maganin dakika batane yasata cikin wannan hadarin gashi tana qoqarin rasa cikin dake jikinta...... Mene????umme tafada da tsananin qarfi tana zaro idanuwanta Ta juyo gun zarah cikin kidima tace" Meyesa Zaki Bata magani bakisan aikinsa ba? Meyasama baki fadawa kowaba zaki dauki magani kawai kibata zarah? Innalillahi Dr Fatima meza'ayi yanzu Dan Allah kada kubari cikin Nan ya zube Dan girman Allah ku taimakamin ku tsaida cikin Nan. Nuratu da anty salamatu ma kusan duk acikin shock sukace Dr Fatima Dan Allah ataimaka. Salman ma cikin tsananin damuwar yace" Maganin da hafsatu takawo Mata dazun shine Kika aiko Mata? Dafe goshi yayi cikin damuwa yace" Dakin Fara tambayana na duba kafin kibata tunda Ina Nan I cud have checked. Mutuwar tsaye zarah tayi tana rarraba idanuwanta a tsakaninsu cikin tsananin firgici da tashin hankali kowa na jeho Mata tambayar meyasa meyasa., Shin suna tunanin kaman da gangan tabata maganin ne? kokuwa suna tunanin zata iya cutatar da Amatun be? Cikin muryarsa data sanyata juyowa ahankali ta kallesa taji ya fuskanci Dr Fatima cikin murya me nutsuwa yace" Na menene ibuprofen din? Na ciwon Kaine Amma irin strong din Nan kwata kwata masu ciki basa shansa infact kamar abortion pills ne ga masu ciki marasa qarfin jini ko kadan, Gskia this is serious sbd gashi ta zubarda jini sosai har jini ma Muna buqata gskia but yanxu dai we are trying our best mugan mun tsaida jinin. Kai tsaye yace" Wat are the chances na cikin? I can't say sir but just pray and have faith we will try all the best we can Dan muma Muna son cikin Sai Maganar jinin daza'a saka zamu Kira blood bank dinmu mu.... No bana buqatan na blood bank din afara Shirin diban ledan jinin kawai. Kallon cikin idanuwansa zarah keyi tanason ya kalleta ta karanci yanayinsa da yanda ya karbi zancen itace tabawa Amatun maganin Amma yaqi kallontan saima qoqarin juyawa dayakeyi yaga Andi da kansa tareda Modibbo a bayansu suna kallonsa cikin nustuwa, Cikin alfahari dashi Modibbo ya jinjina Masa Kai yace" Abinda kace shine daidai bama buqatan jinin wani gurin dabam munada wainda zasu bada jini da dama... Andi na kallon fuskarsa dake sunkuye Yana karantar yanayinsa na kulawa da damuwa da yayi akan iyalin Dan uwansa Khalil alokacinda baya rayen ya jinjinawa qoqarinsa cikin yabawa yace" Bama buqatan jinin kowa acikin dangi ma tunda uban Dan gashinan a tsaye bazai rasa jinin bayarwaba. Office din Dr ashir suka nufa acan yasake musu bayani tareda Basu tabbacin Inshallah komai zai daidaita kafin suka tafi. Iyami da kawu ma tuni suka iso asibitin Hankalin kowa nasake hargitsa musamman yanxu da kowa yaji zancen da akwai ciki kowa yaji batareda dogon nazari ba saiyace meyasa zaa Bata magani ba tambaya Hakan yasa anty zarah komawa gefe ta zauna cikin yanayi na tsananin damuwa da danasanin Bata maganin duk tasan cikin rashin sani tayi Amma yanda firgici kesa kowa tambayar Yana sata muzantuwa duk da Suma ta musu uxuri sbd tasan firgici ne da tsoron Abinda zai biyo baya. Iyami ce tadawo gefenta ta zauna tana qoqarin danne damuwarta ta kalleta tace" Karki damu zarah ko zubewa cikin yayi qaddararsa ce, Koni da agabana take kowane irin magani Zan iya Bata na ciwon Kai tunda bamu sani ba. Daga Mata Kai kawai zarah din tayi batareda ta iya ko magana ba Duk Wanda zaiga gangancin Abinda tayi bazata damuba mutum biyu kawai takeson su fahimci niyyarta da rashin saninta, Daga MAHMOUD sai Amatun Amma sai zuciyarta na ganar mata zaiyi wuya MAHMOUD yayi Mata kuskuren fahimta sbd yafi kowa sanin Abinda zata iya aikatawa musamman akan Amatu da kowa ya shaida da zuciya daya take qaunarta. Cikin ikon Allah ansamu anshawo Kan matsalar jinin ya tsayu cikinma ya tsayu saidai Kam Babu dogon aiki ko motsin dazai iya taba lafiyar cikin Dan haka hutu ne kawai akeso tayita yi jinin ma ansaka Mata roba daya Kuma alhmdlh jikin bai wani Yi baiyiba tafarko har so biyu anty salamatu da iyami na Bata tea sbd sune suka kwana anan. Hankalin kowa ya kwanta musamman umme da tunda safe Takoma asibitin kusan tareda zarah suka iso Dan motarsu atare tashigo harabar asibitin Kuma kowanne da kayan breakfast ya iso. Gaisawa sukayi suka Isa dakin tare alokacin anfito da ita wanka kenan iyami nasaka Mata doguwar riga mara nauyi. Gaisawa sukayi umme na zama kusada Amatun tana qarasa gyara Mata Sanya rigar sai kaffa kaffa takeyi Wanda yasa Amatun kallonta tasaki guntun murmushi tareda riqe hannunta tace" Umme bafa fashewa zanyiba kiketa Yi kaman kwai. Babu Wanda be bayyanarda murnarsaba a fili da Abinda tafada sbd tun bayan rasuwar Khalil yau ne farko datai Abinda yake asalin dabiarta wato yanko Magana ba taunawa. Dariyar farin ciki umme tayi bayan tagama gyara Mata zaman rigar ta zaunar da ita an jingina Mata pillow tace" Ni ummen Kuma ake fadawa haka Amatu. Murmushi tayi tace" Umme ji nayi kamar kina min susa ne Yana sani waiwayi. Kallon anty zarah tayi zatayi Magana saiga MD ZABEERA yashigo atake imperial majesty yacika gurin da sanyin qamshi Wanda yasakata lumshe ido sbd qamshin daya samu karbuwa daga yanayinta na ciki Anty zarah ma lumshe ido tayi cikin yanayi na damuwa sbd jiya baikoma gidan ba sai dare sosai yanzu da safe Kuma tana tashi tahowarta asibiti tayi kawai sbd tayi tunanin Yana Nan din Ashe sai yanzu yake isowa gashi haryanxu basuyi Magana ba tana buqatan Magana dashi taji nasa tunanin akanta. Ahankali ya qaraso ciki Yana gaidasu umme da iyami kafin ya maida kallonsa kadan akan gadon Amatun wadda ta bude idanuwanta adaidai lokacin sukai Ido cikin Ido Da sauri kowannensu ya dauke idanuwansa shi Yana basarwa itakuma tana Dan tsuke fuska. Kasa hkr zarah tayi sbd tanason Jin bakinsu su biyun akan alamarin ta juyo ta fuskancesa cikin tausasa harshe tace" Ina kwana? Kallonta yayi a natse ya amsa Yana qoqarin juyawa ya fice tace" Ba laifina bane Abinda yafaru jiyan inatason inyi bayani Amma kamar kowa yakasa fahimtata. Tsit dakin sukayi sbd Jin zancen nata musamman Amatu datakejin zancen yanzu. Umme ce tayi saurin kallon Amatu kafin ta maida kallonta Kan zarah din tace" Ba kasa fahimtarki akaiba zarah Amma ta Yaya Zaki yanke bata Magani without any consulting? Da idonki Kinga Abinda yafaru da ita akan hakan, Bai kamata ki kasa fadawa kowa Abinda yake damuntaba tun farko you should have told me ko Kuma MAHMOUD. Cikowa idanuwanta sukai da hawaye bayan sunyi jajir ta dago ta kalli MAHMOUD din daya juya baya din bai fita ba yanajin saukar maganganun ummen har cikin ransa sbd idan har zarah tayi Dan kulawa ga Amatun bai kamata suga laifinta ba saidai ba halinsa bane tsayawa hayaniya. Kallonsa zarah tayi ahankali tace" Kana tunanin hakan kaima? Rintse idanuwansa yayi tareda juyowa ahankali ya kalli Amatun da itama idanuwanta sukai jajir kafin ya kalli zarah din cikin radadin Abinda zai fada yace" U could have asked kafin kibata maganin tunda Salman na Nan kokuma kifadawa ummen tun farko This is irresponsible of you zarah... Cikin bayyanarda tsananin damuwarta Amatu tace" Me kukeyi wa anty zarah haka? Kallonsa tayi Ido cikin Ido tace" Kuna tunanin anty zarah zata iya cutatar Dani ne ko me? Ni banganeba, Nice nace anty zarah tabani magani idan tanada bayan haka idan anty zarah tasan Ina tareda wani Abu atare Dani wlh bazata taba bani Abinda zai cutatar daniba bama haka wlh na tabbata a duniya idan akwai meson Abinda yake taredani bayan ni da mahaifinsa da Yana Raye to anty zarah ce idan da ace tasani, Meyasa zaku dasa ayar tambaya akanta Bayan dukkanin shedarta yakamata ku bayar, Umme kadaki zargi anty zarah akaina ko Abinda yake taredani Dan Allah ko anan gabane hakan Yana karya zuciyar me hakuri wlh, Zaku iya dasa Mata wani tunani na dabam Bayan ba haka takeba kunfi kowa sani musamman Kai zatafi Jin zafi idan kayi Mata wannan tunani""taqarasa fada tana dauke idanuwanta daga cikin nasa daya zuba mata Yana kallonta da idanuwa a bude sbd akaro na farko ta tayasa fadar Abinda yake cikin zuciyarsa sbd shine yafi kowa sanin zarah bazatayi ko kusan hakanba Akan wani bare akan wannan silly yarinyar. Numfashi ya sauke ahankali tareda kallon cikin idanuwan Amatun kafin ya juyo ya kalli zarah da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da taushin harshe yace" Lets go. Kallonsa tayi zuciyarta na narkewa,fushinta na wankewa sbd yanda yayi ya nuna kulawarsa gareta tareda nuna damuwarsa akanta Cikin sanyi tace meyasa nakesonka sosai hakane MAHMOUD DAHEER ZABEERA? Ahankali ta sauke idanuwanta daga kansa tana cewa'' Nakawo Mata breakfast inason zanbata da kaina. Wani irin kallon are you kidding me?yayi Mata Yana mamakin halinta na rashin Jin zafi. Murmushi tasake cikin sanyi tareda daga Masa Kai Ahankali yace ok tareda juyowa ya fice zuwa office din Dr Fatima. Qoqarin zuba Mata abinci umme tayi Amatun tayi saurin hanawa tana kallon anty zarah cikin murmushi tace" Umme antyna ce zata bani abinci da kanta Dan Allah. Kallon zarah din umme tayi cikin Jin nauyi kadan duk da ita Bata dauki maganarsu cin fuska ga zarah din ba sbd tun farko yakama kafin kabawa wani magani kabari likita ya rubuta Masa Mana. Iyami ce taqara dorawa da bawa zarah haquri tareda matsa Mata ta matso Dan bawa Amatun Abinda takawo Mata. Cikin farin ciki da cire damuwar Abinda ya wuce din ta zubawa Amatun kunun gyada da plantain ta miqa Mata tana cewa'' Kici sosai sbd kisamu qarfin haihuwa idan lokaci yayi Dan karki manta da alqawarin da kukaimin keda Dr khalil na cewa zaku bani Abinda zaku Haifa tun a wancan cikin na iska. Dariya kowa yayi a dakin Banda Amatu da kewar Dr da tunaninsa ya dawo mata. Yamma sosai aka sallameta Salman ya kalli su kawu da iyami Bayan dukkaninsu sun fito harabar asibitin za'a tafi gida yace" Kawu muje saina saukeku a gida su Kuma su tafi a motar umme ga Kuma motar zarah MD ma Yana cikin asibitin Naga shigowarsa kafin ayi sallamar inaga Yana tareda likitocin. Kallon salman din kawu yayi kafin ya maida kallon gun umme da Amatu yace" Ai Amatu tafiya zanyi da ita tayi takabarta tareda renon cikinta a gida sbd hankalin iyami rabuwa zaiyi da ni kaina.... Zaro idanuwa waje umme tayi hakama zarah dashi kansa Salman din. Cikin rawar murya umme tace" Kawu kayi hakuri Amma bangane ainihin Abinda kake nufi ba. Ina nufin tunda dai dama gida zata dawo ko Bayan takaba gwara Takoma can din tayi zaman idan yaso bayan haihuwar sai asan nayi...... Bayansa dukkaninsu sukabi da kallo Babu me iya Magana sbd girgizar zancensa Ganin suna kallon bayansa yasashi juyawa sai sukai Ido biyu da MAHMOUD dake tunkarosu cikin tafiyarsa me nutsuwa. ##Mamuh# *Littafin Nan na kudine kabiya ka karanta cikin nutsuwa da aminci.* 6/17/21, 8:05 AM - ': *_MQ 34_* Fuska kawu ya sake bayan isowar MD yace" MAHMOUD sannu da qoqari mungode sosai Allah yasaka yayi muku albarka duk ku duka Allah yaji qan Khalilu yayi Masa rahama tareda albarkar Abinda yabari a baya. Amin kowannensu yace jiki a sanyaye kafin umme ta Dora da fadin" MAHMOUD kayi Magana da kawu Dan Allah yabar Amatu harta haihu tukuna ayi maganar tafiyarta. Miqawa zarah takardar dake hannunsa Wanda Fatima tabayar kafin ya kallesu cikin rashin son Jan dogon zance yace" Kutafi zamuyi mgn da kawun Zan wuto da ita idan angama. Kallonsa umme tayi tana miqa dukkanin yardarta akan cika maganarsa na zai dawo da Amatun zabeera idan sun barta. Ahankali ya gyada Kai Yana Dan rufe Ido. Kallon Amatun umme tayi jiki a matuqar mace tace" Ina jiran dawowarki Amatu. Gyada Mata Kai tayi tana murmushin Bata qwarin gwiwa kafin ta kalli anty zarah da ita tayi wani iri tace" Anty ZARAH saki fuskan Mana saikace Rabin ranki ne akace za'a tafi dashi. Guntun murmushi anty zarah din tasake tana Dan hararar Amatun tace" Kina tunanin MAHMOUD zai barni yatafi wani gurin bayan tafiye tafiyensa? Kece dai abin jimamin sbd ba'a shiga Zabeera family a fita saidai mutuwa""taqarasa tana dariyar Amatun qasa qasa. Tafiya sukai suka bar Amatun taredasu iyami dasu kawun Nan kawun da MAHMOUD suka kebe sukai magana sai gashi sun wuce a motar Salman sun barta tareda MAHMOUD din Batareda yayi Mata kallo biyu ba ya nufi motarsa bayan yace suje. Drivernsa ita yafara budewa mota tashiga kafin ya zagaya ya budewa MD din yashiga ya rufe yafada motar shima ya tayar sukabar gurin. Jinginar da kanta tayi baya tareda lumshe ido ta sauke numfashi ahankali sbd imperial majesty dinsa daya gaurayu da AC dakuma qamshin motar saiyake Bata nutsuwa sbd dadinsa. Shikuma wayarsace datai ringing ya dauka yafara waya cikin nutsuwa a harshen turancin dayasata Dan bude Ido kadan ta saci kallonsa sbd ya tuno Mata da Dr khalil dinta idan Yana turanci zaunawa takeyi ta zubawa bakinsa Ido cikin burgewa da son koya sbd abin na matuqar burgeta tana sha'awar zama Yar gayun Yar Boko me zuba turanci Wanda tasan da Dr na Nan da yanzu tafara karatu Inshallah. Ajiyar zuciya ta sauke afili Wanda yasashi Dan waiwayowa kadan ya kalli gefenta kafin yaci gaba da wayarsa. Har bakin qofar palonsu motar ta tsaya direban yafito da sauri ya zagayo ya bude Mata batareda ta juyo ta kallesaba tace" Nagode""ta fice ta shige palon tana sauke numfashi sbd atakure take cikin motar ko dogon motsi bakada ikon Yi kamar an takura Masa ne shiyasa ko matarsa zarah wata ran basa kwana tare sbd yawan juye juyenta da motsi Wanda ke hanasa bacci ko kadan hakan Kuma na saka Rabin kansa ciwo. A palon ta tararda anty salamatu na qoqarin ajiye abincinda tafito dashi daga kicin akan dinning itada shafa'atu me aikinta. Wecewa tayi dakinta Kai tsaye tayi wanka da ruwan dumi sosai kafin ta fito ta sanya jallabiya tayi sallar magriba da akayi suna hanya tayiwa mijinta addua sosai cikin farin ciki da walwala take sbd cikin jikinta ya dawo da duk wani farin ciki datake tunanin ta rasa Dan kuwa Dr khalil dinta Jin take kaman yadawo sbd tasamu Abu mafi soyuwa daga garesa. Shafa cikin tayi bayan ta miqe ta zauna bakin gado ahankali ta tuno da cikin qaryarsu Wanda shauqin abin alokacin yayita shigarsu itada Dr Ashe ita kadai zata qarar da zuwan ranar, Idan namiji na Haifa baida sunan daya wuce na mahaifinsa inshallah. Wayartace tayi ringing ta juya ta kalla screen din wayar taga sunan USI Tasaki murmushi me Fadi tana daukar wayar kusan atare sukace" Lallaima. Dariya suka saki lokaci daya Jin bakinsu yazo daya tace" Allah USI nakusa gayawa kawu ya yafewa Yan can Kai, Yanzu duk yinin yau sai yanzu kake kirana. Dadina dake masifa ko numfashi bazaki Bari mutum ya saukeba, Yaya jikin to? Nayi waya dasu kawu yace ansallameki sunkoma gida. Eh da magribar Nan nadawo. Amah nayi Magana da kawu akan Zaki koma gida sbd zaifi Mana sauki harzuwa lokacin haihuwarki tunda ko haihuwa Kikai bana sakaran zasu karba Abinda aka Haifa din saiyayi wayo sosai kokuma idan Zaki koma makaranta Dagani har kawu Amatu karatu yanzu mukeson kiyi. Numfashi ta sauke tareda gyara zamanta tace" USI Nima naso komawa gidan saidai Kuma yanada wuya su Bari nabar Nan din shiyasama kawai nabari Bayan haihuwar saina koma gida tunda koba komai Ina haihuwa na fita takaba ba sauran dalilin zamana anan din Amma dai kawu yace zaizo gobe zasuyi Magana dasu Modibbon idan sun Bari din zankoma gidan idan Kuma sun buqaci na zauna harna fita takaban duk Babu illa tunda dai lokacin zaizo. Numfashi ya sauke cikin nutsuwa yace" To Allah ya saukeki lafiya shine fatanmu akan komai. Amin ya furta afili kafin suka shiga cikin zancen karatunsa dayayi nisa yanzu gashi Yana bada himma sosai Dan tuni ya goge cikin masu qoqarin makaranta. Da daddare umme da kanta tazo tayi musu fira har kusan qarfe goma kafin ta tafi anty zarah dai ce Bata sake gani ba sai washe gari anacan ana soyewa da Rabin Rai. Washe gari qarfe goma sha daya na Rana kawu ya iso zabeera tareda Dr Salman dayaje ya daukosa akan maganar komawar Amatu gida Dama Suma su Modibbon suna jiransa sbd tun jiyanma da MAHMOUD yayi musu bayanin Abinda kawun ya buqata sukaso zuwa har gida su samesa tun cikin Daren saigashi yace yace zaizo a yau din. Babban palon Andi suka Isa inda andin da Modibbo ke jiran isowar kawun Gaidasu kawai dr Salman yayi ya ficewarsa ya barsu suka Fara tattaunawa. Cikin nutsuwa Andi ya kalli kawu zaifara Magana saiga MD yashigo batareda yasan kawunma naciki ba. Cikin nutsuwarsa da girmamawa ya gaidasu tareda sanarda Modibbo zaiyi tafiyane yau takamasa Kuma zai kwana biyu kafin yadawo. Kallonsa Andi yayi cikin nazari harya miqe zai fice yace" MAHMOUD dawo ka zauna Magana zamuyi akanka da Dan uwanka marigayi tareda Abinda yabari. Maida kallonsa yayi Kan kawu cikin nuna Masa girma amatsayinsa na mahaifin 'yar dasuke son abarta cikin zuriar 'ya ko 'dan da zata Haifa yace" Mal Saleh tun jiya nakejin saqonka bakin MAHMOUD Da tun jiyan mukaso ganinka saikuma dai muka Bari yau din tunda yace kace zakazo din akan maganar, To Mal Saleh munji zancenka amatsayinka na mahaifin AMATULLAH Kuma bamu katsi hanzarinkaba amma maganar barin AMATULLAH kwata kwata zabeera Bata tasoba sbd koba komai dai ga rabo Nan ya ratsa a tsakani Kuma bayan hakan ma tun asali zabeera shiyasa ba'a auren waje sbd irin hakan duk da qaddara ce da Babu me gujewa saidai kuma tunda AMATULLAH tashigo zuria mezaisa ta futa Dan mijinta ya rasu bayan munada Wanda zai Kare mutunci da haqqin iyalin 'dan uwansa ko ayanzu da babu ran nasa?, Mal Saleh Kai ubane,bazaka so 'yarka Takoma gabanka ta Dora sabon zama na zawarci duk da Allah ne yaso hakan shiyasa muke fatan kaima kazabi barin 'yarka a killace cikin inuwar aure sabanin komawarta gabanka, 'yayanmu idan mazajensu sun rasu suna fita takaba da qanqanin lokaci muke aurar dasu ga Yan uwa mafi kusanci na mazajensu sbd dorewa acikin aure shiyasa ba alfahariba bamada tarin zawarawa acikin zuria sbd zawarcin ba Dadine dashiba, Maganar aure ga me takabar dake cikin takaba haramun ne shiyasa bazamuyi maganar auren AMATULLAH ayanzu ba Amma dai muna roqonka a matsayinka na mahaifin AMATULLAH daka barta anan tayi renon cikinta ta haihu bayan haihuwarta zamu nemawa Dan uwan mijinta mafi kusanci agaresa aurenta wato MAHMOUD Wanda Inshallah aranar sunan Abinda ta Haifa tareda radin suna zamu daura musu aure Inshallah idan harka bamu dama tare Kuma da amincewa. Numfashi me qarfi kawu ya fitar a fili tareda jinjina Kai sbd shima kamar yanda suka fada duk duniya Babu ubanda zaiso yarsa tadawo gabansa ta zauna ta dasa sabon zaman zawarci sai abisa qaddara, Qaddara ce ta saukarwa Amatu Kuma Dole sunkarba hannu bibbiyu saidai tunda tasamu wani tayin auren gskia bazaiqi amincewa ba tunda dama suna tunanin tattarawa ne subar gidan sukoma inda Amatun zatafi sakewa da Abinda zata Haifa to tunda har mutanen nan na qaunarta harda basa iya barin ta fita wani gurin dabam tayi aure Babu Abinda yafi Masa wannan saidai tunda ba halaccin maganar neman aure akanta ayanzu zai tafi da ita still idan lokacin haihuwarta yakusa tunda zata dawo daga baya. Aje numfashi yayi tareda koro musu nasa bayanin bayan amincewarsa akan idan takusa haihuwa Zata koma gida ta haihu gaban uwarta. Ba wani dogon sharhi suka amince akabar maganar akan Babu Wanda za'a sanarwa yanda aka aje zancen sai bayan haihuwarta idan lokacin Daurin auren yayi. Komai bai iya cewa ba sbd zancen baiyi Masa Kama da zai yiyu dinba idan har za'a tambaya ra'ayinsu kafin Daurin auren idan lokaci yayi. Sallama yayi musu tareda 'yar godiyar da batakai cikinsa ba ya fice Yana duba agogon hannunsa sbd yakusa lattin Isa airport. ##Mamuh# *_Dan Allah kuyi hkr kuyi manage inada uzurin fita ne amma Inshallah next pg saikun gaji da karantawa sbd tsayi_* 😁 6/17/21, 8:06 AM - ': *_MQ 35_* Godia kawu yasake kafin ya sake gyara zama bayan fitar MD yace" To akwai 'yan burirrika dakuma kamar sharadi zance kokuma dai nace alfarma damuke nema bayan auren. Cikin jinjina Kai Andi yace" Muna sauraronka Mal Saleh Allah yasa me dubuwace wannan alfarmar ko sharadin. Eh wato gskia Amatu dai na sha'awa dakuma ra'ayin zurfafa karatun zamaninta wato na bokon Nan Tajima da wannan burin bama ita kadaiba wannan burinane akansu tun suna Yara gaskia saidai Kuma Hali na rayuwa baibari tasamu ilimin bokon ba sosai, Shi kansa mijinta Allah yaji qansa kafin aurensu yayimin alqawarin barinta tasamu wadataccen ilimi bayan aurensu saigashi Allah bai basa iko ba Dan haka nake bayarda wannan buqatar ta barinta ta ilmantu acikin Boko Dan shi na addini Banda haufi akanta tasamesa yanda yakamata Inshallah, Wannan shine buqatata Idan MAHMOUD daku iyayensa zaku Bata wannan damar to Ina godiya da hakan. Tsit sukayi suna nazartar zancen nasa sbd maganar haqiqanin gaskia yaransu Mata basa karatu anan musamman masu auren sbd qasarmu na daya daga cikin qasashen da Basu dauki Mata da daraja ba idan angansu suna yawon neman ilimi makaranta musamman akan matan aure da akafi buqatar fasikanci dasuba ayanzu akan 'yan matan shiyasa suka zabi gwara sukai yaransu qararda ba'a sansu ba suyo karatunsu su dawo, Amma babbar matsalar anan itace ana maganar karatun Amatun ne bayan aure Kuma har wata qasar. Muskutawa Modibbo yayi ya kalla Andi cikin nutsuwa yace" Inaga Babu wata illa ko abin damuwa musamman tunda shi MAHMOUD din nada gida acan yawancin qasashen saita zaunama acan din shikenan. Numfashi Andi Yakuma saukewa kafin ya jinjina Kai ya kalli kawu yace" Yanxu duk ba lokacin wannan neba yanxu idan lokacin yayi zamuyi maganar insha Allah. Sake goggodewa juna sukayi tareda maganganu dangane da gadon da Khalil yabari shidai kawu baida tacewa hakadai suka kammala kafin aka Kira Salman ta waya yadawo ya daukesa Dan maidashi gida. ***Ahankali tasanyawa kanta hkr ta rungumi qaddarar rasuwar mijinta tareda rungumar Abinda Allah yabata ta maida hankali gurin renon cikinta Wanda kusan yanzu tsakanin itada umme da iyami da anty zarah sai oga kwata kwata MD ZABEERA ba'a San yafi qwallafawa cikin Rai ba, Iyami tuni tafara siyan robar wankan jariri dasu kujeran zaunawa akai ayi Masa wanka harma dasu kayan yajin abincin me jego Wanda kullum lissatafinta kenan, Umme ma Kam tuni akai nisa gurin tariyar kayan jarirai hardasu kayan wasansa, Anty zarah kuwa kayan me jegon tafi maida hankali gurin Dan siya Sai oga MD ZABEERA Wanda ya damesu ya shanye gurin Tara siyayyar kayan jarirai har wainda sai ya iya tafiya da gudu kafin yayi amfani dasu dan sunfi qarfin jariri Wanda daki guda ake Tara kayan acikin sashen Amatun duk yayi tafiya yadawo scan ake Kai kayan Wanda yasa Tunanin Yama fisu zautuwa wannan Rabin ran Anty zarah din. Tsakaninta dashi gaisuwa ne shima sai idan anci sa'a sun hade by mistake sbd saitayi fiyeda wata ko wata biyuma Bata gansa ba sbd sosai yanzu yarage zama sai yawan tafiye tafiye, Dr Salman kuwa yayi tafiya baya qasar tun cikinta na wata hudu yayi tafiyar Amma kusan kullum ayini shida USI batasan Wanda yafi wani kiraba, Cikinta yanzu Yana wata na bakwai Wanda yayi girma Dan daidai ba laifi Wanda yasa qafafuwanta Dan kumbura kadan shiyasa ma kullum ake fita da ita haraba tana Dan zagayowa sbd Dr Fatima tace taringa motsawa tana Dan zagayowa. Duk wani bayani da update Akan lafiyar cikin Dr Fatima MD ZABEERA take Fara Kira sbd agurinsu tamkar shine mahaifin Abinda za'a Haifa din and kowa yasan irin shaquwarta da qaunar dake tsakaninsa da 'dan uwansa kafin ya rasu so koba a fada musu ba sunsan Babu Wanda zai dauki responsibilities na cikin Bayan shi barema Kuma shine yabada wannan odar ta komai asanar dashi har ranar haihuwar ma'ana EDD dinta duk yasani. Zaune suke apalo itada anty salamatu da sai umme datazo dubata and kwana biyu tunda tashiga wata na takwas take fama da ciwon Kai me tsanani Dr Fatima tayita dubata ta sanar musu da tana fama da matsalar high BP ne Wanda Dole suyi monitoring dinsa sbd idan bai sauka ba yakoma normal to yanada wahala ta iya haihuwa da kanta saidai CS. Magani umme ta miqa Mata ahankali ta karba tareda karbar robar ruwan dake gabanta ta bude ahankali tana Dan lumshe ido sbd ko Ido ta bude sosai kanta kamar zai tsage, Maganin ta shanye tana ajiye robar daidai Dr Fatima na shigowa palon daukeda sallama suka juya dukkaninsu suka kalleta suna Mata sannu da zuwa Banda Amatun data kasa ko bude idanuwanta dake lumshe sai kawai taji hancinta na shaqo Mata qamshin imperial majesty sama sama, Bata bude idanuwanta ba sbd tasan baitaba shigowaba Kuma tasan baida dalilin dazai sashi shigowa din dan Daman da cikin yadamu bawai ita ba to Kuma Dr Fatima ma kafin tafada musu komai dangane da cikin saita fada Masa tuntuni haka suke Dan haka Bata sakaran akwai Abinda zai taba sanyashi shigowa.... MAHMOUD Kaine da kanka yau?""maganar umme data sanyata bude rufaffun idanuwanta cikin rashin sa'a sai acikin nasa daya zuba Mata akaro na farko daya kafeta idanuwansa Yana kallon cikinta daya Gama girma. Cire idanuwanta cikin nasa tayi akaro na farko wata irin tsananin kunyarsa ya kamata sbd ganin irin kallon dayakewa cikinta Ta 'dan muskuta ahankali tareda Dan Jan wuyar rigarta sama sbd budadden wuyane Dan doguwar rigace Mara nauyi Sam hannunta ma qarami ne irin na shimi. Ahankali ya dauke kansa Yana zaunawa a kujerar dake fuskantar Tata ya kalli umme ya bude baki cikin yanayinsa na nutsuwa cikin sauti me taushi yace' Barka da yau umme, Na sameku lfy? Lafiya kalau, Yaushe kadawo ne Dan last time Dana tambaya zarah tacemin kana Turkish. I came back this evening. Allah sarki to sannu da hanya. Thank you umme""ya furta cikin qaramin sauti sbd Sam kwata kwata rayuwarsa bai Saba da a nuna Masa kulawaba musamman daga gareta shiyasa yaji abin wani irin har baisan Yaya zai amsa Mata dinba Bayan da qananan kalmomi. Kallon anty salamatu data kawo Masa drinks yayi tareda Dan girgiza Kai Yana cewa'' No thank you bana buqatan komai am ok. Maida kallonsa yayi Kan umme cikin nutsuwa batareda ya kalli Amatu ba yace" Umme Dr Fatima tayi bayanin komai dangane da yanayin da ita take ciki wanda yakamata asan asalin menene yasa takasa kwantar da hankalinta kodan sbd lafiyan Abinda yake tareda ita, Meyasa bazaku fada Mata ta kwantar da hankalinta ba sbd high BP dinnan is a very serious issue and I can't.....sai yayi shiru yakasa qarasa fada ya 'dan kalli gefenta kadan tareda maida kallonsa Kan Dr Fatima yace" Please make her understand illolin BP game ciki please. Kallonsa Dr Fatima tayi kafin tajuyo ta kalli Amatun datake mamakin yanda Ashe dama Yana Magana haka sosai saidai maganar tasa tafi Kama da kamar ransa A 'dan bace yake. Cikin damuwa ma umme itama tace" Hakane kam Amatu Dan Allah ki cire damuwar idanma damuwar tsoron haihuwar kika saka aranki ki cire Zaki haihu lfy munanan munata Miki addua. Idanuwanta be suka ciko da hawaye har suka Fara gangarowa Wanda yasa kowa zuba Mata idanuwansa cikin mamaki da damuwa, Dr Fatima ce ta Kama hannunta tajata daki tareda ce musu karsu damu zata Magana da Amatun zataji matsalarta. Daki suka Shiga tareda rufo qofa suka bar su ummen zaune tsit cikin tsumayi. Kiran wayarsa akayi ya miqe ya fice a natse tareda daukar wayar Yana Magana kamar bayason Yi ya nufi hanyar sashensu. Kallon Amatu Dr Fatima tayi cikin nutsuwa da kulawa tace" Amatu karki damu ni likitarki ce duk Abinda na tambaya kada kiji komai karki boye ki fadamin sbd lafiyanki da abindake cikinki mukeso Kuma kema nasan bazaki so komai yasameku ba, kinada matsalar da kikeji ne dangane da cikin? Kokuma a jikinki? Numfashi ta sauke tareda sauke kallonta daga Dr Fatima din ta bude bakinta dayayi nauyi tace" Dr Fatima kaina ne ke tsananin ciwo sai Kuma kamar na daina Jin motsin cikin tun jiya..... Kallonta Dr Fatima tayi da sauri cikin 'yar razana amm zamtowarta likita saita saki murmushi cikin kulawa da kwantarwa da Amatun hankali tace" Jiya tun yaushe ne bakiji motsin ba? Tun da yamma danaji bansake ji ba. Sake wani murmushin me sauti tayi tareda dafa hannun Amatun tace" Kinga wannan ba wani matsalane babba ba zamu duba mugani inshallah baby lafiyansa kalau Bayan wannan menene Kuma matsalar? Dagowa tayi ta kalleta kafin tayi qasa da Ido cikin damuwa tace" Ciwon Mara saikuma gashi dazu Naga jini kadan kadan kaman Yana zuwa. Kama ne kokuma kingani din? Nagani""tafada Kai tsaye tana bayyanarda damuwarta. Ok Amatu kinaji karki damu sosai Dan akan wannan insha Allah yanzu zanje dake asibiti zandubaki acan sbd Kinga gskia lokacin haihuwarki bai Isa yiba ana haihuwane at 36weeks zuwa 40weeks harma fiye amma ke Kinga yanzu kina cikin 33weeks atleast Koda za'ayi haihuwar gaggawa ne Kikai ko 35weeks haka so yanxu zanje dake asibiti zamu duba matsalar mugani Amma kema saikin taimaka kin rage damuwar komai aranki sbd Kinga damuwace tasaka BP dinki rising and hawan BP Kuma na iya leading to komai so please Amatu kicire damuwa inshallah komai zaizo yanda ake so ake Kuma fata kinji ko?? Ajiyar zuciya ta sauke ahankali kafin ta daga Kai tana cewa Inshallah Dr. Dr Fatima ce kawai ta fito tabaro Amatun cikin daki dan tashirya tafito su tafi. Zama Dr Fatima tayi ta fuskanci umme data zuba Mata Ido tana tsumayin jiran Abinda zata fada musu ta Dan sauke numfashi cikin yanayi na damuwa kadan tace" Gskia akwai matsala dangane da yanda tace batajin motsin cikin gakuma zuban jini datace Dan haka inaga asibiti zamu Bata gado ta kwanta mufara monitoring BP dinta da lafiyar babyn har musamu takai lokacin haihuwar saidaima bazance ga komaiba yanzu sainaje asibiti munyi scanning munkuma dubata mungani musan meye abinyi. Ajiyar zuciya umme ta sauke jiki a mace yace" To Allah yasa miji alkhairi Min barwa Allah komai Allah yayi Mana jagora. Amin anty salamatu da Dr Fatima sukace Suma jiki amace. Dr Fatima ce ta miqe tafara ficewa tana latsa Kiran MD Dan sanar Masa halinda ake ciki. Cikin doguwar rigar jikinta ta fito sai dogon hijabin data sanyo. Fitowa sukayi umme na riqeda hannunta sbd qafafuwanta dasuka kumbura sosai daqyar take takasu ga mararta datai nauyi tana Mata ciwo. Baqar JUGUAR RANGE ROVER suka tarar pake a bakin qofar palon akunne sai qyalli take tana aiki duk da Basa ganin Wanda ke ciki kowannensu Saida ya ayyana MAHMOUD ZABEERA ne sbd shikadaine ke dukan irin wainnan motacin a zabeera duk da kowa na dukan kalar nasa arzikin. Shine da kansa yake tuqa motar Umme ta bude baya Amatun tashiga ahankali Yana kallonsu ta mirror kafin anty salamatu tashiga Umme tace suje zataje ta shirya zatazo daga baya. Jan motar yayi suka wuce Yana tuqin ahankali kamar Wanda ya dauko me naquda. Koda suka Isa Dr Fatima ta shirya komai Nan take aka karbeta akai nufi labour room da ita Dan acan zasu dubata suyi Mata scanning. Anty salamatu ana Shiga da Amatun ta daga waya takira kawu tafada Masa tana kashewa saiga Kiran iyami cewa gatanan zuwa. Tashin farko suna Gama dube dubensu suka gano ruwan dake riqeda babyn saura kadan su Gama tsiyayewa gashi lokaci baiyiba Dan ko kadan Bata Fara budewar haihuwa ba suna saka ran saidai CS gashi Kuma lokaci baiyiba da saura Dan haka mun yanke zamu riqeta anan muna kulawa da lafiyarsu har zuwa Nanda sati biyu tashiga 35to 36weeks sai ayi aikin saidai gskia babyn zaizo ba qwari muna fatan yazamto rashin qwarin kawai sbd irin hakan babies din yawanci na zuwa da matsaloli"""Dr Fatima ce take fadawa MAHMOUD ZABEERA hakan acikin office dinta bayan tabaro Amatun gurin nurses suna shifting dinta zuwa dakinda zasu ajiyeta. Zanyi tafiya Nanda 5 days but Inshallah I will be back before time din yacika Just do the best you can atare matsalar. Karka