Idan zuciya ta gyaru 1-01 Posted by ANaM Dorayi on 07:28 AM, 27-Jan-16 Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU ______________Na ______Fauziyya D Sulaima 19/81992. "Chalo! Chalo! Chalo!" Zazzakar muryar hatsabibiyar yarinyar ta fadi, ko ba'ayi bayani ba kasan abinda kalmar chalo take nufi, wato tsokanar fada ne da 'yan wani layi ke yiwa wani layin, ko 'yan wata unguwa zuwa wata unguwar. Jama'ar dake gefen hanya masu saida rake zuwa goba, da yalo da doya suka fara hada kayansu, daya daga cikin su ke fadin, "Kowa ya hada kayansa don shegiyar yarinyar nan tun da ta ambaci wannan kalmar ta chalo, to kuwa wanda yayi sakaci zai yi a..." maganarsa ta tsaya tsak dai-dai lokacin da ya hango zugarsu sun nufo su da gudu, sun biyo wasu, ya suri farantinsa wanda aci bal-bal ke tsakiya na kifi, suma 'yan uwansa suka rufa masa baya kowa na neman inda zai adana kayansa. "Chalo! Chalo! Chalo!!!" Muryar zugar yaran dake biye da Abu suka cigaba da fadi suna biye da 'yan uwansu wadanda suka biyo, sukuwa yaran da aka biyo sai kuma kara gudu suke yi, domin kada a badesu da barkonon tsohuwar da su Abu ke wulwulawa. Toka ce ake hadata da citta da barkono a dake sai a kulle ta a leda a sanya dutse a tsakiya a sanya zare a dinga wulwula ta, idan aka cillata daga nesa sai ta fashe kamar an cillah tiyagas (barkonon tsohuwa), duk mutumin da ke harabar gurin sai yayi tari ko ya shide, idan kuwa akaci karo da mai cutar (ASMA) kuwa sai ta tashi. "A cilla- A cilla." Muryar Abu ta kuma futowa tana baiwa abokan ta umurni kenan, dan ganin yaran da suka biyo sunyi musu nisa, ai kuwa babu bata lokaci suka hau cillah kullinan tokar dake hannun nasu ji kake tush! tush! tush! Tana fashewa a tsakiyar yaran dake neman tsira daga farmakin su Abu, wadanda Allah ya taimaka sun tsere wadanda kuma keda rabon shan wuya tokar ta fashe a tsakiyar su don haka suka fara tari da atishawa, hatta mutanen dake makota dasu suma sun hau atishawa, balle maza dake zaune a kofar gidaje ana hira duk suma sun hau atishawa. Su kuwa su Abu dariya suka sanya gami da ihu suna fadin "Eye! Eye! Eye! Munci gari ba namu ba, munci gari ba namu ba- munci gari ba namu ba, munzo gidansu mun cisu" Wani mai kanti dake kokarin zuba kananzir dai-dai lokacin da abun ya fashe, ya shide kalanzir din ya zube a kasa ya hasala don haka ya shiga shagonshi da sauri yana atishawa ya dauko dorina yayi kansu yana fadin "Shegun yara masu kama da iblisai ba a sati guda baku bada mana wannan jarabar ba, wallahi yau duk wanda na kama sai na fasa masa jikinsa da dorinar nan" Yayi kansu da gudu, Abu ta fara hangoshi don haka ta kuma fasa ihu tana fadin "Kowa yayi ta kansa! Nima nayi ta kaina, kowa ya guje dai, nima na guje dai, kowa yayi ta kansa." Ko batayi bayani ba sun san abunda take nufi, wato wani ya taho zai doke su don haka kowa ya gudu, wai ai kuwa sai suka kama gudu mai kantin nan ya bisu da wasu samari biyu, da suma ke cin abinci aka bude su su da abincin da kura, basuyi nasarar kama ko daya ba domin yaran sun fisu gudu tamkar barewu don daman sun san za'a biyo su. Don sun saba duk randa aka yi biki ko suna a gidan wasu aka kai musu cingam din fati akube-kube sai anyi fada, don haka iyaye da yawa ke hana 'ya'yansu zuwa akube-kube (fati), yauma haka dince ta faru domin 'yan layinsu Abu (Hatsabibiya ce) ta gayyaci akube-kube (fati) tofa shine wani dan bayan layin nasu ya warcewa 'yar layin.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 yauma haka dince ta faru domin 'yar layinsu Abu (hatsabibiya ce) ta gayyaci akube-kube (fati) tofa shine wani dan bayan layin nasu ya warcewa 'yar layin su kwanonta na akube-kube lokacin da suke tsaka da rera wakar akube-kube sai walo, munje mun dawo sai walo, sannunku da zuwa sai walo, ga kwanan fati sai walo. Tofa shine Abu tace a futo da kwanon suka kiya shine fa fada ya harke ana ta karawa sannan aka bada oda a dauko bom, shine fa aka biyo 'yan bayan layi. A bakin wata makarantar boko suka dinga zubewa suna haki don sun san sun tserewa wadanda suka biyo su. Sai tillikar dariya sukeyi suna mai da yanda akayi. Abu ta fito da kifi a hannunta soyayye tace, banzaye nifa mai kifin nan da yake gudu sai dana suri kifi daya wanda ya fado, nan fa kowa yayi karaf yace raba dai-dai (wato wata sarace ake kullawa idan kuka kulla raba dai-dai to da kaga mutum yana cin abu idan ka riga shi fadin raba dai-dai to sai ya raba biyu ya baka idan shima yaga kana ci yace maka haka to sai ka bashi kaima, idan kuma mai cin abin ne ya riga fadin bazai bada ba). Abu ta sha kunu tace "Dallacan wa zan baiwa wa zan hana" Ta bare ta cire kayar ta lunkuma a bakinta tana muzurai, kowa ya tsaya yana kallonta don dai ita masifaffiyace tsoronta ake ji, wani yaro ne a cikinsu yayi karfin hali yace "Gaskiya mu kwance ke Abun nan." Ya mika mata hannu "Idan kece kika ga mutum yana ci kika ce raba dai-dai idan bai baki ba warta kike yi, amma idan kece sai kiki badawa." Ta cire dankwalinta taci dammara dashi tace "Anyi din, duk wanda ya isa ya kwata wallahi" Habu yace "Banza ai ba tsoronki ake ji ba, daga yau mun kwance nima." "La-la-la, ni kake zagi wallahi ba zan yadda ba." Ta danki kasa a hannu biyu ta matsa gabansa tace "Gata tsiya gata arziki." Ya tankwabe ta tsiyar ai kuwa sai ta rarumeshi, nan fa dambe ya kaure sauran yaran suka rude da ihu eyeh-eyeh-eyeh, sannu suna musu wata waka, "Ku chasu arna ku chasu, ku chasu ba mai raba ku, wanda ya raba su shi yayi barna, kai ku chasu arna ku chasu, ku chasu ba mai rabaku." Su kuma tamkar ana kara zugasu sai dambe suke yi, da yake Abu 'yar dama-dama ce mai kiba gata da karfi da karfin zuciya ta daga Habu ta naka shi da kasa, aka kuma rudewa da ihu da kyar aka janye ta daga kanshi tana fadin "Wallahi da kun barni yau da sai na chas-chas karashi." Shi kuwa ihun da ake masa ya sanya ya fashe da kuka yayi hanyar gida, suma saura suka bishi ana masa ihu, ita kuma Abu sai kuma masifa takeyi tana tafa hannuwa tana fadin "wallahi mutum yaje ya fada a gidansu wanshi yazo ya tabani gobe nima na zane shi." Sauran 'yan fadan ta suna ta zugata tana dariya, a haka suka isa kowa ya nufi gidansu, Abu tace "Bari naje na dauko gyada ta na kasa wallahi kuma naji yaro ya zageni ya sani." Ta shiga gidansu har lokacin da damararta, Babarta dake zaune wacce asalin sunanta Salamatu ne suke ce mata Sala tace "Yauwa 'yar albarka yanzu nake tunaninki tun da kuka tafi akube-kube baku dawo ba." Ta fashe da dariya tace yau na gaya miki Sala wallahi na chas kara yaron nan Habu, daman ya raina ni har kuka na saka shi wallahi ya tafi gidansu yana ta kuka. Sala ta fashe da dariya tace "Yata giwar mata, wanda ya tabaki ya tabo ramin zuma, bana son sanya ki cigaba da chasa duk wanda ya kawo miki wargi ni na saka ki." Tayi dariya tana gyara kashin gyadar tata tace "Ta nawa ce Sala?" Tayi dariya tace "Haba maitsada (Sunan da take kiranta dashi kenan) ai ke ba sai an kirga miki ba, ke ai me kan arziki ce yanzu zaki dawo nasan kudina ba zasu bata ba sai dai ma su karu, dauki kawai kije da dai Karimatu ce mai kan kwantai (kanwar Abu ce)" Abu tayi dariya gami da daukar farantin wanda aci bal-bal ke tsakiyarsa tayi waje da kujerar zamanta. Can hanyar 'yar kasuwa ta nufa inda masu lemo da agwaluma da rake ke saidawa, tun da ta fito aka karbi kujerar wata kawarta Laraba, suka tafi suna tafe suna hirarsu akan fadan da suka yi da Habu, da kuma chalon su. Sanda ta isa bakin 'yar kasuwa ta ajiye farantin ta, samari suka fara zagayeta kowa ya dauki gwangwani guda yana ci ana hira, rabin hirar duk batsa ce, amma da yake Abu ta saba jin irin wannan hirar sam bata damu ba, sai dai ta sheke da dariya tace shege wane, can wani Rosi yace "Ke ai wallahi Abu har yanzu baki waye ba, ki duba ko kwana bakiyi a waje kullum kina gida." Ta mike tsaye tace "Kan Uban can, har zaka ce ban waye ba, don Allah dubeka Rosi din nan kaifa wallahi tsami ne, don dai yayana jarababbe ne wallahi da nima kwana zan dinga yi kamar Laraba ko yaya kikace kawas?" Ta bawa Laraba hannu suka tafa Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 . Mudi Niga yace "A'a ba wani Laraba taso muje muyi zancen mu bayan makaranta kada 'yan sa ido su ganmu." Abu ta tabe baki tace "Wallahi nima don jarababben yayana ya saka min ido ne, yanzu da an ganni za'a gaya masa yaci ubana, wallahi da nima acan zan dinga zancen, amma zan yi maganinsa." Su Laraba dai suka mike suka tafi ita kuma suka cigaba da hira da su Rosi. Karfe goma da rabi sannan ta dauko kayan tallarta tana ta mita a fili "Banza su Rosi din nan shiyasa bana sakar musu fuska, da Kwage ne ko Damisa ai da tuni sunyi mini juye mtss!" Taja tsaki, yanzu da kwantai zan koma gida? bari dai na biya gurin dan Oga dan nasan shi dole ne kila ya siye yanzu. Ta nufi chemist din nasa da fitilar kwai a bisa tebur, yana zaune a bisa kujera mai kama da tsohon soja, babu ko sallama ta bankade dan yalolon farin yadin dake kofar da sunan labule ta shiga tana fadin dan oga kana nan baka tashi ba? Ya mike cike da murna yace Wow! Habu yanzu kana rena wallahi ina son ka da gani (cikin gurbatacciyar muryarsa yake mata magana) ita kuwa ta ajiye gyadar bisa wannan tsohon tebur din ta hure aci bal- bal din tace "Daman zan biyo yanzu ga gyadar zaka siya duka ko?" Ya matsa jikinta yana cewa "Habu Habu, wallahi kana da cho, ina ta sonka da yawa, amman zaka kwana anan ko?" Ta zaro ido waje tace "Kaifa baka da hankali wani lokacin, idan na kwana a gurin ka nace me a gida....." Ya jawo ta jikinsa yana mata abinda ya saba duk da ba gamsuwa yake yi ba, domin dai lalubeta yakeyi, don taki amince masa dari bisa dari sai dai yayi abinda ya samu (Allah ya shirya, jama'a ku duba diya mace ta futa har zuwa wannan lokacin uwarta bata neme ta ba, tur da irin wannan Uwa). . …Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Can tace "Malam na gaji zan tafi kada jarababban can ya biyo sahuna don ma nasan Sala zata kareni sallameni na tafi." Ya mike yana gyara riga yace "Habu-Habu, wallahi yarinyar nan baka da cho kina yawo da akalina, amman zan rama ne." Tayi dariya tana fadin "Dan oga kenan." Ya miko mata Nairori har na Naira ashirin tace "La-la nagode." Ta sunkuci farantin gyadar ta fuce da sauri tana fadin "Duka gyadar ma ta naira ashirin ce amman ya bani Naira ashirin" Shi kuwa sai kiran sunanta yake yana dariya har ta kulewa ganinsa.(Wallahi sai mun zamo masu taka tsantsan da irin kabilun nan da suke mu;amala da yaranmu)….Sanda ta isa gida an turo kofar da tirmi ba'a kulle ba, don haka ta tura a hankali ta shiga da kullin namanta na naira daya da ta siyo don kudin dake hannunta naira ashirin da shida ne ga kuma sauran gyada. Ta shiga dakin Sala ta taddata abisa leda tana ta sharara bacci kamar matacciya (Ku duba irin wannan Rashin tunani, ki tura diyarki talla tayi dare amma ko damuwa bakiyi ba, bacci ma kikeyi hankalinki kwance!!) A hankali ta dinga taba ta tana fadin "Sala! Sala! Sala! Na dawo." Sala ta mike tana magagin har ta wartsake tace "Diyar arziki kin saida ko?" Abu tayi hamma babu ko rufe baki balle salati, sai wani nishi da tayi hmmmammman har bakin ya rufe da kanshi, sannan tace na dawo ga kudin nan da sauran gyadar dai, Sala ta sha kunu tace "Haba Abu, kince fa a kunga-kunga har ta kare...." Tayi shiru da zancen da taga ruwan Nairori a gabanta, ta debo su da sauri tana kirgawa sai ga naira ashirin har da Uku. Ta washe baki tana fadin "Diyar albarka lallai kice samuwa kika yi daga sama, wannan fa shine riba biyu ga kudi ga sauran gyada, na baiwa Shehu da safe ya karasata idan kin tafi makaranta, kin siyo naman? Domin mai nema idan baya ci wata rana shi za'a tafi nemowa." Abu ta nuna mata ledar naman ba tare da tace komai ba ta mike, Sala tace "Gwara dai aje a huta don ai kin gaji na sani, sai da safe mai tsada." Tace to Allah ya kaimu. Ta fuce a tsakar gida taci karo da Sadiku yayanta ya shigo yana huci, ke don Ubanki ina kika biya naje bakin 'yar kasuwa ban ganki ba kuma ban dade da barin gidan nan ba? Ta murguda baki gami da harararsa tace "To ina ruwanka dani eyeh malam...." "Ke don ubanki rashin kunya zakiyi mini? To yau idan baki gaya mini inda kikaje ba wallahi sai na faffasa miki jikinki." Yayi kanta ai kuwa suka kwasa da gudu tayi dakin Sala wacce sukayi karo a bakin kofa. Cikin hargowa da bala'i Sala tace "Malam meye haka zaka biyo mini diya da gudu salon taje ta karye ka cuceni? Wallahi yaron nan ka futa daga idona na rufe kaji ko? Kai waye ne da zaka matsa mata eye? Ko kai ne uwarta daka haifar mani ko kuma kai ne Ubanta eye?" Cikin hargowa take bala'in, ita kuma Abu tana gefe ta rike kugu tana murguda baki da gatsina fuska. Ransa ya kuma baci yace "Haba Sala, yaushe zaki rufe idonki kina ji kuma kina gani Zainabu ta dinga kaiwa dare a waje kuma idan ance za'ayi mata fada kice baki yarda ba, yanzu ki duba agogo karfe sha biyu har da rabi na dare ace sai yanzu yarinya mace zata dawo gida." "To Ubana ai sai kazo ka rufeni da duka, nace kazo ka rufeni da duka!" Ta fadi da hargowa, kana ta cigaba da cewa "Ina ruwana da wani lokaci ko karfe dubu na dare zata dawo bai shafeka ba, ai ba kai ne ka haifar mini ita ba, kuma da kake cewar neman kudi hauka ne inace kaima nan kake shigowa kana rara gefe a sammaka abinci, kato dakai ba don tana nemowa ba zakaci ne? shi solobiyon Uban naku idan muka daka ta tashi zamu rayune? tun yaushe ya bar gidan nan tun asuba ya tsallakemu ya gudu har yanzu bai shigo ba sai mun kuma wani bacci, to zamu zauna ne mu mutu idan bamu nema ba? Wallahi ka fita daga idona ka samawa yarinyar nan lafiya idan ba haka ba ranka zai baci." Ta kuma cigaba da masifa. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 A gidan nan dame zata ji, da tsanar ta da 'yan unguwa sukayi ko ko da jarabarka, yanzu daga safiya suwa yanzu kasan nawa ta samu tun safe kake,zan bata maka rai wallahi." Ya kwantar da murya duk da ransa a bace yake yace "Sala ki fahimce ni, ba wai ina yiwa Zainab fada don bana sonta ba, sai dai a matsayina na dan'uwanta ba zanso ace ta lalace ba, ki dubi yanda kowa ya budi baki a unguwar nan maganarta zaiyi, idan tsokanace itace gaba, Sala yaushe... Kai rufe mini baki sai kwarara zance kake babu kwama babu fulsu tof, ratatata kamar zubar ruwan sama. To tayi din uban wani ya hana, wato kafi so a dinga koro mini ita da duka ko? To ban haifi sallamammiya ba, kai tunda sallamamme ne sai kaje kayi tayi, ta dubi Abu mai tsada shige daki kici namanki kiyi kwanciyarki kamar tsumma a randa, naga shegen da zai kuma takura miki." Abu ta kuma murguda baki gami da yin gatsine ta shiga cikin dakin su ita da kannenta duka uku duk matane ta haye bisa katifarta ta bude namanta tana ci gami da kunna rediyonta da wani saurayinta ya bata, wakar lagireto ta fara futowa a hankali. Itama Sala daki ta shige tabar Sadiku a can tsaye kamar ya hadiyi zuciya ya mutu yake ji don takaici, me ake da irin wannan rayuwa ace kiri-kiri an san gaskiya ake takewa saboda son duniya? Yaja tsaki yana fadin "Allah ya ganar daku gaskiya." Ya nufi dakin sa dake soro yayi fakare cike da tunani, jin kidan dake tasowa a rediyon Abu yake yi har cikin ransa, don dai yana shakkar bala'in Sala ne da wallahi sai ya maka rediyon da kasa uban kowa ma ya huta, yana nan kwance ya jiyo ta kashe da alamu bacci zatayi kenan. Ba'afi minti talatin da hakan ba yaji alamun shigowa, ko ba'a fada masa ba ya san Babansu ne, ya dubi agogo karfe daya da minti goma sha tara, yaja tsaki cike da takaici, yana jinsa ya rufe kofar gidan ya leko ta tsakanin labule yana kallonsa takalminsa a hannunsa suke sai sanda yake sadaf-sadaf! Da haka ya nufi daki, daga inda yake yana jiyo munsharin Sala da alama bacci yayi awon gaba da ita, ya saki labulen ya koma ya kwanta yana tunanin wannan mummunar rayuwa da suke yi da iyayensu, a haka har bacci barawo yazo ya sace shi. Da sassafe ta tashi ta shiga bandaki tayo alwala tayi sallah, sannan aka jawo kayan kwalliya aka maka mai, hoda da jan baki wato dai tayi tsaka tsami kenan. Jagirar nan da aka ja har ta kusa taba kunne ga jambaki an saka shi an kawo baki an zagaye saman leben dashi, anyi wani digo a tsakiyar goshin akayi wani bisa hanci, ga gefen haba,sannan aka bude adaka aka dauko wata atamfa 'yar kaduna Nichem, aka sanya aka yafa gyale a kafada bayan ta daura dan kwali disko, ta kalli madubi tayi kyau matuka, tayi murmushi ta futo tsakar gida. Sala dake can kicin tana suyar funkaso da miya tace "A'a kin shiryo, to maza a dauka mai kan albarka kada lokacin makaranta ya kure gashi nan na zuba miki naki," tace To, kana ta nufi gurin da aka ajiye mata nata din cikin watan fanteka, da miya a cikin bokitin fenti, ta dora a kanta su kuma kannenta suna ta mikawa na kofar gida dake zaune suna siya. To maza mai kan albarka kada a dawo da ko guda daya kinji ko? Bata ce komai ba ta fice da digirgire don gwana ce gurin daukar kaya a kanta. A hanya suka hadu da Laraba, itama tana dauke da waina bandashe mai kuli da mai da albasa) suka tafa kana suka rankaya bakin tashar 'yan kifi, suna tafe suna shan hirarsu suna dariya. Karfe takwas da minti arba'in ta dawo, Sala ta tareta tana cewa "Yauwa diyar arziki maza sauke ki shirya kada ki makara, na zuba miki kici ne?" Tace "A'a naci acan bakin tasha." ta mikawa Sala kudin ta shige cikin dakin ta sanyo kayan makarantar ta bulu din uniform da farin hijab, amman bata sanya hijab din ba sai cin damara dashi tayi ta rumgume littafai a hannu ta fice. Sala tace "Ga kudin mota." Tace, "Ina da kudi ki barshi kawai." "To a dawo lafiya a dawo dai da wuri." Tace to. Ta fuce da sauri, tana fita ta sami hayis ta haye aka sauketa a kofar makarantar 'yan mata ta G.G.S.S Dala. Sanda ta isa ana taron 'yan latti ko ma nace an gama, don wadanda aka tare din an tura su cikin makaranta tsintar bola, sai Discipline master da prefect ne a bakin kofa. Babu ko shayi ta nufi kofar tana taunar cingam din ta kas-kas, malam Kabiru discipling master ya dubeta da takaici sanda take shirin shigewa ko kallonsa ma bata yi ba yace "Ke zo nan." Babu ko shayi ta nufeshi tana taunar cingam. Ya dubeta a kufule yace "Ni sa'an Ubanki ne da zaki tsaya mini?" Ta murguda baki tana kunkuni taki durkusawa, ya zanbada mata bulala yace "Kade doron sha-sha-sha." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta murguda baki gami da cigaba da yin kunkuninta ta durkusa "Me kike cewa?" "Uwarka nace" Ta fada a hankali, da motsin bakin ta yaso ya fahimci abinda tace yace "me kika ce?," Tace "Ni fa bance komai ba malam." Yayi ajiyar zuciya kana yace "Mai yasa ke kullum sai kinyi latti ne eye? Idan baki son makarantar ki daina zuwa mana sai kace an miki dole, shegiya tun baki tafasa ba zaki kone, kina aji daya tal amma kin gallabi kowa, to wallahi idan bakiyi hankali ba sai an kore ki daga makarantar nan,tunda ta uwarkace ba?" Ta fadi a hankali, yaso ya juyo amman bai fahimci abunda tace din ba, don haka yace "me kike cewa?" Ta dubeshi da shagwaba "Haba malam ni fa ban ce komai ba." Yace shikenan tashi kibi 'yan uwanki kuyi tsintar shara. Ta ce "To shege." Ta fada a hankali,Ta mike ta nufi inda ta hango dalibai sunbi, sai a sannan ya hango hijabinta daure a kugunta "Ke! ke!! ke!!! Zo nan." Ya kuma kwala mata kira amman tayi banza "Ke! Zainab ba kiranki nake yi ba?" Ta juya tace "Au ai naji kana cewa ke ne bansan dani kake ba, gani malam." "Ki cire hijabin nan ki saka a jikinki." Ta yamutsa fuska tace "Gaskiya malam zafi nake ji, bazan iya yafawa ba" Da haushi yace "Idan baki yafa ba ko zan zaneki a gurin nan." Lallai Malam Kabirun nan bai san Abu bane, ta murguda baki gami da dafe kugu da hannu daya tace "Allah ko kasheni zakayi ba zan yafa ba don zafi nake ji, haka kawai ba za'a sanya kurajen gumi su futo mini ba, dan babu mai sai mini magani." Ya hasala sosai ya nufeta da fushi ya daga bulalar dake hannunsa zai maka mata, amman ta rike ta gam tace "Allah malam ba zan yafa ba." Can wata firifet ta hasala tace "Malam ka barmu da shegiyar yarinyar nan taurin kai ne da ita bata da mutunci, kusan kullum haka muke da ita taki ta daina yin latti," Bata gama mai maganar ba, ya fisge bulalar daga hannun Abu ya tsula mata, Ai kuwa sai ta fasa wata uwar kara kana tayi kansa ta cakumu wuyar babbar rigarsa ta shige ciki, ya rasa yanda zai yi da ita sai hargowa yake yi yana fadin "futo don ubanki, kina ina ne?" Tana ihu ya rasa yanda zaiyi da ita dole ya cire babbar rigar data makale a jiki ya kalleta da takaici yace "To tashi kije ki wanke bandakin can na seniors." Ta wurgar da malum-malun din "ni gaskiya ba zan wanke kashin wasu garada ba, haka kawai?" Ya rasa yanda zaiyi da ita, yau Allah ya hadashi da shegiyar yarinya mara tsoro, duk yanda ake jin tsoronsa a makarantar banda ita,ya mike ya nufi Ofis din principal yana fadin "Yau zaki ci Ubanki wallahi," babu ko shakka ta bishi wata firifet tace, Zaki ci ubanki yau, za'ayi maganinki. Ta dalla mata harara tace "banza kiji da wadannan hakoran naki masu kama da kaca, "Ke ni kike gayawa haka?" Tayi kanta da bulala, ita ko ta tsaya kyam tana jiran ta karaso ta huce a kanta, wata ce ta rike ta tace ke me yayi miki, Malam Kabiru ya kwala mata kira da yayi nisa, ta debi littafanta dake hannu ta bishi kamar ba zata taka kasa ba. Ya shiga Ofis din principal dake zaune a wata katuwar kujera taci kwalliyarta ta sha glass dinta, daga ganinta kaga tsohuwar 'yar boko. "Yaya dai Malam Kabiru lafiya ne na ganka rai a bace?" Ya sami kujera ya zauna yana huci yace "Hajiya yau wata fitinanniyar yarinya ce ta bata mini rai bari ki ganta." Abu ta shigo Ofis din babu ko sallama ta dubi principal din tace "Sannu Ma." Bata amsa ba illa kara gyara glass dinta da tayi tana duban Abu dake tsaye kerere tace "Kika tsaya mana a kanmu kamar wasu sa'anninki." A hankali Abu tace "Da fa?" Sannan ta tsugunna. Malam Kabiru yace "Kinji ko da kunnenki?, tun dazu wannan kun-kunin take mini bana jin abunda take cewa, sai dai ina zaton zagina take yi." Hajiya Kubra tace "Malam Kabiru sanar dani me ya faru kwantar da hankalinka." Babu bata lokaci ya zayyane mata komai tun daga farko har karshe. Hajiya Kubra ta dubi Abu da harshen nasara tace mata "Haka ne abinda yace?" Da yake Abu jaka ce bata iya turanci ba, domin ba zuwa makarantar takeyi ba sai taga dama, idan tazo kuma din bata yin komai sai hatsabibanci, don haka bata iya komai ba, hakan ce ya sanya ta yiwa shugabar makarantar shiru tana guna-guni. Shugabar makarantar ta hasala ta doka mata tsawa gami da kara maimaita mata abinda ta tambayeta da fari. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Abu tace "Maa nifa bana jin abinda kike fada gwara kiyi mini da yarena, don ni bana jin abinda kike fada." Tana wani fisge-fisge take wannan maganar. Ran Hajiya Kubra ya kuma baci, don haka ta dinga zagin Abu da turanci, tana fada mata "Banza jaka, baki san komai ba sai shegen iskanci da rashin mutunci, a haka za'a gama karatu ba'a san komai ba sai a kare a auren dan dako ko dan acaba."Kalma daya Abu ta fahimta a duk cikin maganar Hajiya Kubra wacce tace mata "donkey" wato jaka, hakan ne ya sanya ta fahimci irin cin mutuncin da ake mata dan haka ta kama guna-guninta tana fadin "gaki nan babbar jaka, ki dubeki fa tamkar kayan wanki." "Me kike cewa?" Shugabar ta tambaya da dacin rai jin Abu na magana kasa- kasa. Ta murguda baki tace, "Ni fa bance komai ba." Hajiya Kubra ta dubi Malam Kabiru tace, "Malan zane mani ita kafin na bata horon da zan bata tukunna." Duk da gabansa ya fadi dan yana gudun makalewar da Abu take masa, amman sai ya daure yayi ta maza ya nufeta da zabgegiyar dorina. Ai kuwa yanda tayi masa dazu haka tayi masa yanzu, ta cukwikwiye shi tana ta zabga ihu, amman babu ko alamar digon hawaye a idonta, da kyar ya samu yayi mata guda Uku yana mai da numfashi.Hajiya Kubra tace "To maza dauki tsintsiya ki share harabar malamai duka yanzun nan." Ta mike tana guna-gunin nata tace "Oho dai! Ko yanzu na wahalar daku,"Me kike cewa?" Ta tambayi Abun wacce tuni tayi fucewarta, ta kuma duban Malam Kabiru tana fadin "Lallai yarinyar nan bata da mutunci, shegiya irinsu ne idan suka hadu da maza jahilai irinsu suke lakada musu duka." Shi dai baice komai ba, yayi godiya ya fuce domin dai Abu ta wuce iyakacin tunaninsa. Abu tayi zaton abun na wasa ne, sai gashi wankin hula yana neman ya kaita dare, dan bata kammala ba har aka fita tara (break), sannan ta nufi Ofis din shugabar makarantar (principal) tace "Maa na gama." Ta dubeta a wulakance tace "Ki yafa hijab dinki, sannan kada ki kuma yadda a kawo mini kararki Ofis dina, idan ba haka ba sai na koreki ko kuma kizo da Baban ki." Abu ta cire hijab din nata ta sanya wanda daman dan mitsitsine tace "To!" Sannan ta fice daga Ofis din. Hajiya Kubra tayi kwafa gami da yin tsaki tana fadin "Dakikiyar banza, bata san komai ba sai iskanci." Ita kuwa Abu tana yin nisa daga Ofis din ta cire hijab din daga kanta ta kuma yin damara dashi sannan ta nufi ajinsu. Kawayenta ne suka tarota ana ta ihu suka rungumeta suna mata kirarinta, domin wadanda abun ya faru a gabansu sun basu labari, da haka suka karasa aji suna shewa har aka koma break. Sai dai da zamanta da rashinsa kusan duk daya ne a ajin, domin dai bata tambayi abinda akayi ba da bata nan ba, sannan yanzu ma da malami ya shigo bata tsaya ta saurareshi ba hirarsu kawai sukeyi da wata kawarta, kusan sau uku malamin yana gargadinta akan tayi shiriu amman batayi shurun ba, har ya gaji dai ya tambayeta kamar haka "Abu, tell me how many are types of letter?" Yana nufin ta gaya masa kashe-kashen wasika. Tayi tsuru-tsuru don bata fahimci tambayar bama balle tasan amsar da zata bashi, sai wani murguda baki kawai takeyi tana guna-guninta. ganin bata da niyyar bada amsar ne ya sanya ya kuma gargadin ta akan tayi shiru ta saurareshi, dan darasin turanci yana da amfani ga dalibai don ta haka ne zasu koyi yanda zasuyi magana dashi, amman har ya fita daga ajin nan Abu bata daina surutunta ba sai dai ta rage murya ba kamar da farko ba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Da aka tashi ma sai da sukayi fada da kwandasta domin dai idan da sabo ta saba, domin dai maimakon ta bashi naira biyar sai ta bashi naira uku ba kuma don bata dasu ba, a'a dan dai neman jidali kawai irin nata. Kwandastan ya dubeta ransa a bace yace "Ke! Malama cika mana kudin mu saura naira biyu." Tayi tafi gami da doka cinya tana fadin ba zata cika ko kwandala ba don haka kudin motar yake. Nan fa rikici ya rincabe amman Abu ta kekashe akan ba zata cika ko kwabo ba. Daga karshe yace wallahi idan bata cika masa ba zai warci dankwalinta, maimakon ta saduda ina sai ma ta cigaba da tsiwarta tana tafa hannu, kawayenta na ta zugata. Abin ya hasala direban yace masa ya cire dankwalinta tunda bata da mutunci, dan haka ya cire dan kwalin nata. Sai dai abu da kwandastan bai sani ba shine tuni Abu ta gama dana masa tarko, don haka da ta sauka kafin ya hau motar tace masa "Malam ka bani dan kwalina." Yace "Na karfi ne, idan kina son dankwalinki ki cika mini naira biyu.......Warce gudar Naira ashirin da fellewarta da gudu ne ya katse masa zancensa, ya saki baki galala yana kallonta tamkar zata tashi sama dan gudu, don Allah ya yi mata baiwar gudu. Direban ya hau masifa sanda ya ankara da abinda ya faru yana fadin "Banza sakarai, kana me wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ta warce kudi a hannunka? ai sai ka shigo mu tafi." 'Yan cikin motar banda dariya babu abinda suke yi, shi kuwa cike da jin haushi yake fadin "Haba Oga baka ga shammata ta tayi ba? An bani murtala ina shirin bada canji ta fisga ba?" "Kawai kazo mu tafi, shegiyar ta bamu a can" Direban ya katse masa magana. Ya dubi inda Abu tabi ko alamunta baya gani dan akwaita da gudu tamkar filfilwa, hayaniyar fasinjoji ce ta sanya shi shiga motar yana fadin "Ai na gane wallahi duk ranar da Allah ya kuma hadamu sai taci ubanta." Ya shiga mota har lokacin wasu fasinjoji suna dariya abinda ya kara kular dashi. Ita kam Abu tunda ta falla da gudu bata tsaya a ko'ina ba sai a tsakar gidan su, ta zube a kasa tana mai da numfashi. Sala dake kwashe wake da shinkafa ta dago tana dubanta a rude tace "Yaya dai Maitsada, lafiya kike wannan hakin kamar wacce tayi tseren gudu?" Sai data numfasa sannan ta kwashe da dariya harda rike ciki, duk da Sala bata san ko dariyar me take yi ba sai ta hau tayata tana fadin "Hatsabibiya, yanzu haka tsiyar taki kika shuka tunda naga kina wannan dariyar." Tayi kokarin tsagaita dariyar sannan ta fara magana "Bari ke dai Sala, yau wani shege na hadu dashi zai nuna mini zara bai san na fishi ba....." Ta kwashe duk abinda ya faru ta sanarwa da Sala din, gami da karasa zancen da cewar "Shegen kinga ashirin din dana warto, gobe ma ya kuma." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Sala ta kuma fashewa da dariya tana fadin "Lallai kinyi maganin dan iska shege, banda iskanci akan naira biyu sai ya warce miki dankwali? Da ba'a cin arziki ai da bai sami kwandastan ba tunda nasan ba motarsa bace, amman maganinsa kenan kinga ai gobe ya kuma. Maza tashi ki shiga wanka kada lokaci ya kure Abulata mai kan alheri, ba irinsu O'o ba mai kan kwantai Wato tana nufin Karima kanwar Abun, domin dai ita bata da hali irin na Abun dan tana jin irin nasihar da Yayansu yake mata, dan haka ma basa shiri da Sala sam. Ta mike har lokacin tana haki da dariya ta shiga bandakin, kwandan wankanta daban ne, dan ita sabulunta dankwali ne kamar yanda take cewa giv da dai sauransu, ba irin nasu Karimaba dan yanka. Bayan ta fito daga wanka aka kuma zauna zaman kwalliya, Jagira kam da aka jata har saida ta tabo kunne, ga kuma dige-dige da aka yi a fuskar ko ina, leben nan kuwa yasha baki sama da kasa, sannan aka cokala daurin dan kwali ture kaga tsiya aka fito. Sala nayi mata kirari ta nada gammo ta dora a kai, akayi digir-gire da fanteka wacce ke dauke da wake da shinkafa da robobi a gefe da mai da yaji duk a kai, sai hannunta data dauki wani bokiti wanda dashi take wanke kwanukan da sukayi datti, aka fice babu addu'a sai da kirarinta data bita dashi, sai da ta fice daga soron sannan Sala ta bita da sauri ta leka duk rabin jikinta a waje ta kwala mata kira ta juyo tana guna-guni. Sala tace "Yi hakuri Abule na dawo dake, na manta ban tina miki maganar makarantar allo ba kada jarababben yayanki yaga ba kije ba ya hadani da malam, wanda yake jin kamar ya jefani a wuta dan dai nafi karfinsa ne kawai. Don ba dan jarabar su ba daga bokon har allon daina zuwa zaki yi tunda dai kin sami na sallah." Ita dai Abu batace komai ba ta juya ta tafi tana kun-kuni tana fadin "Kawai daman akan wannan maganar kika dawo dani, wallahi da na san a kanta ne da ba zan dawo ba." Sala din kuwa tace "Mai kan arziki a kukkunga kada a dawo da ko kwalli daya, na san ki, ai ba kya kwantai." To kawai tace sannan ta wuce. Kai tsaye tasha ta wuce tashar kofar Wambai, tana isa kwastomominta suka yi mata caaa, domin akwaita da araha ga sakin fuska da tsafta, idan kana so takai maka har shagonka zata kai maka Tun karfe hudu saura minti goma abincin nata ya kare amman sai ta tsaya hira da samari da wasan jakai da kawayenta 'yan talla. Can ta hango Rodimasta, wani da take bi kudi tuntini, ai sai ta cire gyalanta tace dammara dashi tana fadin "Yau Allah ya kama tsinannan can, wallahi idan bai bani kudina ba sai nayi masa rashin mutunci wallahi, dan yau sai anyi bala'i a cikin tashar nan wallahi." Laraba kawarta ta riketa tana fadin "Haba Abu yawa ne, ki kyale shi kawai kin san halinsa dan akuya ne..." Ta fincike tana fadin "Dalla malama sakeni ai ya san wadanda yake yiwa akuyancin nasa, ni idan ya kawo raini ai sai inci (ta kunduma zagi)." Ta isa gabansa yana shan tabar wiwi sai wani lumshe ido yake yana rere wakoki kala-kala na gambara zuwa wakokin 'yan dambe da na barayi, kai gasu nan dai barkatai. Abu ta rike kugu tana wani karkada kafa tace "Kai barawo bani kudina, rannan na zuba maka abinci ka gudu baka bani kudina ba, to yau Allah ya kama ka, ko ka bani kudina ko nayi maka rashin mutunci wallahi. Ya dubeta yana murmushin mugunta yace "Banza ke wallahi karamar arniya ce, har kin isa kiyi mini wata barazana, to na cinye na karfi ne ki kwata." Ta tafa hannu tana fadin "Kan Ubancan, lallai yau ka tabo ma kanka, yau zan nuna maka kai karamin dan iska ne, dan ko sama da kasa zata hade sai ka bani kudina." Ta kama kwalar rigarsa ta cukwikwiye tana cigaba da bala'i. Shi kuwa sai dariya yake yana fadin "Yarinya kece mai aikin yi, in dai nine wallahi mu kwana a haka." Ya cigaba da zukar wiwinsa yana lumshe idanu. Jama'a sukayo gurin suna bada hakuri, Abu tace wallahi ba zata cikashi ba sai ya bata kudinta idan kuwa ba haka ba zata dauko masa folis ita kam Laraba da yake matsoraciya ce sai hakuri take baiwa Abun. Maimakon ta hakura sai ta doka mata tsawa tana fadin "Dalla can malama gafara daga nan, Uwarsa ta kauye ce take bani jari ko ubansa na karkar....." "Ke Abu don kazanki ni kike zagi?" Rodimasta ya katseta a hasale dan ya fara kufula da rashin mutuncin da take masa. Babu tsoro balle fargaba tace "An zageka din, kai wanene da ba za'a zageka ba eye?" Ya kuma hasala da zafin rai yake fadin "Ke wallahi idan baki sakeni ba zan tattakaki a gurin nan na farfasa miki jiki." Tayi shewa "Ahayye! wallahi Bismillah dan halak ka fasa, don ka sani duk mari daya a folissitashan naira dari yake, don wata kila sai an hada da gonar kauye sannan za'a biya kudin marin....." "Ke Abu dan Allah kiyi hakuri ki sake shi, wannan ai ba mutuncin ki bane kina mace kina fada da maza." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta kalli mai maganar tana fadin "Kaga Baba mai taba ina ginin mutuncinka dan kana biyana kudina ba irin wannan dan bashin ba, dan haka kawai ka bar gurin nan sai ya biyani kudina zan sakeshi." "Kinga ya isa sakeshi nawa ne kudin naki na biya, tunda shima ya rantse ba zai biya ba dan idan rigimar tayi zafi har mu zaku jawo wa tunda dai haka 'yan sandan can ke so a fara fada suzo kame." Ta murguda baki tana fadin "Ai wallahi nima ba zan sakeshi ba sai dai idan ka biyani, naira biyar ne dan haka sai ka biya." Ya dauko naira biyar a aljihun gaba rigarsa yace "Gata shike nan rigimar ta kare ko?" Ta saki rigar Rodimasta tana fadin "Banza matsolo matsiyaci, yau Allah ya rufa maka asiri da yau kaga karshen rashin mutunci." "Ke! Ya isheki tunda dai an biyaki kudinki 'yar matsiyata, dan wallahi kika zageni sai na tattakaki." Ya fadi yana nunata da yatsansa. Ta tsaya ta rike kugu tana wani girgiza tana fadin "Wanda bai fasa ba baya kaunar uwale da ubale..." Laraba ta janyeta tana fisfisgewa da kyar aka samu ta kama hada kayanta tana cigaba da bala'i ta bar tashar. Tana isa gida ta dire fantekat kayan ta mikawa Sala kudin wacce ke washe baki, ta fada daki ta kwanta. Sala taji shiru ta leka dakin ta ganta a kwance ta bude baki da mamaki tace "Au Abula kwantawa kika yi? Ke da zaki je makarantar allo? kada jarababban yayanki yazo ya ishemu da mita." Ta mike gami da daukar allo ta fice tana kun-kuni. Miskili kafi mahaukaci ban haushi, Sala ta fada tana dariya. ta dora da cewar "Abula diyar Salamatu wani lokaci idan kina shan kunu ko miskilancin naki ya motsa sai na ganki kamar wata diyar wani sarki, sai da lallashi Abula ta." Bata dai ce komai ba ta ficewarta. Makarantar dake kusa da gidansu, dan tsakaninsu gida uku ne, koda taje dinma hira ta kamayi da kawayenta sai da malam din ya doka musu tsawa sannan suka rude da hayaniya wai su nan dole karatu sukeyi. Da ya kirawo ta ta biya allonta kuwa inda-inda ta kama yi, nan fa ya hauta da fada, tayi kum da baki kamar ba Abula diyar Sala ba, dan idan akwai wanda take tsoro da shayi a duniya bai wuce malam da yayanta ba, dan malam din bai mata ta dadiba tun tana 'yar mitsitsiyarta kuwa, gashi babu yanda zasuyi dashi dan shine kamar matsayin kakanta na gurin Uba, ya kuma maimaita mata ta karanta kuwa tsaf. Domin dai duk iskancin da takeyi tana sane don da ace tana maida hankali akan karatu da mai kokarice ita dan kwakwalwarta akwaita da saurin rike abu, sai dai shiririta da wasa da ta sanya a ranta, dan yanzu data koma gida zata fita yawo da wasa dan da kyar gobe zata iya biya yanda ya biya mata, rudewar da akayi da karatun tashi ne ya kwace ta. Ana cewa fatiha kowa ya mike yara suna ta waka suna fadin "Tashiiii." Su Abu da zugar kawayenta kuwa tsayawa akayi ana maida yanda aka yi, dan wai wata Lantana tayi gulmarta, wai yau zasu dirji bakin Lantana da rubabben kwai. Ai kuwa suka saka ihu aka sanya Lantana tsakiya tana kuka, sai waccan tace nima kince mini kaza kince mini kaza, sai ta tabe baki tana fadin, "Laaa! Ni din?" Sai kuma ta sanya kuka, Laraba ce ta kuma tunzura fadan da tace "Eh, nima rannan kince mini wai Abu tana zuwa gurin Dan Oga mai kyamis, Kutumar uban can, lallai yarinya a gulmar taki har da ni? dan ubanki?" Abu ta shiga masifa tamkar zata ci babu, taci dammara da gyalanta tana cigaba da girgiza gami da ambaton sunan iyayanta tana kunduma musu zagi gami da dungure mata kai da lakuce mata hanci, yara sai ihu suke yiwa Lantana wacce banda kuka babu abinda take yi. Malamin sune ya farga da abinda ke faruwa yayi kansu da dorina, ya samu daya ya caula mata ta gantsare gami da fasa ihu, abinda ya ankarar dasu kowa ya bazama da gudu dan gujewa bulalar malam, wannan ne ya ceci Lantana daga fasa mata baki da akayi niyya da rubabben kwai. Ana idar da sallah Abu ta fito daga gida tana rera wakar kiran wasa don tunda ta taso itace ke kiran 'yan wasa don ita ce boss din, don haka ko yara ne ba'a gani ba gidansu ake zuwa nemansu Sala tayi ta bala'i. Ta fara rera wakar wasa kamar haka: "'Yan wasa ku futo wasa, idan baku zo ba ubanku yazo, bani na fada ba bature ne, baturen ma na kasar borno. 'Yan wasa ku fito wasa." Ai kuwa sai sai ga yara suna fitowa daga gidajensu da gudunsu maza da mata.Yayanta Sadiku dake shagonsa yana jinta, ji yake tamkar yaje ya shaketa, sai dai yana gudun jarabar Sala ne, don shi a zatonshi tun da ya samar mata makarantar gaba da firamare zata daina wannan wasan haukan, amman sai yaga babu abinda ta daina, dan haka yayi niyyar hanata da tsiya amman Sala tayi tsalle ta dire tace Wallahi bai isa ba ya kyale mata yarinya ta wataya. "Aljana a kwaba ba tsari, aljana a kwaba ba tsari....." Wannan wakar ce ta katse masa tunanin da yakeyi, ya mike ya leko da sauri don yasan wa suke tsokana. Ai kuwa yana hango su sunyi zuga suna biye da wata karuwa da taci kwalliya da wani matsats-tsan siket kanta babu dankwali balle mayafi, tana tafe da kyar da sauri tamkar siket din zai yage, kanta tamkar tozon rakumi ga takalmi sakadale tumeme da kafarta, amman sunki saurara mata sai binta suke suna mata wakar da ihu gami da bula mata kasa. Can wasu dattawa wadanda ke zaune suma suna zabga uban musu, dan sunan majalisar tasu ma majalisar 'yan musu, suka yo kansu sanda suka ankara da duka. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Nan fa suka runtuma da gudu suna dariya, sai da sukayi nisa sannan suka zube a kofar wani gida sunata dariya. Can Abu tace "Laaa! Ku tsaya kuji wallahi yau mu kai sumame gidan shegun can Karuwai mun dade wallahi bamu je ba ko?" Yaran suka amsa da "Eh! Wallahi mu badawa shegu tiyagas din toka." Abu tace "To kowa ya tsaya bari naje gida na samo toka da citta a gurin Sala." Ai kuwa cikin kankanin lokaci suka hada citta da barkono dakakku da kuma toka cikin ledoji suka kulle da dutse a tsakiya suka nufi gidan karuwai ta bayan layi don kada a gansu. Sun yi sa'a kuwa da yawan karuwan suna daki suna hira da lalatattun maza 'yan uwansu, wasu kuma ma suna caca da masu aikata babbar alfasha. Suka shiga cikin gidan da sanda kamar wasu barayi, har tsakar gidan suka isa, cikin daga murya Abu ta bada umurni, "A fasa! A fasa!!.Ai kuwa ji kake tush-tush-tush, nan da nan karuwai suka kama ihu da atishawa, na daki suka yo waje da gudunsu wasu daga su sai siket, wasu kuma sai zani, harda masu dan kamfai. Su Abu suka fasa ihu suna dariya gami da ficewa da gudu daga gidan dan kada a kamasu, sai da suka isa wani kofar gidan can nesa da gidan karuwan suka zube suna dariya, suna hango yanda suke ta atishawa. Hantsi ya dubi ludayi sanda Abu ta dawo daga tallar waina. gashi anyi sa'a ranar babu makarantar boko, dan haka ta zauna a tsakar gida tana baiwa Sala labarin yanda sukayi da karuwan jiya suna ta kwasar dariya, Sala kam harda durkusawa tana rike ciki. Can suka jiyo sallama, tun kafin sukai ga amsawa aka shigo, mutane guda biyu da kayan 'yan sanda a jikinsu riga da siket, sun daure kugunsu da bel. Sala ta mike cike da mamaki tana tambayarsu "Yaya dai bayin Allah lafiya ko? Don ganinki babu alheri." Daya daga cikinsu ta fara magana "Hajiya munzo mu tafi da 'yarki mara mutuncin can Abu, domin dai ta addabi uban kowa a unguwar nan, idan yaso idan munje folis sitashon kya ji abinda ta yi." Abu ta mike da sauri tana tillika dariya dan tasan kwanan zancen tana fadin "To muje din mana, Sala kiyi zamanki yanzu zan dawo." Sala tace "A'a ba zan iya bari ki tafi ke daya ba muje." Ta dauko gyale akan igiya suka fice tana fadawa Karimatu ta lura da abincin da ta dora kafin ta dawo. 'Yan sandan suka fara kuluwa da dariyar da Abu take musu, dan haka suka ce wallahi idan bata daina ba zasu yi mata shegen duka, ta gumtse baki tana yi a ciki don bawai tsoronsu takeji ba, a haka suka isa har folis sitashon din. Ganin karuwai sun jeru ne har da 'yan daudu ya sanya ta kuma tabbatar da zargin da takeyi, kamar ta fashe da dariya amman dan tana gudun sharrin 'yan sanda ya sanya ta gumtse bakinta. Ta isa gindin kanta inda wani dan sanda yake zaune da gashi buya- buya a bakinsa wai shi nan sajan ne. Yana wani muzurai ya dubi Abu yace "Ke mai ya sanya kika je gidan wadancan masu zaman kansu kuka barbada musu toka hade da yaji?" Abu tayi shiru taki cewa komai, ya kuma maimaita mata maganar amman taki tankawa. Wani kurtun dan sanda dake tsaye ya daga kulki ya maka mata a gadon baya, ta gantsare gami da fasa ihu tana sosa gurin tana fadi "Wayyo Allah na na shiga uku, wallahi idan ka karya mini kashin gadon baya na bazan yadda ba." Ya kuma dagawa zai maka mata amman mai mukamin sajan din ya hanashi domin idan da sabo sun saba da halin Abu, sannan ya maida dubansa gurin Abu ya daka mata tsawa ya kuma maimaita tambayar da yayi mata da gargadin idan ta kuma yin shirun zasu saba mata. Ta murguda baki gami da kallon sa kyar da idonta babu alaman shakka ko tsoro tace "Wallahi ko zaku kasheni ba zan yi magana ba sai dai muje gaban (D.P.O)." Sala tace "Abu kiyi magana kada su tsamama miki jikinki." Ta kuma hasala tace "Sala kiyi shiru, haka kawai sai su kama dukana bayan basu kama ni da laifin komai ba? Ai nasan 'yancina dan haka ba zanyi magana ba sai dai muje gaba." Ran 'yan sandan ya kuma baci suka yi mata caa tamkar zasu cinyeta amman ko gezau batayi ba, ana cikin haka sai ga (D.P.O) din ya shigo, Da mamaki ya dubi Abu yace "A'a, Abu lafiya na ganki a nan?" Ai kamar jira take ya shigo sai ta fasa kuka kamar wacce aka yiwa dan banzan duka, amman fa idon nan nata babu alamar hawaye ko digo sai dai burarin kawai da takeyi tana rike bayanta . (D.P.O) din yace su shigo daga cikin Ofishinsa su duka, Dan daudun dake tare da Karuwan ya rike haba yana fadin "Oh! Ni Hajiya Ladi yau na gamu da shegiyar yarinya mai sharri, wallahi ko kwallaba nan ta ganki ta kyale, ai wallahi ko mutuwa zakiyi ba kuka ba sai kinci ubanki." Ya karasa maganar yana tafa hannu da cinya. "Kai! keep quit kayi mana shiru." Wani kofur ya doka masa tsawa. Yayi fari da ido gami da fadin "Lalala! Ka manta wallah Hajiya Ladi nake ba kai ba." Da haka suka shiga ofishin D.P.O din. Mai tuhumar Abu Sajen Barewa ya karantawa D.P.O tuhumar da ake yiwa Abu, da kuma abinda ya faru. Ya dubi Abu yace "Kina jin zargin da ake miki? haka ne ko ba haka na ne?" Ta lankwashe murya cikin ladabi tamkar mutuniyar arziki tace, "Yallabai karya suke mini, ni jiya da daddare ma ina gurin tallan gyada ta, har kazo wucewa kace na kai maka gwangwani goma a majalisarku ko?" Ya dubi karuwan yace "To ku kunji abinda wacce ake tuhuma tace, ko kuna da wata hujjar da zata nuna mana itace din ta bada muku toka?" Hajiya Ladi ya tafa hannu yana fadin "La'ilaha illallahu, Allah na yarda yarinyar nan shegiya ce kwalba." "La-la-la ka zage ni?" Abu ta fadi ta dora da cewar "Yallabai kana ji yana zagina a gabanka hakama acan waje yayi ta zagina." D.P.O ya doka masa tsawa yana fadin "Kada ka kuma zaginta." Ya rike haba yana fadin "O! Ni Hajiya Ladi na shiga uku, tuba nake Yallabai ayi hakuri na daina zagin, amman kwaran-kwatsa dubu jiya ina suyar doya na shiga bandaki dan na rage marata, na jiyo hayaniyar su Abu, kafin na farga har na fara tari da atishawa a cikin bandaki da kokarin shidewa har zani na yana faduwa, da kyar 'yar fisuwa ta kamoni ina kokarin bankawa cikin masai. Ko ba haka ba 'yar fisuwa?" Ya kalli wata karuwa da taci uban bilicin, kan nan tamkar tozon rakumi daga ita sai gajeren wanda iyakacin gwiwa da riga tishet. Tana tsaye rike da kugu tace "Haka ne yallabai, tabbas yarinyar nan ce ta gayyato mana yara suka watsa mana toka mai yaji, dan da muryar ta ma muka gane ita ce" "Karya kike yi bani bace, daga jin murya sai kice ni ce? Idan kuma kin yarda ki rantse da Allah ko a kawo Qur'ani ki dafa." Abu ta katse ta. D.P.O ya ce "Kunga tunda dai abun nan baku da shaida zargi ne kawai kuke yi, dan haka ki basu hakuri ke Abu, idan yaso a gaba sai kuyi kokarin kama koma su waye ke muku haka." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ya dubi Sala ya cigaba da magana "Ke kuma kije ki baiwa sajan din da ya karbi laifin kudin shan ruwa, na kashe case din kowa ya fita." Sam ba haka karuwan nan suka so ba, amman tunda dai basu da cikakkiyar shaida dole suka hakura suka fice, ita kuma Sala ta baiwa Sajan Barewa Naira hamsin tace ya sha ruwa. A harabar caji ofis din suka kuma cin karo da karuwan da Hajiya Ladi suna mai da yanda aka yi.Abu ta dubi Hajiya Ladi tana dariyar keta har da gwalo, Hajiya Ladi ya dalla mata harara yana nuna ta da yatsa alamun kashedi, ta kuma sanya dariya gami da sanya hannu a wuyanta ta ja shi alamar yanka, sannan ta nuna Hajiya Ladi. Hajiya Ladi ya saka Salati "La'ilaha illallahu, ni zaki yanka? Lallai yarinyar nan baki da mutunci, to gwara na koma na fada su zama shaida tun bamu bar gurin ba." Yana magana da karfi yana tafa hannu da buga cinya, gaba daya hankalin jama'ar dake gurin yayi kansu. Abu ta marairaice tana fadin "Dan Allah jama'a wa yaji sanda na yiwa mutumin nan magana balle har nace zan yanka shi? to muje din mana a kwatar mini hakkina tunda abin naka sharri ne, tunda dai kowa yana ji anan bance da kai komai ba." Sannan tabi bayan Hajiya Ladi da sauri dan su koma ciki tare. Hajiya Ladi ya tsaya da sauri sororo yana kallon Abu, domin dai lallai ya hadu da wacce tafi shi sharri da iya iskanci. Da zolaya Abu tace "Yaya ka tsaya mu tafi mana." Ya dallawa Abu harara yana fadin "Kwalba uwar sharri, kada ki kuma kirana da kai sunana Hajiya Ladi, idan kuma jurinki iskanci zamu kuma gauraya sai na nuna miki ke din baki isa komai ba wallahi." Ya tafa hannu gami da bugawa a cinya yana wani murguda baki da karkafa ido, ya dora da cewar "Kun ga kuzo mu bar harabar police station tun shegiyar yarinyar nan bata haddasa mana ciwon zuciya ba, kunga tafiya ta." Ya gyara daurin zanin dake bisa wandonsa gami da dane hannu yana tafiya yana wani yanga, suka rufa masa baya suna mai da yanda aka yi. Abu ta kyal-kyale da dariya gami da nufar gida. Sala tana biye da ita itama tana dariya da yi mata kirari, "Abula tawa, kowa ya ja dake yaji kunya. Mahassada kun sha kashi. Yarinya mai tsada kalar manyan maza." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 KANO 11 GA WATAN 6, 1993. Rayuwa mai sauyawa, sai dai ga Abu sauyi da aka samu kalilan ne, domin dai cigaban nata bai wuce na daina daukar abinci akanta,sai dai a dorawa dan dako tana biye dashi ba, sai kuma chalo da ta daina zuwa da dibar 'ya'yan jama'a a tafi tsokanar fada duk ta daina. Sannan kyawun ta da kirar da Allah yayi mata mai daukar hankali sun fara bayyana. Sai kuma Abu mafi girma da za'a idar bai wuce daina tallar safe ba, saboda shugabar makarantarsu ta budewa Abu wuta saboda jarabawa da aka yi ta shiga aji biyu na sakandire amman sai ya zamana Abu ce ta dauki na karshe a ajinsu, sannan ko a jikinta (wai an mintsini kakkausa). Abun ya konawa Hajiya Kubra rai, don haka ta sanya aka tara mata duk wadanda suka zo na karshe na kowanne aji, ta sanya su a gaba tayi musu kaca-kaca, sannan tace lallai sai kowacce tazo da mahaifinta domin tana son jin dalilin da ya sanya basu mai da hankali akan karatun ba har suka zo na karshe, dukkansu yaran jikinsu sai kyarma yake yi kowacce a tsorace take amman banda Abu dake ta murguda baki tana magana kasa-kasa, sarai Hajiya Kubra ta ganta amman sai ta rabu da ita da zummar idan mahaifinta yazo za tayi mata hukunci a gabanshi, haka nan suka tashi kowacce ta nufi gidansu tun lokacin tashi baiyi ba. Abu tana shiga gida babu ko Sallama bagazan-bagazan- bagazan ta yadda jaka da hijabin tana fadin, "Wallahi Sala ba zan kuma zuwa makarantar nan ba, don na gaji da masifar shegiyar principal dinmu, sai kace wata uwata haka kawai ta tsane ni." Sala ta dubeta da kulawa tana tambayarta "Mai tsada yaya akayi ne? Mai ya faru naga ko lokacin tashi daga makarantar bai yi ba." Ta tabe baki kana tace "Wai kawai dan munzo na karshe shine ta sanyamu a gaba tanata zaginmu, baki ga sauran ba jikinsu har rawa yake yi, ni kuwa duk abinda tace sai na bata amsa amman dai a hankali, kuma tama yi sa'a dan 'yan arzikin a kaina da saina rama," "Kinyi mini dai-dai, sai kuma aka yi yaya?" Sala ta katse ta. "Wai kuma duk cin mutuncin da tayi mana bai isheta ba wai lallai sai mun zo da Babanmu, ni kuwa wallahi bata isa ba ai dai ba karatun shiga Aljanna bane." Sala ta amshe "Wannan tsabar rainin hankali ne, haka kawai dan kunzo na karshe sai ace wani sai kunzo da Babanku? To ai ba laifinku bane sune basu iya koyarwa ba, ai zuwa makarantar ba dole bane kiyi zamanki kin huta da tashin safe ma." Wannan ne ya sanya Abu ta share gindi tayi zamanta a gida har kusan sati biyu bata je makaranta ba, sai rannan da Sadiku ya shigo da hantsi wajen karfe goma, shima ya dawo makaranta sai kuwa suka yi kicibis, yayi kanta da masifa yana fadin mai ya hanata zuwa makaranta. Ta zura dakin Sala da gudu dan duk iskancin Abu tana tsoron Sadiku dan bai mata ta dadi, dan babu wuya ya lakada ta. Sala ce ta fito tana hargagi gami da sanar dashi yanda aka yi. Ya kuma kulewa yace maza ta shirya ya maida ta idan kuwa ba haka ba sai dai idan ta daina fita ne wallahi sai ya karya mata kafar talla. Sarai Sala ta san halinsa dan haka ta lallaba Abu dake ta kunci ta fita suka nufi makarantar. Sanda suka isa ofishin (principal) shugabar makarantar ya dinga bata hakuri yace Babansu ne baya gari shi ya sanya ba'a kawo ta ba, shi kuma bai sani ba yana makaranta sai yau da ya dawo ya taddata a gida. Da farko Hajiya Kubra tace ba zata saurareshi ba sai dai idan ya nuna mata katin shaidar cewar shi dalibi ne I.D card, tayi mamaki sosai da taga abinda yake karantawa (Law) amman kanwarsa muguwar dakikiya. Ta bashi guri ya zauna sannan ta sanar dashi irin mugayen dabi'un Abu da kuma dakikancin ta. Yayi kwafa cike da takaici yace "Babanmu yace a baki hakuri sannan yace kafin na bar Ofis din na kiyi mata bulala guda hamsin, kuma yace daga yau kowane irin laifi tayi a daina korata gida tunda ba fada takeyi ba dan bata son karatun, a dinga bata horo mai tsanani kowanne iri ne." "Karya kake yi wallahi, yaushe har kaga Baban mu daya fada maka haka?" Ta katse masa magana da rashin kunya da hargowa. Mamaki da takaici ya kama Hajiya Kubra, wato bata bar na gida ba balle na waje ma. Shi kuwa Sadiku saboda tsabar takaici kasa magana ma yayi, sai dai yaga wata bulala a kan teburin Hajiya Kubra dan haka ya dauko ya hau zabga mata, tun tana ihu da makaleshi har ta gaza bakin nan nata sai da ya mutu, gashi babu Sala mai kwatarta ita kuwa Hajiya Kubra dama a cike take da ita dan haka ko uffan bata ce ba, daman duniya idan akwai abinda take tsoro bai wuce dukan Sadiku da na Malam ba, domin basa mata na wasa, gashi sune kadai zasu daketa a duniya su daki banza dan babu abinda Sala zata iyayi, sai dai tayi hargaginta ta gama dan ba zata iya rama mata ba, su kuma bata isa ta dauko musu 'yan sanda ba kamar yanda ta saba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yawan dukan da yayi mata ne ya sanya ran Hajiya Kubra yayi haske, ta tabbatar lallai akwai mai kwabar Abu jine kawai da bata yi. Bayan ya jibgeta ya gaji ya dubi Hajiya Kubra yace "Hajiya ki bata fartanya tayi noma da kuma wankin bandaki." Abu dake kwance tana kuka ta kuma kurma ihi tana fadin "Wayyo Sala na shiga uku kizo da kanki,A zuciye ya kuma kai mata duka a bakinta wanda ya sanya ta yin shirun dole dan sai da bakinta ya fashe, amman bata daina harararsa da murguda baki ba. Haka ya tafi ya barta saida tayi noman nan da wankin bandakin dalibai wanda yayi kaca-kaca da kashi babu kyan gani, dan saida ta daure hancinta da dankwalinta sannan ta iya wankewa, shi dai Sadiku yayi tafiyarsa, amman yasan yau bala'i sai yasha ya more gurin Sala. Ai kuwa haka din akayi domin dai data dawo gida taga idonta da bakinta sun kumbura ta zabura da sauri tana tambayar abinda ya faru. Abu ta zube a tsakar gida ta dora hannu a kai tana zunduma ihu kamar wacce akayi wa mutuwa ko kuma a sannan ake dukan nata tana fadin "Wayyo Sala na shiga uku, wallahi bazan taba yafewa Sadiku ba ko kabarinsa zai dinga balbala da wuta..." "Wai me ya faru? na san za'a rina daman, me yayi miki?" Sala ta tambaya a rude. Ta kwashe duk yanda akayi ta sanarwa da Sala tana ajiyar zuciya dan babu alamar hawaye ko kwalli a idonta. Habawa ran Sala idan yayi dubu ya baci, ta dinga sirfa masifa tana fadin "Ai makarantar ba dole bace da har za'a kama ki da wannan dukan a fasa miki baki da hanci, tunda kin iya daurin dankwali ai magana ta kare, ladan ya isa haka. Shi kuwa dan Baba zaizo ya sameni wallahi sai nayi mummunan saba masa, sai ya yabawa aya zakinta." Haka nan ta wuni tana mita kamar zata ci babu. Shi kuwa Sadiku yana sane yaki dawowa gidan da wuri sai da ya bari dare yayi ya lallaba kicin dan ya dauki abincinsa, ai kuwa tayo waje daman lambo tayi tace dawa Allah ya hadamu, donma dai ya wuce duka ne da ranar sai yasha duka a gurin Sala, shi kam ko kala baice ba da yaga ba'a ajiye masa abincin ba ya juya ya fice. Ta bishi har zaure tana fadin "Babu zuciyar nema sai ta ci, ita dai wacce ka tsana din ce ke nemo abinda kake ci kuma wallahi ko ruwa ba zaka sha a gidan nan ba, idan kayi zuciya ka siya, wanda na san ko sisi baka da shi baya ga tarin takardu da bakar zuciya." Shi dai dakinsa ya shige ya kwanta ranar haka ya kwana da yunwa, ita kuwa saida ta kusa kwana tana mita. Wannan shine sanadiyyar daya sanya dole aka daina tallar safe, domin dai Sadiku yace duk sanda tayi laifi a daina turata gida tayi noma da wankin bandaki, abinda ta tsana a rayuwarta, ya kuma rantse idan ta daina zuwa makarantar sai ya ballata yaga da kan da kafar da zata yi tallan, dole kanwar naki aka hakura da tallan safe dan ta dinga zuwa da wuri. Da farko Sala tace bata yadda ba amman ganin da rana ma ana samun ciniki mai yawa kuma ita Abu tana tsoron bala'in Sadiku ya sanya dole suka hakura, sai dai su Karima suyi tallan safen kafin su tafi makarantar, amman ita da yake ba irin halinsu daya da Abu ba takanyi hanzari ta saida ta tafi makaranta, domin ita halinsu kusan irin na Sadiku ne shiya sanya basa shiri da Sala sosai kullum tana mata fada da cewar mai kan kwantai. Misalin karfe biyu na rana ta fito daga gidansu dan dakonta yana dauke da fantekar abinci da kwanuka da miya a kansa, ita kuma tana rike da farin bokitin roba mai haske an yanka salak da tumatir da albasa, daya hannun kuma kaji ne soyayyu cikin irin farin bokitin, anyi wanka an ci kwalliya, zanin nan an daurashi kwauri a waje anja jagira lebe yasha jambaki da baki, sai dai anyi kilin an daina dige-dige da kwalli, hatta takalmi dan madina dake kafarta yasha wanki sai sheki yake yi, ana tafe dagwas-dagwas kamar mai jin tausayin kasa, domin tun can daman Abu akwai tsafta da kwalliya balle yanzu da aka fara zama 'yan mata, gwalli da feleke ya karu, duk cikin kawayenta tafi kowa iya tsara kwalliya, daman gata ba baya ba gurin kyau. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 zandakata a nan,insha Allahu Zuwa yamma zamu dora,domindai aikin Littafin yayi bisa,Wata tangarda ce ta hanani farayimuku a ana,nagode.. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Idan Zuciya Tagyaru 1-02 Posted by ANaM Dorayi on 05:26 AM, 28-Jan-16 Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU _________________ Na ________Fauziyya D Sulaiman____ Mustafa dake zaune kofar gidansu bisa farar kujera karkashin bishiyar Umbrella, yana karatun jarida kamshin Abu ya bugi hancinsa ya daga kansa da sauri yana dubanta, kusan sati guda kenan yake ganinta tana wucewa irin wannan lokacin, kwarai yarinyar ta kwanta masa a ransa, da kuma dai alamun ba za'a sha wahalar samun kanta ba, kullum yana son yi mata magana amman ya rasa ta yanda zai fara, yau dai dabara ta fado masa dan haka ya fara kwala mata kira. "Ke! Ke mai abinci! Kawo." Ta tsaya turus gami da waigowa tana dubansa, domin bata saba saida abincinta cikin unguwa ba sai ta dangana ga tashar kofar wambai, amman sai taga yayi mata kwarjini ba zata iya kin saida masa ba, domin dai abincinta sai wanda taga dama take saidawa, don haka ta hau kwalawa almajirin dake dauke da abincin kira "Kai Mudi! Kawo abincin za'a siya. Babu musu yayo ribas ya juyo, ya isa gaban Mustafa wanda ke zaune akan farar kujera mai tambarin kamfanin coca-cola ya tsaya kerere. Ta galla masa harara tana fadin "Kai fa tamkar jaki kake komai sai ance kayi zaka yi ko? To sauke kayan." Sannan ta dubi Mustafa tace "Malam na nawa za'a zuba maka?." Yayi wani mayaudarin murmushi yana mata wani duba na yaudara da kwarewa a harkar iya soyayyar 'yan zamani yace "Haba 'yan mata babu ko gaisuwa?" Tabbas yayi masifar yi mata kwarjini, hasalima tunda suka hada ido taji wani abu ya bugi zuciyarta wanda ya sanya ba zata iya yi masa musu ba ko rashin kunya, shi kansa ya gano hakan a kwayar idonta ya kuma san haka nan Allah yayi masa kwarjini da farin jini ga kowa, domin dai da wani ne cewa zatayi, ban iya ba ko kuma tace baka kai matsayin da za'a gaidaka ba din ne, amman shi sai ta tsinci kanta da ce masa "To ina wuni?" Yayi dariya yace "Ko ke fa, lafiya kalau, yaya sunanki ne, dan kallon farko naga kin mini dari bisa dari." Ta kosa da zancan nasa ta daure dai tace "Ka ga sauri nake kada rana tayi mini, na nawa za'a baka? Dan kada kaja nayi kwantai." Ya kuma murmushinsa dake kashe mata jiki yace "Haba dai, ai kyawawa basa kwantai, ko domin kyanki ai a sayi abincinki." "Ka ga nifa zan wuce kana bata mini lokaci, wallahi dan kaine kawai na tsaya." Ta fada tana yamutsa fuska. Ya kanne mata ido daya yace "Haba dai ke kya soma tafiya ban san sunanki ba? domin dai zaman nan naki ne, dan tun randa na fara ganinki Allah ya dasa mini tsiron sonki a raina wanda kullum yake kuma girma, dan haka nake zama kawai naga wucewarki naji dadi. Ta dubeshi cikin ido, yanayin kallon da yake mata ya kashe mata jiki ta gaza masa komai, amman sai ta dubi Mudi da ya baza kunnuwa kamar na zomo yana sauraran abinda suke fada tace "Mudi dauki mu tafi yana bata mana lokaci." Mudi ya yunkura zai dauka amman sai Mustafa ya dakatar dashi yana fadin "Kai ajiye, maza nemo 'yan uwanka almajirai ka raba musu, kyaky-kyawa kamarki ai kin wuce tallan shinkafa, ke fa gimbiya ce." Yana maganar yana dubanta da wani kallo daya bambanta da wanda samarinta kucaku ke mata. Mamaki ya cikata amman sai ta gaza cewa komai tayi shiru kawai tana dubansa. "Kaje mana ka kira 'yan uwanka ka raba musu ka baza kunnuwa ka saki baki sai kuda ke fadawa." Yace da Mudi wanda ya saki kunne da hangame baki yana dubansu. Mudi dai gani yake kamar da wasa yakeyi, amman da yaji ya doka masa tsawa ya kuma nanata masa ya sanya ya fara kwalawa 'yan uwansa kira. "Alalan Alalan almajiri, Alalan Alalan kazoo kaci, Alalan Alalan Alalan kai ba tumatiri." Ai kuwa nan da nan gurin ya cika da almajirai, yace "To maza abi layi." Ya kalli Mustafa dake kallon su. Mustafa yace "Ka rarraba musu mana." Ai kuwa nan da nan ya fara zubawa almajirai kafin kace kwabo sai fanteka da bokitin salad. Abu na tsaye rike da kugu cike da mamaki tana kallonsa, lallai wannan mutumin dan rikice ne, ko tambayarta kudin abincin baiyi ba yasa aka raba, zata yi maganinsa kuwa yau, don wallahi sai ta tsuga masa kudi masu yawa. Ya dubi Mudi yace "To maza a hada kayan a koma gida uwar dakin naka zata taho yanzu." Sai da yaga Mudi yayi nisa sannan ya dubeta na dan wani lokaci tana tsaye rike da kugu da alamun mamaki da shakka a fuskarta. "Adon gari tunanin me kike yi? Har yanzu baki fadi mini sunanki ba." Ta yamutsa fuska tace "Sunana Abu......" "A'a babban suna Zainabu Abu mai tagwayen suna kenan, gaskiya Zainab baki dace da kalar tallah ba, dubeki fine baby ace kina daukar tallah? to gaskiya ni dai daga yau na soke tallar nan." Ta dubeshi a tsiwace tace "Ka ji mu da mutum sai kace wani Ubana? ko kai ne zaka dinga biyana kudin da nake samu eye?" Yace "Eh mana zan dinga biya ko nawa ne, don gaskiya bana son rana tana taba mini kyaky-kyawar fuskarki, kyanki hutu Zainabu." Ta tabe baki don zancen bai gamsar da ita ba, don tasan bai san yawan kudin bane shiyasa yake wani cika baki amman yanzu zata yi maganin firiritarsa. Don haka tace "Ka ga ka cika ni da surutu bayan baka biyani kudin abincina ba." Yayi dariya yace "Haba Zainab, baki yarda dani ba naga alama, ko don kin ganni da dan wando jeans da shet? kin san mu 'yan boko bamu san kaya masu nauyi, amman nawa ne kudin? Kila idan na baki hankalinki yafi kwanciya." Ta murguda baki wanda ya zame mata kamar al'ada sannan tace "Dari uku da ashirin da biyar ne, sai nama na naira talatin da biyu...." "A'a Zainab, duka zaki hade mini?" Tayi dan duru-duru don tasan zulake tayi duka kayan nata basu wuce na dari biyu da tamanin ba, don haka ta kasa hadewa ta fadi don bata iya lissafi ba (bata da Maths tab akin yara), da ya fahimci halin da ta shiga sai ya zura hannu a aljihunsa ya debo 'yan murtala (Naira Ishirin) har na dari hudu yace, "Ga dari hudu ma ni na kara miki." Mamaki ya cikata matuka, hannunta har rawa yake yi gurin karba don tana ganin kamar zai maida yace ya fasa ne. Sai da taji dumin kudin a hannunta sannan hankalinta ya kwanta ta dube shi da mamaki tace "To nagode! Zan tafi gida." Yace "A'a ai dole na yiwa gimbiya rakiya ko don naga gidansu." A wannan karon bata yi masa musu ba don yayi mata ba zata, don haka suka nufi hanyar gidansu, a kofar gida yayi mata sallama yace sai gobe tace Allah ya kaimu. Ta shiga gida da gudunta Sala na zaune tayi tsuru cike da shakkun labarin da Mudi ya bata, gaskiya tafi zargin bari kawai suka yi yace wani wai juye wani saurayi dan gaye yayi mata. Abu na shigowa ta mike da zakuwa tace, "Ke maza sanar dani menene ya faru?" Abu tayi dariya gami da nuna mata kudin da saurayin ya bata, ta fizge daga hannun Abu da azama ta hau kirgawa, Abu kuwa sai dariya takeyi. Sala ta kammala lissafawa ne ta dubi Abu cike da farin ciki tace "Diyar arziki yau kuma wane mai arziki kika hadu dashi? Kai wannan diya da kan arziki kike, shi ya sanya aka tsangwameki a unguwar nan, ki dubi yadda su Sarai da Sakina kawayenki suke kwantai kullum sai sun dawo da ragowar abinci, sai dai a cinye ko kuma akai dakalin 'yan kwantai da daddare abincin naira biyu a karyar dashi naira daya koma sis daya. Abu tace "Bari ke dai Sala, ni tunda nake ma ban taba haduwa da mutum mai ban mamaki irin wannan ba." Sala tace, "Yaya ne sunansa?" Ta tabe baki tace "Oho!!! Ni ko tambaya ma banyi ba." "Kiji sokuwa, arziki yana kiranki kina masa kutufo, to gobe ki tambayi sunansa kuma ki saki jikinki dashi, kin san su irin wadannan basu son ki dinga dari-dari da su, idan abin ma gaba daya....." Abu tayi dariya gami da shigewa dakinta. … Allah ya shirya. Washegari ma haka ce ta faru, Mustafa yayi mata juye ya rako ta gida, sai dai wannan karan ya tsaya sun dan taba hira duk da ya lura sokuwa ce sam bata waye ba, da kuma alama girman jiki ne kawai da ita babu shekaru, sai dai ko menene shi dai yaji ya gani yana kuma so a haka. Yau da gobe sabo da shakuwa ya shiga tsakaninsu har ya zama an daina fita da abincin ko ina sai dai a bawa almajirai a gida. Abu an daina fitowa kamar yadda Mustafa yace bai son kyaky-kyawar fuskarta ta baci da zafin rana don haka tana gida kullum. Wani abu kuma da Mustafa ya koya mata shine cin