[1/29, 1:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL MABUƊI Kashim Ibrahim library (KIL) babban ɗakin karatu ne cikin Jami'ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya. Kamar kullum yauma ɗakin karatun cike ya ke fal da ɗalibai maza da mata kasancewar lokacin jarabawar zango na farko na shekarar (first semester) ya matso. Ɓangaren da ta san ya fi kowanne rashin hayaniya ta samu ta raɓe. Sanye ta ke cikin shuɗin hijab dogo har kasa. Sam ba ta damu da ta shafa ko hoda ba bare a kai ga jambaki, irin bakaken matan nan ne da su ka amsa sunan "black beauty". Duk yadda ta so ta mayar da hankali ta gane karatun da ke gaban ta, hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan zaman da wani ya yi kusa da ita. Zuwan ta be fi da awa daya ba sai gashi shi ma ya zo, kuma ya rasa in da zai zauna sai kusa da ita duk girman library din, mitar da ta ke yi cikin ran ta kenan tana mai jan tsaki ɗaya na bi ma ɗaya. Tana cikin wannan halin ne ta ji kamar an gogi kafar ta wanda hakan ya sa ta saurin janye kafar da sauri, a fusace cike da alamar tambaya ta kai kallan ta gare shi. Tsintar idanun ta cikin na sa ya tabbatar mata da ya na sane ya sanya kafarsa ta gogi na shi, ko shakka babu irin 'yan iskan mazan nan ne ma su yiwa mata goge, da be sami dama ba shi ne ya ke bin ta da kafa. Kallan da ta ke masa ne ya sanya shi janye tashi kafar da sauri tare da faɗin "Sorry Mama na! ..." Maimakon ta ji sanyi cikin ran ta, sai ma daɗa tunzurata da yayi, wato yana nufin bai ma san kafar sa na gogan na ta ba ne, ko tsabagen shaiɗana ne da zai wani kira ta da "Mama na" tunda ya sami kafar tsohuwarsa ai dole ya goga. Take ta ji karatun ma ya fita daga ran ta, cikin zafin nama ta haɗa ya nata ya nata, har ta na bugewa da tebur tsabagen ɓacin rai ko gaban ta ba ta gani da sosai. Fuuu ta fice a fusace. Kai tsaye Queen Amina Hall ta nufa inda nan ya kasance hostel ɗin da take. Da ke bayan isha'i ne, ɗalibai samari da yan mata wanda su ka sha karatu da wanda ba ma su sha ba duk sun taru mararrabar hostel sai cafta ake. Sam ba ta kula da su ba, bare ta damu da sheƙe ayar wasu daga cikinsu ke yi na rungume rungume da shafe-shafe da ta ke jin labarin wasu kan yi, kan ta a kasa ta ke gifta su, zuciyarta na mata tuƙuƙi don gaba ɗaya niyyarta ta shanye handout biyu na course din da za su yi jarrabawa ta gaba. Daf da za ta shiga hostel din ta ji an tab'o kafadar ta, tsayawa ta yi cak kafin ta jiyo a hankali saboda jin da ta yi hannun namiji ne mai taɓo ta, wa za ta gani? Wannan mutumin nan ne dai ya biyo ta, har ya iya daga hannun sa ya taba ta cikin mutane......ji ka ke tas!!! Hannu ta sa ta dauke shi da marin da sai ya ga wuta a idon sa ba tayi tunani kafin aiwatarwa ba don gaba ɗaya ji ta yi banda cin mutuncin matatantaka da yayi har da musulunci da hijabin da ke jikinta ya ci wa mutunci. Gaba ɗaya hankalin jama'ar wajen ya dawo kansu, hasken lantarkin da ke ci a wajen kamar an ƙara masa haske don ya sadar da abin da ta aikata ga bawan Allahn nan. Jikin kowa yayi sanyin ganin wanda ke tsaye gaban ta hannun sa bisa kunci, bai yi zaton haka daga gareta ba hakan ya sanya marin zuwa masa a matsayin ba zata kamar yadda ya zo masu a hakan. Sanannan saurayi ne cikin Jami'ar wanda hatta wanda su ka shigo Jami'ar a wannan shekarar sun san da zamansa saboda shuhura. Ga mamakin kowa har ita mai marin wacce ta yi mutuwar tsaye ba tare da ta yi Dana sanin marin da ta yi ba, don tsayuwar da tayi jira ta ke kome ma zai faru ya faru don kwatakwata babu nadama ko karaya a tare da ita, sai gani kawai ta yi ya mika mata abu, ko da ta ware ido da kyau ta dubi abin da ya ke miko mata sam bata gaskata ba, a hankali ta mayar da kallan ta ga fuskar shi wanda ke dauke da murmushin da ya sanya kwarjini da kyawun fuskarsa bayyana, cikin nuna halin ko in kula da marin da ya sha ya furta "Ga shi, wayar ki ne da ki ka manta..." Hannun ta na rawa ta karɓa ba tare da saurari cigaban abin da yake shirin faɗi ba. Ta na karba ya juya, cike da takama da ko in kula ya ke tafiya yayinda ta bi bayan sa da kallo, shin wannan waye shi? "Ya Allahu ka rufa min asiri ni Amatullah..." Cewarta, a hankali ta juya ita ma cikin sauri ta na harhaɗa kafafu, daliban da ke gurin nan su ke ta cece ku ce akan abin da ya faru gaban su, daga masu ba ta kyauta ba, sai masu da su ne sai sun tattaka ta, sai masu Allah shi Kara " Toh ai shi Dee Yusuf ya ɗauka kowacce mace ce ta rako mata, wallahi ta burge ni da ta kwashe shi da mari" ta ji wasu na faɗi daga bayanta. "Dee Yusuf!" ta so ta sake faɗi amma ina, zancen zucin da ta ke ya sa ta dena ji yadda ya kamata, kwakwalwarta ta dena sawwara mata daidai har ta isa ɗakin kwananta da ke gini na takwas ɗaki na goma sha biyu (block 8 room 12). *** Littafanta kawai ta ajiye saman gadonta, buta ta ɗauka ta fice ba tare da ta ce da Ahalin ɗakin uffan ba, kama ruwa ta je tayi sannan ta yi alwala, ɗakin ta koma ta gabatar da wutiri, sai a lokacin ta samu ɗan natsuwa, duk da haka ba ta motsa daga saman dardumarta ba, sam bata lura da kallon da kawarta ke mata ba. "Amatullah! Amatullah!! Amatullah!!!" sai a kira na uku ta ji ko dan ƙawar ta ɗaga muryarta ne ba ta sani ba. "Zulaikha sai ki firgita mai rai wallahi, ji tsawar da kika min" ta karasa tana mai jan gajeruwar tsaki, mamaki a karo na biyu ya sake kama Zulaikha saboda ta tsaki na ɗaya daga cikin ɗabi'un da Amatullah ta tsana. Tashi tayi ta ninke dardumarta, sannan ta haye gadonta da ke saman na zulaikha ba tare da ta ce da ita da ke jiran bayani komi ba. Ɗauko takardunta tayi don ta cigaba da dubawa amma ina babu abin da ke shiga, ga shi jarrabawar da za su yi gobe na physics department ne da duk wani mai karanta abin da ya jibinci kimiyya da ke aji ɗaya a jamiar yake yinsa, sannan adadin wainda ke maimaita jarrabawar kan fi rabin adadin masu rubutawa a karo na farko, saboda haka dukkan su ke tsorace da darasin. "Zulaikha na sadaƙar kawai zan sake physics dinnan" tace cikin karyewar zuciya. "Allahumma Ajirna" Zulaikha tace iya karfinta. "Kin shigo kafin lokacin da kika ɗibar ma kanki, kin shigo a firgice kin yi gamo ne?" Zulaikha tace tana shafa hannunta cikin sigar lallashi. "Marin wani Yusuf Dee yake ko wa nayi fa anan gaban Amina" tace iya gaskiyarta, yayin da Zulaikha ke hango kwantacciyar firgici a idon ƙawarta. Ba Ta dena shafa hannunta ba, ba ta ce komi ba kuma, so take ta tuna in da ta san sunan Yusuf Dee din, kamar wacce a ka raɗawa ta tuna. "Wai Dee Yusuf kika mara? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, me ya kai ki Amatullah?" ta haɗa duka ta faɗa mata ba tare da ta jira amsar cewa shi ɗin ta mara ko wani ba. Hawayen da ta ga Amatullah na fitarwa ya kara tsinka mata zuciya. Zikiri take a hankali duk wanda ya zo bakinta, yayin da Zulaikha ta haura saman gadon tana lallashinta. "Kinga ba wani abin damuwa bane, Shine Sec Gen na SRC (Student Representative Council) Watau shugabanin ɗalibai masu wakiltar sauran ɗalibai, kuma shine in charge of student affairs department. Wasu sun ce bafullatani ne wasu sun ce babur amma kin tuna Halima ta statistics kin san yar Margi ce, toh ita na ji tana faɗin ɗan garin su, kin san yadda ake rububinsa hakan ya sanya masa girman kai, kuma Kinga kudin SRC na ɗiban su, amma ina jin kamar faculty of medicine yake na ji dai ana fadin first class guy ne, yana dai da yan kora ni shi ne kawai tsoro na amma banda haka bana jin komi" Zulaikha ta ƙarasa cikin tabbatar da abin da ta ke fadi. Kallon ta Amatullah take cike da mamaki, ta san ajinsu ɗaya, kawarta ce, tare su ke komi a ina ta san duk waɗannan bayanan da ita ba ta taɓa sani ba, ƙarshenta ma za ta iya rantsewa ba ta taɓa ganin wani halitta irin ta wanda ake kira da Dee Yusuf ɗin ba. *ZAI DINGA ZUWA MUKU RANAKUN LARABA DA LAHADI NA KOWANE SATI INSHAALLAH* [1/29, 1:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♂ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ƊAYA Allah ya yi dare gari ya waye, jarabawar dai da ta fi firgita Amatullah yau za ta rubuta shi a matsayin jarrabawarta ta farko a jami'a wato ta kimiya Physics 131 (PHY131/ZAKS 131). Course ne da kowani dalibin aji daya da ke karanta wani abu da ya jiɓinci ɓangaren kimiya ke jin tsoro, balle kuma ita da ke ɓangaren Phamarcy, ba don komai ba sai don course ne da ake masa laƙani da "chain prerequisite for pharmaceutical chemistry (Pharm chem)" . Idan ɗalibi ya fadi shi ba zai taɓa yin na gaba da shi ba sai ya gyara wanda ya faɗi haka na nufin tabbatacciyar sake shekara (spill over) ce mai zaman kanta tun ana aji daya. Amma duk da tsoron faɗuwa sai gashi gaba ɗaya hankalin Amatullah ba ya kan Course din, ita babban tashin hankalinta bai wuce marin Dee Yusuf da ta yi ba gaba ɗaya shi ya hana ta karatu a daren jiya ga kuma wani ciwon kai da ya saka ta gaba. Zulaikha ta ce Faculty of medicine ya ke, kuma SEC GEN na SRC hakan ya sa hankalin ta ya dan kwanta ba don komai ba sai don ta na kyautata zaton ba lalle ta kara haɗuwa da shi ba, domin kowa in dai yanda ta faɗa daidai ne ya kamata a ce yanzu Shika ya ke ba nan Samaru ba, duk tunaninta shaf ta manta akwai wasu fannoni a facultyn da su ɗin gaba ɗaya rayuwar su a samaru ne. Haka dai ta lallaɓa ta shiga jarabawar, da ya ke ta safiya ce, karfe 8:30 zuwa 11:30, ko karyawa ba ta samu ta yi ba, yadda ta saba shigar nan na ta cikin hijabi har kasa yau ma hakan ta yi, ba ta zame ko ina ba sai ɗakin jarabawa da ake kira FSLT. Dan wuyar jarabawar, ba ita ta fito ba sai da lokacin kare jarabawar ta yi, aka karɓe tana mai takaicin rashin kammala wasu lissafin. Da sanya tafukan kafar ta waje da sarawar da kan ta yayi lokaci daya ne, sanadiyyar rana mai zafi da ke shirin ƙwallewa. Daga jikin ta har garin babu abin da ke mata dadi, don haka kai tsaye ɗakin kwanan dalibai ta nufa ba tare da ta tsaya magana da kowa ba, balle masu mayar da magana kan jarabawar in ban da fargaba da ɓacin rai babu abin da za su kara mata. Da rokan Allah ya mata katangar karfe da haɗuwa da Dee Yusuf ta ke tafe, zuciyar ta na dukan uku uku. Har ta wuce ta gaban Ribadu hall, ta dau hanyar da zai sada ta da Amina Hall, Sai kuma ta sake shawarar biyawa ta cikin social center ta siya abinci domin kuwa ba karamin yunwa ta ke ji ba, kuma yanda ta ke jin kan ta ba za ta iya tabuka komai ba, gashi idan akwai abin da Amatullah ba ta wasa da shi ya na bayan cikin ta. Social center babban matattaran dalibai ne a cikin jami'ar, wanda ke dauke da shaguna iri-iri, wanda ya hada da business center ne, wajan aski, shagon dinki, shagon dinki, wajan kallan dalibai(Cinema), shagon kwalama da makulashe da dai sauran su. Ba ta da takamamman wajan siyan abinci saboda ba ta fiya siya ba dafawa ta ke, dan haka nan ta fara rarraba ido domin neman restaurant daidai kudin ta. Ko da ta bi gaban wani restaurant da ake kira "Frizllers" wanda kaf social center nan ne matattara cin abincin dalibai ma su ji da kan su, tuni gaban ta ya shiga faduwa. Da sauri har ta na tuntube ta wuce restaurant din, dan kuwa yauma kamar kullum cike ya ke da samari da yan mata. Wani wajen siyar da abinci dan gaba da Frizllers din ta tsaya ta siya shinkafa da miya da salad. Hankalinta na kan wayar ta dake fama ringing ta fito daga restaurant din, wayar ta daga ta kara kunnan ta yayinda da ta shiga amsawa. Daidai gaban Frizllers Kamar ance daga kanki, nan su ka yi ido hudu da shi, Sanye cikin kanan kaya, jar riga da bakin wando, tare da 'yan mata uku sun saka shi tsakiya. Hannun shi na hagu rataye a kugun daya daga cikin su. Idanu ya kafa mata ba ko gizo tuni bugun zuciyar ta ya karu tsabagen firgici, duk yadda ta so ta dake ta kasa hannun ta sai ya ɗau rawa. Ba shiri ta katse wayar da take, ita kan ta ba ta san sanda ta juya ba, restaurant din da ta sayi abincin ta nufa ta na mai jera addu'oi yayinda kanta ke sarawa fiye da da. Shigar ta restaurant din kujera ta ja ta zauna. Ganin yadda ta zauna hannun ta rike da kan ta ya sa daya daga cikin yaran wajan ta zo ta ce da ita "Lafiya kuwa?" Ba ta kai ga amsawa ba ta ji an ce " Ina fa lafiya ta ga katon saurayin da ta mara a tsakiyar mutane.....toh laifi na ne dai har yau ban sani ba fa Mama na.... " ya karasa yana maida akalar maganar ga Amatullah. Baki bude yarinyar ke kallan Amatullah cike da mamakin furucin Dee Yusuf wanda ta ke da yakinin zolaya ce dai irin tashi, ganin yadda Amatullah ta yi tsuru-tsuru da idanu, yayinda tsoro ya ƙara bayyana fuskarta domin kuwa ba ta san ya biyo ta ba. Yanayin da ta gan Amatullah ne ya sanya yarinyar mayar da kallan ta ga Dee Yusuf, wanda kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da jin daɗin yanayin da ya jefa Amatullah ciki, domin kuwa murmushi ne kunshe a fuskar shi. Ganin abin ya fi karfin ta sai ta yi gaba abinta ta bar Amatullah da Dee Yusuf da ya sa ta gaba ba tare da ta ƙara ce da su kanzil ba. *** Wasa ta ke da ledar abincin da ke hannun ta, neman hanyar guduwa take don ba ta ƙi ta buɗe idanu ta ganta a kan gadonta ba. Gyaran murya yayi wanda hakan ya sanya ta daga ido ta kalle shi. Ta tsinci kanta ta na mai nazartar fuskar shi a karo na farko, Fari ne amma ba irin sosai din nan ba, ya na da dogan hanci har baka, yawan suman kan shi da wanda ya zagaye fuskar shi ne zai tabbatar ma ka da wadatar sumar da ke tattare da halittar shi. "Kyakkywar fuskar da na mara kenan" Furucin Amatullah a zuci kenan, kamar ya sani ya ce "Ke na ke sauraro? Me na yi da na cancanci mari? Ki fada min Mamana" Kamar an aje dutse "uhum" ba ta iya furtawa ba balle ta bashi amsa, sun kai kusan minti biyar a haka, ita dai ta sunkuyar da kai ta na wasa da ledar hannunta, shi kuma ya tsare ta ido. Tun da ya ke a rayuwar shi be taba ganin yarinyar da ta tsaya ma sa a rai ba kamar wannan da ke zaune gaban shi, ga ta dai da ka gan ta ka ga mai karancin shekaru, amma yanda ta iya duban tsabar idanun shi ta sharara masa mari babu gaira babu dalili shi ne babban abin da ya tsaya ma sa a ran shi. Wai shi Dee Yusuf mace ta mara a cikin Samaru, ba ma jama'ar wajen ba shi kan shi ya na jinjina abin, dan ma in da Allah ya taimake shi ba tare da abokan sa ya ke ba, su ma labari su ka ji daga baya da ya kade har ganyen sa, yanzun ma neman yarinyar da ta mari Dee Yusuf su ke ido rufe. Wayar shi da ta fara kara ne ya katse masa tunanin da ya ke. Ganin wanda ke kiran sa ne ya sanya shi sake duban Amatullah tare da fad'in "Wannan uzuri ne babba, amma za mu sake haduwa, lalle na cancanci a min bayanin dalilin da ya sa aka mare ni Mamanaaaa" ya ce yana mai jan kalmar karshe. Da wannan ya juya ya fita yayinda ya shiga amsa wayar ta shi. Sai bayan fitar shi da kusan minti biyar ta iya sakin ajiyar azuciya, a sannan ta lura da irin kallan da jama'ar wajan ke mata, idanun kusan kowa na wajen kanta ya ke. Da saurin ta mike tsaye, ta na mai fatan Allah Kar ya sake hada ta da wannan bawa na shi. Allah kuwa ya amshi addua'ar ta har ta kai hostel babu shi babu alamar shi. Shigar ta daki ta yi sa'a babu kowa ciki, daga wacce ta tafi karatu sai wacce ke jarabawa. Bisa gado ta kwanta, gaba daya abuncin ma ya fita kan ta, Dee Yusuf da furunci sa ke mata yawo, tsoro na shigarta a hankali, duk iya tunaninta ta kasa gano mutum ɗaya a dangin ta da zai tsaya mata in zancen zai kai ga hukuma. Tunawa da artabun da aka sha kafin Baban Sasa ya amince da karatunta kaɗai ya sanya ta cikin tashin hankali. Daɗin ƙarawa rikicin nata ba da mace ƴar uwarta ba da namiji, tilawar da ta haddace shine "babu ke babu ɗa namiji, mijinki saifullahi na dawowa daga Rasha zan ɗaura aure ku" karatu ne da duk ta je gaida baban Sasa sai ya biya mata, yanzu kuma sai a ce gata an kore ta daga jamia saboda ta yi faɗa da namiji. "Me ya kai ni fitan karatun dare" tace hawaye na zubo mata sannu a hankali, hakan ya sa yin kuka ma'ishi sannan ta fara tuna asalinta don gaba ɗaya ta sadakar koranta za ayi *** 28th September 1989 Gidan Jamoh babban gida ne a unguwar Amaru cikin birnin Zaria. Gida ne ginin ƙasa wanda ke da sassa daban daban. Sun kasance cikin kason zage-zagi da aka fi sani da mallawa, wainda tarihi ya nuna suna cikin jinsin Zazzagawa uku da ke da gadon sarautan ƙasar Zazzau watau Mallawa, Katsinawa da Barebari. Babba da yaro da ga tsatson gidan Jamoh na da kwale bibbiyu a duka gefen fuskarsu kamar kowane Bamalle. Sanyin iskar damuna ke kaɗawa ƙarfe tara na safiyar Alhamis na ashirin da takwas ga watan Satumba shekara alif ɗari tara da tamanin da tara, Hakan bai hana tsoho Jamoh zama akan kujerarsa ta azara da yake shan hantsi duk safiyar duniya yana mai sauraren radiyo a ƙasar bishiyar da ya yalwata Inuwa a tsakiyar gidan. "Baban Sasa! Baban Sasa!!" yaro ɗan kimanin shekaru takwas ya sheƙo da gudu yana faɗi. "Ja'iri! Sai kace ni ubanka ne, karar min da sunan za ka yi" tsohon ya faɗi cikin sigar wasa. Dariya Yaron yayi yana mai zama akan cinyarsa. "Innarmu ce tace in zo in faɗi maka Goggo Mairo ta sauka an samu yarinya" yace cikin murna yana yi yana wasa da gemun tsohon nan. "Madallah ka ce mun yi mata, dena ja min gemu salon ta ce kai take so ba ni ba" ya karasa yana mai ɗaga Yaron sama ba za ka ce yana da karfin ɗaukan Yaron nan ba in ka kalli furfuran da ya rufe masa fuska. Sashin ɗansa ƙarami a maza ya je don ganin abin da aka haifa, saboda ya san ƙaidar sa ce duk aka haihu da an kimtsa shine mutum na farko da yake fara gani, Hakan aka yi a haihuwa talatin da uku da yaransa maza su ka masa ciki kuwa har na yau. Addu'a yayi mata haɗe da huɗuba tare da raɗa mata suna kamar yadda yake yi a saura, in yayi ba ya faɗi ma kowa sai babban Ɗansa Zubairu. Alhaji Jamoh Bamalle ne Usul, sannan shine cikakken ma'anar maraya, don yana da shekara ɗaya da rabi mahaifiyarsa ta rasu, bai cika shekaru biyu ba Allah ya ma mahaifinsa rasuwa. Ya taso cikin gararanba a tsakar gidan babban gidansu, cikin ikon Allah lokacin da aka zo aka bukaci masarauta su ba da sunayen wainda za su je karatun boko wani kawunsa da ke aiki a fada ya bada sunansa. Hakan ya sanya yayi karatu har ya kammala makarantar Barewa College wanda a lokacin sunansa Kaduna college kafin daga baya ya zama Govt college Zaria kafin daga baya ya koma Barewa college. Tun bayan da ya kammala da shahadar grade II ya samu koyarwa a firamare bai sake komawa aji ba, da albashin sa ya auri matansa uku, da albashin sa ya raini yayansa goma sha shida inda ciki biyar ne mata saura duk maza ne, da Albashin sa ya mallaki filin nan har ya gine in da ya zama musu babban gida a yanzu a nan yaran sa duka goma sha ɗaya ke zaune da iyalinsu. Hajiya Sahura itace uwar gida, yaranta takwas, Zubairu shine babba, sai Idris, sai Hamza, sai Hadiza, Madina, Bilkisu, Yusuf sai autanta Salihu. Hajiya Talatu ce mata ta biyu a gidan ita yaranta shida duka maza, Anas, Dahiru, Yunusa, shuaibu, Mahmuda sai ƙaraminsu Muhammadu. Amarya da yaran ke kira da Goggo Kadarko tun da ta haifi yan biyu Hasana da Husaina Allah ya mata cikawa, haka hajiya Talatu ta haɗa da nata yaran ta rike. Daga Salihu sai yan biyu a tsarin shekarun yaran gidan Hakan ya sanya su ka taso su uku kamar yan uku, yana da shekara goma sha biyar su yan biyu na da sha uku aka tashi auren yan biyu, yayi kuka kamar ransa zai fita saboda shaƙuwa da ke tsakanin su, tun bayan aurensu ya maida hankali a karatun bokonsa don yana ganin shi kaɗai ne zai ɗebe masa kewa. Yayi karatu har matakin digiri a Fannin sadarwa sannan ya samu aiki da radiyo Nijeriya Kaduna kafin yayi aure. Aurensa na cikin auren da aka yi shelarsa a jihar Kaduna saboda duk maabota sauraron radiyo sun san Salihu Jamoh da shirye shiryensa masu ƙayatarwa musamman shirin jakar magori. *** Aurensa da mairo ya samar da karin arziki ta wajen sa don bayan auren ya samu ƙarin girma a wajen aiki, sannan gidan an samu yalwan arziki sannan ita kanta kullum cikin yi ma mutane ihsani take da kaɗan din da ta mallaka. Hakan ya sanya surukan son mairo fiye da sauran matan yayan. Tun ana ƙirga watannin auren har aka fara ƙirga shekaru Mairo ko ɓatan wata ba ta yi ba, nan matan yan uwa Salihu su ka sa mata karan tsana, amma duk sanda su ka jefeta da sharri sai ta maida musu da Alkhairi. Yayin da Allah ya azurta ta da cikin sai su ka fara zunɗenta suna fadin ƙaba ke damunta. Hakan bai sa ta canza musu ba ko ta neme su da sharri kullum dai Alkhairi, babu inda ta ke jin sanyi sai wajen matar Anas mai suna Hama, ita ce ta tsaya mata har ta sauka lafiya sannan ta aika ɗanta Saifullahi ya je ya isar ma kakansa Jamoh albishir ɗin haihuwa. *** Ranar suna aka sanar da sunan jaririya a Amatullah, an yanka rago an ci abinci a wadace an sha kowa yana cikin farin ciki. Rayuwar Amatullah ta kasance cikin gata, haihuwarta ta buɗe ma iyayenta samu yaya don duk bayan shekara biyu sai Goggo mairo ta haihu. Amatullah na da shekara uku ta fara bin yayyinta na gidan zuwa makarantar Allo, tun ba ta fahimta har ta fara ɗaukan karatu. Ko da ta kai shekaru shida aka sanya ta a makarantar islamiyyah kamar sauran yayyinta, gaba ɗaya rayuwarta sai ta zama daga sallan asuba za ta je Allo, ana tashin su karfe bakwai da kwata, nan za su dawo su karya sannan su tafi makarantar boko, su taso karfe ɗaya su ci abincin rana su huta ƙarfe hudu su tafi islamiyyah sai kuma shida, bayan sallan isha'i kuma su yi karatu da dare in da yayyinsu ke musu bitar karatun islamiyyah da Allo. Amatullah hazikace mai saurin fahimtar karatu sannan ba ta da mantuwa Hakan ya sanya da wuya a yi jarrabawa ba ta zo na ɗaya zuwa na uku ba. Da wannan kokarin ta kammala firamare ta shiga sakandire na boko da islamiyyah. Tana da shekara goma sha hudu aka aurar da sa'oi'inta da ke gidan bayan sun kammala hadda izu arba'in, da kyar Baba Jamoh ya amince da cigaban karatun Amatullah Shima bisa Yarjejeniyar ba ta da miji sai Saifullahi a cewar sa tun kafin ta kama nonon uwarta ya ma Saifullahi alkawarin auren Amatullah. *** Da taimakon fitar Saifullahi karatu ƙasar waje ya sanya Amatullah kammala karatun sakandire, samun kyakkyawar sakamako ya sanya mahaifinta rokon Baba Jamoh akan barinta zuwa jami'a, da kyar ya amince bisa sharaɗin ko bayan ba shi aka aura Amatullah ga wanin Saifullahi bai yafe ba. Wannan alkawarin Salihu Jamoh yayi shi a gaban dukkan yayyinsa da ita kanta Amatullah da mahaifiyarta. "Ni dai in karanta pharmacy shi ne damuwata, ko wa Baban Sasa ya so ya aura min" tace a ranta tana murnar amincewar kakanta tsoho mai ran ƙarfe mai ikon akan Ahlinsa. Bisa wannan Alkawari ta fara karatun Pharmaceutical science a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, nisa da rashin son zarya ya sanya mahaifinta tura ta hostel cike da yaƙinin za ta kama kanta kuma za ta zo da sakamako mai nagarta. Wannan kenan.[1/8, 11:26 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: *previous post da ɗan kuskure* FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA UKU A bakin gate ta iske abokan tafiyarta, nan su ka mata caa kowa da abin da yake tambayarta. "Cewa yayi yana sonki hala" shine tambayar da ya fi tsaya mata, Zulaikha dai bata ce komi ba don ta san ita ɗin mai laifi ce. "Haka kawai sai ya ce yana so na? A wajen photocopy fa muka haɗu kwanaki banda canji ya bada Naira 20 din ni shaf na manta ma" ta samu kanta da zabga ƙarya don bata son wani abu ya fito na abin da ke tsakanin ta da Dee. "Har na fara murna, don wallahi ko ni da nake matar aure ina kyasa Dee Yusuf, in fa ya ce yana sonki mu ɗin gaba ɗayanmu za mu shiga wani sawu na masu aji ne" Faɗin Zuwaira da su ke kira da maman Jaafar. Ajinsu ɗaya, a shekarun za ta girme su amma kuma ƙawarsu ce, yanzu ma kasuwar da za su shiga ita za su raka siyayya. Ba ta ce komi ba amma ita da ta san alkawarin da ke kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bane ko da a ce shi ɗin kimtsattse ne ba tambaɗaɗɗe kamar yanda ta ke kallonsa ba. Da hirar Dee Yusuf su ka isa kasuwa, ita dai jin su take yi don ba su isa kasuwa ba har sai da kawayen ta su ka hasko kalan yaran da za su haifa in aurenta da Dee Yusuf ya tabbata. Daga kasuwa gidajensu su ka wuce suna fatan Allah ya Raya su zuwa sati biyu da karatun zango na biyu zai kankama. Sai a lokacin Amatullah ta samu ta keɓe da Zulaikha saboda su biyun hanyarsu ɗaya. "In kashe ni za a yi ma kawai a kashe ko? ke babu abin da yayi tsalle ya tsinka miki mari" Amatullah ta ce tana hararar Zulaikha. "Afuwan bibty, kin san na yi tunanin in na tsaya saura ma za su tsaya kuma ba zamu iya daƙile zancen ba, me ya ce miki?" ta ƙarasa tana mai neman karin bayani akan abin da ya wakana tsakanin kawarta da dodonta. "Me kuwa zai ce min, da na gaji da tsayuwa ba tare da ya ce komi ba na yi wucewata na bar shi tsaye" Amatullah ta samu kanta da yin ƙarya a karo na biyu. 'wai me ye kike ɓoyewa ne' ta samu zuciyar ta da faɗi. 'ai sirri da daɗi' ɗayan sashi na zuciyar ta ke bada wannan amsar. "Toh Allah shiga tsakanin nagari da mugu" ta tsinkayi zulaikha da faɗin haka. "Aameen" tace tana canza labarin su zuwa ga batun jarrabawar da su ka yi a ranar. *** Sai da la'asar ta shiga gidan su, nan ta iske yan uwa da iyayensu kowa yai mata murnar kammala jarrabawa da fatan samun nasara. "Baba mun dawo, ya karfin jikinka" tace yayin da ta shiga ɗakin baban Sasa, Shima addu'a ya bi ta da shi sannan ya ce da ita "Ina so na shaida aurenku Baiwar Allah! Na ce a kira min Saifu, don ba zan so ƙasa ya rufe ido na ban cika ba, tun da har Allah ya bani tsawon ran kaiwa lokacin da duk kuka isa aure" jin sa take yi yayin da idanunta ke kallon laɓɓansa yana faɗa mata su, sai a lokacin ta ga tsantsan kamanninta da shi, sai a lokacin ta ke yarda da zancen da ake na suna kama da Saifullah don tun tana yarinya ta haddace babu mai kama da Baban Sasa sama da Saifullah. "kin yi shiru Amatu" yace yana taɓo ta. "Baaba, ashe haka nake kama da kai" tace tana dariya ƙasa ƙasa, shi ma sai ya shiga dariya. "kin ga kenan duk wanda ya shiga gidanku zai tuna da ni ya min addu'a" ya ce cikin dariya. Haka su ka dinga tsokanar juna cikin nishadi, kiran sallan magariba ne ya tayar da ita bayan ta sa masa ruwan alwala a buta. *** Yana zaune a harabar sashin su a jami'ar kimiyya na gwamnatin ƙasar Rasha da ke birnin Moscow watau MATI Russian State Technological University Moscow, tattaunawa su ke yi da abokan karatunsa akan sabuwar injimin da su ke kerawa don wani baje koli da jami'ar ke shirin aiwatarwa nan da kwana biyar, a nan wayarsa ta ɗauki ƙara. Kamar ba zai ɗauka ba amma jin kiɗan da ya tanadar ma jininsa ne ya sa shi saurin ɗauka, tsoronsa kar a ce Baban Sasa ne ya rasu, don shi ya san son da yake ma tsohon nan ko iyayen sa albarka. "excuse me" ya ce yana mai zuwa gefe tare da tattara duk wani natsuwa da ya mallaka ya doka sallama bayan ya ɗaga. "Saifuna ba zaka dawo in ganka ba" yace cikin halin ciwo. "Alkawari Baba ba zan ƙara sati biyu ba, kai dai kar ka yarda ka bi su ko sun zo ɗaukan ka" yace cikin shaƙiyanci hakan ya sanya baban Sasa tuntsirewa da dariya. Ya tambaye shi jikin sa, da sauran ahlin nan ya amsa yana mai ƙara jin jinjina masa zancen zuwansa. A haka su ka yi sallama, ya koma wajen abokan karatunsa yana mai ba su hakuri. Kwana goma ya ƙara akan ranar da su ka yi waya jirgi ya sauke shi a filin jirgin sama na murtala Muhammad da ke birnin ikko ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare. Kallo ɗaya za ka masa ka san bakin fata ne duk da rinewar da fatarsa ta yi ya rikiɗe kamar wani bakin bature. Shi ɗin ba wani dogo bane sannan babu mai kiransa gajere, zanensa na mallawa na kwance a gefen fuskarsa hakan na ɗaya daga cikin abin da ke ƙara maida fuskarsa abin kauna ga mata kamar yadda wata budurwar sa ta faɗa masa. Daga ikko jirgin da ke tashi zuwa Kaduna ƙarfe shida na safiyar washegari ya bi, daga nan ya ɗauki shatar mota har Amaru. Babu zato su ka tsinkayi muryarsa yana sallama, nan gida ya kacame da murna, duk ihun da ake Amatullah na zaune a ɗaki bata ko motsa ba cike take da fargaba da tsoro, cigaba da karatun ta tayi a cikin littafin Nurturing Eeman in children na Dr Aisha Hamdan. Wannan shine ɗabi'ar da ta fi so in ba ta komi toh ta samu littafin ƙaruwa na addini ta dinga karantawa. *** Tun da ya shigo gidan idon sa ke kan yan matan da yake gani yana kasa kunnen wacce za a kira da Amatullah, dukkansu babu na yarwa saboda wasun su na da gaɓa-gaɓan jiki wasu kuma yan firit amma duk kyawawa ne daidai misali. Bai manta hotonta da ya gani ƙarshe shekarun goma da suka wuce ba, ko a lokacin ya san ita din mai kyauce da abokansa za su yaba da ita. Bare kuma yanzu da aka ce ta shiga Jami'a, ya san zai same ta da wayewa, dan shi a rayuwar sa ya na san wayayyiyar mace. Sunaye mabambamta ya ke ji ana kira duk babu Amatullah har dai ya hakura tare da sa ran ko tana makaranta ne. Washegari Zulaikha ta kawo mata ziyara tare da duba jikin Baban Sasa, sun fito za ta raka ta ne su ka ci karo da shi a ƙofar gida. Sun gaisa cikin mutunci su ka wuce yana mamakin yanda duk in da ya gilma cikin zaria mata sanye da zumbura zumburan hijabi, su wainnan ma abin takaici har da safa ko me su ke rufewa oho 'watakila kutare ne' ya samu zuciyar sa da fadin haka. Tsaki yayi ya cigaba da abin da yake a kan wayarsa, a haka ta dawo, ta sanya kafa ɗaya kenan a cikin gidan kenan ta jiyo muryar yar gidan goggonsu ta bayanta tana fadin "A'ah su Amatullah yan boko ne a garin" Hakan ya sanya ta juyowa cikin fara'a tace "A'ah su matan aure ne a garin" nan su ka sa dariya, Hakan ya zama sarar su duk suka haɗu sai su yi amfani da kasancewarsu abokan wasanta su gasa mata magana akan rashin aure da boko. Shi ke nan da sun kira ta yar boko sai ta kira su matan aure. Gaida Saifullahi tayi ya amsa kamar ya haɗe su ya maƙure, bakin cikin da ya saukar masa ba ƙarami bane don kwata-kwata bai sa ma ransa ko a mafarki aure zai haɗa shi da bagidajiya ba. "Kai impossible!!!" ya faɗi Yana mai mikewa zuwa cikin gida don dai ya tabbatar wannan mai lullube jiki kamar raguwar kuturta ce matar da yake hasko su tare. Yaro ya gani a yana wasa a tsakar gida daidai inda yake wajen zaman baban Sasa, tuno murnar da yake ciki lokacin da ya faɗi albishir din haihuwan yarinyar da aka ƙaƙaba masa da ada murna yake amma a yau gani yake babu bakin fata sama da haka. "kai shiga ka kira min Amatullah" yace ma Yaron cikin tsawa-tsawa, a firgice Yaron yayi cikin gida yana mai kiranta. Sai da ta ɓata kusan minti talatin kafin ta fito wanda hakan yayi nasaran ƙara harzuka shi. Sanye take cikin hijabi ruwan bunsuru ko ganin atamfar da ke karkashi ba ayi, baƙar safa ce a kafafunta hannayenta duk suna cikin hijabi Hakan ya sanya babu abin da ya bayyana a gareshi face fuskarta. "Assalamu Alaikum" tace cikin sanyin murya, kallon ta yake, fuskar nan nata sai sheƙi yake yi saboda rashin hoda, amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba. "ina yini" ta ƙara duk da kunnuwanta ba su ji ya amsa sallamar da tayi ba. Nan ma bai amsa ba, sai ta basar ta tsaya abin ta. Kallonta yake tun daga kai har ƙafa yana jin wani kyankyaminta na cika shi. "Kinga, this will be the first and the last time da magana zai haɗamu, you better find your self a husband, amma ba Saif ba!, ki sani cewa akwai Tazara a tsakanin mu! Bana na san kauyanci! Ba na san gidadanci!! Kinga malam Sambo da ya kika yi allo a wajensa, shi yafi dacewa da ke not an engineer" Yana gama faɗi ya tsidda miyau ya wuce ya barta a daskare. Da kyar ta iya jan kafafun ta ta shige gida, idanun ta cike da kwallar bakin ciki, shin ita bagidajiya ce? Toh me mai ta ma sa na kauyanci da gidadanci?. Abun da ta ringa jinjinawa cikin ranta kenan. *** Tun daga ranar ba su sake haɗuwa ba, ta kiyaye haɗuwarsu ta maida hankali a karance-karancenta. Yau ma kamar kullum zaune take tana karatun "You can be the Happiest woman in the world" na Dr. Aid Al-Qarni, ta baje a falonsu, sanye take da riga da skirt dinkin zamani da ya ɗame ta, nan ta jiyo sallamarsa, bai jira amsarta ba ya kutso ciki, wani irin tsalle tayi ta jawo hijabinta da ta sarkafa a jikin ƙofa ta shiga kokuwan sawa, da ya ke hankalin sa na bisa wayar sa da ya ke ta faman dannawa nan ta ci sa'ar sanya hijabin kafin ya ankara da ita, har dan nufashi ta ke mayarwa cike da godiyar Allah. Kallon ta ya ke cike da kyama ya furta "Ina goggon" "Suna wajen baban Sasa" tace masa. Har ya juya zai fita sai kuma ya sake dawowa, idanun sa kan ta ya kira sunan ta "Amatullah!" Daga idanun ta ta yi ta dube shi ba tare da ta amsa ba, irin kallan wulakancin da ta gani a idanun sa ya sa ta yi saurin kawar da kai. Bai gushe ba, ya cigaba da magana cike da nuna isa. "Ina so ki fahimce ni, ba na son ki ba na kaunar ki, sam ba ki min ba, akwai yarinyar da na ke so....." Kamar takobi haka ta ji maganar ta shi ta soki kirjin ta. Shi kuwa ko a jikin sa ya kara da "dama biyayya ya sanya da zan yi jihadi na aure ki, toh amma sam ban yi tsammanin haka ki ke ba, ni wayayye ne, ina bukatar wayayyiyar mace cikin rayuwa ta!! Na tabbatar cikin samarin unguwar nan ba za a rasa local champion da ke son ki ba, ki rufa ma kan ki asiri ki fito da shi, na tabbatar idan su ka ga dukkannin mu da wanda mu ke so, Baban Sasa zai janye wannan alkawari na shi mai muni, kin gane ko?" Har ya kare maganan shi idanun Amatullah na kan ƴan yatsunta da ta ke wasa da su, tun da take a rayuwarta ba'a ta taba wayan gari ta na ƙin wani ko wata cikin ran ta ba, sai na wannan bawan Allah da ake shirin ɗaura ma ta aure da shi, ba don komai ba sai don kyama da ya nuna kiri kiri gare ta. "Ba da ke na ke magana ba?" Shiru ta masa kamar ma ba ta san yanayi ba wanda hakan ba karamin sosa ma sa rai yayi ba, Wai yarinya bagidajiya bakauyiya sai shegen girman kai da jin kai. A fusace ya furta " Wato ki na ji na ba za ki tankaba ko? Toh ki saurare ni da kyau! Muddin ki ka bari aka ɗaura wannan aure tsakaninmu, ki ka shigo gida na wallahi sai na lahira ya fi ki jin dadi!!! Bagidajiya sakarya kawai!!!!!!!" Ya na gama magana ya fice a fusace, nan Amatullah ta kwantar da kan ta bisa kujera yayinda kwallan da ta yi kokarin rikewa su ka shiga gasar kwarranya daga idanun ta, fadi ta ke "Inna lillaahi wa inna ilaihi rajiun, ya Allah ban iya ba, ya Allah ka iya min! Ya Allah min takangar karfe da wannan bawa na ka Agithnee Yaa mugithu!" A wannan halin Gwaggo ta same ta, cikin tashin hankalin ganin halin da Amatullah ta ke ciki ta shiga tambayar ba'asi. Duk zurfin ciki irin na Amatullah ba ta boye mata ba, ta kwashe duk yanda su ka yi da Saifullahi tun daga ranar da su ka fara magana har zuwa yau. Jikin Gwaggo yayi sanyi, ta na mai duban Amatullah wacce in banda sauke ajiyar zuciya babu abin da ta ke yi tsabagen kukan da ta sha. Cike da tausayawa ta ce " Amatullah ni na haife ki, ba zan so na cutar da ke ba, Baban Sasa mai kaunar ki ne, ba zai cutar da ke ba, ina mai baki shawara ki karfafa addu'a ga ubangijin ki, Allah zai fishe ki alkhairi. Amma ko da wasa kar ki tunkari Baban Sasa da wannan batun, shi Saifullahi da ya ke ganin an ma sa ba daidai ba shi ya je ya same shi ........." "Wallahil azim Gwaggo ba na san shi nima!!" Amatullah ta katseta cikin kuka. "Shhhhh! Kar na sake jin kin furta haka, ki dai yi addu'a, ki rufa mana asiri kar a ji wannan magana daga bangaranmu, ki bari shi can ya je ya shaida mu su, kin ji ko?" Kai ta gyada alamar "eh" "Tashi ki yo alwala ki yi sallah na san ko azahar ba ki samu kin yi ba, Allah ya yi miki albarka, kar da ki yarda maganar ta dame ki, idan ya rasa ki shi yayi rashi babba, babu kauyanci ko gidadanci tattare da ke Amatullah, sai tarbiya, kunya da yakana. Allah wadar wayewar ta shi da ya ke so. Inshallahu Allah zai shige mana gaba" Da haka ta sami kwarin gwiwar dauro alwala. Nan ta kalli gabas ta shiga kai kukan ta ga mai duka. *** Amatullah ba ta sake jin dadin gidan nan ba sai ranar Allah ya sa ta koma makaranta. Duk yanda kalaman Saifullahi su ka so tunzurata ta sami Baban Sasa ta akan rushe maganar auren su abin ya ci tura, ta yi kokarin jurewa ba dan komai ba sai dai alkawarin da daukarwa kan ta da Gwaggo, na duk kiyayyar da take ma Saifullahi ba dai a ji maganar daga bakin ta ba kamar yadda ya ke da buri, sai dai aji daga wajansa. Sati biyun da ta yi a gida har ta rame, ta rage walwala da kuzari. Kullum cikin tunani ta ke hatta lectures ma ba ta samu ta mayar da hankali ta gane a cikin aji. Tun Zulaikha na tambayar abin da ke damun ta, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido. Yanzun ma daga aji su ka fito, tun da Lecturer ya shiga har ya fita babu abin da ta gane, gaba daya hankalin ta ba ya ajin. Tunanin lafazin Saifullahi na cewar idan ta sake aka aura ma ta shi sai na lahira ya fi ta jin dadi ne ya addabi rayuwatar. "Haba mana Amatullah!!!" Zulaikha ce ta faɗa ta na me jijjaga kafadar Amatullah, wacce ta yi firgit ta dawo daga kogin tunanin da ta tsunduma. Ajiyar zuciya ta saki ta na mai duban Zulaikha ta ce "Afuwan yar uwa, me ki ke cewa?" Cikin damuwa Zulaikha ta furta "Wai me ke damun ki ne Amatullah? Yau sati guda da dawowar mu na lura gaba daya kin canza, kai wannan damuwar da ki ke ciki har tafi sanda ki ka mari Dee Yusuf....." "Dee Yusuf....." Amatullah ta maimata, ikon Allah ashe akwai damuwar da zai sa ta manta da Dee Yusuf duk tsoran sa da take ji, abun da ta fada cikin ranta kenan, ta tsinci kan ta tana kewan ganin shi, a zahiri kuma cewa ta yi "ke ni na sha'afa da lamarin wannan mutumin shaf, Allah ya amsa addu'a ta ya min katangar karfe da shi" "Idan ba Dee Yusuf ba menene damuwar ki Amatullah" Zulaikha ta sake tambaya. Kallon Zulaikha ta ke cikin nazari, kamar yanda ta ke sanye da hijabi, ita ma Zulaikha hijabin ne jikin ta, har kasa kuwa. Kai ta girgiza ta na mai fadin "I'm very fine, kar ki damu dani kawata, bari na je KIL akwai wani littafi da na ke nema, daga nan sai na bi wannan course din da mu ka yi wallahi, wallahi sam ban gane shi ba" Cikin nuna rashin gamsuwa Zulaikha ta amsa ma ta da "Ba dai za ki faɗa min abin da ke damun ki ba, ai shikenan duk sanda ki ka shirya magana ina nan Amatullah, adawo lafiya, Ni ban zuwa KIL daga dawowa ta makaranta" Dariya Amatullah ta yi jin furincin Zulaikha na ba za ta je library ba. " Dama ai na san ba zuwa za ki yi ba shi ya sa ban mi ki tayi ba, kin ga tafiya ta, sai na dawo" "Allah ya raba ki da ganin Dee... " Cewar Zulaikha cikin zolaya, juyawa Amatullah ta yi ta na murmushi, akaro na farko da ta ke jin da za ta gan shi ma ai ba wani abu ba ne, duk kauyancin ta ya na jure tsayuwa da ita, ba kamar Saifullahi ba .... Nan ta kwabi zuciyar ta daga tunanin Dee Yusuf har tana gama shi da Saifullahi. Cikin sauri kan ta a kasa ta nufi hanyar da za ta sada ta da KIL. Ta gaban library ta hangi taran samari, dan haka ko da ta zo dab da su sai ta yi kasa da idanun ta, kafafun ta har hardewa su ke tsabagen tsarguwar kar dai kallon ta su ke, musammam yanzu da ta san ita ɗin bagidajiya ce yar kauye a cewar Saifullahi. Ilai kuwa ashe tun tahowar ta ya kafa mata idanu, gaba ɗaya hankalin sa na kan ta yana mamakin yanda a duniya ya sha ganin mata ma su saka hijabi ba wai a ABU kadai ba, amma bai taɓa ganin wacce shigar ke mata kyau ba kamar Amatullah. Ta gaban su ta gifta, ya tabbatar ba ta lura da shi ba, hankali kwance ya daɗa gyara tsayuwa, cikin ran sa faɗi ya ke "Amatullah! Amatullah!! ina nan biye da ke, na yi kewan ganin ki Mama nah" [1/8, 11:26 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA HUƊU "Guys bari na ɗan shiga library kaɗan, I will catch up with you ko zuwa anjima ne, yeah?" Cewar Dee Yusuf yayinda abokan Alutan na shi su ka zuba ma sa idanu cike da mamaki, ɗaya daga cikin su ne ya ce "Dee kai fa ka takura lalle sai mun haɗu akan wannan maganar, hakan nan kuma ka ce za ka shiga library bayan ba a kashe ta ba?" "Abi o help me ask him abeg!! Me ma za ka yi a library? Kowa dai yasan ba wajan ka ba ne, rannan ma da ka shiga raban shan mari ne ya kai ka!" Hamza abokin Dee Yusuf ke magana, wanda dama cikin su shi kaɗai ne ajin su ɗaya, ɗakin baccin su ɗaya, sau da yawa mutane na musu kallon yan uwa ko aminai, tun zuwan su aji ɗaya dukkansu aka basu gurbin karanta Human anatomy a maimakon MBBS da ya ke zaɓinsu, tun a lokacin suke tare saboda su duka biyun masu nacin karatu ne da hazaƙa, kuma duk shaƙiyanci tare su ke yi hakan bai hana su samun lamba ta ɗaya (first class) a duk jarrabawar da su ke yi. . Jin batun Hamza ya sa su kwashewa da dariya, shi kuwa Dee murmushi kawai ya yi, ya na ɗan sosa ƙeya ya ce "Ina wannan course din? Amatology da na ce maka na kasa gane shi? Ka tuna shi? Shi na ke so na je na duba ASAP ko Allah ya sa a dace" Cikin ɗaukan haske Hamza ya dara, ya na mai bashi hannu su ka tafa ya furta "Oya na go kafin ka jawa kan ka spill over, ka san dai final year mu ke, kuma second semester, in dai ba ka dace ba you better change the course, ka yi add and drop kawai a wuce wajen...." "Kai karya ne wallahi Sec Gen guda da spill over!!!!!!" Daya daga cikin su ya fada cikin kuranta Dee Yusuf, shi kuwa gogan hannu biyu ya tusa cikin aljihun wandon sa. Yau ma sanye cike cikin kananan kaya, bakar riga mai karamar hannu, da shudin wando. Juyawa yayi sai da yayi taku hudu sannan ya sake juyowa fuskar sa dauke da murmushi ya ke kallan Hamza, ya ce "Baba in dai kan Amatology ne ba spill over 1 ba ko idan har spill over 2 ne sai dai na yi, ba zan yi add and drop ba, na rantse ma ka da Allah!!" Ya na gama faɗi yayi gaba, ya na jiyo ihun su wanda hakan ya tabbatar ma sa cewa Hamza ya fasa kwai, sauran abokan siyasar na su sun fahimci wannan course din da ya ke magana ba kowa ba ne face yar budurwa. *** Amatullah kuwa ko da ta shiga library, maimakon ta duba littafin da ta zo nema kamar yanda ta faɗawa Zulaikha, sai ta tsinci kanta da neman wannan wajen da ta fara haɗuwa da Dee Yusuf, nan ta samu ta zauna, cikin ran ta kuwa ta na karyata yakinin wani ɓangare na zuciyar ta na ina ma Allah ya sake haɗa ta da shi, ko babu komai duk gidadancinta shi ya nemi yayi abota da ita, duk da dai ta sha maimatawa zuciyar ta da ahir babu abota tsakanin namiji da mace. Littafin da ta ke rubuce rubuce ta dauko, daidai shafin course din da su ka gama ba da dadewa ba, wato CHEM 132 ta buɗe, da ke ita theory na ba ta wuya, gashi wannan duk structures ne gaba ɗaya sanda malamin ya ke mu su bayani hankalin ta ba ya wajen. Tagumi ta yi ta na mai karewa rubutun na ta kallo, rubutun dai ita ta yi shi, amma gaba ɗaya kan ta ya kulle sai kawai ta kifa kan ta bisa teburi idanun ta rufe, littafin bude gaban ta. Bai yi mamakin ganin ta inda zuciyar shi ke da yakinin taradda ita ba. Yanayin da ya ganta ciki ne ya sanya shi zama a kujerar da ke kallan na ta a hankali gudun kar ya tada ita, littafin na ta ya ja gaban sa. Wato yanda Allah ya ma Amatullah kyau da tsari haka ma rubutun ta ya ke. Dee ya tsinci kan sa da shafa rubutun da ɗan yatsa yayinda murmushi ya maye kyakkyawar fuskar shi mai cike da kwarjini, ba dan komai ba sai don ganin course din da Amatullah ke karantawa course ne da ya ke kwararre akai. Kamshin turaren kamfanin Tomford ya bakunci hancin ta kuma ya kasa gushewa ya sanya ta bude idanu, nan su ka yi ido huɗu. Tuni ta yi zumbur ta tashi zaune ta na mai gyara hijabin ta da ya dan kwanta mata a jiki sanadiyyar kwanciyar da ta yi kan sa. "Uhum" Yayi gyaran murya cikin zolaya sannan ya kara da "Sallama gare ki Mama nah, salamu alaikum" "Waalaikumus salam!! Ni ba Mamarka ba ce ba!!!! Sunana Amatullah!!!" Amatullah ta tsinci kan ta tana mai amsa sallamar Dee Yusuf a karo na farko a rayuwatar ta duk da a tsiwace ta amsa masa. Cike da jin dadi ya ce "Kai yau kin amsa sallama ta? Wannan farin cikin ina zan kai shi Mama nah?" Kwayar idanun ta ta kada, irin sai kuma ka ta yi. Hannu ta mi ka da niyar karɓan littafin ta daga hannun shi, ganin ya janye littafin ya ɓoye a bayan shi ya sanya ta yin karfin halin kai idanun ta cikin na shi wanda karfin idanun shi ya haifar ma ta da faduwar gaba, da sauri ta yi kasa da na ta idanun ta na mai tasbihi cikin zuciyar ta. Shiru ne ya biyo baya, ita dai ba ta kara ɗaga ido ta kalle shi ba, shi kuma ya zuba ma ta na mujiya. Jin shirun yayi yawa ya sanya ta furta "Wai me ka ke so ne? Na fada ma ka babu abota tsakanin mace da namiji....." "Amma akwai soyayya ko Mama nah?" Ya katse ta, maganar ta sa ta zo mata a bazata, ta ma kasa ba shi amsa kallan sa kawai ta ke. Hakan ya ba shi damar sake furta " Ba ki amsa min ba, akwai soyayya tsakanin Mace da Namiji?" Da kyar kamar mai rada ta furta "Akwai......" "To ki zaba ko dai ki yi abota ko soyayya...." "Ina da mijin da zan aura!" Amatullah ta tsinci kanta ta na mai bashi amsa cikin faɗa faɗa. Hannu ya daga alamar kwantar da hankalin ki, kana ya ce "Yi hakuri Mama nah ki fahimce ni, yanzu ina laifi idan ina so na kulla kyakkyawar alaka da mu'amala a tsakanin mu?" "Me zai sa ka so kulla alaka da bagidajiya yar kauye kamar ni?" Ga mamakin ta sai gashi ya murtuke fuska, cikin nuna rashin jin dadin maganar ta ya ce " Saboda me ya sa? Saboda me ya sa za ki danganta kan ki da wannan sunaye?" "Saboda haka wasu mazan su ka dauki mata ma su sanya hijabi irina, duka matan makarantar nan ba su ishe ka abota ba ko soyayya sai ni Amatullah yar kauye....." "Shhhhhhhhhh" Ya katse ta ta hanyar dora yatsan sa bisa leben sa, yana duban idanun ta wanda su ka cika da kwalla ya furta "Hijabi ko suturta jiki abu ne mai muhimmanci ga addini, abu mai daraja shi ake suturtawa, fitar da tsaraici shi ne kauyenci da gidadanci Mama nah, hijabin ki abun sha'awa ne ga duk wanda ya san darajar diya mace....." Baki ta buɗe ta na kallon shi, bai gushe ba ya cigaba "Duk Namiji da ya dauki rufe jiki a matsayin gidadanci jahili ne Mamanah, da sutura ba ta da muhimmanci da dabbobi ma za su sanya ai, sutura ita ce banbancin mutum da dabba, hijabin ki shi ne banbancin ki da sauran mata....." Ya na gama magana ya aje mata littafin ta, tashi tsaye yayi, ya na mai tusa hannun sa cikkin aljihu, ya fitar da yar takarda da biro yayi rubutu, kana ya ce " CHEM 132 is my favorite, in ki na bukatar haske kan shi ga number ta ki kira ni, na barki lafiya" Ya juya ya na wannan tafiyar tashi cike da takama, Bayan shi ta bi da kallo, mutanen da su ka san shi sai daga ma sa hannu su ke mata da maza, shi ma ya na mayar mu su, har ya fice. Kai bisa teburi ta kifa, yayinda zafafa hawayen da ba ta san na menene ba su ka shiga gangarowa daga idanun ta. Kiran sallah ya nusar da ita zaman da tayi, ba ta yi mamakin ganin gaban hijabinta a jike da hawaye ba saboda ita kanta ba ta san iya lokacin da ta ɗauka tana zubar kwalla ba. Mamaki, Farin ciki, Nadama su ne su ka cika ƙirjinta. Ba komi ya bata mamaki ba sai kalaman Dee Yusuf don su ne abu na ƙarshe da ta yi tsammanin ji daga bakinsa. Kalaman sun sanya ta farin ciki don tun bayan kalaman Saifullah ta sadakar babu namijin da ke mata kallon mace mai daraja, don har ta danganta rashin samun mashinshini da kasancewarta bagidajiya. Ta Yi Nadama ba ko kaɗan ba don ba tare da ta san waye Dee Yusuf ba ta alakanta shi da mutum mara kamun kai, tambaɗaɗɗe kawai don ya taɓa ta. 'Kuma ai yana rungume mata' wata sashi na zuciyarta ce ta nemi kare ta. Amma hakan bai hana nadama cika zuciyarta ba. Da wannan yanayi ukun ta haɗe kayanta ta kama hanyar hostel, kalaman Saifullah yayin da ya ke kiranta bagidajiya, baƙauyiya cikin murya mai cike da ƙyama su ka dinga dawo mata a kwanya yayin da take tafiya, bakinciki na gaf da mamaye mata zuciya ta jiyo muryar Dee Yusuf daga can ƙasan zuciyarta yana faɗin. 'Hijabi ko suturta jiki abu ne mai muhimmanci ga addini, abu mai daraja shi ake suturtawa, fitar da tsaraici shi ne kauyenci da gidadanci Mama nah, hijabin ki abun sha'awa ne ga duk wanda ya san darajar diya mace' Wannan ya bata ƙwarin guiwar ƙarasawa ɗaki cikin farin ciki, tasbihi take tana mai gode ma Allah da ya jefo mata Dee Yusuf cikin rayuwa. Tana shiga ɗaki ta yi wani murmushi tare da faɗin "Saifullah ba zan auri malamin Allo ba, amma za ka raina kanka in ka ga mijin bagidajiya, Mark my words, today 28th April 2009" Dariya ta yi bayan ta ankara ga kanta take magana ba wai Saifullah ba. Nan ta shiga yi ma kanta dariya tare da jin takaicin kanta. 'Ta ya ma na fara wannan tunanin?' ta tambayi kanta a zuciya tana mai jan tsaki, take sai ta sake kwashewa da dariya tana fadin "Oh! Su Amatullah, watau daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi" kan gado ta kwanta hannayen biyu ta sa ta rufe fuskar ta cike da kunya da yanayi na jin dadi yayinda ta ke yiwa kan ta dariya [1/13, 10:29 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA BIYAR Haka ta ƙarasa yininta cikin matsanancin farin ciki, wanda ya kasa ɓoyuwa ga Zulaikha da ta shigo ɗakin daga baya. "mutumiyas me muka samu ne" ta tambayeta bayan sun zauna cin abinci. Kallon ta Amatullah ta yi cikin murmushi ba tare da cewa komi ba, sai da ta cinye ɗanwaken ta, ta sha ruwa sannan ta kalli Zulaikha tace "Ɗazu kin ishe ni me ke damu na, yanzu kuma kina me muka samu, ɗazu ina cikin yanayin tuna mutuwa yanzu kuma tunawa nayi da ɗimbin rahmomin ubangiji da ya tanadar ma duk macen da ta kiyaye dokokin Allah tun daga shiga, mu'amala da ibadunta sai na ga in Allah ya yarda mun shallake" ta karanto mata yayin da zancen Dee ke mata echo a zuciya. "Ubangiji Allah ya sa mu dace, ciwon Baban Sasa ya sa ki tunawa da mutuwa, Amatullah ciwo ba mutuwa bane, sannan sau da dama jinya kan zama Rahama ga bawa. Insha Allah zai ji sauki" Zulaikha tace cikin sigar rarrashi, faɗin haka ya sanya wasu zafafan hawaye gangarowa daga idon Amatullah, ba don komi ba ambaton Baban Sasa ya sanya gaba ɗaya Amatullah ta tsinci kanta cikin yankewar kauna daga samun wani miji bayan Saifullah da ya ke kallon ta a matsayin kazanta. Hakuri Zulaikha ta cigaba da bata, tana faɗi mata kissoshi da jinyoyi su ka zama Rahama ga bawa, ciki har da kissan Annabin Allah Annabi Ayyuba Alaihis salam, wanda ciwo ya ci shi ya ci shi ya zama babu abin da yake faɗi sai RABBI INNIE MASSANIYAD-DURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEEN kuma Allah ya amsa masa ya bashi lafiya kamar ba wanda ya yi jinya ba. Kalaman Zulaikha sun yi tasiri wajen tuna mata da girman Allah, da kuma kasancewarsa maji rokon bawansa. *** Washe gari sun tashi kamar kullum, shirin zuwa ɗaukan darasi su kayi sanye da hijabansu, Amatullah ta fita cike da buri da addu'ar ɗaura ido akan Dee Yusuf, har sun shirya fita ta tuna da karin maganar hausawa na 'idan kana da kyau ka ƙara da wanka' nan ta ɗauki kwalli ta sanya ta ɗan shafa hoda kaɗan, ganin kallon da yan ɗakin ke mata ya sanya ta fadin "Fuskar ce naga duk naso, kar a ce ina shafa mangyaɗa" nan suka sanya dariya suna tsokanar ta. "Wallahi an ci amanar kyau, yanzu wai haka kike kyakkyawa amma kike sakaci" Salma Ateeku ta ce, nan su ka sa dariya. "Anty Sophie Wai haka" tace tana kallon kawar salma da suke zaune tare Safiyyah Jibril amma anty Sophie su ke ce mata. "Sosai Amatullah, kin yi kyau sosai, ga lip balm can ki sanya, you look so cute and take away" Anty Sophie tace cikin jinjinawa. Da haka suka fice zuwa aji, sun kammala na farko suna zaune zaman jiran wanda za su shiga ƙarfe goma sha biyu ne Maman Jafar ta ja su zuwa community market tana son duba ma Jafar dinta drawing book. Tafe suke suna hira kamar ko yaushe, tun daga nesa ta hango shi tare da yan mata biyu daga ganin shigarsu za ka ce arna ne ko kuma marasa kishin jikin su, ta gefen sa kuma wani namiji zaune cikin shigan English wears, zaune suke gefen Faculty of engineering irin zaman nan nane da juna, akan idonta ɗaya ta saka hannu a aljihun gaban rigarsa ta ciro kudi saboda sanye yake da kaftani da wando har ma da hula kalan sararin samaniya. Ba ta san me ya tokare mata a kirji ba, hakan ba ta san sanda hawaye su ka gangaro mata ba, hannu ta sa ta share, Jikinsa ne ya bashi ana kallonsa yana ɗaga ido sai ga ta gaban shi, sun hada idanu. Kauda da fuska tayi ta cigaba da magana duk da kirjinta bai fasa mata nauyi ba, da haka su ka isa Com market. A ɓangaren Dee Yusuf kuwa bai taɓa zaton ganinta a wannan lokacin ba duk da dai ba wai ya ɗauki ganin shi cikin course mate din shi da ta yi ba a matsayin laifi, sai dai yanda ta ga daya daga cikin su na zarar kudi daga aljihun shi ta karfi da ya ji ne da kuma yanayin da ya ga fuskar Amatullah ne bai ma sa dadi ba. Yunkurin tashi yayi don bin ta nan wayar sa ta ɗauki kuka, ganin mahaifiyarsa ce ya sanya shi ɗauka cikin ladabi. Gaisheta yayi tare da tambayar lafiyan Ahlin gidansu. " Gawar Baffanka Haruna na hanya, tun da karatun bai yi zafi ba ka kamo hanya don kar ka rasa janaza" tace cikin sigar Alhini, tunawa da mutuwar Baffan nasa yayan mahaifinsa ya sa shi sanyin jiki. "Mummy ya wajen su mimi toh, bana son na tuna mutuwar nan fa" yace cikin dauriya, mimi autan mai rasuwa ce da kowa ya shaida shaƙuwarsu. "Sun je tarbo shi, ya aka iya abin da ake jira kullum" ta fadi tana mai kara nanata masa mahimmancin zuwansa janaza. Anan yayi sallama da abokansa tare da fada masu zai wuce Kano ya kwana washegari ya wuce garin su Don halarta makoki da janaiza. Ko da su ka juyo don komawa in da za su yi darasi. Su ka iske babu Dee Yusuf a wajen, nan Amatullah ta kara cika da takaici don a lokacin ta tabbatar da cewa shi ɗin ba wai ya dauke ta yanda take tunani bane. Tun daga ranar take sa ran ganinsa tare da sa ma ranta duk suka haɗu sai ta masa tambayar dalilinsa na rashin bin dokokin ubangiji, sai ta tambaye shi me yasa ba zai dinga rungumar garwashin wuta ba akan ya dinga rungumar matan da ba muharramansa ba? Kamar ya san abin da ke ranta ya ɓace ɓat, tun tana ƙirga kwanaki har aka yi sati ɗaya ba ta ganshi ba, haka ta cigaba da zuwa ɗaukan darasi tare da yin muraji'ar darussan kar ya cunkushe mata, hakan kuma bai hana mata tunanin Dee Yusuf ba da son jin dalilin da ya sa ta dena jin sa. *** Bayan Sallar isha'i, dakin su Amatullah cike da yan kallon series wanda Zulaikha ta saba tara mu sa, tun Amatullah na kokawa ta ce ana hana ta karatu, har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Kwance ta ke bisa daddumar sallah. Ta idar da sallar isha'i kenan ta yi kwance ta na sana'ar ta ta da ta zaman mata jiki kwana kin nan, wato tunanin Dee Yusuf na dalilin bacewar sa da kuma muhawarar da zuciyar ta ke tafkawa na kiran shi dan ta ji lafiya tunda dai Allah ya sa ya rubuta ma ta numbar shi a dan littafin ta. Cikin gargadi zuciyar ta ke ayya na mata " Toh ke Amatullah ina ruwan ki da shi da har za ki addabi kan ki da tunanin shi? Har ki na tunanin kiran shi don zub da aji?" Wani bangaran zuciyar ta kuma ta ji an furta "Menene zubda aji dan ka kula me kula ka? Ai mai kaunar ka ya fi mai kin ka ko yaya ne. Ina laifi idan kin kira kin ji ko lafiya? Idan kuma wani mummnan abu ne ya same shi fa? Irin haka ne sai dai kawai ka ji an wayi gari babu mutum, mutum ya mutu....." Firgit ta yi ta tashi tsaye jin batun mutuwa, da saurin ta ta nufi jakar ta, littafin nan ta dauka tare da zare wayar ta daga jikin chaji, su Zulaikha na tambayar lafiya? Ina za ta je kuma? Amma ina nuni kawai ta yi mu su da hannu alamar tana zuwa, ta fice. Waje mara hanayi ta samu daga waje, hannu na rawa ta kwafi numbar cikin wayar ta. Sai da ta gama kwafewa tas sai kuma ta kasa danna kira. Da kyar ta sami karfin gwiwar dannawa amma kafin ya fara ringing ta yi sauri ta katse. Ta na mai dafe kirji saboda tsabagen faɗuwa da ta ji gaban ta na yi ta dan takaita kusan mintin ta biyar cikin wannan hali, sannan ta kara kiran numbar cikin ikon Allah sai gashi ya fara ringing. Jin wayar ta kusa katsewa ba tare da an daga ba ya sa ta sakin ajiyar zuciya, hakan yayi daidai da daukar wayar yayinda ta jin muryar shi ya daki dodan kunan ta ya na mai fadin "Hello?" Maimakon ta amsa, sai tsuntar kan ta tayi ta na mai runtsa idanu. "Hello? Who is that please? Wanene?" "Amatullah" Ta fada cikin rada yayinda ta ci saukar numfashin sa daga dayan bangaran na alamun ajiyar zuciya. "Amatullah....." Ya sake maimaitawa. "Kin dauki tsahon lokaci kafin ki kira ni ba, har na fara fidda rai Mama nah...." Shiru Amatullah ta kasa magana, ji ta yi kamar an daure bakin ta. Be gushe ba ya kara da "Kin ji ni shiru ko? Tafiya na yi an mana mutuwa ne na tafi jana'iza gida amma gobe zan dawo tunda kin kira ni" "Allah sarki waye ya rasu?" Ta tambaya a takaice. "Baffan mu ne" "Allah ya ma sa rahama" "Ameeen Mamanah, thank you very much for the prayer" "You're welcome" Ta kara amsa ma sa a taikace. Sai kuma ta yi shiru. Cikin zolaya ya furta " Shin akwai abun da ya kamata ki fada min" Cikin tsarguwa kardai ya dago jirgin ta na tunanin shi da ya mamaye zuciyar ta ta furta "Eeeeh? Na'am? Dama CHEM 132 na kasa ganewa....." "Are you sure shi kaɗai ne?" Ya katseta cikin zolaya. Ta na wasa da yatsun kafar ta, cikin jin kunya ta ce " Shi kaɗai ne" "Toh Mamanah Allah ya kai mu gobe da na dawo zan kira ki sai mu sami lokaci da wajen bita ko?" Maimakon ta amsa masa sai ta tsinci kanta ta na gyada kai alamar "eh" sanan ta kara da "Na gode sai da safe, Allah ya kawo ka lafiya...." "Ameeen ameen" Cewar Dee Yusuf, ta na shirin katse wayar ta ji ya furta "Amatullah" Har cikin zuciyar ta taji kiran, a hankali ta furta "Na'am" "I've missed you so much" Kasa bashi amsa ta yi, fuskar ɗauke da murmushi ta katse wayar. Hannu biyu ta sa ta rufe fuskar ta. [1/15, 11:38 PM] Khadija Sidi Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA SHIDA *** Kusan mintuna talatin ta yi nan zaune ta na ta sakar zuci, kafin daga bisani ta koma ɗakin zuciyar ta cike da farin ciki. Washegari kamar yadda ya ma ta alkawari ya na dawowa ya mata waya domin shaida mata ya dawo. Babu damar zuwa library, ɗaya daga cikin ajin su Amatullah su ka zaɓa in da su ka yi za su hadu bayan la'asar. Amatullah ta so gayyatar Zulaikha zuwa karatun amma ta nuna mata ita ba ta da bukata, babu laifi ta na gane course din. Ranar wuni tayi tana duba lokaci. Tana idar da sallar la'asar duk da marar ta na mata ciwo alamar ta kusa fara al'adar ta, hakan bai hana ta fara shiri ba. Atamfa ta sa fara Mai adon koran ganye. Dinkin ya zauna a jikin ta ya mata cicif da ke Amatullah irin matan nan ne da Allah ya ma sura mai kyau. Wata kawar Zulaikha da ta shigo dakin wacce tun da Amatullah ta sanya atamfar ta ke bin ta da kallo ta kasa daurewa ta ce "mashaAllah wannan jiki na ki Amatullah, gashi kullum ki na cikin hijabi abin ki dan kuwa da mazan makarantar nan zasu gan ki babu wannan hijabi ai da an sami matsala" Kafin Amatullah ta bata amsa Zulaikha ta ce "Da hijabin ma makaleta su ke, ba ki ga yanda Dee....." "Zulaikha!" Amatullah ta katseta cikin gargadi. Kafada Zulaikha ta daga ta sauke tare da fadin "Toh baki na kanin kafata" "Ya dai fi mi ki sauki, kun ga tafiya ta ni" Hijabin ta ta zura, ta na jiyo kawar Zulaikha na tambayar wani Dee ta ke nufi, cikin ran ta ta ce kwa dai ji da shi. Tun daga nesa ya hango ta tafe. Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin jamfa, tsaye gaban ajin da su ka yi za su hadu, jingi ne jikin bango kafafun sa harde, hannun sa biyu cikin aljihun sa. ya kura ma ta ido tamkar karo na farko da ya fara ganin ta kenan. Komai game da Amatullah birge shi ya ke. Kamannin ta, kamalar ta, tafiyar ta, muryar ta........ "Salamun'alaikum" Muryarta ce ta katse masa tunanin da ya ke, fuskarsa cike da murmushi ya furta "Wa'alaikum salam Mama nah, na yi kewar wannan muryar Mama nah" Murmusawa ta yi cike da kunya ta ce "Ka dawo lafiya? Ya hakuri kuma?" Baki bude ya ke kallon ta har sai da ta tsargu, ta ce "Lafiya me ya faru?" "Murmushi? Ni kike ma murmushi Amatullah? Ahhh my ancestors will be proud of me o!!! I've made it in life!" Dariya Amatullah ta ke sosai ta ma kasa bashi amsa. Dee Yusuf ya kara da "Alhamdulillah Mama nah, hakuri mun gode Allah. Ina san dariyar ki, dan Allah kar ki dena" Ganin dai idan ta biye shi nan za su tsaya ya ta sakin baki ta daga littafin da take dauke da shi tare da furta "Our tutorial Sir?" Ya na mai murmushi ya nuna mata hanyar shiga anjin ya na mai furta "Yes Ma'am, Lady first" Cikin jin kunya ta wuce gaba, ya na biye da ita su ka shiga ajin. Mutane kalilan su ka tadda ciki, hakan ya ba su damar yin karatun cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Dee Yusuf ya iya koyarwa kwarai da gaske tamkar dama sana'ar shi kenan. Wajan awanni biyu ya dauka ya na koyar da ita har sai da aka kira magariba ya ce da ita. "Toh Mama nah ya kamata mu tsaya anan ko? Kin ga lokacin sallah yayi" Kai ta gyada masa alamar "eh" cikin ranta kuwa cewa ta yi ka dai je ka yi sallah, ni kam Allah ya kawo min sauki yanzu yanzun nan. Har kofar hostel ya rakata, ya tsaya su yi sallama Amatullah ta ce "Kar na sa ka yi missing sallah, na gode gwarai" Yana murmushi ya ke duba agogo, kana ya ce "Ina fatan dai kin gane?" Kai gyada alamar "eh" sannan ta kara da "Sai Allah ya kai mu gobe?" "Toh Mama nah, sai anjima" Sai da ta tabbatar ya tafi sannan ta shige hostel zuciyar ta cike da annashuwa, da a ce Dee Yusuf ne Malamin su ai da ba haka ba. *** Bayan sati biyu, zaune su ke a ajin da yan Agric Education ke ɗaukan darasi a can sashin horar da malamai (Faculty of Education), Jakanta ne su ka sanya marabi tsakaninsu, bayanin Bond yake mata yadda ba a taɓa mata ba, fahimtarsa take cikin haddacewa. Kallonsa ta yi tare da fadin "me ya sa ka zaɓi anatomy maimakon chemistry? Ban taɓa ganin wanda koyar da chemistry ya ma kyau ba sama da kai" Murmushi ya bi ta da shi, sanyin muryarta na ratsa shi. "Ni kuwa menene sirrin muryar nan taki, zan so jin sa yana mai rera waƙa" yace yana basar da tambayar da ta yi masa. "Ayya mana Yusuf, maimakon ka so jin ayoyin Allah da muryar" dariya yayi cikin basarwa ya ce "Kuma fa, yauwa dama akwai abin da nake so na fada miki" ya ƙarasa cikin tattaro duk wani natsuwa na shi, nan gabanta ya shiga faɗi cikin sauri, bata shirya ma jin maganar ba duk da ya daɗe yana cewa za su yi, kullum ya ce sai ta kawo dalilin fasawa yau ba ta san me za ta ce masa ba. "Uhmm ina jin ka" tace masa, duk da ta san zancen bai wuce na tona asirin zuciyarsa wanda ƙwayar idanunsa sun daɗe da tonawa. "Amatology 10CU"aka ce daidai san da ya ɓude baki da niyyar magana. Hamza ne ya bayyana gaban su, sanye cikin riga mara hannu da wando wanda be kai har kasa ba. Amatullah ya tsurawa idanu, idan ya san da Zaman Dee Yusuf be nuna alama ba. Cikin kokarin boye rashin jin dadin ganin sa Dee ya ce " Amatullah meet Hamza, aminina" Yana mai murmushin yake, Hamza kuwa tuni ya gano rashin jin daɗin ganinsa da Dee ya yi. Zama tsayuwa yayi a kujerar da ke gabansu, kallon Amatullah yake na ƙurilla wanda har hakan ya saukar mata da rashin natsuwa. "Malam tashi mu wuce dama mun gama tutorial ɗin yau, sai mun yi waya mamanah" ya faɗi cikin ɓacin rai, yafi kowa sanin halin abokinsa Hamza, ko kara aka ɗaura ma zani in dai zai samu dama toh sai ya kwance, hakan na daga cikin dalilin da ya hana masa ganin Amatullah duk yadda ya so yi. A ɓangaren Hamza kuwa ayyanawa ransa mallakar Amatullah a shimfiɗarsa yayi ko da hakan na nufin ɓata duk wani alaka tsakanin sa da Dee Yusuf. Ba a san ransa ba, haka yana ji yana gani su ka yi sallama da ita, yau ko rakiya ba ta samu ba, nan ya bar ta, ya ja Hamza su ka fice. *** "wa ya faɗa maka inda nake?" Dee Yusuf ya samu kansa da faɗi bayan sun yi tafiyar kurame na dan wasu mintoci "Facebook" ya faɗi yana dariyar ƙeta, "Baba ashe babbar Haja ka samu shi yasa kake ɓoyeta, oboi fully loaded ina ma zan ganta without Hijab" ya ƙara faɗi yana mai kwatanta surarta da hannunsa. Baƙin ciki sosai ya cika Dee Yusuf har ya rasa abin da zai ce. Kafin daga bisani ya tsaya cak, gaban Hamza ya sha, ya na mai daura hannu bisa kafar Hamza ya ke kallan sa ido cikin ido ya furta "Hamza Amatullah mace ce mai daraja a guna, ina rokan ka arziki ka tauna harshen ka kafin ka furta lafazi dangane da ita, na yafe ma ka yanzu, Amma na rantse maka da Allah ka kuskura ka sake sai na bata ma ka!!!!!" Bai ƙara komi ba ya wuce ya barshi a nan, shi kan shi Hamza yayi mamakin Amininsa, kamar yadda Dee ya cika da mamakin kansa, wai shine da kishin mace har haka. Addu'a ya shiga yi bayan ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun simintin da ke gaban hostel ɗinsu na Danfodio. "Yaa Ubangiji kar ka sanya Amatullah juyan baya bayan na yaye mata lullubin da ke tattare da ni. *** Tun bayan da ya amsa kiran Baban Sasa yake cikin ƙunci, gaba ɗaya tunaninsa ya ɗauke akan musababbin kiran. " In ba so kake ƙasa su rufen ido ba ka dawo a ɗaura aurenku" kalaman baban Sasa su ka dawo masa kamar a lokacin ya ke faɗi masa. "Watau wannan bagidajiyar ba ta ji magana ba kenan" ya fadi ya mai jan tsuki, da aka aka kira su jirgin su zai tashi. Jiki a sanyaye ya Mike ya isa inda ake bukatar su, ba don soyayyarsa da Baban Sasa ba babu abin da zai sa ya koma Nijeriya a wannan lokacin. Duk kwanakin da ya ɗauka kafin isowa Nijeriya bai ga daɗewarsu ba illa ma sauri da ya masa, hakan ya sa da ya tsinci kansa a kofar gidan Jamoh kamar yadda ake kiran gidan ya ji gaba ɗaya ya tsani kasancewarsa ahlin gidan. An yi murna da zuwan sa, tarbo na musamman mahaifiyar Amatullah ta yi masa wanda hakan al'adar ta ne tun yana ƙarami. Sai da ya ci yayi Nak sannan ya fara ganin gari, da yake shi ba mai wasu abokai bane tun asalinsa balle yanzu da yake ganin zama cikin masu ƙaramin tunani na nufin koma baya, duk da ma'anar ƙaramin tunani a wajen Saifu daban yake da saura. *** "A sanya biki nan da sati biyu, mu ne dangin amarya mu ne dangin ango" fadin baba Zubairu kasancewarsa babba gaba ɗaya a gidan ya sanya ba wand ya ja da zancen sa. "Kai Saifullah sai ka samu lokaci ka je ka ɗauko kanwar taka don ta san halin da ake ciki" Baba Anas mahaifi ga Saifullah ya fadi. Shi dai Saifullah bakin cikin duniya ya taru ya cika masa ƙirji, bai ce komi na sannan bai iya gardama ba ya tashi ya mike. Bai jira wani ɓata lokaci ba samaru ya wuce. Amatullah na zaune tana jiran kiran Dee Yusuf inda ya kan ce da ta fito zuwa koyon karatu. Karan wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, ganin lambar a kulle ya sanya ta saurin ɗauka don a tsammaninta Dee ne bai network ya sanya haka nan. "Ki fito wajen basket ball din ku" aka ce haɗe da kashe wayar, kamannin muryar da na mahaifansu ne ya sanya ta tunanin ko daga gidan su ne. 