[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* *BISMILLAHIR RAHAMINIR RAHIM* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARREN LABARINE, SUNAYEN GARURUWA DA WASU WURAREN DUK ƘIRƘIRARRUNE* *BAN YARDA AJUYA MANI LABARI TA KOWACE SIGABA SAI DA IZININA, DAN ALLAH A KIYAYE* ____________________ *PAGE* 1️⃣ ....Wallahi ƙarya kake Habib, baka isaba ka hanani zuwa bikin ƙawata dole ne inje duk wani tsoratar dani da kake akan kar inje." Miƙewa yayi a fusace. "Ke harni zaki kallah kice ina maki ƙarya, to in har kika bar gidan nan bada yawuna ba kuma duk abinda yabiyo baya kada ki kuka dani ki kuka dakanki." "Oho dai! Tafiyace ko kana so ko baka so sai nayi, yardarka da rashinta kai suka dama banga wanda ya isa ya hanani tafiyar nan ba." "Haka kika ce?, to Basma jeki zaki gani, sai kinyi nadama kuma kada ki sake ki jemani da Ɗa ko ƙofar gidan nan ne." "Ina zani da Ɗanka haka kawai ya takura mani, shakuruminka Ɗanka gida zani barshi." Ficewa yayi daga gidan zuciyar shi na matuƙar yimashi ƙuna. __________ 💀💀💀💀 ....Kuka take kamar ranta zai fita ga mahaifinta tsaye kanta da wayar wuta, jibgarta kawai yake babu ƙaƙƙautawa, "Ni zaki zubda ma mutunci Salma! Ince maki kiyi hakuri amma ki kafe sai kinje bikin wata ƙawar banza, kinko san illar dake tattare da hanyar da zakubi?, to ƙara in karya ƙafafunki inga da wadanne ƙafafun zaki tafi," "Haba Alhaji!, kasheta kakeson yi?, dan Allah karabu da ita hakanan kada kayi mata zata illar kanakasa ta." "Ki barni in nakasata inga da wadanne ƙafafun zata bar gidan nan, wurgar da bulalar yayi ya fice daga falon." "Yanzu Mama ace duk yadda muke da hajara amma ace Daddy ya hana ni zuwa bikinta, kawai dan ance hanyar nada haɗari." "Ke fah sakara ce, yanzu so kike a gabanshi in goyi bayanki, ai dole ne kije bikin hajara kada ki damu in lokacin yayi ce mashi zaniyi kinje biki a dangin mu." (Kuji abun takaici uwa daya kamata tabada tarbiyya itake watware wadda mahaifin yabada, 🤣🤣 Basma kinyi kuskure kina kai kanki ga halaka dakinsan mizaku iske ga tafiyar da kinyi zamanki gida 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ muje zuwa.) Rungume momyn ta tayi tana murna. "Yawa momy na shiyasa nike ƙara sonki, yanzu Momy zani nunawa daddy na haƙura da tafiyar dan kada yayi zargin wani abu." "Yauwa kinuna mashi, shima nasan dan yaga ke ɗaya ya mallaka shiyasa bai so kiyi tafiyar, ga kuma abokinshi munafuki daya ce mashi Wai hanyar bata da kyau." Tashi Salma tayi ta nufi ɗaki. "Momy na tafi in shirya kayana kinsan wallahi na ƙagara inga lokacin nan yayi." _______________ "Jafar abinda zani faɗamaka kaji tsoron Allah aduk inda kake, tafiyar nan da zakayi nemo Mahaifinka daya daɗe da bacewa aka ce an ganshi achan garin, Jafar ka riƙe addu'a ka kiyaye yin sallah a duk halin daka tsinci kanka, wallahi jinike badan Mahaifinka daya bata zakaje nema ba da na hanaka tafiyar nan saboda an ce hanyar wata shu'umar hanya ce sai dai addu'a." Tunda ta fara maganar kanshi yake ƙasa sai yanzu ya ɗago. "Umma addu'arki nike nema i ta ce kaɗai nike buƙata a duk inda nike Umma." "Jafar Allah ya tsare hanya, Allah ya kareka a duk inda kake, yanzu tashi ka fara haɗa kayanka." "To Umma nagode da addu'arki, insha Allah kamar yadda kika buƙata zani kasance mai ruƙo da addini da kuma addu'a." ______________ "Yanzu Rabi'u tafiya zakayi ka barni, katai maka kada kayi rafiyar nan ance hanyar shu'umar hanya ce, kada kaje a kashe mani kai." Ta ida maganar hawaye na wanke mata fuska. "Haba! Haba!! Haba!!! Kaka nifa kidaina ce mani Rabi'u, Rabson guy nike haba in cikin abokaina ne ai saiki kunyatani." "Nidai ina roƙonka ka janye maganar tafiyarnan Rabi'u." "Kutt! In zanye fa kika ce?, Kaka ai dole in yi tafiyar nan ga inda ɗan ladi yace zani samu kuɗi amma kina maganar in zauna ai sam bazai yiwu ba, kinga bari inje in fara shin tafiya." Ya fice yana tafiya yana yin doro kamar waninzabo irin tafitar gayun zamanin nan. Binshi tayi da kallo zuciyarta na mata ƙuna saboda kinjin maganarta da jikanta yayi, ahalin yanzu shi kadai ya rage mata tun bayan rasuwar iyayenshi sanadiyyar gobara shi kadai ya tsira. Shima gashi yanzu yana shirin kai kanshi ga halaka, dan tun tana budurwa takejin labarin dajin kai kazo, mugun daji ne wanda indai ka fita cikinshi ka auna babban arziƙi ____________ "Biba ba wai banison tafiyarki bane, Aa ina jin tsoron hanyar da zaku bi, Biba Mahaifinku ya rasu tunda Allah ya amshi abunshi ke kike sana'a kina hidima damu yanzu ace kema karatu zaki tafi, ni babbar damuwata wannan shu"umar hanya da zaku bi ta wurinta, in na tuna hankalina na matuƙar tashi Biba." "Mama addu'ar ki a duk inda nike ita nike buƙata, Mama inna zauna banyi karatun nan ba dami zani taimake ku nan gaba nidai kiyi mani addu'a Mama." "Shikenan Biba Allah ya tsareki a duk inda kike, abiba ki riƙe maraicinki kada ki bsnzatar da rayuwarki Allah yayi maki jagora Allah ya kareman ke aduk inda kike." "Amin Mama." "Bari inje in samo rancen sayayyar da zaki ida." "To Mama sai kin dawo." *MUJE ZUWA LABARIN BAI FARABA, SOMIN TABI NE NAN,KUDAI KU BIYONI.* *COMMENT* ✅ *SHARE* ✅ *MEEN@T...* ✍🏼 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBA* *WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARREN LABARINE, SUNAYEN GARURUWA DA WASU WURAREN DUK ƘIRƘIRARRUNE* *BAN YARDA AJUYA MANI LABARI TA KOWACE SIGABA SAI DA IZININA, A KIYAYE* *BANI DA BAKIN DA ZANIYI MAKU GODITA MASOYA, TUN DAGA PAGE ONE NA WANNAN LITTAFI KUN NUNA MASHI ƘAUNA, INA MATUƘAR GODIYA ALLAH YA BIYAKU* ____________________ *PAGE 2_3* ....Fizge akwatin hannunta yayi, yana nuna ta da yatsa cikin tsananin bacin rai. "Yanzu tsabar baki da mutumci in hanaki tafiyar nan amma sai kinyi?." Kallon shi tayi awulaƙance. "Tafiya sai nayi banga ɗan yarinyar daya isa ya hananiba, kabani akwatina kafin in zabga maka rashin mutumci, dan da in fasa tafiyar nan ƙara aurena ya mutum in je bikin." Tsabar bacin rai idanunshi har sunyi jajur jikinshi har kyarma yake, wurga mata kayan yayi yana mai nunata da yatsa. "Basma yau ni kike kira Ɗan yarinya?, har wata ƙawa tafini awurinki?, to bazance maki komiba kije zaki gani, sai kinyi nadamar tafiyar nan sai kinyi kuka da idanunki, sai kin yi nadama a lokacin da bata da amfani a wurinki." Ɗansu dake ta darza kuka amma Basma ko ajikinta bata damu dashiba ya ɗauka yayi daki dashi. "Oho dai ni kaga tafitata." Tayi gaba tana wata rangwaɗa kamar budurwa, ga ɗamammun kaya ansha jikinta duk ana ganin shi ga ɗan figigin gyale ansha. (Ya ubangiji ka shiryi matan auren wannan zamanin, wallahi wata shigar banzar da zatayi ko budurwa bazatayi ta ba, ko ni nan nasha ganin matar auren da tayi wannan shigar samari sun ɗauka budurwa ce sukayi ta tsai da ta, Allah ka shiryemu.) ________________ "Kai Momy! Ni dai kiyi sauri lokacin tafiyar fa yayi, kada inje in iske mota ta tashi." "Kin ci gidanku Salma! Yaushe garin ya waye da har mota zata barki tasha." "Mamana har an shirya kenan?, to i ta tafiya tana buƙatar guzuri ungo nan ki ƙara riƙe wa zasuyi maki amfani, ki gaida mani su kaka da ƴan uwa sosai." Amsar kuɗin tayi tana godiya. "To daddy na zasuji, zanyi missing ɗinka daddy na." "Nima haka Mamana, ki kula da kanki sai kin dawo byee." Ya faɗa yana ida shigewa ɗakinshi. "Momy ki rakani bakin Get ko nasan yanzu idi Driver ya fita." Suna fitowa ya nufosu yana gaidasu, amsar kayan dake hannun Salma yayi yasa a boot ɗin motar, shigeqa motar tayi na ɗagama Momyn ta hannu. Sulalawa motar ta cimin haɗaɗɗen Get ɗin gidan ta fice. Suna fita Momy taji jikinta yayi sanyi, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, jitayi dama ta hana Salma tafiyar alokaci ɗaya, sai dai ina bakin alƙalami ya bushe. ___________________ Tsaye gaban Mahaifiyar ta, cikin shiga ta kamala tasha hijabinta tana sauraren nasihar da take mata. "Biba kiji tsoron Allah aduk inda kike, ki zauna da mutane lafiya, ki riƙe addu'a, ita addu'a takobin muminice, Ki kasance mai riƙon amana da faɗar gaskiya aduk halin da kika tsinci kanki, Allah ya tsareki ya dawo dake lafiya Habibata." "Amin Umman." Juyowa tayi ta kalli ƴan ƙannenta da suka yi jigum_jigum. "Bakuyi mani addu'a ƙannena?, ko baku so in zani dawo inyi maku tsaraba." Hada baki sukayi cikin farin ciki dajin maganarta, "Allah ya kiyaye aunty Biba, sai kin dawo." Sallama tayi da Umma tafito jiki ba kwari tayi addu'ar fita daga gida ta hau a daidaita ta nufi tasha. _______________ "Rabi'u yanzu tafiyar nan zakayi?." "Chan Allah ya haɗaki da Rabi'u, ni Rabson guy nike, kada ki bata mani lokaci ni tafiya zaniyi." "Kakus ki kula mani da Ɗan bunsuruna, dan ranar dana dawo lokacin na samo kuɗi ranar zai sha wuƙa." "Rabi'u kai kaɗai ka rage mani tunda mahaifanka suka yi haɗari suka mutu, yanzu kai ma tafita zakayi ka barni." "Haba kakus! Kuɗi fa zani samo, kuma inna tai ba daɗewa zanyi ba zani dawo." "Ni dai bada yawuna zakayi tafiyar nan ba, in katai komi ya faru ba ruwana tunda bakajin maganata." "Heeey! Chau_chau kakus, kina bata mani lokaci kinga tafiyata." Yafice yana waka abakinshi ba tare da addu'ar fita daga guda ba. Binshi tayi da kallo wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, ji take aranta kamar Rabi'un ta ba zai dawo ba. ________________ Har ka fito Jafar?. "Eh Umma lokaci nata ja." Nan tayi mashi nasiha mai shiga jiki mussam kan ruƙo da addu'a aduk halin da mutum yashiga. Bankwana sukayi jikinsu yayi sanyi. Jafar ya fito na nufi tasha. ________________ Hayaniya ce ke tashi acikin tashar kowa nata hada hadarshi. Basma, Salma, Biba, Rabson guy, da Jafar duk lokaci ɗaya suka iso tashar. Gudu_gudu suka iso gaban motar da kwandastan keta faɗi. "Kai kazo! Kai kazo!! Saura mutum biyar mota ta cika." Basma, Rabson, Jafar, da Biba sunyi nasarar shigewa motar amma banda Salma data bige wata tsohuwa. "Kai amma dai ke wace irin jakar tsohuwace?, idanunki basu gani hanya koko?." "Ɗiyata kiyi haƙuri." amma abinda zani faɗa maki kada ki kuskura kiyi tafiyar nan Ta fada tare da kamo hannun Salma. Tatss! Ta ɗauke tsohuwar nan da mari. "Kina ƙazamarki har zaki kamo hannu na, talaka marar amfani kawai." Tayi gaba tabar tsohuwar tsaye. Abun mamaki tsohuwar dafe take da kumci amma dariya take mai ban tsoro. Salma na isa motar ta cika, dan dama Motace mai cin mutum goma. Sun ɗauki hanya an fara tafiya. Salma da Rabson guy kujera daya suke zaune. Sai Biba da jafar suna gaban kujerarsu Salma. Sai Basma ita da wani mutu aka haɗata. Gudu motar ke shararawa akan titin, in da motanen motar kowa da abunda yakeyi. Biba da Jafar Hisnul muslum ne hannunsu suna karanta azkar. Basma earpiece ne kunnenta tana shan ƙiɗa. Rabson da Salma charting kawai suke sha, Rabson satar kallon Salma kawai yake. Sauran mutanen motar hirarsu kawai suke sha. Wani mahaukacin birki da direban yayi shiya sanya kowa kallon abunda ya haddasa faruwar haka, tuni kowa ya ruɗe wasu suka hau iface_iface wasu suka hau salati. Komi nene suka gani 😜😜 Yanzu labarin ya fara, muje zuwa.💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *INA MATUƘAR ƘAUNARKU MASOYANA* 💃🏼💃🏼💃🏼 *EDITING* ❌ *COMMENT* ✅ *SHARE* ✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARREN LABARINE, SUNAYEN GARURUWA DA WASU WURAREN DUK ƘIRƘIRARRUNE* *BAN YARDA AJUYA MANI LABARI TA KOWACE SIGABA SAI DA IZININA, A KIYAYE* *BANI DA BAKIN DA ZANIYI MAKU GODIYA MASOYA, TUN DAGA PAGE ONE NA WANNAN LITTAFI KUN NUNA MASHI ƘAUNA, INA MATUƘAR GODIYA ALLAH YA BIYAKU* ____________________ *PAGE 4_5* ........iface_iface kai ketashi acikin motar, Jafar da Biba addu'a ce abakin su, sunata mai_maitawa. *LA'ILAHA'ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMINA* suke ta nanatawa, wannan addu'ar in dai ka dogara da Allah kariƙa yinta alokacin da kake cikin bala'i Allah zai fiddaka da izininsa,,,Tunatarwa ce. "Munshiga ukku direba meya faru?." Direba ko motsi baiyi rai yayi halinshi. Suna ganin haka suka ƙara ruɗewa. Duka mutanen motar fitowa sukayi ganin hanya ta tsage gida biyu ya ƙara tada hankulansu sukayi cikin dajin da mugun gudu. Gudu suke ko wai waye basuyi iyakar ƙarfinsun suna ƙara kutsawa cikin dajin. Dajine wanda ko daga yanayin bishiyoyinshi kaɗai sun isa su sa mutum sumewa, wani irin shu'umin daji ne wanda bishiyoyin cikinshi kansu suffar dodanni garesu, ga wata irin duhuwa dake gareshi, duwatsune manya_manya cikin dajin ga wani irin iska wanda shi kaɗai ya isa ya tabbatar maka da kuna cikin tashin hankali,masifa da bala’i. Iskane ke kaɗawa kamar kana cikin maƙabarta wani shuuuuw! Ga iska ya game da kukan wasu irin tsuntsaye, yana bada sauti mai firgitarwa. Gudu suke kamar ransu zai fita, abinda basu sani ba duk gudun da suke haryanzu suna farkon dajin. "Wayyoh zani Mutu! Kutsaya mu huta, wayyoni ƙishirwa ku taimaka mani." Basma ke maganar numfashin ta na fita da ƙyar. Abokin zaman kujerarta a mota afusace ya fara magana. "Kee amma bakida hankali kina nufin mutsaya musanya rayuwarmu ga halaka?, to in bazaki zo mu ida fita adajin nan ba wallahi nan zamu barki muyi gaba. Kafin ya ida rufe baki dajin ya gauraye da wata mahaukaciyar dariya. "Kunyi kuskuren shigowa DAJIN KAI KAZO!! Ku masu taurin kai Dukkan ku babu wanda zai fita da rayuwarshi,zamu riƙa yimaku ɗauki ɗai_ɗai har sai mun ƙarar daku hahaha." Wata mahaukaciyar guguwace tayo kansu. Gudu sukaci gaba dayi suna waiwayen iskar dake biyosu, tim! Daya daga cikinsu ya fadi tsayawa sukayi domin taimakonshi, Jafar ya tsaya suna kokarin isowa gareshi, suna daf da isowa gareshi iskar nan ta sureshi tayi sama dashi. Firgicewa suka ƙara yi masu koke_koke da iface_iface nayi. Sauƙinsu ɗaya duk gudun da suke basu rabu da juna ba. Gudu suke har duhun magriba ya fara. Wani wuri suka tsinci kansu mai yalwar bishiyoyi manya_manya gasu kuma dogaye abun tsoro. "Assalamu alaikum!, jama'a ya kama tafa musan abunyi, kamata yayi musan inda muke kutsa kanmu, karfa wurin gudun ceton rayuwa mukai kanmu ga halaka." "Maganarka haka take, kamata yayi mubar gudun nan musamarwa kanmu mafita ga duhu ya fara." Biba ta fad’a tana mai ƙara dubar mutanen. Wani saurayi mai zubin ƴan daba daga cikin fasinjojin motar ya fara magana. "Yanzu kamata yayi mu samu inda zamu ƙwana shine kawai mafita in safiya tayi saimu nemi hanyar fita daga dajin nan." "Wallahi baka isa ba mu babu inda zamu kwana cikin wannan ƙazamin dajin, in kai ƙazamine toni dubarni da kyau banyi kalar da zani haɗa wurin kwanciya daku ba." Salma ta faɗa tana aikamai da kallon wulaƙanci.(Nikam dake danazo nan seda na shek’e da dariya😂) "Kuturun chan kayyasa! Yau Garba kisane mace ke faɗawa magana, yarinya kinci arziƙin a wani hali muke da hukuncin kisa shi zai hau kanki, amma yanzu sai dai in maki bugun da ko kallon banza bazaki ƙara yi mani ba." Wani wawan tsalle ya daka ya isa gabanta ya fara ɗauketa da ta gwayen maruka. Mutanen wurin sukayo kanshi suna rirriƙeshi ana bashi haƙuri. "Ni ka mara?, wallahi sai kayi nadama sai ka ƙwammace bakazo duniya ba, ko daddy na bai taba marina ba sai kai matsiyaci talaka da kai." Jafar ya daka mata wata irin tsawa. "Keee! Ya isa, yanzu a wannan halin damuke ciki haɗin kai muke buƙata bawai mu tsaya muna faɗa da juna ba, daga yanzu bazamu laminci wannan faɗace_faɗacen naku ba, ku zo muyi gaba muga in da ya dace mu yada zango." Sunyi ƴar tafiya mai nisa suka ga wani gida a gabansu. Gidane wanda aka gina da katako, da alamu gidan ya daɗe a kulle saboda yanar data lullube ƙofar gidan. Hayaniya aka farayi ta wanda zai shiga ya duba. Rabson guy da akace ya shiga su duba karkace kai yayi yace shi in dare yayi bai gani sosai. Cikin abokan tafiyarsu na mota mutum huɗu da suka rage Garba kisa, da wani audu gwarama, sai wani nura shila su duk abokai ne wani aiki na shiyasa suka samu zasuje su tada rikici abiyasu. Sai mace ɗaya mandiya Ita kuma karuwa ce labari ta samu anfi samun kuɗi a abirnin Kai kazo shiyasa ta fito yawon duniya zataje Birnin kai kazo. Jafar, Garba kisa, audu gwarama sai nura shila, su zasu shiga gidan su duba masu. Ƙofar gidan kulle take gam, da ƙyar suka samu suka buɗeta, wata irin k’urace ta ke fitowa daga gidan dole suka ja da baya sai da ƙurar ta gama ficewa sannan Jafar yai bisimillah suka kutsa kai cikin gidan. Duhu ne sosai gidan ko tafin hannunka baka gani, sai lokacin Jafar ya tuna da wayarshi, fiddota yayi amma abun mamaki kwata_kwata babu network gurin ko alamun shi babu. Touchligh ya kunna, tuni haske ya gauraye wurin, wani irin gidane mai wani irin fasali, inda suke tsaye wani tangamemen falo ne mai ɗauke da gadaje uku gefe daya kuma kujerune aduk da katakai akayi su, sai wasu ɗakuna biyu dake kulle, in ka matsa bayan kujerun wurin dafa abincine shima da katakai aka ƙera wurin, amma duk yana ta lullube kayan gidan da kuma ƙura,idanunsu ne suka hasko masu wani hoto amma ƙura ta lullubeshi, matsawa mukayi a hankali Jafar yayi bisimillah tare da goge ƙurar,Hoton Turawane ya bayyana mata da miji da kuma ɗiyarsu, sunyi dariya aka ɗauki hoton su, sunyi matuƙar kyau. Kansu kullewa yayi, suna ma kawunansu tambayar miya kawo turawa acikin dajin nan har sukayi gida?, lallai al amarin nan akwai ban tsoro. Ƙofofin ɗakin suka buɗe da tagogin take haske ya bayyana duk da lokacin duhun magriba ya fara. Sun duba ko ina amma basuga wani abu na cutarwa ba. Ɗakunan nan biyune kaɗai basu buɗeba. Fitowa sukayi suka umarci abokan tafiyarsu dasu shigo daga ciki. Bayan shigarsu ne kowa ya naimi wuri ya zauna yana jimamin halin da suke ciki. Jafar ne yayi gyaran murya ya fara magana. "Ƴan uwana ya kamata mutashi mu gabatar da sallolin dake kanmu, nasan da wuya musamu ruwa a hanlin da muke ciki yanzu amma abinda yafi shine muyi taimama kawai zai fi mana." Basma da Biba, Mandiya tare sukayi sallah, ƙiri_ƙiri Salma taƙiyin sallar cewa tayi ita gobe in an samu ruwa ta haɗa tayi. Garba kisa da yaranshi kuwa sai dai shiriyar, domin tabarsu kusa fiddo daga cikin aljihun wando da ahana suka hau hura hayaƙinsu. Dare yayi nan ido ya raina fata, kowa ka kalla zakaga tsantsar tashin hankali atare dashi. Bayan sun kakkabe ƙurar da yana kowa ya fara neman inda zai kwanta, Mandiya,Basma,Biba da Salma gado ɗaya suka kwanta, inda Salma tayita tsoki wai ita bazata haɗa jiki da su ba nan Mandiya ta taso mata kamar zasu bigi juna, sai da Garba yace duk wadda ta ƙara masu hayaniya zasu fiddata daga ɗakin sai dai ta kwana wajen. Nan Salma tayi zuciya ta sauko ƙasa ta baza ɗan figaggen gyalenta ta kwanta sama. Bayan kowa ya kwanta wasu sunyi addu'a wasu kuma ko uho. Cikin bacci Salma taji kamar ana lasar mata ƙafa, afirgi ce ta buɗe idanunta ta sauke su kan wata irin ƙatuwar mage baƙaƙirin bakinta wasu zara_zaran haƙora jini na ɗiga daga bakinta ga wasu irin idanu manya_manya masu ban tsoro, wata mahaukaciyar ƙara ta ƙwala da tayi sanadiyyar farkawar kowa daga bacci daya ɗauke su. Ganin irin halittar magen ba matan kaɗai ba har mazan sai da hantar cikinsu ta kaɗa. Garba kisane yayi ƙarfin halin shaƙe wuyan magen. "Kuyi sauri ku buɗe mani ɗakin nan." Jafar ne yayi saurin buɗe ɗakin, Garba ya fita da guda magen na hannunshi a shage. Sai dai kash! Daya san abinda zai iske a wajen bazaiyi gigin fitaba. Kan Magen ya riƙa bugawa da ƙasa amma ko gezau batayi ba sai ma hannunshi dayaji kamar an daka mashi kaifaffar wuƙa, ihu ya ƙwala ya wurgar da magen yana duba hannun yaga ashe cizone ta sakar mashi a hannu, take jini ya hau zuba ba ƙaƙƙautawa, nufar hanyar gidan yayi zai shige, juyowar da zai yi yaga abinda ya kusa sanadiyyar tsayawar numfashin shi. Magen nan ce ta rikiɗe ta koma wani basa muden Aljani jikinshi duk jini bakinshi wasu haƙora ne zaƙo_zaƙo irin na zombie, juyawa Garba kisa yayi da nufin komawa gidan horror ɗin yayo kanshi yana ƙoƙarin cizon Garba. A tsorace Garba ya nufi ɗakin zai shige yana ihun su taimakeshi, ganin halin da suke ciki yasa su buɗe ɗakin, yana gabda shigewa ɗakin aljanin na kamo ƙafarshi mutanen daki hannuwan Garba suka kama domin ceton rayuwarshi, da kyar suka jawo Garba ɗakin suka maida ƙyaure suka rufe. Nura ne ya lura Garba ba alamun numfashi a tare dashi, "kai Oga fa yabar numfashi ku duba ƙafarshi ga wani cizon nan ya ƙara samu." Rigar jikin shi suka keta suka ɗaure mashi ciwon, suna yi mashi firfita. "Yau ni Rabi'u nashiga uku na lalace, wayyo kakata ƙila shikenan mutuwa ke kirana ita ta raboni da gida." Kowa ka kalla a ɗakin hankalinshi a tashe yake, yana tunanin makomarsu. A hankali Garba ya buɗe adanunshi da suka yi mashi nauyi, ya sauke su ga ƙafarshi dayaga an ɗaure mashi. Kwance wurin yayi sai dai abun mamaki ciwon ya warke sai dai wuri rauni yayi wani irin baƙi wasu jijiyoyi sun fito sun miƙe har wajen cinyarshi, kamar yadda jini ke gudana haka wannan baƙin abun ke gudana ajikin Garba kisa. Sannu suka shiga yi mashi, baccin da basuyi ba kenan har gari ya waye. Bayan sunyi sallah, nan suka shiga tunani abinda zasu samacikin su, kowa akayima maganar yafito su tafi naiman abinda zasu sama cikinsu sai ya noƙe yaki fitowa. Daga ƙarshe dai Jafar da Biba suka ce su zasu fita su nemo. Tunda suka fara tafiya basu samu komi ba ko bishiyoyin da zasu ciri ƴa'ƴan suci basu samu ba. Ƙorama suka iske ruwa na gudana , tsayawa suka yi suka sha ruwan suka ɗibar ma sauran wanda zasu sha. Sunyi tafiya kaɗan suka fara hango wata bishiyar kwaba a gabansu tsayawa sukayi. "Kin ga dai tun ɗazu bamu samu komi ba duk yawo da mukasha, yanzu ni zani hau in tsinko ke kiriƙa ɗaukewa." Haka kuwa akayi sun ɗibi mai yawa suka nufi hanyar komawa wurin abokan tafiyarsu. Kowa yayi murna da samun abinda zasu sa ga bakinsu banda Salma da ta ce ita tafi ƙarfin cin gwaba, babu wanda ya matsa mata taci cikinta ne inma bataci ba. Shawara suka yanke su ƙara kwana nan in Garba ya ji sauƙi sai su cigaba da tafiyar. Dare yayi sosai kowa ka gani yasha jinin jikinshi yana tunanin abinda zai faru. Garba tunda lamarin nan ya faru jikinshi ke rikiɗewa yana komawa baƙi, amma bai sanar da kowa ba. Zaune yake ya sadda kanshi ƙasa kamar mai bacci, lura abokan tafiyar sukayi kamar Garba yabar motsi, audu ne yayo kanshi da sauri dan ganin halinda yake ciki, ya isowa jikin Garba na ida rikiɗewa ya koma green da baƙi. Duƙawa audu yayi dan ganin mike faruwa da Garba. Shak’arda Garba yayi ma audu gwarama yasanya ƴan ɗakin fara iface_iface ganin yadda kaman nin Garba suka chanza. Rabson guy tsabar firgici sulalewa ƙasa yayi ya sume. Garba ya tsunshi da suka zama zaƙo_zaƙo ya dakama audu su a wuya ya wurgar dashi ya bugu da bangon ɗakin ya faɗo ƙasa ba alamun numfashi atare dashi. Garba juyawa yayi yai kan Salma da tayi mutuwar tsaye hada fitsarin dole yai wani irin kukan kura wanda seda ilahirin dajin yayi amsa kuwwar da ’ya’yan cikin kowa suka kad’a....... Sake kallon Salma yayi akaro na biyu yayin da y..........