ABU NAKA… 1 HAFSAT C. SODANGI Haqqin Mallaka (m) Hafsat C. Sodangi Shekarar Bugu: 2005 An sake Bugawa A: 2015 A lura An xan yi gyara a cikinshi kaxan saboda wasu dalilai, sai dai yana nan a kan tsarinshi na farko. Na gode. 11/8/2006 ABU NAKA-1 M us’ab ya yi parkin xin motarshi qirar peogoeu 504 sabuwa dal sai xaukar ido take yi a rana tana walqiya, baqin fentinta ya yi matuqar dacewa da ita. Mus’ab ya fito daga cikin motar yana sava babbar rigarshi ta farin voil da aka yiwa xinkin Ado Bayer. Dogo ne sosai wankan tarwaxa da ya kusa ya zama fari, yana da xan jikin da ya qara bayyanar da kyakkyawar halittarshi saboda qara mishi kwarjini da hakan ya yi. Qofar gida da ya dosa kewaye yake da darmin zanna wanda aka yiwa turaku da bishiyoyin aduruku. Kai tsaye ya nufi cikin gidan, tun kafin ya yi sallama ya hangeta zaune kan shimfixarta cikin rumfar dake kusa da xakinta. “Hantsi kike sha ne haka?” Ta xago kai ta kalle shi cikin yanayi na mamaki. “Ya ya aka yi ban ji sallamarka ba sai ganinka kawai na yi ka shigo min gida?” Ya yi murmushi haxe da cewa, “Ban tsaya yin sallamar bane Abu, a ina kika ga maigida yana tsayawa neman izinin shiga gidanshi?” “To ban yarda ba koma kawai ka yi sallama in amsa tukunna kafin ka shigo min gida”. Ya sake wani murmushin mai ya ce, “Maigidan kike yiwa haka ke? Xan amsa kawai daga nan. Assalamu Alaikum!” “Wa alaikumus salam”. Ta amsa tana murmushi tare da faxin, “Sannu da zuwa, hala a Vauchi ka kwana?” Ya ce, “Ai a xakina na kwana wai dan kawai na taso tun da sauran dare, don a garin Malewa na yi sallar asuba”. Abu ta riqe baki nuna alamar mamaki, ta ce, “To mu shiga xaki mana”. Ya ce, “A’a, mu yi zamanmu a nan kawai don mu sha iska”. “To bari in qara maka shimfixa”. Ta miqa hannu ta jawo tabarma a bayanta tana shimfixa mishi. “Wato ke da tabarmini ma kike zama a kusa dake?” Ta ce, “To gidan nawa ai na jama’a ne, wannan ya shigo ne, wannan ya fita. Kamar yau xin nan Jum’a, da za ka kai bayan sallar azahar a sauko masallaci, ai in ka soma ganin jama’a sai ka yi zaton xaurin aure za a yi’. Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Ai na lura in har akwai abin da yake da nishaxi a cikin al’amarin tsufa bai wuce zuwa gaisuwar nan da ake yi ba”. Abu ta ce, “Ban da wannan zuwan ai na rahama ne, ka gama quruciya ka girma ka bar aikata abubuwa na ganganci ka yi ta istigfari kana neman gafarar Ubagiji bisa ayyuka na baya, ga rangwame da Ubanjiji ke yiwa xan Adam a lokacin da ya soma gajiyawa, matuqar shi xin ya rayu yana aikata alheri a lokacin quruciyarshi, alherin tsufa yana da yawa. Ba ga shi duk na sanku kun sanni ba, ga shi kuma ana tare”. Mus’ab ya ce, “Haka ne Abu, Ubangiji dai yasa mu dace”. Ta ce, “Ameen”. Suka shiga gaisawa tana tambayarshi abin da ya dawo da shi bayan bai daxe da tafiya ba. “Ka ji Abu, ke ce kika ce ina tafiya can ina daxewa ina mantawa daku, har kina cewa ina da wasu ‘yanmatan ne a can masu shagaltar dani? Ai shine na ce, to tunda abin ya zama haka bari in rinqa zuwa akai-kai don ki san ban da kowa a ko’ina ma ke kaxai ce ki sha kuruminki”. Ta yi dariya ta ce, “Ka ji da shi”. Wasu samari su biyu suka shigo suna riqe da kayansu na cin kasuwa dake nan kusa, suka gaisa da Abu cikin barkwancin nuna alamar suma jikokinta ne, sannan suka gai da Mus’ab a yanayin mutuntawa. Ita kuma ta tsaya tana yi mishi kwatancen iyayensu don ya gane asalinsu. Suka sake gaisawa yana tambayarsu mutanen da ya sani a gidan nasu. Da za su tafi sai suka ce mata, “Mun biyo ne ko za ki yi saqon kaji da manshanu don cin kasuwar qauye zamu”. Ta ce, “Saqo kai, sai dai yau zan huta bayar da kuxina tunda ga babban maigidan ya zo, dama can kuma a kuxin cefanen da yake ban ne nake cin kajin dasu”. Mus’ab ya xan karkace ya jawo wata walet daga cikin aljihunshi ya ciro kuxi ya miqa musu, suka karva suka qirga dubu biyar ne ke hannunshi. Ya ce, “Ku raba kai da xan’uwanka, wannan dubu biyar xin kuma ku sayowa Abu kaji da manshanu”. Suka yi shiga godiya suna faxin “Ubangiji ya qara girma”. Ya ce, “Ameen”. Suka yi sallama suka tafi da alqawarin sai yamma za su dawo su kawo saqon. Abu ta kalli Mus’ab cikin nutsuwa ta ce, “Wai me ya dawo da kai ne yanzu? Ni dai na san mun yi sallama da kai a kan sai wani watan ba ma wannan mai kamawa ba na gaba, ko kuwa dai aikinka ne ya kawo ka?” Ya gyara zama sosai kafin ya zuba mata ido cikin nutsuwa ya ce, “Wurinki na zo, ai kinga ko gidanmu ban je ba shigowata garin nan kenan na tsaya qofar gidan nan”. Ta ce, “To lafiya dai ko?” Ya ce, “Lafiya qalau, kin dame ni kawai da maganar na tsufa ban yi aure ba”. Ta harare shi ta ce, “Au damun ka na yi? Waxannan yaran da suka fita a haihuwar akuyoyi baka haifesu ba ko kuwa dame iyayensu suka girmeka?” Mus’ab ya ce, “Abu kenan, babu halin mutum ya zo gidanki sai kin kashe mishi jiki da maganar tsufa, nifa a gidansu Halliru ne sa’ana”. Ta yi maza ta ce, “Ahaf! Ba cinya ba kenan qafar baya, shi Halliru yanzu aka ce maka xanshi bai kusa waxannan xin ba?” Ya yi maza ya ce, “To shi kenan Abu mu bar maganar na yarda ko a haihuwar mutane na haife su shi kenan ko magana ta qare? Sai a zauna lafiya”. Ta yi dariya ta ce, “To ina jinka”. Ya ce, “Aure nake so in nema nake kuma so ki wuce min gaba”. Da sauri ta tava qirjinta tare da faxin “Ni?” Ba ta jira amsarshi ba ta ci gaba da faxin, “Allah ya kiyaye min ni Abu, wanda rashin sanin hali ya sani na yi dai na yi shi na kuma ji kunya dai-dai gwargwado, amma kan gaba ba zan sake shiga wani zancen neman aurenka ba. In dai aka ce an baka, to zan zo in sanya maka lalle don duk tsufan nan naka in ka samu auren lalle zan sanya maka, ba zan barka haka ba sai in turo ‘yan qannen baya-bayanka su zo su taya ka zaman lallen. Don ba za a samu sa’o’inka ba a garin nan da za su yi zaman lalle, don waxanda suka fara haihuwar da ‘ya’ya mata ma yanzu surukai ne dasu, to wa zan je in kira cikinsu ya zo ya tayaka zaman lalle, wannan abin kunya? Mus’ab ya gyara zama ya ce, “Haba Abu, ai tamu dake ba ta vaci, in kika yi haka ai za ki sa na ayi mana dariya”. Ta yi maza ta ce, “Ai gara ayi mana”. Ya qara matsawa kusa da ita ya ce, “Da gaske nake yi”. Ta ce, “Kullum haka kake yi, ka matsa na yi maka magana a kan ‘yar gidan Na’ibi aka ce ka fito zuwa hira ma ya gagareka, ka dawo ka ce min ba ta yi maka ba. Ka sake cewa ka ga ‘yar gidan Malam Nomau, nan ma ka dawo ka ce ba ta yi maka ba, saboda wai maganarta ba ta yi kamar ta mata ba, baka son mace mai yanayin maganarta”. Ta galla mishi harara nuna alamar har lokacin abin da ya yin yana mata ciwo. Ta qara yin qwafa nuna alamar takaici. “Ka fi son irin ‘yammatanku na birni masu lanqwasa da karairaya suna qirqirar muryoyin qarya, mu nan ai gaskiya da gaskiya ce”. Ya yi murmushi kafin ya ce, “Ki yi haquri Abu, in kin tambayar min wannan ban aura ba kar ki sake shiga harkata?” Ta galla mishi harara ta ce, “To wai ni dole sai na wuce maka gaba ne za ka yi neman aure? Can ‘yammatan ka na bariki ni ke wuce maka gaba kake neman su?” Ya haxa fuska nuna alamar bai son irin waxannan kalaman da take yi mishi. “Wai ni me yasa Abu kike yi min haka ne? Wa….” Bai qarasa yin tambayar da ya yi nufin yin ba ta yi maza ta yi mishi tsawa. “Kai tafi can”. Nan take ta bishi da wata lalatacciyar harara kafin ta ja tsaki ta ce mishi, “Mene ne ban sani ba, ko kuma mene ne sabo a wurina lamarinka?’ Maimakon ya qara xaure fuska saboda yanda ta yi mishi, sai ya yi maza ya saki murmushi tare da faxin “Abu kenan ni kam ai ba zan yarda tamu dake ta yi tsami ba balle ta samu ta kai ga vaci, ni dai ki sani cewar ina son yarinya, na kuma daxe ina son nata, na yi ta zagaye-zagayen maganar ‘yammatan ne ko zan yi dace ki ce min to gata, me zai kai ni wani wuri? Sai ba ki yi min hakan ba, don haka na sake dawowa wurin naki ki yi min jagoranci zuwa neman auren nata”. Kalamanshi suka sanya Abu juyowa gare shi ta kalle shi cikin nutsuwa ta tambaye shi, “Wace ce yarinyar?” Ya xan sassauta murya kafin ya ce mata, “Aisha!” Ta zuraa mishi ido nuna alamar nazari. “Wacce a ciki? Ai ka san Aishan yawa ne dasu, kuma yawancinsu sa’anni ne, akwai ta gidan aminin shi Malam Kallamu, akwai….” Ya katseta da cewa, “Kina kai wa da nisa Abu, ta gidanmu nake so”. Ta qara kallon shi ta ce, “Wacce Aisha ce a gidanku?” Cikin an gyajeran nazari ta sake tambayar, “Ko kuwa dai Saddiqa kake nufi?” Ya ce, “Eh, ita nake so”. Ta yi maza ta xaure fuska tare da faxin, “To baka ji irin abin naka ba, ba auren kke so ba, ga ‘yammata nan a dangi musamman ma ‘ya’yan qannen babanka, ko amininshi ba za ka je ka nema ba sai ka yi maganar wata Saddiqa? Kai ma ka san ba za a baka ita ba, ka fi kowa sanin cewar masu riqon Saddiqa ba za su baka ita ba. In ka ji shawarata ka je cikin gidanku wajen qannen babbanka ka zavi ‘yammata ka faxi ranar da kake so a sanya maka su a lalle. Kai xan gata ma za ka je ka tsoma kanka a neman auren da zai vata maka rai, Saddiqan me kuma?” Ka je gidanku can cikin gida ga kakan ku nan da ya saura Malam Hazo, in ka ce mishi ‘yammata biyu kake so a sanya maka a lalle rana xaya kafin rana ita yau zan sa a kawo maka su har gidanka, ai kai xan dangi ne, nan Misau babu wanda bai san zuriyarkuy ba, ku xin kyawawa ne gaku da asali ga malanta. Idan cikinku ka zavo matarka, kar ka yarda in ji ka zavi xaya haxa biyu kawai, don ka samu ka fanshe zaman tuzurantakan nan da ka yi ta yi shekara da shekaru babu aure”. Mus’ab ya gyara zama cikin nutsuwa ya ce, “Abu Saddiqa nake so, ita ma tawa ce ba a fi ta zamowa kusa dani ba a xakin mahaifiryata na soma xanxanar ‘yancin rayuwa, ba kyau ne ya dame ni ba ita nake so, ki taimakeni ki gayawa Inna da Babana cewar ina son Aisha su taimake ni su bani izinin neman aurenta, tunda na samu labarin Kawuna ya ce ita Inna uwa ce, dama kuma uba ce, don haka al’amarin Aisha yana qarqashin hukuncinta ne ita da mijinta, kowa yake son Aisha yaje wajensu, to nima na zo wajen nasu don su bani izinin nema, ba wai ina nufin a bani bane, a’a’, nima zan shiga cikin manemanta ne nima, a yarda a ba ta damar da za ta yi zavi da kanta”. Abu ta yi tsaki ta ce, “To ita uwarta za ta yarda ne? Ita wannan yarinyar da za ta yarda kam ai da komai ya kwana gidan sauqi”. Ta xan yi shiru nuna alamar nazari kafin ta yi maza ta ce, “Kai ba fa zan tsoma baki ba tunda kai ma kafiya ce da kai ga taurin kai in an baka shawara baka xauka, in ka ce kana yi ko an ce ka bari ba za ka bari ba, in kuma ka ce baka yi, to juyin duniyar nan ma babu mai saka ka yi. Don haka ni babu ruwana ku je ku yi ta yi, don in na ce zan biye ka to vacin rai kawai za ka jawo min. ta babanka ma duk bai sauqi ne, amma ita Innarka”. Ta xan gyaxa kai nuna alamar lamarin ba mai sauqi bane. Ta sake xago kai ta kalli Mus’ab. “Tun bara fa ta ce min Sadisu za ta bai wa yarinyar nan, ta kuma sa Saddiqa ta sallami duk manemanta shi kaxai ne mai zuwa wurinta, yanzu to zan je in ce mata kar ta baiwa Sadisu auren ne? Tare suka yi wasan qasa da uwarshi, ita ce ma ta yi mata babbar qawa. Kuma yanda ka bararraje xin nan shima in ya zo nan gidan haka yake zama ya bararraje muyi ta hira da shi, ko wannan kilishin da na kawo maka ai cikin wanda yake kawo min ne na xan tsakuro maka, anjima kaxan nan ma ana saukowa daga sallar Juma’a za ka ganshi ya zo gurina, to ya ya zan yi da shi? Cikinku wane ne ba nawa ba?’ Mus’ab ya sha mur ya ce, “To ai shi kenan dukkanmu naki ne”. Yasa hannu ya xauki makullin motarshi zai fara tafiya, ta yi maza ta ce, “To baka ci kilishin naka ba?” Ya ce, “A’a, ai kuma na fasa tunda na gane kilishin toshiyar bakin da ake kawo miki ne, sai ki yi ta ci ke kaxai”. Ta yi murmushi ta ce, “To ai hirar ba ta isheni ba zo ka ji”. “Ni ta ishen tunda na yi abin da ya kawo ni kin ce ba za ki taimake ni ba, to me zan ci gaba da yi a gidan naki in dai ba so kike in yi zaman jiran zuwan nashi ba”. Abu ta yi dariya da qarfi ta ce, “Baka son gaskiya ne Mus’ab, ai na mara maka baya ma a neman auren Saddiqa in ce a baka a hana Sadisu, ai na ji kunya. Haba ai sai in kasa fita gari”. Ya ce, “To na ji sai anjima zan zo ki yi abincin dare dani”. Mus’ab ya isa qofar gidansu mahaifinshi yana alwalar tafiya sallar Juma’a, ya fito daga motarshi ya koma can gefe cikin nutsuwa ya tsuguna da nufin gaishe shi. “Sannu da zuwa, sannu da zuwa”. Mus’ab yana amsawa a yanayi na girmamawa, cikin ladabi ya ce mishi, “Ko zan shiga ciki ne Inna ta san na zo sai in fito mu tafi masallacin tare?” Ya yi murmushi ya ce, “Yi sauri ka yi hakan, amma ai mun riga mun ji zuwan ka wurin waxannan yaran da suka zo su karvi kuxin manshanu wurin Habiba”. Mus’ab ya ce, “To muje kawai Baba in mun dawo sai in shiga”. Bayan saukowa daga sallar Juma’a, tunda Mus’ab ya shiga ya gai da mahaifiyarshi ya fito yana wurin babanshi Malam Abdullahi suna hirarsu mai daxi irin ta xa da mahaifi. Malam Abdullahi yana zaune kan kujera ya yin da shi kuma Mus’ab xin yake qasa suna hirar a haka. Kafin zuwa can ya ce mishi, “Yanzu nan kai zamanka a haka ya yi maka dai-dai? A ce mutum ba zai yiwa kanshi faxa ba? ‘Ya’yam qannenka mata ne fa yanzu suka shigo nan suka gaisheka don sun ji zuwan ka, ko wannan bai isheka ka san baka da sauran quruciya a tare da kai ba?’ Ya qara sunkuyar da kanshi qasa cikin ladabi ya ce mishi, “Da yardar Ubangiji wannan karon zan yi, kusan ma abin da ya kawoni garin kenan a yanzu, na ma riga na je na yiwa Abu bayani”. Mahaifin nashi ya zuba mishi ido yana kallon shi. “Ita Innar ta sake sauraronka kan irin wannan zancen?” Mus’ab ya xan yi murmushi a yanayi na ladabi. “Yanzu dai ta ce babu ruwanta sai dai ko a gaba”. Malam Abdullahi ya ce, “Ai in ban da ba a shiga tsakaninku da ko ni sai in ce mata kar ta sake shiga harkarka”. Mus’ab ya qara sunkuyar da kanshi qasa yana sauraro, a hankali ya ce, “Na ba ta haquri”. A gidan Abu bayan sallar isha’I Mus’ab yana zaune a tsakar gidan shi da ita saboda wadataccen hasken farin watan da ake da shi, wanda ya haskaka sararin subhana. Mus’ab yana rungume da gwiwoyinsa saboda kasancewarsu tsaye. Abu ta kalle shi ta ce, “Ka miqe qafafunka mana ka ji daxin zama, ga abincinka”. Ya ce, “Gaskiya ba zan iya miqe qafa a nan ba tsoron damatsiri nake ji”. Cikin sauri Abu ta kalle shi ta ce, “A ina ka ga damatsirin?” “To ko ban gansu ba Abu ai na san suna nan tunda ga bishiyoyin Aduruku duk inda suke kuma ai ana samun su, don haka ni gara mu shiga ciki”. Ya shiga tayata kwashe kayan dake wajen yana qoqarin xaukar tallan mijiya ta ce, “A’a, xauki tabarma ni zan xauko miyata kar ka yi min varinta”. Sun gama cin abinci Mus’ab ya kalli hannunshi ya ce, “Abincin ya yi daxi, sai dai farfesun ya ji daddawa”. Ta ce, “Eh, a haka aka cinye aka kuma shanye romon ba”. Ya yi murmushi ya je ya wanke hannunshi da sabulu mai qamshi, ya dawo ya zauna suka shiga hira. Sai ya ce mata, “Mu yi maganar gaskiya mana Abu ina fa son Aisha, ko kuwa kina son sai ciwon so ya kamani?” Yana kallon ta yana murmushi. “Ai ni iya shegenka ne yake haxani da kai, ciwon so ya kamaka a kan Saddiqan?” Mus’ab ya gyara zama ya ce, “Mu bar maganar wasa Abu, ki taimakeni a kan maganar yarinyar ina sonta ban qara sanin hakan ba irin da na ganta tare da Sadisu a qofar gida xazu suna hira, sai na ji har ina buga tuntuve. Ko na yi miki laifi a baya, ai kuma ba za ki bari alhe ri ya wuceni ba, aurena da Aisha kuma kin san alheri ne, ni da ita duka naki ne. Abu in kika taimaka xin kuma sai ya zame miki kin yi tuwonki ne manki”. Ta ce, “Ai duk daxin bakinka wannan karon haka za ka yi ka barni, ko dama ka xauko abin a inda ya dace balle haka kawai, ban da haka kaima ka san bamu da fada wurin mai abin”. Washegari da safe Saddiqa tana aikace-aikacen gida, Mus’ab ya shiga gidan. “Sannu da aiki Aisha”. Ta yi maza ta xan tsuguna nuna alamar girmamawa. “Sannu da zuwa Yaya”. Bai tsaya ba ya wuce zuwa xakin mahaifiyarshi wacce gaisuwa ce kaxai take haxa shi da ita, bayan wannan ba ta sake sauraron komai daga gare shi, sai ma in ta ga zai daxe a zaune a xaki ta fita ta ba shi wuri. Sanin da Saddiqa ta yi Mus’ab bai cika zama cikin gidan ya daxe ba in har mahaifinshi ba ya nan, ya sanyata barin abin da take yi ta bi bayanshi don ta gaishe shi. “Yaya na ga tsaraba na gode, Ubangiji ya qara girma”. Ta faxi bayan sun gama gaisawar. A hankali ya ce, “Babu damuwa, ina Baba ya je?” Ta ce, “Anyi rasuwa a cikin gari yana wurin karvar gaisuwa”. Ya juya wajen mahaifiyarshi cikin nutsuwa ya tambayeta wa ya rasu Inna? Ta gaya mishi gidan da aka yi rasuwar, ya yi addu’a Ubangiji ya ji qan musulmi suka ce amin. “To bari in je in yi musu ta’aziyya daga nan sai in samu baban”. Ta ce, “To”. Ya tashi ya fita, Saddiqa ta bi bayanshi tana tambayarshi cewa, “Za ka dawo tana nan ne?” Ya buxe motarshi ya zauna a ciki kafin ya juyo ya kalleta a yanayinshi na kowanne lokaci. “Mene ne in zan dawo ta nan xin?” Ta ce, “Akwai xanyen kifi ne masu kyau na san kana son farfesunshi sai in yi maka kafin ka dawo”. Ya juyar da kanshi ga kallon sitiyarin motarshi. “Ai ni na riga na yi fushi dake Aisha”. Cikin sauri ta tambaye shi, “Me na yi maka Yaya?” Ya ce, “Ai suna da yawa ba zan iya faxarsu a yanzu ba tunda sauri nake yi za ni wurin ta’aziyya, ina kuma son ganin Baba”. “To in yi farfesun kenan za ka dawo?” Ya ce, “In kina so insha farfesunki ki kawo min gidana, daga nan sai in samu damar gaya miki laifukan da kika yi min xin a nutse”. Ta ce mishi, “To”. Ya ja motarshi ya tafi, ita kuma ta koma cikin gidan. Gidan Mus’ab hamshaqin gida ne qwarai da ya gina shi a unguwar G.R.A, wato unguwar Turawa na garin Misau. Mafi yawancin gidajen dake wurin gidaje ne na ma’aikatan gwamnati, ko kuma dai masu hannu da shuni da suke sha’awar keve kansu daga hayaniyar cikin gari. Mus’ab ya gina gidan ne shekara guda bayan dawowar shi daga qasar Italy, inda yaje ya yi zama na shekaru