damu Mr zabeera Inshallah zaka dawo kasamu both the mother and the baby lfy. Thank you"yace tareda miqewa Yana dorawa da cewa'' Stefan zaiyi clearing bills na komai zuwa anjima. Kamar zaije dakin datake saikuma ya dakata tareda kallon qofar kawai ya wuce daidai isowar su iyami suka gaisa ya fice asibitin gabaki daya. Da daddare iyami ce kawai ta kwana tareda ita anty salamatu ranar gidansu ta wuce dan dama tanada niyyar zuwa gidan yau yin wani Abu saiga zuwa asibiti ya kamasu. Umme da Haj maryam ne suka Zo da daddare suka kawo musu abinci Anty zarah ma tazo takawo wa Amatun furar datake so, Gaba daya Kwanakin busy take da hidimar gidanta data MAHMOUD da yanzu ta dage sosai take farautar soyayya da kulawar mijinta Wanda Amatun ke sake zugata da Bata qwarin gwiwa Kuma alhmdlh tana samun ci gaba Dan ko last month tare sukaje UK sukaga wani likita Akan matsalar rashin haihuwar ta Wanda itace ta nuna tanason ganin likita cikin sauki kuwa ya amince Mata sukaje UK din daga can Sudan suka wuce Saida sukai kusan wata daya kafin suka dawo wanda tafiyar tasa tafara fuskantar asalin irin rayuwar da mijinta MD ZABEERA takeso wato rayuwar turai shida iyalinsa Wanda duk wayewarta ita Kuma takasa koyawa kanta sbd Sam ita saka qananun Kaya basa gabanta tafi ganin kyan kanta da burge kanta idan ta hade cikin kayanta na yarenta har gwara dogayen rigunan jallabiya taba sakawa sosai saigashi taga yanda yake rayuwa kamar asalin bature idan yabar qasarsa wato wasu irin personalities garesa boyayyu na burgewa ga wasu irin kyawawan manyan 'yan Mata masu aji dasuke huldar business dashi suna jansa da fira sosai Kuma ba laifi Yana 'dan sake musu shiyasa ta Raina kanta suna dawowa tafadawa Amatu damuwarta Wanda hakan ya sanyaya jikin Amatun itama saita Fara zugata akan ta zabure tafara duk Abinda tafara lurada yanaso tunda harta Fara samun Clue. ##Mamuh## 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 36_* Umme da kanta tabata abinci abaki taci tana qara jinjina zancen Dr Fatima data fada Mata kafin shigowarta akan inda aka tsaya da maganar matsalar, Ita kanta Amatun a sanyaye take sbd rashin sanin makomar abindake cikinta, Allah yasani tanason babynta Kuma tanason samun Abinda Bata fatan tayi wahalar banza shiyasama tunda sunce saita kwantarda hankali babyn zai samu shima lafiyar da akeso tafara iya qoqarin kwantarda hankalin saidai Kuma Sam tsoro da shakkar halinda babynta ke ciki ya Hana hankalin nata kwanciya. Iyami ce ta miqa mata kofin maganin tsiyayewar zaqi tana cewa'' Karba ki Dan Sha ko kadan ne zai taimaka idan haihuwar ta taso gaba data. Kallon kofin tayi tareda karba ahankali ta kurba tana rintse ido sbd rashin dadinsa ta ajiye cup din tana girgiza Kai tace" Iyami bazan iya Sha da yawa ba wannan ya Isa Yana sakani zafin zuciya da yawa. Fura me sanyi anty zarah ta zuba Mata ta miqa Mata Wanda itace ke cewa tafisonta da sanyi sosai idan ba hakaba Bata iya Sha abin Sha idan baida sanyi Sam. Karba tayi ta shanye atake tana cewa aqaro Mata saidai aka miqa Mata jug din daya Gama daukan sanyi shima. Shan furar takeyi sunata kawo Mata firarraki kala kala Dan dauke Mata hankali kota cire damuwa da tsoron kwata kwata, Sai dare dukkaninsu suka watse aka barta daga ita sai iyami sai anty salamatu dasuka Zo taredasu maman junior dasu maman basiru Dan dubata kowanne dauke da kularsa ta kayan gargajiya na marmarin me ciki, Maman junior sakwara da jar Miya ta kawo Mata wadda taji yaji sai maman basiru data kawo Mata danwake dayaji salad da kwai anty salamatu ma taga soyayyar gyada ahanya da Madara gasassa ta siyo Mata duk saitaji idanuwanta sun cicciko da hawaye har batasan lokacinda tasakesu tana sunkuyar da Kai sbd ayau tasake tabbatarda ba jininka ne kawai Dan uwankaba wani Dan uwanma yafi na jini, Bata damu da son sanin asalintaba ko jininta wainnan bayin Allahn sune Yan uwanta sune jininta sbd suna qaunarta tamkar jininta Dan haka Bata buqatan sanin inda ta fito Dan kula kawu da iyami tareda usinta sune asalinta hakanma ya Isa rayuwa Alhamdulillah. Share Mata hawaye anty salamatu tayi tana cewa'' To meyene na kuka Bayan Dr tace ko damuwa ba'a so bare Kuma kuka, Wannan abin damukeyi duk yiwa Kai ne sbd mu tamkar zuria daya ne idan baki manta ba yawancinmu dake gidan bamuda zuria,bamuda dangi mune Yan uwan junanmu Dan haka meye abin damuwa aciki. Iyami dai batace komaiba sbd ita wani lokacinma ayanda takejinsu aranta har mantawa takeyi da ba itace ta haifesuba sbd har cikin ranta take qaunarsu a haqiqanin gaskia. Take suka cika dakin da hayaniyar gida dasuka Saba ana tuttuna baya da irin fadace fadacen dasuka sabayi Wanda haryanxu ba dainawa sukayiba Nan take ta sake saigata ta washe acikinsu tana walwalarta harda dariya da qyaqyatawa Taci sakwara kadan hakama Dan waken taci sosai shikam kafin ta Dora da masararta tanaji suna firarsu Basu bar asibitin ba sai goma da wani Abu kafin suka tafi anty salamatu ta rakasu kafin tadawo Amatun tayi bacci cikin nutsuwa Wanda ta kwana biyu batayiba. Washe gari da Dr Fatima ta auna BP dinta taga ya sauka sosai sai abin yabata mamaki takalli iyami cikin Jin Dadi tace" Tayi bacci ne sosai jiya? Eh Kam jiya tasamu bacci Dan sallah ma saidai da safen Nan tayita. Masha Allah gskia idan da zata riqa samun hakan to da Inshallah komai zaizo da sauqi yanda mukeso. Jin hakan yasa iyami ta aika salamatu tayiwasu maman junior Magana akan su riwa zuwa Dan Allah suna kawowa Amatun firar dare Ba musu suka amince sbd Suma zasuso tasamu lafiyar. Aikuwa tuni asibitin Takoma majalisar 'yan gidansu Dan kuwa idan sunayi dariyar Amatun har qofan daki anaji umme ma data ga hakan saita qarawa zuwan nasu armashi ta aiko musu da lafiyayyan abinci da pepper chicken na kaji kullum aikuwa Suma ganin wannan dadin yasa suka sake dagewa da kullum gida suke kwaso abinsu sai sun iso gida araba abawa kowa nasa Kuma kajin ba 'yan kadan ba ga drinks gakuma kudin abin hawa da anty zarah ce itakuma ta Basu Wanda zasu riqa amfani dasu Dan da farko kawu ne duk sukazo yake Basu na komawa sai anty ZARAH ta dauke Masa wannan nauyin. Kwananta takwas a asibitin ranar na Tara ta tashi da wani mummunan ciwon kai wanda yasanya jini da ruwa 6alle Mata take hankalin dukkanin likitocinta tashi musamman Dr Fatima Su kansu su umme dasu kawu kowa yashiga tashin hankali musamman ganin yanda take wani wani Abu kamar jijjiga haka aka kwasheta akai labour room da ita aka barsu tsaitsaye suna Kai kawon jira cikin rashin hankali. Kafin qarfe hudu na yamma dukkanin 'yan uwanta da wasu daga cikin familyn ZABEERA suna asibitin Babu me wata walwala acikinsu sbd har lokacin Babu wani labari daga likitoci sai yawo ake ana fita ana shiga. Dr Fatima ce ta fito Bayan tayi waya da Modibbo ta sanar Dasu komai na halinda ake ciki ta kalli kawu da umme da iyami dake gabanta cikin office dinta dake cikin labour room cikin tsananin damuwa da sanyin jiki tace" Wato Abinda ake ciki shine Amatu bazata iya haihuwa da kanta ba sbd lokacin haihuwar baiyiba gabanta ko kadan bai Fara budewaba gashi baza'a iya jiraba sbd qarfinta zai qare hakama babyn ruwan dayake ciki kowane lokaci zasu iya tsiyayewa Wanda hakan na faruwa hadari ne Mai matuqar girma Kuma barazana ce ga rayuwarsu su duka, Dan haka bazamu Bata lokaci ba na sanarwa su Modibbo zamuyi Mata aiki saidai Abinda zata Haifa din zamu sakasa a kwalba sbd rashin isarsa haihuwa idan Allah yasa andace... Tsit sukayi kamar wainda sukaji mugun labari, Koda yake kusan hakan ne Dan umme tuni tafara hawaye sbd tasan rasa babyn zatayi kamar yanda ta rasa Khalil dinta. Numfashi kawu ya sauke cikin jarumata yace" To shikenan likita ba damuwa ayi aikin Allah yasa hakan shine mafi alkhairi yasa Kuma ayi cikin sa'a. Amin tace tana qoqarin amsa wayarta da Kiran MAHMOUD ZABEERA ke shigowa Dan takirasa dazun bai dagaba. Itace tafara Magana sbd tadan fahimci bai cika maganaba yafi saurare Dan haka Bayan ta Masa ya aiki saita Fara koro Masa bayanin halinda ake ciki ta Dora da cewa'' Modibbo yace Kaine zaka saka hannu a file din gashi Kuma bakanan and bazamu iya wuce Nanda 20min ba bamu Shiga da itaba ba sbd....... Kai tsaye cikin wata murya me sanyi ya katseta da cewa'' I will be there in 10min yanzu nake baro airport. Kafin tayi Magana ya datse wayar ya ajiye gefensa ya sauke sanyayyan numfashi tareda rufe Ido ya bude ya kalli Mal Umar yace" Mal Umar Yi parking. Ba musu yayi parking din saiyaga ya fito daga Bayan motar ya zagayo gurin sit din driver ya bude yace" Fito ka koma baya zanyi tuqin. Fitwo Mal Umar yayi da sauri batareda yace komaiba duk da Yana cikin mamaki Amma dai sanin ba Abinda yafi tsana wani lokacin kamar tambaya yasa baice qalaba ya zagaya ya Shiga dayan gefen ya zauna. Batareda ya kalli gefen mal Umar dinba Bayan ya shiga ya tayarda motar yace" Saka seat belt dinka. Da sauri ya janyo ya saka. Wani lafiyyan speed yabawa motar Wanda yasa Mal Umar saurin hade qafafunsa Yana hadiye yawu tareda damqe qofa Yana zazzare idanuwa dan ba halin Magana bare ya nuna tsoronsa, Allah ya kaimu inda zamu lafiya yafada cikin ransa Yana satar kallon MD din dake sake bawa motar wani mugun speed din Wanda yamanta rabonsa da irin wannan tuqin qila tun Yana cikin samartakarsa idan Khalil ya matsa Masa Akan suyi tseren mota a Sudan idan yaje gurinsa. Fitowa Dr Fatima tayi daga labour room sanyeda kayan CS tana duba agogon wayarta datakeson kashewa kafin Shiga CS din taga minti Tara kenen da wayarsu da MD Amma haryanxu shiru ga kowa jigum jigum shi ake jira yazo yasa hannun ga Modibbo ma ya iso asibitin Amma baisaka hannunba yace ajira MAHMOUD din tunda yace abasa mintuna kadan... Kamar daga sama har zata juya cikin room din saigashi ya doso gurin cikin tafiyarsa me nutsuwa da cika Ido take kowa ya juya Yana kallonsa Yana tahowa in calm Sam baka ganin gaggawa ko sauri ko firgici ataredashi shi mutum ne daya iya controlling yanayinsa duk qwaqwarka baka ganewa saidai idan ka kalla cikin idanuwansa kake iya gane Abinda yake ciki saidai Sam ganin idanuwansa ba Abune me yiyuwaba ga kowa Dan baya Bari. Yana qarasowa ba wata Magana Dr Fatima ta miqa Masa file da biri yayi signing tareda juyawa zuwa blood bank dinsu sbd tun a waya yafada Mata basa buqatan jinin asibiti. Anshiga tiyatar da qarfe biyar na yamma shiyasa gabaki daya ward din cike yake da familyn ZABEERA ko biyowa ta gefen ba'a yi sbd ba'a buqatan hayaniya suna buqatan silence sbd suji da damuwar dasuke ciki, Damuwar iyami da kawu tsakaninsu da Allah tafi karkata ne Akan su samu 'yarsu tukuna kafin suyi maganar abindake cikin shiyasa sukafi kowa damuwa ga USI da Dr Salman sai Kira sukeyi sun Hana kowa sukuni qarshe ma dai kusan wasu kashe wayoyinsu sukayi wasu Kuma suka sanyasu silent. MAHMOUD na tareda Modibbo a office din Dr khalil zabeera Wanda haryanxu wani bai shigaba tukuna suna jira Modibbo ne Dai ke wayoyinsa shikuwa MD ZABEERA Yana zaune ne yayi crossing legs idanuwansa a lumshe yana karkada qafa. Ana fitowa sallar magriba nurse na fitowa daga theatre ta cikin labour room fuskarta daukeda da murmushi da farin ciki tun Kan ta qaraso duk suka miqe suna kallon bakinta tasake sakin murmushi tace" Ansamu baby boy....... Masha Allah, Masha Allah, Masha Allah alhmdlh, alhmdlh" Sune kalmomin da suka karade gurin atake kowa na fada Yana washe baki Umme Kam tana fada idanuwanta na cikowa da hawayen farin ciki hakama iyami da kawu daya kasa zama guri daya yafita waje yadawo. Anty zarah kuwa karo na farko dataji idanuwanta kamar zasu ciko da hawayen kwadayin samun dukkanin Abinda Amatu ke samu musamman irin wannan soyayyar daga kowa ga Kuma babynta tasamu. Hamdala Modibbo yayi lokacinda nurses biyu suka fito da jaririn dunqule cikin wani qaton farin bargon jarirai acikin kwalba., Babu Wanda aka Bari yashiga dakin kwalbar jariran sai Modibbo da MAHMOUD din sbd jaririn baida lafiya sosai Dan gabaki dayama kalar fatarsa ta Dan sauya saidai tubarkalla jaririn Yana haske sosai da dogon hanji kamar dukkanin iyayensa. MAHMOUD Modibbo ya miqawashi Yana tayasu murnar samun qaruwa tareda addua ya fice yabarsa. Shiru yayi akaro na farko yaji hannuwansa na rawa game da daukar Abu sbd kaf rayuwarsa Yana sakaran wannan ne karo na biyu daya taba daukar jariri sbd baida Wanda zai haihu yabasa danshi ya dauka, Karon farko daya taba daukar jariri shine lokacinda wani babban abokin kasuwancinsa ABDUL LAYE da matarsa ta haihu suna Greece shine yayi Masa huduba ma sbd shaquwarsu sai yau da Allah yabasa ikon daukar 'dan Dan uwansa Wanda yake shine ubansa yanzu Koda kuwa ace Khalil din na Raye yasan shine zai Masa huduba bare yanzu dayakeda gaba daya responsibilities din na yaron, Fuskarsa yadan bude ahankali ya kalla wani sanyi da nutsuwar zamowa uba na shigarsa Sai yanxune yakejin Abinda zarah ke fada nason zamowa uwaye suma wata ran, Haka kawai sai yasamu kansa da murmushin dayasa nurse din dake tsaye kusan sumewa tana kallonsa da dukkanin girman idanuwanta kamar zata cinyesa baki sake. Dagosa yayi yakai fuskarsa gurin kunnen jaririn ya karanto Masa Kiran sallah da addua tareda Sanya masa dukkanin albarkarsa dakuma yiwa Khalil addua. Saida ya Dan jima kafin ya miqawa nurse din aka maidashi cikin kwalba ya fice. Office din Dr Fatima data gama sauyawa tagama signing na fitowa tiyata tana zaune tana harhada kayan tafiya gida saigashi yashigo Nan tasake Masa bayanin Alhmdlh Amatu insha Allah komai lafiya data wartsake shikenan ba wata damuwa saidai jaririn Kam baida lafiya sosai saidai yanzu ita matsalar jaririn ba nata bane yanzu Dr fatihu ne zaiji da matsalar jaririn shizai Basu bayanin komai zuwa da safe Dan haka tana tayasu murna da fatan Allah yakawo abin da sauki. Kusan atare itada MD din suka bar asibitin zuwa gida Dan ko dakin da amatun take bai jeba ya wuce gida Modibbo ma tuni ya wuce. Sosai suke ta hidimar kulada Amatun tun cikin dare data farka tuni nurses suka sake gyarata aka kimtsa komai Koda qarfe goma na safe tayi kowa yazo ya tararda ita a zaune sai abin nasake Sanya kowa farin ciki. To kusan dai murna komawa ciki takusa Yi sbd bayanin da Dr fatihu yayi musu dangane da jaririn Wanda yanzu haka da oxygen yake numfashi kadan kadan baya iya shaqar numfashi da kansa, Sanyi ne da rashin motsawar jijiyoyin yawon jini ajikinsa sukai Masa mugun qarfi gashi ko qarfin kuka yarin baida a taqaice dai Yana buqatar blood transfusion. Babu Wanda yakai MAHMOUD da Amatu tashin hankali sai umme ma da abu yadawo na damuwa shiyasa duk abin yakoma ba murna kamar ba haihuwa akaiba. Ahankali ita ta warware tasamu sauki sosai Dan kullum da kanta take zuwa dakin da yake tadubosa, Kwana shida dayin CS din ta murmure matuqa sai Dr Fatima tabata sallama Amma sbd jaririn sai jinyarsa ta dawo musu sabuwa saidai kullum tana zuwa gidansu tayo wanka ta huta tadawo. Batareda sanin kowaba MAHMOUD ya bincika wani qwararran asibitin Yara dake Greece take yasa ayi musu Shirin tafiya Ya sanardasu Modibbo Nan Suma sukai na'am da hakan Dan dama tuni Andi shima yafara bincikawa wasu qasashen., Da Amatu da anty salamatu sai umme datace zata aka hada tafiyar shi MAHMOUD zasu rigasa zuwama sbd baya iya tafiya da Mata sam. Andi dayazo har gidan kawu da kansa da Daren laraba ya gyara zama Kan tabarmar da aka shimfada Masa bakin masallacin qofar gidan yace" Mal Saleh maganar tafiyar yaran Nan inaga zaifiwa kowa kwanciyar hankali idan aka daura auren kafin sutafi sbd su samu isashen lokacin nemawa KHALIL qarami lafiya daga Nan har lokacinda Allah zai basa batareda mu munshiga wasi wasiba Suma Basu Shiga takuraba Shiyasa nace amatsayinka na mahaifinta Zan Sanar maka idan ka amince a daura Bayan sun dawo sauran abubuwan sa biyo daga baya. Numfashi kawu ya sauke Yana muskutawa cikin jinjina kai yace" To Nima dai da bakazoba inada niyyar zuwa da safe sbd zuciya data kasa yardarmin tafiyar hakanan sakaikai duk da ba ita kadai bace Amma hakanan nayita wasi wasin su sauran idan sungaji dawowa zasuyi abarota ita kadai sai hakan bai wani kwantaminba gwara a daura Kam Nima yafimin nutsuwa. To shikenan nagode sosai Mal Saleh Kuma Inshallah gobe za'a aiko kudin auren idan Allah yakaimu juma'a sai a daura tunda ranar juma'ar da daddare zasu wuce shikuma MAHMOUD din asabar da safe zai wuce. ##Mamuh# 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 37_* *_kina da burin koyon sana'a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_* *_kin jima kina sha'awar yadda yake hada BIRTHDAY CAKE DA DECORATION amma kin rasa wajen da zaki koya?,ko FARASHIN YA MIKI TSADA?_* *TOFA MATA!* *_Ga dama ta samu_* *_UMMU AYMAAN KITCHEN ta shirya tsaf don koya muku yadda ake hada gangariyar BIRTHDAY CAKE wanda ya gama hada dukkan gamayyar kayan dadi masu sanya harshe su motsa,gefe guda kuma ta koya miki yadda zaki qawata waje da walwali da kuma walainiyar KAYAN ADO DA QAWA na wajen gudanar da SHAGALIN BIKI SUNA TARON BIRTHDAY WEDDING ANNIVERSARY da sauransu_* *_ba'a nan UMMU AYMAAN KITCHEN YA TSAYA BA,tana da ajujuwa na musamman don koyar da mata nau'in girke girke MAIDA TSOHUWA YARINYA,hakanan tana karbar kwangilar abincin taro kowanne iri_* *_ta fannin kayan maqulashe na fulawa ta samar da abubuwa kamar haka_* Cake perfait Cup cake Samosa Springrolls Meatpie Doughtnout *SIYAN DAYA KO SARI* *_za'a koyar dake BAKING AND DECORATION QIRI DA MUZU ta sigar zancan nan da hausawa kance GANI YA KORI JI,gani ga malama_* *_sa'an nan kuma akwai tanadi na musamman ga masu sha'awar koya ta hanyar yanar gizo wato ONLINE,duka kan farashi mai rangwame_* *_ZA'A IYA SAMUNTA A UNGUWA UKU,LAYIN MAI FATA ZARIA ROAD* KO A TUNTUBETA A WANNAN LAMBAR WAYAR 08032964266 *_ZA'A GUDANAR DA KOYARWA NE ON 5&6,GARZAYA MAZA KI REGISTER*🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀ï¸? Bayan tafiyar Andi gyara zama kawu yayi Yana fiddo wayarsa cikin babbar rigarsa ya Danna Kiran USI Dan sanar dashi komai sbd shi dama iyalinsa sune abokan shawarar sa. Kamar yanda tsammananta Usman din yayi na'am da ayi auren kafin sutafi zaifi bawa kowa nutsuwa dan haka take suka qara tattaunawa suka Kai qarshe Bayan dawowarsu ayi walima saita tare shikenan. Cikin gidama Yana Shiga Kai tsaye dakin Amatun ya wuce dan tadawowarta gida take kwana duk da komai nata na zabeera har lokacin sbd bawai ansallami Khalil qarami bane Kuma Nan gidansu yafi Mata sauqin zuwa asibitin kullum akan zuwa daga zabeera. Kallonta yayi tana waya da umme ahankali sbd gabaki daya ciwon Khalil ya karyar Mata da jiki da zuciya sai tanajin tsoron rasashi kaman yanda ta rasa babansa shiyasama ta dauki burin samu waraka akan tafiyarnan dazasu Yi a matse take dasu tafi sbd ganin takeyi dasun tafi Khalil dinta zai samu lafiya. Ganin tana waya yasa yafasa mgn ya qyaleta har zuwa gobe yayi dakinsa inda ya tararda iyami ita Kuma tana kunna musu tsintsiyar qamshi bayan tagama gyara dakin Wanda tsafta kyakkyawar dabiarta ce Sam Bata rabo da gyara da qamshi. Zama yayi Kan babbar daddumar tsakar dakin bayan ya cire babbar rigarsa ya sauke numfashi Yana cewa'' Iyami zoki zauna Magana zanyi dake akan 'yarki. Juyowa tayi ta kallesa taga Babu alamun fitarsa daya same ataredashi saita kunna sauran dayar tsintsiyar qamshin ta sokata a jikin qofar shigowa ta qaraso gefensa ta zauna Yana cewa'' ALLAH yasa lafiya dai wannan nutsuwa danaga kayi¿ Nufinki banda nutsuwa iyami? Wato dai haryanxu duniya batai Miki darasin yiwa miji biyayya ba kokuwa dai sbd kin Raina........ Katsesa tayi da sauri da cewa'' Dan Allah Yi hkr ya Isa kada mu komawa halin dare ne ana jinka har maqota, Munyi jika yanzu wani abin dai Dole mu barshi Dan haka Yi hkr ba nufina kenan ba. Shiru yayi kamar yafasa maganar tsawon mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya yasake kallonta yace" Andi ne da kansa yazo dazun Nan Sunxo nemawa MAHMOUD auren Amatu abisaga suna neman alfarma sbd basa barin matan yayansu su fita wani gurin dabam suyi aure Kuma dai ba laifi Nima na yaba da shawarar su sbd kwata kwata bana fatar Amatu tadawo gida ta zauna munsamu tayi aure zata samu ingantacciyar rayuwa saigashi Ashe mijin bame kwanakine agaba ba...... Kasa barin ya qarasa zancensa iyami tayi ta katsesa cikin tsananin mamaki da fargabar maganarsa da cewa'' Mijin Zarah fa kuke maganar aurawa Amatu idan dai MAHMOUD din Dana sani kuke Magana akai. Wani kallo kawun yayi Mata cikin rashin fahimta yace" Eh shifa mijin Zarah din ake Magana wani abin ne? Ta Yaya kuke tunanin hada zarah da Amatu kishi fisabillah bayan kunsan yanda suke matuqar qaunar juna ga kishi mugun Abu ne Dan Allah ku sauya shawarar Nan idan basaso Amatun tabar zabeera gaba daya Baga Salman Nan ba sai ahadasu Amma Dan Allah Ina Amatu Ina auren mijin Zarah...... Kallon mamaki da shashanci yake yimata cikin 'yar hasala yace" Meya kawo maganar kishi da rashin yuyiwa? Shine yafi kowa cancantar ya riqe iyalin Dan uwansa dakuma zamowa uban Muhammadu Khalil mu shi muka duba bawai kishi ko wani tunaninku na Mata daban ba, Yanda suke qaunar junan nasu ai shikenan sunsamu damar zama tare har abada Kuma bawai anyi ne Dan cin zarafin ita zarah din ba anyi ne sbd ganin hakan ne ya kamata, Shi MAHMOUD tun ranar farko da akayi zancen gabansa akayi Kuma bai musaba Dan haka ni me 'ya mace bazai yiyu ace ansamu tangarda ta gurina ba Dan gaka ki aje maganar kishi da rashin yakamata a gefe tun kafin Amatun taji ta samu qarfin ji daga gareki, Sannan Banda abinki shin ba abin farin cikinmu bane da Jin Dadi tareda kwanciyar hankali ace mun aurar da yarinyar Nan ba adaidai irin yanxu datafi buqatan Wanda zata jingina dashi amatsayin Miji Kuma uban danta, Kina tunanin duk yanda zabeera suke qaunarta da Bata kulawa idan tana gida zaune wata ran sai ta fuskanci juyin rayuwa wani Kai tsaye zai sheganta danta,wani akan 'dan sai afasa aurenta shin kin manta irin rayuwar data fito ne bayan tsanani da jajircewar Dr khalil aka samu ta watsar da komai shine yanxu zamu vari me tadawo zaman banza Wanda bama fata amma komai zai iya faruwa., Ki aje maganar shaquwarsu da yakamatanki mu fuskanci ci gaban yarmu Dan kuwa aure gareta yanzu shine babban rufin asiri. Numfashi ta sauke me nauyi kafin tace" Dukkanin bayaninka naji amma bana saka ran wannan auren Abune da Amatun zata karba Dan kuwa Ayanda nasan tanajin zarah to zata gwammaci mutuwa ba aure data auri mijin Zarah. Wace irin maganace wannan iyami kike fada? Wlh maganar gskia kenan nake fada maka Amatu bazata yarda da auren mijin antyntaba nake fada maka Tun wuri kafin Azo aji kunya kayi Magana da ita kaji Dan Nafi kowa sanin ba amincewa zatayiba Ai ana barin wani halak din ko Dan kunya, Amatu tafison koba soyayya tsakaninta da salmanu ta auresa idan anyi Mata tilas dadai ta auri MAHMOUD. Shiru kawu yayi zancen iyami na sanyasa nazari, Idan Amatu ta bijire ta dage tabbas zasuji kunya Kuma dai Allah yasani yafi buqatar tayi aure ayanxu data zauna zaman zawarci Kuma, Gskia bazai Bari hakan yafaru ba zai tabbatarda ta amshi wannan auren hannu bibbiyu Amma kafin Nan bazai sanar da ita komaiba sai andaura auren Inshallah ta yanda kotaqi kotaso bazata iya kubucewa aurenba. Kallon iyami yayi Yana tattaro dukkanin hankalinsa yace" Kada ki sanar da ita komai dangane da hakan yanxu sai Bayan auren Kin fahimta ko? Da mamaki tace" Meyasa?? Sbd kada asamu damuwa. Shiru tayi ta danyi nazari kafin ta jinjina Kai tana cewa'' To shikenan Amma dai dakun sanar da ita tukuna zaifi.. Zan aurar da ita amatsayina na ubanta Bayan auren Zan Sanar da ita alokacin danaga ya dace Dan haka na rufe zancen daga Nan. Washe gari kamar yanda Andi yace da yamma sun aiko da kudin aure tareda sadakinsu da katin daurin auren Wanda aka bugo da safen sun karba tareda adduar zaman lfy me dorewa ga auren. Take maganar Daurin aure ta Bazu koina sbd fitar katikan Daurin auren ga Kuma sanarwa agidanjen radio da talabijin musamman daya kasance auren mutum me suna kamar MD ZABEERA guda, Take abokanan hurdarsa manyan mutane suka Fara Kira suna tayasa murna tareda saka zuwa Daurin auren cikin mahimman aiyukansu na washe gari., Umman zarah ce tafara Jin wannan mugun labarin Wanda ya sanyata cikin tashin hankali da rashin nutsuwa saidata Kira zarah din wadda daga bakin umman tata itama tafara Jin wannan mummunan labarin daya sanya qafafunta qasa daukarta ganinta ya dauke ta sulale agurin ta Fadi zaune tana qoqarin Kiran sunayen Allah Amma suna bace Mata sbd tashin hankali daqyar ta iya cafko sunan Allah daya ta furta tana lalubar wayarta tareda shiga social media take kuwa ta ringa cin karo da hotunan katikan Daurin AUREN dakuma masu cewa zasu sako hoton macen datai sa'ar shiga rayuwar MD ZABEERA akaro na biyu bayan matarsa ta farko wadda haryanxu duniya batasantaba. *MAHMOUD DAHEER ZABEERA* da *AMATULLAH K SALEH* sune sunayen datake ta maimaitawa akan hoton Daurin auren idanuwanta nason kawo ruwa Amma tashin hankali da tsoro yaqi Bari. Sama ta nufa dakin MAHMOUD din Wanda tun rana daya dawo ya shige bai fito ba Ashe sbd yasan fitinar daya dauko ne, Babu bugawa yau Kai tsaye ta bude kofar palonsa ta shigo ta nufi bedroom dinsa ta tura ta shige zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sbd gaf kwanyarta take da zautuwa, Bayani kawai takeso daga MAHMOUD din kokuma Amatun sbd wata zuciyarta takasa yadda da wannan Abinda saitana kallon abin tamkar a mafarki Sam takasa gasgatawa. Kwance yake Kan gadonsa ya qure AC idanuwansa a rufe daga gani ba bacci yakeyiba saidai Kuma batada tabbacin idonsa biyu, Farin wando da farar rigace Mara hannu ajikinsa sai fararen qafafunwa dayau bai sakawa safa ba sunyi fari tas dasu tafin qafar kamar Baya taka qasa fuskarsa sai annurin kwarjini yake fitarwa take taji hankalinta yasake tashi da kishinsa duk da tasan bama Abune me yiyuwaba mijinta yaso Amatu sbd halayensu sunyi gabas da yamma sam Babu Abinda zaisa ma ya iya kula Amatun amatsayin Mata. Qarasowa kansa tayi ta tsaya zatayi Magana sai kawai kuka ya kufce Mata Mai Dan qarfi batasan lokacinda ta durqushe agurinba tana rufe fuskarta kukan na qara tsanantuwa. Bude idanuwansa yayi dasukai jajir sbd pressure dayashiga shima akan wannan auren Wanda yayi Magana dasu Modibbon sun nuna babu fashi kawai yaje yayi Shiri, Bai iya hayaniyaba bare gardama da manyansa shiyasa kawai ya taho sbd bazai iya tsayawa hayaniyar gardama ba dasu Modibbo musamman da Andi yafara daukar zafi kamar zai Dora laifin akan Modibbo shiyasa kawai ya taho yabarsu suyi yanda suka dama din, Yaso yayiwa zarah bayani Amma sbd Koda yashigo yaganta cikin walwala saiya share da nufin idan yadawo tafiya zaifada Mata idan Kuma taji shikenan saisuyi mgnar. Tashi zaune yayi ahankali tareda miqewa tsaye Yana zuba Mata idanuwansa dasukai jajir ahankali yaringa nazarinta sautin kukanta na fita ahankali Yana shigarsa sai kawai yaji zuciyarsa da jikinsa sunyi sanyi tausayinta na sake kashe jikinsa ahankali ya durqusa ya kamota ya dagota tareda sanyata cikin jikinsa ya rungumeta sosai Yana Dan bubbuga bayanta batareda ya iya cewa komaiba. Kusan mintuna da dama suka shanye a tsayen Yana sake Bata kyakkyawar runguma harsaida kukanta ya rage Takoma ajiyar zuciya tana sake shegewa cikin jikin nasa. Zaunawa yayi bakin gado tareda zaunar da ita Kan cinyarsa ya kwantar da kanta Kan kafadarsa Yana hade hannuwansu cikin na juna suka damqe ya dago ya kalli cikin idanuwanta da itama shi take kallo ya sakar Mata wani kyakkyawan murmushin daya saka jikinta mutuwa ya bude baki ahankali yace" Zarah kada ki taba tunanin bana son ki sbd irin rayuwar zaman damuke, All my life Babu abin Dana sani Bayan kadaici, Bansaba rayuwa da kowaba, Bansan ta Yaya Zan sake cikin mutaneba nayi rayuwar walwala ba acikinsu, Mutanen waje sune wainda na Dan Saba dasu sbd sune mutanen dasuka Saba Jana ajikinsu batun yanzuba shiyasa su nake iya sakewa acikinsu, Khalil was the only family dana dauka inadashi sai Modibbo Wanda shima tsakanina dashi umarni ne kawai da bada oda, Khalil shine kawai Dan uwana Dana sani Wanda yake tsananin qaunata da damuwa Dani tun Muna Yara harya rasu yabarni ni kadai nasake komawa tamkar banida kowa again, Shigiwarki rayuwana da farko na dauka kamar takurawane Amma daga nabawa alaqar dama da mahimmanci saidai daga gareki ke bakya min kallon miji abokin rayuwar dazamu sake kamar kowane normal couples kina min kallon abin tsoro, Abin shakka dakuma son muyi rayuwa kamar yanda kowannenmu ke buqata wato ta rashin shiga takurawa kowa Wanda yasani Barin muyi irin rayuwar da Kika zaba Mana wato kowa yayi nasa since you don't want to give it a chance., Zarah kadaki dauki wannan auren cin Amana ko cin zarafi daga garemu mu duka sbd you know me Sam Banda sha'awar wani Tara Mata, Dagani har ita yarinyar ma Babu Wanda akai Magana dashi wannan umarninsu Modibbo ne and na amince da umarninsu sbd Inada raayin cigaba da kula da yarinyar da Muhammad so please kadaki ga laifin kowa akan maganar Nan ki mu duka muyi accepting sabon canjin dazamu samu banason doguwar damuwar dazata kawo hayaniya anan, Idan kin kwantarda hankalinki is nothing compared to ace wani labarin ne na daban kiyi sbd kanki kiyi sbd ni Kuma kiyi sbd ita me zuwan sbd kowa ya zauna lafiya, Kinsaba zama da ita ai so Kinga ba sabon Abu bane. Wani qaton Abune yazo ya tsaya a maqoshi kamar zai toshe numfashinta idanuwanta dasuka Fara kumbura sukai jajir ta qurawa fuskarsa Ido tanajin da ace da Hali data cire sonsa aranta ta huta da Abinda takeji kamar zata shide, Sai dai kamar yanda yace kowa ya dauki dangana sbd azauna lfy bazata tayarda hayaniyaba saidai tana buqatar kasancewa ita kadai yanzu sbd tunanin Abinda yakamaceta Dan kuwa idan har Amatu ce za'a aurawa MD din tanajin kamar bazata iya daukaba gwara a aura Masa kowama Banda Amatu bazata iya kishi da Amatu ba zuciyarta bugawa zatayi. Sakinsa tayi ahankali tareda zare hannunta tana kallon cikin idonsa dashima ita din yake kallo kamar bashine yayi dogayen maganganuba yanzu din, Sakinta yayi shima ta miqe tana share hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta bude baki zatayi Magana saikuma ta kasa tayi saurin juya Masa baya ta tattaro jarumta ahankali ta iya bude baki ya furta" Inshallah bazaka samu damuwaba akan hakan ta gefena saidai ka tayani da adduar cigaba da jurewa hakan. Da sauri ta fice ta sauko da gudu ta nufi dakinta tana Shiga ta zauna tsakiyar dakin tareda fashewa da wani irin kukan tsananin baqin ciki tana rufe bakinta sbd kada ya sauko yajita. Amatu kuwa kawu da kansa yasameta har daki cikin Daren ya zauna Kan daddumar dakin Yana kallonta da kyau cikin sauti Me nuna matuqar mahimmancin zancensa a natse yakira sunanta ta dago ta kallesa dakyau tana amsawa gabanta na tsananin faduwa.. Amatu bani na haifekiba Amma wallahi inajinki tamkar 'yar Dana Haifa ta jinina, Kisani duk Abinda Zan iya zartarwa akan 'dan dazan Haifa Zan iya zartarwa akanku ku biyun sbd irin qauna danake muku keda Usman, Ni ubane da bazanso ace 'yata tadawo gabanaba tana zaman jiran wani yazo gareta, Kinyi aure cikin zuriar dasuke tsananin qaunarki da ganin mutuncinki tareda matuqar qaunar 'danki Wanda har suka kasa hakurin jure tafiyarki ki barsu, Amatu amatsayin na na uba gareki kamar yanda na dauki kaina na zarce hukunci akanki batareda na nema shawarar kiba sbd tunanin ke din Zaki karbi duk wani hukuncina da Isa dazan nuna akanki. Mahaifan Khalil sunzo nemawa 'dansu aurenki sun roka alfarma nakuma amince musu gashi min yanke shawarar tunda tafiya zakuyi gwara adaura auren sbd samun nutsuwar kowa duk da bataredashi zakuyi tafiyarba goben..... Kalmarsa ta qarshe tasanyata sauke wata qaqqarfan ajiyar zuciyar da saura kadan zuciyar Tata ta buga Jin yace batare zasuyi tafiyarba kenan ba MAHMOUD bane kamar yanda ta zata da farkon zancen na kawu Wanda saura qiri ta zunduma ihun dabata shiryaba Dan tuni zuciyarta tafara harbawa ashe bashi yake nufiba SALMAN""zuciyarta ta ayyana Mata take tayi saurin rintse ido saidai kalmomin da kawu yayi amfani dasu da farko na ikonsa akanta yasa ta sauke ajiyar zuciya Kai tsaye Dan gajarta zancen tace" Shikenan kawu duk Abinda ka yanke akaina wallahi na amince maka Kuma Dan Allah kadaina cewa bakai ka haifemu ba sbd mu bamuda Wanda yahaifemu agurinmu idan bakaiba, Ni yarkace zaka iya yanke kowane hukunci akaina batareda ka tambayeniba, Tunda Dr khalil ya rasu walh Banda raayi gameda zaben miji sbd ra'ayina ya rasu tareda Mijina Dan haka Banda zabi sai Wanda kayi. Da zallar mamaki iyami da kawun ke kallonta saidai tunda ta gajarta zancen ta amince Babu amfanin dogon bayani Bari abar zancen ahaka har zuwa bayan Daurin aure agani. A daran kukan rashin Dr Khalil yadawo Mata sabo tayi kuka kamar mutuwarsa na sabuwa, Ayau itace zata auri Salman mutumin data dauka aboki Kuma Dan uwa ta Yaya zatai rayuwar aure da wanin Dr dinta, Wayarta ta janyo ta Kira anty zarah ki zataji sanyi Amma Bata daukaba kusan Kira bakwai no answer Miqewa tayi tayo alwala tazo tahau nafila tana jaddada adduar ta ga ubangiji akan yabata juriya da hkr na rashin Dr tareda sanyawa wannan auren dazatayi dawwamà mmiyar albarka. Koda gari ya waye anata Shirin Daurin aure itakuma da anty salamatu sunata Shirin tafiya sbd jirgin qarfe biyu zasubi Daurin auren Kuma daya da rabi ne after jumaat. Ba wani dogon noqe noqe iyami ta hakura hakanan ta babbata wasu Yan magungunan masu kyau da qarfi tareda yimata gyaran jikin gaggawa Wanda Sam duk basa gaban Amatun hardai qarfe daya tayi aka wuce gurin Daurin auren daya Tara dubban JAMA'A aka shaida akan sadaki naira dubu hamsin kacal. Koda Yan Daurin auren suka dawo su Amatun sungama Shirin komai na tafiyarsu sbd qarfe biyu zasu tashi shiyasa Koda kowa yadawo Dan kada asamu Yan kanzaki akayi airport dasu cikin shirinta na doguwar rigar jallabiyar Kuwait datai mugun yimata kyau Muhammad khalil na hannun anty salamatu suka fito cikin mota a airport din wayarta tayi ringin saiga sunan Dr salman zabeera ajikin wayar take taji jikinta yayi sanyi waifa yanzu mijinta ne ta sauke ajiyar zuciya tareda daukar wayar zatai magana ya rigata da cewa'' Congrats Mrs MAHMOUD DAHEER ZABEERA. Ciro wayar tayi daga kunnenta ta kalli sunan Wanda suke wayar takuma mayarwa kunnenta tana cewa'' Salman ne?? Eh Mana nine kokina jiran Kiran mijinkine MD ZABEERA yanzu yabar zabeera Yana hanyar airport yafasa zuwa daga baya tare zasu tafi..... Salman me Keke cewa yimin bayanin dazan fahimta waye aka daura aurena dashi kaine kokuwa sbd banason boye boye fadamin..... Mezaisa adaura Miki aure Dani Kuma? Da MAHMOUD ZABEERA dai aka daura muku aure........ Juwace ta dibeta tayi baya gabaki daya jikinta asaki taji antarota jikin babbar rigarsa Fara qal dabai cireba ta Daurin aure. ##Mamuh# 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 38_* Anty salamatu da umme dake qoqarin fitowa mota jikinta duk a sanyaye itama da wannan auren Dan ganin yau anwayi gari wani ya aure iyalin Khalil dinta, Yarinyar da Khalil dinta yafiso fiyeda komai wadda ya yarda yarabu da kowa da komai akanta yau tazama mallakin wani Wani abin sai mutuwa Dan kuwa da Babu Abinda zai raba Khalil da Amatu idan ba mutuwarba, Amma tunda har MAHMOUD ne ya aureta damuwarta qalilance sbd MAHMOUD dinma mutum ne me matuqar mahimmanci da girma a rayuwar Khalil Dan haka take musu fatan farin ciki me darewa a wannan auren. Fitowa motar taqarasa Yi itada anty salamatu sukai gaba. Qoqarin dawowa tunanin ta takeyi ga bude Ido ta rufe taga tabbas shi din ne take cikin jikinsa da qarfi ta yunqura ta qwaci jikinta tana sake kallon kyakkyawar fuskarsa dayaqi kallonta ya juya Yana cewa Mal Umar ya fiddo Masa luggages dinsa daga mota. Sake tariyo maganar datayi da Salman tayi cikin kanta tana Dan girgiza Kai tana qoqarin yakice zancen cikin kanta sbd bama zai yiyuba ace anyi tunanin hadata aure da MAHMOUD ZABEERA Rabin ran Anty zarah, Sam bazaima yiyuba wannan hadin Bayan ansan tsakaninta da antynta Sam Sam...... Wayarta ta daga hannuwanta na rawa sbd tashin hankali da tsoron Abinda zataji ta lalubo numbern iyami ta Danna Kira tayita ringin no answer Da sauri ta lalubo ta kawun tayita kira shima bai daga ba kasa hakuri tayi cikin tashin hankali ta nufi su umme dasukai gaba sosai ganin Bata sauri yasa ta Fara gudu tana kiran sunan umme cikin ficewar hayyaci Dan gabaki daya kanta ya kunce gabaki daya so kawai take a qaryata Mata zancen salman zabeera a tabbatar Mata daba mijin anty zarah aka daura Mata aure dashi ba..... Hannunta aka damqo tareda birkitota tadawo baya gaba daya cikin jikinsa akaro na biyu wannan karon cikin tsananin masifa ta juyo zatai magana idanuwanta suka Shiga cikin nasa daya zuba Mata Wanda ke bayyanar da seriousness dinsa ya bude baki bayan ya Dan kalli mutanen dake wucewa suna kallonta yanda tafara keta gudu ga jallabiyarta very attractive sbd irin me shape dinnan ce Kuma gyalen jallabiyar kawai ne tayi rolling dashi sai handbag dake hannunta... Murya a daqile yace" Nan ba gurin Wasa bane kokuma Zabeera you better behave yourself.... Kasa hadiye Abinda ya tsaya Mata a maqoshi tayi ta kallesa cikin masifar da batamasan tanayiba tace" Hakama rayuwata ba abin Wasa bace kokuma Zabeera dazaka shigo batareda sani ko damata ba, Nafasa tamabayar kowama kaga agabana Kai Zan tambaya tunda mune abin yashafa inason tabbatarda da cewan da waye aka daura aurena ayau din? Sakinta yayi batareda ya kalletaba ya wuce Yana cewa'' She's crazy. Biyo bayansa tayi tana sake nanata tambayar Amma ko inda take baida alamun kalla saima agogon hannunsa daya kalla yaga time yayi ya wuce Kai tsaye su umme ma tuni suka shige., Ganin zata Tara Masa attention na mutune dasuka Fara Binsu da kallo suna Magana qasa qasa gashi wasu sunfara ganesa Kuma da alama akwai 'yan Media agurin yasan good days dinshi sunzo qarshe dama tunda aka daura Masa aure da wannan crazy yarinyar gashi ranar farko ma zata Bata sunansa a idon mutane..., Juyowa yayi ya fizgota da qarfi tareda kallon fuskarta Yana Kai bakinsa daf da kunnenta cikin bacin Rai Mai tsanani yace" I swear idan baki nutsu kindawo hankalinkiba Zan tabbatarda kinyi nadamar sanin zabeera sbd right this moment Zan rabaki da Muhammad ki koma gida keda ganinsa saina tabbatarda baimasan kece mahaifiyarsa ba.. Cikowa idanuwanta sukai da wasu irin kwallar baqin ciki cikin rawar murya tace" Bakada Imani Rabin ran Anty zarah. Sakinta yayi tareda dagowa ya juya ya kalli yanda mutane ke kallonsu suna washe baki sbd sun burgesu sun dauka soyayya sukeyi yayi gaba batareda ya tsaya ya kalleta ba jiki amace zuciya na tafasa tabi bayansa tana ayyana irin tashin hankalin dazai biyo baya sbd har abada Babu maganar aure tsakaninta da mijin Zarah. Acikin jirgi seat dinta ne gefen na umme sbd shi Yana first class Tana zama ta rufe fuskarta wani irin azababben kuka ya kufce Mata ta rufe baki tahauyi zuciyarta na wani irin quna da qarfi. Umme tasan ayi hakan shiyasa ma batai yunqurin rarrashinta ba sbd tana buqatan kukan ko taji sanyin Abinda akai matan Dan kuwa da tsananin ciwo da kunya Mara iyaka tareda nauyi a aura maka mijin Wanda ya yarda dakai tareda baka qauna Mara iyaka, Duk su dukan Kam sai hkr Amma zarah ce tafi kowa cancantar ban hkr sbd kishiya ba Dadi musamman irin wannan ta bazata Kuma da wadda baka taba kawowaba Gashi Amatu mace ce daba kowane namiji zaisamu ya iya Bari ba sbd ita kanta shaida ce tagani akan Khalil dinta tanadai fatar Allah yabasu rayuwa me albarka acikin wannan zaman nasu. Ganin kukan yaqi qarewa gashi lokaci yaja tafiya tayi nisa yasa umme dafa kanta cikin kulawa da taushin murya tace, Amatu wannan kukan dakikeyi Babu sauki ko mafitar dazai kawo Miki acikin wannan alamarin, Aure dai anriga andaura Kuma banajin akwai abindazai warware hakan Dan haka amatsayina na tamkar uwa agareki Ina baki shawara da umarnin ki daina wannan kukan da duk wata masifa ki aje gefe neman lafiyar danki mukazo ki maida hankali mu dage muga munsamu Abinda mukazo nema, Ki aje komai muyi Abinda yakawo mu idan yaso Bayan munyi nasara idan ankoma gida sai ayi maganar auren kinji. Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya me qarfi akai akai sbd qarfin kukan datasha Wanda har lokacin zuciyarta Bata daina Mata zafi da ciwo ba tunanin anty zarah da halin datake ciki da irin kallon datake Mata sun kasa barinta sukuni saidai kamar yanda ummen tace su maida hankali Kan Abinda yakawosu neman lafiyar Muhammad khalil idan sun koma za'a yi Yanda za'a yi a warware auren kokuma tun anan zatasan yanda zatayi ya sawwaqe Mata tun anan suna komawa gida kowa yakama hanyarsa. Share hawayenta tayi ahankali tareda dago idanuwanta dasukai jajir suka kumbura sbd tsananin kuka ta kalli anty salamatu taga bataga Muhammad din a hannunta ba ta bude maki cikeda mamaki zatai magana antyn ta rigata da cewa'' Yana gurin MAHMOUD. Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda mayarda kanta ta jinginar tana rufe idanuwanta tana tuno zancensa na cewa zai rabata da Muhammad take taji kamar tsoro yanason kamata saidai Kuma ita ba anty zarah bace batajin tsoronsa tafison daganan har qasar sin tabisa akan 'danta duk inda yakaisa. Bacci ne ya Dan dauketa sbd ciwon Kai me tsanani daya saukar Mata sbd kukan datasha har jikinta sai daya dauki zafi Wanda da wuya idan ba zazzabi bane ya damqeta ga tashin hankali,ga kuka,ga pressure,ga fargaba da tsoro duk sun hadu sun dabaibayeta Dole zazzabi ya damqeta me qarfi kuwa. Koda jirginsu ya sauka saidai anty salamatu ta riqota suka fito sbd jiri jiri take gani., Basusan Yaya akaiba sai ganin wata white jaguar XK120 tayi parking gabansu yanayin motar kawai yasa umme gane MAHMOUD din ne sbd kusan duk Wanda yayi Masa farin sani yasan irin motocin dayake hawa ko a Nigeria ko aqasashen waje. Zagayawa tayi tabude gaban motar tacewa salamatu" Zo sakata anan salamatu. Qwacewa tafara qoqarin yi Jin ance zata shiga gaban motar umme ta kalleta ba Wasa a fuskanta tace" Salamatu zoki shiga mutafi tunda ita Bata tashi tafiyarba. Jin kamar ran ummen yafara baci yasa ta shiga gaban motar ahankali tareda rufewa tana jinginar da kanta tana kallo gefe zuciyarta na sake cunkushewa. Shiru dukkaninsu Babu me Magana har suka isa wani kyakkyawan building din dake jerin wasu Athens self-contained flats. Parking yayi acikin qatuwar harabar kafin suka firfito shine yafara wucewa gaba kansa na juyawa sbd baisan ta Yaya zai zauna da mutane acikin gidansa ba Sam baya iya zama da mutane musamman ana inda yake sakewa yayi rayuwarsa gashi harda umme. Forth floor ne nashi Dan haka suna fitowa lift din forth floor da sunansa baro Baro dake rubuce akan qofar shiga sukaci karo *_MD ZABEERA_* da security password yabude qofar yafara shiga tareda kunna fuse na wutar gidan take komai ya kawo haske anty salamatu ta bude Ido da baki tana kallon aljannar duniya tashigo tana kallon sama idanuwanta kaman zasu fado, Haduwarsu da familyn ZABEERA yasa idonsu suka Dan bude da ganin rayuwar masu kudi da Kuma ganin daular masu kudi Amma anan Kam taga Abinda duk kyau da tsari tareda dukiyar zabeera Bata gani acan ba. Umme ma data Saba da yawon qasashe Saida Nan din ha burgeta sosai ta yaba saidai flat din 2 bedrooms ne bayan master bedroom dake Dan daga gefe saman qananun stairs Wanda aka zagaye da glass door. Sauran 2 bedrooms din Kuma sune suke kallon juna daga gefen hanyar dining can umme tace su nufa sbd ganin can ne masaukinsu danshi tuni yayi hanyar master bedroom dinsa yashige qofar glass din kafin ya nufi qofar asalin bedroom din. Umme ce tashiga dayan bedroom din Amatu da salamatu suka Shiga daya bayan salamatu ta kwantar da Muhammad toilet tafada da sauri sbd fitsarin datake ji tun acikin jirgi Amma tsoro ya hanata ko motsawa bare tayi Magana. Amatu kuwa bakin gado ya zauna tareda rafka tagumi tana dafe kanta dake tsananin Mata ciwo ga tunanin duniya daya kasa barinta. Dayake dare ne Babu Wanda yadamu da wani abinci salloli kawai sukai bayan wanka suka kwanta. Dadin AC da qamshi me sanyaya zuciya tareda gajiyar dake taredasu yasasu samun bacci me Dadi da nutsuwa. Qarfe takwas na safe qarar doorbell yasasu fitowa kowanne a shirye sbd zuwa asibiti. Breakfast ne umme tayi odar daga wani restaurant data bincika online Dan haka Babu Bata lokaci sukaci Wanda suka iyaci Amatu da salamatu suda Basu taba fita waje ba. Bayan sungama anty salamatu batareda kowa ya sataba ta tashi tahau gyaran koina tana gamawa me gidan na fitowa sanye cikin qananan Kaya hannunsa daukeda key din mota da wayarsa sai zuba qamshinsa yakeyi ba kowa a palon sai anty salamatun Dan haka suna gaisawa yace ta sanarwa Amatu Yana mota tafito da Muhammad. Yana ficewa tayi daki ta tararda ita zaune tana hawaye bayan Gama wayarta dasu kawu da iyami da wayar umme da layinta na qasar sungama qara Mata zafi da maganganunsu akan auren. Kallonta tayi ta fada Mata saqon MAHMOUD din ko kallon anty salamatun bataiba ta miqe ta dauki Muhammad ta fice zuciyarta a cunkushe. Suna barin gidan umme takira yayarta Prof zainab zabeera tace a aiko driver yazo ya dauketa bazata zauna a gidanba sbd irin wannan auren na Amatu da MAHMOUD suna buqatan abarsu su kadai Dan asamu su fahimci juna su bawa auren dama sbd so take kafin sukoma komai ya daidaita tsakaninsu duk da ita sati biyu zatayi Takoma tabarsu anan din. Anty salamatu dataga ummen zata tafi duk sai taji wani iri za'a barta ita kadai tsakiyar amaren duk da umme ta jaddada mata akan ta bada himma matuqa gurin taimakawa komai yatafi daidai tsakaninsu. Bayan tafiyar ummen wanka tayi itama ta kwanta bacci bayan ta rufe dakinta. A asibiti duk wasu formalities sun cike anyi komai an kwantarda Muhammad din yabiya komai da komai anan zasubarshi saidai su riqa zuwa dubasa shine qaidar asibitin, basubaro asibitin ba sai maraice inda yunwar cikinta ta isheta gashi asibitin da nisa sosai. Ahanyarsu ta dawowa Babu me mgn saishi dayake amsa waya akai akai tanaji hadda anty zarah yayi waya. Wanine ya damesa yanason ganinsa akan project dinsa na Nan Athens daya tsaya sbd wata babbar matsala Dole ya juya Kan motarsa ya nufi private joint dake cikin babban hotel din Athens din Yana daukar baqin mirror goggles dinsa ya sanya daidai lokacinda suka shigo gurin Wanda matakan tsaronsa da securities dinsa sukai yawa sbd girmansa da haduwarsa ga mutane sai abubuwan gabansu sukeyi. Shine yafara fitowa Bayan yayi parking kafin yagama fitowa security ya bude Mata motar itama bataso fitaba sbd bataga dalilin zuwa da itaba Amma tsoron gurin da yanayin yanda gurin yake yasata fitowa ta tsaya gefensa yagama waya kafin suka nufi cikin gurin Yana sake amsa wata wayar. ##Mamuh# 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 39_* Direct wani kebantaccen guri suka nufa daga bayan joint din inda aka tanada domin VIPs itadai komai na gurin bai burgeta ba ko dogon kallo bai ishetaba sbd damuwar dasuke Wanda sukazo gurin tare, Sam ta rasa walwalar rayuwarta tun jiyan data samu sanin shine mijin da aka daura mata aure dashi. Da sauri Jan baturen yataso Yana Masa sannu da zuwa tareda miqa Masa hannu sukai shaking Yana kallon fuskar Amatu dake daure ba alamar fara'a ko wata walwala ya maida kallonsa Kan MD din Yana sake washe baki zaiyi Magana MD din ya katsesa a gajarce Yana zama yace" My wife. Da sauri Mr Jeremy yasake kallonta Yana sake sakin fuska da murmushi yace" Nice to meet you Mrs ZABEERA. Kallonsa tayi ta Dan daga gira daya kadan alamar amsawa ta zauna nesa dasu tana kallon gurin ba cikin dadin raiba sukuma suka zauna tareda fiddo laptop ya kunna yafara nunawa MD din aikin dayakeson nuna Masa. Sauraron Mr Jeremy yakeyi Yana Kuma fahimtar Abinda yake Masa bayani daidai hankalin nasa ya rabu Kashi biyu ne, Waiter""ya furta ahankali cikin nutsuwa daidai lokacinda wani Waiter ya nufo VIP din. Yes sir""Waiter din yafada cikin Yar rusunawa. Amatu ya nunawa waiter din Yana cewa abata menu ta zaba Abinda take buqata. Koda aka miqa Mata menu girgiza Kai kawai tayi batareda ta juyo ta kalli gefensu ba. As you wish"yafada Yana dauke hankalinsa gabaki daya daga kanta ya maida Kan aikin gabansu. Awa daya,awa biyu har uku taga aikin bana qarewa bane ga uwar yunwa kamar zata illatata ta waiwayo ta kallesa akaro na kusan hudu Amma ko inda take baya kallo kamar ma ya manta da ita gabaki daya.. Cikowa idanuwanta sukai kamar zatayi kuka sbd baqin ciki da takaicin yimasa magana takeji Amma haka ta miqe jiki a mace ta nufesu tana sassauta damuwarta sbd kada takaici yasa ta zuzzuduma Masa zagi ayi Mara kyau. Jin mutum tsaye akansu yasa Mr Jeremy dagowa Yana ganinta ya washe baki Yana bata hakurin riqe Mata Miji da yayi itadai ko kallo bai ishetaba ba MAHMOUD din take kallo Wanda ko motsawa baiyiba bare ya juyo ya nuna yasan da mutum agurin A hasale tace" Ka maidani gida sbd Banga amfanin zamana anan dinba. Juyowa yayi ya zuba Mata fararen idanuwansa dasuka sanyata saurin dauke Kai zuciyarta na bugawa da sauri. Fuskarta ya kalla dakyau batareda yace qala ba Jin shiru yasata juyowa zata Kuma mgn idanuwansu suka sake hadewa sbd rikicewa batasan lokacin datace Dan Allah ka maidani gida wallahi yunwa nakeji kaman Zan mutu ana wlh..... Dan bude idanuwansa yayi irin da gaske kike bayan anbaki damar cin abincin kince AA. Dauke Kai tayi zuciyarta na qara Dan daukar zafi saidai Bata sake cewa komaiba ta juya ta nufi hanyar mota. Juyowa yayi ya kalli Mr Jeremy daya Gama washe baki Yana kallonsu cikin burgewa yayi gyaran murya Yana cewa abar sauran aikin sai zuwa gobe zai kirasa. Miqewa yayi tareda karban copies na takardun aikin tareda wucewa yana kunna wayarsa daya kashe tun dazu. Jikin mota ya tarar da ita fuskarta amatuqar tamke tun Kan ya qaraso ya bude motar ta shige ta rufe. Yana shiga ya Dan rage sanyin ACn motar sbd sanyin daya Dan Fara saukowa kafin yaja motar suka bar gurin Yana amsa wayar Modibbo data shigo Masa. Suna Isa gida ta fice motar dayake zata gane tuni tayi gaba Koda ya shigo tana tsaye gurin dining tana kwankwadar grape juice ko sanyi baida Amma Bata damuba sbd gigitar da yunwa tai Mata. Gaisawa da Anty salamatu kawai yayi ya wuce hanyar dainsa bayan ya ajiye odar abincin dayayi tun suna hanya ya hade da delivery man din a qasa ya karba. Tana ganin alamar abinci ne ya ajiye ko daki bai qarasa shigewaba ta nufi ledocin to hau budewa jiki na rawa ta dauki box daya tafara ci duk da abincin kamar zataiwa kanta kuka sbd rashin ma'anarsa Amma hakanan ta tuttura Tasha lemu ta saki qyasa tareda sauke ajiyar zuciya ta kalli anty salamatu dake kallonta cikin mamaki da 'yar dariyar sai alokacin tace" Anty salamatu wlh bandauka Zan iya shigowa da qafafu naba sbd yunwa. Murmushi antyn tayi tareda Fara gyara gurin tana cewa'' Amatu kenan.yanxu Wanda yafita da miji kundawo da yunwa maimakon kifara cire Masa ki Kai Masa Amma kin zauna kin qoshi abinki. Anty salamatu kenan Wane miji Kuma? Ina umme ko bacci takeyi? Dining anty salamatu ta nufa da abincin tana cewa'' Umme ta tafi gidan yarta tace da Dan nisa daga Nan acan zata zauna sai ankwana biyu zata Zo. Kallon tsoro takebin anty salamatun tana cewa'' Meyasa zata tafi to? Da Ina Nan wlh can zanbita nayi zamana acan Nima. Abincin anty salamatu ta jere Masa a dining din bayan ta diba ta wuce daki batareda tacewa Amatun komaiba sbd takaicin zancenta na cewar zatabi ummen. Itama miqewa tayi jiki a sanyaye ta nufi dakin saita tararda anty salamatu ta maida Mata kayanta dayan dakin da umme tabari sbd yafi girma ta jere Mata kayanta tsaf a wardrobe ta sake gyare dakin. Tubewa tayi tayo wanka tazo tayi sallah Tasha maganin ciwon Kai ta kwanta take bacci yayi gaba da ita. Wanka yayi shima ya fito Bayan yayi sallah ya zauna dining ya dauki box din chips daya yaci da Burger yasha energy drink ya dawo Palo ya zauna ya kunna news Yana kallo sama sama Yan amsa wayayo har tsawon lokaci kafin yakoma bedroom dinsa. Washe gari Babu Wanda yagansa acikinsu sbd bai fitoba kwata kwata sai yamma lis yafito ya fice bayan fitarsa ya aiko da mota aka kaisu asibiti Basu jimaba aka dawo dasu. Washe garima hakan ne yafaru ankaisu asibiti Kuma Basu sakashi a Ido ba, Kwanaki suka Fara tafiya Amma Babu wani sabon alamari a rayuwar zaman gidan,gabaki daya Basu cika ganinsa ba sai jefi jefi sbd baya zama idan Kuma Yana Nan bai cika fitowaba, Kullum ana kawo musu abinci so uku a yini har Anty salamatu tagaji dacin na wajen tafara Dan yimusu dubarun abinci dayake ta iya girki sai suka koma cin nata ganin sunfi son na gidan sai yasa akazo aka dauki anty salamatun aka kaita shopping din komai na abincin dazata iya girkawa. Yanayin zaman yafara gundurar anty salamatu sbd Sam ko gaisuwa Bata Shiga tsakanin Amatun da MAHMOUD din saitaji duk ta tsargu da zaman gidan ta sanarda Amatu tafiyarta zatayi yabi umme inda take idan har Bata sauya ba ta ringa gaida MAHMOUD din har dakinsa Koda bai fitoba. Da farko share zancen antyn tayi Amma dataga alamar da gaske antyn tafiya zatayi Dan harta Kira umme saita Fara zaman Palo tana kallo ko wayoyi idan yadawo kokuma idan yafito zai fita takan gaishesa batareda ta kallesa. Ta bangaren Muhammad kuwa suna ganin cigaba sosai sbd sauki yafara samuwa Dan yanzu Yana kuka sosai kamar sauran babies wani lokacin idan taje asibitin sukan batashi tabasa nono da kanta basai ta tatsa Masa a roba kamar yanda ake Masa ada Kuma Yana 'dan kamawa yanzu ba laifi. Yau zaune take a Palo ita kadai tana kallon wayarta data gama waya da USI tanason Kiran anty zarah Amma kamar koyaushe tanajin kunya da nauyinta takasa Kira sbd batasan ta inda zata Fara yiwa anty zarah din bayani ba. Bude qofa taji ahankali cikin nutsuwa sbd baya komai cikin hayaniya yasa tagane shine yafito daga dakinsa batai niyar juyawa Amma ta daure ta 'dan juyo a sace ta 'dan kalli qofar. Sanye yake cikin qananun kayan Shan iska sky blue me haske sosai sai slippers farare dake qafarsa da keys din mota da waya a hannunsa da alamu gurin Shan iska zaije. Anty salamatu ce ta fito sanye da riga da skirt na atampa ganinsa da yanayin shigarsa yasa tadanji kunya tana dauke Kai tareda yaba kyau da kwarjini irin na MAHMOUD, Har zata koma daki cikin Jin nauyi data Zo ta darshe tsakanin amare Kuma qanne saita Dan tsaya batareda tajuyo gaba daya ba tace" Inason zuwa gurin umme nai Mata kwana biyu shine nace ko za'a kaini? Zulum Amatu ta miqe tana kallon anty salamatun cikin mamaki da firgici tace" Nima zanje Bari nashiryo. Ko kallonta Babu Wanda yayi acikinsu ya nufi qofar ficewa Yana cewa'' Muje na ajeki da kaina. Ko Kaya anty salamatu Bata tsaya daukowaba sbd kada Amatu tafito Basu tafiyarsu ba tabu bayansa da sauri. Aikuwa kodata fito cikin Shiri tana gyara zaman gyalen jallabiyar dake jikinta taga ba kowa a palon ta nufi qofa da sauri ta fito ta hau lift zuwa qasa tana Isa suna barin harabar building din ta tsaya tana bin hanyar gate din futa da Ido tanajin wani Abu aranta na baqin ciki Amma hakanan ta hkr ta juya Takoma ko daki Bata shigaba a Palo ta zauna baqin ciki da damuwa na cinta ta Yaya zasu tafi su barta ita kadai a gidan daga ita sai shi. Har kusan qarfe goma sha biyun dare baidawoba tana daki duk da kwance take hankalinta na qofa taji shigowarsa sbd Sam takasa samun sukuni ita kadai cikin gidan aqalla dai taji motsin mutum cikin gidan zai rage tsoronta. Sai qarfe daya saura taji shigowarsa ta sauke ajiyar zuciya daga kwancen tareda juyawa ta gyara kwanciyarta tana rufe Ido. Washe ma haka ta wuni ita kadai gidan bataga dawowarsa ba sai cikin dare ahaka sukai kwana uku take hankalinta yafara tashi sbd tun tashinta Bata Saba rayuwa gurinda Babu hayaniyar jamaa ba Sam Bata taba ma zama ita kadaiba sai abin yake Bata tsoro shiyasa ranar kwana ta biyar tana kwance cikin damuwa tunda safe taji fitowarsa ba Shiri ta wuntsulo daga Kan gadon ta fito ko wula da suturar arziki Babu ajikinta tana futowa shikuma Yana zama Kan Kan dining da cup din ruwan tea a hannunsa sai jinta yayi kwasam akansa ya dago idanuwansa ahankali ya zuba mata ganin suturar dake jikinta take ruwan tea din dake cikin bakinsa suka Dan sarqesa ya dauke Kai Yana Dan tari ahankali batareda ya juyo yakuma kallontaba ya miqe zai bar gurin takuma saurin Shan gabansa tana cewa'' Bazan iya zama anan ba inason zuwa gurinsu umme. Tsayawa yayi cak tareda juyowa ya kalleta da idanuwansa dasukai 'dan ja sbd tarin da yayi Yana kallon fuskarta yace" Su umme nada damar barin Nan ke Kuma akan dalilin me Zaki bar Nan? Sakin baki tayi tana kallonsa Kai tsaye tace" Akan dalilin ni kadai nake rayuwa kamar Mara galihu, Inason zama tareda mutanen dasukan darajata sukasan su...... Idon daya watsa Mata yasa maganarta yankewa tana Dan sauke Kai daga kallon idanuwansa qasa qasa tace" Nagaji. Ringing din wayarsa yasashi dauke idanuwansa akanta ya dauka Yana cewa'' I will be there in 10min and the ticket make it 2. Wuceta yayi Yana cewa'' Kije ki shirya. Juyawa tayi ta koma daki tana cewa'' Dadai yafi sbd nagaji da wannan zaman rashin yancin gwara ka kaini gurinsu Kona farfado rayuwata. Tsayawa tayi gaban madubi zata tube tayi saurin kallon jikinta tana Dan fiddo idanuwa sbd ganin kayan jikinta tana furta taslimah... Rigar bacci ce ajikinta gajera sosai wadda ko cinya Bata Gama hawaba Kuma irin me gidan nonuwan nan ce agabana yadin me sulbi sosai gashi rigar baqace saita fiddo kyan farar fatarta. Dafe goshi tayi tana sakejin damuwar abin tareda kunya me tsanani kafin dai ta tuben ta nufi toilet. Wanka tayo ta Dan shafa man jaggins kadan sai spray da body mist data shafa ya sanya doguwar Turkish gown royal blue tayi rolling gyalen tafito da handbag dinta qarama sai wayarta. Qoqarin zama takeyi saigashi yafito sanye cikin qananan Kaya blue black shima sai qamshinsa ya doke nata ko kallonta baiyiba ya nufi kofa Yana duba agogon hannunsa. Mr Jeremy ne yazo daukarsu atunaninta gidansu ummen zasu Amma taga sunzo asibiti suka Gama Abinda zasuyi kafin suka nufi gurin shiga train Wanda yasata bude idanu tana kallon tsarin gurin suka shige first-class tun kafin su zauna aka Fara gabatar musu da jaridar karatu da abin sha, Wayarsa ce tayi ringing Yana dubawa yaga video call ne zarah ke kiransa Abinda Bata taba ba Da farko yaso qin dauka Amma ya dauka daidai lokacinda Amatu ta juyo zatai Masa Magana saigashi idanunsu sun gane musu juna itada anty zarah baro baro jikin waya take kowaccensu gabanta yayi mummunan faduwa sbd ganin Yar uwarta musamman ganin irin adon dake jikin kowaccensu Amatu ce tayi saurin sauke Kai zuciyarta na harbawa da qarfi adon anty zarah din na cika Mata Ido sbd kwalliya ta musamman anty zarah tayi cikin wasu qananun Kaya ba komai akanta sai gashinta data zubo sbd kawai ta burge mijinta. Itama Kuma anty zarah idanuwanta Basu sauka akan komaiba sai akan fuskar Amatun data canza sosai tayi fresh kamar tana cikin kwanciyar hankali da amarci. Shikuwa ganin yanayin shigar zarah din tun kafin tayi Magana ya datse Kiran Yana kashe wayarsa gabaki daya sbd kada aganar Masa iyali. Take Amatu taji tafiyar tafita ranta jikinta yayi matuqar sanyi batasan lokacinda ta juyo ta quresa da kallo ba tanason karantar yanayin dayake ciki da Abinda yafaru yanzu din ba. Jin idanuwanta akansa yasashi Dan kallonta yaga batada niyar barin kallonsa ahankali cikin cool muryarsa me taushi yayi gyaran murya Ta dauke kanta ahankali har lokacin zuciyarta Bata daina bugawa da qarfi ba. Tafiyar awa daya da rabi sukayi saigasu awani gari dayake da tarin sanyi da qarancin mutane Wanda daga gani garin shaqatawar Yan honey moon ne sbd yanayin tsare tsarensa. Wani boyayyan hotel suka sauka Wanda ya tsarinsa yasa take tunanin shine babba agarin sbd komai nasa farine. Aiki yakawosa shiyasa suna shiga suite dinsu ko zama baiyiba ya fice yabarta bayan yayi odar abinci dakomai yasa akawo Mata. Itakuma zama tayi bakin gado jikin asanyaye sbd har lokacin Bata daina ganin anty zarah da kallon datake Mata a idonta take tasakejin matsuwar gobe tayi sukoma kodan Takoma gurin Muhammad dinta da akace za'a iya Basu sallama kwanakin Gabaki daya Jin haushin komai taji tanasake yi Daqyar tagama Abinda zatayi ta kwanta Bayan ta sanya riga da wandon bacci masu Dan nauyi da aka kawo musu set na mace Dana namiji ta rintse idanuwanta tana son bacci ya dauketa. ##Mamuh# 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 41_* *_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku da Allah idan kunada rabo Allah ya shiryeku_* Wani irin bugu zuciyarta keyi me qarfi da sauri hannuwanta na Yar rawa take kallon anty zarah din da akwatinta datake janye dashi batasan lokacinda wani qarfin hali da juriya suka shigeta ba ta qaqalo wani talwataccen murmushi tana ajiye cup din hannunta ta nufi anty zarah din da itama tafi Amatun dauke wuta tana cewa'' Anty zarah sannu da zuwan bazata. Duk yanda anty zarah din taso Nemo qaqalo murmushi ta nema ta rasa sai kawai ta 'dan washe baki Wanda kowa yagani yasan yaqene Tace" Amatu sannu da gida mun sameku lfy? Akwatinta Amatun ta karba tana qarasa shigo Mata dashi ciki tana cewa'' Alhamdulillah anty. Rasa abinyi tayi sbd ruden datake duk da ba'a iya ganewa sai kawai ta nufi kicin ta hado drinks da snacks a tray ta fito dasu tana 'dan satar kallon inda ya zauna Yana sauya layinsa zuwa na qasar ahankali ta ajiye tray din gabansu tace" Dady sannu da zuwa. Qwarewa anty zarah tayi da ruwan data zuba bakinta duk suka juyo suka kalleta bandashi daya dauke Kai baima Gama juyowarba tace sannu anty ko ruwan yayi sanyi ne da yawa. Batareda ya kalletaba yace" Ki gyaramin dakin and kiban keys din motarki zan fita urgent. Miqewa tayi tana Dan Jin wani iri ta nufi dakinta ta dauko Masa keys din ta miqa Masa ya fice ta juyo ta kalli anty zarah datai saurin dauke Ido daga kallon datake Binsu dashi tace" Anty zarah Bari nakai Miki kayan dayan dakin tunda anty salamatun ma Bata Nan kafin agyara nasa dakin saiki koma can ki shigo kiyi sallah ki huta idan nagama saina Dora dinner. Batareda tace komaiba ta miqe tabi Amatun har cikin dakin ta ajiye Mata akwatinta tareda ficewa tana cewa'' Ina zuwa anty idan akwai Abinda za'a yi Miki ki kirani. Tana fitowa dakin ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya tareda dafe qirjinta tana Kiran sunan Allah. Itama anty zarah Amatun ta fita ta sauke numfashi me qarfi tana cewa'' Ya Salam. Daukar akwatinsa tayi ta nufi dakinsa ta ita ta ajiye kafin tafara aikin gyaran dakin tanayi tana sauke ajiyar zuciya akai akai. Tana gamawa Ta nufi kicin ta Dora girkin pasta da cabbage source me kidney aciki. Har lokacin sallar magriba tayi Bata kammala ba sai guraren 7 ta Gama ta jere a dining ta nufi bedroom dinta ta fada wanka sbd ta 'dan gaji. Sallah tafarayi