TAWA TASAMENI Book 2 Complete Writing by Halima Abdullahi k Mashi Cikin tsoro nake dubansu dukkansu ni suke kallo cikin mamaki da sauri na dubi yayanmu shi kan murmushi ma yake yana rike da hannuna muka isa gunsu Haj Laure ta sakar mishi harara gami da cewa Abdulrahim kana da hankali kuwa?fuskarshi a sake yake cewa me ya faru momi?naga kun zo nan kuda yawa kuna faman rafka salati,haushi ya kara kamata tace kai fa ka iya rainin hankali rungume fa muka ganka da wannan bakar yarinyar amma dayake ka iya duniyanci sai ka nuna ko a jikinka ita kuma tana wani kikkifta ido dama an saba da bin maza ai ka kyauta a kunnan uwarka in ni ka raina ni ka gamu da uwarka,ta juya fuu!sai kawai ya daga kafadunshi gami da fadin ke ya shafa ya juya ga sauran kannanshi uban me kuke jira?cikin sauri suka juya kowa yana yar kunkuni Amarya kadai suka bari tana faman rafsa kuka,ya saki hannu na yaje gunta ya dafa ta yana mata magana,ban dai san me yake ce mata ba, na san dai ba zai wuce lallashi ba har ya ciyo kanta ta fada jikinshi ya rungumeta ganin haka sai kishi yataso min kirjina yasoma nauyi sai na dauki Gwaggwarona da ya fadi na tafi cikin takaici,na dubi wayata da take ta faman ruri a kan teburin robar dake gabana,ban dauka ba bare naga kowaye har ya tsinke,zaune nake kamar gunki ina tunanin rigimar da za'ayi idan zancen nan ya isa kunnen Haj Yaya?sannan in mama taji cewa yaynmu ya rungumeni na ma kasa komawa cikin hall din,kukan wayar nema ya kuma dawo dani daga tunanin da nakeyi cikin rashin kuzari na yunkura na dauki wayar,sunan Mami na gani akan screen din na dauka ina fadin ya dai Mami?tace yaynmu ne yake nemanki,na danyi tsaki gami da fadin me zaiyi min?ni fa ban son a dameni,tace sai ki kirashi ki tambaye shi ni ban sani ba,ta kashe wayar nasan taji haushin tsakin da nayi mata ne Assalam ya yar kyakkyawa na zauna?da sauri na juyo Adams ne nayi ajiyar zuciya sannan nace zauna mana ya zauna gami da fadin ya kike zaune anan ke kadai,nace na gaji da hayaniyar ne shi yasa na fito nan,yace is good nima na nemeki ban ganki ba gashi bani da numbarki so daga baya sai nayi tunanin fitowa shine na fito gashi nayi sa'a baby tunamin sunanki,Amina sunana amma Iman ake ce min ya gyara zama sannan yace sunan yayi min duka biyun yanzu ya maganar mu?nace wacce maganar kenan fa?yace ina sonki gane nifa ina sonki kuma aure ki sannan zaki yi krt ki a England domin can zan tafi dake ki yarda dani Iman ni mai sonki da dukkan gskyta ne,dubanshi kawai nakeyi dan gayan black beauty ne idanunshi masu kyau salon maganarshi da yan da yake kiran sunana sai ya kara burgeni kuma na ji zan iya yin uwar daki a rashin uwa wato zaniya auran shi a rashin yaynmu....ya katse min tunani look Iman bani zuciyarki in dan shiga nasan zaki soni lokaci kadan ba mai yawa ba am yar kyakkyawa kinji?ya kura min ido nayi dariya shima sai dariyar ya keyi,nace kaci gaba da neman fada gurin yayanmu yanxu in yace ya yarda na aureka ni a gurina ba matsala yayi shiru na yan dakikai sannna yace nafiki sanin waye Maska din don in yace abu baya canjawa ni dai zan nemi so gareki tare da yardarki kuma tun da na ganki jikina ya bani kece madam dina da na dade ina nema ashe tana Nigeria,dariya ya bani sosai muna ta hira bamu ankaraba jin hayaniyar mutane mukayi ashe har antashi,yaya kabir ya maida mu gida bayan munyi sallama da Adams akan sai gobe,kafin lokacin kamun Amarya tuni lbr ya bazu yaynmu ya rungumeni na idar da sallar ishai mama ta kirani wane lbr naji ana faman riritawa a gidan nan,cikin in ina na gaya mata abinda ya faru amma bance mata ya rungumeni ba ce mata nayi don ya kirani zai bani sako ko sakon bai riga ya fada min ba sai gasu haj laure shine suke ta surutunsu mama tace ance wai har rungume ki yayi?cikin sauri nace aa bansan wannan ba shiru na dan lokaci sannan ta juya ta fita,washe gari da safe misalin karfe tara ina ta faman yiwa mama gyaran daki ita kuma tana dakin Alhj tana mishi gyara kasancewar yaune daurin aure,karar wayata na juyo daga dakinmu na nufi dakin sai muka hadu da Jamila zata kawo na amsa ina fadin Jamila har ynxu baku wuce haddar ba,ina sagir? tace gashi can yaki yayi sauri ya saka kayan tacigaba da cewa anty don Allah dama mu zauna kinga yau fa bikin yayanmu daidai lokacin dana kara wayar a kunnena nace to anki din maza ku wuce Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Hello yaynmu ne yace kina jina nace eh yace ban fa karya ba bayan haka ina son ki hada mani kayana guri daya kin gane?nace wanne kaya?yace ki dai sama min abin da zan karya tukunna in kin zo sai ki gansu nace to,bayan na gama sai na fito kamar munafuka don tun jiya da abun nan ya faru ban fito ba tun da na shiga daki,ina kicin ina hada mashi breakfast sai ga mami tace wai shin jiya mai ya faru ne?naji wasu surutai itama yanda na fada ma mami haka na fada mata tayi tsaki sannan tace shine aka canza magana surutu kala kala ana tayi ba dan Baba ya taka borki ba da sai anyi rigima,gabana ya fadi nace waye ya gaya ma Baba wannan lbr?tace oho kila yaynmu ne dan sun rasa wanda ya gaya mishi. Nayi sallama a dakinshi da tire a hannuna shi kadai ne zaune kan kujera na ajiye tiren sannan na gaisheshi ya bude kula me kika kawo min?nace gashi nan dai duba,yace to sauran ki hada min kayana nace wane kayan?yace gasu can kinsan yau zanyi kaura shine nake aon insa kabir ya kai min kayana haushi ya kamani ban ce komai ba na shiga dakin a raina nace me shegen zumudin tsiya kawai,ba karamin gajiya nayi bada hada kayan nan akwati hudu na cika banda wata jaka babba wasu kayan ma ina ganin bai taba sa su ba,yawanci kananan kaya ne manyan akwati daya na cika ga kuma sauran nan cikin durowar kayan shi itako babbar jaka duk JC ne da sauransu,na gama ina shirin fitowa naji sallamar Haj yaya can cikin falon ya amsa sannan ta shigo tana fadin kai da waye naga takalmin mata? gabana ya fadi a sauri na shige bayan labule na boye ya amsa mata da cewa ni kadai ne ta leko bedroom din tana fadin wannan kayan fa?yace ina shirya su ne don inason kabir ya kai min can gidan yakubu avenu,ta karasa shigowa cikin bedroom tana fadin matsalarka kenan baka son manyan kaya sai aukin dinkasu tazo kusa dani ta tsaya tana kallon kayayyakin ni kam jikina rawa yake a bayan labule gashi bata magana a hankali don tunda dama haj yaya mafadaciya ce don haka ko maganar arziki takeyi sai kaji tamkar tana fada ne,Yayanmu yana tsaye a bakin kofa yace Haj menene kike nema ne tace magana zamuyi yanzun maganar kayan nan fa ba kace komai ba?yace kaya gasu nan ki diba dama inason rage ma kabir ne don sun min yawa sosai kinga fa ko abikin nan Nasir abokina set ashirin ya dinka min kuma duk acikinsu ba yadin dubu goma sai sama da haka Haj tace ina ruwan Nasiru, ta cigaba dama zancen da nake son in maka akan abubuwan da kake yine,so nake ka gaya min menene tsakaninka da yarinyar nan Iman?ta kuma daga murya iye kai nake tambaya duk iskancin da kakeyi fa ina sane kar kayi zaton ban sani ba ina daga kafa ne kai amma naga alamar sai na warware ka naci mutuncinka ko na tozarta ka ko?sai sannan yayi magana haj tsaya ki jini ya shigo shima zo muje falo miyi wannan zancen don Allah ta bishi suka fita tana fadin nidai ka fita hanyar su bana son hulda da Habiba da ahlinta yace Haj zauna suka zauna duk da kasa kasa yake magana ina jiyo shi daga inda na sandare don na tabbata in har tasan ina dakin kashi na sai ya bushe,yace Haj kin ga yarinyar nan tana dawainiya dani tunda na dawo garin nan abinci gyaran daki aike bafa biyanta nake yi ba sannan......ta katse shi,don Allah ni rufa min bakinka baka da kannan da zasuyi dawainiya dakai?yace to Haj su wadannan yaran me suka iya?sam yarinyar nan ta fisu iya komai......ta kuma katse shi tunda an baka kaci kasha an baka cikin abinci ka kiyayeni, rannan aka ce min ka dauketa cikin motar ka, kaf gidan nan baya ga Kabir wa ya taba shiga motar?ko ni nan da na haifeka ban shiga ba na biyu kaimata dinkuna masu tsada ba kaima yan uwanka ba don wulakanci kuma sai ka ringa masu anko da matar da zaka aura,sannan jiya har cewa akayi ka rungumeta ko ba haka akayi ba?cikin daga sauti yace inji wa?Haj ki daina jin irin wannan surutan da shiri ne maganar shiga mota ta kuma kasuwa muka je ta siyo kayan abinci da aka shiryawa abokaina da suka zo daga England suka sauka gida Nasir,dinki kuma yana da kyau ka kyautata ma mai kyautata maka sannan ni ban wani rungumeta ba duk surutu ne,tace su Haj Lauren ne suke maka surutu ne?yace to in banda abun Momi mene nata na zuwa gun lunchn abin yara tsakani da Allah...ta katse shi to ni ynzu magana ta ta karshe shine ana gama bikin nan ka tattara matar ka ku tafi England,ya danyi shiru sannan yace Haj mai ya kawo maganar tfy da mimi,kinga fa ba gida ke gareni ba a hotel nake ya zan kai matar aure hotel?tayi tsaki zancan banza ne kakeyi ba zan amince ba kaje da ita ku zauna a hotel din tare ta ahiga faa don kar ya soma magiya ni zaka gaya wa zancan banza?bari kaji wllh wllh ba ka isa in maka kaffara ba tare zaku tafi in kuma zaka nuna min cewar ban isa bane to ina jira ta numfasa sannan ta cigaba hankalina zaifi kwanciya in kuna can bata jira yayi magana ba ta fice abinta ya bita a baya don Allah haj ki min hakuri mana,ko sauraronshi batayi ba jikina sharkaf da zufa na fito daga bayan labule a gefen katifa na zauna ina maida numafashina sama sama idona sharkaf da hawaye ba wai ina kukan cin fuskar da tayi min bane a'a ina kukan tafiyar da zasu yi,don ina ganin in har ya tafi da ita ni kuma shi kenan ba zan dinga ganinshi ba zanji muryarshi ba ba xanji kamshinshi ba,tsaye yake bakin kofa yana dubana ya shigo tashi ki shiga ciki share hawayenki kinji karki damu wata rana sai lbr cikin sanyin murya yake magana na mike ya matsa min na wuce. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yau asabar tara ga watan sha daya aka daura auran yayanmu da anty mimi a kofar gidansu dake Malali daurin auran ya sami halartar mutane da dama cikinsu harda matasa sun mafi yawa kasancewar shi fan kwallone sunyi walima bayan daurin aure kamar da gayya nice mutum ta farko da ya fara kira yace min an daura auran a raina nace to ni ina ruwana amma a fili sai nace Allah ya sa alheri,yace me kikeyi?nace ba komai ina kwance yace kin san yau akwai dinner don haka ya kamata ki zama cikin shiri nace ina jin fa ba zan samu zuwa ba don kaina yana min ciwo bayan haka ga rigima nata faruwa kasan ma jiya banda Alhj ya sa baki da rigimar nan bata kasu ba don haka ina jin ba zan samu zuwa ba,yayi shiru yana son yayi sallama amma bai gaji da jin muryarta ba ya kan so tana magana yana kusa shidai baya gajiya da kallonta shi dai ya san yana sonta kuma yasha alwashin in dai yana raye sai ya aureta duk da karancin shekarunta,nace hello danaji shirun yayi yawa yace Iman kin sha maganin ciwon kan?nace eh a takaice yace kin gane ina son gsky kije wurin dinner din nan in kinji kan naki yayi sauki amma ba dalilin wani shirmen fada ba can kin jini?nace in Mama ta hana fa?yace ba xata hana ba zan mata waya nace to sai anjima Amira dake gefena ta dubeni tace ke da wanene haka a waya,nace yayanmu ne Amira ta zuba min ido cikin tuhuma tana cewa anya wannan yayan naku bashi ne gayan nan da kike boye mana ba?na dubi Amira cikin rashin gsky nace haba dai Amira ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi tace Iman bai kamata kina boye mana sirrinki ba musamman irin wannan kina bukatar mai baki shawara sannan mu sai mu dinga kwashe sirrinmu muna fadi maki duk zurfin cikin fulani bana boye maki sirrina amma ke sai kiyi ta nuku nuku,nayi shuru tabbas zancen Amira gsky ne sai dai ina jin nauyin ce mata ina son yayanmu ne dama dai muna yin soyayya ne shi ne amma fa nice nake haukana bai ma san inayi ba,ta yunkura zata dauki hijabi tace daina tunani Iman ban fa ce lallai sai gayan matsalar ki ba ni kin gama tfy ta da sauri na jawo ta muka kara fadawa kan gado,sorry Amira zakiji ta zauna kusa dani sannan tace kin cika abin haushi ne Iman,na nutsu sannan na soma bata lbr sanda na soma son yayanmu nace wllh Amira da ban yarda wai ina sonshi bane na dauki tsoron da na keyi ne yasa na kanji muguwar faduwar gaba a duk lokacin da na ganshi sannan jikina ya shiga kyarma ashe wai duk so ne hawaye ya soma zubo min Amira nayi adduar nayi addua tamkar ina kara zuga son nayi kukan na tsine ma SO,so ko wahala nasa Allah ya isa ga duk wanda yace so na da dadi don nidai cikin wahala nake da kunan rai na soma kuka mai sauti nace Amira ni so bai min adalci ba sona da ya tashi ya kaini inda Allah bai kaini ba zuciyata ta kamu da son wanda yafi karfina na tsaya ina jan ajiyar zuciya Amira batayi min magana ba ta barni nayi kukana mai isata ba ta hanani ba bata fara magana ba sai da nayi ya isheni sannan nayi shiru ta soma magana ki bar kuka kuma kib bar zargin zuciyarki da ganin laifin tsuntsun sonki sannan ki daina cewa ya kaiki inda Allah bai kaiki ba gaya min dalilin da kike ganin cewa yayanmu yafi karfinki,nace na farko ba sona yake ba nayi ajiyar zuciya sannan na cigaba ni ba ajinshi bace sannan ga rashin shirin da ke tsakanin uwata da tashi ba zasu yarda mu auri juna ba koda yana sona bare ma bai taba son ba Amira tace niko ina ganin kamar yana sonki abinda yake maki yafi karfin kyautatawa sai dai SO,nace banyi tsamanin ba shi da yake fadin ba zai auri karamar yarinya ba a gabana yasha fadin wannan zancan ke ko abokanshi sunsha cewa suna sona sai ya hau su da fada gami da cewa shi baya son raini basu san in suna cewa suna sonmu ba zamu raina su ba?na dubi Amira na cigaba da cewa kina ganin asir abokinshi da yake son mami in da yabi ta yaynmu da bai nemi mami ba a gabana wata rana na kai musu abinci naji yana ce ma Nasir mai zaiyi da mami yar cikinashi dan dai rashin sawa kai girma gun kananan yara,ga manyan babys a gari zai ce sai Mami wadda a haihuwar kaji ya haifeta sannan kice zai soni?bayan mami tama girme man da kusan shekara daya,Amira tace to adduar dai zamu cigaba dayi sannan zamuga shawarar da zamu baki ni da Mami sai in mun zauna nace kar mu gayawa Mami,Amira tace dole ne Mami taji zancan nan don bamu boye ma juna sirri kin sani sarai dama ke ce mai mana nuku nuku kuma mun sani mun dai kyaleki ne nace ni dama don ga cewar yayanta ne shi yasa Amira tayi tsaki sannan tace dole ne Amira ta sani nace aishi kenan, mukayi shiru na dan lokaci sannan nace ynxu ma shi yayi man waya wai na shirya muje dinner anjima nifa da bana son zuwa Amira tace me yasa ba zaki je ba?nace ban son abinda ran mama zai ta baci a banza amma shi cewa yayi fadan da akeyi ba dalili bane da zai hanani zuwa,Amira tace su mami ma da kyar in zasu don naji suna cewa yaynku yace kar ya gansu a gun,nace to nima kan ba zanje ba Amira tace wllh sai kinje ai ta haka ne zaki samu ki cusa kanki gareshi kin gane shiga zakiyi ta alfarma ko ba haka ba shi fa da kanshi yace kije nace cewa yayi ma zai sa azo har gida a daukeni don ban ma san gun da za'ayi dinner din ba Amira ta mike tana dariya gami da cewa kune manya a gun. Na dubi kaina a madubi sannan nace kai Allah ya saka ma telolin shagon yaya sulaiman da alkhairi ganin yanda na fito cikin dinkin da ke jikina material ne blue mai filawoyi fari da bakake ga stones suna kyalli nasa sarka da yan kunne fashion blue jaka ta da takalmi karamin gyalena fari ina cikin fesa turare ne wayata ta soma ringin na duba yaynmu ne na dauka kin shirya ne? tambayar da ya soma yi min kenan,na shirya na ce cikin sanyaya murya ya dan ja numfashi to fito waje na ga kwaliyarki kafin in wuce kinsan fa ni zanje can ne mu tafi tare da mimi nace to amma raina nace ina ruwana in ma da mamanta zaku,ya kashe wayar na dubi agogo takwas da rabi na dare nace anya mama zata barni na tafi kuwa mami ta shigo dakin itama cikin less fari tayi kyau nace zakije ne?tace zanje kinsan nasir zanbi nace yawwa har naji dadi tace su Bilki da Sa'a da kyar ne zuwansu amma suna dai can gidan amarya nace har an kaita ne?mami tace an kaita mana daga can zaa dauketa nace mami mamanmu na falo ne?ina son fita bana son ta ganni zata iya cewa na koma dare yayi tace aa bata nan shigowata na ganta da tire tayi sashin Alhj nace yauwa dama yaynmu ne yake kirana nayi kyau mami banji kin yaba ba mami tace kinfa hadu wllh nace nagode,bari naje daga can fa zan wuce sai mun hadu don nima Nasir yace yana hanya sai yazo nan ya daukeni sannan yaje ya dau sauran kawayen Amarya,muka fito a tare tana fadin gara nayi damadama da abuna kada inje wata ta kwace min an ganni yar yarinya mukayi dariya muka tafa kowa ya kama gabanshi,nayi waje ita kuma tayi dakinsu jiran Nasir dinta,na dubi motar da ita kadai ce a harabar gidanmu ban san motar ba na dan tsaya nesa da motar ina ta dube dube to ina yayanmu yayi ne? din din naji hon daga motar gun motar na nufa ba dama kaga na ciki ya sauke glass din motar sai da jikina yayi yarrr yanda na ganshi yayi masifar kyau kyanshi ya kara fito tamkar shi yayi kanshi ya bude min mazaunin gaba,shigo kawai yace min sannan na shiga wow wani kamshi da sanyi baa magana motar sabuwa ce dal,bai min magana ba muka fita munyi tfy sosai ba tare da yayi min magana ba sai wakar mutuniyarshi wato celine dion ke tashi a cikin motar,can wayata ta soma ringin a jaka na ciro ta mama ce,gabana ya fadi na dauka mama tace cikin tsawa ina kika fita yanzu?wurin dinner fa zamu tafi,wa kika tambaya nace don Allah mama kiyi hakuri tace karfe nawa zaku dawo?wllh ban sani ba,to ki kula da kanki ki tsare mutuncinki kinji ko?nace to mama in Allah ya yarda zan kiyaye,tace to don gsky da ina dakin ba zaki fita ba,tara saura sai yauamsh za'a fara bare a gama nace kiyi hkr zamu dawo da wuri,ya juyo ya dubeni bayan na gama wayar sannan ya dauke ido yamai da kan titi sannu a hankali ya tsaya a gefen titi ya kuma dubana kinyi kyau sosai nayi murmuahi nagode,ya zuba min ido ni kuma na kasa dubanahi sai dai wani farin ciki da nake jin shi yaja wani dogon numfashi sannan yace Imman!...ya ja sunan tare da kama hannuna wani irin yanayi mai wuyar fassara na shiga ban taba jina cikin irin wannan yanayin ba ya dan murza min yatsuna sannan ya tsare ni da ido tare da fadin baki amsa min ba na kira sunanki iman nace umm....ya cigaba dan Allah iman ko bana nan kada ki tsaya harkar samari ki taimakeni ki cigaba da karatunki kinji?ki barni na zaba miki miji dai dai da ra'ayinki wanda kike so shima yake mutuwar sonki kinji little sister di ta,wani haushi ya kamani na zunburo baki a raina nace dama nasan ba wani sona yake ba Amira tace min ta ga kamar yana sona ne,ya kai yatsansa kan lebe na ya dan buga kadan sannan ya ce kina da wanda kike so ko?nace a'a cikin kulewa da shagwaba kamar zan yi kuka yace to menene na jin haushi umm?na kara turo baki gami da girgiza kai. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 kafaduna ya dafa,ina kyafta ido sai ga hawaye,kawai ji nayi ya jawo ni ya rungume wai yana lallashina,sorry my sister bar kuka,kan uba jina cikin kirjinshi sai na manta duniyar da nake, kai SO! ba dama ne,duk da na san bai kamata na biye mashi mu hada jiki ba amma sai na kasa janye nawa jikin,cikin taushin murya yace kince min,zakiyi krtn ko?ban motsa ba ya cigaba na san kina kokari da hazaka ki gyara paper ki wannan shekaran kinji ko?karki damu da maganar aure yanzu barshi nan da shekara biyar nan gaba,ya dago ni daga jikinshi yasa hannunshi ya rike fuskata yana duban idona hawaye na zuba, idonshi cikin nawa yake kallona,kin min alkawari zaki yi krt ba sauraron samari?na rintse idona dan ba zan jure kallonshi ba sonshi sai ya kasheni a raina nace ni ba wani krt da zanyi tunda kai kayi naka auran ko menene matsalarshi da karatuna?me zai karu cikin krt oho?kamar yasan tunanin da na keyi sai naji ya ce karki yi tunanin ina ruwana cikin harkar krtn ki akwai dalili kin gane bance komai ba ya sakar min fuska sannan ya bani hankici gashi share hawahenki na karba shi kuma ya anshi jakata yace nasan ba za'a rasa yan kayan shafe shafe cikin jakar ba ko?ya dubeni ko babu?nace akwai yace ni kike wa magana kina yanga?daidai lokacin ya cire sinkin hotunan jiya menene wannan?bai jira amsa ta ba ya cigaba da kallon hotunan yana cewa kai mun yi kyau amma duka nawa ne ni dai kallonshi nake kawai na gyara fuskata sosai shi kuma ya bude wani aljihu yasa hotunan sannan ya dauko wayarshi yana fadin bari na kunna wayar nan na san za'ayi ta nemana a jita a rufe shi yasa nabi wayoyin na rufe, ni sai mamakinshi nake yi kamar ba shi ba, ya dubeni zaiyi magana wayarshi ta soma ringin ya dauka hello Nas yayane?ina juyo muryar Nasir na fadin Maska kai wane irin dan iskan mutum ne kana duba agogon ka kuwa?kasan ynxu tara da rabi kai fa kace tara daidai ba African tym shine ynxu dan iya shege daga dauko mota sai miji ka shiru kama kashe wayoyi,to ka samemu a wajen dinner domin har Amarya tana gun,yayanmu yace ni ake jira kenan yace eh mana kai kadai muke jira Amarya bata shiga gurin ba gata nan a mota sai ka iso ku shiga tare,gani nan yace sannan ya kashe ya ja mota muka tafi,ya dubeni kece mutum ta farko da ta soma shiga motar nan, naso Mimi ta soma shiga sai gashi kin mata shigar sauri kin shige mata mota sannan hotonki shine na farkon zama ajiya cikin aljihun motar kinsan ko a kannena kina da babban matsayin da kannena basu taka ba, nayi murmushi sannan nace nagode,muka isa gurin ya ajiye motar ya fito yana neman Nasir a waya can ya sameshi Nas na iso kuna daidai ina ne,yace gamu na bayanka kai baka ganmu ba,ya dubeni to fito Hajiya,na fito daidai sanda Anty mimi ta fito daga motar Nasir muka dubi juna ni da ita, shadda galila tasa dark green shima yaynmu ita yasa ankon kenan sukayi tayi kyau na fitar hankali ta sa sarka kirar dubai ga ashoben da aka sa mata a kanta ya dauru gashi har kan kafada duk sai naji na raina kaina,ganin ta daure fuska kuma tayi fushi hatta Nasir na kula yayi mamakin ganinmu tare,shi kam gogan ko a jikinshi ya isa gurinta madam kin jirani ko?sorry zo muje ana jiranmu ya kama hannunta muka bisu ni da Nasir sauran abokan ango sun taryi Amarya da Ango,wuri yayi wuri kowanne teburi mutum hudu mata biyu maza biyu,Amarya da Ango su biyu ne a gunsu mu kuma mu uku ne ni sai Mami sai Nasir,can an soma ciye ciye sai ga Adams bansan ta inda ya fito ba sai ganinshi nayi ya dubeni,yar kyakkyawa ina kika shiga ne yau duk banganki ba?kafin nayi magana ya juyo gun Nasir Assalamu alaikum abokina ai min afuwa 'yar kyakkyawa ta tsone min ido bana ganin kowa sai ita yace to ai shi kenan tunda ka ganta ynxu sai mu gaisa waalaikassalam,mu kayi dariya sannan ya zauna bakici komai ba yar gidana ya miko min cinyar kaza saitin bakina ci wannan mana na kauda kaina sannan nace a'a Adam bana cin komai juice zansha,yace sha mana ko na danji sanyi kinga Nasir yasa yar gidanshi a gaba sai ciyar da ita yake ba ruwanshi dake,Mami tayi dariya tace to tunda ynxu kaxo ai sai ka bata yace to ba gashi