[06/09 à 07:17] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR* LoVe and HoRoR StOrY *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya. _____________________ Ƙirƙirarren labari ne👌🏻 Allah ka jiƙan Sarkin Gobir duk wani mai hannu a kashe shi Allah ka tozarta shi ka toni asirin su.Wannan garkuwa da ya adabi mutane Ya Rahamu ka sa ya zama tarihi a ƙasar Nigeriya da ma duk sauran ƙasashe. 1-2 #TIBIRIN GOBIR Wani yanki ne da ke jahar Maraɗ jamhuriyar Nijar , al'ummar yankin sun kasance Gobirawa. TIBIRIN GOBIR ta kasance ƙaramin yanki amman mai ɗauke da ƙatuwar Masarauta wacce ta samu jagorancin wani sarki mai suna *GARBA*.Sarki Garba ya ɗale karagar mulki ne bayan Yayan mahaifiyarsa ya mutu duk da kuwa Marigayin Sarki Salis ya na da Magaji,amman kasancewar Garba ya jima ya na kwaɗayin mulki sannan al'ummar yankin na matuƙar basa girma da tsoronsa haka yasa ya hau karagar mulkin ba tare da kowa ya tuhume sa ba. Ƴan mata ne laye kowacce sanye da zane baƙi da kuma riga fara,abinci karyawa su ke karɓa wanda dogari Ɗan Tani ke raba masu. Tunda suka kama layin ta lula duniyar tunani,sam ba ta san layi ya kawo gare ta ba sai jin saukar dorinar ta yi tsakar kai.A mugun furgice ta ƙwala uwar ƙara wacce sai da masarautar ta amsa,wani banza kallo ya watsa mata kafin ya miƙa mata wainar fulawa wacce ta kasance abincin su a kullum. Hannu na rawa ta karɓa ta bar gun ta na kuka,Prince Khalid wanda a gaban idonsa aka yi komai yayi saurin shan gabanta. Cak ta tsaya ta na dubansa da idonta da suka yi ja,har ya buɗe baki zai yi mata magana ya ji murya Prince Bilal ya na cewa "ke wuce maza zuwa ɓangaren Bayi kika wani tsaya ki na sunne kai gaban Jakin dawa" Da azama Marwa ta je wucewa Prince Khalid ya riƙo tsintsiyar hannunta,cikin sanyi murya yace "kiyi haƙuri da ƙaddarar ki,sannan in kin je part ɗin ku ki samu ruwan ɗumi ki gasa idon ki ga shi nan har ya fara kumbura"ya ida maganar ya na shafa gashin idonta,zafin da taji ne ya sa ƙwalla sake zubo mata.Kai ta gyaɗa masa alamun za ta yi yadda yace ɗin kafin ta wuce ta bar su suna ƴar kallon-kallon,Prince Khalid yayi murmurshi yace "Barka da fitowa Yarima Mai jiran gado"taɓe baki yayi a zuci kuma ya na jin haushin yadda Prince Khalid bai hassala da duk cin fuskar da yake yi masa. Ba tare da ya amsa ba yayi gaba ya na tafiya cikin izza da taƙama,duk inda ya wuce sai kwasar gaisuwa yake daga bayi. Direct palais ya wuce,a hakimce ya tarar da mahaifinsa yayi zaman sarakai gefe da gefe dogarai ne ke yi masa fifita duk da kuwa ɗakin na da sanyi ac. Daga ɗan nesa ya ƙare ma mahaifin nasa kallo,sanye yake cikin ɗanyar gizner fara a sama ya ɗora alkyaba kansa kuma yane da rawani wanda bai ɓoye gobarcinsa na shidda da bakwai da kuma yetali biyun kumatunsa .Murmurshi ɗauke da fuskarsa ya ƙarasa ya zube gaban Sarki Garba ya na mai taɓa ƙafafunsa,ɗagosa yayi kafin yayi magana da muryarsa mai kama da ɓaɓarkiyar yace "Allah maka albarka yarona taso dawo nan"ya nuna masa wata kujera da ke gefensa,cike da izza ya tashi ya na mai harar dogaran kamar haɗin baki suka shiga yi masa kirari "Allah ƙara girma Yarima Mai jiran gado" A ɓangaren Marwa kuwa ta na shiga ta tarar da jikin Saffa ya ƙara tsananta,wainar ta aje ta nufeta da sauri.Murya na rawa ta fara kiran sunanta amman sam ta kasa amsawa,a guje ta nufo waje sai kuma ta ci karo da Prince Khalid wanda ya kasa haƙuri ya biyo bayanta. Goshinta ta dafe wanda ya bugu da ƙirjinsa,"lafiya?ina za ki haka a guje?"ya jero mata tambayoyin,ɓarkewa tayi da kuka tace "Saffa ce babu lafiya"yadda ta ke kuka majina na yi mata zuba yasa shi dafe kai yace "ya Salam!shine kuma kike kuka ?bari na ɗauko mota a kaita asibiti"ya na gama faɗa ya wuce ba tare da ya jira cewarta ba,babu jimawa sai ga driver daga cikin dribobin masarauta.Da taimakon Marwa ta shiga mota,ya na kaita asibiti babu jimawa aka yi mata ƙarin ruwa. "Tas,tas,tas"kake ji Sarki Garba ya ɗauke Prince Khalid da mari har uku kafin yace "cikin motar tawa za ka sa a ɗauki wata ƙaskantaciya a kai asibiti?Mi yasa ba'a kira likitan masarauta ya dubata ba?"kai kawai Prince Khalid ya sunne ya na jin zuciyarsa na ciwo. Sarki Garba ne ya cigaba da cewa "Yarima je ka zartar mata da hukuncin da ya dace da ita,kai kuma biyo ni"kai Prince Khalid ya girgiza ya na kallon Prince Bilal wanda fuskar shi ta cika da annuri tsabar mugunta. Babu yadda Prince Khalid ya iya haka ya bi bayan Sarki yayin da shi kuma Yarima ya fice dogarai na take masa baya. Saffa da Marwa su na tsaka da hira wacce rabinta duk yabon Prince Khalid ne,kawai suka ga dogarai tsaye a gaban su.Babu wani jira dogari ya jawo Marwa kamar yadda Yarima yace masu farar za su ɗauko masa,kasancewar ita Saffa baƙa ce shiyasa suka gane ita ce aka basu umarnin ɗaukowa. Saffa na kuka ta biyo bayan su amman ganin Yarima yasa ta koma ba ta shirya ba,murmushin mugunta yayi kafin yace "ku kaita kurkukun ƙasa ku yi mata horon yunwa"ya na gama faɗa ya bar gun. Prince Khalid ya fashe da kuka ya na mai faɗawa kan Amma wacce ke zaune ta na jan casbi,ba tace da shi uffan ba har sai da ya ci kuka ya ƙoshi sannan ta fara bubuga bayan shi kamar wani ƙaramin yaro,ajiyar zuciya ya fara saukewa ya na jin wani kutulun baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi. "Wane sharaɗi kuma ya sake gindiya maka?"ita ce tambayar da Amma tayi masa,saboda sanin cewa Prince Khalid bai kuka sai in har Sarki Garba ya zalunce sa ko ya yi masa iyaka da wani abun. "Amma..."sai kuma yayi shiru ya haɗiye ƙodagon baƙin ciki ya cigaba da cewa "zan koma sashen Yarima na kasance mai yi masa hidima na tsawon watanni uku" Da sauri Amma ta cije leɓenta na ƙasa ta na jin wani irin raɗaɗi na ratsa ruhinta,gashin kansa ta fara shafa masa haɗi da tofa masa addu'a cikin ikon Allah barci ya ɗauke sa. Washegari Kamar yadda sarki ya zartar da hukunci haka Prince Khalid ya koma sashen Yarima,tun a yau ya fara karantar waye Prince Bilal. Rai ɓace ya ke ƙara kallon shi yadda ya murƙushe ƴar mitsitsiyar yarinyar da ba ta kai 13year ba,duk da ba sex yake yi da ita ba amman ta jigata . Babu kunya balle tsoron Allah ya faɗa toilet,ita kuwa da sauri ta fice ta na kuka.Babu jimawa ya fito ƙugunsa ɗaure da towel,ruwan yatsunsa ya yarfa ma Prince Khalid a fuska da sauri ya dawo cikin hayyacinsa. "Ba'a tunani sashen Yarima yin haka zai jawo tsatsauran hukunci,zo ka zaɓa min kayan da zan saka"cewar Yarima ya wani riƙe ƙugu kamar mace,wani banzar kallo Prince Khalid yayi masa har zai yi magana komi ya tuna sai kuma yayi shiru tare da miƙewa. Har ya buɗe drawer ya tsinkayo muryar Yarima ya na cewa "je ka wanke hannun ka da sabulu"kasa daurewa yayi yace "ban gane na wanke hannuna ba cuta ka ga gare ni?to na ƙi na wanke ɗin in na fiddo ma kayan kar ka saka"ya ida maganar ya na mai baza ido domin zaɓa masa waɗanda suka fi kyau. Shiru Yarima yayi ya na tunanin muguntar da zai yi ma Prince Khalid,can yayi ƙyaci kafin ya fara shafa lotion. "Ka saka waɗannan tabbas za su yi machin da fatar jikin ka"Prince Khalid ya faɗa ya na fiddo wasu kaya kalar zaiba sai ƙyalli su ke. Ba tare da yace komi ba ya ci gaba da gyara gashin shi,Prince Khalid kuwa haushi ya ji kawai sai ya aje kayan kan bed ya nufi ƙofar fita. "Zo taimaka min na saka kayan"Muryar Yarima ta daki dodon kunnensa,sai da yayi ɗan jimmm kafin ya juyo ya na masa kallon ƙasa-ƙasa. Da taimakon Prince Khalid Yarima ya shirya tsaf cikin kayan sarauta,babu ko godiya haka ya fice ya na baza ƙamshi. Prince Khalid kuwa direct sashen bayi ya nufa,a zaune ya tarar da Saffa ta rabka uban tagumi.Sallama yayi amman shiru hakan ya sa ya ɗan taɓa hannunta figigit ta zabura tare da dawowa hayyacinta,gaishesa ta yi ba tare da ya amsa ba yace "ina take?"sai da ta goge ƙwalla tace "har yanzu ba su dawo da ita ba"Prince Khalid ya cije leɓensa na ƙasa ya na jin wani zafi kafin ya fice ita kuwa ta bi bayansa da kallo ta na jin wani yanayi a tattare da shi wanda ta kasa gane na miye. Palais ya nufa,a zaune ya tarar da Yarima kan kujerar sarauta da alamu yau shi ya maye gurbin mahaifinsa kamar yadda yake yi wasu lokuta in zai yin Shari'a . Gefen sa Prince Khalid ya zauna bayan ya amsa gaisuwar da fadawan suka yi masa,a nutse ya ke kallon yadda Yarima ke gudanar da shari'ar wasu ma'aurata da suka kawo ƙarar junan su. "Na baka zaɓi biyu ka rubuta mata takardar saki ko kuma ka rinƙa turo ta nan ta na yi ma masarauta hidima dan samun abincin da za ta ci"cewar Yarima ya na shafa jan gemunsa wanda ya shafa ma colorant,mijin matar wanda ba zai haura shekaru arba'in a duniya ba ya ɗago kai ya dubi Yarima wanda yin haka kuma ya saɓa ma dokar masarauta tuni Dogari ya zabga masa bulala ya na cewa "yi ƙasa da kan ka matsiyaci,ragon namiji wanda ya kasa ciyar da matarsa ƙaryar idon ka su kalli mai girma Yarima Sarkin gobe" Murmurshi Yarima yayi da alamu kirarin ya yi masa daɗi,ya miƙe tsaye ya na mai tattare alkyabbarsa sannan yace "ku shiga da ita daga ciki ta fara aikatau"dogarai biyu suka yi ma Karime jagoranci zuwa can cikin Masarauta yayin da Prince Khalid ya take ma Yarima baya ya na yi kiran sunansa amman ya ƙi tsayawa. Gabansa ya sha kafin ya haɗe girar ƙasa da ta bisa yace "haba Yarima ba girman ka ba ne,ta yaya ka na shugaban gobe amman ace za ka yanke ɗanyen hukunci irin wannan?sannan sabida Allah miye laifin Marwa da za ka hukuntata ta wannan sigar?" Kallon tsaf Yarima ya yi masa nan ya hango tsantsar son da Prince Khalid ke yiwa Marwa,cike da isa yace "wace amsa kake son na baka?ta farkon ko ta biyun?" "Ta biyun"Prince Khalid ya bashi amsa cikin dakewa,kallon masheƙan aya ya yi masa kafin yace "ko za ka hukunta ni ne a kan mace?"kai ya girgiza yace "banda wannan ikon domin kuwa da ina da shi da ko kallonta ba zan bari ka yi ba balle har ka hukunta ta"cike da mamakin lafazinsa Yarima ya matso kusa da shi haɗi da ɗora hannun kan kafaɗarsa yace "kai haba?to ina tabbatar maka ba wai iya kallo ba har taɓata sai na yi in ya so ka haɗiye zuciya ka mutu"ya na gama faɗa ya ture Prince Khalid ya wuce ya na jin zuciyarsa na yi masa ƙuna. Direct sashen da aka kai Marwa ya nufa,umarta masu gadin wurin ya yi da su fiddota haɗi da canza mata waje. Cikin izzar mulki ya shigo ya na ƙare mata kallo,fara ce kyakkyawa son kowa ta na da masifar kyau mai ɗaukar hankali. A zuci Yarima yace ‘ƙila saboda kyawunta ya ke son ta' a zahiri kuma takawa yayi kusa da ita yasa hannu zai gyara mata gashin da ya rufe rabin fuskarta,da sauri ta buge masa hannu ta na mai ja da baya ta na hararsa. Yarima ya waro ido waje yace "iyeee!Ni kike harara da wannan ƙwala-ƙwalan idon kamar kwalshi?"kafin ta samu damar yin magana ya shaƙota tuni ta fara kakarin wahala,da sauri Yarima ya sake ta jin wani azababen zafi a kwanyarsa. Prince Khalid ya jawo Marwa ya mannata a jikinsa murya a matuƙar ɓace yace "zan iya jure dukkanin launukan azabar da za ka min amman kar ka kuskura ka taɓa wannan domin ita ɗin rayuwata ce zan iya yin komi a kanta"ya na gama faɗar haka ya ja Marwa suka fito. Sai da suka zo daidai sashen su sannan ya saki hannunta yace "ki shiga ki yi wanka zan kawo maki abinci sai na kai ki gun Amma"ido Marwa ta zuba masa ta na jin wani irin sonsa ya shigeta ba ta yi aune ba,ba ta san lokacin da hawaye suka shiga zubo mata ba. Bayan hannunsa ya saka ya fara goge mata hawayen haɗi da hura mata iskar bakinsa,sai ta lumshe ido "ina son ki"muryarsa ta daki dodon kunnenta kafin ta yi magana suka ji ƙarar rufe ƙofa "gam" Da sauri Marwa ta ruga ciki dan kuwa ta ga Saffa lokacin da take tsaye, a bisa tabarma ta tarar da ita ta na goge ƙwalla. Marwa ta dafata tace "amadadin farin ciki mi zai kai ki zubda ƙwalla?koko ba ki ji daɗin gani na ba?" Saffa ta waske tare da aro jarumta tace "tsabar farin ciki ne yasa ni kuka" "to amman kamar fuskar ki ba ta nuna alamun farin ciki ba"cewar Marwa ta na ƙara kallon Saffa dan tantance gaskiyar lamarin. Saffa ta haɗiye mugun kishin da take ji game da ƴar uwarta ta miƙe tsaye haɗi da cewa "eh yanayin da na ganku ke da Prince ne ya kawar min da farin cikin,sam hakan da kuka yi bai dace ba kuma ba zan ɓoye maki ba na ji haushi sosai" Marwa ta sauke ajiyar zuciya tace "yi haƙuri ƴar uwata ni ma ban san ya haka ta faru ba amman in shaa Allah zan kiyaye" jikin Saffa duk sai yayi sanyi hakan yasa ta kwantar da murya tace "ba fa da wata niyya na faɗa ba,kawai dai ina son ki tuna matsayin ki ke baiwa ce shi kuma ɗan sarki ne" Marwa ta saki murmurshi tace "kuma fah a hakan wai yake sona" duk da Saffa ta ji ta amman sai ta share ta ma shiga aikin gyaran ɗakin su ganin haka yasa Marwa shiga toilet bayan ta ɗauki kayan da za ta sa. Gabanta ne ya faɗi jin muryarsa daga bisa,ta kafesa da ido ta na jin kamar ta je ta rungume sa tsabar ƙauna. Prince Khalid ya kawar da kai jin Saffa ta ƙi amsa masa tambayar da yayi sai ma ƙure sa da ido da ta yi,ajiyar zuciya ta sauke tace "My prince !"shaye da mamaki Prince Khalid ya juyo ya na kallonta. Marwa ta fito daga toilet sanye da wasu kaya daban,sunne kai ta yi ganin Prince Khalid a tsaye hannunsa ɗauke da kwano ga kuma Saffa ta tsare sa da kallo. Zuciyar Marwa banda dukan uku-uku babu abinda take,a zuciya kuwa addu'a take Allah sa ba wata baƙar magana Saffa ta faɗa masa ba. "Princesse ga abinci nan na kawo maki,ki tabbatar kin ƙoshi Amma na can na jiran zuwan ki"cewar Prince Khalid ya na sakin murmushi mai sauti haɗi da ƙarasawa inda take. Jin hucinsa kusa da ita yasa tayi saurin ɗagowa kafin ta waiga da sauri ta kalli Saffa,uwar hararar da ta jefo mata yasa tayi saurin sunne kai idonta suna masu cika da hawaye. "Ɗas !"hawayenta suka ɗiga a babban farcen ƙafarsa,kamar ɗigar dalma haka ya ji su ya rumtse ido da ƙarfi yayinda zuciyar sa ta shiga girgiza jin shashekar kukan ta. Bai san ya aka yi ba ko kuma abin da ya ja ra'ayinsa da yin haka,kawai samun kansa ya yi da kama hannunta suka fice suka bar Saffa cikin ƙunci. Part ɗin Amma suka shigo,sanyin AC da na turaren wuta suka bugar mata hanci a doli ta ji wata irin nutsuwa ta saukar mata. Amma wacce ke zaune ta na jan casbin da ya zame mata jiki,ta miƙe murmurshi kan fuskarta.Kafaɗun Marwa ta dafa lokaci guda suka ji wani girrr kamar lantarki amman hakan bai sa Amma janye hannuwanta daga gare ta ba. Marwa ta ɗago kai ta kalli Amma,sai kawai tayi luuu za ta faɗi da sauri Prince Khalid ya tareta ta faɗa kan ƙirjinsa.... [06/09 à 08:18] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR* LoVe and HoRoR StOrY *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya. _____________________ 3-4 Wata irin zufa ce ke tsatsafowa daga goshin Marwa,a zahiri za ka ɗauka barci take amman a baɗini farke take mai haɗi da fitar hayyaci dan ba komi take fahimta ba. Prince Khalid ya goge mata zufa a karo na ba adadi,kafin ya dubi mahaifiyar ta sa yace "Amma kin ga fah kamar idonta sun juye babu baƙi sai fari" cikin son kwantar masa da hankali Amma tace "barci ne take,dayawan mutane za ka same su a ido buɗe kamar ita dai a yanzu" Prince Khalid ya sauke gwabron numfashi ya na jin mamakin faɗuwar Marwa har yanzu bai fita daga zuciyarsa ba. ```Gefen fuskarta ya shafa ya na wangale mata bakinsa mai ɗauke da haure ƙwaya ɗaya tal,halshensa ya ziro mai kama da maciji ya saka sa kunnenta ya na zuba mata yawunsa,ido ta rumtse jin wata irin azaba na ɗigar mata a kunne ya na shigewa cikin kwanyar ta.Ihu ta fara yi amman alamu sun nuna sam babu mai jin ta dan kuwa Prince Khalid da ke tsaye kanta bai nuna alamar ya fahimci halin da ta ke ba balle kuma wasu jama'a da ke waje.Tsawon lokaci kafin ya zare halshensa daga cikin kunnenta wanda kuma ya yi daidai da ɓacewar hallitar,atishawa ta yi kafin ta miƙe zaune.