bayan tafito wanka kafin ta sanya doguwar English gown Mara nauyi kwata kwata black ta sanya hula ta fito cin abinci. Tana fitowa Yana dawowa amatuqar gajiye yake Dan haka Kai tsaye ya nufi dakinsa Yana cewa takai Masa abinci can Yana Jin yunwa. Nata tafara zubawa taci ta qoshi tsaf abinta kafin ta hada nasa a tray tareda komai ta nufi hanyar bedroom din nasa tanayin knocking yabude Mata sbd tunanin da Kaya a hannunta sai gashi kuwa hannunta dauke yakeda tray Daure yakeda towel zaishiga wanka kenan yaji buga qofarta shiyasa ya bude matan. Kallo daya tai Masa ta dauke Kai ta nufi table ta ajiye abincin tana cewa'' Ko amaida ne saika fito wankan Dan kada ya huce? No Bari naci kafin nashiga wankan Ina buqatan abincin zansha magani. Zaunawa yayi yafara cin abincin a natse ga ciwon Kai dake matuqar damunsa sbd stress ta juya zata fice yace" Zansha magani Ina buqatan ruwa. Fitowa tayi Dan dauko Masa sai kawai taga anty zarah zaune a Kan dining turuss ta tsaya wata irin kunya da nauyi yasa takasa daga qafa saidata ga kamar anty zarah adin hankalinta nakan abinci kafin taja qafafunta daqyar ta nufi kicin ta dauko Masa ruwan saikuma taji takasa fitowa ta tsaya karba ruwa ahankali tana tunanin yanda zatazo ta keta anty zarah ta shige dakinsa. Jin shiru Bata dawoba gashi yagama ci ruwan yake buqata yasa ya miqe yafito hannunsa daukeda magani Bai lurada zarah dake zaune tsit ba a dining ya nufi kicin inda yake hango Amatu tsaye tayi nisa a tunani Tana ganinsa cikin kicin din ayanda tabarosa daki dagashi sai towel ta zaro idanuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta janyosa da qarfi sukai gefen fridge ta bayan qofa Ido waje da firgici tace" Bakaga anty zarah ba a apalo zaka biyoni Nan Kuma ahaka ba kaya ajikinka me kake tunanin anty zarah zata dauka.. Zuba Mata fararen idanuwansa dasukai laushi yayi Yana kallon tsoron dake bayyane fili akan fuskarta da bakinta dake Magana kafin ahankali ya sauke idanuwansa zuwa kallon hannuwanta dake riqe da qugunsa har hannunta dayama nakan daidai mararsa yaji ahankali gajiyarsa da ciwon kansa na warwarewa ya maido da kallonsa Kan fuskarta ta ankare da inda hannunta yake ta zabura zata janye ya riqeta Yana matseta da bango ga idanuwansa dasuka qarasa hargitsata ta bude baki ahankali murya na rawa tace" Anty zarah na Palo kartayi tunanin wani Abu dabam....... Zancenta yasashi sake matseta jikin bangon tayi saurin rintse iso zuciyarta na harbawa tasake bude baki maganarta na fita a rarrabe tace" Dan Allah anty zarah nake gudun ta..... Bakinsa kawai taji akan nata sbd firgita batasan lokacinda ta qanqamesa da hannuwanta ba tana rintse Ido da qarfi. Qarar faduwar plates yasashi saurarawa daga kissing bakinta dayakeyi cikin nutsuwa ya saketa batareda ya kalli kowaccensuba yabar kicin din Dan yasan zarah tariga taga komai yasamu kansa dajin wani iri kamar nauyintama. Amatu kuwa rawa jikinta ya dauka tahau rawar murya tana zazzare Ido sbd tsananin kunya ko kallon inda zarah din take bata iya yiba ta durqusa tahau kwashe plates din tana cewa'' Anty zarah Yi hkr wallahi..... Katseta zarah din tayi cikin wata irin muguwar dauriya da danne kukan dake zuwar Mata tace" Saida safe zanje na kwanta. Juyawa tayi tabar gurin tana rufe bakinta sbd kukan dayake Shirin kufce Mata. Ajiyar zuciya Amatu ta sauke tana miqewa daga durqushen datake tattara kayan ta ajiye tareda barin kicin din itama tana sake tunano Abinda ya wakana tsakaninta da MD ZABEERA. Tana Shiga daki kwantawa itama tayi tana rufe idanuwanta tana Hana kanta tuno Abinda yafaru Amma kamar bazata hanuba zuciyar. Washe gari tun 6 tafito tafara aikin breakfast sbd tanada karatun dazasuyi da annah wata qawarta a school. Potatoe ball da toasted bread me kwai tayi musu sai lemon tea Takoma daki tayi wanka ta shirya cikin blue straight skirt da light blue chiffon top Me Fadi tayi rolling ta fito riqeda handbag dinta tana duba agogo batason tayi latti gashi key din motarta Yana hannunsa gashi da alama be tashiba tunda bataji motsinsa ba. Zaman jira ta dasa tanayi tana kallon agogo har kusan awa daya sai kawai ta hkr ta miqe ta fice zata hau taxi. Anty zarah ce tafara fitowa Bayan ta Dade da tafiyarta ma anty zarah din na zama a palon sai gashi yafito a shirye shima da kayan zaman gida ta tashi ta nufesa tana qoqarin Hana shedan Sanya Mata tunanin ko tare yakwana da Amatu ta Dan rungumesa tana qaqalo murmushi tace" Good morning. Dafa kanta yayi Yana amsawa kafin suka nufi dining Yana cewa ta dubo Amatu. Tayita knocking shiru saita bude kawai ta shiga taga Bata Nan taje har qofar toilet din dakin takira sunanta shiru saita tura qofar bayin nanma Bata Nan ganin sanyin toilet din yasa ta fahimci tayi wanka may b ta fita to Tazo ta fada Masa sai alokacin yayi tunanin may b tawuce makaranta. Breakfast dinsu sukayi anty zarah ta tattare gurin Bayan sun Gama tadawo gefesa ta zauna tana kallon news taredashi yanayi Yana amsa wayoyi ahankali. Da Rana ganin sun buqaci abinci yasa anty zarah dafa Masa noodles da kwai itakuma tasake cin sauran breakfast din dasuka rage sbd yafi Mata dadi. Wanka takuma yowa ta sanyo riga da skirt na atampa tafito tana waya da ummanta dake sake jaddada Mata tayi hkr da dauke Ido akan duk Abinda zai Bata ranta Dan Abinda bakada maganinsa gwara ka rungumi hkr da dauke Ido Dan ita umman batamaso zarah din tabiyosaba da nufin Wai zata Zo duba Muhammad ne sbd tunda aka taho dashi Bata taba ganinsa ba saigashi suna zuwa sukuma suna tafiya. Zama tayi daidai fitowarsa a shirye kamar fita zaiyi ta miqe tsaye tana Yana kyawu da cikar haibar mijinta Wanda kullum sonsa ke qara Shiga Yana Kama kowane lungu da saqo na zuciyarta.. Gabansa tazo ta tsaya tana kallonsa shima ita din yake kalla ganin irin kallon qurullar datake Masa yasan ba komaine ke dawainiya da itaba sai sonsa sai yaji tausayinta da qaunarta na sake shigarsa ya janyota ahankali ya rungume cikin jikinsa Yana shafa Bayanta ahankali Jin yanda take sauke ajiyar zuciya ta dago kanta ta kalli fuskarsa cikin sanyin murya tace" I love you so very much MAHMOUD ZABEERA.. Dora bakinsa akan nata yayi ahankali Dan nuna godia ga Abinda tafada din. Qarar rufe qofa da qarfi dasukaji yasashi dagowa yana kallon qofar shigowar sukai Ido biyu da Amatu dake Masa wani irin kallon tsana zuciyarta na harbawa da qarfi saikuma ta maida kallonta Kan anty zarah da itama takejin wani iri akaro na farko dataji kaman taji kunyar Amatun ta qaqalo murmushi tana basarwa ta qaraso ciki tana saka wayarta cikin handbag tace" Anty zarah sannu da zaman gida nafita Baki tashiba shiyasa na fice bansanarba gashi ma wallahi lattin danai gudu saidanayi. Ayya bakomai Nima ai nayi tunanin kinjira banfito da wuri ba. Hanyar bedroom dinta ta nufa batareda ko inda yake ta kalla ba batama nuna alamar tasan da mutum ba tana cewa'' Bari nashiga ko sallah banyiba wlh. Kamar bazai kalletaba saikuma ya Dan juya yabi bayanta da kallo kafin ya juyo ya kalli zarah yace suje. Daki taje ta dauko mayafi da wayarta ko jaka Bata daukaba suka fice. Tunda tagama sallah tayi wanka ta fito taci abinci take zaune Palo tayi waya dasu iyami,tayi da kawu,tayi da umme,tayi da Dr salman zabeera tayi da USI Wanda sukafi awa suna Magana duk Dan tasamu sauqin Abinda takeji aranta Amma takasa samun salama sai kawai ta kunna TV tafara kallo tana dariyar qarfin hali kamar wata wawuya. Kallon agogo tayi taga qarfe goma harda minti arba'in ta miqe taje kicin ta hado tea tadawo ta zauna tana durawa cikinta idanuwanta akan kallo. Goma da Sha daya da minti Tara taji bude qofarsu ta Dan kalli agogo taga lokaci taci gaba da kallonta tana Shan tea suka shigo ta Dan dago ta kalli anty zarah ta saki murmushi tace" Lah anty Ashe fita kukayi banma Ankara ba wlh na dauka kina ciki kina bacci. Kallonta yayi da mamaki saidai ko inda yake batada niyyar kalla ta tashi tana cewa'' Anty kawo kayan na riqe Miki. Ta karbi kayan hannun anty zarah din yakai Mata har dakinta ta fito tana cewa'' Bari naje na kwanta gobema inada zuwa makaranta da safe. Shigewa tayi ta rufo qofa ta Isa bakin gado ta zauna tareda sauke ajiyar da numfashi me qarfi idanuwanta na cikowa da hawaye batasan lokacinda ta kifeba Tana sakin kukan kewar Dr khalil dinta. Washe gari ko abincin breakfast qin Yi tayi ta wucewarta makaranta taga keys dinta na mota ya ajiye Mata a palon taqi dauka ta tafiyarta. Bata dawoba sai yamma tayi shigewarta bayan tashiga har dakin anty zarah sungaisa. Washe gari ma haka takuma ficewarta ba Wanda yaganta sai abin yazama kamar tana wasan buya dasune Dan tasawa kanta zama very busy kullum Babu me ganinta take fita har gwara idan tadawo sukan gaisa da antyn tata ogan gidan kuwa Sam taqi Bari suga juna tuni kewar su Anty salamatu da Muhammad suka sanyota gaba gashi meenat batanan bare taje gidanta, Wata Rana idan tafita shopping kawai take zuwa idan ba makarantar sbd kawai ta Hana kanta zama gidan. Kusan kwana takwas kenan tana wannan wasan buyan dasu duk da itama ta matuqar gajiya da wannan yawon hutu take buqata Amma bazata iya zama gidan ba matuqar ba tafiya sukaiba sbd har yau fama take da ciwon zuciyar Abinda idanuwanta sukai Mata gani shiyasa ta zabi raba kanta da zaman gida. Yau sai magriba tadawo gidan amatuqar gajiye take Bata tararda kowa agidan ba da alama sun fita basa Nan Dan har dakin anty zarah tashiga Bata nan sai kawai tayi wankanta tayi sallah ta sanya wata qaramar riga Mara hannu red da bumshort baqi wanda ko cinyarta bai saukaba sosai tafito ko dankwali Babu akanta taje ta sanyawa qofar shigowa key tana sakin numfashi Dan rabonta data sakata acikin gidan tun ranar dasuka Zo tasaba Bata cika son Kaya masu nauyiba yanzu kullum kayanta gajeru ne dasuna sukadai Amma tunda sukazo take a takure. Kicin ta nufa ta hada celeals din Muhammad Tasha acan kicin din Tasha ruwa tadawo Palo zata zauna sai ganin mutum tayi zaune Yana waya a natse cikin tsananin firgici da tsoro ta bude baki Yana lurada Abinda zatayi ya janyota ta Fado kansa ya sanya hannu daya ya rufe Mata bakin Yana kallon cikin tsakiyar idanuwanta dake kallonsa ahankali yace" Shihhh wayana me mahimmanci ne don't make a sound.. Tsit tayi tana kallon bakinsa dake Magana da Wanda yake wayar cikin burgewa da rashin garaje. Maida kallonta tayi Kan qofar shigowa taga tananan rufenta to kenan Yana dakinsa Koda tayi tunanin basa gidan., Qofar dakinsa ta kalla batasan lokacinda tace" Ina anty zarah?? Wani kallo ya juyo yayi Mata na tsawon mintuna kafin ya datse wayar dayakeyi ganin yafara rasa gane Abinda suke tattaunawa ya ajiye wayar Yana kallon fuskarta da ba annuri ya sake matseta cikin jikinsa yace" Mezaki Bata da kike tambayarta? Qin kallon fuskarsa tayi tafara qoqarin qwacewa tana cewa'' Sakeni kada ta fito ta...... Menene koyaushe kike cewa kada ta fahimta? Kallonsa tayi a gundure tana sake qoqarin qwace jikinta tace" Matarka ce Dan haka bazataji dadin ganinka da wata ba.. Bakinta ya kalla cikin taushin muryar son qureta yace" Hakan kikeji shiyasa kike ganin kaman itama hakan takeji. Da sauri ta kallesa tace" Menene? Ni banma San me kake cewaba. Matsota yayi ta qarasa mannewa jikinsa ya kalli fuskarta zuwa bakinta dazaiyi kissing saikuma ya fasa ya miqe da ita a jikinsa ya nufi hanyar dakinsa sbd dukkaninsu idan ya fahimci matsalarsu ta baifi kowacce data Ganshi da 'yar uwarta ba Amma na Amatun yanason tabbatarwa ne idan yashiga zuciyarta kamar yanda yake tunani sbd zafin kishi me tsananin daya hango a idanuwanta. A tsakiyar gadonsa ya kwantar da ita tareda sakar Mata dukkanin nauyinsa ta rintse Ido sbd idanuwansa dake son karya kuzarinta tadan juyarda fuskarta ta bude baki daqyar sbd mutuwar jiki tace" Anty zarah zata..... Rufe Mata baki yayi Ahankali da nasa Yana Dora hannunsa Kan wuyanta zuwa kirjinta dake harbawa da sauri har batasan lokacinda ta qanqamesa ba tana bude idanuwanta akan nasa idanun dake kallonta cikin wani irin yanayin daya qarasa kashe jikinta Ya saka hannu yafara zare qaramar rigar jikinta ahankali tayi saurin rufe Ido sbd rigarce kawai ajikinta batada ko bra... Qarar doorbell ne yasata bude idanuwanta ahankali ta Dora akan nasa idanun dasuka sauya kala ta janye jikinta ahankali tareda mirginawa gefe tana Jan duvet ta rufe qurjinta ya saki wani qaramin numfashi tareda tashi zaune yafara daidaita kansa ya miqe ya fita dakin. Kobaa fada ba yasan zarah ce tadawo daga gidan qawarta dataje Dan haka Kai tsaye ya bude qofar fuskarta daukeda murmushi ta shigo zatai Masa Magana yanayinsa yasa gabanta mummunan faduwa ta kalli fuskarsa da sauri zatayi idanuwanta na cikowa da hawaye ganin hakan yasashi Dan dafe goshi Yana cewa'' Wat a hell""zama da Mata fiyeda daya. Kallonta yayi Kai tsaye sbd bai iya kame kame ba yace" Zan kwanta and kada ki nema AMATULLAH zata Kwana adakina after 2 days Zaki kwana so please don't make it too difficult for me kije ki kwanta I know you're tired. Kadan ya rage anty zarah ta Dora hannu akai ta zunduma ihu Tafi kowa sanin MAHMOUD din Dan Kai tsaye ne bai iya kwana kwana ba Amma Bata dauka rashin kwana kwanarsa yakai hakaba da zai iya haikatata wata ran. ##mamuh# 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 40_* Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana tunanin inda rayuwa ta daukota tun kuriciya da inda zata kaita kokuma inda yakawota yanxu, Auren mijin wata Sam baya cikin mafarkinta ko tunaninta sbd itama tafison ta bugi gaba da mijinta natane bawai na wata tazo ta aura ba Wanda koma dai yayane mijin wata ta aura za'a ce, Babbar damuwarta yanxu shine rashin sanin makomarta a wannan auren yanxu, Tarigada tasani tabbas yaudarar kanta take da tunanin rabuwa da Rabin ran Anty zarah sbd a zabeera Kam ba Maganar saki sai bisaga girmammiyar qadda ko mutuwa, To ita ga mutuwar ma ta raba Amma Basu barta ta tafiyarta ba an daureta da auren Wanda takewa kallon ya haramta gareta sbd Yana mijin Zarah.... Motsin bude qofa taji Wanda yasata sake rintse idanuwanta tana sake yin tsit sbd sanin shine yadawo Bata tunanin iya kallonsa sbd dai ba tantama a daki daya zasu kwana dan haka gwara ta lafe gari ya waye su Dan inda dare yamusu. Kallonta yayi yaga yanda take lullube har Kai sai bai damuba ya nufi closet ya tube yafada toilet yayo wanka Yana fitowa shima kayan baccin ya dauka ya sanya tareda fesa mist ya nufi gadon ya hayewarsa ya kwanta tareda Dan Jan lullubin ya shige a gajiye yake shiyasa Yana kwantawar bacci ya daukesa ba Bata lokaci. Mamakinsa takeyi ta yanda ba wani tunani ya hau gadon ya kwanta bayan yaganta akai kwance,Abinda Bata saniba shi Sam baima San wani Wai ka kwanta qasa ko Kan kujera ko wani dakin Kan kowane dalili ba Abu daya yasani baya sauya gurin kwanciyarsa akan komai, Ko agida zarah ce ma idan ta fahimci Yana tattareda gajiya wani lokacin take komawa dakinta ta kwana tabarsa ya huta shikuma tunda raayaintane wannan baitaba hanata tafiyar ba saima sakewa dayafi Yi da hakan wani lokacin Tana cikin tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita. Da asuba saidata Gama sallah ya tadata ta tashi tayo alwala da jallabiyarta tayi sallar tana gamawa ta cire Takoma tayi kwanciyarta Takoma bacci abinta sbd itamadai bazata iya takura kanta sbd shi ba musamman ma data lura idan ta takura kanta din ko ajikinsa. Shima tana jinsa yagama wayoyinsa yazo ya kwanta kusan atare bacci Yakuma daukesu Basu farkaba sai guraren 10 na safen. Itace tafara bude idanuwanta ta sauke akan fuskarsa dake fuskantar tata tafara kallonsa ahankali tana tuno haduwarsu ta farko data biyu data uku duk agun sata ne take taji kunyar abin nadawo Mata har batamasan tana rufe fuskarta ba tana girgiza Kai saijin tayi cikin muryar bacci yace" Kadama kifara wani banzan tunani akaina I can smell your blushing.. Zaro Ido tayi da sauri cikin wata sabuwar kunya Amma saidatace" Wane tunani zanyi akanka dazaisani Abinda kace kanaji?ni bana tunanin komai....da sauri ta yunqura ta tashi zaune zata sauka ya riqo hannunta Wanda yasata saurin juyowa ta kallesa zuciyarta na Fara bugawa da qarfi shima ahankali ya bude idanuwansa dake rufen bacci baigama dakinsu ba ya sauke akan fuskarta tayi sauri dauke Ido zuciyarta na tsananta bugu har kirjinta na sama da qasa Ya gangaro da idanuwan nasa Kan kirjinta dake sama da qasa da sauri alamar zuciyarta ce ke harbawa da sauri batareda yayi Magana ba sai ya saketa ta dira da sauri ta shige toilet batareda tasan abinyi ba sai kawai ta bude sabbin brushes din data gani ta dauki daya tafara brush tana kasa kallon fuskarta ko a madubi sbd Jin wani iri kamar kunya kamar fargaba da tsoro. Murtsike kunyarta tayi ta fito tana daure fuska ta tarardashi zaune Kan sofa Yana kunna wayarsa daya kashe da asuba ta nufi fridge ta bude ta aduko lemun carrot da lemon ta zauna a wata kujerar ta bude tafara Sha ahankali batareda ta kalli inda yake ba. Yana cikin toilet aka kawo musu breakfast din dayayi oda da kayan sawa ta karba tareda ajiyewa tana qoqarin duba kayan sbd jeans ne da riguna take gani Abinda takeda burin yiwa Dr khalil zabeera kwalliyarsa har saiya manta da kowace mace duniya Bayan mahaifiyarsa Amma Ashe basuda wannan rabon. Astaghfirllah" tace tana ajiye kayan daidai fitowarsa Taso Fara cin abincin Amma gabaki daya Babu Abinda ta taba gani aciki bare tasan ya akecinsu shiyasa ta haqura harya Gama Jan ajinsa da ja Mata Rai yazo ya zauna Kai tsaye tace" Nifa yunwa nakeji bansan wanne ne naciba wanne ba'a ci Yi sauri ka nunamin.... Baisan lokacinda ya juyo gaba daya Yana kallonta ba wato yamayi sauri... Irin yanda take kallon abincin yasashi sakin wani boyayyan murmushi akaro na farko Jin shiru tafara hasala tace" Nifa yunwa nakeji nace fa. Baisan lokacinda bakinsa yace" Ok" ba Fara zuba Mata tea yayi ya miqa Mata kafin yafara zuba Mata egg source cikin boiled veggies sbs taji dadin ci Amma Ina tana shanye tea din taci spoon daya na abincin taji zuciyarta na neman tashi ta ajiye tana kallonsa tana girgiza Kai alamar bazata iya ciba. Tea din yasake zuba Mata kafin yasanya spoon yacire komai na cikin tsakiyar burger dinsu ya miqa Mata yana nuna Mata Tasha da tea din. Kaf tea din ita tashanye shi sbd shikadaine Abinda zata iya sawa cikinta shikuma tana kallo yanacin abincin cikin kwanciyar hankali ganin abin zai tayar Mata da zuciya yasa ta miqe ta shige toilet wanka. Bata San yanzu akeyintaba Saida tagama wanka ta daura towel takasa fitowa ta zauna ciki ta shafa Neutrogena oil din data gani aciki tazo jikin qofar ahankali tace ya miqo Mata kayanta...harta juya ta tsaya cak sbd tuno hadda bra zai miqo kenan saiya taba Mata gidan nono da sauri ta fito tana cewa'' Barshi barshi nafito Zan dauka da kaina,. tsayawa tayi tana Masa kallon mamaki ganinsa zaune ko alamar ma zai miqo Mata kayan beyiba kamar yanda ta zata kenan da barinta zaiyi a toilet din tayita zaman jira. Takaici yasanyata daukar kayan da qarfi tana daure fuska zuciyarta na zugata akan tabi takan qafarsa ta take Amma ta share ta nufi wardrobe ta bude ta dauko undies dinta tana juyowa taga bayanan kenan yashige toilet a fili taja guntun tsaki tana cewa'' Anty zarah kinada qoqari gskia. Turarensa ta fesa kafin ta shirya cikin kayan ta tsaya tana kallon kanta tanajin wani iri sbd irin pencil jeans dinnan ne yakama Yan dogayen siraran cinyoyinta har gwara rigar is loose me Fadi ce sosai Amma ba wani tsayi gyalen jallabiyarta ta daura akai bayan tagyara Daurin talwataccen gashinta daya dan yamutse gurin bacci. Zaunawa tayi abinta tana lallatsa wayarta sbd dama can ita Allah beyita da nuku nuku ba Kuma burintane samun wayayyar rayuwar Jin Dadi da sakewa, Bata samu daga Wanda taketa mafarki da buri ba wato Dr khalil dinta yanzun dinma bawai tana maida burinta akan MD bane kawai dai zata sakewarta ne bazata takura kanta ba shiyasama batai wata doguwar damuwar akan kayan ba. Dagowa tayi Jin motsinsa idanuwanta suka sauka Kan budadden jikinsa dake tsiyayar ruwan wanka qugunsa Kuma daureda towel brown da sauri ta dauke kanta tana Dan Sosa kanta daya dau qaiqayin bazata. Ganin da gaske shiryawa zaiyi gata a zaune yasata saurin miqewa Takoma gaban TV ta qurawa Mata idanuwa ko qyaftawa batayi tana jinjina ko inkularsa lallai wannan mutumin dasuke gani a zabeera Basu sanshi ba. Tsaf ya shirya cikin qananan kayan wainda suke kalar nata sky blue jeans da farar transparent shirt ko zama beyiba ya kalli Inda take yace ta tashi suje. Da sauri ta miqe zata dauko jallabiyarta yace no need for that Aiko tabiyosa suka fice. Wata kyakkyawar mota ya karba daga hotel din tareda driver suka fita. Gurin abokanan aikinsa suka Fara zuwa wani hotel dake kusada wani ruwa acan suka kwasa sukai bakin ruwan taredasu da abokin nasa mr folaye da matarsa me sabon qaramin ciki daya 'dan fito kadan. Sakewa tayi da meenat matar folaye sbd yanda tayita janta ajiki take suka Fara sabo anan ne ma taci abinci sbd na Nan yanada dama sosai akan na hotel dinsu sbd akwai chips da noodles akwai pasta duk tasamu taxi daga Nan suka kwasa zuwa wani farm house inda Nan ma sunyi ciye Amatu tasamu abokiyar ciye Nan tasake suka ringa cin duk Abinda bakinsu zai iya daukar dandanonsa Dan itama meenat zuwansu na farko ne Nan da mijinta yayi da ita. Basu Fara Shirin komawa ba sai dare sosai inda taji tafison masaukinsu meenat yafi Dadi ba kunya ta roqesa su koma can ga mamakinta kuwa baice komaiba Amma saigashi anyi musu folaye yasa anmusu reserving suite sukai kwanciyarsu anan. Washe gari sukaso komawa Amma suka shiririce itada meenat wani gurin shopping da aka kaisu gashi yau dinma qananun kayan ne ajikinsu na yau sunfi daukar kalar fatarsu da yimusu kyau sbd black ne gashi ba laifi dukkaninsu sunada hasken fata matuqa Suna zaune a wani snacks and coffee restaurant dake bakin ruwa saiga Kira yashigo wayarsa Yana dagowa yaga video call zarah na Masa. Sam baisan meyasa zarah yanzu take Masa video call ba Bayan shi tunda sukai aure bai tana cewa sunyi video call. Dauka yayi a natse saigata ta bayyana kyakkyawar fuskarta dataji simple makeup na Masa murmushi Ahankali ya sauke numfashi Yana amsa gaisuwarta da dorawa da cewa'' You look great. Wani irin Dadi ne yakusa kasheta sbd baitaba yaba kwalliyarta ba sai yau din ta washe baki tana kallon kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani sirrin kwarjini da kyau tace" Thank you,ya kake?ya Athens? Dan kallon wuyanta dake bayyane sbd fadin wuyan rigar jikinta yayi ba laifi yanayin shigar ya burgesa baisan yaushe zarah tafara koyan saka irin kayan Nan ba ya bude baki a hankali yace" Alhmdlh.. Amatu dake hotuna da meenat tunda yafara wayar hankalinta ya Dan koma kansa tafara qoqarin sharewa gano da anty zarah yake wayar meenat ta kalleta tana cewa'' Da waye MD ke video call and he seems to be relaxed and cool da yanayin wayar? Numfashi Amatu ta sauke tana murmushi tace" Da matarshi yake waya antyna. Kallonta meenat tayi dakyau tana sake duban MD dako inda suke baya kallo sai kawai tura Amatun kansa da qarfi tana cewa'' Oh I'm so sorry I lost my y balance. Kyakkyawar faduwa tayo ajikinsa sbd Saida gaba daya qirjinta ya hadu ya manne da nasa dayake shima a bazata yajita jikinsa saiya riqeta sbd karsu Fadi qasa daka Kan kujerar dayake. Anty zarah maganar da zatayi bace Mata tayi sbd ganin Amatun jikin MD ba qaramin raunana ganinta da zuciyarta yayi ba ta maida kallonta Kan kayan jikin Amatun saitaga komai iri dayane Dana MD din banbanci nata na Mata nashi na maza hakama budewar wuyan rigar Amatun yasa taji tana kamo nata tana rufewa sbd Abinda taji Yana danne maqoshinta Kai tsaye ta kashe Kiran da kanta tana barin hawayenta saukowa ta kife Kan gadon datake zaune tareda fashewa da wani irin kuka Mai ciwo. Su kuwa can Amatun ce tafara sakinsa ta sauka daga Kan jikinsa tana qin kallonsa sbd yanda taji hankalinta ya tashi da yanda anty zarah ta gansu wani bangaren na zuciyarta Kuma wani irin nauyi takeji saitaji gurin ya gundureta ma gaba daya ta wuce batareda tacewa kowa komaiba. Washe gari Koda qarfe dayan Rana tayi sundawo harsunyi Shirin zuwa asibiti sbd ranar ne ranar sallamar Muhammad shiyasa duk damuwarta ta kau cikin tsananin farin ciki take su umme ma sunyi waya zasu hade a asibitin gurin daukosa sbd zumudi tarigasa fitowa Yana saukowa suka fada mota suka nufi asibitin. Koda suka Isa sun tarardasu umme Kallo daya umme tai Mata tasan komai yafara daidaituwa sbd yanayin 'yar walwalarta daya Fara dawowa. Bayan dogon formalities aka sallamesa aka Basu dansu murna agurin kowannensu ba'a mgn saidai anbasu kakkauran sharadin kada aringa barinsa sanyi na shigarsa sosai sukace sunji. A gida sasai aka ringa kiransu ana murnar samun nasara saidai anhana ashigo jirgi dashi saiyayi qwari sosai yasamu lafiya shiyasa ana sake kwana biyu umme ta tahowarta shima MAHMOUD din wata tafiya takamashi aka bar Mata anty salamatu. Ahankali suka Saba da zaman qasar da Jin Dadinta tareda Fara sanin gurare Dan suke Kai kansu siyayya da sauran wasu abubuwan musamman dasu meenat Suma sundawo garin saita haihu zasu koma, Ga Muhammad tuni ya warware yayi girma abinsa yanzu Yana samun nono koyaushe take ya canza yafara girma gashi hadda jiki sosai yayi gwanin sha'awa, MD na kiranta lokuta da dama Amma iyakacinsu gaisuwa sai ya tambayi Muhammad wani lokacin ma anty salamatu yafi Kira. Abu daya ne matsalarsu a garin shine rashin turancin arziki tayiwa kawu mgn saigashi kawu yaje har zabeera da kansa yayiwa su Andi tunin alqawarinsu na barinta karatu Allah yasa MAHMOUD din na Nan sai sukai Masa maganar yasanyata makaranta acan da zaman banzar. Tunda anty zarah taji tafiya zaiyi zuwa Greece taji hankalinta nason tashi Amma ta danne sbd ba laifi ya Dade sosai a gida wannan karon saita danne harda saqon gaisuwarta ga Amatu sbd har yanxu tunda akai auren basuyi mgn ba sbd kowa bai Gama daidaituwa da al'amarin ba. Zaune suke a Palo itada Muhammad dake koyan zama anty salamatu Bata Nan taje gidan meenat dake Dan zazzabi sosai ta tayata hidima. Riga da guntun skirt ne ajikinta Wanda bai kamata ba ko kadan sai hular babies dake kanta Bata Gama rufe Mata gashin Kai ba Wasa takewa Muhammad sosai Yana dariya taji bude qofa batareda anyi knocking ba ta juyo da sauri cikin mamaki sai idonta ya gane Mata shi batasan lokacinda ta saki baki ba tana kallonsa da dukkanin zuciyarta. Shima ita din yake kallo yanda Takoma kamar wata yarinya qarama Babu me cewa itace uwar yaron gabanta tafi Kama da yayarsa ta kusa bama ta nesa ba. Muhammad dake bangala dariya ya kalla har baisan lokacinda ya sakar Masa kyakkyawan murmushi ba yana nufosu. daukarsa yayi Yana kallonsa cikin tsananin qaunar yaron yace" Muhammad you're looking great and handsome. Kallonta yayi ta sauke kanta tana cewa'' Sannu da zuwa. Bai amsaba bai Kuma dauke idonsa akantaba saima kissing Muhammad da yayi a fuska Yana cewa'' Thank you. Bedroom dinsa ya nufa daukeda Muhammad Yana cewa'' Ko Zaki gyaramin dakin bazai rasa quraba. Bayansa tabi da kallo tana mamakin kyawun daya qaro da wani irin haske Kodan ta Dade Bata gansabane. Akwatinsa ta tura zuwa dakin nasa ta kallo sbd shine shigarta na farko Dakin komai na cikinsa farine Wanda ta fahimci shi din yanason farin Abu ta dauko mop da bucket da sweeper ta a ajiye tafara gyaran dakin bayan ta sauya Masa zanin gadon ta goge komai Yana palo tafito Bayan tagama komai ta karbi Muhammad ya wuce bedroom. Da daddare Koda anty salamatu tadawo ta tararda zuwansa tunda tashige daki Bata sake fitowaba Saida safe shima tana Gama shirya musu komai ta wuce gidan meenat sbd zasu sake komawa asibiti da ita yau. Dakansa ya dauketa yaje ya Samar Mata admission da komai na makaranta ya damqa Mata daga can gidansu meenat sukaje dubata. Dagacan gurin cin abinci suka biya sukaci kafin suka dawo gida. Kwanansa takwas a qasar kafin yatafi da kewar Muhammad daya shaqu dashi cikin kwanaki qalilan Dan kullum a hannunsa yake Rabin kwana sai dare sosai yake maidasa hannun mamansa. Itama bayan tafiyarsa yabarsu da kewarsa sbd kwanakin kullum Muhammad na taredashi. Sosai ta nitsa cikin karatunta gadan gadan musamman dayake me wuyane karatun sbd medical ne tana karantar gynecology sai yazamto hankalinta nakan karatu yanzu fiyeda komai, USI yazo Mata tareda Dr Salman har so biyu Wanda yasata Jin Dadi fiyeda tunani musamman usi daya dauki Muhammad a hannunsa ji yayi kamar zai hadiyesa sbd so da qauna, Kawu da iyami ma kullum cikin waya suke Gama umme Anty zarah ce dai har yanzu ba wani sauyi sbd takirata har so kusan uku Bata taba daukar wayarta ba shiyasa ta Dan dakata tukuna. Ta bangaren MAHMOUD ZABEERA kuwa Babu wani sauyi a rayuwarsu saina qaunarsu data zama kamar daya akan 'dansu sbd tunda Muhammad yayi wayon sanin babansa yake zuwar musu akai akai sbd yaron dako yaushe dadynsa yakeson gani Dan tuni yayi wayo sosai Dan kusan shekararsa biyu kenan harda watanni. Duk Wanda yasanta abaya yanzu bazai iya ganetaba idanba farin sani kayi mataba, Ta sauya sosai daga Amatun blue fox Takoma AMATULLAH zabeera, Sam halayyarta da yanayinta sun sauya, Yanzu ita mace ce me nutsuwa da Kamala, Mace ce me aji da ilimin Boko ya shigeta yake Kuma bayyane atareda ita sbd ko zaman awa daya kayi da ita zaka fahimci da likita kake zaune musamman gashi suna shekarar qarshe ta kammala karatunta, Amatse take data samu hutun wannan shekarar taje gida sbd tayi masifar kewar iyayenta Dan tunda tazo bataje gida ba Har gwara anty salamatu taje gida harta Dade sosai kafin tadawo gashi ko yanzu tana Shirin zuwa ganin gida Kuma tareda Muhammad zataje wannan karon, Ga USI ma yagama karatunsa yanzu yadan Fara aiki a asibitin zabeera. Yau su Anty salamatu da Muhammad suka wuce tana dawowa daga rakiyarsu airport ta shige daki ta tube tayi wanka tana fitowa ta sanya three-quarter pink da farar riga Mara nauyi ta daure gashinta da band ta saka qaramar hula ta nufi kicin ta hado flakes da sabuwar madarar ruwa me sanyi ta fito Palo tanasha taji ana qoqarin bude qofa Kai tsaye tasan MD ZABEERA ne ya shigo qasar sbd tasaba da duk zuwansa saidai suji bude qofarsa kawai baya knocking kamar sauran baqi. Juyowa tayi gaba dayanta daukeda mug din hannunta ta kallesa da fararen idanuwanta kafin ta qyafta idonta saiga anty zarah ta fito daga bayansa tana shigowa tareda rufe qofar take kofin hannunta yaso kubucewa tayi saurin taresa hannunta na rawa. ##Mamuh# 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 42_* Da lakabe anty zarah takai kanta cikin daki sbd dishi dishi da idanuwanta ke 'dan gani hakama kaf kuzuri da qarfin qafafunta sun Gama sarewa tun kafin ta Isa bakin gado ta zame ta zauna tareda sakin wani wahalallen kukan dakeson fito Mata tun lokacinda MAHMOUD yabude baki yafara Mata mgn. Shikuma fridge ya biya ya dauko freshmilk me sanyi da ruwa ya nufi bedroom dinsa yanajin wani irin walwala da nutsuwa na qadatuwarsa. Har lokacin kwance take cikin lullubin data rufe jikinta da Babu riga tayi zuciyarta na qoqarin zuqar numfashin dake neman gagararta, Tasan tabbas anty zarah ce tadawo shiyasa ya, yafi kowa@' try da kansa and xa zuwa ga bude Mata qofa batareda yasamu ko damar ce Mata Yana zuwa ba, 7 ya tube yashiga bai wani jima ba yafito ya sanya kayan bacci kamar koyaushe farare tas dasu yazo ya zauna Yana duba saqonni ta laptop da aketa kiransa akai yanashan freshmilk