taki ci ba na fa dade ina kallonki naga shigowarki tare da Maska da Amarya na dubi gun yayanmu ga mamakina duk hankalinshi na gurin mu ya cika yayi fam tamkar ya fashe Adams ma ya dubeshi yace yar gidana kin ga yanda Maska ke faman hararata?nace to ya maka kashedi kaki ji ba?Adam kana son bata ma kanka lokaci ne kawai yardar yayanmu shine tawa,Adams ya dubi Nasir yace Nasir yi mana sharia,Nasir yace ina jinku,naga yar kyakkyawa ina so ina ruwan yaynsu,Nasir ya nuna mami yace baga yar gidana ba da muka shirya kanmu dole ya barmu,Adams yace to shi ne ta kasa ganewa tabbas in kin yarda na san halin Maska in har yace yes baya yarda yace no kin gane?so in har da gaske kike sona zan aureki kuma zakiji dadi sosai yanda nake jinki a raina, ko! na dubeshi,yace ba sai kin sha wahala wajen zuwa gurin malami ba zaki mallakeni son ranki,Allah sai yanda kikayi dani na rantse miki,na soma dariya shima yana dariya mami suna ta hirar su suma yace a makaranta wane matsayi kike son ki taka? Masters ko Degree ko Professor kikeson zama?zan barki da karfina da Aljihuna burina dai ki aureni ki haifamani yara masu kama da ke har da wannan dan dimple din naki, ya kai hannu zai taba min kumatu na goce ina dariya,sai yaynmu na gani akaina sai huci yake yace tashi a kaiki gida sha daya yayi ,nace yaynmu ka bari a tashi mana mama tasan wannan kuma zan kula da kaina......,ya katse ni tashi ko na mareki,tsoro ya kamani na soma kyarma adams yace Maska ya zaka ruda tane haba.....shima ya katse shi please Malam yi min shiru kajiko,na nuna Mami ga Mami ma nan yace ni na kawota?wanda ya kawo ta shi zai maidata na mike ya dafo min baya har gurin motoci,shiga nan ki jirani tunda ke bakya jin magana,kin je kin saki baki kina faman yi ma Adams dariya zanyi purnish dinki,ya rufe motar da karfi ya tafi.haka na zauna shiru can da na gaji ga wuri yayi shiru sai sautin kidan can gurin dinner kawai sai na kira wayar mami nace wai yayanmu fa?tace gashi can wurin Amaryar shi suna zaune suna hira nace to na kashe wayar duk haushi ya isheni nace wato shi yana can yana hira da matarshi ni kuma ya hana ni neman miji ba wani jiranshi da zanyi tfy ta zanyi abuna wato ga mai gadi! na soma kici kicin bude kofa abin haushi sai na kasa hala kulleni da key ne in ba haka ba na jijjiga murfin ko motsi baiyi ba na kari masifa ta nakoma na zauna na hada kai da cinya na matse nayi shiru,har misalin sha biyu da rabi ni lokacin ma barci ya soma dauka,ta ban ankara ba naji an bude motar an shigo dan ma baccin nawa a dar dar na keyinshi kun sanni da shegen tsoro sai na kware baki zan tsala ihu sai naji an rufe min baki gami da cewa shishit!,ya kunna wutar motar duk da naga yaynmu ne har ynxu jikina bai daina bari ba kin cika tsoro Iman saidai kin fi burgeni in kina cikin tsoro idanuwanki su kan birgeni ya kai yatsansa saman idona na lumshe ido jikina yana wani irin tsuma saboda yanda yake sosa min saman idona ya janye yatsansa sannan ya daure fuska ya dubeni yauwa dazu me Adams ya ce miki kike dariya?nace ba komai yace karya kike yi zan gaya maki abinda ba ki sani ba shi kike so ba kuma ba zaki aure shi ba,kafin ya rufe baki wayata ta soma ringin shi ya rigani daukan wayar yana duban sunan sai yaga ashe mama ce sai ya bani na karba gabana yana faduwa,Iman yayi maki kyau kinji ko,nace dan Allah mama ki yi hakuri yanxu zamu dawo yanzun nan fa aka tashi tace bana ga mami ta shigo ba ynxu nace to ai ni yaynmu ne yace tunda shi ya kawo ni zai maidoni ya min magana a hankali yace kice mata kuma na tsaya sallama da mutane ne,tace to kiyi sauri sha biyu ta wuce banda ma bana dakin kika fita da babu inda zakije ta kashe wayar,na dube shi yayanmu ka kaini gida ni mama ke jira dan na san itace da girki zata sashen Alhj shi yasa yayi wata yar dariya to bari mu tafi kar Alhj na yayi ta jiran mamanki gashi kuma na tsare ki anan yana magana da wata fassara ne na kula sai na kauda kaina gefe,ya tada mota yace yauma gidanku zan kwana ance wai sai gobe zanje gidana suna son yi mata budan kai gsky sun bani haushi menene kuma budan kai?nace nima ban sani ba a raina nace me ya dameni da zaka dameni dube shi kawai, wayarshi ta soma ringin daidai sanda muka tsaya a harabar gidanmu zan bude na fita naji ya jawoni ba tare da ya min magana ba ya dauki wayar na ji yace Alhj Iman gata nan na kawo ta kome Alhj yace mashi sai yace to ynzu zata shigo,ki shiga Alhj na jiran matarshi nima zan shiga daki ne na kira tawa a waya dan kece kika hana na maidata gida sai dai Nasir ne ya kaita,cikin mamaki nace ni?da yaushe nace?yace au baki ma san san da kikace ba ko?to shi kenan sai da safe ya bude min na fita ina dubanshi koda yaushe na ce kar ya kai matarshi oho?yazo ya min sharri kawai. Washegari budar kai da safe nice nayi musu abincin breakfast musa dryva ya kai musu gidan Nasir,da rana ana tafiya gidan Amarya ni kam ban fara ba don nasan magana zai zama kai na gurin Amarya ko ince tamkar naje neman fada,da daddare muna zaune a dakin Amira ni da mami,nan mami ta sameni gidansu Amirar mami na bamu lbr tsaruwar gidan,nace dama shi yaynmu ai dan gayu ne sannan ya saba da rayuwar turawa kinga kuma dole ne ya tsara gida na yan gayu,mami tace gashi kuma da kudin ba,Amira ta dubi mami dama akwai zancen da zamuyi dake,nan ta kwashe maganar son yaynmu da halin da nake ciki ta gaya ma mami,mami ta cigaba da mamaki dama yaynmu kike so Iman?gabana na faduwa hawaye na zubo min wllh mami kinji halin da nake ciki kenan,tayi shiru dan lokacin sannan tace to sai dai muyi ta addu'a amma Haj Yaya da Haj Laure basu da kyau in ma kin shiga gidan ba zasu bari ki samu kwanciyar hankali ba sannan shi kanshi yaynmu a irin ra'ayinshi baya son karamar yarinya yafi son babba nace na sani Amira ta ce ni kam sai naga kamr sonta yake yi nace ke ba wani so jiya kinji yadda yake min zancen matar shi dan haushi ni ko kula shi banyi ba. Mun tsaida shawara akan cewa zamu tsananta addu'a kawai Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Amira ta rakomu har gida dan zata karbi littafinta a hannuna dai dai dakin yayanmu abokanshi ne sun sha kwalliya sai kamshi sukeyi mami ta dubeni yau za'a kai angonki gidan amarya na dubi wajen sannan nace to ni ina ruwana ,dai dai nan Adams ya fito shima sanye da waganbari blue ammy sky yace Iman na juyo ina duban shi amma gurin na tsaya,yazo yau duk bangankiba yar gidana ina kika shiga ne?ina nan banje ko ina ba na fada, su mami suka gaisheshi yace mami ko?mami tace eh yace kefa?ya nuna Amira mami tace Amira yace nice name,suna ta surutunsu ni ko hankalina na can gurin ganin ango ya fito sai ko gashi yasha kwalliya da wani farin yadi mai shara shara fari tas komai fari yasa har glass ban taba ganin yasa glass ba sai yau yayi kyau har ya gaji,takaici da kishi ne ya kamani raina ya sosu sosai na zuba mishi ido duban shi kawai nakeyi ba mamaki ganin karshe ne nake mishi dan yanzu ba gidan mu daya ba bani zan dinga dafa mishi abincin ba ba zan dinga dafa mishi lipton da daddare ba ba zai aikeni ba bare na mishi gyaran daki sai dai anty mimi bayan kwana kadan kuma su tafi England shi kenan nayi rashin yayanmu,nayi zurfi cikin tunani ban san su mami na min magana ba sai da suka dafani nayi ajiyar zuciya na dubesu yayane? Adams yace don Allah ki daina irin wannan tunanin wai ma tunanin me kikeyi?ban ma saurareshi ba na juya ina duban yaynmu ya shiga gaban motar Nasir,Nasir ya iso gunmu Adams zo muje mu kai angon can tun kafin ya kai kanshi,sai masifa yake mana wai in ba zamu je ba ya tafi abunshi,hankalina ya kuma tashi na juya nayi gida na barsu a nan mami da Amira suka shigo, kuka riris suka sameni ina yi dukkansu sun tausaya min tare da bani hakuri sunce na ringa danne kishina a gaban mutane dan kar suni,cikin kuka nace ba zan iya ba dan wani zazzafan so nake mishi ga mugun kishin shi dana ke fama dashi ku tava kirjina kuji ji nake kamar zai bude dan azaba kun san Allah Amira ko mimi bata kaini son yaynmu ba,sai dai tabi bayana,sun zubo min ido suna mamakina daga baya suka koma bani baki gami da kwantar min da hankali suka ce nayi shiru kar mama taji,nayi tsaki sannan nace ynxu bana shakkar kowa ya sani yanda nakeji ni kadai na sani nan dai suka dan lallasheni suka tafi.. So masifa ne yanda naga rana haka naga dare sai bayan nayi sallar Asuba sannan barci ya daukeni nannauyan barci mai cike da mafarkai kala-kala,mama ta tasheni karfe bakwai tayi lokacin da ciwon kirji mai karfi na tashi hankalin mama ya tashi sosai ta yiwa Alhj waya yana dakinshi sai gashi yazo,yace shirya ku je Rimi Clinic zan sameku ina yin wanka mama tace kodai a siyo mata magani a chemist?Alhj yace a'a ku daije in ciwonta ne fa kinsan da kirji yake farawa sannan ta suma ku dai tashi kafin suman yazo,ko wanka banyi ba muka tafi bayan mun ga likita ne sai ya bani gado raina baiso ba amma dole na kwanta an min allurai na samu bacci ya daukeni da sauri ba ni na farka ba sai wurin Azahar mama ta rike min hannu tana min sannu,na yunkura na tashi har yanxu saitin zuciyata bai daina zugi ba,da taimakon mama na samu naje bayi bayan na dawo ne na samu likita ya shigo zai dubani daidai lokacin yaynmu ya shigo shima suka gaisa da mama ya tambayeta jikina tacemashi da sauki,sannan ta fita likitan yace na kwanta sannan yace ya nake jin saitin zuciyata?nace da sauki sosai saidai yana min zugi har ynzu na dubi yayanmu da ya kafa min ido na kauda kai dan ni ko ganin shi bana sonyi,Doctor ya juyo gurin yayanmu yace yallabai tun safe nake neman ka a waya ban sameka ba ko da dai kana Amarci don Allah kayi hakuri na taso ka ko?yaynmu yace no ba komai matsalar ntwk ne shi yasa baki sameni ba,ya cigaba da cewa sanda kika yi min waya ina kan hanyar zuwa nan don Alhj mu ya sanar dani da na kirashi,likitan yace ciwonta yana barazanar dawowa da karfinsa abinda ya haifar mata ada ciwon ta sa wani abu a ranta sosai ta matsa ma kanta da tunaninshi gabanta yana mugun faduwa inta ganshi,ya batun da kai wancan lokacin? kasan fa sai da lallashi sannan zaku san matsalar ta,ku san kuma maganinta sannan muma namu aikin yayi kyau,yayanmu ya dubeni sannan yace kamar yanda na sanar da kai na san matsalarta fiye da kowa a gidanmu ita dai ta cika zafafa abu ne,bata son bin komai a hankali shine matsalarta,yaja kujera ya zauna kusa da gadon Iman!ya kira sunana na dubeshi har ynxu mamakin maganarshi nakeyi yasan matsalata?ke nan ya san ina sonshi?dan ni dai a sanina bani da wata matsala da ta wuce wannan.Anty yagana na shigowa Adams da mami da Amira suka shigo ya rusuna ya gaida mama taja Anty yagana suka fita,Adams ya dubeni ke yar gidana ya haka ta faru?nayi murmuahi sannna nace ikon Allah kenan Adams ba abin mamaki bane ko da mutuwa aka ce nayi,ya tsare ni da ido kar ki ja mon yar gidana karki min fatan mutuwarki dan ban san halin da zan shiga ba a raina naji zan iya auran Adams gsky ba zan tabbatar ma da yaynmu zancenshi ba shi kuma maye ne yake in har zai zauna da mutum sai ya san halin da yake ciki,Adams ya dawo dani daga tunanina kinyi shiru yar gidana ko jikin ne?a'a kadan kadan kirjina ke min ciwo su mami suka min sannu yaynmu ne yayi sallama ya shigo ganin Adams ya bashi mamaki sai naga ya dauke fuska a daure,hannu yaba Adams suka gaisa sannan yace dama naso daga nan gidan Nasir zan sameka muje ku gaisa da Amarya sannan mukai ku airport,ina su john suke?sun fita da Nasir nima ynxu naje sallama da yar gidana shine na samu su mami sukayi min