ABU NAKA… 2 HAFSAT C. SODANGI Haqqin Mallaka (m) Hafsat C. Sodangi Shekarar Bugu: 2005 An sake Bugawa A: 2015 ABU NAKA-2 M us’ab ya wuni cikin matsanancin maye kasancewar shi kanshi ba zai iya faxin adadin kwalaben barasar da ya kwankwaxa ba. Sani ya shigo gidan da saurinshi saboda ihun Mus’ab da yake jiwowa tun daga waje da kuma ta’adin da ya hango Mus’ab xin yana yi na jifa da duk wani abin da ke cikin falon wanda hannunshi ke iya xauka, yana tarwatsa gilasan gidan dasu. Qarfi mai yawa Sani ya saka kafin ya iya riqe hannun Mus’ab, sunyi duru-duru suna kallon juna cikin haki, saboda wahalar da suka yi kafin suka kai ga tsayuwar. Sani ya yi nufin jan Mus’ab zuwa cikin xakin kwananshi bai yi nasara ba, sakamakon tirjiyar da Mus’ab xin ya yi, don haka suka zube kan kujerar dake bayansu cikin haki. “Dame wannan abin ya yi kama Mus’ab?’ Sani ne ya yi tambayar. Mus’ab ya zuba mishi ido a gajiye, da qyar ya buxe baki ya ce mishi, “An rabani da Aisha, kuana kallo baka yi komai ba saboda kai mugu ne ko?” Yana maganar da qyar yana zaro ido tamkar dai yanda aka san bugagge yana yi, ga kuma hannayenshi da ya damqi wuyan Sani dasu sunyi mishi kyakkyawan kamu. Sani ya shiga kici-kicin qwatar kanshi daga hannun Mus’ab. “Ka sato min Aisha ka kawo min ita nan gidan yanzu-yanzu nan ina son ganinta, ina son rungumarta a qirjina, ina son jin xuminta a jikina, ina son ganin no…….” Da sauri Sani ya xoraa hannunshi a bakin Mus’ab ya toshe don rage qarfin maganar da yake yi gudun kar ma’aikatan gidan dake waje su ji. “Mus’ab kanka xaya kuwa, duk barasar ce ta mai da kai haka?” Mus’ab ya tunzura ya qara shaqe shi ya ce, “Nine mashayin?” Sani ya qara tsorata da lamarin nashi ya shiga neman hanyar qwatar kanshi daga hannun shi. Ya ce, “Ban ce maka mashayi ba Mus’ab, cewa na yi ka yi haquri ka sake ni don in samu in nemo varayin da za su sato maka Saddiqa su kawo maka ita, tunda ai ka san ni ban iya sata ba ko da ta kaya ce, balle ta mutum xungurungum!” Mus’ab ya sake shi. Cikin sauri Sani ya miqe ya kama hanyar fita daga gidan, yana jin Mus’ab yana ihun yau xin nan nake so ka sato min ita. Washe gari da safe Mus’ab yana zaune kan dardumar da ya idar da sallar asuba, jan carbinshi yake yi tunda ya idar da sallarshi bai tashi ba, shi da kanshi ya san rabon da ya sha barasa da ta gusar da hankalinshi irin na jiya ya yi matuqar daxewa. Har lokacin kanshi bai bar sarawa ba, ga nauyi da yake yi mishi saboda matsanancin ciwon da yake yi, ga tunane-tunane iri-iri da mafarkai barkatai, har bai iyaa tantancewa da adadin mafarkan da ya yi a cikin daren. Daga ciki wanda ya fi tsaya mishi a rai shine, mafarkin Hamida da ya yi cewar ta shigo gidanshi tana ba shi labari game da bikin Saddiqa da Sadisu, wanda rashin daxin labarin da take ba shi yasa ya yi ta jifanta da abubuwa har ma ya fasa mata kai. Gabanshi ya yi mummunan faxuwa da ya qara tsunduma cikin tunanin mafarkin. Shin mafarkin ya yi ko kuwa Hamida ce ta zo gidanshi da gaske ya fasa mata kan? Wai wane irin maye ya yi ne jiya? Ya qara zurfafa cikin tunani yana nazarin irin jifan da ya ga yana yi mata, ya zubawa wuri xaya ido yana qoqarin tunano maganganun da ta zo mishi dasu sai ga Sani ya shigo. Mus’ab ya zuba mishi ido cikin fargaba da tsoro, cikin qarfin hali ya tambaye shi. “Daga ina Sani?” Sani ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, “Daga inda ka aike ni mana”. Ya sake zubawa Sani ido yana qoqarin tunano aiken da ya yi mishi, bai tuna ba. “Ina na aike ka Sani?” “Sato Saddiqa mana, ba ka ce in tura varayi su shiga gida su sato ta a kawo maka ita ba?” “Ni!” Da qarfi ya yi tambayar tare da miqewa tsaye cikin kaxuwa. Ya sake tambayar shi “Ni? Sani na turaka ka aiki varayi su shiga cikin gidan ubana da ya haifeni su yiwo sata?” “Ai ba sata ka ce suyi ba, Saddiqa ka ce a sato maka”. Mus’ab ya xan yi taku biyu gaba kafin ya sake ja ya tsaya, ya sake juyowa gare shi ya ce, “To yanzu fa me ake ciki?” Sani ya kalle shi ya ce, “Ai anyi an gama, kai kawai ake sauraro”. Kan Mus’ab ya kama sarawa da sauri fiye da da, ya xora hannu ya dafe goshinshi cikin matsananciyar damuwa da fargabar al’amarin. Shi kam ya san babu yanda za ayi a shiga gidansu a sato Saddiqa a fito da ita alhalin Innarshi tana lafiya. Me suka yiwa Inna? A wanne hali suka barta? Waxannan sune tambayoyin da suka tsaya mishi a rai. Nan da nan ya juyo don Sani ya amsa su, sai dai kuma abin takaicin shine Sani ya fita ba tare da ya sanar da shi ba. Mus’ab ya laluba kujera a hankali ya zauna, lokaci mai tsawo yana tunanin ta inda zai bi ya gyara al’amarin da ya riga ya lalace, dama an ce ba za a ba shi Aisha ba saboda shi xan iska ne, to yanzu kuma in aka gane shine yasa aka sace ta me za a kira shi? Anya iyayenshi za su yafe mishi kuwa? Ya ya zai yi ya sake daidaitawa dasu? Shi ba abin ya xauke Aisha ya yi tafiyar shi da ita ya bar qasar yaje wani wuri suyi rayuwarsu ba, aure mai albarka yake nema a tsakaninshi da ita na raya sunnar Manzo, ban da haka ya kai munzalin shekarun da daidaituwar al’amura yake nema tsakaninshi da iyayenshi. Tausayin kanshi ya kama shi da ya tuna in har aka gane abin da ya faru yana da hannu a ciki, to shi da Aisha sunyi bankwana kenan har abada. Amma duk da haka ya qudiri aniyar mayarwa iyayenshi da Aisha, don ba zai yarda a wannan lokacin wani abu mai tsanani ya sake shiga tsakaninshi da iyayenshi ba, musamman ma mahaifiyarshi. Yana kwance cikin ruwan zafi da ya gauraya da turare mai matuqar qamshi cikin tunanin mafita, zai je ya ga Aisha a inda su Sani suka voye ta ya xauke ta ya mai da ita gida, maimakon ya bari sai sun bincika zai gaya musu gaskiyar lamari, iyaka dai ya san abin da yake gudu ne zai same shi. Mus’ab ya kammala kwalliyarshi cikin fararen kaya babbar riga ‘yar ciki da wando na farin yadin boyel ne a jikinshi, hular kanshi da baqaqen takalman dake qafarshi sunyi matuqar dacewa, ga qamshin turaren shi mai sanyaya zuciya, duk da matsanancin vacin ran dake gare shi bai hana shi yin kyau ba, ga kwarjininshi na musamman a tare da shi. Ya fito daga xakinshi zuwa falonshi ya nufi kujerar da ya hangi makullan motarshi a ajiye a kai, yana mai xaura agogonshi qirar Rolex a hannunshi. Motsin da ya ji a bayanshi ya sanya shi saurin juyawa, Sani ne a tsaye a bayanshi. Mus’ab ya zuba mishi ido cikin nuna alamar vacin rai. “Yanzu ina Aishan take?” Kafin ya ba shi amsa sai Mus’ab ya ce mishi. “Ban san baka da hankali ba Sani sai yau, wato kai duk umarnin da aka baka sai kawai ka bi Sani? Ba za ka yi la’akari da yanayin da mutum ke ciki ba a lokacin?’ Sani ya galla mishi harara ya ce, “A’a, kar ka sargeni giya hauka ne?” Ya juya zai sake fita. “To baka gaya min inda take ba don in san abin yi, kaima ka san yanzu ba lokacin wasa bane tunda dai komai ya riga ya lalace, ka ji tausayina mana Sani”. Sani ya kalle shi saboda tausayin da ya bashin ya ce, “Tana gidan Innarta”. Kan Mus’ab ya xaure, ya sake tambayar shi. “Wacce Innar tata?’ Ya ce, “A’a, gidan Inna mana, ai ban aiki wani sato ta ba”. Ya kalli Sani ya yi tsaki. “Wato kai duk halin da mutum yake ciki sai ka zolye shi ka qara mishi damuwa saboda tsabar rashin tausayi, to ka zu muje saboda mu san abin da suke ciki tunda duk wayoyi da na yi ta yi mata ta qi xauka”. Sani ya kalli agogon hannunshi ya ce, “Gaskiya sai dai ka yi haquri ka je kawai, Ishaq ya yi waya kana wanka ya ce yana bisa hanya, ina ganin in jira shi ya zo ya fi in bika ya zo ya smau gida babu kowa. Ko me ka gani?” Ya fita ya tafi ba tare da ya amsa ba. Mus’ab yana tafiya cikin motarshi Marsandi qirar 190, zuciyarshi sai faman shirya mishi kalmomi masu daxi take yi da zai yi amfani dasu wajen shawo kan Aisha don ta sassauto daga tsattsauran ra’ayin da ta xauka a kanshi saboda abin da Gwaggonta ta gaya mata game da shi. Ya yi parking a qofar gidan cikin matsanancin fargaba da tsoro, nan take ya ji zuciyarshi ta shiga dakan uku-uku saboda cincirindon yaran da ya gani a qofar gidan suna wasanninsu alamar akwai taro a cikin gidan. A saninshi yau saura kwana tara ayi xaurin auren Aishaa, to me ya kawo taron jama’a tun a yau? Yana gama yiwa kanshi tambayar mafarkin Hamida da abin da take gaya mishi ya faxo mishi cikin ranshi. “Yaya zuwa na yi in shaida maka cewar Baba da Inna sun dawo da xaurin auren Saddiqa da Sadisu wannan Juma’ar, wai za suyi hakan ne don su shammaceka da jama’ar da za su iya cewa wani abu game da hanaka da suka yi, baka ankara ba sai kawai ka ji an kaita gidan mijinta”. Waxannan sune kalaman da ya tuna Hamida ta gaya mishi a cikin barcin shi. Ya fito daga cikin motarshi cikin sanyin jiki da matsanancin fargaba ya wuce yaran ba tare da ya kula su ba alhalin yin hakan ba xabi’arshi ba ce. Yana shiga zauren gidan hayaniyar muryoyin jama’a mata da ya jiyo daga cikin gidan ya dakatar da shi daga shiga. “Ku miqo min kwandon tsaman can wannan ya cika”. Muryar da ya jiwo kenan wacce ya fahimci mai ita. Cikin sauri ya juya ya fita, ya samu yaro mai hankali cikin yaran dake wasa a qofar gidan ya ce mishi. “Maza shiga cikin gida ka cewa Bilkisu wai ta samu yayanta a gidan Abu”. Ya ce, “To”. Ya shiga cikin gida da gudu, shima Mus’ab ya yi maza ya bar qofar gidan. Mus’ab yana zaune kan tabarma cikin matsananciyar damuwa, ya qosa qwarai ya ga shigowar Bilkisu. Ita kuwa Abu sai qoqarin qarasa kwalliyarta take yi, atamfar ‘yar Ingila ce a jikinta sabuwa dal, ga ‘yan kunne da sarqar zinare da Mus’ab ya saya mata sun kama wuyanta, su ma ranar ta fara sanyasu. Qafarta ta yi shar gwanin sha’awa da lalle, duk da dai ba ta gama yin baqi ba tana riqe da mashayin kwallinta a hannunta tana zizirawa a idonta. “Ni kwalliyar me Abu take yi ne haka?” Cikin qarfin hali Mus’ab ya kawar da shirun dake xakin ta hanyar yi mata tambayar. Ta dakatar da girgiza tandun nata ta shiga qoqarin fito da mashayin nata don ta zizarawa xaya idon nata. Ta zuba mishi ido kafin ta ce mishi. “Yaushe ne ka tava zuwa gidana baka sameni cikin kwalliya ba?” Ya xan qara kallon ta kafin ya ce, “A’a, Abu ba dai irin wannan kwalliyar taki ta yau ba, kwalliyarki ta yau ai ta fi kama da so kike ki cinye wata gasa. Ba don na san tsofaffi basa zuwa gasar sarauniyar kyau ba da sai in yi zaton can za ki tafi”. Abu ta yi murmushi ta ce, “Ko ba za ni cin gasa ba ai na yi kwalliya yau kam ta cinyewa, tunda yau ne saka lallen Saddiqa. Sa’a ma ka ci ka sameni a gida don can gidan nasu za ni yanzu”. “Yau saka lallen Saddiqa?” Ya yi tambayar a firgice cikin faxuwar gaba da razana tamkar Abu ba ta gane yanayin da ya samu kanshi a ciki ba. Sai ta ci gaba da magana. “Iyayen Saddiqa sun matso da xaurin auren zuwa jibi, sun ce ka xaga musu hankalin yarinya kana nema ka sata ta bijire musu bayan ita ba bijirarriyar ba ce, tunda uwarta ta bayyana mata halayenka babu abin da take yi in ban da kuka, ko abinci ta qi ci. Don haka gara suyi maza su kaiwa mijinta ita tun baka yi dalilin da suka kunyata ba, don haka yau ne ake aikin kayan tsarabar biki su cincin, lkaki, nakiya da dubulan. Yanzu haka ma ai ina jin gidan a ciki yake”. Bilkisu ta yi sallama Abu ta amsa mata, ta shigo ta durqusa ta gai da Abu sannan ta juya wajen Mus’ab, bai saurari gaisuwarta ba ya balbale ta da faxa. “Har daku Bilki cikin bukin da su Inna ke shirin yi? Na ce har daku? ‘Yan ina da buki? Ko ba a gayyacesu ba sai sun je? Yanzu ashe har daku cikin wannan bukin?” Abu ta bar abin da take yi ta zuba mishi ido tana kallon shi. Bilkisu kuwa kuka take ta yi, ya yin da shi kuma yake ta faxa. “In ban da rashin hankali da rashin sanin ciwon kai me ya shigar daku cikin wannan bukin? Na ga hanaku auren aka yi aka bai wa wasu, ko kuwa kuma kuna cikin masu marawa Sadisu ne? Ko har daku aka haxu aka yi min taron dangin da aka yi aka hanani auren ne? Ta hanyar gwada min fin qarfi, kuma kun biyewa Abu ne? To ita murna take yi da abin da aka yi min tana farin ciki, kin ganta ai gayenta take yi, yaushe rabonki da ganinta riqe da madubi tana qalqale fuska in ban da yau? Murna take yi tana farin ciki an hanani auren Aisha an qwace min ita, bayan kuma tawa ce saboda kawai bani da gata dama kuma tun farko sai da ita Abun ta sarawa neman auren nawa baki”. Abu ta katse maganganun nashi ta hanyar qyalqyalewa da dariya. Sai da ta yi shiru sai ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce mishi. “Sambatun kayan ne haka ko kuwa har yanzu a buge kake maye ne ya saka waxannan maganganun?” Ya yi maza ya qara xaure fuska ya ce, “Wane irin maye?” Ta ce, “To in ban da haka ka ce don an hanaka auren Saddiqa kar su Bilki suje bikin? Kanka xaya? Saddiqa ba qanwarka ba ce? Ko kuwa barasar ce ta mai da kai haka baka san ya kamata ba sai kanka kaxai ka sani?” “Bana son kina yi min irin waxannan maganganun a gaban qannena”. Ta ce, “Kai tafi can ka bani wuri, mene ne basu sani ba a halayen naka? Mene ne qannen naka basu sani ba game da kai? Ni abin kunyar da ka yi ma da Bilkin ka yiwa zai xaga min hankali ne har ya dame ni ya tayar min da hankali? Ita Bilki ai ta san komai naka tunda tare kuka taso shekaru uku ne a tsakaninku, tun ba ta isa komai ba kuma take cikin lamarinka, babu wani abu naka da ba ta sani ba. Amma Hamida fa? ‘Yar qanqanuwa cikin qannenka, yarinyar da in da kai mace ne ka haifeta da girmanka fa aka haifeta, ba ta san komai game da halayenka ba, in dai ba ta ji a labari ba in wani ya gaya mata”. Mus’ab ya shiga tsoro da fargaba, ya qosa qwarai Abu ta kai qarshen maganar tata ko kuma ta katse dogon bayanin ta gaya mishi me ya yiwa Hamidan? Kar dai fa mafarkinshi ya zama gaskiya? Kar dai fa da gaske ne Hamida ta je gidanshi ya jefe ta ya fasa mata kai? Tambayoyin da suke kai kawo cikin zuciyarshi kenan. Abu ta shiga kuka sai dai ba ta bar magana ba. “Haba Mus’ab, sai yaushe ne za ka bar wannan mummunan halin naka? Duk yanda qannenka suka kai da baqin cikin hanaka auren da aka yi ya ya za suyi? Me za suyi wanda ya wuce abin da suka yi? Dole ne su tsaya ayi hidimar auren Saddiqa dasu. ‘Yar’uwarku ce, hanaka aurenta da aka yi ba zai sa ku yanke zumuncin dake tsakaninku ba, tana da haqqin ku yi zumunci da ita. Kune ‘yan’uwanta da ta fi sani ta fi so, ta kuma fi shaquwa dasu, tunda ba ta da abin da take so take kuma girmamawa irin uwarku. Raina ya yi matuqar vaci sanda Bilki ta zo min da bayanin shirin da ake yi a kan hanaka aure, na kuma yi nufin zuwa gidan naku in samu shi Malam Abdullahi tunda da yardar shi ake yin komai. To amma da Bilki ta aiki ita Hamida gidanka don ta je ta gaya maka abin da ake ciki, saboda ka hanzarta zuwa ku tattauna ku san abin da za ku yi ta dawo. A yanayin da ta dawo na kuma kalle ta na tabbatar ba kukan fasa mata kan da ka yi take yi ba, tana kukan baqin ciki ne na yanayin da ta same ka a ciki. Sai na gane ba komai yasa iyayenku hanaka auren Saddiqa da suka yi ba illa kawai su xin mutanen kirki ne masu gaskiya da riqon amana, Ubangiji kuma zai yi musu kyakkyawan sakamako a kan zumuncinsu. Gaskiyarsu ne, Saddiqa ba matarka ba ce, kai daban ita daban, ka fi qarfinta ba za ta iya rayuwarka ba, kowace qwarya ai da abokin burmin ta. Ka girma ne baka san ka girma ba, in an ganka a tsaye cikin sutura abin gwanin sha’awa, amma hali babu. Da girman nan naka da gwarjinin naka giya kake sha, in ka sha kuma ka yi hauka, qannen ka ma basu tsira ba, to wa zai tsira? A wannan halin naka kuma wane mutumin kirki ne zai xauki ‘yarshi