✍🏻 💀💀💀💀💀 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤪 *COMMENT* ✅ *SHARE* ✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA* 🥰🥰🥰🥰 ____________________ *PAGE 6_7* ......Tamkar yunwa taccen zaki haka Garba yayo kan Salma gadan_gadan, tsabar tsoro ko motsi takasayi ta rufe ido tana sauraren mutuwar data nufota. Ganin halin da ake ciki yasa Jafar yin kabbara ya ya ɗauki wani katako yayo kan Garba kisa gadan_gadan, sai dai kafin ya iso Garba yayi nasarar shago Salma ya fara gama kanta da bango, tsabar azaba nan take ta sume. Ya isa isowa daf da Garba yayi kabbara da ƙarfi ya ƙwaɗama Garba katakon nan a tsakiyar kan shi. Take Garba yayi wata irin kururuwa ya faɗi ƙasa. Salma gwara mata kai da bango ta sume batare da tasan mike faruwa ba. Biba da ke labe bayan kujera tana addu'a tana hawaye gitowa tayi jin abun ya lafa, Ganin Garba da tayi kwace ƙasa Kanshi jini na malala nan hankalinta ya ƙara tashi, abun mamaki jikin Garba lokaci ɗaya yayi wani irin fari fat! Tamkar babu jini jikinshi ko ɗigo, kallon_kallo Biba da Jafar suka hau yima juna. "Biba yanzu ba lokacin kuka bane musamu mafita, ni fa gani nike mu haƙura da dajin nan mu zauna cikin gidan nan kawai in Allah yayi zamu fita shi zai kawo mana ɗauki da kanshi, soboda faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam daya ce in annoba ta samu gari to naciki su zauna a garinsu na waje kuma kar su shigo garin." "Nima ina da wannan tunanin Amma yanzu abinda ya kamata mu samu abokan tafiyarmu su farfaɗo sannan muyi gaggawar rabuwa da gawar nan, kaga fa yadda ta koma, ina tunanin barinta tare damu kamar wani haɗari ne babba." "Maganarki haka take, yanzu bara mu fara shafa masu ruwa su farfado mujita bakunan su." Wurin Audu gwarama suka fara zuwa sunyi sa'a suna shafa mashi ruwa a fuska ya ja a jiyar zuciya yana mai shafa wuyanshi dake mashi tsananin zafi, shi ma dai_dai in da Garba ya yakusheshi wurin ya fara green da baƙi. Sannu sula riƙa jero mashi yana amsawa. Wurin Salma suka matsa ita ma tana nan kwance tamkar gawa. Jafar dubar Biba yayi yana mata magana a hankali yadda in ba kusa kake dashi ba bazakaji mitake fada ba. "Biba Salma kinga mace ce bai kamata in tabata ba ke yaka mata ki fara duba inda Garba ya buga mata kai ki kiyi addu'a nasan a firgice zata tashi saboda halin firgicin da ta shiga,sannan ki shafa mata ruwa a fuska." A hankali ta fara buɗe idanunta ta sauke su kan Biba dake tsugune kanta. "Nashiga ukku ni Salma! Yanzu shikenan nima horror zani zama, wayyoh daddy na danabi shawararka da yanzu ina gida zamana, yanzu gashi na kawo kai na ga halaka." "Aa Salma Garba bai cijeki ba, ya dai bugaki da bango yayi sanadiyyar sumanki." Tamkar wata ƙaramar yarinya haka Salma ta maƙale jikin Biba tana kuka, 😂😂 niko nacr salma ina nuna isar da wulaƙanta muta ne da nuna masu ƙyama. "Addu'a zakiyi ba kuka ba Salma, a wannan halin da muke ciki addu'a kaɗai ce magani, kuka bazai amfane mu da komi ba." Biba ta faɗa tana ɗora hannayenta a kafaɗar Salma. Audu lura yayi da halin da Ogansu ke ciki. Da gudu ya rugo ya rungume Garba yana mai fashewa da wani irin kuka, "Oga shikenan katafi ka barmu cikin wannan halin, Oga ji nike dama nine na mutu na huta ba kai ba, haka muma zamuyi ta mutuwa ana kashemu ɗaya bayan ɗaya, ina nadamar yin Baƙar tafiyar nan yanzu nasan nayi bankwana da kakata." Kukan dayaci ƙarfinshi yasa maganarshi sarƙewa. Jafar ya iso wurin Garba ya rabashi da gawar yana bashi haƙuri, addu'a ce kaɗai zata kawo masu mafita. Lura sukayi da abokan tafiyarsu babu Mandiya da Nura shila da Basma. Sun bincike ko ina amma basu gansu ba. Ɗakin farko sukayi shawarar buɗewa ko ciki suka buya. Sai da suka haɗa ƙarfi wurin buɗe ɗakin, Ɗakine mai yalwar faɗi ba laifi, sai dai tsananin duhun ɗakin ya hana ka ga mike ciki, motsin da suka jiyo ne ya sasu juyowa a razane, Nura shila da Basma suka gani ƙarƙashin wani bencin katako sun boye ganin su yasa suke ƙoƙarin fitowa. Bayan fitowarsu Biba ta fara magana, "Sanin haɗarin da muke ciki yasa daga yanzu ko wani bala'i ya samu ɗan uwanmu kada wanda ya ƙara ƙoƙarin guduwa ya rabu da sauran." Kowa yayi na'am da wannan shawarar Ɗayan ɗakin suka buɗe, buɗewarshi tayi dai_dai da bugawar zuciyoyinsu kallon_kallo suka fara yima juna, wannan ɗakin yasha banban da saura, saboda shi wani abun mamaki babu duhu acikinshi, kayan wasane na yara birjik aciki, su kansu kayan wasan in ka kallesu sau ɗaya bazaka ƙara ba saboda abin tsore, daga ɗiyar robar da aka cirema hannu ɗaya tana hawayen jini sai wadda ta cire kanta ta riƙe a hannu tana murmushi haƙoranta duk jini, wadda tafi masifar tada masu hankali wata ɗiyar babyce girmanta ya kai na jariri, zaune take jikinta jar riga ce hanta gashi ya baje ta ko ina baka ganin ko fuskarta, ga wasu irin wuƙaƙe a hannunta duk jini ya bata su, kallo ɗaya zakayi mata ka ɗauke kanka. Wani yawu Rabson guy ya haɗiye ƙut! Da yayi sanadiyyar juyowar abokan tafiyarshi, sun naimi Mandiya lungu da saƙo sun rasa, motsi suka jiyo bayan ƙyaure, ƙin leƙawa sukayi kowa jininshi kan akai fa saboda tsoron dake ɗawainiya dasu. Jafar ne yayi ƙarfin halin yawo ƙyauren, tsaye take tayi labo bayan ƙyauren jin an jawo ƙyaure yasa ta fara junduma ihu, "wayyoni Mandiyar uwar daba yau nakawo kai na ga halaka, Magaji kin cuce ni da kika bani shawarar zuwa garin Kaika zo! Ashe ajali ke kirana a wannan BAƘAR TAFIYAR, nashiga ukku na balbalce." "Buɗe idonki ki gani mune fa abokan tafiyarki." Jafar ya faɗa yana mai bata hanyar wucewa. Idanu ta buɗe danjin muryar abokin tafiyarsu. Shawara suka yanke suyima gawar Garba sallah su binneta. Ruwan da ya rage masu suka yi alwallar dasu, sun gama sallar sun fara gina zasu binneshi wani baƙin hayaƙi ya bayyana ya ja gawar Garba suka bace. Nan fa suka ɗiba aguje suka koma gidan suka rufe masu kuka nayi masu addu'a nayi. Basma kuka take tana sambato ita kaɗai, "Allah sarki masoyina kuma mijina habibina, dana bi shawararka da yanzu ina gida amma haka na nace dole sai naje bikin ta gaban goshi, Allah ya isa tsakanina dake ta gaban goshi ke kikai ta turani ina ma habib rashin mutumci, yanzu gashi nan na baro ɗana mijina yana fUshi dani nasan mutuwa zaniyi." Babu wanda ya rarrasheta koya bata hakuri domin kowa ta kanshi yake. Nan suka faɗama sauran abokan tafiyarsu shawarar da suka yanke ta barin wannan gidan su ƙara gaba, amma ba haka ya kamata suyi ba, kamata yayi su zauna suga yadda zata kasance. Wasu sunyi na'am wasu kuma sun bada shawarar abar gidan, sun yanke shawarar zasu bar gidan in gari ya waye. Duhun dare ya fara kowa hankalinshi ya ƙara dugumzuma, kingin kwaibar da ta rage masu suka raba suka fara sha, Salmar tun kafin azo kanta ta warci biyu ta faraci. Dare yayi sosai dajin babu abinda kakeji sai kuka tsuntsaye da wani irin iska mai bada wani firgitaccen sauti in ya haɗu da kukan tsuntsaye. Mandiya, Basma, Biba da Salma yau gado ɗaya suka haye ba zancen nuna ƙyama yau Salma. Mazan suma wuri ɗaya suka dunkule. Bacci ma in kaga kana yin shi to baka shiga wani bala'in ba kokoma sai dai in bacci barawo ya sace ka. Duka ɗakin kowa manne yake da ɗan uwanshi,idosu biyu sun kasa bacci gudun abinda zai biyo baya. A hankali tagogin ɗakin (Window) suka fara buɗewa da kansu, jikake kit!_kit! Taga ta bude da kanta, karar da sukaji ce ta maido hankalinsu ga abinda ke faruwa. Dirowa sukayi daga gadon suka cibre wuri ɗaya jikinsu na kyarma, duk wannan halin da suke ciki addu'a ce bakin Biba sabanin su Salma da suka fara kuka. Ƙofofin na ida buɗewa wani farin hayaƙi ya fara shigowa yana dunƙulewa wuri ɗaya. Yana gama haɗewa wuri ɗaya wata irin halitta Mai suffar kare ta bayyan, jikinta ko ina hannuwa ne idonta guda ɗaya ne a tsakiyar goshi, ga bakinta wagege da haƙora masu matuƙar tsini. Dariya halittar ta kece da ita wadda ta haddasa ma ɗakin girgiza. "Kunyi kuskure bil adama masu taurin kai da gadara, yau kwananku ya ƙare, a sannu zaku baƙunci lahira." Jafar yayi ƙarfin halin fara magana. "Ƙarya kike yake wannan la'anannar halitta, ke baki isa ki kashemu ba sai dai in kwanan mu ya ƙare ubangiji ya rabuta zamu mutu yau, amma badai ke ba." "Hahaha! Gaskiya wannan bil adam jarumtarka ta burgeni, amma kayi kuskuren faɗa da ƴar tsito ƙaramar aljanu kuma shaiɗaniyar cikinsu, yanzu zani shanye jinin jikinka inyi gunduwa_gunduwa da naman jikinka." Tana rufe baki tayo kan Jafar da mugun nufi a cikin zuciyarta. Abun mamaki kafin ta ida isa wurinshi sanadiyyar addu'ar da yake ya bace ma ganinta nan ta hau dube_dube amma babu shi babu alamunshi. Ganin haka ya sanya ta wawuro ƙafar Basma, ihu ta hauyi itama ta jawo ƙafar Rabson guy, shima ci gaba da ihu yayi "wayyoh kakata wayyoh ɗan bunsuruna yau nayi bankwana daku, mutuwata ta iso." cikin zafin nama shima ya damƙo ƙafar Salma, ita ma bata tsaya bata lokaci ba ta jawo ƙafar Audu, Nura shi ya riƙo hannun yana ƙokarin cetonsu. Ganin halin da ake ciki ya sanya Jafar shammatar Aljanar yayi tsalle ya bankata ɗaki ya mai do ƙyaure ya rufe. Gidan suka buɗe kowa yayi ta kanshi. Gudu suke wanda su kansu in akace zasu iya yin shi bazasu yarda ba. Gudune gudun yada ƙanin wani kowa ta kanshi yake. duk gudun da suke a haɗe suke ɗayan su bai yarda ya rabu da ɗan uwanshi ba. Gudu kawai suke amma basu san inda suke nufa ba, har sai da asuba tayi sannan suka zube suna mai da wani wahalallen numfashi. Wata azababbiyar ƙishirwa ce ta taso masu, sanadiyyar gudun da suka sha, shawara suka yanke in safiya ta idayi sunemi ruwan sha. Safiya nayi suka ƙara nausawa cikin dajin naiman ruwan. A hankali jikin Audu gwarama yanata komawa green da baƙi, amma babu wanda yasanar halin dayake ciki. Wani irin ruwa ne mai mugun fadi da yalwa gashi wucewa yake da mugun guda, suka iske a gabansu. Nura har gudu yake ya isa ga ruwan ya sha saboda ƙishin daya addabeshi. "Aa Nura kada ka sha ruwan nan ban yarda dashi ba." Jafar ya faɗa yana ƙoƙarin tsaida Nura. "Ya zaka hanani in sha bayan kasan babu abinda muke buƙata yanzu kamar ruwa." ida gangarawa yayi cikin ruwan ya duƙa ya kam fato da hannuwanshi zai kai baki. Wasu dogayen hannuwa ne suka bayyana suka, harya juyo zai fita daga ruwan hannuna nan suka fizgoshi suka nitsar dashi cikin ruwan yayi gaba dashi. Tsabar tashin hankali su Jafar ƙara nausawa cikin jejin suka yi da azababben gudu. *COMMENT* ✅ *SHARE* ✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA* 🥰🥰🥰🥰 ____________________ *PAGE 8_9* ..........Gusu ba tare da sanin in da suke nufa. Iya gajiya sun gaji, tsayawa sukayi suna mai da numfashi, su Mandiya kuka kawai take tan ƙara tsinema magajiya da tun farko i ta ce sana diyyarta shiga karuwanci. Su Rabson guy abun ba magana zama yayi ya miƙe ƙafafu shame_shame yana mai da numfashi, yana jin wata sabuwar nadama nashigar shi, da dana sanin bijirewa maganar Kaka. Ranar nan suka wuni, ga ƙishirwa ka yunwa, sallah ma da suka auna lokaci aransu suka ga yayi nan suka yi taimama su kayita nan. Ƙara nausawa cikin dajin suka yi naiman ko ƴa'ƴan itatuwa ne su sanyama cikinsu. Sunyi tafiya mai nisa suka isa wani wuri mai matuƙar kyau, korayen flawer ne ko ina ga wata ƴar ƙorama ruwa na gudana cikin ta, bishiyoyin kayan marmari ne duk in da ka duba sunyi bul_bul gwanin sha'awa. Kallon_kallo suka hauyi ma junan su, suna mamakin wannan Baƙin daji tunda suka shigoshi basu taba ganin wuri mai kyau irin wannan ba, gashi dai a halin da suke ciki babu abunda suke matuƙar buƙata kamar ruwa da abinci, sai gashi sun samu amma suna shakkar cin shi. Jafar lura yayi basu yadda da wurin ba, dan haka ya fuskan ce su ya fara masu jawabi; "A halin da muke ciki yanzu bamuda mafita face mu dogara da Allah muyi Basmala muci abubuwan da muka samu, Wamanyatawakkalu Alallah! Fahuwa hasbuhu." Har cikin zuciyoyinsu sunyi na'am da maganar Jafar. Ida isa sukayi wurin bishiyar Mangwaro Jafar na tsinkowa Audu na tsincewa. A haka sun tara kayan marar mari mabanbanta masu yawan gaske. Zama sukayi zasu fara sha koya bakinshi dauke da Basmala. Alhamdulillah sun sha sun ƙoshi babu abinda ya faru dasu. Nan suka yada zango suna hutawa, Basma sai yanzu ta lura babu gyalenta ya faɗi sana diyyar gudun da suka sha, ga suturar jikinta ba ta kirki ba duk ta matseta, dubanta ta kai ga Salma wadda ita ma hakan ta kasance gareta dan figaggen gyalenta ita ma tun suna cikin wannan gidan ya faɗi. Duk cikin su Biba Ita kaɗai ce shigarta har yanzu hijabinta bata cireba sai dai cukuikuyewa da ta fara saboda wahalar da suke sha. Abinda su Jafar basu sani ba tunda suka fara gudun nan wata ƴar ƙaramar barewa ke biye dasu. Ba zato ba tsammani suka ga barewa ta nufo inda suke gadan_gadan. Miƙewa sukayi a matuƙar razane suka dun ƙule wuri ɗaya. Rike ɗewa barewar tariƙayi har ta koma wani farin tsoho mai cikar kamala da kwarjini. "Ku kwantar da hankalinku ni taimakon ku nazo yi ba cutar daku ba, nima da kuke gani musulmi ne ɗan uwanki, abunda nike buƙata ku dogara da Allah ku zauna in sanar daku abinda baku saniba game da tafiyar da kuke. Jikinsu kyar ma kawai yake sun kasa zama sai da Jafar da Biba suka ƙara masu tuni akan su dogara da Allah su zauna. Mai da hankalinsun sukayi ga wannan tsoho. "Kamar yadda na faɗa maku a baya ni ba mutum bane, kamarku ni Aljani ne, suna nana Ammar bin asad, basai na sanar daku yanayin dajin nan ba nasan yanzu kun fara sanin yadda yake, wannan daji da kuke gani tun asali ya kasance wani irin shu'umin jeji wanda ko dabba ce ta shigo cikin shi da wuya ta fita araye, asalin fara zaman wannan daji wasu turawa ne ma'aurata bayan aurensu suna binciken inda keda abu buwan mamaki domin su Allah yayi su da son abubuwan al ajabi, nan suka binciko wannan daji, sunyi ƙokarin zuwa dan ganema idanunsu abinda ke faruwa ana hana su zuwa amma suka nace, daga ƙarshe suka sulale suyo Nageria, bayan zuwansu Nageriya basu yadda sun shiga wannan daji kai tsaye ba gida suka kama suka zauna suna hulɗa da hausawan mu har suka iya hausa abakunan su, Alƙawari mijin yayi in matarshi ta haihu ɗiyar tayi shekaru biyu lokacin ne zasu nausa cikin dajin dan gane ma idanusu abunda ke faruwa." "Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba Matar wannan Bature ta haihu, ranar da ɗiyarshi ta cika shekaru biyu ranar suka ɗauki hanyar wannan daji da duk guzirin da suke buƙata, Sanin halin wannan daji yasan ya dereban dazai kai su dajin yace sai dai ya ajesu nesa da dajin su ida isa da ƙafafunsu, idansu ya rufe ga son shiga wannan daji dan haka basuji komi ba suka amin ce , gorinsu ya cika sun samu damar shiga cikin wannan daji daya kasan ce shine zai zama ajalinsu, tun shigar su dajin suke murna ganin dajin ko ƙasashen su basu taba ganin daji mai duhuwa da manya_manyan duwatsu, dajin kallonshi kaɗai abun tsorone amma su a wurinsu wannan shine kaɗan daga cikin abubuwan mamakin da suke naima,itatuwa mijin da matar suka hau sarewa suna haɗa katakan yin gidan da zasu zauna, sunyi aiki natsawon watanni biyu iya wahala sun wahala kafin suyi nasarar i hada gidan, har yau babu abinda ya firgita su koya tsorata su tun shigarsu dajin, rayuwa suke tajin daɗi acikin dajin nan suna ɗiyarsu, ranar da bazasu taba mantawa ba ita ce ranar suna daga wajen gidan ɗiyarsu na nesa dasu tana wasa su kuma suna zaune suna hirarsu, wata irin ƙara kunnuwan su suka Jiyo masu, a firgice suka kwalama ɗiyarsu kira dake wasa nesa dasu baban ya ruga ya ɗauko ta suka nufi gidan, sai dai mi! Suna buɗe gidan suka ga ɗiyarsu nata wasanta ita ɗaya cikin gidan, dagowa tayi ta kallesu tana sakar masu murmushi, sakin wadda ke hannunsu sukayi suna nunata da yatsa suna ja da baya, su duka taran biyu da ta cikin gida da ta hannunsu nufo su sukayi suna momy ni ce Lara ɗiyar ku waccen ƙarya take, ruɗewa sukayi sun rasa gane ainahin ciki wacece ɗiyarsu, Lara ta ƙarya ta shago wuyan ta gaskiyar ta ɗagata sama ta wujijjigata ta wullata gefe, juyowa tayi kan iyayen tana dariya idanunta na zubda jini, nuna su tayi da hannu take wata iska ta yi sama dasu tana bugasu da bishiyoyin wurin tun suna ihu suna kiran abun bautar su har suka daina numfashi, bacewa. Basu farfaɗo ba sai da marece yayi sanyi bugesu sannan suka farfaɗo kan ɗiyarsu sukayi da gudu suna kiran sunan ta, kayansu suka haɗa suka nufi haryar da suka shigo dajin, abun mamaki haka suka ƙaraci yawonsu har duhun dare ya fara amma hanyar ta bace masu, dole suka haƙura suka dawo gidan suna tunanin abunda zai same su nadamar shigowa dajin na shigarsu , dare ya raba babu abuda kunnuwanka ke jiyo maka illa kukan tsuntsaye da ya haɗe da Iska yake bada wani firgitaccen sauti, ƙofar da suka kulle sukaji tana budewa da kanta ɗiyarsu suka jawo suka ƙara rungumewa, wani baƙin wayaƙi ya Cika ɗakin, a hankali ya fara haɗewa wuri ɗaya yana komawa doguwsr halittah mai suffar mutum, ko ina jikinta hannuwa ne, idon ta guda a tsakiyar goshi, dariya ta kece da ita "ku masu taurin kai yau kwananku ya ƙare,yau zaku bar duniyar nan sakamakon ganin ƙwaf daya kawoku dajin nan," tana rufe baki ta chafko miji ta wullashi sama ya fado ƙasa kanshi ya fashe ko shurawa bai yi ba ya mace, matar ta nuna da hannu take wani hayaƙi ya fito ta hannunta ya shigajikin matar da ɗiyarta take jini ya riƙa ambaliya ta hancinsu da baki suka sulale ƙasa matattu, atare gawawwakin su suka bace tare da wannan hali halittar, wannan shine abunda yafaru da waɗan da suke shigowa ɗakin nan, taimako ɗaya zaniyi maku shine kada kusake wannan addu"ar ta fita daga bakunan ku, *LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTUMINAZZALIMIN*, san koda wasa kada kusake ku sake ku rabu da abokan tafiyarku, ƙarfina bazai iya fiddaku daga dajin nan ba addu'ar ku ita zata taimake ku, nabarku lafiya Allah ya fitar sadaku, ya bace." Jikinsu sanyi yayi dajin wannan bayanin, basu ankara ba wurin da suke ya fara duhu bishiyoshin na komawa baƙaƙe flower ɗin wurin suna bacewa, Basma tsalle tayi ta faɗa jikin Biba jikinta na kyarma, Rabson Basma dake kusa dashi ya maƙalƙale. "Bakada hankali?, ina matar aure zaka riƙa shigemani?." "Ke da auren na haɗaku a turmi na Ƙulƙule, kina matar aure tsabar gantali miya fito dake wannan tafiyar?." Kafin ya rufe baki duhu ya ida rufe idanunsu, ji sukayi an shure su anyi sama dasu shuuuuu!