'kila Baban Sasa ya samu cikawa' tace tana mai share hawayen da ya gangaro mata na rashin madafa. Cikin sauri ta ja hijabin ta ba tare da ta damu ta dubi kan ta a madubi ba bare ta dan gyara maikon da ke fuskar ta, ta fice fuuu don ba za ta so abin da take tunani su tabbata ba. Isar ta wajan basketball ta tsaya cak ganin wanda ke tsaye bakin mota, duk da dai baya ya bata hannun cikin aljihu bai sa ta kasa gane shi ba, ba ta san lokacin da ta fara tasbihi ta na mai neman tsari daga ubangijin ta, fad'i ta ke "Allahumma ajirni fi musibati......." [1/19, 6:44 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA BAKWAI "Salamun alaikum" Ta faɗa cikin faɗuwar gaban abin da zai biyo baya. Juyowa yayi fuska murtuke, bin ta yayi da kallo tun daga sama har kasa, irin wannan kallon na hadarin kaji. A wulakance ya amsa da "Waalaikumus salam, na baki minti goma cal ki haɗo kayanki ki fito" Iya abinda ya ce kenan ya buɗe mota ya shige. "Ki haɗo kayan ki mu tafi?" Ta daɗa nanatawa cikin ranta, shikenan ta faru ta ƙare ramamme ya zagi maye. Karfin hali ta yi ta ƙarasa jikin motar, da ya ke ya ɗaga gilashin sai ta kwankwasa a hankali. Sai da yayi minti biyar kafin ya sauke tare da faɗin "Menene kuma? Ba ki ji abin da na ce ba ne?" "Dama cewa na yi ya jikin Baban Sasa?" "Oh so ki ke na ce ya mutu ko? Toh ya nan daram da ran sa......" "Alhamdulillah" Amatullah ta furta ta na mai ajiyar zuciya ta juya ba tare da ta sake tambayar ba'asi ba. Tana zancen zuci ta isa hostel, har ta wuce shi ba ta sani ba sai ji ta yi ya kira sunan ta "Amatullah?" Juyowa ta yi ta na mai murmushin yake domin ɓoye ma sa damuwar da ta ke ciki. Sanye ya ke cikin shadda brown ɗikin yar shara, kan sa sanye da irin wannan hular ta yarbawa, ƙafafunsa cikin baƙin takalmi, hannun shi mai sanye da baƙin agogo ɗauke da leda baka. Kallo daya za ka masa ka amince da jimla daya, "Dee Yusuf namiji ne", namijin ma ɗan kwalisa, amma sam bai ɗaurawa kan sa girman kai kamar Saifullahi ba. Abin da Amatullah ke ayyanawa a ranta ke nan, a zahiri kuma cewa ta yi "Yi hakuri, wallahi ban gan ka ba ne, ka kira ni ko? A ɗaki na bar wayar" Kallo ɗaya ya mata ya gane damuwar da ke tattare da ita, haka kuma bai yi jinkirin tambayar dalili ba, ya na kokarin sanya idanun sa cikin na ta ya furta "You're not ok, me ya faru? Ba ki da lafiya ne?" Kai ta girgiza al'amar "ah ah" kafin daga bisani ta kara da "Lafiya lau na ke, dama Yaya na ne ya zo ya ce da ni ana nema na a gida, amma ina tunanin jikin kaka na ne yayi tsanani" Cike da tausayawa ya ce "Ayya Mama nah, Allah ya ba shi lafiya, Wai da na zo ne mu yi maganar nan da na ce mi ki ina son na fada mi ki, Amma babu komai sai kin dawo ma yi" Ba haka Amatullah ta so ba, duk da dai ta san maganar gizo ba ya wuce na koki, ta dade da dago jirgin sa, maganar ta sa dai ba zai wuce na soyayyar da ta ke gani a kwayar idanun sa ba kamar yanda ita ma ta ke jin sa cikin zuciyar ta, kuma ta ke mai fatan ji daga bakin sa, ba dan zuwan Saifullahi ba da ta ji. "Ko ya ki ka ce Mama nah" Dee Yusuf ne ya sake magana jin tayi shiru kamar mai tunani, cikin jin kunya ta ce "Eh sai na dawo din" Ledar hannun sa ya mika mata "Ga shi Allah ya sa za su yi mi ki, yar ajin mu na ga ta na siyarwa na mi ki sha'awar su....." Ta na mai girgiza kai ta ce "Ah ah dan Allah kar dawainiyar ta yi yawa....." Kallan da ya mata ya sa ta karbar ledar ba tare da sake masa mu su ba, ta na mai fadin "Allah ya saka da alkhairi" "Amen, toh maza je ki fito sai na raka ki ko? daga nan na gaisa da yayan ki....." "Na shiga uku" Cewar Amatullah domin kuwa ta manta da Saifullahi na jiran ta. "Wallahi na manta ya na jira na, na san yayi fushi ma, ka bari za ku gaisa wata rana, today is not a good day, na gode sosai" "Toh Mama nah, zan iya kiran ki ko?" Ta gyada kai alamar "eh" "Take care of yourself, a gaida mutan gida" "Za su ji" Tana gama fadin haka ta shige ciki da sauri dan kuwa ta san ta wuce minti goman da Saifullahi ya ba ta, yana nan ya cika yayi ɓam. Jakar ta kawai ta dauka, sai kuma ledar da Dee ya bata duk da dai har lokacin ba ta san me ledar ke dauke da shi ba. Zulaikha ba ta nan dan haka ba ta samu sun yi sallama ba, cike da fargaban wulakancin Saifullahi ta iske shi cikin mota kan sa kife bisa sitiyari. Bude motar ta yi tare da sallama, yanda ya dago kai ya kalle ta ne ys sa ta yi saurin shiga ta ja murfin motar ta rufe. Yanda ya figi motar ne kamar wanda za su tashi sama ya sanya Amatullah runtse idanu ta na mai addua'ar Allah ya kai su gida lafiya. Tafiyar kurame su ka yi babu um babu um um har su ka isa gida. Isar su kofar gida tun kafin ya kashe motar ta fara kokarin fita, ga mamakin ta sa ya sa lock ya daɗa rufe motar ya na mai faɗin "Ji mana, ban gama da ke ba" Cike da alamun tambaya ta kalli fuskar sa, shi ma ɗin kallon ta ya ke ido cikin ido, dan haka sai ta yi kasa da na ta idanun. "Ba na son ki Amatullah, ba na kaunar ki, sanadiyyar ki Baban Sasa na so ya shiga rayuwa ta, shin ke ba ki da zuciya ne? Ko kare ya cinye ne......?" Ya na maganar ne a hankali be kuma fasa kallon ta ba, haka kuma hawayen da ke fita daga idanun Amatullah bai sa ya fasa maganar da ya ke ba "Hawaye? Ni ma haka na ke hawayen zuci Amatullah......ina da wacce na ke so, wayayyiya ba bagidajiya irin ki ba......." "Dan Allah ka bude min kofa na shiga gida....." Amatullah ta katse shi, domin kuwa zuciyar ta cika ta yi dam, kiris ta ke jira ta fashe. Ya bude baki zai bata amsa ganin fitowar Baba Zubairu ya sake shawara ya cire lock din. Hakan ya ba ta damar fitowa ta na mai share hawayen fuskar ta gudun kar Baba Zubairu ya gani, amma ina ya riga ya lura da ita. Idanun shi kan ta har ta karasa gaban shi ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Yana mai duban ta ya ce "Amatullah lafiya kuwa na gan ki cikin damuwa haka har ki na hawaye?" "Laaaa ba hawaye ba ne abu ne ya fada idanuna, lafiya lau Baba komi Alhamdulillah, dama damuwar na Baban Sasa ne, da fatan jikin na sa da sauki" Ta bashi amsar ne ta na fara'ar yake. "Toh jikin Baban Sasa dai sai godiya kin san jikin tsufa. Ango an dawo? Ina fatan dai ba kai ne ka ɓatawa amaryar ta ka rai ba" Ya karasa maganar ne ya na kallan Saifullahi da ya iso gare su. Gaban Amatullah ne yayi mummnar faduwa jin an kira Saifullahi ango. Ba ta kara tsorata ba sai da ta ji amsar da Saifullahi ya bawa Baba Zubairu. "Ah ah Baba Zubairu, ina ga dai sati biyun da ku ke san sakawa ne bai mata ba" Yayi maganar ne cikin nishadi kai ba ka ce shine ke gasa mata magana duk lokacin da ya samu dama ba. Tashi ta yi da sauri gudun jin amsar da Baba Zubairu zai bayar, ta ce "Bari na shiga gida na ga su Baban Sasa" Ba ta ji ba ta gani, ba ta san amsar da su ka bata ba, haka ma ko da ta shiga gidan ma su mata maraba na yi amma ina babu wanda ta ke gani tsabagen tashin hankali. Dakin Gwoggon ta ta shige nan ta tadda ita zaune kan gado tana ta lissafin kudin kayan kitchen din da za su siyowa Amarya. Kamar daga sama ta ga Amatullah ta zube mata a gaba, hannyen ta biyu ta ruko kafar Gwoggo, kuka take ta na fad'in "Gwoggo ku rufa min asiri, ku ceto rayuwa ta wallahi Saifullahi ba ya kauna ta, ba ya so na ni ma ba na san shi kar ku aurar da ni ga makiyi na Gwoggo......." "Amatullah me zan gani? Yanzu ashe ba za ki ji magana ta ba Amatullah? Ki na tunanin za mu cutar da ke ne Amatullah?" Gwoggon ce ta ke magana cikin fada fada ganin Amatullah na neman kwance mata zani a kasuwa, ba ta gushe ba ta cigaba da fadin "Kin sani gidan nan idan aka dauke Baban Sasa da shi Mahaifan Saifu wa ke kaunar mu Amatullah? Yanzu ba za ki rufa mana asiri ba ashe? So ki ke zaman gidan nan ya gagare ni? Na ce da ke idan har Saifullahi ba ya kaunar ki, ke dai ki yi addua, amma kada ki bari matsalar ta fito daga gare mu, ashe ba za ki ji magana ta ba Amatullah? Ashe ban isa da ke ba? Yau ina ranar haihuwa?" Kai Amatullah ke girgiza mata, cikin shasshekar kuka ta saki kafar Gwaggo tare da fadin "Ki yafe min Gwaggo, zan kasance mai biyayya a gare ki, Allah ya huci zuciyar ki" Jin maganar Amatullah hankalin Gwaggo ya dan kwanta, nan ta cigaba da mata nasiha ta na mai nuna mata muhimmancin auren ta ga Saifullahi ba dan komai ba sai dan kara dankon zumunci. *** Ranar Amatullah ba ta sami kan ta ba sai bayan isha'i, shi kan shi Baban Sasa shiru yaji ta, ba ta je ta gaishe shi ba sai da ya aiko yaro yayi kiran ta. Gwaggo ce ta yi karyan ta yi bacci tun da ta dawo ta ke ciwon kai gudun kar Amatullah ta je wajan Baban Sasa da kumburarran idanu. Bayan ta idar da sallah, zaune cikin dakin ta bisa darduma, ta hangi ledar da Dee Yusuf ya ba ta sai sannan ta tuna tun fa da ta dawo aje kayan ko wayar ta ba ta sake dubawa ba, kuma ta ji karar wayar ba sau daya ba sau biyu ba, babu mamaki ma Dee din ya kira ta. Tashi ta yi ta dauko ledar tare da wayar , tsakiyar gadon tahaye yayinda ta zazzage ledar, idanun ta cike da kwallar farin ciki ganin hijabai gudu hudu sun zubo, sai kuma dan karamin Qur'ani da ta yi saurin riko shi kafin ya kai ga faduwa bisa gadon ta na mai furta "Astagafirullah" Ba ta san sanda ta rungume Qur'anin tare da hijaban ba, kamshin Dee Yusuf ke tashi daga cikin su, wani irin soyayya da ba ta taba yiwa da namiji ba ta ji ya na ratsa zuciyar ta. "Dee Yusuf" Ta ambaci sunan sa a hankali, wayan ta ne ya fara kara. Idanun ta rufe ba tare da ta duba wanda ke kira ba, tsabagen jin dadin kyautar da ya mata ta furta "Dee Yusuf, kai masoyi ne" "Da ki na da masoyi shi ne ki ka liƙe min haka kamar mayya?" Ya bata amsa a wulakance wanda hakan ya sa ta buɗe idanu tare da tashi zaune ta na kallon wayar, maimakon ta ga number Dee da ta yi zato sai ganin bakuwar number, ta sake karawa a kunnen ta domin tabbatar da Saifullahi ne ko kuwa kunnan ta ke zagi. Nan kuwa ya tabbatar mata shi din ne ta hanyar fadin "Ko ba kya ji? If really you have a local champion that you love, wanda na ta tabbatar bagidaje ne irin ki me ya hana ki fadawa su Baban Sasa? Ai kwarya ta bi kwarya......" "Dakata Malam!!!!" Amatullah ce ta katse shi a fusace domin kuwa yau ya wuce gona da iri. Cikin tsiwa da dama ita gwana ce kawai ta na raga ma sa ne ta furta "Kar ka sake danganta Dee Yusuf da bagidaje domin kuwa babu abin da za ka nuna ma sa, sai dai shi ya nuna ma ka daraja da sanin kiman dan Adam!!!" Shiru Saifullahi yayi daga alama dai maganar ta yi masa bazata. Har ta na tunanin ya katse, sai kuma ta ji ya furta "Dee Yusuf din, ki na nufin shi ki ke so Amatullah?" "Eh shi na ke so, shi na ke kauna, daidai da second daya ban taba jin son ka a rai na ba Ya Saifullahi, ya fi ka komai, mutunci, kima, daraja da kuma sanin muhimmancin ƴa mace.....biyayya ne ya sa na ke iya jurewa har na ke iya sauraran wula......" "Kar ki damu Amatullah" Yayi saurin katseta cikin muryar lallashi ya ke magana da har ita kan ta Amatullah sai da ta duba wayar cike da mamakin furucin na sa, fadi ya ke "Ni dan uwan ki ne ba zan so a cutar da ke ba, inshaAllah zan yiwa Baban Sasa bayanin ba kya sona, ba za su mi ki dole ba tun da ba kya so na" Ya na gama magana ya kashe wayar ba tare da ya bata damar sake tanka masa ba. Mamaki da tsoro ne ya kama Amatullah ganin yanda Saifullahi ya canza lokaci guda, ta na mai addua'ar Allah ya sa sauki ne ya zo mata daga Allah. Nan ta kashe wayar dan kar ma ya sake kiran ta. *** Ɓangaran Saifullahi kuwa ya na aje wayar ya saki murmushin mugunta, domin kuwa yau Allah ya bashi sa'a haƙon sa ya cimma ruwa. Takalmi ya sanya, cikin sakar zuci ya fita neman su Baffannin shi da ya tabbatar zai same su a tare a wannan lokacin bisa ga al'adar su. Zaune su ke ta wajen masallacin ƙofar gidan Jamoh, gaba ɗayansu in ka cire baba Salihu kamar yadda yaran su ke kiran su, watau mahaifin Amatullah da yanzu ya ke babban hedkwatan gidan rediyo Nijeriya da ke babban birnin tarayya. Baya shigowa zaria sai ƙarshen mako hakan ya sanya babu shi a zaman da su ka maida al'ada duk bayan sallan isha'i. Su kan yi hira da ya shafi zumunci da ma siyasa da rayuwa na yau da kullum. "Assalamu Alaikum" Saifullahi ya faɗi yana mai tsugunawa haɗe da sunkuyar da kansa kamar wanda yayi wa sarki ƙarya. "Ango ne da kansa" Baba Hamza ya faɗi cikin barkwanci wanda hakan ɗabi'arsa ce. Dariya aka yi duka, kafin aka ba shi damar faɗin bukatar da ya kawo shi. Kara sunkuyar da kai yayi sannan ya ce "Don Allah Alfarma na ke nema a wajen ku a madadin Amatullah, ko babu alkawarin aure tsakanin mu kanwata ce da zan tsaya mata ta samu cikar burinta. Har ga Allah, na so haɗin nan Naji dadinsa ko don kaunar da Goggo mairo ke min amma tun da na faɗa mata musabbabin dawowata take kuka, tare da rokona na janye tana da wanda take so, Baba Zubairu kai ne sheda ai ka ganmu sanda mu ka dawo" Ya ƙarasa domin kuwa yana da tabbacin Baba Zubairu ya kula da yanayin Amatullah ko da su ka shigo gida. "Dalla yi mana shiru sakarai, har mu zaka zo ka yi ma halin yan duniya? Tun da ka tafi ƙasar waje ka waiwayota? Yarinyar nan kowa shaida ne babu wanda ya taɓa mata sallama ta fita" mahaifinsa ne ya tareshi. "Yaushe za a mata sallama tana abar kyama" Saifullahi ya fada a ransa yana mai takaicin mahaifinsa. "A'a Anas, amma kuma duk sanda aka kira shi akanzancen auren haka ya ke tsallake kasashe ya amsa kiran ko, ita dai ce, ai tun da aka tura ta jamia nake tsoro" Fadin Baba Idris wanda ya na cikin masu adawa da karatun ya mace, su yayansa a shekaru goma sha biyu yake aurar da su ko sakandire sai dai wacce ta yi a ɗakinta. "A'a ban ƙi taka ba, amma ku duba ku ga, daidai da wasika yaron nan bai taɓa aiko mata ba, zai aiko sakwanni dubu daga Babanmu sai goggon sa mairo ke da tsaraba, ai zuciya tana tare da wanda ke kyautata mata ne. Zuwan da yayi ƙarshe sai da innarsa ta ce ba ta ga ya kira yarinyar nan ko sau ɗaya ba, ku duba fa" Baba Anas ya sake fadi yana mai jin haushin Saifullah don shi ya sani sarai wannan duk shirin sa ne, ya ari bakin Amatullah ne don ya biya bukatar sa. "Toh in haka ne ya kamata a bata damarta, a kira ta aji wanda take so in ɗan gidan mutunci ne sai mu roki Babanmu ayi abin nan cikin mutuntawa" Baba Zubairu ya faɗi, take wani dadi ya cika Saifullah, yayin da baba Anas ya ji ba dadi don ba haka ya so ba. "Na amince amma rana ɗaya za a ɗaura aurensa da Nusaiba tun da itama zaune ta ke taƙi boko kuma babu miji" Baba Anas ya faɗi yana mai mikewa, nan duk wani farin ciki da ya lullube Saifullah ya ɓace ɓat, Nusaiba dai Jikan kanwar Jamo ce aka ɗauko ta daga ƙauyen farin kasa. Tun da ta gama aji shida ta ki makaranta, kanzantar ta da muninta ya sanya babu namijin arzikin da ya taɓa tunkarar ta da sunan so. "Saifullah ka je za mu nemi Amatullah ɗin" fadin Baba Mahmuda. Nan ya tashi jiki a sanyaye, don a take ya iske ƙoshi ga shi zai yi kwanan yunwa kuma. *** Da asuba bayan ta idar da sallar asuba ta gaida mahaifiyarta sannan ta ɗauko littafin da ta riko ta fara bitar karatunta. "Amatullah wai ki zo inji baban Sasa" Nasir Dan Baba Muhammad ya leko ya faɗi, hakan ya sanya ta ajiye littafin ta, ita kanta rashin ganin Baban Sasa tun dawowar ta ya tsaya mata a rai. Dakin Gwoggon ta ta shiga domin shaida mata kiran, amma sai ganin ta tayi sanye da hijabi, ta ce "Ai har da ni kiran Amatullah, Allah dai ya sa lafiya" Tare su ka tafi, da sallamar su suka shiga dakin nan su ka tadda babanninta zaune da Shi kanshi Baban Sasa sai daga gefe Saifullah ya natsu kamar mutumin kirki. Gaban Amatullah ne ya shiga faduwa yayinda ta sami waje gefe guda ta zauna. Shi kuwa Saifu kallon nan da ya ke mata na kyama shi din ta hango a idonsa. Gaida iyayen ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta gaida shi, don munafunci har da tambayarta ya ciwon kan da fatan ya lafa. Sai ya juya ga iyayen ya ce "Ai jiya ina rabuwa da ku na shiga na iske ta cikin matsanancin ciwon kai" Mamaki ya cika Amatullah wani ciwon kai ta ke yi da yake maganar oho" Idanun ta ta kai ga fuskar Baban Sasa, ganin yanayin da ya ke babu annuri ya sa ta yi saurin sunkuyar da kai, ko shakka babu akwai abun da ya faru, tunanin da Amatullah ke yi cikin zuciyar ta kenan. "Amatullah ya mu ka yi da ke sanda za ki je Jami'a" Baban Sasa ya tambaya kai tsaye hakan ya sanya Amatullah daga kai ta kalle shi cikin jinjina tambayar. Kai ta kara sunkuyarwa kafin ta bashi amsa da "Alkawarin babu soyayya na ɗauka maka" "Yanzu me ya faru?" ya sake tambaya, nan ta yi shiru, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Satar kallon Saifullah tayi, murmushin mugunta ya sakar mata. "Ke mu ke sauraro" Baba Zubairu ne ya yi magana. Baban Sasa ya kara da "Amatullah ki fada mana gaskiya, zamu baki abin da kike so, duk so na da auren ki da Saifullah babu dole a ciki, da gaske kina da wanda kuka daidaita?" Gaban ta ne yayi mummunar faduwa, kai shiga girgizawa alamar "ah ah" musammam da ta kai idanun ta kan mahaifiyar ta, ta ga irin kallan da ta ke aika mata cike da sakon magiya. "Ki dena girgiza kai ki budi baki ki yi magana ke mu ke sauraro!" Baban Sasa ne yayi magana cikin nuna kosawa. Baki na rawa ta furta "Ban karya alkawarin da na dauka ma ka ba Baban Sasa, babu wani da mu ka sasanta da shi...." Daga Baban Sasa har su Baba Zubairu idanu su ka zubawa Saifullahi, Gwaggo kuwa sassanyar ajiyar zuciya ta saki. "Menene ma'anar haka Saifullahi? Shin da ma batun da ka same mu da shi yasasshen zance ne? Mu za ka mayar sakarkaru?" Mahaifin Saifu ne ka maganar a fusace. Shi kuwa gogan cikin rarrashi ya dubi Amatullah, budar bakin sa sai cewa yayi "Amatullah ki fada mu su gaskiya, kamar yadda na ce mi ki babu mai mi ki dole, mu duka ma su kaunar ki ne, dama na san ba za ki iya fada mu su ba dan girman alkawarin da ki ka daukarwa Baban Sasa, ni kuma ina dan uwan ki ba zan bari ki cutu ta sanadiya ta ba, hakan ya sa na yi recording wayar da mu ka yi a daren jiya...." Baki bude dan mamaki Amatullah ke duban sa, ba ta tsora ta sai da ta ga Saifullahi ya fito da wayar shi, ya shiga call recording ya kunna tuni muryar Saifullahi da Amatullah ya gwauraye dakin "Dee Yusuf din, ki na nufin shi ki ke so?" "Eh shi na ke so, shi na ke kauna, daidai da second daya ban taba jin san ka a rai na ba Ya Saifullahi, Dee Yusuf ya fi ka komai, mutunci, kima, daraja da kuma sanin muhimmancin diya mace.....biyayya shi ya sa na ke iya jurewa har na ke iya sauraran wula......" "Kar ki damu Amatullah" "Ni dan uwan ki ne ba zan so a cutar da ke ba, inshaAllah zan yiwa Baban Sasa bayanin ba kya sona, ba za su mi ki dole ba tun da ba kya sona" Ana kaiwa hakan recording ya dauke. Shiru ne ya biyo baya, Amatullah kuwa da za a tsaka jikin ta lokacin da ba za a ga jini ba tsabagen daskarewa da ta yi zaune kamar matacciya.[1/29, 1:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TAKWAS Shirun da kowa yayi ba ƙaramin ɗagawa Amatullah hankali yayi ba, musammam da ta kai kallan ta ga Gwaggo, yanayin fuskar Gwaggo ne ya sanya hawaye zuba daga idanun ta. Cikin ranta fadi ta ke "Allah ya sa za ki yafe min Gwaggo" "Uhum" Gyaran muryar Baban Sasa ne ya dawo da Amatullah cikin hayyacin ta, nan ta tsincin kan ta tana mai faɗin " Wallahi Baban Sasa na rantse da Allah ban karya alkawarin da na dauka ma ka ba..... wallahi, dama shi ne kullum ya ke cewa ba ya so na....." "Shi wa?" Baban Sasa ya tambaya a dake, yayinda ya tsare Saifullahi da idanu. "Yaya Saifullahi" Ta bashi amsa cikin kuka. "Biri yayi kama da mutum, Ni na ce mu ku wannan yaron da kuke gani zai aikata, dena kuka Amatullah, me ma zai sa ka dauki muryar ta haka ba tare da izinin ta ba? Ka mata adalci kenan? " Cewar Mahaifin Saifullahi ya na mai nuna shi da danyatsa, Saifullahi wanda be taba zatan Amatullah za ta ma sa haka ba shi ma kai ya sunkuyar cike da fargaba. "Saifullahi menene gaskiyar wannan maganar?" Cewar Baban Sasa ya na mai kallan Saifullahi, wanda ya dukar da kai cikin ladabi ya furta "Baban Sasa ni kuwa me zai sa na ki jini na? Me zai sa na ki Amatullah? Me zai sa na kasa son abin da ka ke so? Har ga Allah ina nan kan baka na na yi mu ku biyayya, shi ya sa ma na aje duk abun da na ke na taho daga uwa duniya domin cika ma ka buri, da wani ido zan kalle ka? Da wani baki zan furta kiyayya ga Amatullah gare ku?" Idan aka ɗauke Mahaifin Saifullahi da Amatullah babu wanda be gamsu da jawabin Saifullahi ba. Musammam Baban Sasa wanda har gyada kai ya ke cikin gamsuwa da jin dadi, ya furta "Na gode maka Saifullahi, yanda ka faranta min Allah ya faranta ma ka" Saifu kuwa wani dadi ne ya sake rufe shi, in da Amatullah ke fuskantar kishiyar haka musammam jin Baban Sasa ya ce "Ina Amatullah?" "Na'am Baba" "Na ji na amince ba ki karya alkawarin da ki ka ɗaukar min ba, Allah ya gani kauna ce ya sanya na so hadin auren nan tsakanin ku da ɗan uwan ki, amma yanayi ya nuna akwai dan targanda saboda haka ga umarni na gare ki......" Ya dan takaita yayinda idanun sa ke bisa bangon dakin kamar mai nazari. In banda kukan Amatullah babu abin da ke tashi cikin dakin. Kana ya nisa yayinda ya mayar da kallan sa ga Amatullah sannan ya furta "Ki shedawa ko shi wanene wanda ki ke biɗa, mun bashi sati biyu ya zo ya gabatar da kan shi a gare mu, daga randa sati biyun nan ya cika kuma babu wanda ya zo gare mu da batu na auren ki toh fa ku sheda ranar zan sanya auren Amatullah da Saifullahi wata biyu da izinin rabbil samawati......." Yayin da hantar Amatullah ta kaɗa, shi kuwa shi kuwa Saifu bakin ciki ne ya sake lullube shi, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, wannan masifa ta tsoho yaushe za ta kare ne haka! Mitar da ya ke ta yi cikin ran sa. Har Baban Sasa ya sallame su kowa yayi na shi wajan. Baba Anas Mahaifin Saifullahi ne ya kira shi daki domin yi masa nasiha akan abun da ya faru. Ita kuwa Amatullah dakin ta ta koma ta ci kukan ta ta koshi. Babban tashin hankalin ta shi ne shin ya za ta yi da fushin mahaifiyar ta da ta san ko shakka babu a kule ta ke d ita, sai kuma na tuggun da Saifullahi ya kulla mata. Tun da take a rayuwar ta ba ta taba soyayya ba, asali ma bata taba ji tana san wani da namiji cikin rayuwar ta ba face Dee Yusuf, shi kuma ba wai ya furta kalmar so a gare ta ba bare ta sa ran zai iya gabatar da kan sa cikin sati biyu domin kubucewa shiga hannun makirin namiji kamar Saifullahi. Abin da ke dan kwantar mata da hankali shi ne idan ta tuna Dee Yusuf ya na ta jaddada mata akwai maganar da ya ke so su yi, gwara ta koma makaranta idan ma son ta ya ke ya fada mata in ya so ta ce idan da gaske ya ke ya kawai ya zo ya gaida Baban Sasa, da wannan ta sami karfin gwiwar fitawo falo. Kallon da mahaifiyarta ta bi ta da shi ne tun a ɗakin baban Sasa ya kashe mata duk wani kwarin guiwa da take tunanin ta na da shi. Saifullah ya shammace ta, ba ta taɓa jin kunya irin na yau ba duk da ba wani tashin hankali bane iyayen su ka nuna duk da ransu bai so hakan ba. Tsoron keɓantuwarsu da mahaifiyarta take amma duk da haka ba ta fasa zaman jiranta ba tare da ɗauko mus'hafin da Dee ya bata ta shiga tilawa a cikin suratul Yusuf. Tana kai Ayar "WA'UFAWIDU AMRI ILALLAH.." taji wasu hawaye na zubo mata tare da jin wani irin ni'imomi na ratsa ta jini da ɓargo. Lallai Allah mai lura ne a kan bayinsa ta fassara karashen Ayar. 'Gashi ya kawo miki ɗauki cikin ruwan sanyi, ku yi aurenku da Dee hankali kwance' zuciyar ta mai kaunar tarayyarta da Dee ta fadi mata. 'Amma ya za ki yi da fushin mahaifa? Shi Dee din ma ya fada miki yana son ki ne' ɗayan zuciyarta mai fidda gaskiya ta nusar da ita, hakan ya sanya ta ji kawai babu abin da ya fi mata fiye da ta isa makaranta ta ga Dee Yusuf. Shigowar mahaifiyarta ya tsaida mata tunanin da take, bata ce da ita kanzil, amma kwatakwata babu wani rahama ko annuri a tattare da fuskarta. "Ki yi hakuri Gwaggo shi ya tunzura ni na fadi haka ban san zai yi recording ba" tace tana mai kama kafar mahaifiyarta cikin kuka. Janye kafafunta tayi, tace mata "Ai duk wanda yace shi bai haifu ba, zai yi fiye da wannan ma" ta janye jiki ta bar ɗakin. Duk yanda Amatullah ta so ta bata hakuri kafin ta tafi ya gagara saboda gaba ɗaya ba ta dawo ɗakin ba. Haka jiki a saɓule ta yi shirin komawa maranta, cikin shigar ta da ta saba wato hijab. A kofar gida ya ganta, ta tsayar da mai keke kenan domin fitar da ita titin da za ta hau Bus. "Malam jeka abin ka" ya faɗi yana kallon ɗan keke. Kallon sa take, in ba ƙarya idon ta ke mata ba farin ciki ne tsantsa a tattare da shi. "Mrs Danliti Yusuf ya dai? Zo na taimaka na rage mi ki hanya" yace yana mai buɗe mata motar, har ta yi niyyar wucewa ta hango Baba Muhammadu kuma idanunsa akansu. Murmushi ta sakar masa kana ta shiga ciki tana mai faɗaɗa murmushi ta. Suna wuce harabar gidan su ta gimtse fuska tare da fad'in "Menene amfanin hakan da ka ke yi? Menene afanin bata min suna a wajen iyayen mu? Menene amfanin mutum mai fuska biyu?" Shiru ya mata kamar ba zai amsa ba, kafin daga bisani ya ce "Kin san duk a cikin iyayenmu mata ban da sama da mahaifiyarki. Ba wai ina son bata ƙi a wajan iyayen mu ba ne, ba wai na ƙi ki bane fa. Akwai tazara a tsakanin mu, har ga Allah ke ba irin matar da na ke burin aure ba ce, you're too local for my liking, ina san wayayyiyar mace ta burgewa wanda duk wanda ya ganta zai san ta amsa sunan ta mata ga Saif." Ya fada ne ya na mai kallan ta ta wutsiyar ido, ya kara da "Kin ga wannan Danliti da ki ke so?....." "A point of correction, ba sunan shi Danliti ba Dee Yusuf sunan shi!!!" Ta katse shi cikin kuwa "Dee din menene shi?" Nan fa ɗaya dan kuwa ita kan ta ba ta sani ba, kuma ba ta damu da sani ba, ta dai fi dangata shi da Dauda, ko da yake maganar ce ba ta taba tasowa ba, amma kam yau idan ta ganshi za ta tambayi shi, da ma duk wani abu da ya shafe shi. Tunanin da take yi cikin zuciyar ta kenan. "Kin yi shiru kar ki ce min baki san cikakken sunan wanda ki ke ikirarin ki na so ba?" "Ina ruwan ka toh?" Kai ya girgiza ya ce "Babu fa, ruwa na shi ne ki lallabashi ya zo wajan Baban Sasa ko a samu a kashe maganar nan kowa ya huta, dan Allah ki taimake ni Amatullah" ya ƙarasa cikin lallashi. Bata iya ce masa komi ba, don ba ta da abin faɗa masa, bakin cikine ya tokare mata ƙirji ta ji ina ma kisa ya halalta da wuka za ta soka masa. Wa zai burge da matar da bai isa ya bada aronta ko dandanonta ga wani ba, watau shi zai yi aure ne ba don ibada ba sai don ya burge mutan duniya ko ina aka shiga a ce Saifullah Jamoh yana da haɗaɗiyar mata. Har ga Allah tsoran magana ta ke kar ya buye yana recording. Sai da ta ɓata fiye da minti bakwai kafin tace "Menene dalilin ka na kai ni makaranta? Na ce dai ba wani recording ka ke so ka yi ba?" Dariya ya saka duk da dai ba amsar da ya so ya ji daga bakin ta kenan ba. Kana ya ce "Toh ke ai godiya ya kamata ki min, gashi sanadiyyar haka an baki dama ki gabatar da Danlitin ki? Ni dai ki min wannan alfarma shi ya sa ma na kaskantar da kai zan kai ki makaranta" Ta na mai girgiza kai, kasa kasa ta furta "Assha ba ka da girma sai na jikin ka" "Me ki ka ce?" Ya tambaya cikin kokonton ko kunnan shi ke zagi. "Babu komai" Shiru ne ya biyo baya, har su ka isa makaranta babu wanda ya sake tankawa. Bayan sun isa, har ta bude mota za ta fita ya tsayar da ita ta hanyar fadin "Amatullah aure na da ke ba abu ba ne mai yiyuwa ba, ki tabbatar ki gujewa faruwar shi......." Kallan shi ta yi cikin ido wanda hakan ya sanya bugun zuciyar shi karuwa domin kuwa be taba sanin haka kwayar idanun Amatullah ke da kyau da karfi ba, a dake ta furta "Kar ka damu, ni ma ba ka daga cikin mazan da na ke buri a ruyuwa ta, kai da zabin raina kamar haske da duhu ne, inshaAllah Allah zai min katangar karfe da kai!" Ta na gama magana ta fice tare da mayar masa da murfin mota ta rufe. Yayi kusan minti biyar bai motsaba, shi kan shi ya kasa gane dalilin zaman na shi, tsiwar Amatullah ne ko kuwa idanun ta ne. Amatullah kuwa tun da ta isa dakin su ta ke gwada numbar Dee Yusuf, dan Saifullahi ya dada tunzura ta, amma ina numbar ba ta shiga. Yanayin damur da ta ke ciki ya sanya Zulaikha fadin "Amatullah na san ko na tambaye ki ba za ki fada min damuwar ki ba, zan iya cewa tun haduwar ki da Dee Yusuf ba ki kara samin nutsuwa ba....." "Eh Dee Yusuf, shi ne damuwa ta Zulaikha, tun dazu na ke kiran wayar shi ba ya shiga, sati biyu Baban Sasa ya ba ni, I need to talk to him ASAP, yana ta ce min akwai maganar da ya ke so mu yi, na san ba zai wuce na soyayyar da ya ke min ba, Ni ma Ina san shi Zulaikha, gwara mu hadu ya faɗa min ko Allah zai kawo min mafita...." Tana maganar ne kamar ta na faɗawa kan ta. Cikin rashin fahimta Zulaikha ta tashi tsaye, tana mai fad'in "Wata magana kuma? Satin biyu na me Baba Sasa ya ba ki? Me ke faruwa ne Amatullah? " Kai Amatullah ta girgiza, ta na mai sanya hijabin da ta cire tun shigowar ta dakin ta ce "Zan mi ki bayani Zulaikha, bari na je na dawo...." "Amatullah....." Zulaikha ce ta yi niyar tsayar da ita, ita kuwa Amatullah tuni ta yi hanyar fita ta na mai faɗin "Kar ki damu zan mi ki bayani anjima" Ta fice. Bakin gado Zulaikha ta samu ta zauna, cikin ranta kuwa ta na addua'ar Allah ya sa ba abunda ta ke zargi ba ne. *** Amatullah kuwa fitar da ta yi neman Dee Yusuf ta ke ruwa a jallo, duk da dai babu takamamman in da ta ke da yakinin ganin sa. Ba ta yi nisa da Queen Amina ba ta ji kamar ana bin ta a baya, ko da ta juya ta ga wanda ke biye da ita, yanayin da ta ke kallan shi ya sa shi fadin "Malama Amatullah ina ta magana ba ki ji ba, ko dai ba ki gane ni ba? Hamza? Abokin Dee?" Tuni ta faɗaɗa fara'ar ta, ta ce "Haka fa, yi hakuri ai ban ji ka ba ne, ina wuni?" "Lafiya lau Alhamdulillah, ko dan ba ki ga mutumin na ki ba ne?" Tana mai murmushi cike da jin kunya ta ce "Laa ko ɗaya, wayar shi ma ba ta shiga Allah ya sa lafiya" "Lafiya lau ya ke, ai kin san yau Thursday suna evening service ne shi ya sa, amma ina ga ai sun kusa tashi yanzu, kuma ni ma ta wajan na yi yanzu, ko za ki zo mu je?" Yayi maganar ne cikin ran sa ya fatan za ta amince domin ya sami damar hira da ita. Tsabagen idanun ta ya rufe ba ta da buri da ya wuce na ganin Dee Yusuf, sai ta amince, a na ta tunanin ba zai wuce in da su ka saba taran su na Alatu ba duk da dai ba ta gane menene service din da ya ke nufi ba. Tare su ka dauki hanya ya na ta jan ta da hira, tambayar course din ta da level din da ta ke da sauran su. Ta na bashi amsa ne a takaice, in ban da sakar zuci babu abun da ta ke. Ganin sun tsaya gaban katan Chochi da ke cikin makaranta, mutane na fitowa daga ganin alama sun tashi daga adduar yamma ne ta na mai waige waige ta ce "Ya mu ka tsaya a nan? A nan su ke service din ne?" "Eh mana, ai mostly nan su ka fi zuwa......yauwa gashi nan ma ya fito, Deee!" Hamza ya kulla ma sa kira ya na mai daga masa hannu, fitowar shi kenan, sanye cikin bakaken kaya riga da wando hatta takalmin kafar shi baki ne. Tsayawa yayi in da ya ke, ganin Amatullah da Hamza mamaki ne ya bayyana a fuskar shi, kafin daga bisani damuwa ya maye gurbin mamakin yayinda idanun sa suka sauka bisa fuskar Amatullah da ke tahowa gare shi, Hamza biye da ita. "Amatullah......." Dee Yusuf ya kira sunan ta, ta na mai kallan littafin da ke makale cikin hammatar shi ta ce "Yusuf......." "David can you please come?" Cewar wani Pastor da ya fito sanye da fararen kaya. Ga mamakin Amatullah sai ganin Dee ta yi ya juya ya na mai amsa da "Yes Pastor" Baki bude Amatullah ta ke kallon Dee Yusuf yayinda sunan da aka kira shi da shi ke ma ta ihu cikin zuciyar ta "David!!!! David!!!!David" Idanun ta kan Dee ta furta "Dama Sunan shi David?" Ta yi tambayar ne ciki ciki, amma hakan be hana Hamza ji ba wanda ya sha jinin jikin shi bayan fahimtar abin da ke faruwa, haka kuma ya kasa furta komai bare ya amsa mata tambayar da ta yi. Bayan Pastor ya sallame shi, Amatullah ta nufi in da ya ke. A hankali ta ke tafiya yayinda bugun zuciyar ta ke karuwa duk sanda ta daga kafa ta ajiye, haka shi ma Dee wanda ya tsura mata idanu har ta karaso gaban shi. "Yusuf menene addinini ka?" Ta tambaya ta na mai duban fuskar shi. "Amatullah da ma shi ne maganar da na ke so mu yi magana....." "Menene addinin ka?" Ta katse shi cikin kosawa. "Christianity, I'm a Christian" Ya fada cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Cikin sanyin jiki ta furta " Ba ka fada min ba, all this while!!! God you should have told me......!" "Ba ki taba tambaya ta ba, but I tried to, I wanted to tell you Mamanah duk dai ina tsoran kada hakan ya zame mana tazara a tsakanin mu. Ina son ki Amatullah! ina kaunar ki Mamanah, dan Allah kar addini ya zama tazara a tsakanin mu Amatullah" Ji ta ke tamkar a mafarki, yau ga Dee ya na fada mata abin da take buri ta ji daga gare shi, sai dai kash ashe akwai tazara mafi girma a tsakanin su. Hawaye ne ya shiga zuba daga idanun ta, yayinda ta fara ja da baya ta na mai girgiza kai. [1/29, 1:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TARA Ganin ya na tahowa gare ta ya sanya ta juyawa cikin sauri-sauri gudu-gudu ta ɗauki hanyar hostel, ta na jin muryar sa ya na ƙwalla mata kira. Tsaye ya ke kamar gunki har ta ƙurewa ganinsa, Hamza wanda jikinsa ya riga ya gama sanyi ne ya matso gare shi tare da faɗin "Dee I'm very sorry, na zaci ta sani ai...." Hannu ya ɗaga masa alamar yayi shiru, kafin ya sauke hannun bisa kafadar Hamza, ka na ya ce "Kar ka damu aboki, I understand" Yana faɗin haka shi ma ɗin gaba yayi yabar Hamza nan tsaye. Amatullah kuwa ba za ta iya kwatanta halin da ta ke ciki ba, gaba ɗaya ji tayi ta rasa duk wani lakka a jikinta tana mai tsanan kanta. " Christianity, I'm a Christian" kalamansa da ke yawo cikin kwakwalwarta, karin takaicinta ga mahaifiyarta na cikin matsanancin fushi da ita, ya za ta yi da iyayenta in su ka gano wanda ta ke so ɗin ba musulmi bane? "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" ta faɗi tana mai rike wani ƙarfe saboda jirin da ya ɗibe ta. Daidai lokacin Zulaikha ta taho daga famfo in da ta ɗebo ruwa, a kan idon ta Amatullah ta tashi faɗuwa da kuma wasu mata da su ka taro ta. Ita ta yi musu jagora har ɗakinsu don babu nisa da inda abin ya faru. Ruwan sanyi zulaikha ta fita ta siyo bayan ta tabbatar da ta kwanta a kan gadonta, tare da kunna mata fanka. Duk a tunanin ta Baban Sasa ne ya cika. Cike da tausayi ta miƙa mata tare da umurtanta ta shanye. Ajiyar zuciya kawai Amatullah ke yi tana zubar da kwalla mai tsananin ciwo. "Kina tunanin Allah zai taɓa ɗaura ma bawa abin da ba zai iya ɗauka bane? Ina kika kai tawakallinki? Akwai wani rai da baya jiran mutuwa ne? Balle shi Baban Sasa ai kin san ko ba ciwo sa'o'insa nawa ke Raye?" ta faɗi cikin alhini. "Zulaikha in Baban Sasa yajin abin da na aikata take bakin cikina zai kashe shi, ban san ya zanyi ba" tace cikin gunjin kuka. Rungumo ta Zulaikha tayi tana shafa bayanta, tsoron tambayar ta me ta aikata tayi don ba ta son jin abin da ba ta taɓa tsammani ba. Shirun da Amatullah ta ji ne ya sanyata faɗin "Ashe Dee Yusuf Christian ne" tace kamar tana tsoron faɗi. "Na sani ai, menene abin damuwa? Ke dai ba ya koyar da ke bane?" Zulaikha ta ce cikin basarwa kamar bata daɗe da lura da soyayyar da ke gudana tsakanin Dee da Amatullah ba, tun da Amatullah ba ta furta mata itama ba ta yi tajasusi ba. "Ba kamar yadda kike tunani bane Zulaikha" nan ta faɗi mata duk abin da ke aukuwa tun da ga alkawarin aurenta da Baban Sasa ya ɗauka ranar da ta diro duniya har zuwa ga soyayyar ta ga Dee Yusuf, da kuma sati biyun da Baban Sasa ya ba ta ta gabatar da wanda ta ke so gare su. "Zulaikha wallahi soyayya irin wacce kana hango ka da mutum a aljanna na ke ma Dee Yusuf, ashe Ahlil Kitab ne, ashe haramci akan haramci nake aikatawa, ashe babu aure a tsakanin mu" tace cikin hawaye da Dana sani. "Kin san haramcin da kika aikata ɗaya ne, kin san haramun ne ciniki a cikin ciniki sai kika baje hajar da kin san an riga an siya" tace tana share kwallan da ya gangaro mata na tausayin kawarta. "kin san jimlar da ta fi kowace jimla zama ƙarya?" Zulaikha ta tambaya a sukwane. Girgiza kai Amatullah ta yi don bakin ta ya mata nauyi, istigfari kawai take a cikin zuciyarta. "Ina sonki/ka (I love you) Kinga kalmomin sun fi komi zama ƙarya, yau zaku wayi gari Kuna cikin soyayya kamar Romeo da Juliet gobe ku kasance kamar Saddam Hussain da George Bush. Saboda haka maza gyara kuskuren ki. Kin san illar da ke cikin fushin Gwaggo akanki? Kin san mahaifiya ko yaya ranta ya so su a dalilinka kamar zubar da Baraka ne a rayuwarka, san samu ki fara neman gafarar Gwaggo duk da dai ba da niyar ki bata mata hakan ya faru ba" Kai Amatullah ta gyada cikin gasgata abun da Zulaikha ta ce. Cikin shasshekar kuka ta ce " Na shiga uku Zulaikha, ya zan yi da wannan haramtacciyar soyayyar da ke cikin zuciya ta? Ko ina ba dadi, rana zafi inuwa ƙuna....." "Ki roki Allah ya yaye mi ki, Allah ya kawo sauki cikin lamarin ki Amatullah, tashi maza ki yi sallah ki karanta qur'ani za ki sami sauki" Da wannan Amatullah ta tashi, alwala ta ɗauro nan ta dukufa gaban Allah cikin namen ɗoki *** Yanda Amatullah ke cikin baƙin ciki da alhani, ɓangaren Dee ma hakan ya ke, duk yanda ya so yayi magana da ita hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan kashe waya da Amatullah ta yi, ya sha zuwa gaban Queen Amina ya zauna ko Allah ya sa ya gan ta, amma babu ita babu mai kama da ita, haka sati guda ya shude. Amatullah kuwa tsabagen gudun haɗuwa da Dee ya sa ta koma saka nikabi da safa, ta sha wucewa ta gan shi gaban Queen Amina, ko dai ya doka tagumi, ko ya na raba idanu, kuma ta san tabbas ita ya ke nema. Amma gudun abin da zai je ya dawo ya sa ta ƙauracewa kan ta ganin shi duk da kuwa ta na kewansa, sau dayawa idan ta tuna shi har kuka ta ke. Ranar da za su tafi mid-samester break da sassafe ta haɗa na ta ya nata ta yi gida, duk da dai gidan ma wani masifan ke jiran ta, musammam idan ta tuna fushin da Gwaggo da ta ke yi da ita, da kuma Saifullahi, gashi cikin satin biyun da Baban Sasa ya bata sati daya kacal ya rage mata. Kamar kullum, yau ma ya na fitowa daga lectures Queen Amina ya nufa. Kallo ɗaya za ka ma sa ka tabbatar da rashin kwanciyar hankalin da ke tattare da shi. Yanayin zirga zirgan dalibai ya ragu sanadiyyar hutun mako ɗaya da aka tafi, amma hakan bai hana Dee samun waje ya zauna ba idanunsa kan kofar Queen Amina. Kamar kullum yau ma Amatullah shiru, hannu ya sa ya ɗauko wayarsa, ya sake kira karo na ashirin kenan a ranar, abin da ya saba ji yau ma hakan aka ce, wato "The number you dialed is switched off" Cikin damuwa ya na shirin tashi ya tafi ya hango wata ta fito daga Queen Amina, idanun shi kan ta ya na mata kallon sani har ta motso kusa da shi, sai a sannan ya gane ta, ko shakka babu ta na daya daga cikin matan da ya taba ganin Amatullah da su. Cikin sauri ya tashi ya na mai fad'in "Salamun alaikum, sannu ko Mamanah" Ganin da ita ya ke ya sa ta tsaya cikin fara'a ta amsa da "Waalaikumus salam, sannun fa" Ta amsa a takaice. "Ni kuwa kamar na san ki, na taba ganin ki da Amatullah, ke kawar ta ce ko?" "Kwarai da gaske, ashe za ka gane ni, ina wuni ya karatu?" Cewar Maman Jafa'ar wacce farin cikin Dee ya gane ta ya mamaye fuskar ta. " Lafiya lau, mun gode Allah. Ina mutuniyar ne? Ina fatan dai ba har ta wuce gida ba" Dee Yusuf ya tambaya ya na mai fatan samin hadin kai a wajen Maman Ja'afar. Maman Ja'afar kuwa wacce sam ba ta san halin da Amatullah ke ciki ba, zuciyar ta ɗaya ta ce "Ai fa tun sassafe ta wuce dan ko nima ban same ta ba, ka gwada wayar ta kuwa?" "Eh na kira a kashe, gashi kwatancan gidan na su da ta min ne ya dan kwanta min" Cewar Dee, cikin ran sa roko yake Allah ya sa Maman Ja'afar ta bashi abinda ya ke bukata. Nan ta ke Allah ya amsa ma sa, jin Maman Ja'afar na fadin "Ai fa gidan na su Amatullahi ne cikin lungu, bari in gwada sake yi ma ka kwatancen ko za ka gane......." Nan ta kwantata masa gidan tsaf, Dee Yusuf na mai godiya su ka yi sallama. Maman Ja'afar kuwa cikin jin dadin ashe dai Amatullah da Dee soyayya ta habbaka har ya na neman gidan su shi ne ba ta fada mu su ba, Allah ya hada su kuwa za ta sha tsiya, ta tafi zuciyar ta cike da farin ciki. **** Komawar Amatullah gida bai sa ta samu wani kwanciyar hankali ba. Sai da ta gaishe da Baban Sasa da su baffaninta sannan ta shige gida. Daga Baban Sasa har su Baba Zubairu babu wanda ya mata maganar auren ta, ko na wanda ake jira ta turo, wanda hakan ba karamin sauki ta samu ba. Gwaggo kuwa ba ta sake zani ba, har ila yau fushi ta ke da diyar ta ta, dan haka bayan ta gaishe ta dakin ta ta shiga ta yi gum kamar daddawar daka. Da la'asar bayan ta idar da salla ne ta yanke hukuncin fita can babban tsakar gida ita ma ayi kai kawo da ita, duk da dai ta na tsoran abun da zai je ya dawo. Sanye ta ke cikin riga da siket dinkin atamfa, atamfar kore ne da ja. Sanin yanayin gidan na su ne ya sanya ta sanya hijabi. Ta tarar da duka matan gidan zaune a tsakar gida bisa ga al'adar zamantakewar gidan, kowacce mata na hidamar gaban ta, wato kujiba kujibar daura na dare, Matar Baba Zubairu ce ke mai daka, sai kuma matar Baba Muhamadu wacce ke yin tankade. Sauran yanran kuwa tare su ke da Mahaifiyar Saifullahi wacce su ke kira Hajiya tare da Gwaggo, kowa da nashi tiren dauke da shinkafa yar hausa sun dukufa ana ta tsinta. Ganin ta budar bakin mahaifiyar Saifullahi sai cewa ta yi "Ah ah su amare ashe ana ganin ku a tsakar gida?" Sai a sanannan kowa ya lura da ita, Gwaggo kuwa takaici ne ya sa ta dauke kai, dan tabbas ta san fitowar Amatullah tsakar gidan nan babu abin da zai jawo mata sai bacin rai. "Sannun ku da aiki Hajiya" Cewar Amatullah yayinda ta sami waje kusa da daya daga cikin kanan na ta, ta na mai sa hannu cikin tsintar ba tare da ta kula da kallon da Hajiyar ta bi ta da shi ba, cikin ran ta kuwa fadi ta ce ba a banza Saifullahi ke da hali irin na sa ba, gado ba karya ba ne. Daga waje kuwa Saifullahi ne zaune bisa benci, abin duniya ne ya ishe shi, gashi dai sati ɗaya ya rage amma Amatullah shiru ta ki kawo wanda ta ke ikirarin masoyin ta ne, babban abin tashin hankalin sa bai wuce zaman Nigeria ba, Allah Allah ya ke ya hada 'yan komatsan sa ya tafi. Ya na cikin wannan zurfin tunanin sam be ji alamun mota ba, bare ma ya san da tsayuwar ta. Haka kuma jin an furta "Kai yaro ya ka nan, nan ne gidan su Amatullah?" Bai sa shi daga kai balle ya kalli wanda ke tambayar da wanda aka tambaya ba. "Eh nan ne" "Shiga ka ce ta zo ana sallama da ita" Yaro ya amsa da toh, har yayi gaba ya dawo ya na mai faɗin "In jiwa zance?" Shiru yayi kamar mai nazari, kafin daga bisani ya furta "Ka ce in ji Dee Yusuf" Karaf a kunnan Saifullahi, tuni ya ɗago ya na mai duban gefan da mai maganar ke tsaye, jingine jikin mota, irin motar nan ne masu numfashi, yaro kuwa gida ya shige a guje domin kiran Amatullah. Kallon shi ya ke cike da mamakin abin da idanunsa ke gane masa, dan kuwa bai taba tsammanin wanda ya kai daidai da rabin Dee zai kusanci bagidajiya kamar Amatullah ba. Sanye ya ke cikin farar shadda gidzna dinkin nan da ake kira tazarce. Ba wani aiki shaddar ta sha ba amma yanayin kwarjini da jiki irin na Dee Yusuf sai kayan ya karbe shi kwarai. Hular kanshi zannabukar ba karamin Kara ma sa kyau ta yi ba, haka kuma takalmi har da agogon hannun sa babu wanda be sanya gwiwar Saifullahi sanyi ba, dan kuwa in dai kwarjini, wayewa da kuma ado ne kowa ya ga Dee sai dai ya shafa Fatiha. "Wai kuma Amatullah ya zo nema?" Tambayar da ya ke yiwa kan sa kenan yayinda yaji wani abu mai kama da kishi ya tokare masa kahon ciyarsa. Amatullah kuwa kamar daga sama sai ga yaro ya shigo, da karfin sa ya furta "Wai Amatullah ta zo in ji Deee Yusuf" Gaban ta yayi mummunar faduwa, tuni ta kai kallan ta ga Gwaggo wacce ta tsaya cak ba tare da ta dauke idanu daga kan tsintar da ta ke ba, sauran ahalin gidan kuwa idanu su ka zubawa Amatullah, musammam Hajiya wacce da ma kiris ta ke jira, aikuwa sai ta sa guda "Ayyiriri ahayye!! Ashe dai sirikin na mu ne a tafe....." "Ka je ka ce ba na nan" Amatullah ce ta katse harguwar Hajiyar. In da shi kuma yaro ya sake juyawa da gudun shi. Hajiya na fadin "Toh fa, toh menene na munafuncin kin fita? Na ce dama abin da ki ke jira kenan?" Shiru Amatullah ta yi mata, in da ta ke rokan Allah ya rufa mata asiri Dee ya tafi, ko wa ya mata wannan aika aikan be kyauta mata ba. Yaro na fitowa ya dubi Dee wanda idan ya lura da Saifullahi toh sam bai nuna wata alama ba. Ya ce "Amatullah din ta ce ba nan...." Saifullahi ya tsinci kan shi ya na mai sakin numfashi, wanda hakan yayi daidai da saukar Baba Anas, kuma ya ji furacin yaro. Bayan ya sallami mai achaba, ya na duban Saifullahi ya ce "Saifullahi bako mu ka yi ne?" Ganin Mahaifin na sa Saifullahi ya taso, shi kuwa Dee karasowa yayi gaban Baba Anas har kasa ya durkusa ya gaishe shi. Hannu Baba Anas ya bashi ya na mai tada shi tsaye, idanun sa kan Saifullahi, shi kuwa Saifullahi cikin shan kamshi ya furta "Baba ni ma ganina da shi kenan, kamar Amatullah ya ce ya ke nema" Jin haka Baba Anas ya dada faɗaɗa fara'a, cikin farin ciki ya furta "Assha, bakon Amatullah shi ne za ku bar shi a waje haka? Sannu da zuwa, shiga maza ka yiwa Amatullah magana, sai kuma ka kimtsa mu su wannan falon na zaure" Jigum Saifullahi yayi cikin jinjina maganar, shi ne ma zai je ya kira Amatullah? "Ba ka ji ba ne Saifullahi ka tsaya sororo kamar soko?" Cewar Baba Anas cikin nuna kulewa da yanda Saifullahi ya yi. Ran sa idan yayi dubu ya baci haka ya wuce ciki ya na jin Baba Anas na tambayar Dee ya manya da mutan gida. Ganin Amatullah wani saban bakin ciki na ya turnuke zuciyar Saifullahi, tsayawa yayi ya na duban ta takaici ya sa ya kasa bude baki ya aiwatar da sakon da Baba Anas ya aiko shi. Hajiya ce ta ce "Ah ah Saifu yaya ka shigo ka tsaya hakan nan? Na ce dai lafiya?" Kafin ya kai ga ba ta amsa Baba Anas ya shigo, tun daga soro ya ke fad'in "Kai Saifullahi ka fada mata? Ina Amatullahi din ne? Kai ka ji shasha nan ka zo ka yi tsaye?" Ya karasa maganar ne ya na duban Saifullahi wanda ya haɗe fuska kamar wanda be taɓa fara'a ba a rayuwar shi ba. Baba Anas na duban Amatullah wacce ke raba idanu ya ce "Ke Amatullah ba a shaida mi ki kina da bako a waje ba?" Kai ta girgiza al'amar ah ah dan fargaba ta kasa magana. "Ahaf kai kuwa Saifullahi ba ka yi kyawun hali ba, in dai wannan yaro na waje shi Amatullah ke bida wallahi ya min dadi, yaro ana ganin sa an ga dan manyan mutane, ga kamala ga kwarjini wallahi har kasa ya durkusa ya gaishe ni, maza ta shi ki je Amatullah, Allah ya sanya alkhairi, ya tabbatar mana da alkhairin sa" Jin haka ya sanya Gwaggo jin sanyi cikin ranta, ashe dai dan mutunci Amatullah ta samu. Taikaici da bakin ciki ya sanya Saifullahi ji kamar kasa ta bude ya shige, nan ya kara tsanar Amatullah. Juyawa kawai yayi ya fice ya bar mu su gidan. Amatullah kuwa da kyar kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta fita, kan ta a kasa ta wuce su Gwaggo, cikin ranta addua ta ke Allah ya sa kar Baban Sasa ya ji zuwan Dee, da niyar sallamar sa ba tare da bata lokaci ba ta isa ga falon da Baba Anas yayi masa iso. Dan karamin falo ne mai dauke da setin kujerun kushin. Karamar kujera ya samu ya zauna ya na mai sakar zuci, damuwar shi Allah ya sa kar fushin da Amatullahi ke yi da shi ya karu, musammam jin yaro ya ce ta ce a sheda ma sa ba ta nan. Sallaman ta da shigar ta falon lokaci daya ne, ganin ta kamar wacce aka jefo ya sanya Dee tashi tsaye, ya na mai idanun ta da ya cika da kwalla ya ce "Amatullah......" Hannu ta daga masa tare da faɗin " Dakata malam! Ka rufa min asiri ka fita ka bar gidan nan!" "Amatullah........" "Na ce ka fita!!!!!" Amatullah ta katse shi cikin tsawa da fada. Wanda hakan ba karamin motsa zuciyar Dee yayi ba, amma maimakon ya fita, sai ya koma ya zauna abin sa. Cike da takaici yayinda hawaye ke fita daga idanun ta, daya na bin daya, ta zo gaban shi ta tsugunna, cikin murya mai karya zuciya ta fara magana " Me zai sa ka zo gidan mu bayan ka san babu aure a tsakanin mu? Me zai sa ka dada tayar min da hankali bayan tashin hankalin da na ke ciki? Ka rufa min asiri ka tafi, wallahi sati daya ya rage Baban Sasa ya saka ranar aure na da Saifullahi....." Zufa ne ya fara keto masa, hannu ya sa ya cire hular kan shi yayinda shi ma din ya sauko daga kujera, farar shaddar da ke jikin sa bai hana shi zaman dirshen a kan carpet ba. Fadi ya ke "Me ka faruwa Amatullah?" "Ka tashi ka tafi!" Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani ya furta "zan tafi, na mi ki alkawarin zan tafi, Amma sai kin saurare ni, kin kuma faɗa min abin da ke faruwa, dan Allah, dan soyayyar da ki ke yiwa Allah" Hawaye ta share, ka na ta ce "Zan faɗa ma ka, zan kuma saurare ka, amma ka sani wannan shi ne magana ta karshe da zai shiga tsakanin mu" Kai gyada mata alamar amincewa. Nan ta kwashe duka halin da ta ke ciki ta fada masa, ta kare da "Duk yanda na so kujewa auren Saifullahi dole sai na aure shi, duk yanda na so na ji furucin soyayya daga gare ka a banza, domin kuwa bakin alkalami ya bushe, tun ran gini tunran zane......." yanda ya ke zaune dirshen kasa haka ita ma ta zauna, idanun sa sun kaɗa sun yi jawur, ji ya ke ina ma Amatullah halaltacciya ce a gare, da ya janyo ta jikin sa, ya rungume ta har sa ya yaye mata gaba daya damuwar ta, wanda ya ke sila da wanda ba shi ne sila ba. A hankali ya fara magana kamar haka "Ba mu da zabi akan addinin da aka haife mu da shi Amatullah, haka mu ka tashi mu ka tsinci kan mu ciki. Kamar yadda ki ka sani sunan mahaifina Yusuf, Musulmi ne kamar ke...." 1983 "Duk wanda ke Department of Mass communication ya shaidi soyayyar da ke tsakanin Yusuf Haɗeja da Binta Sule. Duk da yana gaba da ita da shekara biyu hakan bai hana soyayyarsu tafiya yadda ya dace ba, Mahaifina asalinsa Fulanin Haɗeja ne, dogo ne fari kyayyawa mai cike da haiba. Ya fito gidan malanta, don a ƙaidar gidansu yaro baya wuce shekara goma sha ɗaya bai haddace ƙur'ani ba. Hakan ya kasance da shi. Ko da ya je ma iyayensa da zancen mahaifiyata ba su yi na'am ba kasancewar ta yar ƙasar gongola, sun ce garin su da nisa, da dadin baki ya sha kan iyayensa su ka amince amma bayan da bincikensu ya tabbatar masu da cewa mahaifiyata ma'abociyar littafi ce da soyayya ya sanya ta amsar musulunci, nan su ka tuɓure su ka ƙi. "Yusufa ka rasa matar da zaka aura sai wacce ta tuba a dalilin soyayyar ka" Baffansa Sheikhi ya faɗi cikin ɗacin rai. "Baffa ka dubi girman Allah kar ka haramta min abin Ubangiji ya halalta min" yace cikin hawaye. Kallonsa Baffan yayi na yan mintoci kafin ya ce "Sannu tatacce ɗan uwan koko, tun da ka matsa zan jagoranci komi" ya faɗi yana mai kauda kai, godiya mahaifi na ya shiga yi har sai da Baffan nasa ya ce ya tashi ya tafi. A karshen shekarar aka ɗaura auren iyaye na. Auren bai hana su kammala karatunsu ba duk da kasancewarsu ƙarkashin gandun mahaifansa. Rayuwa su ke cikin kwanciyar hankali matukar suna cikin garin Kano ne, amma da zarar sun isa Haɗeja duk wani kwanciyar hankali kan kare musu saboda kyara da mahaifiya ta ke samu daga yan uwan mahaifina, wasu kan kira ta da tubabba wasu ma kai tsaye arniya su ke kiran ta. Girkin da ake yi tare a cikin gidan aka ɗauke mata a bisa hujjar ba sa cin abincin arna. Takan zauna a ɗaki ta yi kuka, ta ji takaicin kasancewa cikin mutanen da basu darajar ɗan adam ba. Duk da cewa ta taso cikin al'ummar da akan samu bambancin addini a ahali ɗaya, ta san akwai karramawa ta musamman ga duk musulmin da ya zaɓi barin musulunci zuwa addinin Yesu kiristi duk kuwa da a can ba ta ganin ana wulakanta wainda su ka musulunta. A haka mahaifi na ya kammala jarrabawarsa ta karshe a fanin jarida tare da samun gurbin aiki a gidan rediyo Nijeriya Kaduna. Murna sosai su ka yi don a tunaninsu damar yin rayuwar farin ciki ne ya zo masu. "Wai naga se kumbure-kumbure ka ke, ni da za ka bari da kewa ma farin cikin nasaranmu yafi na kewan" tace tana jan kumatunsa, in idanunta ba su faɗi mata ƙarya ba hawaye ta gani kwance a idanunsa. "ina baƙin cikin halin da za ki shiga bayan na tafi, ki kula da kanki ki kula da ajiyar da ke tattare da ke" yace yana mai rungume ta, jikinta yayi sanyi, amma ta daure ta kara masa ƙarfin guiwa. Cikin kewan juna ya ɗauki jiki zuwa Kaduna in da zai ƙarasa duk wani abin da ake bukata don fara aiki. Ita ta raka shi har tasha in da ya shiga motar da za ta wuce da su sannan ta wuce makaranta in da za ta ɗauki darasi. Kwana uku bayan tafiyar sa tana gida tana nazarin littafanta aka yi sallama. Sai da ta yane jikinta da mayafi sannan ta fita, yayyin mijinta biyu ta iske tsaye kowanne fuskarsa turɓune. Gaida su tayi cikin sanyin jiki tana mai kaucewa daga bakin kofa don su shigo. "kulle gidan ki taho mu je" Nasiru ya faɗi a kausashe, faɗuwar gaba ta ji amma ba ta tuna komi na sharri ba. Babu wanda ya ce da ita komi har su ka isa Haɗeja, taron da ta gani a kofar gida ya sanya ta tunanin mutuwa a ka yi. "wa ye ya rasu?" ta ce a zuciyarta. Haka ta tsallake mazan waje ta shiga gida, duk da ta na ganin yadda ake bin ta da kallo. Dakin mahaifiyar babana ta isa, nan ta iske mutane zazzaune, gaida su tayi amma babu wanda ya amsa mata hakan bai hana mata zama ba, tana zaune wasu mata su ka shigo, "Yusufa kuma sa'i yayi, Ubangiji Allah ya rahama masa" su ka ce suna masu tashi bayan sun ƙarasa musu ta'aziyya. 'Yusufa kuma sa'i yayi' ta kara maimaitawa, tana mai fassara kowane kalma. 'sa'i na nufin lokaci wani lokaci ake ma ta'aziyya?' ta ce a ranta tana ƙaryata tunanin da ke yawo mata a kwakwalwa. Tashi ta yi a firgice ta yi waje dakin sheikhi ta isa idanunta a rufe, bata damu da maluman da aka yi ma masauki a ciki ba ta isa gareshi tana kuka "Baffa na ji ana Yusufa sa'i yayi? Me ya same shi? Don Allah ka faɗa min" tace cikin kuka da tashin hankali. "Dama tun kwanaki ukun nan ba a ɗauko ki ba?" ya tambaya cikin ɓacin rai. "Yau su Nasiru su ka zo bamu dade da isowa ba" tace tana share hawaye. "Binta ki yi hakuri, duk mai rai jiran lokaci yake yi. Yusuf ko kura ba su kai ba motar su ta hantsala. Yau kwanan sa uku a kushewa, sai kiyi hakuri" ya faɗi yana mai jin sabon radadin mutuwar. Bude baki yayi da niyyar cigaba da mata nasiha ya ga ta sulale ta suma. Kwana bakwai tayi tana jinya nan ma babu wanda ya kula da ita duk a dalilin tubabba ce musuluncinta bai cika ba. Bayan an sallame ta babu wanda ya mata bayanin takaba, sai ma juya mata baya da kowa yayi. Babu mai bata abinci, balle a san halin da ta ke ciki. Ranar da mahaifina ya cika kwanaki arba'in da rasuwa ta musu sallama ta koma makaranta, abin mamaki sai ta iske su Nasiru a ƙofar gida, ba su ce mata komi ba su ka kwashe komi na gidan da sunan gadon mahaifi na ne, ita kuma tun da tubabba ce ba ta da gadonsa. Tayi kuka sosai kamar ranta zai fita don hatta katifar kwanciyar su sai da suka ɗauka, cikin wannan yanayi ta shiga makaranta ko za ta samu kawar da za ta laɓata a hostel. "Binta Yusuf" ta ji an kira ta, share kwallan da ya zubo mata tayi ta juyo. "pastor Abu kai ne da kanka" tace cikin murmushi. Ba za ta mance karamcinsa ba don duk da kasancewarsa pastor ya goyi bayan aurenta da Yusuf sai dai shi bai so ta bar addininta ba. "Ina kika bar Yusuf" yace bayan sun gaisa, ba ta iya ɓoye hawayenta ba, ta ce masa "yau kwanan sa arba'in karkashin kasa" sai ta saki kuka, ganin suna kan hanya ne ya ja ta gefe. "kwana arba'in Binta kuma kike nan? Ba kin musulunta ba? Kin manta 4 month 10 days su ke yi? Gidan ku fa da musulmi. Tsaya su dangin sa ya su ka bari kika fito" yace cikin ɗacin rai. "sun ce basu yarda da musulunci na ba, sun ce ni tubabba ce, sun kira ni arniya" ta fadi cikin kuka, nan ta shiga fadin halin da ta ke ciki, shi kuma bai yi ƙasa a guiwa ba ya kaita gidansa. Daki ɗaya suka ware mata, nan take duk wani ibada nata, in ba wani kwakkwaran dalili ba, bara shiga makaranta. Mutane na ta shigowa mata ta'aziyya yayin da mabiya addinin kirista ke bata duk wani kulawa. Bayan ta rubuta jarrabawa ta je garinsu Hong na jihar Adamawa. Sai a lokacin iyayen ta su ka ji zancen rasuwar Yusuf, sun yi alhini kuma sun ji haushin halin da yar su ta shiga. Cikin ta na da wata tara ta haihu, lokacin ta hakura da musulunci ta koma addininta na gado, addinin da ke karrama duk wanda ya shige ta, addinin da ta ga basa nuna yatsa ga wasunsu. Washegarin haihuwarta yayan ta, Baffa na Haruna ya tashi tun daga hong har Haɗeja ya sanar masu da haihuwa, nan su ka ce da shi sun bar musu don basu da bukatar jinin arna. Yana dawowa ya sanya min suna David. Bayan shekara guda ta sake aure, mijin ta shi yayi min komai, dangin mijin ta su suka zame min dagin uba, su na sani Amatullahi......." Nisawa yayi yayinda ya ke kallan furkar Amatullah, be gushe ba ya cigaba "Amatullah, na taso a matsayin Margi ba bahaɗeje ba, duk wani gata da yaro zai samu na samu daga mijin mahaifiya ta da Baffani na. Na taso cikin al'umma da zaki iya iske mata musulma miji kirista ko mata kirista miji musulmi...." Kan gwiwowin sa biyu ya tsaya yayinda hawaye ke zuba daga idanun sa, ya ce "Sanadiyyar abin da ya sami mahaifiya ta, Ni da ke Amatullah kowannan mu za mu iya yin addinin mu, Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki, ki dubi girman Allah ki amince da aurena, in ma so kike na je Haɗeja dangin mahaifi na su zo neman aurena wallahi na amince. Kiyi min rai Amatullah, ki amince da son da nake maki....." [1/29, 1:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA Kamar saukar aradu haka maganar Dee ya sauka kunnen Hajiya, wacce ta yi ƙaryan zagawa bayi amma ta ɓige da zuwa soro domin ganin wannan saurayi da Baba Anas ke ta zuokarin ɓoye fuskarta cikin hijabi gudun kar a gane halin da ta ke ciki ta dada shiga cikin tashin hankali, dama fitowarta kenan ganin tunanin da ta ke yi a ɗaki zai iya tarwatsa zuciyarta fara maganar Hajiya ya sa ta ji ina ma bata fito ba. "Amarsu ki je Baba na kira" ta ce tana kallon Amatullah wacce ke tsure kamar wacce ta yi wa sarki ƙarya. Haka ta tashi sumsum ta wuce hawaye na rigarigen saukowa kuncinta. Tana juya baya Hajiya ta shiga bada labarin abin da ta jiyo, nan yan gidan aka shiga tsine ma boko da abin da ke ciki acewarsu bokon da ta zurfafa ne ya sa ta kula bamaguje a matsayin masoyi. Goggo Mairo ta rasa in da za ta sa kanta yadda ta ga hajiya da ta kawo labarin ko wurin ba ta bari ba amma an fara canza labari da ƙara masa gishiri da Magi. *** Da Sallama Amatullah ta shiga ɗakin, hawayen da ke zubo mata bai fasa zubowa ba tashin hankalinta ya ƙaru ganin mahaifinta zaune a wajen. "Baba gani" tace bayan ta bi su ɗaya-ɗaya tana gaida su. "Yauwa! Amaryas, ko da yake an ce wannan da zai min kwace ya zo ko" ya faɗi cikin sigar tsokana. Girgiza kai ta shiga yi tana so ta yi magana amma halshenta ya mata nauyi. "Baban Sasa wallahi ban karya alkawarin mu ba, zaɓinka shine zaɓina" ta kokarta ta fadi nan ta saki sabon kuka a wajen, wanda ya taɓa zukatan baban Sasa da baba Anas kaɗai. Mahaifinta da ke wajen ji yayi kamar ya mauje ta yanda take kuka. Su baba zubairu kuwa da su ka shigo bayan fitan Hajiya ma duk takaici ta basu. "Toh shi wancan da ya zo wanene shi?" Baban Sasa ya tambaya a dake. Baya son tausayin ta ya ci galaba akansa. "Dee Yusuf ne" ta ce a can kasan muryarta. "Ba shi ne Saifullahi ke magana ba" cewar Baba zubairu a harzuke. Shiru tayi ta kara sinne kanta. "Wanene shi Dee Yusuf din? Me nene ma'ana Dee ɗin" Mahaifinta ya tambaya cike da addu'ar amsar ta ya karyata Hajiya Sadiya. Don duk yadda ya so ya duba bai hango dalilin da zai sa yarsa mai ilimin addini da kokarin kiyaye dokokin Allah ce da soyayya da wanda ba musulmi ba. "Sec Gen din SRC ne, shi ke mana tutorials din chemistry, past question papers ya kawo min" ta samu kanta da fadi, amma sanin da su ka yi ita ba mai karya bace take su ka ɗago ta. "Dauda yake ko Dahiru" Baba Mahmuda ya faɗi ganin ta kife su akan asalin sunansa. "David Yusuf" ta fadi a hankali. Take ɗakin ya kaure da salati, baba hamza ya taso zai kai mata hannu take Baba Anas ya tare shi. "Fisabilillahi karya kuke so ta muku? Bata ɓoye alakar su ba, koyar da su karatu yake, sannan ina ce Saifullahi ya fara kawo zancen Dee din sannan innarsa ce ta fara kawo zancen shi din ba musulmi bane. Haba ku duba mana" Baba Anas ya ce yana kare ta, sauran in banda masifa babu abin da su ke tare da aibata ta. "Babanmu ka duba lamarin nan da kyau, tun kafin a haifi Amatu babu macen da ke daraja ku kamar Mairo, tun da ka ba da ita ga Saifullah ba a taɓa ganin ta da waninsa ba duk da ba a ganta da shi ɗin ba. Duk zamanta a jami'a bincike na ya tabbatar min ba ta fita zancen da wasu ɗalibai ke yi, Babanmu Amatullah ba ta saɓa alkawarin ku ba, kar ka yi mata hukunci akan laifin da ba ta aikata ba" yace yana mai gurfanawa gaban Baban Sasa, hakan ya kara tsinka zuciyar Amatullah tare da ganin rashin kamatan abin da zuciyarta ta aikata na son Dee. "Kai Anas in an yi magana ka dinga kare Mairo da iyalinta kenan, ni ban san me su ka baka ka sha ba, Salihu ka yi magana mana ka yi shiru kana kallon mu" Baba Idris ya faɗi a harzuke. "ni kuwa mai zan ce bayan ku ne iyayenta" Baba Salihu ya ce yana mai mikewa da barin falon. Nan su ka haɗu su na ta masifa tare da aibata karatun ƴa mace da nuna laifin Baba Salihu da ya gagara nuna fushinsa akan abin da yarsa ta aikata. "Baba ba ka ce komi ba" Baba Anas ya ce da Baban Sasa yana mai sunkuyar da kansa. "Amatullah kin ce Alkawarin mu na nan ko" yace yana mai kallon ta cikin tausayawa, kuka take bilhaqqi kamar ranta zai fita. "Ehhhh!" tace tana mai jan majina. "Anas ka amince da bamu ƴarka a matsayin mata" Baban Sasa ya sake fadi yana mai kallon Baba Anas, hakan ya dawo da hankalin sauran da ke falon garesu. "Baba Zaɓinka shine namu ko ƴar Albarka" yace yana kallon Amatullah. Gyaɗa kanta sama tayi, tana mai share hawaye. "Toh ku kawo kawo sadakin Dan ku, gobe bayan sallahn Asuba za'a ɗaura aure, sati mai zuwa kamar yadda nayi alkawari zan sanya ranar tariya a maimakon ranar aure" Baban Sasa yace yana kallon sashin da su Baba Zubairu ke zaune. Da haka ya sallame Amatullah. Cikin sanyin jiki ta ƙarasa ɗakin su, a falo ta zauna amma tana jiyo muryar mahaifinta da goggonta abin da ba ta taɓa ji ba. "me ya sa kike mahaifiya in ƴar ki ba za ta samu Rahma daga gare ki ba? Kin bincike ta kin ji gaskiyar lamarin ko dokin zuciya kawai kika hau? Amanar da na baki kenan" Yace, yana fitowa, ganin da ya mata cikin hawaye ne ya sa ya riko hannunta su ka fita, ko da su ka iso tsakar gida kallon ta yayi ya ga hawaye kawai take yi hakan ya sanya shi sa hannu tare da share hawayen da su ka zubo ma Amatullah. Chan gefen gidan su ka je inda ɗakin kannen Amatullah maza yake, ciro makulli yayi ya bude su ka shiga. Gefen katifa su ka zauna, ya ciro hankici ya bata ta share hawayen da ya take yi sannan ya ce "Amatullah!!!" Ba Ta amsa ba sai ɗago idanunta tayi ta kalle shi. "Faɗa min gaskiyar abin da ke faruwa, na yarda dake, na san ba zaki taɓa manta inda kika fito ba, faɗa min and I will give you 100% support" yace yana riko hannayenta biyu. Nan ta samu ƙwarin gwuiwa ta faɗi masa duk abin da ya faru tun daga farkon haɗuwarta da Dee Yusuf zuwa abin da ya faru zuwan shi. "Wani amsa kika bashi bayan ya faɗi miki uzurin sa?" "Idan za ka karbi addinin ba dan ni ba, ba dan soyayya ta ba, domin soyayyar dan adam abu ne mara tabbas, idan za ka karba domin soyayyar Allah da manzon sa, Ni ma na daukar maka alkawari ba zan cuce ka ba, ba zan bari a cuce ka ba, Zan kare duk wani hikki na ka a matsayin ka na miji na...." Amatullah ta maimaitawa mahaifin ta. Kai ya ke girgizawa cike da dana sani "kin san da na shigo aka faɗi min, na ji tsoro a raina saboda ina tsoron kar ace hakkin Binta Sule ne ya kamani" Ya ce cikin sanyin jiki. Kallon sa tayi cikin neman ƙarin haske. Be gushe ba ya cigaba "Ajin mu ɗaya da Binta Sule, duk mun shaida soyayyarta da Yusuf Haɗeja. Muna cikin wainda ke mata kallon tubabbiya, muna da hannu a komawarta Christianity. Amatullah Al'ummar musulmi Hausawa na da wannan nakasun, ni ma a lokacin ina da ita. Kwanakin baya mun haɗu a taron yan jarida, na yi kokarin neman gafaranta amma tace min abin da mu ka Aikata ya zama mata gobarar titi a jos" Numfashi ya sha cikin dana sani ya cigaba da fadin "Ta so MSS su kula da ita, ta so zama cikin musulunci amma alakar da muka nuna mata mai rauni ce, da shi wannan David din na ki zai karbi musulunci ko shakka babu ni mahaifin ki zan ba ku kowacce gudunmawa, duk da dai zan fi so ki auri dan uwan ki wanda ya ke tsatson ki..."