ya baka in dai ba a kan rashin sani ba, ko kuma yana kwaxayin abin hannunka?” Wasu hawayen masu yawa suka sake zubowa daga idanun nata, dai-dai lokacin da ta xago idanuwanta ta kalli Mus’ab ta ce mishi. “Iyayenka mutanen kirki ne, nima rashin adalci ne ya sani vacin ran abin da aka yi makan, in ban da haka ai dukanku xaya ne a wurina, kai da Saddiqa xaya kuke, ita gaskiya kuma ai guda xaya ce daga kauce mata kuma sai a shiga vata, bai kuma dace in yi hakan ba”. Mus’ab yana zaune ya rasa yanda zai yi, ya rasa inda zai sa ranshi ya ji daxi, ga Abu da Bilki sun qi daina kukan da suke yi, ga shi nashi hawayen sun qi yarda su zubo balle su haxu su duka ukun suyi kukan. Sai dai zuciyarshi ta kai matuqa wajen quntata, zafin da take yi ya wuce duk yanda za a yiwa kwatance, ya rasa me zai yi. A hankali ya miqa hannu ya xauki xan makullin motarshi dake ajiye kan tabarma ya miqe ya fita ba tare da ya san inda zai tafi ba. Tuqin kawai yake yi bai san inda ya dosa ba, zuciyarshi cike da baqin ciki da nadama, da dai da hali to da ya ce daga yau ba zai sake tava barasa da hannunshi ba, saboda baqin ciki da qasqanci ga abin da kunyar da ta ja mishi, a dalilinta ya rasa yarinyar da yake ganin tamkar don shi aka haife ta Aisha saboda tsananin son da yake yi mata. Ga kuma qasqanci da kunyar da ta ja mishi wurin ‘yar qanqanuwar qanwar shi ‘yar autan xakinsu Hamida, wacce ya tabbatar kafin zuwan nata gidanshi ta same shi a halin da ta same shi ba za ta gaskata komai game da labarin da take ji a kanshi ba, da wuya ma ta saurari irin waxannan maganganun saboda tsananin girmamawar da take yi mishi. To wai ya fasa mata goshi da kwalbar giya ya yi mata rotse saboda wai ya bugu, wace irin giya ce wannan? To wai tunda yake shan barasa ma shi wane alheri ta tava haifar mishi ne in ban da sharri. Ya yi nisa cikin tunanin sharrin barasa. Sai kuma ya ji wata zuciyar tana ce mishi, babu ruwan barasa, ba ma laifinta bane, gata ne kawai ba shi da shi, rashin tsayayye a kan al’amari ne kawai ya ja mishi, da yana da tsayayye da ba a jefa shi ba ma cikin damuwa da vacin ran da zai samu kanshi cikin wannan halin ba. Inna ce ta rasu ba ta nan ne, da tana raye da ban ma samu kaina a irin wannan yanayin ba. Kalaman da suka rinqa kai kawo a zuciyarshi kenan, bai kuma ankara ba saia ganin shi kawai ya yi yana shiga cikin unguwarsu ta Tudun Alqali dake cikin garin Bauchi. Ya yi parkinga a qofar gidansu wanda a yanzu ya mai da shi ginin zamani saboda rushe tsohon ginin da ya yi ya yi sabo. Kawu Gixe yana zaune cikin falon shi ya yi sallama ya shiga ya tsuguna. Da sauri Kawu Gixe ya soma tambayar shi. “Me ya same ka Mus’abu? Me ya sameka kake wannan baqin cikin?” Mus’ab ya matse idonshi hawayen da suka taru suka xiga, abin da ya yi dalilin miqewar Kawu Gixe tsaye saboda tashin hankali. “Me ya sameka?” Ya sake yi mishi tambayar bayan ya kafa idanuwanshi a kanshi. “Maraici ne kawai ya dame ni Kawu, tunda Inna ta rasu ta barni na koma watangaririya a tsakanin mutane, bani da wani tsayayye a kan al’amarina, rashinta yasa na samu kaina cikin baqin ciki da vacin rai, da tana raye da ban samu kaina cikin qasqancin da nake ciki ba a yau. Bani da uwa bani da mai tausayina balle ta rufa min asiri, bani da kowa, bani da inda za ni in faxi damuwata. Shi yasa na zo gabanka in yi kuka don ka qara sanin har abada ba zan daina kukan mutuwar Inna ba, inda tana raye a duniya da babu mai yi min irin tonon asirin da aka yi min a Misau, an taro an nuna min fin qarfi an hanani auren Aisha saboda wai ni xin mashayi ne, da tana nan a raye Kawu da tasa an bani auren duk da ita xin ta fi kowa sanin mugun halayena, da ba za ta hanani auren ba, saboda ta san rabani da ita zai iya haddasa min vacin rai na samu kaina a yau cikin baqin ciki da qunci da ciwon zuciya, amma wai a hakan Abu ta sani a gaba tana yiwa waxanda suka hanani auren addu’ar Ubangiji ya saka musu da alheri, don wai gaskiya da adalcin sune yasa suka hanani auren da suka yi”. Kawu Gixe ya koma kan kujerar shi ya zauna ya zubuawa Mus’ab ido, cikin nutsuwa ya tambaye shi. “Dama kai kana son Saddiqa ne baka yi magana ba?” Ya ce, “Eh, Kawu hanani yin maganar aka yi ta hanyar tsoratar dani wai idan na ce ina sonta za a gaya mata halina, to ga shi ban tsira ba, abin da na guda shine ya sameni. Inna ce jagorar rabani da Aisha, su Baba da su Abu suka mara mata baya. Ni ban ma qara sanin da hannun Abu a ciki ba sai da na jita ta dage tana ta yi musu addu……” “Kai tafi can ka rufe min baki, kai ka jawa kanka komai, yanzu ka zo kana wannan surutun da in ba sa a ba zai tashi a shirme da surutu, bayani nake so na yanda aka yi hakan”. Mus’ab ya shiga yi mishi bayani dalla-dalla tun farkon yanda ya faro maganar a gaban Abu, har kawo lokacin da Innarshi ta yiwa Saddiqa bayanin komai, al’amuran da suka biyo bayan hakan da suka yi dalilin bikin gaggawa da suka tayar, har rotsen da ya yiwa Hamida da ya zama hujjar Abu ta fita cikin lamarinshi, da addu’ar da take yiwa iyayenshi bai voye komai ba. Kawu Gixe ya sunkuyar da kai qasa cikin tunanin mafita. Mus’ab ya yi matuqar razana, don tunanin ko shima zai yi fushi da shi ne. nan da nan ya shiga ba shi haquri yana magiya. “Ka taimakeni kasa baki cikin lamarin Kawu ka hana su xaurin auren da suke shirin yi jibi, ka tura shi zuwa wani lokaci dan in samu damar da zan ga Aisha in san yanda na yi-na yi mata bayanin da za ta fahimceni, zan gaya mata irin son da nake yi mata, zan yi qoqari in fahimtar da ita al’amura masu yawa da ke tsakanina da ita a baya, ban samu damar gaya mata abin da ya kamata in gaya mata ba saboda ina tsoron kar a tona min asiri a wurinta, to yanzu kuma tsoron ya qare zan nuna mata……” “Kai rufe min baki mashirmancin banza!” Kawu Gixe ya yi maganar a yanayi na vacin rai. Ya yi maza ya ja bakinshi ya yi shiru. “Kira min Malam Hadi”. Ya tashi cikin nutsuwa ya fita don cika umarnin da Kawun ya ba shi, ya nufi unguwar Railway don isar da saqon. Malam Hadi shine amini na qut da qut a wurin Kawu Gixe. Bai yi qasa a gwiwa ba ya biyo shi suka taho tare, ya wuce cikin gida ya barsu nan suna tattaunawa. Mus’ab yana zaune a wani xaki da ya barwa kanshi a cikin gidan, wanda yake ganin tamkar shine a gurbin na Innarshi da ta rayu a ciki, inda tana nan da ita ce za ta bani Aisha, ba tare da ta damu da cewar ni xin mashayi ne ko manemin mata ba, inda tana nan ma wataqila da ban samu kaina a wannan halin da nake ciki ba. Ya xan yi ajiyar zuciya kafin ya sake ya sake tsunduma cikin tunanin rayuwarshi a gaban Innar tashi, yanda ya zo mata da yanda ta tafi ta barshi. “Wayyo Inna!” Ya yi shiru zuwa wani lokaci kafin daga bisani ya shiga gabatar mata da addu’o’i, tsawon lokaci yana cikin wannan yanayin kafin ya koma kan tunanin Aisha da kalamanta na ba ita ba shi, bayan kuma sun yiwa juna alqawarin kasancewa tare, sai da taimekon shi kan maganar neman auren shi, sai ga shi da abin ya bayyana a kana ta bijire mishi, saboda an gaya mata halayenshi. Sannu a hankali ya sake tambayar kanshi. “Ko meye alherin barasa? Ko ya ya zai yi ya daina shanta? Anya in har ya rasa auren Aisha zai iya daina shan barasa a rayuwarshi? Ina ma dai a ce duk mutanen duniya irin Innarshi ne masu qoqarin taimakon mutum, gyara halinshi da mugayen xabi’unshi ta hanyar janshi a ciki, taimakon shi ta hanyar qarfafawa, mutunta shi da nuna mishi munin abin da yake yin a nutse, maimakon a qyamace shi ko a guje shi”. Kawu Gixe suna tare da amininshi Malam Hadi, kusan minti talatin suna tattaunawa kan hanyar da za su bi su fitowa lamarin. Daga qarshe suka yankewa kansu abin da ya dace suyi, wanda ya sanya Kawu Gixe cikin sauri ya shiga cikin gida ya kira babban xanshi Adamu ya aike shi cikin motar Mus’ab ya zo da ita. Sani da Ishaq suka iso falon Kawu Gixe cikin ladabi suka gaishe shi. “Kawu mun zo wajenka neman taimako ka sanya baki cikin maganar auren da ake shirin xaurawa Saddiqa a Misau jibi”. Ya kalle su ya ce, “Yau ne ya kamata ku sanar dani?” Sani ya gyara zama cikin nutsuwa ya ce, “Kawu ka yi haquri, muma yau ne da muka bi bayan Mus’ab zuwa gidan Abu muka ji cewar jibin za a xaura aure, mun kuma nemi Mus’ab a waya ya rufe, Abu kuma ta gaya mana cewar ta gaya mishi komai, bai kuma ce mata ga inda za shi ba don haka muka ce bari mu zo gabanka mu roqi wannan alfarmar, don mun san duk inda yake in ya samu labarin an xaga xin zai samu sassauci”. Malam Hadi ya shigo tare da wasu dattawa su uku, don haka su Sani suka ja gefe suka takure suna jiran su gama abin da suke yi kafin su sake matsawa gaban Kawu Gixe su qara roqon shi ya yi wani abu kan al’amarin. Suna zaman jiran sai ga Adamu ya shigo da manyan qunshin goro guda biyu. “To ai ma shi kenan mun isa Allah gafarta malam ko kuwa?” Kawu Gixe ne ya yi tambayar. Malamin dake zaune a gefenshi cikin rawani ya ce mishi, “Eh, mun isa ai shaidu ma su kan gamsar wajen xuarin aure, balle mu a nan mu shida ne”. Da sauri Malam Hadi ya ce, “Ai ga su Malam Isa ma sun dawo”. Ya yi maza ya leqa ya kirasu suka shigo, su ma su uku. Nan take Kawu Gixe yasa aka xaura auren Mus’ab da Aishatu, abin da ya yi matuqar baiwa Sani da Ishaq mamaki. An gama xaurin aure an raba goro, jama’a suna watse kowa ya nufi gidanshi, Sani da Ishaq suna durqushe gaban Kawu Gixe sun rasa kalmar da za suyi amfani da ita wajen yi mishi godiya. Sai ga Mus’ab xin ya shigo saboda kiran da Kawu Gixe yasa aka yi mishi. “Ku gama kafin in fito”. Kalmar da Mus’ab ya riska kenan na maganar Kawu Gixe. Ya kuma kalli Mus’ab xin bayan ya nuna su Sani da hannunshi. “Ga masu neman ka can”. Ya wuce ya yi tafiyarshi. Ishaq ya qanqame Mus’ab a yanayi na tsananin farin ciki. “Na rantse yau ne na tabbatar da kalmar da Hausawa ke furtawa ta ABU NAKA…. Wai maganin a kwaveka. Kawu Gixe ya xaura auren ka Mus’ab”. Mus’ab yasa hannu biyu ya hankaxe shi. “Kai bana son irin zolayar da kuke yi min yau? Haka Sani ya ce min wai sun sato Aisha ashe qarya yake yi min, zuciyata a quntace take ina cikin wani al’amari da ban san shi ba……..” Kan ya qarasa maganar tashi Ishaq ya yi mishi rantsuwa. “Yanzun nan muka gama xaurin auren ka Mus’ab, Kawu Gixe ya baka auren, ga goro ga minti ga takardunsu kana kallo”. Sai a lokacin ne hankalinshi ya kai garesu, gabanshi ya yanke ya faxi, cikin fargaba da tsoro kar dai shima Kawu Gixen irin auren da Abu take so ta yi ya yi mishi, auren huce fushi. Hannu ya xora kan qirjinshi saboda harbawar da takeyi. “Kawu Gixe ya xaura min aure?” Da qyar ya iya buxe baki ya sake tambayar su. “To wa ya bani?” Sani yana murmushi ya ce, “Saddiqa”. Mus’ab ya kalle shi haushin zolayar da suke yi mishi ya qara kama shi, me suke nufi dani waxannan? Basa tausayina ne? Ko so suke su mai dani tamkar mahaukaci? Ya juya ya fita wajen Kawu Gixen ya tafi. “Ka taimakeni Kawu kar ka bani auren da ba shi nake so ba, Aisha kaxai nake so in ba ita ba ce gara a barni haka kar a xora min nauyin kowa a kaina, a barni kawai in yi zamana a haka”. Kawu Gixe ya zuba mishi ido. “Me abokan naka suka gaya maka?” Ya buqaci sani. “Kawu rabu dasu, su basa tausayina zolayata suke yi. Sun ce min wai da Aisha ka xaura min auren, amma na san qarya suke yi so kawai suke yi wai su ga na samu nutsuwa, bayan kuma baqin ciki ya sameni”. Cikin nutsuwa Kawu Gixen ya ce mishi, “Ita na baka Mus’abu, da ita na xaura maka aure, ai taka ce. ABU NAKA…. Maganin a kwave ka. Gaskiya ne da ka ce inda uwarku tana raye za ta baka ita ba tare da ta xaga ido ta yi duba kan irin laifuffukanka ba, ba ta nan, to ni ina nan, nima kuma ba zan iya barinsu su rabaka da ita ba. Don haka a zaman da kake yi a yanzu Aisha matarka ce, na baka ita ta hanyar xaura auren sunna a tsakaninku, mallakinka ce tana qarqashin hukuncinka, yanda ka so haka za ka yi da ita a yau”. Mus’ab ya sunkuyar da kai a gaban Kawu Gixe tsawon lokaci bai ita ce mishi komai ba. Sai Kawu Gixen ne yake magana mafi yawancin nasiha shan giya da neman mata. “Manyan musibu ne Mus’abu, aiyukan savo ne masu girma, kai ka sani irin waxannan aiyukan kuma xabi’u ne na mutanen banza, mutanen da basa tsoron Ubangiji, kai ba mutumin banza bane, domin mutanen kirki ne suka haifeka, iyayenka mutanen kirki ne, ka fita cikin wannan rayuwar ko kaxan ba ta dace da kai ba, ba kuma ina yi maka wannan maganar bane a yau wai ko saboda Aisha ta zama matarka, a’a, sai dai don a zuciyata ina burin ganin ka zama cikakken mutumin kirki ba mai yawan cuxanya da zunubai ba”. Cikin ladabi Mus’ab ya ce mishi, “Na sani Kawu, na roqeka ka yafe min rashin kawo maganar da ban yi ba tun farko na rinqa ganin kamar bani da wani tsayayye kan al’amarina, na manta da cewar duk wani wanda ya tsaya min ya taimakeni ko ya soni ya yi hakan ne a dalilin ganin tsayawarka, taimakon ka da kuma soyayyar ka a gareni. Kai ne ka tsamoni cikin halakar da na samu kaina a ciki, ka kawoni gidan nan kuka haxu kai da Inna kuka yi min gata, kuka mai dani mutum na zama cikakken xa mai cikakken ‘yanci, kuka xorani a bisa hanya ta rayuwa. Ga shi a yau kuma ka sake yi min wani alherin na rabani da baqin cikin da ya sameni, ka ceci rayuwata daga shiga halin butulci na ganin tamkar bani da kowa, ka bani yarinyar da nake ganin tamkar ita kaxai ke gareni, in ban same ta ba kuma ba zan mallaki kaina ba, duk da kai xin ka fi kowa sanin mugayen aiyukana, ka fi kowa sanin abin da nake yi. Na roqe ka ka taimakeni ka yi min addu’a Ubangiji ya tsare min aurena da Aisha, ya kuma zaunar damu lafiya”. Kawu Gixe ya ce mishi, “To Mus’abu zan yi maka”. “To Kawu ka yi min addu’ar”. Kawu Gixe ya shirya goro da minti gami da sadakin da ya biyawa Mus’ab na kuxi naira dubu uku ya tashi amininshi Malam Hadi tare da matarshi Furera da tashi matar Raliya, suka koma a cikin motar Mus’ab suka nufi Misau Adamu yana tuqa su, don suje su isar da saqon xaurin auren da ya yi tsakanin Mus’ab da Saddiqa. Suma su Mus’ab suna ganin tafiyarsu suka bar gidan cikin motar Ishaq, su ma Misau xin suka nufa, zukatansu cike da farin ciki da annashuwa, suna tafe suna hirar Kawu Gixe da alherinshi. GARIN MISAU Gidan su Inna Habiba a Misau ya cika ya tumbatsa da jama’a ‘yan saka lalle, ba qaramin cika aka yi ba a gidan kasancewar Inna Habiba ta kwana biyu ba ta yi bikin ba, tun na ‘yar autar ta Hamida. Sai dai ita kam Inna yanzu ne take faxin bikin ‘yar auta, don haka biki sosai ta shirya, ta kuma gayyaci ‘yan’uwa nesa da na kusa, ga kuma abokan arziki. Saddiqa tana kwance a xakinta tun bayan saka lallen da aka yi mata ta kasa fahimtar halin da take ciki, ita dai kawai ta san saka lallen ya haifar mata da matsanancin baqin ciki, damuwa gami da vacin rai mai tsanani, ga shi dai ba son Mus’ab take yi ba saboda ya fita ranta kwata-kwata a dalilin munanan halayenshi da aka gaya mata na kasancewar shi fasiqi. To amma kuma abin takaicin shine, shima Sadisun ba ta son shi shima ya fita ranta, ba ta qaunar ko sunanshi ta ji ana ambata mata. Ta fi so a barta kawai, a barta ta yi zamanta haka babu auren, shima auren ba ta son shi, in ban da kar ta yi savo ma da ta ce ta tsane shi, don daga tasowarshin ta samu kanta cikin yanayin da take ciki a yanzu na baqin ciki da qunci da tsirarar waxanda ake ganin girmansu. Malam Abdullahi ya fito yiwa baqin shi rakiya lokacin da Adamu ya yi parking a qofar gidan cikin motar Mus’ab, da farko ya xauka Mus’ab xin ne, sai da ya ga fitowar Adamu da sauran mutanen da suke