💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 t *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _ZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *FREE..* 🅿️==1️⃣↪️2️⃣ "Subhanallahi! Wannan bala'i ya yi yawa, a ce a kwana uku an kashe mutane goma? Masu kama macizai mutum takwas, wannan wani irin masifa ce ta macizai da ya fara addabar mu haka a gari? abu sai tsamari yake yi, tun ana samun sara kaɗan-kaɗan, ga shi saran macizai din bakinsu da girma! Me yake shirin faruwa ne haka a cikin wannan alƙarya na da mutanen yanki na?" cewar mai garin yankin kauyen kwana dake jihar yola da yake can cikin dajin fulani wanda ya cika da albarkatun korayen shuke-shuke, a wannan sassanin fulani ne suke rayuwa a wannan yanki, kuma su na da yawa dan sun hayayyafa, basu fita cikin gari kuma ba a shigo musu. Jama'ar da suke tsaye a wajen ne cike da jimami da fargaba su na alhini, wani dattijon tsoho cikin harshen fullanci ya ce "Gaskiya muna cikin hatsari a wannan alƙarya, ga shi yanzu an fara samu kisan macizai da yawa, ya kamata mu san abun yi" sai tattaunawa suke yi ta yadda zasu shawo kan wannan babbar matsalar da suke ciki, wata kyakkyawar budurwa ce a tsaye a can gefe fara sol, tana da idanun mage, sanye take da kayan fulani ta naɗa farin mayafi a saman kanta, ta rufe gefen fuskarta da shi, rabin gashinta ya sauko ya rufe mata rabin fuska wanda ya sake hana asalin kyawun nata fitowa sosai a gani,kafarta babu takalmi, a hankali ta bi mai kama macizai wanda aka kashe da kallo, ranta a b'ace ta juya a hankali tana tafiya dukkan sassan jikinta yana lankwasawa, a yadda take taka kasa da ka ganta kasan bata yi maka kama da cikakkiyar mutum ba, daji ta yanka ta shiga cikin korayen bishiyoyi inda zata samu yar uwarta kawai take hari, can kusa da wani rafi mai sanyi da dadin kallo ruwan fari k'al da shi abun sha'awa taja ta tsaya, bata ankara ba taji saukan wani zureriyar wutsiyar maciji🐍, ko kaɗan hakan bai tsoratata ba, tunda ita ma macijiyar ce, d'aga idonta ta yi saman bishiyar da wutsiyar macijin ya sauko mata, ta kalli yar uwarta wanda dukkanta macijiya ce,a hasale ta ce " *AZIMA!!?* me yasa kika son kashe mutane kwanan nan ne kam?" macijiyar da aka kira da Azima a hankali ta sulalo daga saman bishiya ta kanannaɗe yar uwarta tana lasarta da harshe, hannu dayar tasa ta ture kanta a macijiyar, sannan ta ce "Azima tambayarki fa nake yi?" gefe ta koma ya yinda ta saki wani huci ta girgije nan ta zama rabi mutum rabi macijiya, daga ƙugunta abun da ya yi sama mutum ce, daga kugunta abun da ya yi ƙasa macijiya ce. Dariya ta sheƙe da shi cikin wata murya mai amo da rashin dadin sauraro, sai jijjiga take yi tana naɗe jelar macijinta ta ce " *AZIZA!* bana mantuwa kuma bana yafiya!! Duk wanda ya shiga gonata sai na hallaka shi, sai na ga bayansa ko ma waye! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Dan haka bana bukata ki din ga tuhumata akan abun da kike da masaniya a kai" "Amma Azima kisan ya yi yawa! Da an miki laifi kaɗan sai kisa? So kike yi sai an gano mu ba mutane bane macizai ne mu a kore mu a gari?" Rintse blue eyes dinta Azima ta yi sannan ta buɗe tana zaro harshenta suffan na macizai sak ta ce "Ina so na bar wannan alk'aryan, ina so na shiga cikin gari wanda yake da al'umma da yawa ta yadda zan tarwatsa su!" girgiza kai Aziza ta yi ta ce "Ke nan za ki iya tafiya ki bar su Baffa da Hajja?" "Me zai hana Aziza!? Ina da burin shiga cikin jama'a masu yawa duk da na san ni din ba mutum ba ce!" "Shigarki jama'a ba alkhairi bane Azima, dan haka ki bar wannan maganar ki zo mu tafi gida kar mu koma mu samu Baffa ya dawo ya titsiye mu da tambaya daga ina muke, amma dan Allah ki koma mutum tun daga nan" Aziza ta faɗa tana yin gaba, dariya Azima ta yi a madadin ta zama mutum kamar yadda aka ce mata sai ta rikiɗe ta zama katuwar macijiya mai sheƙi da ban tsoro, ko da Aziza ta juya ta ganta a haka girgiza kai ta yi, ba tare da ta ce mata uffan ba. Sai da suka kusan isowa gida kafin ta girgije ta zama mutum, yadda yar uwarta Aziza ke tafiya haka ita ma take tafiya, mayafinta da ta ajiye ne kusa da gida ta dauka ta yi irin lullub'in da yar uwarta ta yi, su na yin wannan lullub'i ne saboda idanunsu da yake abun tsoro barin ma kwayar idon Azima blue, ita kuma Aziza idon mage mai fari-fari, ko kaɗan basu da baƙin ido,shi yasa Hajja mahaifiyarsu ta basu su din ga lullubi, shi yasa idan sun yi lullubin suke saukowa da dogon gashinsu ta gefe ya rufe musu gefen fuska, ga shi dai alk'aryan duk fulani ne kuma kyawawa, amma duk fadin yankin kwana babu mace ko namijin da ya kai su *AZIMA DA AZIZA* kyau. Ko sallama basu yi ba suka shiga gidan suka iske mahaifiyarsu Hajja a jikin murhu tana aikin hura kara, Aziza ta ce "Sannu da aiki Hajja" dagowa ta yi ta kalli kyawawan yan biyun nata ta ce "Yauwa sannu Aziza, daga ina ku ke haka? Tun safe fa ku ka fice a gidan nan" "Amm Hajja muna rafin jimulo" murmushi Hajja ta yi ta kalli Azima wanda idonta yake kan garin Mahaifiyarta, haka kawai take ji ta watsawa garin dafi, Aziza ta ce "Hajja karan ya ƙi kamawa ne?" "Eh Aziza ya ƙi kamawa wallahi ga idona ya yi ja yana min zafi" "Ayya sannu Hajja bari na hura miki!" "Yauwa yar albarka hura min, Azima lafiya kuwa kika ƙurawa garin da zamu yi tuwo ido?" murmushi ta yi ta ce "Lafiya lau Hajja" girgiza kai Hajja ta yi ta duƙa ta shige bukka, ita kuma Aziza Hajja na shiga bukka ta rufe idonta ta rintse nan idon ya dawo ja, bakinta ta buɗe ta fiddo da turirin ta hura a murhu nan kuwa ya kama da wuta, Azima kuwa wajan garin ta je ta bude bakin tana shirin zuba dafi sai ga sallamar Baffa, da sauri ta mai da harshenta, amsa sallamar Baffan suka yi tare yi masa sannu da dawowa ya amsa, fitowa Hajja ta yi,ita ma ta ma sa sannu da dawowa tare da shinfiɗa masa tabarman kaba, ya zauna, Aziza ta ɗiba masa ruwa ta kawo masa, sannan suka zauna dukkansu. Sai da Baffa ya sha ruwan sannan ya saki ajiyar zuciya, cikin fulatanci Hajja ta ce "Baffan Azima da Aziza lafiya kuwa?" "Ina kuwa lafiya, wannan alk'arya ya kafu tsawon shekaru sama da hamsin, anyi gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma a yanzu bala'in da yake tunkaro wannan alk'arya ya yi yawa, ina wannan shahararren mai kama macizai din nan, Ilu Mai Macizai?" Hajja ta ce "Eh na ganesa,waye bai san Ilu mai Macizai ba" "To shi ma an kashesa yau" salati Hajja ta sa tana tafa hannu ta ce "Hande in bone ni Jamila, yanzu shi ma Ilu mai macizai an kashesa?" "Eh har ma anyi masa jana'iza an binnesa, ga shi duk macizan da ake kamawa babu wanda bakinsa ya yi dai-dai da saran da ake samu, ga shi yanzu har zargi ya fara shiga tsakanin mutane da mutane, yanzu haka mai gari ya yiwa Jarman Macizai aike da wasiƙa,kin ganesa?" Hajja ta riƙe hab'a alaman tunani ta ce "Jarman Macizai ba wannan na yankin al'karyan jimo ba?" Baffa ya ce "Eh shi dai, ya ma amsa da gobe zai zo, zai taho da ruwan wani magani wanda za a ba wa kowa ya sha wanda hakan ne zai bayyana waye ba mutum ba a cikin al'umman yankin kwana, kin san titsiyeni aka yi a kan su Azima da Aziza, wai yarana basu abu irin na mutane, shi ne za ayi wannan gwajin" wani firgita Azima har ma da Azizan suka yi, suka kalli juna, ba tare da iyayensu sun san halin da suke ciki ba,tuni idon Azima ya kara komawa blue sosai, nan ta kalli fatar jikinta ta ga ta fara zama blue da sauri ta miƙe ta shige bukka, ita ma Azizan tashi ta yi, Hajja ta ce "Dan kawai yara basu mu'amala da kowa, sannan idonsu ba baƙi ba shikenan sai a saka mun yara a gaba?" Baffa ya ce "Amma kin san dai har da maganar aurar dasu, bisa al'ada ta wannan yanki namu yara da sun shekara 11 ake aurar dasu, yanzu kuma su Azima da Aziza su na da shekara 15 kin ga kuwa dole a saka musu ido mun ƙi aurar dasu, ga shi kullum Arɗo sai ya min magana" tabe baki Hajja ta yi ta ce "Allah ya kyauta amma ai aure lokaci ne" ta miƙe taje duba ruwan tuwonta. A bukka kuwa sadda Azima ta shiga nan kasanta ya koma macijiya har sai da ta cika bukka din, kalar fatarta ta koma blue, Aziza ce ta biyo bayanta ta ce "Azima ki koma dai-dai kar Hajja ta shigo ta ganki haka fa?" A hautsine Azima ta ce "Dole na kashe Jarman Macizai! Nayi alkawari sai na ga bayan wanda yake shirin ya san su waye mu na asali!." 🍃🍃🍃🍃🍃 *HANZARTA BIYAN NAIRA ƊARINKI KACAL🤗 DAN JIN CAKWAKIYAR DAKE CIKIN WANNAN LITTAFI, MOMYN AHLAN TANA KAUNAR MASOYANTA*🤗 COMMENTS AND SHARE BY MOMYN AHLAN🥰🤗 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *FREE..* 🅿️==3️⃣↪️4️⃣ "Ba ki da hankali ne Azima? Jarman macizai za ki kuma kashewa? To bari kiji! Kin ga wannan kashe-kashen shi zai sa a gane su waye mu, dan Allah Azima karki kashesa, bana son kisan da kikeyin nan" Aziza ta faɗa tana bin Azima da kallo, cikin huci Azima ta ce "To tsammaninki me zai faru? Idan har jarman macizai ya kawo maganin gwaji dan a tabbatar da su waye ba mutane ba? Ke a tunaninki mutanen yankinmu zasu barmu a raye ne? Ina kashemu zasu yi, dan haka kafin hakan ta kasance ni nan zan kashe Jarman Macizai kuma ba ki isa ki hanani ba" Azima ta fada tana komawa mutum tare da ficewa a bukkan, tana fitowa hanyar waje ta nufa Hajja ta ce "Azima ina kuma zaki je bayan baku jima da shigowa gidan ba?" kafin Azima ta yi magana Baffa ya fito daga kewaye yana fadin "Ban hanaku fita sakakan ba Azima? Ina za kije?" cikin in-ina da kame-kame ta ce "Zan duba abu na ne a nan waje" Baffa ya ce "Ba za ki duba ba koma ciki" haɗe rai sosai Azima ta yi tare da yiwa Baffa wani irin kallo ta koma fuuu, da kallo Baffa da Hajja suka bi Azima, jiki a sanyaye Baffa ya koma ya zauna, tunanin abunda ya faru shekara ashirin shike dawo masa kwakwalwa, kar dai ace fansar da *Banju ya ce zai dawo ya daukar wa kanwarsa Bahula da kansa shine ya dawo dauka kan yaransa!?* Haqiqa shima zuciyarsa ta fara yi masa saqe-saqe a kan yaransa ba cikakkun mutane bane amma baya so zarginsa ya tabbata, rintse ido ya yi yana karanto kalmar "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!" kallonsa Hajja ta yi ta ce "Lafiya kuwa Baffan Azima da Aziza?" "Haqiqa Jumala ina jin tsoro!" "Tsoron me fa Baffan yan biyu?" "Inajin tsoron furucin Banju lokacin da zan kashesa maganarsa ta karshe, ko kin manta da kalman da ya ce...." Baffa bai karasa ba Hajja ta dakatar da shi "A'a Baffan Azima da Aziza! Karka yiwa yarana baki! Taya wa inda suka mutu shekara ashiri a ce sun dawo? Azima da Aziza dai ni na haifi yarana! Kuma ni mutane na haifa, kwata-kwata wannan maganar bai kamata ace ya fito daga bakinka ba, kai da kanka ka fara zargin yaranka to ba dole jama'ar gari ma su fara zarginsu!" Hajja ta faɗa cikin sosuwar rai, girgiza kai Baffa ya yi ya ce "Ba haka bane Jumala, amma dai jikina ya yi sanyi! Allah ya kaimu gobe jarman macizai zai zo ya warware komai" ita dai Hajja ba ta sake cewa kala ba, illa aikinta da ta ci gaba da yi, Azima kuwa tana saman bukka a macijiya tana jin maganganun Baffa, a ranta take ayyana yadda zata kawar da Baffa!. 🍃🍃🍃🍃🍃 Washe gari tun kafin garin Allah ya waye Azima ta sulale ta fice, hanyar yankin Jimo dai-dai kan layin shigowa yankin kwana a kan wata babbar bishiya ta kwanta ta nannaɗe idonta sun kara komawa blue, tana jiran isowar jarman macizai, awanta kusan uku kafin ta hangosa, wani murmushi ta yi mai tattare da zallar mugunta kafin ta sauko ta koma mutum, tsayuwa ta yi bayan ya gama shigowa yankin kwana. Yana kan tafiya akan dokinsa a hankali ya hangi budurwa tsaye a hanyarsa,magana ya hau mata amma shuru, tana tsaye da lullubi, saukowa ya yi a kan dokin ya tunkaro inda take tsaye, sai da ya zo kusa da ita kafin ya ce " *MUTUM KO ALJAN!?"* Murmushi ta yi tana lankwasa harshe ta ce " *RUWA BIYU!"* sannan ta juyo ta yaye mayafin da ta lullube jikinta ta jefar, jarman macizai na ganin idonta ya yi saurin ja da baya, dariya Azima ta sheqe da shi ta ce "Na ga bai kamata ace kasha wahala ba wajan zuwa gwajin wanene wanda ba mutum ba a wannan yankin! Gani na zo da kaina dan dakatar da kai! Ba zaka shige ba sannan ba zaka koma ba!" da sauri jarman macizai ya yi baya dan dauko kayan aikinsa tsalle daya Azima ta yi ta zama macijiya ta cakume jarman macizai nan suka hau kokawa, duk yadda yaso kwace kansa daga hannun Azima ya kasa, daga karshe ta rufesa da sara, sosai ta yi masa jina-jina sai da ta ga ya daina mutsu-mutsu sannan ta sakesa ta sulale ta yi hanyar rafin jimulo, tana isa rafin ta hau kyalkyala dariya nan ta zube kusa da rafin. 🍃🍃🍃🍃🍃 A cikin unguwa kuwa ana nan ana jiran isowar jarman macizai, tun ana sa ran ganinsa takwas har goma, inda a karshen mai unguwa ya ce aje a duba ko lafiya a binciki hanya aka tura mutum uku. Ai kuwa can suka gano gawar jarman macizai a yashe cikin jini, cikin tashin hankali suka juya da mugun gudu suka koma suka sanar da jama'ar gari an kashe jarman macizai. Fadin tashin hankalin da mai unguwa da jama'ar gari suka shiga b'ata lokaci ne. 🍃🍃🍃🍃 Fitowa Aziza ta yi daga bukka dan tun sadda taji motsin yar uwarta jikin dare kafin garin Allah ya waye jikinta ya bata ta tafi kashe jarman macizai, abunda yasa bata yi yunkurin bin bayanta ta dakatar da ita ba sabida tasan dole Hajja da Baffa su leƙo duba lafiyarsu, tana fitowa dauke da murmushi a fuskarta Hajja ta ce "Aziza ke kin tashi? Azima ta farka ta yi sallah kuwa?" tsilli-tsilli da ido Aziza ta fara kafin ta ce "Eh Hajja ta tashi ta yi har ma ta fita wai ta je rafin jimulo" Aziza ta karasa maganar da in-ina sabida da asuba da Hajja ta shigo tada su kara Aziza ta jera kusa da ita ta yadda zata ga kamar Azima ce ke bacci, dan lokacin da Azima ta fita Aziza ta ji motsinta tsoron kar su fita duka a gane yasa Aziza hakura ta kwanta, dan Baffa kunnuwansa akwai saurin jiyo abu. Kallon Aziza da kyau Hajja ta yi kafin ta ce "Me ku ke zuwa yi kullum ne a rafin jimulo?" "Ba komai Hajja kawai rafin akwai dadi ne, ga iska mai dadi, Hajja kin manta sadda kike kai mu muyi wasa?" murmushi Hajja ta yi ta ce "Eh na tuna, yanzu dai je ki kirawo Azima ku zo kuci abinci" "To Hajja, Baffa ya fita ne?" Aziza ta tambayi Hajja kamar bata san Baffan ya fita ba, Hajja ta ce "Eh ya fita kin san ai jiya yace yau Jarman macizai zai zo, yace min idan yazo zai zo ya kiramu muje gabadaya ayi gwaji" Aziza ta jinjina kai tana fadin "to Hajja bari naje na kira Azima kafin Baffa ya dawo" "To a dawo lafiya,ki tabbatar kinyi lullube da kyau fa" "To Hajja" Aziza ta fada tana ficewa jiki a sanyaye, tana fita da gudu ta yanki rafi inda tasan Azima ba zata wuce can ba. Tana zuwa ta sameta kwance a kusa da rafi. Hannnu tasa ta janyota ta ce "Kin kashesa ko Azima? Na ce kin kashesa ko!?" dariya ta kyalkyala cikin amo marar dadin sauraro ta ce "Ai na gaya miki Aziza sai na kashesa!" Rike kai Aziza ta yi ta ce "Me kika so ki zama ne kam Azima?" "Bana son ganin zaman lafiya a wannan yankin! Na fi so ayi ta b'arin jini! Ina so na haɗa maƙotan yankunan nan faɗa, duk wani mai kama macizai wanda za a yi masa aike ya zo yankin nan sai na kashesa! Kin ga daga nan za a fara yaƙi tsakanin yankuna da yankuna, sannan dama akwai y'ar tsama tsakanin yankin kwana da yankin tudu da kuma yankin Ja'i nasan kuma dole mai unguwa zai bukaci taimakonsu, duk wanda aka turo ni kuma zan kashesa! Na tabbata daga lokacin zaman lafiya ya kare, Baffa shine jarumi na farko a wannan yankin wanda da shi aka yi gwagwarmaya kinga kuwa ba mamaki a wajan yaƙin a kashesa!" 🍃🍃🍃🍃 *DAN ALLAH JIYA NA FARA LITTAFIN NAN, BAN BUƊE PAID GRP BA, SABIDA BAN GAMA FREE PAGES BA,KUYIWA ALLAH IDAN BA KU GA UPDATE DINA A RANA BA KARKU CE ZAKUYI KORAFI, NA SANI DOLE NE TUNDA NA FARA ZAN KARASA DA IZININ ALLAH, SABIDA HAKA KU MIN UZURI RANAR DA BAKU GA UPDATE BA TUNDA BAN GAMA FREE PGS BA, IDAN ZAKI BIYA DARINKI YANZU FYN, IDAN KUMA SAI AN GAMA FREE PG NE DUK DAYA AMMA DAN ALLAH BAN DA KORAFI, MATAR GIDA CE NI MAI IYALAI, UWA UBA KUMA DALIBAR MAKARANTA, FATAN ZAKU FAHIMCENI,INA GODIYA GA MASOYANA MASU GANIN SUN BIYAN KUDIN KARATUNSU, NA GODE DA BIBIYATA DA KUKEYI, ALLAH YA BAR KAUNA, 1 LUV* COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN. [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: https://chat.whatsapp.com/BXDHlYEJdRi65a26Qt5OSe 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 🥁🥁🥁🥁🥁🥁 💃🏻💃🏻💃🏻😍😍😍 *YAU TAMBARINA NA MASOYA NE,INA GODIYA DA SAKONNINKU,KIRAN WAYA, KAI MA SHA ALLAH, ALLAH DAI YA BAR KAUNA,INA ALFAHARI DAKU A DUK INDA KU KE MASOYANA, ALKAIRIN ALLAH YA KAI MUKU HAR KUJERAR ZAMANKU😍* *FREE..* 🅿️==5️⃣↪️6️⃣ Zaro ido Aziza ta yi tana kallon Azima kafin ta ce "Na rasa dalilinki na son ganin bayan Baffa! A yadda na fahimceki, ke ba ki ƙi kowa ya mutu ke ki rayu ba, idan kika samu dama na tabbata za ki kashe Baffa" dariya Azima ta kyalkyale da shi tana kewaye wajan kafin ta koma ta haɗe rai sosai ta ce " *AI BA YAU BANE KAWAI NA SHA GWADA HAKAN!* ko a yanzu na samu sarari sai na kashe Baffa! Ko kin manta na sha yunkurin kashesa!? Lokuta da yawa ke ce kika katse min burikana! Ga shi ke ban san ya zanyi dake ba! Ke ta biyu na ce! Ba zan iya kasheki ba! Sabida duk muguntar gubana naki yafi nawa! Kuma ina sonki yar uwata! Da ace nike da karfin dafin da kike da shi da na jima da shafe wannan yankin kakaf dinta!" Azima ta fada tana daga hannuwanta sama. Aziza ta girgiza kai ta zauna a kasa tare da fashewa da kuka ta ce "Azima ba zan taba bari ki cutar da Baffa ba,ko da kuwa zaki iya,ni dai a gaskiya inaji a jikina kamar ni da mutum ce! Ban san a garin yaya muka zama macizai ba, miye dalilinki na son kashe Baffa Azima!?" Aziza ta faɗa tana haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,duk sadda ta kalli jikinta ta ganta a macijiya tana jin zafi a zuciyarta, ta yi nisa sosai a kuka ta ji wani irin murya na namiji wanda yake abun tsoro an bata amsar maganarta. " *ZUNUBIN DA BAFFANKU YA AIKATA NE YAKE BIBIYARKU!, TARE DA GOYA MASA BAYAN DA JAMA'AR YANKIN NAN SUKA YI!*" da sauri a matukar firgice Aziza ta dago tana waige ta ga daga ina ne maganar ya fito? Amma bata ga kowa ba illa Azima dake wasa a cikin rafi kana ganinta zaka san tana cikin nishaɗi, ta zama macijiya ta koma ta zama mutum. Sauri tashi tsaye Aziza ta yi tana waige a fili ta kara furta kalman da ta ji "Zunubin da Baffanmu ya aikata? Me Baffanmu ya yi kuma?" tambayoyi ne maqil a ranta amma babu mai bata amsa, ko dai zata je ta tambayi Baffa ne? Kai amma kuma idan ta yi haka za a gane su ɗin ba mutane bane, riƙe wuyanta ta yi jin kamar zuciyarta yana shirin fitowa bakinta, kallon Azima ta yi ta ce "Azima ki zo muje gida" "Tare muka zo dake ne?" "Idan ma ba tare muka zo ba Hajja ta ce mu dawo tare yanzu, kar Baffa ya dawo...." Aziza ba ta karasa ba Azima ta fito tana fadin "Ke komai ki ce Baffa?" "To idan ban kira sunan Baffana ba sunanki zan kira?" murmushi Azima ta yi ta ce "Yau bana jin yin faɗa dake, dan yau ina cikin farin ciki, nasan idan sako ta iske sarkin yankin jimo an kashe masa Jarman Macizai me kike tunani zai faru Aziza?" "Ban sani ba!" Aziza ta faɗa a ƙufule ta yi gaba, ita ma Azima a macijiya ta hau bin bayan Aziza, yau tsananin takaici ya hana Aziza ta cewa Azima ta koma mutum, Azima kuwa da gangan take wani abun dan Aziza ta mata magana. A macijiya ta shiga gidan Allah ya so Hajja na bandaki, zama Aziza ta yi ta buga tagumi, Azima kuwa bukka ta shige, bayan Hajja ta fito ta ga Aziza da tagumi ta ce "Ah Aziza kun dawo?" shuru Hajja taji dan Aziza ta yi nisa cikin tunani, sai da Hajja ta tabota tukunna ta dawo hayyacinta ta ce "Na'am Hajja magana kike yi ne?" "Tunanin me kike yi haka Aziza?" murmushi Aziza ta k'wak'ulo ta ce "Abunda yake faruwa a mahaifana shine yake tayar min da hankali Hajja" "Karki ce zaki saka hakan a ranki,addua ita ce mafita,duk abunda ya yi tsanani maganinsa Allah" kuka Aziza ta fashe da shi ta rungume Hajja ta ce "Dole ne na saka a raina Hajja! Idan mun san abunda ya faru yau ba bamu san me zai faru gobe ba Hajja!" sosai Aziza ke kuka yayinda hankalin Hajja ya tashi, Azima ce ta fito daga bukka dauke da abinci a hannunta zama ta yi ba tare da ta kalli Hajja ko Aziza da ke kuka ba,abincinta ta hau ci hankalinta kwance, Hajja ta kalli Azima wacce ta jima da gane ita damuwar wani bai dameta ba, ta ce "Azima meke faruwa da yar uwarki!?" Cikin halin ko in kula ta ce "Oho mata! Tana son ɗorawa kanta damuwar da bata da mafita a kansa, ta ga zata iya ne, Hajja ki daina damun kanki a kanta!" Hajja zata yi magana sai ga Baffa a fujajan ya shigo ko sallama babu, da sauri hankalin Hajja da Aziza ya koma kan Baffa akasin Azima da ta yi kamar bata san da shigowarsa. "Baffan yan biyu lafiya kuwa na ganka a cikin wannan yanayin?" Sharce zufa Baffa ya yi ya ce "Jumala ina kuwa lafiya! Ku zo muje gaban gari ana neman dukka mutanen yanki, kin san an kashe Jarman Macizai kuwa?" hannu Hajja ta zuba a kirji tare da fadin "Ma'asabumin Musibati qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! An kashe jarman macizai to waye kashesa!?" " *MACIJI! SARAN MACIJI NE A JIKIN JARMAN MACIZAI!*" Baffa ya faɗa yana sauke idonsa a kan Azima wanda hankalinta sam baya kansu, Hajja ta ce "Ba ri na dauko mayafina mu tafi gaban gari din" Hajja ta karasa maganar tana shigewa bukka, Aziza kuma tana gyara mayafin kanta hankalinta a tashe! Baffa ya ce "Ke Azima? Ana gaya miki mahaifarki babu lafiya amma kina zaune hankalinki kwance ba tare da kin nuna damuwarki ko a fuska ba kina cin abinci! Za ki tashi ne ko sai na saka sanda na roɗe miki shingen kafafunki nan masu kama da fuffuken sauro!" Baffa ya faɗa yana yin kan Azima da sauri ta tashi tana huci tare da juya baya, hanyar randar kasan dake tsakiyar gidan taje ta ɗibo ruwa a kwarya tare da fakan idon Aziza ta watsa dafi a ciki, sannan ta juyo tana kallon Baffa a ranta take fadin "Ba zan taba samun salama ba idan har ban kasheka ba!" tunkaro Baffa ta yi har ta zo gabansa tana tura baki ta ce "Baffa na ga alama kan ka ya dau zafi kaɗan sha ruwa zuciyarka ta huce! Baffa ita fa damuwar duniya bata karewa barin ma idan mutum yasa hannu ko nace mutane suka sa hannu suka jawo bala'i wa kansu, sannan dole akwai abunda ku ka aikata ma wasu yake bibiyarku! Dan haka Baffa a koma a yi tunani da kyau, ga ruwan ka sha" ta mika masa tana sunkuyar da kai kasa sai kace wata ta Allah, shuru Baffa ya yi yana son yayi tunani a kan maganar da ta fada amma tashin hankalin da suke ciki ya ƙi basa damar haka, hannu yasa ya karbi ruwan caraf idon Aziza ya sauka a kan ruwa ta hangi dafi, cikin azama ta ce "Baffa wani ruwa kuma zaka sha? Ka manta Azima ita bata damuwa da damuwar wani? Kawo ruwan nan Baffa" Aziza ta karba, wani kallo ne Azima ta bi Aziza da shi jikinta har na tafasa tsananin takaicin abunda Aziza ta yi, Aziza na karban ruwan da gangan ta yi tuntube ruwan ya b'are kwaryar kuma ta riɗata da dutse ta fashe, cije baki Azima ta yi, idonta ya kara rinewa tana shirin tunkaro Aziza wacce itama ke kallonta ko gizau bata yi ba, Hajja ce ta kara katse mata hanzari ta fito tana fadin "Yi hakuri Baffan yan biyu! Na zubar da wake ne na tsaya kwashewa shiyasa ban fito da wuri ba,muje" gaba Baffa ya yi Aziza ta bisa a baya, Azima ta zo fita Hajja ta ce "Ina mayafinki?" "Ba zan saka ba! bana jin saka wa Hajja! Raina a b'ace yake karki min maganar wani mayafi!" daskarewa Hajja ta yi jin amsar da Azima ta bata,ita ma Azima bata san lokacin da ta faɗi ba dan bata taba yiwa Hajja magana haka ba,ganin Hajja ta tsaya tana kallonta ne yasa ta cewa "yi hakuri Hajja bara naje na dauko,kuyi gaba zan zo a baya" Hajja dai bata iya cewa komai ba illa bayan su Baffa da Aziza da ta bi wanda sun yi gaba abunsu. Su na kan tafiya Aziza ta ce "Baffa?" "Na'am Aziza yaya ne?" "Baffa baka taba bani labarin kafuwar mahaifata ba, kullum kana cewa an sha gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma baka taba bani labarin kalar gwagwarmayen da ku ka sha dasu ba" "Yo to banda abunki Aziza ana cikin wannan tashin hankali kina maganar labari? Abunda ya kafu sama da shekaru hamsin? Ki bari Allah ya bamu ikon dakatar da wannan ambaliyar wutar masifan dake tunkaro wannan yankin" shuru Aziza ta yi ba tare da ta sake magana ba, da haka har suka karasa gaban gari inda cincirindon fulani suke tsaye kowa ka gari hankalinsa a tashe, har anyiwa jarman macizai jana'iza an binnesa. Ana ta shawaran yadda za a rubutawa sarkin fulanin yankin jimo sakon cewa an kashe jarman macizai wanda yankuna sun san shi jarumi ne, idan ka cire yankin ja'i da yankin tudu za a iya cewa babu wani jarumi wanda ya shahara a kama macizai sama da jarman macizai, amma a yankin Ja'i akwai wanda har aljanun macizai yana kamawa tsananin shahararsa wanda har laƙabi ake masa da INNU MACIJI, daga shi kuma sai na yankin tudu wanda shike takawa Innu Maciji baya wato IRO MAGANIN MACIZAI daga shi sai wanda aka kashe na yankin jimo wato JARMAN MACIZAI, lokacin da aka raba kambun girma na wa inda suka shahara a kama macizai aka ba wa INNU MACIJI lamba daya, aka ba wa IRO MAGANIN MACIZAI lamba ta biyu sai kuma JARMAN MACIZAI lamba ta uku, har ta Ilu mai Macizai da Azima ta kashe na yankin kwana shine aka ba wa lamba ta shidda, sannan aka rabawa na ƙasa dasu, tashin hankalin da yankin kwana ke ciki shine rashin jituwar da basu da shi da yankin tudu da yankin ja'i, barin ma yankin ja'i tsatstsauran gaba ce daɗaɗɗiya, dan kuwa an sha gasan kisa a tsakani, yankin tudu kuwa dan sarkin yankin ne ya zo yankin kwana ya yiwa yar yankin fyaɗe bai kyaleta ba har sai da ya kasheta! Hakan ce tasa ARƊO ya bada umarnin a kashesa shi ma,aka gille masa kai aka turawa mahaifinsa da shi daga nan gabar ta soma, yanzu taya zasu fara neman taimakon Yankin Tudu ko kuma yankin ja'i? Yanzu dai ba shi bane tashin hankalin, tashin hankalinn shine yadda zasu fara tunkaran yankin jimo da sakon an kashe jarman macizai. @@@@@@@ Su Baffa sun iso ana kan shawara ba a tsaida mafita ba, sai da Baffa ya karaso aka sake yin shawara a kan a rubuta sako a tura mutum huɗu da suje yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da rigan Jarman Macizai wanda yake jina-jina da jini, sannan ayi musu bayanin abunda ya faru bai kai ga yin aikin da yazo yi ba aka iske gawarsa, tare da sakon ban hakuri iri da kala daga wajan mai unguwan yankin kwana da kuma sarkin fulanin yanki kwana tare da Arɗo, hakan ce ta kasance aka tura mutum huɗu izuwa yankin jimo, tare da kayan Jarman Macizai da kuma dokinsa da takwabinsa. Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita. Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba. Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce "Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha'i za a zauna ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu" da sauri Baffa ya ce "Arɗo yankin tudu kuma?" "E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan" "To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja'i" Nauyayyiyar ajiyar zuciya Arɗo ya sauke ya ce "To Magaji mai zai hana kai ka maida hannun agogo baya?" "Bangane ba Arɗo?" "Ina nufin ka dawo yadda kake a da dan mu taimaki yankinmu, Kayan aikinka da kaje ka binne kaje ka hakosu saboda......" girgiza kai Baffa ya hau yi yana ja da baya, ya ce "A'a Arɗo na riga da nayi alkawari ba zan sake ba, har kwanan gobe ban manta da kuskuren da na aikata bisa tsautsayi a baya ba, abun shekara ashiri amma a yanzu gani nake yi yanzu abun ya faru, Arɗo ba a son raina na kashe *BANJU* ba, na kashesa ne sabida shafe mutanen yankin nan da ya fara, sannan idan baka manta ba yace zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan! tunda na kashe Banju nayi alkawari na dai na! duk wani abu wanda na gada daga gareka da kakanni! Dan Allah Arɗo a bar wannan maganar" 🍃🍃🍃🍃🍃 WLH IDAN NAYI POSTING A GRP BAN CIKA BI TA CIKIN GRP DIN BA,AKWAI WASU GRP DIN MA BANA BUDEWA INDAI BA GOGE SAKONNI ZANYI BA, IDAN KINA SON BIYAN KUDIN BOOK DIN NAN KI TUNTUBENI TA LAMBAR WAYATA TA SAMA, IDAN TA ACCT NE KO KATI. AND PLS&PLS 4 ALLAH'S SAKE, IDAN KIN SAN BA BIYA ZAKIYI BA KARKI KIRANI KI GAYA MIN MAGANAR DA BA HAKA BA, A BOOK DIN NAN DAI BAN CE DARI BIYAR KO DARI UKU BA,HAR TA DARI BIYU MA BANCE BA, DARI NE NACE DAN MASOYANA,BAN SAKA TA INDA BA ZAKI IYA BIYA BA, SO PLSS A DINGA FAHIMTA,DAN WATA MAGANA JIYA BAI MIN DADI BA SAM.👏🏻 MASU KIRA NA DAN KARA MIN ƘWARIN GUIWA NA GODE,NA SAN ZAKU GANI DIK DA BAN SANKU BA AMMA KUNA RAINA🌹🤝🏻 COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. *JINJINA GAREKI UWA BA DA MAMA, ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA, SHUGABA DAYA TAMKAR DA DUBU,(GWAGGOTA TA KAINA ALLAH YA IYA MIKI.* Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *JINJINA GAREKI HAJIYA MAMAN YUSUF MAI KAYAN MATA😍 SAFIYAR YAU KECE KIKA FARA SAKANI DARIYA😂 DAN HAKA GA KYAUTAR PAGE HAJIYA JIRGIN DANƘARO*😂 *MAMIE'S CLUB HAKIKA SHARHINKU YA TAFI DA RUHINA, A KODAYAUSHE KUNA NUNA MIN E KU ƊIN YAN AMANA NE NA GASKEN-GASKE, AZIMA DA AZIZA FANS GRP, WLH KARKU YARDA A ZO GARINKU A FI KU RAWA AHA TO😜, DAN ARADU YAN MAMIE'S SUN CE BA ZAKU KAMO SU A SHARHI BA,KUMA NA YABA🌹🥰, A KAFTA*🤾🏻‍♀️ *ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA, YA ALLAH KA KARAWA SHUGABA JA GABA ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM DARAJA! DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA DA MAGOYA BAYA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO! HAKIKA AZIMA DA AZIZA YA YI FARIN JINI FIYE DA TUNANINA! ALHAMDULILLAH! MASOYA A CI GABA DA NUNA MIN ƘAUNA TA HANYAR SIYAN BOOK DIN NAN CIKIN FARASHI MAI RAHUSA, ƊARI KACAL*👌🏻 *FREE..* 🅿️==9️⃣↪️🔟 Dambe suke yi sosai a tsakaninsu ba ji ba gani, yayinda Azima ta yanki Aziza a gefen wuya,nan ta koma mutun ta faɗi kasa, ita ma Azimar rabi mutum rabi Macijiya ta zama tana kallon Aziza ranta a haɗe idonta ya kara rinewa zuwa blue, a hankali Aziza ta miƙe tsaye tasa hannu ta karkaɗe jikinta ta juya baya,ta sa hannu a gefen wuyanta inda yake zubar da jini ta lumshe ido, kamar ƙiftawar ido da bismillah ta shafe wajan, sannan ta daga hannunta sama ta haɗa wani guguwa mai karfin gaske ta turawa Azima, Azima bata ankara ba taji anyi sama-sama da ita, sai da taje can sama kafin ta faɗo timm! Da kasa nan ta koma mutum, a hankali Aziza ta juyo tana kallonta yau fuskarta babu fara'a, haqiqa dan faɗa su na faɗa amma basu taba dambe ba, bar su a cacan baki. Saurin tashi Azima ta yi ta sake komawa macijiya ta yi hajijiya ta tada ƙura ta yi kan Aziza, da sauri Aziza ita ma ta sake zama macijiya suka haɗe aka hau dambe, da jelarta na maciji ta nannaɗe wuyar Azima ta shaƙeta sosai, murkususu Azima ta hau yi tana son kwacewa daga hannun Aziza amma ta kasa, inda karfinta ya fara karewa dan duk muguntarta bata kai Aziza karfin dafi ba. Nan numfashinta ya fara yin sama inda a karshen jikinta ya sub'ale ta koma mutum sumammiya, ganin haka yasa Aziza sakinta ta wullata kusa da rafin ita ma ta koma mutum sannan tasa hannu ta dibo ruwa ta watsa mata a fuska, wani wawan ajiyar zuciya Azima ta sauke alaman ta sha wuya, da tari ta farka tana yunkurin tashi ta ce "Duk abun da zakiyi Aziza kema kin sani ba zaki iya kasheni ba!" Kafadarta Aziza ta kama hawaye cike a idonta ta ce "Nima bana fatar kasheki! Har na bar duniya bana fata na kashe ko da tururuwa! Azima kisan ya yi yawa! Azima me kikeson zama ne! Ga shi yau kin sani na aikata abunda bana son aikatawa wanda ban ma taba aikatawa ba! meyasa Azima! Me yasa! Me yasa!" Aziza ta karasa tana sakin kuka mai cike da ruɗani. Zufa Azima ta goge tana ture hannun Aziza daga kafadarta ta ce "Kullum ba zan gaji da faɗin cewa da ni ce da karfin gubarki da na shafe jama'ar yankin nan an wuce wajan! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Bana mantuwa bana yafiya!" A fusace Aziza ta sa hannu ta dago Azima tsaye tare da fadin "Da anyi magana za ki ce ba ki mantuwa ba ki yafiya! Ni a iya sanina ban ga abun da aka miki ba kike wannan kisar! Shin zaki iya gayamin laifi daya tak ƙwaƙƙwara wanda aka miki kike kisa? Mutum ko da ya miki kallon bai miki ba shikenan ya cancanci kisa!? Kina fakewa da cewa dan kar a tona mana asiri da cewa mu ba mutane bane macizai ne, a da ina yarda amma a kwana biyun nan na daina yarda dake! A da kin san da cewa ke macijiya ce amma ba kya kisa kamar na kwanan nan me yasa Azima!? Me yasa!?" Idonta ne ya sake rikiɗewa zuwa blue sosai, fatar jikinta har na caccanza kala ta ce "Fansa! Fansa! Fansa! Fansa nake ɗauka Aziza!" "To fansar me Azima gaya min?" "Abun da mutanen yankin nan suka min shekarun baya" Da mugun mamaki Aziza take kallon Azima dan ba ta taba furta wannan kalman ba sai yau, ta ce "Shekarun baya fa kika ce!? Duka-duka yaushe aka haifeki da zaki dinga lissafin shekarun baya?" Murmushin mugunta Azima ta yi ta ce. "Koma yaushe aka haifeni! Ba damuwarki ba ce! Amma ina so ki sani ki kara sani! Sai na kashe BAFFA! sai na kashe ARƊO! sai na kashe TSOHON SARKIN FULANI KWANA! da kuma wanda suka sauka a bayansa! sai na kashe MAI UNGUWA! kee sai na shafe dukkan mutanen yankin nan! Sannan na shiga birni cikin inda yake da jama'a da yawa na tarwatsasu! Zan bar wannan alƙaryan!" Gabanta Aziza ta tsaya ta ce "NI KUMA AZIZA MAGAJI ARƊO! ZANYI YAƘI DAKE NA DAKATAR DAKE! ZAN TAIMAKI MUTANEN YANKIN NAN KO DA KUWA ZASU GANE CEWA NI MACIJIYA CE SU KASHENI! ZAN TSAYA A GABAN BAFFA NA KARESA BA KI ISA KIYI MASA KOMAI BA!". Murmushi Azima tayi ta ce "Idan kin isa ki dakatar dani Aziza! Na fi ki mugunta! Kin fini karfin dafi! Muje zuwa Allah ya ba wa mai rabo sa'a!" Aziza ta yi murmushi ta ce "Amin!" nan Azima da Aziza suka rabe ko wacce tayi hanyarta daban. 🍃🍃🍃🍃 Hankali tashe Maga Isar da sakon sarkin fulanin yankin jimo ya faɗo fadar sarki Haruna ya ce "Allah ya taimakeka! Mummunar labari! Mai cike da tashin hankali, hakika yau munyi asara! Munyi babbar rashi!" daga nan kuma ya fashe da kuka! Nan hankalin jama'ar wajan ya tashi yayinda Sarki Haruna ya miƙe tsaye ya ce "Maga Isar da sako, me ya faru!?" "Haqiqa mun shiga ruɗu da ruɗani! Munyi sallama lafiya-lafiya da jarman macizai, amma yanzu haka sako ne daga yankin kwana a kan cewa an kashe jarman macizai! Yanzu haka gasu can sun dawo da kayansa da dokinsa! rigarsa duk jini!" ba iyakar sarkin fulanin jimo ba harta jama'ar da suke zaune a wajan sai da suka miƙe tsaye. Waziri ne ya yi karfin halin faɗin "Ce dasu su karaso su mana cikakken bayani dan bamu fahimci maganarka ba Maga Isar da Sako!" da sauri Maga Isar da Sako ya tashi yaje ya ce dasu su karaso, jiki a sanyaye babu kwari suka karaso suka zube a gaban sarkin fulanin yankin jimo, daga kallon da ake musu yasa suka sha jinin jikinsu, da kyar garkuwan fulanin yankin kwana ya ce "Allah ya taimaki Sarki Haruna, da fari kafin muce komai zamu fara da ban hakuri da neman afuwa da gafarar duk wani wanda yake wannan yanki a kan rashin jarman macizai! Haqiqa munji kunya! Mun yarda munji kunya! Amma ba laifinmu bane, mai afkuwa ce ta afku, amadadin Sarkin fulanin yankin kwana da Arɗo, da mai unguwar yankin kwana wato Ori, dani Garkuwan fulanin yankin kwana da Magaji Bawa da duk jama'ar da suke yankin kwana muna mai neman yafiyarku a kan abunda ya faru na rashin jarman Macizai! Haqiqa ya cika jarumi kuma ya amsa sunansa, ba zamu manta da halaccin wannan yanki ba har izuwa karshen rayuwarmu! Mun gode da yunkurin taimakonmu! Haqiqa mu abun tausayi ne, kuyi hakuri ku yafe mana! Bai kai ga aiwatar da aikinsa ba muka iske gawarsa da saran maciji, ba zamu iya kawo muku tashin hankali goma da ashirin bane, shi yasa muka sallacesa muka binnesa muka yi masa sutura, zaku iya zuwa ganinsa tare damu gobe idan Allah ya kaimu sai muje ku ga ƙabarinsa!" Garkuwan fulani ya karasa maganar a sanyaye yana mai duƙar da kai. Tabbas jama'ar yankin jimo sunji mutuwar jarman macizai har can kasar zuciyarsu yayinda suka ji tsanar yankin kwana duk da hakika sun tausaya musu matuƙa, amma zafin mutuwar jarman macizai ya hanasu ce uffan wasu Garkuwan fulanin yankin kwana, ba a wani musu tarba mai kyau ba dan kuwa su na cikin ƙunci da jimanin mutuwar jarman macizai, inda suka sa da washe gari da safe zasu yi asubanci su tafi yankin kwana. @@@@@ *YANKIN KWANA.* Ko da su Aziza da Azima suka koma gida ba su shiga hidimar juna ba, harta abinci da Hajja ta haɗa musu ga mamakinta sai gani ta yi sun raba kwano, sosai abun ya damu Hajja ta yi musu tambayar duniya me ya hadasu, Aziza ce dai ta iya cewa babu komai fa Hajja, amma Azima kam ko kallon Hajja bata yi ba. @@@@@@ Bayan anyi sallar isha'i dukkansu suka hallara a fadar mai unguwa, kowa da kalar shawarar da yake badawa, shi dai Baffa duk sauraronsu yake yi ya gaza cewa kanzil, inda a karshe Arɗo ya ce "Magaji in ce dai lafiya ko? Na ga kowa na ta magana amma kai baka ce komai ba" ajiyar zuciya Baffa ya sauke ya ce "Hankalina yana can wajansu Garkuwan fulani, ko ya Haruna zai dauki lamarin? Abun fa sai wanda ya ɗaure" Ardo ya ce "Tabbas haka ne Magaji, to ya zamu yi? Mu ma ba yin kanmu bane, Allah yasa su fahimce mu" aka amsa da amin, tsohon sarkin fulani ya ce "Yanzu abun duba a nan shine taya zamu shawo kan wannan matsalar? Abun kara yawa yake yi fa? Jarman macizai da safe! Yaro dazu! Ba zamu zauna mu naɗe hannu a kirji mu zuba ido a shafe mu ba, mai zai hana mu aika da kokon barar mu neman taimako yankin tudu?" wani zabura Baffa ya yi yana girgiza kai ya ce "A'a Baffa Mandi, kar mu kara wannan kuskuren! Munyi kuskure na farko an rasa jarman macizai, yanzu kuma sai mu sake aikata wani ta hanyar yin aike yankin tudu! Mu nemi taimakon IRO MAGANIN MACIZAI? Duk shawaran da za ayi a sauran yankuna amma banda yanki biyu, ban da yankin tudu ko yankin ja'i, kar mu taro wani yaƙin ba tare da mun dakatar da wani ba, kun san tsananin gabar da ke tsakanin yankin tudu da yankin ja'i da yankinmu, har kwanan gobe ana samun kisan kai a tsakanin yankin nan da yankin ja'i, har kwanan gobe yankin tudu su na riƙe da abunda ya faru sun kasa mantawa kiris suke jira su fasa abunda yake zuciyarsu, dan Allah ku fahimceni!" Shuru wajan ya dauka kowa da abunda yake tunani, Sai zuwa can anjima Mai Unguwa Ori ya ce "To shikenan, za ayi ƙuri'a duk bangaren da ya fi rinjaye shi za a zaba, idan bangaren kar aje neman taimako yankin tudu ko yankin ja'i sunfi yawa to ba za aje ba,idan kuma bangaren wa inda suka ce aje sunfi yawa to za a je" shi dai Baffa shuru ne ya yi yana hango musu gagarumar balbalin gobarar yaƙin da zai tashi amma sun kasa ganewa. 🍃🍃🍃🍃 COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN. [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *JINJINA GAREKI SIRKATA MAMAN NOOR, 😍 SANNU DA COMMENT,INAYINKI OVER.* *FREE..* 🅿️==7️⃣↪️8️⃣ Shuru Arɗo ya yi yana kallon Baffa na wasu lokuta kafin ya ce "Shike nan Magaji, ba zan takura maka ba, amma ban yi tsammanin zaka tsorata da maganar Banju haka ba" "Ba tsorata nayi da maganar Banju ba a lokacin da ya faɗi, amma a halin yanzu ina cikin zullumi na maganar Banju, dan idan baka manta ba ya ce zamu gani ko ba jima ko ba daɗe sannan kuma zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan, abunda yake faruwa a halin yanzu abun a duba ne, sannan bamu san wani martani sarkin fulanin yankin jimo zai maidowa mutanen da suka je ban hakuri garesu ba, ba kowa bane zai lamunci hakan, munyi aiken neman taimako anzo dan a taimaka mana amma kuma sai a mai da musu da kaya ace an kashesa! Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!" Baffa ya faɗa fuskarsa dauke da zallar damuwar da yake ciki, Arɗo yaja ajiyar zuciya ya ce "Ko ma miye ne idan suka dawo ma ji, yanzu dai ka je amma ka tabbatar bayan sallan isha'i ka halacci fadar mai unguwa" "In sha Allahu zan zo" daga haka suka yi sallama, Baffa ba hanyar gida ya yi ba dan ba gidan zai koma ba illa cewa da ya yi su Hajja da Aziza su koma gida, ina Azima bata zo ba? Aziza ta ce "Eh Baffa bata zo ba" girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Hajja da Aziza suka dauki hanyar komawa gida, su na tafiya su na hira, Hajja ta ce "Ohh Allah ni Jumala, ko me ya hana Azima zuwa? Ita kullum ta fi so ku ta zama a bakin zargi" "Ai ko basu zauna a bakin zargi ba, ba lallai bane yaranki su kasance mutane ne!" da sauri Hajja da Aziza suka juya su na kallon Mairo da Hadi wanda suka riƙe ƙugu sai kace zasu dake su, Hajja ta ce "Mairo me kike nufi?" "Oho miki kuma! Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, yara ko ma dai nace iyayen yara! Ace kamar su Azima da Aziza a wannan yankin gote-gote dasu amma babu aure! Sannan suna tafiya jiki na lankwasa! Daga mai idon mage (wato Aziza kenan) sai mai ido ruwan ganye(Azima kenan) taya kuwa zasu zama mutane, ga shegen kyau! Duk da lokacin da muka yi yan matanci dake duk yankin nan babu mai kyawunki sannan babu jarumi sama da Magaji, ba wai hakan yana nufin zaku haifi yara masu kama da mutanen wani duniya daban bane ehe! Ko ki so ko karki so Azima da Aziza dai ba mutane bane!" Idon Hajja ne ya kawo ruwa ta ma kasa magana, da kyar ta ce "Mairo idan ke kike aurar wa sai ki zo ki aurar dasu, sannan kuma idan kina canza halitta ki zo ki canza musu" caraf Hadi ta cab'e zancan da cewa "Wa ye bai sani ba, ba mamaki duk wannan kisan da ake yi a yankin nan Azima da Aziza suke yi, kuma da saninki ke kike daure musu....." "YAAAA ISAAAAAAAA!!!" Aziza ta faɗa da kakkausar murya, ganin yadda fuskar Mahaifiyarta ya jiƙu da ruwan hawaye, gaban mahaifiyarta ta tsaya yayinda idonta suka kara rinewa zuwa fari-fari ,yatsarta manuniya ta ɗaga tana nuna Mairo da Hadi cikin gargaɗi ta ce "Zan iya jure komai! Zan iya shanye komai! Amma kar na ga hawaye a idon MAHAIFIYATA SANYIN IDANIYATA! ku fita tsabgarmu! Mu mutane ne, maganar da kika fada yanzu kuma Inna Hadi ki bar shi a iya nan kawai kar yaje gaba!" Aziza na gama fadi ta kamo hannun Hajja suka bar su Mairo da Hadi jiki na rawa, Hadi ta ce "Mai....Mai...Mairoo....ban....gaya...miki....da...da..da cewa ba mutane...bane...wollah inaji ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba...kalli ki ga lokaci daya yadda idonta ya canza...anya ma ni kuwa ba su bane....." saurin dakatar da ita Mairo ta yi ta ce "Hadi ki bar maganar nan a nan dan ban shiryawa mutuwa ba, zo mu tafi" Mairo ta fizgi hannun Hadi. @@@@@@ Sun ɗan yi tafiya Hajja ta tsaya, Aziza tasa hannu tana sharewa Hajja hawaye tare da fadin "Kiyi hakuri Hajja, dan kuka mai ja wa uwa jifa ko Hajja!?" Aziza ta faɗa tana fashewa da kuka, Hajja ta ce "A'a Aziza, har ga Allah ni har zuciyata ban taba zargin yarana ba, na san ni dai mutane na haifa" "To me yasa kike kuka Hajja?" "Saboda dukkan uwa ta gari ba zata so a dinga sokin yaranta ba! Har raina nake jin zafi" Hajja ta fada tana mai kamo hannun Aziza, wani tausayin mahaifiyarsu ne ya ɗarsu a zuciyar Aziza, duk yadda take tausayawa kanta da yar uwarta tafi tausayin Hajja, ranar da zata gane cewa su din ba mutane bane MACIZAI NE ranar da zata san duk kisan da ake yi Azima ke yi, shin ya dace ta ci gaba da boyewa Hajja cewa su ba mutane bane? Ko dai ta fito ta gayawa Hajja da Baffa gaskiya? Kai amma kuwa gunduwa-gunduwa za ayi dasu, sannan Azima ta ce ko da ta faɗi ba shi zai hanata cika burinta ba! Girgiza kai Aziza ta yi ta sake rungume Hajja tana kuka, Hajja zata yi magana suka ji nishi na tashi ta gefensu wanda yake ciyawa ne kore shar a wajan, saurin maida hankalinsu suka yi, Aziza ta ce "Hajja kamar fa nishi nake ji?" "E nima naji Aziza, kamar ta nan yake fitowa zo mu duba mu gani" suka yanki gefen ciyawar, wani yaro suka gani kwance fuskarsa ta koma blue bakinsa sai fitar da farin kumfa yake yi tare da jini, salati Hajja ta saka, da sauri Aziza ta dagosa tana kallonsa tare da jinjigasa, gefen wuyarsa ta kalla ta ga saran maciji, wanda bata raba dayan biyun *AZIMA* ce, girgiza kai ta hau yi cikin tashin hankali, ta buɗe baki, Hajja ta ce "Aziza me ya faru da shi?" "Hajja maciji ne ya saresa, bari na gwada yi masa magani" kasancewar lokuta da dama Aziza na gwada wa Hajja kamar tana magani wanda Hajja ke danganta hakan da nasaban Baffa, bata jira Hajja ta yi magana ba ta hura iska a bakinta ta rufe ido gam na wasu daqiqu sannan ta buɗe, yayinda idon ya koma fari sol, hannu tasa a bakinta ta dibo farin yawu ta gogawa yaron a wuyarsa dai-dai shatin saran, sannan ta koma kallonsa, duk fuskarsa ta yi blue, tana saka masa ya hau gurnani yana murkususu sannan ya koma ya yi ɗifff! Hajja ce ta daga hannunsa ta ga ya koma, da sauri ta janye Aziza ta ce "Aziza zo mu bar nan wajan" Kallon Hajja Aziza ta yi cikin damuwa ta ce "Hajja taya zamu barsa bayan yana buqatar taimako,ki bari na taimaka masa Hajja kar ya mutu" "Ai ya riga da ya mutu Aziza! Ki zo muje kar ace kece kika masa wani abun" Suman tsaye Aziza tayi tun sadda Hajja tace ai ya riga da ya mutu, kallon yaron kawai take yi, hannu Hajja tasa ta ja Aziza da sauri suka bar wajan basu tsaya ko ina ba sai gida, suna shiga gida Aziza ta shige bukkansu bata ga Azima ba, duk yadda akayi tana rafin jimulo, hannu tasa ta goge hawayenta tare da daukar mayafinta, Hajja ta juyo zata bata ruwa ta ga ta fice a gidan da sauri Hajja ta bi bayanta tana fadin "Aziza! Ke Aziza!? Azi..." Hajja bata karasa ba sakamakon dakatar da ita da Aziza ta yi, ta rufe mata ido ta hura mata iska, haka kawai Hajja ta tsinci kanta da komawa gida, Aziza kuma hanya ta yanka ta yi rafin jimulo, a yadda take tafiya zaka gane cewa ba mutum ba ce, haqiqa yau Azima ta kai ta karshe! Me wannan karamin yaron ya mata da zata kashesa!. Tana isa rafin ta kwala kiran sunan Azima. "AZIMAAAAA!" sulalowa Azima ta yi hannunta dauke da mangoro fuskarta wasai, ganin fuskar Aziza ya sakata sakin baki dan bata taba ganin fuskarta a haka ba "MACIJIYA AZIZA LAFIYA!" Azima ta fada cikin halin ko in kula. "AZIMA ME YARON DA KIKA KASHE YA MIKI!?" kyalkyalewa da dariya ta yi ta ce "Sabida ya cancanci ya mutun ne, saboda ya ganoni, kuma yace sai ya faɗa kin ga kuwa dole na kashe sa tunda...." dauketa da mari Aziza ta yi, tana dagowa ta sake kai mata wani marin, ran Azima ya tunbatsa nan ta riƙiɗe ta koma macijiya,in da ita ma Aziza yau ta rikiɗe ta zama macijiya fara sol, nan dambe ya kaceme. 