Tawa Tasameni 1-01 Posted by ANaM Dorayi on 12:09 PM, 03-Dec-15 ________________NA _________________ __________ HALIMA ABDULLAHI K/MASHI_______ Na mike a hankali ina ninke sallaya ban kai ga ajiyewa ba naji ana sallama,na juya cikin don san in dauki muryar mai sallamar har kin shigo kenan?nace bayan na amsa sallamar ta shigo sanye da kayan makarantar islamiya masu launin farare kar,riga da wando da hijabi. Tace kina kallona ba zaki yi sauri ba sai munyi latti ko?nace ko munyi latti ai yau akwai layi na nufi daki dama nayi wanka sai kawai na dauki kayan makarantana dake goge kan gado nasa,Amira tace su mama basa nanne?nace eh basa nan gashi har jamila ta tafi a lokacin islamiya yayi amma basu dawo ba,na rungume takarduna da Alkurani na na fito falo muka fita na mika ma amira ta rike min littattafaina don zan kulle kofar,natura key din inda muke sawa in mama zata unguwa ni kuma ban dawo daga makaranta ba sai ta aje min a gun in kuma zan fita tace in aje mata.Amira ta dube ni ta dubi dakin su mami tace yau su mami ba zasu bane?nace da kyar ne don yau ko makarantar boko bataje ba bata jin dadi in mun dawo kin gaida ita.isarmu islamiya kenan muka tarar da an tare yan latti ana yi masu bulala,Amira ta soma dariya don ta sanni da tsoron bulala na dafe kirji ina fadin yau na shiga ukku zamu sha bulala ni iman,Amira tace don Allah mu karasa ba kece kika jamanaba?nace Amira ina jin tsoro ta ja hanuna na bita muna isa gun muka tadda harda Ahmed yayan Amira don shine Amir dinmu yace don Allah ku zo inyimuku ku wuce don yan kwanakin nan kun kware gurin yin latti.Nace don Allah yaya Ahmed kayi hakuri yace wllh sai nayi maku kun fi sauran ne?da zan kyaleku ya ci gaba da cewa kuna bata mani lokaci in har kuka bari kowa ya gama shiga sai na zane ku tas,wani kusa dashi yace to kai Ahmed ka bar su su wuce mana,yace Allah Aliyu bazasu shiga ba sai na dakesu wanda yaya Ahmed ya kira da Aliyu yace to bari ni in dake su to,yy Ahmed yace sai dae kai na dake ka a madadinsu,in ko ba haka ba sai dai suzo ni in dakesu da kaina,Amira na da zuciya don haka sai taje ta mika hannun shi ko bai bugi hannunba ya zuzzuba mata a jiki,ganin haka ya sani na kuma rudewa ina faman magiya don ni kowa ya sanni da shegen tsoro sannan bani son abinda zai taba mani lfyata don haka ma dawuya ka ga nayi laifi nakan yi kokari ganin nabi dukkan dokar da aka shimfida a gida ko a makaranta.Amira ganin zan bata mana lokaci taje gaban yy Ahmed tace ka bige ni a madadinta shiko da gayya ya ringa tsala mata har sai da Aliyun nan suka ce ya isa mana Ahmed niko hawaye na somayi na kama Amira muka wuce ina fadin me yasa kika je ya buge ki?ta soma share mani hawaye muka wuce ajinmu,Shidda na yamma daidai muka tashi dama mu yan aji biyar Ajinmu a sama yake,don haka titin kan layinmu naji an kwala mani kira cikin fada na juyo sai naga anty mariya gabana yayi faduwa don na san ganin ta ba alkhairi bane hakan ce ta kasance domin kuwa tana isowa gun mu sai ta hauni da zagi wai na taho makaranta ban jira su kamal ba don naga ba kannena bane shiyasa ta cigaba da zagina gami dayi mani gorin gida wai shegiya agola yar kara nazo zan fare,Amira tace mani don Allah iman zo muwuce taja hannuna cikin fushi tayi maganar,anty mariya ta koma kanta tace ke kar kiyi mani rashin kunya don zanci ubanki a nan,Amira tace ba dai ubana ba kuma har kika yarda kika buge ni zakiyi da kin sani,cikin rawar jiki na rufe ma amira baki muna cikin wannan hali sai ga anty hadiza da bilkisu da saade dukkansu sai zaginmu suke yi,Sa'a har da dungurina,nan amira ta kai mata duka nayi saurin rike amira don kar suyi mana taron dangi su bugi banza don nasan kadan suke jira anty mariya tace wai ke amira nan da dukan Sa'a zakiyi?amira tace yo da sai in barta ta duke mu,don kunga bata ramawa ne,lman din shi yasa ku ka raina ta, taci gaba da cewa,ai Sa'ar ba girman lman din tayi ba,bilki tace to ta koma gidan ubanta mana in kuma bata dashi bane mu sani,naja hannun Amira muka wuce Amira ta cigaba da lallashina sannan tace min,don Allah lman in tambayeki mana?na share hawayen fuskata da gefen hijabina nace ina jinki tace babanki ya rasu ne ko yana nan? In ya na nan ina yake?na dan yi shiru sannan nace Amira baba na yana nan bai rasu ba wasu hawayen suka kuma zubo mani ban damu da in goge ba na cigaba da cewa yana tudun wada ta nan kaduna,Amira ta ce to ki koma mana don zaifi maki kwanciyar hankali komin talaucin ubanka ya fi zaman agolanci y not ki koma can?nace uhhm Amira mubar zancen nan wata rana zan sanar dake dalili mai karfi da ya hanani in bar gidan nan sannan kisan mahaifina ki kuma daina zargin ko kwadayi ne ya zaunar dani a nan,Amira tayi sauri ta rike ni gami da tsaidani wuri guda tace wllh ni ba nufi na kenan ba naga wulakancin da su Sa'a ke maki yayi yawa ne shi yasa,nayi mirmushin karfin hali nace no a Amira karki damu na fahimceki sannan muka wuce gidan su Amira,kamar minti goma na dauka gidan su Amira sannan ta rakoni kofar gidansu tace min a cikin satin nan ba zata shiga gidanmu ba,ina shiga naga su Anty mariya sun rigani dawowa kuma sun fadi karya da gasky sai faman fada suke su da iyayensu suna ganina ai dawa Allah ya hada su ba dani ba suka hauni da masifa,Haj Kulu mahaifiyar mami harda aibantani gami dayi min gori sannan tace zata ga Amiran don ubanta sai ta gaya mata dalilin da yasa ta zagi su anty mariya don ba sa'anin yinta bane,ni dai sum sum na wuce daki Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Mama na gani a falo ta zuba tagumi da alama taji duk abinda suke cewa(kishiyoyin nata)ta dubeni fuskanta cike da tausayina tace Iman menene dalilin da yasa kika tsokanin mutanan nan bayan kinsan halinsu sarai nace mama wllh ban san me nayi masu ba na dai ga anty mariya sun zo da su Sa'a suna ta faman zagina wai ko na taho makaranta ban jira su Kamal ba ko mene oho mama tace to naji suna cewa kuna ta zaginsu keda Amira nace Allah mama ni sam ban ma yi magana ba Amira dai ce kinsan ta da zuciya shine fa ta tanka masu amma sam bata zagesu ba,mama tace to don Allah ki dai na kulasu sam musamman a kan titi in ma sun zo maki da irin wannan ki dinaga basu hakuri kiyi wucewarki kinji ko?nace to mama muka mike don yin sallar magariba. Misalin sha biyu da rabi muka taso daga harda yau ma yan dakinmu ne kadai ni da jamila da sagir muka je,dama sauran yan gidan zuwa islamiya bai damesu bane bare ma hadda,gara ma mami takan je to amma tun fridy bata jin dadi,muka tadda mama a kicin tana girki na shige kicin din bayan na ba jamila Alkurani na da hijab ta wuce daki nayi ma mama sannu gami da amsar albasar da take yankawa,nace yau me kike dafa mana ne,tace dan wake nayi in kin gama yanka albasar ga mai can sai ki soya shi bari in dauko kular baban ku nasa mishi,don yace zaya aiko a dauka nace dan waken za'a kai mashi kasuwa mama?tace nima haka na ce mashi sai yace yasan komi na dafa ba zaiyi shakkar kaishi cikin jamaa ba,nayi murmushin jin dadin an yabi mamana ai kin iya girki ne mama,ta fita tana dariya ina jin dadin yanda mama take sakar mani fuska duk da kasancewa ta yar fari a gunta sannan mama uwa ce mai wahalar samu takan ki nata don duniya ta soshi bata fada da zagin yayanta sai dai nasiha gami da lallashi.bani manta lokacin da nake karama mama ta kan zaunar dani ta nuna mani girman Allah gami da cusa mani tsoronshi tana nuna mani abinda zanyi da tsira daga azabarshi a wancan zamanin ta kance kar na zagi kowa ko an zage ni kar na rama sannan kar na yarda sallah ta ringa wuceni don haka ma tun ina karama nasan sunnoni da farillai gami da mustahaban sallah da alwala sannan bani zagi in ma wani yayi naji sai na gudu ince kar na sami zunubi saboda jin da nayi shiyasa ban iya zagi ba,sannan mama ta na da hakuri na ban mamaki zata iya zama da kowa ga ladabi don ban taba ganin tana musu da maigidanta ba komai yace tana yi sannan ga tsafta komi namu daban yake duk inda muka shiga ni da kannena mukan zama abin sha'awa gashi mama ta iya girki sosai na zamani da na gargajiya shi yasa maigidanta ya kanyi alfahari da ita baya shayin kawo baki ko shi akai mashi kasuwa haka nan duk da cewar basu shiri da abokan zamanta suma suna farin ciki da ranar girkinta don sunci mai dadi sannan yayansu kanyi rigima a duk lokacin da suka zo cin abincin kai ko ruwan tea ta dafa daban yake don zaka iya shanshi ba sai kasa madara ba.nayi zurfi a tunani bansan har mama ta dawo ba sai dai naji tace haba iman har yanzu kina kan yankan albasar nan baki tashi ba?nayi firgigit na juyo tace ai kina tunanin menene haka?bata saba mana da karya ba don haka na sanar da ita tunanin da nake na kara da cewa mama ina matukar jin dadin zama dake kuma ina alfaharin kasancewarki uwa a gareni tayi murmushi tace sai ki dinga koyi da hakan kuma kiyi watsi da duk wani kuskure da kika ga nayi sai da na zuba albasa a cikin man sannan nace wllh mama ni ba taba ganin wani kuskurenki ba tace kar ki kuma cewa haka babu mutumin da baya kuskure dan adam ai ajizi ne nace to,sai da muka gama cin abinci sannan na nufi dakin su mami don in gaisheta ina son inje amma ina tsoron haj kulu mahaifiyarta ynxu ma ganin ta shiga wanka shine dalilin da yasa xan je duk da dai bayin a dakin yake amma nasan ta shiga wanka ne a bakin kamal inda na tambayeshi ta na nan yace man ta shiga wanka na samu mami zaune a falonsu tana cin kifi nace yan jinya an samu lfy kenan tace kar kice man komi komi tunda baki zo gaisheni ba nace wlh ina son in xo gaisheki ina jin tsoro ynxu ma kamal na tambaya yace mani mominku ta shiga wanka,um kina jin tsoro ne?nace baki yarda bane tace na yarda nace Amira ta na gaisheki tace tana amsawa tace ai naji sauki kwarai don naci dan waken mama sosai kafin inyi magana sai muka ji maganar haj kulu fuskarta a daure ta nuna ni tace wannan yarinyar baki da zuciya in banda rashin zuciya har yaushe zamuce ki bar shigo mana daki amma kin kasa to yi nan ta nuna min hanyar waje.ta cigaba da cewa kekasashiya marar zuciya anyi halin uwa mami tace kai mama don Allah ta kaima mami duka a gadon baya yi min shiru yar iska duk ba kece kika jawota ba in na kuma ganinta anan sai naci ubanki ni dai nayi waje cike da takaicin zagin da nasha. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 washegari monday ga aladar gidanmu duk mai girki itace zata tashi tunda asuba dafa ruwan tea ko wane daki suna zuwa su dibi nasu a cikin flask su kai daki suje su hada,yau haj kulu ce da aiki don haka sai da na bari ta fita sannan naje diba bansan cewa madara ta kare ta kicinba sai da nazo hadawa da sauri na nufi daki na iske mama tana sa ma jamila safa nace mama babu da madara ko kadan ta dubeni tace kash jiya.... amma ga dari biyar can kan mirror dauki ki siyo yanda zata isa in yaso kafin ya wuce sai in sanar dashi nace to na dau kudin na fita,a tsakar gida na iske mami sanye da uniform hannunta rike da safa tace har kun gama karyawa?nace aah ya jiki tace da sauki yau dai zanje makaranta nace da kyau kam ki leka ta dubeni ynxu ina zaki?nace shagon sanita aje safar akan window din dakinsu taje muje in rakaki nace kardai a nemeki tace kedai muje,dashi ke shagon ba nisa nan da nan muka dawo shigowar mu kenan haj kulu ta fito daga daki ganinmu tare da mami ya yi matukar bata mata rai ta hau mami da zagi gami da daukar alkawarin dukan mami,haj yaya uwargida sarautar mata itace ta fito daga dakinta tace ke kulu kina bani mamaki ga yar iskar da zaki jibga nan ta nunoni sai ki hau yarki da zagi kinsan fa ita da uwarta in mutum ya sarkafe masu baya ji baya gani sai Allah da malaman gari indai zakiyi mata addua to kawai kiyi mata,niko uwar tsoro jin ance zaa bige ni sai nayi daki da gudu ko mama ban bari taji xancen ba don bata son tashin hankali kuma Allah ya taimaka ta kunna rediyo inda tasa kaset na kr2n Alkurani kira ar sudes,a gurguje muka karya don kar muyi latti muna cikin sallama da mama kamal ya shigo wai kuyi sauri ko muwuce inji anty mariya mama ta miko mani naira hamsin tace gashi sa jikka nace barta mama gafa ta jiya nan ban kasheba sagir yace meyasa mu ba'a bamu kudin mama tace ku ai ga kwandonku nan cike da kayan abinci amma in kun girma zan dinga baku kuma,jamila tace kai sagir mama tace babu kyau a ba kananan yara kudi yace wai haka mama? Mama tace e mana nace kai muje kar ayi ta jiranmu mama sai mun dawo tace to.. haka rayuwa ta cigaba da kasancewa kuma kusan ko yaushe inada abunyi ban cika zaman banxa ba in bani makaranta to ina kicin in ranar girkin mama ne don haka nima babu girkin da ban iyaba na gargajiya ko na zamani haka nan kuma na kan gyara dakin mama da namu da falo sannan na kware gun wankin bayi nasa turaren wuta shiyasa dakinmu kullum yana cikin kamshi da sanyayar iska mai ddi na kan zauna nida yan kannena in koya masu kr2 Alkurani da sauran littatafai haka ina taimaka masu da homework dinsu shiyasa mun fita daban a gidanmu komi namu tsaf tsaf,a ranar wata sundy lokacin muna hutun islamiya, hadda ma don muna kusa da fara azumin watan ramadan da safe misalin karfe goma da rabi na gama duk wani yan gyare gyare nace da mama bari na shiga gidansu amira dama nan ne gurin zuwana tace to ki gaida mmn faruq nace to,na samu Amira tana faman krtun littafin hausa a falonsu ko sallama ta bata ji ba sai da na zabga mata uban duka sannan na fizge littafin na duba sunan shi naga Allura cikin ruwa,nace kedai kullum kina cikin krtu maman su ta fito na gaisheta tace mani yasu mama nace tama ce a gaisheki tace ina amsawa na dube ta nace mama wai baki hana Amira krtun nan ne?maman su Amira tace nayi nayi taki bari ynxu ma boyewa take don tasan in na gani yaga shi nakenace in tana son tayi karance karancenta ta bari sai ta kai ss sannan ta kijiba sai tayi tayi ba,maman tayi shiru cikin bacin rai na harari Amira nace kinji ddi mama ta bata rai saboda ke?mama tace ai ke kina da hankali ba kamar ita ba ta shige daki Amira ta dubeni tace kinji ddi kin hada ni da mama nace no Amira in iyayenmu sunce mu bar abu muyi kokarin bari don gsky zan gaya maki da ki kijin mgnr iyayenki gara ki bar duniya a guna kenan tace to naji taja hannuna tace zo muje dakina nace ke dai Amira baki son fadin gsky muna shiga na zauna bakin gadon nace mata don Allah Amira kiyi kokari ki barin krtn nan tun da mama ta baki damar yin krtn in kinje ss.Amira tace nayi kokarin na bari na kasa ne,nace ni ko kingani nan ko me mama tace na bari ko da zan rasa raina ne ba zan bari don bani da tamkarta nai shiru ina tunani hawaye ya zubo min na dubi Amira nace don dai iyayenku duka biyun suna nan raye ko ince a tare shi yasa baki san zaman agolanci ba cikin hawaye ban san sanda nace......... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 sunana na gsky shine Amina kuma naci sunan kakata ce mahaifiyar babana ,babana da mamana yan asalin wudil ne a wani kauye da ake kira indabo a jihar kano,babana gidansu sun gaji sarauta don babanshi ne dagacin kauyen,yanxu haka itako mama yar malamai ce don babanta shine limamin garin sunan mahaifina idris kuma shine da na hudu a gurin mahaifinsu yana da yayye yaya samaila sai yaya musa sai babana idi kamar yadda suke kiranshi sannan sai kannanshi biyu bala da sani su shidda ne a dakinsu matan dagaci biyu ne uwargida Amina mahaifiyarsu babana kenan wadda naci sunanta sai abokiyar zamanta basira wacce aka bashi sadaqarta ita kuma yayanta ukku Auwal,salisu sai hindu,suna matukar zaman lafy ba wani bambanci wannan shiyasa yayansu hadin kai da son junansu gashi suna ma mahaifinsu dagaci umar biyayya kuma dukkansu gidan liman suke daukar krt mama ko a lokacin tana kaduna gidan yayanta mai suna mal bashir ya dauko ta ne tunda mahaifiyarsu ta rasu shi babban malami ne a tudun wada daga yawan almajiranci Allah ya zaunar dashi a inda yayi auren shi da baba uwa itama dai yar can din ce da yaje ya auro ta,yana almajiranci a wani zuwa da yayi gida shine ya tafi da wasu almajirai a cikinsu harda idi babana kenan domin yayi sauka tuni,zai dora ne su ko su mama su hudu ne a wurin liman kawu bashiru shine babba sai kawu Aminu sai kawu kabiru sai mama ita kadai ce mace tana da shekara tara mahaifiyarsu Allah yayi mata rasuwa kasancewar ita kadai liman ke aure sai kawu bashir ya dauko mama dama baba uwa bata taba haihuwa ba ko ince har ynxu Allah bai bata haihuwa ba sai ko ta rike mama,shi ko liman isuhu aka bashi sadaqar mata guda biyu da taimakon baba uwa mama mai suna habiba ta samu shiga firamare shi ko baba yana nan yana hadda gidan sai Allah ya hada shi da makocinsu Alh adamu a dalilin dan gwanjo ne a kasuwar bacci yasa baba yana rubutu yana kai masa daga nan yace yana yayi sanaa irin ta gwanjo alh adamu shima dai dan kn ne ana ce mashi adamu garko duk girinsu daya sai dai shi a garko yake bayan nemi izinin malaminsa wato kawu bashir kawu yace tunda kayi sauka hadda kakeyi ba bu komai ko da rana za ka iya haddar ka Allah ya bada saa wannan sanaar itace hanyar arzikin mahaifina tun yana kasawa a bakin titin kasuwar bacci in an kwance dila a bashi ya kasa har ya koma kwance dilar shima kafin shekara ukku har ya sayi rumfa kuma yana sayan diloli a wannan lokacin ne Allah ya ba baba uwa ciki ta haifu da namiji kuma mama a lokacin ta kammala primary shiko babana duk da ba a gidan yake ba yanzu yana zuwa da daddare haddar shi ya sanar da malam kamar yadda suke kiranshi kawu shi dai habiba yake so mutumcin da baba yake dashi a idon malam shi yasa har ya amince koda kauye suka ji wannan zance sunyi murna don akwai zumunci mai karfi tsakanin gidan dagaci da gidan liman,kauye aka koma akayi biki sannan su mama da baba suka dawo shekara biu da aurensu baba yayi kudi sosai da gwanjo tuni ya gina gidanshi a unguwar sanusi ga motocin hawa da na haya da ya sai ma mama sannan ya tallafi yan uwa na kauye hakika yana da halin kanawa na asali don akwai taimakon na kusa dashi haka ya debo yayan yan uwa sa daga kauye ya sasu a makaranta dan yana da haushin rashin bokon da baiyi ba danma cudanya da mutane yasa ya fara jin dan turancin sa na yan kasuwa matsalar baba da mama daya shine rashin haihuwa har wannan lokacin mama ta fishi damuwa shi ko ko a jikinshi yace Allah baya barci a gefen mama ita ma tana taimakawa yan uwanta dama tuni daga dagaci har liman sun keta hazo sannan angyra gidansu tsohuwa Amina(kakata) sun kaita ita da abokiyar zamanta harda yayyan babana,su mama dai kowa a kauyen ya gama zuwa a cikin iyaye da yayye sannan suma suka je ita da babana.kowa yaje sai ya roka masu Allah ya basu haihuwa har cikin dangi sun fara korafi gami da nuna masa ya kara aure ita ko tsohuwa Amina macece mai nagarta da ibada da yarda da kaddara don haka itace mai tsawatarwa sauran yan uwanta da kannen alh idi (wato babana)takan mika lamarinta ga Allah don haka kullum ma tana yi masu adduar Allah ya basu yaya na gari masu albarka,shekaru goma da aurensu Mama na da babana sun dawo ummara ta dawo da jinya mai tsanani bayan jin jiki da jinyar asibiti sakamako ya fito cewa tana da ciki fadar farin ciki ma bata baki ne,anan da kanshi baba yake mata rubutu take sha..... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Wata tara da 'yan kwanaki ta haifo ni sankaceciyar kowa ya zo barka sai ya yaba girma da gashina sai dai ni baka ce tamkar mahaifina tun ina yar jaririyata har yau ban canzaba, dangin babana na dauko domin gaba dayan yan uwanmi dangin baba kamar mu daya muna da dan kyau daidai namu sai anan na dubi Amina nace kin dai ganni har yau ban canza ba na cigaba da cewa dangi sun kwararo daga kauye da birni anan naci sunan tsohuwa Amina, kawar mama kuma makociyarta itace ta ba da shawarar a kirani da iman,na taso cikin gata da tsantsar so gun iyayena da yan aikinmu da yayyena wadanda babanmu yake riko,shekara takwas na halarci makaranta nursery mai suna salmat intl dake kasuwar santara market makarantar yayan masu kudi ce don haka krt ba wasa duk lokacin hutu babana ya kansa a kaini kauye don yace asali mafari wannan yasa na saba da kakata Amina da yan uwana 'ya'yan baba lami mata sa'anina Hassana da Ussaina muna wasa dasu kuma sune suke kaini ganin dangi a sauran kauyukan,ina matukar son kauye musamman yanayin damina tayi min a garin domin muna zuwa gona kakata tana ji dani don haka nima ina sonta suma dangi kowa na sona kawunnaina da liman suma ina zuwa in yi masu kwana biyu yau ina nan gobe ina can gata dai gani nan cikin sai in hutu ya kare zamu dawo wani sain da kuka nake dawowa a hado mani tsarabar kauye mai yawa dangin uwa da na uba sannan mu dawo tare da su yaya Ibrahim da yaya Abubakar,yaya Abubakar dan baba lami ne shiko yaya Ibrahim dan Baba Auwal ne(wato dan kishiyar kakata)tun kan a haifeni suke gidanmu kuma suna makarantar gumi college SS2 don haka tare muke zuwa hutu kauye dasu,kuma muna kama dasu don duk wanda ya ganmu yasan yan uwa ne saboda kokarina a kai ta turanni gaba a makaranta sannan kusan kowanne malami ya sanni don haka ina da shekaru goma sha daya na kammala primary din tare kyaututuka masu yawa muna zaman jiran fitowar sunayenmu ne,na fuskanci matsala ta soma kunnowa gidanmu in da mama ta tada hankalinta ni ban san dalili ba amma nasan nasha ganinta tana kuka in nace mama menene?sai tace idonta ke ciwo kuma koda yaushe zanga anty yagana kawar mama tana zuwa gidan su shiga daki da mama suna yan shawarwari,ni bansani ba wai ashe baba ne zaiyi aure da wata banufiya mai suna fati kuma ance ma mama bata da mutunci shine hankalin mama ya tashi tace da baba gsky ya canza mata sai baba yace karyar mutane ce kawai ya dinga lallashi gami da ban baki sannan ya kara mata jari har na naira dubu dari takwas dama tuni ya sai mata motocin bus guda biyu da babura ana mata haya dasu,anty yagana makociyarmu ce yar asalin maiduguri ce amma zama ya kawo yayarta da mijin yar in da suke zaune kurmin mashi yayarta ce ta aurar da ita ga wanda take so Alh shu'aibu ma'aikaci ne a water board, tana da yara ukku kusan tare aka haifemu da yarta ta fari mai suna saudatu,suna amintaka da mama sosai haka ni da sa'adatu makarantarmu daya,bayan haifuwarmu ne anty yagana ta kara haifuwar yara biyu Nurfa da abida,Mama ko shiru tun daga kaina,anty yagana itace ta ba mama shawarar su hada jari su soma harkar yan kunnen gwal da jallabiya da zannuwan gado suna bada sako ta hannun wani abokin Alh Shuabu ne mai suna Alh Mukhtar Maska Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Dan zinare ne a kasuwar sheikh Abubakar gumi yana da shagunan jallabiya da gwala gwalai,shine yake kawo masu kaya in ya fita dubai harka ta amsu don da an kawo xaka ga matan manya suna zuwa suna dubawa suna saya don haka mama ta cire hankalinta daga batun auren baba,bayan auren amarya Fatima ta tare a dakinta da farko ta kwantar da kai amma ganin yadda mama ke facaka da kudi yanda baba ke ji dani sai hankalinta ya tashi ta shiga tsiro fitintunu iri iri yau tace kaza gobe tace kaza tasa su yaya Ibrahim da yaya Abubaar a gaba,a nan mama ta taka mata birki tace kar ta sake ta takura masu suma gidan ubansu ne in tana jin masifar tata ta yi da wanda ya ajiye ta bada yara ba,wannan rigima har gun baba jin bata sami gsky ba shi ne tayi yaji sai da tayi wata sannan ta dawo,dawowarta shine ya zama sanadin juya mana baya duk yanda baba yayi sam baya sauraron mama da farko ban gane ba saida sunanmu ya fito munci makarantar mu salmat da mama ta sanar da baba sai yace kar mu dameshi ya gaji da biyan kudin makaranta,ni ba wani kokari ba shi maimuna gwarzo zai maida ni na ringa kuka ina rokonshi sai ce min yayi inyi hakuri shi ya gaji,haka na cigaba da zuwa islamiya da hadda boko kam ina ganin saudat tuni har ta shiga SS1 niko ina gida ,anty yagana tace da mama ta biya mani da ita tana da kudi tace ai ta mashi magana yace bai yarda ba,wata rana na dawo daga hadda da rana jugum na samu mama tayi a dole na zauna kusa da ita na dafa ta nace wai mama baki da lafy ne?tace kaina ke min ciwo iman,na tashi na nufi gun da muke aje magunguna na dakko mata panadol na dibo ruwa a kofi na kawo mata ta amsa tasha sannan tace kije dakin yayan ki duk wanda kika gani cikinsu kice yazo zan aikeshi wajen kawunku malam nace nima zanje mama tace to amma sai kinci abinci ko?nace e nayi sashen su yaya da gudu,a kofar dakinsu na tsaya nayi sallama yaya Abubakar shine ya amsa nace in shigo?yace in dai tsohuwa ce kar na ganta anan(haka su kan tsokane ni wai tsohuwa)na shiga nace kaine dai tsoho bani ba yace me yasa zaki sa mana tsufa daki don Allah kije waje nace naki din aje wajen baka girmeni ba ma zaka ce min tsohuwa,ya kwashe da dariya yace waneni da girmanki kece fa kika haifi su kawu da mama da baba anan gidan haushi ya kamani na hau tsaki irin na shagwaba ina son inyi kuka nace sai na gaya ma mama na juya zan fita ya jawo ni zo mana yar kanwata tawan zo mana kiji mama ta aiko ki guna ne?nace eh tace kazo zata aikemu gidan kawu malam ya mike ya dungureni shine baki fadi mani tun dazu ba?ya rike min hannu muka tafi dakin mama ban san me tace mashi ba na dai ga ta bashi kudi sanna tace in tafi falo inci abinci kafin ta gama bashi sakon,na kunna tv na kamo cartoon ntwk ina kallo ina cin abinci sai naga anty Faty ta fito ni ban ma ganta ba sai gani nayi an kashe tv din na dube ta nace aunty ina kallon tom and jerry ne,tace na kashe ko zaki kunna ne?niko ban san gatse ba sai nace eh cikin masifa tace to zo ki kunna har ga Allah ni ban san gatse tai min ba sai kawai na tashi na kunna tv din remote din na hannunta kafin na juyo sai saukar mari naji dau na yanke da ihu sai ga mama da gudu ita da yaya Abubakar dama shi akwai shi da zuciya yace faty me tayi maki,anty faty tace in dole sai kasan abin da tayi min to ka nemi sani daga gareta dube ka dan kauye don kazo ka waye shine zaka kawo mana raini ko?yace naji ni dan kauye ne ke baa ma san asalin naku kauyan ba,don ba muga yanuwanki ba waya sani ma ko daga sama kika fado banza yar iska haka zaki kare a neman asiri,sai tayi kanshi da zagi harda duka nan da nan ya sharara mata mari gami da ture ta mama da tuntuni take tsaye tace kai Abubakar wuce kasai kabar aiken sai anjima,ta nuna ni ke kyma yi daki na mike sannan na jiyo mama tana cewa kin gani ko faty wannan shine abinda na jima ina sanar dake ki daina shige ma yarannan kinki ji to kinga irin.......kan mama ta karasa sai ta katse mata hanzari da masifa ke munafuka bake kika sasu ba?to albishirinki yau dinnan zaki san matsayi na bakinsa Abubakar ya mareni ba?zaku gane baku da wayo yau,nayi shiru a daki ina kuka mama tace to ina jiranki da alkhairi anty Faty tace ni kuma da sharri nake jiranki yau da nai nasarar rava alkhairi da tunanin wata ya mace haka zan rabaku da gidan nan mama ta ce to ai Allah ya fiki kuma ba ya barci kuma yana tare da masu hakuri ta cigaba da cewa ke ko nasan baki san haka ba tunda kin yi nisa ba zaki taba jin kira ba to sai muce Allah ya shiga tsakaninmu da ke in kuma mai shiryuwa ce Allah ya shiryaki,Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 ta shigo ta sameni inata faman kuka ta zauna kusa dani ta jawo ni jikinta tace iman wace adduar kike min,nace ina rokon Allah yasa ki daina samun matsala da baba,mama tace ki hada da babanki shima ki dinga yi mishi ki roki Allah ya kareshi sannan ya raba shi da dukkan sharri da ake mashi,nace mama wanene yake ma baba sharri?tace aa mugun abu ai ba sai kasan me maka zaka roki Allah ba,nace to insha Allahu zan dinga yi mishi,da dare sai ga dan aiken baba,yaya Ibrahim ne baba ya aiko wai muzo ni da mama babban falo babu neman ba'asi ya dauki hannu a gaban mutane ya mari mama ga yan aiki ga yayyena ga ni ga anty faty bayan marin ya cigaba da fada wai kar ya kuma jin an taba mishi mata inko ta kuma marinta ta mari aurenta mama tana rike da kumatu sai nan tace cewa tayi maka na mareta?yace to yau kuke me yasa tun da kuke tare bata ce kin mare ta ba sai yau kuma tace tana son in rama mata shi yasa mama tace shi kenan ni Allah ya rama mani ta shige daki,duk da karancin shekaru na sai da nayi mamakin baba wai ya rama wa anty mari?na juya na dubi anty sai naga tana wani ciccika tana batsewa wai an rama mata, na bi mama daki na iske tana kuka na dafa ta nima na soma kuka ina cewa mama kiyi hakuri Allah ya saka maki. Anyi haka da kwana biyu na dawo daga kitso in da yaya Abubakar ya kaini tudun wada na mari yaya Abubakr din da wasa don ya dameni da tsokana tun a mota wai tsohuwa mai dan koko Allah kashe ki musha gumba,nayi banza dashi sai da ya tsaida mota sannan na dan kai mashi marin wasa kadan na bude motar nayi cikin gida da gudu,yace ni kika mara?sai na rama shima ya fito yana dariya ya biyoni yana kirana nayi falo da gudu ina cewa so kake in tsaya ka rama ban kula ba na bude labulen falon na fada sai kawai naji na bige mutum lokaci guda kuma naji anyi jifa dani ashe nayi karo da anty faty ne shine ta jefar dani kuma ta biyoni da duka takeyi yaya da har ya juya da yaga na shige falo sai kuma yaji kukana nan da nan ya dawo ya iske anty nata faman dukana cikin zafin rai yake ma anty magana yace don Allah me yarinyar nan ta yi maki kike dukanta haka?yanzun nan fa muka shigo?ta juyo kanshi da zagi da gori,jin hayaniga shi yasa mama ta fito ta dubeni ta dubi yaya sannan tace Abubakr ba zaku daina daukar min magana ba ko?yaya yace wllh mama bamuyi mata komi ba niko sai faman kuka nake ita ko anty faty sai zage zagenta takeyi jin mama bata kula ta ba sai kawai ta shaki kwalar rigar mama tana cewa yau din nan na tsara zaki bar gidan nan duk na cinki miji ya wulakanta ki amma don bakin naci kin dage kin ki tafiya ko,ta cigaba da cewa to yau din nan za'a kama kai a koma wurin mai dattin hula,yaya ya fincike hannunta a wuyan mama sannan ya daura mata mari yace marar mutunci yar dangin jaraba rigima dai ta ki karewa har yamma sai da tayi ma babana aike har kasuwa wai yazo nan da nan sai gashi lokacin ma kowa ya kama gabanshi yaya Abubkr bai ma nan ni kuma ina daki mama tana koya mani karatu sai ganin baba mukayi ya shigo ko sallama babu ya jawo ni a gaban mama ya hau duka da wayar wuta ina ta ihu gami da neman taimaki amma ina mama ko kallo ban isheta ba sai da ya gaji sannan ya barni don kanshi,sannan ya dubi mam yace ke kuma in tambayrki?mama ta dubeshi ba tare da tayi magana ba yace dake muka hada muka sayi gidan nan?mama tayi shiru yace ba dake nake magana ba mama tace ai ina jinka yace to ina son daga yau na sakeki saki daya sannan na barki minti goma ki barmin gidana.....Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Duk da nike karama ina jin ya ambaci saki sai na kara yanka ihu itako mama duk da dauriya da tayi don kar tayi kuka ace gabana sai da kuka na ya sata hawaye koda mama ta gama kimtsa kayan ta ta fito falo zata tafi na biyo ta da gudu ina kuka babana yana zaune yana cin abinci da bai tanka ba sai da anty tayi mashi wata magana sai yace da mama ki tafi da yarki in kinji shawarata don ni ynxu nafi son yaya maza daga tsatson faty ga mamakina sai naji mama tace to Allah ya baku sannan na gode da shawara amma ko mun tafi da iman ai kanan nan a matsayin ubanta ko?maimakon yayi magana sai kawai ya kalli anty faty komi tace mashi oho sai ya juyo ya kalli mama yace kuje dai sai yanda hali yayi idan nine ubanta to na aiko maki amma fa gunki zata ci gaba da zama ba ba tare da mam tayi magana ba ta jani ko takalmi babu mukayi waje,wannan fita da mukayi itace fita ta karshe daga gidan babana mahaifi kuma har yau ban kuma zuwa ba ban kuma ganin babana ba ko anty fati ba. Muka koma gidan kawuna marikin mamana daki guda kato bayan sati biyu babana ya aiko ma mama da dukkan kayanta haka mama ta cigaba da zaman iddarta har ta gama, itace tayi mani komi na shiga SS1 a makarantarmu wato salma,ina jin dadin zama da baba uwa wato matar kawuna suna da yay biyar yaya suleiman shine babba sai yaya nura,anty rukayya ke binshi sannan sai nana itace sa'ata sai karamin su mai sunan kakanmu liman ake kiranshi don sunan liman din yaci wato isuhu,nana maimuna gwarO take itama js1,yaya suleiman tela ne kuma yana zuwa poly ko da yake san da muke a maigidansu saura yan kwanaki ya gama shi ko yaya ustaz ne don yanzu haka ya na koyarwa a wata islamiya nan kusa da gidansu,sannan shima zuwa tashi wato sanawiyya a unguwar ma'azu,anty rukayya kuma tana aure ne a badarawa yaya suleiman yana debe mani kewar su yaya Abubakar don shima yana tsokanata kasancewar mu abokan wasa ne ya kance mani matar ni kuma ince mashi ya mani tsufa bana sonshi yaya nura baida faraa shiya sa nima ban cika kulashi ba,Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 wata rana ina zaune daki sai mama ta shigo lokacin kuma gab da babbar sallah ne mama tace iman shirya muje kasuwa nace to dama na riga nayi wanka sai kawai na dauki hijabina mai less a kasanshi nasa takalmina nace mama na shirya muka nufi kasuwa,bayan mama ta gama mana yan saye sayenmu nida nana sai tace muje wajen yan zinari zata sai wani nace to muka je shagon shi makare da gwala gwalai kala kala da fara'arshi ya tari mama,naji yana cewa haj Habiba sai yau kikazo kasuwa?mama tace wllh ko Alh mukhtar maska inafa son nazo amma ban samu lokaci bane sai yau ya turo mana kujera yace mu zauna ya nunani yace wannan yarki ce ko?mama tace aa yace ke yarta ce ko yan mata?nayi murmushi yace ga murmushin nan irin naki ke ya sunanki?nace sunana iman yace suna mai dadi,sannan ya juya gun mama yace kin sami sakona a gun yagana? don tazo shekaranjiya ta kawo wasu karyayyun yan kunne,mama tace bamu hadu ba gsky mun dai rabu akan zata zo nan din yace sakona bai isa ba kenan?mama tace eh sai ya dubeta ya ce zaki samu ganina zuwa yaushe?sai nazo gidan naku,mama tace lafy dai ko?yace sai alheri mama tace to ko yaushe kaxo zaka sameni sai dai da safe ina zuwa islamiya yace ba matsala zan shigo tudun wadan yanzu me kike so?mama tace ina son in saima Iman dubai ne kasan da na daukar mata a cikin kayan da ka kawo mana wancan sati ukkun da suka wuce to sai na ga kuma sun mata girma sai naba yagana tace kace mata sai bayan sallah shine nace bari nazo gunka ko zan samu wani,yace ba zaa rasa ba in kuma kinga ba wanda yayi miki to ki sai mata saudiyya mama ta zabar kirar dubai na wajen dubu tamanin har da abin hannu guda biyu yace gasky kina ji da wannan yar taki mama tace kai maska don na sai mata yan kunne?yana dariya yace sai nazo zan amshi kudin mam tace a'ah ga dubu hamsin nan bansan zan sami masu tsada haka ba mukayi sallama ya bani dubu daya yan hamsin hamsin a cikin kudin nayi godiya muka tafi,bani manta ana jajibir sallah Alh mukhtar maska yazo gun mama ni dai na dawo daga kitson sallah nida Nana na iske bako a dakin yaya suleiman da zai tafi mama ta shigo tace naje na gaida shi don yana ta faman magana in na shigo nazo mu gaisa,na zauna a kasa dashi na gaishe ahi yace kin dawo muga kitson na nuna mishi yace iyye yayi kyau sosai yasa hannu a cikin aljihun shi ya dauko kudi sababbi yan naira ashirin bandir daya yace ga goron sallah don kilan ba zaki ganni ba naki karba nace ka barshi muna musu mama ta shigo jin musun da mu ke ne tace sunyi yawa ne alhaji ka rage yaki dole na amsa nayi godiya.Amira wacce tayi shiru tun da na soma magana kamar ruwa ya cita sai da nayi shiru sannan tace gsky iman ke yar gata ce to amma sai nan gaba zaki sani in Allah ya kawo karshen muguwar matar babanki,nace Allah yasa,Amira ta gyara zama sannan tace anty faty matar babanki ta haihu?nace kai har yanzu Allah bai basu ba tace to ina yayyenki Abubakar da Ibrahim kuma?yanzu basa zuwa nan?nayi murmushi nace kin cika tambaya Amira zaki yi kyau da yar aikin da nake ra'ayi wato yar jarida Amira ta basar da abunda nace tace baki amsa mani ba nace basu san nan gidan ba don kwanaki baba uwa tace masu mama tayi aure,sai kuma ta kuma cewa to ina yayansu mami abdul wa ma kika ce mani?nace abdulrahim sunanshi mami tace yana england shi dan wasan kwallo ne nima ban sanshi ba amma ya sha masu aike nima na gani,shi kuma kabir aikinsa shi dai amira tace haba nasan shi mana ba shi ne yake karatu a kano ba,tace ai shi naga ba ruwanshi don naga yana maki wasa nace gsky shi kam ba ruwan shi ko zai zo hutune ya kanzo da yar tsaraba su sweet biskit da yan kayan lashe lashe ya ba kannenshi tonima yanda ya basu haka yake bani don haka nima nake sonshi a raina ganin shi nake kamar yaya abubakar duk da bai tsokanata irin na yaya abubakar din amma kinga yayan nasu da ke waje ina tsoron ranar da zai dawo,ta dube ni don mi kika ce haka?nace don ina jin yanda suke lbr shi wai ya cika masifa ga duka sannan nasha jin yanda suke bada lbr irin son da yake ma hajiya yaya,sunce yana son mamarsa kamar ransa don bai hada ta da kowa ba yanda mami take bada lbr sai kinyi mamaki sosai abin kamar ba gaske ba to kuwa ai kinsan dole ne ya kuma ki duk abunda taki gami da tsanar shi tunda sunce komi tace mashi yayi,don haka ina jin ance yau zai dawo zan hada ya nawa yanawa na kama gabana na koma can gidan kawu na malam,Amira ta dinga man dariya wai na cika shegen tsoro nace ai ke dariya ma nabaki?lallai Amira, tana dariya tace dole ne nai maki dariya ma naga dai komai son uwar shi sai kin mata abu sannan zata sanar dashi sannan in baki sani ba su maza ba yawancinsu basu da daukar zance na tsegumi haka wannan sai mata sai ko sakaran namiji ina jin wannan ba zai maki haka ba don shi dan boko ne nayi shiru ina nazarin maganarta can nace wannan gasky ne to Allah yasa dai kar ya kulani,Amira tace amin,mun kaure munata zuba lbr sai kawai ganin yaya Ahmed mukayi nace a'a yayanmu ustazi ba sallama ne?yace ku dai bakujin sallamar to mama tace a tashi ayi sallah dama masallaci zani,yasa kai ya yi waje na mike nace bari na wuce gida kawai,Amira tace ai baki isa ba sai kinyi sallah kinci abinci sannan zaki bar gidan nan,na kwace daga riko da tai min nayi waje ina dariya nace yaushe rabon da ki shigo gidanmu,ta biyo tana kira na gudu gashi nayi sa'a mamansu tana daki tana sallah a gidanmu ma mamanmu sallah na sameta tanayinima sai na shige dakinmu naga jamila tana barci na tashe ta muka yi alwala muna idar da sallah nima na kishingide. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 DOCUMENT CREATED BY ZAHARADDEEN SHOMAR WHATSAPP ,08168575100 Tawa Tasameni1-02 Posted by ANaM Dorayi on 01:20 AM, 20-Dec-15 Under: TAWA TASAMENI TAWA TA SAMENI NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Ranar lahdi da daddare sai gasu yaya abubakr sunzo nan muka sha fira, ynxu anty faty ta gama mallake babana sai abinda tace gashi har ynxu Allah bai basu haifuwa ba sai karyar bari,na tausaya ma mahaifina kuma na yi alkawarin sa shi a addua insha Allahu zan kuma roki mama ta barni inje na gaida kakata in munyi hutu mun jima dasu sannan sukayi sallama damu suka tafii,muna shirye shiryen soma jarabawa zango na ukku don shiga SS2 aka yaye mu a islamiya inda mukayi walima a gidansu Amira duk gidanmu ni kadai nayi sauka mami kuma sai shekara mai zuwa don tayi wasa da karatun mama da maman su Amira harda Anty yagana duk sun mana bige bigen abubuwa irin su kalanda da robobi,hankici da sauransu,da zamuyi rabon katin walimar har su yaya Abubkr sai dana bawa Amira nayi mata kwatancen taje takai masu kuma sunxo mani da kyautututukan su inda suka bani waya a kwalinta wai inji babana na amsa cikin fargaba na kai dakin kwananmu na boye shima yaya Sulaiman yazo kuma shine ya dinko mana kayan da muka sa ranar walima nashi gudummuwar kenan wata shadda ce galila mai kyau da hijabai. Sai da komai ya natsa sannan na dauko wayar dasu yaya suka bani na kai ma mama na mika mata leda ta amsa ta gami da tambayar menene a ciki?nace su yaya Abubkr ne suka kawo wai inji babana na fada mata cikin tsoro,ta saki ledar daga tsaye tace ke kuma ki ka amsa to ko menene ma a ciki zan maida musu ni,haka kuwa akayi ta kira yaya Abubkr a waya ta bashi gami da yi mishi gargadin karta kuma ganin wani sako daga babana da sunan wai nawa ne tun daga nan suma su yaya Abubkr din ta daina sakar masu fuska.mun shiga SS2 cikin sa'a da nasara ranar wata jumaa mun tashi daga makaranata na tsaya ina amsar sakon wani littafi da zan amsar ma Amira gun wata yar ajinmu Hauwa aminu don yanxu in tana karantawa nakan zauna ta bani lbr ko ta karanta mani na amsa na isa gurin da Musa yake tsayawa wato direbanmu ban sameshi ba na tsaya nayi sororo can na hango wata yar ajinsu mami don yanxu ba aji daya muke dasu ba ni ina A su suna C na isa gunta sai na tambayeta ko taga su Sa'a?don mami bata zo ba tace mani sun tafi abinsu nayi shiru na kuma ce mata motar tazo?tace ba bus din gidanku ba?na daga kai tace to sun dade da tfy,sai da nayi nisa a tfy kasa sannan wani tunani yaxo mani na tsaida mashin na hau sai da muka zo har kofar gate din mu sannan nace bari na shiga na amso maka kudinka ina shiga harabar gidanmu naga matasan layinmu sun cika a kofar dakin yaya Kabir har da wadanda ban taba ganinsu a layinmu ba,nace a raina ko yaya Kabir ya dawo ne?don ynxu yana bautar kasa ce a Bayelsa na shiga gida na sanar da mama abinda ya faru tace to a nawa ya kawoki?nace 40,ta bani 50na kai mashi a hanyar dawowa cikin gida ne nayi karo da Anty Hadiza dasu Anty Mariya suna dauke da manyan tururuka da kuloli a kai,Bilkisu kuma tana dauke da dauke da plates da cokula ga wani kwando mai dauke da kayan shaye shaye na dube au na kauce a hanya,amma duk da haka sai da anty Mariya ta daka min tsawa ke akuya ban hanya,na matsa musu suka wuce,na shiga ina mamakin wane bako ne yaxo ake mashi hidima haka?bayan naci abinci nayi wanka nayi sallah na shirya cikin riga da siket yan kanti ina zaune a tsakar daki ina yin note sai ga mami da gudu ta shigo tana kwala min kira iman! iman!!na tashi da sauri ina fadin gani nan nace menene?don duk na tsorata sai tace min ki tayamu murna yayanmu ne ya dawo ya bamu waya nayi ajiyar zucya na dungure mata kai nace har kinsa duk na tsorata na amshi wayar kirar nokia yar karama mai murfi gsky ta burgeni sosai nayi mata murna tace su dasu Sa'a iri daya ya sai masu don dama ya sai ma su anty Mariya tun tuni,nace kunji dadin wllh tace muje ku gaisa mana ko zai baki kema na dube ta cikin sauri nace ki rufa mani asiri ai ni ynxu ba zan taba yarda ya ganni ba bare da hankalin kaina naje inda yake ta soma dariya gami da fadin kin fiye tsoro me zaiyi maki?daga ganinki sai ya hau dukanki sai kace mahaukaci?tacigaba da dariya na ture littafin gabana na dube ta nace don Allah ki sanar dani wani abu game da yayanmu mana, Tace Abdulrahim sunanshi na gasky wato Abdulrahim mukhtar maska a yanda naji ana cewa tun yana dan karamin shi sam baida yawan fara'a ga miskilanci don zai iya kwana bai damu da yayi ma wani magana ba in ana son aga fara'arshi to a bashi kwallo sannan kwallonshi ta samo asali ne tun yana makarantar primary inda yayi ta cin gasar da aka sha hada su da wasu makarantun,haka yacigaba har secondary,bayan kammala yaso a barshi yaci gaba da kwallonshi amma sai babanmu ya kiya sam dole yaje ABU zaria inda ya karanci politics har ya samu degree bayan ya gama sai ya shawo kan babanmu da kyar yayi wasanni da dama a nan gida nigeria kafin ya fita england inda wani coach yayi mishi hanya, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na dakatar da ita nace ke ni ban tambayeki lbr kwallo ba,kunce yana dukanku ko?mami tace Allah yana duka sosai ma,amma sai ka mashi ba daidaiba,na dubeta nace kamar yaya ba daidaiba?tace baya son ya saka abu kaki ko kai shirme,bai son kazanta kuma in ka ganshi yana son ka gaisheshi amma baison yawan gaisuwa ,kana ce mashi ina kwana is ok,yana da cin abinci kinsan yan kwallo gashi da tsafta yana son kamshi ke gadai abubuwa nan,in har kin kiyaye komai babu abinda zai faru tsakaninku ko ynxu ki tashi muje ki gaishe shi mana,nace a'a mami gaisa wata rana nace to ynxu ya dawo kenan?tace aah bai dawo ba kenan,zai koma wannan zuwan ma in gaya maki haj yaya ce ta matsa yazo don su gana da yar gidan haj laure,anty mimi nace ita zai aura kenan?mami tace kuma abinda baki sani ba yana matukar bin maganar iyayenshi don ko wuta suka ce ya shiga zai iya shiga musamman haj yaya bai hada ta da kowa ba yana matukar jin maganarta,na dube ta cikin tsoro nace kinji ko?tana ce mishi ya koreni zai koreni ko dai ma in tafi ne?mami sai dariya take yi min,Kamal ne ya shigo ya sanar da mami mamansu na kiranta.Bayan kwana biyu ya raba tsaraba har su jamila da sagir ya basu,mama ma ta samu less da shadda da takalmi sagir din ma harda Jc shi da kamal,su mami english wax ya kawo masu ni dai banje ba kuma bai sani dani ba don ban yarda ya gani ba,ran da ya yi kwana ukku da dawowa mama ta amshi girki da rana ina tayata aikin burabisko mami ta same mu a kicin tace yaya yace a kai mishi abinci,nace yana cin birabisko ne?tace oho nace to inbazaki laifi ba kije ki ce mishi burabosko ne don kar a yi mishi laifi,tayi musrmushi sannan ta fita,anty yagana tayi sallama ta shigo na fito daga kicin na amsa,sannan na gaisheta gami da tambsyarta saudat tace tana gida sannan ta wuce ciki tana ce min maman naki na ciki? nace eh,mami ta dawo tace yace akai ma abokanshi shi kuma a dafa mashi indomie amma ke zaki dafa ko? tace eh nace to don kar inyi kuskure mami tayi dariya tace kai ke kam kin cika tsoro,sababin kuloli mama ta bani na zuba masu birabisko da miyar kaji yaji curry sai kamshi yake,na dauka na tafi nayi sallama a kofar dakinshi aka amsa mani cikin faduwar gaba na shiga nace sannunku mutum uku suka amsa kaina a kasa ban kalli kowa ba nace a ina zan ajiye?cikin dauriya nake magana gabana sai faduwa yake wani daga cikinsu yace maska tana magana,da sauri na dan dubi wanda aka kira maska yana ta faman danne danne waya tamkar ba dashi ake magana ba,dayan yace ke ajiye kan wancan table din,na dubi table din sai naga akai yayanmu ya dora kafarshi ,na dubi mai maganar nace ai yasa kafa a kai yayi murmuahi sannan yace ajiye ko ina kinsan halin yayan naku sai hakuri na ajiye a gabansa don mami tace dama su ne zasu ci na juya zan tafi sai naji murya mai sanyi amma cikin fada akace ke haka ake bada abinci a gidanku ko?na juyo da sauri ga mamakina yana danne danne wayarshi kamar yanda na sameshi,sai a lokacin ne ma na dan kalli fuskarshi, kykkyawa ne na ban mamaki don duk gidan yafisu kyau sak kamarshi daya da hajiya yaya,tsawa naji in ba zaki zuba musu ba dauki ki tafi,da sauri na duka jikina na kyarma na zuba musu nan dakin ya bude da kamshin miyar kajin na mika wa kowa sannan na mike dayan yace dan bamu ruwa nace to zan fita dayan kuma yace ga fridge nan na nufi gun fridge ina tunanin yanda zan bude dan ban taba ganin irinshi ba cikin sa'a ina dafa shi sa i naji na latsa wani abu sai ko ya bude kayan shaye shaye ne kala kala na rasa wanda zan dauko musu sai na dauko musu ruwa a babban gora na dauko five alive na aje masu da na duba saman fridge din sai naga kofuna irin na wajen na dauko tiran kofunan gaba daya na aje a gabansu,ina kokarin mikewa ne mami tayi sallama suka amsa har da yayanmu ta shigo dauke da kula da plate da cokali na fita na dan tsaya a kofar dakin ina jiran mami labarin abinda yayanmu yayi mani sai na jiyo itama tana shan nata fadan,muryar yayanmu ne yana ce mata yar iska haka ake dafa abinci?indomie ne din ba za ki iya dafawa ba?ina cewa ganin kin danfi su mariya abin kirki ashe kema useless ce,sam ban ga wani amfani ba gun mace matsawar bata iya abinci ba,ko aure kukayi irin abinda da zakuyi kenan ko?sai naji muryar wani acikin abokan yaya yana cewa to kayi hakuri mana maska,ai yara ne sai naji muryar yayanmu din yana cewa no....... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Nasir kar ka goyi bayan wadannan yaran sam basu iya komai na mata basu iya girki ba basu iya gyaran daki ba,sam basu iya komai na mata ba yan iska sai dare yayi ka gasu suna surutu da samari sannan ace masu yara?yaci gaba da cewa bari kiji ba za'a yi asarar wannan abincin ba maza ki dauka kije ki cinye shi ina nan shigowa har dakinku inci ubanki in baki cinye shi ba ina nan yanda kuka sanni ban canza ba fita useless kawai,nan mami ta same ni a kofar daki duk na kara firgicewa na dubi mami wadda ke zubda hawaye nace mami yanzu ya zakiyi da wannan uwar taliyar don Allah?tace zo muje sai da muka isa gun lungun shiga cikin gida sannan ta dubeni tace don Allah iman ci wannanabincin kiji nasa hannu na dandana daidai kam yayi sai dai da ta dam kara wasu abu zai danfi wannan dadi,nace yayi mana tace to kinji shiyasa ni sam bana son ya sani wani aiki ga tozartani a gaban abokanshi nace to ki kai ma masu wanke wanke su tafi dashi gida mana tace wai in kaiwa su lami masu aiki?nace eh tace baki san yayanmu bba kenan kar kiyi fata irin haka ta hada ku kuma duk matar da ta aureshi ta shiga uku,nace anty mimi zatayi fama muka wuce cikin gida bansan yanda mami ta kare ba,sai washegari a school take ce min zubar da rabi tayi ya sameta tana cin rabin.Washe gari gab da magriba na dawo daga islamiya da shike ina zuwa sanawiyya na shigo gida,zaune a kofar dakin yayanmu samari ne su hudu sai shi yayanmu yana tsaye yana daddana waya,nadan yi mamakin yanda baya gajiya da danne danne waya ban taba ganinshi ba waya ba kuma ko da yaushe cikin danna ta yake tun daga nesa nake kallonshi sanye yake da dogon wando da riga daga nesa nake kallonshi sanye yake da dogon wando da riga mai gajeran hannu masu ruwan bula da ratsin fari an rubuta adidas a jikinsu,gsky yafi yan gidanmu kyau,maza da mata dogo ne yana da dan fadin ga kwarjini gashin kanshi a nannade ina tsammanin yana sanya mai ne akan ko kuma haka gashin nashi yake?oho ban san dalili ba duk sanda na ganshi sai gabana yayi wani mugun faduwa bana raba daya biyu don ina jin tsoronshi ne,na iso daf dasu kanshi a duke yana danna waya amma sai naji yace ke in kin shiga kice Sa'a ko Bilki su kawo mana butoci,to ba ma magana dasu Sa'a ko ince basa min magana kuma ban ga mami ba sai naje dakinmu na dauko butoci guda biyu na kai masu shi baya gun ina zaton bayinshi na daki zaiyi sagir na tura sagir ya kwaso mana butocin,wata rana asabar zan tafi islamoya don yanzu bana jiran kowa a yan gidanmu dan ba lokaci daya muke karatu dasu ba sai dai na biya wa Amira mu tafi,sanye nake da hijab har kasa nasa safa da nikab yayanmu na gani yana kulle dakinshi sanye yake da gajeren wando da yar rigar nike kafarshi da safa da takalmi but na kwallo da alama zai motsa jiki ne,nazo zan wuce ya dan dubeni ina jin yana son ya gane kowacece kamar na gaishe ahi sai kuma na fasa ina zaton bai gane ni ba,na gota shi kadan sai ya juyo yace ke gabana ya fadi dama cikin faduwar gaba nike,na dawo kaina a kasa nace gani baiyi magana ba ya gama rufe dakin ya matso gab da ni sannan yasa hannu ya dage nikab din idona ya firfito don tsoro yace ooh na dauka mami ce,ya cigaba da magana fuskarshi a daure ke na lura sam baki gaida mutane ko?na dan saci kallonshi fuskata yake kallo na kali kasa sannan nace ina kwana?yace wuce bani so sai da na roka kenan dubeta ,a raina nace masifaffe kar ka amsa din na tafi abina. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Zama da Amira yasa yau da gobe nima na soma karanta littafi kuma sai da na tambayi mama tace amma na dinga karanta masu kyau kuma masu amfani sannan in har zan karanta to ya zama bani da aiki ko na makaranta ko na gida shi yasa ma nafi yin karatun da daddare kasancewar bana fita ko ina ko samari sunzo kirana mama bata matsa mani ba don tace in kr2 nake son nayi to na tsayar da hankalina gun karatun.Yau monday muna hutun easter bani da wani aiki duk na gama kwance nake bisa gadona ina karanta wani littafi mai suna auren kisan wuta ina jin dadin lbr banji sallamar mami ba sai dai naji an fisgw littafin daga hannuna cikin sauri na tashi tana dariya tace kai iman,ke dai kina krt nan baki jin komi,nace lbr ya hadu,tace hala na soyayya ne?nace eh tace ai na sani nace kin san me?ai ku ne kuke soyayya ni kin ganni da saurayi ne?naci gaba da cewa wallahi ni banma yarda akwai wata soyayya da kuke cewa ba,mami ta soma dariya tace lallai yarinya da sauranki ke da kike karanta littatafai ai ke zaki ba wani lbr yadda ake soyayya,nace suma duk jinsu nake sai kiji an ce wai tana tuna shi tana mafarkinahi,don Allah da gaske ne?mami tace aa karya ne randa baku iya nutso a cikin soyayya ba ba zan yi magana ta katse ni da cewa ke ni ba wannan ya kawo ni ba an sa ranar su a anty Mariya wannan Alhajin kin ganeahi?nace mai katon cikin nan?tace eh shi ita kuma Hadiza wannan Sanusin mai jar motar nan,nace na ganeahi wanda ya taba cewa na kirata,don ya bata kudi ta bani shine ake cewa kar na kuma gaishe da saurayinta,don mu duk wanda ya dafe mana ya dafe mana kenan mami tayi dariya tace to shi. Yaya a Abubakr yana zuwa gidanmu haka yaya ibrahim dukkansu suna min hidima sannan yaya Sulaiman shima yana zuwa sai dukkansu sun daina shiga wurin mama sai dai su gaishe ta waya,wani abin mamaki kuma yaya Abubakar shi kadai yake zuwa haka ma yaya Ibrahim din duk babu wanda ya taba min maganar soyayya ina ganin take takensu kuma bana jin zan iya amince ma dayansu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yaya Kabir ya gama bautar kasarshi ya dawo gida,to shi dama muna shiri dashi rannan na fita da safe zani shagon mal Sani dan sayan sabulu naga yaya Kabir yana tahowa daga bakin kasuwa na jira ya iso nace kai kam ka cika yawo daga ina? Na duba wani abokin bab can da bashi da lfy nace ko Alhaji isa naji mami tana maganar zuwa duboshi yace yea shi ne,muka jero muna tfy har gida na tsaya daidai kofar dakinshi zai bani kwanukan dana kawo mishi abinci da daddare ya fito dasu kenan yayanmu shima ya fito daga dakinshi cikin sauri na gaisheshi sau daya wato ina kwana yace lafiya dama shi gaisuwarshi bata wuce haka in ma ka kara to ba zai amsa ba na amshi na wuce sai naji yayanmu na cewa kice mami tazo tayi mani shara kan nayi magana sai yaya Kabir ya riga ni yace ai yaya Abdulrahim dama wannan din kasa da kafi ganin daidai dan ta kware yacw to gashi in kin gama ki rufe mani dakin kiba brother key din,nasa hannu biyu na karba gami da cewa a dawo lfy bai amsa ba yayi gaba,na dubi yaya Kabir nace don Allah shi yayanmu baya amsa gaisuwa ne?Kabir yace yayanmu kenan ai shi daban ne duk yanda kika so ki san halinshi ba zaki iya ba mutum ne mai ban alajabi na wuce ina dariya,na sanar da mama aikin da yayanmu ya sani tace to na bar wankan naje na gyara mishi dakin zatayi ma su jamila in na dawo sai nayi nima nace to na shiga dakin yayanmu sai yau na yima dakin kallon tsaf,leather sit ne kujerun shi bakake ne masu girma setinau sai kayan wuta kafet da labulaye jajaye dakin sai kamshi yak nan na soma da bedroom din katuwar katifa irin wadda ba asa ta a gado din nan ce sai hanga na kayan sakawa a saman hangar akwatuna ne saiti biyu na dubi hangar rataye da kaya jibge a kan katifar ma duk kaya ne dai dai ko ina kwashe masu datti nayi a cikin wani dogon kwando irin na zuba kayan na gyara uwar daki tsaf sannan na koma falo shima nayi mishi aiki sosai na goge electronics din komai yayi tsaf sannan na dauko turaren daki na feshe ko ina na kulle dakin,na kaima kabir,wanan shine silar fara sani aikinshi na zama mai gyara mishi daki har ya zama dayan key din dakin ma a hannuna yake kullum da safe sai na gyara nake tafy makaranta wata ranar laraba na isa dakin da sauri dan in gyara na tura naga dakin ya bude a raina nace yau yayanmu bai je training bane?na shiga ban ganshi ba na cire hijabina na ninke na ajiye a saman kujera kaina tsaye na shige uwar dakin kayan barci ne a jikina doguwar riga da wando,sam ban san yana bedroom ba na shige toilet na gyara tsaf na fito bedroom din sai a lokacin na kula da mutum kudundune cikin bargo nayi sauri na duba kan gado dan na tabbatar yayanmu ne a kwance,ya kudundune da sauri na juya zan fita sai naji yace zo nan muryarshi irin ta marassa lfy nazo na dan duko yacw ki dafa mani ruwan lipton nace to na fita zuwa dakinmu mama na samu tacw har kin gama?nace ban ma gyara ba don yana nan ne yace akawo mashi ruwan lipton inaga bashi da lfy ne,mama tace ga wannan dibar mashi a ciki na baban sagir ne da yasa na dafa mashi dan yana fama da mura sai dai nasa kayan kamshi,nace zaisha ai yana shan na gida kuma yana sawa na diba na kaimashi na rusuna na bashi da kyar ya mike ya zauna akan gadon ya amsa duk naji banji dadi ba nace yayanmu baka da lfy ne?yace eh nace sannu,haka na koma naci gaba da gyaran falon har na gama na kara lekowa nace sannu na gama ko za'a kawo maka wani abu ne?yace ki shiga ki sanar da hajiyata sannan in ba zakiyi latti ba to ki dafa min indomie nace to cikin mintuna da basu fi biyar ba na dafa mishi hadaddiyar indomie na kai mishi.... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Afalo na sameshi zaune kan doguwar kujera yana sanye da singilet da gajeran wando naja dan karamin table din glass din dake tsakar dakin na dora cooler fin a kai na zuba mishi a cikin plste nasa cokali nace a baka ruwa?ya girgiza kai a raina nace yau dai ba danne dannen waya ba tare da ya dubeni yace kin fada ma hajiyata din ne?nace bata bude kofa ba,yace bani waya a cikin bedroom na shiga na wayar na kan katifarshi na dauko na duba fuskar wayar gabana yayi wani mummunan faduwa sakamakon ganin hoton anty mimi a fuskar wayar na kai mishi sañan nace bari na gyara cikin,na shiga na gyara na fito yana cin abinci yace bani abinsha a fridge na bude coke na gwangwani na dauko mishi dan ina yawan ganin gwangwanayen coke din a cikin bolarshi na hado mishi da ruwan Cway na aje na wuce ban wani karya ba shiryawa nayi kawai nasha ruwan tea kadan don kar mama tayi min magana na fito su mami sun jima da shiryawa shi yasa ma ban tsaya saka safa ba,haj yaya mukayi karo da ita ta dawo daga dakin yayanmu ta dubi bilkisu tace yayanku bashi da lafiya ku shiga ku gaishe ahi keda saa da mami sukace to sun shiga ni kuma na tsaya daga waje ko yaya akayi ya ganni sai ji nayi yace ba zaki shigo bane ke? Na shiga da sallama na ce sannu bai amsa mani ba ya cigaba da cewa in kin dawo makaranta ki dafa mani wani abu ,karfe nawa kuke dawowa?nace biyu yace to zan je na ga likitane sai ki samar mani wani abu nace nace me zaa dafa yace komai ma,muka fito su bilkisu sai wai hararata suke yi ni ko tausayin halin da yake ciki shi ya dameni ko a mota sam na kasa sakewa duk tunanina yana can gunshi sai kuma abin da yafi tsaya mani a rai hoton anty mimi dake cikin wayar yayanmu tana sanye da jar riga kanta ba dankwali tana ta faman murmushi duk sanda na tino sai gabana ya fadi a ranar sukuku na yini ko yan ajinmu sai da suka tambayeni nace banjin dadi haka a mota da muna dawowa na kifa fuskata kan jakata ban da tunanin yanda yayanmu ya yini da jiki bana tunanin komai har naga karfin halina irin wannan daga hankali haka,mami ta dafa bayana tace iman wai yau me yake damunki ne?nace banjin dadi ne tace sannu na amsa muna isowa gida kowa na kokarin leka dakin don naga an karo kofar saa ta harareni tace neman suna shishigi babu kwarjini ban kula ta ba na shige dakin da sallama yana kwance sambal a kan 3sitter barci yake amma fuskarshi a sake tamkar yana murmushi don ko idonshi biyu bai cika faraa ba,wayarshi a ajiye kan kirjinshi ina mamakin irin son da yake ma waya na dubi fuskarshi gsky yana da kyau sosai cikinshi a dame tamkar baya cin abinci na kuma duba sa amma shi dogo ne don kanshi a hannun kujerar yake taga ba ma kafar shi ya dora amma duk da haka kafar sai dai karfinashi ne ya haukan hannun kujerar farin gajeren wando da yar tshirt itama fara sune jikinshi,na juya da niyar in fita sai naji ance me kike so?gabana ya yi mumunan faduwa nasa hannu na dafe kirjina jakata ta fadi kasa na kuma kasa juyowa jikina sai rawa yake yi nayi waje da gudu a firgice na shiga daki Allah yasa mama bata falo don haka sai na shige dakinmu,sai da na nutsu sannan na fito na shiga dakin mama ta dubeni tace ya sauran yan uwanki suka rigaki shigowa?nace yayanmu ne ya kirani yace na dafa mashi abinci kuma yaki fada min wane zan dafa yace wai kowanne na dafa,mama tace tunda bashi da lfy ne to ki dafa mashi wake da alayyahu ki sa kayan ciki akwai a fridge ki mishi hadi sosai yanda zai mishi dadin ci nace to.Da yake tun a makaranta mukayi sallah sai na shiga aiki kawai uku da kwata na kammala aikin sai da na watsa ruwa sannan na aiki sagir ya gani ko kofar dakin yayanmu bude take bayan ya duba ina sanye da riga da siket na farin lesi na shiga da sallama shine ya amsa gaba na na faduwa na shiga abinda na gani shine ya tsorata ni,anty mimi zaune a gabanshi a kan kujera shi kuma yana kwance tana rike da hannunshi bansan dalili ba sai naji duk banji dadin ganin haka ba sannan ga wani abu da ya tokare mani kirji wata tsawa da anty mimi ta dakan ita ce kuma silar rudewa ba zaki ajiye abin da ke hannunki bar nan ba?useless kawai kin wani tsaya akan mutane,na ajiye kan table zan juya sai sannan yayi magana yace baki zuba mani ba zaki tafi,,Najuyo da sauri ban dubesu ba na dauki plate daya da na kawo don haka na zuba mashi cokali ma daya na kawo na sa mashi na tura table din gabanshi dan ya tashi zaune,dakin ya dauki kamshin abinci yace ki kawo wani cokali da plate din tace no ba zan ci ba barshi,na bude fridge na fito mashi da coke da ruwa na ajiye tunda na fito nake mamakin yayanmu iya kwanakin da na dauka ina mishi aiki ban taba jin yace mani sannu ba haka ban taba jin yace abincin nan ko dakin nan baiyi daidai ba sam.Wasa wasa na zama baiwa,gyaran daki nice girki nice aike yanzu duk inda naje sai ya jirani na dawo sannan zai aiken abinda ke ban mamaki bai taba nuna min yana jin dadin abinda nake mashi ba sannan uwarshi da kannanshi sun kara sani a gaba wai mun shanye mata da kabir ma ya kan sani nayi mashi aiki amma ba kullum ba kwana biyu uku hakan ya kan ce a share mashi daki kuma idan na dafa ma yayanmu abinci shima ina zuba mashi to a cikin satin nan ya soma aiki shima aikinshi ya ragu, Kwanaki sun shura ana saura sati ukku bikin su Anty Mariya mami take bani lbr komawar yayanmu in anyi biki da kwana biyu nan duk naji ba dadi nace mata sai ya dade zai dawo?tace a'a yace duk bayan wata shidda zai dinga zuwa saboda zancen bikinshi da mami da zaran ta gama HND dinta nace Allah ya kaimu..... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Baba shine yayi mana ankon bikin gaba daya ko da yake kala biyar suka fitar shi kuma biyu yayi mana, ana sauran kwana goma biki da misalin karfe uku na yamma ina tsaye bakin kofar yayanmu ina sanye da atamfa sai karamin hijabina mai less fari takalmina fari yayanmu yace nazo zai aikeni kafin ya fito daga daki sai ga wasu abokanshi suka min sallama na amsa sannan na gaishesu suka amsa min gami da cewa mai dakin yana nan?nace yana ciki suka ja fararen kujerun roba da yayanmu ya zuba a gurin suka zauna,sai gashi ya fito guna ya nufo da leda an rubuta SI super market a jiki,yace ga wannan ki hau mashin ai kinsan gidan su mimi ko?nace e yace to ki kaimata kuma ki yi sauri yanzun nan,ga wannan ya miko mani dari biyar na fita ba wai don nasan gidansu anty mimi ba bana dai iyayi mashi musu ne,bansan dalili ba na dai san malali suke,gidansu Amira na shiga sannan nace don Allah ta kira mani mami da wayarta mami tace gata nan ma zuwa gidansu Amiran dana soma mata bayanin cewa ta min kwatancen gidan su Anty Mimi sai tace min me zan je inyi?nace yayanmu ne ya aikeni,suka rakani su da Amira don na hau mashin tayi ma mai mashin din kwatancen inda zai saukeni muka tafi yanda Mami tayi mani kwatance haka nabi bayan na sauka a mashin nan da nana sai gani a gidansu anty mimi na shiga kannanta na samu suna wasa a harabar gidan sune suka yi min jagora har ciki nan na sami Haj Laura da wata kawarta suna hira na gaishesu da farko bata ganeni ba sai da na gaya mata daga inda nake sannan ta murtuke fuska tace zauna nan na zauna.Ta daga murya ta kwala ma Mimi kira kan Mimi ta fito sai wannan kawar tata take tambayarta wannan yar gidan wacece?maman tace yar gidan kishiyar hajiya ce yar'uwata itama ta yatsuna baki tace ai har ta haifi yar da takai girman haka?ko ba amaryasu ba?tace itama mana amma ai wannan agola ce sai shegen kankanba kan ta kuma cewa wani àbu sai ga Anty Mimi ta fito tace gani Mumy, Hajiya ta dube ta sannan ta nuna mata ni tace ga mai nemanki nan muna hada ido gabana ya fadi tace meye kike nemana?nace yayanmu ne ya aikoni tace yace me?na isa gunta nace gashi yace na baki ta dubi kayan tace duk gidan ba zai aiko kowa ba sai ke ko?shegu mayun asiri ni dai nayi shiru na kasa magana,Haj laure dake zaune can gefe tace to ko bata kayan ta maida mashi mana,tace tabdi ai shi momy daban yake in har na bari aka maida kayan nan ai sai nayi dana sani,ta fincike daga hannuna tace ai zamu hadu ni dashi,a raina nace kamar zata iya mashi wani abu,ina jinsu sai faman masifa suke nace ai sai kuyi a raina,ina fitowa daga gidan na soma raba ido ko zan ga mai mashin amma ban gani ba na soma tafiya sai naji ihu ban juya ba naci gaba da tafy mai motar yaja ya tsaya ya fito ya biyoni yace ke yan mata ina magana,na juyo cikin dardar don ban taba tsayawa da wani ba nace lfy?ya ce kalau in har ba zaki damu ba ina son sanin sunanki nace don Allah mallam kayi hakuri,nacigaba da tfy ganin yana ta bina gashi ban sami mashin ba ko wane yazo sai ka ganshi da mutum akai nace sunana Amira yace to ina ne gidanku nan dai nayi mashi kwatancen gidansu Amira muka rabu dashi lfy,da kyar na samu mai mashin na isa gida in da na bar su yaya nan na samesu na dan rusuna nace na kaimata yana sanarshi(wato danna waya)ba tare da ya dubeni ba yace ki shiga daki ki dauki wata leda ke ma kije kiyi amfani dashi nace to nagode kwarai,bai amsa ba na mika mashi kudin hanuna nace ga canjin kai kawai ya girgiza mani na nufi dakinshi,irin ledar da ya aike ni da ita ce akan kujera don haka nasa hannu na dauka na nufi cikin gida ni da mama muka duba less ne me shegen kyau kala biyu sai wani yadi mai santsi shima kala biyu takalmi da jakka kala biyu mama tace kin gode,nace mama ki bani da na kamu dana su Jamila sai na kaima yaya Sulaiman a tudun wada tace sai dai gobe nace mata dama ai. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 A ranar yaya Abubkr yazo da daddare kofar gida ya tsaya ya aiko Kamal wai nazo,na fita muka gaisa muka shiga hirar duniya can ya ce kanwata yau nazo da alamurra masu girma nace to yace zancen na zama ne na isa kofar dakin yayanmu ganin baya nan sai na dauko kujerun shi na robana aje mana a kofar dakin yaya kabir muka zauna ya dubeni yace lman nace na'am yace ya kamata ace tuntuni kinsan inda nasa gaba,nace kamar yaya kenan?yace yau dai na gaji ina son in fadi maki cewar ina sonki kuma da aure ba da wasa ba,nayi shiru don banyi wani mamaki ba don na kula da hakan shima yaya Ibrahim kwana hudu kenan da yazo min da irin wannan maganar,yace sister naji kin yi shiru,nace to me zance?gasky yaya ni bazan boye maka ba karatu zanyi har sai naga karshen biro,ya tsura min ido sannan yace in har zaki yarda ki aureni to ni kuma na miki alkawarin zan jira ki,na dan bata fuska nace gsky kar katsaya jirana don ni sai nan da shekara ashirin zanyi kai kuma kila a lokacin kace na tsufa ko ni naga tsufanka,yace inda so ai tsufa ba matsala bane nayi shiru ina tunani shi ma fa haka mukayi dashi (wato yaya Ibrahim)sam wai jirana zaiyi,yaya abubkr yaci gaba da matsa min nace yaya mubar maganar nan in lokaci yayi sai ayi na sako mashi wani zancen muna cikin hira yayanmu ya dawo a motarshi na raya a raina cewa daga gidansu Mimi yake sai kawai naji banji dadi ba kuma wancan abin dake samani nauyin kirji ya taso,sau daya ya dubi inda muke ya shige dakinshi sai naji ma duk hirar ta gunsheni nace da yaya Abubkr zan shiga gida yayanmu ya dawo kuma fada yake mana ya dubeni yayi shiru sannan yace har yanzu bakida waya a hannunki ko?nace eh amma mama tace ina gama secondary zata sai mani ya juya gefenshi ya dauko wata leda yace min gashi wannan ni na sai maki ba Baba bane bare mama tace ki maida,nace to bari sai na fara fadi mata in ta yarda sai na amsa yace dole sai na amsa ko ya kwana a gidan nan,dole na amsa yana tfy na dauki kujerun yayannu na nufi kofar dakinshi cikin sanda na ajiye zan tafi naji yace wanene a nan?nace nice yace me kike nema?nayi shiru sai gashi yazo bakin kofa fuskarshi a murtuke yake magana wayace ki daukar min kujera? nayi tsuru tsuru yace wannan shine na farko kuma inason ya zama na karshe kar ki yarda ki kuma daukar min kujera ko ni sa'anki ne?nace a'a na durkusa nace yi hakuri bai min magana ba ya wuce daki ni kaina dari dari nake bansan yanda zanyi da waya ba. Washe gari nayi kuru da safe na nuna mata tace ke bakya jin magana ko?nace miki sai kin kammala karatunki sannan zaki ci gaba sai na sai maki waya amma kinje kinsa Abubakr ya sai maki ko?to shi kenan,na soma hawaye ina cewa wllh mama bani na sashi ba tace ki maida mishi in yazo nace to har tara na safe ban daina kukan wannan magana ba ni ba wai wayar da Mama tace kar inyi amfani da ita bane ya dameni a'a sai dai ganin da tayi tamkar na roka,tafe nake ina share kwalla zanje gun mamansu Amira in amso ma mama kanunfari zata yi ma su sagir kulin kamu yaya Kabir naci karo dashi zai shigo gidan yace Iman me ya sameki?na cigaba da kuka yana ta magana nayi shiru,yace nasan su hajiyarmu ne ko?nan nayi magana nace basu bane ni da mamanmu ne,yace duk yanda akayi kece kika tabo ta nace wani ne ya saya mani waya shine take ganin kamar na rokeshi ne,yace to ta kwace wayar ne? nace nifa ba kwace wayar ne ya bani haushi ba,yace na fahimceki kafin ya kara wata maganar sai ga yayanmu sun nufo cikin gidan shi da Anty Mimi shima ya ja birki yana ce ma yaya Kabir brother me ya sameta?kabir ya soma yi mashi bayanin cewa bafa wani abu bane wai yayanta ya bata waya shine maman Sagir tace wai ta rokeshi ne,ya dan dubeni sannan ya dubi yaya Kabir yace to yanzun ta kawo karanta ne? yaya Kabir yace no na dai tambayeta ne shine take min bayani,ya dubeni yace wannan marar kunya da ya zauna mani a kujera shine yayanki?daka mani tsawa yayi nace shine yace good gara da ta kwace wannaki bashi da kunya bai iya gaida mutane ba sai aikin kallon mutane don haka in ya kuma zuwa kice mishi ya tsaya daga bakin gate sannan ki san kin maida mishi wayar nan,a fusace ya yi cikin gida daga ni har yaya Kabir da kallo muka bishi Kabir yace ki tafi inda aka aikeki,na tafi ina mamakin wannan karfin hali wai (barawo da sallam) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ashe yana shiga gida dakinmu ya shiga dama shima duk safiya yakan shiga falonmu ya gaida mama tamkar yanda yake gaida mama tamkar yanda yake gaida sauran matan babansa,bayan sun gaisa ne sai yake ce mata maman Sagir mai ya sami yarinyar dakin nan na ganta tana kuka? Sai mama tayi mishi bayani ta kara da cewa nasan ba zata rokeshi ba na dai mata haka ne don kar ta kuma karbar wani abu gunsa,yace hakan na da kyau ta maida mashi zan sai mata waya bansan bata da waya ba kuma sanda na dawo ban san tana nan ba,mama tace ka barshi kawai yayansu nima zan sai mata nafi son sai sun kammala krt don yan satittuka ne suka rage masu su soma jarabawa yace haka ne in ta gama ko ba na nan zan aiko mata da waya,mama tayi godiya sannan ta kara da cewa ga kuma dawainiyar kayan da ka sai mata jiya an gode,na dawo na samu zai fita daga dakinmu na dan dube shi harara ya watsa mani nayi sauri na dukar da kai,na shige daki. Sam ya manta da cewa tare da Mimi suke sai da ya shiga dakin Haj yaya sannan ya ganta zaune tana cika tana batsewa ya zauna a kan kafet din dakin kasancewar mahaifiyarshi tana kan kujera ya gaisheta ta amsa a ciki ciki sannan tace kai wai ba zakaji magana ba ko?ya dubeta yace haj me ya faru?tace ai kafi kowa sanin abinda ya faru don tsabar iskanci ku taho da mimi amma ku taho amma sai ka bar ta anan tana ta faman jiranka kuma kasan makaranta zata je tace tun tara take da lectures yanxu goma da rabi a ina kasa gaba?kafin yayi magana mimi tayi saurin cewa wurin fa bakar yarinyar nan ya tsaya wai sun ganta tana kuka suka firgice shida Kabir sai tambayarta sukeyi ban.......tsawa ya daka mata ke shiga hankalinki ni sa'anki ne?uban wa yace da zaki makaranta ki biyo ta nan?me zan miki?karki sa ma bakinki kwado zaki sha mamaki duk sanda ana min magana kika tsoma baki ya nuna kofa da hannunsa yace see your way,fita a nan ta mike jiki na rawa mama ki daina min fada a gabanta kin manta ita ce matar da kika zaba mani na aura?zata raina ni ne hajiya in kina min haka a gabanta har tana sa baki dan raini,wllh taci albarkacinki ne da sai na mata dukan tsiya,ya cigaba da cewa bata san cewa ni saboda ke ni zan aure ta ba ba wai don tayi mani ba?haj yaya tace tsaya tsaya ba na son cin fuska ka manta ni da uwarta nono daya muka sha?bayan haka ma mimi bata da makusa ubanta balarabe ne ka kuma sani inma ilimi ne akan nema take gashi tana sonka sosai amma kai sai faman goce goce kake yi shi yasa na canza shawara kafin ka tafi sai an sa ranar aurenku,ya dubi haj yace ki dai yi hakiri na dawo don kar aje ana dagawa tace sam ban yarda ba yace to shi kenan ta juya zancen dake cewa wacece take kuka ku ka tsaya kai da Kabiru?yace waccan yarinyar da nake aike ce,nan ta hau bala'i da masifa tace dama in banyi da gaske ba sai Habiba ta shanye min yara yanda ta shanye babanku kallonka kawai nake yi wannan mummunar yarinyar yanzun itace abincinka gyaran dakinka,aike yanzu itace tunda haka kafi so ai sai kayi sauran ka ka soma kai shawara gun Habiba haka tayi ta sababi yana bata hakuri har dai ta sauka,Niko tuni nakai dinkinmu gun yaya Sulaiman nan da nan kuwa sai ga kaya ya kawo,na rakoshi zai hau mashin nan mukayi kicibis da yaya Kabir suka gaisa da yaya Sulaiman ga mamakina sai naga yaya Kabir ya daure fuska ya dubeni yace na lura baki jin magana ko Iman?me yaya Abdulrahim yace maki?na dibe yaya kabir nace ai to wannan ba yayan da ya bani waya bane wannan wani ne bai saurareni ba yayi cikin gida muka fita ina ta mamakin wannan abu da yaya Kabir yayi na dubi yaya sulaiman da nufin nayi magana sai kawai shima naga yayi fuskar shanu(wato ya hada rai)yace wannan kuma wanene?nace yayanmu ne yace ni ba wani yayanku na kula ke sam baki ma san halin da nike ciki ba ko? gabana ya fadi nace me kake nufi?yace ina cikin mayen sonki,na dade da yin nutso cikin kogin sonki don Allh ki taimaka min da ganin wannan da ya wuce sonki shima yake yi,nan take hankalina ya tashi na gudu nayi cikin gida dakinmu na fada na kwanta a kan gado rigingine nayi fuskata na kallon silin na soma tunani, yaya Abubakar sona yake,yaya Ibrahim sona yake,yau ga yaya sulaiman da wannan zancan har kuma yana tunanin wai shima yaya Kabir sona yake, ban ganeba? na mike zumbur tamkar an tsunguleni nace da na shiga uku ni Iman muddin Haj Yaya taji wannan lbr na ciji yatsana na soma sintiri a tsakar dakin tabbas da zan so yaya kabir ko ba komai yana dan yanayi da yayanmu wata zuciyar tace min in yana yanayi da yayanmu shi kenan sai ki soshi a matsayin da yayan naku ya taka a zuciyarki?shin kina neman ma kanki rigima da mahaifiyarki?menene laifin Abubakar da ba zaki soshi ba?ya jima yana maki dawainiya dake in ba ki son shi ga Ibrahim nan shima dan uwanki ne sannan in dama za kuyu adalci to da Sulaiman kika zaba ki tuna shine yake maki hidima ta fannin dinki tun kina karama har yau dinnan shi ke maki dinki, ****hhh! Lallai yariya taki tasameki,duk cikin wayit blood ne***** ban san shigowar mama ba sai dai naji an girgiza ni sannan nayi sauri na jiyo cikin tsoro naga tana kallona tace iman me kike tunani haka?na shiga uku ni Habiba na soma in ina,ina cewa ba komai ta girgiza kafaduna da karfi cikin daga murya murya tace kinsan tsawon lokacin dana dauka ina maki magana nan kuwa baki sani ba,na jima a nan ina kallonki kina safa da marwa tamkar wadda abin duniya ya dama,ta ja hannuna muka zauna a bakin gado ta sanyaya murya tace Iman sanar dani matsalarki don baki da wanda ya fini kuma na jaki a jikina don irin wannan ranar wato don neman shawara kar kiji komai sanar dani ta fada tana kallona nayi shiru ina tunanin mama gaskiya dole ne ma na sanar da ita sai dai ba zan gaya mata maganar kabir ba, na dubi mama nace yayyena duka uku sune suka sani shiga wannan tunani,tace kamar yaya?na dukar da kaina kasa sannan nace yaya Abubakar da yaya Ibrahim da kuma yaya Sulaiman kowanne yazo wai yace yana sona,Mama tayi shiru kamar ruwa ya cita tace ke me kika gani?ta cigaba da cewa Abubakar da ne ga yayar mahaifinki cikinsu daya,Ibrahim kuma dan kanin mahaifinki ne da suke uba daya shi ko Sulaiman dan wana ne nima cikinmu daya sai ki fadi min wanda kika zaba?nayi shiru tunani ya dawo sabo mama tace ba tunani zakiyi ba sanar dani abinda kikace masu ke kin amsa musu dukansu ne?nace aa duk hakuri na basu,nace ni karatu zanyi amma tamkar sun hada baki kowa sai yace zai jirani yaya Sulaiman ne ma ban tsaya yi mishi magana ba,mama ta dafa ni sannan tace yanzu gaya mani a cikinsu wa kikafi so?sai na baki shawara nace gsky mama ni cikinsu bana son kowa,ta mike tana fadin alhamdll gara hakan don dama ko da dole sai na zabi daya ne,to nace gara Sulaiman yaron na da mutunci,kuma naji ma ina fuskantarshi game da ke ma na dade da gane cewa sonki yake nayi kwadayin dama shi kadai ne yace yana sonki taci gaba da cewa yanzu in naceki amince dashi sai ace don yaron danuwana ne shi yasa don haka ki kwantar da hankalinki kinga jarabawa na matsowa kar ki yarda na kuma samunki kina wannan tunani ba yarda za ai ki auri wanda bakiso ba mai matsa maki don karatu ma zakiyi,haka mama tayi ta lallashina har dai na saki jiki sai dai a raina maganar yaya Kabir itace a raina. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tun ana saura kwana uku bikinsu anty mariya dangi suka cika gidan,fannin Haj Shuwa da yanuwa Haj Yaya,sai yan uwan Alh Mukhtar wato yan maska Aunty Mimi ma a ranar tazo don ranar ne za'ayi dayis,yayanmu ranar bai wuni gida ba sai yamma dama ni banje masu wurin da suke yin lalle ba nida Amira mukaje mukayi kitso sannan mukayo namu lallen a can don dama mu ba ma saka mai a kanmu. Misalin karfe biyar na yamma yayanmu ya aiko Kamal ya kira ni nazo yace na kawo masa wani abu tabawa in akwai dan yinwa yakeji na koma ba wani abin kirki sai na rana kuma ya huce nasan ba zai ci ba,don haka sai na dafa mashi indomie da kwai na kawo mishi natarar da Aunty Mimi a dakin sai naji raina ya baci na ajiye zan juya yace ke kizo ki zuba mani mana na dawo sai tace ka barta sai na zuba maka ,bai dubeta ba yace min samin mana kina kallona baki sanni bane?nayi kasa da kaina sannan na zuba mishi na dauko mishi coke da ruwa sannan na juya zan fita sai naji yace shiga bedroom ki dauko wayarki tana nan a kan katifa,na dauko sannan nayi mashi godiya,washe gari a command quest za'ayi kowa ya shirya cikin anko nima na sanya nawa ankon nayi kyau sosai na fito harabar gidanmu a nan ne ake daukan yan matan tuni kowa ya tafi sai Amarya da kawayenta wadannan kuma bana tunkare su ba itako mami tuni dama tana can don sune masu shirya gurin dasu bilkisu da sauran kawaye,ina tsaye na jingina da bangon dakin yayanmu ina kallon kawayen amarya suna ta kai da kawowa kowacce na rike da waya tamkar masu gasarta nan na tuno da tawa mama tace na aje sai mun gama zana jarabawa ina wannan tunanin naga anty mimi sun fito itada yayanmu itama anko ne a jikinta irin nawa tayi matukar kyau dama anty mimi ba dai kyau ba gata fara yanda mami ke gaya mani mahaifinta balarabe ne zamanin da Haj Laure mahaifiyarta suke zuwa kano to jidda a can Allah ya hadata da wani balarabe ta aura shekarunsu ko goma ne da aure ya rasu lokacin Anty Mimi na shekara shidda shine ta gudo da ita ba tare da sanin dangin babanta ba,sannan ta sake aure shine ta haifi yaya uku sanda naji wannan lbr a raina nace ashe jirgi daya ya debomu ni da ita.....Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 DOCUMENT CREATED BY ZAHARADDEEN SHOMAR WHATSAPP 08168575100 Tawa Tasameni 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 02:31 AM, 29-Dec-15 Under: TAWA TASAMENI __________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Garama ni ubana yana nan, haka danginshi, nayi nisa cikin tunani na ji horn ba karewa na juya can wajen da ake horn din bakin gate sai naga ashe su yayanmu ne zasu tafi ban fahimci wai ni suke ma horn ba sai da anty Mimi ta bude gaban mota tace ke na dubeta na dafa kirjina nace ni?eh da Allah zo nan ana maki horn kinyi banza da mutane, na nufi gunsu ina zuwa naga yayanmu ya sako hannu ya bude baya yace shiga,gabana na faduwa na shiga motar don nasan ba wanda ya taba shigarta a yan gidanmu sai yaya Kabir na zauna sannan na rufe sanyi da kamshi sune suka ziyarceni tamkar wata munafuka haka na zauna a motar kaina a kasa, suko suna ta labari bana jin dai muryar yayanmu sai ta anty .Mun yi nisa sannan na dago idona sai kawai muka hada ido da yayanmu ta madubi nayi sauri na sunkuyar da kaina kasa har mukaje ban tanka ba,ban kuma daga idona ba,sai da naji an tsaya sannan na dubi gurin yan mata ne cike na buda zan fita sai naji yayanmu yace karba,na juyo sai naga yana bani kudi ne sababbi yan naira hamsin na amsa nace Allah ya saka da alkhairi,anty Mimi ta shaka sosai da na kalli fuskarta ni dai nayi ciki ko zan ga Mami, ana cikin hidima shalele suka kira don haka gun ya cika da karan kidan police band Sa'a tazo tace kije ana kira gabana yana faduwa nace inji wa?ta harareni dole sai kinji? ki zo mana na bita can baya mukaje ganin Anty Mimi da Amare da kuma kawayensu yasa wata faduwar gaba ta sameni na dai daure na isa wurin,Anty Mimi ta kai mani rankwashi akai tace ina jakarki?nace tana gun Mami tace nawa yayanmu ya baki?nace ban kirga ba nan ta shiga zayyane masu wai wannan wace irin yarinyace,Anty Hadiza tace ai wannan daga ita har uwarta annoba ce,Anty Mimi ta cigaba da cewa kunga jiya a gabana ya bata waya irin tawa ce sak koda ganin kwalin sannan yau zamu taho nan ta zo ta rabe ya dauko mu tare kunji biyu,cikon na uku kuma sai gashi ya raba mana kudi kilan ma daidai ya raba tamkar wasu kishiyoy,nan suka taru a kaina wannan ya kai mani bugu kowa dai na fadin albarkacin bakinshi, Mami ta iso daidai lokacin da wasu kawayen Anty Mimi suke cewa asiri tayi mishi daga gani,in ba haka ba me zaiyi da wannan mummunar yarinyar gara ma ki dauki mataki tun da wuri akan abin, Mami tazo tana cewa Anty Mariya kuzo anguna sunzo fa ana ta nemanku,kan suyi magana Anty Mimi tace Mami muga jakar wannan jakar,sai sannan Mami ta ganni ina kuka tace Iman menene?Bilki tace ba'a sani ba ke dai ki bada jaka a kace Mami tace bazan bayar ba nace Mami bata ta mika mata sai da suka kirga kudi daidai da nata dubu ashirin da biyu ne dama ban kirga ba,saura sukace kar ki bata ko sisi Mami tace wllh sai naga ya wa yayanmu in har kika dauki kudin nan,Anty Mimi ta watso kudin da jakar a jikina sannan tace ki jira abinda zai biyo baya ta wuce sauran suka bi bayanta aka bar daga ni sai Mami inata kuka,Mami ta kwashe tana tambayata abinda ke faruwa na zayyane mata komai itama na kula ta dan yi mamakin kudin da ya bani tace Iman yayanmu yana ji dake fa nace Nami ku kula da wani abu daya yayanmu nice nake mashi aiki,shiyasa yake mani alheri amma wai suna zargin wai yana sona ne ni nasan ko mata sun kare yayanmu ba zai taba cewa yan sona ba ke kinsani balle yana da kamar Anty Mimi,Mami tace ai itama anty Mimin ba wani kyau ne da ita ba uban gashi ne kamar jirgi ya daso tasha kuma a tsaye take ba wani diri kirji kamar na bera ba wasu nonuwan kirki nace to shi dai tayi mashi Mami tace ke zo muje ba wani yi mashin da tayi kawai saboda mamansu zai aure ta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 TAWA TA SAMENI,haka na fada ranar daurin auren anty mariya ba wani abu yasa na fada ba sai ganin munsa less iri daya da Anty Mimi wato wanda yayanmu ya bani nasa daya daga ciki me ruwan lemun tsami takalmi da jaka iri daya itama ni take kallo ta zauna kofar dakin yayanmu a fararen kujerunshi ranta yayi matuka gun baci naga ta yi cikin gida ni kuma sai na nufi gidan su Amira,dama dazun ta aiko Faruq wai ta dawo dama jiya ne ta tafi unguwar dosa gun kanwar mamansu da suka dawo kwanan nan shine taje kwana,ta fito wanka na sameta nan nake zayyane mata abin dake faruwa ta dinga mamakin karfin halin irin na nasu Aunty Mimi dan yayanmu ya min kyauta ta kara da cewa komai ya sai maki ba zai biyaki ba irin dawainiyar da kike mishi ba nace suna zargin fa wai sona yake yi,Amira tace haba dai nasan ma ba zai fara ba domin kin......na katse Amira nace ni ba ajinshi bane nasan da haka kuma ko mata sun kare ba zai so ni ba Amira tace ba nufi na kenan ba ina nufin matsalar dake tsakanin mahaifiyarki da tasa ai yasan da wannan matsalar ba zaima ce yana sonki ba.Nace ato su sai hauka suke yanzun nan na hadu da anty Mimin shine ta ganni da kayan nan har jakar to tayi cikin gida ban san me zai faru ba,dama bikin nan sai yan tsegungumi sukeyi dangin Haj Yaya naci gaba da cewa kinsan abin da ya faru ne da babansu Mami ya tambayi Haj Yaya game da kayan da za'a siya don yayanmu ya riga ya sai masu sai yace to suyi mashi list din kudin sukayi mashi hauka to hauka mana wai fa miliyan daya da rabi suka rubuta shiko ya kira mama tayi mashi lissafin kayan dakin mata mata har da na jere da na kicin duk ta sanar dashi naji ya bata kudi sukaje ita da Anty Yagana suka sawo mashi komi don Mama cewa tayi sai da tayi ciko suka kawo ya dinga sa mata albarka itama ta bashi nata gudummuwar na zannuwan gado to wannan abin shi yayi matukar tada hankalinsu Haj Yaya da har sunce sam kayan nan bai masu ba shine baban yace yayi in baiyi masu ba to su sai nasu da kudinsu kafin Amira tayi magana sai ga Jamila kanwata da kukanta wai ana fada da Mama nace mama da wa tace Mama da mutane yan biki nace yau mun shiga uku ko takalma bansa ba na nufi gida Amira ta biyoni,tun a harabar gidan nake jin hayaniya yaya Kabir na gani ya fito daga cikin gidan ranshi a bace da ganina ya nufoni yace kar ki shiga zo nan,na soma kuka ina cewa ni dai na shiga uku ya ja min hannu zo muje karki shiga,nace ina kuka yaya Kabir barni naje naga Mama yace Mamanki tana dakin Alhajinmu zo muje ya jani dakinshi ya zaunar dani kan kujera sannan ya tsugunna gabana yace kiyi shiru zan tambayeki ne,nayi shiru ina share hawayena yace yaya Abdulrahim yace yana sonki? nace aah yayi ajiyar zuciya sannan yace alhmdll yayi shiru zuwa can yace a gaskiya Iman na dade ina sonki shiyasa ma har yau na kasa kula duk wata ya mace da sunan so na mike tsaye na ce Kabir tun ina ganinka da gashi kar ka yarda na kuma jin wannan zancen kana ganin balain da muke shiga kullum a gidan nan sannan zakace wai kan sona ni dai ba ruwana,ya zaro mani ido gami da tasowa kamar zai bugeni yace sai kin soni kuma ni da ruwana ba abinda ya dameni da fadan iyayenmu,na mike zan fita yace kar ki yarda ki fita su Haj Laure zasu dake ki muddin kika shiga,jin maganar duka ni uwar yan tsoro na dawo na zauna na sanyaya muryata nace sun doki Mama ne?yace suna hauka ne?ita ko kulasu ma batayi ba shine yar Alhajinmu da tazo daga maska tace ta shuga dakin Alhajin tasa na mashi waya yanzun nan yana zuwa shiyasa nace kar kije,na cigaba da kukana yaya Kabir yana lallashina har nayi shiru ya dinga shigar dakan shi a guna yana ce min in na yarda yasan Akhajinsu zai tsaya man kuma zai nemi canjin gun aiki mu bar kaduna haka ya yi ta cusa min raayi har na soma yarda,sai dai ina tunanin mama ba zata amince ba na dai yanke shawarar zan ci gaba da addua. wayar yaya kabir tayi kara yace in dauka don nafi kusa da wayar,na dauka sai naga sunan yayanmu sai na mika masa yace ya baki dauka ba?nace yayanmu ne ban san mai yake ce mazhi ba na dai ji yace gata nan sai na kuma jin yace dakina sai gabana ya fadi,sai naji yace to gata nan zuwa,ya dubeni yace alhaji yazo yana dakinshi an ce kije,nace yayanmu na gurin ne?yace shi ne yayi min waya wai Jamila tace nine na tare ki ina kike yanxu sai shine nace gaki nan ki tafi ko na raka kine?nayi saurin cewa a'a don kar agan mu tare,cikin dar dar na shiga gidan yan biki sai ni suke kallo gashi ko takalmi babu a kafata na shiga ciki nayi sallama a kofar falon Alhaji na shiga Alhaji na kan wata kujera irin ta karfen nan ne dama nan ne gun zamanshi sai Mama akan kujerar gefen damanshi dayan gefen Haj Yayace sai Haj Shuwa kusa da ita Haj Kulu na dakin sai yaya ta maska(wato yayar Alhj)yayanmu na kan kafet kusa da kafar Alhaji nima na shiga na samu guri kusa da Mamana na zauna a kan kafet. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Alhj na gaisar sannan yayi gyaran murya yace to gara ke Murja(haj yaya)menene sanadin wannan fadan?na tambayeki dazu kince sai an kira Iman gata tazo sai ki fda muji ynxu,ta soma magana cikin sababi ni dai Alhj kawai kayi mani tsakani da Habiba da kuma 'ya'yana in kai ta gama da kai to ni da 'ya'yana li'ilafi,,tashanye min yara basa cin girkin kowa sai na 'yarta sannan yanzu shi wannan miskilin dana gani kamar zai zama namiji amma ba haka bane ya tashi sai kashe mata kudi yakeyi harda yi mata anko da matar da zai aura me hakan yake nufi? na dai san rokonshi sukayi don haka ayi mana iyaka dasu ba 'ya'yanta ba nawa,tun da ta soma bata tsaya ba kuma ba a katse ta ba,jin tayi shiru sai na dago kai na dubi kowa kowa dai ita yake kallo sannan na dubi yayanmu wanda kanshi yake kasa Alhj yace to naji naki ke kuma Habiba ya abin yake?Mama ta soma magana cikin sanyin murya lafuzza masu kyau tace ni dai Alhaji a gefena ba wani matsala yarinyar nan dai itace matsalar, da zaka amince min da sai na dauketa na maidata wajen kawunta don inda bata nan gidan da baza ta ga ma 'ya'yan Haj Yaya ba bare su sata aiki sannan muddin tana nan gidan ba zan hanata aiki ma kowa ba har Hajiya Yaya inda zata sata,amma kiyi hakuri Yaya zan maido maki da dukkan abinda Abdulrahim ya sai ma Iman sannan kuma sai kiyi mashi magana ya daina sata aiki a zauna lfy,na dubi Mama hankalinta a kwance tayi maganar sabanin Haj Yaya wadda ke cika tana batsewa. Dakin yayi shiru sai can a Alhj ya soma magana yace Murja! Haj Yaya tace na'am da karfi tana karkada kafa yace ina son kisan cewa 'ya'yan nan nawa ne kuma wancan ma tawa ce don ni da kaina na daukota ko uwarta bata san zan kawo ta sai dai ta ganmu Allah yasan wannan don haka ba zaki raba min kan 'ya'ya ba kinyi kadan,Habiba yarinya ce a kanki amma tafiki hankali da tunani saboda haka kar ki yarda ki amshi duk wani abu da yayi mata kuma aiki duk wanda yayi niyyar sata kar ya fasa don haka na gama wannan maganar sannan ki gargadi laure ta kiyayeni da wasa naji ta taba Habiba ko Iman sai nasa an daureta gara ma ta tabaki zaifi mata sauki,Haj Maska tace yayi daidai hakan,Murja in ka girma to kasan ka girma don haka sai ta soma kuka tana cewa dama namiji ba dan goyo bane nan na dauki kudina na baka ko basu ne silar arzikin naka ba?daban haka ai da har yanxu kana a fakirin ka dole ka min sakamako da mun wulakanci ta nuna ni tace ke kuma zakiga hukuncin da zan yanke a kanki muddin kika kuma ko kallon min 'ya'yane na durkusa da sauri(don har ta mike)nace don son Annabi(SAW) kiyi hakuri bankade ni tayi waje sauran kishiyoyinta suka take mata baya,Alhj ya bisu kallo sannan yace Allah sarki to Allah ya sa ku gane,ya dubi yayanmu yace kaima kayi hakurin dai zan baka cikin sanyin murya yace Alhj kaimin izinin na koma england jibi,yace na maka amma yaushe zaka dawo?kar kaje ka kuma zama yace nan da wata shida ne yace to Allah ya kaimu ya fita na bishi da kallo. Karya ne gane halin da fuskarshi take ciki wato laifinmu yake gani ko na uwarshi,ban taba ganinshi cikin dogayen kaya ba tunda yazo sai yau boyel ne baki amma kanshi ba hula Alhaji ya dubeni yace Allah yayi maki albarka Iman kiyi koyi da halin mahaifiyarki kinji?na daga kai ya cigaba da cewa muddin kikayi halin uwarki to kin dace,sannan mijin da zaki aura ma yadace,su Abdulrahim da Kabir duk yayyanki ne duk abinda suka saki kiyi,sannan in sun maki kyauta ki amsa kice kin gode nace to Alhj na gode,na mike na fita dakinmu na wuce kai tsaye kan gado na fada raina a cunkushe na rasa me ke daga min hankali son da Kabir yace yana min ko matakin da Haj Yay tace zata dauka a kaina ne?wata zuciyar tace duk ba wannan bane tafy yayanku ce wannan amsar da zuciya ta bani itace sanadiyar tashina zaune saboda tashin hankali da naji ni a ciki na mike ina safa da marwa nace a fili ban so akayi wannan rikicin ba ba zanji dadi ba muddin yayanmu ya tafi kai zanje na bashi hakuri in ya tafi na mutu,da sauri na dauki hijabina na fita falo nan nayi turus ganin mama a falon tace ina kuma zaki?karon farko da na soma yi mata karya nace gidansu Amira tace me xakiyi?nace takalmina da gyalena dauko tace ko bari zata aiko maki ko ki aika Jamila kar ki fita ko ina ynxu zo nan kiji,na isa gunta na zauna tace kin dai ga abinda ya faru ko?nace eh tace to ina son kiyi taka tsan tsan da kowa a gidan nan banda yawan shigewa duk wanda ya saki aiki to kiyi masa kamar yadda kikaji Alhaji yace maki,nace to ta kuma duba na tace yanaga kinyi wani sukuku dake?nace bani son tashin hankali ne mama shiyasa tace kar ki damu aikin shedan ne kuma ki cigaba da addua sannan daga ynxu zan na tashin ki duk dare in tashi yin nafila sannan zaki dinga yin azumin litinin da alhamis,sai mu dinga tare in kuma an gama bikin nan zanje wurin kawunki na samo mana addu'o'i na tsari mu dukufa,Allah ya ja mana gaba,sauran maganganun da mama takeyi duk banji su ba ina ta tunanin yanda zan ga yayanmu don nasan nice na jawo wannan tashin hankalin gaisuwar da naji mama ta na amsawa shine yasa na juyo Mami ce ta dubeni tace ya dai?na mike muka shiga dakinmu kan gado muka zube na dube ta nace ya dai tace ina gidan walima muna shirya guri sai ga Sa'a wai ana fada da mamanku da su Haj Laure har sunce sai sun zane ku?nayi tsaki nace kan fa kaya ne kin gansu nan jikina yayanmu ya bani ashe irin na Anty mimi ne shi kenan sai tashin hankali gashi yanzu ma yace zai koma jibi,Mami tace ai dama bayan biki da kwana biyu yace zai koma nace to ai gashi ba'a gama bikin ba ni gani nake ma duk laifina ne hawaye suka zubo mani akan kumatu Mami ta tsaya kallona baki bude shi ne harda kuka?kuma