ciki nan da nan ya yi sallama da baqin nashi ya juyo tarar Malam Hadi. “Barka da zuwa”. Ya isa da shi xakinshi na waje. Su Baba Furera kuma suka wuce cikin gida inda su ma suka samu tarba mai gamsarwa. Bayan sun ci sun sha an kuma gaggaisa anyi raha yaushe gamo? Inna Habiba tana tambayar Inna Raliya. “Yanzu nan dama za ku zo amma baku iso da wuri aka yi saka lallen nan daku ba?” Ta yi murmushi ta ce, “To ba gashi anyi ba? Ai barinki dai na yi ki yi yanda kike so, tunda ke ce uwar ke ce uban”. Mutanen dake wurin suka taya su dariyar da suke yi. “Sallamu alaikum! Gwaggo tana ciki?” Muryar Malam Abdullahi ne daga waje-wajen zaure saboda cikowar mutane. Da sauri Bilkisu ta iso cikin ladabi tana tambayar shi. “Baba Abu za a kira maka?” Ya ce, “Eh, maza kira min ita”. Ta yi maza ta nufi xakin da Abu ke ciki tare da ‘yan tsofaffi aminanta suna hirarsu. Tana jin kiran ta yi maza ta fita ta nufi inda Malam Abdullahi ke sauraron zuwan nata. Sai da ta gama sauraron bayanin nashi sannan ta shigo gida tana salati. “Iko sai Ubangiji, wani baya auren matar wani. Shi aure dama ya gaji haka, koma in ce abin da ya fi haka, dama kuma an ce matar mutum kabarinsa”. Gaba xaya wuri ya yi tsit! Ana sauraron kalaman nata. Ta leqa falon Inna Habiba inda jama’a ke cike ta ce, “A’a, ke Furera ashe kun baiwa xanku auren shine da kuka zo baki gaya mana ba?” Inna Habiba ta zuba musu ido tana kallo cikin yanayi na rashin fahimta da son jin bayani. Inna Furera ta ce, “Eh, Gwaggo gani na yi mun zo da amininshi”. Ta ce, “Haka ne ta xaga ido ta kalli taron jama’ar dake wurin, ta ce, “Jama’a aure fa ya zama a kan Mus’abu yake, don xazu da yamma Kawunshi ya xaura mishi aure da Saddiqa, ga goro nan da minti da kuma sadakinta dubu uku ya bayar ya ce a kawowa uwarta”. Kukan da Inna Habiba ta saka shine ya taqaita farin cikin su Bilkisu da ‘yan’uwanta, gaba xaya aka taru a kan Inna Habiban ana ta faman ba ta haquri. Baba Furera kuwa cewa take yi, “Babu wata kunya da aka baki tunda ya ce a gaya miki ki sa a xaurawa Sadisu aure da Kubra, ba shi kenan ba magana ta qare”. Ita kuwa Saddiqa tana kwance a xakinta ta yi kasaqe tana sauraro tare da tambayar kanta me yasa Gwaggonta kuka haka a cikin taron mutanen da ta tara? A daidai lokacin ta ji wayarta tana qara, rabon da ta ji qaarar an daxe, don haka ta miqa hannu ta xauka don ta ga waye. Duk da ta daina amsa wayarshi sai ta yi nufin amsawa, wai ta ji me zai ce mata. Yana jin ta xauka bai jira ta ce komai ba ya soma ce mata. “Ina miki barka tare da albishir na zama amarya ta har abada, Aisha ina tabbatar miki da cewar daga yau kin shiga amarcin da ba zai tava qarewa ba har abada, dama can ni dake abu xaya ne Aisha, za kuma mu ci gaba da zama abu xaya”. Saddiqa ta rasa me za ta ce mishi tunda ba ta gane me yake nufi da kalaman nashi ba balle ta gane inda ya dosa. Abin mamakin dai shine, muryarshi ba ta cikin yanayi na tashin hankalin da ya kirata a baya, ba ta san yanda aka yi ba sai kawai ta ji ta fashe mishi da kuka. Ya yi maza ya katse layin. Qawarta da ta fita tsakar gida don wanke hannu ita ce ta shigo tana ce mata, “Na fa ji kamar ana cewa wai yau a Bauchi an xaura aurenki da Yaya Mus’abunki, shi kuma Sadisu wai an ce a bashi ‘yar’uwarki Kubra”. “Yaya Mus’ab?” Da qarfi Saddiqa ta yi tambayar. Nan take kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka mai tsanani. Su Bilkisu da ‘yan’uwanta suka yi maza suka fice daga gidan saboda ganin an samu an shawo kan mahaifiyarsu ta daina kukan da take yi. Kasancewar dare ya riga ya fara yi bai hanasu nufar gidan Mus’ab ba dake can bayan gari don su taya juna murna. Qwayayen fitilu sun haske ko’ina na harabar gidan, tun kafin ka qaraso kuma kana jiyo sautin jama’a, ga kuma motoci a tsaitsaye a harabar gidan alamar tuni har abokanshi dake kurkusa sun fara isowa. A haka suka qarasa shiga gidan, daga nesa suka hangoshi riqe da sigarinshi a hannu yana kuma amsa waya. “Yaya Mus’ab ashe kuma sai zama ango?” Ya yi murmushi ya ce, “Eh, Bilkisu abin kamar babu wuya amma mu kam ai mun san mun ji jiki, ko kuwa?” Gaba xaya suka yi murmushi. Nan take kuma suka shiga gaishe shi da yi mishi murna a yanayi na girmamawa. “To ya ya Inna ta karvi labarin?” Cikin nutsuwa ya yi musu tambayar. Suka gaya mishi komai. Ya yi ajiyar zuciya a hankali ya furta kalmar. “Ta yi haquri, ku taimake ni ku ba ta haquri, ku ba ta haquri Aisha matata ce ta yi haquri ta karvi hakan, Kawu ya riga ya bani ita, qaddara ce hakan don haka ta yi haquri”. Sun xan fara yin magana sai ya xaga ido ya kalli Hamida a wani yanayi da ya fi kama da kunya ko nadama tare da shan mur! “Ba ki dai gayawa mijinki abin da ya sameki a goshin ba ko?” Ta yi maza ta sunkuyar da kanta qasa tare da jan gyalenta ta qara rufe fuskarta dake goshin nata ta yi shiru saboda jin nauyinshi. Suna cikin zancen da suke yi Bilkisu ta ce, “Shi kenan ‘yan ina da biki, biki ya zama nasu sai ya ya kenan?” Ya yi murmushi ya ce, “Sai ku yi sabon shiri Balki, sabon biki sabon komai”. Su Ishaq suka shigo, Sani ya wuce kicin Ishaq ya tsaya wurinsu yana faxin “Qannen ango ne a daren nan?” Suna gamawa gaisawa Sani ya sake shigowa cikin falon da abubuwan ci da na sha yana ajiye musu, yana yiwa Mus’ab bayani. Ishaq ya katse shi ya ce, “Bilkisu ku fita a mai daku gida mu zamu koma Bauchi yancu zamu je musa ango a lalle, a can zamu yi hidimar bikinmu, zamu xora muku nauyin haxa mana kayan aure duk da mun san kuma hidimar taku tana da yawa, don haka mota za ta zo ta xauke ku gobe, sai ku samu Atika a Kano ku haxu ku yi sayayyar ko kuwa?” Suka amsa “To”. Mus’ab ya miqe ya shiga xakinshi ya fito rungume da wasu lesuna ya zube, ya sake komawa ya fito riqe da akwatin matafiya ya zo ya miqa musu suka buxe suna dubawa. Sarqoqi ne masu asalin kyau haar kala uku, kowanne kuma yana haxe da wara-waran da suka dace da shi. Mus’ab da Ishaq suka yi singing xin cek guda biyu suka miqa musu. “Ga shi nan in kun je yin sayayyar kar ku mance da kawunanku”. Suka sa hannu biyu suka karva tare da godiya gami da fatan alheri. Biki sosai su Mus’ab suka yi a Bauchi, don can suka yi hidimar tasu a gidan Kawu Gixe. Ko ita ma kuwa Inna Habiba duk da vacin ran dake cikin ranta voyewa ta yi, hidima sosai irin wacce ba ta tava yi ba, ga kuma su Bilki da suka qara qayatar da bikin ta hanyar sakar mishi kuxi sosai. Anyi xaurin auren Kubrah da Sadisu, an kuma kaita gidan mijinta duk wani shiri da Inna Habiba ta yiwa Saddiqa ta kwashe ta bayar an kai wa Kubrah gidan Sadisu. ‘Yan biki sun watse an bar Saddiqa da Innarta a gida kamar yanda dama suke. Suna zaune a falon Innar suna hira, akwatinan auren Mus’ab ne a gabansu suna qara dubawa. “Ai zan yi maganinshi, wai shi ya iya shege ko? Ya za ga yaje ya kaiwa Yaya maganar shi kuma Yaya da yake bai ganin laifinshi duk da ya fi kowa sanin shi, ya xauki auren ya ba shi. To ai zan ga mai kai mishi ke, kar ki yarda zuciyarki ta karyo a kan qiyayyar da kike yi mishi, don wannan aure da Yaya ya xaura ba komai bane illa fitina, ba zamu iya shi ba don haka bake ba shi, kar ma ki yarda ki saurare shi, don ba za ki tare a gidanshi ba ma, kuma nan ina jiran randa zai shigo gidan nan titsiye shi zan yi sai ya rubuta takardar sakin auren ya bani sannan ya fita”. Saddiqa ta kalleta cikin nutsuwa ta ce, “To amma Gwaggo kin san da haka kike ta bani kayanshi ina xaurawa? Ko jiya fa tirmi goma kika bayar a xinko min?” “Ai ba zan mayar mishi da kayana ba har zinaran sun zo kenan ladan kukan da ya sani na yi a cikin mutanen da na tara ana kallona ina sharvar majinar baqin ciki”. Saddiqa ta vata ido ta ce, “Dama an bar mishi kayanshi kawai Gwaggo, da wanne zai ji?” Ta yi maza ta ce, “Kul! Na sake jin wannan maganar a bakinki, kwalliyarki za ki yi ta yi dasu”. Da daddare misalin sha biyu da rabi Mus’ab yana kwance a xakinshi dake gidanshi na Misau, ya yi sha’awar a ce shima an kawo mishi Aishanshi kamar yanda aka yiwa Sadisu tashi matar, ina ma dai a ce a gefenshi take yana a kwance, ga shi kuma daren mai cike da iska ne mai xauke da saqon sanyi a cikin shi. Ko sai yaushe ne haqqina da damuwa ta za su zamo abin dubawa wajen Inna? Shima Baba ya yi shiru ya zuba ido yana kallon abin da ake yi min xin bai tanka ba. Ya xan yi tsaki mara sauti, a dai-dai lokacin da ya miqa hannu ya xauko wayarshi dake gefenshi a ajiye ya soma dannaa lambobinta. Ko ba ta amsa maganar da nake yi mata ai tana jina, bari in gaya mata abin da zan gaya mata. Tunanin dake zuciyar shi kenan. Saddiqa wacce Gwaggonta ta dawo da ita kwana a xakinta, a nan gadonta suke kwana tare tun bayan watsewar ‘yan baki, saboda tsoron da take yi na kar Mus’ab ya shigo cikin gidan ba ta sani ba. “Xauki mana ki ji abin da zai ce miki”. Don haka ta miqa hannu ta xauka. “Aisha!” Ya kira sunan a hankali cikin jan hankali da nutsuwa. “Wai ni me yasa haqqi in nawa ne taka shi bai da wuya wurin Inna? An fi sati guda yau tunda Kawuna ya bani aurenki amma har yanzu ba a ce min ga lokacin da za a kawo ki ba, an xaura auren Kubrah da Sadisu ne bayan nawa xaurin auren, amma tuni da yake shi xan gata ne an kai mishi tashi matar. Ki taimaka ki yiwa Inna magana mana tunda ke ‘yar lelenta ce ki gaya mata kema kina buqatar mijinki, na rantse miki zama dani zai fiye miki na zaman gidan daxi, ba zan rinqa barinki kina kwanciya a kan kafita ba kan qirjina zan rinqa shimfixe ki, kin san kuwa xuminshi ba zai tava yin daidai da na katifa ba. Zan jiyar dake daxin da baki tava xanxana ba, zan yi miki tausa da sumba….” Ya yi maza ya katse layin saboda kukan da ta soma yi mishi. “Uh-uhm! Abin da ya iya kenan”. Mus’ab yana zaune gaban Abu, hira suke yi mai daxi, sai qamshi yake yi yana kuma cin dambun zogalen da Abun ta yi musu. “Ai na zo ranar talata bakya nan Abu, za ki ce wai angwanci ya voye ni. Kuma ni wane angwanci zan yi tunda an qi a bani matata”. Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “To ba dai zamanka take yi ba? Ko ba daxe ko ba jima ai za ta baka ita”. “A’a, Abu ni kawai a bani matata babu maganar ko ba daxe ko ba jima, ni na xauka ma za ki je wajen ta maganar a bani itan”. Ta ce, “A’a, ranar talata gidan Kubra na je saboda ‘yan’uwan mijinta sun zo nan sun kawo kaya na abin arzikin da taje musu da shi, suka ce a shaidawa iyayenta cewar ‘yarsu ta kai ‘yancinta, don haka na je don ba ta daga can kuma na je na gayawa Innarku na kuma kai mata abin da suka zo da shi”. Mus’ab ya ce, “Kai wannan al’ada taku Abu sai yaushe za ku barta?” “Mu barta a kan me?” A hankali ya yi tsaki, ya ce, “Haba, abin da ya kamata ya zamo sirri tsakanin miji da mata wai sai ayi ta bi ana yayatawa, ai ni ba zan yarda ayi min irin wannan bankaxar ba”. Ta galla mishi harara ta ce, “Eh, ai ku dama ‘ya’yan zamani ko in ce yanzu duk wani abu na al’ada dake taimakawa wajen kame mutunci da gudun abin kunya bakwa son shi, faxin budurwa ta kai budurci bankaxa ne amma neman matan banza ayi ta lalacewa dasu wannan ba bankaxa bane?” Ya yi murmushi don ya san inda ta dosa. “Abu kenan, mai da wuqar ni yanzu zuwa na yi in roqeki ki taimakeni ki sa baki a bani tawa matar nima”. Ta ce, “To zuwa yamma zan je gidan in ji abin da suke ciki”. Abu tana zaune a falon Inna Habiba suna gaisawa, Saddiqa ta fito daga can cikin xakin ta sha kwalliya cikin sabbin kayan aurenta, ga zinare ya kama jijkinta, duk da ba a kaita gidan miji ba sheqe take yi saboda qarin kulawar da ta samu. Abu ta harareta ta ce, “Uu-uhm! Ita kuma wannan amaryar a gidansu take kwalliyar amarcin? To wai me ya hana a kai Saddiqa gidan mijinta ne?” Ta zubawa Inna Habiba ido tana kallon ta tare da sauraron amsar tambayar tata. “Kin san dai baki da ikon riqe mishi mata a wannan lokacin, matarshi ce in dai ba so kike ki shiga alhakinsu ba”. “Alhakinsu Inna?” Ta yi tambayar cikin wani yanayi. Abu ta ce, “Eh mana, alhakinsu su duka, an ce miki ita ba ta son mijinta ne? Ko yaushe rabon da ki ganta tana kuka? Wannan kyau da sheqin da take yi an ce miki na zannuwa da zinaran da kike ba ta tana xaurawa ne? Basu bane kwanciyar hankali ta samu a dalilin an ba ta mijin da take so, da kin ba ta shima da yanzu ta fi haka, don da ta fi haka samun nutsuwa a wurinshi. In kuma kina jira ne sai ta sulale ta je ta same shi kin yi abin kunyar da gaske to”. Saddiqa ta sawa Abu kuka cikin yanayin shagwava ta ce, “Ni bana so, bana so Abu, bana so”. Ta soma kuka har tana shure-shure. Abu ta gallla mata harara tare da faxin, Tafi can munafuka”. Ta kalli Inna Habiba ta ba ta umarnin cewa, “Ki hanzarta xaukar yarinyar nan ki kaita gidan mijinta tun bamu kai ga vacin rai ba”. A nutse cikin ladabi ta ce mata, “To Inna, to ko za ki turo min shine ya zo mu san abin da muke ciki, kin san fa duk xan tanadin nawa na kwashe na kai wa Kubrah, kuma tunda aka yi xaurin auren fa bai leqo gidan nan ba, ina ce ya dace ya zo?” Ta ce, To bari zan turo shi tunda kuna son ganin shi”. Ta tashi ta fita ta nufi gidanta. Mus’ab ya yi murmushin jin bayanin da Abu ta yi mishi, ai bai kamata in fiki saninta ba Abu, so take in ji gabanta ta tilastani sakin aurena, tana shawara dani ne balle aa kan wannan auren da ta riga ta qi? Bana son shirin a bani matata kawai, ai ko wani za ta aura ni mai yi mata komai ne balle kuma ta zama tawa”. Abu ta yi kasaqe cikin yanayi na gaskata kalaman nashi, a hankali ta ce, “To kan wannan kam ai ka fini sanin nata, ina na yi wannan tunanin. Wato iya shege nima za ta yi min? To tashi ka tafi ka bar mata ita mu gani ko za ta yi ta riqe ta da auren naka a kanta”. Mus’ab yana kwance a falonshi, sigarinshi yake zuqa yana kuma tunanin rabonshi da wurin aikinshi. Lokacin da ya ji wayarshi ta yi qara yasa hannu ya xauka, lambobin Saddiqa ne. Ya xauka ya kai kunnen shi. “Ran amarya ya daxe, yau kin yi sha’awar jin muryata ne kika bugo min waya?” Shiru ta yi ta kasa amsawa. Ya ce, “In ce ko dai lafiya?” Ta sake yin shiru. Ya ce, “Ko ina son ganina ne?” Da qyar ta iya buxa baki ta ce mishi, “Eh, ka zo”. “In zo?” Ya tambaye ta. Ta ce, “Eh”. “Kina son ganina?” Ya sake tambayar. Ta ce mishi, “Eh”. Ya saki lallausan murmushi saboda abin da zuciyarshi ta raya mishi. “To ki gayawa Inna zan turo direba ya xauke ki”. Da sauri ta ce mishi, “A’a, kai ka zo”. “To shi kenan ki fito mu haxu a gidan Abu”. Ta yi maza ta ce, “A’a, sai dai ka zo nan gidan”. Ya ce, “A’a, Aisha in zo wurinki kina cikin gidanku ai ba zan iya ba, wai ba ki san ko ban yi surukuta da kowa ba dole in yi da Inna, ai in ba ita ce ta ce ki kira mata ni ba a yanzu babu abin da zai sa in shigo muku gidanku saboda kunya da girmamawa irin ta surukuta”. Da sauri Saddiqa ta ce, “Ai ita xin ce ta ce in yi kiranka”. Ya ce, “A’a, ban yarda ba wayo kawai kike son yi min”. Ta kama rantsuwa ta ce, “Ita ce ta ce na kira ka amma kar in ce in jita ne in ce in jini wai za ka fi saurin zuwa”. Ya ce, “Naqi yarda da wannan maganar taki, saboda a bakinki na saba jin kina cewa, wai maganar fari ita sarki yake karva, don haka sai anjima”. Ya ajiye wayar cikin nazarin abin yi tunda ya gane Innarshi ta matsu tana son ganinshi. Nan take ya qara sanin akwai abin da take shiryawa a kanshi. Yana zaune cikin ladabi a gaban Kawu Gixe bayan ya gama mayar mishi da bayanin halin da ake ciki. “To kai me ya hanaka zuwa ka ji kiran da take yi makan?” “Tsoro nake Kawu kar in je ta bani umarnin da zan kasa cika mata, har yanzu auren bai kwanta mata ba, sai nake ganin kamar so take in je ta titsiyeni ta tilastani yin abin da ba zai yi min daxi ba a kan auren”. Kawu Gixe ya xan yi shiru zuwa wani lokaci kaxan kafin ya dawo da nutsuwarshi gare shi. “To wai kai me ma ya zaunar da kai ne? Ka baro wurin aikinka kusan sati uku tuni abokanka sun koma kai kana zaune kana zirga-zirga a hanya, ka kama hanya ka yi tafiyarka ka koma wurin aikinka”. Mus’ab ya sake kallon shi cikin ladabi ya ce, “To Kawu Aishan fa?” “Ka yi tafiyarka ka barta mana ba taka ba ce? Ko za ta sake xaura mata wani auren ne a kan naka? Tunda zamanta da ita bai isheta ba ta je ta yi ta yi, kana can wurin aikinka ma in ka yi haquri za ka ga ta turo maka ita, ai matarka ce”. Mus’ab ya yi kamar ya ce ba za ta turo ba Kawu. Sai kuma ya haqura ya amsa umarnin da yake ba shi na kar ya yarda ko aike ya ji shi yana yi musu. Ya ce, “To”. Ya yi mishi sallama ya fita, maimakon ya nufi Ajakuta sai ya koma Misau don yin shirin tafiya Ajakuta. Mus’ab yana zaune gaban Abu suna magana kan tafiyar da zai yin, ya fiddo kuxin da ya sunne cikin babbar rigar shi ya ajiye a gefen Abun. “Ki kaiwa Inna”. Ta kalli tudun kuxin kafin ta mai da kallon nata gare shi ta ce, “Ba ka ce Kawun ka ya hanaka yi musu aike ba?” Bai amsa ba. Ta buxe ledar da kuxin ke ciki ta ce, “To na mene ne, me za ta yi da shi? Ko kuwa na sayayyar ne?” “Bana son sayayya Abu, ki kai mata ki kuma ba ta haquri kan rashin zuwana, na roqeta ta yafe min”. Tausayinshi ya kamata. Ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ubangiji ya yi maka albarka, ya rufa maka asiri ya kuma azurtaku kai da ita da samun zuriya xayyaba”. Daxi ya kama Mus’ab, sai dai bai ya cewa komai ba, sai a zuciyarshi ne ya amsa amin xin. Ya sake miqa mata wasu. “Na waye su kuma?” Ya ce, “Naki ne Abu, ki sha fura”. Ta yi murmushi ta ce, “Har da zuma da kaji. To ina na baban ka?” “Sai da na je wajen shi a kasuwa kafin na zo nan”. Ta ce, “To madalla”. Ta shiga qara yi mishi addu’o’in da ta saba yana cewa “Amin”. Ta biyo shi don rakiya tana cewa, “To baka faxi yaushe zamu sa rai da kai ba”. Ya ce, “Abu kenan, mata fa zan tafi in bari ai kema kin san ba wani daxewa zan yi ba”. “To ba Kawunka ya ce ka tafi ka mance dasu ba?” Ya yi murmushi ya ce, “To zan iya ne?’ MUS’AB YA ISA AJAKUTA Mus’ab ya koma Ajakuta, bayan komawar Sani da daxewa, don haka tuni labarin yin auren nashi ya bazu a ko’ina. Tarba mai yawa da girmamawa ya samu a wurin abokan harkoki daban-daban, abokan arziki na wurin aiki, da na sha’anin gari sun shirya mishi liyafar taya shi murnar auren nashi. Su ma abokan bariki ba a barsu a baya ba, sunyi mishi irin nasu shirin. Kwananshi uku da komawa Jennifer ta isa gidan nashi a dalilin labarin dawowar shi da ta ji. “Oh Darling!” Ya faxi hakan dai-dai lokacin da suka haxa ido. Ta qara xaure fuska sosai nuna alamar ba wasa ya kaita ba. “Kar ka sake Darling ya fita daga bakinka, kar kaa nemi ka mai dani qaramar yarinya, maciyin amana kawai”. Ta ja tsaki ta sake galla mishi harara kafin ta ce, “Wai ka yi aure? Imgine. Uh-uhm! Ko wace ‘yar iskar ka samu ka aura?” Mus’ab ya kalleta cikin murmushi da nutsuwa ya ce mata, “Ba ‘yar iska ba ce, Jennifer da za iya auren ‘yar iska ai da ke na aura. Yarinya ce mai asali da tarbiya wacce mutunci, zumunci da kawaici irin na iyayenmu yasa na sameta, in ban da haka da iya shegen da kuka koya min a bariki yasa na rasata. To sai na yi sa’a iyayenmu mutanen kirki ne, zumuncinsu ya kan fiye musu komai, shi yasa na sameta. Yarinya ce ‘yar qarama, don ba ta fi sha bakwai ba”. Ta ja tsaki ta ce, “Mai abin kunya, kai kuma irin lalacewar da ta same ka kenan bin yara ‘yan qanana sa’o’in ‘ya’yan cikinka? Ina tausayin wannan yarinyar da ka je ka baiwa ubanta kuxi ya baka ita”. Ya yi kamar maganar tata ba ta soke shi ba, ya daure ya haxiye sai ya ce mata, “To, quruciya ai ba qarya bane Jennifer, in ka bi mai ita kuma baka yi laifi ba, ba ga shi nima kin manne min ba, ni ina bin wasu ne ai kema kina bina kina dangwala tunda ni dai na san ni ba sa’anki bane kin girmeni”. A fusace qwarai ta ce mishi, “Haihuwar ka na yi ba girma ba”. Sani dake gefe yana jinsu ya yi qoqarin danne dariyarshi, ya yin da Mus’ab ya ci gaba da magana. “Ai ya riga ya bayyana kin san in ya riga ya zo shaf-shaf bai voye shi”. Ta ce, “Eh, ai na ce kai na haifa”. “A’a, ni kam ai kin yi kaxan ko in ce baki isa ba, ni ai masu mutunci ne suka haifan, gamuwa daku ne ya yi sanadin da na zama haka. Amma mai shekaru irin nawa dai kam talatin da biyar na san ba za ki rasa shi ba a qauye an barwa iyaye”. “Kai Mus’ab wai meye haka ne? Ina laifin Jennifer da ta zo gidan nan ta nuna kishinta kan auren da ka yi, ai qauna ce ta kawo hakan. Maimakon kawai ka ba ta haquri ka yi mata alqawarin auren naka ba zai kawo qarshen mu’amalar dake tsakaninku ba?” Ta yi maza ta ce, “Qyale shi kawai Sani, laifina ne da na zo gidanshi, ba ya yi aure ba? Ai gara ya wulaqantani, ni dai na san auren shirme ya yi don babu inda zai je, biki ne kawai don ba za ka tava daina neman mata ba ya riga ya zama jinin jikinka haka za ka mutu”. “A’a-a’a!” Sani ya tsoma baki. “Ke Jennifer…..” Kafin ya yi magana sai Mus’ab ya ce mata, “Eh, na ji ba zan daina neman mata ba, to amma ai zan iya daina neman tsofaffi ko in koma neman yara sa’o’in matata, ai na samu ci gaba idan na yi hakan”. Mus’ab ya ci gaba da harkokinshi na sharholiya kamar yanda dama ya saba. ‘Yammata sai wacce ya zava, ita kanta Jennifer da suka yiwa juna cin mutunci sun sake shiryawa, suka mannewa juna har ta dawo gidaan shi da kwana. Sai dai hakan bai hana shi yin wasu ‘yammatan baa, sai dai baya kawo su gida ya kan yi harkokinshi ne in ya fita yawon shi na qa’ida. A garin Misau kuwa, fiye da wata guda ne da tafiyar Mus’ab ko waya baya yiwa Saddiqa balle wani aike. Inna Habiba ta rasa inda za ta vullowa al’amarin. “An xauki auren yarinya an ba shi ya tafi ya yi banza da ita, rabon da ya xauke qafa zuwa gida haka ai an daxe. To ya samu yanda yake so an damqa mishi auren da bai san darajarshi ba, shi yasaa na yi ta fatan ya zo gabana in titsiyeshi ya saki auren don kar ya tafi ya barta da auren shi a kanta hakan bai yiwo ba, ba kuma wani ne yaja min wannan vacin ran ba illa Yaya Gixe, ya kuma zuba ido yana kallo ba zai neme shi don a sana bin da ake ciki ba, babu kuma wanda ya san ranar dawowar shi”. “Assalamu alaikum”. Muryar da ta yi sallama daga cikin zauren ita ce ta yi dalilin katsewar tunanin zucin nata tare da haifar mata da faxuwar gaba. Cikin nutsuwa ta kalli Saddiqa da suke zaune tare tana zanen lallenta, ta ce, “Kamar muryar Yaaya Gixe?” Da sauri Saddiqa ta miqe ta fita, ta dawo ta ce, “Ai kuwa dai shine Gwaggo”. Ta yi maza ta shuri tabarma ta nufi zauren don yi mishi shimfixa tana faxin “Yaya sannu da zuwa”. Sai ga Abu ta shigo da xan qunshinta a hannu. Inna Habiba tana gaisheta tana kallon qunshin nata. Ta wuce ta barsu tare da xan’waunta. “Yanzu nan Habiba har yanzu zaman yarinyar nan a gabanki bai isheki ba, kwana wajen arba’in da tafiyar yaron nan amma baki yi tunanin bari ki tura mishi matarshi ba?” “Bai fa damu da auren ba Yaya, don bai san darajarshi ba, dama duk kai kawon da yake yi na a bashin ne kawai, amma tunda aka ba shi ya sake nuna damuwarshi a kanta ne? Sau nawa ina cewa ya zo ya qi?” “Ai ya san halinki ne, ya san in ya zo gabanki ba za ki yi mishi adalci ba. Yanzu zuwa na yi ki gaya min me kike ciki?” “To yanzu dai ina wani adashi ne nake son in xauka sai in yi mata tata sayayyar”. “To gaskiya sai dai in kin xaukan ki aike musu da abin da za ki aike musu, amma yau za ta kwana gidan Mus’abu da yardar Ubangiji”. Kafin ta san abin da za ta ce mishi sai ga mota peogeout ta yi parking a qofar gidan. Adamu ya fito daga ciki alamar shi ya zo da direban. “Shiga ki fito da ita ga mota nan da na tura Adamu ya yiwo shatarta don ta kai su ita da Inna ta yi mata rakiya”. Nan take ta soma kuka tana faxin “Wannan haxi da ka yi fa bai haxu ba, kai ma ka san wannan yaron kama fi kowa sanin shi, ka kuma fi kowa sanin bai bar komai ba cikin halayenshi sai ma abin da ya qaru kan abin da ka sani”. “Ni ban san wani hali nashi ba ke kika snai, ki ba da matarshi a kai mishi kawai”. Ta ce, “To gaskiya a bari ya zo nan tukunna don a sa shi yaje ya yi irin gwajin nan da ake yi na zamani a tabbatar da lafiyar shi”. Kawu Gixe ya miqe tsaye yaa ce, “Haba Habiba kar ki vata min rai mana, kina kallo mutane suna tsaye suna jira, wurin nan kuma ba nan kusa bane”. Inna Habiba ta shiga cikin gida, Saddiqa da take zaune tana adon lallentaa ba ta san me ke faruwa ba, ta ga Gwaggonta tana kuka, ta yi maza ta ture abin lallen ta shiga tambayarta menene ya faru Gwaggo? Abu ta ce, “To in kina da abin da za ki yi gaya mata”. “Fitina ce kawai Yaya yake nema ya jefamu a ciki ya kuma zama xan kallo in ta same mu, ban tava ganin…..” Abu ta yi maza ta katseta ta hanyar jawo qaton zaninta mai girman yadi uku dake rataye ta lulluvawa Saddiqa ta kama hannunta tana ja ta yi waje da ita. Kawu Gixe dake tsaye yana jiran fitowarsu yana ganinsu ya sanya su cikin motar, ya kuma sallami direban suka kama hanyar tafiya suka tafi. Kusan awa uku da soma tafiyar tasu Saddiqa ba ta daina kuka ba, tun kukan bai damu Abu ba tana goga goronta tana watsawa a baki tana taunawa cikin nishaxi, har dai abin ya gundureta ta shiga yi mata faxa, har ta gaji da faxan ba ta daina kukan ba, sai kuma ta shiga rarrashinta. Babu abin da ya fi komai vatawa Saddiqa rai irin ranar xaurin aurenta aka sa Gwaggonta kuka, yau ma da za a kaita gidan miji akaa fito da ita aka barta tana kuka. To ita kuwa wane daxi auren Yaya Mus’ab zai yi mata? Abu ta shiga hira da direban motar. “Kai wannan gari da nisa yake”. Ya ce, “Eh, Baba ai Nigeria qasa ce mai faxin gaske, ga albarka da Ubangiji ya zuba a cikinta na arzikin qasa, illa iyaka dai bamu yi dacen shugabanni masu tausayin talakawansu ba”. Abu ta ce, “Shugabannin yanzu kam ai sai sha’ani, tausayin talakawa sai su Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, su kam duk abin da suka yi don talaka suka yi shi, Ubangiji ya gafarta musu”. Direba ya ce, “Amin Baba”. Suna cikin hirar ta waiwaya wai ta ga halin da Saddiqa ke ciki don ta ji ta yi shiru, sai kawai ta ga bacci ya xauke ta. Ta cewa direban “Tunda wannan ta yi bacci, to bari nima in tava, in lokacin sallah ya yi dai sai ka tsaya muyi”. Ya ce, “To”. Wajen sha xaya da rabi na dare suka shiga garin Ajakuta, a lokacin nan daga Abu tsohuwa har Saddiqa mai quruciyar babu wanda bai galabaita ba. Kasancewar direban tsohon direba da ya saba zuwa Ajakuta, basu wahala ba wajen neman unguwa da gidan da Mus’ab yake ba, saboda gamsasshen kwatance da kuma kajin da Kawu Gixe ya ba shi. Suna tsaye a qofar gidan dai-dai lokacin da Abu ke magana kan hadarin da ya taso. “Nan ne Baba, ina ganin ga gidan can”. Ta bi can xin da kallo tare da faxin, “To ai gara ka je ka qwanqwasa musu qofar tun ruwan nan bai sauko ya tsinke ba”. Ya ce, “To”. Ya fita daga cikin motar riqe da katin a hannunshi don qara tantancewa. Sai da ya qara tabbatar da lambon sannan ya shiga qwanqwasa gidan har aka fito, sai dai savanin yanda ya yi zato maimakon ganin namiji tunda a hirar da suka yi da Abu ta gaya mishi jikanta ne da ya tsufa bai yi aure ba yau za ta kai mishi matarshi. Mace ya gani a tsaye cikin shigar mutanen garin. “To, bana jin Turanci, amma bari in kira su ko su suna ji ku yi dasu”. Ya gayawa matar da ta fito xin bai kuma tsaya ba ya juya ya nufo wurin su. Abu ita kuma ta bishi da kallo ba tare da ta san abin da ya gaya mata ba. Ya isa jikin motar dai-dai lokacin da iska ta taso mai haxe da ruwan sama da feshi a ciki. “Ai sai ku fito”. Su Abu suk biyo bayanshi har suka haura barandar gidan tana tsaye tana kallon su. “Ke Saddiqa yi mata Turanci ki tambayeta ina yake?” Abu ce mai wannan umarnin. Saddiqa ta ji kamar ba ta ji ba, cikin zuciyarta tana tunanin maganar Gwaggo, ta tabbagar manemin mata ne na qarshe, ina jiye miki ranar da za ki ganshi da wata!’ Kalmar Gwaggonta ta tuna. Nan take wasu sabbin hawayen suka soma zubo mata. Abu ta gaji da jiran Saddiqa ta yiwa Jennifer magana ta juya ta kalleta ta soma yi mata magana tare da kwatancen Mus’abu muke nema, nice kakarshi Abu. Ta nuna qirjinta da hannunta, kafin ta nuna Saddiqa ta ce, “Wannan kuma matarsa ce, an ce nan ne gidanshi, ina yaje na ganki a ciki?’ Ko da Jennifer ba ta jin Hausa ta gane wannan matsanancin kwatance da Abu ta yi mata. Nan take zuciyarta ta hautsine kishi mai tsanani ya lulluve ta, ta yi matuqar kaxuwa da ganin Saddiqa, wannan ce yarinyar da ya aura? Cikin ranta ta tabbatar ta haife ta, in za ta yiwa kanta adalci ma ta san ta haifi wacce ta fita. “Wurin Mus’abu muka zo”. Abu ta sake nanata mata. “Come in”. Ta faxi dai-dai lokacin da ta ja baya don basu hanyar shiga, suna shirin shiga direba ya fara yi musu sallama. “To da safe za ka zo ne”. Ya ce, “A’a, ai an riga an biyani zan yi sammako kawai in xauki hanyar komawa gida, Ubangiji ya sanya alheri”. Ta ce, “Amin”. Suka yi sallama ya tafi. Abu da Saddiqa suna zaune cikin haxaxxun falon gidan sai rarraba ido Abu ke yi, cikin hanzari ta cewa Saddiqa. “Ba shakka gidan ne, don ga hoton shi can”. Saddiqa ta yi kamar ba ta jita ba, a zuciyarta ta ce, “Sai yanzu kika gani kenan”. Abu ta saake buxa baki, “Wai ina Mus’abun yaake ne?” Ta sake yin wata tambayar saboda ganin Jennifer da ta yi ta fito za ta shiga wani wurin. Jennifer ta fahimci tambayar ta juya tana yi mata bayani cikin Turanci tare da nuna mata agogo. “Yanzu sha biyu da rabi ne na dare lokacin dawowar shi gida bai yi ba tukunna yana can club inda zai sha barasarshi, wataqila in kun yi sa’a ya dawo zuwa ukun dare, in kuma ya gaamu da wata ‘yar iskar a can to sai gobe in ya taso daga office ya dawo gida”. Ta wuce ta shiga xakin da take nufin shigar. Abu ta kalli Saddiqa da tuni hawaye ke zuba a idonta ta ce, “Me kenan ta ce?” Ta yi shiru ba ta tanka ba. Haushinta ya kama ta, ta ce, “In dai kin kasa jin wannan cakwalkwalallen Turancin da matar nan ke yi to zirga-zirgar bokon naki bai magunta ba, don ko ni xin nan inda zan kasa kunne da kyau zan ji abin da take faxi. Me ta ce?” Ta qi tankawa. Ta vata rai ta ce, “Ai sai ki yi ta yi, ana tambayarki kin yi shiru kin qi ki cewa mutaane komai”. Jennifer ta dawo falon xauke da tiren gasassun kaji guda biyu, sai kuma manyan dogayen kwalabe su ma guda biyu, ga kuma kofunan tangaran masu dogayen mariqai su ma guda biyu. Abu ta miqa hannu ta sunkuto kwalbar ta miqawa Saddiqa ta ce, “Sa qarfin quruciyarki ki buxe kwalbar da mai ruwa-ruwa zan fara”. Saddiqa tana kallon kwalbar ta qwala ihu ta ce, “Yarda kwalbar Abu barasa ce”. Abu ta kixime, maimakon ta yar sai ta jefar, kwalbar ta daki teburin gilashin da ke falon ta fashe. Nan take warinta ya mamaye ko ina, da gudu Saddiqa da Abu suka yi waje suna faman kwara amai. Sunyi tsumu sun takura waje xaya jikin bango saboda matsanancin ruwan saman da ake kwarawa kamar da bakin kwarya. Jimawa can suka hango fitilar wata mota ta haske gidan, ta kuma nufo su. Sai da ta zo jikin matakalar hawa barandar sannan ta ja ta tsaya. Mus’ab ya fito daga cikin motar da karan sigarinshi a bakinshi, cikin sauri ya hayo matakalar zuwa barandar alamar shima bai son ruwan ya jiqa shi. Walqiya ta haske wurin dai-dai lokacin da tsawa gami da aradu suka mamaye duniya. Hankalinshi ya kawo kan tsugunon da ya hanga, hakan ya sa shi jin maqyarqyatar da ake yi. “Su waye a nan?” Ya yi tambayar daidai lokacin da ya kai hannu ya kunna fitilar da ya tarar a kashe haske ya bayyana. Abu ce mai maqyarqyatar, rawar sanyi take yi. Ya zuba musu ido yana kallon su tamkar bai taba ganinsu ba, cikin wani irin yanayi na tsoro, fargaba gami da razana mai tsanani. Ina ma dai a ce mafarki yake yi. Da qyar ya iya buxa baki ya ce, “Abu ce?” Cikin rawar sanyi ta ce mishi, “Eh, sannu”. Kamar a ce yana da layar zana ya vace, ko kuma ya yanka da gudu ya shiga jerin dake bayansu ya yi tafiyarshi. Babu hali sun rigaa sun ganshi ba kuma zai yiwu ya gudu ya barsu cikin halin da ya same sun ba. Ya daure ya ce, “Ya ya za ku zo ku tsuguna a nan Abu, ku tashi mu shiga cikin gida mana”. Abu ta ce, “A’a”. “Haba Abu, ku yi haquri”. Ya sunkuyo tare da matsowa ya tsuguna a kusa dasu yana rarrashi, hayaqin sigarin dake hannunshi da hatsaniyar barasar da ya kwankwaxa da ba ta rabu da shi ba suka haxu suka tayar da hankalin Saddiqa, ta sake kwaro wani aman. Ya yi maza ya ja da baya tare da wurgar da guntun sigarin dake haannunshi. Ya miqe ya shiga cikin gidan, karon da ya yi da kwalbar barasa a fashe ga kuma kaji a kan tire ya qara faxar mishi da gaba. “Kar dai barasa Jennifer ta basu?” Ya yiwa kanshi tambayar cikin rawar jiki. Da sauri ya nufi cikin xakin nashi, tana kwance tsirara daga ita sai xan kamfai wai tana shan iska. “Wane ne ya yi ta’adin da na gani a falo Jennifer?’ Ta yi kamar ba ta jishi ba, ta yi lamo tamkar tana barci. Sai da ta ji ya xaxa mata duka ya shige ta sannan ta yi zumbur ta miqe zaune. “Ina jin wannan tsohuwar ce”. Jikinshi ya kamarawa. “Kakata kika kaiwa giya ta sha Jennifer?’ Ya zuba mata ido cikin matsanancin baqin ciki. A yatsine ta ce mishi, “To mene ne, ba da shi kake saukar baqinka ba a gidanka?” Yasa hannu ya xauke ta da mari yana zaton zai kwashe qalau kamar yanda ya saba kwashewa, har ma a ba shi haquri. Sai kawai ya ga tasa hannu biyu ta cakumoshi alamar dama ta shirya mishi, abin da ya haddasa Mus’ab rufe ta da duka mai tsanani ta shiga ihu tana kururuwa tare da ruwan ashar, a hakan kuma duk abin da ta raruma sai ta yi wurgi da shi wai ta same shi ko ta yi mishi wani ta’adin. Rigima mai tsanani ya kaure, ihunta ya qara tsananta. Su Abu suka yi matuqar tsorata, maimakon tsuguno suka koma tsayawa suna tunanin inda za su nufa cikin tsohon daren da ake tsuga ruwan sama kamar da bakin qwarya. Sani ma ya iso ya yi parking a qofar gidan da sauri ya fito ya nufi shiga cikin gidan don yin rabo. “Kai Mus’ab baya jin shawara ya sake kawowa matar naan wata matar kenan”. Ya yi kamar ya haxiye maganar tashi da ya yi a bayyane ya mai da ita cikinshi ta zama bai yi ba, saboda ganin da ya yiwa su Abu a tsaitsaye. “Abu! Abin mamaki, kune a gidan namu? Ai sai ku zo mu shiga wancan sashin”. Ta ce, “A’a, shiga dai nan ka yi rabo don kar ayi kisan kai”. Da gudu ya shige ciki gidan, sai ga shi ya fito da Jennifer daga ita sai tawul xin da shine ya xaura mata. Ya yi maza ya jefata a motar da ya zo a ciki ya juya ya koma inda ya fito. ‘Yan mintina kaxan sai ga Mus’ab ya fito daga cikin gidan tsab da shi, kuma cikin nutsuwa tamkar dai ba da shi aka yi wannaan ba ta kashin ba”. “Ku shigo daga ciki Abu”. “Kul! Kar ka sake cewa in shiga gidanka”. Tana magana tana vari saboda sanyin dake kaxata. “To muje in samar muku hotel don ku samu wurin kwanciya”. Kalmar sama musu hotel xin ta sata fashewa da kuka tare da salati. “Ni da nake neman cikawa da imani me zai kai ni kwana a hotel”. Nan take ya gane kuskuren da ya yi wajen faxin hakan da ya yi, ya koma ba ta haquri. “To faxi inda kuke so in kai ku Abu, amma saboda girman Ubangiji kar ki ce za ku kwana a nan a wannan halin da kike ciki”. Magiyar da ya yi ta sanyata buxe baki ta ce mishi, “Kai mu gidan liman”. Ya xan yi nazari kaxan kafin ya ce mata, “Nan inda muke muna wajen gari ne Abu, liman kuma yana zaune cikin gari, don haka ki yi haquri ga jikan liman ina maqwabtaka da shi mutumin kirki ne yana kuma tare da iyalinshi, muje in kai ku can gidanshi”. Ta ce, “To”. Gidan Idris gida ne da komai nashi irin na Mus’ab ne, kasancewar su dukansu ma’aikatan Steel Rolling xin ne, bai da nisa sun kuma daxe suna maqwabtaka mai daxi. Sai da suka buga qofar gidan sosai kafin aka zo aka buxe. Yana ganinsu ya basu izinin shiga falon. “Sannun ku da zuwa”. Sai da ya yi gaisuwar kafin ya waiwaya ya kalli Mus’ab. “Kar dai a ce baqin amare muka yi cikin daren nan?” Ya ce, “Eh, sune”. Ya sake wani murmushin. “Hala uwargida ce da amarya?” “Eh, sune”. Mus’ab ya sake amsawa. Sai dai qarfin hali kawai yake yi yake ba shi amsar, shi kaxai ya san yanda zuciyarshi take. “Abida ai sai ki fito ga baqin amare kin yi”. “Ayya! Da ka barta ta yi baccinta wuri kawai za ka bamu mu xan miqe, don jikinmu ya yi tsami da yawa”. In ji Abu. Bai saurara ba ya shiga ya tasota suka fito tare. Kyakkyawar yarinya mai matsakaicin tsawo wankan tarwaxa, mai yalwataccen gashin kai. Sanye da kayan bacci tana muttsuke ido tana fara’a saboda ganin baqi. “Sannunku da zuwa”. Ta faxi cikin murmushi. “A’a, lallai amarya ce ta yi mana saukar dare cikin ruwa?” Abu ta ce, “Cikin ruwa fa kam gamu nan jage-jage”. Daga cikin xakin da ta fito yaro ya qwalla qara ta yi maza ta shiga ta xauko shi za ta baiwa Idris shi, Abu tasa hannu ta karve shi tana cewa, “Dama da babban mutum ne a gidan?” Mus’ab ya ce, “Eh, mai sunan liman ne Umar”. Ta yamutsa fuska jin ya tsoma baki cikin maganarta. Abida ta sake fitowa tana murmushi. “To ga gajiya ga yunwa da wanne za a fara, wanka ko cin abinci?” Abu ta ce, “Da wurin kwanciya kika bamu muka kwanta kawai”. Ta yi murmushi ta ce, “Ai yanzu huxu da rabi ne na asuba, gara kawai ku yi haquri in mun yi sallar asuba sai ku kwanta ku huta”. “To bamu ruwan mu yi wanka don yarinyar nan ma ta xan ji daxin jikinta, ta wahala ta yi amai yau har ta gaji, a jigace take, ga shi ko kaya ba ayi dabara an zo mata da shi ba, to ba a san abin da za a zo a tarar ba kenan na vacin rai da tashin hankali, yanda mace ba ta yi sa’ar miji ba ta gamu da matsala”. Abida ta bita da kallo ta ce, “Amma a haka Baba ai kin fita alamar jigatar”. Mus’ab da ya san da shi Abu take yi ya cewa Idris, “Bari in shiga gida ina zuwa”. Ya ce mishi, “To, a fito lafiya”. Da sauri ya fita Kafin Saddiqa ta fito daga wanka har ya dawo, ya zo ya miqawa Idris leda mai xauke da sabbin riguna guda biyu dogaye da aka yiwa xinki mai kyau a jikin asalin galila, ga ‘yan kwalayensu da gyalensu, under wear da qananan ‘yan kunnaye. Ya miqawa matarshi ita ma ta kai wa Saddiqa dake shafa, tasa hannu biyu ta karva ta saka cikin murna da farin ciki, saboda ba ta san daga inda suke ba. Ana idar da sallar asuba Abida ta kewaye su Abu da nau’’o’in abinci iri-iri na ci da na sha, ga shi dama ta iya girki, ta tsara su ta tsara shi ta yanda ko baka jin yunwa sha’awa zai sa ka ci. To balle su Abu da suka wahala wajen tafiya suka iso ba su ci komai ba, suka kuma kwana suna kwara amai. Sai da suka ci suka qoshi har Abu tana cewa a kunna mata fanka sai ga Abida ta sake shigowa da wani kwanon abincin za ta ajiye kusa da Abun, ta yi maza ta ce mata. “Ke ‘yar nan in dai ba so kike mu ci sai mun kasa tashi ba gara ki barmu haka”. Abida ta yi murmushi ta ce, “Ba za ku kasa tashi ba ai babu wani abu mai nauyi cikin abin da kuka cin”. Abu ta ce, “Ba zamu sake cin komai ba”. An xan jima kaxan Abida ta ce, “To ai sai muje ku kwanta ku huta”. Abu ta ce, “A’a, mu yanzu mota kawai za a kawo mana ta xebe mu ta mai damu inda muka fito”. Idris da tuni ya gane akwai matsala tsakaninsu da Mus’ab, ya ce mata, “To ku xan miqe mana kafin in je in zo muku da motar”. Ta ce mishi, “To”. Saboda mutuncinshi da na matarshi da ta gani. Suna kwanciya kuwa bacci ya yi maza ya xauke su, basu sake sanin abin da ake yi ba. Mus’ab yana tare da Idris yana ba shi labarin abin da ya faru, bai voye mishi komai ba. Idris ya kalle shi cikin vacin rai da nadama ya ce, “Yanzu wannan abin da me ya yi kama? Ni dama ina kallonka ne tare da mamakin wannan rayuwar da kake yi, saboda daga ganinka sai a gane kai xin mutum ne mai asali da ya fito daga wuri na mutunci, amma ka zo ka biyewa wannan sharholiya. Yanzu ina alherin wannan abin da ya faru? Me za ka cewa wannan yarinyar?” Suka xan yi shiru. Jimawa kaxan ya yi tsaki ya ce, “Kai da aka yiwa gata da irin wannan lafiyayyar yarinyar me za ka yi da waxannan da kake kwasa masu gashin doki a ka?” Mus’ab ya ce, “Uhm! Don ma baka san artabun da aka yi da mahaifiyata ba kafin aka bani ita”. Idris ya sake wnai tsakin ya kawar da maganar ta hanyar qwalawa matarshi kira. Ta amsa da “Na’am, gani nan zuwa, minti biyu. Ta iso kafin cikar minti biyun da ta ambata cikin kwalliya da qamsohi, tana goye da xansu dake ta miqe-miqe nuna alamar bai son goyon. Hannunta kuma xauke da tiren abincin da ta shiryo musu ta ajiye a gabanshi. “In zanin ya kwance ya faxi fa Abida?” Ta ce, “Sai ya ji da shi”. Ta faxa daidai ta kwanto shi za ta ajiye mishi shi, ganin irin kallon da ya yi mata yasa ta yin murmushi tare da faxin “To ka yi haquri”. Ta samu wuri ta xan zauna tare da sauraron abin da yake gaya mata. “Babu zuwa cikin gari yau”. Ta yi murmushi ta ce, “Na sani ai tunda muna da baqi”. Ya sake cewa, “To muna da ‘yar matsala tare da baqin namu”. Ta sake cewa “Na gane, don na ji Abu tana cewa Aisha gaskiyar uwarta ne da ta cewa fitina kawai aka xauko mata, don haka ba za ta barta cikin fitinar ba za ta tasa ta a gaba ta mayarwa uwarta da ita”. Gaban Mus’ab ya sake faxuwa. Idris ya cewa matarshi “To a irin hikimarku ta mata ki san yanda za ki yi ki rarrasar mana su mana, musamman Abu ta yi haquri”. Ya miqa hannu ya jawo musu tiren abinci ita kuma ta miqe ta shiga ciki. Wajen sha biyu da rabi na ranar ne Abu ta farka cikin salati da miqa, tana buxe ido ta xaxawa Saddiqa duka. “Ke tashi sakarya mara zuciya, kin kwanta kin saki jiki kin hangame baki kina ta yin bacci sai ka ce ba da vacin rai kika kwanta ba”. Saddiqa ta ce, “Kai Avbu kenan, sai ka ce ba tare muka yi baccin ba”. “Tashi ni mu shirya mu tafi”. Saddiqa ta yi maza ta miqe. “Fita ki tambayi matar gidan ko an kawo mana motar?” Ta fita tana magana da Abida, ita kuwa sai kallon Saddiqa take yi cikin sha’awa. Gasu nan dai a falo yanzu suka dawo bari in tambayesu. Ta ce, “To”. Ta koma xaki tana yiwa Abu bayani, ita kuma Abida ta nufi falon mijinta ta gaya musu tambayar da Abu ke yi. A hankali Mus’ab ya buxaa baki ya ce, “Xan kira mana ita Abun”. Ta ce, “To”. Ta tafi. Idris da Sani suka gaisheta ta amsa, ta qi amsa ta Mus’ab. “Haba Abu, ai tamu dake ba ta vaci, muna ‘yar haka dake ne? Ai Aisha ce ya kamata ta yi fushi dani, ke kuma sai ki haxamu ki yi mana faxa ki sasantamu ki ce mu zauna lafiya, tunda na saba jinki kina cewa shi aure sasanta shi ake yi ba lalatawa ba”. Da sauri ta ce, “Ba irin naka auren ba, ai kaimaa baka nufin yinshi, mai nufin yin aure ba zai yi wannan abin da kake yi ba, tunda dai duniya ka tasa a gaba ai sai ka je ka yi ta yi, amma Saddiqa kam zan mayarwa uwarta da ita, don suna kuka aka raba su ta kuma roqeni in har na ga ba daidai ba kar in bar Saddiqa don ba za ta iya da kai ba”. Sani ya yi murmushi ya ce, “Haba Abu…..” Kan ya yi maganar da zai yi ta yi maza ta kwave shi, ta ce, “Kul! Kar ka ce za ka ce min komai, ina ce ku dukanku iya shegen kuka tasa a gaba, ai ina ganin lokacin da ka dawo. To ko varawo ne ya dawo gidanshi a wannan lokacin ai yaa isa lalaataccen varawo”. Idris ya ce, “Gaskiyaa ne Abu, ita wannan rayuwar ai ba rayuwa ba ce, yaushe za a haxa matan bariki da matan da kuka bamu?” Abu ta ji daxin zancen shi, ta saki jiki suka yi ta hira. Ta kwashe bayani duk ta yi mishi, tun daga ranar da Mus’ab ya zo gidanta da zancen neman auren Saddiqa, har kawo barowarsu gida jiya da abin da ta zo ta tarar a nashi gidan, wanda idonsu ya ganar musu ba ta rage komai ba sai da ta gaya mishi. Cikin nutsuwaa ya ce mata, “Ya gayaa min Abu, saboda shima ya san bai kyauta a. to amma kuma abin da ya yin bai kai na ki tafi mishi da maatarshi ba, ki yi haquri”. Ta yi maza ta ce, “A’a, abin da ya kamaceni kenan in yi adalci a tsakaninsu, ba za ta iya da shi ba ya fi qarfinta, baqin ciki kawai zai yi ta qunsa mata, yarinya ce ‘yar qarama”. Idris ya ce, “Na ganta ai”. Ta yi maza ta ce, “Yauwa, to wannan randa ya ce zai yi mata irin dukan da na ga ya yiwa wata jiya ai falle-falle za a xauke ta. Amma da yake ita wancan xin mai qoqari ce sai na ga ta fito da qafarta tinqis-tinqis har tana iya magana”. “To amma Abu”……. Abun ta yi maza ta kalli Mus’ab ta ce, “Kai kar fa ka ce za ka rinqa tsoma min baki”. Ya yi maza ya yi shiru. Idris ya ce, “To ki yi min wata alfarmaa mana”. Abu ta ce, “Ta mene ne in ji in zan iya”. A hankali ya ce, “Za ki iya, so nake ki bar maganar tafiya a yau ki haqura har zuwa jibi, ke da kanki kin ce yarinyar nan a jigace take, ke kanki ba ta fiki jigata ba. To ku xan hutaa mana kafin ku tafi”. Ta ce, “To sai dai gobe, amma jibi kam ya yi yawa”. Ya ce, “To na gode, Ubangiji ya saka da alheri”. Ta ce, “Amin”. Da yamma Abida tana aikin abincin dare, ta bari ta leqa xakin da su Abu suke ta kira Saddiqa. “Aisha ko za ki fito ki xan taimaka min ne?” Cikin sauri ta tashi ta fito suka shiga kicin xin tare suna aikin tare da hirar da Abida ce mai kawo zancen, ita amsa ne kawai nata shima a taqaice. Zirga-zirgar Umar ta dame su, Saddiqa tasa hannu ta xauke shi ta goya shi suka ci gaba da aikinsu. Idris ya shigo kicin xin riqe da ledar yankakkun kaji, Abida ta karva tana yi mishi sannu. Ya yi murmushi ya ce, “Amaryar kike sawa aiki? To bari in kira angonta ya ganta”. Saddiqa tana jin haka ta yi maza ta bar kicin xin ta xauka da gaske kiran nashi zai yi. Abida ta ce, “To ai sai ka shigo ka tayani tunda ka korar min ita”. “Haba Abida, ai sai Abu ta ce yanda kika ga damaa kike juyani”. Abu dake kusa bai sani ba ta yi maza ta ce, “Ai gara maka haka, a juya kan da wannan tanbaxa da su Mus’ab suke yi”. Da daddare bayan cin abinci Mus’ab da Idris suna tare da Abu, saqarta take yi tare da sauraron bayanin nasu. “Haba Abu, ki taimaakeni mana irin taimakon da na saba ganin kina yi min, kar ki tafi min da Aisha ki yi haquri ki samu kwanaki biyar zuwa bakwai don ki rarrasar min ita. Shi Kawuna da ya ce zai kawo min ita ai bai ce miki in kinga ba daidai baa ki mai da ita, ke kin san ba zan cuceta ba, don kin fi kowa sanin ina sonta, don haka ki taimakeni ki rufa min asiri”. Ta harare shi ta ce, “In yi qarya kenan?” Idris ya karve da cewa, “Ba qarya bane Abu gyara ne, ai kinga ni bana goyon bayan abin da yake yi, zan sa miki ido a kan zaman ina ganin ba daidai ba ko somi-somin wulaqanci zan sata a mota in kawo miki ita har gida Misau, don ba ta cancanci ganin irin wannan baqin cikin ba”. Abu ta yi shiru cikin nazari, zuwa can ta ce mishi, “Kai a’a, ba zan iya barinta ba, na kuma roqeka kaima kamar yanda ka ce min in yi maka alfarma in qara kwana, to nima ka yi min alfarma ka kawo min motar da za ta mai damu gida gobe”. Da sauri ya ce mata, “Cikin yardar Ubangiji zan kawo muku”. Ta ce, “To, na gode”. Ta miqe ta shiga ciki ta barsu a nan. Ya kalli Mus’ab cikin nutsuwa ya ce mishi, “In har baka samu wata hanya ta hanasu tafiya ba zan ba da motar da za ta mai dasu, saboda ba zan yarda in vata