bayanin tana nan sai mukazo amma fa ina ganin ba zamu tafi tare da su john ba,because of what?yaynmu yayi saurin tare shi da tambaya,Adams yace kana son sani ne?to saboda sister dinka yaynmu yace yana da kyau ka san su ma ta lagos zasu tafi dan haka muje mu sallamesu,Adams ya dubeni zan dawo yar gidana kinji ko?gira na daga shiko yaynmu harara ya sakar min ya wuce abinshi,mun jima dasu mami sannan mukayi sallama,sukan su yaynmu suna fita sai gidan Nasir inda rigima ta sarke tsakanin yaynmu da Adams yaynmu ya nunashi kai Adams kana mantawa da halina kasan fa in har nace no ba mai canja min ra'ayi ko?kasan haka kafi kowa ma sanin hakan amma kana bata ma kanka llokaci ne a banza,Adams ya dafa yaynmu Maska na maka alkawarin barin kanwarka akan sharadi guda biu na farko in tace bata sona na biu kuma in ka gaya min hujja mai karfi da ba ka son na nemeta ka fahimta?yaynmu yace don so bata sonka maganar hijja kuma babu kasan baka isa in maka karya ba baya ga tana da wanda takeso da na tsaya maka ka aureta amma ynxu am sorry to say bazata aure ka ba in kuma ba zaka bata lokaci ne to shi kenan,Adams ya kule Maska na gama sanin cewa kaima son yarinyar nan kakeyi tun lokacin da nasamu lbr ba dadynka ya haifeta ba,yaynmu yayi wata dariya mai kama da yake sannan ya dubi su nasir wayanda sukayi cirko cirkk suna duban abokan juna mafi kusanci da juna a england suna rigima a kan yar yarinya kamar yanda maska ke kiranta,kunji shi da wani magana kai kanka ka san in ina sonta baka isa ka nemeta ba bayan haka ba ni da ra'ayin auran kananan yara don bana son raini so please and please kabar maganar nan ma dan zamu iya rabuwa da juna,Adams yace and so what idan mun rabu?na shirya,Nasir yace dan Allah ku saurara haka kai Maska kayi hakuri mana tunda ka san ko shi wane ne in yana da wata matsala ne sai ka mishi bayani ga matsalar ka shi yasa kaga in da gyara sai ya gyara,yaynmu yace Adams yace namiji ne,bashi da wata matsala sai dai ya nemi matarshi a gaba Adams yace ai na samu yanxu kai kuma baka isa ka hana ba,Ok! zamu gani kana proud din baka taba neman abu ka rasa ko?to zaka fara akan wannan inji Maska,su John dasu Nasir sune suka bada baki kafin sukayi sallama amma banda Adams yace sai ya kara kwana biu,sun kaisu airport sannan suka wuce gidan amarya wacce ta cika fam da fushi,yaynmu ya dubeta madam kimin afuwa kinsan ina tare da baki yau zasu tafi ko shiyasa ya fada lokacin da yake zaunawa kusa da ita su Nasir da Adams ma suka zauna,ta dan yatsina fuska sannan ta gaishe su yace yunwa fa mukeji fa,ta dube shi baku ci binciba?ayya gashi nayi bakin kawaye momina ne ta rako su shine suka cinye Dukda,ranshi ya sosu amma bai nuna ba sai yace shi kenan kawo masu wani dan abin sha mana,ta mike tana karairaya Nasir ya bita da kallo sannan ya dauke kai shima irin matan nan basa birgeshi sam bata son mutane yaci ace yanda suke abokan Maska ace sun saba amma ita sai girman kai kamar yar wani da wata gashi daga gani za tayi rowa kai shi kyanta ma bata birge shi mace a bushe haka?fari ne da hanci kawai shi kuma bai ma cika son dogon hanci ba,tunanin shi ya katse lokacin da taje musu da robar ruwan Cway da kofuna,kunya ta kama yayamu ya dubeta ke ba wani mai dan zaki ne?bana yiwa Kabir waya ya kawo drinks ba?ta dan yatsina fuska zata tashi Nasir yace no yi zamanki don ni dam nake sai dai ko Adams, Adams da ya zuba tagumi yana tunanin Iman ya ce am ok nima a koshe na ke,sun dan yi hira sam ita bata sa masu baki ba TV kawai take kallo ko da zasu tafi ba tayi musu magana ba sai Nasir ne yace mu mun wuce,to kawai tace suka fita yayi masu rakiya ya dawo su kuma su ka nufi gurinmu a Asibiti. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Washegari aka sallame ni na dawo gida da kundurin cusa son Adams a zuciyata don haka duk sintirin da yaynmu yake yi bai burgeni ba duk da in har ina ganshi sai gabana ya fadi, kuma sonshi na nan daram a raina,daren ranar sai ga Adams ya zo mani sallama yana min bayanin dan dai zasu yi wani wasa ne a club dinsu kuma wasan yana da muhimmanci sosai da ba zai tafi ba gashi ba Maska bai kamata kuma shi ba ya nan ba,nace ba komai naji sauki kuma ga waya ai,ya ce to bani no naki in yaso in naje sai na dinga kiranki sannan ki bani tabbacin kina sona dan Maska ya gaya min kina da wanda kike so,haka ne?nace batun wanda nakeso dai bai taso ba dan babu sai dai game da kai,in mun waya zan sanar da kai ina jin kunya ne yanxu,yayi murmushi shi kenan yar gidana a zuciyata nace kunyar karyar da zan maka ne ya sa ba zan iya fadama baki da baki ba dan na san ba wani sonka nakeyi ba ne burgeni kawai kakeyi,kyautar wani kyakkyawan agogo da turare ya yi min nayi mishi godiya mukayi sallama sannan yace min idan ya sami sukuni zai zo ba da jimawa ba kuma jiya ya gabatar da kanshi a gurin Alhj,da sauri na dubeshi me yace maka?ya ce yace kar na damu gurin su manya ba matsala in dai sunyi bincike sun gano asalina a Ghana,nace yauwa Adams kana da yare ne?ya ce eh yace mu asalinmu fulanin yola ne yan Adamawa zama ne yakai kakaninmu suka haifi iyayenmu muma aka haifemu a Ghana,nayi karatuna duka zuwa Degree wasan kwallo kuwa ina primary nake zakara kuma ni ne babba a kaf gidanmu kanne na hudu maza da mata,matan babana biyu ne kuma har ynxu muna zuwa Adamawa kuma suna zuwa babana yana da sarautar matawalle dan haka duk salla familynmu a can muke yi ko ni in ina gida tare muke zuwa,kin fahimci takaitaccen tarihina? nace na gane yace to muna da yawa sai ki shirya in munyi aure duk sallah zamu zo daga England Adamawa zamu sauka haka nan in kin haihu a can zaki zauna ko in baby yayi kwari sai nazo na tafi da ku dariya nayi nace Adams kenan har ka tsara komai yace yes haka kullum nake mafarki nace to ba ka fadamin me kayi Degree a kai ba sannan cikakken sunan ka,yace nayi Degree akan,cikakken sunana shine Adamu Salisu Adamu, Abokaina su suka sa min Adams sai ya zama har JC na Adams suka samin kinji yanda abin yake,sai naji Adams ya kara bani sha'awa kuma zan iya kukutawa in aure shi,mun yi sallama dashi nayi mishi rakiya har wajen gate mukayi sallama akan sai naji shi a waya. Ni,Mami da Amira tafe muke kan hanyar mu ta zuwa kasuwar unguwar Rimi zamu raka Mami ne amsar dinki muna tafe muna hirar Adams,nace mami ni fa yanxu Adams kawai na tsaida ma zuciyata duk da na san cewa bashi ne zabin zuciyata ba zai fi min kwanciyar hankali,Amira tace na goyi bayanki Mami tace sam ba zata yiwu ba kina tunanin shi ba wata matsala daga dangin shi?sannan ba shi kike so ba in kika jure wani abu wani ba zaki jure ba musamman ma da yake ba shi kike so ba gara wanda kake so zaka hakura da wani abun albarkacin son nan shiko daban ne,nace Mami Haj Yaya da Haj Laure ba zasu bari na zauna lfy ba sannan da wanda na ke sonshi baya so na gara wanda nake ki yake sona zan lallaba da Adams,mun tsallaka daidai shagon Ubale zamu shiga cikin kasuwa sai ga wata mota ta tare mana gaba baka ce wuluk Mami tace motar nan tayi min kyau,kafin nayi magana har mai motar ya fito wani mummunan fduwar gaba naji yayin da muka hada ido da mai motar,shima ni ya tsura ma ido yana kallona mami ta ce kin sanshi ne?nayi karfin hali nace a'a naja hannun Amira jikina ba karfi sai mutumin yace uwata ni zaki gani ki wuce uwata?kin bani mamaki uwata zo kar ki tafi ina Habiba? Sai na soma kuka mai karfi mutane kallona sukeyi ya bar jikin motar ya nufo ni da gudu na tsallaka titi na nufi layinmu ina jiyo muryar shi yana fadin uwata kar ki kuma tfy ki barni zo mana mamana,ai sai gida ina tafe ina kuka kamar wadda aka ce uwarta ta mutu ban damu da kallon da mutane suke min ba jikin Mama na fada tana zaune a firgice ta tashi tana fadin lfy?menene? Ina sai kuka ruri nake Mami da Amira suka shigo a sukwane Mama tace Amira me ya faru? hankalinta a tashe ta ke magana Amira tace mama muna tfy zamu shiga kasuwa sai muka ga wata mota har muna cewa kai motar ta hadu kawai sai mai motar ya fito yana ganin Iman kawai sai mukaji ya hau cewa uwata dama kina nan uwata?zo nan kawai sai muka ga tana kuka ta rugo shine mutumin yace mun san gidansu? mukace eh shine ya dauko mu ynxu yana nan waje wai mu kiraki,mama tace baku da hankali daga ganin mutum sai ku nuna masa gidanku?dama ya tafi daku,ta daka masu tsawa me zakuje ku ce masa ba zan fito ba a ina ya sanni,Amira da Mami suka kada baki wllh mama yayi kama da Iman sosai mama tace ba shi bane nace kuje ku sallame shi mana,cikin kuka nace mama baba ne fa,mama tayi shiru dama nasan ta gane can sai tace Amira kije kuce mishi mijina baya nan dan haka ba zan iya ganinshi ba su Mami suka sameahi ya kifa kai jikin sitiyarin mota mami tace baba da sauri ya juyo yaushe rabon da yaji wannan kalmar yana kishin jin kalmar nan ga zatonsa Iman ce amma sai yaga yaran dazu,ya dubesu ina Habiban?suka ce tace mijinta baya nan shi yasa ba zata iya ganinka ba ba. Na idar da sallar magriba ina zaune a takure duk tausayin mahaifina ya cika ni Alhj ya shigo da sallamarsa ba sosai yake shiga dakin matanshi ba sai in bukatar hakan ta taso ya karaso gurina yaya dai Iman?lfy dai ko? nace lfy klau ka dawo lfy ya kasuwa?Amalhmdl Iman kuma lfy lau muka dawo ina Habiban fa?nace tana cikin dakinta,ya nufi dakin mama yana fadin Habiba sarkin hidima hala wani aikin takeyi,sun jima sannan suka fito naga fuskar mama murtuk babu alamar dariya ta zauna kan kujera shima ya zauna kan daya kujerar dake kusa dani yana fdin ban sanki da fushi ba ba halinki bane ruko,kuma ba kya gaba,uhm kuskure mutumin nan yayi ya kuma gane har kasuwa ya sameni shi da wani Ibrahim ban san wanda ya nuna musu ni ba sai dai ganinsu nayi nace miki har kuka yayi gabana yanzu kiyi hakuri ki zo muje suna falona ku gaisa,mama ta ce cikin fushi Alhj Mukhtar na taba yi maka musu?yace a'a tace to tin da kaji nace ba zani ba itama ni na haifeta ba zata ba to,ko kukan jini yakeyi ba zamu ba,yanzu ne ya san damu?ba zan iya ba wllh in kuma ya matsa min sai na maka shi kotu da sauri na dubi mama kalmar ta bani mamaki sam ban taba tunanin mama tana fushi haka ba hawaye ya soma zarya a kumatuna sam ba zan so haka ba Alhj da shima mamaki ya hana shi magana sai ya mike ya fita falon shi ya sami babana da yaya Ibrahim hakuri ya basu gami da ce masu su je su sami kawu malam can kuwa suka tafi kawu malam ya jima yana yima babana nasiha sannan ya ce je gobe ya dawo suje unguwar Rimi Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Misalin karfe biu saura kwata 1:45,zaune nake kan sallayar da nayi sallah na jima ina adduoina game da matsalolina, mama dake kan kujera ta dubeni Iman ynxu ya zaki hada lesson da comp school din na ce nifa mama ynxu duk basu dameni ba krt ma ya fita daga raina mama ta kafa min ido sannan tace to me zakiyi in baki krt ba?nayi shiru ta saka salati ku jimun yarinya aure kike so ke nan ko?nan ma banyi magana ba tace shi kenan kudina sun huta sai ki fito da mijin ko,na dubi mama nace bafa dan haka dan haka bane dan....sai kuma nayi shiru,yi min magana dan menene?nace dama wani abokin yaynmu da yake can England yake sona yace kuma a can zamu zauna can zanyi karatuna,mama tace Alhj yayi min maganar shi yo koma zakiyi krt ai dai sai da sakamako mai kyau ko?nace to wane ma lesson zan shiga,mama tace ga wata nan ramat road ki shiga tunda an kusa fara jarabawar ina gama salamat tsohuwar makarantarku zaki zana jarabawar a can,nace yauwa dama yafi,...Alhj ne yayi sallama mama tace lfy Alhj?na ganka da rana yace