[3/19, 8:30 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 1️⃣+2️⃣ Ukraine..... "Didih! Don Allah ki rage tunani, da damuwa wallahi jinin ki yayi mugun hawa, ga abin cikin ki yana bukatar kulawar ki, tun yanzun kin saka damuwa idan cikin ya tsufa ba zasu barki ki haihu da kanki ba, sai dai Cs. Don Allah ki rage damuwa kodan Albarkacin Ablah." Lap Kura mishi ido nayi na wasu dakikai kafin na sauke nannauyar ajiyer zuciya kafin nace. "Abdul bana tunanin komai kawai ina mamakin yadda tawa kaddarar ce." "Karki yi mamaki da abinda Allah ya shirya a rayuwarki kawai ki gode mishi da ya baki rai da lafiya, wanda har kike fuskartan matsalar ki dashi da ace baki da lafiya da duk abinda ke faruwa sai dai ki kalla da ido, ya zame miki zafi biyu. Kuma ai ke da ilimin ki duk abinda ya faru da bawa mujarabbi ne. Ko ba haka ba, kinga kenan babu ta inda mutum. Zai ce Allah bai mishi Adalci ba, tunda ya jarabeka sannan ya baka lafiya, toh me zaka yi idan baka gode mishi ba, sannan mutanen da Allah yake jarabta, yakan tacce sune ya jarabe su, sannan idan suka cinye ya musu tanadin alkhairi." Duk sai naji jikina yayi sanyi sosai, sannan na d'ago kai na kalle shi nace. "Nagode Dudu! Insha Allah zan yi aiki da abinda kace, kuma zan rage damuwa. Yawwa Ummun Ablah." Kwalla ne ya zubo min sakamakon tuno yarana, ina matuƙar kewarsu sai dai na bisu da Addu'a, Allah ya bi min hakkina dan sun zalunci mu. Shigowar Sophia tare da Ablah wacce ta sake kamar tana gida kodan taga Affan ne yasa tasake dan shima yana janta a jikin shi, abincin ta ajiye min sannan tace. "Didih ya kamata ki rage tunani, kamar yanzun naji ake miki magana, amma har kin koma." Murmushi nayi mata sannan dan kar su dauke Ni ina nan da halina, na dauki abincin na fara ci dukda cusawa nake amma kodan farin cikin su dole naci, cokali uku nayi naji na koshi, ajiyewa nayi sannan na ture gefe nace. " Na koshi!" Magani ta mika min nasha sannan nace mata. "Zanje na kwanta." "Don ALLAH Didih banda dogon tunani." Murmushi nasaka mata sannan nayi wuccewa ta, na shiga d'akinta a lokacin zuwan su, kwana uku da suka wucce bar min d'akin. Yadda Allah ya bani ikon arcewa daga jordan, lokacin da na fito daga gidan na hadu da Ghaniyu, amma bai gane Ni ba, har na bar cikin masarautar da unguwar baki daya, sai da na fita a ta unguwar sannan na buɗe jakata na ciro karamin gyale na rufe fuskana, sannan na same taxi ɗin da ya dauke Ni har airport na saya mana ticket din Ukraine. Bamu tashi ba, sai kusan Asuba. Sannan muka bar Jordan dan duk bani da nutsuwa. Kuma dama Ummi ce ta bani shawarar haka, lokacin da tashigo dakina tace. "Idan kinga da Matsala ki tattara ki bar musu gidan suci kansu, karki zo naija domin zasu biyo ki Abbanku zai mika musu ke, ki tafi gurin Dudu, ki zauna abinki." Dan haka lokacin da yace min. "Ki fita a rayuwata, SAFINAH ki nisance ni, in ba haka ba zan miki lahani, bana kaunar ganin fuskar ki SAFINAH kije na tsane ki" Wannan kalmomin jin su nake kamar wuta Ashraf yake watsa min domin ya gama cuta ta, amma ba komai Allah shi zai bi min hakkina. ★★★ Jordan...... Wato halin da ake ciki a jordan sai Addu'a, domin kuwa Ashraf sau biyu yana bada umarnin a yanke kan mutum, tsabar baya cikin nutsuwa shi gashi dan abu kad'an yake fusata shi, ko kuma yaga suna mishi kallon mahaukaci, Sai ya daina zuwa padar ma, baki d'aya. Ya tara uban gemu, baya magana da kowa har Nannah. .... A bangaren Zoyah kuwa yan kabilar su ne suka dawo da ita, gurin Salman Bin Abul Bashari suka kaita, shi da kan shi ya dawo da ita, tun da ya fara magana Sultan kwanta a kujera tare da lumshe idanunshi, bai kuma buɗewa ba sai da ya gama, dake Dattijo ne Bini Abul Bashari, dakyar Ashraf yace mishi. "Nagode sosai." Daga haka ya bar musu falon.. Tun daga ranar bai kuma shiga har kowa ba daga ita har Nannah, lokacin da Nannah ta ganta ha'inta ya tashi, amma sai yayi kamar baya ta damu ba.. Ashraf ya zuba musu ido. ★★★ Abubuwa suna faruwa sui na faruwa, maganin su shine Addu'a, kuma takobin musulmai dan haka na cire Ashraf a rayuwata na shiga kula da cikins, iya kokarina ina kiyayye komai. A hankali rayuwar ke sabunta kan shi, musamman idan ka dauki kazamar buri yayi tasiri akan. Daga kanina har matar shi bana jin komai sai ma birgeni da suke dan tsakanin da Allah suke ƙoƙarin sani farin ciki. ★★★ "Assalamu alaikum! Hmm Ummi ina gajiya, dama na kiraki Ni Ko Safinah tana gurinki, yau kusan kwana uku kenan bata gidan ban kuma san inda take ba Don Allah kuyi hakuri idan tana nan." Murmushi tayi sannan tace. "Ga irin abinda nake guje maka, Ashraf kai da Mahaifiyarka,. Allah sai ya sakawa SAFINAH Domin ta kyautata muku,ban san ita ba da baka san waye kai ba, Sannan itama Mahaifiyarka, badan SAFINAH ba ko a hanya ka ganta bazaka ganewa ba, amma SAFINAH tayi kasadar sayar da Rayuwarta kuka saka mata da haka Wallahi Kun bani mamaki, Safinar kuka zalinta ba komai ya Allah yana tare da mai gaskiya, ita kuma Allah yasa tana hannu na gari, dan Ni dai nasan sabida ku SAFINAH ta bijire man, shine kuka sata tabar muku kasar." Inda take ba nan take shiga..... Wallahi Ni barci nake ji😪😴 [3/20, 11:32 AM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 _An same spelling errors sosai a pagen jiya dan haka zan tashi dai dai inda Ashraf yake tambayar Ummi SAFINAH domin Jiya barci ya cika min ido ne wallahi_ 3️⃣ "Assalamu alaikum! Hmm Ummi Barka dai, dama zan tambaye kine ko SAFINAH tana gurinsu, yau kwana uku kenan muna nimanta" Murmushi Ummi tayi sannan tace. "Ga irinta nan, ga abinda nake guje maka, da kai da Mahaifiyarka kun sakata a gaba da fitina, ko tausaya mata baku yi, kun lalata mata rayuwa baki d'aya sannan kuma sakata a gaba, sabida rashin adalci duk abinda ya faru da SAFINAH sabida kune, ko mu da muke iyayenta bata sadaukar da Rayuwarta sabida mu ba, shine kuka saka mata da wulakancin, wallahi Ashraf ina jiye maka hakkin Safinah, domin idan ya tashi kamaka bazai maka da sauki ba, wato ga uwar da bata san ciwon haihuwa ba, shine ka kirani ka gaya min, SAFINAH ta b'ace ko tunanin halin da zan shiga idan naji labarin ba kayi ba bari kawai ka gaya min, toh Ni shawara biyu zan baka na farko ka nimo min SAFINAH na biyu kuma ka turo min sakon Sakinta ko kuma Ni nazo na amsa na gaji da wannan fitinar da yaki ci yaƙi cinyewan." Bala'i Ummi yayiwa Ashraf sosai, sai da yasan ya tab'o mata y'a sannan kashe wayar, zama yayi ya cusa hannun shi cikin gashin kan shi, ji yaƙe kamar ya kurma ihu amma ba hali. ★★★ "Ni kika juyawa Baya Ammyn! Bayan na gama taimaka miki amma kika juyawa min baya da Sultan ya kore Ni." "Zoyah zauna muyi magana ta gaskiya." "Ki min shiru!" Ta dakawa Nannah tsawa. Cikin b'acin rai tace. "Bazan miki yadda nayiwa SAFINAH da Yaranta ba, sai dai zan azabtar dake, ta Hanyar da zaki rabu min da D'ana." Dariya zoyah tayi sannan tace. "Yaushe zaki fara? Kafin nan sai kiyi, kinci abincin da aka girka da guba, a wancan madarar dan haka karfin bala'i karfin tasirin shi, kuma zuwa nan da awa daya zaki daina amfanuwa da gab'ob'in jikinki." Ai lokaci guda Nannah ta rud'e. Ta mik'e ta zauna da gudu ta fita daga falonta, ta nufi gurin SAFINAH, tana shiga ta fashe da kuka tace. "Ashraf ina cikin tashin hankali zoka kaini Asibiti bani da lafiya, yanzun naci wani abu." Bai ce mata komai ba, ya mike sannan ya koma ya zauna, kiran Ghaniyu yayi. Can sai gashi ya shigo, nuna mishi Ummi yayi sannan ya bar musu falon, al'amarin Ashraf da daure kai dan yanzun padar ma ya daina zuwa, da suka takura mishi ya yace ya gaji da mulkin, kuma mutane na jin daɗin mulkin shi, shi yasa basu takura mishi ba, suka bishi da toh. D'akin SAFINAH shine matattarar farin cikin sa, dan haka yana shiga d'akin ya shaki kamshin humran da take amfani da shi, tsabar yadda take amfani dashi, kwanciya yayi. "SAFINAH! Ina kika shiga ne? SAFINAH Kiyi hakuri mu koma yadda muke dake da can baya" Haka yayi ta surutu shi ɗaya, ya gaji yayi shiru kuma,. Duk inda Ashraf yake tsammani ganin SAFINAH ya tambaya. Zumbur ya mike kamar wanda kunama ta harbe shi, ya shiga had'a kayan shi, sannan ya kira Fahad ya gaya mishi abinda yake bukata. Ina wanka Fahad ya kira shi bai dauka ba, sai da ya fito yaga kiran sai yabi bayan kiran sun jima suna tattaunawa, kafin ya gaya mishi abinda yake bukata sannan suka yi sallama. ★★★ Wai ina labarin Dr ne?! Share zufar da ta karyo mishi yayi lokacin da ya fito daga dakin wanke da ya kwantar da matar shi, Ammah ya samu a tsaye cikin damuwa tace. "Ya cikin yana nan?!" Girgiza mata kai yayi a sanyayye yace. "Ya fita!" "Allah ya bada na mora" "Amin Ya Allah! Kuma an mata daurin mahaifa, amma dake Ubangiji yafi mu son abin cikin kinga mahaifar ta bud'e." "Allah ya baku ikon cinye jarabawarku" "Amin Ammah!" Ofishin sa ya wucce tare da cire kayan jikin shi na aiki ya zauna a kujeran, yana me dafe goshinsa. "Hakkinki SAFINAH yaki barina na huta! Yaki barina na sami Sallama, Ya Allah ka yafe min" Tunda suka rabu da SAFINAH, matar sa tana da ƙaramin ciki a lokacin, bayan kwana biyu da rabuwar su, ne matar shi tayi barin wata biyu,, tun daga wannan ranar da zaran ta sami ciki toh baya wucce wata biyu zai zub'e, kuma duk irin kulawar da zasu bawa cikin bazai tsaya ba, yayi imanin da Allah kamar yadda ya zubda mata cikinta shine shima yake fuskanta. Ajiyar zuciya ya sauke sau biyu ya zubda na SAFINAH yau gashi na hudu ya zuba, tausayin matar shi yake, dan iya wahala tasha, yasan SAFINAH itama tasha wahalar da yafi nata. Tunda shi yayi ta zubda na SAFINAH, a yanzun yayi dana sani yafi kwandon dubu, ya tsani kan shi