🍃🍃🍃🍃 WAI YAU MACIZAI NA FAƊA,NAYI NAN🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ A lallaba chaji wala🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️ *WANNAN DUƘAWAR NAKI NE SISINA, DAN ALLAH KIYI HAKURI KI HUCE KINJI🙇🏻‍♀️😟 KAR AYI MANA DARIYA, ALLAH YA HUCI ZUCIYARKI🥰 AMEENATUNA SLIMZY BABY🥰 MATAR MIJINTA🥰* *FREE..* 🅿️==1️⃣1️⃣↪️1️⃣2️⃣ Da washe gari asubanci yankin jimo suka yi, takwas na safe su na yankin kwana,a maƙabarta jikin ƙabarin Jarman macizai, kuka sosai sarki Haruna yake yi shi da jama'ar yankinsa wa inda suka zo, an sha musu mutuwa amma farat ɗaya na Jarman macizai wanda yake jarumi a yankinsu ya gigita tunaninsu, haka suka ƙarashi koke-kokensu suka gama dan ba dawowa zai yi ba, haka jamar'ar kwana suka taru ƙwansu da ƙwarƙwatansu suka sake yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da ban hakuri, daga fuskarsu kawai zaka kalla ka gane su na cikin mugun damuwa da tashin hankali, babu yadda yankin jimo suka iya dole suka hakura tunda dai Jarman Macizai ba dawowa zaiyi ba ya tafi kenan, sai dai fatan Allah ya yafe masa. @@@@@ Bayan kwana biyu an gama ƙuri'u, inda aka samu sab'anin ra'ayi, jama'ar da suka fi rinjaye shine wa inda suka ce aje yankin ja'i neman taimako kar aje yankin tudu a fara zuwa yankin ja'i, dan ba za a zauna da matsala ba tare da an bukaci taimakon Allah da wa inda zasu shawo kan matsalar ba, shi dai Baffa shuru ya yi bai ce kanzil ba, haka aka sa mai rubuta wasika ya rubuta aka yiwa yankin ja'i aike da shi. 🍃🍃🍃🍃🍃 Sarkin fulanin yankin ja'i na zaune Maga Isar da Sakon yankin ya zo ya zube a gabansa yana fadin "Allah ya taimakeka! Hakika a yau nasara tamu ce" wazirin fulani ya ce "Maga Isar da Sako meke tafe da kai ne?" murmushi Maga Isar da sako ya yi ya ce "Hakika yau muke da nasara, sako ce ta isko mu daga yankin kwana! su na cikin bala'i shine suke bukatar taimako daga yankinmu, yanzu haka ga takwabi sarkin kwana wato Chubaɗo ya aiko mana da shi alaman sun sakar mana igiyar, munyi nasara su sun faɗi, wannan takwabi da Chubaɗo ya aiko mana da shi alama ce na sun duƙawa wannan yanki tamu" Sarkin fulanin yankin ja'i ya ce "Maga Isar da sako, zai fi kyautuwa da kayi mana bayani dalla-dalla, ko kuma ka buɗe wasikar da suka aiko da shi ka karantawa dukkan wanda yake zaune a wannan fada dan jin meke tafe da sakon" Ƙara russunawa Maga Isar da sako ya yi ya buɗe wasikar ya fara karantawa kamar haka. " _ASSALAMU ALAIKUM, SAKO CE DAGA YANKIN KWANA IZUWA YANKIN JA'I, MUNA FATAN WANNAN SAƘO TA ISA GAREKA SARKIN FULANIN JA'I WATO SARKI JAWO TARE DA MAI UNGUWAR YANKIN JA'I WATO MAI UNGUWA SODANGI, A YAU MU YANKIN KWANA MUN WAYI GARI CIKIN RUƊU DA RUƊANIN TASHIN HANKALI DA RASHIN ZAMAN LAFIYA, WA HAKA NE MUKA RUBUTO SAƘO DAN YA YI TATTAKI ZUWA GA YANKIN JAMA'AR DA SUKE JA'I GABAƊAYA, AMADADIN NI SARKIN FULANIN YANKIN KWANA CHUBAƊO DA MAI UNGUWAR YANKIN KWANA ORI, DA ARƊO DA TSOHON SARKIN FULANI MANDI, DA MAGAJI BAWA DA DUK WANI WANDA YAKE YANKIN KWANA MUNA NEMAN TAIMAKONKU! MUN GAMU DA IFTILA'IN MACIZAI WANDA SUKE KASHE MANA MUTANE! AN KASHE DUK WASU MASU KAMA MACIZAI NA YANKINMU! MUN NEMI TAIMAKON YANKIN JIMO INDA SUKA TAIMAKA MUKA ROƘI ALFARMA DA JARMAN MACIZAI YA KAWO MANA DAUKI WANDA SHI MA AKA KASHESA KWANA BIYU DA YA WUCE, GA WANNAN TAKWABIN DA MUKA AIKO YANA NUNI NE DA MUN ZUBAR DA MAKAMAN YAƘIN GABAR DAKE TSAKANINMU NA TSAWON LOKACI MUN DUƘAWA YANKINKU, MUN YARDA KUNYI GALABA A KANMU! BA DAN KOMAI BA, SAI DAN MUNA NEMAN ALFARMA DA A TAIMAKA MANA DA TAIMAKON *INNU MACIJI* MUN SAN SHI KA ƊAI NE KAWAI ZAI IYA, TUNDA HAR TA ALJANUN MACIZAI DA MAYU DA ALJANU DUK YANA FAƊA DASU, DAN ALLAH SARKI JAWO DA MAI UNGUWA SODANGI A TAIMAKA MANA, KANMU A ƘASA! A YAU MUN YARDA YANKINKU YANA SAMAN TAMU, SAƘO DAGA YANKIN KWANA, SAI MUNJI DAGA GAREKU, MUN GODE_" Wani murmushi sarkin fulanin ja'i ya yi yana mai kallon Maga Isar da Sako,yayinda jama'ar ja'i suka hau murmushin nasara, dan sun jima suna neman cin galaba a kan yankin kwana amma sun kasa, hakan ya samu asali ne da nasabar da Baffa yake da shi,amma wai yau sai ga shi su da kansu suke cewa sun zubar da makaman yaƙinsu? Wannan ai nasara ce babba a garesu, wakilin yankin ja'i ya ce "Allah ya taimakeka! Ai mu nasara ce ta tako da kafarta tazo mana har gida, wai shanu daga sama gasheshshe!" Wazirin ja'i ya ce "Ai ranka ya daɗe abunda muka jima muna nema ne, shine suka sakar mana shi yanzu,tun yaushe muke neman nasara a kan yankin kwana amma mun kasa samu sabida Magaji Bawa" wazirin fulanin ja'i ya karasa maganarsa yana murmushi, wakilin fulanin ja'i ya kuma cewa "Ranka ya daɗe kar mu b'ata lokaci kawai mu amsa da cewa e mun amince da bukatarsu" girgiza kai garkuwan fulanin ja'i ya hau yi ya ce "Shekara da shekaru ake ɗibi ba daɗi tsakanin yankinmu da yankin kwana, rana daya tak su aiko mana da sako su ce sun janye anya babu lauje cikin naɗi? A gaskiya ni ban yarda da yankin kwana ba, sai dai wani shirin kawai suke yi ta yadda zasu shafemu!" garkuwan fulanin ja'i ya karasa maganarsa yana haɗa rai sosai, sarki Jawo ya ce "Bana tunanin haka! Idan ma kuma hakane karka manta muna da fidda kunyar gasa a yankin nan wato *INNU MACIJI* wanda a halin yanzu shi suke bukatar taimakonsa,Innu Maciji dai duk faɗin yankuna sun san shahararsa! Tunda shi ya lashe kambu na daya a gasar fidda gwajin macizai! Innu Maciji bai ci sunansa a banza ba! Tunda har aljanun maciji da mayu yana yaƙi dasu kuma ya ci nasara, dan haka idan muka tura Innu Maciji dan zuwa taimakawa yankin kwana kamar yadda suka bukata yaje ya dawo ya kake tunanin martaban da yankin ja'i zai samu tare da karramawa daga sauran yankuna?" Ajiyar zuciya Garkuwan fulanin ja'i ya sauke tare da kallon Sarki Jawo ya ce "Ranka ya daɗe bana so mu manta da abu daya, a lokacin da aka raba kambu Magaji Bawa ya jima da sauke duk wata gab'ob'in baiwa da yake da shi, na san idan har zaka manta da tarihin Magaji Bawa da Tsohon sarkin ja'i ya baka ba zaka manta da sunansa da ya shahara a sauran yankuna ba, *GWARZON DAFIN MACIZAI!!* ka tuna?" Garkuwan fulanin ja'i na furta wannan kalma sai da mutanen da suke wajan suka firgita, Wakilin Fulanin Ja'i ya ce "A gaskiya na so na yarda da maganarka Garkuwan ja'i! Me yasa Magaji ba zai yi wani abu a kai ba da zasu dinga bukatar taimakon yankuna! A da shi Magaji a ina ne bai yi taimako ba, gaskiya maganarka abun dubawa ce" Maga Isar da sako ya ce "Amma shekaru ashirin Magaji Bawa ya ce ya daina duk wani abu na yaƙe-yaƙe da yake yi, bayan ya sauka ne shine aka naɗa Firi jarumin yankin kwana ko ba haka bane? Ni a tunanina da ace Magaji Bawa zai iya wani abu a kai da ba za a zo neman taimakon Innu Maciji ba har su russunawa yankin nan" "Amma dai kun san da cewa duk wata shahara da Innu Maciji zai yi ba zai taba kamo ko da tsilen takalmin Magaji Bawa ba ko?" Maga Isar da sako ya ce "Ni dai bana tunanin haka gaskiya, da ace zai iya da ba zasu zo nan ba" Sarki Jawo ya ce "tabbas haka ne maganarka Maga Isar da sako, yanzu abunda za ayi,aje a cewa mai unguwa Sodangi akwai magana ta gaggawa, a biya a kira Innu Maciji, a rubutawa yankin kwana da cewa su tsumayemu zuwa gobe idan muka gama shawara da tattaunawa zamu tura musu da sako idan ma mun amince ko akasin haka" Sarkin fulanin Ja'i yana gama magana ya miƙe tsaye ya bar wajan. 🍃🍃🍃🍃 *YANKIN KWANA* Maga Isar da sakon yankin kwana ne ya gama karanta wasikar da yankin ja'i suka aiko musu da shi, sarki chubaɗo ya ce "Ba komai yau da gobe duk daya ne a wajan Allah, Allah ya nuna mana" mai Unguwa Ori ya ce "Amma Allah ya kara maka yawan rai, anya yankin ja'i zasu yarda su taimakemu kuwa? Gani nake kamar su na neman hanyar da zasu wofantar da bukatarmu ne, tunda mun sanar dasu yankin jimo sun rasa jarman macizai, da mun sani da bamu rubuta musu da cewa an kashe jarman macizai ba" Arɗo ya girgiza kai ya ce "Maganar duniya bata b'uya, gwanda dai da muka gaya musu gaskiya zai fi, balle kuma abu babba irin haka ya faru ace manyan yankuna basu sani bane? Ai hakan ma ba mai yuwa ba ce, dan naji ance yankin gangare da yankin jauro da yankin ulela da yankin nasare duk sunje yiwa yankin jimo ta'aziyyar jarman macizai" Sarki Chubaɗo ya ce "Mu jira har zuwa goben muji sakamakon abinda zasu ce" Arɗo ya yi murmushin karfin hali ya ce "Bana tunanin yankin ja'i zasu wofantar da bukatarmu! Abunda muka jima da sanina suna neman yankin kwana ta duƙa musu, sai ga shi laluri tasa duk taurin kan da fulani ke da shi mun russuna musu da muka ji uwar bari, dan muna da bukatar mu san waye ba mutum ba a yankin nan! WAYE MACIJI! a yankin nan! Dole azo ayi gwaji dan a fidda zargin juna a zukata, gwanda a nuna mana inda matsalar take mu kuma mu san ta inda zamu shawota" Aka amsa da haka ne,nan dai suka gama tattaunawa suka ajiye maganar tasu akan su saurari yankin ja'i. Bayan an watse a fadar Sarki Chubaɗo Arɗo da Baffa ne suke tafiya a hankali su na magana kasa-kasa,Arɗo ya ce "Magaji, fatan kana sa a ido sosai a kan su AZIMA DA AZIZA?" "E Arɗo ina iyakar bakin kokarina wajan saka musu ido, ita Azima baka iya gane gabanta,gwanda Aziza, gasu dai a tare aka haifesu amma halayyarsu ta sha bamban, a kwana biyun nan basu kula juna, Jumala sai korafi take yi a kan nayi musu magana ko me ya haɗa su, amma ban dauki hakan da mahimmanci ba sabida ba shi ya kamata na kula ba, kare rayukan yankin nan shine abu mafi mahimmanci" Arɗo ya gya ɗa kai ya ce "Tabbas hakane, ba mamaki sun ɗan yi faɗa ne tinda ana samun irin haka" Baffa yace "Eh nima haka nake tunani Azima bata da dadi ko kadan, Arɗo barin wuce gida" "To a gaida Jumala da Azima da Aziza" "Zasu ji" Baffa ya fada tare da yiwa Arɗo sallama. 🍃🍃🍃🍃 Tun safe Aziza ke rafin jimulo tana wanke kayan Hajja da na Baffa, Azima kuwa dan Aziza na rafin jimulo yasa ita bata je ba tana gida, abinci Hajja ta ɗora amma Azima ta hana abincin dahuwa, har la'asar tana zaune a kan tabarma kaba tana saƙe wani igiyoyi, Hajja ta kalleta ta ce "Wai ni kam Azima wannan saƙe-saƙen da kikeyi na miye ne? Tun safe kike zaune a wajan ba sallar azahar bare la'asar ki tashi kiyi sallah" ba tare da ta dago ta kalli Hajja ba ta ce "BANA SALLAH!" 😏 Baki sake Hajja ta kalli Azima ta ce "Kina fashin sallah ne?" kafin Azima ta bada amsa Aziza ta yi sallama da kaya a hannunta ta shige bukkan Hajja ta ajjiyesu sannan ta fito ta duƙa ta ce "Sannu da gida Hajja" "Yawwa sannu Azizatuna, kin dawo?" "E Hajja na dawo" "Ayya Aziza maimakon idan kin wanke kayan ki dawo gida idan ya bushe anjima a kwaso shine kika zauna har yamma a rafi ba tare da kin dawo gida ba? Ga shi haka kika fita ba ki ci komai ba" murmushi Aziza ta yi a ranta ta ce "Idan na so zan iya wanke kayan nan na busar da shi a lokaci guda sabida karfin dafin da nake da shi,amma bana son hakan nafi son na samu ladar iyayena" a fili kuma ta ce "Wlh ba komai Hajja bana jin yunwa ai" "Allah ya miki albarka Aziza ke da yar uwarki, kinyi sallah ne?" "Amin, E Hajja nayi sallolina a rafin jimulo ban bari lokaci ya shige ba" Hajja ta kalli Azima ta ce "Azima kince baki sallah kina fashi ne?" da blus eyes dinta ta dago ta kalli Hajja ta ce "Ni sallah ne kwata-kwata bana yinsa a rayuwata!" dam!dam!dam! Ƙirjin Hajja ya bada ta b'ata shuru tana bin Azima da kallo, da kyar ta buɗe baki zata yi magana amma Azima bata jira hakan ta faru ba dan kamar ƙiftawar ido ta tashi tare da tattare dogon igiyar da ta saƙa ta shige bukka, Aziza ganin yadda hankalin Hajja ya tashi da maganar da Azima ta faɗa ya sakata faɗin "Karya take yi Hajja, kin san halinta bata damuwa da maganar da zata faɗi zai yi maka dadi ko akasin haka faɗi kawai take yi" sai a lokafin Hajja ta sauke ajiyar zuciya, Aziza ta ƙwaƙulo murmushi dan sallah kam Azima baya yi, ta ce "Hajja ba a gama abinci ba?" "Wollah Aziza ban san wani irin abinci yau nake dafawa ba, tin rana na ɗora kafin ayi azahar amma har yanzu ta ƙi nuna" shuru Aziza ta yi tana kallon tukunyar kasan na wani sakanni kafin ta ce "To Hajja je ki ciki ki huta yanzu zan karasa" "A'a Aziza yanzu fa kika dawo daga...." "Ohh dan Allah Hajja ki je ki huta" murmushi Hajja tayi tana shigewa bukka, Aziza ta buɗe abinci ta ga rashin dahuwarsa yana da nasaba da sa hannu da Azima ta yi, rintse ido ta yi ta buɗe nan idonta ya koma fari sosai ta zaro harshenta ta hura wani hayaki a cikin tukunyan, nan kalar abincin ya canza alaman ya dahu, sannan ta rufe tana miƙewa tsaye ya yi dai-dai da shigowar Baffa da kuma fitowar Hajja daga bukka, sannu da dawowa suka masa, Baffa ya amsa yana zama a inda Azima ta tashi, kallon baƙin igiyar da Azima ta yi saƙa da shi ya gani guntun, dauka ya yi a fili ya ce "Zaran saƙar dana? me yake yi a gidan nan? Wa ya kawo?" 🍃🍃🍃🍃 COMMENTS AND SHARE BY MOMYN AHLAN [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *NA GAISHEKI SIS NA🥰 SURRY BABY, ALLAH YA BAR MIN KE.* *AZIMA DA AZIZA GRP NA GAISHEKU😂 MASU MAFARKAI DA TSORATA NA JINJINA MUKU, A CI GABA DA CHAPTAWA.*🤙🏻 *FREE..* 🅿️==1️⃣3️⃣↪️1️⃣4️⃣ "Zaran saƙar dana kuma?" Hajja ta faɗa tana kallon hannun Baffa da ya riƙe zaren yana kalla, Aziza ce ta matso kusa da Baffa ta duƙa ta ce "Baffa me zaran ya ƙunsa?" shuru Baffa ya yi na wasu lukota kafin ya ce "Ba ƙaramin hatsari wannan zaren yake da shi ba, ana amfani da shi wajan yaƙi! Ko kuma a ɗaure takwabi da shi, duk wanda aka sara ko aka yanka da takwabin da aka d'aure da shi to sunansa gawa! Walau mutum ko aljan! " a firgice Aziza ta ce "Kenan mutum mutuwa zai yi?" "E Aziza, wa ya kawo zaran nan gidan nan? Sannan ta ya aka samo shi? Dan nasan ba a samunsa nan kusa sai an je can cikin jejin lore, wanda wannan jeji tun kafuwarsa shekaru aru-aru babu wani ɗan adam din da ya taba zuwa idan ba ni ba" Hajja ta ce "Ai kuwa dai Azima ce na ganta da shi dan tun safe take zaune a inda ka tashin nan take saƙa shi,bayan ta gama ta shige ciki, bata jima da shiga ba ka shigo" da sauri Baffa ya miƙe tsaye ya ce "Azima! Azima! Azima!?" ya kwala kiran sunanta da karfi, Aziza ta ce "Bari na kirata Baffa" cikin faɗa Baffa ya ce "Nan da bukka ta ce bata jin kiran da na mata?" Hajja ta ce "Ayye Baffan yan biyu ka bi a hankali mana, watakila bacci ne ya kwasheta Aziza kirawota" Baffa ya ce "Ke da kika ce ina shigowa bata jima da shiga ciki ba shine har bacci zai kwasheta?" "Ai Azima bata da wuyan bacci" cewar Hajja, shi dai Baffa shuru ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya maida hannunsa baya yana jiran fitowar Azima. Tana kwance a gadon kara, rabin jikinta macijiya sai juyi take yi kanta a hargitse, Aziza ta shigo da sallama ko amsawa Azima bata yi ba, Aziza ta ce "Ba ki jin Baffa na kiranki ne?" "Mtswwwww! Na ji mana, tunda dai ni ba kurma ba ce! Je ki ce ba zan zo ba!" a fusace Aziza ta sa hannnu ta janyo wuyar Azima ta ce "Wallahi! Wallahi! Wallahi! Kinji na rantse miki ko? To sai kinje, kuma dole ki ba wa Baffa amsar tambayoyin da zai miki, za ki tashi ne ko sai na b'ace dake a dakin nan na wujijjigaki!?" Aziza ta karasa maganar idonta da fatar jikinta suna canza kala, ganin haka yasa Azima miƙewa fuuuu ta fice, rufe ido Aziza ta yi ta dawo dai-dai sannan ta bi bayan Azima, a tsaye ta sameta Baffa na tuhumarta inda ta samo zaren sakar dana, cike da rashin tsoro da rashin kunya ta ce "A inda ake samu na samo!" "AZIMA!!!" Aziza ta faɗa a tsawance ta yi kanta dan ta kai mata mari, da sauri Hajja ta ja hannun Aziza sannan ta fashe da kuka, murguɗa baki Azima ta yi ta fice a gidan ma gabadaya, Baffa kuwa suman tsaye ya yi, Aziza kuma tana lallashin Hajja dake kuka. Cikin kuka Hajja ta ce "Wai ni meke shirin faruwa dani ne kam? Me yasa Azima ta zama haka? Kwata-kwata yanzu bata shakkar gaya mana magana! Aziza dame ku ke so naji? Idan ba ki taimakawa yar uwarki ki gyara mata halinta wa zai iya yin hakan?" Hajja ta ci gaba da kuka, Baffa kuma bukka ya shige ya zube a bakin gadon kara jikinsa na rawa, hakika jejin lore ɗan adam baya shiganta ya fito lafiya, duk ɗan adam din da ya shiga jejin lore to sunansa gawa! Shi ma sanadiyyar shigarsa jejin lore ya yanko zaren saƙar dana sadda zasu gwabza da Banju ne, rass! rass! rass! gaban Baffa ya bada nan zufa ta shiga tsatstsafo masa ta ko wace kusurwar gashi dake gangar jikinsa, a fili ya ce "AZIMA BA MUTUM BA CE! TAYA ZAN GWADATA NA GANE HAKAN DAN NA WARKARWA ZUCIYATA TANTAMA DA ZARGI!? INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! YA ALLAH KASA KAR ABUN DA NAKE KWANA NAKE TASHI DA SHI YA ZAMA GASKIYA!" Baffa ya karasa maganarsa hannunsa a sama hawaye na gangarowa. Da kyar Aziza ta ɗaga Hajja ta shigar da ita bukkarta tana lallashinta amma ina Hajja ta kasa tsaida hawayenta, kasa juran kukan nata Aziza ta yi ta miƙe a hankali ta fita zuwa randar kasar dake tsakar gidansu ta ɗibo ruwa a kwarya ta bude bakinta ta zuba abu a ciki sannan ta koma ta ba wa Hajja, ƙin karba Hajja ta yi ta ci gaba da kuka, Aziza ta ce "Dan Allah Hajja kiyi shuru ki daina kuka, kin ga gidan nan bamu da sauran ganyen magunguna balle na haɗa miki ki sha idan kanki ya fara ciwo, zan yiwa Azima magana ga ruwan nan ki sha zuciyarki ta yi sanyi" da kyar Hajja tasa hannu ta karbi ruwan ta sha, tana shan ruwa ko minti uku bata yi ba, ta zube a jikin Aziza, hawaye ne masu zafi sosai suka zubowa Aziza a fuskarta a fili ta ce "Kiyi hakuri Hajja ki yafe min ba zan iya ci gaba da kallon kukanki ba, baccinki shine mafi alkhairi, tun a yau da ba ki san su waye mu ba kina irin wannan kukan ran da kika sani za ki hadiyi zuciya ne Hajja? Ina ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan iya rasaki ke da Baffana ba! Zan ci gaba da boyewa tare da dakatar da yar uwata, ko da kuwa zamu kashe juna" Aziza ta karasa maganarta tana sake rungume Hajja, ta sha kuka sosai kafin ta gyarawa Hajja kwanciya ta fita. sallama ta yi a bukkan Baffa, da sauri Baffa ya share hawayensa ya ce "Shigo Aziza" cikin natsuwa ta shigo,zama ta yi kusa da kafarsa ta ce "Baffa kuka kake yi?" girgiza kai Baffa ya yi ya ce "A'a ba kuka nake yi ba Aziza" shuru Aziza ta ɗan yi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Baffa ina so na san meke ƙunshe da wannan zaren da Azima ta saƙa" "Me kuma kike so ki sani bayan wanda na gaya miki Aziza? Hatsarin da ke cikin wannan zaren ba zai faɗu a baki ba tsananin yawanta, da ace za a dauki kwaya ɗaya tak! A jefata a cikin rafin jimulo, ina mai tabbatar miki duk wanda ya sha ruwan wannan rafi zai mutu!" dam! dam! dam! gaban Aziza ya bada nan ta shiga saƙe-saƙe a ranta tare da tunane-tunane, shin wa Azima take son kashewa da wannan zaren? *"BAFFA"* wata zuciyar ta bata amsa da sauri ta miƙe tsaye a firgice tana zare ido tare girgiza kai gami da fadin "A'a karya ne! Ba zai yu ba! Ba zan bari hakan ta faru ba!" ganin yadda ta ruɗe lokaci ɗaya ne yasa Baffa tashi da sassarfa ya kama hannunta ya zaunar da ita ya ce "Aziza natsu mana! Tsaya...kina ji? Menene? Gaya mini? Miye ba za ki bari ya faru ba?" kuka Aziza ta fashe da shi mai tsanani tana kwanciya a jikin Baffa, sosai hankalin Baffa ya tashi yana tambayar Aziza meke faruwa!. Cikin kuka Aziza ke faɗin "Me yasa! Me yasa! Me yasa!" da kyar Baffa ya shawo kan Aziza ta yi shuru ta daina kuka, Baffa ya ce "Aziza meke faruwa ki gaya min gaskiya karki boye min komai, ni mahaifinki ne" saita natsuwarta Aziza ta yi ta ce "Baffa, haihuwarmu ta yi muku rana?" "Subhanallahi! Wannan wace irin magana ce kike faɗi Aziza?" "Baffa kukan da Hajja ta yi a kan Azima dazu bazan sake bari hakan ta faru ba, ba zan sake bari ba!" ajiyar zuciya Baffa ya sauke,ita kuwa Aziza ta yi hakane dan kawar da shakku a zuciyar Baffa, shuru na ɗan wani lokaci ne ya ratsa wajan kafin Aziza ta ce "Amm Baffa? Taya za a lalata zaren saƙar danar da yake hannu Azima?" "Wannan ba shi bane abunda nake tunani Aziza, yadda aka yi Azima ta samu zaren nake tunani" "Amm amma Baffa ta ce inda ake samu ta samu! Ya matsayin hatsarin jejin lore yake?" "Aziza faɗin hatsarin jejin lore ba zai yu ba, dan yafi karfin ki fasalta shi da komai, taya har Azima zata shiga wannan ƙasurgumin jejin ta fito tana yar adam? Wannan shine tambayar da nake yiwa zuciyata amma na kasa samun amsa, ban san meke shirin faruwa da mahaifana ba" "Baffa ka rabu da maganar Azima, kasan wani lokaci ba hankali gareta ba, yawwa kuma Baffa na mance ne ban gaya maka ba, Azima kamar tana da aljanu! Dan cikin dare sai na dinga ji kamar tana ta buge-buge da sambatu ita dayanta, Baffa na tabbata su ne suke saka ta rashin kunya,kuma ba mamaki karya take yi ba ita taje jejin lore ba, sai dai idan aljanun ne suka je suka kawo mata, ka yarda dani Baffa gaskiya nake gaya maka" Aziza ta karasa maganarta tana riƙo hannun Baffa, jinjina kai Baffa ya yi ya ce "Kenan wani irin aljanu Azima ke da shi? Wanda har zasu iya kawo mata zaren saƙar dana? Me zata yi da shi? Kuma har tasan yadda ake saƙata?" zare ido Aziza ta yi ta hau rawar murya tare da in'ina "Amm....eh.....umm....ohh...Baff....Baffa ....kar...ka...da..mu...da...Azima...ni nan zanji da ita, zan mata hayaƙin aljanu zata warke da yardan Allah na san ka yarda dani ko Baffa?" murmushi Baffa ya yi yana jin kaunar Aziza a cikin ransa, hakika ba zai ce baya son Azima ba tunda ita ma ƴarsa ce, amma aka ce mai kyautata maka shi ne wanda yake rayuwa a cikin zuciyarka, "Na Yarda da ke Aziza, Allah ya miki albarka" murmushi Aziza ta yi ta miƙe tsaya tare da fadin "Amin Baffana" fita ta zo yi a bukkan har ta duƙa sai kuma ta ɗago tare da juyowa ta ce "Amm Baffa? Baka faɗa mini abunda zai iya lalata zaren saƙar dana ba?" "Aziza sanin wannan ba sauki garesa ba, har sai an koma jejin lore, jejin da mutane ba su shiga" "To amma Baffa kai a garin yaya ka shiga ka fito?" "Tsoron tarihi ne Aziza, kun dai sannin a matsayin mahaifinku! Amma har kwanan gobe baku da tarihin mahaifinku, na sha miki alƙawari zan baki tahirin jarumtar mahaifinki! Abunda yasa bana son faɗi yanzu sabida jarumtar bata jawo min komai ba sai babban kuskure" Da sauri Aziza ta dawo ta zauna ta ce "Baffa kamar ya? Dan Allah ka gaya min" "A'a Aziza dama kin tashi kin tafi ne da ya fi miki alkairi, dan ba zaki ji komai ba a yanzu" ganin yadda Baffa ya yi maganar yasa Aziza miƙewa a hankali ta fice, tana fita ta koma bukkansu tana tsaye tana ta saƙa da warwara, a fili ta ce "Kenan domin dakatar da Azima nima sai naje jejin lore? Idan kuwa hakane! *yau din nan zanje domin dakatar dake, amma kafin nan sai kin gaya min wanda kike hari da zaren sakar Azima!" Aziza ta faɗa tana harɗe hannuwanta. 🍃🍃🍃🍃🍃 Zaune suke a fadar sarki Chubaɗo, da sauri Maga Isar da saƙon kwana ya zo ya zube a gaban sarki ya ce "Ranka ya daɗe! Sako ce daga yankin ja'i" da sauri wa inda suke zaune a wajan suka mai do da kallonsu kan Maga Isar da Sako, wazirin kwana ya ce "Maga Isar da sako, buɗe ka karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuta" jiki na rawa Maga Isar da saƙo ya zo zai buɗe sakon sarki Chubaɗo ya dakatar da shi da cewa "Dakata! Maga Isar da Saƙo, wannan saƙo ba na iyakar mu na nan kawai za a karanta ma wa ba, a'a yanzu maza kuyi aike a tara mutane,kuje ku sanar da Mai unguwa Ori, ku kira Arɗo tare da Baffa Mandi, da Magaji Bawa duk a hallara yanzu" Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya mike da sauri dan isar da saƙon sarki chubaɗo. A cikin yan mintuna ƙalilan kowa ya hallara a fadar sarki Chubaɗo , kowa yana fargaban kar yankin ja'i ace sun rubuta ba zasu taimake su ba. Bayan kowa ya bada hankalinsa sarki Chubaɗo ya ce "Maga Isar da sako karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuto" Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya buɗe wasikar yankin ja'i ya fara karantowa kowa naji. " _Wa'alaikumussalam, da fatan yankin kwana su na lafiya? Ya kuma fargaban iftila'in da ku ke ciki? Kashh! Ayya! Allah Sarki! Wasikarku ta iso garemu na neman taimako! Tunda har yankinku ya duƙawa tamu yankin,mun yarda zamu taimaka muku da Innu Maciji! Zai zo gobe, amma abun mamaki ace kuna da mutum a yankinku kamar Magaji Bawa har sai kunzo yankinmu neman taimako? Koma miye daukakarmu ce, tunda yankuna yanzu zasu shaida kun watsar da makamanku wa yankinmu, saƙo daga yankin ja'i, mun karb'i ƙudirinku!_" Maga Isar da sako yana gama karantawa Baffa ya miƙe cikin fushi ya ce "Sadda muka tura wasika yankin jimo dan su taimaka mana da jarman macizai magana mai dadi suka mana sannan suka jajanta mana suka amince da bukatarmu, amma yanzu wannan wasika na yankin ja'i har da izgilanci a ciki" Arɗo ya mike shi ma ransa a b'ace ya ce "Duk abunda aka gaya mana laifin waye Magaji? Na ce laifin waye!?" tsohon Sarkin fulanin kwana Baffa Mandi ya ce "Yanzu ba lokacin nuna fushi bane sabida halin da muke ciki, tunda sun amince zasu taimaka mana shikena!" Garkuwan fulanin kwana ya ce "Amma abunda Arɗo ya faɗa gaskiya ne, Magaji da ace ka yi wani abu a kai da yanzu wannan bala'in an gama shi, me yasa ba zaka dawo yadda kake da ba? Idan ka manta da takenka sai a tuna maka....!" "Ya isa haka Garkuwa!" Baffa ya dakatar da shi idonsa jajur, Ori ya ce "Garkuwa yana da gaskiya Magaji, da ace kayi wani abu a kai da yanzu yankin ja'i basu gaya mana magana ba" Wazirin kwana ya ce "Tabbas hakane Magaji, da ace kayi wani abu a kai da har yaushe zamu duƙawa yankin ja'i balle su mana izgili kamar mu muka ɗorawa kanmu masifar!" haka kowa yasa Baffa a gaba ana cewa duk abunda yankin ja'i suka faɗi har da laifinsa, jikin Baffa ne ya hau rawa ya daka tsawa da faɗin "NA CE YA ISAAAAA!!" ya juyo yana kallon mutanen da suke wajan ya ce "Wai ku baku duba gagarumin bala'in da nake hangowa ne? Na koma na haƙo kayayyakina da na binne tamkar haƙo maƙabarta ne wa yankin nan! Dan karku manta da aljanun da mayun da na rufe! Duk abuna ban cika kisa ba sai inta kama dolen- dole! Tunda na kashe Banju nayi sallama da kwanciyar hankali, wanda a yau duk faɗin yankin kwana babu yaran da ake zargi kamar yarana AZIMA DA AZIZA! duk da ba zan hanaku zarginsu ba, amma ko da sau daya ne zaku min uzuri! na rayu ne wa yankina inda nayi aikin tuƙuru da jinina da lafiyata! naje na haƙo abunda na binne duk aljanu da mayun da na ɗaure tass zasu kunce, me ku ke tunani zai faru da iyalin da nake da shi a halin yanzu?" Baffa ya faɗi yana fashewa da kuka yana dukawa, jikinsu ne ya yi sanyi sosai, yayinda Arɗo ya dago Baffa yana rarrashinsa inda sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suka hau ba shi hakuri tare da nadaman ganin laifinsa, Arɗo ya ce "Kayi hakuri Magaji, yanzu abunda za ayi a rufe wannan maganar, Allah ya kaimu gobe Innu Maciji ya zo ya warware mana wannan sarƙaƙiyar" Sarki Chubaɗo ya ce "Kowa zai iya kama gabansa" Da kaɗan-kaɗan aka fara watse wa, Arɗo da Baffa Mandi da Baffa ne suka fara tafiya, Baffa Mandi ya ce "Amma na rasa me yasa Magaji kake yawan maganar Banju" Baffa ya ce "Sabida ni kaɗai nake ganin abunda nake gani a gidana" yana gama faɗin haka bai jira amsarsu ba ya yi gaba, Arɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Mandi, akwai abunda yake damun Magaji" Baffa Mandi ya ce "Nima haka nake gani, amma anya baya da nasaba da yaransa da ake yawo dasu ake zarginsu kuwa? A gaskiya Magaji ya yiwa yankin kwana hidima bai kamata a dinga masa haka ba" "Gaskiya kam hakane" tafiya sukeyi a hankali suna tattaunawa, Baffa kuma hanyar gida ya ɗauka. 🍃🍃🍃🍃 Zaune ta sameta a rafin jimulo, ita ma zama ta yi kusa da ita ta ce "Azima tambayarki na zo yi" "Wai ni Aziza me yasa kika rainani ne? Ba nice gaba da ke ba?" murmushi Aziza ta yi ta ce "Au haba dai da gaske? Rainin babu dadi ne? To haka iyayenmu suke ji a ransu idan kika musu, balle ni da ba ki bani ko da kwana daya bane, kawai iskar duniya kika rigani shaƙa" Azima ta kyalkyale da dariya ta ce "Macijiya Aziza me ya kawo ki wajena?" Kallonta Aziza ta yi ta ce " ZAREN SAƘAR DANA! WA ZA KI KASHE DA SHI!?" sake kyalkyalewa da dariya Azima ta yi ta ce "Idan naki faɗi fa me zakiyi?" "Sai na gwada ta wata hanyar!" Aziza ta faɗa tana mikewa tsaye, da sauri Azima ta mike ta ce "Muje zuwa" tana gama faɗi ta hau ajijiya, Aziza na tsaye tana kallonta. 🍃🍃🍃🍃 COMMENT AND SHARE BY MOMYN AHLAN [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *IDAN AKA CE ƘAWANCE ANA NUFIN AMINTAKA! WANDA WANNAN AMINTAKAR WATA DANƘO CE MAI MANNUWA,ANA SAMUNSA NE IDAN AKA SAMU YARDA DA AMANA! IDAN NA KIRAKI DA SUNAN ƘAWATA BAI KAI INDA ZAN NUNA YADDA NAKE YINKI A CIKIN RAINA BA, HAKIKA MU DIN BA IYAKAR KAWANCE BANE,INAJINKI TAMKAR WACCE MUKA FITO CIKI DAYA,INA MIKI SON SO SABIDA ALLAH! ALLAH YA BAR MINKE ƘAWALLITA _RASHEEDAT USMAN UMMU NASMA&NASREEN_ ALLAH YA ALBARKACI ZURI'ARMU ALLAHUMMA AMIN, INA KU KE MAKARANTA? UWAR NASMA TA YUNƘURO FA A BOOK DINTA MAI SUNA _GELLE 'BINGEL_ WANDA ZAKU SAME SHI CIKIN FARASHI MAI SAUKI, KU NE ME NI TA LAMBATA DAN ISA GA FASIHIYAR MARUBUCIYAR KAI TSAYE, KARKU BARI A BAKU LABARI, SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*👐🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *FREE..* 🅿️==1️⃣7️⃣↪️1️⃣8️⃣ A wani ƙasurgumin jeji Aziza ta tsinci kanta, jeji mai cike da wani mugun duhu da abubuwan tsoro tare da wasu mugayen halittu marasa kyawun gani da ban tsoro, haƙiƙa ganin wa innan abubuwa sun tsorata Aziza, amma tunowa da maganar Inno Fandi da cewa kar ta tsorata yasa ta takure tare da tattaro jarumta, ta hau tafiya, tare da furta kalman "makarin zaren saƙar dana!" wani sowa ne taji na tashi ta tsakiyar kanta da wani irin mugun jijjiga nan wasu halittu suka yi sama da ita, saura qiris Aziza ta saki ihu amma kuma ta daure tana karanto dukkan adduar da ya zo zuciyarta, nan halittu suka dauketa suka kara yin sama da ita suka hau tafiya da ita a cikin duhu,amma duk wannan duhu ba shi ya hanata ganin mugayen halittu marasa kyau da ban tsoro ba. Wa inda suka dauketa basu ajiyeta a ko ina ba sai a gaban wani katon halitta wanda bata san dame zata fasalta halittarsa ba sabida tsananin muni da girmarsa, ana ajiyeta muryar wannan katon abun ya ce "Keeeee! Me ya kawoki jejin lore!!!" a yadda muryarsa take ɗan adam idan ya jita ya ci ace ya mutu tsananin amo marar daɗi da kaifi, cikin dakiya Aziza ta ce "Makarin zaren saƙar dana, shi nake so" shewa wannan halittar ya yi,sannan ya ce "Ya matsayinki yake a halittu!?" " *NI MACIJIYA CE!*" Aziza ta bada amsa, wannan halittar ya ce "Ke ba iyakar macijiya ba ce, akwai wani sirri a tattare dake, dan haka ko ba mu baki makarin zaren saƙar dana ba,kaifin gubar dake jikinki zai iya ƙonasa! Amma kasancewar sau daya tak! Muke bada alfarma zamu baki taimako guda daya, zamu ƙara miki karfi, da kinje ki hurawa zaren wuta ta idon ki zai ƙone ƙurmuss! Ga wannan" ya faɗa yana daukar wata kyakkyawar dutse mai cike da hasken gaske ya hura mata shi ya shige ta goshinta, abun na shiga jikin Aziza sai da ta girgiza ta yi kamar zata faɗi amma ta yi iyakar iyawarta bata faɗi ba,dama tana tsaye ne ita ba a sama ba ita ba a kasa ba, abun na shiga jikin Aziza nan ta kalli fatar jikinta ta ga yana sab'ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama dawowa hayyacinta tuni ta fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce "Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah" "To Baffa" Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta jima tana addua sannan ta tashi. Abu na gaba da zata yi shine daukar zaren saƙar dana taje ta kona shi, to amma abun tambayar a nan shine a ina Azima ta ajiyesa? "zaki iya dubawa ki gani ta tafin hannunki ai an baki karfi a daren jiya a jejin lore" wata zuciyar ta bata amsa da haka, da sauri ta buɗe tafin hannunta na dama tasa hannun hagunta tana shafe tafin hannun daman tare da lumshe ido, nan ta ga ashe ma a cikin kayanta Azima ta ajiye zaren saƙar danar, tasan tabbas Aziza sai ta binciko,kuma duk bincikenta ba zata duba kayanta ba tunda ba zata yi tunanin zata saka a ciki ba, da sauri Aziza ta buɗe ido tana fadin "lallai Azima ke shaiɗaniya ce! A cikin kayana kika ma ajiye?" da sauri ta wargaza kayanta ta dauki zaren wanda Azima ta saƙa shi ya yi tsayi, lullubi ta yi ta boyesa a cikin mayafinta ta fito a hankali dan gari ya yi haske, har ta kai bakin kofa zata fita ta ji Hajja na kwala mata kira da gudu ta fice dan bata son ta rasa wannan damar, jejin kwana taje ta ajiye zaren bayan ta duba babu kowa a wajan, da ido ta kalli zaren yayinda idon nata ya koma jajur kamar garwashin wuta,nan wani jar wuta ya fito daga idonta ya kama zaren,nan zaren ya kama da wuta har yana wani irin ƙara passpasspass! Da sauri Aziza ta ja da baya, nan zaren ya ƙone ƙurmuss! tokar Aziza tasa hannu ta shafe shi ya b'ace nan ta sauke ajiyar zuciya mai karfin gaske tare da fashewa da kuka tana zubewa a kan guiwowinta tasa goshinta a kasa ta yi sujjadar shukur, ta yi tsammanin ta kashe wannan bala'in bata san wanda yake shirin ci ba. 🍃🍃🍃🍃 *AZIMA.* tun fitarta a gida tana kwance a kan bishiya a macijiya tana jiran isowar Innu maciji, sai bayan da garin Allah ya fara wayewa ta ga wasu yan matasan samari biyu sun zo sun tsaya a jikin bishiyar da take kwance, dayan ya ce "To ma ban da abun Mai Unguwa taya zamu iya kare Innu Maciji da za a wani turo mu dan mu tarbesa" "Nima dai abun da na gani kenan" saurin zare ido Azima ta yi ta kallesu da kyau sannan ta yi murmushi "Ohhho kenan yan fadar mai unguwa ne! Aiko su ya yi, shin na bar ma su bada labari ne? Idan kuma suka tona min asiri fa?" nan ta haɗe rai tare da sulalowa daga bishiyar ta zama mutum, hannu ta miƙa sama sai ga kwaryan nono, murmushi ta yi ta buɗe kwaryan wanda yake cike da nono kindirmo fari sol abun sha'awa ta watsa dafi a ciki sannan ta gyara mayafinta tayi lullubi ta rufe fuskarta ta nufi inda suke, cikin karairaya ta musu sallama, su kuwa sun ga ƴar budurwa har rige-rigen amsawa suke yi,cikin harshen fulatanci suke magana ta ce musu "Ga fa nono, daga ina ku ke da sassafen nan haka ku ka zo ku ka zaune a tsakanin yanki?". "Wlh mai unguwa ne ya aiko mu, kin san ai masifar da ake fama da shi a yankin nan na macizai, to yau Innu Maciji zai zo wanda yake yankin ja'i shine mai unguwa ya aiko mu dan mu tarbesa,kin san kwanaki da Jarman macizai ya zo gawarsa kawai muka gani, kai duk wannan macijin da yake kisan nan ko take kisan nan ko humm idan Innu Maciji ya zo zan ce ya bani dama na kashesa da hannuna" cije baki Azima ta yi ta ce "da gaske?" "Aradun Allah kuwa! Sanda zan sha na dinga roɗewa macijin kai har sai ya koma ga Allah" damƙe hannu Azima ta yi jin yadda ranta ya b'aci zuciyarta na tafasa amma ta daure tare ta k'wak'ulo murmushin mugunta ta ce "Ai kuwa nima ina da wasu sirrika a kan macizai, kafin na gaya muku ga wannan nonon ku sha" ta fada tana tura musu kwaryan, dayan ya ce "Allah sarki! Ashe kin san yau da yunwa muka tashi, ga shi kafin mu karya karin kumallo aka turomu yanki" murmushi kawai Azima ta yi ba tare da ta sake magana ba, nan suka buɗe nonon nan suka hau sha, sai da suka shanye tass har suna mata godiya, Azima ta kyalkyale da dariya tare da yaye mayafin fuskarta nan blue eyes dinta ya bayyana, tare da rikiɗewa ta hau komawa macijiya, tsananin tsoro da firgici yasa suka kasa motsi illa junansu da suka rungume gagam!, bayan Azima ta zama macijiya sannan ta koma ta zama mutum ta matso kusa dasu ta duka ta ce "NI CE AZIMA MACIJIYA! WACCE DUK KASHE-KASHEN DA AKE YI NI NA KE YI! NI! NI! NI CEEEE! SANNAN KU TAKU TA KARE DAN DAGA NAN BABU WANDA ZAI MOTSA A CIKINKU, DAN KUN SHA GUBANA" tana gama faɗi kuwa suka hau aman jini, su na riƙe wuyarsu tsananin azaba, jini na fita ta baki da hanci, suna birgiman fitar rai Azima na ta sheƙa dariya, da haka har suka daina motsi, bayan sun mutu ta kwashesu ta maida su gefe ta ajiye sannan ta ci gaba da tsumayin jiran isowar Innu Maciji, ba jimawa sai ga shi nan kuwa ya yanko a kan dokinsa, daka gansa ka ga basamudan bafulatani mai ji da kansa, wuyarsa rataye da maciji, Azima na ganinsa ta hau murmushi tare da gyara lullubinta ta zo ta tsaya a kan hanya, (ga Azima ga Innu Maciji, ya zata kaya?). Kamar yadda ta yiwa jarman macizai haka ta yiwa Innu Maciji, shi ma kalar tambayar da jarman macizai ya mata shi ya mata "Mutum ko aljan?" murmushi ta yi tare da fadin " *RUWA BIYU!*" sannan ta juyo gami da yaye mayafinta, Innu Maciji na ganin kwayar idonta nan ya sauƙo da sauri tare da zare takwabinsa yana fadin "Keeeee!" haɗe rai ta yi ta ce "Ajali ya kiraka!" Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce "Kina tunanin zan mutu a hannunki ne?" "Ashe dai baka cika ba! Tunda har ba zaka iya bambance wacece ni ba, amma ina so ka sani ba zaka shiga yankin nan ba,kamar yadda ba zaka koma yankinku ba" tana gama fadi ta yi kansa tare da komawa macijiya,ganin haka yasa Innu Maciji saurin b'acewa dan ya ga da karfinta ta nufosa, Azima gani ta yi Innu Maciji ya b'ace yasa ta koma mutum tana ta kalle-kalle,ji tayi an tokareta ta baya nan ta fadi kasa ta bugu tukunna Innu Maciji ya bayyana yana dariya yana kallonta ya ce "Ba mamaki baki da labarin waye Innu Maciji ko? Humm ni ne nan mai fada da aljanu da mayu, sabida shaharata yasa sadda aka raba kambun girmamawa ni ne nan nayi na daya, dan haka sai na baki wahala! Na galabaitar dake sannan na daukeki na kaiki wajan mutanen yankinku na nuna musu ke!" yana gama fadin haka ya zaro wani dogon igiya ya naɗe Azima da shi, ya hau bugunta tare da watsa mata wani ruwan magani wanda da ya watsa mata zata kurma ihu, fatar jikinta ya koma blue sabida karfin dafinta ne ke raguwa, haka Innu ya ci gaba da ganawa Azima azaba wanda izuwa yanzu fadin halin da take ciki b'ata lokaci ne, sai da ya ga bata iya motsin kirki sannan ya kyaleta yana shirin daukarta ya ɗorata a dokinsa yaje ya nunawa jama'ar yankin kwana, har ya dauketa Azima ta buɗe ido a galabai ce, a ranta ta ce "Yanzu idan aka kaini Baffa da kansa na san zai kasheni! To ina kuma daukar fansata!? Inaaa ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan bar yankin nan ba, ba tare da burina na son maida yankin kwana maƙabarta ba, sannan ba zan bari na mutu ba tare da na shiga cikin gari ba" tana gama fadi ta yanki gashin kanta ta haɗiye ta rintse ido ta mamayi Innu Maciji wanda ya sab'ata a wuya yana shirin ɗorata a kan doki, nan ta zama macijiya tasa jelarta ta shaƙe wuyar Innu Maciji, shaƙa bana wasa ba, sannan tasa hannu ta b'abb'alle guru da layoyin dake jikinsa ta zubar, sannan tasa ihu ta koma macijiya gaba dayarta ta hau sarensa,duk yadda Innu Maciji ya so kwacewa ina hakan bai samu ba, Azima sai da ta ga Innu Macijiya ya zube kasa babu rai a tattare da shi sannan ta sulale gefe ta koma mutum tana sauke ajiyar zuciya idanunta jajur, kallon Innu Maciji take yi na wasu lokuta sannan ta ja samari biyun da ta kashe ta haɗa da innu maciji sannan ta bar wajan. 🍃🍃🍃🍃 Bayan Aziza ta koma gida aikin gabanta ta ci gaba da yi, ko kaɗan bata tambayi ina Azima take ba, nan ta yiwa Hajja shara da girki sannan ta hau ɗibar ruwa, sai da ta cika babbar randar kasarsu sannan Hajja ta ce "Ayye Aziza ba za ki huta ba?" murmushi ta yi ta ce "Hajja hutuna shine naga Allah ya rabani dake lafiya" Hajja ta yi murmushi jin dadi tare da sa mata albarka,nan suka zaune hira suka shantake sai zuwa anjima Hajja ta ce "Wai ni ina Azima ne kam?" "Wa ya san mata" cewar Aziza, "Bata rafin jimulo ne?" "Ni dai wlh Hajja har na gama jido ruwa ban ganta ba, da ace tana can dana ganta" "Ikon Allah!" Hajja ta fada, Aziza ta ce "Hajja miye amfanin damuwa a kan Azima ita da ba jaririya ba,duk inda taje zata dawo ai" Hajja ta ce "Hakane" suka ci gaba da hirarsu, sai zuwa can Aziza ta ce "Hajja wai ina Baffa? Tun fitarsa sallar asuba fa bai dawo ba ga shi yanzu ana neman lokacin azahar" Hajja ta ce "Oh! Kinga na mance ban gaya miki ba, ai suna can fadar sarkin fulani, Chubaɗo" "Wani abun ake yi ne?" Aziza ta tambaya cikin rashin sani tana kallon Hajja, Hajja ta ce "E lafiyar kenan, kin san ai an yiwa yankin ja'i aiken wasikar taimako, har Innu Maciji ma ya ce zai zo yau, to jiran Baffan naku nake yi idan Innun ya iso zai zo ya gaya mana muje can fadar sarkin fulani" Wani firgita Aziza ta yi ta miƙe tsaye ta ce "Hajja yaushe aka yi aike yankin ja'i har Innu Maciji yace zai zo?" ita ma Hajjar miƙewa ta yi ta ce "Aziza lafiya kuwa?" Kama hannunta Aziza ta yi ta ce "Hajja tun yaushe ne Azima bata gida?" Hajja ta ce "Ban sani ba Aziza, dan ni tun wayewar garin yau ban ga Azima da idona ba, ba shine nake tambayarki ko kin ganta rafi ba" "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Aziza ta faɗa tana jan mayafinta zata fita Hajja na tambayarta ina zata je, har ta kai bakin kofar zanar gidansu bata kai ga fita ba suka yi mugun karo da Baffa wanda ya shigo a fijajan hankalinsa a tafin hannunsa, da sauri Hajja da Aziza suka tare Baffa,ganin yanayin da Baffa yake ciki yasa Aziza fara addua a ranta Allah yasa dai Azima ba Innu Maciji ta kashe ba,idan kuwa ta kashesa tabbas ta b'allowa yankin kwana yaqi. Da sauri Aziza ta ɗibawa Baffa ruwa ta kawo ta ba wa Hajja, Hajja ta karba ta ba wa Baffa wanda da kyar ya yi kurbi daya wanda ya taho masa da kuka,ganin haka yasa ita ma Aziza ta fashe da kuka, Hajja na ganin Aziza ta fashe da kuka ita ma tasa kuka,nan aka rasa mai rarrashin wani,da kyar cikin kuka Aziza ta kama hannun Baffa tana faɗin "Dan Allah Baffa ka gaya mana meke faruwa!" " *AZIZA? JUMALA! AN KASHE INNU MACIJI!! DA MASU TARBAN BAƘIN SHIGOWA YANKIN KWANA SU BIYU!