Ajininsa yake 2-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:39 PM, 11-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Gaba daya tsarguwa ta kama shi, dole ya sake kallonta, ya kirkiro murmushin karfin hali yace " an dawo lafiya? tace "lafiya lau" shiru ya sake yi yana tunanin me kuma zai sake cewa? ji yayi tace " Ya wasan Polo? ya dan dube ta ya amsa, " muna dan tabawa." Abba ya ce yayi sabon Jah- Jah, shine ya-ce har Yakubu ya tsufa ne? yayi dan Murmushi yace ai komai lokaci ne, mu ma wata rana daina yayin mu za'a yi." ta ce "Gaskiya ne. To ya antin tawa? Ya amsa "Tana gaishe ki." "Ina amssawa." Tayi shiru kamar yadda shima bai kara cewa komai ba. Wayar sa ta hau ruri, ya jawo ta ya duba. Nan da nan ya dauka, "Hurul aini." Da sauri ta daga ido ta dube shi yayin da ya ci gaba da fadi" An dawo school din ne? Ta ce na dawo, to yaya? Ya-ce "Muna tare da ita." "Ban yarda ba". Ya ce kin san ba zan miki karya ba. Shi yasa ma tun jiyan na kira ki na gaya miki." Ta ce in da gaske ne, ban ita mu gaisa.' Kai tsaye ya dubi Nusaiba, ko dama shi take kallo, kuma sai taji kamar kishi zai kamata. Mika mata wayan yayi ya ce "ga Zarah." Tana yar fara'a ta amsa,............ Tayi mata sallama, haka kawai ita ma taji kishin ya dirar mata, Ta daure ta amsa sallamar, Nusaiba tace 'Ya school? Ta amsa, "Lafiya lau, Kin ga Maigidan namu ko? Tayi dan Murmushi, Ta ce "Na gan shi" Ta ce Zaki sha surutu har sai kin gaji, ta dan saci kallonsa, don ita bata ji surutun ba, Hankalinshi bashi kanta, shi dayar wayar ma yake faman latsawa, tana kallonsa ta ce "Yarima kam bakunta na damunsa." Shi yasa ya dubeta ya tabbatar da shi su ke, Ta janye idonta a hankali, tana mai bayyanar da murmushi. Shi kuwa takaici ne ya tokare wuyansa. " Wane shisshigi kuma Zarah ke yi? ya tambayi kansa, wani asirtaccen tsaki yayi, ya dauke kai, Nusaiba da Zarah kam hira ce ke neman gocewa, basu ma san lokacin da zukatansu suka saba da juna ba, kawai ji suke sun amince da juna har suna dokin ganin junan su.Domin a halin yanzu Nusaiba ke fadin,"To yaushe za ki zo? Kodayake ni ce k'arama, ni ya kamata in fara zuwa." Zarah ta ce,"Yanzu na ji magana, to yaushe za ki zo? Ta ce,"Ki saurare ni zuwa karshen satin nan, ki turo min lambarki, ni ma zan turo tawa." Ta amsa, "O.K, zan turo miki. Bari in bar ki da ogan, kar in yi laifi." Tana dariya, ta ce,"Tsaya in mika masa ku yi sallama." Haushi Zarah ta ba shi, don haka tana mika masa wayar, ya kashe, ya zira ta gaban aljihu. Kashewa tayi?" Ta tambaya. Ya ce,"Uhm......... Ta ce,"Anti na kenan. Da ji za ta yi kirki." Ya ce ,"Sosai take da kirki kuma tana da halaye masu yawa wadanda kullum suke kara min son ta. Iyayen ta talakawa ne iri na. Sai dai Allah yayi mata baiwar da bai yi wa kowane mahaluki ba. ZARAH, sunanta kadai ya kan sanya ni nishadi, ballantana ita kan ta. Kar fa ki ji wani abu a rai, ba wai ina fad'i bane, saboda wata manufa. No, ina son ki sani ne, ba kowace mace zata yi abin da Zarah tayi ba. Tun muna yara mu ke tare, sai da biki ya zo gaf, sannan aka ce ga wata a hada 2, ina nufin kishiya, ko ke ce yaya za ki ji? Gaba daya jikin ta yayi la'asar, ba don komai ba, sai don tausayin Zarah d maganganun Naseer suka sanya ta. A take nan ta ji kaunar Zarah na shiga jikin ta. Tabbas Zarah tayi bajinta, kuma abar tafa mata ce. Ta sauke numfashi. "Gaskiya ne, ko ni ta burge ni, sannan bayanin ka a yanzu ya sanya min kaunar ta cikin raina. Hakuri babban Jari ne, kuma ita rayuwar duniya mai karewa ce, shi yasa ni ma ban ga dalilin daukan ta da zafi ba. Tsakanin mai kudi da talaka kuwa, wata hikima ce irin ta Ubangiji. Ya kuma halicce mu ne saboda mu taimakawa junan mu. Da ya so, da gaba daya masu kudi zai hallice mu. Haka ku ma daya ga dama, da sai ya aje mu dukkanmu a talakawa. Mai hankali idan ya natsu, zai gane dimbin dalilan da su ka sa Ubangiji ya bambance ababen halitarsa. Saboda haka kar ka yi tunanin komai akan zama na tare da Zaraha, wai don ni na fito gidan wadata. Insha-Allahu za ka same ni da irin halayen da ka ke so." Yayi dan shiru, tunanin sa Nusaiba na da kalamai, sai dai ba su wani girgiza shi ba, saboda ya saba jin kyawawan lafuza a wajen Zarar sa A takaice ma dai ji yayi kamar tana son tayi gasa da Zarah, don ya ce ta ji yana yabon ta. Ya girgiza kai, ya ce,"Shi kenan." Ya duba agogon hannunsa, ya ci gaba,"Bari mu yi sallah ko? Karfe daya ta gota." Yana rufe baki, ana kwala kiran sallah. Ta mike ta ce,"Za ku shiga masallaci ne? Ya ce,"Sosai kuwa." Ta fice ta bar shi yana zancan zuci, "Ka ji 'ya da a dakin ki za mu yi sallar? Ya dan ja tsaki, sannan shi ma ya fita ta kofar da suka shigo. Ita kuwa wajen Sageer ta nufa, ta kira shi ya fito, ya iske Naseer a waje, suka tafi masallaci. Nusaiba na sallamewa sallar. Wayar ta ke ruri? Ta dauko ta, ta duba Kausar ce, ta dauka tasa wa kunnen ta,"Ban son wulakanci, ba za ki zo din bane? Ta ce,"Gaskiya zai yi wuya. Wallahi lakcas sun yi yawa yau. Ko wacce kuma na da muhinmanci da sai in tsero. Sorryy kwata, ki ce da Jah-Jah gaisuwa na ke.:" Ta dan ta6e baki, ta ce,"Ban fad'i." "Ai na ce sorry. Ke ma kin san sbd karatu ne kawai.." Ta ce,"Shi kenan, ni zan zo gobe, idan kin dawo ki kira ni." "O.K Matar Jah-Jah. Tana murmushi ta ce,"Kya ji da shi." Suka yi sallama. Kowa ya aje waya. Madubi ta nufa ta sake gyara fuskarta da daurin dan kwalinta, ta suri waya ta bar dakin. Mariya ta kira, ta tambaye ta maganar abinci, ta ce duk ta shirya su a can falon. Kai tsaye can ta wuce. Takalman su Naseer na kofar falon, don haka ta shiga da sallama. Duk suka amsa. Kai tsaye wajen abinci ta wuce ta bubbude kulolin, ta ce kowa ya bi abinda yake so. Sageer ta za6i Frie rice, shi kuwa dan gogon da kyar ya cusa lafiyyan (Coleslaw). Sun dan ta6a hira zuwa karfe 3, Naseer ya ce tafiya za su yi. Sageer ya ba su wuri su yi sallama. Tsawon minti 2, bai ce da ita komai ba, sai ta mike ta ce bari ta kawo masa sakon Zarah. Shi ma ya tashi ya ce ta same shi a mota. Suna tsaye jikin mota, ta fito da manyan jakunkunan leda guda 2, cike suke da kayan shafe-shafen mata. Ta mika wa Sageer ta ce,"Leda 1 Zarah, 1 ta amaryar ka, don ni ban yarda ba da ka ce babu ita. Dariya yake yana fadin me zan 6oye miki? Kin san Allah babu ita a halin yanzu sai an kammala karatu. Kin san taura 2 basa taunuwa a lokaci guda." Ta ce,"Gaskiya ne, to mun gode, amma ki rike wannan, tunda dai yanzu babu ita." Ta ce,"To lodawa Antina duka." Ya ce,"Lallai Zarah ta gode. Allah ya saka da alkhairi." Naseer ya dube ta tsakar ido, ya ce,"Kayan nan sun yi yawa da kin rage." Ta dan kada kai, ta ce,"Ba su yi ba, kuma ai Antina na ce akai ma wa ko? Ya ce,"Shi kenan ta gode. Sai wani lokaci." Ta ce,"Ni ma na gode, a gaida kowa da kowa. Za su ji." Ya fadi yana shiga mota. Tuni Sageer ke mazaunin direba. Ya tada mota. Mai gadi ya bude get, suka fice, sannan ta wuce gida." A falon sama ta iske Umminta. Gefen ta, ta zauna ta ce "Wash! Na gaji." Aikin me ki ka yi? Ta ce,"Haka kawai na ke jin kasala." Sun tafi ne? "Eh, sun tafi yanzu." Ta dan yi shiru, kafin ta ce," O.k." Ta dan dafa kan ta." Ko dai yunwa ki ke ji? Fuska yamutse ta amsa. "Wallahi kuwa. Don ko dan ruwa ban kurba ba." Ta ce,"To maza tashi ki je ki sami abinda za ki ci." Ta mike ta wuce, tana jan takalma, da gani ta gajin da gaske. Umminta tayi kasake, tana tunanin ya dace ace Naseer ya shigo ya gaishe ta. Da ta rasa dalili, sai ta watsar da zancan, ta kama abinda ke gaban ta. Sageer ya ja na dogon salati. Da sauri ya dube shi, "Menene? Ya ce," Zuwan duk bai da amfani." Da aka yi me? Ya ce,"Ka san tamkar a kan kaya na ke zaune cikin gidan nan, maimakon ka ce min mu je mu gaida Hajiya....... Shi ma salatin ya dauka ya dire,"Girman Allah na mance, abinka da ba sabun ba. Gaskiya ba'a kyauta ba. Kuma anyi abin kunya. Yanzu ka kira wayar Nusaiba, ka ce ta ba Hajiya hakuri, mantawa mu ka yi. Ai kowa yasan ajizani na Dan-Adam." Naseer ya ja tsaki,"Zancan banza. Ni ina da lambar ta ne? Ba ka amsa ba? Ya tambaya a firgice. Wani tsakin ya sake yi. Sageer ya hau fada.Ka na ta tsaki, wannan ai wulakanci ne, ka ma nuna zahiri ba ka damu da ita ba, ai ko da ba'a sai ka ce ta ba ka lambarta, tunda dama can zuwan ba don Allah ka yi shi ba! Amma wannan rashin mutuncin da me yayi kama? Ya balla masa harara, ya ce,"Don Allah ya ishe ka Malam. Ka fi ni jin zafin abin ne? Saboda me zan ki gaishe da Hajiya? Bayan kodayaushe na je gun Alhj, zan shiga wajen ta mu gaisa. Kawai mantawa na yi." Ya ce,"Ai saboda rashin daukan wannan zuwan da muhanimanci, duk shi ya kawo hakan." Eh, kai haka din ne, sai me? Kai da ka dauka da muhinmanci me yasa ba ka ce aje a gaishe ta ba? Yayi shiru ya ci gaba da kallon gaban sa. "Mts.......... Naseer yayi tsaki. Ka fein ya ce "Wallahi da gangan ka ke ba ni laifi. Ya dan dube shi, ya sassauta murya,"Yanzu saboda Allah Naseer ina abin kushewa a wajen yarinyar nan? Ya gyara zama sosai, ya ce,"Ni ka ji na kushe ta ne? Nusaiba tayi. Wallahi babu gatse a cikin magana ta, duk inda ake son mace, yarinyar nan ta kai wajen kuma har ga Allah ta wuce da aji na da ace haka kawai na gan ta a titi, babu yadda za'ayi in tunkare ta da maganar soyayya, saboda ba aji na bace. Saboda haka na ke son ka gane. Allah bai sa min son ta ba ne. To wa ya isa ya sanya min? Shi fa so gamuwar jini ne, kuma mu2m ya kan ji shi ne kawai cikin ran sa. Ka san Allah, har mu ka bar wajen nan, babu komai cikin raina, sai k'unci, to ina son yake anan? Sageer ya numfasa, tausayinsa ne ya kama shi, wannan murdaddan al'amari da me yayi kama? Ya kara kwantar da murya ya ce,"Sarai na fahimce ka Naseer, amma shawarar da zan ba ka, ita ce ka rinka yaki da zuciyar ka. Kullum ka rinka nuna mata rayuwa na iya sauyawa a kodayaushe. Domin ba ka san abinda Allah ya 6oye a cikin wannan aure ba. Please! Ni rikon ka na ke? Ya mirgina kai gefe, ya ce, "Na ji." Aiki da shi ba dole ba kenan? Ya dube shi ido warwaje,"Yau na ga ikon Allah! Abinda fa ke hada ni da kai kenan. Kai komai ayi shi dole. Na ce na ji, sai ka bar shi a anan jin. Shine za ka bude min ido? Ya juya yana guntun murmushi, "Kai kai, Sageer Tela kenan.!."Allah yasa su Baba su samo maka mata a kauye." To menene? Ya ce, "Ba komai. Har na hango mu ne mun je tadi, ta ci uban jan baki da gaxar ga uwar dammara." Yayi 'yar dariya, ya ce,"Duk babu komai, a hankali zan canza ta. Kai ba ma za ka ta6a gane ta ba, idan ta waye." Ya jingina da kujera ido rufe, yana fad'in ,"Ya Allah ka amsa. Allahumma amin." Sageer ya ce,"Please stop that nonsense, ba shine a gaban mu ba. Ka yi kokari ka kar6i lambar Nusaiba, ka wanke kan ka." Ya bude ido yana duban sa a karkace, bai ce komai ba, haka shi ma Sageer bai k'ara cewa uffan ba. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Ba k'aramin farin ciki Umma tayi ba, lkcn da su Naseer suka dawo. Shi da kansa yake gaya mata irin kayayyakin da Nusaiban ta bayar a kawo wa Zarah." Ba ta ma rude ba, sai da Sageer ke gaya mata kyautar gida da sabuwar mota inji Alhj." Ta tallafe ha6a ta ce,"Dole mu je Kaduna godiya, bari Malam ya dawo. Oh ni 'ya su. Allah ka k'ara had'a mu da masoyan mu." Ganin Umma na ta murna tana k'ara masa takaici, shi yasa ya ce zai k'arasa gidan su Zarah ya kai ma ta sakon ta. Sageer ya sallame ta, suka fito tana ta sa albarka. Gida ya fara aje shi, sannan ya juya akalar motar sa zuwa gidan su Zarah!.Yana tafe zuciya na masa saka iri-iri, tana aibanta masa auran Nusaiba. Tana nuna masa Zarah fa kallon sa kawai take yi. Allah kadai ya san abinda ke cikin ran sa. Watakila ma yana so gulma ce kawai. Nan da nan ran sa ya shiga kuna da kiyayyar Nusaiba ta tokare masa zuciya. Dole ya taka birki ya kashe mota, ya jingina da kujera ya runtse ido ya na kiran, "Inna-lillahi"Wa-Inna- ilaihir-raji'un! A zahiri ya nuna masifa ce babba ta same shi, domin anyi masa dabaibayi ta k'oina, an daure shi da jijjiyoyin jikin sa. Tasbihin da yake wa Allah, shi ya taimake shi zuciyarsa ta sassauto ta daina bugawa. Ya bude ido jajur! Ya numfasa, sannan yayi hucin zafi. Ya kada kai, yayin da yake tayar da mota. A haka dai ya lalla6o kofar gidan su Zarah. Nan ma ya jima zaune kafin ya dauko sakon ta ya fito, ya kulle mota ya shige gidan. (DUHUN KAI, GABA DA KISHIYA).Shine sunan littafin da Zarah ke karantawa a tsakar gida, wanda Ustaz Abubuakar Abbas Rjiyar Lemu ya rubuta. Sallamar Naseer yasa ta cira kai, ta dube shi tana amsawa tare da wani kayataccan murmushi. "'Yan Kaduna. Har ka yi me? Take zuciyar sa ta wadata da farin ciki. Amma fuskar sa, ba walwala sosai, ya zube ledoji gabanta ya ce,"Na dawo. Ina Inna?"Ta ce,"Bata dan jin dadi ne, shine ta kwanta, ina jin ma barci ne ya kwasheta." "Ya ce, "Assha-assha, ta sha magani? Ta sha. To ya hanya, ya aka baro amarya? Ya kara kirne fuska ya ce, "Tana gaishe ki. Wannan kayan ma sakon ki ne, wai a kawo miki." Ya wuce dauko kujera, ya bar ta nan tana bubbude ledojin. Ta wangame baki cike da mamaki, ta dube shi yayin da yake zaune bisa kujerar yana fuskantar ta, ta ce,"Wadannan kaya, yayana ai sun yi yawa." Ya ce." Ah to, ai dole a baki kaya da yawa, tunda an cuce ki. Abin ba siyasa ba ce." Ta dan daure fuska, ta ce "An cuce ni fa ka ce? Haba yayana bai kamata ka fadi haka ba, ina laifin mai son ka? Ya ce,"Babu ai ke ba za ki gane wayon ba. Wai ni ma ina zuwa Alhjn ke gaya min zai ban gida a Hanwa da sabuwar mota. Duk kallon su na ke, me ya sa da can bai ba ni ba? Kin ga ya nuna min ginin da na daddage na yi, ya raina shi kenan. Saboda haka ki karbi duk abinda su ka ba ki, ki ci banza, ni Naseer na ki ne har abada, ruwa da iska, babu mai raba mu, balle karfin dukiya. Tayi zuru tallafe da ha6a, tana kallon sa ya kai aya. Idanuwan ta suka dan jirkita, na rashin jin dadin maganan. Ta dan kada kai, ta ce,"N kuwa yayana ban ta6a zaton ka na da irin wannan tunanin ba akan mutane. Zato? Zunubi ne ko ya tabbata gaskiya inji Manzon Allah (S.W.A). Saboda haka na ke shawarta ka, da ka daina wannan zargin a ran ka. Komai za ka yi, ka yi shi don Allah, hakan shine cikar mummuni. Na san ka na kaunata............Yayana ni ma kuma ina tare da kai." Ya sauke numfashi ya ce,"Ba kaunar ki kawai na ke yi ba, son ki na ke mai tsanani, irin wanda ban jin sa ga ko wace 'ya mace. Na je Kaduna na ga Nusaiba kuma ina mai tabbatar miki bata da makusa, amma ko alama ban jin son ta cikin raina ba. Na san ba dole bane ki yarda da abinda na ke fada, sai dai ya zama dole in gaya miki, anyi min fin karfi. Anyi min tilas, ancusa ra'ayin da har abada ba shi cikin tsari na. Gaba daya an rusa ginin da na tsara zuciya ta, wanda bai wuce son da na ke miki ba, in zauna da ke cikin gidan da wasu ke rainawa. Saboda haka kar ki ga laifi na akan duk abinda na fadi, bacin rai ne." Ta ce,"Duk na ji, kuma na tabbata idan za mu kwana anan, ba zan ta6a kada kai ba, don ka fi ni baki. Amma ina son in roke ka arziki, saboda girman Allah, ka yi min alkawari za ka rike ni da Nusaiba a matsayin 'yan uwa daya a muslunci? Shiru yayi, yana kallon ta sama da kasa. Ta sake fadin,"Yayana........."Kar ki hada ni da addini. Ki tauye ni Malama! Yayi saurin taran numfashin ta, don haka ta bi shi da kallo." Gaskiya na fada, kin san na fi ki sanin 'yar uwa ta ce a muslunci. Ubangiji kuma duk ya fi mu sani, shi yake sanya kauna da soyayya, to bai sa min ta, sai yaya? Ta dan yi jim! Tana masa kallon mmk kafin ta k'ara kwantar da murya ta ce,"Ni kuwa yayana ganin na ke duk zance ka ke yi, a hankali za ka so ta." To fa! Ta tsokano tsuliyar dodo. Mintoci barkatai ya kwashe yana kallonta kawai, da gani, ta san ta ta6o shi, don haka ta sunkuyar da kai ta sake fadin,"Allah ya huci zuciya yayana." Ji tayi kawai ya shura takalman sa, ya wuce. Ta bi shi da kallo har ya fice. Ta kama baki tana sallami,"Yayana kamar kuturu? Nan da nan zuciya iya wuya. Dama ya lafiyar kura? Da anyi magana, ya tashi yayi waje, ai za mu sha fama, gara in sami mai taya ni." Ta shiga fiddo kaya daga leda, kaya ne 'yan waje. In banda setin kayan Nivea da Naseer ke siyo mata, babu wanda ta ta6a gani cikin su. Turare kam sai ta gaji da fesawa. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Nusaiba kwance bisa gadon ta shiru, ta rasa abin da take tunani. Ta dubi agogo karfe 5 daidai, nan da nan tayi tunanin yakamata ta tambayi su Naseer, ya suka isa gida? A lokacin guda wani sakon ya sake zuwa kwalkwarta, Ashe, ba mu yi musayar lamba ba. Tayi wuf, ta tashi zaune,"Yaya aka yi haka? Ta tambayi kan ta. Abin ya bata mamaki kwarai, saboda shi ya bata lambar Zarah, tayi amfani da ita ta aika mata da ta ta lambar. Ta kada kai tana dan murmushi, kafin ta ce,"Ban ma san wanda ya fi shirme ba tsakanin ni da shi." Wayar ta dauka gefen filo ta nemo Zarah. Wayar na jikin ta a lokacin da take ta ba ido abinci, ta shafa wancan mai, ta goge (Lotion) ta fesa turare. Kukan Wayar ta ji a jikinta, ta daga da sauri ta dauka, ta dubi lamba. Nan da nan ta dauka, " Hello! Hello Antina." Ta ce,"Wallahi ban so ki ka kira wayar nan ba yanzu, domin na baza sakon ki ne ina ta gani, jira na ke in gama, sannan in kira, in yi godiya." Tayi dan murmushi ta ce,"Antina kenan ashe har sun iso? Ai kuwa sun dawo tun dazu, yanzun nan ogan ya bar nan. Ta ce,"Ba ki san wani abu ba. Ashe ba mu amshi lambar juna ba, ni ban tuna ba, sai yanzu da na ke son inji yaya suka je gida? Shi yasa ma na kira ki, ki ba ni lambar in masa gori." Mamaki ya kashe ta, ta ce,"Ta6d'i, ai kuwa abinda ya fi gori ma ki yi masa, ni ma zan taya ki." Ta ce,"Na ko gode miki." Ta ce,"Na ga sako, gaskiya amarya kayan sun yi yawa, har yanzu kallon su na ke yi." A'a Wallahi bakomai. To na gode. Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa,"Amin, sai kin sake ji na. A gaida mutan gidan." Za su ji, na gode." Kowa ya kashe wayar. Take nan Zarah ta tura mata lambar Naseer. Tayi shiru tana mamakinsa, domin tuni ta gano manufar sa. Ta numfasa ta ce,"Abinda yayana ke yi sam-sam ba shi da amfani." Ta hade kaya cikin ledojin su ta kwashe ta shige da su daki. Inna na ta barci, ta aje gefe kafin ta tashi. Riginginen da Naseer yayi bisa gadon dake dakin barcin sa, babu abinda yake tunani, illa kalmar da Zarah ta gaya masa. Ba karamin kona masa rai tayi ba, haka kuma yake mata fassara kala- kala. Ko shakka babu, abinda yake zato, ya tabbata gaskiya. Zarah kallonsa kawai take yi. Rashin sanin yadda zai yi, ya wanke kan sa shi yasa shi cikin damuwa tare da k'ara tsanar auran sa da Nusaiba. Wayarsa da ke ta faman ruri, bai sami daga ta ba har ta katse, ta sake dauka. Sannan ya ja dogon tsaki, yasa hannu ya lalubo ta a aljihun gefen rigar sa. Kawai O.K ya dannan, ya kanga wa kunnansa, "Hello! Ya fadi murya dakushe. Ta ce, "Hello, Nusaiba ce." "Wuf ya tashi zaune, shiru yayi, yana tambayar kan sa, ina ta samo lambar sa? "Hello! Ya sake fadi ya ce. "Hello, ya ki ke? Ta amsa, "Kalau. Kawai na kira ne inji ya ku ka iso? Ya ce,"Lafiya, na gode." Koda yake lambar ma sai da na roka. Ban cancanci samun ta ba ko? Ya kara 6ata rai, kamar ya amsa da eh. Abban sa kadai yake dubuwa,"Ya dan lumshe ido, ya bud'e ya ce,"Ba haka bane, amma ba za ki gane ba. So ki bar shi a mantuwa kawai.". Ta ce,"Na yarda, ai kowa na mantuwa, sai dai wani lkcn akwai rashin kulawa." Jin za ta gano shi, yasa yayi mata dabara ya ce ,"Ke ma ai ba ki ba ni ta ki ba, ba ki damu da in sami lambar ba kenan? Tayi dan murmushi, ta nuna masa ta fi shi, duk abinda yake tak'ama da shi." Tsakanin na da kai wa ya kamata ya tambaya? Tambayar ta, ta kure shi, kuma tuni hirar ta ginshe shi, don haka ya gunutle ta da fadin "Na ce mantawa na yi, ina ganin ya wuce, tunda kin samu, wannan ce ta ki? Ta ce,"Kwarai, ya wuce, in dai Antuna na nan ban da matsala. Lamaba ta kenan. Sai na ji ka." "Shi kenan nan gode." Ya kashe wayar yana dan tsaki." Washe gari tun safe ya wuce Kano, don gudanar da wasan su da (Kano Riders). Ko alama Naseer bai da kuzari, domin tun ranar da Alh. Basheer yayi masa albishir da auran Nusaiba, ya rasa duk wata natsuwa ta sa. Gaba daya ya dora wa kansa damuwa. Ya dawo tamakar maras lafiya. Tambayoyin da Yakubu ya rinka yi masa kenan a dakin (Hotel) din da aka sauke su, amma ya ce babu komai, kawai jikin sa ne bai masa dadi. Sannan yana jin kamar baya sha'awar yin wasan. Yakubu yayi ta kwantar masa da hankali, yana kara koda shi tare da nuna masa nan fa garin bayinsu suka zo. ***hhh wai bayinku,hada rai,dan karamin tsaki,,mttssswww.. Maji magani**** Ya zama dole ya zage damtse ya ba mara da kunya, su nuna masu sun zo garin su, sun fi su rawa.Ya ji ya amince da shawarwarin Yakubu, amma ba su cire masa damuwar sa ba. Karfe 2 saura 'yan mintoci, gasa ta kankama. Naseer dai ya hau doki ne. Alh. Basheer na ta yi masa addu'ar samun Nasara. Yakubu ya bubbugi kafadar sa ya ce,"Ja mu je, dan gidan Alhj, ba wani bayan kai! Ya zaburi doki, ya fada sahu. Duk dawakai sun jeru izini. Kawai suke jira su tashi jimawa kadan aka ba su izinin tafiya. In ba ka yi, ba ni wuri. Naseer fa ya cilla, sai dai tafe yake yana tunanin zuci. Babu abinda ya fi masa yawo a rai, sai zancan Zarah muryar ta yake ji tana fad'in **"Ni kuwa yayana gani na ke duk zance ka ke yi. A hankali za ka so ta!** Yana tafe, yana girgiza kai da karfi, don bai son jin muryar. Kamar ma karuwa ta rika yi. Shine akan gaba,"Jama'a na ta hargowa, muryoyin su suka yamute masa tare da ta Zarah. Kiris ya rage ya iso karshe, bai san lkcn daya saki linzami ba, ya kame kan sa, yana layi tare da kiran "Inna- lillahi"Wa-Inna-ilahir-raji'un! Duk su Alhj suka kame kaf, suna hangen sarautar Allah. Ko kafin su gama mamakin meke shirin faruwa? Naseer suka hango yana mulmulowa kasa. Alh. Basheer ya keto fili a guje, dukkan yaran sa suka rufo masa baya, yayin da tuni 'yan taimakon gaggawa suka kai wa Naseer dauki. Ya ji ciwo sosai, in ban da jini, babu abinda ke fita ta hanci ta baki. Kowa ya rude musamman Alh. Basheer da Yakubu. Nan take motar asibitin ta dauke shi zuwa asibitin Murtala, inda ya sami taimakon Likita. Bayan an gama bincikarsa babu karaya, inda ya ji raunuka, an daure su da magani, sai Alhj ya dauko shi zuwa gida. Ba su tsaya Zariya ba, kai tsaye Kaduna ya wuce da shi asibitin Likitansa, yasa aka ware masa daki na musamman shi kadai. Daga bisani ne suka sanarwa duk wad'anda suka dace su sani, musamman su Abba. Kan ka ce kwa6o? Asibitin ya cika da iyaye da masoyan Naseer, duk da dare ya fara yi. Anan Zaran da Nusaiba suka fara haduwa ko da ganin junan su, babu gabatarwa, take nan suka shaida junan su. Nusaiba ta rike hannunta, ta nuna ta ga su Alhaji. Ta gaida su cikin ladabi da girmamawa, su ma suka amsa cikin fara'a, tare da nuna kauna gare ta. Shi kuwa Naseer barci kawai yake yu, bai ma san wad'anda suka zo ba. A daran nan suka sake biyo hanya, suka dawo Zariya, aka bar Abba tare da shi. Zarah da Nusaiba kan ba su runtsa ba, saboda tunanin yanayin da suka baro Naseer. Duk da cewa Likita ya ce da saukin jikin amma abin akwai tausayi. Abu kamar hadarin mota, ko ina ciwo. Haka hankalin Alh.Basheer ke tashe, domin bai bar asibitin ba, sai 12 dare, suna tare da Malam Balarabe. A lokacin ne suke shawarar dole a rink'a yiwa Naseer addu'a, saboda yanayin bakin mutane. Don Yakubu ya gaya wa Alhjn labarin da Naseer din yake fadi, kafina fara wasar. Washegari haka su Umma suka dawo mota guda (Bus). Naseer na kwance baya ko iya tashi, saboda tsamin jiki. Komai da ake bukata, sun iske direba ya kawo daga gidan Alhj. Bayan kamar awa daya, motar ta juya da su Inna. Aka bar Umma da Zarah tare da Sageer. Su Biyun ma kadai ke tare da shi lkcn da Direba ya sake dawowa da Nusaiba da Umminta. Ummi na gama gaishe shi, suka sake fita tare suka bar Nusaiba tare da su. Kowacce na zaune, sun tasa shi gaba. Sageer ya dube su, yayi dan murmushi ya kada kai. Naseer ya dago ido, ya ce,"Lafiya? Ya ce,"Lau. Me aka yi? Ya amsa,"Gatan yayi maka yawa. Kamata yayi ka mike kawai, ka ce ka warke. Ko me ku ka ce tagwayen Jah-Jah? Lumshe ido yayi, ya kauda kai, yayin da Zarah ke fadin,"Gaskiya ne, amma don ragwanci ko motsi bai iya yi." Nusaiba ta ce,"Ina fatan ma dai ya ci abinci? Don na lura, baya son cin abinci." Ya bude ido, ya kwada mata harara, in ban da salo, yaushe ta san ban son cin abinci? Ya maida idon ya runtse, yana wani gajeran tsaki. Zarah ta cafe,"Babu 'yar tsaki anan yayana, ina jin Abba na gaya wa Umma ko dan Tea kadan ka sha. Ba tare daya bude idanuwan sa ba, yake fadin,"Ai sai ku yi min dure."Ta ce,"Yanzu kuwa, amarya hado min Tin ya gani, idan gatse yake yi." Ta kuwa mike ta hado shi. Yana kallon su. Sageer na ta dariya. Sageer dago mana shi." Inji Zarah. Ya dubi Sageer din, ya kara daure fuska,"Ta6a ni, ka ga yadda zan fasa ma baki." Ya ce,"A hakan? A hakan kuwa." Nusaiba ta ce,"A janye 'yar wasa, yakamata ka sha Tin nan. Daurewa za ka yu." Ya rufe ido,"Na koshi." Da anyi magana kuwa, sai ka rufe ido, zama da yunwa ai wani ciwon zai sa maka." In ji Zarah. Wani irin kallo yai mata, bai ce komai ba, ya maida idon ya sake rufe shi. Shiru bai kara tankawa kowa ba, har suka gaji da rarrashin sa ya sha Tea. Alhaji na shigowa Nusaiba ta labarta masa. Bakin gadon ya zauna ya ce Sageer ya kama shi ya tashi zaune. Da kyar ya iya zama, saboda ciwo ga takaici. Alh. Basheer yasa aka miko masa kofin Tin. Ya debo a cokali ya ce,"Ungo ka sha Naseer ciwo da yunwa mazaunin su daya, gaba daya suke mukurkushe mu2m." Malam Balarabe da Umma suna ta murmushi. 'Yar kunya ta kama shi, ya sunkuyar da kai." Kar6i mana, menene abin kunya, ni ba Abbanka bane? Ya miko hannu ya kar6i kofin." Zan sha Alhaji, kawo." Ya mika masa yana 'yar dariya. Kur6a yake a hankali. Alhj na rarrashin sa har ya shanye, a je kofin. ~~~~~~~~~~~~~~~ Sati 2 yayi a asibitin, shi kan sa idan zai fadi tsakani da Allah, ya san shi dan gata ne, kuma Alh.Basheer ba karamin so yake masa ba.Hatta Hajiyar su Yakubu, miyar kajin turawa tayo masa dakwale cikin kwano, ta kawo masa. A 'yan tsakanin nan shakuwa tsakanin Zarah da Nusiba tayi karfi sosai, sun fahimci juna kwarai da gaske. Kausar kanta, ta yaba da Zarah kuma tana mata kallon wacce za'a zauna lafiya da ita. Shi kuwa uban gayyar tamkar ya dauke kan sa ya maida gida yake ji, saboda ginsa da yayi da zaman Kaduna. Abu mafi ban haushi a gun sa, wanda yake k'ara sanya shi damuwa, shine gaba daya aka hade masa kai. A ganinsa kenan babu wanda zai kai wa kukansa, illah mutum daya, watau Naseer B. Shi yasa daya zo asibitin, ba shi da abokin hira, sai shi. Yayi ta yi ma sa famfo, yana k'ara cusa masa kiyayyar Nusaiba a rai. Koda aka sallame shi, haka a kodayaushe Alhj ke tafe masa da abubuwan alkhairi., sai da ya tabbatar da Naseer ga gyagije sosai. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Watannin 4 suka shude a cikin wannan hali, babu abinda ya sauya a zuciyar Naseer a game da auran Nusaiba. Yana zuwa wajen ta, don bin umurin kawai, haka ya kan kira waya, ya ce mata ya take? Sai dai idan ta turo masa (Text) da ingatattun kalamai, shi sai ya tura na shi babu komai ciki (Blank) Ga musun tsiya, idan za ta shekara gardama, ba zai ta6a sakar mata, dole ne ta yarda, ya turo sako, wayar ta ce mai matsala. Saboda haka ne ta daina ba ma kanta wahalar aika sako. Sai dai abin yana bata mamaki yana kuma sanya ta a tunani. Me yasa sauran sakwannin ke shigowa dai-dai, amma ban da na shi?Musamman sakwanin gaisuwar Ibrahim da take yawan samu. Kodayaushe baya gajiya wajen aiko mata da (Text) din gaisuwa da addu'o'i, wani lokacin har da kalaman so da kauna masu neman dagula lissafin ta. Haka nan take dauke kai, ta fuskanci zabin Abban ta, koda sau daya, za ta ga murmushi sa a sati. Wannan ta aje shi a kila haka halittar sa take, miskilanci. Kuma haka kawai, ta ji miskilancin yayi mata dai-dai, domin ita kanta bata cika son namiji mai yawan dariyar tsiya ba. Karshen watan nan su Zarah suka kammala jarrabawrsu ta karshe. Ko dama ita kadai ake jira. Nan da nan shirye-shiryen biki ya kankama musamman a Kaduna gidan Alh. Basheer. Ba k'aramin gagarumin biki aka shirya ba. Gidan daya ba su, tuni aka gama gyare-gyaran cikinsa, aka fent shi ciki da waje. Sannan yasa aka zuba tsaddadun abubuwan bukata na gani na fada har sashin Zarah. Duk da haka Naseer ya kashe wa Zarah makudan kudade wajen siya mata kayan daki, musamman kayan kicin, kuma kullum gaya mata yake yi ta rage shishshigewa Nusaiba, don kar ta raina mata ajinta. Ko alama Zarah bata son irun wadannan kalamai na sa, a kodayaushe, tana nuna masa ita da zuciya daya take kaunar Nusaiba. Biki saura kwana 7, Alh. Basheer ya kira Naseer, abinda ya gani ya daure masa kai, wasu kaya setin akwatuna ne guda 2, gaba daya shakare da kaya. Ummi ta bubbude masa daya bayan daya,kafin Alhj ya ce. Wad'annan akwatuna seti daya Zarah ne, daya kuma na Nusaiba ne. Kamar yadda yake a al'ada, kowace amarya ana kai mata. Wannan tsakani na da kai ne ko Umminku na gargade ta, ban ce ta gaya wa kowa ni ne na yi su ba, kai ne ka kawo wa Nusaiba. Wancan setin kuma ka kai wa Zarah. Shiru Naseer yayi, ya rasa ta cewa, domin zuciyarsa cunkushe take fa mmkn Alhj. Watau ya dai dage sai ya siye shi da karfin Naira. Kudi shegu ne. Ya karkada kai,"To ni me zance yanzu? Idanuwansa suka cika fal da hawaye. Irin wannan hidima ko kallon banza na yi wa Nusaiba, idan Abba ya sani, ai na kade, sai ganye na." Bai san kwalla ya zubo masa ba, sai da ya ji Alhaji ya dafa shi, yana fadin. "Haba Naseer, menene haka? Kai ba Da na bane? Kullum ina gaya maka hakan, amma kamar har yanzu ba ka yarda da ni ba. Look! Ka na ji na? Nusaiba kawai gare ni, sai Allah ya k'ara min da kai, na kuma gode masa. To kai ma ka gode masa domin kyautar daga gare shi take. Share hawayen nan don Allah."Ya kai hannu ya goge kuncin sa, yayin da Ummi ke fadin,"Namiji ai jarumi aka san shi, kar ka ba matan ka kunya mana." Ya kara sunkuyar da kai Alhj na dariya., Mai-gadi ya loda masa akwatunan a bout, shi kuwa yana zaune, yana zuba godiyar karfin hal. Nusaiba bata nan? Sun shiga gari da Kausar shirye-shiryen biki." Saboda haka ba 6ata lokaci, ya damko hanya, ya dawo cike da aljabi tare da wasi-wasi wai kauna ce ta sa Alhj ke masa hidima? Shi kam bai yarda ba, saboda 'yar sa da yake son lik'a masa ne kawai. ****Kai jama'a nifa Naseer dinnan yafara bani haushi**** Ga Abba tare da Umma, sun baje akwatuna ba sa aikin komai, face sa albarka. Umma har kwallanta sharaf-sharaf. Bayan sun natsa. Naseer ya ce dole a kaiwa Zarah gaba daya kayan, watau da nasa setin akwatunan da yai ma ta., Abba ya ce hakan bai zama adalci ba, zai fi kyau ya aje su, bayan sun tare gidansa, ya raba masu kowacce ta kwashe kason ta. Umma ma ta goya wa Abba baya. Akan dole Naseer ya karbi wannan shawarar. A yammacin ranar. "Yan-uwa da abokan arziki suka kai kaya gidan su Zarah. Hakika iyaye da 'yan uwan Zarah sun ga abin mamaki, domin sun ga kaya iya ganin su. Su kuwa Abba da Umma a kodayaushe a cikin dogiya da shi wa Alh. Basheer albarka suke har zuwa ranar daurin aure, yayin da hidimomi da dama na shagalin biki akai tayi a Kaduna da Zariya. Nusaiba tana zuwa na Zarah. Ita ma Zarar ta halarci walima da (Mother's day) a Kaduna. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Ranar asabar da safe karfe 11, aka daura auran Naseer da Zarah. Karfe 2 dai-dai ita ma Nusaiba ta tabbata mata Naseer, tun daga lokacin duk wani farin ciki da ke zuciyar ango ya rufe kofar sa. Wani irin yanayi daya rinka yi a wajen, shi ya tabbatar wa Sageer lallai abokin sa na cikin wani yanayi na daban, don haka ya ja shi gefe, ya kare masa kallo, gaba daya idanuwansa jajur! Suke. Ya sanyaya murya ya ce,"Ka ga yadda ka dawo kuwa Naseer? Bai kamata ka rikide haka ba a wajen nan, don ba haka aka san ango ba." Ya sauke numfashi, a yamute ya ce,"Ban son yarinyar nan Sageer, ka na zaton wasa na ke yi? Mts! Yayi dan gajeran tsaki, ya kauda kai, "Rayuwa ta vata damu kowa ba, sai shahalinku ku ke yi, ni kadai na san abinda ke damu na. Ka je ku ci gaba da hidimomin ku. Ka kyale ni kawai." Jikin Sageer yayi sanyi, tausayi ya kama shi, ya kamo hannu Naseer ya ce, "A hankali za ka so ta mutumi na. Please ka jure, ka zama namiji, kar ka mance kuma har da Zarah yau ta ka ce, halas-malak. Yakamata ka gode Allah, domin yayi maka kyautar da ba kowa ke samu ba. Mata 2 a lokaci guda ko a zamanin da, sai dan gata. Illar kawai da ba ka son Nusaiba. Amma ina gaya ma za ka so ta, saboda yarinyar bata da wata mishkila." Ya dauke numfashi." Sageer ba zai gane ba, menene amfanin maimaita magana 1? Ya fada a ran sa. Ya daga ido zai ce wani abu. Kausar ya hango tana dube-dube, da gani, su take nema, don haka ya ce,"Ha sarkin kaudin can zuwa, da alama mu take nema." Sageer ya juya, ko kafin su fito fili ma, ta hango su. Wajen ta nufo,"Haba ango kuma sai ka 6oye, ina ta billayin nema? Ya ce,"Magana muke." Ta ce,"Ummi ce ta ce in tambayi motoci nawa ku ka zo da su? Sageer ya bata amsa." Akwai kanana 10, ga kuma wata Bus can, sun isa ko a karo? Ta ce,"Bari na tambayo. Ta sake duban Naseer." Ango! Ango!! Ya dan murmusa, ya kauda kai, ta ce, "Har yau din ma murmushi kawai zan samu? Bakin ango ai baya rufuwa, balle kai mai Double. Zan so in ga Competition din. Ni zan ba ka abinci a baki, ni zan kai ka ka sha madara! Dole ta sanya shi dariya. Sageer kam har da kyalkyawa. Ta wuce da sauri, tana fadin " Ku jira ni, na tambayo, Naseer ya gintse dariyar, ya ce,"Wannan 'ya da tsanannan surutu take." Ya ce,"Ba ga shi ta sa ka dariya ba? Mts! Ni yanzu ma zan sa6e." Ka je ina? Ya ce, "Zariya zan koma." Wajen Zarah ko? Me za ta yi min? Ban da ta k'ara 6ata min rai? Ai duk bakin ku daya. Makullin Naseer B zan kar6a, in je dakin sa, in huta awa 2, kafin ku iso."Sageer yayi dariya, ya ce,"ANGO kenan, kai wane hutu ka ke nema a wannan yamutsin? To Allah ya kiyaye hanya, amma ka san duk taron nan, saboda kai aka yi shi ko? Hakkin ka ne ka ba kowa kulawar da ta dace." Ya ce,"Menene amfanin ka? "Ba wasa na ke yi ba, tafiya zan yi idan na ci gaba da zama wajen nan, jini na zai hau. In wannan kwakwazon ta dawo, ka san yadda za ka yi da ita. Sai kun taho. Kamar wasa, haka Sageer ya saki baki yana kallon Naseer ya amshi makullan Naseer B, ya wuce ya fada mota. Jama'a da maroka na bin sa, yana fadin yanzu zan dawo. Yana nan tsaye. Mamaki ya kusan kashe shi. Kausar ta dawo ta shaida masa moticin sun isa, idan ma da k'ari. Ummi ta ce ba matsala. Abba ya ware wasu masamman, don dibar jama'a. Naseer bai san lokacin da barcin takaici ya sa ce shi ba, bisa katifar Naseer B. Can a mafarki yake jin wayarsa na bugawa. Ya bude ido da kyau, duk jikin sa yayi tubus! Saboda tsabar gajiya, da gaske wayar ta sa ce ke bugawa. Ya lalubo ta, ya duba Sageer ne akan layi. Cikin muryar barci ya ce,"Ya aka yi? Ya ce,"Me kuwa aka yi? Dan rainin wayau. To mun iso muna fly-over yanzu. Idan ka ga dama, mu hadu a can ,"Yanzu da gaske kun dauko yarinyan nan." Haushi ya kama Sageer, ya rasa me zai ce? Sai yayi tsaki ya kashe wayar sa, ya ci gaba da tuki. Naseer ya dubi agogo karfe shida da kusan kwata. Ya mike da kyar, yayi mika, kansa kawai ya ji ya dauki ciwo, ba kadan ba. A haka ya fito ya kulle dakin ya shiga mota, ya nufi (Hanwa Low-cost). A hanya ya kira wayar Umma, ya shaida mata bakin sun iso. Nan da nan aka shirya kayayyakin abinci kala-kala. Bus guda tare da 'yan tar6ar baki suka tafi. Naseer na isowa. Jeep din Antin Jordan na fakin. Ta fito da yaranta, wajen ta ya nufa, ya dan rankwafa, yana mata sannu da zuwa. Bakinta har kunne, ta bubuga kafadar sa. "Angon Nusaiba. Angon Zarah. Ina ka shige, na yi neman duniya, ban gan ka ba? Ya shafi k'eya, ya ce,"Kira na aka yi nan Zariya, dole na dawo." Anti ta ce,"Haka wannan abokin na ka ya ce, "Dama an daura aure, ban ga ango ba, ko sau daya, shi yasa na tambaya. To Allah yasa albarka." Ya ce, "Amin." Ta wuce ciki, shi kuwa ya wuce wajen su Sageer. Yana wa Allah godiya da karyar sa ta zo dai-dai da wacce Sageer yayi. Karfe 9 saura kwata aka kawo Zarah, a lokacin bakin Kaduna duk sun juya, wadanda suka rage, ba su fi mu2m 10 ba. Antin Jordan da kan ta, ta jagorance su zuwa sashin Zarah. Bayan yan kawo amarya sun gama ba ido su abinci, motoci suka koma da su gida. Aka bar mu2m 3, suka taya ta kwana. Haka ma Zarah ba karamin mamaki ta sha ba da ganin dakin auranta. Ko a mafarki bata ta6a tunanin irn sa ba, saboda haka ta kwana yi wa Allah godiya tare da rokon sa zaman lafiya dauwamanme. Washegari safiyar lahadi, karfe 9 za'a gudanar da hawan Yakubu. Sukuwa ta musamman wacce Yakubu ya shirya. Filin sukuwa ya ci ka fal da Zaratan 'yan wasan tseren Polo daga ko'ina 'yan kallo kuwa babu masaka tsinke maza da mata. Alh.Basheer da tawagar sa ma suna wajen. Tsofaffin 'yan wasa irin su Yakubu da shi kan sa Yakibu su suka fara sharar fage, inda dokin Yakubu yayi wa saura fintinkau. Daga nan sukuwa ta ci gaba. Kowa na nuna bajintr sa, abin gwanin sha'awa, sai wanda ya gani. Karfe 11 dai-dai, rana ta soma zafi, wasa ya zo karshe, kamar yadda Yakubun ya shirya. Ango shine zai rufe fili, don nuna farin cikin sa ga dimbin masoyan sa da suka taru. Saboda haka Yakubu ya mike ya dau lasifika yayi wa ango kirari, ya kwarzanta shi, sannan yayi kiran sa, "NASEER, ta so ka ja mu je! Yana mike wa, duk wuri ya yamutse da hargowa da tafi, shi kuwa kansa ne ya ji yana sara ma sa. Domin duk lokacin da aka kira shi angon Nusaiba, ya kan ji jinin sa ya k'ara hauhawa. Ya tsaya gaban dokin da ya saba hawa, ya cire kuben da ke kan sa. Yakubu ya dora masa ta kwano. Ya taka ya haye doki. Ji ka ke tafi, ta ko'ina. Yayi karfin hali, ya daga hannayen sa sama, yayi gaisuwa ga kowa, sannan ya tsala wa doki bulala, yayi haniniya ya zura a guje. Naseer fa bai san abinda yake yi ba, gudun kawai yake yi kura na tashi., Rayuwar sa gaba daya cikin kunci take har ya kan kai ga lokuta da dama yana mancewa da tunaninsa. Abinda ya faru da shi kenan a halin yanzun. Ya sakarwa dokin sa linzami, ba san irin gudun da yaje yi ba. Ai kuwa ba a jima ba, kafafuwan dokin suka sarke, yayi haniniya, yayi sama, me jama'a za su gani? Ango ya watso k'asa warwars! Wuri yayi tsit!Na 'Yan dakikai, sannan gaba daya jama'a suka dauki salati, yayin da tuni jama'a da ke kusa da wajen, suka yanyame shi. A sume suka wace da shi asibiti. Ba 6ata lokaci aka kai shi (Emengency). Kowa ka duba, hankalinsa tashe yake, musamman da Likita ya ce yana da karaya 2, a hannun sa na dama. Alh.Basheer zufa kawai ke keto masa, fadi ya ce, "Inna-lillahi"Wa-Inna-ilaihir-raji'un! Ana cikin halin haka, su Malam Balarabe suka iso, ba'a jima ba Jeep din Antin Jordan ta aje su tare da amare. Kowacce ido warwaje, ta sha kuka. Ba su ma yi kuka ba, sai da suka ga angon su magashiyyan a kwance, bai san halin da yake ciki ba. Antin Jordan kuwa tunda ta iso ta tsinke da fada, kamar ta ari baki, wai me yasa za'a bar ango yayi sukuwa? Duk laifin na su Alhaji ne, haka take ta fad'a. Sam ta mance haka Allah ya kaddaro. Bai farfado ba, sai la'asar, ya sha mamakin ganin sa a gadon asibitin. Wani sabon bakin ciki ya sake turnike shi. Wannan wace irin masifa ce? Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 2-02 Posted by ANaM Dorayi on 11:41 PM, 11-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Gaba daya an gur6ata masa rayuwarsa? Take nan ya kara tsanar Nusaiba, ba wai a zuci ba ya kadai ba, har cikin jinin jikinsa yake jin bai sha'awar zama tare da ita...Lallai iska na wahalar da mai kayan kara, domin Alhj ba karamin hidima ya sha ba a asibitin nan da kudin mai dorin gargajiya. Angwanci dai ya dawo asibiti. Anan abokansa da suka zo daga nesa suka yi bankwana, suka koma zukatan su cike da tausayin Naseer. Baya magana da kowa, illah iyaka eh, ko a'a, ko kuma ayi masa sannu ya amsa. Hatta ita kan ta Zarah kallon ta kawai yake da ido, domin haka ya fiye masa kwanciyar hankali, kar a gane da ita kadai yake magana. Kwanansa 3 a Shika. Likita ya gama tabbatar wa Alh.Basheer babu wani rauni a jikin sa, sannan aka sallame shi. Aka dawo da shi gida. Haka suka wuni kar6ar baki, a cikin su harda su Lubabatu, Hauwa'u da Maryam, watau mutanen Zarah na makaranta. A daren wannan rana Zarah ta feso wanka, ta sa wani dan karamin dinkin atamfa riga da siket, ta fito ta leka sashin Nusaiba, ita ma wankan ta shiga, saboda haka ta wuce sashin Naseer. Bisa kafet ta same shi zaune, ya jingina da bango, idanuwansa rufe suke, sallamar da ta yi. Shi yasa ya bude idon, yana kallon ta har ta zo kusa da shi, ta zauna. "Yayana tashi ka yi? Ya ce,"Na gaji da kwanciya, jiki na duk yayi tsami."Ta dan dube shi, ta ce,"Sannu yanzu me za ka ci? Ya dan kada kai,"Ban jin yunwa." Suka yi dan shiru 'yan dakikai, ta dago ido ta dube shi. Ita shi ma yake kallo, don haka tayi dan murmushi, ta sauke na ta idon. Hannun sa ta ji ya riko na ta, jikin ta yai sanyi, ta kasa motsi." "Zarah!" Ya kira ta a wata siga mai taushi. Kunya kawai ta ji ya lullube ta, ta kasa duban sa. Ya kara kwantar da muryar ya ce,"Ki dube ni, na ce, ni ba angon ki bane? Ko don kin ganni a karye? Hannun ta daya, ta dan kare baki, tana murmushi. Ya kara runtse yatsunta ya ce,"Kin ga irin ta, ba don kun jawo min ba, ai da tuni na kauda wannan kunyar." Ya kara bata kunya, kamar ta tsere. Ya jawo ta, ta matso shi sosai, ya rungumo kafadarta ya ce, "Zarah kullm ina yiwa Allah godiya daya ba ni ke, saboda ke kadai na ke so a rayuwata. Sai dai yanayin da na ke ciki, ya zame min wani jarabci, wanda na ke ganin sai kin taya ni addu'a. Allah ya kawo min iyakar sa. Allah yana gani, kuma ya ga abinda ke zuciya ta, tamkar kan k'aya na ke cikin gidan nan. Saboda haka na ke neman hadin kan ki, ki taimaka min kullum ki kasance tare da ni, domin ke kadai ke yaye min bakin cikin da ke rai na."Ta sauke numfashi, cike da tausayi, ta dan dube shi ta ce,"Kullum ina tare da kai yayana, na sha gaya maka, ka daina damuwa. Ka kuma daina daukan wannan aure a wani matsayi na daban, face hadin Allah. Ba ka san abinda Ubangiji ya 6oye a cikin sa ba. Ba wai ba na kishin ka ba ne, ko alama ba haka bane. Ban ki in kasance ni da kai a gidanka ba, amma na yi imani da cewa, duk wanda zai yi jayayya da shinrin Ubangiji. Tabbas yana tare da wahala, ga kuma tarin zunubi. Domin daga nan ne mutum yake fadawa muguwar hanya, saboda bakin kishi. Na san ka na so na yayana, amma ka sa ni. Nusaiba ma amanar ka ce." Shi fa ba ya ma ko son ya ji an ambaci wannan sunan, sai ya ji kamar ya kurma ihu. Yayi ta maza saboda Zarah da ke kusa da shi. Ha6arta ya dago ta dube shi, yayi murmushi sosai, ya ce,"Na ji maganar ki, kuma zan yi iya kokari na. Abinda ba na so kawai a rink'a saurin kama ni da laifi.." Ta ce,"Kamar yaya? Ya kada kai, ya ce,"Wannan sirri na ne, ba zan fada ba, na samu ana kallo na, kunya ta sa a daina. Kinga na yi wa kai na." Ta sa hannu ta dan buge hannun sa da ke ha6ar ta, ta kauda fuska, tana 'yar dariya. Shi ma dariyar yake yi, ya sake juyo fuskar ta, ya jingina gashin sa jikin na ta, ya ce,"Kin min alkawari kullum ki na tare da ni, me yasa za ki kauda min fuska? Ta kwantar da ido k'asa, bata tanka ba." Kin sa tayi 'yan sumbatar kuncinta,"Da ke na ke magana." Ta ce,"Bari in kira amarya mu shirya yadda za mu rink'a girki." Ta yunk'ura za ta mik'e, ba tare da ta ji ta bakin sa ba. Hannun ta gam!Ya rike shi. Ta juyo dauke da murmushi ta ce, "Don Allaj bari in kira ta." Ya lumshe ido, yana girgiza kai,"Ban ce ba." Ta dade tana kokarin kwacewa, amma ta kasa. Motsin bude kofa suka ji. Tare da sallama, ta dage da karfi ta fizge hannun a lokaci guda, shi ma ya sake ta yayin da Nusaiba ta kawo kai. "Bata fahimci komai ba, domin Zarah a tsaye take. Shi kuwa dan gogan tuni ya dauke kai cike da haushin Nusaiba, ta katse masa hanzari." Ke za ni kira amarya, na lek'o dazu ki na wanka." "Ta ce,"Ni ma na shiga, ina ta sallama, na ji shiru. Ya jikin na sa? Na gan shi a k'asa ne." Duk suka zauna suka sanya shi tsakiya. Zarah na fadin,"Ni ma na shigo, na gan shi zaune ana. Wai ya gaji da kwanciya." Ai da gajiya, kwanciyar." Koma yau da bango ya jingina, ya rufe ido. Ta ce,"Sannu." Da kai ya amsa. Ta mike ta dauko filo, ta tsugunna gabansa,"Dan daga in sa maka filo, zai fi maka dadi." Yayi shiru kamar ba i ji ba.Yayin da Nusaiba ke fadin,"Shi ke nan gara da ka sa baki. Da su Antina za'ayi min wayau." Ya kalle ta a dage ya ce,"Kyale ta kawai, tashi ki tafi abin ki." Ta kuwa mike za ta wuce, Zarah ta rikota,"Wai sai ki tafin kuwa? Ta ce,"Me zan jira Antina? Ai na yi ma ku hira, yakamata in je in barci." Karfe 9?" "Eh mana. A kwanta da wuri, a tashi da wuri." Fuska yamute ya ce,"Don Allah ki kyale ta, ta wuce mutun na jin barci a hana shi? Tana can tana kallon Naseer, ya 6ata rai ba sauki, Nusaiba ta zame hannunta,"Allah ya ba mu alkhairi. Yayanmu Allah ya karo sauki." Amin." Ya fada a fizge. Ita kuwa Zarah ta kasa ma motsi tayi. Tana kallo Nusaiba ta bar dakin. Dariya ya kamayi, ganin yadda Zarah tayi sukuiti duk jikinta ya mace." Ta nuna shi da yatsa ta ce,"Ka daina sa mana baki idan muna magana." Fuskar ta kunshe da shagwa6a. Dariya ya ci gaba da yi mata. Suka ci gaba da hira. Karfe 11 da kyar ya bar ta ta koma dakin ta, ta yo shirin barci ta kulle dakinta, ta dawo wajen sa. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Bayan kwana 2. Nusaiba ta kar6i girki, a ranar kuwa gidan cike yake da baki da 'yan dubiya har da iyayen su. Tare suka hada suka yi girke-girken abincin su kuma tare suka ji ta kula da bakin su.Kamar yadda suka saba gwanin sha'awa. Zarah ta gaji tu6us! Don haka tana yin ishha'i, tayi wanka ba ta jira komai ba, ta bi lafiyar shimfidadden gadon ta, babu 6ata lokaci, barci ya sace ta. Nusaiba kuwa bayan ta gama shirin ta, sashin Zarah ta soma zuwa, kofar falon na garkame. Ta tsaya kame da ha6a,"Ba dai hat Antina tayi barci ba? Lallai Antina." Ta jinjina kai ta wuce wajen Mai-gidan. Yana kwance, gaba daya dakin yayi masa bakikirin. Babu abinda yake tunani illah Zarah, abinda ke 6ata masa rai kuwa, yai ba ita zai gani a dakin sa ba. Ko sallamar ta bai iya amsawa ba. Ta zauna gefen gadon, tana fadin,"Ka san wani abu? Wai Antina har tayi barci." Ya baki taso ta ba? Ta kulle kofar falon ma Ya ce,"Yayi mata dai- dai. Daga nan bai sake cewa komai ba, nan ya bar ta zaune, a zaton ta ma barci ne ya sace shi. Yana jin ta, ta rufe shi, sannan ya kwanta, sai da tayi barci, ya jawo filon sa, yasa kasa ya dawo nan ya kwanta. Karfe 2 dare, ta farka, don yin sallar dare. Can ta hango shi bisa kafet Mamaki ya kamata. Ta sakko ta tsaya kan sa tana kallo. Kamar ta tashe shi, wata zuciya ta ce ma ta kila ya fi son kwanciyar kasa ne. Don haka ta wuce bayi, ta kama ruwa, ta yi alwala ta fito. Motsin ta ya farkar da shi barci, amma san bai bari ta gane ba. Ta daura zani, ta dora hijabi ta haye sallaya ta fara sallah. Shi kan sa ta burge shi, da zai fadi gaskiya. Ta jima bisa sallaya tana addu."a kafin ta mike, ta nufo gunsa ta tsugunna. Yadda ya kwanta a yaye babu lullubi, sai ta ga kamar sanyi yake ji, don haka ta mika hannu ta janyo bargo ta sake lullube shi. Ta koma gado tayi kwanciyar ta. Naseer yayi shiru ya rasa me yake sakawa a zuciyar sa. Har asuba bai koma barci ba, haka kuma bai daina sake-saken iska ba cikin ransa ba. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Tsawon wata 1, Naseer yana samun kulawa wajen amaransa da wacce yake so da wacce bai damu da kulawar ta ba. A son ra'ayin sa ko sannu baya buk'ata daga gare ta, shi yasa kullum yake jin sa kamar bisa k'aya cikin gidan nan. Kuma bai san dalilin da yasa kodayaushe k'ara tsanar Nusaiba yake yi ba, duk da bajintar da suke nuna masa ita da iyayen ta. Wani lokaci har tsoron zuciyar sa yake ji, ta yadda ko alama ta k'i amsar Nusaiba. Hannun sa yayi sauki sosai, domin har ya kan fita ya je wajen iyayen sa, ya gaishe su. Bai ta6a shiga sabuwar kerarriyar Jeep din sa ba, wace Alhj ya sake masa, sai da Zarah ta goranta masa. Shagon dinkin Sageer ya iso yayi fakin ya fito duk jama'ar wajen idanuwan su akn sa. Idan ka dube shi sai ka rantse da Allah wani hanshakain dan kasuwa ne. Gaisuwa jama'ar wurin ya rinka amsawa, sannan yayi sallama shagon. "Allah ya kiyaye min na Zarah, angon Nusaiba." Ya wuce shi ya zauna a kujera. Sauran yaran shagon suka gaishe shi da jiki, ya amsa. Sageer ya biyo shi, shi ma ya zauna kujerar gefen sa ya ce,"Duk na zura ido in ga wa zai fito daga wannan shimfidediyar mota, ashe Alhaji na ne, ka gan ka kuwa?Ai za'a ce ka ba wata biliyan dari baya mutumina." Ya ce,"Ka bari kawai, ni kai na tsoron gidan nan na ke yi da motar nan. Zarah ce ta matsa min na kinkimota." Yayi dan murmushi ya ce,"Arziki. Kashi Naseer, ka riga ka tako kuma kowa yana da hanyar da Allah ya shiryo masa inda zai sami abincinsa. Allah ya kara hada mu da masoyan mu." Ya dan nisa kafin ya ce,"Yanzu tsakanin ka da Allah ba ka min kallon auran jari na yi? Kyar Sageer ke kallon sa,"Me yasa kai ka cika tsarguwa ne? To idan ma auran jarin ka yi, ina ruwan mutum? Ina cewa shi ma mu2m ya sami damar yin hakan, sannan zai yi? Naseer, ba auran jariba, ko auran damfara ka yi, babu ruwan ka da mutane kowa ta shi ta fishshe shi. Abinda Allah ke duba ita ce zuciya, shi yasa ake so a kodayuashe ta kasance tsarkakkiya." Ya dan yi hucin zafi ya ce,"Na fahimce ka, amma kar ka manta ba kowa ke da irin tunanin ka ba. Ni kuma na tsani zargi, ina fitowa motar nan kowa sai kallo na yake yi, har da gaisuwar gulma, dole in na shiga wannan, ayi magana ta. Ka san ban da hakuru, idan na ji ba za'a kwashe ta dadi ba, komai gemun mu2m." Ya dan bubbuga kafadar sa, yana dan murmushi,"Allah ya ki yaye min angon amare, hakan ma ba za ta kasance ba. Insha-Allahu. Ai yanzu ka wuce da ajin fada, sai dai ka yi rabon na 'ya'ya a cikin gida ko ba haka ba? Wani dan bazawarin murmushi yayi ya ce,"Aje wannan maganar, ka san ina son yara, kar ka tada min kwadayin su." Ko?" Sageer ya tambaya, ido waje. Ya ce, "Ah? To mece ce ribar auran?, Ita Zarah ma ta ki fara laulayi, sai ja min rai take yi." Sageer ya fashe da dariya suka tafa. Sannan ya nuna shi,"Zarah kadai? Har da amarya, lokaci guda za su zazzage ma tagwaye." Take nan ya sauya wani shafin." Ka san wani abu? Na kusan fara zuwa koyon dinki, jira na ke hannu na ya gama warkewa." Baki sake yake kallon sa."Ina son ka ranar yanko zance, babu seti. Mutumin da hidiman karatu ke gaban sa, ga fita wasanni, yaushe za ka sami lokacin zama nan? Lallai za ka sha mamaki, kai ba ka na karatun ba, ka rinka koyon dinkin? Ya ce,"Ai na ma riga na sha mamakin. To wai me yasa ka ke son koyon dinkin yanzu?" "Ra'ayi na ne ya sauya, yanzu kuma dinkin na ke so." 'Yar dariya Sageer yayi,"Allah ya nuna mana lokacin." Ya ce ,"Amin. Ya dan jima nan suna ta hira, sannan ya je ya gaida Umma. Abba ya riga ya fita kasuwa. Daga can gida su Zarah ya nufa, suka sha hira da Innar sa. Haka yayi ta yawon sa a gari, ba shi nan, ba shi can. Saboda yasan Nusaiba ke da girki, bai koma gida ba, sai gab da Sallar magariba. Suna zaune a falo, kowacce ta tsala don mamaki. Yayi sallama ya shigo, suka amsa dauke da fara'a, sannan suka yi masa sannu da zuwa. Idon sa akan Zarah yake amsawa. Kan sa tsaye ya wuce kujerar da take, ya zauna bisa hannun kujerar, yayin da take fadin. "Haba yayanmu, kuma tun safe har magariba ba'a ko waiwayen gida? Haka ake yi? Kawai yadda take motsa bakinya, shi ya tsura wa ido,, yake kallo. Nusaiba ta ce,"Ai ni ban ma san abinda zance ba Antina." Ya dan lumshe ido kadan, ya bude su, kafin ya ce, "Na yi laifi kenan? Ta ce,"Tambaya ma ka ke? Kodayake babu ruwana, tsakanin ka da amaryar ne. Aron bakin ta na yi, na ci mata albasa. Bari na yi haramar sallah." Ta mike za ta wuce, yayi wuf ya cafke hannunta. Adon ta kawai ke kidima shi, tayi masifar kyau,(Material) din ya amshi jikinta sosai." Ta waigo a firgece, ta rasa ma me za ta ce?" Zo in ji warin albasar da ki ka ara ki ka ci." Ta dubi Nusaiba da ke kallon su, tana dariya ta ce,"Au dariya ma ki ke yi, ba za ki kwace ni ba, ki na kallo zai kar ya ni." Ta gintse dariyar ta ce,"Duk zan iya jinyar ku." Ya janyo ta, ta fada da karfi ta dawo inda ta tashi ta sake zama. Ya matso ta sosai, ya ce,"Haba Fati na,, daga shigowa ta kuma sai ki tashi, don me? Ta dan kalle shi a karkace ta ce,"Sallah zanyi,ga ta can ana kira." Ba ta jira komai ba, ta shammace shi, ta wuce." "Zarah! Ya kira ta, ta waigo. Yayi dan jim yana kallon ta, kafin ya ce,"Kin yi kyau." Ta dan kama kugu, ta sauke numfashi ta dubi Nusaiba,"Kin ji abinda ya ce? To kar ki yarda ya kallame ki, sai ya gaya miki inda ya je ya ki dawowa ya ci abincin rana. Ni babu ruwa na." Ta wuce, ta bar Nusaiba na murmushi. Shi kuwa ita ya bi da kallo har ta shige sashin ta. Ya ja gajeran tsaki, wani kullutu ya tsaya masa a wuya. Ga wacce yake so ya sakata ya wala da ita, ance ba haka ba. Mutane na ganin auran gata aka yi masa. Ina gatan? Bayan rayuwar sa na cikin kunci, bai da walwala ko alama. Can cikin tunanin sa, ya ji kamar Nusaiba na kunkuni. Ya daga ido har sun fara ja, saboda damuwa, ya ce,"Mene ne? Ta ce,"Sannu da zuwa na ce." Ya dai amsa ne kawai, amma bai ga dalilin sake yi masa sannu da zuwa ba, bayan sun yi masa tun shigowar sa. Ta ce,"Shiru ka ki dawowa, muna ta tararrabi, duk da dai abincin ba cinsa ka ke sosai ba, ai da dadi ka dan dawo mu gan ka ko saboda yanayin jikin ka."Yayi shiru yana dubanta, sanaben da take yi, shi ya sa shi 'yar dariya. Ya gyada kai,"Yaro man kaza." Ya fada a ran sa. Ta ce,"Dariya ma na sa ka? "Na dai sa kai na, ai kin san ba za ki iya sa ni dariya ba. Ko za ki iya? Ta kada kai,"Wace ni, amma kasan bai kamata ka rinka dogon yawo ba ko? Ya ce, "Na daina Hajiyar. Zan iya zuwa in yi sallah? Tayi dan murmushi, ta ce,"Ruga da gudu, ka yi sallah, ina nan zuwa da kayan abinci." Kya ci abinki." Ya wuce yana fadi a ran sa. Ta bi shi da kallo, yanzu kam ta yarda son Naseer ya fara shiga ranta, sai bata san abinda ke damun sa ba, ba baya sakin jiki da ita sosai ba. Ta sauke numfashi ita ma ta tashi. Ya dade da yin barci tsakar daki bisa lallausar kafet, lokacin daya ji ana kwankwasa kofar dakin ya farka firgigi, ya dubi agogo karfe 4 saura kwata na asuba. Tuni Nusaiba ma ta tashi zaune bisa gado, tana tambaya,"Waye? Bai amsa ta ba, ya wuce kofa yana fadin ,"Zarah! Menene? A lokaci guda yana bude kofar. Me zai gani? Wasu Samudawa ne majiya karfi cikin shigar bakaken kaya, tun daga bisa kan su har kafafuwa, ba ka ganin komai, sai kwayar ido. Sun tado Zarah da bakin bindiga. Ko kafin ya gama shan mamaki, sun hada da Zarah da kofa tare da shu sun bankado su tsakar dakin." Ganin haka yasa Nusaiba ta aza hannu bisa kai, ta kwarara salati mai karfin gaske! Bata karasa ba, wani daga cikin su ya kwashe ta da mari. Ya daka mata tsawa,"Shutu.! Ta rarrafa da gudu ta kwakumi Zarah, suka dunkule waje daya, bakinta na ta tsato jini. Naseer ya bi su da kallo ya ce,"Me ku ke so? Wanda ya fi kowa rashin imani ya dubi hannun Naseer da ke rataye a wuyansa, yasa kwafcecen takalmin da ke kafar sa, ya togar hannun, sannan ya aje kafar bisa hannun ya murza son ran sa.Daga yadda Naseer ya ji yanayin hannun, ya tabatar da babu makawa ya sake karyewa. Amma saboda taurin ran sa, ko kara bai yi ba, ya sake cira kai ya dubi wanda yayi dakali da hannun sa, ya ce,"Menene abin duka bawan Allah? Ina cewa abinda na ke da shi, su zan ba ku? Magana ta gaskiya, kun yi rashin sa'a ban da komai gaba daya cikin kudina cikin gidana na dubu talatin ne, suna cikin jakar can, ku je ku dauka." Ya maka masa kasan bindiga ya ce,"karyaKi na yi segiya, ina kudi? "Abinda na ke da shi na gaya maku." Baba tausayi ya shiga tafka masa takalmi. Nusaiba tayi karfin hali, ta durkusa hawaye na zuba murya na rawa ta ce,"Don Allah ku yi hakuri, ku daina dukan sa, muna da gwalagwalai masu yawa da tsada, akwai wayoyi kuma a waje na. Akwai dubu hamsin, duk zan hada ma ku. Don Allah ku kyale shi, ba shi da lafiya. Zarah kuwa kamar ta mutu, ko numfashin kirki bata iya yi. Take nan ogan ya hada su da yara 2, kowacce aka rakata dakin ta, ta hado duk abinda take da shi. A wajen Zarah ma an sami dubu goma ragowar sadakin ta da Malam Umar ya ce dole sai ta kar6a. Amma gwalagwalan Nusaiba iyaka ne, domin a cikin su akwai na dubu dari biyu da hamsin. Ganin su ne ma yasa ogan 6arayi ya kyale Naseer, ba don haka ba da sai ya kwashi kashin sa a hannu. A ce gida kamar wannan, ya 6ata lokacin sa ya shigo bai sami komai ba? Dole kuwa ya debo rabon sa a jikin Mai-gidan. Amma duk da haka warwas suka bar Naseer. Matansa suka tarairayo shi. Sai a lokacin yaje jin kansa kamar ba a jkin sa yake, shi yasa ma ya kasa tashi tsawon lokaci. In ban da kuka babu abinda su Zarah ke yi, shi kuwa fadi yake,"Hasbinallahu-wani-imal-wakil........ Wasa-wasa fa Naseer ya kasa motsi, abin ya kara firgita matansa. Nusaiba ta bazama falo ta nufi gefen da wayar gida take (Land-line) jikin ta na rawa ido na tsiyaya, ta nemi lambobbin gidan su a Kaduna. Hankali tashe Alhj Basheer ya dauka, don ya tabbatar da babu lafiya, wannan waya karfe 4 da rabi." "Hello." Muryar Nusaiba ya ji cikin kuka yana fadin. "Abba na! B'arayi sun ku san kashe Naseer, ga shi can kwance, ya ka sa motsi! Gabansa ya yanke ya fadi, ya dauki salati, bakin sa na rawa kafin ya ce,"Harbin sa suka yi? Ta ce,"A'a tsabar duka ne Abba na. Don Allah ku taimake mu, sun kwace komai, har wayoyin mu balle in kira wasu anan. Ya ce,"Ku kwantar da hankalin ku, kin ji? Zan kira Abban sa, ni ma ina tafe Insha-Allahu. Ina Zarah take? Ita ma lafiya ko? Ta amsa,"Eh tana can wajen sa." To shi kenan, ki koma ku natsu, kin ji? Ta ce,"To." Ta aje waya tana share hawaye, ta koma dakin ta gaya wa Zarah ta kira Abbanta. Suna nan zaune, sun ta sa yayan na su, sun rasa abinda za su yi masa, kan sa na bisa cinyoyin Zarah. Ya bude ido da kyau, ya ce,"Mai gadi ya shigo kuwa? Suka girgiza kai a tare, suka amsa,"Bai shigo ba." "Ko sun kashe shi ne? Ya kara firgita su. Nusaiba ta mike,,"Bari in dubo shi." Ta mike Zarah ta riko ta,"Yanzu ke sai ki fita? Yana daga kwance ya zura mata ido ya ce,"Lallai ke ba ki da hankali, to fita, su kashe ki ke ma. Ba ta ce komai ba, ta dawo ta zauna. Amma a son ranta da sun kyale ta fita za ta yi, ta dubo lafiyar Mai-gadin su. Tunda ba su ga ya shigo ba, bayan fitar 6arayin, tabbas akwai dalili. Wani sabon tausayin su ya sake rufe ta. Nan da nan hawaye suka tsinke. Nusaiba akwai tausayi, sam-sam bata son ta ga mutum cikin wani yanayi na rashin jin dadi, gaba daya hankalin ta tashi yake yi. Tun daga Kaduna Alh.Basheer ya debo 'Yan sanda mota 1, motar sa na gaba, suna bin sa a baya. Hajiya Zulai tayi shiru tallafe da kuncu bata tunanin komai, illa tausayin sirikin ta. Allah ya sakko masa da jarabci kufi da kufi. .Tayi ajiyar zuciya, ta ce,"Allah ka mayar masa da alkhairi." Alh.Basheer ya ce,"Amin dai, wannan Yaro ai sai an mike masa tsaye da addu'a. Domin ina ji masa tsoron mahassada." Ta ce,"Kai dai bari. Allah abin tsoro,mutum abin tsoro. Ubangiji ya raba mu da kowanne irin sharri." Ya sake fadin Amin. Cikin mintoci 45 suka iso Zariya. Gidan su Abba suka fara wucewa, suka dauko su kamar yadda Alh. ya ce su jira shi, yana tafe da "'Yan sanda. Gari ya fara shaa! Zai waye, suna iso wa (Hanwa Low-coast). Get din gidan na bude, shigewa kawai suka yi. Tun daga nan 'Yan sanda suka fara ganin shaida, domin kuwa Mai- gadi na daddaure, an like bakinsa banda dan banzan dukan da ya sha na fitar hankali. A bakin kofar falo, suka ci karo da su Zarah, wani sabon kuka suka fashe da shi. Gaba dayan su, su Ummi suka rungume suna rarrashi, sannan suka dunguma inda Naseer yake, yana kwance gefen idon sa ya kumbura sumtum! Wajen da aka buga masa kan bindiga. Sallallami kowa ke yi. Su Abba suka tarairayo shi, ya na fadin," "Sun k'ara karya ni Abba. Sai an sake min dori." Babu 6ata lokaci suka sa shi a mota zuwa gidan dori, suka bar 'yan sanda na yi wa matansa tambayoyi. Shi