mata ba, saboda tsohuwa ce mai mutunci da addini”. Mus’ab ya yi shiru sai dai hakan bai hanasu ci gaba da tattaunawa ba. Washe gari da asuba daga fitowarsu daga masallaci ya bar unguwar a cikin motarshi, daga Idris har matarshi dama Abun sunyi zaton bai son ganin tafiyarsu ne yasa ya yi hakan. Suna ciki suna shirye-shiryensu na lodin tsarabar da Idris ya yi musu, ga kuma Abida da take ta yi musu girke-girken da wai za su riqe su ci a hanya. Qarfe bakwai da rabi daidai motar da za ta xauke su ta iso aka shiga fitar musu da kaya saboda ba qaramar tsaraba Idris ya yi musu ba. Suna cikin haka sai ga Mus’ab ya iso gidan xauke da limamin babban masallacin garin cikin motarshi, wanda kuma shine kakan Idris. Dattijo mai kimanin shekaru tamanin a duniya, yana riqe da sanda a hannunshi saboda matsalar qafa da yake da ita. Gaba xaya su Idris suka iso wurinshi suna yi mishi sannu da zuwa. “Har baqin namu sunyi harama ne?” Idris ya amsa “Eh, malam ai har sun kammala shiri”. Ya ce, “To ai sai mu xan shiga daga ciki don mu gaisa”. Ya ce, “To”. Ya gayawa Abu ta amince da hakan cikin yanayi na girmamawa. Liman ne kaxai zaune a kan kujera, sauran duka a qasa suke har da Abu suna sauraron shi bayan an gama gaisawar. “Ki yi haquri, ki yi haquri da duk abin da ya yi, mu yi ta addu’a muna roqon Ubangiji ya shirya mana su. Ai abin da ya saura tsakaninmu dasu kenan a yanzu, don haka kar ki tafi mishi da matarshi na roqi wannan alfarmar ina fata za ki yi min ita”. Abu ta gyaxa kai nuna alamar za ta yi tare da faxin “To Allah gafarta malam Ubangiji ya yiwa zuriyarta albarka, ya kuma sa ta gama da duniya lafiya”. Aka ce “Amin”. Sai ya yi tambayar cewa, “Ina yarinyar take?” Abida ta yi maza ta miqe ta shiga ciki ta fito tare da Saddiqa, ta zo ta durqusa ta gaishe shi ya amsa tare da sa mata albarka. Da aka sake nutsuwa sai ya kalli Abu cikin fara’a ya ce, “Kin kawo mishi alheri irin wannan kuma ki ce za ki tafi da shi? Bar mishi ita ai tashi ce, Ubangiji zai daidaita tsakaninsu, mu dai mu yi ta addu’a. in kinga ka dage a kan roqon abu, to kuwa Ubangiji ya yi nufin biya maka buqatarka ne, in ba haka ba, ba ma zai baka ikon ka roqa ba”. Ta sake cewa, “Haka ne”. “Mu yi sallati ga manzon rahama” Liman ya ba da umarni. Nan da nan aka shiga yi, liman ya yi addu’o’i ga ma’auratan dama sauran jama’ar musulmi baki xaya aka shafa. Ya miqe nuna alamar tafiya, Mus’ab ya yi maza ya bishi suka tafi ya mai da shi gida. Abu ta bi bayan Saddiqa zuwa xakin da aka sauke su. “To haka kuma abu ya kasance, wannan dattijo bawan Allah ya zo ya xaure ni da jijiyoyin jikina babu yanda zan yi in yi musu da shi, da dai na san wani yaje xaukowa ai da sammako muka yi muka tafi”. Saddiqa tasa hannu ta share hawayen kukan da take yi. Ta kalli Abu cikin nutsuwa ta ce mata, “Dama shi kike jira, ai tunda kike cewa ya gudu don bai son ganin tafiyarmu na ce miki ba zai gudu ba wani abin yaje yi mu hanzarta tafiya kawai kika qi, kika ce mu tsaya jiran girke-girken da ba ci kike ba. Dama ni Gwaggona ta gaya min cewa babu wanda kike so a cikin jikokinki sai shi”. Ta kama kuka sosai. Abu ta kama salati tana faxin “Ka ji ja’irar yarinya, kamun bakin da za ki yi min kenan? Yanzu a wannan zuwan da na yi me na yi na son Mus’abu? To ban fi son shi ba, gaya min yanda kike so in yi yau na ji”. Ta juya ta fita ta je ta yi alwala ta soma gabatar da sallar walaha saboda sallamar da Idris ya ce mata ya yiwa mai motar a qara natsuwa kafin ta tafi. Ta daxe a zaune tana addu’o’o ya yin da Saddiqa ke kwance lamo a kan shimfixarsu, sai aka leqo aka cewa Abu Idris yana son ganin ta a falo. Ta shafa fatiha ta shiga falon, maimakon Idris Mus’ab ta gani a zaune. Yana ganinta ya yi murmushi alamar samun nutsuwa, ita kuma ta yi maza ta tsuke tata fuskar. “Wane ne mai kiran?” A hankali ya ce mata, “Nini Abu”. Kan ta yi magana ya yi maza ya kai gwiwoyinshi qasa ya durqusa a kansu. “Ki yafe min abin da na yi na laifi kike fushi dani, Abu ban saba irin wannan mu’amalar dake ba. Na yi baqin ciki tare da nadamar al’amurana da na sameki a wurin nan, da kuma na gane fushin da kika yi dani mai yawa ne sai na ji tamkar na tozarta kaina ne, na wulaqanta saboda na gane na qure haqurinki a kaina. Sanina dake tun ina yaro duk wanda ya faxi laifina a gabanki korarshi kike yi, ki ce sharri ake yi min aniyar kowa kuma za ta bishi, in kuma iyayena ne suka faxi laifin nawa tunda su kin san ba masu yin sharri bane a gare ni, sai ki shiga yi musu faxa kina faxin wai komai qanqantar abin da na yi ba za su zauna suyi ta yi min addu’a ba, sai su rinqa taya masu neman vatani su yayata qarya a kaina. To amma wai a irin wannan haqurin naki da qaunarki a gareni na qureki, ni wane irin mutum ne Abu?” Abu ta nemi wuri ta zauna saboda hawayen da suka soma zubo mata tana sharewa da bakin zanin dake yafe a jikinta. “Ban sani ba Mus’abu, ni dai na san kullum ina addu’ar Ubangiji ya shiryeka”. Ta soma kuka sosai. Ya qara matsawa kusa da ita yana rarrashinta, har ya samu ya shawo kanta suka fita waje suna xan takawa. “Ga gidana can Abu mu shiga ki ga irin gyaran da ake yiwa Aisha”. Ta yi maza ta ja ta tsaya, “Kai, a’a, wannan gida naka ai ba zan sake shigarshi ba”. “Babu komai a ciki da za ki gani ya vata miki rai, wurin da Sani ya bari nake gyara mata, shi ya koma cikin garin, dama a can yake ni na kira shi ya dawo nan saboda bana son zaman kaxaici”. Ta ce, “A’a, hali dai da ya zo xaya, amma kai ma ai kai kaxai kake zaune ba”. Ya yi shiru ya qi tanka maganar tata. Da yamma suna zaune a falon da ya ce mata shine na Saddiqan, komai na wurin a kammale yake an gyara shi, an sauya duk wani abin da ya kamata a sanya, wuri ya yi matuqar yin kyau, sai mai shi ake jira ta shiga. Mus’ab xin ne yaje ya lallavo Abun ta zo nan suke hira. “Kar ki damu da maganganunta Abu, ba ki yi komai na fifitani a kanta ba, wurin Inna kawai ta ji wannan maganar cewar kin fi sona a kan kowa. Amma in ba haka ba me kika yi mata? Ita da kike ta rarrashinta ma kina ta tarairayarta, ni kuma kina ta fushi dani kina ta zare min ido, ki kawo ta xakinta kawai Abu sai ki yi tafiyarki gida ki gayawa su Inna kin barmu lafiya, in ina tare da ita ba zan barta ta yi ta wahala ba, balle ta je tana zama da yunwa ko xurarta sai in rinqa yi”. Abu ta yi kamar za ta yi murmushi ta kasa saboda halin da Saddiqa ke ciki na yawan kuka da qin cin abinci yasa ba ta jin daxin zuciyarta, ga kalaman da take ta furtawa na wai son da take yiwa Mus’ab ya hanata yi mata adalci, bayan su dukansu biyun jikokinta ne. “Abu!’ Abu ta yi maza ta katse maganar ta shi ta hanyar faxin, “Ni dai abin da nake so in roqeka shine, duk abin da za ta yi maka na vata rai kar ka ce za ka buge ta”. Ya yi maza ya ce, “Haba Abu, Abu ki daina yi min irin wannan maganar, sai in ga kamar kin xaukeni mara hankali”. Da daddare ranar Abida ta yiwa Abu rakiya aka kai Saddiqa gidan mijinta, babu abin da bai tsaru ba, komai ya yi daxi gwanin sha’awa, ta ko’ina sai qamshi kake ji, ga kuma ni’ima. Abida ta yi musu hira har zuwa goman dare, da za ta tafi kuma Mus’ab ya yi mata kyautar leda mai shaqe da turaruka masu tsadar gaske. Tunda aka shigo da Saddiqa gidan ta nemi wuri ta zauna ba ta sake xaga ido ta kalli wani ba, balle ta ji wani abin gidan ya burgeta, balle ta buxe baki ta amsa wata magana da suke yi mata, balle a samu ta yarda ta ci wani abun da ya kewaye su da shi, sun yi rarrashi har sun gaji. Mus’ab yana zaune kan kujerar roba a qofar gidan, duk da daren ya yi nisa sigarinshi yake sha lokacin da Abu ta fito ta same shi. “Na ce ba”. Ya xaga ido ya kalle ta bayan ya wurgar da sigarin dake hannunshi. “Ko za ka haqura ne kawai in tafi da yarinyar nan in yaso daga baya……..” Bai jira jin daga bayan yanda za ayi ba ya ce mata, “A’a, abu ai don kina nan ne yasa hakan, in mu biyu ne daga ni sai ita na san yanda zan yi da ita, don haka zan shirya miki jibi ki tafi gida”. Ta yi maza ta ce, “Gobe dai, me zan zauna in yi kuma har jibi?” Ya ce, “To shi kenan”. Washegari sun idar da sallar asuba Mus’ab yana kicin yana qoqarin shirya musu abin karyawa, Abu ta leqo ta ganshi a hankali ta ce mishi. “Ban fa san yanda aka yi ba sai na ga yarinyar nan ta gaji ta kwanta har bacci ya xauke ta”. A hankali ya ce mata, “Ta wahala da yawa”. Ta tave baki ta ce, “To ni dai zan tafi duk da zuciyata ta qi yarda ta ji daxin barin yarinyar da zan yi, na kuma kasa yin jarumtakar xaukanta in tafi da ita ba tare da yardarka ba, ko kuma zargin da ta yi min xin ne yake nema ya zama gaskiya a kaina na fifitakan oho!” “Ba ni kika fifita ba Abu, aure kika girmama. In ban da darajar tashin ai ba za a baki ita a ce ki kawo min ba. Amma da yardar Ubangiji ba za ki yi nadamar bar min ita da za ki yi ba, saboda ba zan barta ta shaidi komai daga gareni ba sai alheri”. Ta ce, “To, Ubangiji ya shiryaku”. Ya ce, “Amin”. Saddiqa tana ta sharar barcinta lokacin da Mus’ab ya gama shiryawa Abu tafiyarta zuwa gida, tsaraba mai ximbin yawa ya yi mata, ga maqudan kuxaxe da ya ba ta gami da wasiqu zuwa wurin Kawu Gixe da kuma Baban shi. Qarfe bakwai da minti arba’in dai-dai direban ma’aikatarsu ya iso qofr gidan kamar yanda Mus’abu ya yi mishi umarni, su Abida da Idris suka zowa Abu sallama, suna nan ma motar ta tashi ta tafi. Mus’ab ya koma cikin gida ya yi shirye-shiryen da zai yi na kintsi, ya yi wanka ya shirya cikin qananan kaya coporet wears. Ya shiga wurin Saddiqa daidai lokacin da ta buxe ido. “Kin tashi Aisha?” Ba ta yi mishi magana ba. Ya zauna a bakin gadon yana kallon ta, kanta a sunkuye ba ta xaga ta kalle shi ba, sai dai ta shaqi daddaxan kamshin shi. “Kin rame da yawa Aisha, ga wahalar tafiya, ga shi kin zo kin ga abin da bai kamata ki gani ba, ga kuma zama da yunwa da kike ta yi. Na roqeki ki yi haquri ki mai da komai ba komai ba mu fuskanci abin da ke gabanmu na zaman aure mai daxi. Mu biyu ne dake yanzu a gidan nan, in ban da abubuwa marasa daxi da suka faru da wannan lokacin shine lokaci mafi soyuwa da zaquwar zuwanshi a gareni na ganina tare dake mu biyu kina matsayin matata”. Ta xaga ido ta kalle shi saboda nanata kalmar mu biyun da yake ta yi, idanuwansu suka haxu daidai lokacin da ya furta mata kalmar “Abu ta tafi”. Kurma mishi ihu ta yi, nan take ta mimmiqe ta soma shessheqa tana qoqarin sandarewa tamkar wacce take shirin suma. Dr. Usman ya iso gidan saboda kiran da Mus’ab ya yi mishi, yana tsaye a kanshi ya gama yi mata komai. “Za ta daxe tana baccin, ina kyautata zaton ruwan zai qare kafin ta tashi, za ta xan samu kuzari saboda akwai duk wani abin da take buqata a ciki mun saka”. “To Doctor na gode”. Sai cikin dare ta farka, yana kwance a gefenta. Yana ganin ta tashi zaune shima ya miqe ya zauna yana kallon ta, ya yin da ita kuma ta sunkuyr da kanta qasa hawaye suka soma zuba. Ya yi maza ya ce mata, “Look Aisha, ba fa irin zaman da zamu yi dake ba kenan, don kuwa ba auren qiyayya aka yi mana ba, ina sonki ne kina sona kafin Inna ta gaya miki halina kyakkyawar mu’amala ce a tsakaninmu, zuwan da kika yi kika ga wata a gidana kuma ba yana nufin kin kamani da wani mugun abu bane. Zaman da zamu yi dake ne nan gaba zai zama in kin kama ni da laifi kin kama ni, amma abin da aka gaya miki a kaina na hali ko kika ga na aikata wannan abin da ya shafeni ne ni kaxai, yanzu ne kike da haqqi a kaina, kamar yanda nima nake da shi a kanki, don haka ki yi haquri abin da ya faru a baya ya wuce mu fuskanci wanda yake gabanmu kawai”. Ba ta tanka ba shima bai sake mata magana ba, ya miqe ya nufi banxaki ya haxa ruwan wanka ya gaurayashi da turare mai qamshi, ya fito ya ce mata “Kina da haqqi a kaina, na yarda zan tsare miki shi ko wane iri ne, na yi miki alqawari zan kiyaye. Amma nima zan tsaya in ga kin kiyaye nawa haqqin ko da ba duka ba. Ga ruwan zafi can na zuba miki ki je ki yi wanka”. Shiru ta yi ba ta tanka ba, ba ta kuma nuna alamar za ta yi abin da ya ce ba. Don haka ya naxe hannun riga sai kwai ta ji ya sureta yaje ya tsomata cikin ruwan har da rigar dake jikinta. Ya kama zai tuveta ta qanqame jikinta wuri xaya. Ta ga dai hakan ba zi mata ba, ta yi maza ta qwallara mishi ihu. “Zan yi”. Ya sake ta tare da faxin ya fi sauqi hakan. Ya fita ya barta. Ta gama sanya kayan da ta samu ya ajiye mata ba tare da ta tsaya shafa mai ba, ya shigo ya kalle ta ya ce, “Ga abincin ki na kawo miki falo zai fiye mana sauqi ki yi haquri ki ci da kanki, don ba zai yiwu in yi ta zuba miki ido kina wuni da yunwa kina kwana da ita ba. Kina jin bayanin da likita ya yi cewar ba wani abu ne ya sae ki ba illa yunwa, kin kuma san mijin kirki ba zai juri ganin matarshi cikin yunwa ba. Muje wurin abincin”. Ya fita ya dawo ya samu ba ta motsa ba, ya ce, “Baki gane irin zaman da nake so mu yi ba, ni don bakya magana dani zan jure, don na tava zama da wani bebe a Italy, zama mai daxi kuma muka yi, yana sha’anin shi ina nawa. Sai mun ga dama mu yiwa juna magana, don haka ki ci abincinki kawai sai in qyaleki ki yi sha’aninki nim in yi nawa”. Ya fita ya nufi masallaci saboda kiran sallar asuba da aka yi. Har ya yi sallar ya dawo ba ta ci ba, sai ma ta sake miqewa bayan ta idar da tata sallar. “Zaman namu zai koma irin zaman tabbataru kenan, kin san shi tabbatara kullum xura yake yiwa matarshi a baki, ina ganin cikin tsuntsye babu wanda ya kai shi yiwa matarshi hidima, ya kuma yi mata kirri da wasannin bajinta da kwarkwasa don ta ji tamkar babu kamarta a duniya. In hakan kika zava ai sai in yi miki don kin cancanci ayi miki komai”. Hannu ya miqa ya surota ya xora kan cinyarshi, ya ce, “Ni inda kike ganina xin nan babu abin da ban iya ba na reno, sanda nake yaro har xura nake yiwa qannena dama ‘ya’yan malamina can inda aka kai ni almajiranci, saboda barni da halina amma ban son ganin xan Adam yana jin yunwa”. Kwantar da ita ya yi kan cinyarshi duk da mutsu-mutsun tirjiyar da take yi yasa hannunta na hagu qarqashin qafarsa ta dama ya matse, zafin matsin gami da takaicin cin zarafin da yake mata yasa ta soma kuka sosai, ya yi amfani da hakan wajen xura mata kunun gyaxa dake wurin, ta yi maza ta haxiye gami da qwarewa, wani kuma ya zube a jikinta. Ya sake surarta ya nufi byan gida da ita yana faxin “Wannan wankan ai dama ba wanka bane, tunda ba a yi mishi shafa ba balle kwalliya”. Dolen Saddiqa ta yarda da bin umarnin wanka da na cin abinci, in ya ce ta yi ta yi, ko da kuwa ba ta son yin hakan. Kuma qa’ida ne in ta yi wankan ta yi shafa ta yi kwalliya, ta kuma sanya kayan da ya ajiye mata. Rannan ta shiga wanka saboda umrnin da ya ba ta na ta yi wankan, yana zaune yana tunanin abin da zai yi ya kawo qarshen wannan zman nasu, don ya fara isarshi. Tunaninshi ya kai kan faxaxa mu’amalar ta hanyar shigo da wasu abubuwan da yake ganin tamkar za su taimaka mishi, yana tashe da sabbin zannuwan da ya karvo mata daga wurin xinki, ta fito tana goge gashin kanta da xan qaramin tawul xin dake hannunta. Ya bita da kallo ya ce, “Yau kam bari in shafa miki man nan Aisha”. Ta yi maza ta kalle shi, shima ya tsareta da idanuwanshi ya qara cewa, “Bari in shafa miki man”. Qarar da waya ta yi ya katse shi, ya yi maza ya xauki kan wayar dake xakin. “Hello!” Nan take ya mai da kan ya nufi wurinshi cikin sauri. Ganin yanda ya yin ya sanyata matsawa kusa da wayar a hankali tasa hannu ta kai kunnenta. Ko shakka ba ta yi ba matar da ta samua a gidan ne, ga abin da ta ji tana cewa. “Na