*" BAFFA na fadin haka Aziza ta sake hannunsa tare da yin zaman yan bori! "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! mai Azima take son zama?" kasa motsin kirki Aziza ta yi illa komawa da ta yi tana bin Baffa da Hajja da suke kuka da ido, sai zuwa can Hajja ta ce "Ya aka yi da gawar har an binne su ne?" Baffa ya girgiza kai ya ce "Ba zamu iya hakan ba, ana ganin gawar ba shiri Arɗo da Chubaɗo da Ori suka ce garkuwan fulani da Galadima da Liman da mutum biyar a fada su tafi yankin ja'i da gawan, yanzu Allah ne kadai yasan me zai faru an kashewa yankin ja'i Innu Maciji, taya zasu fara fuskantarmu su fahimce mu? Innalillahi wa inna ilaihirrajun!" nan suka ci gaba da jajinta lamarin inda a karshe Hajja da Baffa zasu fita Hajja ta ce "Aziza zo muje" murya can kasa wanda take ji da kyar ma take maganar ta ce "Hajja kuje zan zo" "To amma kiyi lullubi kafin ki fito anani ko?" Aziza ta gya ɗa kai, kanta a sunkuye, Hajja da Baffa suka fice,dan Aziza tana ji ba zata iya tafiya ba jin kamar kafafunta basu gangar jikinta. Bayan fitar su Hajja da Baffa kamar da rabin awa sai ga Azima ta shigo babu sallama kamar an wurgota ko kallon Aziza ba ta yi ba, da ido Aziza ta bi Azima tana ji kamar ta haɗa musu guba su sha su mutu ko duniya zata zauna lafiya. Azima na shiga bukka ta hau dariya kasa-kasa gami da faɗin "Innu Maciji na kashesa! Yau kuma *MAGAJI BAWA* zaka mutu! Sauran mutanen yankin nan za a kashesu ne idan tarzoma ta tashi, dan nasan yankin ja'i ba zasu hakura ba, ta fada tana murmushi tare da zura hannu dan ta dauko zaren sakar dana da ta saka a kayan Aziza amma ta ji wayam,ido buɗe take warware kayan Aziza amma bata gani ba,kamar mahaukaciya haka Azima ta fito ta zo ta tsaya a kan Aziza "Ke Aziza Magaji! Nayi ajiya a kayanki amma ban gani ba" dago kai Aziza ta yi ta kalli Azima sannan tasa hannu ta share hawayenta ta miƙe a hankali cikin sanyin murya ta ce "Me kika ajiye a kayana?" "Mtswww! Bana son rainin hankali Aziza! Ki bamu abuna!?" "Wani abunki?" "Zaren sakar dana da na ajiye a kayanki" Aziza ta jinjina kai ta ce "Owoohhh zaren dana? Na ƙonasa!!" wani zabura Azima ta yi tasa hannu ta shaqi wuyar Aziza ta ce "Kin ƙona fa kika ce!? Ke meyasa baki son mu dauki fansa ne kam!? Me yasa ba zaki bari na rama mana abunda aka mana ba! Kin ƙonasa!? Aziza ke mahaukaciyar wace al'karya ce? Na ce ke....." ture hannunta Aziza ta yi daga wuyarta sannan ta kwalfa mata mari ta ce "Kin kashe Innu Maciji da samarin fada mutum biyu! Akan me!" Ɗagowa Azima ta yi ta wanke Aziza da mari ita ma, ta kuma shaƙe mata wuya "Kin min asara! Shin kin san da cewa jejin lore sau daya tak suke ba wa mutum abu? Kuma dole da zaren sakar dana zan iya kashe Baffa me yasa! Aziza na ce me yasa! To wlh kin jawowa kowa, yau kisan da zanyi ban ga mai dakatar dani ba!" tana gama faɗi ta zama macijiya ta sulale ta fice, ganin haka yasa Aziza ita ma ficewa da gudu. 🍃🍃🍃🍃🍃 COMMENT AND SHARE BY MOMYN AHLAN BAIWAR ALLAH MASOYIYAR ANNABI MUHAMMADU S,A,W,🙌🏻🥰 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️ *KASSH! WLH ALLAH TAMBAYAR NAN TA ISHENI! TUN BAN SO NAYI MAGANA BA AMMA INAJI DOLE NAYI YAU DA MANYAN HARUFA! FISABILILLAHI MUTUM NA GANIN ABU DA IDONSA AMMA A ISHENI DA TAMBAYA MARAR AMFANI! (BOOK DIN NA KUƊI NE? SANNAN NAWA?KO KUMA AU DAMA NA KUDI NE?) HABA DAN ALLAH! TUN A FARKON SAMAN PAGE NA RUBUTA NA KUƊI NE NAIRA ƊARI KACAL DAN MASOYANA, KI DUBI ALLAH IDAN KIN SAN BA ƊARIN ZA KI BIYA BA KI DAINA KIRANA KO TURO MIN SAƘON CEWA KINA BUKATA BA DAN NI BA DAN ALLAH,👏🏻 MAZA KUMA MASU DAUKAR LAMBATA KU MIN MAGANA MAY BE TA FACEBOOK NE,KU MA KU DUBI ALLAH KU DAINA KARKU JAZA MIN MAGANA, GRP DINA BABU MAZA👏🏻* *MASU CEWA CMPLT SUKE SO, ABUNDA KO SATI INAJI BAN KAI DA FARA SAKIN BOOK DIN BA, YANZU NAKE TYPING DINSA.* *SANARWA* _WA INDA BASU BIYA KUƊIN KARATUNSU BA, SU KOKARTA SU BIYA NAN DA KWANA UKU, SABIDA NA BUƊE PAID GRP YAU, SANNAN FREE PAGE ZAI IYA YANKEWA NAN DA KWANA UKUN IN SHA ALLAHU, DAGA NAN ZAMU ƊORA NE DAGA PAID GRP, BANA SO AYI WANNAN CAKWAKIYAR BABU KU DAN CAKWAKIYA BA A MA YI KOMAI BA😊 KU DAI KU BIYONI DA NAIRA ƊARINKU DAN KUJI YADDA ZATA KAYA A CIKIN LITTAFIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, NGD MASOYANA MASU NUNA MIN ƘAUNA_😊🤙🏻 *FREE..* 🅿️==1️⃣5️⃣↪️1️⃣6️⃣ Bata motsa ba, har Azima ta gama hajijiyarta, ta girgije ta zama macijiya daga ƙasanta, ta ce "Mu gwada mana Aziza, yau inaji da abunda ba ki ji" murmushi Aziza ta yi ta ce "Dan kin saƙa zaren dana shine kike tunanin zaki iya dani? Kawai cewa nayi ki faɗa min wanda za ki kashe da shi, idan ba haka ba na gwada ta wata hanyar" sosai Azima ta haɗe rai fuskarta ya fara komawa blue ta ce "Idan zakiyi kawai kiyi! Bana son magana a baki sai dai a aikace!" Azima na gama faɗi ta daga hannunta ta huro wuta, Aziza na tsaye na kallonta, sai da Azima ta gama hura wutar ya yi jajur sannan ta yi wani gurnani ta hurawa Aziza, Aziza na ganin yadda wutar ya nufota ta yi tsalle ta haɗa wani farin hayaki ta maidawa Azima abunta nan ya sameta patttt! A ƙirji! Zubewa ƙasa ta yi tare da komawa mutum, a hankali Aziza ta zo gabanta ta ɗurkusa tana shirin yi mata magana taji yankan wuƙa a kafadarta ya shige, kafin ta farga Azima ta yi mata kafa ta nausheta a ciki nan ta faɗi kasa numfashinta nayin sama, Azima kuma ta miƙe tana dariyar mugunta gami da cewa. "Gaskiya bana da burin kasheki yar uwata, amma ya zama dole ko dan na kammala aikina a kan lokaci! dan zaman wannan dajin ya isheni ina da bukatar shiga gari, to amma idan kina raye taya burina zai cika? Ba ki san ta yadda akai na samu zaren saƙar dana ba taya kuwa zan gaya miki wanda zan kashe da shi!? To ba zan faɗa ba! Yanzu kuma idan na kasheki bani da wata sauran damuwa a rayuwata ko abunda zai dinga kawo min cikas da burina!" Duk maganar da Azima ke yi Aziza na jinta yayinda hannunta daya tana riƙe da kafadarta da yake zubar da jini dayan kuma yana kan cikinta da Azima ta yi mata naushi da kafarta, tsoronta daya shine Allah yasa wuƙar da Azima ta yanketa da shi babu zaren saƙar dana a jiki, idan hakane yana nufin Azima zata yi b'arna? Idan ta kasheta zata kashe sauran mutane sannan ta shiga cikin gari ta tarwatsasu? Inaaa! Hakan ba zai yu ba, dole na dakatar dake ko ta wace hanya! To amma me zanyi yanzu? Aziza take tambayar kanta mafita, Azima kuwa na tsaye ta juyawa Aziza baya tana ta zuba kamar indararo, wata zuciyar ta cewa Aziza "Kin manta ba zaku iya kashe juna ba? Amma ke zaki iya kashe Azima! Duba Taurarinku dake haɗe ke kaɗai aka yarjema wa dan ki gani da mai zaki dakatar da Azima" a hankali Aziza ta miƙe ta kama bishiya ta ɗan jinginu, ta lumshe ido, nan ta hau gane-gane, tabbas ba zasu iya kashe juna ba amma zata iya karyawa Azima kwarin guiwa, sannan wukar da ta yanketa da shi babu zaren sakar dana a jiki, Aziza na ganin haka tasa hannu ta shafe inda Azima ta yanketa nan wajan ya koma kamar ba a taba saka ma shi wuƙa ba, sannan a ranta ta ce "Inno Fandi! Yau inaso ki bani abunda kika sha miƙa min ina ƙin karba,ko ta wace hanya ce ina so na dakatar da Azima,ina so na san wa zata kashe da zaren saƙar dana dan na basa kariya,duk da zuciyata tana zargin Baffa Azima take son kashewa! Amma ita baka iya tunanin abunda zatayi dan komai ma zata iya yi! Inno Fandi yau ina so ki bani" Aziza a ranta take magana idonta a lumshe, wata farar tsohuwa ce fara sosai tsohuwa tukuff ta bayyanawa Aziza tana murmushi ta ce "Wani lokaci domin tsaida zubda jini! Muma sai mun wanke hannayenmu da jini! Magaji Bawa ya ajiye baiwarsa yayinda ya binnesa, na zabi shiga jikinki dan taimaka miki ke da mahaifinki a lokacin da na hango bala'in da zai faru a rayiwarku bayan an haifeku, Magaji ya yi tunanin binne baiwarsa zai ce wannan yanki ta yi sanyi, amma kashe Banju shine babbar bala'i ma wannan al'karya dan yace zai dawo, ba zaki iya jin komai a bakina ba Aziza dan alƙawarin da muka yiwa Magaji cewa daga bakinmu wani nasa ba zai ji tahirinsa ba sai dai idan shine ya bayar, sabida alkhairin da Magaji ya mana ba zan manta da shi ba, hakika Magaji Bawa jarumi ne, Aziza wannan abunda zakiyi ba ƙaramin yaƙi bane wanda ke daya ba zaki iya yi ba,ni kuwa bazan iya tayaki ba, amma ga wannan ki ɗora shi a ɗamtsen hannunki zai taimaka miki sosai,sannan karki taba rabuwa da shi dan wani sirhitaccen karfi ne, duk sadda kike bukatar taimakona ki kirani zan zo!" tana shirin b'acewa da sauri Aziza ta ce "Inno Fandi! Jejin lore! Ina so naje" zaro ido Inno Fandi ta yi ba tare da ta yiwa Aziza magana ba ta b'ace, a hankali Aziza ta buɗe ido ta kalli Azima wacce har yanzu take tsaye take magana a kan zata kashe Aziza. Ɗora zaren da Inno Fandi ta bata ta yi a damtsen hannunta sannan ta juya baya ta rintse ido nan fatar jikinta ya hau sab'ulewa alama ce na zata koma macijiya, nan ta zama wata katuwar macijiya🐍fiye da yadda take zama a da, fara sol sai kyalli take yi, Azima dake ta zuba tin dazu bata san abunda ke faruwa a bayanta ba, sai bayan da ta gama maganarta na karshe da fadin "Sai fa hakuri! Amma yau za ki mutu! Ni haka nake! Muguwa ce ni! Ban san sani ba! Ban san sabo ba!" tana gama faɗi ta juyo dan cakawa Aziza wuka nan ta ga babu Aziza, ɗaga kan da zata yi ta hangi kanta a can sama, Aziza ta zama katuwar macijiya mai cike da tsoro da firgici, da mugun tsoro Azima ta ja da baya tana fadin "Ya haka?" bata ankare ba ta ji anyi sama da ita an yi kasa da ita, kafin ta girgije ta ji an dauketa ana zagaye iska da ita, sai da aka wujijjigata sosai sannan aka yi wulli da ita, faɗuwa ta yi ta bugu. Buɗe baki Aziza tayi a tana macijiyar🐍ta hau yiwa Azima ruwan macizai🐍 su na fita suna saren Azima, sai da ta cikata da macizai sannan ta koma mutum tana tsaye tana kallon Azima wanda macizai ke sara, Azima ta kasa tabuka komai, da taji jiki taji tabbas zata iya mutuwa ita kuwa ba zata yarda ta mutu ba tare da ta dauki fansa ba yasa ta ce "DAN ALLAH AZIZA! KI KWASHE MACIZANKI! ZAN GAYA MIKI WANDA ZAN KASHE!" jin haka yasa Aziza ware hannu ta janyo macizan sannan ta b'acer dasu, tana janyesu Azima ta zube kasa a galabaice, Aziza ta ce "Gaya min! Wa za ki kashe da zaren saƙar dana?" " *BAFFA*" Azima ta faɗa cikin muryan galabaita, saurin ja da baya Aziza ta yi ta ce "Baffa?" Da jan ido a tsawance Azima ta ɗago idonta ta watsasu a cikin na Aziza ta ce "Eh Baffa zan kashe da zaren saƙar dana! Ban san wani irin kalar baiwa Baffa yake da shi ba, amma abunda na sani shine duk wata hanyar guba da nabi dan son kashesa duk basu aiki! Tun ina gwada kashesa a boye har na fara bayyanawa kika sani! Bincikena ya nuna min cewa zaren saƙar dana ne zai kashe Baffa wanda da shine ya......." maganar da Azima bata karasa ba kenan Aziza ta wanketa da mari, za ta kara Azima ta riƙe hannun Aziza ta ce "Karki kuskura idan ba haka ba a yau din nan wannan al'karya zata koma toka, kodayaushe kina nuna min karfin dafi da baiwar da kike da shi, ga taken kalmata ta karshe wanda kika sani Aziza, *IDAN KIN ISA KI DAKATAR DANI!*" miƙewa tsaye Aziza ta yi ta ce "Na yarda da maganarki Inno! Domin tsaida zubda jini! Dole ne muma sai mun wanke hannuwanmu da jini! Ke dodon mutan yankin nan ne da Baffa ko Azima? To ki sa a ranki ni nice dodonki, dakatar dake kamar na yi na gama" dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce "Muje zuwa, ai ba a buga komai a wasan ba! " ba tare da Aziza ta sake magana ba ta bar wajan, a hankali Azima ta miƙe ta b'alli gashin kanta tsili ɗaya ta hura wani hayaki a jiki sannan ta haɗiye nan inda macizan Aziza suka sareta wajan ya koma ya yi fess sannan ta dauki hanyar gida, Aziza kuwa ba gida ta yi ba, dan bata ga ta zaman gida ba,dole ne taje jejin lore dan lalata zaren sakar dana in ba haka ba kuwa Baffa da sauran jama'a zasu mutu. 🍃🍃🍃🍃 A tunzure ta zo shiga gidan, amma jin maganar da Baffa da Hajja ke yi ya sakata maqalewa a jikin zana tana sauraronsu, Hajja ke faɗin "Innu maciji kam ina da sa rai a kansa sosai, zai iya kawo mana karshen wannan matsalar da yardan Allah, tunda yana gwagwarmaya da aljanu, a goben zai zo?" "In sha Allahu! Haka suka ce zai zo a gobe, amma a gaskiya da a so samuna ne da bamu nemi taimakon yankin ja'i ba sam wollah, karki so ki ga izgilancin da suka mana a cikin wasikarsu kafin su amince da bukatar yankin nan" Ajiyar zuciya Hajja ta sauke ta ce "Koma miye tunda sun amince shikenan Allah ya shiga mana gaba! Idan kuma tsohon gaba ne yanzu kuma ta kau ai, tunda yankin kwana ta duƙa musu" girgiza kai Baffa ya yi ya ce "Jumala! Ba shi bane abunda nake hange! Idan wani abu ya samu Innu Maciji ko da ƙwarzani ne to fa! Sabon yaƙin da ba ayi ba kwanakin baya shi za ayi yanzu! Duk inda ake neman rashin hakuri masu jiran sammacin yaƙi idan aka samu yankin ja'i to an kai karshen magana, mutanen da jira suke a tab'osu ko kaɗan ne su yiwa mutane cin mutunci, meyasa gabanmu dasu yafi tsanani? Ina sabida yankin kwana taƙi daukar cin mutunci ne, amma al'ummar yankina sun kasa fahimtar abunda nake gaya musu, idonsu ya rufe da neman mafitar wannan bala'i shiyasa duk shawaran da zan basu, ba su gani inda a karshe ma laifi ne suke gani, suna ganin kamar zan iya wani abu a kai amma naki, duka so suke naje na haƙo kayana da na binne wanda haƙo wannan kaya sabon bala'i ne da barazana wa rayuwar su Azima da Aziza har ma dake! Balle kuma ace ni da ake neman fansa a kaina! Su tsaya su saurareni na gaya musu yadda za ayi amma sam!" Baffa ya faɗa yana riƙe kansa dake sara masa, shuru Hajja ta yi ta ce "Komai ya yi zafi maganinsa Allah Baffan yan biyu, mu dage da addua Allah na nan!" "Haka ne Jumala, Allah ya shige mana gaba" "Amin" Hajja ta fada tana miƙewa da fadin "Ko inasu Azima da Aziza suke? Kai wannan yara yanzu haka suna can rafin jimulo" Baffa dai bai kuma cewa uffan ba. Wani murmushi Azima ta yi da saurin komawa baya, ta ce "Kai ashe dai ina da babbar mugun ƙulli! Gobe Innu Maciji zai zo, ayya Innu Maciji ashe kwana ya kare! Ajali ya yi kiranka gobe, wayyo dadi zan so na ci gaba da ganin tashin hankalin wannan yanki, hakika Innu Maciji gobe asalin Macijiya Azima zata kasheka! Wayyo farin ciki! Zanyi tsumayen jiran zuwanka yankin kwana!" ta faɗi tana dariya tare da gyara mayafinta, sannan ta shiga gidan da sallama wanda rabonta da sallama harta manta,tana yin sallamar taji har wani ɗaci wuyarta ke mata, da mamaki Hajja ta amsa ita da Baffa dake zaune, kusa da Baffa Azima ta zauna tana murmushi sai kuma ta koma tayi fuskar tausayi tana kallon Baffa ta ce "Baffa kayi hakuri da abunda nayi dazu ban san nayi ba, amma Aziza ta fahimtar dani, ka yafe min Baffa ba zan sake ba, ban san lokacin da nake yi ba dan Allah Baffa👏🏻" shuru Baffa ya yi yana kallon Azima a ransa ya ce "Kenan da gaskiyar Aziza, Azima aljanu gareta?" a fili kuma Baffa ya ce "Shikenan ya wuce Azima,Allah ya miki albarka, amma ki gaya mini gaskiya ina kika samu zaren saƙar dana?" Turo baki ta yi ta ce "Baffa ganinsa kawai nayi a hannuna! Yanzu kuma ya b'ace, ban gansa ba" Baffa ya sauke ajiyar zuciya har yana hamdala, Azima ta miƙe taje ta rungume Hajja wacce rabon da ta rab'eta ba zata iya tunawa ba ta ce "Hajja ke ma kiyi hakuri" murmushi Hajja ta yi har kwalla na taruwa a idonta tana shafa fuskar Azima, yatsine fuska Azima ta yi a ranta tana kallon Hajja ta ce "Ni dai bana jin shaukin komai a tare daku, ko da ba zan ji a kan Baffa ba a matsayinki ta mahaifiyata ya kamata ace naji shaukin uwa da 'yarta, amma bana ji saboda ni ba mutum ba ce! muguwar macijiya ce, shiyasa ma babu amfanin na dinga rab'anku, abunda nake so shine....." maganarta ce ya tsaya jin Hajja ta jijjigata tana mata magana, dan tun dazu Hajja ke mata magana amma hankalinta ya yi nisa da tunani "Na'am Hajja me kika ce?" "Tunanin me kike yi Azima?" " kawai Hajja babu komai mai kika ce?" "Ina Aziza?" tsaki Azima ta yi a boye da tana shirin tace bata sani din ba, sai kuma ta tuno da abunda take son yi ta ce "Na barota a rafi, Hajja bari na tayaki aikin gida yau" tana gama faɗi ta hau gyara kara a murhu,Hajja har can kasar zuciyarta take jin farin ciki, Baffa ya miƙe yana fadin "Ba ri naje na gaida Inna Wuro (matar Arɗo) kwana biyu ma tace ba kuje kun gaisheta ba, wai dama Aziza ce yar albarka yar dakinta, ke kam ma Azima ko meyasa jininku bai zo daya ba oho!" "Ai ni babu wanda jinina ya zo daya da na shi!" Azima ta faɗa tana murmushin gefen baki mai ciki da ma'anoni, Hajja ta ce "Kinyi magana ne?" "A'a Hajja ban ce komai ba, bari naje na ɗibo ruwa" ta faɗa tare da daukar tulu ta yi waje. 🍃🍃🍃 Tsaye take a wani jeji suna magana da Inno Fandi, Inno Fandi ta ce "Aziza jejin lore ba kamar sauran jejin yankin kwana bane! Jeji ne da bai tara komai ba fa ce sai manyan aljanu masu mugun sihiri, babu abunda babu a jejin lore,kina tunanin zaki iya zuwa?" "Inno Fandi Azima ma taje ta dawo balle ni? Ba ma Azima ba, Baffa da yake mutum ma yaje" murmushin manya Inno Fandi ta yi na yaro-yaro ne ta ce "Aziza tabbas Baffanku mutum ne amma ba kamar kowa ba" "Eh ni dai Inno Fandi ko ma miye zanje" "To shikenan Aziza, dokar tafiya jejin lore, ba a yinta da rana, sai dai ki bari da magriba ki tafi, sannan ki tabbata kafin garin Allah ya waye kin baro jejin! Za ki ta gane-ganen abubuwa amma karki tsorata, dan tsoronki barazana ce ga rayuwarki!" "To amma Inno Fandi ina ga hakan ai babu amfani tunda ni ba mutum ba ce macijiya ce" sake murmushi Inno Fandi ta yi ta ce "Sanin kasancewarki ba mutum ba shiyasa nake gaya miki hakan, da ace mutum dan adam ne da ya kama hanyar sunansa gawa! Tun kafin ma ya kai ga shiga" Aziza ta jinjina kai, nan Inno Fandi ta gama gaya mata matakin da zata bi taje jejin ta dawo, godiya sosai Aziza ta mata daga nan Inno Fandi ta b'ace, Aziza ta kamo hanyar gida, tana cikin tafiya har ta kusa isa gida ta haɗu da wasu yan matan yankinsu wanda za a kamasu nan da sati daya wato amare kenan, wanda dukkansu babu wacce ta haura sama da shekara shaɗaya, su hudu suka sha gaban Aziza, dayar mai suna Lantai ta ce "Ke wacece Azima ce ko Aziza!?" Aziza ta ƙara gyara lullubinta tana rufe gefen idonta da gashinta da ya sauko mata har kirji ta kara dukar da kanta kasa ta ce "AZIZA" wata mai suna Huwe ta ce "Yau kwayar idonki muke son gani, da asalin fuskarki!" gaban Aziza ne ya faɗi ta ɗan dago a hankali ta ga rana ya faɗi ga shi dole taje gida ta yi shiri, dan haka ta ce "Kun ga bana son kalen rigima da jan faɗa ku barni naje gida ni ba sa'arku ba ce!" dariya suka kwashe da shi inda suka hau tureta tana ja da baya, har suna faɗin wai gandamemiya marasa farin jini sun ƙi aure, babu mai sonsu! Gajiya Aziza ta yi inda ta daka musu tsawa sai da suka dare, hannu tasa ta kwashe gashinta na gefen fuskarta farin eyes dinta na mage suka bayyana, da mugun gudu wannan ta yi gabas,daya ta yi kudu,daya arewa,daya kuma ta yi yamma, Aziza ta ce "Alhamdulillahi! Ni ku ka samu, da ace Azima ce sai dai a aurar da wasu amma ba ku ba" tana gama fadi ta wuce da sauri tana sake rufe gefen fuskarta. 🍃🍃🍃🍃 "Assalamu alaikum" Aziza ta yi sallama Hajja dake kwashe kaya ta amsa ta ce "Aziza sai yanzu? Tun dazu nake tambayar Azima tace min kina rafi, sawunta yau biyar tana ɗibo ruwa" "AZIMAR!?" Aziza ta tambaya a mamakince, Hajja ta ce "Eh wollah, yana ganki haka Aziza ba ki da lafiya ne?" "E Hajja kaina ke ciwo sosai, shiyasa ma na zabi na zauna a rafin yau, ammm Hajja ga wannan ki sha" "Inji waye?" Hajja ta tambayi Aziza "Ba kowa nina haɗa miki sabida ciwon bayan da kike fama da shi" "Ayye Aziza ai naji sauki tun wanda kika bani kwanakin can" "E duk da haka ma ki sha wannan Hajja" ba tare da Hajja ta sake magana ba tasha, tana gama sha Aziza zata yi magana taji ana shelan kiran sallar magriba, hakan ne yasa kawai ta rungume Hajja wacce taji komai na kanta ya dauke, sun ɗau lokaci a haka kafin Aziza ta saki Hajja ta yi alwala ta gabatar da sallar magriba ta jima tana addua kafin ta tashi ta canza kaya ta ɗauki abubuwan da zata dauka ta kara da wa inda Inno Fandi ta bata ta fito ta fice a gidan kafin Baffa ya dawo, tana zuwa bayan zanar gidansu ta rufe ido nan ta b'ace b'atttt!!. 🍃🍃🍃🍃 Ko da Azima ta dawo gida ita ma shiri gwabzawa ta yi da Innu Maciji,dan ta lashi takwabin kashesa!. Hajja kuwa bata tambayi inda Aziza take ba. Tun tsawon dare Azima ta zama macijiya ta sulale a hankali ta fice a gidan, bata zarce ko ina ba sai tsakanin shigowa yankin kwana da yankin ja'i. 🍃🍃🍃🍃 HAHAH NA HADA MUKU DA PG DIN JIYA DA NA YAU, MUN RABU LAFIYA🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ COMMENTS AND SHARE by Mom Ahlan, macijiya🐍😂 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *IDAN DAI BAKI BIYA KUDIN KARATUNKI YANZU BA LALLAI BANE IDAN NA GAMA KI SAMU CMPLT A #100NAIRA BA, ZA KI SAMU NE A #300 DAN HAKA YAR UWA WANNAN BONUS DIN KAR TA WUCE KI.* *REMAIND 1 FREE..* 🅿️==2️⃣1️⃣↪️2️⃣2️⃣ "Garkuwa suna can, ya ƙi tahowa wai sai ya musu bayani, da wuya yanzu idan su Garkuwa su na numfashi" Liman ya karasa maganarsa yana zama sharaf a ƙasa yana fifita da hularsa irin na fulanin nan wanda ake saƙa shi, cirko-cirko suka tsaya, yayinda Mai Unguwa Ori ya ce "Mu ba mu kashe Innu Maciji da gangan ba,akasari ba bamu ne muka kashesa ba! Me yasa zasu kashe mana garkuwa!?" cikin fusata wanda yake nuni da damuwa da ɗimauta Baffa ya ce "Laifin su waye!? Na ce laifin su waye!? Ga irin abunda nake gaya muku amma kun kasa fahimta, ai shikenan sai mu jira har ta Allah ta kasance damu! Ga bala'in kisan macizai! Ga bala'in yaƙi dame zamu ji ne kam! Ya Rabbi gamu gareka! Babu yadda banyi daku karku aikawa da yankin ja'i wasika ba, yanzu mai hakan ta haifar!? Da ace kun saurareni duk ba za a kai ga haka ba, amma mu da shike fulani Allah ya yi mu da taurin kai bamu jin shawari, wlh da kun bi abunda zan shinfiɗa da mun magance matsalarmu da ikon Allah sabida ina da imanin za a....." "Ka rufe mana baki Magaji!!Ya isheka haka!!" Jauro ya katse Baffa, Jauro shine mai magani na yankin kwana "A kan me zamu bi abunda zaka gindaya!? Kana da halin da zaka taimakemu amma kayi hakan ne? Duk wani yaƙin da zai kunno kai kasa a ranka har da sa hannnunka a ciki! Da ace ka taimaki yankinka har za a yi aike a wani yanki mai suna yankin ja'i ne! Dan haka babu abunda zaka gayawa mutanen yankin nan! Sai ka bar mu mutu! Idan an kashe Garkuwa da yan faɗa biyu sai mu ma mu jira mu ga mai zai yi ajalinmu,Macizai ne ko kuma jama'ar ja'i!" "Haba Jauro miye haka ne kake yi! Bai kamata ka faɗawa Magaji wannan maganar ba! Kwata-kwata ma yanzu ba lokacin musayar yawu bane!" cewar Arɗo, Jauro ya ce "A kan me ba zan faɗa masa ba! Karya nayi ne! Na ce karya nayi ne!!?" sarki Chubaɗo ya ce "A gaskiya ban san me zance a wannan lamari ba, amma zan iya bin maganar Jauro! Magana ta domin Allah wannan yanki ya kafu tun kakanni, wanda ya taimaka ya kara tsayawa ma wannan yanki kai ne Magaji! Tun ban san da cewa zan zo na zama sarkin fulanin kwana ba, ni dai roƙonka zanyi da girman Allah ka taimakemu Magaji! Muji da masifa ma daya ta ishemu ba sai an ɗaɗo mana da na yaƙi ba" Sarki Chubaɗo ya faɗa yana haɗa hannunsa alaman roƙo,Baffa ya jinjina kai tare da faɗin "Naji! Kuma na yarda! Abunda aka binne shekaru ashirin shine zanje haƙosa yau! Shin zaku iya fama da masifu biyar!? E ko a'a? A da masifa daya ce, sannan ku ka kuma janyo mana wata da hannunku, yanzu kuma kun bada dama aje a kara haƙo wata shin zaku iya tayani tareta? Nayi imani a yanzu yankin kwana babu mai iya tayani yaƙi da aljanu babu shi!" " *AZIZA!* Baffa ya ji an raɗa masa a kunne, da sauri ya dago yana waige amma bai ga kowa ba, "Aziza kuma?" Baffa ya tambayi kansa a zuciyarsa yana shirin faɗawa kogin tunani ya tsinkayo muryan Arɗo da Baffa Mandi suna fadin "Gaskiya ba zamu yarda a haƙo ba,ta bakinka Magaji babu wanda zan iya wannan yaƙin kawai a bar maganar mu sake neman taimako ku kuma ka faɗa mana hanyar da zamu bi" Sarki Chubaɗo ya ce "E hakane magaji, ka gaya mana wace hanya ce zamu bi?" "Inaaaaa! Sam-sam ba zai yu ace Magaji bane zai bamu mafita sam ban lamunta ba! Ni fa wlh ina zargin Magaji, duk yadda aka yi yaransa ne *MACIZAI!*" Jauro ya faɗa yana huci, saurin dagowa Baffa ya yi yana kallon Jauro, dama ya jima da sanin jauro baya sonsa yana baƙin ciki da shi, ya jima yana masa ƙulli amma kawai bai san yadda zai yi da Baffa bane, shuru Baffa ya yi yana kallon Jauro, yayinda Arɗo ya katse Jauro da fadin "Wai lafiyarka kuwa Jauro? Ko dai akwai wata a kasa ne tsakaninka da Magaji?" "Miye haɗi na da shi?" Jauro ya faɗa yana yiwa Baffa kallon ƙasƙanci, "Kawai dai gaskiya abunda na sani ne,meyasa ya ƙi aurar dasu yara duk sun gandare a yanki babu mai rab'arsu, shekarunsu goma sha biyar oh Allah ni Jauro, yara na tafiya jiki na lankwasa ace mutane ne! Taya hakan zata kasance!? Kullum fuskarsu a rufe sabida babu ido mai kyau, sannan duk taron da za ayi na magani basu zuwa, dan Allah a cikinku nan ku gaya min suwaye suka yarda da yaran Magaji mutane ne?" nan wa inda Jauro ya haɗa baki dasu suka amsa da basu yarda da Azima da Aziza ba, sannan Jauro ya matso kusa da Baffa wanda ya koma tamƙar wanda aka dasa bishiya ya ce "Zan fara sakawa yaranka ido fiye da yadda na saka musu a baya, idan har na gano cewa su ɗin ba mutane bane na maka alkawari da hannuna zan kashesu a gabanka!!" rass!rass!rasss! Gaban Baffa ya bada yana kallon Jauro, shi kuwa Jauro yana gama faɗi ya juya zai bar wajan ya tsinkayi muryar Baffa na faɗin "Allah ya baka sa'a,ni nan zan baka takwabin da zaka kashe yarana a gabana!" ko uhum Jauro bai ce ba ya bar wajan, Baffa Mandi ya ce "Wai miye haka ne kam?" murmushin takaici Baffa ya yi ya ce "Ba komai! Ni na jawowa kaina ai!" shi ma ya juya zai bar wajan sai gasu Garkuwa a muraran! Da sauri aka tarbesu kowa yana furta kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Da sauri aka sauko dasu daga dokin yayinda Garkuwa ana sauko da shi yana sumewa, ba shiri aka ce a kai sa wajan Jauro ya duba sa. @@@@@@@ A ranar yankin kwana babu wanda ya rintsa, Aziza kuwa ta yi neman Azima ta rasa hakika Aziza idan tace akwai natsuwa da sauran hankali a tare da ita ta yi karya. Da washe gari Aziza na idar da sallar asuba ta fice, jejin kwana ta nufa, tana zuwa ta kirawo Inno Fandi, Inno Fandi na zuwa Aziza tasa kuka, girgiza kai Inno Fandi ta yi ta ce "Aziza ba kuka bane mafita, abu mai mahimmanci shine a yanzu ki maido da natsuwarki, rashin natsuwarki shi ya hanaki ganin Azima, zaki iya ganinta amma sai kin samu natsuwa, sannan zaki iya zuwa dan ki gayawa Baffanku gaskiyar su waye ku, dan ba zaku ci gaba da boyewa ba Azima na kashe mutane,idan ba haka ba a duban da nayi kowa na yankin nan ya kusan mutuwa! Abunda Magaji baya so dole karshe shi zai aikata, wato haƙo baiwarsa da ya binne shekaru ashirin, sannan duk yaƙin da zata kama da wuta kece garkuwar mahaifinki Aziza,ki koma gida Magaji ya ba ki asalin tahirin rayuwarsa na abunda ya faru shekara ashirin amma har sai kin gaya masa gaskiyar su waye ku!" Inno Fandi na gama faɗi ta b'ace, Aziza kuka takeyi kamar ranta zai fita,taya zata fara faɗawa Iyayenta su ba mutane bane Macizai ne? Taya!? Ya Hajja da Baffa zasuji? Idan suka gano cewa duk kisan da akayin nan Azima ta yi su?" kuka sosai ta yi ta godewa Allah fuskarta ya yi jajur idonta ya ƙara komawa fari sol, tashi tayi tana ajiyar zuciya tare da tattaro natsuwarta kamar yadda Inno Fandi ta gaya mata sai ta samu natsuwa kafin ta iya sanin ina Azima in ba haka ba yau ma kisan da zatayi sai Allah ne yasan adadi, a hankali ta rintse ido tana karanto adduar samun natsuwa ta hanyar tasbihi ga Ubangijin talikai, sai da taji zuciyarta ya samu natsuwa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta rintse ido nan ta ganota kwance a jejin hayi, da sauri ta buɗe idon tana me daukar hanyar jejin hayi ba tare da bata lokaci ba gwanda taje suyi na yau. @@@@ Maga Isar da Sakon yankin kwana ne yake karantawa fada sakon yankin ja'i kamar haka " _DAMA MUNYI MAMAKI ACE KUNA DA MUTUM A YANKINKU KAMAR MAGAJI BAWA AMMA ACE KUN ZO YANKINMU NEMAN TAIMAKO DA INNU MACIJI! HAKIKA MUMA MUN ZAMA SHASHASHU DA MUKA YARDA DA KUDIRINKU! BAYAN MUN SAN DA CEWA KU ƊIN ABOKAN GABANMU NE NA TUN TULI-TULI! A KODAYAUSHE KU YANKIN KWANA KUNA SO KU DINGA NUNAWA KUN FI SAURAN YANKUNA! TO MUNA SO KU SANI KU KARA SANI, LOKACI YA YI DA ZAMU MAIDA YANKIN KWANA BABBAR MAƘABARTA! DAN KUWA MUNYI SAƘO YANKIN JIMO MUN ZUGASU NA JARMAN MACIZAI DA KU KA KASHE! TUN KAFIN KUYI AIKE YANKIN TUDU MUN RIGAKU DAN BA ZAMU YARDA DA KASHE MANA INNU MACIJI DA KU KA YI BA, MUN GAYAWA YANKIN TUDU KUN KASHE MANA INNU MACIJI SANNAN BA MAMAKI KU MUSU AIKE A BAKU IRO MAGANIN MACIZAI TO MUN TOSHE WANNAN HANYAR DAN MUN TONOWA SARKIN TUDU TSOHON RAUNIN DA YANKINKU SUKAYI MASA TA HANYAR KASHE MASA GUDAN JININSA, DAN HAKA KU FARA SHIRYAWA TARBAN YAƘI NA YANKUNA GUDA UKU, YANKIN JA'I: YANKIN JIMO: YANKIN TUDU: SAKO DAGA YANKIN FULANIN JA'I._" Maga Isar da sako yana gama karantawa aka hau kallon-kallo, Mai Unguwa Ori ya ce "Yaƙi da yanki uku a kan yankin daya?" "Kuma lokaci daya?" cewar Sarki Chubaɗo,Arɗo ya ce "Mu dai mun san bamu aikata komai ba, mu sa a ranmu wannan wata jarabawa ce daga Allah, kuma yana sane damu, shi zai kawo mana dauki, kar mu ce zamu yi wani shirin yaƙi, mu zubawa sarautar Allah ido" kowa ya amsa da haka ne sannan kowa ya watse cike da alhini. 🐍🐍🐍🐍🐍 Azima na kwance a kan bishiya rabinta mutum rabinta macijiya, jelarta na lilo a ta saman rashen bishiya fuskarta a haɗe har gefe da gefe ya yi jaa! Idonta kuwa ya kara rikiɗewa ya rine ya koma blue sosai harta fari babu, Aziza tana zuwa jejin hayi jelar Azima ta fara hangowa, saurin karasowa ta yi ta ce "Azimaa!?" jin muryar Aziza yasa Azima sulalowa tare da komawa mutum, a fusace tayo kan Aziza tana isowa gabanta kafin ta yi mata magana Aziza ta yi saurin dafe goshin Azima nan take taji abu ya shige mata kai sai da ta girgiza. Ganin yadda Azima ta tsaya yasa Aziza faɗin "Azima lokaci ya yi da zaki saduda! Ki dakata haka" murmushi Azima ta yi tana yiwa Aziza kallon baki da hankali "Ni kike cewa na saduda? To naji zan saduda, amma bayan na kashe Baffa!" ta faɗa tana cije baki, Aziza ta ce "Wai ke wace irin dabbace Azima?" murmushi Azima ta kuma yi ta ce "MACIJIYA! ina kina tambaya ne wace irin dabba ce ni? To ni Macijiya ce kamar ke amma bambancin shine ni muguwa ce ke akasin haka! Har yanzu ban huce da abunda kika min ba, ki bar ganin kinsa jikina ya yi sanyi kin kafar min da dafina! Ba shi zai dakatar dani ba, na iya yau ne kawai, amma gobe zan haɗa da kisan da banyi yau ba!" Aziza ta jinjina kai ta ce "Kin sha fadamin idan na isa na dakatar dake! Ni kuma na sha fada miki cewa bazan bar hakan ta faru ba, shine zan kara nanata miki, ba zan bar hakan ta faru ba! Dan haka muje gida, kafin Hajja ta titsiyemu da tambaya!" a hankali Azima ta juya tana dafe kirjinta dan abunda Aziza ta tura mata ya shigeta sosai, a hankali suka jera suna tafiya dan Azima na da bukatar ta kwanta dan jikinta da ya mutu, sabida abunda Aziza ta tura mata a hankali yake bin jikinta yana kashe mata shi, dan makarin dafi ta tura mata. Da haka suka iso kofar gida Aziza ce ta fara shigewa da sallama ta samu Baffa da Hajja suna zaune yana labarta mata wasikar yankin ja'i wanda kaff abunda Baffa ya faɗi a kunnen Azima, a tana rarrafawa da kyar amma wani dadi ne ya mamaye zuciyarta nan ta hau murmushi tare da fadin "Yankuna uku zasu yaƙe yankin kwana? Wayyooo Dadi!bari na ɗan daga kafa dan ganin yadda za a shafe yankin kwana idan ya so na kashe Magaji Bawa daga baya!" ta faɗa gami da sallama ta shiga gidan, Hajja ta ce "Azima ina kika je ne? Ni anya jiya na ganki kuwa? Yana ganki haka kamar wacce bata da lafiya?" "Kin ganni mana Hajja! Ko dai wannan bala'in ne yasa kanku ke da Baffa ya kama da wuta!? Sannan da kika ganni haka ba wata matsala bace babba kaina ke ciwo, da nayi bacci na farka zan dawo dai-dai" Azima ta fada tana kallon Baffa, da ido Baffa yake bin Azima yayinda take yi masa wani irin kallo, Hajja ta ce "Allah ya kyauta, jeki kwanta" Hajja ta shige bukka, Azima ta juya kenan zata shiga bukka idon Baffa na kanta dan ya kasa kauda ido a kanta, wuyarta taji ya mata ƙaiƙaiyi tasa hannu ta sosa, tana sosawa sai ga sab'ar maciji ya fadi carab a idon Baffa, wani wawan firgita Baffa ya yi,ya tashi jikinsa na rawa ya karasa ya dauki sab'ar yana kalla,saurin girgiza kai ya yi yana fadin "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! Me hakan ke nufi?" jikin Baffa ya yi mugun sanyi dan ya tsorata ba kadan ba, bukkarsa ya shige yana jeka ka dawo dauke da fatar a hannunsa, cikin rawar murya ya ce "me ya kamata nayi? Dole na haɗa maganin ganowa idanuna, amma kafin na samu furen surfa sai naje jejin gangare, kuma kafin na dawo sai na samu kwana biyu sabida dogon tafiya ne ban ci ta zama ba, In sha Allahu zan tafi gobe" yana gami fadi ya fito ya shiga bukkar Hajja ya gaya mata gobe da safe zai tafi jejin gangare Hajja ta ce "Me zaka je yi?" "Akwai maganin da nake son haɗawa ne, kuma furen da ganyen dole sai naje jejin gangare" "To Baffa yan biyu Allah ya kaimu lafiya" Baffa ya amsa da amin ya fice, bai zarce ko ina ba sai wajan Ardo bai boye masa komai ba kasancewarsa mahaifinsa ya gaya masa komai, sosai hankalin Arɗo ya tashi ya kallesa ya ce "Magaji bana so ka gaya ma kowa wannan batun ka ji ko? Har sai ka tabbatar" Baffa ya gya ɗa kai cike da damuwa, nan suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin. 🐍🍃🐍🍃🐍🍃 COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *STILL FREE..* 🅿️==1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣ Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba, riƙe kai Aziza ta yi tare da furta "YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala'i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama'ar mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!" Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta iske wata budurwa kwance bakinta sai jini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota, tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu tana furta "AZIIIMAAAAAAA!!!?" da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue. Duk inda Aziza take tunanin zata ga Azima amma da ta je sai dai ta iske gawa, hakiƙa fadin yadda hankalin Aziza ya tashi b'ata lokaci ne, ga shi ta rasa yadda zata yi, bata kara shiga ruɗu ba sai da ta yi gamo da gawar mutum takwas wanda Azima ta kashe, daga karshe Aziza ta koma tayi zaman yan bori. 🍃🍃🍃🍃 *YANKIN JA'I.* a lokacin da garkuwan fulanin yakin kwana suka isa yankin ja'i da gawar Innu Maciji hakika sun ga tashin hankali, sun ga masifa da bala'i a wajan jama'ar yankin ja'i, ko kaɗan sarkin fulanin yankin ja'i wato Jawo da kuma mai unguwa Sodangi da sauran duk wanda yake yankin ja'i basu tsaya sun saurari su Garkuwan fulanin kwana ba, suna isa da gawar fadar sarki Jawo nan yankin ya ɗauka daga tafiyar Innu Maciji yau yankin kwana sun kashesa, nan jama'ar yankin ja'i suka janyo wuƙaƙe da adduna da sanda kokara,suka yi kan su garkuwan fulanin kwana tare da fadin su ma ba za a barsu a raye ba, Galadima da Liman suka ce yadda suka tunzura gwanda kawai su gudu, garkuwan fulanin kwana ya ce bai kamata su gudu ba tare da sun musu bayanin abunda ya faru ba" Galadiman fulanin kwana ya ce "Baka da hankali ne garkuwa? Ka ga yadda suka haukace suna ihu ka ce mu tsaya musu bayani taya zasu sauraremu? Ka zo kawai mu gudu dan ceton ranmu daga baya idan suka yi sanyi sai mu dawo! Amma kaga yanzu suna abu kamar wa inda mahaukacin zaki ya cije su" Garkuwa ya ce "A gaskiya ba zamu tafi ba tare da munyi musu bayani ba,tunda duk abunda ya faru mu muka ja wa kanmu! Da ace mun bi shawaran Magaji da ba haka ba" "Amma dai garkuwa kasan rashin hakuri irin na yankin ja'i da haukarsu ko? Ka zo mu gudu idan ba haka ba zasu iya kashe m...." maganar da Liman bai karasa ba kenan yaji saukar dutse a goshinsa,nan ya riƙe goshin yana faɗin "Ya Rabbi!" kafin su Garkuwa su dago nan suka ji ihu, inda gaba daya ahalin yankin ja'i mata da mazansu kowa ka gani da makami nan suka yo rututu suna shirin kai wa su Garkuwa farmaki,nan suka hau musu ruwan manyan duwatsu kafin su isosu,ganin haka yasa Galadiman fulanin kwana da Limamin fulanin kwana suka kwasa a guje dan tseratar da ransu, sauran mutum biyar na fada mutum uku su ma suka arce da gudu aka bar Garkuwan fulanin kwana da mutum biyu na fada su uku kenan, kafin Garkuwan fulani ya yi kokarin faɗin wani abu tuni, an rufesu da duka da sanda, yayinda ƙanin Innu Maciji yasa adda ya sare daya daga cikin ɗan fada a wuya yana sare san nan ko minti daya bai yi ba yace ga garinku, ganin haka yasa garkuwan fulanin kwana yace shi da dayan ɗan fada su gudu, da kyar suka kwace suka hau dokinsu ba shiri suka sab'i hanya jikinsu jina-jina da jini, dan garkuwa ma kam an saresa a hannu. Har mutanen yankin ja'i zasu bi su garkuwa, Sarki Jawo ya ce su dawo ai sun b'allowa kansu yaƙin da basu san wanda zai tare musu ba, za ayi wasika a tura musu su shirya tarban yaƙi,kuma suna da yaƙinin zasuyi nasara ta hanyar shafe al'karyan kwana tunda Magaji Bawa ya yi murabus!. @@@@@@ *YANKIN KWANA.* haqiqa yau yankin kwana tana cikin ruɗu da ruɗani,yayinda suka jera gawawwaki har na mutum sha ɗaya wanda saren maciji ne a jikinsu. Yau da safe mutum biyu sun sha dafin maciji sun mutu, Innu maciji saran maciji ya mutu,yanzu kuma ga gawawwakin mutum sha daya, tsananin tashin hankali yasa suka kasa yiwa gawawwakin jana'iza ga magriba ya gabato, ganin haka yasa sarki Chubaɗo bada umarnin a musu sutura a binnesu kar su yi kwanan keso, da kyar suka yi musu jana'iza suka binnesu, bayan sun fito daga maƙabarta sai ga isowarsu Galadiman kwana shi da Liman a fujajan, da sauri mutanen yankin kwana suka tarbesu suna tambayarsu me ya faru? Baffa ya kalli goshin Galadima dake zubar da jini an fasa masa goshi,Baffa ya ce "Daga ganin goshin Galadima ba sai an tambaya ba! Mun taro yaƙi ko? Ina su Garkuwa!?" 🍃🍃🍃🍃 😔😔😔 1readmore For ur sake yar gidan Anty Zahra,Slimzy☹️ [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *YAR UWA ZO BIYA KUDIN KARATUNKI DAN JIN YADDA ZATA KAYA A CIKIN BOOK DIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, BIYA DARINKI KACAL YANZU,IDAN KUMA NA KAMMALA CMPLT DARI UKU ZAKI SAMESA.* *LAST FREE..* 🅿️==2️⃣3️⃣↪️2️⃣4️⃣ Da washe gari asubanci Baffa ya yi ya bar yankin kwana dan bai ga ta zama ba, ko da Aziza ta farka ita ce kawai ta tambayi ina Baffa yake nan Hajja ke gaya mata ya tafi jejin gangare dan samo wasu ganyen magani, Aziza ta ce "Allah ya dawo min da Baffana lafiya" Hajja ta amsa da amin. Ita kuwa Azima tunda ta fara bacci ba ita da farkawa ba sai gefen sallar la'asar, ko da ta farka Aziza na shirin ɗora mata hannu a goshi ta yi saurin rike hannun Aziza ta ce "Ba bukata Aziza, yau ina cikin farin ciki babu wanda zan kashe amma za a mutu dayawa gobe! A'a ba wai ina nufin ta hannuna ba fa,dan naga kina min wani kallo! Wallahi babu wanda zan kashe! Amma gobe akwai zubda jini a yankin kwana!" tana gama fadi ta tashi ta fito ta samu Hajja a tsakar gida, Hajja ta ce "Azima wannan baccin naki ya yi yawa, haba dan Allah mutum ya ta faman bacci ba sallah ba salati ko kina fashin sallah ne?" Yatsine fuska Azima ta yi kafin ta ce "Ni fa Hajja wannan fashin sallan da kika fadi me ma yake da suna? Al'ada ko? To ni banayi! Kuma ban taba yi ba! Sallah gabadayanta ne bana yi,kuma ma Hajja sadda Aziza ke zuwa islamiyyar Malam Saini ni kin taba gani naje ne? Har Aziza ta yi sauko ni ban taba zuwa Islamiyyar Malam Saini ba,ko kuma kin taba gani da watan ramadan ina azumi? Ki kyaleni da maganar wani abu wai shi sallah!" tana gama fadi ta fice, Aziza na tsaye a bukka tana kallon Azima, bayan Azima ta fita Hajja ta kalli Aziza hankali tashe ta ce "Aziza meke damun yar uwarki!?" murmushin tausayin Hajja Aziza ta yi ta matso kusa da Hajja ta kama hannunta ta ce "Kun kusa ku sani Hajja nan ba da jimawa ba, dan bazan iya jure ganin hawayenki na zuba a kanmu ba, zan gaya miki gaskiya da zaran Baffa ya dawo ko da kuwa za a kashemu!" Hajja ta bude baki za ta yi magana da sauri Aziza ta ce "Dan Allah Hajja karki ce komai, Azima bata sallah bata salati bata Azumi duk wani aikin ibada bata yi,na gaji da miki karya Hajja, bazan iya jure miki karya ba!" tana gama fadi ta fice da gudu da kuka. Aka bar Hajja da kakkarwar jiki. @@@@@ Da yamma sai ga wasika daga yankuna uku izuwa yankin kwana, zasu kawo musu farmaki gobe da safe, hakika wannan sako ya hautsine hankalin jama'ar kwana inda mata da dama har ma da mazan wasu suka fara kuka, sarki Chubaɗo da mai unguwa ori suka ce ga shi Magaji baya nan, kuma babu halin yi masa saƙo har sai ya dawo, saukinta ma Garkuwa ya ɗan samu lafiya, kafin kace me Sarki Chubaɗo ya bada umarnin ayi shela a yankin kwana gabadayanta za a kawo farmakin yaƙi gobe kuma yankuna uku,dan haka kowa ya kasance cikin shiri amma bana tarban yaƙi ba. @@@@@@ Hajja da Aziza sun kasa zaune sun kasa tsaye sabida tashin hankali sai jeka ka dawo suke yi a tsakar gida amma Azima na zaune hankali kwance tana fizgar dogon gashinta, Aziza ce ta kallenta ta ga babu alamun damuwa a tattare da ita,cikin haushi da tsanar Azima da ya fara ɗarsuwa a zuciyarta ta ce "Wai ke Azima wace irin dabba ce ke ana maganar kawo farmakin yaƙi amma kina zaune kina tsifar kai?" "Macijiya!" Azima ta faɗa ba tare da ta ɗago ta kalli Aziza ba, Hajja ta juyo a firgice ta ce "Ma mai kika ce Azima! ?" tana shirin kara nanatawa Aziza tayi saurin faɗin "Mahaukaciya kawai!" "Ga ki kuwa babbar mahaukaciya!" Azima ta faɗa tana dagowa a fusace. "Dan Allah fadan ya isa haka!" Hajja ta katsesu, "Kuyi ta addua kawai Allah ya bamu mafita yafi wannan fadar naku" ko uhum basu kuma cewa ba. 🍃🍃🍃🍃 Da washe gari kamar yadda sako ya iskesu haka kuwa ta kasance inda yankin ja'i da yankin jimo da yankin tudu sukayi cincirindo sun zo yaƙar yankin kwana, amma abun mamaki babu wani daga yankin kwana da ya dauki makami, abun ya basu mamaki, Arɗo shine wanda ya fito ya fara magana kasancewarsa Babba, tsohon bafulatani mai dattako "Mu ba zamuyi yaƙi daku ba, idan har kuna so duk ku sa takwabi ku kashemu! Har ga Allah munyi imani wannan ita ce kaddararmu! Bamu kashe Innu Maciji ba, a ranar da aka kashe Innu muma munyi rashin mutane a yankin nan har mutum sha huɗu, haka ma jarman macizai, sannan sarkin fulanin tudu bamu aikata muku komai ba kawai neman fitina kukeyi,idan kuma yaronka da aka kashe a yankin nan ne laifi ya aikata aka masa hukunci, na rantse da wanda ya busamin numfashi idan har aka samu ɗan wani yankin kwana da laifi makamanciyar wanda ɗanka yazo yankin nan ya aikata wlh mun yarje muku ku fille kansa ku kawo mana kamar yadda mukayi, ba a barin laifi a ɗoran kasa, dan ba a san mai zai kuma aikatawa a gaba ba, mu sabida muna bin al'ada da ibada shiyasa yankinmu ta yi baƙin jini a wajan sauran yankuna, idan har maganar da nayi baku gamsu ba kuna iya shafemu a doron kasa ko kwayi farin ciki" Arɗo na gama fadi jama'ar kwana suka miƙa wuya,ganin haka yasa yankin jimo jikinsu yayi sanyi suka ce ba zasuyi yaƙi da yankin kwana ba,nan take suka juya, yankin tudu da yankin ja'i kuwa sunce suna nan, sai sun shafe yankin kwana. @@@@ Gudu Baffa ke yi a dokinsa dan haka yake ji a jikinsa mahaifarsa babu lafiya. A kwana kuwa ganin yadda yankin ja'i suka fara zubar da yara da manya ta hanyar saresu da takwabi yasa garkuwan fulanin kwana cewa Sarki Chubado da Ardo "Ranka ya dade, hakika ba zamu tsaya a shafemu ba tare da mun sa hannu ba dan bamu aikata laifi ba, burin yankin ja'i shine su ga sun shafe yankin kwana, dan haka kowa ya dibo makamai mu gwabza tunda haka suke so" mai Unguwa Ori ya ce "Tabbas hakane" nan garkuwa ya bada umarnin a dauka takwabi a fara maidawa yanki biyu martani. Duk wannan tarzoma da akeyi Azima na saman bishiya tana kallo tana dariya, Aziza ganin kisan da ake yiwa mutanen yankinta ya yi yawa ne ya sa ta fadi a ranta "inaaa! Burin Baffa shine ya ga ya mutu ya bar yankinsa lafiya, dan haka dole ne na dakatar da yaƙin nan ta ko wani hanya in ba haka ba, tabbas yau babu sauro da zai rage a yankin nan" ta kalli Hajja dake tsaye tana kalman shahada dan yawancin mutane sun sadakar da zasu rayu ta ce "Hajja ina jin fitsari zanje gida na dawo" ta karasa fadi tare da juyawa,saurin kamo hannunta Hajja ta yi ta ce "Aziza bakki hankali ashe ban sani ba?kina ganin yadda ake zubar da jini tamƙar ana ɗibo ruwa a rafin jimulo ne ake watsawa kice zaki koma gida kiyi fitsari? Idan kika bincika wasu a nan har da kashi sukayi a jikinsu,dan haka Aziza yi fitsarinki kawai a jikinki, gwanda mu tsaya ta nan idan har Allah yasa aka gama da sauran kafin a iso kanmu,idan kuma Allah yasa Baffanku ya dawo a kan lokaci to, dan shiyasa nace miki mu tsaya a nan sabida ga hanyar da zai fito nan" Hajja ta faɗa tana kara riƙe hannun Aziza, girgiza kai Hajja ta yi ta ce "Hajja to ni kin riƙeni babu fa Azima a nan" da sauri Hajja ta ce "Na shiga uku! Azimaaaa!?" "Kwantar da hankalinki Hajja bari na je nayi fitsari sai na dubota mu dawo tare" "To dan Allah Aziza ki kula,ki min alkawari zaki dawo lafiya?" "Na miki alkawari Hajjata zan dawo lafiya" sai da Aziza ta faɗi haka kafin Hajja ta saketa,da gudu Aziza tayi hanyar gida dan ta shirya ta dawo ta tare yaƙin. @@@@ Haka Baffa ya shigo yankinsa ya samu gagarumin yaƙi, amma da shike baya da lokacin tsayawa gida ya wuce kai tsaye ya haɗa maganin furen surfa, sannan yaje ya kirawo Hajja a inda ya ganta sadda ya shigo, amma ita bata gansa ba, yake tambayarta ina Aziza da Azima? Hajja ta ce "Aziza tace min zata zo gida ba mamaki tana kewaye cikinta ya tsure sabida wannan tashin hankalin,Azima kuma ban ganta ba dan Aziza tace min idan zata dawo zata dubota su sameni a can" Baffa ya ce "Boye a can,ni kuma zan boye a nan karki kuskura kiyi magana kinji ko?" Hajja tana shirin tambayar Baffa me yake son yi ya ce "Jumala karki tambayeni komai! Zaki ganewa idanunki!ke dai kiyi abunda na sakaki! Yaƙi kuma inada yaƙini a kan garkuwa zai tarewa yankin kwana tunda yasa hannu kafin na gama wannan binciken da zanyi, dan haka karki tambayi komai kawai je ki boye,kuma karki kuskure ki fito" Hajja ta amsa da to, maganin da Baffa ya haɗa ya kewaye kofar shigowa gida da shi, sannan ya zuba wani ya koma ya maqale, Azima dake kwance a jikin bishiya haka kawai taji kamar an tsikareta saurin saukowa tayi a saman bishiyar idonta ya kara canza kala nan ta nufa hanyar gida ba tare da tasan dalilin hakan ba wanda take ji kamar an saka mata kuran karfe ne yake janta. @@@ Aziza ce ta fito daga kewaye idonta jajur alama ce na taci kuka, tana fitowa ta shige bukkarsu, Baffa dake maqale ta zanar kofar waje ya hangi Azima na tahowa tana layi, tana zuwa zata shiga gidan da aka yi wani sama da ita aka bugata da kasa, yayinda taji ko wani fata ta jikinta na mata zafi, ihu ta saka tana rirriƙe jikinta, ta kafarta ta fara rikidewa, wani wawan zare ido Baffa ya yi,yayinda yayi sumar wucin gadi, wannan shi ake kira tashin hankalin da ba a sa masa rana. Aziza kuwa shiryawa tayi dan taimakawa yankinta ta zo fitowa kenan har ta sa kafa akayi sama da ita ma, ihu ta saka ta fadi kasa wanwar, girgiza kai ta hau yi jin yadda jikinta ya amsa tana shirin rikidewa ta koma macijiya,cikin dimauta take furta "furen surfa na macizai? Wa ya kawo ya zuba a kofar gida? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! a'a a'a a'a!!" bata bari hakan ya faru ba ta shige bukka da gudu, Hajja dake kallonta ta zaro ido waje,to meke faruwa da yarta ga Baffansu yace karta fito? Anya zata iya kuwa ba zata fita ta je ta duba me ya samu Aziza ba? Hakuri dai ta yi amma hankalinta na kan Aziza, Aziza kuwa tana shiga bukka ta hau kwalawa Inno Fandi kira yayinda fatar jikinta ya koma fari sol, daga kugunta abunda yayi ƙasa ta koma macijiya🐍, cikin matsanacin kuka Aziza ke kiran Inno Fandi har ta bayyana, ta ce "Na shiga ukuna Inno Fandi furen surfa na macizai wa ya zuba?" Inno fandi ta ce "Yanzu za a fara Aziza! Ba kowa bane ya haɗa maganin furen surfa illa Magaji, wanda a halin yanzu Azima tana waje tana rikidewa,ke ma haka gaki nan, a yanzu *BAFFANKU YA GANE CEWA AZIMA MACIJIYA CE!* kece kawai bai gani ba, dan haka ki gaya masa gaskiya dan a san yadda za ayi a yi maganin abun" "To wani irin maganin abun Inno Fandi? Karshe dai nasan kashemu Baffa zaiyi da hannunsa" Inno Fandi ta ce "Bana da ikon gaya muku komai, idan har na gaya muku zan iya mutuwa, Magaji shine zai gaya muku, yanzu dai me kike da bukata na miki?" "Ina so naje na tsaida yaƙin da akeyi ne kafin na dawo ayi ta gida, ki taimaka min na fita a gidan nan" Inno fandi ta ce "An gama" sannan ta dauki Aziza suka b'ace dan zuwa tsaida yaƙi. A waje kuwa fadin halin da Baffa yake ciki bata lokaci ne bayan ya farfaɗo daga suman da yayi, a hankali yake tunkarar Azima dake birgima tana ihu jikinta na kan rikiɗewa, rasa abun yi Baffa yayi kawai yasa kuka ya duƙa a gaban Azima, ganin haka yasa Azima b'acewa b'att! A wajan Baffa ya yi zaman yan bori. @@@@ A wajan gari kuwa sadda Inno Fandi ta fice da Aziza nan Aziza ta b'ace tana kwasar mutanen yankin ja'i tana watsar dasu, mutum na tsaye sai dai yaji an dagasa an wurgasa, idan ta tashi kwasa kuwa sai ta kwasa kusan mutane goma da jelarta ta watsar dasu, mutanen yankin tudu jin sun daina yaƙi da mutane sun koma yi da aljanu ya sakasu fara arcewa suna fadin kaff! yankin kwana ba mutane bane, harkazalika yankin ja'i da suka fara jin jiki su da kansu suka tsare, su Garkuwa gani kawai suka kafin kiftawar ido da bismillah duk yawan rundunar da suka zo sun watse, hamdala suka fara yi suna godiya ga Allah, amma tabbas an kashe musu mutane. A hankali Aziza ta bayyana ta zama mutum tana ganin mutane kwance a cikin jini yara da manya mata da maza, hawaye ta share gami da kama hanyar gida,tana cikin tafiya Inno Fandi ta kira sunanta "AZIIIZAAA!" cak Aziza ta tsaya, sannan Inno Fandi ta ce "Idan kinje gida ki tambayi Baffanku Magaji Bawa su waye *BANJU DA BAHULA!*" Inno Fandi tana faɗin haka bata kuma cewa komai ba, da gudu Aziza ta yi hanyar gida,ko da ta isa har yanzu Baffa na zube a kofar gida ya kasa tashi, da sauri Aziza ta dagasa tana kiran sunansa "Baffa! Baffa! Baffa!" a tsorace dan tayi zaton Azima ta yi masa wani abun ne dan zata aika, da kyar Aziza ta kama Baffa ta zo shiga gidan ta ga har yanzu da sauran furen surfa a kofar gidan, ga shi babu abunda zata iya yiwa furen surfan, abu daya zata iya yi shine ta nemi taimakon Inno Fandi, tun kafin ta kirata ma ta bayyana ta kwashe sauran na bakin kofar kafin Aziza ta ja Baffa suka shiga gida, suna shigowa Hajja wacce har yanzu tana maqale ta kasa fitowa bisa da cewa Baffan yan biyu bai ce ta fito ba shiyasa ta ci gaba da maqalewa, ganin Aziza ta shigo da Baffa a hannu yasa Hajja fitowa a kiɗime tana fadin "Subhnallahi! Aziza me ya faru da Baffanku?" Aziza bata tsaya ba wa Hajja amsa ba illa randar kasa da ta nufa ta dibo ruwa mai sanyi ta watsawa Baffa nan ya sauke ajiyar zuciya yana ji kamar numfashinsa zai dauke, ruwan Aziza ta ba shi da kyar ya karba ya sha sannan ya dafe kansa, sannu suke jera masa ba tsayawa, sai zuwa can Hajja ta ce "Wai ni kam Aziza kamar dazu na ga shigarki bukka,amma tayaya kika fita a gidan ban gani ba? Ko b'acewa kika yi?" Hajja ta tambayi Aziza ne kawai amma ga mamakinta sai ji ta yi Aziza ta ce "e Hajja b'acewa nayi, sabida bazan iya bi ta bakin kofa ba, Baffa ya zuba furen surfa!" zaro ido Hajja tayi bama Hajja ba harta Baffa da bai gama dawowa dai-dai ba ya ɗaga kai yana kallon Aziza wacce ta miƙe tsaye tana ja da baya tana girgiza kai tare da hawaye mai ban tausayi tana fadin "Gwanda ayita ta kare, yau zaku san wani irin yara ku ka haifa, Hajja Baffa kuyi hakuri hakika baku haifi mutane ba, Baffa na san da hannunka zaka kashemu bayan kasan mu ɗin su waye! Na san ka gama gane Azima nice kawai baka gane ba,bazan iya munafurtanka ba Baffa!" da sauri Hajja ta miƙe tana fadin "Me kika faɗi ne haka Aziza!" "KARKI MATSO INDA NAKE!!" Aziza ta fada da karfi, Hajja ta ce "Sabida me Aziza? Nifa mahaifiyarki ce!" tana fada tana kara tunkaro Aziza dake matsawa baya, rintse ido Aziza ta yi ta buɗe ta haɗe rai cikin daga murya ta ce " *SABIDA NI MACIJIYA CE! AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE!*" Aziza ta faɗi tare da komawa Macijiya! Wani mahaukacin kara Hajja ta saka tare da yin baya-baya ta faɗi timmm! A kasa, ganin haka yasa Aziza komawa mutum ta yi kan Hajja tana jijjigata tare da ambatar sunanta,amma ina Hajja bata motsi numfashi ya tsaya cak, cikin kuka Aziza ta ce "Hajja ba dai hadiye zuciya kikayi ba!? Na shiga ukuna Baffa!!" Aziza ta fada tare da juyowa wajan Baffa nan ta ga ashe shima ya suma! Randar ruwan kasar gabadaya Aziza ta dauka ta juye a kan iyayenta, da kyar suka saki ajiyar zuciya, suna dawowa Aziza ta ce "Baffa waye su *BANJU DA BAHULA!!!?*" wani zabura Baffa ya yi yana kallon Aziza, da sauri ya miƙe tsaye ya ce "Dole kafin nasan abunda ke yawo a jikinku saina haƙo abunda bana son haƙowa, Aziza na fahimci ke ba kamar Azima ba ce, da ace ke kamar Azima ce yadda muka suma da kin kashemu! Na sha zargin Azima na son kasheni amma naki ba wa shaidan damar da zai saka min waswasi a zuciyata a kan 'yar da na haifa ta cikina! Dan haka zan gaya miki waye Banju da Bahula da abunda ya shiga tsakanina dasu, amma kafin nan zo muje jejin firi" Saurin riƙe hannun Aziza Hajja tayi idonta jajur ta ce "Ya isa haka Baffan yan biyu! Ka sha saka rayuwarka a hatsari ga shi yanzu ta shafi yarana!" Hajja ta fashe da wani matsinacin kuka tana zuba guiwowinta a kasa, da sauri Aziza ta kama hannunta, ko kaɗan Hajja bata ji tsoron Aziza ba, cikin kuka ta ce "Macizai! Macizai! Macizai! Ni Jamila na haifi Macizai! Inaaa ba zai yu ba ni kawai a dawo min da yarana!" Hajja ta kuma sa kuka bai tab'a zuciyar mai sauraro, rungumeta Aziza ta yi cikin tausayawa domin kuwa Hajja abun tausayi ce ita da Baffa, fita Baffa ya yi yaje ya kirawo Arɗo da Yawuro, da Inna Wuro, da kuma tsohon sarkin kwana wato Baffa Mandi, bai boye musu komai ba ya gaya musu komai, hakika hantar cikinsu ya kaɗa fiye da tsammani, Arɗo ya ce "Lallai kuwa idan har Banju ne ya dawo daukar Fansa! Kisa bai ma yi komai ba kenan! Ashe kuwa idan ba a dakatar da Banju ba idan har shine sunanmu toka" Baffa ya ce "Bazan bari hakan ta faru ba, yanzu daga nan jejin firi zamuje nida Aziza, zanje na haƙo kayana dan nasan taya zan taimaki yankina da kuma yarana" Baffa Mandi ya ce "Magaji!? Hakowa fa kace? Aljanu da mayu ayi yaya dasu?" Arɗo yace "Buhun bala'in Banju gwanda haƙo aljanu da mayun da Magaji ya kulle, dan ba karamin babban shaidani bane Banju! Ko ka manta b'arnan da Banju ya yi kafin Magaji ya kashesa?" "Taya kuwa zan manta Arɗo? Bayan dukka ahalina Banju ne ya kashesu!" Baffa wanda ke goge gumi ya ce "Aziza tana tare dani, dan haka yanzu a gayawa su sarki Chubaɗo halin da ake ciki, sannan a cewa yara da manya kar wanda ya fito ko da kofar gida ne, domin kasan aljanun da aka ɗaure duk wanda ya samu damar guduwa zai fito ne da haushi da b'acin rai na dauresa da akayi na tsawon shekaru, dan haka duk wa inda suka samu zasu bugesu ne, Yawuro, Inna Wuro ku kula da Jumala, Aziza muje" Aziza ta amsa da to Baffa a sanyaye abun tausayi, zasu fita Hajja ta kuma sa kuka tana salati dan ita kadai tasan abunda yake damunta, su Yawuro da Inna Wuro suna dannarta, yayinda Arɗo yace bari yaje wajan Chubaɗo su zanta a kan lamarin. 🐍🐍🐍🐍 B'acewar Azima jejin hayi ta nufa tana kan ihu fatar jikinta na mata zafi sosai,zubewa tayi a kasa tare da furta "KARYANKA! NACE KAYI KARYA MAGAJI! FANSA NE DAI SAI NA DAUKA! AMMA NA RASA MEYASA KAKE GALABA A KAINA TUN TSAWON SHEKARA ASHRIN! YANZU MA SO KAKEYI KA SAKE KASHENI! INA HAKAN BA ZAI YU BA, DOLE NA MAKA MUGUN TABO! TA HANYAR CI GABA DA RAYUWA A GANGAR JIKIN 'YARKA AZIMAAA!!" Wannan murya na gama fitowa ta b'alli gashin kanta tasa a baki nan taji sauƙin raɗaɗin, sannan ba tare da bata lokaci ko dogon tunani ba Azima ta dauki hanyar barin Al'karyan yankin kwana dan ta shiga cikin gari ta cika burinta na tarwatsa jama'a da hanasu kwanciyar hankali. 🍃🍃🍃🍃 Baffa da Aziza suna isa jejin firi ba bata lokaci Baffa ya fara haƙo abunda ya binne, yana gaff da gama cirowa ya kalli Aziza ya ce "Kin shirya?" Aziza ta gya ɗa kai gami da cewa "e Baffa a shirya nake" "Fara" Baffa ya faɗa,yayinda Aziza ta daga hannu sama ta fara haɗa wani baƙin guguwa mai cike da rami dan tare mayu da aljanu ya kasance ko da zasu gudu kaɗan ne, da karfi Baffa ya fizgi wani abu kamar irin akwatin karfe na tun tsawon wasu shekaru, yana fizgowa take wani mahaukacin guɗa ya tashi, wanda ba iyakar jejin firi ba dukkan jeji sai da ya amsa tare da dukkan mutanen yankin kwana babu wanda bai ji wannan gudar ba, Aziza na tsaye sai haɗa zufa takeyi yayinda take riƙe da wannan baƙin guguwar wanda ta riƙe aljanu da mayu, ganin halin da take ciki da sauri Baffa ya buɗe akwatin wanda da ka gani kasan ya daɗe ya dauki guru da layarsa ya maida (Allahu Akbar Baffa an tuno baya) duk wani abu da Baffa ke amfani da shi sai da ya dauka,na ɗaurawa ya ɗaura na sakawa ya saka, na mannawa ya manna, ya fiddo wani tulu mai murfi, yana fiddowa ya sake kama wasu aljanu da mayun ya rufe yayinda wasu suka gudu, Aziza na sakewa ta zube sumammiya, Baffa bai damu da sumar da tayi ba dan na hucin gadi ne, ta ma yi namajin kokari, dan ko shi iyakar abunda zaiyi kenan,kuma dabadin ita ba da yana haƙo abun nan ba tare da an rikesu ba bala'in da zata kunno yankin kwana sai Allah. Baffa na ciro kayansa ya haɗa wasu taurari guda biyu wanda suke kamar dutse mulmulen laka, sunan Azima da Aziza ya rubuta a kai, nan wani haske ya bayyana, na Azima ya fara gani, nan ya hangi Banju a gangar jikinta, Azima a sume take, wasu hawaye masu zafi ne suka wanke wa Baffa fuska, sannan ya duba taurarin jikin Aziza, nan ya ga Bahula ce ke rayuwa a jikinta, sannan ita an maidata Macijiya ba wani ke rayuwa a jikinta kamar Azima ba, cikin ruɗu da tashin hankali Baffa ya watsawa Aziza wani farin kasa nan take ta sauke ajiyar zuciya ta farka, ya ce "Aziza muje gida" girgiza kai Aziza ta yi ta ce "Baffa ba zan je gida ba har sai ka gaya min waye Banju da Bahula" Baffa ya ce "Yanzu kuwa zan gaya miki Aziza, yau zan baki labari" 🍃🍃🐍🍃🐍 *Tabb cakwakiya! Shin ya zata kaya ne? Idan Baffa ya ba wa Aziza labari taya za a rabasu da wannan bala'in? Ga shi Azima ta bar yankin kwana ta do shi hanyar shiga gari,Dukkan wasu manya tambayoyi yana sauran shafuka da suka rage a gaba, naira darinki ya isheki! Idan kuma kika jira cmplt dari uku. Karku bari ayi babu ku.* COMMENTS AND SHARE BY MOMYN AHLAN [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 GODIYA TA MUSAMMAN GA DAUKACIN YAN PAID GRP DIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, HAKIKA SHARHINKU YANA KARA MIN ƘARSASHI, KAUNA CE TASA KUKA KASANCE A PAID GRP DINA, DAN HAKA NIMA INA KAUNARKU🥰, KU MORE KUJI DADINKU. *PAID.* 🅿️==2️⃣5️⃣↪️2️⃣6️⃣ Gyara zama Aziza ta yi ta naɗe kafarta sannan ta ce "Ina sauraronka Baffana!" miƙewa tsaye Baffa ya yi ya juya baya gami da maida hannunwansa baya ya yi tsayuwar da jaruman maza ke yi wanda suka yarda da kansu ya koma ainahin asalin MAGAJI BAWANSA sannan ya ce "Aziza! a da an yi wani mutum jarumi! sadauki! jajircacce! tsayayye! marar tsoro da fargaba!, da tare dukkan wani faɗa! kin san ana cewa ba a faɗa da aljani ko? to wannan mutumin yana yi! wanda a yanzu shike tsaye a gabanki! Wanda wannan mutumin mahaifi ne gareki da kuma 'yar uwarki Azima, kamar yadda kika sani Ardo mahaifina ne wato kakanku! Inna wuro mahaifiyata ce! wasu daga mutanen yankuna suna fadin cewa nayo gadon Arɗo a lokacin yana saurayi, amma kin san me Arɗo ya ce?" Aziza da ta ƙurawa Baffanta ido tana yi masa kallo kamar bata taba ganinsa ba dan gani ta yi gabadaya ya canza mata ya tashi daga Baffanta da ta sani ya koma wani mutum daban ta girgiza kai alamun a'a, Baffa ya ɗora da cewa "Arɗo cewa ya yi ni daya ne tak a wannan yankin dama sauran yankuna babu na biyuna! domin kuwa baiwata daga Allah ne, tun ina yaro nake mu'alama da aljanu sannan nake taimako! a taimakon da nakeyi ba iyakar mutane ba har ma da aljanun,a lokacin na shiga yankuna da dama dan kai wa wasu dauki! Yankin kwana ta shahara ta yi suna ta sanadina, tun a lokacin nake cin karo da abokan gaba da maƙiya wa inda basu sona sabida farin jinin da nayi a wajan yan mata a lokacin babu wani kyakkyawan jarumi ka ma na, shiyasa na kara yin baƙin jini, mahaifiyarku kamar yadda ku ka sani 'ya ce ga Ƙanwar Arɗo wanda suke uwa daya uba daya, Jumala yarinya ce mai kunya da natsuwa da hankali da sanin ya kamata, tun ranar da naje gidan Inna Kab'o na ganta naji na kamu da sonta amma ban san taya zan bayyana mata ba, Jumala ta ta so ne a babban gida wanda suke da tarin iyalai masu yawa, wanda a yanzu Jumala ita daya ce tal ta rage a danginta duk Banju ya kashesu!" Kasa hakuri Aziza ta yi ta ce "Baffa miye dalilin Banju na kashe mutane? Sannan naji Baffa Mandi ma ya ce shi ya kashe masa ahalinsa! Sannan wanene shi Bahula din?" "Bahula mace ce ba namiji bane Aziza! Saurin me kikayi Aziza? Zaki san komai a yau! duk wani jeji babu wanda bana shigansa da ikon Allah sannan na fito lafiya ba tare da wani abu ya sameni ba, domin nayi imani da Allah da ANNABI MANZON ALLAH S,A,W, nayi karatuna a wajan wani Babban malami a nan yankin kwana mai suna MALAM SHAINI wanda shima ahalin yanzu baya raye Banju ya kashesa! shi da iyalansa!" "Kenan Baffa yawancin mutane Banju ya kashesu?" Juyowa Baffa ya yi ya kalli Aziza sannan ya yi wani murmushi ya ce "Kisan da Banju ya yi ba zai kirgu ba, dan zan iya ce miki a cikin kashi dari na mutanen yankin kwana Banju ya kashe kashi arba'in! Banju mugu ne, na kasance ina shiga jeji dan nemo ganyayyaki na haɗa magani, akwai wani jeji mai sunan jejin 'Bingel, hakika har kwanan gobe ban kara shiga jejin 'bingel ba" "Kenan Baffa akwai jeji mai suna jejin 'bingel?" Baffa ya gyaɗa kai "E Aziza, akwai a wannan jejin ne na tafka babban kuskuren da ban taba yi ba a rayuwata, ko kuma nace ya haɗu min har da tsautsayi! dan a wannan jejin ne tsautsayi ta haɗani da Banju, a da ban san wani abu mai suna tsoro ba a rayuwata! Banju shine mutum na farko da ya fara shuka min tsoro a zuciyata, ba dan komai ba sai dan ikirarin da ya yi a kaina da mutanen yankina a sadda zan kashesa! ba dan komai na tsorata da Banju ba illa ta'adi da b'arnan da ya yi a yankin nan" "Ranar wata laraba ba zan taba mantawa ba naje jejin 'bingel dan nemo wani ganyen magani da zan haɗawa Inna Kab'o mahaifiya ga Jumala Hajjarku ciwon kafa ya sakata a gaba, a lokacin kuma an gano cewa ina son Jumala ita ma kuma tana sona har an fara maganar haɗamu aure, na shiga jejin 'bingel har na tsinƙe ganyayyakina zan fita, da shike duk inda zanje ina tare da addana kin san fulani da takwabinsu suke yawo ni kuwa harda kifiya nake yawo, kifiyata kuma tana da guba a jiki, sabida shige-shigen da nake yi na saka rayuwata a hatsari dole na dinga tafiya da kariya duk da nasan ni Allah shike kareni, kifiyata ba mutum ba duk wani abu da zan harba da shi sai ya mutu walau na harbi aljanu ko mayu ko wani dabba ko ma me da kika sani, na juyo zan bar jejin bingel ban ankara ba na hangi wani zureren 🐍 jelar maciji mai cike da ban tsoro, dama kafin nan a kwanaki muna samun koke-koke daga maƙotan yankuna a kan saren maciji wanda nike zuwa dubawa,saren macijin kuma ya fita daban da saren macizan da na sani, to ganin wannan macijin ke da zuwa ban tsaya dogon tunani ba sabida na ɗan firgita na ciro kifiyata har uku na saita macijin na harba, kin san wane harba?" da sauri Aziza ta girgiza kai " *BAHULA* wanda ƘANWA take a wajan Banju, wanda yake haukan sonta yake ji da ita, ban taba sanin suna rayuwa a wannan jejin ba, sannan ban san da cewa aljanun macizai bane,ni dai na ga Babban maciji kuma na harba, ina harbinta nan naga abunda ban taba gani ba, wato nan ta rikiɗe ta zama mutum kifiyar da ma harbeta da shi daya a kirji daya a juya daya a baya, kafin na farga da abunda na aikata nan naji ihun Banju yana furta "BAHULAAAAA!!" wanda sai da jejin bingel ya girgiza, a lokacin da Banju ya zo ga Kanwarsa Bahula ina tsaye ina kallon Ikon Allah, yayinda lokaci daya naji jikina na rawa, ko a lokacin da Bahula zata mutu sai da ta cewa Banju Dan Allah ya gyara halinsa na mugunta bata so a sake koransa a wannan jejin kamar yadda ya buwayi asalin garin da suke a jejin aka koresu ta hanyar yi musu turaren barkono dan tun asalin Banju mugu ne fiye da misali, a lokacin da na ga haka na matso kusa ina bai wa Bahula hakuri, murmushi ta min bakinta na fitar da baƙin jini ta ce min ba komai tasan ba da gangan nayi ba, sannan ta roƙi alfarma a kan cewa na bar ɗan uwanta Banju yayi rayuwarsa a jejin bingel, sun taso tare kamar yadda aka haifesu tare dan su ma yan biyu ne, a hannun Banju Bahula ta cika, Bahula tana mutuwa Banju ya hau kuka ina basa hakuri dan babu taimakon da zan iya yiwa Bahula dan guba ya shigeta,hakika nima nayi kukan kuskuren da na aikata, nan na dinga ba wa Banju hakuri, amma abunda ya ce min shine, shi *BAYA MANTUWA,KUMA BAYA YAFIYA* a lokacin Banju ya yi yunkurin kasheni amma ya kasa, yayinda ni kuma na gudu,ina zuwa gida banyi nauyin baki wajan faɗawa mutane abunda ya faru ba,tabbas a lokacin mutanen kwana sun tsorata matuka,inda aka yi cincirindo aka je aka ba wa Banju hakuri amma ya nuna sam ba zai hakura ba, bayan kwana biyu da faruwan haka nan yankin kwana ta koma mace-mace na hanyar kisan maciji ko kuma kisan gilla ta sanadin wani gurb'ataccen guba wanda Banju ne ke yi, a kwana biyu Banju ya kashe mutane sama da dari a yankin kwana, nan fa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kare mana, ba mu sake yin kasa a guiwa ba muka sake zuwa wajan Banju basa hakuri amma kamar mun sake zugasa ne muna tunzura shi, ba zan iya ƙayyace miki mutanen da Banju ya kashe ba Aziza, haka ya bi dangin Jumala mahaifiyarku ya kashesu ita daya kawai ta tsira, a lokacin Arɗo ya dauketa ya kaita gidansa sannan ya daura mana aure da ita, a lokacin Baffa Mandi shi ne sarkin fulanin kwana, haka shima iyayensa matansa yaransa da duk wani danginsa sai da Banju ya kashesu! a lokacin ko yaro aka haifa yau Banju ya samu zai kashe, babu kalar farmakin da Banju bai kawo min, akwai sadda yankin kwana ya koma zallar ƙura ne ke tashi tare da jinin mutanen da basuji ba basu gani ba,nan nayi tattaki naje na samu Banju nace masa daukar Fansansa a kaina ne meyasa yake so ya shafe yankina, ina nine na masa laifi to ya kasheni ya kyale jama'a amma nan yace min ko da ya kasheni ya min alkawari babu wanda zai rage a raye a mutanen yankin kwana sai ya kashe kowa! ko da kuwa ɗan da yake ciki ne sai ya kashesa! a lokacin nayi niyyar na miƙa wuyata ga Banju amma na fahimcesa kamar yadda ya faɗi ba zai kyale kowa ba, nan jama'ar kwana aka hadu aka yi tattaunawa inda kowa ya kawo shawara a kan na kashe Banju dan abun nasa yayi yawa,da fari naqi amincewa sai daga baya na amince, a lokacin da zamu gwabza na fahimci ba zan iya kashe Banju kai tsaye ba,kamar yadda shima ba zai iya kasheni kai tsaye ba, a lokacin ne na tafi jejin lore aka bani zare mafi hatsarin gaske, wato zaren saƙar dana, a wajan yanki muka gwabza da Banju gaban dukkan mutanen yankin kwana, kin ga wannan takwabi da shi na kashe Banju bayan na saƙa zaren saƙar dana na naɗe a jiki na sokesa da takwabin a ciki, nan ya fadi yana aman jini amma jinin ba ja bane kore ne, kafin ya fadi kasa shine ya mana alkawarin cewa zai dawo daukar fansa a kaina ta ko wace hanya dani da mutanen yankin nan, to kinji abunda ya shiga tsakanina da Banju!" Baffa na gama ba wa Aziza labari tasa kuka tana fadin "Kenan yanzu Baffa Fansar da Banju yake dauka a kanmu ne? Innalillahi wa inna ilahirrajiun! Yanzu Baffa kashemu zaka yi?" Baffa ya girgiza kai yana fadin "A'a Aziza! Kin taba ganin Uban da ya kashe yaransa ne? Amma idan ta kama zan iya Kashe Azima dan tsaida wannan bala'in,idan ba haka ba tabbas ba a fara mutuwa ba, ke rabaki da Bahula ba zai yi wuya ba, amma ko da an rabaki da ita ke Banju ya maidaki Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinki ba sai ta jikin Azima, kuma ni bana da masaniyar makarin abunda Banju ya miki, amma akwai wani Babban Malami mai suna Malam Shadi a can yankin ja'o zamu je wajansa dan ya mana bayani,ki kwantar da hankalinki, amma kafin nan muna da bukatar tsaida Azima mu ɗaureta, ki daina kuka kinji? Tashi mu tafi gida" Aziza ta miƙe tana share hawayenta suka nufi gida, a hanya kafin su karasa Baffa ya haɗu da Salti ɗan gidan Jauro mai maganin kwana aljanu sun bugesa, da sauri Baffa ya yi kansa yana dubasa,girgiza kai ya yi yana fadin "Sai da nace kar wanda ya fito ai ga irinta nan, taurin kan Salti iri daya ne da na Ubansa Jauro" Baffa ya faɗa yana daukar Salti, gida suka nufa suna isa Baffa bai yi nauyin baki ba ya gaya musu ai Banju ne a jikin Azima, Bahula kuma tana jikin Aziza, sannan ko an raba Aziza da Bahula Banju ya maidata Macijiya, wani kuka mai rikita zuciya Hajja ta kuma sakawa, yayinda Aziza ta faɗa jikinta suka hau yi tare, Baffa Mandi ya ce "Abun da za ayi yanzu shine, ya kamata muje wajan wannan Malamin wato Malam Shadi na can yankin Ja'o mu je zuwa gobe kawai dan bamu ga ta zama ba, amma kafin nan dan Allah kar a fadawa jama'ar gari dan ba a san me hakan zai haifar ba har sai munje an dawo, mu da muka sani ya tsaya a iya mu kawai" aka amsa da hakane, nan Arɗo ya ce "Magaji? Ana ta wannan maganar ina Azima?" 🐍🐍🐍🐍🐍 COMMENTS BUT PLSS DON'T SHARE BA DAN NI BA DAN ALLAH DA MANZON ALLAH 🥺👏🏻[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️==2️⃣7️⃣↪️2️⃣8️⃣ "Azima?" Baffa ya nanata sannan ya kuma cewa "Tun sadda ta b'ace ban ganta ba" Aziza dake kuka a jikin Hajja ta miƙe tana goge hawaye ta ce "Baffa bari na dubota na gani tana ina" Baffa ya ce "To dubota Aziza" rufe ido Aziza ta yi ta shafa hannun damanta da hannun hagunta,amma abun mamaki bata ga Azima ba, saurin bude ido tayi tana fadin "taya hakan zai faru?" "Menene Aziza?" Arɗo ya tambayeta "Arɗo bana ganin komai,bana iya ganin Azima amma taya hakan zai kasance?" "Ki sake dubawa Aziza" Baffa ya faɗa Aziza ta gya ɗa kai tana fadin to Baffa, ta sake rintae ido amma wayam, sake buɗe ido ta yi ta ce "Wlh bana ganinta, Baffa ya ce zan duba da kaina amma sai bayan munyi sallar magriba fatana dai daya kar ace Azima taje ta yi wani ɗanyen aiki" "In sha Allahu ma ba zata yi ba" cewar Baffa Mandi, kamar yadda Baffa ya faɗa bayan sallar magriba ya hau duba inda Azima take amma abunda bincikensa ya nuna masa shine kwata-kwata Azima bata yankin kwana ta fice gabadaya daga wannan sassanin, a firgice Baffa ke furta kalman "INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATIHI WA AKHLIFNI KAIRAN MINHA!" da gudu Hajja da Aziza suka shigo suna tambayar Baffa menene? "Azima bata yankin nan kwata-kwata,bata wannan al'ƙaryan! ta bar wannan sassanin, Banju ya ja min 'ya sun bar wannan yankin!" cewar Baffa hankalinsa a matuƙar tashe, Aziza ta ɗora hannu a kai tana fadin "Wlh Baffa ta sha fadin tana son shiga cikin inda yake da mutane da yawa ta tarwatsasu,kenan ina Azima ta nufa!? Duk inda zata je dai ba alkhairi zata shuka ba,dan nasha gaya mata shiganta mutane ba alkairi bane, yanzu miye abun yi Baffa?" girgiza kai Baffa ya yi ya ce "Ban sani ba Aziza! Allah ya kaimu gobe asubanci zamuyi mu tafi yankin ja'o dan zuwa wajan Malam Shadi" Aziza ta juya tana kallon Hajja wacce ta kasa tsayar da hawayen da ke zuba a idonta, a hankali Aziza ta fice a bukkar tana sharan hawayen tausayin iyayenta, Aziza na fita Baffa ya matso kusa da Hajja dake hawaye tun tana kuka mai sauti har ta koma kukan baya fita sai ambaliyar hawaye, cikin sigar rarrashi Baffa ya ce "Jumala kiyi hakuri! Ki dage da addua muna kai wa Allah kukanmu! Dan Allah ki daina wannan kukan kar ya jawo miki ciwo, kinji!?" dago jajayen idonta Hajja ta yi ta watsasu a cikin na Baffa wanda tun tahirin aurensu bata taba kallon tsakiyar idonsa ba sai yau, muryarta a dashe ta ce "Ciwo? Ciwo fa ka ce Baffan yan biyu? Wani irin ciwo ne ya fi na zuciya? Shin kasan ya nake ji a raina?" "Ko ma ya kike ji ki yawaita nanata kalman Innalillahi wa inna ilahirrjiun! ya zaki dinga jin sassauci a ranki, sannan....." "Don Allah Baffan 'yan biyu!" Hajja ta kasa Baffa ba tare da ya idasa maganarsa ba, cikin zafafan hawaye ta dago ta ce "Ni dai kawai abunda nake bukata a wajanka shine ka dawo min da yarana! Ka dawo mini da Azima da Azizana, ni dai ban haifi macizai ba! mutane na haifa,idan wani abu ya samu Azima da Aziza hakika zan iya mutuwa kawai ka dawo min da yarana!" ta tashi ta fice da gudu a bukkan, Aziza dake maqale a jikin bukkan tana sauraronsu ta riƙe bakinta gam tana kuka itama da gudu ta fice a gida ta yi rafin jimulo, taje ta ci kukanta har ta godewa Allah kafin ta dawo gida, bukkar Hajja ta shige ta sameta zaune ta zauna kusa da ita ta ɗora kanta a kan cinyar Hajja ta ce "Hajjana! Inaji a jikina kamar na kusan barinki! Ba wai ina gaya miki dan na tashi hankalinki bane, duk duniya babu abunda na tsana kamar na ganki ke da Baffa cikin tashin hankali,abunda yasa nake gaya miki Hajja dan na nemi yafiyarki ne! Hajja ki yafe min idan har nayi miki wani abu a zaman da muka yi dake! Kowa da kalar kaddararsa amma mu wannan shi ne namu kaddara! Ba mu kasance cikin mutane da zamu yi rayuwa dake ba Hajja,dan Allah ki yafeni! Ki yafemini!!" Aziza ta karasa da sakin kuka mai ban tausayi da karya zuciya,tana sa kukan Hajja ta rungumeta tana bubbuga bayanta dan tama kasa magana ko tace zatayi maganar ma muryarta ba zai fito ba dan ya dashe!" su na nan suna kuka har dare ya tsaga kafin Baffa ya shigo ya musu umarni da suyi alwala suyi sallah, hakan kuwa ta kasance, Baffa ne yaja su sallah suna gayawa Ubangiji, da haka har asuba ta yi basu rintsa ba. Bayan Baffa ya dawo daga masallaci tare suka shigo da Ardo da Baffa Mandi, a lokacin Aziza da hajja suna zaune sunyi jingum-jingum, Baffa ya ce "Aziza ta shi mu tafi, Jumala ke kuma ki tafi gidan Arɗo" ko uhum Hajja bata ce ba tana riƙe da hannun Aziza,fuskokinsu a kumbure,shima Baffa ɗaurewa kawai yake yi baya so ya kara karya musu guiwa amma da zai samu dama da shima ya sha kukan nan ko zai samu mai rarrashinsa, da kyar Aziza ta zare hannunta daga na Hajja ta fice da sauri jin wani kukan na shirin cewa a ba shi hanya, Hajja kuwa tuni ta sake saka wani kuka tasa hannuwanta a fuska, saurin ficewa Baffa ya yi jin hawaye ya fara bin fuskarsa, yana fita babu b'ata lokaci suka hau doki, da Baffa da Baffa Mandi da Arɗo sai Aziza, suna hawa doki suka dauki hanyar yankin ja'o ba tare da bata lokaci ba. 🐍🐍🐍🐍🐍 Tun bayan da Azima ta bar yankin kwana take aikin tafiya ba tare da ta gaji ba dan bata jin gajiya a tattare da ita, hakika tana shan tafiya, dan kuwa ace mutum wanda yake ba aljani ba idan zai fita daga yankin kwana zuwa cikin garin kafin ya iske titi a kan doki sai ya shafe sati biyu, shiyasa su haka suke ba a shigo musu su ma kuma basu shiga gari dan nan ne rayuwarsu a kauyensu mai cike da abun burgewa da albarkatun korayen shuke-shuke, a kwana daya Azima ta yi rabin tafiya abunka da ba tafiyar mutane ba. 🍃🍃🍃🍃 Sai kusan gaff azahar su Baffa suka isa yankin ja'o ba tare da bata lokaci ba aka musu iso izuwa ganawa da Malam Shadi, suna shiga bukkarsa Malam Shadi na haɗa ido da Aziza ya hau salati yana sanar da Ubangiji nan gaban Baffa ya bada dammm! amma ya daure suka zauna ana gaisawa cikin mutunci da mutuntawa, Malam Shadi ya kalli Baffa ya ce "Ohh Allah Magaji Mazan fama kana raye? Yaushe rabonka da yankin nan? Inaji fa tun sadda wan can muguwar mayyar ta sakamu a gaba kazo ka rabamu da ita ban sake ganinka ba sai dai kayi aike" Baffa ya yi murmushin boye damuwa ya ce "Wlh kuwa Malam Shadi,tun sadda na daina shige-shige naji komai ya fita a raina" "Allahu Akbar" cewar Malam Shadi yana kallon Aziza da ta dukar da kai gabanta na faduwa, ya kalli Baffa cike da al'ajabi ya ce "Magaji Bawa ina ka samo *MACIJIYA!?*" juyawa Baffa ya yi ya kalli Aziza da ta rakube ta dukar da kai kasa kamar ma kuka take yi,sannan ya maida kallonsa ga Malam ya ce " 'yata ce Malam, na kawota ne wajanka dan ka duba min ita, Banju da na kashe yace zai dawo shine ya dawo daukar Fansa a kan yarana, yanzu haka dayar ta bar yankin kwana kwata-kwata, ita kuma wannan ka ganta nan, shine nace bari na kawosu wajanka dan a san ta yadda za a rabasu da su,bana so gwagwarmayan da nayi ya shafe yarana" "Shafa kuma ta nawa magaji? Ai shafa kam an gama shafansu tunda gasu nan a macizai" cewar Arɗo, Malam Shadi ya gya ɗa kai yana fadin "Ya Hayyu Ya Qayyum Ya Zuljalalu wal'ikram, hakika Banju mugun aljani ne, Banju mugu ne fiye da tunanin me tunani, amma Magaji kai ma zaka iya yiwa yaranka magani ai" Girgiza kai Baffa ya yi ya ce "Zan iya sake kashe Banju, amma abunda nake tsoro shine Banju na rayuwa ne a cikin Azima yana tafiya ne da kafafunta, yana aiki ne da hannuwanta,yana gani ne da idanunta,yana motsi ne da motsinta, sannan a binciken da nayi Azima a sume take a jikin Banju, idan har na kashe Banju to tabbas Azima ma ta tafi, na duba na ga ita Aziza rabata da Bahula ba wata damuwa ba ce, amma kuma tashin hankalin a nan shine,ko Bahula ta bar jikin Aziza, Aziza ba zata samu lafiya ba dan Banju ya maidata Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinta ba" jinjina kai Malam Shadi yayi bayan Baffa ya gama yi masa bayani, Baffa ya kuma cewa "Ina da bukatar taimako dan bana so na salwantar da rayuwar yarana! Jumala ba zata yafemini ba,sannan nima bazan yafewa kaina ba Malam Shadi" "Matso nan kusa dani Aziza karki ji tsoro" Malam Shadi ya fada yana kallon Aziza, a hankali ta taso ta matso kusa da shi ta duka, wani magani ya ɗiba a kasko ya watsa mata a fuska,ihu Aziza ta saka tana furta "Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah! Baffana zafii!!" abun tausayi, hawaye ne ya cika a idon Baffa yana ji kamar ya tashi ya fita amma ina ba hali, Malam Shadi yasa hannu ya damƙi goshin Aziza da karfi, murkususu ta hauyi tana son kwacewa amma ta kasa,rintse idonsa ya yi yana gane-gane da hange-hange, ya dau lokaci yana riƙe da goshin Aziza wacce ke murkususun azaba har sai da ta suma kafin Malam Shadi ya saketa, Baffa ya yi saurin taro 'yarsa ta fada jikinsa,jikinsa na rawa hawaye na zuba a idonsa ya d'ago ya kalli Malam Shadi yana fadin "Malam me ya sameta?" "Haba Magaji! Sai kace baka san yanayin aiki ba,ka kwantar da hankalinka zata farfado, amma gaskiya akwai babbar matsala wanda ba zan iya ce muku komai a kai ba, akwai aikin da nake so nayi cikin dare ina so na bincika na ga taya za a rabasu da mugun nan Banju, sannan Babban tashin hankalin shine 'yar uwarta Banju ya jata sun bar al'ƙaryan nan,ina take? Ina za a ganta? Duk babu wanda ya sani" Arɗo da Baffa Mandi suka sharo zufar tashin hankali, Malam Shadi ya ɗora da cewa "Babban damuwar shine abunda Banju zai ja Azima ta aikata,amma zanyi bincike a kai yau In sha Allah,ina dai a nan zaku kwana?" Baffa suka amsa da eh, sannan Malam Shadi ya kira wani almajirinsa yace ya kawo masa tarbama wanda yake na kara ne, bayan an kawo ya ce a shinfiɗe Aziza a kai, bayan Baffa ya kwantar da Aziza Malam Shadi ya kunna mata hayaki, sannan suka fita waje suka zauna suna tattauna yadda zasu yi a kan lamarin. 🍃🍃🍃🍃 Sarki Chubado ne da mai unguwan kwana ori suke tattaunawa a kan batun Azima da Aziza Macizai ne,suna ta alhinin lamarin, su biyu suke magana a kan cewa suna tausayawa Baffa, a garin yaya sai ga Salti ɗan gidan Jauro mai maganin yankin kwana yazo wucewa caraf a kunnensa, dan Salti ba dai gulma ba,nan yaji duk wani tattaunawa da Sarki Chubado da Ori ke yi a kan lamarin har da tafiyar da su Baffa suka yi yankin ja'o, da gudu Salti ya kwasa yana fadin zai je ya gayawa Baffansa dan yasan zai yi farin ciki da wannan labarin da zai kai ma sa. 🍃🍃🍃🍃🍃 Comments Vote By Momyn Ahlan [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *INA GAISHEKU KYAUTA YAN PAID GRP MASOYAN........BAN DAI KARESA BA KU KARASA DA KANKU* *PAID.* 🅿️==3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣ Sarki Chubaɗo cikin fushi ya kalli mutanen da suke wajan ya ce. "Amma wallahi kun bani mamaki! Kuma kunji kunya! Yanzu akwai masifar da zata samu Magaji wanda har zai sa ku juya masa baya? Idan har ku wa inda ku ka zo bayan shekara ashirin baku san gwagwarmayen da Magaji ya yi ba, to ku wa inda ku ka zo kafin bayan shekara ashirin zaku ce kun manta da wannan halaccin ne? Dayawanku a nan wasunku basu da dangi kaff Banju ya kashesu! dabadin Magaji ba babu ko da ƙwaro da zai rage a wannan yankin!!" Sarki Chubado ya karasa da tsawa idonsa jajur dan ransa ya b'aci matuka "A ce ina sarkin fulanin yankin kwana amma Jauro ya ja ku ba tare da sanina ba ku zo yiwa Magaji rashin mutunci da dibar albarka! Jauro ne sarkinku!! Na ce Jauroo neee sarkinkuuu!!!?" shuru jama'a suka yi masu zare ido da masu tsilli-tsilli da ido suna yi, Mai Unguwar yankin kwana bayan Sarkin fulanin kwana Chubaɗo ya dasa ayar tasa shima ya karbe da cewa "Jauro dai mai maganin yankin kwana ne kamar yadda ku ka sani, amma a da kun san waye GARKUWAN YANKIN KWANA KAFIN A ƊORA GARKUWA NA YANZU!! TO GA SHI NAN SHINE DAI! *MAGAJI BAWA!!* kafin ya sauke duk wata baiwa tasa ya binne bayan yasha wahalan kama aljanu da mayu ya kullesu!! Ya sauka ne a kan matsayinsa da yake da shi bayan ya kashe Banju! Amma har kwanan gobe! kai ba ma kwanan gobe kawai ba! HAR GABAN ABADA BABU WANI GARKUWAN FULANIN YANKIN KWANA SAMA DA MAGAJI! SANNAN BABU WANI MAI MAGANI SAMA DA MAGAJI! Har ta Garkuwan fulanin yankin kwana na yanzu da Magaji yake tunkaho" Garkuwan fulanin kwana na yanzu ya fito ya ce "Tabbas hakane, da taimakon Magaji Bawa na zama Garkuwan fulanin kwana shi ya maidani mutum, gaskiya baku kyauta ba" wasu ne jikinsu ya fara sanyi ganin haka yasa Jauro ƙara tattaro sauran munafurcinsa dan shi baya so ace mutane su banzartar da maganarsa idan ba haka ba ba zai cika burinsa ba,baya so yaji sunan Magaji na daukaka! yafi so duk yankuna yadda ake kiran sunan Magaji Bawa! Magaji Bawa! ya kasance shi Jauro Mai Maganin yankin kwana shi ake kira ba wani Magaji Bawa ba, ace shine shahararsa ta kai inda yake so kuma yake bukata, saurin cewa ya yi "Babu wani borin kunyar da za ayiwa mutane an dai cutar dasu! Wa inda aka kashe musu yara su ce mai? Sannan tunda daɗewa Magaji yasan yaransa Macizai ne amma ya boyewa mutane bai gaya musu dan yanzu yana da mugun nufi a ransa!" "Magaji baya da masaniya a kan cewa *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* taya idan ya sani har zai barsu su yi kisan kai!? Da kake maganar su na kisa Aziza bata taba kisa ba,akasari ma ita dabi'un Magaji ne tattare da ita, ku a tsammaninku da Azima ce har kwa fara yi mata abunda ku ka yiwa Aziza? Inaaa! Da kafin mu iso wlh sai dai gawawwakinku!" cewar Baffa Mandi, jauro ya ce "Owoohh! Kenan da saninku ma kamar yadda na faɗa! Jama'a kuna dai ji ko? An zalinceku an munafurceku an kashe muku! Kuma ta yadda zaku gane Magaji ya san yaransa Macizai ne shine basu zuwa bikin gargajiya ta al'adun fulani wanda ake gabatarwa duk shekara, sabida sun san a lokacin ana amfanin da magungunan macizai! Sannan......" "Ya isheka haka Jauro!!" Baffa ya katse Jauro jikinsa na rawa, ya tako ya zo gabansa ya ce "Da ace da sanina yarana macizai ne da tuni na dauki mataki wani zancan 7ake yi yanzu ba wannan ba, a da nace maka muddun ka gano yarana macizai ne nina maka lamuni ka kashesu! Amma tunda na gano cewa ku ɗin ba mutane bane dabbobi ne wanda shanu ma sun fiku hankali ko da Azima da Aziza sun dawo yankin kwana duk wanda ya yi gigin taba min yara a lokacin zan basu umarni su kashe min koma waye!! Sannan ka zuba ido ka gani, zan maida yarana mutane ko da kuwa hakan zaiyi sanadiyar mutuwata, a yau kuna zaginsu macizai kuna ci min mutunci, amma ku sani ko nace kai jauro ko sani, MAGAJI BAWA KAFIN ALLAH NE BA KAFIN MUTUM BA! KO DA ACE MISALI BANA RAYE! AZIMA DA AZIZA SAI SUNANSU YA BUGA TAMBARI A YANKUNA BA MA IYAKAR YANKIN KWANA BA! KAMAR YADDA NA MAHAIFINSU NI MAGAJI BAWA NAYI! NA MAKA WANNAN ALKAWARI! BAIWA DA FARIN JININMU DAGA ALLAH NE KA ZUBA IDO KA GANI JAURO!!!" Baffa na gama faɗi ya bar wajan tare da daukar Hajja suka yi gida yana tunanin tashin hankalin da Hajja zata farka da shi, da fari yara macizai yanzu kuma babu su ma kwata-kwata, amma ya zata yi dole su rungumi kaddara. Bayan Baffa ya bar wajan Sarki Chubaɗo ya kalli Jauro ya ce "Ka dai ji kunya wlh! Da ace nima tsoron kar nayi abun kunya ba wlh da yau a yanzu na koreka daga yankin kwana, ku kuma idan dai Jauro ne gaku ga shi,in dai ba a mutu ba to ba shakka ba a daina kallo ba, ba fata nake muku ba amma na tabbata akwai jarabawa,sannan Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wani abunda ya sameku karku sake kuce zakuje wajan Magaji ya taimaka muku! kuje wajan Jauro ya taimaka muku, wannan umarnina ne a matsayina na sarkin wannan yankin!! Idan kuma na ga akasin abunda nace mutum zai fuskanci mugun hukunci!" Chubaɗo na gama faɗi ya yi gaba ya bar su a tsaye a wajan, wasu jikinsu yayi sanyi inda nadama ta kamasu wasu kuwa zuciyarsu kamar busashshen itace!. 🍃🐍🍃🐍🍃🐍 Azima kwananta biyu tana tafiya kafin ta fito bakin titi, tana fitowa wani guɗa ta yi da dogon harshenta, duniya sabuwa! Tana nan tsaye a kan titi da lullubi tana tunanin hanyar da zata fara dosa, nan ta yanke shawara kawai ta bi dogon titi ta ga iyakar karewarsa, haka ta hau tafiya a tsakiyar titi tana murmushi, kamar daga sama sai ga wani mota ta yanko da gudu amma sai ganin yarinya ya yi tana tafiya akan titi sai horn yake danna mata amma a banza! Azima kuwa tunda farkon fitowarta kenan ba fahimta tayi ba, da kyar mutumin ya taka burki ya fito a motar gami da daka mata tsawa "keeeeeeee!!" wani tsayuwa Azima tayi tare da ware blue eye dinta, babu wanda ya taba mata irin wannan ihun, a hankali ta kara jan mayafinta ta rufe fuska sannan ta juya a hankali kanta a duke, mutumin kallon sama da kasa ya mata yana yatsine fuska dan ya ganta da shigar fulani ba mamaki irin kidahuman nan ne na jeji dan haka cikin izgilanci ya hau ta da zagi. "Ke wace iriyar bagidajiya ce da ana miki horn amma da shike kin fito a cikin jeji baki ganewa kwakwalwarki a toshe yake kina tafiya a kan titi banza ballagaza daƙiƙiya ƙidahuma tunkiya!!" hakika zagin ya soki zuciyar Azima, zaro ido ta yi tare da yaye mayafinta rai b'ace cikin hausar da babu sosai a kan harshenta ta ce "Ba dai tunkiya ba, sai dai *MACIJIYA!🐍**" ta faɗi tare da komawa macijiya ba ta jira ya gama firgita ba ta kai masa sara a wuya nan ya fadi kasa yana shure-shure,komawa mutum ta yi tana dariya ta ce "Kaina mutum na farko da na fara kashewa daga fitowata,hakan na nufin cewa zan sha jini da yawa kenan sabida mutanen cikin gari basu da ɗa'a,ni kuwa AZIMA MACIJIYA bana daukar wargi!" ta faɗi tana murmushin gefen baki ta leƙa cikin motar ta wargaza ta ga kuɗi ta kwashe duk da bata san amfanin me zasu mata ba, ta ci gaba da tafiya, ta yi tafiya sosai inda ta iske tasha wanda yake cike yake da jama'a a hankali ta ƙutsa kanta cikinsu tana ji ana ambatar sunayen garurruka, garin da taji ya mata masauki a kunneta shine *KANO TUMBIN GIWA KO DA MAI KA ZO AN FIKA!* murmushi ta yi ta kara nanata KANO ranta, sannan ta afka mota ta nemi can baya ta zauna tana murmushi yau burinta ya cika ta bar yankin kwana. Kuɗi aka fara karba aka zo kanta, ana cewa kawo kuɗinki nan kuwa ta cire ta miƙa ba tare da tayi magana ba ko tasan nawa ta bayar ba,duk da zuciyarta na raya mata da sun isa kanon da zasuje zata kashe mutanen da suke motar!. Bayan yan wani lokaci ƙalilan mota ta tashi daga tasha ta hau tafiya, inda Azima ta ji ta gaji dan gani take yi motar bata mata sauri,amma ance biyan bukata yafi dogon buri dan haka ta kara rungume hakuri. Basu da isa kano ba kuwa sai magriba, ganin tsananin girma da faɗi da cikowa irin na garin kano yasa taji ma ta fasa kashe mutanen da tayi niyyar kashesu, ta shagala da kalle-kalle ta ji ana mata magana ta bayanta "Barka dai 'yar fulani" 🍃🍃🍃🍃🍃🍃 😭😭😭😭 Yau baƙin ciki ne a raina sau biyu ina cin uban typing yana gogewa, Allah dabadin bana son nayi missing update ba da ɗiff zaku jini😭 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️==2️⃣9️⃣↪️0️⃣3️⃣0️⃣ Ko da Salti ya isa gida ya kwashe kaff yadda yaji su Sarki Chubaɗo da mai Unguwa Ori suka tattauna ya gayawa Baffansa, a hankali Jauro ya mike yana murmushi ya ce "Salti,tun da kake kwaso gulma baka taba kwaso mai amfani ba sai yau, jeka dole nayi maka kyautar shanuwa daya" da sauri Salti ya miƙe yana murna ya fice,Jauro ya dungule hannu yana dukar iska ya ce "Lokaci ya yi da zan fatattaki Magaji Bawa, ka fi ni a komai kyau,martaba,baiwa,kyakkyawar mata Jumala,ga kuma yara kyawawa! kai kana gani ka fi kowa ne! zargin da nake yiwa yaranka ya tabbata, wato ma har b'oye-b'oye ake yiwa mutane ana munafurtarsu kar a gaya musu gaskiya, to ni nan zan bayyanawa jama'a su waye Azima da Aziza!" ya faɗa yana murmushin mugunta. 