kan sa Mai-gadi tare da shi suka tafi, aka ja masa targade 3 ajikinsa. Daga can suka kai su asibiti, don samun magunguna. Karfe 10 na safiya suka dawo. Gida ya cika. Inna ta dubi Naseer, duk ya muzanta, ya sauya kamanni. Hawaye fal ya cika idanuwan ta, ta ce,"Wannan Yaro ka na ganin tashin hankali. Allah ka yaye mana masifa." Duk saura suka ce Amin. Kowa ya ga Naseer yadda ya galabaita, sai ya tausaya masa. Haka Sageer da Yakubu suka yi shiru, suna masa duban tausayi. Naseer B kuwa fadi yake cikin ransa,"Ba shi fafa ba? Ya wani fito da mota mai nishi, yana kece raini a gari. Ba dole 6arayi su biyo shi ba. Ai ga irin ta nan. Allah sarki, ko alama Naseer B bai yi wa takwaransa halacci ba. Da Naseer zai gane daya tabbar da cewa lallai ba k'aramin sa'a yayi ba a rayuwa, tunda har Allah yayi masa baiwar da wani yake kallo, yana masa hassada." Bayan sallar azahar iyayen su suka koma gidajen su. Alh.Basheer kam ya kara jaddadawa Malam Balarabe maganar nemar wa Naseer taimakon addu'a. Malam Balarabe, ya san yana yi masa cikin sallolin sa , farilla da nafila, amma duk da haka, ya amsa wa Alh. Basheer da lallai za su kara kaimi shi da Umman sa. Shi kuwa Naseer bayan tafiyar kowa, yana zaune bisa Canis kafet. Falo jingine da kujera. Su Zarah na kicin suna wanke-wanke. Ya kwala mata kira ta zo. Ya dube ta fuska daure, ya ce,"Ki je maza daki, duk abinda ki ka san nawa ne, ki zuba min a jaka. Ke ma ki hada da na ki kayan za mu koma Tudun Wada? "Saboda me? "Saboda ra'ayina can ya koma. Ta kada kai, "A'a yayana, 6arayi sun firgita ka, kawai za ka ce. Amma ni ban ga dalilin komawar mu Tudun Wada ba." Haushi ya kama shi ya ce, "Eh haka ne, koma me za ki ce. Za ki je ki hada min kayan, ko in tashi da kai na? Ta kwala wa Nusaiba kira, ya 6allo mata harara ya ce,"Ke na ce ki hado kaya, ina ruwan ki da ita? Bata tanka masa ba har Nusaiba ta iso,"Menene Antina? Ta ce,"Ki zo ta mu ta same mu. Yayanmu ya ce mu hada kayan mu Tudun Wada za mu koma." Saboda me? Kafin ta ba amsa. Naseer ya yi kukan kura ya tashi ya bar falon. Suka bi juna da kallo, kafin Nusaiba ta matso kusa da Zarah, ta ce,"Me ya faru Antina? Fuska yamutse ta amsa, "Ooho, amma zai wuce maganar 6arayin nan ne? Ni ma shi na gani, zo dai mu je mu same shi."Cikin daki Naseer ke ta hada kayansa da hannun daya, cikin jaka. Gaban sa suka tsaya Zarah ta fara cewa,"Yanzu yayanmu da gaske ka ke yi? Ai da ka san haka ne, sai ka tada maganar a gaban su Abba ka ji me za su ce? Ya ce,"Kuma shi kenan ba ni da wani ra'ayi nawa, komai sai an takura ni? Ba zai yuwu ba, kin gane ko? Ke ba ki da wata hujjar ma da za ki ce ba za ki koma Tudun Wada ba. Gara wannan ita nan gidan Babanta ne, ko bata biyo mu ba, tana da hujja. Idan kuma duk anan za ku zauna, ba matsala, na gama magana, kar wace ta sake yi min wata." Ya suri jaka yayi waje. Su kuwa sansarai suka tsaya suna kallon ikon Allah, duk jikin su yayi sanyi, ba ma kamar Nusaiba, domin kalaman Naseer ba su yi mata dadi ba. Hawaye suka cika idon ta, ta dubi Zarah ta ce,"Antuna, me yasa yayan mu ke fadar wannan maganar ko gidan Baba na ne, zaman wa na ke yi a cikinsa? Hasalima Abba na bai ce ni ya ba gida ba." Zara ta kamo ta cike da tausayi, ta ce,"Kar kiyi kuma amarya. Ba wani dalili yasa yayan mu wannan abin ba, illa firgici 6acin rai." Ta ce,"Amma ai mu yakamata ace mun shiga wannan halin ba shi ba." Koma dai menene, ki manta kawai amarya, yanzu menene abin yi? Ta ce,"Abin yi bai wuce mu bi shi ba, duk abinda Abbansa ya ce, shi za'ayi ko? Shi kenan, je ki hado 'yan kayan bukata, mu tafi."Kowacce ta nufi dakin ta. Nusaiba kam jikinta a salibe yake akan maganganun Naseer, musamman da ta tuna da hudubar Abbanta kafin a kawo ta gidan miji: "Nusaiba, babu abinda za ki yi a rayuwar ki gaba daya a halin yanzu, wanda ya fi biyayya ga mijin ki. Ki sani da Ummanki da ni Alh.Basheer, ba mu da ikon komai a kanki, saboda girman darajar aure. Sai abinda mijinki ya hukunta akanki. Saboda haka Nusaiba kar ki dauki aure da wasa, ki yi amfani da ilimin ki, domin a yanzu ne yake da amfani a gare ki. Magana ta gaba wacce na ke son gaya miki, ita ce, koda wasa ban lamunce miki yin wata magana akan abubuwan da na mallaka wa Zarah da mijinku ba. Ina nufin gori, da babbar murya na ke miki wannan maganar. Duk ranar da ki ka gorantawa daya daga cikinsu, ban yafe miki ba, domin kin watsar da mutuncin ki, kuma kin rusa tarbiyar da muka baki. Ba kuma sai na gaya miki ba, kin san matsayin matar da ta yi wa mijinta gor.......... Ta share hawaye, ta zage zif din jaka, tana fadi a ranta,"Har abada ba zan baka kunya ba,"Abbana." Muryar Zarah ta jiyo tana fadin,"Amarya kin gama? Ta amsa, Eh. Suka kwaso kayan bukata, suka kulle ko'ina, suka fito. A zaton su Naseer na waje, yana jiran su, tunda ba su ji tashin mota ba. Ashe shi tunda ya fito, ya tako ya tsare aca6a, ya haye yayi tafiyar sa. Mai-gadi ke gaya ma su tuni ya fice. Kallun juna suke yi baki sake. Dole Nusaiba ta koma ta dauko makullan motar ta, ta ja suka bi shi. Ita Zarah ta san rigimar Naseer, shi yasa, ma abin bai dame ta ba. Nusaiba kuwa abin 2 ya hade mata, damuwar da Naseer ya shiga, ga kuma maganganunsa, ba su yi mata dadi ba. Sannu a hankaki Zarah ke ta warware mata kullin zuciyar ta, ta hanyar dibar ta da labaran wasu abubuwan da Naseer din yayi na jarunta. Al'amarin kuma ya koma daure mata kai. Ta saki waccan maganar, ta koma tana tambayar kan ta, me yasa yau ya tashi hankalinsa haka akan 6arayi? Zarah ma oho ta ce, shi yasa har suka iso kan ta na daure. Suka yi sallama cikin gidan dauke da jakunkunan su. Umma ta fito ta tar6e su,"Ku shiga yana nan falo. Ko kunya bai ji, wai ya taho ya baro ku can. Naseer ai baya gajiya da abin fad'i. Yana zaune gaban Abba suka zube suka yi gaisuwa. Malam Balarabe ya dube shi, ya nuna su "Yanzu ba ka ji kunya ba? Koma menene, ai sai ka hado matan ka ku tahu tare, kai dai kullum bahagon mu2m ka ke. ba ka sauyawa. Wai ma in tambaye ka, me ka ke nufi da kun baro can? Rai 6ace ya ce,"Ni fa gaskiya Abba ba zan zauna gidan nan ba. B'arayi na ganin bangajejen gidan suna shigowa ba sa mun komai, wata rana kashe ni za su yi, kar fa ka mance Abba ni fa ba mai kudi bane, rufin asiri ne kawai. Saboda haka nan zamu zauna, idan ina son asirina ya kara rufawa.Malam Balarabe yayi dan shiru, saboda Naseer yana da dalilai masu karfi. Can ya dan nisa ya ce,"To ka gaya wa Alhj ko? Ya kada kai,"Ban gaya masa ba." Umma ta amsa,"Ka ji matsalar ka, tunda ya zo yakamata ka yi maganar nan a gabansa, amma ka ki, me zai ce? Malama, ni ban goyi bayan zaman su anan ba. Su koma. Ya kira Alhjn a waya, ya gaya masa tukuna." Ran Naseer ya k'ara 6aci, ya zuba wa Ummansa ido, tunanin sa kuwa, shi kenan kuma yanzu ba shi da wani ra'ayi, sai abinda Alhj ya ce, ya runtse ido, ya cije le6e,"Na shiga uku. Alhj ya mallake min iyaye. Ya fada cikin ran sa. Ya bude ido, ya dubi Umma,"Gaskiya Umma, sai dai ki yafe min, na riga na baro Hanwa, ba zan koma ba, Idan kuma ba kya son rayuwa ta, shi kenan, zan kai kaina a kashe." Nusaiba tayi wuf ta ce,"Umma, ku kyale mu mu zauna anan din. Ni na san Abba, ba zai ce komai ba. Kuma kula da kaya, ai ya fi ban cigiya. Tunda yana ganin nan zai fi mana sirri, sai mu zauna, ko Antina? Ta ce,"Gaskiya ne,Umma ku kyale shi kawai."Umma ta nisa kafin ta ce,"Ka ji Malam, yanzu wa zai kira Alhjn yayi masa bayani?" Ya ce ,"Shi mana. Ba shi ke da uzirin ba? Je ki dauko masa makullin sasan su, su gyara."Umma ta mike, ta wuce dakin barci. Malam Balarabe ya ci gaba da fadin,"Ka dauki waya yanzu-yanzu ka kira shi, ka gaya masa." Ya dauko wayar sa ya mika mai,"Ungo yi anmfa da tawa." Yasa hannun hagu ya amsa yana neman layin. Umma ta kawo makullan, ta mika wa Zarah. Ta kar6a suka fito tare da Umma. Tsarin ginin yayi matukar burge su, musamman Nusaiba. Ita kan ta, ta tabbata babu laifi Naseer ya kashe wa gidan kudi. Umma ta kawo tsintsiya da abin goge-goge, ruwa cikin bokiti da Omo. Nan da nan suka gyara wuri ko wacce ta za6i dakinta. Alh. Basheer kuwa abin dariya ma ya ba shi. Nan take ya yanke hukuncin ya ce duk su zauna har zuwa lokacin da hankalin su zai kwanta. Babbar mota yasa Sageer ya samo, su Zarah suka je suka kwaso iya kayayyakin da zasu iya debowa. Suna ta aikin gyaran Waje. Umma na taya su. Shi kuwa dan gogan yana kwance karkashin inuwa inda aka zuba masa shimfidar karamar (ChaniS Carfet) suna hira da Sageer. "Ai ni ban san cewa kai matsoraci bane, sai yau. Ashe gaba da gabanta. Aljani ya taka wuta. A taurin rai irn na ka, ban ta6a zaton akwai abinda zai hana ka sukuni ba." Yayi wata 'yar dariya, shi kadai ya san ma'anar ta, kafin ya ce,"Kowa ma hakan yake fadi, dazun nan Inna ta zo ta gama min tsiya. Amma ka san wani abu? Ina sane da abinda na ke yi. Kawai yarinyar nan na ke so na kure, a zato na za ta ce ba za ta biyo ni ba, ko iyayen ta. Ka ga na sami wata kafar taso da rigima. Sai kuma ta ba ni kunya mayyar." Wani zabgegen tagumi Sageer yayi, yana kallonsa, wani haushi ya kama shi, ya jima kafin ya ce,"Ni kai na da ni na aikata ba na ji kunyar. Yanzu kuma sai yaya? Ya ce,"Haushi ka ji? Idan ba na yi, ina nuna ni ma na isa ai raina ni za'a dama ta samu kuwa, dole in yi amfani da ita tun kafin yarinyar nan ta yi min gori waya rana. Ka san mata. Ni ban damu da shirgin ta ba, ta nemi ta raina min wayau." Sageer ya kada kai, ya ce,"Duk rashin soyayyan ta ya kawo wannan matsalar. Saboda haka magana ma 6ata baki, sai dai a kullum ba zan daina gaya ma ka, ka bi a hankali ba. Ni zan koma. Allah ya k'ara lafiya, ya kuma tsare na gaba." Ya ce,"Amin." Je ka, kai dama ai ba abokin kuka bane." Na ji, a nemi abokin kuka a gaya masa, ranar da ta dariya ta zo, kar ace an san mu." Ya mike ya wuce, yayi sallama da Umma da su Zarah. Suka yi masa godiya, ya fice, ya bar gidan, ba tare da sun sake cewa juna affan ba, shi da Naseer. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ BAYAN WATA BIYAR a hankali Nusaiba ta fara fahimtar irin zaman da su ke yi da Naseer, tamkar zaman doya da manja ne. Haka ya bata daman gane banbancin karara yake nunuwa tsakanin ta da Zarah. Al'amarin ya soma damunta, saboda ta ka sa gano dalilin da yasa hakan ke faruwa? Su kuwa iyayenta a kodayaushe kokarinsu ta zauna gidan mijinta tana mai ladabi da biyayya. Watannin 5r kenan da barin su Hanwa, kuma tuni hannun Naseer ya warke, amma Alh. Basheer ko Umminta babu wanda ya sake ta da zancan su koma can. A tunanin su babu komai, tunda suna jin dadin zaman su anan Tudun Wada, kusan duk abubuwan da aka sace masu, sun maida masu sabbi. A yanzu ba abinda Alh.Basheer ya fi maida hankali a kai, shine ya g a Naseer ya koma makaranta sosai,hankalinsa ya karkata ga karatun sa, akan ya dawo wasa gadan-gadan. Shi kuwa Naseer kallon hadarin kaji yake wa kowa. Komai aka ce yayi, sai ya nishadantu sannan yayi shi. Shi a dole da kan sa yake so ya ja akalar sa. Safiyar wata juma'a Zarah ta tashi da wani azababben zazza6i mai dafa jiki. Hankalin Nusaiba ya tashi lokacin da ta shigo dakin, don ganin yaya Antinta ta kwana? Nusaiba ke da girki, kuma wannan al'adarsu ce kullum safiyar su binciki yadda dayansu ya kwana. Wannan halastacciyar dabi'a mai kyau ce, kuma hakan shi ya wajabta ga kowanne musulmi a hakkin zaman tare. Da gudu ta koma dakin Naseer, barci mai dadi ne ya dauke shi. Bata san lokacin da ta dasa hannunya a jikin sa ba, ta hau bubbuga shi, "Yayanmu! Yana ji, ya kyale, haushi da takaici duk suka yi masa bargo. Idanuwanta suka kawo kwalla, muryar ta, ta soma rawa,"Yayanmu, don Allah ka tashi,"Antina ba lafiya......... Bata gama fada ba, ta ga yayi wufe ya mike, ita da ke duke gefen gado har ya riga ta ficewa. Ta biyo bayansa, cikin sauri ta iske shi a dakin. Bisa gadon ya haye, ya yaye bargon yana kira. "Zarah! Menene? Jikinta yayi zafi sosai, tana rawar sanyi, ta kasa magana. Ya rumgumo ta jikinsa." Zarah! Bude ido ki dube ni, ina ke miki ciwo? Da kyar ta iya fada,"Zazza6i.""Tun yaushe? Ta ce"Da shi na kwana. Ku kai ni asibiti." Idanuwan sa suka kada nan da nan. "Haba Zarah, ya za ki kwana da ciwo ba ki yi Magana ba? Ai haka babu kyau. Zarah menene amafani na a gidan nan? Hawaye suka tsunke wa Nusaiba, ta juya da gudu, tayi waje ta nufi sasan su Umma. Shi kuwa Naseer tuni ya kule, iya wuya. Duk yadda yake ji da matarsa, ace ta kwanta cikin wani hali babu taimakon kowa, alhali yana cikin gidan nan da ransa. Me ya jawo wannan, in banda zaman Nusaiba cikin gidan nan. Ba don haka ba, me zai nisanta shi da abar son sa na tsawon awa daya balle a kai ga kwana? Har ta kwana yashe ita kadai cikin mawuyacin hali, abin tausayi. Ya runtse ido, tamau, kamar ya kwarma ihu. Tabbas an rusa masa shirin tsarin rayuwar da ya ci burin yi da Zararsa. Ya kuwa zama dole ya tsani duk wanda ya zama sila ko shi waye. Muryar su Umma ya ji suna fad'in, "Ka zauna ka rike ta a daki? Asibiti ya kamata ayi maza-maza a kai ta." Umma ta amso ta daga hannun sa, suka shirya ta tare da Nusaiba. Suna tafe a mota, yana k'ara wa kan sa zafi da tunanin abinda ba shine ba, a iska yake sawa ransa kunci, har ya soma sambatu cikin zuciya. "Gaskiya ina son na sake da mata ta. Wannan ai cutarwa ce." Ya daki sitari tare da ajiyar zuciya. Umma ta ce,"Je ka a hankali Naseer, za ta sami sauki da yardar Allah." Sun ga Likita, ta sha bincike da gwajegwaje, sakamako ya fito k'arara Zarah na dauke da ciki wata 2 cif. Ba karamin girgiza Nusaiba tayi ba, kuma take nan ta warware wa zuciyarta sark'ak'in da ta shiga na me yasa Naseer yake nuna bambanci a tsakanin su? Amsar kawai baya son ta ne. To me ya sa ya aure ta? Tambayar da bata gano amsar ta ke nan ba, har suka dawo gida. (Tofa me Nusaiba take nufi Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 2-03 Posted by ANaM Dorayi on 11:45 PM, 11-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______. . . Cikin Zarah wata 3 kenan har yanzu ba wata lafiyar kirki ta cika ba. Duk ta rame ta dushe. Gaba daya ayyukan gidan Nusaiba ta dauke mata, ga shi kuma tana kula ita sosai, a lokutan da Naseer baya gida. Sai dai tsakanin ta da shi ido ne kawai. Ba wai abubuwan da yake yi ba sa damun ta ba ne. A'a kokari take yi tana hadiye wa, saboda farin cikin Abbanta. Shi kuma Naseer matsalarsa ke nan, rashin nuna damuwar ta, so yake ya cusa mata, ta ji haushi ta nuna 6acin ranta a fili. Amma ko alama ta ki. Yau yana Kaduna don amsa kiran Alh. Basheer. A offi ce ya same shi. Yayi gaisuwa kamar yadda ya saba. Alhj ke fad'in,"Saura kwana hudu mu tafi Katsina, ban ga ka na zuwa atisaye ba, kamar yadda ka saba? Ya shafa keya, ya sunkuyar da kai,"Kodayake ku manya ne, ba ha bukatar atisaye." Ya kada kai,"Ba haka bane Alhj. Ka san jibi za'a fara rubuta (External WAEC), ina zuwa wasu 'yan (Lesson) ne shi yasa, "O.K." na ji. Yana da kyau haka. Za ka sami zuwa Katsina kuwa? Ya ce,"Watakila in sami zuwa, sai dai na duba (Time table) tukuna." To Allah ya bada sa'a." Amin." Ya amsa. Yayi shiru, kamar wanda ruwa ya