bakwai bayan kammala karatun da ya kai shi. Ya gina gidan ne a Misau don cika burin da ya dawo a kai na kyautata mu’amala tsakaninshi da mahaifinshi, wacce ta gurvace tun zamanin quruciyarshi. Gidan Mus’am gida ne da ya amsa sunanshi, a garin Misau kawai ba har a garuruwa dake kusa duka kwatancenshi ake yi, shi da kanshi kuma ba zai iya faxin ga iyakacin dukiyar da ya kashe ba wajen gina gidan. Tun dawowarshi daga wurin ta’aziyyar zaune yake shi kaxai a cikin falon, zuciyarshi sai kai kawo take yi kan shirmen da ya yi na cewa Saddiqa ta kawo mishi farfesun gidanshi bai ce mata zai turo direbanshi ya xauke ta ba. To in ba ta zo ba fa? Ya tambayi kanshi. Dai-dai lokacin da ya sake mai da idanuwanshi kan agogo don ya qara ganin lokaci, qarfe uku ne da minti biyu, wajen awarshi biyu uku kenan rabonshi da ita. To farfesun kifi wani daxewa yake yi? Maigadin gidan ya yi sallama Mus’ab ya amsa da fitan isowar Saddiqa zai gaya mishi. Sai ya je ya ce mishi “Wasu mutane ne suke son ganin ka ranka ya daxe”. Takaici ya kama shi, ya ce, “Basu haquri Baba ka ce musu sai gobe su dawo”. Baba ya xan rusuna kafin ya ce mishi, “Masu lalura ne na kuma ji ka ce lalura ta ciwo in aka zo da ita……” Bai qarasa ba ya sake kallon Mus’ab a yanayin girmamawa ya ce, “Taimako suka zo nema suna mara lafiya ke garesu a asibiti”. Mus’ab ya miqe tsaye ya ce, “Jira ni”. Ya shiga xakinshi ya fito ya miqa mishi bandir xin dubu ashirin. “Ungo ka basu”. Baba maigadi yasa hannu biyu ya karva tare da yi mishi addu’a. “Yallavai Ubangiji ya saka maka da alheri, ya baka abin da kake nema na alheri duniya da lahira”. Addu’ar ta yi mishi daxi. Ya ce, “Amin Baba”. Huxu ta wuce Mus’ab yana zaune wurin da ya idar da sallar la’asar, har ya soma fidda rai game da zuwan Saddiqa, ya mai da hankali wurin jan carbinshi, lazimin yamma yake yi. Sai da ya gama ya yi addu’o’inshi ya shafa ya tashi, juyowar da zai yi sai ya ganta a zaun, cikin zuciyarshi daxi ne ya kama shi, amma bai yarda ya nuna ba. Sai ya ce mata, “Ke Aisha kin shigo min gida babu sallama, ya ya aka yi haka?” Ta ce, “Na yi hankalinka yana wurin sallar da kake yi shi yasa baka ji ba”. Ya ce, “To na yarda”. Ya zauna can gefe kan wata kujera suna fuskantar juna. “Ina jin dai da an fasa kawo min farfesun nan ne ko? Ko kuma an gama samari suka zo taxi aka mance da Yaya”. Cikin nutsuwa da girmamawa ta ce mishi, “Ka yi haquri, cewa na yi tunda zan kawo maka to bari in yi maka abincin dare”. Ya kalle ta ya ce, “Ke, ki ce min hankali ne dake ban sani ba”. Cikin zuciyarshi kuwa yanayin girmamawar da Saddiqa ke yi mishi ne ya fi tsaya mishi, so yake ta rinqa sakewa sosai don ya ji daxin jawota a jikinshi ta yanda zai canza yanayin shaquwar dake tsakaninsu daga yanayin shaquwa irin na qaunar zumunci da girmamawa, zuwa shaquwa ta mu’amala mai sauqi. “To me kika girka min?” Ya yi tambayar cikin sakin fuska sosai. Ta tashi ta xebi kwanukan ta kawo gabanshi tana buxewa. Ya zubawa abincin ido yana kallo cikin sha’awa. “Ashe dai aiki kika yi sosai, Ubangiji ya baki miji na kirki mai sonki ya sha lagwada a wurinki”. Ya tsareta da ido don ganin yanayinta. “Ba fa wannan saurayin naki nake yiwa wannan addu’ar ba, wani daban don ni bai kwanta min a zuciyata ba, sai nake ganin kamar akwai wanda ya fishi cancantar samun ki. Amma fa in maganar tawa ba ta yi miki daxi ba to ki yi haquri”. Bai kawar da kai daga gareta ba, ita ma tana nan a yanayinta na sunkuyar da kai qasa. “Kinga Baba maigadi da za ki shigo?” Canzawar yanayin maganar tashi ya ba ta damar da ita ma ta canza. Ta ce, “Eh, har ma ya tayani shigo da kwanuka”. Ya ce, “To dama shi nake so ki xibarwa abincin nan, bi ta can za ki ga qofa kicin ne, ki buxe ta ki shiga ki xebo plate nawa da naki da na Baba maigadi”. Ta ce, “Ai ni na qoshi”. “A’a, to a ina ake yin haka Aisha za a kawowa mutane abincin da kai ba za ka ci ba”. Ta sake cewa, “Na riga na ci a gida”. Ya ce, “To shi kenan, kawo mu ci zubana”. Ta tashi ta nufi inda ya yi mata kwatance, kicin xin da Saddiqa ta gani irin wanda take gani ne a mujallun Turawa da take karantawa, ko kuma a finafinan Indiya da take kallo, kusan mancewa ta yi da aiken da Mus’ab ya yi mata ta lalace wajen kallon tsarin kicin xin, bai da mace a gida amma ya yiwa kicin….. Kiran da ta ji ya yi mata ya dawo da ita cikin yanayinta, ta yi maza tasa hannu ta xebi plate xin da duk wani abin da ta san za ta buqata ta fita. “Hala kin tsaya kallon kyanki ne a madubi”. Maganar tashi ta sata jin kunya, ta sunkuyar da kanta. “Ai ba sai kin kalli mudubi za ki gane hakan ba, Aisha ke mai kyau ce, ko kina so ne ki nuna min cewar shi wannan saurayin naki bai gaya miki irin kyan dake gare ki ba?” Shiru ta yi ba ta tanka mishi ba, sai dai kuma ta kasa zuba abincin a sunkuye kawai take. “Ai in nine saurayinki kullum sai na gaya miki kina da kyau Ai…..” Yanayin da ya gani a fuskarta ya sa shi hanzarin canza maganar tashi. “To zuba mana abincin mana”. Ta zuba ta haxa a kan madaidaicin tire da nufin ta kai wa Baba maigadi, ya yi maza ya miqe ya xauka. “Yi zamanki bari ni in kai mishi”. Ya gama cin abincinshi ya qoshi ya xan kishingixa suna hira bayan ta kawar da komai daga wurin ta gyara ta mai dasu mazauninsu. “Hala Abu ke koya miki girki?” Ta yi murmushi ta ce, “Gwaggona fa?” Ya ce, “Uhm! Kin san ni ban cika sanin daxin abincin Inna ba, saboda sanda nake yaro sau da yawa na kan ci abincin ne bayan an yi min duka, ina kuka kuwa ai ba zan ji wani xanxano ba ko kuwa?” A hankali ta xago ta kalle shi a yanayin muryarta mai cike da nutsuwa ta tambaye shi, “Dama Gwaggo tana duka ne?” “Saboda bakya gagara shi yasa ba za ki san hakan ba, amma ni sanda nake yaro rigama ce dani, kina nufin baki tava jin labarin gagarata ba?” Ya yi tambayar yana mai kallon ta. “Uhm! Ai ba ta yin hirarka”. Suka xan yi shiru, jimawa kaxan sai ya sake shigo da wani zancen. “Wato kenan tunda kika gama sakandire shi kenan kin gama karatu ko? Kin dena neman ilimi kin fi so ayi miki aure ko?” Ta ce, “A’a”. Ya ce, “A’a, ya ya ne?” “Gwaggo ce ta ce ya isa haka”. “Shi yasa kike hira da samari? Kullum na zo garin nan sai na ganki kina hira da saurayi ko kunyata bakya ji ko?” Ta sunkuyar da kanta qasa. “Wai jiya ma har na shiga gidan na fito ko zuwa mu gaisa baki samu damar yi ba don kina tsoron kar ya yi fushi ko?” Ta ce, “A’a, ba zai yi fushi ba, ai shima ya ce wai zai zo ya gaishe ka kafin ka koma”. Mus’ab ya ce, “A’a, ya sha zamanshi bana son gaisuwarshi”. Ta xago ta kalle shi saboda maganar tashi, idanuwansu suka haxu ta yi hanzarin kawar da nata. “To meye gamina da shi da zai zo gaisheni? Ba yana zuwa gai da su Abu ba? Ki gaya mishi ni na ce bana son gaisuwar shi don ba zan yi surukuta da shi ba, ya rinqa zuwa gidan su Inna da su Abu da suka san da zaman shi suke kuma xaure mishi gindi, sai ko ke da na ji an ce wai kina mutuwar son shi”. Ta sake xagowa ta sake kallon shi a wani yanayi. Bai kawar da kai daga gareta ba ya ce, “A to, nima a bakin Abu na ji, abin da ta gaya min kenan wai kuna mutuwar son juna”. Ta sake kallonshi, “In ji Abu?” Ya ce, “Eh, ko ba haka bane?” Ta yi shiru. Ya ce, “In ba haka bane ai sai ki gaya min in ji”. Ta ce, “Ai ni na daina yin wannan maganar alqawarin da na yiwa Gwaggo kenan”. “To na ji kin yi alqawari, amma kina son shi ko bakya son shi?” Ta ce, “Ina son shi”. Falon ya yi shiru na wani tsawon lokaci saboda faxuwar gaban da Mus’ab ya samu. Ya yi qoqarin kawar da damuwar ta hanyar yin jarumtakar faxin “To ko kina sonshi ai yin karatu ba laifi bane”. Ta langavar da kai kafin ta ce, “Tunda Gwaggo ba ta so shi kenan na haqura”. Ya ce, “Haka ne Aisha, ga dukkan alamu dai kirki ne dake, don waxannan kalaman naki alama ne na zurfin nazari”. Ta ce, “Zan tafi, don Gwaggo ta ce kar in daxe”. Ya ce, “To Aisha, ai na gode miki kin yi min abinci mai daxi na ci na qoshi, ban da haka kuma kin yi min hira, iya kai dai hirar taki ba ta ishe ni ba, na kuma san in na ce zan biyoki gida mu qara ba yarda za ki yi ba, za ki ce saurayinki zai zo kar in zo in yi muku buqulu in hanaki hirar soyayya”. Ya zuba mata ido a yanayin zolaya, “Ga kuma irin toshin nan da samari ke yiwa ‘yammata in sun zo hira”. Ta yi murmushi ta ce, “Ba fa kullum nake hira ba Yaya, sau xaya nake yi a sati Juma’a, dace kake yi kana samuna ina hirar saboda qarshen sati kake zuwa”. Ya ce, “Ai shi kenan Aisha, zan iya yarda dake a kan komai tunda na san ba za ki yi min qarya ba”. Ya ce, “To yanzu tunda nima kin zo min hira me kika gani ya baki sha’awa a gidan nan?’ Ta yi murmushi ta ce, “Komai na gidanka ya bani sha’awa, musamman kicin xin. Sai dai ban buqatar ka bani komai na gode”. Ya tashi ya shiga xakinshi ya fito da kwalin handset ya miqa mata, ta zuba mishi ido nuna alamar ba za ta karva ba. “Gaskiya kyautukan da kake yi min sun yi yawa, ni wani lokacin ma har tsoro suke bani”. Ya tsareta da idanuwanshi ya ce, “Wace irin magana Aisha ke gaya min? Nine mai yi miki kyautar da take baki tsoro? Kina nufin su Bilki sun fi kusa dani ne? Don dai baki da wayo ne sanda Inna take raye ko? Ina ganin da ba sai na tsaya ina gaya miki muhimmancinki a wurina ba, ba sai na tsaya ina gaya miki cewar bani da wata wacce zan yiwa alherin da zai sani jin daxi fiye dake ba. Ni dama na daxe na gane yanda nake jinki ba haka kike jina ba”. Da sauri ta ce mishi, “Ba haka bane Yaya”. “To in ba haka bane ya ya ne? Yanzu da kin mai dani nine na fi kowa kusa dake kamar yanda kike a wurina kya gaya min wannan maganar don kawai na ce ga waya, ko gaisuwar safe ma rinqa yi da safe”. Tasa hannu biyu ta karva tare da yin godiya. Ya miqa hannu ya xauko xan makullin motarshi dake ajiye ya ce, “Muje in kai ki gida”. Ta ce, “To”. Sun fito harabar gidan kenan su kai kicivis da wata mota qirar Honda mai nambar Azare tana shigowa. Mus’ab ya kalle shi ya ce, “Sai dai ka jira ni in je in dawo don ba zan fasa mai da yarinyar nan gida ba”. Mutumin ya fito yana murmushi, ya ce, “To ka tsaya in zo mu gaisa mana don mu san juna ko kuwa?” Ya ce, “A’a, ba sai kun san juna ba qanwata ce wannan, don na ga kana wani murmushi”. Ya ce, “Eh, in dai gantan a haka tunda ku dama Fulani ai qannenku ne suke rikixewa su zama matanku”. Mus’ab ya ja mota ya tafi, sai da suka hau hanya sosai sannan ya ce mata, “Aisha”. Ta yi maza ta juyo gare shi. Ya ce, “Wannan fa shine Sham’unu abokina da nake zuwa wurin shi a Azare”. A nutse ta ce mishi, “Na gane shi, watannin baya ka zo bikin shi”. Ya ce, “Haka ne baki manta ba”. Qofar wani hamshaqin kanti ya tsaya, fuskarshi a xaure ya kalli Saddiqa a yanayi na rashin wasa ya ce mata, “Muje ki duba man shafawa”. Ta xan yi shiru. Ya fita ya rufe motar. Ya kusan minti talatin kafin ya fito, ana biye da shi da manyan ledojin sayayyar kantin guda biyu. Ya sake tsayawa a wani wurin ya sayi gasassun kaji sannan suka tafi gida. A qofar gidan ya sauke ta da kayan ya juya ya tafi. Cikin dare tana kwance a xakinta Mus’ab ya yi mata waya. “Tun xazu na so na bugo in tambaye ki wani abu sai na fasa don tsoron in bugo in sameki kina taxi”. Ta ce, “Taxi kuma Yaya? Ba ka ce in na gaya maka magana za ka gaskatani ba don ka san ba zan yi maka qarya ba?” Ya ce, “Qwarai kuwa Aisha, ai na yarda dake da kuma zan samu yanda nake so da kema sai ki yarda dani mu yarda da juna”. Ta ce, “To ai na ce maka sau xaya nake hira a sati, kuma xazu ka ce min in na zo gidanka za ka gaya min laifin da na yi maka na zo baka ce min komai ba”. “Dama maganar karatunki zan yi miki, to kuma na gane bake ce bakya son yi ba Inna ce ta ce ya isa haka ki yi aure. To ai ba zan ce kar ki yi ba Aisha, tunda na san alheri ne nima da kika ganni ina zaune haka tuzuru don tawa uwar ta rasu ne da ban kawo yanzu a hakan ba”. Ta kawar da zancen nashi ta hanyar tambayarshi, “Me kake son tambayata?” Ya ce, “Lokacin da nake yaro na san Inna da yawan nafilfilin dare, har nima ta kan tasheni ta ce wai in yi sallah in roqi Ubangiji ya shiryar dani, kema tana yi miki haka?” Ta ce, “Ai na riga na saba yanzu ba ma sai ta tashe ni ba da kaina nake tashi”. “To in roqe ki mana Aisha”. Da sauri ta ce mishi, “To”. “Ki rinqa yi min addu’a”. Ba ta ja maganar ba ta ce, “To zan yi”. Ya ce, “To sai da safe”. Saddiqa ta ajiye wayar tana tunanin tsakaninta da Yaya Mus’ab, a saninta dai tun tana ‘yar qanqanuwarta yana cikin mutanen da suke da muhimmanci a wurinta, saboda xinbin kulawarshi a gareta. Shi mai sonta ne, mai kula da ita, mai yawan alheri a gareta, a dalilin hakan ne ma ta fi kowa farin cikin dawowar shi. To amma a yanzu halin da take ciki, tana cikin ruxani ba ta fahimtar al’amuran, varin dukiyar da yake yi mata bai yi mata daxi, a ganinta ko ‘yan’uwanshi da suke ciki xaya ba ya yi musu haka. Washegari da safe ta idar da sallar asuba kenan ta ji qarar wayarta, ta sa hannu ta xauka. “Ina kwana Aisha?” Ta amsa, “Lafiya lau Yaya, ya ya gidan?” Ya ce, “Lafiya, sai dai ban yi bacci ba jiya”. Da sauri ta mishi, “Nima haka?” “Me ya hana ki bacci Aisha?” Ta yi shiru. Sai ta ji ya soma yin bayanin cewa, “Ni kin san ban iya voye-voye ba, tunanin aure ne ya hanani bacci, Aisha sai na ga ke gaki yarinya ‘yar qarama don sanda aka haifeki ina ganin kamar in ban yi sha bakwai ba na kusa, amma ga shi iyayenki sun tsaya suna son ganin sun aurar dake, ni kuma ina zaune a haka. Sai na ga to ai dama an ce wai in ka rasa uban da zai yi maka faxa sai ka ga wani yana yiwa xanshi faxa. To sai ka rava kusa ka ji abin da yake gayawa xan nashi, don kai ma ka amfana da kalaman nashi. Shi yasa na ce to bari nima dai in hankalta da abin da ake shirin xora ki a kai in yiwa kaina qiyamullaili, ko kuwa?” Cikin nutsuwa ta ce mishi, “ Haka ne”. Ta ja bakinta ta yi shiru. “To ni na gaya miki abin da ya hanani bacci ke fa? Me ya hanaki yin bacci?” A hankali ta ce mishi, “Anti Kuluwa ce ta zo gida jiya da daddare suna rikici da mijinta, ka san zai yi aure?” Mus’ab ya ce, “A’a, wa zai gaya min Aisha in ba ke ba? Inna ba ta hira dani, Baba kuwa cewa zai yi nima ba auren gare ni ba balle aje ana tsomani cikin lamarin rikicin aure, amma in zai yi aure Aisha sai ta je tana rikici da shi?” Ta ce, “Ai shi ya ja bai biyo ta hanyar son a zauna lafiya ba, lokacin da ya zo gaya mata zancen auren shi sai ya yi mata alqawarin canza mata kayan xaki, yanzu kuma bikin ya zo ya ce mata wai hidima ta yi mishi yawa bayan da can ba roqon shi ta yi ba. Shine abin ya tsaya min a rai, na ce to dama haka ake yi ne in za a kawo sabuwa sai ayi kamar ta gida ba sonta ake yi ba?” Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “To ni kam ina zan sani tunda ani ko xayar ma ban yi ba. Ai shi yasa na tsarawa kaina tunda dai ni na san kaina ni ba wani jarumi bane fitina tsoro take bani, don haka na ce to in dai har na samu na auri matata guda xaya in dai har na samu wacce nake so xin to ta isheni”. “Ai nima shine na ce ko randa za a yi min tawa amaryar ya ya zan ji oho”. Mus’ab ya qyalqyale da dariya ya ce, “Ya ya za ki ji kuwa ban da yanda sauran mata suke ji, ga dukkan alamu dai ina jin kishi za ki yi Saddiqa?” Ta ce, “To a yanzu dai kam ban sani ba tukunna sai a nan gaba”. Ya ce, “To da na y niyyar sai na dawo daga Kano in zo gidan, amma ina ganin zan zo yanzu kafin in tafi”. Ta ce, “To, sai ka zo”. Ta ajiye wayar. Mus’ab yana zaune a falon baban shi bayan fitar Malam Abdullahi jiran shigowar Saddiqa yake yi. “Wa alaikumus salam”. Ya amsa. Ta shiga ta zauna ta ce, “Ga ni Yaya”. Ya xauki rubutaccen chaque xin dake ajiye a gabanshi ya miqa mata ya ce, “Ki kai wa Kuluwa wannan chaque xin ta karvi kuxin ta yi hidimomin gabanta, ki gaya mata kar ta sake yiwa mijinta wata magana su zauna lafiya kawai”. Daxi ya kama Saddiqa ganin kuxin dake rubuce. “Yaya Ubangiji ya qara maka arzikinka”. Ya sake miqa mata envelop guda uku, “Ki kawai Bilkisu xaya, Hamida xaya, kema xaya, na san in za su sayayyar bikin za ki raka su”. “Mun gode Ubangiji ya dawo da kai lafiya”. Ya ce, “Ameen”. Da yamma Mus’ab yana gidan Abu, hirarsu suke yi irin wacce suka saba, yana kuma cin dambun zogalen da ta yi mishi. Saddiqa ta yi sallama ta shigo cikin kwalliya sosai mai ban sha’awa, ga yafen lafayan da ta yiwa jikinta ya yi matuqar karvarta. Rungume take da leda a hannunta, tana ganin Mus’ab ta qara fara’arta. “Ashe har ka dawo?” Ya ce, “Eh, tun la’asar nake nan gidan”. Ta tsuguna ta gaisheshi shi da Abu. Ta miqawa Abu ledar dake hannunta ta karva tare da faxin “Tsaraba aka kawo min?” Ta ciro ta, atamfar Diamond ce mai kyau, tare da kwalbar turare. “Atamfa na samu? To Allah ya yi albarka, hala yau ma zannuwan kika saya?” “Ka ji Abu, me zan saya? Su Yaya Hamida ne suka yi sayayyar kayan xaki, ni kuwa na sayi kayan ado. Yaya Kuluwa kuwa…. Ta qyalqyale da dariya kan ta yi bayani. Tsakin da Abu ta ja ya katseta. Abu ta ce, “Sakarya, ‘yammata suna tari ran bikinsu ka ga sun fito da kaya gwanin sha’awa amma ke kullum kuxinki a zannuwa kina tsoma su a ruwa shi kenan kin wanke kuxinki”. Ta yi dariya ta ce, “Amma ai kuma kwalliyar tawa tana burge ki ko. Tunda na sha jinki kina cewa daxin ki dani akwai ni da kwalliya, shi yasa ma duk tsiyata ba ta dame ki ba”. Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Aisha wani iya tsiya ne dake?” Abu ta yi maza ta riqe baki ta ce,”Wuuu! Ai ko sarkin fawa ya san da ita”. Mus’ab ya yi dariya ya ce, “Mahauta su ji abin da kike gayawa sarkinsu”. Ya yi dariya yana kallon Saddiqa ya ce, “Bani ruwa mai sanyi a randar Abu”. Ta miqe ta fita ta bar Abun tana cewa, “Kai kam tunda tana ganin girmanka ai ba za ka san iya shegenta ba”. Suna jiran dawowar Saddiqa yana yiwa Abu mitar “Kin bani dambu baki bani ruwa ba”. Ihunta suka jiwo ta qwalla qara mai firgitarwa, da gudu suka isa inda take tsugune a bakin randa, kuka take yi da iyakacin qoqarinta tana kuma riqe da qafarta da iya qarfinta da hannayenta duka biyu. “Mene ne? Me ya same ki?” Mus’ab ya tambaye ta. Ba ta yi magana ba kuka take yi sosai tana faxin, “Wayyo! Wayyo Gwaggona, a kira min Gwaggona”. “Me ya same ki Aisha?” Ya sake tambayarta a yanayin tashin hankali. “Gwaggo nake son gani”. “Me za ta yi miki in an kira miki itra?” Ta qara tsananta kukan tana faxin, “Zan gaya mata ne maciji ya sare ni”. “Maciji?” Da qarfi Mus’ab ya yi tambayar. Bai saurari amsarta ba ya sureta ya nufi waje da gudu da ita, ya bar Abu tana faxin “Babu maciji fa a gidan nan sai dai ko damatsiri”. Tana kwance shame-shame a motar tana ta faman kuka, sai salati Mus’ab yake yi, babu fa maciji a gidan nan damatsiri ne. Mus’ab ya dafe kai da hannu xaya saboda takaici. Haba Abu da kin bar wannan maganar, mene ne damatsiri mene ne maciji? Kina jin yarinyaa har ta fara sambatu. Suna isa asibitin ya sake surarta ya rungume a qirjinshi da gudu ya haura da ita saman benen ya shimfixe kan gadon da ba marasa lafiya. “Cizon maciji ne, likita cizon maciji ne”. Bayanin da yake yi kenan. Nan da nan aka shiga gwaje-gwaje da bincke don gano inda cizon macijin yake babu, sai kuma ya shiga gwajin dafi tsawon lokaci yana aikin. Ita kuwa Saddiqa ba ta ko buxe ido sai faman salati take yi Mus’ab yana taya ta tare da yi mata bayani, babu fa abin da zai same ki Aisha, ai ba za ki mutu ke kaxai ki barni ba, ai sai maraicin ya yi min yawa ni dake ai….” Tsakin Abu ya katse shi, ya yi maza ya koma inda take, ashe ma ta daxe tana harararshi bai lura. Haushi da takaicin Abu suka tarar mishi, ga shi babu halin ya ce ta koma gida saboda shakkar barin ta da yake yi. “Yallavai bana jin akwai dafin maciji a jikin yarinyar nan”. Tsit! Gaba xaya xakin ya yi har ita ma Saddiqan. Nan take ta tsai da kukan nata. “Babu dafin maciji, bamu samu wani dafi a jikinta ba”. Mus’ab ya juya ya fuskanceshi yana share gumin fuskarshi da hankicif. “Ban gane ba likita”. Likita ya yi cikakken bayani, ya ce, “Babu dafin maciji babu ma alamar cizon sa a nan, wannan kuwa ai bai wuce cizon kwarkwasa ba zo ki gani babu”. Ya juya yana kallon Abu. Abu tana matsowa a hankali tana faxin “Ni kam ai na santa likita, ai wannan ma ba komai bane cikin irin tsiyar da ta iya, babu shakka ita ce”. Mus’ab ya matsa jikin Saddiqa ya ce, “Aisha kin ga macijin da ya cije ki ne da idonki?” Ta ce, “A’a, amma dai na ga shukar bayan randar tana motsi”. Abu ta galla musu harara su dukansu, bayan ta ja tsaki mai qarfi haxe da faxin, “Aikin banza kawai har da na wofi”. Su Gaggo suka turo qofa hankal a tashe, da sauri Abu ta ce musu, “Duk ku kwantar da hankalinku, iya shegenta ne kawai ya motsa ta yi sha’awar ta-ta da hankalin mutane, gata nan ita ma ta amsa ba ta ga maciji da idonta ba, shukar bayan randa ta gani tana motsi”. “Sannu Saddiqa”. Gwaggo ta faxa tana mai kallon ta. “Yauwa Gwaggo”. Ta amsa cikin shagwava. Likita ya shigo da takarda yana nufin yin sallama, “Babu cizon maciji sallama zamu ba ta……” Mus’ab ya ce, “Ina ganin a barta a nan zuwa gobe ta qara samun nutsuwa”. Ya ce, “To, babu laifi, bari mu ba ta xaki”. Abu ta ce, “Ashe ba gara mu koma gida ba tunda dai yarinyar nan lafiyarta qalau?” Ya ce, “A’a, gara dai tana kusa zuwa goben in an qara tabbatarwa sai a tafi”. Suka koma xakin da aka basu, Abu tana mitar yanda Saddiqan ta kaxa musu ciki babu gaira babu dalili. Kafin yamma asibiti ya cika da jama’a, sai shiga suke yi suna fita, duk masu dubiya ne. Abokan Mus’ab ma suka yi ta kaiwa da kawowa. Gwaggo kam tuni ta bar wurin saboda ganin Mus’ab ya qi barin asibitin, sai Abu ce a zaune. Ita kuma tuni ta kawo Mus’ab iya wuya saboda yanda take yiwa masu zuwa dubiya bayani lafiyarta qalau iya shegenta ne dai da ta saba ya motsa, ana ta kwashewa da dariya. Mus’ab ya gaji ya kirata gefe ya ce, “Abu so nake…” Gane abin da yake nufi yasa ta galla mishi harara ta ce, “Yanzu ashe samarin nan da na ga kana tura min cikin gida sare min bishiyoyin gidan kasa suke yi?” Mus’sab ya ce, “A’a Abu, ni cewa na yi nemo macijin da ya sari Aisha su kashe shi a biyomu da shi asibiti, ina jin gurin neaman shi ne suka sare miki bishiyoyin”. “To in sunyi min ta’adi kuwa ni da kai ne”. ta juya ta tafi. Har wajen qarfe goman dare abokan Mus’ab sai isowa suke yi rungume da tsarabar majinyata niqi-niqi su ajiye, su kuma miqa abin miqawa wanda Abu ke karvewa tana adana abinta. Sadisu shima ya iso da tashi tawagar, sai dai ganin yanda Mus’ab ya kasa ya tsare ya hanashi iya zaman asibitin. Kwana biyu da sallamar Saddiqa daga asibiti tana kwance kan katifa a falon Gwaggnta, Abu da Gwaggon suna hira bayan tafiyar Sadisu da abokanshi. Ta ce, “Abu ba ki fa bani komai na abin da aka tara a asibiti ba”. Ta kalleta ta ce, “Tsarabar mara lafiya biyu na raba na xauki rabi na kawo muku rabi, kuxi kuwa qwandala ba zan bayar ba na riqe su ladan kwanan asibitin da aka sani”. Mus’ab ya yi sallama aka amsa, ya shigo cikin falon cikin shirin tafiya Ajakuta. Ya gai da mahaifiyarshi cikin girmamawa, sannan ya gai da Abu. Saddiqa ta ce, “Yaya kar dai tafiya za ka yi?” Ya ce, “Zan tafi Aisha yanzu cikin yardar Ubangiji”. Ya miqa hannu kusa da mahaifiyarshi ya ajiye mata envelop xin da yake sunne da shi. Ta ce masa, “Su Hamida sun je gidanka jiya za suyi maka godiya basu same ka ba”. Ya ce, “Eh, baba maigadi ya gaya min na kuma yi magana dasu a waya yau da safe”. Ya zaro walet xinshi ya qirga dubu biyar ya miqawa Abu, Saddiqa ta ce, “Duk kuxin nan da aka bayar a asibiti Yaya ba ta bani qwandala ba riqesu ta yi”. Ya ce, “Ba komai Aisha bari a qara mata”. Abu ta galla mata harara, ya yin da bakinta ke ta faman yiwa Mus’ab addu’a. Ya miqe ya doshi qofar fita, Saddiqa tana daga kwance ta ce, “Yaya Ubangiji ya tsareka”. Abu ta yi maza ta daka mata tsawa ta ce, “Tashi ki je ki yi mishi rakiya, ja’ira shagwavavviyar wofi, kin naxe wuri xaya kamar wata mai jinyar gaske?” “Kar dai a ce in ban da Abu ta yi miki magana ba za ki zo mu yi sallama ba?” Ta ce, “Uhm! Yaya Abun ce komai na yi ban fita a wurinta, in ta ga ma in zan yi rakiya ta ce ina vare-vare, in ban je ba ta ce ban san yanda ake girmama baqi ba”. Ya yi murmushi ya ce, “To gaskiyarki gara da kike yi mata hakan, in ta ce kije-kije, in ba ta ce kije ba ki yi zaman ki”. Ya zuba mata ido ya ce, “Amma kin san ba ki tava sha’awaa don ra’ayin kanki kin ce Yaya ga hotona na baka ba ko?” Ta ce, “Lah! To ai ban tava sanin kana so ba, to amma tunda ahaka ne kafin ka dawo zan ajiye maka su kala-kala”. Ya ce, “To shi kenan”. Ya buxe aljihun motarshi ya ciro envelop mai xan nauyi ya miqa mata, tasa hannu ta karva haxe da faxin “Wa zan kai wa?” Ya ce, “Naki ne ki qara kwalliya ki qara yin kyau Inna da Abu suyi ta ganinki suna qara jin daxi, kafin in dawo ina so ki cika min alqawarin da kika yi min”. Ta yi maza ta ce, “Insha Allahu”. Suka yi sallama ya tafi, ita ma ta shiga gida. RAYUWAR MUS’AB A AJAKUTA Gidan nashi babba ne qwarai, irin gidajen nan ne na ma’aikatan Ajakuta Star Rollin Company, yana zaune a gidan ne shi da wani tsohon abokinshi xan Bauchi da suka yi sabo tun sanda yake karatu a A.T.B.U. Mus’ab ne ya gayyato shi ya dawo gidan, duk da shi ba ma’aikatar yake ba don ya ragewa kanshi zaman kaxaici, ga kuma yawan tafiye-tafiye da yake yi, haka nan abutar tasu ta yi dai-dai, dan kuwa halayensu xaya ne. Mus’ab da Sani suna zaune a falo, karan sigari ne a hannayensu, labarin tafiyar Mus’ab ke ba shi. “Ai sa kai kawai za ka yi ka bar wani kamun qafa wurin kakarku, ka san su iyayenmu su kullum ya kamata suke basu san tuni aka bar wannan ba, ga na gida yana so yaushe za aje ana maganar na waje? Ina ce sai na gida ya qoshi ake miqawa na waje shima ya samu? Ka janyota a jikinka ka yi hikimar da za ka yi ta yanda za ka shiga tsakaninta da saurayin cikin hikima”. Mus’ab ya zuqi sigarinshi cikin jin daxi ya fitar da hayaqin a nishaxance ta baki ta hanci, ya kalli Sani a hankali ya ce mishi, “Ba fa yarinyar nake tsoro ba, mahaifiyata nake tsoro, ita ce kuma take riqe da ita”. Sani ya ce, “Ka dai yi qoqarin kammalawa da yarinyar tukunna”. Ya ce, “A’a, ana ga qura kai kana ga hayaqi, in baka sani ba Aisha za ta iya cewa tana sona mahaifiyata ta ce ba ta yarda ba”. Da sauri Sani ya tambaye shi ya ce, “A kan wane dalili?” Ya gyara zama ya ce, “Saboda tana ganin ban dace da auren yarinya irin Aisha ba, tunda ina shan wannan”. Ya xaga karan sigarin dake hannunshi ya nuna mishi. “Ta kuma riga ta san game dani, in na voyewa Aisha ba zan iya voyewa Inna ba. Ita kuma mai qyamar irin waxannan xabi’un ne, ina kuma tabbatar maka cewa ko cikin ‘ya’yan da ta haifa ban ga tana yiwa wani irin son da take yiwa Aisha ba”. “To yanzu kai tunda haka ne me ka shirya?” Mus’ab ya wurgar da guntun sigarinshi cikin ashtry ya sake xauko wani ya sake kunnawa, sai da ya yi mishi kyakkyawar zuwa ya fitar da hayaqin a hankali cikin nutsuwa, kafin ya ce mishi, “To gani nan dai Sani, ban san abin yi ba tukunna, na daia san kawai ina son Aisha, zan kuma tsaya in yi komai haar sai na ga abin da ya turewa buzu naxi”. Jeenifer ta shigo, daga xakin shi ta fito, banbancinta da mai tsirara kaxan ne. Ta nemi wuri a gefe ta zauna, ita ma sigari take sha, sai da ta zuqa sau biyu ta nisa sannan ta ce, “Ba fa faxan ya qare bane, don kar ka xauka tilastani da ka yi na yi abin da bana so yana nufin ya qare kenan, na gaji da abin da kake yi min kullum ina tare da kai amma wai ban isa in za ka Misau ka gaya min ba, sai kawai in zo gida in samu ka tafi, ni dama ba zuwan arziki na yi ba, don kawai ka gwada min fin qarfi ne kuma ba zai hanani yin faxar da ya kawo ni ba”. Sani ya qyalqyale da dariya ya ce, “Haba Jeenifer faxa ai ya qare tunda har aka yi haka sai dai nan gaba kar a sake tunda kin ce bakya so, nima shaida ne don haka kai Mus’ab ka ba ta haquri”. Mus’ab ya kalle ta ya ce, “To a kan wane dalili za ayi hakan? Kar in je ganin iyayena sai na sanar na nemi izini wajen wata? Ko kuwa don an ganni a bariki? Ko na tava gayawa wani cewa daga sama na faxo ba daga jikin iyaye na fito ba?” Sani ya ce, “Kai fa tsiyata da kai kenan, in an ce ka yi laifi ka ba da haquri sai kawai ka fi wanda ka yiwa laifin fushi”. Mus’ab ya ce, “A’a, rainin hankali ne bana so, iyaye wasa ne? Daina xaurewa qarya gindi Sani, bariki na je? Ba za a tambaye ni lafiyar mutanen gida kafin a ce min ga abin da na yi ba sai a rinqa muzurai ana yi min barazanar tashin hankali wai za a min tsiya? To tsiyar me za ayi min? Ko na tava cewa wani ina tsoron tashin hankali ne? Ni ba rufe ni da duka za a yi ba surutu ne kawai in na ga ya ishen kuma in yi waje da mutum in rufe gidana”. Jennifer ta zovara baki. Sani ya ce, “Gaskiya kema baki kyauta ba, da kika san gida yaje ai da sai ki tambaye shi mutanen gidan kafin ki yi maganar da za ki yi daga baya, don haka a dai yi haquri kawai maganar ta qare”. Ta zauna nan suna hira da Sani, Mus’ab ya kalle ta ya ce, “Zan fa ci abinci”. Cikin hanzari ta miqe ta shiga kicin ta soma aikin abincin da za su ci. Tana cikin shiryawa a falo bayan ta kammala ya yin da shi kuma Mus’ab yake tsaye yana gyara hannun rigarshi da ya naxe saboda alwalar da ya xauro, sai ga wata sisin ta shigo gidan tana takun qwas-qwas, tun daga bakin qofa ta sakar mishi murmushi. Ya ce, “Welcome Blessing”. Ta iso gare shi, kafin ya ankara har tasa hannayenta biyu ta rungumoshi tare da sumbatar kumatunshi, da sauri ya ture ta cikin takaici. “What nonsese is this Blesssing? Kina ganin ruwa a jikina ke baki san in anyi alwala ba a irin waxannan abubuwan ba?” Bai saurari maganarta ba ya fice cikin sauri don ya sake wata alwalar don kar ya rasa jam’in masallacin unguwar. Mus’ab ya dawo ya samu Sani a tsakiyarsu yana ba da haquri, ya kalles hi bayan ya wurga carbinshi kan kujera. “Kar dai yau ma baka je masallaci ka samu jam’I ba?” Sani ya ce, “Ai inda na tafin kuwa da ba ta yi kyau ba, don dambe suke yi mana a gida”. Mus’ab ya harari Sani ya ce, “Suyi mana dambe a gida hauka suke yi? Wace ce matata a cikinsu? To ko matan aure ai huxu aka bani ikon yi balle haka kawai daga ana zaman cin arziki sai kuma wata ta ce ba ta yarda a ci da wata ba. Ni duk matar da ta shigo gidana saboda ni sonta nake yi, in na ga dama in haxa biyu ko uku a kan gadona duk zan iya daku, gadon kuma mai faxi ne kar wata ta ce za ta tayar min da hankali”. Ya xebi abincinshi ya soma ci hankalinshi a kwance, ko kallon inda suke ba ya yi. Jenifer za ta yi magana ya katse ta. “Look, I want peace? Kin gane?” Ya tsareta da ido. Ta tsuke baki, ya tashi ya shiga xakinshi ya fito kowacce ya ajiye mata dubu goma a jikinta ya ce, “A gai da gida, in na yi marmarin ganinku zan nemo ku”. Jennifer ta watsa mishi kuxin da ya ajiye mata ta ce, “Azzalumi”. Ta wuce ta yi tafiyar ta. Ya bi bayanta da kallo tare da faxin “Kin huta”. Kwana biyu da dawowar Mus’ab yana kwance cikin kujerar kwando a harabar gidanshi da yamma yana shan iska, ya danna lambobin Saddiqa yana jin muryarta ya yi ajiyar zuciya a hankali. “Ya ya jikin naki Aisha?” Ta amsa da cewa, “Abu fa ta ce lafiyata qalau wai shagwava ce kawai”. Ya ce, “To ai ta dace dake, kin san ba duka mata ne suke kyau da yin shagwavar ba, amma ke kam taki tana bani sha’awa, sai in ji tamkar ina ma dai nima budurwata haka take kamar ki, da sai in rinqa barin komai in yi ta lalacewa wajen tarairayarta. Shagwava tana cikin abubuwan da suke burgeni, ban sani ba ko don ni xin ban tava samun damar da na yi ta bane”. Ta yi murmushi ta ce, “Yanzu nan kana nufin ko cikin quruciyarka baka yi shagwava ba?” Ya ce, “To wa zan yiwa Aisha? Inna dai kema kin san ban yi mata ba, dama a gaban Abu ne na xan fara aka kuma yi maza aka rabani da ita, ita kuma Innata da ya kamata in yi mata tunda ita ce ta jani a jikinta ta yi min duk wani abin da uwa ke yiwa xa na zo wurinta ne da wayona, ban kuma ma riga na saba da shagwavar ba. A lokacin nan qoqarina kawai bai wuce in jiyar da ita daxi ta hanyar yin abin da ta ce min in yi ba, in kuma bar abin da ta ce min in bari, wanda gaba xaya abubuwan da za su taimaki rayuwata ne, ban kuma gama mallakar hankalina ba sai kawai na rasata kwatsam, wanda ban tava zaton zan rasata ba”. Ya xan yi shiru kaxan, kafin ya ci gaba da cewa, “A kullum na tuna rayuwata a gaban Inna na kan tambayi kaina, ko inda na gama girma na gama mallakar hankalina a gabanta da wane irin mutum na zama?” “Irin yanda ka zama a yanzu mana Yaya, rayuwarka ai rayuwa ce da ta yi nasara…” Ya yi maza ya ce, “A’a, Aisha bar wannan maganar kawai, ni dai na sani ni da Kawuna muka fi kowa rashinta, don kullum na tuna ta tausayin kaina yana kamani, in kuma ji tausayin Kawu, mune har yanzu muke fama da maraicinta, ke kam kin daxe da mancewa da ita. Ko da yake dai dama can ba wani saninta kika yi ba”. A hankali ta ce, “Na santa mana”. Mus’ab ya ce, “Aisha wani saninta kika yi? Lokacin da ta rasu ai baki da wayo”. Ta ce, “Tafxijam! Shekarata fa bakwai ne”. Ya ce, “To na ji gaya min me kike tunawa da shi game da ita?” Ta ce,”Tana aikena in kai sadakar qosai wurin yara”. Mus’ab ya yi ajiyar zuciya ya ce, “Eh, xabi’arta ce yin hakan”. Ya sake yin ajiyar zuciya a hankali. “Kullum a cikin kewarta nake, na sani da tana nan da ban samu kaina a cikin halin da nake ciki ba a yanzu”. Ta ce, “Kai Yaya kullum sai ka ce matsaloli ni kuma bana ganar maka su”. Ya ce, “Uhm! Don ke yarinya ce da kin san ina dasu da yawa, yanzu misali zan miki ina da budurwa a nan Misau wacce nake so kamar raina, amma na kasa fitowa in nuna ina sonta saboda tsoron rashin samun goyon bayan iyayenta, da Innata tana raye da ba sai na buxe baki na ce ina son yarinyar ba za ta bani ita. To balle in ce mata ina so, ai da iyakar abin da zan yi kenan sai kawai ta gama min komai. To yanzu fa?” Ta ce, “Yanzu ma ai kana da yanda za ka yi Yaya, bana ganin kamar tsoro ko rashin samun goyon baya daga wurin wasu zai hanaka samun matar da kake so”. “To bani shawara mana Aisha na yanda zan yi in same tan”. Ta yi murmushi ta ce, “Ai ba sai na koya maka ba, hikimar samun macen da namiji ke so irin ganin xabi’arshi ne ba koya mishi ake yi ba. To balle ma kai ka girmeni nesa ba kusa ba, Inna ma cewa ta yi wai xan qiris ya rage shekarunka su wuce nawa”. Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Yawan shekaru ba shine hikima ba Aisha, yanzu ni xin nan da kike gani da qasumbar nan tawa da yawan shekarun nan nawa da Inna take gaya miki, da hali zai yi mu zauna wuni xaya ni dake da kin gane shekarun ne kawai da qasumbar amma bani da wata dabara”. Ta yi dariya mai qarfi ta ce, “Haba, haba ai kuwa da sai ayi mamaki”. Ya ce, “To shi kenan, amma ai kin san dama can dabarar maza ba ta kai ta mata ba”. Ta ce, “Haka nake ji wai”. Ya ce, “To madalla na yi sa’a da ba a bakina kika fara ji ba. To mazan da suka samu damar kusantar iyayensu mata ma kenan a shekarunsu na quruciya, to balle ni da ban samu hakan ba. Shi yasa nake jin wani lokaci zuciyata tana raya min to ko dai zan qulla abota ne ni dake”. “Abota kamar ya ya?” Da sauri ta yi tambayar. Ya ce, “Kamar ta baiwa juna shawara in ina da matsalar da ta shafi budurwar tawa in gaya miki komai, in kina tare dani xin za ki qarfafa min, kin sani ko cikin ‘yan’uwa Aisha akan samu wanda ya fi kwanciya maka a rai, sai ki ga bayan qaunar zumunci dake tsakaninku sai ki ga kuma akwai wata fahimta ta daban da take haddasa musu shaquwa. Yanzu in da za a tambaye ni a ce Mus’ab cikin ‘yan’uwanka duka wa ka fi so? Ai in aka barni sai in ce kece, in aka sake tambayata shaquwa fa? In sake cewa Aisha, kamar yandaa na san kema za ki ce nine”. Ta yi maza ta ce, “A’a, ya ya ka yi ka sani bayan ga ‘yan’uwa da yawa ina tare dasu a Misau?” Ya ce, “To ai kin ji, dama na gaya miki bani da wayo, ganin da na yi in na zo gida kina tarairayata kina girmamani sai na xauka ko yanda nake jinki a jikina haka kema kike jina, ni in ina kusa dake wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa nake samu, na kan kuma barki ne don tsoron kar in gundureki. To amma tunda kin faxi haka, to gaya min tsakanin ni da saurayinki wa kika fi shaquwa da shi?” “A’a, Yaya ai maganar ‘yan’uwa muke yi”. Ya yi maza ya ce, “Eh, haka ne maganar ‘yan’uwa ne, to wa kika fi shaquwa da shi a ‘yan’uwan?” Hankalinta a kwance ta ce mishi, “Anti Hamida, bana iya yin kwana biyu ban je gidanta ba”. Ya xan yi murmushi saboda jin da ya yi tamkar taya shi son Hamidan take yi. “To ai ita kun girma xaki xaya ne Aisha, ba shekaru biyu da suka wuce bane ta je gidan auren ta? Ban da ita gaya min wani”. Ta ce, “Yaya Bilki”. Tsoron kar ya sake tambayarta ta sake faxin “Yaya Kuluwa”. “Ko wani can ma daban”. Ya sanya shi yi mata maganar. “To yanzu xin ni dake mun qulla abota a yau, don ki rinqa bani shawara kan neman auren da zan fara in na yi sa’a yarinyar ta soni to nasarar taki ce, in ba ayi ba ma na san ke ce, don haka mu fara daga yau. Mene ne abin yi tunda na riga na bayyana miki komai?” Ta ce, “Ka fuskanci yarinyar kawai ka daina maganar tsoro, ai kana da kwalitis xin da za ka nemi aure a ko’ina ne a baka, don kai kanka ba sai anyi maka jagora ba”. Ya ce, “Haka kike gani ko Aisha?” Ta yi maza ta ce, “Eh mana, kana da ilimin addini, kana da na zamani, kana da matsayi irin wanda mutane da yawa suke buri basu samu ba, kana da cikakkiyar halittar da zance ‘yammata da yawa za su yi burin samun miji irinka”. Kamar ya tambayi Saddiqa har da ke? Sai ya kanne ya ce mata, “Ai inda matsalar take ban tsoro shine wurin iyayen yarinyar, sun riga sunyi min wani irin sani basu bar ‘yarsu ta yi min irin wannan kallon ba, amma tunda kika faxi haka to bari zan gwada in bi shawarar ki na yiwa yarinyar magana ni da ita, zan taho Misau kwanan nan amma zan qara kintsawa. Ke kuma sai ki qara sani a addu’a don yarinyar samari ne da ita”. Ta yi dariya ta ce, “Baka dai daina tsoronta ba kenan?” Ya ce, “A’a, na daina……” Fizge wayar da aka yi shine ya katse zancen nasu. Cikin takaici ya zuba mata ido. “Who are you talking to?” Ta yi tambayar cikin takaici. “You are stupid florence”. Ya faxa mata. Sannan ya ci gaba da yi mata magana cikin Turanci. “Kin san da wa nake magana? Daga Misau ne fa”. Ta ce, “Sai me? Duk Misau ne iyayenka? Wannan hirar kai da budurwa ne tun daga nesa nake hangen nishaxinka, wacce ‘yar iska ka samu a can xin da ta sameka haka?” Ya ce, “A’a, kar ki zageta”. “Me za ka yi in an zage tan? Ai dama da cikinka na zo gidan yau ina son jin inda ka samu shegiyar da na ganka da ita jiya”. Ya yi murmushi ya ce, “Florence kenan, daxina dake akwai ki da bagu”. Ya miqa hannu ya jawota jikinshi. “Tunda kin bar maganar farko to zauna mu yi wannan a zaune ai zamu sasanta, tun jiya ai na gaya miki ba budurwata ba ce”. Ta galla mishi hara ta ce, “Ba budurwarka ba ce ka gabatar mata dani a matsyin budurwar abokinka”. Ya yi maza ya ce, “Ni?” Yana mai nuna qirjinshi da xan yatsanshi. “Kece na gabatar a matsayin budurwar abokina Florence ba ita ce na gabatar miki a matsayin buduwar abokina ba”. Ta ce, “Abin da na ji ka faxa kenan nice budurwar abokinka”. Ya ce, “To baki daidai ba, kuma na gane kina da munafukan kunnuwa waxanda basa jin magana daidai saboda suna son ganin ana faxa ni, ni kuma ba abin da yake gabana ba kenan yanzu”. Ta buxe mishi baki za ta yi magana ya yi maza ya ce, “Ina jin dai kin samu wani saurayin ne yasa kika matsa sai anyi faxan nan don ki samu hanyar rabuwa dani”. “Ba haka bane”. Ya ce, “To in ba haka bane zo ki gani”. Ya miqe ya kama hannunta ya ja ta zuwa xakin kwanciyar shi. Ranar litinin a wurin aiki bayan sallar azahar ya fito daga masallaci yana nufin komawa ofis xinshi ya hango Jennifer tana sauri saboda ganin da ta yi mishi, shima ya xan xaga kansa kaxan. Tana shiga ta yi nufin turo qofar ta rufe ya yi maza ya tare qofar da hannunsa, ya shiga ya turota. Yana shiga ya cafketa ya xora bakinshi a nata tsawon, har sai da ya haxata da jikin bango saboda kici-kicin qwatar kanta da take yi. “Me na yi miki kike guduna?” “Fita min daga ofis xina”. Ta faxi cikin tsananin vacin rai. Bai kula ba ya ce mata, “Ki zo gida yau sai mu yi magana”. “Never in my life”. Bai kula ba ya ce, “To shi kenan ni zan zo gidanki hira yau, amma in na zo na samu wani kema kin san sauran”. “To ka bari sai na neme ka mana ka sa min doka”. Ya yi murmushi ya ce, “Ai ba haka nake ba, na kan daidaita al’amura ne in zan yi su”. Idanuwanta suka cicciko. Ya fita ya bar ofis xin ya nufi nashi, yana shiga ya danna lambobinta. “Kar ki ajiye min waya Jennifer, gaya min kawai za ki zo xin ne ko ni in zo naki gidan?” Cikin takaici ta sake ce mishi, “Na daina zuwa gidanka”. “Ai babu damuwa, ni zan zo”. Ya ajiye wayar. Jennifer ta zubawa wayar dake hannunta ido cikin takaicin al’amarinta, ga samarin dake sonta kamar suyi hauka ta qi basu haxin kai sai Mus’ab, mutumin da kullum sai ranta ya vaci a kanshi, ga shi ko ta yi niyyar xaukar mataki mai tsanani game da shi tana ganinshi sai ta kasa aiwatar da komai a kanshi sai yanda ya yi da ita. Yana kwance a xakinshi bayan ya dawo daga yawonshi na qa’ida zuwa club, juyi yake yi a kan gadon barci ya qi xaukar shi duk da sai da ya kora barasarshi da ya fi ta’ammali da ita wato ‘Bacchus’ kafin ya iso gidan. Ya sake wani juyin a hankali kafin ya kira sunanta “Aisha”. Ya buxe idonshi a hankali ya ga tamkar ita ce a gefen nashi a kwance, da sauri ya sake rintsewa ya sake buxe su “Wato ni kike wa gizo ko? Ja’ira zan kama ki”. Tunanin kama tan ya shigo cikin ranshi, nan take ya tambayi kanshi anya zai kamata kuwa? Nan take ya kunna fitilar xakin saboda wattsakewa da ya yi, biyu da rabi ne na dare, ya rasa me zai yi ya miqa hannu ya xauko wayarshi da nufin ya tura mata saqon da za ta gani da safe, ya yi rubutu kamar haka. “Aisha! I wrote a list of my friends I smile. I wrote a list of my those I still have. I still smile I wrote the list of those lam keeping for ever I still smile because your name of still there. Mamaki ne ya kama shi yanda minti biyu kawai bayan tafiyar saqon ya ji wayarshi ya kama ruri, a hankali ya tambaye ta me kike yi yanzu idonki biyu Aisha? Ta ce, “Na idar da sallah ne ina istigfari”. Gabanshi ya ba da ras! Nan take ya qara dawowa cikin nutsuwarshi. “Kin yi min addu’a?” Ta ce, “Eh, na yi maka na yiwa Inna ma tare da sauran musulmin da suka rigamu, ai tun ranar da ka ce min in rinqa yi ban tava fasawa ba”. “To na gode Aisha, na gode da kike xaukar maganata da muhimmanci, ga shi kina yi min addu’a ni ina kwance”. “A kwance kake?” Ya ce, “A kwance naka amma na kasa yin bacci saboda damuwa ta min yawa, ina cikin soyayya mai zafi, ina son yarinyar da nake gaya miki xin nan, ina cikin zullumi Aisha, ina cikin fargabar abin da zai biyo bayan fuskantar ta da nake shirin yi”. “Amma mun yi dai a kan ka daina tsoro”. Ya ce, “Eh, fargaba nake da zullumi ba tsoro ba, abin da zan tarar wurin iyayenta ne ya fi damuna, kin san ni xin tsohon mai laifi ne, Inna ba ta tava baki labarin laifina ba?” Ta ce, “Ai na gaya maka ba ta hirarka da wani, kuma ba zai yiwu a ce yanda Inna take kallon ka haka suma iyayen yarinyar za su kalle ka ba, don haka kar ka sake jin zullumi ko faxuwar gaba”. Ya ce, “To na gode da shawararki Aisha, sai da safe”. Mus’ab yana kwance tare da Jennifer a xakinshi wunin ranar asabar ne, tausa take mishi saboda kukan kasalar da ya yi mata. Wayarshi ta yi qara yasa hannu ya xauka, Sani ne a kan layin. “Kana fa da baquwa a nan falon za ka samu fitowa ne ko in ce baka nan?” “Wace ce?” Ya ce, “A’a, ba zan faxa ba in dai in sallameta kawai to”. “Gani nan zuwa”. Ya yunqura ya tashi daga kan gadon ya xauki shirt xin da ya cire yana mayarwa tare da valla botir xin. “Ina za ka ne?” Jennifer ta yi tambaya. Bai kalle ta ba ya ce, “Na yi baqi a falo”. Da sauri ta ce, “Baqi ko ‘yan iskan ‘yammatan da suka saba biyo ka gida?” Ya ce, “Ai dukanku xaya”. Ya fita. Ta yi maza ta wuto shi ta riga shi shiga falon. “Yi maza ki bar falon tun ban ci mutuncinki ba”. Ta baiwa yarinyar umarni. “Yi zaman ki Sarah tunda wurina kika zo”. Daga bayan Jennifer ya yi maganar. Ta juya ta kalle shi ta ce, “Amma kai ka ce min in zo gida ka yi tsari mai kyau na wanda ya riga zuwa shine maigida”. Ya ce, “Eh, amma ai hakan ba yana nufin ba zan ga baqi bane, ina son ganin Sarah”. Ta qara fusata ta ce, “Ai tunda ka gaya min haka ka sani na zo sai na fidda wannan ‘yar iskar daga gidan nan”. Ta yunqura za ta cafketa ya yi maza ya kamata ya riqe, ta xago hannu da nufin wanke shi da mari ya yi maza ya kama hannun ya murxe. Kafin ya sake shi cikin nutsuwa ya ce mata, “Kar ki fara don zai sa ki gane baki da wayo”. Ya jawota suka fito harabar gidan tana antaka ashar, hankalinshi a kwance ya ce mata, “Haba Jennifer a gaban wannan ‘yar qanqanuwar yarinyar kike wannan haukan, kin kusa ki haife ta fa, wannan ai abin kunya ne”. Haushin shi ya sake kamata, cikin takaici ta ce mishi, “Tsohon banza kai meye? Kai baka girmeta ba?” Ya yi murmushi ya ce, “Na girmeta mana amma ke kam ai sai dai mu yi sa’o’i ko in xan baki shekara haka”. Ta zuba cikin takaici, ta gaji ta ce, “Laifina ne da na zo gidanka”. Ta juya ta kama tafiya. Shi kuma ya wuce ya shiga cikin falon yana murmushi, ya ce, “Sorry Sarah”. Ta xan yi murmushin qarfin hali. Ya ce, “Me zan kawo miki?” Ta xan yi shiru. Ya sake tambaya “Bacchus ko Whiskey? Wanne zan kawo miki?” A hankali ta ce, “Za ta gwammace whiskey”. Ya yi murmushi ya koma, jimawa kaxan ya shigo da tire mai xauke da kwalbar whiskey tare da kofi guda xaya ya ajiye ya zuba, ya xauka ya miqa mata ya koma kan kujera ya kunna karan sigarinshi na Rothmans. Ta bishi da kallo alamar tambaya, ya xan yi murmushi ya ce, “Yi haquri ki sha ke kaxai kinga azahar ta yi zan yi sallah”. Ta yarda da uzurin nashi, ta ci gaba da sha shima yana zuqar sigarinshi cikin nishaxi. “Amma ai ba kina nufin tun gamuwarmu dake a liyafar Bola sai yau ne kika tuna dani ba ko?’ Ta yi murmushi ta ce, “Tafiye-tafiye ne suka yi min yawa, yanzu ma gani na yi bai kamata in yi Birthday xina ban gayyace ka ba shi yasa na zo”. Kiran sallar da ya jiyo yasa shi ya miqe. “Sarah za ki xan jirani kaxan”. Ta ce, “Babu damuwa”. Ya fita ya barta ita kaxai a zaune, ita ma ta samu damar da ta yiwa falon kallon kyau, tsarinshi ya kai yanda ya kai, ga kuma hotonshi dake ajiye a can gefe. Ta yi ajiyar zuciya, komai nashi ya yi, sai dai da alamar manemin mata ne sosai. Yaron gidan ya kawo mata gasasshiyar kaza da abubuwan ci da na sha. Fiye da wa xaya da rabi tana zaune kafin Mus’ab ya shigo. “Yi haquri Sarah na tsaya ne a masallaci na yi la’asar. Sun kawo miki abinci kuwa?” Ta ce, “Eh, sun kawo na ci har na qoshi”. Ya ce, “A’a, ba ga salad na ga baki tava ba? Me za ki ci a shirya miki?” Ta ce, “Ai ni yanzu ma zan tafi”. Ya ce, “A’a, to ai ba ki gayyace ni Birthday xin ba kenan, kina nufin in karvi gayyata a kwali ko a fatar baki?” Ya tashi ya shiga xakinshi ya fito riqe da dairy da biro a hannunsa ya koma kusa da ita ya zauna. “Yaushe ne Birthday xin?” Ta faxa ya rubuta, “Saura kwana biyar kenan?” Ta ce mishi, “Eh”. “To ai akwai shirye-shirye kenan”. Ta sake ce mishi “Eh”. Ya sake zuba Whiskey a kofi ya sake miqa mata ta karva. “Nawa kike ganin za a kashe?” Ta soma magana cikin yanayin rangwaxa ta ambato abin da take ganin ta yi qoqari. Yasa hannu ya karvi kofin dake hannunta ya ajiye. “To zo daga nan mana”. Yasa hannu ya kama nata ya ce, “Muje in ga abin da zan iya bayarwa”. Suna kwance a xakin nashi cikin yanayin gajiya, kowanne a cikinsu mai da numfashin shi yake yi a hankali. “Sai yaushe za ki sake zuwa?” “Ai kuma na ji tsoron zuwa gidan naka tunda ga abin da na gani”. Sai da ya fitar da hayaqin sigarinshi da ya zuqa sannan ya ce, “Da kika ganin me ya same ki? In dai kina da aiyuka da yawa shi kenan babu matsala”. Ya miqa cek xin dubu hamsin tana daga kwance. “In kin fita sai ki xauka Acces Bank, bana zaton zan iya zuwa Birthday xin don zan tafi Misau a ranar, in na dawo zan zo in kawo nawa gift xin, in kuma kin rigani samun sararin zuwa gidan to sai ki zo ki karva da kanki”. Ta yi godiya cikin jin mamakin kyautar da ya yi mata. Mus’ab ya isa Misau, Saddiqa ce kaxai a tsakar gida tana wanke-wanke lokacin da ya yi sallama ya shiga gidan, ta xago kai ta kalle shi cikin mamakin zuwan nashi. Suna haxa ido ta kwashe da dariya, ya ja ya tsaya yana kallon ta cikin mamakin dariyar tata, ita kuwa sai qyalqyala dariya take yi. “Me ya faru?” A yanayin mamaki ya yi tambayar. Ta ce mishi, “Haba Yaya, yanzu nan qasunbarka ka aske?” Ta sake fashewa da wata dariyar ta ce, “Ai kuwa dai baka ga yanda fuskarka ta yi ba, sai ta yi sarari”. Ya ce mata, “Eh, canji-canji zan rinqa yi, in yau an ganni da qasumba wani zuwan sai in aske, saboda in yau ta ganni a dattijo gobe sai ta ganni a yaro, in ba hakan nake yi ba zuge min ita za ayi a ce mata ni xin tsoho ne”. Saddiqa ta ce, “Tafxijam! Ai kuwa in nice budurwar taka duk randa ka zo da askakken qasumba sai in qi yin hirar, kayi-kayi kuma in qi gaya maka abin da yasa ka ga canji”. Leqowar Inna tana tambayar “Ke da waye”. Shi yasa hirar tasu ta katse. Ya nufi falonta suna gaisawa, ita kuwa Saddiqa ta ci gaba da aikinta har ya fito ba ta gama ba. “Hala askin ne ya hana ki zuwa gaisheni”. Ta sake wata dariyar ta ce, “A’a, ban san za ka fito yanzu bane”. Ta biyo bayanshi suka fito inda ya yi parking xin motar da ya zo a ciki Bora qirar Vokewagen. Ya buxe but xin yana cire kayan da ya zo dasu yana ajiyewa, ya xan kalle ta. “Wato ma ni kike yiwa dariya ko Aisha?” Ta yi murmushi ta ce, “To ka yi haquri kasa daurewa na yi, ka san ni ban tava saninka babu qasumba ba”. Ya ce, “To na ce baki da wayo sanda Inna take nan kin ce kina da shi, ai ni qasumbata ina Italy na barta, kuma ai kin san wannan zuwan taxi na yi”. Ta ce, “To maimakon ka je da kwarjininka sai kuma ka ragewa kanka kwarjini? Gaskiya ni ban ji daxin askin da ka yi ba”. Ta zovara baki. “Yi haquri Aisha, nan gaba ba zan sake ba ko da kuwa ita budurwar tawa ba ta son qasumbar. Ko da yake ma ina ganin kamar ra’ayi xaya ke gareku”. Ya gama sauke kayan ya kalle ta ya ce, “Za ki iya zuwa gidan Abu yau da yamma? Ko da yake ma yau ne ranar zuwan saurayinki”. Ta ce, “Eh, sai dai in Inna ba ta barni ba”. Ya ce, “Gara dai ta barki”. Cikin sauri ta ce mishi, “Zamu wurin ta ne?” Ya ce, “Eh, in hali ya yi sai muje xin”. Ta ce, “To zan zo”. A gidan Abu bayan sallar la’sar Mus’ab yana zaune a rumfarta suna hira, yaron da ya aika Bauchi ya shigo rungume da qatuwar takarda a naxe, ya zo ya ajiye musu. Mus’ab ya sallame shi ya tafi. Abu ta jawo takardar gabanta ta buxe, cikin mamaki ta ce, “A’a-a’a, duk wannan kilishi ne haka?” Ya ce, “Eh, ai tunda na gane da shi ake yi miki toshiyar baki, to kullum shi zan rinqa kawo miki”. Abu ta yi dariya ta gutsiri kilishin ta saka a baka tana taunawa a hankali suna hirarsu cikin nutsuwa. Mus’ab ya ce mata, “Abu ina so ki isar da saqona wurin Inna na riga na yi niyyar neman auren Aisha ba zan fasa ba. To amma kuma ina ganin bai kamata in yi ta yi kai tsaye ba a sanar dasu ba saboda girmamawa, don haka a sanar dasu ina cikin manema ‘yarsu don su sani a wurina girmamawa ne”. Abu tana cin kilishinta tana korawa da ruwan lemon kwali ta ce, “Kai kam kafaffen mutum ne, in da rabon za a lissafaka cikin waxanda aka kayar ai babu makawa sai anyi hakan”. Ya yi murmushi ya ce, “Eh, babu komai tunda ba zan zama nine na farko ba a jerin mazan da aka tava kayarwa wajen neman aure ba, ba kuma zai yiwu a ce nine zan zama na qarshe ba, a ce daga kaina an daina, ko shi gwanin da kike so xin ai an gaya min aure ya nema aka ka da shi, shine aka yi fushi aka yi nufin share mishi hawaye da Aishan”. Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “Kai kuwa a ina ka samo wannan labarin?” Ya yi shiru yana kallon ‘yan yatsun hannunshi. “Ka kuwa san shima ya tsargu da kai?” Mus’ab ya xago ido ya kalle ta cikin sauraro, a zuciyarshi kuwa daxi ya ji, sai dai ya voye. Tana murmushi ta xan rage murya wai za ta yi mishi tsegumi. “Ai na je gidan su Saddiqa na samu rigima tsakaninta da Gwaggonta wai ta qi fita hira wajen Sadisu, shine na tambaye ta dalili ta ce, wai kullum ya zo sai ya yi maganar Yaya Mus’ab, ta ce mishi ya daina ya daina tunda ba alheri yake faxi a kanshi ba ya qi dainawa, don haka ta daina zuwa hirar tashi. Na ce to ta yi haquri ta je in sake yi mata maganar ka ta gaya min ni zan ce mishi ya daina don a zauna lafiya”. Sallamar Saddiqa ta hana Mus’ab faxin komai, ta shigo cikin kwalliya sosai, wani haxaxxen leshi ne a jikinta mai ruwan bula, ga duwatsunshi sun haxu sai xaukar ido suke yi, tana tafe a yanayin takun ta mai cike da rausaya ta qaraso tana kallon Mus’ab ta saki wani lallausan murmushi. Ya ce, “In kika sake yi min irin dariyar da kika yi min a gidan Inna ba yarda zan yi ba”. Ta rufe baki da hannu xaya wai tana qoqarin danne dariyar, ta wuce can gefen Abu ta zauna tana gaisheta. “Abu ke baki yiwa Yaya magana a kan askin qasumbarshi ba?” Abu ta xago kai ta kalli Mus’ab ta kawar tana sha’aninta. “To ni ina gamina da shi da zan tsura mishi ido sai na gane abin da qasumbar shi ke ciki, da ta fi haka kenan?” “To ai kuwa dai da ta yi yawa”. Saddiqa ta ce, “Ka ji Abu”. Ita ma ta kawar da zancen. “To wai ni ba an hana mata fita da irin wannan qamshin bane?” Ta ce, “A’a, Abu na aure ba? Ai ni ba matar aure ba ce”. Abu ta tave baki ta ce, “Ai sai ki yi”. Har kusan awa guda da zuwanta hira ake yi. Ta kalli Mus’ab. “Yaya ba zamu bane?” Ya ce, “Zamu”. Yasa hannu ya xauki xan makullinshi ya ce, “Abu zamu unguwa Aisha za ta rakani wajen budurwata ta ganta”. Abu ta ce, “Sai kun dawo”. Ya yi parking xin motarshi a harabar gidanshi. Ta ce, “A’a, gidanka kuma muka zo?” Ya ce, “Eh, nima zan yi wanka in yi kwalliya don kar ki fini cinyewa a wurinta, don haka fito mu shiga”. Ta yi murmushi ta ce, “Amma sai dai ka yi sauri don kar dare ya yi”. Da sauri ya ce, “Af! Hakaa ne fa, yau ranar taxi ne ga shi kuma da so nake ki yi min girki kafin mu tafi don yunwa nake ji, ko za ki vata kwalliyarki”. Ta ce mishi, “A’a”. Ya miqa hannu yana tayata zare gyalen dake jikinta tare da faxin “Kawo mayafin in ajiye miki don saurayin ki zai zo hira ai ba za ki bar yayanki da yunwa ba ko kuwa? Ban yarda na ci wani abu tunda na taso, na xauka zan zo in samu kin yi min wani tanadi”. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ai ban san da zuwan naka bane”. Ta xan kalle shi ta ce, “To yanzu me za ka ci?” “Oho! Duk abin da kika yi kika bani zan ci, ni dai kawai in ji na qoshi buqatata ta biya kenan”. Ta ce, “To shi kenan”. Ta shiga kicin ta soma shirye-shiryen yin girki. Mus’ab ya biyo ta ganin yanda ta sake a ciki ya ba shi sha’awa, ina ma dai bayan aurensu ne take wannan aikin. Ta kalle shi da gefen ido saboda ganin tsayuwar da ya yi. “Ai na xauka wankan za ka yi akfin in gama”. Ya xan qara matsowa ya ce, “In ina jin yunwa ai bana iya komai, har gara ma in zo nan ina taya ki wasu abubuwan don ki fi saurin gamawa”. Ta ce, “To bari in yi maka jelof”. Ya ce, “Babu matsala, sai dai zan sha farfesu”. Ta ce, “To”. Yana taya ta aikin yana yi mata hira. “Za ki yi kyau da karatu Aisha”. Ta ce, “A’a, bai dame ni ba Gwaggo ba ta so”. Ya ce, “Eh, ai daxina dake kenan biyayya, in Inna ba ta son abu shi kenan sai kema ki qishi, ina fata dai kin cika alqawarin da kika yi min na hotuna”. Ta yi murmushi ta ce, “To me za ka yi da hotunana bayan ga sabuwar budurwarka ka samu kuma ban ganka da hotonta ba”. A hankali ya tambaye ta ya ce, “Kina kishi ne?” Da sauri ta juyo ta kalle shi, ya yi kamar ba daga bakinshi maganar ta fito ba, don haka ta ci gaba da aikinta, shima yana nashi na yankan albasa da tafarnuwa. “Kishi!” Ta faxi kalmar cikin zuciyarta. “To a kan me za ta yi hakan?” Nan da nan ta ji wani bayanin na daban yana zuwa mata. “Ai kuwa Abu ta tava gaya mata cewar akwai aure tsakaninta da yayan nata, ban da haka jangwarzo ne da iya gaskiyarta kuma ta faxa kowace budurwa za ta yiwa kanta sha’awarshi”. Ta yi maza ta tsayar da wannan tunanin ta hanyar tunawa kanta Sadisu Gwaggo take so ta aura, don haka maganar ta qare. “Ga albasar Aisha”. Ta juya ta karva, maimakon ya bar wurin sai ya qara matsowa ya ce, “Na ce ba Aisha”. Ta ce, “Na’am”. A hankali ya tambaye ta, “Kina son wannan mutumin ko son baki ne, ko kuwa dai kin yarda ne don ki farantawa Gwaggonki rai?” Ta dakatar da abin da take yi kafin ta xago da nufin kallon shi, kallon da yake yi mata ya sata sunkuyar da kanta qasa, amma hakan bai sa ta fasa gaya mishi abin da take nufin gaya mishin ba. “Bana son irin wannan tambayar na rufe wannan hirar a tsakaninmu, in kuma ba haka ba yanzu zan gudu in bar maka girkin…. In bar maka gidanka”. “To a kan me za ayi hakan Aisha? Ai faxin bakya so xin ya wadatar da komai, ba zan sake ba, wannan da na yin ma na tuba”. Nan take kuma ya canza hirar da faxin “Abu ta yi min maganar idonta, shine na ce ko za ki taimaka ne gobe mu kaita Kano ta ga likitan ido, kin san za ki yi mata amfani sosai ko a wajen layi ne”. Ba ta ce mishi komai ba, shima bai sake maganar ba. Ya ci abincin sosai, Saddiqa ta zuba mishi ruwan lemo a kofi, maimakon ya karva sai ya ce mata. “Aisha sau nawa kike jin mutane suna cewa kina da kyau?” Ta ce, “Zan gudu in barka in ka sake, don ni na tsani a sani a gaba ana cewa ina da kyau”. Ya ce, “To ki yi haquri amma taimakeni ki yi min adalcin barina in faxi magana guda xaya”. Ta ce, “Faxi”. Ya ce, “Kin iya kwalliya, wani lokaci sai in ga tamkar ba a garin nan kika koyi kwalliyar ba, gaki da murya mai daxi, ga shi duk abin da kika sawa jikinki sai ya karveki, gaki da nutsuwa, gaki da girmama iyaye, ga shi kin iya girki, gaki da kamun kai. Ni gaskiya….” Ya yi maza ya yi shiru saboda ganin hawaye sun fara cika idanuwanta, cikin hanzari ya miqe. “Bari in watsa ruwa in fito mu tafi”. Wani lafiyayyen Kaftani ne a jikinshi da ta yi matuqar dacewa da hular dake kanshi, ya yi matuqar yin kyau, ga qamshinshi dake iya nutsar da zuciya. Kallo xaya ta yi mishi ta kawar da kai zuwa ga kallon agogo. “Da alama dai ka fasa zuwa hirar nan yau tunda kalli lokaci”. A zuciyarshi ya samu nutsuwa don ya san ita ma tata hirar babu. Ya ce, “Eh to, sai in fasa zuwa tunda na ga kina yiwa askina dariya sai na mai da qasumbata kar in je ita ma ta ce na ragewa kaina kwarjini”. Ta yi murmushi ta ce, “Ta a kaini gida”. Ya ce, “Yanzu kuwa”. Sun fito harabar tsakar gida take tambayar shi cewa, “Yaya ni su waye suke sha maka sigari ne a gida?’ Ya taya ta kallon guntayen sigarin da take magana a kai ya ce, “To ya ya zan yi Aisha gida na jama’a? Wani abin ai dole sai ka yi haquri, kema bakya son shi ko?” Ta yamutsa fuska ta ce, “Ai ni warin taba amai yake sani”. Bai yi mamakin yanayinta da ya gani ba, saboda ya san sanda yake yaro ya san Innarshi kan ware abin amfani na daban saboda baqin da ta san mashaya sigari ne. Wani hamshaqin kanti suka je ya tsaya yana kallon ta ya ce, “Muje ki zavi abin da kike so”. Ta xaure fuska ta ce, “Bayan tsarabar da ka zo min da ita?” Ya yi shiru ya tsareta da idanuwanshi ya ce, “Kin dai koyi yin jayayya dani”. Ta yi maza ta ce, “Ba haka bane”. Ya ce, “To ya ya ne? Sai kuma ki zo gidana ki tafi haka ko ‘yar tsarabar ‘yan oyoyo babu. Shiga ki duba wani abu”. Suna cikin kantin wanda babu komai a ciki in ban da kayayyakin mata, yana cikin tayata zaven takalma sai ga Sadisu ya shigo cikin kantin. Mus’ab ya yi kamar bai ganshi ba ya ci gaba da abin da yake yi. Ya iso wurin da suke ya ce, “Barka dai”. Ya cewa Mus’ab. Ya yi kamar bai ji shi ba sai da Saddiqa ta ce mishi, “Yaya ana magana”. Ya xaga ya ce mishi, “Barka”. Vacin ran Sadisu ya qara bayyana, ya ce, “Saddiqa me kike yi a nan yanzu?” Ta kalle shi cikin sakin fuska ta ce mishi, “Sayayya”. Ya ce, “To ina son ganinki a waje”. Ya yi maza ya juya. Ta xaga ido ta kalli Mus’ab a hankali. Ya ce mata “Jeki mana”. Ta bi bayan Sadisu. Shi kuwa ya ci gaba da tsintsintar abubuwan da yake ganin za su yi mata kyau, har minti goma sha biyar ba ta shigo ba. Ya fara tunanin me suke faxa haka? Ko dai sun wuce ne suka tafi suka barshi a nan? To ko dai ya leqa ne ya ganewa kanshi? Kai a’a, gara dai ya qara haquri kar yaje leqawa Sadisu ya ganshi. Ya koma wajen zaven agigona sai ga Saddiqa ta shigo. Da sauri ya yi kamar bai samu wata matsala ba, haka nan bai gane yanayin da ta shigo a ciki ba. Ya ce mata, “Mu ga xan hannun ki ko wannan zai yi miki?” Ta ce, “A’a, ni ka kaini gida kawai”. Ya ce, “To”. Ya mayar ya ajiye. Ya rungumo ledojin ya zo ya biya kuxin suka shiga mota, ko tsayawa wurin sayen kaji bai yi ba ya kaita gida ba tare da ya ce mata komai ba. Washe gari da safe tun tara Saddiqa ta isa gidan Abu cikin kwalliyar wani lallausan voil mai ruwan madara, ta yi kyau sai qamshi take yi. Tana sallama a qofar xakin Abu Mus’ab ta fara gani yana zaune kan tabarma yana cin ximamen da Abun ta yi mishi. Ya kalle ta cikin nutsuwa ya ce, “Ni dai sai dai duk yanda za ki yi dani ki yi, amma ba zan daina cewa kina da kyau ba”. Abu ta ja tsaki ta ce “Matsa ni ka gani in wuce, in dai Saddiqa ce mai kyau a wurinka ai baka more ba, tunda baka san kyan ba kenan”. Ta fice ta barsu. Ya xaga ido yana kallon ta cikin nutsuwa, ya ce mata, “Zolayar ki fa take yi don kuwa ta fini sanin kina da kyau, sbaoda ta fini sanin da su wa kike kama”. Ta xaure fuska tare da juyar da idanuwa nuna maganar ba ta dame ta ba. Hakan da ta yi yasa shi bin idanuwan nata da kallo, zuciyarshi ta raya mishi kuka ta yi. Kamar ya tambaye ta abin da yasa ta yin kukan, sai kuma ya ga to a na me? Alama ne dai na wata qila saqon shi ya fara tafiya. “Za ki ci xumame?” Ya yi tambayar don ya kawar da shirun da ta yi. Ta ce, “A’a, na qoshi, kuma ma ni bana cin abu mai nauyi da safe”. Ya yi murmushi ya ce, “Ai kina da kyau ne”. Ta yi maza ta vata fuska. Abu ta shigo daga wurin alwala take, sallar walaha ta soma gabatarwa. “Siraran mutane basu cika cin abu mai nauyi ba, musamman ke gaki ‘yar gata, yanzu ni yanda nake qaton nan in ban ci abu mai nauyi ba in yi me?” Maganar tashi ta sata murmushi, ta ce, “Kai ba wani qato bane fa Yaya, ai kai dogo ne jikinka ya dace da kai kwarjini kawai ya qara maka, in ban da haka da ka yi tsayi mai yawa”. Ya yi murmushi ya ce, “Dame na fiki tsayin Aisha? Qafa shida ne fa dani”. Ta ce, “Lah!” Ya katse ta da cewa, “To bari Abu ta idar mu gwada tsayin ni dake ta gani”. Ya kalle ta ya ce, “Bani ruwan sha”. Da Sauri Abu ta shafa fatiha ta ce, “A’a, kar ki je min bakin randa barni in kawo mishi, haka kawai kin yi dalilin da aka sare min bishiyoyina na shekara da shekaru”. Mus’ab ya ce, “Aka rage musu ganye dai Abu, kuma ai kema hakan ya fi miki dan za su fi ba da iska mai kyau”. Qarfe goma da rabi suka bar Abu suka kama hanyar Kano. Mus’ab da Saddiqa suna gaban mota, ita kuwa Abu tana baya, Saddiqa tana karanta mujallun da ta samu zube a cikin motar, shi kuwa Mus’ab yana hira da Abu. Ta xauko goron ta za ta gutsira ta ce, “Nifa wannan goron ba isana zai yi ba, in an gani a tsaya a saya min”. Mus’ab ya ce, “Ki rinqa shan Ice-cream Abu bana sonki da cin goron nan bai da wani amfani a jiki in ban da cutar da lafiya”. Ta harare shi ta ce, “Au haba? Na ce to da goro da taba fa?” Ya yi shiru bai amsa mata ba. Ta sake faxin “Na ce shi da sigari fa?” Mus’ab ya yi kamar ba da shi take yi ba. Ta ce, “Hhm! Mai sigari kuma har ya cewa mai goro wani abu? Abin da masu yinta ma kashedi suke yi muku suna faxin tana cutar da lafiya, mashayanta kuma za su iya mutuwa tun cikin quruciyarsu saboda cutar da take yiwa lafiyarsu”. Da sauri Saddiqa ta rufe mujallar dake hannunta ta juyo ga kallon Abu ta ce, “Ya ya kike danganta shi da shan sigari?” Gaban Abu ya faxi, ashe ba su biyu bane a motar. “Ke tafi can shashasha”. Ta ci gaba da cin goronta. Ta sake juyawa wajen Mus’ab ta ce, “Yaya kai kana shan sigari ne?” Bai juyo ya kalleta ba balle ta ga yanayin fuskarshi, ya ce, “To ina na san wannan bayani Aisha, ai Abun kawai za ki tambaya ta gaya miki”. Jin da ta yi Abu ce za ta yi mata bayani yasa ta haqura. Tamkar Mus’ab jira yake yi a ambatar mishi sigari, nan da nan kwaxayinta ya taso mishi, sai hamma yake yi yana qarawa. Ya gaji ya ce, “Sammin goron naki Abu in xan tauna”. Ta ce, “Haka kuma?” Ya ce, “A’a, bani kawai in gutsira”. Ta ce, “To”. Ta miqa mishi yana duba goron kafin ya jefashi a baki, ya juya ya kalli Saddiqa ya ce, “Ke kam na san bakya cin goro”. Ta ce, “A’a”. Ya ce, “Nima yau ne saboda na ji kamar zan yi gyangyaxi”. Abu tana daga baya ta ce, “A’a, ai haka tsiyar goro da taba yake”. Saddiqa ta valla mata harara ta ce, “Ni bana son ana ambaton sunan taba a kusa dani”. Abu dai suvutar baki take yi tana yin maganar, ta yi nufin kame bakinta daga hirar shima Mus’ab ya yi nufin daina jan Abu da hira don gudun kar ta yi mishi tonon asiri. Asibitin ido na Niger Optical Service suka je, sun ga kan lokaci da aka yi alqawari, an kuma sallame su da magunguna bayan an tabbatar musu da cewar idon bai da wata matsalar da ta wuce shekaru ke haddasawa. Daga can Mus’ab ya zarce dasu Cort Road gidan abokinshi na makaranta Ishak, suna yin parking maigidan ya fito, yana ganin baqin ya buxe baki yana faxin, “Amma yau ka burgeni, ai ban san ka da irin wannan kirkin ba, ko da yake ga waxanda suka kawo ka, uwargida ne da amarya ko?” Ya shiga yiwa Abu da Saddiqa sannu da zuwa. Ya matsa kusa da Abu saboda ganin fitowar matarshi Atika don tarar Saddiqa. “Ai ni yau shar dani tunda ga amaryata ta zo”. Abu ta yi murmushi tare da faxin “Yi dai a hankali kar matar gidan ta ji ta qi yi min malmala mai auki”. Gaba xaya suka yi dariya. Atika ta wuce gaba tana yiwa Saddiqa jagora zuwa saman gidan, ita kam Abu wurinsu Mus’ab ta yi zamanta. Nan da nan Atika ta zagayesu da kayayyakin lashe-lashe da tanxe-tanxe. Ta kalli Abu ta ce, “A’a, ke kuma a nan za ki hakimce wurin maigidan?” Ta ce, “A’a, ni bana zama xakin kishiya”. Suka yi dariya. Atika ta zauna suka gaisa, sannan ta xebowa Abu nata plate xin ta kawo mata kusa da ita, sannan ta juya da sauri ta haura sama inda ta bar Saddiqa tana jiran dawowarta. Mus’ab ya kunna sigarinshi ya sanya a baki bai cewa kowa komai ba, sai da ya zuqe kara biyu. Ishak ya kalle shi ya ce, “Yallavai wannan shirun duk a daxin yake?” Mus’ab ya kalle shi ya ce, “Yau ai ba qaramin wahala na sha ba”. Ya kwashe bayanin duka ya yi mishi na yanda suka yi a mota. Ishak ya yi murmushi ya ce, “Ai in har ka saba shan sigari bayan ka ci abinci, to bari cin abincin ka zauna da yunwarka ya fi sauqi, ko kuma in ka ci ka san yanda ka yi ka yi dabarar da ka xan xorata, amma kai a ina ake yin haka?” Yana tambayar yana dariya ya ce, “Har sigarin ba ta san kana sha ba? Tafxijam! Ai za ka wahala, ka voye wuta ka voye hayaqinta? Ai in aka voye wasu abubuwan shi sigarin sai kawai a nuna mata ana sha, in yaso sai a roqeta ta ba da lokaci za a daina kafin nan ta shiga gida shi kenan”. Abu ta qyalqyale da dariya tana kallon su, ya sake wani murmushin ya zubawa Mus’ab ido ya ce, “Ai haka ake yi, amma ka tattara komai ka voye, ni da ban voye duka ba ma ai da aka gano abin da ake ciki ba qaramin bori aka yi ba”. Mus’ab ya gyara zama ya ce, “Ni neman auren nawa ne babu gata a ciki, nan inda kake ganin Abu ma ba ta tare dani, shi yasa ta yi ta qoqarin tona min asiri a gabanta”. Abu ta yi dariya ta ce, “Ubangiji ya shiryeku yaran nan”. Suka ce, “Amin”. Ita kam Saddiqa tana can suna shan hira da Atika tamkar sun daxe da sanin juna, rayuwar da Atika ke ciki ta ba ta sha’awa, saboda ganin da ta yi tamkar komai nata ya yi dai-dai. “Ya ya ban ga yara ba a gidan?” Ta yi murmushi ta ce, “Yanzu ne fa nake da cikin bai ma fi wata uku ba, Mus’ab bai baki labarin wahalar da muka yi wurin neman haihuwa ba?” Saddiqa ta yi murmushi ta ce, “Kun daxe da auren?” Ta yi maza ta ce, “Shekara uku fa, abokan aurenmu wasu ma sunyi biyu”. Saddiqa ta yi dariya ta ce, “Yanzu nan in an shekara uku ba a haihu ba sai hankali ya tashi? Ai bai wuce amarci ba”. Atika ta zaro ido tare da faxin, “Tafxijan! To bari mu ga ku yanda za ku yi naku amarcin, in baki sani ba in gaya miki, Mus’ab yana ganin kin wuce wata uku za ki ga ya fara…..” Ta katseta da cewa, “Lah, Yaya Mus’ab fa Yayana ne ba saurayina bane”. Atika ta zaro ido haxe da cewa, “Kina nufin ba kece nake jin suna labarinki da Ishak ba?” Ta ce, “A’a, bani ba ce”. Ta yi maza ta miqe ta nufi matattala inda za ta hango mijin nata a falo, “Na ce ba”. Ya ce, “Na’am”. Ta ce, “Ba wannan ce yarinyar nan ba?” Ya yi maza ya ce, “A’a, ba ita ba ce, wannan ai qanwarshi ce”. Ta juyo tana faxin “Ai ashe kuwa ba ke ba ce”. Sai da suka yi sallar la’asar sannan suka yi sallama, Ishak ya kawo turamen holland guda biyu tare da wani rantsattsen leshi ya bai wa Saddiqa, ita ma Abu ya ba ta turame biyu tare da dubu biyar wai ta ci goro kafin ya zo. Suka yi godiya suka tafi. Mus’ab yana barin gidan bai zarce ko’ina ba sai shagon Alhaji Ibrahim Umar a cikin kasuwar Sabon Garin Kano. Saddiqa tana zaune kan kujerar da aka ba ta, mamaki take yi na yanda aka maqare shagon da zinare Gold qirar daban-daban, cikin fara’a da iya karvar baqi Alhaji Ibrahim ya ce, “Barka da zuwa ranki ya daxe, hala amare ne suka zo ziyara?” Mus’ab ya ce, “Babbar ta fara zaven abin da take so”. Alhaji Ibrahim ya bi Abu yana nuna mata don ya tayata zave, shi kuma ya yi amfani da hakan ya matsa kusa da Saddiqa ya ce, “Aisha misali a ce kece budurwar da nake shirin ki rakani wurinta taxi na kawo ki nan me da me za ki zava?” Ta yi shiru cikin tunanin maganar tashi, sai ya yi maza ya ce, “Taimakeni ki tashi ki duba mata sarqoqi don ina ganin kamar ra’ayinku kusan xaya ne”. Ta yi murmushi ta ce, “To”. Ta miqe ta soma duba sarqoqin dake rataye cikin kabet-kabet, ta nuna wasu guda biyu aka ciro su aka xora kan sikeli ana gwada nauyi. Alhaji Ibrahim da kanshi ya jinjina zaven da ta yi, ya yiwa Mus’ab kuxin. Ya kalli Saddiqa ya ce, “In an haxa da abin hannu bai fi ba?” Ta ce, “Ya fi”. Ya ce, “To zavo kamar na hannunki kala biyu”. Ta ce, “To”. Nan ma ta zuba ido ta zavo abin da take ganin in ita ce abin da za ta xaukawa kanta kenan. Ya biya suka fito suka shiga mota suka xauki hanyar komawa Misau. Abu tana kwance a baya barcinta take yi, ita kuwa tana jingine sai dai can cikin zuciyarta Yaya Mus’ab da budurwarshi take tunawa, irin sayayyar da ya yi mata bayan ko fara zuwa wurinta bai yi ba. Wannan ranar da ya fara zuwa ko me zai yi oho. Ta yi maza ta kawar da tunanin ta hanyar tunawa kanta shi xin mai alheri ne ga kowa. Shi kuwa Mus’ab yana tuqi ne tare da tunanin abin da ke tsakanin shi da Saddiqa wanda ba ta ma sani ba, sai dai zuwa yanzu kam yana ganin Innar shi ta soma sansano wani abu. Sai da suka isa qofar gidan Abu ya sauke ta ya rakata ta shiga ciki, sannan ya dawo da nufin kai Saddiqa gida. Saddiqa ta buxe qofar motar ta fita tare da faxin “Yaya ka huta gajiya”. Ya ce, “Amin, to zo mana”. Ta juyo tana kallon shi. “Ai kin yi mantuwa”. Ya xauko ledar dake xauke da sarqoqin ya miqa mata. Ta yi saroro tana kallon shi. “Karvi mana Aisha”. Ta ce, “A’a, ai budurwarka ka sayawa”. Ya zuba mata ido ya ce, “Kin tava ganinta ne? To karvi mana”. Ta sake cewa, “A’a”. Da sauri ta juya ta nufi gida za ta tafi ta barshi dasu. Ya yi maza ya tare ta a zauren gidan ya ce, “Haba Aisha, ni dake ai abotarmu ta hana mu yiwa juna haka”. Ta maqure kanta jikin bango, shima ya mamayeta ta ko’ina ta zama ba ta shaqan komai sai qamshin jikinshi. “In kika qi karva wa zan kai wa? Ki karva