✈️✈️ 😜😜😜 *MASOYANA KU KOYAMA WANNAN LITTAFIN YAWO, YAJE KOWANE GROUP NA NOVE💃🏼💃🏼💃🏼* *COMMENT*✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA* 🥰🥰🥰🥰 *WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA* __________________ *PAGE 10_11* .....Lulawa akayi dasu a sararin samaniya, addu'ar da suke ta sanya aka yo ƙasa dasu ba shiri. Wuri ne mai tsananin huduwa da manya_manya duwatsu, ga bishiyoyi masu wata firgitacciyar suffa ko ganye ɗaya babu jikin su, sai wasu irin dogayen saiwa ajikinsu. Aka watsosu, sanyin daya fara ratsa jikinsu ya sanya su buɗe idanu suka miƙe a firgi ce. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Mi mukeyi nan?, ina sauran abokan tafiyar mu." Jafar ya faɗa yana mai kallon mandiya da Basma da suke rarraba idanu ido. Hannu Basma ta ɗora akai ta fashe da kuka. "Wayyo Ɗana wayyo Mijina ashe kallon ƙarshe nayi maka bazamu sake haduwa ba ajali ke kira na." Ya isa, Jafar ya daka mata tsawa, "da kukan ki zamujin ko da halinda muke ciki, harkin manta da nasihar Ammar?, babban tashin hankalinmu ayanzu shine an raba mu da abokan tafitayarmu." Sai lokacin su Mandiya suka lura da basu tare da abokan tafiyarsu. Nau sawa suka ƙarayi ciki jejin suna kwalama abokan tafiyarsu kira. Tun suna kiran sunayen su da ƙarfi har muryoyinsu suka shaƙe amma ko alamunsu babu. Tsayawa sukayi suna mai da numfasha saka makon tafiyar da suka sha. "Ni fa ina ganin an rabamu da abokan tafiyarmu ne dan ayi galaba akanmu." Mandiya ta fada tana fuskantar Jafar. "Nima zuciyata ta kawo mani wannan tunanin tuni, amma duk da haka mu dage da Addu'a, Allah shine kaɗai mai iya fitar damu daga cikin wannan halin." Tashi sukayi suka ci gaba da tafiya, sun ɗanyi nisa da wurin da suka baro sukaji takun tafiya a bayansu. A hanzar ce suka juyo suna dunkulewa wuri ɗaya. Sal...Sasa..Salma!. Baku nan su, suka furta suna in ina. Salma dake nesa dasu takowa ta farayi zuwa inda su Basma suke. Mandiya murnan sun fara ganin abokan tafiyarsu ya sanyata rugawa ta maƙalƙale Salma. "Muna ta naimanku ina kuka shige Salma?." Shirun da taji anyi mata ne ya sanyata dago fuskarta tana kallon Salma. Ganin fuskar Salma da ta chanza ta koma irin suffar Horror, rabin fuskarta ya kowa abun tsoro duk yayi dameji wani farin ruwa mai haɗe da jini na zuba,idanunta ɗaya babba ɗaya ƙarami ga bakinta daya rabe biyu jini na ɗiga, faratan hannuwan ta sunyi zaƙo_zaƙo irin na Horror. Razanan niyar ƙara ta fasa tana ƙoƙarin kwace kanta a hannun Salma. Sai da ta makaro domin Salma ta rigada ta mata kyakykyawan ruƙo. Dariya Salma taci gaba da 6a66akawa da ta sanya dajin amsa kuwwa. Kunyi kuskuren shigowa dajin nan yau sai dai wasu baku ba. Ɗaga Mandiya tayi da ta wullata sama, tayi nuni da hannunta wata iska ta riƙa wulwula mandiya tamkar yadda fanka ke gudu, tun Mandiya na ihun naiman taimako harta daina motsi. Nuna ta tayi da hannu take wannan iskar ta tsaya nan Mandiya ta faɗo ƙasa tim!. Darita ta kuma kecewa da ita, sai da tayi mai isarta sannan ta turbune fuska, "ku masu kunnen ƙashi, yau zakuga yadda zamu ƙare daku musamman kai, tana mai nuna Jafar da yatsa." "Na haɗa maku tarko amma nasara ya akayi kuka tsallake shi, kunci ƴa'ƴan itatuwanda nina san da kunci to mutuwa zakuyi, kai kasa suka furta wata kalma wadda lokacin da zakuci wadda ita ta sanya kuka tsira da rayuwarku abinda kukaci bai kasheku ba, dan haka yanzu anan take zani raba gangar jikinku da numfashinku." "Baki isa kiyi mana abinda Allah bai rubuta zai faru damuba, kamar yadda Allah ya tseratar damu a wanchan lokacin nan ma muna sa ran zai tseratar damu." Kafin tayi wani yunƙuri cikin jarumta da dakewar zuciya Jafar ya ɗaga murya ya fara karanto Ayatul kursiyu, ita ma Basma ta ɗauka sukaci gaba dayi tare. Ƙara Aljanin yake jikinshi na tsagewa ba shiri ya zama guguwa ya bi iska ya bace. Tsagaita karatun sukayi, suka nufi inda Mandiya ke kwance shame_shame ba alamun tana motsi....... ____________________ Tunda Aljanin ya wurgar dasu, buguwar dasu kayi ta sanya su sumewa. Rabson ne ya fara farkawa, a hankali ya matsa kusa da Audu yana bubbuga jikinshi har yayi nasarar ta dashi. Hayaniyar da su Rabson keyi suna naiman sauran abokan tafiyarsu ita tayi nasarar tada su Biba suka tashi. Sun duba ko ina amma babu abokan tafiyarsu. Tashin hankalin da suka shiga bai misal tuwa musamman su Rabson da Salma. Gajikin Audu sai ƙara rikiɗewa yake yana komawa green da baƙi. Duk cikin babu wanda ya lura da halinda Audu ke ciki tashin hankalin da suke ciki yasa sunmata da komi. Ƙara nitsawa suke cikin dajin suna naiman su Jafar, amma ina sai da suka gaji liƙis basu ga koda sawayen ƙafarsu ba. Zama sukayi suna mai da numfashin wahala. "Mu yanzu haka zamu ƙare acikin wahala ga rashin tabbas na zamu fita daga jejin nan, Daddy dana bi maganarka da banzo wurin bikin nan ba, Hajara ban yafe makiba duk ke kika jawoni cikin wannan bala'in, gashi nan ke kinyi aurenki nikuma gani nan cikin masifa." Salma ta ƙarashe maganar ta rashe hawayen fuskarta. Jugum_jugum suka yi kowa da abinda yake tunanin. Yana yin wurin da suke zaune bakajin motsin komi sai sautin numfashinsu dake fita. Motsin tafiya sukaji alamun ana nufo in da suke. Miƙewa sukayi jikina kyarma Salma ta kama hannun Biba ta riƙe gam kamar wani zai rabasu. Motsin takun naƙara kusanto su, suna ƙara shigema junansu. Abinda idansu ya hasko masu ne ya sanyasu suman tsaye la66ansu na makyarkyata suka furta Garrrba!.... ___________________ Da ƙyar suka samu Mandiya ta farka daga sumewar da tayi. Tana tashi ta riƙa ƙwala ihu tana gasu nan gasunan zasu kasheni. Saida Jafar ya dage mata da addu'a sannan ta dawo dai_dai. Shawara suka yanke bazasu ƙara zaunawa wuri ɗaya ba sai dai in dare yayi su yada zango su kwana su ci gaba da tafiya in gari ya waye. Tafiya suke baji ba gani ga yunwar da ta addabesu da ƙishirwa. Sunyi tafiya mai nisa suka iso wani wuri mai yalwar bishiyoyi masu suffar dodanni, wasu sun rankwafa kamar zasu faɗi ga jikinsu babu ganye ko ɗaya, wasu kuma Suffar mutumce tsaye ya buɗe baki yana dariya,wata bishiyar in kayi mata kallo ɗaya bazaka kuma kallonta ba. Tunda suka shigo wurin suka sha jinin jikinsu, ba su Basma kaɗai ba hatta Jafar sai da zuciyarshi ta buga ganin yanayin wurin, sai dai shi bai fiddo tsoranshi ba a fili, sa6anin su Basma ita da Mandiya da suka maƙale juna suna bin bayan Jafar. Busassun ganyayen dake baje wurin suka riƙabi ta saman su suna takawa domin su fita daga wannan sarƙakiya. Takun da suke da sauri yasanya duk busashshen ganyen da suka taka yake bada wata ƙara rumutss! A hankali wata iska ta fara kaɗawa ganyayen wurin suka fara tashi sama. Lokaci ɗaya wata guguwa ta turniƙe wurin, dale su Jafar suka duƙa tare da rufe idanunsu. A hankali iskar ta fara lafawa, buɗe idanunsu sukayi dan ganin mike faruwa. Bishiyoyin wurin suka gani da wasu jajayen idanun tamkar garwashin wuta, sun buɗe bakunan su suna wata irin dariya mai kama da kukan jarirai. Tsoron da ya kamasu bai hanasu miƙewa su falfala da azababben guduba. Duk bishiyar da suka gitta ƙoƙari take ta kawo masu Chafka. Gudu suke ba ƙaƙƙautawa, suna ƙoƙarin tsira da rayuwarsu. Wata bishiya ce tayi nasarar sanya jijiyarta ta chafko ƙafar Basma dake gudu. Ihu take janyo ta bishiyar keyi da ƙarfi jikinta na karcewa da ganyayyakin dake ƙasa. Ganin halin da Basma ke ciki ya sanya su jafar juyowa domin kawo mata agaji. Gudu suke suna binta bishiyar na ƙara janta. Jafar ne yayi nasarar danƙo sauyar bishiyar. Ƙoƙarin kufcewa sauyar keyi amma ta kasa saboda ruƙon da yayi mata. Da ƙyar da addu'ar dake bakinshi yayi nasarar karya sauyar. Bata damu da ciwokan dake jikinta ba tana samu ya kwanceta ta miƙe sukaci gaba da gudu........ __________________ Garba da kamanninshi suka gama rikiɗewa jikinshi yayi fari fat, idanunshi baƙin ciki ya bace sun koma farare tas, ga farautanshi sun ƙara tsawo, duk ya zama abun tsoro. Wasu yawu Salma da Rabson suka haɗiye atare kutt!. Biba tunda tayi mashi kallo ɗaya tashiga karanto duk wata addu'a da ta zo mata. Kafin su ankara Garba yayo kukan kura ya turmushe Rabson yana kokawar kai mashi cizo. Wato wani bala'in inka ganshi tsoro barinka yake ka hau ƙoƙarin ceton rayuwarka. Rabson ƙoƙarin yakice Garba yakeyi bakinshi na karanto addu'o'in da ya koya tunlokacin da Kaka ta sanyashi islamiyyah. Inya fara karanto kul a'uzu kafin ya ida ya kamo Walfajir, ita ma ya saki, ya kamo Wata,ranar Rabson har addu'ar shiga kewaye (Toilet) sai da yayi. 😂😂😂 Allah ya dubi Rabson ya bashi sa'ar wurgar da Garba ya kwasa a guje su Salma suka take mashi baya. Miƙewa Garba yayi yabi bayansu da azababben gudu suka ƙara nausawa cikin jejin. *COMMENT* ✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA* 🥰🥰🥰🥰 *WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA* *MASOYA INA MAI BADA HAƘURI BISAGA JINA DA KUKA YI KWANA BIYU SHURU, HAKAN YA FARUNE BISA GA MATSALAR NEPA DA MUKA SAMU, AMMA YANZU KOMI YA DAI_DAITA, INA GODIYA MASU TURO MANI SAƘONNIN DA KIRANA DAMA WAƊANDA BASU SAMU DAMABA INA MATUƘAR GODIYA,ALLAH YABAR ZUMUNCHI* 🥰🥰🥰🥰 ___________________ *PAGE 12_13* .......Gudu suke iyakar ƙarfin su, domin ceton rayuwarsu. Basu ankara ba suka gansu gaban wani kogo, basu tsaya 6ata lokaci ba suka kutsa kai cikin kogon. Cirko_cirko sukayi suna mai da numfashi saboda gudun da suka sha. Sai lokacin suka lura da inda suke, "Mun shiga ukku minike gani nan?, ina muka kawo kanmu." Salma ta faɗa tana nuna masu ƙwarangwal ɗin mutane birjik wurin. Kogon ko ina ka kai dubanka ƙwarangwal ɗin mutane ne birjik ga yana duk ta mamaye wurin. Ido suka fara rarrabawa suna ƙara bin wurin da kallo. "Kada tsintar kammu a wannan ya tada mana hankali, mutsaya mu naimi mafita mu dage da addu'a,kada mu kuskura mu rabu da junan mu." Biba ta faɗa tana binsu Rabson da kallo. "Eh haka ya kamata mu riƙa tafiya tare da junanmu, kada muyi kuskuren rabuwa da ƴan uwanmu." Salma ta faɗa muryar ta na kyarma tana ƙara shigewa jikin Biba. "Muje mu naimi abinci nidai jina nike cikina kamar an hura wuta." Rabson ya miƙe tare da yin gaba. Bayanshi suka bi tare da nausawa ciki kogon. Tunda suka fara tafiya Basu gamu da komi ba sai ƙasusuwan mutane da yanar da ta tare hanyar sai sun ɗebe ta da hannunsu suke samun hanyar wucewa. Tirjiya suka ja ganin Mutum tsaye. Salma cikin in iyna ta furta da..da..daddyy..... ____________________ Sunyi gudu har sun galabaita. Tsayawa sukayi ganin sun baro wurin duhuwar, sun bullo wani wuri mai yawan kwazazzabai ruwa na wucewa a hankali ta ƙasansu. Yanayin wurin gwanin ban sha'awa. Nan suka tsaya suka gabatar da sallolin da ake binsu. Cikin ruwan da ke wucewa suka shiga suka ci gaba da tafiya, suna jan ƙafafu a hankali. Jafar ne gaba sai su Basma a bayanshi. Mandiya ji tayi kamar an tsunkule ta a ƙafa, a zabure ta yi tsalle ta ruƙunƙume Basma tana. "Nashi ga ukku na lalace miye ya cijeni a ƙafa?, wayyo uwar daba da magajiya Allah ya tsinemaku albarka, duk ku kuka jefani ciki halinda nike ciki." "Ke ki sakini ya kike ƙoƙarin kayar dani, dake zaniji ko da yunwar dake ɗawainiya dani." Basma ta yakice Mandiya ajikinta. "Ya isa! Ku fahimci halinda muke ciki, ku daina yawan hayaniya kuna ɗaga muryoyinku hakan zai iya janyo mana wata matsalar." Cigaba da tafiya sukayi. Tim! Sukaji ƙarar faɗuwar Mandiya cikin ruwan. Janta ake ba ƙaƙƙautawa ana gwarata da dowatsun wurin. Ganin wanda ke janta ya sanya su haɗiye wani yawun tashin hankali. Nura shila suka gani kamanninshi sun sauya jikinshi yayi fari sol ya koma suffar horror yana jan ƙafar Mandiya. Ihu take tana kiran sunayensu, su taimaka mata. Nura nasarar ida janyo Mandiya yayi, ya dasa mata haƙoranshi a ƙafa. Wata irin kururuwa tayi jin azababben cizon da Nura yayi mata a ƙafa. Ganin halinda Mandiya ke ciki ya sanya Jafar da Basma fidda tsoron da ke cikin ransu, Basma ta kamo hannuwanta tana janyota tana kuka. wani dutsi Jafar ya ɗauka ya bugama Nura a tsakiyar baya. Wata ƙara ya ƙwala da tayi sanadiyyar sanya wurin amsa kuwwa, tsuntsayen dake wurin suka yi sama. Hannun Mandiya Basma ta kama suka yi cikin dajin da azababben gudu. Nura ganin su Basma sun Tsere mashi ya ya sanyashi bin bayansu shima......... ____________________ "Daddy kai nike gani ko idanu nane ke yi mani gizo?." "Nine Salma, Mahaifiyarki ta sanar dani abinda ya faru shiyasa na biyo bayanki nazo in fitar dake daga jejin nan, Zo muje kinji Mamana." "Aa Salma kada ki yarda dashi, wsnnan ba Mahaifinki bane, yaudara ce kawai." Biba ta faɗa tare da kamo hannun Salma tana ƙoƙarin hanata ida isa wurin Babanta. "Dallah malama rabu dani, dan kinga ba mahaifinki bane yazo tafiya dake shiyasa kike ƙoƙarin hanani isa gareshi, ninasan dama zai zo da bataliyar sojoji ya fitar dani daga wannan jejin ." Fizge hannunta tayi tare da rugawa ta rungume daddyn ta. Wata Mahaukaciyar dariya taji an barke da ita, wadda ta haddasama Kogon girgiza. Tuni su Rabson da Audu gwarama suka haɗe wuri ɗaya suna sallallami. Biba baiwar Allah idanunta ta rufe taci gaba da kwararo duk addu'ar da tazo bakinta. Salma jin Daddyn ta da ta rungume ne ke wannan dariyar ya sanya ta ɗagowa a matuƙar tsorace. Ja tayi da baya ganin ya chanza suffa ya koma wannan tsohuwar da ta mara lokacin da zata shiga mota. Cikin kakkausar murya tsohuwar ta fara magana. "Ina kuma zakije ɗiyata?, ko har kin manta marin da kikayi mani?, bai kamata kiji tsoro tun yanzu ba." Zubewa Salma tayi bisa guiyoyinta ta fara ba tsohuwar haƙuri. Ƙara tun tsurewa da dariya tayi."Dole ki ɗauki hukuncin abinda kika aikata kigane wulaƙanci ba abu bane mai kyau." Hannu ɗaya tasa ta suri Salma ta buga da ƙasa kanta ya bugu da wani icce take goshinta ya haye yayi suntum, jini yaci gaba da zuwa. Hayaƙi Aljanar ta koma ta shiga jikin Kwarangwal ɗin dake wurin take suka fara motsi suna miƙewa. Salma miƙewa tayi da ƙyar ga zafin da goshinta ke mata ga lebenta daya haye yayi suntum ga hannunta da ta faɗa samanshi yana mata azababben raɗaɗi. Ganin kwarangwal ɗin sunyo kansu, yasa suka fara ja da baya tsabar firgici kasa gudu sukayi. Rabson cikin daga murya yace. "Kuna gani ana naiman hallaka mu amma kunyi tsaye sororo, toni nayi gaba saikun taho." Zabgawa yayi da gudu ko waiwayowa bayayi. Suna gani yayi gaba suka take mashi baya. Kwarangwal ɗin suka bi bayansu a guje. Gudu suke suna waiwayen kwarangwal ɗin. Sunyi nasarar fita daga cikin kogon sukaci gaba da gudu. Turjiya suka yi ganin wani wawakeken tsauni da suka tsinci kansu samanshi,ƙasan tsaunin ruwane ke gudu. Basu da wata mafita face su dira cikin ruwan nan. Juyawa sukayi gani sukayi kwarangwal suna ƙara kusanto inda suke baki buɗe suna wata irin kuwwa mai razanar da rihin bil adam. Rabson cikin kyarmar murya yace dasu Audu. "Nidai da in tsaya waɗan nan halinttun su kasheni a banza ƙara in faɗa ruwan nan." Ƙafar wandonshi irin na gayun nan wanda ake kira Inna tayani cirewa ya duƙa ya nannaɗe ya nufi ramin yana nayi gaba sai kun iso. Tsalle yayi ya dira ƙasan ramin, suma sauran take mashi baya sukayi suka tsunduma ƙasan ramin. Lokacin da kwarangwal ɗin suka iso, har sun ɗira ƙasan. Lokacin da suka dira cikin ruwan wani rin ruwane mai matuƙar yawa ga zurfi, iyo suka ci gaba dayi amma babu alamun zasu kawo ƙarshen ruwan, gilmawar wani baƙin abu suka gani ya wuce ta gabansu. Tsananta yin iyon sukayi domin iskar da suka yi guzurinta ta kusa ƙaremasu. Abun mamaki kowanensu cikin kwarewa yake iyo tamkar dama chan sun saba. Rigar Audu akaja tareda yin ƙasan ruwan dashi, cikin kwarewa Rabson yayi saurin ruƙoshi yayo sama dashi. Da kyar suka iso bakin gabar ruwan kowanensu yana jan dogon numfashi. Basu bar wurin ba nan suka gabatar da sallolin da ake binsu, zama sukayi suna hutawa, domin a halin da suke ciki baza su iyacigaba da tafiya ba. Jikin Audu ne ya ida zama green da baƙi, ga wasu iri jijiyoyi baƙaƙe da su ka bayyana a fuskarshi. Kamar an ɗauje shi anyi jifa dashi haka aka wullar dashi gefe ko numfashi babu a tare dashi. Cikin firgici su Biba sukayi kanshi suka tsaya chirki_chirko. A hankali kamanninshi suka fara sauyawa yana komawa Horror. Ganin haka ya sanya su Biba ja da baya cikin tsananin tsoro. Tamkar an harba kibiya daga cikin kwari haka Audu yayi wata alkafira ya dira gabansu Rabson....... *KU ƘARA DA HAƘURI, MATSALAR NEPA MUKA SAMU, AMMA YANZU ALHAMDULILLAH, MASOYA INA GODIYA NAGA SAƘONNINKU DA KIRANA DA KUKA RIƘAYI KUJI LAFIYA, INA MATUƘAR GODIYA ALLAH YA BARMU TARE* 🤗🥰🥰 *COMMENT ✅* *SHARE ✅* *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA* 🥰🥰🥰🥰 *WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA* *MASOYA INA MAI BADA HAƘURI BISAGA JINA DA KUKA YI KWANA BIYU SHURU, HAKAN YA FARUNE BISA GA MATSALAR NEPA DA MUKA SAMU, AMMA YANZU KOMI YA DAI_DAITA, INA GODIYA MASU TURO MANI SAƘONNIN DA KIRANA DAMA WAƊANDA BASU SAMU DAMABA INA MATUƘAR GODIYA,ALLAH YABAR ZUMUNCHI* 🥰🥰🥰🥰 ___________________ *PAGE 14_15* ............Ganin sun tserema Nura yasan ya Mandiya faɗuwa ƙasa tana maida numfashi. Dafe ƙafarta dake yi mata raɗaɗi tayi. "Wayyoh ni Mandiya na bani na lalace, yanzu shikenan nima Horror zani zama." Sauran maganar maƙalewa tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta. Matsowa sukayi fuskokinsu da matuƙar tausayi suna mata sannu. Ƙafar suka kallah, abin mamaki jinin dake zuba ya tsaya, wurin yayi wani irin green da baƙi. Su kansu sun san nan da lokaci ƙanƙani itama zata zama Horror. Allah sarki Jafar duk halin tsananin da suke ciki zuciyarshi tana wurin Biba kullum cikin tunaninta yake zuciyarshi tana hasko mashi hoton fuskar Biba. Basma ta taimaka ma Mandiya sukaci gaba da tafiya har duhu ya farayi. Ƙarƙashin wata itaciyar Kuka suka yada zango, daji Jafar ya shiga ya samo masu ƴa'ƴan itanuwa sukaci. Fuskokin su duk cikin tashin hankali suke, kowa da irin tunanin dake cikin zuciyarshi. Motsin da sukajine ya sanya su dawowa daga duniyar tunanin da suke. Tamkar walƙiya haka sukaga wani farin abu ya gilma ta gabansu. Basma da Mandiya rirriƙe juna sukayi ido ya raina fata. Miƙewa Jafar yayi a hankali cikin sanda ya dudduba ko ina amma bai ga komi ba. Dawowa yayi ya zauna zociyarshi cike da tunane_tunane. "Jafar ka duba sosai kuwa?, ni fa kamar fatalwa nagani wallahi baka gani ta gifta tanan." Basma ta ƙarashe maganar tana ƙara dudduba wurin. "Tabbas nima ita na gani, amma komiye mu dage da addu'a babu abinda yafi ƙarfin Allah." A ɗarare suke jininsu kan akaifa. Dare yayi dare bakajin motsin komi sai kuka tsuntsaye da wani irin gurnani da suka rasa gane namiye. Jafar gani yayi zaman zugum ɗin yayi yawa nan ya buƙaci jin miya fiddo da su daga gida. Basma ta fara basu labarin abinda ya fito da ita, Jafar ya girgiza sosai dajin labarin yayi mamakin yadda ta bijirema umarnin miji ta taho biki, wai kuma bikin ma na ƙawa. Nan itama Mandiya ta fara bada labarinta kamar haka; "Kamar yadda kujaji da farko nidai sunana Mandiya, garinmu ɗaya daku wato gefen Kai kazo, na taso babu uwa babu uba, natsinci kaina a gidan karuwai hannun wata mata mai suna uwar daba, tun da na taso banida kunya ko kaɗan ga taka mutane da bi ta saman duk wanda ya so kawo mani raini, tun ina da shekara 20 uwar daba ta ɗorani a hanyar karuwanci, in da ni dana tashi sai karuwanci na yayi zarra saboda rashin kunyata nayi suna duk inda kashiga indai gidan karuwai ne to an san da zamana, abinda yayi sanadiyyar fitowata wannan tafiyar Magajiyar karuwai tai ta kwaɗaita mani inzo garin kai kazo zani tara dukiya mai tarinn yawa, domin chan karuwanci yafi tsada, kunji abinda ya fiddoni, har yanzu ina dana sanin fitowata da kasancewata karuwa ina nadamar rayuwar da na tsinci kaina ciki." Kukan dayaci ƙarfinta ya sanyata kasa ida maganar. Sun tausaya mata halinda ta tsinci kanta. Nan Jafar ya ƙara jan hankalinta Allah gafurun rahimun ne, ta tuba har cikin zuciyarta Allah yana karbar tuban bawanshi madamar baizo gargara ba. Nan shima Jafar Ya basu labarin abinda ya fito dashi gida, sun jajantama juna suna addu'ar Allah ya fitar dasu a wannan jejin. Tsit! Wurin yayi kowa da abinda yake tunani, Jafar yana gefensu ya takure wuri ɗaya yana addu'a a zuciyarshi. Dariya aka kece da ita wadda ta tilasta masu toshe kunnuwansu da duka hannayensu biyu. "Hhh! Wane ganganci da ƙarar kwana yayi Sanadin kawoku cikin jejin nan, kamar yadda muka rasa rayuwarmu muka koma fatalwa haka kuma zaku rasa taku rayuwar bazaku taba fita a jejin nan ba." Kawunansu suka ɗaga suna ƙarema halittar kallo, sanye take da farar riga da tayi face_face da jini, ilahirin