ci. Da ka kalle shi, ka san a susuce yake. Alhj kan sa ya gane hakan, shi yasa yake ta kallo sa. Jim kadan ya dago, ya dube shi, suka hada ido, ya ce,"Zan karasa wajen su Yakubu.Ya ce,"To shi kenan. Daga can za ka wuce gida ne? Ya mike yana fad'in, "Eh!" A gashe su don Allah." "Za su ji." Ya wuce. Alhj ya raka shi da kallo. Kai bai yarda ba, akwai abinda ke damun Naseer, don haka har ya kai kofa, ya kira shi, ya dawo ya ce da shi,"Zauna Naseer." Ya ja kujera ya zauna. Alhj Basheer ya dube shi da kyau ya ce,"Naseer ni na gaba daya ka sauya min. Ba ka da kuzari kamar yadda na san ka. Me ke damun ka? Gaya min." Yayi dan yake ya ce,"Babu komai Alhj." Ya ce,"A'a ban yarda ba. Look Naseer, ni Babanka ne na dauke ta tamkar dan na haifa a ciki na. Kar ka 6oye min komai, idan akwai abinda ke damun ka, ka gaya min, muddin bai fi karfi na ba, zan maka maganin sa." Ya sake girgiza kai ya ce,"Allah, Alhj babu komai." Yayi jim, yana kallon sa kafin ya numfasa ya ce,"Shi kenan, ina sauraron ka, idan dai ka ga da matsala tafiyar nan, mu na iya dage wasan har zuwa lokacin da za ku gama (Exams) din, ko me ka ce? Ya ce,"To zan duba in gani." Ya mike,"Zan tafi." Ka gaida Abban ka da kyau." Ya wuce yana amsawa, Alh. Basheee yayi shiru, yana tunanin, amma sam ya kasa gane kan al'amari, ga shi a zahiri ya san Naseer ya canza, ba haka yake ba, musamman idan suna da wasa, ya fi kowa kosawa a tafi. To ko har sha'awar wasan ma aka cire masa a rai? Ya tambayi kan sa. Wani sabon tausayi ya lullube shi, ya ce,"Allah ka shiga tsakanin mu da makiyan mu." Shi kuwa dan gogan tafe yake, yana mamakiin yadda aka yi ya koyi shara karya. Shi da ko biyan kudin jarabawar bai yi ba, amma yayi ruwa yayi tsaki akan zai rubuta jarabawa. Yayi dan murmushi, ya ce,"Allah ka shirye ni." Ya jima wajen su Yakubu, suna ta hirarrarkin duniya, sannan ya baro Kaduna, ya dawo Zariya. Kai tsaye shagon dinkinsa ya wuce, ya iske Sageer na zaman jiransa."Dariyar me ka ke ta faman yi ne haka? Ya jawo wata dirowa, ya dauko ambluan ya mika masa,"Ta mece ce? Ya ce,"Kai dai bude. Ka gani." Ya bude, ya duba sannan ya dube shi baki sake." "Teaching ka samu a (Barewa College)." Yaushe Appointment din ya fito? "Dazu aka kira ni, aka ba ni. Ban dade da dawowa ba. Ina samun (Part-time) kuma zan wuce in ci gaba da Digree dina. Yayi murmushi ya ce,"Ka haye Yaro." Allah ya sanya albarka." Amin." To kai ya bayanin karatun? Yayi dan tsaki,"Zan yi mana." Kullum haka ka ke cewa har an gama biyan kudin (External) ka na kallo, ka ki biya. Me yasa saboda Allah? Yakamata ace rashin son karatunka tun na yarinta ya wuce." Ya ce,"Ni na gaya ma ban son karatun ne? Kawai haushi aka ban, na fasa." Ya 6alla masa harara,"To wa kai ma wa? Ya ce,"Kai nai mana." Bata yuwuwa haka Naseer, abinda zai amfane ka, har wani zai ba ka haushi ka fasa?Ya ce,"Zancan ka ke so. Ai ni ma na san abinda na ke yi., Wai don ranin wayau, sai da zai ban 'yar sa yake tambaya ta, ya maganar karatu? Diploma gare ka ko Degree? Ya fadi yana kwaikwayon salon maganar Alhajin. Sageer ya tsura masa, ido,"Ba ka da kunya Wallahi, sirikinka? Ya ce ,"Kyale ni, lokacina na ke ci. Duk lokacin da na nishadantu, na koma makaranatar! Kai me ma sunan ka? Kullum mancewa na ke." Ya tambayi cikin yaran shago. Ya ce,"Abbas." Yawwa Abbas, kwaso min kayan koyon dinkin nan, ka ji? Ya tashi yana fadin,"To." Ya dubi Sageer ya ce,"Yanzu fa sai ka ji haushi na ko? Wai me yasa ba ka goyon baya na ne? Yayi dan tsaki mai dauke da takaici, ya mike ya koma bisa keken aiki, ya ci gaba da yi wa kayan gaban sa aiki." Yayin da Abbas ya kawo wa Naseer kayan koyon dinkin sa. Maida su kawai, maida su." Yaro ya juya da su. Shi kuma ya mike, ya fice daga shagon yayi gida." ********************** Zarah na jingine da gado. Nusaiba na bisa Kujera, suna ta faman hira. Sallamar yayansu suka amsa. Sannan suka hada baki yi masa sannu da zuwa. Wajen Zarah ya nufa, ya zauna bakin gadon ya sumbaci kuncinta, ya ce,"Zarah ta kenan. Maman Bebi ya kike? Ta dan kirne fuska rumgume da hannayenta a kirji, ta zura masa fararen idanuwanta da su ka kara tabbatar yana yin da take ciki. Shi yasa take kara masa kyau. Yayi murmushi sosai, ya sake fadin,"Bebina ya kara miki kyau, ba ki ga yadda ki ka dawo ba. Balarabiya sak! Yana sa aya. Nusaiba ta mike ta bar dakin." Ya bita da kallo har ta fice, sannan ya maido da fuskar sa ga Zarah, ya ja dogon hancin ta, ya ce,"Me ki ke marmari, in je in nemo shi? Ta ce,"Abinda ka ke yi ba shi da kyau, kuma baya min dadi, kullum ina gaya maka zancan nan. Ga shi nan tun bata jin haushi, yau ka kure ta. Ya ja ha6arta, ya ce,"Shine ki ke 6alla min harara? Ba zan yi wasa da mata ta ba? A wane nafsin aka haramta min hakan? Ta ce,"Ba'a haramta maka ba, amma an umurce ka da dalci, kuma an wajabta maka shi. Gaskiya ba na son abinda ka ke yi." Ya dan mari kuncinta, ya ce,"Ni ina so, ba ki ji dadin da na ji ba yau, ba na bata haushi." Ta dan lumshe ido, ta kauda fuska." Nusaiba ta yi sallama. Zarah ta amsa. Ta shigo dauke da tire karami. Ruwan sanyi ne da Jus na kwali da kofuna 2, ta aje gaban sa. Yadda ya zura ido, yana kallon ta, tana zuba masa ruwa. Shi ya ba Zarah dariya. Ta gode Allah da Nusaiba ba haushi ta ji ba, hasali ma ruwan sanyi ta je kawo masa ya sha, ya ji dadin rashin adalci." Ta sa hannu ta, ta mintsile shi, ya dan zubara, ya dube ta. Ta daga gira, tana masa murmushi mugunta. Ya juya kan Nusaiba, ya ce,"Daina zuba ruwan nan, ba sha zan yi ba. Ta aje, ta mike ta ce,"Antina bari in je in dan kwanta, tunda ga yaya na nan ko? Ta ce,"Ayi barci lafiya amarya." Bata saurari komai ba, ta koma dakin ta, ta kwanta tana ta sake-sake har barci ya sace ta. ***************** Yana zaune a shagon dinkinsa, baya aikin komai, alhalin suna da wasa A Kaduna, amma ya ce wa Alhj ana neman su a makarantar da ya ce ya samu. Sageer na ta dinkin wata atamfa. Naseer ya katse shi da tambaya. "Ban gane bane, kodayaushe yarinyar nan ta kawo dinki, sai ka aje na kowa, ka kama na ta. Ta fi sauri biyan kudi ne?" Yayi 'yar dariya, ya ce,"Sa'ido kuma ka koma?" Fa'iza ai kostoma ta ce, dole in yi mata dinki." Ya kalle shi a dage,"Amma kai ba karamin dan rainin hankali bane,"Don tana kostomar ka, sai ka aje dinkunan da suka yi sati 4, ka kama wanda aka kawo jiya? Jiyan ma da yamma." Fada ka ke min, kome? Ya ce,"Ban sani ba. Bari kuma ta zo, sai kun gaya min abinda ke tsakanin ku, kafin a bata dinkin nan. Ina nan ina jiranta." Sageer yayi wata bazawarar dariya,"Ashe za ka kwana anan. Kai idan ma ka ban haushi, sai in kai mata gida, in ce ta bar kudin." Ya nuna su Abbas,"Ka ga 'yan yaran nan? Su za ka yi wa barazana, ba ni ba. Za to zo ta same ni, ka san halina, ban kyalewa." Ya dan kura masa ido, sannan ya baro inda yake, ya zo wajen sa ya kamo shi,"Zo ka ji wata magana." Ya fizge hannun sa,"Babu abinda zan ji Malam." Ya jawo shi da karfi."Taso mana, wani sirri za mu yi.". Ya taso suka fita waje. Me yaran 2 za su yi, ba dariya ba, suna wa juna rad'a,"Yau an k'ure oga Sageer." Suna fita. Naseer ya ce,"Yi sauri ka fadi abinda za ka fada, in koma." Ya ce,"Don Allah kar ka yi min fallasa gun yariyar nan." To menene na aje dinkin wasu ka yi na ta? Ya ce,"Gaskiya sonta na ke yi, ta kuma jima tana kawo min dinkunan ta da na 'yan gidan su, amma ni ban yi karanbanin gaya mata ba." "Saboda me?" Ina tunanin wasu abubuwa ne. Ka ga bai kamata in fara neman yarinya ba. Tunda ba aure na shirya yi ba. Amma yanzu zan taya, in gani idan tana so, shi kenan." Ya kai masa duka a kafada, yana 'yar dariya." Shine za ka dame mu da cuwa-cuwa a shago, ai gara a gaya mata, mu san cewa ta mu ce. Ka ga ko ni, sai in dinka, bari, mu je ka gama dinkin, a sa a leda mu kai mata gida. Ka san gidan na su? 'Yar layin Rimi ce." Ba matsala. Allah yasa kar ka sha kaye." Daina fadi, kar ka sani hawan jini." Suka dawo ciki, suna dariya tare da tafawa. Karfe 6, dai-dai, suna dawowa daga layin Rimi. Cike da farin ciki Sageer yake, domin Fa'izah bata ba shi kunya ba. Da hannun bibiyu ta kar6i tayin sa. Kusan ita ma ta dade da kaunar Telanta Sageer cikin ranta. Kofar shago suka yi fakin, lokacin da wayar Naseer ta dau kuka, ya zaro ta, gaban aljihu ya duba.Tsaki yai, ya mika wa Sageer, ya ce,"Don Allah gaya mata na bar wayar caji ne a shago." Ya amsa, yana dubawa, sai ya ga sunan Nusaiba. Ya dube shi a yamutse ya ce,"Ban gane ba? Ka san abinda ke faruwa a gidan? Kuskure ne wannan. Naseer ka daina." Wayar ta katse. Yana can yana tunani. Gaskiya ne kuma, haka banza Nusaiba bata kiran sa a waya. Shi yasa tana kara daukar ruri, ya figi wayar a hannun Sageer, ya danna O.K. Ya sawa kunnan sa, "Menene? Murya na rawa, ya ji tana fadin,"Jikin Antina ya rikice, ka zo a kai ta asbiti." Ido waje ya aje waya, yayi wa mota key, ya ja ta a guje." Menene? Sageer ya tambaya. "Wai jikin Zarah ya rikice. Ka ji ba...........?" " Yi shiru haka, don Allah." Ba zan yi ba, kai gaskiya ce ba ka so, ba kuma zan daina gaya ma ba." Yayi banza da shi, yana ta surutun sa. Baya ma jin abinda Sageer ke fadi, don ba shine damuwar sa ba. Yana fakin kofar gida, ya fito cikin sassarfa, ya fada gida. Sageer ya biyo bayansa. Suna tare da Umma a dakin Zarar, sai murkususu take, ciwon ciki da mara, nan da nan suka dunguma asibiti, ko kafin su isa, jini ya tsinke mata, shi yasa suna zuwa dakin 'yan 6ari suka wuce da ita. Hankalin kowa ya tashi, ba kamar Naseer da yake jin zuciyar sa na kokarin tsago kirjin sa. Saboda tsabar firgicewa. Haka idanuwan Nusaiba ya raina fata, tana zaune ta cusa kai cikin guiwa. Addu'a kawai take yi, kama-kama har bayan isha'i, sannan cikin dan wata 4 ya fita.Idanuwan Naseer suka yi ja, amma jin Zarah na nan lafiya, sai yayi wa Allah godiya. Anyi mata wankin ciki, ta dan hutu zuwa tara da rabi, na dare, suka dawo gida. Washegari Nusaiba, ta hado kayan karin safe, ta shigo masu da shi dakin Zarah. Tana zaune gefen gado, ta dubeta, ta ce,"Mun yi waya da Kausar dazu, ta ce, in gaishe ki, su Ummi ma ta ce za su zo anjima." Ta ce,"Ina amsawa. Kausar ta ba mu kewa, tunda muka dawo nan, ko ta leko mu." Ta ce,"Kausar ai ba mutunci, da anyi magana, ta ce karatu." Tana da gaskiya." Ba wata gaskiya Antina, ke dai sakko mu karya." Ta jefa filon kujera bisa kafet, suka fara karyawa. Naseer ya shigo ya dau wanka, kananan kaya ya sanya. Ya zauna gefen gado. Zarah ta hada masa Tea ta mika masa. Ya kar6a yana sha, suna 'yan hirarraki tare da Zarah. Wani lokacin Nusaiba kan tsoma baki, musamman idan ta fahimci Naseer ya ya6o mata magana. Bai tashi a dakin ba, sai da Inna ta zo duba jikin Zarah. Kwarai ta ji dadin yadda ta same su. Ba ta jima da zuwa ba,"Direba ya kawo Ummi. Sun dade suna hira a dakin Zarah, kafin Ummi ta koma dakin Nusaiba, suka gana tsakanin da da Mahaifi.. ********************* Shekara guda da rabi kenan da auran su, sau 2 Zarah na samun ciki, yana zubewa duk da dabarar da ake mata a asibiti na daure mahaifarta, saboda sun gano ita ce bata da karfi.Da zarar cikin ta ya kai wata 4, sai a daure, amma kash! Yana kai wa wata 5r, dole a bude ta, don samun lafiyar ta. Zuban jini kamar famfo, har sai cikin ya fita. Wannan shine ciki na 3n, kuma an daure mahaifar har bata hutu a asibitin watau (Bed rest). Wata 2, ta samu, bata aikin kome, illa ta ci, ta sha, tayi wanka ta kwanta. Kusan Naseer a asibitin nan ya tare a 'yan tsakanin nan, musamman da ya ga cikin ya tsaya har ya kai wata 6 da shiga na 7. Zaran kuwa zaman asibitinya ishe ta, ta damu kwarai, tana son su sallame ta, ta koma gida. Yau Naseer na Kaduna. Suna da wasa. Dole ce ta sa shi tafiya wasan, domin yau lahadi ce babu wata karyar da zai wa Alhaji. Ta karatu. Nusaiba ke tare da Zarah a asibiti tun safe. Abincin da soye-soye kala-kala tayo mata, irin wanda take sha'awar ci. Musamman (Cole-slow), tana bala'in son cin sa fiye da komai, ga shi Nusaiba ta iya yin sa, yadda ya kamata. Shi take ci. Bayan sallar azahar, hira tayi hira har suka fada zancan zaman ta asibitin. Ita ta fara fadin,"Asibitin nan ya ishe ni amarya, amma kowa ya ki bada goyon baya, in koma gida ko na dan sakata, in wala." Wata 'yar harara ta sakar mata,"Lallai Antina, da wa ki ka so ya goya miki baya?Ki na ganin an fara samun nasara, muna ta murna, shine za ki ce gida za ki." Ta ce,"Koma ke ki ke zuga yayanmu, kullum yana like da Doctor suna kus-kus? Ta ce,"Allah ko daya. Amma Ubangiji yayi wa mai zuga shi albarka. Me za ki zo ki yi a gidan? Ta nuno ta da cokali." Ki na son in kwashe hakoran ki kenan, kin san na koya wajen yayanmu." Tana 'yar dariya ta ce,"Allah Antina a daina maganar wasa, zaman ki anan yana da muhimmanci, su Doctors din ai sun san abinda suke ji." Tayi dan tsaki,"Don dai ba ke ki ke zaune wajen nan ba, shi yasa. Wai ma to ko a gidan na ke, aikin me zan yi? Taimakon da ki ke min, ai iyakar sa kenan, ko Inna hakan za ta yi min. Ga mai wanke-wanke Ummi ta turo mana. Dama can wanki yi mana ake yi, menene kuma ya rage, saboda Allah. Gaba daya babbar ka'idar ba'a son miji ya matsa min, yayanmu kuwa ba shi da matsala, matansa 2 ne. To ki gaya min menene bambancin zaman nan da gida? Ta sauke numfashi ta ce,"Ni dai ina shawartar ki Antina, ki yi zaman ki anan ba. Ta aje filet ta ce,"Sai ki ban hujja. Idan kuwa babu, kin san Allah ba zan sake kai wani sati anan ba. Sai na na san yadda na yi na tsere." Ta tsura mata ido,babu alamar wasa a zancan ta. Ina sauraron ki." Ta dan yi jim, kafun ta ce,"Hujja ta daya ce, akan babbar k'a'idar nan da ki ka fadi, gara a kiyaye, kin fa san yau da gobe sai Allah. Ta harare ta,"Ban son iskanci, ke zaman me ki ke yi,?" "Aure mana. Amma ina gaya miki ki yi zaman ki anan, shine rufin asirin mu, don Allah ki bar mu mu sami Bebin goyo." "Lallai kin maida abin wasa, za ki sha mamaki na." Ta ce,"To Anti ba sai ana son mutum ake kula shi ba? Ke ba za ki gane ba Anti, amma ina gaya miki, ki yi hakuri, saura 'yan watannin kadan ne." Gaba daya zuciyarta ta girgiza, domin nan take ta gane abinda Nusaiba ke nufi, sai dai a fuska bata nuna mata ba, kara maka mata harara tayi,"Ba ki da hujja amarya, so ku ke kawai ku azabtar da ni da zama waje daya kamar 'yar gidan yari ." Ta kamo hannun ta, tana 'yar dariya,"Antina kenan, Allah ya bar min ke. Ai shikenan, an wuce wurin ko? Ta ce,"Ya zan yi?" Tunda haka ku ka fi so. Ta mike ta dawo gefen gadon, ta dan rungumota,"Da me da me zan kawo miki gobe?" Ta ce,"Za6in ki, za6i na ne amarya. Ki kawo komai, zan ci. Yanzu za ki tafi? Ta duba agogo, sai zuwa 3 da rabi. Ta ce,"To kin ga idan za ki tafi ko ki rage kayan wajen nan sunyi yawa, ki bar min kwandon wanka da na burosh kawai.Wadannan zannuwan duk ki koma da su, gobe a kawo min wasu." Ta ce,"An gama Antina." Suka ci gaba da hira har zuwa 3 da rabi. Nusaiba ta kwashe kaya, kamar yadda Zarah ta ce. Tun da Nusaiba ta tafi. Zarah ke zaune bisa sallaya, 6acin rai cunkushe cikin zuciyar ta, bata san lokacin da hawaye ke satata ba, Sabida tsabar tausayi da takaici. Tana ganin wayar Naseer na ta kururuwa. Amma ta ki dauka, yayi kira ya fi sau 5, sannan ya aiko sako, shi ma bata bude ba, balle ta san me ke ciki. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Karfe 8 bayan sallar isha'i, Zara ta had'a 'yan abubuwan da suka rage, cikin jakar hannun ta, ta faki idon kowa, ta fiyo a hankali ta bar asibitin. Aca6a, ta haye ya aje ta gida. Bata yi sallama ba, har ta shigo cikin gida. Umma na can ciki tana sallah. Abba kuwa bai dawo daga masallaci ba. Don haka ta wuce da sauri sasan su, ta tura falon ta shiga. Shirin na ta gwanain sa'a, domin Nusaiba na can bayainta tana wanka. Saboda haka ta wuce dakin ta. A rufe yake, amma ba da makulli ba, tayi hamdala ta shige, ta mayar a hankali ta rufe. Ta aje jaka ta koma gado ya kwanta don hutawa, don bin dokar likita. Naseer bai shigo Zaria ba, sai tara saura kwata, kai tsaye asibiti ya wuce don ganin Zarah tare da neman sanin dalilin rashin daukar wayar sa.Kowa na bisa gado, amma gadon Zarah babu kowa. Ya tambaya. Suka ce su ma ba su ganta ba, babu ma wanda ya san lokaci da ta bar asibitin. Hankalin Naseer in yayi dubu, ya tashi, ya bude wa Nosis wuta masifa yake kamar ransa zai fita. Da kyar suka samu ya sassauto ya saurare su. A inda suka shawarce shi da ya je gida ya duba, tunda ga shi babu kayanta ko daya sai 'yar karamar kular abinci kan dirowa. A fusace ya fice asibitin baya ko ganin titi sosai, saboda tsabar fushi. Lokacin daya shigo gida karfe goma saura 'yan mintoci ne, su Umma har sun rufe sasan su, wucewa kawai yayi ya fado falon. Nusaiba ma ta jima da rufe dakin ta. Sai dai ba barci take yi ba tunanin duniya ya ishe ta, tare da juyayin irin yanayin da ta tsinci kanta, wanda a kodayaushe take aje shi a matsayin kaddara daga Allah. Kofar dakin Zarah ya wangame, cikin zafi da fushi. Kwance ya ganta ba kuma barci take yi ba, domin idanunwanta ya fara arba da su. Bai rufe kofar ba, ya wuce da sauri yana fadin." Zarah kin kuwa san abinda ki ke yi? Don me za ki baro asibiti, ba tare da izinin kowa ba? Ta dauke kan ta, tayi banza da shi har zai ga zama bakin gadon." Ba za ki yo magana ba?" Shi yasa na ke ta kiran wayar ki, ki ka ki dauka? To kar ki ji da wai, yanzun nan za ki koma asibitin, tashi- tashi! Kar ki 6ata min lokaci." Ta dube shi, ido fal da hawaye ta ce,"Ba zan koma ba yayana." Ta yunkura ta tashi zaune, yayin da ya saki baki yana al'ajabinta, "Ba za ki koma ba? Ta ce,"Kwarai ba zan koma ba Ai ban san rashin adalcin ka har ya kai haka ba yayana. Don me? Saboda me? Ka na cutar da 'yar mutane ka na so ka ci wutar Allah ne? Hawaye suka soma zuba. Ya ce,"Nusaiba ba matar ka ba ce? Don me za ka aje ta shekara daya da rabi, ka na cutar da ita? Kuma tana kallo na, tana sane da abinda ke Faruwa. Wannan zalunci ne. Allah ba zai bar ka ba yayana, gara ka san halin da ka ke ciki, ka gaggauta yin gyara........... Ya daka mata tsawa wacce ta kara jawo hankalin Nusaiba da tuntuni take jin 'yan surutan da bata gane daha inda suka fitowa ba, don haka ta taso a hankali ta fito. "Ya isa Zarah! Ya isa! Dama saboda wannan maganan ki ka baro asibitin ba izini? To ina son ki sani, babu ruwanki a ciki wannan maganar, ban kuma ce ki sa kanki a ciki ba, zamanta daban, zaman ki daban, kar ki sake yimin wannan maganar." Tayi zuciya sosai, idanuwan ta suka kara yo waje, ta ce,"Kwarai akwai ruwa na a ciki domin ni ban dauki Nusaiba a matsayin kishiya ba, 'yar uwa ta ce, kuma ina kaunar ta tsakani da Allah. In don akan wannan cikin yasa ka ke kumfar bakin, don me na baro asibti, bari ka ga yadda za'ayi da shi, tunda shi kadai ka ke so, ba ka tsoron Allah." Tana fada ya ga ta mike bisa gado ta hau buga tsalle sama tana direwa da karfin tsiya, hawaye na zuba bakinta na fadin,"Ban son shi, sai ya zube wallahi! Nusaiba ta kara mannewa da bango, ta fasa kuka sosai, ciwon zuciyar ta ya karu, har sai da ta sulale kasa. Da kyar ta rarrafa ta koma dakinta. Nan bisa kafet ta kife, tana rusar kuka, wanda ita kanta ba za ta iya tantance dalilin yin sa ba,Illa iyaka ta san ita abar tausayi ce, sai dai kuma ai bata ratayawa ranta son Naseer ba, tana dai zaune ne kawai, don farin cikin Abbanta kamar yadda ta fahimta shi ma Naseer ya amshi auranta ne saboda girman Abban na ta a idonsa. Amma da ciwo, ka na zaman mu2m bai damu da shirgin ka ba. Sai da yayi ta maza sosai, sannan ya cukuikuyo Zarah yayi iya kokarinsa kafin ya samu ya manna ta ajikin sa,"Kin yi hauka ne Zarah?? Za ki kashe kan ki ne? Ta rushe da kuka sosai, bai ta6a ganin tashin hankalin Zarah irin na yau ba. Gaba daya jikin sa yayi sanyi,"Ki yi shiru Zarah, na ce na ji, na yi laifi, zan gyara." Ta sulale a hankali ta zauna, saboda yadda take jin jikin ta ko'ina ya daddure. Ya biyo ta da sauri, ya dago fuskarta,"Za ki takaita ni ne Zarah? Don me za ki min haka? Murya na rawa ta ce,"Dole in yi maka yayana. Domin rayuwar ka na cikin hatsari, kai har da ni ma, tunda ta gaya min na sani, hakki na ne in gaya ma ka gaskiya. Zalunci babu kyau yayana, kar shaidan ya kai ka ya baro, shi gaba daya mece ce rayuwar? Ya tallafi kuncinta, ya goge hawayenta." Duk na ji, na ce zan gyara. Amma ita ma bai dace ta gaya miki ba, wannan rashin kunya ne." Ta ce,"Tayi rashin kunyar. Ai ba kanta tsaye ta gaya min ba. Magana mu ke akan zamana asibitin, na ce ya ishe ni, zan dawo gida, tunda tana nan za ta dauke min komai. Ka ji abinda ya kawo maganar. A hakikanin gaskiya ka cutar da........ Ya toshe bakinta,"Yi shiru, ya isa haka. Na dauki kuskure na, shi kenan? Saura gyara." "Ai zan gyara. Yanzu da ki ka baro asibiti me su Umma suka ce? Ta ce,"Ni ba wanda ya san na shigo gidan nan, har ita amarya." Ya ce,"To ki taso bakin ki alaikum in maida ki." "Muryar Umma ya jiyo tana kwala ,"Naseer! Naseer!! Ya runtse ido, "Shi ke nan ga Umma can ta fito." Ya mike yana amsawa ya fito. Tana tsaye kofar falo. "Hayaniya na ke ji, wai me ke faruwa? Ya rasa me zai ce, sai kawi ya ce,"Umma Zarah ce ta gudo daga asibiti." Zarah? Ta fada cikin al'ajabi. "Ina take? Ga ta nan cikin daki, na yi na yi ta zo mu koma ta ki."Jin muryar Ummar yasa Nusaiba ta buda kofa ta fito. Tare suka cusa kai dakin, tana zaune tana faman share kwalla. Nusaiba ta ruga ta rungume ta,"Antina, me yasa? Ganin Zarah na kuka, ita ma na ta ya dawo. Umma ta ce,"Amma dai Zarah ba ki da hankali, ki na wasa da lafiyar ki ko? Maza mike ku koma, kafin in kira Abbanku, ba na son jin wata magana." Nusaiba ta sake ta, ta kamo hannayenta,"Tashi Antina mu je a maida ke." Ta mike Umma na fadin"Nemo mata hijabi." Kafin Nusaiba ta dauko hijabin, jini ya malalo har bisa diddigen ta. A hankali ta yaye zane ta duba, ido waje ta kalli Umma. Wasu hawayen suka tsirgo. "Umma duba ki gani." Ta hau salati da tafa hannu. Naseer ya rude,"Kin ga irin ta ko? Kafin su yi haka ya sunkuce ta yayi waje. Nusaiba ta biyo su da gudu hijabi a hannu. Umma ta kwala wa Abba kira ya fito a rude. A rudan take gaya masa, ta fice da gudu. Kafin ya fito waje. Naseer ya ja mota sun wuce, nan ya tsaya yana ta sababi shi kadai. Da ka gan su ka san a rikice suke gaba dayan su, babu mai takalmi balle mayafi. Zarah ta sha fada wajen Likita da Nosis. Suka yi mata allura maimakon jini ya tsaya, sai ciwon mara kamar za ta wuce barzahu.Dole a kwance mahaifa. Haka Likita ya gaya wa su Naseer. Zufa ta keto masa, babu abinda zai iya yi, tunda hakan shi ne samun lafiyar ta. In anyi sa'a a sami dan.Komai na Allah ne, haka nan suka fauwala wa Allah. Ana kwala kiran sallah ta haiho dan ta namiji. Sai dai yayi k'ank'anta. sosai. Naseer yayi kamar zai rasu, don murna, haka Nusaiba ke sauke numfashi tana kokarin dai-daita shi. Ba su ga Yaron ba, saboda an hanzarta sa shi a kwalba. Bayan an kintsa Zarah, an fito da ita dakin hutu, can suka kutsa kai suna rige-rigen gaishe ta. Minti 15 bayan fiddo ta. Naseer ya koma da Umma gida, don kwaso kaya da dukkan abinda ya dace. Nan suka bar su tare da Nusaiba, duk doki ya ishe ta, ta kosa ta ga Baby. Tare suka dawo da Inna. Daga bisani ne su Abba da Malam Umar suka zo asibitin, suka duba Zarah! Zarah kam ta sha fada wajen iyayenta akan baro asibiti da tayi. Ta amsa laifin ta, ta kuma bada hak'uri saboda bata son kowa yasan dalilin barinta assibiti. Babu wanda ya ga Baby, domin likita ya hana, ya ce sai karfe 6 yamma za'a fito da shi, idan ya sha nono a maida shi.Ai kuwa Umma sai da ta jira lokacin yayi. Wata Nos ta fito da shi don koridon dakin aje jarirai wanda shi ma a rufe yake ruf. Kai! Wannan Yaro Allah ya zuba halitta mai kyau a wurin nan. Tamkar Naseer yayi kaki, kamanin su daya, amma ya zarce Naseer kyau, nesa ba kusa ba. Tun da yayi arba da Baben nan, jikinsa ya dauki rawa, ya ji gaba daya duniya, babu abinda yake so fiye da Bebin. Da haka Nusaiba ta tsinci kaunar Bebin nan cikin ranta, kamar ta gudu da shi. Amma ina. , Minti 30 aka ba su, su gan shi, lokacin na cika, da kyar Nos ta kar6e shi hannun Naseer, ta koma da shi. A ranar Abba ya rada wa Yari sunan sa watau Iliyas!. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Satinsu 3 a asibiti sai dai Zara ta zo gida tayi wanka ta koma. Babu wanda bai zo ganin su a asibitin ba, hatta Fa'iza. Sageer ya kawo ta, ta gaida Zarah. Haka Kausar bata yi kasa a guiwa ba ta zo, ta kuma ce za ta dawowa ranar da aka tsaida shagalin suna. Cikin wayoyin Naseer hotunan Iliyar (Ameer) ne birjik iri-iri. Babu yadda za'ayi ya wuce awa, bai bude ya gan shi ba, kwarai ya kwallafa Yaron nan cikin ran sa, kamar shi kadai ya fara yin Da.Sun shafe sati 3n nan cif! Sannan aka sallami Bebi. Nusaiba na son ta rike shi a mota, amma ubansa yayi kane- kane. Sageer na tuki, yana masa tsiya, ganin yadda yake ta kara rurrufe shi da shawaul, don Likita ya ce kullum ya kasance a lullu6e. Ranar da ta zagayo, aka shirya gagarumin shahalin suna. Nusaiba ta kashe kudi, abubuwa kala-kala tayi na ci da na rabo, balle uban gayya. Ko lokacin bikinsa bai saki jiki da aljihu irin na wannan yaron ba. Mai-jego kuwa ta kwashi kaya akwatuna 2 manya. Nusaina ta shirya kayan Bebi da zannuwan Mai-jego. Banda wasu tarkace cikin (Ghana most go). Bayan kowa ya watse. Nusaiba da Naseer na zaune suna kallon yadda Umma ke wanke Bebi da ruwan zafi, yayin da Zarah ke bayinta tana na ta wankan. Nusaiba ta dube ta, ta ce,"Ni kuwa Umma in ki na wankan nan, sai in ta mamaki." Mamakin me? Ta ce,"Ni gani na ke kamar zai sumbule, ke kuwa ki na tayi masa, ba kya jin komai." "Dariya Umma tayi. "Nusabai oho! Ka ji Naseer, ashe in ta haifi na ta, ba za ta iya wanke shi ba." Tare suka kalli juna da Naseer, yayi yaken dole, ita kuwa kunya ce ta rufe ta, ta mike za ta wuce, ya ce,"Ina za ki kuma? Ba ke ki ka dauko zancan ba?Tsoma bakin sa yasa ta k'ara azama ta bar dakin. Umma na dariya. Naseer na murmushi, yana fad'a a ran sa, "Yarinya sai salon tsiya."Umma ta nade Yaro a tawul mai laushin gaske, tana fadin,"Ita ma Allah ya kawo masu albarka." Ya shafa k'eya ya ce,"Umma hanzarta ki sa masa kaya akwai iska. Ta zubo masa ido ta ce,"Na k'i, ka fi ni son shi ne? Ya kada kai yana murmushi,"Tuba na ke UmmaTa." Yana rufe baki. Abba yayi kiran sa, ya tashi ya fice. Abban na falon sa a zaune bisa kafet, shi yasa yana zuwa ya tamkwashe kafa gaban sa, ya ce,"Ga ni Abba.." Ya dube shi da kyau ya ce,"Na yi maka zuru in ga irin hankalin ka, sai na lura lallai ba ka da hankalin." Gabansa ya fad'i, ya k'ara matsowa ya ce, "Me na yi Abba? Ya ce,"Maganar komawa Hanwa, na ji ko tada zancan ba ka yi, me ka ke nufi? Ya dan sunkuar da kai, ya sauke numfashi,"Yaya mu2m zai ba ka gida, amma ka ki zama? Saboda 6arayi sun shiga ma sau 1? Anji ba ka da lafiya wancan karon, har yanzu ba ka warken bane? Yayi dan shiru kafin ya ce,"Abba ba haka ba ne. Ni kai na ina son komawa can, amma da zarar na tuna da irin dukan da na sha wajen 6arayin nan, ni kan ji tsoro ya kama ni. Kar ka damu Abba za mu koma."Ya ce,"To ka hanzarta sa ranar, ku koma. Na san Alhj na da kawaici, ba zai ce komai ba. Amma babu dadi mu2m yayi ma ka kyauta, ya ga ka na yi wa abin rikon sakainar kashi, ko kai ne ranka ba zai maka dadi ba." Ya ce,"Haka ne, insha-Allahu zan san yadda za'a yi." Yauwa sai ka yi wa Allah godiya kawai kan matanka a hade yake, asirinka ya rufu dari bisa dari, domin zaman lafiyar iyali a cikin gida, shine kwanciyar hankalin Mai-gida." Ga su dai yara k'anana, amma Allah yayi masu kaifin hankali, shi yasa a kodayaushe na ke k'ara jawo hankalinka a kan kamanta adalci tsakaninsu. Ba cuta ba cutarwa,Naseer wannan shine tsoron Allah, ka sani zai tsaida ku ranar da ni da Umman ka ba za mu iya cetonka ba. Ina fatan ka ji ni da kyau? Ya numfasa sosai, ya ce,"Na ji Abba, na gode." Ya ce,"Ita kenan maganar, je ka wajen iyalinka." Ya mike jiki babu kwari, ya fito kai tsaye dakin sa ya wuce, bisa gado ya kwanta rigingine. Tunani ya addabe shi, ya rasa ta inda zai 6ullowa al'amarin. Sati 4 kenan da suka yi sa'insa da Zarah akan Nusaiba, sam ya rasa ta yadda zai fuskance ta, domin shi mu2m ne mai tsananin son ra'ayin sa. A JININSA YAKE!." Idan ya so abu, ya so shi har abada, inda ya kyama ce shi baya waiwayar sa balle ya daga masa hankalli Sai dai a yau Abbansa yayi maganar da za ta sa dole ya waiwayi abinda ba shi cikin tsarin sa, wanda a da yake ganin sai dai rai yai halin sa ko in ta gaji, ta nema wa kan ta mafita. Ya tashi zaune yayi wawan ajiyar zuciya, ya dubi agogon hannun sa karfe 9 na dare. Ya diro daha gado, ya fice ya dauki mota iya bar gidan. Kwana 2 tsakani. Ya kama ranar juma'a. Wannan rana za ta iya zama daya daga cikin ranakun tarihin rayuwar Nusaiba. Shigowar ta daki kenan, sun gama shan hirar su da Antinta, misalin karfe 10:30 na dare. Ta yi shirin barci ta haye gado, ta jawo littafin turanci (Novel), ta fara karantawa, don kauda tunani, kafin zuwan barci. Bata wani jima ba, ta ji an dan kwankwasa kofar ta, ta aje littafin ta taso ta sa makulli ta bude. Sai da gaban ta ya fadi, saboda wanda ta gani tsaye a kofar dakin ta. Ido waje take kallon sa, shi kuwa bai saurari komai ba, ya wuce ciki, hannun sa dauke da lemun gwangwanin. (Coke). Tsakar daki ta iske shi, ta nemi gefen gado ta zauna tana mai tsananin mamaki. Lemun hannun sa ya miko mata. Ya ce,"Ki sha yanzu." Ta kar6a ta duba, bakin gwangwanin a bude yake, ta sake kallon sa, bata iya cewa komai ba. Ya zura hannaye aljihu ya ce,"Ko ba za ki sha ba? Ta gyada kai, ta ce,"Zan sha mana." Ya ce,"To ki shanye, kin ji? Ta amsa da kai. Ya juya yayi waje. Ta bi shi da kallo, sannan ta juya bisa lemu, ta tsura masa ido,"Menene dalilin bani lemu in sha da tsohon dare? Kashe ni kuma yau zai yi? Gara ya kashe ni ma kowa ya huta, shi kenan an raba gardama." Kwalla suka tsatso mata, ta goge su. Kan ta tsaye ta kafa gwangwanin lemu ta yi sha, har ya kare. Tayi zuru gefen gado tana jiran abinda zai biyo baya. "Yan mintoci kadan ta fara hamma, idanuwanya su ka yi nauyi. Kafin ayi haka, ta rasa duniyar da take, nan ta wuce lauuuuu........bisa shimfida warwas! Minto 