[2/2, 4:48 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA DAYA Shigowa ya yi don amsar abincin dare duk da hakan ba al'adarsa bace amma yanayin da yake ciki ya isa ya hana masa cin abin da yafi soyuwa a gare shi da dare. Har yayi hanyar ɗakin gwaggo Mairo kamar yadda ya saba sai ya canza don baya fatan abin da zai haɗa shi da bagidajiyar yarinyar nan, ya ayyana a ransa. "Amma dai an yi sakarai wahalalle ya rasa wacce zai ci burin sakawa a motar nan sai bagidajiyar yarinyar nan" ya fadi ya na mai dafa bango jin wani abu ya tokare shi a ƙirji. "2008 Suzuki SX4 ce fa" ya faɗi tunawa da cewa a ƙarshen shekarar da ta gabata a ka fitar da motar, yayi maitan mallakar ta amma shi a karan kanshi ya san motar ta girmi duk wani ahlin gidan Jamoh a wannan lokacin, sai gashi wacce ya fi gani a kaskantaciya da bai yi tunanin mamallakin keke zai kalle ta da soyayya ba mamallakin dream car dinsa ya zo afujajajan idanunsa dauke da tsantsan soyayya gareta. Sai da ya kwashe kusan mintuna goma sha biyar yana maida numfarfashi da tattaro natsuwa kafin ya karasa cikin ɗakin mahaifiyar sa . "Ku tashi ku bamu wuri" hajiya ta faɗi ma kannensa ganin suna zaune ba mai shirin fita duk da ba wai don sun saba fita bane in ya shigo ɗakin. "Saki Ranka yayansu, ashe yaron nan da Amatullah ke so arne ne, in faɗa maka ina ji na yi wuf na iske baban Sasa na faɗa masa" tace cikin raɗa, fuskar ta cike da annuri, rasa me zai ce mata yayi, ya rasa yanayin da ya tsinci kansa haka yake kallonta sheƙeƙe bai ga ta in da tayi gwaninta ba balle ta birge shi. "Kin ga matsalar shegiyar al'adar nan taku ta banza wai kunyar ɗan fari ko, ni na ce miki ina son Amatullah da har za ki taya ni kishi" ya ce yana kokarin saita fushi da ya ji yana taso masa da ga kasan zuciya. 'watau ba ma musulmi bane balle a ce shima ustaz ne yana son ustaziyya' zuciyar sa ta dinga nanata masa. "Na ga dai duk gidan nan babu wacce ta kamo kafafunta ne a haɗuwa boko da islamiyya, in ka aureta zan tabbata na zarce duk wata mace a gidan nan" ta katse masa tunani, magana take ƙasa-ƙasa gudun fitar da wani gun, duk da ta san ana faɗin bango na da kunnuwa. "A tunanin ki hajja zan auri wacce ta taso a cikin manyan biranen ƙasar nan ne balle kuma wacce ta taso a cikin zaria, matan da ba su san komi ba sai lulluɓe jiki kamar sauran kuturta. Hajja ki min jagora kar a aura min bagidajiyar can, zan auro miki wacce ta haɗu, wacce duk ta wuce sai an saki baki an bi ta da idanu, ki amince min Hajja" ya ƙarasa rauni cike da muryarsa, shiru ta yi ta lula mafarkin ido biyu, babu abin da ta ke hangowa sai surukar da sanadin ta za ta dinga zuwa haji duk shekara. "Amma kuma mahaifin ka fa? Ɗazu fa kiris ya kwaɗe ni gaban su Baban Sasa" tace sa'ilin da ta tuna babu wanda zai kawo masu cikas sama da shi. "Hajja matarsa fa kike, kiyi amfani da damar nan" yace mata kai tsaye. Tunawa da tayi da Madina, kanwar mijinta kuma aminiyarta wacce ba ta san wa yafi tsanar Goggo Mairo ba cikin su biyun. "Zan nemi madina gobe inshaAllah, duk abin da ake ciki za ka ji" da haka su ka yi sallama, ya wuce ɗakin sa ya rufe, baya ko fatan abin da zai sa ya haɗu da mahaifinsu hakan ya sa ya kuduri niyyar ba zai fita sallan asuba ba. *** Kwance ya ke bisa gadon sa, duk yadda ya so ya cire tunanin Amatullah da maganganun da su ka yi abin ya gagara. Hamza yayi kokarin jan shi su fita amma hakan ya ci tura, rokan sa yayi da dan Allah ya rabu da shi sam ba ya jin dadi dan haka ba ya san damuwa. Sanye ya ke cikin farin singileti da gajeran wando. Tun yana juye-juye har ya tashi yana mai lalubar wayar shi da tun dawowar shi daga wajan Amatullah ta ke kashe. Kunna wayar yayi, idanun sa kan fuskar wayar in da agogon kan wayar ya nuna karfe goma sha daya da rabi na dare, lalle ya daɗe kwance domin kuwa Allah kaɗai ya san awanni nawa ya ɗauka nan kwance. Ba tare da ta san abin da ya ke ba ya tsinci kan sa ya na mai danna number Amatullah, ta yi ringing har ta katse ba ta ɗaga ba. Ajiyar zuciya ya saki, yayin da ya furta "Oh lord I'm so confused I'm going crazy!!" Number Mahaifiyar shi ya shiga kira ba tare da yayi la'akari da lokaci ba, har sai da wayar ta kusa tsinkewa sai gashi ta daga a tsorace ta furta "Dan albarka lafiya kuwa ka kira cikin dare haka?" "Mummy.........." Dee ya amsa mata yayin da ya nemi abincewa ya rasa. Jin haka Mahaifiyar shi wacce wayar Dee din ne ya tashe ta daga bacci, tashi ta yi gudun kar ta tayar da mijin ta daga bacci. Sai da ta koma falo ta sami waje ta zauna sannan ta ce "Owk David, yanzu ina jin ka, me ke faruwa? Ba ka da lafiya ne?" "Lafiya lau Mommy, kawai dama na kasa bacci ne....." "No David, na san ka kamar yunwar ciki na, hakan nan dan ka kasa bacci ba zai sa ka kira ni cikin dare haka ba, me ya faru my baby?" Ta katse shi ta na maganar ne cikin nuna damuwa. Numfashi ya sauke sannan ya furta "Mommy idan har addinin musulunci ya yarda namiji musulmi ya auri mace Christain ko da kuwa ba ta musulunta ba, me ya sa kika musulunta?" Shiru ne ya biyo baya, domin kuwa tambayar da Dee ya mata ya zo mata a bazata, har yayi tunanin wayar ya katse, ya sake furta "Hello Mummy? Hello?" "Yes Son, I can hear you....well kyawawan halin mahaifin ka da kaunar da na ke ma sa ya sanya na ga hasken da ke cikin addinin sa, ya sa min kwaɗayin shiga addidnin, duk da ya ce zan iya addini na ba tare da mun bari dangin sa sun sani ba. Your Father was very kind, da haka duka musulmai su ke da har yanzu ban bar musulunci ba" Ta amsa masa ta na mai jin dacin rashin mahaifin Dee da har yanzu be bar zuciyar ta ba. Jin Dee yayi shiru ta kara fadin "Oya it's your time to answer me now, me ya sa ka ke min wannan tambayar? Na san hakan nan baza ka kira ni cikin dare ka na min wannan tambayar ba tare da wani dalili ba, so tell me what is going on, I mean tell me everything kar ka ɓoye min komi" Shiru Dee yayi yana mai muhawara cikin zuciyar shi na fada mata ko rashin fada mata. "David......" "Na'am Mummy" "Start talking, your Mommy is here for you" Cikin sassanyar murya ya furta "Mummy Amatullah ce......" Sai kuma yayi shiru, ya kasa cigabawa. Cikin bashi karfin gwiwa ta ce "Ina Jin ka, wacece Amatullah? A ina ta ke? Wani irin dangantaka ce a tsakanin ku? Me ya faru?" Tambayar da Mahaifiyar ta jero ma sa ne ya sanya Dee bude mata cikin sa, tun daga haduwar shi da Amatullah har izuwa ranar yau in da ya je gidan su Amatullah. Ya kare maganar ne da "Wallahi Mummy ina kaunar Amatullah, babu abin da ba zan iya yi ba a dalilin ta, ko da kuwa hakan na nufin zuwa Hadejia ne....ki taimaka min Mummy....." "David ka san me ka ke faɗi kuwa? Ka na tunanin dangin mahaifin ka za su karɓe ka ne after all this years? Ka na jinjiri, innocent child ba su karɓe ka ba sai yanzun da ka zama saurayi ka tashi cikin addinin da ba na su ba? Ka na tunanin za su karbe ka ne ka na Christain? " Cewar Mummy cikin nuna bacin rai Jin Dee na zancen zuwa Hadejia, dan kuwa idan akwai wainda ta tsana su na bayan dangin mahaifin Dee. Ga mamakin ta sai ji ta yi ya ce "Mummy in dai zuwa Haɗeja gun dangin baba na shi zai sa su yarda su nema min auren Amatullah, Mummy zan yi, ko da kuwa za su min korar kare......" Shiru Mummy ta yi na ɗan wani lokaci, daga bisani ta furta " Oh Lord Jesus! This is history repeating itself!!!" "Mummy please understand me, Ina son Amatullah, ban taba son kowace ɗiya mace ba kamar yanda na ke son Amatullah..." "Ita Amatullah ta na son ka ne? Ya za ka yi da tazarar da ke tsakanin ku? Shin kana tunanin iyayen ta za su yarda su aura ma ka ita ka na Christain? Ko ba ka san addidinin su ya hana ba?" Mummy ce ke maganar cikin faɗa -faɗa. Shi kuwa Dee daɗa sassauta murya yayi kamar ya na gaban ta ya ce " Mummy na sani, I mean ta fada min a addidinin su haramun ne mace Musulma ta auri Christain, Amma idan na musulunta shikenan......." "Za ka musulunta ne David saboda yarinya da soyayya? Shin rayuwata ba zai zame ma ka makaranta ba David?" "Mummy..... please try to understand me, please!" Ya faɗa cikin rauni. Shirun da Mummy ta yi ba karamin tayar ma sa da hankali yayi ba. Idanunsa na fitar da hawaye ya furta "It's not just about Amatullah kawai, har da mahaifina wanda ki ke kauna har gobe, da kyawawan halin sa da ya kwaɗaita mi ki son shiga musulunci, Mummy ina laifi idan ɗa yana so ya gaji uban sa? Ina laifi dan ina son kasancewa kamar mahaifi na........?" "David......." Mummy ta yi kokarin katse shi, Dee wanda ke gudun jin abin da za ta ce ya tari numfashin ta "Mummy kasancewa na musulmi zai zama abin alfahari ga mahaifina, abin kaunar ki.....kar ki manta addinin musulunci addidinin shi ne, please Mummy understand me...." " I understand David, na fihimce ka, you have my blessings son today and always addini ba zai taba zama tazara a tsakanin mu ba, a Musulmi ko Christain you will always be my blood and flesh" Cike da murna wanda ya ke bayyane cikin muryar sa ya ce " Na gode Mummy, na gode, I love you so much" Tana murmushi ta amsa da "I love you more son, but David?" "Na'am Mummy" "Shin ka faɗa mata za ka musulunta? Ita Amatullah ɗin ta ka? Ka ga ka ce ana shirin ɗaura mata ɗan uwan ta nan da one week, kar fa ka makara" Nan gaban shi ya faɗi, yana ɗan sosa kyeya ya ce "Ah ah Mummy ban faɗa mata ba, dama I wanted to tell you first, bari in je faɗa mata yanzu....." "Toh Alhaji ɗan gidan Yusuf, ka duba agogo ka ga lokaci kuwa? Sha biyu ya wuce fa, gidan mutane za ka je mu su da wannan daren?" Cewar Mummy ta cike da fara'a. Shi ma ɗin dariya ya ke, har ran sa da zai samu dama babu abinda zai hana shi zuwa gun Amatullah domin yi mata wannan kyakkyawan albishir ɗin. A zahiri kuwa cewa yayi "Toh da asuba kuwa zan je, ana buɗe kofar gidan su Amatullah za su ganni bakin kofa domin ta san cewa I mean business, I love her Mummy" "I know right, I hope she loves you too son, Allah ya mu ku albarka ka ji dan albarka?" "Ameeen, you're best, thank you" Da wannan su ka yi sallama. Ciwon rashin masoyin ta ne ya tashi, Nan ta zauna ta na mai zubda hawaye domin kuwa mahaifin Dee ya so ta, soyayyar da har yau ba ta sami irin shi ba, ya tararraye ya ta kuma ya kare hakkin ta, ya kance da ita yana yi mata hakan ne domin cika hakkokin ubangiji, haka addinin shi ya koyar. Ina ma ace mutuwa ba ta raba su ba. Dee kuwa yanda ya ga rana haka ya ga dare dan kuwa ya nemi bacci ya rasa, Allah Allah ya ke Allah ya wayi gari ya ga Amatullah. Haka ita ma Amatullah wacce tun rabuwar ta da mahaifin ta ta shiga yanayi mai wuyar fasaltuwa, ta nemi bacci ta rasa akan dalilin da ita kan ta ba ta sani ba. Kawai dai gaban ta na faduwa da wani tashin hankali da tsinci kan ta ciki, haka har aka fara kiraye kirayen Sallar asuba sannan bacci ya fara sace ta. *** A cikin masallaci bayan an idar da sallar asubahi, Baban Sasa wanda tunda su Baba Anas su ka ga ya fito sallar asuba su ka san ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, ya matsa kusa da liman ya ce da shi "Allah gafarta Malam akwai auren da mu ke so a daura a yau, tsakanin jikoki na biyu, dan wajan Anas da diyar Salihu....kai Ina Saifullahin ma ya ke?" Ya tambaya ya na mai wage wage. "Ina ga fa yau be sami damar fitowa ba ko kuma masallacin bayan layi da ya fara zuwa ya je" Baba Anas ne ya bashi amsa, shi kuwa Baba Salihu da ya san halin da ƴar sa ke ciki na game da auren Saifullahi ne ya sa jikin sa yin sanyi dan kuwa dai be yi tunanin Baba Sasa da gaske ya ke zai daura auren a yau ba sai yanzu da ya ga zahiri. "Ah toh madallah, ai sai a ɗaura me za a jira in dai akwai waliyai, shedu da sadaki?" Cewar liman yana mai baza babbar riga. Ba tare da ya damu da rashin Saifullahi a wajan ba sai ga Baban Sasa ya fito da kudi daga aljihun rigar sa, ka na ya mika ma Baba Zubairu ya ce "Amshi nan Zubairu, kudi ne dubu hamsin sadakin dan ka ne, kai na umurta ka zama wakilin Saifullah, Ni kuma ni zan kasance waliyi ga Amatullah, kai yaro yaka nan shiga gida, ɗaki na za ka ga alawa da goro maza kwaso su nan...." Da saurin yaron da aka aika ya tashi ya fita, nan aka fara shirin daurin aure, inda Baba Anas da Baba Salihu su ka zama yan kallo. ***** Tun kafin a idar da sallar asuba Dee ya shiga wanka. Ana idarwa shi ma din yana fitowa daga wanka a gurguje ya shirya cikin shadda brown dinkin jamfa. Alkawarin doka sammako zuwa gidan su Amatullah din da ya dauka na gaske ne. Domin kuwa yau da shi za a bude gidan. Kasancewar Hamza baya nan tun jiya da ya fita be dawowa ba, yaci sa'ar fita ba tare da ya sha tambayoyi ba, yanda ya sha hula da turare kai ka ce ango haka ya shiga motar sa cike da nishadi ya nufi gidan su Amatullah. **** An ɗaura aure an shafa fatiha in da Amatullah ta tabbata matar Saifullahi. Cikin wanda su ka shaida ɗaurin auren, In aka dauke Mahaifan ma'auratan biyu wato Baba Anas da Baba Salihu babu wanda abin bai masa dadi ba, musamman Baban Sasa wanda zama yayi dirshen cikin masallacin ya na raba alewa da goro cike da jin dadi. Lokacin da Dee ya sami isowa gari yayi haske, haka kuma yayi mamakin ganin kofar gidan su Amatullah a bude. Ya na mai tunanin kila sammako su ke yi wajen buɗe gidan ya sami gefe ya faka, sannan ya fito ya tsaya kofar gidan ya na shawarar kiran Amatullah ko kuwa dai ya jira gari ya daɗa wayewa. Ganin fitowar Baban Sasa daga masallaci hannun sa rike da sauran alawa da goran da ya rage, tare da su Baba Anas sun nufo gidan yayinda jama'a wanda su ka shaida auren da kuma wanda su ka ji labari daga baya ya sanya Dee ɗan ja da baya ya koma jikin motar shi. Kamar yanda ya kula da su haka suma su ka lura da shi, musammam Baba Anas wanda ko cikin bacci zai gane shi, shi kuwa Mahaifin Amatullah kallon sa ya ke ya na mai mamakin kamannin sa da marigayi wato Mahaifin Dee Yusuf Haɗeja. Ko da su ka isa kofar gidan sai Baban Sasa ya tsaya yana mai tsurawa Dee ido, ganin haka suma kawun nan nata tsayawa su ka yi, su ma din Idanun su kan Dee din ya ke. Cike da fargaba Dee ya ƙarasa gaban su har kasa ya durkusa cikin girmamawa ya shiga gaishe su. "Yaro daga ina? " Baban Sasa ya tambaya. Cike da jin nauyi Dee ya ce "Dama na zo ne...." Sai kuma yayi shiru, ya kasa magana. "Ka zo me?" Baban Sasa ya sake tambaya. Jin shirun yayi yawa Dee ya kasa magana Baba Anas ya ce "Shi ne wanda ya zo neman Amatullah jiya" "Auho kai ne Dee Yusuf din da na ke ji gurin jikata?" Jin Baban Sasa ya kira sunan sa ya sanya Dee jin dadi har cikin ran sa, wato har iyaye da kakannin Amatullah sun san da zaman shi. Ya na mai murmushi ya ce "Eh ni ne Dee Yusuf" "Kai ne kirista da ke kokarin hurewa jikata kunne, ka ke kokarin ruguza tarbiyar da mu ka bata ta hanyar sauya mata addini da dabi'a ko? " Tambayar Baban Sasa ba karamin tayar da hankali Dee ya yi ba, in da ya dago kai da sauri ya na mai fadin "Wa'iyazubillah!!! Afuwan Baba, amma dai ina ga an sami rashin fahimta ne, ko kusa ban taba tunanin aiwata haka ba, na zo ne a yau domin shaidawa Amatullah zan karbi addinin musulunci, ta kuma shige min gaba domin shaidawa iyayen ta, ina mai neman izinin turo iyaye na neman auren ta......." "Kai tafi can rufewa mutane baki!!!" Cewar Baban Sasa cikin tsawa da tsangwama, yayinda Baba Salihu ya runtse idanun sa cike da tausayin Dee da ya rufe shi. Baban Sasa be gushe ba ya cigaba da fadin "Ku ji fa dan Allah yana kirista shekara da shekaru kawai an wayi gari wai ya zo wajan mu karbar musulunci da ke ka mayar da mu shashashe irin ka! Mu za ka zo ka yaudara? Toh ka ruke tubar ka ka kai can ba dai gare mu ba! Ahir din ka! Jika ta dai na aurar da ita ga jika na musulmi dan musulmai!!" Jin maganar ya ke tana shigar sa kamar kibiya tsabagen ciwo, hawayen da shi kan sa bai san da zubar su ba ke gangarowa daga idanun sa yayinda ya dukar da kan sa kasa. [2/8, 12:21 AM] +234 803 579 6693: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA BIYU Baba Anas wanda shi kan shi maganar Baban Sasa ya masa tsauri girgiza kai ya shiga yi, Jan hannun Baban Sasa cikin dabara tare da faɗin "Baba ai ina ga zai fi kyau ka ɗan shiga ciki ka huta, ka jima a waje" Cikin cijewa yayin da Baba Anas ke jan sa be fasa faɗin "Ai to ka bari Anas na yi masa wankin babban riga, ɗan tselan uwa, ta Allah ba taka ba, jika ta dai na maka katangar karfe da ita....." "Baba faɗa ba naka bane tun da TAZARAR da ke tsaƙaninsu ya ƙara ƙarfafa" Baba Anas ya ce yana jan Baban Sasa zuwa cikin gida. Su Baba Zubairu ma baya su ka rufawa Baban Sasa, mahaifin Amatullah ne kaɗai ya rage tsaye gaban Dee wanda ya sunkuyar da kai kamar an ajiye dutse. Cikin sassanyar murya Baba Salihu ya "Ban san da wani ido zan kalle ka ba, ban san da wani baki zan baka hakuri ba, ni mahaifin Amatullah na so ka da ɗiyata, ko ba don komai ba ko don kuskuren da na aikata dangane da Mahaifiyar ka a baya....." Yanda yaga Dee ya ɗago kanshi a karo na farko su ka haɗa idanu, da yanda ya ga idanun sa sun kaɗa sun yi jajur ya sanya Baba Salihu shanye maganar sa, kana daga bisani ya furta "Allahu akbar Allah ya jikan Yusuf da rahama, babu shakka kai jinin sa ne, ina mai fatan za ka yafe mana a karo na biyu Yusuf" Yana gama faɗin haka shima ciki ya shige cike da danasani, dan kuwa da ya taimakawa Mahaifiyar Dee da ya girma cikin musulunci. Allah kaɗai ya san tsahon mintocin da yayi nan tsugunne, har sai da jama'a su ka fara taruwa suna tambayar lafiya? Sannan ya tashi da kyar ya na mai goge hawayen da suka rufe fuskar shi. Har ya karasa ga motar shi kafin ya juya ya kalli kofar gidan su Amatullah, gani ya ke kamar za ta fito ta ce duk ba gaske ba ne, ganin babu ita babu alamar ta ya sanya shi buɗe motar, ya shiga ya zauna, Amma kunna motar ya gagare shi "Amatullah shikenan yanzu na rasa ki?" Cewar Dee ya na mai kifa kan sa bisa sitiyari yayin da maganganun Baban Sasa ke masa yawo cikin kwakwalwar kan sa. "Amatullah..... Amatullah........." Amatullah kuwa tana cikin tilawa saƙon ɗaurin aurenta ya isa kunnuwanta, ba ta yanke da karatun ba cigaba ta yi tana mai godiya ga Allah ba don tana son auren ba amma don ta san aure wata dama ce da Allah ya ke ba wanda ya so, ba wayon mutum ba dabararsa ke sanya ya yi aure a duniya ba, sannan matukar lokacin mutum yayi to babu shakka za a ɗaura ga kuma mijin da Allah ya riga ya tsara. Shigowar Mahaifinta ne ya sanya ta kasa kunne Jin ya na magana da Gwaggo, ya na mai rokan Allah kariya daga dukkan sharri a gidan auren Amatullah. "Mairo na so a ce yaron nan ya iso kafin a ɗaura auren nan, wallahi sai dai a yi duk abin da za ayi shi zan ba Amatullah." Amatullah ta tsinkayo mahaifinta na faɗi, ajiye Qur'anin tayi don jin wani yaro babanta ke magana akai. "Wa kenan baban Hafiz?" ta tambaya a sanyaye don za ta iya rantsuwa ta dade ba ta ga mijinta cikin tashin hankalin nan ba. "Wancan da Amatullah ke so" ya faɗi kai tsaye. "Wanda Hajiya tace bamaguje ne?" ta ce a ɗan firgice. "Ahlil kitaab ne, ya zo da shahadar sa a zuci so kawai yake a sanya masa a laɓɓansa amma ya zo an riga da an ɗaura auren Amatullah." Amatullah tana jiyo tausayi da buri a cikin muryar mahaifinta. 'Dee Yusuf ya zo don ya musulunta' ta faɗi a cikin zuciyarta tana mai jin wasu zafafen hawaye suna gangarowa kuncinta. " Baban Hafiz mu kaddara hakan ne Alkhairi, ka manta duk wani abin dai auku a rubuce yake, Allah da kansa ya faɗi a zancensa mafi gaskiya LIKULLI AJALIN KITAAB" tace muryarta a sanyaye, Amatullah ba ta iya jin sauran zantuttukan iyayenta ba ta tashi ta jiki na rawa ta fice waje, jama'ar gidan na amarya amarya amma ina hankalin ta yayi waje domin kuwa ba ta da buri da ya wuce kanin Dee Yusuf ko da kuwa shine gani na karshe da za ta ma sa a rayuwar ta. Sai da ta ganin motar ya dauke ma ta, sannan ta juya a hankali kamar wacce kwai ya fashewa ta shige gida. Dakin ta ta koma tana mai kuka kamar ranta zai fita, shike nan Tazarar da ke tsakanin su ya tabbata, shike nan za ta rayu da wanda ya fi kowa ganin ta a matsayin kaskantaciyar halitta. Tunanin da su ka dinga tunzura kokenta kenan. Fadi ta ke "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Ni Amatullah na rasa masoyi!!!" *** Baban Sasa kuwa ɗakinsa Baba Anas ya wuce da shi, nan ɗin ma baki ya dinga bashi yana mai koɗa haɗin da yayi wanda hakan ya zama ruwan da ya dinga wanke zuciyar Baban Sasa da ganin Dee yusuf ya sanya shi cunkushewa kamar tuƙuƙin hayaƙi. "Anas a ce Arne har ya ga fuskar da zai ce yana son ta, shi yasa na tsani bokon ƴa mace" Baban Sasa ya nisa ya faɗi, sai da baba Anas ya ɗauki wasu yan daƙiƙai kafin ya ce "Ka san Arne da tsaurin ido, dama an ce su kan janye yayanmu cikin hilla da kyautatawa. Amma ni ban shakkar Amatullah ko da na daƙiƙa ne, Allah ya albarkaci Auren nan nasu, Baba ba zan iya kwatanta farin cikin da nake ciki ba. Allah ya saka da Alkhairi" murmushi Baban Sasa ya yi cike da farin ciki da alfahari da abin da ya yi. Nan Baba Anas ya zauna su baba Zubairu su ka shigo su ka dasa hira, ba su suka bar ɗakin ba sai da baban Sasa ya fara gyangyaɗi bayan ya sha maganinsa na safe. Ba su yi mamakin ganin yanda mata su ka cika gidan ba saboda mafi akasarin su na yan tsakankanin Amaru ne. Farin cikin da ke tattare da muryar Baba Anas yayin da yayi sallama a ɗakin matarsa ƙadai ya isa ya fassara tarin farin cikin da yake ciki. "Wai ni kam Alhaji Anas wannan farin ciki duk akan samun kwancen surika ne" Madina ta tambaya tana wani yamutsa fuska. "aikuwa ke ma kya faɗi a ce mutum Sam bai san abin da ya kamata ba" Hajiya ta amshe tana ƙarasawa da ƙaramin tsaki. "Ohhh toh ni ban fahimci in da kuka sa gaba ba, ke madina abin kunya ne ma a ji zancen nan daga bakinki, in ita sadiya karere ce a gidan nan ke kuma fa? Nono ɗaya kuka sha fa da mahaifin yarinyar nan" yace yana gimtse fuska. "Toh ni dai ban ga mai Mairo ta tsinana a gidan nan ba in banda raba tsakaninmu da iyayenmu, sannan shi Salihun da kake magana sai naga ɗan uba ne a gareka, har wani cancanta yayi ka sayar da farin cikin ɗanka akan tashi ɗiyar, wacce Allah kaɗai ya san abin da ta shuka a jami'a" Madina ta faɗi cike da bakin ciki da takaicin yayanta, shirun da yayi ya sanya su tunanin cin galaba akan tunaninsa, na hajiya ta ɗaura " ai in za a ci kwaɗo ai gara a ci me mai. Shi yayan nasu ma ya riga ya shirya da wata tun a can Turan. Yar babban gida wacce ko ba komi mun san ba hayen boko ta yi ba" tace, cike da alfahari don tun jiya ta kwana da mafarkin suruka yar baban gida da za ta zama silar komawar ta haji ba ma sau ɗaya ba duk shekara. Shiru yayi yana kallon sa suna magana wanda duk akan kushe Amatullah ne da mahaifiyarta da kuma ƙawata masa zaɓin Saifullah. "Madina ki zama shaida, Duk abin da ya sami auren Amatullah kwatankwacin sa ne akan Sadiya. In kun ga dama ku sanya shi ya yaƙice auren" yace bayan ya gaji da jin kalamansu, bai jira sun farfaɗo daga kaɗuwar da su ka yi ba ya sa kai ya fice daga ɗakin. *** "Wai ko yau baban Sasa ya rasu zai rasu da cikar burinsa, aure da subahi sai kace ana neman kai" maganar da ya daki kunnen Saifullah kenan ya yi saurin tashi daga kwance ya zauna don tabbas in ba ƙarya kunnensa ke masa ba muryar Shahid ne Dan wajen baba Mahmouda. "Kai dai bari, ai Saifullah yayi mugun dace, ina ma ni ne aka ma wannan alkawarin, kana ji murya kamar ana busa sarewa, wani abin ma hmmmn ba a ko magana wallahi Amatullah ne ake kira da wife material" abokin hirar Shahid ya faɗi wanda muryar sa ta faɗi ma Saifullah Yasir ne ɗan Baba Zubairu. "Yaya Yasir bari anty Amina ta jiyo ka, kasan kishin ta babu part 2" Shahid ya faɗi cike da shaƙiyanci. Saifullah bai ji amsar da Yasir din ya bada ba saboda yawo da kalamansu na fari ke yi a kwakwalwarsa. Bai san lokacin da ya miƙe ya ja jikinsa zuwa ɗakin Baban Sasa ba, yana isa ya iske shi yana bacci bai tuna da halin da yake ciki na ciwo da tsufa ba ya fara magana yana jijjiga shi. "Why Baban Sasa, me yasa za ka min haka, ka aura min wanda duk duniya na tsana, bagidajiya, baƙauyiya wacce ba ta san kanta ba, why Baban Sasa" yace yana kuka shaɓe-shaɓe kamar ransa zai fita. Kamar a mafarki Baban Sasa ya ji kalaman nan, a hankali ya bude idonu ya ke kallan Saifullahi. "Baba ko mace an hana a mata auren dole balle ni namiji, auren dolen ma ga bagidajiya irin Amatullah" ya sake faɗi yana girgiza kanshi alamun shi kanshi bai yarda ba. Kallo mai cike da firgici Baban Sasa ke masa, shi bai taɓa tunanin Saifullahi baya so ba duk kuwa da a lokacin ya dinga taro duk abubuwan da su ka gudana. Take tausayin Amatullah ya cika shi, yana mai tuna tsantsan soyayyar da ya gani a idanun Dee Yusuf yana mai jin haushin abin da ya aikata masa. "Bagidajiya ce bana sonta, aurenta abin kunya ne a gare ni Baba, ka taimaka min" saifu ya faɗi yayin da ya hango ta cikin hijabinta da safa a ƙafa da hannu. Faɗin irin mamakin da Baban Sasa ya shiga ba zai misaltu ba, zufa yake yi yana kallon jikan da yake masa kallon gudaliya wajen kauna, wanda duk inda ya zauna zai ba da shedar irin biyayyar Saifullah gare shi amma shi ne zaune yana masa ɗibar albarka akan abin da bacci ya ɗauke shi yana mai alfaharin aikatawa. Shirun baban Sasa ne ya sanya Saif ɗaga ido ya kalle shi, sai a lokacin ya dawo cikin hankalinsa ya tuna gaban wanda ya ke, ya tuna duk wani shirin sa ba zai yi tasiri ba matukar bai goge abin da ya aikata ba. "April Fool!!!" ya samu kansa da faɗi yana mai kirkiro murmushi da kuma rungumar Baban Sasa da ya zauna kamar mutum-mutumin da aka danka. "Baba Nagode da wannan kyauta, cikin bacci na ji su Shahid na maganar baka ji farin cikin da na shiga ba, amma na ce bari in dan ɗanaka duk da dannen kirji yaci in maka" ya faɗi yana mai rike hannun baban Sasa kamar wanda ke tsantsan farin ciki. Shi dai baban Sasa zaune yake yana mai cike da waswasi don in ba ƙarya idanunsa ke masa ba toh tabbas Saifullah a haukace ya shigo ɗakin babu wani zancen wanawa. "Ka san halin da na shiga da tace min wani Danliti ta ke so, Nagode Allah mai kyauta mai ƙari, na gode Baban Sasa ina mai farin cikin kasancewa tsatsonka. Na maka alkawari zan riƙe maka Amatullah fiye da yanda kake tsammani" ya faɗi cikin farin ciki tsantsa wanda gaba ɗaya na abin da zuciyar sa ta raɗa masa ne akan zai iya aikatawa ga Amatullah. Baban Sasa bai iya cewa komi ba don kaɗuwar da yayi tun farko, shafa kan Saifullah ya shiga yi yana murmushi da addu'ar Allah ya kauda idon makiya da shaiɗanu a auren su. [2/10, 9:28 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA UKU Ɗago kai Saifullah yayi ya ga me Baban Sasa ya ke yi ya dai ji yana shafa masa kamar mai neman tubarrukin maraya. "Watau Baban Sasa in a ce kowa zai dace da fitowa daga tsatson mutum irin ka ai ba sauran tashin hankali" ya faɗi bayan sun haɗa idanu. Dariya Baban Sasa yayi yana mai jin wani sanyi na ratsa shi don ya kasa gaskata abin da kunnuwar sa su ka jiye masa. "Nagode da biyayyarku gareni Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya" Baban Sasa ya ce yana mai murmushin farin ciki, Aameen yayi nauyin fita daga bakin Saifullah, sai yaƙe yake yi don shi bai son a tsawaita addu'ar ma balle a dace da yinsa a bakin ƴan Aameen. "Bari na shiga wajen amaryar in tabbatar da dagaske na kada kai" yace yana mai miƙewa. "Ja'iri ai ni ɗin nan nine masoyinta na asali kai sai manaji" baban Sasa yace shima cikin dariya. Ficewa Saifullah yayi don ya gaji da ɓoye halin yake ciki, neman inda zai zuba su yake yi. Bai ɓata lokaci ba ya wuce ɗakin mahaifiyar sa ba tare da ya ankara da mahaifinsa da ke zaune a ƙarƙashin bishiya ba tare yake da Baba Salihu suna tattauna abubuwa da su ka jiɓinci danginsu. Haka su ka ɗaga kai su ka kalle shi, kallo ɗaya za ka masa ka san yana cikin tsananin tashin hankali. Shiru Baba Salihu yayi yana mai addu'a a cikin ransa yayin da Baba Anas ya tashi kamar wanda aka tsikare shi ya bi bayan Saifullah. *** Zaune ya iske Hajiya tayi tagumi da hannunta duka biyu, tun bayan fitar mijinta ta rasa ina za ta sa ranta taji sanyi, shike nan mafarkin da tayi ba mai tsawo bane balle ta sa ran tabbatuwarsa. Ba za ta ce ga lokacin da Madina ta fita daga gidan ba. "Yanzu Fisabilillahi kin yi abin da duk wata uwa yaci tayi kenan? Kalli lokacin da Amatullah ta nuna ba ta so kina ganin in uwarta ba ta mara mata baya ba za ta iya furtawa ne? Ku kenan Ɗanku banza ko? Ni wallahi sakin ta zanyi ku neme ni ku rasa" ya ce yana mai sakin kuka kamar wani ƙaramin yaro. Har cikin ranta take jin kukansa tsanar Amatullah na ƙara mamaye zuciyarta. Ko Baba Anas da ke tsaye bakin ƙofa ya ji kukan Saifullah har cikin ransa har ya fara tunanin bai yi ma ɗansa adalci ba. Yana shirin shiga ɗakin ya ji hajiya ta ɗora da faɗin "kul! Sakin Amatullah daidai yake da nawa sakin" tace cikin muryar lallashi da son tare kuka. "What!!! Hajiya me kike faɗi ne" Saifullah ya faɗi a firgice. "Eh haka mahaifinka ya ce, yanzu maganar da ake sai dai muyi mata gashin ƙuma, kar ka kuskura ka nuna baka son auren, mu bi ta da kisar mummuke" tace kai tsaye, hakan ya sanya Baba Anas yaye labule. "Kin san Allah sadiya, daidai da kuka na tabbatar Amatullah ta yi a gidan aurenta sai kin yi mafiyinsa. Ba zan hana ku ba fa, duk abin da kuka shirya ku aiwatar ni kuma zan tabbatar da na aiwatar da mafiyinsa gareki" ya ce daga bakin ƙofa ya juya ya fice daga ɗakin. Shiru duk su kayi babu abin da ake ji a falon se shesshekar kukan hajiya wanda maimakon ya sanyaya zuciyarta ƙara rura wutan ƙiyayyar Amatullah da mahaifiyarta kawai yayi.. Sun zauna fiye da mintuna goma sha biyar kafin Saifullah ya samu ƙarfin tashi ya bar ɗakin sakamakon kiran Sallah da aka yi. Jiki a sanyaye ya bi jam'i ya koma ɗakin sa, duk wani notin tunaninsa ya kwance akan mafita kafin can da kyar ya tuna da ai dama kiran gaggawa aka yo masa ya dawo, kuma kullum hanyar da aka hau ta nan ake sauka. Ji yayi kamar ya jawo lokaci zuwa tsakankanin magariba da isha'i da iyayensa kan zauna. *** Tuki ya ke kamar wanda ya ke shirin rasa ransa da gangan, zagi kuwa ya sha ba adadi a haka har Allah ya isar da shi gidan da su ke zaune. Nan ma fitowa daga motar ne ya gagare shi, kansa ya kifa bisa sitiyari ya na mai zubda hawaye. Karar da wayar shi ta ke bai sa ya ɗago ba balle ya duba ya ga wanda ke kiransa har wayar ta katse, aka kara kira karo na biyu, ta sake katsewa. Sai a karo na uku ya dago a fusace da niyar kashe wayar gabada ɗaya. Ko da ya ga number da ke kiran sa tuni ya daga ya na mai faɗin "Mummy......." "David na shiga uku David, dama nima na mutu na huta, na ƙara rasa miji! Philemonis dead, my husband is dead!! life is never fair to me!!!!" Mummy ce ta katse shi cikin ihu da kururruwa wanda hakan ba karamin gigita shi ta yi, cikin tashin hankali ya furta "Mummy calm down and talk to me, mai ya samu Dady?" "He is dead, Philemon is dead!" "Jesussssss" Cewar Dee yayin da maganar Mummy ya daki kunnan shi a karo na biyu. Kuka da kururruwa jama'a da ya ke ji ya na tashi shi ya daɗa gasgata abin da zuciyar shi ke kokarin karyatawa. "But why? How? When?" Tambayar da ya jero mata kenan. kuka ne ya ci karfin ta har ta kasa buɗe baki ta bashi amsa. Tausayin ta ya lullube shi, ya na kukan rashin Amatullah, ashe shi ba rashi yayi ba, Mahaifiyar shi ita ce ta yi rashi babba. "It's ok Mummy, ki yi hakuri gani nan zuwa" Ya aje wayar cikin zafin nama ya shiga ciki. Cikin kankanin lokaci ya shirya tsaf, kamar goma daidai ya hau titin da zai sada shi da birnin tarayya. **** A daddafe Saifullahi ya iya hakurin jiran ayi sallan magariba. Bai ko tsaya azkar ba ya tashi ya je wajen zaman iyayensa ya zauna yana jiran su. Ɗaya bayan ɗaya su ke fitowa nan yake gaida su, amsawa su ke suna mai masa fatan alkhairi a aurensa. Bai ji dadin fitowar mahaifinsa ba amma sai ya ji sanyi ganin baban Sasa ya fito "Fitinannen tsoho dole ka yi ƙarfin fitowa sallah tun da ka gama haɗa fitina" ya samu kansa da fadin haka a zuciyar sa duk da murmushi ke kwance a fuskar sa. "Baban Sasa gara da ka fito dama ina shirin shigowa in same ka ne, wannan makaranta tamu yan bakin ciki ne, sun min kiran gaggawa" yace yana yamutsa fuska kamar wanda aka shiga hakkinsa da gaske. "Subhanallah! Yaushe ake bukatar ganin ku" Baban Sasa ya faɗi ba tare da ya samu shakku a maganar saifu ba. "Wai nan da Laraba fa Baban Sasa, ka ga ba samun jirgi zan yi ba gara na kama hanya zuwa Lagos gobe na fara rage zango, domin fara Shirin tafiya, idan na ci sa'a nan da kwana biyu ma zan iya samin jirgi" ya fadi yana mai sinne kai. "Amma da matarka za ka wuce ko? Ko jiƙa jibge kake tunanin mu ka yi?" Baba Anas ya ce yana ƙara yamutsa fuska cikin takaicin hali irin na ɗansa. "Anas!!!" Baba Zubairu da Baban Sasa su ka faɗi a tare cikin sigar tsawatarwa. "Saifullahi zango nawa ya rage maka a Rasha" Baba Zubairu ya faɗi yana kallon Saif. "Zangon Ƙarshe nake zan haɗa masters ɗina, inshaAllah nan da wata uku na kammala da yardan Allah" yace cike da ladabi, kallon sa Baba Anas yake kamar ya kwaɗe shi. "Toh madalla, abu ya kawo gangara, tun da buri na ya cika ka je, in ka dawo nan da wata uku sai matarka ta tare inshaAllah" fadin Baban Sasa yana mai mikewa don shiga gida. "Amma Baba sai ku ta biye masa" Baba Anas ya ce don ba haka ya so ba. Ko ta kansa Baban Sasa bai yi ba illa ya wuce abin sa ya tafi don ya shiga cikin gida Saifullahi na bin bayan sa yana mai cika shi da daɗin baki. "Ni Anas na rasa irin ka, wai me Mairo ta baka ne? Kwatakwata in dai abin da ya shafe ta ne ko yaranta idonka rufewa yake yi. Ina laifi yaron nan bai nuna rashin so ba amma ita yar gwal din ƙaton arne ta kawo don ta aura. Wallahi ka yi ma kanka faɗa" Baba Zubairu ya ce cikin fushi. Nan duk su ka shiga faɗin albarkacin bakin su akan bakin halin Amatullah da mahaifiyar ta duk da cewa su kansu ma su faɗin sun san ƙarya su ke shirgawa. *** A bakin mahaifin ta Amatullah ta ji batun tafiyar Saifullahi wanda hakan ba karamin kwantar mata da hankali ya yi ba, domin kuwa idan akwai abin da ta ke fargaba ya bi bayan ranar tarewar ta gidan Saifullahi. Washagari da safe Saifullahi yayi harama duk da kuwa jirgin sa na zuwa Lagos na yamma ne, gani ya ke zaman jiran lokacin tafiya tsautsayi ne. Sanye ya ke cikin kananan kaya, shuɗin riga mara hannu da shudin wandon jeans yayi kyau kamar bakin bature. Bayan ya sallami Hajiya har zai fice daga gidan ya hangi ɓangaran su Amatullah, Gwaggo ce ta ratsa zuciyar sa, ya tuna alkhairin ta gare shi kuma ya san tabbas idan ya je yiwa Baban Sasa sallama sai ya tambaye shi ko ya shiga wajan amaryar ta sa ta dole, dan haka ya yanke hukuncin shiga ba dan komai ba ko dan darajar Gwaggo. 'Allah ka min katangar karfe da ganin bakar fuskar yarinyar nan!' Addua'ar da ya ke yi kenan yayin da ya nufi bangaran su Amatullah. Da sallaman shi da shigar shi falon lokaci daya ya yi su, tsayawa yayi baki bude tamkar wani soko sanadiyar abinda idanun sa yayi tozali da shi, Amatullah ce kwance a bisa kan doguwar kujera, irin wannan kwanciyar na rigingine. Bai san sanda ya bi ta da kallo tunda daga dogayen yatsun kafarta, har zuwa dogon wuyar ta, zuwa kanta da ke daure da kallabi ba, Yayinda bugun zuciyar sa ta karo cikin kaduwa da ganin baiwar ubangiji. Sanye ta ke cikin koran materials riga da siket, da ke Amatullah mashaAllah akwai diri, kayan ya zauna jikin ta ya yi mata cif cif. Littafin husnul muslim ne kife a kirjin ta, hawayen da ke gangarowa daga idanun ta da yake a lumshe ne ke nuna alamun ba bacci ta ke yi ba. A hankali ya furta "Hasbiyallahu wani'imal wakil" Hakan yayi daidai da fitowar Gwaggo daga dakin ta, ganin yanda Saifullahi ya shagala ya na kallon Amatullah wacce daga ganin alama ba ta san da shigowar shi ba, da niyyar Amatullah ta farga ta furta "Ah ah Saifullahi shirin tafiyar kenan!" Jin haka a zabure Amatullah ta bude Idanun ta su ka yi ido hudu da Saifullahi wanda yayi tsaye bakin kofa. A rikice ta tashi da sauri ta nufi dakin ta, Saifullahi kuwa ganin Gwggo bai sa ya fasa bin ta da idanu ba har ta shige daki. "Saifullahi ka na ji na kuwa?" Gwaggo ta sake magana a karo na biyu ta na mai duban Saifullahi wanda sai a sannan ya lura da fitowar Gwaggo, cike da jin kunya ya durkusa har kasa, yana mai sosa kyeya ya furta "Iyye? Na'am Gwaggo barka da asuba, ai ban ga fitowar ki ba ne" Gwaggo na murmushi ta ce "Eh gaskiya dai ba ka gani ba, cewa na yi shirin tafiyan kenan" "Eh Gwaggo, dama sallama na zo na mi ki, sai Allah ya dawo da ni" Ya bata amsa a takaice domin kuwa Allah Allah ya ke ya fita daga gidan tsabagen kunyar da ya rufe shi. Kamar wanda ya ke kan ƙaya yayiwa Gwaggo sallama a gaggauce ya fito. Haka ma Baban Sasa, sallamar a tsatsaye aka yi ta domin kuwa sam ba ya cikin hankalin sa. Cikin ikon Allah ya samu motar da zata kai shi Kaduna tun kafin ya isa tasha saboda fitowar direbobi masu lodin Kaduna Abuja. Gidan baya ya shiga a cikin Sharon ɗin da ya samu. Wayar sa ƙirar Sony Ericson ya ɗauko yana karanta abu a yana gizo duk don ya cire tunani a ransa amma ina, maimakon ya ga rubutu, surar Amatullah kawai ya ke gani a fuskar wayar sa. Yana jin ana faɗin mata masu mazauna da dukiyar fillo bai taɓa haɗuwa da wanda nata su ka zauna daidai da jikinta ba. Lumshe ido yayi maimakon ya bar gani sai hango ta yayi kamar ta nufi shi cikin murmushi. "Yaa Rabbi" ya samu kansa da neman agajin Ubangiji. [2/15, 3:53 PM] +234 814 945 8522: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA HUƊU Amatullah da tun bayan fitar Saifullah gaban ta ke faɗi, ta san tsayuwar da yayi kallon nan na kaskanci ya ke mata. Ta ji haushin ganin ta da yayi a haka. Kirjinta ne ya mata nauyi duk da ba ta son tuno halin da Dee zai kasance abin ya gagara. Saboda kwallafa rai har mafarki ta yi ya zama gawurtaccen pastor hakan ya sanya ta tashi da nannauyyar ƙirji. Tun da ta yi sallah ta yi azkar ɗinta na safe ta ke karanta addu'ar da ake lokacin ƙunci da damuwa, can dai ta Hau kan kujera ta miƙe baya. Rashin jin dadin kwanciya da hijabi ya sa ta cire ashe za ta yi mummunar gamo ne. Sai da ta tabbatar da ya fice da daɗewa ta sanyo hijabinta don zuwa gaida iyayenta a cikin gida. "kuma in kin shiga ɗakin hajiya ka da kiyi gaggawan fitowa, yanzu banda Kasancewar ta matar babanki uwar mijinki ce, saura kije kina soliɓiyanci" ta tsinkayi mahaifiyarta na faɗi yayin da za ta bar ɗakin. Haka kuwa aka yi, sai da ta gaida sauran ta shiga ɗakin hajiya. Sai da ta zauna a ƙasa sannan ta gaida ta cike da ladabi. Hango hawayen Saifullah da hajiya tayi ne ya sa ta kauda ido gefe ba tare da amsawa ba. Sai da ta yi zaman mintoci sannan ta Mike don gaida Baban Sasa. A nan ta iske wasu daga cikin Baffaninta ta gaida su kafin ta isa kusa da baban Sasa kamar za ta shige jikinsa. "Jiya ban ganki ba, nace har kin fara kewan na ainihin ne" yace cikin sigar tsokana. Sinne kai ta yi tana dariya sannan tace "Ai zan dinga ganin fuskarka kullum a tashi fuskar in maka addu'a da ka zaɓa min baƙin bature, nagartacce tsatson Muhammadu Jamoh" ta ce tana kwantar da kanta a jikinsa. "Ki yi hakuri kinji. Ke kin san shi ma, hajiya Sahura ba ta san ni ba sai bayan ta tare, hajiya Talatu na haka, kadarko ce kawai mu ka yi soyayya kan aure. Kinga a tsawon zaman mu da su ban taɓa ganin halittu mafi soyuwa a gare ni sama da su ba. Ki zama nagartacciyar mata soyayya zai zo daga baya. Ki yi hakuri ki yafe min... " " shisssssssssssshhhhhh!!! " tace tana rufe bakin sa. " Babu abin da ka min sai gata da kauna. Ka tabbatar min da duk cikin zuri'a ni ce ta ƙasan heart" ta ce tana dariya, shi ɗin ma dariya yayi. *** Tun isar sa Abuja jiya da azahar ya ke rarrashin Mahaifiyar shi, mijin na ta ya mutu ne irin wannan mutuwar fuji'a, babu ciwo aka wayi gari babu shi Allah ya ma sa cikawa. Alhinin mutuwar da kuma shirye shiryen bikin birne mamacin bai bashi daman zama yayi tunanin Amatullah ba, duk da kuwa zafin rashin na ta ya zame masa tamkar gyambo cikin zuciyar sa. A safiyar aka shirya mamacin tsaf cikin riga da wando suits, kwance cikin akwati da ya sha ado da furanni iri iri. Akalla motoci uku ne su ka jeru wajan rakiyar mamacin, in da Dee ke tuka motar da ke dauke da Mamacin, hanyar Yola su ka dauka in da za a yi bikin birne mamacin. **** Igiyar auren Saifullahi bai hana Amatullah tunanin Dee ba, wanda hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali ya ke ba, ta na matar aure ta na tunanin wani namiji daban, har ta na duba wayar ta ko za ta ga sako ko kira daga gare shi ya shigo. Ganin hankalin ta na shirin gushewa ya sanya ta ɗauro al'wala, sanye da hijabi ta kalli gabas, da kyar ta iya idar da raka'a biyu. Tun tana addua a hankali har kuka ya ci ƙarfin ta ta fara addua a bayyane, tana cewa "Ya Allah ka rufa min asiri, ya Allah kar ka kamani da laifin soyayyar da na ke yi wa wanin mijina, ya Allah ka yaye min wannan masifar da na ke ciki, Allah kar ka jarrabe ni da wannan masifar bayan ka sanya tazara mafi girma a tsakanina da wannan bawa na ka, ya Allah.....ya Allah...ya Allah..... ya Allah......" Kuka ne ya ci karfin ta, ta kasa magana sai shasshekar. **** Yanda Amatullah ke cikin halin ha'ulai, haka Saifullahi ke cikin halin damuwa, tun barowar shi Zaria babu abinda ya ke tunani face kyakkywar surar Amatullah, haka zalika ko ya rufe idanun sa da niyar runtsawa ita ɗin dai ya ke gani. Abin takaicin shi shine wai kamar shi Saifullahi duk surar da ya sha gani birjik a titin Allah a kasar turai ya rasa wanda zai gigita shi wai sai na bagidajiya, yar kauye kamar Amatullah!! Zaune ya ke Airport ya na jiran isowar jirgin da zai tashi da su zuwa Lagos, dake an sami delay na wajan minti talatin kafin isowar jirgin. Idanun shi lumshe yayinda ya kifa fuskar sa cikin tafikan hannun sa, yayi kusan minti goma cikin wannan halin kafin daga bisani ya dago yana mai zaro wayar shi daga cikin aljihun wandan sa, kai tsaye wajan hotuna ya shiga in da ya lalubo hoton budurwarsa Aysha Ayuba Daneji, wacce aka fi sani da Ayush. Ayush 'yar Kano ce, irin 'yan matan nan ne marasa kamun kai, da tarbiya, Amma idan wajan wayewa, ado, matse jiki da fidda tsaraici idan aka same ta sai dai a shafa fatiha. Kasancewar ta ɗiyar hamshakin mai kudi, primary school kaɗai ta yi a Nigeria, hatta secondary turai ta yi, saboda haka za a iya Kiran ta rainon turawa. Tare su ke masters da Saifullahi, duk duniya ta ce babu wanda yayi mata sai Saifullahi, shi kuwa dama faɗuwa ce ta zo ma sa daidai da zama, domin kuwa burin shi ne auran wayayyiyar mace. A shekaru Ayush ta girmewa Amatullah, saɓanin Amatullah ita fara ce tas, duk da dai ta kan ƙara da na kanti. In aka dauke fari da wayewa babu abin da za ta nunawa Amatullah. Idanun sa kan hotan Ayush, wanda take sanye cikin kananan kaya riga da wando, kan nan ba dankwali an zubo da gashi har kyeya. Ajiyar zuciya ya saki, a zahiri ya furta "Me zan yi da wannan bagidajiyar when I've someone like you? Haba ga mace nan har mace zuciya ta za ta addabe ni da wata yar kauye mamalam!" Jin ana sanarwar jirgin su zai fara boarding ya sanya shi tashi da sauri ya na mai tura wayar cikin aljihu. [2/17, 9:31 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA BIYAR Allah ya kai su Dee Yola lafiya, kasancewar da daddare su ka isa, Nan family house din mamacin aka sauka, in da su ka tarar da yan uwa da abokan arziki suna tsimayin isowar na su. Tun a daren ranar Dee da ƴan uwan mamacin su ka fara shirye-shirye bikin birne gawar, wanda za a yi nan da kwana goma sha biyu zuwa sha uku. Kamar yanda kwanaki su ka yiwa Dee tsawo, haka su yi ma Amatullah, kwana bakwai da aka ba su hutun midsemester ɗin ya zame mu su kamar shekara bakwai, a ɓangaran Dee; rashin Amatullah da mijin Mahaifiyar ta shi ba karamin karamin girgiza shi ya yi ba, gashi shirye shiryen birne gawar kaɗai ya isa ya gajiyar da ɗan adam. A ce an rasa mutum amma sai an yi gagarumin biki ranar da za a rufe shi? Shi kam Dee wannan na ɗaya daga cikin al'adar kiristanci da sam bai ma sa ba. Amatullah kuwa a nata ɓangaran yanda matan gidan kan kira ta da Amarya duk da tana hango isgilanci a sautinsu yayin da su ke ambato mata wannan sunan ya hana ta sukuni, Ba wai isgilancin ke ƙona mata rai ba, jin da take hakan kamar danganta ta da saif ne ya fi komi ɓata mata rai. Angon na ta kuwa tun da ya sa kafa ya tafi babu wanda ya sake jin ɗuriyar shi, hatta Baba Anas yayi kokarin samun shi a waya, amma abin ya gagara, shi kuma bai kira ya shaida mu su isar sa Russia ba. Ranar Laraba da safe ta tashi da matsanancin tsanar gidan, tunanin wajen zuwa ta ke yi don ta samu sauyin iska. "Zulaikha" Kawai taji ɓarin zuciyarta ta ambato mata hakan ya sanya ta sakin murmushi. Kamar yadda ya ke al'ada garesu gaida iyayensu bayan sun idar da azkar hakan ta tashi ta yi, haka kuma kamar yadda mahaifiyarta ta umurce ta duk ta shiga ɗakin Hajiya ta kan ɗan ɓata lokaci, don ko jiya sai da ta kama mata ninkin kaya sannan ta fito. Cikin sa'a ta samu Baba Anas zaune yana sauraron sashin hausa na radiyon BBC, gaishe su tayi a ladabce sannan ta yi shiru tana ƙara sunkuyar da kai. "Ƴar Baba Anas da magana a bakin nan" Baba Anas ya ce cikin sakin murmushi. Ƙara sunkuyar da kai ta yi. Harara Hajiya ke watsa mata tana zagin ta a zuciya, ita da Amatullah za ta hakura da shigowa ɗakin ta da ya fiye mata komai. "Ehmm! Amatullah Ina saurarenki" ya ce yana mai rage sautin radiyon sa don ya ji me take tafe da shi. "Baba don Allah izininka nake nema, ina son in duba ƙawata Zulaikha" tace gaban ta na faɗuwa, tsoro bai sake cika ta ba sai da ta ɗan ɗaga kai ta kallo sashin Hajiya ta ga harar da ta watso mata, ta ke ta shiga da na sanin tambaya tun farko. Gani ta yi shine mahaifin mijinta a tunanin ta zai iya bata izini makwafin mijin nata. "Allah ya dawo da ke lafiya, kar dai ki kai almuru a waje" yace yana murmushi. "Na gode Allah ya kara girma da lafiya" ta ce cikin farin ciki. "Aameen Ƴar Baba" yace Shima cikin farin ciki. Da haka ta tafi ɗakin mahaifiyarta cikin farin ciki, jinta take zaman ta a gidan Jamoh kamar wacce ke zaune a gidan maza. Da wannan farin cikin ta iske mahaifiyarta ta faɗi mata yanda su ka yi da Baba Anas, tana kallon yadda murmushin fuskar mahaifiyarta ya ke dusashewa a hankali. "Yanzu ke sai ki ɗauki jiki ki fita tsigau tsigau se kace wacce ba ta da mafaɗa, ko da can kan ki yi aure haka kike fita kamar baƙar Leda balle yanzu da aure ke kanki? Mijinki kawai zai baki izini in bari ki fita, sakarai mara kishin kai" Gwaggo ta faɗi tana tashi daga wajen. 'Oh ni mai na yi na laifi yanzu da Gwaggo ta ke kausasa halshe akai na. Allah na tuba ka yafe ni ba zan sake ba' ta ce cikin ranta tana mai tausayin kanta. Wayarta ta ɗauko ta kunna cike da addu'ar ganin saƙo daga Dee, maimakon nashi sai na mahaifinta ta gani wanda ya wuce Abuja a safiyar Litini, nasiha ce da addu'a haɗe da fatan alkhairi gareta. Tayi murna sosai, kaunar mahaifinta na ƙara cika ta, gani take wacce ta rasa uban da zai bata kariya da tallafi a duk halin da za ta shiga lallai ta yi rashin majingini babba. Ba ta fita daga akwatin tura saƙo ba ta lalubo lambar zulaikha ta aika mata da sako, daga nan ɗauko littafin 'the end of the world' na Dr. Muhammad Abdulrahman Al-arifi ta fara dubawa cikin natsuwa, tsoron Allah na ƙara ratsa ta. Ba ita ta tashi ba sai wajen ƙarfe goma sha ɗaya na rana in da ta tashi ta je taya mahaifiyar ta ɗaura sanwar abincin rana. *** Zulaikha ba ta ga saƙon ba sai kusan ƙarfe goma sha biyu, "An ɗaura aure na da yaya Saifullah ranar Asabar bayan sallar asuba" ta karanta ta ƙara karantawa tana mai ƙaryatawa. Numbar Amatullah ta latsa kira ya ci ringing har ya tsinke ba tare da an ɗaga ba. Haka ta dinga kira ganin ba a ɗaga bane yasa ta kira maman Jaafar. "Zully ke ce yau da kira" tace tana ɗagawa. Su kan yi ma zulaikha tsiyar ba ta kiran waya walau ta turo sms ko kuma ta ishe mutum da flashing. "Yoh maman Jaafar ai dole na kira yanzu, kinji an ɗaura auren Amatullah wai" tace cikin mamaki da rashin yarda. "Aure kuma, sai kace ƴar takarda" maman jaafar tace cikin ƙin yarda. "Yanzu na ga text ɗinta, na kira kuma bata ɗaga ba, amma Daman akwai alkawarin aurenta da Yaya Saifullah ɗin" Zulaikha ta faɗi tana son ta haska ma maman Jaafar yiwuwan auren. "Allah sarki Dee Yusuf kuma kin san ranar Juma'a na kwatanta masa gidansu, yanzu shike nan ba rabon sa bane" maman jaafar tace cikin tausayawa don ba za ta mance tsantsan son Amatullah da ta hango a idanunsa ba ranar.. "Haba! Ai in har Dee ya isa gidan su Amatullah toh tsaf Baban Sasa zai sa a ɗaura auren nan. Ai jin auren nan yake kamar in ba ayi ba ya rasa wani sashi na jin dadin duniyar sa ne" Nan zulaikha dai ta ba maman jaafar labarin da ta sani a takaice. Tayi mamaki kwarai musamman da ta ji Dee Yusuf ba musulmi bane. Da ga baya su ka yi sallama akan sai sun ji daga Amatullah. **** Ana sauran kwana biyu bikin birne mijin mahaifiyar Dee aka koma makaranta. Da sassafe Amatullah ta hada nata ya na ta cike da farin cikin za ta bar gidan ta huta da habaice habaice. Kafin ta ta tafi sai da Gwaggo ta zaunar da ita ta mata fada sosai, irin wannan fadan mai shiga jiki. Har sun yi sallama ta dau jakar ta Gwaggo ta dakatar da ita ta na mai fad'in "Amatullah?" "Na'am Gwaggo" Amatullah ta amsa jiki a sanyaye. "Na yarda da ke tun kafin nauyin aure ya hau kan ki, bare yanzu, dan Allah ki tsare mutuncin ki, dan Allah Amatullah, kin dai san ke matar aure ce, wannan yaran da na ji ana magana akan shi......" "Gwaggo....." Amatullah ta katse ta yayinda idunun ta ke fidda kwalla. Kana ta kara fadin "Gwaggo kin ce kin yarda da ni....." Tashi tsaye ta yi ta zo gaban Amatullah, ga mamakin Amatullah sai ga Gwaggo ta ruko hannayen ta biyu, cikin sassanyar murya ta furta " Na yarda da ke ɗiyata, Amma zuciya ba ta da kashi, ba na so in ji ance ko sannu ta haɗa ki da wannan yaron, dan Allah Amatullah ki rufa mana asiri, kar ki ga kamar ban damu da lamarin ki ba, kawai ina kawaici ne" Kai Amatullah sannan ta ce "Na mi ki alkawarin cigaba kare mutunci na da hakkin addinina kamar yanda na saba Gwaggo" Cikin jin dadi Gwaggo ta rakota har kofar falo, sannan ta umarce ta da ta je ta yiwa Hajiyar Saifullahi sallama. Ta ci sa'a ba ta sami Hajiya ba, Baba Anas ma gun Baban Sasa ta same shi tare da su Baba Zubairu. Nan duka su ka mata nasiha tare da sa albarka, Baba Anas ne ya bata kudi a cewar shi yanzu dole ya na wakiltar Saifullahi, gashi babu yawa. zuciyar ta cike da farin cikin addu'oi da ta sha daga gare su ta wuce makaranta. Tun da ta sa kafar ta cikin makarantar gaban ta ke faduwa ba dan komai ba dan Dee Yusuf da ta ke fargaban gani, da ta hangi namiji ya doso ta sai ta yi saurin kau da kai, kai har gani ta ke kamar ma gizo ya ke mata. Kirjin ta na dukan uku uku yayinda ta ke karanta 'Lailaha illaanta subhanaka inni kuntu minil zalumin'. Ba ita samu kwanciyar hankali ba sai da ta ganta cikin hostel. Kaf ɗakin ita ta riga kowa kowa dawowa. Mayafi da jaka ta aje ta shiga gyaran daki.. [2/20, 8:39 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA SHIDA Tun tana tsumayen Zulaikha har ta tabbatar da ba za ta dawo a ranar ba, hakan ya sanya ta zama sukuku kamar raguwar ciwo, duk yanda ta so kar ta zurfafa tunani ta gaza hakan ya sa ta ɗauki littafin da ta fi so watau Don't be Sad ta fara bibiyar hikimomi na samun nagartaccen kwanciyar hankali,da haka bacci ɓarawo ya sace ta. Washegari Monday basu da aji sai ƙarfe tara na safe, hakan ya sanya ta ɗaukan lokacin ta wajen shiryawa. Takwas da rabi daidai ta fita daga hostel. Sauri take don ba ta fatan ganin Dee. Ta kai daidai biological science da za ta bi ta je chemistry department in da za su yi ajin ta jiyo sallama. Ƙara sauri ta yi don ba ta da niyyar tsayawa duk da sautin muryar kamar wanda ta sani. "Anty Amatullah an tashi lafiya" ya faɗi hakan ya sanya mata juyawa, tana ganin fuskarsa ta juya cikin sauri ta cigaba da tafiya. Ba za ta ce ga yadda aka yi yazo gabanta ba. "Don Allah kiyi hakuri, wallahi na yi tunanin ya faɗa miki ne shi ya sa na kaiki don Allah ki gafarce ni" yace cikin sanyin murya. "Babu laifin da ka yi min Yaya Hamza, ban tsaya bane saboda guje ma keta haddin aure. Babu sauran Alaƙa tsakanina da Dee. Ina masa fatan Alkhairi" tace tana mai jan jikinta ganin Taran na gabatowa. "ban gane haddin Aure ba, ai ba a sanin maci tuwa" yace yana dariya. "wannan miyar ta daɗe da ƙarewa. Yau kwana goma kenan da ɗaura min aure, David bai faɗa maka ba?" tace tana ƙirƙiro farin ciki. "Kinga yau kwana goma kenan da mutuwar mahaifin Dee Yusuf. Kice double rashi yayi" ya faɗa cike da Alhini tare da tausayin amininsa. "Allahu Akbar, Allah ya jikan musulmai, su kuma Allah ya basu hakurin rashi. Bari in je kar in latti" tace tana barin sa tsaye. Mamaki ya cika shi ainun, duk ya cika da tsarguwa akan tashin hankalin da ya gani a idon Dee. Amatullah kuwa tana gama magana da shi ta juya ta isa aji cikin sauri, ta shiga ko hutawa ba ta yi ba malamin ya shigo, karatun rabi da rabi ta fahimta saboda tsilla-tsilla da zuciyarta ke mata akan halin da Dee Yusuf ke ciki da istigfari da take yi. Sai da azahar ta samu ganin su zulaikha wainda su ka zo latti. "Amarya!" su ka haɗe bakin faɗi. Dariya ta bi su da shi wanda ko laɓɓanta bai wuce ba. Nan su ka zauna suna mata tambayoyi kamar wacce ke gaban kuliya. Wasu ta amsa musu wasu ta sa musu dariya kawai. "Kinga Amatullah ki kwantar da hankalinki, zan kawo miki littafan hausa ki karanta saboda ki san yanda za ki tafiyar da Megida Saifullah. Duk taƙamarsa da ya ɗanɗana zumarki dole ya so ki, dole yai marmari ki" maman Jaafar tace tana mai dulmiyar da Amatullah cikin duhu don ita ba ta san wani abu zuma ba, ita Sam ba ta damuwa da sanin abubuwan da su ka shafi wannan, ita dai a barta da karanta littafan addini sun fi komi sa ta nishaɗi. Haka dai Maman Jafar ta shiga yi mata bayani akan yanda za ta sace zuciyar angon na ta, ita kuwa Amatullah jin ta take kawai, gani ta ke soyayya tsakanin ta da Saifullahi abu ne mara yiyuwa. Sai dai biyayyar aure. *** Ranar talata ya kama ranar bikin birne mamacin ƴan uwa da abokan arziki sun yi dandazo a Coci, duka sanye cikin bakaken kaya mazan su da matan su. Gawar mamaci aje gaban jama'a cikin akwatin da aka kayata da furanni. An bude taron ne da yiwa mamaci addu'a bisa ga al'adar kiristanci na raye-raye, bayan an gama minister ya ba da taikaiceccen jawabi akan rayuwa da mutuwa, haka kuma aka bawa ɗan uwan sa mafi kusa da shi damar jawabi akan halayyar mamaci da abinda ya bari na iyali. Tun da aka fara Dee bai bar gefen mahaifiyar shi ba, wacce in ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanun ta. Minister ne ya bada taikaiceccen lokaci ga jama'a domin mika ta'aziyan su ga iyalan mamacin, kafin aka dauki gawar zuwa makabarta su na mai cashewa yayinda kiɗa da waƙa ke tashi, da ya ke babu laifi mamacin mai jama'a ne, na kasa da na mota haka aka dunguma zuwa makabarta. Hankalin mahaifiyar Dee bai tashi ba sai da ta ga an ɗauki akwati an sa cikin rami, nan ta ƙwalla ihu ta na mai kiran sunan mamaci yayinda da ta ke kokarin shiga ramin, da kyar Dee tare da taimakon kannen mahaifiyar ta shi su ka fitar da ita daga makabartar. Babu laifi an cashe, an kuma ci an koshi domin kuwa gangarumin biki aka yi a ranar, idan aka ɗauke Dee da mahaifiyar sa, da kannan sa biyu babu wanda bai cashe ba. Ranar haka aka kwana ana raye raye da ciye ciye family house ɗin gidan mamacin. *** Bayan kwana uku Dee zaune a falo, hannun sa biyu bisa kuncin sa ya rasa abin da ke masa daɗi a duniya, idan akwai tunanin da baya so ya bi bayan na komawar shi makaranta ba, ba dan komai ba sai dan Amatullah, Sam ba ya fatan sake saka ta a Ido alhalin ta na matar wani, tsananin kishi da bakin cikin auren ta ya fi komai damun shi a halin yanzu. Babban falo ne mai dauke da manya manyan kujeru, da ya ke family din mamacin babu laifi suna da arziki. Bai ji shigowar ta ba, kamshin turarenta ne ya bakunci hancin shi. Dab da shi ta zauna kugunta na gogan na shi yayin da ta ɗaura hannu bisa kafaɗar shi ta na mai fadin "Dee is owk na, ka fa tuna sanda Dady ya mutu kai ne kan gaba wajan kula da ni, you told me Dady will not be happy if I keep crying.......Dee" "I'm not crying Mimi" Cewar Dee yayinda ya dago ya na duban cousin ɗin ta shi da ya kira Mimi. Mimi diyar Yayan mamacin ce, ma'ana uncle din Dee da ya mutu watanni uku da su ka wuce. Yar matashiyar buduwar ce mai kimanin shekara goma sha bakwai a duniya, irin wannan siraran da ake danganta su da model, mashaAllah idan kyau ne ko cikin larabawa ta shiga ba a mata kushe ba, Mimi kamar dawisu ga kyau ga ado. Kusan yanayin farin ta daya da Dee, haka kuma dangantakar ta da Dee dangantaka ce na shakuwa kwarai, hatta mamatan biyu sun sheda wannan shakuwar. Kanta ta daura bisa kafadar Dee, cikin alhini ta ce "It's so sad you know, just three months fa da mutuwan Dady, yanzu kuma uncle sai ka ce abin sa hannu....." "Shhhhhh" Dee ya katseta ta hanyar dora hannu bisa lebenta, hannun sa ya sa cikin na ta sannan ya ce "Such is life, we lost people we love, ko da kuwa babu mutuwa, so let's just be strong and pray whoever we lost ta mutuwa ko ba mutuwa, are in a better place, owk?" Kai ta gyada alamar eh. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani ta furta "Dee?" "Yes dear" Dee ya amsa mata a takaice. "Please ka yi ma Mum magana ta barni na zo school din ku, na ci Jamb fa, I want to study pharmacy" Gaban Dee ne ya fadi jin ta furta pharmacy yayin da Amatullah ta sake faɗowa ran shi. Cikin kokarin boye damuwar sa ya amsa mata da "Ke din ce Mimi kin fiya rawan kai shi ya ba ta so ki yi nisa da ita, well Pharmacy is good course, plus you have the brain, but why ABU?" "Because you are in ABU...." Ta amsa cike da shagwaba har sai da ta sanya ya murmusa, shi kan shi ya manta rabon da yayi fara'a. "Mimi rigima, me wey dey graduate in the next 6 weeks? Abi you want make I spill over? Infact makarantar ta fita rai na" "No I want you to stay for me, go for your masters mana...." Ta fada cikin magiya. Kai ya girgiza "Ah ah Mimi, zan dai yiwa Mum magana ta bar ki, saboda ABU is a great University, Amma I can't stay darling, I really I can't... " Yana maganar ne yayinda ya ke hango Amatullah cikin zuciyar sa. *** Ango a na shi ɓangaren tun komawar sa Russia ya ke neman hanyar da zai shaidawa Ayush maganar auren da aka ɗaura masa a gida, amma ya kasa tsabagen shakkar ta da ya ke. Haushin Baban Sasa ya sanya shi canza layin waya ya kuma ki kiran gida da sabuwar number din ta shi. Zaune su ke cikin ajin su, kusan miti talatin da fitar lecturer, kowa ya watse ya bar su. Idanu ta kafe shi da su cikin kallan zargi ta ce "Saif ni fa na kasa gane ka, are you owk?" Kyeya ya sosa, da ka gan shi ka ga mara gaskiya. Ya na dan murmushi ya ce "No babu komai fa, tunanin wani lamari da ya sami abokina ne ke damuna" Ya tsinci kan sa ya na mai mata karya. "Abokin ka? Wani abokin na ka? Menene ya same shi?" Cewar Ayush yayinda ta tattaro duka nutsuwar ta gare shi. Kai ya girgiza mata tare da cewa "never mind, yanzu in tambaye ki misali, just misali fa, ace kawai muna zaune kasar nan kawai sai a min waya a ce an daura min aure a gida......." "Burauba!!!!" Ayush ce ta katse shi, kana ta kara da "Za ma a kwance ne!! Kut rainin wayo ma kenan! Shi abokin na ka ne yayiwa budurwar ta shi wannan rainin wayo? Cousin aka ɗaura masa halan? Dan rainin wayo wallahi ya na sane! Karya ya ke wallahi, akwai wanda ya isa ya tinkare ni da wannan rainin wayon ma!!!!!!!" Jikin Saifullahi tuni ya kara sanyi, yayinda yayi sororo ya na duban ta. Cikin ran sa kuwa cewa yayi "Baban Sasa ya kwanto min kura......" [2/23, 9:18 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA BAKWAI "Ya na ga ka wani saki baki ka na kallo na? I don't get you! Yanzu kamar kai wa ya isa ya maka auren dole? Sai dai ka na so kai ma" Cewar Aysuh cike da tsiwa, ta na magana ne idanun ta cikin na sa. Ganin dai in yayi sake allura ce za ta tono garma, dan haka Saifullahi na mai sosa kyeya ya furta "Ayush kenan, Allah ya sa mu dace...." "Ba Allah ya sa mu dace ba, answer me! Yanzu akwai wanda zai iya ma maka auren dole?" Ayush ta sake katse shi ta na masa irin kallon nan mai cike da alamar tambaya. "Aysuh?" Ya kira sunan ta da kakkausar murya. "Yea? Ina jinka" "Kin yarda da ni?" Kai ta gyada masa ala'mar eh. Hannun ta biyu ya riƙe kana ya ce "Alhamdulillah, toh ina so ki yarda ki kuma amince babu wani mahaluki a duniyar nan da ya isa ya sanya tazara a tsakanin mu" Cikin jin dadin maganar ta sakar masa murmushi mai kayatarwa tare da faɗin "I trust you Boo, and I love you so so much" "I love you more Ayush" Cewar Saifullahi, cikin ransa ya na mai yakinin kare hakkin soyayyar su daga dukkanin fitinar Baban Sasa. **** Sai da ya ƙara kwana uku bayan bikin jana'iza kafin yayi haramar komawa Zaria. Ranar juma'a da safe ya tashi da shiri cikin ran sa ya na mai baƙin cikin komawar sa makaranta. A ɗaki ya tadda mahaifiyar shi, zaune bisa gado, kallo daya za a mata a tabbatar da damuwar da ke tattare da ita. Gaban ta ya je ya durkusa, cike da lababi ya ce "Mummy, wannan damuwar da na ke ganin ki ciki ya na breaking heart ɗina, it makes me want to stay with you and forget about going back to school Mummy...." "Shhhhh!" Ta katse shi ta na mai dafa kan sa, kan ta ce "David my son, damuwa ya zama dole, rashin masoyi abu ne mai wuya, you will not understand, I hope you don't have to experience it in your life my son....." 