🍃🍃🍃🍃 Kamar yadda Malam Shadi ya faɗa da daddare ne ya yi bincike mai zurfi dangane da matsalar su Azima da Aziza,inda ya hangi gagaramin matsala mai rikitarwa inda tausayin yaran ya kamasa dan kuwa da wuya a samu maganin warakarsu. Da washe gari bayan sun idar da sallar asuba ana gaggaisawa bayan sun gama gaisawa Malam Shadi ya kalli Baffa sai kuma ya duƙar da kai, Baffa ya yi murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo ya ce "Malam Shadi karkiji komai gaya min ko ma miye ne,ni musulmi ne kuma nayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, ka gaya min kawai" Jinjina kai Malam Shadi ya yi ya ce "Tabbas ni shaidan hakane Magaji, wato a gaskiya ba zan boye maka ba, samun lafiyar Aziza yana tattare ne da Azima, domin kuwa wanda yake da alhakin abun ya ja Azima basu yankin kwana balle a musu magani, kai ko da Azima bata bar yankin kwana ba da wuya a samu wanda zai yi jahadin taimaka musu" goge gumi Baffa ya yi ya ce "Malam Shadi ka gaya min kai tsaye kawai zan fi ganewa,dan a yanzu ji nake kamar kirjina zai tsage zuciyata ta faɗo kasa" Malam Shadi ya gyara zama ya ce "Dole sai sunyi aure kafin Banju ya rabu dasu, barin ma Azima ita ce wacce take bukatar taimakon gaggawa, sannan wannan miji da zai auresu sai ya sadu da Azima kafin Banju ya fita a jikin Azima, idan Banju ya bar jikin Azima a cikin kaso dari mun yaƙesa kaso sittin, idan aka yi sa'a idan Banju ya fita a jikin Azima, Aziza zata iya samun lafiya,idan kuma bata samu ba ita ma dole sai wanda ya aureta ya kusanceta kafin makarin sihirin da Banju ya mata na siddabarun maidata macijiya ya karya" "Ma'asabamun musibatin Qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Innallahi wa inna ilaihirrajiun! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" shine abunda Baffa da Baffa Mandi da Arɗo suke iya nanatawa suna fifita da hannunsu,Arɗo ya girgiza kai ya ce "Tabdijam kawai Allah ya jikan Azima da Aziza, dan kuwa na tabbata babu namijin da zaiji cewa su macizai ne ya taimaka ya auresu har mu sa ran zasu samu lafiya" "Kuma dole wanda zai aure su zai fuskanci ƙalubale kafin ya kusancesu,sannan bayan ya kusancesu zai iya kamuwa da mugun ciwo amma ba ina nufin ba zai warke ba amma tabbas zaiji a jikinsa,idan an samu damar hakan zaka iya kara kashe Banju a karo na biyu" hawaye ne Baffa ya hau yi yana kan tasbihi ga Ubangijin talikai, Baffa ya ce "Tabbas da ace na dinga ganin tashin hankalin nan na b'arna da ta'adin da Azima ke yi da ni da kaina zan kasheta! to amma yanzu tana ina? Me take yi? Su wa da wa zata kashe!? Akwai tambayoyi dayawa a raina wanda babu wanda zai amsamin" Baffa ya hau kuka Arɗo da Baffa Mandi suna rarrashinsa, Baffa Mandi ya kalli Malam Shadi ya ce "Malam Shadi, yanzu ya maganar raba Aziza da Bahula?" "A gaskiya Mandi ni a ganina a shawarce, kar a raba Aziza da Bahula, tinda bata cutar da ita, sannan ko an raba Aziza da Bahula Aziza fa ba zata taba komawa mutum ba, ni a ganina tunda Banju yana son kanwarsa Bahula sannan yasan cewa tana rayuwa a jikin Aziza dole wata rana zai dawo, karku manta kamar yadda Azima da Aziza suke 'yan biyu haka ma Banju da Bahula suke 'yan biyu, zamu iya samun dawowa da Azima gida ta hanyar Bahula dake jikin Aziza,ni a ganina kar a raba Aziza da Bahula a barsu tare idan ya so aka samu wanda zai yi jahadin aurensu bayan an raba Azima da Banju sai a raba Aziza da Bahula" "Tashin hankali wanda ba a sa masa rana" cewar Arɗo yana kan rarrashin Baffa dake kuka wi-wi, da kyar suka rarrashi Baffa ya samu ya tsaida hawayen idonsa sannan ya miƙe yana yiwa Malam Shadi godiya ya ce masa zasu wuce yau, Malam Shadi ya ce "Ba damuwa Magaji,karka damu Allah zai shiga cikin lamarin" Baffa bai iya ya kara cewa kala ba, Malam Shadi ya miƙa masa wani ganyen magani ya ce "Wannan idan ka je ka haɗawa Aziza,ita kuma Azima Allah ya dawo da ita cikin gaggawa, bari nasa a kira muku Azizan sai ku wuce" su Baffa Mandi da Arɗo suka yiwa Malam Shadi Godiya sannan suka fito a tare,bayan an kira Aziza ta fito Baffa ya kama hannunta idonsa jajur ya ɗorata a kan doki, Aziza tunda ta ga yanayin Baffanta tasan cewa kwai gagarumin matsala, haka sukayi sallama da Malam shadi cikin amince suka kama hanyar yankin kwana. 🍃🍃🍃🍃🍃 Sai da lokacin sallar azahar ya gauta kafin suka iso yankin kwana kai tsaye gidan Arɗo suka nufa, Hajja na zaune tayi zugum Yawuro ta ajiye mata kwaryan nono a gabanta amma haka nonon ke kallonta, Yawuro ke fadin "Haba Jumala! Dan Allah ki sa wani abu a cikinki mana, ga jikinki da zafi, kiyi hakuri mana haba dan Allah" hawaye Hajja ta goge ba tare da ta cewa Yawuro Uffan ba, sallamarsu Baffa ne yasa Hajja ta dago da sauri ta sauke idonta a kan Aziza da ta shigo kanta a sunkuye, duk irin kunya na Hajja amma da sauri ta tashi ta rungume Aziza wacce itama ta saki kuka take ji a ranta da ace kisan kai ba haramun bane babu abinda zai hanata bata sha guba ta kashe kanta ba, kuka sukeyi sosai sai da Inna wuro ta dakatar dasu, sannan Inna wuro ta hau tambayarsu ya suka yi a can yankin ja'o ɗin, Baffa Mandi ya ce "babu amfanin a boye muku, gwara a gaya muku gaskiya" Ardo ya ce "tabbas dan wannan ba abun boyewa bane" nan Arɗo ya kwashe yadda suka yi da Malam Shadi ya gaya musu, wani mahaukacin zare ido Aziza ta yi jin bala'in da suke ciki wai sai sunyi aure an sadu dasu kafin su warke! Wa ma zai auri macizai!? Barin ma wanda zai auri Azima ya ji labarin kisan da Banju ya yi tayi a jikinta ai ma babu mai aurensu,in kuwa dole sai hakane sun zama annoba a cikin jama'a barin ma yanzu da Azima bata nan. Sallallami su Inna wuro da Yawuro suke yi suna tafa hannuwa yayinda Hajja ke girgiza kai tana fadin ita a maido mata da yaranta tana wani irin kuka, Arɗo da Baffa Mandi suka ce Baffa yazo su je wajan Sarki Chubado da mai Unguwa Ori su gaya musu halin da ake ciki, a tare suka fita aka bar Hajja da kuka ita da Aziza, su Inna Wuro suna rarrashinsu. @@@@@@ Bayani dalla-dalla suka yiwa su Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori yadda Malam Shadi ya shaida musu, Sarki Chubado ya ce "Tashin hankali, gaskiya Banju ya mana illa dayawa, amma ina da shawara mai zai hana a gayawa mutanen gari halin da ake ciki, idan ya so sai a nemi wanda zai auresu ko da ba zai zauna dasu ba dai da sun samu lafiya sai ya sake su!" "Nima na fara wannan tunanin a raina ranka ya dade,amma abun dubawan a nan shine wa zai auresu?" cewar mai unguwa Ori, tattaunawa suke yi sosai ta yadda za a shawo kan matsalar amma duk inda aka dafa babu mafita, su na nan suna kan shawara sai ga Sanda da mugun gudu kamar wanda yake gudu a iska yana zuwa gabansu sarki Chubaɗo ya zube yana haki, Sanda jika ne ga Yawuro, Arɗo ya ce "Sanda mahaukacin ina ne kai? Wannan gudu da ka zo a haka sai kace an kawo mana farmakin yaƙi miye haka? Meke faruwa?" kasa magana Sanda ya yi illa hanyar gida da yake nunawa da kyar ya furta "ADDA AZIZAAA!!" da sauri Baffa ya ce "Me ya samu Azizan?" ya fada yana miƙewa tsaye, Sanda ya ce "Baffa Jauro ne ya gayyo duka mutanen yankin nan wai zasu kashe Adda Azima da Adda Aziza wai macizai ne sune suka dinga kashe-kashe sune suka kashe su Ilu mai maganin Maciji dasu Jarman Macizai da Innu Maciji, yanzu haka ma sun saka wuta a gidan Arɗo ƙarami" da sauri su Chubado suka miƙe suna salati tare da al'ajabin ina Jauro yaji wannan maganar? Baffa Mandi ya ce "Kafff yankin kwana da kewayenta babu munafuki sarkin gulma sama da ɗan Jauro Salti, to amma taya akayi ya ji wannan maganar?" Sarki Chubaɗo ya ce "Yanzu babu lokaci maida magana muje kar su kashe Aziza" da gudu Baffa ya yi gaba idonsa har yana rufewa, ya rasa matsalar dake tsakaninsa da Jauro,bai san me ya tarewa Jauro ba a rayuwa da baya sonsa baya kaunarsa sam. Ko da su Baffa suka isa, sun samu gidan Arɗo karami na ci da wuta, ga Hajja a sheme a kasa an fasa mata kai, Aziza kuwa sun ɗaureta a jikin bishiya sai dukanta suke yi duk sun fasa mata jiki, a ranta take kalman shahada dama su kasheta kawai ta huta da wannan rayuwar, ihuuu Baffa ya yi ganin matarsa kwance a sheme a kasa an fasa mata kai ga 'yarsa da aka yi mata daurin mayu ana dukanta, ihun da Baffa ya yi yasa hankalin jama'a dawowa kansa, Jauro ya yi murmushin gefen baki kafin ya matso kusa da Baffa yana magana yana daga murya "Hakika bai kamata ace daku za a haɗa baki a munafurci mutanen yankin nan ba, (yana yi da sarki chubaɗo da mai unguwa ori) sannan kai kuma Magaji idan ka manta na tuna maka,kaine kace min duk ranar da na gano *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* kaine wanda zaka bani takwabin da zan kashesu! Dan haka yau sunan Aziza gawa,ita ma Azimar da ta bar yankin nan da ace tana nan da yau gunduwa-gunduwa zamuyi musu" murmushi Baffa ke yi hawaye na zuba a idonsa yana yiwa Jauro wani irin kallo wanda ko idonsa baya kiftawa, Jauro ya kuma cewa "Shin zaku yarda ku rayu da macijiya mai kisa a cikinku?" jama'a suka amsa da a'a, Jauro ya kuma cewa "Idan kuwa hakane ku ci gaba da dukanta har sai ta mutu!!" Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suna dakatar da jama'a amma ina kamar kara ingizasu akeyi, wani ne da ya daga wani babbar sanda ya roɗawa Aziza a kai jikake kwasss!! Wani ihuuu Baffa ya kuma yi ganin yadda sandar ta shigi Aziza dan har sai da ta girgiza, Baffa ya kalli Jauro cikin jan ido ya ce "Karka bari na nuna maka waye asalin Magaji!!" "Zan so hakan" Jauro ya fadi yana dariya, ci gaba da dukan Aziza mutane suka yi, wani gurnani Baffa ya yi mai taken muryan zakin dawa, sannan ya rintse ido ya haɗa wani guguwa mai cike da barkono ya kwashi jama'ar da suke dukan Aziza ya watsar dasu, a take ya yi tsalle daya yaje gabanta yasa hannu ya shafe igiyar da suka daureta igiyar ta tsinke, sannan Baffa yasa hannu ya shafe mata inda suka ji mata ciwo ya kamo kafadunta cikin daga murya ya ce "AZIZAAA!! NA YARDA DA KEEE!! INA SO NE KI BAR YANKIN NAN!! BANA SO SU KASHEKI ALHALI 'YAR UWARKI TA BAZAMA GARI! INASO KIJE KI NEMOTA SANNAN KI DAKATAR DA ITA,IDAN HAR KU KA HADU KIKA GA B'ARNARTA YA YI YAWA NA MIKI IZINI KI KASHETA ITA DA BANJU!! IDAN KUMA KE MA TAKI TA ZO KARSHE DAMA BA ZAMA MUKA ZO YI BA,IDAN KUMA KIN SAMETA KU DAWO! NINA SAN TA INDA ZANYI MAGANIN BANJU!! AZIZA TAFIIIII!!" girgiza kai Aziza tayi tana wani irin kuka alaman ba zata iya tafi ta bar Hajja da Baffa ba, rai b'ace Baffa ya kara cewa bar yankin nan na ce Azizaaaa!! da gudu Aziza ta yankin jeji dan barin yankin kwana, Jauro ya yi yunkurin binta Baffa ya ce "Kana bin bayanta zan mata umarni ta kasheka! Ka godewa Allah Aziza ce ba Azima ba ce! Da sunanku gawa gaba daya!! Ni zaku yiwa haka! Sabida su waye yanzu nake fuskartar wannan bala'in!!?" 🍃🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN CE✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *ASSALAMU ALAYKUM, SAKO ZUWA GAREKU MASU FITAR MINI DA BOOK DA MASU KARANTAWA BASU BIYA BA, DA WA INDA SUKE GANI SUKE KARA WATSATA A DUNIYA,DA FARI ZAN FARA DAKU MASU FITARWA DAN BABU MASU LAIFI SAMA DA KU! HAUSAWA SUKA CE SAI BANGO YA TSAYE KAƊANGARE K......! DAYAWANKU WASUNKU SUN JAHILCI WANNAN LAMARIN NA CEWA WAI KUDINSU SUKA CIRE SUKA BIYA YA ZAMA NASU MALLAKINSU, YAR UWA TA INA LITTAFI YA ZAMA NAKI? LITTAFI HAKKIN MALLAKAR MARUBUCIYA CE ITA DA TA ZAUNA TA TSARA LABARINTA SANNAN TA RUBUTA TA WALLAFASHI TA WATSA SHI HAR KIKA KARANTA SHI,KE KIN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI,KI KARANTA KI BAR WA MARUBUCIYA ABUNTA, KUNA FADIN YANZU MISALI KUJE KASUWA KU CIRE KUDI KU SIYI ABUN SAI ACE MUKU KARKUYI KYAUTA DA SHI KO KU BADA ARO? TO INASO KI SANI AKWAI BAMBANCI TSAKANIN ABU A ZAHIRI DA SOCIAL MEDIA, YANZU NE AKA SAMU CI GABA KINA DAGA KWANCE A DAKI BA SAI KIN SHA WAHALA BA KINJE KASUWA KIN SIYO LITTAFI BA, A DA KAM WA INDA SUKAYI KARANCE-KARANCE SUN SAN TSADAR LITTAFI DARI BAKWAI DARI TAKWAS KAI HAR DUBU DAYA, SANNAN MIYE RIBARKI FISABILILLAHI DAN KIN CIRE DARI! NAIRA DARI KIN BIYA KUDIN KARATUN LITTAFINA SANNAN KI DAUKA KI WATSAWA MUTANE SAMA DA DUBU DARI DA BASU BIYA BA? ANYA KUWA AKWAI ADALCI A LAMARIN? DUK TALAUCIN MUTUM MAGANA TA DOMIN ALLAH ZAI CE BAI DA NAIRA DARI DA ZAI BIYA YA KARANTA LITTAFINA NE? BAN TSAULAWA BA SABIDA NA SAN KUNA SON LITTAFIN SHIYASA BANSA TA YADDA BA ZAKU IYA BIYA BA, WLH WLH WLH AZIM DA ACE KUN SAN WAHALAR RUBUTU KO A SHAFI DAYA ZAKU DINGA BA WA MARUBUCIYA DARI BIYAR A DUK SAKIN PAGE WLH BAKU BIYATA BA, BALLE KUMA NI DA NA ZAUNA NA TSARA MUKU LABARI NA CE KU BADA NAIRA DARI KACAL! YAKE MAI FITAR MIN DA LITTAFI INASO KI SANI HAKKINA NE,KUMA DUK HAKKIN DA KA RAINA SHI KE GIRMA YA TSOLE MAKA IDO, IDAN HAR BA ZAKI DAINA TOZARTANI BA TA HANYAR WATSA MIN LITTAFI BA TO INASO KI SANI BA ZAN MIKI ALLAH YA ISA BA, AMMA SHURUN DA NAYI WLH SAI ALLAH YA SAKA MIN, MASU CEWA SAI SUN SATO KUMA SAI SUN KARANTA ALLAH YA BAKU SA'A, A AL'ADANCE SATA SUNANTA MA BABU DADI BARE A ADDINANCE HARAMUN NE! SANNAN WANNAN ALLAH YA ISAN DA KUKEJI MARUBUTA NA FADI BA KARAMAN KALMA BA CE WLH,KE IDAN KINA DA TUNANI KI ZAUNA KIYI NAZARI A KAN KALMAN ALLAH YA ISA! SANNAN NA DAWO KANKU MASU KARANTAWA HARDA TAMBAYAR CI GABA,IDAN HAR KINA KAUNAR ALLAH KINA GANIN GIRMAN DARAJAN ANNABI MUHAMMADU SALALLAHU ALAIHI WASALLAM! KI DAINA KARANTA MIN LITTAFI BAKI BIYA BA,KI NEMENI TA LAMBATA KI BIYA NA SAKAKI A PAID GRP DINA IDAN KUMA KIN SAN ZAKI BIYA NE DAN KI WATSA SHI DAN ALLAH BA SAI KINZO GARENI BA🙏🏻, HAKA KEMA MAI YADAWA DUNIYA INA ROƘONKI DA GIRMAN ALLAH DA DARAJAN IYAYENKI KI BARI! BAKI SIYA BA AMMA IDAN KIKA GANI JIKINKI NA RAWA KI TURAMA WASU KEMA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA, ALLAH YA BAKU IKON FAHIMTAR ABUNDA NA FAƊI, WA INDA BASU SON SU CI HAKKI SAI KU NEMI NAKU!* *PAID.* 🅿️==3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣ Cikin gari ya nufa inda ya kaita asibiti mafi kusa, yana shiga ya ce a bata taimakon gaggawa,inda wasu nurses suka hau masa iskanci a kan ba zasu karbeta ba, hannu yasa a aljinun wandonsa ya ciro wallet dinsa ya bude ya ciro ID Card dinsa ya nuna musu, suna gani suka hade gefe suna sorry sir, ya ce "Baku da tausayi ko kaɗan! haka ku ke yiwa jama'a da haka idan yazo da ƙaran kwana sai marar lafiya ya mutu amma kune sanadi! An san likitoci da tausayi dan haka ku gyara,ina mai wannan asibitin ina son magana da shi idan har yana kusa" jiki na rawa suka ce bari su nuna masa office din, har bakin kofar office ɗin suka kaisa, ya kallesu su biyu ya ce "Ku fara duba yarinyar nan kar ta mutu ina zuwa bari nayi magana da shi zan zo nayi mata dressing da kaina" "Ok sir" suka fadi shi kuwa ya shiga ciki da sallama. Amsawa wanda aka yiwa sallama ya yi, ya kalli wanda ya masa sallamar ya ce "Bismillah ƙaraso ga waje zauna mana" ƙarasowa ya yi cike da jin kansa ya zauna,sannan ya miƙawa Dr din hannu suka gaisawa, Dr din ya ce "Amma ban gane ka ba daga ina? sannan baka yi kama da marar lafiya ba" murmushi ya ɗan yi na gefen baki, sannan ya miƙa masa ID dinsa,yana dubawa ya kallesa ya ce "Doctor?" ya yi murmushi yana gya ɗa kai, tashi ya yi da sauri yana fadin "Allah dai yasa sa'a ce ta sameni har office zaka fara aiki a hospital dina" shi ma tashi ya yi tsayen ya ce "A'a ko ɗaya wlh,ai ni ba a nan yola nake da zama ba,ina zama a kd ne akwai aikin da ya kawoni ne,tun jiya ma ya kamata ace na bar yola to ashe tsautsayi ne ya tsayar dani dan na buge wata yarinya ne da mota shine na kawota asibitin,inaso nayi treatment dinta sai mu wuce dan bana so na ƙara kwana a garin nan" "Ya Subhanallah! tana ina yarinyar? muje sai ka dubata ai ba komai" ba tare da ya sake magana ba ya bi bayan Dr har izuwa dakin da aka kwantar da Aziza, suna shiga ya hau dubata ya ga bata mutu ba, kayan aiki yace a ba shi ya fadi abubuwan da za a ba sa aka kawo masa sannan ya hau dubata,ya mata su allurai ya sakawa kanta bandage ya mata komai sannan ya ɗora mata ruwa, ya duba agogon dake daure a hannunsa ya ga sha ɗaya, ya kalli Dr ya ce "Tnk u so much Dr on my way" ya faɗi tare da kokarin daukar Aziza, Dr ya ce "Haba Doctor ka bari mana ko zuwa gobe sai ka wuce idan ta farka,ga shi kace baka santa ba,duk yadda akayi inaji irin fulanin rugan nan ne, yanzu idan ka wuce da ita kd alhali ba yar kd ɗin ba ce fa?" shuru ya yi yana nazarin maganarsa kuma gaskiya ne tunda a nan ya sameta miye hujjarsa na tafiya da ita? Kawai ya barta idan ta farka taji sauki sai su sallameta ta koma inda ta fito, da wannan tunanin ya ce Dr ɗin ya ba shi acct number ya masa transfer'n kuɗi ya kula da ita idan ta warke sai su sallameta,haka kuwa aka yi bayan ya masa transfer ɗin nan ya fito da sauri ya shiga mota ya tayar yaja ya bar asibitin, har ya fara tafiya ya ɗan yi nisa sai yaji hankalinsa bai kwanta ya tafi ya barta ba,ko ba komai shi ya bugeta sannan bata farfaɗo ba ya tafi ya barta anya ya kyauta kuwa? Saurin juya kan motar ya yi ya koma asibitin, yana zuwa ya ce a ba shi ita kawai, Dr ya ce "Haba Doctor baka yarda damu bane?" "No ba haka bane ba wai ban yarda daku bane,kawai ban yarda da shawaran da zuciyata ta bani bane na in tafi in barta alhali ban san a wani condition zata farka ba that's why, amma yanzu zan tafi da ita,idan ta farka lafiya taji sauki zan sa a maidata gidansu" da haka yasa hannu ya dauketa tare da drip ɗin da ya ɗora mata, har yanzu tana bacci, ya gyara bayan motarsa ya kwantar da ita ya ajiye drip ɗin a gefenta yana duba agogo tare da auna tym din da ruwan zai ƙare" da sauri yaja motar yanayi yana duba tym. 🐍🐍🐍🐍 Horn ta yi a wani madaidaicin gate da sauri gateman ya zo ya buɗe yana zuba mata kirari, hannu ta daga masa sannan ta danna hancin motar cikin gidan,tana parking ta fito tana fitowa ita kam ma ta manta da ta saka mutum a bayan both cikin gida ta wuce tun kafin ta shiga take kwalawa Lantana kira, da gudu wata 'yar dattijuwar mata ta fito ta zube a gabanta ta ce "gani *Hajiya Zubaida*" "Oh dan iskanci dama kinaji ina ta faman kwala miki kira amma ba zaki iya amsawa ba sai dai ki wani fito da mugun gudu sai kace ana gasan tsaren karnuka, ki fa kiyayeni kiyi hankali!, ina Hajiya?" "Tana ciki" "Hajiya! Hajiya! Hajiya!" ta hau kwalawa Hajiyan kira. An ɗau kusan mintuna uku kafin Hajiyar ta fito tana hamma tana matsa ido alamun bacci take yi kiran Zubaida ne ya tayar da ita "Zuby me ya faru?" Zama ta yi tana fadin "Wlh Hajiya sai na ci uban baban mai aikin nan, kin san wai har da kai karar mu police station wai mun yi 'yarsa duka a bi masa kadi" "To yanzu ya aka kare?" Hajiya tana tambaya tana zama kusa da inda Zubaidan ta zauna,ta ce "Na basu kudi nayi gaba abina,kee! Lantana kawo min ruwa mai sanyi" tashi tayi da sauri tana fadin to, sannan Zubaidan itama ta tashi ta shige wani daki wanda yake nuni da nata ne, kaya ta shiga canzawa ta ga ko gyara mata dakin ba a yi ba, da sauri ta cire na jikinta ta watsar dan haka dabi'unta yake, ta saka wani riga iyakarsa guiwarta sannan ta fito tana masifa tana zama "Haba Hajiya ashe ba a gyara min bedroom dina ba?" "To Zuby wa zai gyara? Masu aikin duk sun gudu sai Lantana ce kawai ita kuma aiki ya mata yawa" tsaki ta ja tana shirin faɗin yanzu wa zai gyara mata daki sai ta tuno da ta sa mutum a bayan mota, tashi tayi da ɗan sauri tana fadin "Wayyo na manta da wan can bagidajiyar bafulatanan" a haka ta fita riga iya guiwa kai babu ɗan kwali sai uban attachment, Azima kuwa tana kwance a both a macijiya hankalinta kwance tana bacci, jin kara ne ya sakata buɗe ido tayi saurin komawa mutum,tana zama mutum tana bude both din ta kalleta a wulakance ta ce "Fito" a hankali Azima ta fito tana gyara mayafinta tana tafiya tana lankwasa kamar yadda take tafiya a yankin kwana. Shiga parlourn sukayi, Zuby ta ce "Hajiya naji dama kina neman mai aiki to gata nan, a hanya na tsinceta, sai ta ɗora da aikin da Kuluwa ke yi" Hajiya ta kalleta tana toshe hanci ta ce "Ya sunanki?" "AZIMAA!" ta faɗa da kaushin murya dan duk tana kula da yatsine fuska da toshe hancin da Hajiya ke yi. "To dubu biyar zamu dinga baki a duk wata, zaki dinga share-share da goge-goge,inada yara guda uku, ga Zuby nan akwai Yayarta mai suna Baby sai kuma Babban ɗana namiji yayansu kenan, sunansa Munir dik basu nan sun fita idan suka dawo zaki gansu, ke ce zaki dinga gyara musu bedroom dinsu!" Azima dake duƙe ta ce "Hajiya miye shi badorom din?" Zuby ta ce "Hajiya ƙidahuma ce daga jeji take taya zaki mata turanci,keee Bagidajiya ana nufin daki,nasan bukka ku ke kira a can jejinku" cije baki Azima ta sake yi, jin yadda zuciyarta ke tafasa idan bata tashi ba komai zai iya faruwa,hannunta ta kalla ta ga ya fara sab'ulewa yana zama blue saurin ajiyar zuciya ta koma yi dan zuciyarta ta yi sanyi, Zuby ce ta sake kwalawa Lantana kira ta amsa da ta zo tace mata ta tafi da Azima ta nuna mata yadda zata yi wanka ta bata wasu kaya da turare dan Azima na wari,sannan idan ta nuna mata ta taho ta saka musu turaren wuta, Lantana ta amsa tana kamo Hannun Azima suka shige daki, suna shiga Hajiya ta ce "To ita haka zata dinga rufewa mutane fuska a gida?" "Hajiya manta da wannan kin san bata taba shigowa birni ba,dan haka bata waye ba" "Kuma hakane fa" cewar Hajiya, Zuby ta ce "Wai ina Munir da Baby suka je ne?" "Wa ya san musu" share zan can suka yi suka kamo wata hirar, da Lantana suka shiga daki ta kalli Azima ta ce "Baiwar Allah zauna ki jirani kinji bari naje na saka musu tiraren na dawo" ta fita da sauri, buɗe ido Azima tayi tana fadin "Babu wanda ya isa ya zageni ya tafi a banza ba tare da nayi masa hukunci ba! Babu shi!" ta faɗa tana lankwasa yatsun hannunta, an dauki mintuna sha biyar kafin Lantana ta shigo, ta ce "Azima ko?" Azima ta sunkuyar da kai tana fadin "E" a sanyaye kaman wata ta kwarai, Lantana ta kama hannunta suka shiga bayi,ta haɗa mata ruwan wanka ta dauko soso da sabulu da shampoo dan ta ga tana da ga shi mai tsayi, ta ce "Na wanke miki kan naki naga gashin naki da tsayi sosai" Azima ta gyaɗa kai, Lantana ta bata fallan zani ta ce ta cire na jikinta ta ɗora, ba musu Azima ta cire kayanta ta ɗora fallan zani lantana ta jiƙa mata kayan a ruwa tace zata wanke mata su, sannan ta bata kujera ta zauna, Lantana na fara kwashe gashin Azima tayi saurin lumshe ido dan bata son Lantana ta ga kwayar idonta. Shampoo sosai Lantana ta zuba a kan Azima amma ta ga idan har ta juye ba isa wanke mata kai zaiyi ba, haka yasa ta dauke ledar omo sai da ta zuba ya kai kwankwani ɗaya da rabi kafin ta fara dirzan kai Azima wanda yake fitar da datti, sun kai mintuna talatin tana wanke mata kai kafin gashin ya fito baƙi da shi ga tsamtsi yayi fess! Lantana ta yi murmushi ta ce "To kiyi wanka,bari na baki waje" har Lantana ta kai bakin kofa sai ji tayi Azima na faɗin "Miyatti Inna" karo na farko da ta fara yima wani ɗan adam godiya a rayuwarta, murmushi Lantana ta yi ta fice, sai a lokacin tunanin 'yan yankin kwana ya faɗowa Azima a rai,dariya ta hau yi tana fadin "Ko ina Macijiya Aziza sarkin tausayi oho! Watakila sakaran tana can an kasheta a jeji! Ko da yake ba zasu iya kasheta ba! Amma nasan shanuwar tana can suna jibgarta" ta karasa maganar tana haɗe rai, wanka ta yi sosai ta dirje jikinta ta fito, sai da jikinta ya bushe ta kuma saukowa da gashin kanta kafin ta fito ta samu Lantana ta ajiye mata fallan zani da t-shart da su mai da turare, kayan ta saka, sannan ta dauki kum ta sharce gashin kanta ta zubo da wanda yake rufe masu gefen fuska sabida kar ana ganin kwayar idonsu, gashin ya sauko har ƙirjinta, kallon kanta ta yi a madubi ta ga ta yi kyau,murmushi ta yi, sai ga Lantana ta shigo "Wa Subhanallahi bi'ahsanul Khaliƙin!" cewar Lantana Azima ta sunkuyar da kai, Lantana ta ce "Zo muje na nuna miki ayyukanki" Azima ba ta kuma magana ba ta bi Lantana a baya, nunnuna mata komai Lantana ta yi har da dakin Baby da dakin Munir, Azima ta ce ta gane, sannan Lantana ta ce "Yanzu ki fara gyara dakin Munir dan bai da mutunci ko kaɗan duk wulakanci Baby da Zuby suna bin bayan Munir ne, idan ya dawo ba a gyara masa daki ba ya ganki ba zaiyi la'akari da cewa ke sabuwar zuwa bace ya yi ta kwallo dake" "DA KUWA KO ƘASHINSA BA ZAN RAGE BA!" Lantana ta ce "Iyeeee!!?" sauri saita kanta Azima ta yi ta ce "Inna je ki kawai zan gyara yanzu" fita Lantana ta yi,Lantana na fita Azima ta bi lafiyar gado ta kwanta dan tayi wanka mai dadin da bata bata yi ba taji bacci takeji. 🍃🍃🍃🍃 Karfe sha daya saura ya shigo kd bai wuce gida ba ya wuce asibitinsa da ita, har yanzu kuma bata farka ba,bai damu ba tunda ya mata alluran bacci mai karfi ne, bayan ya mata komai ya ba wasu nurse mutum biyu kula da ita wanda zasu yi nyt duty, kafin ya wuce gida. A wani katafaren gate yayi horn da sauri aka zo aka buɗe masa, ya shiga ya yi parking din motarsa, da fari ji ya yi kamar ya shige part dinsa dan ya gaji,amma kuma gwanda ya shiga ya yiwa Mom sai da safe, da wannan tunani ya yi babbar parlon nasu da sallama,kanwarsa Sultana tana zaune wacce ba zata wuce 18 ba tana kallon wani horror seris film tana jin sallama ta miƙe da gudu tana fadin "Oyoyoo *BROS NAWAZZ!"* 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *INA GAISHEKU KYAUTA YAN PAID GRP MASOYAN........BAN DAI KARESA BA KU KARASA DA KANKU* *PAID.* 🅿️==3️⃣3️⃣↪️3️⃣4️⃣ Saurin juyowa Azima ta yi ba tare da ta dago ba Ya yi murmushi ya CE "Yan mata magana nakeyi fa" da sauri ta matsa gefe ta hau tafiya tana sake rufe fuskarta, shi kuwa binta ya hauyi yana kan yi mata magana,da ya ga ba zata tsaya ba ya sha gabanta, cije baki Azima ta yi tana hade rai,babu abunda ta tsana kamar a sha gabanta,Cikin murya da yake nuna taji haushin takura mata da yayi tace "Malam wai lafiya?" Dariya ya hau yi jin yadda kalar Hausar ta ta ke fita, a ransa yake fadin "wow! Wannan daga ganinta bagidajiya ce daga jeji take,bari nayi mata wayo, ko Allah zai sa na shana da ita daga dawowata!" "Amm yi hakuri ba nufina na ɓata miki rai ba,naga yadda kika ta kalle-kalle ne kamar baki san kowa ba, shine nake so na taimaka miki" ya karasa maganarsa yana murmushi, itama Azima murmushin ta yi ta ce "To taimakona da me? ko nazo nace da kai inada bukatar taimako ne iyee!!? Na ce maka ina da bukatar taimako ne?" "Allah ya huci zuciyarki sarauniyar kyawawa, Kano gari ce mai girman gaske da faɗi kuma ke naga alama kamar baƙuwa ce, dan haka ki yarda na taimaka miki naga ke mace ce,ki zo muje gidanmu" mutuwa da mamaki Azima ta yi ko me ta tuna ta yi murmushi ta ce "Na gode da taimako muje" "Ina kayan ki?" "Wala!" Ta ba shi amsa hankalinta yana can wajan kalle-kalle, jakarsa da ledarsa ya dauka ya ce "Muje" ya yi gaba ta bisa a baya, kekenapep ya tare musu suka shiga, wani farin ciki ne ke mamaye zuciyar Azima sai magana yake mata amma ina hankalinta ya yi ƙololuwa wajan ganin girma da faɗi da cikowa irin na NA DABO TUMBIN GIWA, ana cikin tafiya sai ji ta yi kekenapep din ya tsaya sai a lokacin ta maido da dubanta ga wani ƙazamin gida wanda ko bukkarsu na yankin kwana ya fi sa kyawun gani, bata damu ba, yayinda ya ce mata ta fito a keken, ba musu kuwa ta fito tana kallon mutanen da suke zaune a kofar gidan masu caca da masu shan wiwi da sigari har ma da masu shan giya, jin yadda ta hadiyi hayakin sigari da wiwi yasa ta hau tari kadan-kaɗan tana yamutse fuska, mai kekenapep ya biya sannan ya kalleta ya ce "Mu shiga ciki ko?" ya yi gaba ta bisa a baya mutane sai kallonsu suke yi har suka shiga,suna shigewa a cikin wa inda suke zaune a kofar gidan wata mace tayi shigar riga da wando,duk da babu mai kayan mutunci a cikinsu, tab'o dayar dake kusa da ita ta yi ta ce "Kee Bariki Dadi, baki ga Hoge ya wuce da wata bafulatana ba?" wacce aka kira da sunan Bariki dadi tana riƙe da sigari a hannunta tana zuga suna buga caca ta ce "Hoge dai? Yaushe ya dawo?" "Ba mamaki dawowarsa kenan dan na gansa da kayansa" miƙewa tayi da sauri ta ƙudundumo wani ashar sannan ta yi cikin gidan da sauri wa inda suke zaune a tare suka hau zugata suna fadin "idan kinje kici uwarta da ubanta! Bariki dadi! Baki da kyau baki da dadi!" suna fadi suna ihu,ita kuwa fuuuu tayi ciki,a lokacin Hoge har ya buɗe a kulkin dakinsa ya kalli Azima ya ce "Shigo mana yar fullo" a hankali Azima ta sa kafa ta shiga, a wani jagalgalalliyar katifa ta zauna tana saƙa abubuwa dayawa a ranta, tana zama sai ga Bariki dadi ta banko kofar kamar zata b'alla shi, Azima bata dago ba illa Hoge dake fadin "Wannan wani irin iskanci ne haka?" "Ga ka nan kuwa babban dan iskaci baƙin munafuki! Ka hanani kula ko wani bunsuru, sannan ka dauko wata banziya daga dawowarka ka huce da ita a gabana! To wallahi sai naci Uwarta! Ke kuma munafuka zo nan! Sai wani rufe fuska kikeyi sai kace wata ta Allah kina sunkuyar da kai, to idan baki sani ba ki sani! Kina sa kafarki a nan gidan dukkan wata mutuncinki ya zube kuma saina koya miki hankali!" murmushi Azima ke yi a ranta ta ce "Inason mutane irin haka! Wa inda basu shiga gonata ba ina kau dasu balle wa inda suka shiga" bata gama maganar zucinta ba Bariki dadi ta shaƙo wuyarta, tashi tsaye Azima tayi,tana tunanin dame zata kasheta! ta sareta ne ko ta watsa mata dafi? Hoge ne ya fizgi Bariki Dadi ya koɗa mata mari sannan ya ingizata waje ya juyo yana ba wa Azima hakuri, bata ce masa ci kanka ba,illa da ya gama rawar bakinsa ya fice wai zai kawo mata abinci, bai jima ba kuwa ya shigo da bakar leda ya ajiye mata, budewa Azima ta yi nan tayi arba da kayan dadi murmushi tayi dan bata taba ganin kalar abincin ba, da sauri ta buɗe ta hau ci tana lumshe ido tana gya ɗa kai, shi kuwa yana zaune a gefe yana kallon gashin kanta da ya rufe mata fuska aransa ya ce "Hummm! dama ana ganin irin wa innan matan a gaske? Dole na shana wlh,daga ganin wannan ɗanya ce jaƙab, zatayi ruwa zata kai yadda ake so, idan tayi daga nan zata zama cikata!" sai sambatu yakeyi a zuciyarsa yana hadiye yawu,Azima kuwa fess ta cinye abubuwan da ya kawo mata, ta kwankwaɗe maltina har tana lashe baki, tana gamawa ta koma ta jinginu da banko tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido,jin saukar numfashi ta yi a wuyarta, saurin buɗe ido ta yi ta gansa ya matsota sosai, sai wani washe baki yake yi, bata gama karantarsa ba taji yana fadin "Meyasa kike rufe baiwar kyawun da Allah ya miki da wannan dogon gashin naki? Duk da ba a ganin fuskarki da kyau amma da an ganki an ga kyakkyawa ajin karshe, dan Allah ki buɗe idanunki na ganki,sannan ina so ki bani hadin kai nayi miki alkawari zan baki duk abunda kikeso zan miki komai" cije baki Azima ta yi jin yadda wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarta,daurewa ta yi tasa yatsarta babba manuniya a kan goshinsa, ta ture kansa daga wajan saitin wuyarta sannan ta ce "Kasan daga ina nake? Sannan ni fuskata kallo daya ake mata,idan har ka gani babu fuskar da zaka kara kalla a rayuwarka" "E na yarda ni dai ki bude fuskarki na gani, sannan zan baki abun dadi" ya fadi yana shirin kai hannunsa kirjinta,da sauri Azima ta ja da baya tana fadin "Owohh kenan kai ɗan iska ne! Zan koya maka hankali, ka taba ganin maciji?" "E amma a zahiri sau daya na taba gani kuma ƙarami ne ma,amma ina gani a fina-finai" "To yau zaka ga Babban a zahiri ido da ido!" ta faɗi tana dariya yayinda ta kwashe gashinta ta maida su baya,blue eye dinta ya bayyana, a gigice hoge ya ja da baya, yayinda ta hau rikiɗewa,tun kafin Azima ta taba Hoge numfashinsa ya fara barazanar daukewa, yana ganin zureren Maciji har na sheƙi a gabansa nan ya fadi sumamme, Azima ta sa baki ta saresa a gabansa, sannan ta koma mutum ta fice, ta zo fita kenan suna karo da Bariki dadi,shaƙeta bariki dadi tayi,Azima tace "Dama kafin na tafi ina nemanki!" tana gami fadi ta zaro harshenta ta watsa mata dafi sannan ta bar gidan. 🍃🍃🍃🍃🍃 Kuka Hajja keyi yayinda Inna Wuro da Yawuro suke ta aikin bata hakuri suna rarrashinta,amma pinaa Hajja kamar ba da ita ake yi ba, idonta ya kumba ya yi him sabida kuka fuskarta ya yi jaa! Baffa ne ya duka a gabanta ya ce "Jumala? Kiyi hakuri,In sha Allah idan anyi duniya DAN MANZON ALLAH S,A,W, Azima da Aziza zasu dawo garemu In sha Allah,kuma yaranki zasu dawo mutane ko da kuwa zan rasa raina na miki alkawari!" ita dai Hajja bata ce komai ba, tun daga wannan rana Hajja bata um bata um-um, idan ta zauna idonta na kan bakin kofa,ta ajiye idanunta har izuwa ranar da yaranta zasu dawo gareta. 🍃🍃🍃🍃 Fitan Azima yawatawa ta ci gaba da yi,dama ita ba sallah take yi ba balle ya dameta, idan kuma wani mai kararren kwana tsautsayi tasa ya shiga hidimarta ta kashesa ta yi gaba, yau kwananta uku da shigowa garin kano bata damuwa da wajan kwana idan dare ya yi duk babbar bishiyar da ya mata zata zama macijiya ta hau ta kwanta tayi bacci ko ta huta, yau ta fito tana cikin tafiya taji ƙaran mota ƙiiiiiii! da sauri ta juyo ta ga wata matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekara ashirin da biyar,fitowa tayi tana zazzagawa Azima zagi, yayinda take binta da ƙaramin kallo "Ban da hauka taya zaki rufe fuska ki dinga tafiya a kan titi! Sakarya kawai bagidajiya!!" cije baki Azima tayi meyasa ake son ce mata bagidajiya? duk da bata san ma'anar kalman ba amma taji ta tsani kalman, lankwabe murya ta yi ta ce "Dan Allah ki taimaka mini, ni yar gudun hijira ce an kashe dukkan yan uwana a rigarmu ni daya ce kawai na rage,ban san kowa ba ban san inda zanje ba, dan Allah ko aiki ne a gidanku ki nema mini zan dinga yi" yatsine fuska ta yi tana fadin "Kuma fa kamar naji Hajiya na neman mai aiki,to amma gaskiya sai dai na sakaki a cikin both dina dan ba zaki shiga mini mota ba" "Ina ne shi hakan bat din?" "Banza jahila both nace, nan kenan zo ki shiga" ta fada tana mata nuni da both tana budewa,Azima ta shige tana murmushi tare da fadin "Matakin farko!" tana rufe murfin both din Azima ta koma Macijiya, shiga motar tayi ta ja tana tsaki. A kwana ukun nan Aziza ta fito daga bakin titi ita ma,tana fitowa ta zube a kan titi tana sakin kuka tana kiran sunan Hajjanta da Baffanta, Inno Fandi ce ta taimaka mata ta fiddota bakin titi sannan ita ta koma, kuka sosai Aziza ta yi kafin ta tashi ta hau tafiya, tana ganin kamar ta shigo wani sabuwar duniya ne, bata ma san a inda take tafiya ba, shi kuwa da sauri yake jan mota,yana driving yana duba tym, wayarsa ce ta yi kara yana dubawa ya ga Friend 4 Life, dagawa ya yi, ya ɗan yi shuru tukunna kafin ya ce "Hey Dude bazan maka karya ba,wlh bazan je na dubasa ba,guy din nan ya raina min hankali, jiya banyi niyyar kwana a garin yola ba amma ya sakani kwana, yanzu haka ma nikam gani a hanya ko kwana zanyi sai dai na kwana amma yau din nan sai na kasance a cikin garin Kd in sha Allahu!" yana magana a waya ransa a b'ace sai ji ya yi, ya yi sama da mutum, wani mahaukacin burki yaja ya fito da gudu, yana isowa gareta tana lumshe ido, duk da bai ga fuskarta da kyau ba gashi ya rufe amma daga ganinta a jeji ta fito, kallon gabas ya yi,ya kalli kudu,ya kalli arewa,ya kalli yamma bai ga wani ɗan adam ba, shi a tunaninsa sun fito kiwo ne yan uwanta suka tafi suka barta, to amma idan haka ne shi ya zaiyi da ita? Ga kanta ya fashe yana zubda jini, "No dogon tunani ba nawa bane i need to save her lyf first" ya faɗa yasa hannu yana shirin daukarta, wani mummunar faduwar gaba ce ta riskesa inda yaji dukkan wata gab'a ta gangar jikinsa ya sake, saurin kauda abun a ransa ya yi ya dauketa ya sakata a mota ganin bata motsa, yana addua Allah yasa dai bata mutu ba. 🍃🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️==3️⃣7️⃣↪️3️⃣8️⃣ Murmushi ya mata ta zo ta rungumesa tana yi masa sannu da hanya, ya amsa da "yawwa sannunki,ina Mom kar dai har tayi bacci?" "Kai anya kuwa, da muna zaune da ita a nan bata jima da tashi ta hau sama ba" "Okay bari na dubata" ya faɗa yana maida dubansa ga tv'n ya ce "Ke da kallon horror ko, sai kin fara ganinsu a gaske zaki sani" murmushi Sultana ta yi ta koma tana zama shi kuwa ya hau sama,dakin Mom ya shiga da sallama tana zaune tana waya, zama ya yi kusa da kafarta har sai da ta gama wayar ta ajiye kafin ta kallesa cikin kulawa ta ce "Nawaz sai yanzu? Ya hanya an dawo lafiya?" "E wlh Mom, Alhamdulillah! ina wuni? Ya gida? na sameku lafiya?" "Alhamdulillahi Doctor, fatan dai lafiya ko? Ko dai gajiya ce dan fuskarka ta tuna,yanzu haka ma da Amminka muka gama waya wai ta kiraka wayar bata shiga nace ba mamaki hanya ce ba netwrk" "E hakane zan kirata gobe yanzu dare yayi zan shiga part dina,kunyi waya da Son dinki ne Mom?" "E dazu ya kirani dan albarka" "Mom muna cikin waya da shi dazu tsautsayi tasa na buge bafulatanan yarinyar mutane" "Subhanallahi!" Mom ta faɗa tana zabura "Kwantar da hankalinki Mom tana hospital dina" nan ya bata labarin yadda hatsarin ya kasance har izuwa shawaran da ya yanke na tahowa da ita kaduna idan taji sauki sai a maidata gida, Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Shawaran da ka yanke mai kyau ne Nawaz, Allah ya bata lafiya, ma je mu dubata gobe idan Allah ya kaimu ni da Sultana" "Allah ya kaimu Mom" ya faɗa yana duba agogon hannunsa "Dare yayi Mom zanje na kwanta na huta akwai gajiya a tare dani" "To Allah ya tashemu lafiya a huta gajiya,Allah ya yi albarka" Nawaz ya amsa da amin yana tashi ya fice a dakin, yana saukowa ya kalli Sultana ya ce "Idan baki kashe tv'n nan kinje ki kwanta ba Allah sai na zaneki" da sauri Sultana ta miƙe ta kashe tv'n kasancewar tasan halin Yayan nata, sai da ya ga ta hau sama kafin ya fice ya nufi part dinsa, wanka ya yi ya gabatar da salloli har da nafila ya jima yana addua kafin ya tashi ya koma gado ya kwanta,har ya lumshe ido ya buɗe ya dauki wayarsa ya kira Amininsa suka hau ɗan taba hira inda yake ba shi labari ya buge bafulatana, Allah ya kiyaye gaba ya masa,sannan ya ce "Yaushe zaka dawo america?" Nawaz ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Nan da 2wks In sha Allahu,but idan nazo ina shekarar karshe zamuyi mu dawo gida gabadaya?,dan gaskiya na gaji da zaman outside" Daga can bangaren ya ce "In sha Allahu, duk da ni bana son zaman nigeria gaskiya" "To ya zaka yi dole ka dawo,duk lalacewa kasarka kasarka ne, sannan karka damu da abinda Momma take maka, ka ci gaba da yi mata biyayya a matsayin uwa,wata rana zata gane In sha Allah" ajiyar zuciya ya sauke, nan Nawaz ya gane damuwar dake damunsa dan haka ya kau da hiran ya jawo musu wata, sun kai biyun dare kafin suka yiwa junansu sallama, yana ajiye wayar bai jima ba bacci ya kwashesa,yana cikin bacci ya hau mafarkin yarinyar da ya buge da mota, suna cikin wani ƙasurgumin jeji sai faman ihun take zabgawa tana fadin ya taimaketa ya taimaki rayuwarta, tana ihu tana gudu yana binta a baya, da haka har suka je jikin wata babbar bishiya taja ta tsaya kanta a sunkuye tana sanye da kayan fulaninta,ta ƙanƙame jikinta tana ihu, shi kuwa yana riƙe da fitila a hannunsa yana haskawa sabida tsananin duhun jejin, yana shirin matsowa gareta ya ga mummunar tashin hankali dan kuwa gani ya yi ta koma wata zabgegiyar macijiya🐍 fara sol sai ƙyalli take yi,tana ci gaba da ihun ya taimaketa. A mugun gigice Nawaz ya farka yana fadin "INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!³" hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin ya rike kansa da karfi dan ji yakeyi kamar kan na shi zai faɗo kasa, gabadaya jikinsa ya jiƙe da gumi, yayinda ko wani kofar gashi ta gangar jikinsa ya buɗe sun miƙe tsaye, jijiyoyin wuyansa duk sunyi waje, jikinsa sai b'ari yake yi har yana jin wani zazzabi, da kyar ya jawo wayarsa ya duba tym ya ga karfe biyar, tashi yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala ya tada sallah, yana nan zaune yana addua har aka kira sallah, sai da yayi raka'atul fajir sannan ya miƙe da kyar ya fita zuwa masallacin da yake wajen gate ɗin gidansu, bayan an idar da sallah ya shiga ya gaida Mom bai wani zauna ba yace mata kansa na ciwo zai sha magani ya kwanta dan bai samu bacci daren jiya ba, Allah ya kara sauki Mom ta masa ya koma part dinsa ya kwanta, ba jimawa bacci ya sake kwasansa amma still mafarkin daren jiya shine ya kara tayar da shi, cikin kiɗima ya zauna a bakin gado yana tunani barkatai. "To miye haɗina da wannan yarinyar? daga haɗuwa da ita jiya shikenan sai na kasa bacci? ni da ko fuskarta ban gani da kyau ba gashin kanta ya rufe! sannan me hakan yake nufi nake ganinta a macijiya!? ko dai ba mutum ba ce? kai inaa a'a ko dai wani abu ya sameta ne a asibitin?" sauri tashi ya yi ya dauki jallabiyarsa yana kiran nurse's din da ya basu kula da ita,amma babu wacce ta daga a cikin su biyun, tym ya duba ya ga 7:30 da sauri ya zare car'key dinsa ya fice ya bar gidan ya nufi asibitinsa mai suna *ALWAZ HOSPITAL KADUNA.* Yana isa ko parking bai gama ba ya shiga ciki da sauri,yana shiga reception ya samu nurses ɗin suna bacci, a tsawance ya tayar dasu nan ya hau su da faɗa a kan basu san aikinsu ba, hakuri suka hau ba shi amma bai tsaya ya sauraresu ba illa dakin da Aziza ke kwance,kamar yadda ya barta jiya haka ya sameta tana bacci gashinta ya rufe mata fuska,yana ganin lafiyarta ya saki ajiyar zuciya wanda bai san dalilin hakan ba bai ma san lokacin da ya saki ba, dubata ya sake yi ya ga zata iya farkawa ko da wani lokaci, hannu yasa da niyyar kwashe gashin fuskarta a fili ya ce "Wai meke damuna ne kam? Mtsww!" ya ɗan ja gajerar tsaki yana fita a dakin, gida ya koma dan kansa ke masa ciwo sosai,magani ya sha cikin ikon Allah bacci ya kwashesa bai farka ba sai daya saura,yana tashi ana kiran sallar azahar, bai tsaya bata lokaci ba ya yi alwala ya tafi masallaci bayan ya dawo babban parlour ya wuce ya samu Mom da Sultana suna zaune suna hira, gaishe da Mom ya sake yi ta amsa Sultana ta gaishesa ya amsa yana haɗe rai da fadin "Keee me ya hanaki zuwa skull?" "Brother yau bani da komai shiyasa ban je ba" "Kin san dai bana son wasa da karatu ko?" "E Brother bana wasa da karatu ko Mom?" ta fada a shagwabe tana kallon Mom,Mom ta yi murmushi ta ce "Ai kai ma kasan yadda Sultana ke son karatu,ya gajiyar hanyan da kuma jikin?" "Alhamdulillah Mom na warware" "To Ma sha Allah haka ake so, dama mun gama shiryawa kai muke jira idan ka farka sai mu gaya maka zamu je asibitin duba yarinyar" "Okay Mom bari nayi wanka sai na kai ku,nima akwai marasa lafiyan da nake son dubawa, gobe kuma zanje abuja akwai aikin da nake da shi" "Kuma?" cewar Mom,ya ce "E wlh Mom,ai idan har mun samu sauki sai dai idan mun dawo kasarmu gabadaya,tunda ko kaɗan zuwan nan wan can guy din dan ya raina min wayo ba zuwa yakeyi ba,ya maqale a kasar wasu" murmushi Mom tayi ta ce "Ka kyalesa mana Nawaz,kasan fa ba jin dadin zama yakeyi dasu Hajiya Lawiza da Hajiya Luba ba, kai mutanan duniya sai Allah wlh,ace kuna zaune karkashin mutum kuna cin albarkacinsa kuna rayuwa da dukiyarsa amma kun tsanesa kuna cin dunduniyarsa,kai Allah shi kyauta" Nawaz ya amsa da amin yana fadin "Ba ri na shirya nazo na kaiku nima na samu nayi aikin dake gabana a hospital din" "To a fito lafiya" cewar Mom. Mintuna sha biyar ya daukesa ya gama shirinsa ya shiga ya yiwa su Mom magana suka fito suka nufi asibiti,ko da sukaje kwatanta musu room din ya yi shi bai shiga ba ya tafi dan akwai cs din da zai yi, su Mom ne suka shiga suka zauna da ita,Sultana tasa hannu ta kwashe mata gashin fuskarta ta ce "Woww! Allahu Akbar! Ma sha Allah!" "Menene Sultana?" "Wlh Mom kyakkyawa da ita, ki ga gashi, wayyo Allah na ni,wlh Mom kamar ba yar nigeria ba" Mom tayi murmushi ta ce "Baki rabuwa da shiririta Sultana ba bafulatana ba ce" "Ai wlh Mom ko a fulanin ba kowa ke da kyau ba" "To anji ki rufe min baki, karki cika marar lafiya da surutu Yayanki ya shigo ya sameki kina zuba zaneki zaiyi kema kin sani" zare ido ta yi tana riƙe bakinta dan tasan sarai zai zanetan sai dai idan bata cika masa ciki ba dan akwai sa da saurin zuciya abu kaɗan ke tunzura shi ransa ya b'aci. Su na zaune a asibitin sai wajan uku da rabi kafin Aziza ta fara farkawa, farkawartata yazo mata da mugun mafarki Azima ta biyo Baffa da wani zabgegen takwabi tana shirin kashe Baffa bayan sun gama dambatuwa In da Baffa karfinsa ya ƙare ya hau kwalawa Aziza kira ta kawo masa dauki Banju zai kashesa! Ga Hajja a sume a kasa, wani ihu Aziza ta yi dai-dai da lokacin da Nawaz ya sako kafarsa dakin ya zo dubasu ya iske ihunta tana fadin "BAFFAAAANAAAAA!!! HAJJAAAAA!! KEEEEE!!! AZIMAAAAAA!! KARKI KASHE BAFFAAAA!!" sauri yin kanta suka yi Nawaz ya tallabota kirjinsa ya kalli Sultana yace "maza je ki kirawo min wasu nurses ko Dr duk wanda kika samu su zo yanzu" da gudu Sultana ta fice suka dawo da nurse mutum hudu, nan yace su ba shi allurai, bayan sun miƙa masa ne tana ta faman buge-buge, Mom tana tsaye daga saman kanta tana mata tofi, yana mata alluran ta koma ta yi lamo a kirjinsa tana kan ambatar sunan Baffanta da Hajjanta, kamar da minti biyar abun ya lafa,Mom ta ce "Nawaz ya dai?" "Ba komai Mom,nan da 30mins zata farka zata dawo dai-dai In sha Allah" Mom ta ce "Ka gani ko Nawaz? Gwara da Allah yasa baka barta ba ka taho da ita, Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗunta" ya amsa da amin yana me leƙa fuskarta ya ga gashi ya rufe,kwantar da ita ya yi ya fice, Sultana ta zauna kusa da ita tana kamo hannunta. Kamar yadda Nawaz ya fada haka kuwa ya kasance 30mins ta farka, tana buɗe ido ta hau bin inda take da kallo, ba dai har ta mutu bane yanzu haka tana lahira? Take tambayar kanta,kallon hannunta ta yi ta ga wata budurwa zaune kusa da ita, ga wata dattijuwar mata zaune hannunta dauke da carbi tana lazimi, budurwar kuma hannunta da waya tana dannawa,saurin janye hannunta Aziza ta yi ta matsa baya, tana dafe kanta da kafarta da ta ga an daure mata shi,nan abunda ya faru ya dawo mata kai, Sultana ta ce "Sannu kinji! Ya jikin naki?" "Sultana kira yayanki mana" cewar Mom "To Mom" Sultana ta faɗa tana ficewa. Tare suka dawo da shi, a lokacin Aziza na maqale can jikin gado tana wani irin kuka kanta a sunkuye tayi mayafi da gashin kanta, jin magana yasata dagowa kaɗan ganin mutum na matsota ya sakata fashewa da sabon kuka tana fadin "Aradu karka matso kusa dani" a yadda take magana zaka san babu hausa a harshenta,banza da ita Nawaz ya yi yasa hannu zai tabata ta saki ihu tana kiran sunan Baffa, haushi ne ya kama Nawaz ya daka mata tsawa "Keeeee!!! Bana son hauka!! Ki natsu!!" Mom tace "Haba Nawaz!? Miye haka? Ka mata a hankali mana" wani tsoro ne ya kama Aziza,ganin haka yasa Mom matsowa kusa da ita ta ce "Ɗana ne! Ba zai cutar dake ba, wancan kanwarsa ce, shi kuma likita ne, ya bugeki ne bisa tsautsayi sannan wannan asibitinsa ne yana kula dake,alhamdulillah kin farka, yanzu haka kina garin kaduna ne,munji kina ambatar sunan Baffanki, da kinji sauki zamu maidaki gida kinji ko? Karkiji tsoronsa zai duba ki ne uhum?" Mom ta faɗa tana bubbuga Aziza, dubata Nawaz ya yi ya fice cikin haushi. 