ki yi kwalliya in na gani a jikinki zan ji daxi, bani da wata budurwa tunda na kasa yin jarumtakar gayawa wacce nake so xin. Karvi kawai ki yi amfani dasu”. “Ni da Gwaggo dukanmu bama son kyaututtukan da kake yi min, in jita wai akwai abin da zai biyo baya, kuma in yi hankali da kai”. Ta soma kuka ya rasa yanda zai yi da ita, shi ba abin ya sake ficewa da ita zuwa wani wurin ba, ya san Innar tana jin isowarsu. “Ni bani da abin da zan ce miki a yanzu illa in roqe ki duk abin da za ki ji a kaina ki taimake ni ki yi min adalci, ki bani damar da zan yi magana dake kullum ina gaya miki kina ganin kamar wasa nake yi bani da wani gata, in har ba ke ce kika tsaya min ba to zan shiga matsalar da ban san qarshenta ba. Na dogara dake ne saboda qarfin zumuncin dake tsakaninmu da mutumta juna da muke yi, ni dai na san ko baki yi hankali dani ba, ba zan iya cutar dake ba, ke ce baki san yanda kike ba a wurina, nine nake rayuwa ni kaxai a wurin Innata sai ga shi kin shigo cikinmu, ina murnar nima na samu qanwa wacce zan yi ta tarairaya, wacce zan yi ta so ina tausayawa kamar yanda Inna ta yi min, sai kuma ta tafi ta barmu, sai kuma in rasa wacce zan cutar sai ke. Ke kaxai fa ta bari a duniya sai in cutar da ke? Ai ni tunanina da burina da sha’awata bai wuce mu dunqule ni dake mu zama abu xaya ba, da tana nan a raye kuma ina tabbatar miki da abin da za ta yi mana kenan”. Saddiqa ta xago ta kalle shi cikin kuka mai yawa, ta ce mishi, “Ba na gane abin da kake nufi da irin maganganun da kake yi min ban san me kake nufi ba”. Ya ce, “To ki yi huquri ki karvi waxannan sarqoqin tunda na riga na saya sai ki yi min ado da guda xayan zan ji daxi sosai, gobe ki zo gidana don mu warware al’amuran dake tsakanin mu”. Ta ce mishi, “Inna ta yi min kashedin zuwa gidanka, sai dai ko gidan Abu”. Ya zuba mata ido yana kallon ta ya ce, “Haka ne?” Ta gyaxa kai nuna alamar eh. Ya ce, “To kin gani Aisha karvi sarqoqin ki kai mata, gaya mata kawai ni na sai miki ita ta san abin da nake nufi”. Tana sa hannu ta karva ya yi maza ya fice daga zauren don ya ji motsin fitowar Innarshi tsakar gidan. Saddiqa na tsaye a zauren ta shigo riqe da tochlight xinta tana haskata. “Me ya faru Saddiqa? Kukan me kike yi? Ya tava ki ko? Ya yi miki wani abu ne?” Ta shiga haskata ta ko’ina, ta ce, “Nifa dama can ban yarda da kusantar juna da kuke yi ba”. Cikin kuka Saddiqa ta ce mata, “Haba Gwaggo, Yaya Mus’ab ba xan’uwana bane?” Maganar ta zo mata a bazata, ta tsaya tana kallon Saddiqa, matsanancin kukan da take yi ya qara mata tausayinta. Cikin zuciyarta ta ce, “Uh-uhum! Shi kenan wannan yaron ya gama da Saddiqa, don kuwa matsanancin kukan da ta yi jiya da wannan da take yi a yau ba komai bane illa SO, wanda ya san shi ya san abin da yake sanya zubar hawaye”. Tausayin ta ya sake kamata da ta qara taabbatarwa kanta da cewar, “Wanda bai kamata a so bane Saddiqa ta kamu da sonshi”. Ta miqa hannu ta riqo nata ta jata suka shiga gida tana rarrashinta. Shi kuwa Mus’ab yana barin gidan bai nufi gidanshi ba wurin Abu ya koma, har ta kwanta ta ji shigar shi cikin xakin nata, ta fito tana haskashi da fitilarta. “Lafiya? Me ya faru ka dawo cikin wannan tsohon daren?” “Abu ki ji Inna wai Aisha ta yi hankali dani”. “Hankali da kai kamar ya ya?” Ya ce, “To ina na sani Abu? Tana son rabani da Aisha, za ta rabani da ita”. Cikin matsanancin yanayi yake maganar. Ya ba ta labarin yanda suka yi da Saddiqa duka. Ta ce, “To bari kawai tunda abin nata ya zama haka tun ba a ce komai ba za ta fara tsoratar da yarinyar ba za ta tsame hannunta cikin lamarin ta barta ta yiwa kanta zavi ba, to za ni gidan nasu zan gaya mata komai don ta san gaske kake yi”. Ya ce, “Yauwa Abu, nima na c Aishan ta zo nan ta same ni ta kuma yarda”. Ta ce, “To Ubangiji ya zava mana mafi alheri”. Ya ce, “Ameen Abu”. Washegari da sassafe Abu tana idar da sallar asuba ko laziminta ba ta tsaya ta yi ba ta lakato man shafawarta ta muttsuka a hannayenta da qafafuwan ta, ta miqe ta xauki carbinta da mayafinta ta yafa, ta sagala murfin qofar xakinta ta nufi gidan Malam Abdullahi, a zuciyarta tana fatan ta same shi suyi wacce za suyi don ta riga ta yi nufin taimakon Mus’ab a kan auren Saddiqa da ya yi nufin yi. A tsakar gida ta samu Saddiqan tana yawo cikin rigar barcinta, idanuwanta a kumbure alamar daren jiya kukan da ta yi ba kaxan bane, ta yi kamar ba ta ganta ba ta nufi xakin ‘yarta tana sallama. Da sauri Innar ta leqo ta ce, “Inna lafiya kika fito da sassafen nan?” Ta ce, “Lafiya qalau, wurinki na zo ke da mijinki”. Ta ce, “Ayya! Ai kuma ya fita don an sanar da rasuwa a cikin gari”. Ta ce, “Wayyo babba ne ko yaro?” Ta ce, “A’a, ya xan manyanta”. Abu ta ce, “To, Allah ya ji qan musulmi”. Ta shiga ta zana suna gaisawa. Saddiqa ta biyota da abin karyawa. “In ce ko dai lafiya kike son ganin Malam Inna?” Ta sake cewa “Qalau, dama qarfin zuwan nawa naki ne, don na san komai a gidinki yake Malam kam ai ba zai hana Mus’abu aure ba”. Nan take ta shiga yi mata bayanin saqon nashi. Sai da ta ji ta yi shiru ta tabbatar ta kai qarshe sai ta xan yi murmushi. “Uhm! Ai dama na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, kyautar rashin hankali da yake yiwa Saddiqa shi ya qara fahimtar dani akwai yaudara a cikin lamarinshi, ko kin san tun yaushe rabon Sadisu da ya ji daxin yarinyar nan ko maganarshi ba ta son ji? To haka ake yi ba zai yi neman shi ba kawai sai ya rabata da wanda ya same ta da shi? Sannan sau nawa ya turaki wajen nemar mishi aure Inna? Ya fito ake cewa sai ya qi zuwa ya bar yaran suna ta shirmen sonshi, haka nima yake so ya yi min?” Abu ta yi nufin yi mata dabara ta ce, “Yauwa, to tunda an san halinshi ba sai kawai in ce mishi ya fito ba? Kinga ai sai ya yi tafiyarshi kowa ya huta”. Inna ta ce, “A’a, a kan wannan kam kar a ce mishi ya fito tunda ko ya fiton ba bashi ita zan yi ba. Saddiqa marainiya ce, Innar kar ki shiga cikin maganar yaron nan har ya samu damar da zai cutar da ita. Ba mijinta bane, ni dake mun san komai in har qa’idar bayar da aurenmu za a bi ai ba tarin dukiya muke dubawa ba cancanta muke bi da asali da mutunci, da sanin ya kamata. Don haka ayi mishi kashedi kawai Inna ya fita hanyarta, in ba haka ba kuma zai gamu da vacin rai mai yawa, sai in yi mishi…….” Abu ta yi maza ta soma salati tana tafa hannu, ta ce, “Ki yi mishi me? Lallai kuwa da kin yi hauka. A kan ya ce yana son Saddiqa? Ki ce min kin yi hauka ban sani ba. To yi maza ki yi mishi baki a gabana don nima in zama shaida in qara sanin kema kin haihu. Zancen banza zancen wofi, xanki guda xaya kin yi qememe kin qi yarda ki shirya da shi, kin takura kanki kin hana kanki sakat, kullum tsakanin ki da shi muzurai da xaure ido. Yana iyakacin bakin qoqarinshi a kanki, yana yi yana iya yinshi kina shirmenki. Sakarwa kawai ki ce min kina shirin tonawa kanki asiri don shine ke”. Ta miqe ta fita ta bar Inna tana kuka saboda ganin vacin ran mahaifiyarta. “Zan dawo in samu Malam Abdullahi in ji ko shima bakinku xaya, Saddiqan me kuma? Shima Mus’abun maganinshi kenan ja’iri mai taurin kan tsiya, ai babu abin da ban gaya mishi ba”. Saddiqa tana xakinta adon lalle take yiwa hannayenta ta hango ficewar Abu cikin sauri, ta tabbatarwa kanta akwai wani abin da ke faruwa. Sai dai ba ta san mene ne ba, koma mene ne kuma ba ta jin daxin yanda Gwaggonta ke yiwa Yaya Mus’ab, kullum mamakinta take ji yanda ta mallaki xa jan gwarzo irin Mus’ab amma lamarinshi baya gabanta, ko tausayi kuma ba ya ba ta, kullum a cikin qoqarin kyautata mata yake, a cikin yi mata alheri yake, kusan kullum sai an zowa mahaifiyarshi godiya kan wani alherin da ya yiwa wasu amma ita ko a jikinta. Mus’ab yana zane a xakin Abu jiran dawowarta yake yi, yana kuma sauraron zuwan Saddiqa cikin zullumu da tunanin abin da ake ciki. Abu ta yi sallama ta shiga, ya bita da kallo gabanshi ya faxi saboda ganin yanda fuskarta ke xaure. “Ya ya dai Abu? Ta yarda kuwa?” Ta balbale shi da faxa ta ce, “Ta yarda dame? Tun farko mene ne ban gaya maka ba? Ban ce maka ka fita hanyar yarinyar nan ba? Ba dai kaima kafiyar tsiya ce da kai ba, in ka so abu kamar xa ya so waje. To ba ta yarda ba sai ka san yanda za ka yi”. Ya sunkuyar da kanshi qasa ya yi shiru cikin nazarin abin yi, zuwa can ya xago ya kalli agogon hannunshi ya ce, “Goma ta wuce”. Gabanshi ya sake faxuwa. “Kar dai ita ma ba za ta zo ba?” Ya yi maza ya xauko wayarshi ya dana lambobinta ya ji ta xauka. “Za ki zo kuwa Aisha?” Muryarta tana rawa ta ce, “Gwaggo ta hanani fita, ta kuma ce wai in ka yi waya in gaya maka tana son ganinka”. Gabanshi ya ba da ras! Ya kalli Abu ya ce mata, “Inna tana son ganina bari in je in ji”. Ta ce mishi, “To”. Mus’ab yana zaune a gaban mahaifiyarshi cikin ladabi yana sauraron abin da take gaya mishi. “Na ji saqonka wurin Inna, shine na ce bari in kira ka muyi magana ni da kai, abin a ce kai ne waliyinta wanda amanar al’amuranta suke hannunka, za ka bai wa mai hali irin naka ita?” Ta zuba mishi ido tana kallon shi. Shi kuwa yana kallon qasa cikin ladabi ya ce, “Ina sonta Inna ba zan iya kwatanta muku yanda nake jinta ba in ban da hakan da ban zo gabanku neman auren nata ba, ina cikin wani irin hali ne”. Ta katse shi ta hanyar faxin “Ai ba dogon bayani na nema ba tambaya kawai na yi maka baka bani amsa ba, cewa na yi in kai ne waliyinta za ka bai wa mai hali irin naka ita? Eh, kawai nake son ji ko kuma a’a”. Ya sunkuyar da kanshi qasa ya ce, “A’a”. ta ce, “To shi kenan magana ta qare tashi ka tafi”. Ya ce, “Ki yi haquri ki saurareni Inna, ni da mai hali irin nawa ba xaya bane, in a kan maganar Aisha ne Inna zan riqe miki ita fiye da duk yanda ake zato, babu wani wanda za ki baiwa ita ya fini yi mata adalci ko ya fini ganin darajarta, don ni bayan son da nake yi mata ina kallon ta a matsayin wacce zan riqe in yiwa gata don in sakawa mahaifiyarta alherinta a gare ni. A wurinta na soma xanxanar ‘yanci, ba ta yi yawan rai ba, ba ta mori komai a cikin wahalar da ta yi a kaaina ba sai dai kullum ina yi mata addu’a. Ki taimakeni kar ki hanani ‘yarta, da tana raye na san za ta bani ita ba tare da ta tsaya kallon munin halina ba, na yarda ki bani ita bisa sharuxa da shaidun da za ki saka, zan cika duk wani alqawari da zan xauka a gabansu”. Ta kalle shi a lalace ta ce, “Saboda yanzu kana cikin natsuwarka ne yasa kake tuna alherin mahaifiyar Saddiqa, haka nan yanzu ne za ka iya shaida alqawari da cikawa, amma in ka shawo barasa ta yi maka karo fa? Kana nufin zan yarda Saddiqa ta zama matar mashayi ko manemin mata? Yarinya ce da ba ta san komai ba sai ladabi da biyayya. Me kake so in ce mata randa ta gane na san komai game da halayenka amma na xauke ta na baka don kawai ka yi min alqawarin da na san ba za ka cika ba, ba zan fifita sonka a kan nata ba, in na yi haka ban yi mata adalci ba, alhakin zumunci kuma ba zai barni ba, don haka fita hanyarta kawai don ba zan baka ita ba”. A kixime ya ce, “A’a, Inna kar ki hanani ita, na rantse miki ina sonta, ki taimaki rayuwata ba zan iya haqura da aurenta ba”. Ta ce, “Za ka yaudari kanka ne kawai in ka yi mata irin wannan son, don babu gami tsakaninka da ita, in dai ka kuma in alhakin wasu da suka rinqa binka kana wulaqantawa ne ya kama ka”. Mus’ab yasa hankicif ya share gumin dake feso masa a goshi. “Ki taimakeni Inna na tuba kar ki kamani da laifukan da na yi miki a baya ki hukuntani ta hanyar hanani samun matar da nake so”. Ta ce, “Ba ni na hanaka ita ba Shari’a ce ta hanaka ita, da ta ce mazinaci matarshi mazinaciya, don haka zan qara yi maka kashedi ka fita harkar yarinyar nan kar ka yarda ka ce mata kana sonta, in kuwa ka yi hakan to ni kuwa zan rabaka da ita ta hanyar gaya mata halayenka, sigari, giya, neman mata, babu abin da zan rage a ciki don ta san ban cuceta ba”. Tsawon lokaci suna zaune shiru, da qyar Mus’ab ya iya yunqurawa saboda sarawa da kanshi yake yi ya ce, “Inna ni zan koma”. Ta ce, “To, Ubangiji ya kiyaye”. Ya ce, “To, amin”. Mus’ab yana fita gidanshi ya nufa, kai tsaye ya wuce xakin kwanciyarshi. Wunin ranar bai yarda ya ga kowa ba, babu abin da yake yi in ban da nazarin hanyoyin da zai bi. Ya riga ya san Innarshi za ta raba shi da Saddiqa ta hanyar gaya mata halayenshi, to in har ta yi hakan wace hanya shi kuma zai bi don ya mallaketa? Abu kuwa tana gidanta hankalinta yana wajen sauraron dawowar Mus’ab don ta ji bayanin da zai yi mata, shiru babu shi babu dalilinshi har yamma, har dare. Abu ta tabbatar babu lafiya, domin qa’idarshi ne in dai yana garin to zai ci abincin dare a wurinta. Gari yana wayewa ta yi sammakon tafiya gidanshi don ta ga halin da yake ciki. Muryarta da ya jiyo tana qwala sallama cikin falon ne ya yi dalilin fitowar shi sanye da doguwar jallabiya, Ta zuba mishi ido tana nazarin canzawar da ya yi a ‘yan awowin da ba ta ganshi ba. “Ba ka zo ka ci abincin dare ba lafiya?” Ya ce, “Inna ce ta ce in fitar hanyar Aisha, Abu ya ya zan yi? Tana da haqqin in yi mata biyayya ita ce ta haifeni ko ba shi kenan ba”. Abu ta zuba mishi ido tana nazarinshi. “Amma ai kin san Aisha matata ce ko? Ko baki sani ba?” Bai jira amsarta ba ya ci gaba da cewa, “To na rantse miki zan yi ta’adi, zan yi varna”. Abu ta katse shi da cewa, “Kai Mus’ab hala maye kake yi na ga alamar baka cikin hankalainka, ina jin jiya kwana ka yi kana sha, wato ba za ka daina wannan halin naka da yake ja maka tsana a wurin su ba ko?” Ya ce, “A’a, Abu so nake in gaya miki gaskiya cikin biyu ki zavi xaya, wanne ya fi?” Ya tsareta da idanuwanshi da suka riga suka kaxa. “Da in vatar da Sadisu da in sato Aisha in kawota gadona in voye ayi ta nemanta ba a gani ba wanne ya fi miki? Ki faxa”. Ta yi tsaki cikin takaici ta juya za ta bar falon, ta ce, “In ka wattsake dagaa shirmen naka sai ka zo gida ka same ni”. Tana tafiya cikin ranta tana addu’ar Ubangiji ka shiryar da wannan yaro. Ta fita ta barshi a zaune. Malam Abdullahi yana zaune kan tabarma a xakinshi shi kaxai, karatun Alkur’ani mai girma yake yi, matarshi ta yi sallama a bakin qofa har sau uku kafin ya dakatar da karatun ya amsa sallamar. Ta shiga ta tsuguna a gefe ta ce, “Ina kwana Malam?” Ya amsa. Suka gaisa sannan ta ce mishi, “Inna ce ta zo tana son ganinka”. Ya ce, “To gani nan zuwa”. Ya mai da Alkur’ani wurin zaman shi ya ajiye, sannan ya shiga falon matarshi inda ya san a nan take jiran nashi. “Lafiya dai ko Inna?” Ta ce, “Lafiya wurinka na zo kai da matarka kan maganar Mus’abu”. Da sauri ya kira matar tashi, “Ke Habiba!” Ta amsa ta shigo ta ce, “Gani”. Ya ce, “To zauna mana”. Ya ba ta umarni. Don haka ta koma gefe ta zauna cikin sauraro. Abu taa gyara zama ta ce, “Wurinka na zo Malam in ji wai da gaske kuke yi ne ba za ku ba Mus’abu yarinyar nan ba?” Malam Abdullahi ya sunkuyar da kai qasa ya ce, “Inna da baku shiga maganar nan ba, ai kun san komai, wani abin ma ni kun fini sani. Ba muna son yin jayayya daku bane a kan maganar maraicin yarinyar muke dubawa, nutsuwarta da irin halayenta da irin xabi’unta, kun santa kun san Mus’ab. Inna kun san komai. don haka na roqe ki in kin kalli vangarenshi kin tausaya mishi saboda son da kike yi mishi, to ita ma ki kalli nata vangaren ki tausayawa rayuwarta kar ki fifita wani kan wani, dukkansu naki ne ki yi hukunci kawai na adalci a tsakaninsu”. Ya xago a hankali ya kalli Abu, ya ce, “Qila dai Inna ta fara mancewa da shine ko?” ASALIN RAYUWAR MUS’AB DA IYAYENSHI Iyayen Mus’ab fulani ne na asali waxanda suka taso suka samu kansu zaune cikin garin Misau, a dalilin zaman iyayensu a wuri xaya a cikin gari suka koma neman ilimin addinin musulunci. Malam Abdullahi da Habiba sune mahaifan Mus’ab, su kuma ‘ya’ya maza suke aka haxasu aure na zumunci. Mus’ab shine babba cikin ‘ya’yan da suka haifa guda huxu, mata uku namiji xaya, matan gaba xaya anyi aurensu suna gidajen auren su tare da ‘ya’yansu. Gidan su Malam Abdullahi gida ne na malanta, gudun duniya, sanin ya kamata da gudun abin kunya. Kusan kowa a zuriyarsu in dai namiji ne to alaramma ne, mata ma basa aurar dasu sai sun yi sauka. Yaro bai fi sha biyu sha uku ba sai ka ga tilawa yake yi yana kuma neman sanin litattafan addini, kusan a ce a zuriyarsu basu tava ganin taqadari ba. Mus’ab ya fara yarintarshi ne a gaban Abu, ita ta xauke shi yaye, ko da yake tun yana qarami gagararre ne, sai kuma ya samu shagwava wurin kaka, saboda dalilai da yawa. Na farko dai ita Habiba ita kaxai ce ‘ya mace wurin Abu, na biyu Malam Abdullahi xan lelenta ne, ita ce ma ta sa aka ba shi Inna Habiba. Na uku Mus’ab tun yana xan qaramin shi kyakakyawan yaro ne, waxannan dalilai sai suka sa Abu ta zama quda ba ta son ganin ya sauka a kan Mus’ab balle ta samu lokacin kwavar shi, har da ya kai munzalin zuwa makaranta in ta tura shi ya qi zuwa saia ta ce mishi yi zaman ka karatu in ana gadonshi ai ka gaje shi, in kuwa ba a gadon shi, to randa ka koma gidanku ka yi naka tunda na san ba bar min kai za suyi ba. Mu’amalarshi da gagararrun yara da basu san mene ne bari ba, sai ya taimaka qwarai ya zamo gagararren sosai, tunda shima ba barin ake yi mishi ba. Nan da nan sai labarinshi ya bazu cikin dangi, kowa yana faxin albarkacin bakinshi kan gagarar tashi da irin riqon da aka gane Abun tana yi mishi, kan wannan dalili ne Malam Abdullahi ya tafi wurin Abu ya roqeta ta dawo mishi da xansa gida, wanda dole ta yi hakan. Yana dawowa sai ya sanya shi a makarantar wanshi da suke uba xaya. Maimakon Mus’ab ya yi karatu sai ya zama babu abin da ya sanya a gaba sai rigima da dukan ‘ya’yan jama’a, daga nan aka mai da shi wata makarantar. Nan ma bai yiwu ba har dai Malam Abdullahi ya gaji ya dawo da shi tashi makarantar, in da ya xauki matakin horo mai tsanani a kanshi, ba shi ba, ba matarshi ba wacce babu wata mu’amala tsakaninta da shi in ban da duka, saboda vacin ranshi da take ji. Mus’ab ya zama ko