'I have Mummy, I've lost Amatullah forever' Cewar Dee cikin zuciyar shi. "Amma rayuwa ba za ta tsaya ba, life goes on, so ina ba ka umarnin komawa makaranta, ka gama karatun ka, make sure you graduate with flying colors, kar ka manta ka na da ƙanne that are looking up to you, make us proud as always" Ta karasa maganar ne yayinda ƙwalla ya cika idanun ta. Cikin sassanyar murya ya furta "I will Mummy, I shall make you proud" "Ni kuwa David ya batun yarinyar nan da ka ke so? Kasan mutuwar nan bai bari mun yi magana ba, Kun sasanta? Yaushe za ka je Hadeja?" Gaban sa ne yayi mummunar faɗuwa, ya so Allah ya mantar da ita ba dan komai ba sai dan gujin bacin ran da za ta shiga idan ta ji yanda aka wulakanta shi kasancewar ya so ya musulunta sanadin soyayya. "Ina jin ka David, ko dai da matsala ne?" Ta sake tambayar shi cike da damuwa ganin yayi shiru. A hankali ya furta "Mummy forget about that girl, she is as good as dead to me" Shiru ta yi ta na duban sa, cikin ran ta tana so ta tambayi dalilin canjin ra'ayin Dee, amma kuma yanayin sa da kuma yanda ta ji muryar sa yayinda da ya ke maganar ya sanya ta sake shawara. Ta ce "I understand" Tashi yayi tsaye gudun kar ta sake jan maganar ya furta "Mummy bari na wuce, ranar Monday za ki wuce Abujan ko?" "Yes my dear" Ita ma ɗin tashi ta yi, tare da shi su ka fice tana masa nasiha, sai da ta tabbatar ya yi wa kowa na gidan sallama kafin ta raka shi har bakin gate, tana sa masa albarka idanu cike da ƙwalla haka su ka yi sallama, Dee ya ɗauki hanyar Zaria zuciyar shi ya kuna kwarai da gaske. **** Kamar yadda Zuwaira ta yi alkawari sai gata da littafai cikin jakar viva. Dariya sosai Amatullah tayi tana ɗaga su ɗaya bayan ɗaya. "Yanzu da wanne zan ji? Su chemistry dinnan masu shegen chain ko hadisan Kanon nan" tace cike da shaƙiyanci don ita dai ba za ta ce za ta yarda da kalaman maman Jaafar ba duk da cewa ta san bature na faɗin experience is the best teacher. "Samar masa lokaci za ki yi, don mahimmancin su, in kuma so kike ki zama bora a gida shike nan" maman Jaafar ta ce a dake. Dariya Zulaikha da Amatullah su ka sanya mata ganin yadda ta ke haɗe gira don Amatullah ta ɗauki zancenta da mahimmanci. "Ni fa tsoro na shine anya ma zai karɓe ni a matsayin mata mai daraja, duba da yanda yake hantarata ya ke min kallon wata ƙaskantaciyar halitta" tace cikin tausayin kanta. "By the time ya ci gasasshiyar hanta, sabuwar gashi ai dole ya sauko. Ke dai ga wainnan littafan ki karanta" tace mata cikin jadaddawa. Zuwan wasu yan ajinsu wajen ya sanya su chanza akalar zancen su nan aka koma zancen karatu tare da yi ma juna bayanin abubuwan da suka shige duhu. **** Yanda Amatullah ke fargaban haɗuwa da Dee, haka shi kuwa sam ba ya kaunar ganin ta ba dan komai ba sai dan tsananin kishi da takaicin ganin ta a matsayin matar wani. Tun isar sa Hamza ya faɗa ma sa haduwar shi da Amatulah, tare da masa jajen rashin ta, ga mamakin Hamza sai ji yayi ya ce idan ya na so su shirya kar ya sake ma sa maganar matar wani. Tun daga ranar ya ja bakin shi yayi shiru dan ya san halin Dee ba dai fushi iya fushi ba. **** Kwanci tashi asarar mai rai, haka karatun su Amatullah ya dinga tafiya, sosai ta dage da karatu saboda samun sakamako mai kyau ganin result dinsu na zangon farko ya fita tana da 4bisa biyar (4.00)ya sanya ta dagewa don samun fiye da haka ko kuma tsayawa a daidai hakan. Karatu ta ke yi babu dare babu rana duk da sau da yawa takan ɓace cikin tunanin Dee Yusuf da gaba ɗaya ba ta sake ɗaura idanunta a kanshi ba. Sau da yawa ta kan roki Allah da ya jiɓinci Al'amarinsa a duk inda Yake. Tun da ta dawo hutun mid semester sau ɗaya ta je gida, shima a kan tunanin Baban Sasa. Halin da ta rike shi ya bata mamaki, domin Baban Sasa kamar ba shi ne ƙoda ya kwantar ba. Yayi kyau har da ƙibansa hakan ya bata mamaki. "Megida wannan kyau haka, Allah abin godiya" tace masa cike da farin ciki. Shima dariya yayi mata ya ɗaura da fadin "Ciwon nan har da fargaba ya ƙara kwantar da ni fa" kallon sa ta shiga yi cike da alamun tambaya shin wani fargaba kuma, hakan ya sanya shi ɗaurawa da "wallahi Amatu, tun da na fara ciwo sai nake ganin ba zan ga aurenku ba, Allah Laɗifu sai gashi ya aminta na gani, yanzu hankali na kwance" dariya ta shiga yi da mamakin ƙarfin hali irin nashi. "Allah mun gode maka, yanzu ina ke maka ciwo?" ta ce cikin kulawa. "Toh yanzu dai ba inda ke ciwo, ina shan habbatus saudah kuma yana taimakawa. Ai yanda nake jin jikin nan se naga auren yayanku" yace yana dariya. "Allahu ya amince" ta fadi itama cikin dariya. A nan ta ke jin labarin tun bayan tafiyar Saifullah ba sake samun shi ko da a waya bane. Ba ta yi mamaki ko bakin ciki ba don ta san har abin da ya fi ɓata zai iya yi. Tun wannan zuwan ba ta sake zuwa ba, duk da sun rabu da mahaifiyar ta cikin kewan juna amma burin ta na samun sakamako mai kyau ya danne duk wani kewan gida da take yi. **** Duk wani lungu da saƙo da ya san zai iya ganin Amatullah daina zuwa yayi, hatta ajin da su ka saba zama ya koya mata karatu ji yayi duk duniya babu inda yake shakkar shiga tamkar ajin. Wani shiga jama'a da hayaniyar aluta duka aje su yayi, haka duka activities da wani cultural weeks da ake yi cikin makarantar bai yi participating ba. Tun su Hamza na kokarin jan shi ciki, har su ka hakura su ka sa masa idanu kawai. Zuwan Mimi Post -ume ne ma ya dan sa ya saki ran sa, kwanan ta biyu kacal ta koma Kano abin ta. Ana gobe za su fara jarrabawa sakon dawowar Saifullah ya isko Amatullah daga ƙanin ta Hafiz. Tsoronta ya zo bai karɓe ta a wata aba mai daraja ba, amma littafan da ta karanta ya sa ta aminta da cewa ana auren kiyayya miji ya so matarsa bayan ya ci sadakinsa, sannan ta yarda da duk abin da miji ke ma mata na tozartarwa matukar yana kiranta makwanci toh yana sonta. Ta wannan fannin sai ta ga kawai ta gama samun Saifullah ta gama don ba za ta taɓa hana masa ba. Da wannan cikin ranta ta aje tunanin Saifullahi ta dukufa wajan karatu da neman sa'ar jarabawa. **** Rana ɗaya Dee da Amatulah su ka gama jarabawa, banbanci shi ne ita Amatullah jarabawar na ta na safiya ne, shi kuma Dee da rana. Ko da ya fito da ga jarabawar bai iya tsayawa murnar da celebration da dalibai su ka ba na gama makaranta ba, motar shi ya shige kai tsaye gate ya nufa da niyar komawa gida ya haɗa na shi ya na shi ya bar Zaria, ya na mai fatan bayan clearance da karban result, kar Allah ya kara kawo dalilin da zai sa ya sake dawowa makaranta. Dan karamin go slow da ya tadda a bakin gate kasancewa ababan hawa sun yawaita saboda dalibai dayawa ranar su ke komawa gida. Kamar ance Ya kalli gaban sa, nan ya hango ta bakin gate ta na faman jan katon akwatin da ya karfin ta, daga dukkan alama ita ma ɗin gida ta yi. Kallon ta ya ke yayinda ya ji wani abu ya taso ya tokare sa a kirji. Sanye ta ke cikin farin hijab har kasa, kafafunta sanye da safa, abinka da sha'anin sheɗan gani ya ke tun da ya ke ganin ta ba ta taɓa masa kyau ba kamar yanda ta yi yanzu da ya ke kallan ta. "Amatullah......." Ya furta a bayyane. "Ina fatan wannan shi ne gani na karshe da zan mi ki a rayuwa ta, ba dan komai ba sai dan tazarar da ke tsakanin mu, Amma soyayyarki ta riga min shigar gaggawa, ta min illa...." Motsawar da motan da ke gaban sa yayi ya sanya shi yin gaba da tashi motar, ya zo daidai gaban ta, daga idanun ta ke da wuya su ka yi ido biyu, gaban ta yayi mummunar faɗuwa amma ta kasa ɗauke idanun ta daga kallon sa "Dee....." Ta tsinci leɓan ta na mai fitar da sautin sunan sa. Securityn da ke karbar gate pass ne ya tura hannun sa cikin motan Dee domin karbar pass daga hannun Dee, amma ina Dee be ma san yanayi ba. Karar horn da kuma yanda security ya kwankwasa motar ya sanya Dee ya farga daga barin kallon ta, cikin bada hakuri ya mika masa pass din, yana mai taka motar ya fice daga makarantar ba tare da ya sake waiwayan in da Amatulah ke tsaye ba. Amatullah kuwa da kyar ta ƙarasa jan akwatin zuwa gate in da ta tadda Hafiz tare da sauran kayan ta, bakin gilashin motar da su ka zo daukan ta da shi ya sa aka hana su shigowa. Gaban ta bai daina faɗuwa ba har ta isa gida. [3/2, 10:52 PM] +234 703 484 8802: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA TAKWAS Ganin Dee da ta yi ba ƙaramin fama mata gyambo ta yi ba, haka ta maƙale a ɗakinsu ba tare da ta fito ba don gaba ɗaya ta rasa gane kanta. Ko ɗakin Baban Sasa ba ta shiga ba, haka ɗakin Hajiya iyaka wainda ta ci karo da su kafin ta shige su ne su ka san da dawowarta. A nan tsakar gida Hajiya ta tsinci labarin dawowarta, duk da ba lale tayi da dawowarta ba sai ta tsinci zuciyarta da yi mata ƙuna akan rashin shigowar ta gaisheta. *** Angon Amatullah wato Saifullah kuwa bai so dawowa Nijeriya ba duk da kuwa ya kammala karatun shi sakamako kawai ya ke tsimayi. Ayush ce ta takura lallai su dawo a yi maganar auren su a wuce wajen. Gashi har yanzu ya kasa buɗa baki ya faɗa mata halin da ake ciki na game da auren shi da Amatulah, ya so ya hure mata kunne su yi zaman su can su nemi aikin yi ko da kuwa na shekara guda ne amma Ayush ta yi kememe ta ki, ita aure ta ke so, in kuma auren na ta ne ba zai yi ba sai ya faɗa mata. Akan wannan batu su ka dawo gida, in da Saifullahi ke cikin halin haula'i. Bayan Sallar isha'i Saifullah ya shigo ɗakin mahaifiyar tasa, so yake ya nemi shawararta akan yanda zai faɗi ma Ayush ba tare da ya rasata ba sanin da yayi in dai wannan fannin ne Hajiyarsa ba ta da part two. "Ka haɗu da yarinyar nan ne?" Ta tambaye shi, yanayin da ya kallo ta cikin rashin fahimta ya sa ta ƙara da "Amatullah fa" tace tana kallon sa. Tsoro take kar ya zo ya faɗa tarkon son yarinyar don ta san kwana bakwai Baban Sasa da Baba Anas su ka ɗauka suna addu'ar gina soyayya tsakanin wa'inda ke samun saɓani. Sannan ta yarda da ƙarfin addu'ar don tana yi a duk lokacin da su ka samu saɓani da megidanta. "Ni wallahi gaba ɗaya na manta da wata halitta haka, ni yanzu mafita na zo ki sama min, Ayush! Ban son na rasa ta Hajiya" ya ƙarasa yana marairaicewa. Shiru ta yi tana tunani kafin ta samu mafitar da cikin farin ciki ya bar ɗakin tare da niyyar ɗaukan hanyar Kano Washegari. "Ka nemi yarinyar can dai komi dare yau, na san yan sa ido sun fi ɗaurawa a kanka" ya tsinkayi muryar hajiya sa'ilin da ya ke barin ɗakin. Ficewa yayi yana tunanin yanda zai yi da ita, ji yake ina ma kashe rai ya halatta a duniya da tuni ya aika ta lahira don ya ji dadin rayuwarsa da Ayush. Har ya zo wucewa ya ga Siddiƙa kanwar Amatullah za ta shiga ɗakinsu. "Uhmmmn wacece nan" yace cikin ɗan ɗaga murya. "Siddiƙa ce" ta faɗi tana ɗan tsayawa. Sai ta ya matso kusa da ita sannan yace "ki ce ma Amat ta kawo min abinci ɗaki" yana gama faɗi ya sa kai ya fice. Da murna ta shiga ɗakin lokacin Amatullah na zaune suna hira da mahaifiyarsu wanda rabi da rabi ne hankalinta a wajen. "Yaya Amatullah wai ki kai ma Yaya Saifullah abincinsa ɗaki, kin ji yanda ya kira sunanki, Aamat ya ce, wallahi Yaya Saifullah ɗan gayu ne..." "Dilla rufe ma mutane baki, ba ɗan gayu kaɗai ba" Amatullah ta katse ta cikin tsawa, ba ta ga dalilin da zai sa ya nemi ta kai masa abinci ba. 'Zai so ki fa, kuma ki saki jiki ki sabar masa da jikinki, da farko a kwai wuya amma shine soyayya' ta tuna kalaman maman Jaafar. Nan sai ta ji sanyin jiki. Kenan har ya fara sonta tun da har ya nemi ta kai masa abinci. 'da farko a kwai wuya' ya sake faɗo mata a rai, nan ta tsorata ainun don in akwai abin da ta tsana abin da zai sa ta ji zafi a jikinta. Ta tuna a littafan da ta karanta yanda aka sa amare na sumewa in aka kai su. Ba ta san lokacin da hawaye su ka soma gangaro mata ba, kawai ɗuminsu ta ji. "Amatullah haramun ne tsaurara kiyayya, balle wannan mijinki ne wanda Aljannarki ke tafin ƙafarsa. Ga abincin sa can maza ɗauka ki kai masa" Goggo mairo ta faɗi bayan ta sa hannu ta goge mata hawayen. Cikin sanyin jiki ta ɗauki abincin ta kai masa ɗaki. Film yake kallo ƴar America, ganin ta bai sa ya kashe ba duk da kuwa abin da ake haskowa ya saɓa ma shari'a. Duƙar da kai tayi don tun da take abin da bata taɓa gani ba kenan. "Daga kai ki gani, ki ga yanda su ka dace da juna, shin ni ɗin ya dace na gauraye gumi da bagidajiya irinki? Kalle su fa, wai ke har kina tunanin kin kai mace da za a gani a so? Na so tsine ma ranar da aka ɗau cikinki don ranar bai zama mai adalci a rayuwata ba" yace yana mai jan farantin da ta shigo da shi ya soma cin abincin da hankali kwance. "Hijabin nan naki ƙarni ya ke yi, ki yi hakuri ki bani waje ko iskan zai yi daɗi" ya ce yana nuna mata hanyar fita. Tsoro ya hana mata fita tun a farko, don ta san yana iya ƙulla mata wani sharrin, ga shi ta zauna, amma zaman bai mata amfani ba. Kuka ya taso mata bayan fitowarta daga ɗakin, tsayawa ta yi ta tattaro duk wani natsuwa nata kafin ta isa ɗakin Baban Sasa, nan hira sosai su ka yi, sannan ya bata tukuicin hira da sanya tariyarsu sati biyu masu zuwa. Yana faɗa mata lokacin za ta tafi ne, take ta ji duk wani natsuwar tafiya ya ɓace. "Baban Sasa zan yi missing ɗinka don Allah kara lokaci" ta samu kanta da faɗi. Kallonta yayi cikin dariyar su ta manya ya ce "Ai muna tare, ki yi hakuri kuma ki bi mijinki, Allah ya sanya alkhairi ya muku Albarka, Nan da sati daya Saifullahi zai haɗo mana lefan ki bisa al'ada, kasancewar tsatso ɗaya kuka taso ba zai sa a toye mi ki hakkin ki na lefe" ba ta amsa ba anan ta sanya kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya ta haɗa masa tun daga wanda ta ƙunso daga ɗakin Saifullah har zuwa na Tariya ga fuskar Dee Yusuf da ta gani a gate sai mata gizo ya ke a idanu. *** Baban Sasa ne ya ruguzawa Saifullahi shirin shi na zuwa Kano a washagari, maganar tarewa nan da sati biyu, da na lefe da gidan da za su zauna ne gaba ɗaya ya ɓata masa lissafi. Yayi kokarin ɗaga tariyar ta hanyar ba da uzirin rashin kammala ginin sa da ya fara, Amma Baban Sasa ya ce wannan ba wani abu ba ne, zai iya zama ɗaya daga gidadan shi, ya zaɓi duk wanda ya masa a fara gyara. Haka ya kasance cikin bakin ciki da dana sanin biyewa Aysuh da yayi su ka dawo. Magungunan mata da su tsumin da 'yan uwan Gwaggo ke angaza mata ba karamin tayarwa da Amatulah hankali su ke ba, tun tana musu alkunya ta na karɓa in ta shiga bandaki ta zubar har ta gaji ta fili ta ce musu su daina ɓata lokacin su, ita ba sha ta ke ba kuma ba ta ga dalilin sha ba. Haka kuma baccin ran da su ka nuna bai sa ta canza ra'ayin ta, har su ka gaji su ka bar ta da halin ta. Satin biyun nan sun zo masu ne kamar kyaftawar ido, ba ta wani wahalar yin gayya ba sai su zulaikha da ya zama mata dole. Ana saura kwana uku aka nuna lehenta, wanda ya fi na duk wata ya mace da aka aurar a gidan. Ranar bikin ta ci leshin ta masu kyau da atamfa ta dinga canzawa kowanne da hijab da ya shiga da shi. Wannan shigan ya fi komi ɗaga hankalin Saifullah don a rayuwarshi bai taɓa fuskantar tozarta wa irin sa ba, wai shi kamar sa ana bikin sa duk da auren suna kawai ya tara amma a ce matarsa zulum zulum cikin Hijabi. [3/2, 10:52 PM] +234 703 484 8802: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA GOMA SHA TARA Rana ɗaya aka yi komai aka gama. La'asar na yi Baban Sasa ya ce a shirya amarya a kai ta ɗakin mijin ta. Nan fa amarya kuka har da majina, musammam da aka ce ta zo ta yiwa Gwaggo sallama. Hannayen ta biyu ta sa ta riƙe ƙafar Gwaggo da kyar aka iya bambare hannun aka wuce da ita ɓangaran Hajiya. Nan kuwa ruwan habaice habaice su ka sha daga dangin Hajiya. Haka ma Hajiya wacce ta dubi Amatullah da ke tsugunne gaban ta fuskar ta rufe da lafaya, buɗar bakin ta sai cewa ta yi " Toh mu dai babu abin cewa tunda ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, Allah dai ya sa za ki iya kula da mijin na ki, dadin ta dai namiji mijin mace hudu ne....." "Bare ma ɗiyar ta mu ai san kowa kin wanda ya rasa ce, wajan kula da iya zaman duniya ba a ce mata komai, uwar gida sarautar mata ba, kowa ya zo bayan ki ya ke...." Cewar kanwar Gwaggo yayinda yan uwa Gwaggo su ka kara karfafa mata gwiwa da guɗa. "Toh ai sai ku tashi a kai ta, Allah ya sa a dace" "Allahumma amen" Cewar dangin Gwaggo, in da su ka tayar da Amatulah. Kamar yanda su yan uwan Hajiya da yayyan Saifullahi ba su fasa yada habaici ba haka su ma dangin Gwaggo ba su fasa guɗa ba. Ɗakin Baba Sasa aka kai Amatullah, nan aka tarad da Mahaifin ta tare da su Baba Zubairu da Baba Anas. Daya bayan ɗaya haka duka su ka mata faɗa tare da sanya albarka, ko da aka zo kan Mahaifin Amatullah sai cewa yayi "Tashi ki tafi dakin mijin ki ɗiyar albarka, duk abinda za ki yi ki yi da halin ki, ba ni da haufi kan ki, kin haifu Amatullah, Allah ya sanya mi ki albarka" Ya karasa maganar ne yayinda yar kwalla ke shirin fita daga idanunsa. Nan ma fa Amatullah ta ce ba ta tashi, aka yi aka yi, ta cije kuka ta ke harda wayyo Allah. Mahaifin ta ne da kan sa ya riko hannun ta, sannan ta yarda ta mike, har mota ya kai ta sannan ya barta hannun manya ya koma ciki. Yan uwa da abokan arziki su ka shige mota, aka dauki hanyar gidan amarya. *** Tafiya ce ɗoɗar daga Amaru zuwa filin mallawa da ke sabon layi, filin cikin na gadon su Baban Sasa ne ya mallaka, sanda ake yanka filayen ana siyarwa ya so ya siyar sai kuma ya yi tunanin gine shi. Babu laifi gidan ginin zamani ne, flat ne, drive in mai dauke da daki uku kowanne da bandakin shi ciki, da kuma madaidaicin kitchen, sai kuma katon falo guda. Su Zulaikha ne su ka yi kokarin zauna mata kafin ango ya zo kar a barta ita kadai. Amma shiru babu Saifullahi babu alamar shi, dan haka sallama su ka mata, ta na ji ta na gani su ka barta ita kaɗai duk magiyar ta da su zauna amma umurni ne daga baban Sasa cewa kada wanda ya kwana a gidan duk da hakan al'adar mutan zaria ne. Amatullah gwanar tsoro, suna fita ta sa mukulli ta garkame ɗakin ta, ta shige toilet ta dauro alwala bisa dadduma ta shiga jera salloli ta na rokan Allah sauki bisa lamarin ta, nan bacci mai nauyi ya sace ta. Yunwa ne ya tada ita da asubar fari. Sai da ta yi sallar asuba, ba tare da ta cire hijabin da ta yi sallah da shi ba, a hankali ta bude kofar ɗakinta ta ɗan leƙa falon, duhun da ta gani ya bata karfin gwiwar fitowa ta na mai haska falon da wayan ta domin neman hanyar kitchen. Babu shakka su Gwaggo sun tsantsara mata falon na ta da kayan alatu, kujerun ta ruwan zuma da kanana filullukan da aka jera ba karamin shiga yayi da labulen falon ba. Ganin kofofi hudu daya ya ɗan yi kusa da dakin ta, sai kuma ɗayan bangaran yamma kusa da kofar shigowa falon, sai kuma ɗayan wanda ke can gefe guda ya sa Amatullah ta yi turus, dan kuwa ba ta san wanene wanne cikin su ba, gashi yunwa ta ke ji kamar ta yi ihu. Lissafin ta wannan na kusa da ita zai iya kasancewa dakin mai gidan, wancan na kusa da kofa ya zama na baki, dan haka na can gefe shi ne kitchen, kai tsaye to nufe shi. Zuciyar ta daya ta kama mubudin kofar ta bude ta na mai tura kan ta ciki. Hasken wutan lantarki ne ya fara ziyarta idanun ta, kafin idanun ta ya gane mata wanda ke tsaye gaban fridge daga shi sai gajeran wando, ya bata baya hannun sa dauke da gorar ruwa. Da sauri ta juya cikin rawar jiki, wayar da ke hannun ta ce ta sullube ta faɗi kasa. Karar faduwar wayar ya sanya shi jiyowa fuskar shi cike da mamaki. Bacin rai ne ya maye gurbin mamakin da ya bayyana fuskar shi ganin Amatullah, cikin sauri da tsungunna ta dau wayar da niyar ficewa, ya dakatar da ita cikin tsawa ya ce "Ke wace irin bagidajiya ce wai? Zo nan Malama!" Tsayawa ta yi cak idanun ta kasa, ita ba ta fita ba, haka kuma ba ta karasa in da ya ke cikin kitchen ɗin ba. "Ba da ke na ke magana ba! Ki zo na ce!" Ya kara daka mata tsawa a karo na biyu in da ta tsinci kan ta tana mai karasawa gaban sa, da kyar ta yi karfin hali ta kai kallan ta ga fuskar sa ba tare da ta kalli kirgin sa ba, yanayin kallan takaici da ya ke mata ya sa ta sake yin ƙasa da na ta idon ka na ta furta "Ban san kana kitchen ɗin ba......" "Iya ka tarbiyar da aka koya mi ki kenan? Ba ki iya gaisuwa ba? Ga gidadanci ga rashin tarbiya...." Lebben na kasa ta cije cikin takaici da jin zafin furucin Saifullahi, kafin ta kai ga ba shi amsa sai ji ta ya ce "Bani hijabin nan!!!!!" Jin maganar kamar kunnen ta ke mata zagi ya sa ta ɗaga kai da sauri ta na mai fidda idanu. Kai ya girgiza ya ce "Yes kin ji ni da kyau, ki ciro hijabin jikin ki ki bani yanzun nan!!!!" Baya ta ja tana mai girgiza kai yayinda zuciyar ta ke dukan uku uku ta furta "Dan Allah dan annabi ka yi hakuri....." "Dalla malama hakurin me ki ke bani, just do as I said ko kuwa ni na cire mi ki! you are so irritating!!!!" Hawaye ne ya fara zuba daga idanun ta, ganin ba ta da niyar bin umarnin shi ya sanya shi tinkarar ta, ganin haka itama ta fara ja da baya tana fadin "Menene haka wai ya Saifullahi?" "Just remove the damn thing and give it to me!" Jiki na rawa ta ciro hijabin, ta rike hannun ta idanun ta kallan kasa yayinda hawaye daya ke bin daya. Kallo ya bita da shi, kasancewar ba shiri bacci ya sace ta daren jiya, atamfar da aka kai ta da shi ne jikin ta. Kai ya girziza ya na mai nuna ta da hannu tun daga sama har kasa ya ce "Just imagine! Na tabbatar da wannan atamfar a jikin ki ki ka kwana tsabagen gidadanci! God you're so local Amatullah!!!" Ya sa hannu ya fizge hijabin daga hannun ta ya yi wulgi da shi cikin kwandan sharan da ke cikin kitchen, in da Amatulah ta bi shi da kallo, kafin ta dawo da kallan ta ga Saifullahi. Ya na nuna ta da dan yatsa ya ce " Ni Saifullahi, wanda aka ɗaura min auran ki akan dole, daga yau har ki karaci zaman ki gida, na umarce ki da ki dena saka waccan abu, Kar na sake ganin ki da hijabi Amatullah! Na haramta mi ki saka hijabi cikin gida na!!! Bagidajiya kawai!!!" Ya na gama magana ya fice yana huci kamar zaki. Ya bar Amatullah zube a kasa ta na sharbar kuka, shin ashe akwai ranar da za a haramta mata sanya hijabi? Kuma mijin ta? Wannan masifa har ina! "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun" Furucin da ta ke yayinda tsanar Saifullahi ke kara ratsa zuciyar ta. [3/5, 8:50 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN Sannu sannu har mun yi sati goma a cikin wannan tafiya tamu, godiya ta Musamman ga duk wanda idonsa ke kan saƙon nan, mun gode, Saifullah da Amatullah na gaida ku cikin kwando. Dee Yusuf da mimi na muku fatan Alkhairi.. Baban Sasa na jiran ku kai masa farfesun Hanta. Muna ƙaunar ku Fisabilillah. Umdija😍😘🌹 *** Jan jiki ta yi zuwa ɗaki bayan ta nemi abin da za ta riƙe hanjinta da shi. Allah ya isa kuwa ta masa ya fi sau a ƙirga don ba ta ga dalilin da zai sa ya haramta mata sa hijab ba, haka kawai ta dinga tallan jikinta gareshi kamar wacce ba ta da kishin kanta. Da ire-iren tunanin nan ta kammala cin abincin, miƙe kafafu tayi ta jingina nan ma wani sabon bacci yayi awon gaba da ita. Hayaniya ya tayar da ita sa'ilin da yan gidansu su ka iso wainda mafi akasarinsu innoninta ne, bayan ta gaida su, wasu na mata tsiya ne su ka sanya ta je ta yi wanka saboda masu shigowa ganin amarya. Atamfarta ta sanya ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya zauna a jikinta, golden color din da ke jikin atamfar wanda ya sakaya cofee da peach ya fito da kalarta tare da bayyana madarar kyawun da ta mallaka. Hijab golden ta ɗinka ma kayan har ta ɗauko za ta sanya "A matsayina na mijinki, na haramta miki sanya hijabi a cikin gida" take wasu hawaye su ka zubo mata, jujjuya hijabin ta ke a hannun ta hawayen ba su daina zubar mata ba, takaicin ta yanda cousins ɗinta maza ke kaikomo a cikin gidan suna taimakawa wajen ƙara kimtsa gidan. "Ga wannan ki yafa" cewar innarta Aisha, kallon gyalen ta yi, kamar ta ce A'a amma shakkar Innar tata da take yi yasa ta amsa. Ana faɗin matar soja sojace bata yarda ba sai akan innarta Aisha, don in ta rikide musamman akan abubuwa da ya jiɓinci ado da kwalliya sai ka rantse wani hafsin soja ne a fagen yaƙi. Gyaran da aka ma fuskarta da yanda ta yane jikinta da gyalen ya fito da ita ainun. "MaashaAllah! MaashaAllah!!" kawai ake faɗi, nan sai ta hau Saman gado fuskarta lulluɓe da gyalen amma tana iya hango su. "Ai ni jiya hankali na ya ɗauke wajen hidimar yaya mairo, a ce amarya da hijabi, kai ke kuwa izalarki ta yi yawa wallahi" inna Aisha ta faɗi tana mai yaba kyawun yar tata. Zamanta a legas ya sanya duk wani darun da aka yi ba ta da labari, itace ke bi ma Goggo Mairo, sun yi aure da mijinta tun tana shekaru goma sha huɗu shi kuma an yaye su a depot din zaria. Allah cikin ikonsa ya haɗa mijin nata da oga nagari ya masa hanya ya tura sa makarantar horar da sojaji ta NDA yayi shekaru biyar ya fita da anini. Yanzu har ya kai ga Jan wuya a aikin soja. "Ai yaya indo ni na rasa kamun jiki irin na Amatullah, su ne yan fatawar ko hoda mace ba ta sawa, amma wainda su ka san darajar mata sun san su ake kira first class ladies" faɗin Inna Hafsatu kanwar su goggo mairo ce, hakan ya sanya yan uwan hajiya da su ka shigo fita cikin sanyin jiki, da sun shigo suna musu yatsina ne. Suna fita kannen Goggo Mairo su ka sanya shewa. Haka su ka yini suna gyara da taya Amatullah zama sai da aka kira magariba sannan duk su ka watse a gidan, suna mai masu fatan Alkhairi. Kamar juya Amatullah ba ta jira shigowar Saifullah ba ta kulle ɗakinta, sai dai ta iya canza kaya zuwa na bacci kafin ta bi lafiyar gado. *** Washagari da misalin karfe goma sha biyu Saifullahi ya isa Kano gidan su Ayush. Kamar yanda aka saba karɓar shi cikin mutunci da girmamawa haka yau ma aka masa. Duk da kasancewar ba wannan ne zuwan shi gidan na farko ba bai hana shi bin gidan da kallo ba tamkar bakauye tsabagen tarin dukiyar da ke gidan. Falon baki aka sauke shi, in da ma su aiki su ke ta kai kawo wajen kawo masa abinci da kayan marmari. Sai bayan sun gama da minti ashirin sannan Ayush ta shigo ta na taku ɗai ɗai da rangwaɗa, baki da hanci da idanu gaba ɗaya Saifu ya saki ya na kallon ta. Sanye ta ke cikin doguwar riga ja, rigar ta kamata kwarai ta zauna jikin ta, ko mayafi ba ta saka ba, sai daurin da ta yi da kallabin kayan, irin wannan daurin da ake kira ture ka ga tsiya. Kusa da shi ta zauna kamar wacce za ta shige cikin sa. Tuni kamshin turaren kamafanin the body shop ya mamaye hancin sa. Fuskarsa cike da fara'a ya ruko hannun ta ya na mai faɗin "Ayush mine, queen of beauty" Idanun ta kaɗa ta yi fari, cikin kissa ta ce "Saif Man, wallahi na yi kewan ka ina fata dai ka zo min da sakon turo iyayen ka su kawo gaisuwa, tun da dai ka ki yarda mu yi maganar a waya" Hannun ta ya saki, yayinda ya shafa kyeyar sa cikin kame kame ya ce "Haba mana ke kuwa, daga zuwa babu sannu bare ya hanya?" Kunya ne ya rufe ta, kana ta ce "Afuwan, Dad ne ya ke ta min maganar wallahi. Ya hanya? Hope ka iso lafiya" "Lafiya lau Alhamdulillah, dan bani ruwa ni zafi ma na ke ji' "Kai Mine duk AC da ke busowa ka ce zafi? Ko dai ba ka da lafiya ne?" Cewar Ayush yayinda ta zuba masa ruwan ta mika masa. Sai da ya sha kofi biyu, ga mamakin Ayush har zufa ya ke. "Lafiya lau na ke, oya gist me, have you missed me?" Nan ya fara Jan ta da hira, tun tana biye ma sa, har ta gaji ta sake tambayar abin da ke ran ta. "Aisha......" Jin ya kira ta da sunan ta na ainihi ya sanya ta dagowa da sauri ta na duban shi. "Ki yafe min na zo mi ki da labari mai muni, wallahil azim ba da san rai na aka yi ba, kuma na mi ki alkawarin hakan ba zai sa a fasa auren mu ba......" "What are you saying ne? Ka yi min gwari gwari dan Allah" Ta katse shi cikin nuna gajiyawa. Hannun ta ya sake rikowa sannan ya ce "An daura min aure da yar uwa ta....." "Hahahahahahaah" Ayush ta katse shi da dariya mai cike da keta. Cikin yanayin firgici da tsoro ya ke duban ta, sai da ta yi dariyar mai isar ta har da kwalla sannan ta furta "You must be kidding me, Kai amma Mine ka iya zolaya wallahi, dan kuwa wannan wasan na ka ai tsokana ne" "I'm serious Ayush, wallahi I'm serious..." "Bura uban nan kayyasa!!!!! Ni za ka kalla ka yiwa wannan maganar Saifullahi? Ka kalli tsabar idona ka ce min an yi maka auren dole? Do you think I'm stupid?" "Ayush calm down, ina san ki, ina kaunar ki, wallahi ba zan iya zama da bagidajiyar da aka aura min ba, I want to marry you....." "Get out!!!" Cewar Ayush yayinda da ta tashi tsaye, hanyar fita ta masa nuni da shi tare da sake faɗin "Get out!!!!??" Jiki sanyaye ya tashi, a hankali ya furta "Ayush, listen........" "Damn you!!!!! Fitar mana daga gida Malam" Jiki sanyaye Saifullahi ya fice. Sai da ya fita sannan ta saki kukan da ya tsaya mata can karkashin makogoro, duniyar nan babu wanda ta tsana kamar Saifullahi. Saifullahi na fita daga gidan masallaci ya nufa yayi sallah ko zuciyar sa ta dan yi sanyi. Yana idarwa ya shiga Kiran wayar Ayush amma ta ki dagawa. Haka ya ɗauki hanyar Zaria ba tare da ya tsaya neman abinci ba, yayinda tsanar Amatullah ke kara ratsa zuciyar sa. *** Ranar da Amatulah ta cika kwana biyar gidan miji Maman Jafa'ar da Zulaikha suka kawo mata ziyara. Ranar Amatulah murna kamar ta goya su. Daki su ka zauna, Zulaikha ce ta takura ita lalle sai ta ga ango, Amatullah ta Kira shi su gaisa. Amatullah da ta yi kokarin buye mu su halin da ta ke ciki, tuni ta fashe mu su da kuka, nan takwashe komai ta fada musu, ta kare da "Kuma rabona da ganin shi cikin gidan nan kwana uku kenan....." "Ki na nufin ba gidan ya ke kwana ba?" Cewar Maman Ja'afar cike da jimami "In ma nan ya ke kwana ban sani ba, babu abin da ke hada mu" "Toh ai Amatullah laifin ki ne wallahi, mace kamar ki, mace har mace akwai namijin da ya isa ya wulakantaki Amatullah? Wai tsaya duk tarin littafan da na haɗa ki da shi karatunsu ya tashi a banza kenan?" Maman Ja'afar ta faɗa cikin nuna ɓacin rai, ita kuwa Zulaikha tagumi ta yi ta ma rasa na cewa. "Ba dai ya haramta mi ki saka hijabi ba? Toh ai kuwa ya tsokanowa kan sa rashin kwanciyar hankali daga yau Amatullah kanana kaya shi ne kayan sakawar ki, ki karkada masa kugu a sannu zai dawo tafin hannun ki sai yanda ki ka yi da shi...." "Ayya mana Maman Ja'afar...." Cewar Amatullah, kunya ne ya rufe ta. Ita kuwa Zulaikha shewa ta yi tare da faɗin "I trust you Maman Ja'afar, Amma fa mutuniyar ban ji ta na da kananan kaya fa" "Kar ki damu, gashi ai dama na ruko guda biyu, short gown ne duka, kuma in sha Allah ni da kai na zan shiga kasuwa na karo mata" Jakarta ta bude, ta fito da kayan ta mikawa Amatullah tare da faɗin "Oya tashi ki saka mu gani" "Caf wannan mitsitsiyar rigar zan saka?" "Eh yanzu ma kuwa Amatullah" "Gaskiya ba zan iya ba sai ka ce wata yar iska?" "Ni da na kawo mi ki halan ni ce yar iska" Cewar Maman Ja'afar cikin gatse, in da Zulaikha ta kwashe da dariyar mugunta. "Ni ah ah ba haka na ke nufi ba Maman Ja'afar, kayan ne....." "Idan ba haka ki ke nufi ba toh ki saka kayan mu gani" Amatullah na gunguni ta shige bayi, sai da tai kusan minti goma da saka kayan amma ta kasa fitowa, Zulaikha ce ta buɗe bayin ba ta san sanda ta saka ihu ba, kunya ya rufe Amatullah kamar ta nitse. Riga ce koriya, mai dan ƙaramin hannu iya ka gwuiwa, duk da dai ba wani kama ta yayi ba amma yanayin dirin Amatullah ya sanya rigar kayatuwa jikin ta. Da zuga suka sanya ta sake gwada dayar, wacce ta ke jar body fitting gown mai tafiya da hankalin duk wani mai kallo, rigar mara hannu ce kuma bata karasa gwiwa ba. Ba ƙaramin kyau Amatullah ta yi ba kamar aljana. "Tsira da aminci ya tabbata ga mahaliccin wannan halitar" Cewar Maman Ja'afar, in da Zulaikha ta kara da "Wow, wallahi kin haɗu Amatullah babu karya!!!" Ita dai Amatullah ta kasa sakewa gaban su ma, bare kuma uwa uba uban gayyar. "Fisabilillahi wannan ba sutura ba ce....." "Ai dai yau dinnan za ki saka, yamma na yi ki wanka na tsantsara mi ki ado Amatullah, sai Mijin ki ya kasa gane ki" Maman Ja'afar ta faɗa cikin jaddadawa. "Yo ina ma zai ganni, na manta rabon da na ji motsin shi" "Yau kuwa za ki ji" Duka suka sa dariya, ita kuwa kayan ta cire cikin ranta ta na faɗin sa ga wacce za ta saka kayan. Sai da su ka yinan mata, bayan la'asar kamar yanda Maman Ja'afar ta ce , wanka ta tursasa Amatullah ta yi, sai da ta yi mata kwalliya kafin su yi diramar sanya kaya. Ganin an fi karfin ta Amatullah ta sanya yar karamar jar rigar da Maman Ja'afar ta zaba ma ta, ta na mai kudirin cire kayan da sun tafi. Ita kanta ta san ta yi kyau na burgewa da ban sha'awa. Ga body komai cif cif da ta taka sai komai ya motsa. "Big sai bigi babban goro sai magogin karfe.." Zulaikha ce ta ke mata kirari. "Bari Zulaikha, irin su Amatullah ake kira da zaratan mata...." "Ni dai ku bar zigani haka dan Allah" Amatullah ta katse ta tana mai tifke gashin ta da ribon. Nan fa baki su ka ce za su yi halin su. Amatullah ta ja hijabi za ta saka domin rakiya Maman Ja'afar ta kwace tana faɗin "An dai haramta mi ki sanya hijabi cikin gida" Baki bude Amatullah ta bata amsa da "Haka zan fita na raka ku toh? Kai jama'a Allah ya sauwake na fita haka" "Ke Malama wa ya ce fita za ki yi? Iyakar ki bakin kofar falon ki ko gate ba za ki kai ba, dan haka mayar da wukar" Akwatin lafen ta ta bude ba tare da basu amsa ba, kayan kwalliya ta dauka har da body spray da sabulu, ta zuba a leda. Ba su fasa tsokanar ta ba har ta raka su, kayan ta ba su tare da godiya, ji take kamar ta bi su kawai su koma makaranta ta huta. Ran ta ba dadi su ka yi sallama ta rufe kofar falon. Har za ta shiga ɗakin ta ji an kwankwasa kofa, zuciyar ta daya su Zulaikha ne su ka yi mantawa ta koma ta na faɗin "Na face duk wacce ta yi mantuwa ya zama nawa" Yayin da ta bude kofar, ganin wanda ke tsaye gaban ta ya sanya ta mummunar faduwar gaba. Saifullahi ne sanye cikin kanana kaya, farar riga mara hannu da bakin wando. Kallan da ya bi ta da shi tun daga sama har kasa ne ya sa ta tuna da yanayin shigar da ta yi, 'Kai amma su Zulaikha sun cuce ni!' abin da ta ce cikin ran ta kenan yayinda ta juya ciki da sauri da niyar komawa dakin ta, nan Saifullahi ya sami damar karewa bayan ta kallo, sai da ya bari ta kai dab da kofar dakin ta ya ce "Malama tsaya!" Turis ta yi ta tsaya, dan kunya kamar kasa ta tsage ta shige. Ta kasa juyowa ta kalle shi, In da ta ke ya karasa duk ya bi ya susuce. Cikin kame kame ya ce "Ba ki iya sannu da zuwa ba ko? Haka aka koya mi ki?" "Sannun da zuwa" Ta furta da sauri ba tare da ta juya ta kalle shi ba. "Ba za ki juyo ki kalle ni ba iye Amat? Haka mace ta ke yiwa mijin ta sannu da zuwa a garin ku?" Jikin ta ne ya fara rawa, yayin da ta juyo a hankali. Ganin yanda idanun Saifullahi su ka fara juyewa cikin wani yanayi ya sanya ta saurin yin ƙasa da idanun ta. Muryar shi ƙasa ƙasa ya kai hannun shi ga na ta, ya ce "Bari na koya mi ki yanda ake yiwa miji sannu da zuwa Amat" Ba ta ankara ba sai ga ta jikin shi, ba karamin firgita ta yi ganin yanda ya kamkame ta ya na mayar da numfashi. Kuka ta sakar masa mai karfi ta na faɗin "Dan Allah Ya Saifullahi ka yi hakuri, wallahi ba zan sake ba" Maimakon ya sake ta, sai ji ta yi ya fara shafa bayan ta, nan fa Amatullah ta yi kicin kicin ta shiga ture shi, har Allah ya ba ta iko ta kwaci kan ta, Saifullahi yayi baya kamar wanda ke shirin faduwa. Cikin zafin nama ta shige dakin ta tare da sa mukulli ta kulle. Ta faɗa kan gado ta na kukan da ita kan ta ba ta san dalilin sa ba. Kamar wanda kwai ya fashe haka Saifullahi ya ja jikin sa ya zauna kan kujera. Ya san Amatullah ta na da diri amma bai taɓa tsammanin za ta iya rikita shi haka ba, ace kamar shi Saifullahi bagidajiya irin Amatullah ta sanya hankalin shi ya gushe haka! "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Cewar shi a sarari, ya kara da "Kai dama hajar da Baban Sasa ke hango min kenan, gwara na kwashi rabo na na mure tunda kuwa halak dina ce, kan uba Amatullah mace ce!!!" Kai ya ci gaba da jinjinawa dan kuwa dai jikin sa ya mutu murus, gashi Ayush ta dena daga wayar sa, ta kuma ki ma sa reply na sakonnin alkawarin auren ta da ya ke tura mata kullum bare ya kira ta ko a waya ne ya rage zafi. Nan yayi kwance inda surar Amatullah ke ma sa gizo. Sai da aka kira magariba ta iya tashi ta yi sallah. Bayan ta idar ne ta kira Maman Ja'afar ta na mata mitar masifar da ta jaza mata ranar. Ta kare da "Dama Ya Saifullahi dan iska ne Maman Jafa'ar!!!" Dariya ta yi mata, ita lamarin daidai ya mata sannan ta yiwa Amatullah faɗa da Kar ta sake ture mijin ta, haramun ne, itama ai mai sani ce ta san tsinuwar malaiku dai babban lamari ne. Nasiha ta mata sosai, ta kara jaddada mata gobe goben nan za ta aiko da sauran kayan. Ita kuwa Amatullah ta ce Allah kashe ta ba za ta sake saka irin kayan ba. Da haka su ka yi sallama Maman Ja'afar na murna ta kira Zulaikha ta labar ta mata. Amatullah ba ta kara yarda ta fita daga dakin ta ba bare ta haɗu da Saifullahi, daren ranar haka ta kwana da yunwa. **** Washagari da safe, sai da ta tabbatar ba ta jin motsin Saifullahi ta fito kitchen sanye da material shudi, riga da siket ne ya karbe ta kwarai. Yunwar da ta ke ji ya sanya ta yagar buredi ta na ci hakan nan kafin indomie din da ta daura ya nuna. Daf da kunen ta ta ji ya furta "Ni ki ke gudu ko Amat?" Da sauri ta ja gefe, yayin da da hanjin cikin ta ya kaɗa ganin Saifullahi tsaye gaban ta, kamar ranan yau ma daga shi sai gajeran wando. Idanun ta a kasa ta ce "Ina kwana?" "Lafiya lau, ki dafa da ni ina jiran ki falo" Ya na gama magana ya fice. Bin shi ta yi da kallo cike da mamaki, yau kuma ita ce za ta dafa ma sa abinci? Yau ga saban salo barawo da sallama. Ruwan indomie ɗin ta kara, ta dafa da shi din, tare da soya kwai. Ko da ta kai ma sa sai ya dage sai ta zauna sunci tare. Kai ta girgiza ma sa ta ce "Nawa ya na kitchen ai" "Toh dauko ki zauna ki ci anan ina kallan ki" Hakan kuwa aka yi, ita kan tun abin yana ba ta mamaki har ya fara ba ta tsoro. Saifullahi kuwa jikin Amatullah ya ke yiwa, babu abinda ke burge shi nan duniya kamar sura da diran Amatullah. Sama sama haka ta caccaki indomie duk ta kasa nutsuwa, gashi Saifullahi bai sa ka riga ba haka ya zauna mata hankali kwance ya na yi ya na kallan ta ta wutsiyar ido. Ta shi ta yi za ta shiga kitchen, ya tsayar da ita tare da tambayar "Ina za ki? Har kin yi me?" "Na koshi ne ......" "Gudun mijin ki ke Amat?" Shiru ta masa tana jinjina maganar cikin ranta. Jin ba ta da niyar amsa masa ya kara da "Je ki aje plate din ki dawo" Da sauri ta wuce kitchen. Maimakon ta yi yanda ya ce mata sai ta bige da wanke wanke da gyaran kitchen, tun ya na sa ran komawar ta ya gaji ya bita kitchen din. Ganin ta na tana aiki na ba gyara ba dalili ya rabu da ita, ya san duk daren dadewa za ta shigo hannu, 'duk wayon amarya sai an sha miyar ta' Da wannan tunanin ya shirya ya fice yana mai saƙe-saƙe a zuciyar sa. Kwanakin da su ka biyo baya rashin ji daga Ayush da kuma wasan ɓoyo da Amatullah ke yi ya sanya shi ɗaukan alwashin kyale ta har iya adadin zaman ta a gidanshi kafin yacillar da ita ya auro Ayush dinsa. Nan ya shiga takaicin kansa da ba kansa laifin cin amanar Ayush na kallon watan ta a matsayin abar marmari. *** Kwanci tashi asarar mai rai, auren Saifullah ya cika wata biyu ras, wanda duk an yi shine cikin hutun karshen shekara na su Amatullah. Duk zaman nan shi ma Saifullah yana gida, sau da yawa ya kan baje a falo yana kallo ne. Babu abin da ke haɗa su da ya wuce gaisuwa, ta yi girki ya ci, ya gayyato abokai su zauna su ci. Tun ranar da su ka fara zuwa Amatullah ta koma a guje ta sanya hijabi bai sake yarda ta fito ba, ya gwammace ta yi abincin ta bar shi a kitchen ya je ya ɗauko da a ce matarsa ce ta zo ga abokansa bulum bulum cikin hijabi. Yau ɗinma kamar kullum, fankasau ta yi masu da miyar hanta. Bayan dawowarta daga makaranta in da su ka fara registration ɗin sabon Zango. "Baaba kai dai ka mana zarra Billahil lazi, kai mace har mace, ga kyau ga diri ga iya girki. Wallahi ka more aure, na san a can wajen ma abin ba kanta wannan teɓa da ka fara ajiyewa" cewa Yunus abokin Saifullah na tun sakandire. "Ka san abin da ya ke ƙara birge ni, yarinyar nan ustaziyya ce, jiya na ganta a Samaru wallahi ta rufe masa kayansa amma wallahi tafiyarta ma cikin hijabi abin sha'awa ne. Saif ka gode Allah, Sadiya na nan nayi nayi ta dinga sa pashmina ma gyalen ta ƙi tana tafe ana bin ta da heys! " Salis ya ce yana mai jan tsaki. Wani loma da su ka sake kaiwa baki ba su san sanda su ka ce " Allah ya ma Amatullah albarka" sai da su ka faɗi sannan su ka kwashe da dariya. "Ba fa santi bane, amma girkin nan ya kai kololuwa wajen shiga kwanya" Yunus ya faɗi. Shi kuwa Saifullah wani yanayi ya shiga yan mai jin kansa na ƙara girma, murmushi yayi yana mai kallon abokansa. Duk sun san Ayush, sun san tsakanin sa da ita, amma ba su yarda da alkawarin da ya ce ya ɗauka mata ba, gani su ke yayi ne kawai don jin dadin bakinsa. "Kun ci amanar Ayush! Duniya babu wani nawa da ta aminta da shi sama da ku biyun nan amma kuma nan ku ke koɗa wata" yace yana taɓe baki haɗe da girgiza kai. "Jamoh!!!" Salis ya kira shi da sunan da in ana zancen gaskiya yake kiransa da shi. "Ka san Allah ɗaya! Amatullah ce full option amma Ayush tsohuwa da ina mai yakinin in baku zo sa'a ba toh tabbas ta girme ka. Ita auren Jari za ka yi da ita, wannan kuma matar da za ta tarbiyyantar da yayanku. Ko ba komi ai zaka ci abinci mai gina jiki" yace yana kai lomar karshe tare da kora ruwa. Nushi Saifullah ya kai masa amma ya kauce. "Ku taso mu fita in kun gama ci" Saifullah ya ce a dake. Nan su ka shiga bambamta masa Amatullah da Ayush tun zuciyar sa na ƙaryatawa har ta gaji ta yarda gaskiyar kenan. Tun bayan fitar su ta kimtsa wajen ta sanya turaren wuta tare da kunna kallo. Tashar Iqra TV ta kunna tana sauraron shirin da ake akan da'awa. A nan wajen bacci yayi awon gaba da ita. Sanye take da doguwar riga mara hannu, gaban rigar an masa kwalliya da duwatsu masu kyau. Kallar rigar na ruwan ƙasa ya kwanta sosai a jikinta, ɗame ta da rigar tayi ya bayyana halittar Allah da ke jikinta. Ya shigo daga rakiyan su Yunus inda su ka shiga Congo ya siyo fura don ya lura tana so. Bai san iya lokacin da ya ɗauka yana ƙare mata kallo ba, karshe dai tsintar kansa yayi lullube da ita. Cikin mafarki ta ji alamun mutum tattare da ita, a hankali da baƙin abubuwan da ta ke ji ya sanya ta tabbatar da gaskiya ce ba mafarki ba. Buɗe baki ta yi don yin ihu take ya liƙe mata shi da nasa. Ba ta san yanayin ba, wannan shine mafari, ba za ta iya tantance me take ciki ba ta ji gaba ɗaya an ɗaga ta. Bai ɓata lokacin kauda doguwar rigar ba balle aika mata sakwanni hakanan bai ɗauki doguwar lokaci ba ya gauraya kwayoyin halittarsu su ka tabbata ɗaya. *** Kiran Sallar magariba yayi daidai da samun natsuwarsa, kallon ta yake cikin mamaki da takaici. Tsaki ya ja kana ya tashi ya shige banɗaki in da yayi wanka ya fice masallaci. Sai a lokacin Amatullah ta saki kukan da ta dinga maƙewa, kuka sosai ta ke yi duk da cikin ranta ta gode ma Allah da ya bata ikon rike mutuncin ta har sai da ta miƙa shi ga mijin aure ba mijin dandi ba. Tunawa da littafan da ta karanta tayi, ta tuna yanda miji ke surar matarsa zuwa banɗaki ya mata wanka ya bata kyaututtuka amma ita ba ta tsira da komai ba sai tsaki. 'Ai ke ma ba ki suma ba, ance ana suma ne' wata sashi na zuciyarta ta faɗi mata hakan.. "Toh ai bai dade ba, su an ce ana yin awanni, toh ko bai da lafiya ne" ta faɗi a sarari sai da ta fadi sanan ta ji kunyar kanta. A hankali ta isa banɗaki ta yi wanka, ta lallaba ta bada farali. Nan ma godiya ta yi ga Allah da ya tsare ta sannan ta roke shi da ya ƙara kare ta daga afkawa sharrin zina. *** Kwana uku aka ɗauka duk dare sai ya zo gare ta kuma duk zuwa kyautan tsaki ya ke bin ta da shi. Washegarin na huɗu ne ya tsare ta ya ce "Wai ke ina iliminki yaje ne, ko yarinya yar shekara goma sha biyu aka aura ta san yanda za ta yi sarrafa amma ke kin wani baje kin bar mutum da aiki, mtswwwww" ya fice ya barta cikin ƙunan rai da tunani. Wannan wani irin abu ne, kullum ya je sai ya dawo amma kuma bai hana a bi ta da tsaki ba. Ta tuna littafin da ta karanta ƙarshe auren dole aka musu amma tun da ya tara da ita sau ɗaya ya bata kyaututtuka haɗe da yi mata alkawura, ba za ta manta labarin ba don ganin kamanceceniya da yake da su amma ita ga shi ta ga akasin haka. Shima ranar da takaici ya fita, haduwar da yayi da su Yunus ne ya sa ya faɗi masu damuwar shi. "Kun sa na kula yarinyar nan amma in ban da takaici ba abin da take cusa min, in kana neman bahar maliya ka sameta ka gama samun komi amma wallahi yanda kuka san sanda haka fa take min" yace cikin takaici. "Hahahhhhhh wayyo Saif, kace a gajimare kake yawo, ai daga ganinta ka san can wajen natural spice gareshi" Yunus ya ce cikin shakiyanci. "Natural spice din banza, ai bai kamata ta maida min shi abu mai wahala ba" ya kara faɗi a ƙufule. "Kaga Saif, duk ba wani tashin hankali bane, Kaga am very sure ita ba kallon porn take ba, ita ba karanta explicit abubuwa take ba, ita kuma ba wai yar hannu bace wai ba za ka gode Allah ba. Ka dena haɗa aure da duniyanci Saif, koya mata ka mori ƙuruciyarta ni dai shawaran da zan baka kenan. In ba ta iya ba ai kana da Ayush, ita sai tayi maka abin da Amatullah ta kasa maka" Salis ya ce masa yana mai tabo kafadunsa. Da wannan tunanin ya dan ji salama har ya cire alwashin da ya ɗauka akan ba zai sake kallon ta ba. [3/12, 11:55 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA Kalamansa sun tsaya mata a rai, duk iya tunanin ta rasa gane mai hakan ya ke nufi, ita dai ta san ba ta ji azaban da ake lissafawa a littafan hausa ba duk da dai ba za ta ce babu zafin ba, sannan bata ga an yi tun dare har asuba ba, sannan kwatakwata mintunan da yayi bai kai wanda ta karanta ba. Ita ba ta abin daɗi a ciki ba. "A haka kuma wasu ke kwasan zunubi da shi" ta ce tana mai ƙarasawa da jan tsaki. Wayarta ta ɗauko tana mai tunanin ko ta kira goggonta ne, amma kunyar da ya rufe ta bayan ta tuna haka ya sanya ta yi ma kanta dariya. "Inna Hafsatu" tace a bayyane tana tunawa da kanwar goggo Mairo, wacce ita ce karamar su baki ɗaya. Sau da yawa idan inna Hafsatu na bukatar shawara, Amatullah ta ke nema su ci su suɗe tsakaninsu. Latsa lambar ta yi, bugu biyu a na uku ta ɗauka "ɗiyata amarya!" tace cikin dariya da farin ciki. Ita kanta Amatullah dariya ta yi sannan su ka gaisa, bayan nan sai ta yi shiru tana tunanin ta ina za ta fara. "Darling Daughter ko dai in zo ne" Inna hafsatu tace ganin da alamu Amatullah na da magana a bakin ta. "A'a fa, dama, Hmmmn dama shine wai ban iya komi ba" tace kamar ta sa kuka don ji tayi ta gama tona asirin ta watau dai yanzu innarta ta san me suke yi. " Ai shi kuma dai, ai a hankali ne abin, ba wanda aka haifa da iyawa" tace mata, jin haka Amatullah ta samu ƙarfin cigaba da faɗin "kuma fa Shima ɗin baya kai asuba fa, kwatakwata 20min fa, sannan wani kyauta wani alkawura duk baya yi ko duk rashin iyawan ne" Dariya sosai inna Hafsatu tayi kana tace "A ina kika ji anayi tun dare har asuba, sannan wani kyauta kuma za a baki" "Kai inna ai na karanta littafan hausa da dama na ga duk haka ake yi" tace iya gaskiyanta. "Toh ke girki kala nawa kike masa kafin ya farka baccin" inna ta tambaya, shiru Amatullah tayi, don duk tunanin ta akan yin girki kala kala kafin ya farka ya kan kulle, ta kan masa farfesu dai duk rana breakfast ko dinner amma ba ma za ta iya yin girke-girke da taga ana lissafa wa ba. "kin yi shiru Darling" inna ta katse mata tunanin ta. " Kinga Amatullah ki ajiye rayuwar novel ki rungumi rayuwar zahiri. Mijinki mijinki ne, in ba mai shan magani ba babu mai lafiya da zai yi awa yana abu ɗaya, sannan ai ke ba injin ba ce, zancen kyaututtuka in ya baki ci da sha, bai wulakanta ki ba, bai barki cikin tsumma ba ai gama miki duk wani soyayya. Aikin me yake yi da zai baki mota ko wani ubansu kyauta kawai don kin rike mutuncin kanki? Ai kyautan kenan ya ƙara daraja ki, sannan duk wulakancinsa ba zai taɓa danganta ki da matar banza ba. Zancen baki iya ba, ki duba ki ga abin da ya miki ki kwatanta hakan, kina lakantar me yafi so. Sannan kar ki manta Addu'oi. Ina Littafin Gidan Aurena, ki karanta it can serve as a guide Kuma da Addu'oi a ciki don samun kan mijinki" haka inna Hafsatu ta dinga mata nasiha da bayanai har sai da ta tabbatar da ta fahimta sannan su ka yi sallama. Da karfinta ta tashi ta shiga kitchen nan ɗin ma abincin da ta san yana so ta shiga haɗa masa, farar shinkafa da miyar ganye amma maimakon taushe sauce take masa ya ji nama da hanta. Duba fridge ta yi ta ga suna da sauran kankana ta yi haramar yi masa lemun kankana da madara. *** Cikin ikon Allah sai da ta kammala komi har ta yi wanka kafin ya shigo bayan la'asar, sanye ta ke da doguwar riga ta atamfa amma gaba ɗaya bai wuce guiwanta ba. Dinkin ya kamata daga sama sai ƙasan aka yi mata kamar lema hakan yayi daidai da zamansa a kan mazaunanta ya fito da kyawu ta. Hoda kawai ta sa a fuskar ta, kanta kuma da ya ji kitso ta barshi a buɗe. Babu abin da ke fita daga jikinta sai ƙamshi. Tun da tace masa sannu da zuwa uffan bata sake haɗa su ba, amma tana zaune a kujera ya natsu yana cin abinci haɗe da kora lemun. "akwai saura da yawa" yace bayan ya idar da na gabansa, shiru tayi kamar hankalinta na ga talabijin sai da ya sake maimaita mata sannan ta yi firgigit ta amsa da akwai. "Zuba ma Baban Sasa ki zo mu je mu kai masa" yace yana mikewa. Wani murna ta ji bata san lokacin da ta rungume shi ta baya ba, shi kuma a hankali ya juyo da ita, kallon da yake mata duk ya tafi da imaninta. "Kin san ban masa godiya daga ƙasan zuciya ta ba, yau zan masa, don ba ƙaramin gata ya min ba, Ubangiji Allah ya miki Albarka Amatullah" ya faɗi yana mai haɗa laɓɓansu. Yanda ta saki jiki ya bashi mamaki, ita kanta sai a lokacin ta san garɗin abin. Bayan yan mintuna su ka je don su shirya zuwa ga Baban Sasa. *** "Yaya Amatullah oyoyo!" da yaran gidan ke faɗi ya isa ga kunnuwan matan gidan, sosai mahaifiyarta ta shiga farin ciki haka baba Anas da ke zaune yana sauraron radiyo France shirin almuru. Tare su ka shigo tamkar wasu taurari, sanye yake da shadda wanda ya ji aikin hannu ruwan samaniya, hulansa yayi daidai da kalar aikin jikin shaddan. Ita kuma Amatullah sanye take da material fari mai adon fulawa na kaloli, ta ɗaura hijabi ja wanda ya shiga da jan da ke cikin fulawar, kafunta sanye da takalmi ja mai tsini. Babu wani ado a fuskarta face hodar da ta sanya don rage maiƙon fuska. Fuskar nan tata cike da annuri, ji take kamar ta sheƙa a guje ta ga goggo maironta. Sanin da ta masa na son aji ya sa ta danne murnarta har su ka isa ɗakin Baban Sasa a tare. Shima zaune ya ke yana kallon Aljazeera su ka yi sallama su ka shiga. Wangale bakin da ya yi kaɗai ya isa ya bayyana farin cikin da ya ke ciki. Nan su ka zube su ka gaishe shi, ya amsa yana mai shi masu albarka. Kwandon abinci da Saifullah ya riko ya ajiye gabansa yana mai cewa "Kaci ka ji irin daɗin da ake ciyar da ni, kai Tsohon nan ka fi kowa iya match making" ya ƙarasa cikin tsokana. Zama su ka gyara da su ka ga da gaske baban Sasa santi yake bayan Saifullah ya zuba masa abincin. Suna cikin masa shaƙiyanci su Baba Anas su ka shigo, nan Amatullah ta ji duk wani kunyar duniya ya rufe ta. Gaishe su tayi ta tashi sum za ta fice, take Saifullahi ya tashi ya bi bayanta, ya bar iyayensu da mamaki. "Allah ya saka da Aljanna Babanmu, ka gansu ko" Baba Anas yace cikin murna, nan saura su ka shiga farin ciki suna fadin yanda Saifullah ya yi ƙiba. "Ai tsatson Mairo gwanaye ne a mallaka, ku duba ku ga, yaron nan ba so yake ba amma yanzu ya zama bindi. Kaico!" Baba mahmuda ya faɗi wanda hakan ya ɗanyi tasiri a zukatan wasu daga cikinsu. "Ko me zata yi ta daɗe bata yi ba, balle wannan girki haka, kai ko zaku ɗanɗana ne" Baban Sasa yace yana tura musu raguwar abincin nan sai su ka yi shiru. *** A cikin gida ɗakin Hajiya ya ja ta, bayan sun gaida matan da ke wajen gida, ji tayi kamar ta rusa kuka ganin yanda ya hakince a kujera. Hajiya ma da ke zaune in ban da tururi babu abin da zuciyarta ke mata ganin fara'ar da Saifullah ke ma Amatullah da yanda ya ke sako ta a cikin hirar su. Rasa yanda za ta yi ta cusa ma Amatullah haushi bayan ta fito da turarruka biyu ta ba hajiya a sunan nata da na Baba Anas, Saifullah da bai san da turare ba ya dinga shi mata albarka ba tare da ya ba hajiya damar cewa uffan ba. "Hajiya wallahi turarruka ne masu shegen tsada kin gansu, ni ban ma san ta riko muku ba, ke abin da kike da pocket money dinki Kenan" ita dai Amatullah murmushi kawai ta ke yi, duk da bata san darajan turaren ba, zuwan da mahaifin ta yayi ne ya bata da umurnin duk ranar da ta je gida ta kai a hajiya da baba Anas. "Toh ni in ba don ka faɗi ba ai sai in ce yan uku da hamsin ne" tace tana yatsina. Dariya Saifullah yayi ba tare da ya auno komi ba. Su ka cigaba da hira, anan ne Hajiya ta ce. "Ni kuwa ina Ayush ne? Yaushe za aje gaisuwa ne?" tace tana tsare shi da ido, kallon Amatullah yayi cikin sauri ya ga babu wani sauyi a fuskar ta, haka kawai ya tsinci kanshi da jin haushin hajiya, bai ce da ita kanzil ba, sai da ta sake maimaitawa. "Hajiya da kin manta da Ayush da duk yafi, ba ta ban damar yi mata bayani ba, ta daina ɗaukan wayata, ni bata sake nema na ba sai ɗazu, na ga kiranta sau uku duk ba wanda na ɗauka" yace kai tsaye. Duk da Amatullah ta ji ɗacin zancen sa ta ɗaure ba tare da ta nuna masu ba, tashi yayi yana riko ta kamar mai koyon tsayawa tare da faɗin "Muje wajen goggona sharp sharp mu wuce" Kamar jela haka ta bi shi tana mai ma hajiya sallama. Takaici bai rufe ta ba sai duk yanda ta so su keɓe da mahaifiyarta bai bari ba, zama yayi ya dinga janta da hira kamar Saifullah kafin dawowarshi daga Rasha. Nan su ka ci abincin dare ba su suka bar gidan ba sai bayan sallan magariba. Tun da su ka dauki hanya maganar Hajiya ce ke damun zuciyar ta, dan haka ta yanke hukuncin tarar aradu da ka, ta mai nisawa ta furta "Yaya Saifullahi wacece Ayush?" Kallon ta yayi na wani ɗan lokaci, har ta fitar da ran jin amsa daga gare shi ta ji ya ce "Budurwa ta ce........." Gaban Amatullah ya faɗi, shi kuwa gogan na ta ko a jikin sa bai gushe ba ya cigaba da faɗin " ita na so aura kafin Baban Sasa ya aura min ke, kuma har yanzu ban fitar da ran za ta zama mata a gare ni ba" Ya karasa maganar ya na duban ta da wutsiyar idanu. Daurewa ta yi duk da bakin kishin da ya tukare ta a kirji, ta na mai murmushin ya ke ta furta "Ai namiji mijin mace huɗu ne, Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa" Shi ma din murmushin ya sakar mata yayinda da ya saki numfashi da shi kan sa bai san ya rike, kana ya ce "Dadi na da ke hankali Amatullah, Aameen dan rasulillahi" Haka su ka cigaba da tafiya, ya na ɗan jan ta da hira amma ita Allah Allah ya ke su isa gida ko ta samu ta shiga dakin ta yi kuka ko ta ji sauki a ran ta. Ko da su ka isa dakin ta ta shige, cikin bandaki ta sha kukan ta, sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi wanka da alwala. Da wuri ta kwanta dan kada ma Saifullahi ya rabe, shi ma Saifullahi da tun a mota ya gano halin da ta ke ciki, daren ranar sarara mata yayi, ya na mai fatan daga ranar dai ba za ta dauki sarar hana shi hakkin sa ba, dan kuwa in dai wannan ko gaban Baban Sasa sa je. *** Rayuwar su suke gwanin ban sha'awa, in da ta yi watsi da maganar Ayush ta mayar da hankalin ta wajan kula da mijin ta. Ba ta wasa da cikin sa, tana masa biyayya sosai sannan ta fannin ƙishinsa kullum cikin koyon salon da za ta kashe masa ƙishinsa ta ke, shi ma baya gajiya da koyar da ita. Ranakun karatun ta shi ke kaita ya ɗauko ta, sannan duk wani abin da ba ta fahimta ba duk da aji biyu karatun fannin kwas dinsu ne mafi akasari yana kokarin nuna mata. Lokaci ya ware mata wajen karatu, ya kan fita ya bar mata gidan tayi karatun ta, lectures ko ƙarfe bakwai aka sanya sai ya tabbatar da ba ta makara ba. Uwa uba baya gajiya da gayyatarta makwanci, ba ta san lokacin da ta zama majuniniya a soyayyarsu ba. Duk kulawar da ya ke nuna mata bai hana masa yin waya da Ayush ba, wacce daga baya da kan ta ta kira Saifullahi ta ba shi hakuri, ta kuma amince da auren ta da zai yi a matsayin mata ta biyu, Amma fa da sharaɗin tun da auren dole ya ce aka ma sa, kada ya kuskura ta ji sun hada shimfiɗa da matar shi bare ta ji tana da juna biyu. Jin ta kawai Saifullahi yayi dan kuwa aikin gama ya gama, bare kuma babu yanda za a yi yana ganin mace kamar Amatullah ya zuba mata idanu, shi ma ya san da Ayush ta san wacece matar da aka aura masa da ba ta yi wannan yasshesshen zancen ba. Ya kan kai mata ziyara lokaci zuwa lokaci kuma ya mata alkawarin zai aure ta matsayin matarsa ta biyu kuma ta ƙarshe nan da shekara daya da rabi, yanda Babab Sasa ba zai hana shi kara aure ba. Bai ɓoye ma Amatullah ba don a cewarsa kar ta yaudari kanta. Sannu a hankali su ka cika shekara da aure, a ranar ya mata kyautan zinari na naira dubu dari biyu da hamsin. "Kinga kin zama min haske tun cikin 2009 har 2010, ina fatan ki zama tauraruwa, wata kuma ranar da zata dinga haska rayuwata har ƙarshen ta. Amatullah ke ɗin Alkhairi ce, na gode" yace yayin da yake miƙa mata. Ji tayi gaba ɗaya ba ta da wani damuwa, nan ta ƙara son mijinta, ta kuma so Baban Sasa don shi ya zama silar samun gatanta. "Na Gode Saahib, Ubangiji Allah ya bar mu tare har a Aljanna" tace tana mai rungume shi. Sati uku bayan cikar su shekara ɗaya yayi daidai da lokacin ganin baƙon watanta, amma shiru ake ji, ga duk wani alamu na zuwansa ta gani amma shiru babu shi babu alamunsa. Inna Hafsatu ta kira ta faɗa mata, nan ta mata alkawarin biyowa in ta taso daga aiki. "Alhamdulillah!!! Amatullah addu'ar mu ta amsu, bayan shekara ɗaya fa, Alhamdulillah!!" tace bayan ta ɗaga tsinken gwajin cikin da ya nuna Amatullah na ɗauke da shi, rufe fuska Amatullah tayi cike da jin kunyar innarta. " Daina kunya, ciki da ubansa, kar na zama babbar kwabo da na yi ma Saifullah albishir" tace cikin dariya. Nan ta bata shawarwari tare da mata addu'ar samun sauki wajen rainon ciki da haihuwa sannan ta tafi. *** Faɗin irin ƙosawar da Amatullah ta shiga akan dawowar Saifullah wanda ya je Kano wajen Ayush. Ji tayi kamar ta masa waya don ta hango farin cikin da zai yi in ta faɗa masa. Tashi tayi ta kimtsa tare da shirya masa abinci, sannan ta samu waje ta zauna tana duban agogo. Biyar da minti shida ya shigo, nan ta rungume shi cikin tsantsan farin ciki. Kallon ta yayi cikin murmushi yace "Hala mafarki kika yi bazan dawo ba" "Haba Saahib, kawai dai farin cikin samun ka a matsayin miji nake kullu yaumin" tace tana kanne masa idanu. Sai bayan ya gama cin abinci ya miƙe ƙafa yana bata labari ne ta ɗauko masa tsinken da ba ta yar ba. Kallon ta yake a sheƙe, cike da tuhuma da son musanta zargin sa, ganin yayi shiru ya sa tace "Saahib duba fa, kyautar Allah bayan shekara ɗaya" tace tana mai tsananin farin ciki. "Ni wallahi ban taɓa ganin Jarababba irin ki ba, har yaushe aka yi auren da za ki ƙunso ciki" yace a hasale wanda hakan ya sa ta yin mutuwar zaune. "Saahib shekara ɗaya fa, ba wayonmu ko dabara fa" tace a marairaice. "will you shut up!" yace cikin tsawa. Hango ta haihu yake yi shike nan yan biyunsa zubewa za su yi, ita kanta buɗewa za ta yi, ba zai sake jin daɗin da yake ji ba, ga Alkawarin da ya tabbatar ma Ayush ita za ta fara haihuwa a gidansa. "Allah ya isa! Allah ya isa Amatullah!! Me ya sa kika bari ciki ya shiga, muna zaman lafiya abun mu why? Why Amatullah" ya ce a rikice yana mai jifa da kofin tangaran din da ke kusa da shi. Take ya tarwatse gaba ɗaya. Riko ta yayi idanunsa cikin nata ya ce "kina so na?" bata iya amsawa ba sai gyaɗa kai da ta yi. "Muje a cire abin nan, mu cigaba da rayuwar mu hankali kwance kinji" ji tayi gaba ɗaya ba za ta iya masa musu ba. Ta gwammace ta zubar da cikin, ta gwammace ta jira har zuwa lokacin da zai shirya haihuwa su haihu. Ba musu ta tashi ta shiga daki ta ciro hijabinta.[3/15, 11:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA BIYU Ko da ta fito tashi yayi tsaye su ka fice, a mota ya kira Salis ko yana asibitinsa kasancewarsa likita ma'aikaci a asibitin gwamnati na Gambo sawaba, mahaifin sa kuma ya buɗe masa nashi a cikin GRA, mutane na son asibitin saboda kwarewarsu da kula da marasa lafiya. Minti Ashirin ya ɗauke su kafin su ka isa Umjad clinic and maternity. A dirare Amatullah ta gaida Salis don cike take da waswasi duk da cewa a shirye take da ta yi komi don farin cikin mijinta. Ai ko ba komi Aljannarta na ƙarkashin ƙafafunsa ne, da wannan take ba kanta haƙuri da ƙwarin gwuiwa. "Bari mu yi scan mu ga girman cikin don kamar ya fi wata ɗaya fa" Salis ya ce bayan ya ɗan dudduba ta. "Kai likita ban son shegantaka, watan nan ne kawai ta yi ɓatan sa amma duk saura suna zuwa" Saifullah ya ce a ƙufule, shi kawai so yayi a mata allura ko ya bata kwaya ta haɗiya cikin ya zube. "Engr. Ai wasu ma har su haihu su na yi, wasu in sun kammala wata ukun farko, wasu sai ya kai shida, amma mafi akasari daga ciki ya shiga wata ɗaya ko sati biyu yake ɗaukewa" Da haka ya tura ta scanning wannan ake yi a wani sashi na asibitin. Saifullah bai yarda ta tafi ita ɗaya ba, tare su ka je bayan an tabbatar da a matse take aka sa ta hawa gadon gwaji. "yaushe kika ce kin ga hailan ki ƙarshe, first date of your last period" ya ƙarasa cikin turanci ganin bata fahimci hausar ba, bai san cewa tsananin tsurewa ne da tunane tunane ya cika mata ciki. " 5th August" tace kai tsaye "Wow, Kuna cikin ƴan baiwa" ya ce yana kallon allon kwamfutarsa yana cigaba da dudduba ta, bayan ya gama ya fitar da sakamako ya basu don maida ma Salis. "Ai na faɗi maka, kallo ɗaya na mata na san ya wuce haka, cikin ta satinsa goma sha biyar da kwana uku ko ba kwana uku (15weeks +/- 3days)" Salis ya faɗi yana mai addu'a a ranshi ko Saifullah zai canza shawara. "Sai a burge shi kawai Salis, ni dai ya fita, ban shirya zama uba ba, beside kwatakwata yaushe aka yi auren, ace mace daga an kalle ta se ciki" ya ce cikin fushi yana mai bankawa Amatullah harara. Ganin haka Salis ya bashi takarda ya sa hannu, itama ta sa hannu akan da amincewarta za ayi. "Za ka iya zama da ita sanda za a cire....." "Ina ba zan iya ba, just let me know idan ka gama" Yana gama fadin haka ko kallan Amatullah wanda idanun ta su ka ciko da hawaye bai yi ba, ya sa ƙafa ya fice. Dakin da aka tanada na musammam Wanda ake kira da Gynae Emergency Room Dr Salis ya shigar da ita, hankalin Amatullah bai tashi ba sai da ta ga wani gado dan siriri, gefe da gefen sa wasu karafuna ne. Dr Salis na mai duban Amatullah ya ce "Madam zan ba ki dama ki shirya kafin nan an gama sterilizing kayan aikin, wannan gadon za ki hau, and remove your pant please" Ya na gama maganar ya juya ya fice. 