lfy lau ya dubeni nayi mishi sannu da zuwa yace kuzo Habiba ke da Iman ku sameni a dakina gabana ya fadi mama tace in fa baban Iman ne ba zani ba yace ina dai jiranku,falon cike yake da mutane Alhj ne a kujerar bakn kofa 2 sitter sai kawu malam can gefe na gane yaya Ibrahim da kuma babana sai wasu mutane uku da ban sansu ba nan da nan mama ta dunke fuska kusa da Alhj ta zauna nima na zauna kasa gefen mama,sai baba yace uwata zo nan kusa dani mana ,na dubi mama sai naga bata kalleni ba dan haka sai na nufi babana kasa na zauna ya jawo ni kaina ya dora kan gwiwowinshi naji wani irin muguwar soyayya irin ta da da mahaifi na ratsani kawu malam ne ya soma magana Habiba ga uban Amina ya zo bada hakuri akan irin kuskuren da ya aikata a can baya,mama tace ai bai min komai ba,babana yayi karfin hali yace haba Habiba nasan nayi maki kuskure dan Allah ki yafe ni nasan baki da ruko habiba,mama tace ai ni Idris dan ka sakeni ba laifi kayi ba tunda halas ne sannan Allah ya bani wani mijin wanda yafi ka komai nima sakamakon hakurina kenan,na dubi mama banji dadin maganar data fada ba babana akafi?na kuma gyara kwanciyata a jikin shi ni ina sonshi nace a raina,kawu malam yace yanzu dai yace ki yafe mashi babna yace yauwa nidai kimin aikin gafara mama tayi shiru sauran mutanen sukayi tasa baki mama tace meyasa sanda ya zalunceni ba wanda ya bada baki sai yanzu da ya milla da kanshi zaizo ya wani ce wai na yafe mishi,kai Idris kai ne mutumin da banyi tunanin yi maka afuwa ba,ta soma hawaye kai ne ka aure ni tun baka da komai kai ne ka fara sanina ya mace kai na fara haifa ma 'ya amma daga karshe ka ce na tafi da yata kai kafi son 'ya'ya maza daga tsatson fati ka manta?dan haka ynxu ma sai kaje gurinta Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tawa Tasameni 2-02 Posted by ANaM Dorayi on 08:27 PM, 03-Jan-16 Under: TAWA TASAMENI __________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI________ Tunda muke da kai ko ince tunda muka rabu da kai ka taba kawo daidai da pant aba Iman,Alhj yace kiyi hakuri Habiba ya wuce kice kin yafe masa,mama tana kuka Alhj da sauran mutane ma suna bata hakuri kawu malam ya soma mata fada to tunda duk nan ba mu isa ba shi kenan karki yafe ko Allah ana mishi laifi yana kuma yafewa bare ke,ganin ran kawu ya soma baci sai tace shi kenan ya wuce ya shiga godiya yace Alhj Mukhtar kaima na gode da irin rikon da kaima uwata Allah ya saka da alheri ya dubeni uwata ynxu wacce makaranta aka gama?ko shirin aure akeyi?na boye fuskata a gwiwarshi,Alhj yace sun kammala sec bara to paper din tata batayi kyau bane shine zata gyara sannan asan abinyi, babana yace to batun miji fa? Alhj ya ce eh akwai wani Adamu abokin Abdulrahim tare suke sana'ar tasu can a England shi nake zaton take so,amma sai mun gama bincike mutumin Ghana ne ina da abokin kasuwanci a can binciken ba zai bamu wahala ba tunda Abdulrahim yace min game da halayen Adamu babu matsala karatun ma yace a can zatayi shi ne nace ya nemi iso gurinta,babana ya dubeni uwata kina sonshi?na kada kai alamar eh sannan na boye fuska ina kuka dan na san ba shi nake so ba,babana yace Alhj kaga wani sakarci?wai kuma kuka take yi,mama dama tuni ta tafi nima na tashi zan tafi babana yace uwata wai yaushe zaki zo mana kwana biyu ne?na ce sai na tamabayi mama Alhj yace ko zuwa jibi ne ai na kawota dan Habiba sai da lallashi yanzu, babana yace ba komai kasan fushin irin na mai hakuri bai iya ba har na fita babana ni yake kallo bakinshi yaki rufuwa. Goman dare ina kwance kan gadon na murna duk ta cika ni don munyi settling da babana wayata ta soma ruri na duba Adams ne na danyi tsaki sannan na dauka yace yar gidana ya garin?nace yana hannunku yan England to haka ne ni dai na kira ne inji batunmu na runtse ido raina a jagule nace Adam na yarda zan aureka da karfi yace da gaske kikeyi?nace kwarae kuwa,ashe kina sona Maska yace min ba kya sona karo na farko kenan da Maska yayi min karya,na numfasa sannan nace zancen so ai ya kare ko ina sonka ko bana sonka tun da dai nace zan aureka ai shi kenan sannan kayi hakuri Adams ina son barci ne shima sai naji muryarshi tayi sanyi ya bar murnar yace to sai da safe na kiraki kinji?to na gode na tsaya ya kashe wayar sannan na ajiye,daren nayi kuka sosai ba kukan komai nayi ba sai na rasa abin sona shi kenan Adams ne rabona zan auri Adams dan in nuna ma yaynmu cewa tunanin shi ba gasky bane tunda baya sona ne da dai yana sona ne da sai na tabbatar mishi da cewa nima ina sonshi.Washe gari ina zaune akan kujera karama a nan kkfar dakinmu sauran mutanen gida kowa yana yan harkokinsa safa da pant dinsu jamila nake wankewa Sa'a da Bilki suna lido a kofar dakin su mami haj shuwa ce da girki dan haka tana ta kaiwa da komawa,lami mai aiki kuma tana wanke wanke anty mimi ta shigo tayi sallama ban san mai yasa ba duk sanda zanga anty mimi sai gabana ya fadi ita kuma a nata bangaren haka ne abin yake muna hada ido sai ta daure fuska gami da jan tsaki sannan ta kauda kai,su Bilki da Sa'a suka rugo suka rungumeta suna mata sannu da zuwa ta durkusa tana gaida haj shuwa sai ga yaynmu shima yayi sallama daidai sanda na gama shanya pant din ina wanke nawa pantys din,tun shigowarshi idonshi na kaina ni kuma duk da son ganinshi da nakeyi sai naki dubanshi dan ga matarshi kusa da inda nake zaune ya tsaya suna gaisawa da haj shuwa anty mimi kuma ta shiga dakin su mami dan gaida haj kulu,ba kya gaisuwa?ban dubeshi ba nace ina yini?yace ba zan amsa ba tun da ko kallo ban isheki ba bai san duk haushin su nake ji ba shi da matar shi ba,menene wannan kike wankewa a gaban mutane?sai naji kunya duk ta kamani,anty mimi ta fito daga dakknsu mami zata wuce sai yaynmu yace mimi baki gaida maman sagir ba ranta bai so ba haka ta shiga dakinmu data fito yace ta gaida ni na kwanta asibiti tayi jim can tace ya jiki?tayi gaba nima sai nace da sauki shima ya shiga ya gaida mama ya fito lokacin su bilki sunbi anty mimi dakin haj yaya sai haj shuwa a kicin ya dan duka saitin kunnena baa wanke irin wadannan abin a waje sai atoilet kin ji ko?ya wuce na bishi da kallon mamaki na rasa mai yasa yanzu duk ya canza min baya jin nauyin yi min wasu maganganun daidai zai shiga dakin hajyarshi sai ya juyo muna hada ido sai ya kashe min ido daya ya shige dakin na kasa ci gabada wankin dan duk ya saukar min da kasala kamshinshi kawai nake shaka raina yayi fari tas na tattara na koma toilet dana gama kan gadona na haye na dau wayata na kunna dan kasheta nayi saboda ban san Adams na kirana duk sai inji na tsaneshi,text ya shigo min na bude sai naga show message i love you forever na duba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yauma kamar kullum zai kai kusan sati biyu kullum sai an min wannan short msg na rasa waye?amma ina ganin Adams ne sai ya wani boye no naja tsaki ya karata nidai ba zan nuna mishi nasan yana yi ba ina yan fadace fadace na sai call ya shigo na duba sai naga yaynmu ne da sauri na dauka hello ki samenj dakin Kabir,hijabi na saka na fito falo mama yaynmu na kirana zai aikeni,to tace min Na fita zaune kan kujera na sameshi da remote a hannu gani na fada ina fubanshi sai naga ya daure fuska dan haka sai nima na shiga taitayina cikin dakewa da miskilanci na shi yace zauna,na zauna ya dubeni da farko ina maki murnar daidaitawa da mahaifinki da fatan ki zama mai mishi biyayya ya cigaba da cewa naji batun Adam's da kuma na gyara papers dinki kin zabga karya kince kina son shi ya harareni ya harareni makaryaciyar banza innaso in miki gata ki samu krt ko da Degree ne ynxu kuma baki son krt ko?nayi shiru ya daka min tsawa bakya jina?bakina na rawa na ce ina son krt mana yace karya ne da kina son krt da kin tsaya kan ra'ayina na sonki yi krt amma sai kika ki kika dauki son aurr kika dora a ranki to muddin kikayi aure ba wani krt da zakiyi lokacin kiyi kuka da kanki ba da ni ba,na dube shi ai Adam's yace zan ci gaba da krtna ya harareni wannan ra'ayin shi ne ina sonki san cewa ba dole bane Adams ya zama mijinki,don ba shi zuciyarki take so ba,haushi ya kamani nace ina sonshi yayanmu ya fusata zan mareki fa,karya na maki kenan?gara ma ki fito ki fadi wa wanda kike so ko zai taimaka miki da sauri na dubeshi yace shiii yi min shiru kin san siyasa na karanta ko?ya cigaba in ina son bararda Adams a wajen su a Alhj a guna abu mai sauki ne sai dai ba halina bane yanzu zan fada miki sirrin zuciyarki,kin kamu da ciwon son wanda kike so tun shekarun baya sai dai baki da tabbacin ko yana sonki dalilin shi ne kika kamu da ciwon zuciya dan kin kasa neman shawara ko mafita kar ki min musu kuma kar kiyi mamaki mutane da dama suna zaton na karanci halayyar dan Adam ne saboda yanda Allah yayi min baiwar saurin fahimtar mutane kin yarda ko har yanzu kina nan kina nan kan cewa ba haka bane?wata zuciyar tace min ki fada mishi gsky wata kuma tace kar ki bada kai,sai nace ni fa ba wanda na taba so ni Adams kawai nake so,ya zuba min ido ranshi in yayi dubu ya bace shi in ban dama yana ganin zubar da girma ne yace yana son yarinyar nan da dai ta yarda da abinda yace to sai ya nuna mata cewa zai taimaka ya aureta dan dai shi ba zai taba cewa yana sonta ba ta raina shi,to ita kuma ga shegen taurin kai ynxu yaya zaiyi kenan?kai shi ai daya san inda ake ajiye so da ya cire inda nata yake ya yar ya huta ya mike tsaye yana dubana sannan yace na zone nayi sallama dake don gobe kamar yanzu muna hanya duk yanda kika ga dama kiyi sai dai zan fada miki wani abu komai ya biyo baya kiyi kuka da kanki zan maimaita miki kiyi kuka da kanki yace kina iya tashi ki tafi sannan in kina bukatar taimako ko na menene kina iya nemana ta waya jikina babu karfi na mike a raina na raya bari na mishi kallon karshe dan haka sai na dube ahi shima ni yake kallo na juya daidai kofar fita na kuma juyowa na dubeshi sannan na fita,gidansu Amira na nufa tana kwance tama aikin karanta littafi kanta na dafaa ina kuka tayi jifa da littafin hannunta ta juyo lfy Iman?me ya faru?cikin kuka nace shi kenan mun rabu tace dawa?nace da yayanmu,sannu kan hankali na zayyane mata komai ta ce kash! Kinyi wauta dakin sani kince mishi kina sonshi menene?ba zan iya ba Amira tunda shifa ba sona ya keyi ba cewa fa yayi wanda nake son zai taimaka min gara na hakura sam ya ma ki nuna cewa shi nake so da kyar Amira ta lallasheni sannan na dawo gida. Kwana biyu duk na rame na fita hayyacina saukin tama naje gidan Babana kamar yanda Alhj yayi alkawari gata dai na duniya ba irin wanda ban gani ba har kasuwa yaje dani can naga yaya Abubkr da yaya Ibrahim don ynxu sun kyaleni,kyauta dai na sameta gurin abokan babana yace yaya Ibrahim ya dawo dani gida ya maida ni Anty Fati sai huci take yi niko ko kallonta banyi ba Anty Maijidda itace matar da babana ya sake aura itama yar cikin kano ce shekara biyu kenan da auran,itama dai shiru ba haihuwa tana da kirki sosai kuma ta nuna tana sona har kitso tayi min dan haka sai nake gurinta,da babana ya dawo kuma sai na koma gurin shi tare muke cin abinci muyi hira ya kan tambaye ni me nafi so ko kuma me na ke so ya sai min?na dinga mishi lissafi ranar da zan dawo sai da muka shiga kasuwa dashi siyayya har ta banza kuma daga kan sutura kayan shafe shafe turarurruka da takalma su Jamila da Sagir kai har su Mami sai da nayi musu tasu tsarabar,Mama da Alhj turare na sai musu sai kace daga wani gari na dawo da ya kawo ni gida kamar kar mu rabu nace zan kuma zuwa ai ya kara bani wata wayar yace shi kadai zai dinga kirana ya samin layin glo ya zuba min no dinshi da ta tsohuwa kakata yace na kira nace zai kawo ni na kwana biyu nace babana na tafi ka gaida Anty Maijidda ta bani tirare tace na ba Mama yace shine baki fadamin ba? nace ita tace kar na fada maka yace to zan mata godiya ki ce ina gaida Habiba har na kai bakin kofa sai yace kin manta da tsarabarki nace lah na mance na dawo ya kwaso min, duk wani motsina idonshi yana kaina kai Babana na sona matukar so.