data rage sanyi yanayi Yana kallonta cikin kulawa tunaninsa tayi bacci. Rufe aikin yayi ya miqe tareda qarawa AC din dake aiki qarfi sbd lullubin dazaiyi shima ya nufi gadon yahau tareda shigewa duvet din inda fatar bayanta da Babu komai ta hadu da fatar qirjinsa dake bayyane sbd rufe botiran rigar baccinsa da bayayi a qaida. Rufe idanuwa da qarfi tayi zafin zuciyarta na tunzuro Mata da fitar da yayi dazun ta yunqura zata matsa daga jikinsa saiga wayarsa na qarar data sanyasu tsayawa su dukan musamman ita data gama sanyawa ranta Anty zarah ce sbd idan ba ita matarsa ba waye zai kirasa cikin dare daidai wannan lokacin. Shi Sam baida niyar ko kallon wayar sbd Koda Rana ma daukar wayarsa ganin dama ne bare yanzu da dare, Katsewa Kiran yayi yakai hannu ya dauko wayar da niyar kashewa saiga shigowar massage daga umman zarah ne ya tashi zaune Yana duba Kiran daya katse yaga ita 'dince takira saiya koma ya bude massage dinta, "_Mahmoud Dan Allah kaje kayi mgn da zarah ka fahimtar da ita qarin aurenka ba Wai qarshen rayuwarta bane tanata kuka hankalina yatashi nakasa samun nutsuwa nasake kira Bata dagaba morethan 8times. _" Yana Gama karanta saqon ya 'dan dafe goshi Yana Jin tun yanzu kamar kansa na neman qullewa, Ta Yaya zarah zata damu kanta da kuka Bayan bawai yanxu ne akai aurenba, Auren da shekara uku yanxu Amma tanason saka Masa ciwon Kai ga Amatun ma yaga alamar ita buga kansa zatayi ma da rigimarta. Bai sake kallon Amatun dake kwanceba har lokacin taqi motsawa ya sauko Kan gadon ya zura slippers tareda aje wayarsa ya fice dakin. Yana fita ta rintse ido sai alokacin hawayen dasuka bushe Mata suka Fara gangarowa ba qaqqautawa Zuciyarta wani irin radadi da bugu takeyi kamar zata fasa qirjinta, Wannan wace irin qaddarace tahadata auren Dame Mata, Wace irin masiface wannan takejin kanta ciki sbd tiririn dake fita daga qirjinta Jin takeyi gwara ta mutu tabi Dr khalil dinta ba aure da wannan masifa, Uban me yasa zai ajiyeta Dan ya ringa barinta Yana tafiyarsa saikace wata Mara sanin ciwon Kai. Ta sauko daga gadon tabar dakin ma takasa sbd Sam ko qafafuwanta bataji ajikinta sbd rufewar zuciya, Hawayentane ke tsananta gudu suna jiqa pillon da kanta yake kai. Tashi zaune tayi ta kalla agogo idan tana qirgen mintuna daidai to yafi mintuna talatin da barin dakin. Tana Nan zaune idanuwanta na sake rinewa har tsawon awa daya da mintuna ta miqe tsaye ta janyo towel ta daura ta nufi qofa ta fice bayan ta share idanuwanta dasukai jajir ta nufi dakinta. Tana Murda qofar dakinta Yana fitowa dakin anty zarah din ko kallon inda yake bataiba ta shige kafin ta rufe saigashi a bayanta Yana kallon idanuwanta dasuka bayyanar Masa da halinda take ciki ya riqo hannunta ta janye batareda ta dago ta kallesaba ta nuna Masa qofa tace" Bacci zanyi can you leave please. Kallon fuskarta yasakeyi yanason ta kallosa su hada Ido Amma taqi saima gado data nufa ta haye zata kwanta cikin qosawa da fitinarsu yace" Akan zarah ne?? Tsayawa tayi tareda dagowa tayi Masa wani irin kallo sai alokacin shedan ya lurar da ita kamar rigarsa jikinsa tayi squeezing ta maido kallonta Kan fuskarsa tace" Meya kawo sunan anty zarah anan? And akan wani dalili zaisa naji haushin kebantuwarka da matarka bayan nafo kowa sanin kanada iko zuwa inda take aduk lokacin dakaga dama Koda kuwa waye agabanka ko atare dakai. Idan kinsan hakan then wats all this drama da kukan nan.??? Wani mugun takaici ne ya ciyota ta sauko Kan gadon tazo gabansa ta tsaya tace" Idan har kana tunanin nayi kuka kokuma kukan danayi akan kaje gurin matarkane then u're dreaming sbd hakan baya gabana and idan kana buqatan kebewa da ita meyasa ka zabi zuwa Nan da ita akwai guraren dazakuje da basai ka tsaya yiwa wani bayanin Abinda yakaika dakin matarka, Matark,Matarka,Matarka,Matarka please spare my life nagaji da Jin wanna hayaniyar infact inaga I will have to give you guys a break ta yanda zaka...... Will you just keep quiet" yafada a Dan hasale shima sbd tashin hankali da fitinar daya samu kansa ciki kaf rayuwarsa wannna shine karo na farko da wani ya tsaye yake fada Masa magana mace ma kuma bama namiji ba shi baima taba sa'insa da wani ba. Kukane ya balle Mata tace" Nazamar muku lalura da zamana atsakaninku Nima kun Hana zuciyata nutsuwa da shigowarku cikin rayuwata ta bangaren aure.. So yayi yai Magana Amma yafasa sbd juyawar da kansa keyi tuni idanuwansa suka sauya ya juya yafice daga dakin. Bakin gado ta koma ta kwanta tareda sakin wani sabon kuka tana Kiran sunan Dr khalil daya tafi yabarta har haka ta sameta. Washe gari gidan kaf cikinsu Babu Wanda yayi bacci musamman shi da sautin kukan daya baro tanayi ya hanashi ko rintse idanuwansa Wanda ya haifar Masa da ciwon Kai me tsanani Dan haka Koda gari ya waye ya yanke shawarar zaiyi tafiya kozai samu samu nutsuwar zuciya data cikin kansa. Tun kafin su tashi Amatu tariga kowa tashi ta wucewarta makaranta bayan ta barwa anty zarah note din ta tafi school bakin qofar dakinta Dan batai niyar Shiga dakinba sbd kada antyn ta fahimci halinda take ciki, Itama zarah din daga ciki ta rufe qofar yau batada niyar budewa Amatun sbd kada ta fahimci halinda take ciki sbd nemawa kanta sauqi ma cikin Daren tayiwa kanta booking ganin likita a _Santorini_ ta Dan samu tabar gidan na kwana biyu ko zata samu nutsuwa Dan haka tanajin ficewar Amatu itama ta tashi ta shiga wanka tana fitowa ta shirya ta dauki duk abin buqata ta dauki waya takira numbern MD cikin sa'a kira 'daya tana daf da katsewa ya dauka tafara gaidashi cikin sanyi da nutsuwa Ya amsa Mata kamar ko yaushe kafin tayi Masa bayanin tafiyarta ganin likita yayi shiru da farko saikuma yadan gyara murya kadan yace ta fito idan tashirya su tafi tare sbd shima Dana Santorini din yayi niyar zuwa. Jin hakan ta fito cikin farin ciki harta hada musu tea saidai itakadai Tasha yace shi Yana azumi. Wayar Amatu yakira so daya Bata dauka ba sai kawai yayi texting dinta kafin suka wuce itadai Anty zarah mamaki da ikon Allah kawai take kallo MAHMOUD dinda wani lokacin saiya Isa inda zaije yake fada Mata yayi tafiya wani lokacinma sai idan taga baidawoba takira yace Mata sorry ya aiki yadauki hankalinsa bai fada Mata yayi tafiya ba bayanan Amma gashi agabanta yake Kiran Amatu zai sanar da ita zaiyi tafiya 'yar ikon Kuma taqi dauka qarshe ya qare da rubuta text. Jin tayi tafiyar tafita ranta Amma Kuma sbd lafiyartane Dole zataje kodan Allah yabata haihuwar Nan dai itama ko ALLAH zaisa hankalin MD din ya tsaya akanta itadake son abinta. Lokacinda Text din ya shigo wayarta tana zaune cikin wani restaurant tareda annah sunacin abincinda Sam batamada appetite cin kawai takeyi tana karanta massage din tagama tabbatarda MAHMOUD ZABEERA qarshenta yakeson gani wato ta mutu ya huta, To baza'a yi hakaba zaisan dawa yakeyi. Gida Takoma ko makarantar Bata komaba tana zuwa tahau hada kayanta tana qoqarin danne hawayenta daga saukowa. Saidata hada kayanta acikin akwati biyu kafin takira annah tace ta tayata ayi Mata arranging room a hostel zata dawo Nan. Ba musu suka shigarda application din accommodation akace sai Nanda 7 to 8 days zata samu. Dole ta hakura har zuwa lokaci tanata fatar asamu kafin dawowarsu din. Daina fitama tayi Sam tana tsumayin jiran akairata akan angama Mata arranging komai na zaman hostel din wani gefen Kuma har yanzu zuciyarta batada nutsuwa bare sukuni gashi tun Yana Kira Bata dauka harya tattarata ya share dama baiwani Saba da duk irin wainnan abubuwan ba. Kwanansu biyar suka dawo da anty zarah kawai ta gaisa ta shigewarta Bata sake fitowaba sai dare data fito cin abinci tagansu a dining ta wucewarta kicin ta dafa noodles taci tafito ta wuce daki Anty zarah data fahimci da akwai matsala wato a tsakaninsu taso yin Magana saikuma tafasa tana cewa'' Kama kanki zara'u kafin abin ya juyo kanki Dan abin juyi juyi ne kowa da ranar baqin cikinsa indai zaman kishi ne. Data lurada shima ko kallon inda Amatun tabi baiyiba saita sake Kama kanta da shishigin shiga tsakani karta jawowa kanta fitinar da gwara tasu musamman da yanzu magungunan da likita ya dorata akai yace ba'a son tana saka damuwa ko kadan shine zasufi aiki da yardar Allah zata samu ciki Dan haka saurin dauke kanta tayi akansu ta maida himma taci abincinta ta qoshi Tasha ruwa Tasha magani tana satar kallonsa sbd kobai Bari angani ba a fuskarsa tana iya hango tension ataredashi. Kwana biyu gidan ana zabga rayuwar ba ruwan wani da wani tsakaninta dasu anty zarah ce kawai take zuwa har daki ta gaidata musamman dataga tana Shan magunguna ta tambayeta batada lafiyane ta sanarda ita na neman haihuwar tane take ta Kama kanta saima taji son komawa hostel dinta yaqara qarfi. Duk wata hanyar haduwarta dashi ta toshe duk da dai yanzu futowarta take Palo tayi abindake gabanta sai hakan yaso ya daga hankalin anty zarah Kuma yanayin shegun kayanda Amatun ke sawa kamar wata baby ko ita dake mace idan taganta dasu dauke Ido takeyi bare ace namijine yaganta ahaka. Ranar daya dawo idanuwansa suka sauka akanta da wata riga guntuwa Mara hannu tana kicin tana dafa taliya saura kadan yafadawa anty dake Masa sannu da zuwa ta kallesa tana mamakin irin yanda idanuwansa suka kasa daukewa daga Kan Amatun sai kawai ta juyawarta tabarshi tsaye Yana nufar hanyar kicin din Amatu hangosa tafe ta sauke abincin ta fitowarta tana dauke kanta daga kallon inda yake harta gotashi taji yadawo da ita gaba dayanta ya matse cikin jikinsa Yana kallon idanuwanta datake dojewa kallon cikin idanuwansa tana qoqarin janye jikinta ya matseta dakyau cikin jikinsa gudun zarah ta fito tagansu wani aikin yasamesa yasashi dagata gabaki daya ya nufi dakinsa da ita bai sauketa ko inaba sai Kan gadonsa yaqi sauketa daga Kan jikinsa Kai tsaye yace" Ankirani daga hostel na makarantarku cewan ur accommodation is ready, Abinda banganeba anan waye zaikoma hostel din? Sai alokacin ta dago da idanuwanta ta kalli cikin idanuwansa tace" Nice zankoma hostel. Wani wadataccen murmushin da Bata taba ganin yayiba yasaki Yana sake tungumarta yace" Keep dreaming. Daure fuska tayi tana qoqarin qwacewa daga jikinsa tace" Nagaji da zama anan zantafi I need a break. Serious yayi da fuskarsa Yana sakinta yace" You are not going anywhere ki cire ran zama koina. Masifa takeson suyi Dan haka Kai tsaye tace" Bazan zauna anan ba nafi son zama can din. Kallon fuskarta ya Dan Yi zuwa lokacin ransa ya Dan Fara baci ya sauko Kan gadon Yana cire agogon dake hannunsa tareda links din rigarsa yacire takalmin qafarsa ya nufi toilet Yana cewa'' Zangani idan kina zaman kanki ne coz I can see hankali bai isheki ba ita wadda kike kishin tafiki iya son mijin sbd tana kiyaye bacin ransa. Kadan ya rage ta Dora hannu akai ta kurma ihun Abinda yafada idanuwanta sukai jajir ta sauko gadon ta nufi qofa ko gani batayi sosai sbd masifa ta fice tana cewa'' Yau wallahi bazan kwana a gidan Nan ba tunda dai kafito fili kafada Banda amfani. Tana shiga dakinta ta janyo jallabiya baqa ta sanya tareda janyo akwatinta dasuke dama a shirye ta adauki Jakarta tafara Jan akwatin tana fitowa dasu ta nufi qofa idanuwanta na zubo cikowa da hawaye taji anriqe anruqota ta baya tareda zagayowa gabanta Yana mamakin fitinarta da yanda rigima Bata isarta ya rasa ma yazaiyi Mata azauna lafiya gabaki daya neman zaitashi take ya karbe akwatin hannunta cikin sarewa yace" For God sake AMATULLAH meke damunki? Qin Magana tayi tana qwace hannunta yasake riqewa Yana rintse ido cikin rashin sanin mafita yace" Kince kin gaji da Nan ko To Zan canza Miki gida Zaki zauna ke kadai Babu Wanda zaizo ya zauna shikenan.. Kallonsa tayi zatayi Magana cikin wani irin sanyin murya dake nuna galabaitarsa da rigumar yace" Please" Yanayin yanda yayi maganar yasa jkinta neman mutuwa ta dauke Kai tana cewa'' Bance haka ba nidai bazan kwana agidan Nan ba kawai ka... Daukarta yayi gaba daya har handbag dinta ya nufi dakinsa da ita Yana cewa'' Wannan kishin naki Mara dalili ne Bari na nuna Miki wani Abu tukuna saikiyi me dalilin. Tanajin haka tayi saurin kallonsa daidai lokacin dayake shimfideta Kan gadon Yana sakar Mata wani sahirtaccen murmushin daya kashe jikinta Nan take ya hanata motsi saima lumshe ido datayi tana lafewa cikin jikinsa ya shafa kanta ahankali ya furta" My stubborn wife kina mantawane ke uwa ce kokuma duk zafin kishine zaisa ki zauce ki zauta MAHMOUD ZABEERA, Rufe idonta tayi qasa qasa tace" Waye zai jawo to? Wani murmushin me sanyi Yakuma saki Yana shafo gashinta da Rolling dinta ya zame yakawo bakinsa daf da kunnenta ahankali yace" Tell me meyasa? Bude Ido tayi ahankali ta zuba Masa ta kalli bakinsa dake daf da nata tasan ko budewa tayi zatai magana sai lebanta ya hadu da nasa ta sake maida idanuwanta cikin nasa saitaji kunyarsa na shigarta ta juyar dakai ahankali tana kallon ta rufe Ido taji saukar hannunsa Kan cikinta taja numfashi daqyar tana rufe Ido ya Kai bakinsa ahankali yayi kissing din idanuwanta dasukadaine suka Isa su kalla cikin nasa idanuwan ya gangaro ya Dora bakinsa Kan nata Yana qarasa janye doguwar rigarta daya jima da zarewa zip din gaba ya jeho rigar qasa Yana shafa hooks din white lace push-up bra dinta dazai balle ya balle ya jehota qasa itama tayi saurin qanqamesa tana sake rintse Ido wani numfashi me wahalar fita na fito Mata shikuwa haduwar qirjinta da nasa Babu Kaya yasa numfashinsa daukewa na daqiqu kafin ya zura hannuwansa bayanta zuwa wuyanta. Qarfe Tara da mintuna hudu tasamu damar fitowa daga dakinsa tana tahowa ahankali sbd gajiya da Kuma uban tsamin da jikinta keyi da akwatunanta na jiyan tafaracin karo a Palo kafin anty zarah dake zaune tana Shan maganinda daqyar yake samun hanyar wucewa a maqoshinta sbd Abinda ya tare Mata maqoshi sukai turus sunayiwa juna kallon kallo Amatu wata irin masifaffiyar kunya da girman anty zarah data iya zama gidan datake kallon mijinta da wata hartana iya bacci tabbas tana qara jinjinawa antynta babu kamar anan kusa itakuma anty zarah wani irin kallone takewa Amatun zuciyarta ma takasa daukar tunani daya acikin tunani fiyeda dari data keyi akanta. ##Mamuh# 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 43_* _*INA MASU NEMAN MAGANIN INFECTION SADIDAN? MAGANIN NI’IMAH, MAGANIN GYARAN HIPS AND BOOBS? MAGANIN BASIR....NA HAUSA BANA BATURE ME KWANTAR DA CIWO BA? TO KU MARMATSO KUSA, DOMIN YAU MUNA TAFE DA ALBISHIR WANDA ZAI FADADA MURMISHIN FUSKOKIN KU.. YA KUMA KAWATA ZUKATAN KU. MUN GWADA MUN GANI, MAGUNGUNANTA SUNADA KYAU KUMA SUNA DA AIKI.. BABU SIDE EFFECT, ANYI SU NE DAGA TSAFTATTUN KAYAN ITATUWA, DA SIRRIN CHADIAN HERBALS.. KARNA CIKAKU DA SURUTU;_ _*AISHA S BAYERO TRADITIONAL MEDICINE AND HERBAL RESEARCH CENTER..._* _KUNJI SUNAN KO? CENTER CE TA MAGUNGUNAN GARGAJIA, WANDA DUK WANI DAMUWA DAKE DAMUNKA IDAN HAR KAZO WAJEN S BAYERO TA KARE DA YARDAR ALLAH.._ _KADAN DAGA MAGUNGUNANTA SUN KUNSHI:_ _MAGANIN SANYI _ _MAGANIN NIIMA SET_ _MAGANIN NANKARWA _ _MAGANIN KIBA BABBA DA _KARAMI _ _MAGANIN HIPS _ _MAGANIN GYARAN NONO _ _MAGANIN RAGE KIBA _ _MAGANIN SAKA FEELING _ _MAGANIN CIDA KWAI _ _ZUMA YAR ASALI_ _MAGANIN BASIR KOWANNE IRI _ _HODAR NI’IMA _ _MAGANIN MALLAKA _ _GUMBAR NONON RAK’UMI _ _GUMBAR MADARA _ _TURAREN FARIN JINI _ _KAZA MARA KWAI _ _TURAREN MALLAKA 3 STEP _ _HAD’IN MATAR MINISTER 1_ _KAZA ME KWAI_ _STEP 2:_ _TURAREN MALLAKA ME KWALBA _ _ME KUNAMA DAN MATSI _ _TURAREN GOSHI _ _TURAREN QIRJI _ _TAUWADAR MATA _ _MEMORY _ _KAHON MALLAKA_ _YAJIN MAZA_ _TEA DIN MAZA _ _DAMBUN MATSI_ _MAN AYU_ _MAN DAMO PURE _ _KWALLIN IDONKA IDONA _ _GARIN SHA DAKA ME KYAU _ _KUBEWAR MATA_ _DUKA WADANNAN INGATTUN MAGUNGUNA NA GARGAJIYA HAJ AISHA NA DASU GANGARIYA.. HERBAL MAGUNGUNA NE MASU KYAU DA INGANCI.. TAFIYAYYU NA KASAR CHAD. CHADIAN HERBAL MEDICINE AND RESEARCH CENTER.. KYAU, INGANCI.. RAHUSA... SAI MAGUNGUNAN *AISHA S BAYERO TRADITIONAL MED AND HERBAL RESEARCH CENTER...._ _NUMBER WAYAR WHATSAPP: 08121491609 KO KIRA TA NUMBER 08145873617._ _ADIRESHI: KUNTAU KARSHEN KWALTA KAN A KARASA YAN TIFA, DAIDAI GADON KAYA CEMENT.._ ********* Daqyar Amatu ta iya daga hannu takai wuyanta tana Dan sosawa akunyace zuwa kanta sai alokacin taji gashin kanta azube Kan kafadunta Wanda kallo daya zakamai kasan a jiqe yake duk da bawai tsiyayar ruwa yakeyiba, Tayi saurin kallon anty zarah da itama sai alokacin ta lurada sanyin kan Amatun take ruwan bakinta suka qwareta tafara tarin dayasa Amatu Jan akwatinan tabar gurin da sauri tana sakejin kunya da takaicin kanta da fitowa ahaka Amma Kuma batai tunanin ganin anty zarah a palon ba adaidai lokacin ita gabaki dayama ta manta da itada antyn tatace keda MAHMOUD din. Zama tayi bakin gado tana Dan shafa goshinta cikin yanayin datakejin kanta da zuciyarta akan MAHMOUD ZABEERA, Wani boyayyan murmushi tasaki ita kadai tana rintse idanuwanta tana Jin kowace irin kalmar daya fada Mata a Daren yau din suna zagaya jini da jikinta, Idan har samun kalmomin yabawa daga garesa ya sanyata cikin wannan daddadan yanayin to Yaya anty zarah daya Dade Yana furtawa kalmarso takeji ita.... Faduwa gabanta yayi da qarfi harsaida ta Dora hanunta Kan qirjinta ahankali tana lumshe ido tunanin yanda zasu riqa sharing dinsa na sata Shiga wani rububi tsawon mintuna Jin zuciyarta na neman tarwatsewa yasata miqewa ta nufi toilet tashige ta sakarwa kanta ruwa tana rufe idanuwanta. Anty zarah ma daddafawa tayi takai kanta daki tana Jin zuciyarta na radadin mema yakaita biyo MD Nan tun farko sbd duk wannan abin tasan Dole Yana faruwa tsakaninsu tunda zaman aure suke Amma to ganewa idonta shine babbar masifar gashi tazo ta zauna tana ganin Abinda zai iya Sanya zuciyarta fashewa wlh badan zata koma Santorini ganin likita harso biyuba da ayau saita koma Nigeria Dan tafi ganin darajar kanta Dana aurenta acan Dan ko shi mijin acan yafi ganin girma da darajarta sbd anan tazama kamar baquwar data kawowa matar gidan cikas ne Amma ko ahaka Dole tana buqatar fita Tasha iska sbd acikin gidan yau numfashinta sassarqewa yakeyi. Wanka tayi ta shirya tafito ko qofar dakin Amatu kasa kalla tayi sbd kada taci gaba dajin zafinta Sam Bata iya tsanar Amatun duk da mijinta data aure Mata Koda yake ummantace koyaushe akan taimaka Mata da addua da shawarwari da nuna Mata kulawa akan kada ta dauki zafin kishi me tsanani da hauka tazo qarshe tayi biyu Babu sbd dangi da mijin zasu tsaneta idanma tasamu anbarta da igiyar auren kenan shiyasa itama take iya qoqarinta sbd sanyawa ranta salama duk da akwai zafi da ciwon kishi me tsanani saitana duba wani lokacin ko ba kishiya ya kaqare da baqin ciki da takaicin namiji Wanda sometimes ma kishiyar is just an excuse dakake sauke haushi da laifin akanta Amma mijin ne me asalin baqin cikin wani lokutan. Text tayiwa MAHMOUD din na tafita zuwa gida momy professor, Bata tsaya jiran reply dinsa ba ballantana tasan ba lallai yayo reply dinba musamman yanxu datake zargin da wuya idan wayarsa Bata kashe ta ficewarta. Shine yafito da wayarsa Kan kunnensa Yana amsa waya cikin nutsuwa da wani irin izzar dake qarawa kwarjininsa cikawa mutane ido, Dogon wandon Lou's ne fari qal ajikinsa sai sky blue transparent shirt Mara nauyi ko kadan data bayyana jikinsa sosai ya nufi dining yaga bakomai ya juyo ya nufo hanyar bedroom din Amatun ya tura yashiga Kai tsaye. Tsaye take gaban madubi sanyeda bra Fara qal sai towel dake daure iya qugunta tana shafa body mist ajikinta ta dago Kai ta kalli cikin madubin taga shine yashigowa ya tura qofar ta qura Masa Ido ta cikin madubin har batasan lokacinda ya qaraso bayanta ba sai saukar hannuwansa Kan shafaffen cikin tayi numfashinta yayi sama tayi saurin dora hannunta akan nasa din tana dafewa ta kallesa ta cikin madubin tana girgiza Masa Kai a kasalance tace" Anty zarah na Palo kashigo Kan?? Share tambayarta yayi Yana kallon white pushup bra dinta yakai hannu akai Yana tabawa yace" I love white colours. Inda hannunsa ke yawa ta kalla tareda sake zamewa zata Kira Masa sunan anty zarah ya Dora hannunsa Kan bakinta tareda waiwayawa ya kalli wardrobe dinta yaja hannunta zuwa bakin wardrobe din yace ta bude. Saidata kalli idanuwansa dake kallonta ta saki murmushin dake bayyanarda farin cikin da zuciyarta ke ciki ta bude wardrobe din still tana kallonsa cikin dinbin mamaki da farin cikin data rasa Kona meyene. Wasu Kaya ya nuna Mata batareda shima yasan ko wainne iri bane ya nuna Ta janyosu tana Masa kallon mamaki saidai tunda ya zabesu itakuwa sanyasu zatayi duk da tasan anty zarah na gidan Amma dai zata Sanya saidai zata kaucewa ganinta. Riga da mini skirt ne skirt din blue rigar white, Toilet tashiga ta sanyo ta fito tanason taji kunya Amma yanayin rayuwarta ta yanzu da yanda ta Saba da rayuwar turawan yahana taji kunyar yanda yakamata. Daure kanta tayi da band baqi ta nufi hanyar fita dakin tana cewa'' Zanje na hada breakfast. Riqota yayi yadawo da ita gabansa Yana kallon fararen cinyoyinta dake tafiya suna daukar hankalinsa zuwa cibiyarta dake fili rigar Bata rufe ba ya maida kallonsa Kan wuyanta zuwa Rabin qirjinta dasuma suke a bayyane ya maida kallonsa Kan lips dinta data shafawa hot red lipstick suka zauna daram ba inda ya durje yakai bakinsa ahankali ya shanye jambakin tsaf kafin ya janye band dinda ta daure Kai dashi Yana cewa'' Yafi kyau ahaka. Da wani sabon mamakin ta kallesa tana murmushin mamakinsa ta zame hannuwansa ahankali tana cewa'' Muje kaduna idan anty zarah tana Palo. Wucewa gaba yayi Yana cewa'' Ta fita Batanan Ina buqatan abinci am going out too. Tea da fried eggs sai toasted bread kawai tayi musu sukaci. Baifitanba sai maraice Yana fita Takoma tasake wanka ta sanya doguwar fitted grown ta kanti ta rufe kanta da hula bayan tayi drying dinsa tazo kicin ta Dora abincin dinner. Tana cikin aikin anty zarah tadawo tana bude Mata guda suka sakarwa juna murmushin daya zama Dole sukayo ciki tana cewa'' Anty zarah sannu da dawowa Ashe fita Kikai bansaniba Saida dady yace bakyanan. Idan Amatu na kiransa da dady tanajin abin har ranta Amma tasan badan Dadi aure yasa take kiransa dadynba sbd Muhammad ne ya saki numfashi tana nufar dakinta tace" Wlh gajiya nayi da zaman shiyasa nafita nadan Sha iska gashi Kuma wlh naji dadin fitar. Daki tashige tayi wanka ta sauyo Zuwa doguwar riga itama tafito tazo kicin din tana cewa'' Bari natayaki fira koban tayaki aikin ba Naga dare yayi kinje makaranta ne? Aa banje ba wlh baccin yamma nayi shiyasama nayi lattin aikin. Boye Mata cewan sai yammar MAHMOUD yafita tayi sbd gujewa bacin Rai da damuwa ta fake da cewar baccin yamma tayi. Sai Bayan duhun magriba suka kammala Amatu ce ta jera abincin a dining kafin itama ta nufi bedroom dinta tayi sallah Bata sake wani wanka ba sbd ba wani jigatar dasukai a aikin tabari sai idan zata kwanta tayi wani. Baidawoba sai dare sosai shiyasa Basu wani jirasa ba sukaci abincin su tana waya da USI harta bashi anty ZARAn suka gaisa Yana qara yimata godiya akan yanda ta fahimci auren Amatun da MAHMOUD tace Masa ba komai dai Amma har yanzu tunda akai auren haryanxu takasa zama tayi tunanin irin daukar dazatayiwa Amatun Wanda take ganin kamar ba yanzu ne lokacin dazata zauna yin wannan tunanin ba Kuma tana riqon Allah dakuma fatar kada tasamu wannan lokacin har abada sbd tana zama shaidan ne zai zauna shawarar da ita. Tashi tayi ta shigewarta bayan tayiwa Amatun Saida safe itama Amatun miqewa tayi tattara dining din tasake jera Masa nashi abincin tana gamawa Yana shigowa a gajiya Dan haka Kai tsaye daki yanufa Yana cewa takai Masa abincin can wanka zai shiga. Kadan ta dibar Masa tareda fruits data San yanason sha yawanci da daddare takai Masa tareda ruwa power drink dinsa Tana zaune yagama ci ta kwashe kayan ta fita dasu ta sake gyarawa tareda fesa Masa peach blossom airfresh ta qara Masa sanyin AC kafin tashiga wanka anan dakin nasa qarshema shirt dinsa Fara tasanya wadda Tai mata yawa ta kwana da ita. Washe gari tanada zuwa makaranta daqyar ta tashi ta shirya ko aikin abinci bata iya yiba hakanan suka fita bataci komaiba driving dinma cemasa tayi bazata iyaba very weak take jinta shiyasa yakaita da kansa Bayan yakaita wani private restaurant din dayafi so taci abinci kafin ya jiyeta makarantar yadawo gida. Kamra Wasa da zazzabi ta yini ko makarantar da qyar ta lallabo tadawo gida tashige ko abinci Bata fito ci ba tace ta qoshi sbd kada abin yayi Mata yawa Dan tasan yau anty zarah ce zata Kwana gunsa. Annushuwar da zarah take ciki bayason Bata Mata ita Dan haka bai nemi Amatun ba yadai Yi Mata text takuma yimasa reply. Kwanan zarah biyu Amatu ta karbi girkin ta ringa Jin wani iri kamar bazata iya wannan rotating din ba shima daya lura da ita gudun tashin hankalinta da rigimarta yasa yaqi nuna yagane tana cikin damuwa. Sannu ahankali yafara sabawa da canjen kwanan har tsawon wata daya ana haka saiga anty zarah tafara rashin lafiyar ciwon baya da zazzabin dare ga Amatu Kuma Kai yadauki zafi exams sukeyi Bata cika zamaba shima MAHMOUD din bai cika zamaba ga ciwo kadan kadan Yana cin anty zarah din basuda masaniya. Ranar wata talata tadawo daga makaranta ta tararda anty zarah Bata Nan sai Bata damuba harsai dataga dare yayi sosai Bata dawoba takira wayarta Bata daga ba harso uku sai hankalinta ya tashi takira MAHMOUD din Yana dauka ko gaisuwa bata tsaya Masa ba tace" Dady anty zarah fa Bata gida inata kiranta wayan ba'a dauka.. Numfashi ya sauke Kai tsaye yace" Tana taredani muna Santorini batada lafiya. Santorini?" Tafada cikeda mamaki tana qarawa da cewa'' Yaushe kadawo ne dahar kuka tafi yau din? I came back because you're too careless ta Yaya Kuna tareda mutum Yana fama da rashin lafiya haka sosai Amma kice baki sani ba this is unbelievable... Tayaya zangane tunda Bata fadaminba Kuma kullum ni lafiya nake ganinta Kuma karka manta ni makaranta nake zuwa tayaya kake.... Kashe wayar yayi Yana cewa'' Idan nagama Abinda yakawoni I will call you back. Wayar tabi da kallo zuciyarta natafarfasa dama kwanakin kullum zuciyarta a kusa take batasan dalilina, Take tadauki mugun zafi tana cewa ni zai datsewa waya cikin wulaqantawa sbd nace bansan ciwon anty zarah dinba?? To uban kowa da kowama tace Bata saniba ayi Abinda za'ayi din. ##mamuh# Manage please. 6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 44_* _INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._ _LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._ _WANDA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYA_ _*NIMCY LOVE*_ _TA RUBUTA._ Zaku iya payment dinku na wannan daddan labarin na *UNCLE NE* ta wannan numbrn dake rubuce👇👇 08119237616 ****** Zama tayi a palon zuciyarta na wani irin tiririn takaici da baqin cikinsu su dukan sbd itama anty zarah din taga damane su hadu su Bata laifin daba nata ba Dan me daga abin arziki zai cillo Mata maganganunsa bacin Rai? Miqewa tayi ta nufi kicin ta dauko ruwan sanyi Tasha ko zataji saukin zafin zuciyar Amma a banza qarshe tsoki taja tabar kicin din Takoma dakinta tayi kwanciyarta. Da safe sanyawa gidan key tayi takuma qi ajiyewa a inda suke ajiye keys na gidan Dan idan waninsu ya dawo ta sakasu jaka ta tafiyarta makaranta tana ganin kiransa taqi dauka. Bayan zuwanta makaranta da kusan awa shida Yayi Mata kusan Kira fiyeda biyar Taki dauka ganin hakan tasan zasu iya zuwa makarantar nemanta Dan haka tayiwa annah Magana ta tafiyarta tabar cikin makarantar. Duk yanda sukaso ganinta su karbi keys na gidan taqi Bari Dan blocking dinsa ma tayi a qarshe anty zarah ma Kira daya tayi Mata Bata Bari tai Mata na biyu ba ta sanyata blacklist tana cewa'' Kun Manta waye Amatu idan shi baisaniba aike matarsa kinsan waye Amatu halina Babu inda yaje boye abuna nayi. Sai dare tadawo gidan ga mamakinta sai Bata tarar dasuba a gidan suna jiran isowarta ta bude tashigewarta ta rufe dayake taciyo abincinta sai kawai tashige tayi wankanta ta kwanta sai bacci. Washe gari ma haka ta tafi da keys ta wuni a school taqi dawowa da wuri sai dare Kuma still ma dai Babu ko inuwarsu. Al'amari na Wasa Wasa saigashi ta share sati guda cur babusu Babu labarinsu Kuma ko awaya Basu taba maganaba duk inda zuciyarta takai ga girma ta 6aci Dan kuwa iya qonuwa ranta ya qonu wato ko ohon Mata tunda ta rufewa shida matarsa gida ko ohon Mata sunyi tafiyarsu sun bar Mata gidan ita ciwon idan yazo kanta tadade Bata mutu ba kenan. Exams suka kammala ta daina fita gabaki daya abun duniya yazo ya sanyata gaba Babu Abinda ke sake sanyata baqin ciki irin yanda ita ko oho da ciwonta da lafiyarta tunda matarsa taso na taredashi ita Kuma tunda a tausaya Mata a taimaka Mata itada 'danta dasuke marayu shiyasa aka maqalo Masa ita ya aureta gashi tun yanzu ya nuna Mata iyakarta dashi biyan buqata tunda matarsa ta auren so ce agabansa. Kukan datasha a Daren ranar saidaya sanyata zazzabi me qarfi ga ciwon Mara daya sanyota gaba ga zuciyarta baqin ciki kawai takeji daqyar taga safiyar ranar ta lallaba takai kanta asibiti duk da alamomi da yanda takeji tana tunanin ciki atareda ita zamtowarta gynecology student datake gab da zama likitar. Lokacinda aka Bata result din she's 2month pregnant wani yanayi na tausayin rayuwarta tasamu kanta har Saida hawaye suka ciko idanuwanta suka sauko Kan kumatunta ta share ta kamo hanyar gida tana sakawa ranta tunanin komawa Nigeria Dan zamanta anan baida amfani gwara takomawarta inda akasan darajarta cikin iyayenta masu qaunarta idan yaso zabeera ta Dade Bata Yi abun kunyar anyi rabuwa acikintaba Amma rabuwa zatayi da MAHMOUD ZABEERA ta huta sbd yagama nuna Mata baisan darajartaba ko daya. Ta waya tayi booking ticket din komawa Nigeria Amma Babu jirgin zuwa Nigeria a ranar saidai Nanda 4 days ba Bata lokaci tayi booking tayi payment tana isowa gida ta wuce daki ta zube Kan gado wani wahalallen bacci yayi gaba da ita. Cikin bacci taji doorbell na qara sama sama ta bude idanuwanta dake cikeda baccin wahala takalli agogo taga yamma tayi sosai ta murgina ta tashi ta sauko gadon tashiga toilet ta wanko fuskarta tareda yafo qaramin gyale Kan doguwar rigar dake jikinta Mara hannu ta nufo qofar tana cewa'' Am coming. Bude qofar tayi bama tareda tafara duba ko wayeba ta camera. Da MAHMOUD ZABEERA tafaracin karo yayi fresh Abinsa cikin brown Armanis sai Zarah zabeera a gefensa itama tayi fresh haddasu manyan kumatu da Naman wuya sai qananun luggage dinsu ko kallon second daya Bata qarai musu ba ta juyowarta tana zame gyalenta ta nufi hanyar kicin tana receiving call din daya shigo wayarta batareda ta nuna tamaji sannu da zaman gidan da anty zarah ke mata ba tayi banxa da ita. Bayanta anty zarah tabi da kallo tanajin rashin dadin yanda Amatun ta kwashesu ta watsar ba musamman MAHMOUD dayake mijinsu ai ya cancanci sannu da zuwa. Hanyar bedroom dinsa yayi Yana janyeda akwatinsa ita Kuma anty zarah kasa hkr tayi tabi Amatun kicin. Tana shiga Amatun na qoqarin juyowa daga hada tea da biscuits din dazataci ta kalli fuskarta tana cewa'' Amatu lafiya Naga munshigo ko gaisuwa Kuma MD ma Naga ko sannu baki..... Wani kallo Amatun tafara aiko Mata dashi kafin tabude Baki tace" Anty Ina ganin girmanki kabari muje ahakan. Wucewa tayi tabar anty zarah tanabinta da kallon mamaki da tsoro kafin itama tabar kicin din takama hanyar dakinta. Sanin sundawo sunajin yunwa gasa anty zarah fitowa tai musu Abinda zasuci taje har dakin Amatu takirata