dadi, yanzu abincin kala-kala take ci ba irin wanda take ci ada can ba, ga kaya da yake kawo mata na kwalliya da na sanyawa, sai ga Abu ta kuma futowa fes da ita kuma yanzu da motar Babansa ma yake zuwa zance gurinta ko ta Mamanshi don haka cikin motar suke zancensu. Ta futo daga wanka tana tsakar gida bisa tabarma da kayan kwalliya a gabanta ana ta kwalliya da hasken wutar nefa, dan Mustafa na gab da zuwa, Sala ta zauna daga bayan ta tana kallonta cike da murmushi tace, "Kai diyar nan wallahi akwai ki da kwalliyar daukar ido, dubeki kamar wata sarauniya. Ai ba don bamu gama cin kudin ba da kin auri yaron nan don ya dace dake, ga kyau ga kudi, sai dai na lura kamar dai iyayensa ne masu kudin ba shi kansa ba ko?" Abu ta tabe baki tace, "Oho! Ni ban sani ba, ke idan banda abinki ma Sala yaushe na isa aure? Ni yanzu ma sai nayi digiri, don Mustafa yace mace idan tayi ilimi wai tafi kyau da tsada. Ni fa yanzu Sala dan-na-sanin talla ma nake yi, ki dube ni ki gani yanzu kamar wata diyar wani basarake." Sala tayi shewa gami da rangada guda tace, "Kai Allah nagode maka, ai abinda nake ta nusar dake kenan tun da can, ki sami samarin da zasu dinga kashe miki kudi mu huta da tallan, yanzu ba gashi munyi kyau ba? Ga kudi suna shigowa, wannan shegen yayan naki yana saka mana ido." Ta ja tsaki, "Mtsw! Wallahi idan ya sake sai nayi masa baki, wai har ni zai kalli idona yace mini sai Allah ya tambaye ni duk abinda muke aikatawa, wai don kina zance a mota, wai 'yan unguwa sai zarginki sukeyi gashi kin daina talla ma a ina kike samun kudi yanzu? Nace a gidan ubansa. Sai fa da nayi masa wuta-wuta sannan na samu ya fice daga gidan nan, kuma nayi masa barazanar duk randa ya kuma shiga shirginki sai na tsine masa, idan muka biye ta tashi zamu rayu ne? Da yanzu mun mutu, Mtsw!" Ta kuma jan tsaki. Abu ta hasala ta murguda baki gami da tsiro shi gaba tace, "Ki fita harkarsa kawai Sala, na lura talauci ne ke damunsa, kuma wallahi yayi sa'a shi yayana ne da wallahi 'yan sanda zan dauko masa." Sala tace, "Ai bake ba ni kaina ba don gudun abin kunya ba da saka ido irin na tsinannun mutanen unguwar nan, da wallahi sai na hadashi da 'yan sandan sun lallasa mini shi." Sallamar da wani yaro yayi ce ta katse musu hirar tasu tamkar wasu kawaye, su kuwa sauran kannan nata duk sun bazama tallar gyada a can kofar gida. "Kai!! Meye ka ishemu da sallama?" Sala ta katse shi cike da haushin katse musu hirarsu da yayi ba tare da ta kai aya ba don ko amsa sallamar ma bata yi ba. "A'a daman wani ne a mota ke sallama da Abu..." "Au! Yi hakuri na hauka da fada, kace tana zuwa dan albarka, ka ji?" (HMMM) Yaron ya fice yana fadin to. Ta dubi Abu da ta mike ta nufi daki don sanya kaya tana dariya tace, "Yau dai naga kwalliyar nan ta daban ce, kiyi sauri kada ki bata masa lokaci." Ita dai bata ce komai ba ta shirya ta fito sai kamshi take yi, kai tsaye ta fice ta nufi gurin da Mustafa yake, yana hango ta ya bude mata gaban motarsa wato kusa dashi sai wani malalacin murmushi yake mata na tsananin yaudara irin na gogaggun samari, ita kuwa sokuwar sai wani kara zobara baki takeyi tana wani yauki har ta shiga ciki ta zauna tana wani fari kamar 'yar tsana. Ya shaki kamshinta gami da lumshe ido, cikin mayaudariyar muryarsa yace, "Kai Zainabu, kin yi kyau kamar wata sarauniya." Tayi dariya cike da jin dadi tace, "Haka ma Sala tace wai nayi kyau sosai." Yayi murmushin jin wautarta, Ya riga ya gama karantar halin Abu da Sala, don haka ya san ba zai sha wahala gurin samun hadin kan Abu ba, don haka ya mika hannuwansa ya kamo hannun Abu yana wasa dashi yace, "Kai yatsunki akwai ban sha'awa, dube su zara-zara. Dadi ya kuma cika ta na yabon da yake mata tace, "Haka kowa ke cewa, wai yatsuna da na hannu da na kafa suna da kyau kamar ba nawa ba." Yayi dariya yace, "Gaskiya haka ne, amman kyanki ai yaci suma suyi kyau." Cikin dabara ya jata jikinsa yana fadin, "Ya dace dai yau na shaki kamshin nan naki da kullum ke ruda ni." Ga mamakinsa sai yaga Abu ta saki jikinta har ma tana kokarin taya shi, abin ya bashi mamaki don yayi zaton sai yasha wuya zai sami kanta, sai gashi ya same ta a ruwan sanyi, amman sai ya danne ya dinga aiwatar da mugun nufinsa da zuciyarsa ke ingiza shi. (Allah ya kiyashe mu da aikin assha. amin). Da ya tabbatar ba zai sami wata matsala da Abu ba, sai ya lankwashe murya yace, "Abu ko zaki rakani wata 'yar unguwa?, daga can kin ga sai mu wuce nayo miki siyayya ko?" Tace "Babu damuwa muje kawai." Ya dubeta ta dan hasken dake cikin motar na farin wata da ya shigo yace, "Kina ganin babu matsala idan Sala ta aiko bata ganki ba? dan kada tayi fada." Ta tabe baki tace, "Kada ka damu ba zata ce komai ba tunda dai ta san siyayya zaka yi mini, kuma ta san ai muna tare." Yaji dadin abinda tace dan haka ya tada motar gami da karo sautin wakar dake fita a cikin rediyonsa, muryar Bob Marley ce a wakarsa ta One Love, duk da Abu bata jin turanci wakar tana mata dadi musamman da yake koda yaushe za kaji kaset din Bob Marley Mustafa ke sanyawa, har ma ta iya bin wakar tana girgiza kai duk da ba daidai take fadin wasu kalmomi ba. Suna tafe a hanya suna hira har suka isa wani hotel, kasancewar kaurin sunan da hotel din yayi baka ganin jama'ar kirki a cikinsa domin kada sunansu ya baci, wannan ya kara baiwa 'yan iska damar cin karensu babu babbaka, gurin shiru babu alamun jama'a, sai ka shiga daga ciki zaka ga kamar tsakiyar rana ce dan haske da tashin kida. Ya dubi Abu yana murmushi yace, "Zainabu ya dace mu dan tsaya a nan musha lemo mu huta, kafin na wuce yi miki siyayyar domin har dan kunne da sarka na gwal zan sai miki, kema ki shiga sahun manyan mata ko?" Yana mayaudarin kallonsa yake maganar. Tayi dariya cike da jin dadi tace "Babu damuwa." Ya sami guri ya faka motar tasa, ya bude ya fito sannan ya bude mata ta fito suka jera, Abu jin kanta take yi da girma saboda ta fito daga mota, a ganinta ta gama cinyewa. Sanda suka isa cikin reception din hotel din sai ta kama zare idanu cike da kauyanci, domin tunda take bata taba ganin guri mai kyawun wannan ba, ta saki baki galala tana kallo ga hasken wuta ga fankoki suna juyawa ga A.C da Tibi, ga 'yan mata nan kala-kala kowacce da shiga ta rashin mutunci, sai taji ta raina kanta, lallai ta yadda da Mustafa da yace zai nuna mata rayuwar 'yanci da wayewa, gashi kuwa ta fara gani. Sai ta kama muzurai kamar ta koma gida ta sanyo atamfarta Wagambari da tafi kowacce kyau da tsada, amman sai taga ai ko ta sako ba zata yi kyawun wadannan ba, ta shagala da kallonsu tana fadin dama itace wannan, can kuma idan taga wata sai taji tafi waccan tace, kai waccan zan zama, shi kuwa yana can yana biyan kudin dakin da zai kama musu. Ya kammala ya amshi makulli ya nufe ta, sai yaga sam hankalinta baya tare da ita har hannu take sanyawa tana taba duk abinda ya burgeta, ya kama hannunta suka nufi dakin da ya kama musu. Sanda suka shiga dakin kuwa sai labari ya sha bamban, sai taga ai can wajen ma ba'a sanya komai na more rayuwa kamar nan ba, ta fada kan tumemiyar kujerar dake falo da karfi tana fadin, "Kai bari muga za ta loma kuwa?" Ta saka wata dariya ganin ko motsi sosan baiyi ba, can idon ta ya hango mata wani gilas dake dauke da ruwa da kifaye da wasu 'yan kananan bishiyoyi, ta mike da sauri ta isa gurin, ta saki baki tana kallo da shafawa, can ta kuma fashewa da dariya tana fadin "Wallahi kifin da ransu kuma yawo suke kamar a teku." Shi kam Mustafa yayi tsaye yana dubanta, hannuwansa cikin aljihu yana dariya saboda ganin irin kauyancin da take yi, lallai ya kuma tabbatarwa Abu sokuwa ce mara wayo, sai dai rashin kunyar, domin da ace tana da wayo ba zata yi wannan kauyancin ba, ko kuma dan bata da wasu shekaru da yawa ne? Can ya hango ta tana kiciniyar bude wata kofa sai turawa take iyakacin karfinta. Ya karasa yana dariya yace "Dakin bacci ne, bari kiga yanda ake budewa." Ya kama marikin kofar ya murda a hankali sai gashi ta bude. Ta kuma bude baki cike da mamakin ganin wani irin katon gado kuma dan karami ba irin na Sala mai rumfa ba, ta nufi gadon da gudu tayi tsalle ta fada tana kyalkyala dariya har da rike ciki tana kuma birgima. Can kamar wacce aka kuma tsikara sai ta kuma mikewa da sauri saboda hango wata kofa da tayi ta san lallai wani abin kallon zata kuma gani, wannan karon bata sha wahala ba ta bude domin taga yanda ya bude waccan, ta rufe bakinta cike da tsananin mamaki taca cewa "Na shiga Uku ni Abula, menene wannan kuma?" A cikin kunnenta taji yana mata rada, "Wannan bandaki ne gurin wanka irin na 'yan gayu, idan kina son irinsa zan gina mana." Ta juya tana dubansa da mamaki dan bata yarda da abinda yace ba, yaya ma za'a yi aga bandaki a cikin daki kuma ga wasu irin abubuwa a ciki kamar daki ma? Ya daga mata kai alamar haka ne da gaske, ta nufi gurin kwamin wanka ta shiga sai ya sakar mata shawa, ta firgita ta fito da gudu tana ihu,ta kankame shi domin ta firgita, ya fashe da dariya. Lallai Unguwarsu da manyan gidaje amman bata taba shiga ciki taga yanda suke ba, domin ita kam bata iya jure wulakanci ko kaka yake, su kuwa 'ya'yan masu kudin unguwarsu wulakanci ne dasu, sam basu kula su ko fita zasu yi ma sai dai a mota, shi kansa Mustafa sanda ya fara cewa yana sonta tayi mamaki sosai, sai daya dinga yi mata kalamai masu dadi da yaudara sannan ta yarda, har yana cewa shifa so babu ruwansa da mai kudi da talaka duk yana shigarsa, da haka ya samu kanta dan wani lokacin har mamakin kanta take yi data afka son wanda ta tsana a da can. Tasha yiwa motocin jama'a faci domin ta tsani gudun da sukeyi a layin suna kade kaji da akuyoyi wani lokaci harda mutane, idan anyi magana sai su biya dan suna da kudi, sai da takai duk kofar gidan da aka ganta sai an koreta domin idan ta kullawa mutum duk sanda taga mota a kofar gidansa koda ta baki ce sai ta koma gida ta dauka kibiya ta kitso ta sossoka a tayoyin, dan masu gadin da sun ganta zasu bita da bulala. Ya janye ta yana dariya saboda yanda ya ga ta tsorata yace "Bari naje na samo mana abinci da dan ruwan lemo." Bata ce masa komai ba illa tafiya da tayi gurin wani abin tana tabawa. Ya dawo dauke da wani katon faranti mai dauke da abinci da manyan kwalabe na giya (wa iyazu biLlahi) ya ajiye bisa tebur din dake falon kana ya shiga ya kirawo ta, da kyar ya samu ta baro bandakin tana cewa ya tsaya tana kallo, yace In dai kina son kallon kullum zan dinga kawo ki." Dadi ya cikata, da wannan dabarar ya samu ta futo. Abinci ya mika mata mai dauke da naman kaza zuku-zuku, ta amshe kuwa da azama ta fara ci, shima yaja nasa farantin yana ci yana kallon ta yana dariya ,Can ya dauko kwalbar Shandy dinsa ya bulbula a kofi ya kafa kai ya kyankyama ya dire kofin. Ta dubeshi da mamaki a tsorace tace, "Kai Musty (haka take ce masa) Giya ce fa? ba zata bugar da kai ba? Naga dan tasha idan ya sha yayi ta maye har kwata yake fadawa." Yayi murmushi gami da lumshe idanuwansa kana ya bude a hankali, "Ai shi karamar giya yake sha wato burkutu shi ya sanya yake maye, amman wannan original ce wato mai kyau din ce, bata sanya maye bari na zuba miki ki sha kiji." Ta manne kafada da sauri tana fadin "Kai bana sha tsoro nake ji ni dai." Yace, "Haba dai tawan don Allah kisha wallahi ba zaki bugu ba sai dai kiji karfi." Da kyar ya samu ta sha kofi guda, can kuma sai ta wawuro kwalbar ta kafa kai ta dinga kyankyama, ta dire kwalbar bisa tebur din. Ya fashe da dariya gami da tafa mata yana fadin Wonderful, wato mamaki ta burge shi, ya zira hannu cikin aljihunsa ya zaro tabar shedan wato wiwi) ya kunna ta ya zuka kana ya mika mata, wannan karon batayi gardama ba ta amshe da azama ta zuka domin bata cikin hayyacinta, sai dai zuka daya ta kware ta kama tari, ya tashi da sauri ya nufe ta yana rike ta har tarin ya lafa. Amman don ta saba maimakon ta hakura sai ta kara zuka don abin ita sha'awa ma ya bata, don ta dade tana sha'awar yanda ake shan taba musamman idan taga wanda ya kware mai fesar da hayaki ta baki ta hanci. Dadi ya kama Musty sai ya kuma zaro wata cikin aljihunsa ya kunna ta ya hau zuka. Ta fashe da dariya karan tabar na tsakiyar yatsunta guda biyu shima ya taya ta suka dinga dariyarsu da zukar tabar shedan din har suka gama, sannan ne kuma Abu ta soma tangadi tana zage-zage da yarfe hannuwa. "Wallahi karya ne! Babu wani sauran shege da zai raina mana hankali wallahi! Ha-ha- ha." Ta fashe da dariya. Ya isa inda take da azama yana fadin "Kwantar da hankalinki yarinya." Ta fada jikinsa shabar tamkar kayan wanki, ai kuwa ya sami yanda yake so don haka ya shiga aiwatar da mugun nufin da zuciyarsa ke kintsa masa, da fari bai samu matsala ba sai da abu yayi nisa data fara jin zafi sannan ta nemi kwace kanta, amman da yake a buge take hakan bai samu ba har sai da ya cimma burinsa a kanta (Wa'iyazu billahi). Duk irin iskancin Abu da gantalinta namiji bai taba aike mata kai tsaye ba don tana tsoro da gudun kar aji mata ciwo, ko su Dan Oga da dan tasha da suke siyan abincinta, basu taba samun hadin kanta haka kai tsaye ba sai Musty, yau ya samu daga sama don haka shine mutum na farko da ya fara sanin Abu diya mace, abunda ba zata taba mantawa ba a kundin tarihin rayuwarta. A nan bacci ya dauke su don duk cikin su babu wanda ke cikin hayyacinsa. Basu ankara ba sai da gari ya waye tangararau, sannan suka farka a firgice Abu ta saki kuka da ta tuno abinda ya faru a daren jiya, shi kuwa Musty kwantar da kansa yayi ya dinga bata hakuri harda guntun hawayensa, karshe dai yayi mata alkawarin kaya da zai sai mata kala-kala har ya samu ya shawo kanta don ya lura muguwar kwadayayyiya ce, ya samu ya lallaba ta ya hada mata ruwan dumi cikin bahon da tayi kauyanci daran jiya ta shige ciki. Shigar ta bandaki da kuma tuno irin alkawarin kayan da yace zai siyo mata ne ya faranta ranta har ma ta daina ganin aibun abinda suka yi din, don haka da kwarin gwiwarta ta fito shima ya shiga don ya shirya. Sanda ta kammala shiryawa ne gabanta kuma ya soma dafuwa tana tunanin me zata ce da Sala yanzu don ta Babanta sam bata jinsa, domin sam ba zai lura bata gidan ba, domin bai shigowa gidan sai dare ya raba, haka nan daga gurin Sallar Asuba yake wucewa majalisarsu, idan ka ganshi a gida da rana to lallai Alhazan da suke wa a dawo lafiya sun kawo musu zakka zai zo yaci abincin rana a kudinsa, yakan ce sai ya ci guminsa wai, sai kuma jarababban yayanta da take tsoro kada ya gane bata kwana a gida ba. Ya fito shima ya gama shiryawa, ya dubeta sanda suke karya kumallo sai ya ga ranta har lokacin a bace yake, gabansa ya shiga faduwa domin shi yanzu ma yaji ya fara sonta, don haka ya kwantar da murya ya kamo hannunta yana fadi, "Wayyo masoyiya ta, mene ne? Har yanzu fushin ne? Ko baki huce bane?" Yanda yake maganar ya kashe mata jiki, ta dinga jin soyayyarsa da kaunarsa suna ratsa jikinta, ga wani shaukinsa, ta kwantar da kai tace, "Wallahi na huce, ina dai tunanin yanda zan sanar da Sala ne, don ka san ban taba kwana a waje ba." Ras! Ras! Shima gaban sa ya fadi don sai yanzu ya tuna ya fito da motar Mominsa gashi ya kwana, me zai ce mata yanzu? Lallai yasan zai sha fada a gida, amman sai ya dake domin dai yanzu matsalar Abu ce a gabansa. Ya kuma kwantar da murya yana wasa da hannunta yace, "Kada ki damu za muje nayi miki siyayya ta ban mamaki wacce zata faranta ran Sala din, na san ba zata yi fada ba muddin taga kayan, ga kuma kudi da zan baki, kada ki damu kinji ko?" Tayi ajiyar zuciya gami da cewa, "Shi kenan." Wani katon kantin sayar da kaya suka je. Bayan sun shiga yace ta zabi duk abinda take so. Lallai kam yaga hauka domin dai haka ta dinga jidar kaya kala-kala tana sanyawa cikin dan keken da suke turawa har sai da taga babu gurin da zata sa ta hakura, dan wani abun ma sam bata san amfaninsa ba take dauka, in dai taga kwalin yayi mata kyau to an gama, domin har abin aski na maza sai da ta dauka, shi dai binta kawai yake yi da kallo cike da mamaki, amman bai ce komai ba domin dai lallaba ta yake yi kada yayi magana yayi laifi. Da suka isa gurin biyan kudin aka lissafa aka gaya musu, kudin tsababa ne amman shi ko a jikinshi domin dai yasan ta cancanci ya sai mata abinda yafi haka ma. Ita kuwa 'yar jidalin wani kallo tayi wa mai karbar kudin tana fadin, "Kai malam dan wannan kayan ne zaka tsugawa wannan kudin wanda yafi na buhun shinkafa 'yar gwamnati? Kawai kayi mana ragi idan ba haka ba mu fasa saya wallahi." Ta karasa maganar tana tafa hannu da doka cinya. Kunya ta kama Mustafa dan dai ta nuna cikakkiyar 'yar kauye ce ita wacce bata taba zuwa irin wannan wajen ba. Ya dubi mai karbar kudin sanda yake ajiye masa kudin yace, "Ka yi hakuri daga kauye aka kawo ta." Cikin harshen turanci yayi maganar dan haka sam bata ji abinda yace ba. Mai karbar kudin yace "Babu damuwa." Tana kallo ya biya kudin don ma kada tayi magana ya kama hannunta suka fice yana fadin ma'aikatan su biyo shi da kayan, kamar jira ake su fita sai wadanda ke gurin suka kama dariya. Tana daga can ta hango suna mata dariya dan haka ta kutuntuma wani zagi tana fadin, "Lallai ma wadancan mutanen 'yan rainin wayo ne, ni sukewa dariya? Wallahi bari naje nayi maganinsu." Ta nufi gurin nasu da sauri. Ya riko hannunta yana fadin, "Haba Zainabu na kada ki mai da kanki 'yar kauye mana, ki zama wayayyiya." Tayi kwafa tana dubansa tana huci tace, "Wallahi sunyi sa'a da yau sun gane kurensu, ni kawai ka fasa siyan kayan ma ka bani kudin kawai na rike abuna." Yayi murmushi yace, "Don Allah kiyi hakuri in dai kudi ne zan baki." Da haka ya lallaba ta suka saka kayan a mota suka wuce gida. Bayan sun shiga motar ta turo baki gaba tana fadin, "Gaskiya wadannan mugaye ne, dan wannan kayan zasu ce kudinsu kenan, wallahi zai sayi buhun shinkafa har da na wake ma, kai zai iya kai mutun Makka da Madina ma." Dariya ta kwace masa har yana dukan sitiyari yace, "Kai Zainabu akwai ki da wauta wallahi, koma dai nawa ne yawan kudin ai kinfi karfinsu a gurina, fatana dai kawai ki dinga bani hadin kai, zaki zama tauraruwar mata gagara-gasa a cikin unguwarku, zaki zama abin kwatance." Ranta yayi fari kal! Amma bata ce komai ba har suka isa kofar gidansu ya tsaida motar. Ta dubeshi bata ce komai ba amman ya lura da fargaba take yi dan haka yace, "Kin ga kada ki damu tsaya kiga dabarar da zamu yi." Ya bude motar ya fito ya kirawo wani yaro yace maza ya shiga da kayan cikin gida zai bashi lada, nan da nan yaron ya fara jidar kayan yana shiga dasu cikin gida, su kuwa suka cigaba da hirarsu, har saida yaron ya gama shiga da kayan ya sallame shi. Ya dube ta da salon da yake kashe mata jiki yace, "Yaya dai Zainabu ina fatan babu matsala." Bai jira ya ji abinda zata ce ba ya zura hannu cikin aljihunsa ya zaro wata sabuwar ambulan mai dauke da sabbin murtala (N20) ya mika wa Abu yana fadin, "Ga wannan kyautar faranta mini rai ce, sai da daddare idan na dawo." Ta fizgi kudin da sauri kamar wani ne zai kwace, ta bude murfin motar babu ko sallama ta fada gidansu da sauri. Ya girgiza kai cike da dariya sannan ya tuka motarsa ya nufi gidansu amman gabansa na faduwa dan bai ma san irin karyar da zai shirya ba. Abu ta fada gidan babu ko sallama kamar wacce aka hankada, a tsakar gida ta tadda su Sala da kannanta suna kallon kayan da aka shigo dasu, fuskar Sala cike da annuri. Tana shigowa Sala ta mike da azama ta rungume ta tana fadin "'Yar albarka, jiya sam banyi bacci ba na dinga darura da sake-sake ko 'yan yankan kai ne suka yi gaba da ku, sai yanzu da naga ana shigowa da kayan nan hankalina ya kwanta nace na san dare ne yayi muku a inda kuka je kuka ki dawowa saboda 'yan sa ido, ai gwara da kika kwana a can din ma dan baki ga yadda jarababban yayanki ya dinga sintiri ba, sai da nace masa kina daki kina bacci sannan ya hakura ya kwanta, shi ya sanya na dinga fargaba kada ki dawo ki buga kofar yaji ya hau surutu da wa'azin nashi tamkar dan sarkin Limamin Makka." (Kuji fa irin wannan Uwa, wacce ya dace a ce hankalinta ya tashi saboda kwanan da diyarta tayi a waje amman ko a jikinta saboda tsabar kwadayi da son duniya, Allah dai ya shirya). Abu kam da taji abinda Sala ta fadi sai taji hankalinta ya kwanta, don haka ta share karya da ta shirya da zata fada, cewar wai mota ce ta lalace musu a hanya da suka dawo daga siyo wadannan kayan, sai da gari ya waye sannan suka sami masu gyara. Sai kawai ta dauko kudin da ya bata na ambulan tana fadin "Sala har da kudi fa ya bani." Sala ta amshe da sauri ta kama kiciniyar farke ambulan din ta hau kirgawa, Naira dubu biyu cif! Nan fa suka kama tsalle da murna Sala tana fadin, "Kai wannan yaro dan arziki ne, dan haka Abu ki rike shi da kyau, Ubangiji ya sanya ya gama da duniya lafiya." Haka nan suka dinga murna, ranar nan dai ko abincin sayarwa Sala bata dora ba. ga Abu kuwa wannan daurin gindi da ta samu daga gurin Sala shine ya kaita ga fandarewar da duk wanda yake da hannu gurin lalacewar tata sai yayi da-na-sani wata rana, rana mara alkhairi a kansu gaba daya, da-na- sani mara amfani. (ALLAH YA KIYASHE MU DA SHARRIN SON ZUCIYA, WANDA BAHAUSHE YACE “BACIN ZUCIYA” Ameen) KANO: 22|12|1993 Rayuwar Abu gaba daya ta sauya daga fari zuwa baki, idonta ya kuma budewa da harkar banza, domin wannan dan lokacin ta iya shan tabar shaidan ta hanci ta baki, sannan kowane dare kai wata rana ma har da rana Mustafa sai ya zo ya dauketa sun tafi hotel sun sheke ayarsu. Amman fa a wannan dan tsakanin sun sami kudi mai dama a jikinsa, wanda duk iyakacin shekarun da Abu tayi tana talla basu samu ba, karatunta na boko kam sai dai muce sam barka, domin Mustafa mai son ilmi ne dan shi ma dan boko ne, dan ya kan sanar da ita irin yanda mutum kan zama idan yayi karatu, yana zama wani a duniya. Karatun allo kuwa tuni ta watsar, Malam yayi hargagin a banza dan ba sai ya ganta ba ma sannan zai doka ba. Sai dai kullum tayi wanka taci kwalliya tana taku daidai a unguwa, su Larai duk ta raina su yanzu idan tayi kwalliya takan zagaya su tana musu yanga idan sun dawo daga tallah. Baba Abubakar ma sanda ya isa da fuffukarsa da Malam ya sanar dashi halin da Abu ke ciki, ya shiga gidan da fuffukarsa yana yiwa Sala korafi. "Yanzu Sala ba zaki dinga tsawatarwa da yarinyar nan ba tana neman ta jawo mana magana a unguwar nan, kina kallonta....." "Kai Malam rufe min baki!" Sala ta katse shi, ta dora da cewar "Kai har wani namijin arziki ne da zaka zo kana mini wata maganar banza, to tsaya kaji na gaya maka, wallahi babu shegen da zai takura wa Abula a garin nan, tun da dai ba Uban wani ya haifar mini ita ba, kuma Uban wa muka je muka ce ya taimaka mana da abinda zamu ci? Ko uban waye ke ciyar damu? don haka babu wanda ya isa yace mata 'yar iska na kyale shi. Shi kansa Malam din da yake wannan fuffukar 'ya'yan nasa ba karatun boko suke suna sheke ayarsu a can ba? Har makarantar kwana sukayi fa, don ni Allah ya bani yarinya mai kashin arziki za'a saka mu a gaba? To wallahi ba'a isa ba, kuma daga yau idan ka kuma zuwar mini da irin wannan maganar sai ranka yayi mummunan baci, soko sobarodo da baka yin maganin sisi, sai yau zaka hau ni da fada." Duk da tsananin hakuri irin na Baba Abbakar sai da ransa ya baci da tijarar Sala yau, ya dubeta a hasale sanda ta diga aya yana fadin "Au dan na gaya miki gaskiya shine kike mini wannan tijarar? Wato dan kinga bani da shi ko? Don da ina da shi baki isa kiyi mini irin wannan rainin hankalin ba, dan haka ki shiga taitayinki, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan baci wallahi Salamatu." "Ahayye ayyururuuuiii!" Ta rangada guda da tafa hannu sannan tace, "Lallai yau mazantakar za'a nuna mini kenan ko? To tsaya kaji Abbakar, wallahi baka isa ba, ka yi kadan, idan kuma kayi wasa a cikin daren nan sai mu baiwa hammata iska." Ta kama cin damara da wani zani dake yashe a gefenta tana wani girgije-girgije da buga kafa. (Tambaya: wai shin akan samu masu irin halin Sala a wannan Zamanin kuwa????) Ya fi kowa sanin halin Sala, don a shekarun baya gidansu kamar silima yake gurin kallon dambensu, sai dai shi da jarabar ta ishe shi ya sallama mata, don haka yanzu ma ba zai iya biye mata ba, don haka yabi lafiyar gadonsa na karfe yana fadin, "Kanki ake ji, wai mahaukaci ya fada rijiya, da girmana da 'ya'yana aga muna raba hali a titi, ki yi da wani ba dai dani ba." Ya runtse idonsa duk da ba bacci yake ba. Ta ja dogon tsaki gami da fadin, "Oho dai! Kai dai kawai kace ka ji tsoro, wallahi da ka tsaya da ka gane kurenka yau, munafuki kawai wanda ake gulmar 'ya'yansa da shi maimakon ya hana sai maya kara tunzira abin." Ta haye gadonta na katako tana cigaba da mita, "Ba ku da aiki sai zaman gindin bishiya kuna gulma, sam ba a iya juya kwandala ta koma Naira, ba don Allah ya bani mata masu daukar min tallah ba ai da nasha haushi, ka dubi wannan yaron da ya kwaso matacciyar zuciya irin taka, idan don taku ne sai dai yunwa ta kashe mu." Haka nan take ta bala'in ita kadai, shi dai bai kula ta ba har bacci yayi awon gaba dashi don dare ya tsala, domin bai shigowa gidan da wuri sai dare yayi sosai. Duk yaran nasu suna jiyo abinda suke yi amman basa fahimtar maganar da suke yi sai dai hayaniya kawai da suke ji, Sadiku yafi kowa tashin hankali don tun yana yaro yake takaicin abinda iyayan nasa keyi don ma abokinsa Zaid na bashi baki. Sai dai addu'a al'amarin nasu, lallai ba a sakewa tuwo suna, haka nan ba'a sauya iyaye, shi kam da tuni ya sauya da ace suyo su ake yi, domin kowanne da tabonsa. Sala masifaffiya mai shegen son kudi da abun duniya da son 'ya'ya, yayin da Baba Abbakar ya kasance mai matacciyar zuciya da gulma da munafurci, don sana'arsa kenan kullum yana gindin dirimi shi da abokanan sana'ar ta shi (magulmata) suna ta sana'ar tasu, bai saida komai balle ya sanya ran zai samu ya kaiwa iyalansa, 'yar sana'ar tasa ta saida shayi ya watsar tuni zuciya ta mutu, sai dai gulma a gindin dirimi. Don haka a cikinsu akan rasa na zaba, shi dai yana godewa Allah da ya sanya bai dauko halin ko daya ba a cikinsu, amman dai yana takaicin irin rayuwar da 'yan uwansa da iyayensa ke yi, don haka ranar da bakin ciki da takaici ya kwana, amman yayi alkawarin zai yi maganin abun da kansa, koda kuwa Sala zata tsine masa ne Allah dai yaga niyyarsa. ******************* Karfe takwas na dare Mustafa ya tsaida motarsa a kofar gidansu Abu, ya tura yaro ya kira masa ita, kusan tare suka futo da yaron taci uwar kwalliya da atamfa mai barewa, tayi daurin Hindu Rufa'i, ana wani tauna cingam wai ita dole ga 'yar gayu, leben nan ya sha jambaki a sama baki da kasa, an ja jagira mai cin birki a gefen kunne. Ta hasken wutar lantarki ya hango ta kamar ya yi dariya, don kwalliyar tata kamar 'yar kauye tayi mata, sai ya dake don kada ya tsokanowa kansa don yasa halin tsiwar Abu. Ta isa ta bude gaban motar aka zauna irin a karkacen nan ana wani fari da ido wai ita a dole ga 'yar gayu. Ya kamo hannunta yana dariya kasa-kasa yace, "Kai gimbiya, kin ga yanda kika yi wani kyau kuwa? Irin wannan kwalliya ai sai....." Finciko ta da aka yi ne ya sanya shi yin shiru cike da mamaki da razana. Sadiku ne ya finciko ta ya watsar a tsakiyar titi, sannan ya kalli Mustafa dake kallon sa sororo cike da mamaki yace, "Kai dan iska mara mutunci wallahi daga yau na kuma ganinka a kofar gidan nan sai nayi maka rashin mutunci, don haka ka ja tsummar rayuwarka ka bar kofar gidan nan tun ba sanya yara sun maka atile ba." Ya juya kan Abu wacce ta mike tana goge jikinta wai ita nan ya bata mata kwalliya, sai murguda baki take yi tana kun-kuni wanda ya san zaginsa kawai take yi, ai kuwa yayi kanta ya zabga mata mari sannan ya sanya kafa ya haure ta. Ta zube a kasa gami da rike cikinta ta fasa ihu gami da fadin, "Wayyo Sala na shiga uku!" Ya kuma kai mata duka amman ta yunkura ta mike ta kwasa da gudu ya rufa mata baya da bel din wandonsa da ya zare. A soro suka ci karo da Sala wacce ta futo a gigice saboda jiyo ihun 'yar lelenta da tayi. Ai kuwa Abu na ganin Sala din ta zube a soron tana fadin, "Wayyo Sala na shiga uku zai kashe ni cikina Sala, zan mutu na shiga uku (Kuji Makirci). Sala tace "Na shiga uku, wane shegen ne ya taba mini ke Abula?...." Shigowar Sadiku yana huci ne ya sanya ta gano abinda ya faru. Sala ta zaro ido waje cike da bacin rai tana fadin, "Lallai ka cika mara mutunci, yarinyar tana zancen ta kawai za ka kama dukanta, to me tayi maka, mugu?" "Haba Sala wane irin zance? Iskanci dai kawai. Waye a unguwar nan bai san abinda yarinyar nan takeyi ba? Haka kawai ta sanya ana zaginmu da raina mana hankali, wallahi na kuma ganinta da shegen mutumin nan sai na karya ta." Sala ta kuma yi masa kallon banza tana fadin, "Sannu Abbakar Ubanta da yayi cikinta, to tsaya kaji na gaya maka, kayi kadan kai uban da ya haife ka ma yayi kadan balle kai karan kada miya, haka kawai ka takurawa yarinya ka hana ta rawar gaban hantsi? Kai ne ka haifar mini ita ko kaine ka halicceta, eye? Bala'in naka ya wuce na baki har ka fara kai hannu kana dukan ta? Za ka zo kana gaya min ana gulmarku a unguwa, ina ruwana da wasu 'yan unguwa 'yan saka ido sana'ar banza ana ruwa suna kirgawa, su bari su koma sata yafi. To bari inyi maka mai gaba daya ta mahaukata tunda naga abun naka yana neman ya wuce gona da iri,Wallahi daga yau idan ka kuma taba mini yarinyar nan ko ka kuma shiga rayuwarta da sunan fada ban yafe maka nonona da ka sha ba!" Sadiku ya dafe kai cike da tashin hankali yana fadin, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Sala mai yasa haka? Yanzu dan ina gaya muku gaskiya dan gudun kada ku fada cikin halaka ya sanya zaki tsine mini....."gaskiya ko kuma munafurci da sanya ido? Kai waye ya shiga rayuwarka? Kullum kana yawo da kodadden wando jins da rigar gwanjo kamar tsohon matsiyacin bature." Ya girgiza kai cike da takaici yace, "Shike nan Sala Insha Allahu kome Abu zata yi a unguwar nan da gidan nan na daina yi mata magana, taje in dai duniya ce ta ishe ta riga da wando, za ta koya mata hankali." "Ka ga malam kada kayi mata baki, koda yake ai ba kai ka haife taba balle bakin ka ya bita ba, wadanda ma suka fika sunyi sun gama babu abunda ya same ta sai ma cigaba balle kai, don kurwar Abu kur! Maye yaci kansa." Sadiku bai kuma cewa komai ba ya juya ya fice daga gidan, don sai yaji gaba daya gidan ma ya ishe shi. Sala ta kama Abu dake zaune dirshan tana kallonsu don taji yanda Sala ke afke masa ta wanke mata zuciya, Sala din tana fadin "Tashi muje gida ki kwanta kinji? Koda yake Alhaji Mustafan yana can yana jiranki. Goge idonki kije ku cigaba da zancenku, ki gaya masa ya kwantar da hankalinsa kamar tsumma a randa, nayi masa maganin dan saka idon can, ba ku da sauran mai matsa muku yanzu, muje na raka ki ko yana kofar gida a labe bai tafi ba." Ta daga ta tana goge mata idon ta wanda babu ko alamun kwalla ko guda daya, daman kukan nata na sharri ne bawai na zafin duka ba. Suka nufi kofar gidan tare, sai dai babu motar Mustafa babu alamarta sai dai filin wajen kawai, dan yana ganin sun yi cikin gida ya ja motarsa yayi gaba don kada Sadiku yazo yayi masa tijara a cikin jama'a har asirinsa ya tonu, don haka ya ja motarsa ya gudu. Ai kuwa suna ganin baya nan ran Sala ya kuma baci suka koma cikin gida tana ta masifa da bala'i, wanda har makota suna jiyota, ita kanta Abun ma taji takaicin tafiyar Mustafa dan ta saka ran ya bata wasu kudi yau na ankon bikin Larai, dan haka dai sun dauki laifi gaba daya sun dora akan Sadiku wanda ya bar musu unguwar ma gaba daya. A daran nan Sala batayi baccin kirki ba sai bala'i da masifa kawai take yi har Baba Abbakar ya dawo tana yi, shi dai yayi mata banza bai kulata ba dan dai yasan 'yan bala'in ne suka motsa, idan kuma suka motsa babu wanda take saurarawa dan haka shi dai ya lallaba ya haye gadonsa na karfe yayi lamo kamar mai yin bacci amman a zuciyarsa Allah wadarai yake yi da halin Sala, har ya tuno wata mata data wuce ta gabansi dazu suna majalisa wani yayi subutar baki a cikinsu yace "Ka ga wannan matar idan ta fara bala'i sai ta kwana tana yi." Ashe matar nan ta jiyo shi don haka ta dawo ta tsaya a kansu gami da rike kugu tana kallonsu shekeke tace, "Mai kuka ce, eye?" Wanda ya fadi maganar ya yi murmushi irin na matsorata yace, "A'a Hajiya ai yabonki muka yi nace duk unguwar nan babu irinki a mutunci, ba irin babata ba 'yar bala'i, idan ta kama masifa sai ta kwana tana yi." Jin abunda yace ne ya sanya tace, "Allah ya so ka wallahi, da yau na lakada maka duka a unguwar nan na ga mai kwatarka, da sai kaga karshen masifa ta." Sai da tayi nisa sannan suka fashe da dariya suna zolayarsa sai yace, "Ku ai gwara da na yi haka, dan wallahi yanda na ga tana wata girgiza bata ki mu casu a tsakiyar titin nan ba, ni kuwa ina zan iya da ita kana ganin mace kamar bishiyar kuka? Ai irin wadannan sai da lallashi." Lallai kam haka ne sai yanzu ya gano gaskiyar Malam Sabo, masifaffu ba'a iya musu sai dai a bisu da lallashi ko kuma ayi musu banza kawai. Shi dai har bacci ya dauke shi bai san sanda Sala ta gama masifarta ba. Da safe ma da bala'in Sala ta karya dan Sadiku ko koko da kosan da ake bashi ranar ba'a bashi ba sam, shima bai nema ba ya tafi makarantar sa da yake yana karatun Low ne a B.U.K, karatun da yake matukar shan wahala a kansa dan babu wanda ke taimaka masa a iyayansa sai Malam ne ma yake taimaka masa wani lokaci da kuma rufin asirin Allah, dan ya iya zane idan ya samu ya kan yi, ko kuma idan bashi da lakca ya tsaya shagon wani abokinsa ya taya shi aski a bashi wani abu, da kuma tallafi na karatu da suke samu (Scholarship), haka nan yayi ficewarsa da yunwarsa gashi banda kudin mota bashi da ko kwandala. Ita kuwa Abu 'yar mulkin ko shirin makaranta bata yi ba, don kwanciyar ta ma tayi tace kanta ciwo yake yi, yinin ranar a daddafe tayi shi dan takaici, ita kuwa Sala sai kawo mata kayan dadi takeyi kala-kala wai dan ta kwantar mata da hankali. Yamma na karatowa aka yi wanka aka ci uwar kwalliya ta jiran Mustafa aka kame akan kujera, duk yaron da ya shigo gidan sai taji kamar ita zai ce ana kira, gashi ita yanzu ta daina kula samari dan a ganinta ita kalar manya ce kamar yanda Mustafa ke gaya mata. Sai dai me? Har kusan karfe goma na dare babu Mustafa babu alamar sa, har gajiya tayi da lekawa amman babu shi babu alamunsa. Daga karshe dai ta sanyawa Sala kuka tana fadin "Sala ina ga fa Mustafa fushi yayi da wulakancin da Sadiku ya yi masa jiya, dan baki ji maganganun da ya dinga gaya masa ba, shi ya sanya ya yi fushi ya ki zuwa." Sala tace, "Bari ke dai Abula ai wannan yaron ya goga mana bala'i, yanzu idan yaron nan ya daina zuwa ina zamu sanya kanmu? Ki duba ki ga irin kudin da yake bamu a sama ba tare da mun sha wahala ba, yanzu idan ya daina zuwa sai dai mu koma abincinmu kenan." "Abinci Sala? Cabdijam!! Wallahi Sala na fi karfin tallar abinci yanzu, dube ni fa ki gani? Ni samari ma tsami na daina harka da su balle wani tallah, idan mutum bashi da kudi ko kallo ma bai ishe ni ba." Sala tayi dariya tana fadin, "Ho Abulata, kinyi gaskiya wallahi kin fi karfin talla yanzu, tunda Allah ya baki abun neman kudi ai shike nan. Ki sha kuruminki na ma sani zai dawo, watakila wani abin ne ya tsre shi, dan na san ba kowa ne zai sami kamarki ya yasar ba... Ke kamar na ji karar mota ma." Sukayi shiru, can Sala tace, "Allah karar mota ce." Suka bazama suka yi kofar gida har suna karo da juna, sai dai me? Kurar mota kawai suka gani ta wuce tuni, haka nan suka dawo suna zaman tsammanin warabbuka, Malam ya ki noma yana jiran sadaka. Sai dai har suka fara gyangyadi babu Mustafa babu alamarsa, haka nan suka hakura kowacce ta kama makwancinta cike da takaici. Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba inji Garba Sufa, dan yau kwanaki shida kenan amman babu Mustafa babu alamarsa, uwa da 'ya sun shiga tashin hankali, tun suna tunanin zai zo har sun hakura sun fidda ransu da zuwan nasa, shi kuwa Sadiku da har yau bai daina shan bala'in Sala ba murna yake yi don ko babu komai ya kori Mustafa, lallai barazanar da ya yi masa tayi tasiri a kansa. Daran daya cika kwana bakwai suka yanke shawarar zuwa gidansu dan su bashi hakuri, domin dai kudi sun fara musu karanci don ma su Karimatu suna daukar abinci da funkaso, don ita macece mai jarababban neman kudi dan tun tana budurwa bata iya zama babu sana'a ba. Washegari da yamma Abu taci kwalliyar ta duk da kanta da yake mata ciwo, ana taku dai-dai kamar ba zata taka kasa ba, aka nufi gidan su Mustafa wanda yake can gangaren layinsu. Sanda ta isa ta tsaya tana kallon gurin da yake zama bisa farar kujera karkashin bishiyar Umbrella, lokuta da dama da jarida a hannunsa, sai dai yanzu babu ko alamarsa ko kujerar tasa ma babu a gurin. Katuwar koface wacce ke garkame, bata mantawa da can suna zuwa tsokanar kare, idan ya biyosu su zunduma da gudu ko kuma suyi ta jifansa, wata rana sun taba fasa masa kai mai gadin ya bi su da gudu ya kama daya a cikinsu ya zane, shine fa suka kulla masa, ai kuwa rannan maigidan ya futo da motar zai tafi sai kuma yayi mantuwa ya koma cikin gidan, su kuwa daman suna fakonsa dan haka suka dauko wani abu mai tsini suka soka a tayar gaba ta sace, ai kuwa sanda mai gidan ya futo ya gani ya dinga yiwa maigadin fada daga karshe dai sai wata ya hau ya bar wannan a nan, bayan maigidan ya tafi suka dinga yiwa maigadin ihu da tsokanarsa, ai kuwa ya bisu da gudu sai dai kasa kama kowa yayi dan 'yar zilliya suka dinga yi masa, haka nan ya gaji ya koma yana nishi, don haka yanzu take fargaba kada ya gane ta. Ta daure dai ta kwankwasa kofar, ya bude ta 'yar karamar taga ya leko dan yaga wanda ke magana, yana ganin ita ce ya zaro ido waje yace, "Me kike nema a anan, eye?" Yana maganar fuskar nan tasa a murtike. Ta rike kugu da murguda baki a hankali tace, "Banza dan gadi, kai ba don ta kama ba ka isa a wani tsaya ana magana da kai, dalla ka bude da wani bakinka duk gansa-kuka." Ya kuma hasala dan dai bai ji abinda tace ba amman da alama zaginsa take yi, dan haka ya bude ya futo da wata zungureriyar bulalarsa yana muzurai. Ko a jikinta bata ji ko dar ba don ba dabi'ar ta bace tsoro, ta kuma ayyana a ranta wannan tsohon ya tabata zai gane kurensa dan wallahi sai ta yi masa sharri, ta kuma gyara tsayuwa. Ya hasala matuka dan haka da zafin rai ya fara magana, "Ke yarinya bana son rashin mutunci, don a haife kin san na haife ki ko? Don haka ki bar gurin nan tun ban zane ki ba." Ta yi masa kallon baka isa ba sannan tace, "Ka ga Malam ni ba wani abu ya kawo ni ba Mustafa nazo nema, idan yana ciki kace masa Abu tana magana da shi, ka daina mini surutu kana feshe ni da yawu." Mamaki ya bayyana a kan fuskarsa, mai ya hada Mustafa nutsatstsen yaro da wannan hatsabibiyar yarinyar? Amman bai san alakarsu ba, dan haka ya dan saki fuska ya ce, "Mustafa fa kika ce?" Ta motsa fuska tace, "Ko kana mamaki ne?" A ransa yace, "Kai wannan yarinyar 'yar bala'i ce, gwara ya lallaba ta su rabu lafiya. Don haka ya kuma gyara tsayuwa ya fara kora mata bayani, "Ai Alhaji Mustafa ya koma don daman hutu yazo da kuma ciwon Babansa da ya tashi na hanta, dan a can kasar waje yake karatunsa, yau kwanansa shida da komawa, kuma ba shi da ranar dawowa dan tun da ya tafi shekara uku sai wannan karon ya dawo." Ta dafe kirji cike da tashin hankali ta ce, "Yanzu ya tafi wata kasar babu daman na ganshi dan Allah?" "Af! Ai kuma sai kiyi, mutumin da aka ce miki bai kasar gaba daya ma, kinga komawa ta ma." Ya koma ya garkame kofar tasa. Kafarta ta yi mata nauyi ta kasa dagawa, yanzu yaya zata yi da rayuwarta? Don Mustafa ya koyar da ita darussa masu wuyar mantawa, yanzu waye zai dinga bata shandy tana sha? Waye zai dinga bata tabar shaidan tana sha? Waye zai dinga kai ta hotel taci kayan dadi ta hau gado mai laushi?, waye zai dinga bata kudi mai yawa irin na Mustafa? amsar ita ce babu, babu wanda zai maye mata gurbin Mustafa ko ta ina. Da kyar take iya gane hanyar da take sanya kafarta duk hankalinta a tashe yake, don ma Allah ya taimake ta ba wata tafiya bace mai nisa, da kyar ta samu ta lallaba ta isa gidan dan zazzabi da ciwon kai sun hadu sunyi mata taron dangi. Bisa wata tabarma da ta tadda a tsakar gidan ta zube, wacce Sala ta shimfida ta shiga kicin dora sanwar dare, ta zauna idonta na zubar da hawaye, azaba biyu take ji a jikinta gata rabuwa da Mustafa ga kuma ta ciwon da ke addabarta, ta zame ta kwanta ta kama juyi da malailaikuwa a tsakar gidan tana kuka mai ciwo da taba rai. Sala ta futo daga kicin dan ta dan huta, sai dai mai zata gani? Abu ce 'yar lelenta tana birgima a tsakar gida tana kuka dafe da kanta. Ta isa gurin da sauri tana tambayar ta, "Abula diyar kirki yaya aka yi? Bai hakura ba ne Mustafan? Idan bai hakura ba ni sai naje da kaina na bashi hakuri. Kwantar da hankalinki, banda abun dan yau ma ai saurin fushi ba nasa bane ba, idan yayi mana haka ai yayi mana tsiya, bari naje da kaina na bashi hakuri ina ne gidan nasu?" Ta mike tana neman gyalen da za ta yafa. Abu da taga da gaske take yi ta ruko hannunta, ta juya tana kallon ta amman ta gaza cewa komai, cikin kuka Abun tace, "Kada ma kije Sala, ko kinje ba zaki same shi ba don baya nan wai daman a kasar waje yake karatu hutu ya zo, yanzu ya koma yau kwanansa shida da komawa. Wayyo Sala cikina zan mutu." Ta karasa maganar da kuka tana rike ciki. Sala ta rude sosai ta ruko hannun diyar tata tana mata sannu gami da lallashinta tana fadin, "Kiyi hakuri Abula na san zai dawo ya nemeki komai dadewa, domin ke din mace ce da duk namijin da ya ganki sai ya rude balle shi Mustafa da yake sonki, share hawayenki ki daina kuka kinji Abula ta? Na san zai dawo komai dadewa." "Ni fa cikina ne yake mini ciwo. Wayyo Sala ciki....." Sai ga amai kyah! kyah! kyah! Tana kwararawa. Sala ta kuma rudewa ta mike da azama tana neman fo don taimakawa diyar tata, tun tana yin amai na abinci da ruwa har ta koma na majina take yi, da kyar suka samu aman ya fada. Sala ta taimaka mata ta raka ta bandaki dan ta wanke jikinta, ita kuma ta dawo dan ta gyara gurin zuciyar ta na cike da tsananin tausayin diyar tata, dan ta gano ta fada kangin soyayyar Mustafa. Haka nan ta karasa yammacin a kwance ga juwa da tashin zuciya dake damunta, daga karshe dai Sala tace bari ta je gurin dan Oga ta karbo mata magani ko aman ya tsaya. Tana isa dan oga ya kama wage baki yana fadin, "A'a mana ne? Sannu ka da zuwa. Ina Habu ne dan bana ganin shi yanzu?." Sala tace, "Abu tana nan, yanzu ma ita na zo na karbawa magani bata da lafiya." Ya kuma wage baki yana fadin, "Habu babu lafiya? Bari a bata magani mama, ka bari kudinka ma." Ya kama hada magunguna bayan ya kammala yayi mata bayanin yanda za'a sha kowanne, ta amsa da azama ta nufi gida. Sanda ta sha maganin kamar gaske dan aman ya tsaya har ta sami bacci, sai dai wajen karfe goma sha daya aman ya kuma dawowa dan shi ma ya tashe ta daga bacci, sai da ta amayar da duk maganin da ta sha samman ta sami sa'ida, sannan ta sami wani bacci ya dauke ta. Da safe kuwa sai ta tashi jikin babu laifi dan aman ya tsaya, sai dai jikin nata babu kwari daga kwanciya sai kwanciya, har ta samu ta tsakuri abinci kadan ta ci, Sala sai ta kama murna jiki yayi kyau. Sai dai yamma tana yi amai ya dawo sabo, har dare yayi ana abu daya, sai da aka kuma samo wani maganin. Sala kam bala'i ta hau yi tana fadin, "A'a na gamo lagon abin ma, wato marasa mutuncin nan ne ke neman kama mini diya (mayu), lallai kam zan yi maganinsu, don ga alama nan ciwo baya tashi sai almuru yayi, wallahi duk shegiyar matar da na san mayyace a unguwar nan sai naci ubanta, za su san wannan karon sun ciwo mai zafi, dan ba zan yadda da rainin hankali ba, dan sun ga diyata ta taso bul- bul da ita gwanin sha'awa ga farin jini shine zasu lashe mini ita? To wallahi kurwarta kur! Kai bari ku gani ma ba'a bori da sanyin jiki, ai mune maganin mayu." Ta debo garwashi ta gumbuda garin tazargade da wani maganin mayu, nan fa gida ya tirnike da hayaki sai tari suke yi. Sannan ta kuma jika tazargadan a cikin ruwa ta mikawa Abun tana fadin, "Amshi nan shanye, mayu za su ci kan ubansu yanzu a gidan nan." Cikin ikon Allah har ta gama shanyewa ba tayi amai ba don da duk abinda ya shiga cikinta sai ta amayar da shi, amman wannan ya zauna. Sala tayi dariya tana fadin, "Ahaf ai na sani, mu za'a gayawa zancen banza? mu maita ma bamu so yi bane, abinda ake saidawa a kasuwa." Haka nan ta dinga mita da balokoko a tsakar gidan kamar wadan da take zargin suna nan a tsakar gidan. Cikin kwana biyu sai jikin yayi kyau, domin in dai ta sha ruwa da tazargade a ciki bata yin aman, hankalin Sala ya fara kwanciya da ita kanta Abun, sai abu daya da ya dawo musu da hannun agogo baya bai wuce dawowar aman ba. Tana tsaka da bacci aman ya taso mata, tayi kokari ta fita amman ina ya riga ya yunkuro dan haka ta zauna a nan ta dinga kelayawa. Kanwarta Karimatu ce ta mike ta yi dakin Sala da gudu tana gaya mata, ai kuwa a rude Sala din ta taho, ta rike Abun kam-kam tana mata sannu har dai suka samu aman ya lafa ta dan sami bacci. Sala ta koma daki ta kwanta, sai dai ba'a yi awa guda ba Karimatu ta kuma komawa da gudu taba buga kofar dakin Sala gami da fadin aman ya dawo. Sala ta tashi a rude, sai ta kalli Baba Abbakar dake ta shararar bacci ta kuma hasala, ta daddage iyakacin karfinta ta maka masa duka, ya tashi a gigice yana ta soshe-soshe, ta galla masa harara tana fadin, "Ka saki baki kana ta sharara bacci bayan ka san Abula bata da lafiya, ko sisi baka taba bayarwa kace a sai mata magani ba sannan sannu ma ta gagara? To ka zo muje ka ga jikin nata kada ta mutu." Ta shiga gaba yana binta a baya zugui-zugui kamar makaho da dan jagora, ai kuwa yanda suka ga Abu hankalinsu ya tashi dan ta galabaita sosai. Sala ta rude matuka ta saki kuka tana fadin, "Wayyo Abula! Dan Allah kada ki mutu ki barni, na shiga uku ni Salamatu." Baba Abbakar ne ya dinga lallabata da kwantar mata da hankali, zuwa gurin asuba kuma sai Abu ta fara suma, dan haka gari yana dan kara haske aka samo mota suka kwashe ta sai asibitin murtala (Murtala general hospital). Sun yi sa'a suna zuwa aka karbe ta, nan da nan aka rubuta musu abinda zasu siyo, Baba Abbakar babu ko sisi a jikinsa don haka ya zame ya gudu, Sala ce ta kwance jakarta ta dauko kudin ta bada, nan da nan aka daura mata karin ruwa, sai da babbar leda ta shiga jikinta sannan ta fara dawowa hayyacinta. Cikin ikon Allah kafin azahar ta dawo hayyacinta, da taimakon Allah da taimakon karin ruwan da aka yi mata. Sai washegari da likita ya dawo yaga jikin ya dan fara kyau ya rubuta mata gwaje-gwaje bayan 'yan tambayoyi da yayi mata, gwaji kala uku aka rubuta mata, akwai na taifot da na maleriya sai kuma wanda yake tantama a kansa dan ance masa budurwa ce, amman dai ya zama dole a yi din don ya tabbatar da binciken sa gwajin masu ciki. Sala ce ta taimaka mata suka nufi dakin gwaje-gwajen aka auna komai aka basu sakamako cikin ambulan, suka ce ta kaiwa likitan da ya turo su, suka koma dakin da aka kwantar dasu suna jiran zuwan likitan. Sai da ya gama ganin marasa lafiya sannan ya dawo dakin nasu, ya fara bin gadaje yana dubawa har ya zo kan na Abu. Ya gyara gilashin din idonsa gami da kara tambayarta jikin nata, Sala ce ta amsa sannan ta bashi sakamakon dake cikin ambulan. Ya amsa ya farke yana dubawa, ya kuma gyara gilashin din dake idonsa yana kallon Abu, sannan yace da Sala, "Baba kika ce budurwa ce ko?" "Fil ma kuwa a ledar ta. Don ko kudin toshi ba'a kawo ba balle a sanya rana balle kuma ta kai ga biki ba." Sala ta bashi amsa da sauri. Ya girgiza ka ya ce, "Haka ne." Yace, "Baba ku same ni a ofis dina yanzu zan baku sallama dan ta warware." Bai jira jin amsar su ba ya wuce gado na gaba. Sun dade tsugunne a kofar ofis din nasa da kayansu a zube suna jiransa, har ya zo ya bude ya shiga suka rufa masa baya, ya nuna musu gurin zama sannan ya dauki wata takarda ya fara rubuce-rubuce a cikinta Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Idan zuciya ta gyaru 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 07:50 PM, 28-Jan-16 Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU _________________ Na ________Fauziyya D Sulaiman_____ Bayan ya gama ya daga kansa yana kara kallon Abu wacce tayi wuki-wuki, ya ma rasa ta inda zai fara, can dai ya daure yace, "Baba wannan diyarki ce?" Batayi mamakin tambayar ba don jama'a da dama kanyi mamaki idan aka ga 'ya'yanta wanda sam basa kama da ita, dan kamar mahaifinsu suke yowa wanda idan ka gansu tamkar Larabawa suke, ita kuma gata nan bakikkirin, don haka baki a hangame tace, "Ka ga bamuyi kama ba ko? Ai mutane da dama na mamakin ace 'ya'yana ne don idan suna yara suna kuka a gidan biki har cewa ake na maidawa uwarsu sai anga na ciro mama ina basu tukunna ake yarda nawa ne, ai diyata ce ta biyu. Ha ha ha" Ta saki dariya daga karshe. Ya girgiza kai cike da takaici ya ce, "A yanda na gani a jikin kati yanzu shekararta goma sha hudu ko?" Ta kuma yin dariya tana fadin, "Haka ne likita ka ganta gaba-gaba haka nan take da girman jiki babu shekaru, ka ganta kamar 'yar shekara ashirin ko? Girman jikin ne kawai musamman yanzu da take cin kayan dadi sai tayi wani fari da kiba kamar diyar wani basarake, bul-bul da ita gwanin sha'awa." Likitan yayi murmushi don ya gano inda Abu ta samu matsala, wato rashin uwa tagari ne, dan haka babu wani boye-boye ya ce, "Hajiya ke da yarinyarki ta sauya kin tambayeta dalilin da ya sanya ta sauya?." "Haba dai likita wace irin tambaya ai jin dadi shi ke sanya mutum ya sauya, ka ga dai yarinyar nan kullum da sai ta dauki talla safe da dare, yanzu kuwa ta samu mai ba ta kudin sai dai taci ta kwanta sai dai makaranta." Ya girgiza kai cike da takaici ya ce, "Haka ne, to tsaya na gaya miki diyarki tana dauke da juna biyu, ma'ana ciki, dan haka wannan sauyawar da tayi ba wai ta jin dadi bace illah ta ciki....." Sala ta mike da tashin hankali ta dafe kirji cikin karaji tana fadin, "Me? Likita cika fa kace? Lallai baka san aikin ka ba, dubi Abulan duka nawa take da zata yi ciki? Kai dai ka kara dubawa ka gani ko katin wata ka dauko." Ita ma Abu dake zaune tana jin caftar da Likita da Sala ta dafe kirkji da sauri tana fadin, "Na shiga uku ciki ne dani." Sai ta saki kuka. Sala ma ta sanya kuka tana fadin, "An ya likita ba karya ka fadi ba? Ko kuma aljanu ne suka hura mata ciki ka ga kamar ciki ne da ita, dan yaushe ma ta fara al'ada duka, ka dai sake dubawa." Shi dai rubutunsa kawai yake yi akan wata takarda, sai da ya gama sannan ya daga kansa ya mika mata kayin yana fadin, "Ko ki yarda ko kada ki yarda 'yarki tana da ciki, dan haka idan baki yarda ba sai kije wani asibitin a duba miki ita, na gama daku sai ku tafi, a gaba a dinga kula da tarbiyyar yara." Ta kuma fashewa da kuka tana fadin, "Don Allah likita ka taimake mu, yanzu yaya zamu yi da wannan abin kunyar? Na shiga uku ni Salame....." "Kinga Hajiya ku fita can kuyi kukanku don na tashi zan kulle ofis dina." Ya mike yana hada kayansa. Ta tsagaita kukan tana fadin, "Likita yanzu babu wani taimako da zaka yi mana?" "Kinga Baba babu wani abu da zanyi bayan addu'a Allah ya rabata da shi lafiya, kuje waje zan kulle ofis dina nace." Yana magana yana kallon agogonsa. Haka nan suka fice daga Ofis din Abu tana kuka Sala kuma duk ta gigice, suka yi zaune turus a gaban kayansu kowacce tana kuka, har yazo ya wuce su bayan ya kulle Ofis din nasa. Can dai Sala ta daure ta ce, "Wai ni Abula garin yaya kika yarda har yayi miki ciki ne ma? Ai da kince yayi wasu 'yan dabarun da bazaki samu ciki ba" (Fauza tace, kuji fa jama'a bata bakin ciki da lalata mata diyar da aka yi sai ra samun cikin, shima don tana jin kunyar idon jama'a ne, kai tir da irin wadannan iyayen). Abu ta cuno baki gaba tana wani kumbure-kumbure tace, "To nima na san zan sami cikin ne Sala? gashi yanzu ya gudu ya barni da ciki. Kuma na san 'yan gidansu ba zasu yadda shi yayi ba, na shiga uku yaya zanyi da gorin 'yan unguwarmu? Ga shi dama sun tsane ni, yanzu idan suka ji ina da ciki zasu dinga tsokana ta." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Sala ta fyace hanci wanda ke kwaranyo da majina ga hawaye sun hadu sun cakude sannan tace, "Au!! Gaya musu zamu yi? ai kama bakinmu za muyi muyi shiru, ko Abbakar ba za'a gayawa ba, dan kada dadin hira ya kwashe shi a majalisarsu ya kwaza, kin san shi da shegen surutu, kija bakinki ki yi shiru har mu zubar da shi....." "Zubarwa Sala?" Abu ta fadi a kidime. "Eh mana zubarwa zam yi, dan da kunyar duniya gwara ta lahira, kuma ma ai ma tuba kafin mu mutu. Goge hawayenki ni na san ta inda zan bullowa al'amarin, ki sha kuruminki, bari na samo mana mota mu tafi gida." Ta fita ta samo musu mota suka loda kayanzu suka nufi gida da sunan Abu ta warke. Tana isa gida ta sanya aka samo mata madaci ta hada da darbejiya da omo da kanwa ungurnu ta dafa su suka dahu sannan ta kawo wa Abu daki. Tana kwance lamo ta ce, "Abula na tashi ki kafa kai maza ki shanye wannan." Ta mika mata kwanon dake dauke da hadin. Babu musu Abu ta karba ta kafa kai ta kama kyankyama tana rintse ido saboda rashin dadinsa da daci kamar zai yanka mata harshe, ko kofi guda bata sha ba amai ya ciyo ta, ta yadda kwanon ta kama amai, gaba daya hadin ya zube, wanda ta sha kuma ta dinga dawo dashi tamkar zata amayar da 'ya'yan hanjinta. Sala tana tsaye ta yi tagumi, sai dai tana ganin aman ya lafa ta kuma dauko wani kwanon cike da maganin tace, "Maza Abula na daure ki shanye wannan....." Ta girgiza kai cike da fargaba tana fadin, "A'a Sala gaskiya babu dadi, hanjina kamar zasu tsinke ji nake kamar zan mutu." Sala ta waro ido waje tana fadin, "To dama waye yace miki dadi ne da shi, eye? Daman ai za ki sha ne dan ki rabu da wannan jarabar dake tare dake, da don dadi ne yaushe zan baki? Da dadi nake so kiji sai na sayo miki kaza da madara, amshi ni ki sha tun raina bai baci ba ko asirinmu ya tonu ba." Abu ta amsa idonta na fidda hawaye ta amsa ta kafa kai tana sha, ai wannan karon ko rabin kofi bata sha ba aman ya kuma dawo wa, ta dinga yunkuri kamar za ta amayar da 'ya'yan hanjinta, hankalin Sala ya kuma tashi, haka nan suka hakura dan babu yanda zasu yi suka yi zugui-zugui da su cike da tashin hankali. Sadiku ya shigo gidan da Sallama, Sala tace da Abu, "Maza kwanta ki rufe idonki zan ce bacci kike yi, Waye......? Tsaya ina zuwa." Bakinta yana kyarma take fadin, ta fita da sauri tana kokarin gyara daurin zani dake shirin faduwa. Ya dubeta da mamaki dan ganin yanda ta fito a firgice, idanuwan nata duk sun yo waje. Ya kalle ta da damuwa a ransa ya ce, "Lafiya Sala ko ba ki jin dadi ne?" Da sauri Sala tace, "Lafiya ta kalau me ka gani? Jiya ne dai 'yar uwarka ta tashi da ciwon kai har muka kai ta asibiti kana makaranta, amman yanzu jikin da sauki dan har an sallamo mu." Yace, "Allah ya sawake." Ya dauki bokiti ya zuba ruwa ya shiga bandaki, ta yi tsaye tana muzurai wai dan kada ya shiga dakin, har ya gama ya futo daga bandaki. Sanda ya futo har tsoro ya ji dan ganin yanda ya bar ta haka ya tadda ta tana tsaye, ya dube ta da mamaki ya ce, "Sala yaya dai, lafiya?" Ta gatsina fuska ta ce, "Lafiya kalau, ina shan iska ne kawai." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ya dubeta sosai ya ji gabansa ya fadi dan ganin yanayin ta, amman sai ya dake kawai ya wuce, har ya isa soro sai wani tunani ya darsu a ransa, sai ya juyo har lokacin tana tsaye tana dubansa. Ya kalle ta da kyau yace, "Sala kunje asibiti kika ce? Me suka ce yana damunta?" Munje mana da Baba Abbakar muka je ma jiyan ta sami sauki yanzu haka bacci take yi. Bai yadda da abun da tace ba, dan haka ya ce, "Ki bani katin na duba ko da wani abu da suka ce." Kululululuuu! Cikinta ya duri ruwa, amman sai tayi saurin yanko karya tace, "Laaa! Ka ga sai yanzu ma na tuna da katin, ai mun baro shi a can asibitin wallahi, ai tama warke idan ka ganta kamar bata yi ciwon ba ma." Kamar ya kuma yin magana, amman sai ya ga rashin dacewar yi din dan haka kawai ya juya ya fita ya nufi dakinsa, sai dai ransa cike yake da zargi kala-kala amman yana ta addu'ar Allah ya sanya abin da yake zargin ya zama ba gaskiya ba ne. Sai da Sala taga ya shige dakinsa sannan tayi ajiyar zuciya gami da shiga dakinta da sauri tana fadin, "Oh! ni Salame yaro sai shegiyar tambayar tsiya kamar dan jarida? Koda yake an ce ai karatun Lauya yake yi sun iya sharri, ai da na gaya masa abinda ya faru na shiga uku da surutunsa kamar wani ubana." Kusan daran nan a zaune suka kwana suna sake-saken abinda zai fish-she su, daga karshe dai sun yanke shawarar komawa asibitin watakila su sami wanda zai zubar musu da cikin tunda an ce ana zubarwa. Amman sun yanke shawarar ba zasu je asibitin Murtala ba za suje Kuroda ne dan kada Likitan jiya ya tona musu asiri. Sanda suka isa asibitin suka bi layi har ya kawo kansu suka shiga, bayan sun zauna likita ya dubesu yana tambayar abinda ya faru. Sala ce ta fara kwantar da murya tana fadin, "Wallahi likita tsautsayi ne ya faru da yarinyar nan, yarinya ce 'yar albar....." Ya dubi katin yana magana, "Hajiya kece Zainabun ne?" "A'a ba ni bace gata nan." Ta nuna Abu. Ya maida dubansa ga Abu ya ce, "Zainabu me ke damunku?" Idonta ya kawo kwalla ta dubi Sala tana matse idanu, Sala ta daga mata kai alamar ta yi magana, ta kwantar da murya ba kamar da ba da take magana a tsiwace tace, "Daman kaina ne yake ciwo da ciki na da kuma amai....." Ya dubeta da kyau sannan ya maida kansa ga katin yana rubuce-rubuce, ya daga kansa bayan ya gama ya ce, "Hajiya zaki kai ta ayi mata gwajin fitsari da jini." Ya dubi wata ma'aikaciyar jinya (nurse) yace, "Sister nuna musu dakin gwajin jini." Ma'aikaciyar jinyar ta mike tana fadin, "Hajiya taso muje mana." Abu ta kalli Sala wacce ko motsawa bata yi ba, Sala kam wani busashshen yawu ta hadiya da kyar sannan tace, "To likita ai daman a babban asibiti anyi mata gwajin, an gano tana da ciki ne.... Daman zuwa muka yi ka taimaka mana kamar yanda Allah ya taimake ka ka zubar...." "Me?" Likitan ya tambaya da mamaki, ya dora da cewar, "Hajiya an gaya miki muna zubar da ciki ne mu?" Bai bari ta bada amsa ba ya cigaba da maganarsa, "To ki sani mu bamu zubar da ciki a nan, idan kika kuma kasadar zuwa wani asibitin na gwamnati da sunan a zubar miki da ciki za'a iya kama ki a daure, wato kina jin kunyar duniya ba kya tsoron Allah ko? Wato kinfi jin kunyar duniya ba kya tsoron Allah ko? Me yasa kika yi sakaci da tarbiyyar 'yarki har tayi ciki? A ce kamar wannan karamar yarinyar da bata gama sanin kanta ba balle ma ta san mecece rayuwa ta yi ciki....." "Ai dai kaddara ce ba ta wuce kanka ba kai ma." Abu ta katse shi tana murguda baki da wani kyafta idanuwa. Sala ta kai mata duka tana fadin, "Kin ci Ubanki nace, ana neman ya raba ki da wannan kajagar kina masa rashin kunya?" "Kin ga Hajiya ku tashi ku fita na gama da ku, don ina da marasa lafiya dake jirana." Likitan ya katse mata maganar. Sala ta gurfana bisa gwiwowinta za ta fara roko, amma ya katse mata hanzari ya daga mata hannu yana fadin, "Hajiya I said get out of my Office, (Na ce ki fita daga Ofis dina)." Jikin Sala ya yi sanya ta mike duk da bata ji abinda yace ba ta gane korarsu yake yi, Abun ce ma ta dan gane wani abu tunda ta san (get out) dan haka suka fice babu shiri. A bakin titi suka yi tsaye cike da tashin hankali, dan duk iyakacin dabararsu ta kare. Abu ta fashe da kuka tana fadin, "Yanzu Sala shi kenan gorin da nake yiwa Ladi mai danwake ta haifi shege nima haka za'a dinga mini? Kin gani har hana ta fitowa muke muna bula mata kasa idan ta fito, gaskiya Mustafa ya cuce ni, Gashi ya gudu ya barni da abin kunya." Sala ta matse ido cike da takaici tace, "Bari ke dai diyar nan, na rasa inda zan tsoma kaina da wannan abun kunyar, wallahi yaron nan ya shammace mu, da ina ganin sa yaron arziki ashe dan tsiya ne." Tayi kwafa gami da fyace majina da hawayen dake zubo mata da gefen gyalenta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Abu ta dube ta tace, "Sala yanzu gida zamu koma?" Sala tace, "Eh, to! Ko dai zamu je gurin bokan can na kan tudu mu gani ko za'a sami maganin zubar da ci....." "Sannu Hajiya." Wata murya ta katse mata magana daga bayanta, gaba dayansu suka juya da sauri dan ganin mai musu magana. Ma'aikaciyar jinyar nan ce da suka gani a dakin likita, wadda ya ce ta raka su dakin gwajin jini. Ma'aikaciyar jinyar ta fara magana, "Ina ta addu'ar Allah ya sanya daman baku tafi ba, na dan tsaye bata lokaci ne dan kada likitan ya gane ku na biyo. Ai shi na gaya muku dan ka'ida ne ba ya zubar da ciki, yana wani fama da gemu kamar gaske. Don ma bai kama yi muku wa'azi ba, shi ya sanya sam bama shiri da shi, amman daman ka'ida ce duk asibitocin gwamnati ba'a zubar da ciki idan na da matsala ba, sai dai zan taimake ku yanzu dan kun bani tausayi, bai dace yarinya karama kamar wannan rayuwarta ta lalace tun yanzu ba." Fuskarsu ta fadada da fara'a Sala ta ce, "Kai amman likita mun gode miki kuwa, Allah ya sanya ki gama da duniya lafiya." Ma'aikaciyar jinyar tace, "Amin." Sannan ta fara yi musu kwatancen wani asibiti mai zaman kansa inda za'a cire musu cikin. Sala ta dinga godiya kamar ta kwanta don durkuso tana godiya. Ma'aikaciyar jinyar ta ce, "Babu komai idan baku gane ba dai ku fada mini, sai dai yanzu rana ta yi gobe da sassafe za kuyi sammako kuje." Sala tace, "Mun gane ma." Haka nan sukayi Sallama suka tafi suna ta godiya. Daren ranar dai cikin farin ciki suka kwana, sai zumudi suke yi gari ya waye su tafi, dan abun da ya so tauye musu farin cikin su ma da farko bai wuce rashin kudi ba, sai dai da yake ance mai kadara ba matsiyace bane, sai suka daga wasu kayansu na sawa har da wani saitin dankunnen gwal wanda Mustafa ya saiwa Abu suka kai kasuwar Rimi da kasuwar 'yan tsaye suka saida, Cas suka amso kudinsu, dan haka suka daina fargaba suka kwana da farin ciki wanda rabon su dashi tun ranar da suka ji Abu tana da cikin. Sai dai idan za suyi magana kasa-kasa sukeyi dan sun lura da Sadiku ya sanya musu ido, ko ma su kulle kofar. Da sassafe suka yi sammakon shiryawa suka nufi kwatancen asibibin da Ma'aikaciyar jinyar nan ta musu, basu wani sha wahala ba suka gano a nan cikin Sabon gari yake. Sanda suka isa suka cika da mamaki dan ganin wannan Ma'aikaciyar ta jiya, ta tare su tana dariya tace, "Kun gan ni anan ko? ai ina aiki anan ma sanda bani da aiki a can. Dan haka ne ma ya sanya nayi muku kwatancan nan din, kuzo muje gurin likitan." Wani katon Inyamuri ne kansa da sanko ya sha kot, idanuwansa jajir suke da alamun shan taba a lebensa, ta cikin gilashinsa ya dinga leken Abu yana wani lasar lebe. Cikin harshen turanci Ma'aikaciyar jinyar ta yi masa bayani duk abinda ke damun Abu. Ya yi dariya cikin gurbatacciyar hausarsa ya ce, "O.k na gane, Yarinya ka zauna mana." Yana magana yana dubanta kamar maye. Duk rashin tsoro irin na Abu sai da ta tsorata da ganin mutumin, dan haka ta tsaya ta kasa zama. Sala ta dubeta da kulawa tace, "Abula zauna mana, shine zai raba ki da wannan kajagar da ke tare da ke." Ta zauna tana cigaba da kallon sa har lokacin hankalinta bai kwanta dashi ba. "Hajiya ciki wata nawa take?" Ya tambayi Sala. Tace, "Ban sani ba likita, sai dai ka duba ka gani." Ya Umurci Abu da ta kwanta a wani gado da aka zagaye da labule sannan ya shiga yayi mata awo. Sai da ya kammala sannan ya fito ya dubi Sala ya ce, "Hajiya yarinyarka tana da shiki na wata uku ne, amman kada ka damu idan da akwai kudi za'a cire shi yanzu." "Nawa ne kudin? Mun zo da shi." Sala ta fada da saurinta. "Ka je can waje ka biya za su gaya maka kudin." Sannan ya dubi Abu yana fadin, "Ka sauko za muje da ke dakin aikin yanzu." Sala ta je ta biya duk kudin da aka caje ta suka bata takardar shaidar ta biya, duk yawan kudin bata ji kyashin biya ba. Bayan ta karba ta kai masa ya amsa ya karanta ya umurci Abu da ta shiga wani daki ita kuma Sala ta jira a can wajen shakatawa. Sai da ya sanya ta tube kayanta sannan yace dole sai ya fara kusantarta sannan zai mata aikin. Hankalin Abu ya tashi matuka ta mike ta daura zaninta tana masa wani duba na tsana da tsiwa ta ce, "Sannu tsohon dan iska Bunsuru, bayan an biya ka kudinka, to na fasa ai ba kai kadai bane mai aikin ba, ka biya mu kudinmu mu tafi wani gurin." Hankalin likitan ya tashi don ya kwadaita da Abu dan ya jima bai yiwa yarinya karama mai kyau da kyan sura irin tata aiki ba, dan haka ya kwantar da kai da gurbatacciyar hausarsa ya dinga lallashinta, amman fir Abu taki yadda. Da dai ya ga ba zai shawo kanta ta haka ba sai ya ce, shikenan ya fasa ta hau gadon yayi mata aikin, bata yi musu ba ta kwanta, tana ji ya zurkuda mata wata allura wacce ko minti uku bata yi ba taji duk jikinta ya mutu ko hannu ba zata iya dagawa ba, bakinta ma ya kasa buduwa balle tayi magana, za mu iya cewa tayi karamar suma ne, Amman tana jin duk abinda yake faruwa sai dai ba zata iya yin ko motsi ba dan allurar bacci yayi mata da yake tana da karfin jini ya sanya ba tayi baccin ba. Tana ji tana gani katon Iyamirin likitan nan ya biya bukatarsa amman bata da halin hanawa, sai da ya kammala dan kansa sannan ya dauko kayan aiki ya fara yi mata. Sanda ya tura karafunan da zai dagargaza abinda ke cikin nata ji tayi kamar ana zare mata rai dan azaba, amman ko motsi ba zata iya yi ba, sai dai hawaye dake zubowa ta gefen idonta. Shi kuwa katon kedarin ko a jikinsa, ya sanya karfan ya burge abun da ke cikin kamar yanda ake markada kayan miya, bayan ya gama watso abinda ke cikin ya kuma sanya wani ruwa mai magani ya fara wanke cikin, sai da ya wanke shi tas sannan ya maida mata kafafunta yanda suke. Azaba dai ta sha ta, hawaye sai da ya jika gefen da take kwance, ajiyar zuciya kawai take yi amman ba zata taba mantawa da wannan azabar a rayuwarta ba har abada. Yayi mata wasu allurai na rage radadi sannan ya tura ta can dakin hutu, cikin dan kankanin lokaci duk kamanninta sun sauya saboda tsabar azaba. Sala ta isa kanta da sauri tana mata sannu sanda aka sanar da ita an gama, sai a lokacin ta sami bakin magana ta fashe da kuka mai ciwo. Wannan Ma'aikaciyar jinyar ce ta shigo dakin hannunta rike da magani ta yiwa Abu sannu sannan ta ce, "Likita ya gama da ita babu komai a cikinta dan haka nan da awa uku idan ta huta zaku iya tafiyarku, sai dai Hajiya daga yau sai ku daina sakaci ciki yana shigar 'ya'yanku, don ke Zainabu yanzu kin ji azabar da kika sha, dan haka gwara ku dinga rigakafi kafin ciki ya shiga." Sala ta dube ta da mamaki tana fadin, "Dakta yanzu akwai wani abu dake hana daukar ciki dama?" Ma'aikaciyar jinyar ta ce, "Eh akwai mana, allura ce da magani har da kulle mahaifa ana yi, in mace tayi daya daga cikinsu ba zata sami ciki ba." Sala ta amshe cike da mamaki a fuskarta, "Oh! Ni Salamatu ki ji wata fasaha, rashin sani yafi dare duhu, da mun sani da yaushe za mu sha wannan wahalar? Kin ji fa Abula." (Sala ba ta ji tsoron Allah ko yin nadama da abin da ya sami Abu ba, ba ta hankalta da isharar da Allah ya nuna musu ba har take neman hanyar da diyar ta ba za ta kuma yin ciki ba, hakan ke nuna daman tashin hankalin da suka shiga na samun ciki ne ba na gyaruwar zuciya ba. Menene amfanin irin wadannan iyaye? Kai, tir! Da su, domin su ne tushen gurbacewar al'umma a ganina). Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ma'aikaciyar jinyar ta yi ta musu bayani, Sala tana ta girgiza kai cike da mamaki, ita kam Abu ita kadai ta san abunda take ji, sai dai tana jin dadin bayanin likitar, ta kuma yi alkawarin ba zata kuma samun ciki ba, yanzu ma rashin sani ne. "To, yanzu likita a ina ake samun maganin tsarin iyalin?" Sala ta tambaya. Sister din tace, "Ai ana samu a duk asibitocin da kika je, sai dai su asibitin gwamnati suna da ka'ida, basu bayarwa sai matan aure, ko kuma idan kinje da mijinki, har wasu masu zaman kan nasu ma akwai wadanda ba sa zubar da ciki saboda rakiyar asara, amman kin ga mu nan babu ruwanmu za ki iya zuwa ki siya ko a chemist dina." Sala ta ce, "Kai likita mun gode da wannan kirkin naki." Ta yi murmushu ta ce, "Suna na Sister Asibi, ko da wata rana kunzo neman wani taimako,ta yi musu kwatancen gidanta ta tafi ta barsu cike da murna, dan itama tana da nata kason, don ka'idar asibitin nasu idan mara lafiya ya zo ta sanadiyyar ka kana da kaso mai tsoka musamman ma zubar da ciki. Karfe biyar suka koma gida, shatar mota ma suka dauka, da kyar Abu take iya taka kafarta, san da suka isa jama'a na ta kallonsu, masu zargi na yi masu addu'a kuma na yi, da haka suka shige gida. Da suka isa daki suka baje Sala ta dauko naman da suka yo tsaraba da shi suna ci suna mayar da yanda aka yi suna ta dariya ta abunda suka dinga yi jiya har da kukansu. Ita kuma Abu sai baiwa Sala labarin irin azabar da tasha take yi. Sala ta ce, "Ai an gama, da kin samu kwarin jikinki zamu koma su yi miki allurar da suka ce din, tunda dai duniyar ta sauya gwara mu fizgi rabonmu muma, dan na san idan kika murje kika goge, Alhazan birni ne zasu yo miki caaa, tun da dai kina da kyau da sura mai daukar hankali." Suka kwashe da dariya har da shewa. Sadiku da duk maganar da suke yi a cikin kunnansa ya daga labulan ransa a bace hankalinsa a tsananin tashe, nan fa suka yi tsamo-tsamo kamar wadanda aka watsawa ruwa, cikinsu aka rasa ko mai tari balle su yi magana, dan daga ganin fuskarsa sun san ya ji duk abin da suka ce. Shaf! sun manta basu rufe kofa ba, ko su yi a hankali ba. Da kyar ya iya bude bakinsa cike da takaici ya ce, "Sala yanzu tsakaninki da Mahaliccinki Ubangijin da ya halicce ki kun kyauta abinda kuka yi? ko tsoron Abu ta rasa ranta a gurin zubar da cikin nan baki yi ba, daman tun ranar da na ga kin gigice na yi zargin wani abu na shirin faruwa koma ya faru, na yi iyakacin iyawata a kan tarbiyyar yarinyar nan har kina jin haushina. Sannan wannan abu da ya faru bai zame muku ishara ba sai ma kara kangarewa da Abu ta yi? Shin Sala kun san sanda zaku mutu? Ba kwa tsoron Allah? Ba kwa tunanin Ubangiji ya dauki rayuwarku kuna cikin wannan mummunan sabon? Da nayi niyyar fita daga harkarku sai dai ya zama dole na tunatar da ku gaskiya koda kuwa zaku tsireni ne nauyi ne a kaina, tunda shi Babanmu ya gaza. Sannan ke Abu azabar da kika sha ba zata zame miki ishara ba? dan bata kai kashi daya cikin dubu ta azabar lahira ba, dan haka ki hankalta ki san..." "Kai! Ya isa haka malam." Sala ta katse shi. Ta dora da cewar, "Ka wani saka mu a gaba kana mana surutu mara ma'ana sai kace wasu 'ya'yanka, idan aljannar ta ubanka ce ka hana mu shiga, sannan idan kace za'a yiwa Abu azaba dan tayi ciki shi kuma mai saka ido sana'ar da babu uwa babu riba yaya za'a yi dashi? Ka saka mana ido kamar wani Ubanmu, wallahi ba dan a tsakar dakin nan na haife ka ba da asibiti ne sai nace musanya miki kai aka yi, dan baka kaunarmu ka tsane mu, to ta Allah ba taka ba dan saka ido." Yayi wani murmushi mai cike da takaici yace, "Sala ina kaunarku a matsayin wadanda bani da kamarsu a duniya, wannan ya sanya ni nake gaya muku gaskiya, dan wanda baya kaunarka bai gaya maka gaskiya.......Malam ka ishe mu haka, ba'a san gaskiyar taka soko shashasha, har ni zaka ce zaka gayawa gaskiya? Tun kafin a haife ka na san gaskiya. Bace min da gani tun ban daga maka nono kabi duniya ba." Ya saki labulen jikinsa sanyi kalau zuciyarsa tana suya. Abu tace, "Sala kiyi masa kashedi kada yaje yayi ta fadi a duniya yace nayi cikin shege mun zubar." "Hakane fa." Sala ta fadi da sauri ta daga labulan tana fadin, "To, saura naji wannan maganar a bakin wani, ranka zaiyi mummunan baci Sa'idini, sarkin sa-ido." Shi dai baice komai ba don ko juyawa ma baiyi ba ya cigaba da tafiyarsa ransa yana cigaba da suya. Sala kuwa cigaba tayi da balbalin bala'inta tana fadin, "Haka kawai an saka wa yarinya ido dan anga Allah ya bata kirar da zataji dadin rayuwarta, dan haka babu ruwan uban kowa koda sadaka take bada kanta balle ma da makudan kudi ne." (Ubangiji ya shirya mu har wadanda suka bata, mu gane gaskiya kuma ya bamu ikon binta, Amin).Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 KANO: 15/5/2003 Kyakykyawar budurwa fara tas, sai dai bata cika tsawo ba dan haka koda yaushe zaka ganta da dogon takalmi,ba ta da gashi mai tsaho amman akwai yawan gyara shi, tana da dogon hanci wanda ya fito da ainihin kyawunta, bakinta kuwa irin dan karamin nan ne kamar na yara, sai idanuwanta wadanda ke ruda 'yan maza duk sanda ta kalle su da shi saboda girmansu da kuma kyansu, har wata digon zaiba ce a ciki, ga ta da dan karan yanga da iya kwalliya, wadannan abubuwan suka hadu suka maida ta irin matan da zamani ke yayi. Tana sanye da riga da siket na atamfa wanda ya matse ta tsam-tsam daga kugunta, 'yar kibarta ta yi cas- cas cikin kayan, fatar jikinta na da laushi tamkar 'yar jaririya, tana sanye da katon takalmi mai kama da tsani don tsaho, fuskar nan tasha ado irin na wayayyu, sai ta shafa jambaki kalar kayan jikinta, bata sanya kwalli ba, sai dai ta zizara jagira cikin idon nata, gashin girarta ya kwanta luf-luf gwanin sha'awa, daga yanayin shigarta da tafiyarta kadai ya isa ya yaudaro 'yan maza dan duk inda Zainabu ta bi sai an kalle ta. Kayanta kalar katuwar jakarta ce, ga wani kamshi da ke tashi a jikinta kamar kana kantin sai da turare, tana da matukar fizgar hankalin duk wanda ya dora idonsa a kanta, sannan hatsabibiya ce ta fannin mu'amala, domin ta kware ainun a iyar tafiyar da namiji don haka duk mutumin da ya kusance ta ko sau guda ne sai ya kidima a kanta. Ta fito daga dakin nata bakinta sanye da wata alawa mai tsananin kamshi tana tsotsa, Sala dake shan kayan marmari wanda Zainabun ta kawo musu tsaraba jiya da ta dawo daga Abuja, zaune ta bararraje a tsakar gida tana kallon Zainabu, duk da ranta a bace yake sai da ta yi murmushi dan ganin yanda Zainabu taci uwar kwalliya, tana dubanta da fara'a tana fadin, "A'a 'yar albarka kin fito? Sannu da fitowa." Zainabu ta yamutsa fuska gami da amsawa. Salan tace, "Jiya na so muyi maganar yarinyar nan sai naga kin dawo a gajiye, ga shi kun yo dare....." "Wani Abu ne kuma ya faruwa?" Zainabu ta katse Sala din (don yanzu ta tashi daga Abu ta koma Zainabunta). "A'a a kan dai maganar nan ce ta kwanaki ta matsiyacin yaron nan da ta nacewa, shi kuma wannan yaron dan saka ido yana ziga ta kamar shine uwarta, to yanzu wai iyayansu za su aiko, ni kam sam ba na son tayi auren nan, me take da shi? Ita ko sha'awarki bata yi, koda yake ko ba tayi auran ba ma bata da wani amfani tunda ta ki yarda ta ciwo arziki, dan haka sai kiga shegiyar tayi sati biyu bata da ko kwandala, sai dai idan an yi musu albashi ya sanmata, wanda duka albashin nasa bai wuce kudin takalmi da jakarki ba."Zainabu ta yamutsa fuska tana fadin, "Sala ki barta ta yi auran nan taji, in dai Maza ne ai zata gane kurenta, banza ana neman a samo mata mai maiko tun da ta nace sai tayi auren tana ki tana wani rawar kai, ki rabu da ita kawai, dan rannan baki ga wani abokin Alhaji T.J ba yanda ya mato a kanta, har na nuna masa ya rabu da ita kanwata ce, sai ya rantse mini da cewar shi da aure yake sonta, amman babu yanda banyi ba yarinyar nan ba taki ko kula shi, haka ya hakura ya kyale ta don ya yi-ya yi ya gaji, shi da mata ke sonsa kamar me? Shine fa kwanaki ya bani kujerar Makka guda ukun nan da na kai ku ke da Baba." "La'ilaha Illallahu, kai amman yarinyar nan bata da rabo, arziki yana kiranta tsiya tana janye ta, ina ga fa matsa mata zamuyi ta aure shi kawai ko ta tsiya ko ta dadi." "A'a Sala ina ruwanmu? Ita ce fa zata zauna da mijinta, sannan yanzu idan muka hada su haushinmu zata dinga ji, gwara mu kyale ta ta yi hankali, ni bari na wuce kada na yi latti, kin san nace miki muna da bikin cikar Asma shekara ashirin da biyar, zan je mu fara shiri saboda shi na dawo jiya." "To-to, Allah ya kiyaye, zaki dauki shatar mota ne?" Zainabu tace, "A'a Alhaji Danlami sabon kudi yana waje yana jirana." "To Allah ya tsare, ya bada sa'a." Tace, "Amin." Gami da ficewa. Yana cikin mota zaune ya sha manyan kaya kamar wani mutumin arziki, tunda ta fito ya zuba mata ido tamkar maye, ita kuma tana tafiya tana rangaji tamkar ganyen bishiyar da iska ke kadawa, tafiyar dake dauke hankalin 'yan maza. Tana isowa ya bude mata kofa yana murmushi gami da fadin, "Barka da warhaka Hajiya, irin wannan shanyar haka har na bushe?" Tayi wata mayaudariyar dariya ta jan hankali, tace, "Lallai kam, to waye ya gayyace ka? Ina ga kaine fa ka sakani fitar nan, da ka gaji ba sai ka tafi abinka ba na huta." Ya kanne ido yana mata wani kallo yace, "Ni na isa? ai kina da tsayawa mutum a rai Zainabu, kusan duk aikin da nake fa idan kika fado mini bani samun sauran sukuni muddin ban iso gareki na ji duminki ba, ko matana na kasa zama da su kamar ke, anya Zainabu kina tausaya mini kuwa? Dan Allah ki daure ki aure ni mana ko na sami nutsuwa." Tayi masa wani malalacin kallo ba tare da tace komai ba ta kauda kai gefe, ya kuma rudewa ya matsa kusa da ita jikinsa har rawa yake yi. Ta kuma matsawa gefe tana harararsa gami da fadin, "Haba Malam, ko dai dan bunsuru ne ka saurara mu bar kofar gidan ubana da kuma tsakiyar ranar nan, duk iskancina ban taba yi a kofar gidan ubana dan ina mutunta gidan." Ya ja baya yana shafa haba yace, "Kai Zainabu kina juya ni wallahi kamar waina, amman babu komai zan matsa lamba har ki zama mallakina." Ya tada motar yana ta sumbatunsa, ita kuma murmushi kawai take yi, ta gama kashe shi da kissarta da kallonta gami da tsananin kamshinta. Sai da ya kaita wani babban gidansa na shakatawa suka gama watsewarsu sannan ya cika mata jaka da kudi dan ya san Zainabu mai tsada ce, sannan suka dauki hanyar gidan Asma, har lokacin yana ta sumbatu a kanta da yaba kyanta da iya mu'amalarta. Sanda suka isa gidan Asma ya kwantar da murya kamar wani abun tausayi ya ce, "Yaya dai Hajiya, karfe nawa zan dawo na dauke ki?" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta galla masa harara tana fadin, "Kai fa tsiyata da kai kenan ba ka iya cin kwan makauniya ba, to ai ni din ba matarka bace da zaka hana ni sakewa." Ta kammala maganar tana murguda baki. Ya lankwasar da kai yana fadin, "Tuba nake Hajiya, kece din sai a hankali, amman na hakura sai gobe zan bullo." Ta daga kafadarta gami da fadin, "Kai dai ka sani, sautun mahaukaciya." Ta fice daga motar. Har tayi nisa yana kallonta kamar ya kuma binta yake ji. Zainabu macece hatsabibiya mai tsayawa mutum a ransa, ta san yadda take iya tafiyar da shi kamar wacce ta karanci abun, ya rasa abinda ya sanya matansa ba sa masa irin yanda Zainabu ke masa, da zai sami mai masa kamar Zainabu cikin matansa ai da babu abinda zai sanya shi yawo ana wulakanta shi, dan yana ga idan ya sami Zainabu ta aure shi yana jin ko kofar gida sai anyi da gaske zai fita, da kyar ya samu ya iya jan motarsa ya bar kofar gidan. Ta shiga gidan da ihu babu ko sallama, Asma dake zaune daga ita sai gajeren wando da 'yar rigar mama tana busa tabar wiwi tana wani lumshe ido, ta mike tana ihu suka rungume juna. Asma ta ce, "Shegiyar, wallahi na yi zaton ba zaki zo ba, da kin kwafsa mini." Suka zauna suna mai da numfashi, sannan tace, "Haba Hajiyata ai kin san dole na zo, yaushe zan yarda chasun nan ya wuce ni?" Asma ta fashe da dariya tana fadin, "Dan akuyan naki ne na san shi da jaraba ko bunsuru ya rufa masa asiri, na san da kyar zai barki ki dawo, ko da yake Zainabun akwai iya iskanci, har tsoro nake ji idan na ga saurayina yana kallonki, don har ta kafa sigina kike yiwa namiji,suka fashe da dariya gami da tafawa. Zainabu tace, "Wai ni yaya shirye-shiryen fatin ne? Ina fata kin tanadar mana komai?" Asma ta tabe baki tace, "Kin san akwai maza 'ya'yan wahala wadanda iyayensu da matansu suka sallama mana, sun gama komai. Senator Tanko ya kama mana hotel dama komai da za'a ci a gurin, sai dai shegen wai ba zai zo ba dan kada 'yan adawa su sami abin da zasu soke shi a kafafan watsa labarai. Oho, ni ko a jikina dan daman bana son ganin wannan mummunar fuskar tasa wacce zata hana samari 'yan bana bakwai isowa jikina mu sha minti, dan kin san sun kwana biyu sai a hankali, dan wallahi duk sanda na kalli fuskarsa sai ta tuno mini da wani tsohon goggon biri." Suka kuma fashewa da dariya gami da tafawa. Zainabu ta zira hannu cikin jakarta da dauko kwalbar Shandy ta kama tsotsa, ta jingina da kujera tana lumshe idanuwa Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Asma ta kalle ta gami da fadin, "Ke 'yar duniya babu ko dandano? Kin kafa kai kina tsotsar abun ki?" Zainabu ta dube ta da ido daya dayan kuma ta kanne shi, "Malama kada ki matsa mini ki bar ni na yi dif! Ina ce tadda ke na yi kina busa tabar mulki kin mini tayi ne?" Ta kuma matsawa gabanta tana kwantar da kai tace, "Haba tawan ki yiwa Allah ki ba ni na kurba ko sau daya ne, na kwana biyu ban tsotsa shandy ba" "Amshi 'yar jaraba ba zaki bar ni na sha ta ishe ni ba." Ta mika mata kwalbar giyar, sannan ta dauko nadaddiyar tabar shaidan a jakarta ta bata wuta, hayaki ya fara gauraye dakin, Asma ta sakar musu kidan Bob Marley nan fa suka tashi suna cashewa suna wani gantsare- gantsare, daman Zainabu gwana ce gurin rawa. Misalin karfe goma na dare motoci suka fara sauke mata a kofar hotel din da zasu yi fatin, sun ci uwar kwalliya sai dai babu wacce zaka kalla kace diyar Hausawa ce balle Musulmai, don duk irin shigar turawa suka yi, daga masu gajerun wanduna sai masu damammnun kaya da 'yan kananan wanduna. Dakin taron kuwa kida ne kawai ke tashi kamar zai tsaga daki, kowacce da saurayinta take shigowa. Shigowar Zainabu da Asma ne ya sanya kallo ya koma kansu, dan komai iri daya suka sanya, wani gajeren siket suka sanya wanda ya tsaya iyakacin gwiwarsu ya matse su sosai yana ta kyalli, sai wata 'yar yalolowar riga mai rawa ta zauna das a jikinsu, takalmansu har gwiwarsu, sai gyaran gashi da suka yi, duk da Zainabu bata fiye sanya gashi ba yau ta sanya, fuskar nan ta dauki kwalliya sai wani kamshi ke tashi daga jikinsu. Mai jawabi sai kwarara musu kirari yake, "'Yan mata adon gari, 'yan matan da duniya ke yayi, Asma ta Zainabu manyan Bebis da duniya ke yayi, kun girmi kwailayen Kano, kuna ruda mazan kano." Aka fashe da ihu. Zainabu sarkin rawa sai ta hau taka rawa dan daman yanda ka san mazari haka take, gaba daya sai ta dauke hankalin mazan dake gurin dan Zainabu daban ce, irin matan nan ne masu kamar fitila duk inda suka je sai sun haske shi, nan fa maza suka yi caa a kanta, ana ta mata liki amman miskilar ko a jikinta dan babu wanda ta baiwa fuska.Zainabu daban ce ko a duniyar barikin tasu, dan idan namiji bai yi mata ba duk kudinsa bai isa ko kallo a gurinta ba, tana jan zaranta yanda take so, dan ta san Allah yayi mata kirar daukar hankalin maza, an sha dambe da yanke-yanke a kanta, ko waye kai idan zaka kwana dubu kana mata magana ba za ta tanka maka ba, musamman idan tayi dif da Shandy dinta. Sai karfe hudu na dare aka tashi daga fatin nasu, an rakashe an cashe an sha kayan maye kala-kala, Zainabu kam tangadi take yi dan ta cake da yawa, ganin haka ya sanya Asma ta sanya ta a motarta suka nufi gidanta don ta san 'yan gidansu basu san tana shan giya da wiwi ba sai dai tana fita yawon gantalinta. Sai da gari ya waye sannan ta dawo hayyacinta, bayan ta farka ta shiga ta yi wanka ta yi ramuwar Sallar dake kanta sannan ta yi shirin tafiya gida. Tana sanye da doguwar riga ta atamfa super da aka ciwa mutunci, dinkin ya kama ta tsam daga kirjinta yayin da yayi baza daga kasa, hannun rigar tamkar shimi yake, ta yafa karamin gyale, sai tsireren takalminta mai kama da tsani, ta sanya zobba na gwal kirar dubai, da wani dogon dan kunne a kunnenta, kamshin dake daga jikinta tamkar kamfanin turare dan Zainabu ma'abociyar son kamshi ce. A adaidaita Sahu ta sauka dan bata nemi dan rakiya ba, duk yawan mazan da ta dauki hankalinsu daran jiya dake neman shiga, ta shiga gidan nasu da sallama muryarta tamkar sarewa. Sala da ke zaune ta mike tana hangame baki gami da fadin, "A'a diyar albarka har kun dawo? Har an gama fatin kenan." (Kuji wannan Uwa fa, diya budurwa ta kwana ta hantse a titi amman wai mahaifiyarta tace har ta dawo? Hmmm, su Sala ko sai yaushe za’a dawo kan hanya). Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta zauna jabar bisa tabarmar da Sala din ke kai tana fadin, "Mun dawo Sala, wallahi fatin yayi kyau.Yaya na ji gidan shiru ne ko duk ba sa nan?" Sala ta tabe baki gami da fadin, "Yaran dai basa nan amman Karimatu na nan, dan jiya nayi wa yaron nan tas mai hure mata kunne, nace kada ya kuma zuwar mini gida shine take ta kumbure-kumbure, motarsa fa daya ce tal Abula, mai na sama ya ci balle ya baiwa na kasa, mtsw!" Ta yi tsaki cike da takaici. Zainabu ta yi kwafa kana tace, "Ke ma Sala da son bata ranki kike a banza, ina ce tun jiya mun gama maganar, tunda ta dage sai shi ai sai ki rabu da ita ta aure shi, kowa rai yayi ma dadi baya ga mai shi ne." Sala tace, "Ai shike nan, kina ji ke Karimatu sai ki gaya masa ya turo iyayen nasa ko ma huta da naci kamar maye." Sala dai kamar tsoron Zainabu take ko dan tana kawo mata kudi? Duk hukuncin da ta yanke a gidan babu wanda ya isa ya ja da shi koda yayanta kuwa. Karimatu dake daki tana karatun Kur'ani dan ta sami sassauci a zuciyarta saboda kwana tayi tana kuka saboda yanda Sala ta bada ita ga saurayin, wanda ko da ya aure ta ba zai kuma ganin darajar Mahaifiyarta ba, tayi hamdala ga Allah gami da yin Sujjada tana kara gode masa, don Allah ya sani tana son Abbas kamar ranta, shima yana masifar son ta, soyayya suke mai tsafta, sai dai tun da ta kawo shi gidan da sunan wanda zata aura Sala take aibata shi, daman yaya lafiyar kura balle ta yi hauka? Don daman basa shiri sam da Sala, dan tun tana yarinya taso ta yi hali irin na Abu amman ita Allah ya tsare ta shine fa Sala ta tsangwame ta kamar ba diyarta ba, ko da harkar karatunta Sadiku ne ke tallafa mata da komai,Don zamu iya cewa kusan su kadai ne shiryayyu a gida, dan kannanta dake bin ta maza duk sun fara shaye-shaye, Sadiku ya yi dasu har ya gaji don yana tufka Sala na warwarewa ne, su kuma 'yan kannansu mata kanana guda biyu suma tallan suke yi, kusan hanyar da Zainabu tayi rayuwa suke kai, sai dai karamarsu ce ta dauko halin Karimatu da alama sai kuma autansu. Bayan Karimatu ta gama godiya ga Allah ta dauko wayarta da sauri duk da tana jin nauyin Abbas din amman haka ta yi kiransa, bugu daya ya dauka don tun jiya yake neman wayarta har ya gaji ya hakura, ita kuma ta rufe ne saboda nauyinsa da take ji don ma kada ya kira ta bata san mai zata ce masa ba kuma. Gaba dayansu suka yi shiru kowanne yana jin nauyin dan uwansa ita kam har da kunya ma. Shine ya daure ya ce, "Yaya dai Karimatu, tun jiya nake neman wayarki a kulle, har hankalina ya tashi na yi zaton ko kin daina daga waya ta ma." Tayi wata doguwar ajiyar zuciya kana tace, "Abbas kunyarka nake ji ban san da idon da zan kalle ka ba, don na sani Sala jiya tayi maka cin mutuncin da ina jin ba'a taba yi maka ba, sai dai ba kai tayi wa ba illa ni, don Allah ka yi....." Kuka ya kwace mata ya hana ta karasa maganar tata. Ya kwantar da murya yana fadin, "Kin ga Karimatu ki kwantar da hankalinki, na riga na san halin Sala tuntuni na kuma ji na gani don babu gudu babu ja da baya a son ki, na san tayi haka ne dan na yi fushi na rabu da ke, ni kuwa sai na ji ma yanzu na fara son ki, dan haka ki kwantar da hankalinki mu yi batu a kan abinda zai fishshe mu." Ta dan ji sanyi a ranta dan haka ta sami kwarin gwiwar gaya masa abunda ake ciki, na yanda Sala ta amince ya turo da iyayensa, abin ya bashi mamaki sai ya ga kamar mafarki yake yi don shekara nawa suna fama da Sala, amman ace lokaci daya ta amince? Sai Karimatu ta nuna masa kawai karfin addu'ar da suke yi ne ya sanya hakan ta faru, ya amince da lallai hakan ne dan haka ya dinga hamdala ga Allah, daga karshe suka yi sallama cike da farin ciki. Abbas kam jin sa yake kamar yafi kowa farin cikin zai mallaki Karimatu, duk da sanda ya fara nuna wa abokansa yana son Karimatu sun kwabe shi dan suna cewar waye bai san iskancin da yayarta Zainabu ke yi a unguwar ba ‘karuwar gida’ haka suke kiranta a bayan idonta, yace shi kam ya ji ya gani dan ko Allah bai kama wani da laifin wani, Tunda kowa ya san halin Zainabu da na Karima ba daya ne ba, don babu wanda zai ce gida daya suka taso ma, sai dai kamar su da tayi daya baya ga Zainabu gajera ce amman ba can ba, sannan tana da dan jiki yayin da Karimatun ta kasance doguwa siririya, Allah ya kuma sanya iyayensa masu ilmi ne kuma wayayyu dan haka suka goya masa baya gami da yi masa addu'a ta gari, wacce ita ce ke dawainiya da shi a duk inda ya sanya gabansa. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 ************* Ba da wani dadewa aka sanya rana ba wata uku ne kacal, sai dai tun da aka sanya ranar Sala ke mitar bata da shi, dan bata ga abinda Karimatu ta yi da zata mata kayan daki ba, dan ko sanda suka yi talla banda kwantai babu abun da take yi, balle yanzu da bata da ko na sayen kwalli. Shi kuwa Baba Abbakar ba'a ta tasa, don kudin da aka kawo na zance ma so ya yi ya cinye sai da Sadiku ya yi masa jan ido, shine ya ji haushi shima yake fadin, "Ya ga mai yin gadon." Shi dai Sadiku kallon su kawai yake yi yana ta kokarin ya rufawa 'yar uwarsa asiri. Biki ya rage saura kwana uku Sadiku ya shigo da kayansa na katako irin wanda ake yayi, da kujerunsa masa kyau da tsada. Maimakon Sala ta yi murna da sanya albarka sai ta hau tabe baki tana fadin, "Eh! Da yake Karimatu ce kayi mata kaya masu tsada, da Abula ce da ka tsana da ko tsinke ba zaka yi mata ba." Sadiku yayi murmushi ya ce, "Sala kenan, da Zainabu da Karimatu duk 'yan uwana ne, ita ma ta daina iskancin ta fito da miji kin ga idan ban mata wanda ya fi wannan ba." Zainabu da ke zaune tana yankan kumba tana zaune bisa darduma ta doka tsalle tana tafa hannu ta ce, "Wallahi karya ne, na fi karfin na tsaya ka yi mini kayan daki, dan yanda kake aiki nima ina yi, da kake ce mini 'yar iska ai na gode Allah tunda ba na neman mata, ka duba ka ga yanda yanzu mata ke neman....." "Dalla can, rufe mana baki marar kunya, ki yi abinda duk kika ga dama ai rayuwarki ce, na san komai dadewa zaki gane kurenki, Karima dai Allah ya rufa mata asiri, ba ta yi irin halinki ba, dan haka kuka tsane ta gidan nan....." "Ahaf! Ahaf!, Wato dai ni kake gayawa magana ko?" Sala ta amshe da saurinta, "To ka ga fita daga gidan nan tun ban bata maka rai ba, duka yaushe ka fara samun kudin? Kafin ka fara rike dubu daya Abula ta rike dubu goma, kuma duka albashin naka nawa ne? Abin da ko kudin takalmi da jakarta ba su kai ba? Ka da ka kuma furta mini ko kala, fice ka bani guri tun ranka bai kai ga baci ba." Ya gallawa Zainabu harara wacce ta rama sannan ya fice, yana yiwa Karimatu magana, "Ki lura da yanda za'a shiga da kayan kada fentin su ya goge." Tana daga can zaune gefen kicin tana yanka Salad da zasu ci abincin rana da shi tace masa "To." kawai. Ai sai bala'in Sala ya koma kanta, ina wuta ta jefa ta, zagi ta uwa ta uba da gori tana fadin, "Dadin abin dai da abincin da Abula ke ciyar da ke kika rayu ke da shi din." Ita kam ko kala bata ce ba, dan idan da sabo ta saba, ita kam aikin ta ma ta cigaba da yi ko a jikinta. Zainabu ta ce, "Haba Sala, ki yi shiru haka mana ka da muyi bakin kunya." Ai kuwa tamkar ta ji wahayi daga mala'ika ta yi shiru. Ita dai Karimatu dariya ma abin ya bata ta ce, "Idan ka ki sharar masallaci kayi ta rumfar kasuwa ai." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 CALIFONIA: 30/9/2003 Yana tsaye jikin window hannuwansa nannade a kirjinsa, dogo ne ba sosai ba yana da dan jiki irin na maza majiya karfi, jikin nasa a murde yake, yana da kyau irin na gogaggun maza da suka san duniya, bai cika fari ba amman ba zaka sanya shi a layin bakake ba, yana da irin gashin nan da samari ke ajiyewa a fuskarsu, ya iya daukar kwalliya irin ta namijin duniya. Bai fiye hayaniya ba, miskili ne ga wanda bai san shaidancinsa ba, ma'abocin farin jini ga shan yabo ga jama'a saboda faran-faran din sa da sakin hannu (kyauta), amman a badini mutum ne mai tsananin son holewa, sai dai yana da matukar taka tsantsan don yana gudun bacin ran iyayensa. Ransa a cunkushe yake, lokuta da dama idan abin ya motsa masa sai ya ji kamar ya zama tsuntsu ya bar garin, ya dade yana tausar zuciyarsa a kan abinda yake gani ba komai ba ne, sai dai yanzu abin yana neman fin karfinsa da shallake iyakacin dauriyarsa. Abin da ya faru dashi tsahon wasu shekaru da yake ganin a can baya mara amfani da muhimmanci, har idan ya tuno abin yakan kira shi da tsuntsu daga sama gasashshe, sai dai tunda ya yi nisa abin ya fara damunsa, da farko yakan ga kamar abin nan ne da Hausawa kan kira 'Sabo tirken wawa' sai dai da yaga duk kwanan duniya abin yana kuma tsiro a zuciyarsa har ya kai matsayin da ya cika zuciyar tasa babu sauran wani gurbi na tirjiya da dauriya. Ya yi kwafa a karo da dama ya juyo yana kallon kayataccen falonsa wanda ya sha kayan alatu kamar ba za'a mutu ba, ya isa dan gurbin shan lemo, ya zuba lemo a kofi ya hada da shandy ya cilla kankara ya daga ya shanye wai ko zai ji sanyi a zuciyarsa, sai dai har lokacin abin yana nan, sai yaga kamar ma karuwa ya yi saboda mutuwa da jikinsa ya yi sabon tunani ya shige shi. "Me ya sa haka ne?" Yayi wa kansa tambaya, wadda tsawon lokaci yake yiwa kansa, ya dauko taba ya kunna ta ya bata wuta a hankali yana lumshe idanuwansa amman har lokacin bai ji sanyi a ransa ba. Ya jawo takardar da ya bayar da irinta a Ofis dinsu jiya ta barin aiki yana kuma dubawa, wayarsa ta fara kara ya dauka da kyar yake magana, abinda aka gaya masa kamar kara hasala shi aka yi don haka da zafin rai yake magana cikin harshen nasara. "Eh! Ni ne na rubuta dan na yanke shawarar barin aikin nan don jama'ar kasata na bukatar gudummawa ta, sannan iyaye na sun damu da su ganni,haba Mustafa kada ka yi mana haka, idan albashinka ne ya maka kadan zamu iya kara maka mu." A ransa yace, "A wannan karon babu wanda zai hana ni tafiya dan zan biyawa raina bukatarsa ne, dan idan na cigaba da zama a haka zan iya asarar farin ciki da kwanciyar hankalina." Amman a fili sai yace, "Oga kuyi hakuri ba zan iya janye kudirina ba a wannan karon na tafiya ko da nawa zaku kara mini, nayi muku alkawarin dai duk sanda na sami dama zan dawo muku gaba daya, amman yanzu hankalina ya yi kasata." Dan Baturen da suke maganar ya sare, dan 'dan zaman da suka yi sun san Mustafa mutum ne kaifi daya, idan ya sanya abu a gabansa babu wanda ya isa ya hana shi aiwatarwa, dan haka ma ya rike aikinsa da gaskiya da amana, dan haka suke masifar ji dashi, shine zai bare inji ba tare da ya tsaya ya kalli 'yar takardar bayani ba ya maida ya hada shi kuma ya tashi tsaf, ba kamar sauran Turawan da sai sun duba ba a rubuce, ya dai daure yace, "Shike nan Mustafa muna maka fatan alkhairi, sai mun hadu a Ofis din. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Shike nan Oga sai mun hadun." Ya kashe wayar tasa gami da lumshe idanuwansa, wata rayuwa ta dinga bijiro masa wacce ta wuce shekarun baya wacce a da can yake daukarta shirme, sai dai yanzu ya tabbatar ita ce rayuwarsa mai cike da ainihin farin ciki da sanya shi nishadi da dariya, sai dai duk sanda yake tunanin wani abin mai fadar da gaba kan fado masa, sai dai yana addu'ar Allah kada ya tabbatar da wancan abinda ke fadar masa da gaban. Washegari jikinsa babu kwari ya fito daga Ofis din nasu dan alhinin rabuwa da abokan aiki, sai dai daman haka rayuwa ta gada dole wata rana za'a rabu, walau ta gurin zama ko aiki ko kuma ta har abada ma (mutuwa). Daga nan kai tsaye gurin neman Visa ya nufa ta komawa kasarsa ta haihuwa wacce rabonsa da ita tsahon shekaru. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 KANO-NIGERIA: 15/10/2003. Bayan ya sauka ya dauki shatar mota tun daga filin jirgi har gidan Mahaifinsa. Maigadi ne ya fara ganinsa don haka ya zuro da gudu cike da murna da doki yana fadin, "A'a Alhaji Mustafa yau kake tafe? Marhabun lale, sannu da zuwa." Mustafa yana murmushi yake amsawa ya sallami mai tasin, sannan ya dubi maigadin ya ce, "Malam Bala a shigar da kayan ko?" Daga nan ya shige cikin gidan kai tsaye, ya yi sa'a kuwa jama'ar gidan duk suna nan domin la'asar ce. Da Mominsa ya fara cin karo tana zaune a falo tana karatun jaridar Leadership Hausa, tana sanye da (Medicated glass), ya shiga da sallama bakinsa a washe. Ta daga kai cike da tsananin mamaki, suna hada ido dai ta tabbatar da lallai shine, ta mike cike da murna tana fadin, "Babana! Da gaske kai ne ka iso garin ba tare da ka sanar da mu ba?" Ya isa gaban Mahaifiyar tasa cike da farin cikin ganin Mahaifiyar tasa don ya kwana da dama bai ganta ba, dan ma wani lokacin ta kan bi Mahaifinsa suje ganinsa, don shi tunda ya tafi bai kuma waigo wa Nigeria ba, wanda shi wai nan dabara ya yi dan ya manta da abinda ke damunsa a ransa, a cewarsa idan ya yi nisa da abin zai samu sassauci koma ya manta gaba daya, sai dai yanzu ya gano dabararsa ba za ta kai shi ko'ina ba. Ya ce, "Momi barka da gida, na same ku lafiya?" "Lafiya kalau muke sai dai mamakin dawowarka yanzu babu sanarwa, Allah dai ya sanya lafiya." "Momi Lafiya kalau wallahi, na so kwarai na ba ku mamaki ne dan na sha sanya rana zan zo amman bana zuwa, dan haka nace wannan karon sai dai ku gan ni kwatsam." "Lallai kam ka ba mu mamakin, bari na je na samo maka dan abin tabawa." Ta mike ta nufi kicin din gidan. Tana isa kicin ta tadda 'yan matanta suna ta faman kacaniyar girkin dare, ta ce, "Albishirin ku?" Gaba daya suka ce, "Goro Momi." "To yayanku ya dawo yanzun nan, yana falo dan haka sai a hado masa abin motsa baki kafin a kammala girki." Gaba daya suka yi falon da gudu suna murna suna ihu, sun ma manta da abinda aka ce su dauka, ta yi murmushi sannan ta dauka ta tafi da shi. Yana ganinsu ya ce, "Lallai 'yan matan Momi an girma, kalle ku don Allah." Suka kalli juna suna dariya. Ya so tun daran ya fita ya fara aiwatar da abinda ya kawo shi garin, sai dai gajiya ta hana shi dan haka dole ya hakura har gari ya waye. Washegari ya shirya cikin manyan kaya wadanda suka kara fito da kimarsa da martabarsa, duk da zaman da yayi kasar waje bai daina sanya manyan kaya ba, musamman yakan aiko a yi masa, idan ya sanya turawan suyi ta sha'awarsa musamman idan zai je gidan biki ko wani fati, yawaita sanya manyan kayansa tun yana nan gida ya kara masa martaba a idanun jama'a har suke ganinsa wani mai hankali da tsantseni. Motar Babansa ya hau dan na shi yayo Odarsu ba su karaso ba, yana tafe yana jin wakar Bob Marley don mutuminsa ne, sai kada kai yake cike da nishadi, yau ce ranar da zai cikawa ransa burinsa, yau ne zai je ga Zainabu Abunsa karo na biyu da sunan soyayya, idan ya tuno abinda ya faru a baya sai ya dinga jin wani farin ciki da nishadi. Sai dai abinda ke fadar masa fa gaba idan ya tuna anya Zainabun tasa ba tayi aure ba? Idan aka ce Zainabunsa ta yi aure kuwa lallai yana cikin tashin hankali da rashin nutsuwa, dan ya gano yanzu itace rayuwarsa, sai yake ganin nisan gidan nasu da yake su sun tashi sun koma cikin G.R.A. Ya isa kofar gidan yayi fakin yana kallon gidan, kusan yanda ya san shi haka yake yanzu, sai dai wasu sauye-sauye da aka samu, mutane ne a kofar gidan can da can suna cikin kwalliya. Gabansa ya tsananta da faduwa da ya ga Sadiku sanye da manyan kaya da gani sababbi ne sai daukar ido suke ya zama babban mutum mai kamala, sai fito da abinci yake shi da wasu cikin farantai. Ya zubawa Sadiku ido har lokacin gabansa na faduwa, ya zuge gilas din motar a hankali yana kara kallon jama'ar dake kai kawo kofar gidan. Can ya hango wani maroki yabi Sadiku yana masa kirari ya sanya hannu a cikin aljihu ya dauko kudi ya ba shi, da alama yana cikin farin ciki, daga ganin alamun babu ko tambaya aure aka daura sai dai bai san ko na waye ba, ya yafito wani yaro da yazo wucewa ta kusa da shi yana kallon motar. Yaron ya karasa yana kallonsa a alamun rashin sani a fuskar yaron, "Dan Allah yaro daurin auren wa aka yi a kofar gidan ne?" Ya nuna kofar gidan da hannunsa. Yaron yace, "Daurin auren wannan din nan aka yi 'yar gayun nan mai kwalliya ni na manta sunan ta ma." Ya rasa gane wacce yaron ke nufi sai dai hankalinsa yayi kololuwar tashi don yana ganin kawai Zainabun sa ce ma, ammai sai yayi ta maza ya ce da yaron, "Na gode ka ji abokina, un go wannan." Ya mika masa Naira dari biyu, yaron ya amsa cike da murna ya tafi. Yana cikin mota yana ta sake-saken yanda zai yi, shin kundumbala zai yi ya futo ya tambayi wacce aka daurawa aure ko kuma hakura zai yi ya koma.Tunaninsa ya tsaya cak sanda ya hango wasu hadaddun mata sun nufo shi, dayar doguwa ce sosai fara amman da alama ta dan kara da na kanti, sai dayar gajera ce amman ba can ba, tana da wani irin kyau na daukar hankali, daga shigar ta har tafiyarta sun yi matukar burge shi, yana hango su suna doso shi, sai yaga mara tsahon da yawa fuskarta tana masa gizo kamar ya santa. Suka zo suka gota shi suna taku sannu a hankali, gaba daya sun tafi da hankalinsa, wani irin kamshi ya ji ya bigi hancinsa san da suka wuce, ya lumshe idonsa saboda kamshin da ya ji Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 "Anti Abu ga wayarki in ji Sala ta ce kin manta ta." Wata 'yar yarinya da ta fallo da gudu ce ke fadin haka. Mustafa ya bude idonsa da sauri. Wacce tafi tafiya da hankalinsa yaga an mikawa wayar, ta amsa ta sanya a jaka, yayi wata sanyayyar ajiyar zuciya mai cike da rudani yana fadi a ransa, "Yanzu wannan Abu ce da ya sani a can baya 'yar mitsitsiya da ko kwalliya bata iya ba, 'yar tallan abinci da ya wayar da ita, ita ce ta zama wata irin tauraruwar mata ta wuce yanda duk yake tunanin zai gan ta?" "Ya Salam" Ya fadi a fili. Ko da wasa ko a mafarki bai taba zaton Abunsa zata yi irin wannan wayewar ba, ya daukarwa kansa zai dawo Kano na Nigeria ya auri Zainabu, ba don tsananin kyau, ilmi ko dukiya ba sai dai dan tsananin sonta kawai da Allah ya jarabce shi, sai dai abun mamaki da tsoro sai ya ga Zainabu ta sauya ta wuce iyakacin tunaninsa gaba daya. Tashin motar da yaga sun dosa ne ya farkar da shi daga dogon tunanin da ya fada, ya tada ta shi ya bi bayan ta sun sai dai ina sun riga sun yi masa nisa, dan haka ko hangosu baya iya yi, dan hala dole ya dauki hanyar komawa gidan su dan ya ji kiran wayar Dadin su. Karfe takwas na dare ya kuma dawowa kofar gidan su Zainabu, don yinin ranar haka ya yi shi sukuku, ya dinga tuno yanda ya ga Zainabu na tafiya da kamshinta na yanzu, musamman yau Babansa bayan sun gaisa sai yayi masa maganar aure dan sun jima suna masa maganar yana cewa suyi hakuri har yanzu baiga wacce ta yi masa ba ne. Cikin wata shigar ya iso ya yi kyau matuka, shaddar har wani kara take yi saboda tsabar bugu da ta sha, sai dai ya tarar da cincirindon mata a kofar gidan, sai motoci ne ke diban su, sai dai addu'arsa Allah ya sanya ba Zainabunsa aka daurawa aure za'a kai dakin miji ba. Yayi fakin ya fito ya jingina da motar yana kallon matan dake kaiwa da komowa cikin hasken fitilar da ya haske kofar gidan. Har ya gama kalle-kallen sa bai hango Zainabu ba, wata budurwa mai shegen yangar tsiya da take ta wucewa ta gaban sa ko zai taya ya daure ya yafito, babu musu ta nufe shi kanta ya kuma fasuwa don ga dan gayu mai hadaddiyar mota yayi kiran ta zata buda gurin 'yan matan gurin, ta nufe shi tana kara salon tafiya tana wani girgiza, duk da ba wani kyau ta cika ba amman daga gani tana ji da kanta. "Barka da yamma adon gari." Ya fadi da wata mayaudariyar muryarsa, yayi mata kuri da idanuwansa wadanda ke ruda 'yan mata. Tayi wani far da idon ta da kyar kamar bata son magana ta ce, "Yauwa ya kake?" Yayi dan murmushi yace, "Kalau nake. Na ce banga amarya Abu ba ko har sun wuce ne?" Ya shirya hakan ne don ya tabbatar da gaskiyar abin. Ta yi masa wani kallo mai cike da mamaki sannan ta ce, "Hala dai mantuwa ka yi naji kana cewa Abu, dan dai na san Karimatu ce amarya ba Abu ba, yaushe Abu zata yi aure ita da ta daurewa bariki gindi?" Ta karasa maganar tata tana yatsina fuska da alamun kishi a muryarta jin ya ambaci Zainabu don ta zaci cewa zai yi yana son ta. Ransa yayi wani wasai cike da farin ciki da yaji ba Zainabunsa ce aka yiwa aure ba, duk da bai ji dadin abinda ta ce din ba amman sai ya dake ya ce, "Kai na shafa'a ne, yi hakuri Karimatu nake so na ce miki na manta." Ta dan saki ranta tace, "Babu damuwa idan gurin fatin za ka mu zo ka rage mana hanya mana ni da kawayena?" "Me zai hana, ki shigo na kai ki mana." Ya yi haka ne dan yayi amfani da wannan damar ya ga Abun a can. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Idan zuciya tagyaru 1-04 Posted by ANaM Dorayi on 01:13 PM, 30-Jan-16 Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU _______IDAN ZUCIYA TA GYARU_____ _____________ Na _______Fauziyya D Sulaiman______ Dadi ya cika ta ta yafito kawayenta da ke can tsaye suna kallon su da mamaki da sha'awar ina ma ace su yace yana so. Ta shiga motar tana fadin, "Ga kawaye na nan zaka rage musu hanya." Yace, "Su shigo mana." Dadi ya kuma cika ta tace musu, "Ku shiga baya mana." Ta umurce su sanda suka iso jikin motar. Ta so ya dan ja ta da hira sanda suka hau kan kwalta don ta kara budawa a gurin kawayen nata, sai dai shi kaset kawai ya kunnan na mutumin na sa, yana gyada kai zuciyarsa na can ga Zainabu Abu yana kwadayin yanda zai ganta ko da sau daya ne. A haka suka isa har inda za'a gabatar da fatin, hotel ne hadadde, tun daga waje za ka san fatin na manya ne dan manyan motoci ne a gurin. Sisters night aka rubuta da kyalli baro-baro wanda ke haske a gurin. Fatin Abu ce ta shirya shin don taya kanwarta murnar biki, Malam ne ya daura auren sannan 'ya'yansa suka shige gaba gurin bikin dan duk yawancinsu suna auran masu hali ne suna tukinsu, don haka a motocinsu aka dinga dauko mata ma. Bayan yayi fakin sauran 'yan matan suka fice da saurin su, ita kuwa 'yar gwallin ta tsaya tana wani yauki da fari, har zai ce ta fita mana sai ya tuna yanda take masa wani yauki da yanga. Dan haka yayi murmushi ya ce, "Ga shi har zamu rabu ban san sunan Hajiyar ba." Tayi dariya mai cike da nishadi ta ce, "Sunan ai ba wani na ku zo mu gani ba ne, sunana Salimat." Yace, "Lallai nice name, suna mai dadi." Ya zaro kudi a aljihunsa ya mika mata ya ce, "Ga wannan kya yi liki kafin na shigo zan ga wani abokin da bai karaso ba, idan na shigo zan gan ki." Yayi mata haka ne dan ta rabu da shi. Ta yi wani fari da idonta don ta yi zaton da gaske yake musamman da taga ya bata kudi masu yawa, dan haka ta ce, "Babu damuwa, amman fa ban ji sunanka ba." Da sauri yace, "Sunana Mustafa." Don ya gaji da ganin ta ya matsu ta bashi guri ya shiga ya ga rabin ransa. Ta ce, "Shi kenan na gode Mustafa sai ka shigo." Ta fita tana wata yanga. Ya bita da kallo har ta kule sannan ya yi tsaki yana fadin, "Ki ga mace kamar an zana one amman sai wani firirita da iyayi take, ita wannan ko a kafa aka daura mini ita ai zan yage ta na zura da gudu ne." Ya kuma gyara fakin ya kwantar da kujera gami da kara sautin wakar da yake ji, ya kunna taba yana sha yana kada kai kamar kadangare, ta cikin hasken gurin yake karewa matan da ke shige da fice kallo. Ya dan jima a haka sannan ya bude motar ya fice ya kukkullo ko ina, sannan ya nufi inda ya ji kida yana tashi na Mahmud Nagudu don shine yake taya su shakatawa. Gurin ya tsaru matuka, mawakin ya dage yana ta rera wakarsa cikin tattausan lafazi, amarya da ango suna tsakiyar makeken filin suna takawa a hankali, yana daga inda yake tsaye ya gane Karimatu dan ya santa tun tana karama, sai dai daman can ita tafi Zainabu hankali da nutsuwa. Ya sakale hannuwa a kirji yana ta waige-waige, bai kula da matan dake ta kallon sa wasu ma har sukan yi masa sigina. Can ya hangota ta shiga filin rawar tana sanye da wani irin material golden anyi masa wani matsiyacin dinki da ya kama jikin ta tsaf kamar a jikin ta aka kera shi, ta daura wani nadi mai kyalli shima, wani dan ziririn gyale a kafadar ta, sai wani katon takalmi da ta sanya mai kama da tsani dan tsaho, ta yi kyau matuka, ta zaro kudi daga jakar dake hannunta ta fara watsa musu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tana yi itama tana taka rawa a hankali, da yake gwana ce gurin rawa sai abun ya kayatar da jama'a da dama. Sai mawakin ya koma kanta da waka, "An gaishe ki yayar amarya karkada tsiwar ango, magajiyar uwa, manyan matan da duniya ke yayinsu, Zainabu tauraruwar zamani mai haske duniya, kin dade kina tashe har gobe ke ce tauraruwa farin wata sha kallo." Kanta ya kuma fasuwa ta dinga zaro kudi tana zuba masa, Asma ta shigo filin da irin kayan Zainabun komai da komai, ita ma tana shiga ta hau yiwa Zainabu likin kudin. Ango ya kama hannun amaryar suka fice yana dariya yana fadin, "Kada ta gaji ta isa haka rawar." Suna fita ya kuma mai da kidan kansu yana wakesu su kuwa sai rawa suke yi ta burgewa. Mustafa dake gefe a tsaye bai san sanda ya kutsa filin rawar ba don Zainabu ta tsumo shi da yawa, yana shiga ya zura hannu a aljihu ya dinga debo daloli yana manna mata, ta dinga dubansa da mamaki sai dai tana ganin kamar gizo idonta ke mata ko kuma mai kama da shi ne, amman da yake miskilar kanta ce sai ta dake kawai ta yi kamar bata gane shi ba, sai da ta gaji don kanta da rawar sannan ta fice daga filin, yana ganin ta fita shima ya bi bayanta, duk wanda ke shirin yiwa Zainabu liki sai jikinsu ya yi sanyi dan sun ga mai liki da daloli, gurin ya kacame da ihi da tafi na burgewa. Ita kam can wani tebur ta nufa dake can baya da jama'a, Asma ta bita da gudu har suka zauna. Asma ta dube ta tana fadin, "Shegiyar ina kika sami wannan hadadden gayen ga kyau kuma ga 'ya'yan banki? Ya yarfawa 'yan mazan gurin nan wallahi." Zainabu tayi mata wani kallon banza sannan ta sanya hannu cikin jakarta ta dauko tabar shaidan ta kunna ta, ta jingina da kujera tana fesar da hayakin ranta ya dauki zafi. Lallai ko a duhu taga Mustafa ba zata manta shi ba, shine mutumin da ya fara lalata mata rayuwarta kuma ya gudu ya barta a lokacin da take matukar bukatarsa, ba ta taba son wani mutum kamar Mustafa ba sanda ya nuna mata kulawa da soyayyar da sai daga baya ta gane tsananin yaudara ce, sannan a yanzu bata da wanda ta tsana a mutane sama da shi din. Asma kam sai maganar Mustafa take mata ita kuma zafi take ji a ranta dan haka ta kulle idonta kam har Asma din ta gaji ta yi shiru, a tunaninta ko ta bar gurin ne don haka ta bude idon ta. Tsaye ta gan shi a kansu ya nannade hannuwansa a kirji yana kallonsu, babu wani abu da ya sauya na daga kamanninsa sai kiba da haske da ya kara, yana nan har yanzu a dan gayunsa, yanda ya kura mata ido itama haka ta kura masa har lokacin tana cigaba da shan tabarta ta shaidan, Asma ta dinga kallonta tana kallon sa ta gaza gane abun da suke nufi, ta dai tabbatar da lallai yau kawarta ta hadu da daidai ita. Ya jawo kujera dake kusa da su ya zauna sannan ya jawo jakarta dake ajiya, ba ta ko motsa ba balle ta yi masa wani abu, ya dauko tabar shaidan shima ya kunnata, a hankali ya dinga fesar da hayakin sannan ya kai dubansa ga Zainabu wacce ke wurga masa wata uwar harara kamar idon ta zai fadi kasa. Yayi wani murmushi wanda ya kuma futo da haibarsa ya ce, "Zainabu Abun Musty!" Ta ja tsaki kana ta mike a fusace ta rike kugu bayan ta kashe tabar ta ce, "Malam lafiya dai ko? Don ni ban sanka ba ko don ka ga na kyale ka kayi mini liki kake neman zakewa da yawa?" Ya yi murmushi ya ce, "Zainabu kenan, kina tsammani ko a buge kike zan yadda baki gane ni ba? Na san na yi laifi amman na san zaki yafe mini dan Mustafa naki ne." "Ka ga Malam ni fa ban sanka ba, ban san daga inda ka futo ba, ka je can ka nemi wacce kaka nema, idan kuma buguwa ka yi kwakwalwarka ke gaya maka karyane to ka bari ka nutsu ka dawo hayyacin ka sai ka nemi wacce kake nema." Yayi dariya sosai wacce ta kara kular da Zainabu sannan ya dora da cewar, "Haba Zainabu, ai kinfi kowa sanin giya ko taba basa bugar dani, sai dai ke farin shiga balle yanzu ma na daina shan giya dan haka ya dace kema ki daina." Ta doki tebur gami da fadin, "Karya kake yi wallahi karamin kwaro, ka dube ni da kyau ban yi maka kama da wacce ka sani ba a da, dan kuma baka bar gurin nan ba zan sanya yanzu a yi maka rashin mutunci wallahi." Asma dake kallon su ta zunguri Zainabu wai tayi shiru, amman kamar ta kuma zigata sai cewa ta yi, "Dalla Malama ki kyale ni, ba irin wadannan ake saurarawa ba, wannan da kike gani cikakken dan iska ne da bai dace a dagawa kafa ba." Maganar tayi masa zafi a ransa amman da ya tabbatar dai ta gane shi din tsiya ce kawai sai yayi murmushi ya ce, "Ni dai na sani Zainabu ko giyar wake kika sha ba zaki manta dani ba, dan haka na dawo rayuwar ki bada wasa ba, ina fatan zaki manta da duk abinda ya faru a baya." "Wallahi karyarka ta sha karya, ka dube ni da kyau, sama da kasa zaka ga ba Abun da ka sani da can bace, wannan Zainabu ce, dan haka ka ja tsummar rayuwarka ka bar nan gurin idan ba haka ba zan rotsa maka kanka da kwabar nan." Ta nuna masa wata kwalba da ke kan tebur din da suke zaune ta lemo. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ya yi murmushi gami da gyara zama har lokacin yana zukar tabar sa yana kallonta babu ko kyaftawa. Ta san halinsa mutum ne mara tsoro sannan duk abin da ya sanya kansa babu mai hana shi, dan haka tasan babu wata barazanar ta da zata bashi tsoro, idan har ta yadda suka cigaba da zama guri daya komai zai iya faruwa, dan haka ta ga barin gurin kawai shine mafita a gare ta, dan haka ta dauki Jakarta ta bar gurin tana huci. Ya bita da kallo har ta bace wa ganinsa, yayi murmushi sannan ya dawo da dubansa ga Asma wacce ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, ta san lallai kawarta ta debo mai zafi dan barazanar da takewa maza suna tsorata shi tayi masa amman ko gezau bai yi ba. Ya yi dariya ya ce, "Kawarmu yaya gida?" Ta yi wata wawiyar ajiyar zuciya dan maganar ta zo mata a bazata, sannan ta ce, "Lafiya kalau." "Kinga yanda muka yi da kawarki ko? Na san halin Zainabu muguwar 'yar buyagi ce zata iya yin abinda ya fi haka ma, sai dai ban damu ba ko dar ma banji ba, don na gano tsagwaron sona a cikin idon Abu" Ya nuna kirjinsa da yatsansa yana cigaba da fadin, "Ni ne mutum na farko da ya san wacece Zainabu, duk wani iskanci da Zainabu ke takama da shi nine na koyar da ita, ba wai ina alfahari da haka bane, a'a zuwa yanzu ma duk sanda na tina ni ne silar lalacewarta na kan ji takaici kuma na ji haushin kaina, don haka nayi alkawari yanda na zama sanadiyyar lalacewar rayuwar Zainabu zan kuma zama jagora gurin ganin na shiryar da ita." Ya manta Allah shi ne ke shiryar da wanda ya so, ga shi ya yi hasashe ba tare da ya nemi yardar Allah ba. "Amman ki bar ni da Zainabu ni da ita kar ta san kar ne, na san na yi mata laifi amman zata yafe mini komai dadewa tunda nine mutum na farko da ta fara so a rayuwarta." Gaba daya ya gama burge Asma har ma take ganin inama ace itace ke da wannan hadaddan gayen, amman ta san tunda Zainabu ce a gabansa ba zai kalli kowa da daraja ba musamman da yace shine masoyin ta na farko, dan haka da wuya ya kalli wata mace da daraja. Don haka ta share wannan tunanin ma a ranta dan ta san ba mai yuwuwa bane, yanda kuma suke da Zainabu ma ba zata iya yi mata zagon kasa ba, dan haka ta fara jan sa da hira ta Zainabu kawai, ya ma manta da Zainabu 'yar buyagi ya zauna suna ta hirarsu har aka tashi daga fatin, sannan ya nufi gurin Zainabu wacce ke ta hada kayan su na fatin da ta san nasu ne, ya isa gabanta yana dariya ya ce, "Yaya dai uwar dakina ko za'a taya ni kwana ne yau dan ina tare da gajiya wallahi na yo doguwar tafiya mai nisa." Ba ta kalli inda yake bama balle ya sanya ran zata kula shi, ya cigaba da surutunsa don a ganinsa dole zata bi shi don yanda dare yayi kuma kowa ya watse a gurin har amarya da ango dole ta bishi dan babu wanda zai dauke ta, don haka nema ya share guri ya zauna yana ta cigaba da surutunsa. Can wata dankareriyar mota ta kutso kai harabar da suke zaune, Zainabu ta mike tsaye gami da kallonsa sama da kasa ta ja tsaki sannan ta ce, "Malam ina gargadinka karo na biyu da ka fita daga rayuwar Zainabu, ka kuma gane yanzu Zainabu nake ba Abu ba." Tana gama fadin haka ta nufi motar da salon tafiyarta na yanga da jan hankalin maza. Ransa ya yi masifar baci har yana ganin ba zai dauki wannan raini wayon ba, don yana da masifar kishin tsiya. Don haka ya nufi motar da sauri cike da bacin rai, amman ina tuni ta riga ta shiga, bayan ta zauna ta kalle shi yana wani huci kamar tsohon zaki, ta yi wata mayaudariyar dariya mai kularwa sannan ta rufe murfin motar, yana kallo suka fice a guje, ya ji kamar ya rufa musu baya a guje amman ina sun yi masa nisa. Ya doki iska yana huci gami da fadin, "Ba zan taba daukar wannan rainin hankalin ba wallahi, zamu gauraya ne." Ku ji fa karfin hali namiji da suna Hajara Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 . Suna daukar hanya DPM ya kalle ta yana wani lasar lebe yace, "Yaya dai gimbiya za'a taya ni kwanan ne mu wuce gidan shakatawa ta?" Ta galla masa harara ta ce, "Au abinda kake yiwa kenan shiya sanya ka nace daman zaka dawo ka dauke ni? Tsaya ka saukeni dan ka san kuna da yawa 'yan iskan garin zan sami mai kai ni gida, dan ni na gaji babu wani abinda zan iya yi." Ya ce, "Kai Zainabu ke fa 'yar buyagi ce wallahi, daga dan tayi sai jidali, shi kenan na hakura muje kawai." Bata kuma cewa komai ba ta jingina da kujera ta lumshe idonta tana tuno abinda ya faru, wani ciwo mai zafi da ya dade yana damun zuciyarta ya fara taso mata, tsigar jikinta ta fara tashi yar-yar kamar mai jin sanyi "Mustafa! Mustafa!" Ta fadi a cikin ranta gami da girgiza kai. Lallai ta sani abu ne gingimeme a gabanta, dan Mustafa da ban ne a cikin maza a gurinta, kuma tayi wa kanta alkawarin a can baya duk sanda Allah ya hada su ko a hanya ne sai tayi masa rashin mutunci, amman sai ga shi a gabanta amman ta kasa aiwatar da komai a kansa, sai ma wani abu da yake neman ya dawo mata da shi. Har suka isa kofar gidan su bata san sun iso ba don tayi nisa a tunani, sai da ya kai hannunsa yana shafarta tamkar wani maye sannan ta farga, ta yunkura da masifa ta hambare hannunsa gami da dalla masa harara. Ya kama sosa keya yana dariya ya ce, "Tuba nake yi, ai na zaci ko kinyi bacci ne, Allah Zainabu sam ba na gajiya da ke, ke din ta daban ce, kamshin ki kawai kan tayar mini da hanlaki, yanzu ji yanda kamshin ki ya cika motar nan tamkar ni ban sanya turare ba, wai ni da wane turare ki ke amfani ne ma?" Ta yamutsa fuska ta ce, "Su kuma wadanda ka ajiye a gidan fa meye amfanin su? Dan haka wallahi nake tsoron aure, sai ku baro matan ku a gida kuzo kuna hurewa kadangarun bariki kunne da naira, yanzu haka matan ka suna can suna jiranka kana nan kana gantali da wannan daran." "Ke rabu da wadannan matan, babu wani abu da suka iya sai jarababban kishi da shegen bin Malaman Banza, burin su kawai su tara kudi, da kun hau gado su yi maka wani sumbukaka kamar jakai, babu wani salo da suka iya wai su kunya, sau da dama idan nayi niyyar daina bin matan titi na zauna da su idan suka gaza gamsar da ni sai kiga na dawo ruwa, balle ke Zainbau daban ce wallahi kin san kan da namiji matuka, ko makarantar kika yi ne na kawo matan nawa ki koyar da su?" Ta yi dariya sannan ta ce, "Matsalarka ce wannan, wata kila kai ma da laifinka, kana shigar musu gida ne tamkar mala'ikan tsaron wuta babu fara'a shi ya sanya suke kasa sakin jikinsu, ni dai yau duk jarabar ka nan gani nan bari, ka ga fitata ma. Ta bude kofar ta fice tana fadin, "Asuba ta gari." Ya bita da kallo har ta shige cikin gidan na su, yayi tsaki da damuwa gamida kifa kansa bisa sitiyarin motar tasa, Zainabu ta zame masa masifa a rayuwarsa, muguwar hatsabibiya ce, muddin ka yarda ta lasa maka zumar ta a baki to lallai ka shiga uku, idan ba kana da kwararriyar mace mai iya salo-salo ba sai ka ji ka rainawa matan ka.Ya figi motar tasa ya bar kofar gidan tamkar mai tsere da iska, ita kuwa tana isa gida ta tadda gidan shiru kowa ya gaji da kacaniya ya yi bacci, ta shiga ban daki ta dauro alwala ta sanya kayan ta na sallah, ta shimfida sallayar ta wacce ke ta kamshin turare ta haye ta fara gabatar da Sallah. Idan ka ga yanda take nutsuwa idan tana Sallah zaka rantse idan aka sanya mata hannu a baki ba zata iya cizawa ba, dan duk iskancin ta bata wasa da Sallah, tunda ta taba jin wa'azi akan Sallah da irin azabar da mara yinta ke sha ta nutsu da yin sallah, wannan shine kadai abinda zaka daga a rayuwar Zainabu ta yi tutiya da shi. Mu dai bi ta a sannu don duniya ai takaitacciya ce. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Mustafa kam da kyar ya iya komawa gida, ya dade a dakin sa yana sintiri hannuwansa sakale a bayansa, wani masifaffan kishi da zafin Zainabu ke addabarsa, lallai yau da yana da hali da sai yayi wa Zainabu da wanda ya dauketa dan banzan duka, gaskiya ba zai iya lamuntar wannan halin nata ba na kula kowa, lallai dole ta daina harka da kowa indai tana son kanta da zaman lafiya, ya dade yana sintiri da kyar ya iya daurewa ya dan kishingida har bacci ya dauke shi. Da safe ya so yaje amman ya san da kyar zai sami ganin ta don hidimar bikin da sukeyi dan ya ji suna cewa yau din ne yinin biki, dan haka ya yanke shawarar sai dare sannan zai shiga. Karfe tara na dare ya isa gidan nasu ya rasa ta yanda zai yi ya ganta, sai can ya sami wata budurwa yace ta kira masa ita. Ta dube shi ta ce, "Ai Anti Abu tun da aka yi Sallar Magariba suka fice da kawarta Asma." Ya yi mata godiya ya koma motar sa ya zauna, Allah ya sanya jiya ya amshi lambar wayar Asma din, dan haka bayan ya shiga motar ya zauna ya fara neman layin Asma din. Da yanga ta dauka a yauki take maganar sanda taji kira, "Hello wa ke magana?" Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Mustafa ne, don Allah ina son ki bani kwatancen inda kuke, amman kada ki sanar da kawarki yanzu zan zo." Ta dubi Zainabu da ke zaune tana zukar tabar shaidan ta dora kafa daya kan daya, tunda suka iso gidan abun da take yi kenan dan cewa ta yi ba zata je kai amarya ba don ranta a bace yake su wuce gidan ta ta sami hutu, amman tun da suka karaso din ta gaza tabuka komai baya ga busa taba, dan haka ta riga ta gano kawar tata tunanin Mustafa ne kawai don bata taba dora hankalin ta ga namiji kamar haka ba. Sai ta ce, "Shike nan zan yo maka text." Daga haka suka yi sallama. Minti talatin da biyar kacal ya kwashe ya iso gidan ya danna kararrawar kofa, Asma ta mike da sauri don ta san Mustafa ne. Zainabu ta bita da kallo ta ja tsaki tana fadin, "Banza, kin gayyato mana wani kwarton ko? Ni da nazo dan na huta zaku dame ni, daman tunda naji kina magana kasa- kasa a waya na san jarabarki ta motsa." Bata ce mata komai ba sai dariya kawai da tayi ta nufi kofar, yana tsaye sanye da kananan kaya, wando ne na jeans bulu da shet fara tas mai taswirar birnin London, da silifas na fata a kafarsa dan gasken, sai agogo na azurfa da wani kwalelen zobe shima na azurfar, ya yi kyau matuka. Suna hada ido da Asma ta yi ajiyar zuciya sai taga yau yafi kyau ma fiye da jiya, dan ta kuma yadda irin gogaggun mazan nan ne ma, ta kwantar da murya tana fadin, "Yallabai barka da isowa." Ya yi murmushi gami da fadin, "Yauwa kawarmu ya gida?" Tana amsawa ta bashi hanya ya wuce ciki, sannan ta kulle. 'Yar buyagin tashi tana zaune tana ta busa hayakinta bata ko kalli inda suke ba balle ma ta gane waye ba. Ita ma Asma tana shigowa kiran wayar Alhaji Buba ya shigo wayar ta, yace ga direba nan ya turo su taho, dan shi baya zuwa da kansa dan kada masu ganin sa da daraja su ganshi girma ya fadi, dan haka sai dai duk sanda ya bukace ta ya turo direbansa a kaita can gidan sa ta kwana, dan haka dakin ta ta wuce ta hado 'yan kayanta. Har ya isa kusa da ita ya zauna bata san ya zo ba, dan tabar shaidan din ta fara gaya mata karya, ta jingina da kujera ta lumshe idanuwanta tabar tana tsakanin hannunta.A hankali ya zare tabar dake tsakanin hannunta, kamar wacce ya tsikarawa allura ta bude idonta firgigit ta ware manyan idanuwanta a kansa suka yi ido hudu, sai ta yi zaton ko gizo yake mata kamar yanda yake mata tun dazu. dan haka ta mai da idanuwanta ta lumshe wai ta daina ganin gizon sa, sannan ta kai tabar ta bakin ta da zummar ta kuma zuka, amman sai taji wayam babu komai, ta bude idonta da sauri a kansa, shine din dai da gaske yana taya ta shan tabar tata. Haushi da takaici ya cika ta tama rasa yaya za tayi masa, amman ta san ba kowa ne yayi mata wannan iskancin ba illah Asma, dan haka ta mike da bala'inta ta nufi dakin kwanan Asma din, sai gata sun ci karo a hanya, ta ci uwar kwalliya sai kamshi take zubawa rataye da jaka a jikin ta. Ta rike kugu tana harararta, ita dai Asma dariya ta sanya sannan ta nufi Mustafa ta cilla masa makullin tana fadi cikin harshen turanci "Take care, good night." "Wai Asma wannan wane irin iskanci ne?" Zainabu ta tambaya a kule. Asma ta daga kafada alamar Oho sannan ta fice da saurinta tana dariya. Ta kulu matuka, ta mai da kallonta ga Mustafa dake kallonta yana murmushi ta ce, "Wai kai kana gani kayi mini dabara ne, to ka sani a yanzu na girmi wayo da dabararka, sanda ka yi kaci nasara dai ka yi amman ban da yanzu, don haka sai ka zauna ka jire mata gida." Ta dauki dan yalolon gyalenta da jakarta ta nufi kofa. Sai dai ina ya rigata dan mikewa yayi da azamarsa ya sanyawa kofar makulli ya cilla makullin cikin aljihun wandonsa. Ta yi tsaye tana kallonsa cike da takaici da masifa, ya isa gaban ta ya tsaya cak ya zira hannuwa cikin aljuhunsa ya ce, "Ga ni gabanki kiyi mini hukunci daidai da laifina zan iya dauka, amman ki yi mini alfarma ki daina gudu na sannan ki dai na mini kallon kiyayyar nan dan yana bakanta mini raina, domin Allah ya jarabceni da son ki Zainabu, na gaza kallon kowace mace da daraja a rayuwata, ki taimaka ki yafe mini laifin da nayi miki nasan mai girma ne, amman na yi ne ba da son raina ba." Ta rike kugu tana kallonsa idanuwanta sun sauya launi zuwa jawur, duk wannan farin da kyallin babu saboda tsabar dacin ran da take ciki, tayi wani yake wanda yafi kuka ciwo sannan tace, "Mustafa na sanka tuntuni gwani ne kai gurin iya yaudara, da irin wadannan kalaman ka sami nasara a kaina a wancan lokacin hadi da kuruciya da talauci da son kudi irin na Mahaifiya ta, sai dai ka sani a yanzu Zainabu Abu ta wuce duk iyakacin tunanun ka, baka da sauran kalmar da zaka iya yaudararta da ita, baka da kudin da zaka iya yaudararta dasu, domin ina mu'amala da wadanda suka fika kama daga Gwabnoni sai Sanatoci da Ministoci zuwa manyan 'yan kasuwa dake rike da akalar Nigeria, dan haka yanzu ina da kudi da farin jikin da nafi karfinka, a yanzu idan na buga waya kadai duk abinda nake nema zan samu, dan haka kaga baka da makamin da zaka yaudari zuciyata a yanzu, duk da kana takamar kaine silar fadawa ta a wannan muguwar harkar da kullum nake tsinewa mara albarka." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ya kuma kwantar da murya ya ce, "Zainabu tunda na diro garin nan na ganki nasan lallai ba Abun da na sani da can bace, kuma ban dawo rayuwarki dan na nuna miki kudi ko kyau ko mukami ba, na zo ne da sunana Mustafa masoyin ki nida zuciya ta kadai ina fata zaki yafe mini abinda nayi miki can baya, sannan na mai da matsayina da martaba ta a zuciyarki kamar da, koma yafi haka don a yanzu Mustafa bai zo da zummar fasikanci ba sai dai da zummar auran Zainabu, domin a yanzu Ubangiji ya jarabi zuciyar Mustafa da tsananin son Zainabu." Ta kalleshi a lalace tamkar ta ga mahaukaci sabon kamu tace, "So! So! Lallai ka hadu da mugun ciwo idan har da gaske kake, balle na san karya kake yi, domin kai mutum ne mai yaudara da karya, don haka ka bude mini kofa na fice kawai, dan bana son ko kallon fuskar ka domin kai ne mutumin da ya sanya rayuwata a cikin fargaba da tashin hankali, nasha azabar da har abada ba zan manta da ita ba dan haka bude mini kofa na fita ko na daina ganin azzalumar fuskarka!" Ta karasa maganar tana hargowa. Ya hadiyi wani miyau mai daci, maganganunta suna yi masa zafi da suya a cikin zuciyarsa, dan haka da kyar ya iya buda baki yace, "Zainabu ba zan bude miki kofar nan ba har sai kin amince dani kin yarda yanzu ni ba mayaudari ba ne..." "Ba zan taba yadda da kai ba, ka bude mini kofa kawai na fita tun ban maka rashin mutunci ba wallahi." Yana tsaye kyam babu alamun zai ko motsa, ranta ya kuma baci matuka, ta ga lallai da gaske yake dan haka ta nufe shi da azama ta kama kokarin kwatar makullin, nan fa suka fara kokawa amman ina namijin duniya ne maji karfi dan haka ta gaza kai hannunta balle ta iya dauka har karfinta ya kare, tayi kokarin janye jikinta amman ya hana ta hakan dan ta tuno masa da wani lokaci da wasu al'amura da ke masa dadi da sanya shi nishadi a duk sanda ya tuno. Tayi kokarin ta kwace amman ta gaza sai ma wani abu da yake shirin jawo mata dan shin din daban ne a zuciyarta ya san kanta da yanda yake samun ta a sama, daman haka yake so ta shiga jikinsa dole sai ta sakko don dai shine ya santa ya san wacece ita, tayi luf a faffadan kirjinsa mai kirar zaki ta gaza kasa aiwatar da komai. Ya sami yanda yake so dan haka yake da salon yaudarar da sace zuciya, yanzu kam ya soma nasara a kanta dan tana jin zafinsa a ranta amman tana matukar son sa, dan haka komai ya kwance mata, Mustafa ne namiji daya tal da idan tana tare da shi take manta kowa, amman duk sanda take tare da wani sai ta tuno shi da soyayyarsa, don haka bata da karfin halin da zata kwaci kanta duk da haushinsa da take ji, dan haka sai ta fashe da kuka kawai. Jikinsa ya dauki rawa don yasan ba karamin abu ke san ya Zainabu kuka ba, don tana da taurin zuciya, dan haka cikin tausasa murya da rada ya ce, "Zainabu don Allah ki yi hakuri ki yafe mini na tuba....."