yafi sau dubu, babbar burin shi yadda zai hadu da SAFINAH ya nemi yafiyarta, ko zai samu salama, a zuciyarshi. Gyara zama yayi tare, kurawa wayar shi ido Dr Kyari yake son kira ko zai same number SAFINAH kunya da laifin shi suna dawainiyya da shi, dan haka ya ajiye kudirin shi ya cigaba da Addu'a ko Allah zai sa a dace. Mik'ewa yayi ya fita ya duba halin da take ciki, yana shiga ya samu tana ta barci tayi fayau, kamar wacce jininta ya kare, zama yayi tare da riko hannunta, ya saka a fuskarshi, yana cewa. "Laifina ne! Ni na aikata Allah yake hukunta ki da laifina, ki yafe min Ni naja miki komai, gashi kin rasa d'anki, ki yafe min ko nauyin da yake kaina zai ragu," Mik'ewa yayi ya bar d'akin, cike da tausayinta, da lokacin da jinin ya fara zuba ce mishi take. "Dr kayi wani abu don Allah kar na rasa baby a wannan karon Dr ka dakatar da jinin." Duk da sun zo asibitin akan lokaci bai hana cikin zub'ewa ba, suna cikin jarabta sosai. ★★★ An gama duba Nannah aka samu babu komai a jikinta da jininta, dan haka suka baro asibitin ta tsinewa Zoyah yafi cikin kwandon. ....... Ya juya daukar wayar shi idanunshi ya sauka akan sakon da Ta rubuta mishi, dauka yayi ya zauna sai da ya karanta tsaf, cikin sanyin jiki ya ajiye takardan. "Ba yanzun kika so fita a rayuwata ba, SAFINAH tuntuni kike da burin haka, amma kaunar da kike min ya hanaki tafiya. Me yasa sai da idanuna suka rufe zaki tafi? Me yasa baki hakura kin zauna dani a haka ba, SAFINAH ina kewarki da Yarana, kin tafi kin barni cikin kad'aicin da kika." Daukar park bag din shi yayi ya fito, haɗu yayi da Nannah. Tana kallon shi, cikin ki d'imauta tace. "Ina zaka? Ko ka manta kai din shugaba ne?" Takowa yayi har gabanta yace.. "Me zanyi da shugabancin da ya hanani fahimtar matar da tasani zama mutum, a da baki tuna dani ba! Sai da kika lalata tarbiyyar yar mutane sannan tazo ta miki sanadin gani na, amadadin ta samu jinjina da kambamawa, wai ita ce kika tsana, kuma kika tsamgwame ta shin Ammyn meye laifin SAFINAH? Meye tayi miki da zafi haƙa, Ni A sani na abin arziki tayi me yasa ya zame mata sharri." "Har ka manta itace ta kashe maka yara biyu! SAFINAH da ta zage ni, kake magana akanta yarinyar da bata ji maganar iyayenta ba! Ka farka mana" Kura mata ido yayi, sannan yace. "Tabbas Kinyi gaskiya kuma Mahaifiyarta tayi gaskiya da tace Allah sai yabi mata hakkin Yarta da muka zalunta, Ammyn kece kike cewa SAFINAH taki jin maganar iyayenta bayan kece kika daurata akan wannan hanyar, kece kika nuna mata komai tayi dai dai ne, yau gashi kina kiranta sunan mara jin magana, nayi Imani da Allah SAFINAH bazata tana kashe abinda ta haifa ba, dan koni da nake Ubansu bazan nuna mata kaunarsu ba, shine kike tunanin zata kashe Yaranta Ammyna yarinyar da tasha wahalar rayuwa saboda suce zata saka musu guba, wai meye nayi haka na hadu da uwa Mara Adalci irin tabbas ke baki min Adalci ba shine kike tunanin itama bazatawa Yaranta ba." "Amma ai kasan dole yaran ma su mutu tun da shegune, meye naka makin zafin dan a rage mata nauyin wulakancin da zata fuskanta." Sake baki yayi yana kallon ta cike da mamaki, sannan ya mai maita kalmar da ta furta. *Amma kasan dole yaran su mutu? Meye naka na ɗaukar zafi tunda shegune nauyi aka rage mata* Kamar wanda aka make take lokacin da likitan nan da ya amshi apple a hannun Ablah ya dawo mishi, sai bayanin da Dr Fu'ad yayi mishi. *Yaran an ciyar dasu guba ne? Sannan itama me nakudar guba aka bata, sai dai bata ci sosai ba dan babu abinda ya same yaron cikinta* Kallon Nannah tayi sannan saka ya fita, har ya isa bakin kofa yace. "Da hannunki a kashe min Yarana? Da Hannunki A ciwon Natashah? Ammyn na barki da Allah, Ammyn na bar muku Mulkin dan na ajiye, bazan muku hukuncin ba, amma Allah da kanshi zai hukunta ku." Komawa cikin gidan yayi ya kuma diban abinda zai diba, sannan ya je ya saka a mota, daga nan gidan yarin ya wucce yasa aka fidda Bilal, ya mika mishi dukiyar shi, sannan yace. "Daga Ni har kai dole mu hakura da Mulkin jordan domin yafi ƙarfin mu, matukar kace zaka yi sai ka rasa wani abu me daraja naka, kaje Sandia da Ummanshi suna jiranka, nima na bar barwa Ammar mulkin dan naga Adalci a cikin idanunshi." Rungume juna suka yi sannan Bilal yace. "Zan koma inda muka fito ne, Moscow ko zamu koma tare, sai mu sayi gida a can" Murmushi Ashraf yayi sannan yace. "Toh haka ma duk shawara ce, ka saya mana babba wanda zamu zauna da jama'ata dan akwai abokaina biyu." "Ai idan ma da duk jordan nan ina tabbatarwa da Sarkin Jordan da yayi murabus sabida mace" Murmushi yayi kawai sannan yace. "Muje" Haka suka jera har cikin masarautar, inda ya same Ghaniyu da Fahad sun had'a kan jama'an padar, shiga suka yi sannan ya nemi guri ya zauna. Shiru yayi kafin ya mik'e yace. "Natara kune dan ku fahimci abinda nake son nayi, Yau 24-5-2018 Ni Muhammad Ashraf bini Abdullahi bini Yasir na ajiye." Shiru padar yayi sakamakon nauyin abinda zai fada, sannan ya cigaba da cewa. "Na ajiye mulkin jordan baki d'ayan,. Na bawa Ammar bini Abu Zarri." Toh fa ga Ashraf ya ajiye mulki, wata fata kuke mishi...... [3/21, 11:28 AM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 4️⃣ "Ina me baku hakuri abinsa murabus din da nay, Ni kaina bani da yadda na iya ne." Muryan shine ya kama rawa, sannan ya d'ago kai ya kalle su sannan yace. "Na rasa mata na biyu da yarana, don Allah ku manta na zama wani abu a cikin masarautar nan, don Allah karku nime dan yin haka zai sanya Ni a damuwam" "Insha Allah! Ashraf bazamu tab'a damunka ba, sai dai idan kujeran taki wanda aka bawa dole zamu nimeka tunda kana kuma raye, bawai ka mutu ba, ban ji dad'in abinda ya faru ba, amma Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Jingina kai yayi sannan ya mika musu takardan, murabus ya juya gurin Ammar ya mika mishi hannu yace. "Ina taya ka murna! Allah ya tayaka riko." Jingina kai Ammar yayi, yana zubda kwalla saboda tashin hankali dake cikin mulki, masifa ce idan baka bida ita yadda ya dace ba sai ta kaika ga hallaka. Godiya da ban hakuri yayi musu sannan ya bar cikin padar, tausayin Mahaifiyarshi yake ji sabida shi ta wurga kanta cikin wannan matsalar, sai dai bazai tafi da ita ko ina ba, Oman yake son fara zuwa yaga halin da Natashah take ciki, kafin ya diro naija. A hankali yake tafiya suna bin bayan shi har inda Ghani ya ajiye motarshi, sannan suka bar Masarautar. "Sultan ina zamu nufa?!" "Gidan su Sandia inda Umma take" Sun isa gidan, suka tattauna da Mahaifin Sandia, sannan suka bar gidan. Dan Ashraf yace musu shi Oman zai je, zai bar Bilal a cikin Jordan dan iyayen yarinyar sun bashi aurenta. Tun kafin Ashraf ya isa Oman ya aikawa Amirah Khadijah cewa gashi nan zuwa, ★★★ Shiru nayi ina kewar shi, wanda ya cika min zuciya, tsigar jikina har mik'ewa yake. A hankali cikin raina na ambace shi. *Ashuuna* Tunanin irin zargin da yake min ne ya sani jin kwalla sun cika min ido, tabbas Ashraf zargin nice na kashe yaranmu yake, meye yasa haka me yasa ya gaza fahimtar bazan kashe abinda nafi kauna a duniya ba, yarana nafi son su da komai, nafi kaunar su da komai. Kuka ne ya kwace min, na tashi zaune sai da nayi me isata sannan, na mike zuwa ban daki nayi uzurina sannan nafito. Shigowar Ablah da Affan ya katse min tunanin da nake. "Ummu! Affan" Murmushi nayi domin idan ta tsokano shi,sai tazo da gudu ta b'oye a bayana ko Bayan Dudu. Cirota nayi na kalle shi yana goge jikin, nace. "Abbana meye ta maka!" Nuna min gefe fuskar shi da ta yakushe shi naga yayi ja, juyawa nayi na kalleta sai ta saka dariya, rike kunnen ta nayi ta cilla kara, zare mata ido nayi nace. "Idan kika kuma sai na cire kunnen, bana son mugunta irin taku ta gado." Yadda take ihu sai ka rantse na riƙe kunnen da karfine kuma babu wani rikewa da nayi da karfi. Dudu da Sophia suka shigo da sauri, Ni kuma ina ce mata. "Idan kika kuma yakushinsa sai na cire kunnen yar me halin gado kawai." Cire hannuna Dudu yayi yana murmushi yace. "Ai ba sai kin zagi halinsu ba kawai kice me irin halin kakar ta." Dariya ma suka mai da fadan da nake mata, sannan suka fita da ita ni kuma na ce Affan ya zauna muyi hira dan yana rage min kewarsu Aamih. ★★★ Jordan.... "Ai bazan kashe ki ta sauki ba, tunda d'an da kike gudun kar a rabaki dashi ya tafi ya barki, zan ta gasaki har sai kin mutu dan kanki." A fusace Nannah tace. "Tir da halinki, ai Ni nacewa nayi kiyi kokarin da zamu kori SAFINAH da Natashah, bawai ki kashe wani a cikin yaran ba, me kika ce a'a zaki basu guba bata da karfi sai nace Uwarsu ce ta basu, toh gashi daga ci sun mutu." "Duk abinda zaki ce sai dai kice amma tare muka yi komai." "A'ah Zoyah! Kece kika kashe su Husnah" "Kedai!" Nan rigima ta kaure a tsakanin su, Zoyah nacewa ba ita ta kashe yan biyu Nannah tana cewa ita bata sata ta kashe mata jikokinta ba, karshe dai Zoyah taji da zuci ta ture Nannah akan wani karfe, take ya hudata har sai da ya fito ta gefen hakarkarinta na dama. Ihun Zoyah tayi tare da fita da gudu, koda ta isa wajen ba kowa. Tana son fita kuma tsoro ya hanata domin gurin ya koma tankar babu wanda ya tab'a rayuwa a gurin, wuf taga kamar abu ya wucce ta bayanta da sauri ta juya, aikuwa aka sake wuccewa da gudu,.ai bata san lokacin da ta shige gidan ba, ta koma inda Nannah take cikin jini, Wutar gidan ne ya dauke, aikuwa aka shiga zane su da bulala, tun suna ihu da karfi har suka daina, kuma ba a fasa dukar su ba. ★★★ Oman... Dakin da aka kwantar da Natashah ya shiga, ya ganta tayi kare ta koma abin tausayi, hawayen tausayinta ne ya zubo mishi. Rungume ta yayi sosai tace. "Ashuuna" D'agota yayi yana