Amma tayi bugun duniya ko cewa waye Amatun taqiyi bare tasa ran zata bude Mata ganin haka MAHMOUD yace tadawowarta tazo taci abinci Tasha maganin taje ta kwanta tana buqatar hutu, Yasan masifa da rigimar dake cin Amatun shiyasa shima bazai shige mataba duk da yayi matuqar kewarta Amma rigimarta har fargaba take sakashi Sam bayason tashin hankali musamman yanxu da zarah Allah yabata Abinda takeso bayan shekarun jira masu tsayi, Harga Allah shi baisaka damuwar rashin haihuwa aransa ba kodan yataso cikin kadaicinda har yake sha'awa da son rayuwa shikadai ne? Sai lokacinda aka haifi Muhammad yaji son 'yaya yashigesa Amma dai still bai saka abin a Rai ba zarah ce ta qwallafa Rai ason haihuwa yanxu gashi Allah zai Bata sanin yanda ta dauki alamarin cikinta yasa yake tayata tattalawa da kulawa sbd taji farin ciki Amma wainnan kwanakin a Santorini shikadai yasan yanda yayi su day tunanin yanda Amatu take anan. Abincin sukaci sama sama kafin ya miqe yashige Yana sake trying numbern Amatu daya Gama tabbatarda blacklist tasanya shi. Washe gari dukkanin wasu kayanta masu daukuwa ta hadasu a akwatina ta rufe na Shan iskar dazata Sanya yau da gobe kafin jibi ranar tafiyar kawai tabari a waje ta shige toilet tayo brush da wanka tazo tayi sallah Dan tayi lattin tashi ta sanya jeans da baqar cardigan sbd sanyi sanyi datake ji Wanda tasan hadda na zazzabin dayaqi sakinta Wanda a nazarinta kozata daina qananun zazzabi zazzabin saita fita early months dinta na pregnancy. Fitowa tayi taje cikin ta soya kwai da uban tomato sauce da bread ta dama oat tazauna a qaramin table din kicin din nacin abinci tana breakfast dinta cikin nutsuwa. Ta windon kicin taji motsinsa yana balcony tasan geamin yakeyi a balcony kullum safe, Batason ganinsa Dan haka taqarasa cinyewa Dan tabar kicin din Takoma daki sbd Yana gamawa kicin yake yowa direct Dan amfani da ruwan sanyi. Bata shanye sauran oat dinba ta dauka zata Sanya fridge cikin tsautsayi kofin ya subuce daga hannunta ya fashe oat din ya zube gurin tareda glasses na cup din. Juyawa tayi zuwa store dauko mop da Abinda zata kwashe glasses din kafin tayi mopping tana cikin tsore din saiga anty zarah tashigo kicin din idanuwanta plates din Kan table da akaci abinci dasu take kallo Bata ankara da abindake qasaba ta taka lokaci daya akai sama sosai da ita tafado da qarfi Kuma ta saki wani razanannen ihun dayasa Amatun fitowa batareda ta dauko Abinda taje daukowa ba. Cikin sauri tace" Sorry sorry nice na zubar wlh Bari nakoma na dauko mop sorry... Juyawa tayi da sauri Takoma daidai shigowarsa ya qaraso gun zarah din da sauri ganin tana juye juye cikin azaba cikin sauri ya riqota Yana kallon fuskarta da tuni ta hada uban zufa yace" Me wannan abin yakeyi a qasa Kika Fadi?cant you watch where you are going... Fitowar Amatu da mopa a hannu yasashi dagowa ya kalleta ta dauke Kai tana qoqarin tattara gurin Kai tsaye cikin fada fada yace" Ta Yaya wannan abun yake zube qasan kicin din?Kai tsaye tace" Nice na zubar Kuma banzubar ba Dan wani ya Fadi duk Wanda yafadi qaddararsa ce ahaka, Idan zaka dauketane na tattara gurin to.... Rintse Ido yayi ya bude akanta Yana cewa'' Meyasa kullum kinfison tashin hankali akan zaman lafiya? Wannan kishin da kike is nothing but madness idan zaki ji haushin wani come to me not my wife sbd itane tafi cancantar wannan madness din not you sbd itace aka aurewa Miji.... Na aka aure mijin inaga ai bani nace a auramin ba sbd Nima inada nawa mijin qaddara ta rabani dashi harna qare anan and idan kanajin ka gaji da da madness dina bana tunanin akwai Wanda yasaka zama Dole Dani infact ma ni nagaji da auren na mijin wata sbd Nima bashine gabana ba Mijina da duk duniya yafimin kowa na Rashi na dangana to waye Zan rasa ban hakura...... Cikin wata irin tsawa data Sanya anty zarah bude idanuwanta ta kallesa cikin tsoro sbd Bata tabajin ya daga murya hakaba kaf zamansu ita ko sa'insa haka Bata taba Jin yayiba idanuwansa na sauya launi da bacin ran kalamanta yace" Get out of my sight. Not only your sight am going out of your life gaba daya... Daqyar anty zarah ta bude baki ahankali tace" Amatu Dan Allah kiyi shiru meye amfanin tashin hankali.... Hannu ta daga Mata idanuwanta na rufewa tace" Dashi nake magana sbd shiya kawo zancen, Kuma tashin hankalin waye yajawo tun farko ayishi? Muna zaune gida daya muna kwana cikin guri daya gari baitaba wayeba ba banje har dakinki na gaidakiba, Bantaba fita makaranta ba banzo nace Miki na tafi ba Amma da ciwo ya kamaki nida nake cikin gari baki kirani kin sanar daniba Dan nice akusa saikina Kirasa shida baya gari sbd shine zai baki lafiya nikuma ciwo Zan qara miki, Daya Kira Yana kirana careless meya Hana ki sanar dashi baki kiraniba kokuma bansan bakida lafiyaba? Anty zarah Ina ganin girmanki haryanxu so please stay out of this. Wurgi tayi da mopar Tana ficewa zuciyarta na mugun tafarfasa idanuwanta dasukai jajir suna bushewa. Su duka kallonta sukeyi shi cikin mamaki da takaicin kansa dayake kasa daukan mataki akanta itakuma anty zarah sai alokacin tasan eh lallai bata kyautaba Amma Kuma itama ba laifinta bane Babu Wanda ya cancanta ta sanarwa batada lafiya bayan mijinta. Daukar zarah din yayi Wanda sai alokacin su dukan suka lurada jini yafara gangaro Mata batasan lokacinda tasaki wani razanannen kukaba tana qoqarin qwacewa daga jikinsa Dan ta miqe yayi saurin riqota Yana daukarta gabaki daya ya fito ya fice zuwa asibiti da ita lokacin mararta tafara mugun ciwo sosai tuni tafara ficewa hayyacinta ga wani irin hawayen tsoron karta rasa cikinta datakeyi Dan kuka Yama daina fita. Suna Isa asibitin aka karbeta ya nufi reception ya cika duk wasu formalities ya zauna zaman jira. For morethan 3hours Yana jira kafin likitocin suka fito suka sanar dashi tayi loosing jini sosai Amma sun samu sun tsayar cikin baiyi komaiba Yana nan saidai akwai yiyuwar zai iya barewa sbd mahaifarta batada qwari ko kadan Dan haka zasu daure Mata sbd kada cikin ya zube. A asibitin suka yini sai dare sosai akai discharging dinta suka dawo gida duk da taji jiki Amma zuciyarta farin ciki ne fal sbd tunda ta auri MAHMOUD baitaba Bata lokacinsaba bare irin wannan kulawar datake samu a yanzu daga garesa wadda ta tabbatarda bawai Dan tanada ciki bane sbd tun kafin samuwar cikin ya sauya Mata tana samun kulawarsa Wanda tasan ba kowa bace tafara sauyasa qarfi da yaji sai Amatu Dan Nan gaba ma qila abin yafi haka Dan qila har kalmar so zata samu wata ran ya furta Mata. Murmushi tasakar Masa tana riqo hannunsa ahankali tace" Thank you. Batareda ya kalletaba ya Dan jinjina Kai Yana lumshe idanuwansa zuciyarsa gabaki daya batada sukuni har lokacin kalmomin Amatu na dazun akan mijinta daya rasu dashi kansa suna yawo cikin kansa da kunnuwansa ko asibiti zaune kawai yake amma kalmomin suke ihu cikin kansa. Meyasa zuciyarsa zata kasa sukuni akanta Bayan itace ciwon kansa gabaki daya ita Bata tsoron tashin hankali ko fitina,rigima cikinta take Bata ko gajiya ya tabbata yanzu tanacan tana zafin zuciya ko abinci qila bataci ba. Suna shigowa har daki ya raka zarah data gama yanke shawarar komawa gida cikin satin data samu qarfin jiki kafin ya fito. Ya jima tsaye a qofar dakinta hannuwansa zube cikin aljihu Yana tunanin halinda take ciki yasan koya buga bazata bude ba Dan haka ya sauke ajiyar zuciya tareda juyawa yabar gurin ya nufi dakinsa. Washe gari daga zarah harshi Babu Wanda tabari yaganta a daki tayi komai nata amatse takeda gari yasake wayewa ta tafiyarta. Ranar dazata tafi Kwana tayi kuka zuciyarta mugun zafi take Mata, Ranar harda kukan mutuwar Dr khalil saidaya dawo Mata sabo. Marartace tafara ciwo kadan kadan ta tashi zaune tana dafe cikin saigashi ciwon yafarayin gaba gaba ta rarrafo ta sauko gadon tana duba agogo taga qarfe ukun dare tana qoqarin komawa gado qafafunta suka riqe azabar tafara fin qarfin ta zube agurin tana Kiran sunayen Allah cikin tsananin azabar da Bata taba jiba tafara rarrafowa tana hawaye ta bude qofa ta fito tana Jan numfashi daqyar tanajan jiki ta Isa bakin qofar dakin anty zarah a taba qofar batada qarfin bugawa sbd qarfinta da ciwon yaci sosai sbd zuwa lokacin ciwon ya zaburo gabaki daya take ta zube gurin tana numfashi daqyar idanuwanta na gangaro da hawayen azaba. Anty zarah dataji kamar antaba kofarta tana zaune ne farko Tasha ruwa ta kalli qofar cikeda mamaki ta taso ahankali ta bude kofar batasan lokacinda takira sunan Amatun da qarfi ba tana zare Ido akan jinin dake kwance qarqashin Amatun tace" Innalillahi Amatu?? Hanyar dakinsa ta nufa ta Murda Kai tsaye tashiga tana Kiran sunansa a rude ga mamakinta shikuma zaune ta tarar dashi ya dafe kansa Sam ba alamar yayi bacci kozaiyi bacci ataredashi tana kallonsa da mamaki take cewa'' Amatu ce gatacan kwance ba lafiya. Dagowa yayi ya kalleta saidata Kuma maimaita sunan Amatu ya dawo hayyacinsa ya miqe Yana ficewa dakin. Yana ganin jinin jikinsa yabasa cikine da ita take wani irin mutuwar jiki takamashi bai damu da jininba ya rungumeta gabaki daya ya fice Yana mantawama da zarah dake tsaye. Tun a hanya yake Kiran sunanta Yana shafa fuskarta cikin tsananin damuwa da kulawa yake cewa'' Please please please Amatu I can't bear to loose this pregnancy idan babyna ne ajikinki please ki daure karki Bari yafita..... Tanajinsa sama sama Amma Bata iya motsi sai hawaye dake gangaro mata har suka Isa asibiti Suna Isa ana karbarta cikin na qarasa barewa. MAHMOUD ZABEERA baitaba sanin yanason haihuwa hakaba saidaya rasa cikin jikin AMATULLAH Wanda yaji dukkanin burinsa da farin cikinsa kamar ya ruguje ne musamman yanda Amatun ke hawaye ko kallonsa batason Yi taqi bude idanuwanta ko kallonsa tayi. Duk yanda yaso kusantota taqi Bari qarshema kuka ta fashe Masa dashi na tana buqatar kasancewa ita kadai. Dole ya fice yabarta yadawo harabar asibitin ya zauna cikin mota tareda Kiran Gida Nigeria yacewa kawu Dan Allah anty salamatu ta shirya tadawo zaisa asiya musu tickets itada Muhammad dake hannun umme yanzu. Gida yakoma yayi wanka ya sauyo Kaya sbd har qarfe goman safe tayi Masa tun asibiti, Tea kawai yasha yakoma asibitin yabar anty zarah da kallon ikon Allah Koda yakoma har an taimaka Mata tayi wanka an sauya Mata Kaya da green patient cloth zuwa blue tana zaune anbata tea da magani Tasha tareda snacks. Tunda yashigo ko dagowa batayiba sai sauraron nurse din dake qoqarin cheering dinta up take ga idanuwanta dasukai jajir bayan uban kumburin dasukai tabbas MAHMOUD ZABEERA baisan waye AMATULLAH ba, Zaisan ita Bata cikin matan dabasusan darajar kansu ba, A banza yasameta shiyasa baisan darajarta ba Amma yanzu sai San AMATULLAH SALEH daban ZARAH ZABEERA daban, Sunansu ba dayaba,halinsu ba dayaba hakama yanayinsu ba dayaba. Agogo ta kalla taga akwai sauran awanni biyar kafin jirginsu ya tashi Dan haka tana buqatar komawa gidan kafin ta dauki komai nata ta wuce airport kafin lokacin. Qarfe biyar na yamma yabar asibitin ta karbi discharge papers dinta ta fito ta tari mota ta fada. Koda suka Isa gida Bata sallamesaba tashiga gidan Kai tsaye dakinta ta nufa ta sauya Kaya ta janyo kayanta tafara fitowa dasu takai qasa tadawo tadauki handbag dinta ta jakar labtop dinta ta fito ta bugawa anty zarah qofa tana budewa batareda ta kalli fuskarta ba tace" Anty Zan wuce Nigeria Kuma Ina baki hkrn maganganun Dana fada Miki idan na Bata miki Rai. Juyawa tayi Bata jira Abinda antyn zatace ba ta fice. Koda ta Isa airport lokacin tafiyarsu yayi Dan haka kawai ta wuce ta karbi ticket dinta ta bada ta wuce. Ko mintuna arba'in basuyiba jirginsu ya tashi suka bar qasar. ##Mamuh# _INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_ _NA ZINNEE SMART DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU TA WANNAN NUMBERN_ 👇👇👇 08080840567 6/17/21, 8:08 AM - ': *_MQ 45_* Sai Bayan sallar asuba jirginsu ya sauka Nigeria ta dayake ta Kira USI ta ta sanar dashi dawowarta Bata mayi tunanin ganinsaba harta fito zata dauki drop saigashi ya tsaya gabanta cikin wata EOD dark blue sabuwa shine yake tuqin tana ganinsa ta saki murmushin farin cikin ganinsa idanuwanta na cikowa da hawayen murnar ganin 'dan uwanta Rabin jikinta Kuma abokin shawara, Dr Usman Saleh usi Wanda shine sunan da akafi saninsa dashi yanzu Yayi wani irin hasken samun hutu da nutsuwar rayuwa ga wani irin sajen daya Tara da sumar Kai sai qyalli takeyi duk da baiyi wankaba sbd kayan jogging nema ajikinsa ga wani irin girman gabban jiki dayayi sbd geaming dayakeyi kullum shiyasa ya zama wani irin qaqqarfan namiji Wanda yanzu haka 'yan Mata masu aji da wayewa suke rububinsa musamman sbd kyawunsa dayafi rinjayarsu. Fitowa yayi shima Yana kallonta cikin kulawa da tsananin qaunar 'yar uwarsa dabaida kamarta kaf rayuwarsa sbd kallon dasukewa juna na uwa daya uba daya. Kai tsaye Yana hango damuwa da rashin nutsuwar zuciya tareda rauni atareda ita musamman yanda idanuwanta sukai laushi ya saki numfashi sbd yariga yasan dawowar Bata lafiya bace ya qaraso kusa da ita ta karbi kayanta ya zagaya ya bude Bayan motar ya sanyasu ya rufe ya zagayo ya bude Mata gaban motar Yana cewa'' Bismillah mummy Amatu"ya qarasa fada cikin sigar tsokana dason dawo da dariya da walwalar Amatunsa. Murmushi tasaki tareda Shiga ta zauna ya rufe ya zagaya yashiga ya tayarda motar suka kama hanya. Suna fitowa daga airport ya kalleta yana qara qarfin AC din motar ganin kamar sanyinsa bai ishetaba sbd 'dan warware rolling dinta dayaga tayi alamar zafi ya maida kallonsa Kan tuqi Yana cewa'' Gida ko zabeera? Batareda ta kallesaba tace" Uban me zanyi a zabeera tunda ko can farkon auren ba tarewa nayiba acan daga gidanmu na tafi Greece Dan haka daga Greece gidanmu zani. Dariya tabasa ya murmusa Yana cewa'' Amah Wai meyasa bazaki canza ba bayan kinriga kinzama uwa fa., Wanda yake tareda miji for morethan 3 years now Amma kike cewa uban me zakiyi a gidansu. Muguwar hararar data sakar Masa tasashi yin shiru Yana dariya ya kamo wani zancen har suka iso sabon gidansu da batasan dashiba duk da acikin dai anguwarsu din ne Amma tsarin ginin yafita dabam da kusan duk gidajen anguwar sbd kyawunsa duk da baida mugun girman Nan Amma ba qarami bane yanada nasa kalar girman. Tsohon gidansu dake gefen sabon ta waiwaya ta kalla cikin yanayi na farin cikin dawowarta gida cikin Yan uwa da abokanan hurdar arziki dasuka taso taredasu aka buga gwagwarmayar rayuwa iri iri ta arziki data rashin arziki data rigingimu iri iri musamman fadace fadacen dasuka Saba Wanda duk anguwa an shaidi gidansu da zaman masifa da tashin hankali kafin shigowar Dr khalil zabeera cikin rayuwarsu Wanda ya fahimtar dasu mahimmancin zaman lafiya da qaunar abokin zama tareda mutunta juna Wanda yakaisu ga zama tamkar zuria daya yanzu. Juyowa tayi ta kalli USI da shima wasu abubuwan yake tunowa sbd fahimtar itama baya take tunawa cikin shauqi da tausayi da baqin cikin wata rayuwar dasukai a baya. Kayanta yaja yafara shiga dasu cikin gida dayake katangarsu ta gate irin guntuwar Nan ce me qarafuna wadda ake ganin komai na waje Wanda kawune yace hakan yakeso sbd yaringa sanin komai dake wakana cikin anguwa tunda yasaba zaman qofar gida yanzu kuwa cikin harabar gidansa yake zama Kan kujerunsa na musamman da USI yasiyo Masa na zaman Shan iska Yana ganin komai na waje daga cikin harabar gidansa da surukinsa guda sukutum ya gida Masa da MAHMOUD ZABEERA tareda zuba musu furnitures na alfarma dajin dadin rayuwa Dr USI Kuma daya Fara cin qashin kansa yanzu shine daukeda nauyin komai na Jin dadin rayuwarsu yanzu Dan tuni ya ware kudi ya Kai iyami babbar kasuwa ta saro kayan siyarwa buhuhuwan takalman Yara Dana manya sosai Kuma kasuwancin nata yakeci shiyasa komai nasu yanzu sai hamdala Dan kuwa yanzu sune masu taimakawa wasu, Anty salamatu dama marainiya ce gaba da baya Dan haka tuni tadawo cikinsu kodan irin dawainiya da wahalar datakewa Amatu da Muhammad. Anty salamatu ce tafito daga kicin riqeda kofin Lipton data hado Yana hayaqi zata Sha sbd ciwon Mara data kwana dashi na period dinta dazaizo taga USI Yana shigowa palon janye da akwatina Niki niki ta tsaya tana kallonsa zatai magana saiga Amatu tashigo daga bayansa Cikin tsananin mamaki dakuma farin ciki tasaki ihun ganinta tana Kiran sunanta da qarfi Wanda yasa Amatun washe baki cikin murna da farin ciki suka rungume juna saiga iyami da kawu sunfito daga palonsa harsuna rige rige Jin an ambaci sunan Amatun gakuma muryarta dasuke jiyowa. Iyami na ganinta ta tsaya idanuwanta na cikowa da hawayen tsantsar farin cikin ganin 'yarta bayan shekaru gashi yanayin yanda take ganin 'yar tata tazama yaqara habbaka farin cikinta ga bayyanuwa saijin Amatun tayi ta fado jikinta da qarfi ta qanqamesa tana fashewa da kukan farin cikin ganinsu itama. Kukanta yasa iyama maida hawayenta tana washe baki da farin ciki take cewa'' Meyene na kuka Kuma abun farin ciki da murna. Dukkanin annashuwar kawu da haqoransa a bayyane suke Yana kallon Amatun cikin kewa da farin cikin ganin dukkaninsu sun Sami nutsuwa a rayuwa. Zama sukayi dukkaninsu a palon Amatu na zaune tsakiyar kawu da iyami sai kallonsu take tana washe bakin farin cikin yanda suka sauya sosai tace" Kawu nayi kewar gida sosai nakuma ji dadin ganinku. Saikuma zuwa ba sanarwa Amatu" iyami tafada tana kallon Amatun da USI daya daukota. Iyami bazata nakeson muku Danma anty salamatu ta Bata bazatan tawa so nayi saina saikun fito zuwa anjima ku ganni kawai zaune Ina cin abinci kokuma Ina muku Ina kwana saigashi ihunta yasa kunji kunfito musamman kawu so nayi Yana fitowa yaganni ya dauka inuwatace zuciyarsa ta kusa harbawa. Dariya dukkaninsu sukayi kawu yace" Wlh zuciyata na harbawa kun shiga uku Dan uwarku ma tata bindigewa zatayi kunga kunzama marayu kenan har gwara ke kina gidan mijinki shi wannan qaton banzan gantalewa zaiyi gurin siyan abinci ma kawai it's kuwa salamatu zaman tunanin kadaici kawai ya isheta Dan haka gwara ku taru kuyita yimin adduar tsawon kwana. Kaikuma dason tsawon kwana kullum adduarka kenan"cewar iyami. To karar kwana kikeson nayi fata? Zaki Fara halin naki kenan muyi Abinda nace nadaina. Dariya sosai Amatu tayi tana sake jinjina halinsu kawun da basa taba canzawa. Daqyar dai aka tsagaita tasamu Shiga dakin iyami inda aka shigar Mata da kayanta tashiga tana kallon tsarin dakin dayayi Mata kyau sbd simple furnitures dinsa ta zauna bakin gado tana zare doguwar rigarta tareda warware Daurin gashinta Dan taji sauki ta miqe ta Shiga toilet sbd fitsarin daya Fara matsarta ta fito ta kwanta sbd hutun gske take buqata take bacci ya dauketa bayan Tasha magungunan ta. Sai kusan azahar ta tashi bacci shima sbd qarar loudspeaker da ake Kiran sallah Wanda ta manta rabonta dajin hakan ta tashi tayi wanka ta sanya riga da skirt na atampar cikin kayanta data Bari tun na legend auren Dr khalil Kuma cikin ikon Allah sun Mata saidai sun Dan kamata kadan ba sosai ba sbd ita acan din Bata qara jikiba saidai kyau da gogewar da fatarta tayi sai cikowar albarkatun jiki. Fitowa tayi Palo ta tarardasu anty salamatu da iyami saisu maman junior dasuka shigo ganinta aikuwa Nan aka hau ihu da hayaniya ba itaba ba mutuniyarta maman junior ba hadda junior daya girma yafara zama Dan saurayi Nan suka hau fira tana cin lafiyayyar sakwara da miyar Ganda da maman junior din takawo Mata da zafinta iyami dai Dole Takoma palon kawu tabar musu Nan sbd shegiyar firar iya shegen da maman junior tafara kawo musu suna dariya tana sake fesowa Amatu kalolin iya shegen da akeyiwa miji. Firar nawa anty salamatu da maman basiru Dadi hakama Amatun datake sauraronta tanajin qaruwa aciki Amma sai tanajin abin wani irin banbarakwai sbd ba sa'aninta bane duk da duk kwamacalar duniya sunsaba yinta tare tun Ada can Amma wannan sbd ta rayuwar aurece sai kamar tanajin nauyi Amma dayake maman junior din ba ruwanta Dole wani abin saikayi dariya ba qaqqautawa. Sai magriba majalisar palon tasu ta watse suka tashi yin sallah tukuna iyami tasamu kanta duk da wata firar tasu tanaji sama sama wani abin saidai ta girgiza kanta sbd rashin kunyar tayi yawa. **_Athens GREECE_ Kiran wayar USI yake sakeyi kusan akaro na goma sha wani Abu Amma Bata shiga yakoma Kiran anty salamatu itakuma tanata ringing Amma sbd suna Palo fira tayi Dadi Bata jiba yasaki tsoki ahankali ya Nemo numbern kawu yakira shikuma ya fita waje tsohuwar majalisarsa tasu alhaji mande yabar wayar gida. Ki yayi kamar ya fasa wayar hannunsa ya rintse idanuwansa dasukai jajir ya budesu ya miqe daga zaunen dayake a palon zai bar gidan Dan Yana buqatar ticket din Nigeria koman dare idan dai akwai flight zai tafi. Da sauri anty zarah takira sunansa zatai magana ya juyo yayi Mata kallo daya da idanuwansa dasuka Sanya gabanta faduwa yace" Please zarah karki Bari nayi Miki fada kizo kema ki qaramin wani ciwon Kan sbd idan maganata tana daidai you are completely at fault anan, How can you be so selfish kina kallo ta fita Amma baki daga wayana kin kiraba you're telling me ma har bankwana tayi Miki Wai zata tafi A woman who had a miscarriage kice Wai kin dauka na sani zata tafi kona sani ke baki fahimci batada cikakkiyar lafiyaba bai kamata tayi tafiya ahaka ba Kona barta tunda kinada hankali bazaki nada shawaran abar tafiyarba hartaji sauqi Amma Zaki ce Wai you thought nasani to hell with your thoughts... Please I need some air kije daki kema ki kwanta ki huta kada wata damuwa ta baki matsala kema idan munsamu tickets zamu tafi gida I don't feel like staying Kuma sbd inada aikin da ake nemana a gaggauce. Ahankali ta iya bude baki tace" Sorry. Kafin ta juya ta nufi daki tashige tana Hana kanta Jin damuwa ko haunshin zancensa sbd ta yarda kaman yanda yafada tanada laifi sosai anan, Ko tambayanta ya jiknta bataiba, Rintse Ido tayi tana cewa'' Zarah meyasa Kika kasa tunani anan. Dakinsa ya nufa bayan yayi booking tickets dinsu na tafiya saidai bazasu samu jirgin Nigeria ba direct yanzu saisunyi kwana biyu kafin su Isa sai an tsaya qasashe dasu Dole ya amince ya zauna Yana dafe kansa dake neman bugawa sbd tension, A rayuwarsa baisan gwagwarmayar rayuwar aureba da fadan yau da gobe da ake cewa sai yanzu, Gabaki daya sai yanzu yasan me ake nufi da hakuri a zaman aure Dan gashinan kansa na neman kamawa da wuta Yama rasa ta Ina zai faro da kowaccensu ka taba sai wannan tace taji haushi, Babban burinsa dai yanzu kada Amatu tadauka zafi da yawa Dan baisan ya zaiyiba idan ta dauka zafi Dan saukowarta qila saiya hada da neman agajinsu Andi. Wayarsace tayi qara baiyi niyar dubawa ba Amma sbd jiran kira daga gidansu Amatun saiya duba wayar cikin sa'a kawu ne Dan haka ba Bata lokaci ya dauka suka gaisa Yana tunanin ta inda zai Fara tamabayar ko Amatun ta iso sai kawun ya rigasa da cewa'' Saiga Amatu tazo baku sanar Mana ba MAHMOUD, Ana zuwan bazata ne a irin wannan doguwar tafiya saika biye Mata kaima kaki fada Baku kyautaba gskia. Ajiyar zuciya ya sauke yabawa kawun hkr kawai a taqaice kafin suka Dan qara gaisawa suka aje wayar yana Jin wani irin nauyi na raguwa daga zuciyarsa da kansa. ##Mamuh# 6/17/21, 8:08 AM - ': *_MQ 46_* _INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_ _NA ZINNEE SMART WANDA TSARUWAR RUBUTUNSA DA TSAFTARSA TAREDA DADINSA SAIZA KU KAMU DA QAUNAR RUBUTUNTA A KARATUN LAYIN FARKO DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU TA WANNAN NUMBERN_ 👇👇👇 08080840567 Yau kwananta uku da dawowa batareda ta sanarda kowa dalilin dawowarta ba tadai ce musu hutu tasamu me Dan tsayi shiyasa tazo Dan haka Babu Wanda yasa ko kawo tunanin komai cikin ransa gameda zuwan ko tsakaninta da mijinta sai suka hau shaanin gabansu aka bude majalisar me zaman kanta gidan kawu tasu maman junior Dan har wasu abubuwan gyare gyare suka Fara Shirin Fara harhadawa Amatun na gyaran jiki Dana cikin jiki musamman ma iyami da dama batai gyaran yarta ba lokacin da akai auren Dan haka yanzu zata gyara abarta. MAHMOUD ZABEERA kuwa tunda yaji daga bakin kawu tana gida taredasu sai hankalinsa yadan kwanta Amma duk da hakan a matse yake daya dawo Nigeria din tun kafin kowa yasan halinda suke ciki Dan shi kunyama zaiji ace matarsa ta tafiyarta Yana yawon neman komawarta ko Modibbo saiyace ba MAHMOUD ZABEERA din dasuka sani bane gashi kamar zuwan nasa Kai tsaye bazai samu ba sbd wani urgent work Kuma daya taso Masa Wanda dole saiyaje Dan haka zarah kawai zata taho Nigeria shi zai wuce inda zaije daga Nan daga can zai wuto Nigeria din. Yau kwananta bakwai da zuwa zaune suke suna fira itada anty salamatu da iyami Dan yau Yan firar tasu duk basanan sunfita anguwa Dan haka yau gidan tsit ba hayaniya sai su kadai USI ma yadawo asibiti da wuri yau Yana dakinsa baccin gajiya yakeyi sbd a asibitin ya kwana yau. Sallamar umme sukaji Muhammad na bayanta tafe cikin gudu hannunsa riqeda Ben10 soldier dinsa dayafi so cikin kayan wasansa Yana Kiran sunan anty salamatu yana shigowa yaga mummynsa a zaune da gudu yayi kanta Yana cewa'' Mumma mumma. Rungumesa tayi tana cewa'' My Muhammad has become a superman ji wannan gudu fuiiiiii. Dariya yayi Yana Jin dadin Superman data kirasa Yana sake hayewa jikinta yace" Mumma where is my Daddy? Inason ganinsa i miss him""yafada Yana leqa bayanta da kallon koina Yana son ganin baban nasa. Murmushi tayi tana zaunar dashi gefenta tace" Muhammad look"tafada tana nuna Masa su iyami tace" Baka gaida grandma ba da antyty dinka"cewar anty salamatu. Gurin iyami ya nufa Yana miqa Mata biscuits din daya Ciro aljihunsa wanda yakawo Mata yace" Kaka iyami ga biscuits da umme ta siyomin ki ajewa kawu. Dariya dmtayi tana jawosa jikinta suna sake gaisawa da umme data zauna tana amsa gaisuwar Amatu data salamatu tana cewa'' Amatu wato muda muka matsu dason ganinki gamu munzo Muhammad ya isheni Wai babansa yakeson akaisa gurinsa shine nace Bari muzo dai idan yaganki qila ya rage fitinar neman uban. Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba saita kamo wani zancen suka fada wani zancen Bayan anty salamatu takawowa ummen ruwa da brabiskon dasukai Wanda ummen na sonsa sosai musamman yanda iyami keyinsa yayi wani irin laushi. Sai dare umme ta tafi tabar Muhammad dayace gurin mamansa zai zauna. Washe gari kwananta Tara kenan da zuwa suka shirya itada anty salamatu suka fita da motar USI daya bar musu Wanda duk yanda taso taja motar kasawa tayi sbd yanda ta koya tuqi a Greece daban da tuqin nan din Dan haka Dole tabar anty salamatu da USI ya koyawa tuqi sbd fita da iyami ko lalurar gida idan antashi Dan yakan bar musu mota ya tafi asibiti musamman idan acan zai kwana. Family house dinsu maman basiru sukaje barkar haihuwar da qanwar maman basirun tayi shiyasama kwana biyu basa zaman fira sun Dan jima acan kafin suka baro suka nufi kasuwa siyayyar takalman iyami data Basu saqon anaso sun qare daga Nan gurin bada dinki suka Amatu tabada dinkuna sai yamma sosai suka dawo gida Dan haka suna komawa sallah kawai sukai sukaci abinci Amatu ta kwanta Dan matuqar gajiye take. Washe gari tana buqatan gyara kanta daya Fara damunta suka shirya zuwa blue fox itada anty salamatu Dan haka guraren 12 suke fice bayan sunfara biyawa sun ajiye Muhammad a zabeera taje ta gaidasu Andi dasukai mamakin Jin zato hutu Ashe Amma sanin ba ayi maganar tarewarta ba yasa suka barta takomawarta gidansu inda ta sauka saidai Kam tunda har tazo Dole ayi maganar tarewarta ta tare sbd daga yanzu idan tazo ta sauka a gidan mijinta dama tuntuni anyi gyaran sashen marigayi Dr khalil an rushe komai ansauya tsarin gurin gababaki daya Kuma sai akai qatuwar katanga aka zagayayesu cikin qaramin gate me kyau tareda sashen zarah sai harabarsu ta zama daya me girman sosai. Daga zabeera blue fox din suka wuce suna Isa Allah ya hadata da manager kuwa ai Nan ya tsaya kallonta cikin girmamawa da sauri ya qaraso Yana cewa'' Ran Amaryar zabeera ya dade yau an tuna baya kenan. Dariya taso Yi ta gimtse tana kallon gurin da aka sauyawa tsari me kyau fiyeda da ga girma da fadada gurin da akayi ya sauya matuqar Dan yanzu ma tun a gate Saida tickets ake shigowa ga uban securities tana jinjina kai tace" Manager komai na blue Fox yasamu sauyi Banda Kai kana Nan yanda kake har halayen. Dariya yayi Yana cewa'' Allah ya taimaki Amatun zabeera ai mu Babu wani sauyi daya fiyemin blue fox musamman yanzu datake zaman mijinki Dan kuwa ya jima ya siyeta gabaki dayanta Kuma nasan idan Allah ya yadda sbd ke ne tunda kowa yasan har yanzu kina qaunar blue fox dinnan shine yayi Mana dukkanin wannan gyare gyaren Takoma kamar turai yanzu hadda sashen geaming da sports munada aciki haka Kuma komai namu anqara fadadashi daga restaurant din har spa din dasauransu. Girgiza Kai tayi tana kallonsa tace" Ga antyna dai ku gaisa sbd Naga ko ganinta bakayiba sbd dadin labari. Da sauri ya kalli anty salamatu dake sanye cikin riga da skirt na red embellished atampa da gyalenta red shima sai tsawonta me tsari ya fito cikin dinkin riga da skirt din ya washe dukkanin haqoransa da fara'a yace" Sannu da zuwa blue fox Ina Miki barka da zuwa sirikar me gidanmu. You'll never change manager" Amatu tafada tana yin gaba Yana biye dasu Yana musu bayanin yanda tsare tsaren gurin yake ayanzu da kansa yaje jiki na mazari ya karbo musu tickets na komai da zasuyi yakawo musu a kebantaccen gurin da sai oga zabeera din yazo da kansa shikadai ke zama acan suka Fara cin snacks kafin suka nufi spa Dan komaima yimata zaayi. Da gyaran Kai aka Fara musu kafin da aka gama aka koma gyaran qafafuwa daganan aka koma gyaran jiki. Basu baro blue fox ba sai magrib suna isowa gida itace tafara fitowa tana juyowa sai Jin Muhammad tayi a jikinta ya Fado Yana mata "oyoyo mummah" Da mamaki take kallonsa suka nufo cikin gida tana cewa'' Waye ya dawo da Kai?bakace Kuma gurin umme kakeso ba sbd ka ringa wahalarda mutane zaka ringa saka masu kaika da dawo dakai yawo. Daddy yazo Dani... Kallonsa tayi da sauri tana kallon bakinsa daya furta dadyn tace" Dadynka Kuma? Eh dady ne yadawo yau yazo Dani yace muzo mutafi da mummah. Kallon inda yake kalla tayi numfashinta nason sauya fita ta hanyar qara sauri tana dannewa ta kalli gurin tagansa zaune Kan kujerun harabar gidan tareda kawu Kawu sai zuba yake Masa Amma shi idanuwansa na kanta ya zuba Mata su cikin yanayi da kasalar da ganinta ya sakar Masa idanuwansa na bayyanarwa sbd wani lumshewa dasukeson Yi Amma Basu lumshe din ba. Bugawa ZUCIYARTA ke Naman Yi sbd wani irin kyau da sheqi tareda qwarjinin da Allah ya horewa wannan bawa nasa MAHMOUD DAHEER ZABEERA ta dauke idonta ahankali tareda juyawa ta shige ciki batareda tabari kawu ya gansu ba Dan yanzu zai Fara kawo Mata zantukan tazo ga mijinta. Suna shiga daki tashige ta tube saidatai wanka kafin tayi sallar magrib da yanzu aka gama ta sanya doguwar riga mara nauyi me kamar boubou ta fito tana tambayar abinci ta nufi kicin ta dauko zobon da iyami keyi tana sawa a fridge sbd baqi dakuma kawu dakeson ruwa me kala ta fito tana Shan zobon saiga USI yashigo yace taje palon kawu yana namanta. Can ya wuce Kai tsaye sbd ta daina Jin hayaniyar Muhammad tasan sun tafi ne tunda dare yafara Yi takumasan babansa bai Bari ana fitar dare dashi. Tana shiga da Muhammad din tafara cin karo kwance yayi bacci jikin kawu tana ganin hakan saita daure fuskarta taqi kallon dayan gefen Dan taji ajikinta MD ne agurin. Kallon kawu tayi muryarta