ma ina wani laifinki anan? nace nasa kayan tace to baya baki don kisa bane?shi yayanmu in zai ma mutum kyauta ba ruwanshi da wani nuna bambanci nace rakani na bashi hakuri,Mami tace tab ai sai dai kije ke kadai yayanmu ba ya son ai ta faman bashi hakuri musamman in yana cikin tashin hankali gara makin zauna,ke menene naki na damuwa? kina ganin zaki iya hana shi ya tafi ne?nace bani na ja komai ba,tace sannunki da kai ta mike zo muje gidan walima nace ni kaina ma ciwo yake bazan sami zuwa ba ta tafi na koma na kwanta na cigaba da kuka rurus,saidai za'a a tsira ni ko da bindigane ba zan ce ga abinda nake ma kuka ba sai da nayi ya ishe ni sannan ciwon kai ya yomin sallama kafin wayewar gari nayi rigif ko sallar asuba kasa yi nayi sai wurin bakwai na safe yinin ranar nan haka nayi shi, misalin karfe uku Alhj ya shirya da Yaya Abdulrahim yace Habiba danku zai wuce fa,kan Mama tayi magana shima Yayan namu ya shigo ban san lokacin da na mike ba ya zauna a kan kujera yana gaida mama bayan ta amsa sannan ta ce ikon Allah tafiyar ta tashi ne Abdulrahim?na dauka gobe ne?yace eh gobe ne zanje lagos ne na kwana shida na safe jirginmu zai tashi yanzu ma jirgin karfe biyar zanbi zuwa lagos din yana magana niko bakinshi nake kallo da sauraron muryarshi mai dadi tamkar ba namiji ba ne yake magana ba Mama da Alhj suka shiga dakinta ya bisu da kallo sannan ya juyo ya dubeni na dukar da kai gabana sai faduwa yake yi,ga mamakina naji yace Amina nayi sauri na dago kai baki bude ina dubanahi shima ya kafa min idanu na sunkuyar da kai don ba zan iya cigaba da kallon kwayar idonshi ba sai ina ganin wani abu yana fitowa daga idon shi,yana shigowa nawa,murya kasa kasa yace zan tafi kiyi mani addua kaina a kasa nace adawo lfy Allah ya bada sa'a,a lebanshi naga ya amsa,Alhj ne ya fara fitowa yana cewa Abdul walarka nace Mam zata baka?yace no Maman Sagir kar ki damu ba sai kin bani komai ba Mama ta fito da dambun nama dayawa tace to ka tafi da dambun naman nan Iman tayishi shekaran jiya ya dubeni sannan yace to zan amshi wannan sai naji wani sanyi a raina suka fita nima na daga labulen dakinmu ina kallo ga yan biki nan sai a dawo lfy suke mashi harda su Haj Yaya dasu mama aka fita harabar gidan wajen ajiye motoci nima na fito ina daga can baya ina kallonsa har aka shigar mashi da jakunkunan shi cikin boot din motarshi yaya Kabir ne zai jashi,ga wasu abokanshi suma zasu shiga wata motar ya fito daga dakinshi har ya sauya kayansa da jc jajaye masu ratsin fari dogon wando da riga mai dogon hannu sai takalmin kwallo Anty Mimi ma ta fito sai kuka takeyi haushinta ya kamani a ganina nice yafi dacewa inyi kuka ba ita ba ko mai yasa oho zai shiga mota kenan ya hango ni sai naga ya tsaya yana kallona har Anty Mimi ma ta juyo taga wa yake kallo?sai taga ni yake kallo sai naga ta kawar da kai niko sai na kwantar da kaina a jikin bango sannan na daga mashi hannu alamr bye bye sai ya shige mota suka tafi Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tun daga wannan rana ban kuma wani sukuni ko walwala ba har mamakin kaina nakeyi kullum cikin damuwa bana wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane halin da nake ciki a gida da makaranta sai dai kowa ya tambayeni sai nace bani da lfy ne.Azumi da nafilflii kullum cikinsu nake ,ranar da yayanmu yayi kwana biyar da tafy Mama taga abin ya isheta bani magana sosai koda yaushe a kwance ga jarabawa ta matso amma bana wani krt sati da lahdi suka zo suka wuce amma banje islamiya ba wato (sanawiyya),Ranar monday mama tace kar naje makaranta na shirya muje Asibiti nace lfy ta kalau tace na dai shirya muje kawai rimi clinic mukaje mama tayi ma likita bayanin yanda nakeyi,likita ta barshi dani bayan fitar mama sai likita ya dubeni yace sanar dani yadda kikeji sai nace kasala nikeji sai kirjina da ke min nauyi kuma bani son yawan surutu yadan gwaggwadani sannan yace kina yawan tunani ko?nace eh yace to tunanin me kikeyi?nace ba komai yace karya ne da na rasa ta cewa sai na ce jarabawa ce nake tunani ba dan ya yarda ba yace to shi kenan ki daina yawan tunani kisa Allah a gaba ya rubuta mana magunguna muka tafi,haka nayi ta shan magunguna amma tamkar ana zugani Mama ta koma na gargajiya ni dai nawa shane a haka jarabawa ta same ni mukayi ta nidai ban sa rai da zanci ba ranar da muka gama ne a nata murna masu hoto nayi,niko sai kallon mutane nake,Mami ta dafa ni tace ga wata yar ajinku can tana nemanki nace ina take?ta nuna min ita ashe Hauwa'u Aminu ce nan tamin korafin rashin sanin gidanmu ita kuma ta bani no wayarta ni kuma nace mata in na fara anfani da tawa sai taga tawa lambar,sai da zamu bar harabar makarantar ne sannan naji duk kewar makarantar ta ka mani.Abdulrahim zaune a kan kujera a cikin falon Hotel din da yayi masauki, ko nace nan ne dama club dinsu suka kama mashi tun farko,kanshi yana jingine a bayan kujera, tebur ne dan karami cike da kayan ciye ciye da shaye shaye amma sam ya kasa cin komai tunanin yakeyi wayarshi tayi kara ya juyo ya dube ta kamar kar ya dauka sai kuma ya dauka Mimi ce ta kirashi bai san dalili ba sai yaji wani kunci a ranshi amma sai ya daure ya dauka,tace yayanmu kana lfy?yace lfy kalau,yake dinfa?tace ina nan lfy dama naga tunda ka tafi baka kira ba ne,yau kwana shida kenan?yace ban sami dama bane,tace to ina jiran kiranka,yace to kawai ya kashe wayar juyawa yayi ya dubi abincinshi kusan minti arbain kenan da kawo abincin amma ya kasa ci ya kai hannu ya bude plate din abincin da yafi so yayi order amma sam sai yaji kamshin abincin ma baya mishi dadi kokadan a fili yayi magana yace yarinyar nan ta bata ni da kalolin abincinta masu dadi,yayi shiru yana tunani tun zuwan shi kasar nan bai wani ci abinci ba daga ruwan lipton sai dambun naman nan,kwankwasa kofar akayi ya bada izinin a shigo ne abokinshi ne shima dan kwallo ne amma shi bature ne ya dubi Abdulrahim sannan yace cikin turanci Maska naga baka shirya ba ne,wannan karon baka so dawowa ba ne tunda ka dawo sam baka da kuzari,me yasa?Abdulrahim ya mike yana fadin tunanin gida nakeyi ya shige dakin barcinsa shima ya shiryo cikin JC na training suka fita.A daran daya cika kwana bakwai da zuwa yana zaune a harabar Hotel din haske ne ya kewaye gurin kamar rana gabanshi gwangwanin coke ne da dan karamin plate cike da dambun nama sannan ya kai hannu ya dauki wayarshi ya soma sana'ar wato danne danne wayarshi can yayi tsaki ya kashe wayar ya mike,da ya kamata ya nufi gurin abokanshi ne tunda ba dare ne yayi sosai ba kuma yasan zasu sa ran zuwansa, amma sam sai yaji ba zai iya ba saboda wani abu da ya taba zuciyasa sama ya nufa dakinshi ya zauna a bakin gado sannan ya aje tarkaccen hannunsa a kasa wayarshi ya rike sannan ya soma sarrafata cikin kwarewa, Babanshi ya kira bayan ya dauka sai yace Alhj ina yini?bayan sun gaisa sai yake cema Alhj dama ya kira ne dan ya amshi lambar wayan Maman sagir domin yana da lambar kowa a gidan itace bai da ita,Alhj yace gata nan ma Habibar ku gaisa,bayan sun gaisa ne sannan ya bukaci lambarta ba tare da wani tunani ba ta bashi,ya jima yana tunanin dalilin karbar no kafin daga karshe ya gane sai dai wani tunaninshi abin zai zamar mashi abin kunya da nunawa cikin abokai,muddin suka san halin da yake ciki,nan a dalilin wata kankanuwar yarinya wacce da yayi auren wuri tabbas zai haifi kamarta.Kwance yake akan gadonshi amma sai sautin daddadar muryar yarinyar yake dawo mashi ya tuno ranar da bashi da lfy duk gidan ba wanda ya kula dashi tamkar ita muryarta ya tuna sannu yayanmu za ai maka wani abu ne?ya sake tuno yanda ya kara tsorata ta ranar da ta daukan mashi kujera tabbas in tana cikin tsoro tana matukar burgeshi yayi magana a fili inda yace nayi missing din ganin tsoranki. (Lallai Iman kinga takanki, mudai daganan sai muce! Allah yakyauta) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ya cigaba da juyi a kan gado ba komai ke dawainiya dashi ba sai begen yarinyar da yake gani abin kunya ne ace ya sota ya tuna da mimi yarinya mai kyau jinin larabawa sai dai shi baya jinta a ranshi yanda yake jin wannan yar mitsilar yarinyar zai auri Mimi ne kawai don bin umarnin mahaifiyarshi kuma ya san duk inda suka shiga ba zai ji kunyar nunata ba a matsayin matarshi shekarunta ashirin da biyar shi kanshi shekara biyar ya bata bugu da kari gashi ta soma zurfi a karatunta,amma in yace wannan yarinyar zai aurà shima yasan rigima zai jawo,yanda mahaifiyarshi ta tsane su wata zuciyar ta ce mashi ga yaran nan da rashin kunya tana jin kace kana sonta to raini ya shiga tsakaninku gara ma Mimi hadaku akayi kuma kasan ta mutu kanka don haka baza ta maka wani rawar kai ba,"A dawo lfy Allah ya bada sa'a" ya kuma tuno muryata da yaji na karshe sannan lokacin da ta rakube a jikin bango tana mashi bye bye ya dawo mishi tausayinta yaji lokacin kuma jikinshi na bashi kamar itama tana jin yanda yake ji a ranta,zaune ya mike yana magana shi kadai tamkar wanda ya tabu yana fadin Amina kiyi hakuri bani da shà'awar auran mata biyu ki bari in runtsa ya kuma fadawa kan gado.Niko yanzu na zama kurma bana magana sosai ban kuma cika son magana ba sai dai maganar su Amira ce ke damuna da suka ce wai ina ciki mayen soyayya na dai ki sanar dasu wanda nake so,inko har zancensu gsky ne to na debo da zafi don ko in har yanda zuciyata ke mani game da yayanmu so ne to ko shakka babu gara na rufa ma kaina asiri nayi shiru da bakina don nasan ko yaji ubana zaici don nasan ni ba ajinshi bace,me kamar Anty Mimi? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 kammala karatuna shi ya ba samari damar damuna tamakar anbi su an gaya musu musamman ma yaya Kabir shine yasani wannan ya sani wancan,su yaya ma suna zuwa,ban manta wata rana yaya Kabir ya aiko Sagir dinmu ya kirani na fito na sameshi a daki kan kujera na zauna fuskata na kallon wani katon hoton yayanmu sanye yake da JC kore da fari irin na yan wasan Nigeria hannunshi a kan kirjinshi daga gani lokacin suna taken Nigeria ne aka dauke shi,muka gaisa da yaya Kabir ya soma yi min zancen soyayya niko hankalina ba ya tare dashi, yayanmu kawai nake kallo da kyaun da Allah yayi mashi ba abinda ya birgeni irin shedar sallah daya fito mishi a saman goshinshi yayi baki tamkar ya diga ina cikin wannan tunanin ne naji yaya Kabir na min magana da karfi nayi ajiyar zuciya sannan na dube shi nace ka gama?zan shiga gida yace na tambayeki baki bani amsa ba nace ni ban wani jika ba na mike nayi waje yana kirana na fito kirana naji anyi daga bakin gate ko ban juya ba nasan yaya Abubakr ne dogon tsaki naja sannan naje ina zuwa na hau shi da masifa shima kallona naga ya tsaya yi,ina cewa nace ni ba aure zanyi ba amma kun dameni don Allah ku rabu dani ko dole ne?na juyo abina wani abin haushi ina shiga falonmu sai ga yaya Suleiman zaune suna hira da Mama...(hhhhhhhhha.yarinya taki tasameki.) dakin kwananmu na wuce nayi kwanciyata naki fitowa ban fi minti goma ba mama ta shigo ta dubeni tace Sulaiman ya dade yana jiranki wai me kika tsaya yi wurin Kabir din?nace ya aike nine bayan na dawo kuma sai na gamu da da yaya Abubkr na cigaba da cewa gsky ni dai mama ki samu su yaya Abubkr kiyi musu magana nifa ba aure zanyi ba su rabu dani mana,mama tace aike ma yan uwanki ne kuma nasan in ki sanar dasu zasu kyaleki sannan suna ganin girmana sosai bazan iya tunkararsu da wannan zancen ba, nace haka fa shekaran jiya yaya Ibrahim yazo wai har yana takama zaije ya samu babana kuma ko ina so ko bani so shi zai bashi ni mama tace to bisimilla ai ga kinan taci gaba da cewa don haka ma ni koda auren ne cikinsu gara Abubakr din nace ni dai dukkansu har yaya Sulaiman din hakuri zaiyi dani dan bana son auren zumuncin nan mama ta fita tana cewa dai gashi can ku gaisa,na dauki hijabina na fito falo fuskata a daure muka gaisa yace to Iman gani dai na kuma dawowa duk da kin sanar dani krt zakiyi shine na yanke shawara ki yarda a daura mana aure ni kuma zan yarje maki kiyi krt har kiga karshen biro nace mu bar zancen nan, ina Nana?yace Nana tana nan jiya aka sa ranarta goron ne ma na kawo ma Mama nace lallai Nana yanxu itama auren zatayi?yace shine mutuncin duk wata 'ya mace nace to Allah yasa alkhair ni zan shiga na kwanta ka gaida min da su baba uwa kace da Nana inna jiran zuwanta, yace amsata fa? ko zaki yi min waya don Mama tace kin soma amfani da wayarki nace jiya na soma sai dai ni bata dameni ba don haka ko lambar ban rike ba in Nana tazo taje maka da lambar yace ai bazaki min ko flashn bane tunda kinsan tawa nace to na maka na shige daki ina jinshi yana fadin barakiya? Sannu a hankali zuciya da gangar jiki suka tsananta da so kauna da kuma begen wanda bazasu samu ba sannan ni naki yarda da cewa sonshi nake ban yarda da nayi nutso a kogin sayayya ba sai da na samu kaina da rashin barci,sannan na kama karatun littatafai na soyayya,kallace kallace da basu dameni ba yanzun nakan zauna nayi duk saurayin da aka nuno sai naga bai kai yayanmu komai ba ni fa gani nake ba wani namiji wanda ya amsa sunan namiji in ba yayanmu ba,yauma kwance nake akan gado yar karamar Rediyon da nike yin karatu ce na manna a kunnena kaset na wakar fim din kugiya na sa wakar na ratsani Idona a lumshe sai nakejin kamar nice nakeyin wakar, duka naji an dada min da sauri na tashi ganin Amira da Mami shine yasa nayi ajiyar zuciya nace kin dau alhakina Amira ta cire wayar kunnena sai ta dauke Radion ta sa a kunnenta dajin wakar sai naga ta cire da sauri tace Mami ji wannan kaset din Mami ta sa taji sai naga sun dubi juna sukayi dariya nace wai menene?suka zauna suna cewa zancenmu gasky ne nace kamar yaya zancenku gsky ne?Amira ta dauke fuska tace Iman mun gamsu nace me na muku?Mami tace akwai abinda yake damunki amma kin kasa sanar damu,Amira ta amshe damu ne da munhau gaya maki nayi shiru ina tunanin me zan ce masu can dai nace Amira,Mami kunsan yayyena Abubkr,Ibrahim da Sulaiman?suka ce sosai ma kuwa nace dukansu sunce suna sona ni kuma bani son ko daya sannan yaya Kabir shima yace wai sona yake na mike tsaye don girmama maganar da zanyi na cigaba da cewa ni kuma zuciyata da gangar jikina sun nutse a son wanda bai san inayi ba kuma koda ya sani ba zai soni ba don yana da wacce ta fini kyau da ilimi da kuma shekaru,hawaye suka soma zubo min na juyo da sauri na rike kafadun Mami da karfiina cewa ku bani shawara kawayena ku taimaka min da maganin da zan daina sonshi don kukan ku da zaku san ko wanene da kunce lallai zuciyata tayi wauta,suka kamani suka zaunar dani tsakiyarsu suka yi shiru dakin ya yi tsit daga ajiyar zuciata da nakeyi sai karan fanka can Amira tace a ina yake?kuma yaya sunanshi?nace kuyi hakuri wata rana zan gaya muku don ba anan yake ba Mami tace dakin gaya mana ai da mun san yanda zamu bullowa abin nace no ko zan mutu bazan taba tunkarar wani da namiji da sunansa ba yanzu ku bani shawara yaya zanyi na daina tunaninshi suka yi shiru can Mami tace rokon Allah zakiyi muma zamu taya ki nace sai dai mukara don kullum yi nake amma ba sauki sai dai abinda ya karu nan dai suka lallashe ni gami da bani shawarwari. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Haka naci gaba da rayuwa cikin kunci,wata safiya misalin karfe takwas Mama tana dakin Alhaji ta kai masa abin kari ni kuma ina ta faman gyaran dakinmu na gama na koma dakin Mama ina cikin aiki naji wayar Mama tana ringin na dauka sai ga lambobin rakwacam na dauka nace Assalamu alaikum sai naji ance Wa'alaikummussalam,jin muryar da ta amsa nan da nan na gane yayanmu ne farin ciki da na ji baya misaltuwa ina wannan tunanin ne naji yace Naman Sagir ina yini? nace ba ita bace ni ce Mama tana dakin Alhaji yace ok! nace ina kwana?yace lafiya amma mu nan rana ce kuna lfy?nace lfy lau yace to kice da Maman Sagir ina gaishe ta dama don mu gaisa ne na kira kafin nace to har ya kashe ranar nayi walwala har yamma don jin muryar abin sona. Share DOCUMENT CREATED BY ZAHARADDEEN SHOMAR WHATSAPP 08168575100 Tawa Tasameni1-04 Posted by ANaM Dorayi on 10:13 PM, 30-Dec-15 __________ NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI__ Lokacin da zai tfy nan ko ince da zaya koma ina cikin wannan tunani sai naji yace kin gama?dama na gama sai nace e yace to gashi na isa na dan rage tsawo yace wannan ya turo mani akwati naki ne sannan daya kuma zaki kaima Mimi nata nace to nagode Allah ya kara daukaka duk da bai amsa ba nasan yaji dadin adduar,na dau akwatin nayi cikin gida Allah yasa ba kowa a tsakar gidan ni da mama muka bude muna ganin kaya nayi mamakin kayan domin suna da yawa bayan haka kuma zasuyi tsada english ne kala bakwai sai jakunkuna da takalma sai rigunan barci masu kyau sai wani zobe cikin akwatinsa mai kyallin gaske,na dauka ina dubawa zobe ne na zinari mai nauyi akwai stone mai kalar ruwa gargar tamkar kankara in ka kura ma stone din ido zaka ga an rubuta A guda biyu daya kan daya nace la mama duba ki gani harda farkon sunana tace kin gode sai dai fa in har irin na 'yan uwanshi ne to ba zaki sa su ba na dan bata rai sannan nace bama iri daya bane na tashi na soma gwadawa duk wanda nasa sai su zauna min tamkar a jikina aka kerasu,da yamma ina zaune a daki ni dai bani son zuwa aiken yayanmu domin na tsani ganin Mimi nasan ma wulankanci zasu min Sagir ne yace yayanmu na kirana dama a shirye nake ina son inga ko ya manta ne in share in ya tambayeni daga baya sai nace na manta ne nima haka na tashi na tafi dakin mama na sanar da ita tace sai na dawo,su hudu na samu na gaishesu suka amsa dayan cikinsu yace Maska wannan ma sister ka ce?yace ban sani ba ya wani daka min tsawa yace shiga ciki ki dauko jaka adidas kizo ki wuce kin wani tsaya kina kallon mutane na shige dakinbarcinshi da sauri ya juya gun abokanshi yana ce mishi dj bana son aboida kuke min baku san yaran nan da raini ba sai taga kamar sa'aninta ne mu wani yace to Nasir fa da zai auri Mami kanwarka?yayanmu yace ai yaga zai iya ne sannan nace mishi kar ya yarda ya kawo min karanta raina shi ga manyan babys a gari yazo zai nace gun wadannan yaran,jikina yayi sanyi na sabi jaka na fito ya dubeni yace kikai mata saura ki dade na fito ba tare da ya bani kudin mashin ba, gidansu Amira na shiga bayan mun gaisa da mamansu tace min tana cikin dakinta na shiga tace daga ina haka?nace ina zani zaki ce ta ce to sai ina?na zauna bakin gado na ajiye jakar a kasa na dubeta na nace don Allah zaki raka ni?tace ina? nace malali gidansu Anty Mimi tace to jeki ki gaya ma mamanmu sai na shirya kafin ki dawo nace to amma fa kece zaki biya mana kudin mashin tace wane irin ni zan biya nace to bai bani kudin mashin ba gashi har yana cewa inyi sauri ni kuma ban fito da ko sisi ba na fito gun mamansu na sanar da ita tace sai mun dawo muka fito muka hau mashin sai malali Yanda na zata hakan ce ta faru domin da Mamnsu wato Haj Laure ta ganmu haka ta hau zaginmu wai mu juya da kayan ba'a so inshi ba zai kawo ba to ya bari,Anty Mimin itace ta hana tace mu kawo Amira tace ki barshi mana sai mu maida Anty Mimi tace ke bani son rashin kunya Amira tace ba rashin kunya bane ance ne mu juya dashi na dubi Amira nace don Allah ki rufa mani asiri Amira ta jani zamu juya Anty mimi ta biyomu ta fisge jakar ta juya ni dariya ma abin ya bani,muna jiran mai mashin wani yazo da mota a gabanmu ya tsaya ya dube mu yace kuzo muje yanmata ina za'a kaiku?kafin nayi magana Amira tace unguwar rimi na dubi Amira nace kina hauka ne?tace zauna nan in ba zaki ba sai dai kiyi ta zama anan yace magana fa nakeyi nace ku shigo muje nima can na nufa,nace nidai ba zan shiga wannan motar ba Amira ta bude baya ta shige sannan tace ai kina da kudin mashin ko?nan na tuna bani da ko sisi nayi tsaki,saurayi mai mota yace yar kanwata shigo mana jan ajinki ya burgeni kuma na yaba,na dubi Amira ta wani kame tamkar motar kanin babanta nace bani naira dari tace nace maki bani da kudi ko?in zaki shiga ki shigo dole,dole na shiga motar nima bayan na shiga yace yi hakuri kanwata dan dawo nan mana na koma don surutun ya soma isata yaja muka tafi,sannu a hankali yake jan motar sunana ya tambaya nace mashi Amira, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Amira da take baya ashe taji tace yar iska sunanta Iman yace yauwa mai sona fada min gsky Amira ta cigaba da cewa xan kaika har gidansu yanda tace maka haka takeyi ma samari tace sunanta Amira kuma ta yi masu kwatancen gidanmu ina jinsu ban kuma magana ba sai su keta faman labarinsu,muna zuwa kofar gidanmu ya faka a daidai lokacin yayanmu yayo ma abokanshi rakiya kallon motar ya tsaya yi da sauri na bude na fito daga motar ido hudu mukayi da yayanmu nan da nan fuskarshi ta sauya yayi murtuk tamkar bai taba dariya ba koda dai dama ban taba ganin dariyar tashi ba,a hankali yake tahowa har inda muke nayi zaton zai mare ni ne sai naga ya wuce ya isa gun motar daidai kofar dreba ya kwankasa gilashin motar,ina zaton Amira da bata fito ba ita ce tace masa yayanmu ne sai naga ya fito daga cikin motar da sauri sannan ya mikawa yayanmu hannu gami da sallama,yayanmu nokewa yayi yaki bashi hannu sai dai ya amsa sallamr a ciki ya dubeni yace menene dalilinki na shiga motarshi?nayi shiru shi kuma saurayin mai motar sai cewa yayi yallabai ai ina sonta ne kuma banzo da wasa ba,sai ya kara daure fuska sannan yace ita me tace maka?yace bamu yi magana ba tukunna,yayanmu yayi mishi wani kallon wulaknci sannan yace kar na kuma ganinka a gidan nan ka fahimceni? yarinyar nan krt zatayi ku ne masu hure ma yaran mutane kunne suki krt bani bukatar sake ganinka understand?so kama gabanka ya juyo ya kalleni wata uwar harara ya sakar mani ba zaki wuce a nan ba? Da gudu nayi cikin gida. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tara daidai na dare na gama shirin kwanciya kamal ya shigo ya dubeni ke Iman yayanmu yace kikai mashi tea,ban tsaya dogon turanci ba na fito falo dakin mama na shiga ko zan samu ta dafa ma Alhj bata cikin dakin na fito falo kan tebir naga ples din shayi na duba naga akwai a ciki yar butar shayi na dauka na zuba na dora kan tiranshi na hada da kofunan na fita sam na manta ban sanya hijabi ba rigar bacci ne a jikina mai hawa biyu sai hular hijabi nayi sallama da kyar ya amsa na dan dube ahi fuskarshi a daure cikin tsoro na shiga zaune yake kan kujera mai zaman mutum biyu ya dora kafarshi suna kan teburin tsakar dakin irin dan karamin nan na rage tsahona na ce gashi ya zuba min harara na ajiye da sauri na zan fita sai naji yace ke zo nan na daqo ya dubeni yace zauna na zauna kan kafet cikin hankali ya sauke kafafuna daga kan tebur din ya zauna da kyau,Amina naji ya kira sunana a hankali yar naji cikin jikina gashi ya iya fadar sunan a gajiye na dubeshi sannan na amsa yace na lura dake kina shaawar ganin bacin raina ko? (hhahhh su yaynmu anyi nisa) na girgiza kai alamar aa yace haka ne mana(a raina nace to me nayi maka?) Yaci gaba in ba haka ba so nawa zance miki bani son kina kula samari ko kema auren kike so?nace aah yace kar ki damu in ma auran kike so to sanar dani don akwai wani da yayi mani maganar yana sonki,gabana yayi mugun faduwa a raina nace ni kai nake so ya kara tausasa murya yace in har kina so ya kara tausasa murya yace in har kina so ki kwantar min da hankali to ki tsaya kiyi karatunki kar ki damu da su mami basu san matsalolin da ke cikin auran ba,kinga kema karamar yarinya ce baki san komai game da aure ba undaerstand me?na gyada kai alamar eh yace to yi min alkawari da bakinki cewa ba zaki kula kowanne da namiji ba ko bana garin ko bana kasar har sai na dawo na bada izini ba tare da wani tunani ba nace nayi alkawari ba zan kula kowa ba ko ba kanan yace promise nima nace promise yace good ya saki fuska tashi kije ki kwanta na mike sai da naje kofar fita na juyo shima ni yaje kallo ga mamakina sai naga ya min murmushi mai tsayawa a rai na saki labulen na tafi zuciyata na dauke da murmushin da yayi min,haka na kwanta ina juya maganganun da yayi min musamman in da yake cewa in har kina so ki kwantar min da hankali to ki daina sauraron samari me yake nufi?wata zuciyar tace min abokinshi mana haka nayi ta juyi har barci ya daukeni Washegari da safe ina shirin tfy comp Jamila da Sagir suka shigo da gudu suna rige rigen fada min kiran yaya Kabir na daka musu tsawa nace kai ba makaranta zaku je ba?suka ce ai mun fita sai yayanmu yace kizo nace yayanmu babba?suka ce a'a Kabir,na dan yi tsaki sannan nace kuce gani nan,sagir yace anty kizo muje yace in kika zo muje yace in kinzo zai bamu naira 100 nace ku bace min da gani a nan suka fita sai da na gama sannan nayi wa mama salla.a sannan na fita,na dauka ya tafi gun aikinshi sai na ganshi a kofar dakinshi sai faman duban agogo yake yi na isa gurin shi fuskata babu walwala nace ina kwana?bai amsa ba sai dubana yake yana murmushi yace da raina ya baci domin kin shanya ni amma yanzu kin wanke min zuciyata na dubeshi nace kamar yaya?kinyi dressing irin nawa,na dubi kayan jikinshi kampala green nima haka sai naji tamkar na koma na cire ya dube ni zo muje na saukeki nace ka barshi yace duk da nayi latti sai na kaiki,dole na shiga muna shirin fita yayanmu ya shigo shi da wasu abokanshi cikin kayan training duk da kaninshi ne sai da gabana ya fadi yako tsira mana ido sai ya tsaida motar ya dubeni yace kin mani shara?na dubeshi yayi wani kicin kicin nace a'a yace to fita ki min bai saurari amsata ba yayi gaba na dubi yaya Kabir nace to kaji fa abinda yace,yaya Kabir yace don Allah ki rabu dashi bari mu tafi,nace wai ba haka a tsakaninmu haushi ya kama yaya Kabir yace toko dai yana sonki ne?nace kaji ka da wata magana kaima kasan ko mata sun kare yayanmu ba zai soni ba yace saboda me kikace haka?nace ni nasan bani da kyau kuma gani baka yayi murmushi sannan yace ganinki kenan kina abubuwa masu fizgar hankali so ni dai yanzun ki yarda na fito sai a hada da nasu Mami,haushi yasa na bude motar na fito shima yayanmu na sameshi ya cika dam ina shiga ya dube ni duban wulakanci yace me kika tsaya yi a gunshi?nace ba komai ya nuna ni yace look ba zaki min yawo da hankali ba bani son na kara ganin kin shiga motar Kabir kina jina?ya daka min tsawa nace to,ya fita na shiga gyaran daki ina mamakin wannan ikon Allah.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ina cikin goge TV ya shigo yana waya ya zauna kan kujera yanda naji yana amsa wayar ne yasa naji duk bakin ciki ya kamani ko bai fada ba nasan da Mimi yake magana har yana cewa karki damu nima kin manne cikin raina kuma ki saurareni in anjima da sauri na shiga bedroom dinshi har lokacin wayar yakeyi ranar da takaici na yini wata zuciyar tace min kina kishin banza kina wahala bai san ma kinayi ba Kwana biyu ni dasu yaya Abubkr da duk wani mai son ganina in dai saurayi ne sai dai a waya ranar juma'a ina zaune da yamma tsautsayin jin takaici ne yasa nace da mama bari in shiga gun Amira ina isa daidai dakin yayanmu shi kuma yana fitowa tare da abokinshi sun kai su bakwai daya ne naji yana cewa ango ango to Maska wata nawa aka sa yayanmu ne naji ya amsa da cewa sati biyu suka sa da sauri na juyo cikin sa'a muka hada ido shima sai naga yayi wani iri tamkar bai so naji zancan ba wani abu mai nauyi naji ya tokare min wuyana kirjina kuma ya hau zugi da kyar nake janyo numfashina kokari nayi naci gaba da tfy amma bana ganin gabana sosai jirin da naji ya soma dibana shi yasa na juyo na koma gida ikon Allah nema ya kaini kofar dakinmu a nan na zube ban kuma sanin in da kaina yake ba na dai farfado na gani a gadon asibiti Mama tana zaune a kan kujera tana rike da hannu na wanda aka sa min karin ruwa ta min sannu na amsa da kyar a hankali na soma tuno abubuwan da suka faru shi kenan yayanmu ya zama na Anty Mimi ko shakka babu yana mutuwar sonta,na tuno wata rana ina shara a dakin yaynmu har na gama zan fita yace nazo nan na juya na koma nace gani yace baki sa turaren daki ba nace na mance ne,na shiga bedroom din shi idona ya sauka akan wani kyakyawan frame kamar kaida in dai zan shiga uwardakin yayanmu to ba abinda nake fara kallo sai wannan frame din yana da kyau ga dauakar hankali gashi saitin kofa da ka shigo shi zaka fara gani,na manta batun turaren daki na tsaya duban frame rubutun jiki yan kanana shi yasa ban taba karantawa ba amma lokacin sai na hangi rubutun saman kamar hausa akayi nayi mamaki frame mai kyau da shegiyar tsada irin wannan amma da hausa na ce kai yau sai na dauko shi na karanta duk da wane yare ne na duba dakin ko naga abinda zan taka don yayi sama sosai ba wani abu mai tsawo sai tebur karami kuma na glass ne na jawo shi a hankali na taka daya ke nima ina da tsawo na dauko,tabbas da hausa akayi rubutun a saman an rubuta: Zinariyata Zuciyata ta jima tana begenta daga lokacin da idanuna suka fara ganinta,na tsunduma a sonta duk karancin shekarunta duk sanda na dubi idanunta sanyi kasala sha'awa suna gajiyar dani bare in naji kamshinta,a lokacin da nayi nisa da ganinta sai barci ya kaurace ma idanuna sai tunaninta bana jin dadin wani girki sai nata Allah ka azurtani da aurenta domin na samu ni'imarta har ka azurtani da 'ya'ya masu albarka daga gareta (A)amin. jikina yayi sanyi sai dai abin daya bani mamaki shine yanda (A)a cikin (A)tamkar irin na zoben da yayanmu ya bani a cikin kayan tsaraba nace kai kilan ma ba (A)guda biyu ba ne wani tambarin ne na wani camfanin a can England din,na dubi fulawoyin dake jikin frame din da tsuntsaye masu ban sha'awa ina cikin juya shi ina cewa nasan Mimi yake nufi,shine Mami tace min baya sonta ashe ma ya jima yana sonta gashi yace tun tana karama,ina cikin tunani naji yayanmu daga falo yace baki ga turaran bane?nan jikina ya soma rawa ina kokarin maida wa ne tsautsayi yasa na goce,frame din ya fado sai kan tebur din glass ji kake tats,jikina ya hau bari na soma tsuma tamkar mazari,na dauki frame din baiyi komai ba teburin ne ya fashe naga an daga labule da sauri na dubi kofar yayanmu ne tsaye nayi duba zuwa ga fuskarshi ya wani daure fuska me ya kai ki gurin frame kina ganin sirrina ko?hawaye ya soma zarya a kan kumatuna nace a'a zan goge ne yayi kura ya daka mani tsawa yi min shiru kuma sai kin biya dukkan abinda kika fasa min,na durkusa kan gwiwoyina na soma cewa don Allah kayi hakuri yace ai zaneki zanyi yanzun nan muryata tana rawa nace please yayanmu ya dubeni cikin wani yanayi mai wuyar fahimta sannan yace gyara min wirin ki wuce,ban san kan kwalba nasa gwiwata ba sai da na gama gyra dakin sannan naji zafi na duba.kamshin turaren da naji shi ya dawo dani cikin hayyacina ko ba'a fada ba nasan yayanmu ne ya shigo Asibitin nan ban gama tunani ba ya kwankwasa kofa ya shigo dama fuska ta kofa take kallo don haka yana shigo dani muka soma hada ido sai naga tamkar an kara mashi wani kyau.... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na lumshe ido sai naji wasu hawaye sun zubo min ina jinshi suna gaisawa da mama ya tambayeta jikina tace da sauki ban ma san har na kwana ba sai da naji yace tun jiya bata tashi ba?mama tace dazun nan ta farka ina mata magana banji ta amsa ba nayi mata sannu ta amsa bata kuma magana ba sai hawaye da ke zuba daga idonta shiru yayi na dan lokaci sannan yace bari inga likitan mama tace yanzun nan babanku ya tafi gurinshi tun jiya ma yace ciwon zuciya ne yake son kamata ni na rasa mai yarinyar nan ta nema ta rasa da har ta sa kanta cikin tunani,muryar yayanmu naji cikin sanyin shin nan yace ai maman Sagir cututtuka sunyi yawa ba sai mutum yana wani tunani ba Allah dai ya sauwake ya juya zai fita sai ga a Alhj ya turo kofa yayanmu ya matsa Alhj ya shigo yana ma mama bayani sun tabbatar da zuciyata na son ta harbu sannan yace su tuhumeni ko akwai wanda takeso ne ko abinda ya shafi haka yayanmu yace Alhj bari nima na ganshi likitan sukace to lokacin Alhj yasa an tashe ni zaune ni kaina nasan na rame sosai cikin kwana daya yayanmu ya dubeni yace sorry Iman na dubeshi yaune na fara jin ya kirani da Iman na daga kai alamar amsawa,yace maman Sagir me taci?mama tace bata ci komi ba yanzu ne dai zan hada mata to amma tace sai tayi sallah tukunna,ya dubeni zaki iya yin sallar ne?nace eh tare da taimakon mama nayi alwala muna fitowa daga bayi yayanmu yayi mana sallama yace da daddare zai dawo haka na cigaba da jinya har tsawon kwana uku kullum yan dubiya suna zuwa,Amira da Mami nan suke yini haka yayanmu da yaya Kabir nan sau uku suke zuwa sai dai duk lokacin da yayanmu yaga yaya Kabir haushinshi yake ji, gudun fadan alhj yasa kishiyoyin mama suka zo sau daya kuma basu kawo mana abinci sai dai anty Yagana da maman su Amira kayan ciye ciye kam yayanmu ya kashe kudi har Anty Mimi ya kawo ta gaisheni nasan dai dole tazo ba don son ranta ba,niko ban ma ji wani dadin zuwanta ba don ma kadan ya rage ciwona ya dawo musamman ma da naga sun sa anko yellow kampala sun man kyau sai dai kishi da ya sani gaba,ban san yanda akayi su yaya Abubkr sukaji ba sai dai ganinsu nayi yaya Ibrahim ne yake ce min babana yana nan zuwa,yace a gaisheni naji dadi har ina tambayarshi yaushe zaizo?yace kilan yau ko gobe nace kilan a sallame ni yau ai a ranar aka sallameni kafin sati na dan girgije,yan skull dinmu na comp ma sun zo duba ni randa na cika kwana goma ranar na koma zuwa makaranta lokacin saura kwana hudu bikin yayanmu su Mimi duk sun damu da bikin sai rawar kai suke yi har Mami na cewa da ban warke ba bikin ba zai mata dadi ba sannan suna son kudi gun yayanmu nice ma zan amsar musu nace ke Mami ki rabu dani ba wani kudin da zan tambaya a raina nace in baku san dan dole zan zauna a garin nan ayi biki ina nan ba da ba dan mama ba zata yarda ba da naje tudun wada gidan kawuna sai angama sai na dawoa dare yayanmu ya aiko nazo lokacin ina zaune a falo ni da mama tana nuna min memo data buga da sunansu au Jamila da Sagir sai agogon bango suma guda dari wai in bashi ince ni na buga na dauki guda daya ina dubawa hotunansu ne sunyi kyau sosai na hadiye wani abu da yazo min wuya na dubi mama nace sunyi kyau amma kin sha kudi tace yaya za'ayi ai yana da mutunci sosai Abdulrahim na ce umm waya baki hoton su?tace gun Kabir na amsa na rike hawayen idona lokacin da naga sunana a matsayin wacce ta buga kafin nace wani abu ne jamila ta shigo anty Iman kizo inji yayanmu na danyi tsaki nace kice kaina na min ciwo ba zan iya zuwa ba a raina nace ba zanzo ba tunda ka kama matarka a hannu kasata aikin,Mama ta dubeni kije mana Iman kije mishi da agogunan nace banjin dadi ne mama tace daure na mike na ciccibe kwalin agogunan na ce bari na kai wannan sai na kuma zuwa na dauki dayan da kyar nakai dakin nayi sallama na shiga yana zaune da kaya a gabanshi fuskarshi babu walwala ya dago kai ya dube ni yaya kai din na dan lumshe ido sannna nace da sauki na kula tun da nayi rashin lfy sam baya son yimin tsawa ko fada ya dubi kwalin dake gabana yace menene wannan?mYaya gudummuwata kenan a ba jama'a. Ina zuwa na koma na dauko dayan kwalin na samehi yana duba wa ya dubeni yace amma sunyi kyau mun gode,na danyi yake nace um ya turo min kayan gabanshi yace ga naki kayan bikin harda ankon,nace ai Baba yayi mana ankon,yace duk da haka ki dauka ina son ki kaima telanki da yake maki dinki don ya iya sosai nace yaya Sulaiman ne ya ma samu aiki yanzu bai cika zaman shagon ba sai dai yaranshi,yace to kikai inda za'ayi maki mai kyau,takalman ki jakunkuna sai yau za'a kawo anjima kadan gidan Nasir na manta su nace na gode ya kuma duban hannuna ke bakiyi lallen bane?nace eh yace kiyi gobe zanzo na kaiki saloon mamaki ya kamani nace ko dai yana zaton da Amaryar yake magana ne?ni da ban taba shiga motar shi ba,na boye mamakina nace ai bana sa relaxer kitso nakeyi yace to kiyi kitson kinji ni?nace to.kaya ne kala shida less biyu super biyu sai material daya sai shadda,shaddar din kakkiya ce ta sha aiki riga da zani sitayal din ya hadu ga shaddar mai tsada,turare kala uku masu kyau da mayukan shafawa sai sarka da 'yan kunne,Mama ta dubeni tace oh ni Habiba wannan hidima tayi yawa, shida ke cikin biki kayan nan Iman ba'a karbe su duka ba bani wayata gata can a chargy,na dauko mata shi ta kira tana mishi korafin yawan kayan bansan me ya ce mata ba naga tayi murmushi tace ai kanwarka ce kowane ai ta maka kabiyata kenan?can kuma tace to shi kenan an gode Allah yasa ayi wannan biki lfy ya kuma bada zaman lfy.Washe gari na shirya sai tudun wada na kai dinkunan a can nayo kitsona da lallen filawa mai ratsin ja,gidansu Amira na biya tace min zakije Arabian day din ne yau?nace Mami tay min magana amma da kyar in zani kinsan bana shiri da Amaryar, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Amira tace indai ba zakije ba nima ba zani ba dama domin ke zani nace to bari in zani zan maki waya ba karfe hudu bane?na duba lokaci a wayata karfe biyu da minti arbain nace bari na shiga gida dama dinki nakai tudun wada,Amira ta dubeni tace name kuma ba kinyi anko ba?nace jiya yayanmu yace ga nawa ankon dana duba sai naga ba anko bane ya dai minne ne kala shida harda takalma yau da safe ya bani takalman kala uku,Amira tace gsky jininku ya hadu,sanda baki da lafiyannan kar ki ga yanda ya damu ba dan munsan yanayin rayuwar shi kenan yin alkhairi ba damin zargi ko sonki yake na kai mata duka nace me zukekiyar mace kamar Mimi me zaiyi dani?Amira tace Iman kina da kyau amma sihirtacce ne sai na kusa dake komai sonki ko kuma yasan kyau zai gane kiga Mimi mai mata kallon gane muni zai ga muninta don tana da goshi da kuma....na katse ta mu bar zancan nima ai in an kura min ido za'a ga muni nawa,Amira tace Allah baza'a gani ba sannan ne ma za'a ga kyaun ki nace um bari na shiga gida. A gurin Arabian day kowa yayi kyau Amarya cikin jallabiya baka da dan hijabi tana zaune a gun da aka tanadar mata muka shigo nima