🐍🐍🐍🐍🐍 Tun shigan Azima dakin munir da niyyar gyarawa ba a sake ganin mai kama da ita ba, har dare, kuma cikin wani ikon Allah babu wanda ya nemeta,dan sun manta da ita,tunda sun san mai aikinsu ta gudu sun manta sun dauki sabuwa, sai wajan karfe tara Munir ya dawo shi da Baby, bayan sun yi magana da Zuby da Hajiya Baby ta wuce dakinta,Munir ma ya wuce nasa,yana shiga ya yi turuss yana ganin ikon Rabba, Azima ta yi ɗaya-ɗaya a kan gado ta bararraje an samu gado mai laushi bana kara ba, sai kwasar baccinta take cikin salama hankali kwance, gashinta da ya sha wanki sai kyalli yake yi duk ya baje ya rufe mata fuska, wani yawu muqut Munir ya hadiye yana fadin "Kai daga ina wannan balarabiyan?" ya fada yana yin kanta ba tare da yayi dogon tunani ba shin aljana ce ko mutum. 🍃🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️==3️⃣9️⃣↪️4️⃣0️⃣ Hannu yasa jikinsa na rawa yana lashe baki yana kwashe gashin da ya rufe mata fuska cikin bacci Azima ta ji mutum a kanta, bata gama tabbatarwa ba sai da taji saitin hannun mutum a wajan dukiyar fulaninta, nan da nan ta farga da abunda ke wakana a kanta, idonta ne ya sauya, da tafin hannunta ta tokari kirjin Munir kamar kiftawar ido da bismillah sai ga Munir ya yi sama ya bugu timm da kasa!! Saurin tashi Azima ta yi,ta dauki mayafinta ta yi lullubi sannan ta yi kan Munir,tana zuwa ta shaƙosa da hannu daya ta haɗasa da bango,nan idon Munir ya yi waje yana so ya yi ihu amma baya so kannansa suji su rainasa, lallai yau ba shakka ya yi gamo da aljana a garin ɗan banzan son matan tsiya tun bai tsaya ya ga wacece ba ya afka mata ga shi tana neman kashesa, lokuta da yawa Munir ya sha yiwa yaran aikinsu fyaɗe,da anyi kara kuwa uwarsu zata zuba kuɗi ta karbo ɗanta tace an masa sharri. Cikin zafin zuciya Azima ta kamo hannun Munir wanda ya taba mata kirji da shi, matse hannun tayi jikake ƙashi na haɗewa yana bada ƙaƙassƙasssƙass!! Ihu Munir ya sake na azaba, Hajiya da Zuby dake parlour suka ji ihun Munir da gudu sukayi dakinsa, a lokacin da ya yi ihu Azima ta sakesa ta koma gefe jin kafar mutane da gudu, kafin su shigo Azima ta duƙa kasa a gaban Munir, Hajiya da Zuby suna shigowa Munir ya yi saurin maida hannuwansa baya, Hajiya tace "Munir ihun me kakeyi haka?" "Ha...ji....ya...wa..ce..ce...wan...nan...yarinyar.." sai a lokacin suka maida kallonsu ga Azima da take duƙe tana murmushin mugunta ta cikin mayafi, tsaki Zuby tayi tace "Mtswww Munir amma dai wlh kaji kunya,duk iya shegenka amma wannan yarinyar kake yiwa ihu? Sabuwar mai aikin da hajiya ta dauka ne fa, wlh nikam har na manta da ita a gidan,ke dan uwarki miye kikeyi a dakin nan tun rana har yanzu?" matse hannu Azima tayi tana cije baki, da kyar ta ce "Da na shigo na manta abubuwan da Inna Lantana ta gaya mini nayi ne,kuma da nazo fita ban san ta inda zan fita bane shiyasa na zauna, shi kuma da ya shigo ya ganni sai ya tsorata" Hajiya ta ce "Ba dole ba!, fuska a rufe kina dukar da kai, banza kawai maza ki tashi ki gyara masa dakin yanzun nan idan kin gama kije ki gyarawa Baby da Zuby nasu, sannan ni kuma kije ki wanke min toilet, ohh ina nufin bayi ko kewaye ku ke cewa oho,dalla tashi!!" Hajiya ta faɗa da tsawa suna ficewa a dakin ita da Zuby, Munir ya ce "Kee dan ubanki! Dama ke mai aiki ce shine kika shaƙeni! Kin san waye ni kuwa?" waigowa Azima ta yi ta ce "Kamar yadda kaima baka san wacece ni ba! Ka kiyaye! Bana gargaɗi sai dai zartar da hukunci!" tana gama fadi harta juya zata fita ya ɗan sake ihu yana maqale hannunsa, juyowa Azima ta yi ta dawo ta cafke hannu yayinda ta sake matsewa ta ware hannun ya sake sakin kara, hannun nasa ya dawo dai-dai ta ce "Ban taba lalata abu na gyara ba! Sai dai idan aka gyara na b'ata!" tana gama fadi ta fice, wajan Lantana a kitchen taje Lantana tana ganinta ta ce "Ahh Azima tun rana ina kika shiga haka?" abunda ta gayawa su Hajiya shi ta kara nanatawa Lantana daga nan ta hau tayata aiki suna girkin Azima taji tana bukatar watsa dafi a cikin abincin,amma kasancewar tasan Lantana zata ci yasa ta hakura da watsa dafin,bata taba jin bata son kisa ba sai a kan Lantana ko meyasa hakan oho, bayan sun gama kowa yaci abinci suka gyara kitchen har sun kwanta Hajiya ta kwalawa Azima kira, cike da takaici da haushi Azima ta dauki mayafinta ta fice tayi dakin Hajiya, ko sallama ba tayi ba ta shiga Hajiya na zaune a gefen gado,tana ganin shigowar Azima kamar an bankota yasa Hajiya miƙewa da masifa "Ke wace iriyar jahilace! Ƙidahuma bagidajiya! 'yar can cikin jeji kawai! ban gaya miki ki zo ki wanke mini bayi ba?" Azima na shirin magana Munir na kwala mata kira, Hajiya tace "Maza je kiji me yake da bukata ki gama masa ki zo ki wanke min toilet dina yau din nan, ai babu ke babu bacci" fita Azima ta yi ta nufi dakin munir yana tsaye daga shi sai gajeran wando,kallonsa tayi ko gizau bata yi ba balle taji dari-dari dan ta gansa a haka "Keee!! Banza 'yar jeji, gyara min gadona" "Kaiiii!! Banza shanu ɗan iska ban gyarawa!" ta juya zata fita Munir yasa hannu ya fizgota ya ɗaura mata sannan ya tureta gado ya bita ya danne, wani gurnani Azima ta yi tare da rikiɗewa rabinta mutum rabinta macijiya! A haukace Munir ya tashi a saman kanta ya yi baya-baya ya faɗi a gado jikinsa na rawa, gashinta ta kwashe blue eye dinta ya bayyana ya ƙare rinewa "Ban ce maka ka kiyayeni ba! Baka san wacece ni ba ko!?" Cikin shiɗewar numfashi sabida tsananin tsoro da firgici Munir ya ce "Dama ke ba mutum ba ce!!?" Murmushi Azima ta yi ta ce " *RUWA BIYU!* Mutum Macijiya!" "Dan Allah kiyi hakuri karki kasheni!" "Duk wanda ya ga kwayar idon Azima baya sake ganin wani!" tana fadin haka ta koma macijiya ta saresa a bayan wuya nan munir ya faɗi ya hau murkususu yana birgima har ya dai na! rai ya yi halinsa, sai da Azima ta ga ya mutu kafin ta zama mutum ta fice a dakin taja ta rufe shi, ta koma dakin Hajiya da take ta sababi, Azima ta ce Hajiya "Ki ɗan jira a parlour na gama gyara miki dakin" "Saura kuma karki gama da wuri ki ga yadda zanyi dake a cikin daren nan 'yar can cikin jeji kawai!" Hajiya ta faɗi tana ficewa, Hajiya na fita Azima ta kulle kofa ta hau gadon Hajiya ba daɗewa bacci ya kwasheta, Hajiya kuwa tana parlour tana jiran Azima ta gama gyara da fito yau ne gobe ne shuru,har bacci ya fara kwasar Hajiya, ta farka taje ta tura kofar ta jita a gangame! Bugawa Hajiya ta hau yi amma a banza har ta gaji, tana bugawa tana aunawa Azima zagi, dakin Zuby taje ta buɗe mata Zuby tace ita ba zata tashi ba ta riga da ta kwanta,haka ma Baby ita kam har da yiwa Maman tsawa ta tayar da ita a bacci, haka Hajiya ta dawo parlour ta kwanta a kujera nan ta kwana. Azima bata farka ba sai bakwai na safe tana tashi ta wargaza dakin Hajiya ta kwashi kudin dake dakin kafin ta buɗe dakin ta fito,nan ta ga Hajiya na bacci wani murmushi ta yi na gefen baki, dakin Lantana ta nufa taje ta sameta zaune tana karatun al'kur'ani mai girma, wani wawan jiri ne ya ɗibi Azima,Lantana ganin haka yasata rufewa ta tashi da sauri ta kamo Azima tana tambayarta lafiya? Azima ta ce "Lafiya lau! Ga wannan kudi ke da mai jiran ƙyauren gidan nan(gateman) ku bar gidan nan ku koma garinku,ke yar wace gari ce?" "Ni 'yar can cikin kauyen kano ne, amma meyasa zamu tafi?'' cikin tsawa Azima tace "Bana son tambaya zaku tafin nan ne ko zaku shiga sahun wa inda za a binne?" jin haka yasa Lantana karban kudi jikinta na rawa dan bata taba jin murya nai amo da firgici irin wannan ba harta kayanta tace ta yafesu dama tsumokara ne, ta ce "ki yafeni Hajiya Azima idan na bata miki sai wata rana" bata jira amsar Azima ba ta fice, ta kai wa Mai gadi yana tambayarta miye tace masa kawai ya yi ta kansa, sai da Azima ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta ja kofa ta koma, shiganta parlour ya yi dai-dai da farkawar Hajiya, bata yi wata-wata ba tasa hannu ta fizgi Azima ta gaura mata mari dai-dai sadda Baby da Zuby suke buɗo kofa dan lokacin haɗa musu tea ya yi, Zuby ce ta ce "Hajiya me ya faru haka?" cikin kumfar baki Hajiya ta ce "Wannan 'yar jeji ni zata bari na kwana a parlour?" "A parlour kuma?" cewar Baby tana bin Azima da kallo da kanta babu dankwali sai gashinta da ya rufe mata fuska "Ke ba magana ake miki bane?" cewar Zuby tana hararan Azima dake tsare jikinta na tsuma, hannu Baby tasa taja gashin Azima yana kwashe na fuskarta nan Azima ta ware kwayar idanunta a kan Baby,wani ihu Baby ta saki tana ja da baya, Zuby tasa hannu zata juyo da Azima dan ta ga me Baby take yiwa ihu kafin ta juyo da Azima, Azima ta juyo ta hura mata baƙin hayaki a fuskarta, kafin su farka tuni Azima ta yi juyi ta zama rabi mutum rabi macijiya, fadin yadda su Hajiya suka shiga firgici ba zai misaltu ba, ihu suke yi suna kiran Munir,dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce "Ya ri ga ku mutuwa! Yanzu a cikinku wa zai bisa na biyu? Bari na kawo muku shi ku gan shi" Azima ta faɗa tana shiga dakin ta naɗo munir da jelarta ta zo ta jefar da shi a gabansu a tsakiyar parlour, wani kuka su zuby suka saka ita da baby hajiya kuwa jiki na kyarma ta takure jikinta gefe daya. A tsawace Azima tace "NA CE A CIKINKU WA ZAI BISA NA BIYU!!?" cikin kuka da tashin hankali suka hau fadin tayi hakuri karta kashesu basu so su mutu, Azima tace "Akwai abu daya da zan muku, ruwa zaku sha? Ko abubuwan da kuke sha a robobi zaku sha?" cikin kuka da majina da zufa suka ce ruwa, Azima tasa hannu ta janyo ruwa ta zuba a kofi uku ta ce "Duk wanda baya son mutuwa ya sha wannan ruwan!" jikinsu na rawa suka dauka suka kafa baki suka kwankwaɗe suna kan bata hakuri, kamar da minti biyu tsakani Hajiya ta hau tari tana rike wuya, da sauri Zuby ta tashi tana fadin Hajiya meya sameki,nan ita ma ta hau riƙe wuya tana tari, Baby ma haka, tari sosai suke yi jini na fita baki da hanci, Azima ta miƙe ta ce "BANA MANTUWA! BANA YAFIYA! NA RIGA DA NA ZUBA DAFI TA YATSAR HANNUNA!" tana gama fadi ta shiga ta dauki kayanta na fulani da Lantana ta wanke mata ta saka ta fice ta bar gidan. 🍃🍃🍃🍃 Kwanan Aziza biyu a asibiti jikin nata alhamdulillah duk da da ace taso zata iya warkar da kanta amma bata so ta sakawa su Mom da Sultana shakku a ransu su fara zarginta, sannan yanzu idan tace zata gudu bata san duniyar da Azima take ba kuma tana ji a jikinta duk inda Azima take bata shuka alkairi, abu biyu ne ya haɗe mata waje guda ya jagula mata lissafi, bata san taya zata fara neman Azima ba tunda basu al'karya daya, sannan bata san wani hali iyayenta suke ciki ba,duk da tana da yaƙini a kan Baffa zai kula da Hajja sosai shima zai kula da kansa, tana zaune tana tunani, wani dabara ne ya faɗo mata, wannan dabara kuwa shine ta fara yawon bin garurruka! duk garin da suka haɗe da Azima idan ta lumshe ido zata iya hangota ta cikin tauraronsu, da wannan tunani ta samu karfin guiwa,lumshe ido tayi ta shafi tafin hannunta amma bata ga Azima ba, a fili ta ce "Hakan na nufin bamu gari daya kenan, wannan hajiyar (Mom kenan) ta kira sunan wannan yankin da kaduna ko? Ina gani gwara na tambayi wannan yarinyar tata sunayen yankuna sabida naje na dudduba Azima, amma kuma kafin na tafi dole ina bukatar kudi, hakan yana nufin dole na yi musu aiki dan na tara kudin neman Azima? Idan kuwa haka ne Banju ya cuci rayuwarmu,ga shi wahalar a kaina da Baffa yake karewa" ta karasa maganar da sakin kukan tausayi, tana sakin kukan su Mom da Sultana suna shigowa. Ganin tana kuka yasa suka karaso wajanta da sauri suna tambayarta ko akwai inda yake mata ciwo ne? ta girgiza musu kai alaman a'a, Mom ta ce "Yarinya? Kiyi hakuri kodayaushe kina cikin kuka, ina yan uwanki suke? A wani ruga kuke a garin yola idan yaso gobe sai a maidaki" jin haka yasa Aziza kara sakin sabon kuka,inaa ai ba zata so ta koma ba tare da burin Baffa na su dawo tare da Azima ba, mafita daya ne shine kawai ta yi karya,cikin kuka ta ce "Yan fashi ne suka fada rugarmu suka kashe mana kowa, nima da kyar na sha,dan Allah Hajiya ki taimaka mini na dinga yi miki aiki kina biyana,yanzu idan na barku ban san inda zan hadu da mutane nagari kamar ku ba dan Allah Hajiya!" Aziza ta fada tana kuka sosai,jikin Mom ne ya yi sanyi sosai, Sultana ma kwalla ya cika a idonta ta kalli Mom ta ce "Mom mu dauketa kawai,tunda dama kinga Haule ta yi aure,ita wannan ma zata jima " Mom ta ce "To shikenan kira mana wani Dr ya zo ya rubuta mana sallama,dan munyi waya da Nawaz yace sai gobe ko jibi zai dawo,kuma yace idan har jikin nata da sauki mu koma gida, to gwanda gidan dai zaman asibiti ba dadi garesa ba" "To Mom" Sultana ta fice bata jima ba suka dawo da wani likita ya rubuta musu sallama suka yi gida, dakin masu aiki dake kasa wajan cikin parlour bayan step dakin mai aikinsu na da Haule wacce tayi aure,bama iyakar Haule ba duk masu aikinsu nan ne dakin da suke zama,babban daki ne dasu babban gado da wardrope da toilet da komai da komai, Sultana ce ta nuna mata yadda zata yi amfani da komai,bayan ta nuna mata Aziza ta kalleta ta ce "Na gode Anty Sultana" Sultana ta yi murmushi ta ce "Ba komai mai kyau, amma meyasa kike son rufe fuskarki? Har yanzu baki saba damu bane?" Cikin in-ina Aziza ta ce "Inada matsalar ido ne, tun ina yarinya bana son haske, sannan bana iya kallon mutane da idona shiyasa mahaifiyata ta bani wannan mayafin ina lullubi da shi, gashi na kuma na fiddo da shi dan ya rufe min daya idon da zan dinga ganin hanya" "Ayya Subhanallah! Idan Brother ya dawo zan gaya masa sai ya duba miki idon, watakila idan aka dace sai ya miki magani" Da sauri Aziza ta ce "A'a Anty Sultana karki gaya masa halittatace a haka aka haifeni" "To shikenan,bari na bar ki ki huta sai na shigo anjima,idan kika warke sosai akwai abunda zan dinga koya miki,ina sonki da ƙawa! kinga bana da ƙawa bana shiga hidimar mutane amma ke kin shiga raina" murmushi kawai Aziza ta yi dan ita kadai tasan yaƙin da yake gabanta, tashi Sultana ta yi tana fadin "Bari naje na kawo miki wasu kayana ki saka yanzu kiyi wanka duk da nasan kayan zasu miki yawa, amma ki canza na jikinkin nan" Aziza ta amsa da to na gode sosai, Sultana tana fita Aziza tayi shuru tana saƙa da warwara, zuwa can ta mike zata shiga bayi har ta manta da ciwon kafarta sai ji ta yi ta takesa, zafi taji ta saki kara sannan ta koma ta zauna tana fadin "Ba zan iya jurewa ba" hannu tasa ta shafe wajan nan kafarta ya dawo dai-dai sannan ta shiga ta yi wanka kamar yadda Sultana ta nuna mata amma bata wanke kanta ba,tana fitowa Sultana na shigowa ta kalleta ta ce "Ba ki wanke kanki ba? To ki bari karki wanke,idan kikaji sauki sosai sai muje a wanke miki, wannan gashin naki ai sai wajan masu salon, yanzu ga wa innan kayan ki fara lallabawa da shi Mom ta ce zata siyo miki wasu" godiya sosai Aziza tayi,ta dauki wani dogon abaya ta saka ya mata kyau duk da ya mata yawa tasa ta dau hijabi ta tada sallah,ta jima tana addua Allah ya bata mafita a kan wannan babban lamari nasu, kafin sultana ta shigo ta kirata ta fito taci abinci. 🐍🐍🐍🐍 *KUNTAU.* wani hamshakin gate Azima ta tsaya tana kallon gate din, ganin tsaruwarsa da haduwarsa zuciyarta ne ya raya mata wannan gida taji gidan ya kwanta mata a rai,kuma dole uwar naki sai ta zauna a wannan gida ko ana ha maza ha mata, da wannan tunani ta yi gate din ta hau kwankwasawa. 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *ALLAH KA RABANI DA ZUWA GABANKA DA HAKKIN WANI, WANDA KUMA YAJE DA NAWA ALLAH KANA GANI ALFARMAN WANNAN WATAN DA ZAMU SHIGA,WATAN FALALA,WATAN TUBA,WATAN MAI ƊINBUN YAFIYA, A YAU DAI NA YAFE MASA,IDAN KUMA HAR ZUCIYARSA BAI JI TSORONKA BA,YA ALLAH KAI KASAN YADDA ZAKA YI DA SHI, ALLAH KASA MU DACE DUNIYA DA LAHIRA,ALLAH AMIN* *PAID.* 🅿️=4️⃣3️⃣↪️4️⃣4️⃣ Da sauri Sultana ta fito tana kwalawa Aziza kira, fitowa Aziza ta yi ta ce "Gani Anty Sultana" "Yawwa Aziza dan Allah zo ki tayani kwashe tray zan kai wa Yaya abinci ashe ya dawo" "Oh har ya dawo?" "Nima wlh ban sani ba sai da ya kirani a waya" "Ayye" cewar Aziza ta duƙa tana daukar tray din da Sultana ta gama jera su plates, sannan itama ta dau ɗaya tayi gaba Aziza ta rakata a baya. Da sallama suka shiga Sultana ce a gaba sai Aziza dake binta a baya kanta a duƙe cikin hijabi gabanta na faduwa, yana kwance a dogon kujera yana sanye da jallabiyya, amsa sallamar tasu ya yi yana tashi zaune, da sauri Sultana ta ajiye tray din hannunta ta zauna kusa da shi tana masa sannu da zuwa,kanta ya shafa cikin kulawa yana amsawa, duƙawa kasa Aziza ta yi bakinta na rawa ta ce "Ina wuni *HAMMA NAWAZ* ya hanya?" rassrassras! gaban Nawaz ya faɗi ya ƙura mata ido amma ta gefen ido yana kallon yadda take rirriƙe yatsun hannunta jikinta na rawa daga nesa yake karantar yanayinta duk da ta boye fuskarta cikin hijabi sai saitin ƙaramin bakinta da yake iya hangowa wanda shi ma ke b'ari, "HAMMA NAWAZ!" yake ta nanatawa a ransa, Aziza kuwa jin bai amsa mata gaisuwarta ba alhali ya amsa na kanwarsa yasa ta tashi a hankali jiki a sanyaye zata fita, watakila baya amsa gaisuwar masu aiki, har ta kai bakin kofa sai taji Sultana na faɗin Aziza ina kuma zakije?" "Amm dama Anty Sultana dama akwai kayan da ban....kwa. She...ba...ina...so..ne...naje....na kwashe" ta karasa maganar da in-ina tana fita da sauri, cikin fuskar tausayi Sultana ta juyo ta kalli Yayanta ta ce "Bro,wlh Aziza bata ji dadi ba, ta gaisheka baka amsa ba fa,kuma kamar ma naga tsoronka takeji" "Za ki yi serving ɗina ne ko zaki cika min ciki da magana?" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, kasancewar tasan halinsa yasa ta zuba masa abincin ta ajiye masa komai sannan ta fice itama,tana fita ya dauki spoon zai kai abincin bakinsa sai ya tsinci kansa cikin rashin jin dadin amsa gaisuwarta da bai yi ba, HAMMA NAWAZ! ya faɗa a fili ya saki murmushi jin yadda ta kira cike da harshen fullaci kuma sai sunan ya yi daɗi a bakinta, da kyar ya lallaba ya ci abinci dan kuwa yaji dadin abincin sosai yaci yasha zobon da suka haɗa ya yi hamdala, nan ya zauna suna waya da amininsa yana gaya masa ranar thursday In sha Allahu yana hanya zai bi jirgi amma sai ya ƙara komawa ta abuja, Allah ya kawo shi lafiya ya yi masa,yana kan waya har aka kira sallar magriba dan haka yace masa za shi masallaci suka yi sallama akan cewa sai sunyi waya anjima, alwala Nawaz ya yi ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya haɗa da isha'i, ko da ya shigo gida babban parlourn gidansu ya wuce da sallama ya shiga a lokacin Aziza na riƙe da kaskon turaren wuta ita kadai ce ma a parlourn, jin sallamarsa yasa jikinta ya dauki rawa wanda bata san dalilin hakan ba, cikin rawar murya ta amsa sallamar ta shi ta ajiye kaskon hannunta tana shirin shigewa daki da gudu taji muryarsa kamar daga sama "Ya kike? ya jikin naki? Yanzu babu inda yake miki ciwo ko?" ya faɗa lokaci daya,cak Aziza taja ta tsaya,a iya saninta Sultana da Mom suna sama,to kenan da ita yake yi? take tambayar kanta, bata amsa ba bata juyo ba sai da taji ya sake fadin "AZIZA baki ji ina miki magana ne?" sai a sannan ta juyo murya na rawa ta ce "Alhamdulillah na warke" tana gama fadi ta shige daki, shuru ya ɗan yi yana nazartan yarinyar daga baya kuma ya yi tsaki ya hau sama,dakin Mom ya je ya kwanta a gadonta suna hira, Mom ta ce "Bana ma kenan a kasar waje zaku sake yin Azumi ga Azumi ya ƙarato, meyasa ba zaka sa amininka ya dawo nigeria kuyi azumi a gida ba? Bana dai ace kunyi sallah a kasarku tare damu" "Mom kema kin san ba zai dawo ba ko da na faɗa masa, azumi kuma In sha Allahu mai zuwa idan rai ya kaimu ai muna nan a gida In sha Allah" Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai ya kamata,ni na ƙagu ku dawo dan ku nemo matar aure ku aura,barin ma Son yana da bukatar mata wacce zata kula da shi" "Ai ya samu Mom" Mom ta ce "A'a gwara dai fa ya samo mai tarbiyya da natsuwa da hankali" Nawaz ya tabe baki ya ce "Humm wanda yake fadin zai aura ni kwata-kwata bata min ba,bamu shiri da ita ko kadan amma shi yace zai aureta,kuma abun takaicin fa Mom shima ba sonta yakeyi ba" "To ina ruwanka? kai fa matsalarka Nawaz zafin zuciya" Mom ta fada tana kallonsa "Mom ai ba zan can ina ruwana bane ko zafin zuciya,magana ce ta gaskiya,kuma ai abunda ya shafesa ya shafeni" "To kawai ka tayasa da addua shine babban soyayyar da zaka ci gaba da nuna masa" "In sha Allah Mom" daga haka suka ci gaba da hirarsu,bai baro dakin Mom ba kuwa sai sha biyu na dare yana fitowa ya shiga dakin Sultana bata nan,tana can dakin Aziza tana koya mata karatu,cikin ikon Allah Aziza ke ganewa, da bai ganta a dakin ba ya yi tunanin ko tana toilet ne dan haka ya wuce part dinsa ya kwanta, sai sha biyu da rabi Sultana ta miƙe tana fadin "To Aziza bari mu dakata da karatun haka sai Allah ya kaimu gobe kuma, yanzu akwai wani horror series film din da nake kalla, 12 ake farawa a gama 1:30 ga shi yanzu har sha biyu da rabi sai dai na kalli karashi,ko zaki zo muje ki kalla ne?" Aziza ta ce "Me hakan ke nufi? shi horror din" sai da Sultana tayi dariya kafin ta ce "Ina nufin fina-finan dodanni, kamar irinsu abun tsoro haka da film din macizai!" rassssss! gaban Aziza ya buga ta yi sauri dago fuskarta ta kalli Sultana ta tsakiyar gashinta da ya rufe mata fuska,Sultana ta kwashe da dariya ta ce "Matsoraciya kawai,daga faɗa miki har kin firgita, wlh kuma fa Yaya ya hanani kalla har cewa yake min ranar da na fara ganinsu a zahiri zan sani, yanzun ma inada tabbacin ya tafi part dinsa,kinga sai da safe" tana fadi ta fice ta bar Aziza da zare ido tana tunanin ranar da Sultana zata ganta a macijiya mai zai faru? Saurin kau da tunanin ta yi tana fadin "taya ma hakan zata faru?" ajiye tunanin tayi a gefe ta shiga ta ɗauro alwala ta tada sallah,ta jima tana addua tana kuka tana neman taimakon mahaliccinta. 🍃🍃🍃🍃🍃 Kwana a tashi ba wuya a wajan Allah, Azima duk hankalinta ta karkata shi wajan sakawa su Maman Hanan da Maman Beenah ido ganin manaƙisan da suke kullawa wanda bai ji ba bai gani ba, ta sha jin haushin kanta a kan ƙutse da take yiwa wanda bai san da ita ba kamar yadda itama bata san da shi ba, ga shi duk sadda ta yi yunkurin barin gidan sai taji kamar an ɗaure mata kafafu,wannan gida ya zame mata karfen kafa. 🍃🍃🍃🍃 Ana gobe Nawaz sai tafi abuja jibi kuma zai wuce america ya yi wani mugun mafarkin da ya gigita duniyarsa, Aziza ce ya gani a jejin da yafi na kullum muni tana kuka tana miƙa masa hannu ya taimaketa, kar ya tafi ya taimaka mata,ƙiri-kiri ya ganta a macijiya. 🍃🍃🍃🍃 A Lallaba yau aiki yamin yawa🏃🏻‍♀️ MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=4️⃣1️⃣↪️4️⃣2️⃣ Mai gadi ne ya leƙo jin ana kwankwasa kofa ya ga bafulatana tana tsaye kanta a duke, "Baiwar Allah lafiya kuwa?" cewar Mai gadi,kuka Azima ta saka tana fadin ya taimaka ya yi mata magana da masu gidan,mai gadi ya ce "Baiwar Allah zan gaya miki gaskiya,me wannan gidan baya ma kasar gabadaya! Ya jima baya nan,iyayensa ne a gidan,idan kuma wani neman taimako kikeyi to wallahi ba zaki samu komai a wajansu ba,dan basu kyauta" Azima ta ce "Ina da bukatar yi musu aiki ne,don Allah kayi mini magana dasu, ni ba kudinsu nake so ba" Ganin yadda ta dage yasa Mai gadi fadin "to ɗan shigo daga ta ciki sai nayi miki magana dasu" Azima tana sa kafa a gidan gabanta ya bada dammmm!! Da karfi sai da ta danne saitin zuciyarta,mamakin faduwar gaban nata take yi, a kan benci mai gadi ya nuna mata ta zauna shi kuwa ya nufi babban parlourn gidan da sallama, wata mata ce zaune a hakimce a kujera ta ɗora daya a kan ɗaya tana danna waya,sallamar mai gadi ya sakata ɗagowa tana kallonsa da kyar ta amsa, "Allah ya taimakeki ranki shi daɗe" "Lafiya kuwa Ɗan'Bala?" "Wlh Hajjaju wata 'yar fullo ce a waje take ta faman kuka a taimaka mata tana neman aiki, ina ga irin wa inda 'yan fashi suke kai musu farmaki rugarsu ne, su kashe musu kowa su kwashe shanukansu, wlh Hajjaju abun tausayi" shuru Hajjaju ta yi kafin ta kalli Dan'Bala ta ce "Je ka shigo da ita" Ɗan'Bala ya amsa da to sannan ya fice da sauri ya zo ya samu Azima dake zaune ya ce "Zo mu shiga Hajjaju na kira" ba tare da Azima tayi magana ba ta tashi ta bi bayansa, suka shiga parlourn, sosai Hajjaju ta karewa Azima kallo sannan ta kwala kiran wata mai aikinsu "Hadiza! Hadiza! Hadiza!" wacce aka kira da sunan Hadiza ta amsa da na'am da fito da sauri ta duƙa a gaban Hajjaju, Hajjaju ta ce "Hadiza je ki yiwa Maman Hanan magana ki ce mata da sauko kasa yanzu" Hadiza ta amsa da to,sannan ta hau da sauri, a tare Hadiza suka sauko da wata dakekkiyar mata wacce ita ma da ka ganta zaka san ta yarda da kanta, tana tafiya a gaba Hadiza na binta a baya,tana saukowa ta ce "Lafiya kuwa Maman Beenah?" "E lafiya lau mai aiki ce dama za a dauka shine nace a kiraki tukunna" "E ya kamata ai, idan yaso sai ta dinga gyara su dakuna tana sharewa da gogewa dan aiki ya masu Hadiza yawa" "To shikenan sai mu kirasa anjima mu gaya masa mun kara daukar mai aiki dan ya tanadi kudin biyanta ita ma" "Ah to shine magana ai,idan bai kashe mana kudin ba munyi wadaka yadda muke so ma wa zai yi ma wa? Tunda Uwar da Uban duk sun mutu" Maman Beenah ta yi murmushi ta ce "Ai muyi kokari da ya dawo mu haɗa masa kannanmu ya aura dan mu ci gaba da tatsarsa" "Wannan magana taki haka take, Hadiza shiga da wannan ki nunnuna mata abunda ya dace, su dakuna zata dinga gyarawa, dakin su Hanan da Beenah da Hanif sai kuma namu dakunan, sai idan *AL'MAZEEN* ya dawo zata dinga gyara masa nashi dakin dan haka har part din Al'mazeen zaki nuna mata amma ba yanzu ba" "Tukunna ma ya sunanki?" "AZIMA BANJU!" cewar Azima kanta a duƙe "To kin dai ji aikin da zaki dinga yi mana ko? Za a dinga baki dubu goma a wata" "Na gode sosai" cewar Azima, Maman Hanan ta ce "Kuje da ita Hadiza" "To Hajiya,Azima zo muje ki ga dakinmu" da kyar Azima ta miƙe dan tun lokacin da aka kira sunan *Al'mazeen* ta nemi natsuwarta da karfin halinta ta rasa, a zuciyarta take tambayar kanta waye shi Al'Mazeen din? dole ta ga waye shi dan daga kira sunansa sai jikinta ya yi sanyi? anya zata iya zama a gidan kuwa? daga fara saka kafarta a gidan tayi tuntube da faɗuwar gaba,yanzu kuma an kira suna zuciyarta ta tsinke, jin babu kuzari a gangar jikinta yasata b'allan gashin kanta ta sa a baki ta lumshe ido tukunna taji ta dawo dai-dai, Hadiza ce ta nunnuna mata abubuwa dasu dakunan da zata dinga gyarawa a sama da kasa,amma bata haura da ita part din Al'mazeen ba, kasancewar an ce mata ba yanzu za a nuna mata ba,Azima kuwa tace ba zata iya jira ba ko da yaya ne sai ta shiga part din ta gani. 🍃🍃🍃🍃🍃 Yau kwanan Azima biyu a gidan,kuma cikin ikon Allah babu wanda ya shiga hidimarta kamar yadda bata shiga tsabgar kowa, sunan wanda ake kira da AL'MAZEEN shine ya tsaya mata a rai, ga shi bata san part dinsa ba,kuma ba zata iya tambayar su Hadiza ba,dan bata son yawan magana , Beenah har kyautar kaya suka mata,kuma babu wanda ya taba yi mata magana a kan rufe fuskarta da take yi kasancewar ansan kunya gado ce ta fulani, ko Hanif da yake namiji baya shiga hidimar Azima,idan kuma gyaran daki ne tana shiga zata hura iska ta bakinta dakin shi da kansa zai gyara kansa,idan ta shiga daki ko minti goma bata yi zata fito da an shiga za a gansa fesss! shiyasa daga Maman Hanan har Maman Beenah suke jin dadin zama da Azima,ita kuwa Azima yanzu tunanin kisa ya fita a ranta sai son ganin waye AL'MAZEEN. 🍃🍃🍃🍃 A kwana biyu kuwa Aziza ta ɗan sake dasu Mom da Sultana barin ma Sultana da bata nuna mata ƙyama tana janta a jiki, ranar da ta cika kwana biyar a gidan ganin jikin nata da sauki sosai yasa Sultana zuwa wajan Mom tace Mom ta basu kudi zata kai Aziza wajan gyaran gashi, Mom tayi murmushi sannan ta bata kuɗi ta ce driver ya kai su. Bayan sun je shagon salon din za a buɗewa Aziza fuska ta hanyar kwashe mata gashi tayi saurin saka tafin hannunta a fuskarta dama da kyar ta yarda ta cire hijabinta, dariya Sultana ta sa tana fadin "Duk rowan da kike mana na ganin fuskarki yau dai dole ki bude" da kyar mai salon ta lallaba Aziza tana kwashe gashin Aziza tayi saurin rufe idonta gam, kan aka hau wanke mata kai ɗin, Sultana na zaune a gefe wayarta ta yi ƙara tana dubawa ta ga Brother da sauri ta daga tace "Assalamu alaikum, Brother ina kwana?" Daga can ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Lafiya lau Sultana ya kuke? Ina Mom? Na kira wayarta bata ɗaga ba,ki gaya mata yau ina hanya" "To Brother sai dai nima na kirata a wayar" "Sabida me? yau ba saturday ba ai ba skull, ko kina skull din ne?" "A'a Bro ina shagon salon na raka Aziza ne a wanke mata kai" jin sunan da ta kira yasaka shi katse wayar da sauri, dan tun ranar da ya buge yarinyar nan yake mafarkin tana neman taimakonsa,tun abun baya damunsa har ya koma damunsa, da fari ya yi tunanin ko dan ya bugeta ne amma a yanzu ya kasa fahimtar halin da yake ciki, da ya ji Mom tace ta dauketa aiki har cikin ransa bai so ba amma dai bai ce komai ba. Sultana kuwa mamakin katse wayar ya yi tayi,daga baya kuma ta ce "Uhum Yaya kenan" wayar Mom ta kira bata ɗaga ba itama, ta kalli mata mai salon din ta ce "Dan Allah Anty ki gama mata da sauri zamu tafi gida Yayana wai yana hanya" "Ai gashin nata ne dayawa wlh ga tsayi ga cika tabarkallah Ma sha Allah!" Sultana ta yi murmushi. Kusan mintuna talatin aka kwashe ana wankewa Aziza kai idonta kuwa yana lumshe ko da wasa bata buɗe ba, bayan an gama ne aka busar mata da kai din aka shafa mata mayuka masu kyau da ƙamshi aka taje mata shi sannan aka sa ribbom aka daure mata shi, Ma sha Allah! shine Abun da Sultana ta faɗa ta ciro wayarta tana daukar Aziza hoton wacce ta yi saurin maida hijabinta tana rufe fuskarta,bayan Sultana ta biya kuɗin mai salon suka mata godiya suka fice tana ta yabon kyawun Aziza da dogon gashinta,ita dai Aziza tana murmushi ne kawai sama-sama, bayan sun shiga mota Sultana ta ce "Yanzu mu fara biyawa mu karbo kayanki na wajan tela, yawwa dama ina so na tambayeki,kin iya karatu?" Aziza ta gya ɗa kai ta ce "Nayi sauƙan al'kur'ani mai girma a kauyenmu, sannan na karanta litattafai da dama,na iya rubutu kamar irinsu ko da wasika idan Baffanmu zai rubuta idan rubutun tayi masa yawa ina tayasa rubutawa amma ba da irin rubutunku ba, da harafin su Alif kamar ajimi haka" Sultana ta ce "Ahh Ma sha Allah ki ce malama ce" ta faɗa a mamakince dan kuwa ta sha mamaki ɗin sosai, murmushi Aziza ta yi ta ce "A'a ina dai kan neman ilmin" To shikenan zan koya miki karatun hausa da turanci ta yadda zaki iya duka,idan har kina ganewa da wuri zan cewa Yayana ya nema miki skull mafi kusa da saurin ganewa,sannan matsalar idonkin nan ya nema miki medicalglass" "A'a Anty Sultana karki gaya masa,ki bari kawai idan kika koya mini ma ya isa, idona kuma haka yake haka aka haifeni dan Allah ko wa Mom ne karki ce mata komai" Sultana ta yi murmushi ta ce "To shikenan" Bayan sunje sun karbo kayan suka koma gida a daki suka samu Mom, Mom tace "sannunku da dawowa 'yan matana har kun dawo" Aziza ta duka kasa Sultana kuma ta zauna a gefen gadon Mom, ta ce "E Mom mun dawo barka da gida, dazu muna shagon salon Yaya ya kirani wai yana hanya mun kiraki baki daga ba" "E munyi waya da shi daga baya,kema na kiraki bai shiga bane, lokacin da ya kirani ashe na tashi na bar wayar a parlour shiyasa, yanzu dai ku tashi kuje ku gyarawa Yayan naku dakinsa, idan kun gama sai ku shiga kitchen" dan mom bata yarda da lalaci ba dan babu irin girkin da Sultana bata yi shiyasa da shike basu da yawa a gidan kuma ba yara garesu ba shiyasa mai aiki daya kawai suke dauka, suka amsa da to, Aziza ce ta fara tashi ta fita, Sultana ta ce "zo muje part din Yayan" tayi gaba Aziza na binta a baya, suna fita sai ga wani ɗan ƙofa madaidaici Sultana ta buɗe suka shiga,parlour a kasa har da step wani sashene mai zaman kansa a wajan tabbas an tsara parlourn ya tsaru, Aziza matowa tayi da kallon parlour,idonta ne ya sauka a wani pic babba a parlourn shi daya da kuma wani a gefe su biyu, dukkansu fuskarsu babu murmushi,tabe baki Aziza ta yi,dan ita bata ga abum gyara a wajan ba,ganin yadda take kallon hoton ne yasa Sultana fadin "wannan shine Babban Aminin Yaya baya da wani sama da shi, a tare suke a america tare suka yi karatu gabaɗayansu kuma likitoci ne, karki ga fuskarsu haka a haɗe barin ma yadda kika ga na Abokin Yaya,to wlh yafi Yaya Nawaz sauƙin kai,kawai dai shi magana ce bai cika yi ba da dariya,amma idan kina neman zafin zuciya kika samu Yaya Nawaz kin gama" jinjina kai Aziza tayi ba tare da tayi magana ba,suka hau sama yadda k'asan ya tsaru haka ma saman ya tsaru haka de ta dinga bin Sultana har suka gama suka saka masa turaren wuta sannan suka wuce kitchen suka hau girki, dama Sultana na koyawa Aziza yanayin girkinsu,duk abunda ta koya mata sau daya kuma cikin ikon Allah ta riƙe kenan babu mantuwa, idan tazo yi kuma sai tayi wanda yafi na Sultana daɗi, haka suka yi girki a tare suka gama duk da ba wani hira sukeyi ba,tunda Sultana ta fahimci Aziza bata son yawan magana yasa itama bata takura ba,ita kuwa ba zata fahimci tashin hankalin da take ciki bane,bata fata su gano cewa ita ba mutum bace macijiya ce har su rabu tinda zama dasu na wucin gadi ne, bayan sun gama girki Sultana ta ce "Aziza je kiyi wanka ki canza kaya, sai ki kwanta ki huta idan kika huta da dare sai mu fara karatun ko?" "Dazu fa kafin muje wajan wankin kai nayi wanka" "E na sani,ai ita tsafta bata yawa sai dai tayi kaɗan, zaki dinga yi ne dai-dai gwargwaɗon iyawarki,kuma gwara ki saba da shi tun daga yanzu dan bamu sani ba watakila Mom ta samu surki a nan garin" wani wawan faduwar gaba ne ya ziyarci Aziza ta sake maimaita kalman sirki a ranta, da kyar tayi murmushin karfin hali ta amsa da to a sanyaye sannan ta wuce daki,itama Sultana sama ta haura, Aziza na shiga daki ta wuce toilet, tana shiga ta maida kofa ta rufe ta rintse idonta ya sake komawa fari, fatar jikinta ma fari yana sab'ulewa, daga ƙasarta ta fara rikiɗewa nan ta zama rabi mutum rabi macijiya sannan ta zauna a gefen bath din wanka ta hau kuka, tunowa da maganar Arɗo da Baffa Mandi, na cewa ba zata warke ba har sai sunyi aure, kuma ita warakanta yana tattare da Azima wacce bata ma san a wani duniya Azima take ba, sai bayan da ta gama shan kukan nata kafin ta yi wankan ta fito. 🍃🍃🍃🍃 Sai huɗu Nawaz ya samu damar isowa, ko da ya iso wajan Mom ya nufa nan take masa sannu da zuwa tare da fadin "Nawaz sai yanzu?" "Wlh Mom motata ce ta ɗan samu matsala a hanya sai da aka mata gyara" "Subhanallahi! Karfen nasara babu tabbas Allah ya kara kiyayewa" "Amin Mom bari na samu na ɗan watsa ruwa sai na fito na ci abinci,ina Sultana?" "Ba mamaki tana dakinta,bata ji shigowarka ba ai da ka ganta da gudu" murmushi ya yi kawai ya fice, part dinsa ya shiga ya samu na tashin kamshi bai tsaya wani bata lokaci ba ya yi wanka ya shirya ya fito, ji yayi ba zai iya komawa babban parlour ba dan haka ya kira Sultana ta kawo masa abincin part dinsa. 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 GARKUWAR MACIZAI🐍😂 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=4️⃣5️⃣↪️4️⃣6️⃣ Hakika wannan mafarki ya tayar masa da hankali, ko da ya farka da washe gari jikinsa a mace, da kyar ya gama shiryawa ya fito ya yiwa Mom sallama da shike driver ne zai kaisa ya dawo, shiyasa zasu yi fitar wuri, bayan sun gama sallama da Mom suka rakasa har bakin mota, sai ware ido yake yi inda zan hangi Aziza amma bai ganta ba, kallon Sultana ya yi ya ce "Ina Aziza ne?" "Ina ga tana dakinta bari na dubota" "Noo leave her" ya faɗa yana jan murfin mota Mom tana kan yi masa addua yana amsawa da amin, Mom da Sultana basu koma cikin gida ba har sai da motar ta fice a gate gabadaya aka ja gate din kafin suka koma,ko da suka shiga Sultana ta wuce dakin Aziza ta sameta zaune tana ninke kayan Mom da ta wanke, Sultana ta ce "Aziza baki fito kinyiwa Yaya Allah ya kiyaye hanya ba har sai da ya tambayeki wlh" "Ayye ban san ya fita ba da shike ina nan ina ninke kayan Mom ne" ta faɗa ba tare da ta dago ba, alhali taji sadda suka sauƙo dasu Mom har sadda ya shiga mota duk tana tsaye tana leƙensu ta window, sai da ta ga motar ta fice a gidan kafin ta koma daki, Sultana ta ce "To ke miye haɗinki da kaya ina Buba yake?" "Wlh jiya ne yaji ciwo a hannu shiyasa na karba kayan na wanke" "Subhanallahi! Allah ya kiyaye gaba amma ai sai ki faɗa ba wai ki wankesu da kanki ba da an nemo mai wankewa,yanzu dai ki gama ɗin sai ki zo muje Mom ta aike mu karbo kulolin azumi wanda ake abincin sadaka dasu gidan wata kawarta a nan malali" "To Anty Sultana bari na karasa gani nan zuwa" "To kiyi sauri ki shirya, saura kuma wlh ki zunduma hijabin kin nan, dan Allah ki nemi abaya ki saka ki yafa gyale akwai gidan da zaki rakani mu shiga tare Mom ta bamu sako ma a gidan" da to Aziza ta kara amsa Sultana, Sultana tana fita Aziza ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "Allah ya kaika lafiya Hamma Nawaz, ba mamaki ba zaka dawo ka sameni ba" ta fada tana mai lumshe ido, saurin kwashe kayan ta yi ta kaisu dakin guga, sannan ta koma ta shirya shap-shap tasa doguwar abaya baƙi ta dauki ash'color din gyale taja gashin kanta ta nannaɗesa ta daure a tsakiyar kanta ta dau hula ta saka kafin ta dauki mayafin ta yi lullubinta kamar kodayaushe,ko da ta fito parlour Mom da Sultana suna parlour Mom tana kara ba wa Sultana saƙo, itama ta yi shigar bakin abaya, tana fitowa Sultana ta ce "Yawwa ko ke fa" murmushi kawai Mom tayi ta ce "Ma sha Allah 'yan matana, Allah ya kawo miji na gari,kodayake ma yanzu kam sai dai nayiwa 'yata Aziza dan ita Sultana rana kawai za a saka" A sanyaye Aziza ta ce "Lahh Anty Sultana shine baki gaya mini ba? To Allah ya kaimu Allah ya sanya alkhairi" Mom ta amsa da amin Sultana kuwa ta dukar da kai tayi tana murmushi,bayan Mom ta gama basu saƙon ta ce "Dan Allah karku kai magriba,Sultana karki ga dan Nawaz baya nan ku kai magriba kin san dai ko da wani lokaci kiran waya yake yi,da ya kira kuma zai ce ina kike, dan haka kuyi ku dawo" "In sha Allahu Mom" suka faɗa suna ficewa, duk inda aka aikesu nan suka je, har gidan surakanan Sultana, a gidan kuwa wani ƙaninsa ya ga Aziza sai kallonta yake yi, har sai da ya biyo Sultana yana faɗin "Anty dan Allah wannan fa?" Murmushi Sultana ta yi tana faɗin "Kanwata ce,kana ciki ne?" "E wlh Anty ina ciki" "Lallai kam to sai ka gayawa Yayanka" "To Anty shi da baya kasar ki kirasa ki fara gaya masa,kinga ma sai a haɗa bikin da naku" "Ahh lallai Walid baka da kunya, wato ma a haɗa da namu?" "E mana Anty,kodayake ma ku da ba a saka ranar ba, sai a fara namu kafin Yaya ya dawo ke kuma kin gama skull kafin nan kema kin kara girma Anty" ya faɗa cikin tsokana, Sultana ta ce "Wlh Walid ka rainani,zan haɗaka da Yayanka kuwa" "Allah ya baki hakuri Anty,ni dai dan Allah ki fara min kamu" banza da shi Sultana ta yi ta shiga mota ta cewa driver yaja su tafi,basu tsaya ko ina ba sai gida,suna isa Mom ta musu sannu da dawowa tace musu idan sun huta su shiga kitchen suyi girki suka amsa da to. @@@@ Da washe gari sai dare Mom ta samu damar yin waya da Nawaz ya shaida mata cewa ya isa lafiya, Mom ta ce "Ma sha Allah haka akeso,Allah ya taimaka ka gaishemin da son" "Zaiji Mom,ina Sultana?" "Suna can daki ita da Aziza suna karatu, dama kuwa ni ina son yi maka magana a kan yarinyar inaso zan nema mata makaranta, tana da kaifin basira, wlh basu kai sati da fara karatu ba amma karka ga yadda kanta ke ja,abun mamaki" Shuru Nawaz ya yi na dan wani lokaci har sai da Mom ta kuma cewa "Nawaz bakaji me nace bane?" "Naji Mom duk yadda kikayi dai-daine, Allah ya baki lada" "Amin Nawaz" hira suka ɗan taba kafin suka yi sallama da shi. 