jikin ta farine sol idanuwanta babu ɗugon baƙi ko kaɗan ga dogayen hannuwa masu ɗauke da farata dogaye masu tsananin tsini, doguwace sosai tsaye take saman iska kamar tsuntsu doguwar rigar dake jikinta dogowace har ƙasa shiyasa ko ƙafafunta baka iya hangowa. Jikin su Mandiya da Basma tuni ya hau mazari. Jafar ji yayi kamar an sanya sarƙoƙi an ɗaure bakinshi addu'ar ma ya kasa gurta koda kalma ɗaya. Wannan damar Fatalwar ta samu ta nunasu da yatsa wani farin hayaƙi yafito ya zama guguwa yayi sama dasu Jafar. Tamkar yadda fanka ke wulwulawa haka aka riƙa wulwula su Mandiya tun suna ihu har ƙarfinsu ya ƙare sukayi tsit iskar ta watsar da su wani bangare daga cikin jejin batare da sun san mike faruwa ba. ___________________ Kamar yunwa taccen zaki haka Audu yayo kan Salma da tayi mutuwar. Tariga ta bada sadaƙar yau kwananta ya ƙare jira kawai take ya kasheta ta huta. Kamar daga sama sukaji ƙarar wani abu kamar an buga bindiga. Mace da namiji suka gani tsaye gabansu da wani abu kamar sanda a hannunsu. Dubansu suka kai ga audu dake kwance ƙasa yanata bullayi da alamu ƙoƙarin tashi yake. Mace tace dasu Biba mubar wurin nan kafin ya tashi domin gaf dake da miƙewa. Su duka suka bar wurin suka yi wata siririyar hanya da guda. Gudu suke ba ƙaƙƙautawa tamkar bazasu tsaya ba. Ganin sunzo wurin wata gadar icce suka ja suka tsaya suna maida numfashi. Rabson da sai yanzu hankalinshi ya dawo jikinshi ganin bakin fuska ya sanyashi yin tsalle ya koma gefe. "Innahu min sulaimanu...., bayin Allah mutane ko aljannu, daga ina kuke mijya kawoku jejin nan?, ko dai kuma Horror ɗinne sukazo mana da taku salon yaudarar?." Namijin daya gama ƙuluwa ya watsama Rabson kallon zaka gane kurenka. Macen tayi ƙarfin halin fara magana. "Tsautsayi ne da rabon wahala ya fiddomu daga gida har muka tsinci kanmu cikin Wannan halin, ni sunana Kulu amma ana kirana Kulu ganin ƙwam, sai abokin tafiyata sunanshi Nasir, sai kuma abokan tafiyar mu su biyu da suka bace mana Jamcy da Tukur muna kiranshi Tk, mun kasance masu son kallon abubuwar mamaki ne, Rannan malamin mu na mana lecture yake sanar damu wannan jajin da haɗarindake tattare dashi, da kuma abubuwan mamakin dake cikinshi tundaga lokacin muka yanke shawarar guduwa daga gidajenmu domin muzo ganin abubuwan Al ajabi, mu hudu haka muka shigo dajin nan bala in da muka shiga ya sanya muka rabu da abokan tafiyarmu batareda mun saniba. Halin da suke ciki bai hana Rabson fashewa da dariya jin waɗan da suka fisu gantalewa, Nas a fusace ya taso ganin Rabson ya raina masu wayo, cikin hanzari kulu ta tareshi tana bashi haƙuri. Rabson kallon Salma yayi gsnin yadda bakinta yayi Suntum ya haye ga goshinta daya yi ranƙwalele. Sake fashewa yayi da dariya yana riƙe ciki, yana nuna Salma da hannu yanaci gaba da dariya. Tamkar zata kai mashi bugu haka Salma tayo kan Rabson, Biba tayi saurin riƙeta tana bata haƙuri, ashar kawai take dannoma Rabson amma bai daina dariyar ba. "Haba Rabi'u! Miye haka Kana ta taƙular mutane bakaga halin da muke cikiba amma har kuke ƙoƙarin fada?." Bai daina dariyarba yaci gaba da magana"Habibalo kiyi haƙuri wallahi inna kalli bakin Salma yadda yayi tsawo kamar shantu bani iya danne dariyata, masoyiyita Salma kiyi haƙuri kinji nifa tunda muka shigo jejin nan nike jin ƙaunarki na ratsa jinin jikina." Ya ƙarashe maganar yana dariya. Salma kamar ana zugata haka ta riƙa zagin Rabson tana fadar tafi ƙarfin tayi soyayyah dashi, da Ƙyar Biba ta shawo kan Salma tayi shiru. Gurnanin da sukaji bayansu ya sanya bashiri suka fara bi ta saman gadar katakon ba shiri. Doguwar gadace wadda aka ƙerata da katako gefe da gefe kuma iggiyace wadda zaka riƙe hangu da dama, kasanta ramine mai tsananin zurfi baka iya hango ƙarshenshi. Tafiya suke da sauri Rabson na taka wani katako ya balle yayi ƙasa , lokaci ɗaya gadar ta fara karairayewa ta yin ƙasa, hankulansu atashe wasu suka fara ihu, wasu suna addu'o'i. Rabson atake ya fara bada wasiyyah yana; "Salma masoyiyata inkin samu komawa gida kice ma Kaka na barmata ɗan bunsuru na duniya da lahira ta yafe mani , wayyoh kaka lokacin mutuwata yayi." Igiyoyin gefen gadar suka rirriƙe suna gudu gadar na ƙara karairayewa......... *COMMENT* ✅ *SHARE* ✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA* 🥰🥰🥰🥰 *WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DAƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰 ____________________ *PAGE 16_17* ........Sanyin da sukaji yana ratsa fatar jikinsu ya sanyasu fara bude idanunsu. Jamcy da Tk dake tsaye kansu da wani icce ahannuwan su, suna jiran farkar warsu, a tunaninsu suma Horror ne lambo sukayi masu. A firgice suka miƙe, Mandiya ganin mutane biyu saman kanta ya sanyata kwala ihu cikin tsananin kaɗuwa, kafin ta rufe baki Jamcy dake tsaye kanta atunaninta horror ce bata 6ata lokaci ta kwadama Mandiya sandar nan, a take Mandiya ta baje ƙasa a sume. Sallallami su Jafar suka hauyi tare da yo kan Mandiya. "Mutane ko Aljanu?, mikuke naima awajenmu da har kuka sumar da abokiyar tafiyarmu." Tk da idanunsu suka raina fata cikin ƙarfin hali ya fara jawabi. Nan ya kwashe komi ya fada masu har batan abokan tafiyarsu wato Kulu da Nas. Sun yi matuƙar mamakin ƙarfin hali irin nasu Jamcy, kawai saboda ganin ƙwam irin nasu zasu baro gida. Mandiya da ta samu ta farfaɗo buya tayi bayan Basma tana mai da numfashi. Bata yarda dasu Jamcy ba sai da Jafar yayi da gaske sannan ta yadda su ɗin mutane ne. (😂🤣 Niko nace Mandiya anji sambaɗebaɗe) Wurin da suke wurine mai wuyar misaltawa, domin tunda suka fara tafiya basu taba tsintar kawunan su a irin wannan wurin ba. Tsabar duhuwar dake wurin tamkar dare ya fara haka yanayin wurin yake. Kallon_kallo suka shiga yi, tamkar yau suka fara ganin juna. Da dai sukaga basu da wata mafita face su ci gaba da tafiya, miƙewa sukayi tare da kakka6e jikinsu suna makyarkyata saboda tsananin sanyin da ake zabgawa wurin. Mandiya kai ko ɗan kwali babu ga kitson attach ansha ga kayan jikinta sun matseta, Basma riga da siket ne jikinta wanda suka sha ɗinki yayi rigar nan daga sama ta matse ƙasa kuma ta buɗe, ga siket ɗin irin wanda ƴan mata ke yayi wanda ake kira mai guiwa. Uwa uba Jamcy da ta takesu wurin wayewa zamuce ko gantalewa, jikinta T.shirt ce ta ɗan kawo guiwa sai wandon ta jins wato crazy wanda matasanmu ke yayi. (Wasu mutanen ganewace basuyiba wani fa inya kalleka bada halayenka zai duba ya gano kai waye ba, shigar jikinka ita zai fara kallo yayi maka hisabi, dan haka musan irin shigar da zamu riƙayi, in bakajin tsoron Allah to akwai lalatattun mutane in babu su akwai Shaiɗanun Aljanu.) Tafiya suke suna bankar juna saboda sanyin da suke ji bakunan su har farin hayaƙi ke fita. Tun suna tafiya iyakar ƙarfinsu har ƙarfin ya ƙare suka koma jan ƙafa. Tsayawa suka yi da tafiyar tare da bajewa ƙasa suna huttai. Ga yunwa ga ƙishirwa da basu iya tantance yaushe rabon da su kai wani abu bakinsu. Fashewa da kuka Basma tayi tana faɗar; "Wayyo mijina! Wayyo gidan aurena, shikenan a haka zani ƙare nayi bankwana da asuwaki da cinyoyin kaji gani nan abinda zanisa cikina yana gagarata,da gida nike da ina chan ina asuwaki da naman kaji abinci sai wanda naga damarci, amma yanzu ganinan na ƙare a daji,Ta gaban goshi Allah ya isa tsakanina dake da kika turani na bijiirema maganar Habib nafito damin halartar bikinki, Wayyo Ɗana wayyo mijina." Haka taita sambatu tana kuka kamar ta 6a66a. Kece wa da dariya Jamcy tayi tareda kallon Basma. "To la'anan na mai kama da ƴa'ƴan yahudawa wakikema dariya?." Ci gaba da dariyar Jamcy tayi ta nuna Basma da yatsa. "Wa fa nike ma dariya in ba ke ba, tsabar gantali da aurenki amma kika baro mijinki kika taho bikin wata ƙawa." Ashariya Basma ta tattaro ta ɗurama Jamcy tare da miƙewa tayo kanta gadan_gadan. Da ƙyar Jafar yayi nasarar raba wannan faɗan daya yaso barkewa. Ƙutawa kawai Basma keyi tana hararar Jamcy, ita kau Jamcy da sun haɗa ido saitayima Basma kwalo tana mata dariya. Iya ƙuluwa ta ƙulu da Jamcy, jira kawai take Jafar ya ɗan kauce tasamu sa'ar tumurmusa Jamcy. Jafar daya lura Tk ɗan zafin kai ne tunda suka haɗu sai wani shan ƙamshi yake yana hura hanci. "Tk ka taso muɗan zagaya cikin jejin nan musamu abinda zamu sama cikunnan mu." Kallon up and down Tk yayima Jafar. "Ok muje." Yafaɗa yana yamutsa fuska kamar yaga kashi. "Ku su Basma ku tsaya nan kujiramu mu dawo." Tsalle Mandiya tayi ta dire ita bazata tsaya nan ba wani abu yazo ya hallakata. Suma sauran mara mata baya akan bazasu zauna ba. Sunyi tafiya mai ɗan tsayi suka iso wani wuri mai yalwar ganyayen bishiyoyi. "Laaah! Kuduba ku gani chocolate da sweet a chan." Dubansu suka kai wurin suna masu mamaki ganin kayan daɗin da ko a cikin gari sai kanada manyan kuɗi zaka mallakesu. Hannun Jamcy Tk ya kamo saboda yasan mayyar kayan zaƙice. "Sweety ka sakeni in ɗauko, kasan fa yadda nike bala'in son chocolate." "Aa ƙaunata kada ki ɗauka zai iyafa cutar mani dake, kinsan da wani abu ya sameki ƙara ni ya sameni." Shamatarshi tayi ta fizge ta ruga tana dariya ta nufi wurin chocolate ɗin. Kafin hannunta ya ida isaga chocolate ɗin tuni sun rikiɗe sun koma wani jibgegen baƙin kumurci ya fasa kai yayo kanta. "Nashiga ukku nalalace, Sweety ka kawo mani ɗauki wayyo na bani ni Jamilatu." Cikin firgici da hargagi yake faɗar" kada ki motsa ƙaunata gani nan zuwa gareki." Cikin zafin nama ya jawo Jamcy suka ɗiba ana kare,su Jafar take masu baya sukayi, ganin haka macijin ya bi bayansu. Abinda suka lura macijin yabar binsu sai yanayin wurin daya chanza duhun wurin ya ƙaru. Ƙarar tsuntsaye sukaji saman kawunansu. Ɗaga kan da zasuyi suka ga Wasu irin jibga_jibgan tsuntsaye masu suffar jemage sai dai su sunfi jemage girma da suffa mai ban tsoro. Ganin haka suka ƙara ƙaimi wurin gudun, tsuntsayen na biye dasu. Ƙarar da sukaji an kwala ce ta sanyasu tsagaitawa da gudun suka juyo, Basma suka gani tsuntsayen sun sureta sunyi sama da ita........... ____________________ ........Gudu suke gadar na ƙara karairayewa, sunyi nasarar ida ƙara sawa ƙarshen gadar, suna ida tsallaketa tana Rubzawa ƙasa. Duƙawa sukayi wurin wasu kuma suka baje suna maida numfashi. Mtsw Salma taja dogon tsoki. "Aikin banza mutum gashi nan mugun rago da anshiga bala'i sai ya hau ihu yana cika ma mutane kunnuwa yen_yen_yen, mtsw sauna kawai." Fashewa Rabson ya ƙarayi da dariya. "Bakomi masoyiyata mai bakin shantu, kin ga yadda bakinki ke ƙara tsayi da kina kwaikwayar maganata kuwa." A fusace ta nufo inda yake tana zazzaga masifa. Ganin da gaske take ya sanya Rabso fara magana. "Masoyiya kina ƙarasowa wurin nan zani chakumeki muyi ƙasan ramin nan muyi mutuwar shahada irinta masoya." Ya ƙarashe maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya. Tsayawa tayi daga nesa tana aiko mashi da baƙaƙen maganganu. "Heeey! Yau ni naga marasa hankali, yanzu ku a halinda muke ciki har kunada bakunan yimana faɗa, to duk ɗan....Ta ɗura wata ashariya Daya ƙara mana fada saina hankaɗashi ya faɗa cikin ramin nan." Kulu ta fada tana nuna Salma da yatsa. "To ɗiyar matsiyata waya sako dake?, gantalalliya uwar ƴan yawon ganin ƙwaf." Salma ta ƙarashe maganar kamar zata kai ma Kulu bugu. "Wa'iyazubillah! Ku kam ko gasar ƙunduma ashariya muka fito sai haka, abinda ya kamata mu dage da addu'a amma kun dage sai zagi da ashar kuke ɗurawa, kuyima kanku faɗa kufa ƴa'Ƴan musulmai ne." Shiru suka yi kowa na hararar ɗan uwanshi. "Haba babynah, ki rabu da ita Ke ba sa'ar yinta bace." Nas ya karashe maganar da sigar rarrashi. Nausawa suka kuma yi ciki dajin suna rarraba idanu. A hankali wata iska ta fara kaɗawa tamkar irin in hadari ya fara tasowa. Jin wannan baƙon lamari ya sanya suka ƙara matsewa wuri ɗaya. Duhu wurin ya farayi tamkar ruwan sama zai balle. Gudu suka farayi suna sassarfa,kafin su ankara an kece da wani irin mamakon ruwan sama mai haɗe da iska mai ƙarfin gaske. Gudu suke idanunsu rufe basu ganin gabansu saboda Iskar da ake, wani wawakeken kogon dutse suka gani basu yi wata shawara ba suka afka cikinshi, suna ida shigewa ƙofar kogon Wani dutse ya tugo ya rufeta garam!...... *NIMA KAI NA JIN ƘARAR RUFEWAR ƘOFAR SAI DA WAYATA TA KUSA KUFCEWA* 😂😜 *COMMENT* ✅ *SHARE* ✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DAƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰 *NASADAUKAR DA WANNAN PAHE ƊIN GAREKI KHADIJA S SAMSHARE AR GATAN MAMA, ALLAH YA ƘARA ZAƘIN HANNU* ______________________ *PAGE 18_19* .........Ihu Basma keyi tana naiman agajin su Jafar. Lokaci guda ƙwalwarta ta fara tunano mata inda Ammar ya basu addu'a insun shiga bala'i. "LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN." Basma ta furta da ƙarfin gaske. Tsunsun jiyayi kamar ya ta ɗauko garwashin wuta, bai bata lokaciba ya sakota ƙasa shida sauran ƴan uwanshi suka bace bat! Kamar basu ta6a wanzuwa a wurinba. Duk da buguwar da Basma tayi sanadiyyar faɗowar da ta yi amma haka ta miƙe tana gudu tana ɗingishi. Tun kafin dare yayi sosai suke gudu har saida duhun dare ya raba sannan suka zube suna maida numfashi. "Wayyoh! Zani mutu, wayyo Umma na, na shiga ukku, shikenan mu haka zamu dawwama cikin bala'i muna mutuwa ɗaya bayan ɗaya, koda waɗan nan Aljanun basu kashemu ba yunwar cikin mu kaɗai ta isa tayi sanadin mutuwarmu, wayyo Ummana shikenan bazan ƙara ganinkiba."Jamcy ta ƙarashe maganar tana harba ƙafafu a ƙasa kamar ƙaramar yarinya tana kuka tana kuka. Tk jiyayi kamar ya mangare Jamcy, amma soyayyar daya ke mata bazata bari ya iya yi mata komiba. Dare ya raba sosai ga wani irin sanyi da ilahirin dajin ya ɗauka. Matan su duka haɗe suke wuri ɗaya suna gyangyaɗi ga kyarmar sanyi sunayi. Tk da Jafar wuri suka gyara da hannuwansu tareda kwantawa. Wuri yayi tsit! Bakajin mitsin komi sai kuka tsuntsaye, bacci yayi nasarar sace su. Cikin Bacci Basma taji kamar ana ja mata ƙafa, ƙara gyara kwanciyarta tayi. Fizgar ƙafar akayi da ƙarfin gaske aka jawota daga inda take kwance. Ƙara ta ƙala da tayi sanadiyyar farkawar su Jafar suka miƙe a firgice. Wasu irin mulmula_mulmulan halittu masu kama da dodanni jikinsu duk gashi,ga wasu zara_zaran farata masu tsini, in ka kallesu sau ɗaya bakayi Marmatin sake kallonsu ba saboda tsananin muninsu. Kafin suyi ko ƙarin guduwa tuni dodannin sunyi nasarar kamesu sun sa awani keji, suka ɗauki kejin da hannu ɗaya suka ci gaba da tafiya. Ihu kawai suke in banda Jafar da tuni bakinahi ya fara ambaton Allah da naiman agaji a wurinshi. Tsawa ya daka masu wadda tayi sanadiyyar yin shirunsu. "Bashakka ina ga mun kusa raba tafiyar nan daku, kuna ganin halinda muke ciki amma kun wage baki kuna wani kukan banza da bazai amfanemu da komiba, Shawara ɗayace muyi ƙokarin tseratar da rayuwarmu domin bashakka in muka bari dodannin nan suka ida isa damu lofa lalla mun zama nama cinyemu zasuyi." "Eh musan yadda zamuyi mu buɗe kejin nan mu kubutar da rayukanmu." Tk ya ƙarashe maganar yana ƙara riƙe hannun Jafar kamar za'a kwace mashi shi (😂😂 Niko nace Tk ina ɗagin kan? Ko ka sauko tun yanzu.) "Amma abinda nike gani naga mun fara hango alamu kamar a kwai kogi nan gabanmu in muka buɗe saimu faɗa ruwan, abinda nasani dodanni basu san ruwa mu bari sai muna gaf da ida isa wurin sai muhaɗa ƙarfi mu buɗe ƙofar nan." Sun yi na'am da wannan shawarar ta Jafar, suna gani sun doshi gefen ruwan suka fara koƙarin tserewa. Da ƙyar da ji6in goshi suka samu ƙofar ta ɗan buɗe yadda mutum zai iya fitowa daga cikin kejin. Da ɗai ɗaya suka riƙa dirowa suna ficewa a guje, Mandiyace ƙarshen fitowa tana dirowa Dodan daya ɗauko kejin yaji kamar kejin ya rage nauyi. Kejin daya gani a buɗe duk sun fice ya sanyashi wata irin kuwwa da sai da dajin yayi amsa Amo!. Jin wannan ƙarar ya sanya sauran Dodannin rugowa domin sun fahimci naman da suka kamo ya sun tsere,agujsuka bi bayansu Jafar suna gudu suna daka wani irin tsalle tamkar ƙwaɗanni. Gani irin azababben gudun da Dodannin keyi suna ƙoƙarin iskosu yasa su Jafar ƙara ƙaimi suna ƙoƙarin isa ga wannan kogi. Sunyi nasarar isowa Tk ya fara isowa wani irin birki ya ja ya tsaya ganin irin zurfin da ke akwai kafin ka isa zuwa ciikin kogin, Jamcy na isowa batare da ta luraba ta banka Tk sukayi ƙasa, suma sauran baya suka mara masu. Dodannin na isowa basu iske kowa ba, ganin haka ya sanya suka fasheda wani irin kuka daya sanya wurin amsa kuwwa. Abinda ya basu mamaki kuma ya tsorata su shine ganin ƙasan ruwan haske fayau tamkar ba dareba. Iyakar ƙarfinsu suke iyo amma abinda suka lura shine duk ƙokarin da suke suna nan tsaye a wurin da suka faɗo, wannan al'amari ya matuƙar ɗaga masu hankali. Ga iskar da suka shaƙo ta kusa karewa. Lokaci ɗaya ruwan ya fara wani irin motsi tamkar wani abu ya fao cikinshi. Duk ƙoƙarin da suke amma a banza, sai da Jafar ya fara karanto addu'a cikin zuciyarshi sannan suka ga kamar an saki jijiyoyin jikinsu sun fara wuce wurin. Tamkar an wulloshi haka suka tsinci Nura gabarsu kamanninshi su sauya yakoma Horror idanunshi babu ƙwayar baƙi sunyi fari tas!. Kafin suyi wsni yunƙuri ya warci Mandiya yayi ƙasan ruwan da ita......... __________________________ "Allahumma ajirnifiy musibati wa'aklifini khairan minha." Biba ta ƙarashe Addu'ar yayin da taga ƙofar na rufewa. Tsaye suke ido ya raina fata, kowa ka kalla zaka hango tsananin firgici atattare dashi. Ko ƙwaƙwƙwaran motsi bakaji kogon yayi tsit! Jin motsi bayansu yadawo dasu daga duniyar tunanin da suka lula. Kulu da Nas su suka farayin gaba sai Biba Rabson da Salma suka take masu baya. Tunda suka fara tafiya basu haɗu da komi ba sai yana da ta dabaibaye ilahirin kogon sai sun sanya hannu sun ɗebeta sannan suke samu su wuce. Abinda suka lura kogon wata irin doguwar hanya gareshi tunda suka fara bi har yanzu basu zo ƙarshenta ba. Wani irin daddaɗan ƙamshin abinci hanci nansu suka fara shaƙo masu. "Wow! Nas kaji abinda hancina ya jiyo mani?." "Nima shinike jiyowa masoyiya." Sauri suka riƙayi tamkar zasu tashi sama, turus! Suka ja wani birki yawunsu na tsinkewa. Abinci ne aƙasa cikin filattai jere reras!, shinkafa damiya hada naman kaji zuƙu_zuƙu. Rabson wani yawu ya haɗiye ƙut! Tare da lasar la66anshi. "Kada kuci abincin nan, wani tarko ne aka haɗa mana, kuyi tunani." Biba ta ƙarashe maganar tana riƙo hannun Kulu dake ƙoƙarin bin Nas daya kusa isa ga abincin. "Malama sakar mani hannu, ke in bakici muki ƙyalemu muje muci iya cin mu." Ta fizge hannuta tayi gaba. Salma gallama Rabson harara tayi. "To jikan ƴan lasau, kaje kaci naga tun ɗazu sai lasar baki kake kamar sabon kamu." "Hhh! Haba my Salmaty na hanaki yawan magana fa, kinga yadda kike komawa bakinki har hawa yake kamar tsohuwa zata kira tukur." Ya ƙarashe maganar yana cigaba da dariyarshi. "Bani da lokacinka marar aikinyi kawai mtsw!." "Niko nike da aikinyi, in zauna inta kallon bakinki yadda yayi suntum ɗin nan in kina magana tamkar yadda kikasan bakin aku haka kike komawa." Iya ƙuluwa Salma ta gama ƙulewa da rainin wayon Rabson, a fusace tayo kanshi tamkar zata kai mashi bugu. Ihu Kulu ta fasa wanda ya jawo hankalinsu Biba. Abincin da suka fara ɗiba ne ya koma tsutsotsi Nas da ya kai abincin cikinshi tuni ya baje ƙasa ko motsi bai yi. Ihu take tana girgiza Nas Amma babu alamar zai tashi. Biba ta matso tahau tofa mashi addu'o'i a hankali ya fara buɗe idanunshi, wata mahaukaciyar ƙasa da sukaji tasanya shi ida miƙewa tsaye. Tsutsotsin ne suke haɗewa wuri ɗaya suna zama ƙatuwar tsutsa mai hannuwa bila adadin. Salma da Rabson wuri ɗaya suka haɗe tana ihun kiran sunan dadyn ta shikuma yana kiran Wayyo Kaka wayyo bunsurunleee.... 🤧🤧 Kuyi haƙuri da wannan, banijin dadi alƙawarin danayi makune yasa naƙoƙarta nayi wannan.