'and remove your pant please' Maganar da ya tsaya mata a rai kenan, kallan gadon ta ke cikin tashin hankali, komai na dakin ma abin tsoro ne. A sanyaye ta zame pant din ta, ta ninke ta sa a jaka. Amma sai ta kasa hawa kan gadon, hawayen da take ta kokarin rikewa tuni suka fara gangarowa bisa kuncin ta, yayin da ta ke gogewa da bayan hannun ta. Bayan minti goma Dr Salis ya shigo dauke wani ɗan tire. Amatullah ta bi tiren da idanu in da idanun ta su ka yi kacibus da kananan karafuna, wasu kamar aska, sai mai ɗan lankwasa kamar kugiya, sai wasu kamar kananan wuka, da wasu ma su zubin almakashi. "Madam da fatan kin shirya, before then zan mi ki allura, ta Pentazocine domin kashe zafin wajan ko?" Cewar Dr Salis ya na mai sanya safa a hannun shi. Sai da ya mata allurar kafin ya sake cire safar hannun ya fita. Kusan minti biyar ya sake ɗauka kafin ya dawo, ganin har lokacin Amatullah ba ta hau gadon ba ya ce da ita "bisimillah madam, ki cire zanin ki ki hau gadon" "Shin ba ku da Doctor mace ne?" Cewar Amatullah cikin tashin hankali. Murmushi Dr Salis yayi, kana ya ce "Unfortunately babu, Amma kar ki damu ai duk cikin neman lafiya ne, ni ma ina da iyali kamar ke a gida" "Za ka bari a yiwa iyalin ka abin da za ka min yanzu? Za ka bari a zubar mata da ciki? " Ta sake tambayar sa. Ya na mai yamutsa fuska ya ce "Idan iyalina ba ta da lafiya kuma babu Doctor mace sai namiji why not? But batun bari a zubar da cikin wannan ra'ayin ki ne ke da mijin ki ai" Shiru ta yi tana mai duban gadon, hannun ta bisa cikin ta. "Idan kin shirya please" Dr Salis ya sake maimaitawa a karo na biyu. Jiki sanyaye Amatullah ta cire zanin jikin ta ya rage sai under siket, yayinda da ta tattare hijabin ta zuwa wuya. A hankali ta haye bisa gadon. Ganin Dr Salis ya gyara karafunan da ke gefe da gefen gadon yayinda da ya umarce ta da ta sanya kowacce kafa bisa karafunan yanda kafafun ta za su bude sosai ya sanya Amatullah girgiza kai. Cikin kokarin ganar da Amatullah ya ce "Madam in ba ki saka kafafunki na ɗaure su jikin karfen nan ba, za ki iya zube kafafun ina cikin aiki kuma hakan zai iya jawo matsala......" Ga mamakin shi sai ganin Amatullah yayi ta diro daga gadon ta na mai sakin hijabin ta, ta ja zanin ta daura. Hannun ta rike da jakar ta ta dubi Dr Salis ta ce "Ka kira shi ka sheda ma sa na ki baka haɗin kai, dan kuwa wallahi babu wanda ya isa ya min abin da ka ke shirin yi min!!!!" Ta na gama fadin haka ta fice, shi kuwa Dr Salis har cikin ran sa ya ji dadin maganar Amatullah. 'ashe dai da sauran wayon ta' cewar Dr Salis cikin ransa. Hankali kwance ya kira Saifullahi ya shaida masa halin da ake ciki. Kamar zai yi hauka dan bacin rai inda ya zo ya tadda Amatullah tsaye bakin kofar Dr Salis. "Malama me ki ke yi anan? Me ya sa ba ki tsaya an cire mi ki wannan abin ba?" Kallan sa ta ke cikin Ido, duk wani shakka na shi da ta ke ji ya gushi, cikin dakewa ta ce "Kai na ke jira ka kai ni gida, wannan abin da ka ke so a cire ba zai yiyu ba, ina san abu na idan kai ba ka so......." Takaici ya sa ya kasa ba ta amsa, cikin bacin rai ya shiga zirga zirga, ya kai ya kawo. Ita dai Amatullah ta zubawa sarautar Allah ido. Cikin wannan hali Dr Salis ya fito ya same su "Ya za ka min haka Dr Salis bayan na saka hannu a cire mata wannan jarabar?" "Ya ka ke so na yi bayan Madam ta ce ba ta so? I can't force her you know, Zai dai fi kyau ku kara shawara......" "Malama wuce mu tafi!" Ya katse Dr Salis, ya wuce fuuu, in da Amatulah ta bi bayan shi. Yanda ya ke tuka motar kamar zai tashi sama, ita dai adduar ta su isa lafiya. Gashi allurar da aka mata ya dan fara saka ta jiri, haka kuma duka jikin ta ya mutu. Suna isa tun kafin ta fito daga mota ya riga ta fita, a falo ta taddashi ya na ta kai kawo kamar wanda ya hadiyi gatari. Sim sim ta shige shi za ta wuce dakin ta ya daga ya tsayar da ita ta hanyar daka mata matsawa "Malama ji mana!!!!!" Amatullah ta tsaya, gaban ta ya sha ya na mai nuna ta da dan yatsa ya ce "Wato komai aka haɗa da jaki sai ya ci kara, so ina so ki zaɓa ko ni ko cikin da ke jikin ki!!!!" Kasa magana ta yi, kai kawai ta ke girgiza masa yayinda hawaye ke gudana daga idanun ta. "Malama dallah ki amsa min!!!!" "Ya Saifullahi dan Allah ka yi hakuri....." "Ni ko wannan abin da ke cikin ki?" Hannu ta kai ga cikin ta, ta dago idanun ta ta sanya cikin na shi, murya a sanyaye ta ce "Ciki na, na zaɓi ɗan da ya ke ciki na...." Kallan ta ya ke tsana karara cikin idanun sa "Amatullah yau kin tabbatar mi ni ke butulu ce! Kin zaɓi cikin ki? Fine! Very fine ki je ki auri cikin na ki!! Shashasha bagidajiya!!!!" Ya juya ya fita a fusace. Baki buɗe ta bi bayan shi da kallo, a karo na farko ta nemi kuka ta rasa, fadi ta ke "Inna lillahi wa inna ilaihi ilaihi rajiun" Ta fada ta kara maimaitawa. Jikin ta babu nauyi saboda allurar da aka mata, haka ta lallaba ta shiga daki, ba ta san sanda bacci ya sace ta ba. *** Washagari kamar yanda ta saba ta haɗa masa karin kumallo, amma shiru ya ki fitowa daga dakin sa. Gashi lecture din sassafe gare ta, na 8:30, kuma test za a mu su. Saifullahi da idan ta na da lecture din safiya karfe bakwai shirya tsaf sun ɗauki hanya. Ganin shirun yayi yawa ta je ta buga masa kofa, har ta fitar da rai za a bude kofar, sai gashi ya bude, sanye cikin singileti da gajeran wando. Kallan banza ya bi ta da shi, ya na mika ya furta "Malama lafiya?" Tana inina dan shakkar amsar da zai ba ta, ta ce "Dama school...ka manta ..dama ina da lecture din safe" "Oh toh shi cikin na ki ba zai kai ki makaranta ba?" "Ya Saifullahi........." Hannu ya daga mata tare da faɗin "Shut up!!! Duk sanda ki ka shirya zubar da wannan abin da ki ke dauke da shi toh sai ki tafi makarantar, but for now ki saka a ranki cikin ki ki ke aure, kuma wallahi ki ka saka kafa ki bar gidan nan wallahi sai na lahira ya fi ki kin daɗi! Bagidajiya kawai!" Ya na gama magana ya ja kofa ya mayar ya rufe. Kuka Amatullah ta saki mai karfi har da shashsheka, da sauri ta koma ɗakin ta, in da ta ɗauki wayar ta, numbar Baban Sasa ta shiga kira, bugu na uku Baban Sasa ya dauka ya na mai faɗin "Amaryar yau kewata ake da sassafe?" Maimakon ya yaji muryar Amatullah cikin walwala kamar yanda ya saba ji, sai ji ta yi tana kuka har da shashsheka, ta ma kasa magana. "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!!! Lafiya Amatullah? Ina Saifullahi? Me ya same shi? Wani abu ne ya same shi" "Dama shi ne ya ce ba zan je makaranta ba ...." "Akan wani dalilin kuma????" Baban Sasa ya tambaya cikin nuna bacin rai "Wai dan na ce.....Wai dan ina dauke. . wai dan...." Amatullah ta tsinci kan ta tana mai kame kame, jin haka Baban Sasa ya ce "Wai dan me Amatullah?" Wuf Saifullahi ya fuzge wayar, dama tun da ya juyo kukan Amatullah ya san za a rina, hankalin sa ya kasa kwanciya ya biyo bayan ta, ya kuwa tadda ta tana shirin shaidawa Baban Sasa halin da su ke ciki. "Baban Sasa, shagwaba ce irin na Amatullah" "Shagwaba irin na Amatullah? Me ya sa ka hana ta zuwa makaranta?" "Ba hana ta zuwa makaranta na yi ba, yanzun haka ma shirin kai ta makarantar, ka san halin matar ta ka ne sai a sannu" Shiru Baban Sasa yayi kafin daga bisani ya ce ya bawa Amatullah wayar. Maimakon ya bata wayar, sai ya saka ta handsfree, ya na mai yi mata gargadi ta san amsar da za ta bawa Baban Sasa. "Amatullah shin akwai wani damuwa na bayan zuwa makarantar?" Idanun ta kan Saifullahi ta ke girgiza mata kai, Amatullah ta ce "Ah ah Baban Sasa, dama shi ne kawai" "Kin tabbatar? Kar ki boye min komai" "Babu komai Baban Sasa" "Maza ki shirya yanzu zai kai ki, Allah ya mu ku albarka" Ta amsa masa da amen. Saifullahi na kashe wayar maimakon ya bata, sai ya tusa shi aljihun sa, baki bude Amatullah ke duban shi. Ganin ya juya ya fice daga ɗakin ta biyo shi da sauri zuwa falo, ko a jikin sa ya wuce zai shige dakin sa ta yi saurin tsayar da shi "Wallahi Yaya Saifullahi test gare ni, idan na yi missing carry over ce......" Ya na murmushin mugunta ya ke kallan ta "Toh ke a na ki wautan makarantar zan kai ki? Saurare ni da kyau, Wallahi! Wallahi! Wallahi! Babu ke babu makaranta matukar ba ki yarda an zubar da wannan abin da ke cikin ki ba!!!!" Yayi maganar ne ya na mai nuni ga cikin ta, bai gushe ba ya kara da "Ba ke mai Baban Sasa ba? Sai ki je gida ki fada ma sa ai, shashasha, ba carry over ba, Allah ya sa spill over ne!!! What a local human being!!!!!" Fuuu ya wuce dakin sa, in da Amatulah ta bishi da kallo, hannun ta bisa kirjin ta tsabagen zafi da zuciyar ta ke mata. [3/18, 11:07 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA UKU Ɗakinta ta koma, ta ɗauko jakar ta da take ɗan ajiyar ta, ko da ta ƙirga chanjin da ke ciki ko makaranta ba zai kai ta ba, balle ayi maganar dawo da ita gida. Bakin gado ta zauna tana zancen zuci. Ta san duk abin nan da Saifullahi ke mata dan cikin da take ɗauke da shi ne, cikin da ba ita ta sakawa kan ta, tsabagen rashin adalci irin na mijin ta. Nan ta sha alwashin hafe cikin ko da kuwa hakan na nufin karshen zaman ta da Saifullah ne. Wasa wasa Amatullah na ji ta na gani ya hana ta zuwa makaranta, wayar ta kuma ya kashe, Su Gwoggo kuma ya tsara mu su karyar wayar Amatullah ta sami matsala, idan kuma suka kira daga ya ce ta na makaranta nan za ta wuni, sai ya ce ta na bayi. Tun abin ba ya damun Gwaggo har ta fara tunanin ko lafiya. Gashi ko abinci idan ta girka ba ya ci balle a kai ga magana mai daɗi ta shiga tsakanin su. Duniya ta yiwa Amatullah zafi, ji ta ke kamar ta na gidan kurkuku har tsawan kwana uku. A na hudun ne da safe Saifullahi na fita, itama ta sanya hijabin ta. Dan kudin da ke hannun ta ta biya kudin mota ba ta zame ko ina ba sai gida. A zaure ta tadda Baban Sasa zaune bisa tabarma tare da Baba Anas. Yanda ta shigo mu su afujajan kamar an koro ta ne ya sa suka tsora, in da a tare su ke tambayar lafiya? Gaban Baban Sasa ta zauna ta na kuka hawaye ɗaya na bin ɗaya, ta ce "Baban Sasa ya hana ni zuwa makaranta, kwana uku kenan ya hana ni, ya ki kai ni ya kuma ki ba ni kudin mota da na tafi....." "Innalillahi wainnailaihi rajiun, wai shi Saifullahi ya hana ki zuwa makaranta? Bayan nan ya zo ya gaishe mu kafin ya shige cikin gida ya ce da mu ya dawo daga kai ki makaranta ne? Shin dama ba lafiya lau ku ke zaune ba Amatullah? Me ya sa ba ki kira kin sheda mana a waya ba?" Tambayoyin da Baba Sasa ya jero mata kenan. Shi kuwa Baba Anas gyada kai kawai ya ke. "Wallahi Baban Sasa karya ya ke, ya hana ni zuwa makarantar, hatta wayar ma shi ya kwace tun ranar da na kira... .." "Daina rantsuwa Amatullah, wallahi idan dai Saifullahi ne zai aika, jairi ka na ganin shi sim sim yaran nan bai da girma sai na jikin sa!" Baba Anas ne ya katse ta. Cike da bacin rai ya tashi ya shiga ciki a fusace kafar shi ko takalmi Babu. Baban Sasa kuwa shi har a lokacin bai yarda Saifullahi zai iya aikata hakan ba, duk da kuwa Amatullah ba ta taba masa karya ba. A dakin Hajiya ya tadda shi, yayi rashe rashe ya na cin wainar gero da kunu. Kallo ɗaya ya yiwa mahaifin na sa ya tabbatar da bacin ran da ke tattare da shi "Babu shakka, dole ka rashe a nan kana cin kumallo hankali kwance tun da ka hana 'yar mutane zuwa makaranta" Cewar Baba Anas ya na kallan sa cike da takaici, in da Saifullahi ya kware ya na mai fuzar da wainar da ya kai bakin sa jin maganar da mahaifin na shi yayi, har ya na kwarewa. Baba Anas bai kula da kwarewar da Saifullahi yayi ba, ya kara da "Matar ka tana zaure, ka taho maza ka yiwa Baban Sasa dalilin hana ta zuwa makarantar da ka yi har tsahon kwana uku, da kuma dalilin kwace wayar ta da ka yi, mugu azzalumi! " Har ya juya zai tafi ya dawo, ya na mai nuna sa da dan yatsa ya ce "Ka tabbatar ka na da kwakkwarar hujja na aikata wannan zalincin, ka da ka manta na ɗau alkawarin yanda ka yiwa Amatullah kwatankwacin yanda zan yiwa uwar ka...." Furucin yayi daidai da fitowar Hajiya daga uwar daka, ta na mai sallallami ta ta ke tambayar Baba Anas ko lafiya. Saifullahi ya nuna da danyatsa ya ce "Ga ki ga shi ai! Ka da ka sake ka kara minti biyar cikin gidan nan! Ka fito maza ka same mu!" Ya juya ya fita a fusace. Saifullahi ma aje abinci yayi ya biyo bayan sa, Hajiya na tambayar ba'asi ya ce da ita ta jira zai mata bayani. Shigar sa zauren ya tadda Amatullah zaune kusa da Baban Sasa har lokacin ba ta dena kuka ba. Bakin ciki da takaicin ganin ta ne ya tokare ma sa ƙirji, Baba Sasa kuwa bin shi yayi da kallo mai wuyar fassara. In da Baba Anas ke bin shi da harara. Kusa da Amatulah ya tsungunna, cikin nuna kulawa ya ce "Amatullah me ya faru? Me ya sa ki ka zo gida ki dagawa Baban Sasa hankali? Ba kya la'akari da rashin lafiyar shi ......" "Ungo nan!" Baban Sasa ne ya masa dakuwa, kana ya kara da "Kai din ka yi la'akari da rashin lafiyar ta wa ne da za ka hana diyar mutane zuwa makaranta? Akan wani dalilin ma?" "Ban fa hana ta zuwa makaranta ba Baban Sasa....." "Wallahi ya hana ni, rabona da makaranta kwana uku kenan!" Kallan sa su ke in da yayi kasa da na sa kan. "Yau da na tambaye ka na ina yarinyar nan ta ke ina ka ce ka baro ta?" Baban Sasa ya sake tambayar shi, shiru ka ke ji Saifullahi ya kasa amsa masa. "Shirun da ka yi ta tabbatar mana da gaskiyar Amatullah, menene hujjar ka?" Shiru ka ke ji, duk bakin Saifullahi yau Amatullah ta daure shi da jijiyoyin sa, bai taɓa tsammanin za ta masa haka ba. "Tun da shi ya ka sa amsa mana, ke Amatullah sai ki fada mana, a wani dalili ya hana ki zuwa makaranta?" Cikin faduwar gaba Saifullahi ya daga kai, ya kai kallan sa ga Amatullah, ita ma din kallan sa ta ke. Idanun sa cike da magiya ya ke duban ta, cikin dabara ya dan girgiza mata kai alamar ta rufa masa asiri. Amatullah ta kawar da kan ta da sauri. "Ke mu ke sauraro Amatullah, kada ki ji komai ki faɗa mana gaskiya, idan ba ki faɗa mana damuwar ki ba wa za ki faɗa mana" Cewar Baba Anas wanda ya lura da irin kallan da Saifullahi ya ke mata. Murya sanyaye ba tare da ta sake yarda sun hada idanu da Saifullahi ba ta ce "Wai cewa yayi....dama cewa yayi sai an zubar....." Nauyi ya sa ta kakare ta kasa karasa maganar, Saifullahi kuwa kallan ta ya ke cikin fargaba, cikin ran sa ya ke 'ashe yarinyar nan ba matar rufin asiri ba ce!!' "Sai an zubar da me? Baba Anas da ya fara dago jirgen ne ya tambaye ta, cikin adduar Allah ya sa zatan shi ba daidai ba ne "Juna biyun da na ke dauke da shi......" "Laa ilaha illa Allahu Muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasallam!!!" Baba Anas ne ya doka Salati, in da shi kuwa Baba Sasa hannun ya sa bisa kirjin sa tsabagen yanda maganar ta dake shi. "Kai Saifullahi ba ka da daraja! Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun" Faɗin Baban Anas cikin jimami, shi kuwa Saifullahi ji yayi kamar ya rufe Amatullah da duka tsabagen sabon tsanar ta da ya ji ya mamaye zuciyar shi. Kai a sunkuye ya furta "Ba wai na ce a zubar da cikin ba ne dan wani mummunar manufa, gani na yi fama ta ke da makaranta yanzu aka ce ta yi nauyi ko ta haihu wahala za ta sha, ita a wahale abin da ta haifa a wahale karshen ta ma karatun na ta ya lalace........" "Ungu nan!" Baban Sasa da har yanzu hannun sa ke bisa kirjin sa ne ya katse shi ta hanyar masa dakuwa. "Dan tselan uwa kai!!! Ka damu da makarantar ta shi ne ka hana ta zuwa makaranta har tsahon kwana uku? Yau na yi danasanin aura maka yarinya mai daraja irin Amatullah, da gaskiyar ka Anas wannan yaro be da daraja! Ashe dan aure zai guji dan sa na aure....? Har ka hana yar mutane zuwa makaranta saboda ta ki aikata mugun nufin ka!! Wannan rayuwa ina za ta kai mu....... " Baban Sasa ya fashe da kuka. Hakan ba karamin tadawa Amatullah hankali yayi ba, shi kuwa Baba Anas daɗa hasala yayi in da ya rufe Saifullahi da zagi ta inda ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Sai da aka dau wasu mintina kafin a samu Baban Sasa ya yi shiru. Ya na mai share hawaye da hannun rigar sa ya ce "Wallahi Saifullahi ka ba ni kunya, ka ci mutuncin zumunci! Albasa ba ta yi halin ruwa ba" "Allah ya ba ka hakuri Baban Sasa, na yi kuskure ina mai neman afuwan ku" Cewar Saifullahi, cikin ran sa kuwa lissafin yanda za mayarwa da Amatullah kwatankwacin tozarcin da ta masa a yau, dan gani ya ke duniya ba shi da makiyi da ya wuce ita. "Wallahi, wallahi, wallahi ba ka bi na bashin rantsuwa ciwon kai idan Amatullah ta yi a sanadiyar cikin nan, kuma ya zamanto kai ne sila Allah ya isa ba zan kuma yafe ma ka ba!" Baba Anas ya furta ya na mai nuna shi da dan yatsa. Kana ya kara da "Makaranta wajibi ne, ko da wasa kada ka kuskura na ji ka sake hana ta zuwa makaranta, wallahi sai na tsine maka Saifullahi!" A firgice ya dago ya na duban Baba Anas, in da ya girgiza masa kai cikin jaddadawa ya ce "Kwarai da gaske! Kalle ni da kyau! Ba ka isa ka shiga tsakanin mu ba, ba isa ka ɓata zumuntar mu ba, ka yi kaɗan! Ilimin ka da wayon ka su amfana ma ka da komai ba! Allah wadar da ilimi irin na ka! A sanadiyar ka mahaifina ya zubda hawaye wanda ni ina ɗan sa ban saka ya zubar ba, sai kai jika! Allah wadar na ka ya lalace. ... " "Ah ah Anas kada ka masa baki, yanzun ma yaya bare kuma ka masa baki! Ace ɗan sunnah ya ki ɗan sunnah?" Cewar Baban Sasa, "kai Saifullahi ka ba ni kunya, albasa ba ta yi halin ruwa ba!" Saifullahi da ya gama haɗa zufa faɗi ya ke "A yi hakuri Baban Sasa, in sha Allah za a gyara" "Ina wayar ta da ka karbe" "Dama ba karbewa na yi ba, sabuwa na yi niyar siya mata, Amma in sha Allah zan mayar mata da kayan ta" "Eh ka gaggauta mayar mata da shi! Yanzu karfe nawa ki ke da lecture?" Baba Anas ya tambayi Amatullah, ta wutsiyar idanu ta dubi Saifullahi, ganin yanda ya ke kallonta ta kasan idanu cike da tsana ya sanya ya yin karya, ta ce "Dama na safiya ne, kuma lokacin ya kure yanzu, sai dai gobe idan Allah ya kai mu" "Allah ya kai mu, kai ka ji Saifullahi gobe ta na da makaranta, ka kai ta, ka kuma dauko ta, kuma juna biyu in ka ga ba ta haife shi ba toh Allah ya rubuta dama ba zai zo duniya ba, Amma ciki dai sai ta haife, ta shi ki shiga ciki Allah ya maki albarka" Dama umarnin da ta ke jira kenan. Cikin sauri ta tashi ta shige ciki, nan ta bar Saifullahi gaban su Baban Sasa har lokacin ba su daina masa faɗa ba. [3/23, 8:42 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA HUDU Gwaggo ta yi mamakin ganin ta dan a tunaninta Amatullah na makaranta. Kamar yanda ta faɗawa su Baban Sasa haka ta labartawa Gwaggo. Sam Gwaggo ba ta ji daɗin yanda ta yiwa Saifullahi ba, a cewar ta me ya sa ba ta fara faɗa ma ta ba. Hajiya kuwa idan ran ta yayi dubu ya baci musammam yanda Baba Anas ya haɗa ta da Saifullahi ya mu su wankin babban mayafi. Bayan fitar Baba Anas Hajiya ta dada jaddawa Saifullahi maganar auren Ayush, ta ba shi shawarar ya fito fili ya shaidawa su Baban Sasa muradin shi na kara aure. Sai da yamma likis Amatullah ta yiwa Gwaggo sallama ta koma gida dan kuwa mijin na ta tun azahar ya bar gidan. Haka ta wayi gari ba tare da ta sanya shi a idanun ta ba, sai gani ta yi ya aje mata kudi bisa centre table tare da yar takarda wanda aka rubuta "Jikar Baban Sasa ina da tabbacin wannan zai kai ki makaranta ya dawo da ke" Ko da ta dirga da gaske zai kai ta din ya dawo da ita, sai dai iyakan abin da zai mata kenan, babu batun kudin cin abinci. "Oh ni Amatullah ciki ya jawo min zama da yunwa, amfanin sana'a kanan! Allah na rokeka ka ganar da miji na" Cewar Amatullah yayinda ta zura kudin cikin jakar ta. Dakin Saifullahi ta je, kofa a rufe, da kwankwasa ta ji shiru sai ta yanke hukuncin kila ba ya ma gidan. Bayan ta tabbatar ta aje masa komai na karin kumallo ta ɗauki hanya. Saifullahi kuwa tun sassafe ya ɗauki hanyar Abuja domin karbar offer din aikin da ya samu a ministry of power and housing a matsayin injiniya. Ya doka sammako ne ba dan komai ba sai saboda ganin Amatullah da ba ya son yi, dan gani ya ke idan su ka hadu Allah kaɗai ya san yanda zai kasance tsakanin su tsabagen haushi da tsanar ta da ya yi. Ranar da yunwa Amatullah ta wuni, in da ta yi danasanin rashin kullo wani abinci da ba ta yi daga gida ba. Ganin abincin Saifullahi yanda ta barshi ya tabbatar mata Saifullahi ba ya gida. Cikin sosawar rai da damuwa ta shiga kiran wayar shi, Amma babu amsa har ta hakura. Abincin na shi ta ci, da niyar girka ma sa wani. Hakan ko ta yi amma har bayan Isha'i babu Saifullahi, ta fara tsorata ta na kokarin kiran Baban Sasa sai gashi ya dawo. "Sannu da zuwa ya Saifullahi" Cewar Amatullah in da ta tashi ta na kokarin karbar jakar hannun shi. Hannu ya daga mata cike da hantara ya ce "Ke tafi can!! Wa ya ce mi ki ina bukatar sannun ki bare ki karbi jakar hannu na? Salon ki ƙala min sharri gun Baban Sasa ki ce na haɗa ki da jaka mai nauyi ɗan gwal din na ki ya zube?" "Ya Saif...." "Yiwa mutane shiru dallah!" Ya tsayar da ita ta hanyar daka mata tsawa. Shiru ta yi tana duban shi har ya shige dakin sa. Yanda ta jera masa abinci haka ta sake kwashe su da safe, kamar jiya yau ma ya aje mata kudin mota babu na abinci. Haka ta ɗauki kuɗin ta na mai rokan Allah ya sa ya gane, dan kuwa dai ba karamin kewan mijin ta take ba, yanda ya kaurace mata ba ta jin za ta iya jurewa. Karin kumallan da ta yi musu ta ɗan ɗiba cikin yar karamar kula ta saka a jaka, dan kuwa jiya ta ji a jikin ta. Haka rayuwa ta kasancewa Amatullah har tsahon sati guda suna zaman doya da manja. Ranar da ya kaiwa Baban Sasa offer letter ɗin shi ranar ya masa batun karo auren da ya ke son yi. Baba Anas wanda ya zo ya tadda Saifullahi na shaidawa Baban Sasa lamarin ne ya so ya hana. A hasale ya ce da Saifullahi " Shin har yaushe ka yi auren da za ka zo mana da maganar kai gaisuwa wajan wata kuma? Kai mai gudun haihuwa ina kai ina kara aure?" Shiru Saifullahi yayi ya na mai dukar da kai. Duk da maganar ta sosawa Baban Sasa rai, sai ya kawar da san zuciya ya na mai murmushi ya ce " Ai ina ga Anas zai fi kyau mu kalli wannan magana ta shi ta fuskar arziki, ka ji dai yace yarinyar nan tun kafin auren shi da Amatulah su ke tare, duk da kuwa ya san da maganar alkawarin da na ɗauka, kuma gashi yanzu ya sami aiki Alhamdulillah, kuma karin aure abu ne da Allah ya halatta mana, fatan mu Allah ya sanya alkhairi" Farin cikin ran Saifullahi ba ya misaltuwa. A lokacin ya ji duk wani bakin cikin Amatullah da ya kunsa sanadiyar kawo shi kara da ta yi ya gushe. Ta je ta yi ta haihuwa ta lalace tunda zai auri Ayush din shi ya more rayuwa. "Sai ka shaidawa Anas sunan mahaifin yarinyar da unguwar da su ke dan a yi bincike ko cikin satin nan ko? Idan Allah ya sa aka sami yanda ake so zuwa karshen wata sai a kai gaisuwa kamar yanda ka bukata" Cewar Baban Sasa ya na mai duban Saifullahi da farin ciki ya bayyana karara a fuskar shi. "Toh Baban Sasa na gode kwarai Allah ya kara lafiya, bari na je na rubutu yanzun nan ma" Cike da annashuwa ya tashi ya shige ciki ba tare da ya tsaya jin amsar Baban Sasa ba. Baba Anas na mai girgiza kai ya ce "Ka ga yanda yaran nan ya ke rawan kai! Allah ya sa ba lasisin wulakanta mana diya ya samu ba" Baban Sasa na mai jinjina kai ya ce "Ko shakka ba na yi Saifullahi ba zai wulakanta Amatullah ba, Amma tun ranar da Amatulah ta kawo karar sa wajan mu, na dan yi danasanin auren nan, Allah ya sa karshen danasanin kenan" "Amen dan son Rasulillahi" Cewar Baba Anas. Kamar yanda ya ce ba a jima ba ya kawo takarda mai ɗauke da sunan mahaifin Ayush da sunan unguwar da su ke a Kano ya bawa Baba Anas kafin ya mu su sallama ya tafi. Ranar ba Saifullahi ba hatta Hajiya wuni su ka yi cikin farin ciki. Amatullah kuwa ko da ta dawo daga makaranta a gajiye, gashi zuciyar ta na tashi ta yi amai ranar ya kai su uku, gashi ko ta yi girki ma ba ci Saifullahi ya ke yi ba sai ta yi kwanciyar ta falo. Nan bacci ya fara ɗaukar ta sama sama. Kamar daga sama ta ji ana tashin ta. Cikin wannan hali Saifullahi ya dawo ya tadda ita. Ganin babu kular abinci ya tabbatar mishi cewa yau ba ta kawo ma sa abinci ba yanda ya saba gani, kai tsaye kitchen ya nufa ba dan yana jin yunwa ba, sai dan ya tabbatar da abin da ya ke zato. Aikuwa dai zatan shi ya tabbatar ba ta yi girkin ba. Falo ya sake dawowa ya na duban ta. Yanda ta yi rashe rashe ta na bacci hankalin ta kwance ba karamin kular da shi ta yi ba. Wato ta samu hutu ta dena girki tunda ba ya cin abinci maimakon ta zo ta lallabe shi ta bashi hakuri ganin ya dena cin abincin ta yanda yayi zato. Ransa bai kara baci ba sai da ta gyara kwanciya ta na mai ajiyar zuciya yayinda rigar jikin ta ya dan daga, dan shafaffen cikin ta ada wanda ya dan tasa yanzu ya bayyana gare shi, kallan cikin ya ke cike da takaici ya san nan da wani dan watanni cikin zai zama kato kamar kwarya, duk wannan shape din na ta ɓaci zai yi ta koma kamar buntuntuna. 'gwara ma na aje girmen kai na more rayuwa ta kafin cikin ya girma ta zama mara fasali!' Cewar Saifullahi cikin ran sa yayinda sha'awar ta ya taso masa har cikin ran sa. Dakin sa ya nufa yayi wanka sannan ya fito. Nan ya tadda ta tana ta baccin ta har lokacin ba ta tashi ba. Cikin takaici ya shiga kiran sunan ta "Amatullah! Ke Amatullah!!" Cikin magagin bacci ta ke duban Saifullahi da ya ke tsaye gaban ta "Malama ina abinci na?" Tambayar da ya jefe ta da shi kenan. A hankali ta murje idanu, kana ta tashi zaune duk da jirin da ke dibar ta. Kallan sa ta ke cikin nuna rashin fahimtar maganar da ya furta mata. Ganin haka ya sake faɗin "Kin dena ji ne? Na ce ina abinci na?" Sai da ta yi hamma, ta na mai rufe bakin ta da tafin hannun ta sannan ta ce "Ganin ka dena cin abincin ne gashi kuma ba dadi na ke ji ba ya sa ban dafa ba Ya Saifullahi" Amsar ta ba ƙaramin batawa Saifullahi rai ta yi ba, a fusace ya ce "Idan ba ballagaza ba wace mace za ta yi tunani irin na ki? Mijin ki ya dena cin abincin ki maimakon ki duba dalilin yin haka ki bashi hakuri ina ke lasisin dena girkin gaba daya ki ka samu ko?" "Ayya mana ya Saifullahi, me ya sa ba ka min adalci ne saboda Allah da manzan sa? Kullum fa ina ma ka girkin nan kafin na je makaranta na aje maka, Amma haka zan dawo na kwashe kaya na, hakan kuma ba zai hana na maka na dare ba, shi ma haka zan kwasa da safe ba tare da ka taba ba, dan yau daya ban iya yi ba saboda ba na jin dadi sai ya zama matsala? Wani dalili zan tambaye ka bayan na riga na san dalilin na ka ba zai wuce na cikin da na ke dauke da shi ba?" A fusace ya na mai nuna ta da dan yatsa ya ce "Ni ke mayarwa magana haka? Har kin iya tsaurin idanun da za ki iya mayar min da martani?" Amatullah na mai dafe kai tsabagen yanda ta ji ya na sara mata ta ce "Auzubillahi minan shaidanir rajim!" "Ni ne shaidani Amatullah? Ni ne shaidanin na ki?" Cikin sanyi ta na mai kaskantar da kai ta ce "Allah ya ba ka hakuri, dan Allah ka yi hakuri wallahi ba na jin dadi Ya Saifullahi, Allah ya huci zuciyar ka" Ya na mai huci kamar maciji ya ce "Malama ba hakurin ki na ke bukata ba! Ki tashi ki shiga kitchen ki dafa min abinci, tuwon shinkafa na ke so da miyar bushesshen kubewa" Kallan sa ta ke cike da mamakin rashin imanin sa, a hankali ta ce "Wallahi ban da lafiya...." "Ina ruwa na? Ba ke ki ka zabi ki yi rashin lafiyar ba! Ki tashi ki dafa min dinner jor!" Ya koma kujera ya kame ya na hura hanci. A daddafe Amatullah ta tashi ta shiga kitchen jiri na dibar ta haka ta kokarta ta daura tuwan nan. Kafin ta gama ta zauna a kasan kitchen din ya kai sau goma. Ko da ta gama ta shiga falo ɗauke da kula sai ganin shi ta yi da robar take away gaban shi, ya hakimce ya na cin fried rice da kaza. Idanu cike da kwalla ta ce "Ayya mana ya Saifullahi, duk wahalar nan da ka bani ashe ka na da abin da za ka ci dan Allah? Me ya sa haka?" "Saboda na isa, dole sai na ci abin da ki ka dafa ne? Ina da damar canza shawara" Kular ta aje in da ta saba ba tare da ta sake tanka masa ba ta shige dakin ta. Shi kuwa dadi har ran shi dan ko shakka babu ya san yau ba karamin kuntatawa Amatullah yayi ba. Ta na yin sallar Isha'i ta yi wanka ta bi lafiyar gado tsabagen yanda ta ke jin jikin ta, gashi gobe ta na da sammako lecture din safe gare ta. Ba ta yi cikakken awa da kwanciya ba bacci ya dan sace ta sai ji ta yi mutum kusa da ita. Hankali tashe ta ce "Ya Saifullahi lafiya?" Dankuwa ba ta yi zatan zai shigo mata ba. Cike da takama ya na mai jawo ta jikin sa ba tare da ya damu da kunna wutar dakin ba ya ce "Hakki na za ki bani" Hankalin Amatullah ba karamin tashi yayi ba jin abun da ya zo da shi, kana cikin magiya ta ce "Dan girman Allah ka yi hakuri, wallahi, wallahi ban da lafiya ya Saifullahi, ka bari na sami sauki...." "Ki na nufin na bari ki haihu? Wa ya ce mi ki za ki sami lafiya muddin ba haihuwa ki ka yi ba ko zubar da cikin nan? Ba zan iya jira ba, hakki na nake so yanzu ma kuwa..." Ganin abin da ya taka ya sanya Amatullah ta yi shiru ba ta sake tanka masa ba, kyele shi ta yi yayi kidin sa yayi rawan sa, sai hawaye da ke bin kuncin ta daya bayan daya. Sai da ya gama biyawa kan sa bukata ba tare da ya tausaya mata ba sannan ya ja gefe yayi kwanciyar shi. Tsanar da ba ta taba yiwa wani ɗan adam ba haka ta ji na Saifullahi na ratsa zuciyar ta. A daddafe ta shige bayi domin ji take ba za ta iya kara minti biyar ba ba tare da ta yi wanka ba. Ta yi wankan ne tana mai fatan ba za ta fito ta tadda shi a dakin ba, Amma abin takaici haka ta fito ta ga ya kunna wutar dakin in da yayi rashe rashe bisa kan gado ya na waya. Kallan sa ta yi cike da takaici Jin ya na furta "Haba mana Ayush kin san yanda na ke san ki kuwa? Ke kaɗai ce macen da na ke kauna, sauran mata ai suna su ka tara...... " Amatullah na mai kawar da kai ta bude wardrobe din ta domin neman wata rigar baccin, tsabagen tsanar Saifullahi ya sa ba ta san mayar da wanda ta cire, Jin Saifullahi ya ce "Albishirin ki toh? Baban Sasa ya amince next week za su zo kawo kudin aure gidan ku......." Cak Amatullah ta tsaya yayinda wani sabon jiri ya shiga kwasan ta har sai da ta sami waje gaban wardrobe din ta zauna dirshen. Saifullahi kuwa da ya lura da halin da maganar ta shi ya sanya Amatullah ciki tuni ya cigaba da jaddada soyayyar shi ga Aysuh. Zafafan hawaye ne su ka shiga fita daga idanun ta, ta na mai neman taimakon ubangiji ta samu ta ja wani doguwar riga da Allah ya sa ta kai hannun ta kan shi, tana rike da rigar ta bar masa dakin. A falon ta sanya kayan ta, kan doguwar kujera ta kwanta, maganar Saifullahi ke mata yawo a kunne 'Albishirin ki toh? Baban Sasa ya amince next week za su zo kawo kudin aure gidan ku' Duk da dai ta san yayi ne dan ya bakanta mata, kuma ya ci nasara kwaran gaske. Ta na mai tuhumar Baban Sasa akan amincewa da yayi akan auren Aysuh, duk da dai ba za ta yarda ba sai ta tabbatar da maganar tukun, dan kuwa idan haka ne da Baban Sasa bai kyauta mata ba cewar Amatullah cikin ran ta in da Tasha kukan ta ta koshi, ta na ji Saifullahi ya koma dakin sa amma ta kasa tashi ta koma na ta, sai wajan ukun dare bacci barowo ya sace ta. **** Washagari ta nemi izinin zuwa gida idan ta tashi daga makaranta, ya hana ta. Dan haka sai a waya ta samu ta yi magana da Gwaggo. Yanda Gwaggon ta ke mata hanya hanya na game da batun auren Saifullahi ya tabbatar mata da maganar hakan ta ke. Gaba ɗaya ta rasa nutsuwa, hatta lectures din ranar kasa gane su ta yi. Gashi Saifullahi ya fito mata da saban salo na neman hakkin sa duk dare, kuma bayan ya gama kuma ya kira Aysuh a waya Amatullah na ji ta na gani, idan ta yi magana ya ce matar da zai aura ne ko za ta hana shi abin da Allah ya halatta ma sa ne. Ranar da abin ya ishi Amatullah ta yanke hukuncin zuwa gida gun Baban Sasa sai ta taradda Saifullahi ya riga ta, ya je wai Baban Sasa ya kira Amatullah ya mata nasiha, jin zai kara aure gaba daya ta tayar da hankalin ta, shi tsoran sa kar wani abu ya same ta ko ɗan da take ɗauke da shi. Dan takaici ma kasa magana ta yi sai hawaye kawai, shi kuwa Baban Sasa da ya hau magana ya yarda da shi musammam ya san yanda mata ke daukar maganar kishiya tuni ya shiga mata nasiha da rarrashi, har da kada ta bashi kunya yana yaban ta sallah ta kasa alwala. Hajiyar Saifullahi kuwa ko da Gwaggo ta takura Amatullah ta je ta gaishe ta sai ta hau ta da faɗa , har ta na fadin da ba a auren a auri Amatullah. Wannan tashin hankalin da kuma ɗan laulayin da Amatulah ke fama da shi ya sa ta zama koma baya a makaranta, gaba ɗaya ta zama mara nutsuwa dan ko tayi karatun ma ba koda yaushe ya ke shiga ba, haka kuma ta na yawan fashi saboda rashin cikakken lafiya. A wani asibitin na gwamnati Saifullahi ya mata rigista na awo, cewar shi abubuwa sun masa yawa ba zai iya kai ta na kudi ba, aure ne gaban shi dan kuwa ba gaisuwa ba, hatta ranar auren shi da Ayush an saka, wata tara cif. A wannan hali jarabawa ta gabato har ta yi yi ta gama a daddafe. *** Cikin Amatullah na wata takwas aka kafe mu su result din first semester, haka kuma ana saura sati biyu su fara exam din second semester. Da in ta ji mutane na kiran sakamakon jarrabawa da dodon bango dariya ta ke yi, amma wannan karan ta tabbatar da zancen su zahir ne. A daddafe ta iso inda ake manna sakamako da sanarwa (notice board) Bayan sun ji labarin an manna. "Wannan ai mugunta ce, a rasa yaushe za a manna sai ana sati biyu mu fara jarrabawa" maman Jaafar ta faɗi cikin mita, da isar su kowa ya shiga duba na shi. GPA dinta ta duba kafin komai, wanda hakan ya girgiza mata kayan ciki don kuwa 1.26 ta gani, tana matsawa Ramin gaba na CGPA ta iske 2.13, motsin da yaron cikin ta ke yi bai sa ta duba sashin darrusa nan ta iske duk sun dawo mata. "Inna lillaahi wa inna ilaihi raji'un" ta ce tana mai zama a ginin da aka ma fulawowi da ke gefen su. Ko wancan jarrabawar ta fita da 4.51 dinta, duk wanda ya Santa ya san ta a matsayin ɗaliba mai daraja ɗaya (first class student). Addu'a ta shiga yi a zuciyar ta don neman ɗauki da agaji wajen Ubangiji. "muguntar ABU akan ki yau Amatullah, ba fa zai yiwu ba" cewar Maman Jaafar da itama sakamakon ya rikita wa hankali. "Kin manta C courses uku muka yi kuma duk Kinga ban zarce 47 ba" Amatullah tace cikin ƙarfin guiwa. "Even though, mu ka dai samu B balle ke, ni takaici na ba wai kasancewarsu C courses ba, kowannensu lamba uku (3 credit unit) gareshi, sannan chain prerequisite ne fa taso Amatullah mu je mu ji ina matsalar take" Maman Jaafar ta ce tana kamo hannunta, bata ce komi ba sannan ba ta Mike ba. A cikin darrusa bakwai ta ci guda biyu, ta faɗi biyar. Wanda duk son mai sonta bai da abin da zai ce da ita da ya wuce za ta sake maimaita aji uku. A rayuwar ta Sam ba ta san wani abu wai shi damuwa ba sai a Yan watannin baya. Shafo cikin ta tayi cike da so da kaunar abin da ke ciki duk da tana da masaniyar yana da hannu a faduwar ta jarrabawa. "Allah ya fi mu sanin daidai maman Jaafar" tace tana mai murmushi. Ba kawayenta kaɗai ba gaba ɗaya faculty of pharmaceutical sciences an girgiza da sakamakon Amatullah S. Jamoh, maluma da dama sun girgiza saboda an jinjinawa kokarin ta a shekaru biyun farkon ta a jamiar. *** Sai dare ta samu ta kira mahaifinta, bayan ta kammala duk wani abin da ta san Saifullah na bukata sannan ta shige ɗaki. Kuka sosai ta sanya masa tana faɗi masa sakamakon ta. "Babanmu Saura sati biyu jarrabawa, ko na yi ba zan gyara ba sai ma in ɓata, wallahi komi ban iya ba, Babanmu kar a yi withdrawing ɗina" tace cikin Kuka mai tsuma rai. Shiru yayi yana sauraren ta don shi Sam bai san ta inda zai kamo zaren ba. Ya dade da sanin tana cikin damuwa ɓoye masa ake hakan ya sanya shi mata aiken kudi lokaci zuwa lokaci. "a ina kike zuwa awo" ya samu kansa da tambayar ta. Shiru ya biyo baya don bata son yi masa ƙarya kuma ba ta son sa shi cikin damuwa. "ki samo medical report Sai ki yi deferring semester ɗin, inshaAllah shekara mai zuwa zaki dawo kan digadiganki" yace ganin ta yi shiru. Nasiha ya cigaba da yi mata yana mai faɗi mata mahimmancin da ke tattare da lafiyarta fiye da komi. A haka su ka yi sallama. [3/26, 10:18 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA BIYAR Cikin iko na Ubangiji da taimakon wata malamarsu Dr. Mu'azatu Usman El-Yakub ta samu tayi differing semester ɗin nata, hakan ya sanya ta daina fita makaranta. Cikinta kullum girma ya ke ƙarawa yayin da motsinsa ta zama mata abokin hira abokin ɗebe kewa. Idan ya motsa har shafo shi take cike da ƙauna ta ce "Ubangiji Allah ya nisanta ka da mummunar halin mahaifin ka" wani lokaci kuma ta shagala wajen ba shi labarin duniya. "ka ga rayuwar duniya da daɗi amma cike yake da ƙalubale, kar ka damu ina son ka, ba zan taɓa juya maka baya ba, come sun come rain" ire-iren hirarrakin da ta ke yi da ɗan Cikinta kenan. Wani lokaci ta bashi jinsin mace wani lokaci na namiji. Banda pad, zaitun, sai riga ƙwaya ɗaya bata ta siya komi ba, su ɗin ma da kyar ta iya fitar da kudin su saboda gaba ɗaya ba ta da hanyar samu. Saifullahi kuwa sashin da aka tura shi aiki babu wani tsauri, ya kan yi sati biyu bai je Abuja ba in ya je kuma baya wuce kwana biyu zuwa uku. Ko da cikin ta ya cika wata tara babu abin da ta ke sai addu'a, sosai ta rike YAA HAYYU YAA QAYYUM BI RAHMATIKA ASTAGITHU saboda samun sauƙin haihuwa. Yanda Saifullahi ya maida hankali wajen kammala gininsa a cewarsa nan Ayush za ta tare har mamaki ya ke ba Amatullah, ganin gaba ɗaya bai wani hoɓɓasa ba wajen tanadar mata abin haihuwa tun daga kanta har zuwa na jaririn ya sanya ta sadakar da cewa tabbas Saifullah ba ƙaunar ta yake ba. Duk halin da take ciki baya dubawa yake kwasan romon sadakinsa. Bata taɓa hana masa ba, ta yanke ƙauna daga sake samun jin dadin aure, ta kaddara a ranta kila cikin ya zama ajali a gareta. "Ki dage da Addu'ar sulhu da ƙulla soyayya tsakanin mutane" shine shawarar da goggonta ke bata a duk lokacin da ta kai mata kokenta ya sanya ta ke barin ma cikin ta. Hakan bai hana mata yawaita faɗin ALLAHUMMA ALLIF BAYNA ƘULUBINA, WA ASLIH ZATA BAYNINA WAHDINAL SUBULA-S-SALAM. ALLAHUMMA ALLIF BAYNA ZAUJIE WA IYAYYA BI SHAFAQATIN WA RIDAAN WAL WI'AAM. Tana yi don samun salama da soyayya a gidan aure, ta san Alƙalamin kaddararta ya riga da ya bushe amma wani sa'in ta kan ji ni'ima da rahman Ubangiji ya lulluɓe ta. *** Ana saura sati uku su koma makaranta sabon shekara ta fara naƙuda. Da farko ba ta ɗauka da gaske ba sai da ta fara jin ba za ta iya jure zafin ba. A hankali ta isa ga Saifullah wanda ya zauna ya tasa kallo a gaba yana yi yana kyakyata dariya shi kaɗai yana jefa ci cin ɗin da ta masa a baki. "Ya Saifullah taimaka ka kai ni asibiti, inaga haihuwar ce ta zo" tace cikin cije leɓe. Kallonta yayi a sheƙe wanda hakan yayi daidai da ƙarar wayar sa, bai kula da ya bata amsa ba ya ɗaga wayar. "Babe how far" ya faɗi wanda hakan ya tabbatar ma Amatullah Ayush ce ta kira. Nan ta ji wani murɗawan ciki da bata san lokacin da ta tsuguna tana mai ambatan "Wash!" ba. Maimakon ya kula ta sai tsallake ta yayi ya fice daga gidan. Hawaye mai zafi ya zubo ma Amatullah, gaba ɗaya ta sadakar a wajen za ta cika don ba ta da mai taimakon ta sai Allah. Tana cikin mukurkusun ta jiyo sallama, hamdala ta yi don ta san in ba Allah ba babu wanda ya turo mata ɗauki. Makociyarta ce ta shigo sa charji, nan ta ganta cikin naƙuda. "Subhanallah! Pharm kashe kanki za ki yi?" tace tana tallafo ta zuwa kujera. "bari na ma Baban Huda magana ya kaimu Layin sarki" tace tana mai ficewa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta dawo ta kamo Amatullah ta taimaka mata zuwa cikin mota, sannan ta koma ɗauko kayan da Amatullah ta faɗi mata in da ta ajiye. Asibitin primary health care da ke Layin sarki su ka nufa, da kyar aka amince da ta haihu a wajen saboda ƙaida ba sa karɓa haihuwar fari da na wacce ta yi fiye da biyar. Bayan doguwar naƙuda na kusan awa uku Amatullah ta sambaɗo ɗanta da daga faɗowarsa ya karaɗe asibitin da kuka. Nan aka kimtsa ta, aka ɗinke ƙarin da ta samu, sannan aka kai ta ɗakin hutu. *** Saifullah kuwa fitan da yayi saƙo ya amso na wani leshi da Ayush ta sanya ya siya mata don sawa a akwati, leshin yayarta ke siyar da shi Dubu ɗari da hamsin. Saman gadan ɗanmagaji yaje ya same su in da za su wuce Abuja daga Kano su ka tsaya su ka bashi. Tun a hanyar dawowa halin da ya bar Amatullah ke masa gizo, nan ya tuna da zancen "mai naƙuda ƙafarta ɗaya na duniya ɗaya na lahira ne" Hakan ya ƙara masa matsanancin tsoro ya ƙara gudun motarsa zuwa gida. Kamar yadda ya sa rai tana ciki, ya zata ganin gate ɗin gidan kamar yanda ya barshi. Cikin sassarfa ya isa cikin gida amma babu ita a falo da ya barta tana muƙurƙusu, ya shiga ɗakuna babu ita, ya duba bayan kitchen babu ita, take ya ji wasu zufa su ka fara keto masa. "Inna lillaahi wa inna ilaihi raji'un" yace yana mai kai komo a cikin gidan ko tana wani lungu ne cikin rashin hayyaci. Wayar sa ya ɗauko ya kirata sai jin ƙarar wayarta yayi a ɗaki. Addu'a yake ba kakkautawa don baya son abin da zai haɗa shi da Baba Anas a wannan Marra. A haka ya fito zuciyarsa na bugu da niyyar zuwa Amaru don yana da yaƙinin can ta nufa. Ya fito kenan ya iske makocinsa na shirin shiga motarsa. "Engineer ashe kana gari" ya ce masa bayan sun yi musabaha. "Eh wallahi amma shigowata gidan kenan, na fita da safe" ya faɗi yana mai saurin tada motar. "Can Layin sarkin zan je dama, amma tun da can kayi ga wannan ka kai musu na san za su buƙata" yace yana mai miƙa masa filas ɗin ruwan zafi da kulan abincin da ya riga ya sanya a motar. "Ai inshaAllah yaci ta sauka yanzu, Allah ya buɗe idanunsu lafiya" Baban Huda ya sake faɗi ma Saifullah da gaba ɗayansa yayi mutuwar tsaye. Godiya ya shiga yi ma Baban Huda ganin da gaske ba Amaru ta nufa ba. "Nagode fa, Allah ya saka maku da Aljanna" ya sake faɗi har da yar duƙawarsa. "Haba Engineer wannan godiya haka, ai yi ma kai ne. Ka yi sauri ka isa na san yanzu kila suna bukatar sa, it's over 3 hrs fa da muka isa, don ma da kyar su ka amsheta ne" yace yana taɓo kafaɗun Saif. Jiki na ɓari Saifullah ya isa tudun wadan, ko da ya isa Amatullah na barci, wani sabon ni'ima ya ji ya saukar masa ganin bai ga kowa daga Amaru ba. Har ƙasa ya durƙusa ya gaida maman Huda duk da a shekaru ba zata girme shi ba, amma har cikin ransa yake jin rufin asirin da su ka masa a matsayin gagarumi. "Ga Danlami fa, ka ji murya da ya saki kukan maraba da duniya" tace tana miƙa masa jariri naɗe cikin zani babu ko rigar sanyi sai wata yar shalaushalon riga. Tunanin in da Amatullah ta samo rigar yayi don shi dai ya san bai saya ba. Hannu ya sa ya karɓe shi yana kallo, tsantsan kamar da yaron yayi da su ya sanya shi jin wani iri, bai sani ba ko hakan ne soyayyar ɗa da mahaifi da ake faɗi ko kuma kiyayyar da yake ma cikin ne ya shafi yaron. "Allah ya raya mana Muhammad Jamoh" yace yana mai miƙa ma maman Huda. A wajen ya sanya waya ya kira Baban Sasa. "Muhammad Jamoh ya iso fa Baban Sasa" yace cikin shaƙiyanci bayan sun gaisa. "In yi guɗa ne Saifullah" yace cike da murna "Ka taso kawai ka tare shi, amma kuma kar ka shafa masa tsufa. Wallahi bana tunanin za a samu wani tsatsonka da zai yi kama da kai kamar shi" yace yana ƙara leƙen yaron. Baban Sasa ya kasa ɓoye murnar sa, a haka su ka yi sallama ya tashi yana mai dogara sanda zuwa cikin gida. Abin da yafi shekaru rabon da ya taka, nan ya faɗi masu haihuwa gida ya karaɗe da murna. Saifullahi kuwa sallama yayi ma maman Huda ya shiga kasuwar tudunwada ya siyo kayan maza, da shawul da kayan sanyi. Ko da ya koma asibiti Amatullah ta farka har ana shirin sallamarsu. *** Ko da su ka isa gida, maman Huda taimakawa tayi ta wanke Jamoh tas, ta sa masa kaya masu kyau cikin wanda Saifullah ya siyo, jariri ya shiga bacci cikin kwanciyar hankali. A lokacin ne yan Amaru su ka shiga tururuwa, suna shiga da fice, ga lafiyayyen tuwo da Goggo mairo ta bayar a kawo mata, taci ta hantse. "ku haɗa mata kayan amfaninta, mu samu mu wuce bayan la'asar" kawai yaji Inna Hafsatu ta faɗi. Bai ɓata lokaci ba ya kalle su yace "Babu fa inda za ta je, anan za ta zauna, na riga da na tanadi wacce za ta zo ta mata wanka, mun yi ciniki har na biya rabi" yace yana cijewa. "An taɓa haka ne Saifullahi. Haihuwar fari fa, kuma kwatakwata Amatullah sha tara take fa bana. Don Allah ka duba dai" inna Hafsatu ta sake fadi cikin magiya. "Gaskiya mun gama magana da iyayenmu maza, kuma sun amince da tsarin" ganin saurin da yake amfani da shi ya sa tayi shiru kafin ya kai ga zagin ta. A haka suka yini cur suka tafi ba tare da Amatullah ba, ko da suka koma ma Goggo Mairo da yanda aka yi, har cikin ranta taji babu daɗi amma sanin mahimmancin bin umurnin miji ya sa ta ce a bar zancen dawowarta. [3/30, 12:08 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA SHIDA Gaba ɗaya Saifullah ba zai ce ga halin da ya shiga ba, ya kan ji wani irin zugi tun daga tafin ƙafarsa har saman kansa in ya tuna da wai shi aka haifa wa ɗa. Ƙanwarsa Asiya ya nema ya bata kuɗi naira dubu talatin ta shiga kasuwar sabon gari ta haɗo duk wani abin buƙata na jariri. Sannan ya ware wasu kudaden ya ba da aka siyo Rago aka yanka ma Amatullah na ƙauri. Bai gushe ba sai da ya ɗauko Ƙanwar Hajiyarsa Inna Jamila don ta zauna da Amatullah. Ranar a gajiye ya kwanta cikin wani annashuwa dan ko ba komai ya san yayi bajin ta gurin Baban Sasa, ya samu ya dan wanke kan shi daga bakin cikin da Amatulah ta ku kuntsa masa. Amatullah kuwa ko da aka watse aka barta da inna Jamila mamaki komai ya dinga ba ta, wai itace yau da ɗa, ɗan ma ita tayi nakudarsa ta haifa. In ta fakaici idon inna Jamila sai ta tsura ma yaron idon cikin so da ƙauna. Tayi godiya ga Allah ya fi sau a ƙirga, ta ga mugun wautarta na amincewa cire cikin da farko. "Ashe dai haihuwa kyauta ce da bawa bai isa ya siyo ma kansa ba" tace a ranta tana mai istigfari na kusan butulce ma Allah a farko. Cikin kwana biyu Saifullah ya shayar da ita mamaki, kula sosai yake ba ta da yaron ta, duk ya fita sai ya shigo mata da tsaraba, wani irin rawan jiki ya ke musamman idan Inna Jamila na kusa ba, ita dai na ta ido, na ciki na cikin, dan kuwa ta tabbatar komai ya yi na ganin ido ne, Saifullahi ba kaunar ta ya ke ba bare ɗan da ta haifa, ba za ta taɓa mance yanda ya tsallake ya barta ta na tsaka da nakuda ba. Zirga-zirga da yake wajen tabbatar da komi ya zo cikin sauki ya sanya gaba ɗaya baya ba Ayush wani kulawa, da ita yake kwana ya tashi cikin begenta da kidayan kwanakin da yayi saura na bikin su. Kullum ya ƙirga ya ga saura fiye da kwana ɗari sai ya ji inama ana fast-forward a rayuwa. *** Bayan kwana uku, Amatullah zaune bakin gado ta ci ado cikin atamfa. Sun gama rigima da Inna Jamila wacce ta ke yiwa jariri wanka ya na mai tsallar kuka, akan Amatullah ba ta san ɗaure cikin ta, ita kuwa azabar ciwon da ta ke ji saboda dinkin da aka mata ga wani ciwon ciki da take fama da shi ya sa sam ɗaure cikin baya gaban ta. Saifullahi ne ya shigo gaishe da Inna da Jamila kamar yanda ya saba, kallo ɗaya Amatullah ta ma sa ta kawar da kai. Ganin ana yiwa jaririn wanka ba karamin dadi ya ji ba, ya na mai godewa Allah yau ba sai Inna Jamila ta masa gwalegwalen ɗaukar jinjirin ba, ya durkusa har kasa ya gaishe ta. Ita ma Amatullah a dake ta gaishe shi duka gudun kar Inna Jamila ta dago jirgin ta. Bayan sun gama gaisawa Saifullahi ya tashi ya na shirin fita Inna Jamila ta tsayar da shi ta hanyar faɗin "Ni kuwa Saifullahi sai na ga zai fi idan ka mayar da Amatulah gida, ka ga dai haihuwar fari ne, gashi an mata dinki yanda ta ke da raki ba na ji za ta iya kula da kan ta" Saifullahi na mai sosa kyeya ya ce "Ai Inna Jamila kar ki damu, Zan kasance mai kula da ita da kai na, ba na so su yi nisa da ni ko kadan....." Ya karasa maganar ya na mai ƙasa da kan sa, cike da takaici Amatullah ke kallon sa, a sanin ta ba dan komai ya ke gudun komawar ta gida ba sai dan gudun kar asirin shi ya tonu. Ita kuwa Inna Jamila kai ta jinjina ta na mai faɗin "Yaran zamani, toh ai shikenan" Sinsin ya fice gudun kar Inna Jamila ta sake furta wani abu. "Yanzu Inna haka za ku bar ni da shi? Wallahi babu abin da zai yi min, Yaya Saifullahi macijin sari ka noke ne....." "Kul!" Inna Jamila ta katse ta cikin tsawatarwa, ta kara da "Kar na sake ji, ku yaran zamani sam ba ku da godiyar Allah, ki duba yanda yaron nan ke mi ki hidama Amatullah, tsabagen rashin godiyar Allah ki kira shi macijin sari ka noke?" "Duk wannan hidimar da ki ga yanayi na ganin ido ne. ..." "Lahaila!" Cewar Inna Jamila ta na mai jinjina kai, ba ta gushe ba ta kara da "Ba ki da godiyar Allah ƴar nan! To kuwa duk wanda bai godewa Allah ba ya ƙi godewa azabar shi ba!" Shiru Amatullah ta ma ta, cikin ran ta kuwa faɗi ta ke ai shikenan, duk randa ya kashe ni kwa gane. Haka Inna Jamila ta kare wankan jinjira ta na mita har sai da Amatulah ta yi danasanin lafazin ta tsabagen mitar Inna Jamila. **** Zaune suke suna kallo, hankalinsu ya ɗauku ga series ɗin Korea da suke kallo, Zainab, Sa'adah da Farida sun natsu gaba ɗaya. Ayush rike da waya tana mai jan tsaki, hakan bai sanya sun waigo sun kalle ta ba, wani dogon tsaki ta sake ja wanda yayi daidai da shigowar Antyn ta mahaifiyar su zainab Anty Ruqayya wacce aka fi sani da Hajiya Haske. Gidanta Ayush ta wuce a Abuja lokacin da ta ajiye ma Saifu leshi. Tun rabuwar su ta lura gaba ɗaya hankalinsa ba shi a kanta, ita da kanta ta neme shi ta sanar masa da isarsu, tun ranar kuwa ba su sake wayar minti ɗaya ba, free call din sha biyu da rabin da su ke yi ma ko ta kira sai ta iske wayarsa a kashe. "Baby Ish lafiya kuwa, don dai hankalinki baya kan talabijin balle na ce kallo kike" Hajiya Haske tace tana zama gefenta. Ita kanta Ayush ta san Anty Ruqayya na cikin wainda ke shagwaɓa ta, kanwar mahaifiyarta ce da ke sonta kamar ƴar da ta haifa. In dai ka ji su a rana toh akan rashi suturta jiki ne, don Hajiya haske irin matan nan da kuɗi bai sanya su canza shigarsu ba. "Maami Saif ne fa, yau kwana biyar kenan sai share ni yake, yanzu ina shiga Facebook na iske an ɗaura hoton jariri har ana tagging dinsa, the baby looks so much like him" tace cikin shagwaɓa "Common baby, ba yana da aure ba, menene in matarsa ce ta haihu" Hajiya Haske ta faɗi tana rungumar Ayush. "Maami Alkawari ya min fa, cewa yayi ni zan fara haifar masa yara". Tace tana dakin kukan da ta makale shi a makoshi. Rarrashinta Hajiya Haske ta dinga yi tana bata baki yayin da su zainab su ka zo su ka tsaya cirko cirko cikin tausayin yar uwar su. "Common Ayush, we are in 21st century fa, 2011 muke ba 90s ba, har namiji zai ce miki haka ki yarda, ni wallahi shi ya sa na so ki amince ma Baba Hashim ɗinmu, ga kyau ga ilimi ga naira, amma kin nace ma baƙauyen zaria" zainab da suke sa'anni da Ayush ta faɗi cikin jin zafi. "Ba Baba Hashim kaɗai ba, shin wa ya kira ku nan ma" hajiya haske ta ce tana janye Ayush cikin ɗaki. Nasiha sosai ta ke mata akan haihuwan Saif ba komi ba ne in har da gaske yaron da ta gani ɗansa ne. Kuma tun da su duka sun shaida son da yake ma Ayush sun san tabbas tana shiga ragamar gidan zai koma hannunta. "Ki yarda da kanki, sannan kada ki ce zaki dinga soloɓiyanci, ba a taɓa aurenmu mun zama bora ba, tabbas sai dai mu mulki gida" hajiya Haske ta ƙarasa da faɗin haka. Wanda hakan ya fi komi kwantar da hankalin Ayush, ta san iyayenta tsaye su ke akanta. Komawa wajen yan uwanta tayi su ka cigaba da kallo, da ga baya kuma su ka fara hira inda Sa'adah ce ta buɗe musu ƙofa da faɗin "Wai ni Ayush me kika shirya ma Saif dinnan ne, makaho fa bai san ana kallonsa ba sai ka zungure shi" ta ce tana mai sassauta muryarta. "Kuma fa wallahi haka ne, shi wai ga munafuki ba, yana can suna soyewa da matarsa ke yana bin ki da daɗin baki, watau shi ya san daɗin haihuwa ko" Farida ta ce tana mai jan tsaki. Hankalin Ayush yayi matukar tashi ta maida hankalinta gaba ɗaya gare su tana son jin me suke nufi. Su kuma ganin haka ya sanya su fadi kamar haɗin baki "Comment on the pic" sai a lokacin taji wani daɗi, take ta ɗauko wayarta ta shiga Facebook tare da neman hoton don tayi sharhi akai. "Me zan sa?" tace kamar za ta yi kuka. "Welcome to the world darling. May Allah bless your parents with much love and harmony" zainab ta amshi wayar ta rubuta tare da karanta musu. Shewa su ka yi gaba ɗaya suna tafawa. "Kin san yana gani dole ya shiga tsilla-tsilla" zainab ta fadi cikin dariya. Da haka su ka cigaba da kallo suna sharhi zukatansu fal da murna. *** Saifullah na zaune bayan isha'i, ya dawo gidan da balango in da ya miƙa ma Amatullah nata kamar yanda yake mata tun bayan haihuwarta. Sam ba ta mamakin kyautata mata da ya ke kokarin nunawa Inna Jamila ya na yi, ta san kaɗan daga aikin Saifullahi. Tun da ya dawo ya ɗauki wayarsa ya shiga Facebook, nan ya iske sanarwan sharhin Ayush a kan hoton da bai san da zaman sa ba. " Hasbunallah" yace yana mai miƙewa tsaye. Shi dai ya san bai faɗi mata komi dangane da cikin ba balle a je zuwa haihuwa. 'in ta fasa fa' sashin zuciyarsa ta faɗi masa hakan ya sa ya ƙara firgicewa. Wani takaicin Amatullah da abin da ta haifa ya tokare masa ƙirji, cikin rawan hannu ya lalubo lambar Ayush ya kira. "He is calling" tace cikin murna ta na nuna ma yan uwanta. Dama ta faɗa musu zai kira daga gani don son da yake mata bata da haufi akai. "Ki ɗauka, kar ki nuna ɓacin rai ki ce ya haɗa ki da matar za ki mata barka, make sure you leave him in suspense" zainab tace yayin da sa'adah da farida su ka amince da shawarar. "how far babe" yace bayan ta ɗauki wayar. Danne zuciyarta ta yi kar ta ƙunduma masa Ashar. "maimakon ka sanyo ni muyi jegon tare sai a yi min wariyar launin skin" tace cikin dariya. Shiru yayi kamar ruwa ya ci shi, sai da ta sake faɗin "Hello" sannan yayi gyarar murya ya ce "Kiyi haƙuri, ni mai laifi ne, wallahi ba yanda kike zato bane, duk yadda na so a zubar da cikin nan ta ƙi amincewa. I did all I could wallahi" yace kamar zai yi kuka. Dariya ta yi sosai, zuciyar ta fal da murna ta ce "Subhanallah! Saboda so na zaka saɓa ma Allah, ai tun da dai aka yi kuskuren shiga inda ba muhalli ba ai hakuri ake da duk abin da ya biyo baya. Yanzu dai bani maman Babyn na mata barka" tace muryarta sarai ba alamun ɓacin rai. "Bana gida ai, rabon da na sa su a ido tun washegarin haihuwan. I've been busy ne a kammala gidan ki, jiya na ga wani gu da ba'a yi da kyau ba, gaba ɗaya can na yini har yau. Ni gaba ɗaya auren mu ne gaba na" ya samu kansa da shirgo ƙarya. "Amma ai ba zai hana ka kashe kudin suna ba ko, don duk son mu da yin classy biki, taron sunan nan ma is very important" tace tana mai addu'ar haƙanta ya cimma ruwa. "Suna kuma, ai in kin ga nayi recognizing wani ɗa a gidan nan toh Queen Ayush ce ta haihu, kin san Allah ɗaya tun ranar da ta haihu na faɗi suna but yanzu ba sai gobe ba zan kira na ce ba suna kar ma su da rai" yace cikin rudewa. Bai kashe wayar ba ya kira Baban Sasa yana mai haɗa conference call. "Baban Jamoh jikan Jamoh" baban Sasa ya faɗi cikin raha. Gaishe shi Saifullah yayi suka dan yi raha sannan yace. "ni dai Baban Sasa ban son taron sunan nan, taron gulma ne kawai, ka ga a ɗan zuwa barka ana neman zuga yarinyar nan. Don Allah ka tsawatar, kowa yayi zamansa ya mana addu'a daga can" yace cikin muryar magiya. Shiru Baban Sasa yayi ya ce "Ayi haka Saifullah, kar mu tauye ma yarinyar nan fa da yawa" "Baban Sasa ni duba zaman lafiyar mu nake, nan jiya na shigo na ji ana mata kirarin jinin Jamoh ba su zaman kishi, Baban Sasa in ba dai fasa auren nan zan yi ba" ya ce sanin da yayi baban Sasa ba zai taɓa yarda da fasa auren ba. "mu kuma ka maida mu mutanen banza ko, iyayenku ne matsorata amma ni cikakken bazazzage ne, cikin zage-zagin ma Bamalle, sai da na yi huɗu ras" yace cikin dariya, shima Saifullah dariya yayi. "Zan faɗa masu, Allah ya raya mana Muhammad Jamoh" Baban Sasa yace nan su ka yi sallama Saifullah cike da farin ciki. "Babe believe me, wallahi ba abin da ba zan iya yi don farin cikinki ba" yace bayan ya ajiye wayar baban Sasa. Tsaki ta ja cikin nuna takaici ta ce "Toh wai ka birge ne nan, ku yi sunanku lafiya ni bacci zan yi" bata jira amsarsa ba ta kashe wayar. Kansa ya rike gaba ɗaya ya rasa me zai yi ya wanke kansa wajen Ayush, ya san ta sarai a haukarta ma sai ta iya fasa auren. Kwata kwata bai yarda da amincewarta ba yafi ganin sa a shigo shigo ba zurfi ta masa. *** Kamar yadda ya tsara ilai kuwa hakan ya faru, Amatullah na ji tana gani baban Sasa ya sanya dokar rashin bikin suna tare da tsawatar ma yaya da jikokinsa akan zuwa gidan Amatullah akai akai. Mamaki sosai ya cika ahlin gidan don shi bai furta cewa ga yanda su ka yi da Saifullah ba balle wani ya zarge shi. "Aure mijinta zai ƙara, yarinyar nan ta amince ta yi tawakalli na zan laminta ba a fake da taron suna a zuga ta" shine hujjar da ya bayar wanda sosai yaransa maza su ka yi na'am da hakan. Har gida Baba Salihu ya je ya samu Amatullah ya mata nasiha sosai, ya nuna mata rayuwar ma gaba ɗayansa guda nawa ne, da suna ko babu suna abin da ya ke rabon ta ba zai wuce ta ba. "Baabaa!!!" tace tana mai son fadi masa halin da ta shiga lokacin rainon cikin ta da halin da suke ciki a yanzu. Damuwar da ta hango a kwayar idanunsa ya sanya ta faɗin. "Next week za mu koma makaranta, ina jin tsoro kar na kasa making result ɗina" kallon ta yayi a matsayinsa na ɗan jarida yana son ya fassara ma'anar abin da ta ce. Saifullah da ke maƙe bakin ƙofa ma saukar da ajiyar zuciya yayi da ya ji abin da ta faɗi, kafin Baba Salihu ya kai ga cewa komi ya shiga falon haɗi da sallama. Sai da su ka gaisa da Baba Salihu sannan ya kalli Amatullah ya ce "Baba yarinyar nan da ita ce auta ban san ya za ta yi ba, kin wani tasa Baba kina hawaye" Dariya Baba Salihu yayi ya ce "Wai tsoron boko take yi kuma sai kace kanta farau boko da goyo. Ni dai abin da zan ce miki shine ki sani gatanki ne bokon nan, kar ki ji tsoro ki dage ki fauwala ma Allah komi sannan ki yi addu'a. In an buɗe portal ki cire transaction ID zan sa a ƙarasa miki registration, Allah barshi sai ki koma in an fara lectures." yace zuciyar sa cike da tausayin ƴarsa. Nan dai su ka cigaba da hira su ukun, kafin da ga bisani Baba Salihu ya tashi ya tafi ba don ya so ba. *** Tun bayan da aka yi kwana bakwai, Saifullah ya sallami innarsa Amatullah ke yin komi, tun daga yi ma jariri wanka har zuwa yin nata wankan. Ga shi dinkin ta sam ko hanyar warkewa bai dauka ba, ko da ta yiwa Gwaggo korafi sai cewa ta yi tsabagen raki ne irin na Amatullah, dama Inna Jamila ta ce ba ta san shiga ruwan zafi to ina kuwa din ki zai warke? Lalle ta dage da shiga ruwan zafi. Ana cikin haka wayarta ta lalace, gaba ɗaya sai ta koma kurma, ba ta jin kowa babu mai jin ta, ga zamansu ba laifi yau lafiya gobe akasin haka. Kamar yadda baba Salihu yayi alkawari shi ya tsaya ta kammala registration sannan ya ɗauki dubu goma yace ta rike ko za ta bukaci wani abu. Sai kwana uku da fara lectures ta koma makaranta, duk dai har lokacin ta kan ji dinkin da aka mata ya na sukar ta, idan ya tashi mata ciwo har kwakwalwar kan ta take ji, ga wani dan hamami hamami da ta kan ji ya na tashi duk sanda ta ɗan bude wajen. Ranar da ta fara zuwa ranar lectures din Dr. Muhammad Zayyad ne ta shiga kusan a makare ga goyo kuma. Kujerar da ke kusa da ita ta zauna inda wacce ke zaune ta matsa mata cikin fara'a. Karatu yake musu cikin gwaninta da iya koyarwa a fannin clinical pharmacy. Sosai ta ke jin daɗin karatun, cikin rahamar Allah har ya gama awa biyunsa Emjay bai tashi ba. Bayan fitarsa ne su ka gaisa da wacce ke kusa da ita. "Great pharmacist ce yau a ajinmu" tace cikin fara'a "suna na Hannah Dawud ana ce min mimi, tun da nazo 100level nake son zama da ke, like sosai kike birge ni, ba ruwanki da gayu always in hijab kuma first class student" tace cikin tsantsan farin ciki. "mimi kenan, to tell you nothing is permanent in life yau gani repeating 300lvl. Anyway it's nice meeting you" tace tana miƙa mata hannu. Nan Amatullah ta faɗi mata courses din da za ta yi, mimi ta bata update akan su. "in ba za ki damu ba, let's be friends please, na san circumstances su ka yi leading to carry over ɗinki, Kinga ni Christian ce daga Adamawa, amma family ɗinmu duk mix ne, I hope ba zaki damu ba" ta ce cikin fara'a, yayinda ta ji mummunar faduwan gaba jin ta ambaci ita christain ce, kuma daga Adamawa. Dee Yusuf ne ya faɗo mata, yayinda ta ke kallonta tana mamakin kyanta da gayunta haɗe kuma da surutun Mimi, amma ace christain ce, wannan asara har ina. Tun daga ranar gaba ɗaya harkan karatu tare su ke yi, su na ba juna assignment su na ma juna bayani. Mimi ta bata shawaran samun cikin masu shara da zata kula mata da Emjay( sunan da take kiran babyn ta kenan) sai dai in sun samu sarari ta je ta bashi nono. Duk wanda ya san Mimi a gidansu da hostel ya san Maman Emjay ko a labari ko a fuska. Haka Amatullah bata kyashin kiranta da mummyn Emjay saboda kulawar da mimi ke bashi. Abin da ta lura da shi shi ne shakuwar da ke tsakanin Mimi da cousin ɗin ta, wanda kullum ba ta da magana sai na shi, bini bini ta kira shi, ko kuma ta ce da Amatulah ta raka ta office din shi nan bayansu a faculty of medicine da yake ta ce da ita assistant lecturer ne, wannan session din ya fara koyarwa. Amma hakan nan Amatulah ta ji ba ta son raka ta, har Mimi ta gaji ta daina mata tayi, a cewar ta kila Oga ya hana ki zuwa office din lecturers, ciki har cousin din kawar ki, ita kuwa ta bi ta eh ba tare da ta taɓa tunanin jin sunan cousin din na Mami ba, ta kan tsoka ne ta da Mimi cousin. Tsakanin ta da su Zulaikha kuwa sai dai idan ta shiga hostel ko sun haɗu wajen sallah dan kuwa yanzu sun zama seniors din ta. **** Dinki ta ba karamin damun ta ya ke ba, Amma duk sanda ta tunkari Saifullahi da maganar sai ya ce tsabagen gudun kar ya koma mata ne, ta kwantar da hankalin ta shi kan shi ba ta bashi sha'awa yanzu, dan kuwa ba dan ba dan ba sai ya ce ya kan ji dan wari wari na fita daga jikin ta, in dai haka ake jego Allah wadar jego irin na ta. Ranar haka ta sha kuka har ta yi mai isar ta, duk tsafta da kula irin na ta Saifullahi ya ce ta na ɗan wari wari, duk da dai ita kan ta ta san ba daidai ta ke ba. Washagari ya kama satin da za tafi mid semester, Amatullah na zaune da Mimi suna bitar wani course dinsu na pharmacology da za su yi test ranar Juma'a da za a tafi midsemester. "Maman Emjay me ke faruwa ne? Na ganki kwana biyu wata iri, yau idanun ki a kumbure" Mimi ta tambaya cike da damuwa. "wallahi mummyn Emjay, ina fama da ciwo sosai a ƙasa na, tun bayan haihuwa da aka min dinki ban sake jin dadin gurin ba, har ruwa yake yi, I think I got infected, idan ya tashi min ciwo har tsakiyar kai na, yau har jiri na ke ji" tace cikin hawayen da kamar dama suna jiran izinin fitowa. "kin kula yana wari kuwa, tun last week na ji, amma ina ta neman hanyar faɗa miki, me Dadyn Emjay yace" mimi ta faɗi cikin kulawa. "Mimi me zai ce, aurensa saura wata biyu, gaba ɗaya hankalinsa na wajen ne, labari na mai tsawo ne wata rana zan baki" tace tana murmushin takaici. "tashi mu tafi asibiti, ki na ɗiya mace be kamata ki yi wasa da abu irin haka ba, darajar ki ne fa, yanzu haka za ki zauna har a kawo mi ki kishiya jikin ki da wannan ciwo haka? Ai ya zama ciwo Maman Emjay, tashi mu tafi gaskiya......" Duk da Amatulah ta ɗan girme mata, yau sai Mimi ta zama kamar ita ce Yaya gurin ta. Amatullah na mai raunana idanu ta ce "Ki na gani za su karɓe mu? Har biyu fa Mimi?" "Kar ki da mu, ai nan shika za mu ce, akwai wata Anty na da ke aiki wajan, na san za ta iya taimaka mana" Cikin jin dadin yanda Mimi ta damu ya sanya Amatullah jin dadi, ga ta dai ahlil kitab amma sai zuciya mai kyau kamar 'Dee Yusuf...' Karo na hudu da ya kara faɗowa cikin ran ta kenan, ta na mai kokarin cire shi daga cikin zuciyar ta, tare da kwabar zuciyar na ta ta tashi, su ka ɗauki hanyar fita daga ajin ta na mai yiwa Mimi godiya. Wata coursemeta din su ce su ka samu ta rage mu su hanya. Kamar yanda Mimi ta faɗa Anty din ta ce ta taimaka su ka ga wata Gynecologist. Ko da Amatulah ta bude mata ga halin da ta ke ciki kuka ne kawai ba ta yi ba in da ta rufe Amatullah da faɗa sosai. Ya ta na ƴa mace za ta bari ta lalace haka? Shin ina iyayan ta su ke? Kuka Amatullah