``` "Kin tashi?"ita ce tambayar da Prince Khalid ya yi mata,kai kawai ta gyaɗa ta na jin wuyanta ya ƙage ga wani irin sarawa da ɗaya-wajen kanta ke yi mata. Amma ta yi murmurshi tace "Barka da zuwa Princesse" da sauri Marwa ta dafe kai jin muryar ta ruɓayan gida biyu inda ta ji wata tace ```"ki fita daga harakar Prince Khalid"``` kai ta ɗago ta dubi Amma wacce a zahiri murmurshi ne kan fuskarta amman a wajen Marwa wata fuska ta ke gani kamar dodanniya. Da sauri ta sunne kai zuciyarta na halbawa,Prince Khalid ne yace "Amma ina ga surukar nan ta ki har yanzu ba ta warware daga sumen da ta yi ba" 'Suma?'Marwa ta maimaita kalmar cikin ranta,cinkayo muryar Amma tayi ta na cewa "ƙila turaren nan da na saka ne ya juya mata kai,ka san kwanaki ma haka ya sumar da jakadiya" Prince Khalid ya kai dubansa ga Marwa wacce ta sunne kai sannan yace "ya kamata ki bar kunna sa kar ya zo ya hana surukar shigowa nan sashen" Da sauri Amma tace "wane shigowa kuma?ai ta shigo kenan daga yau nan sashen za ta ci gaba da zama"cike da firgici Marwa ta ɗago ta kalli Amma,wata uwar harara ta aika mata babu shiri ta mayar da kanta yadda yake wato ƙasa. Ɓangaren Yarima kuwa ba ƙaramin jin zafin bugun da Prince Khalid ya yi masa,dauriya ya aro ya fice. Direct sashensa ya nufa,zarya ya fara yi ya na tunanin mafita dan sam bai so Sarki ya san da maganar. Wani murmurshin mugunta yayi bayan ya hango hanyar ɓullewa ta har abada wacce zai yanke farin cikin Prince Khalid ga baki ɗaya. Toilet ya shiga yayi wanka,kayan shan iska ya saka bayan ya fito kafin ya ɗauki waya ya kira wata lamba "a kawo min ita"kawai ya faɗa bayan an ɗaga kiran. Babu jimawa jakadiya ta shigo yayin da a bayanta matar mutumen nan ce wanda Yarima ya yi masu Shari'a. "Ranka shi daɗe ga ta nan na kawo,an yi komi kamar yadda ka buƙata fatan komi yayi yadda kake so?"Jakadiya ta tambaya ta na wani yin ƙasa da kai kamar tantabarar da hauka ya kama. Tun daga ƙafafunta wanda suka sha lallen Hausa ya fara bi da ido har izuwa fuskarta wacce aka yi ma simple kwalliya,kai ya fara gyaɗawa kamar wani ƙadangare kafin ya yiwa Jakadiya alamu da ido ta fita. Fitar ta ke da wuya Yarima ya miƙa ma Maryam hannu alamun ta tawo,jikinta ne ya fara rawa duk da cewa tun kafin su shigo an yi mata bayanin komi. Wani irin fizgota yayi ta faɗa jikinsa ya lumshe ido ya na shaƙar ƙamshin turarenta wanda ya san aikin Jakadiya ne,shafar ta ya fara yi gami da aika mata saƙonni a ɓangarori mafi daraja a jikin mace. ★★★ MADARUMFA Kwalokwalo(jirgin ruwa) ya gyara ma zama kafin mutane su fara shiga shi kuwa gefe ya koma ya na kallon wata bafulatana ta kasa shiga tsabar tsoro. Ya gyara tsayuwa ya na ƙara kallon ikon Allah yadda bafulatanar nan ta ke shiga jirgi sai ta zauna sai kuma ta fito ta na zarar ido, murmurshi yayi a zuci yace "ashe dai dagaske ne Fulani sokwaye ne,yanzu miye a cikin jirgin ruwa da har ta ke tsoro?" Maganar waɗanda suke tare da ita ne ta katse zancen zucin Amadi, "Fatimah ki shigo ki zauna kin ga saura mutum biyu kawai jirgin ya cika kuma in wasu suka zo shikenan za mu bar ki a nan"Lauriya ke faɗa yayin da sauran suke kallon wacce aka kira da Fatimah suna masu haɗin baki wajen cewa "ki shigo dan Allah" Fatima ta maƙe kafaɗa tace "aradun Allah ba zan higa ba,wannan ai mun yi mashi yawa sai ya nutse da mu cikin ruwan" Dariya Amadi ya ɓarke da ita yace "halan daga ƙauye kike?" Fatimah ta waigo bayanta ta na mai dubansa wanda shi ɗin ma ita ya ke kallo. "Daga ƙarƙashin ƙasa na ke"ta bashi amsa cikin jin haushi kafin ta daure ta shiga jirgin,duk da maganar ta yi ma Amadi zafi hakan bai sa ya fusata ba sai ma cewa yayi "to madallah zan tabbatar"ya na gama faɗa shi ma ya shiga jirgin ya na mai tsoma muciyar da suke tuƙi da ita cikin ruwa . A sannu suka fara tafiya cikin tabkeken tabkin,ba ka jin komi sai kukan tsuntsaye da ƙwari,iska mai haɗe da sanyi da ƙamshin ruwa sai kaɗawa ta ke. Sun zo daidai tsakiya Fatima ta ji tamkar ana yafito ta,cike da tsoro ta buɗe idonta wanda ta rufe tun farkon soma tafiyar su ai kuwa kamar walƙiya haka ta ga wani abu "wuuul!"ta cikin ruwa babu zato ba tsammani sai jinta tayi ta faɗa canɓal cikin ruwan. Ihu su Lauriya suka fara yayin da Amadi ke gumtse dariyarsa,can kuma ya tsayar da jirgin haɗi da ce ma wani namiji "ka ida fitar da ku,ni zan shiga na cirota"ba tare da wani jinkiri ba ya faɗa "tsumbul". Ko da suka isa gaɓar ruwa duk cirko-cirko suka yi su na kuka ganin har yanzu babu labarin Amadi balle Fatimah. Tsawon lokaci kafin su tsinkayi Amadi saɓe da Fatimah a hannu kamar wata jaririya,a ƙasa ya kwantar da ita dogon gashinta wanda ya warware ya baje a ƙasa yayin da kayan Fulanin ta suka jiƙe sharkaf. Cikinta ya shiga dannawa ruwa na ta ɓulbulowa daga hancinta,bakinsa ya sa a nata bayan ya matse hancinta ya hura iska. Da sauri ya janye jin ruwan da ta sha sun shiga bakin sa,tari ta soma sosai ta lumsar ido kamar wacce ta yi maye gabanin ta fara kallon mutanen gun da suka taru su na yi mata sannu. "Sannu Fatimah,ya kike jin kan ki yanzu?"Lauriya ta tambaya cike da tausayi,kawar da kai ta yi gefe ta na mai tashi tsaye ta na son tuna abin da ya faru da ita lokacin da ta faɗa cikin ruwan. Amadi yayi murmurshi yace "ƴar fullo ko zaki koma inda kika baro ne"da sauri ta kalle sa nan take jikinta ya hau tsuma a guje ta arta da gudu ƴan uwanta suka shiga kiranta Amadi kuwa sai dariyar ƙeta ya ke kwasa. Fatimah ba ta zarce ko ina ba sai gidan Abdu wanda dama can sukan je kafin zuwan gulbi,Nana matar Abdu ta fito jin an shigo a guje. "Fatimah?lafiya daga ina kike?waye ya biyo ki haka a guje?"Nana ta jera mata tambayoyin,Lauriya ce ta bata amsa "ruwa ta faɗa sai da mai jirgin ya shiga ya tsamota,shine fah mafarin gudun"Hannuwa Nana ta fara taɓawa ta na salalami kafin ta yi masu iso zuwa cikin ɗaki. Sai yamma lis sannan su Fatimah suka baro gidan Nana,wannan karon zagaye suka yi ba su bi ta gulbi ba dan kuwa aradun Allah wacce Fatimah ta ja a kan ba za ta shiga jirgin ruwa ba ta cika buhu. Amadi bawon Allah tun ya na zuba ido ya ga dawowar su Fatima har ya haƙura ya nufi gida. Tun a bakin ƙofa ya ke jin ihun wani ƙaton saurayi,tsuki yayi a fili ya furta "aikin kenan kullum cikin ihu kamar gidan mahaukata mtws...kawai an mayar mana da gida faɗar cirar aljanu" "Amadi tare min shi kar ya fice"cewar Malam mahaifi ga Amadi,babu yadda ya iya haka ya tare saurayin ya riƙe sa tamau kamar ɗaurin goro.Har cikin ɗakin da Malam ke Ruƙiya Amadi ya kai wannan saurayi,cikin daka tsawa yace "zauna nan kuma in ka saki ka fita sai na gundile ma kai,bari ganin ka na da Jinnu to na bisa kaina sun fi ƙarfin naka"abu kamar almara haka saurayin nan ya lafe waje guda ya na kallon Amadi fuskarsa ƙarara tsoro. Malam yayi murmushi yace "yawwa Amadina gwara da ka gargaɗe sa na san kuwa in ba ni nace ya fita ba to fah babu inda zai je"Amadi yace "to Malam in ba abun ka ba waye bai tsoron Tabarno,su kansu aljanun yanzu tsorona suke"cike da murna Malam ya kuma cewa "shi yasa nake ma kwaɗayin shiga sahun maluman Ruƙiya"ɗif fara'ar fuskar Amadi ta ɗauke yace "haba Malam sai kace dan aljanu mu ka zo duniya?a bar ni da iya sarautar Sarkin ruwa"Malam bai ce komi ba saboda haushi dan ya jima ya na son saka yaron nasa harakar cire ma mutane Jinnu duba da yadda ya ke da ilimi sosai ga kuma wata baiwa da aljanun ruwa suka bashi. Alwala sallar magrib Amadi yayi kafin ya wuce masjid,ko da ya dawo ya tarar da Inna ta zuba masa abinci. Kan tabarmar kaba ya zauna ya tanƙwashe ƙafafunsa kafin ya jawo langar tuwon dawa, Bismillah yayi ya ɗibi abinci zai kai baki kwatsam sai Fatimah ta faɗo masa a rai. Lomar tuwon ya mayar ya na mai sakin murmushi ya dubi Inna wacce ita ma shi ta ke kallo "Inna albishirin ki?" "Goro"cewar Inna, Amadi yace "na samu matar aurena, bafulatanar da na ke baki labari ta na zo min cikin mafarki to yau dai kam na gan ta a zahiri" Inna tace "Amadi ban son shirmen banza,ta ya aka yi ka gane ita ce ?"ya ɓata fuska yace "Allah Inna ita ce,dan tabbatarwa har masarauta na kai ta" "wace masarauta?"Inna ta tambaya ta na mai ƙure sa da ido,ƙeya ya sosa da alamu yayi suɓul da baka kawai sai ya jawo abinci ya fara ci. Sai da ya ci ya ƙoshi sannan ya miƙe,hannu ya wanke ya cika moɗa da ruwa ya shanye kafin ya shiga ɗakinsa. Wata ƙwarya ya fiddo daga ƙarƙashin gado mai cike da ruwa,iskan bakinsa ya hura ruwan suka rausaya kafin hoton fuskarta ya bayyana a ciki ƙwaryar na ɗaukar wani irin haske kamar an saka fitila. Kwance take sanye da kayan Fulani farfaru,gashin kanta a warware duk ya zuba kan jikin Innaro wacce ke shafa mata ɗanyen man shanu a kai. Murmurshi Amadi ya saki daga nan ya hura iska gashin kanta wanda ya rufe gefen fuskarta ya ɗan tashi sama,wata zabura ta yi ta tashi zaune Amadi kuwa kallonta kawai ya ke. Ɗif hasken ya mutu sakamakon shigowa da Inna ta yi,da sauri ya mayar da ƙwaryar kafin ya maido hankalinsa ga Inna wacce ke yi masa kallon tuhuma. "Amadi tsafi kake?kenan har yanzu ba ka bar wannan rufa idon ba?"Inna ta tambaya murya na ɗan rawa. Cikin alamu na maras gaskiya yace "a'a fah Inna kawai baiwa ce Allah ya bani,kuma ke da kan ki kin faɗa kin ce tun ina ɗan yaro nake abubuwan mamaki"Inna ba ta sake cewa komi ba ta fice daga ɗakin. ★★★ MARADI "Wai Marwa gaske ne can sashen su Prince Khalid za ki koma da zama?"Saffa ke tambaya ta na kallon Marwa wacce ta zube ƙasa ta na zaɓen kayan da za ta tafi kamar yadda umarnin Amma ya bada. "Ki na fah ji na shine kika yi banza da ni ?" Marwa ta ɗago ido taf hawaye tace "ya zan yi Saffa?ban san mi yasa ta ke son na koma can ba,tun jiya zuciyata ta kasa nutsuwa dakyat fah barci ya ɗauke ni a can sashen" Cikin jin haushi Saffa ta mayar mata da "babu wani ba ki ji daɗi ba,ina ce can da AC sannan a bed kika kwana amman da yake baki son ki nuna min shine kike zancen wahala.Marwa ki je ki sha daɗi ke ɗaya na ji na gode da haka,dama tunda na ga wannan jararababen ya lanƙame maki na san da sai ya raba zumuncin mu" Marwa ta tashi tsaye ta na ma ƴar uwarta duban mamaki,ko kafin tace wani abu sallamar Jakadiya haɗi da kirarin ta ya iso gare su. "Taka ranki lafiya gimbiya sarauniya uwa ga Prince Khalid,gafara dai masu abu da abunsu kura da kallabin tumbi ,gafara dai masu sarauta za su shigo" Amma ta fara shigowa Jakadiya na take mata baya,sanye take cikin kayan sarauta kai kace ita ce matar sarkin.Lokaci ɗaya zuciyar Marwa da ta Saffa suka buga yayin da kuma jikin Marwa ya ɗauki wata irin rawa ita kuwa Saffa ƙuri ta yi ma Amma ta na yi mata kallon ido cikin ido. Ba Amma ba hatta Jakadiya ta ɗan razana ganin yadda idon Saffa ke fitar da wani hayaƙi ya ɗauki kalar kore,a hankali Amma ta fara taka ƙafa zuwa gunta sai dai ko kafin ta kai hannu ta dafata abun cikin idon Saffah ya ɗauke cak. Girgizata Amma ta yi amman tsit ba ta ji komi ba,da sauri ta yi ƙasa ta na kwasar gaisuwa ita kuwa Amma ɗago Saffa ta yi ta haɗeta da jikinta ta na cewa "tashi Ƴata gaisuwar ta isa haka"sannan ta juyo gun Marwa wacce jikinta yayi sanyi laƙas duk wata laka ta jikinta ta mutu murus. "Kin gama kimtsawa ne?"ita ce tambayar da Amma ta yi mata,kai ta girgiza alamun a'a ta sakar mata murmushi ta na mai kuma cewa "ok toh in kin gama ki jira za'a zo a tafi da ke,zan wuce palais dan isar da saƙon mallakar ki"ba tace komi ba a haka Amma ta fita Jakadiya ta take mata baya. "Ban yarda da wannan matar ba,sam ba ta yi kama da mutumniyar kirki ba amman ban san mi yasa kuma na ji zuciyata ta kamu da sonta farat ɗaya"Saffa ke magana ta na wani jujuya ido,Marwa kuwa kallon sabon al'amarin da ke tattare da ƴar uwarta kawai take. Saffa ta girgiza ta tace "ko baki ji abin da nace ba?"Marwa ta nisa tace "na ji mana,amman ki iya bakin ki nan masarauta ce fah za'a iya yi maki hukunci mai tsauri"Saffa ba ta iya cewa komi ba sakamakon wani abu da take ji ya na yawo a kwanyarta doli ta kwanta nan ta ɓingire da barci. A can ɓangaren Amma kuwa su na isa palais dogarai suka fara yi mata kirari,duk da kasancewar ba kasafai take zuwa nan ɗin ba sai ta na da wata muhimmiyar magana. "Ran sarki ya daɗe Sarauniya Amina na son ganawa da kai akwai Magana a bakinta,a bani izini dan sallamar dogarai"Jakadiya ke wannan maganar bayan ta yi gurhano a gaban sarki,cike da izza yace "na baki dama"Jakadiya ta miƙe ta na yi ma dogarai alama da su fice ita ma fita ta yi ta tsaya bakin ƙofa. Bayan fitarsu ne Amma ta yi wani murmurshi mai ɗauke da ma'anoni dayawa,duk da kasancewar Sarki Garba na da iko sosai amman sam bai san mi yasa ya ke shakkar Amma ba kusan ma ta zame masa ƙarfen ƙafa. Zagaye ta fara ta na magana "babu shakka ƙarfin mulki ya ratsa jikinka sosai,dukiya na ta ƙara hauhawa amman har yanzu ban ga alamun za'a baiwa Prince Khalid gadon mahaifinsa ba" Cike da dakiya Sarki ya miƙe tsaye yace "Amina ki yi maganar da ta kawo ki,banda isasshen lokaci" Amma ta juyo ta ɗan taɓe baki tace "dama maganar *Tawaye* ne ina son ɗaya ta koma sashena " Sarki ya murmusa har gemunsa ya motsa kafin yace "a kan wane dalili ne za ta koma part ɗin ki?"sai da Amma ta ƙanƙance ido sannan tace "kar da ace Sarki ya mance da sharuɗan masarauta?"ya girgiza kai yace "ban mance ba,sai dai ina son sanin dalilin ne"kai tsaye ta basa amsa da "Prince Khalid ke sonta kuma sai na ga bai dace ba ta ci gaba da yin bauta a matsayin ta na sarauniyar gobe" Sarki ya tako har izuwa inda Amma take yace "Dama bauta ce suke?tun yaushe aka yi jera su cikin jerin bayi alhalin sashen su daban yake da na sauran sannan kuma in ban manta ba babu wani aiki da suke yi" Amma tace "ko cin abincin bayi da suke shi ma bauta ne,balle kuma wani sa'in sukan ɗebo ruwa" Sarki yace "ya isa haka nan,ki je ki tafi da ita sai mi kuma?"Amma ta yi ƙofar fita ba tare da tace komi ba nan suka yi karo ita da Yarima wani kallon ƙasƙanci ya yi mata,kafin ita kuma ta kafesa da ido na wani ɗan lokaci ta yi murmushin da ita kaɗai ta san ma'anarsa. "Ya mahaifina miye dalilin da kake barin wannan matar na shigowa palais mi yasa ba ka yi mata iyaka ba?"Yarima ke faɗar haka sa'ilin da ya isa gun Sarki. Sumar kansa ya shafa kafin yace "har yanzu kai yaro ne,da sannu za ka gane taƙon saƙar.Wannan masarauta na da rikici sosai babu wanda ya isa ya san inda ta dosa sai Allah amman da sannu komi zai warware" Yarima ya sauke ajiyar zuciya yace "to amman miye ta faɗa ma?" "Ɗaya daga cikin tawayen masarauta za ta koma sashen ta saboda Prince Khalid na sonta"a hasale Yarima yace "in dai har ina da rai ba zan taɓa bari ya aureta ba saboda ni ma sonta nake"Sarki ya girgiza kai yace "tabbas alƙalumana sun daɗe da nuna min Prince Khalid zai aureta sai dai ban san wacce ce a cikin su ba har yanzu sai in Amina ta kaita sashenta zan tabbatar,maganar kuma ka na sonta wannan ƙarya ne sha'awarta ce kake" Da sauri Yarima ya kalli mahaifinsa ya na mamakin ya aka yi ya san sha'awarta kawai ya ke?bai tsinke da lamarin ba ya ji muryar sarki na cewa "in kuma tunanina ya zamana haka ne to kai ne namiji na farko da za zai kusanceta kafin shi wanda zai auren nata ya same ta "tsabar farin ciki ya saka Yarima rungume Sarki yace "na gode mahaifina dama kamar ka san plan ɗina haka na tsara"Sarki ya murmusa yace "wani hanzari ba gudu ba,ƙa'idar ita ce sai ta sha wasu ruwa kafin ka kusanceta"Yarima ya ɓata fuska tare da tambaya "wane irin ruwa kuma?akan wane dalili?" Sarki yace "saboda muddin ta na cikin hayyacinta aljanin da ke jikinta ba zai taɓa barin hakan ta faru ba" Jikin Yarima yayi sanyi yace "to in kuma na bata ruwan ta ƙi sha fah?" Sarki ya nufi kujerarsa ya na mai cewa "ba kai za ka bata ba ƴar uwar tawaicinta za ta bata su,sannan ta hanyar lalama za ka nemi wannan alfarma muddin ka tursasata gari zai kwaɓe ma saboda ita ma ta nada nata aljanun" Cike da ƙosawa Yarima yace "wai ni kam su Tawayen nan ba mutane ba ne ko mi? Naji sai wasu sharudda kake gindiya min akan bayi"Sarki yayi murmushi yace "mutane ne sai dai ba kamar kowa suke ba,su ɗin *Tawayen* masarauta ne" Yarima kai ya dafe saboda caji da ya ɗauka sam ya kasa fahimtar komi. Bayan kwana biyu Tunda Marwa ta koma sashen Amma sam barcin dare ya ƙaurace ma idonta,a ko wane dare cikin dararen biyu da irin masifar da ta fuskanta. Daren farko barci na fara ɗokarta , ta fara ganin wata ƙatuwar halitta tamkar za ta cika ɗakin,dare na biyu kuwa gawar Prince Khalid ta ke gani akan makara yayin da wata murya cikin siririn amo ke gargaɗarta a kan ta fita harakar Prince Khalid. A mugun furgice ta farka ta na dafe da saitin zuciyarta,a hankali ta saukar da ƙafafunta daga makeken gadon.Ta kama ƙofa za ta buɗe kenan Saffa ta shigo hannunta riƙe da kofi,Marwa za ta tambaye ta kawai ta kafa mata kofin ruwan ta na cewa "sha wannan sai mu yi magana"sai da Marwa ta shanye ruwan tas sannan ta janye bakinta. Murmushi kan fuskar Saffa ta kama hannun ƴar uwarta tace "zo mu je na gwada maki wani abu "babu muso ta bi bayanta kamar raƙumi da akala. Har suka fito farfajiyar gidan babu motsin kowa,Marwa ta fara jin jiri kafin daga bisani idonta su juye ta dubi Saffa tace "kin ci amanar zumunci tunda har za ki iya cutar da ƴar uwar tawaicin ki" ita ma Saffa kamar almara haka idonta suka koma kore sannan tace "akan Prince Khalid babu abin da ba zan iya yi ba"ba su sake yin magana ba Yarima ya fito daga cikin wani lambu ,hannun Marwa ya kama tare da janta zuwa sashen shi yayin da ita kuma ta waigo ta na kallon Saffa idonta taf hawaye ita kuwa Saffa cike da murna ta koma ɓangaren Amma ta shige ɗakin da aka saukar da Marwa tare da haye gadon. Tamkar wani gumki haka Marwa ta tsaya Yarima na cire duk wani abu da ya shafi tufafi a jikinta. Gefe ya koma ya na ƙare ma surar jikinta kallo wacce zai iya cewa duk neman matan da yake bai taɓa cin karo da wacce ta kai kwatankwacin Marwa ba. Yarima ya hura mata iska a idonta,luf ta lumshe ido ya ɗauke ta cak ya ɗora kan bed tare da yi mata rumfa,hasken ɗakin ya kashe can tsawon lokaci Marwa ta yi ƙara guda tal daga ita ba ta sake ko da motsi ba. A ɓangaren Amma kuwa,ta na can ɗakin sirrinta.Ido rufe ta ke gudanar da aikin kafin daga bisani ta ji saukar wata tukunyar laka cikin tafin hannuwanta,ta miƙe tsaye ta nufi ƙofa wacce ta buɗe da kanta duk da idonta a rufe suke bai hanata nufar sashen da ta ajiye Marwa ba. Ta na shiga ta fara kwarara ma Saffa wannan ruwan,da sauri Saffa ta buɗe idonta ta na jin yadda ruwan ke shiga cikin ɓargonta haɗe da jinin jikinta. Wata guguwa ce ta taso,duk window sashen Amma da na Yarima suka shiga buɗe kansu,wani numfashi Marwa ta ja ta dawo daga doguwar sumen da ta yi.A hankali ta buɗe idonta ta sauke su kan fuskar Yarima,ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta yunƙura ta tashi babu alwala balle wanka ta saka kayan jikinta. Farfajiyar masarauta ta fito ta nufi ƙofar fita,ta na zuwa kusa da ƙofa sakatar ta fita daga gidanta yayin da ƙofar ta buɗe ita ma da kanta Marwa na saka ƙafarta a waje taguwar masarauta ta yi wani irin kuka..... [06/09 à 08:38] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR* LoVe and HoRoR StOrY *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya. _____________________ 5-6 Guguwar da ta taso haɗi da iska mai ƙura yasa Marwa rufe ido kan ta farga numfashinta ya rabu da gangar jikinta.Cikin iska aka dinga hura gangar jikinta da ruhinta izuwa wata duniyar. Kwance take bisa wani aga-lemu gefenta wata tsohuwa ce ta na jujuya wasu ganyayyaki a ƙwaryar ruwa.Kamar mai wankan biƙi haka ta rinƙa yi ma Marwa har sai da ta dawo hayyacinta,idonta ta buɗe ta na jin sun yi mata nauyi.Bisa fuskar dattijuwar ta sauke idonta,hasken da ke tsakiyar goshinta ya sauka cikin idon Marwa tamkar yadda ruwa ke shiga ƙarƙashin ƙasa. Zumbur Marwa ta tashi zaune ta na raba ido kafin ta maido dubanta ga dattijuwar cikin wani yare wanda ita kanta ba ta san na miye ba Marwa ta fara magana "Maa sun cutar da kansu da kansu,a duniyarmu kowanne ɗan Adam kansa kawai ya sani saboda biyan buƙatarka sai ka cutar da wanin ka..."Marwa ta ja numfashi yayin da Maa wacce ta kasance baƙar mace tace "kamar yadda kika faɗa ɗin dai tun farko kansu suka cuta ba ke ba,amman ki sani wannan al'amari ya na cikin kudin tsafi a rubuce.Ita kanta Amina da ta san wahalar banza take da ba ta raini ajalinta ba" Marwa ta dubi Maa da alamun tambaya sai dai ba ta ga fuskar yin tambayar ba,hakan yasa ta miƙe kamar yadda ta ga Maa ta yi. "Biyo ni"shine abin da ta faɗa tare da yin gaba,daji ne suka shiga ratsawa wanda sai an ɗauki tazara sosai sannan ka hangi gidajen mutane. Marwa ba ta yi ƙasa da gwiwa ba wajen tambayar ma "ina ne nan?" Ba tare da Maa ta juyo ba ta bata amsa da " *Yanki Ifiritu* ne"Marwa ta kuma sake tambayarta da "amman ya aka yi na ga bil'adama ne ke rayuwa ba Jinnu ba kamar yadda na ji sunan?" "Saboda ƙarni biyu ne,akwai gidajen Jinnu fiye