na daidaituwa cikin nutsuwa tace" Kawu likita yace kana kirana. Eh mijinki ne gashinan zaune yazo tun dazu bakwanan yanata zaman jira. Miqewa kawun yayi daukeda Muhammad ya fice yakaiwa iyami dakinta ya fita zuwa gurin abokanan hirarsu ta dare a qofar masallaci. Kawun na fita ta nufi qofar fita itama batareda ta kalli inda yake ba ko qofar Bata qarasa isaba taji yariqo hannunta tareda dawo da ita baya har bayanta na gugar qirjinsa ya bude baki da muryarsa me taushi yace" Why? Meyasa Zaki taho a irin yanayin da kike ciki Kuma ki dauki fushi Bayan nine yakamata na dauki fushin tunda kin baro batareda sanina ba. Juyowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta zame hannuwansa cikin nata daya riqe ta wuce tabarshi tsaye Yana kallonta. Qofar data fice yabi da kallo Yana Dan rintse idonsa ya sauke numfashi Yana komawa zaune dama yasan Amatu bazata sauko acikin sauqi ba. Hakanan ya fito ya wuce batareda kowama yasaniba Yana Isa gida ko abincin dare daqyar yaci sbd kada Zarah daya lura kamar itama tafara iya Magana akan Abu tayi Magana bazai iya daukar wani stress Bayan Wanda yake daukaba yanzu aikin dayayi a Sudan duk tsawon kwanakin baiwani bada hankali yayi Abinda yakaisa ba sbd har lokacin komai Kiran dazaiyiwa Amatu baya samunta, Wanka yayi ya kwanta kawai dama akwai gajiya a taredashi sbd yau din ya dawo. Washe gari ma taso fita Amma iyami ta hanata sbd cewar mijinta na gari ba Maganar yawo yanzu Dan haka Dole ta zauna gida tana kallo su Anty salamatu hadda iyamin suka tafi gurin sunan qanwar maman basiru suka barta. Tana zaune Palo tana kallo sama sama bayan la'asar har bacci ya Dan Fara daukarta taji qamshin imperial majesty na shiga hancinta kobata juyoba tasan shine zai shigo palon ta tashi zata shige daki tun bai qarasa shigowaba tana kaiwa tsakiyar palon Yana shigowa da sallamar cikin sauti me taushi ya tsaya gabanta Yana kallon fuskarta dake daure tam sai yaji jikinsa yayi sanyi ya rasa kalmar furtawa ya riqo hannunta cikin nasa idanuwansa na kanta a gajiye da wannan fitinar yace" Wannan shirun naki is killing me Kiyi mgn Koda zakiyi fada ne I'm ready Zan dauka infact I won't say a word indai har Zaki sauko. Bata kallesaba ta kwace hannunta a hankali kafin tace" Zan kwanta Kuma bakowa a gidan nikadai ce. Tunda yadawo gida zarah ta rasa gane kansa abun duniya ya isheta ga cikinta nada damuwa an hanata sakawa Rai damuwa Amma wlh bazata iya rashin damuwarba sbd Abinda take gani shi ake Kira da asalin damuwar, Yau satinsa guda cif da dawowa Amma yarasa gane Kan Amatun tun abin na iya tsakaninsu har gidansu Amatun dai kowa yasan Abinda yake faruwa kawu dayaji hadda 6arin ciki tayi sai baiji dadin yanda MAHMOUD din yabari tadawo ba ita kadai cikin yanayi irin wannan Amma zamansa uba saiya ringa bin Amatun da rarrashi har gwara iyami na Dan Mata zafi wani lokacin Amma duk da hakan shidai MAHMOUD baiga sauqi ba saima yakoma ya hurawa su Andi wutar batun tarewar Amatun Wanda yabar Andi cikin mamakinsa dakuma tunanin shima wato lokacin gyaransa yayi a hannun Amatu sai suka aikawa kawu yace zai Basu ranar tarewa idan yayi mgn da Amatu. Jin hakan sai tension dinsa yafara bayyana ga aikinsa Dan duk wasu ayyukansa da meetings dinsa na watan kusan duka yayi postponing dinsu sbd kwanakin Yana samun matasalar saurare a bangaren aikin shiyasa ya tsayar. Batareda tsayawa neman bayanin kowaba yasa aka Zo aka zubawa sashen sabbin royal furnitures masu kyau da tsari saidai har lokacin Amatu takasa tsayawa dashi ko Magana suyi tun Yana daukar Muhammad Yana zuwa dashi harya Bari kada ya kwashi sanyi da yawa Zaune yake Yana duba wayarsa hankalinsa gabaki daya baya Kan wayar Yana wani gurin.. Fitowa tayi daga dakinta cikin Dan adonta na riga da skirt na atampar data Dan fitar da qaramin cikinta daya Fara Dan turowa ta kallesa tana nazarinsa tsawon lokaci kafin ta sauke numfashi ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko Masa lemondrink da cup ta Dora Kan tray ta dawo takawo gabansa ta ajiye tareda zama gefensa ahankali tana budewa ta zuba Masa ta miqa Masa ahankali tareda Kiran sunansa cikin sanyin murya. Waiwayo yayi ya kalleta tareda kallon kwalliyar jikinta datai Masa ya karbi drink din Yana qaqalo sahirtaccen murmushi ahankali yace" Thank you and you look great. Kurbawa yayi ya ajiye Yana kashe wayarsa gabaki daya ya ajiye ya qara daukar drink din yanasha harya shanye ya ajiye cup din yasake Dan juyowa ya kalleta Yakuma cewa'' Thank you"Yana maida kallonsa kan TV Yana kallon news. Jinjina Masa Kai tayi tareda fuskantarsa gabaki tana jinjina qarfin Rai irin na MAHMOUD din dayake dannewa da boyewar abindake ransa kamar yanda ya Saba boye al'amura saidai yanxu wannan damuwar ta dabance Dan itadake taredashi tana iya hango damuwa ataredashi. Numfashi takuma saukewa akaro na biyu kafin ta Kai hannunta ta Dora Kan nasa ya juyo ya kalleta da idanuwansa dasukai laushi sbd rashin isashen bacci ta bude baki ahankali tace" I'm really sorry MD sbd tun farko daban Bari ta tahoba da duk haka bai faruba, Laifina ne na yarda Kuma Inshallah idan munhadu Zan fahimtar da ita hakan but for now idan akwai ta inda Zan taimakawa alamarin let me know please.. Shiru yayi idanuwansa a rufe na mintuna kafin ya budesu ahankali ya juyo ya kalleta na mintuna Yana NAZARIN yanayinta ya bude baki yace" She respects you fiyeda komai sbd tanajin nauyinki fiyeda komai because of the old relationship that you two shared Wanda deep down haryanxu tana Miki kallon yayarta. Kallonsa take da dukkanin girman idanuwanta bugun zuciyarta na sauyawa sbd Fara tammahar inda zancensa keson dosa muryarta na rawa tace" To ta Yaya hakan zai..... Ki tayani fahimtar da ita Abinda nakeson tagane please. Saura qiris zuciyarta ta buga daga cikin qirjinta ta da Abinda ya fada din, Wani dishi dishi take neman Fara gani sbd bugawar da zuciyarta keyi da sauri, Wani irin zafi yafara taso Mata tun daga cikin qasan zuciyarta Yana mamaye zuciyar Tata take taji tsanarsa nason darsuwa a zuciyarta akaro na farko a rayuwarta Amma ta yakice hakan tareda kallonsa cikin Ido ta bude baki Kai tsaye tace" For the first time yau MAHMOUD ZABEERA ka farkar Dani daga wani babban kuskuren danake ciki, Miqewa tsaye tayi ta kallesa cikin muryar dake bayyanarda jarumtarta tace" Zuciya ce a kirqina ba dutse ba dan haka inaga ko dan Abinda yake cikina na cancanci wata karramawar Amma duk da hakan tunda ka buqata Zanyi mgn da ita Amma bisaga sharadin idan Bata dawoba Nima nagama zaman gadin gangar jikinka sbd inason ayau kasan sonka zuciyata ya Kama bawai zuciyar ya cinye ba. Zaiyi mgn tabar gurin batareda ta tsaya sauraronsa ba ta nufi dakinta ta shige tareda rufowa ta Isa bakin gado ta zauna tana son fashewa da kuka Amma Abinda takeji yafi qarfin kukan sai kawai ta miqe ta zari doguwar hijab da keys din motarta ta fice tanajin idan Bata bar gidanba komai zai iya faruwa. ##mamuh# 6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 48_* *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da: Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da: Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA Gashe gashe da soye soye kamar su Kaza Kifi Nama Doya Dankalin turawa/hausa Awara Danwake Gurasa Kwado da dai sauransu.... Ba Mu tsaya anan ba—â€? The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da Hoppers wato Fara Milky candies wato alawar madara da kuma Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata... Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka IG: @the_flavorland Whatsapp:08104673847 Sending Some treats your way.... l Let us satisfy your cravings: We Deliver anywhere and everywhere. ******* ********* Suna Isa zabeera Kai tsaye motar data daukota sashen Andi aka nufa dasu sbd har Modibbo da umme na can dashi kansa MAHMOUD din Wanda ranar yakoma MD ZABEERA dinsa sak miskilanci da izzarsa sun motsa ko wayoyinsa duk akashe ma suke Abu daya kawai yakeji atare dashi shine nutsuwar zuciya data ruhi harma data gangar jikinsa Wanda yagama tabbarwa da kansa cewa tabbas Amatu tarigada tazama wani babban bangare an zuciya,jiki da rayuwarsa tunda haryakejin wannan nutsuwar me sanyin Dadi tattare da dawowarta garesa. Suna shigowa akansa idonta yafara sauka ta dauke Kai Yana sunkuyarwa ta zauna daga qasa gefen umme dake kallonta fuskarta na bayyanarda farin ciki da murmushi. Da MAHMOUD din Andi yafara nasiha akan haqqoqan Mata dake Kan mijinta dakuma ire iren halayen .ata da Dole namiji saiyayi hkr dasu sbd rauninta dakuma rashin zurfin tunani da Rashi haquri irin na wasu matan kafin yadawo Kan Amatu da nasihar zama da miji da girman haqqoqinsa akanta da girmansa dayafi na kowa akanta yanzu yaqara da nasihar adalci tsakanin mataye biyu dakuma haqurin zama da abokin zama Dana rayuwa kafin daganan Andi yayiwa Amatun kyautar aure ta sabuwar mota fil sak irinta zarah datake hawa banbancin kalane kawai dayace Tata Ash ce ta zarah farace. Godiya sosai sukayi suka fito umme na riqeda hannun ta saka Mata wani acikin hannun dayake rufe cikin qaramar kwalbar roba suna shiga mota tace" Shanye kiban roba. Kallon ummen tayi tana sake kallon abun ta Dan 6ata fuska zatai mgn tace" Bansan Jin komai hanzarta kishanye kiban. Marairaice fuska tayi tana kallon abun. Anty salamatu dake sit din gaba ta juyo ta kwace kwalbar ta bude tareda Dora Mata abaki tana cewa'' Dallah shanye da abin dadine da yanzu kinfara maganar qari to wannan dadinsa saikin fi kowa..... Rufe Mata baki Amatun tayi da sauri tana zaro Ido kunyar umme kamar ta nitse ta saci kallonta tace" Haba anty salamatu nidai karki fara zancenki Dan Allah. Itama anty salamatu kunya taji sbd mantawa tayi da umme da iyami dasuke taredasu sbd sun Saba zantukansu na banza dasu maman junior shiyasa. Shanyewa tayi ta miqawa umme kwalbar daidai isowarsu qofar part dinta motar har qofar palonta ta faka suka fito umme na riqeda hannunta tana fada maganganu qasa qasa na rikita miji wainda sukafi qarfin duk rawar Kan Amatun kunya kamar ta qwace hannunta ta zura da gudu Amma ummen ba ruwanta fada Mata takeyi har suka shiga suka zauna palon tana sake zayyano Mata zantuka masu qarfi wainda wasune suka samu damar shiga kanta wasu kuwa nauyinsu yasa suna kasa shigewa Kan nata. Turaruka ummen ta fitar cikin jakar hannunta ta fesawa Amatun ko Ina jikin masu wani irin sanyin qamshi dagaji tasan bazasu wuce ouds ba masu tsananin tsada take qamshinta ya qaru tana fitarda wani qamshi me ni'imtaccen sanyin dadi suka Fara qoqarin tafiya anty salamatu tace" Zarah ko lafiya Naga banganta ba na dauka ma zamu sameta anan gashi har zamu tafi. Umme tace' Eh Kam gashi dai Nima duk yau banganta ba Nima nai zatan zamu sameta anan din tana jiran isowarmu. Iyami data miqe tsaye tana gyara zaman mayafinta yace" Mezaisa zarah tazo ta zauna anan tana jiranmu karku manta bafa kamar da bane yanzu ana Magana akan Amatu tazama matar mijintane Dole wani abun zata Kama kanta ba kamar da ba da Amatun take matsayin qanwarta yanzu kishiyarta ce Dole akwai radadi ko yayane aranta. Tsit Amatu tayi tana saurarensu sbd duk lokacinda akai Mata tunin kishiya saitaji kamar hankalinta nason tashi saidai girma da nauyin anty zarah da haryanxu take gani da ji atareda ita yana danne kishin datakeji shiyasa take sauke zafin kishinta agun MAHMOUD sbd bazata iya kallon fuskar anty zarah tayi fitinar kishi da ita ba duk zafin kishinsa kuwa sbd Abu daya data fahimta takuma lurarwa kanta MAHMOUD da kansa zai iya kiranta butulu akan zarah idan bata nutsu ta iya zama acikinsu ba yanzu Kam akwai aiki agabansu su dukan na iya zama da juna. Bayan tafiyarsu iyami kasa tashi tayi daga Inda take zaune tashiga tunani daban daban akan rayuwarta da Kuma ranar farko da aka Fara kawota cikin part dinnan amatsayin matar KHALIL DAHEER ZABEERA yanzu Kuma gashi ankuma kawota amatsayin matar Dan uwansa MAHMOUD DAHEER ZABEERA, Duk da ansauya sashen gabaki daya Babu inda zaka iya gane shine wancan din Amma dai memories diinsa suna cikin zuciyarta. Hawayene suka ciko idanuwanta suna qoqarin gangarowa taji bude qofa Bata dagoba Amma qamshin daya shiga cikin hancinta da motsinsa da baya qarfi yasa ta fahimci waye yashigo ta rufe idanuwanta ta bude ahankali batareda ta dago ta kallesa ba saima sake lumshe idanuwanta datai. Qarasowa yayi cikin nutsuwarsa da kamalarsa ya zauna kusada ita sosai qamshinta ya Shiga hancinsa yanl dago fararen idanuwansa dasuka Gama gabalaituwa a sonta ya zuba Mata tareda riqo hannuwanta ya sarqe da nasa ya sauke ajiyar zuciya wadda itama ta sauke tata a boye cikin cikinta. Kasa Magana yayi sbd bayajin yin maganar ya kwantarda kansa Kan kafadarta Yana sake sarqe hannuwansu ya lumshe idanuwansa sukai shiru ahakan sai numfashi da qamshin juna dasuke shaqa nutsuwa na shigarsu duk da Babu Wanda yafito yagfada Amma numfashinsu dake fita ya bayyanarda hakan. Sun jima ahakan Babu wani motsi Saida yagama samun dukkanin nutsuwar daya rasa kafin ya sauke numfashi tareda dagowa ya kalli fuskarta suka hada idanu ta sauke nata tana qoqarin rufesu ya Kai hannu ya juyo da fuskar tata Yana kallon halittar da ita kadai ke iya rikita MD ZABEERA baisan lokacinda ya saki wani irin murmushi ba yana kallon bakinta daya iya fidda Magana ta arziki data tsiya. Fuskarsa yakai dab da tata Yana kallon cikin idonta yabawa bakinta light kiss Yana sake sakin murmushi cikin taushin muryar data sanyata dago idanuwanta cikin rashin yadda ta zuba Masa yace" I can't live without you Mrs MD ZABEERA so kada ki sake tunanin barina sbd komai zakiyi bazaki iya barin rayuwa Dani ba. Miqewa yayi tsaye hannunta cikin nasa har lokacin ya miqar da ita Yana cewa'' Let's have dinner zarah is waiting. Ba musu tabiyosa suka fito hannunsa na riqe da nata itama saiyi takeyi tana kallonsa duk da tasan so yake azauna lfy Amma dai mamakinsa bai daina kamata ba sbd ganin yanda ya sauya din dama ita batada niyar zama da miji Babu shaquwa Babu Wasa da dariya Babu hayaniya Babu muguwan wasan gudu gudu idan ma takama to Ina dadin rayuwar auren take tanason morewa sauran kuruciyarta a tareda mijin aurenta Dan haka Babu wani daga mulki sai oda a Shirin zamanta dashi. Suna shiga anty zarah na fitowa daga bedroom dinta cikin adon riga da skirt na lace maroon tayi Yar simple makeup ga qaramin cikinta daya Dan fito tayi kyau itama sai qamshi take saidai suna qarasa shigowa qamshin dake fita cikin Amatun saita ji ta daina Jin natan ta qurawa Amatun idanuwanta dake son raunana da irin dacewa da kyan dasukai tareda juna ta kalli hannuwansu dake sarqe tafara Kiran sunayen Allah tana kore shedan daga zuciyarta ta saki murmushi tana kallonsu tace" Sannu da zuwa Amatu. Murmushi Amatun ta saki tana kallonsa da shima ita yake kallo tace" Thank you anty. Kallon MD din zarah tayi tana dauke idonta daga Kan hannunsa dake riqe Dana Amatu tace" Dinner is ready fa. Dining suka nufa su dukkansu suka zauna zarah ce ke zaune kusada MAHMOUD din sukaci abinci itadai Amatu drink kawai Tasha sai spoon biyu datai ta miqe tace ta qoshi. Shima ba wata yunwa yakeji ba Amma ya zauna yaci abincin sosai tareda zarah haryana yaba abincin sosai sbd Fara sanin halin Mata dayayi ya fahimci sunfi son ko yaushe ka nuna musu yabawa da kulawa. Aikuwa hakan ya faranta ran zarah musamman daya nuna Jin dadin abincin a fili saitaji damuwarta ta ragu sosai suka baro dining din itama Yana riqeda hannunta suka iso ya zaunar da ita Kan kujera ya zauna gefenta Yana kallon Amatu data matsu tawuce yafara musu bayani da nasiha tareda roqon Dan Allah a zauna lfy plus respecting juna duk da yasan suna ganin qimar junansu sosai kafin ya sanar dasu 2days ne kwanan daga haka aka tashi Amatu tafara wucewarta shikuma zarah yabi Dan sake lallasarta Abinda Baya faruwa a zamansu mamakinsa da Jin dadin hakan ya sanyaya zuciyarta sosai harta cemasa yatafi gurin Amatu tana jiransa. Bedroom dinsa ya nufa yashiga wanka Yana fitowa Saida ya tsaya wata waya kafin ya fice. Bedroom 'dinda ta tabbatarda shine nata tashiga data dawo daga sashen na zarah ta ajiye wayarta ka bedside drawer ta warware lafayarta ta nade takai wardrobe tana budewa ta tsaya kallo cikin mamakin ganin Kaya a shaqe maqil da hadda wainda aka dinka da wainda ba'a dinkq ba ga qananun Kaya da jallabiyas ire iren wainda yasan tana sanyawa. Murmushi ne yaso subuce Mata data Kai hannunta Kan tarin qananun kayan dake jere Wanda taga bumshorts ne sukafi yawa abin data lura yafiso kenen wato shigarta zata fiddo cinyoyinta duka a waje. Rungumeta taji anyi tayi saurin juyowa sbd bataji motsin shigowarsa ba, Kallon fuskarsatayi cikin basarwa ta zame daga jikin nasa ta jefa lafayar ta rufe wardrobe din ta bar gurin ta nufi toilet ta jima ciki Babu Abinda zatayi tana saqa da warwara kafin dai ta wanke hannuwanta tayi alwala kawai ta fito tana goge fuskarta da qaramin towel sai ganin lafayarta tayi ya miqo mata Yana cewa'' Ki mayar inason nizan cire miki inason sake ganinki cikinta you look innocent acikinta. Batareda ta kallesaba ta karba ta nufi gaban mirror tana nadawa ya zauna Kan sofa Yana kallonta hannuwansa nade da qirjinsa. Tana gamawa ta juyo ta kallesata ta gefen Ido ya taso Yana murmushi ya Kama hannunta suka nufi bedroom dinsa suna shiga wani sanyin qamshi ya doki hancinta sbd kalar turarukansa ba Arabians bane nasa designers Eglh perfumes yake amfani dasu, As she expected komai na dakin fari ne da milk sbd sune colours dinsa. Daddumar sallah ya Ciro itama milk color ce ya shimfada Yana kallonta yace" Kinyi alwala right? Saida ta dauke Kai kafin tabude Baki daqyar tace" Yes. Yanda taketa daure Masa din Yana sake burgesane Bata saniba sbd shi fushin ma nata Yana Masa kallon wani sabon feeling. Sallah sukayi ta nafila rakaa biyu kafin ya juyo ya riqo hannuwanta duka biyun Yana kallon fuskarta ahankali ya furta" Sorry. Qin juyowa tayi ta kallesa ta zame hannuwanta zata miqe ya matse hannun Kai tsaye yace" I love you.. Cak ta tsaya daga qwace hannun dazatayi zuciyarta ta Fara tsananta bugu takasa motsawa hakama takasa juyowa ta kallesa. Ya lumshe idanuwansa yasake budewa ya Dora akan hannuwanta dayake riqe dasu cikin murya me taushi yasake cewa'' I love you AMATULLAH K SALEH and I am saying sorry so please wannan fushin yakamata ya sauka please. Juyowa tayi tana kallon fuskarsa zuciyarta na qarasa bugawa da qarfi ta kasa yadda da Abinda taji idan MAHMOUD ZABEERA dinda tasani ne yake furtasu saidai zumudin zuciya dakeson kamata gudun bada kanta yasa ta miqe ahankali tana zare hannuwanta ya dawo da ita jikinsa ta hanyar fixgota ta Fado qirjinsa ya Bata kyakkyawar runguma Yana fada Mata Magana cikin kunnenta data sanyata saurin zaro Ido waje tana kallonsa takaici da muguwar kunya suka dabaibayeta batasan lokacinda ta Fara mintsinansa ba ta bude baki Dole tana cewa'' Wlh ni sharri ne wannan kakemin, Allah bazan yaddaba.... Dariya yakeyi Mara sauti da hayaniya wadda yaune karonta ba farko ganin dariyarsa ba murmushi ba. Ganin ta kunnu sosai da Abinda ya fada din yasashi miqewa Yana Sosa inda ta mintsinesa Yana cewa'' Zaki fasamin fatane da wannan mintsinin naki.. Biyosa tayi tana sake kunnuwa har lokacin kunyar zancen bai saketa ba ta nufesa tana cewa'' Saika janye wannan sharrin dakamin bazan yadda ba.. Tana isowa gurinsa ya riqe hannuwan tareda shigar da ita jikinsa ya Kai fuskarsa Kai tsaye ya hade da Tata ya hade bakinsa da nata yana Bata wani ni'imtaccen kiss daya kashe jikinta harya warware Mata lifayar jikinta Bata saniba Saida ya cirata gabaki daya zuwa Kan qaton gadonsa Yana rage musu hasken dakin ta makunnin gefen gadonsa. ##Mamuh# *_Thank you 4 d prayers_*🥰🙏 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 47_* _INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_ _NA ZINNEE SMART WANDA TSARUWAR RUBUTUNSA DA TSAFTARSA TAREDA DADINSA SAIZA KU KAMU DA QAUNAR RUBUTUNTA A KARATUN LAYIN FARKO DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU TA WANNAN NUMBERN_ 👇👇👇 08080840567 ******* . Tana Isa gidansu Kai tsaye dakin ummanta ta wuce ta zube Kan gado sai alokacin wani gigitaccen kuka ya 6arke Mata me ciwo. Umman data fito toilet taganta tana kukan sai kawai ta barta tayi me isarta kafin tabar gefenta Takoma Kan kujerar dakin ta zauna tana kallonta tace" Wannan kukan dakikeyi ki Dena zarah sbd Abinda yake taredake Wanda baya buqatan irin wannan tashin hankalin tunda kinfi kowa sanin yanda cikin baida qwari. Tashi zaune tayi tana share hawayenta ta zare hijabin jikinta ta dago ta kalli umman dake Mata kallon jiran jin dalilin wannan kukan. Bude baki tayi ta korowa umman bayanin komai zata Dora da wata maganar umman ta daga Mata hannu cikin takaicin ZARAn da cewa'' Zarah kinada matsala babba idan har Baki dawo hayyacinki ba, Shi so da zaman aure duk ba hauka bane, Ta Yaya Zaki maida kanki doluwar qarshe akan gudun zuciyar namiji, Shin meye amfanin rayuwar aurenda babu fahimtar tunani ko Babu so ana zaman aure me Dadi idan kowa yasan mutunci da darajar kansa data abokin zamansa, Matsalarki zarah itace kin kasa bawa kanki darajarda shima abokin zaman naki zai baki, MAHMOUD ya zauna dake cikin girmamawa da mutuntawa tsawon shekaru masu tsayi batareda ya taba complain ko nuna muzantawa garekiba duk da kece Kika kasa kawo sauyi da shaquwa acikin auren naku sbd kece mace kinada hanyoyi da damarmaki da Zaki sauya MAHMOUD tun kafin wata tashigo rayuwarku Amma Kika kasa yanzu abin yazo a biyu na farko koki yarda ko karki yarda MAHMOUD son mararsa AMATULLAH yake so me tsanani musamman tunda yanzu gatanan tana bude Masa hanyoyin sanin zamantakewar aure sannan akwai fadanda ko sunyi abunsu na tsakanin ma'aurata ba huruminkineba Shiga gashinan yanzu kin qare zuwa bikon kishiya Wanda idan dai baki koyi sanin darajar kankiba data Kama kanki akan Abinda Babu ruwanki har ruwan wanka kina Kan hanyar daukarwa kishiya Dan haka kada kiga laifin mijinki laifinkine Da Zaki farka ki nuna Masa kinsan darajar kanki data aurenki da zamanki matarsa tsaf zakiga yazo yazauna daku anbawa kowacce haqqinta anzauna lafiya. Bance kinyi baya ba sbd wannan halindakike ciki Allah na gani Kuma Yana sane wlh zakiga irin tanadin sakamon da Kika samu agaba Amma gskia zarah ki farka Babu Wanda zai qwaceki a cikin wannan yanayin sai kanki da kanki Zaki qwaci kanki ki tashi kije bikon naki dakika daure kanki da zakiyi Danni bana cikin wannan mutuwar zuciyar. Mutuwa jikinta yayi ta miqe ta wanko fuskarta tadawo ta dauki keys ta fice batace qala ba ta shiga mota ta nufi gidansu Amatu. Tana Isa tayi parking ta fito tana daidaita kanta da nutsuwarta ta nufi ciki ta Isa qofar Palo tashiga da sallama Su iyami dake zaune palon duk suka juyo suna kallonta Saiga Amatu ta fito daga kicin daukeda indomie data dafo tana ganinta itama ta tsaya cak tana kallonta. Anty salamatu ce tayi saurin miqewa tana cewa'' Zarah kece da yamman Nan sannu da zuwa. Iyami ma cewa take" Qaraso ki zauna zarah kinji sannu da zuwa fitar yamma. Murmushin qarfin hali tasaki tana qarasowa ta zauna tana kallon Amatu dake kallonta tana Mata sannu da zuwa itama. Murmushi tasaki tana cewa'' Amatu idonki kenan. Indomin ta ajiye tana murmushi tace" Anty zarah kedai karkice komai nakira wayarki Allah harso biyu bana samu. Zobo anty salamatu takawo Mata suna qara gaisawa zarah tace" Iyami wannan 'yar Taki zaneta zamu farayi sbd tashin jinta yanzu kiduba kiga yanda takasa aje fushin datakeyi damu shiyasa nazo da kaina nabata hkr tunda taqi sauraron mijinta to gani nazo Dan yau bazan fita gidan nanba saida ita. Kallonta Amatu tayi cikeda mamaki tace" Anty zarah. Tsit antyn tayi sbd tsawon lokaci sai yau takirata anty zarah complete. Juyowa tayi ta kalleta zuciyarta na rauni da damuwar datake ciki Amma tana daurewa kada ta gasa ta bude baki zatayi mgn sukaji sallamarsa dukkaninsu suka juya. Iyami na ganinsa gaisawa kawai sukayi ta miqe ta bar gurin hakama anty salamatu. Kallonsa zarah tayi harya qaraso gabanta baice komaiba ya kamata hannunta ya miqar da ita yace" Let's go. Kallonsa tayi da idanuwanta dake son cikowa ya sakar Mata murmushin dake nuna banhaqurinsa Yana girgiza Mata Kai yace" Ita tariga ta taho gidansu ke dakike taredani bazan Bari ki barni ba, Bazaki bawa kowa hkr ba sbd selfishness ba. Wani irin sanyin Dadine yake kwaranya cikin zuciyarta haryana bayyanuwa Kan fuskarta tasaki wani yalwataccen murmushi tana girgiza Kai tace tunda nazo zankoma da ita idan har da akwai mutunci da ganin girma a tsakaninmu. Gyaran muryar kawu sukaji daga bayansu suka juya Banda Amatu da abun duniya ke neman shawa Kai. Palonsa suka nufa aka zazzauna Nan ya rufe Ido duk su dukan yayi musu fada tareda sanarwa da kowa laifinsa Kuma ya buga rantsuwar yau Amatun a gidanta zata kwana da daddare iyami da salamatu zasu kawota. Godiyar da MAHMOUD din yaringa yiwa kawun yasa su iyami Jin wani iri sbd zarah din. Bayan tafiyarsu Amatu Tasha kuka harta gaji iyami ta kalleta tana cewa'' Amatu kiji tsoron Allah kobaki zauna da mijinki lfy Dan Allah ba Kya zauna dashi lafiya kodan baiwar Allan Nan tasamu nutsuwa gidan aurenta, Karki manta shifa aure hkr ne cikinsa kusan gabaki daya, Bakiyi rayuwar zaman aureba da Khalil ya rasu sai yanxune zakiyi rayuwa Kuma wlh duk Kika dagawa MAHMOUD hankali har hakan yasa aka Shiga haqqin zarah Allah bazai barki ba, Matar Nan koba komai wlh duk Wanda yasameta abokiyar zama ya huta a rayuwa sbd matardake danne kishin Mijinta Dan kawai a zauna lfy ai itace abarso da tattali Banda shi so yake wani dabam, Dan haka Amatu Dan Allah ki dauke Ido ki koyi hakuri Kuma ki zauna da Matarnan tsakani da Allah kamar yanda kuke ada ni wlh tausayi take bani Kuma Ina tsananin ganin girmanta. Itadai Amatun Banda hawaye Babu Abinda takeyi sbd hukuncin da kawu ya yanke akanta ta wani bangaren Kuma yanzunema zasu Fara tsara zaman auren dakuma kishin tunda yanxune za'a hadesu araba musu kwanan aure da komaima. Daki Takoma anty salamatu na hada Mata sauran kayan Sha da iyamin ke hada Mata kullum tun ranarda aka Fara maganar tarewarta. Har dare Basu Gama Shiri ba sai Bayan ishai tayi wanka ta shirya cikin wata farar lafaya da wani lace me taushi aka bita da turaruka masu sanyin qamshi suka fito bayan kawu yaqara tashi nasihar. Andi ne dakansa ya aiko drivern dayazo daukarsu suka nufo zabeera inda ake jiran isowarsu. ##Mamuh# 6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 49_* *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da: Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da: Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA Gashe gashe da soye soye kamar su Kaza Kifi Nama Doya Dankalin turawa/hausa Awara Danwake Gurasa Kwado da dai sauransu.... Ba Mu tsaya anan ba—â€? The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da Hoppers wato Fara Milky candies wato alawar madara da kuma Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata... Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka IG: @the_flavorland Whatsapp:08104673847 Sending Some treats your way.... l Let us satisfy your cravings: We Deliver anywhere and everywhere. ************ Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda nauyin baccin dabai Gama isarta ba sbd sai Bayan sallar asuba ne tasamesa tana Gama budesu da kyakkyawar fuskarsa tafara cin karo daf da tata numfashinsu na sarquwa cikin na juna,ta kalli idanuwansa dake lumshe ta gangaro da idanuwanta Kan lips dinsa wani gajeran murmushin samun nutsuwa ya subuto Mata ta motsa hannuwanta dake sarqe cikin nasa taji yasake matsesu ta maida kallonta Kan fuskarsa da mamakin da alama idanuwansa biyu kenan? Hancinsa taji akan nata ya hade fuskarsu ya Dora mata ta Kai idanuwanta Kan idonsa daidai Yana budesu cikin kasalar baccin dabai Gama sakinsa ba ta dauke idanuwanta ahankali daga nasa zata sake zamewa yasake qin Bata damar motsawa. Ahankali ta bude bakinta dake daidai kunnensa cikin qaramin sautin daya qarasa kashe jikinsa da saukar Masa da kasalar tace" Yunwa. Daqyar ya iya bude idanuwansa dasukai laushi da yanayin yanda dumin numfashin bakinta ke shiga cikin kunnensa ta maganar datai Masa. A kasalance ya saketa ta tashi zaune ta sauka daga Kan gadon ta nufi toilet ta Shiga. Wanka tayo tana fitowa daureda towel brown ta nufi closet dinsa ta dauko wani sabon towel din qarami Tana sake goge kanta ta nufi gaban mirror Yana duba dryer Amma Babu a dakin ta waiwaya ta kallesa taga idanuwansa qyam akanta Yana binta dasu kamar wani mayen qarfe saita fasa tambayarsa sbd ganin hadda miskilancinsa daya hanasa tashi bare Magana sai binta yake da idanuwa ta nufi qofa ta fice zuwa bedroom dinta sbd akwai acan taganta jiya gaban mirror. Tana Isa dakin ta zauna gaban madubin ta jonata ta kunna ta hau busarda gashin tana kallon fuskarta dake wani irin blushing da qyalli ta cikin madubi, Tana gamawa ta gyara Kan ta daure ta shafa Neutrogena oil sai bodymist dasu spray ta qara da humra me sanyin qamshi ta miqe takoma jikin wardrobe ta bude Bata wani tsaya zabe ba ta dauko wani plain drylace peach ta saka riga da skirt ne saita fito Palo tana qoqarin nufar kicin akai Knocking ta nufi qofar ta bude, Cikin sa'a kuwa abinci ne anty zarah ta aiko musu Dan haka saita fasa aikin ta ajiye a dining ta Kama hanyar zuwa tadoshi aka Kuma knocking taje ta bude wani abincin ne daga umme itama ta karba duk ta hada ta ajiye a dining tana juyowa da nufin zuwa tadosa saigashi yafito shirye tsaf cikin wani milk yadi me tsananin taushin daya bayyanarda tsadarsa fili ya nufota Yana kallon kwalliyarta tareda nuna yabawarsa a fili Yana Mata kallon qasa qasa daya sanyata Jin kunya me tsanani sbd kallon ya qunshi yagama da saninta cikinta da wajenta ga sauke Kai daga kallonsa tana juyawa ya riqota ya dawo da ita gefensa suka nufi dining din Yana kallonta qasa qasa da wani irin murmushi harsai data gaji cikin muryar shagwaba tace" Dady Allah zantashi na tafi. Qaramar Daria Mara sauti ko kadan yadan saki Yana sauya kallonsa daga kanta yace" Ok sorry sorry na daina Zo Nan lemme feed you. Akan cinyarsa taci abincin tana bashi Yana Bata sai sake kashe Masa jiki takeyi da rashin zamanta guri daya ajikinsa daqyar dai aka gama cin abincin ya dauketa suka koma daki tana wani zille zillen daya qarasa juyar dashi daga MD ZABEERA. Qarfe goma sha daya harda kusan rabi suka fito tana riqeda hannunsa ta sauya wasu kayan sbd wani wankan datayi tayi simple makeup da wani irin hot red lipstick daya zauna daram Kan lips dinta dayaketa saukar hankalinsa Amma Dole ya dauke Kai suna shiga palon zarah ya saki hannunta ya nufi sama inda hafsatu tace musu tana can yatafi yabarta tana kallon hannunta daya saki domin zuwa ga wata wani rashin Jin Dadi ya taso ya rufe zuciyarta ta zauna Kan kujerun dake palon Ahankali tana Kiran sunayen Allah tareda kore shedan daga cikin Kai da tunaninta taji motsin saukowarsu ta daga Kai tana kallonsu hannuwansa duka biyun riqeda zarah din suna saukowa yanajin kamar ya daukota gaba dayanta ya sauko da ita sbd ganin yanda take tafiyar sbd tace Masa da ciwon qafafu ta kwana. Har Kan kujerar yakaita ta zauna Rana kallonsa cikin farin cikin kulawarsa gareta tace" Thank you MD. Murmushi me sanyi ya sakar Mata Yana zama kusada ita yace" Akwai godiya tsakanin miji da Mata ne? Dariya tayi tana kallon Amatu dake qaqalo murmushi tace" Amatu Yana tambaya tayani bashi amsa sbd zaifi ganewama idan Kika fada Masa Dan Naga yafi gane yarenki. Maganar ta daki zuciyarsu daga Amatun har shi Musamman shi ya tsura Mata idanuwansa yanajin wani irin yanayi me nauyi na rashin Jin Dadi wato tariga da ta amincewa kanta yafi son Amatu kokuwa yafi daukar Amatun da mahimmanci akanta ko me? Amatu ma Jin tayi nauyi da rashin Jin Dadi ya dabaibayeta take sbd maganar antyn Magana ce data fito dauke da raunin da zuciyarta ke ciki batareda tasani saitakejin sabon mutuncin antyn na sake shigarta koba komai haryanxu anty mutum ce me tsananin mutunci da ganin qimar Dan Adam duk wannan auren na bazata da akaiwa mijinta da qanwar data ke yiwa kallon uwa daya uba daya bai canzata zuwa wata daban hakama vai sauya kyawawan halayenta ba. Kallonta tayi taga cikin Yar dariya tai maganar bakin gskiyarta batasan tayi mgnar da wata manufa Abinda yake gskia ta fada Dan haka sai itama ta qirqiro murmushi cikin batar da zancen tace" Anty baya buqatan amsa yasan akwai godiya tsakani ma'aurata musamam ma keda kikeji da Rabin ranki godiya bakomai bace. Dariya anty zarah tayi tareda kallon Amatun tana jinjina sunan Wanda rabonta dataji tun zamansu asibiti jinyar Muhammad. Yanason fita Amma sbd yakira Dr Fatima yasa ya jira harsaida tazo ta duba zarah din ta tabbar Masa da bakomai bane duk cikin laulayin cikine sai nauyi da cikin zai Fara shiyasa Dan haka bayan fitar Dr Fatima fita yayi shima ita Kuma Amatun ta Dan jima kafin ta tafi sbd qafafun anty zarah din ciwo sukai Mata sosai Sai data Dan tattausa Mata su tasamu tayi bacci kafin ta fito Takoma tayi sallah ta kwanta tanajin bacci. Da daddare Takoma tasake dubo anty zarah din duk da ba wani Abu dake Mata ciwo kawai qafafun ne acan tabarosa tadawo Saida antyn tayi bacci yadawo sukai wanka suka kwanta. Washe gari zai bar sashenta yakoma na anty zarah Dan haka tun safen bai fita ko Ina ba suna Palo suna shiririta ita ala Dole saiya lallasheta yasata bacci kafin yatafi haka dai suka shiririce har sallar magriba tayi ya tafi. Zarah duk yanda tayi tunani da Shirin dauriyar abubuwan dazataita gani tareda daukarwa kanta alqawarin dangana tayi Shirin zaman hkr sai abin yazo Mata a baibai yabarta da mamaki sbd MD sauya Mata yayi daga MD ZABEERA zuwa asalin miji, Ya sauya ta bangarori dabam dabam, Babban mamakinta ayanxu shine zaman gida daya koya sosai yake zama agida wani lokacin Yana yini guda cikin zabeera bai fita ba Yana tareda iyalinsa ga yawan fara'a daya samu kansa aciki Abu daya datake maimaitawa shine Bata taba Tunanin ummanta datace Mata wata kishiryar kamar alheri ce sbd tana gyara maka mijin daka jima Yana wahalarda rayuwar aurenku hakama wasu yancin naki wata kishiyar itake kwato muku keda yayanki gurin miji ta hanyar sauyasa, Tabbas ta yadda da hakan, Akwai Abinda bazaka iyaba arayuwar zamantakewarka da mijinka sbd ka kashe zuciyarka Dan haka kodai duk wadda za'a auro kingama cutarta sbd kin sabawa mijin da yin shiru akan haqqinki Dan haka itama bawani dadinsa zataji ba kokuma kisamu wadda zata sauya mijin kisamu rayuwar dabaki samuba abaya, Kishiya ko wace iri kasamu ta gari ko akasinta tasan da akwai ciwo Amma dai duk da hakan tana jinjinawa Amatu sbd ta taimaketa tanan Dan ita dai daza'a barta saidai suyi rayuwarsu sugama ayadda suka Fara bazata iya yiwa MD hayaniya ko yunqurin sauyashiba sbd yafison rayuwar kadaicinsa kamar tafi Masa nutsuwa takega shiyasa batason shige Masa sosai. Abu dayane data lura dashi shine wen ever Amatu is around idanuwansa akanta suke sbd bazai iya Hana zuciyarsa Abinda takeso ba saidai Bata damuba sbd itama aduk lokacinda take kusa to hannuwansa bazasu iya zamaba sai acikin nata Koda Amatun na kusa Wanda hakan ya tabbatar Mata da tanada nata bangaren me mahimmanci a rayuwarsa. Anasa bangaren kuwa yasamu kwanciyar hankalinda baitaba samuba a rayuwarsa tun bayan rasuwar mahaifiyarsa tabarsa, Yasamu nutsuwar zuciya da rayuwa, Yasamu kwanciyar hankali data ruhi, Rayuwa cikin iyalin dakake matuqar so suke sonka tareda baka nutsuwa shine asalin Abinda baisaniba sai yanzu, Amatu ce takawo sauyi arayuwarsa da zuciyarsa Amma Kuma zarah ce abar jinjinawa kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwar dasuke sbd itace ta dauki komai da salama da dangana tareda sawa kanta nutsuwa batareda damuwa ko tashin hankali ba azaman Wanda yasa ake zaune kalau, Da Bata bada wannan gudunmawarba da duk yanda suka Kai ga tsananin son juna shida Amatu bazasu samu wannan kwanciyar hankalinba da nutsuwar zaman lafiya. Nuratu tazama tamkar aminiyarta yanzu sbd kusan kullum gurinta ma take yini hardai ranarda anty salamatu tazo gidan yini sukeyi fira USI ma da tintini yarinyar ta fice Masa arai sbd kusan itace silar komai tun Yana shareta har suka Fara sabawa sbd Amatu dakuma yaganta Dr salman dayake babban abokin shawarar USI dabaida amintaccen Dan uwa irinsa da hakan dai suka Fara sabo da ita sosai. Satinta hudu da tarewa tafara Shirin komawa sbd school karatunsu yadauki zafi Dole zata koma Dan haka duk sukabi suka wani sukukuce musamman ita dazata Koma ita kadai ko Muhammad gurin umme zaiyi zamansa daqyar ma dadynsa yabari Dan acan yaso sanyashi school Amma ummen ta toqa hakama shima Muhammad din yafison gurin ummen yanzu sbd tana sakaltashi da yawa gashi Kuma yaga Yana ganin dadynsa anan. Ita kanta anty zarah zatai kewar Amatun sbd sunyi sabon sabo duk da har abada zasu taba komawa yanda suke Ada ba Amma ko yanzu sunyi sabon shaquwarsu suna tsananin mutunta juna da gujewa Shiga haqqin juna. A gidansu ta yini Daren ranarda zata koma canma Saida tayiwa su iyami kukan barin gida kafin yazo da daddare ya dauketa suka koma gida. Washe gari Saida tayiwa kusan kowa dake cikin zabeera bankwana kafin suka wuce USI ne dakansa yakaisu airport suka wuce yadawo. Sbd son cire Mata damuwar data sanyawa ranta yasa Basu koma Greece ba direct suka nufa US. Wata irin rayuwar Jin Dadi da sakewa sukai a US tamkar turawan qasar Dan sai alokacin tasake sanin asalin waye MAHMOUD ZABEERA sbd wani bangarensa data gani na dabam wato Dan rayuwa. Duk yanda zatai rayuwa bazata manta wainnan kwanakin dasukai a US ba sbd ya shayar da ita soyayyarda har abada bazata barta ba, Ya sanyawa zuciyarta wani sabon maganadisun sonsa da qaunarsa. Kwanansu takwas suka tattara suka nufi gida saidai Kuma kamar karsu dawo tunda suka dawo tafara zuwa school kwana biyu shikenan ciwon zazzabin dare ya sanyota gaba sunyi yawon asibitin hardai aka tabbatar musu da ciki ne Dan haka ba wani magani haka suketa fama duk wani aikinsa ya ajiyesu jinyar matarsa yake cikeda kulawa da tsananin qauna. Ganin harya share kusan wata daya da rabi yasa ta daure ta bawa kanta qwarin ta nuna Masa ta warke sarai kafin yafara maganar komawa sbd tarin ayyuka da Kiran dayaketa faman Sha dazai tafi ita dakanta takaisa airport suka fito motar ya kamo hannunta ya matso da ita cikinsa Yana kallonta da fararen idanuwansa dake bayyana newarta tun kafin ya tafi ya bude baki ahankali Yana shafo cikinta cikin laushin murya yace" I will miss you wife. Dan dago qafarta tayi sbd yafita tsayi takai bakinta Kan nasa ta Dora ahankali ta zura Harshenta tabashi wani irin kiss tana kallon cikin idanuwansa tace" I will miss you More. Rungumeta yayi tareda sauke ajiyar zuciya Yana shafa Bayanta yace" I love you. Qanqamesa tayi kalmarsa na sake kashe jikinta. Sun jima ahakan kafin lokacin tafiyarsu yayi yabata kiss a goshi ya wuce tana kallonsa harya shige ta juya jiki amace ta shiga mota tabar airport din tana Jin kewarsa kamar tabisa. ##Mamuh# ZAFAFA BIYAR 2021 Hafsat miss xoxo🥰 KIBIYAR AJALI......!    (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗        Mamu gee🥰 MIN ƘALB!!😋🤗     Hafsat rano🥰 ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗     Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗      Bilyn Abdull🥰 SARAN ƁOYE🤗😋   Duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO 0812652655 ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO BANK NAME: ACCESS BANK. saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇  09033181070 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻. 6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 50_* https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg Please subscribe to our YouTube channel 👆👆👆 Tana komawa gida kwantawa tayi tun anan Palo tana waya da anty salamatu akan maganar zuwan datakeson tayi suna gamawa anan palon bacci ya dauketa. Bacci me nauyi tayi sai kusan yamma ta farka ta tashi zaune tana Dan dafe kanta dayayi Mata nauyi sbd baccin datai dakuma Dan ciwon dayake Mata. Miqewa tayi ta nufi daki Kai tsaye toilet ta wuce tayo wanka dan jikinta yasaki tayo alwala tafito ta sanya riga da wando me Fadi ta sanya dogon hijab tahau dadduma ta tayarda sallah. Bayan tagama sallar kicin taje ta hado tea da biscuits tazo ta zauna Tasha tana kallon agogo tasan zuwa yanzu ya Isa sauka Amma bazata kiraba zata Bari idan yahuta yasamu lokaci zai kirata. Washe gari da wuri ta wuce school sbd akwai asibitin dazasuje daga school din, Tunda safe shine ya tayarda ita daga bacci suketa waya Saida zata Shiga wanka suka aje tana Shirin fitowa yasake kiranta harta Isa school suna waya har Anty zarah yabata suka gaisa tayi Mata ya jiki daga Nan daqyar tasamu yayi hanging wayar ta maida hankali Kan Abinda yakawota, Sai yamma likis ta dawo gida amatuqar gajiye Dan haka ko abinci Bata tsaya Ci ba wanka tayi ta kwanta baccin gajiya da daddare data tashi bayan tayi komai tasake komawa ta kwanta suna waya ta rikice Masa akan sai anturo Mata anty salamatu wlh bazata iya rayuwa ita kadaiba. Dole ya amince wa buqatarta yaje yasamu kawu da kansa yayi Masa roqon zuwan anty salamatun wannan karon hadda iyami ya roqa taje tadubota tunda batada lafiya zataji dadin ganinta sosai. Kawun bedai cemasa ya amince da zuwan iyaminba tukuna Amma dai ita salamatun zataje itama bazata jimaba sbd maganar neman aurenta da Andi ya nemawa alhaji qarami Wanda yake autansu Modibbo basason doguwar bidia kamar a taqaice suke son ayi auren. Da kansa yasa akawa anty salamatun shirye shiryen tafiya sbd kusan shima a matse yake dataje din yasamu me kula Masa da Amatun Dan gabaki daya hankalinsa ba'a natse yakeba Jin yake kamar yaje da kansa yayi jinyar abarsa Amma Kuma ayanzu zarah dake kusan haihuwa tafi buqatarsa shiyasa ma duk wasu tafiye tafiyensa ya rage saita haihu sbd Bata kulawar datake buqata. Duk yanda yaso anty salamatu ta Isa cikin kwanaki qalilan bai yiyuba sai bayan sati biyu da maganar ta tafi tareda USI dazaiyi 6month program acan aikuwa Nan suka dasa sabuwar rayuwa a Greece hakan kuwa ba qaramin nutsuwa yabawa MD din ba Dan dama shineya tsayawa USI akan zuwa Greece din yin program dinsa acan infact ma shine yadauki nauyin komai sbd kawai Amatun tasamu Yan uwanta atareda ita hakan ne kawai zai bashi cikakkiyar nutsuwa sbd yanayin datake ciki. Zaman USI agarin tareda zuwan anty salamatu ya kawarda duk wata damuwarta da rage Mata kewarsa sosai Dan haka saita kwantarda hankalinta take karatunta cikin kwanciyar hankali da bada himma musamman yanzu da cikinta yafara girma Dan kusan wata hudu cikin na biyar kenan ita Kuma zarah ayanzu tana gab da shiga cikin watan haihuwarta shiyasa Koda yazo gurinsu bai wani dadeba yakoma yasake barinta cikin sabuwar kewarsa Dan har wata qaramar tafiya sukai dayazo din. Zaune suke apalo tana duba wasu textbook na school anty salamatu Kuma tana yanka Mata gwaibar data siyo daga wani superstore ahanayarta ta dawowa school suna Dan fira sama sama sbd Rabin hankalinta nakan books din wayarta tayi ringing tun daga Kan kalar ringtone din tasan waye me Kiran ta Kai hannu ta dauki wayar tana sake wata qaramar ajiyar zuciyar son mijin nata ta daga cikin kasalalliyar murya tace" AMATULLAH's husband.. Duk da Yana cikin wani yanayi na damuwa Saida yadan murmusa hartaji sautin murmushin ta cikin wayar ahankali tace" Barka da yamma. Barka wife, Hw are you and my baby? Ya anty salamatu hope duk Kuna lafiya? Yes lafiyanmu kalau it's just that we're missing you badly. Numfashi ya sauke Wanda yasata Dan gyara zama tana ajiye books din jikinta cikin sauti me nutsuwa tace" Lafiya kuwa? You sound worried. Dafe goshinsa yayi cikin yanayi na damuwa yace" Zarah na asibiti tun safe she can't deliver by her self itama aiki za'a yi Mata. Faduwa gabanta yayi cikin tsoro da damuwar itama zatazo wajen ga tausayin anty zarah din sai jikinta yayi sanyi da rawar murya tace" Yanxu tun cikin dare anty zarah take cikin wannan halin Amma baka fadaminba dady sai yanxu? Wlh na tausaya Mata yanxu kenan suna ZABEERA specialist? Yes yau sukeson ayi aikin sbd qarfinta harya qare nagaji da ganinta cikin wannan halin. Kwantar da murya tayi cikin tausayawa anty zarah din da tausayinsa shi kansa sbd tana iya Jin irin damuwar dayake ciki a muryarsa tafara qoqarin kwantar Masa da hankali tana sake bashi qwarin gwiwa akan Allah yasa ayi aikin lafiya akuma dace. Bayan sungama waya tana fadawa anty salamatu tana lalubo numbern umman zarah din ta Danna kiranta, Tana dauka ta gaidata cikin ladabi ta Dora da cewa'' Umma Ashe anty zarah haihuwar tazo wlh bansaniba sai yanzu dady yake fadamin tun safe Kuna asibiti. Amatu antynki Kam tanajin jiki kitayata da addua Allah yarabasu da bbyn lafiya. Inshallah Allah lafiya kalau zasu rabu Allah yasa ayi aikin cikin sa'a Nasan bazata iya mgn yanzu ba Ina Mata sannu zuwa anjima zansake Kira naji Inshallah. Shikenan Amatu angode Allah yayi albarka. Amin umma ngd sai anjima. Aje wayar tayi tana kasa cigaba da karatun ta shiga damuwa da tunani tasake Kiran MD din takuma kwantar Masa da hankali. Haka Takoma sukuku tunda sukai Magana takasa sukuni sbd hadda tsoro tsoron zuwan tata haihuwar yake sake shigarta takasa zama sai kiransu takeyi akai akai tana tambaya har lokacinda aka shiga aikin da zarah Amatun kiransa takeyi tana Kiran umman zarah din harsaida umman tace Mata" Amatu ki kwantarda hankalinki tunda kema bake kadaiceba kada ki daga hankalinki wata matsalar ta taso Kuma ku rabawa mijinku hankali Kashi biyu. Ana fitowa sallar magriba aka fito da lafiyayyan jaririn zarah cikin qoshin lfy sai kuka yakeyi cikin qoshin lfy aka wuce dashi sukai duk aune unen dasuke buqata kafin aka shiryasa cikin fararen overall masu kauri nurse ta fito dashi fuskarta daukeda murmushi ta nufo inda MAHMOUD yake tareda mahaifinsa Modibbo daya iso asibitin alokacin tareda umme da Haj maryam. Modibbo aka miqawashi ya karbesa cikin farin cikin ganin jikinsa 'da na farko ga MAHMOUD dinsa. Addua yayiwa jaririn kafin ya miqawa MAHMOUD da idanuwansa suke Kan fuskar yaron Wanda tunda nurse tafito dashi kafin yashigo hannunsa zuciyarsa tagama cika da soyayyar 'dansa. Zarah tabasa farin cikin rayuwarsa, Ada baidamu da samun 'dan kansaba Amma tun Bayan haihuwar Muhammad zuciyarsa ta cika dason Tara zuriar me yawa kodan ya Gina tashi zuriar sbd fita rayuwar kadaici. Addua yayiwa yaron tareda Masa huduba yakirasa da sunan Muhammad DAHEER Modibbo. Godiya Modibbon yayi cikin Jin dadin takwaran da akai Masa. Nan kowa yafara karban yaron ana Yaba kyawunsa da kamannin babansa daya Dan dauko. Saida aka gama murnan samun Modibbo aka koma murnar samun nasarar aikin da akayi umman zarah kuwa farin cikinta a bayyane yake ganin yanda kowa ke murnar haihuwar 'yarta. Babban tashin hankalin dasuka shiga na samun mugun labari daga bakin likitoci shine ba lallai zarah din tasake haihuwa ba sbd rashin qwarin mahaifarta data fashe kafin Cs din. Hankalin ummanta yatashi sosai hakama da duk Wanda yake gurin Saida jikinsu yayi sanyi Amma ganin MAHMOUD dakansa ya dauki qaddarar ya dauki juriya yasa kowa ya hkr suka buge da tarairayar zarah wadda tayi kukan wannan mugun labarin MAHMOUD na aikin lallashinta cikin nuna Mata tsananin damuwarsa Dole qarshe ta dangana tabarwa Allah akan hakan shine qila mafi alkhairi. Amatu data sake Kira kusan karo na biyar kenan bayan haihuwar sai yanzu tasamu damar Magana da anty zarah din Tai Mata barka tana sake Mata sannu daga Nan suka Dan gaggaisa da jamaar dake asibitin ta kashe wayarta. Kallon babynta takeyi idanuwanta na cikowa da hawayen farin ciki Dana damuwa taji an zauna gefenta tareda zagayeta da hannunsa har ita har Modibbon Yana kallon Modibbo dake baccinsa cikin nutsuwa ya shafa fuskarsa tareda maido kallonsa Kan fuskarta Yana riqo hannunta cikin kulawa da nutsuwa yace" Zarah ki daina damuwa akan Abinda ba Allah ne yafadaba, Banson Baki empty hopes Amma Dan ance bazaki sake haihuwa ba ba lallai bazaki sake haihuwar ba sbd ba fadan Allah bane ki dauki qaddara ki rungumeta Allah nason bayinsa masu yadda da qaddara. Dago jajayen idanuwanta dake tsiyayar ruwan hawaye tayi ta kallesa cikin tunani daban daban Wanda ya kunshi irin hope din data hangowa kanta na samun soyayyarsa ta hanyar Tara zuria me albarka dashi sbd gano burinsa da qaunarsa tason Tara Yara. Kamar yasan Abinda take Tunani ta ganin irin kallon datake Masa ya rungumeta ahankali tareda shafa Bayanta cikin murya me taushi yace" Zarah yanzu ke ba matata ce kawaiba ke uwar 'yayana ce, Ayanzu kin riga kinzama wani sashe na rayuwata da zuciyata, Samun haihuwa a tsakani wani alamarine me girma Dan kuwa kinriga kinzama tamkar jagoran zuriar dazan Tara a gaba ko ba naki yayanba, A da ke zarah ce matar MAHMOUD yanzu Kuma ke zarah ce matar MAHMOUD uwargidansa Kuma uwar Dan haka ki cire kowane irin tsoro ne kikasa acikin ranki sbd mi MAHMOUD DAHEER ZABEERA Ina baki tabbacin mutuwace kawai zata cireki daga rayuwata. Wani irin kuka tasaki tana sake qanqamesa zuciyarta na cika da farin ciki da nutsuwar zancensa.... Ahaka ummanta tashigo tagansu Dadi yasake kamata ta karba Modibbon ta fita dashi sbd su iyami dasu maman junior dasukazo ganinsa. Kwanansu shida a asibitin aka sallamesu suka dawo gida inda kowa keta zuwa barka da farko gida taso komawa MAHMOUD din yace tazauna a gidanta bayason zuwanta ko Ina. Amatu kullum tana kiransu Jin takeyi kamar tazo Amma Babu dama Dole saidai take ganinsu ta hotuna shikansa MAHMOUD din bataga alamar zai barta tabiyo hanyar zuwaba sbd ko school yanzu ya hanata tuqi da kanta anty salamatu ke kaita wani lokacin Kuma USI idan yanada time kenan sbd akusa da street dinsu yakama apartment yake zaune. Ranar data Fara Masa maganar tanason zuwa Kai tsaye yace" No,Babu inda Zan iya Bari kije until you deliver. Dama tasan haka zai fada Dan haka Bata wani damuba ta bar zancen ta maida hankali Kan rainon cikinta da karatunta ta bangare daya ga MAHMOUD din dayanzu wani soyayya yakeji kodan itama lokacin haihuwarta ya matso ne Amma sam yanzu ko barinta bayayi ta sarara akan Kiran wayarsa. Bayan sunan Modibbo da sati uku yayi daidai da Gama exams dinsu tana gida kwana biyu Babu inda take fita ga nauyin cikinta ya dameta ma gabaki daya. Zaune take ita kadaice agidan anty salamatu sunfita da USI siyayyar wasu daga cikin kayansa na lefe dayake siya tun anan sbd Shi da Nuratu sungama daidaicewa tsakaninsu yana dawowa yakeson ayi idan son samunsanema to ahade aurensu danasu anty salamatu sbd dagashi har nuratun kamar zasu cinye juna sbd soyayya shiyasa itama yanzu nuratun kamar ta hadiye Amatu sbd qauna Dan sai yanzu take qara sanin mahimmanci Amatu agurin USI da irin tsananin qaunar junansu dake tsakaninsu. Kallon wani tv program na likitoci takeyi a CWTv hankalinta rabi nakan waya sbd tun safe take kiran wayarsa Bata shiga Kuma shima tun Daren jiyan raban daya kirata. Sake Danna kiransa tayi akaro ba adadi still Bata shiga tana qoqarin sake Kira taji ana qoqarin bude qofarsu ta shigowa ta juyo tana kallon qofar da waya a hannunta sukai Ido biyu itada shi ta Dan zaro Ido tana kallonsa tareda miqewa tsaye komai nata na bayyanarda mamakin ganinsa shikuwa kallonta yakeyi cikin kewa da soyayyarta ya tsaida kallonsa Kan cikinta dayayi girma cikin wata free doguwar rigar masu ciki data saka wadda batakai qasa ba sbd kada ta takurata ya ware Mata hannu Yana kallon fuskarta daukeda boyayyan murmushi da gudun dabatasan zata iyaba tayo kansa ta fada jikinsa ya rungumeta Yana Dan dagata sama cikin farin ciki da murna tace" I love this surprise of urs Husband. Sauketa yayi tareda Kama hannunta suka qarasa shigowa taso karban luggage dinsa ya hanata suka nufi dakinsa tafara gyarawa Yana tayata suka gyara dakin duk da Babu Abinda yayi 'yar qurace kawai. Wanka yashiga ta fita zuwa kicin hada Masa abincin dazaici. Cikin farin ciki tafara dafa Masa pasta da carrots sai beef meat ta hado Masa Kan tray takawo Masa har bedroom dinsa yaci tana zaune tanata tambayarsu Modibbo Wanda kamar ubansu daya da Muhammad sbd suna dibar kamanni. Yana gamawa ta kwashe kayan ta maida ta dawo ta zauna Kan cinyarsa tana sake tambayarsa meyasa be fada Mata zaizoba. Fuskarsa ya Dora kan tata Yana sauke ajiyar zuciya a boye yana kallon cikin idanuwanta da itama shi take kallo ya Dora hannuwansa Kan cinyoyinta Yana shafawa cikin malalacin sauti yace" Sbd inason ganin farin cikin bazata a kyakkyawan fuskan matana. Murmushin Jin Dadi tasaki tana sake shigewa jikinsa ahankali tana qara cukuikuyesa qasa qasa da murya tace" Ko acikin barci MAHMOUD ZABEERA yazomin farin cikina bayyananne ne bare ganinka a zahiri so lovely husband zuwan bazatanka ya tafi da zuciyan AMATULLAH K. sake matsota yayi cikin jikinsa Yana shaqar qamshin jikinta ya shaqi numfashinta dake sauka Kan fuskarsa sbd matsuwar dasukai da juna ya Dora bakinsa Kan nata Yafara kissing dinta Yana zame hannuwansa zuwa wuyan rigarta. Koda anty salamatu suka dawo da daddare guraren 9 Bata tareda wata gajiya sosai sbd sun Dan bibbiya guraren hutawa sun shaqata bataga Amatun ba a apalo ta shige da kayan zuwa dakin Amatun inda sauran kayan lefen suke Nan na Bata ganta ba sai tayi tunanin toilet Dan haka dakinta Takoma ta fada toilet itama tayo alwala tazo ta tayarda sallah. Jin shiru shiru ba motsin Amatu yasata fitowa tana zuwa kicin ta duba ko tana can, Ganin anyi sabon girki a kicin din yasata bubbudewa tana dubawa tafito Palo ta nufa dining tana ganin plates da kayan da akai amfani dasu ta fahimci oga kwata kwata ya taho kenan ta fito kicin tana kallon hanyar zuwa dakinsa tasake tabbatarda shi dinne yazo ta wucewa daki tana cewa'' Naji dadin zuwanka nasamu yanzu nabi usi next week idan zaije gida. Washe gari tana kwance cikin jikinsa tana bacci cikin nutsuwa sbd irin kyakkyawar rungumar da yayi Mata suna bacci cikin baccin tafara Jin kamar ciwo ciwon Mara na damunta Wanda yasata bude idanuwanta tana sake saurarawa Abinda takejin saitaji da gaske ciwon yake ta yunqura zata tashi zaune yabude idanuwansa Yana kallonta ta yunqura ta tashi zaune ya tashi shima Yana riqota yace" Lafiya kuwa? Kallonsa tayi da sauri tana dafe qasan cikinta a Dan tsorace tace'' Ina ganin labour ne..... kasa qarasawa tayi cikin tsananin azaba da firgici tace" Hospital hospital hospital take me" duk arude take maganar a jujjuye batareda tasaniba Ganin hakan ya sauko gadon ya nufi wardrobe ya dauko shirt da wando yasaka cikin sauri tareda dawowa ya dauko Mata riga kamata ya sanya Mata suka fito tana sake dafe cikinta cikin azaba tana Kiran sunan Allah Dana MAHMOUD din cikin ciwo. Jin dogon salati da qarfi yasa anty salamatu fitowa daidai qarasowarsu tsakiyar palon a Dan rude ta kallesu tana maida kallonta Kan Amatun daketa faman salati ba qaqqautawa cikin mamaki tace" Subhanallah haihuwar ce ko me? Lafiya kuwa? Muje asibiti"kawai ya iya furtawa anty salamatun Yana nufar qofa da matarsa. A gigice suka Isa asibiti musamman da ciwon ya taso Mata gabaki daya suna Isa ruwan haihuwa na fashewa akai labor room da ita. Zama yayi Kan kujerun jira Yana kashe wayarsa sbd baya buqatan ko hayaniyar ringing waya. Suna zaune saiga USI shima ya iso Nan suka Fara zaman jigum jigum cikin zullumi da fargaba, Wannan zaman jiran dayakeyi yau yana daya daga cikin ranakun tsananinsa na rayuwa sbd gabaki daya Jin yake kamar nutsuwarsa zata bar jikinsa Amma haka dai yake zaune shiru kamar ba Wanda ke cikin tension ba. USI da anty salamatu ne ke samun damar waya da Yan gida sunajin yaya kota haihune? Zaman awa uku sukayi cikin ta hudu kafin Allah yabata ikon haihuwar baby girl lafiyayya da ita saidai ba qatuwa bace sosai sai kuka takeyi aka shiryata aka miqowa familynta ita ya karbeta Yana kallonta cikin wata irin nutsatsiyar sonta da qaunarta ya shafa Dan qaramin kumatunta Yana Mata adduoi da murmushi akan fuskarsa yace" De symbol of my love FADIMATU ZARAH MAHMOUD ZABEERA. Aikuwa cikin farin ciki anty salamatu itama ta karbi babyn tana kallon fuskarta cikeda murna tace" MAHMOUD wannan 'ya da yayunta take Kama. Murmushi kawai yasaki zuciyarsa na sake wanzuwa da farin ciki sai alokacin ya bude wayarsa da atake Kira suka Fara shigowa ya fice Yana amsawa. Yana dawowa ya tararda anfito da Amatun ankaita dakin hutawa ya shigo Yana aika Mata da wani irin kallon samun nutsuwa ya qarasa bakin gadonta ya zauna tareda Dan rungumota yabata kiss agoshi yace" Thank you. Murmushi tasaki tana Dan harararsa tace" Bazan qaraba daga wannan. Dariya maganar tabawa anty salamatu takuwa ringa qyaqyata dariyarta shikuma wani guntun murmushi ya sake Yana sake kissing hannunta dake cikin nasa batareda yace komaiba. Acan Nigeria kuwa cikin both families din haihuwar ta Isa kunnen kowa akaita Sanya alkhairi da yiwa FADIMATU ZARAH adduar Allah ya raya Akan sunna, Zarah da akaiwa takwara kuwa rasa abin cewa tayi sbd farin ciki shiyasa ma tace zatazo taga takwara da kanta. Kwananta daya a asibitin suka sallamota suka dawo gida Nan anty salamatu tayita hidima dasu ganin suna hutu Kuma gashi umme da zarah hadda Nuratu since zasuzo yasa ya yanke shawarar su dawo gida bayan ko 30days ne saita dawo. Kwana biyar da haihuwar suka dawo Nigeria Nan aka kacame da sabuwar murnar zuwansu 'yan barka suka Fara sintiti musamman aminanta su maman junior da kullum saisun Zo iyami ma kwana biyu ta jera tana zuwa Saida akai suna tukuna suka samu sauqin baqi sai alokacin tafara samun kanta. Yau satinsu uku da zuwa tuni tafara Shirin komawa musamman ganin yanda ogan yafara shishige Mata tanason Takoma tasamu matakin dauka kafin wani abun yasake Shiga sbd taga alamar son dawowa bakin aiki yake. Ana gobe zata koma tafito palonta zuwa sashen anty zarah saigasu taci karo dasu sunfito itada MAHMOUD din Yana daukeda Modibbo hannunsa daya Kuma Yana riqedana ZARAn sunci ado cikin traditional attire sai murmushi suke ta qaraso suka hade tana murmushi ta gaida anty zarah tana cewa'' Fita zakuyi? Eh Amma ba dadewa zanyi ba gurin umma zai ajeni. Ok to adawo lfy Ina gaida umman bansamu nazo nayi Mata bankwana ba. Kallonsa tayi shima tana sauya kalar murmushinta zuwa na neman mgn tace" Take care. Fuskar fadimah ya shafa Yana gyada Kai. Suna wucewa Takoma ciki taqarasa sauran parking din da bataiba. Washe gari anty zarah ce takaisu airport suka wuce dagacan ta wuce gidansu gurin ummah. Bayan dawowarsu Greece da sati biyu yakoma bayan sun dauki me aiki da Nanny hakan saiya taimaka Mata sosai sbd samun damar maida hankali ga karatunta. Rayuwa ahankali tafara sauri fadimah tayi wayo sosai tana cikin final exams dinta ta fahimci tanada wani cikin hankalinta yatashi sbd fadimah Bata Isa yayeba Dan haka taso cire cikin saigashi kamar Wanda aka fadawa yayi Mata zuwan bazata cikin sa'a kuwa kafin yatafi Saida yasanda zaman cikin Wanda yasama ya daga komawarsa yaqara kwanaki Saida tagama exams dinta akai duk wata hidimar daza'a yi ta karbi takardunta suka dawo Nigeria sbd shagulgulan bikinsu USI da aka Fara Wanda aka hade danasu anty salamatu Dan haka biki sosai akeyi a zabeera Koda ta iso ta fada cikin hidimar gadan gadan sbd dama amatse ake ta iso sbd wasu abubuwan da akeson gudanarwa Wanda suke buqatar kasantuwarta bikin USInta guda dakuma antynta anty salamatu. Ranar asabar aka gama bikin amare kowacce ta tare gidanta Anty salamatu zabeera ita Kuma Nuratu cikin sabon qaton sabon gidanta da USI ya Gina musu Wanda zasu zauna tareda iyayensa. Ana kammala bikin ta yaye fadimah wadda anty zarah ce ta hadasu ya yaye tareda Modibbo takwashesu suka koma gurin umma tace sunyi yayen acan. Ganin zarah batanan dazaiyi tafiya saitace zata bisa takuwa shirya tabisa suka tafi sudan. Satinsu biyu suka dawo anty zarah ta karba miji daganan zaman ya Dore ahaka cikin kwanciyar hankali ba hayaniya sbd kowacce ta shafawa kanta lafiya sbd fitinar wani lokacin Hana komaima takeyi a tsaya guri daya akasa gaba akasa baya. Lokacin haihuwarta nayi ta haifi baby boy aka saka Masa sunan kawu suna kiransa ABBA bayan haihuwarta da wata shida anty salamatu ta haihu a hannunta a asibitinsu wadda MAHMOUD yasake sauya Mata tsari da girma tafara aiki tun bayan haihuwar ABBA shiyasa itacema ta karba haihuwar antu salamatun data samu BBY girl itama bayan sunan anty salamatu da sati biyu Nuratu ta haihu itama a hannunta tasamu Me sunan kawu DR USMAN K SALEH yasawa babyn. Fadimah a hannun anty zarah take Dan haka ita ABBA ne kawai agabanta Muhammad ma tuni yafara zama saurayi Yana gurin Rabin ransa umme wadda takejinsa fiyeda sauran 'yayanta Dan haka Babu me tabasa. Shima ABBA Yana Isa yaye iyami ce tayi yayensa Nan MD yasata gaba akan sabon baby yakeso tanajin yafara fadar haka taso daga hankalinta Saida anty zarah Tai Mata waazin damace Allah yabata tayi haihuwar ta huta tunda gashi ita tanaso Allah be Bata ba. Kallonsa tayi lokacinda tafito daga toilet daureda qaramin towel da ko Gama rufeta baiyiba ta qaraso inda yake zaune Yana aiki da laptop ta zauna Kan cinyarsa tana tanayi kamar zata saki towel din ta marairaice murya tace" Positive. Dagowa yayi Yana kallonta da fararen idanuwansa Yana Mata kallon are you serious? Daga Masa Kai tayi yayi saurin rungumeta Yana zura hannu cikin towel dinta Yana cewa'' Thank you love. ##Mamuh# ALHAMDULILLAH. Da yardar Allah anan mukazo qarshen wanann littafin namu me suna MIN QALB wato DAGA ZUCIYA, IDAN NAYI MANTUWAR WANI ABUN DABAN QARASA FADABA A LABARIN KUMIN UZURI KU DAUKESA AMATSAYIN AJIZANZI IRIN NA DAN ADAM. INA ROQON ALLAH YABAMU IKON AMFANI DA ABIN ALKHAIRIN DAYAKE CIKI SABANINSA KUMA ALLAH YA MANTAR DAMU YAKUMA YAFE MANA, AKWAI WAINDA TUN BAAZO QARSHE BA SUNA MAGANAR DANGINSU AMATU DA USI, ANSAN KOWA BA DAGA SAMA YAFADO DUNIYA BA AMMA KADA KU MANTA AKWAI MARAYUNDA ADUNIYA HARSU BARTA BASUSAN ASALINSUBA BARE DANGINSU, AKWAI WAINDA SUKE RAYUWA BATAREDA SUNSAN ASALINSUBA KO INDA SUKA FITO AMMA SAI ALLAH YABASU IKON GINA TASU RAYUWAR SU GINA ZURIAR KANSU DAN HAKA KU SANYA SU AMATU AKAN MASU IRIN WANNAN QADDARAR SBD A DUNIYA BAKOMAI KAKE SAMUBA. ALLAH YA GAFARTAMANA AMIN. ZAFAFA BIYAR 2021 Hafsat miss xoxo🥰 KIBIYAR AJALI......!    (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗        Mamu gee🥰 MIN ƘALB!!😋🤗     Hafsat rano🥰 ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗     Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗      Bilyn Abdull🥰 SARAN ƁOYE🤗😋   Duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO 0812652655 ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO BANK NAME: ACCESS BANK. saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇  09033181070 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