maganar iyayen nashi ya ji sai ya tsorata, maimakon al’amura su gyaru sai suka qara lalacewa, ya zama baya iya zaman gida sai bin jeji kamo tsuntsaye ko wanka a rafi tare da abokai, in kuma dare ya yi maimakon ya dawo gidansu kamar yanda sauran abokanshi ke yi, sai ya rinqa rave-rave saboda ya san akwai hukunci mai tsanani da yake jiranshi a gida. Ana cikin haka ne aka kwana ba a ga Mus’ab ba, aka yi nema har aka gaji gaba xaya gidajen dangi babu inda ba a je ba a same shi ba, sai kawai Malam Abdullahi ya ganshi cikin kasuwa tare da abokanshi suna turaWheelbarow. Wannan shine abin da ya fusatar da shi har ya xauke shi ya kai shi qasar Bagah wurin wani malami da ya sani don ya karantar da shi Alkur’ani. Zaman Mus’ab a Bagah sai ya samu kanshi cikin wata irin rayuwa da bai saba da ita ba, saboda a gida ko an yi mishi hukunci mai tsanani to zai kwana a wuri mai kyau mai tsabta, ya kuma ci abinci mai kyau. Nan kuwa babu ko xaya, bai xauki wani lokaci ba sai wahala ta same shi, yunwa ta kama shi. Bai iya cin abinci in ba ya ji kamar zai galabaita ba, saboda kasancewar shi mai tsantsani da qyama, ga aikin gona in da damuna ne, don malamin ya kan ba da su suyi aikin qwadago a ba shi kuyxin, in kaka ta zo kuma ya kai su roro, ga kuma tallan da matar malam ke xora musu ranar kasuwa. Rannan Mus’ab yaje tallan funkaso a kasuwa cinikin da ya yi ba mai yawa bane, yana cikin wannan zullumin sai kuma wani xan tasha ya kira shi ya ci mishi fankaso, sai da ya qoshi sannan ya qi biyanshi, ya yi kuka har ya gaji bai tausaya mishi ya ba shi kuxin ba, har ya gaji ya shiga tunanin yanda zai yi, don ya san in ya koma gida babu kuxin nan, to ko shakka babu a mari zai kwana. Don haka ya gwammace gara mishi kwana a kasuwa. Tunanin da ya yi za a iya turo almajirai ‘yan’uwanshi su nemo shi yasa shi yagar takarda ya qunshe sauran fankasonshi ya maqa, ya faki idon mutane ya shige cikin wata motar katako da ake yiwa lodin buhuna ya vuya a ciki. Ana idar da sallar isha’i direba ya tashi mota ya nufi Kano, inda zai kai kaya. Wajen asuba suka isa, cikin hikima Mus’ab ya fice ba tare da direba ko kwandasta sun ganshi ba. Kwana biyu yana rave-rave a tasha, daga wurin mai wannan abincin ya koma wurin wancan, yana yi musu wanke-wanke suna ba shi abinci yana ci yana qoshi. A nan wurin abincin ya gamu da wani direba wai shi Xanjuma, shine ya ce mishi “Kai wanke-wanke ai aikin mata ne, sai ko maza masu matacciyar zuciya. Me zai sa ka zauna kana yi zo muje ka rinqa bina zan koya maka tuqin mota”. Shi kenan sai Mus’ab ya koma bin motar Xanjuma, yau suna nan gobe suna can, daga wannan garin su nufi wancan. Saboda son da Xanjuma ke yiwa Mus’ab yasa ko nawa za a biya shi ba a xaukar kayan Misau, saboda labarin da Mus’ab xin ya ba shi. Wurin Xanjuma Mus’ab ya koyi shan sigari da wiwi da kuma neman mata, a dalilin kwanan da suke yi a gidajen karuwai in sun sauka a wasu garuruwan. A garin Bagah kuwa watanni huxu cif Malam yana neman Mus’ab babu shi babu dalilinshi, don haka ya shirya ya tafi Misau cikin qarfin hali ya sanar da iyayen Mus’ab labarin vatanxansu. Hankula suka tashi aka shiga neman Mus’ab ta ko’ina, ta inda ake zato da ta inda ba a zato. Shekara guda ana abu xaya har dai aka gaji aka haqura aka dangana aka barwa Ubangiji lamarin aka koma roqonshi ya dawo da Mus’ab lafiya. Shekaru uku Mus’ab yana tare da Xanjuma, a lokacin nan babu wani shaqiyanci da bai gama qwarewa a kai ba. Suna yaba a can a Lagos cikin tasha suna sauke cittar da suka tafi da ita daga arewa, shi kuma Malam Gixe wan Habiba ya je saro kaya kamar yanda ya saba, sai kawai suka yi kicivis da Mus’ab a cikin tashar. Nan Mus’ab ya yi qoqarin vace mishi amma ina? Ya riga ya ganshi ya kuma gane shi. Ganin haka yasa ya haqura ya kama shi. “Kai ni wurin wanda kake tare da shi”. Ya ce, “Ni kaxai ne Kawu”. Babu yanda bai yi da shi ba amma ya qi nuna Xanjuma, saboda yana tsoron abin da zai samu Xanjuman. Don haka sai ya taso shi suka dawo Misau ya dawo da shi gaban iyayenshi, shi kuma ya koma Bauchi inda yake da zama. Dawowar Mus’ab gida gaban iyayenshi maimakon su daidaita sai al’amura suka qara lalacewa, tun kafin ya zama taqadarin gaske iyaye da sauran dangi sun ce ya fi kowa, to balle yanzu da ya je ya koyi taqadaranci a yawon duniya. Duk da mahaifinshi ya yi ta yi mishi taimako don ganin ya nutsu ya zauna a gida, ya mai da hankalinshi da nutsuwarshi kan karatu da son karatun, cikin ‘yan makonnni kaxan ne sai ya dangana ya haqura da son zaman nashi, saboda ganin irin halayen da ya dawo dasu. Labari ya watsu cikin dangi cewar har sigari Mus’ab yake sha, a wancan lokacin kuwa kusan sai a ce shi kaxai ne yake shan sigarin. Ba a yi nisa ba sai aka kama shi yana koyawa yara sa’o’insa shan sigarin, dama waxanda basu kai shi ba. Inna Habiba wacce take ganin Mus’ab ba komai bane face jarrabawa ga zuriyarsu, saboda abin kunyar da yake ja musu ta rinqa fatan ganin ya koma inda ya fito, ta qauracewa magana da shi, ko ya yi mata ba ta amsawa, ta qauracewa duk wata mu’amala da shi. Ran nan Malam Abdullahi yana makarantarshi yana ba da karatu wani mutum ya zo mishi, tun dagaa nesa yake aiko mishi da maganganu. Almajirai suka miqe da nufin su tare shi don jin kalaman da yake yiwa malaminsu, ya yi maza ya dakatar dasu cikin zuciyarshi dai ya san Mus’ab ne ya je mishi, addu’a yake yi kar ya zama ko ya lalata musu wata yarinya ne, don abin da bai bayyana nashi ba kenan. A nutse ya tambaye shi dalilin cin zarafin. Sai ya ce mishi, “Xan isakn xaanka da ka haifa ka kasa yiwa tarbiyya ka barshi yaa lalace yake kuma nema ya lalatawa wasu nasu, yana nema ya mayar mana da ‘ya’ya mashaya sigari, kai ba ita kaxai ba har da qwaya”. Malam Abdullahi wanda bai tava ganin qwaya ko saninta ba sai ko yanzu, ya yi shiru sai da mutumin nan ya gama bambamin shi ya yi shiru don kanshi, sannan ya xago ya kalle shi ya ce mishi, “Ka yi haquri kan laifin da aka yi maka, zan kuma xauki matakin da hakan ba zai sake faruwa ba, amma ba don ni ba don gaba zan baka shawara, kar ka sake yiwa wani uban gori kan lalacewar xanshi, ba abun ne da yake samun iyaye a kan suna so ba, musifa ce da ya kamata a tausaya musu a kai. In ka lura da rayuwar Mus’ab sai ka ga tun farko makaranta na kai shi, da yanda na so na samu da ba haka ba. To amma har yanzu ban fidda rai ba a kanshi, don babu mai fidda rai ga samun rahamar Ubangiji sai tavavve”. Mutumin yana tafiya Malam Abdullahi ya suri takalmanshi ya shiga gida, ya shiga xakin da Mus’ab ke kwance yana ta bacci, yasa hannu ya tashe shi ya tashi ya zauna suna kallon juna. Ya ce, “Saurareni da kyau Mus’abu, ka ga garin nan garin iyayenmu da kakanni, yanda duk nake da son zaman ka kusa dani dole ne in haqura, don ba zan barka ka zamewa zuriyarmu abin gori ba. Saboda haka ina so ka tashi ka xauki qunshin kayanka ka bar garin yau, yanzu kuma ka tafi duk inda ka ga dama. Na roqe ka kar ka sake dawowa matuqar baka shirya barin abin da kake yi ba, don haka tashi muje ungo kuxin mota”. Ya ajiye mishi ya juya ya fita ya bar gidan. Bilkisu wacce ita ke bin Mus’ab tana jin abin da mahaifinsu ke gaya mishi, ta ruga da gudu ta nufi gidan Abu tana kuka ta kai mata labarin abin da ke faruwa. Cikin sauri suka taho tare, ta samu Mus’ab a tsugune gaban babanshi a zaure riqe da qullin kayanshi. “Me ke fa ruwa Malam?” Ya ba ta labari. Ta ce, “Ka yi haquri?” Ya yi maza ya ce, “A’a, Inna da kamar shi kaxai yake yin abinshi da sai in qyale shi, tunda na san ana yi mishi addu’a. amma tunda har zai koyawa wasu ai gara ya tafi kawai”. Kafiyar Malam Abdullahi kan lallai sai Mus’ab ya tafi ya sanya Abu shiryawa ta tasa shi a gaba ta nufi Bauchi da shi gidan xanta na fari wanda yake shine wan Habiba wato Malam Gixe. Zuwanta na farko gidan shi ba ta kuma kwana ba. Malam Gixe yana da matanshi na aure guda biyu. Mama wacce take matarshi ce ta zumunci abokiyar wasanshi, kuma Innar Mus’ab saboda abokiyar wasan Habiba ce, ga shi kuma wabin ‘ya’yanta take yi, ita ya baiwa Mus’ab. Sai amaryarshi Raliya wacce a lokacin ‘ya’ya uku ne da ita. Yana zaune tare da matarshi a xakinta, ya kalle ta cikin nutsuwa ya ce mata, “Mama ga fa yaron nan an kawo shi wurinmu, ba sai na ce miki komai a kanshi ba xanki ne, ba kuma a kanshi kika fara riqe ‘ya’ya ba balle in ce wani sabon abu naa kawo miki, taimakeni a kanshi kamar yanda kika saba taimakona a baya”. Ta ce, “Babu komai Malam, Ubangiji dai ya shirya mana”. Ya ce, “Amin”. Mama mace ce mai haqurin gaske, gata da juriya da kuma iya zama daa jama’a. Cikin xan lokaci kaxan na zaman Mus’ab a wurinta sai ta gano yanda yake, saboda sa ido da ta yi a kanshi. Naan da nan sai ta gane hanyar tafiyar da shi, ganewar da ta yi babu abin da yake irin ayi mishi faxa yasa ta yi qoqarin janshi a jikinta suka yi matuqar shaquwa, ta yi hira da shi ta yi mu’amala kullum za ta nuna mishi muhimmancinshi. Shekarunka shaa biyar ne fa amma har ka iya shan sigari, ni kunya nake ji a ce qannenka sun gane abin da kake ciki, kar hakan ya jawo zubewar girmanka a wurinsu, tunda kai ne ya kamata suyi koyi da kai, in suka yi kuskure a gaya maka don ka gyara musu. To sun gani a wurinka ya ya kenan? Da irin waxannan kalaman da nasihohi da ja a jiki, maimakon gidansu da ba a hulxa da shi sai ya ga a nan kullum tare da Kawu Gixe yake cin abinci, duk da sun san halin da yake ciki. A haka sai Mus’ab ya soma jin kunyar halayenshi, ya soma voyewa don kunya ba don tsoro ba, a haka sai ya zama mai ganin girma, daraja da kuma qaunar iyayenshi, musamman Mama, bai son ganin ranta a vace ta ce laifinshi ne ya vata mata rai, sai ya zama ya yi watsi da shaye-shaye. Sallah kuwa ba sai an ce mishi tashi ka yi ba, shi kuma dama jarumi ne mai aiki saboda ya riga ya saba da wahalar rayuwa. A haka sai ya samu farin jini har wurin manyan unguwa, saboda aikin da aka sa shi da ma wanda ba a sa shi ba shi yi yake yi. Kawu Gixe ya sanya shi makarantar boko, inda ya fara daga sakandire aji biyu a dalilin a yawace-yawacen shi ya xan koyi wasu abubuwa. Mus’ab ya kama karatu cikin hazaqa da basira, ga karatun addini da dama tun farkon zuwan shi gidan ya kama a wurin Kawun da Mama, da kuma makarantar Allon dake unguwar. Cikin xan taqaitaccen lokaci sai ya zama har malamai sun san shi, a wannan lokacin ba a cewa ga farin cikin Kawu Gixe da Mama. Mus’ab yana aji uku a makarantar sakandire Innarshi ta haifi ‘ya mace, babu mai kwatanta farin cikin Kawu Gixe kan wannan haihuwa da aka yi mishi, to balle kuma Mus’ab da bai tava so ko jin wani a matsayin da yake jin Mama a rayuwarshi ba. Sai ya xauki son duniya ya xora a kan yarinyar, duk wata hidima ta Aisha ko Saddiqa yanda Mama ke kiranta shi yake yi, har wankinta kan ya tafi makaranta ya gama komai. Wankin Mama da na Saddiqa, share-share da zuba ruwa a randuna. In ya dawo kuma ya yi reno, duk inda za shi yana maqale da ita, ko wace qwandala ya samu ita yake kashewa, suka yi matuqar shaquwa. Saddiqa ta taso cikin kulawa, tsabta da kuma tarbiya. Har Mus’ab ya gama karatunshi na sakandire ya samu shiga A.T.B.U labarin da Innarshi ke ba shi na yanda take fama da rikicinta in baya nan yasa shi xaukar matakin ya rinqa zuwa gida duk qarshen mako, wato juma’a da yamma, lahadi da safe ya koma. In ya zo xin kuwa zai yiwa Innarshi da Saddiqa, da ma Kawu Gixe wankin kayansu ya goge. Suna nan a haka Mus’ab yana karatun shi, shekara ta uku a jami’a aka zo kiran shi ranar wata talata da yamma. Ya hanzarta tahowa gida saboda a zaton shi jikin Saddiqa ne ya tashi, saboda ranar lahadin da ya koma ya barta tana zazzavin baqon dauro. Yana isa gida ya samu ana zaman makoki, ya yi zaton Saddiqa ce ta rasu, sai daga baya ya gane Innarshi ta rasu a sanadin ciwon cikin da ta tashi da shi a ranar, wanda bai wani xauki lokaci mai tsawo ba. Mus’ab ya kixime ya yi kuka har ya ji tamkar bai da sauran hawaye, ya samu kanshi cikin wani matsayi da ba zai kwatanta ba. Da aka yi kwana bakwai Kawu Gixe ya zaunar da Mus’ab a xakinshi yana yi mishi nasiha. “Ai haka rayuwa take Mus’ab, Mama kwananta ya qare bamu da abin yi sai haquri da bin bayanta da addu’a, sai ka shirya in anjima da yamma sai ka koma wajen karatunka, ita ma Habiba na gaya mata in za ta koma Misau ta tafi da Saddiqa ta koma can wajenta da zama”. Mus’ab bai iya ce mishi komai ba in ban da kukan da yake ta yi. A haka ya fita ya je ya yi mata sayayyar ‘yar tsarabe-tsaraben yara ya kawo mata, shima ya shirya ya koma wajen karatunshi. Sati biyu a jere Mus’ab yana zuwa gida kamar yanda ya saba, daga nan ya xauke qafa ya yi zamanshi a makaranta har tsawon wata guda. Ran nan Kawu Gixe da kanshi ya je ya same shi, Mus’ab yana isowa inda Kawu Gixe yake ya tsuguna gabanshi ya kama kuka. “Haba Mus’ab, in babu Mama ba za ka zo gida ba? To ni fa? Kuma ai akwai wata uwar taka a gidan, ga kuma sauran ‘yan’uwanka. Ba za ka tausaya min ba? Na rasa Mama kuma in rasaku ‘ya’yanta duka? Babu Saddiqa babu kai, to da wanne zan ji?” “Ka yi haquri Kawu, na so zuwa wannan satin sai na ce bari in je Misau in dubo Aisha, amma zan zo gida sati mai zuwa”. Suka xan tattauna yaa kawo bain da ya zo mishi da shi ya ba shi sannan ya tafi. Tunda Mama ta rasu sai Mus’ab ya rasa farin ciki, kewa ya addabe shi, ya rasa yanda zai yi ya ji daxin zuciyarshi. Sai ya shiga tunanin yin nesa da gida, nesa da dangi, nesa da mutanen da ya sani. A ganin shi har da mu’amalarshi da sune ya hana shi mancewa da rashin da aka yi mishin. Sau biyu yana roqon Kawu Gixe ya amince mishi neman tafiya qasar waje don ci gaba da neman iliminshi. Bai yarda ba saboda a ganin shi a hali da shekarun da Mus’ab ke ciki kusan ashirin daa biyu zuwa da uku, ba wani wuri ya kamata ya tafi ba, qarasa karatun shi ya kamata ya yi, ya yi aure shima ya samu nutsuwa tare da iyalinshi. Kafewar Mus’ab tasa Kawu ya haqura, sai dai kuma ya qi yarda da barin karatun nashi saboda ganin yana kusa da kammala digirinshi na farko. Don haka a daddafe Mus’ab ya gama watanni biyar, bayan nan kuwa ya yi sallama da gida da dangi ya nufi qasar Italy, inda yaje ya yi digirinshi na biyu, ya karanta Archtectual Engineering, ya kuma yi zamanshi a can har tsawon shekaru bakwai. Zaman da Mus’ab ya yi a can lokacin ne ya koma kan xabi’unshi na sigari, neman mata ya haxa har da barasa. Hakan kuma ya qara wani rashin jituwar tsakaninshi da mahaifiyar shi. Abu ta kalle shi ta ce, “Wannan ne dalilin hana shi auren Saddiqan?” Malam Abdullahi ya ce, “To Inna in zamu bi qa’idar da muke bi wajen ba da aure ayi bincike kamar yanda muke yiwa mazan qannen shi mata, ai ba zai ci jarrabawar ba. Don haka ki yi haquri”. Ta ce, “To ai babu laifi”. Ta tashi za ta fita Malam Abdullahi yana ce mata, “Ga goro”. Ta ce, “Nima ina da shi a gida”. Ta yi tafiyarta ta barsu. Saddiqa kuma tana kwance a xakinta ta qosa ta san me ke faruwa a gidan wanda aka qi shaida mata. Tana cikin wannan tunanin yaro ya kwaxa sallama a tsakar gida ya ce, “Wai ana sallama da Saddiqa in ji Sadisu?’ Kusan minti goma da kiran nata babu alamar za ta fita. Innarta ta leqa xakin ta ga kamar Saddiqan ba ta ji ana kiranta ba. Ta xaure fuska ta ce, “Gaskiya ni ba za ni hira yanzu ba da tsakar ranar nan”. Inna ta tunzura ta ce, “Wacce magana ce Saddiqa ke yi? Ashe ba ina jinki ba shekaran jiya da ya zo kika ce kin daina hirar dare kamar wasu munafukai, jiya ya zo da yamma kika ce sanyi kike ji. Yanzu ya dawo da rana kin ce ba za ki yi hirar tsakar rana ba, to sai yaushe? Na ce sai yaushe zai zo ki fita?” Ta tsare Saddiqa da idanuwanta, ita kuma ta sunkuyar da kanta qasa. “Tashi ki fita tun muna shaida juna dake cikin mutunci”. Ta tashi ta fita tana kuka. Inna ta koma wurin mijinta hankali a tashe ta ce, “Malam yaron nan fa zai kangarar da Saddiqa mu kasa jin daxinta”. Ta ba shi labarin canzawar da Saddiqan ta yiwa Sadisu. Malam Abdullahi ya ce, “Bari zan tura iyayenshi su zo in sanya musu ranar biki sai ayi kowa ya huta”. Ta ce, “To madalla, in ka yi hakan ai kuma shi kenan magana ta qare kenan”. Abu tana isa gidan ta samu Mus’ab tare da wasu tsofaffin abokanshi da suka zo mishi hira kan qatuwar tabarmarta a qofar gida sai cin gasssun kaji suke yi ana hirar da ana dariya. Sai da ta tsaya suka gaisa sannan ta wuce cikin gida. Kusan minti goma da shigarta kafin Mus’ab ya nemi izininsu ya shiga wajen Abu. Bayan ya bayar da kuxin qaro masu kajin saboda qaruwar ‘yan hira. A tsakar gida ya samu Abu tana ‘yan kintse-kintse. “Wa ya zuba min ruwa a randa ne?” Ya ce, “Nine na kuma sa aka share miki tsakar gida”. “Ubangiji ya yi maka albarka”. Ya ce, “Ameen”. Ya bi bayanta zuwa cikin xaki. “Ya ya kuka yi dasu Baban Abu?” Ta ce, “Dukkansu sun qi, ko da yake da na je gidanka ai a cikin maye na same ka, sai yaushe za ka kama kanka ka zama mutum na sosai ba riga ba Mus’ab? Sai yaushe. In na yi nufin taimakon ka kan auren yarinyar sai kuma tausayinta ya kama ni, ba za ta iyaka ba ka fi qarfinta, ba za ta iya da kai ba Mus’abu”. Ya matsa kusa da ita yana kallon ta ya ce, “Haba Abu, dambe zamu rinqa yi da ita ne da za ayi ta cewa ba za ta iya dani ba? Nine fa nake sonta, kin tava sanin so kuwa? Baki san mutum bawan abin da yake so ne ba”. Harara ta galla mishi kafin ta ja tsaki. “To gaskiya zan gaya miki Abu, in na rasa Aisha kema za ki rasani, don tafiyata Italy zan yi in yi zamana ba zan sake dawowa ba”. Ta sake jan wani tsakin ta ce, “Uhm! Sai me in ka yi hakan?” Ya yi murmushi ya sake matsawa kusa da ita ya ce, “Taimake ni Abu ki rufa min asiri kar ki bari su rabani da yarinyar nan, taimake ni ki gaya min abin da kike ganin ya dace in yi”. Ta ce, “Ka tafi ka koma wurin aikinka ka ga yau kwananka uku, zan yi nazarin abin yi ai ba bikin suka sanya ba”. Ya ce, “To Abu”. Ya ciro kuxi masu yawa ya ajiye mata ya ce, “In kin yi min addu’a ki rinqa haxawa da