🤧🤧 *COMMENT*✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰 _______________________ *PAGE 20_21* ............ganin anjanye Mandiya yasan ya su Jafar tsananin ruɗuwa suka ƙara himma wurin yin iyo. Da ƙyar suka samu suka ƙaraso ga6ar ruwan. Kowa ka kalla fuskarshi cikin firgice take da tsananin tashin hankali. Basma tunda suka fito take zazzaga uban aman ruwa, saboda ruwan da ta shaƙa. Aman da takeyi kamar zata amayo ƴan hanjinta. Jamcy kuka kawai take tana tashiga ukku lokacin mutuwarta yayi, da ta sani da bata fito ganin kwaf ba. Tk bai hanata yin kukan ba dominshima a halinda suke ciki inda zaiyi kukan zai fijin sauƙin abinda Yakeji cikin zuciyarshi. Sun ɗan jima awurin suna jimamin abinda ya faru da Mandiya. Ɗunguma sukayi sukabar wurin suna tafiya da ƙyar jikinsu babu kuzari. Jamcy faɗuwa tayi ta tare da fashewa da kuka. "Wayyo masoyi, Mutuwa zaniyi bani iya tafiya, ga yunwa nikeji, dan Allah koɗan naman kifi kayo iyo cikin ruwan nan ka gasa mani inci , ni bazan iya cigaba da tafiyaba." Taci gaba da kukanta. Galala suka yi suna kallonta. Basma kallon bakida hankali tayi mata cikin 6acin rai ta fara zazzaga bala'i. "Ke yanzu in baccin kin maidamu marasa hankali da tunani irinki, gidan ubanwa zamu samu maki irin waɗan nan kayan?, ko kitashi mutafi ko muyi gaba mubarki nan wurin." Zagita aikoma Basma dashi cikin masifa dake cinta ta miƙe tayo kan Basma. "Ke harkin gaya mani wannan maganar?, kinsan ko wacece Jamcy bala'i, nayayimi kankazar_kazarki kaga tunkiya uwar tan6ele ke in banda gantali miya fiddoki kika baro mijinki kika fito yawon gantali." Tatss! Kakeji Basma ta ɗauke Jamcy da kyakykyawan mari, chakumar juna sukayi sukai faɗi kowa tana naushin ƴar uwarta, an rasa mai raba faɗan sunyi tsaitsaye sunkasa koda furta kalmar kudaina faɗan. Ƙyalesu sukayi suka samu wuri suka zauna suka zuba masu ido. Sun bugu sunjigata. Jamcy da taji bugu fuskarta ta chanza kamanni samu tayi ta kubce daga hannun Basma takoma gefe tana maida numfashi ta fara magana da ƙyar. "Muguwa azzaluma, wannan ai zaluncine ace ana faɗa bazaki bari a huta ba sannan muci gaba dan zalunci ,muguwa mai suffar agwagwa Allah ya isana ban yafe maki ba." "Nikike kira mai suffar agwagwa?, kiƙara maimaita abinda kika faɗa yanzu in take maki kai in maimaita maki bugun da yafi wannan 6allagaza mai zubin muciya." Basma ta ƙarashe maganar tana huttai. "Idan kun gama faɗan kutashi mucigaba da tafiya, nikam kunkusa daina ganina dan tsaf zani rabu daku in raba tafiya daku." Jafar ya ƙarashe maganar ranshi a 6ace. Harararshi Jamcy tayi tana gunguni. "Kai kuma maloho kayi sakaka kana kallo wannan matar tayi mani wannan bugun, wallahi zaka gane in muka koma gida." Tk banza yayi ya kyaleta kamar baijita ba, domin shi yanzu abinda ke damunshi taya zai tseratar da rayuwar da daga wannan Baƙar tafiyar. Sunyi tafiya mai ɗan nisa suka samu bishiyar ruman suka tsiga suka sha suka zauna suna hutawa. Motsin da sukaji alamun takun sawun mutum ya nufo inda suke yasanya su ɗago kawunansu. A firgice suka miƙe tsaye suna kallo cikin matuƙar mamaki atare suka furta Rabson!. Tsaye yake yana kallonsu yana murmushi. "Nine zuwa nayi domin intafi daku wurin sauran abokan tafiyarmu, tunda kuka bace mana muke yawon naimanku sai yanzu Allah yasa na ganku." Cikin zaƙuwa Basma tayo wurinshi, "yauwa Mutumina Rabson ina su Salma da su Biba." Jin an ambaci sunan Biba yasa Jafar matsowa domin yaji inda aka baro mashi abar ƙaunarshi. "Suna chan suna jiranku, kuyi sauri mu ƙarasa wurinsu." Ɗunguma sukayi suka mara mashi baya. Sunyi tafiya maitsananin nisa har suka fara gajiya da sunce Rabson har yanzu bamu iso ba sai yace masu ku ƙara haƙuri munkusa ƙarsawa. Wani wuri suka iso mai matuƙar duhuwa ga yawan bishiyoyi ganyayen jikinsu duk sun zubo ƙasa, ta cikin duhuwar suk riƙa ratsawa har suka iso wani bangare daya matuƙar basu mamaki. Gani sukayi Rabson ya tsaya yaƙi gaba yaƙi baya. "Rabson mun iso ko?." Basma ta faɗa tana ƙoƙarin shan gabanshi, dariyar daya tuntsire da i ta ce tasanyasu ja da baya bashiri. Suffarshi tariƙa rikiɗewa tana kasuwa kashi_kashi yana komawa wasu irin maridan Aljanu hannuwansu ɗauke da muggan makamai tamkar waɗanda zasuje yaƙi. Ga wata iriyar guguwa da ta turniƙe wurin........ __________________________ .......Ida haɗewa tsutsar tayi wuri ɗaya tana wata irin dariya mai haddasama kunnuwan bil adam ɗaukewar jin su na wucin gadi. Rabson da Salma haɗe suke suna kuka suna sambatu domin yau sun fidda rai da rayuwarsu, Salma wani zazzafan fitsarine ya wanke mata ƙafafu batareda tasani ba. Tsutsar dariyar datake ta tsagaita tafara magana cikin amon sauti tafara magana. "Yaku waɗannan halittu masu tsananin taurin kai yau kwananku yazo ƙarshe kushirya baƙuntar lahira." Jin wannan jawabi ba ƙaramin tada hankalinsu Kulu da Nas tuni jikin Nas ya fara rawa tsabar tashin hankali. Tamkar maciji haka tsutsar tasulalo tayo kan Kulu da Nas. Ihu suke suna naiman agajin abokan tafiyar su, amma ina suma ta kansu suke. Tsalle tayi tadira jikin Kulu, ƙara Kulu ta fasa tana"Nawan kataimaka mani kacire mani ita, kayi sauri wayyo nashiga ukku Nas kodai bakajin minike faɗa ne?." Nas cikin muryar da ta gama karaya yafara magana tsoro ya gama baibayeshi. "Aa Kulu na barki har abada kiyafe mani Allah yatsayar da mutuwarki ke kaɗai kinga tafiyata kiyafe mani, in ana doyayyah alahira muyi a chan." Ya ruga aguje yayi bayansu Rabson da suke ƙoƙarin guduwa bankesu yayi ya ƙwara kan Salma dana Rabson yayi gaba. Basuji zafin abinda Nas yayi masuba suka bi bayanshi. Biba kowace addu'a tazo bakinta furta ta take tana naiman kariyar ubangijinta. Kulu tariga ta yanke rai da tsira ta sadaƙar yau mutuwa zatayi. Ganin halinda Kulu take cikigasu Nas sun gudu, wani ƙarfin hali taji yazo mata lokaci ɗaya ta furta, "LA'ILAHA ILLAH ANTASUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIM, ya Allah ka kawo mana ɗauki, kafitar damu daga wannan bala'in ya Allah mundogara gareka ya Allah kakawo mana mafita." Tashi tayi tanufi inda Kulu take ga wannan tsutsa ta kanannaɗe ilahirin jikinta, wani ƙarfe tagani mai suffar wuƙa, ɗaukarshi tayi ta nufi inda Kulu take, shammatar tsutsar tayi ta luma mata wannan ƙarfen ajiki bakinta ɗauke da addu'a take ta saki Kulu ta ƙwala wata irin ƙara, take wurin ya6ule wani ruwa green mai kauri ya riƙa fita tamkar anbuɗe famfo, nan tagama bullayi ta mutu. Kamo hannun Kulu Biba tayi tana mata sannu, tashi tayi jikinta duk ya baci saboda faɗuwar da tayi, lura Kulu tayi daga ita sai Biba da ƙyar tabuɗe baki tana tambayar ina sauran abokan tafiyarsu. "Yanzu dai ki miƙe musamu mafita daga nan." Biba ta kamo hannunta. Wata kunya ce takama Kulu da ta tuna da rashin kunyar da ta yima Biba ɗazu amma yanzu gata itake taimakonta. Lallai duniya kakiyayi wulaƙanta mutum bakasan ranar da zai maka wata rana ba, ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane duk yadda ka ganshi. Abinda idanuwanta suka hasko mata ya kusa datse numfashinta na wucin gaɗi, jikinta kyarma ya ɗauka tamkar mazari, hannunta yana kyarma ta ɗagoshi tana nunama Biba abinda idanuwanta suka hasko mata. Ruwan jikin wannan tsotsane ya dunƙule ya rarraba kashi_kashi yana wata irin kumbura tamkar zai tashi sama, a hankali yake miƙewa tamkar yadda hayaƙi keyin sama yana miƙewa,wasu irin halittu masu suffar ƙwarangwal saidai su basukai tsayin ƙwarangwalba gasu da ƙaton kai yatsun hannuwansu kwara ukku rak!,idanuwansu jajur tamkar garwashin wuta jikinsu irin na ƙwarangwal sak. Misalta halindasu Biba suka shiga bai misaltuwa, ga halittun sun fara miƙewa,Biba hannun Kulu ta kamo suka bi bayansu Rabson aguje. Sunyi rasarar riskarsu Rabson, "ya kunkashe tsutsar?." Salma ta tambaya tana maida kallonta ga Biba. "Ta mutu amma kuduba bayanmu wani sabon bala'in ke tunkaro mu."ta ƙarashe maganar tana maida numfashi da ƙyar. Hayaniyar da sukajiyo tasasu juyawa ganin abinda ke faruwa, halittun ne sun nufo inda suke bakunansu buɗe. Ganin haka yasasu bin wata wangamemiyar ƙofa dasuka gani tabi tacikin kogon. Bawan Allah Rabson yana gudu wani dutse ya taɗe shi ya faɗi kasa warwas, da rarrafe yasamu yana bin bayansu Alkah yabashi sa'a yayun ƙura yamiƙe tare dayi bayansu, ga waɗannan halittu biye dasu bakunansu buɗe. *COMMENT*✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰 🤧🤧 _kwana biyu kunjini shiru, hakan ya farune sanadiyyar rashin lafiya danayi, masoya na haƙiƙa naga saƙonninku ina matuƙar godiya,Allah yabar zuminci_ ___________________________ _dan Allah ku sanya auntynah cikin addu'a, yau kwana Ukku tana labour Allah ya sauketa lafiya_ *PAGE 24_25* ..........A guje sukayo wurin Basma domin ceton rayuwarta. Sunyi iya ƙoƙarinsu wurin fiddo Basma a cikin ruwan amma abun yaci tura, saboda ruƙon da Mandiya tayi mata bana wasa ne. Ƙarfi suka haɗa suka fizgota daga cikin ruwan. Tare da Mandiya da ta yi mata mugun ruƙo suka fiddota. Ganin yadda Mandiya ta koma yasa sauran abokan tafiyar ja da baya in banda Jafar da yake naiman hanyar da zai taimaki Basma. Tamkar yunwataccen zaki haka Mandiya tayi wurgi da Basma tayo kan Jafar gadan_gadan. Da nufin cizonshi ta iso takamashi da kokawa sukayi ƙasa. "A'uzubillah! Subhanallah!!." Jafar ya furta ganin mace wadda ba muharramarshi ba ta ta6i jikinshi suna kokawa a ƙasa. Tunyana kare kanshi daga muggan hare_hare da take kawo mashi harya fara mai da mata martani. Su Jamcy ba kata6us tsaye suke sun haɗe wuri ɗaya ita da Tk suna surutan da ko su basu san mi suke faɗaba. Ƙoƙarin yakiceta Jafar yayi ya wurgar da ita can gefe. Abinda ya lura da waɗannan Horror ɗin basu taba mutuwa sai dai suyi doguwar suma inkayi nasarar luma masu wani makami ta bayansu. Dube_dube ya fara naiman inda suka yada itatuwanda suke kamun kifi da su. Can nesa da inda suke ya hango su. Da gudu ya nufi inda suke, yana gaf da ida isa yaji an warto ƙafarshi ba shiri yayi ƙasa. Ganin Mandiya na ƙoƙarin kawo mashi hari ta kowace hanya ya sanyashi kai mata harbi da ƙafafunshi cikin zuciyarshi yana karanto duk wata addu'a data zo mashi, yana ƙara ƙaimi wurin isa ga iccen da yake ƙoƙarin kaiwa. Yayi nasarar ɗauko icce inda yayi nasarar luma matashi a tsakiyar baya, wata firgitacciyar ƙara ta kwala ta faɗa cikin ruwan ta 6ace 6at. Wurin Basma dake kwance magashiyan dafe da wuyanta suka yo aguje. Jamcy ta yagi rigarta ta ɗaure mata raunin Jafar ya tofa mata addu'o'in suna mata sannu. Basu ɗauki lokaci ba Jamcy ta kamo Basma suka bar wurin saboda ganin abinda ya faru. (Ni nace Su Jamcy ina aka baro faɗan ko harkun sauko 😂🤣 Hanya mai haɗin zumuntar dole) Tafiya suke batare da sanin inda suke nufa ba. Ga wata ƙishirwa da ta addabesu kamar su zube. Wata inuwa suka samu domin su huta saboda zafin ranar da ake zubawa. Tunaninsu ɗaya shine imna zasu sami abinda zasu ci dazai Gusar masu ƙishin da suke ji. Ƙarar faɗuwar wani Abu sukaji a bayansu, Suna juyawa sukaga bishiyar kwakwa ce gasunan sun nuna manya sun Zubo ƙasa birjik. Kallon_kallo suke an rasa wazai je ya kwaso masu suci. Jafar ne yayi ƙarfin hali yayi addu'a ya duƙa ya fara tsinta yana tarawa. Sai da ya tsinto masu mai yawa ya fara fasawa sukayi Basmala suna shanye ruwan ciki. Sai da suka gama shanye ruwan sannan suka fara cin kwakwar. Sunci sun ƙoshi lokaci ɗaya sukaji wani irin bacci na ɗibarsu, kwanciya sukayi domin su huta Jafar yayi Basmala tare da kwanciya. Tunkafin baccin ya ida ɗaukarsu sukaji iska mai ƙarfi tana iso inda suke, kafin su ankara wata irin guguwa mai matuƙar ƙarfi ta kwashesu tayi sama dasu...... _____________________________ ...............Abinda suka gani shi yakusa sanadiyyar datsewar numfashinsu. Tsintar kansu sukayi a saman wani ƙaton tsauni wanda ƙasanshi ya kasance wasu irin itatuwane masu tsawo naban mamaki, itatuwan sune zaka kama ganyayensu masu tsananin faɗi da ƙauri da suka rufe saman tsaunin In kana da sa'a ka isa ƙasan tsanin da rayuwarka. Gashi duk iyakar hangensu sun duba amma basuga Wata hanyaba saidai wannan. Tafiya sukaji tamkar irinta ƙwaro in ya doso inda kake. Amatuƙar firgice suka juyo danganema idanunsu mike faru. Wasu irin ƙwarine masu kama da gizogizo. Idanunsu jajur tamkar garwashin wuta, ga jikinsu duk wani irin gashi abun kwanin ban bantsoro. Wani yawu suka haɗe atare ƙuutt!, Salma da Rabson tuni suka rungume juna suna salallami kamar basu bane suka gama gwabza faɗa ɗazu. Ƙwari gudu suke suna ƙoƙarin isowa wurinsu Biba, ganin haka ya sanya su Biba ja da baya har suka iso ƙarshen ramin, ganin basuda wata mafita lokaci ɗaya tamkar sun haɗa baku suduka suka daka tsalle sukayi ƙasan ramin. Ganin haka ƙwarin suka mara masu baya. Saman ganye ɗaya suka faɗa su dukan su suna rarraba ido da tsananin mamakin wannan wane irin ganyen bishiyane?. Basu ankara ba sukaji dirowar ƙwarin saman ganyen. Suna son miƙewa amma tsoron in suka tashi tsaye tabbas sil6in ganyen zai kayar dasu. Rabson da dai yaga bashakka in suka tsaya mutuwa zasuyi, wuf! Yayi ya miƙe "Ku miƙe muyi ta kanmu, bashakka in muka tsaya ƙwarin can zasu zuƙe jinin jikinmu abanza." "Kai kam bakada tunani arayuwar, yanzu in bayaga kanada tunani irin na bunsurunka ta ina zamu gudu bakaga ƙasa rami bane?." Salma ta ida maganar tana aikoma Rabson da kallon raini. "Hhh, sai shegen surutu kamar aku, ja'ira mai zubin muciya baki kamar na agwagwa, nan gabafa nine mijinki kuma Oga awurinki kisan irin maganar da zaki riƙa furta mani." Ya ƙarashe maganar yana dariyar mugunta dan yasan ya gama tunzura Salma. Ashar ta mulmula ta dura mashi tana Allah ya tsareta da auren faƙiri talaka irinshi. Biba da taga faɗan nasu bamai ƙarewa bane tsalle ta daka tayi ƙasan ramin. Bayanta suka bi suma, saman ganyayyaki suka riƙa faɗawa kafinsu ida isa saman wani ganyen sul6i ya kwashesu sunyi ƙasa, haka aka riƙa tilli_tilli dasu. Masu ihu nayi masu addu'a nayi. Rabson daya bugu kanshi ya fara juyawa idanunshi suka fara hango mashi mutane suna komawa bibbiyu. "Ƙalu innalillahi, la'ilaha'illallahu, shikenan namakance nalalace wayyoh busurulle wayyoh kaka uwata,Salma masoyiyi bibbiyu nike ganinku, lokacina yayi wayyon nazama makaho, yau Rabi'u nike ba Rabson ba namakance nadaina gani shikenan nayi Expired Salma ko auren mukayi saidai ki riƙa yimani jagora, inkuma namutu inkin koma gida kice ɗan busurulle Nabarma kakata ta yanka ta cinama ta ƙoshi, wayyoh nazama makaho." (🤣🤣🤣 Wuya ba daɗi, yaji wuya ya ɗauka makancewa yayi) Duk da har yanzu gwarasu ake sunayin ƙasa masifar dake cin Salma saida ta tanka. "Allah ya ida makantar da kai, bakinka yasari ɗanyen kashi, mai muguwar fata,kaga ɗan bunsunru can inka mutu." Bugata da akayi ta bugu da reshen wani icce ya sanyata yin shiru ta sume a take. Sai da aka kawosu ƙarshen ramin suka faɗo tim! Batare da sanin inda kansu yake ba. Wata guguwa mai masifar ƙarfi ta kwashesu tayi sararin samaniya dasu...... 🤧🤧 A haɗa da haƙuri Har yanzu kwance nike, ƙarfin hali yasa nai maku wannan. **COMMENT* ✅ *SHARE*✅ *_MEEN@RT...✍🏻_* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰 _____________________________ *PAGE 22_23* ..................Iskar lokaci ɗaya ta tsaya tamkar anyi ruwa an ɗauke. Ganin waɗannan halittu ba ƙaramin dugunzuma hankalinsu Basma yayiba. Jamcy da Basma tuni suka runƙunƙume juna jikinsu na mazari. Wata mahaukaciyar dariya suka fashe da ida, wadda ta haddasama dajin. Girgiza. "Kun ɗauka zaku iya guje mana ne,kunyi kuskure yanzu zaku girbi abinda kuka shuka ." Asuƙwane suka yo kan su Jafar tamkar yunwatattun zakunan da suka shekara basuci abunci ba. Muggan makaman dake hannuwansu Suka fara kaima su Jafar hari da su. Kowa kagani wurin takanshi yake yana ƙoƙarin ceton rayuwarshi. In suka kawoma mutum harida makaman hannunsu ya kauce ya samu wani icce take iccen yake darewa gida biyu, in ƙasa ce makamin yasama sai dai kaga wurin yayi rami. Basma da Jamcy wani Aljani yayo kansu da mugun nufi , sun riga sun sadakar yau kwanansu ya ƙare jira kaiwai suke ya iso garesu. Shurun da sukaji ta sanyasu buɗe idanunsu cikin kaɗuwa. Ganin Jafar sukayi tsaye riƙe da wani abu mai kama sa sanda gefenshi gawawwakin Aljanun nan yayi nasarar kashe wasu. Cikin kakkausar murya ya fara magana. "Yanzu ba lokacin tsoro bane, lokacine na tashi muyi fafutukar tseratar da rayukan mu ko mu mutu ko muyi rai, dan haka ku kasance masu ruƙo da addu'a domin ta tasa nayi nasarar kashe wasu daga cikin Aljanun nan dako taruwa mukayi bazamu iya yaƙarsu ba,amma saboda tasirin addu'a gashinan Ubangiji yasa nayi masarar kashesu, dan haka kumiƙe kuceci rayuwarku ko kuma kuyi asararta nan bada jimawaba." Yana ƙarashe maganar yayi wurin sauran Maridan bakinshi ɗauke da kabbara. Kafin Maridan su ankara Jafar yayi masu gagarumar 6annan domin dayayi kabbara yadaka tsalle ya kaima tsakiyar bayan Aljani bugu saidai kaga yayi kururuwa ya zube ƙasa matacce. Ganin irin illar da Jafar ke masu yasa mukayo kanshi da mugun nufin su raba kanshi da gangar jikinshi. Addu'a yaci gaba da kwararowa abakinshi yana mai dogaro ga ubangijin shi tare da naiman ɗaukinshi. Ƙarfin kabbarar da yake ta sanya Aljanun wasunsu yada makamai suna toshe kunnuwansu domin ji suke tamkar ana zuba masu ruwan tafasashshiyayar darma a kunnuwansu, ganin haka su Tk dake boye a mabanbantan wurare yin koyi dashi suna masu ɗaga murya tareda ƙwala kabbara. Damar da Jafar ya samu ga Aljanun ta sanyashi ƙara ƙaimi wurin ragargazar aljanun, cikin ikon Allah yayi nasarar ƙararda Aljanun wasu kuma suka 6ace. Iya jigatuwa Jafar ya jigata ga wata yanka da wani Aljani ya shammaceshi yayi mashi a hannu, yana gama faɗan ya yanke jiki ya faɗi. Tk ganin Jafar ya ƙarar da Aljanun ya sanyashi fitowa suka yo kan Jafar. Duk iya ƙoƙarin su akan jafar da wani taimako da zasu bashi sunyi, ga hannunshi dake zubda jini, Tk rigarshi ya yaga ya ɗaurema Jafar hannu yayi nasarar tsaida jinin, sunyi duk abubuwan da suka san anayi ma wanda ya suma domin ya tashi amma abin yaci tura domin ba alamun zai tashi. Sunyi jigum_jigum suna tunanin halinda zasu shiga indai da gaske Jafar mutuwa yayi to bashakka kashinsu ya bushe a tafiyar nan. Sunan nan zaune jikinsu ya gama mutuwa, zuciyoyinsu sun sadaƙar lallai Jafar bazai tashiba, ga duhun magriba daya farayi wurin ya ɗauki wani irin sanyi mai shiga ƙashi. Hannunshi dake ɗaure yafara motsawa a hankali yana ƙoƙarin buɗe idanunshi bakinshi ɗauke da addu'a. Ganin haka yasa su Tk sukayo kanshi zuciyoyinsu cike da wani irin farin ciki marar misaltuwa. Kamashi Tk yayi ya ida miƙewa zaune. Sannu suke ta keta kwararo mashi yana binsu da yawwa. Sai da Jafar ya ida dawowa cikin hankalinshi sannan ya umarcesu dasu tashi suci gaba da tafiya, domin zama bai gansu ba. Tafiya suke ga duhu daya yayi tsayawa sukayi sukai taimama suka gabatar da sallolin da aka biyo su. Ƙara nausawa sukayi cikin jejin duk da yunwar da ta addabesu ga matsanancin sanyin da ake zubawa hakan bai hanasu cigaba da tafiyaba. Yada zango sukayi saboda baccin daya rinjayi idanuwansu. Wurine mai yalwar ciyayi ko ina ka wurga idonka lullube yake da ciyawa tamkar cikin yanayin damuna. Kwantawa sujayi Jafar ya umarci kowanensu da yayi addu'ar kwanciya bacci kafin ya kwanta. Bayan kwanciyarsu Jafar ya warware hannunshi domin ganin yadda raunin ya koma. Abunda ya tada mashi hankali kuma ya bashi mamaki bai wuce ganin yayi wani irin rami tamkar an yanke fatar wurin, addu'o'i yacigaba da kwararowa yana tofama raunin domin yasan babu abinda ya gagari Allah. Kowa yayi bacci wurin in banda Jafar da sai da yatofe jikinshi da addu'a ya kuma tofe inda suke kwance ya kakka6e inda zai kwanta ya kwanta bakinshi ɗauke da Basmala. Wurin yayi tsi! Bakajin motsin komi sai munsharin da Tk ke yi kamar wani bujimin sa. A hankali wata irin iska mai kaɗawa cikin natsuwa ta gauraye wurin, ciyawar dake ƙasan wurin a hankali ta fara kaɗawa rana motsawa, Bayyana sukayi cikin muguwar suffar mai tsananin ban tsoro. Rashin sani yafi dare duhu, domin dasu Jafar sun san inda suk kawo kawunansu da tuni tun bar wurin. Tsaye suke jikinsu baida maraba da jikin Fatalwa, gasu wasu irin dogaye fuskarnan tasu ba kyangani idanunsu guda ukku jere reras basuda hanci sai wani irin bakuna tanan suke shaƙar iska, fuskar su cike take da gashinda yayi nasarar lullu6e ilahirin fuskar,ga jikinsu sanye da wasu fararen kaya da jini yayi nasarar mai dasu jajaye. Cikin tsananin 6acin rai macen takawo hannu da nufin ta ɗauko Jafar ta tsotse jininshi, sai dai mi, hannun na ida isa inda Jafar ke kwance taji wani irin zafi Kamar ta sanya hannunta cikin Wuta, bashiri tayo baya tana mai yarfa hannunta da fatar wurin ta dare jini Ya fara zuba. Ganin abinda ya samu matar ya Sanya mijin zura hannuwanshi biyu da nufin ya tattaro su Jafar su duka ya hallakasu. Abinda yaji yasanyashi ja da baya ga hannuwanshi dasuka fara ƙonewa. Yaja matarshi suna mamakin abinda ya yi masu shamaki da kashe waɗan nan halittu, bacewa sukayi zuciyoyinsu cike da ƙudirin ɗaukar fansa. Kamar cikim bacci Jafar yaji hayaniya amma yana buɗe idonshi yaga babu kowa. Addu'a ya ƙarayi tare da komawa ya kwanta. Sanyin asubar daya ratsasu shine yayi nasarar farkawarsu daga bacci,buɗe raunin hannunshi Jafar yayi, abun msmaki raunin nan ya warke tamkar bai ta6ajin ciwoba wurin, taimama sukayi suka kabbara sallah bayan sun gama suka zauna suna tunanin inda zasu samu abinda zasu sama bakinsu. Gari na ida yin haske