da na bil'adama ke ba kya ganinsu ne saboda ƙarfin power ɗin ki bai da yawa,duk wani bil'adama da za ki gani a nan to ya na aiki da aljanu ne.In ma dai shi matsafi ne,ko ɗan siddabaru,ko kuwa Mayu"jikin Marwa ya soma rawa tace "amman ni mi ya kawo ni nan?"Maa ta ja ta tsaya ta dubeta da kyau tace "ƙaddarar ki,ko dama can nan ne asalin ki yanzu kuma kin dawo gida" "Ban gane ba,dama can na taɓa rayuwa a nan?" "A'a ba ki taɓa rayuwa ba amman ainahin tsatson ki a nan suka rayu,kuma cibiyar ki a nahiyar nan aka rufeta"Maa na gama bata amsa ta yi gaba sai kuma ta tsaya tare da waigowa tace "ya aka yi kuma kika tsaya?Tafo mana"jiki babu ƙwari Marwa ta bi bayanta suka ci gaba da tafiya har sai da suka zo daidai wata bishiya sannan suka zauna dan hutawa. "Ya aka yi na tsinci kaina a nan Nahiyar?"Marwa ta tambaya,Maa ta murmusa tace "lokacin zuwan ki ne yayi shi yasa" Marwa ta ɓata rai ta kuma tambaya "ina son sanin yadda aka yi na zo wannan duniyar alhalin ni a ƙofar Masarauta kawai na iya tunawa" Maa tace "ɗaga kan ki sama"a hankali Marwa ta ɗaga kanta sama abun mamaki kanta ta gani lokacin da ta fito daga masarauta har sadda guguwa ta taso ta dabaibaye ta kafin ta wuwulniya da ita cikin iska,sai kuma ta faɗo cikin ciyayi ba'a ɗau lokaci ba sai ga dattijuwar nan mai suna Maa ta ɗauketa cak izuwa inda aga-lemunta yake shimfiɗe daidai nan girgijen da ke kamar magiji ya ɓace ɓat. A maimakon Marwa ta ji tsoro sai kawai ta ji wani ƙarfi da kuzari sun zo mata,ido ta lumshe ta na sauraren bugun zuciyarta "tabbas wannan ya na ɗaya daga cikin jerin mafarkan da nake yi"tayi furucin idonta a rufe. Masarauta Wani sanyi laƙas ne ya shiga ɓargon Saffa yayin da zuciyarta ke tuƙiƙin baƙin ciki,wanda ba komi ya haifar mata da haka ba sai jin furucin Amma "da taimakon wannan sihiri kin zamanto matar Yarima Bilal,babu ɗaurin aure ko siga balle wani rabon goro kawai zuwa gobe za'a kai ki sashensa,a yadda nake faɗa maki wannan lafazin to haka duk sauran al'ummar da ke cikin masarauta za su ji tamkar an ɗaura auren ku ne shagalin biki kawai za'a yi.Kar kiyi baƙin ciki ƙaddarar magajin masarautar nan ta zo da wannan"Amma ke magana idonta a rufe kafin ta ci gaba da yin tsafe-tsafenta ita kuwa Saffa ƙuri ta yi mata ta na auna ko wace kalma bisa sikelin hankali,abin da ta fahimta zaman dadiro za su yi ita da Yarima Bilal. Saffa ba ta tsinke da lamarin ba sai da ta ji busar algaita yayin da gefe ɗaya kuma dogari ke shelar shagalin bikinsu,abin da ya fi ɗaure mata kai shine ambaton sunanta da ya ke a maimakon na Marwa. Da sauri Amma ta buɗe ido ta zuba su cikin na Saffa wacce ke kwance wiƙi-wiƙi da ido,Amma ba tace komi ba ta fito. Ɗakin sirri ta shiga sai dai allon tsafinta ya ƙi bata amsar komi dangane da canji da aka samu maimakon Marwa ta ga Saffa ce .Ta sauke ajiyar zuci a fili ta furta "ƙila ita mai ƙohin ni ce ban gama tantancewa ba,amman alƙalamin ƙaddara ba zai taɓa canza abin da ba haka yake ba"da wannan ta yi murmushi ta shige toilet saboda sallar asubah tuni ta wuce. A nutse Prince Khalid ke shirya Yarima fuskarsa fal annuri yayin da ta Yarima take a turɓune baƙi ƙirin duk da kuwa yau ta kasance ranar walimar bikinsa wacce shi ma tashi kawai yayi ya ji hakan a ran sa kamar sauran al'umma. "Ina ta ya ka murna, yau za ka yi daren farkon ka da zarar an gama shagali"Prince Khalid ke magana lokacin da ya gama kimtsa Yarima. Bai amsa ba sai tunanin Marwa da ya adabi rayuwarsa,ya rasa sam nutsuwarsa idonsa ita kawai suke son gani ga wani irin ciwon sonta da ya shige shi daga jiya zuwa yau. Wasu kuyangi suka shirya Saffa tsaf cikin kayan amare irin na sarakai,sosai ta yi kyau. Kujerar kusa da Yarima waɗanda suka yi mata rakiya suka yi mata masauki,nan hall ɗin ya hau taɓi ana ihu haɗi da shewa. Amma na can gefe ta hakimce fuskar nan kicin-kicin babu annuri yayin da Sarki Garba bakinsa ya zama kamar gonar auduga. Kiɗa aka sa,Yarima ya dubi gefenta ya na mai miƙa mata hannu.Jiki a saɓule Saffa ta ɗora nata a kai shi kuma ya ja su izuwa cikin filin suka taka rawa,nan Mai martaba ya shiga ɓarin kuɗi Amma ta yi wani ƙyaci. Prince Khalid kuwa ya na lura da ita kasancewar kusa da ita yake,amman ya kasa cewa komi saboda wani dutse da ya zo ya tsaya masa a zuciya wanda ya kasa gane na mine ne?abu guda yake ji shine kamar ya na son wani abu amman wani mai ƙarfi ya dishashe abun ta yadda ya kasa tunawa da muradin zuciyar. ★★★ MADARUMFA Wani irin zazzaɓi ne ya rufe Fatimah,magani kullum cikin bata kaloli ake amman kamar ana ƙara ma abun ƙarfi. Cikin ƴan kwanaki ƙalilan duk idonta sun rumza,yayin da suka yi wani ja saboda rashin gamsashen sauƙi. Ta na kwance sai ta ji kamar an dadaɓata,buɗe ido ta yi a hankali sai ta ga wulgin wani baƙin abu ya wuce da sauri ta tashi haɗi da ƙwala ƙara.Innaro ta haska fitila ko kafin ta tambaye ta lafiya ta faɗa jikinta ta na kuka, addu'a ta fara tofa mata sai tayi luf sai barci. Washegari Innaro da kanta ta je gidan su Amadi wajen Malam ita da Fatimah,su na shiga gidan Fatimah ta arta a guje cikin rashin sa'a ta ci karo da Amadi. "Ƴar fullo har kin zo?dama na san sai kin zo nan saboda ke ma ki na sona"maimakon Fatimah ta ƙwace daga riƙon da yayi mata sai ta sakar masa murmushi tace "Ahamadina dama nan ne gidan ku?"murmushin nasara yayi ya jawota zuwa ciki. Inna ta dube sa da kyau tace "dama ka san ta ne?"Amadi ya washe baki yace "matata ce wacce nake gani a mafarki,ƴar fullo ta"cike da mamaki Innaro ke kallonsa,malam yace "ka ga Amadi wannan marar lafiya ce da aka kawo min yanzu fah" Yace "na sani malam ,in shaa Allah ni zan warkar da ita ku bar komi cikin hannuna" Innaro ta shiga yi masa godiya tunda dama tun kafin ta zo an shaida mata Ɗan har ya fi uban iya aiki. Tun daga wannan rana Amadi ke baiwa Fatimah magani wanda ba komi ba ne sai sihirin son shi da yake ɗura mata,a sannu jikinta ke yin sauƙi ta na samu barci babu wata matsala sai dai soyayyar Amadi ta cika zuciyarta da ɓargon jikinta. A kwana a tashi soyayyar Amadi da Fatima ta girma har ta fara hayayyafa,Amadi bai ƙasa da gwiwa ba wajen neman aurenta amman Innaro mahaifiyar Fatimah ta yi tsalle ta dire tace ba ta san wannan ba sam ba za ta aura masa ƴar ta ba. Tashin hankali maras misaltuwa ya shigi Amadi, Fatimah ma haka dan kusan ma ta fi shi damuwa. Amadi ne zaune gaban gaɓar ruwa jikinsa babu kaya tumɓur yake haihuwar uwarsa,idonsa a lumshe ya na motsa bakinsa.A sannu a hankali ruwan suka fara tunkuɗowa suna zuwa gunsa har ya zama sun kai shi can tsakiyar gulbin,wani haske ya gewaye shi mai kama da garwashin wuta kafin wata murya ta fara yi masa magana kamar haka ```baƙar akuya mai gemu,jajayen bunsuru biyu sai budurwa kaza wacce ba ta taɓa yin ƙwai ba.Ka yanka su ka zubar da jinin cikin gulbin mawaliya``` Kamar walƙiya sai kuma ruwan suka janye suka koma inda suke,Amadi ya tashi ya ɗauki kayansa da ya maida sannan ya wuce gida. Washegari gari kuwa Amadi ya bazama cikin kasuwa ya sawo abubuwan da aljan nunsa suka buƙata,zuwansa gida ke da wuya ya yanke su kaf bayan ya tara ƙwarya jinin ya zuba a ciki. Duk abin da yake Inna na kallonsa sai dai ita zuwa yanzu al'amarin Amadi tsoro yake bata,Amadi bai taushe hannu ba ya isa gulbin mawaliya ya zuba jinin.Da farko jinin sama ya yi ya takure gu ɗaya kafin daga bisani a fara jansa zuwa ƙasa kamar yadda yaro ke shan daddaɗar madara. Wani gurnani haɗi da nishi ya taso daga ƙasan ruwan can kuma ya ɗauke,ganin haka Amadi ya nufi gida. Mutane ya tarar ƙofar gida sun yi cirko-cirko ana leƙen gidansu kafin a juyo duk ana kallon sa....... [07/09 à 07:40] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR* LoVe and HoRoR StOrY *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya. _____________________ 7-8 Ko kafin Amadi ya kai ga tambayar lafiya,Innaro wato mahaifiya ga Fatimah ta kuma sakin wani ihun ta na suratai maras kan gado yayin da kuma ta ke tiƙar rawa irin yadda ƴan bori su ke yi. Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Amadi,da farko ya ji tsoro kar ace Malam ko Inna aka ɗauka matsayin sacrifice kasancewar lokacin da zai bayar da jinin da yayi alƙawari ya gabato. Cikin gidan ya wuce tare da samun waje ya zauna ya na kallon yadda Innaro ta rasa hankalinta lokaci guda ba tare da ta shirya ba,a idon mutane aljanu ne suke ganin ta na da amman wurin Amadi shi ya san haukacewa ne ta yi. "Innaro je ki zauna"Amadi ya faɗa cikin bayar da umarni,cak ta tsaya da rawar sai kuma dare-dare irin na sabon kamu. Innuwa ta samu ta zauna,a zuci Amadi yace 'au !haukan bai gama rufe ki ba tunda har kin san banbancin innuwa da kuma rana' Inna ta leƙo ta na mai ɓoyewa bayan ƙyauren ɗakinta,ta na tsinkayar Amadi ta ƙwala masa kira ya taso ya na ƙumshe dariya ganin Inna ta ɓoye a ɗaki har da saka sakata tsabar tsoro. Ya na zuwa tace "dan Allah ka taimaka kace ta tafi gida, wannan masifa da mi ta yi kama mu na zaman zamanmu ka ɗebo mana fitina" Amadi yace "Ni kuma?"Inna ta harare sa tace "eh kai ɗin ko ka zata ban san aikin ka ne ba?"Amadi ya sosa ƙeya kafin yaje gun inda Innaro ta ke. Duƙawa yayi ya fara magana "Innaro kin yarda da auren mu ni da Fatimah ko kuwa?"da sauri ta gyaɗa kai shi kuma ya saki murmushi yace "to tashi ki tafi gida"kamar wata doluwa haka ta yunƙura ta tashi tare da fita waje ba ta zame ko ina ba sai gidanta nan ta tarar da Fatimah da Abdu. Da sauri ya nufota ya na tambayar ta "Innaro lafiya?na zo na tarar Fatimah na kuka,ke kuma ba kya nan yanzu da kika dawo kayan ki duk sun yi dauɗa?" Innaro ba tace komi ba ta wuce ɗaki,Abdu ya take mata baya.Ko kafin ya sake yin wata magana tace "maganar auren Fatimah a fara shiri,ban so ya haura sati biyu a kaita kowa ya huta"cike da mamaki Abdu ya kalleta yace "haba Innaro matsafin za mu bai wa aure?"Inna ta yi masa daƙuwa kafin tace "gidan uban wa ka ga yayi tsafin?kawai sharrin mahasada ne dan sun ga duk illahirin garin nan babu mai maganin aljanu kamar sa" Abdu ya yi ajiyar zuciya kafin yace "to Allah kyauta"Innaro ta amsa masa da "amen" ta na mai bin bayansa da harare a zuci ta na cewa 'Ni ai nafi kowa sanin matsafi ne ,ni da ya turo ma ciwon hauka da rana tsaka duk da na ƴan mintina ne amman ai na wahala' Fatimah wacce ke waje duk ta ji hirar da suka zanta,cike da murna ta cika bokiti da ruwa ta kai ma Innaro banɗaki kafin ta ɗaga labule tace "ki tasho kiyi wanka na kai maki ruwa"kai ta gyaɗa mata alamar toh kafin a zuci tace 'muguwa ai doli ki kai min ruwa tunda kin kwaso mana masifa mu na zaman-zamanmu'Innaro na shiga bayi Fatimah ta arce ba ta zame ko ina ba sai gidansu Amadi. Da sallama a bakinta sai dai babu kowa sai kukan wani maras lafiya mai cutar Jinnu da aka kawo ma malam,har za ta fito sai ta tsinkayi riga da wando rataye a katangar banɗaki. Fatimah ta saki murmushi ta nufi ɗakin Amadi domin jiransa,ba ta wani daɗe da zama ba ya shigo.Kanta sunne a ƙasa ba tare da gaisuwa ba tace "Innaro ta amince da aurenmu shine nace bari na zo na faɗa ma" Amadi yayi murmushi yace "ai na sani,yanzu haka wankan zuwa gidan ku ne na yi amman tunda ga ki kin zo mu je kawai gaɓar ruwa" Babu wani muso ta miƙe tsaye ta bi bayansa,su na tafe su na hirar soyayya har suka kawo gaɓar ruwa. Amadi ya ɗauki ƙanƙara ya jefa a ciki ta bada sautin "tsulum"can sai ga kifi ya fito daidai inda babu ruwa ya na motsi,Amadi ya duƙa ya ɗauki ƙaton kifin kafin ya koma gefe ya cire masa wuya.Wuta ya hura ya fara gasa kifin,ita dai Fatimah na gefe ta na kallon siddabarun Amadi kala-kala. Cike da burgewa ta ƙaraso gun sa,cikin muryata ta Fulani tace "yanzu in nace sai ka mayar da kifin nan ɗanye ya za ka yi?"Amadi wanda ke ƙoƙarin juya kifin dan ya fara gasuwa ya ɗago ya dubeta yace "tsaf zan maidosa ɗanye kuma da ransa"Fatimah ta waro ido tace "da gaske?"ya jinjina mata kai.Ta rufe baki da dukan hannuwanta kafin tace "to mayar na gani"wata formula Amadi ya faɗa nan take kifin da ke kan wuta yayi tsul ya faɗi a ƙasa ya dawo ɗanye har ya na motsi.Fatimah ta waro ido tace "to mayar da shi gasashe"ko ida rufe bakinta ba ta yi ba kifin ya koma yadda ya ke a gashe bisa garwashi. Ganin yadda Fatimah ta shiga nishaɗi yasa Amadi mayar da abun wasa sai kifin ya gasu sai kuma ya mayar da shi ɗanye ita kuwa wawiya sai dariya ta ke saboda ita ba ta ganin dogon hannun da ke yin masanyar kifin balle ta farga da rufa ido ake yi mata. ★★★ MARADI "Ta ya aka yi kika shigo rayuwata ba tare da na shirya ba?"Yarima ya tambaya bayan ya hau kan gadon da Saffa take zaune a tsakiya. "Ta yadda ka yaudare ni kace za ka sa Prince Khalid ya so ni bayan na ci amanar ƴar uwata"Saffa ta basa amsa "Ban yaudare ki ba,akasi aka samu ko da na farka ban ga Marwa ba sannan sai naji wai an shirya hidimar auren mu"Yarima ya faɗa,Saffa ta taɓe baki tace "dama ranar da Amma ta zo sashen mu na yi mafarkin haka,ƙaddara za ta raba mu kuma za mu sake kasancewa a tare sai dai ban san tsawon wane lokaci hakan za ta faru ba" "Ko da ta dawo nan to za ta zo ne a ƙuraren lokaci,saboda sai bayan Yarima ya hau karagar mulkin da ta ke tamaƙa za ta ɗora wanin Yarima"murya Amma ta daki kunnuwansu duk sai suka waigowa su na kallonta cike da mamaki saboda sun kulle ƙofa ta yaya ta shigo kenan? Amma ta saki murmushi tace "da zarar kun raya daren farkon ku to wannan tsohon banzar zai sabka daga karagar mulki kai kuma Yarima ka hau"a zafafe Yarima ya yo kan Amma ya ɗaga hannu zai sharara mata mari ta riƙe hannunsa ta na "kul!kul!Kar ka soma taɓa fuskar nan yin haka zai sa ka samu tsinuwar Mala'iku saboda wannan fuskar ta mahaifiyar ka ce" "Mahaifiya?"Yarima ya maimaita kalmar ,Amma ta juya baya tace "tabbas Yarima kai Ɗana ne,na jima ina jiran wannan ranar wacce za ta zo na fasa ƙwan" sam Yarima bai samu bakin magana ba sai Saffa ce ta tambayi Amma "ta yaya kika zamo mahaifiyarsa?sannan shi kuma Prince Khalid fah?" Amma tace "labari ne mai tsayi,yanzu dai zan barku domin raya wannan daren zan koma sashena jiran har izuwa lokacin da zan ji an buga tamburan juyin mulki"ta na gama faɗa ta fice ba tare da ta jira cewar su ba. Saffa ta dafa Yarima tace "tabbas biri yayi kama da mutum,sai yanzu na ida fahimtar mi yasa Amma ba ta son Prince Khalid ya auri Marwa" Yarima ya dubeta yace "mi kika gane?"ba ta basa amsa ba ta fara tura masa saƙon da ya zautar shi izuwa raya daren farkon su. Washegari Masarauta ta tashi da wani firgici sakamakon wani mummunan ciwo da ya kama mai martaba,wanda aka kasa gane taƙamaimai na miye. A rikice Yarima ya nufi palais bai ma tsaya bin ta Saffa ba wacce ke cikin mugun hali. Sarki ya kalli Yarima sai dai babu bakin magana sakamakon wasu gunduma-gunduman ƙuraje da suka fito masa a dukan jikinsa har ma da cikin bakinsa. Idon Yarima taf hawaye yace "Baba..."daga can bayansa Amma ta katse sa wajen cewa "kul kar ka kuskura ka sake kiransa da Baba,domin shi ɗin ba mahaifin ka ba ne.Wannan azzalumin da kake gani shi ya kashe mahaifin ka domin ya hau sarauta sai dai ka sani daga yau shikenan taka ta ƙare,kai da ganin kujerar mulki sai kuma a lahira dan yau ba sai gobe ba zan sa a mayar da can ɓangaren bayan masarauta shegen yaron ka yayi jinyar ka"Amma na faɗar haka ta zo ta janye Yarima daga gare sa ta na mai kuma cewa "taso yarona yau zan guntsura maka labarin masarautar nan mai cike da abun al'ajabi" "Ba na so ki bari zuwa wani lokaci yanzu zan kai Sarki a duba sa,ko da ace zancen ki gaskiya ne to doli na yi biyayya ga Sarki dan ko ba komi shi ya raine ni tun ina ɗan yaro"Yarima ke faɗa kafin ya fita waje dan zaɓar masu maganin da aka kirawo dan duba Sarki. Amma ta ƙyalƙyace da wata dariya tace "kai da tashi har abada a haka za ka ƙarasa rayuwar ka cikin datti ka na ɗoyi ka na wari,yadda ruwan ƙoramar kuffa suka ratsa gangar jikin Saffa haka ciwo zai rinƙa nuƙurƙusar ka ta ciki hhhh"Amma ta fara dariya sai kuma ta gumtse sakamakon ganin Sarki na murmushi cikin ƙarfin hali ya buɗa baki duk da ya san in yace yayi magana zai ji zafi kamar ransa zai fita amman ya gwammaci ya mayar mata da martani. "Ba'a yabon ɗan kuturu sai ya girma da yatsun sa goma,tun kafin ki shigo wannan masarautar na san da zuwan ki da kuma ƙudirin ki.In ba ki manta ba kece mace ta wajen goma da Sarki Salis ya auro amman duk sun mutu sai ke ce kawai kika rayu,kin san dalili?"Sarki na kawowa nan yayi wata dariya wacce da ace akwai ƙaramin yaro kusa da sai ya ruga tsabar tsoro. Shiru Amma ta yi ta na nazarin lafuzansa,tabbas ita ce ta goma cif kuma ita ɗaya ta yi rai sannan ta rayu.Jikinta ne yayi sanyi amman ta dake tace "ina jin ka miye dalilin?" Sarki ya girgiza kai maƙoshin sa na ciwo kamar ana zuba masa ruwan dalma ya daure yace "ki jira lokacin zai zo"daga nan Yarima ya shigo da wani mai bayar da magani,kallo guda malamin yayi masa yace "mugun sihiri ne aka yi masa,ba zai taɓa warwarewa ba har sai wanda ya yi sa ya bada makarin" Prince Khalid wanda ke shigowa yace "gyara maganar kai mai bada magani,babu cutar da Allah ya sauko face sai yayi maganin ta .Kuma Allah SW ya ```«Wanunazulu minal ƙur'ani mahuwa shifaa, mun saukar da alƙur'ani ne domin ya zamo waraka a gare ku»``` In ba za ka iya ba ni ka bar ni zan yi jinyar mahaifina" Amma wacce ita ce Ummul aba'isin cutar ta dubi Prince Khalid,wani banzar kallo ya watsa mata wanda mamaki da firgici suka bayyana ƙarara kan fuskar ta. Mai magani ya ji haushi yayi tafiyar sa,Yarima ya kalli Prince Khalid cike da haushi yace "mi ka yi kenan?" "Miye ruwan ka? Ina ce dai mahaifina ne ba na ka ba ko?ko kuwa ba ka ji abinda uwarka ma ciyar amana ta faɗa ma ba?"Yarima ya cakumi wuyan Prince Khalid sai kuma kogo ya juye da mujiya sakamakon bugasa da ƙasa da Prince Khalid yayi tare da hayewa bisa kan ruwan cikinsa ya na ta bugu. Wani kullu mai ɗauke da furanni Amma ta ɗauka ta bugawa Prince Khalid a kai ya saki wata irin ƙara kafin ya faɗi a sume cikin jini . Cikin ƙanƙanan lokaci aka kwashi tsohon sarki izuwa ɓangaren baya kamar yadda Amma ta zarta kafin a wuce da Prince Khalid asibitin masarauta. Ɓangaren guda kuma tuni an fara bushe-bushen algaita da kiɗa ganguna,ba'a wani ɓata lokaci ba aka naɗa Yarima sarkin MASARAUTAR GOBIR. Amma ta tura Jakadiya gun Saffa ta kimtsata da taimakon wasu kuyangi,sosai ta jigata shiyasa ma ba ta samu halartar taron naɗin