kallon fuskarta, murmushi tasake mishi sannan ta cigaba da cewa. "Ciwon yaci karfina! Bazan tashi ba, kuma dama addu'ar da nayi Allah ya amsa min, cikin ku biyu Allah yasa na mutu a gaban ku, kai da SAFINAH. Sultan ba dan Ni ba kodan albarkacin Yaron mu kace kana sona!" Sake rungume ta yayi ya sumbaci goshinta sannan ya gyara mata zama a kirjinshi, yace. "Waye ya gaya miki bana sonki! Ai idan kaji so d'aya kenan, ina kaunarki da duk zuciyata." D'ago kai tayi tana murmushi tace. "Kana fushi da Ammyn ko? Kayi hakuri ki nima mata tafiya dan tayi nisa. Idan ka had'u da SAFINAH kace na bar mata, Amir" Gyara kanta tayi a kirjinshi, tana sauke ajiyar zuciya, tana kuka. Share mata hawaye yayi jikinshi yayi sanyi yace mata. "Cuta ba mutuwa bane, idan kika yi hakuri Allah zai baki lafiya." K'amk'ame shi tayi tare da kifa kanta a kirjinshi tace. "Inji wa yace maka bazan mutu ba? Aini kadai nasan yadda nake ji, ciwon da ya tab'a hanta da koda itace za a rayu, nasan ba zan tashi ba. Duk wanda yace zan tashi sai naga kamar yaudara ta yake." "Ni nace zaki tashi!" "Ni kuma nace bazan tashi ba, ga Yarona nan na bar muku." Abin tausayawa domin dukkan su kuka suke, yana kara jin tsanar Nannah. Tarin da take ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yake ciki, d'agota yayi cikin tausayawa yaga yadda bakin jini ke fita ta bakinta da hancinta, tana Son magana amma jinin dake zuba ya hanata cewa komai, ko sai bud'e bakin take tana rufewa, kuka yake itama hawaye na zuba mata. Abin tausayi yana ji yana gani, Allah da yafi shi sonta ya amshi Rayuwarta a hannun shi, rungume tayi. Yana kuka dan bai taɓa sanin yana sonta ba sai da yaga tana kokuwa da rayuwa, sannan yaji yana son, kuma koda babu SAFINAH zai sota, sai dai abinda Bature kecewa too later shine abinda Ashraf yayi, ya makaro, dakyar mahaifinta ya zare shi a jikin gawar Natashah yace. "Ita din kyautar Allah ce, dan a cikin maza uku manyan Allah ya bamu ita, Shi yasa muka ambaceta da Natashah (Gift Of Allah) toh wanda ya bada ya amshi abinda sai Hakuri." Jaririnta wanda ake bawa madara, ya shiga callara kuka kamar yasan da mutuwar Mahaifiyarshi, kukan yaron ya sashi kuka. Wayar shi ya dauka ya kira Ummi yana kuka yace. "Ummi bani da kowa! Bani da komai Ummi Natashah ta rasu, ga jaririn da tab'awa SAFINAH, Ummi Ni me laifine, ku dubi girman halin da nake ciki ku tausayawa jaririn da yarasa Mahaifiyarshi, Ummi ki fada min irin abinda baku so ayi mata, wallahi zan k'iyayye, kuma zan bata dukkannin soyayyar da ta rasa, Don Allah Ummina." Shiru Ummi tayi bata iya cewa komai ba, har kiran ya katse dai dai lokacin da aka fidda gawar, yana kuka iyayenta na kuka, a hankali yake takawa har ya fito Wajen Asibitin, karar da wayar shi tayi ya tab'a sannan ya saka a kunne. Kuyi hakuri wallahi ina fama da barci🤣😂 [3/21, 7:56 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 5️⃣ Ɗaukar wayar yayi, sannan ya maida aljuhun wandonshi, hawaye na cika mishi idanu, me rarrashi yake nima, amma babu tun yana ƙaramin shi ya rasa soyayyar Uwa da Uba har ya girma, SAFINAH itace soyayyar shi ta farko, ta jure komai na shi. Tayi hakuri da shi iya hakuri ta jure duk wata matsala daga gare shi, bai tab'a ganin mace me hakurinta ba, an mata abu bai rama mata ba, sai ma hakurin da tayi dashi da kuma Mahaifiyarshi, yayi imanin kafin ya samu mace me hakurin ta zai dauki lokaci, yana cikin kewarta, Natashah ta tafi ta barshi. Ta kuma bar shi da damuwa me tarin yawa, Mota ya shiga rike da yaron suka nufi gidan sarautar Oman, tun a hanya yakira Ghaniyu ya gaya mishi ya dauko Ammynshi ya kawota cikin yan uwanta . Ghaniyu ya tausayawa Ashraf sosai, koda suka isa akayi mata sutura sannan aka kaita makabarta cikin masarautar aka binneta, zama yayi a jikin kabarinta, sai da Mahaifinta ya riko hannunshi, suka fita idan ka ga Ashraf dole zuciyarka tayi rauni. Tun da aka dawo ya shiga shashinsa na gidan wanda yake had'e da na Nannah ya zauna yana tuna, darensu na farko da ita, tare da wasu abubuwanta masu tsayawa a rai. ★★★ Tunda Ummi ta gaya min mutuwar, Natashah gabana ya fad'i jini ya shiga zuba a jikina sai da muka dangana ga Asibiti dakyar aka tsayar da cikin. Bayan an fito dani ne, na lumshe idanuna, fuskar shi kawai nake gani a cikin kwayar idanuna, Shigowar Dudu da Sophia ya sani bude idanuna, nace. "Please phone!" Number shi na Oman na gwada kira, aikuwa ya shiga amma yaki dauka. "Dudu! Yaki d'aga kiran" Na fada mishi a raunane, hawaye na zuba daga idanuna. Tab'e baki yayi a ran shi yace. *Allah Nagode maka da ban shiga rigimarku ba, da yanzun an dawo ana jin haushinsa an kirani da munafuki* "Didih kinsan yana cikin halin rashi, dole sai Kinyi hakuri zuwa nan da sati biyu." "Sati biyun fa" Yadda nayi maganar shi kan shi sai da ya zaro ido waje, kamar na zan zabga mishi naushi. "A'ah toh kiyi hakuri nan da sati toh" Kauda kaina nayi ina share kwalla, nace.. "I love him!" "Ba sai kin faɗa ba, tunda kika iya bijirewa kowa sabida shi ai." Ɗaukar pillown da kaina ke, bisan shi na jefe shi da shi. Ina dariya. "Ko ke, miss love matar Sultan." "Dudu yaushe muka fara da kai." "Wallahi Didih keda Ashraf had'inku daga Allah ne." Natashah ta tab'a gaya min haka, share kwalla nayi bayan na sunkuyar da kaina nace.. "Shi din Sirrina ne, jin dadina da farin cikina na zauna inuwar shi." Ban san ya akayi bakina ke yake yabon Ashraf, da fadan duk wata abu me darajar shi, Ashraf shine duniya na, farin ciki na rayuwata kimata, duk shine babu ranar da zata bud'i ban ambace shi a zahiri da badili, Rayuwata dashi kamar zanen ƙaddara ce, domin ban shiga tashin hankali ba sai da nayi gamo da soyayyarshi, nayi kuka nayi bakin ciki taya zan tsinci soyayya ban san waye shi ba, amma ban fasa jin komai ba, Idan akwai abinda naso tsayin rayuwata Ashuu ne, na soshi tun ban gan shi ba, na kuma cigaba da son shi tunda naga shi a matsayin shugabana. Zan iya kiran soyayyar shi, da zakarar gwajin dafi." Tafa min yayi sannan yace. "Didi kina son Sultan da yawa." "Idan kace haka baka mishi Adalci ba, dan ita ce maka yafini nuna soyayyarmu a fili, banda ina jin kunyar Ummi da na kira shi." "Babu ruwan bawan Allah." Murmushi nayi sannan nace. "Aikuwa nace mata a wayarka na kira shi." Abinda yasa Dudu yake biye min, likitan da ya amshi case d'ina yace mishi matukar na cigaba da zama Ni ɗaya , toh za a iya rasa cikin jikina saboda tunanin da nake yawan, wanda har ya tab'a min zuciya. Shi yasa yake ta biye min. Shigowar Sophia da yara tare da, Ada wacce take mata renon. Har gadon Affan yayi, ai kuwa Ablah tasa kuka, ya kwace mata Mamanta, dama akaina suke fad'a. Gyara mishi zama nayi cikin wasa nace. "In-law haka zamu yi dakai kana saka, kishiyar Ummi kuka, anya za ayi abun kuwa." "Allah ya kiyaye mu bashi gimbiya guda, ai sai dai ya komo matar shi a waje." "To shima me zai yi da nunar rana mace ba kwari, sai kukan banza ana tab'a ta tace Appa." "Allah Didih ki daina haka." "Kuma ku daina mana, ku gani." Haka muka cigaba da hirar mu, amma cikin raina ina jin rasuwar Natashah, ji nake kamar nayita kuka sabida na saba da ita ko Zoyah ce itama ta rasu zan tausaya mata balle kuma wacce ta nunawa yarana wata irin kauna, tun daga lokacin da ta nuna min ita tana kishi dani amma bata kishi da yaran na bata matsayi a raina dan lokaci da hannun Mariamah ya goce, nayi mata magana, tace min. " Kuyi hakuri, wallahi gurin cillata ne amma bazan kuma ba." Ko lokacin da nace sai na watsa mata mai me zafi naga, tsorona da kuma firgice a idanunta, Ashe ba nisan rayuwa zata yi ba. ★★★ Jordan.... Cikin mugun yanayi, Ghaniyu da Fahad suka fidda Nannah wacce rabin jikinta ya shanye har yayi Kore kore, mamaki da al'ajabi ne ya kamasu, basu ga Zoyah ba, ga gidan sai warin bala'i yake, dole aka shiga duba inda Zoyah take tana can wani daki wanda aka azabtar da Safinah lokacin zuwan ta, dakin zafi suna bude ta suka ga tayi wani irin baki tsabar azaba, dan ko numfashi bata iya ja..... Kuyi hakuri 😎 Kiuya mood [3/22, 2:00 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 6️⃣ Haka suka fidda ta daga d'akin, aka wucce dasu Asibiti, an karb'e su cikin tashin hankali, ya kira Ashraf yake gaya mishi halin da ake ci yace babu ruwan shi, kawai idan jikinta yayi sauki, ya kaita Oman. ★★★ Yau kwana goma sha biyar kenan da rasuwar Natashah, ya had'a kayan shi, bai iya sallama da kowa ba ya bar gidan. Domin niman SAFINAH, cikin zuciyarshi tsoro yaƙe ji kar yaje ace bata nan, duk ya rasa wata kwarin gwiwar da yake da ita akan inda take. ......... A safiyar jumma'a ya sauka a garin Abuja, da Khalil suka haɗu. Dan ya gayawa Ummi gashi nan tasowa, sai ta tura Mishi khalil, tun da ya shiga motar ya kwantar da kanshi jikin sit, bai kuma d'agowa ba, dan gabaki d'aya kunyar a halin SAFINAH yake, duk duk maganar da khalil ke mishi bai cika amsawa ba, har suka isa gidan. D'akin Khalil din ya sauka dan yaki zuwa shashin Nannah na gidan, bayan yayi wanka ya huta. Sannan ya saka kayan ya tafi zuwa cikin gidan, su Ummi suna falon da sallama ya shiga falon, amsa mishi suka yi zai zauna a capter kamar yadda Khalil yayi Umma tace min shi. "A'ah zauna a kujeran, kai bakon mune me daraja, kuma sirikin gidan nan zauna a kujeran." Duk sai yaji kunya ta kama shi, jiki a dararre ya zauna kanshi a sunkuye, ya kasa koda dogon magana, gaisawa kadai ya had'a su, kallon shi Ummi tayi sai zuciyarta yayi rauni duk ya gigice, ya zabge sai uwar idanu da hanci. "Ya hakurin rashin da akayi." Sake sunkuyar da kai yayi, sannan yace. "Alhamdulillah! Ummi" Duk sai taji bazata iya barin shi