suka tafi naiman abinda zasuci. Ƙoramace mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kana hango yadda kifaye ke wasansu saboda ruwan ba zurfi. Shawara suka yanke sukama kifayen su gasa su ci. Jafar da Tk su suka shi suka samu wasu dogayen tsinkunan icce suka riƙa chako kifayen dashi. Basma da Jamcy suna daga wajen ruwan suna kallonsu, Basma jitayi kamar ankira sunanta waigawa tayi tareda hango wasu kyawawan kifaye sunata iyo nesa kaɗan da inda su Jafar suke kama kifayen. Zuciyarta kwadaituwa tayi data matsa taganema idanunta waɗannan kifaye, duƙawar da zatayi domin ta kamo kifin Taji an fizgi wuyanta anyi Cikin ruwan da ita, ƙarar faɗuwar ta tajawo hankakinsu Jafar suka nufo inda take aguje, abinda suka gani ne yasanya numfashinsu yakusa ɗaukewa na wucin gadi, Mandiya suka gani kamanninta sun koma na horror, ƙarar dasukaji Basma ta ƙwala ce ta dawo dasu cikin hankalinsu, Mandiya suka gani ta kasama Basma haƙora awuya jini yafara malala, wata wahalallar ƙara Basma ta Ƙwala...................... ______________________________ Gudun ceton rai su Rabson suke tamkar zasu tashi sama ga waɗannan halittu Dasun Juya sai suka sun kusa cimmasu. Abinda basu saniba halittun nan kamar fara haka suke Tashi sama. Basu ankaraba sai gani sukayi halittun nan sun dira gabansu, ja sukayi suka tsaya kafin su ankara halittunnan sun lullu6esu tamkar yadda fara ke lullu6e ganye. Biba gani tayi halittun nan da ƙarfi taɗaga murya tana ƙwararo addu'a tana kai masu naushi da hannuwanta, duk wadda ta kaima bugu saida kaga tafaɗi ƙasa ƙasusuwanta sun karairaye. Rabson dayaga biyu sunyo kanshi gudu yafara kafin ya ankara sun wawuro ƙafafunshi, ganin sun buɗe baki sunyo kanshi ya fara ihu yana karanto duk addu'ar da tazo bakinshi "Innalillahi, la'ilaha illallahu, inna ansarnahu, amanarrasulu, wayyo kaka ɗan bunsurulle, wayyo Salma masoyiya ku kawo mani ɗauki." Haka yaita ihu, ganin babu mai cetonshi yafara gano mutuwa ido buɗe yasa ya dage iyakar ƙarfinshi yana kaima halittun harbi da ƙafafunshi. Kulu da Nas wuri ɗaya suka haɗe Nas ganin halittun sun nufoshi Ya koma bayan Kulu yana. "Kulu ki taimaka mani wayyoh Allah innalillahi nashiga ukku, Kulu kin cuceni da kikasa mukayi wannan Baƙar tafiyar." Yaƙarashe maganar yana ƙara shigewa jikon Kulu. Ganin addu'ar da Biba tayi Allah ya kawo mata mafita, ta ɗaga murya tana mai umarta su Rabso dasuyi koyi da ita. Sunjigatu sun matuƙar jin jiki kafin suyi nasarar gamawa da halittun. Fuskar kowa tasha karta duk sawune jiki in banda Biba. Bayan sun sun dawo cikin hankalinsu Rabson yayi ƙarfin halin miƙewa. "Kun lura kuwa har yanzu muna cikin kogon nan? Kamata yayi mubar kogon nan nidai bazan tsaya in mutu a banza ba." Ya ida maganar yana dudduba inda Salma ta shige. Chan ya hangota ta tayi ɗai ɗaya a ƙasa tana maida numfashi. "Hhh, Salma masoyiya kece kika zama haka?, kinga yadda kikayi buɗu_buɗu, wayyo masoyiya miya karceki a fuska taimaka kitashi muƙarasa fita." Ya ƙarashe maganar yana yimata dariyar mugunta. "Allah ya isa inka ƙara kirana Masoyiyarka, mugu mai suffar mutanen 6oye." Taƙarashe maganar tana ƙoƙarin miƙewa. Baikulata ba dariyarshi yacigaba dayi. Kulu kallon Nas tayi tare da jan dogon tsoki. "An daiji kunya, kabani mamaki lusarin banza kawai wanda mace ma tafishi jarunta." Ta kuma jan wani tsokin. "Am..uhm..kingane Kululu wallahi kawai kinsan ni ina tsoron ƙwarangwal, amma kin gane kibari a karo nagaba zani baki mamaki, haba my sweet Kululunah." Ya ƙarashe maganar da daɗin baki. "Allah dai yasa da gaske kake." Tafaɗa tana yamutsa fuska domin yau Nas ya matuƙar bata haushi. Sun yi yawo cikin kogon harsun gaji basu samu hanya ba. Har sun haƙura da fita daga kogon sai suka hango wata ƴar hanya ƙarama wadda mutum ɗaya zai iyabi ya wuce, haka suka riƙa fita da ɗai ɗaya. Ganin sun fita kogon wani irin farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu. Abinda idanuwansu suka hango masu ne yasasu ja da baya cikin matsanancin tashin hankali da kuma tsoro........... *COMMENT*✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰 ______________________________ *PAGE 26_27* ..............Ahankali iskar da ta kwasosu ta fara lafawa. Tare da 6acewa 6at! Tamkar bata ta6a wanzuwa ba. Hannu Jafarne ya fara motsi, idanunshi suna ƙoƙarin budewa, samun kanshi yayi da furta, " _ALHAMDULILLAHILLAZI AHYANA BA'ADA MA AMATANA, WA ILAIHINNUSHUR_" Kanshi daya ji yana barazanar tarwatsewa ya dafe yana Ambaton " _INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJIUN, ALLAHUMMA AJIRNI FIYMUSIBATI WA'AKLIFINI KHAIRAN MINHA_ Ya ubangiji ka kawo mana ɗauki akafitar damu daga wannan musiba." Dubanshi yakai inda su Basma ke kwance basu san mike faruwaba. Abinda idanuwanshi suka hasko mashi ya sanyashi idan miƙewa daga kwanciyar da yake yayi saurin zaunawa, hannuwanshi yakai kusa da idanunshi ya murza idanun yaga kodai gizone suke mashi. Ƙara tabbatar wa yayi ta hanyar tsinkulin kanshi yaji kodai mafarki yake, da gaskene su Rabson ne ba gizo idanuwanshi keyi mashi ba. Wani farin ciki marar misaltuwa ya wanzu azuciyarshi baisan lokacinda ya kalli alƙibla yayi sujadar godiya ga Allah daya bayyanar masu da abokan tafiyarsu. Motsin dayaji ne ya sanyashi saurin juyawa. Su Basma, Jamcy da Tk ne yaga sun farka lokaci ɗaya suna dafe kansu dake masu tsananin ciwo. Rabson ne yafara harba ƙafarshi saman wuyan Salma, ita ma motsi ta fara alamun zata farka Kulu da Nas suma farkawa sukayi. Rabson waige_waige yafara kamar yana naiman wani abu, su Jafar daya hango yasashi fara ja da baya yana salallami. " _INNAHUMIN SULAIMANU, LA'ILAHA ILLALLAHU_, ku kuke ganinmu bamu muke ganinkuba,wayyo namutu na lalace, shikenan gasunan sunzo mana da suffar abokan tafiyarmu, wayyoh Salma masoyiya kina ina."? Ya ƙarashe maganar yana janƙugu yana baya_baya. "Hhh! Kai Rabi'u Rabson ɗin Kaka, munefa da gaske ba horror bane." Jafar ya ida maganar yana dariya. "Mtssw! Sauna kawai, kabi ka cika ma mutane kunne ko ina kaga horrorn."? Salma ta faɗa tana hararar Rabson. Wiƙi_wiƙi Jafar yayi yana rarraba ido. Gaisawa sukayi ta yaushe rabo, bayan sun gama shan hira da taya juna jimamin rashin fitarsu wannan baƙin daji. Shawara suka yanke ta yanzu bazasu ƙara tafiyaba gudu zasuci gaba dayi sallah da abinci kaɗai zai tsaidasu. Matsawa sukayi wurin wani iccen gwaba suka tsinka, Jafar ne yafara rarrabama masu. Salma gani tayi Jafar bai kawo kantaba, miƙewa tayi a fusace ta bangaje Jafar gwabar ta 6are ƙasa, taga_taga Jafar yayi zai faɗi ya tsaya, wani icce ya kama ya riƙe yana mamakin halin irin na Salma. Salma gwaibar ta hau tsinta tana tattarawa, tatss! Kake ji Biba ta ɗauke Salma da wani irin gigitaccen mari. "Tabbas rashin tarbiyya da rashin sanin darajar ɗan adam babban ciwo ne, ke yanzu in banda bakida wayo wanda yakasance shine jigon tafiyarmu shikike bangajewa?, ke kowa baki ɗaukarshi da mutumci kin raina kowa, sakara wadda batasan indake mata ciwo ba." Zafin marin da Biba taima Salma ya sanya ta zunduma mata duk wani irin zagin dayazo bakinta tana faɗar in suka koma gida saitasa anɗaure Jafar da Biba. Haukan da Rabson yaga Salma nayi yasanyashi fashewa da dariya tareda tashi ya kamo hannunta. "Haba Sweet Salma ta Rabson na Kaka da Busurulle!, miye nasa ke bakida hankali da kuma wayo, ya kamata fa kisan yanzu tare kike da mijinki, kisan abinda zaki faɗama mutane kowa da kika gani yanada rana fa." Ya ida maganar yana dariya. "Ba'a sani, inka ƙara kirana da matarka saina samu dutse na rotsa maka kai dashi, mtssw aikin banza kawai." Ta ƙarashe maganar tanajan dogon tsoki. Kowa banza yayi da ita suka haushan gwaibar su. Biba dasun haɗa ido da Jafar saisu sakarma juna zazzafan murmushi ta sadda kai ƙasa. "Abokai kamar yadda na faɗa maku yanzu bazamu sake tafiyaba, gudu kawai zamu riƙayi daga sallah sai cin abinci zamu riƙa tsayawa." Oga Rabson wandonshi inna tayani cirewa ya nannaɗe suka fara gudu ba kama hannun yaro. Gudu suke irin gudun da ake kira gudun yada ƙanin wani, yunwar cikinsu ita ta tsaida gudun da suke, tsayawa sukai suna maida numfashi. "Wayyoh Momy, Daddy ina bataliyar sojojin da nike mafarkin ka turo afiddani adajin nan."? "Hhh! Shegiya ƙarya, ko gidan wane baban ne zakiga wata bataliyar sojoji, nabi bataliya da gudu, bataliyo." Ya tuntsure da dariya. Jikin Basma a hankali yake komawa green da baƙi tana canza kala. Nan suka tsaya suna hutawa. Motsi sukaji alamun tafiyar mutane Nufo inda suke. Zumbur suka miƙe tare da cibrewa wuri ɗaya suna jiran bayyanar abinda ke tunkarosu. Abinda majigin idanuwansu suka hasko masu yasa su ƙara dunƙulewa wuri ɗaya. Garba kisa, Nura shila, Audu gwarama da Mandiyane suka nufosu da wasu irin wuƙaƙe a hannunsu. Cikin Salma wani irin sauti yabada ƙuu. Ganin wannan bala'i yasanya su Jafar da Biba fara ƙwararo addu'a. Wani wawan tsalle sukayi tare da rabuwa suka yimasu Rabson ƙawanya. Harshe suka riƙa fiddowa tare dayin wata kuwwa marar daɗin saurare. Tuni Rabson ya maƙalƙale jikin Jafar ya fara kuka yana sabbatu. Tsawar da Jafar ya Ƙwatsama Rabson ya ɗora da faɗar; "Yanzu lokacin yaƙine domin a ceci rayuwa, tabbas yanzu lokacine da kowa zaiyi takanshi kuma zaiyi ƙoƙarin ceton rayuwarshi domin in Allah ya ƙaddara musamu ko mutum ɗayane ya kai labari." Bashakka jin wannan maganar jikinsu yayi sanyi sun sadaƙar zasuyi faɗa su mutu ko suyi rai. Garba Jafar ya warto da nufin ya luma mashi wuƙar hannunshi, kokawa suka hauyi da Jafar bakinshi ɗauke da addu'a. Nura Rabson ya jawo, Rabson naganin haka ya jawo ƙafar Salma suka tai tare. Rabson baisan yanada ƙarfi ba sai yau dayaga mutuwa tsirara, yaga ya dage yana kaima Nura naushi ta kowane 6angare. Kulu da Nas tare Audu ya fizgosu, Kulu itace mai ƙoƙarin ceton rayuwarta tasa ƙafa tana kaima Audu duka ta ko ina. Su Jamcy da Tk su biyun sun bada himma suna zabga kabbara suna ƙoƙarin ceton rayuwarsu. Bashakka wannan yaƙin na ceton rayuwa yazo da abun mamaki, domin duk da su Garba sunjima kowa ciwo da makaman hannunsu amma haka suka dage. Wata ƙaƙƙarfar guguwa dasu Rabson sukaji ita ta sanyasu zubewa ƙasa, mahaukaciyar ƙara Rabson ya ƙwala ya dafe hannunshi da Garba yayi sanadiyyar gutulema Rabson ƙaramin yatsan hannunshi. "Nashiga ukku sun maidani gundul sun guntule mani yatsa, wayyoh Kaka wayyo Salma masoyiya, Wayyoh ni Rabi'u nakoma Rabson gundul na busurulle." Wannan guguwar ta kwashe su Garba kisa tayi sama dasu....... *COMMENT*✅ *SHARE* ✅ *_MEEN@RT...✍🏻_* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗 _____________________ *PAGE 28_29* ................Kuka take tamkar ranta zai fita, ga wani gumi daya wanke mata fuska duk sanyin da ke gauraye ɗakin. "Wallahi ko ki fiddoman ɗiyata ko kuma kiyi ta bakin aurenki, kinji na faɗa maki, ace yau tsawon wata hudu kenan kinturata biki ashe bama bikin danginku bane can biƙin ƙawar dana hanata zuwane, tsabar kin ɗaukeni banda mutumci a wurinki shine kikayi mani ƙarya,to kinji na rantse maki indai ɗiyara ta ƙara kwana goma bata dawoba kema saidai kitafi gidanku."Alhaji Abdallah Ya ƙarashe maganar yayi waje ranshi a matuƙar 6ace. Cikin muryar daga jinta kasan tasha kuka harta gaji, ga idanunta da suka kumbura saboda kukan da ta sha ta fara magana; "Yau ni Zaliha nashiga ukku, watan tonen asirina ya kama, nibama sakin da Alhaji zai mani ke damuna ba face muggan mafarkan danike da Salma, ya Allah nagane kuskurena Allah ka maido mani ɗiyata gida lafiya." Kukan dayaci ƙarfinta ne yayi sanadin haɗiye sauran maganar. _________________________ "Habib wai bazaka cire damuwar yarinyar nan aranka bako?, yau wata huɗu da tafiyar ba ba bamo ba labari ga Ɗanka kanata fama dashi,sai wani ciwo ya sameka ita batama san kanayiba tana can wurin biki, to munyanke shawara da kawunka ga Hanan nan da aurenta ya mutu ƴar ƙanwata, yarinya mai hankali da natsuwa, gata yarinyace ko haihuwar fari batayiba,tunda ta gama idda ranar Juma'ar nan za'a ɗaura maku aure ranar zata tare tunda komi nata yana nan, Allah yasa wannan za6in danayi maka yazame maka Alkhairi arayuwarka." Tunda ta fara maganar kanshike sunkuye aƙasa cikin girmamawa da yin na'am da za6in da Hajiyarsu tayi mashi yace; "Amin Hajiya, insha Allah nimai biyayyane a gareki, bazakiyi kuka daniba." "Nagode Habib, Allah yayi maka albarka, Allah ya shirya maka zuri'a." "Amin Hajiya." Yaune jama'a da dama suka shaida ɗaurin auren HABIB BELLO da amaryarshi HANAN HANIF, ɗaurin aurene daya samu halattar manyan ƴan kasuwa da ma'aikatan gamnati harma da ƴan siyasa ta 6angaren abokan Alhaji Bello mahaifin habib da kuma shi kanshi Habib ɗin. Ƙarfe huɗu dai_dai aka ɗauki amarya zuwa gidan mijinta. Zama suke irin wanda inka gani saiya birgeka, Hanan wayayyar yarinyace mai ilimin addini dana boko, shiyasa bata sha wahalaba ta sace zuciyar Habib tasamu babban gurbi azuciyarshi ta zauna daram, ga Walid da take kula dashi ta maidashi tamkar ɗan da tahaifa acikinta, shiyasa Habib ke ƙara ƙaunarta. Allah sarki Habib duk auren dayayi bai manta da Basma ba, kullum cikin yimata addu'a yake, saboda muggan mafarkar da ye da ita, yana mata fatan tadawo dumin har yanzu akwai ƴar sauran soyayyarta kaɗan azuciyarshi. (🤣😂 Basma ana can cikin daji ana gantalewa, Habib yayi sabon aure yana nan ysna soyewa, kina can kina shirin zama horror.) ___________________________________ Uban tagumin da ta yi hannu bibbiyu ta lula duniyar tunanin Rabi'un ta jikanta ɗaya ƙwali daya rage mata, da yau har tsawon wata Huɗu bai dawoba shiru kamar Malam yaci shirwa, abinda yafi ɗaga mata hankali shine munanan mafarkan datake tana ganinshi cikin mawuyacin hali. Kukan da Busurulle ya fasa da ƙarfine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula. "Kai nikam nagaji dakai wannan bunsuru, ga abincinka yau ya ida ƙarewa, yanzu nike tashi in kai ka wurin tsalha sarkin fawa in saida in raba ƙuɗin biyu in sawo kyan abinci sauran kuma in ajema ɗan kaka inyadawo." Ta miƙe ta zari mayafi ta kwance bunsuru tajashi tayi waje. Tsalha sayen wulaƙanci yayima bunsurun, wai yunwa ta kamashi ya saya dubu ukku. "Kai tsalha kaji tsoron Allah, wannan Bunsurun alalace ai zaiyi dubu goma." Ta ƙarashe maganar tana kamo iggiyar ƙafar Bunsurun. "Iyakar yadda na saya kenan hajiya, nifa bama zani sayi Bunsurun nan ba, saboda jikanki ko kin saidashi inya dawo nasan nizaima wulaƙanci in biyashi." "Kai arr! Shiyasa kai mashi tayin wulaƙanci?, to nima nafasa saidawa." Taja Busurulle ta mai da gida ta ɗaure tana mai addu'ar Allah ya mai do mata Rabi'unta gida lafiya. __________________________ "Umma wai yaushe Aunty Biba zata dawo."? Ƙanwar Biba ta jefoma Ummansu tambayar. Tagumin da ta zuba da hannu biyu ta cire tana mai kallon Siyama. "Siyama ku taya Habiba da addu'a, insha Allah jikina yana bani tabbas Habiba nacikin mawuyacin hali, duba ga muggan Mafarkan da nike da ita, insha Allah darajar addu'ar danike mata zata dawo gidannan." "Umma ki kwantar da hankalinki insha Allah aunty zata dawo ta samemu cikin ƙoshin lafiya." "Amin siyama, Allah ya maidota lafiya." Alwallah sukayi tareda kabbara sallah suna masu kai ma Allah kukansu, domin Allah gafurun rahimunne. ________________________________________ Giɗan yayi tsit, Umma da Hanifa kowa da abinda yake saƙawa cikin zuciyarshi. "Ni ko Umma ƙwanan nan sai inta ganin Yaya Jafar cikin mawuyacin hali cikin wani baƙin jeji." Jin wannan maganar ya sanya jikinta ya ƙarayin sanyi, cikin ƙarfin hali da nuna mafarki ba duka ne gaskiyaba ta fara kwantarma Hanifa da hankali. "Marfarki ba duka ne gaskiya ba kinji Hanifa, Yayanki yana nan dawowa kiriƙa yimashi addu'a inkinyi sallah , yana nan dawowa insha Allah." "To Umma Allah ya maidoshi lafiya, amma Umma mike danmunki kwanan nan sai inta ganinki cikin damuwa."? Duk yadda take ƙoƙarin 6oye damuwarta amma tasan fuskarta ke fallasa sirrin zuciyarta har agano halinda take ciki game da mafarkan da take da Jafar. "Lafiyata lau Hanifa, wani lokaci ina fama da zazza6i shiyasa kike gani na haka, amma nasha magani, yanzu tashi kiyi shirin islamiyya lokaci yayi kadaki makara." "To Ummu." Ta miƙe tahau shirin tafiya makaranta. Wasu guntayen hawaye Ummu ta sharce tare da addu'ar Allah ya maido mata ɗanta gida lafiya. ____________________________________ Zaune suke Saman kujerun Alfarmar da suka zagaye tsakiyar falon. Kallo ɗaya zakayi masu kasan hutu ya zauna ajikinsu. Hajiya kubra momyn jamcy dogon tsoki taja tare da kaɗa kanta ta fara magana cikin takaici; "Wato idan Jamcy ta dawo gidannan ta iskeni saina karya mata ƙafar gaba data baya, shegun ƙafafu kamar na Zal6e, yau wata Huɗe kenan sun faki idanunmu sun tafi ganin ƙwam." Hajiya Hafsa mahaifiyar Kulu ita ta amshe zance; "Ke kike faɗi anaji, wato ni idan Kulu ta dawo innayi mata Wata zauna sai ƙasusuwanta sunkarairaye, kaga yarinya ta sani cikin masifa mahaifinta gani yake kamar nice na sanyata ta tafi Baƙin dajin nan ganin ƙwam." "Ai ni narasa yadda zaniyi da Daddyn Nas, kullum cikin tada mani hankali yake yana tunanin dasa hannunna nasani Nas yabar gida, ai yadda Nas ya tada mani hankali in Allah ya maidoshi saina gwara kanshi da bango ko naji sauƙin abinda nikeji azuciyata." Hajiya asabe Mahafiyar Nas ta ƙarashe maganar tana huci. "Ai ni dangin Mahaifin Tk gani suke kamar dan Mahaifinshi ya rasu shiyasa nabarshi sakaka harya tafi dajin nan, wallahi sun sakoni gaba niduk nafiku shiga matsala." Ranar haka suka wuni suna jimamin halinda ƴa'ƴansu suka jefasu ciki, yamma nayi kowacce ta nufi gidanta cike da jimamin halinda suke ciki. _____________________________________ Ihu Rabson keyi iyakar ƙarfinshi ga hannunshi nata zubar da jini. Ganin halinda yake ciki yasa Jafar rugowa yana duba yatsan, ashe duk ihun da yake yatsan yankarshi kawai akayi ba gundulewa yayi ba. Tsoki Jafar yayi ganin asheba datse yatsan akayiba tsabar rikicewa sai cewa yake yatsanshi ya gundule. "Kanatsu Rabson, yatsanka ba gundulewa yayi ba yankarshi akayi." Ihun da yake ya tsaida; "Da gaske kake Jafar yatsana nan."? Ya jefoma Jafar tambayar yana mai kallonshi. "Eh yana nan." Ya faɗa a taƙaice. "Alhamdulillah, Allah nagode maka ashe banida rabon zama Rabson gundul, Allah na godemaka." Biba kallabinta ta kwace ta yaga aka ɗaurema Rabson Hannu. Zaune sukayi sunyi jigum_jigum ga yunwa ga ƙishirwa da suka addabesu. 6angare ɗaya kuma ga jikin Basma nata ƙara rikiɗewa. "ALHAMDULILLAH." Jafar ya furta fuskarshi ɗauke da murmushi. Kallinshi sukayi cikeda son jin abinda ke faruwa suka furta, "Jafar miya faru."? *COMMENT*✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗 ____________________________ *PAGE 30_31* ........... "insha Allahu matsalarmu tazo ƙarshe da izinin Allah." Jafar ya faɗa yana fuskantarsu Rabson. Cikin zaƙuwa suka fara tambayarshi ta yaya matsalarsu tazo ƙarshe?. "Haƙiƙa Alƙur'ani cikinshi akwai waraka, ubangiji ya sanya na tuno da wani malami na daya koyar damu yadda ake karya sihiri da wasu daga cikin ayoyin Alƙur'ani mai girma, domin wannan annobar ta zama Horror da wasun mu suka yi sihirine, kuma da izinin Allah zamu karyashi, dan haka yanzu wasu daga cikinmu zasu tafi naiman ganyen magarya wasu kuma su tafi naiman ruwan da zamuyi amfani dashi, dan haka yanzu Rabson da Salma ku zaku naimo mana ganyan magarya guda bakwai." Rabson wata irin miƙewa yayi jin ance su biyu zasu tafi. "Kwarankwatsi dubu babu inda zani, yoce maku akayi Kakata bata sona zaku turamu mu biyu aradu babu inda zani, haka kawai so kuke inje acinyeni shikenan Bunsurulle ya zama maraya." Ya ƙarashe maganar yana zare idanu kamar ankama 6era a buta. "Kai dai kam anyi ragon maza lusari marar amfani, to nida Tk zamu tafi tare daku munzama muhuɗu ko." Jamcy ta ƙarashe maganar tana hararar Rabson. "To masha Allahu, yanzu cikinku wayasan yadda ganyar magaryar yake."