sarautar ba. Cike da ƙasaita irin ta sarakai ya shigo ɓangaren da Saffa take "Queen fito ki ga mijin ki cikin kayan sarauta,daga yau za mu koma sashen tsohon Sarki dan tuni an fara gyara shi"Sarki Bilal ke faɗa yayinda ya buɗe hannuwansa ya na yiwa gimbiyar tasa jawabi,cike da murna Saffa ta shiga jikinsa.A ƙasan ranta ba ta son shi amman ganin ta shiga daula yasa hankalinta ɗan kwanciya kuma ko ba komi za'a kirata da matar sarki,uwa uba za ta iya taka duk wanda ta so ciki kuwa har da Prince Khalid dan ta sha alwashi ko sau ɗaya ne sai sun haɗa shimfiɗa. ★★★DUNIYAR IFIRITU Tuni Marwa ta saba da Maa,abu guda ke damun ta soyayyar Prince Khalid.Duk yadda ta so hakice sa daga ranta amman abu ya gagara,yanzu haka ma zaune ta ke ta na tunanin sa. Ba ta san da zuwanta ba sai ji ta yi ta dafa kafaɗarta,ta ɗago ta kalleta gami da yin murmushin ƙarfin hali.Maa ta girgiza kai tace "ba zan hana ki tunanin Muradin Ruhin ki ba,sai dai ina son ki ɗaura ɗamara yaƙar maƙiyan ki tun kafin yaron cikin ki ya zo duniya"Marwa tace "yaron cikina?"Maa ta bata amsa da "ƙwarai kuwa,ki na da juna biyu kuma a yadda ya zo a littafin taswira namiji ne za ki haifa,wanda shine kuma zai zamanto ƙaddarar komawar ki masarautar" Tashin hankali ya bayyana ƙarara kan fuskar Marwa ,murya a ɗan harɗe tace "Maa ta ya aka yi kika san ina da ciki kuma har da abinda zan haifa?sannan duk ba wannan ba ni gaskiya ba zan koma masarauta ba" Murmushi kawai Maa tayi haɗi da tona ƙasa ta fiddo wani littafi wanda duk ya tsufa sosai,Marwa ta miƙa masa shi tace "ki ajiye sa gun ki,duk dare na Allah zan karanta maki page guda sannan nayi maki bayani ta yadda za ki gane" Marwa ta karɓi littafin abun mamaki sai da zuciyarta ta motsa ga wani irin gumi da ya keto mata,Maa tace "iya wannan kawai ya isa ya tabbatar min da komawar ki masarauta domin ke ce fitilar da za ta haska ta" Kan Marwa ya ƙulle ta tambayi Maa "fitilar masarauta kuma?" "Ƙwaran gaske domin ke ce ke ɗauke da kabewar kan kabari ba Saffa ba" Marwa dai sam ta kasa gane inda zancen Maa ya dosa wannan dalilin yasa ta shiga ƴar bukar su ta ajiye littafin kafin ta fito ta nufi inda ƙorama take. Sawun tafiya ta fara ji a bayanta,da zarar ta waiga kuma sai ta ga babu kowa.Wannan ya sa tsoro wanzuwa a ranta,innuwar mutum ta gani ta na biye da ita kawai sai tayi tsaye cak ita ma innuwar ta tsaya. "Amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar haƙuri"ta ji muryarsa daga bayanta,da sauri ta juyo saboda zaƙin muryar sa ya wuce misali sai dai tozali da kyakkyawar fuskarsa ya haifar mata da tsoro. "Mutum ko aljan?"ta samu bakinta da furtawa,shi kuwa ya bata amsa da "aljan" Maa da ke bayan sa tace "Maheer kar ka firgita ta mana"yayi dariya yace "Maa tambayata ta yi ni kuma na bata amsa" Maa tace "amsar ce ba ta dace ba dan kwanyarta ba za ta ɗauka ba"ya kuma yin murmushi yace "daga faɗin gaskiya?" Maa ta murɗe kunnensa tace "kai dai ba ka jin magana"ya kama gun ya na mai fidda sautin "Washhh!" Marwa kuwa sai kallon sa take sosai ta shagala sai da muryar Maa ta maidota hayyacinta inda ta ke cewa "Ɗan Sarkin Aljanu ne amman shi ɗin ya kasance Musulmi ,shine malamin da zai koyar da yaron ki karatu daga zarar kin haihu" Marwa ta murmusa ta na mai kallon Maheer,so take ta tantance shin da gaske aljanin ne ko kuwa? Maa tace "ki gaishe sa" "Assalamu alaikum"ta faɗa kamar wacce aka yi ma doli,Maheer ya amsa mata sallamar sannan ya ƙara da "da ace addinin Musulunci bai soke auren jinsi biyu ba da tabbas Yarima ya samu matar aure"ambatar sunan Yarima ya saka zuciyar Marwa motsawa daga tabon da ke cin ruhinta,Maa ce ta basa amsa da "da kam na tsaya maka har inda ƙarfina ya ƙare duk da dai littafin taswira ya gama tsara mata kudin ƙaddararta" Maheer ya ɓata fuska yace "littafin tsafi har wani littafin ƙwarai ne da mutum zai yarda da shirmen sa?mu Addinin Musulunci ce mana yayi komi na Allah ne,daga gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma sannan shi ya tsarawa kowa rayuwar da zai yi.Misali kamar gimbiya Marwa daman Allah ya ƙaddara za ta zo nan sai dai kawai ace sharrin tsafin ku ne sila" Fuskar Maa ce ta yi baƙi ƙirin jin Maheer na sukar su amman babu yadda ta iya saboda sanin kanta ne Maheer bai taɓuwa gare su saboda ƙarfin imaninsa. "Ya kamata ka koma kar Sarki yayi neman ka"Maa ta faɗa ta na mai kawar da kai,Maheer yace "kin matsu na tafi ne dan kar na rinjaye ta ko kuwa?" Maa tace "ai ko yanzu ta na yin sallah da sauran ibadun ta, wannan dalili ya sa mu ka tsaya bakin gari saboda isar ta can da matsala ka san tsakanin sihiri da Alkur'ani kamar wuta ce da karmami" Maheer ya ƙanƙance ido yace "Maa kenan kin san alƙur'ani jagaba ne akan komi na duniya?amman miyasa ba za ki aje bokanci ki tuba ga Allah ba?" Maa ta dube sa tace "a'a kudin ƙaddara ya tsara min haka"ganin dai Maa ba za ta fahimta ba yasa Maheer yi masu sallama ya fara tafiya bai yi nisa ba ya ɓace a idon Marwa. Ta sauke ajiyar zuciya "Maa miyasa ya ke zuwa nan alhalin shi ya kasance Musulmi kuma kin ce sai Ifiritu da masu aiki da su kawai ke wannan Nahiyar?"Marwa ta yi wannan tambayar ta na mai maida dukan hankalinta ga Maa. "Shi ɗin zuciyarsa tsarkaka ce,a kullum burinsa bai wuce ya mayar da wannan Nahiyar ba yankin Musulmi.A lokacin baya duk ranar juma'a ya ke ziyartar mu,zai zo yayi wa'azi wani sa'in kafin ya gusa sai ya rinjayi wasu sun shiriya kama daga bil'adama zuwa Jinnu " Maa ta bata amsa ta na mai sunkuyawa ta ɗauki wata sarƙa. ★★★ MADARUMFA Yamma lis su Amadi suka dawo gida ,a bakin ƙofar gidan su Fatimah suka tsaya su na hira. Abdu ya zo suka gaisa da Amadi sannan ya shaida masa saƙon Innaro,kamar wani mutumen kirki haka Amadi ya shiga godiya. "Ki shiga ciki amaryar Amadi magrib ta gabato zan je na yi sallah na je bakin gulbi yau aikin dare zan yi" Fatimah ta ɓata fuska tace "Ni dai gaskiya ka canza sana'a dan ba zan lamunci wannan ba" Amadi yace "mi kenan?"ta bashi amsa da "fitar dare mana" "Kar ki damu in dai wannan ne,ina ce ma dai gulbin ya kusa tafiya sai kuma wata shekara.Am...ki shiga gida sai gobe da safe zan zo nan kafin na wuce aiki" "To ya maganar turo da magabatan naka ko har ka manta?"Fatimah ta tambaya "Ta ya zan manta ke ma,ai sai in babu rai a gangar jikina dan na tabbata ko haukacewa na yi ba zan manta wannan babban abun farin cikin ba.In shaa Allah gobe zan turo da komi kin ji amarya ta?"da sauri Fatimah ta rufe ido dan kunya gami da rugawa cikin gida shi kuwa Amadi ya na dariya ya nufi na su gidan. Washegari Sai da amadi ya cika alƙawarin sa na zuwa ya ga Fatimah kafin ya wuce bakin rafi. Duk wunin ranar Fatimah cikin murna ta yi sa ganin dangin mahaifanta tuni sun hallara domin tarbar bakinta. Lauriya da sauran ƙawaye sai murna suke taya Fatimah yayinda tuni dangi Amadi sun hallara sai buɗa ke tashi,bayan an karɓi sadaki aka ɗaura aure kamar yadda al'adar garin ta ke.An tsayar da sati biyu ranar da za'a yi walima kafin amarya ta tare gidan mijinta. Ana shirin magrib Amadi ya shigo gida kamar kullum,bayan sun gaisa da Inna ne ta ke shaida masa an tsayar da bikin su sati biyu masu zuwa.Babu kunya Amadi ya fara taka rawa kafin ya wuce cikin ɗakinsa,ƙwarya da ke ƙarƙashin gadonsa ya ɗauko ya duba ya gani ruwan cikinta sun yi ƙasa hakan na nuni da gulbi ya kusa ƙwafewa.Ya mayar sannan ya fito yayi wanka ya tafi masallaci,ya na dawowa Inna tace "Amadi ga abincin ka nan rufe da faifai"ya girgiza kai yace "ai yau ba zan ci komi ba saboda murna,amman ina son na je wajen Ɗan Ladi mai balangu na saya mana mu ci ni da Fatimah kin ga sai mu taya junan mu farin ciki.Ke ma kin faɗan abinda kike so sai na biyo maki da shi" Inna tace "a'a ni kam ba zan ci komi ba amman in ka fita ka biyo ma malam da fura sai na dama masa "da "toh"Amadi ya amsa kafin ya fice. Direct wajen mai balangun ya nufa ,bayan ya saya sai ya wuce gidan su Fatimah.Har ciki ya shiga yayi sallama jin ta amsa masa yasa shi fitowa waje ya zauna kan dakali zaman jiranta,ba'a jima ba can sai gata ta fito cikin shigar atamfa da zane ta ɗaura kallabin wani yadi daban. A kunyace ta zo ta zauna kafin ta gaishe sa,ya amsa ya na mai tambayarta mutan gida ta amsa masa da "alhamdullah,ya naku gidan fatan su Inna na lafiya?" "Lafiyarta lau tace na gaishe ki sannan na kawo maki balangu"Amadi ya faɗa ya na mai buɗe ledar ya aje a tsakiyar su yace "Bismillah mu ci"a al'adar Fulani budurwa ba ta iya cin abinci a gaban namiji,amman kasancewar Amadi ya gama sihirce Fatimah haka ta saka hannunta suka cinye bulangun nan tas har da shiga gida ta ɗebo masu ruwa. Hira suka yi sosai game da kawo lefen da aka yi da kuma yadda bikin su zai kasance,a ƙarshe suka yi ma juna sallama. Bayan sati biyu aka yi walimar bikin su Amadi,dangi da ƙawaye suka rako amarya ɗakinta wanda ya kasance gidan iyayen Amadi a nan cikin ɗakinsa wanda ya sha gyara. Bayan kowa ya watse Amadi ya shigo ɗakin amarya shi ɗaya, kasancewar duk garin Madarumfa ba za'a nuna wani ba a matsayin abokinsa. Cike da bege da shauƙi irin na amare Amadi ya yaye maluluɓin da aka rufeta,a kunyace ta so ƙwace darar sai dai tuni Amadi yayi mata dirar mikiya.Duk yadda Fatimah ta so ƙwatar kanta abu ya cuttura saboda da dukan alamu shi Amadi so ya ke kawai ya cimma burinsa wanda kuma kusan agonye ne ne haka. Ƙarar da Fatimah ta yi yayi daidai da faɗuwar Malam wanda shi kuma shigowar sa kenan,da sauri Inna tayi kansa ta na "Innalillahi wa'inna iley raji'un"ruwa ta yi ta zuba masa amman shiru. Tsawon lokaci sosai Amadi ya fito daga ɗaki jin kukan mahaifiyarsa ya ƙi tsayawa,da sauri shi ma ya nufi malam ɗin kafin ya koma ɗaki ya ɗauko fitila ya haska malam. Da sauri ya saki fitilar ya na mai furta" Innalillahi wa'inna iley raji'un" yayinda ita kuma Inna ta faɗi a sume..... [08/09 à 08:24] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR* LoVe and HoRoR StOrY *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya. _____________________ 9-10 Jini ne ke fita a duk wasu ƙofofin fuskar malam,hanci,ido, kunnuwa da kuma baki. Amadi ya saki fitilar zuciyarsa na bugun tara-tara,a doli ya fita ya nemo mai mota aka kai shi asibiti sai dai daga zuwansu aka tabbatar masu da rai ya riga da yayi halinsa. Inna ta turje ta ƙi baro asibiti,Amadi ya dawo gida ya taimaka ma Fatimah ta gyara jikinta sannan ya canza zanen gadon. Ya rungume Fatimah a jikinsa ko zai ji sassauci,ita kuwa ta na son tambayar shi lafiya don kuwa duk ta ji koke-koken Inna sai dai yanayinsa da kuma rashin jin ƙwarin jikinta yasa ta share zancen. Washegari duk garin Madarumfa ya ɗauka malam ya rasu,sosai Fatimah ta yi kuka musamman da ta ji an fara yada mata magana ana cewa "Amadi ya auro mai farar ƙafa,yo wa ya sani ma ko mayya ce". Tunda aka yi rasuwar yanzu tsawon kwana uku kenan in Fatimah ta gaishe da Inna ba ta amsawa,wannan abu na damunta duk da a ɓangaren Amadi bai nuna mata canji ba sai ma ƙara nuna mata ƙauna da yake. "Ina kwana Innarmu ya kwanan kewa?"Fatimah ta faɗa ta na mai zama kan tabarmar da Inna ke zaune a kai.Da sauri Inna ta tashi ta na cewa "tambayar mi za ki yi min bayan kin lashe kurwa mijina?Ko kuwa ni ma zowa kika yi ki lashe ni ?"Fatimah ta fashe da kuka ta na cewa "haba Inna ke ma yadda mutanen gari suka laƙa min sharri..."ko kafin ta ida Inna ta shige ɗaki ta barta nan zaune. Jiki babu ƙwari Fatimah ta miƙe,ta saka takalmi ta nufi ƙofar fita suka yi kiciɓus da Amadi "ina za ki je?"ya tambaye ta ya na kallonta,kai tsaye tace "gidanmu, Amadi na gaji da zaman ƙunci yau kimanin sati biyu da rasuwar Baba malam amman har yanzu Inna ta ƙi fahimta ta da ba ni ce silar mutuwar sa ba,mutanen gari in sun ce yanzu ita Inna ya kamata yayi ita ma ta faɗa?"duk tana kuka ta ke yi masa wannan jawabin. Amadi ya kama hannunta ya ja ta zuwa ɗakin Inna ,da sallama ya shiga kafin yace "Inna wannan matata ce,in har ke baki yi shedar ta ba ta yaya sauran al'umma za su yi? Sanin kan ki ne Fatimah ba wani sona ta ke ba amman nayi shige da fice har na same ta.Inna duk ɗan Adam ba zai wuce lokacinsa ba,mu ma in lokacin mu yayi doli mu tafi.Ki sa a ran ki malam ya mutu ne saboda lokacinsa da yayi sannan dan Allah ki zauna da Fatimah lafiya na roƙe ki,ita ce farin cikina,sirrina in babu ita rayuwata ragaga ce" Tunda ya fara maganar Inna ke kuka ba tace komi ba,Amadi ya ci gaba da cewa "haba Uwata!kar fah ki manta a kullum ke ce ke faɗa min قُل لَّن يُصِيبَنَآ إِلَّا مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَنَا هُوَ مَوۡلَىٰنَاۚ babu abinda zai samu bawa baya ga abinda ga Ubangijinsa ya rubuta zai same sa,sannan وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ gare shi masu Imani ya kamata su mayar da yardarsu kenan yanzu ki na nufin ba ki yarda da Ayar ba komi?"cikin kuka Inna tace "na yarda Amadi Allah jiƙansa da rahama,Ƴata Fatimah ki yi haƙuri ruɗin sheɗan ne shiyasa sam na kasa fahimta"Fatimah ta faɗa jikin Inna ta na kuka. Tun daga wannan rana zama mai farin ciki haɗi da zaman lafiya ya wanzu a gidansu Amadi,duk da wasu lokutan Inna ta kan ɗaure ma Fatimah fuska saboda masu zuga da kan zugata da cewa Fatimah dai ce ta kashe malam ana su tunani duk bai tashi mutuwa ba sai da Fatimah ta shigo gidan a matsayin mata? Ita kuwa Fatimah da zarar ta ga Inna cikin wannan yanayin sai ta bar mata wajen gaba ɗaya wani sa'in ma gidan su take tafiyarta. A kwana a tashi asarar mai rai,yau auren su Amadi ya cika shekara guda cur amman shiru kake ji Fatima ko tsallaken wata ba ta taɓa yi ba balle a sa ran ciki. Wannan batu shi ya dagula lissafin Amadi,tun ya na haƙuri har ya kasa ya ƙara aure inda ya auro wata mata mai suna Hassia. A budurwa ya aureta, duka-duka ba za ta wuce sa'ar Fatimah ba.Tsohon ɗakin malam ta tare,watan farko Hassia ta fara amai isar su asibiti aka tabbatar da ta na da shigar ciki.Murna gun Amadi ai ba a faɗa,uwa uba Inna wacce duk duniya ba ta da maƙiyiya kamar Fatimah. Tunda Hassia ta samu cikin nan kullum cikin gori take yi ma Fatimah,ita kuwa baiwar Allah sai dai ta yi kuka ta rarrashi kanta sauƙin abun ma dai dan Amadi na haukan sonta har yanzu. A wani yammacin juma'a Hassia ta fara naƙuda,Inna ta kaita asibiti babu jimawa Allah ya sauketa lafiya ta haifo ɗanta namiji.Amadi yayi masa huɗuba da sunan Yakubu wato sunan Marigayin malam,har washegari Fatimah ba ta san an yi haihuwar ba saboda ciwon mara da ta tashi. Kwaramniyan ƴan Barka yasa ta farga da haihuwar,da jan ƙafafu ta isa banɗaki dan watsa ruwa amman kafin ta kai ga shiga jiri ya kwasheta ta faɗi.Amadi wanda tunda aka sallamo su daga asibiti bai fita ba ya yo kanta,da taimakonsa ta miƙe ta na cewa "jiri nake gani ka riƙe ni"Amadi ya ƙwala ma wata yarinya kira yace "je ki taro min taxi"da to ta amsa kafin ta fita,zuwa can ta dawo ta shaida ga mai taxi nan ƙofar gida. Tambayoyi likita ya fara yi mata kafin a sa mata ledar ruwa,a kwance ta ke Amadi na gefenta fuskar nan fal farin ciki sakamakon albishir ɗin da likita yayi masa Fatimah na ɗauke da ciki. Lokacin da ta farka Amadi ya shaida mata har da kuka tsabar murna,Innaro wacce ke gefe ma murnar take ita ma za ta ga jikanta. Amadi ya koma gida ya bar Innaro tayi jinyar ƴarta saboda likita yace sai ta yi traitement na 6days kafin a sallame su duba da yadda jininta ya hau saboda damuwa. Bayan kwana shidda aka sallamo su,a cike suka tarar da gidan da ƴan biki. Innaro ta ɗauki robar da kayansu suke ciki yayinda Fatimah ta shige gaba,ta buɗe ɗakinta wanda Amadi ya share sa tsaf ya saka turare. "Fatimah ki kula da shan magani banda saka damuwa a rai,ki kula da kyau ni zan wuce gida"Innaro ta faɗa kafin tayi ma Fatimah sallama. Da rana bayan Fatimah ta tashi daga barcin da ya zame mata jiki tayi wanka ta saka sabbin kaya,kuɗi ta ɗauka kafin ta fita zuwa ɗakin Hassia. Da sallama ta shiga dagin Hassia ne suka amsa ita baya da cije fuska babu abinda ta yi saboda haushin Fatimah da ya ƙaru a zuciyarta jin tana da ciki. "Ashe Allah ya sauke ki lafiya? To Allah raya kan sunnah ga shi a saya ma baby kwalli "ta miƙa kuɗi yayar Hassia ta karɓa ta yi godiya. Fatimah ta yi tsaye tana kallon Hassia na shayar da kyakkyawan yaronta,a zuci tace 'Allah sa ni ma yarona yayi kyau kamar wannan,ji yadda yake da kyau kamar aljani' Jin sallamar Lauriya ya saka Fatimah fitowa suka taɓa kafin su tafi ɓangaren ta,su na tsaka da hira suka jiyo kururuwa Hassia "wayyo Allah na shiga uku na lalace mayya ta lashe min yaro sai bulle-bulle yake wayyo jama'a ku taimaka min"zuciyar Fatimah ce ta fara dakan uku-uku tuni suka fito ita da Lauriya,jariri kuwa sai canyara kuka yake kamar ransa zai fita kafin wani lokaci duk ya wahala jikinsa yayi jajur duk ko ina burdi ne... ★★★ TIBIRIN GOBIR 👑 Duk wani tsarin masarauta Yarima wanda ya kansace sarki a yanzu ya canza su ya ɗora jadawalin rashin mutumcinsa.Kwana uku kacal da hawansa kan karagar mulki al'ummar yankin Tibiri suka gane ashe gata ne Sarki Garba yayi masu,saboda yadda Yarima ya tara mutanen gari ya ɗora dokoki wanda ko a mulkin mallaka sai haka. Dogari Ɗan Tani wanda ya kasance mai kula da abincin bayi gaba ɗaya na masarauta ba ƙaramin haushi ya ji ba,dama can Sarki Garba ya sakar masa ragamar store tsabar ƙeta ya sa shi rinƙa yiwa bayi wainar fulawa a kullum sai ya na yin ƙasa da faɗi wajen kwashe kayan masarufi.To yanzu kam Sarki Bilal ya ɗora sabon jadawali inda ya zartar da hukunci bayi za'a rinƙa yi masu tuwon jar masara a duk daren Allah,da rana a jiƙa masu kwakwi a barbaɗa ɗan gishi. Waziri wanda ya kasance aboki ga tsohon Sarki,ya shigo palais ya na mai rusunawa ya kwashi gaisuwa ya na mai cewa "Allah ja da zamanin mai martaba,al'ummar ka na son ganin ka su na can a waje su na ƙus-ƙus akan hukuncin da ka yanke na duk kowane magidanci zai biya kuɗin lanwo ko wacce safiya,su na son a sassauta a mayar da shi ko da duk bayan sati ne " Sarki Bilal ya miƙe cike da ƙasaita dogarai na take masa baya,waje ya fito inda mutane suka yi cincirindo. Duk tashi suka yi domin girmamawa ga shugaba,ya gyara tsayuwa haɗi da gyaran murya yace "Sultan ke magana,na ji koken ku sannan na karɓa sai dai ku sani da sharaɗi guda duk wani mutum da ke nan yanki zai bayar da yaro guda domin yin hidima ga masarauta.Abu na gaba da zan shaida maku shine ban yarda wani ko wata ya ɗaga