🍃🍃🍃🍃 Bayan sati biyu da tafiyar Nawaz abubuwa da yawa sun faru daga ciki kuwa harda fara azumi da aka yi, sosai a wannan wata ta ramadan Aziza ta dage da addua Allah ya takaita mata wahalar neman yar uwarta su samu su koma gida, dan ta ƙosa ta koma ta ga iyayenta,kullum da Hajja take kwana take tashi a ranta har ma da Baffanta, ta maida lamuranta ga Allah. Ta bangaren Azima kuwa ta kasa gane meke mata dadi, dama duk azumin duniya ita kam ba yinsa take yi ba, to wannan din ma haka ta kasance dan ko daya bata yi ba, sosai kuma take sakawa su Hajjaju ido, duk wani ƙullin da suke yiwa AL'MAZEEN. Ana azumi lafiya da yardan Allah, tunda Nawaz ya bar nigeria ya kasa samun natsuwa, ga mafarkin Aziza da ya gallazawa rayuwarsa wanda ya rasa ya zaiyi da wannan mafarki, ga shi ya kasa gayawa kowa, wanda hakan har rama ya fara saka shi, wanda da an tambayesa zai ce azumi ne kuma ya haɗa masa da ba a gida yake yi ba shiyasa. Ana saura kwana uku sallah Sultana ta kai musu dinki wajan telarta inda ya cire musu zuƙa-zuƙan dinkuna na gani na fada, laces kala biyu, atampa kala uku, sai shadda da material kala ɗaɗɗaya, da gyalensu da takalminsu dasu sarƙa da ɗankunne, da komai da komai, hakika Mom ta yi kokari,Sultana kuwa ta yi bajinta wajan zabo musu kaya masu kyau, ita ma Azima anyi mata, amma sam basu gabanta dan bata saka a ranta zata yi wani kwalliyar abu sallah ba. Ana gobe sallah sai aikin suke yi dukkansu a kitchen har da Mom, Sultana ta ce "Mom wlh zan yiwa Walid ba dadi, kinga yadda ya takura min wai yana son Aziza?" Mom ta yi murmushi ta ce "Kai yarinta, duka-duka nawa kike bare kuma Walid? to kuma aje ga maganar Aziza wacce take da 15, Aziza ki maida hankalinki a kan karatunki kinji ko? In sha Allah bayan sallan nan zaki fara zuwa university dinsu Sultana tunda Allah ya baki kwakwalwa karki biyewa shirmen Walid kar ma ki fara kulasa, idan Khalil yaji ma ransa ne zai b'aci" Aziza a ranta ta ce "Ina kuwa nake da lokacinsa,da yasan wacece ni ba zai so kara yin magana da mai irin sunana ba ma" a fili kuma ta ce "Ni Mom ina da burika da yawa bana da lokacin kulasa" "Yawwa Azizata" cewar Mom suka ci gaba da aiki har karfe sha biyun dare kafin suka tattara suka kwanta, da washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, abinci sukayi dukkansu har da Mom, karfe takwas da rabi suka gama, Sultana ta ce "Aziza kiyi wanka da sauri ki zo muje masallaci" Aziza ta amsa da to. Wanka sukayi suka saka shaddarsu, sannan suka saka hijabansu mai alkebba da takalmansu, suka fito har da Mom itama da ta dake cikin lace dinta, gabadayansu zasuje masallaci dan Mom tace abu daga shekara sai shekara nan ma sai mai tsawon rai wanda Allah ya nufesa da gani. Haka akayi idi lafiya, sai fatan Allah ya amshi ibadunmu na alkhairi ya yafe mana kurakurenmu amin. @@@@@@ Bayan sun dawo gida, nan yan uwa da abokan arziki suka hau zuwa ana yiwa juna barka da sallah, masu kawo abinci suna kawowa wa inda ake kai musu ana kai musu, Mom tana haɗawa tana bayarwa ana miƙawa bayin Allah, dasu lemuka da purewater, da kuɗi haka Mom ta dinga rabo, Sultana kuwa tana cikin yan uwanta ana shan su pics ana gaisawa an dade ba a hadu ba, Mom ce ta shigo babban parlour ta kira sunan Sultana ta ce "Sultana ina Aziza ne kam?" "Wlh Mom tun da muka dawo inaji bayan mun gama hada abincin da za a fita da shi ban ƙara ganinta ba, dan tun sadda baki suka fara shigowa ban ganta ba" Mom ta ce "Kin san Aziza bata son mutane kamar ma kunyarsu takeji yanzu haka to ba mamaki tana daki" "Wlh kam Mom kunyar mutane takeji,ko mu a gida Aziza bata gama sabo damu ba bare kuma yau ta ga mutane ai ba zata fito ba,amma bari naje na fito da ita dan yau yawon sallah zamu je a ga yan uwa da abokan arziki" Mom ta ce "dubota to, sai ku shirya ku fita nima zanje gidan Hajiya Hauwa(gidan sirkan Sultana, Hajiya Hauwa ita ce Mamansu Khalil wanda zai auri Sultana) dan yau muma zamuje ziyara ne" "To Mom" Sultana ta faɗa tana tashi da sauri ta yi dakin Aziza a lokacin ta gama kukanta tana tunanin wan can sallar tana gida tare da Hajjanta da Baffanta, Sultana tana shigowa Aziza na fitowa daga toilet ta wanke fuskarta, Sultana ta ce "Ohh Allah Aziza, sabida kinji gidan a cike shine kika boya a daki? To maza ki shirya, zamuje yawon sallah" "A'a Anty Sultana bana son fita,bazan je ba" "Wlh sai kinje, Mom ma fita zata yi,yau ranar zumunci ce, yau fa ranar farin ciki ne amma ke na ga kamar ba baki farin ciki ko mun yi miki wani abu ne?" Aziza ta girgiza kai, "To idan har ba mu miki komai ba ki shirya yanzu ki canza kaya ki saka atampa,bari nima naje na canza kaya" Aziza ta gya ɗa kai, Sultana ta fice. har Sultana ta shirya ta sha makeup ta kashe ɗauri ta yi pics ta turawa Khalil dinta, sannan ta fito dauke da handbag dinta ta shiga dakin Aziza ta sameta ta canza kaya amma tana zaune tana riƙe da ɗankwali a hannunta, Sultana ta ce "Ba kiyi kwalliya ba?" "A'a Anty Sultana ba zan yi ba" "A yau sallan? Wlh baki isa ba" Sultana ta fada tana daukar powder ta hau gogawa Aziza a fuska, sannan ta shafa mata red lipstick, duk da fuskarta taki bari ya fito sosai amma ta yi kyau, sannan Sultana ta kashe mata ɗauri, Subhanallahi! Aziza ta yi kyau sosai, nan Sultana ta daukesu hoto, duk da Aziza bata ɗago fuskarta sosai ba, sannan bata ɗaga idonta ba. Bayan sun fito parlour suka sake yi da Mom, sannan suka fice a gidan, a mota Sultana ta turawa Nawaz pics din tare da rubuta masa HAPPY SALLAH BRO NAWAZ. Ko da Nawaz ya buɗe ya ga hotunan yan uwa da abokan arziki, Allah Sarki gida dadi,ya fada yana murmushi a ransa, wani hoto ya bude ya ga Mom sai da ya sumbaci hoton, sannan ya sake buɗe wani ya ga Sultana ta yi kyau sosai ya ce "nice sis" ya sake bude wani ya ga da Mom da Sultana ya yi murmushi yana faɗin "My world" wani hoton ya sake buɗewa ya ga Sultana da Aziza amma bai ganeta ba, sai da ya kara buɗe wani ya ga tana dukar da kai kamar amarya kafin ya ganeta, sun sha lalle kuwa, wani hoton ya sake buɗewa Aziza na zaune a mota bata ma san sultana ta dauketa ba, lumshe ido Nawaz ya yi yana karanto adduar masifa dan Aziza ji yake yi ta zamo masa masifa, kansa ne ya hau sara masa sai da ya ɗan ji dai-dai kafin ya fita dan yaje ya samu amininsa su ɗan fita suma. 🍃🍃🍃 Kwana hudu su Sultana suna yawo,kullum kuma idan suka yi wanka sai Sultana ta musu hoto ta turawa Nawaz, tun yana buɗewa har ya daina buɗewa,dan ganin hoton shike kara masa mafarkai a nasa ganin kenan. 🐍🐍🐍 Ta bangaren Azima ko kaɗan bata yi wankan sallah ba bare shigar sallah, haka ranar sallar ta wuni tana jin haushin kowa,kiris ya rage abincin sallar ma bata watsa masa dafi ba, dan haka kawai ta ga kowa na murna da farinciki ita kuma tana ji kamar zuciyarta ya fashe da baƙin ciki da takaici, haka aka gama cin sallah Azima bata yi shigar sallah ba illa kayan fulaninta da ta dinga yawo da shi har satin sallah. Bayan komai ya daidaita haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, bayan sallah da sati biyu Aziza ta fara zuwa university din su Sultana, bata shiga hidimar kowa kasancewar tasan ita din ba mutum ba ce,haka zata je ta dawo,idan kuma Sultana na da paper su kan je tare su dawo tare, tana nan tana tara kuɗinta har ma da wa inda ta samu da sallah dan tace kwanan nan zata bar gidan. 🍃🍃🍃🍃🍃 "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Dan Allah Jauro ka taimakawa ƴata kar mayyar nan ta kasheta!" ya faɗa yana mai riƙe kafar Jauro, Jauro ya ce "Wlh Malam Halliru na kasa yiwa 'yarka magani, wannan mayyar tana da taurin kai" Salti dan gidan Jauro ya ce "Wlh Baffana baya da baiwa irinta Baffa Magaji, dama wajan Baffa Magaji kuka je da yanzu ta samu sauki, amma ku fara zuwa kuyi kamun kafa da Sarki Chubaɗo" "Wlh zanci ubanka Salti! Zaka fita mini ka bani waje ko sai na bazar da kai da sanda?" Salti ya miƙe yana kunkuni yana fadin "To dan na fadi gaskiya kuma Baffa" Salti na fita, Malam Halliru ya ce "Hakika munyi kuskure, dole wajan Magaji zamu je neman taimako" 🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=4️⃣7️⃣↪️4️⃣8️⃣ Wajan Sarki Chubaɗo Malam Halliru yaje yana kuka yana ba wa Sarki yankin fulanin kwana hakuri a kan ya taimaka yasa baki ya yiwa Magaji Bawa magana ya taimaka ya duba masa 'yarsa, Sarki Chubaɗo cikin tunzura ya ce "Ayhoo!! Ashe ku kuna son yaranku, shi da ku ka kora masa nasa ya yi yaya kenan? har kwanan gobe Jumala bata magana bata um bata um-um,nan ku ka daure Aziza kuna shirin kasheta! anyi haka ko ba a yi ba?" cikin kukan nadama Malam Halliru ya ce "Munyi kuskure ranka ya dade! Amma ba laifinmu bane Jauro ne ya zugamu ya sa mana tsoro da shakku, dan Allah a taimaka mini" Sarki Chubaɗo ya ce "Idan Jauro ya ce ku faɗa wuta zaku faɗa ne? idan har Magaji zai taimaka maka a nasa ra'ayin farillahi hamdu! amma idan ya ƙi wlh daga nan fada babu wanda zai saka baki" Malam Halliru ya amsa da ya yarda shi dai ayi masa izini yaje gidan Baffa, Sarki Chubado ya daga masa hannu alamun yaje godiya sosai Malam Halliru ya yi ya tashi da gudu har yana tuntube, bayan Malam Halliru ya tashi Wazirin kwana ya ce "Ranka ya dade bana tunanin Magaji zai ƙi taimakawa Malam Halliru" Garkuwan Fulanin kwana ya ce "Tabbas haka ne maganarka Waziri, Magaji Bawa Allah ya masa kyakkyawar zuciya,yana da tausayi da hakuri, yanzu haka sai ka ga ya taimaka masa" Sarkin Fadar kwana ya ce "Ai Halin Magaji Bawa sak wannan Yarinya tasa Aziza, amma ka ga wannan shaiɗaniyar Azima hummm!" Sarki Chubaɗo ya ce "Barewa ba zata yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, itama Azima Banju ke rayuwa a jikinta,ba zamu iya tantace ya halayyarta yake ba har sai an rabata da Banju wanda yake rayuwa a jikinta,ko kun manta da komai na jikinta yake rayuwa? Azima fa ba Azima ba ce BANJU ne, amma ni dai nasan Ɗawisu ba zatayi k'yal-k'yal banza ba" Garkuwa ya ce "Tabbas hakane, ranka ya dade, an fa ja watanni rabon da su Azima da Aziza a wannan yankin, wlh har bana son haɗuwa da Magaji sabida tausayin da yake bani, ga shi dole mutum ya dinga tunanin yaran suna lafiya ko akasin haka! Babban abunji ma ita ce Azima,mu nan da muke yankin jeji ne ya muka iya da ita,bare kuma aje ga mutanen cikin birni da suke da yawa ɗin nan" "In Allah ya yarda suna lafiya, Allah kuma shi zai ƙare bayinsa daga sharrin Banju, ina da kyakkyawar zato wa yarinyar nan Aziza, zasu dawo In sha Allah, sannu-sannu baya hana zuwa sai dai a daɗe ba aje ba, duk tsawon watanni ko shekaru su Azima da Aziza zasu dawo" cewar Wazirin kwana,Sarki Chubado ya ce "Haka shima Magajin yake faɗi, zasu dawo In sha Allah,yanaji a jikinsa yaransa suna nan lafiya, kuma zasu dawo garesa" "To Allah ya dawo mana dasu lafiya,ni kam ma Azizan nake son haɗawa da ɗan wajena" cewar Garkuwa, Waziri ya ce "Kai yanzu Garkuwa a tunaninka ɗanka Garbiyo zai yarda ya auri Aziza ne? Ai kai ɗanka bai yi halinka ba sam, tsoron bala'i garesa sai kace ba bafulatani ba" Sarki Chubaɗo ya yi dariya ya ce "Wlh ko cewa akayi Azima da Aziza sun warke bana tunanin Garbiyo zai yarda ya auri Aziza" Garkuwa ya yi murmushi ya ce "Garbiyo kam ai sai a hankali amma idan ya samu Aziza rayuwarsa zata yi kyau dan na yaba da halin yarinyar sosai wlh" "Hakane kam, yanzu dai adduar shine Allah ya dawo dasu lafiya" aka amsa da amin. @@@@@@@ Baffa na zaune a bukka yana lazimi, Hajja kuwa ta samu zaman kofar bukka a kan tabarman kaba,idonta kamar kullum a bakin kofar gida, sallah ce kawai yake tayar da Hajja sai kuma tsakar dare idan zata shiga ta kwanta,duk da bacin sai dai sama-sama, ta ajiye idonta a bakin kofa tace ba zata gaji da jiran dawowar yaranta ba, zasu dawo gareta tanajin hakan a jikinta In sha Allah. Sallamar Malam Halliru ne ya fargar da Hajja, amma bata amsa ba, sai Baffa da ya fito yana amsawa, Hajja ta jawo mayafinta tana gyara lullubinta, Baffa ya bada izinin shigowa, Malam Halliru ne da matarsa da 'yarsa a hannunsa suna kuka, suka zube a gaban Baffa, shuru Baffa ya yi yana kallon Malam Halliru kafin ya ɗora idonsa a kan 'yar dake hannun Malam Halliru,yana ganinta ya gano matsalar dake damunta, shuru Baffa ya yi ba tare da ya yi magana ba, Malam Halliru cikin kuka yake fadin "Dan Allah Magaji ka taimakeni, wlh ita kenan mini yarinyar,na jima kafin na samu haihuwa ga shi Mayya tana shirin kashe mini ita ka taimakeni Magaji" Shuru Baffa ya yi na wasu lokuta kafin ya ce "Nima su kenan gareni, ɗaya ta gudu da kanta daya kuma kun kusa kasheta,inda daga karshe na koreta da kaina!" "Hakika munyi kuskure Magaji kayi hakuri" shuru Baffa ya yi bai yi magana ba,ganin haka yasa matar Halliru zuwa ta kama kafar Hajja tana kuka, kallonta Hajja ta yi cikin sanyin muryarta ta ce "Na san abunda kike ji a ranki a matsayina ta uwa na fahimci hakan, Baffan Biyu ka dubata dan Allah, su ci albarkacin macizai" Hajja na gama faɗi ta miƙe ta shiga bukka, Baffa kuma ya duƙa ya kama goshin yarinyar ya matse, ya rintse ido, ya gane mayyar dake jikinta, tana ɗaya daga cikin wa inda suka gudu ranar da ya haƙo kayansa, jin Magaji a kanta yasa ta hau kururuwa,Baffa ya ce "Ai kin sake kawo kanki" cikin gurnani ta hau bai wa Baffa hakuri, Baffa ya ce "Tun asalinki dama ke annoba ce, a wan can karan da ban ƙonaki ba dan na rufeki ne,yanzu kuma ƙonaki zanyi, dan idan na barki ban san wa inda zakiyi kokarin kashewa ba" Baffa na faɗin haka ya rintse ido tare da ɗora wa yarinyar wani farin dutse a kirji, ta sake ihu mai cike da amo, kafin ta koma tayi shuru zuwa wani lokaci aka ji ta ɗiff! Malam Halliru ya ce "Magaji ba dai 'yata ta mutu ba?" " 'yarka bata mutu ba Malam Halliru amma ta samu lafiya In sha Allahu, ku tafi gida, ga wannan kuma idan ta farka kuyi mata hayaki da shi" hawaye Malam Halliru ya goge ya ce "Tabbas mutane irinka basu da yawa a wannan duniyar namu Magaji, dan Allah ka yafe mini, wlh Jauro ne, kayi hakuri dan Allah, Allah kuma ya dawo da Azima da Aziza lafiya" Baffa ya amsa da amin, Malam Halliru da matarsa suka fita suna kan yiwa Baffa godiya, Baffa kuma bukkar Hajja ya shige ya sameta zaune a bakin gadon karanta, ta yi shuru, zama ya yi kusa da ita ya ce "Jumala?" hannu Hajja ta daga, ta ɗan yi shuru kaɗan kafin ta ce "Karka damu Baffan Biyu,na rungumi kaddarata,amma ka san ita zuciya bata da ƙashi sai tsoka, duk yawan watanni ko da an shekara ni kullum abu daya nake gani" tana gama fadi ta tashi ta fice, Baffa ya ce "Duk inda kuke Allah ya kareku, hakika idan har na kama Banju kisan da zan masa wannan karon ƙare ba zai tona ba, dama irin wa innan hatsabiban aljanun basu gane rarrashi , nima zan nuna masa waye ni!" 🍃🍃🍃🍃🍃 *Bayan wata biyar.* Abubuwa dayawa sun faru a wata biyar din nan, daga ciki kuwa har da 'yar gayu da Aziza ta zama turanci a bakinta raɗau, ga shi shaƙuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da Sultana,haka ma Mom bata nuna mata bambanci tsakaninta da Sultana, lokuta da yawa Aziza ta sha yunkurin guduwa amma sai ta kasa hakan, sakamakon yardan dasu Mom suka yi da ita, ga shi ita ba zata iya gaya musu gaskiya a kan ƙaryar da ta musu ba, ta rasa yadda zata yi, ga shi a wannan lokacin tana da bukatar ta canza wani gari ko Allah zai sa a dace. akwai ranar da suke hira da Sultana take gayawa Aziza zasu je zaria bikin ƙawar Sultana din, to yanzu shirinta idan suka je bikin daga nan kawai ta gudu,idan har ta duba bata ga Azima a zarian ba, to zata sake canza wani gari, dan yanzu alhamdulillah ko da Mom ba ta bata kudin aikinta ba, a kudin da take samun alkairi ya isheta yawatawa neman 'yar uwarta, bare kuma alkairin da su Mom suka mata yafi abunda zasu bata sau dubu dari. Ta bangaren Azima itama tana nan ta zama wata iri da ita, sai faɗi take yi ta shigo gidan da ya dameta duk sadda ta shigo gidan taji kamar an ɗaureta, ga shi duk yadda ta ci burin hawa can sama part din AL'MAZEEN abun ya ci tura, ala dole ta yi hakuri tana jiran dawowarsa,dan ta fara jin ƙishin-ƙishin a bakinsu Maman Hanan cewa nan da wata shidda AL'MAZEEN zai dawo, dan haka Azima ta koma tsumayin jiran dawowar Al'mazeen. @@@@@@ Yau saura kwana uku su tafi zaria, Aziza na zaune Sultana ta shigo da sallama da waya a kunnenta hannunta dauke da kaya ta zuba a kan cinyar Aziza,kaya ne kala shidda kala uku iri daya, Aziza ta hau ɗaga kayan tana mamaki, zama a gefen gadon Sultana ta yi, tana ci gaba da wayarta bisa alama kuma da ƙawarta wanda za ayi aurenta suke waya, sai da ta gama wayar tsaf ta tabbatar mata cewa gobe da wuri zasu fito kana suka yi sallama,sannan ta waigo wajan Aziza ta ce "Azizi baby, ga anko ɗinmu fa" "Ankonmu kuma?" Aziza ta faɗa tana cikin mamaki tana ɗaga kayan, Sultana ta ce "E mana, zamu je biki ne ba tare da kinyi anko ba? Wlh muna zuwa zaki zama kamar bare, shiyasa da na tashi na cewa Bros Nawaz ya turo mana da kudi nayi mana mu biyu" shuru Aziza ta yi sai kuma ta sa kuka, Sultana ta ce "Miye haka kuma Aziza?" cikin kuka Aziza ta ce "Anty Sultana, anya dawainiyyar ba zaiyi yawa ba? aiki nake muku amma kun maidani tamƙar yar gida, ni kuwa dame san saka muku? Sai dai na bi ku da addua ke da Mom,Allah ya saka muku da mafificin alkairi" hannu Sultana tasa tana sharewa Aziza hawaye ta ce "Ni da Mom kawai? Shi kuma Yaya ɗin fa! Yana yawan tambayarki wlh idan muna waya da shi, Aziza kin riga da kin shiga ranmu ne wlh, muna jinki ne a jikinmu, shekaran jiya Mom ke faɗamin cewa ita tana miki kallo ne tamkar ita ta haifeki,kuma tana tausaya miki na rashin iyaye da yan uwa da kika yi, tace ba zata taba wulakantaki ba, dama wulakanci mu ba halinmu bane, duk wanda ya riƙe maraya tsakani da Allah,Allah zai ba shi lada, In sha Allahu ko neman aurenki aka zo yi ba zamu taba cewa ke ba yar gidan nan bane, Allah ne ya saka mana kaunarki a ranmu, sabida hankalinki da natsuwarki, wlh Aziza ina jinki tamkar kanwata uwa daya uba daya, a rayuwata ina son na ganni da ƙanwa, amma ana haifata Allah ya dauki ran mahaifinmu, har kwanan gobe Mom taki kara aure, Yaya shike mana komai da shike Allah ya dafa masa, idan har Allah ya baka dama da dukiya amfaninka shine kai ma ka taimaki wa inda basu da shi, dan haka ki daina sa damuwa a ranki ki saki jikinki nan gida ne, bari naje nayi waya da My Khalil" share hawayen da ya sake zubo mata Aziza tayi ta ce "Na gode sosai Anty Sultana, Allah ya shayar daku ruwan alkausara, Sultana ta amsa da amin tana fadin "An fa fara maganar tsaida aurena,wlh ana maganar sai da naji zuciyata ta buga" "Kai Anty Sulty waya gaya miki?" "Nima ba gaya min akayi ba,dazu ne zan shiga dakin Mom naji suna magana da Hajiyar su Khalil, akan cewa za a tsaida lokacin bikin" "To shi da baya kasar ma?" Aziza ta faɗa tana ninke musu anko din, Sultana ta ce "To nima dai naji Mom na cewa a bari sai Yaya ya dawo, kin san fa sun kusan dawowa gida gabaɗaya, shima Khalil din ya kusan dawowa, wai ko kuma a tsaida ranar sai ya kasance lokacin da zasu dawo kar bikin ya wuce saura wata biyu, na dai ji Mom na cewa wata takwas ko wata tara,kafin nan sun dawo dukkansu kuma sun huta" Aziza ta gya ɗa kai tana fadin "Allah ya tabbatar mana da alkairi" "Amin ya Allah, da bikina fa ke ce zaki yi min babbar ƙawa wlh" Aziza na shirin magana wayar Sultana ya dauki ruri tana dubawa ta ga Khalil ɗinta, da sauri ta miƙe tana fadin "My love ya yi kira sai anjima" tana fadi ta fice da gudu, Aziza kuwa ware idanunta tayi tana jinginuwa da bango sabon hawaye na sake zubo mata, komai yana shirin kwab'e mata, kawai mafita shine zatayi addua Allah ya zaba mata abunda yafi mata alkairi,bata so sam Nawaz ya dawo ya sameta a gidan, dan haka taja akwati ta haɗa kayanta tun daga yau, anko din kuma dakin guga ta yi dasu idan aka goge sai ta miƙawa Sultana nata. 🍃🍃🍃🍃🍃 Yau ce ta kama ranar da zasu tafi zaria, gaban Aziza ke dukan uku-uku tun farkawarta bata da kuzari,ganin haka yasa Mom cewa Aziza meke damunki ne? "Ba komai Mom" "A'a Aziza karya ba halinki bane, karki fara meke damunki?" a sanyaye ta ce "Kaina ke ciwo Mom" "Subhanallahi! Idan ba zaki iya tafiyar ba ki bar shi ki huta abunki ita mai biki sai ta tafi" nan Sultana ta yi tsalle ta dira da cewa wlh Aziza bata isa ba,kawai dai son mutane ne da bata yi, Mom ta ce "A'a Sultana baki zo da gaskiya ba, yarinya tace miki bata da lafiya kice bata isa ba,kinga wuce ki tafi kawai Allah ya kiyaye hanya" Sultana tace ita kuwa idan har Aziza ba zata je ba itama ta fasa, Aziza ta ce "To ba kin riga da kin gaya mata yau kina hanya ba?" "Sai na ce mata na fasa😏, kuma ai ba ina hanya nace mata ba muna hanya nace mata" Aziza ta yi murmushi ta ce "A'a ba za ayi haka ba Antyna ta kaina tashi mu tafi" Mom ta ce "Ki biyewa Sultana ki kashe kanki" "A'a mom ai nasha magani, ciwon kan zai sakeni" "To Allah ya kiyaye hanya, a gaida su Hajiya Habiba, ai da ace zaku biya ta kano da na baku sako wa su Hajiya Lawiza" haɗe rai Sultana ta yi ta ce "Gaskiya Mom ba zamu kano ba, daga zaria sai kaduna In sha Allahu" ganin yadda Sultana ta haɗe rai yasa Mom dariya ta ce "To shikenan Allah ya kare" ta faɗa tana rakosu har jikin mota, ta ce "Ina dai ba zaku wuce kwana biyun ba ko?" "In sha Allah Mom ba zamu wuce ba,ai ba zamu je mu zauna mu barki ke ɗaya ba" daga haka driver ya jasu ,Mom tana ɗaga musu hannu. Kasancewar tsakanin kaduna da zaria ba nisa nan da nan suka isa aka hau shagali dasu, haka sauran ƙawayen amarya Sulaiha suka ja Aziza a jiki, amma matsalarsu daya da ita shine rufe fuskar da take yi, sai da Sultana tace musu ai ko a gida ma haka take wuni fuska a rufe kasancewar tana da matsalar ido, daga haka suka fara yi mata fatan sauki, sai yaba kyawunta sukeyi da dogon gashinta,ita dai Aziza nata murmushi da godiya, dan duk tunaninta ya raja'a a ta hanyar da zata bi ta gudu, dan suna isowa zaria bata yi kasa a guiwa ba ta duba amma bata ga Azima ba, yanzu garin da take hari taje shine garin da Mom tace zata aiki Sultana idan har zasu je, wato KANO. Ranar da suka zo anyi party da washe gari asabar aka ɗaura aure, bayan an daura aure da daddare akwai dinner daga wajan dinner za a wuce da amarya gidan mijinta da washe gari kuma sai su koma kaduna, a daren yau idan suka je dinner shine Aziza tasa a ranta zata gudu. @@@@@ Sun sha makeup dinsu, suka cakare cikin net dinsu kalar sky blue sunyi kyau sosai,ita dai Aziza taƙi yarda ayi mata makeup har amarya Sulaiha take fadi cikin wasa ai ita da kyau ɗinta ba sai an mata kwalliya ba tunda bata so a barta. Suna can babban hotel din da aka kama ana ci gaba da gudanar da abunda ya tara jama'a, Khalil ya kira Sultana a waya kasancewar bata ji a ciki yasa ta fito waje tana wayar. Wasu maza ne su uku a wajan gate din hotel din suna cikin mota sai aikin busa hayaki suke yi, wani ne ya daga ido daga cikinsu ya sauke a kan Sultana dake waya, sai da ya kara goge idanunsa kafin ya ce "Kaii Ɗan Gidan Alhaji? Wa nake gani a can kamar kanwar Doctor Nawaz?" wanda aka kira da sunan Ɗan Gidan Alhaji ya dago yana ƙarewa Sultana kallo ya ce "Jar Uba! Ita ce wallahi! To me ya kawota zaria?" ɗayan ya ce "Ko ma me ya kawota, lokaci ya yi da zamu rama abunda Yayanta ya mana a kanta" Dan Gidan Alhaji ya ce "To yanzu ya kuke ganin zamuyi?" dayan ya ce "Ah mu kwamusheta kawai,muje mu huta da ita, ya ɗanɗani abunda mukaji sadda yasa aka kullemu a kan wasu banzan talakawa!" "Lallai Shaho ka kawo shawara, kuma dabadin Baban Ɗan Alhaji ba wlh da mun ƙare rayuwarmu a kurkuku" Dan Gidan Alhaji ya ce "Yanzu ku daina wannan maganar tunda ba mutane yanzu a kusa ku fita ku dauko mana ita" sai da suka leka suka leka kafin suka fito daukar Sultana wanda hankalinta ya yi nisa sosai a wayar da take yi da Khalil. Aziza na zaune cikin kawaye da ta waiga ido bata ga Sultana ba ta tashi a hankali tana fadin "Ki yafeni Anty Sultana zan tafi, ba zai yu ba rayu daku ba danni ba mutum bace,zanje neman yar uwata dan mu koma duniyarmu!" Da wannan tunani zuciyarta babu dadi kamar karta tafi dan an saba, ta fito saɗaf-saɗaf. Fitowar Aziza ya yi dai-dai da lokacin da su Shaho suka roɗa ma Sultana katako a bayan kai a kan idon Aziza,ihu Aziza ta saka tana fadin "Antyyyy Sultanaaaa!!!" ganin haka yasa Ɗan Gidan Alhaji Faɗin su haɗa da Aziza su kwamuso. 🍃🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 _GOOD MORNING😄_ ☕☕🍵🍵 *PAID.* 🅿️=4️⃣9️⃣↪️5️⃣0️⃣ Dan haka suka bugawa Aziza katako a kai sau daya,jiri ne ya ɗibeta amma bata suma ba, ta hau kokawa dasu dan ta kwace Sultana daga hannunsa, Shaho yasa katako ya dinga sauke mata shi a gefen kai har ta suma kanta ya fashe yana zubar da jini, sannan suka daukesu suka saka a mota. Basu zarce ko ina dasu ba sai wani gidan Ɗan Gidan Alhaji da Babansa ya gina masa, suna zuwa su Shaho suka fito dasu Sultana da Aziza wanda suke sume, suka shige dasu, suna shiga dasu suka kwantar dasu a parlour, D'an Gidan Alhaji ya ce a bari su farka, Shaho yace ba sai an jira sun farka ba dan babu lokaci, a yayyafa musu ruwa kawai su farka, ga wannan yarinyar ba mamaki ita ma kanwarsa ce dan naji ta kiran wannan da Anty, wai cakwai kenan gata kirjinta a cike yake,yaran dai za a shana fa" Dan Gidan Alhaji ya yi murmushi yana lashe baki tare da binsu da kallo, Shaho ne ya kawo ruwa cikin bokati ya shekawa su Sultana da Aziza tun daga kansu har kafarsu, a firgice Sultana ta farka ita ce ta fara dawowa hayyacinta tana riƙe bayan wuyarta dake mata tsami, ware idanunta ta yi a kan Ɗan Gidan Alhaji, tayi saurin ja da baya tana girgiza kai,tana juya idonta ta sauke shi a kan Aziza wacce bata riga da ta farka ba, a razane Sultana ta hau jijjiga Aziza tana kuka tana kiran sunanta ganin yadda jini ke b'ulb'ula a kan Aziza, cikin kuka Sultana ta ce "Wlh idan Yayana ya sani dukkanku babu wanda zai tsira" D'an Gidan Alhaji ya ce "Kafin nan Ubana ya min biza na bar kasar, kuma ko da zai sani sai mun miki mummunar tab'o,ko nace sai munyi muku mummunar illa!" Ya fada yana sa hannu zai damki Sultana Aziza ta cafki hannunsa gam tana daga kwance dan duk taji abunda yake fadi, cafka bana wasa ba Aziza ta yiwa hannun Ɗan Gidan Alhaji, da mugun mamaki Sultana ke kallon Aziza wacce take kwance idonta rufe ga jini, cikin rawar murya Sultana ta ce "A....ziii.....zaaa...! dan Allah ku kai min ƙanwata asibiti kar ta mutu, baku da imani!! Ku azzalumai ne!!" Shaho ya yi kan Sultana yana zuwa zai kai mata mari Aziza tasa kafa ta tokaresa sai da ya yi sama kafin ya bugu da bango ya faɗi kasa, da sauri Dan Gidan Alhaji ya ce "Kai wannan yarinyar fa na ga alama tana ji da kanta, ga shi ta riƙe min hannuna kamar zata b'alla, ke dan uwarki da Ubanki! Sakar min hannuna" ya fada yana jan hannunsa da karfi amma Aziza ta ƙi sakewa, Sultana kuwa tana takure a jikin Aziza tana kokarin yadda zata tsaida jinin da ke fita akan Azizan. "Shaho, yarinyar nan fa taƙi sakina!!" Shaho wanda ya sha ƙasa ya miƙe a fusace yana fadin "Wannan yarinyar sai fa mun nuna mata cewa ni cikakken dan iska ne, ban taba kisan kai ba, amma inaji zan fara a kanta, dan naga tana fama da tashen balaga, ko dazu bugu ɗaya nayi wa dayar ta suma amma ita sai da na mata biyar! dan haka ba zata sakeka ta dadi ba,bari ka gani" Shaho ya faɗa yana jan wani karfe a bayan windown labule, ganin haka yasa Sultana fasa ihu dan ta ga gadan-gadan ya nufi Aziza dake kwance, a haukace Sultana ta hau faɗin "Dan Allah Aziza ki sakesa, ba danni ba Dan Girman Allah, kinga munyi sallama da Mom lafiya-lafiya kar a koma mata da gawawwakinmu, dan Allah Aziza ki sakesa! Ki sakesa nace!!" Sultana ta faɗa da karfi a tsawance, sake masa hannu Aziza ta yi, tana sakinsa ji ya yi tamƙar kashin hannunsa ta tsatstsage,a hankali tasa hannu a tsakiyar gashin kanta ta dafe,da kyar ta miƙe zaune sabida jirin dake dibarta dan ta bugu sosai a kai,inda yake saurin musu illa kenan shine duka a kai, amma duk sauran jiki dan sun bugu aikin banza ne. Kanta a duƙe tana riƙe da kai da hannunta daya, dayan hannun ta yi musu nuni da yatsarta manuniya cike da gargaɗi ta ce "Duk wanda baya so Uwarsa! ta haifi wani, to kar ya kuskura ya sake ya taba mini Antyna, ku maidamu inda kuka dauko mu!" dariya Shaho da ɗan Gidan Alhaji da ɗayan suka yi, ƊAN GIDAN ALHAJI ya ce "Zamu maidaku bayan mun yaga muku rigar mutunci! Ke kuma mai bamu umarni kar mu tabata, Yayanta ne yasa aka kullemu watanmu biyar a kurkuku da kyar mahaifina ya fiddomu, dabadin shi ba ma da har yanzu bamu fito ba, ai kema bamu san kanwarsa ba ce! Mun daɗe muna neman hanyar fansa! Sai ga shi ta kawo kanta har zaria, abun ya bada kala fa, dan haka ke ki fara zuba ido ki ga yadda zamu mata kafin a gama da ita a zo kanki, Shaho ku banƙaremin ita!" kukan tashin hankali Sultana ta saka tana kokarin kama Aziza su Shaho suka fizgota suka bajeta a kan carpet ɗaya ya riƙe mata hannaye ɗaya ya riƙe mata kafafu, kuka Sultana take yi tana ambatar sunan Allah da Yayanta da Mom da Aziza da Khalil, Aziza sai yunkurin tashi take yi ta kasa, ganin Ɗan Gidan Alhaji ya fara sa hannu yana tattaro doguwar rigar dake jikin Sultana yana yin sama da shi rintse ido Sultana ta yi, ta sadaƙar kawai,ganin haka yasa Aziza ware gashin kanta tasa hannu ta b'alli daya tasa a bakin, wani gurnani ta saki tare da hucin Maciji🐍, jin hucin maciji yasa Sultana buɗe ido da sauri dan tasan irin wa innan abubuwan tunda tana yawan kallonsu, saurin juyowa suma Ɗan Gidan Alhaji da muƙarrabansa sukayi suna kallon Aziza wacce take tsaye gashi ya rufe mata fuska, kwashe gashin ta yi ta tattare ta maida shi baya ta ƙulle,bata da wani mafita wanda ya wuce haka, idan har ta bari tana kallo aka yiwa Sultana fyaɗe ba zata yafewa kanta ba, dole Sultana tasan asalin wacece ita a yau, tana tsaye jini na kan wanke mata fuska, dama idonta a rufe yake,hannu tasa ta shafe kanta nan take aka nemi ciwo aka rasa, bama iyakar Ɗan gidan Alhaji da mutanensa ba, harta Sultana ware ido ta yi kamar zasu faɗo kasa yayinda zuciyarta ya yi wani mugun tsinkewa, Shaho ne ya yi karfin halin faɗin "Waike wacece ke!?" "MACIJIYA🐍, AZIZA MACIJIYA!!" tana faɗi ta buɗe idonta nan take ta rikiɗe ta sama katuwar Macijiya fara sol sai kyalli takeyi, ba shiri Su Shaho suka saki Sultana wanda ganin Aziza ta koma Macijiya ta saki ihu tana sumewa. neman hanyar guduwa su Shaho suka hau yi, Aziza ta naɗosu da jelarta, sannan ta koma rabin mutum rabi macijiya, kafin ka ankara masu sakin zawo a wando da masu fitsari duk sunayi, cikin tashin hankali da kiɗima da ɗimauta Shaho ya ce "Dama ke ba Mutum ba ce?" " *RUWA BIYU*" (taken Hajiya Azima kenan). "Ku godewa Allah bana kisa,bana fata kuma ranar da zanyi kisa! Inaso ne na muku gargaɗi da kakkausar murya, babu ruwanku da Hamma Nawaz shi da familynsa, sannan duk ranar da dayanku ya ƙara aikata abu marar kyau zan maida shi kwaɗo, sannan idan har ku ka ba wa wani labarin abunda ku ka gani yau a take zaku mutu, kuna jina!!?" "E wallahi Mamanmu mun ji ki,mu dai dan Allah kiyi hakuri!" suka haɗa baki wajan faɗi, watsar dasu Aziza ta yi, sannan ta zama mutum, su kuwa da mugun gudu suka watse nafsi-nafsi kowa ya yi ta kansa. Da sauri ta yi kan Sultana yayinda hawaye ya hau wanke mata fuska, zata tab'ata kuma sai ta fasa, zata tashi sai koma ta kara komawa tasa hannu ta shafi inda aka buga mata katako a bayan wuya, sannan ta mike zata tafi taji Sultana ta riko hannunta, ganin haka yasa Aziza hura mata wani farin hayaki, nan take Sultana ta buɗe idonta, tana buɗe ido ta saukesu a kan Aziza, nan ta saki wani kuka tana fadin "Dan Allah kice min film nake kalla,ko kuma duk abunda ya farun nan ki ce min mafarki ne ba gaskiya bane" tana maganar ne a ruɗe tana juyi ta rasa inda zata sa kanta dan firgici ganin haka yasa Aziza ɗora hannunta a goshin Sultana, lokaci daya ta samu natsuwa, hawaye ne ya zubowa Aziza ta ce "The game is over Anty Sultana! da,fari naso nayi tafiyata ba tare da kun san wacece ni ba, amma ke Allah ya nufa zaki sani, ba zan iya yarda na watsar da yardan da kuka mini ba,ko ba komai yanzu idan na tafi zanyi farin ciki idan kika koma zaki gayawa Mom cewa ni ba mutum ba ce,bazan taba manta alkairinku a tare dani ba, hakika Anty Sultana ni ba mutum ba ce MACIJIYA CE!!" Girgiza kai Sultana ta hau yi tana fadin "Gaskiyan Yaya ne da Mom wata rana sai na fara ganin abunda nake kalla a gaske, to ko dai na samu tab'in hankali ne sabida dukan da aka min? Amma taya mutum zai ga maciji a zahirance irin haka?" hannu Aziza tasa ta kamo fuskar Sultana ta ce "Kalli cikin idona!" ɗagowa Sultana ta yi ta sauke idonta a cikin na Aziza nan ta ganshi sak idon mage mai fari-fari "Wannan shine dalilin da yasa bana buɗe fuska sabida idona! Ki yarda Anty Sultana ni ba mutum ba ce,duk labarin da na baku a kaina karya nake yi, wannan shine asalin gaskiyata, ni macijiya ce,na zo neman 'yar uwata ce ta biyuna, shine dalilin da yasa na shigo cikin gari, idan kinason jin labarinmu ba zan boye miki komai ba, ki kasa kunne ki sha labari" Aziza ta fada tana gyara zama,ita dai Sultana banda rawa da jikinta ke yi sai b'arin baki babu abunda takeyi tana yiwa Aziza kallon tsoro, nan Aziza ta dauko mata labari tiryan-tiryan a natse take warwarewa Sultana zare da abawa, bata boye mata komai ba ta gaya mata komai tsaff! Wani gauron ajiyar zuciya Sultana ta sauke ta ce "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Ai ko a fina-finan da nake kalla ban taba ji ko na gani ba, to meyasa baki gaya mana gaskiya ba?" murmushi Aziza ta yi ta ce "Babu wanda zai zauna da macijiya, da ace a lokacin na gaya muku zaku koreni,idan kuma baku koreni ba zaku dinga tsorona, na zauna shuru a gidanku ne dan na tara kudin da zan nemi yar uwata mu koma al'karyarmu, dan Allah ki ba wa Mom hakuri idan kin koma, sannan ki nema mini yafiyarta idan na mata abu a rashin sanina, haka ma dan Allah ki nema min yafiya a wajan Hamma Nawaz, sannan kema ki yafe mini" Aziza na gama faɗi ta fashe da kuka ta tashi da sauri zata fita,sultana tace "A yau kin ceci rayuwata, da ace ba dan ke ba, abunda nake yiwa gidan mijina tanadi da yanzu an karbe shi, bani da sauran wani mutunci da kima, da na koma matatta ko da ina raya, a yadda naji labarinki ke abun tausayi ce ba abun gudu ba daga ke har Baffanki da Hajjanki da kuma yar uwarki! Ai ke ba abun a gujeki bane Aziza, dan ke din mai tausayi ce, idan har kin yarda dani kuma kin yarda munyi miki halacci ba ki so ki saka mana da butulci to ki biyoni gobe mu koma kaduna,nayi miki alkawari zan tayaki neman yar uwarki gari ya gari, idan har kin yarda dani fa amma" wani kuka ne ya sub'ucewa Aziza ta ce "Anty Sulty?" rungumeta Sultana ta yi ba tare da tsoro ko fargaba ba, "Dama akwai mutane irinku a duniya? Tabbas duk lalacewar mutanen duniya na Annabi basu ƙarewa" cewar Aziza tana kuka, Sultana tana bubbuga bayanta ta ce "Ni dai ki min alƙawari ba zaki gudu ba,kuma karki kara tunanin guduwa,Mom mutum ce mai zargin kanta a koda wani lokaci zata dinga zargin kanta da bata miki riƙon tsakani da Allah bane shiyasa kika gudu, dan Allah karki saka mata da haka" "In sha Allah Anty Sulty babu inda zani" daga haka Sultana taja hannun Aziza suka fice a gidan ga dare ya tsaga ana neman gaff kiran sallan assalatu, fitowa bakin titi sukayi, Sultana ta ce "Muna waya da Khalil yan iska sun bugeni wayar ta faɗi, na san za a nemu kam kuma hankalinsu zai tashi" Aziza ta ce "Nima takalmina kafa daya ya fadi, yanzu ya za ayi kenan?" "Kawai ki daukemu mu b'ace muje gida" zare ido Aziza ta yi ta ce "A'a Anty Sulty,mu nemi wani hanyar dai" suna nan tsaye har aka kira assalatu, Aziza tace mu zauna a nan mu jira har ayi sallar asuba nasan a lokacin motoci zasu fara wucewa sai mu wani wanda zai kai mu gida, tunda bamu sallah ba da sauki ai" "Yan iska mutanen banza! Da yanzu sai su mana fyaɗe muna period ko?" "To suna tsoron Allah ne, ai basu tsoron Allah" zama Sultana ta yi a kasa tana fadin "Ai shikenan" itama Azizan zama ta yi, nan kuwa aka yi asuba kafin motoci suka fara gilmawa da kaɗan-kaɗan har suka tare mai taxi, Sultana ta gaya masa unguwar da zai kaisu ya daukesu. A gate din gidan mai taxi ya ajiyesu, suna fita suka samu harda yan sanda, mutane ana tsaye cirko-cirko daga ciki kuwa harda amarya da ango, wanda jiya da aka tashi a wajan dinner amadadin ayi gida ai sai hankali ya tashi, kuma ga wayar Sultana da suka samu a gate din da kafar takalmin Aziza guda daya, shiyasa suna gani suka sa a ransu ai kawai an sace su Sultana ne, sai kuma ya haɗe da Khalil da yake ta faman zabgawa wayar Sultana kira dan yaji lokacin da Aziza ta kwala mata kira sadda aka buga mata katako a kai wayar ta fadi kasa,kuma yaji sadda suke cewa a dauko da Aziza, itama aka dinga buga mata katako, sannan sun ga jini a wajan, jinin kan Aziza wanda ya fashe. Hajiya Habiba mahaifiyar amarya Sulaiha ganinsu yasa ta ta tarosu da kuka tana tambayar lafiyarsu, nan suka tabbatar mata da suna lafiya, aka tambayesu me ya faru,nan Sultana tace daukesu aka yi, yan sanda suka tambayesu waye suka ce basu gane mutanen ba, dan sun rufe fuskarsu, "Taya aka yi kukayi escaping daga hannunsu?" Sultana ta ce "Ashe bamu zamu dauka ba, su da kansu suka sakemu, a bakin titi muka kwana kasancewar dare ya tsaga, sai da akayi asuba muka samu mota ya kawo gida" "Ina dai basu muku komai ba ko" cewar Hajiya Habiba "E Ammi basu mana komai ba" "Na godewa Allah, da me zan cewa Hajiya yara daga zuwa biki ni Habiba,tana can hankalinta tashe wallahi, dan ma dai tana da karfin zuciya" nan aka shiga jajinta lamarin, aka ce su shiga su huta Sultana tace sam ai yanzu kam gida zasuyi, anyi-anyi su bari sai anjima tace sam,ganin haka yasa Hajiya Habiba cewa to jami'an tsaro su rakasu har kaduna har cikin gida, kayansu kawai aka fiddo musu aka sa a both, Sultana ta rungumi Sulaiha ta ce "Ƙawata kuyi hakuri fa jiya hankalinku ya tashi ga shi ko gidanki ba a kai ki ba" "Haba Sultana ba dole ba" "To shikenan ai muna lafiya, kiyi hakuri ba zan samu zuwa gidan ba amma na miki alkawari zan zo idan an kwana biyu, a sha amarci lafiya" daga haka sukayi sallama wata ƙawar Sulaiha ta mikawa Sultana wayarta da kafa ɗayan takalmin Aziza,bayan mota suka shiga jami'an tsaro suka rakasu a baya, har kaduna. @@@@@@ Suna isa da gudu Sultana ta shige gida,Mom tana tsaye a parlour ta kasa zama, Sultana na shigowa ta ce "MOM!?" da sauri Mom ta juyo tace "Sultana" rungumeta tayi, cikin hawaye Mom ke tambayar lafiyar Sultana, shigowa Aziza da yan sanda sukayi, Mom na ganin Aziza ta yi saurin zuwa ta rungumeta tana tambayar lafiyarta,jikin Aziza ne ya kara sanyi, da yanzu ta gudu wani tashin hankali zasu shiga? Da yanzu wannan abun bai faru ba da shikenan ta b'ata rawarta da tsalle, hakika zamanta dasu akwai wani babban sirri da Ubangiji ya boye, shin yanzu su gayawa Mom gaskiya ne ko yaya zasuyi?" Mom ce ta shafo fuskarta tace "Kina lafiya 'yata?" Aziza ta gya ɗa kai,nan yan sanda suka kara yiwa Mom bayani kafin Mom ta musu godiya suka fice,suna fita Hajiya Habiba na kira,nan Mom ta shaida mata ta kwantar da hankalinta sun zo gida lafiya, dama tsautsayi ai baya wuce lokacinsa Allah ya kiyaye na gaba kawai, daga haka suka yi sallama aka rabu lafiya, Mom ta kallesu tace "Bakuyi wanka ba ko?" suka gya ɗa kai "Kuje kuyi wanka ku kwanta ku huta idan kuka tashi sai ku ci abinci, tunda yanzu ana neman shaɗayan safe ne" suka amsa da to, Aziza a sanyaye ta shige dakinta, Sultana kuma ta haura sama, sai da ta yi waya da Khalil dinta ta tabbatar masa tana lafiya dan hankalinsa ya tashi bai rintsa ba jiya, ta ba shi labarin ai Aziza ce ta taimakesu, amma bata gaya masa komai a kai ba, dan tayi alkawari ko wa Mom ne ba zata gaya ba har sai Aziza ta yarda, wanka ta yi sannan ta bi lafiyar gado dan bacci takeji sosai, haka ma Aziza ita ma wankan ta yi ta kwanta zuciyarta a cin kushe, ga tunani fal a cikin ranta,ji take kamar kanta zai fashe, ta ɗau minti talatin tana juyi kafin bacci ya kwasheta. Basu farka ba kuwa sai hudu na yamma,Mom ma bata tashesu ba, ta dai musu odern abinci, bayan sun farka ruwa suka sake watsawa kafin suka ji sun watstsake, kasancewar suna fashin sallah dukkansu shiyasa basu wani damu ba, Sultana ce ta fara fitowa ta shiga dakin Mom ta sameta suna waya da Nawaz,sai da suka gama Mom tace "Kin tashi? Kinyi sallah?" "A'a Mom ina fashin sallah, Aziza ma haka" "Yaushe kuka fara?" "Ranar da muka isa zaria" "Ok ya yi kyau,banda shan zaƙi dai da abu mai sanyi" "To Mom" "Kije ki ga idan Azizan ta farka,ku ci abinci" "To Mom, amm Mom Khalil yace zai dawo a satin nan" "Lafiya dai ko?" "Nima ban sani ba, amma yace ya fasa cike sauran watannin" gya ɗa kai Mom tayi ta ce "Nima maganar da muke yi kenan da Nawaz yace zasu dawo, jin abunda ya faru yace gwara kawai ayi auren kwanan nan a kaiki hankalinsa da nawa ya kwanta nima kuma nayi na'am da abunda yace, dan haka yace zasu dawo dukkansu shi da Son,idan suka dawo sun dawo kenan, nan da wata daya" shuru Sultana tayi dan bata so haka ba, ba tare da tayi magana ba ta fice, kasa ta sauko bata ga Aziza a parlour ba dan haka ta zuba musu abincin tayi dakin da sallama Aziza na zaune a bakin gado, tana sallaman Aziza ta amsa tana shirin rufe fuska, Sultana tace "Babu amfani ai tunda nasan komai, zo muci abinci" ta fada tana zama kan carpet, zamowa daga gadon Aziza tayi ta kalli Sultana ta ga jikinta a sanyaye Aziza ta ce "Anty Sultana yana ganki haka akwai matsala ne?" "Babba ma kuwa Aziza, Khalil jin abunda ya faru yace zai dawo a cikin satin nan, Yaya kuma yace shima zai dawo nan da wata daya dan ayi aurena hankalinsu ya kwanta shi da Mom,kuma Mom tace shi da amininsa zasu dawo, dama yanzu dawowa mai gabadaya zasuyi" Aziza ta ce "A'a bangane ba,ina da tambaya, shin Hamma Khalil ba shi bane abokin Hamma Nawaz ba wanda suke kasa daya?" dariya Sultana tayi ta ce "Taya? Khalil fa shi yana paris ne, su Yaya Nawaz kuma suna america ne, sunan babban aminin Yaya ba Khalil bane, ke yanzu duk zamana dake baki san my husband to be ba? sunan babban aminin Yaya Nawaz *AL'MAZEEN NE* shi kuma ɗan Kano ne ba dan kaduna bane,gidansu ne Mom tace zata aikemu nace bazan je ba. 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=5️⃣3️⃣↪️5️⃣4️⃣ Cikin girmamawa Hadiza ta amsa da to, sannan ta yi waje can wajan kofar baya na kitchen, ta samu Azima zaune tana tsinke fulani tana wurgarwa, Hadiza ta ce "Azima meke damunki?" ɗagowa tayi ta girgiza kai alaman ba komai "To ki zo mu haura sama na nuna miki part din Oga Al'Mazeen zai dawo nan da sati biyu, Hajiya Lawiza tace Ki fara karkaɗe kura" zunbur Azima ta miƙe tana fadin "muje" saman suka haura step na hawan uku can ne part din Al'mazeen, kasancewar baya son hayaniyar gidan, shiyasa idan yana gari ya dawo office yake hawa ya zauna a can shuru abunsa, harta ƙaramin kitchen akwai a saman, shiyasa baya damuwa da a kawo masa abinci, dan baya so ma yana cin abincin gidan dan bai yarda dasu ba, suna iya zuba masa abinda ba haka ba a cikin abinci. Tunda suka fara taka step din bugun kirjin Azima ya tsananta, Hadiza ke gaba Azima na binta a baya, har suka je bakin kofar parlourn Hadiza tasa key ta buɗe suka shiga, duk da mai dakin ya shekara baya nan amma har yanzu da kamshin turarensa na tashi, sai kuma uban kura kasancewar idan baya nan babu mai cewa a dinga bude dakin ana karkaɗewa, Hadiza ce ta kalli Azima ta ce "Azima bari na tayaki dan kuran yayi yawa" "A'a ki bar shi kawai Hadiza, ai aikina ne je ki kawai" "Yanzu zaki iya wannan aikin ke daya?" shuru Azima ta yi bata ba wa Hadiza amsa ba,ganin haka yasa Hadiza ajiyewa Azima su tsintsiya da mopa dasu omo da dai kayan aiki, har Hadiza zata fita Azima tace "Dama kin tafi da wa innan kayayyakin naki dan ba amfani zanyi dasu ba" da mamaki Hadiza ta juyo ta ce "To idan ba kiyi shara da tsintsiya ba dame zakiyi?" "Ban taba shara da tsintsiya ba" Azima ta faɗa tana zuwa wajan jikin hoton da ta hango, hannu tasa ta goge hoton, nan take fuskar AL'MAZEEN ya bayyana, rasssrasssrasss!! ƙirjinta ya buga ta ja da baya tana girgiza kai, Hadiza ta ce "Karki tsorata, shine Al'mazeen ɗin, karki ga fuskarsa a haɗe mutum ne mai saukin kai, nan gidansa ne, amma idan kika ga yadda yake rayuwa a cikinta sai kin tausaya masa" Hadiza ta fada tana matsowa kusa da hoton tasa tsummar dake hannunta ta goge wani wanda suke su biyu ta ce "Kinga wannan? Sunansa NAWAZ babban aminine ga AL'MAZEEN,idan har kika ga Al'Mazeen na fara'a to yana tare da Nawaz, shi Nawaz a kaduna yake,kuma dukkansu likitoci ne, sabida tsananin shaƙuwa da son da suke yiwa juna,bayan sun bude asibitinsu suka saka masa suna mai harufan sunayensu *ALWAZ HOSPITAL* na Nawaz na shi na kaduna, shi kuma Al'Mazeen na shi na nan kano, yana da kyauta,baya da kyashi, yana da taimakon duk wani na kasa da shi,duk yadda zan baki labarin Al'Mazeen yafi haka, amma idaa ya dawo zaki tabbatarwa kanki" Hadiza na gama fadi ta juya ta fice. Girgiza kai Azima ta hau yi, Banju dake jikin Azima yaji a jikinsa tabbas idan bai bar gidan nan ba, AL'MAZEEN shine makarinsa na farko a karo na biyu, to amma taya zai bar gidan? dan ya sha yunkurin haka amma zaiji kafafunsa tamkar an dauresa ne. Baya-Baya Azima ta yi ta koma jikin kofa ta bude blue eye dinta ta zaro dogon harshenta tana busar da wani tururi shi ba fari ba, shi ba baƙi ba, shi ba blue ba, tana hura wanna iskan hayakin nan take parlour da dakin da toilet din da kitchen din suka zama sabbi dal, harshenta ta maida sannan ta saka key a kofar ta shige bedroom ta zama macijiya ta hau gado ta kwanta dan bacci take ji, a macijiyar tayi kwanciyarta ta hau bacci. 🍃🍃🍃🍃 "To yanzu Aziza a ganinki taya zamu je kano? Khalil ya hana, Mom kuma ta biye masa,kuma kinga yanzu ne nake da freedom bayan aure kuma sai abunda Allah ya yi, ga shi yanzu bikin saura wata daya da sati biyu, bai ma cika da sati biyun ba, wlh na rasa yanda zanyi" ajiyar zuciya Aziza ta sauke ta ce "Anty Sulty, abubuwa suna shirin cakuɗe mana,ni a ganina ya kamata mu maida hankali a guda daya" "To wanne kenan Aziza?" "Bikinki! Kinga kamata yayi ace mu maida hankali a kan shirye-shirye,idan yaso bayan anyi auren a lokaci hankalu zai kwanta,idan ya so sai mu dubi gaba" "Tabb lallai Aziza na tabbatar har yanzu da ƙuruciya na yawo a kanki, taya Khalil zai bar ni da aurena muje yawon gari ya gari neman Azima? A yanzu ma da ba ayi auren ba ya na ƙare? Gaskiya wannan shawara taki bata yi ba, ni wlh wannan biki da an bar sa idan na cika shekara ashirin sai ayi! tinda yanzu ina sha tara" ta faɗa da fuskar haushi, waro ido Aziza ta yi ta ce "Cab Anty Sulty shekara ashirin fa kika ce? to wlh da a rugarmu na yankin kwana ne ace kamarki bata yi aure ba wollah ko zanar kofar gidanku bakki iya fita sabida gori da habaici da bakar magana, kin ganmu nida Azima, shekararmu sha biyar amma yadda kika san kamar mun shekara dari ne bamuyi aure ba, dan a al'adan rugar yankin kwana yarinya tana da shekara goma za a fara yi mata wankan kindirmo, tana shiga sha daya za a aurar da ita" " a shekara sha dayan!?" Sultana ta faɗa tana zaro ido Aziza ta ce "Wlh da gaske Anty Sulty" "Tabdijam, lallai kam, ai mu kam nan ke baki isa aure ba, amma da shike zamani ya canza ana iya miki, amma karatu ne yafi dacewa dake, ina son zuwa kauyenku" "Tab to mu dai a can kinga bamu san wani abu karatun boko ba amma akwai manyan malaman Muhammadiyya,kasancewar muna can cikin jeji ne amma bamu da wannan duhun kan na jeji muna da ilmin addini sosai, amma In sha Allah idan na koma zan wayarwa da mutane mahaifata kai ta hanyar karantar dasu ilmi daga cikin wanda na samu daidai gwargwado, tabbas na yarda ilmi ginshiƙi ne na rayuwa,ilminka baya cika kuma sai ka haɗa duka biyu a kanka, farko sai ka ajiye ilmin da zai ceceka ranar lahira, sannan ka kara da na bokon wanda shima ta sanadinsa zaka iya shiga aljanna, Allah ya bamu ilmi mai albarka, rugarmu kuma In sha Allah idan Hamma Khalil ya bar ki zakije, amma fa karkije ki ƙi dawowa"🤪 "Amin ya Allah Aziza, hahaha taya zan ƙi dawowa?" "Idan kikaji dadin rugarmu mana" "Humm ke dai, ai kya bari naje na ganewa idanuna ko?" Aziza ta yi murmushi ta ce "Ai shiyasa ban baki labarin ni'imar dake yankin sassaninmu ba" Sultana ta yi dariya ta ce "To naji, kar dai ki shashantar da maganata" "To abunyi shine kawai ki ƙara tuntubarsa" Sultana ta jinjina kai tana fadin "Ok zanyi hakan In sha Allah,ina zuwa" ta faɗa tana ficewa a dakin. @@@@@@@ Kamar yadda Aziza ta cewa Sultana ta kara tuntubar Khalil da maganar ya bar su suje kano hakan kuwa akayi, ganin ta takura yasa yace ta bari to idan su Nawaz suka dawo aka karasa saita komai sai taje tayi kwana biyu idan ana biki saura sati daya, tasan halinsa baya canza magana dan haka ta amsa da to, amma a zuciyarta ta yi lissafin garin da zasuje ya kai shidda, tace ai ba ayi auren ba, balle idan ta tafi tana tafiya akan wutar jahannama (Allah ya kiyashemu amin). 