."Me ya sanya ka tafi ka bar ni sanda nake tsananin bukatar ka a rayuwa ta eye?" Ta tambaye shi tana kuka. "Ki yi hakuri na san nayi miki lafi, sai dai na yi miki alkawarin ba zan kuma barinki ba har abada, ni din naki ne ke kadai, ba zan iya kuma barinki ba Zainbau, ni kaina na sha wuya, na yi miki alkawari." Ta yi luf ta gaza cewa komai dan yayi mata yanda ba zata iya kuma musa masa ba, anan suka baje suna shashancin su. Sai karfe goma na safe suka sami sukunin tashi suka fada wanka sannan suka yi sallah, sannan Zainabu ta fada kicin da sauri don ta samar musu abin da zasu karya dan yunwa suke ji matuka. Ya bita kicin din tana sanye da wani dan guntun siket, tare suka yi aikin suna ta dariyarsu. San da suke karyawa yayi mata kuri da ido yana kallo don Zainabu ta bashi mamaki, ta wuce duk yanda ya santa, gaba daya ta gama haukata shi a daran jiya, yanzu abu daya ya rage masa ya auri Zainabunsa ya huta, kullum yana manne a jikin ta shi kadai, sai ya ji wani kishi ya kama shi mai tsanani dan bai san iyakacin adadin mazan da ta yi mu'amala ba, sai yake da na sanin tafiya da yayi ya bar ta, da shi kadai ya san abarsa. Ita ma wani irin farin ciki take ji a cikin zuciyarta, dan ta sha karo da maza kala-kala a yawon iskancinta, amma bata ji wanda ya taba yi mata dai-dai da Mustafa ba, don haka tana yin bariki ne bawai dan dadi ba sai don neman abun duniya(Allah ya kyauta), Zainabu hatsabibiya ce ta kin karawa, dan haka maza da dama ke shan wahala a kanta, yanzu ma mikewa tayi tsam ta isa inda yake ta zauna cinyarsa, ta sakala hannuwanta a wuyansa ta mika masa bakinta wai ya sammata abin da yake taunawa (wainar kwai), bai yi mata gardama ba dan shima gwani ne, dan haka ya hada bakinsa da nata yana ciyar da ita abinda ke bakinsa, da haka ta dinga kara susuta shi tamkar wani karamin yaro ta mai da shi. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Bayan sun kammala cin abincin suka yi masauki a doguwar kujera mai cin mutum uku. Ta kwanta lamo a kirjin sa tana shafar sa tamkar mage, cikin kunnensa ta ce, "Musty wai me ya sanya ka tafi ka bar ni sanda nake tsaka da bukatarka?" Yace, "Sai kin sanar da ni irin wahalar da kika ce kin sha sannan zan sanar dake nima." Ta yi kwafa tana fadin, "Labarina mai cike da abun tausayi ne da takaici, domin daga ranar da na nemeka na rasa na shiga tashin hankali, naje har gidanku aka ce mini daman hutu kazo wai a kasar waje kake karatu, na shiga tashin hankali da ciwo mara misali, abu fa kamar wasa sai ciwo ya dinga yin gaba, da farko na zaci ciwon soyayya ne, sai da abu yaci tura aka gano ashe ciki ne dani....." "Ciki da gaske Zainabu ko na wasa?" Ya tambaya da sauri. Ta yi dariya tana fadin, "Da gaske Musty wallahi ciki ne na gaske, kai ai munga tashin hankali ni da Sala a wannan lokacin." "To yanzu ina abun da kika haifa din?" Ya kuma tambaya. Ta tabe baki tana fadin, "Cabdijam, ai tuni muka zubar da shi." Ya dafe kai yana fadin, "Ya salam, ai sam ban san kina da ciki ba, har na ji ina son abuna wallahi Zainabu." Ta warware masa duk abin da ya faru sannan ta dora da cewar, "Bayan mun gama da wannan muna murna mun dawo gida da kwanaki kuma sai ciwon ciki ya balle mini ga zubar jini kamar jinina zai kare, amman da muka je gurin shegen likitan da ya zubar mini da cikin ya caje mu kudi masu yawa gashi a lokacin bamu da komai duk mun saida 'yan kadarorinmu, don haka yace ba zai taba ni ba, sai nurse din da tayi mana hanya ce tace muje asibitin kuroda tun da dai yanzu ba zubar da ciki bane zasu karbeni, gahi an kwana biyu da zubar da cikin sai nace ina da aure bari na yi, sai ta shige mana gaba da sunan ni 'yar uwarta ce daga kauye aka kawo ni. Amman duk da na Gwabnatin ne ma sai da aka rubuta mana magunguna masu tsada ga karin jini, sai yaya na ne ya bada jininsa aka diba, sannan Sala ta je ta ciwo bashi aka sayi magunguna, lokacin adadin kudin kusan dari shida ne. Bayan na warke muka fara tunanin inda zamu samu kudin da zamu biya dan daman irin kayan nan na bashin watan nan ta amsa ta karyar da su ta saida sannan aka sami kudin, don ma matar tana shakkar Sala ba tayi magana ba, da na samu sauki sosai Sister din nan ta bani shawarar na dinga fita good evening (karuwanci), cikin kankanin lokaci komai ya sauya domin dai kasan ni ta daban ce." Suka yi dariya gaba dayansu sannan ta cigaba da maganar, "Yaya Sadiku kamar zai shake ni ya kashe ni don tsabar tsana da yayi mini, don har cewa yayi da ya san ci gaba zanyi da iskanci da bai yadda an kara mini jininsa ba, gwara na mutu kowa ma ya huta, sai da Sala ta tsawatar masa harda barazanar zata tsine masa idan bai fita harka ta ba sannan ya saurara mini. Sister ce tace na koma karatu domin rayuwa babu ilmi tana tawaya don haka Sadiku na komawa ya maidani makaranta wacce na yi kusan wata shida banje ba, da farko yace ba zai maida ni ba sai da nayi masa alkawarin ba zan kuma yawo ba sannan ya yadda ya kwashi katina da zai tabbatar da bani da lafiya ne sannan muka wuce makarantar. Sanda muka isa Principal dinmu ta ce ba za ta amshe ni ba domin dai nayi wajen wata shida ban zo ba 'yan ajinmu har sun zana jarabawar sake aji . Sadiku ya marairaice yana bata hakuri, ji nake kamar na harbe shi don haushi, daga karshe ya dauko kati ya bata don ta tabbatar bani da lafiya ne. Ta ware idanuwa domin dai duk da bata fahimci abinda likitan ya rubuta ba ta fahimci kalmar (bleeding after abortion), wato zubar jini bayan bari, ta daga katin cike da tsana da takaici take kallona sannan ta fara magana. "Lallai yarinyar nan kin cika tantiriyar 'yar iska, bayan iskancin da rashin kunya har karuwanci kike tabawa, kamar ki ace an zubar miki da ciki? Kai tir da halinki, Allah ya wadaran halinki." Sai ta jefeni da katin akan fuska ta. Sadiku ya mike jikinsa yana rawa domin bai san likitocin da suka yi mini karin jini sun rubuta bari nayi ba don bai san karyar da muka shirya ba, sannan bai tsaya ya duba katin ba duk da ba komai zai gane ba ma, ya fara magana da rawar jiki, "Don Allah Hajiya kiyi hakuri kaddara ce da tsautsayi....." "Da kuma sakaci da rashin tarbiyya." Ta karbe daga bakinsa, sannan ta dora da cewa, "Wallahi ka ji na rantse yarinyar nan ta gama zama a makarantar nan, alfarma daya zan iya yi maka na rubuta maka takardar (transfer) canji zuwa wata makarantar, don ban ga amfanin zama da daliba irin ta ba, ita ba kokari ba sannan ga shegen iskanci ta addabi dalibai da malamai tun yanzu tana matsayin kwaila, ina ga ta zama babbar mace? (No i can't) ina ba zan iya ba." ta karasa maganar a hasale. Ni kuwa ina gefe na cika nayi fam, domin Sadiku ya gaza rama mini cin mutuncin da matar nan take mini, don haka na mike daga tsugun nan da nake yi na dole, domin tun a gida ya gargade ni na durkusa da munje kuma na gaida ta don ta san na yi hankali. Ke! Ma ya ishe ki haka, haka kawai zaki sanya ni a gaba kina zagina kamar wata uwata? Ko abun da yafi ciki nayi ina ruwanki, idan ba zaki karbe ni a makarantar ki ba kawai kice ba zaki karbeni ba amman kin saka ni a gaba kina zagina, ke wayasan iskancin da 'ya'yanki suke..... Marin da Sadiku ya dauke ni dashi ne ya sanya ni yin shirun dole, na dinga dubansa da jin haushi kamar nayi masa Allah ya isa, amman tunda lallabashi nake yi ya sanya na hakura ina ta kunkune dai. Kana ji a gabanka tana zagina ma ko? To maza ku bar mini Ofis dina tun ban hada ku da (security) ba, ta fadi a hasale. Ya dauki katin da yake a kasa yace, Malama nagode, kiyi hakuri hali ne kowa da irin nasa, sannan ya dubeni yace idan kin ga dama sai ki taho mu tafi. Bai jira abinda zan ce ba ya fice daga Ofis din. Na dalla mata harara ina fadin, "Allah ya sanya ba kece kika kawo ilimin boko duniya ba, sannan Mangwafak ba dan gidanku ba ne, don haka zanyi karatu a wata makarantar ko kina so ko baki so....." "Ki fitar mini daga Ofis dan ubanki ko na sanya a zane mini ke ko na hada ki da 'yan sanda su kulle mini ke wallahi shegiyar yarinya mara kunya kawai karuwa..... Na ce, "Kin ga karuwa dai a gidanki ba niba." Ina gama fadin haka na ficewata ina hangota sanda ta zauna a kujera cike da bacin rai da bakin ciki mara misaltuwa, na dai ji dadi don na rama wulakacin da tayi mini. Bayan mun dawo gida Sadiku ya yi kamar ya cinye ni don bala'i, yace kuma babu ruwansa da ni, don haka na rasa yanda zan yi na koma karatun, don na gane idan mutum yana zuwa makaranta yakan rage 'yan sa ido. Daga karshe dai Sister Asibi ce ta yi mini hanya na koma Sheka da karatuna, acan dai na kammala Secondary dina, bayan sakamako ya fito babu lafi na samu admission a FCE, domin a wancan lokacin ba'a tsaurarawa gurin makin jarabawa, don haka da 2 credits 2 passes na sami admission. A wannan lokacin ne na kuma wayewa na san lallai da kai na a duhu yake, duk da dai ba wani karatun ne a gabana ba, na hadu da malamai 'yan ban gishiri na baka manda da taimakonsu na kammala. Dai- dai lokacin da na kammala karatuna na hadu da wani dattijo ma'abocin son holewa DPM ne a wata karamar hukuma. don haka tunda ya kyalla idon sa a kaina ya makale mini, shine dai ya kawo min takardar fara aiki (upper) har gida tun sakamako na bai fito ba, don haka na fara aiki na, amman fa a kanyi wata banje Ofis ba domin dai ina da manya a sama, sun ajiye ni a cikin Sakateriya bangaren (Accountant), mai raba kudi, don haka Salary bana wasa nake samu ba, duk da ba abinda na karanta kenan ba kasan Nigeria jaga-jaga inji wani mawaki, don wallahi wadanda muka yi karatu dasu da dama basu sami aiki ba har yau, kuma yawancinsu sune masu kokarin sun fito da first class amman da yake basu da wani a sama suna zaune, kai Nigeria sai a slow wallahi." Ya yi dariya yana fadin, "Wallahi ke din nan 'yar buyagi ce, ni kaina wani lokacin tsoro kike bani, barin ma yanzu, don haka ne ma na dinga jin tsoron dawowa don kada kiyi mini buyagin naki." Ta yi dariya gami da kai masa bugu na wasa, suka kama dariya gaba dayan su, sannan ya gyara zama yana kuma shinshinarta kamar wata diyar mage sannan ya fara bata labari kamar haka.Kamar yanda kika sani daran da yayanki Sadiku ya yi mini wannan wulakancin na tafine raina a tsananin bace, domin tun da nake ba'a taba mini wulakanci kwatankwacin wannan ba, don haka na kudirta a raina na hakura dake tunda daman yace duk randa ya kuma ganina a kofar gidan ku sai ya sanya an jefe ni, ni kuwa bana son iyayena su san halin da nake ciki sam. Sai da na koma gida ne ma sannan na tuna da abinda ya kaini gurin ki, don muyi sallama ne ni zan koma makaranta duk da na san ban taba gaya miki hutu nazo ba. Sai da tafiyar ta kama gadan-gadan sannan na ji wani irin masifaffan son ki yana bijiro mini da kewar ki, amman na dake don ina ganin da zarar na bar garin duk zan daina ji, don haka na bar Kano da zummar na bar Zainabu Abu na nufi birnin Califonia. Sai dai tunda na isa garin na jini kamar wani mara lafiya, surarki da kamar ki ta dinga bijiro mini don haka na yi zaton ko kewar ki ce, don haka na fara mu'amala da mata kala-kala masu kyau masu ilimi har ma da masu dukiya, amman sun gaza gamsar dani kamar 'yar kwaila Zainabu, amman na dinga yaudarar kai na da lallai sai na manta Zainabu, duk macen da na kalla sai naji na raina ta burin yana ga Zainabu, na ki na dawo hutu don ina ganin idan na dage zan manta dake din, sai dai iyayena suzo mini hutun can, har na kammala karatuna kina nan a raina na kuma baiwa kai na wani lokacin na mantawa da ke, don haka na fara aiki a can duk da ba haka iyayena suka so ba, sai dai shi Mahaifina mutum ne mai saukin kai da baiwa mutum damar sa inda yaga babu cutarwa a kanta. Dare daya na ji duk iyakacin dauriyata ta kare, musamman da nake ta fama da yawan ciwon kai da aka auna ni akace na rage sanya damuwa a raina, na yadda muddin na cigaba da zama a can ciwon zuciya yana gan da kamani saboda yawan tunani, na yanke shawarar zan dawo Nigeria na neme ki amman a wannan karon auranki zan yi, don na gane kece kadai nake so a rayuwa ta, na kuma yi kokarin jifan tsuntsu biyu da dutse daya don daman iyaye na sun damu da lallai na dawo nayi aure.Sai dai idan na tuno ki sai naga kamar na rasa ki ko kin yi aure, da zarar na tuno hakan sai naji duk hankalina ya tashi, na yawaita sallah da rokon Allah ya sanya baki yi aure ba, da wannan shawarar na dawo gidan Nigeria, da zummar ko a yaya na sameki zan aure ki, don ban yi zaton Abun da na sani zata koma mace mai girma da daraja da aji kamar haka ba, don dai a yanzu so ne tsagwaransa a raina ba wata sha'awa ba. Sai dai na sha mamaki a yanda na ganki a yanzu, nasan tun a can baya kina da kyau don yana daya daga cikin abunda ya sanya nayi mu'amala dake, ga tsabta koda yaushe zaki wuce ta gaba na sai na ganki tsaf dake, takalminki kamar ba kya sakawa.Don haka Zainabu ba da wasa na dawo ba da zummar na aure ki na dawo, don haka bana son a dauki wani lokaci mai tsaho, sannan dole ki daina kula 'yan iskan samarin nan naki don ina da kishi mai tsanani, shi ya sanya a wancan lokacin ma nayi kokarin ganin baki kula kowa ba, don haka Zainabu gani gabanki da kokon barata ina fata zaki amince da bukata ta." Tayi dariya cike da jin dadi ta ce, "Lallai Mustafa ka debo ruwan dafa kanka, ta yaya zaka ce kai kadai zan dinga kulawa bayan ba mijina kake ba? Ai hakan ba mai yiwuwa bane ba." Ya mike zaune yana mata wani duba idonsa fal da masifa ya ce, "Wallahi kina so ne na fara rotse a kofar gidanku, don duk dan iskan da yayi mini rainin wayo a kanki zan yi maganinsa, da can sun yi yanda suke so, yanzu kuwa mai guri ya zo kowa sai ya matsa ya bashi gurin sa, duk mai neman kansa da arziki. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta makalkale shi tana dariya ganin yanda yake masifa kamar zai rufe ta da duka, suka kama dariya don tana masa irin salon ta da take siye masa zuciyarsa. Bugun kofar da akeyi ne ya fargar da su, Zainabu ta mike da sauri tana fadin, "Ina zaton shegiyar nan ce ta dawo." Ta dubi agogo sha daya da minti uku, sannan ta nufi kofar da sauri tana kokarin budewa. Asma ta shigo da gudu tana ihu da dariya tana fadin, "Shegiyar ashe akwai mai maganin iskancinki, gaskiya Mustafa ka ci a baka na daya, ya ci a sara maka wallahi, don kayi mana maganin mai shegen taurin kan nan." Mustafa ya mike tsaye yana dariya sannan ya ce, "Daman ke muke jira mu wuce." Ya mika mata makullin sannan ya dubi Zainabu ya ce, "Ke madam sai ki shirya na sauke ki a gida ko, don na san idan na tafi wannan dan iskan ne zai zo ya dauke ki." Suka fashe da dariya ita da Asma har da tafawa, yayi murmushi yana fadin, "Lallai kwa yi mini dariya don kun san kun kama wuya na, ni kam na wuce mota kya tadda ni a can." Har ya kusa kaiwa kofa sannan ya tsaya yana fadin, "Ahaf! Hajiya Asma na gode kuwa zan gan ki." Tayi dariya tana fadin, "A'a don ni kada ka damu babu damuwa ai duk yiwa kai ne, don bani da kamar Zainabu duk Kano." Yayi murmushi ya ce, "Na dai gode din sai mun sake haduwa." Sannan ya fice. Asma ta kalle ta gami da fashewa da dariya su dukan sannan suka tafa Asma ta ce, "Wallahi kawata kin iya iskanci, ki dubi yanda kika juyar da zuciyar dan talikin nan a lokaci kankani don Allah, don Allah yaushe ne zaki sanar da ni sirrin nan ne?" Zainabu ta tafi tana fadin, "Sirri ne abin." Asma ta bita da gudu tana fadin, "Haba kawar, ki taimaka mini don Allah." Zainabun tayi dariya sannan ta ce, "Ki bari sai mun hadu kinga yanzu lokaci ya kure, don zumana yana jirana a mota." Suka kuma fashewa da dariya, sannan Asma tace, "Lallai Mustafa ya ciri tuta don ban taba jin kin ambaci wani namiji da ko sunan da iyayansa suke gaya masa ba, daga shashasha sai dan wahala ko dan akuyan can, amman Mustafa yaci Zuma gaba daya ma." Zainabu ta zame da sauri ta falla da gudu tana fadin, "Malama ki kyale ni haka nan, kina bata mini lokaci." Sanda suka isa gida duk 'yan biki sun gama watsewa sai dai sauran kwadayayyu, sun jima a mota suna sallama sannan ta fita tana takawa da tafiyarta ta daukar hankalin 'yan maza, sai da yaga shigarta gida sannan ya ja motar tasa cike da tsananin sonta, da wani nishadi da farin ciki. Tana shiga Sala ta kama yi mata sannu da zuwa, ta sami kujera 'yar tsugunne ta zauna don cike take da nishadi. Sala din ta kama murmushu don ganin diyar tata a cikin farin ciki sannan ta ce, "Hala yau diyar tawa ta hadu da mai barin dala ne naga bakin naki ya ki rufuwa." Ta yi 'yar dariya sannan ta ce, "Sala kin san abun mamakin da ya faru kuwa tun daran jiya?" Bata bari ta bata amsa ba ta dora da cewar "Mustafa ya dawo." Da mamaki Sala din tace, "Mustafa kuma? Waye me wannan sunan, ba dan dan banzan yaron nan da ya cuce mu shekarun baya ba can?." Zainabu ta bata rai matuka kamar zata yi kuka, ganin haka ya sanya Sala din ta tsuke bakin ta, don ta yi zaton zata yiwa Zainabun gwaninta ne, don ta san irin alwashin da taci akan Mustafa. Ita kam mikewa tayi tana fadin "Ashe daukar hakkinsa muka yi daman, don ba laifin sa ba ne." Ta sha ruwa a randa sannan ta dawo ta gaya mata duk yanda suka yi da Mustafan. Sala din tayi dan murmushi tana fadin, "A'a lallai bashi da laifi to mun yafe masa." Zainabu ta ji dadin abunda Sala din ta fadi, don haka ta mike tana dariya sannan ta ajiye mata damin 'yan dari dari na dubu ashirin tace, "Sala gashi nan kya kashe." Sala din ta dauka tana dariya sannan ta ce, "Ke Zainabu ba kya gajiya? Na ga fa kin sha kacaniyar biki kwanan nan." Zainabu tayi dariya tace, "Ai Mustafan ne ya bada ya ce a baki kya sha ruwa kafin yazo bada hakuri da kansa." Sala ta fashe da wata wawiyar dariya sannan ta ce, "Kayya ki gaya masa ya kwantar da hankalin sa komai ai ya wuce gashi kin ce daman ba laifinsa ba ne." Ita dai Zainabu daki ta shige domin tayi baccin gajiyar kwanakin da bata yi ba can baya, kafin yamma tayi su hadu da zuman nata ************ Cikin kwanaki kalilan soyayya da shakuwa ta kuma shiga tsakanin su, duk da suna rikici duk lokacin da Mustafa ya ga Zainabu da wasu Musamman Alhaji.... Dan haka duk inda tasan zata gamu da samarin ta kan guje masa don bata son ace kullum suna samun sabani da Mustafa dan yana da matukar kishi, su kuma sun gaza hakuri dan duk kusan namijin da ya fara mu'amala da Zainabu bai iya daina wa dan ta fiye fitina da yawa, sai dai idan Allah ne ya kwato shi daga hannunta. Shi kam Mustafa kullum hankalin sa a tashe yake dan bai kaunar ya ga Zainabu da wani, dan haka nema suka yanke shawarar yin aure a wannan lokacin. Shi kam yana shakkar tinkarar Momin sa da maganar auren nasa don ya san ta bata san wargi sam ita, ga shi daman kullum tana masa maganar ya zabo mace cikin 'yan matan gidan ko kuma ya duba cikin 'yan uwa masu tarbiyya dan bata son yayi zaben tumin dare, sai dai shi a iyakacin ganinsa daga 'yan matan dake cikin danginsu har na waje bai ga wacce tayi masa kamar Zainabunsa ba. Yau ya tadda Momin nasa a karamin falo, 'yan matan ta suna karamin falo suna kallo sai musu a keyi tsakanin 'yan matan, don gidan nasu bai rabo da 'yan mata na 'yan uwa dan su basu da yawa su biyu ne kacal, gashi Momin su tana da son jama'a dan haka koda yaushe gidan a cike yake banda masu zama dindindin, banda kuma wadanda aka aurar, dan haka tunda ya ga take-taken Momin na su na son ta hadashi da wata a cikinsu shi ya sanya ba ko da yaushe yake sakar musu fuska ba. Ya shiga falon da sallama, ita kadai ce don ya baro Alhajinsu a falo da baki, ya isa gaban ta ya gaishe ta, sannan ya koma babbar kujera ya zauna, ya dubi tibin inda yaga hankalinta ya karkata. Yakin Falastinawa ne dai da Isra'ilawa wadanda kanwa uwar gami America ke daurewa gindi, ana nunowa a tashar C.N.N. "Kai wadannan mutanen wallahi azzalumai ne, ka dubi yanda suke kashe farar hula da basu ji ba basu gani ba, sannan su yi farofagandar basa taba farar hula, Allah dai ya bi musu hakkinsu kuma ya nuna musu karshen su, Amin." Hajiya Kubra ke fada da bacin rai. Mustafa ya ce, "Haka ne Momi, sai dai idan kika duba daman can zaki ga abun nasu bawai suna yi bane don wani abu sai don su yaki addinin musulunci kawai, yanzu fa idan kika shiga kasashen turawa da gemu sai kaga an mai da kai wani abin tsoro saboda sunyi farofagandar batawa musulmi suna a idon duniya, dan ma yanzu Allah yana nuna musu ishara mutanan su turawa sai musulunta suke, musamman matansu kamar su Kristian Barkeu da 'yar uwar tsohon shugaban kasar Birtaniya Tony Blair, Laurent Bothh wacce ma'aikaciyar jarida ce, da sauransu, shine fa muke dan samun sassauci a gurinsu, abun nasu dai sai addu'a." Ta amsa da "Amin, ina wai ka shiga ne?, tun da safe nake saka rai da shigowarka amman shiru." Gabansa ya fadi, don yanzu sam bai zama a gida kullum suna makale da Zainabunsa, amman sai ya dake ya ce, "Momi kin san ina fafutukar fara aikin tun da sun bani (offer), takardar daukar aiki, shi ya sanya yanzu bana zama." Ta ce, "Lallai kam haka ne, Allah dai ya taimaka ya sanya a fara a sa'a." Ya ce, "Amin." Sannan ya kama inda-inda don ya rasa ta yanda zai gaya mata. Hajiya Kubra ta dube shi tana dariya tace, "Babana duk yanda aka yi da magana a bakin nan naka." Da yake sunan Baban ta ne da shi. Ya yi murmushi yana sosa keya ya ce, "Momi sirika na yi miki shine nake kunyar sanar da ke."tayi dan murmushi dan ba hakan taso ba taso ace anyi 'yar gida, amman sai ta danne dan tana son yayi auren, dan haka tace, "Lallai kam kace yau zanyi kwanan farin ciki, a ina ka samo matar taka ko a can American ne?" Yayi dariya ya ce, "A'a Momi a can dai unguwar da muka taso take, can kasan layinmu na da, sunan ta Zainabu." Ta ce, "Lallai kam, Allah ya tabbatar mana. Waye kuma Babanta, a wane gida take ne ma?" Da sauri ya ce, "Sunansa Malam Abubakar." Tace, ai shike nan bari Alhaji ya shigo sai a sanar da shi, amman dani na so ace cikin 'yan uwanka da suke gidan nan ka zaba, amman tunda Allah ya kaddara matar taka a waje take ba zamu ja da ikon Allah ba, sai dai muyi addu'a Allah ya tabbatar mana da alkhairi kawai. Ya ji dadin abunda ta ce, yayi mamakin kuma saurin shawo kanta da ya yi, duk da saurin daukar zafin ta. Daga nan suka cigaba da hirar su a cikin hirar nema take cewa tana fatan zainabun tasa mai hankali ce da nutsuwa. Ya ce, "Momi ko ke kika ga Zainabu sai kinyi sha'awarta, ta kammala diplomarta yanzu haka tana aiki ne." Tace, "To ai shike nan, na san dai sai Baban ku ya sanya anyi masa bincike don kada ayi zaban tumun dare." Kirjinsa ya bada ras-ras, amman dai ya dake yace, "Na san ma babu wani aibu da zai tadda ga Zainabu in dai ya sanya mutanan kirki a binciken ba munafukai ba." Tun daga sannan ya ji hirar ta fita daga ransa gaba daya, don bai san irin abinda za'a ce akan Zainabunsa ba, shi kam yaji ya gani dan haka koma me zai faru sai dai ya faru amman shi dai da ikon Allah sai ya aure ta. Da haka yabar dakin mahaifiyar tasa ya nufi na shi, amman yana cike da tunanin abunda zai biyo baya idan suka san wacece Zainabu. Kwanaki biyu shiru babu wanda yace masa ko kala akan maganar, shi kam ya damu kwarai ya ji anyi masa zancan, dan Baban sa ma da suka yi maganar da Hajiya Kubran abinda ta fadi ya maimaita, cewar zai sanya ayi masa bincike sosai. Ya sami wani tsohon abokinsa acan unguwar da suka taso ya ce don Allah ya bashi amana ya binciko masa labarin wata yarinya Zainabu diyar Malam Abubakar kamar yanda aka ce masa, sai dai abokin nasa ya dan sami matsala da farko dan duk wanda yace wa sun san Zainabu diyar Malam Abubakar sai suce gaskiya basu san taba, mutum hudu ya tambaya amman duk ba'a dace ba. Sai da ya isa majalisar da yake zama ya fara kawo maganar neman Zainabu da yake yi, sai wani cikin abokan hirar tashi yace, "Ko dai Zainabu diyar Baba Abbakar mutumin Sudan din nan ake nufi, in dai itace kuwa bai yi mata ba, domin dai kowa yasan karuwar gida ce, duk da babu kyau suka akan maganar aure amman tunda dai amana ya baka sai ka sanar da shi gaskiya in dai ita ce din, da dai kanwarta da aka yiwa aure kwanaki ce ma da sauki dan ba halinsu daya ba." Nan suka hau sanar dashi irin halinta dan gaskiya shi ma'aikacine bai fiye zama ba sai karshen sati kuma yawanci hirar siyasa suke yi da matsalar da kasar ke ciki. Ba shi da wani ja Zainabu diyar Baba Abbakar ce dai dan abokinsa yake nema, dan haka ya je ya sanar dashi yanda suka yi, daga karshe har kofar gidan su Zainabun suka zo tare ya nuna masa. Haka nan Alhaji Abdullahi ya koma gida jikin sa sanyi kalau, domin dai ya tabbatar da lallai itace wacce dansa ke so, shi kuwa duniya sam bai san ya takurawa dan sa, yaso ace Zainabu da dan sa yake so ta kasance kamila ce ba lalatacciya ba, kafin ya shiga sallar Magariba ya kirawo wayar Mustafa yace lallai idan an idar da sallah yana son ganinsa,babu bata lokaci Mustafa ya iso gidan dan kusan tare ma suka yi sallar Isha'i da Baban nasa, ya dade a raka'ar karshe yana addu'ar Allah ya sanya Zainabu ta zama rabonsa, don yaji muryar Mahaifinsa kamar da zafi shi ya sanya duk ya kidime. Ya riga Baban nasa shiga gida, Momin nasa ta zuba masa abinci amman ya gaza ci duk da uwar yunwar dake addabarsa, dan kada ma Momi ta zargi wani abu ya sanya ya dinga tsakurar kadan yana ci har ma taso ta gane. Ta dubeshi da kulawa ta ce, "Baba anya wani abu baya damun ka? Na ga kwana biyu duk ka wani shiririce, balle yanzu ka gaza cin abinci sai tunani." Ya kakalo murmushi yana fadin, "Laaa! Momi me kika gani? Babu komai gajiya ce dai kawai." Ganin tana son ta gano shine ya sanya ya saki jikinsa yaci abincin sosai, har Baban nasa ya shigo, ya shige sashinsa ya kira Hajiya Kubra ta wayar gida (land line) ya ce, "Baba ya shigo ne? Idan ya shigo kuzo tare ke da shi." Ta amsa da "Ya shigo, ga munan zuwa." Bayan ta ajiye wayar ta dube shi duk ya sha jinin jikinsa ta ce, "Alhaji yana kiranka." Sannan ta mike ta nufi sashin Maigidan nata yana biye da ita a baya har suka isa. Mustafa bai zauna akan kujera ba a kasa ya zauna ya sunkuyar da kansa yana gaida Baban nasa, fuskar sa babu annuri yake amsawa, ba kamar yanda ya saba amsa masa da sakin fuska ba, hakan ne ma ya sanya gaban Mustafa ya cigaba da faduwa dan yana ganin lallai wani abu yana shirin faruwa. Sun jima a haka yana cigaba da duba jaridar leadership da suka taddashi yana dubawa, labarin ya dauke masa hankali wanda aka ce wai waye ya haifi Obasanjo, sai da ya karasa shafin da yake sannan ya daga kai yana duban Mustafa kur da idonsa, abinda ya kuma fadar da gaban Mustafa. Can ya daure ya ce, "Baba ka ce yarinyar da kake nema acan kasan layin da muka taso take har ma ta kammala karatunra a F.C.E ko?" Bakinsa yana rawa yace, "Haka ne Baba." Alhaji Abdullahi ya kuma gyara zama ya ce, "To nayi bincike kamar yadda addini ya umurci muyi a duk sanda aka tashi neman aure, sai dai abun takaici duk mutanen da aka tambaya wadanda ba zasu yi karya ba sun sanar dani ko wacece Zainabu, dan haka sam ban yarda da tarbiyyar ta ba da ta gidansu ba ma gaba daya, don haka kaje ka nemo wata, ba zan maka auren dole ba amman ya dace ace ka samo mace mai mutunci da daraja a idon duniya." Hankalin Mustafa ya yi mugun tashi ransa ya baci, makwallaton sa sai kaiwa da komowa yake yi, duk da sanyin A.C da fankar dake dakin basu hana shi yin gumi ba, da kyar ya iya bude bakin sa yace, "Baba kayi hakuri bawai zan maka musu bane, ni na san Zainabu diyar kirki ce, ka san halin mutanan yanzu ba duka ne ke fadar gaskiya ba, dan haka ma yanzu idan za'a yi aure ba'a cika zuwa a tambayi mutanen unguwa ba, dan basu kaunar wani ya cigaba, dan haka nasan zasu iya yiwa Zainabu sharri dan haka ina neman yardarka akan na auri Zainabu, watakilama ba wacce nake so aka gaya maka ba." Alhaji Abdullahi yayi dariya dan shi yana da hakuri da bin komai a sannu ba kamar Hajiya Kubra ba mai saurin daukar zafi ba da saurin fushi, sannan ya ce, "Baba bana shakkar ba Zainabun da kake nema aka sanar dani ba, amman bari nayi maka wasu tambayoyi idan har ba ita bace shike nan." Ya goge zufar dake tsats-tsafo masa ba tare da ya iya cewa komai ba Baban nasa ya fara jeho masa tambaya"Asali Abu ake ce mata sanda tana yarinya, yanzu ne ake ce mata Zainabu ko?" Ya ce, "Haka ne." "Kuma da can tana tallar abinci da gyada da dai sauransu ko?" Ya hadiyi wani yawu dan dai ya san lallai Baban nasa ita ya gano, da kyar ya iya cewa, "Haka ne." "Tana da wani Yaya mai suna Sadiku wanda shi ba irin halinta gare shi ba, da kuma wata kanwarta da aka yi mata aure kwanaki ba ko?" Yayi shiru bai bada wannan amsar ba dan dai ya san Babansa yayi bincike matuka akan Zainabu. Alhaji Abdullahi ya cigaba da bayanin sa duk da bai bashi amsa ba, "Babanta mutumin Sudan ne, sunan shi Baba Abbakar, kuma ana kiran Babarta da Sala....." "La'ilaha Illallahu! Yanzu wannan karuwar yarinyar kake so Baba?" Hajiya Kubra ta amshe zancen tun bai kai ga bada amsa ba. Jikin sa ya kama rawa da rawar murya ya ce, "Momi ba karuwa bace, don dai tana aikine a (Local Govt.) ne shi ya sanya ake mata kallon 'yar iska, wallahi ina sonta Baba kayi hakuri don Allah, sharri kawai aka yi mata." Hajiya Kubra ta amshe, "Sharrin gidan Uwar wa? Ai ni sai yanzu ma na gane da ka fadi sunan Mahaifinta Abbakar da sunan Babarta, yarinyar da tun tana 'yar labubuwarta take iskanci, har ciki aka zubar mata tana da shekara sha hudu a duniya." Mustafa ya ce, "Kin ji ba Momi, sharri ne aka yi mata dan ana....." "Sharrin Uwarka? to tsaya ka ji na sanar da kai, na san Zainabu shekarun da suka wuce, yarinya ce mara mutunci kuma mara kunya dakikiya, ta addabi kowa, duk wannan lami ne ma akan iskancin da take yi." Ta dubi mijin nata tana magana, "Alhaji idan baka manta ba na taba baka labarin wata 'yar iskar yarinya shekarun baya da tayi mini rashin kunya har cikin Ofis dina, lokacin ina makarantar 'yan mata ta Dala (G.G.C DALA), dan ranar da tayi mini rashin mutuncin nan kasa bacci nayi, don har sai da jinina ya hau, har yau ina addu'ar Allah ya hadani da yarinyar nan nayi mata rashin mutunci amman har yau Allah bai hada mu ba, sai daga baya ma na ji 'yar unguwar da muka baro ce a bakin wata 'yar ajinsu, sai yanzu zaka ce kana son ta wai kuma da aure ma? Ai ko da ku biyu kuka rage a duniyar nan ba zaka aure ta ba muddin ina raye." Ya dafe kansa idonsa ya kada yayi jajir yana fadin, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Dan ya riga ya gano Momi ta san komai, ta san Zainabu farin sani, ashe ita ce wacce take bashi labari din nan, sai dai ya rasa ta yaya zai sanar da su wannan cikin da take tsanar Zainabu saboda shi dan ta ne yayi shi, ta yaya zai ganar da su shine ya fara lalata Zainabu tun a wancan lokacin da take zarginta, duk da ya tadda Zainabu da wasu muggan halaye amman shine ya koyar da ita kashi saba'in cikin dari. Ya yi tsamo-tsamo da shi kamar wanda kaza ta fashewa a cikin sa, bashi da damar da zai kuma musa musu abinda suka fadi, don idan yace na Babansa sharri ne to na Momin sa fa wanda Zainabu da bakin ta ma ta bashi labari, a sanda take bashi labarin bai yi zaton Mahaifiyarsa bace dan shi ko tambayar ta makarantar da take bai taba yi ba balle har ya gano hakan ba. Alhaji Abdllahi ya katse masa tunaninsa ta hanyar fadin, "Baba ka sani ba wai muna kin Zainabi akan kanta bane, A'a muna kin Zainabu saboda halinta, don babu wanda zai so ace yau ya hada zuri'a da lalatacce, da ace irin halin kanwarta gareta babu abinda zai hana mu kyaleka ka aure ta, dan haka ina baka shawara da lallai ka koma ka sake nemo matar aure dan wannan bata yi ba." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Idan Zuciya Tagyaru1-05 Posted by ANaM Dorayi on 08:00 PM, 03-Feb-16 Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU _____________ Na ________Fauziyya D Sulaiman_____ "Yo to banda abunsa ma a gidan nan wacce irin mace ce babu kuma masu tarbiyya da kyau idan ma shine ya rufe masa ido, don haka ka kwantar da hankalinka ka zabi wacce ta dace da kai duk 'yan uwanka ne." Alhaji Abdullahi ya amshe, "Ki na ji Kubra, ba wai dole sai anan gidan zai zabi mata ba don zai iya yiwuwa bai ga wacce ta dace da ra'ayinsa ba, ya je ko ina ya samo mata in dai diyar musulunci ce kuma mai tarbiyya." Shi kam duk bai fahimtar duk abinda suke fada don sam hankalinsa baya jikin sa, ji yake kamar ya dora hannu a kansa yayi ta zunduma ihu kawai ko ya ji sanyi a ransa. Alhajin na sa ya ce, "Ka tashi ka tafi Allah ya zaba maka abinda yafi zama alkhairi." Ya mike da kyar yake iya daga kafarsa yana hada hanya tamkar wanda ya sha giya ko kwayar sanya maye, idanuwansa sun kada sun yi jajir da su kamar gauta, har ya fice basu ce komai ba illa binsa kawai da suka yi da kallo. Hajiya Kubra ta ja tsaki tana fadin, "'Ya'yan yau ba'a iya musu, banda haka daga ganin yarinya baka san halin ta ba ka dage sai ka aure ta, ni abun ma mamaki yake ba ni, yaushe har ya dawo garin nan suka kulla soyayya da hatsabibiyar yarinyar nan har ta dauke masa hankali haka? Duka baiyi ko cikakkaken wata guda a garin nan ba, ni ko bayan raina ba zan so ya auri diyar nan ba, Wallahi Alhaji dan baka san ta bane sam bata da kunya da ladabi ko miskala zarratin, tuntuni na tsaneta wallahi." Alhaji Abdullahi ya kuma gyara zama cike da tashin hankali dan dai yana tausayin dan sa, don ya gane ba karamin so yake yiwa Zainabu ba ya ce, "Ai haka Allah yake ikonsa, shi kadai yasan a inda suka hadu, sai dai muyi masa addu'ar samun mace ta gari, da addu'ar ita kuma Allah ya shirya ta." Hajiya Kubra ta ce, "Amin dai." Shi kam Mustafa da kyar ya iya kai kansa sashinsa saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki, dan Allah ya sani duk duniya baya ga iyayansa babu abinda yake so sama da Zainabu, ya sani Zainabu wata tsoka ce a cikin jikinsa mai yawo da jininsa, a da can baya yana daukar son Zainabu shirme kuma shiririta a zuciyarsa, sai dai a yanzu ya sani muddin bai auri Zainabu ba lallai kam rayuwarsa tana tare da hatsari. Ya kwanta rigingine a gadonsa ya rintse idonsa, ina ma zai iya kuka da lallai yayi ko ya sami sassauci a cikin zuciyarsa. "Zainabu! Zainabu!" Ya fadi a hankali ko ya ji sanyi a zuciyarsa, ya sani hakkin Zainabu da sauran matan da ya cuta ne Allah ya saka musu ya jarabce shi da son macen da ya raina a da can, lallai da iyayansa sun san irin yanda yake son Zainabu da sun barshi ya aure ta ko yaya take. Haka nan ya dinga juyi a gadonsa bai san sanda bacci barawo ya silalo ya dauke shi ba, don yana cikin tsananin tashin hankali. Da asuba da kyar ya iya tashi dan jikinsa duk ya masa nauyi, a masallaci ya jima yana addu'ar Allah ya karyo da zuciyar iyayansa su amince ya auri Zainabu, har gari ya waye yana ta lazimi, sam ya manta da zuwa Ofis dan haka sai da ya makara. Ko da ya isa dinma kasa tsinana komai ya yi, banda kallon hoton Zainabu dake bisa tebur dinsa babu abinda yake yi, ya sani muddin iyayansa suka hana shi ya auri Zainabu to kuwa lallai zai jima bai yi aure ba, kai babu ma rana. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ya nufi kujerar da ke Ofis din doguwa ya kwanta yana neman layin wayarta, bugu daya ta dauka. Ita ce ta fara magana, "Hello My honey, Zuma ta."Ta fadi da wata irin murya mai tsananin fisgar hankalinsa, wacce ta ke siye zuciyar 'yan maza da ita. Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Zainabu ina tare da matsala mai girma, na rasa yanda zanyi da rayuwata ba ni cikin hayyacina da walwala ta." Ta ji gabanta ya fadi amman sai ta dake ta ce, "Ayya Zumana ka kwantar da hankalinka komai zai zamo da sauki Insha Allah, ka na ina ne yanzu?" Ya lumshe idon sa kana ya bude ya ce, "Ina Ofis yanzu amman na gaza komai, ji nake kamar bani da lafiya ma." Ta kuma kwantar da murya ta ce, "Kana jina ko zumana, ka kwantar da hankalinka gani nan zan zo yanzu Ofis din naka don bani son bacin ranka....." "A me zaki zo ne?" Ya tambaye ta da sauri. Ta yi murmushi don ta san Mustafan ta da shegen kishii ta ce, "Ka kwantar da hankalinka zan zo a shatar tasi ne, don nima ina Ofis yau." Ya ce, "Yayi kyau, ina jiranki kada ki jima." Ta dubi abokin aikin nata da yake kallonta tamkar maye sai dai duk iyakacin jarabarsa da gulmarsa ya gaza jin abinda take cewa, ta galla masa harara kana tace, "Wallahi Oga kai mugun dan saka ido ne, wannan kallon da kake mini fa kamar maye?" Yayi dariya yana sosa keya ya ce, "Ke din Zainabu da tsokano mutum kike, banda ni waye zai daure zama da zukekiyar mace irinki yana kallonta..... yanzu dai ina zaki naga kina shirin fita bayan yanzu D.P.M yayo waya zai zo." Ta yamutsa fuksa tana fadin, "Idan yazo kace masa na fita idan da dama zan dawo." "Zainabu ki yiwa Allah ki tsaya idan ba....." Ko kuma bi ta kansa bata yi ba ta fice abunta ya bita da kallo yana girgiza kai sannan ya ce, "'Yar jidali, yarinyar nan kina gara zama wallahi, ko da yake kin isa ne." Ta isa Ofis din nasu cikin wani ubansu leshi, zanin ya zauna dam a kugunta rafa ne,rigar bata fiye girma ba don da kadan ta iya wuce cibiyarta, sai dai hannunta dogo ne, yanayin kirarta ta kalangu ya fito sosai duk wanda ya kalleta sai ya kara sai dai mai karfin zuciya, kamshinta ka dai zai iya sanya ka kalle ta balle kyau da tsarin tafiyarta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta murda kofar Ofis din ta yi sa'a kuwa a bude take don yasan zata zo, ta san Ofis din dan kusan tare suka tare ma, ta shiga da sallama, yana bisa kujera yayi tagumi, har ta isa inda yake bai motsa ba sai dai idonsa yana kanta har lokacin. Matuka kwalliyar ta burge shi, ta isa ta zauna bisa cinyarsa ta janye hannunsa daga tagumin da ya yi, ta shafi gurin tana magana kasa-kasa, "Zumana waye ya taba mini kai?, hankalina a tashe na iso Ofis din nan." Ya daga idonsa yana dubanta, abinda ya kuma bata tsoro don ganin idon yayi jajir da alamar tashin hankali, ta kuma shafar fuskar sa abinda ke sanya shi jin sanyi a ran nasa ta ce, "Zumana ka sanar da ni abinda ke faruwa wallahi hankalina a tashe yake." Ya lumshe idonsa sannan ya fara magana har lokacin tana shafar fuskarsa yace, "Hajiya Kubra tsohuwar Shugabar makarantar ku ta G.G.C Dala wacce kika yiwa rashin kunya itace Mahaifiya ta....." Ta mike a zabure gami da dafe kirji tana fadin, "Innalillahi wa inna ilahihi raji'un, na shiga uku, Mustafa yanzu Hajiya Kubra Mominka ce? Wayyo Allah na yanzu ya ya zan yi? Ina fatan baka sanar da ita ko ni wacece ba?"Ya ware idanuwansa wadanda suke jawur yana fadin, "Zainabu babu hanyar fita, Momi ta sanki farin sani kuma tasan kece Zainabun da nake so yanzu a raina, Baba na ya sanya anyi masa bincike a kanki matuka, ina sonki Zainabu amman iyayena sun hanani auranki, abunda basu sani na yanda Zainabu take haka ma dan su yake, amman na rasa ta yanda zan sanar dasu abinda suke gudun Zainabu saboda shi na dansu ne." Jikinta ya dauki rawa dan ta shiga tsahin hankali matuka, ya kamo ta ya tallafe ta a jikinsa yana shafar ta, ta yi lamo a jikinsa tana ajiyar zuciya tamkar diyar mage, ta ayyana a ranta wannan wace irin masifa ce ta doso su, yanda suke son juna ace an haramta musu auran juna, don dai duniya bata da abin so kamar Mustafa, ta gama sallamawa kanta a yanzu shine bango majinginarta, don ta gaji da walagigin yawon iskanci da shan bakar azaba ta saida mutunci a gurin maza, domin dai ta lura yanzu ta sani babu abinda ke tattare da bin maza sai bata da sai da mutuncin kai, amman gashi wani katon abu na neman ruguza mata wannan burin nata. Ta san halin Hajiya Kubra mace ce mai kafiya da dagewa bisa duk abinda ta sanya a gaba, wuya da dadi basa sanyawa ta sauya daga kan ra'ayinta, bata manta kirarin da malamansu ke mata lokacin tana makaranta, "Mace mai kamar maza kwari ne da babu." Sun yi shiru na tsahon lokaci kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa, sun gaza sanya kansu farin ciki kamar yanda suka saba a duk lokacin da suka hadu don basu gundurar junansu. Ita ce tayi karfin hali tace, "Musty zumana yanzu yaya zamu yi, ko shike nan mun rabu babu mafita?" Ya kuma rungumar ta tamkar zai maida ta cikin sa kada wani ya kuma ganinta sannan ya ce, "Zainabu abinda nake tunani kenan tun daga daran jiya har zuwa yanzu amman na gaza samun mafita, sai dai na sani ruwa ko iska da duk wata azaba basu raba ni da sonki, ko da an rabani dake a fili ba za'a iya cire sonki a raina ba, son ki shine so na gaskiya mai wahalar da ruhin Mustafa da zuciyarsa." Tayi sanyayyar ajiyar zuciya mai cike da jin dadin kalamansa, sannan tace, "Shike nan zumana kada ka damu ka kwantar da hankalinka mu cigaba da addu'a, sannan mu tsaya kan ra'ayinmu na son juna duk wuya da dadi ina ganin zamu yi nasara komai dadewa." Yace, "Hakane Zainabu kin kawo shawara mai kyau, har naji raina yayi fari." Ta kuma kwantar da murya tana fadin, "Kada ka damu ka kwantar da hankalinka ni din taka ce har abada." Ta fara masa salon nata na jan hankali a cikin kunnensa take fadin, "Musty zumana (I love you so much) Ina sonka da yawa." Bai iya hakuri da Zainabunsa musamman idan tana masa salonta na kauna dan haka sai ya shiga maida mata martaninta, ya ma manta inda suke. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 ************** Abubuwa sun hadu sun jagulewa Mustafa har ma da Zainabun kanta, don dai yanzu ba ta iya kallon kowanne da namiji da gashin arziki idan ba Mustafa ba, wadanda take watsewarta dasu a da can ma ta kisu yanzu, kawarta Asma tayi mata lallashin duniya akan ta cigaba da harkarta ko da a boye ne amman ta gaza, dan sai dai tayi mata wani kallon ta ce, "Asma baki san Mustafa ba ne, shine namijin da idan ya baki zumarsa baki iya jin dadin ta kowa, shine namijin da ya iya soyayya mai kwantar da zuciya, shine mai kula da duk wasu bukatu na macen da yake matukar so, shine ya sadaukar da kansa ga Zainabu, shin kina tunanin yana gabana da ransa zan iya kula wani da namiji? Ki barni kawai baki san Mustafa ba kina kallonsa ne kawai." Don haka Asma sai dai ta zuba mata ido kawai don ita da kanta ta san Mustafa daban ne a cikin maza kamar yanda kawarta ke fadi. Samarin ta da dama sun damu da wannan sabon halin da ta bullo musu da shi musamman Alhaji Jamilu da kuma D.P.M, don haka ma ta kashe duk wayoyinta, idan kaga ta kunnasu lallai Mustafa zata kirawo. Hankalin Sala idan yayi dubu ya tashi, domin dai tana ganin kamar ana son kashe mata jin dadin diyar tane da walwalarta, dan da farko ma fada ta kama yi mata tana fadin, "Haba maitsada yaushe zaki zauna namiji kwaya daya yayi ta gare-gare da rayuwarki a banza, ki dubi irin wahalar da kika sha a baya, amman yanzu duk kin daga hankalinki don uwarsa tace ba zai aure ki ba, ga maza nan kala-kala suna binki wadanda suka fishi komai kamar su cinye ki amman kin makale masa, dan haka ki rabu dashi kawai tunda dai yanzu ba da bace." Ita dai shiru kawai tayi tana ayyanawa a ranta, "Sala baki san so bane shiya sanya kike fadin haka, da kin san irin abunda nake ji akan son Mustafa da kin tausaya mini, zan iya jure rashin komai amman banda Mustafa, wannan wata jarabta ce da Allah ya doro mini." Da dai Sala taga fada da mita ba zasu yi magani ba sai ta koma lallashi, amman duk a banza wai talaka ya girmi Sarki, su kuwa abokan watsewar ta sai kyauta ta bajinta suke mata wai ko zasu shawo kanta, amman idan an aiko ma sai dai Sala ta karbe tana godiya tace bata jin dadi ne shiya sanya bata fito ba. Idan mutum ya fiye matsa mata da aike kuwa fita take yi tayi masa rashin mutunci, don dai muguwar 'yar buyagi ce.Haka zaka tadda ta tayi dif da tabar shaidan ko shandy din ta a gidan Asma dan can Mustafa ke tadda ta suyi watsewarsu acan da lallashin juna, don ma dai shi yanzu Mustafa bai son shaye-shayen da take yi don shi kam baya ga taba yanzu bai shan komai sai dai idan wani yana shan tabar shaidan a kusa dashi ya amsa yayi ja uku ko hudu, amman giya kam tuntini ya daina sha, don haka take rage shan su don su kan yi fada idan ya tadda ta tana sha. Al'amura sun kuma tsauri a gare su, don Momi ta kama shi da hoton Zainabu wacce tayi tunanin ya rabu da ita tuntuni ya fara neman wata ma, ta yi matukar girgiza musamman da taji kalaman da yake furtawa akan Zainabu din. Ta yi neman wayar sa ne ta sanar dashi sallahun da Babansa ya bari ya kaiwa kanin sa Kawu Sale, amman duk wayoyin nasa a kulle suke, gashi kuma ta ga motar sa a kofar gida abun da ya tabbatar mata yana ciki kuma dai lokacin babu yara a gidan don haka ta nufi sashin nasa da kanta don ta sanar dashi sakon Baban nasa. Ta tadda shi zaune bisa kujera ya dora (laptop) akan cinyar sa ya kura mata idanu wadanda suke rine saboda tsabar tashin hankali, a fili yake fadin, "Zainabu yaya zanyi da son ki a zuciyata, ni kadai na san irin azabar da nake sha saboda raba mu da ake shirin yi, na gaza ganin ko wace mace da kima da daraja don kece kadai kika san Mustafa, ba zan iya auran wata mace ba muddin kina raye a duniyar nan ba, san yani a kafadarki ko naji sanyi a raina, na zama mutum-mutumi sai yanda kika yi dani Zainabu." Hankalin Hajiya Kubra yayi mugun tashi da jin kalaman da Mustafa ke furtawa, ta kuma jin tsanar Zainabu ta lunku a ranta don sai taga kamar yanzu yafi son Zainabu sama da ita ma daga yanda take jin kalamansa, kai ita tana ganin wannan son da yake wa Zainabu ma bana Allah bane asiri kawai tayi masa, banda haka meye hadin shi da ita, don ya fita komai a ganinta, ta nufe shi da sauri dan ta bayansa take baiga shigowarta ba, sai ta tsaya turus tana kallon abinda ya dauke masa hankali har bai ji shigowar ta ba. Wani katon hoton Zainabu ne ta dauka da wani yadin material (light purple), mai yarfin fulawowi jajaye da ruwan zaiba, tana sanye da wani dankunne na fashion mai kyau, ta tallafe habarta da tafin hannunta tana dariya, (dimple) dinta ya fito sosai, fuskar ta yi fayau, gashin idonta ya tashi gazar-gazar, girarta ta kwanta luf-luf, labbanta sun sha jambaki kalar kayanta sai walkiya suke yi tamkar ba a hoto ba, hoton ya dauko matuka don an futo da ainihin kyan Zainabu. Lallai ba Zainabun da ta sani da ba ci, don ta goge matuka tana kuma da kyan da lallai zata iya yaudarar Mustafa ya sota, sai dai ita kyanta baya gabanta tunda bata da kyan hali. Zuciya ta dauke ta don ganin wai har lokacin bai san ta shigo ba hankalinsa yana ga Zainabu ne kawai, ta fisge laptop din ta kwadata da kasa, ai kuwa sai gashi ta bare gida biyu, da alama da kyar zata kuma moruwa gashi mai kyau ce dan daga kasar waje ya taho da ita.ya daga kansa a gigice dan yaga wanda yayi masa wannan yankan kaunar sai yaga Momin sa a tsaye tana ta huci ta cika fam, nan da nan gumi ya fara karyo masa don yasan Momi babu wargi ba iri Babansa bane mai sanyi ba. "Mustafa! (ta kirawo sunan sa yau babu sayawa saboda bacin rai), wato dama baka rabu da wannan karuwar ba ko? to tsaya kaji na gaya maka ko mutuwa zaka yi akan sonta ba zaka auro mana jaraba ka kawo mana gida ba, da mun sakankance ka rabu da ita, ashe 'yar jarabar tana tare da kai. Shin wai ni me ka gani a jikinta da har tafi sauran mata da ka kasa kalla da daraja ne eye? Kai yanzu ba zaka ji kunya ba ace matarka tsohuwar 'yar tallan goro bace mara tarbiyya ba? Bata gaji tarbiyya daga uwa ko uba ba sam?, to tsaya kaji na gaya maka ta mahaukaci, ko bayan raina ka auri Zainabu ban yafe maka ba, sannan daga yau idan ka kuma zuwa gidansu ko inda zaku hadu ban yafe maka ba." Ya runtse idonsa gami da dafe kai hankalinsa yayi mugun tashi, babu abinda yake fadi sai, "Innalillahi....." Ta kuma kufula tana fadin, "Kai ko mutuwa zaka yi babu kai babu Zainabu na gaya maka in dai nice na haifeka dan halak." Tana gama fadin haka ta juya ta fice sam ta manta da abinda ya kawo tama sashin nasa. Ya zauna jabar a kujera har lokacin bai cikin hayyacinsa, ya kuma fadin, "Ya Salam! Ya Salam!" Har lokacin zufa tana karyo masa duk da sanyin A.C da fankar dake dakin. Maganar Momin ta dunga masa amsa kuwwa a kunnensa sai yake ji kamar har lokacin tana tsaye a kansa tana ta maimaitawa ne, don haka ya sanya hannuwansa ya toshe kunnuwansa wai ko ya daina ji, amman da yake abin daga zuciyarsa yake fita sai ya cigaba da ji kamar ma karuwa ya yi. Lallai ko yaki ko ya so yasan rabuwar sa da Zainabu ta zo kenan, idan har ya kasance da mai albarka, don dai ya san duniya bai hada Mahaifiyar shi da kowa ba, ko da kuwa zai mutu din kamar yanda Momin nasa ta fada din ya rabu da Zainabu har abada. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 WAI WACECE ZAINABU-ABU MAI TAGWAYEN SUNA NE? Asalin Salamatu mahaifiyar Zainabu 'yar cikin birnin Kano ce, ta tashi babu arabi balle boko, bata da aiki sai dai ta dauki tallan soye (dan tayi da ake cirowa daga dabbar da aka yanka na kasa mata a kokuna sannan a jera a cikin faranti). Don haka kullum da sassafe zata yi sammako ta tafi Mayanka ta siyo dan tayin wanda zama suke kusa da dabbar da ake yankawa da zarar an hango da dantayi sai a kwasa da gudu, wacce ta fara kamawa nata ne sai ta saka a kwanonta ayi ciniki sannan su kuma matsawa gaba da haka har ka tara na iyakacin kudinka, sannan sai ta tafi gida a yayyanka shi a soya, a zuzzuba a kokuna sannan a tafi tallanshi kasuwanni. Idan ta dauki tallan tun safe sai yamma likis take komawa gida, don haka bata da lokacin karatu, sai dai ran da taso sai ta tafi makarantar dare ita ma bata fahimtar komai dan banda gyan-gydi babu abinda take yi, don an sha yawo an gaji, idan kuma ranar alhamis da Juma'a ce a tafi gidan amare a yita wasan 'yar carafke ko lido da sauransu. Mahaifinta yana so tayi karatu sai dai bai isa ba dan matar sa tafi karfinsa, don haka yana ji yana gani 'yarsa ke wannan rayuwar babu kwaba balle harara, sannan idan dare yayi wani lokacin zaka ga samari sun cika kofar gidan anata zance da shewa da kawayenta kuma bana aure bane illah ayi shashanci da zancen batsa a watse, amman babu na aure a cikinsu. A gurin da take sai da soye wani mutumin Sudan sunansa Abbakar, shayi yake saidawa irin na babbar butar nan wanda ake dauka a hannu da biredi da kofuna a faranti, Abbakar mutum ne mai kirki da hakuri dan kullum Salamatu sai ta tsokane shi dan hausar sa bata fita sosai, gashi kuma da shegen surutu da son tsegumi. Duk danginsa suna can Sudan, yaki ne ya sanya suka watsu suka yo Nigeria da 'yan uwansa, sai dai tun da suka zo kowa ya nemi masauki, shi kam yayi sa'a ya fada hannun wani Malami Malam Nadabo mutumin kirkine ya bashi gida inda yake saukar baki ya zauna cikin almajiransa, yana fita neman abincinsa don shine ma ya bashi jarin da ya fara sana'a tun yana zagaye cikin unguwar har ya koma yana shiga kasuwanni.Da yake ya iya shayin sai ya samu kwastomomi dan irin na larabawan nan yake yi, a haka suka hadu da Salamatu ma, don Allah yayi shi mutum ne mai shegen surutu da son gulma dan haka duk abinda ya gani sai ya nuna mata ko ya tambaye ta da haka har soyayya ta shiga tsakaninsu. Abu kamar wasa sai gashi sun saba matuka, sai dai tun a wancan lokacin tayi mugun raina shi tayi ta masa masifa bai damuwa, domin yana da matukar hakuri sai dai zancan gulama amman sam baida abokin fada, sai dai mutane da dama suna ganin abun nasu kamar ba zai yiuw ba don shi fari ne tasa kamar balarabe gashinsa ma a nannade yake sai dai wahala ta sanya shi ya dan dafe, yayin da Salamatu take baka, amman bata da muni, sai dai bata da tsawo gajera ce sosai mai jiki. Malam Nadabo dai shine kamar matsayin mahaifinsa don haka shine ya tsaya masa har aka yi wannan auren, suka tare a nan gidan Malam din da yake zaune da almajirai, wasu suka koma shagon gidan wasu kuma suka koma daya gidan. Ta addabi kowa a gidan don gidan kusan a hade yake da na Malam kasancewarta masifaffiya ce, su dai matan malam bata yi da su don sun ja girman su haka malam, sai dai duk 'ya'yan gidan 'yan dakinta ne musamman matan, amman duk kusan almajiran malam tayi fada da su don ma malam yakan yi mata fada, don haka babu wanda take shakka kamar malam don babu wargi, a nan gidan ta haifi dan ta na fari Sadiku wanda aka haifa rana daya da dan Malam Zaidu, don haka rana daya aka yi suna Malam ne ma ya rada musu sunansu duka. Sun tashe tare da Zaidu da yake Sala bata wani damu dashi ba don ita ta fi son ta haifi mace wai itace abokiyar neman kudi, don haka kullum a cikin watangariri yake a cikin gidan musamman da ta yaye shi sai ta bar musu a can, don haka kusan a gidan nasu ya taso.Tare Malam ya sanya su a makaranta Ma, sannan ta kuma samun wani cikin tayi ta tanadin kayan mata har su dankunne da awarwaro amman sai gashi ta kuma haifar namijin, shima din haka ya taso a gidan malam din, sai dai daga kansa bata kuma samun haihuwa ba har ya shekara biyar, sai wata annoba ta zo ta kyanda shima yana ciki, ai kuwa dai wannan kyanda itace ta yi ajalin Sabitu. Rashin samun cikin nata ya sanyata fara tunanin wai matan Malam ne sukayi mata asiri don ta fara haihuwar da namiji, su a kan Zaidu suka fara haihuwar namiji duk mata suke haifa, ita fadi take banzaye ni da ana musanye da munyi don nafi son matan, sai dai bai ya wata goma ba da rasuwa Sala ta kuma samun wani cikin. Ai kuwa dai wannan karon tayi sa'a a wannan karon ta samu abinda take so din, don haka murna ba'a magana, sai da dauki son duniya ta dora akan Zainabu sunan Mahaifiyar malam din ya sanya mata kenan, da farko tace bata yarda ba sunan Sima take son a sanyawa diyarta, shi kuwa malan sunan matarsa ta fari ne da ta rasu yana son sunan, sai da Abbakar yayi ta lallaba ta sannan ta amince, akan Zainabu sai tayi fada da uban kowa a kuma sannan ne Abbakar ya kammala ginin gidansa da taimakon malam, don haka suka tattara ya nasu-ya nasa suka koma, amman banda Sadiku wanda sai dai yaje gidan nasu ya koma gidan malam don kamar ba Sala dince ta haife shi ba musamman idan Zainabu tana kin ji yana mata fada, dan haka shima bai fiye zuwa gidan ba sai da ya shiga sakandire ne ma yake zuwa sosai.Sala kam sana'a ta kafa sosai a gidan ta, don daman tun tana gidan malam jarabar neman kudi ne da ita, don haka ba ta zama kullum cikin neman kudi take. Tun daga wannan lokacin shike nan haihuwa ta bude a gidan nasu, sai dai yaran suna tashi babu tarbiyya, da farko malam ya fara kiran Baba Abbakar akan halin da yaransa suka tashi da shi, don haka yayi masa nasiha mai shiga jiki, sai dai idan aka ce namiji bashi da katabus a gidansa babu tarbiyya, don haka san da Baba Abbakar yaje mata da abinda Malam din ya ce, tsalle tayi ta dire tana fadin, "Wallahi baka isa ba, wacce tsiyar kake tsinana mana da har zaka yi mini wannan tsarin (don a lokacin babu ciniki a sana'ar ta shi sai dai yayi ta yawo bai samun ciniki sosai, daga karseh sai ya koma kame-kame)." Malam Nadabo yana ji yana gani gidan Baba Abbakar ya koma yanda yake don dai yayi har ya gaji, sai dai shifa duk wani abu na tsawatarwa yana musu dan haka shi kadai suke shakka a rayuwarsu, don duk wanda ya doki Zainabu sai inda karfin Sala ya kare, amman idan Malam ne sai ta ce, "Sai kiyi hakuri na gaya miki ki daina zuwa gidansa mana." Shi kam Sadiku ya sami karatu mai kyau don ya sami makarantar firamare mai kyau da sakandire, daga nan ya wuce kwalegin share fagen shiga jami'a, shi kuma Zaidu da yake bangaren Arabic ya dauka yana Jami'atu Ummul Qura dake birnin Makkah yana karantar harshen larabci, wannan shine mafarin komawar Sadiku gidansu don dai babu abokinsa. Da kyar da sidin goshi Sala ta bar 'ya'yanta suke makarantar boko da ta allo don Malam yana fada ne da kuma Sadiku, sai dai duk da haka Zainabu ba kullum take zuwa ba sai jefi-jefi. Sai dai da yake ba karatun ne a gabanta ba sam bata yi, Zainabu ta taso da hali irin na Babarta don haka bata da wargi duk wanda ya taba ta sai ta rama, don dai Sala ta bata ta tun tana yarinyarta, ga fadan ta baya mutuwa kamar fadan kurma, don sai tayi wata tana fada sai dai idan iyayen yaran sun gaji su zo gidan a baiwa Sala hakuri sannan za ta hakura, idan mutum yafi karfinta ba ta raga masa don da cizo da yakushi zata kwaci kanta, ko kuma idan ka doke ta tayi ta jifanku ko duk inda kuka hadu sai fadan ya tashi. Wannan halin nata ya sanya duk unguwar kowa yake shakkarta, abinda ke farantawa Sala rai kenan don takan ce, Abulata da na kai kararki gwara a kawo mini wallahi, don haka duk wanda ya taba ki koda gemunsa yana jan kasa kada ki kyale shi ki rama, daga nan har ofishin kwamishinan 'yan sanda zan iya zuwa a kanki Abulata. Don haka har siyan fada take yi, duk wanda bashi da karfi Zainabu kan sayi fadan ta casa wanda ake fadan da shi don akwai ta da karfi, idan kayi gulmarta za ta sanya a kama ka a tura ka lungun ka-ci-uwaka a tura maka kashi a baki ko bara-gurbin kwai, don haka ta addabi kowa a unguwar tasu. Ko fakin din mota aka yi bai gamshe ta ba sai tayiwa mutum faci a motar tasa, don haka duk kofar gidan masu hali na unguwar da an gan ta masu gadi zasu bita da gudu tana dariya. Idan aka tura ta makarantar firamare kuwa masu kosai da 'yar tsala na sadaka take bi da waina wadanda ke yawo da almajirai mutane na siya suce su raba wa almajirai sai an fita tara take tafiya makarantar. Yawo kuwa ko kare ya gan ta ya kyale, don kullum za ta hada zugar yara suna shiga karkashin manyan motoci da ke fakin a nan kan tudu, dan haka duk wanda baiga dan sa ba yana tare da Zainabu, yawo bola-bola sun iya shi, gashi babu dama kayi magana sai Sala ta hau bala'i tana fadin, "Kun ga kada ku sanya mini diya a gaba, waye Abula ta daurawa igiya a wuya kowa na ga da kafarsa ya bi ta, don haka duk matar da ta kara cewa Abula ta ja mata 'ya'ya yawo wallahi sai na dirji bakinta, duk wacce ba ta son 'ya'yanta su je yawo ta daure a kofar gida, kurwar Abula kur! Na gaya muku." Wannan shine kadan daga cikin labarin Zainabu Abu mai tagwayen suna. **********Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ubangiji babu ruwansa yakan bar bawa ya sakata ya wala ya yi sabo son ransa ba tare da ya matsa maka ba a duniya, amman abu kalilan zai jarabce ka dashi duk sai ka gigice ka ga ashe kai din ba komai bane, ka koma abin tausayi. To, Lallai kam hakan ce ta faru ga Mustafa, don bai taba zaton zai shiga ko da kwatankwacin wannan matsalar a rayuwarsa ba, Allah ya jarabce shi da son Zainabu wacce ita kuma mahaifiyarsa ta tsana kamar mutuwarta, Zainabun da ya raina a baya, sai ga shi son ta yana neman raba shi da duk jin dadin rayuwarsa, don wacce ta kawo shi duniya ta yi musu katangar karfe a tsakaninsu. A da can da suka hana shi auran ta bai damu kamar yanzu ba, don yaka je gurinta ya kwanta a kafadarta ta lallashe shi, amman yanzu babu dama don haka abubuwa suka masa yawa, yanza haka yana ofis ya hada tagumi da hannuwa biyu- biyu kamar wani karamin yaro, wani inji aka ce ya je ya duba amman ya gaza tashi, gashi yafi kowa iya gyara a sashen nasu, yanda kasan maye haka yake idan ya sanya gyara a gabansa sai ya ga ya gyaru, don haka suke ji da shi.Yana nan zaune ya ji kiran wayarta ya shigo, ya zabura da sauri ya dauka ya kara a kunnensa. Da kashe murya da shagwaba ta ce, "Zumana shiru kwana biyu babu kai babu wayarka, ko Zainabu ta yi laifi ne bata sani ba?" Ya lumshe idonsa gami da kwanciya jikin kujera, ransa ya yi fari tas saboda jin muryar Zainabu kawai da yayi, sai dai ya gaza bude bakinsa ma balle yace wani abu. Hankalin ta ya kuma tashi da jin shirun da ya yi mata, ta kuma duban wayar ta ga lallai a kunne take, da tashin hankali ta ce, "Mustafa ka ce wani abu mana, ko dai ka manta da Zainabunka ne?" Hankalinsa ya kara tashi don jin muryarta kamar za ta yi kuka, ya daure ya bude bakinsa da kyar ya ce, "Zainabu baki yi mini komai ba, illah dai Mahaifiya ta ta kafa mini mummunan sharadi a kan idan na kuma zuwa inda kike ko duk inda na san zamu hadu, to lallai ba ta yafe mini ba....." "Me ka ce Mustafa? Yanzu kana nufin shi kenan mun rabu har abada? Yanzu yaya zan yi da sonka a raina Mustafa na? Anya zan iya rayuwa babu kai, Zumana?" Yayi kokarin jawo dauriya ya sanyawa ransa ya kwantar da murya da lallashi ya ce, "Kin ga Zainabu kwantar da hankalinki, ni din naki ne har abada ba zan iya rabuwa da son ki ba, sai dai dole zanyi biyayya ga maganar Mahaifiyata don ina son na rabauta duniya da lahira, na yi miki alkawari ni naki ne har abada, sai mu cigaba da addu'a komai ya zo da sauki, don ina ji a jikina ke matata ce da zan rayu da ita cikin ni'ima da soyayya." Hankalinta ya dan kwanta ta yi ajiyar zuciya tana fadin, "Zumana yanzu yaya za muyi kenan? Don na san zan sha walahar rashin ganinka matuka." Ya lumshe idanuwansa wadanda yake jin suna masa nauyi ya ce, "Ki bari zan ga Babana idan ya dawo zan sanya shi ya lallasar mana Momi din, ina ganin shi zai tausaya mini idan ya ga halin da nake ciki, don yafi Momi saukin kai." Ta ce, "Shike nan zumana, amman zan dinga jinka a waya ko?" Ya ce, "Dole ne ai Zainabu na kiraki a waya, idan ba haka ba zuciyata ai bugawa zata yi." Ta yi murmushi gami da fadin, "Ina sonka matuka zumana." Ya yi dariya ya ce, "Nima haka Zainabu, sai dai ina son don Allah ki yi mini alkawarin kin bar hulda da maza kamar kina ganina, don na danka miki amanar kanki, ina jin kamar zuciya ta zata babbake idan na ganki da wani, shin zaki iya rike mini kanki da alkawari har komai ya lafa?." Ta yi murmushi gami da fadin, "Mustafa ko da ba kace ka ba ni amanar kaina ba ba zan iya hulda da kowanne namiji ba, don kai din kayi mini yanda ba zan iya kallon kowa da gashi ba, ka kwantar da hankalinka a yanzu Zainabu taka ce kai kadai." Da kyar suka iya rabuwa a wayar don suna ta sanar da kawunansu irin son da suke yiwa junansu ne kawai. Sai a sannan ya sami karfin gwiwar da zai iya tunkarar aikin da ke gabansa, don haka ya shiga dan wani daki ya sauya kayansa daga na gida zuwa na aiki ya nufi inda injin da zai gyara yake. Ita kuwa Sala ce a kanta a tsaye tana rike da kugu jira kawai take ta kammala amsa wayar, ai kuwa tana ganin ta gama wayar din ta dirar mata da jaraba. "Yanzu Abula shi kenan zaki zauna namiji daya tal yana miki yawo da hankali? Ga wadanda ke son ki kuma sai wahalar da su kike yi? Yanzu jiya Alhaji Hayatu Tumbin kudi sai da ya kashe kunyarsa ya zo ya sameni ya ce don Allah ki fito ko gaisawa ne ku yi, shi da gaske yake auranki zai yi ma, ya cake mini dubu hamsin a hannuna ke kuma ya ce idan kin fita zai baki duk abinda kike so, amman yarinyar nan kika bada mini kasa a idona, har mutumin ya gaji da jiranki ya yi zuciya ya tafi, kin kwallafa ranki a kan shegen mayaudarin yaron nan, kin ki ki saki zuciyarki ki ci arziki ki bar arziki a mazauninsa? Wallahi kin bani mamaki Abula ban taba zaton zaki koma sokuwa a hannun namiji ba, su da kike juya su kamar waina?." Zainabu ta dinga duban Sala da mamaki da takaici da kyar ta iya buda bakinta ta ce, "Sala kin san So kuwa?" "Ban san shi ba sai ke diyar zamani, ba kuma na fatan na san shi tunda shi din masifa ne da jaraba, ki dubi yanda ya maida mini ke, wallahi da zan gan shi shi So din dana rade masa kai don Ubansa, tunda ya hana ki ki zauna lafiya." Ta dafe kirji gami da jingina da kujera tana fadin, "Sala ki kyale ni kawai tunda dai kin ce baki san So ba, yanzu haka kirjina ciwo yake mini, lallai idan na rasa Mustafa na san mutuwa zan yi don Allah ya jarabce ni da tsananin son sa, zan iya yin komai don na same shi Sala, yanzu kam na gane so yana gaba da kudi da komai, ki rabu dani kawai don na yiwa Mustafa alkawarin ba zan kuma kula kowa ba zan yi ta jiransa har ranar da Allah ya sanya iyayansa suka amince ya aure ni din." Sala tayi Salati tana tafa hannu tana fadin, "Shike nan an sammace mini ke Zainabu, don in dai ba asiri ba babu abinda zai sanya ki gaza hulda da kowa sai shi kadai, kuma yanzu ba ya nan baya ganinki ba kya ganinsa ma, amman kin ce ba zaki iya kula kowa ba, to wallahi ya yi a banza, don ni ma ai ba'a zaune nake ba, duk neman sa'ar da nake miki a ce ya tashi a banza, bari na tafi gurin boka na kan tudu zan sanya ya raba min ku, idan ya so sai na ga karshen shegen So din, tunda dai shi ciwon masifa ne." Zainabu ta riko hannun Sala da ke shirin fita daga dakin nata tana fadin, "Sala kada ki rabani da Mustafa idan dai ba so kike na mutu ba, shin wai kin san abinda ya sanya iyayan Mustafa ma suka hana ni aurensa? To ba wani abu bane illa yawon da nake yi na bin maza tamkar karya, kowa ya zo ya dauke ni a mota ya je yayi abinda ya ga dama da ni kan kudi, sun ce ni karuwar gida ce, yanzu me ye amfanin irin rayuwar iskancin da na yi? Ni kam zuciyata ta gyaru don haka na bar abinda kike so na yi." Sala ta kuma shiga rudu ta ce, "Ahaf! Kinji ba? Ai na sani asiri yayi miki, banda asiri ke da bakinki ki dinga kiran kanki 'yar iska, yanzu kin yarda ke din 'yar iska ce? Kalmar da da idan aka gaya miki sai inda karfinki ya kare amman yanzu kike gaya wa kanki, to ba karuwa ba ko ke mecece kinfi karfin danta wallahi, idan tace kuma ke karuwa ce shi dan nata ai karuwi ne tunda dai shine ya watsa miki rayuwa, sai nayi maganinsu shi da uwar tasa in dai sunana Sala." Ta warce hannunta daga rikon da Zainabun tayi mata ta nufi waje tana cigaba da bala'inta.... To, masu karatu, mu hadu a littafi na biyu don jin yadda Sala zata aiwatar da wannan mataki. Take cewa kar ku damu na dayan tare suka fito da na biyun,Mai kaunarku da yi muku fatan alkhairi a kullum: FAUZANKU CE! Mrs Q for Q, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.co Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347