ya cigaba da wahalar niman SAFINAH ba, Shima a bangaren shi, so yake ya tambaye ta, ko anga SAFINAH amma kunyar abinda yayi sai yasa shi yin shiru, fitowar Batul da waya tana cewa. "Ummi ga Didih zata yi magana dake." Ya sashi d'ago kai kamar ya kwace wayar a hannun Batul, fuska Ummi tayi ta amshi wayar ta kara a kunne, shiru tayi can tace. "Idan ban isa dake ba, ki dawo karki zauna na saya miki kima, tunda ke sakarya ce." Dake da harshen Shuwa tayi mata fad'ar duk sai ya damu, yana son tambayarta, amma yaga taki sakin fuska, sai ya mike yace. "Ummi bari naje na huta." "Yayi kyau, ai kayi dogon tafiya." Haka ya fita daga falon, ta kalli Khalil tace. "Ka dauki abinci ka kai mishi, saura ya tambaye ka inda Didih take ka gaya mata, sai na cire kunnenka." . Zaro ido Khalil yayi cikin dariya yace. "Ummi yanzun don Allah, magidanci irina me yara tako ina zaki cirewa kunne, toh idan nayiwa yarana fad'a ai ba zasu ji ba, tunda gashi uncle dinsu an cire nashi." "Allah ka wucce kabani guri da shegen surutu kamar ka had'iyi aku." Shiru yayi tare da zaro ido kitchen ya shiga ya dauko abincin yana dariya. Sannan ya fita daga gidan, ya nufi inda d'akin shi yake, ya ajiyewa Ashraf abincin. Zai fita Ashraf yace min shi. "Khalil baka san inda Didinku take ba ko?!" Girgiza kai yayi, cikin tausayin Ashraf dakin yace. "Ban sani ba!" Murmushin ƙarfin hali Ashraf yayi sannan, yace. "Toh ba damuwa." A sanyayye Khalil ya bar d'akin, ya nufi falon Ummi zuwa yayi gabanta ya zuba gwiwarshi a kasa, sannan ya daura kanshi a cinyarta, tausayin Ashraf ya gama cika mishi zuciya. "Auta lafiya kazo zaka karya min kashin." D'ago kai yayi cikin damuwa yace.. "Ummi!!" "Menene Autana!" "Dan girman Allah ki bashi Didih itace farin cikin sa" Ture kan shi tayi daga cinyarta, tace. "Wallahi idan ka kuskura nayi ya tafi, Ukraine sai na sab'a maka.". Shiru yayi, tare da barin jikinta. "Ummi rashi yayi fa! Ummi kira yadda ya koma, yana cikin damuwa sosai, Didih yake nima a cikin rayuwarshi don Allah Ummi ki bashi Matar shi." Hararar shi tayi sannan ta mik'e tare da barin falon dan Umma ta jima da barin falon. Tausayin Ashraf ne ya kama shi, dan dai yana tsoron Ummi ne da sai ya gaya masa inda Didih take. ★★★ Kwana uku da zuwan shi kasar, sam ya kasa gane kan Ummi, abinda ya fara yi, shine ya shirya ya tafi Maiduguri, har gidan Sheikh Hayatudeen yaje, suka gaisa. Kwanan shi biyu amma babu SAFINAH babu labarin ta. Yaje gidan Hajja, dakin da suka zauna da SAFINAH ya, sauka sai zaman su da ita ya shiga dawo mashi. Fita yayi daga d'akin yazo waje ya zauna, wayar ce tayi kara, ya daukar wayar yayi yaga code din kasar waje, kundubala yayi ya dauka. Abinda kunnen shi ya fara jiyon mishi muryan Ablah tana cewa.. "Ummu Affan" Ita kuma tana ce mata. "Shiiii" Murmushi yayi idanunshi na kawo ruwa yace. "SAFINAH!" Kashe kiran tayi baki daya, aikuwa yabi kiran koda ya shiga muryan Ablah yaji tana cewa. "Appa." Ta kinkimo turancin da larabci ta kwaba mishi, dariya ya saka sannan ya cigaba da biye mata suna hira. Ihu tasaka tare da fashewa da kuka, yana jin Safinah tana cewa. "Dan gidan ku, idan ya damu da mu, ya nime mu mana." "Har yanzun ana nan da Yarinta kenan, bari nazo sai ki gaya min waye bai damu da kuma." "Ba sai kasan inda muke ba." "Yarinya karki yi min iyayi gobe ki ganni cikin garin da kike." "Kamar da gaske." "Toh da wasa nake miki da zaki ce kamar da gaske." "Eh nasan baka da masaniyar inda muke dan haka ka gama bilayinka bazaka san inda muke ba" "Haba baby na Ni din ne toh ina zuwa." Kashe kiran yayi ya kalli code din, sannan ya bude data din shi ya shiga Google, ya shiga nima kasar da suke da wannan code din, murmushi yayi lokacin da suka nuna mishi Ukraine ce me wannan number, Kiran ta yayi sannan ya sake murmushin jin dad'i yace. "Kinsan iya adadin lokutan da na b'ata ina tunanin ki?! Kinsan iya adadin ranakun da na b'ata, ina nazarin inda kike, SAFINAH nayi laifi bakin saurarar ki, amma fitarki a rayuwata ta sani na fahimci inda gaskiyar take, Safinah ki bani dama na gyara kuskure na " "A'ah Ashu! Bazaka tab'a gyara halin ka ba, sabida ka aureni ne dan ka sanni bawai dan kana sona ba. Abinda yafi dacewa mu hakura da juna, shine mafi alkhairi na gaji da tashin hankali, shekaruna ja baya suke, ba karuwa ba, taya zan zauna cikin damuwa kullum, a madadin na sami nutsuwa sai na buge da zama cikin damuwa, kawai kan kaje ka zauna da Zoyah ita da Nah" Rintsa idanunshi yayi da mugun ƙarfi, kafin yace. "Don Allah ki daina gaya min haka, kuyi hakuri dani mana wallahi bazan kuma sanyaki a damuwa ba, dukda nasan inda kike amma zan jira Ummi ta bani izini zuwa ganinki." Yana gama fad'ar haka ya kashe wayar, dan yanzun hankalin shi a kwance yake, tunda yasan inda take. Washi gari ma sun jima ana tashan love, da yamma ya bar garin Maiduguri, zuwa Abuja bai fada yana hanya ba sai Ganin shi sukayi kwatsam, kuma har zuwa lokacin Ummi bata nuna mishi ta damu da halin da yake ciki ba, sai ma nuna mishi ko in kula akan batun Safina, Dake Abba baya gari, kwanan shi biyu da dawowa. A masallaci suka haɗu, Abba yayi mishi ta aziyar matar shi, yaji dad'in haka, dake bai san basu tare da SAFINAH ba, dan haka sai yake tambayar shi ina amaryan Mota. Dariya yayi sannan yace.. "Amaryanka da Mamarta suna lafiya." So yake ya fad'a mishi gaskiya basu tare da ita Safinar amma yana gudun kar ya janyo musu rigima, dan haka yayi shiru Khalil da yake kusada shi ne yace. "Abba! Didih tana gurin Abban Affan, Ummi taki na gayawa Sultan, don Allah Abba karka ce mata mune muka gaya maka dan fada zata min," Shiru Abba yayi yana mamaki sauyin Halayyar Mariamah, dan yasan ba haka take ba lokaci guda ta sauya hali kamar wacce aka mata wani abu, idan domin laifin da Nana Asma'u tayi ne, ai yaci ace an yafe mata, kodan Albarkacin zuri'a da aka had'a ai tayi hakuri balle shi bai ga abinda damuwa a nan ba da ta dauki zafi haka, aiko A Shari'a yafita iko da matar shi, dan haka da akayi sallar isha ya shiga gidan, sai da ya fara cin abincin ya bari har ya kusan gamawa sai ya tsare hannunshi yace. "Ashraf shi d'aya yazo ina SAFINAH da Balarabiya yarta?!" Shiru tayi tare da shan jinin jikinta, sannan tace. "Alhaji kenan baku haɗu dashi bane a waje?" Murmushi yayi sannan ya tura filet din, yace. "Mun haɗu Kafin muyi dogon magana mutane sun shiga tsakanin mu, ina son magana da SAFINAH, kona kira Number ta na jordan baya shiga." Wuta ta dauke, tare da kallon shi tace. "Toh! Toh! Ko d'azun munyi waya da ita." "Ai ba damuwa bari na kira Abdullahi ya bani numberta." "Haba Alhaji wannan ujilar fa, kawai ka bari idan Allah ya kaimu gobe sai na baka." "A'ah na kwana biyu banji muryan SAFINAH ba, gwara na kirata ko zuciyata zata nutsu." "Toh ka bari gobe mana, tunda kaga dare yayi kuma suna ganin kiran mu zasu ɗauka na wani abu ne." "Ita da waye zasu ɗauka wani abu ne? Sannan kiji tsoron Allah ki bari ma'aurata su zauna a karkashin inuwa d'aya, abinda kike yi bazai tab'a kakaro miki daraja ba, sai ma zubda miki da kimarki a idanun surikin mako, banga laifinki dan ki jawa yarki kima ba, amma ki duba halin da yaron yake ciki da gatan shi da komai nashi ya ajiye ya biyo yarki, ki duba tarin izza da jin kai irinta larabawan, amma ya tsallake yazo. Haba Mariamah yayi laifi eh yayi laifi amma bai kai wanda za'a hana shi matar sa ba, komai yayi ayi hakuri ya rufe kodan kishiyar ki me gashi yala yala sannan ki duba girman rabon dake tsakanin su." Shiru tayi tana kara juya maganar shi a ranta da kwanyarta, lumshe idanu tayi Sannan ta bude akan fuskar shi, tace. "Ni tashin hankali ne bana, so kuma yanzun ana bashi ita zasu koma gidan jiya, dan Mahaifiyarshi ba don SAFINAH take kaga babu amfanin bad'i ba rai, shi yana sonta uwar shi bata sonta, kaga akwai damuwa, shi yasa na hana khalil ya gaya mishi inda take, dan nasan sarai zai iya zuwa inda take, Ni kuma abinda bana so kenan. Dan ba wani lafiya ce da ita ba, suna haɗuwa wani abu na daban zai biyo baya, shi yasa na kwaɓe shi da surutun banza mara kadari" Gyara zama Abba yayi sannan yace. "Yana son matar shi, kuma zai zauna da ita, aike a daɗin ki tunda mijinta na sonta, sannan ita ma yar taki kinsan irin nata halin da kike ganin laifin shi, zatayu shima hakuri yake da itama amma kike ganin kamar, ita ake cuta, dukkansu miskilan banza kowa da laifin shi kuma iyayensu mata da maku laifin tunda kun gazawa yaranku Adalci....... Ya kuka ji batun Abba.... Karku manta yau Sunday ne kuma d'aya nake badawa, Sai ko Parih, Mi gitin tem to tafin kuruciyar Jan Parih 😎🤣 [3/23, 2:09 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 7️⃣ "Nifa shawara na baki, tun da sauran kimarki a idanunshi ki bashi Matar shi, idan kuwa kika ki. Darajar ki da yake gani ne zai sauka kasa sosai, kinga kenan zamu iya cewa ina dajarar take, tunda kin zubda shi garin kare ta yarki, Don Allah ki bar shi ya dauki matarsa shi Kinji," Daura hannunshi yayi saman nata, yana kallon fuskarta. Tare da jinjina mata kai, kwalla ce ta sauko daga idanunta ta bud'e baki zata magana ya dakatar da ita, sannan yace. "Ban da sakalci ke kiyi kuka SAFINAH tayi kuka, toh waye zai rarrashi wani?! Ki daure ki a bashi matar shi mana." Sake bud'ar baki tayi zayi magana yace. "Allah Kiyi hakuri ki bashi matar sa, munyi laifi dan ko maso ki fahimci abinda nake da tabbacin sa ba ganewa zaki, Allah ki bamu matar mu." Ya mai da al'amarin wasa, sosai sannan ya kara da cewa. "Bari na miki wata magana wanda zai tabbatar miki SAFINAH tana tare da mijinta, ba wai zarginta nake ba, amma ina da Yakinin suna tare da juna, kirata kice mata ta kyauta miki da kika ce karta kirashi sai da takira shi, zaki ji abinda zata ce." Shiru Ummi tayi kafin tace. "Alhaji ita tace da bazata kuma kiran shi ba, koda yazo a karba mata takardanta.".. Duk yadda yaso ta fahimta taki sai ya zuba mata ido a ranshi yace. *Ba dai SAFINAH nace zata kunyataki* ★★★ Washe gari da wuri ta tashi bayan ta gama komai na al'adar gidan, sannan takira Safinah abinda ta fara cewa. "Wato SAFINAH da nace karki kira Ashraf sai da kika kira shi ko!? Ban isa dake ba? Namiji yafi iyaye ko?!" "Ummi kiyi hakuri! Ablah ce take kuka sai na kata gurin Appanta." Jikinta ne yayi masifar Sanyin. "Safinah wacce irin so kikewa Yaron nan ne da baki iya kame kanki daga gare shi." Kuka ne ya kwacewa SAFINAH, tace. "Ummina! Wallahi ban san iya adadin son da nake mishi ba, Ni dai bana iya jure nisanta kaina daga gare shi, zan iya hakura da komai ban da Son Ashu, Ummi kiyi hakuri bazan kuma kiran shi ba." Ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan tace. "Toh duk abinda kuke jibi ku dauko hanya." "Ummi kiyi hakuri! Bazan kuma ba" Yadda tayi maganar sai ya kara kashewa Ummi jiki, tace. "Wata sati ina son ganinku a Abuja." "Toh Ummi naji! Amma Kiyi hakuri ba zan kuma ba." "Allah yayi miki albarka." Haka suka yi Sallama da Ummi, kowanne su yana jin ba dad'i, musamman Ummi da ta shiga tsakani tayi kabe-kabe (🤔) ★★★ Jordan..... Dama ita rayuwa dama ce Allah da ya bamu, domin kambamawa da kuma gwarzantawa, sannan suna tafiya akan hanya me matukar ƙayoyi da tarin fasasun kwalaben. Ita rayuwan nan ko anki ko anso turare bata da uwar da ta wucce kwalba, Yau ina Abu Zarri, ina Yasir bini Alhashmiyya, Ina Abdullahi bini Alhashmiyya, Yau rayuwar da aka jingina ta domin wasu ta kare , ina kuma wanda ya jingina tashi rayuwar domin kansa, Duk wata dama da ake samu na rayuwa An bawa Ukshe, amadadin ya gyara sai ya kuma lalata komai, mutumin da duk abinda yake so ake mishi yau shine ake juya akalar rayuwarshi, abinci sai lokacin da ake bukatar yaci ake basu ba lokacin da shi yake bukata, wannan ita sirrin rayuwa, kayi amfani da Damarka kafin lokacin da zai subuce maka. Kwallar nadama ce ta sauko mishi, tunawa da yayi dukda tawaye da yake da ita, haka bai hana shi samun damar da za a kira shi wani a kasar ba, sai gashi garin son kai da son zuciya irinta dan Adam, yau Gashi ta kare mishi a gidan ajiye tsofi. Dan shi Uzaif ya manta dashi, sauran al'umma yana kyautata zaton sun manta da babin shi, rayuwa kenan kayi dai dai ya aka cika balle kuma bakayi dai dai ba,(_Shi yasa nake mamakin yadda kai baka kashe wutar gabanka ba, amma kana saka ran kai zaka iya kashe wutar Wani, kowa yayi abinda yaga yayi mishi ra'ayina daban na Mrs Jmoon daban, haka ma na Mrs G daban, sannan dukkan mu uku babu wanda zai ce wance zaki bi ra'ayina, dan ke ba akan dai dai kika daura ra'ayin ki, ba, duk wanda yake da hujjar kare kanshi, kare da kuɗin shi , a wannan lokacin da zaran ka fadi gaskiya an kiraka da munafuki, idan kayi shiru akirana da Annamimi 🤣😂🤔 har kaji a ranka kabar kowa ya tsula tsiyar shi ko ba haka ba😜🤪_) Tura kekenshi yayi zuciyarshi a cunkushe, yaje ya amshi abincin da yake ci, har zai wucce yaji sanarwar da ake na sabon sarkin Jordan, Ammar sunkuyar da kai yayi cikin jin kaskanci, yau kujerar da yake hari gashi ta fita daga gidan da suke ta yakarta dan samun ta, yau gashi D'an Abu Zarrin da ya kashe shine akan mulkin da ko yaran shi baya kaunar so ambaci suna son zama sarakuna, kaicon Rayuwar da bata amfane shi da komai ba, sai bakin ciki da damuwa, saukar hannu yaji a kafad'arshi, ya d'ago kai yana kallon mutumin da ya dafa shi, goge fuskar shi yayi sannan yace. "Kuka baya magani kuma baya goge bakin fentin da kayi, aikin alkhairi tare da tuba tsakanin bawa da Allah yana rage wasu abubuwan, idan kaji abinda na aikata kai kanka." Girgiza kai yayi cikin damuwa, sannan yace. "Wani alamarin sai Allah! Ka cigaba da niman gafara." Sun jima sosai suna tattaunawa, har Ukshe ke gaya mishi irin abinda ya aikata, shima ya kuma gaya mishi irin nashi laifin, da yadda zasu yi tunanin me kyau. ★★★ Oman.... Ghaniyu da kan shi ya isa da Nannah wacce ake turata a kan gadon marasa lafiya, zuwa cikin gidan Sarautar Oman. Jiyar da kai Mahaifin Natashah yayi, hawaye nazm zuba daga idanun shi, yau yar uwarsa wacce take da yawan alkhairi itace me mugun laifi har haka, idan aka mikata ga kuliya hukuncin kisan kai za a yanke mata, amma sabida lalurar ciwo yasa sun barta da halinta yadda ta iya ha'inta dan cikinta babu wanda bazata cuta ba. Dan haka suka mai da ita Asibiti aka cigaba da jinyar ta. ....... A can Jordan kuwa Yan uwan Zoyah suka juya mata baya, dan ta b'ata musu sunar kabilar su, tare da zubda musu da kimar su, sannan tayi dalilin da babu wani Bahashmin da zai kuma auren Yar kabilar su ba, koda kuwa a k'ork'ora suka je balle kuma a musu tayin aurenta, sannan tasanya musu hijaba tsakaninsu da sauran kabilun babu su babu magana a cikin k'asar baki d'aya, dan kowa yasan yadda ake kare mutumcin tare da kankaro darajar su, amma dare d'aya ta rusa musu mafarkinsu, tasan musu jin tsoron shiga cikin masarautar Jordan, ta kuma rufe musu goben da sauran ga samun Mulkin jordan. A da cikin izza da alfahari suke maidawa kowa magana cikin iko da d'agawa amma yau an wayi basu da ikon haka gudun kar a musu gori. Jigun jigun suka zauna kafin Abu Darda ya mike cikin damuwa yace. "Yaku banu Hussain! A yau zan ajiye wakilcin kabilar mu, Ni Abu Darda na hakuri da wannan mukamin dan ina jin kunyar masarautar da kuma yadda zan fuskanci Al'ummar cikinta, musamman ƙabilar Hashimawa." Duk suka dukar da kansu kasa cikin damuwa, sannan ya cigaba da cewa. "Da ina da yadda zan kakkare abinda Zoyah tayi da nayi haka, amma babu halin haka, shi yasa naga dacewar na hakura da wannan muƙamin sannan zamu cire kanmu da shiga duk wani abu da ya shafi masarautar da sauransu ko ya kuka gani." Shiru ne ya gifta tsakanin magana da yayi, wani dattijo a cikin su me yawan shekaru ya mike cikin mutumtaka yace. "Ya shugabana Ni a nawa ganin ajiye mulki bazai karo mana darajar da aka zubda mana, kawai abinda ya dace. A tura da sakon ban hakuri da abinda ta aikata, sannan mu nemi jin wani hukunci suka dauka abinsa laifin da aka musu." "Wannan maganar da Shah Nawaz yayi itace gaskiya. Ko ya kuka ce, kuyi magana wannan abun dan kare kimarmu ce." "Ghaiyyas kayi gaskiya haka ma Shah Nawaz yayi gaskiya, sauran Al'umman baku ce komai ba, muna son muyi abu da murya daya karku nuna gazawarku mana, mafita muke nima." Duk suka amince da yin mubaya'a da abinda suka tattaunawa akan bawa masarautar Jordan hakuri a bisa laifin da Yar su Kanwar su, ta aikata. Wannan shine matsayar da suka cimma a zaman su na yau, Kuma haka ya yi musu dad'i. ★★★ Ukraine... Tunda muka idar da waya da Ummi, share kwalla nayi sannan na kalli Sophia wacce suke wata da Babanta. Takaicin Ashraf ne ya kama Ni, na shiga niman number shi, yana ɗauka na mike na koma d'akin, na zauna a bakin gado cikin jin haushi nace mishi. "Wannan wani irin hauka ne da zaka gayawa Ummina muna waya da kai, kasan irin fadar da tayi min kuwa." "Wallahi ban gaya mata komai ba, Ni har yanzun ban mata maganar dawowarku ba, ina jiran ta bani umarni." A madadin na saurare shi, sai ma maida al'amarin ya girmama, haushi ne ya turnike shi cikin tsawa yace.. "Kee! SAFINAH Ni sa'an kine da zan rantse miki bamu yi haka da ita ba har ki karyatani, ina wasa dake. Toh na gaya mata ina waya so What sakarya kawai wacce bata san ciwon kanta ba har kin isa nayi na baki hakuri kina ce min nayi miki shiru, toh Kizo ki dake Ni wawuya kawai" "Ashu! Ni ka zaga?" "Kinga mu bar maganar haka, bana son tashin hankali, lafiyar ki ita damuwata" "Nace Ni ka zaga?" Shiru yayi ya rasa yadda zai yi da Safinah a rayuwarsa, idan akwai abinda ke bashi matsala Safinah ce, dan yana da kwarin gwiwa akan komai na rayuwa idan tazo mushi amma SAFINAH kadai ce zata had'a mishi zafin da lokaci guda zai shiga zufa. "Kinga SAFINAH mu fahimci juna mana Ni bana son muna rigima a gaban danginki, sai naji a raina suna dana sani bani Aurenki." "Dana sani na nawa kuma, wannan kaddararren Aurenka mara albarka." "Haba SAFINAH! Auren kike kwashewa albarka." "Banzan aure na tsane ka, ka rabu dani, tunda babu wani abinda ya hadani da kai mugu me son kanshi." "Innalillah! SAFINAH zagiba kike akan abinda bai kai haka ba, Haba SAFINAH, duk laifin da nayi ai naci Arzikin Fatimah," "Baka ci Arzikin ba, kuma wallahi sai na gudu inda bazaku kuma gani na ba, tunda halinka had'ani da mahaifiyata mugu kawai." Kashe kiran nayi ina jan tsaki yafi a kirga, tsabar naji haushin kaina, da zagin da nayi mishi wallahi naji zafin amma ban san me yasa nake saurin jin zafin shi ba, kodan faɗar da Ummi.. [3/24, 7:03 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* 8️⃣ Abuja..... Shafa kanshi yayi cikin damuwa, sannan ya juya zai bar cikin gidan. Ido biyu suka yi da Khalil, shan jinin jikinshi yayi cikin nuna babu abinda ya faru, yace. "Ya dai? Kana son wani abu ne?!" "Gaskiyar nake son Sani! Didih taci mutuncinta ba?!" "A'ah Khalil! Ba wani abu bane, dan ai mun saba haka, kuma zaka ga mun dai-daita kanmu." Shiru Khalil yayi dan yayi alƙawarin sai ya gayawa Ummin su. "Ai shikenan tunda kace ba komai, baka son a mata fada bayan abinda tayi ba dai dai bane" "Amma juya naji kana cewa kana son bike, bari nasaka a kawo maka." Murmushi Khalil yayi wato shine Ashraf zai ma wayo, sai shima ya share tunda Ashraf ya nuna baya son maganar sai yaja bakin shi yayi shiru. ...... Bayan sallah magarib, Khalil na zaune yana cin abincin dare a gaban Ummi, ya d'ago kai sannan yace. "Ummi Ya kamata kiyiwa Didi magana, domin ban tab'a ganin kinyiwa Abba magana mara daɗi ba, amma yau naji da kunne na. Sai magana take gaya mishi shi kuma sai bata hakuri amma bata fasa ba, yau ummi misali idan SAFINAH ta rasu, aka ɗauki Adda Batul ko Khalilah aka bashi bazai amsheta ba, sabida bai ji dad'in yar Uwarsu ba, don Allah Ummi ki mata magana wallahi da kunnena naji yana cewa shi baya son tana jan rigima a cikin danginta don Allah ki mata magana, wallahi naji zafin abinda tayi mishi sai kace ba tarbiyyarki ba." Duk sai jikin Ummi yayi masifar sanyi, musamman yadda Khalil ke kalublantar. Har ya gama cin abincin ya bar falon Ummi bata bar gurin ba.. ............ "Ghaniyu ka fahimce ni, na gaji da Halin SAFINAH, idan muka sami matsala da ita, a madadin ta mutuntani sai zagina. Haba Ghaniyu yaushe zanyi kima a idanunta, zan rabu da ita na kuma yi hakuri kafin Allah ya bani wacce bata fita ba." Shiru yayi yana jin abinda Ghaniyu yake gaya mishi. Murmushi yayi sannan yace. "Ba dai SAFINAH ba, dan bata da sauki kawai zan hakura da ita ne." Kome Ghaniyu ya gaya mishi ya sanya hannu a goshinsa, tare da lumshe idanunshi Kafin yace. "Shi kenan, amma bazan cigaba da jin cin kashin da take min nan, wallahi Ghaniyu SAFINAH ta fice min a kai, sam bana jin kamar yadda nake ji da" Shiru yayi sannan yace. "Ba wai bana sonta bane kawai ta ficce min akai ne, wallahi da gaske nake ta renani sosai." "Nagode sosai da shawarar da ka bani." Kashe kiran yayi sannan ya ajiye wayar ya kalli bakin kofar da Khalil ya shigo, murmushi yayi sannan yace. "Shigo mana." Zama yayi sannan ya kalli Ashraf yace. "Nasan bata kyauta ba, amma don Allah karka juya mata baya. Insha Allah bazata kuma don Allah." Wani iri Ashraf yaji a ran shi, Anya Safinah tasan yadda yan uwanta suna sun zaman su kuwa. "Ba damuwa." ★★★ Ukraine... "Haba Didih! Mijinki kika zaga fa, meye laifin Ashraf dan yana sonki? Kike wulakantaka shi, tabbas baki san darajar aure ba, yin auren kike kawai baki san hakkinshi akanki ba, shi yana ƙoƙarin kare kimar shi a idanun mu amma ke kina zubda baki, Yanzun Abinda kika yi ya dace, kin zauna kina zagin shi kamar kin samu d'anki haba SAFINAH, ina ilimin ki ya tafi, dan haka ki kira shi a gaba na, ki kuma bashi hakuri. Wallahi hakurin da yayi dake in Ni ne bazan iya ba, kina ganin Sophia ita da gaskiyar ta ma, amma ita ke bani hakuri, ku mata kuna da Matsala, da zaran namiji ya nuna muku ya haura bishiyar kace akan sanku toh a lokacin kike jin wulakancin a ranki da tijara, kece ki ce mishi munafuki, gulmamme, mugu, Haba SAFINAH,. Idan shi zai mutu dan ke, me yasa ke bazaki yi sumar shi ba, kin zauna kina zagin mutum me daraja dan kinga yana aurenki." Jin haushi yayi ya fita daga dakin, ma ban kira Ashraf ɗin ba, .... Ba Dudu ta zaga ba, amma ji yaƙe kamar ya rufe ta da duka, cikin masifa yacewa. "Don Allah meye amfanin haka?! Daga Namiji ya raba shimfida daku sai ya zama mara daraja, ai ko dan Yaran shi ta mutunta shi amma ta zauna ta zage shi tass." Inda yake shiga bana yake fita ba, abinda ya faru kuwa Ummi ce ta kira shi ta gaya mishi yayi wa SAFINAH rashin mutunci, sabida tozarta Ashraf da tayi kuma ko bata gama shiri ba ta dawo gida. ....... Nayi kuka har Nagodewa Allah, sabida surutun da Dudu yayi min ya bani haushi, ina ƙoƙarin kiran Ashraf sakon ya shigo min. _Ni kika tozarta ko? Safinah ince Ni kika wulakanta? Wallahi tun da Yaron nan yazo bai taɓa min maganar yana nimanki ba, yana dai zaune a gidan. Wallahi kiyi gaggawar niman yafiyar shi idan kika mutu ba tare da niman yafiyar shi ba, kinsan sakamakon_ Kukan da nake ne ya tsananta, sabida tsoro dan wallahi ina da matukar tsoro, dan haka na shiga niman shi, kiran na shiga bai dauka ba, har ya yanke ban hakura ba na kuma kiran shi, yana ɗauka fashe da kuka. "Don Allah kayi hakuri bazan kuma ba, wallahi bai na zaga ba kaina na zaga kayi hakuri bazan sake ba." Sautin murmushin sa naji, har sai da tsigar jikina ya mik'e ,nace "Kayi hakuri kaji." "Toh SAFINAH! Gobe ma bashi zai hana kice min mugu azzalumi ba. Ke ko kunya baki ji idan kin zage ni? Baki san kimar kice take ragewa a idanuna ba, Na rasa muguntar da na miki, idan sabida Rape dinki da nayi ne toh ina baki hakuri ban tab'a zina ba, kuma abinda ya faru tsakanin mu, Kaddararmu ce. Ban san me kike so nayi miki ba, amma kiyi hakuri bazan takuraki ba, tunda baki Son zama dani zan ajiye miki sako a gurin Ummi zata baki shikenan, idan." "Don Allah kayi hakuri bazan kuma ba." Kashe kiran yayi, kamar doluwa nabi wayar da ido hawaye na sauka a idanuna, me yasa nike haka ne Ni kaina abin na damuna, Allah ya bani mijina Ni daya ba mijinmu ba, amma na gaza fahimtar shi, Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un. Na shiga hallaka da kafana, zai kai kaina wutar Jahannama. Manzon Allah yayi gaskiya da yace mafiya akasarin mu mata yan wuta ne, gashi nan garin rashin kai na daga muryana sama da namijina. Kuma ya nuna min zai rabu dani. Na shiga tashin hankali sosai dan cikin lokacin ƙalilan jini na ya haura, kafin wani lokaci na fara hali, kasan cewa shekaruna sun ja, kuma wannan cikin yana matukar bani wahala, dan damuwa kadan zan ji cikin ya kume min, wato ya cure a gurin daya. Dakyar na rarrafa na fita, su Affan da Ablah suna wasa, ganina Affan yayi sheka a guje ya kira Iyayen shi. Ai dukkan su suka fito, komawa daki Dudu yayi ya dauko kayan aikin shi, ya shiga bani taimakon gaggawa. Har zai saka min ruwa, Sophia tace mishi. "D karka sa mata drip, ka manta wancan zamanta a asibitin yan tana da diabetis na cikin kar ka sa mata ruwa sabida wannan akwai glucose." "Nagode da kika tuna min " yace mata, Karshe dai Asibiti ya kai Ni, ya kuma kira Ummi ya gaya mata, sannan ya kira Ashraf ya gaya mishi. ★★★ Dakyar ya wani gari dan barci barawo ne ya dauke shi, gari na wayewa, bai kai ga yin haske ba, ya bar gidan bayan yayiwa Khalil bayani. ★★★ Jikin Nannah kan za ace da sauki tunda babu halin tafiya sai dai a turata a keke, an sallamota zuwa gida. Kuma an zuba mata masu kula da ita, bata cika magana ba amma kuma bata cikin wani mugun yanayi, dan takan ce. Mata abinda take so. ★★★ Sai da nayi awa biyu sannan na farka, lokacin dare yayi sosai dakin ba kowa ban daki na shiga nayi alola. Nazo na gabatar da Sallah, ina idarwa na jima ina addu'o'in kafin na mike na kwanta a gadon. Ina kwanciya ban kuma farkawa ba sai da gari ya waye, jin hannun mutum ya rike hannuna yasani bud'e idanun na tsura mishi ido. "Ashu" D'ago kai yayi sannan ya zare hannun shi yace.. "Ya kike ji?! Ko zamu wucce Rasha ne dan can zasu fi baki kulawa me kyau." "Zan yi sallah tukun." Zare min hijab yayi sannan ya koma ban dakin ya dauko ruwa a cikin wani bowl na silver. Ya kawo min na wanke hannu sannan ya koma ya kawo min wani nayi alolan sosai. Yazo ya kad'e abin sallar ya sake shimfida min, nayi sallar ina idarwa sai fadin Dudu. Sun gaisa tare da tambayar shi ya muka tashi, kallon shi nayi sannan nace. "Yaushe ya tawo." "Uku da rabi ya shigo kasar, ya kuma kirani shine naje na ɗauko shi." Sunkuyar da kai nayi kunya na dawainiyya dani. Sun fita da Dudu, can sai gasu nan sun dawo, kallona yayi yace. "Zaki iya takawa ko na daga ki." "Zan iya tafiya da kafata" Koda muka fita a hankali muke takawa, har gurin motar Dudu. Koda muka isa gidan kayanmu Dudu ya haɗa mana, muka bar Ukraine. Shi ya kaimu airport, tunda muka shiga ya dauki Yar shi, suka shiga hira ban kuma gane kan shi, sai dai idan yaga na juyar da kaina ko na yatsina fuskana, yace " lafiya" "ina ke miki ciwo?!" "Babu " shine amsar da nake bashi, har muka shiga rasha da karfe biyu, sabida babu nisa tsakaninsu. Bilal da Ghaniyu suka zo daukar mu. ★★★ Tunda muka isa ya bani dama nayi abinda raina ke so ta hanyar nisanta kanshi dani, haka ba karamin ciwo yayi min ba, taya zai juya min baya. Haka nayi ta bin shi yana juya min baya, A gurin Umman bilal nake samun sauki, ban san ya zanyi da Ashraf ba dan ko irin sumbatar da yake yi a goshin nan babu, kuma sai ya tsaya nasha magani kafin ya koma inda yake, Ablah kan bana ganinta, sai ta gadama take zuwa gurina. Sosai na shiga damuwa dan na tsani shariya ko nace mun tsani shariya dan shima baya son haka amma idan na duba girman laifina sai na kwantar da kai, muna zuwa asibiti ganin likita sabida sugar na da yake yawan hawa, dan duk bayan 15hour yake hawa, akwai ranar da ya hau sai da na daina gani, Allah ya taimaka yana dakin na, zan sauka daga gadon kenan na tafi zan hantsila ya kamo ni. Wallahi ban tab'a ciki irin shi ba, iya wahaltu na wahala da cikin. Wannan dalilin yasa na koma asibiti da zama, bana ganewa komai, ga sabon laulayi a cikin wata shida zuwa bakwai tunda Ashraf yaga haka ya sami likitoci akan a min aiki, Kiran Ummi nayi na gaya mata, ita kuma takira Ashraf tace don Allah a dakatar da haihuwar haka, sabida yawwan haihuwa yayi shi ya haifar min da ciwon sugar shi yasa tace a hakura da haihuwar. ...... A ranar Laraba naka ciro min yaro na dan karamin dashi sak Ashraf........ *Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un* *Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un* *Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un* *Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un* Muna baran Addu'ar ku Governo Bauchi yana cikin wannan tashin hankali 🤧😭😭😭 [3/26, 10:02 AM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 🔟 "Ammyna gani nan zuwa" Ya faɗa mata cikin wani irin murya wanda yake cike da bakin ciki tare da damuwa, ya shiga ban daki yayi wanka, sannan ya fita zuwa gurin ta. Turata a keken ta yayi har zuwa d'akinta, sannan ya zauna a kasa.. Ita kuma ta koma bakin gadon ta zauna, irin zaman da yayi sai ya bata tausayi tare da jin ba dad'i a ran shi. "Muhammad Ashraf" D'ago kai yayi ya kalleta sannan ya maida kan shi ya sunkuyar. "Kayi hakuri! Ni kaina ban san me yasa nake jin ba dad'i idan ina tare da SAFINAH ba, amma nasan Yarinyar bata da matsala, kawai ina." "A'ah Ammyn kawai ki nima min abinda zan kashe Ni, yadda bazan iya aikata komai ba, kinga sai tayi tafiyar ta Ni kuma na zauna dake tunda haka kike so." "A'a Ni ba haka nace ba." "Haka ne mana! Ammyna, SAFINAH mata ta ce, ke kuma Mahaifiyata ce, toh me zanyi miki, idan banyi tarayya da Safinah ba Zina kike so naje nayi ko me kike bukata dani." Shiru tayi sannan yace. "Ni danki ne! Ni ba mijinki bane, babu amfanin kina kishi da Mata ta, kiyi hakuri da abinda na fada iya gaskiyar kenan, wallahi kina kuma shiga tsakani na da ita Ammyn zan saka a kai ki inda bazaki ku ganin mu ba, haka zaki rayu a gidan Tsofaffi wanda yake Jordan, na rantse da Allah, bazan fasa abinda nayi niyya ba, ke Uwa ce ki zauna a matsayin ki, Ammyn kiduba Umman Bilal man ko kunya baki ji ba, Ni kawai kika hana na samu nutsuwa da matata toh gani kiyi yadda kike so dani shikenan." Tunda ya fara magana take kuka, sannan ya mike ya barta zaune a gurin. Ya dawo d'akina ya same Ni nayi wanka har na sauya zanin gadon na koma na kwanta, cire rigar jikin shi yayi sannan ya shiga cikin bargo ya janyo Ni jikin shi, sai a lokacin na sake kuka, bai hanani ba har sai da yaga nayi shiru dan kaina sannan ya lallubo fuskana ya cilla min harshen shi bakina. Daga nan kuma komai ya kunce min, dan Ashu mayye na ne. ★★★ Tun daga ranar bata kuma shiga harkar mu ba, sai ma kame kanta da tayi wai nace Allah yasa a dore a haka. Bayan shekara biyu Allah yayiwa Ammar Rasuwa ta hanyar tsarin jirgin sama, koda muka je gaisawa Suka riƙe Ashraf dan dole suka mika mishi mika min shi, ina zaune rike da Yar Batul Aafreeda (ma'anar sunan Yar Batul created ko ace produced, sunan Mahaifiyar Fahad, Bilal kuma ya sanyawa dan shi Asadullah, Sunan yaron Aliyu inkiyar sunan ne Asadullah,( wato Zakin Allah). A gigice ya shigo d'akin ina ganin shi, na kalli su Batul fita suka yi, nake inda yake tsaye na riko hannunshi, na zaunar dashi, sannan na zauna tare da daura kanshi a kafad'ana. "Sun mai dakai matsayin ka ba! Shine kake jin tashin hankalin ko" "Toh meye a ciki da kake damuwa zab'in Allah ne, dan haka ka amshi tayin su tun kafin su ma na karfi." Na maida abin wasa, sannan na nuna mishi girman abinda suka yi da ya dace, sannan na kuma bashi goyan baya. Ranar da akayi addu'o'in a ranar aka mai dashi kujeran shi, na dindindin. Sai dai wannan karon anga tsarin matashin Basaraken, dan komai sai da aka zamanantar dashi, aka mai dashi boko zalla. Amma batun abinda ya shafi addini yana nan, bisa tsari. Bayan shekara biyar, kwance nake a jikinshi bani da lafiya, amma dan bakin jaraba sai da ya cinye ni (🤣😂) sannan ya dawo yana tausayin gulma. "Anya SAFINAH ba ciki ne dake ba kuwa? Dan naji kin kara armashi" Make hannunshi nayi wanda yake kan shafafeffen cikina, kamar ban juyen yara ba, kodan banda jikine yasa haka oho, amma a kwana biyu nan nayi kina har idanuna irin na yan Chinese ya koma ciki. Tabbas nima ina zargin cikin ne dani, sabida kuwa robar bakin mahaifa suka saka min, kuma ba. Kafe shi nayi da ido, nace. "Please Dr Fu'ad zaka kira." "Toh muje muyi wanka." Kamar na saka kuka haka nake ji, dakyar na mike ya tallabe Ni, muka je wanka muna fitowa yakira Dr Fu'ad, yazo duba Ni sosai. Sannan ya tabbatar ina dauke da cikin wata uku (🤣shashanci irin na SAFINAH ba ita daya ba mata dayawa haka suke fama dashi sai ayi tsarin iyali da zaran rabo yazo Alkur'an sai dai wata taji haihuwa kawai, sabida Ni naga haka da idona) Kamar mara gaskiya haka nake ji, dan Ni nasaka a raina na gama haihuwa, shi kam murna zai sake samun haihuwa a gidan shi, Ablah zan iya cewa shekarunta bakwai, sai Amir me Shekara shida, sai Artah me shekara biyar, kuma kana ganin su kasan yaran kwakwa ne, koma nace kunika. Kuma mazan basu da Fitina kamar Ablah, wallahi bata ji ga shegen taurin kai da kafiyar bala'i, idan tayi haka zaneta nake muyita rigima da Ubansa har yace nice na lalata mishi Y'a da rashin ji. Sai dai fatar shirya. ★★★ Kwanci tashi aran me rai, har za ayi bikin Khalilah, Ni ban samu zuwa ba Amma Ashraf ya tafi, harsu Ghaniyu nice dai Ashraf ya hana. Kwanansu uku suka dawo dama abokin Dudu ta aura Dr Muhsin. Sun dawo suka same Ni nayita fushi dasu, da zasu zo ne aka tawo da Hajja nace shikenan Aljanun batsa sun zo naga takaina. ........ Sha'anin rayuwa sosai Nannah ta zubawa alamarin mu ido, har cikin ya shiga wata tara wannan karon zan haifu yan wata tara. Wasa wasa sai da na shige wata tara, sannan na haifo yan mata na biyu, masu mabanbantar kama, dan mun rasa da suwaye suke kama, a ranar da na haihu nasaka aka juya mahaifar, Har muka dawo gida kallon Yaran yake, sannan yace.. "Wani sunaye ya kamata su ci" Juya idanuna nayi nace. "Me ban purple sunanta Amatul Islam Me ban pink Amatullah" Da haka yayi musu hudubar, ranar da yaran suka cika bakwai aka fadi sunan sai da naga rashin jin dadi Nannah a fili dan taso a mata takwara Ni kuma naki yarda dan tun kafin na haihu nake tanadin sunan yaran. ... Watanmu biyar muka zo naija har da tazuje na, wato Ashraf kai jama'a ina ganin bibiko yoh ko jela sai haka. Munyi yawon cikin yan uwa da dangi sannan muka dire Maiduguri dan maida Hajja, A jirgi muka hadu da Dr inda ya nemi yafiyata baki kula shi sai da Ashraf yasaka baki sannan na yafe mishi, munyi kwanaki sannan muka baro Abuja zuwa jordan, tunda Allah ya nufa a can zanen Kaddararmu take. .... Ina samu Amatullah tayi barci na gungurata can gefe nace. "Zo na baka labari me dad'i." Daga nan muka lalace a duniyarmu....... ★★★ Ina zaune muna hira da Batul, sai gashi ya shigo yace. "Kizo munyi baki" Mik'ewa nayi ina mamakin suwaye bakin haka. Har Palourn bakin shi naje nasame su anata hira wajen maza da ban mata daban cikin shiga irinta Alfarmar, duk cikin biyu ne muke kusan shekaru d'aya dasu. Da sallama na shiga, matan suka zuba min ido. K'asa-k'asa naji wata me ƙaranci shakaru a cikin su tace. " Itace Sarauniya SAFINAH?" "Eh ita ce." "Assalamu alaikum! Yan uwan ga SAFINATA nan itace mata ta, kuma Sarauniyata" Juyawa yayi zuwa gare Ni sannan yace. "Tawa! Wancan me rawanin buzayen Shine Maude amma sunan shi Asadullah Aliyu Haidar, Na cikin Zanen kaddarata, ga matar shi can WEEHIDAN, sai wancan dan gayen Sadiq ga matar shi can Amrah na ciki da ciwo a rayuwata, sai Wancan dan Sanda, Mansoor ga matar shi can Muwaddah, na cikin ina da Buri, sai Babban Yayanmu Yunus me nasara na cikin matar so tare da MariamSajidah, ga Soja Aliyu Indimi mijin meenarsin na cikin Abadan Da'iman, sai Wancan dan kwallon golf Abu turab, mijin Aleeshbah, sai kuma Amiduddawlah mijin Jal Parih dan kwallon Real Madrid ne, sai Likitan can da matar shi Khadijah, Dr Maheer na cikin Yar gidan Yaddiko. Me gayya me aiki Yaya Malam na cikin Matar Malam tare da Matar shi Neeha. Yawwa ban gabatar miki da babban abokin Sadiq ba Wato Imran da matar sa Sarauniya Zuljah amma dukkan sai dai jinsin Aljanun ne, bismillah ku." Haka Imran da Zuljah suka bayyana, sannan aka, dariya suka saka yan matasan masu jini a jika Imamu da Mai Nasara murmushi suka yi, Ya Man ya mike yace. "Wai don Allah ya akayi muka zo nan ɗin nan" Tab'e baki Ya Abu Turab yayi sannan yace. "Mai Dambu itace ta hado mu nan tun zuwa na naganta a bayana labule fito kafin mu baki mamaki" Haka na fito tsamo tsamo, ina zare idanuna, Haidar ya fidda bindiga yace. "Daga nan ina zaki nufa" Kallon buzayen nan nayi Asadullah da matar shi Weehidan, sannan na koma kan Jan Parih nace. "Ita Soja Damagaran da Bauchi zan tsaya bayan nan nayi muku alqawarin bani sake gulmar kowa" Murmushi Suka yi Imamu yace. "Ya sunan labarinsu, Zanen Kaddarata shine labarin Weehidan da Asadullah, sai Mrs Amiduddawlah, kuruciyar Jan Parih, suke nan ai akwai TSUNTSUN DA YAJA Ruwa. Labarin Mahnoor" "Toh ina take?" Wata budurwa ce ta shigo, sannan na nuna musu ita. Alhamdulillah Alhamdulillah mungodewa Allah da ya bani ikon gama wannan labarin cikin kwanciyar hankali da nutsuwa Inda nayi kuskure Allah ya yafe mana, inda nayi dai dai Allah yasa muyi tarayyar akan dai-dai..... Da wannan nake muka fatan Alkhairi sannan anan nake ajiye alkalamina, zan tafi hutu, Insha Allah sai Bayan sallah, idan labari na ya iso muku toh ina niman yafiyar ku, domin Ni yafe muku. Ana nake cewa duk wanda na mishi ba dai dai ba yayi hakuri Ajizanci ne na dan Adam, wanda ya cuce Ni da kalma d'aya Allah zai bi min hakkina. Fatan Alkhairi Idan da nisan kwana Mrs Amdud ZANEN QADDARATA TSUNTSUN DA YAJA.... Insha Allah... Allah ya kawo mana karshe wannan Annoban Nagode taku har kullum Mai_Dambu Oum Muwaddah.... [3/26, 10:13 AM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah* *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah* MJ3 9️⃣ Lokacin da aka fito da Babyn, aka kawo musu k'in karb'a yayi yana kallon Nurse din da ta kawo babyn, dakyar ya bud'e baki yace. "Ina mata ta?!" Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin jiki tace. "Tana ciki sai dai muna kokuwar dawo da numfashita ne, dan yana kwacewa." Kamar wacce zai bugata da kasa yayo kanta. "Ina mata ta nace." "Kayi hakuri sir! Muna bakin kokarin mu akanta." Shigewa tayi ta barshi a gurin, sai Safa da marwa yake. Ko kallon yaron dake hannun Ghaniyu bai yi ba, suna tsaye Nurse din ta kuma fitowa ta amshi yaron ta shiga dashi, sannan ta koma, ciki bayan mintuna goma sha biyu ta kuma fitowa da sauri, ga baki daya sun birkitawa Ashraf lissafi. Dan kaiwa da komowar da suke kad'ai ya isa ya tabbatar maka SAFINAH tana cikin wani hali. Zama yayi ya cusa hannunshi cikin gashin kan shi, yana jin tashin hankalin da ya ci kaniyar wanda suke ciki. Kuma abin takaici duk yadda Bilal yaso su mishi bayani basu kula shi ba, haka suka zuba musu ido har suka gama abinda zasu yi. Sannan suka fito daga d'akin kowanne su fuskar shi a cike da alhini suka fito. Dafa kafad'arshi likitan yayi yace. "Kayi hakuri!" Ya wucce shi jikin shi ne ya dauki rawa, yace. "A'ah!!! Wallahi bazata mutu yanzun ba, karku ce min haka" D'akin ya shiga, cikin d'imuwar da damuwa, ya isa gaban gadonta. Ya kura mata ido cikin tashin hankali ya rike hannunta, sannan yace. "Me yasa bana jin komai akan abinda idanuna suke nuna min, wallahi na kasa gasgatawa wai kece a kwance ba rai! Kinsan yadda nake jinki kuwa? SAFINAH ta ba haka ta shirya mana rayuwarmu ba, don Allah tashi kinji Safinatu na, don Allah ki rufa min asiri karki tafi ki barni Ni d'aya ina bukatar ki a rayuwata." Ya jima a kanta yana magana, sannan yayi shiru yana kallonta, a hankali ya juya zai bar d'akin dan sai lokacin hawaye Masu zafi suka biyo fuskar shi yace. "Na yafe miki!" Rike hannunsa yaji anyi da sauri ya juya, sannan nace mishi. "Gawa ta tashi." Murmushi yayi tare da jan kumatuna, ya dawo ya rungume Ni, tare da sake dariya yace. "Me yasa?!" Kwantar da kaina nayi a kirjinshi nace. "Sabida ina matuƙa sonka! Fushin da kake yi dani ne yaja nayi haka, amma kayi hakuri." Lumshe idanunshi yayi yana jin farin ciki amma ya kasa nuna min, sai janye Ni da yayi daga jikinshi ya fita. Yana fitowa ya sauke ajiyar zuciya yace. "Safinah bata da tunani ban ciwon jikinta sai na falla mata mari." Dariya suka saka mishi shi kuma ya shafi kwantaccen beard dinshi, can sai ga Nurse suka zo suka fitar da Ni, zuwa d'akin da zan huta sannan suka min alluran barci. ★★★ Sati uku da cire min yaron da yaci Sunan Abban shi, muna kiran shi Artah,(sunan daya daga cikin masu rawaito hadisi ne Artah bini Ashath) Duk wani kulawa ina samu a gurin Mahaifiyar Bilal, dan ji yaƙe kamar ta lashe Ni, har muka yi suna bani komai sai na da nono, ita ke min komai na yaro a hankali take bani labarin irin Wahalar da tasha da bilal. Bayan tayiwa ya gashi ta shafe shi da mai, ya shigo d'akin sanye da manyan kayan sanyi da lokacin ana ganiyar sanyi a Moscow, kuma abinda na fahimta larabawa da turawa basa iya jumirin zama inda babu sanyi sabida yanayin su, fita tayi da Artah da kuma Ablah da ta isheni da rigima sai na nuna mata ciwon ta gani, Kallona yayi kasa kasa, yana lashe bakin shi, yace. "Saura wata nawa abani hakkina?!" Takawa nayi har inda yake, nace. "Hakkinka dole abaka shi matukar ina da koshin lafiya. Idan zaka iya bina a sannu, tsaf na shirya na baka hakkinka." Mik'ewa yayi yaje ya rufe kofar sannan dan ba abin mamaki bane muga Ablah akanmu. Al'amarin Ashraf me girma ne a gareni, dan a sannu ya jiyar dani duk wata kewar shi, dan tun da muka dawo babu abinda ya shiga tsakaninmu, sai yajin da yayi min. Shafa fuskana yayi cikin nutsuwar da ya sameta a lokaci guda yace. "Sannu kinji! Na takura ki ko? Sannu bayi na bane soyayyarmu ce take motsa min" Shiru nayi tare da lumshe idanuna, nace. "Ni kuma nayi kewar ka sosai." "Ni kuma kewar tsiwar ki." "Ashu! Nice matsiwaciya" "Ya hakuri! Ummun Artah" Gyara zaman duvet nayi a kirjina sannan nace mishi. ,"Ina ka ajiye Ablah?!" "Yar Bilal ce!" Tsuke fuska nayi sannan nace. "Kayi hakuri bazan bada Y'ata wa kowa ba, sabida ban shirya ganin b'acin rai ba." Jan hancina yayi sannan yace. "Toh Madam" .......... Busar da gashin kaina nayi sannan na saka dogon riga kirar baharin, bayan na yafa gyale na fita dan har lokacin yana kwance, sai zare min ido yake. "Ni dai ka bar zare min ido," Murmushi yayi sannan ya sauko daga gadon ya nufo Ni, da sauri na ficce daga d'akin dan ba abu me wuya bane ya mai dani ruwa. ★★★ Ukshe a gidan tsofaffi, idan ka ganshi sai ya baka tausayi, dan duk ya motse, da Uzaif yazo yaga yadda ya koma, farin ciki yayi babu izza babu mulki, sai tsoron Allah tare da tsoron duniya, da Uzaif ya so sukoma gida yace. "A'ah a nan rayuwata take, kayi tafiyar ka kawai" Haka Uzaif ya bar shi a gurin, amma yana kawo mishi ziyara. ..... A gefen Sarki Ammar kuwa yana gudar da mulkin shi cikin Adalci da gaskiya, kuma yana ƙoƙarin sosai akan haka, sai dai sha'anin mutane baka iya musu. ★★★ Watanni mu uku aka saka bikin Batul da Fahad, Bilal da Sandia. Duk da Artah yayi wayo, amma sai da Ashraf yayi ta mita shifa baya son aje a kwasowa dan shi sanyi. Babu yadda na iya dole sai da na lallaba shi. Kayan d'akin anan Rasha na saya musamman Ashraf ya kaini naje na zabo mata abinda take so, bayan kwana muka je muka kuma sayo kayan kitchen, tare da Suba'aya matar Ghaniyu. ......... Duk abinda aka saka mishi lokaci toh zai karato, bikin su aka fara gabatarwa, duk wani hidima na ɗaukar hoto Ashu yaki shiga har aka daura auren sannan muka dibo jiki tare da wasu dangin muka dawo Rasha inda aka cigaba da bikin a nan ɗin. Sai da akayi kwana biyu sannan suka dawo gida, daga nan nake aika mata da abinci da kuma abin buƙata, Tsakanin bikin da nasu Bilal sati biyu, dan haka muka je har jordan amma Ashraf yaƙi zuwa, kuma sai da suka tambaye shi, dan sun shirya bikin har dashi, haka akayi komai lafiya sannan muka dawo gida. ....... A yanzun na fara fahimtar waye Ashraf, dan burin shi a duniya ya kyautata alakar shi da kowa, musamman na kusada shi. Muna nan bamu san abinda ya faru ba, Ashraf an damfara sun damfari, Abba inda samu karayar arziki ga kuma bashin banki, kusan miliyan saba'in, an b'oye sabida mu. Ya san halina da shiga damuwa, dan haka sai yaki gaya min, sai da ya gama dai daita komai, dan abin ya bani mamaki. Tafiyar da yayi tayi zuwa Nigeria, koda na tambaye shi, ce min yayi ba kome. A gefen guda bazan manta taron alkhairin shi ba, sabida yayi amfani da dukiyarsa gurin farfaɗo da mahaifina, banda Khalil da ya biya mishi kudin makaranta a Spain, sai Khalilah da take nan ya maida ita Novena can niger Delta, a can take karasa karatunta, sai sauran yaran gidan mu da yayi ƙoƙarin sanya musu hannu musamman Abba lawan. Mijina kenan wanda yafi kowa sanin wacece SAFINAH. ★★★ Da karfe biyu na rana muka sauka, a garin Oman daga nan muka wucce mota , muka nufi gidan sarautar Oman ɗin, mun same tarb'a me kyau a gurin. Iyayen Natashah, inda suka bamu kulawa na Musamman, Amir yana ganin Baban su ya shiga mika mishi hannu, murmushi nayi hawaye suka zubo min, nice na rigarshi daukar yaron, na fashe da kuka. Ina ƙara rungume yaron a kirjina. Suma Iyayenta sai da Mutuwarta ya dawo musu sabo. Sai da ya amshi yaron yace. "Sai da nace ban da kuka amma kika buɗe baki kina min kuka, Don Allah bana so" Gyad'a kai nayi sannan muka, gaisa da iyayenta kana nayi musu ta'aziyar rashin Natashah. ..... Bayan mun huta muka wucce gurin Nannah, yana rike da Artah Ni kuma ina rike da Amir, muka nufi part ɗinta, tunda mukayi sallama, fuskar ta a safe ganin D'anta. Tana gani na tab'a rai, a dararre na zauna. "Sannu Ammyna ya jikinki? Mun same ki lafiya!" Can kasa kasa tace. "Lafiya! Me yasa baka gaya min tare da Fatimah Khatoon zaki zo ba, nasaka a nimo mata kayan ciye." "Toh zuwan ba nawa bane Zuwan SAFINAH ce tazo ganin D'anta kuma ina kyautata zaton zata koma da shi, taje tayi hidimar su tare." Shiru tayi kafin tace. "Nima zan biku, na gaji da zaman nan ." Ji nayi zuciyata kamar zata fado dan tsoro. Amma haka na b'oye abin a raina, na cigaba da kallon ta. Koda muka shiga d'akin shi na shashin ta, kin kallon shi nayi na cigaba da bawa Artah nono, murmushi yayi sannan ya zauna kusada Ni, yasaka hannun shi ya shafi nonon sannan yace.. "Daga Ammyna tace zata bimu shine kike fushi?" Sunkuyar da kai nayi, muryana yana rawa nace. "A'ah" "Toh meye?!" "Kawai tsoronta nake ji,!" "Wannan ba hujja bane! SAFINAH mahaifiyata ce kuma aljanna ta tana kasar kafarta, me zai hana ki tayani nasamu shiga" Shiru nayi kuma Na rasa tacewa. "Aljannah mace yana kasar mijinta, Aljanna namiji yana kasar kafar Mahaifiyarshi Don Allah Safinah ki taimaka min na samu shigewa" Gyad'a mishi kai nayi dan bakina bazai iya furta komai ba.. ........ Kwana shida muka yi amma kamar akan k'aya muka yi shi, dan wulakancin Nannah bata tashi yin sa, sai mun kwanta zata buga mana kofa, har zai fita yaje ya mata abinda take so ya dawo. Dan haka nayita ƙoƙarin mubar Oman, ashe wasa farin girki. Dan muna dawowa da ita ta tsiro da wannan halin, haka na zuba musu ido ban ce komai ba. Haka lokaci yayi ta tafiya, ina kuma ƙoƙarin na shanye iskancin Nannah, wacce sai da suka yi fada sosai da Umman Bilal, tace mata. "Wallahi zaki koma Inda kika fito bazata sabu ba, ki baro can kizo zaki d'agowa yarinya hankali ba, me zaki yi da danki idan ta bar miki shi, ke ko kunya baki ji ba, baki ga Bilal ba yadda na wofantar dasu saboda bana son reni, kuma Yarinyar nan tana bakin kokarin ta, karki janyowa kanki abinda zai dame ki.". Hmm nace a raina Allah yasa taji fadar ki Umma, tunda ta mata komai yayi sauki. Bayan kamar sati biyu ne, da dare fa muna tsaka da raya daren, wallahi Nannah yazo ta buga mana kofa. Haka ya mike a kaina ina ji ina gani, ban san lokacin da na rike shi ba, Muryar ta muka kuma ji dole ya zare jikin shi ya....