? Jafar ya jefo masu tambayar yana mai ƙare masu kallo. "Ni nasani saboda nata6ayin projet akanshi." Tk ya faɗa yana hura hanci. "Ku tabbata kunyi addu'a kafin kubar wurin nan." Jafar ya faɗa cikin taushin murya. Su duka kowa yayi addu'a musamman Rabson a bayyane ya ƙwararo abunshi, Salma ko bata ce uffan ba tana hura hanci tana taka ƙasa da ƙyar haka suka nausa cikin jejin naimo ganyan magarya. Sunyi tafiya harsun gaji amma basu samu koda itaciyar da zusu tsuguna susha inuwa ba bare kuma ta ganyen magarya. "Wash!." Rabson yafada yana riƙe ƙugu kamar zaiyi kuka. "Ka taka ƙafa muyi gaba yanzu ba lokacin lalaci bane, in kuma kasake muyi gaba mubarka." Salma ta ƙarashe maganar tana aikama Rabson kallon banza. Murmushi Rabson yayi, "to masoyiya Matar Rabson mu tafi." Daddagewa tayi ta danna mashi wata gagarumar ashar taɗora da faɗar "In ka sake kirana matar ka tsaf zani biyemaka mu dambata a wurin nan, maye sai naci saikace talauci Mtssw." Fashewa da dariya yayi "in kina tunkuɗo bakin nan sai yayi yanayi da in tsohuwa zata kira tukurr." Ya ƙarashe maganar yana kwaikwayar ta. "Kutt! Amma gayen nan nikake zagi ka kira sunana kana iya shege, yanzu ko zani tumurmusaka ka gane shayi ruwa ne." Tk yayo kan Rabson gadan_gadan. Ruƙoshi Jamcy tayi cikin matuƙar 6acin rai ta fara magana; "Yanzu naiman abinda muka fito kenan?, kun rinca6e da faɗa, so kuke ayita yimana dauki ɗai_ɗai saboda mugun hali irin namu muntsaya faɗa amaimakon naimo abinda aka aikemu naimowa." Kowa tsit yayi suka ƙara gaba naiman abunda suka fito. Sun ƙara tafiya mai nisan gaske sannan suka iso inda ya kasance ga ganyayen magarya birjik aƙasa. Hamdala sukayi wani irin farinciki ya ziyarci zuciyoyinsu. Tsugunawa Tk yayi ya tsinci guda bakwai. Yajuyo yace masu suyi gaba su koma wurinsu Jafar kawai. Ihun da Salma ta ƙalla ne yayi sanadiyyar janyo hankalinsu, abinda suka gani ne yayi sanadiyyar daskarewarsu suka kasa koda ƙwaƙwƙwaran motsi. Mandiyace tsaye cikin mummunar kama, jikinta yayi kacha_kacha da jini, tazarar dake tsakaninsu da Salma batafi taku biyu ba tsakaninsu. Kafin Salma ta ankara tuni Mandiya tayi wawan tsalle ta dira gabanta, wuyanta ta raruma sukayi ƙasa atare. Zafi gami da azabar cizon da Mandiya tayima Salma a wuya yasanyata fasa wata mahaukaciyar kuwwa. Wannan mummunan gani da Rabson yayi yasanya shi sakin wani zazzafan fitsari yana kuka yana kiran "Salma masoyiya shikenan bakida rabon ganin bunsurulle, naci gurin yanka maki shi in munyi aure muci amarci dashi." Ganin surutan bazasu fishsheshi ba yasanya shi runtse ido ya ɗauki wani reshen iccen magarya daya karye ya faɗo. Mandiya da ta riƙe da wuyan Salma jini nata tsiyaya. Shammatar Mandiya yayi ya buga mata iccen a tsakiyar baya, sakin wuyan Salmatayi tare da fasa wata firgitacciyar kuwwa. Ganin haka yasa Rabson fizgo hannun Salma data galabaita ga jini na ɗibarta, ganin haka yasa su Jamcy maramasu Rabson baya sukaci gaba da gudu. Gudu suke na ceton rayuwa ga Rabson guy riƙe da hannun Salma. Da ƙyar da ji6in goshi suka isa inda su Jafar suke, suna isa Salma ta zube ƙasa tana maida wahalallen numfashi kamar ranta zaifita. Ganin irin jinin da Salma ke zubdawa yasa Biba cire kingin gutsuren ɗan ƙwalinta ta ɗaurema Salma wuyan. Ganin taimakon da Biba tayima Salma ya sanya Salma jin wasu hawaye sun wanke mata fuska, yanzu gashi mutanen data gama wulaƙantawa hartana iƙirarin inta koma gida saitasa an ɗauresu, yau sune ke taimakonta, lallai duniya kabita sannu ba matabbata bace. Jitayi wuyanta kamar ana hura mata wuta ansa wuƙa ana daddaka mata a wuya. Jin wannan sabuwar azaba ya sanya ta fasa wata ƙata tareda faɗuwa ƙasa tana harbe_ harbe. Sunyi matuƙar mamakin baƙon yanayin dake shirin samunsu, sudai iya saninsu sunsa ko harror yacijeka baka abinda Salma keyi. Babban abinda ya ƙara tayar da hankalinsu bai wuce ganin cikin lokaci ƙanƙani jikin Salma yafara komawa green wasu jijiyoyi naƙara bayyana. Ganin haka yasa Jafar umartar matan dasu danne mashi Salma, haka akayi suka danneta da ƙyar tana fizge_fizge ya fara yin auziyyah yayi basmala ya fasa karanto suratul baƙara cikin daddaɗar muryarshi. Jitayi karatun da yake mata tamkar yana watsama wuta feturne tana ƙara ƙonata, ƙoƙarin fizgewa take ganin haka yasa Rabson riƙe hannuwanta gam. Jafar bai tsaya da karatun ba face ƙara himma da yayi wurin rero karatun. Lura sukayi Salma ta daina motsi, hankalinsu yayi mummunan tashi sun ɗauka mutuwa tayi, saida Jafar yace masu bacci ne ya ɗauƙeta sauƙi ne taji. Fuskar kowa ka kalla wurin jimamin wannan al'amari yake. Jafar ne yayi ƙarfin halin fara masu bayani kamar haka; "Tabbas wannan al'amari sai mun tashi tsaye mundage da addu'a, lokacinda zaku tafi gudun faruwar haka saida nayi maku tuni da kuyi addu'a, inagani kowa yayi amma Salma taƙiyi, to kunga abinda ake gudu gashinan yadda ta kasance da ita, jikina nabani in bamu gaggauta naiman ruwaba mukayi mata addu'a da ganyen magaryar nan ba to bashakka bazata ɗauki lokaciba zata zama horror." Sunyi na'am da wannan shawara sun jinkirta Salma ta tashi daga bacci su ƙara gaba su naimi ruwa. Anɗauki lokaci sosai sannan Salma ta fara buɗe idanunta da take jin sunyi mata nauyi. Tana ida buɗesu ta sauje su kan Rabson da tun lokacin da yaga ta fara motsi ya kafeta da ido. Abinda Rabson yagani cikin idanun Salmane ya sanyashi miƙewa jikinshi na mazari. Idanunta wannan baƙin na idonta ya rikiɗe ya koma green. Ganin wannan al'amari Jafar ya umarcesu suyi azamar tashi su samo ruwa. Salma kallon jikinta tayi da tufafin harsun fara yagewa, ga ƙasar da ta kwanta ƙasa duk ta ida bata jikinta ta koma kamar wata mahaukaciya, hawayen dake jerangiya afuskarta ta sharce, wai yau i ta ce ahaka, Salma da take ƴar gayu mai ƙwalisa bashakkayanzu ta koyi darasin yadda rayuwa take. Nas da Kulu ganin yadda Salma ta koma yasa suka matsa daga inda take cike da tsoronta azuciyoyinsu. Ganin su Nas sun matsa daga inda take ta sakejin wani sabon kuka ya kufce mata, wai yau i ta ce ake gudu, lallai rayuwa ba tabbas. Biba ce take kwantar mata da hankali ta ɗauki Ƙaddara musulmi da ɗaukar ƙaddara mai kyau ko akasin haka aka sanshi. Wata soyayyar Biba ce Salma taji ta ƙara shigarta da kuna nadamar abubuwanda ta aikata masu a baya. Biba ita ta kama kannun Sallam ta ranƙwafo ta aza wuyanta bisa kafaɗar Biba sukaci gaba da tafiya. Sunyi tafiya mai nisa sosai suka isa wani wuri da ruwa ke gudana ta cikin wani dutse. Su duka nan suka zube suna masu kamfatar ruwan da hannayensu tare da bismala suna kaiwa bakunansu. Basma jitayi wani jiri na ɗibarta, bashiri taji ta kaima Jafar karo tayi ƙasa tareda dafe kanta dake bara zanar tarwatsewa, ga jikinta da saura kaɗan ya ida komawa green.......... _ina matuƙar godiya da addu'o'inku ga Auntyna, Allah ya sauketa lafiya ta samu baby girl, godiya ta musamman masoya nagode da addu'o'inku_👏🏼❤️ *COMMENT*✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗 ____________________________ *PAGE 32_33* ...........Biba da Kulu da sauri suka riƙo Basma da ta fara chanza kamanni. Ganin haka yasa Jafar juyawa domin samun wani abu wanda zai iya zuba ruwa ciki, ya duba ko ina baisamu inda zai zuba ruwanba, chan gefenshi ya hango wani fasasshen ƙoƙo, ɗaukoshi yayi tare dayin basmala ya wankeshi tas, ya ɗauki ganyan Magarya guda bakwai ya zuba cikin ruwan tareda kanga bakinshi kamar zaisha ruwan ya fara karanto fatiha iskan bakinshi na bugun ruwan, saida ya karanta fatiha ƙafa bakwai, ya nufo inda Basma ke kwance batare da tasan wandake kantaba. Biba ya miƙama ruwanya umarceta da ta bata ruwan ta kur6a sauran kuma ta shafa mata ajiki. Kulu da Jamcy suka taimaka mata ta samu da ƙyar Basma tayi kurba biyu, sauran ruwan ajikinta ta ida shafe mata ajiki, Jafar umartarsu yayi su Kwantar da ita. Matsawa sukayi daga inda take. Kama an tsikareta da allura haka tayi wuf tamiƙe zaune tafara kwarara wani irin amai baƙiƙirin, tamkar zata amayo ƴan cikin ta. Fuskarta kaɗai zaka kalla ka tabbatar ta wahala iya wahala. Tana gama aman tayi baya luuu! Ta sume. Biba hada gudunta zata kamo Basma Jafar yayi saurin tsaidata. "Alhamdulillah da alamu maganin ya fara aiki, kada wanda ya matsa inda take har sai ta farka." Cikin jimami da matuƙar tausayin Basma su duka suke kallonta kwance kamar matatta. Abinda majigin idanuwansu suka hasko masu ne ya sanyasu matuƙar kaɗuwa zuciyoyinsu suka fara bugawa da sauri da sauri. Aman da Basma tayine ya zama wasu irin baƙaƙen tsutsotsi sunata bille_bille, lokaci ɗaya suka kama da wuta suka ƙone ƙurmus. Jikin su yayi matuƙar sanyi, wasunsu wani sabon imani ya riƙa shigarsu. Dubansu suka kai ga Basma dake kwance, ilahirin jikinta yadawo lafiya lau takoma ainahin Basmarta, sai dai abinda ba'a rasaba na baƙar azamar da suke sha a wannan Baƙar tafiya. Hamdala Jafar yayi tare da kallon Salma data ke raku6e wuri ɗaya tamkar wata mairainiya. Itama ruwan ya ɗebo yayi mata ƙwatan ƙwacin yadda yayima Basma. Tana gama shan ruwan ta maka sauran a kanta, yana ida isowa inda Mandiya ta cijeta ta ƙwala wata gagarumar ƙara tareda faɗuwa ƙasa ta fara bille_bille tana tada ƙura tamkar ana yaƙi. Mamaki ya kashesu Jafar ko motsi suka kasayi, su dai sunyi tsaye suna kallon ikon Allah. Ihun da Salma ke ƙwalawa ta tsaida tare da dafe wuyanta, alamar kamar wani abu zai fito tacikin wuyanta tayi, ba shiri ta janye hannunta tare da ƙwala ƙarar da tafi ta ɗazu jin fitowar wani abu daga wurin. Wani abu ne mai kama da maciji ya fito daga cikin wuyanta yajo kansu Rabson dake gefe tamkar yayima Salma kuka. Ganin wannan abu yayo kansu a take suka tarwatse kowa yayi ta kanshi, Nas da Tk sune kan gaba wurin gudun. Rabson tinti6e yayi da wani dutse atake yafaɗi ga wannan halitta tayo kanshi baki buɗe. Ihu yake yana kuka ga hawaye ga wata majina sun wanke mashi fuska. Ganin ya kasa tashi dagewa yayi ya miƙe tanufi inda rafin nan yake, cikin rashin sa'a yasake faɗuwa yacigaba da mulmulawa ya faɗa cikin ruwan. Wannan halitta ita azabar da takeji ajikinta ta sanyata biyo duk wanda tagani gabanta, kamawa tayi da wuta ta fara ƙonewa tana wani irin kuka marar daɗin sauti. Ganin wannan halitta tagama ƙonewa yasa su nufar inda Salma ke kwance, kamata Biba tayi suka miƙar da ita. Wani baƙin ruwane ke fita awuyan Salma, saidai Biba ta yanki gefen hijabinta suka tare ruwan. Yadda kasan fanfo inya fara zuwa kafin yayi ƙarfi yana kawo ruwa haka wuyan Salma ke tsiyayar da wannan ruwan. Ƙallen hijabin Biba sai da ya gama jiƙewa da ruwan sannan ruwan ya tsaya, jefar da ƙyallen sukayi atake ya kama da wuta ya kone shima. Hamdala sukayi ganin jikin Salma ya dawo dai_dai, cizon dake wuyanta kaɗai ya rage ya warke. Lura sukayi babu Rabson, motsin da sukaga ruwa nayi ya tabbatar masu da Rabson na cikin ruwan, Jafar yayi ƙarfin halin fiddo Rabson da yayi tsamo_tsamo, da ruwa. Jafar faɗa ya fara yimashi akanmi zai faɗa ruwa bayan yaga halinda suke ciki. Baki yabuɗe da ƙyar ya tofar da ruwanda ya cika mashi baki yafara magana; "Kawai sai in tsaya wannan halittar ta cijeni nima inzama Horror abanza, amma kaga inna faɗa ruwa in na mutu ciki nayi shahada." Ba Jafar kaɗai ba harsu Nas halinda suke ciki bai hanasu fashewa da dariyaba saboda jin abinda Rabson y faɗa. Bayan sun lafa da dariyar Jafar ya fara masu bayani kamar haka; "ALHAMDULILLAH godiyata tabbata ga Allah mai fidda matacce acikin rayayye, kuma ya fitar da rayyaye acikin matacce, cikin ikonshine ya sanya abokan tafiyarmu suka samu lafiya, Muna ƙara miƙa godiyarmu ga Allah, yanzu abinda yayi saura kuma yafi komi haɗari shine mu naimo su Mandiya dasuka zama Horror suma muyi masu magani, Abinda zamuyi shine yanzu fantsama zamuyi cikin jejin mu jawosu saimu rugu izuwa wannan rafin mai ruwa mu faɗa ciki, mu kuma dama munriga da mun yima wannan rafi addu'ar da mukayimasu Salma, idan Allah ya ƙaddara suma su komo mutane." Ya ƙarasa maganar yana dubansu Rabson. Kowa yayi na'am da wannan shawarar sunan sun fara shirin tinkarar su Mandiya. Basma tunda ta farka daga nannauyan baccin daya ɗauketa take godiya ga Allah, ga wata gagarumar nadama da kewar mijinta da kuna Ɗanta, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska ba, tayi kukanta mai isarta tana mai addu'ar Allah ya maidata gida kodan ta gyara kuskuren da tayi a baya. Kwanansu biyu a wurin jikin Basma da Salma ya warware sunji sauƙi sosai sun warke, tun bayan warkewarsu Salma ta dawo cikin hankalinta take daraja ɗan adam, wani irin girma takema Jafar da yayi silar warkewarta. A yaune zasu fita naiman su Mandiyi, kowa ya kimtsa. Alama sukayima rafin domin in suka jawo su Mandiya su gane wurin. Nausawa suka ƙarayi cikin jejin suna masu addu'ar samun nasara. _________________________________ Cikin tsawa da hargagi yake magana tamkar zai kai mata naushi. "Yau tsawon kwana goman dana ɗibar maki ya cika, dan haka kije gidanku na sakeki saki ɗaya, duk radda ɗiyata ta bayyana zani naimeki, yanzu zanije in samu shugaban sojoji abokina da kika sani in naimi taimakonshi atura wasu iyakar dajin koda Allah zaisa su Salma suna fitowa ayi sa'a su maido manasu gida, maganar ƙarshe da zaniyi maki i ta ce kitattara duk abinda kikasan naki ne ki bar gidan nan kafin in dawo." Alhaji Abdallah mahaifin Salma ya ƙarashe maganar zuciyarshi na matuƙar yimashi ƙuna. "Dan Allah ka gafarceni wallahi nayi nadama, kada ka tona mani asiri, yanzu innaje gida muzanice?, dan Alkah ka rufa mani asiri." Ta ƙarashe maganar muryarta na sarƙewa saboda kukan da take cizga. Bai ko kalli inda take ba yayi ficewarshi ya barta nan tsugunne. ____________________________ Basu yi nisa sosai da inda suka baroma suna cikin tafiya Jamcy taji kamar wani abu ya gilma da gudu ta bayanta. "Wayyo Allah! Yauni Jamila nashiga ukku." Ta ƙanƙame jikin Tk tana ƙyarma. "Miya faru Jamcy?, yau ke ce ke faɗar ainahin sunanki wanda kin hana mutane kiranki da Jamila sai dai Jamcy, to wai mima ya firgitaki har haka."? Tk ya Ƙura mata ido tare da jefo mata tambayar. "Uhm! Ai wani abu nagani ta baya ya gilma." "Haba Jamcy babu komi fa, kawai tsorata kikayi." Jinin Jamcy kan akaifa sukaci gaba da tafiyar. Kamar daga sama Jamcy taji an warci hannuta an jawota da ƙarfin tsiya ta faɗi ƙasa. Ƙarar faɗuwarta ita tayi sanadiyyar jawo hankalinsu Jafar. Ganin Jamcy ƙasa warwas ga Mandiya kuma sunata kokawa yasa Jafar fara dube_dube ko zai ga wani mabigi, sai dai duk iya dube_dubenshi bai samu komi ba. Ganin bai samu komiba ya dunƙule hannuwanshi ya kaima Mandiya wani wawan bugunda yayi sanadiyyar rabata da jikin Jamcy ta faɗi chan gefe, ganin aka ya sa su duka suka fara gudu Mandiya ta mara masu baya. Gudu suke suna waigen mandiya har suka iso inda rafin nan yake, basu bata lokaciba suka faɗa ciki, Mandiya da idanunta suka rufe itama bin bayansu tayi ta tsunduma cikin ruwan. Ida isarta cikin ruwan yayi dai_dai da ƙwala wata gagarumar kuwwa da tayi ta haddasa ma wurin amsa kuwwa........... *COMMENT* ✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗 _______________________ *PAGE 34_35* .......Kamar yadda kibiya ke fita daga cikin ƙwari haka Mandiya tayi tsalle ta fito daga cikin ruwan, abin al ajabi tana fitowa kafin tayi ƙoƙarin guduwa kamar an fizgota haka ta faɗa cikin ruwan, tun tana ihu iyakar ƙarfinta har tayi tsit. Su Jafar da suka samu suka baro cikin ruwan jin shirun Mandiya tayi yawa yasa suka fara tunanin ya zasuyi su samu su fiddota. Jafar kallonsu Biba yayi fuskarshi da alamun damuwa ya fara magana. "Yanzu ba lokacin yin dogon tunani bane, kamata yayi musan yadda zamuyi mu ceci rayuwar Mandiya kada ruwan nan yayi mata wata illar, garin naiman magani kuma asamu wata matsalar, niba muharramata bace da sai in fiddota, amma cikinku yakamata ku yi ƙoƙarin fiddata a ruwan nan." Tsuru_tsuru sukayi tamkar basuji abinda ya faɗaba, Biba ita tayi ƙarfin halin fara magana. "Jamcy da Kulu ku yakamata mu haɗa karfi mu fiddota tunda mune mata." "Wa! Allah ya tsare gatari da sarar suka, haka kawai kinta6a ganin wanda yakai kanshi ga halaka yanaji yana gani?, to nidai har yanzu ina son rayuwata inku bakuda buƙatar taku." Jamcy ta ƙarashe maganar tana jan kitson attach ɗinta dayaji wuya yayi burcin_burcin. "Mtssw! Allah wadaran naka ya lalace, yanzu ke ki taimaka aceci rayuwar baiwar Allah amma kitsaya kina 6ata mana lokaci, Biba zo muje ni koda wannan aikin da zaniyi zai zamto ƙarshen rayuwata ba shakka zani aikata, ina roƙon Allah sanadinshi yasa mahaifana su yafe mani laifinda nayi masu na barin gida batare da izininsu ba." Tana ƙarashe maganar taja hannun Biba suka nufi ruwan. Suna shiga sukayi nasarar samun Mandiya amma babu alamun tana motsi. Da ƙyar suka samu sukayi nasarar fitowa da ita, kowa yayi tsit ganin kamar Mandiya ta mutu. Fuskarta da suka kalla ganin ta koma suffarta ta ainahi yasan yasuka ji wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyoyinsu. Motsi da suka ga hannunta nayi wadunsu suka dare daga wurin, Rabson bayan Jafar ya koma yana leƙe yaga yadda zata kaya. A hankali take ƙoƙarin buɗe idanuwanta da sukayi mata matuƙar nauyi,ɗaya bayan ɗaya tariƙa ƙarema su Jafar kallo. Yunƙurawa tayi ta miƙe zaune tana murmushi ɗauke a fuskarta. Rabson gani yayi kamar shi ɗaya take kallo tana dariya tana lashe baki, ihu ya ƙwalka tare da cikuikuye Jafar yana ƙoƙarin kayar dashi. "Innahumin sulaimanu..., La'ilaha illallahu, shikenan kallona take tana lashe baki zata cinyeni, wayyo nashiga ukku lokacina yayi, Busurulle da Salma zaku zama marayu, shikenan Kakata yau zani mutu in barki." Ganin Rabson na ƙoƙarin kayarda Jafar ya sanya Jafar mangarema Rabson geya. "Kai ko anya zaka yi hankali?, mufa take yima murmushi ba kaiba, yanzu ta dawo ainahin Mandiyarta ba horror bace, kadawo cikin hankalinka." Jin wannan maganar tasa Rabson ƙara kallon Mandiya da kyau, gani yayi ita ɗince ta dawo ainahin mutum ɗinta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da fadar; "Wai Allah nagode maka, ashe inada sauran shan ruwa nan gaba, inada rabon auren Salma masoyiya." Kaɗan ta hana su dara ganin wannan wauta ta Rabson. Wurin Mandiya suka matsa suna mata sannu. Amsawa taruƙayi hawaye na wanke mata fuska tana ƙara nadamar rayuwar da tayi abaya, tayi alƙawali har cikin ranta insha Allah bazata ƙara karuwanci ba har ƙarshen rayuwarta. Jafar ya ji daɗi sosai, domin ya tuno da wani hadisi dayace, _KASHIRYAR DA MUTUM ƊAYA YAFIYE MAKA JAJAYEN RAƘUMA_ Allah sukayi ma godiya suna masu ƙara tawakkali da addu'a, domin sai yanzu suke ƙara tabbatarwa a baya sunyi sakaci da addu'a. Yunwar dake cikinsu ce ta fara addabarsu, tunanin inda zasu samu abinda zasuci suka farayi, sallolinda ake binsu suka farayi, inda Biba ita tafarayi sannan ta anshi ɗankwalin kulu ta yafa ta basu hijabinta da ta Sha gwagwarmaya amma har yanzu tana nan saidai cukuikuyewa da tayi. Bayan gama sallar wasunsu kwanciya sukayi suna hutawa, su duka sun lula duniyar tunani. Ƙarar da sukaji ce ta sanya su miƙewa tsaye tare da dunƙulewa wuri ɗaya duna masu dafe kunnuwansu dake bara zanar tarwatsewa. Tsagaitawa sukayi tare da rufe wangama_wangaman bakunansu. Ɗago kawunansu sukayi jin ƙarar da sukeji ta tsaya, abinda majigin idanuwansu suka hasko masu ya sanyasu ƙara matsewa wuri ɗaya tare da fara sallallami wasu kuma suka fara hawaye tareda sabbatu. Wasu irin maridan Aljanune mace da namiji tsaye fuskokinsu a matuƙar murtuke ba alamun imani a tattare dasu. Namijin ya wangame baki ya fara 6a66aka dariyar da ta haddasa dajin girgiza, tsaida dariyar yayi tareda tur6une fuska ya nunasu da yatsa ya fara magana. "Yau kwananku yazo ƙarshe, a baya kunyi nasara a kanmu mun iskeku kuna bacci kun ƙona mana hannuwa nida matata, na tsananta bincike aka wane irin sihiri kuke amfani dashi inda na gano kai wannan matsitsiyar halitta kai ka yi sanadin faɗawarmu wannan hali." Ya nuna Jafar dake taye. "Alokacin nayi ƙoƙarin ɗaukar fansa a kanku amma wannan sihiri da kuke amfani dashi nakasa koda taba akaifarku, nafara ɗaukar fansa akan abokan tafiyarku dana haɗu dasu su Ukku maza a hanya ta ta zuwa inda kuke tuni na hallakar dasu, yanzu kuma zani kashe ku in ba matata Matsayi kyautar masoya saboda tsananin ƙaunar da nike mata." Jin an kashe Garba, Nura da Audu Jafar yaji zuciyarshi ta fara tafasa, wani irin ƙarfi yaji yazo mashi yayo kan waɗan nan halittu ba tsoro ko fargaba a tare dashi, ya nunasu da yatsa tare da fara magana. "Ƙarya kuke yaku waɗan nan la'anannu kuma ta6a66u, ubangijinmu bai koya mana sihiri ba Sai dai addu'a wadda insha Allah ko a yanzu da ita zamuga bayanku, kun kashe mana ƴan uwa amma nasan lokacinsune yayi, domin bawa baya mutuwa sai Kwananshi sun ƙare, ku baku isa kuyi mamu komiba sai in Allah ya rubuta hakan zai faru damu." "Hhhh! Yauni hatsabibi marz mijin marhaz naga halitta mai ƙarfin hali da taurin rai, tunda nike a dajin nan na kaikazo bantaba arba da halittu barasa tsoroba kamarku, yanzu zaniyi fata_fata da naman jikinku in shayar da matata jinanenku." Ya ida maganar tare dayo kan Jafar da mummunan nufi a zuciyarshi. " _LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNIKUNTUMINAZZALIMIN._ " Jafar ya furta a bayyane. 