kansa sama ba balle har na ji wani sabon ƙorafi,dogarai ku bi gida-gida ku fito min da yaro ɗaya-ɗaya ku tabbatar kun shiga gidan kowa da ke wannan yankin"ya na gama faɗa ya juya izuwa ciki,jama'ar gari kuwa kamar ruwa ya ci su haka duk suka fita jiki duk a mace yayin da dogarai suka fara aikin da Sultan ya saka su. A ɓangaren Sarki kuwa banda rikicewa babu abinda ciwonsa ke yi,sai allurai ake yi masa amman ga banza. Ranar da Prince Khalid ya dawo normal ne ya koma sashen da aka kai Sarki,kallon tsaf yayi masa kafin daga bisani yace "shi yasa ake so a ko wane lokaci mutum ya kasance na ƙwarai,miye ribar ka a yanzu ? Ka raini yaron da ba naka ba ka nuna masa ƙauna ka susuta shi amman yanzu daga ƙarshe ga yadda ya mayar da kai nan"ya tsagaita ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ci gaba "ba zan ce ban sonka ba,saboda kai mahaifina ne sai dai ka sani ka zalunce ni tunda har ka raba ni da abar ƙaunata." Idon sarki suka ciko taf da ruwa ya na son yin magana sai dai bai iyawa,aka turo ƙofa aka shigo wani dogari ne riƙe da ƙaton gora mai cike da ruwan zam-zam. Prince Khalid ya karɓa sannan ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya shimfiɗa tapis ya zuba ruwan zam-zam ɗin a kofi ya ɗago kofin kusa da bakinsa. Da Bismillah ya fara sannan ya karanta wannan surorin: Alfatiha⁷ Falaq³ An Nas³ Al kafirun ³ Ayattul ƙursiyu¹ Amanar Rasuluh² Ya na gamawa ya je ya buɗe bakin Sarki ya fara ɗiga masa ruwan,har zai aje sauran ruwan kawai sai kuma ya shiga yayafa masa su a jiki.Nan take jikin Sarki ya fara rawa ya na mai jin sassaucin azabar da yake ji,ganin haka ya sa Prince Khalid ɗaura niyyar zuwa maraice zai yi masa ruwan wanka.Waje ya fita ya bai wa wani bawa ƙaton buhu yace ya figo masa ganyen magarya. Bayan an kawo masa ne ya ta saɓa sa a turmi kafin ya samu bokitin ruwa ya fara karanto surorin da ke karye sihiri kamar haka: Suratul Fatiha¹¹ Falaq¹¹,Nas¹¹,Kafirun ¹¹ Ayattul ƙursiyu¹¹ Shafin suratul Safat na farko Suratul Yaseen¹ *Ayoyi daga cikin wasu surori* Alhqaf Aya ta 31 Al isra Aya ta 82 An nisa Aya ta 54 Ashu'ara Aya ta 80 At tauba Aya ta 14 Fusilat 44 Al hashir Aya ta 21 Al Mulk Aya ta 3 Al Qalam Aya ta 51 Al'araf Aya ta 117 zuwa 199 At tauba Aya ta 26 da kuma ta 40 Al fatahi Aya ta 26, 18,da kuma ta 4 Bayan ya gama karanta wannan ayoyi sai kuma ya ƙara da: _As'alullahu azhim,rabbal arshil azhim an yashfiyak⁷ _A'uzhu bikalmatillahi tammati min kulli shaitanin wa hammat wa min kulli ainin lammah ³ _Allahumma Rabban nas,adbihil ba'asa ishfi anta ash'shfi laa shifa'ia illa shifa'uka,shifa'an laa yugadiru saqama³ _Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa aleyhi tawali'u wa huwa Rabbul arshil azhim ⁷ _Bisimillahi³ _A'uzhu bi'izzatillahi wa ƙudiratihi min sharri ma'ajidu wa'uhazhir Tsawon lokaci Prince Khalid ya ɗauka ya karance duk wannan ayoyin kafin ya zuba saura a cikin flask na ruwa,sauran kuma wanka ya yiwa sarki a nan inda ya ke kwance kamar yadda aka haramta yin wanka da ruwan da aka yi ma ruƙiya a banɗaki. Wani irin siraci ke fita daga jikin Sarki kamar tukunyar da aka ɗora kan ruwa,tuni jikinsa ya fara saɓewa daga kumburin da yayi. "Alhamdullah , Sarki ka ga ikon Allah ko? To ina so daga yau ka cire hannun ka da dukan wasu saɓon Allah ka tuba ka koma garesa shi ɗin mai yafiya ne kuma mai jinƙai"murmushi kan fuskar sarki ya jinjina kai. Tun daga wannan lokaci Prince Khalid ke kula da mahaifinsa,sosai kuma suke ganin sauƙi dan yanzu sarki ya na iya tashi da kansa haka ya na yin magana saɓanin da. *BAYAN WANI DOGON ZANGO* ★★★ DUNIYAR IFIRITU Marwa ce duƙushe cikin jini Maa na gefe ta na ƙoƙarin yanke ma jinjirin cibi,shi kuwa sai canyara kuka yake. Cikin zane ta naɗe yaron kafin ta fara kimtsa Marwa,ta na gamawa ta miƙa mata yaron wanda kamar an tsaka kara shi da mahaifinsa. Da sauri ta kawar da kai zuciyarta na halbawa,Maa tace "ki shayar da shi kafin isowar Maheer"idonta na ɗigar ruwa ta shayar da shi. Guguwa ta taso kamar daga bisa,can sai ga shi ya bayyana cikin fararen kaya "Assalamu alaikum, Marhaban bika Ɗana Mahadee!!!".... A nan na kawo ƙarshen free page wato na kyauta,yanzu duk mai son ci gaba za ta tura 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 .Labarin fa yanzu ne zai fara sai yanzu aka haifi jarumin littafin fatan kun fahimci haka? Wannan duk shimfiɗa ce💃🏻💃🏻💃🏻ƴan Nijar carte moov za ku turo ta 500f. NB: Kawai ki tura kuɗin ki ga detail can a sama ki turo min evidence sai na saka ki group,wacce ta san ba ta shirya ba ta yi wa girman Allah kar ta min magana [09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 1-2 “ Gulbi ya zo” Laila ta faɗa ta na mai ajiye hullar gashin dokin da na bata ta sharce mini. “Za mu je mu yi wanka da zarar mun gama” Farida ta ɗora. “Ni dai ba zan je ba,ina da aiki sosai” na faɗa ina mai ci gaba da saƙa sabuwar hullar gashin doki. Duk suka matso kusa da ni kowacce da nata kalaman har suka ci galaba kaina na yarda ba tare da na san abin da ke jirana can gulbin ba. Na ce “ amma za ku taya ni sayar da abinci ” “Mun yarda” suka haɗa baki wurin faɗa . Sunana Sarah ,Laila da Farida ƙawayena dukkanmu ba za mu wuce shekara sha uku-uku ba.Muna da ra'ayi kusan duk ɗaya,ciki kuwa har son wasar ruwa ko ruwan sama ake yi sai mun san yadda muka yi muka fito muka yi wanka. Ƴar talakawa ce ni,boyi-boyi shi ne aikina ina taya wata mai gidan gyaran gashi aiki da kuma mai sayar da abinci aiki duk don na samu abin da za mu rufawa kanmu asiri ni da Kakata. Fitowa muka yi mu duka ukun na rufe salon ɗin kafin mu kama hanyar da za ta kai mu wajen magudanar ruwa.Tun a hanya muke ta zancen har muka iso,duk tsaye muka yi muna kallon yadda ruwan ke ta zubowa daga wani dogon tsauni su na cika makeken wurin da muke kira Gulbi . Tuni sun shige sun fara wanka,ƙafa ta ɗaya na saka da niyyar isa wurin su sai na ji kamar an riƙe ni. “Sarah ki shigo mana” shine abin da suke faɗa ,na amsa da “ tooo” ina mai ɗora ɗayar ƙafar tawa ta dama a can gaba. Dodon kunnena na ji ya tsira kamar wacce aka cakawa allura,kafin kuma na fara jin wani irin zafi daidai saitin zuciyata yayin da wani abu ke min yawo a maƙogoro kamar wacce ta ci yaji. Na ɗaga idona na kalli sararin samaniya sai na ga hadari baƙi ƙirin ya na haɗuwa ,ya na yo ƙasa kamar zai rubto cikin ruwan gulbin.Wani tsoro ne ya ziyarce ni nan take, kwacaaaa na faɗi rub da ciki cikin ruwan “Saraaaaah!” na ji muryar ƙawayena wacce ita ce ta ƙarshe daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai tashi na yi na gan ni kwance kan yamutsatsar katifar mu. A hankali na tashi zaune ina mai dafe gaban goshina da ke yi min mugun ciwo. “Kin tashi?” Kaka ta tambaye ni ta na tsure ni da ido. Na ce “ eh! Amma....” sai kuma na yi shiru. “Ki kwanta ki sake hutawa na san kin galabaita ” ta faɗa tare da miƙo min wata ƴar madaidaiciyar ƙwarya,na karɓa da niyyar shan ruwan da nake kyautata zaton magani ne sai kuma na tsaya cak ina kallon can ƙasan ƙwaryar da nake hango wasu halittu masu motsin rai. “Kaka mine ne nan kika bani?” na yi tambayar ina mai maido dubana gare ta. “Ruwan floris ne” ta bani amsa, floris wata itaciya ce mai warkar da dukkan wata cuta musamman wacce ta shafi mugaye,na sha jin masana na faɗar ta don ba zan manta har a cikin wani littafin Mrs Sadauki na RUHIN ALJAN na ta taɓa jin an yi amfani da ita.Sai dai sam wannan launin ruwan ba su yi kama da waɗanda aka yi siffanta na floris ɗin ba,duk da hakan dai bai hana ni na sha su ba. Ƙwaryar na ajiye ko minti biyar ba a yi ba na soma jin goshina na yin wata ƙara kamar irin ana son ɓara shi gida biyu.Dunƙulallar kwanyata ce ta fara motsi a cikin ƙoƙon kaina,yayin da hasken abin da ya faru da ni a cikin ruwan ya dawo min. Kifaye ne irin masu rabi mutum suka tarbe ni a ƙarƙashin ruwan ,tamkar wata sarauniya haka aka dinga yi mini wanka da wasu ruwa sannan aka shafa min wani abu cikin tafin ƙafa ,mundun wuyana wani matashin saurayi mai hatsabin kyawu ya cire ya saka a wuyansa kafin ya cillo ni gaɓar ruwa.Na ja wani dogon numfashi bayan na gama samun flashback ɗin da aka gama yi min,wuyana na shafa tabbas babu sarƙar munduwar (irin sarƙar nan da ake yi da kuɗi mai tambarin kan mutum....) Kaka ta matso kusa da ni ta na cewa “Sarah faɗa mini mi kika gani?” shiru na yi na ƙo bata amsa sai ma kwanciyata da na koma na juya mata baya. Ta yi wani “hum!” kafin ta fice,ganin haka yasa ni kuma na tashi da sauri na jawo wani tsohon akwatin ƙarfe da Kaka ke ajiyar shi shekara da shekaru don ko da na buɗe ido na ganta da abin ta sannan in ciwon mutum yayi ƙamari wasu na zuwa ta basu magani. Sosai na yi mamaki ganin tsofin hotuna waɗanda za su kai ɗaruruwan shekaru a cikin akwatin.A hankali nake dubawa har na zo kan wata sarauniyar kifaye,yanayin fuskarta kawai zai tabbatar ma ita ɗin muguwa ce.Abubuwan ban tsoro na ta ci karo da su waɗanda na cika kallo kuwa sai na ji idona sun yi wani zuuuuu! Kamar su na zuƙo wani abu.Jin kamar motsinta kawai sai na yi saurin na mayar da komai na tura akwatin. “Ku shigo” cewar Kaka alamun baƙi ta yi ,don dama jefi-jefi ta kan same su. “Sarah ki fita waje ina har mu gama” Kaka ta umarce ni. Fitar na yi kamar sauran lokutan da in ta samu ziyara haka za ta ce na fita ni kuma sai na yi amfani da wannan na je wurin wasa sai dai yau wani abu ya shiga kwanyata na son sanin shin mine ne Kaka ke yi da kullum take fiddo ni waje? Sai da na bari an ɗauki kamar minti biyar sannan na yi ƙoƙarin tashi daga inda nake saboda yadda zuciyata ke azalzala ta sai dai abun mamaki ji na yi ƙafafuna sun riƙe ba zan iya tashi ba kamar wacce ta samu shanyewar jiki.Ina nan cikin wannan hali har baƙin suka fito waɗanda suka kasance mata biyu ne uwa da kuma wata budurwa.Abun mamaki sai a lokacin ƙafafuwana suka saki,Kaka ta bini da wani kallo ta na mai jingina da lanlaga-langan ƙyauren ɗakinmu. “Tun yaushe kika fara jin wannan canjin?” ta jefo mini tambaya. Na miƙe tsaye ina cewa “wane irin canji?” “Na son ganin abin da nake yi” ta bani amsa kai tsaye.Na turo baki gaba na ce “to mine ne kike yi?” “Ki na son sani?” ta tambaye ni,na gyaɗa kai alamar eh tace “sai kin faɗa min mi ya faru da ke cikin ruwa” ban san ko mine ne dalili ba haka kawai na ji ina son ɓoye mata,na ce “babu komai ni da na faɗa ruwa ta ya za a yi na san abin da ya faru? Ki tambayi su Laila kawai” “To shikenan” Kaka ta faɗa amma tabbas a cikin ƙwayar idonta ina ganin ƙin yarda da zancena wanda kuma ban san dalili ba. Da dare bayan mun ci abincin Kaka ta soma yi mini gatana irin ta ababen tsoro,don ina son irin wannan labaran a haka na soma jin bacci kamar kullum sai dai na yau ya sha banban da sauran baccin da nake yi don kuwa idona a rufe suke amma ras nake ganin Kaka wacce take yi mini wasu abubuwa da na kasa gane su. Gashin kaji ne na ga ta maƙala bayan kunnuwan ta,ban gama mamakin dalilin yin haka ba har sai da na ga ta rikiɗe ta zama kaza sannan ta tashi sama.Maimakon ni da ke kwance cikin ɗaki na zamana a nan a'a duk inda Kaka ta nufa ina kallo,gidajen mutane ta dinga bi ta kasaye rufin ɗakinsu ban san dalilinta na yin haka ba sai da ta gaji da yawo kafin ta dawo ta gida.Siffarta ta ɗauka ta mutum daidai nan kuma baccin gaske ya ɗauke ni ban farka ba sai washegari,babu sallah babu salati haka na fita na yi fitsari na wanke ido.Wata irin yunwa nake ji,sai yanzu na nufi Kaka wacce ke zaune kan tabarmar kaba ta na zuba taba cikin leda.Tsaye na yi cak ina kallon ƙafafunta da suke sak irin na kaza,da sauri na ɗauke idona da na ga za ta ɗago kai. “ lafiya kika yi tsaye nan?” ta tambaye ni. “Yunwa nake ji,kuma kin san jiya ban je na taya Lantana sayar da abinci ba ballantana ta bani” na bata amsa,ko kafin ta ce wani abu Sailuba ta shigo gidanmu da sallama. Da sauri na gaishe ta,ita kuma ta shiga gaida Kaka kafin ta maido dubanta gare ni ta ce “jiya ba ki gama mini aiki ba kika rufe shago ina makullin yake?” Na waro ido kafin na fara lalubar riga ta ai kuwa na ci sa'a ya na ciki,na fiddo na bata ta karɓa kafin ta ce “mu je to ki ƙarasa” haka na bi bayanta muka tafi salon ɗin inda take yi wa mutane gyaran gashi da farce ,ta na yin kitso kuma da lalle. Tun da na ga mota a parker na san hajiyar birni ce ta zo,don haka duk muke kiranta.Duk bayan watan-wata take zuwa ta na sayen gashin mutane da ya zubo wurin gyara,ban san iya lokacin da suke tare da Sailuba ba amma dai na san wannan shine business ɗin su. Bayan Sailuba ta buɗe ɗan madaidaicin shagon ta ɗauko wata ƙatuwar leda ta zazzage duk gashin mutanen da aka tara, sai a lokacin Hajiya ta shigo ta karɓa ita kuma ta bata maƙudan kuɗi ta karɓe ta na godiya tare da cewa “hajiya sai kuma in kin sake dawowa”har mota ta yi mata rakiya kafin ta dawo sai fara'a take ta na ƙirga kuɗin.Karon farko da na ji ina son sanin dalilin business ɗin sayar da gashin mutane,na ce “anty wai don Allah mi hajiyar birni ke yi da gashi nan” “Ina na sani Sarah ? Ni dai ba ta bani kuɗina ba? Can ita ta sani in ma dai dafa shi za ta yi ta ci.Ɗauki tsintsiya ki share wurin kafin mutane su fara zuwa sannan ki ɗauki allon sanarwa ki fidda shi waje” ta na gama faɗa ta fice ta bar ni da tambayoyin da bani da amsar su sai dai na sha alwashin sai na binciko su..... *Gajeren labari ne*🌚 [09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 3-4 Cikin sauri na share shagon na goge tile da kuma ƙaton bancin da aka jera mayuyuka na wanke gashi da kuma wanda ake shafa wa bayan an fiddo mutum daga tukunya. Zaune na yi na ɗauki hullar jiya da ban ida saƙawa ba,ina tsaka da yi sai ga anty Sailuba.Leda ta miƙo min ta dambu na karɓe na huda bakin ledar na soma ci ina shan ruwa har na gama. Ɗan ƙaramin rediyo anty Sailuba ta kunna muka fara shan kiɗa,wasu ƴan mata uku ne suka shigo ɗaya na santa ta na zuwa gyaran gashi, biyun kuma baƙin fuska ne. “Sannun ku da zuwa ku zauna,Sarah kawo musu ruwan sanyi Watsima sai yau aka dawo ina ta zuba ido shiru” anty Sailuba ta faɗa fuskar nan tata cike da fara'a don a haka take saye customer ɗinta. Kan kujera duk suka zauna yayin da Watsima ta biɗe kai ta na cewa “wallahi anty Sailuba gashina duk ya lalace dubi yadda ya koma,shi yasa na zo ki gyara min shi da kyau biki ake na ƙawarmu” Ruwan sanyin na miƙa wa kowacce leda ɗaya,kafin na zuba idona kan gashin Watsima da ya cicire a gaba sannan tsayinsa ya rage ba kamar wancan zuwan da ta yi ba. Anty Sailuba ta shiga tatataɓa gashin ta na cewa “ doli gashin ki ya lalace mana Watsima,ba ki zuwa saloon sai fa in za ku yi sabga da ace ki na zuwa akai-akai wallahi tsaf za ki ga ya miƙe yayi tsayi.Bari na nuna miki wani sabon man tado gashi,zan saka miki shi yanzu in na wanke miki kai in ki yayi miki kuma sai ki saya” ta faɗa tare da zuwa gaban table ɗin ta ɗauko wata ƴar kwalba ta miƙa wa Watsima kafin ta ce “ wannan ƙawayen ki ne?” “Eh su ne nake baki labari waɗanda na ce miki ƴan uku ake kiranmu ” ta bata amsa. Anty Sailuba ta ce “ Allah sarki ga shi kuwa har kun so ku yi kama da juna,su ba za a yi musu gyaran gashin ba?” Watsima ta kalle su kafin ta ce “ kun yi shiru sai kace wasu kurame ita wannan kitso za a yi mata ita kuma wai a ɗinka mata gashin doki ya haɗe da na ta” Anty Sailuba ta yi dariya kafin ta ce “ Sarah zo ki yi mata kitso ki aje hankali sosai kin ga yau ta fara zuwa ina son ayi mata wanda za ta jawo mana customers” ta ida zancen cikin raha. Wacce aka ce zan yi wa kitson ta ce “ wannan ƴar yarinya ? Na zata ke za ki yi min” sai ta ɓata rai. Anty Sailuba ta ce “ wai don a yi sauri ne na ce haka,amma in ni kike son duk ɗaya ne .Watsima ke zauna ta wanke miki gashin in ta gama miki sai ta ɗinka wa wannan gashin dokin” Ita Watsima ta san ni sarai,shi yasa ba ta yi gardama ba ta zauna na shiga wanke mata gashin nata.Bayan na tsane shi da towel sai na soma saka mata kwarkwaro daga nan ta shiga tukunyar busar da gashi. Na maido dubana ga wacce zan saka wa gashin dokin na ce “ kin zo da mèche ɗinki ko saya za ki yi?” “A'a saya zan yi ai ku na sayar wa ko?” ta tambaye ni,na bata amsa da “ eh bari na ɗauko ki zaɓa” kalolin na kawo mata bayan ta zaɓa ta koma ƙasa ni kuma na hau kujera na soma saƙa mata ita tsawon lokaci muna abu ɗaya don akwai wuya kafin na je na duba gashin Watsima tuni ya bushe kuwa.Na kashe casque ɗin ita kuma ta fito ta zauna kan kujera,mai na ɗauko da niyyar shafa mata sai kuma na ƙure gashin da ido. Wani haske na ga ya dalle gashin wanda kuma ina da tabbacin daga cikin idona yake,haka kawai na ji ina son gwada wani abu da ban san taƙamaimai mine ne ba.Can ƙasan zuciyata na raya ‘ gashi tsiro ka yi tsayi’ ai kuwa haka na ga ya ƙara tsayin na saki murmushi ni ɗaya zan sake ƙara gwadawa Watsima ta ce “ wai ba za ki gyara mini gashin ba ne na tashi?” da sauri na shiga shafa mata mai sannan na shace. Daga can anty Sailuba ta ce “ kin ga kuwa wallahi gashin ki har ya ƙara tsayi yanzu da kika shiga tukunya,mutane sun kasa ganewa ka wanke gashi gida ba ɗaya yake da ka zo saloon ba” Cike da murna ita ma Watsimar ke duba ƴar jelar gashinta da na ɗaure,ta ƙara tsayin ba ƙarya wanda kuma ni kaɗai na san wannan sirrin. “ A gaishe ki ƴar yarinyata aikin ki na kyau” anty Sailuba ta faɗa bayan na kammalawa ɗayar ita ma. Wacce ta ke yi wa kitson ta yamutsa fuska ta na kallona kafin ta ce “ ɗiyar taki dai ƙazama ce dubi jikinta kamar almajira da wani baƙi nata kamar zunubi” Anty Sailuba ce ta shigar min “ a'a yau dai ne ta tsaya da dauɗa shi ma don ba ta shirya ba na je na kirawo ta amma ta na da tsabta” Ta tuntsire da dariya ta na kallon kaina wanda yake ɗauke da kitso ƙire-ƙire saboda yadda banda gashi kafin ta ce “ da wani gashi nata kamar gammo! Ko da yake yawancin ƴaƴan masu salon suke babu gashi duk aci gwaigwai ne” Zuwa wannan matakin tuni raina ya ɓace amma ban ce komai ba sai gashinta da na ƙurawa ido, dogo ne mai santsi duk yadda aka yi ta gama iri da Fulani .A take kuma baƙin ciki ya kama ni ‘ Allah sa gashin naki duk ya zube’ na faɗa a zuci ina mai ci gaba da kallon gashin yayin da idona kuma sai vibration suke suna min wani zuuuu! “ Je ki yi wanka ki dawo kar ki biye mata,ni kam mine sunan ki?” anty Sailuba ta buge da tambayarta bayan ta umarce ni na je na yi wanka. “ Leemat” ta bata amsa nan ne na san sunan nata da haushinta kuma