sanye nake cikin Jallabiya mai hawa biyu baka da ja hijabina da takalmina jajaye ne, Hijabin dan karami iya wuya su mami da Anty Mariya da kawayenau sai kai kawo suke ni kam guri guda na kame mai kyamarar sai daukata yake tamkar nice Amarya,ga masu Hotuna,Amira tace kai Iman kin tafi da imanin masu hoton nan sai ke suke dauka kafi n inyi magana Bilkisu tazo tace kai bafa wannan bace Amaryar ba kun ganta tayi maku kama da Amare?nan suka juya suna daukar ko ina haka taro ya tashi lfy ba tashin hankali,washe gari sister day da safe yayanmu ya aiko nazo dakinshi na same shi ya dubeni me kike yanzu?nace ba komai yace to abokaina ne na england yau zasu iso ina sonki shirya masu abinci kaloli masu dadi don gidan Nasir zan saukesu kamar nawa ake bukata?ko muje kasuwar tare in yaso sai ki duba abubuwan da zakiyi amfani dasu gaba daya a wajen girkin?nace to bari na sanar da mama yace shima bari yayi wanka,cikin riga da wando na material ruwan madara da filawoyi jajaye dan hijabina dan karami sai takalmi sai abinda ya kamata na siya da kulolin girkin da zan masu har da na sha ina tsaye jikin motarshi ya fito daki sai da ya shiga su Sa'a da Bikisu da Maryam kanwar anty Mimi dukkansu ni suka tsura ma ido na shige mukayi gaba,ba wani hira muka yi ba ya dai sa wakar tashi dakusan duk kullum sai naji ta a dakinshi tun ina jin haushin wakar har yanzu nima ina sonta kuma nama sai album din wakokin mata celine dion ina wakokin don sanyin muryarta,wayata ta soma kidan kuch kuch hota hai na kai hannu zan dauka sai naga yayanmu ya dafa wayar ya dauka ya duba sunan Amira ya gani sai ya mika min nayi ajiyar zuciya sannan na amsa hello,Amira yaya dai?tace kina ina ne?nace muna hanyar kasuwa ne menene?tace na sha kina gida ne na shigo,nace bana gida in na dawo zan shigo gidan muyi aikin abincin baki tace to sai kin dawo. Sayayya mai yawa mukayi komai nace biyu sai yace na dau uku,gidansu Amira ya saukeni ta fito muka kwashe kayan,mun shirya abinci kala kala dana sha a sabbabin kulolin da muka siya muka shirya muna gamawa muka yi wanka na shiga kenan don nasa kaya yayanmu ya kira ni nazo yace kun gama?nace eh yace to ga musa dryva nan ya kaiki gidan Nasir ni kuma zamuje mu dibo su sauran minti biyar su shigo KD daga Lagos nace to,banyi wani shafe shafe ba nasa atamfa charas babba riga da siket ne dinkin shot play sai karamin gyale muka jera abincin nace Amira tazo muje tace aah ba ruwana da wannan yayan naku zai iya kado ni,nayi dariya nace shi kenan,nayi kusan minti talatin da zuwa sannan suka iso cikin harshen turanci suke magana nima na gaishesu cikin yaren nasara,Nasir yace ko inyiwa Mami waya ne tazo ta taya yarinyar ne?ya harareshi yace ban ce ba nikuma bayan sun zauna na gabatar masu da kayan ciye ciye da shaye shaye na gida dana company,wani shima bakin fata ne duk sanda na dubeshi sai mun hada ido dashi haushinsa ya kamani can kuma wani daga cikinsu yace Maska wannan itace Amaryar?yace a'a ita kanwata ce sai yace to zaka bani kanwarka?don tana da kalar asalin yan Nigeria yayanmu ya daure yace baya son wannan maganar bakin fatar dake kallona yace Maska ni zaka ba wannan mai kyaun din,don bana neman wata kasani,y hiayanmu bai kuma magana ba ya dubi Nasir yace bari na kaita gida na dawo,ya dubeni tashi muje na dube su nayi musu sallama, a mota yace in zaki fita ki daina shafe shafen nan na dubeahi nace ban shafa komi ba sai hoda,yace duk inda kikaje sai ance mun ana sonki ni kuma krt nake son kiyi ni dai nayi shiru yace kin tuna alkawarin da kikayi min ko?nace eh yace to kar ki yarda ki yi wasa da cika alkawari kin jini?nace e.A kurarren lokaci muka isa gun Sisters day Angoma bai zoba na tambayi Mami tace min yayi ma Amarya waya yana tare da baki muka zauna,nanma ba laifi bikin yayi kyau ranar ne akayi sa lalle banje ba, washe gari lunching a hamdala hotel za'ayi sanye nake cikin dogayen riga na shiga dakin yaynmu dan amsa kkranshi yace zauna na zauna a kasan carpet ya dubeni yace yau wane kayan zakisa,nace anko zamu sa yace to kar kisashi kisa sky blue din less din nan,na gama kanki ba tare da wani tunani ba na zame dan kwalin kaina kananan kitso ne 2step mai zigzag,yace to rufe ki shirya sosai ya dubi dakinshi yace ga kayana nan dukkan abinda kike so ki dauka na baki ki dauka nayi shiru na sunkuyar da kaina ya taso ya tsugunna gabana Aminatu ya kira ni a hankali cikin sanyin nan nashi na dube shi nidai da zance frame din nan nake so amma sai nayi shiru ya kuma kiran sunana na dube shi yace kina son Fridge?nace a'a TV fa?nace a'a,Radio fa?nace a'a yace to me kike so?na dubi hotonshi yana sanye da farin JC mai ratsin ja yayi tsalle zai kama kwallo ina balain son hoton ya dube ni shi kike so?na kada kai alamar eh bayan shi fa?nace ba komai ya mike ya ciro min hoton ya hado da wani shima mai kyau cikin jan JC kan kujera ya zauna sannan ya kama hannuna gabana ya fadi naji wani yarr a jikina ya rike yatsuna da zoben nan yake jiki wanda ya kawo min tsaraba kar ki rabu da wannan zoben komin wuya kinji? kasa magana nayi,yace wannan lallan ya min kyau waya miki?kafin na bashi amsa sai akayi sallama gami da shigowa gaba daya tsoro ya kamani da na juya naga Anty Mimi itama tsoron ne da mamaki a kan fuskarta na dubi yayanmu shi ko namijin duniya ko a jikinshi ya saki hannuna yace Mimi lfy na ganki yanzu?ta juya da gudu tana kuka yace me aka mata oho,yayi tambaya ya ba kansa amsa na mike da hotuna sai nayi gidan su Amira ban koma cikin gida ba ita ko Anty Mimi dakin Haj Yaya ta nufa da kukanta da komai,ta sanar da hajiyan komai haj yaya ta cika tamkar zata fashe ta dubi mimi tace kince yana rike da hannunta?Mimi tace sai kallon juna suke yi,haj yay tace lallai ma yaron nan jiya fa haka su Bilkisu suka ce min sun ga ya shiga mota da ita banyi maganin abun ba bari in kirashi,ta soma daddana waya tana fadin kannanshi bai taba sa su a motarshi ba sai wannan bakar mummunar yarinyar,ta soma magana kazo yanzun nan ta kashe wayar taci gaba da fadin sun asirceshi shima kamar babanshi na shiga uku ni Murja tsakanina da Habiba Allah ya isa ban yafe mata ba,yayanmu yayi sallama ya shiga dakin tana zaune kan kujera sai cika takeyi ya ballama Mimi harara sannan ya shiga ya zauna,duban wulakanci ta mishi sannnan tace yanzu kai saboda Allah me ke tsakaninka da yarinyar nan Iman yar karama da ita shine ta ke juyaka ta shanye ka nan gaba ma kila kace aurenta ma zakayi ko?ya sunkuyar da kai kasa bai amsa mata ba tace jiya ina kukaje?yace Haj waya kawo maki wadannan kananan surutan ne?nifa mutunci ne tsakanina da yarinyar nan tana hidima dani sosai don Allah haj ki daina jin zancan mutane yarinyar nan ita da uwarta suna da kirki kum....ta katse shi an baka kaci a cikin abinci ba dole kace haka ba na gaya ma ka koyaya ni zan mummunan saba maka ta nuna Mimi wannan ita menene laifinta?da zaka sasu a kasuwa sai kowa ya riga zabar Mimi kuma zanyi maganin agola a gidan nan wayarta tayi kara ta dauka ta duba ka dai ji na gaya maka ga babanku nan ma ya dawo shi ne yake kira bari naje,ta dube shi sai ka bata hakuri ai,tana fita ya galla ma Mimi harara sannan yace ke ma zan yi maganinki bakina hada ni da uwata ba ya mike ya zo kusa da ita wllh wllh in kika kuma hada ni da ita sai na fasa auran nan ke ko an daura sai na sakeki akan Iman, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yayi waje ya barta cikin mamaki da tsoro koda haj yaya ta dawo bata sanar da ita yanda suka yi ba ta dai ce ya bata hakuri ya tafi haj yaya tace ai nasan zai rabu da yarinyar nan sai ma kin shiga gidanshi Mimi tace haj ce min yayi fa in anyi bikinmu da sati biyu zai tafi england ya barni dama yaje dani don akwai masu mata a can,haj yaya tace gsky haka za'ayi sai dai za'a yi fama kafin ya yarda na ma huta hankalina ma ya kwanta baya kusa bare in ta fargaba kar yace yana son yar iskar 'yar can shima Kabiru zuwa zanyi na matsa mishi yayi auran tunda yana aikinshi dama jira nake yayanshi yayi tukunna cikin farin ciki Mimi ta fita ta san da haj yaya ta mishi magana shi kenan zai yarda su tafi tare. Da yamma na dawo daga gidansu Amira in da ta nuna min gwaggwaro ba tace don Allah kisa yammata kowa zai sa mu uku iri daya ?ami ta sai mana kalar namu daban ne ma nace to in ya shiga da kayana zansa danni ba anko zan sa ba tace me zaki sa?nace kayan gun yayanmu,a falonmu su hajiyar maska ce da sauran dangin alhj wadanda suka zo biki na rusuna na gaishe su sannan na shiga dakinmu sai da naci abinci sama sama sannan nayi wanka ina gaban madubi ina shafe shafe waya tayi kara na dauka ga mamakina sai naga lambar yayanmu ina da lambar amma bai taba kirana ba nima ko da wasa ban kirashi ba nasa kunnena ban ce komai ba inaji yace hello?sannan yace kina jina?a kasalance nace umm da wani abu nake ji yana fita daga wayar zuwa cikin kunnena yana raba ma jikina qani sako ne mai wuyar fassara yace me kike yi yanzun?na samu kaina da rike murya nace mashi ina shafa mai ne yace to kiyi kwaliya da kyau amma kar ki kula ko wanne saurayi kinjini?nace eh dukkanmu muka yi shiru bai kashe wayar ba nima haka can yace to sai mun hadu a can ya kashe na rungume wayar a kirjina ina jin tamkar shi na rungume,soyayya kenan ban taba tunanin akwai ranar da zata zo na shiga irin wannan halin ba sai gashi yanzu ina ta nutso cikin kogin son wanda bai ma san inayi ba,Allah kenan shi ne mai iya sanya fari ya koma baki.Kwaliya sosai nayi tamkar ni ce amarya nasa lesa din da ya umarceni nasa ya shiga da gwagwaron sai takalmi da jaka su ma kalan gwagwaron ne ni kaina dana dubi madubi sai da naji tsoro don kyan da nayi wayar Mami na kira tace min tana can hotel din na kira Amira tace min tana mota ne taga an gama kwashe mutane shine taga kabir ta tambayeshi ni shine yace kamar ya ganni a can ace mata ina gida ko fitowa banyi ba na mike na cire gwagwaron na rike na fito falo dankwalin na rufa kaina nayiwa mama sallama tace kai kin ko yi kyau,iman yau dai ba zancan hijabi kenan?nayi murmushi na fita ina isa harabar ajiye motoci duk an gama kwashe mutane sai kawayen amarya na nufi waje da nufin in hau mashin sai ga yaynmu shi da Nasir da wani abokinshi ya dubeni yana daga cikin yayi min alamar in tsaya da ido na ko tsaya ya fito ya kirani gefe yace kin ganki kuwa?kinyi kyau fa nace nagode yace to ya baki tafi ba?nace ai yanzun na fito shine naga an watse sai kawayen Amarya yace kina da kudin liki ne?nace ina dasu amma ba sababbi bane yace ok bari mu shiga ki amsa na bishi abokanshi na zaune a falonshi ya shige uwar dakinshi jim kadan yace Iman na ce na'am yace zo na shiga da sallam ya amsa sannan yace shigo mana kin tsaya nan kudi na gani a kan katifarshi ga yan ashirin ga yan hamsin har zuwa dari biyar,ya dubeni dauka wanda kikeso na sa hannu zan dauki ashirin ya dafe hannuna sannan yace ki dau wannan yan dari biyu ne,ya samin a tafin hannuna na gode na fada ina kallon idonshi,Man din akwai sirrin kyau mai birgewa muka fito falo ismail ya dubeni yace kai maska wannnan yarinyar ko dai kai kake ma kanka farauta ne? Sai naga yayi kicin kicin da fuska ya harari Ismail yace ku kun cika yarda girma ban da yarda girma menene na cewa inayi ma kaina farauta? bani son haka,jikina yayi sanyi zan fita yayanmu ki jirani zan sa akaiki Ina tsaye a bakin gate yazo ya dubeni menene kike bata ranki?na dubeshi ba komai ya juya ya kira musa musa direba yazo yace ina zaka na ganka da key a hannu?yace haj ce ta aikeni gidan haj laure,yace to ka kai Iman gurin party nan hotel yace to can na sami su Mami da kowa yana ta hidimominsa inata neman Amira sai can ita ce ma taganni muka zauna kujerun gaba na ce uwar sauri shine kika wani taho Amira tace kar kiga laifina yayanku Kabir shi yace min kina nan,nace don ni ce zan shirya gun ba?dole na riga kowa zuwa yana sani don dai ya dauke ki ne ta ce anji ki min shiru mu bar zancan.Biyar saura ango da amarya suka zo less dina na gida irinshi amarya tasa nace gara da na sa wannan din na dubi ango sanye yake da wata dakakiyar shadda ruwan sararin samaniya tamkar less din jikina ina cikin mamaki Amira tace kunyi anko ke da ango sanya gwagwaron ki nasa na gyara cikin raina nace kila ma don muyi anko ne yasa yace nasa,mai gabatarwa ya fito yana kiran kawayen Amarya bayan bude taro da addua suma abokan ango an kirasu yawanci duk turawa ne,sai kadan,Nasir da Mami aka hadashi tako sha harara gurin ango can aka kira sunana Iman idris zata ba amarya shawara ba don na iya turanci ba da nasha kunya Amarya ta cika don haushi niko duk na tsargu Amira tace don Allah tashi kije mana nace Amira bansan me zance ba dadai tun a gida ne aka sanar dani da na rubuta ana ta kiran suna na na dubi yayanmu yamin kar da ido fuskarshi ba walwala na mike daidai lokacinda mai gabatarwa yace ko bata nan ne?Iman Idris a hankali nake tafiya har naje kan abinda aka tanada don hawan mai magana da sallama na soma sannan nayi wa Annabi salati kafin na soma bata shawara akan zaman aure na kawo ayoyi da hadisai wadanda sukayi magana akan zaman auren da hakkokin auran kansu. Dana gama na sha tafi gun mutane na koma na zauna haka akayi ta gabatar da komai har zuwa sanda zasu ciyar da juna don kar in gani na dauko wayata ina ta danne danne zuciyata kuwa sai zugi takeyi,can na mike zan fita Amira tace ina zaki je gashi shalele na ta waka yanxun za a soma rawa dole na tsaya suna shiga yayanmu a tsaye yake baya rawa amma Amarya har da juyi nace wawiya ba kunya ba jan aji nice na fara liki ina ta zuba musu kudi cikin dauriya yayanmu ya juyo ya fara zuba min na juya zan fita ya rike min riga amma ba wanda zai kula don ta gefe ya rike ya dan matso kusa da kunnena kar ki fita yanzun ki min rawa din dan ban iya rawa ba nima ai ban iyaba Amarya ranta ya baci ta dubeni ashe ita ta kula da abin da mukeyi guri ya kaure liki wasu sun sha nice amaryar ne?ko ra'ayi ne?oho sai ni suke ma liki gudun rikici yasa na fita abina na koma na zauna,Amira tace yar gori a ina kika sami kudi kike bari dasu?nace shi ya bani dubu ashirin kuma na like musu abinsu Amira tace duka?nace a'a Mami ta iso gunmu taja hannuna zo muje ki dan taka nace bana rawa fa ta dubi Amira tace duk yanda suke da yayanmu wai bazata yi rawa a bakinshi ba Amira tace ai ta basu shawara yanda zasu zauna da juna,Mami tace yauwa na tuna dazun me yace miki da naga ya wani karkato dai da kunnank?nace ba zan fada ba Amira tace ashe kin lura kema?sunyi kyau tamkar itace amaryar nace kun cika sharri Mami tace to zamuje kiga hitunanku da masu hoto sukayi suna ta saidawa a waje mu uku muka fita wajen hall din gsky mami ga hotunanmu nan nida yayanmu wani tare mukayi wani ni kadai wani shi kadai an barbaza wanda yafi birgeni wanda mukayi da yayanmu ya dan karkato yana min magana fuskarshi a sake ni kuma ina murmushi fuskata tayi fayau idanuwana sunyi haske kitsona ya zuba a kafaduna Duk masu daukar hoton nan sai da na bisu na saye hotunanmu sannan muka koma ciki nace kije kunnan gidado tace a ina zaki ganshi ta fita kiran,ni kadai na zauna can ji an min sallama cikin hausa da bata goge ba yace na zauna?nace zauna mana ya zauna nadan dube ahi kamar na so na gane fuskarshi yace baki ganeni ba?nace ban ganeka ba yace abokin Maska da muka zo daga England nace ok na ganeka,yaci gaba da cewa ina sonki amma Maska yace krt zakiyi? nace haka ne yace toh zan jiraki mana nace kayi hakuri dan zan dade ban gama ba,koyaushe zan jiraki,muna cikin hirar ne can idona ya kai Ango da Amarya harara ya sakar min na dauke kaina daga duban gunshi a raina nace kai gara kai ka kama taka naci gaba da hirata jim kadan wayata tayi kara na duba sai naga lambar yayanmu da sauri na dubi gurin da yake bashi nan sai na dauka nace hello ya katseni ki sameni a wajen hall din nan gurin wayoyin nan ta kofar baya na fita da sauri can bayan wasu furanni na ganshi na isa cikin fargaba ya dubeni fuskarahi ba annuri yace me gayen nan yace miki?nayi shiru ba zaki gaya min ba?ya daka min tsawa jikina yana rawa nace yace ne yana sona,da sauri ya dubeni sonki?.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na gyada kai alamar eh yace oh my God bana sanar dashi krt zakiyi ba?to naji me ke kikace mishi?nace nima haka nace mishi ya dunkule hannunshi ya naushi dayan hannun sannan ya dinga kai kawo a filin gun mamakin shiga damuwar dayayi na tsaya yi a raina nace ya bar amaryarshi yana yin abin da bai dameahi ba,kamar ya san tunanin da nakeyi sai naji ya dawo gabana daf dani yasa hannuwanshi ya rike kafaduna yace kar kiga na shiga wannan halin kiyi tunanin inayin shishigi ne a cikin abinda bai shafeni ba,no yin karatunki shine kwanciyar hankalina kuma muddin na yarda wannan dan iskan ya soma cusa maki ra'ayin sonshi to zai min illa domin nasan Adam ba sanin yau ba yana da sa'a a rayuwarshi zai yi wuya ya nemi abu bai samu ba tamkar ni yake,so bazan yarda da huldarku ba,nayi shiru ina tunanin wannan iko na yayanmu tunda yace tamkar shi yake sai ma naji ya burgeni na dubi yayanmu nace to in dai zai bari na gama karatuna why not na aureshi in kasan yana da hali mai.....kafin na karasa sai saukar mari naji cikin firgici na dube shi shima ni yake kallo ranshi a bace,hawaye ya zubo min a kan fuskata yace kina hauka ne?kike kiran wani ya aureki?sai kuma naga yayi shiru ya juya min baya,Aminatu yaja sunan kafin na amsa sai ya juyo da sauri ya zo guna ba zato sai gani nayi ya rungume ni tsam tsam a jikinshi gabana yana faduwa jikina na kyarma amma na kasa kwacewa ,nama kasa kokarin kwacewar gwaggwarona kaina ya fadi gashina ya bayyana a waje kitsona ya sauka a kan kafaduna ni kam tamkar an jona ni a lantarki haka nake jina,cikin sanyin murya yake magana,Amina bana son ki saurari Adams zaiyi ma rayuwata illah nafi son sai kin gama karatu ne kafin ayi maganar auranki,ki fahimceni ba ina nufin hanaki aure bane a'a ina son kiyi krt ne,wani haushi naji ya kamani domin a lokacin nayi zaton zai ce min yana sona ne,yanda naga yayi mugun shiga damuwa sannan ya kamani ya wani rungume yana faman ajiyar zuciya tamkar jinjirin daya kwana uku ba tare da ya sha nonon uwarshi ba ina fama da sonshi tamkar na mutu shi kuma ya nan yayi aurenshi sannan ya zo ya wani rungumeni yana min maganar banza nasoma kici kicin kwacewa ya girgiza ni yace come on my sister ki.....kafin ya karasa maganar da zaiyi sai jin salati mukayi akanmu,cikin tsananin tsoro na juya su dayawa daga cikinsu akwai kannanshi da Amarya da Haj Laure uwar Amarya da wasu daga cikin danginsu,duk tsoro ya kamani,Amarya tasa kuka na dubeshi shi kuma ko ajikinshi duban su ma yake yi na tattare zani zan gudu sai naji ya sa hannu ya riko ni.......Masha Allahu Alhamdulillah, mun Kammala littafi na daya Mu hadu a littafi na biyu jinjina agareki HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Share DOCUMENT CREATED BY ZAHARADEEN SHOMAR WHATSAPP ,,08168575100