10 tsakani ya dawo dakin, ya zura mata ido. Sai kuma ya ji tausayinta ya kama shi. "Tabbas kwayoyin nan sun fi karfin jininta ga shi yayi mata (Over dose)." Ya gyara mata kwanciya, ya dafa goshin ta yayi addu'a. K'arfe shida na safiya, ya shigo dakin Zarah rike da carbin sa, yana ja. Ko gaisawa ba su yi ba, ta ce,"Ban ga amarya ba, bari in duba ta." Ya ce,"Barci take yi, tunda ta tashi tayi sallah, ta zube kamar matacciya." Wayyo, gajiya ce, bari in kyale ta, ta huta baiwar Allah. Tun da ka yi haihuwar nan bata yi sukuni ba? Ya zauna kusa da ita ya ce,"Ke ba kya gajiya da wasa amarya."Ta watso masa harara ta ce,"Me ye na ka a ciki? Ya langwabe kan sa a kafadar ta ya ce,"Babu komai Antin amarya. Ni matsala ta na yi missing din ki da yawa, yaya bayanin yake ne? Ta janye kafadar ta, ta ce,"Koma dakin ka yanzun Umma za ta kwaso ruwan wanka." Turo mata fuskar sa yake yi kamar zai cinye ta, kawai muryar Umma suka ji daf da kofar daki tana fadin,"Jama'a, wai yau ina Nusaiba ne? Yayi zumbur ya suro Ameer yana girgiza shi," Kai sarkin kuka ne ko? Ka hana mutane barci da sassafe kuma ka tashi. Dariya ta kullewa Zarah ciki, da kyar ta kirne ta ba Umma amsa,"Barci take yi Umma." Ta ce,"Allah sarki, gajiya ce, komai sa ta ce ita ce za ta yi." Ta dire bahon wanka Zarah ta miko mata kujera da kayan sabulu. Naseer ya miko Bebi, sannan ya tsugunna ya gaishe ta, ya samu ya sulale ya koma dakin sa. Agogo ya fara duba wa kafe 7 sau kwata. Yayi kasake yana tunani,"Kai 'yar mutane fa shiru? Ya tambayi kan sa. Ya zubara ya fito. Kofar ya murda a hankalu ya bude. Kwance ya hango ta yadda ya bar ta, tun kiran sallar farko. Ya shigo ya maida murfin a natse ya rufe. Ya matso ya shiga bubbuga ta, "Ke! Tashi! Ba ki san gari ya waye bane? shiru ka ke ji. Malam ya ci shirwa.Tsoro ya fara kama shi, bai san lokcin daya haye gadon ya tarairayi ta ba, ya dan bubbuga kuncin ta,"Ke Nusaiba! Ke! Can cikin sambatu take ta surutan da bai san abinda ta ke cewa ba. Tayi lauuu.....ta fada bisa filo. Idon Naseer fa ya raina fata. Bayi ya shige ya debo ruwa ya tarairayo ta, yana shafe fuskarta, yana kira tare da bubbuga kuncinta. Da kyar ya samu ta dan budr ido jajur! Ta dube shi,"Ki tashi aka ce, gari ya waye, kowa sai tambayarki yake yi." Ahaf, ashe duk surutun banza yake yi, zurun da tayi ma sa a cikin barci ne. A hankali ya ga idon ya karasa rufewa. Ya dafe goshi, ya runtse ido, ya ce,"Na shiga uku.!" Da ya rasa na yi, sai ya gyara mata kwanciya, ya rufe ta ya bar dakin. Mota ya dauka ya nufi gidan Yakubu ya dauki doki ya bazama filin sukuwa yayi ta zagaye, ba ji, ba gani, saboda damuwa. Ba shi yasan halin da yake ciki ba, sai da ya ji shi cikin ciyayi yana birgima. Yayi lamo kamar ya mutu. Wasu mutane 2 suka dago shi suna tambaya,"Ba ka ji ciwo ba? Ya mike ya na fadin,"Ban ji, ba na gode." Ya kar6i akalar dokinsa a hannun su, ya taka ya haye, nufi Tudun Jukun. Karfe 10 saura kwata, yake fakin, ya shigo gidan yana fargabar me zai shiga ya ji? Yana yin sallama kuwa. Umma ta kwala masa kira. Ya nufi gunta ajikinsa a sanyaye,"Ga ni Umma."Ta ce,"Nusaiba barci har tara da rabi, da kyar muka tashe ta ni da Zarah. Wane irin barci ne haka, yarinya bata ko iya tsayuwa? Ya zaro ido, ya ce,"Ina take yanzu? Ta ce,"Tana daki, ta ce kanta ma ciwo yake yi, shine na ce ko asibiti za ka kai ta? Ya wuce da sauri, yana shiga falo yayi karo da Zarah ta fito kicin,"Yayanmu, barcin amarya yau ya ba mu tsoro, kamar wacce ta sha wani abu? Tana nan kai na faman ciwo." Tana daki ne? Tana nan akwance." Ya wuce dakin, ya bude ya shiga. Tana kwance Idanuwan ta rufe, ya tsaya kan ta yayi kira,"Ke! Ki tashi aka ce a kai ki asibiti." Ta bude ido jazur, ta dube shi, wani sabon takaici ya lullube ta, hawaye suka cika idanuwanta fal, ta ce,"Na sha magani, ya daina." Umma ta ce,"A kai ki asibiti, ta so mu tafi mana." Tayi shiru tunani ya rufe ta, bata ta6a zaton Naseeer yana kin ta haka ba, sai yanzu ta tabbatar da bata da makiyi kamar sa. Shi yasa tunda ta wartsake, ta tantace halin da take ciki, ita ma ta fara tsanar sa, irin wanda bata ta6a ji ba. Tayi kuka cikin bayi, ta kuma roki Allah yayi mata sakayya, idan har akwai cutarwa a cikin abinda Naseer ya yai mata. Yayi sauri ya kauda kai, jikinsa ya k'ara la'asar. Ya kama hanya da sauri zai bar dakin. Zarah ta kawo kai." Asibitin za ku? Ya ce," Ta ce bata zuwa." Saboda me? Ta wuce gun ta, "Amarya! Me yasa? Ta goge kwalla ta ce,"Na sha Panadol Antina." Ta ce,"Ai yanayin barcin da ki ka yi ba'a gane masa ba, shi yasa Umma ta ce ki zo a kai ki."Tayi shiru bata da niyyar tashi. Can ta jiyo muryar Umma,"Ina Nusaibar? Nan da nan ta sakko daga gado, ko kafin Umma ta karaso cikin dakin, ta dauko hijabi. Ya ce,"Kin ce ba za ki ba?" Za ni Umma, hijabi zan sa." To ki je yana jiran ki a mota." Suka fito Zara ta rako ta bakin kofar gida. Ta shiga mota. Suka tafi, babu mai yi wa wani magana. Sun iso cikin asibitin. Nusaiba fa ta kafe ta ki fitowa daga mota. Yadda bai ce mata fito ba, haka ita ma bata motsa ba daga inda ta ke zaune ba. Haushi ya kume shi, yana ganin kamar tana son ya rarrashe ta ne." "Lallai yarinyar nan ta raina ni." Hannu yasa ya zaro wayarsa, ya danna (Ear piece) yana jin gindan Rediyon (Queen FM). Ga hotunan Ameer yana kallo hankalin sa kwance. Kusan minti 30 suna zaune, ita ji take kamar ta fice daga motar tayi tsuntsuwa ta ganta gidan iyayen ta. Da ya ga abin na ta da gaske ne, sai ta buga tsaki. Shi take 6ata wa lokac, sai ya buga tsaki yayi wa mota key, ya figeta a guje. Yana yin fakin kofar gida, ta bude ta fito ta shige cikin gida. Ya bi ta da kallo, kafin ya ce aran sa,"Duk su Zarah su ja siyo min raini." Yayi tsaki ya fito ya shiga ciki. Suna tare da su Umma suna tambayar ta yadda aka yi? Yana isowa, tana fadin,"Babu komai Umma, dama maganin barci na sha, don un sami barci, ashe ya fi k'arfin jini na, amma Likita ya ce ba komai zai sake ni." Umma ta ce,"Ai shi ke nan, sai ku kiyaye shan maganunguna haka kawai. Don Allah kar ki sake, kin ji? Ta ce,"To Umma." Yinin nan guda, bata iya cin abincin kirki ba. Saboda tsabar tunanin kaddarar da Allah ya sauko mata. Washegari ta tambaye shi zuwa Kaduna.." A dawo lafiya." Ya ce da ita. Da kan ta ta tuka motar ta tafi.."Can ta wuni tare da Umman ta, suna hira ta ji dan sanyi a ranta. Kamar kar ta dawo ta rink'a ji, shi yasa ta rink'a nuk'u-nuk'u. Yamma tayi sosai. Abban ta kuwa ya ce ba za ta kwanan ba. Direba yasa, ya ja mata motar ya dawo da ita. Shi ya koma a ta haya. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Sannu a hankali Zarah tayi arba in. Kodayaushe Ameer na wajen Nusaiba, ita ke masa komai, ta shaku da shi sosai, kuma tana son Yaron, duk da irin cin kashin da Baban sa yake mata. Wanda har yanzu abinda yai mata, yana cikin ranta. Ta sa ido ta ga ko zai sake kwantawa, amma baiyi gigin k'arawa ba, saboda shima al'amarin ya dan sanya shi nadama, bata dai isa ya nuna mata ba, balle ya bada hakuri. Saboda haka suka ci gaba da zaman da suka saba tuntuni. Kwanan Ameer 50 dai-dai, yayi wayo ya kumua shiga ran kowa. Da asuba Zarah ta farka tana mamakin irin barcin da tayi. Lallai Ameer ya sha kuka, bata ji ba. Domin tayi tunanin tun lokacin da ta bashi nono take barci. Tausayin shi ya kamata, ta tashi ta dauki shi. Kara bude ido tayi sosai, don sai taga kamar. Gaba daya jikin sa ya sandare Tsoro ya kamata, jikinta ya dauki rawa ta dan girgiza shi, ina rai ya riga yayi halinsa, da sauri ta diro daga gado tare da shi ta nufi kofar dakin Naseer ta bubbuga, ya fito ya bude mata. "Duba Yaron nan ka gani ko motsi ba yayi. "Inna-lillahi"wa-Inna-ilaihir-raji'un! Haka yake ta faman fadi yana girgiza shi. Tuni Nusaiba ta ji, sai ga ta a gigice. Naseer yayi waje da shi, suka biyo bayan sa, suka dunguma sasan su Umma. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 2-04 Posted by ANaM Dorayi on 08:19 PM, 20-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Abba ya kar6e shi, ya rungume a jikin sa ya ce,"Ku yi hakuri. Allah ya kar6i abin sa." Nusaiba ta sulale nan hawaye suka tsinke mata. Zarah kuwa dakin ta ta koma ta zauna bakin gado tana sallallami. Shi kuwa Naseer kafewa yayi kai da fata aje asibiti a duba masa Yaro, k'ila suma yayi. Ya dube shi ya ce,"Hakuri fa za ku yi Naseer, wannan yaron ya riga ya rasu, babu abinda za'a iya yi masa. Kujera ya zauna dabbas! Idanuwansa suka bushe kamas! Kirjinsa na bugawa. Abba ne ya iya gayawa duk wanda ya kamata ya sani. Nan da nan jama'a suka taru. Umma tayi masa wanka, aka shirya shi, cikin likafanin sa, suka sallace shi, aka wuce da shi makabarta. Naseer bai iya zuwa ba, saboda ba zai iya jurewa ba, yana kallo a cusa masa Ameer cikin rami. Yana zaune kai cikin guiwa a falon Abba, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Ji yayi an dafa kansa, ya dago a natse, yadda ya bi wanda ya dafa shi. Alh.Basheer ne a gabansa, yayi mamakin da bai ji sallamar su ba. Ya mike yana masa sannu da zuwa, ya amsa, ya ci gaba da fadin." "Zauna ka ji?" Suka zauna tare, ya gaishe shi. Bayan yayi masa gaisuwa, ya ce, "Umman ku ta ce an je kai shi ko? Ya ce,"Sun tafi tun dazu." Ya ce,"Allah ya kara mana hakurin rashin sa. Tare muke da Ummin Nusaiba, tana can sasan wajen Umma." Ya ce,"Bari in je mu gaisa." Ya mike ya fice. Alhj na masa kallon tausayi. "Yan mintoci kadan ya dawo, ya sake zama. Bai iya cewa k'ala ba, har zuwa wani lokaci, kafin Alhj ya katse shirun,"Naseer! Ya dan dube shi ya amsa. Ya ce,"Don Allah ka daina yawan tunani, komai ya sami bawa da izinin Allah. Ba kai kadai ba ne, Ubangiji na jarabtar bayin sa da masifu iri daban-daban. Amma idan bawa yai hakuri, ya jure komai wucewa yake yi, tamkar bai ta6a faruwa ba. Abinda na ke son ka da shi shine. Ka k'ara yawaita sadaka da addu'a, domin ita sadaka tana yaye masifa da damuwa. Sai kuma hamdala ga Allah. Ko wane yanayi ka tsinci kan ka, to ka gode wa Allah. Ubangiji na wadata mai yawan yi masa godiya. Ba wadatar kudi kawai na ke nufi ba, har da wadatar zucci. Ka sani idan zuciya ta wadatu da imani, duk abinda zai zi wa bawa, zai kasance mai mika wuya ga Allah. Kar ka damu, ka ji? Ya sauke numfashi ya gyada kai, ya ce,"Na gode." Sun jima. Alhj Basheer na yi masa nasihohi kafin su Malam Balarabe da sauran jama'a suka dawo daga makabarta. Nan ya bar su ya fita,Suka yi sallama da jama'a, yayi masu godiya kowa ya kama gaban sa. Aka bar su su 2 da Sageer. A hakikanin gaskiya Alh.Basheer na son Naseer, shi yasa duk ya damu da irin halin damuwar da ya shiga, tunda yayi aure. Yau wannan, gobe wancan. Shi kuma Naseer na masa kallon duk matsatsin daya shiga. Alhj ne sila, don haka babu wani dadin bakin da zai masa. Ya fadi, kunni yaji, amma aiki da shi ba zai ta6a zama dole ba. Naseer kenan. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Wata 2 da rashin Ameer. Bikin Sageer da Fa'iza ya rage saura sati 2, ka na Kausar tsakanin su sati 1. Watau na sati 3 ya rage. Angwaye da amare na ta fafutikar shirye-shiryen biki, ita kuwa Nusaiba wani abu ke daure mata kai, mai kama da al'amara. Al'adar ta d'if, ta dauke wata 2 kenan. Ana neman a shiga na uku. Ga wani ciwon kan safe da take fama da shi, yawan kasala da taruwar miyau a bakin ta. Bata gane kan gadon ta ba, ko alama sai dai bata fidda shakkun ciki take dauke da shi. Ta runtse idonta tamau? Ta dauki salatin Manzo ta yi wa Allah tasbihi mai yin yadda ya so." Watau rabon Da, ya kawo ni cikin gidan nan kenan? Ta dan yi murmushi, domin take nan ta tsinci soyayar abinda ke cikin ta.Tana so ta nuna wa Antin ta alamomin da za ta gane, amma tana jin tsorin kar Naseer ya sani. Watakila ba zai so haihuwa da ita ba, tunda baya sonta. Kar ya munafunce ta da wani abin, ya zubar da cikin. Saboda haka ta ci gaba da 6oye yanayin ta, babu wanda ya fahimce ta, illa tsiyar k'iba da Antin na ta kullum take yi mata. A haka suka sha bikin Sageer. Amarya ta tare kusa da gidan su Sageer din, ya kama hayar gida karami dakuna 2, kicin da bayi. Sageer ya kama angwanci, babu kama hannun Yaro. Sati da ya zagayo tun ranar alhamis Nusaiba na Kaduna, ko dama duk ta kosa ta sami 'yar damar da za ta gida, ta dan kwana 2. Tana like jikin Umminta, dadi ya ishe ta, ga madarar Holandia mai sanyi take ta faman sha, tun isowar ta. Haka Ummi ke cikin farin ciki ganin yadda Nusaiba tayi k'iba, ta k'ara haske sosai. Tana ta kallon ta, tare da lura da yanayin ta, ita kuwa Nusaiba ta k'i yarda wani abu yanke a bakin ta, kar miyau ya taru, kamar dai yadda take yi a gida Zariya. Bikin Kausar yayi armashi kwarai da gaske, angonta Injiniya Abdul-Malik yayi bajinta. Haifaffen Unguwar Sarki, amma yana aiki da hukumar gida da ke Lagos.Ta tare a makeken gidan sa da ke (Abuja Road) kafin lokacin da za su d'aga Lagos. Ranar asabar Zarah ta zo, kuma ta so kwana. Kiri-kiri Naseer ya hana, ya kasa, ya tsaye da yamma dole ta biyo shi, ya dawo da ita. Nusaiba kuwa sai da ta kai litinin. Alh.Basheer yayi ta ciwon baki, yana wa Ummi fada yana ganin kamar da hadin bakin ta Nusaiba ta kai Mondy. Karfe 4 kayanta an gama kintsa su a mota. Direba zai maida ta. Tayi tsaye tsakar falo tana kallon iyayen ta, kamar kar ta tafi. Hawaye ya gangaro kafadarta,"Kuka za ki yi shagwa6a66iya? Ta tsura masa ido, hawayen suka zubo shar-shar! Yasa hannu ya goge su, ya sake cewa,"Menene abin kuka? Kin ga kama hanya ku tafi. Allah ya kiyaye hanya. Ki kula da kanki da kyau. Kin ji? Ga katon 4 nan na Holandia, na ce a sa miki a but." Umminki ta ce,"Yanzu shan ta ki ke yi sosai ko? Ta dan sadda kai kasa. Yayi murmushi, ya dago ha6arta,"Haka Umminki ga gaya min, ga ta dai a tsaye, ko ba ke ki ka gaya min ba? Ta wuce shi da gudu ta koma gun Ummi, rungume ta. Ya ce,"Ummita, sai mun yi waya." Kafin ta ce wani abu, ta bar wajen da gudu, ta fita. Me za su yi, ba dariya ba, kamar almara ta ga Naseer na fakin a harabar aje motici. Ta ja tsaya, tana kallon sa. Mamaki ya ishe ta. Daga bayan ta, ta ji muryar Abbanta na fadin , "Ah , ga ma mijinta nan ya zo." Ya zo ya wuce ta, ya nufi wajen Naseer da ke fitowa daga mota. Da sauri ya tsugunna. Alhj ya mika masa hannu tare da sallama. Ya mika na sa yana amsawa. Sannan suka gaisa, kafin Alhj ya ce,"Ashe za ka sami zuwa? Ai tun jiya na tambaye ta, ta ce min ka na da.(Exams), ba za ka zo ba." Kan sa tsaye ya ce,"Mun fito da wuri, shi ne na ce bari in zo kawai in dauke ta." "Yayi kyau. Dama fitowar na ta kenan zu su tafi. Bari direba ya kwashe kayan, ya mayar but din ka." Ya bude but din. Direba na juye kaya, shi kuma ya shige cikin gidan, don gaisawa da Ummi. Ko dama Nusaiba tuni ta koma ciki, kan ta daure, tana tambayar kan ta." Wai ashe maza ma sun iya kisisina? Kurame sak! Suka zama cikin mota, yadda ya like kunnensa da Ear piece haka ta manne na ta da sauraren tafisr din Marigayi Sheik Jafar Mahmud Adam Kano. (Allah yajikan Mallam Ja'afar na Gadon kaya me Ahlussuna, tare da iyayenmu baki daya Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100