ta saka mata dan kuwa dai rasa da mai za ta ji ta yi, ciwon da ta ke ji ko kuwa masifar gynecologist da ake kira Dr Hajara. Sai ta karaci masifar ta har ita kan ta Antyn Mimi da ba ta ji daɗin halin da Amatulah ke ciki ba ta saka baki, dan kuwa Dr Hajara cewa ta yi ba za ta iya taba Amatullah ba. Dr Hajara na mai kallan dinkin Amatullah da har kore kore yayi tsabagen rashin kula ta ja tsaki a karo na uku kafin ta ce "I'm doing everything a fresh, kankare shi zan yi na sake buda ta, a sake mata wani dinkin, wajan is infected, Allah ya sa bai zama sepsis ba, fatana dai shi ne ace iya ka dinkin infection din ya tsaya!" Ta na gama faɗin haka ta tashi ta fice daga office din. Antyn Mimi na mai taɓa hannun Amatullah cikin bata karfin gwiwa dan kuwa gaba daya hankalin ta tashe ya ke. Mimi wacce ke rike da babyn Amatullah Antyn ta kira, in da ta ke shaida mata halin da ake. Mimi na mai duban Amatullah wacce idanun ta ya cika da hawaye ta ce "You will be fine Amatullah, don't worry, ga waya ta ki kira Dadyn Emjay ki fada ma sa halin da ake ciki" Hannun ta na rawa ta karbi wayar a hannun Mimi, ta kira number Saifullahi har sau wajan biyar amma bai ɗaga ba. Murya sanyaye ta ce "Mimi ya ki dagawa...." "Toh ko Momcy za ki kira?" Cewar Mimi cike da damuwa. Amatullah na mai girgiza kai te ce "Ah ah, kar na ɗagawa Gwaggo hankali, dama shi din dai zan iya faɗa ma, amma tunda bai daga ba, a yi min kawai na huta da wannan masifar" Da wannan Mimi ta shaidawa Antyn na ta, da izinin Amatullah tare da ƙwarin gwiwar Mimi da Antyn ta, wajan karfe uku aka shigar da Amatulah daki na musamman da aka ware domin aiki da ya shafi mata. Allurar kashe wajan da kuma girman dakin bai hana Mimi jiyo ihun salatin Amatullah ba, tun ta na iya jurewa har ta kasa, tashi ta yi tana da jijjiga Emjay da ya ɗan fara koke koken yunwa, su ka fice can waje. Sai wajan biyar da rabi aka gama Antyn Mimi ce ta kira ta in da ta ke shaida mata an ci sa'a infection din be shiga cikin tsokar ta ba. Cike da fargaba Mimi ta tambaya ko za ta iya ganin Amatullah. "Sosai ma kuwa, Nan da one hour ma da ta ji dan dama dama za ta iya tafiya, Amma gaskiya ki jawa kawar ki kunne ta bi duk dokokin da Dr Hajara ta ba ta in dai ta na so ta sami sauki" Da wannan Mimi ta sami ganin Amatullah da har lokacin ba ta dawo cikin hayyacin ta ba. Mimi ce ta kara kiran number Saifullahi amma har lokacin bai dauka ba, sai kawai ta tura ma sa sako kamar haka "Hello Dady Emjay, his mom, your wife Amatullah is very sick and in the hospital, kindly call me back it's urgent" Ta tura ma sa, har tsahon minti 30 shiru, dan haka kawai sai ta kira cousin din ta, ta roke shi alfarmar ya zo ya same ta hospital. Da ya ke ya ji batun asibiti sai yayi tunanin Mimi ce ba lafiya, dan haka ba tare da bata lokaci ba ya garzaya asibitin. Mimi ce ta taro shi daga in da yayi parking, dauke da Emjay wanda ya sha kuka ya gaji har bacci ya sace shi kwance bisa kafadar ta, suna tafe ta ke shaida masa halin da Amatulah ke ciki, ta kare da "Har yanzu dai mijin na ta bai kira ko ya min reply ba, shi ya sa ma na kira ka ko za ka taimaka ka bani 15k dan biya kudin asibitin, sai mu kai ta gida I take God beg you..." Bakin kofar ɗakin da Amatulah ke kwance su ka tsaya, ya na mai kallan ta ya ce "Mimi rigima, like how can you get your self involved in something like this? Mijin ta ba ya daga waya ba sai ta hakura ta je gida ta faɗa ma sa..." "Believe me, it was an emergency, please ka taimaka....." Ta fada ta na mai marairace masa Cikin dariya ya lakace hanci ta tare da fadin "As usual dole na yi yanda ki ke so Mimi, you always have that power over me, wanna shi ne babyn na ta ke nan" Ya na maganar ne yayinda ya ke kai duban sa ga fuskar yaran a karo na farko, wani iri mummanar faduwar gaba yaji yayinda yayi ido hudu da Emjay. "Eh Emjay kenan, yayi kuka ya gaji ya fara bacci" Hannu ya sa ya shafi fuskar Emjay, yayinda kamanin ta ke dawowa zuciyar sa "Ya sunan ta ne? Maman Emjay?" Zuciya daya Mimi ta ce "Sunan ta......." "David dantawaye idanun ka kenan?" Antyn Mimi ce ta katseta, yayinda Dee Yusuf ya ja ajiyar zuciya ya na mai duban Antyn ta su ya ke murmushi, ya ba ta amsa da "Ni na isa Anty, ai tuwo tuwo ne ba a sake ma sa suna Mama na" "Ka dai yi bayani, yaushe rabon da na saka ka a ido na? Ko ka dena iyayen da mu ne?" "Kai na bisa wuya na Anty, ai ban isa ba, aikin ne sai a hankali" Nan ya gaishe ta cike da girmamawa, kafin ta shedawa Mimi kawar ta fa ta dan sami dama dama, za su iya tafiya gida. Dee Yusuf da tun ganin Emjay gaban sa ke faduwa tuni yayi gaba, ya ce da Mimi su same shi a mota bayan ya ciri kudin da Mimi ta tambaye shi, naira duba goma shabiyar ya bata. Sai da ta yi biya komai sannan ta koma gun Amatulah wacce ta tabbatar mata ta na cikin hayyacin ta, za ta iya gane hanyar gida sannan ta sheda mata cousin din ta na mota ya na jiran su. Hannun Mimi ɗauke da magunguna Amatullah, Daf da magarib, Amatullah na godiya babu adadi, ta na tafiya kamar mai koyan tatata har su ka isa motar Dee Yusuf. Ya na daga zaune bai damu da ya fito daga motar ba su ka yi sallama da Antyn su, bayan mota Mimi ta budewa Amatullah ya zauna sannan ta zaga dauke da Emjay ta zauna gaban mota. Sai da ta zauna ta ce "Maman Emjay yau dai ga cousin dina da ki ke min tsaya akan shi, Dee meet Maman Emjay" Duk radadin da ta ke ji bai hana gaban ta faduwa ba jin Mimi ta furta 'Dee' shi kuwa zuciyar shi daya ya juyo ya na fadin "Sannu Maman Emjey......." Nan ya tsaya cak yayinda yayi ido biyu da fuskar da ya kasa mancewa a rayuwar sa "Amatullah" Ya tsinci bakin sa na furta sunan ta cikin numfashi, Amatullah kuwa gaba ɗaya rudewa ta yi, ba ta taɓa zaton za ta karasa shi a Ido ba, haka kuma ba ta so a ce cikin halin nan da ta ke za ta gan shi ba, ba ta yi shirin sake ganin shi ba. Shirun da ta ga sun yi suna duban junan su ya sanya Mimi faɗin "I'm missing something here? Dee dama ka san ta ne?" Dee na mai jinjina kai, ya juyo ya tada motar, ya ce "Na san ta sanda ina under graduate, Amatullah......" Ya fadi sunan ta yayinda ya tada motar su ka fara tafiya, cikin ran sa ya na jin ciwon da ke kasan zuciyar sa da Mimi ta fama masa. Mimi kuwa gyada kai ta ce "Oh yes guru dole ya san guru duk da dai akwai tazara a tsakanin ku, idan na yi lissafi daidai su na hundred level ka yi graduating ko?" Kai kawai ya gyada mata, daga nan bai sake furta komai ba domin kuwa gaba ɗaya rasa abin da ke ma sa daɗi, ashe Amatullah ce Maman Emjay din Mimi? Ashe duk wannan azabar da Mimi ta ba shi labarin Maman Emjay ta sha wajan dinki ashe Amatullah ce? To ina mijin ta? Wani irin soko Amatullah ke aure? Zance da ya ke yi cikin ransa kenan har su ka isa bakin gate din asibitin. Amatullah kuwa mutuwar zaune ta yi, sai da Mimi ta tambaye ta sau uku sannan ta fahimci da ita Mimi ta ke magana, ta faɗa ma su sunan unguwar da su ke zaune. Cike da tausayawa Mimi ta ce "Maman Emjay please ki rage damuwa, Allah zai ba ki lafiya kin ji?" Kai Amatullah ta jinjina mata ba tare da ta iya furta komai ba, Allah Allah ta ke su isa gida ta fita daga motar Dee, ba dan halin da ta ke ciki ba da tuni ta sauka ta gwammaci ko machine ne ta hau, fatan ta Allah ya sa har su ajiye ta kar su hadu da Saifullahi, duk da dai ba ta da tabbacin ya san Dee, ko ya san shi ba lalle ya gane shi ba. Ganin yanayin Dee ya canza sam Mimi ba ta kawo komai cikin ran ta ba, duk a tunanin ta tsabagen haushin involving kan ta da ta yi cikin lamarin Amatullah da ta yi ne. Dan haka duk surutun ta sai ta sami kan ta da kame bakin ta. Haka su ka yi tafiyar kurame har su ka isa unguwar su Amatullah. Mimi na tambayar ta kwanar da za a shiga ta na fada mata shi kuma Dee na karya kan motar shi har su ka isa kofar gidan Amatullah, nan su ka yi kacibus da Saifullahi, ya fito daga gidan kenan ya ga wata hadaddiyar mota ta faka kofar gidan sa. Tuni ya shagala da kallon motor ya ma manta ya fito ne domin ya je gida ya shedawa Baban Sasa Amatullah fa ba ta dawo daga makaranta ba, gashi yayi neman duniya cikin makaranta har department din su amma be gan ta ba. Hasken farin wata da kuma hasken fitar layin ne ya haske fuskar Dee da ke hakince gaban mota shi sam bai lura da Saifullahi ba, wanda ko a mafarki aka nuna masa Dee zai gane shi. Ran Saifullahi bai baci sai da ya ga Mimi ta fito dauke da Emjay bisa kafadar ta, ta zo gidan baya ta budewa Amatullah wacce ta fito da kyar ta na faɗin "Na gode sosai, madallah" Dee wanda ya tabbatar da shi ta ke kai ya jinjina mata ta na mai sakar mata murmushin nan na sa mai kayatarwa. Duk abunda ke faruwa a kan idanun Saifullahi wanda ya cika yayi fal tsabagen wani bakin kishin da tun da ya ke a rayuwar sa be taba zatan ya na da shi ba. Ita kan ta Amatullah sai a sannan ta lura da shi, ganin yanda ya hade girar sama da na kasa ya na huci kamar macici ya sanya Amatullah kokarin karbar Emjay daga hannun Mimi, ita kuwa ta ce "Ah ah mana Maman Emjay bari na shigar mi ki da shi ai" Amatullah na mai tasbihi da neman tsarin Allah daga halin Saifullahi wanda Sam bai lura da yanayin tafiyar da Amatullah ta ke yi ba tsabagen masifa ya rufe ma sa idanu su ka iso daf da shi, cikin sanyin murya ta ce "Ya Saifullahi yi hakuri daga asibiti......!" "Ke dallah yiwa mutane shiru!" Saifullahi ya daka mata tsawar da ita kan ta Mimi sai da ta ja baya da sauri har ta na tuntube, Emjay tuni ya razana ya fashe da kuka, hakan ne ya ja hankalin Dee Yusuf, har ya sauke gilashin motar shi cike da mamakin abun da ke faruwa. Saifullahi wanda bai yi la'akari da ba su kadai ba ne ba, kuma a kofar gida su ke ya cigaba da bambami, ya na mai zargin Amatullah ta hanyar furta munana kalamai gare ta, fadi ya ke "Macuciya! Azzaluma! Ashe da auren ki ba ki rabi da wancan arnan ba? Da auran ki kina bin namijin da ba na ki ba! Kin yi asara Amatullah......!" "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun!" Iya ka abin da Amatullah ke iya furtawa kenan. Ita kuwa Mimi hankalin ta ne ya tashi, Ganin Dee ya fito daga mota a fusace ya tabbatar mata Dee Yusuf din ne arne kuma tsohon saurayin Amatullah da Saifullahi ya ke nufi, da sauri ta sha gaban shi ta na mai girgiza ma sa kai, idanun ta cike da magiya ta ce "Dee I beg of you..Kar ka yi haka, kar ku tara mata mutane, she is ill for goodness sake! please ka koma mota, bari na kai ta ciki" Saifullahi kuwa ya na huci ya ke fadin "Ki bar shi ya karaso mana, me zai iya min kwartan banza kwartan hofi, ko da yake ku kwartanci a addinin ku ba komai ba ne, ita dai da ta ke musulma ita ta yi abin kunya....." A fusace Dee ya furta "Mimi!" Mimi da idanun ta su ka cika da kwalla ta ce "You're better than this, you can do better, please Dee" Ya na mai jinjina kai ya koma mota, Mimi ta ja hannun Amatullah da tashin hankali ya sa dishi dishi ta ke gani. Allah ya so Saifullahi bai kai ga datse gidan ba su ka karaso, dan haka Mimi ce ta tura kofar gidan, hannun ta cikin na Amatullah su ka shige ciki suka bar Saifullahi tsaye ya na huci ya ke duban Dee da ya shige motar shi ya na mai dage gilashin mota. Har ga Allah ya so yiwa Saifullahi dukan kawo wuka, Amma halin da Amatullah ke ciki, da kuma Mimi ya sanya shi zama cikin mota zuciyar shi na tafasa. Ganin Dee Yusuf yayi banza da shi, ya sa ya shige ciki a fusace. A falo ya tadda Amatullah zaune, rike da Emjay da ke ta kuka amma ta kasa ko kallan sa bare ta kai ga rarrashi ko ba shi nono. Mimi da ke Allah Allah ta koma wajan Dee kar ya biyewa Saifullahi ta yi mata sallama, tare da bata hakuri sannan ta juya, ba ta kai ga fita ba ta ji Saifullahi ya ce "Wannan yaron da ki ke rike da shi, ina kyautata zaton ba dana ba ne shi ya sa ki ka dage ba za a zubar da cikin ba, dan wancan kwartan na ki na waje ne...!!!" Ba Amatullah ba ita kan ta Mimi a razane ta juyo ta na duban Saifullahi, Amatullah kuwa neman hawaye ta yi ta rasa, salatin ma ya kafe a bakin ta, duban shi kawai ta ke da idanun ta da su ka su ka yi jajur. Bai gushe ba ya kara da "Ki hade na ki ya na na ki ki bar min gida, Ni Saifullahi na sake ki Amatullah, na sake ki! Na sake ki!"[4/1, 9:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI kafin su samu farfaɗowa daga suman zaunen da su ka yi su ka tsikayo shi yana faɗin "Sannan wallahi kar ki bari na dawo na isko ki a gidan nan, banza fasiƙa" Wani irin abu ya tokare ma Mimi a wuya, ta na jin ana faɗin maza ba su da kirki ba ta taɓa yarda ba sai yau da ta ga zahiri. Yanda Saifullahi ya gifta ta a fusace ya sanya Mimi jan gefe gudun kar ya buge ta. Ta koma wajen Amatullah ta na kokarin karɓan Emjay daga hannun ta ta ce "Yi hakuri Amatullah, I don't even know what to say, da na san zuwa asibiti da zuwan mu gidan nan abin da zamu jawo mi ki kenan wallahi da ba mu zo ba, kin ce cousin din ki ne ko? Tashi mu kai ki gida kafin ya riga mu" Maimakon ta sakar mata Emjay, sai daɗa riƙe shi ta yi gam. Ta na mai duban Amatullah da idanun ta da suka riga su kafe ta ce "No Mimi, ba zan bi ku ba, ki tafi kawai" "Why? Saboda me?" Mimi ta tambaya cike da mamaki. Amatullah ta ɗaura Emjay kafadar ta, ta na mai jijjaga shi, cikin wani irin yanayi mai wuyan fassarawa, yanayi na tsantsan kunar zuciya ta ce "Ya kira ni fasiƙa, ya shegentar da ɗan sa, duk dan a dalilin na shiga motar Dee, kuskuren shiga motar ɗan uwan ki ya janyo wannan kazafin a gare ni Mimi, yanzu sai na ƙara shiga ku kai ni gida? iyayen mu su gan na fito daga motar ɗan uwan ki? Ta Yaya zan wanke kai na?" "Iyayen ki sun san wacece ke Maman Emjay, they know what their daughter is capable of doing saboda sun san sun bawa diyar su tarbiya mai kyau..." "Hakan ya sa ba zan bari daidai da second ɗaya zargi irin wannan ya gifta a zukatan su ba, na gode Mimi.....I will find my way" "Maman Emjay a wannan lokacin har kina tuna wani bayan ke, ba ki tunanin halin da ki ke ciki? you have to wake up and start loving your self" mimi tace tana mai danne takaicin da ya taso mata. Ba ta san me yasa mata da dama basu damuwa da ƙaunar kansu ba, a dai barsu da son zuciya (selfishness) amma sam ba su san wani abu wai shi self love ba balle self esteem. Amatullah na mai runtse idanu, murya can kasa ta ce "Go ...... just go Mimi" "I'm so sorry Amatullah" Cewar Mimi kafin ta juya ta fita jiki a sanyaye. Sai bayan fitar ta Amatullah ta sami damar bawa Emjay nono, gaba ɗaya kwakwalwar ta ce ta daskare yayin da idanun ta ke kan Emjay wanda yana shan shanono ya na mai sakin ajiyar zuciya. *** Yanda ya ga Mimi ta shiga motar ta zauna jiki sanyaye ya sanya shi faɗin "How is she?" "Very hurt....." Cewar Mimi, kafin ta juya ta na kallon Dee, cikin neman bayani ta ce "Menene dangantakar ku? What was she to you? Me ya sa mijin ta zai zarge ka da neman matar shi na aure? What is happening Dee?" Ajiyar zuciya ya saki, ya na mai wasa da sitiyarin motar ya ce "It's a long story Mimi, Zan ba ki labari. Amma zancen neman matar shi wallahi sharri ne irin na namijin da bai san ciwon kan sa ba, Amatullah is the most decent person I know in my life, please mu tafi kafin wannan jahilin mijin na ta ya dawo, wallahi zan iya bugun shi...." "Ya sake ta!" Cewar Mimi ba tare da ta kalli Dee Yusuf ba. Ji yayi kamar kunnen sa ne ke masa gizo. "I beg your pardon!" Cewar Dee cikin kaɗuwa. Mimi na mai jinjina kai yayin da hawaye ke zuba daga idanun ta "Ka ji ni da kyau, an saki Amatullah, that useless person accused her of sleeping with you, kuma hatta Emjay ya ce ba ɗan sa ba ne, ɗan ka ne......" "Waiyazubillah!" Cewar Dee ya na mai doka hannu kan sitiyari. Mimi ba ta gushe ba ta kara da "Ya ce kar ya dawo ya same ta, Amma ta ki yarda mu kai ta gida, Ni damuwa ta a yi clearing wannan misunderstanding ɗin kar ya je ya maimaitawa iyayen su abin da ya furta mata, I'm feeling very bad Dee, Ni na jawo mata, da na sani da ban ce mu je asibiti ba, da mu ka kira wayar shi bai ɗaga ba da mun hakura ta koma gida, da ban kira ka ba....." Ta karasa maganar cikin shashshekar kuka. Motar ya kunna ba tare da ya tankawa Mimi ba, zuciyar shi ke tafasa yayinda ya ke Jin duk duniya babu jahili mara ilimi kamar Saifullahi ba. Motar ya ja, Mimi na tambayar shi ina za su je bayan sun bar Amatullah cikin halin haula'i, ya mata shiru. Tun ta na tambaya har ta gaji ta ma sa shiru ta zubawa sarautar Allah ido. *** Saifullah kuwa ko da ya fice Amaru ya wuce, zuciyar sa in ban da ƙuna babu abin da take yi, hango Amatullah da Dee ya ke a shimfiɗa, tiryan tiryan idanunsa ke masa gizo da abin da kwakwalwarsa ke sauwara masa. Da haka ya isa gidan Jamoh. Kamar yadda yake al'adar su yau ɗin ma zaune suke, su takwas ciki har da mahaifin sa da mahaifin Amatu. Bai tsaya rufe ƙofar motar sa ba ya isa garesu a firgice. "Lafiya? Me ya samu Amatullah?" Baba Anas ya tarye shi cikin matsanancin tashin hankali. "Baba Amatullah ta cuce ni, shege ta kawo min... " wawan marin da ya sauka a fuskar sa ya sa ya kasa ƙarasawa. "Ko mutuwa na kunyan idon mahaifa balle kai sakarai gaja, kalli nan mahaifinta ne, kalle mu nan mu bakwai duk ba wanda zai yarda a ci zarafin Amatullah" Baba Anas yace cikin Dana sanin tambayarsa. "Baba wallahi bata rabu da Arnen nan ba, yau a kan ido na ya sauke ta a ƙofar gidan aurenmu" yace yana sunkuyar da kai, nan gaba ɗaya su ka ɗauki salati. "Saifullahi shin wani laifi Amatullah ta yi ma ka da za ka jefe ta wannan mugun zargi haka? Idan mai magana wawa ne ai majiyinta ba wawa ba ne" Cewar Baba Zubairu cikin adduar Allah ya sa dai Saifullahi bai san abin da ya ke fada ma. Shi kuwa mahaifin Amatullah mutuwar zaune yayi duk da kuwa ko duka jikin shi kunne ne ba zai taɓa yarda da wannan maganar ba. "Allah ya wadar na ka ya lalace! Saifullahi sakayyar da za ka yiwa zumunci kenan?" Cewar Baba Anas wanda kunyar mahaifin Amatullah ya rufe shi, ji ya ke kamar kasa ta tsage ya shige. Motar Dee da ya faka daga gefen su ne ya ja hankalin su, kallan motan su ke cikin jiran tsammani. Shi kuwa Saifullahi da ya san motar Dee ne, tsabagen idanun sa sun rufe be ma iya gane daga Dee sai Mimi ne tafe cikin motar ba, cikin farin cikin Allah ya kawo ma sa sheda har gida ya ce tsaya, "Kun ga ni ko Baba, ga shi dai kun ga zahiri ya kawo ta har gida dan rashin daraja!" Duka motar su ke kallo, da ya ke fitilar kofar gidan Baba Sasa ba ta da haske sosai dan haka ba su iya tantace wacce ke zaune gaban motar ba, shin Amatullah din ce kamar yanda Saifullahi ya ke jaddawa? Tambayar da ke yawo cikin kwakwalwar Baba Anas kenan. Shi kuwa mahaifin Amatullah adduar neman tsari daga abin da ke shirin faruwa ya ke, dan kuwa idan ya kasance Amatullah ce da tsohon saurayin ta zaune cikin motar nan, to lalle diyar shi ba ta ma sa adalci ba. Mimi da tun isar su ta ke duban Dee ta ce "Dee ina ne?" "Gidan su Amatullah..." Ya amsa mata a takaice, kai Mimi ta jinjin kafin ta ce "Da gaske ne kenan you guys had a relationship? Oh Lord Jesus!" Cewar Mimi ta na mai dafe kai, ba ta gushe ba ta kara da " Ohh She is the one! That Muslim girl that made you......" "Mimi babu lokaci, please za mu yi magana, for now you have to this for Amatullah, you call her a friend, da ke aka yi komai, kin ga wannan mutanen da ke zaune?" Ya nuna in da su Baba Anas ke zaune "I'm very sure uncles din ta ne, or maybe da Baban ta, ina wayar ki? Jiki sanyaye ta ce "Ga shi nan" "Ina receipt din hospital bill da ki ka biya?" Ta na mai dafe kai ta ce ya na jakar Maman Emjay. "Na so ya na gun ki, but wannan ma zai yi, I know you're smart, I trust you, only you can clear Amatullah, please go and explain everything to them!" Cikin karfin hali Mimi ta girgiza kai, kana ta ce "Tare za mu?" Dee ya girgiza kai tare da faɗin "I don't need to be there, you can do it" Kai ta girgiza alamar toh, kana tayi yunkurin buɗe motar. " kun gani ko, har yanzu ta kasa fitowa tsabagen borin kunya" Saifullahi ya faɗi yana tashi kamar wani sabon hauka ya dumfari motar Dee. "Idan ka ƙara taku ɗaya Allah ya tsine maka Saifullah" Baba Anas ya ce, wanda hakan yayi daidai da fitowar Mimi. Nan Saifullahi ya tsaya ya na raba idanu domin ganin Amatullah ta fito bayan Mimi, amma babu ita babu alamar ta. Baba Anas kuwa da Mahaifin Amatullah ajiyar zuciya su ka saki a lokaci ɗaya, su na mai godewa Allah ganin watan Amatullah ce ta fito daga motar, maimakon Amatullah da Saifullahi ya ce. "Haba Anas, wai duk gaskiyan nan da ke bayyane, me ze sa makamashin nan dawowa kofar gidan nan in ba dai akwai kamshin gaskiya a maganar Saifullahi ba? Ku duba da kyau ku gani wannan arnan nan ne dai cikin motar can" Baba Mahmuda ya faɗi cikin hasala. Sallama Mimi ta musu duk da kuwa gaban ta na dukan uku uku, cikin girmamawa ta gaida su, su ka amsa suna kallon ta a kyamace. "Yarinya ke kuma daga ina?" Ba ta kai ga amsawa Baban Sasa ya aiko Hafiz da ya kai masa rahoton abin da ke faruwa da duk su shiga ciki. Dan haka duka su ka garzaya, Baban Anas ne kafin ya tashi ya dubi yarinya ya ce "Za ki iya jiran mu yarinya?" Mimi ta ce "Eh Baba, dama na zo ne kan batun Amatullah ta nan can gida yanzu haka ba lafiya....." "Amatullah ki ka ce?" Mahaifin Amatullah wanda shi ma ɗin tsayawa yayi dan sauraron Mimi. "Ai ina ga zai fi ita ma din ta biyo mu" Cewar Baba Anas, ya na mai kallon Mimi ya ce za ki iya shigowa daga ciki. Baba Anas da Mahaifin Amatullah tafe, Mimi na biye da su haka su ka shiga ciki gurin Baban Sasa. Nan su ka tadda su Baba Zubairu zaune, Baba Anas yayiwa Mimi wacce tun shigowar su Baban Sasa ya bi ta da kallan tuhuma, wuri da setin in da Saifullahi ke zaune taje ta ɗan raɓe. Su ma din waje su ka samu su ka zauna. Baba Mahmuda da Baba Idris ji suka yi kamar su hau mimi da duka saboda kafiɗirinta. "Me ke faruwa da kuke min tallan martaba a idon duniya, a'a kai!" Baban Sasa ya ce cike da takaici yana mai bin su da kallon tuhuma. "Baban Sasa, ashe ɗan can ba nawa bane, ashe Amatullah ta daɗe tana cin amanar aure na Ban tashi sani ba sai yau, ashe shi ya sa lokacin da na ce a zubar da cikin ta ƙi amincewa saboda riban soyayya ne" ya faɗi ba tare da tunanin abin da yake faɗi ba sai da ya ga kallon da baba Anas ke watsa masa, bai gushe ba ya cigaba da fadin. "Tun la'asar nake makarantar su don ɗauko su aka ce min ta tafi, wasu suka ce ba ta ma zo ba, na dawo gida shiru shiru kawai na fito na sanar da ku sai na ga wannan tsinannen tsohon saurayin ta kawo ta, yau dubun su ya cika" ya karasa maganar ne cikin dacin kishi. Salati Baban Sasa ya saka, ya na mai dafe kirji ya ke faɗin "Kai Amatullah ta ba ni kunya, Amatullah ta cuce mu ta ci mutuncin aure!" Mahaifin Amatullah ya sunkyar da kai cike da kunya da takaici. Ita kuwa Mimi jikin ta har rawa ya ke tsabagen yanda ta ke so a bata dama ta yi magana. "Baba ban tari numfashin ka ba, zai fi kyau a bi wannan lamari daki daki a yi bincike kafin yanke hukunci! Ga wannan yarinya ta zo mana da batun rashin lafiyar Amatullah, ya na da kyau a saurare ta" "Shin yaushe mu ka fara sauraran magana daga bakin bare?" Cewar Baban Sasa ya na mai kallan Mimi a wulakance. Haka ma Saifullahi wani mugun harara ya jefi Mimi da shi, cikin jandadin furucin Baban Sasa ya yi saurin fadin "Yo to wannan ai bakin su daya ma, ai dai ku na gani tare da arnen ta zo, da ita su ke bugewa suna aikata masha'an su" "Aw ku na nufin ya zo har gidan nan!" Cewar Baban Sasa cike da nuna bacin rai. Ita kuwa Mimi da ran ta ya fara baci ganin yanda su ke kyamar su kiri kiri, ba tare da jiran izini ba ta fara jawabi kamar haka "Sunana Hanna Dauda, resiting 300lvl da Amatullah ke yi ya sa na zama kawarta don na dade da saninta a matsayin mai ƙoƙari. Handout, abinci, duk Amatullah bata san su ba, duk rana duk sanyi a motar haya take zuwa duk da ɗanyen jego......." "Dakata yarinya, wannan wani irin zancen banza ki ke faɗa mana! Ita Amatullah din ce ta fada mi ki haka? Kai Saifullahi ina gaskiyar maganar nan" Baban Sasa ne ya katse Mimi, in da duka dakin kallon Saifullahi da ya fara zufa har ta kan hanci su ke. Ya na mai girgiza kai ya shiga karyata Mimi, faɗi ya ke "Karya ta ke! Wallahi karya ta ke min babu abin da ban ɗaukewa Amatullah ba!" Mahaifin Amatullah wanda idanun sa suka cika da kwalla ne ya furta, ke mu ke sauraro yarinya. Mimi ta nisa sannan ta cigaba kamar haka "Tun last week na lura da tana wari kaɗan kaɗan duk da kasancewarta mai tsafta, Amma na kasa faɗa mata, sai ɗazu da kan ta tazo min da maganar, cewar dinkin da aka mata tun na haihuwa ya nan ya zame mata ciwo, shi ne ya ke fitar da ɗan wari......" "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun" Cewar Mahaifin Amatullah. Baban Sasa ya kara da "Amatullah mai tsafta ce ta ke da ciwo a jiki har ya na fitar da wari? Saifullahi ka na da masaniya akan haka?" Saifullahi na mai share zufa da bayan hannun sa, shirun da yayi ya tabbatarwa ya san da wannan lalurar. Hakan ya bawa Mimi damar cigaba da faɗin "ko da mu ka je asibiti, likita ta duba Amatullah ta mana bayanin cewa ta na cikin tsaka mai wuya, muddin ba a yi mata aikin gaggawa ba, Baba a duba wayar Saifullah Amatullah ta kira shi, kusan sau biyar ta kira shi tun kan a shiga da ita tiyata, bai daga ba, da aka fito da ita na sake kiran shi, be daga ba, shi ne na tura ma sa sakon text......" "Wa ki ka kira? Wa ku ka kira? Wa ki ka turawa sakon text? Ga dai waya ta nan tun safe ta ke hannuna! Kuma in banda sharri da wata wayar Amatullah zata kira ni ita da wayar ta ta lalace kusan wata ɗaya ta wuce?" Saifullahi ne ya katse ta cikin rashin sukuni, dan kuwa dai idanun sa sun fara raina fata. Maimakon ta bashi amsa, sai ta budi na ta wayar ta ce "Malam Saifullahi halan wanna number din ta ka ce 080********" "Kwarai kuwa numbarsa ce kuwa" Baba Anas ya amsa mata, shi kuwa Saifullahi wani gumi ne ya shiga keto masa dan jin ta karanto numbar shi na karamin waya, Dan kuwa dai wannan wayar ta shi a silent ta ke tun shigar sa masallaci da ya saka ya manta bai cire ba. "Ba ni wayoyin ka Saifullahi!" Baba Anas ya faɗa cikin umarni. Jiki sanyaye Ya mika ma sa wayoyin. "Wanne daga ciki numbar da ta kira yanzun nan ta ke?" Yayi nuni ga ɗan karamar wayan cikin ran sa ya na adduar Allah ya sa ba wuka ya dabawa kan sa ba. Baba Anas na dubawa sai ga missed calls ba adadi, ya umarci Mimi ta karanto numbar ta, ta karanto. Nan maganar Mimi ya tabbata, missed calls dai gasu nan reras, haka zalika sakon da ta turawa Saifullahi, wanda shi kan shi bai san da shi ba. Baban Sasa kallon Saifullahi kawai ya ke. Mahaifin Amatullah ne ya ce da Mimi "Yarinya dan Allah karasa jawabin ki ko ma san halin da yarinyar nan ta ke ciki" Mimi na mai gyada kai ta cigaba da magana kamar haka " Wallahi ban san cousin ɗina ya san Amatullah ba, kiran sa kawai nayi ya zo ya cece mu don Bill dinmu 15, 000 wanda an mata aikin ne don emergency mu ka je. Baba lokacin da Amatullah ta ga Dee wallahi ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta biyo mu don ni na san da lafiyar ta lau ba za ta ko kalle shi ba, haka mu ka kai ta gida, Nan kofar gidan mu ka ga Saifullahi in da ya shiga aibantata tare da faɗi mata kalamin zargi tare da shegenta ɗan sa na cikin sa" Mimi ta karasa maganar ba tare da furta sakin da Saifullahi yayiwa Amatullah ba, tsabagen nauyin da kalmar ta yi mata. Zufa ne ya rufe Saifullahi, shi kuwa Baban Sasa hawaye ne ke fita daga idanun sa wiwi, Mahaifin Amatullah kuwa wani sanyi ne ya ratsa zuciyar sa an wanke diyar sa akan zargin da mijin ta ya ke mata. "Allah ya isa, Saifullahi Allah ya isa tsakanina da kai, ka zalinci Amatullah, ka haince ni, da ka fada min ba ka san yarinyar nan da ba mu cuce ta mun aurar da ita ga kai ba!" Cewar Baban Sasa hannu bisa kirjin sa da ke harbawa tsabagen ciwo da ya ke ma sa. "Saifullahi za ka gama da duniya lafiya kuwa?" Cewar Baba Anas. Baba Zubairu na mai girgiza kai ya "Ah ah kar ku masa baki, kuskure ne da aikin shedan......" "Akwai shedanin da ya wuce shi kan shi Saifullahi? Ya azabtar da ƴa, ya kuma saka mata da zargi, kazafi fa? Allah ya wadar na ka ya lalace, na dai faɗa ma ka yanda ka kuntata mata haka zan kuntatawa ita uwar ta ka mai zuga ka!" Nan fa gaban Saifullahi ya fadi, dan kuwa dai ya saki Amatullah, gashi Baba Anas na maganar ramuwar gayya. Cike da nadamar abin da ya aikata, dan kuwa be taba tunanin abin zai juye ma sa haka ba "A yi hakuri Baba, wallahilazim na rantse da Allah ban san ta je asibiti ba, ban ga kiran su da sakon wayar na su ba, wayar tawa a shiru ta ke " Cewar Saifullahi ya na mai share zufa. "Ba ka san tana asibiti ba? Ba ka san ta na da ciwo ba har ya kai da fitar da wari? Saifullahi ai ko babu dangantaka na aure ai Amatullah kanwar ce Saifullahi" Cewar Mahaifin Amatullah cikin nuna rashin jin dadi, in da su Baba Zubairu su ka shiga tofa albarkacin bakin su. Cikin jin daɗin yanda ta wanke Amatullah, ya na duban Mimi ya ce "Yarinya ba mu san da wani baki za mu gode mu ku ba, ba mu san yanda za mu gode mu ku ba" Cikin jin dadi da gamsuwa Mimi ta bashi amsa da "Ba sai kun gode min ba ai yiwa kai ne, ni dai fata na a duba lamarin Amatullah, Allah kaɗai ya san halin da ta ke ciki...." "Bari na koma gidan yanzu!" Saifullahi ya katse Mimi yayin da ya tashi zumbul ya na kokarin sanya takalmi. "Ka koma wani gida? Mahmuda je ka dauko min yarinyar nan kafin ya je ya karasa mana ita, nan za ka zauna har sai an kawo ta babu in da za ka!" Cewar Baba Anas. Saifullahi da ya so komawa gida domin ya san yanda zai yi ya shawo kan Amatullah, dole ya dawo ya zauna. Nan Mimi ta musu sallama zuciyar ta cike da annushawa. Ganin Mahaifin Amatullah ya rakota har kofar gida ya tabbatarwa Dee haƙan su ya cimma ruwa, ko shakka babu Mimi ta wanke Amatullah, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar sa, wanda har sai da Mimi ta gane yayin da su ka hau hanya. Ta na mai jinjina kai ganin yanda Dee ke murmushi, baki har kunne ta ce " By the way ka ke murmushi na san ka gane mun yi nasara, but ina bin ka bashin bayani ka sani ko?" Cike da jin dadi ya figi motar yayinda su ka hau bisa kwalta ya na mai maimaita "Na sani Mama na, na sani Mama na!" Ita ma din murmushin ta ke cike da annushawa. **** Amatullah kuwa kamar yanda Baba Anas ya ce, Baba Mahmuda ne ya je gidan, ya tadda ta zaune dai in da su Mimi su ka bar ta. Ganin shi ta san Saifullahi ya je ya faɗa mu su ita mazinaciya ce, dan haka ko da ya ce ya zo ne su tafi, ba ta tambaye shi dalili ba, tashi ta yi tana tafiya da kyar. Ba karamin tausaya mata yayi ba, ya na mai mamakin rashin imani irin na Saifullahi, yana dana sanin kiyayyar da ya ke mata ita da mahaifiyar ta, a sanyaye ya ɗaukar mata Emjay, da sannu a hankali, ya na mata sannu har su ka isa motar, ya bude mata gidan baya ta zauna. Sai da ya bata Emjay sannan ya karbi mukullin gidan ya rufe ba su zame ko ina ba sai gidan Baban Sasa. Ganin Amatullah babu wanda bai tausaya mata ba, hatta Saifullahi sai shigowar ta ya lura da yanayin tafiyar ta, wani kunya da nauyin iyayen su ne ya rufe shi, ina ma zai iya mayar da hannun agogo baya, da bai aikiata abin da ya aikata ba. "Sannu, sannu Amatullah" Kalaman da ta ke ji daga bakin iyayen ta kenan wanda shi ya ba ta ɗan kwanciyar hankali, ko babu komai sun san ba ta da lafiya. Kan katifa kusa da shi Baban Sasa ya umarci Amatullah ta zauna. Burin ta kar ta hada idanu da Mahaifin ta, bayan kazafin da Saifullahi ya mata, kuma ta tabbatar ya faɗa mu su ba ta san da wani ido za ta iya kallan sa ba. "Sannu Amatullah" Cewar Saifullahi wanda ke kallan Amatullah idanun sa cike da magiyar neman rufin asiri. Amatullah kuwa ko kallan sa ba ta yi ba bare ta san ya na wajan. Maimakon ta ji tsinuwa da la'antar da ta ke tsammani, sai ji ta yi Baban Sasa ya ce "Amatullah ashe haka mu ka cutar da ke ba mu sani ba? Mu ka aurar da ke ga mara kaunar ki? Amatullah za ki iya yafe mana kuwa?" Cike da mamaki ta daga iduna ta dubi Baban Sasa, wanda kallo ɗaya za ka masa ka tabbatar da tashin hankalin da ya ke ciki, cikin awa biyu kacal ya kara tsufa, numfashi na neman harde ma sa. Sai a sannan ta iya kallon mahaifin na ta, wanda idanun sa ke cike da kwalla. Kan ta ta sunkuyar, dan kuwa dai ba ta da ta cewa, ta faru ta kare an yiwa mai dami daya sata. Baban Sasa bai gushe ba ya cigaba da faɗin "Nan gidan za ki zauna har ki gama jinya, ba dan saki babu kyau ba da na umarci ja'irin nan ya sake ki a yau Amatullah..." Cike da mamaki Amatullah ta ɗago kai ta na mai duban Saifullahi wanda ya shiga girgiza mata kai, alamar ta yi shiru. Cikin taikaci ta ce "Baban Sasa ana yin wani saki ne bayan saki ukun da Allah ya halatta ma da namiji? In dai kuwa ba a yi ina mai tabbatar muku Saifullahi ya sake ni, ya sake ni saki uku!" "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun" Cewar dukkan wanda ke cikin ɗakin har da uwa uba Saifullahi, in da wani ni'ima da farin ciki ya saukarwa mahaifin Amatullah, ya na mai hamadala cikin ransa. Saifullahi kuwa na shi salatin ba na komai ba ne sai na tsoran masifar da kalaman Amatullah za ta haifa masa. Hannu bisa kirji sai ga Baban Sasa na zubda hawaye, fadi ya ke "Saifullahi ka shayar da ni bakin ciki, bakin cikin da tun da na zo duniya babu wanda ya shayar da ni kwatankwacin shi, Saifullahi ka cuceni ka cuci zumunci!" "Ah ah Amatullah kada ki min haka, kar da ki sanya tazara a tsakanin mu ba zan iya jurewa ba! na yi kuskuran furta saki gare ki, Amma ban fadi iya adadin sakin ba, har ga Allah saki daya na mi ki ba uku ba, Allah ya ga zuciya ta! Dan Allah Baba ku duba lamarin nan" [4/5, 5:49 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS Hawaye bai daina zuba daga idanun Baban Sasa ba yayin da ya ke duban Saifullahi, cikin dashassheyiyar murya ya furta "Saifullahi har ka iya buɗar baki ka furta saki ga Amatullah? Ashe za ka iya sakin Amatullah?" "Kukan nan na ka shi ke ɗaga mana hankali Baba, dan Allah ka sawa zuciyar ka salama ɗan yau ba a biye masa, sai ya kara ma ka ciwo" Cewar Baba Zubairu cikin rarrashi. "Ni kuwa na ke iya masa! Kai waye nan! Hafiz! Hafiz! ya ka nan!" Baba Anas ne ya shiga kwallawa Hafiz Kira, in da ya shigo da saurin sa dama nan soro yayi laɓe ya na jin komai. "Je ka kira min uwar yaron nan!" Ya fada ya na mai nuna Saifullahi da ɗan yatsa. Gaban Saifullahi ne yayi mummunar faɗuwa ganin Hafiz ya fita da sauri, cikin sanyin murya ya ce "Dan Allah Baba...." "Dakata! Ba na so na sake jin ka tanka a nan idan har ba ni na ba ka izini ba!" Jin haka Saifullahi ya sunkyar da kai. Amatullah kuwa burin ta a sallame ta shiga gida ta mike kafa ko ta sami saukin zugin da ciwon da ya ke mata. Jim kaɗan sai ga Hajiya ta shigo da da sallamar ta. Gani yanda aka taru daki, fuskar Baban Sasa fal da hawaye, kuma ciki har da Saifullahi da Amatullah ta sha jinin jikin ta. Bai bari ta iya gaisar da Baban Anas na mai duban Saifullahi ya ce "Zan ma ka tambaya ɗaya, kuma ka bani amsa cikakkiya, saki nawa ka yiwa yarinyar nan?" Daf gaban Hajiya ya yanke ya fadi, ta na mai dafe kirji ta furta "Saki?" Saifullahi na mai sin da kai ya ce "Saki daya na mata Ba.....!" "Wallahi saki uku ya min......!" Amatullah ta yi saurin katse shi. Kallan ta ya ke kallon da ta kasa gane manufar shi. Kai ta kawar gefe cikin halin ko in kula. "Ina ga zai fi a bar shi a sakin ɗaya tun da shi yaro ɗaya ya ce yayi, kuma shi ne gaba da ita" Baba Mahmuda ya ara ya yafa ba tare da ya san dalilin da ta sa Baba Anas ya ke tambaya ne. Baba Anas na mai gyaran murya ya ce "Toh sai fa ku shaida, bisa ga alkawarin da na dauka, ni Anas na saki mata ta.......!" "Inna lillaahi wa inna ilaihi ilaihi rajiun!" Duka dakin su ka hau salati, wanda haka bai hana shi karasawa ba sai da ya dire da "Saki daya kamar yanda Saifullahi ya ce ya saki Amatullah saki daya!" "Inna lillaahi wa inna ilaihi rajiun" Amatullah ce ke na ta salatin akan abu biyu, na farko sakin Hajiya, na biyu kuwa Jin Baba Anas ya yarda saki ɗaya Saifullahi ya mata ba uku ba. Kukan Hajiya ne ya garwaye ɗaki, in da idanun Saifullahi su ka kada su ka yi jajur. "Haba mana Anas! Ya za ka biyewa ɗan yau ka yi wannan danyen aika aika! Ya mu na so mu toshe wani ramin za ka bude wani?!!!!" Cewar Baba Zubairu cikin faɗa faɗa. Baba Salihu mahaifin Amatullah kuwa cewa yayi "Assha! Assha! Assha! Malam Anas ba ka kyauta ba! Saki kuma? Ana zaune shekara da shekaru? Yanzu yaran nan za su sa ka furta saki hakan nan bakatatatan!" "Ban yi dana sani ba! Wallahi da ya amsa ukun ya mata a yau sai na sau tashi uwar saki uku!" Cewar Baba Anas in da maganar ta shi ta soki Hajiya da har lokacin kuka ta ke, da Saifullahi wanda zuciyar shi ke masa Kuna. Baba Sasa wanda kiris ya rage ya hadiyi zuciya dan takaici ya ce "Anas ashe har yanzu akwai sauran ka a rayuwa! Ka dubi tsabar ido na! A gaba na ka furtawa mai dakin ka kalmar saki?" Cike da ladabi Baba Anas ya sunkyar da kai ba tare da ya tankaba. "Toh ina mai ba ka umarni ka mayar da ita ɗakin ta yanzun nan!" Baba Anas na mai dukar da kai, har ran sa ba haka ya so ba ya ce "Na mayar da ita Baba, na mayar da ita, Allah ya huci zuciyar ka" Cikin dakiya da umarni Baban Sasa ya dubi Saifullahi ya ce "Kai ma tun da saki daya ka mata, ina so ka mayar da ita a take kuma ......" Kukan da Amatullah ta saki ne ya dakatar da Baban Sasa, cikin kunar zuciya jin za a mayar da ita gidan Saifullahi ta ce "Ka duba girman Allah Baban Sasa na tuba, ka yafe min, tun da na ke ban taba ma ka musu ba, wallahi babu aure tsakani na da ya Saifullahi, wallahi saki uku ya min....." Nan ta mayar da kallan ta zuwa ga Baban ta, ba ta gushe ba ta cigaba da fad'in "Baba ko ba uku ya min ba, ai aure ya haramta tsakanin mu! Ai ba a zaman aure da zargi! Wallahi cewa yayi ba ɗan shi ba ne,! Ya kira ni mazinaciya! Na rantse da Allan da ya halicce ni ban taba kusantar zina ba bare na kai ga aikatawa! Tun ina budurwa ballanta sanda igiyar aure ke kaina! Da ku mayar da ni gidan Saifullahi gwara kun kai ni kushewata....!" Cike da mamakin kiyayyar da ta ke masa Saifullahi ke kallon ta. Shi kuwa Baban Sasa mamakin yau Amatullah ce ke masa musu haka ya ke yi. In da nauyi da taikaicin Saifullahi ya kara mamaye Baba Anas. Mahaifin Amatullah ne ya runtse idanu ya ce "Yi shiru Amatullah, babu wanda zai kai ki kushewar ki, auren Saifullahi ne daga yau kin gama shi da izinin Allah, na san Baba zai mi ki adalci" Baban Sasa wanda kalaman Baba Salihu na karshe ne su ka ɗaure shi da jijiyoyin sa, duk da kuwa ya ga baƙin Baba Salihu, cikin danne bacin rai ya ce "Tashi ki shiga ciki, zuwa gobe za mu yanke hukunci" Da kyar ta ita tashi, in da ta karbi Emjay daga hannun Baba Mahmuda ta shige ciki ta na takawa da kyar. Hajiya ma Baban Sasa ne ya sallame ta, ta na kukan takaici ta shige gida. Ɗakin kaf idan aka dauke Baba Anas babu wanda bai ga bakin Baba Salihu mahaifin Amatullah ba, ba dan komai ba sai dan furucin da ya yi yana mai kare Amatullah, a na su ya nuna san diyar shi karara bai yi kara ba. Baban Sasa wanda ya fi kowa jin zafin Baba Salihu ne ya ce "Toh kai Saifullahi ka dai ji abin da yarinya ta ce, ka kuma ji hukuncin da uban ta ya yanke, ba ka kyauta min ba, duk yanda na so na haɗa wannan zumuncin, a yau an ruguza shi, dan haka sai ka sa a ran ka aure tsakanin ka da Amatullah ya kare....." Wani irin yanayi mai kama da tashin hankali da bakin ciki na babu gaira babu dalili ne ya lullube shi, a da yayi zaton rabuwa da Amatullah zai zama tamkar an ɗauke masa dutse mai nauyi daga kan kirjin sa, ga mamakin sa sai gashi ya ji sabanin haka "Baban Sasa a duba ......" "Ka yiwa mutane shiru!" Baba Zubairu ya dakatar da shi. Baban Sasa bai gushe ba ya cigaba da faɗin "Bayan wannan danyan aikin da ka aikata ga yar uwar ka jinin ka, ka sani wasi wasi shin za ka iya ruke gidan ka kuwa? Wannan auren na ka da za a yi nan da wata biyu shin ba wani zanin za ka kwance mana a kasuwa ba?" Cikin kaduwa bai san sanda ya furta "Na yi kuskure Baban Sasa, a gafarce ni kar ka hana ni auren nan!" "Aure babu mai hana ka, mu ɗin ba kanana mutane ba ne ko sakarkaru kamar ka! Duk abin da ya faru har da laifin mu, da mu ka yi sake mu ka bari ka bar gaban mu, ka tafi can uwa duniya ka ci karen ka ba babbaka, da ka na gaban mu duk abubun nan da su ka faru da ba su faru ba! Wancan dakuna biyu na kusa da bangaran mahaifiyar ka, in da ta ke kiwon kaji nan na ke so ka gyara ka saka matar ta ka ciki" "Allahumma ajirni fi masibati!" Cewar Saifullahi ya na mai goge zufa. Ya kara da "Afuwa Baban Sasa, wallahi wancan gidan kiris ya rage a gama gyarawa....." "Ba dai gida na ba ne? Na karɓe kaya na! Haka wanda tsohuwar mata ke ciki a da, kudin da ka kashe wajan gyara ka lissafa min zan biya ka in ya so ka gyara dakunan da shi. Yanda iyayen ka ke zaune cikin gidan nan haka kai ma za ka zauna da mu!" Baban Sasa ya karasa maganar cikin jaddadawa. Shi kuwa tunanin yanda za a yi mace kamar Ayush yar gayu diyar masu kudi ya iya zama gidan nan na su babban damuwarsa. Wani Sabon zufa ne ya sake karyo masa, bai san sanda ya ya ja rigar sa ya shiga gogewa da shi ba. Babu wanda ya kula shi, a haka suka watse taro zuciyar kowa babu daɗi. *** Cikin wani irin yanayi Amatullah ta shiga ɗakin mahaifiyarta wanda Hafiz ya gama feshe musu mummunar labarin sakin Amatullah. Tafiyar ta Goggo Mairo ke kallo cike da tsusayawa, so take ta rungume ƴarta ta lallashe ta amma kawaicin da aka tayar da ita ana ma ƴan fari ya sa ba za ta iya hakan ba. Siddiƙa ce ta tashi ta amshi Emjay a hannun yayarta, kallon yaron take cike da ƙauna da soyayya. "idanunki kenan? Shi kenan son miji da boko su rufe miki ido, ko yawon Arba'in ki gagara yi" Goggo ta ɓige da faɗa ba tare da nuna ta san wani abin ya faru ba. Murmushi Amatullah ta yi don ta daɗe da sanin salon soyayyar Goggo gareta kenan yi mata faɗa da basar da ita. "Goggo yanzu ai komi ya zo ƙarshe, zan zauna nan babu mai hana mini zuwa ganinki" tace cikin danne kukan da ke neman zuwa mata. Sai da idon ta ya sauka akan Goggo sannan ta ji ɗacin sakin da aka mata. Tsawon zaman ta a gidansu babu ƴa macen da ta taɓa yin aure ta fito a dalilin saki, sai gashi ta zama farau a gidan. "Assalamu Alaikum! Ina Amatullah ɗin take" Hajiya Zainab matar Baba Hamza da yaran gidan ke kira da Mama ce ta shigo cike da tashin hankali. Rungume Amatullah ta yi tsam cike da hawaye ta ce "Bamu kyauta miki ba Amatullah, wallahi bamu kyauta ba, muna mata muka shashantar da ke a lokacin da kika fi buƙatar mu, kaico!" tace tana share hawaye da gefen zanenta. "Yanzu Babansu ke faɗa min, sakin bai min zafi ba kamar ɗinkinta da aka ce sai da aka sabonta Mairo ki duba ko sabo ya mutum ke yi balle a ce sai an kankare wajen kafin nan fa" tace tana magana cikin tausayawa da jinkai ga Amatullah. Zama su ka yi nan Amatullah kamar wacce aka buɗe ma baki ta shiga faɗin abubuwan da ta fuskanta na cin kashi a gidan Saifullah daga lokacin da ya ce ta je a cire cikin. "Kin ga ni ba, barewa zai yi gudu ne ɗansa yai rarrafe, ai duk abin da ya fito daga tsatson Sadiya zai aikata fin haka don an samu ma Baba Anas na ɗan sirka su da halin kwarai" Mama ta faɗi cikin takaici. Duk wanda ke gidan ya san yar tsamar da ke tsakanin Hajiya da Mama. Tare a ka yi aurensu kasancewar mazajensu sa'annin juna ne, Mama yar gidan matawallen Zazzau ce ta wancan lokacin saboda haka garanta da jerenta ya sha bambam da na Hajiya, ba'a shafe shekara ba hajiya ta siyar da nata tas, ta sa irin na mama hatta kala ɗaya, bayan sun haifi yaya uku Matawalle ya biya ma Baba Hamza da Mama aikin haji su ka je su ka dawo, tun kafin su dawo Hajiya ta sa yaranta su koma kiranta Hajiya ba innarmu da suke cewa ba. Kasancewar Mama ta iya faɗin gaskiya ya sa mafi yawan matan gidan ke tare da Hajiya a ƙulla sharri a kwance a alkhairi. Shekara na zagayowa Hajiya ta siyar da gidan gadon ta ta biya kujerar haji itama ta dawo liƙe da haƙorinta biyu a Saman dasashi. Bayan auren Baba Salihu da Goggo Mairo da irin ladabin da take ma surukanta da kula da su da ya sanya su ka so ta fiye da saura, duk matan gidan sun tsane ta in ka cire tsirarunsu kamar su Mama. Ita kuma mama ba ta girkin gaba ɗaya, bata wani shiga taron facaloli hakan ya san ba kasafai ake ganin ta cikinsu ba. Ita ce kaɗai sasanta ke kewaye a gefe, duk da ta aurar da duk yaranta mata hakan bai sa ta nema a cikin gida ba. "Kinga Sasarmu za ki koma, duk mai son ganinki ya biyo ki, sabon jego za mu fara" tace tana mai ɗaukan Emjay ta fice don ta san Amatullah na da bukatar ganawa da iyayenta. Sosai Goggo Mairo ta ji sanyi a ranta, don tun da Hafiz ya faɗi mata take tunanin yanda za ta yi, duk da a lokacin ta sadakar za ta zaƙe ta kula da ƴarta. Bayan shigowar Baba Salihu ya iske su jigum jigum kamar ma su makoki ne Goggo kefaɗi masa yanda su ka yi da Mama. "Ke ba za ki iya kula da ƴar ki bane Maryam" ya tambaya yana mai tsare ta da ido. Sunkuyar da kai tayi tace "Ka dai san zuciyar Hajiya Zainab mai kyau ce, ina laifi ta fitar da ni tsaka mai wuya. Yar fari ce fa Babansu" ta ƙarasa tana rausayar da kai gefe. "ƴar fari ko? Sannu mai ƴar fari, al'adar da ta sa kika kasa gane ukubar da ƴar ki ke ciki, ba damuwa kije Amatullah, amma ko kallon banza ta miki ki dawo kina da ɗakin uba, Nima zan maida hankali mu koma ginina, na gaji da wannan koma bayan gidan gandun nan" yace yana jan tsaki. Tare duk su ka ci abinci kafin saddika ta raka ta sashin Mama, inda su ka iske ta ware mata ɗaki ɗaya, ta sa ma ɗakin rushi kamshi na tashi daga ɗakin, ga makewayi maƙale da ɗakin. "InshaAllah gobe mai hidimar ki za ta iso daga gidanmu tun da ba zan iya wahalar ɗaura ruwa" mama tace cike da ƙauna. Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Amatullah, jin kaunar mama na ratsa take, nan ta tabbatar lallai ko me ɗan Adam ke yi yana da dalili. Ta san dai Mama bata nan aka yi rikicin auren su amma da ta dawo ko sau ɗaya bata taka gidansu ba. Kenan da ta ɗauki zafi da ta sha kunya. *** Jumma'a na zuwa Baba Anas da kanshi ya tuƙa ta zuwa zana test ɗin da za su yi, ta matsu ta ga Mimi ko don ta gode mata, lokacin da mahaifinta ke faɗa mata ƙoƙarin da Mimi ta yi ba ƙaramin jinjinawa soyayyarta da amanarta ta yi ba. "Sai a ce Ahlil Kitaab ba masoya bane" ta faɗi a ranta, duk da ta san ba za ka saki ɗan uwanka musulmi ka riƙe su ba amma tabbas annabi ya zauna da su cikin zama na amana da jin ƙai, tana mamakin musulmi mai taƙamar koyi da karantarwar Manzon tsira SAW amma ya zama mai rashin kyautata mu'amala da wainda ba musulmi ba. Tara da minti ashirin su ka isa Faculty of pharmaceutical sciences inda za su yi test ɗin da ƙarfe goma. "Nagode Baba Allah ya ƙara girma da ɗaukaka" tace cikin jin nauyi da farin ciki. "zan jira ki kammala sai mu wuce inshaAllah, Allah ya bada sa'a" yace mata yayin da take ficewa da ga motar. Tun bayan hargitsin sakin ta wani girmansa da ƙaunarsa ya ƙaru a zuciyar ta. Tabbas Baba Anas ya kasance cikin mutane ƙalilan masu ƙin nasu su so gaskiya, sannan ya kasance mutum mai riƙo da igiyar zumunta, har abada ba za ta daina gode ma Allah da ya yi Baba Anas ya kasance kaka ga gudan jinin ta. Rungume Mimi ta yi tsam da su ka haɗu har wasu yan ajin na masu tsiyan kwana ɗaya kawai da ba su haɗu ba. Dariya kawai su ka yi amma ita Mimi kanta ta hango soyayya da kaunar ta mai matsanancin yawa a idanun Amatullah. Hannun ta taja su ka zauna a kujera, "Na gode Mimi, Ubangiji Allah ya baki Alkhairin duniya da lahira" Amatullah ta faɗi cikin nuna alamun ƙarancin kalaman da za su bayyana godiyarta. Amma tun ranar ta ke ma Mimi addu'ar jinkai da samun rabon imani. "Common Maman Emjay, what are friends for" ta faɗi mata cike da ƙauna. A takaice Amatullah ta faɗi mata halin da ake ciki wanda hakan ba ƙaramin faranta ran Mimi yayi ba. Daga nan su ka duƙufa bitar karatu, har zuwa shigowar malamin. Ba za su ce ya musu sauƙi amma kam sun ji dadin sa sosai, don Allah ya basu sa'ar amsa duka don haka sun fito suna gode ma Allah. "Abuja zan je mid semester tare da Dee. In na ce in je Yola yanzu wahala zan yi" Mimi ta ce mata sa'ilin da su ke sallama. "Allah ya kaiku lafiya, ki masa godiya don Allah" tace cikin sanyin jiki. "Ki sani fa maman Emjay, babu wanda zai so ki sama da ke kan ki, sannan babu wanda zai wahala in kika yi sakaci da kanki sama da ke kanki. Duniya wani na tayaka son ka ne, sannan waninka iyaka ya yi imagining pains ɗin da kake ciki amma kai ke da wahala. Use this break wisely, breakups should not crash us, they are meant to make us stronger" Mimi ta ce mata tana riƙe da hannunta. Tare su ka fito Facultyn, har zuwa inda Baba Anas ya ke jiranta, nan Mimi ta gaida shi cike da ladabi suka yi sallama su ka wuce. [4/13, 8:29 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA ASHIRIN DA TARA "Abuja zan je mid semester tare da Dee. In na ce in je Yola yanzu wahala zan yi" Maganar da ke ta shawagi cikin zuciyar ta kenan. 'Shin bayan dangantakar jini akwai dangantakar zuci tsakanin Dee da Mimi ne? Kamar dai akwai, toh idan ma akwai ni tawa a wa? Ko ba komai ai addini ya riga yayi tazara a tsakanin mu.. .. ' Da wannan muhawarar cikin ran ta su ka isa gida. Godiya ta yiwa Baba Anas sannan ta shiga ta gaida Baban Sasa wanda har lokacin ya na da burin komawar ta gidan Saifullahi. Gwaggo kuwa gaisuwa ke haɗa ta da Amatullah, da ta gaishe ta ɓangaran uwar jinyarta ta ke wucewa. Ba ƙaramin kula da gyara ta ke samu wajan Mama ba, duk ta na ji a jikin ta dan kuwa in dai wajen gyara ne Mama ba ta tausaya mata. Yau ɗin ma gaishe da Gwaggo ta yi in da ta aje mata Emjay kafin ta wuce wajen Mama. Ferfesun naman rago mai romo da kunun gyada Mama ta ajiye mata, Sai da ta tabbatar ta ci da shanye roman tas sannan ta ce maza ta shirya ta zo ta zauna ruwa mai dan zafi da ta tanadar mata domin a samu ɗinkin ya fara haɗe kan sa. Saifullahi a na shi bangaran tun bayan da Amatullah bar gidan sa gaba ɗaya gidan ya daina masa daɗi, wani sa'in ma kukan Emjay har gizo ya ke masa a kunne. Tsananin yanda ya ke kewar su ya sanya ya ke Allah Allah ranar auren sa da Ayush ya zo, kila idan ya ga masoyiyar ta shi kusa da shi ya manta da batun Amatullah. Toh amma sharaɗin da Baban Sasa ya yanke ba ƙaramin damuwa ya ƙara masa ba, kullum da tunanin yanda zai bulluwa lamarin ya ke kwana ya ke tashi har dai ya yanke hukuncin tunkarar Ayush da maganar a yi ta takare ko zai sami sauki cikin ran sa. Sati biyu kenan da yanke ɗanyen hukuncin dole ya ajiye ta a gidan wanda yayi daidai da saura sati shida ɗaurin auren su. Shiryawa yayi asubar fari ya nufi hanyar Kano. Kallo ɗaya za a gano tsananin damuwar da ya ke ciki, duk yanda ya so ya ɓullo ma Ayush da zancen ya kasa ga bikin sai matsowa yake yi. Kamar ko yaushe tarbo ya samu cike da maƙulashe, Ayush ta cika shi da kwalliyan ta mai rikita shi, ga ƙamshin da ke fita daga jikinta na ƙara narkashi duk da ba su yi tasirin cire masa firgicin da ke ransa ba. Hira su ke jefi - jefi yana mai kara bayyana mata sirrin zuciyar sa da kuma tarin burikan da yake da na rayuwar auren su. Sai da ya gama samun ta, ya tabbatar da ta gama natsuwa da Kalamansa haɗe da yarda da dacen da tayi na samun sa a matsayin miji sannan ya ce "Aisha...." Har cikin ranta ta ji muryar ta shi musammam yanda ya kira ainihin sunan ta, kallon shi ta ke ba tare da ta amsa ba, ganin haka ya cigaba da faɗin "Ban san yanda zan mi ki bayani ki gane ba, amma zan yi iyakar kokari na, kuma kin san dai ba zan taɓa cutar da ke ba ko?" Ayush da gaban ta ya fara faɗuwa ta ɗan gyara zama sannan ta ce "Ina Jin ka, Baban Sasa ya ce ba za ka aure ni ba ne?" Kai ya girgiza ya na mai mamakin yanda ta kama sunan Baban Sasa haka, ya ce "Ya sallam! Ko kusa! Me zai sa ki yi tunanin haka?" Cikin yatsine ta ce "Toh ai yanda na ga ka na ba da labarin kakan na ka ne ai komai mai ma zai iya faruwa, bare kuma ka ce shi ya aura maka matar ka" "Auren ya mutu....." "Sorry?" Ayush ta faɗa domin son Jin ya sake maimaitawa, dan gudun kar dai kunen ta ke zagi. Shi kuwa Saifullahi ya girgiza kai sannan ya kara da "Na sake ta" "Ka sake ta fa ka ce? Saboda me ya sa? Kar dai saboda auren mu ne?" Cewar ta, ta na mai fatan hakan ne, shi kuwa Saifullahi nan ya sami hujjar da zai fake, ya tsinci kan sa ya na faɗin "Na so jurewa na haɗa ku ba don komai ba, sai dan biyayyan iyaye, Allah na gani yanda na ke kaunar ki ban ji zan iya adalci tsakanin ku ba, saboda haka sai na sauwake mata" Wani irin daɗi da annushuwa ne ya mamaye Aysuh duk da kuwa ta so ta ɓoye shi, amma hakan ya gagara. Ta na mai danna fara'a ta ce "Ayya Honey pie ai da ka barta, ko dan gujewar fushin su Baban Sasa" Ta tabuwa Saifullahi in da ya ke masa kaikayi, ya na mai share zufa ya ce "San ki da na ke ya sa idanuna rufewa Ayush, yanzu haka ina kan fuskantar fushin na su, saboda na saki yarinyar nan yanzu sun ce a lalle sai dai mu zauna cikin family house din mu......" "Allah ya sauwake na zauna gidan gandu in yamutse se kace dambu!" Ayush ta katse shi cikin tsawa, ta kara da "Ka san me ka ke faɗa kuwa Saif? Kamar ni? Ni Ayush ka ce na zauna family house din ku? Dama hakan nan zaman family house masifa ne bare kuma a ce ka saki cousin ɗin ka saboda ni? Na zauna a kuntata min kenan? Wallahi ba ka isa ba! Ko dai ka aje ni gidan da ka ce ka gyara min, wanda shi ma din ka san is not up to my standard, ko kuwa a fasa auren nan!" Ta kare maganar cike da tsiwa. Jikin Saifullahi yayi sanyi hankali tashe jin Aysuh na batun fasa aure "Ayush kar ki min haka, ki rufa min asiri ba zan iya rayuwa babu ke ba, ba kuma zan iya bijirewa maganar iyaye na ba, ki tuna fa kasa jure soyayyar ki ya sanya na saki Amatullah, su kuma dan su kuntata min ya sa suka bijiro da wannan hukunci....." "Malam ni ina ruwa na! Ba zan zauna family hause ba!" Ayush ta kara jadadda masa. Juyin duniya da rarrashi babu wanda Saifullahi be yi ba, Amma ta ki. Ranar haka su ka rabu kowa babu dadi. **** Tun bayan tafiyar Saifullahi ta shiga tsaka mai wuya, gashi ba ta san jama'ar gidan su san halin da ta ke ciki dan tabbas su ka sani aure tsakanin ta da Saifullahi ba mai yiyuwa ba ne. Da zaman gidan ya ishe ta mayafi ta saka in da ta neme izini gurin mahaifiyar ta, ta figi motar ta kirar honda, ba ta zame ko ina ba sai gidan su kawar ta Sameera da ke hotoro GRA. Ba ta boyewa Sameera ko mai ba dan kuwa abokin kuka ba a boye masa mutuwa. Jiki sanyaye Sameera ta ce "Ayush kin san duk wannan abin na su ba dan komai ba ne sai dan su hana auren nan na ku, kuma gashi kin sa burin su zai cika!" Ayush na share kwalla ta ce "Ya ki ko so na yi Sameera? Kin fa san muddin aka ji wannan maganar a gida ba za su bari a yi auren nan ba!" "Idan har ki ka tsaya tsayin daka walllahi dole su hakura, Saifullahi na san ki fa Ayush! Maza da idan su ka ce an aura mu su cousin shikenan tsakanin ku, Amma shi ya rike alkawari har ya saki matar shi saboda ke? Ai ke ma kin san dole akwai consequences ai, bai kamata ki juya masa baya ba Ayush" Cewar Sameera. Shiru Ayush ta yi cikin nazari kafin ta ce "Yanzu haka zan zauna na haihu gidan gandu?" Sameera na girgiza kai ta ce "Kash wa ya ce mi ki zuwa za ki yi ki haihu? Ai idan kin ga kin haihu da Saifullahi to kun tashi daga gidan nan Ayush, inaaaa ko ni ba zan yarda ki haihu ba, emergency contraceptives pills za ki sha, within 72 hours za ki sha idan wani abu ya faru tsakanin ku you know, amma ya fi aiki idan ki ka sha immediately after sex, shi ne zai lalata kwaiyoyin sinadarin haihuwa da su ka shiga cikin, ya hana su developing zuwa kwayoyin halitta" Cikin farin ciki Ayush ta ce "Dadi na da ke Sameera sanin duniya wallahi! Ai shikenan zan bi shawarar ki, zan faɗa ma sa na hakura zan yi zaman shekara ɗaya family house din na su, Amma fa ki samo min pills din nan, kin ga dai sati shida ya rage" "Kar ki ji komai mata a gidan Saifullahi, kuma wallahi kar ki saurara mu su in dai ki ka shiga family house ɗin nan, yanda su ka mi ki rama, musammam wannan tsohuwar matar ta shi da ya ke kira bagidajiya!" Su ka yi shewa su ka tafa. Nan Sameera ta cigaba da kimtsa mata yanda za ta yi gidan auren ta. Ita kuwa Ayush ta na mai maraba da gangar shaidan ɗin da Sameera ke buga mata. Daren ranar ta shaidawa Saifullahi amincewar ta na zama gidan su. Duk da yayi mamakin yanda ta canza ra'ayi cikin kankanin lokaci amma ya kasa tambayar ta dalili. Soyayyar su suka cigaba cikin jin dadi. **** Da yardar Allah da kuma taimakon kula da Amatullah ke samu wajan Mama jikin ta yayi kyau sosai. Har aka gama mid semester break ba ta iya daga waya ta kira Mimi ba sai dai Mimi ta kira ta, wai a nata kar ta kira Mimi ta na tare da Dee Yusuf. Duk yanda ta so ta yaki zuciyar ta akan wani abu mai kama da kishi da ke taso mata duk sanda tunanin dangantar da ke tsakanin Dee da Mimi ya zo mata. Fatan ta dai Allah ya sa ba abin da take tunani ba ne, saboda tazarar da ke tsakanin ta da Dee Yusuf bai hana ta kishin sa ba. Amatullah ba ta sami damar komawa makaranta ba satin da aka koma saboda yanda Mama ta dage lalle sai ta zauna a gida ta murmure, dan haka Mimi ce ke mata attendance da assignment har satin nan ya kare. Dangane da Saifullahi kuwa ta yi kokarin cire shi daga zuciyar ta duk da dai hakan ya ci tura saboda Emjay. Zaman taka tsantsan take yi a gidan gudun kar Allah ya hada ta da shi, ko yara sun bi da Emjayi ta bangaran Hajiya sai ta koro su, haka kuma ba ta fasa yaɗawa Amatullah da Gwaggo habaici ba musammam da ta ga auren Saifullahi ya taho gangaganga, komai na tafiya yanda ta ke so. Mimi kuma tun ranar da auren Amatullah ya mutu sanadiyar Dee Yusuf ta ke addabar shi da maganar Amatullah. Tun ya na share ta har ya mata alkawarin ta same shi office ɗin sa bayan ta gama lecture zai fada mata abin da ta ke son ji. Ana gama lecture din ta yiwa Amatullah waya, in da take shaida mata suna da test gobe in za ta iya ta samu ta shigo. Bayan sun gama waya ta wuce department din su Dee. Cikin office din na sa ta tarar da shi, sanye ya ke cikin farin yadi dinkin jamfa ya masa kyau na kwaran gaske. Ganin Mimi ta shigo sanye cikin hijabi da ya tsaya mata iya gwiwa ya na murmushi ya ce "Zama da madaukin kanwa, so Amatullah ce ta koya mi ki sa hijabi haka Mimi?" Ita ma din murmushi ta ke in da ta zauna kujerar da ke kallan ta sa tare da faɗin "Ban son sharri fa Dee, dama tun kafin na san Amatullah din ta ka na ke ɗan sa hijabi na" "Amatullah dina? Kin ba ni ita ne?" Cewar Dee ya na mai sosa kyeya "Do you still love her? Do you have feelings for her?" Kai ya girgiza, ya bata amsa "It doesn't matter how I feel about her Mimi, she can never be mine....." "But y? Ba dai saboda ta yi aure ba ne? Ai ya sake ta! I'm sure dan ta taɓa aure ba zai zama dalilin da za ka guje ta ba" Cewar Mimi cikin nuna rashin fahimtar Dee Yusuf. Kallon ta ya ke kafin daga bisa ya ce "Mimi ba za ki gane ba" "Try me" "Owk, iyayen ta ba za su taɓa bani auren ta ba, ba sa san tsatson da na fito daga ciki" "But Dee ai ya wuce, da ne, y not try your luck again? I mean everything has changed..." "Nope, not everything Mimi, expecially my background Mimi....wanda bai so ka da kwana ba ba zai so ka da wuni ba" Shiru ne ya biyu baya, kafin daga bisani Mimi ta ce "Idan ita kuma ta na son ka fa?" Kafaɗa Dee ya daga ya sauke, sannan ya ce "I love her too, babu yanda zan yi Mimi" Cike da farin ciki ta ce "Akwai yanda za ka yi, ka ga yanzu ta na idda ne ko me suke kiran waiting period ɗinsu, last time da ta ke min bayani ta ce min until then ba za ta iya kula kowa ba, so you have enough time, ka shirya yanda za ka sace zuciyar ta da na iyayen ta, Amatullah ta sha wahala a rayuwar ta na aure, in ba haka ba you will end up with me, you know I love you right?" Dariya mai fitar da sauti ya ke yi jin furucin Mimi na karshe, ya daɗe da sanin Mimi ta na son shi, amma hukuncin addinin christain na hana auren cousin ne yayi tazara a tsakanin su, har ita da kan ta ta yi wa kanta gata ta yi watsi da wannan lamarin, abin mamaki sai gashi yau ita ce ke kokarin daidai ta shi da Amatullah. Cike da fara'a ya ce "Allah ya baki miji wanda ba zai ga laifin ki ba Mama na, yanda ki ka ce din shi zan yi, I don't want to end up with beautiful Mimi, ba zan iya faɗa da samari ba" "Kaii Dee!" Dukan su dariya su ke cike da jin dadi su ka cigaba da hira. *** Kwanci tashi asarar mai rai, duk wani shirye shirye da ke gaban Saifullahi ya yi kokarin saukewa, ya gyara in da Baban Sasa ya umurce shi da tarewa, wanda hakan sai da ya kai shi ga cin bashin banki don ya gyara ginin da zata ji dadin zama. Ranar da za a kai lefe ya kama ranar asabar, Amatullah ta yi rashin sa'a ta na gida, ta so fita ta bar mu su gidan amma Gwaggo ta hana. Guɗa da habaici babu wanda Amatullah ba ta ji ba daga dangin Hajiya. Gwaggo da Amatullah na zaune a falo sai gashi an fara shigo da akwatuna ana ajewa gaban ta, da ta tambaya daga ina, kanwar Hajiya ta ce "Abin arziki Hajiya ta ce a kawo ki gani, kayan lefan Saifullahi ne, Allah yayi" Ta karasa maganar ta ba mai rangwaɗa guɗa. Kallon Amatullah Gwaggo ta shiga yi, wanda idanun ta sun ɗan ciko da kwalla tsabagen takaicin zaman da Gwaggo ta sa ta yi a gidan. Daki ta tashi ta shige ta tarar da Emjay na shan baccin sa, ita ma ɗin kusa da shi ta kwanta, hannun ta bisa jikin sa yayinda ta shiga karanto adduoin samun kwanciyar hankali. Gwaggo kuwa biye mu su ta yi, aka bude kaya da ita, ta na mai sanya albarka ba tare da ta kula da habaicin da ake yada mu su ba, dan kuwa ta san kawo kayan bagaran ta ma da biyu aka yi. ***** Ana saura sati ɗaya biki, yana shirin tarewa a Kano saboda bukukuwan da za su yi mahaifin sa ya kira shi. "Ango ka sha miya, amma na ga ka manta da wajibi kana ta ɓarin kudi a wanda ke shirin zama wajibi" yace cikin sakin fuska. Zai iya rantsewa tun bayan sakin Amatullah bai ga fuskar mahaifinsa a sake ba, sai ranar. Kallon sa yake cikin rashin sani. "Yarinyar nan Amatullah ka manta tana cikin idda ne, ko ka manta har yanzu cinta da shan ta yana wuyanka, bana ko zancen Babana don kace ba naka bane, amma kam yanzu ka ciro kuɗi ka bani na abincin Amatullah, kuma bana son harkan ƙaranta" mahaifinsa ya faɗi cikin dakewa. Gaba ɗaya kan Saifullah ya kwance, ita da ake maganar akanta tun daren nan bai sake ɗaura ido akanta ba, ba zai iya tantance tana gidan ko bata ba, ya san ya kan shiga ɗakin iyayenta ya gaida su amma ko Emjay bai sake kuskuren gani ba. Aljihunsa babu komi sai kudin da ya je ya canzo bandir ɗin yan hamsin hamsin, kallon mahaifin sa yayi yana mai sunkiyar da kai ya ce "Baba da za a min haƙuri na gama wannan hidiman zan bada" yace cikin muryar neman ɗauki. "A'a fa Saifullah, ba zamu yi haka da kai ba, duk wata dubu hamsin zaka bata har ta gama idda, yanzu dai bani nan in ga" yace yana miƙa hannu. Gaba ɗaya kudin Aljihunsa dubu hamsin da biyar ne, su kaɗai su ka rage masa gaban sa da bayansa. "Baba..." "A'a fa engineer, miƙo kawai ga kuɗi nan ina hange a aljihunka" Cikin sanyin jiki Saifullah ya ciro sabbin kuɗin da ya yi niyyar zuwa yayi liƙi da su, ji yake kamar ya ɗaura hannu a kai ya dinga kuka don gaba ɗaya Baba Anas ya shiryi tona masa asiri. "Madalla, Allah sa a watse taro lafiya" Baba Anas ya fadi tare da jingina sosai a kujerar da yake zaune, zuciyarsa ƙal da farin ciki. Ya san ya katse masa da Hajiyarsa wani yanki na jin daɗi, sarai ɗazu ya ke jin tana faɗi cikin fariya Saifullah ya je ya canzo kuɗi, da yanda za ayi liƙi kada dangin Ayush su raina su. Dariya Baba Anas yayi, yana jin ko a haka ya barsu ya rage wani sashi na takaicin su da yake ji. A ranar Baba Anas ya damkawa Amatullah kudin, in da ta ce dan Allah ya taya ta neman izinin Gwaggo ta koma makaranta tun da exam za su fara, yanayin taro na biki ba zai bari ta sami nutsuwan karatu ba. Hakan kuwa aka yi, da sa bakin Baba Anas ta hade dan kayan ta da na Emjay cikin farin ciki ta yiwa Mimi magana. Gidan dalibai da Mimi ke zaune ta koma, dake