6acewa Jafar yayi a idanun aljani Marz, dube_dube yahauyi amma bai ganshi ba. Gefe dasu Jafar ya hango wani irin icce mai tsinin gaske, ɗaukarshi yayi ya daka ma Aljanin a zuciya tare da kwala kabbara bakinshi ɗauke da sunan Allah. Kuwwa aljanin ya ƙwala dayayi sanadin jawo hankali matarshi itama tayo kanshi da azababben gudu, kafin ta iso har yafaɗi ƙasa jini na malala ta hancinshi da baki. Kafin ta iso wurin mijinta sul6i ya kwasheta ta faɗa cikin wannan ruwa da Mandiya ta faɗa. Ihu take tana naiman taimakon mijinta, amma ina tana samu tafito daga cikin ruwan ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus shima mijin ƙonewa yayi iska ta kwashe tokarsu tayi sama. Ganin wannan al amari daya faru su Nas da Tk mamaki suka riƙayi na yadda Jafar yake da ƙarfin hali. Jimamin rashin abokan tafiyarsu suka yi tare dayimasu fatan rahamar Ubangiji. Sunyi kwana biyu a wurin saida jikin Mandiya da Su Salma suka gama warkewa. Sun yanke shawarar zasuyi tafiya batareda tsayawaba ko da cin abinci Sallah ce kaɗai zata tsaidasu. Sunyi kwana yakai biyu suna tafiya ba ƙaƙƙautawa batare da sun samu abinda zasuciba koda ƴa'ƴan itatuwane. Kallo ɗaya zakayi masu kagane sun fita hayyacinsu, ga bakunansu sun bushe jikinsu duk yayi yaushi. A kwana na ukku ne suna tsaka da tafiya ƙarfinsu ya kusa ƙarewa kamar daga sama bazato ba tsammani suka gansu bakin hanya, wasu mutane suka hango sunyo kansu amma ina kafin su ida ƙarasowa wurinsu tuni su duka sun yanke jiki sun sume. Ogan sojojin ne ya ƙarema Salma kallo dan gano ko i ta ce wadda suke naima, ganin tafita hayyacinta tamkar ba itaba. "Yess." Ogan ya furta ganin i ta ce wadda suke naima , umarni yayi akira motar asibiti domin abasu taimakon gaggawa.... *COMMENT*✅ *SHARE*✅ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798 [10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀 ( *HORROR STORY* ) *BY MEEN@T A YANDOMA* *MARUBUCIYAR FATALWA* 🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼* *ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA* *MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE* 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA* *ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗 __________________________ *PAGE 36,37,38,39 and 40* الحمدلله! الحمدلله!! الحمدلله!!! _End_ ..............."Assalamu alaikum, kiranka nayi in sanar da kai ansamu yarinyar nan yanzu haka gamunan motar asibiti ta kwaso mu domin suna cikin mawuyacin hali." Cikin hanzari gami da zaƙuwa daga ɗayan 6angaren aka fara managa. "Kuyi sauri kukaisu asibiti, nima gani nan zuwa." Asibiti mafi kusa Pravet hospital suka kai su, suna isa Emergency aka nufa dasu likitoci suka duƙufa ceton rayuwarsu. Alhamdulillah ansamu nasarar ceton rayuwarsu, anyi masu allurar bacci da sun tashi zasu dawo cikin hankalinsu. Dukkansu a ɗaki ɗaya aka ajesu, gadajensu ajere suke. Ƙofar ɗakin likitocin suka jawo, suna niyyar barin wurin. Har tuntu6e yake ya kama hannun likita ya riƙe gam yafara magana muryarshi na Kyarma. "Likita!, ina Mamana?, ina ɗiyata?, wane hali take ciki."? Ya ƙarashe maganar cikin zaƙuwar jin amsar da zai bashi. "Ka kwantar da hankalinka, yarinyarka tana nan lafiya Ubangiji ya taimakemu munyi nasarar ceto rayuwarsu, yanzu allurar bacci mukayi masu da sun tashi insha Allah zasu dawo cikin hankalinsu, saidai zamu riƙesu harsu dawo ciki hayyacinsu, domin yanzu suna buƙatar kulawa jikinsu ba ƙwari." "Zani iya shiga inganta."? Ya faɗa a hanzarce. "A'a, yanzu suna buƙatar hutu sakamakon allurar bacci da mukayi masu." "Zaniyi haƙuri harsu tashi, ina nan." Ranar nan Alhaji Abdallah ya yini bayan ya sallami yaran abokinshi da suka samo su Salma, tare da yima amininshi godiya. Ɗakin yayi tsit bakajin komi sai ƙarar A.C da ta gauraye ɗakin, A hankali ma'aikatan jinya mata suka turo ƙofar ɗakin domin bin umarnin Ogansu daya umarce su suzo suka insun farka, su duddubasu sunje kan Rabson, yatsun hannunshi yafara motsawa tare da ƙoƙarin buɗe idanunshi. Ida buɗesu yayi ya saukesu akan ma'aikaciyar jinyar dake kanshi, a firgice ya ida buɗe idanunshi tare da ƙwala wata mahaukaciyar kuwwa. "Innalillahi, nashiga ukku, lawakiri ki taimaka kada kiyi mani komi, wayyo ashe mutuwa nayi, yau ni Rabi'u na lalace kodai lahirama akwai Horo, wayyo bunsurulle shikenan na mutu na barka." Yana ƙarashe maganar yayi tsalle ya diro daga saman gadon yayi hanyar ƙofa tare da cigaba da darza ƙara yana naiman taimako. Sistocin kallonshi suke suna mamaki kodai baida hankali, ko kuma haɗarin daya samune ya maidashi haka. Rabson jin ƙofa akulle babu hanyar fita ya juyo wutsiya zage yafara bin sistocin da kallo. Wani tunani yazo kanshi, wata kujera dake nesa dashi ya raruma ya nufi sistocin da niyyar zai Make kawunansu sumutu kowa ya huta. Ganin haka suka ƙara tabbatarwa bashakka Rabson mahaukacine, ihu suke suna naiman taimako, da ƙyar suka buɗe ƙofar suka fice a guje Rabson ya mara masu baya. Alhaji Abdallah dake zaune yana dakon farfaɗowar Salma ganin mutane sun nufi inda yake a guje ya sanyashi miƙewa ya riƙe Rabson. "Bawan Allah mizakayi masu daka biyosu da wannan makamin a hannu."? "Kada ka yarda da waɗannan Horunan a nan lahirar ma biyoni sukayi su ƙara kashewa, dan haka barni dasu yanzu inga bayansu duk in kwaɗe masu kawuna da wannan kujerar." Jin wannan wautar ta Rabso ba sistocin dake 6oye bayan Alhaji abdallah ba har shi kanshi saida ya tuntsure da dariya. "Bawan Allah waya ce maka ka mutu?, kata6a ganin wanda ya mutu yana magana har ya riƙa fallawa da gudu da ƙafafunshi, alamu sun nuna kai majinyacine ba mutuwa kayiba nan asibitice aka kawoka." Wata iriyar kunyace ta lullu6e Rabson jin ashe yana raye bai mutu ba. Likitane ya ƙaraso wurin jin hayaniya ta yawaita. Ganin Rabson tsaye yasa likita fara tambayarshi miya fiddoshi?. Nan Alhaji Abdallah ke sanarda likita abinda ya faru. Saida likitan yayi dariyarshi mai isarshi sannan ya lalla6a Rabson akan ya koma ɗakin da aka kwantar dashi. Suna tura ƙofar ɗakin suka hango su Jafar duk sun farka suna jingine da gadajensu. Salma ganin mahaifinta da tayi tamkar a mafarki yasa tayi wani tsalle ta rungumeshi batare da tunanin shiɗinne ko bashi bane. Wani kukane ya kubce mata , ashe tanada rabon sake ganin mahaifinta, tana roƙonshi ya yafe mata ta tuba da sa6ama umarninshi, bazata sake tsallake maganarshi ba. Rarrashinta yake yana jin wani sabon tausayinta na ratsashi. Kowa wurin sai yanzu ya fahimci wannan shine mahaifin Salma. Rabson da dai ya lura tabbas mutumin ɗazu shine sirikinshi,wata irin kunyace ta rufeshi, sulalewa yayi ya haye gado tare da rufe ido kamar yana bacci. Bayan komi ya lafa, mahaifin Salma Odar abinci yayi masu sukaci suka hantse, domin rabonsu da irin wannan abincin tun kafin su fara Baƙar tafiya. Salma ita ta gabatar da sauran abokan tafiyarta ga mahaifinta bayanta ƙwashe labarin dukkan abinda ya faru a tafiyar ta faɗa mashi, yaji irin gudumawar da Jafar da Biba suka bata a wannan tafiyar. Juyowa yayi da nufin yimasu Jafar godiya, saidai suna haɗa ido da Jafar yaji gabanshi yayi wata irin mummunar faɗuwa Saboda kama da Jafar yayi da wani ƙanenshi daya 6ata. Godiya yayi tare dayi masu alƙawarin zai sanar da iyayensu Halinda suke ciki zai samesu har gidajensu, suyi masu kwatancen unguwannin da suke bama yara zai aikaba shi da karan kanshi zaije. Kamar yadda yayi alƙawari tunda safe ya fara da gidansu Jafar, ya aika ayimashi da matar gidan, ƙanwar Jafar ce ta leƙo, ya sanar da ita halinda ake ciki tare da faɗa mata halinda ake ciki, rugawa tayi ta faɗama Ummansu abinda ke faruwa. Suna isowa har Alhaji Abdallah ya 6ace a wurin ƙurar da motarshi ta tayar kaɗai ta rage, a hanzarce suka shirya suka nufi asibitin. Lokacinda Alhaji Abdallah ya faɗama Kaka jikanta na asibiti, kuka ta fara tana shikenan Rabi'unta zai mutu shima ya barta. Saida Alhaji yayita kwantar mata da hankali. Shiryawa tayi itama ta nufi asibitin. Da habib yaji abinda ya samu Basma bai wani kaɗuba dominshi yanzu matarshi Hanan ta gama mashi komi. Badan yasoba sai dan Hanan da ta sanya baki ta lalla6ashi akan yaje ya dubo Basma, asibitin yanufa kai tsaye yana jin wani irin haushin Basma a zuciyarshi. Haka yabi gidajensu Kulu, Jamcy, tk, da Nas ya sanar da iyayensu. Hanyar asibiti ya ɗauka domin sanar dasu Jafar ya cika alƙawarin daya ɗauka. Yana isa Kaka na isowa da gudu ta shige ɗakin tana mararin ganin tilon jikanta. "Labson ɗina, wayyo jikana sannu , haka ka koma duk kafita hayyacinka."? Ta ƙarashe maganar batare da tasanin ko sunan Rabson ɗin bata faɗa dai_dai ba. Hannuwanta ya kama ya riƙe gam Tamkar za'a ƙwace mashi ita. "Da farko dai kaka yanzu Rabi'u nike ba Rabson ba, kaka ki yafeni dan girman Allah, bazani ƙarayimaki gardama ba, nabi Allah nabiki Kakata." "Tuni nayafe maka Rabi'u na, kullum banida gurin daya wuce Allah ya maidomani kai marayan Allah." Shigowar iyayensu Kulu yasa kaka yin shiru. Su Kulu kam sunsha bala'i da masifa wurin iyayensu, dan Nas Mamanshi cewa tayi saita kwara kanshi da bango zata huce, Momyn Jamcy kuwa yi tayi kamar zata jawota daga gadon ta karya mata ƙafar da ta yi alƙawari. Alhaji Abdallah mamakin halin iyayensu Jamcy ya bashi mashi mamaki, haƙuri ya rinƙa basu akan suyima Allah godiya da bayyanar ƴa'ƴansu basu hau bala'i da masifa ba. Jikinsu sanyi yayi sukayi tsit. Umman Biba ce da ƙanwarta suka iso. Har kukan murna saida Mahaifiyar Biba tayi tare dayima Allah godiya. Biba kuwa tsabar farin ciki jitake kamar ta koma cikin mahaifiyarta ta kama ta ta riƙe gam. Sallamar maman Jafar ce ta sanya kowa kallon ƙofar. Zabura Alhaji Abdallah yayi ya miƙe tare da nuna Maman Jafar ya furta Hindatu!. Maman Jafar itama kallonshi take da mamaki ta furta Abdallah......... Juwar dayaji tana ɗibarshi ce tasashi yayi saurin zamewa ƙasa tare dayin zaman ƴan bori. Hindu kuwa wasu hawaye ne taji sun wanke mata fuska, wai yau i ta ce take ganin Abdallah, anya kuwa ba mafarki takeba. Jafar ganin mahaifiyarshi yasa yayi yunƙurin tashi. Ganin haka ummansu tayi saurin ƙarasowa wurinshi cike da farin ciki marar misaltuwa. Alhaji Abdallah hawaayen fuskarshi ya sharce, ga wani gumi daya tsatstsafo mashi ta ko ina ajikinshi. Kallon Jafar yayi yaƙara tabbatarwa tabbas yanzu yaƙara ganin kamarsu da husaininshi. Abdallah tashi yayi ya isa gabansu Hindatu tare da zaunawa amma bakinshi ya kasa furta koda kalma ɗayace. "Umma! Dama kinsan Mahaifin Salma?, koɗan uwankune."? Ya ƙarashe maganar ya mai ƙara fuskantar Mahaifiyarshi. "Ɗana ne kai, Jafar tunda na haɗa ido dakai jikina yabani kai ɗin jinina ne, Jafar Ashe kaine ɗan, ɗan uwana Husaini daya bata, babu inda ban bancika ba domin ganin nasamuko amma abin yaci tura ban gankuba." Alhaji Abdallah ya ƙarasa magana muryarshi a matuƙar karye. Hawayen dake fuskarta ta share ta ɗora da faɗar. "Tun bayan rasuwar iyayenku, Husaini yashiga wani mawuyacin hali, saiya zaunar dani yayita yimani wasu maganganu masu kama da wasiyya, ana cikin haka Allah ya nufeshi da 6acewa inda haryau bamu ganshiba." Kukan da taji yana naiman ƙwace matane yasata yin shiru. "Mahaifanmu mu biyu suka haifa taƙwaye, muntashi muna matuƙar ƙaunar junanmu, har mahaifanmu suka rasu lokacinne kuma Husaini ya bata, na nemeku lungu da saƙo amma ko labarinku bansamuba, kullum cikin yima iyayenmu addu'a nike da Husaini har izuwa yau da Allah Ya bayyana mani ku." Jafar ji yayi anya ba mafarki yake ba, ace wai yau shine gashi ga yayan mahaifinshi, Allah mai yadda yaso, yana ƙara roƙon Allah ya bayyana mahaifinshi aduk halinda yake ciki. Salma wata gagarumar kunyace ta ƙara rufeta, wai yau ace wanda ta gama wulaƙantawa ashe yayantane, yanzu ta ƙara tabbatarwa ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane, wata sabuwar nadama taji tana ƙara shigarta. Mahaifiyar Habib da Alhaji Abdallah gaisuwar yaushe gamo suka hauyi ciki da farin ciki da ƙaunar juna. Sallamar Habib dasukaji ta maido hankalinsu ga ƙofar. Basma tunda taga Habib wani farin cikin marar misaltuwa ya ziyarci zuciyarta, ashe tanada rabon ganin mijinta farincikinta, tana ƙara miƙa godiyarta ga Allah. Bayabo ba fallasa bayan gaisawarsu da ƴan ɗakin ya dubi Basma yana mata ya jiki. Ba ƙaramin mamakin Habib Basma tayiba, ya matuƙar chanza mata sai wani shareta yake ga wani haske da yayi da wata ƙiba da yayi abinshi. Haƙuri ta hau bashi tana kuka ya yafe mata tayi nadama, ko kallonta baiyi ba ya furta naji kanshi na sunkiye yana kallon screen ɗin wayarshi. Tamkar Alhaji Abdallah zai maida su Hindu da Habib ciki haka ya riƙa nuna masu soyayyah. Batare da sanin su Hindu ba Alhaji Habib yaje yasamu wasu malamai yayi masu fatawar ɗan uwanshi da yayi shekara ishirin da bacewa yabar mata shin zai iya auren matar da ya bari.? Bayan gama tattaunawarsu sun yimashi fatawa iya iliminda Allah ya hore mashin cewar zai iya aurenta. Farin ciki marar misaltuwa yaji acikin zuciyarshi, domin shidai harga Allah yanada gurin auren Hindatu kodan ya taimaka mata, bai da gurin ganinta cikin wahalar rayuwa. Ba ƙaramin artabu yayi da Hindatu ba kafinta amince da auren. Sai da suka shafe wata huɗu a asibiti lokacin kowanensu ya samu lafiya yayi ƙiba abinshi. Soyayya mai ƙarfi ce ta ƙara shiga tsakanin Jafar da Biba har iyayensu suka fahimci abindake faruwa, sunyi murna sosai domin ba wanda zai guji haɗa zuri'a da Jafar. Oga Rabson ma yanzu Salma ta bada haɗin kai, soyayya suke sha ba kama hannun yaro. A yau ne likita yayi alƙawari sallamar su saboda yaga sun warke yadda yake buƙata. Sabo shi akema kuka ba mutuwaba. Fuskokinsu yau suna cikin damuwa da kuma jimamin rabuwar da zasuyi. Rabson hada hawaye na rabuwarsu da abokan tafiya. Su Kuluma hada hawaye sukayi, ana kuka suka rabu da juna tare da yima juna fatan alkhairi. Alhaji Abdallah bai yarda Hindu tashiga gidanshiba saida igiyoyin aurenshi akanta. Bayan su huta Salma ke tambayar mahaifinta ina mahaifiyarta?, tunda aka kai su asibiti baga tajeba. Nan ya sanar da ita abinda ya faru. Allah sarki ɗa da uwa sai Allah, kuka Salma ta riƙayi tana roƙon mahaifinta akan ya dawo da mahaifiyarta. Dakatar da ita yayi, ya sanar da ita shifa yanzu yayi aure ya auri Hindu. Jafar da Salma sunji daɗin wannan al'amari, amma Salma tana addu'ar Allah ya huci zuciyar mahaifinta ya maido mahaifiyarta. Alhaji Abdallah da Hindu soyayyarsu sukeyi hankali kwace. 🤣😂 Su Hajiya Zaliha ana gida ana zawarci, Alhaji nan ya angwance😂. Rabson tsabar murna da farin ciki yana Shiga gidan yayi wuf ya kwance bunsurulle ya ɗagashi rama yana hajijiya dashi yana dariya yana murna. Bunsurulle jin wannan jijjigashi da ake ya tabbatar mashi lallai Rabson yadawo, shima kuka ya riƙayi. "Yau ni naga lalata, Rabi'u daga dawowarka zaka dasa daga inda ka tsaya?, yanzu saika karya busurun nan, kasaukoshi nace maka." "Kaka kibarni yaushe rabonda in ganshi, bakiga yadda yake farin ciki ba shima."? "Kaci gidanku nace! Maza saukeshi." Yana saukeshi Bunsurulle ya manne mashi, duk inda yayi yana biye dashi. (😂😂 niko nace Rabson da Bunsurulle wannan ƙauna har ina) Ba'a ɗauki lokaciba Alhaji Abdallah ya ɗauke kaka da Rabson ya basu wani haɗaɗɗen gida tare da ɗaukar Rabson aiki a kamfaninshi na sarrafa shinkafa. Murna da farin ciki ba'a magana wurin kaka da Rabson, Kaka ƙauye taje ta sanar da ƴan uwan mahaifin Rabson sukaje naiman aure gidansu Salma. Alhaji Abdallah ya karramasu inda yasa bikin wata ukku. Abdallah bai manta da gidansu Biba ba, suma gida ya ƙyara masu ga kayan abinci daya loda masu a store. An haɗa bikin su Jafar danasu Rabson nan da watanni ukku. Da ƙyar da ji6in goshi Hindu ta samu Alhaji ya yarda zai maido Hajiya Zaliha. Tayi matuƙar mamaki data dawo ta iske gidan da wata mata. Salma ta kwashe komi ta sanar da Mahaifiyarta. Kuka Hajiya Zaliha ta riƙayi tana nadamar abinda ta aikata, tana zaman_zaman ta ita ɗaya a gidan mijinta, yanzu gashi nan i ta ce hada kishiya, ta ɗauki ƙaddara tare da wata irin nadama datayi, domin yanzu ta ɗauki darasin rayuwa. Zaman lafiya suke tsakaninta da Hindu tare da girmama juna. _________________________ Suna isa gida Basma ƙamshin wani daddaɗan abinci ne ya daki hancinta. Abinda ya ɗaure mata kai bai wuce ita dai tasan Habib bai iya girki ba balle tace shi yake girkin. Matashiyar budurwa da taga tafito da tsohon ciki tana tafiya a hankli, hannunta riƙe da Walid daya sha wanka ansa mashi kaya masu kyau sai ƙamshi suke zubawa. Gabantane ya yanke yafaɗi dafe ƙirji tayi tare faɗar. "Yau ni Basma nashiga ukku! Minike gani haka?, Habib yaushe kazama ɗan iska ka aje mace gida harda ciki dan kaga baninan." Kallon bakida hankali Habib yayi mata. "In kika sake bakin ki ya ƙara faɗar kalma ɗaya mara daɗi ga mamata zani shayar dake mamaki, wannan da kike gani wallahi badan itaba da yanzu sunanki bazawara, ita taita rarrashina harna yarda inci gaba da zama tare dake, dan haka ki shiga hankalinki." Wata irin ƙuna taji zuciyarta nayi mata, wai yau i ta ce da kishiya, ita kam ta gama shiga ukku, rayuwa ta koyar da ita darasinda harta mutu bazata manta ba. Hannu tamiƙa da nufin ɗaukar Ɗanta Walid, tsalle yayi ya fashe da kuka tare da maƙalƙalewa jikin Hanan yana magana cikin hausar da bai ida ƙwarewa ba. "Wayyo Momy foyeni, wannan matar bani sonta kice kada ta ɗaukeni nidai." Ya ƙarashe maganar yana ci gaba da kuka. Basma jin abinda Ɗan cikinta ke faɗa jitayi ƙafafunta sun daina ɗaukarta sulalewa ƙasa tayi tare dayin zaman ƴan bori ta saki wani marayan kuka. Habib tsoki yayi tare da shigewa ɗakin Hanan. Hannan bin bayanshi tayi takai walid ɗakin ta ajeshi itakuma ta fito. Kuka Basma keyi tamkar ranta zai fita, i ta ce yau ɗan da ta haifa yake gudunta yama manta da ita, wannan duk laifintane ita tajama kanta, kuka ta fashe dashi tare da ɗaga hannuwanta sama. "Ya Allah ka yafe mani, Allah ni mai laifice a gareka na sa6ama mijina Allah ka yafe mani." Kukan dayaci ƙarfintane ya sanyata yin kasa cigaba da addu'ar. Kafaɗunta ta dafa Cikin taushin murya ta fara mata magana. "Kiyi haƙuri Basma, banshigo gidan nan ba dan in fiddaki ki kwantar da hankalinki, insha Allah zani shawo kan mijinki, Walid kuma sai a hankali zai saba dake." "Nagode maki Hanan Allah yayi maki albarka, Allah ya zaunar damu lafiya." Hanan tasha wahala kafin Habib ya yarda ya yafema Basma, zaman lafiya suke a gidan nan duk da a yanzu Habib ya yafison Hanan akan Basma, amma yana ƙoƙarin 6oyewa, sai dai har yanzu Walid yaƙi yarda da Basma shicewa yake Hanan ce Momynshi. Allah ya sauki Hanan lafiya, tahaifi tagwaye mace danamiji. Basma anata rawar ƙafa kamar ita ta haihu kullum macen na wurinta, da hanan taga soyayyar da take nunama babyn saita barmata ita. Haka sukaci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. __________________________________ Su Nas iyayensu yanke shawarar haɗasu aure sukayi. Ba'a ɗauki sati biyu ba aka ɗaura aure Jamcy da Tk, Kulu da Nas, sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya. _____________________________________ Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. A yau jama'a da dama suka shaida ɗaurin auren Rabi'u Mukhtar da Salma Abdallah, tare da Jafar Abdurrahman da Habiba Hashim. Bayan anɗaura aure aka gayyaci malamai suka gabatar da wa'azi akan zaman takewar aure. Kowace amarya an miƙata gidan mijinta. Wani katafaren gida Alhaji Abdallah ya mallakama Jafar anan aka kai amarya Biba, sai dai muce masha Allah kwatanta haɗuwar gidan 6ata lokacine, domin ya haɗu haɗuwa mara misali. Rabson ma Cikin gidajen Alhaji Abdallah ya mallaka mashi wani haɗaɗɗen gida nan aka mallakamashi suka tare shida amaryarshi. Rabson bai manta da Bunsurulleba, wani wuri yaɗiba aka gyara ya kawo bunsurulle ya ɗaure ya ɗauko mai kula dashi, rayuwa tayi daɗi arziƙi ya bunƙasa Rabson yanzu yake Rabson guy. Bunsurulle ya girma ya koma kamar bijimin sa. In Salma naso ta tsokani Rabson saitace ita fa tana ƙwaɗayin naman Bunsurulle, nan zai tubure yace shifa shida bunsurulle mutu ka raba, nan zasu tuna da baya suci dariya abinsu. Biba da Jafar rayuwa suke cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, ga kuɗi sun zauna masu sai da muce Alhamdulillah. *END* *TAMMAT BILHAMDULILLAH.* _YAU MUN KAWO ƘARSHE WANNAN LABARI, KURAKUREN DANAYI ALLAH KA YAFE MANI, ALLAH KASA MUYI AMFANI DA ABUBUWAN DAMUKAJI MASU AMFANI, ALLAH KA GYARA KASATA KA ZAUNAR DA ITA LAFIYA, MU HAƊU A LABARI NAGABA MAI SUNA RAZANI KADA KU BARI ABARKU BAYA DOMIN WANNAN LABARI AKWAI FAƊAKARWA NISHA ƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA, KUDAI KADAKU BARI ABAKU LABARI._ *MEEN@RT...✍🏻* 08133562798