bugo ne in ji yanda kuke ciki kai da amaryar taka”. “To ina gaminki da ita da za ki so jin abin da muke ciki?” “Saboda ka wulaqantani a kanta ka ci mutuncina saboda ita”. “Ai baki da wani mutunci da za a ci Jennifer”. “Da ka yi a hankali Mus’ab ka daina cin zarafin mutane a kan ‘yar wannan yarinyar da ba wani abin arziki za ta iya tsinana mka ba, ni na san nan ba da daxewa ba za ka zo nemana da abinka a wandonka kana tuba kana in yi haquri”. Saddiqa ta rintse ido jin kalaman nasu, a hankali ta mai da kan wayar ta ajiye kamar yanda ta same ta, ta koma wurin shafarta ta yi abin da za ta yi na gyaran jikinta, ta gama ta xauki xaya daga cikin atamfofin da ya ajiye a wurin ta saka. Kwalliya sosai ta yi, atamfar kuma ta yi matuqar karvarta, ta fesa turare ta ji ni’ima cikin ranta, ta koma gefen gado ta zauna tana tuna Gwaggonta da halayenta na faxin gaskiya a kan koma waye. Sai ga shi ya shigo yana murmushi, ya ce, “Kinga yanda kika yi kyau kuwa? Kin kalli kanki a madubi?” Ba ta tanka mishi ba kallon shi kawai take yi, a zuciyarta tana mamakin al’amarinshi, ko ya ya aka yi ya zama haka oho! Tamkar dai a ce ba Gwaggonta ce ta haife shi ba, mutumin da ta rinqa ganin tamkar ya fi kowa kirki da kyawawan xabi’u, take yi mishi kallon kamammen mutum mai tsabta, take ganin tamkar duk macen da ta same shi a matsayin mijinta na aure ta morewa rayuwarta. Sai ga hi a yau ya zube mata ta kuma gane matarshi ba komai za ta sadu da shi ba a rayuwarta illa baqin ciki da vacin rai mai tsanani. Ta sake tunawa da Gwaggon nata da irin halayenta, nan take ta sake fahimtar bai zama lallai ba ashe a ce dole sai xa ya yi hali irin na iyayen shi. Gwaggo halinta daban na xanta daban, haka na Abu ma daban, don da Gwaggo ce ta ga abin da Abu ta gani da babu yanda za a yi ta sulale mata ta gudu ta barta cikin halin da ta barta. “Aisha yanzu in ina so in tsotsi bakinki ya ya za ayi?” Ya yi tambayar a yanayin dake nuna yana son yin abin da ya ambata. Tana xaga ido ta kalle shi takaicin shi ya qara kama ta, ta soma yi mishi kuka. Ya yi maza ya juya ya nufi kicin ya shiryo abinci a tire ya shigo yana faxin, “Gaskiya ai dole ki yi min kuka, ban baki abinci kin ci kin qoshi ba ina yi miki maganar tsotson baki, da wanne za ki ji?” Ya ajiye tiren a gabanta ya ce, “Za ki ci da kanki ne ko in baki?” Ya jawo hankicif ya riqe alamar wai zai iya bayarwar, gudun kar ya yi mata abin da ya saba yi matan yasa tasa hannu ta xauki cokali ta soma ci da kanta, shi kuma yana kallon ta. “Haba, to ko ke fa Aisha, me ya fi haka daxi? Bari in zauna ina zuba miki”. ABU TA ISA GARIN MISAU Wajen qarfe takwas na dare motar dake xauke da Abu ta yi parking a qofar gidan Malam Abdullahi a cikin garin Misau. Malam Abdullahi da kanshi ya fito yiwa Abu oyoyo tare da sannu da zuwa, tana amsawa tare da xan xingisa qafa, cikin tafiyar tata ta wuce ta shiga cikin gida, inda nan ma Inna Habiba ta karveta hannu bibbiyu cikin murna mai yawa. Nan da nan ta shiga gabatar mata da abubuwan ci da na sha, ta kuma zauna kusa da ita tana qara yi mata sannu da hanya da kuma gaisawa. A waje kuwa shima direba ya sha tarba wajen Malam Abdullahi, ganin shine mai kwashe tsarabar zuwa cikin gida a dalilin rashin yara a kusa yasa shi sa hannu wajen taya shi kwashewa saboda girmamawa. Suna gamawa ya gabatarwa da direban abin ci da na sha, sai da ya ci ya qoshi sannan ya tafi. Inna Habiba tana zaune gaban Abu bayan Malam Abdullahi ya shigo ya gaisheta ya fita. “Ba ki fa ci komai ba Inna, in ban da surkin farau-farau xin surkin da kike ta kwankwaxa”. Abu ta xan yi tsaki kaxan ta ce, “To gajiya, wannan gari da kafirin nisa yake”. Ta ce,”Haka ne Inna, ai qasar tamu faxi ne da ita. To ya ya kika baro su?” Abu ta ce, “Qalau, duk sun ce a gaishe ku”. Tana maganar Inna Habiba tana kallon idonta cikin nazari da lura. “To ai ba za ki tafi gidanki yau ba Inna tunda kin gaji da ga shi dare ya yi, kwananki huxu ne kuma da barin xakin ko don a karkaxe miki qurar ciki kafin ki shiga ai sai ki kwana a nan, ga gado can sai ki hau ki yi kwanciyar ki”. Abu ta zuba mata ido ta ce, “Mene ne haka kuma, kwana a gidan suruki bayan ga naka a kusa?” Inna Habiba ta yi murmushi ta ce, “Amma kuma ai na sha jinki kina cewa bakya surukuta da Malam xanki ne”. Abu ta gyaxa kai ta ce, “Qwarai kuwa”. Suna xan tattaunawa sai ga Malam ya shigo da qunshin tsire a cikin leda, ya miqawa Inna Habiba ya ce ba, “Gwaggo”. Ta ce, “To, Ubangiji ya saka da alheri”. Ya juya ya fita, ita kuma ta miqa hannu ta xauko faranti ta juye mata a ciki ta miqa mata gabanta. Abu ta kalli naman duk da qamshin shi da tururinshi dake tashi ba ta xora hannu a kanshi ba. “Anya zan ci nama kuwa?” Inna Habiba ta ce, “Haba Inna, a kan me?” Ta ce, “Gidan Mus’abu fa na fito, ai bani da kwaxayin komai”. Inna Habiba ta sake kallonta cikin nutsuwa ta ce mata, “Duk da haka kuma bakya murna, da rama kuma kika dawo”. Abu ta yi maza ta kalleta, ta ce, “Ke fa haka kike, za ki fara ne?” Ta yi murmushi ta ce, “To ki yi haquri, bari in juyo miki ruwanki ki yi wanka”. Ta ce, “To”. Washegari da safe Malam Abdullahi ya sake shigowa wurin Abu don su qara gaisawa, suna cikin hirar tafiyar ta shiga yi mishi bayani kan ximbin tsarabar da ta zo da ita. Ta miqa mishi kuxin da Mus’ab ya aikota dasu ya ce na Babanshi da Kawu Gixe, tare da wasiqunsu. Ya karva ya sanya musu albarka tare da addu’ar Ubangiji ya zaunar dasu lafiya. Abu ta yi maza ta ce, “Amin”. Ya sake kallon ta cikin nutsuwa ya ce, “To ai shi kenan faxuwa ta zo daidai da zama, dama yau za ni Bauchin sai kawai in je mishi da saqon, daga nan kuma in ba shi labarin dawowarku gida lafiya”. Ta ce, “To da kyau”. Ya tashi ya fita ya barsu nan suna ‘yar hira. Inna Habiba ta tashi ta fita ta dawo xauke da baho mai ruwan xumi a ciki ta ajiye a gaban Abu ta ce, “Tsoma qafafuwanki cikin nan Inna in xan matsa miki su don ki ji daxinsu”. Abu ta yi yanda aka gaya matan don ta san daxin shi tare da faxin “To, nasa”. Inna Habiba ta zauna tana matsa mata qafafun, daxi ya kama ta har ta zurfafa cikin tunani. Inna Habiba ta xago kai ta kalle ta, ta ce, “Me ya faru haka na ji kina ajiyar zuciya?” Abu ta yi maza ta ce, “Babu komai”. Nan take kuma ta shigo da zancen Mus’ab don kawar da Inna Habiba daga wani zato. “Yaron nan Mus’abu nake tunawa, ba qaramar jarumtaka ke gare shi, kin ga nisan wurin nan kuwa, amma tunda ya soma zancen auren nan bai tava rufa sati biyu bai zo garin nan ba”. Inna Habiba ta ce, “Ai shi yasa kanshi Inna, baki ji Hausawa suna cewa, ‘wai sa kai wanda ya fi bauta ciwo ba?’ Tunda buqatarshi ta biya baki ga ya xauke qafarshi ba? Dama ai yaudara ce ya yi yanda zai samu, to ya samu ya yi dalilin da aka xauki Saddiqa aka kai mishi gari mai nisa, inda kuma ba ta da kowa sai Ubangijinta. Dawowar nan da kika yi kuma ni na san da akwai wani abin da ya tsaya miki a rai baki faxe shi bane kawai, na kuma san da wuya in ba kan baro Saddiqa da kika yi a garin nan bane ita kaxai”. Abu ta yi maza ta katseta da cewa, “Ke kam daa mita kike, mijinki yana haquri dake, in kika tasa magana a gaba kin rinqa yinta kenan kina nanatawa. A kan ‘yarki ne aka fara xaukar wata yarinya aka kaita nesa? ‘Yammata naw ne aure ya raba su da iyayensu da garuruwansu ya kai su inda basu da kowa? Ashe darajar aure ba zai sa ayi abin da ya fi haka ba?” Ta ce, “Uhm! Zai yi ko in ce yana yi, amma ganewa na yi Inna farin cikinki da kuzarinki lokacin tafiyarku ya fi na yanzu da kika kai mita ita yawa, sannan ximbin tsarabar da kika taho da ita bai sa annurin fuskarki daidaituwa ba, ni na san kin fi kowa murnar ba shi ita da aka yi daren jiya, kuma duk da gajiyar dake gareki ina jin motsinki ba wani baccin kirki kika yi ba”. Abu ta katseta, “To ya ya zan yi in yi bacci bayan kin sani na sha qwayoyin da ban san kansu ba?” Ta yi maza ta kalleta ta ce “Panadol na baki Inna, maganin gajiya ne”. Ta kawar da kanta ta ci gaba da cewa, “Ni ai na sanki Inna, ina ganin kamar ma babu wanda ya kai ni saninki tsawon rayuwata ina tare dake ne, bana kwana bakwai ban zo inda kike ba, babu yanda za ayi wata matsala ta voyan nan da kin yarda kin gaya min yanayin da kika barota a ciki don mu san mafita, na riga na gargaxeta in zama da shi akwai vacin rai a ciki ta yi hanzarin dawowa gida, na kuma ba ta kuxi tare da ita kar ta kuskura ta ce za ta yi haquri da shi, don kuwa ba abokin haxinta bane, ya fi qarfinta. Tana isowa kuwa zamu san abin da muke ciki ni da Yaya, don shi ya haxa ba kuma zai bari a cuci marainiya ba, na yi mata sanadin faxawa cikin baqin ciki da takaici irin na matan da basu yi sa’ar mazan aure ba”. Abu ta zuba mata ido tana kallon ta, jimawa can ta ce, “Ai sai ki yi, ke dama ai bakya yi mishi fatan alheri sai dai tunanin abin da in ya faru ba zai zama mai daxi ba”. Ta miqe ta kama tafiya, ta ce, “Ki xorawa yara kayana su kawo min”. Inna Habiba ta biyota tana cewa, “To Inna ku huta gajiya sai na zo duba ku”. Ta ce, “To”. AJAKUTA Satin Saddiqa biyu a garin Ajakuta, tana kwance kan doguwar kujera a falonta, kallon t.v take yi, sai dai a zahiri ne kawai idonta yake kan kallon, hankalinta ba a nan yake ba, kalaman Gwaggonta take tunawa. “Fita harkarshi Saddiqa in har kika yarda kika ruxu da shi, to wahala kawai za ki sha, ba za ki xanxani komai ba game da daxin aure. Shi farin cikin aure ba a tarin dukiya yake ba, yana tare da zaman lafiya ne da kwanciyar hankali. Ki samu mijin da zai so ki ya yi tattalinki ya tarairayeki ya kyautata miki, ya gamsar dake cewar shi xin naki ne, shi kenan magana ta qare. To ba za ki samu hakan ba wurin wannan yaron, don ba zai tava mallaka miki kanshi ke kaxai ba, ba za ki samu wannan daxin ba a wurinshi, manemin mata ne. ina jiye miki randa za ki ganshi da wata a irin kishin dake gare ki, ga ki da kishin matsananci”. Ta tuna irin murmushin da ta yi a lokacin da Gwaggon nata take jaddada mata kishin nata, “Ni kishi ne dani Gwaggo?” Ta yi maza ta ce mata, “Qwarai kuwa, ai mu muka haifeki mu kuwa kishi wahalar damu yake yi”. Hawaye masu yawa suka zubo daga idanunta. Abida ta yi sallama rungume da xanta a qirji, da sauri Saddiqa ta miqe tare da amsa sallamar, hannu biyu ta saka ta karvi yaron. “Cavxijan! Ga wuri ga wuri amma sai yau kuka zo duba mu?” Abida ta yi murmushi ta ce, “Yau xin ma nice na matsawa Baban Umar da qyar ya bari”. Ta tave baki tare da zubawa Umar xin ido tana kallon shi cikin nazari, cikin nutsuwa ta ce, “Lah! Kinga xan sati biyun da na yi ban ga yaron nan ba har ya qara qiba”. Abida ta yi murmushi ta ce, “Ni da babanshi ne gayawa maigidan ana sallama da shi a waje”. Fara’ar Saddiqa ta ragu, ta yi maza ta mane kai da kafaxa nuna alamar qi kafin ta ce, “A’a, ni bana magana da shi”. Abida ta zuba mata ido ta ce, “Bakya magana da shi wane irin zama kuke yi? Ya yi miki wani abu ne?’ Ta yi shiru hawaye suka soma zubo mata shar-shar-shar! Ta ce, “Ni na fi so ya kaini gida ne”. Ta sake kallonta, ta xan yi murmushi ta ce, “To kawo min ruwa in sha ko baki da komai ne a gidan?” Ta yi maza ta miqe sbaoda tunawar da ta yi ashe ba ta gabatar mata da komai ba. Maimakon taa ajiye mata yaron sai ta sanya shi a bayanta ta xaure shi da zanin dake jikinta, qafafuwanta suka fito har sharabarta ta bayyana. Abida ta bita da kallo sai da ta shige cikin kicin xin dake wurin sannan ta mai da kallon nata cikin falon, tuni ta gano canjin da falon ya samu a sati biyun da ta shigo cikinshi ba ta dawo ba. Saddiqa ta fito riqe da tire mai xauke da abubuwan marmari na kayan itace, inibi, tuffa, ayaba, gwaba har da su ube ta ajiye mata. Ta koma gefe ta zauna. Abida ta ce, “Ya ya za ki ajiye min ki koma gefe? Ai in kina so in ci to ki matso mu ci tare muna hirarmu”. Ta yi yanda Abidan ta ce saboda tana girmama karva da xawainiyarsu da ta yi ta yi a gidanta, sai take ganinta kamar ‘yar’uwarta, hira ta yi daxi a tsakaninsu, duk da dai yau ma Abidan ce mai ba da labarin. Sai ga Mus’ab ya shigo yana murmushi, ya ce, “Sai yau su Umar suka zo duba amarya?” Ta yi murmushi ta ce, “A to, maigidan ne ya ce wai ba kowanne lokaci ake zuwa gidan amare ba, musamman ma da yake ya ga ba fita kake yi ba, wai ko ofis baka zuwa”. Mus’ab ya yi murmushi daidai lokacin da ya kama Umar ya zare a bayan Saddiqa, ya ce, “Kin kama yaro kin xaure kina zaune?” Sai da ya xan yi wasa da shi kafin ya kalli Abida ya ce mata, “Gidan ne babu kowa in na fita sai ta zama ita kaxai, ba ta kuma saba da hakan ba, sannan ni ke yi mana girki ba ta yarda ta fara shiga kicin ba wai tana amarci”. Abida ta riqe baki tana dariya ta ce, “Ai kuwa in dai haka ne to lallai kuna buqatar mai taya aiki, za ta yi muku girki in baka nan, kuma za ta taya Aisha zaman gidan, in yaso randa ta wattsake sai ta karvi girkinta ita ta rinqa wanke-wanke da shara, tunda ni dai ban ga amfanin a barwa mai aiki girkin gida ba matuqar ba yawan nashi ya kai yawa bane”. Ya yi murmushi ya ce, “Ita ma amarci ne bari ta wattsake ki gani, gwanar girki ce amma a yanzu dai kam taimaka ki samar mana mai aikin”. Ta ce mishi, “To, yarinya kake so ko babba?” Ya yi kamar zai faxa sai kuma ya fasa, ya ce, “Da yake bani za a kawowa ita ba, ita matar gidan ta gaya miki wacce iri take so kawai, ni a wurina in dai ta yi aikinta shi kenan”. Yana jin ta soma tambayar Saddiqa ra’ayinta ya miqe rungume rungume da Umar a qirjinshi ya tafi wurinshi. Yana barin wurin suka shiga hirarsu mai daxi suna dariya. Mus’ab da Idris suna tasu hirar a nashi wurin. “Kai angwaye suna qibar jin daxi kai kana zubewa?” Mus’ab ya yi tsaki ya ce, “Wane angwanci nake yi ni da amarya ba ta magana dani, ba ta ma yarda ta ci abinci sai in ta ga zan danneta in xura mata”. Idris ya qyalqyale da dariya ya ce, “Borin nata har ya kai haka?” Ya yi tsaki tare da sosa gefen fuskarshi da yatsanshi. “To amma wannan borin ai ya yi yawa, in da nine kai sai in kawo qarshen abin gaba xaya, in yaso in yi ta yin rarrashin mai dalili”. Mus’ab ya yi shiru kamar bai gane abin da yake nufi ba, ya sako musu wani zancen, suna hira Mus’ab yana kallon agogo, a zuciyarshi yana tunanin lokacin xora girki ya yi, sai dai ya ya zai yi ya yiwa Idris wannan maganar. Tashi zai yi cikin hikima ko kuwa shiru kawai zai yi? Saddiqa tana tare da Abida suna hira, ganewar da Abida ta yi maigidan ne mai girkin gidan ya sata kallon Saddiqa ta ce mata, “To muje kicin mana muna hirarmu muna aikin abinci sai mu yi mu gama kafin baban Umar ya ce mu tafi”. Ta ce mata, “To”. Suna girkin suna zancensu, mafi yawancin maganar Abida ce take yi mata, nasiha ne kuma kan ta daina fushin da take yi ta yarda ta zauna lafiya da mijinta. Saddiqa ta ce, “Uhm!” A zuciyarta kuwa tunani take yi, wannan ba ta san halin Yaya Mus’ab ba. Kalaman Gwaggonta suka sake zuwa mata. “Zamanki da shi wahala ne saboda kishinki”. Ta xan rage fara’a kafin ta ce, “Gwaggo kullum sai ki rinqa dangantani da kishi bayan na ji an ce bai da kyau”. Gwaggo ta ce, “Eh, to ya dai wahalar da mace mai shi kam, musamman a ce ba ta yi dacen mijin da zai tausaya mata ba, tausayinki ba zai sa wannan yaron ya haqura da son ranshi ya barki ki mallake shi ke kaxai ba”. Ta girgiza kai don qara tabbatar mata da abin da ta gaya matan. Abida ta katse tunanin nata ta hanyar tambayarta cewa, “Kin san daxin amarci kuwa?” Ta xan yi murmushi kaxan da nufin zolayarta, ta ce, “Da kin san yanda abin yake da baki tsya kina yi muku wannan takurar