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Kwanaki suna shudewa,Lokaci na kara wucewa mun gama Diploma a Comp, sannan munyi jarabawa sai dai jiran abin da zai biyo baya Adams yana kirana a waya duk da bani sonshi a raina ina dan sauraranshi yaynmu kam bai taba kirana ba sonshi dai yana nan makale a raina ,Alhj da Babana sunyi bincike akan Adams ashe ma mahaifin shi abokin Alhaji Adamu garko ne me gidan Babana dan haka basu sha wata wahala ba wurin bincike sun shirya magana tasu ta manya sannan sunce sai sunji ta bakin Adams sun kira shi sun mishi bayani yayi murna sannan sun bukaci ya fadi daidai lokacin da yake son a sa bikin yace su bashi kwana biyu zai sanar dasu, a son Alhj ayi bikinmu rana daya dasu Mami da Sa'a da Bilki,to amma da kyar hakan zata samu. Yau laraba zaune nake gonar kawu kabiru kanin mama a kauye gefena Jimmala ce kanwar yaya Ibrahim tunda naje kauye kullum sai naje gona kota dangin mama ko ta dangin babana,daga inda nake ina hangen kawuna yana bawa masara ruwa wayata ta soma ringn Adams ne na sani dan haka sai na dauka gami da sallama yar gidana na jima ina nemanki ban same ki ba?nace matsalar ntwk ne yace to ya gari?nace gari na hannunku mutanen England yayi dariya,to yaya?na me? na zancen mu mana kinsan yau ne na yanke musu zan sanar dasu date din daya kamata a sa fa,na dan yatsina baki nace kai yaushe kake so,nafi so asa watan goma kin ga yanzu muna watan hudu nan da wata shida kenan ko?nace to hakan ma yayi daidai, su Mami zasu rigamu dan su saura wata biyu yace insha Allah dani za'ayi bikinsu Mami,Amira fa?nace ita sai tayi HND tukunna yace Ok! to duk yanda sukayi zan kiraki nace kai yaushe zaka zo yace sai bikin su mami zamu zo tare da yaynku ne,gabana ya fadi sam bana son tuna shi dan yaynmu shi kadai nake so so mai tsanani rabona da ganin shi tun bankwanan nan da mukayi yace kina jina?nace ina jinka Adams wai dan Allah kuna shiri da yaynmu?yace sosai ma dashine muka sa date din bikinmu gabana ya fadi nace haba yace Allah gaske ne fa nace suna lfy yace kalau shine ma ya tsaida date don nace nan da four month yace gara six din,nace Allah ya kaimu yace amin... Adams kan abin motsa jiki yaynmu ne ya hada zufa tamkar mai tukin mota yanata faman yi can ya dubi agogon dake manne jikin bangon dakin karfe takwas na safe ya jawo tawul ya soma share gumin da ke zubo mishi sannan yasa baki ya kira Mimi,Mimi ta shigo da sauri gani ya dubeta ina shayin wai yaushe ne zaki koyi yanda ake kula da miji ne?kin san kawo shayin nan aikin ki ne daidai wannan lokacin amma kullum sai nace ki kawo?to za kije ki kawo din koko?kin tsaya min akai,ta juya shi kuma ya ja tsaki sannan ya sauka daga kan abin motsa jikin ya hau kan wata kujera a gefe ya zauna yaci gaba da share zufar,ta shigo rike da kofin tangaran babba da karami,ta ja wani dan tebur ta tura mishi ta juya ba tare da magana ba ya bita da kallo sannan ya girgiza kai sam Mimi bata dace dashi ba ta kowanne fanni sannan yana son a inganta mishi ciki dan kowa ya san yan kwallo da cin abinci,ya kurbi ruwan na lipton mai hade da wasu ganyayyaki can sam sai yaji komai ya ishe shi ya kwana biyu kenan baya cin wani abin kirki tunda Adams yazo mishi da zancen sa ranar shi da Iman ya kuma nemi shawarar sa ya bashi shawara ya bari sai nan da watan goma ne dan yana son ya nemi mafita sam ba zai bari adams ya auri yarinyar da yake masifar so ba,so mai tsanani sannan yasan tana sonshi taurin kaine yasa taki fadi to shima yayi alkawarin sai ya aureta muddin yana numfashi a doron kasa,yayi lissafi Mimi tana da ciki wata biyu zata haihu watan sha daya yana son sai mimi ta haihu sannan ayi bikin nashi ,amma ba zai yiwu ba,ya danyi shiru na wani dan lokaci sannan yace na san abinyi ya mike tsaye ya fita bayi ya shiga a cikin dakin shi ya hada ruwa yayi wanka a gagauce ya shirya cikin JC blue da ratsin fari ya daura takalmi mimi ta shigo kana da bako,ya dubeta wanene?ta dan tsina baki ko Adams yake ne oho?haushi ya kama shi me yasa yarinyar nan batada kunya ne yanxu?amma zaiyi maganainta yace fita anan banza kawai ni zaki cewa baki san Adams ba? ta fita tana yin kuna kunai na gaji da wulakancinka komai kace sai an maka ni ko gsky ko a gidanmu ban kauda tsinke bare wani girki ina dan wanda zan iya kai kuma kana ganin kasa wata yana jiyota sai dai bai san me take fada ba yace zaki gane kuskurenki.Ya sami Adams zaune shima da shiga irin ta Maska Adams ya dubeahi kace ka shirya Maska ya zauna sai dai ban karya ba,haba baka karya ba kai da kake da iyali ma,Maska yace kasan bata da lfy gata dama da son jiki sam bata son aiki Adams yace sai hakuri nidai Allah yasa nayi dace in har ka dace ka sameta din to Adams kar kayi shakka zaka sami yanda kake so,Adams ya ce ya kake cewa in har na sameta?kana ma shakka kenan?kar ka manta fa har na biya sadaki an sa mana rana kuma kaine ma ka tsaida min har na sanar da manya,Maska yayi wani murmushi Adams ya kalleshi Maska bana son wannan murmushin naka fa tuni na sa mashi suna murmushin mugunta dan ko a fili muke gurin wasa abokan wasa suka sako mu a gaba kana irin wannan murmushin sai kaga Allah ya bamu nasara,Maska yace tashi mu tafi a can zan yi break kafin mu shiga fili. Ni kam lokacin ina kauye ranar kwana na sha takwas daga sati daya ina jikin tsohuwa kakata tana fadin daga ni takwara kar ki karasa ni nace kai dan Allah ki barni na dan huta mana infa na tafi sai na dade zan zo tace ai ba zaki kawo min Adamu mu gaisa ba?nace ni ina naga wani Adamu yana can kasashen turawa yana kwallo tace ai Ball yake?ynxu dan Ball din zai rike ki?nace to ai tasu ta gaske ne ba irin ta nan ba,ta tureni ke ja can da ban haushi baga su nan muma muna dasu ba yan bal din yanxu jibi yaron nan na gurin karima shima aikinshi kenan bal asubar fari yasa gajeran wando da wani kwandallelen takalmi raf raf ya tafi bal kusan shekara biyar ance har yau baa taba nuno shi a cikin talabijin ba shi bai tsaya yayi noma ba shi kuma bai tafi rani ba,sai dai yau yana waccan unguwa gobe yana waccan yawon bal,tunda ta soma magana nake dariya,tace dariya ma na baki? dama wannan shirmen Adamun keyi shine za'a bashi mata?ko mu da muke karkara dan gidan karima an hanashi mata,na kuma tuntsurewa da dariya ta dau mafici ta bini kki bani guri ta kai min duka da gudu na fita ina kwasa dariya sai naji tsayuwar mota da sauri na leka motar babana na gani da gudu na fita na taroshi,Ya kira wasu yan samari suka shigo da kayan abinci na rike mishi hannu muka shigo, dakin Baba ya soma shiga kafin ya shiga dakin Tsohuwa na nufi madafi na dauko masa abinci a kwano na debo masa ruwa a randa na aje a gabanshi ina fadin Babana kamar nasan zaka zo na yi abinci da yawa,yace to na gode,nace yasu Mama?yace suna lfy sune ma suka matsa min akan na daukoki daga sati har kin kusa wata jiya Alhj ya kirani a waya yace in mashi kwatance yaje ya daukeki,nadan yatsina fuska nace ni ban son tfy tsohuwa tace to ai ya zama dole nace muna gama bikin su Mami zan taho nan,baba yace a'a muma muna son ki zo mana kafin bikinki daga nan nayi shiru ban sake magana ba,tsohuwa tayi caaraf tace yawwa ashe kai yanzu Adamun dan bal ne?shi ne zaku bashi yar? Babana yayi dariya sannan yace ai sana'a ce sosai suna samun kudi fa shima dan mai gidan Habiba kwallon yake tare ma suke, ai shi kenan amma ko ga tarihi bal ance bata da kyau,yace to ai wasu malaman sunce za'a iya yi in ta zama lalura saboda kishin kasa tace tunda kuna so ai komi ma cewa zakuyi ni dai ina jin su har suka gama. Adamssalin tara text din da aka saba yi min tsawon watanni kullum ba fashi ya shigo,very soon zamu kasance tare domin nasan i am always lucky akan duka abinda nakeso,ban ma gama dubawa ba na kashe yau kamna gane Adams ne yake min text yana boye no haushin shi ya kara kamani na hau fada ina cewa nufin shi sai ya min haka zan so shi?to yayi kuskure ni ba sonshi nakeyi ba zan dai aure shi ne dan hujjar da na ba yaynmu nace kai bari ma in mashi karara don ya daina damuna na soma neman layinshi ai cikin sa'a na sameahi ashe lokacin suna tare da yaynmu a wani club ya dubi yaynmu yace ga yar gidana sannan ya dauka,in kaga yaynmu zaka dauka bai damu da wayar da Adams keyi ba amma ya tattara dukkan hankalinshi gurin sauraron Adams dan ta maganr da Adams keyi zaka gane me nace,ni kam Adams na dauka nace hello Adams menene na boye no kana yi min text in ma kana yi ne dan ka birgeni to wllh haushi ma kake bani,tunda na soma maganar bai tare ni ba sai da nayi shiru,yace calm down my wife wllh ba ni bane ba ban ma taba yi maki text ba nace to wanene?ina zan sani inji adams sannan yace don Allah kiyi hakuri karki damu kanki kashe na kiraki,nace yanzu zanyi shafai da wutiri ne sai da safe yace sai da safen yanda ya amsa har tausayi ya bani,Maska ya dubi Adams dan san jin karin bayani,Adams me Iman tace maka ne?Adams yace wai cewa tayi ina boye no ina kiranta wai bata so Maska yayi murmushi to dama kai kake mata ko?Adams yace bani bane Allah maska yayi tsaki sannan yace kaga abinda nake gaya maku ko ku nemi manyan babys ynxu gashi kana yi ma yar cikinka rantsuwa ita kuma sai masifa take maka ynxu ina girma?babu babba wani abun ma sai taga gadon kwananka Adams yayi murmushi yace wannan ra'ayinka ne kawai niko ina son in auri yarinyar dan na more sadakina da kyau Maska yace in ka samu big girl shine zaka more sadaki Adams yace mu bar zancen haka Maska yace kai dai ka sani yaushe zan bar yar yarinya ta juyani? ai ni in babbar ce ma sai ta raina kanta in tace zata kawo min iskanci Adams yace in baka sonta ba ba in kana sonta komai zatayi maka zaka jure sai kaga karamar ta juya ka babbar bata juya ka ba,tsaki Maska yayi sannan yace baka gama sani na ba har ynxu don ina son mace tayi kadan na jure iskanci, sannan ya mike ya tafi Adams na mishi dariya. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Muna zaune a dakinmu muna aikin gyaran katunan bikin su Mami yau saura kwana takwas bikin kuma yaune su yayanmu zasu iso shine babban abokin ango kuma babban yayan Amare,na dubi Mami nace ya kan Badarawa,Malali,da Unguwar sarki ya kamata muje dan yan skull zamu gayyace sosai mun dade bamu hadu ba mami tace haka ne yi sauri mu biyama Amira,tare muka shiga gari sai magriba muka dawo sai dai in lokcin sallah yayi mana mu tsaya muyi,shirye shirye sunki karewa saboda wasu abubuwan bada su Sa'a zamu hada ba walima ce kawai tare sai Sisters day da su Anty Mariya suka shirya a gidan yaynmu in sun iso a Yakubu Avenue amma mu zamuyi lunchn sannan angwaye sun shirya dinner,mun dawo mun sami yaynmu ya iso saboda gidansu sai an gyara da yan share share gurin su Sagir na sami lbr isowarsu sai ga kuma wayar Adams yana ce min sun iso ynxu suna tare da ango nace to sannu da zuwa me zan shirya maka?yace komai ma nace to an gama nadai daure ne nayi wannan maganar dan kar ya ce ban yi murna da zuwansa ba amma zahiri hankalina yana kan yayanmu da kuma masifar son ganinshi,nan na dan yi girke girke na san Adams na zaci zan sameshi tare da yaynmu a dakin yaya kabir din ina sai shi kadai na samu dan haka shi kadai yayi ta surutanshi Adams ya dubeni kin kara cika fa yar gidana ina son Maska ya ganki shi da yake cewa zan auri yar cikina nace um! Sama sama mukayi hira sannan na koma gida shi kuma ya nufi gidan Nasir har ramar lalle banga yaynmu ba ko anty mimi ban gani ba mu da yake gidansu Amira mukayi namu lallen su kuma gidan Anty Hadiza sukayi,sisters day shine abu na farko da kamar kar naje mami tace in banje ba bazata ba dole tasa nace to zanje,da yake dama gurin babana naje na amshi kudi na shiga kasuwa materials da lace sai da naga karshen tsada na sai mana takalmi da jaka ai fdi ma bata bakine ganin abin rabawa na buga jaka na buga bokitai na roba sai na buga agoguna har fada mama tayi min wai naje ina amso kudi masu yawa haka shi kuma ya biye min,nace to mama kiyi hakuri ni ban yana cewa in basu isa ba zai kara min wasu wai dan ni kadai yake neman kudi,mama tayi tsaki ta shige daki mu da Amira ba muje shirya gurin da zaayi sisters day din ba dan gudun rikici sai bayan an gama komai an soma kai kawaye sannan muka shirya,jan material dan dubai shi na dinka riga da siket nasa duk yanda mutum ya kai ga hassada ba zai kusheni ba a wannan rana takalmi da jaka bakake nayi amfani dasu kafin amira ta gama shiri na shiga gidan mu na fito wata mummunar faduwar gaba naji sanda na hangi yaynmu a kofar dakin yaya Kabir shi da Nasir sanye yake da wando jeans baki da riga fara ta kama jikinshi kyau annuri ne ke fita a fuskarshi yana da kyau na karshe fatar shi ta kara zama smooth giran gashin shi kuwa abin birgewa ne,kamar na juya sai na dake tunda bai ganni ba gara na nuna ban ganshi ba sai da nazo daf da su sai Nasir yace kai Iman wannan dauke kai haka?na juya da sauri ango ban ganka ba ne,na isa wurinsu na dubi yaynmu wanda yayi wani kicin kicin da fuska nace sannu da zuwa yaynmu kunzo lfy?a ciki yace lfy duk sai naji ba dadi dan haka sai nace Nasir a kirata ne?yace a'a ba gurinta nazo ba sai na wuce ciki,ganin yaynmu sai tsohon ciwona ya tashi wutar sonshi ta soma ruruwa a cikin zuciyata ranar dai sai a hankali mun isa gidan yaynmu sai naga ma ashe duk yanda suke bada lbr haduwar gidan ya wuce nan gefen da ake sister day lambu ne yanda suka shirya yayi kyau Amare kaya iri daya suka sa tunda muka zauna bamu tashi ba sai da aka soma liki sannan ne na shiga nima na bada tsoro da kudi na fito,anty mimi tayi kyau sosai cikin farin tattausan leshinta rigar fitet ce don haka cikinta ya dan fito dan das daga mun hada ido sai ta dalla min harara har Amira ta lura da ita tace ke kefa matar can take harara nace tayi ta gama abinda yasa ma bata neme ni da rigima ba dan tasan yanxu bama shiri da mijinta ko ince an samin rana shiyasa Amira tace haka ne kam,wayata ta soma ringin na duba sunan yaynmu na gani gabana yayi mummunan faduwa na dauka yace ina jiranki a falon gidan nan cikin in ina na ce ban san hanya ba ki tambaya sai ya kashe wayar na dubi Amira kinji yaynmuda rikici ko wai na sameshi falonsu bayan dazu da ya ganni sai ya wani daure fuska Amira tace kije mana nace to ai tana kallona matarshi Amira ta ce to zauna ina ruwana,na mike na nufi hanyar waje nan na kirashi nace ban gane hanyar ba gani a gurin bakin gate,yace ni kenan kike nufin in zo ko?sai ya kashe,gun mai gadi na nufa nace mishi dan Allah ina kofar falon,ya nuna min sannan na nufa sanyi da kamshi da kuma laushi su naci karo dasu ina shiga falon,yana zaune yana shan coke na isa gurinshi har ya canza kaya daga bakin jeans zuwa blue da yar shirt,na dan rusuna gefenahi yace tashi ki zauna kan kujera na tashi nabi umarninsa yana kallona kamar hoto ko TV yana shan coke na gaji kar matar shi tazo sai nace gani yace na ganki sai yaci gaba da abinda yakeyi da danne dannen waya,can sai yace ke kamar ni nazo garin nan ace ki gagara zuwa ki gaisheni?sannan da muka hadu sai kika wani dauke kai ke kin girma wai shekarar ki nawa ne?nayi shiru dake nake na dubeshi fuskata a daurena kauda kai,ba kya jina nace sha takwas yace to me na miki kika kasa gaidani?nace ban gane kaba ne shiyasa shi yasa kika manta dani ko?baki taba yi min waya ba tun da natafi me yasa?nayi shiru can nace to kayi hakuri,aikin ki kenan bada hakuri to na hakura menene shirye ahiryen na ki bikin?na dubeahi ni bani da wani shiri yace ki dai fada tun da wuri kinsan ance mai kwarmin ido da wuri yake sa ma kuka nine uban Amarya kuma nine abokin ango,haushi ya kamani nayi kicin kicin yace to menene na bata ran kamar ba ke kika zabi mijinki ba?sai ya canza magana baba kwana biu ban kirashi ba kuma tun da nazo banje ba amma zanje mu gaisa nace dama kana kiranshi ne? sai ya share zancen,kun zan jarabawar?munyi,to Allah ya bada saa amin ina yan waige waige yace me kike kallo ne ki saki jikinki gidana kike ba na wani ba ni ko yaynki ne,Amira da Mami sai doko min waya suke ina cewa gani nan yaki sallamata,har suka tashi sai ga mutane na mike da sauri harara ya sakar min ba shiri na koma na zauna a raina nace kai dai kana shaawar kowane biki sai ka sani a problem,sunyi mamakin ganina sosai fuskar anty mimi a kaina,Nace don Allah zamu tafi shi kuma sam ya ki sai da yayi raayi sannan yace to wa zai kaiku?nace mashin yace bana son kina hawan mashin fa nace to nabi motar Nasir ni da Amira,to sai yaushe nace ai yanzu kuna nan zamu yi ta gaisawa ko yaushe yace shi kenan,washe gari lunchn tun safe ba hutu sun tafi gyaran gashi ni kam da bani kona gashi sai na tafi kitso biyar daidai kowa ya shirya sai mu kawaye da Amarya ake jira dan har an soma dibar kawaye bayan na shafa mai sai inner wears na dakko less wanda ya amsa suna less kalarshi ba zaa kirashi milk ba kuma ba zaa kirashi yellow ba shi kuma ba light brown ba yana dai tsaka tsaki na saka shi sannan nayi shafe shafe kai ni kaina nayi mamakin kyan da nayi sai da na gama shiri tsaf sannan na fito kai Iman inji Mami gsky ko ni amarya kin fini haduwa gsky cire inji Mami nayi murmushi nace ba wani kyan da nayi,kafin tayi magana sai ga su Amira da sauran kawaye kowacce sai da ta raina kwalliyarta ynxu burina inga yaynmu shima inji ta bakinsa mun fita harabar gidan mu yan mata ne tsantsam nan kallo ya koma kanmu Adams ne tsaye suna magana da sauran abokan ango yana hango ni sai kawai ya wani washe baki yana kallona amira tace iman ji mutuminki nace naganshi share kawai,ya iso gurinmu Amarya gsky ba tare da ango zamu kaiku ba sai dai ya haura ma kanshi daga baya,Mami tace saboda me kace haka Adams?Ya nuna ni yace ga yar gidana da Amira ku zauna tare a motata don ni ne zan tuka ku na juya zan mishi magana sai wata masifaffiyar hadaddiyar mota ta kunno kai harabar gidan duk mutanen dake gurin sun raja'a ga ganin motar, baka ce wuluk haka gilashin ta ni kam shashancewa nayi ina duban motar dan tunda nake ban taba ganin mota irin wannan ba,Adams ne yace sai Maska dai dai lokacin da yayanmu ya fito cikin wata shadda galila yar gaske sai maiko take,hatta numfashina sai da ya dauke na yan dakiku sannan ya dawo daga nesa damu yake amma kamshin sa har gurinmu,Adams ya ce sai Maska yaynmu ya dago mishi hannu ya mishi alamar yana zuwa 'yan mata suka bishi da kallon birgewa yayin da wasu suka kyasa A hankali nayi ajiyar zuciya sannan nace Adams kun damu mu fito ga mutane ba'a gama kwashe su ba ya za'ayi mu tafi?ya ce to ynxu ya za'ayi kenan? Amira tace don Allah ku gama kwashe su mana sauran abokan suka ce to,yaynmu ya kuma fitowa gurin motarshi ya nufa Adams ya bishi ya bude mota suna magana da Adams ko me suke cewa oho?sai Adams ya dawo shi kuma ya shiga cikin motar sai kuma ya fito ya dubi gurinmu da hannu ya yafito ni gabana ya fadi nace Amira yayanmu yana kirana mami tace karki dade fa banko iya magana ba na nufi gurin motar sai na samu kaina da canza salon tfy cikin isa da kasaita na iso gurin motar gefen kusa da dryva ya bude dan haka sai na zagaya nayi magana sai naji yace shigo ba musu na shiga kamshi da sanyi sukaimin sallama cikin isa da jan aji ya tashi motar ba tare da ya dubeni ba cikin gwaninta ya fusgo motar da gudu sai da muka hau titin Bako Road sannan ya kara sautin wakar p square cikin wakar su ta no one lyk u,na jingina da kujera ina sauraro wakar na zata gurin lunchn zamu je sai fa naga mun dau wata hanyar ban ankara ba sai gamu gaban gidan yaynmu dake Yakubu Avenue gabana ya fadi sannan tsoro ya bayyana a fuskata yaynmu ya dube ni sai ya fito da waya yana yan danne danne shi ban sani ba ashe hotona yake dauka ban sani ba,na rufe wayar sannan yace bisimillah mu shiga nace me zan yi yaynmu?kasan fa gurin Lunchn zamuje,yace nima bazaniba dan haka kema ki hakura da sauri na dubeshi cikin damuwa nace mami ba zata ji dadi ba fa yanda muke da mami ban kyauta mata ba,dubana kawai yake sannan yace to mimi taje mana ni dake dan haka ynxu ma ni yunwa nake ji mu shiga ki min abinci na dubi fuskar shi ba alamun wasa amma duk da haka sai da nace bai dace matar gidan ba ta nan ba na shigar mata gida ya daka min tsawa gami da cewa tsaran ki ne ni kike yi min musu?bayan mun shiga ya tsaya da motar na fito shine a gaba ina binshi a baya har falo ya zauna nace inane kicin din bi nan ya nuna hanyar,na tafi komai na kicin da ake bukata akwaishi dan haka na shiga aiki gasky na raina tsaftar matar gidan banyi karambanin gyra mata kicin ba nidai nayi iya aikina farar taliya da miyar kwai da hanta nayi mishi a gabanshi na jera komai na koma na zauna ya dubeni zo mu ci kai kawai na girgiza dai dai lokacin da naji ringing a cikin jakata na ciro wayar har ta katse na duba 11 miss call na duba su Mami ne da Adams na dubi yaynmu dake faman cin abinci nace su mami na jirana ya dubeni kin san bana son nacin magana ko?ya kamata ki rike wannan ya cigaba da cin abincin shi sai da yayi dam sannan ya shige dakinshi wanda an rubuta master bed room a jikin saman kofar dakin da yellow din kala kamar minti biyar ya fito zo muje Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 A ranar haka muka yi ta yawo a gari dan mugunta har magariba kuka ne kawai banyi ba dan haushi wai ace biki kamar na mami bana guri ai da takaici gashi ya amshe wayata ya kashe na rasa irin wannan ikon, gidan shi muka koma ya tafi masallaci ya barni wai nayi sallah cikin dardar na zauna sai bayan ishai ya dawo ko sallar ma banyi ba ya kuma daukata ya shiga gari sai tara ya maidani gida lokacin an tashi daga lunchn din dan haka dakinmu na wuce na fada gado ko da mami ta shigo da fushi ganin ina kuka sai ta sakko tana tambayata menene?cikin kuka nakece mata yayanmu ne ya daukeni sai yawo yake dani ya hanani zuwa gurin lunchn dinki tace ba komai kila shima yana da dalili nace wanne dalili?shidai burinshi ya ga raina a bace nan dai ta shiga lallashina. Washe gari aka daura wasu mami aure, da daddare aka kai mami gidan Nasir dake unguwar sarki tun fara bikin sai yaune muka sake nida Adams dan yayanmu ya kasa ya tsare yaki barina na cashe ashe shi yana can suna yinta da anty mimi yace ba zata zo ba ita kuma tace sai ta zo ya gama shirinshi tsaf ta taso har gun mota ta biyo shi tana cewa sai taje,ta shige mota itama tata kama murfin motar yace sake min tace sai fa naje yace ke kina fa cin darajar cikin jikinki ne bayan haka dakin san ina fada kina fada ba zata yiwu ba amma zaki haihu ba zan dau wannan iskancin ba wata macen arziki ce zata bar gidan aurenta karfe goma kuma bata san sanda