na fita na wuce gida. Ina shiga na tarar Kaka ba ta nan sai ɗaki da ta rufe shi ma ba kwaɗo,na buɗe na shiga.Jakar kayana na jawo don fiddo kayan da zan saka abun mamaki kuma sai na tarar da munduwa ɗina a sama .Cike da murna na ɗauke ta na mayar a wuyana,tsakar gida na fito na cika buta da ruwa na je na yi wanka da wani guntun sabulu .Ina fitowa na saka kayan da na fitar kafin na nufi gidan anty Hinda mai sayar da abinci.Ta na gani na ta haɗe rai na san fushi take da ni saboda jiya ban zo ba,na sosa ƙeya na ce “ ina kwana anty?” “Lafiya!” ta amsa mini da shi kafin ta ɗauko wani bokiti mai ɗauke da wasu ruwa kamar sauran wanka don har da sabulu-sabulu amma haka ta buɗe tukunyar mita ta juye su. Sai kuma na ga ta kalle ni a ɗan daburce kafin ta ce“am...yau ba ki je wurin Sailuba ba ne?” ni kuwa ganin ta saki ranta yasa na watsar da zancen ruwan dauɗar ta zuba a miya na ce “na je yanzu ma can zan koma,dama biyo wa na yi na baki haƙuri abin da yasa jiya ban zo ba ruwan Gulbi na faɗa sai bayan magarib na farfaɗo ” ta shiga tashin hankali sosai kafin ta ce “Allah tsare gaba,to in kin tafi don Allah ƙarfe biyu na ɗaya na buga wa ki wuce can inda muke sayar da abinci kin ga dai yau mai yawa na yi fiye da na kullum” da to na amsa mata kafin na koma saloon har an kusa ida mata kitson ,yanzu ma da na dawo sai da ta tsokane ni “aci gwaigwai an jiƙa dauɗa da sunan wanka” Anty Sailuba ta ce “Leemat ban son haka fa” dariya ta yi tare da ci gaba da yi min sharri,tsabar iskanci ma da za su tafi haka ta sa yatsa a fuskata ta na dirzawa ta na cewa “wallahi duk baƙin ta ne na zata ko dauɗa ce” na ture hannunta ina hararenta ta dungure min kai ta na sa tissu ta goge yatsanta ta ce “na shafo dauɗa” sai ta kai yatsan ga hanci ta na sunsuna wai wari nan fa suka shiga yi mini dariya,ni kuma kawai sai na fashe da kuka bayan tafiyar su ne anty Sailuba ke ce mini “ke wasa fa take yi miki kawai don a yi dariya” sai dai duk yadda ta so shawo kaina ƙin yarda na yi kawai dai na haɗe abin a zuci na kammala mata aikin da zan yi kafin na wuce wurin sayar da abincin. Yadda na ga dandazon mutane duk sun yaɓe anty Hinda sai abin ya bani mamaki don mun sha yin kwantai sai mun dawo da abinci gida yau kuma abun mamaki tururuwa saya ake.Ashe farkon mamakina ne ban ma ga komai ba,sai da na ƙarasa na soma taya ta sayarwa hatta yadda ake zuba abincin an rage awo amma haka muka sayar da shi tasss sai wanda ta zuba mini .Sai da na wanke robobin da aka ci abinci sannan na zauna na soma cin abincin hannu baka hannu akushi,daga nan gida na wuce amma har yanzu Kaka ba ta nan ganin haka na koma saloon ba ni na koma gida ba sai wajen taran dare. A zaune na tarar da Kaka ta na sauraren rediyo ,bayan na gaishe ta tare da tambayar inda ta je na samu wuri na zauna.Amma sai na ga Kaka ta ƙure cikina da ido,ban kai ga tambayar ta lafiya ba kuma na ji ya fara mirɗa mini.Maimakon in yi zawo a'a kumfa ne ya soma fito mini ta baki kamar akuyar da ta haɗi leda.Kaka ta yi ƙyaci kafin ta bani magani na sha nan na soma amai kamar zan amayar da hanjin cikina,“haba Hinda da ni kike zancen!” ta sake yin wani ƙyacin..... *Gajeren labari ne*🌚 [09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* *NB:* Maitar ido iri-iri ce akwai ta tsafi,akwai kuma wacce ake haifar mutum da ita irin tace wacce in mai ita ya kalli abu da ya burge shi ko akasin haka sai kuka abin ya lalace.Itaciyar bedi ta sha mutuwa silar Maitar ido,wasu sun san su na da ita wasu kuma ba su sani ba.In sha Allah a sannu zan faɗi alamominta da kuma yadda mutum zai yi rabu da ita. 5-6 Na sha baƙar azaba sosai kafin na samu aman ya tsaya,Kaka ta ce “je ki kwanta ” ban musa ba na haye katifa a gajiye,sai dai tuna abin da Leemat ta yi mini yasa na ji baƙin ciki ya rufe ni.Na yi ƙwafa kafin na ce “wai Kaka don Allah baƙin nan na wane ne na kwaso? Tsakanin Inna da Abba waye baƙi?” Abun mamaki tambayar tawa ce na ga ta razana Kaka,sai ta kasa bani amsa sai motsi take da baki ni kuma na ƙara jin haushi na ce “a gaskiya ko ma dai wane ne na biyo ya cuce ni,yau an wulaƙanta Ni an tozarta ni saboda kawai ni BAƘA CE(Sajida Nijar)” Kaka ta ce “mi ta yi miki? Sannan wane mataki kike son a ɗauka kanta?” Jin abin nema ya samu har da tashi na yi zaune ba tare da na san wannan ne farkon jefa rayuwata a cakwalkwalin ruɗani,na ce “so nake ta zama baƙa kamar dai ni,sannan gashin kanta wanda ta yi mini gori a ɓata shi ya zamana nawa ma ya fi nata kyau da tsayi” Kaka ta saki murmushi wanda a cikinsa na hango tsantsar farin ciki kafin tace “Sarah kin tabbata ki na son haka?” Ba tare da wani tunani ba na ce “eh sosai ma Kaka” Ta ce “kin shirya?” “A shirye nake ai” na faɗa ba tare da na san shirin mi Kaka ke nufi ba,ta ce “to babu damuwa yau za mu je ki ɓata rayuwarta da kan ki,don haka kwanta ki yi bacci tun kafin dare ya tsala ” Cike da murna na kwanta ina tunani ƙila acid za mu je mu watsa mata sannan mu datse gashinta,da haka bacci ya ɗauke ni.Na ɗauki lokaci mai tsayi a cikinsa kafin na ga Kaka na yi min irin wannan abun na jiya,wasu ruwa ne take yayafa min ta na yin wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anar su.Abu guda na sani shine bacci nake,amma kuma abun mamaki sai na irina ta miƙe tsaye ta na tambayar Kaka “har lokacin tafiyar tamu yayi?” “Eh fito mu tafi jirgi na jiranmu” sai ta ja hannuna muka fito,ni kuwa sai ware ido nake na ga inda zan ga jirgi sai dai ina abin ya wuce tunanina.Turmi Kaka ta kada kwance hannuna na cikin nata muka shiga turmin nan kawai sai gani na yi ya tashi da mu sama.Da mamaki na tambaye ta “amma Kaka dama turmi ya na iya tashi sama?” Ba ta bani amsar tambayar da na yi mata sai bayani ta soma yi mini,“leƙa ƙasa ki ga yadda duniyar da muka baro take” na je na kama bakin turmin na leƙa sai na duk ga gidajen mutane nan da kuma ababen hawa,na waro ido ina mamaki na ce “ya na ga garin duk yayi duhu alhalin nan sama kuma hasken rana?” “Duniya biyu ce mabanbanta,daren can shine safiyar wannan duniyar.A sannu za ki saba za ki ji wannan ɓoyayyar duniyar ta fi waccan daɗi,tun tuni nake son kawo ki amma kika ƙi bani haɗin kai sai yau da zafin ɗaukar fansa ya ci galaba a kan ki” ina shirin yi mata wata tambayar ta ce “shuuut! Mun kawo Dutsen Muradi ki nutsu ki aiwatar da komai yadda ya kamata” Kan wani ƙaton dutse jirginmu na turmi ya sauka,yanzu ma Kaka ce ta kama hannuna muka fito “ ki faɗi abin da ya kawo ki mana kin yi wani tsaye” Kaka ta faɗa ta na kallona,“ to ai ni ban san ya zan yi ba” na faɗa ina ƙyafƙyaf da ido. “Sunan ta za ki kira ” “Leemat!” na faɗa cikin rawar murya,wani haske ne ya soma sauko wa daga sama mai gamar gajimare kafin ya tsaya a gabanmu,ta cikinsa nake hango Leemat a kwance jikin wani matashin saurayi sai shafar mata gashin da aka kitse yake. Maimakon muradin gashin ya zube kamar yadda na zo da niyyar,a'a sai na canza ƙudiri na kafe tsorayen da ido ina mai cewa “ ku zama macizai ta yadda saurayin kawai zai iya ganinsu” ko baki ban rufe ba kuwa tsorayen suka fara motsi kafin su zama macizai su na fiddo halshe.Saurayin ya fasa ihu tare da koma gefe ya na rawar sanyi tuni fitsari ya soma yi masa zuba,sai haƙuri yake bai wa Leemat kar ta cutar da shi ita kuma ta na tambayar mine ne gashin kanta yake yi mata nuni wanda yasa ta nufi madubi don dubawa sai dai kafin ta isa ne Kaka ke ce min “ da zarar ta isa ga madubin mutuwa za ta yi don shi mirror bai ƙarya ki yi saurin dakatar da ita” Take na ruɗe jin zan yi kashin kai na ce “ ta yaya Kaka? Ya zan tsayar da ita ?” kafin kuma ta bani amsa na ƙure ƙafar Leemat da ido nan take ta ɓangwale ta faɗi ƙasa timmm daidai nan kuma Kaka ta yi wani furuci komai ya tsaya cak ciki kuwa har da tsintar kaina kan katifa kuma numfashina ya dawo gangar jikina. A firgice na tashi ina dafe zuciya,sai kuma na yi saurin sauka na ɗauko ruwa na sha ina mai cewa “ na yi mummunan mafarki ” don ni duk a tunani mafarkin ne na yi ba gaske ba.Kan shimfiɗa na je kwanta,sai kuma na shiga tambayar to ina Kaka ta tafi cikin daren nan ƙila ko banɗaki.Ban kai ga samo amsa ba na ji wata uwar ƙara rudududuuu kamar ta sama za ta faɗo,tsoro ya kama ni na ƙanƙame jikina.Ina cikin wannan yanayi Kaka ta buɗo ɗaki ta shigo cakwal-cakwal da ƙafafunta na kaza,ido na murza na dai ga har yanzu ba su canza izuwa na mutane ba sai kuma na tuna tun jiya fa haka suke har lokacin da anty Sailuba ta zo ta ja ni muka tafi saloon. Na buɗe baki da niyyar tambayar ta “ Kaka wai...” amma sai ta katse ni ta hanyar cewa “ rufe mini baki tun da ke ba ƴar goyo ba ce,na taimaka miki don ɗaukar fansa shi ne kika baro ni can don ki nuna mini wuyan ki ya isa yanka ƙarfin ikonki(ƙarfin tsafi shine sai miyagu ke ɓoye shi su ce ƙarfin iko) ya ma fi nawa.Ina ce dai ni ce nan na raine ki tun ki na tsuman goyo,kuma ki sani daga yau na raba hanya da ke sai ki yi abin da kika ga dama tun da kin ishi kan ki.Sai dai ki sani tsohon kai ya fi sabon kai dafi ” ta na gama faɗa ta yi gaba ta nufi wani ɗan lungu da muke aje kaya.Wani ƙaton bindi na ga ya na yi mata reto kamar jela,duk ɓaɓatun da gama yi sam ban fahimci abin da take nufi ba don har zuwa yanzu duk na ɗauka mafarki ne na yi. Kayan jikinta ta canza sannan ta raɓa gefe na ta kwanta,hakan ya bani damar ganin salewar da gefen fuskarta yayi kamar wacce aka ƙona ga wuta. “Mi ya same ki kuma haka?” na yi tambayar ina shirin ɗora hannuna kan ciwon amma sai ta yi amfani da nata wurin buge ni tare da ɗora min yatsunta sak irin na mage don firgici har sai da na yi baya “ in kika kuskura kika taɓa ni zan yayage miki fuska” a tsorace na kai kaina na jingine ga bango. Ƙiri-ƙiri yau Kaka ta fito mini da ɓoyayyar siffarta,“ don Allah ki yi haƙuri ni ban mi na yi miki ba” na faɗa a tsorace ,“hum” ta yi wani ƙyaci kafin ta juya min baya ƙaton bindinta kuwa sai wani motsi yake kamar yadda mage ke yi. Muƙut! Na haɗiye wasu yawu kafin na ce “ wai Kaka wannan duk mine ne? Ƙafafuwan kaza ga kuma bindin mage a bayan ki?” Ba ta juyo ba ,amsa ta bani kai tsaye “ iya nawa kawai kika gani? Ke naki fa?” “Ni ai banda ƙafar kaza” “To ki duba wane kala gare ki” ta bani amsa . Furucinta yasa na tashi zaune don duba ƙafafuna sai dai mi zan gani? A madadin ƙafafu wani shabcecen bindi kifi ne tun daga wajen ƙuguna zuwa ƙasa na kifi ne.Ban san lokacin da na fasa wani uban ihu ba ina motsa bindin mai ɗauke da wasu ababe kamar mafarfeci. Ihun da na yi yayi daidai soma zubar ruwan sama masu mugun ƙarfi kafin ƙyaftawar ido ɗakinmu ya cika da ruwa.Hankalin Kaka a tashe ta soma tsalle-tsalle don kamar yadda mage ba ta son ruwa to ita ma haka take,ni kuwa maimakon ace na ji tsoron ruwan a'a sai na ji kamar ma na zo gidana ne .Ko kaɗan ban ji irin wannan yanayin ba na son fiddo kai waje,hasali ma wutsilniya na soma yi cikin ruwan ina yawo kamar wata ƴar ruwa.Munduwar wuyana ce ta soma fitar da wani haske mai ƙuna ,tsabar yadda hasken ke da ƙarfi har sai yasa na wani abu ya caki kwanyata da kuma daidai saitin zuciya ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai a washegari na tashi tuni kuma rana ta fito wantsar.Na yi miƙa na tashi zaune ina hamma,Kaka ta shigo ɗakin ta na mai cewa “sai yanzu kika ga damar dawowa?” Ban fahimci tambayarta ba hakan yasa na ce “Kaka ni da ke bacci ina kuma na je? Bari na yo fitsari na baki labarin mafarkin da na yi cabbb wai Allah na gode ma da mafarki ne” sai na sauka daga katifar na fita waje abun mamaki duk ruwa ne a kwance.Buta na ɗauka na raɓa ta inda babu ruwan na je na shiga banɗaki,ina fitowa na wanke fuska da ƙafafuwana sannan na koma ɗaki ina tambayar Kaka “wai ruwa aka yi jiya? Kuma ba lokacin damina ne ba” “Sarah kar ki raina mini hankali ki dinga yin abu kamar ba ki san mi kike yi ba,wuce dai ki tafi tun ɗazu Sailuba ke ta aikowa kiran ki” ficewa na yi na nufi saloon.Ina shiga na tarar da Leemat zaune a ƙasa yayin da kuma ƙawarta Watsima ke kwance kitson da aka yi mata jiya sai faman faɗin “washhh! Washhh” take yi yayin da ita kuma anty Sailuba ke ta masifa ta na cewa “ in ba abun ki ba Leemat daga saurayi ya ce kitson bai yi ba shikenan sai ki kwance?Allah duk da kin biya ni na ji zafi fa” “Anty Sailuba wallahi a rayuwata dama ban son kitso ,saboda na ci kuɗinsa ne na zo kika yi mini amma don wulaƙanci ba ki yadda ya fita daga ɗakin a guje ba kamar ya ga wata aljana” Watsima ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “In dai ya baki kuɗin iPhone ɗin ai shikenan ” “Ai ban yarda ma na raɓe shi ba sai da ya damƙa mini ita ga hannu,ta na can na baro ta a caji yanzu in gama wanke mini zan je na kunna ta na yi ta selfie ” Daga wannan ban sake sanin abin da suke tattauna wa ba sakamakon duniyar tunani da na lula ‘ kenan dama ba mafarki ne na yi ba a daren jiya?’ na tambayi kaina kafin kuma na yi wani makirin murmushi na ƙara cewa a zuci ‘ in dai haka ne kuwa Leemat ba zan bari ki yi selfie ɗin nan ba,wato za a yi mana burga da dogon gashi ’ Ina nan zaune ina ɗinka hulla aka gama kwance mata gashin,anty Sailuba ta wanke mata shi ta saka mata kwarkwaro sannan ta je ta zauna kan kujera aka ɗora mata tukunyar busar da gashi. Sai da na kwatanci gashin ya kusa bushewa kafin na ƙurawa tukunyar ido ina bata umarnin ta ja gashin Leemat ya shige can ciki ko minti biyu ba a yi ba kuwa tukunyar ta soma yin wata irin ƙara ta na fitar da haƙi haɗi da ƙauri. Hankali tashe anty Sailuba ta je za ta cire wayar lantarkin da ganga na kalli ƙawarta na ce ‘ɓangwale ki faɗi’ ji kake timmmm anty Sailuba ta faɗi tuni Leemat ta soma kuka haɗi da ƙoƙarin tashi amma ta kasa saboda yadda tukunyar ta riƙe gashin gam.Hayaƙin da ya soma fita na baiwa umarnin ya ƙara farashi ai kuwa shagon ya turniƙe da hayaƙi,Watsima sai tari take ta na cewa ta shiga uku ba ta ganin komai yayin da kuma anty Sailuba ke kukan ƙafarta.Sai a lokacin na miƙe na nufi Leemat,daidai gabanta na tsaya kafin na ƙuwara casque ido sai komai ya tsaya cak na jawo ta ina cewa “yi sauri ki tashi tun da an samu kin fito” Anty Sailuba da Watsima sai salati suke yi su na taɓa hannu ganin yadda gashin Leemat duk yayi wani iri kamar an kaɗa taliya ƴar murje.Kan kujera anty Sailuba ta zauna da Leemat wacce ke ta matsar ƙwallla,ɓarin mai aka yi mata iri-iri kafin a soma shatar gashin nan take ya soma zubewa ya na faɗuwa ƙasa sai ga Leemat da ƙwaiƙwayayen gashi.... [09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️ 👁️👁️👁️👁️👁️ HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 7-8 Wani irin daɗi yake ratsa ni ganin Leemat na kuka ta dalilina, wannan kuma bai rasa nasaba da MAITAR IDOna don duk wani mugu ya na jin daɗin mugunta musamman ga waɗanda suka taƙile shi. Leemat za ta kwashe gashinta don tafiya da shi amma anty Sailuba ta yi saurin hanata “ haba ke kuwa in kika tafi da shi a zai dinga tuna miki baƙin ciki,bari na baki mai ki dinga shafa wa gashin in sha Allah zai dawo normal” cike da siyasa anty Sailuba ta yi mata wayo ta karɓe gashin ta haɗa ta da mai ita kuma doluwar ta karɓa ba tare da ta san sayar da shi za a yi ba. Ko kuɗin gyaran gashin ba ta karɓa ba suka yi tafiyar su,ita kuwa anty Sailuba tamkar ma ta yi murna da hakan .Ƙaton gwangwanin da take ajiyar gashi ta buɗe ta zuba kafin ta juyo ta kalle ni ta tuntsire da dariya ta ce “ ikon Allah! Ki na ga fa jiya Leemat ta yi ta miki sharri yau ita ma gashinta ya koma irin naki ” Na saki murmushin ni ma kafin na ce “anty yunwa nake ji” “To acici ga abincin ki can tun ɗazu na ajiye miki shi” ta nuna mini da yatsanta na je na ɗauko. Zazafen tuwon shinkafa ne da miyar kuɓewa sai ƙamshi yake da alamu kuma girkin gida ne,ido kawai na ƙura ina kallon abincin wanda zuciyata ta shaida mini ‘an saka maganin mallaka’ da mamaki na ɗago na dubi anty Sailuba na ce “wai anty tuwon nan tun na yaushe ne?” Cike da masifa ta ce “babu ruwana da iskanci kamar ya na yaushe ne? Na sunan haihuwata.” “Daga tambaya?” “Ni na girka shi da kaina,kin samu ma na zuba miki sauran abincin mijina duk da uban kishin da nake da ” Anty Sailuba ta na da aure sai dai kusan shekara biyar ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba,ta na da mugun kishi sannan ta na son mijinta sosai kamar ta mutu.Duk in ta ji labarin yayi sabuwar budurwa haka za ta samo lambarta ko kuma ta je har gidansu yarinyar ta ci mata mutumci. A zuci na ce ‘shikenan Bilal ka shiga uku , Allah kaɗai ya san bayan maganin mallaka wane iri ake baka kuma’ a zahiri kuma cewa na yi “a'a gaskiya ba zan ci tuwon nan ba,yo ai in na yi hakan kamar na nuna raini ne a gare shi ” na kuwa rufe abincin. Anty Sailuba ta ƙure ni da ido kafin ta ce “ki ɗauka ki ci babu ruwana da shashanci” “Allah anty na ƙoshi ba zan ci wannan ba” na bata amsa don kuwa na san abu da magani ba zan cuci kaina ba. “Ke kika sani yi ta zama da yunwar don kan ki” ta faɗa tare da ficewa.Ina zaune ina tunanin ina zan samu abinci sai ga ƙawayena,da murna muka rungume juna kafin na ce “ ku shikenan tun ranar nan ba ku neme ni ba” Laila ta ce “ ke ɗin ce kin bamu tsoro sosai nitsewa kika yi cikin ruwa fa,hankali tashe muka je nemo masu ceto har sarkin ruwa fa sai da ya shiga neman wai a bai gan ki ba ” sai ta yi shiru hakan yasa Farida ci gaba da cewa “ amma Kaka na zuwa ta yi wasu bubuwa sai ganin ki muka yi gaɓar ruwa kamar wacce aka jefo,to shine fa duk muka ji tsoro saboda mutane na ta cece-kuce akan lamarin” “Don mi?” na yi tambayar,sai da suka kalli juna sannan Laila ta ce “ wai Kaka bokanya ce” na waro ido Farisa ta harare ni ta ce “ kamar ki ce ba ki yarda ba don dama tun tuni ana zarginta da hakan” Na haɗe rai na ce “ kun ga ban son wannan...” Laila ta katse ni “ to in ba boka ba wake bada magani? Kar ki manta in ciwo ya ta'azzara har gidanku ake zuwa karɓar magani” “Ni dai duk a bar wannan zancen yunwa nake ji” na faɗa don haka kawai na ji ban so a ci gaba. “ Ina da kuɗi mu je tashar kwaɗayi ” Farida ta faɗa ta na buɗe tafin hannunta kuɗi ne kuwa masu ɗan yawa,na ce “ ku je ku biyu ku sayo ni zan zauna nan kar anty Sailuba ta yi faɗa ” ba su musa ba suka fita ai kuwa ina nan zaune sai ga wata mata ta kawo ƴarta ƴar shekara goma a wanke mata gashi. Zaunar da ita na yi na soma wanke mata da sauri don haka kawai ban so ace ita ma ƴar mitsitsiyar nan an sayar da gashinta