sadaka”. Ta ce mishi, “To”. A waje ya yi bankwana da baqinshi bayan su ma ya yi musu alheri, sannan ya nufi gidan iyayenshi. A waje ya samu Saddiqa tana sharar qofar gida, ya ce, “Yauwa Aisha, ai gara ki shareni kinga shi kenan sai a bar mikini”. Ta xago ta kalle shi fara’ar dake fuskarshi ta kau, cikin sanyin jiki ya isa gareta. “Kuka kika yi haka? Me ya same ki?” Ta soma wani kukan. “Anyi miki wani abu ne?” Ta yi shiru. Ya ce, “Gaya min mana, ko kuwa nine na ja Inna ta yi miki faxa?” Ta ce, “A’a”. “To mene ne?” Tana kuka take gaya mishi “Bana jin daxi, ban san abin da ya same ni ba, qirjina yana yi min nauyi”. Ya qara matsawa kusa da ita ya ce, “Yi haquri Aisha, don wannan kar ki rinqa kuka, yawanci haka mutum ke yi in zai girma. Yanzu na zo ne mu yi sallama zan koma Ajakuta”. Da sauri ta kalle shi ta ce, “Yanzu?” Ya ce, “Eh, ki yi min addu’a kawai bari in shiga gida in yi musu sallama, ki jira ni a nan”. Ta ce mishi, “To”. Da sauri ya shiga ya fito ya sameta a inda ya barta, ya xauko zoben da yake sanye da shi ya matsa kusa da ita ya ce, “Kin gani Aisha zobe ne ya yi min kyau, sai na yiwa yatsanki sha’awarshi, yngo saka mu gani”. Ba ta yi musu ba. Ya yi mata dai-dai, ya kuma dace da yatsun nata. Ta xago yatsun tana nuna mishi, “Ka gani”. Ya yi murmushi ya ce, “Dama yatsun masu kyau ne Aisha, taimakeni ki yi min alqawari ba za ki cire zoben a jikinsu ba”. A hankali ta buxe baki ta tambaye shi, “Babu wani abin da yake faruwa kuwa?” Da sauri ya ce mata, “Akwai, sai dai tunda su Innan basu gaya miki ba to ki yi haquri lokaci zai yi da za ki ji komai, kin gane?” Ta ce mishi, “To”. “In gaya miki wata magana?” Ta yi maza ta ce mishi, “Eh”. A hankali ya ce mata, “Kina da kyau Aisha, kul kika yarda wani abu ya dameki, ni zan tafi na roqeki ki rinqa yawan tunawa dani kina tausayina saboda bani da kowa babu wani wanda yake sona, Inna ce kawai dama to na riga kuma na rasata, kin gane?” Ta ce mishi, “To”. Kwana uku da isar Mus’ab Ajakuta yana kwance tamkar mara lafiya, wurin aikinshi ma ranar Mondy bai iya zuwa ba, yana gida abin da ya yi matuqar tayarwa Jennifer hankali duk da ba kula juna suke yi ba. Mus’ab yana kwance Sani yana zaune a gefenshi ya ce, “Wai ni ciwon gaske kake yi ne ko damuwa ce ta yi maka yawa?” “Gani nan ne kawai Sani, ka duba ka gani wai ‘yar wayar da nake samu muna ‘yar hirar ma ina tahowa sai Inna ta karve”. Sani ya ce, “Nifa inda nine kai da tuni na tafi wurin Kawu Gixe na gaya mishi komai”. “To ai Kawu Gixin ne ya ce ita ce wuqa da nama a kan maganar yarinyar”. Sani ya ce, “Duk da haka tsananin ai ya yi yawa, ita yarinyar da alama ai in ta samu an ci za ta ce ba ta son wancan mutumin, sai kawai ka yi qoqari ta amsa da bakinta tana sonka”. Da daddare suna hirarsu a falo bayan sallar isha’I sai ga Jennifer ta shigo, ganin Mus’ab a zaune riqe da karan sigari ya sata tambayar abin da ta fara gamuwa da shi. “Wannan kuma wace ce na gamu da ita yanzu?” Ya yi murmushi ya ce, “Gaisheni ta zo yi mene ne?” Ta tave baki ta harare shi ta ce, “Ka dai ji kunya, yarinyar cikinka ka koma nema, wanan ai ba ta fi sha takwas ba, in ta yi qoqari ashirin”. Ya ce, “Jennifer kenan, to ni xin dame na fi haka, ai nima yaro ne ba shi yasa kema kike biye dani ba”. Jennifer ta zo har wuya ganin Sani yana dariya. Ta ce, “Ba laifinka bane ni na zo gidanka. Uhm! Tun farkon mu’amalata da kai da ka nuna kana sona sai da Felicia ta yi min kashedi a kanka ta ce kar in yarda za ka yi amfani dani ne kawai ka awurgar a lokacin da ka ga dama, bayan ka rabani da samarina na gaskiya”. Mus’ab ya yi dariya bayan ya fitar da hayaqin sigarin, a hankali ya miqa hannu ya kaxe tokar kafin ya kalle ta cikin murmushi ya ce, “Sai dai baki ji kashedin da qawar taki ta yi miki ba, saboda kin mato a kaina, kinga santalelen yaro. Haka nan ita ma qawar taki da take yi miki kashedi, kashedin nata bai hanata amsa kiran da na yi mata ba sai da na gaji da ita na watsar don kaina”. Ta yi magana cikin yanayin xaci, “Babu laifi, wata rana ba za ka yi ba, don wata matar ma dole ka ganta ka qyaleta”. Ya ce, “Ehm, babu matsala tunda dai na samu na bi ta kanki ke da qawar taki ai ni shi kenan buqatata ta biya”. Sani yana danne dariyar shi yana faxin, “Kai ku kam kuna da abin mamaki, in baku ga juna ba babu zaman lafiya, in kun haxu kuma sai kunyi faxa. Wace irin soyayya ce wannan? Kai Mus’ab ko gaishe ka aka zo yi wai sai anyi faxa da kai a baka da lafiyar ma?” “A’a, to in an zo gaishe ni sai a zageni in qyale? Ta zo gaishe ni ta coge a nan?” Sani yana murmushi ya ce, “Kema Jennifer har dake, mara lafiya ai kusa da shi ake zuwa. Dawo ta nan ki ji damuwar shi”. Ya miqe ya fita ya basu wuri yana faxin “Dawo ta nan Jennifer in dai dubiyar kika zo yi da gaske ba qarasa shi kike son yi da baqaqen maganganunki ba”. Mus’ab ya fara nishi “Wash! Ya kalle ta cikin murmushi, kafin ta ce za ta yi wata magana tuni yasa hannu ya cafkota ya shiga sumbatarta. Sani ya shigo ya gansu ya yi kamar bai ga abin da suke yi ba, ya wuce ya yi tafiyarshi. Saddiqa tana Misau ta rasa inda za ta sa ranta ta ji daxi, an sanya bikinsu da Sadisu sati biyu kawai aka xiba. Qunci da takaici ne suka gallabeta, sai dai in an tambayeta ba za ta ce ga taqamaiman abin da ya haddasa mata hakan ba. Tana kwance cikin kasala da rashin sanin abin yi, wayarta ta yi motsi alamar saqo ya shigo a cikinta. Duk da ta daxe ba ta samu wayar Mus’ab ba saboda daxewar da ta yi ba ta riqe wayar ba, miqa hannu ta yi ta xauko wayar, ga abin da ya ce mata. Aisha! Mutane suna rayuwa, mutane suna mutuwa, wasu su ce sai anjima, wasu za su iya mantowa amma ni kam har abada kina cikin zuciyata. Mus’ab Abdullahi! Ta sake kallon kalmomin cikin tunani, ba ta gane komai game da kalamanshi ba. Ya ji labarin bikin ne? Ta tambayi kanta. Ta yi kamar ta kira ta tambaye shi sai kuma ta fasa. Mus’ab yana kwance a xakinshi wasanni suke yi da Jennifer lokacin da wayarshi ta yi qara, a haka ya miqa hannu ya xauki wayar cikin sauri ya kaita kunnen shi. “Hello Ishaq”. Qoqarin faxin hakan ya yi saboda yanda Jennifer ke sarrafa shi. “Yaushe rabonka da Misau?’ Cikin hanzari ya bar komai ya miqe zaune. “Me ya faru?’ Ishaq ya ce, “Na fa ji kamar sun sanya bikin yarinyar nan, don shekaranjiya na je gai da Abu ita take bani labari”. Mus’ab ya zama tamkar mutum-mutumi a zaune a kan gadon, ya rasa me zai ce in ban da gumi babu abin da ke keto mishi a jikinshi. Jennifer ta kixime tana faxin “Me ya faru? Anyi mutuwa ne?” Tana qoqarin qanqame shi take faxin “Maman ka ce ta mutu”. “Shut up Jennifer!” Ya faxi da qarfi tare da yin jifa da ita ta faxa can gefe. Banxaki ya shiga ya yi wanka ya fito ya kama shirin tafiya ba tare da ya jira wayewar gari ba. Sani ya shigo xakin saboda kiran da Jennifer ta je ta yi mishi saboda tsoratar da ta yi da yanayin Mus’ab da ta gani. Cikin harshen Hausa yake yiwa Sanin bayani za su kasheni ne Sani, za su aurar da yarinyar nan Aisha suna son ganin na yi mutuwar tsaye. Ita kuwa Jennifer sai faman sorry take cewa tana qoqarin rarrashi da kwantar da hankali. “Bari in fito mu tafi tare kawai don bai kamata ka yi wannan doguwar tafiyar a wannan tsohon daren kai kaxai ba kana kuma tuqi”. Tare suka fito da ‘yammatansu su biyu da dama suka kawo don su taya su kwana, suka sauke su a hanya suka wuce suka kama hanyar Misau. Qarfe shida da rabi na safe Mus’ab da Sani suna zaune a falon Mus’ab xin a gidanshi na Misau, yana yiwa Saddiqa waya lokacin ta idar da sallar asuba. “Me yasa za ki yi min haka Aisha? Me yasa?” A kixime ta tambaye shi cewa, “Me na yi maka kuma daga ina kake maganar?” A hankali ya ce mata, “Gani nan a gidana Aisha na zo Misau yau kuma maganar aurenki ya kawo ni, ina son ganin ki yanzu, ina so mu tattauna al’amuran dake tsakaninmu, mu gamu yanzu a gidan Abua ina son sanin abin da ake ciki”. Mus’ab yana zaune gaban Abu yana kallon agogon hannunshi yana kuma kallon hanyar da Saddiqa za ta vullo. Ita kam Abu haquri take ba shi tana kuma gaya mishi wai har ta samar mishi wata yarinyar da take shirin sawa ayi xaurin auren rana xaya da na Saddiqan sai gata ta shigo. Ramar da ya gani a tare da ita, ita ce ta fara sanyaya mishi jiki. Mus’ab ya kalle ta cikin nutsuwa. “Kin yi ciwo ne Aisha?” Ta sunkuyar da kanta qasa hawaye suka soma zuba daga idanunta. “Daina kuka ki gaya min Aisha kina sona?” Da sauri ta xago ta kalle shi idanuwansu suka haxu, ta yi maza ta sake sunkuyawa. “Gaya min kawai Aisha, ai ni na daxe ina sonki, na daxe ina burin mallakar ki a matsayin matata, na daxe ina buri da fatan in samu damar da na sanyaki a gabana na gaya miki wannan kalmar ina sonki Aisha, ai bani da wata budurwa a Misau in bake ba, kece yarinyar da nake so ban samu damar da muka zauna muka tattauna matsalolin da masoya ke fuskanta ba saboda tsoro”. “Tsoro kuma?” Ta yi tambayar cikin wani yanayi. “Yanzu tsoro ne ya hanaka gaya min abin da ya kamata a ce tuntuni ka gaya min?” Ya yi maza ya ce, “Eh, Aisha tsoro ne, in ban da haka ai da tuni na gaya miki cewar duk duniya bani da abin da nake so kamar ki”. Ta miqe da niyyar tafiya ta barshi. Ya yi maza ya kama hannunta ya riqe. “Kar ki tafi ki barni Aisha, kar ki yi fushi dani taimakeni ki rufa min asiri, ki taimakeni kamar yanda Innata ta taimake ni a farko, ai ita ta haifeki Aisha, taimakeni ki yi min kwatankwacin gatan da ta yi min a farko”. “In ma ban yi ba, ba laifina bane kai ne tsoro ya hanaka yin abin da ya dace ka yi”. “Ai tsoron ni kar a rabani dake ne Aisha, Inna ta ce in na ce ina sonki za ta baki labarin mugun halina, tana qina dake ne wai a dalilin tana tsoron kar in cutar dake. Na rantsre miki ba zan iya cutar da ke ba Aisha, don haka ki toshe kunnuwan ki a kan abin da za ki ji an gaya miki a kaina”. Ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce, “Kana nufin ba gaskiya bane?” Da sauri ya ce mata, “Gaskiya ne Aisha, gaskiya za ta gaya miki, ni ban tava jin wata magana ta fito bakin Inna ba sai gaskiya, don haka gaskiya kawai za ta faxa, ni xin ne ita ta haifaeni ta fi kowa sanina, tana qina dake saboda wasu halaye nawa da take ganin basu yi mata ba. To amma kar ki manta na zauna gaban Innata ta tausaya min ta taimakeni ta rabani da duk wani abin da nake yi a wancan lokacin, don haka na roqe ki duk abin da za ki yi a kaina ki tausaya min kar ki juya min baya”. Saddiqa ta miqe da nufin tafiya gida Mus’ab ya biyota. “In kin je gidan za ki yiwa Inna maganar ne?” Ta ce, “Ai nima tsoro nake ji”. “Haba Aisha, ki taimakeni mana kar ki bari su aurar dake ga wannan mutumin na fishi dacewa dake, na fishi sanin darajarki, zan fishi girmamaki in kika daure kika toshe kunnuwanki kan abin da za ki ji a kaina kika amince kika aureni. To ni kuwa ba zan tava baki kunya ba”. Suna isowa qofar gidan ta shige ciki ta barshi nan a tsaye. Innarta tana ta aikin qunshe goron da take aikewa da shi na gaiyatar mutane biki, ta kalli Saddiqa yanda fuskarta ta canza. “Hala daga wurin yayanki kike?” Ta koma gefe xaya ta tsuguna alamar tana son yin magana, sai dai ta kasa, ta rasa ta inda za ta faro zancen. Ta kalli Inna cikin rawar jiki da rawar murya ta ce mata, “Inna mene ne?” Ta yi shiru saboda yanda jikinta da muryarta suke rawa. Inna Habiba ta zubawa Saddiqa ido cikin tausayi, zuciyarta ta tabbatar mata da cewar son Mus’ab take yi, sai dai ba za ta barshi ya yi nasara a kan yarinyar ba. “Me ya faru Saddiqa? Me kike son gaya min? Tambayi duk abin da kike son sani zan gaya miki ba tare da raina ya vaci ba, ba zan yi fushi dake ba balle in je ina yi miki faxa, ai baki da wata uwar da ta wuceni, nice uwarki. Yayanki ya gaya miki wata magana ne?” Saddiqa ta soma kuka, ta ce, “Yana sona, Inna ya ce kece kika hanashi ya gaya min yana sona bayan kuma shine xan’uwana”. Gwaggo ta yi murmushi ta ce, “Ke yarinya ce Saddiqa shi yasa baki gane dalili ba, ke da yayanki ‘yan’uwa ne da zumunci ya haxaku, sai dai halayenku da xabi’unku ba xaya bane, shi ba abokin haxinki bane, hanyar jirgi daban ta mota daban, ba zamu iya dashi ba halayensa sun fi qarfinmu”. Ta ce, “A’a, Gwaggo ni zan iya da shi, ni shi nake so ba Sadisu ba, dama na yi shiru ne kawai don bai riga ya furta min ba, amma yanzu tunda ya gaya min ya yi min rantsuwar bai da wata budurwa a Misau in ba ni ba. To ki taimakeni ki yafe min kar ki baiwa Sadisu ni, Yaya Mus’ab nake so”. Ta kai gwiwpyinta qasa ta durqusa a kansu alamar roqo cikin kuma kuka mai tsanani. Inna Habiba ta zuba mata ido tana kallon ta, ta ce, “To Saddiqa ni dama ai ba wai bana sonki da shi bane, savanin dake tsakaninku ne na ga ya yi yawa na ce gara miki inda za ki samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma tunda haka ne ai shi kenan, ni na gane ke ko warin sigari baki so a kusa dake, to shi kuwa na ji labari an ce lokacin da kamfanin sigarin da yake sha na Rothmans suka yi bikinsu har kyautar girmamawa suka yi mishi saboda cinikin da yake yi musu. To wannan ma da xan sauqi a awurina da ya tsaya a haka nan, inda kike ganinshi mashayin barasa ne na qarshe”. Saddiqa ta qwalla qara da iyakacin qarfinta tare da kama kanta da hannayenta duka biyu. “Wayyo Inna! Wayyo Allah!!” Inna ta samu damar xora bayaninta da cewa, “To shi nake jiye miki, kin san halin mashayi bai da wata amana, ga shi manemin mata. A nan garin ne kawai baya yi, amma an tabbatar min da cewar duk inda yake in ba a nan bane bai rabo da matan banza suna biye da shi, shi yasa nake tausayin quruciyarki. Kina da sha takwas ne yana da talatin da biyar, ina tausayin ki zama matar mashayi ko manemin mata, shi yasa na zava miki Sadisu yaro qarami, bai girmeki da wasu shekaru masu tsanani ba, za ku yi quruciyarku tare ne ku girma tare, a kan idonmu aka haife shi har ya girma, bai da wani halin assha, shi yasa na zava miki shi ku biyun dukanku yaran kirki ne masu biyayya masu ganin girman na gaba. Ko kuwa har yanzu kin fi son auren yayanki a kan Sadisu?” Cikin kuka ta ce, “Na haqura Gwaggo, na yarda da zavin da kika yi min na auren Sadisu”. Daxi ya kama Inna Habiba, ta shiga sanyawa Saddiqa albarka, cikin zuciyarta kuwa faxi take yi ja’irin yaro kawai, ba zan barka ka yi galaba a kanta ba balle ka sanyani in ji kunya, bayan na riga na yi alqawarin baiwa xan aminiyata ita za ka zo ka bijirar min da ita. Mus’ab kuwa yana can gidanshi tare da Sani suna tattaunawa kan yanda za ayi, sai dai maganar kawai yake yi amma hankalinshi yana can wajen sauraron wayar Saddiqa, don ta gaya mishi yanda suka yi da Gwaggonta shiru babu wayar. Hankalin Mus’ab ya kai matuqa wajen tashi. Sani ya kalle shi cikin raxa ya ce, “Ina ganin tunda ni a gida ba a san na zo ba, tunda da sauran duhu muka iso muka kuma taho nan kai tsaye, ko in ka ga da matsala abin zai mana gardama in xauke maka yarinyar mana in tafi da ita sai kai ka yi zaman ka, ka yi ta taimakawa wajen neman ta, ka ga babu mai gane kana da hannu cikin vacewar tata, in yaso daga baya in hankula suka kwanta sai a dawo da ita sai a xaura muku aurenku”. Mus’ab ya zuba mishi ido cikin nazari ya ce, “Da zan yi jarumtakar yin hakan to da na ji daxin shawarar taka, to ba zan iya ba saboda dalilai guda biyu. Na farko bana so wani savani ya sake shiga tsakanina da iyayena, a yanzu mun shirya ni da babana, ni da shi muna da fahimtar juna, zamu zauna tare mu yi hira, zai bani shawara zai yi min nasiha har muna zuwa unguwa tare. Inna ce bani da wannan fahimtar da ita, ina kuma qoqarin ganin mun samu daidaituwa sai kuma in zo in tafka musu irin wannan laifin? Bana zaton in ya bayyana zamu sake samun wata fahimta dasu. Na biyu duk matsanancin son da nake yiwa Aisha ina son mallakarta ne ta hanyar aure, in babu auren to bani da wata buqata irin wannan a tare da ita, don ba zan iya keta haddinta ba, don haka na fi so iyayenmu su yarda su bani ita in mallaketa ta zama matata da izininsu don mu samu albarka, in kuma yi qoqarin gyara abin da na riga na vata a baya. Yanzu fatana bai wuce komai za a gayawa Aisha ta yarda ta daure ta bani haxin kai ba, in har ta yi min haka, to komai zai zo min da sauqi. Don in har ta dage ta ce ni take so, ina ganin kamar Innar za ta yi sassauci”. Gajiya ya yi ya xauki wayarshi ya danna lambobin Saddiqa, kwance take a xakinta har lokacin kuka take yi ba ta daina ba. Kamar kar ta xauki wayar sai kuma wata zuciyar ta ce ta xauka. “Na ji shiru ne Aisha shine na ce bari in bugo in ji me kike ciki? Sai dai na ji kamar kina kuka, me ya same ki?” Ta ce, “Kukan baqin ciki nake yi”. Gaban Mus’ab ya faxi ras! Ya daure ya tambaye ta. “Baqin cikin me kike yi Aisha?” Ta ce, “Baqin cikin da ka yi min dalilin shi”. Ya sake wani mummunan faxuwar gaban mai qarfi. “Ki taimakeni Aisha ki tausaya min ke kaxai nake dake, Aisha in kin barni za ki barni cikin qunci da wahala, taimakeni ki bani haxin kai ki zama matata”. Ta yi maza ta katse shi da cewa, “Kana nufin in zama matar mashayi?” Ya ji tamkar guduma ta buga mishi. Ya yi qarfin hali ya ce, “Ba haka nake nufi ba”. Ta ce, “To abin da Gwaggo ta gaya min kenan game da kai, ko kuwa me ka ce game da maganganun da ka ce za ta gaya min?” Ya ce, “Na ce miki gaskiya ne ban tava ji ta faxi wata magana ba sai gaskiya, ita ta haifeni ta fi kowa sanina. Sai dai komai ta gaya miki ki daure ki taimakeni…….” Kafin ya qarasa ta katse shi da cewa, “Ba zan iya ba, tunda ban ga alamar kaima kana taimakon kanka ba, don haka ka yi haquri ka taimakeni ka fita hanyata, ka taimakeni kar ka sake shiga al’amurana ka barni in yiwa iyayena biyayya. Dama ni abin da na saba kenan, don haka daga yau bani ba kai……” Ta katse layin ta bar Mus’ab riqe da kan wayarshi a hannu cikin kaxuwa da firgita, a zuciyarshi kuwa cewa yake yi “Wayyo Aisha! Za ta tilastani yin abin da bani da niyyar yi a kanta!” Mu haxu a littafi na biyu. ABU NAKA wai maganin a kwaveka. Taku; Aunty Hafsat.