gida ne irin na dalibai 'ya'yan manya, gidan yayi kyau ba laifi. Nan Mimi ta bata ɗaki ɗaya, ta na murna lalle Dee zai yi alfahari da ita. *** Washe gari yan danki su ka iso, motocin ɗaukan kaya biyu su ka zo da shi cike da kaya, duk da iyayenta sun rage yawan kayan a dalilin faɗin Saifu na zamanta gidan Jamoh. Ta kofar kuyanbana su ka shigo tare da tahowa kamar za su fita gari su ka shigo ta ƙofar kona. "Kai cikin kuttu za ta zauna dama" faɗin ƙanwar mahaifin Ayush da ta san kan zaria sosai. Yanayin da ta faɗi cike da takaici ne da jin alamun kaskanci ga zuriar su. Shiru matan wajen su ka yi suna mai kallon yanayin anguwar, gidajen gandu ne mafi akasari sai sabbin gine-gine ɗaiɗaiku. Gaba ɗaya bakunan su kamar an ɗinke duk da dama ba wai zuga su ka yi ba, kannen mahaifinta ne guda uku tare da yar mahaifiyarta da kannen mahaifiyarta biyu. Hajiya Haske kuwa da ta san ƙanin mijinta mai kuɗi da gadon kuɗi ya so Ayush amma na nace ma Saifullah bata san lokacin da ta ja tsaki ba sa'ilin da motar ta tsaya a kofar gidan Jamoh. Gini ne na da amma da gani ya sha gyara, tambari alamun gidan sarauta liƙe a ƙofar gidan nasu. Kallon makotan gidan su ka yi sai su ka ga sabbin gine-gine masu kalar zamani uku ne kuma duk ba a kammala ba. "Marhabin sannunku da zuwa" Habiba matar Baba Mahmuda ta faɗi tana mai musu iso.. Turkewa su ka yi a ƙofar gida ba tare da alamun niyyar shiga ba, sai da ta sake faɗin "Hajiya bismillahnku ai sasan su na da ga ciki ne" tace kamar zata musu sujjada saboda ladabi ganin kallo ɗaya ta musu ta gane sun tsumu da Naira. "Anty wai har dankin a family house za ayi" hajiya haske da ta kasa hakuri ta ɗaga waya ta kira yayarta ce ta faɗi cikin tsananin ɓacin rai. Hakuri ta ba ta daga can ɓangaren tana mai nanata ai ƴar su ce ta ja musu wannan kaskancin. Hakan ya sanya su ka shiga ciki ba tare da ba da umurnin a sauke komi ba na kayan. "Don Allah muna son a mana iso wajen babba a gidan nan" faɗin Hajiya Jamila kanwar mahaifin Ayush. Kallon ta Habiba ta yi sannan ta aika a faɗi ma Baban Sasa kafin su isa, cikin ikon Allah Baba zubairu da Baba Anas na nan a wajen sai su ka ce a faɗi masu su shigo. Ƙatuwar dardumarsa mai cike da ƙamshi aka shimfiɗa musu, ko da su ka shigo sun iske ɗakin bai rasa komi na nagarta ba sai kuɗi amma su ka tsunga kamar masu kyamar ɗakin. Sun gaida Baban Sasa babu yabo balle fallasa a nan ne Hajiya Jamila tace "Sunana Hajiya Jamila, ina aure da aiki a birnin California, ni ƙanwar mahaifin Ayush ce, mun zo jere ne Baba amma Sam ba mu ga muhallin da za a sa kayan da mu ka zo da ita ba, balle har mu ce zamu ajiye ɗiyarmu a ciki" tace tana mai yatsina fuska, saura su ka amsa da Aikam dai. Baba Anas har zai magantu sai Baban Sasa ya hana masa, kallonsu yake yana raya a ransa har za su nuna ma bazazzage jin kai, bazazzagen ma Bamalle. Murmushi yayi yace "MaashaAllah! Allah ya ma rayuwa Allah, ai Muhalli nagarta da soyayya ke samar da ita ba kuɗi ko Nasaba ba. Ga ɗakuna can da mijin Ayush zai iya affording, if she really love him, she will be ever happy to live in it" turancin da ya ƙarasa maganarsa da ita ya sanyaya masu guiwa, saboda turanci ne irin na sarauniyar Ingila, duk a tunaninsu bai taɓa zuwa aji ba dole jin California ya San ba ƙaramar yarinya za a kawo ahlinsa ba. Jiki a sanyaye Hajiya haske ta ce "Baba ba mun raina bane, ganin kayan daidai wancan ginin da Saifullah ya nuna ne, garanta kaɗai ma ya isa ya ɗauke duka ɗakunan komi ashirin da huɗu ne" Tace cikin sanyin murya da fariya. Dariya Baban Sasa yayi ya ce "Ana iya siyarwa a ba amarya ta ja jari, tunda dai kun ga irin gidan da ta shigo" bai sake faɗin komi ba su ma suka ɗan ƙara zama na yan mintuna su ka miƙe. Daidai gwargwado Saif ya zuba kayan zamani sasan, ɗakuna biyu ne da kitchen da store da bayuka a kowane ɗaki. Nan dai suka shirya kayan da suka iya shiga ciki, sosai waje yayi kyau amma sun ji takaici da kayansu da dama basu samu waje ba. Motar ta da suka zo mata da ita su ka ajiye a wajen adana motoci duk da dai ba an tanadar da wajen don haka bane amma ahlin gidan anan su ke ajiyewa. Ko da suka shiga sashin su Hajiya, sakin maganganu kawai su ka dinga yi, matan gida aka samu chapter badawa. *** Bukukuwa sosai na gani na faɗa aka yi a ɓangaren su Ayush. Ango da Amarya sun yi kyau sosai, yan mujallu sun hallara sun ɗauki hotuna a duk wani event da aka yi. Faɗin farin cikin da ma'auratan su ka shiga ba zai misaltu ba. Ranar Lahadi da ƙarfe tara da rabi na safe aka ɗaura auren Saifullah da Aisha, ɗumbin masu kudin Nijeriya da kasashen da ake maƙotaka duk sun halarta. Bayan ɗaurin Aure aka ɗauko zuga zuwa gidan Amarya. Tafiyar Awa uku ya kawo su gidan Jamoh tun daga ƙofar gidan mahaifin Ayush, nan ma yan uwanta da kawayenta su ka shiga yaɓa magana. Duk kokarin Ahlin gidan Jamoh bai birge su ba, suna miƙa ta suka nemi hanyar tafiya, faɗi suke "Allah ya baki ladan zaman talauci, gida a ƙuntace, ina aka samu wajen zama a wajen nan balle ki miƙa ƙafa" haka suka dinga faɗi har su ka fuce su ka barta cikin ƙunci. Kamar yanda su ka tsara da Saifu ana jibi biki cewa kwana bakwai na amarcin su a hotel za su yi Don ba za su iya da takuran gidan gandu ba. Ana idar da isha'i su ka fice daga gidan, ba su tsaya ko ina ba sai cikin GRA inda ya kama musu ɗaki. Sosai su ka mori darensu, don duk wani salo Ayush ta yi kwas a kai kuma ta ba shi. Hakan bai sa ya gamsu ba, asali ma tuna masa yayi da kwanakin sa da Amatullah, kenan da gaske suturta jiki na ƙara taimaka wajen bambance zuma da suga ko kuma dai dan sun dan saba dan wasanni tun kafin su kai ga auren. Duk wannan tunanin bai hana masa yi mata alkawura ba tare da bata duk wani yanci da take so a rayuwarsu. "Kaga ita Ayush matar so ce ita Amatullah sai ka rike ta don samun cikon natsuwa da kamala" ya tuna hirar abokin sa bayan an sanya ranar sa da Ayush. Tabbas ga shi ya zahir, duk da ita ɗin ma shine farkon ta, amma tazarar da ke tsakanin Amatullah da Ayush mai faɗi ce. Ayush kuma neman yanda za ta sami damar hadiyar kwayoyin da Sameera ta siyo mata ta ke yi, bata shirya bacci ba sai da ta haɗiyi kwayoyin don gudun ɗaukan ciki, a tsarin ta ba ta ga za ta iya ɗaukan ciki kafin shekara uku bayan aurensu ba, bare yanzu da take zaune gidan gandu. A haka dai suka kwashi kwana bakwai ɗinsu sannan su ka koma gida, babu wanda ya ce da shi kanzil kamar yadda babu wanda ya ma sallama kafin ya tafi. *** Babu abin da ya fara ɗaga hankalin Ayush bayan dawowarsu sama da tashin ta da yayi ƙarfe bakwai ta je ta gaida iyayensa. Kallonsa ta yi sheƙeƙe tace "Honey pie, ba zan yi bacci ba Fisabilillah, wani irin in je in gaida mutan gida, ni fa bana son fara abin da ba, zan ɗore ba, ha'an" tace tana harararsa kamar ta yi kuka. "A'a fa babe, kinga duk wannan na ɗan lokaci ne kafin mu tafi gidan mu, sai mun so zuwa za su ganmu, ki yi haƙuri daga kin dawo shike nan" yace yana rungumar ta. "Ɗakin Hajiyarka kawai zan shiga, wancan tsohon ma bana auren da shi don shi bakin cikin kasancewarmu tare yake" tace tana mai faɗin iya gasikyar ta, shi kuma ya dinga wangale baki yana tunanin wasan jika da kaka ta ke da Baban Sasa. "Shike nan mu je kin ji" yace yana mai miƙo mata gyale ta yafa akan kayan jikinta wainda su ke ƙanana masu bayyana sura. "Au ba zan iya fita haka ba, ni dai Allah zaka haramta min zuwa gaisuwan nan, what is wrong with my dressing for goodness sake" tace cikin tsiwa. "A'a muje, ba komi, naga amarya ce ai" "Amarya baka ci sadakinka bane" tace tana watsa masa harara. Tunawa da garar da ya kwasa da yanda ya san kowace rijiya da yanda take amsar guga. "Babe oooo muje muyi mu dawo kiji" ya ce yana miƙewa, haka suke tsallake mutane tana gaida su a tsaitsaye har ta isa ɗakin hajiya. Kujera ta samu ta zauna, sannan ta gaida Hajiya tana mai ƙare ma ɗakin kallo tana tsine ma soyayya a zuciyar ta, 'in ban da soyayya wai nan ne za a kira ɗakin uwar mijina' tace cikin ranta. "Ai na sha bacci za ku yi, hayaniyar biki ai sai da hutu" hajiya ta faɗi cikin murmushi, kallon Ayush take tana ƙara gode ma Allah da ta bata surukar da tafi ta kowa. "A'a ai muna neman Albarka ne" tace a yatsine. "Allah ya muku albarka" Hajiya ta caɓe cikin sauri. "Aameen" Ayush ta faɗi cikin miƙewa. Shi ma a mike su ka fice duk yanda Hajiya taso ta ɗan keɓe da shi. Haka rayuwar su ke tafiya kullum safe zata gaida Hajiya ta koma ɗakinta, abinci kuwa in bata soya dankali ba zata girka musu taliya ko farar shinkafa da wake su ci da mai da yaji. Tun yana ganin hakan a matsayin amarci ne har dai ya lura da gaba ɗaya cikin sa baya samun lafiyayyen abinci kamar da. *** Zaman Ayush a gidan bai tsinana ma kowa komi ba ciki har da hajiya, don cin abin hannun Ayush wahala ne, daban ta sa ƙannen sa Najaatu da Aisha su dinga zuwa suna mata gyaran gida da wanke wanke, hakan bai sa ta musu ihsani ba. Tun ranar da su ka dawo gidan ta ke raba idanu domin ganin Amatullah ko dan Saifullahi, amma babu su babu alamar su, har ta gaji ta tambayi Najaatu, in da take shaida mata ai tun satin biki ta ji Gwaggo ta ce ta koma makaranta saboda jarabawa. Hakan sam bai mata dadi ba, amma ta ce ba komai ta na nan tana jiran ta. Shigar da take musu a cikin gida kuwa babu ruwanta da wa zai gani, kwatakwata ɗan kwali bai dame ta ba haka za ta dinga tsallake matan gidan da sannu in zata shiga ɗakin hajiya. Abu ɗaya ne bata wasa da shi watau maganin ta, ko da wasa ba ta yarda ta yi tsallake ba don ba ta ga wajen haihuwa a gidan ba. Yau ma kamar kullum sanye take da doguwar riga mara hannu, tayi sabon kitso da lallai wanda ya kwanta a kan farar fatanta. Tuwo yace mata yana jin ci kuma ita har ga Allah ba ta iya ba, Najaatu take son kira ta tayata ta shiga wajensu tana tsallake su Hajiya da sauran matan gidan suna hidimar su, ganin ba sa wajen sai ta wuce soro in da ta ga su Baba Anas, Baba Idiris, Baba Zubairu da Baban Sasa zaune bisa tabarma. "Sannun ku" Abin da ta furta kenan, kafin ta gifta su ta leka waje. "Wacece wannan kuma" Baban Sasa yace bayan sun amsa mata sannu da tace. "inaga baƙuwa matar saif tayi" Baba Idris yace yana mai basarwa. Dawowar da ta yi tare da Najaatu ya basu damar gane ta. Cikin jinjina kai Baba Idiris ya ce "Wannan fa Aisha ce matar Saifullahi" Baban Sasa na mai kame baki ya ce "Wai matar Saifullahi ce ta zo ta tsallake mu da wannan shiga haka?" "Toh ai in dai wannan yarinyar ce kaɗan ku ka gani, wani shigar idan ta yi sai dai a kau da kai tsabagen munin shigar" Cewar Baba Zubairu cikin al'ajabi, ya kara da "tashin hankalina yanzu shi ne Kar Allah ya sa yaran gidan nan su dauki dabi'a irin na ta" "Ah ah, 'ya'yan mu masu tarbiya ne, Allah ya tsare mu da ganin dabi'a irin wannan a zuri'ar mu, ina Anas surukar ka ce, ina fatan za ka yiwa tufka hanci!" Cewar Baban Sasa cikin jaddadawa. Kai Baba Anas ya gyada kawai, ya san dai in har hawan jini ya kama shi toh ko shakka babu Saifullahi shi ne sila. Baban Sasa be gushe ba ya kara da "Ai ni daga ganin dangin yarinyar nan na san Saifullahi ya saki rashe ya kama ganye, mu ka bashi diyar mu diyar mutunci ya watsa mana kasa a Ido, ai ga irin ta nan, ga irin wacce ya je ya kwaso" Ya karasa maganar ya na fitar da kwalla. Takaici ne ya dada rufe Baba Anas, in da ya tashi ya shige ciki. Ganin yanda ya shigo a fusace ya sa Hajiya bin bayan shi. Cikin ɗaki ya kwance mata kwandan takaicin da ya kwaso, ya kuma umarce ta da ta je ta yiwa surukar ta magana, ba sa shigar mutanen banza a gida, idan ba haka ba shi da kan sa zai mata magana kuma ba zai mata ta dadi ba. Ya na magana ya fice fuu, jiki sanyaye Hajiya ta nufi bangaran Ayush. A falo ta tadda ta, kwance bisa kujera. Ganin Hajiya bai sa ta tashi zaune ba, daga kwance ta ke duban ta, ta ce "Hajiya lafiya mu ke ko?" Cikin kame kame ta ce "Eh kwarai yar nan, lafiya lau, dama na zo ne da yar wata magana" Jin haka ta tashi zaune, ta ce "Bisimillah zauna mana Hajiya, na mi ki laifi ne?" Hajiya ma ta zauna, ta na mai girgiza kai ta ce "Ah ah ko kadan, dama yar shawara ce" "Uhum?" Cewar Aysuh ta na mata irin kallon nan na hadarin kaji, Hajiya ba ta kula ba ta cigaba da faɗin "Kinga a matsayi na uwar mijin ki, na ke son jan hankalinki akan shigar da kike yi, tabbas babu haramci a ciki saboda a gidan mijinki kika yi, amma ki sani fitowa a haka ya saɓa ma addini da al'ada. Don Allah ki ɗan dinga yafa mayafi kinji, Allah ya muku albarka " ta fadi cikin sakin fuska. Takaici da bakin ciki ya sanya Ayush kasa cewa komai har Hajiya ta mata sallama ba tare da ta amsa ba ta fice, ta na fita ta kora Najaatu cikin zage-zage ta sa ma ƙofar sashinta makulli. Saifullah da ya shiga Abuja ya dawo gaf da magariba, yunwa ce sosai yake ji ga gajiya yana zuwa ya iske gidan a garkame. Komawa ɗakin hajiya yayi ya tambaye su ko Ayush ta fita ne nan Najaatu ta fadi masa abin da ya faru. "Amma Hajiya ya za ki biyewa Baba fisabilillahi ku ɓatawa yarinyar nan haka daga tarewar ta! Haba Hajiya!" Kafin Hajiya ta kai ga bashi amsa ya tashi cikin sassarfa ya isa ga ƙofar tasu, magiya yake da ban hakuri akan ta buɗe masa ita kuma faɗi take "Ba zaman kulle na zo yi ba, babu wani ɗan bura uba da zai sa nayi kulle" hakuri dai Saifullah yake bata inda mutane ke tsallake su tare da ganin halin da ya ke ciki. Yana kan bada hakurin ne Amatullah ta wuce shi tana mai waya, ga Emjay yayi ɓulɓul da shi rike a hannun ta. Shagala yayi yana mai mamakin dama a sashin Baba Hamza suke? Dama gidan nan take ko zuwa tayi? Idan idanunsa bai masa ƙarya ba kyau tayi ba ko kaɗan ba, surarta ya ƙara fitowa tayi shar da ita. "Haba Don Allah ki buɗe ki ji hukuncin da zan yanke Amatullah... " ya ce hankalin sa na ga Amatullah da ta ɓace ma ganin sa. Babu shiri Ayush ta buɗe haɗe da jawo shi cikin ɗakin da rufewa. [4/15, 10:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN Jawo shi ciki da aka yi ne ya ankarar da shi abin da ya faɗi. Nan ya sanya dariya cikin borin kunya haɗe da faɗin "Haba Babe, kawai ki zauna kina sa mutane na min gani gani" yace mai rungumarta. "Wallahi ka sake ambaton sunan nan a gidan nan wallahi a bakin aurenmu" tace cikin ƙara haɗe rai. "ki gafarce ni Babe, wallahi sai da na faɗi ma Hajiya ina ruwansu da ke, ina ce dai ni kike aure" yace yana mai ƙara manne ta da jikin sa. "Ba kowa ya ja wannan abin ba na tabbata sai tsohon nan da ya kamata a ce ya rasu tuni amma ya tsaya cin zamanin wasu" tace cikin takaici, duniya babu wanda take tsana cikin birgewa dama da Baban Sasa. Tun farkon labarinsa da ta fara ji a duniya na yanda ya ke kawo mata cikas ne a rayuwa, ta san kuma ta ganshi da ta je kiran Najaatu. "Barni da shi zan same shi, inshaAllah nan da ƙanƙanin lokaci za mu bar musu zariar gaba ɗaya" yace duk da ya ji haushin kalamanta ga Baban Sasa amma sulhun da ya ke so daga ita yafi komi. "Allah ya amince Honeypie, zan kira Anty Rukayya akan issue din allocation na estate ɗin don mu samu" tace cikin farin ciki. Satin da ya gabata su ka ji labarin gidajen da ake rarrabawa ma'aikata gwamnatin tarayya don a rage masu matsalar samun gida a Abuja. *** Amatullah kuwa hutun karshen zango ta dawo, sun yi jarrabawa cikin sauki da fatan samun nasara. Ko da ta dawo Sasan Mama su ka sauka, cikin murna ta tarbe su, nan ta cika musu ciki da abinci. Emjay da yake wata shida a duniya yayi ɓulɓul da shi, fuskar sa sak na Saifullah haske kawai zai nuna masa. Mama wasa ta shiga yi da shi tana hurga shi sama tana caɓewa. "Ya karatun Amatullah, dafatan megidan nan nawa baya hana ki" Mama tace tana mai cigaba da wasa da Emjay. "Alhamdulillah! Ai mama Baaba tana mana kokari" Amatullah ta ce tana mai nufin yar aikin da mama ta haɗa ta da ita, duk da ba kwana take da su a samarun ba amma ko da za ayi takwas ta isa gidan. Sai yamma can ta fito don zuwa gaida Baban Sasa. Ta fito kenan za ta wuce ta ci karo da Saifullah yana buga ƙofa cikin magiya. Dariya sosai tayi a ranta, tana ganin yanda ya bi ta da kallo, maƙe dariyarta tayi har sai da ta tabbatar da ta ɓace ma ganin sa. Nan ta zauna a kan dakali, ta dinga tuntsira dariya. "Emjay ka ga abin da na gani kuwa, ka taya ni dariya mana" tace ma Emjay shi ma kamar ya ji abin da ta faɗi nan ya shiga wangale baki yana dariya shima. Sai da su ka yi mai isarsu sannan ta tashi ta nufi wajen Baban Sasa. Sosai yayi farin cikin ganinta duk da in ya tuna cewa ba ta gidan Saifullah sai ya ji babu daɗi a ransa. "Oh jikan yara wannan ƙiba haka se ka karya min mata" yace yana mai amsar Emjay. "Aikuwa Baba gashi se muni yake, ai kwalelenka matanmu ba sa sonka" Baba Zubairu ya ce, su baba Anas ya taya shi. Ita dai Amatullah banda murmushi babu abin da take yi, son iyayenta na ratsa, ita a halin yanzu ba ta da lokacin jin haushin kowa, lokacin da take ɓatawa wajen son kanta da neman cigabanta ma ya mata kaɗan. " Amatullah!!!" Baban Sasa yace wanda ya dawo da hankalin su wajen shi. "Ki dubi yaron nan ki tausaya masa ki koma ɗakin ki Amatullah, Don Allah ba don ni ba" yace cikin sigar roko. Jin zancen tayi kamar saukar aradu amma ta ɗaure ta ce. "Wallahi Baban Sasa saki uku ya min, da tuni na koma" tace tana mai danne hawayen da ke neman fitowa. "Shi fa yace saki ɗaya ne, kaddara ukun ya miki a take zamanin Annabi SAW, da khalifancin ABUBAKAR RA zuwa Farkon Umar RA duk saki uku a lokaci ɗaya ana kirga shi a matsayin ɗaya ne, dalili yasa Umar RA ya maida shi uku, maluma na ganin ana iya ɗaukan hukuncin farko" yace yana mai ƙara narkar da fuska. "A'a fa Baba, zance mafi inganci Shine a yi amfani da hukuncin sayyidina Umar RA. Annabi da kansa ya ce ALAIKUM BI SUNNATIE WA SUNNATU KHULAFA'UR RASHIDUN ka ga hadisi ne ingantacce da ya wajabta amfani da hukuncin su a fage na addini" Baba Anas ya tare shi, hakan ya saukar ma Amatullah natsuwa. "Kuma Babanmu wallahi yaron nan bai yi hankali ba, ka daina damuwa da lamarinsa, lusari ne ba ko ƙarami ba" Baba Anas ya ƙara faɗi ganin baban Sasa bai gamsu da shi ba. "Shine dalilin da ya sa nake son komensu, ka ga za ta gyara shi, da wuya amma da nasara a gaba" Baban Sasa yace a maraice. "Zata koma Baba, ka bar komi a hannuna inshaAllah" Baba Hamza yayi karaf ya faɗi yana mai musu signal da ido. A nan gaɓan Saifullah da Ayush su ka shigo wanda Ayush ta tabbatar da ta in gizo shi da su zo yayi magana da Baban Sasa akan a fita rayuwarsu. Babu bambanci a shigarta ta ɗazu su ka shigo da Sallama. Kallo ɗaya su ka yi ma juna ita da Amatullah su ka shaidi juna. Ta san dai za ta nuna ma Amatullah fari da tsawo amma diri da tsananin kyau ko kaɗan ba za ta kamo Amatullah ba. Sanye take da atamfarta riga da skirt da hijabinta da ya shiga da kayanta amma sheƙi da Amatullah ke yi ya ɗan rikitata don natural glow ne da ta fara koyon sirrinsa daga mimi. Ɗaukan Emjay tayi ta fice tana ma iyayen sallama su kuma suna masu bin ta da Albarka, kafin duk su gimtse fuska. "Baban Sasa Ƙaran Hajiya na kawo" yace yana mai yamutsa fuska ganin yanda iyayensa su ka yi fuskar shanu. "Toh me hajiyar tayi?" ya ce yana ƙara haɗe rai. "Ta fita idon iyali na, ko a musulunci an yarda ai mace ta yi shiga irin shigar da mijinta ke so, Baba ni ke auren Ayush ba kowa ba, haka nake son ganinta don haka ka ja masu kunne" yace yana mai kumburewa. "Tohhh Madalla da tabbatacce mara kishi, shi ne ka..." Baban Sasa bai ƙarasa ba saboda sarƙewa da maganar ta yi amma bai fasa nuna Saifullah da Yatsa ba, nan take ya faɗi a wajen sumamme. Ruwa suka ɗauko su ka watsa masa amma ko motsi bai yi ba, duba shi su ka yi nan su ka ga maɗiga na bugawa, ɗaga idon da Baba Anas yayi ya ga su saif tsaye a firgice ya ce "Saifullah Allah..." bai karasa ba dalilin rufe bakin sa da baba Zubairu ya yi. "Fice mana da gani Saifullah" Baba Idris ya faɗi cikin tsawa nan su ka fice sum sum shi da Ayush, ita tana addu'a Allah ya sa Baban Sasa ya margaya a huta shi kuma tsoro da Dana sani ne ke cike da kirjinsa. *** Asibitin Koyarwa ta Shika su ka nufa da shi, addu'a su ke kada ya rasa ranshi. Sashin gaggawa da hatsari su ka yi da shi inda take aka mika shi sashin masu fama da ciwon ƙoda bayan an duba an gano jininsa ne ya hau da kuma kodarsa guda ɗaya ta lalace, dole a cire ta in ba haka ba ciwon zai iya taba dayar kodan. A asibitin su ka kwana don likitoci a kansa su ka kwana, kafin su ka samu ya farfado amma nan aka nemi jini saboda saboda za a shiga da shi aiki. "Sai dai a siya duk mu nan da muke nan babu mai kalar jininsa, Salihu ne da mahmuda su ke da shi amma duk mu positive gare mu" Baba Zubairu ya ce ma likitan cikin damuwa. "Yaa salam, samun jini 0 negative yanzu aiki ne, amma kuje bankin jini ko za a dace" yace yana komawa wajen tawagarsa da ke duba Baban Sasa. Baba Anas na sauri don zuwa ya bincika ko zai samu ya bangaje mutum. A tare su ka ba juna hakuri nan su ka shaidi juna. "Baba ina kwana, da fatan lafiya na ganka a asibiti da safen nan" Yace fuska a sake. "Kai dai bari ɗan nan, Baba ne ake bukatar jini 0- ne, shine zan duba ko za a samu, ina ne ma blood bank ɗin" yace cikin ruɗu. "Subhanallah, Nima ai 0- din ne muje baba a yi min gwaji in lafiya lau sai a ɗibi nawa, Nima na zo wajen supervisor na ne" yace yana mai kamo hannun Baba Anas ganin yanda duk ya rude. An ci sa'a jinin Dee lafiya lau ya ke, haka kuma ya na da ishasshe dan har leda uku aka samu daga wajen shi. Godiya mara adadi Baba Zubairu da Baba Anas su ka ta yi masa, da shi aka zauna har aka shiga da Baban Sasa aiki. Awanni aka dauka ana yiwa Baban Sasa aiki, har Allah ya ba su iko su kammala masa aikin aka fito da shi rai a hannun Allah. Yanayin da aka fito da shi ba su Baba Anas ba, shi kan shi Dee sai da ya sha jinin jikin sa, dan kuwa hatta su likitocin da su ka masa aiki ba su da tabbacin ko zai tashi. Daki na musammam aka kwantar da shi, Baba Zubairu ne mai dauriyar kai kawo, shi kuwa Baba Anas tun ganin yanda aka fito da Baban Sasa bakin shi toshe da abin bada taimakon numfashi ya ke fidda kwalla. Sai da aka kwantar da Baban Sasa, Dee Yusuf ya mu su sallama tare da alkawarin zai dawo jiki sanyaye ya tafi. Ranar daga Baba Zubairu har Baba Anas babu wanda ya runtsa, haka ma Baba Salihu tuni ya ɗauko hanya, in da Baba Muhamuda shi ma ya karaso tare da Baba Hamza da Baba Idiris. Har dare yayi Baban Sasa bai farfado ba nan aka shiga muhawarar wanda zai kwana da shi, dan kowannan su gani ya ke idan har ya tafi kafin ya isa gida za a kira a ce Baban Sasa ya cika. Daga karshe su ka yanke hukuncin barin Baba Idris, su kuma sauran su ka kama hanyar gida. Isar su kofar gida nan su ka taradda Saifullahi zaune, abin duniya ne ya isheshi tun bayar faduwar Baban Sasa wanda ya ke gani kamar shi ne sila, gashi kunya da tsoro ya sa kasa tunkarar asibitin. Ganin su ya tashi da saura ya na faɗin "Sannun ku da zuwa Baba, ya jikin Baban Sasa?" Babu mahalukin da ya amsa masa, Baba Anas kuwa ko kallon in da ya ke be yi ba, su ka shige gida su ka bar shi nan tsaye. "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Ba zan iya jure fushin iyaye ba! Allah ya tashi kafadar tsohon nan ko Allah ya sa ku yafe min" Cewar Saifullahi yayinda ya koma in da yake zaune da ya zauna zuciyarsa cike da da na sanin biyewa Aysuh da yayi. Cikin gida kuwa, idan aka ɗauke Ayush kowa cikin zulumi ya ke musammam Amatullah wacce ta wuni ta na kiran wayar Baba Anas domin jin yaya jikin Baban Sasa. Gidan tsit kamar gidan makoki, jin motsin shigowar su ya sanya kowa fito ana tambayar "lafiya? Ya Baban Sasa ya ji da jiki?" "Babu sarki sai Allah, ku yi addua idan na tafiya ne Allah ya ba shi saukin tafiya, ya sa ya cika da imani, idan kuma mai tashi ne Allah ya saukaka masa ciwo, dan kuwa dai Baba na cikin wani hali!" Cewar Baba Zubairu wanda har lokacin shi ne ke da karfin halin magana. Abin ku da mata nan gida ya kaure da salati har da masu kuka. Sai da Baba Anas ya tsawatar mu su sannan kowa ya shiga hayyacin sa. Ayush da ke jiyo komai daga bangaranta ran ta ne yayi fari tas, Alhamdulillah tsoho zai mutu ta bar zaman gidan gandu, ta na mai adduar Allah ya sa ya tafi kenan. Jiki sanyaye Amatullah ta koma ɗakin in da ta dauro alwala ta shiga nafilfilu domin nemawa Baban Sasa sauki, ko da kuwa na tafiya ne. Dan kowa ya fidda rai Baban Sasa bai taba jinya da ta kai wannan tsanani ba. Ranar kowa kwanan zulumi yayi, cikin daren Mahaifin Amatullah Baba Salihu shi ma ya iso. Hatta Ayush da ke farin cikin rashin lafiyar Baba Sasa ba ta ji dadin daren nan ba, dan kuwa Saifullahi juya mata baya yayi a karan farko tun da ya auro ta. Da asubar fari su Baba Anas har Baba Salihu su ka dunguma asibiti, Nan ma su ka tadda Baban Sasa bai farfado ba, haka aka sake wani wunin zulumi da fargaba. Da la'asar Dee Yusuf ya koma duba Baban Sasa, Nan ya tadda duka baffanin Amatullah. Bayan ya gaishe su, su Baba Muhamuda, Baba Hamza, Baba Idris su ka amsa da kyar cike da kyama. Baba Anas ne ya ce "Ya ka nan zo zauna kusa da ni ɗana, abin da ka mana Allah ya ma ka, wannan yaron da ku ke gani shi yayi mana abinda duk cikin mu idan ban da Salihu da Muhamuda babu wanda zai iya ko da kuwa muna da niyya, wannan da kuke gani shi ya ba da jini har leda uku, wanda aka karawa Baba, duk da kuwa ya san kyamar shi da mu ke yi ........" "Yanzu jinin arne aka sanyawa Baba? Haba mana shi ya sa gashi har yanzu bai motsaba ba shi ba raye ba shi ba a mace ba! Kwa bari a ɗura masa jinin mushe fisabilillahi!" Cewar Baba Hamza ya na mai kumfar baki. Shi kuwa Dee idan har maganar ta ba shi haushi sam bai nuna a fuska ba, dan kuwa ya san za a yi hakan. " Baba ina ga babu ruwan bambancin addini a wajen ceton rai, nayi imani da littafi mai tsarki babu haka a cikin addinin ku, saboda Ubangijina na bashi, ina fatan Allah ya bashi lafiya" Dee ya faɗi cikin sanyin murya, kalaman sa be sanya sun ji sanyi a zukatansu ban na bakin ciki da takaicin jinin Arne ke gudana a jikin mahaifin su. "Sannan Baba in ma a blood bank a ka siyo, ana bambance jinin musulmi da Christian ne, sai naga aka yi rashin sa'a kila na mara addini kwata kwata zaku siya" Dee ya sake faɗi ganin yanda suke gimtse fuska, ya tashi tare da faɗin "Na bar ku lafiya, ubangiji ya tashe shi lafiya" Ya juya ya tafi abin shi. [4/18, 9:49 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA ƊAYA Gaba ɗayansu bin sa su ka yi da kallo har ya fice, nan ne Baba zubairu ya ɗan muskuta ya ce "Nifa ban ga laifin yaron nan ba, na tabbata da ace shi mu ka gani a wannan hali ba zamu taɓa waiwayensa ba balle mu taimaka masa, bayan mu ne addininmu ya koyar da mu kyautatawa" yace yana mai kallon ƙanensa zuciyarsa cike da Nadama. "Gaskiya ne, don wallahi ba ruwan bambancin addini a kyautata mu'amala ko sauke hakkin makotaka. Yanda ya wajaba a kan musulmi haka ya wajaba akan wanda ba musulmi ba, sannan a ko ina cin fuska haramun ne" Baba Anas ya ce yana mai goyon bayan Baba Zubairu. "Amma kuma aka ce kada mu riƙe su aminai" Baba hamza ya ce a ɗan hasale.. "Eh an ce kada ka rike su aminai don za su cutar da kai amma ba a ce kada ka rike su da amana ba, kun manta zamanin Annabi SAW sau da yawa kafirai na zuwa da niyyar kashe shugaban halitta amma su ɓige da musulunta ba su kaɗai ba har mutan garin su, duk saboda kyakkyawan mu'amala da musulunci ya koyar da ayi ga kowa ciki har da wanda ba musulmi ba." Baba Anas ya ce kai tsaye. " Ni dai babu wani kame kame da za ku min, kun ci amanar Babanmu, kun sani sarai yanda yake ƙyamarsu don su ɗin najasa ne, da kuke maganar na siya ba a sanin ko nawaye me yasa kullu. Muke addu'a muke faɗin RABBANA LAA TU'AKHIZNA INNA SINA AU AKHƊA'ANA toh shi Ubangiji ai mai Rahma ne, ba zai kama mu da laifi ba amma kuma yanzu fa? Haba! Haba!! " faɗin Baba Hamza ransa a ɓace. " Kunga matsalar Bahaushe kenan, shi a duniya gani yake babu wanda ya kai shi zama kusa da Allah, haka kuka dinga tada jijiyar wuya lokacin da ɗan wajen madina ya auro Gara, a bakin bahaushe za ka ji yana kaskantar da wani jinsi in dai ba yarensa ɗaya ba da kiransa ƙabila. Shi bahaushe shi dai wanda bai cikata farillansa ba amma a duniya ba wanda yake nuna wa Yatsa sai wanda ba musulmi ba, shi ne zai kalli malamin addini ya kira shi da tubabbe matukar daga baya ya musulunta. Da haka manzo SAW yayi da ya tara manyan sahabbai da yake da su? don dukkansu tubabbu ne a fassaran bahaushe." Baba Salihu ya faɗi kai tsaye. " Shine ai nagani, gashi kiri kiri wanda kuka zaɓa akan arnen yana shirin kashe muku mahaifi. Na gwammace a ce Arnen can ne ɗa na in dai zai tuba ya musulunta akan wancan sakaran" Baba Anas ya sake fadi cikin takaici. "Ko me zaku ce muna dai jin ku ne kawai don ba zai wanke cewa baku kyauta ma babanmu ba kunci amanarsa ba ko kaɗan ba, Jinin Arne fa ke gudana a jikin Baba, mutumin da yayi rayuwar sa kaf cikin musulunci" Baba Mahmuda da tun farko bai maganta ba ya ce yana mai tsananin jin takaici. Tun da suka fara magana Baban Sasa ya dawo hayyacin sa, idanunsa a rufe sai yake jin zantuttukan su kaf a kunnensa inda yake ji kamar mafarki yake yi, so yake ya fahimci me su ke faɗi amma ya gagara, idanun sa sun masa nauyi dan haka ya kasa bude so, bubu abin da ke motsi jikin sa face yan yatsun hannun sa. Baba Idris wanda tun da aka fara magana bai tamka mu su ba, shi ne ya lura da halin da ya ke ciki. Cikin hanzari ya tashi ya na fad'in "Ina ga fa Baba ya motsa, yi maza kira likita! Baba Muhammadu ne ya fita cikin sauri sauri gudu gudu, in da gaba ɗayan su suka zagaye shi suna masu faɗin "Sannu Baba! Allah ya tashi kafadar ka" *** Faɗin Damuwar da Amatullah ta shiga ba zai misaltu ba, don gaba ɗaya kanta ta ba laifi don gani take damuwar rashin komenta ne ya kwantar da Baban Sasa. Addu'a kam ta yi sosai akan ya samu lafiya. Zaune take tana tunanin zuwa shika Amma wa zai kai ta? Lokaci take kallo tare da tsimayen kiran sallan la'asar domin ta ba da farali. Ɗumi ta ji ya fito mata wanda ta dan razana tare da gyara zama yayin da taji fitowarsa a karo na biyu. Ajiye littafin 'Ina Darajar take?' da take karantawa tayi ta shiga bayi don gane ma idanunta. Abin da bata zata bane ta gani, wani irin yanayi ta shiga don gaba ɗaya ba za ta ce murna kaɗai ta ke ba. Gyara kanta tayi ta isa ga mama da ke ɗaki tana hutawa tace "Mama abin ya zo, na kusa fita idda" tace cikin farin ciki. Kabbara mama tayi tana mai gode ma Allah sannan ta ce "Kiyi shiru da bakinki, ba za su ji ba sai kin yi wankan na ukunki, kai Alhamdulillah Alhamdulillah" mama tace cikin farin ciki. **** Ayush kuwa tunda garin Allah ya waye take cika ta na batsewa musammam da ta ji Baban Sasa ya farfaɗo daga bakin su Naja'atu. Gaishe da Hajiya da ta ke zuwa kowacce safiya ma yau ki ta yi. Hajiya da ta ji ta shiru, tunanin ko lafiya ya sanya ta shiga bangaran Aysuh din. A falo ta tarar da ita, sanye da wando wanda ko gwiwa bai kai mata ba, da riga damammiya mara hannu. Ta yi dai dai bisa doguwar kujera, ƙafa ɗaya kan ɗaya, yayinda ta ke cin gashesshiyar kaza ta na korawa da lemo mai tambarin five alive. Yanayin shigar Ayush ya sanya Hajiya tsayawa bakin kofa ta ɗan yi Jim, ganin Ayush ba ta da niyar tashi ta rufe jikin ta bare ma ta nuna ta san da zuwan Hajiya, Hajiya ta ɗaure ta karasa cikin falon da fara'ar ta ta ce "Assalamu Alaikum, Aisha sannu" Sai da ta kora kazar bakinta da lemo, sannan ta amsa da "Yauwa Hajiya barka da maraice fa, da fatan dai lafiya ko? Dan dai yau ko fita ban yi ba inan dakina bare ku ce na fito mu ku cikin tsiraici!" Jikin Hajiya yayi sanya kamar wacce aka zubawa ruwan sanyi, ta ce "Haba yar nan, kar ki ce haka ai gyara kayan ka ba zai zamto sauke mu raba ba, rannan da ki ka ga na tanka shi ma ai da dalili, yanzu na ji ki shiru ne ba ki zo an gaisa ba ya sa na biyo sahun ki na ji ko lafiya" "Lafiya lau na ke, gudun kar na fito ku ce na fito mu ku zindir ya sa na yi zama na ɗaki, gidan ubana ba a takura min ba, ban ga dalilin da zai sa a takura min a nan ba, ehe!" Ba ta damu da yanayin da Hajiya ta shiga ba, ta kara kora lemun ta, sannan ta ƙara da "To Hajiya ma fisabilillahi ɗan ki ya ajiye ni a gida kamar bukka sam babu ventilation kuma you guys are still expecting me to dress like the local woman you're?" "Iyye? me ki ka ce? Na ji kina turanci kin san ba ji na ke ba" "Aw haka fa, yi hakuri hajjaju ashe ba boko, dama cewa na yi tunda ɗan ki ya aje ni gida irin wannan dole na ke shigan shan iska, na saba da AC gidan uba na" Kai Hajiya ta girgiza, sannan ta ce "Eh da gaskiyar ki, mun takura ki zaman gidan nan tun da ba ki saba ba, amma kar ki damu komai zai wuce, za ki koma na ku gidan daga ke sai mijin ki" Hajiya ta faɗa ta na mai kallan kazar da Ayush ta ke ci. Ganin in da idanun ta ke kallo ta ce "Ragowar kazar da Saifullahi ya saba siyo min ne duk dare, na ga kamar ran ki ya biya, za ki iya ɗauka Hajiya" Ran Hajiya ba ƙaramin motsawa yayi ba, dan kuwa rabon da alkhairi ya shiga tsakanin ta da Saifullahi tun sanda ya ke auren Amatullah, lokacin su kazar nan babu laifi ya kan kawo mata, yau gashi sai dai ta gani ɗakin matar shi, har ta na mata tayin wulakanci. Hajiya na mai kokarin ɓoye bacin ran ta tace "Ah ah madallah, na gode, idan yayi niya shi Saifullahi zai kawo min tawa ai" "Eh toh nan fa ɗaya , kun fi kusa ai ɗa da mahaifiya, na gode Hajiya, Allah ya huta gajiya" Jiki sanyaye Hajiya ta ce "Ameen" Har ta juya za ta fita ta kara dawowa ta ce "Baban Sasa ya farfaɗo, sai ki shirya da anjima kaɗan in za a je duba shi a tafi da ke ko?" "Saboda mai ya sa!" Cewar Aysuh ta na mai aje lemon hannun ta kasa, ta kara da "Miji na bai ce na je ba, duk sanda na sami lokaci zan je dan Allah Hajiya kar ku matsa min! Ai da ya na so na je ai da ya faɗa min ko?" "Eh gaskiyar ki yar nan, Allah ya sa mu dace" Hajiya ta ce yayinda ta juya da sauri ta bar dakin zuciyar ta na tafasa, ba dan Aysuh Amarya ba ce, kuma ta na shakkar zuri'ar da ta fito da yau sai ta sanya Saifullahi ya saba mata! Tunanin da Hajiya ta ke yi kenan, har ta kusa buge Amatullah ba ta sani ba. Amatullah sanye cikin hijab din ta har kasa, ruwan kwai dan kyau har sheki ta ke, dauke da Emjay. Fuskar ta cike da fara'a ta ce "Afuwan Hajiya ban gan ki ba ne" Takaicin yanda Amatullah ta yi bulbul ta yi kyau, wanda kallo ɗaya za ka manta ka tabbatar da kwanciyar hankalin da ke tattare da ita, ba ƙaramin baƙin ciki ya karawa zuciyar Hajiya ba. Amatullah ta kara da "Barka da maraice, ina wuni?" "Lafiya lau" Amatullah ta wuce abin ta, da yake dama fita za ta yi, za ta je asibiti duba Baban Sasa. Ta bar Hajiya da bakin ciki fal zuciya. Da fitowar ta, da tsayuwar motar Saifullahi lokaci guda ne. Tun kafin ya fito daga motar ya kura mata idanu, gani yayi ta zame masa sabuwa gal, dan ko sanda ta ke buduwar ba ta taɓa masa kyau da kwarjinin da ta masa a yau ba, abin mamakin shi ne ba wai ta yi ado ba ne, wannan hijabin nan dai da ya tsana shi ne sanye jikin ta. Fitowa yayi ya tsaya jikin motar, ganin ta nufo in da ya ke bugun zuciyar sa ya karu, bai taɓa tunanin ganin Amatullah zai sanya shi cikin mawuyacin yanayi da shiga ba. Ya sakankace gun shi ta nufo, in da murmushi ya bayya fuskar sa, wani daɗi ne ya mamaye zuciyar sa. Amma da Amatullah ta zo dab da shi sai ya ga ko kallon sa ba ta yi ba bare ma ta nuna da wani ɗan adam nan tsaye, wucewar ta tayi ta, in da ya bi ta da kallo tamkar sa ƙara'i. 'ashe Amatullah za ta iya ganin sa ta ki gaida shi?' Tambayar da yayiwa kan sa kenan cikin zuciya, a zahiri kuma bin ta yayi da sauri ya na kiran sunan ta "Amatullah! Amatullah! Amatullah!" Amatullah ta tsaya, juyowa ta yi fuska ɗaure ta na duban Saifullahi fuskar ta ɗauke da alamun tamabaya. Saifullahi na duban ta kamar zai haɗiye ta ya ce "Haba Amatullah, yau ina ɗa'a da tarbiyar na ki? Ko babu komai ai ni yayan ki ne ko Amatullah? Ya kamata ana gaisawa" Ta na mai ɗan sakin fuska ta ce "Ban san kai na wuto ba ai, na dai san akwai wani tsaye jikin mota. Da fatan ka na lafiya" Amsar da ta ba shi ba ƙaramin sosa masa zuciya ta yi ba. Ya ɗaure ya amsa mata da "Alhamdulillah, ya Emjay? I missed you guys .." "Lafiya lau Alhamdulillah, sai anjima ko?" "Ina za ki je ne, ai sai na ajiye ku kin ga yamma na yi" Cewar Saifullahi ya na mai fatan Amatullah ta yarda ya ajiye ta, dan har ga Allah ba ya so ya dena magana da ita. Kai Amatullah ta girgiza tare da faɗin "Thank you, we are very fine, we can manage" Ta na faɗin haka ta yi gaba. Nan ya tsaya ya na duban ta, har sai da ta ƙurewa ganin sa sannan ya hakura ya shige gida. Ɗaki ya tarar da Hajiya tana matse kwalla, ganin Saifullahi ta fashe masa da kuka, wai ta na da ɗa kamar shi a cikin gidan nan sai dai ta ga kaza ɗakin matar shi, ya na neman albarka kuwa? Saifullahi kallon ta kawai ya ke har ta gama kukan ta, ta share hawayen ta dan kan ta. Sannan ya ce "Hajiya da kin san abin da ke damuna da kaza ba ta saki kuka ba Hajiya, tun ba a je ko ina ba, zuciyata ta fara konuwa da barin Amatullah, Allah ya sa ba dana sani zan yi ba Hajiya!" Nan fa ta haushi da faɗa, ta in da ta ke shiga ba nan ta ke fita ba, ta kare da "Idan ni na haife ka Saifullahi maganar wannan bakar yarinyar ta fita bakin ka! Ina tunanin dai ba haka uwar ta ta bar ka ba!" Saifullahi ya tashi zai fita ba tare da ya sake furta komai ba, har ya kai kofa Hajiya ta tsayar da shi ta hanyar faɗin "Kuma ka tabbatar kazar yau da ni za ka siya! Na dai faɗa ma ka! Wanda ba ya neman albarka!" Takaici ya sanya shi girgiza kai ba tare da ya furta komai ba. Ya wuce bangaran sa. *** Sai da Baban Sasa ya kwana biyar kafin ya dawo cikin hayyacin sa, babu wanda bai zo ya duba shi ba, hatta Saifullahi ya samu ya lallaɓa ya je ya duba shi, Amma ban da Aysuh. Dee Yusuf kuwa duk sanda ya je wajan supervisor din shi ya kan yi kokarin leƙa Baban Sasa, duk da har lokacin ba su gana ba, kullum ya zo sai su Baba Hamza su ce bacci Baban Sasa ya ke, ba ma sa bari ya shiga. Shi kuwa dama ya na zuwa ne saboda Baba Salihu, waje su ke zama su ta hirar mahaifin Dee, kasancewar ya faɗa masa makaranta daya su ka yi. Hakan ba karamin fahimtar juna da sabo su ka yi ba cikin kankanin lokaci. Baba Salihu kan yi tunanin ina ma Dee musulmi ne da tabbas sai ya ba shi auren Amatullah, dan kuwa ya yaba da nutsuwa da hankalin Dee, babu shakka ya gaji mahaifin sa, haka kuma bai fidda ran zai musulunta ba dan hakan ma ya sa ya ke jan sa a jiki sosai. Kamar yanda su ka saba, yau ma da yammaci, sun shafe wajan awa ɗaya suna hira da Baba Salihu, kafin Dee ya ma sa sallama, ya ce ya na so ya koma gidan sa. Baba Salihu ya ce "Ka tafi hakan nan ba ku gaisa da Baban ba?" Ya na mai sosa kyeya ya furta "Ai ina ce har yanzu bai tashi ba Baba, wani karan na zo ma gaisa" "Ah ah yau kam za ku gaisa, mu je ku gaisa" Ba a san ran shi ba, amma ba ya so yayiwa Baba Salihu musu haka ya bi shi. Baba Salihu na tafe, Dee na biye da shi har su ka isa dakin kwanciyar Baban Sasa. Baban Sasa kishingide kan gadon shi, Alhamdulillah jiki yayi kyau, a kasa kan tabarma Baba Anas, Baba Hamza, Baba Idris da Baba Muhmuda ne zaune, in da su ke zantawa Baban Sasa na ɗan sa mu su baki jifa jifa. Ganin Baba Salihu da wanda ke biye da shi tuni kowannen su ya tsuke fuska. Baba Anas ne ya yiwa Dee iso cikin sakin fuska. Gaban gadon Baban Sasa Dee ya tsuganna, yanda Baban Sasa ya haɗe rai bai hana Dee murmusawa ba, cikin girmamawa ya furta "Baban Sasa sannu da jiki? Ya saukin jiki?" Da kamar ba zai amsa ba, dan har Dee ya fidda rai, sai kuma ya amsa masa da "Lafiya, asibitin ma sai ka biyo ni yaro? Wannan naci har ina?" "Yo ai Baba tun randa ya ba ka jini kullum sai ka gan shi asibitin nan, na kasa ganewa ko jinin na sa ya ke so a biya sa......" Cewar Baba Idris cikin dacin rai. Maganar ta shi ce ta firgita Baban Sasa, ya na mai rike kirji ya ce "Waye ya ba ni jini? Eye?" Shiru ne ya biyo baya, dan kuwa takaicin furucin Baba Idris ne ya hana su magana. Baba Anas na mai duban Baba Idris ya ce "Yanzu Idris menene amfanin kalaman ka?" "To to ai gwara ya sani, dan dai kun san da Baba ya na cikin hayyacin sa ba zai yarda a kara masa jinin arne ba!" Baban Sasa da hankalin sa ya gama tashi ya kara da "Yo 'ya'yan nan kwa min shiru? Na ce jinin wa aka karamin!" "Jini na ne Baba, kuma har leda uku ma kuwa!" Cewar Dee cike da tsokana, dan kuwa ya gane Baban Sasa irin wannan tsofaffin nan ne ma su kafiya, tun kalaman na sa na bata masa rai, har ya dena. "Jinin ka aka kara min yaro?" Cewar Baban Sasa ya na mai fidda idanu, Shi kuwa Dee ya gyada masa kai alamar "eh". "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Shikenan ni Jamoh yara sun kashe ni da rai na! Yanzu Anas ka na ina aka karamin jinin arne! Yanzu da ku za a ci amana ta?" Kunya ne ya cika Baba Anas da Baba Salihu, su Baba Idris kuwa da ma abin da su ke so kenan, Baba Sasa ya san abin da aka masa dan an ga ya na kwance rai a hannun Allah. Ganin yanda Babab Sasa ya rikice, idanu na fidda kwalla hannu bisa kirji ya na faɗin "Jinin arne ke gudana a jiki na, an ci amana na, an cuce ni!" Dee ya ce "Kwantar da hankalin ka Baba, ni ma ɗin aro na ba ka ai ba kyauta ba, ka dawo min da kaya na, shi yasa ai kullum na ke zuwa duba ka, in ba haka ba ina ruwan arne da kai" Jin haka Baban Sasa ya tsaya ya duban Dee, irin wannan kallon na kar ka maida ni shasha mana. Su kuwa Baba Anas da Baba Salihu dariya ce fal bakin su ganin kallon da Baban Sasa ya ke yiwa Dee, amma su ka kunshe gudun bacin ran Baban Sasa. "Ku ji mu da yasasshen zancen! Ta yaya zan dawo ma ka da jinin na ka?" "Ai wannan abu ne mai sauki, da ka warke duka jinin jikin ka za a zuke, in ya so sai a tace min nawa daga na ka, dan ko nima ba na son jinin tsoho ya gwarwaya da nawa, hakan nan da kuruciya ta!" Cewar Dee da mayar da zafafan maganar Baban Sasa zolaya. Baban Sasa na mai duban Baba Anas ya ce "Anas ka ga ɗan butan tsiya! Da ka samu ma aka sanya jinin ka jiki na mai daraja! Sai ka zo ka zuke jinin na ka na gani! Dan tselan uwa kai!" Daga Baba Anas har Baba Salihu kasa rike dariyar su ka yi, dariya su ke sosai, cikin wannan yanayi likita ya shigo. Ganin yanda su Baba Anas ke cikin nishadi ya ce "An ya kuwa Baba ana bari ka huta?" "Ina za su bari na huta bayan sun kashe ni da rai na? Sun gaji da ni so su ke na mu su huta! Jinin arne su ka ƙaramin, gashi nan gaban ka ya na faɗa min wai biyan sa zan yi bayan na warke?" Ya na maganar ne ya na mai nuna Dee da ɗan yatsa. Ko da Doctor ya kalli Dee su ka hada ido sai ya fadada fara'ar dan kuwa ya san Dee tun suna makaranta. " Ah Dee Yusuf! Har da kai ake daga hankalin Baba?" Dee na murmushi ya tashi ya na mai bawa Doctor hannu su ka gaisa, kana ya ce "Dr Abba Ai tsohon nan da ka ke gani ran karfe gare shi, mun yi kaɗan mu daga ma sa hankali, kawai dai jina na ne sai ya biya ni!" Dr Abba shi ma ɗin dariyar ya ke yiwa Baban Sasa ya ce "Dr kada ka daga ma Baba hankali, Baba rabu da shi, shakiyanci ne irin na jikoki....." "Kai ni ba jika na ba ne! Ina ni ina jika da arne ne!" "Toh Allah ya ba ka hakuri Baba, Dee ko za ku fita daga waje? Ina so na duba Baba" Kai ya gyada, in da yayiwa Baban Sasa sallama, maimakon ya amsa masa sai ma kawar da kai gefe yayi. Aka bar Baban Sasa da Doctor. A waje Baba Salihu yayiwa Dee godiya, tare da bashi hakuri bisa lafazan Baban Sasa. Dee ya ce da shi kar ya damu, ai babu komai shi ɗin yanzu ya gama fahimtar Baban Sasa, ai shekaru sun ja. Cike da sha'awar hali irin na Dee Yusuf su ma yi sallama, bayan tafiyar sa Baba Anas ya ce da Baba Salihu zai so ace Dee musulmi ne, ko zai musulunta, da ko shakka aure tsakanin shi da Amatullah alkhairi ne, ya kare da "Ka ga fa yanda ya iya tafiya da Baba cikin sauki da lumana, duk da cin fuskar da mu ke masa, ina ma Saifullahi ke da wannan halin" Kai Baba Salihu ya gyada tare da faɗin "Yusuf sak, haka uban sa marigayi ya ke wallahi, Allah ya masa rahama" Baba Anas ya amsa da Aameen. Su Baba Idris kuwa ba su fasa tuhumar su Baba Anas ba, dan kuwa wannan karan laifin biyu ya zama, wai har da na rashin kunyar sa su ka bari Dee yayiwa mahaifin su. Haka kan baffanin Amatullah ya rabu biyu, masu son Dee, wato Baba Zubairu, Baba Anas da Baba Salihu, sai kuma masu nuna masa kiyayya karara, Baba Hamza, Baba Mahamuda da Baba Idris. **** Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, sai da Baban Sasa yayi sati uku kwance gadon asibiti kafin a sallame shi, cikin satin ukun nan kuwa Dee Yusuf na yawan kai masa ziyara, acewar shi dubawa ya ke ya ga ko ya warke dan kar Baban Sasa ya warke ya cika rigar sa da jinin sa. Tun idan ya zo ya na kin amsa gaisuwar shi, har ya zo ya na amsa sama sama, Har dai ya dan saba da ganin sa. Haka duk sanda Dee ya tashi zuwa ya kan zo masa da kayan marmari, kamar 'ya'yan itatuwa haka. Amma fa duk ran da ya zo ba sa wanyewa lafiya, hakan ya sa Su Baba Idris su ka yi kokarin hana shi zuwa ba tare da sanin Baban Sasa ko su Baba Anas ba. Ganin an sallame su, kuma kusan kwana uku kenan bai ga Dee Yusuf ba ya sanya Baban Sasa raba idanu. Kayan sa ake kwasa ana sanyawa cikin mota, cikin masu kwasar kayan har da Saifullahi. Baban Sasa zaune kan kujera, tun da aka sallame su aka ce ya zo a kai shi mota, ya ce ah ah a fara kwashe kayan tukun. Amma a zahiri jira ya ke ko Dee Yusuf zai zo. Baba Anas da Saifullahi ne su ka dawo tafiya da shi bayan Baba Hamza yayi gaba da ragowar kayan. "Wai lafiya yaron nan ya daina zuwa?" Cewar Baban Sasa yayinda Baba Anas da Saifullahi su ka riko hannun sa suna mai sanya shi tsakiya. "Wani yaro fa Baba?" Baba Anas ya amsa masa da tashi tambayar. "Wannan arnan mana! Dan Yusuf" Gaban Saifullahi ne ya faɗi jin Baba na maganar Dee Yusuf, shi kuwa Baba Anas darawa yayi ya ce "Ah Baba yau kuma kewan sa ka ke kenan?" Shiru yayi, sai da su ka isa mota kafin ya shiga ya amsa masa da "Ka san zuciya ba ta da kashi Anas, yaron nan duk da arne ne na gane ya na da hali mai kyau" "Ko dai kana jin tsoran kar ya zo a zuke masa jinin sa da ya ba ka ne" Cewar Baba Anas cikin zolaya yayinda ya taimakawa Baban Sasa ya shiga mota ya zauna. Shi kuwa Saifullahi wani malulun kishi ne ya taso ya tokare shi a kirji jin ana yaban tsohon saurayin Amatullah, dan kuwa duk duniyar nan idan akwai wacce ya ke so ta bi bayan Amatullah, so ya ke Baban Sasa ya sami sauki sosai ya lallaba shi ko Allah zai sa a mayar da auren su. Wai kuma har jinin sa aka sanyawa kakan sa! Wannan abu ya tsaya masa a rai, ya na kuma daga masa hankali. Daga cikin mota Baban Sasa ya dan leko, kana ya ce "Anas ba na son shakiyanci, amma dan Allah idan da hali a shaida masa an sallame ni, ka ga yana yawan zuwa duba ni, kar ya zo ya ga ba na nan" "Toh Baba za a sheda masa kuwa" Baba Anas ya amsa zuciyar sa ɗaya ba tare da ya lura da halin tashin hankalin da Saifullahi ke ciki ba. Haka su ka koma gida Baban Sasa na yaban Dee Yusuf, ihu ne kawai Saifullahi bai kurma mu su cikin motar ba tsabagen kishi. ***** Ranar da Baban Sasa ya koma gida murna gidan kamar sallah. Ayush kuwa ranar wuni ta yi cikin taikaci. Ko da Amatullah ta je gaishe da Baban Sasa, nan ma sai da ya mata maganar Dee Yusuf, cewar shi "Jinin Dan Yusuf aka kara min Amatullah, kin ga rayuwa kenan, na ki hada jini da shi sanadiyar sabanin addini, ashe akwai lokacin da jinin sa zai ratsa nawa, har ya ke gudana a jiki na!" Mamaki ne ya cika Amatullah, dan kuwa ko da wasa ba ta ji maganar nan ba, ba ta ji ko Mimi ma ta sani da ta fada ma ta. Haka su ka sha hirar su, nan ya jara jaddada mata ta shedawa wannan yar uwar Dan Yusuf din, cewar an sallame shi fa, dan Allah ta fada masa dan kwana biyu ya rabu da lekowa. Amatullah ta amsa da toh. Da haka su ka yi sallama. *** Sai da Baban Sasa ya kwana uku a gida su Amatullah su ka fara Lectures gadan gadan. Jin Dee shiru Baba Anas da kan sa ya tambayi Baba Salihu number Dee, dan ya tambayi Amatullah ta ce ma sa ba ta da shi, kuma da gaske ba ta da shi din. Kamar daga sama Dee ya ji kiran Baba Anas, ko da ya gane Baba Anas ne sai gaishe shi cike da girmamawa, in da Baba Anas ya ce ya Kira yayi biko ne, kwana biyu sun ji shiru, ko dai ya fasa karbar jinin na sa ne? Baban Sasa ma ya na kyewar sa. Dee ya masa alkawarin zuwa tare da bashi uzurin komawar makarantar da dilibai su ka yi ya sanya hidama su ka yi masa yawa, ba tare da ya sheda masa su Baba Idiris ne su ka ja masa kunne akan zuwa gun Baban Sasa ba, a cewar su ya na hana shi samun kwanciyar hankali. Kamar yanda yayi alkawarin washagari sai gashi kofar gidan su Amatullah. Baban Sasa bai iya ɓoye farin cikin ganin sa ba, duk da kuwa har lokacin bai fasa zolayar sa ba. Dee sanye ya ke cikin shadda ruwan toka dinki buba, kan sa dauke da hula zanna bukar mai ratsin ruwan toka da kore. Waje gaban sa Baban Sasa ya bashi ya zauna, ya na mai duban sa ya ce "Kai Dan Yusuf sai kawai ka ɗauke kafa mu dena ganin ka haka ake yi?" "Sunana Dee Yusuf Baba, ka ce Dee ba Dan ba" Cewar Dee cikin zolaya. "Kai tafi can! Wannan ruwan ka ne ba nawa ba! Yaro na gode fa, ashe dai za ka min rana? Allah ya saka maka da alkhairi" Cewar Baban Sasa idanun sa na mai kawo kwalla. Ganin haka Dee ya ce "Ah ah Baba godiyar me ka ke min? Sai fa ka biya ni jini na? Haka za ka zauna da jinin arne?" "Yo to da haka sai ka kashe ni ai ka huta!" Dariya Dee ya saka. Nan su ka cigaba da hirar su tamkar jika da kaka, dan kuwa wasa da tsokanan shi da Dee ya ke ko Saifullahi ba ya yi. Sai da su ka gaisa da Baba Anas da Baba Zubairu sannan yayi musu sallama. Ya na shirin shiga mota ne sai ga Amatullah dauke da Emjay sun dawo daga makaranta. Ganin ta ya sanya Dee tsayawa ya na kallan ta yayin da zuciyar sa ke dada kamuwa da soyayyar ta. Sai da ta zo dab da shi sannan ya mayar da kallan sa ga Emjay wanda ke kwance kan kafadar ta. Kamar kullum yau ma hijabi ne jikin ta, fari kal. Zuciyar ta ke harbawa tun da ta yi tozali da Dee bai hana ta murmusawa ba yayinda da ta furta "Sannu da zuwa, ashe ka zo" Shi ma dai murmushin ya ke, ya na mai mayar da kallan sa ga fuskar ta, in da ta yi kasa da na ta idanun. Shi kan shi ya san Amatullah ta canza, Amma ba ya ce menene takamamman canjin ba. "Amatullah how are you? Ya babyn ki!" Ya tsinci kan sa ya na fada, dan kuwa ya biyewa zuciyar sa zai shagala ne nan tsaye ya na kallan ta. "Alhamdulillah, gashi nan bacci ya ke yi ya gama rigima" Ta juya masa fuskar Emjay, hakan yayi daidai da fitowar Saifullahi. Ran shi idan yayi duba ya baci ganin Dee da Amatullah, musammam yanayin da Dee ke kallan ta fuskar shi ɗauke da murmushi. Bai san sanda ya tunkare su ba, kamar daga sama sai gashi gaban su. "Amatullah ba ni yaron nan ba ki ga ana rana ba za ki tsaya da shi haka?" Cewar Saifullahi ya na mai kokarin karbe shi daga hannun Amatullah ba tare da ta ankare ba. Ganin haka babu shiri ta sakar masa Emjay, fuu ya wuce ciki. Daga Amatullah har Dee bin sa su ka yi da kallo cike da mamaki, musammam Amatullah da ta san tun da ta bar gidan Saifullahi bai taɓa nuna wani kulawa ga Emjay ba. Kallon Dee ta yi ta na mai murmushin yake dan kuwa hankalin ta na kan Emjay, shi ma Dee ya lura da hakan dan haka sai ya mata sallama ya tafi. Saifullahi kuwa bangaran sa ya wuce da Emjay, ya na shiga tsakar gida ya ci karo da kwanukan wanke wanke fal tsakar gida, daga gani an san kwanukan tun na jiya ne, kudaje ke bi gashi warin ruwan wanke da ke aje cikin kayan wanke wanke ne ke tashi. Dama ya kwaso bakin cikin Amatullah da Dee Yusuf. Jikin sa har rawa ya ke tsabagen bacin rai, "Aisha! Aisha! Aisha!" Ya shiga kwalla mata kira da ƙarfi har sai da Emjay ya tashi daga bacci ya sa masa kuka. Amatullah da ta biyo sahun ɗan ta da sauri ta nufi bangaran Saifullahi jin kukan Emjay, shigar ta yayi daidai da fitowar Aysuh sanye cikin rigar bacci, wanda hakan ke tabbatar ma sa har lokacin ba ta bar gadon ta ba, bare a yi maganar yin niyar wanka da gyaran gida, bare uwa uba girki. Wani irin kallon tsana karara ta ke yiwa Saifullahi da Amatullah, yayinda Amatullah ke kokarin karbar Emjay. hannu bisa kugu Ayush ta ce "Malam lafiya? Wannan wani irin wulakanci ne za ka shigo min da tsohuwar matar ka gida ka na kwalla min kira haka kamar sakarai?" Bakin ciki da kunyar yanda Aysuh ke masa magana gaban Amatullah babu da'a bare tarbiya, ya ce "Aisha ni ki ke yiwa magana haka?" Amatullah da ta samu ta karbe ɗan ta gaba ta yi ta bar su nan tsaye Saifullahi na mai kumfar baki, ta na jiyo Aysuh na faɗin "An maka din! Akan wani dalili za ka kawo min tsohuwar matar ka gida? Ka kawo ta ne ta ga yanda ka ke kuntata min?" A fusace ya ce "Waya ya damu da ke da har zai kawo wata gurin ki? Why? Me ya sa ki ka cika lalaci ne? Why are you so dirty? God ban taba ganin kazamar mace kamar ki ba Aisha! Ace tun safe rigar bacci ne jikin ki? Kalli tsakar gidan ki kaca kaca! Wanke wanke fal guri! Kin mike kafa ki na ta baccin asara!" Yatsune ta yi, cikin halin ko in kula ta ce "Gidan da ka dauko ni ko tsinke ba na daukewa, diyar hutu ce ni ka sani sarai ka san in da ka ɗauko ni! Ni ba baiwa ba ce bare yar aiki! Nan su Naja'atu suna shigowa suna taya ni aiki kai da Hajiya ku ka haɗa baki ku ka hana su, saboda haka idan ya maka ciwo kai ma kana da hannu ka gyara! In kuwa ba ka iyawa sai ka yiwa Hajiya magana ta zo ta gyara ma....." "Shut up!!! Mahaifiyar tawa ce za ta zo ta gyara mi ki gida? Ashe ba ki da mutunci Aisha?" Ya katse ta cikin tsawa. Kallon sa ta ke a wulakance ta ce "Wallahi na yi da na sanin auren ka Saifullahi, dan haka a yau da za ka sauwake min ba ƙaramin farin ciki zanyi ba....." "Na sauwake mi ki? Haka ki ce?" Ta na murguda baki ta juya da niyar komawa daki, wani irin wari ne ya buso su sanadiyar iskar da ta kado ruwan waken da ke wajan wanke wanke, Saifullahi yayi saurin ja da baya yana mai toshe hanci, ita kanta Ayush sai da ta rufe hancin ta, murya kasa kasa ta ce "Hmmmm Hajiya ta yi hamma!" Hakan ya sa Saifullahi harzuka dan kuwa ya so ya ji abun da ta ce "Ke! Me ki ka ce? Me ki ka ce Aisha?" Daki ta shige ba tare da ta amsa masa ba, cikin masifa da bambami kamar wanda ya zautu Saifullahi ke faɗin "Da mana ki maimaita! Ashe ke maraya kunyar karya ce! Ki maimaita mana! Da yau na tattaka ki, sakarya wacce ba ta san darajar iyayen ta ba!" Baba Anas ne ya zo wucewa, jin muryar Saifullahi ya na bambami ya sa ya ɗan tsaya, ya lekoshi tare sa faɗin "Saifullahi a na yin hakuri, zama da mata ai sai da hakuri, amafanin dace da kamular mace kenan ai Saifu" Yana maganar ya wuce abin shi ba tare da ya jira amsar shi ba, dama shi ma Saifullahi da ya san magana ya faɗa masa bai da niyar amsa masa. Ciki ya shiga ya nemi su Naja'atu ya ce su zo su gyara masa gidan dan ko ruwan gidan ba zai iya hadiya ba muddin ba gyarawa aka yi ba. ***** Washagari a makaranta tun safe Amatullah da Mimi su ke fafutukan lectures, duk da tun safe jikin Emjay ya ki dadi, kuka ya ke mata na babu gyara babu dalili gashi ya ki shan nono. Sai da ta goya shi yayi bacci sannan ta samu sauki. Kusan minti ishirin yayi ya na bacci, suna gaban notice board suna kwafar timetable da aka canza kawai ta ji ya na mimmike mata a baya. Cikin damuwa ta ce da Mimi "Mimi kin ga yanda Emjay ya ke mimmike min a baya, ina ga yaran nan be da lafiya dan Allah kama min shi na kwanto shi" Mimi ta amsa da "toh" yayinda Amatullah ta sauko da Emjay da tuni ya gama mimmikewa kamar mai shirin suma. Ganin haka Amatullah ta "Na shiga uku me ke damun yaron nan haka!" Mutanan da ke kusa da su duka hankalin su ya koma kan Emjay, nan aka zagaye su in da aka basu shawarar kai shi asibiti da gaggawa. Dan ajin su Amatullah ne ya karbi Emjay, ya wuce gama Mimi da Amatullah na biye da shi. Allah ya so nan cikin department ya aje motar shi, ko da su ka shiga motar Mimi ta karbi Emjay dan kuwa Amatullah jikin ta har rawa ya ke tsabagen tashin hankali, ba tare da bata lokaci ba su ka wuce asibiti. Yanda Emjay yayi wata mika tare da sauke numfashi ya sanya Mimi ta san rai yayi halin sa, amma ta kasa faɗawa Amatullah. A haka su ka isa asibiti. Haka shi ma ɗan ajin na su da ya dauki Emjay bayan da su ka isa, ya ji ya kara nauyi ga idanun sa sun kafe ya san Emjay kam ya kare, kallan Mimi yayi in da ta gyada masa kai. Haka jiki babu sanyi su ka shige asibitin, Amatullah da ba san halin da ake ciki ba tuni ta yi gaba da saurin ta. Suna isa emergency tun kafin Doctor ya taba shi ya ce da su "Ku yi hakuri, yaran nan ai ya cika....." Cak Amatullah ta tsaya ta na kallon Doctor, kafin daga bisani ta mayar da kallon ta ga gawar Emjay da ke kwance gaban su, a hankali kamar mai rada ta ce " Ko taba shi ba ka yi ba ka ce ya cika? Haka ku ke aikin asibitin? Bai cika ba Doctor, duba ka gani ai suma yayi fa, dan Allah ka tayar da shi......" "I'm sorry Madam" Ganin yanda Amatullah ta dauki gawar Emjay ta na mai rungume shi a kirjin ta, ya na kallan Mimi ya kara da "ina ga zai fi kyau ku tafi da su gida, she is in shock". Shi kan shi dan ajin na su ya tausayawa Amatullah, bare Mimi da Emjay ya zame mata tamkar dan cikin ta. Dan ajin na su ne ya ce zai kai su gida, amma har lokacin Mimi ta kasa tabuka komai, bare uwar gayya Amatullah da ta rungumi gawar dan ta tana mai raba idanu. Mimi na share hawaye ta ce da Amatullah "Amatullah" Karo na farko da ta Kira sunan ta kenan, maimakon ta amsa mata, kawai sai ta zuba mata idanu. Mimi ta ce "Tashi mu tafi gida" "Mimi bai mutu ba, Emjay bai mutu ba, dana bai mutu ba, ku kai ni wani asibitin wannan ba su san abun da su ke ba" Hawaye ne me zuba daga idanun Mimi, ta ma kasa magana sai kawai ta ruko Amatullah ta na kuka. Da kyar dan ajin na su ya shawo kan Mimi, ta taimaka su ka samu Amatullah ta shiga mota. Mimi ce ke nuna masa hanyar zuwa gidan dan kuwa tun da Amatullah ta shige gidan baya dauke da gawar Emjay, ba su kara jin ko tarin ta ba, idanu ta tsurawa gawar har su ka isa gida. A kofar gida ta tarar da Saifullahi, daga ganin alama fita zai yi. Ganin shi Amatullah tun kafin su faka mota Amatullah ta bude murfin motar, dan haka dole dan ajin na su ya tsaya nan tsakiyar hanya, da sauri ta fito gun Saifullahi ta nufa ta na mai nuna masa gawar Emjay ta ke faɗin "Ya Saifullahi ka ga wannan Doctor din sam be san abin da ya ke yi ba, ya kalli tsabar idona ya ce min Emjay ya cika!" Kallan ta ya ke tamkar ba hausa ta ke masa ba yayinda yayi kokarin karbar Emjay daga hannun ta amma ta hana shi. Cike da alamar tambaya ya ke duban Mimi da ta biyo bayan Amatullah. "Me ke faruwa ne? Me ya same shi? Saifullahi ya shiga jerowa Mimi tambaya. Cikin sanyin murya ta ce "Sai dai ku yi hakuri, Emjay ya koma ga Allah" Wani irin razana Saifullahi yayi ya na mai kokarin duba gawar Emjay. Amatullah kuwa cikin gargadi ta ce da Mimi "Ina ganin mutuncin ki Mimi, kar da ki sake cewa dana ya koma ga Allah! Emjay na nan tare da ni!" *** Ba da sadaka sai mai tsananin rabo, sai Allah na baiwa wanda ya so zuciyar ba da sadaka. Azumi ya gabato, muna ta hidimar haɗa kayan abinci da kayan sallah. Su kuma marayu marasa galiho fa? A dalilin haka gidauniyar Nisaau Ahlil Jannah Charity Foundation wacce aka assasa ta don cigaban marayu ta ke rabon abinci da kayan sallah ga marayu a cikin shirin ta na Ramadan sabil. Idan zamu sanya kaɗan din da Allah ya hore mana zai haɗu da na wasu ya wadatar wajen ciyar da marayu. Ku zo mu ba Allah rance, mu samu ladan kula da marayu mu kuma samu ladan ciyar da mai azumi. Zuba a 0334993079 (Naira) 0334993093 (Dollars) Nisaau Ahlil Jannah cha. Fdn Gtbank Don ƙarin bayani kira su 08157284164 Ko whatsapp 08025968968 Jazakumullahu khairan [4/21, 10:23 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA UKU Kasa zama sallahn yayi, shigewa cikin gidan yayi kamar mai shirin tashi sama. Koke-koken mata ya ke ji zuciyar sa na ƙara tsinkewa. Haka ya lallaɓa ya shiga sasansa ya zauna a kujerar falo. Ba komi ke masa yawo a idanu ba sai yanda da hannunsa ya cusa ɗansa a cikin rami, sannan yana kallo aka maida ƙasa aka rufe shi. Tiryan Tiryan komi ya dinga dawo masa kamar mai bita, tun daga kai ta asibiti don a cire cikin, zuwa haihuwar da tayi bai dire a ko ina ba sai inda ya sheganta ɗansa. "Yaa Rabbi ka yafe min, Emjay ka yafe min" ya ce yana mai dafa kansa. "Ai da bin sa ka yi ƙarshen soyayya" Ayush da tun shigowar sa take kallonsa tace tare da jan tsaki. Sai a sannan ya ɗaga ido ya kalle ta haɗe da kula da zaman ta a wajen. "Ayush Muhammad Jamoh yaro na ya rasu" ya ce mata cikin sigar neman ɗauki, kallonsa take cikin yanayin rainin wayau, ba ta san sanda ta kece da dariyar rainin wayau ba haɗe da ɗiban dambun naman da take ci tare da kai shi baki. "Wai dama kana da ɗa ne? Ina ce tuni ka yar da kwallon mangwaro" tace masa cikin tuna masa Kalamansa gareta lokacin da ya faɗi mata ya saki Amatullah. "Aisha!!!" yace cikin daka mata tsawa, ita kuma tattara kwanon dambunta tayi, ƙara kallonsa tayi ta saki dariya kafin ta shige ɗaki ta rufo ƙofa har da saka makulli. Ɗumin da yaji na sauka a fuskar sa ne ya sanya shi sharewa, sai a lokacin ya tabbatar da kuka fa yake, kuka akan mutuwar yaron da ya ce ba nashi bane. *** Dee Yusuf na idar da sallah ya kauce zuwa gefen Baban Sasa saboda sallah da su baba Anas ke yi. Azkar ɗin da annabi ya koyar na bayan sallan farali yayi, cikin natsuwa wanda hakan ya zama masa jiki tun bayan da aka koyar da shi. Fara'a sosai Baban Sasa yake yi yana mai jin ƙauna Dee na ƙaruwa a zuciyarsa, Godiya ya shiga yi ma Allah da ya sa hakan ya tabbata. A kan idonsa Dee ya yi Raka'a biyun da zai cika na sallah, mamaki sosai ya cika Baban Sasa ganin sallah yayi a natse cikin kwarewa. "Dan Yusuf jika na" Baban Sasa ya ce yana mai shafo shi cike da ƙauna. "A'a fa, ka ji min tsoho, ni dai jini na kawai zaka bani" yace cikin shaƙiyanci. "Ja'iri!!!" Baban Sasa yace yana mai kai masa duka. A wannan gaɓan su ka idar da sallah, baba Zubairu tsam ya tashi ya nufi Dee ya miƙa masa hannu. "Allah ya ƙara ma rayuwa Albarka, mene sunan" yace masa bayan sun yi musabaha. "Dawood!" Dee ya amsa cikin farin ciki. "Dauda dai ko?" Baban Sasa ne ya tambaya. Dee na girgiza kai ya ce "Ah ah fa tsohon nan kar ka ɓata min suna, Dawooda ne, haka sunan ya zo cikin alqur'ani, inda Allah ya jero sunayen annabawa 25 acikin suratul An'am, haka kuma suratul Saba'i inda Allah yayi magana akan falalar da ya bawa annabi Dawood, haka suratul Namli in da Allah yayi magana akan ilimin da ya bawa annabi Dawood, haka kuma suratul Saad inda Allah yayi maganar Khalifancin da ya bawa annabi Dawood a doran ƙasa, haka da sauran wajajen ma" "Ummmmm" "ummmm" Abin da ke fita daga bakin su kenan jin yanda Dee ke musu bayani cikin nutsuwa da tsari. Dee ya kare da "A cikin Bible kuma sunan a David ya zo....." "Allahu akbar! Allah shi ne mafi girma! Allah ya sa mu cika da imanin mu! Allah ya maka baiwa yaro, ka gode masa!" Cewar Baba Anas cikin sauki da kaunar Dee. "Bamu labari ma" Baban Sasa ya ce yana mai riƙe masa hannu cike da ƙauna. Dariya Baba Anas da Baba zubairu su ka yi, yayin da Baba Mahmuda ke yaƙe, Baba Idris da Baba Hamza kuwa zama su ka yi don jin ƙarshen ƙarya. "Bayan zuwa na gidan nan, na taradda auren Amatullah, lokacin gaba ɗaya na amince da babu addinin gaskiya sama da musulunci. Zuciyata ba ta karye ba, amma ina barin gidan nan na samu saƙon rasuwan uban riƙo na mijin mahaifiyata, haka na isa gida na tsaya mata a lokacin da ta fi bukatata sannan aka yi makoki da ni. Bayan kammala karatu na, duk lokacin ina cikin waswasi tsakanin amsar addinin musulunci ko kuma maida hankali wajen gyara rayuwata ta duniya. Na koma gida a wannan halin, ban ɓoye ma mahaifiyata komi ba game da halin da nake ciki. A bisa umurnin ta na isa Haɗeja, ban sha wuya ba wajen gane gidanmu, kamanni na da mahaifi na ya sa ba su gardama kasancewa na tsatsonsu ba. Sun min tarbo na musamman ba tare da sun damu da sanin addini na ba, sun yi farin ciki ainun sannan na ƙara da musu albishir din son amsar musulunci. Sai da nayi wata ɗaya a Haɗeja sannan na kai ma mahaifiyata ziyara a lokacin na iya izifi huɗu daga tabara zuwa nasi. Ko da mu ka tashi zuwa bautar ƙasa na yi yanda za a tura ni jihar Jigawa daga nan na nemi hanyar yi a Haɗeja, a nan na yi amfani da shekara ɗayan nan na nemi ilimin addini sosai, nayi fiqhu na yi tauhidi ga Hadisai duk na nemi ilimin su. Muna kammalawa na samu gurbin aiki a ABU saboda fita da sakamako mai lamba ɗaya da nayi, sannan na cigaba da masters dina, bayan dawowan ne na fara zuwa ɗaukan karatu wajen Ustaz Yunus inda nake haddan Ƙurani, yanzu Allah cikin ikonsa na haɗa izifi Arba'in, daga Nasi zuwa Tauba" Ko da ya kai ƙarshe hawaye sosai Baban Sasa yake, imani na ƙara ratsa shi, ya san cewa akwai wainda aka haifa a cikin musulunci da basu samu ilimi mai zurfi da Dee ya samu ba. Ko a zaria da yake matattaran ilimin addini, inda duk in da ka zaga ina ka fito islamiyya ina zaka majalisi ne akwai da yawa da suke da shekarun Dee kuma ba su samu gatan ilimin ba. Kenan ba ruwan sanda ka shiga addini da yanda za ka riƙe shi. "Dawooda Ɗan Yusuf, Na maka murna, lallai kai din mai tsananin rabo ne, Ubangiji Allah ya baka dukkan alkhairi duniya da lahira" Baban Sasa ya faɗi zuciyarsa cike da Nadamar abin da ya aikata a baya. Nan dai Su baba Anas su ka haɗu suna masa fatan alkhairi. Sai wajen ƙarfe biyar da Rabi ya nemi Mimi ta fito su ka tafi. A hanya ya ke tambayar ta halin da Amatullah ke ciki, ta amsa "Sai ka tausaya mata Dee, she is in pain, wallahi ta na ganin rayuwa" "She will be fine in Sha Allah, I will give her the best I can when we unite" Baki washe jin maganar Dee Mimi ta ce "Yessssssss! That's the spirit!" Dariya yayi, cikin ran sa ya na mamakin yanda Allah ya haɗa jinin Mimi da Amatullah. ***** Dee bai sau damar yiwa Amatullah gaisuwa ba sai da aka yi uku. Daga soro ta fito sanye cikin hijabi. Muryar ta dashe saboda murar da ya kama ta. Ya na mai tsura mata idanu ya ce "Amatullah, ki yi hakuri, Allah zai musanya mi ki da alkhairin sa, Allah na sane da ke" Kai ta gyada masa ala'amar "eh" sannan ta kara da "Ina wuni?" "Lafiya lau Alhamdulillah, ya hakuri?" Cewar shi cike da tausayawa. "Alhamdulillah" "Allah ya masa rahama, ya sa mai ceto ne" "Allahumma Aameen" Shiru ne ya biyo baya, daga bisani ya mata sallama ta koma ciki shi kuma ya koma wajan Baban Sasa. Duk wannan hidimar da ake yi akan idanun Saifullahi, idan akwai wanda ya tsana duk faɗin duniyar nan ya bi bayan Dee Yusuf. Nan ya kara shan alwashin tsananta tazara tsakanin Dee da Amatullah ta hanyar tunkarar Baban Sasa da maganar komen Amatullah, da zarar An yi bakwai din rasuwar Emjay. **** Ranar da aka yi bakwai da daddare Saifullahi ya sami Baban Sasa, Nan ya kalallame shi har ya na fitar da kwalla ya ke faɗin "Baban Sasa ka rufa min asiri ka mayar da aure na da Amatullah, wallahi na yi kuskure na yi nadama, ka duba girman zumunci ka min wannan alfarmar Baban Sasa, ka bani damar gyaran kuskuren da na yi, na ma ka alkawari zan zamo abin alfahari a gare ka" Ganin yanda Saifullahi ke fitar da kwalla, da kuma yanda ya rame yayi baki gaba daya ya fita daga hayyacin shi ya sanya zuciyar Baban Sasa karyewa. "Saifullahi" Ya kira sunan sa a sanyaye. "Na'am Babab Sasa" "Amatullah ta ce saki uku ka yi mata, ka yi hakuri" "Wallahi Baban Sasa daya dal na mata, ina ga zafin sakin ya sa ta dage a ukun na mata, Baban Sasa Amatullah na jin maganar ku, yarinya ce mai hankali, ladabi da biyayya, na tabbatar muddun ka ba ta umarni za ta bi, ka taimaka min Sasa" Ya kare cikin shasshekan kuka. Shiru Baban Sasa yayi ya na mai ɗan tuntuntuni, kafin daga baya ya furta "Kar ka damu Saifullahi, zan yi iyakan kokari na in Sha Allah, idan Allah yayi da rabo za ta koma, ka kwantar da hankalinka kar ciwo ya kama ka" Cikin jin daɗi Saifullahi ya riko kafafun Baban Sasa, faɗi ya ke "Na gode! madallah, na san za ka min rana, Allah ya saka da alkhairi, yanzu zuwa gobe za ta komo min ko?" Kai Baban Sasa ya girgiza ya ce "Nan fa daya, ka yi hakuri zafin mutuwar nan ya ɗan bar ta, nan da sati biyu haka sai a mata magana" Murna sai ta koma ciki, ran sa ya ki ya motsa dan kuwa gani yake in har ya tsaya kallon ruwa kwado zai iya masa kafa. "Amma Baban Sasa ba ka gani jinkiri na iya haifar da fitina?" "Fitinar me kuma? Ah ah kar ka damu in Sha Allah" Jiki sanyaye yayi masa sallama. Kai tsaye dakinsa ya nufa. Ya na zancen zuci ya manta bai yi sallama ba, kan gado ya tadda Ayush ta yi daidai cikin shigar nan nata da ta saba ta na bacci har da mun shari, shigar da take rikita Saifullahi da shi a da, Amma yanzu kuwa sam ba sa burge shi, bare ta ɗaɗa shi da kasa. Ya na mai girgiza kai har zai juya ya fita idanun sa suka sauka kan ɗan karamin kwalin magani gefe a ƙasa, haka nan ya ji ya na so ya ga maganin menene. Ko da ya ɗauka ya duba sai gashi an rubuta "emergency contraceptive" Ya faɗa , ya maimaita! Wai shi Saifullahi matar shi, matar ma ta so ce ke shan Emergency contraceptive? Wato tsabagen dan kar ta haihu da shi? Ɓacin rai ya sanya ya manta makoki ya ke, dan kuwa idanun sa sun kada sun jajur. Nan take ya karasa wajan Ayush. Sam be damu da baccin da ta ke ba cikin nuna isa, ya shiga neman hakkin sa. Duk yanda ta so ta kaurace masa ta kasa har sai da ya biyawa kan sa bukatan sa. Ta na samun ta kan, ta tashi cikin sauri naɗe cikin bargo, cikin tashin hankali ta shiga binciken maganin ta kwali daya dal da ya rage, domin kuwa ta sa a samo mata cikin unguwar ba a samu ba sai Jamila ta yiwa waya, ta mata alkawarin turo mata da shi nan da kwana biyu. Ya na daga kan gado ya ke kallon ta, ta ƙaraci dube duben ta, Amma babu magani babu alamar sa. Ganin babu sarki sai Allah ta dubi Saifullahi ta ce "Malam menene haka za ka far mani ina bacci kamar dabba! Wannan wani irin gidadanci ne! Kai wani irin bagidaje ne! God Saifullahi you so local! Too local for my liking! Wallahi da na san haka kake bagidaje da ban aure ka ba!" Yanda ta ke maganar ne, da kalaman ta da ke shigar sa kamar kibiya tsabagen ɗaci ya sanya shi tunawa da lafuzzan sa ga Amatullah, 'bagidaje? Shi Saifullahi ne matar shi ta aure ke kira bagidaje? local? Shi Saifullahi shi ne local?' Abin da zuciyar sa ke faɗi kenan, azahiri kuma kallon ta ya ke cike da tsana. [4/21, 10:26 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA BIYU WANNAN BABI SADAUKARWA NE GA DUK WATA UWA DA TA RASA ƊANTA, WALAU TA HANYAR ƁARI KO MUTUWA. UBANGIJI ALLAH YA BAKU LADAN HAKURI ƳA SA SU ZAMA MASU CETO A GARE KU. Much love UMDIJA❤️💖💕 "how? Menene ya same shi? Me ya faru?" Saifullahi ya sake tambaya jiki na rawa. Amatullah ta wuce ciki rugume da gawar Emjay, ɗakin Baban Sasa ta shige nan ta tadda shi kwance. Ganin shigowar ta ko sallama babu ya sanya shi tashi zaune, ya na mai faɗin "Amatullah lafiya?" Gaban sa ta shimfide gawar Emjay, ta ce "Ka ga Emjay Baban Sasa, lafiyan sa lau mu ka tashi, Wai dan kawai ya ɗan yi mika mu ka kai shi asibiti, likitan ya ce wai ya mutu!" Kallo ɗaya Baban Sasa ya masa ya san ko shakka babu tabbas babu rai jikin Emjay. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya faɗa da kakkausar murya. "Baban Sasa karya su ke, dan Allah ka tada min shi, Emjay tashi, tashi ɗan albarka" Ta shiga jijjiga kafadar gawar. Ganin haka Baban Sasa ne ya mike tsaye, hannun Amatullah ya kama, ya na mai janye ta daga jikin gawar, ta na cijewa, faɗi ta ke "Baba Sasa tsaya mu tashe shi" Fitowa yayi da ita, ya na rike da hannun ta su ka nufi cikin gida, Amatullah ba ta fasa waigawa ba tana cewa "Baban Sasa kar mu bar shi shi kaɗai cikin ɗaki, idan ya tashi bai ganni ba kuka zai yi" A haka su ka isa har ɓangaran Gwaggo, in da ganin Amatullah da Baban Sasa ya sa duka ahalin gida su ka biyo bayan su. A tsakar gida su ka su ka tarar da Gwaggo, cikin alhini Baban Sasa ya ce "Yaro ɗan wajan Saifullahi dai Allah ya amshi abin sa, sai ki masa addua Allah ya masa rahama, yanzu za mu shirya shi a kai shi" Salati Gwaggo ta saka, haka ma sauran jama'ar da ke gurin. Amatullah har lokacin ba ta fasa karyata maganar mutuwar ba. Gwaggo ce ta shiga da ita ciki, in da yanayin gidan gaba ɗaya I ya canza, daga masu kuka sai masu salati da sallallami. Baban Sasa ya koma ɗakinsa bayan ya shaidawa su Baba Anas a yi shirin yiwa Emjay wanka, a shirya shi cikin gaggawa, su Baba Idiris kuwa su ne su ka tafi makabarta domin haka kabari. Saifullahi zama yayi dirshen a ƙasa in da Amatullah ta bar shi tare da Mimi. Surutai ya ke mara kan gado tamkar wanda ya zare. A haka Baba Anas ya zo ya same shi, ya ce da shi maza ya zo a shirya ɗan sa tare da shi. Sai da Mimi ta nemi wayar Dee har sau wajan uku ta na Kira ba ya dagawa, daga bisani ta masa text, dan kila ya sa wayar a chaji ne ya shiga aji ya na bawa dalibai karatu. Gab da la'asar aka shirya Emjay tsaf. Kafin a fita da shi aka ce da Amatullah ta zo ta masa sallama. Mama ce da Mimi su ka kai ta dakin Baban Sasa. Sai da ta ga an rufe Emjay cikin lin kafani sannan ta yarda lalle da gaske mai raba ɗa da mahaifiya yau ta mata yankar ƙauna. Gaban gawar ta zauna, hannun ta bisa gawar ta furta "Yaro na? Ka na jin Maman ka? Yaro na naso ka, Ina son ka, Amma Allah ya fini son ka, ya karbe ka, na yafe ma ka, Allah ya rahamshe ka Emjay.....Allah....Alllah....Allah......" Kukan da ya ci karfin ta ya sanya ta kasa karasa maganar, kawai sai ta sunkumi gawar ta na kuka ta na faɗin "Ya Allah....Allah.....ya Allah!" Daga Mimi har Mama duka kuka su ke, shi kan shi Baba Anas hawaye ke gudana daga idanun sa, bare Baban Sasa, wanda ji ya ke dama shi mutuwar ta ɗauka ta bar masa ɗan jikar sa. Saifullahi wanda tun shigowar Amatullah kan sa ya ke sunkuye, ya taso daga in da ya ke, cike da tausayawa ya shiga kokarin karɓe Emjay, shi ɗin ma hawaye ya ke. Da kyar ya iya karɓan shi, su Mama su ka janye ta ciki. Nan ɗin ma su duka su ka shiryo cikin alwala don halartar sallah gareshi. Ba tare da ɓata lokaci ba aka sallaci Emjay, amma tun a kabbarar farko Saifullahi ya gaza, sai kuka haka har aka idar da sallah. Mata su ka koma cikin gida yayin da maza su ka doshi hanyar maƙabarta. Saifullah ya ɗauki gawar cikin tabarma lullube da zanin goyan sa, ya ki bawa kowa har su ka isa makabarta. Baban Sasa kadai aka bari waje bisa tabarma kasancewar jikin sa ba zai bari ya iya zuwa makabartar ba. Ganin har la'asar ta gota sosai ba su dawo ba ya sanya Baban Sasa tayar da sallar la'asar, hakan yayi daidai da isowar Dee Yusuf wanda bai sami sakon Mimi ba sai bayan da ya fito daga aji, kai tsaye ya nufo gidan su Amatullah. Ganin babu kowa wajan ya tabbatar ya makara an tafi kai Emjay. Dan haka gudun kar shi ma ya makara ya ɗora alwala, Baban Sasa ya kai raka'a biyun farko ya zauna tahiya shi ma yayi yi harama, ya na mai kabbara ya zauna gefen shi in da ya shiga mika tashi sallah ta hanyar bin Baban Sasa. Sai da su ka zauna tahiyar karshe sannan jama'ar da su kai Emjay su ka shigo layin. Sam babu wanda ya lura da wanda ke bin Baban Sasa sallah, sai da su ka zo dab da su, wato daga Baba Mahmuda, Baba Anas, Baba Idris, Baba Hamza, har zuwa Saifullahi tsayawa su ka yi cirko cirko suna duban su, hakan kuma yayi daidai da lokacin da Baban Sasa yayi Sallama, ganin yanda su ka yi tsaya kamar sokwaye ya sanya shi waigawa gefensa, me zai gani? Dee ya tashi tsaye ya na mai kabbara ya shiga rama raka'oi biyun da ya rasa. "Lahailaha illallahu!" Cewar Baban Sasa! "Kai Dan Yusuf dama ka na sallah?" Ya faɗa tsabagen mamaki ya ma manta ba a yiwa Wanda ya ke sallah magana. Shi kuwa Baba Idris hargiza yayi cikin nuna bacin rai ya ce "Isgilanci ne irin na arna! Mu za ka yiwa shakiyanci! Karya ya ke yi ba ya sallah! Yaudarar ku ya ke so yayi, dan ni wallahi babu arnan da zai yaudare ni!" Baba Anas na mai taɓa kafadar Baba Idris ya ce "Bari mu idar da sallah kila ma iya sauraran yashesshen zancen nan na ka!" Ya na mai duban sauran jama'ar ya ce "Ni dai ina da alwala, Idan da mai alwala ku zo mu yi jam'i ko? Lokacin sallah ya riga ya kure" Ya na gama faɗin haka ya cire takalmi ya bi bayan Dee, haka ma Baba Mahmuda da wasu makotan su biyu da su ma din su ka ce suna da alwala. Takaici ya sa Baba Idiris shigewa ciki. Shi kuwa Saifullahi sallah Dee zame masa ta yi tamkar an sake masa wani rashin, lalle lokacin komawar Amatullah yayi ko da kuwa da tsiya da tsiya tsiya ne sai ya sake mallakar ta, ba zai yiyu ya na ji ya na gani ya rasa Emjay ya rasa uwar Emjay ba. [4/23, 12:50 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA HUƊU Buɗe baki yayi don ya mayar mata da martani, Amma ya kasa cewa komai dan takaici, kallon ta ya ke in da har lokacin ta dage tsakanin ta da Allah neman maganin ta take. A fusace ta sake waigo shi ta ce "Wai dan Allah Saif menene haka?" Can ta sake wani tunani, cikin sigar kissa da tausasa murya ta ce "Saif wani kwallin magani na ke nima, dan Allah ba ka gan shi ba?" Hankali kwance ya na mai ɓoye ɓacin ransa ya amsa da "Wani cikin ɗan karamin kwali haka? An rubuta post pill kamar?" Ras gaban ta ya faɗi, ta na mai fatan Allah ya sa bai karanta kwalin maganin ba ya san maganin menene ta ce "Exactly, shi ne, maganin ciwon mara na ne" Sai da ya tashi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce "Eyaaaa Ina ga wani daban na gani ba wanda ki ke magana ba" Ta na mai hadiyar yawo dan jika makoshin ta tsabagen tashin hankali ta ce "Ba ni wanda ka gani din....." "Ni na ce mi ki na ga wani abu?" Idanun ta na mai kawo ruwa ta ce "Saifullahi don't play smart with me! Na san ka gani wallahi! Dan Allah ka bani!" Kallon ta yayi tun daga sama har kasa, sannan ya ce "Ni da na ke bagidaje how can I play smart? Kar ki matsa min dalla malama! Ina da abin yi! Shirin dawowar uwar gida na dakinta na ke yi!" Ya faɗa ya na mai kokarin wuce ta ya na mita, wani kukan kura ta saka ta na mai cinkwalar rigar shi ta ce "Burauban nan kayyasa! Kai ka isa! Na ce Saifullahi ka isa ka dawo min da wannan bakar yarinyar bagida....." "Ke Aisha!" Ya daka mata tsawa, cikin gurnani da daga murya ya ce "Wallahi na rantse da Allah ki ka sake ki ka zagi Amatullah sai na tattaka ki nan! Ta fiki daraja! Ta fiki ɗa'a! Ta fiki tarbiya! Ta fi min ke komai a rayuwa! Shasha wacce ba ta san ciwon kan ta ba!" Ya na gama faɗin haka bai damu da kukan da Ayush ta saka ba, ko zagin da ta rufe shi da shi, ya fizge hannun ta daga cikin rigar sa, nan ƙasa ya zubar da ita ya fito ya barta ta na kuka ta na surfa masa zagi. Bakin hanyar fita yayi kacibus da Hajiya ta na shirin shiga wajen na sa, cike da damuwa Hajiya ta ke duban sa, ta furta "Saifullahi gidan na ka lafiya kuwa? Duka gidan nan fa ihu da kukan matarka ake ji sai ka ce ana zaman bariki?" Saifullahi na mai girgiza ka ya ce "Hajiya menene bambamcin yarinyar nan da ƴan bariki? Ina ƴan bariki ne ke shan maganin hana daukar ciki gudun kar su yo cikin shege? Idan dai haka shi ne wayewa Allah wadar da wayewa irin na Aisha!" Hajiya na mai dafe kirji ta ce "Me ka ke faɗa ɗan nan!" Nan ya bawa Hajiya labarin maganin da ya tsinta ɗakinsa, ya kare da "Ko tausayi na ba ta ji ta na gani na rasa ɗana, ashe ita kuma ta na nan ta na min bita da kulle dukan kabarin kishiya! Hajiya tun rasuwar Emjay Allah ya jarrabe ni da kewar yaron nan! Ba ni da buri da ya wuce na sake ganin jini na Hajiya!" Kai Hajiya ta ke jinjinawa kawai, Saifullahi bai gushe ba ya kara da "Saboda haka na yanke hukuncin dawo da Amatullah, Hajiya Amatullah ita ce cikon farin cikina! Hajiya ba zan iya rayuwa idan babu Amatullah ba, Hajiya Amatullah kaɗai za ta iya sharen kuka na, Hajiya ku taimaka min!" "Amatullah fa ka ce Saifullahi?" Hajiya ta fada a sanyaye, Saifullahi na mai jinjina kai ya furta "Amatullah Hajiya" Cikin sauri kar Hajiya ta ga kwallan da ke idanun sa yayi sauri ya wuce ta ya fice. Jim Hajiya ta tsaya ta na mai jinjina maganar dawo da Amatullah, tabbas ta san Saifullahi bai yi sa'ar mace ba, dan kuwa Ayush sam ba macen arziki ba ce, ga kuɗin ga wayewar amma babu hali bare a moru da ita, ita sai da so samu ne da Saifullahi ya duba ya nemi wata diyar masu hannu da shuni, ko da kuwa nan cikin Zaria ne ba sai ya kai Kano ba, tunda diyar Kanawan ba ta zo da halin kirki ba. Da wannan tunanin ta ja jikin ta ta koma na ta bangaran kafin Aysuh ta fito ta Bata rabon ta. Daren ranan duka gidan kwana aka yi ana gulmar Saifullahi da matar shi, dan kuwa zagi da ihun ta babu wanda bai ji ba. Ita kuwa Amatullah fama ta ke da period da ya yi mata bazata tsabagen tashin hankalin da ta shiga na rashin Emjay. Washagari duk yanda Ayush ta hargitsa gidan domin neman maganin nan, sama ko kasa ba ta gani ba. Hauka ne kawai ba ta yi ba. Gashi tun daren jiya ta ke neman wayar Jamila amma ta kasa samu, sai da yamma dabara ta zo mata, ta kira gidan su ta ce da Mahaifiyar ta dan Allah ta tura ko da driver ne gidan Jamila ta na so ta yi magana da ita amma ta kasa samin ta. Mahaifiyar ta ta tambaya lafiya? Ya ta ji muryar ta haka. Ta na mai tabbatar mata lafiya lau kawai dama da sakon da za ta tura mata ne amma ta ji ta shiru. Da wannan ta amince ta tura driver gidan Jamila amma ya tarar ba ta nan. Hakan ya sa Ayush kara tsanan Saifullahi, ta kuma sha alwashin ba za ta kara bari ya kusance ta ba matukar ba maganin nan ta samu ba. *** Sati biyu da rasuwar Emjay Amatullah ta koma makaranta, duk abin da take babu wani walwala dan kuwa har lokacin ba ta daina kukan rasuwar ɗan na ta ba. Cikin dare ta sha kukan ta kenan yanda ta saba kafin ta yi bacci ta ji wayan ta na kara. Da kamar ba za ta ɗaga ba daga bisani ta sake shawara ta daga. Gaban ta ne ya fadi jin muryar da ya bakunci kunnen ta ya na mai faɗin "Assalamu Alaikum" Ta na mai gyara kwanciya, murya dashe ta amsa da "Waalaikumus salam" "God kar dai har yanzu kuka ki ke yi? Um Mama nah?" Yanayin muryar tashi da kuma yanda ya ke mata maganar ne cike da rarrashi ya sa ta kasa amsa masa ta na mai runtse idanu. Babban farin cikin ta tun bayan rasuwar Emjay shi ne labarin musuluntar shi da ta ji Baba Anas Yana yiwa Baba Salihu bayan dawowar shi satin da ya wuce. "Amatullah....." Ya sake kiran sunan ta. Amatullah ta masa da "Um" Ya furta "Ki yi hakuri Mama na...." Shiru ne ya ƙara biyo baya, dan kuwa wani nauyi da kunyar Dee ta ke ji na babu gyara babu dalili. Dee kuwa da ya san ba amsa masa za ta yi ba ya kara da "Dee ne sorry I called you this late,I couldn't help it, you keep crossing my mind. Amatullah I've been trying to stay away from you kasancewar sai kin gama idda" Cikin zuciyar ta fadi take 'na kusa gama Idda Dee, na yi period har sau biyu bayan mutuwar aure na, na ƙarshe nake jira' Azahiri kuma shiru ta yi masa, sai murmushi kawai ta ke tamkar ya na ganin ta "amma abin na neman rikita tunani na, ba na so na rasa ki a karo na biyu duk da dai ban sani ba ko kina da wanda ki ke so already......." Ji ta yi kamar ta na jiyo bugun zuciyar ta tsabagen yanda gaban ta ke faduwa, idanun ta runtse yayinda murmushi ya bayyana a fuskar ta Jin Dee ya ce " Idan ma akwai, I will still fight for sai in da karfina ya kare, please let me know idan kin gama idda sai na zo mu yi magana idan kin amince sai na tunkari tsoho mai ran karfe da sojoji na, I love you Amatullah, I still do. Allah ya tashe mu lafiya" Ya kashe wayar. Wani irin daɗi ne ya ringa ziyarta zuciyar Amatullah yayin da maganar Dee ke mata shawagi cikin kwakwalwar ta "I love you Amatullah, I still do" Tun bayan rasuwar Emjay Amatullah ba ta sami baccin kirki ba sai a daren ranar. Ta yi bacci mai nishadi, cikin dare ta tashi ta yi nafilan dare ta yiwa Emjay addua tare da neman taimakon ubangiji akan maganar Dee. **** Kamar yanda Amatullah ta tashi cikin walwala, haka Aysuh, dan kuwa ta samu Jamila ta turo mata maganin nan fargaban kar Saifullahi ya mata bazata irin daren rannan ya kau, dan tun ranar ba ta kara yarda sun hada shimfida ba. Gogan na ta kuwa tun da garin Allah ya waye ya je kofar gida ya zauna, ya kasa ya tsare ya na jiran fitowar Amatullah ko ya ganta ya sami sanyi cikin ran sa. Ile kuwa sai gata ta fito cikin shigar nan nata da ta saba. Ganin ta ya tashi da sauri ya na faɗin "Amatullah an fito?" Fuskarta babu yabo ba fallasa ta amsa da "Eh, ina kwana ya Saifullahi?" Ya na murmushi jin dadin yanda ta amsa masa ya karasa gaban ta, tare da faɗin "Lafiya lau, kin tashi lafiya? Ya karin hakurin na mu?" "Alhamdulillah" Ta amsa a takaice. Saifullahi be gushe ba ya ce "Amatullah ina so ki san na yi matukar bakin cikin rashin ɗan mu, Amma babu komai Allah da ya karbi Emjay zai ba mu wani in Sha Allah" Daga idanu ta yi ta kalle shi jin kalaman shi na karshe, ganin yanda ta ke kallan sa ya gyara tsayuwa ya ce "Wato Amatullah ina so ki yi hakuri ki mance rayuwar da mu ka yi a da, ki sani cewa na yi nadamar duk kurakurai na, haka kuma na yafe na ki kurakuren, ina fatan za ki yafe nawa, ya kamata mu sasanta mu gyara zumuncin mu, abin da ya wuce ya wuce....." Fuskarta ɗauke da murmushi irin na ya ke ta ce "Ya Saifullahi na makara, bari na tafi makaranta dan Allah" "Oh maganar tawa ba ta da muhimmanci Amatullah?" Kai ta girgiza tare da faɗin " Ko kusa ba haka na ke nufi ba" Amsar na ta ya bashi damar faɗin "Na sani Amatullah, na san ki na so na, kamar yanda ni ma na ke son ki, duk abin da ya faru tsakanin mu sharrin shedan ne" Nan zaton Amatullah ya tabbata, na Saifullahi ya ɗan fara samun matsala sanadiyar rikicin matar shi, dan shi ne kadai bayanin yanayin da ya ke ciki. Sai a sannan ta lura da lalacewar da yayi, yayi baki ya rame. Ta na mai kallan agogan hannun ta ta ce "Ya Saifullahi na makara, bari na tafi" "Toh ko na sauke ki ne......?" "Toh tantabara uban Alkawari! Idan ka gama yamadidin ka zo ina jiran ka!" Cewar Ayush, wacce ta leko ko mayafi babu bare hijab sanye cikin kananan kaya riga da siket. Hannun ta rike da kugu. Kallo ɗaya Amatullah ta yi mata cikin ran ta tace 'eh lallai wayayye sai wayayyiya' A zahira kuma kallon Saifullahi ta yi, wanda kunya da takaicin Ayush ya lullube shi kamar kasa ta tsage ya shige, ta ce "Ah ah ba dumuwa, zan tafi kawai, na gode" Ta juya ta yi tafiyar ta, ta na jiyo Ayush na faɗin "To ko za ka bi ta ne? Ina ga kai ka ce bagidajiya ce amma ji yanda ka ke makalkale ta kamar bunsuru!" A fusace ya nufota ya na fad'in "Ni ne bunsurun Aisha? Me ya sa ba ki da mutunci ne ke" Ayush ta shige ciki da sauri Saifullahi ya bita ya na faɗa tamakar mahaukaci. Jama'ar gidan har sun saba da ya wuce sai a bishi da zunde da baki, su Baban Sasa kuwa suna sane su ka masa kunne uwar shegu, babu mai shiga lamarin sa tun ranar da yayiwa baban Sasa dibar albarka har ta kai shi ga kwanciyar abisibiti. *** Hutun mid semester ta dawo bayan sun shafe sati tara suna karatu,ganin zarya daga amaru ba zai fishe ta ba ya sa ta koma wajen mimi suke zaune a ɗakin ta, sosai ta ke jin sassauci na damuwar rasuwar Emjay, da taimakon Mimi, da addu'a har ma iyayenta ta samu ta ɗan ribaci damuwar. Zaune take tana taya Mama gyaran Alayyaho yaro ya shigo ya sanar mata da saƙon Baban Sasa. Ba ta kawo komi ba ta isa gareshi amma ganin Saifullah, Baba Anas, Baba Salihu da Baba Zubairu zaune ya sa ta ɗan sha jinin jikinta. Gaida su tayi sannan ta samu waje ta zauna cikin zulumin kiran da ake mata. "Amatullah!" Baban Sasa ya kira ta ya na mai kallon ta. "Na'am" Tace cikin sanyin murya. "Mijinki ya zo ya same mu nan ya ce ya maida aurenku, kamar yadda musulunci ta bashi damar maida aurenku. Ki yi hakuri, ki rungume ƙaddararki ki cigaba da biyayya. Ubangiji Allah ya miki albarka ya dubi gabanki da bayanki" Baban Sasa ya ce yana mai yin fuska irin na tausayi da rokon alfarma ta amshi bukatarsu. Shiru ya biyo bayan wajen, murmushin da ke fuskar Amatullah ya sanya ma Baban Sasa saukin raɗaɗin da yake ji na ganin kamar bai kyauta mata ba, don shi burinsa ɗaya ya buɗe ido ya ga Amatullah da Ɗan Yusuf a matsayin ma'aurata, ɗazu kamar ya taya ma Dee da ya kawo masa ziyara amma baya son abin da zai sa a gaba ya kalli Amatullah da wannan duban, hakan ya sa ko da wasa bai taɓa yi ma Dee yusuf maganar ta ba shi ma bai masa ba. Bayan fitar Dee ne Saifullah ya shigo masa a fujajan ya sanar masa ya maida auren Amatullah, tunda yana da yaƙini ba ta fara jini ba, yanzu kila ta fara tun da ba shayarwa take ba. Bai amsa masa ba sai da ya tara iyayensa sannan ya aika a kira Amatullah. "Yanzu sai ku natsu ku fahimci juna tare da tsaida ranar tariya" Baban Sasa ya ƙara ganin tayi shiru tana murmushi. "Baban Sasa ai na fita idda tun sati uku zuwa huɗu da suka wuce" tace tana sunkuyar da kai haɗe yin murmushi mai sauti. Ajiyar zuciya Baba Salihu da Baba Anas su ka yi a tare. "Ƙarya ta ke wallahi Baba, ai mace bata al'ada in tana shayarwa kuma bai isa a ce tayi tsarki uku bayan rasuwan Emjay ba" Saifullah ya ce a rikice. "Na rantse da Allah" tace cikin ƙara gaskata kanta. "Baba a kira Mama ita ce shaida, tun Emjay na da wata shida na fara, kuma ban taɓa tsallake wata ba" tace tana mai neman agajin Allah don gaba ɗaya bata yi tunanin zai ƙaryata. "Kwantar da hankalinki Amatullah, rabu da shi da guntun jahilcin da ke ɗan tafiya da shi" Baba Anas yace yana mai jan tsaki a ƙarshe. "Ke haka ake yi ba sanarwa, ai sai ki faɗi gudun faɗawa halaka" Baban Sasa ya ce yana mai jin wani iri a zuciyarsa, ba zai ce yana cikin farin ciki gaba ɗaya amma tabbas ya dawo daga rakiyar auren Saifullah da Amatullah. "Yanzu ai shike nan, tun da kin gama idda ke ce ke da damar zaɓa ma kanki miji, muna masu baki shawara da ko ji tsoron Allah yayin zaɓenki. Allah ya tabbatar da Alkhairi" Baba Anas ya sake faɗi, nan saura duk suka mara masa baya. Mutuwar zaune Saifullah yayi, ya rasa ina zai tsoma kansa, kallon su yake kamar mai neman ɗauki. Gaba ɗaya rayuwa ta tsaya masa chak. Ta ina zai fara, ya san ba yanda za a yi Amatullah ta saurare shi, kamar ba wata hanyar da zai sa a mata dole. Hakan ya sanya bai ko san sanda Amatullah ta fice daga ɗakin ba, dawowa yayi daga duniyar tunani ya iske babu Amatullah ba mahaifinta a ɗakin. Ba ƙaramin natsuwa ta samu ba ganin babu wanda ya tursasa ta akan amince ma Saifullah, da farin ciki ta baro ɗakin, ba ta yi tafiya mai nisa ba Mahaifinta ya tsaida ita, shi kanshi yayi farin ciki da ganin farin ciki kwance akan fuskar ƴar sa. "kiji tsoron Allah Amatullah, in kin tabbatar da saki uku ya miki ki sani babu sauran halaccin zama tsakaninku har sai kin yi wani auren, amma in dai shi ke da gaskiya kiji tsoron Allah, kada ki haramta masa abin da Allah ya halalta masa, babu mai miki dole" yace mata suna masu jerawa zuwa sashin su. "Wallahi Babanmu sau uku yana furta cewa ya sake ni" tace cikin shagwaɓa. "toh shi kenan. Allah yayi albarka" yace yana murmusa mata. "Aameen Yaa Rabbi" *** Tun kusan sati biyu da ya wuce ya kamata Ayush ta ga period din ta, Amma shiru ta ke ji, abu tun ba ya damun ta har ya fara ba ta tsoro. Babu shiri ta kira Jamila ta shaida mata halin da ta ke ciki, ta kare da "Wallahi idan har cikin Saifu na ɗauka sai na zubar!" "Dole ki zubar Ayush, ko ni ba zan ba ki shawarar haihuwa wannan gidan en kauyen ba!" Cewar Jamila cikin jaddadawa. Kana ta kara da "Kin san Allah tun wuri ki nemi pregnancy test strip, da kin ga positive ki kira ni, kuma kar ki bari kowa ya sani, in da hali ma ki fita ki samo da kan ki" Aysuh ta tashi cikin sauri kamar wacce aka tsikara, ta ce da Jamila "Yanzu ma kuwa" Ta kashe wayar. Cikin kankanin lokaci ta samu ta shirya, ta yi ficewar ta ba tare da ta faɗawa kowa ba. Sai da ta taka da kafar ta har zuwa titi sannan ta samu chemist ɗin da ta siya. Da kyar ta iya dawowa gida tsabagen gajiya. Sai kuma da ta dawo tsoro da fargaban result din ya sanya ta kasa yi nan ta ke, ta yanke hukuncin bari sai da safe ta na tashi daga bacci dama ya fi ba da sakamako mai kyau. Daren ya mata tsawo sosai, a kan kunnuwarta aka yi kiran sallah farko, cikin sauri ta shiga bahaya ta yi fitsari tare da tsoma tsinken gwajin. Ganin yanda layuka biyu ke ƙara fitowa raɗa raɗa ya sanya ta firgita, Sam ta manta cewa sun yi da Jamila akan kada wanda ya sani. "Wayyo! Saifullah ka cuce ni, Allah ya I'd shege tsinanne" ta ce iya ƙarfinta tana sakin robar fitsarin a ƙasa. A firgice ya tashi ya nufota yana tambayar lafiya, ransa duk a jagule saboda tabbacin ahlin gidan sun gama jiyo ta. Idanunsa suka fara sauka a tsinken gwajin sakamakon ya fito raɗoraɗo a kai, bai san lokacin da ya sa hannu ya ɗago ta tare da haɗa ta da jikinsa ba, dukansa take ta ko ina tana zagi don gaba ɗaya cikin da ta tsinci kanta da shi ya fi kibiya zafi a ƙahon zuciyarta. [4/24, 12:28 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: [4/23, 6:30 PM] +234 809 229 4372: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA BIYAR TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA BIYAR "Ban kyauta ba na sani Babe, kin dai san ke nake so, ki yi shiru ki faɗa min abin da kike so ayi, yanzu kina ihu cikin dare kowa zai san ciki gare ki kuma ba za mu iya ɗaukan ko wani mataki ba" yace mata cikin raɗa, sai a lokacin ta tuna zancen ta da Jamila, take ta haɗiye duk wani kuka da kururuwa da ya ke zuwa mata. "Ba wai bana son haihuwa da kai bane honey pie, Kai ma ka san son da nake maka ya sa na bar kuɗi da jin daɗin rayuwa don na kasance tare da kai" tace ganin ya bata goyon baya, ita kanta ta san wasu abubuwan da take masa ne ya sanya ya ke mata abin da ya ke mata, itama ba yin kanta bane, shi ya kulle ta a akurki. "Na sani babe, amma ai baki taɓa natsuwa kin min bayani ba, na taɓa hana ki abin da kike so ne?" ya sake fadi bayan ya janyeta daga bahaya zuwa cikin ɗakin ta su ka zauna a kan gadonta. "Tell me what you want babe, your wish is always my command your highness" yace mata yana kallon cikin idon ta. Nan ya mata kwarjini sosai ta kasa cewa komi, shiru tayi ta sunkuyar da kai amma tunawa da tayi dama na zuwa ne sau ɗaya in ta wuce dole sai mutum ya jira wata. "A cire cikin nan don Allah, mu jira har mu koma gidan mu, ka ga a gidan nan wace tarbiyya zamu ba yaya, ko mun yi a ɗaka da ya shiga cikin gida za a wargaza masa" ta faɗi a hankali. Kiris ya ƙunduma mata Ashar, amma ya danne saboda in ya biye mata da faɗa shi ke da asara in ta zubar. "Haka ne kuma fa, kinga ban taɓa tunanin nan ba, yanzu dai ki bari sai mu kai ayi flushing din sa out, this week will be a very busy week Amma I promise you ba za a wuce next week ba zai bi ma kwararar" yace yana rungumarta, ji yake kamar ƙaya yake runguma a jikinsa, tunanin dole ya nemo yanda zai shawo kan Amatullah yake don tabbas itace macen rufin asiri macen arziki. Lallashinta ya dinga yi yana mata alkawura na ƙarya da in da kan aurensu ne toh tabbas za su zama na gaskiya ne. Kiran sallah na biyu ya tayar da shi daga gareta, alwala yayi ya gabatar da raka'atanil Fajr sannan ya wuce masallaci. Daga yanayin kallon da ya ga iyayensa na masa ya san tabbas sun ji muryar Ayush, addu'a yayi Allah ya sa Hakan ya sa su tausaya masa su maida masa da auren Amatullah. *** Sati ɗayan da ya wuce babu abin da yake sai fafutukar son Magana da Amatullah, kasancewar ta koma makaranta ya sanya abin ya masa wahala. A tunaninsa hostel take, sai ya kwashi jiki ya je gaban Amina hall ko Ribadu hall ya zauna yana ƙirga masu shiga da fita hostel ɗin. Ganin hakan bai cika masa burinsa ba ya koma zaman faculty of pharmaceutical sciences. Nan ma haka yake ƙarasa shawagin sa ba tare da ya ganta ba, sau biyu yana hango ta a aji suna ɗaukan darasi nan zai hakince ya jira amma kamar wacce ke rufe ido ba ya sanin lokacin da suke ficewa. Asali duk zuwan shi Mimi ce ke ganinsa sai ta fitar da su ta wata ƙofar ba wanda ya ke jira ba. "Ai nan gani nan bari malam" takance a ranta a duk lokacin da ta hango shi. Ya kan kira Amatullah amma in zai kira sau ɗari ba ta ko ɗagawa, haka saƙonni daban daban na ban hakuri, soyayya da alkawari duk sai dai ta karanta ta share. Yau ma kamar yanda ya saba ya shigo sashin na su, ya iske suna karatu, nan ya nemi izinin malamin akan yana son ganin matarsa. Amatullah bata an kare da shi ba sai ganin da tayi yana nuna ta da yatsa. Nan malamin ya kalle ta ya ce " Oya Go and meet your husband" ji tayi duk wani bakin ciki ya taru ya tsaya mata a maƙoshi, niyyarta ta ƙaryata saninsa amma tunawa da tayi kallon matar aure ake mata har lokacin ya sanya ta mike jiki a sanyaye. Tana fita ta tsaya a kansa ba tare da tace kanzil ba, "Don Allah muje ki bani minti ɗaya kacal, don Allah ba don ni ba" yace kamar zai mata kuka. Da har za ta juya sai kuma wata zuciyar tace da ita ta bishi. Sun Kai daidai matakalar benen da za ta saukar da su ƙasa su ka ci karo da Dee ya hawo kenan. "Cutie ina zuwa ne haka, Prof ya fita ne" yace yana mai tsare ta da idanu yana mai isar da wani irin saƙo mai narka zuciya. Murmushi ta yi tare da raɓewa gefe, ita ba ta sauka ba ita ba ya juya ba. Waigawa yayi ya ga Saifullah ya tsaya yana huci kamar kumurci. Dawo da kallonsa yayi gareta ya na mai murmushin da ke rikitata ya ce "okay Mamana" yace yana mai sunkuya mata kamar mai ladabi haɗe da nuna mata hanya ta wuce. Sai da ta zo daidai saitinsa sannan ya ce "I love you" cikin amon da hatta Saifullah da yaji sai da tsigar jikinsa ya tashi saboda sanyin da amon ya fitar. Tsaki ya ja yayi gaba, Amatullah kuwa da yake jin kanta kamar wacce ke yawo a gajimare da kyar ta iya kai kanta ƙasan bene inda Saifullah ke tsaye. "Kar dai ki ce iskancin da kike kenan a makaranta kina zubar da mutuncin hijabi" yace a hasale "ka ga ai wainda ba sa son ganin iskancin ba su biyo ni ba, lafiya kake nema na" Tace cikin tsiwar da ita kanta bata san tana da shi ba. Kallon ta yake cike da mamaki, don shi a iya zaman da su ka yi na shekara biyu a matsayin mata da miji zai rantse ko Yatsa aka sanya mata a baki furzarwa za ta yi ba za ta ciza ba. "Ki dubi girman Allah ki amincewa son da nake miki, Amatullah wallahi duk lalacewana ba kamar tubabbe ba wanda ba tabbas a musuluncin sa, wallahi Amatullah warin Arnanci yake dana wuce shi" yace yana mai rage murya zuwa na mai roƙo. "Allah" tace a mamakance. "Wallahi kinji na rantse miki" yace yana yar dariya, itama taya shi dariyar ta yi kana ta ce. "ni kuwa sai nake ganin kamar warin nan ya fi komi tafiyar da tunani na, amma dai ka bani lokaci zan yi istikhara akan aurenmu. Kuma ka ga jarrabawar mu na kusanto mu, zuwa dai ƙarshen semester dinnan sai mu tsayar da magana. Bari na koma aji kar na rasa da yawa" Juyawa tayi tana kai aya. Farin ciki sosai ya shiga yi, don gaba ɗaya ya hango nasara ne a cikin haka. Tayi dan tafiya kaɗan ya ɗan ɗaga murya ya ce "Don Allah a dinga ɗagan waya" Kai kawai ta ɗaga ta wuce abin ta. Addu'a ta ke ta sake ganin Dee don tun da ya kirata din nan ba ta sake ji daga gare shi ba, ya kan aiko mata da kyaututtuka da gaisuwa daga Mimi amma bai kira ta ba balle ya nemi ganin ta. Addu'ar ta bata amsu ba don bata ganshi ba, aji ta wuce ta iske malamin ya fita, Mimi kuwa kallon tuhuma take ta mata, sai ta bata dariya. "Kin san tun last week yake zarya" Mimi tace tana yamutsa fuska. Dariya Amatullah tayi ta ce "Wallahi ba ki da kirki, baban babyn naki" "A'a fa shi da kanshi ya ce ba na shi bane, atoh!" nan din ma dariya Amatullah ta yi sosai, ita kuwa mimi cunkus tayi kamar za ta fashe. "Wai har period nawa ake a gama waiting period din ne" Ta tambayi Amatullah cikin tuhuma, dariya tayi ta ce. "Wani waiting period kuma, ba ki ga sai samari nake yi ba, ai yanzu yanda kika san iska haka nake free" tace tana mai shagala hannu ta wuyan Mimi. Ita kuma ba ta ce komi ba sai wayar da ta kara a kunne. "Kasan Allah Dee ta gama, ka tsaya kana kallon har kwaɗo ya maka ƙafa" ta ce tana katse wayar, ba ta ce ma Amatullah komi ba, ta haɗe littafanta ta saka a jaka, ta fice daga ajin a nufin ta yi fushi. Cikin sauri ta bi ta, tana mata magiya. "Ai na ga baki da kirki ne, and I wanted telling you something, shike nan kowa ya riƙe sirrin sa" tace tana fisge hannun ta da ta kamo. "Nooo Mimi, wallahi ba haka bane, kiyi hakuri, kin san dai a kan Dee na san soyayya, kuma so ɗaya shi na ba, Haba ƙanwata" tace tana mai rungumarta. Dariya Mimi tayi kana ta ce "Laa ilaha illah Allah Muhammad Rasulullah, tabbas babu addinin gaskiya sama da musulunci, na yi imani da Allah ɗaya ne kuma Annabi Isah Annabin Allah ne ba ɗansa ba" Kuka Amatullah ta saki, kuka sosai take tana rungumar Mimi. "Muje Mimi kiyi wanka, Mimi kin musulunta, Mimi yanzu duk wani zunubi da kika aikata an yafe miki, Mimi littafinki sabo ne dal babu datti ko ɗaya a ciki" Amatullah tace kamar mai sumbatu, abin da bata taɓa tunani ba, bata taɓa taya ma Mimi musulunci ba tana dai ƙokari wajen haska mata ni'ima da ke tattare da musulunci. "Wai tun yaushe kika niyyata" tace mata yayin da su ke tafiya. "Tun bayan musuluntar Dee, sosai yake bani littafai na musulunci ina ganin babu addini da ya daraja mutum sai musulunci, it's a religion full of humanity. A musulunci fa na ga in kana son ka ci nasara sai ka sa wani yayi nasara, a musulunci na ga yanda ake bayani akan duk abin da ya shafi rayuwa, daidai da yanda za a zauna a toilet. Maman Emjay sai in na yi comparing da halin musulmi sai naga gaba ɗaya ya sha bambam da abin da ke littafansu. Dan zaman da muka yi da ke, naga yanda kike da tsantsan amana, idanunki basu taɓa rufewa akan abin da zaki samu ba balle ki hillace mutane ki samu, naga abubuwa da dama kina kamanta yanda aka siffanta manzo SAW ne, sai na yarda da cewa, lallai musulunci ba halin musulmai kaɗai za a duba ba, a karanta a Santa sai a kamanta. Dee ya taɓa ce min in duniya sun haɗu suna aikata abu, ba zai taɓa canza haram ya zama halal ba, abubuwa dai da dama mai cike da jinkai na gani a musulunci" Tun da ta fara Amatullah ta ke kallonta, zuciyar ta fal da farin ciki, godiya take ma Allah har su ka isa. *** Ayush ta gama amincewa da kalaman Saifullah, hakan ya sanya gaba ɗaya ba ta tuna ta nemi Jamila ba har sai da ta ga an yi satin da ya ce aiki zai masa yawa, an yi na biyu ana sati na uku sannan hankalin ta ya tashi. "Saif ni kam wai me muke ciki ne" tace bayan ta tsaya jiran sa har ƙarfe sha biyun dare da ya kan shigo mata gida. "ki duba ki ga fa yanzu nake dawowa, na gaji aiki ne sai godiya wallahi, amma ki shirya jibi inshaAllah sai mu je" yace yana wuce ta zuwa ɗaki. Bata musa masa ba ta amince. Haka su ke rayuwar su, ba a sake jin su ba amma kuma ba wai suna cikin jin daɗi bane. Ko da ta ga an ƙara kwana huɗu sai ta kira jamila, ba ta ɓoye mata komi ba ta faɗa mata. "Amma ban san ke ɗin wata bi can bace sai yau wallahi. Aka ce miki zai amince ne, kuma kin san ƙarin sati huɗun nan ƙarin wata ɗaya kenan. Gobe zan aiko miki da maganin nan" tace a hasale. "nagode Jamila you are indeed a savior" tace cikin farin ciki. Washe gari ko da aka yi azahar an Kira ta saƙonta da aka sa a filin parking ya iso zaria, cikin murna ta figi motar ta taje ta amso. Sai da ta karanta takardar maganin sannan ta haɗiye guda biyu ta je ta kwanta. Tun tana tsumaye ta ji shiru ba ta ga komi na fita daga jikinta ba. Haka ta yini kwance tana jira, da ta gaji da jira kuma ta fara dubawa nan ma shiru ba komi. Ganin har an kwana an tashi cikin bai motsa ba ya sanya ta ɓalle kwayoyi huɗu ta jefa a baki bayan ta gama cin kalaci. "in aka yi azahar baka fita ba don uban ka sauran huɗun zan haɗiye" tace tana ajiyewa kusa da ita. Bacci ne yayi awon gaba da ita, cikin bacci ta fara jin murɗawan ciki kaɗan kaɗan, ta ɗauka duk wasan yara ne sai da taga gaba ɗaya ta kasa motsin kirki, ga jini ya ɓalle mata ga bayanta ya riƙe sosai. Da kyar ta ɗago wayarta ta kira saif yana ɗaga wa tace "zan mutu Saif zan mutu" "Hello! Hello!!" yake faɗi amma ina bakin nata ya ɗauke gaba ɗaya. Hakan ya sa shi zuwa gidan cikin sauri, ko da ya ido a sume ya ganta cikin jini, ɗaukan ta yayi ya fice ba tare da nemi ɗaukin kowa ba. Asibiti mai zaman kanta nan kusa da su ya kaita, babu ɓata lokacin aka fara dubata. Addu'a sosai yake yi da fatan Allah ya sa ta tashi don bai san me zai ce ma iyayenta ba in ta mutu. Awa uku yayi zaune yana jira kafin likita ya fito ya nemi ganin sa a ofishin sa. "Gaskiya akwai abin da ta sha da ya nemi ɓarar da cikin jikinta, an yi hoto cikin na nan ɗan sati goma sha biyu da kwana uku. Sai ta huta sosai, sannan sai ta kiyaye abin da za ta dinga kaiwa bakin ta saboda lafiyanta da na yaron" yace masa bayan sun gaisa "Na gode Dr." Saifullah yace yana miƙa masa hannu. Sai yamma lis suka koma gida bayan ta sha ledan ruwa ta dawo da ƙarfinta kaɗan. "Don Allah Ayush kiyi hakuri, kinga garin gajen hakuri kin sa rayuwarki a hatsari. Gobe nake da niyyar kaiki fa, amma kin kasa yarda da ni, yanzu Dr yace any attempt is a threat to your life" yace yana share kwalla, shi hawayen farin ciki yake na yanda Allah ya kare masa ɗan cikin sa, ita kuwa gani take hawayen so da tausayin ta yake yi. "Naji, amma gaskiya mu bar gidan can, na tsani gidan ni shine kawai damuwata da kai" tace a wahalce. "daga kin haihu zan kama mana haya, it's a promise. Yanzu kiyi hakuri, ko don samun masu miki hidima ki yi hakuri" haka ya dinga bata baki har su ka isa gida. Nan ya shiga ɗakin hajiya ya tasa su Najaatu ya sanya su gyara gidan da sanya turare. Suna kammalawa ya sa su yin girkin da za su ci. Ba su suka samu kansu ba sai wajen bakwai na dare sannan suka sallame ta ba tare da sun bata ki cokali ta lasa ba. Tun daga ranar Ayush ta maida Najaatu mai aikin ta Sam babu kyautatawa balle tausayawa. A rana sai ta mata girki kala biyar, kala shida ita ba a bata taci ba sannan Ayush ba lallai ta ci ba, a ƙarshe sai ta iske a wanke wanke an ajiye ta wanke raguwa. Ba ta taɓa fadi ba amma ta fara ba almajirai raguwan abincin da ta gani cikin wanke wanke. Haka ya faru yau, ta yi farfesun kifi, tun yanka biyu da Ayush ta ci ta ajiye saura, Saifullah da ya zo ya dan taɓa kaɗan aka bar kifi cikin tukunya. Ko da Najaatu ta ga tukunyar a cikin wanke wanke sai ta fita ta nemi Almajirai ta basu da sauran cuscus su sake. Ta shigo da tukunyar kenan Ayush ta fito inda take wankewaken ta ganta da tukunyar abinci. Ba ta tambayi ba'asi ba kawai ta fara dukanta, duka sosai ta ko ina. "Shegiya ɓarauniya meye na kwasan min abinci ki kai ma mayunwaciyar uwar ki, ba cewa nayi ki wanke ba? Ko baki nayi?" tace cikin hayagaga wanda hakan ya tunzura Najaatu ta tunkuɗeta da faɗin "uwar ki dai na aika mawa" hakan yayi daidai da shigowar Saifullah da Hajiya da aka je aka faɗa mata kamar dukan Najaatu ake. "Baki da hankali ne Naja, uwar wa kike kira haka, da kika tunkuɗeta in wani abin ya same ta fa?" ya ce yana taro Ayush. "ai ba laifin ta bane, ka ga wacce ke aiko min ita nan, kai ba zaman gidan nan kake ba, ni kuma bana son ka dinga ganin bakinsu wallahi kashe ni suke da niyyar yi" Ayush ta ce tana rushewa da kuka. "Ke Naja me ya haɗa ku" faɗin Goggo da ta shigo Sasan don a idon ta Najaatu tayi rabon abincin. Tiryan Tiryan ta faɗi masu buɗe bakin Saifullah sai cewa "Toh in ba sata ba me kika yi? cewa aka yi ki ba almajirai, don ta ce uwar ki kika kai ma abincin ƙarya tayi? Ko ba ɗan kuka ke jawo wa uwarsa jifa ba" ya faɗi yana yunkurin marin Naja. "Saifullah a kan ido na ta sake ma Almajirai" Goggo ta faɗi tana mai janye Najaatu. "Toh Goggo in ba hajiya ta kai mawa ba ai hajiya ta sanyata, gaskiya hajiya ki fitar da idon ki akan iyali na, ke kenan ki rasa wacce za kiyi gasa da ita sai matar ɗanki? Ina aka ce dole se na ciyar da ke tunda kina da miji, in dadin kike son ci mijinki ya miki itama mijinta ke mata Haba " yace cikin tsawa tsawa, Hajiya mutuwar tsaye tayi tana nuna shi da yatsa. " Ni Saifullahi, ni ta kan mace? Allah ya isa nono... " " A'a hajiya kar ki masa. Yi hakuri, muje don Allah " Goggo tace tana kamo ta, sai a lokacin hajiya ta tuna goggo fa mahaifiyar Amatullah ce, kuma yanzu ita ce ke tallafo ta a lokacin da rayuwa ke shirin kayar da ita. *** Ayyiriri!!! Ga biki zuwa maza nemo zanin ɗaurawa Kun taɓa jin labarin Diamond package? Idan ba ku da labari ku zo ku ji da ɗumiɗuminsa. Ba komi bane face DANGARTAKARMU mai cike da SARƘAƘIYA wanda ke haddasa AUREN SHEHU. Package ne da Ummu-Abdoul, Aisha Yau Kura da Khadija Sidi suka haɗa don Ilmantar da mai karatu gami da Nishaɗantarwa. Tikitin Karanta littafan nan guda uku Naira dubu ɗaya ne kacal, za a fara siyar da Tikitin 4 ga watan shawwal 1441 in da za a rufe siyarwa 24th ga watan shawwal.. Biki ne na wance da wance, ku hanzarta nemo kuɗin zanen ɗaurawa don kar a bar ku a baya. [4/23, 10:08 PM] +234 809 229 4372: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA SHIDA "ki yafe min, ina Amatullah ita ma na yi mata ba daidai ba, a yafe ni" Cewar Hajiya ta na mai share kwalla. Kai Gwaggo ta girgiza ta ce "ah ah sam ban taɓa rike ki cikin rai na ba, balle kuma Amatullah da take ɗiyar ki, Allah ya yafe mana baki daya" "Aameen ya Allah, na gode Allah ya saka da alkhairi, ya bawa Amatullah miji na gari" Gwaggo na mai darawa ta ce "Ai kuwa dai Allah ya riga ya bata, sai dai fatan Allah ya ara mana rai mu sha biki" Cike da mamaki Hajiya ta ce "Toh madallah, Aameen, ko gun su Baban yaran nan kin ga kuwa ban ji ba" "Eh ai dazun nan shi Baba Anas da Baban ne tare da mahaifin Amatullah su ka yanke hukuncin, idan Allah ya tabbatar nan da wata daya ma su ke so a yi auren" Gwaggo ta karasa maganar daidai lokacin da su ka zo mararrabar bangaran na su. Nan ta yiwa Hajiya sallama tare da bata shawarar fita sabgar Saifullahi da matar sa. Ta bar Hajiya cikin tunanin ko wanene mijin da Amatullah ta samu haka? *** Dee Yusuf kuwa tun da Mimi ta faɗa masa Amatullah ta fita idda ya ke mata naci, yayi yayi Amatullah ta dinga zuwa office din sa, ta ƙi, dan haka in dai ba shi da aji toh lalle za ka ga motar shi department din su Amatullah, ko kunya ba ya ji a matsayin shi na malami cikin makarantar. Duk in da aka gama lectures kuwa shi ne ke mayar da su gidan daliban da Mimi ta ke. Kamar yanda su ka saba, zaune su ke dan harabar gidan Mimi, kasancewar waje ne mai sirri. Tun da ya ɗauko su daga makaranta ya lura da yanayin Amatullah, kamar ta na cikin damuwa. Amatullah ta na zaune da shi ne, Amma zuciyar ta tunanin wayar da ta yi da Baba Anas a safiyar ranar ne, maganar sa ke ta dawo mata cikin ran ta, "Amatullah na kira ne a matsayin waliyin auren ki da Baba ya bani, ya ba ni wuka da nama akan hukunci da hidimar auren ki, shin akwai wanda kuka sasanta? Idan akwai ki sheda masa muna so mu gan shi gobe idan Allah ya kai mu, bayan magariba in Sha Allah....." "Amatullah!" Da sauri ya dago ta na kallon Dee da ya kira sunan ta a karo na uku. "Wai menene?" "Babu" Ta bashi amsa a takaice. Shiru yayi ya na nazari akan ta, ita kuwa rasa yanda za ta tunkare shi da maganar Baba Anas ta ke "Maman Emjay stop behaving like a chikala! Please kin riga kin wuce wajan!" Abin da Mimi ta ce mata kenan lokacin da ta faɗa mata yanda su ka yi da Baba Anas, ta kuma ce mata ba ta san yanda za ta faɗa masa ba. Kamar wacce ake zaro maganar daga bakin ta ta ce "Baba Anas ya kira ni, ya ce ya na so ya gan ka gobe after magrib" "A haba da Allah?" Cewar Dee ya na mai washe baki, cike da ɗoki ya ce "Halan cewa zai yi ya bani ke for better for better" "In sha Allah" Cewar Amatullah ba tare da ta san sanda kalmar ya fito daga bakin ta ba. Hakan ba ƙaramin burge Dee yayi ba, ya ce "Iyye ashe dai ana so ake ta ja min aji har haka" "Ayya mana Dee" Cewar Amatullah ta na mai rufe fuskar ta da tafin hannun ta. Ita dai duk sanda take tare da Dee ta kanji ta kamar ƴar budurwa, ta kasa gane yanda aka yi ya ke saka ta cikin wannan yanayi. "Oh ba ki Sona?" Ta girgiza kai alamar ah ah, Dee ya ce "no ban yarda da maganar kurame ba, tun da mu ke da ke ba ki taɓa furta kalmar so gare ni ba Amatullah, do you even love me?" Amatullah ta sunkayar da kai, ta ce "Yes I do" "Yes you do what? Look at me Amatullah" A hankali ta ɗago kan ta su ka haɗa ido. Idanun shi cikin na ta ya ce "Say you love me" Murya can kasan makogaro ta ce "I love you......" Idanu ya lumshe sannan ya sake buɗewa, wani kyau da kwarjini ya ƙara a idanun Amatullah da ya sanya ta kasa daina kallon sa, wanda hakan ya sanya shi shagala da kallon kwayar idanun ta da ke sheki. Ya kara faɗin "Kara faɗa min dan Allah, Say you love me...." "I love you Dawood, I will always do with all my heart" Idanun sa cike da kwallar farin ciki ya ce "Na sha mafarkin wannan ranar, kullum cikin kewar ki na ke, daidai da sakan daya ban daina son ki ba Amatullah duk da TAZARAR DA KE TSAKANINMU a lokaci" Kasa ta yi da na ta idanun ta cike da nishadi da jin dadi. Ta ce "Thank you" "For what?" Fuskarta ɗauke da murmushi mai kayatarwa ta amsa masa da "For not giving up on me" Kallon juna su ke yi cike da so da kauna, haka su cigaba da soyayya cikin Jin dadi da annashuwa kamar ba za su rabu da juna ba a ranar. *** Washagari Dee ya amsa kiran Baba Anas in da ya umarce shi da ya turo iyayen sa a yi maganar aure. Ranar Dee har sujjada yayi ya godewa Allah. Mahaifiyar shi ya fara shaidawa kafin ya nufi Haɗeja gun dangin Mahaifin sa. Sun so ace Amatullah budurwa ce kasancewar Dee bai taba aure ba, Amma haka babu yanda za su yi su ka niki gari sai ga su a birnin zazzau, in da aka yi maganar aure, aka sanya wata ɗaya kacal ranar daurin aure. Tun da aka saka ranar bikin Amatullah ta dawo gida, gun Mama ta sauka in da Mama ta shiga tsuma ta tana mata gyara na musamman kai ka ce wannan aure shi ne na fari. Ana saura sati biyu aka kawo lefe, ita kan ta Aysuh hadiyar zuciya ne kawai ba ta yi ba tsabagen yawa da haɗuwan kayan lefan Amatullah, dan kuwa rabin sa Saifullahi bai yi mata ba. Ganin lefen ya sa ta ji ta na so ta ga Dee ta kuma san shin dan gidan wanene haka? Saifullahi kuwa bai tabbatar da tazaran da ke tsakanin sa da Amatullah ba sai randa akan idanun sa Baba Anas ya karbi sadakin Amatullah daga hannun wakili Dee Yusuf. Kuka yake wiwi ba tare da ya damu da jama'ar da ke gurin ba, tsabagen takaici ranar sai da ya fara tunanin anya kuwa Baba Anas mahaifin sa ne? Shi kuwa ango sanye cikin farar shadda ya sha dinkin babban riga da aka yi mata aiki da farar zare, da ka gan shi ka ga angon zamani. Nan gaban gidan ya tsaya tare da abokan sa ya kira Mimi ya ce ta fito masa da amaryar sa ba zai iya tafiya ba idan har bai gan ta ba. Amatullah da ta sha ado cikin farin leshi, ta yi kyau matuka har sheki ta ke. Jin umarnin Dee ta fara girgizawa Mimi kai, ita kuwa ta ce "Toh ango yanzu za mu fito" Ta na aje wayar ta ɗauko farar lafaya ta ce da Amatullah "Oya we no go do hijab today, maza tashi ki naɗa mu fita Dee na jiran mu" "Ni gaskiya ba zani ko ina ba!" "Wallahi sai kin je!" Nan musu ya kaure har sai da su Mama suka sa baki, Mama ce da kanta ta nada mata lafaya, hannun ta cikin na Mimi su ka nufo kofar gida, ashe Dee ya shigo daga zaure, ya na ganin su ya karasa gaban Amatullah, ya janyo ta jikin sa ya rungume ta tare da faɗin "you're mine Amatullah, you're my halal!" Mimi ta saka guɗa yayin da Amatullah ta ke kokarin zillewa daga jikin Dee cike da kunya. Yana dariya ya sake ta tare da fadin "Lalle akwai rigima Mama nah, dole fa ki saba zama jiki na" Cike da kunya Amatullah ta ce "Ayya mana!" Duka dariya su ke mata, yayin da su ka fito waje hannun ta cikin na ango, duk yanda ta so ta kwace ya hana ta. Saifullahi da ya ke waje tuni ya shige mota ya bar wajen ganin yanda Dee ke nan nan da Amatullah, ana ta daukan hoto tare da yan uwa da abokan arziki. A daren ranar aka kai Amatullah gidan Dee ke zangon shanu gidan ya tsaru ainun irin wannan ginin zamanin ne da ake kira aljannan duniya. Da Ƴan uwan Dee da aka kai amarya da su sun nuna karbuwar Amatullah gare su, musammam yanda su ke jin labarin ta gurin Dee da Mimi. Sai bayan da kowa ya watse Dee ya shigo gidan shi kaɗai dauke da ledar sa na kaza da yourgot. Ganin har lokacin Amatullah ba ta daina kuka na shi ya sa ya zauna ya rarrashe kayan sa, dan ya tabbatar har da kuka rashin Emjay ta ke. Sai da ta yi shiru sannan ya sa ta dauro alwala su ka yi sallah. Kan ta ya dafa yayi mata addua tare da tambayar hukunce hukunce na game da wanka, da kuma abin da ya danganci sallah, ba dan ya fita sani ba kamar yanda ya ce mata, sai dan su kara karuwa da juna. Ita kanta ta yi mamakin yanda Dee ke bin kaidojin musulunci tamkar dama ciki aka haife shi. Yanda ya ga Amatullah ta na dan rabe rabe ya gane sam ba ta sake da shi ba, cikin dabara ya jawo ta falo, nan ya sata gaba sai ta ci abinci. Haka nan ta ɗan tsattsakura, cikin sauri ta tashi ta ce bari ta je ta kwanta. Maimakon ta shiga ɗakin sa, sai ta wuce na ta ɗakin . Bin ta yayi da kallo ya na mai murmushi a zahiri kuma cewa yayi "Amatullah ni mai hakuri ne, balle yanzu da babu wani tazara a tsakanin mu?" Ya gyara zama ya na mai ƙara yiwa Allah godiya da hasken da ya bashi, lallai musulunci haske ne a rayuwar sa, haka zalika Amatullah haske ce a rayuwar sa, wannan shi ne haske kan haske. Amatullah kuwa ko da ta je ɗakin ta, wanka ta yi, ta sanya kayan baccin ta tabi lafiyar gado. Amma sai ta nemi bacci a idanun ta ta rasa duk da kuwa ta kashe wutar dakin. Kusan minti ashirin ta yi kwance ta juya nan ta juya nan. Jin alamar an buɗe kofar ta an shigo tuni gaban ta ya shiga faduwa. Ba ta gasgata shigowa Dee yayi ba sai da ta ji ya kwanta bayan ta ya na mai janyo ta jikin sa. Ta yi kokarin kwacewa ya ce "Shhhhhhhhh tsaya mana Mama nah, babu abinda zan mi ki" Yanda ya yayi maganar tare da kwantar da kan sa jikin ta ya sanya ta daina kokarin kwacewa. Cikin jin dadi Dee ya ce "That's my Girl" Amatullah ta saki sansayyar ajiyar zuciya duk da har lokacin ba ta saki jikin ta ba. "Amatullah?" Amatullah ta amsa da "um" Dee ya ce "You know I love you ko?" Amatullah ta amsa da "um" "Owk, ina so ki saki jikin ji, just relax and sleep owk?" Jin haka ta ce "um" Amma cikin ranta cewa ta yi "Relax a ina bayan ka kamkame ni haka!" A zahiri kuma sai ta ɗan saki jikin ta, Dee na mai faɗa mata kalaman soyayya har bacci ya sace ta. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Ayyiriri!!! Ga biki zuwa maza nemo zanin ɗaurawa Kun taɓa jin labarin Diamond package? Idan ba ku da labari ku zo ku ji da ɗumiɗuminsa. Ba komi bane face DANGARTAKARMU mai cike da SARƘAƘIYA wanda ke haddasa AUREN SHEHU. Package ne da Ummu-Abdoul, Aisha Yau Kura da Khadija Sidi suka haɗa don Ilmantar da mai karatu gami da Nishaɗantarwa. Tikitin Karanta littafan nan guda uku Naira dubu ɗaya ne kacal, za a fara siyar da Tikitin daga yau za a rufe siyarwa 24th ga watan shawwal.. Biki ne na wance da wance, ku hanzarta nemo kuɗin zanen ɗaurawa don kar a bar ku a baya. Biya 1000 0069724232 Abubakar Safiyyah Jibril Sterling Bank Sai ki tura shaidan biya ta whatsapp ga 07010137848.. Ku zo mu haɗe mu gwangwaje. [4/24, 12:29 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀ ✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL BABI NA TALATIN DA BAKWAI In da Dee da Amatullah su ka yi kwanan farin ciki, Saifullahi da Ayush a nasu ɓangaran kwanan tashin hankali su ka yi, Dan kuwa Saifullahi ranar kamar wanda aka yiwa mutuwa, wani bakin kishin yau Amatullah za ta kwana da wani ba shi ba ne ya addabi rayuwar sa. Matar shi da ta gane yanayin da ya ke ciki ba ta saurara masa ba, ba ta yi la'akari da jama'ar biki da ke gidan ba haka ta ringa neman sa da tashin hankali ta na mai daga murya. Sai barin ɓangaren sa yayi, ya koma falon Baban Sasa, nan ya sha kukan sa ya koshi kamar yaro dan goye. Yanda ya ga dare haka ya ga rana. **** Sai da Amatullah ta yi kwana uku a gidan ta, a daren na hudu su ka raya sunnar manzon Allah SAW, cikin aminci da yardan juna, so da kauna tare da tausayi. Farin cikin da Amatullah ta ji ko rabin sa ba ta ji ba sanda ta kasance da Saifullahi a daren su na farko. Dee ya mata alkhairi babu adadi, ya Kuma mata albishirin zuwan su umarah da za su yi wata mai zuwa. Tun da aka yi auren Dee da Amatullah Ayush ta dena ganin Saifullahi da gashi, musammam yanda ta ji labarin gidan Amatullah bakin jama'ar gidan. Kullum cikin gorin takaici ta ke yiwa Saifullahi, da ta kira shi bagidaje, sai ta kira shi local. Babban tashin hankali gare shi shi ne yanda in za ta yi kwatancen Mijin da ya hadu sai ka ji ta ambato mijin Amatullah. Wanan shi ne babban dalilin da ya kara lalata zaman auren su. Kafin su tafi Umarah Dee ya kai Amatullah Abuja wajan mahaifiyar su, so da tararraya babu wanda ba ta sha ba. Ita kan ta Amatullah ta san ta yi dace, ba ga mijin ba, ba ga surikar ba. Dee ne ke kai ta makaranta ya ɗauko ta, shi ya tsaya tsayin daka akan karatun ta, su na gama exam su ka keta hazo zuwa kasa mai tsarki. *** A kwana a tashi haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin Ayush ya tsufa sosai har ta wuce EDD ɗin ta sannan aka yi inducing din ta, har an fidda rai ana shirin shiga da ita Cs Allah ya sauke ta lafiya, ta haifi ɗan ta namiji. Sai dai Allah da ikon sa yaron ya zo da matsalar down syndrome, irin wannan yaran masu halitta daban, wanda sukan dalalar da yawu haka kuma hannun sa daya shanyayye ne. Tun da aka nuna mata ɗan da ta haifa ta ke kuka, haka ma Saifullahi wanda ya hau ta da faɗa, a cewar shi ita ta jawo musu masifar haihuwar nakasasshan ɗa, sanadiyar cikin da ta yi kokarin zubarwa, ta cuce shi ta zalunce shi. Sai da su ka yi kwana huɗu a kwance gadon asibiti saboda yaron bai da isasshen lafiya, wata tsohuwa aka turowa Aysuh daga Kano domin kula da ita dan Hajiya ta juya mata baya. A kwana na biyar ne da kyar Amatullah ta lallaba Dee ya yarda ya kai ta asibiti ta duba shi, kasancewar Baban Sasa na ta tambayar ta ko ta je ta duba Ayush, bai san ita ma fama ta ke da laulayi ba. Najaatu da Baba Anas ya tilasta mata zama da Ayush ce su ka gani a harabar gaban ɗakin. Gaishe su tayi a mutunce tana mai cike da fara'a, nan Amatullah ta ce ta shiga ta musu iso. Tashi tayi ta shiga ɗakin fuska ba yabo ba fallasa. "Yaya Amatullah ce da mijinta su ka zo gaida ki" Wata irin zabura da Ayush ta yi sai da ya firgita tsohuwar da ke zaune mata "Kutmesi, watau don munafunci zuwa su ka yi su ga abin da na haifa su min dariya ko, toh wallahi ubansu yayi kaɗan" tace cikin hayagaga. "Haba Aisha, ina laifin wanda ya gaishe ka, ai sau dubu ya fi wanda ya zage ka, ce musu su shigo yarnan" ta ce tana ƙarewa da isar da sakon ga Najaatu. Tun da su ka shigo Ayush ta ɗaga idanu ta kalli Amatullah gaban ta yayi mummunar faɗuwa, ta ga yanda ta yi kiba ta yi kyau, abin ka da mai yaron ciki nan har wani sheki ta ke na musamman. Da ya ke dare ne Amatullah sanye ta ke cikin bakar abaya da aka yiwa ado da shuɗin duwatsu, Daya daga cikin abayar da Dee ya siya mata zuwan su umarah ne, ta naɗe kanta da shudin mayafin kamar diyar larabawa, haka kuma bakar safar da ke sanye kafar ta bai hana shudin takalmin ta mai tsayi haskawa ba. Hankalin ta bai tashi ba sai da ta ga wanda ke biye da Amatullah ya yiwa mijin ta tazara a komai nesa ba kusa ba. Sanye ya ke cikin kananan kaya, shudin riga da bakar wando, kusan ma anko su ka yi. 'kar dai wannan shi ne mijin na ta?' Tambayar da ta yiwa kan ta kenan. Yanayin kallon da ta ke masa ya sanya Dee riko hannun Amatullah. Amatullah na gaishe da tsohuwar tare da yiwa Ayush ya mai jiki, amma ina gaba ɗaya hankalin Ayush na kan Dee. Namiji har namiji, kyau, kwarjini da wayewa wane Saifullahi, bare nakasassan ɗan shi da ta haifa. Amatullah da idan ta lura da halin da Ayush ta shiga sam ba ta nuna ba, ta karɓi dan ta na mai faɗin "Allah ya raya mana" Tsohuwa ta amsa da "Aameen" Ana haka sai ga Saifullahi, wanda kamar Ayush, shi ma ɗin ganin Amatullah ba ƙaramin firgita shi ya yi ba, ashe haka Amatullah ta ke da kyau bai taɓa sani ba, lalle ya yi asara babba a rayuwar shi. Shi kuwa Dee shigowar Saifullahi da kuma yanayin da ya ga yana kallon Amatullah ne ɓata masa rai. A murtuke su ka gaisa da Saifullahi, ya ce da Amatullah "Madam mu tafi ko?" "Amatullah ta amsa da toh Mijin so" Ta sa hannu a jaka ta ɗauko kudi dubu ashirin ta ajiyewa Ayush bisa gado. Ayush ta bi kudin da kallon takaici, wai ita Aysuh tsohuwar matar Saifullahi ke yiwa kyautar kudi tsabagen lalacewar mijin ta. Amatullah ta musu sallama, hannun ta cikin na Dee su ka fice in da Ayush da Saifullahi su ka bi su day kallo cike da sha'awar ina ma dai su ne. Zuwan Amatullah ne ya haddasa masifa tsakanin Ayush da Saifullahi, don cewa ta yi tir da bagidajen miji irin shi, dan Allah ya kama kafa da mijin Amatullah ko ya dan waye, abin ya masa yawa ga talauci ga gidadanci shi ya sa Allah ya bashi nakasassan da daidai da shi Wannan maganar da Aysuh ta yi ba ƙaramin daci ta masa a rai ba, dan ko sallama bai mata ba ya tafi, ashe karshen ganin shi da ita kenan. Washagari da sassafe ta haɗa nata ya nata, da kudin da Amatullah ta bata, ta tsallake dan jinjirin da ta haifa ta gudu gida ita da tsohuwar da aka aiko mata, wacce da ƙyar ta hillace ta, ta amince su ka gudu. Ƙarfe goma ta musu a gidan su Ayush, kallon mamaki iyayen ke mata, har cikin ransu baƙi da ramar da tayi ya taɓa su. "Wai idanunki kenan? Kin gama shanye romon Saif din ne kika dawo?" mahaifiyarta ta ce cikin tsananin ɓacin rai. "Ummah!!" Ayush ta ce cikin hawaye. "Ai tuni muka yafe ma Saifullah ke, ace don kin yi aure ba zaki waiwayo iyayenki ba, ko sau ɗaya baki zo ba, ko talaucin ya kai kun rasa na mota ne" tace ranta a ɓace "Ummah ku yi haƙuri" Ayush ta ce cikin tausayin kai, haka dai suka haɗu suka wanke ta tas, sannan aka tabbatar tayi wanka ta ci lafiyayyen abinci, daga nan sai bacci ba tare da tuna wani ɗa da ta haifa ba. Naja'atu ce ta ka kira Saifullahi ta shaida masa Ayush dai ta cika rigar ta da iska, bayan ta zauna ta jira ta ga in da za su ɓullo har ta gaji. Saifullahi bai yarda ba sai da ya zo ya ga zahiri, da gaske ta tsallake ta bar masa jinjiri. Nan ya tabbatar kiyayyar da ta ke masa kiyayyar gaske ce, tashin hankalin da ya shiga baya musaltuwa. Daukan jaririn yayi in da yake kuka wiwi jinjiri na kuka, dan kuwa lokacin da ya kamata a bashi nono yayi, duk dama dai bai iya sha da kan sa sai dai a tatsa masa. Tun da har ta na uwa za ta iya tsallakewa ta bar ɗan da ta haifa ya san lalle Ayush ta kai matuka wajan rashin mutunci. Saboda haka ya lashi takobin kin waiwayar ta har illa mashaAllah, duk sanda ta yi shirya ta turo ta karbi takardar ta. Gun Hajiya dai ya koma, ya nemi yafiyar ta da kuma rokon ta da Allah ta koma asibiti ta na kula masa da Muhamad Jamoh, da ya ke sunan Emjay jinjiri ya ci. Hajiya ta ki yafe masa, sai da Baban Sasa ya sa baki sannan ta amince ta ce ya ci darajar masu daraja. Baban Sasa na mai duban Saifullahi ya ce "Saifullahi duk yanda na so na tausaya maka, yau na kasa, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, ka ga dai yanda ta kasance da kai, ka ga kuma yanda Allah ya sakawa Amatullah, duk sanda yaran nan Dan Yusuf ya zo gare ni sai na yi da na sani , ina ma tun farko na yi imani da hukuncin Allah na aura masa jika ta, da yanda ya ke faranta min yanzu tun daga lokacin zan fara mora, wannan yaron Dan Yusuf ya koyar da ni ilimi a shekarun da na riga na tsufa, ya wayar min da kai cewa babu wani tazara tsakanin ni'imar ubangiji da dan adam, muddin ya kasance mai tsoran Allah, Allah yayiwa Dan Yusuf albarka, amma ka sani, yanda ba ka ci riba ba itama matar taka babu riban da zata ci, dubu sunyi kafin ku wani riba suka sami?" Kai Sunkuye Saifullahi ya gaza motsawa ya yin da hawaye ki fita daga idanun sa cike da nadama, Nadama a lokacin da shi kanshi ya san ya makara. ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH Godiya ta musamman gare ku, mun gode kwarai da kasancewarku cikin wannan tafiya namu. Ku sani muna ƙaunar ki Fisabilillah. Akwai sabuwar tafiya inshaAllah da zata zo bayan Sallah, ka da ku bari ayi babu ku.. Me za ku ce game da TZDM? Mun gode Ummu-Abdoul da Khadija Sidi ke muku fatan yin Ibada Karɓaɓɓe🌹💖❤️