za'a tashi ba to tunda lallashi baya miki zan biki da zafi yaja murfin motar ya rufe sannan yaja motar,muna tsaka da fira sai ganinshi mukayi tsakiya suka sani shida Adams,Adams ya dubeni mun zata ba zaka zo dinner kanwa ba?yace kasan mai iyali saida na lallameta tayi barci Adams yana yayi kyau muma dai Allah ya kaimu ga jarawa ,ni kam kumallon ya motsa don haka duk haushi suka bani Adams ya dubeni yar gidana kina gaya min kince zakuyi lunchn da mene?nace sai mun zauna dasu Amira menene na sauri Adams da sauran lokaci fa,yace ba wani lokaci gara ki fada min don in na tafi sai ana sauran kwana daya biki zanzo in nasan komi tun yanzu zaizo da sauki,na dubi yaynmu wanda yake ta aikin danne dannan waya tamkar baya jin mu nan ko yana sauraren komai nace to kafin ka tafi zamuyi zancen, gobe fa zan tafi cikin kosawa da maganar nace to baga waya ba Adams yace to shi kenan ya canja zancen da hajiyata tana son jin muryarki bari na kirata ku gaisa,nace haba dai daren nan?ka bari sai da safe yace to na bari kinsan ni ba dai cikin gimbiya ba nayi dariya nace to Allah yasa ka dore ba sai naje gidan ba a canza min yace haba aini din nan ko bawa kika samu kinsan yanda nake son ki kuwa?kin san nutson da nayi a kogin kaunarki?in da ace kinsan yanda jiki da jijiya da bargo da kashi da tsoka........kai yaynmu ya daka tsawa ya cigaba haba Adams ka tasa yarinya karama kana wannan kauyancin?ai wannan soyayyar dace in kana sonta idonka kadai ya isa sheda ba sai kanata wannan batun ba ka gane wannan ai yar da girma ne da ga ni har adams kallonshi muka tsaya yi sai da ya gama sannan yace Maska kai komai naka daban ne kana da hali irin na masu girman kai...yaynmu ya daga mishi hannu ya isa yi tayi,Sai karfe sha biyu muka tashi daga dinner washe gari muna sallama da Adams yace sam bikin nan bai min dadi ba,dan naso muyi hotuna muyi hira mai isarmu amma haka bai samu ba nace kar ka damu tun daga waya maganar hoto sai na shiga na miko maka munyi sallama nabashi hotuna ya diba son ranshi mun rabu akan sai naji shi a waya haka muka rabu,bayan gama bikin mami yaynmu bai kuma damuna ba sam gaisuwa ke hada mu sai dai da naje gidan babana ne yake cewa yayanmu yana zuwa yana gaisheshi har yazo da mai dakinshi ya yabeni tare da fadin kirkinshi,ranar ma muna zaune a falon babana dani da Anty Maijidda sai ga yaynmu sun gaisa da anty maijidda sannan na gaisheshi anty tace kije ki kira babanki na tashi na dauki dan kwalina naje na sanar dashi,yana fitowa naga ya soma fara'a ganin yaynmu suka gaisa sannan yace yazo ne ya mishi sallama dan gobe zasu koma sai kuma nan da wata hudu lokacin bakina da abokinshi babana yayi mishi godiya gami da sa albarka sañnan yace ga kanwar ka nan dama ta dameni wai nayi sallar magariba na kaita gida don haka sai ta tashi ku wuce,na ce sai gobe zani,babana yace a'a ni kinga gobe kwatano ma zamu,na soma shagwaba nayi takwa takwa da fuska nace nidai to ai baka sai min abinda kace ba yace me nace zan sai maki? computer yaynmu ya harareni na kauda kai babana yace to in na dawo ranar sati monday sai na sai maki shi kenan?nace eh yace to uwata maza tashi yaynki na jiranki na mike ina fadin ko kana korata ne?ba zan sake zuwa ba suka sa dariya shida anty Maijidda yace wane ni na kore ki ban isa ba nayi kadan anty tace naje daki na dauki kayana na dauka tace na gaida mamana,tunda muka dau hanya ni da yayanmu ba wanda yayi magana can yace gobe zamu koma sai kuma bikinki na dubeshi to Allah ya tsare hanya na fada cikin karfin hali,tunda muka zo gida muka samu haj yaya a harabar gidan na soma tsuma,cikin tsoro nace gasu haj,to menene yace yana fakin na fito da ido suka bini shi kuma ya nufi gurin su ni kam gida na wuce,yace haj daga ina?ta daure tace nan makwafta muka shiga barka ta cigaba matarka tana jiranka ashe kai kuma kana nan kana yawon banza daga ina kake?daga tudun wada,gurin wa?gurin baban iman ta kuma dubanshi muje ciki gani nan tana mamakin halinshi shi mutum ne wanda baya shakka ko karya komai zai fada in dai gsky ne zai fada sai dai a mutu Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Haj yaya fada take tana karawa tace eh dan shashanci matrka ta na nan tana jiranka kai kuma ka tafi gidan kanin ubanka yace to haj dan naje munyi sallama shine damuwa?to kiyi hakuri ta dan sassauto kai baka da tunani yanzu in kai wanine yaushe zaka bar Adamu abokinka ya nemi yarinyar nan ga kannenka?yace wadanne kannen kuma bayan sunyi aure?ko ba ma haka ba ai matar mutum kabarinsa....tace nasan haka amma ni na sha alwashin sai na hana auran Iman da Adamu in dai ina numfashi yanda bana son ta rabeni kaima bana son ta rabi na kusa da kai kaf yayana wacce ce ta samu mai kudi dan mai kudi kamar Adamu?babu dan haka itama ba zata aureshi ba,sororo yayi yan dubanta sai da ta gama sannan yace to haj ke me zakiyi akai?dan Allah ki bar maganr nan,tace nasan abinda zanyi kai dai tashi ku tafi Allah ya tsare hanya kana can zakaji lbr,yaso yayi mata nasiha gami da shawara amma sai taki ta hau shi da fada,dan haka sai yace to haj zan wuce ba zan samu dawowa da safe ba saboda sammako zamuyi ta kano zamu tashi sakon ki gobe in Kabir ya kaimu kano ya dawo zaije banki ya amso maki kudin,ta ce zaka kara min dubu talatin akan na da yace ba komai zai kawo maki ina Mimin mu wuce,haj tace tana gidansu, ya dubi haj wa yace taje jiya fa can ta yini haj tace ai ba'a gajiya da gida ka dai biya ka dauketa yace Allah ba zan biya ba tunda ban aiketa ba in ta dawo shi kenan in bata dawo ba ta zauna,Haj ta dubshi gara da ka nuna na gani dama ta kawo min kara kana wulakantata son ranka yace haj ni kinsan abinda take min ne? bata san kula da miji ba bata san darajar miji ba bare yanda zatayi biyayya son jiki bata iya girki ba,ni nasan ina da mata amma sai na fita yawon gidajen cin abinci,tace to ai komai dan lallashine yace wane lallashi ne ban mata ba amma nasan maganinta zata gane bata da wayo,ya mike mun tafi haj tace Allah ya tsare kar dai ka yarda naji wata magana. Sosai su haj yaya suka hau shiga malamai duk wai dan araba Iman da Adams ko ina ruwansu oho?nikam bansan me suke ciki ba,muna hira da Adams yanzu na sadaqar shine mijina kuma na hakura shirye shiryen dasu mama keyi na bikin nan ba dama har dubai su mama sukaje da anty yagana ga wasu jike jike da suke faman dirkamin bansan ko na menene ba sunce ma in saura sati biu bikin zamuje maiduguri a gyarani bansan gyaran da za'a min ba tunda dai nasan nima ba dan laifi baka ce amma ba bakikkirin ba hancina ba dogo bane kuma ba gajere ba bakina mai dan fadi da sirrin lebuna idona farare kal kuma ba kanana ba ne gudar gadar ne musamman ma in na tsorata kamar yanda naji ana cewa,sai muryata ni kaina nasan ina da murya mai shegen dadi game dajiki nasan akwaini dan kasa da sama ba matsala mutane da yawa jikina ke rudarsu ba wai so ba to ban san gyaran da suke nufi ba.Yau ni da Amira gidan mami muka je dan shirye shirye bayan munci munsha sai muka shiga abinda ya kawo mu can nayi tsaki gara mu tsaida magana don sati na sama zamuje maiduguri mami ta ce yin me?na dan tabe baki wai gyarani za'ayi har ma dariya abin yake bani mami tace ba sauki nace dan Allah wai gyaran menene? sukayi dariya Adamu zai baki amsa gabana ya fadi nace kuyi min bayani mana,mami tace kefa mukayi magana dake kwanaki nace ni duk ynxu tsoron Nasir nakeji kikace ke bakya tsoron Adams to zaki ji tsoron nesai kin shiga hannu,mu dai ynzu mun ketare sai ku, gashi har wani gyara za'ayi mashi Amira ta yi dariya tace nidai hankalina kwance nace zaima tashi ne na dubi mami nace da wuya ko?mami tayi dariya tace bance ba sai ta kuma kwashewa da dariya nace muguwa tace ba komai zan dai ji jiki ne.Tin ana sauran sati uku biki Adams ya aiko min da katuna ban taba ganin kati mai kyau irin wannan ba tunda naga katin sai jikina yayi sanyi na shiga daki sai kuka,babana ya kirani yace duk abinda nakeso na fada nace komai yayi min yayi,yayi yayi muje kasuwa na zabi kayan daki da kaina naki,yan uwan Adams sun kawo kaya akwatina saiti biu sai naga ma kamar ba gaske ba,yau juma'a maiduguri ta dauka tun da muka je sai aka shiga gyara ni daki aka ware mani nida mai gyarani nan gidansu anty yagana satinmu daya mun dawo ana saura sati daya bikinmu ni kaina nayi mamakin kaina dana dubi madubi sai kace bani ba yanzu kam na yarda gyara na mukaje dan nayi kyau san da na dawo su Amira sunyi nisa da rabon kati duk wanda ya kamata sunkai mishi batun yan gidan mu su haj yaya sunsha mamaki ganin shirye shiryen da ake ganin gyare gyaran da ake min ya kara firgita su gashi boka ya masu alkawari za'a fasa auren gashi har lefe yazo mai yawa koda mama tace sujesuga kaya ba kunya sukaje don gulma ganin kaya da gwala gwalai sai jiki ya kuma sanyi waya haj yaya tama laure akan tazo da magana bayan sun shiga uwar daki haj yaya tace laure zama bai ganmu ba kaya tun ana kirga zannuwa da nazo hamsin sai na daina ganin gwala gwalai sai hawan jini na yaso taso ya tashi ba arziki na fito daga dakin haj laure tace ynxu menene abinyi?yaya tace innaga gurin malamin nan zamu koma.... Adamszaune gaban malami ko nace boka ya dubesu kin cika gajan hakuri an daura auren ne?suka ceaah yace to na gaya muku ba shi ne mijinta ba zaa ba wani ne adakaa zaku sha mamaki kuje ku nutsu nan da kwana uku zakuji lbr ya canza rauhanai sunanan suna aiki yanda ya kamata nan suka yi godiya suka fita.Yau sauran kwana uku biki zaune nake akan kujera a wani daki gidan anty yagana nan muke nida kawayena yar borno wacce ta gyarani a maiduguri itace ta zo yau danmin lalle na musamman an zana shi hannu da kafa an ratsa jan rani dama kafin a fara sai da aka milkeni da wasu mayuka na gani na fada masu tsananin kamshi da su launin fata dama tun da muka dawo daga maiduguri kamshi duk inda na ratsa sai na barsu da kamshina yar borno na zaune tana kankare min lallan ba bose wata mai gyaran gashi ce ma kwaf tun su anty yagana ne ta hadda ai gyaran gashi ita ce tasa man gashi mai tsada tana min shampoo sai tabke min gashi takeyi wai nayi dabara da ban fara sa mai ba sai da na tashi aure ni dai jinsu kawai nakeyi saboda yau haka nake jin jikina,can text din da aka saba yimin ya shigo Amira ce ta miko min waya gashi ango yayo text nace ba ango bane na duba sai naga ina miki murna amma har ynxu bancire rai da samun ki ba har sai na ga an daura miki aure abinda bana fata dan ban san ya zan kasance ba wannan ranar,nace kaini wannan mutumin ya dameni Amira karanta ki gani wanda nake gaya maki din nan ne ta amsa tana kokarin dubawa tana cewa kila ma Adams ne kin kasa ganewa kafin ta gama dubawa sai ga call ganin sunan Adams ya sanya ta bani tace to ga ango ki ce mishi ya fa iso yau don gobe zamu soma shagali kuma muna so kowanne yaje,duk surutun da take yi ban saurare taba dan sai samu kaina da wata mummunar faduwar gaba na amshi wayar na daga sai naji muryar Adams cikin sanyi da sakewar murya yace Amina gabana ya fadi dan bai taba kiran sunan ba,na kwace kaina daga hannun bose nace Adams menene yace dan Allah kiyi hakuri banyi niyar yaudarar ki ba amma am sorry ba zan aure ki ba na fasa sai dai still ba zan daina sonki ba,jikina ya soma rawa nace adams ka cuceni me nayi maka? A...A....Adam...ka,ban karasa ba sai kirjina ya tokare jikina yana ta karkarwa,na dai ji su bose da yar borno suna tambayata lfy?Amira na salati daga nan sai na fadi Kash sai mun hadu a na uku don jin yadda zata kasance Halima Abdullahi k/mashi