ba, kin qi ki kwantar da hankalinki balle ku ji daxin zaman naku, kin tsangwameku gaba xaya kun zube kun rame, ban ga abin da kika rasa a wurin mijinki ba, a shirye yake ya kyautata miki. Dubi yanda ya qara qayatar miki da wurinki a sati biyunki na zaman wurin kawai, in kika saki jiki da shi kina zaton akwai wani abin da ba zai yi miki ba”. Ga mamakinta sabodaa ta saba yin magana Saddiqan tana shiru, sai dai ta saurareta kawai sai ta ji ta ce mata, “Ai ni ba abinshi nake so ba”. Da sauri Abida ta kalleta cikin nutsuwa ta tambayeta, “Me kike so nashi?” Ta yi shiru ta sunkuyar da kanta qasa nuna alamar jin nauyi. “Ni yarki ce Aisha, in baki yi magana dani ba da wa za ki yi? Randa Abu za ta tafi da na zo mata sallama kuka ta rinqa yi tana cewa, in riqe ki amana. Jin hakan yasa ita ma Saddiqan ta soma yi mata kukan, ba ta hanata ba sai ta ci gaba da yi mata magana. “Ni dake dukkanmu jirgi xaya ne ya xauko mu, auren zumunci aka yi mana, yanda na san ba zan ce auren dole aka yi min ba, haka kema na san bana dolen bane. Don kun zo kun samu abin da ya vata muku rai a cikin gidan nan bai zamo hujja a wurinki ba da za ki yi ta bijire mishi, ba a kan idonki ya kawota ba, a yanzu in har kuka shirya ke da shi zai yi matuqar kiyaye abin da bakya so, ba ma sai kin tsaya kina ce mishi ga abin da bakya son ba, ai shima ya xanxana wahalar wannan dogon fushin da aka yi mishi”. Har suka gama girkin nasu suna hirarsu, suka gama suka shirya komai tsaf. Abida ta kalli Saddiqa ta ce mata, “To sai ki xauka ki kai musu”. Ta ce, “A’a, ke daai ki kai tunda ni kam ai ban tava leqa wannan falon nashi ba”. Abida ta ce, “A’a, ai yanzu suna tare da abokinshi don kin kai ba wani abu bane, sia ma ya ji daxi ya kuma san kina shirye da a shirya”. Ta yi maza ta ce, “Tafxijam! Wato ma nice mai neman shirin? Lallai ba za a shirya ba, ajiye musu nan in ya zo wucewa ya gani zai xaukar musu”. Abida ta qyalqyale da dariya ta ce, “Kin gani kuwa da yake na san daxin nawa auren bana yarda maigida ya yi fushi dani, ina ganin alamar vacin rai a tare da shi nake yin maza in shawo kan abina don bani da jarumtakar irin wannan zaman da shi”. Hira sosai ta yi mata, sai wajen yamma suka tafi gida. Washegari kuwa da yamma sai ga Abidan ta dawo tare da wata lafiyayyar yarinya budurwa, ta shigo falon Saddiqa, Mus’ab yana ciki yana nazarin wata mujalla, ya yin da Saddiqan ke cikin xakin a kwance. Sun gaisa ta soma yi mishi bayani. Saddiqa ta fito tana mata sannu da zuwa, “Ku shigo”. Mus’ab ya bi bayan kyakkyawar yarinyar da kallo, ya yi kamar ya tambayi sunanta sai kuma ya fasa saboda kar Saddiqa ta ji shi yana maganar. “Aisha ga qanwata na kawo miki Zainab, ‘yar Kawuna ce kwanan nan ta gama karatunta na sakandire, baban Umar ne ya bani shawarar kawo miki ita ta xebe miki kewa kafin a samo miki mai aikin”. Wannan shine bayanin da Mus’ab ya jita tana yiwa Saddiqa. Tun zuwan Zainab gidan al’amura suka soma daidaita, Mus’ab ya smau damar komawa kan aikinshi, sai dai kullum in zai fita zai kukkule ko’ina na gidan, ta yanda wani ba zai shigo ba na ciki kuma ba zai fita ba sai in ya dawo ne yake barin ko’ina a buxe. Saddiqa kuwa tana tare da Zainab a gida ta mai da ita tamkar ‘yar’uwarta saboda yanda take jin daxin zama da ita, zuwanta ya rage mata kewa da damuwa, ta fidda ita daga zaman shiru da take ciki, matuqar suna tare zai jisu suna ta raha da dariyarsu. Cikin qanqanin lokaci suka shaqu da juna, har girkin ma in za suyi tare suke shiga kiin xin suna aikinsu suna hirarsu, tamkar sun daxe da sanin juna. Shima Mus’ab ganin yanda ta saki jiki da Zainab xin yasa shi samun nutsuwa da kwanciyar hankali, saboda ya lura Saddiqa ta samu sassaucin damuwa. Ganin haka sai ya fara tunanin hanyoyin da zai bi wajen ganin al’amura sun daidaita tsakaninshi da ita, ya shiga qoqarin keveta ita kaxai ya xan yi mata kalamai masu nutsar da zuciya, duk da dai ba wani amsa mishi take yi ba. Haka nan yana kiyaye lokacin dawowar shi gida, yana tasowa daga ofis bai yarda ya tsaya ko’ina sai gida, ga kuma hidimomi iri-iri don dai ya faranta mata rai. GARIN MISAU Abu tana kwance a xakinta cikin dare iska sai faman kaxawa take yi, kasancewar lokacin kaka ne. Abu ta miqe zaune a tsakiyar gado ta yi tagumi zugum, tunanin yanda ta baro Saddiqa take yi a gidan Mus’ab. Mafarkinta na daren jiya ne ya fi tsaya mata a rai, ta tuna yanda ta ga Saddiqa a mafarkin, bayanin dukan da Mus’ab ya yi mata take yi, tana nuna mata raunukan da ya yi mata. Ta yi shiru cikin tunani mai zurfi tare da tuna irin dukan da ya yiwa Jennifer a kan idonta, jikinta ya xauki rawa saboda tabbatarwar da ta yi in har ya ce zai yiwa Saddiqa irin wannan dukan to ba za a haifi xa mai ido ba. Dare ya yi nisa Abu tana zaune a bakin gadonta taqi yarda ta kwanta balle ta samu ta yi barci, saboda babu halin ta rufe ido ko gyangyaxi ya xan xauke ta sai ta ga Saddiqa tana tsaye gabanta tana kuka tana faxin “Ke kika ja min wannan musibar Abu da kika qi yarda ki tahowa Gwaggona dani kika barni wurin Yaya Mus’ab, saboda kin fifita sonshi a kaina, bayan kuma Gwaggona ta roqeki ki tausayawa maraicina in kinga ba daidai ba ki dawo mata dani gabanta”. Abu ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji daxi, ita da kanta ta zargi kanta da rashin iya tsai da adalci a tsakanin Mus’ab da sauran jikokinta a ko’ina, ba ta iya voye shi daban ne, ba ta iya voye sonshi a zuciyarta, ba ta barwa kanta wannan sirrin. To wai ma mene ne dalilin da yasa ta fi sauraranshi a kan sauran? Ta fi tattalin farin cikinshi a kan kowa? Ta fi son ganin ya samu abin da yake so a kan kowa? Me yasa take yi mishi irin wannan son? Mus’ab ne ya fi kowa biyayya a cikin jikokinta ko kuwa ba haka bane, shine ya fi kowa jawo musu magana, shi ya fi kowa taqadaranci, ya fi kowa rashin tsoro, ya fi kowa yin yanda ya so. Amma ta je ta kasa hana shi Saddiqa saboda ta gane babu abin da yake so irin a bar mishi ita. Nan take ta soma kuka tana faxin bai cancanci abin da take yi mishi ba, ba ta yiwa kanta adalci ba da ta bari sonshi ya rinjayeta. Ta miqe ta yi alwala ta dawo ta soma gabatar da addu’o’i na Ubangiji ya kare Saddiqa daga dukkan sharri. Nan take ta qudurawa ranta gari na wayewa za ta je gidan Malam Abdullahi ta gayawa Inna Habiba halin da ta baro mata ‘yarta na gaskiya, don ta san abin da za ta yi ta taimaketa ta san matakin da za ta xauka. Saddiqa tana kwance kan doguwar kujera tana nazari da tunanin al’amuranta da Mus’ab kan irin kai kawon da yake yi da yanda yake nuna qauna da kulawa a gareta, yanda yake qoqari da tattalin ganin sun shirya shi da ita. Duk da har yanzu ba wani amsa maganarshi take yi ba, ba ya fushi ko nuna vacin rai game da abubuwan da take yi. Kalaman Abida kashedin da ta rinqa yi mata kan haqqin aure suka dawo mata. “Ki fa yi hankali Aisha kar ki yarda ki shiga haqqin mijinki. Wannan bijirewar taki tana nema ta wuce gona da iri, don kun same shi da wata a gida bai zama miki dalili ba fa, don kuwa samun ta kika yi ba ita ta zo ta same ki ba”. Ta yi ajiyar zuciya daidai lokacin da Mus’ab ya shigo falon. “Ajiyar zuciyar me kike yi? Ko kina jin yunwa ne?” Ta xaga ido ta kalle shi, kwalliyarshi ta qananan kaya ta burgeta, ga qamshinshi mai daxi, in a Misau da Bauchi kaxai ka san shi ba za ka tava sanin yana amfani da qananan kaya ba. Zuciyarta ce ta raya mata hakan. “Bari in shiryo miki abincinki”. Ya juya zai shiga kicin. Da sauri ta ce mishi, “Ni babu halin in yi wani motsi sai a ce yunwa nake ji?” Ya yi maza yaja ya tsaya nan take, ya juyo ya fuskanceta can cikin zuciyarshi daxi ne ya kama shi, bai tava jin ta yi mishi wata magana da jimlarta ta yi tsawo kamar wannan ba. “Za ta fara magana dani kwanan nan”. Tunanin da ya zo mishi a ranshi kenan. “To in ba yunwa ba ce mene ne Aisha?’ Ya yi tambayar daidai isowarshi kan kujerar da take zaune. Maimakon ta zabura ta miqe kamar yanda ta saba yi mishi sai ya kamota, sai ya ga ba ta motsa ba. “Zan iya zama kenan?” Zuciyarshi ta sake raya mishi, don haka ya smau wuri a gefenta ya zauna, ita ma ta miqe daga kwance ta zauna cikin nutsuwa kanta a sunkuye. “Kina son wani abu ne ko kina da wata damuwa ne?” Ta girgiza kai tare da faxin “A’a”. “To in baki da ita ni ina da ita Aisha, ko baki da damuwa da abin da ya dame ni?” Ba ta tanka mishi ba, sai dai ganin ba ta yi yunqurin tafiya ta bar mishi wurin ba yasa shi jin daxi, nan take kuma ya yi nufin amfani da damar da ya samu wajen yi mata magana. “Ban tava tunanin don an gaya miki mugun halina ko kin kama ni da wani laifi za ki nuna min qiyayya da tsana irin wacce kike yi min ba, saboda ni na san waxannan abubuwan guda biyu ba sune matakan da ake xauka wajen gyara mutumin da ake ganin yana buqatar gyara ba. Sanda Abu ta kaiwa Kawu Gixe ni shi kuma ya damqa al’amurana a hannun Mama, ko in ce Innata, ni da kaina qyamar kaina nake ji, zuciyata ta yarda da cewar ni xin ba komai bane face wata jarrabawa da aka jarrabi iyayena da ita, saboda kullum abin da ake gaya min kenan. Don haka sai na zama a takure bana ko iya sakewa in shiga mutane balle in yi mu’amala dasu, saboda ko da na kasa barin abin da ake so in barin to kuma bana jin daxin vata musu ran da nake yi, da yanda nake ja musu magana. Tunda a gabana an yiwa babana gori a kaina, ba sau xaya ba, ba sau biyu ba. Don haka ko da aka kawowa Kawu Gixe ni na bi umarnin Abu ne kawai na biyota, amma cikin zuciyata na yi niyyar fakon idonsu in yi tafiyata don kar suma in ja musu irin abin da na jawa iyayena a Misau. Sai dai ban iya tafiya na barsun ba Aisha, saboda cikin xan qanqanin lokaci ne na fahimci su basu xaukeni abin kunya ba balle su kalleni a matsayin jarrabawar rayuwarsu, ban tava sani ko tunanin ina da wani alheri a tare dani ba sai da na ji Mama tana rama gorin da aka yi mata a kaina da wasu kalamai da ba zan furta miki su ba. Amma bayan lokacin ne ni da kaina na gane ashe duk abin da na yi a rayuwata ban tava xaukan abin wani ba, haka nan na kan faxi laifina ni da kaina, ko kuma in faxi gaskiya kan abin da aka tambaye ni. Sai da na ji wannan shaidar a bakin Mama kafin ni kaina na san eh, ashe haka xin nake. Da na zauna da ita sai da ta yi min wani irin riqo, ta yi mu’amala dani wata irin mu’amala da ta tilastani jin kunyarta, na zama mai gudun vacin ranta, na zama ban da abin da nake so irin na burgeta, in sata ta ji daxi, in jita dai tana sanya min albarka tana roqon Ubangiji ya shiryar mata dani. Ba duka ta rinqa yi min ba, ba zagi ba, kalamai ne kawai masu sauqi da suka fi kama da nasiha. Yanzu mene ne amfanin yaro kamarka a same shi yana irin waxannan abubuwan da kake yi? Yanzu ko don in ji daxin zuciyata ba za ka daina ba? Ba za ka bar abin da nake cewa ka bari ba? Don Inna ta ji daxi, don in sata ta yi farin ciki. Sai na wayi gari na daina abubuwan da take faxin in daina, duk da wuyar barinsu”. Ya xan yi shiru kaxan kafin ya buxe baki cikin nutsuwa ya ce mata, “Na xauka tunda ita ta haifeki halayenki za su zamo masu sauqi irin nata”. Duk da kalaman da ya yi mata sun ba ta tausayi, sun kuma kashe mata jiki hakan bai hanata xagowa ta kalle shi ba, kan ta gama tunanin dake zuciyarta sai ta ji ya ce. “Ko da yake dama an ce wai a kan haifi xa ne ba a haihuwar halinshi”. Ta yi maza ta gyaxa kai. Ya yi murmushi ya ce, “Nima da halin Inna ne dani ai da bamu samu matsala dake ba ko?” Ta sake sunkuyar da kanta qasa. “To amma ko baki yi min yanda Inna ta yi min ba tunda Kawuna ya riga ya bani ke duk da ya fi kowa sanin yanda nake xin, ai ina ganin ba irin wannan zaman ya kamata mu yi ta yi ba, ya kamata ne mu yiwa juna adalci ni in rage wasu abubuwan ke kuma ki yi haquri da wasu, sai mu haxu a wata matsaya da zamu ragewa kanmu damuwowin da muke ciki ko kuwa?” Kan ta yi magana sai ga Zainab ta shigo cikin falon xauke da tiren abincinsu. “Yaya za a kawo maka naka nan ne ko falonka za a kai?” Ya ce, “A’a, bar shi a kicin xin in ina buqata zan xauka”. Ta ce, “To”. Ta juya ta fita. “Aisha!” Yana nufin ci gaba da maganar ta hanyar ba ta umarni ta kai mishi nashi abincin wurinshi, sai qarar wayar landline ta katse shi. Ya yi maza ya miqe ya nufi falonshi don amsa wayar a can, zuciyarshi cike da farin cikin damar da ya samu tare da Saddiqa. “Kwanan nan zan shawo kanta ta yanda al’amura za su daidaita a tsakaninmu”. Kalaman zuciyarshi kenan. Ita ma Saddiqa ta miqa hannu cikin dabara ta xauki kan wayar dake ajiye kusa da ita a tata zuciyar tana tunanin, “Ai ko za ta saki jiki da shi kyakkyawar mu’amala ta shiga tsakaninsu to sai ta tabbatar ya rabu da ‘yan iskan ‘yammatanshi tukunna”. Tana jona wayar da jikin kunnenta sai ta jishi yana cewa, “Zan amsa gaisuwar nan kuwa Sarah? Aui na yi zaton kin riga kin share sunana a dairy xinki”. Ta yi ‘yar dariya ta ce, “A’a, sai dai in kai ne ka yi hakan, tunda baka tava nemana ba gara ni ai na je ofis xinka aka ce min kana gida kana hutun angwanci, shine na ce to ango kuwa ai bai da lokacin sauraron abin da ke waje, musamman ma a ce bai danganci amarya ba. Shi yasa na ce bari in saurara sai ka fito tukunna, yanzu ma dai na bugo ne in ce maka congratulation, ina tayaka murna”. Ya yi dariyar jin daxi ya ce, “To na gode Sarah, sai dai ko ina angwanci ai bai kamata in rasa lokacinki ba, kina gida ne?” Ya ce, “Eh, to yanzu dai bana gida amma zuwa awa xaya xan isa gidan”. Ya ce, “To sai na zo”. Ya ajiye wayar, ita ma Saddiqa ta mai da tata ta ajiye. “Aunty kin gama wayar ne?” Saddiqa ta xago ido ta kalle ta jikinta sai rawa yake yi, zuciyarta tana raya mata zai fita ya barni ya tafi wurin ‘yammatanshi na banza saboda na tsare mishi inda zai kawo su. Gara in ba shi wuri, bari kawai in tafi in bar mishi gidanshi ya sake ya yi abin da ya so, dama abin da ya saba yi kenan. “Mu ci abinci mana”. Zainab ce take yi mata magana saboda ganin halin da ta shiga shirunta ya yi yawa. “Ci ki bar min Zainab, kinga ai xazun nan na karya”. Ta miqe ta shiga xakinta ta shafa jikinta ta ji lalitar kuxinta da Gwaggonta ta ba ta, ta duba kuxin suna nan a ciki. Ta yi saxaf-saxaf cikin sanxa ta wuce Zainab a kicin tana gyare-gyare tana tsaftace wuri ta fita harabar gidan dake buxe, cikin sa’a babu kowa balle ya ganta. Tana baro gidajen nasu da kaxan ta yi sa’a ta samu mashin ta xane zuwa tashar motar garin dake kusa. Shigarsu tashar ta ji ana Kano ciko mutum xaya a tasi. Tana jin haka ta faxa ciki a zuciyarta tana tunanin daga can sai ta shiga mai zuwa Misau ya fi mata ta zauna jiran ta Bauchi ta cika don kar ya gane ta fita ya biyo bayanta ya sameta. Nan da nan aka gama haxa kuxin fasinja aka sallami direba yaja mota suka soma tafiya. Saddiqa tana zaune cikin mota sai faman sharara gudu take yi, zuciyarta cike da farin ciki yau kam za ta koma Misau gaban Gwaggonta. Ta tuna Gwaggon nata da irin kalamanta da ta sha gaya mata a kan Mus’ab. “Halin wannan yaron sai shi babu mai iya mishi sai mace ‘yar bariki irinshi, amma bake ba Saddiqa”. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Ubangiji ka sakawa Gwaggona bisa gaskiyarta da riqon zumuncinta, babu wani abin da ta gaya mata a kan xan nata face sai da ta ganshi a zahiri”. Za ta koma gaban Gwaggonta, za ta je can ta same ta suyi zamansu ta qara sonta a kan son da dama can take mata, don ta qara gane ba ta da masoyi a duniya wanda ya wuce ta. Mu sadu a littafi na uku don jin yanda za a kwashe. Taku. Hajiya Hafsat Sodangi.