ga hajiyar birni.Sai dai duk saurin da nake a banza,ina daf da idawa anty Sailuba ta dawo idonta duk sun yi ja sosai.Sama-sama suka gaisa da Uwar yarinyar kafin ta samu wuri ta zauna ta na kallon yadda nake yin komai.Bayan na gama mata ta biya kuɗi suka tafi,gashin yarinyar nake son ceta sai dai na rasa ta ya zan yi haka. Anty Sailuba ta ɗauki masharcin da na shace mata kai ta shiga cire gashin da ya laƙe,ina ji ina gani ta jefa shi cikin gwangwani. Su Farida suka dawo,taliya ce suka sayo mini sai hanjin ligidi na karɓe na shiga ci yayin da anty kuma ta aike su . Haka muka yi ta samun customer har lokacin tafiya ta yayi gidan anty Hinda,ina zuwa sai na ga ta haɗe rai amma ban damu ba na shiga taya ta sayar da abincin yau ma dandanan muka sayar sai dai ko loma ɗaya ba ta bani ba. Na yi rau-rau da ido na ce “ anty ina nawa” “ Ni ai ba zan sake baki abinci ba,yau tun safe Kakar ki ita ta tashe ni daga bacci ta yi ta min masifa ta na zagina wai kar na sake baki abinci to wannan ma yasa na yanke shawarar sallamar ki” ta faɗa tare da ɗauko kuɗi ta miƙa mini. Na ƙi karɓa ina bata haƙuri amma ta ƙi haƙura har gidanta na bita,muna shiga ƴarta budurwa mai sunan Sharifa ta taso cike da wulaƙanci ta na cewa “ uwar mi kika zo yi gidanmu? Dama shi talaka bai iya samun wuri ba,ɗazu don rashin mutumci kika turo mana wannan tsohuwar Kakar taki ta zo ta yi wa mutane hauka.Duk alherin da muke yi muku ba ku gani ba har da wani cewa an zuba miki guba a abinci” Anty Hinda ta ce “ kin ga Sharifa zo ki ƙirga kuɗin nan mu ga ribar da muka samu” ta na hararena ta karɓi kuɗin da ke cikin wata roba ta koma gefe ta na ƙirgawa ta na masifa “ daga yau ni zan dinga taya uwata sayar da abinci sai ki tafi ba mu buƙata” da ta ga na ƙi gusawa ta juye kuɗin ƙasa tare da cika robar da ƙasari ta watsa min a fuska har sai na ji tsoro.Duk wannan bai ishe ta ba sai da ta wani ja ni ƙiiii ta cillo ni waje ,zuciyata ce ta soma tafasa yayin da duk illahin jikina nake jin ya ɗau zafi kamar garwashin wuta.Ni kaina ban san lokacin da na ɗauki hanyar Gulbi ba,kawai haka na ji a can ne kawai zan samu salama.Tun daga nesa da na fara hango ruwan sai nake jin kunnuwana na amsa kira, ina isa daidai gaɓarsu na yi tsaye ina kallon yadda suka soma yin zillo tuni munduwar wuyana ta fara motsi ta na ɗaukar wani haske.Ido biyu ba cikin bacci ba na soma jin tafin ƙafata na yi mini ƙaiƙayi,ko kafin ƙyaftawar ido na rikiɗe na zama Siren (sirène ) ina daga kwance gaɓar ruwa nake ƙarewa bindin nawa na kifi kallo sai motsi yake ya na fitar da haske.Kamar wata kifanya na yi tsalle na faɗa ruwan,ƙasa sosai nake nitsawa ina jin wani sanyi da daɗi na ratsa ni. Idona buɗe suke taram haka kuma sheɗa ta daidai take babu alamun gargada irin in mutum ya shiga ruwa.Ina tsaka da yawo cikin ruwan na soma jin dariya,na juya na soma bin inda sautin ke fitowa har na iso kusan wani dutse.Wata budurwa da saurayi na gani su na wasa haɗi da hirar masoya,su ma iri na ne rabi mutum rabi kifi.Budurwar na gani na ta nufo ni ta na cewa “ waooo! Princess” ƙyafƙyaf kawai na yi da ido ina kallonta har ta iso gare ni ta na shafa goshina wanda sai a yanzu na farga akwai wani tambari a jikinsa na haske. “ Ya aka yi kika zo wannan ƙasar? Ko wani aiki kika zo yi?” abun mamaki kasa magana na yi duk da kuwa na so buɗe baki,saurayin ne ya zo da sauri ya ja ta gefe ya na cewa “ Sarlah ya kike tsayuwa kusa da ita ko ba ki tambarin Masarautar Goma ne da ita ba?” haka suka tafi suka bar ni cike da mamaki. Sama-sama na soma yi har na fito gaɓar ruwan ,so nake na koma gida.Sai bayan na fito ne bindin ya ɓace na dawo da ƙafafun mutane,na saki murmushi ina jin wani daɗi yayin da kuma zuciyata ta yarda ta lamunce mini tabbas ina da wata baiwa ba daidai nake da sauran mutane ba. Ina zuwa gida na ga takalmin mutane a ƙofar ɗakinmu,ban nemi izini ba na shiga. Sai na tarar da wata mata a zaune yayin da Kaka kuma ke ta wasa da ɗiyan wuri ta na zayyano mata abubuwan da za su faru gobenta.Wato dibo Kaka take,macen ta yi godiya ta biya kuɗi irin sosai ɗin nan kafin ta fice.Na dubi Kaka wacce ke ta faman ƙirga kuɗi kamar ba ta gan ni ba,na yi gyaran murya na ce “Kaka...” ta yi saurin katse ni da “kin ga Sarah wuce ki bani wuri ban ƙaunar ganin ki,rainon ki bai yi mini rana ba sam.Ban ga amfanin zama da ke ba don haka ki kwashi inaki-inaki ki bar min gidana” Wata irin dariya na soma wacce sama ban lura da ruwan da suka fara ɓulɓulowa daga ƙasa ba har sai da suka kawo daidai wuyana.Tsit na yi ina kallon Kaka wacce ke ta ƙoƙarin fita daga ɗakin amma ta kasa,“za ki mayar da ruwan nan ƙarƙashin ƙasa ko sai sun kashe ni ” ta faɗa a tsorace ta na riƙe bango hakan kuma sai ya ƙara bani wata dariyar amma na gimtse munduwar wuyana na lalubo na riƙe ina yi wa ruwa magana da idona,a sannu a hankali suka yi ƙasa har suka ƙwafe. Da wani irin saurin Kaka ta cillo ni waje ta na mai cewa “ashe duk yadda nake tunani kin wuce nan,ke annoba ce ba zan iya zama da ke ba” Zuwa wannan lokacin na fahimci Kaka ba da wasa take ba,hakan yasa hankalina ya tashi na soma roƙonta “Kaka in kin kore ni ina zan je? Ke ce komai nawa ke kika raine ni ban san kowa ba sai ke” “Ban haɗa komai ba da ke wallahi tsintar ki na yi da tunanin za ki yi mini amfani a gaba ki gaje ni ashe musamman da na ga ki na ɗauke da *MAITAR IDO* ashe ban san bala'in naki ya wuce nan ba sai yau na ida ganewa Mamy Water ce ke ” Idona na zubar da ƙwalla nake kallon Kaka,tuni kuma ƙwaƙwalwata ta soma hargitse wa.Ana kiran sallar magrib haka Kaka ta jefo ni waje ni da jakar kayana ta kama gidanta ta rufe,kan dakali na zauna ina ta wasiƙar jaki har aka yi sallar isha'i.Ganin dare na ta ƙara yi na miƙe tsaye na soma tafiya,direct gidan anty Sailuba na nufa don ita ɗaya ce yanzu ta rage min wacce nake tunanin za ta zame mini bango.Da sallama na shiga gidan,tun kafin na ƙarasa nake jiyo sautin muryar mijinta Bilal ya na cewa “wallahi Sailuba ko mi za ki yi sai na ƙara aure,kuma goben nan zan je na yi wa Hajiya bayani ta samo min mata cikin danginta tun da ni ko na nema ba za ki bari ba” kai na kutsa na shiga ɗakin,anty Sailuba ta juyo ta na kallona a zuciye “uban mi kika zo yi kuma yanzu cikin dare?” ban bata amsa ba sai mijinta da na ƙure cikin ido ina mai taɓa munduwa ta ni kaina ban san dalilin yin haka ba. “My Lub Baby wane ni na yi miki kishiya don Allah ki kwantar da hankalin ki ina mugun son ki” Bilal ya faɗa ,ni kuma na saki murmushi ashe duk anty Sailuba ta ga komai.Hannuna ta ja muka fito waje kafin ta ce “ke mine ne kika yi wa mijina? Ko ke ma bokancin kike yi kamar Kaka” na girgiza kai na ce mata “a'a ina da MAITAR IDO ne mai sarrafa abin da duk nake so,kin ga gashin Leemat ma ni ce nan na mayar da shi yanzu kuma na juye tunanin mijin ki babu ke babu kishiya” anty Sailuba ta rungume ni ba tare da tunanin wannan ɗin fa abun gudu ne,ta ce “ina na za ki je?” bayani na yi mata kan cewa Kaka ta kore ni daga gidanta sai a lokacin kuma na ji hawaye ,ta goge mini su ta na cewa “sai ki zauna gidana” sai ta ja hannuna muka koma ciki..... Ga waɗanda suke son fara payment ƙofa a buɗe take 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO* HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 9-10 Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan. Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda. Na fito na wanke jikina na koma ɗakina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da samun wuri ta zauna. Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari” “ Shikenan ya bar zancen auren?” ita ce tambayar da na yi mata. Ta ce “ eh ya bari sai kuma ya ɓullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can gidan da ɗan uwansa ya gina kin san nan haya muke” Na ce “ to ai hakan ba matsala ba ce kin ga kuɗin da yake biya na haya sai ku yi wani abu da su” Ta girgiza kai ta ce “ uwar mijina ƴar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ƴar aiki na ɗauke ki” Tashi na yi tsaye na ce “ babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ƴar aikin sai na zama” tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a ƙarshe na je na yi wanka sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na ƙoshi.“ Ki shirya za mu je kasuwa abokan Bilal yau a nan za su ci abincin dare” Na ce “ kenan yau ba za mu buɗe shago ba?” “ Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su” Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ƙofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na ƙa'ide ta faɗi ƙasa.Na yi murmushin mugunta har na matsu ƙarfe sha biyu ta yi,da muka shiga kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki waɗanda normal mutane ba su iya gani.Yawancin ƴan kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba tare da sanin ita fa wannan layar ta na ɗauke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi da ka bar kuɗin ka. Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta miƙa min su na riƙe,daga nan muka wuce wurin ƴan yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan yaji wanda ake kira tsidagu irin ƴan mitsimitsi ɗin nan. “ In ɗauki guda?” na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce “ ɗauka mana” Cike da masifa anty Sailuba ta ce “ mi za ki yi da tsidagu kuma?” na ce “ kawai ya burge ni ne sai na ɗauki ƙwaya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen ƴan sayar da nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji ina son ganin shi ɗin kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na duƙa ina kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na miƙe tsaye sai idona ya sauka kan wasu ƙafafuwan jaki a tsaye daram,a hankali na miƙe sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido huɗu muka haɗa da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba ballantana ace mutane za su ji. “ Mi kuma ya kawo macen Siren cikin mutane? Ko da yake ba abun mamaki ba in ka shigo kasuwa babu kalar jinsin da babu” Ni ma ta idon na mayar masa “ wane ne kai? Ya aka yi ƙafafunka suke na jaki?” “ Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni ” Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu ɗaya na ƙwarai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya ɗauko su inda aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka faɗi rashin lafiya. Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar anty Sailuba na cewa “ Sarah ke? Tun ɗazu fa nake yawon neman ki” sai kuma ta harari mai sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta “ amma anty mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha” Ta ja baki ta ce “ arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na taɓa saya lokacin da abokan Bilal za su zo amma abun mamaki suka ƙi ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin warinsa.A ƙarshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga ƴar rige-rigen shiga banɗaki” na ƙyalƙyace da dariya kafin kuma na ce “ to anty mi yasa kuka ci alhalin an faɗa muku ya lalace?” Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina ‘ saboda ita da mijinta normal mutum ne!’ sai kuma zuciyata ta bada darammm ‘ to in haka ne su abokan Bilal waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai gida babu wanda ya ce komai. Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama. Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki. #GIDAN ANTY HINDA Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke. Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi” Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar bokanya ” “Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi” Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan tukunyar miyar kwacaaaa. Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar . Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba” “Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba” cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu. Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa” Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa. “ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu masu saya” Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi shiru da bakin ki” “ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa. Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi” “Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?” “Allah Mama na cire” “Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu” “To wannan ɗin ya za mu yi da shi?” “Ko almajirai sai na rabawa ” Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda . “ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe. “ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa ,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi. Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne” “Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin” Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara. # GIDAN BILAL Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan sun tafi ” Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi alamun baƙin ne suka zo. Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita” “Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu” “ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar” “ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi magana. “ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa. Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna” Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin. Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya. Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?” Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ” “Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo” A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idonsa ya sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi ......... Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f. NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne. 29 jully 2024 MRS SADAUKI ce 🌚 [09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO* HoRrOR story☠️ Na © Chamsiya Laouali Rabo #MRS SADAUKI💫✍️ *FCWA ☀️* 9-10 Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan. Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda. Na fito na wanke jikina na koma ɗakina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da samun wuri ta zauna. Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari” “ Shikenan ya bar zancen auren?” ita ce tambayar da na yi mata. Ta ce “ eh ya bari sai kuma ya ɓullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can gidan da ɗan uwansa ya gina kin san nan haya muke” Na ce “ to ai hakan ba matsala ba ce kin ga kuɗin da yake biya na haya sai ku yi wani abu da su” Ta girgiza kai ta ce “ uwar mijina ƴar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ƴar aiki na ɗauke ki” Tashi na yi tsaye na ce “ babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ƴar aikin sai na zama” tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a ƙarshe na je na yi wanka sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na ƙoshi.“ Ki shirya za mu je kasuwa abokan Bilal yau a nan za su ci abincin dare” Na ce “ kenan yau ba za mu buɗe shago ba?” “ Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su” Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ƙofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na ƙa'ide ta faɗi ƙasa.Na yi murmushin mugunta har na matsu ƙarfe sha biyu ta yi,da muka shiga kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki waɗanda normal mutane ba su iya gani.Yawancin ƴan kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba tare da sanin ita fa wannan layar ta na ɗauke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi da ka bar kuɗin ka. Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta miƙa min su na riƙe,daga nan muka wuce wurin ƴan yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan yaji wanda ake kira tsidagu irin ƴan mitsimitsi ɗin nan. “ In ɗauki guda?” na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce “ ɗauka mana” Cike da masifa anty Sailuba ta ce “ mi za ki yi da tsidagu kuma?” na ce “ kawai ya burge ni ne sai na ɗauki ƙwaya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen ƴan sayar da nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji ina son ganin shi ɗin kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na duƙa ina kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na miƙe tsaye sai idona ya sauka kan wasu ƙafafuwan jaki a tsaye daram,a hankali na miƙe sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido huɗu muka haɗa da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba ballantana ace mutane za su ji. “ Mi kuma ya kawo macen Siren cikin mutane? Ko da yake ba abun mamaki ba in ka shigo kasuwa babu kalar jinsin da babu” Ni ma ta idon na mayar masa “ wane ne kai? Ya aka yi ƙafafunka suke na jaki?” “ Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni ” Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu ɗaya na ƙwarai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya ɗauko su inda aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka faɗi rashin lafiya. Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar anty Sailuba na cewa “ Sarah ke? Tun ɗazu fa nake yawon neman ki” sai kuma ta harari mai sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta “ amma anty mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha” Ta ja baki ta ce “ arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na taɓa saya lokacin da abokan Bilal za su zo amma abun mamaki suka ƙi ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin warinsa.A ƙarshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga ƴar rige-rigen shiga banɗaki” na ƙyalƙyace da dariya kafin kuma na ce “ to anty mi yasa kuka ci alhalin an faɗa muku ya lalace?” Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina ‘ saboda ita da mijinta normal mutum ne!’ sai kuma zuciyata ta bada darammm ‘ to in haka ne su abokan Bilal waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai gida babu wanda ya ce komai. Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama. Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki. #GIDAN ANTY HINDA Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke. Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi” Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar bokanya ” “Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi” Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan tukunyar miyar kwacaaaa. Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar . Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba” “Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba” cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu. Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa” Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa. “ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu masu saya” Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi shiru da bakin ki” “ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa. Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi” “Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?” “Allah Mama na cire” “Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu” “To wannan ɗin ya za mu yi da shi?” “Ko almajirai sai na rabawa ” Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda . “ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe. “ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa ,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi. Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne” “Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin” Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara. # GIDAN BILAL Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan sun tafi ” Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi alamun baƙin ne suka zo. Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita” “Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu” “ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar” “ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi magana. “ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa. Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna” Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin. Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya. Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?” Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ” “Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo” A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idona ya sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi ......... Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f. NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne. 29 jully 2024 MRS SADAUKI ce 🌚 [09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: ```MRS SADAUKI💫✍️``` My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500₦ ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuɗin karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne . *FCWA ☀️* 11-12 https://chat.whatsapp.com/FMimfpwTVDDBjZmDZw2Uhs *Inda muke turo available products din mu don ki gani, ki zaɓi wanda kike so sannan ki siya ko ki tallata kema kisami naki*🥰 *Kayan mu order muke daga ƙasashen waje, foreign ne masu kyau da quality* *Duk abinda mukayi posting available ne, daga kin siya za'a turo miki abinki ba ɓata lokacin jira*. 08032350261 😍😍😍DAMARKUCE LOKACINKUNE MUN RAGE FARASHI SOSAI DAN KUMA KUSAMU KOMAI DA KUKA SANI ZAKU SAMESU KWASHA KWASHA ARHA GARABASA 🤝🤝🤝KUMA DUK INDA KIKE KAYANMU ZASU SAMEKU CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH Da sauri na saki labulen ina jin zuciyata na dukan uku-uku,ina nan daga tsaye dafe da saitin zuciya na ƙara jiyo amon muryar su “ zarginmu ya zama gaskiya fa mine ne abun yi?” “ Ta fito kawai mu gane wa junanmu tun da duk bisa hanya ɗaya muke” “Hhhh ai kuwa dai ƙila ita ma da nata plan ɗin a kansu” Shine abin da na ji su na faɗa ,amma na yi mamakin haka a gaban sun anty Sailubar suke faɗar haka ko dai sun tashi ne? Don gusar da zargina sai na ƙara kama labule don na sake leƙawa,ina buɗe wa na yi tozali da ƙaton ido manne a jin ƙofar ɗakin nawa ban san lokacin da na fasa wani matsanancin ihu ba da ya karaɗe duk illahin gidan.Ruwa ne suka soma ɓulɓulowa su na cika gidan ga baki ɗaya hatta cikin ɗakuna. Tuni siffata ta canza zuwa kala biyu bindin kifi ya fito min,ruwan su suka ja ni izuwa falo. “Waooo!” suka haɗa baki su na kallona sai nitso nake ina kaɗa bindi cikin ruwan,sai wannan lokacin kuma na ankare anty Sailuba da mijinta Bilal sai bacci suke yi kamar waɗanda ba su da rai. “ Azo ka na gani abin da nake gani?” “Yes Musty ina gani” “Naser kai fa?” “Ina gani ni ma ” duk suka tsoma bakinsu a nan ne na san sunan kowa daga cikinsu. Musty ɗin alamun ya fi su ƙarfi da surutu ya dube ni da kyau ya ce “ muna so mu san plan ɗin ki akan wannan ahalin?” Idona na buɗe ina kallonsa waɗanda har yanzu ba su bar mugun hasken nan ba,“ku fara sanar da ni naku plan ɗin tukuna” na faɗa tare da dukan ruwa da bindina suka bada wani bacaaal. Suka ƙara kallon juna kafin shi Musty ɗin ya ce “ ki yi mana alƙawari za ki taimake mu” Na juya baya ina mai cewa “ tun da ba za ku faɗa ba kun ga tafiyata” “Tsaya mana ,Musty kawai mu sanar da ita zai fi.Muna zuwa nan ne don jawo hankalin Bilal ya shigo a tsagenmu amma mun gagara yin galaba kansa,ruhinsa na da mugun ƙarfi shi da matarsa” Na juyo ina duban Naser ya faɗa wanda na fahimci kuma duk cikinsu ya fi sauƙi don ya na da tsoro.“ Ta ya aka yi duk ƙarfin ikon ku amma suka fi ƙarfin ku?” na jefo tambayar ina kallon Naser ,sai da ya ɗan yi shiru kafin ya ce “ kin san su na da yawan addini su na salloli kan lokaci ” Na lumshe idona ko da ya zo nan da zancensa,ina jinjina wa anty Sailuba wacce ta yi riƙo da Addini duk matsatsin aikin shago bai hana ta yin sallah muddin lokacinta yayi na fahimci hakan tun lokacin baya da nake wuni wurinta kafin na soma yi wa anty Hinda aiki. “Na san ke ma shine dalilin da ya hana ki cin galaba kansu duk da ba mu san ke mi yasa kike bibiyar rayuwarsu ba” Azo ya faɗa ya na matso wa kusa da ni. Wani irin zafi ne na ji gangar jikinsa na fesar wa duk da kuwa ina cikin ruwa,na ce “ ta ya aka yi ka san ina bibiyarsu?” Yayi murmushin gefen baki ya ce “ in ba haka ba mine ne zai fito da ke daga can cikin asalinki ki zo nan? Tun daga Gombo kike sannan a yadda kike Siren kika juri zama a wajen ruwa kawai don ƙudirin ki.Faɗa mana mine ne shi?” Ban da lokacin tunani ,na kuma fahimci ko masu ganin abin da normal mutane ba su gane ba komai ne suke da sanaya a kai ba.Ba don haka ba tabbas da za su fahimci ban zo nan da niyyar cutar da su anty Sailuba ba,amma don kar su raina mini fiƙirata sai kawai na ce musu “ yanzu dai kawai mu zama ƙawaye daga baya duk za mu tattauna akan abin da ya shafi duniyarmu,tun ɗazu kun saka bayin Allahn nan bacci ya kamata ku tashe su haka” Azo yayi wata dariya ya na mai cewa “ da alamu fa Siren tausayin su kike” Na girgiza kai na ce “ ko ɗaya,kawai ban so su zargi wani abu ne” “Kuma kin yi gaskiya komawar ki ɗakin ki” “Kafin nan ta janye ruwan nan da ta cika mana ɗaki da su” Murmushi na yi ina mai kai hannu ina taɓa Munduwar wuyana haɗi da kallon ruwan da ido ina basu umarnin su koma,a haka na shige ɗakina ni ma tuni ruwan kuma sun ƙwafe tsab .Na kwanta kan shimfiɗata ina kallon rufin ɗakin ina cewa “ karo na biyu kenan da na ji sunan Gombo,shin ina ne ? Wace ƙabila ce?” ban ida rufe bakina ba kafin wani girgije ya danno kai tamkar shine rufin ɗakin.Munduwar wuna ta soma zuƙo girgijen nan a hankali ya soma tarwatsewa na zamar haske mai kamar mai sai kuma ya shiga radadowa ina fasa ƙirjina ya na shiga “ Mamaaa!” na furta da ƙarfi saboda amon muryarta da ya cika mini kunnuwa ,yayin da kuma hoton siffarta wacce take flou ta bayyana gare ni ga wani Baby a hannunta kafin ta aje shi tsakiyar daji ta ce “ sunan ki Sarah !” Hawaye suka zubo mini kan kumatuna,na samu abu na farko daga cikin tarihina wato jefar da ni mahaifiyata ta yi sai dai ban san dalilinta na yin haka ba. Daga can falo ina jin su Musty na yi wa su anty Sailuba sallama,babu jimawa kuwa ta shigo ɗakin ta na mai kiran sunana “ Sarah taso ki yi kallo baƙin sun tafi” na girgiza mata kai saboda ba na cikin yanayi,“ fushi kika yi don na hana ki fitowa?” Kai na girgiza tare da tashi na zo na rungume ta da ƙarfin tsiya ina mai cewa “ anty Sailuba ina son ganin Mahaifiyata,ina jin kewarta.Ina son jin soyayyar nan da ke tsakanin uwa da ƴa amma ni wurin Kaka Anaba na taso wacce babu alaƙar jini ko ɗaya a tsakanin mu” Anty Sailuba ta riƙe ni ta na cewa “ haba Sarah kar ki sa na yi kuka mana,kin ga dama yanzu haka ina cikin wani yanayi.Sannan wa ya faɗa miki Kaka ba jininki ba ce,ƙila ta faɗi haka ne don ta hora ki ” Na sake ta na ɗan ja baya ina mai girgiza kai na ce “ a'a gaskiya ta faɗa don yau ɗin nan aka nuna min lokacin da Mamana ta jefar da ni a cikin jeji” Anty Sailuba ta jefo min wani kallo “ don Allah kar ki sa na fara jin tsoron ki,wa ya sanar da ke to?” Shiru na yi don ni kaina ban san ya ko wane ne ba. “ Kin ga sai da safe bari na je na yi karatu ” har ta kai bakin ƙofa na tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta,ta juyo na ce mata “ ki ƙara dagewa da addu'a haka ma mijinki” ba ta ce komai ba ta fice. Sailuba Ita tun farkon zuwan su Naser gidanta sam ba ta so haka ba,sai dai babu yadda ta iya saboda su ne manyan abokan mijinta duk da ba ta san su ba kafin aurensu da Bilal amma a yanzu bai da wasu bayan su. A duk lokacin da za su kawo musu ziyara haka za ta kwana cikin kasala da mugayen mafarkai,sai dai ba ta taɓa alaƙanta hakan da su ba abu guda kawai ta riƙe shi ne addu'a sannan ta na yin sallolinta kan lokaci wannan kuma na ɗaya daga cikin turbar da Bilal ya ɗora ta don shi Ustaz ne ya na da karatu sosai saɓanin Sailuba da ko izo ɗaya ba ta da. Yanzu bayan fitar su Musty haka kawai ta ji ta na son yin tilawar karatun da ta iya,Bilal ya sanar da ita zai wuce makarantar da yake bada karatu wannan yasa ta shiga ɗakin Sarah don ta zo ta yi kallo.Sai da ta yi alwala sannan ta soma karatun fatiha,falaqi da nasi zuwa suratul Masad.Sam ba ta raina karatun da take da haka bayan ta gama ta shiga yin addu'o'i na neman tsari da kuma neman buɗi. A can gidan Hinda kuwa hatta salloli ba su sa sun zubar ruwa a jikinsu ba, ƙememe suka bari ta wuce su.Sai faman saƙa da warwara suke,Sharifa da ta gaji da abun ta ce “ Mama ina ga kawai mu je gidan Kaka ta bamu magani tun da dama aikinta ne bayar da magani” Hinda ta ce “ wa ya sani ma ko ita ce ta yi mana ture? Kin ga babu inda zan je in zuwa za ki yi ban hana ki ba sai kin dawo” Sharifa ta saka kuka ta na yi “ shikenan in na mutu sai ki huta” “ Tashi mu tafi tun da kin fara jawo mana mutuwa” cewar Hinda ta na mai zarar mayafi, Sharifa ma haka . Gidan Kaka suka nufa sai suka tarar da shi a rufe suka shiga bubuga shi , Sharifa ta ce “ dubi langa-langar ƙyauren nan wai shi ne ya rufu ruf ko rawa bai yi” Hinda ta ce “ banza wa ya faɗa miki normal ƙyaure ne? To aljanu ke rufe shi ” sai kuma suka ci gaba da bugawa. Kaka wacce ke can ɗaki ta na shagali ita da ƙawayenta bokaye da suka kawo mata ziyara ta ce “ ku na ga zan je na ga ko waye ke bugun ƙyaurena” Ɗaya daga cikin tsoffin ta ce “ kika sani ƴar tsintuwar ki ce ta dawo” sai duk suka kwashe da dariya,Kaka ta ce “ ai na bar zama da ita,ina dalili ta min kisan gilla tsakar dare” sai kuma ta je ta buɗe gidan. Hinda ta ce “ gafara dai Kaka,ki daɗe ki yi ƙarko akwai wata bayan ke ne mai bayar da magani ? Kai babu guda ɗaya ce rak Hajiya Kaka mai abun ban mamaki,mun zo ne a bamu magani sakamakon wata cuta da ta shafe mu” Kaka ta basu wuri suka wuce sannan ta ƙara jan ƙyauren ta rufe,ta yi musu iso suka zauna kan tabarma.Kayan aikinta ta fidddo ta ɗora fitila aci balbal sannan ta soma wasa da ƴaƴan wuri,tsawon lokaci ta na yi kafin ta ɗago ta dube su ta ce “ duk wanda ya ce muku zai iya karye asirin nan da aka yi muku kawai yaudarar ku ce zai yi ya ci kuɗin ku,sihiri ne wanda ba a cika samunsa ba a wannan duniyar amma ku jira na kira ƙawayena mu ji mi za su ce” Kaka ta kira su kuwa,tsofi ne biyu har sun fita tsufa abin da Kakar tace su ma shi suka faɗa kafin ɗaya ta ce “ Anaba wannan ai sihirin ruwa ne ,doli ya na da alaƙa da wanda yake aiki da Mamy Water ko kuma sam wanda ba nan duniyar yake ba ” ɗayar ta cabke zancen da “ ko kuma duk duniyoyin biyu mabanbanta ya na rayuwa cikinsu ba” Furicin nan ya haskawa Kaka fitila har ta fahimci tabbas aikin Sarah ne,ta gyara zama ta ce “ Hinda mu ga kuɗin da ke gare ki zan yi miki aikin nan don yanzu na fahimci tushensa ” Ba tare da wani tunani ba Hinda ta kwance kuɗin da ke ɗaure da ga haɓar zanenta ta bai wa Kaka,ƙawayenta suka shiga tambayarta “ wai mi za ki yi? Anaba kar ki jefa kan ki cikin masifa aljanun ruwa ƙarfi ne da su sun fi waɗanda muke aiki ƙarfin iko” Kaka ta ce “ babu wani nan ku dai ku jira ni yanzu na dawo” ta faɗa tare da ɗaukar wata ƙwarya ta fice,ba ta zarce ko ina ba sai gaɓar ruwa.Ƙwarya ta aje gabanta sannan ta soma wasu suratai daga ƙarshe ta jefa kuɗi cikin ruwan,canɓallll sautin faɗawar kuɗin ta fito kamar ƙyaftawar ido kuwa ruwan suka fara tashi sama su na hargowa kafin wata murya ta soma yi wa Kaka magana “ faɗa mana mi kike da buƙata?” “ Magani domin warkar da wasu” “Ai kin san da cewa komai ya na da farashi ko?” “Na sani a bani maganin” Kaka ta faɗa ba tare da ta tsaya tambayar mine ne farashin ba,ƴar ƙwaryar da ta ajiye ce ta soma cika da ruwa tsulululu har sai da ta cika tab kafin Kogin ya bar motsi.Cike da murna Anaba ta ɗauki ƙwaryar ta koma gida,da kanta ta yi wa su Hinda wanka abun mamaki kuwa sam ba su ji ƙaiƙayi ba. “Mun gode sosai Kaka Anaba haƙiƙa ke shararriya ce kuma gwana wurin warkar da cuta” Hinda ta faɗa kafin ta ja hannun Sharifa su koma gida.Sai a lokacin suka samu suka yi sallah,da suka zo kwanciya bacci suka kasa saboda uban zafin da suka ji sai zufa suke .Wanka suka yi,Sharifa ta kunna masu fanka a haka suka samu suka yi bacci,sai dai abu kamar wasa sai gumi ya jiƙa shimfiɗar tasu.Da farko Hinda ce ta soma tashi ta sake yin wani wankan kafin sharifa ita ma ta yi,sam ba su kawo komai a kansu ba kawai sun ɗauka yanayin garin ne ya ɗau zafi. SARAH Da tunanin Mamana na samu bacci ya ɗauke ni,ko minti biyu ban yi ba tsinci kaina can ƙarƙashin ruwa ina wasa da su cike da nishaɗi.A inda nake ƴan mata ne kewaye da ni su na min taɓi kowacce da bindinta na kifi ga dogon gashi sannan fuskokinsu masu kyau ne farare tas saɓanin ni da ke baƙa ƙirin.Na tsaya da wasa da ruwan na ce “ ya aka yi dukkan ku farare ne amma ni kuma baƙa ?” Wata murya ta namiji ce ta bani amsa “ saboda ke Mamarki kika ɗauko” da gudu na ga ƴan matan na tserewa su na cewa “ ga sarki nan ! Ga sarki nan!” Na juyo muna kallon juna da wani kyakkyawan namiji zai kai a ƙalla shekara arba'in da biyar,kansa ɗauke da kambun sarauta na zinari haka ma daidai damatsansa an yi masu ado da wani ƙaton awarwaron zinari.Wuyansa kuwa sarƙar Munduwa ce irin tawa sai dai tasa ta fi tawa girma ,ya zo kusa da ni ya jawo ni ya na shafar gashina idonsa ne suka ɗau wani haske ya dinga juya su ya na umarta gashina ya ƙara tsayi sai gashi kuwa gashin nawa ya zama dogo har bisa gadon baya .Sosai na ji daɗi,cikin murna na ce “ wane ne kai?” “Ni ne Babanki Sarah ” ya bani amsa tare da ɗora min wata gyanɗama a baki ya ce “ sha! Ruwan ƙarfin iko!” ban musa ba na soma sha,shi kuma ya na shafar gashina ya na mai ci gaba da cewa “ barkar da ranar zagayowar haihuwar ki” sai ya cire kambun sarautar kansa ya ɗora min . “Sarah? Sarah keeee!” muryar anty Sailuba ta tashe ni daga bacci,a hankali na ware idona sai na ga ɗakin da duhu. “Ƙwan lantarkin ɗakin ki ya ƙone sai an saka sabo ,tashi dai ki yi sallah lokaci yayi” sai kuma ta fice. Zaune na yi kan shimfiɗa mafarkin da na yi ya na dawo min,ina nan zaune sai na ga ɗakin ya cika da wani mugun haske kuma .Ban yi wani dogon tunani ba na fahimci daga inda hasken ke fitowa,na kai hannu na laluba kaina .Wani irin taushi da santsi ne suka ziyarce ni,wato gashina ya zama dogo irin na turawa hatta Kambu sarautar da na gani a mafarki ga shi a hannuna.Juyasa na soma yi kafin na soma shafarsa,ƙaton jan dutsen da ke tsakiya ya fitar da wani farin haske hakan ya bayyana mini kyakkyawar baƙar fuskata.A karon farko da na fara ƙarewa kaina kallo,ina da doguwar fuska mai siririn hanci idona sun so su yi shige da na mage,gashin girata da na idona su na da yawa sosai yanzu kuma ga wani ƙarin adon wato gashin kaina ya koma mai yawa.Shafar shi na soma yi ina jin tsantsar farin ciki tare da tambayar kaina ‘ shin gaske mafarki ne na yi ko kuwa rayuwar zahiri ce na je can ɗin a gaske?’ banda amsa,kawai sai na je na ɓoye Kambu sarautar cikin kayana tuni kuma haskensa ya ɗauke yayin da kuma na lantarki ya dawo. Gashina na harɗe wuri guda da abun ɗaurewar da ni kaina ban san inda na same shi ba,sai kuma na laulaye gashin yayi tudu kamar na sa a cuci maza sannan na ɗaura kallabi. Fita na yi na je na yi fitsari tare da wanke jiki na dawo na kwanta,sai dai sam na kasa komawa bacci har rana ta fito wantsar na fita na yi shara na wanke kwanuka a ƙarshe kuma na yi wanka na zo na canza kaya . Sai na tsurawa Kambun ido ina kallo ina murmushi tuna wai mahaifina ya bani shi, “ Ke lafiyar ki?” na ji muryar anty Sailuba.Da sauri na rufe kayan na ce “ babu komai ina kwana anty?” “Lafiya lau,ungo ga makullin shago ki je ki share shi ki goge komai sannan a cika manyan bokitan ruwa yadda ba mu yi aiki ba jiya ai na san yau aiki sai mun ture wa buzu naɗi wasu ma har sun fara kirana ” Makullin na karɓa,har zan fita ta ce “zo ki karɓi kuɗin da za ki ci abincin kari,don mayun jiya duka suka cinye komai mtswww” ta ja tsuki. Na dube ta da kyau na ce “kenan kin san Mayu ne su?” Yadda ta tsure ni da ido yasa na yi saurin canza tambayar “ina nufin kenan Mayu ne?” “Hum! Ungo dai ban iya surutun ki da kika iya ba” kuɗin na karɓa na fice,maimakon na je shagon a'a sai na wuce gidan anty Hinda don ina son ganin yadda suka kwana tun a hanya nake tuntsira dariya har na isa.... Littafin kuɗi ne Hajiya domin samunsa tun daga farkonsa har zuwa ƙarshensa ki yi payment ɗin 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 Ni kuma sai na saka ki paid group inda nake posting.