🍃🍃🍃🍃 Tunda aka shiga saura sati su Nawaz su dawo, Mom dasu Sultana da Aziza wacce faduwar gabanta ya tsananta a kwana biyun nan wanda ta rasa dalili hakan, suke shirye-shiryen dawowarsu Nawaz da Al'mazeen, da aka shiga satin karshe murna a wajan Mom da sultana abun sai wanda ya gani, Aziza ta kasa gane ita wani hali take ciki, shin murna take yi ne ko akasin haka, ta bangaren Azima ma kullum tana sama part din Al'mazeen zata shiga ta gyara ta zama macijiya ta kwanta tayi baccinta. @@@@@ *MA SHA ALLAH.* A jiya ne su Nawaz shi da Amininsa Al'mazeen suka samu damar sauka a kasarsu nigeria, sun sauka ne a airport din abuja, Al'mazeen ya kalli amininsa ya ce "Dude mu wuce kd kawai" "No wlh sai na huta, mu wuce hotel kawai mu watsa ruwa mu huta idan yaso gobe da safe tunda driver ya zo 10 ma muna kd in sha Allah, ka ga kaima idan ka so zaka huta kafin ka wuce kano,ko ya kace?" "As u wish" Al'mazeen ya faɗa yana shiga mota. A waya Nawaz yake gayawa Mom cewa sun sauka lafiya sai gobe da safe zasu shigo Kd, sannu da gajiyar hanya mom ta musu,sannan ta ce Allah ya kaimu goben lafiya,bayan ta katse take gayawa Sultana sun iso amma Nawaz yace sai gobe zasu shigo, itama dai Allah ya kaimun ta yi, ko da Sultana ta gayawa Aziza sai gobe su Ya Nawaz zasu shigo kd amma sun dawo nigeria suna abuja,itama Allah ya kaimun tace jikinta duk a sanyaye, ta bangaren hajjaju Azima,itama da taji kishin-kishin watakila sai gobe ko jibi Al'mazeen zai shigo kano amma ya dawo nigeria ko kaɗan bata ji dadin hakan ba, amma tace tayi hakurin jiransa na watanni masu tsayi dan dai kwana biyu babu damuwa. Washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, suka share cikin gidan tass suka goge, Aziza ta ce "Anty Sulty kije ki k'ara gyara part din Hamma Nawaz, ni zan tsaya a kitchen" Sultana ta amsa da to sannan ta fice ta bar Aziza ta hau aikin haɗa su abinci,ko da Mom ta shigo kitchen Aziza ta ce "Haba Mom kina damu a raye me zaki zo yi a kitchen, dan Allah kije ki kwanta ki huta" murmushi Mom ta yi ta kalli Aziza ta ce "Hakika mahaifiyarki tayi farin haihuwa da ta haifeki, na yaba da hankali da natsuwarki, Allah ya miki albarka ƴata" Aziza ta dukar ta kai tana juya white eye dinta ta ce "Amin Mom ɗinmu" fita Mom tayi tana wasu tunani a ranta, hakika da ace Aziza mutum ce babu abunda zai hana bata yiwa Nawaz kwadayin aurenta ba, duk da Nawaz Allah ya yisa da rainakon mace, yanzu zai iya cewa Aziza tayi masa yarinya,ita kuwa zata so Allah ya bata sirka kamar Aziza wacce zata maye mata gurbin Sultana idan tayi aure, ga shi dai Aziza ta shiga ranta sosai, duk da ita bata taba ganinta a macijiya ba, bata ma fatan ganinta a macijiyan, amma taya zata fahimtar da Nawaz har ya aureta? Dan Nawaz murɗaɗɗan mutum ne, zama tayi a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya mai karfi,ta jima tana tunane-tunane sannan ta hau adduar neman zabin Allah wa ɗanta da kuma Aziza wacce bata so ta rabu da ita. Karfe tara da rabi suka kammala komai suka jera a dinning, sannan suka sakawa gidan turaren wuta ya dauki kamshi, Sultana tace "Aziza je ki dau wanka nima bari na tafi" "To Antyna a huta gajiya" Sultana ta hau sama, aziza kuma ta shiga dakinta, toilet ta wuce dan tana da bukatar wankan nan sai kamshin abinci take yi,bayan ta fito ta dan murza mai kaɗan a fatarta wanda yake sheƙi, wani doguwar abaya ta saka, ta shafawa kanta mai,ta daure gashin, bata sa hula ba,illa lullubi da ta yi ta rufe fuskarta wanda ta jima bata rufe ba Mom ta hanata rufewa tace tayi rayuwarta ta daina takurawa kanta tunda sun san gaskiya, amma da shike yau Nawaz zai dawo harda bako yasa tayi lullubin. Tana nan zaune a dakinta har wajan goma da minti asharin, ihun Sultana ta jiyo tana fadin "Oyoyooo my 2 Brother's!!" wani wawan faduwar gaba ne ya dira a zuciyar Aziza jikinta ya dauki rawa, tana ji ana oyoyo tare da fadin ya hanya, muryan Sultana ta jiyo tana kwala mata kira, a hankali ta miƙe ta gyara mayafinta ta fito jikinta na rawa, a lokacin Nawaz da Al'mazeen suna rungume da Mom, Sultana na tsaye a gefensu tana dariya bakinta yaki rufuwa dan murna, bayan sun saki mom take kara musu ya hanya suna amsa da lafiya alhamdulillah, nan Mom ta rufesu da addua na nasarar da suka samo,zama sukayi a kujeran cikin parlourn, Sultana ma ta zauna kusa da Yayanta, tana kara gaishesa ya amsa yana tsokanarta amarya-amarya, rufe fuska tayi da tafin hannunta jin Al'mazeen shima ya hau tsokanarta, ganin yadda suke murna da nishaɗi yasa hawaye zubowa a idon Aziza tana kallonsu tana murmushi dan sun burgeta, a hankali ta juya zata koma daki idon Sultana ya sauka a kanta, ta ce "Aziza kina jina tun dazu nake kiranki Yaya sun dawo amma kika min shuru?" tun sadda Sultana ta kira sunan Aziza hankalin Nawaz ya koma kanta yana kare mata kallo kirjinsa na bugawa, tunda ya bar nigeria mafarkin yarinyar nan ya hanasa kiba, Al'mazeen ya kalleta shima yaji gabansa ya fadi, Mom tace "Karaso mana ɗiyata" a hankali Aziza ta fara taka kafarta wanda take jinsa tamkar baya jikinta dan kafafun sun mata nauyi, ta karaso ta duka tana gaishesu kanta a duƙe fuskarta kuma a lullube, amsawa Al'mazeen ya yi sabanin Nawaz da yake ji kamar zuciyarsa zata tsaga kirjinsa ta fito waje, bayan ta gaishesu ta mike ta kawo musu abun sha, suka ce ba zasu ci abincin yanzu ba, zasuje su kwanta su ɗan yi bacci zuwa azahar, sai sun farka kafin su ci abinci, a tashi lafiya Mom ta musu suka miƙe a tare, har sun kai kofa Mom ta ce "Al'mazeen amma ba yau zaka tafi kano ba ko?" "E Mom sai Allah ya kaimu gobe" "To Allah ya kaimu lafiya" "Amin" ya amsa a sanyaye yana bin bayan Nawaz wanda shi bai tsaya ba. Kwanciya sukayi ba jimawa kuwa bacci ya suresu, karfe daya da rabi suka farka suka yi sallah, Nawaz ne ya fara tashi yana fadin "Yunwa nakeji yanzu kam, ka zo muje muci abinci" "Okay muje" Al'mazeen ya faɗi shima yana tashi, wayar Al'mazeen ne ya dauki ruri Nawaz na ganin mai kiran ya yi tsaki yana fita. A hankali take tafiya Mom ta bata sako ta kai wa driver zai kai wa Hajiya Hauwa, kanta a sunkuye ga shi ta yi lullubi ga tunani,tana tafiya tana tunani, shi kuwa Nawaz hankalinsa na cikin waya yana dannawa, dai-dai wajan kofar shigowa babban parlour sukayi karo nan kafarta daya ya zame yana shirin wucewa ƙananan step guda uku na shigan parlourn ɗin, ganin haka yasa cikin saurin Nawaz yasa hannu ya fizgota, mayafinta ya faɗi kasa, gashinta da bata yi masa daurin kirki ba ya koma baya yana lilo, tsoro yasa ta waro idonta gabadaya waje, caraf sukayi 4 eye da Nawaz, wani mahaukacin bugawa kirjin Nawaz ya yi ganin white eye ɗin Aziza, saurin saketa ya yi ta faɗi ta bugu da duwawu, taji zafi dan haka tace "Washhh Allah na!" Al'mazeen dake waya ya ga Nawaz ya saki yarinyar mutane a kasa ta bugu dan ya ga sadda sukayi karon zata faɗi ya riƙeta amadadin ya tsaidata da kafarta sai kuma ya saketa?. "What's wrong with u dude?" Al'mazeen ya faɗa yana shirin sa hannu ya dago Aziza,kafin Al'mazeen ya ɗagata,tuni Nawaz yasa hannu ya sake fizgota ya tsaidata da kafafunta, ya duka ya dauki mayafita ya sa mata a kai, murya a daqile yace mata bar nan, da sauri kuwa Aziza ta bar wajan, Al'mazeen ya kallesa ya girgiza kai ya wuce ya bar sa tsaye, jikin Nawaz ne ya dau rawa yana kara tariyo yadda ya ga idon Aziza, me hakan ke nufi? Ya tsaya yana tambayar kansa. 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 TNK U 4 CMMNTS MY PPL'S. *PAID.* 🅿️=5️⃣1️⃣↪️5️⃣2️⃣ "To meyasa kika ce ba zaki je ba? Ni wlh na zata Hamma Khalil shine Abokin Hamma Nawaz" cewar Aziza,Sultana ta ce "A'a kinga hoton Khalil" Sultana ta faɗa tana nunawa Aziza hoton Khalil a wayarta, Aziza ta yi murmushi ta ce "Ma sha Allah,kun dace sosai, Allah ya kaimu musha shagali" "Amin-Amin" "To ke yanzu Anty Sulty miye abun damuwa dan za a saka bikinki?" "Ke Aziza baki da hankali ko? Ke kin san takura irin na Khalil kuwa? Wlh idan ya dawo ba zai bari na dinga motsawa ko nan da can ba,kuma duk abunda ya faɗi Mom zata hau kai ta zauna, taya zamu fara tafiye-tafiye wajan neman Azima? Sannan ma duk ba wannan ba, wannan babban lamari bai kamata ace zamu iya mu biyu ba, Mom tana da fahimta ni a ganina tun a ba kowa mu gaya mata gaskiya, dan kar a zo wata rana ta sani kuma abun ya kwab'e mana" jikin Aziza ne ya dauki rawa ta kalli Sultana ta ce "Anty Sulty Mom zata koreni!" ture abincin gabansu gefe Sultana ta yi ta kamo hannun Aziza ta ce "Taya Mom zata koreki Aziza? Babu amfanin boye mata abunda zata sani duk daren daɗewa kamar yadda nima na sani a yanzu, dan haka gwara mu gaya mata a san abun yi tun a yanzu, ga shi ana maganar tsaida bikina kwanan nan, tsammaninki yanzu Khalil zai dawo a cikin sati, su Yaya Nawaz zasu dawo nan da wata daya,ina mai tabbatar miki za a iya aurar dani nan da wata biyu, dan haka gwara muyi da gaske, yanzu ki tashi muje mu samu Mom mu gaya mata gaskiya, dan hausawa na cewa da zafi-zafi ake dukan karfe" "Wani gaskiya zaku gaya min?" suka ji magana daga bayansu, ba iyakar Aziza ba, har ta Sultana sai da ta kwalalo ido waje, Mom ta ce "tambayarku nake yi, sai zazzare idanu kukeyi ku min magana mana, dan wannan idon naku baku da gaskiya" Sultana ta kalli Aziza wacce take girgiza mata kai alaman kar ta faɗa, Sultana ta hau in-ina tama kasa magana,idan ta kalli Mom, Mom zata ce ta gaya mata me suke boyewa,idan ta kalli Aziza zata girgiza mata kai kar ta faɗi, dan haka Sultana ta kasa magana banda in-inar da takeyi dan an sakata a tsakiya, ganin ta ruɗe har zufa take yi, ga Aziza da ka kalleta kaga tashin hankali a fuskarta ganin haka yasa Mom kamo hannun Sultana ta ce "A iya sanina ban yi miki tarbiyyar k'arya ba,ba halinki bane, sannan baki boye min abu, duk da ban san Aziza sosai ba amma zan iya tsayawa na bugi kirji na faɗi halin Aziza, dan haka karku fara min karya daga yau, karku boyemin komai, tun dawowarku nake ganin damuwa a fuskarku, ku gaya min meke faruwa" kuka Aziza ta fashe da shi tana duƙawa ta rufe fuskarta da tafin hannunta, Sultana tace "Aziza ki kwantar da hankalinki, Mom zan gaya miki" Sultana ta zaunar da Mom tace "Ban san taya zaki fara daukar maganar ba, watakila da ace ni daya ce zakice nayi gamo da aljanu" Sultana bata fara cewa Mom Aziza macijiya bace,tun daga tushen labarin ta dauko mata tana bata tiryan-tiryan har ta kawo mata shi karshe ta dasa aya, wani ware ido Mom tayi tana bin Aziza da kallo wacce ta haɗa kai da guiwa tana kuka, hakika hankalin Mom ya tashi, Sultana kuwa ta gaya mata ta ga Aziza a macijiya kuma ita ce ma ta taimaketa daga hannun su dan gidan Alhaji wanda da badin Aziza ba da sunyi mata fyaɗe, jikin Mom banda kyarma babu abunda yakeyi, ta jima tana karanto kalman "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" kafin ta fara jin tana samun natsuwa, sai da ta ware tukunna ta yi kan Aziza ta duka duk da zuciyarta na dukan tara-tara ta kama Aziza ta rungumeta tana rarrashinta, cikin kuka Aziza tace "Mom dan Allah karki tsaneni! Dan Allah karki koreni! Dan Allah karki ji tsorona!" girgiza mata kai Mom ta yi ta ce "Ko daya ba zanji ba, kamar yadda kike a da haka kike a yanzu, ai ba laifinku bane, a gaskiya Banju ba karamin mugu azzalumi bane marar imani, Allah sai ya saka muku, Allah ya bayyana mana Azima lafiya, Allah kuma ya kare bayinsa wanda Banju yake shirin tarwatsawa" suka amsa da amin,bayan sun gama yan koke-kokensu da jajinta lamarin Mom ta miƙe ta fice zuciyarta cike da zullumi, abu sai kace a film, bata fata ta ga Aziza a macijiya a labarin ma ya isa, Mom na fita Sultana da Aziza suka sauke ajiyar zuciya, Sultana ta ce "Alhamdulillahi! Mom ta rage mana aiki" "Kamar ya?" "Da taji mana, da yanzu muna nan muna wallahi tallahi dake" murmushi Aziza ta yi tace "Duk da haka ku zuciyarku daban yake, mutane irinku kaɗan ne" "Humm! Yanzu ke kuma kenan dole kafin ki koma mutum sai kunyi aure?" "Ai babban damuwar yana jikin Azima, idan har ta warke nima na warke In sha Allah, amma da kamar wuya a samu wanda zai auremu har ya taimaka mana mu dawo mutane kamar kowa" "In sha Allahu, Allah zai kawosa,kuma zaki gani,muddun kunyi tawakkali Allah zai dubi hakurin da kukayi na cinye wannan babban jarabawan, sannan ya saka muku ta yadda baku tunani" "Haka ne kam" Aziza ta faɗa tana gyara zama, sun jima suna hira. 🍃🍃🍃🍃🍃🍃 Bayan kwana biyu komai ya dawo dai-dai, kamar yadda Khalil ya faɗa zai dawo cikin sati to hakan ne ta kasance,dan kuwa shirye-shiryen dawowarsa akeyi,dan da ya dawo biki kawai za a sha, yace ayi biki a ba shi matarsa. Ranar lahadi da da daddare ya iso gari, bayan da ya huta maganar biki Hajiyarsa ta hau masa, yace tunda yau ya dawo a bari nan da kwana hudu ko biyar sai aje dan a saka rana, duk da shima Nawaz ɗin yace zasu dawo su ma kwanan nan, da haka suka ajiye maganar. Washe gari da misali karfe goma na safe yasha wankansa yasa manyan kaya na mutunci ya shiga ya gaida hajiyarsa, ta ce "Khalil ina zuwa ne haka? Ko dai za a je ganin ɗiyata Sultana ne?" "E wlh Mom, zanje dai gaishe da Mom ne" "Ah ba wani nan kar ma ka wani fara fakewa da Mom Ah to ,a gaishe min da su Sultanan" tashi ya yi yana dariya yace zasuji sannan ya fice. @@@@@ Bai gayawa Sultana a kan cewa zai zo da safe ba, ya dai gaya mata ya shigo kaduna da daddare da misalin takwas da rabi, ko da ya isa gidan kasancewar mai gadi ya san shi ya hau masa sannu da dawowa, Khalil ya amsa yana dariya, da shike gidan ba baƙonsa bane, nan ya shige kansa tsaye yana buga sallama, Aziza ce kawai ta farka a lokacin ta gana mopping kenan, ta ga mutum,tana ganinsa ta ganesa ta ce "Lahh Hamma Khalil marabalale" ta fada tana hawa sama da gudu ya yi murmushi ya ce. "Kanwarmu kenan" ya nemi waje ya zauna, da gudu Aziza ta shiga dakin Sultana ta haye gadon ta janyeta, Sultana ta bude ido cikin haushi ta ce "Dan Allah miye haka Aziza!?" "Kai Anty Sultana kin san da cewa Hamma Khalil zai zo shine kike bacci har yanzu baki masa girki ba, ba kiyi wanka ba haba dan Allah" ai Sultana tana jin an ambaci sunan Khalil yazo ta miƙe zunbur, ta ce "Ke Aziza da gaske Khalil yazo?" "Wlh yazo yana parlourn kasa" da sauri Sultana ta miƙe da kayan bacci ta ɗiro a gadon ta fita ta shiga dakin Mom ta ce "Mom wai Khalil yazo" "E na sani" "Shine Mom ni ban sani ba, bai fa gaya min zaizo ba, ga shi ban shirya masa komai ba, ban yi wanka ba" Mom ta dauki mayafinta tana fadin "Too idan kin gama mitan saiki haɗa masa komai ɗin sannan kiyi wanka" ta fice, fita itama Sultana ta yi, ta samu Aziza na kwashe kaya a parlourn sama,ta ce "Aziza yanzu ya zanyi?" "Karki damu Antyna,yanzu kedai kawai kije ki cakare wanka, zan kula da saura" "Thats my lil'sis" Sultana ta fada tana shiga daki da sauri, kasa Aziza ta sauko ta shiga kitchen, a cikin mintuna qalilan ta jera tray ta haɗa abubuwa a kai na burgewa da ban sha'awa tazo ta ajiye a gaban Khalil wanda yake duƙe a gaban Mom suna magana, sun jima suna magana da Mom kafin Mom ta tashi ta koma sama, ba jimawa gimbiyar tasa ta sauko, nan aka hau hiran soyayya na yaushe gamo, sannan ta kara gabatar masa da Aziza. Kamar yadda Khalil ya fada bayan sati daya da dawowarsa aka zo aka tsaida ranar aurensa da Sultana wanda za ayi nan da wata daya da sati uku,wanda Nawaz shi da Khalil ɗinne suka yanke wannan shawara. Tunda aka saka wannan rana Khalil ya hana Sultana sakat, tayi-tayi ya bari suje kano amma ya ƙi, yace ta bari ba yanzu ba,ita da basu shiri da yan kano din ma, bayan sunyi haka da shi ta gayawa Aziza, Aziza ke tambayarta meyasa bata son kano, Sultana ta ce "Ni da Hanan yadda kika san kamar wuta da auduga, sannan rashin kirki da mugunta irin na Maman Hanan da Maman Beenah abun ba a magana karki so ki yadda suke yiwa Yaya Almazeen, kuma shine mai kudin fa, gwara ma dai Beenah muna ɗan shiri amma banda Hanan, bana son halinsu ne sabida muzgunawa Yaya Al'mazeen da sukeyi" "Mutane kam ai sai addua, Allah ya kyauta kawai" Sultana ta amsa da amin. 🐍🐍🐍🐍 Hadiza! Hadiza! Hadiza!. Da gudu Hadiza ta fito ta zube a gaban Hajiya Lawiza Maman Hanan kenan, cikin yauki ta kalli Hadiza ta ce "Hadiza, maza ki kirawo Azima ki haura da ita can sama part din Al'mazeen ta fara gani da tattare ƙura, suna nan dawowa nan da sati biyu" 🍃🍃🍃🍃 *BACCI NAKEJI WLH🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🥱😴🏃🏻‍♀️* [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=5️⃣7️⃣↪️5️⃣8️⃣ Damm! Gaban Azima ya buga tayi saurin ware blue eye dinta, ta maimaita "Azizaa! Aziza dai!?" Maman Beenah ne ta kallesa ta ce "Al'mazeen kasanta ne dama? Sannan sunanta ba Aziza bane, wannan sunanta Azima ne" girgiza kai Al'mazeen ya hau yi yana ƙarewa Azima kallo,yatsar hannunta ya kalla yaga irin zoben da ya gani a hannun Aziza dazu, sannan ace kuma ba Aziza bane? Ko dai ya yi gamo ne? da sauri ya haura sama, yana shiga part dinsa ya ga sai kyalli yakeyi an gyara sosai bai tsaya karewa ɗakin kallo ba, wayarsa ya ɗaga zai kira Nawaz sai kuma ya fasa ya kira layin mom,ringing uku mom ta daga suka gaisa yace mata ya isa lafiya,mom tayi hamdala ta masa sannu da hanya ta kara da cewa "Ya ka samu mutanen gidan,su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba?da kuma yaran?" "Lafiyar su lau" "Ya naji muryarka haka Al'mazeen? Kamar kana cikin tashin hankali ko damuwa, ba dai daga dawowarka suka fara cusa maka baƙin ciki ba?" "A'a mom basu bane, amm nace ba mom? Aziza fa? Ya jikin nata?" "Alhamdulillah da sauki, ko ba sauki musulmi ai ba zai ce babu ba sai dai yace alhamdulillah, Sultana tana tare da ita dik da naji tace tana da paper 12 zataje skull ga abokin naka ma shima baida lafiya, bayan tafiyarka da ya shigo idonsa a kumbure wai kansa ke ciwo" "Subhanallahi! Allah ya basu lafiya, dama tunda na ga yanayinsa na san bai da lafiya dan ina kyautata zaton jiya bai yi bacci ba dan a parlor na samesa zaune da asuba, amma da na tambayesa yace min ba komai,zuwa 12 in sha Allah zan kirasa naji ya jikin nasa maybe yanzu yana bacci, bari na kira sultana naji ya na Aziza yake" nan ya yiwa Mom sallama yana katse wayar, sultana ya kira a lokacin tana magana da wata classmate ɗinta a waya,tana gaya mata ba zata samu zuwa skull ba, Brothern'ta da sistern'ta basu da lafiya, suna cikin magana ta ga wayar Al'mazeen ya shigo dan haka sukayi sallama da kawarta ta daga na Al'mazeen, sai da ta masa an isa lafiya kafin yace mata "Ya jikin Aziza?" kuka ta sa tana kara masa wayar a saitin fuskar Aziza dake fidda huci tana gurnanin zazzabi,bayan ta kara masa wayar yaji kafin ta maida wayar kunnenta tana ci gaba da kuka tana fadin "Bro ka ji ta ko? Yadda ka barta haka take sai ma abunda ya ƙaru" "Subhanallahi! Allah ya bata lafiya kin bata wa innan maganin kuwa?" "E bai jima ba da na bata,amma kamar bai yi aiki ba" "Karki damu kinji zai mata a hankali kiyi ta yi mata addua, Allah ya bata lafiya!" daga haka ya katse wayar,ya hau jeka ka dawo a daki yana saƙa da warware, "AZIMAA!?" ya faɗa yana rike kai "To ko dai yar uwar Aziza ce? Tunda sunansu mai haɗi iri ɗaya ne? Amma kuma Nawaz yace an kashewa Aziza kowa bata da kowa! To ba mamaki kamanni ne" daga haka ya miƙe ya shige toilet abunsa ya watsar da tunanin jin yana shirin saka masa ciwon kai. A kasa kuwa ba ƙaramin daru aka sha da Azima ba a kan abincin da za a kai wa Al'mazeen, ta dage ta kafe tace wlh ba zai ci wannan abincin ba, Maman Hanan ta ce "E lallai kam Azima, wato kin samu waje kinyi freesh shiyasa zaki fara murza iskanci son ranki ko! To wlh ki bi a hankali" ba tare da Azima tayi magana ba ta karbi abinci a hannunsu Hadiza tayi wajan kitchen da shi ta ajiye ta hau yiwa Al'mazeen sabo, girki takeyi duk da ba wai ta wani iya sosai bane, amma da taji ance Al'mazeen zai dawo yasa kullum tana kitchen dasu Hadiza tana ganin yadda ake girkin barin ma wanda aka ce mata Al'mazeen ɗin ya fi so. Tana girki tana tunanin sunan da Al'mazeen ya kirata da shi,hakika hankalinta ya ɗan tashi "Aziza! Aziza! Ina Al'mazeen ya san Aziza? Shi da baya ma kasar, to ba mamaki wajan kiran sunanta aka samu kuskure zai ce Azima yace Aziza" share zancan tayi ta ci gaba da aikinta dan ta san wan can sakaryan tana can jeji, sai bayan da ta kammala ta jera a tray ta dauka ta haura sama. A hankali ta tura kofar ba tare da tayi sallama ba, Al'mazeen na zaune a parlour da system a gabansa da alama aiki yake yi, yaji mutum ya shigo ba sallama, haɗe rai ya yi, ita kuwa Azima sallama baya daya daga cikin dabiunta, abunda Al'mazeen ya tsana kenan, dan shi mutum ne mai girmama addininsa fiye da komai a rayuwarsa, Al'mazeen da na riƙo da addini fiye da tunanin mai tunani, murya can kasa yace "Fita ki min sallama, karki sake ki min magana ba tare da kin min sallama ba" juyawan kuwa tayi ta fita ta sake shigowa tare da fadin "Salamu alaikum" tana tura bakin, bakintan kawai yake iya hangowa yadda take tura shi tana murguɗa shi tunda fuskarta a rufe yake, abun dariya ya ba sa dan haka ya ɗan murmusa ba tare da ta gani ba, abincin ta ajiye tare da fadin "Kayi hakuri" bata ma san sadda tace masa ya yi hakurin ba, jinjina kai Al'mazeen ya yi,ya ce "Kece Azima?" ta gya ɗa kai, "Daga ina kike?" damm! gabanta ya buga, amma da shike zuciyarta a tsaye yake ƙyam tace "Daga can cikin kauyen kano a wata rugar fulani" Al'mazeen a ransa ya ce "E tabbas to basu da alaƙa da Aziza" "Ina abincin da aka dafa min?" murguɗa baki Azima tayi tace "Na ajiye musu a bayan kitchen idan sun ga dama su dauka su ci ko su san yadda zasuyi da shi" tana gama fadi ta mike fuuuu ta fice, girgiza kai Al'mazeen ya yi ya ci gaba da aikinsa, sai wajan sha daya da rabi ya ja tray din da ta ajiye masa ya buɗe yana kan buɗewa sai ga ta ta shigo ta duƙa tunowa da dazu ya koreta akan bata yi sallama ba sai ta kara ficewa da sauri ta shigo tana fadin "Salamu alaikum! ai saika kirani nazo na zuba maka" "Kina da waya ne?" girgiza kai Azima ta yi ta ce "A'a bani da shi,amma idan kace AZIIIMAAAA!!🗣️Ai zanji na taho da sauri!" girgiza kai Al'mazeen ya yi ya tashi zai shiga daki, da sauri ta ce " *HAMMA MAZEEN* abincin fa?" Cak Al'mazeen ya tsaya yana nanata sunan "Hamma Mazeen!" kirjinsa ne ke bugawa da sauri-sauri, "Ina zuwa ki zuba kawai ki tafi" ya faɗa yana shigewa bedroom, Azima haushin kanta ne ya kamata, wai meyasa take masa abu kamar wanda ake sakata ko ana bata umarni ne? Meyasa take jin faduwar gaba a kansa, meyasa take jin makarin gubarta yana tattare da shi? Amma kuma tana ji kamar ita da shi an jona musu kuran karfe, saurin tashi tayi ta fice. 🍃🍃🍃🍃🍃 Sai 1 Nawaz ya farka ya ɗan ji kan nasa da sauki amma kan ya yi masa nauyi, wanka ya yi a nan daki ya yi sallah, sannan ya lallaba a hankali ya shiga cikin gida, ba kowa a parlor dan haka ya fara haurawa sama, sai kuma ya juyo yana kallon kofar dakin Aziza, saukowa ya yi ya nufi dakinta, a hankali ya tura da sallama, mom da sultana ma ashe suna dakin, Aziza na jingine tana sallah a zaune a kan gado, saurin karasowa kusa da mom ya yi ya ce "Mom jikin nata ya yi tsanani ne haka shine baku tasheni munje asibiti ba?" "Humm! Nawaz kai ma fa ba lafiyar gareka ba, ka ganta nan jiya bata rintsa ba" "Bari ta idar da sallar sai a kaita asibiti" "A'a Nawaz ba sai anje asibiti ba, babu amfani, zaku ƙara huda mata jiki ne kawai, yanzu sai kuce zaku sossoka mata allura a ɗaura mata ruwa aja jini, wanda hakan kuma...!" sai Mom tayi shuru, a lokacin Aziza ta sallame sallarta, Nawaz ya miƙe yana fadin "Mom dan ta gaya miki bata son allura sai a biye mata dan lafiyar wa akeyi? Ina dan lafiyarta ne!" ya faɗa cikin haɗa fuska, ya nufeta yana faɗi wa Sultana ta tashi taje ta cewa driver ya juya mota. Aziza kuwa ganin ya nufota yasa ta kwalalo ido waje, dan kuwa jikinta yana fidda farin sab'ar maciji idan ya gani fa? Saurin girgiza masa kai ta hau yi muryarta a shaƙe da baya fitowa sosai ta hau fadin ya kyaleta kar yazo inda take, ko kaɗan bai tsaya ya saurareta ba yasa hannu ya yaye bargon jikinta ya kamo hannunta,ji yayi kamar wani fata ya maqale masa a hannunsa, sake hannun nata ya yi yana kallon tafin hannunsa, wani zare ido Nawaz ya yi sai kace idon zasu faɗo ƙasa,ganin sab'ar fatar maciji fari sol a hannunsa, Aziza kuwa banda kakkarwa babu abinda jikinta ke yi,tana sake boye hannunta a cikin hijabin dake jikinta tana jan bargo tana son rufe kafafunta, saurin fizgar bargon Nawaz yayi jikinsa na kyarma, yasa hannu ya figi hijabinta ganin haka yasa mom cewa da sauri "Nawaz ka haukace ne!? baka da hankali ne!? mai kake shirin yi!?" ba tare da ya saurari mom ba ya ɗago Aziza tsaye wacce jiri ke kwasarta, hannunta ya riko ya ware nan kuwa ya ga jikinta duk b'awu, a lokacin kuma Aziza ta suma, dagota ya yi yana jijjigata cikin tashin hankali yana tambayarta wacece ita. Cikin kuka Sultana tasa hannu ta kwace Aziza daga hannun Yayanta ta rungumeta ta ce "Yaya ta suma fa? Dan Allah Mom kiyi wani abu a kai" Nawaz yasa hannu zai kara jan Aziza daga jikin sultana, sultana tayi saurin juyawa da ita ta kwantar da ita tana murza tafin hannunta tana kuka "Zan fa karyaki Sultana ina wasa dake ne!!?" "Wlh Yaya ko kasheni zakayi ba zan bari ka kasheta ba, dan Allah mom kiyi magana ki gaya masa gaskiya,babu amfanin wannan boye-boyen" "Nawaz ya isa haka! Aziza Macijiya ce!" Mom ta faɗa a tsawace, Nawaz ne ya yi baya-baya yayi zaman yan bori sharab, mom ta karaso ta kama hannunsa. kenan mafarkinsa akan yarinyar macijiya ce gaskiya ne? Kallon Mom ya yi da jan ido ya ce "Mom da macijiya muke rayuwa kuma ke ma kin sani? Taya hankali zai dauka ace mutum maciji? Da ace sultana ce ta faɗa ba abunda zai hanani ban kaita asibiti an duba min kwakwalwarta ba" Ajiyar zuciya mom tayi tace "Zaka iya tsayawa ka saurareni uhum? Nawaz magana nake maka" kifa kansa ya yi a kafadar Mom hawaye suka hau gangaro masa wanda bai san dalili ba. "Nawaz labarin Azima da Aziza da baffansu da kauyensu abun tausayi ne mai cike da zallar al'ajabi" cikin taushin murya Mom ta hau zayyanawa Nawaz labarin Aziza bata boye masa komai ba kamar yadda Aziza ta ba su haka ta bai wa Nawaz, mom tana gama ba shi labarin ya dago yana fadin "Wlh mom yawancin abun da kika faɗa min ina ganinsa a mafarkina, tun ranar da na bugeta a mota na kawota kaduna tun daga ranar na daina bacci kirki,mom ina yawan ganinta a siffar macijiya tana kuka tana neman taimakona!" jinjina kai Mom tayi ta ce "Ba mu san me Ubangiji ya boye tsakaninka da Aziza ba Nawaz, amma inaso muyi wani jahadi wana Allah ya zama silar shigarmu aljanna, Nawaz har zuciyata ina jin Aziza,yarinya ce mai hankali da natsuwa da sanin ya kamata duk da tana da kananun shekaru amma tana da hankalin manya da imani da kaddara ga tawakkali da miƙa wuya,kuma dama abunda akeso kenan ga musulmi mumini ko mumina, Nawaz sultana zata bar gidan nan kwanan nan, dan Allah ina so kayi jahadi ka *AURI AZIZA!!*" dummm!! gaban Nawaz ya bada ya kalli Mom da sauri, Mom ta gya ɗa kai tana fadin "Tun kana yaro ban taba cewa ina neman alfarma ka kasa min ba, ina so ka taimaka ka auri Aziza, ka zamo silar warkewarta, duk wanda ya zama silar farin cikin mutum daya Allah zai zama silar farincikinsa a ranar da babu wani mai gata sai fiyayyen halitta, Nawaz kana da ilmi duk abunda zan gaya maka ka sani sai dai na kara yi maka tuni, idan ka auri Aziza ka zamo silar warkewarta hakika zaka saka mutane dayawa ne farinciki, zaka fidda UWA da UBA daga ƙunci, da sauran yan uwansu, wlh har zuciyata na aminta" kallo fuskar Aziza Nawaz ya yi, hakika daga fuskarta zaka san cewa tana jin jiki "NA AMINCE MOM! ZAN AURETA!" da sauri Sultana tazo ta duƙa ta rungumesa cikin murna, "da gaske yaya zaka aureta!? Wayyo dadi wlh nayi farinciki" "Allah ya maka albarka Nawaz" cewar mom tana shafa kansa. Nan suka zauna a dakin har sai da aka yi sallar la'asar kafin suka fita da niyyar sallah, nawaz msallaci yaje, bayan sun idar ya jima yana kwararo adduoi a kan wannan lamari da yake gani tamkar a mafarkin da ya saba ne. Bayan ya dawo part dinsa ya wuce, ya dauki wayarsa ya ga miss calls din amininsa,kiransa ya yi ya daga yana tambayarsa ya jikinsa,Nawaz ya amsa da sauki shima yana masa ya gajiyar hanya, Al'mazeen ya amsa da alhamdulillah ya kara da fadin ya jikin Aziza, alhamdulillah Nawaz ya fada, sun ɗan jima suna magana inda Nawaz yake ji ko ya gayawa Al'mazeen? Daga baya kuma ya fasa har suka gama wayar sukayi sallama. Sai wajan shidda Aziza ta farka sultana ta taimaka mata tayi alwala tayi sallah a zaune kamar dazu, bayan ta idar tayi addua sultana ke gaya mata sadda ta suma mom ta gayawa Yaya Nawaz komai, a lokacin da sultana ke gayawa Aziza Nawaz sun shigo shi da mom, kuka Aziza ta saka tana fadin "Shikenan zai koreni! Dan Allah Anty Sultana ki ba shi hakuri kar ya koreni, wlh da na samu Azima zan tafi da kaina,tafiya na har abada ba zai sake ganina ba in sha Allah" rasss! gaban Nawaz ya buga jin tace zata tafi na har abada, a hankali Nawaz ya juya ya fita ganin yadda take kukan duk sai yaji babu dadi yana danasanin abunda ya mata, tayi mugun karya masa zuciya. Mom tace "Injiwa yace zai koreki a gidan nan? Bana so na ƙara ji kince zaki bar gidan nan na har abada, dan kuwa kina nan a gidan nan har abada In sha Allah,kinji ko?" Aziza ta gya ɗa kai tana kuka. @@@@@@@@ Da washe gari tana kwance tana fama da kanta,bata san ta yadda zata samu furen huriri ba, da ace ta samu da tuni an wuce wajan, turo kofar akayi da sallama, jin muryan mai sallaman yasa gaban Aziza bugawa, murya na rawa ta amsa, karasowa yayi a hankali ta dago idonta ta kallesa a tsorace, ta gansa da plate a hannu, mamaki ne ya kamata, zama yayi a gefen bedside'drower fuskar yau da sassauci, murya a can kasa ya ce "Ya jikin naki?" "Alhamdulillah, ina kwana?" "Tashi kici abinci ki sha wannan rubutun, wani babban aminin Daddyna ne malami ne wajansa naje jiya da daddare na masa bayani a kan matsalarki, yace na baki wannan zakiji dama-dama duk da ba lallai bane ya dauke miki abunda kike ji gabadaya ba, amma zaki samu karfin jiki" mamaki ne ya ƙara kamata, amma bata da lokacin tsayawa mamakin, a hankali ya dagata ya jinginata da pillow, ya dau spoon ya ɗibi abincin ya kai mata shi saitin bakinta, tsananin mamaki ya hana Aziza buɗe baki taci dan ji take kamar mafarki takeyi, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Nawaz furta kalman "I'm sorry Aziza" a sanyaye, sake yin ƙasa da kanta Aziza tayi gabanta na ci gaba da bugawa, muryarsa taji yana kara fadin "Na sani, na cusa miki tsorona a zuciyarki, am sorry once again" kuka ta fashewa da shi, ya ɗan rintse ido ya ce "Kamar na gaya miki bana son kuka ko?" ta gya ɗa kai "To meyasa kikeyi?" "Na...ba...ri" ta fada murya na rawa, "To kici abincin" ya fada yana bata a baki cike da tausayinta, bata wani ci sosai ba ta ce masa ta koshi, cup ya dauka ya tsiyaya mata rubutun ya bata tasha tana sha taji kanta na wani mugun juyawa, ba jimawa ta zube ta hau bacci, ganin tayi bacci yasaka shi tashi ya fita,a parlour ya samu Mom da sultana, zama ya yi kusa da mom, ta ce "Allah ya maka albarka Nawaz, Allah ya faranta maka duniya da lahira" a tare suka amsa da amin shi da sultana. Ko da ta farka taji jikin nata da dama-dama,dan kuwa ta miƙe da kafafunta har tana iya tafiya, jirin ne dai bai daina dibarta ba. 🍃🍃🍃🍃🍃🍃 Bayan kwana biyu taji sauki alhamdulillah amma lokaci zuwa lokaci jiri na zubar da ita, tsakaninta da Nawaz kuma yanzu babu tsangwama, sai tausayawa, har mamakinsa take yi,ita dai ba zata gushe ba tana yiwa su mom addua. 🍃🍃🍃🍃🍃 Bayan sati daya da dawowar Al'mazeen kano komai ya canza a gidan, Azima ke zuba mulki son ranta, ga shi yanzu tana kwatowa Al'mazeen yancinsa a cikin gidan, duk wani guba da maganin mallaka idan aka zuba masa a cikin abinci sai dai azo a samu Azima ta juyewa karnuka abincin, su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba sun rasa yadda zasuyi da Azima, ta bangaren Al'mazeen kuwa a sati ɗayan nan kacal ya shaƙu matuƙa da Azima dan har zuciyarsa yake jinta, shi mutum ne mai son kulawa da soyayya amma bai samu ba, sai ga shi rana tsaka ya samu a wajan mai aiki dan ba karamin kulawa da shi Azima ke yi ba. Kamar yadda Azima bata son dogon magana haka ma al'mazeen, amma su kan zauna suyi hira, inda take gaya masa ai itama bata da kowa duk an kashesu, idan Azima na magana ya kan ji muryan Aziza, duk da ba wai ya taba ganin fuskokinsu sosai bane, dan itama Azima duk shaƙuwan nan bata buɗe fuskarta, bayan dawowarsa da kwana uku taso guduwa ta bar gidan amma haka ta kasa har ya kai sati daya,inda takeji kafafunta sunki amincewa da barin gidan. Yau ma kamar kullum ya shirya zai tafi asibiti, yana kan saukowa kasa har ya zo step din karshe sai ga Hanan, tana ganinsa sarai ta bangajesa briefcase dinsa ta faɗi, amadadin ta tsaya ta ba shi hakuri sai tana shirin rab'awa ta gefensa ta wuce, Al'mazeen cikin haushi ya ce "Kee Hanan! Baki ga abunda kika min bane! Zo ki dau jakata ki bani" "Wlh Al'mazeen sauri nake yi inaso naje na gwada wannan memoryn ne" ta faɗa tana shirin hawa sama taji an wani fizgota ta baya, ta ma zata Al'mazeen ɗin ne amma tana juyowa ta ga Hajja Azima wacce yau tayi shigan riga da wando idonta sanye da wani black shadow, Al'mazeen ne ya siyo mata jiya kasancewar itama ta masa karya da cewa ai idonta na ciwo. fuskarta a haɗe da ka ganta sai tayi maka kama da irin bosawan film din indian nan, ashar Hanan tayi ta kalli Azima sama da kasa tace "Wato na kauye ya shigo gari ko?" "Ki duƙa ki ɗau jakarsa ki basa sannan ki ba shi hakuri" Azima ta faɗa cikin murya mai nuna umarni take badawa ba shawara ba. "Lalala! Wlh ni ba irinsu Hajjaju bane, da zaki dinga yab'a musu magana kina juyasu kina basu umarni kina gasasu! Wlh ni karyaki zanyi! dan ni bana son raini!" Hannunta Azima ta kama ta murɗe Hanan tasa ihu, Azima ta cije baki tace "Kinga ni nayi miki kama da wacce take son raini? Tun kafin ki san wacece asalin Azima dau jakarsa ki ba shi sannan ki ba shi hakuri!" Maman Hanan da Maman Beenah da beenah da Hanif ne suka sauko jin ihun Hanan. Nan suka ga Azima murɗe da hannun Hanan Al'mazeen na cewa da Azima a kan ta saki hannun Hanan, ita kuwa tace ba zata sake ba, sai Hanan tayi abinda ta sakata,jin wuya yasa hanan cewa zata yi yadda Azima tace, sakinta Azima ta yi ta duka ta dau jakar ta ba shi ta ce "Kayi hakuri" "Kayi hakuri wa?" Azima ta faɗa a tsawa ce. "Kayi hakuri Al'ma...." dauketa da mari Azima tayi har saida Hanan ta kai kasa,Azima tace "Hamma! Daga yau idan na cire su Hajiya duk gabadaya Hamma Mazeen zaku na ce masa tunda ya girmeku, maza gaya masa!" "Kayi hakuri Hamma Mazeen" Hanan na faɗi ta hau sama da gudu, Maman Hanan da Maman Beenah da Beenah suka bi bayanta, Al'mazeen ya haɗa rai yace "Ina bakijin maganata? Ina cewa ki saketa amma kinki ko?" turo baki tayi tace "Ba komai nake yi daukawa ba,kuma ma ai sabida kai nayi" tana gama fadi ta fice tana tura baki ta bar shi tsaye, murmushi Almazeen yayi ya fice ya tafi office. Ko a office din ya kasa aikin kirki tunanin Azima kawai yakeyi, wayarsa ce tayi kara yana dubawa ya ga Alisha,guntun tsaki yaja,yau kusan sati tin dawowarsa kano take kira baya dagawa. @@@@ "Yanzu me zamuyi wa wannan yarinyar dan tana son fin karfinmu?" cewar Maman Hanan, Maman Beena ta ce "Shegiyar taga kudi duk yadda akayi sonsa takeyi" "Abunda za ayi muyi mata sharrin sata na san shi da kansa zai koreta, dama yau su Summy da Sady zasu zo ko?" "E sunce ma sun kusa isowa". (Summy da Sady, kannan Hajiya Lawiza da Hajiya luba, wanda suke so su aurawa Al'mazeen). 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=5️⃣5️⃣↪️5️⃣6️⃣ Da kyar ya tattaro jarumta jin yadda kafafunsa suka yi sanyi ya shiga parlourn, ya samu Al'mazeen zaune yana cin abinci, zama shi ma ya yi Sultana ta zuba masa ta tura masa gabansa, amma tunani yasa ma yaji abincin ya fita kansa, Aziza kuwa tin sadda ta ba wa driver sako ta maqale ta kasa shiga gidan ganin yayi babakere a bakin kofa, sai da ya shiga ta siɗaɗo a hankali ta shige dakinta da gudu,tana shiga ta zube a gado ta saki kuka, ba jimawa Sultana ta shigo ta sameta tana kuka ta ce "Subhanallahi! Aziza lafiya me ya faru?" Cikin kuka ta dago ta ce "Anty Sulty Hamma Nawaz ya ga idona" "Mtswww! To sai me dan ya ga idonki?" "Wlh tsoro nakeji kar ya koreni, dan naga yana mini kallon tuhuma kamar yasan wani abu a kaina" "Kinga Aziza dan Allah ki kwantar da hankalinki ki samu natsuwa kinji? Babu abinda zai faru,na san me zanyi, kuma ma ai idan ya san wani abu a kanki ai ya rage mana aiki, balle ina ma zai sani? daga wajena sai wajan Mom,kuma Mom da kanta ta kwabeni tace kar na gaya masa ta san ta yadda zata gaya masa,na tabbata mom bata gaya masa ba,dan da ta gaya masa zata gaya min, dan haka ki dai na damun kanki" rarrashinta Sultana ta yi har ta samu tayi shuru, kafin suka koma hiran karatu. Da kyar Nawaz ya yi cokali uku a abincin ya tashi, Al'mazeen ya ce "Dude ka ce yunwa kakeji amma ka kasa cin abinci i hope dai komai lafiya?" "E lafiya,ina zuwa" ya fada yana ficewa, part dinsa ya koma ya kwanta a dogon kujera, hakika idonta babu bambanci da wanda yake gani a mafarkinsa, wai wacece wannan yarinyar nan ne kam? Ya zama dole ya tambayeta ita wacece sannan miye haɗinsa da ita,idan ma mayya ce to wlh shi namansa da ɗaci,kuma sai ya danna mata kashedi ta fita rayuwarsa ya huta, ya kara jan tsaki. Bayan Al'mazeen ya gama cin abinci ya koma part din Nawaz ya samesa yana kwance a dogon kujera,zama ya yi a 1siter yana fuskantar Nawaz ya ce "Dr lafiya kuwa?" "Nml, kawai kaina ke ɗan min ciwo" "Ayya sorry, to ka sha magani mana" "No ba yanzu ba, bari na gani zuwa dare idan banji dai-dai ba zan yiwa kaina allura ko kuma ka min" "Ok, Allah yakara sauki" "Amin" Nawaz ya fada yana lumshe ido, wayar Al'mazeen ne ya sake ƙara, Nawaz ya bude ido yana jan dogon tsaki "Mtswwwwww!!! Wannan mayyar ce ko!?" "Meyasa kake ce mata mayya bayan kasan ita zan aura?" "Wlh Allah ya sawwake maka da aurar wannan kakar taka, duk da nasan bana son yarinya karama amma ina zaka kai Alisha? ni fa wlh na rasa meke damunka, duk matan duniya ka rasa wacce zaka zab'a ka aura sai Alisha? Ga uban saka gashin doki a kai, ga ƙarin farce, ga saka gashin ido, ga rashin kunyar taunar cingam, gabakidayanta ma wlh zube take da karuwai! Dan Allah ka bar batun auren Alisha!" "Haba dan Allah Nawaz ya isheka haka mana! Kai kullum baka da aiki sai kushe Alisha? A tsammaninka dadi nakeji idan kana kusheta? Shuru fa kawai nake yi" Al'mazeen ya faɗa ransa a haɗe, Nawaz ya yi tsaki ya ce "Aikin banza! Abunda kai ma ba sonta kake yi ba, dan an kusheta miye naka na jin haushi,wlh da ace kana son Alisha yadda nake kusheta da mun jima da rabuwa da kai" girgiza kai Al'mazeen ya yi ya ce "Mace ba zata rabamu da kai ba Nawaz, idan na rabu da kai waye zai dinga supporting dina? Plss karka kara fadin haka, abunda yasa nake son auren Alisha ita tana sona sosai,kuma ina sa ran zata bani kulawar da na rasa da soyayyar da ban samu ba" ya karasa fadin idonsa na canza kala,ganin haka yasa Nawaz matsowa kusa da shi ya zauna a hannu kujera ya riƙo kafadarsa yace "Karka fadi haka, In sha Allah Aminina ya kusa fara dariya, ka tsaya kuma ka gani,mahakurci mawadaci, na fadi dai-dai?" Nawaz ya fada yana murmushi tare da miƙawa Al'mazeen hannu, shima Almazeen murmushin ya yi yana haɗa hannunsa da na Nawaz sannan suka rungume juna. Yau wuni zunbur Aziza ta yi a daki ta ki fitowa, bayan sallar isha'i gabadaya suna zaune a parlour suna hira, Aziza kuma na daki tana rike da book amma a zahiri ba karatun take yi ba,tunani takeyi na yadda idan mom ta gayawa Nawaz cewa ita macijiya ce ya zai dauki lamarin, tayi nisa sosai a tunani taji an turo kofar da sallama, amsawa tayi tana ɗaga idonta ta sauke a kan Mom, Mom ta ce "Lafiya kuwa yau kika wuni a daki Aziza? Ko wani abu na damunki shine kika kasa gaya min?" murmushin yaƙe Aziza ta yi ta ce "A'a Mom, yau din ne dai nake ɗan jin zazzabi amma ba sosai bane" "Subhanallahi! Ai saiki faɗi ba wai ki zauna shuru a daki ba, gamu da likitoci har biyu a gida, bari nayi wa Nawaz magana ya zo ya dubaki, ko allura ya miki" zare ido Aziza ta yi sai kuma ta koma ta hau narai-narai da fuska, Mom ta ce "Ai ba zaki zauna da ciwo ba" Mom ta fita tana ambatar sunan Nawaz, wanda suke lissafin bikin sultana shi da Almazeen "Na'am Mom" Nawaz ya amsa yana maida hankalinsa ga mom "Nawaz dan Allah zo ka duba Aziza kayi mata allura, ashe bata jin dadi ne shiyasa ta wuni yau a daki" Sultana ta ce "Ya Salam! Aziza akwai zurfin ciki wlh,nan fa dazu babu kalar tambayarta da banyi ba amma tace min babu komai, dan Allah Bro Nawaz muje ka dubata" "To ba ga Al'Mazeen ba" Nawaz ya fada yana shagwabe fuska yana kallon Mom, mom ta ce "E ai naga Al'mazeen din nace kai kaje ka dubata, idan kuma ba zaka dubata ba sai ka gaya min na cewa Son yaje ya duba min ita" Nawaz ya miƙe yana fadin "Yaushe na isa, yi hakuri Mom luv ɗina, yanzu kuwa zan dubata, Sultana je ki dauko min box ɗina" Sultana ta amsa da to ta fice da gudu, shi kuma ya yi hanyar dakin,yana zuwa ya tura kofar ya sameta kwance ta zubar da gashinta a kan pillow, a ransa ya ce "Wai idan wannan gashinta ne ma sha Allah" sai da ya yi gyaran murya kafin ya yi sallama, da sauri Aziza ta mike tana jan hularta dan ta rufe kanta, tana saka hular wanda bai rufe mata gashi ba sauran ya kwanta a kafaɗunta, ta dukar da kai jikinta na rawa, kallonta Nawaz ke yi yana yaba kyawunta a zuciyarsa sai furta ma sha Allah yake yi, har Sultana ta shigo dakin tana masa magana amma bai ji ba, sai da ta tabosa kafin ya juyo, dariya Sultana ta hau maqalewa tana miƙa masa box din, ganin haka ya dalla mata harara ba shiri ta hadiye dariyarta, murya can ciki yace "Me kike ji a jikinki?" Murya na rawa Aziza ta ce "Amm.....uhum......zazzabi ne sama-sama" "Kinci abinci?" "E naci" "Tun yaushe?" "Tun karfe biyu" "Na rana?" "E" "Baki da hankali ne! Taya zaki zauna da yunwa bayan baki da lafiya! Ko baki san shima wani babban ciwon bane! Sultana je ki kawo mata abinci yanzun nan taci a gabana, na duba na gani allura zan mata ko magani zan bata" jin ya kira sunan allura yasa Aziza ta ɗago, nan hawaye suka b'alle kamar an buɗe pampo, cikin fuskar tausayi ta ce "Dan Allah Hamma Nawaz zan sha magani amma banda allura,bana son allura" ta hau masa magiya tana kallonsa amma shi idonsa a kwayar idonta yake yana kalla bugun zuciyarsa yana kara tsananta, da kyar ya dauke idonsa a kanta ya juya baya, sultana ce ta shigo da plate da abinci da ruwa ta mikawa Aziza dake kuka wiwi, Nawaz ya ce "Na fa tsani kuka, kici abincin nan idan baki son allura,bana son shirme, idan kuma baki ci ba alluran zan miki" jin haka yasa Aziza fara ɗurawa cikinta abinci, sai da taci rabi ta kalli Sultana da tayi shuru kamar bata wajen, ta ce "Anty sulty na koshi, Hamma Nawaz bani maganin" kallon Sultana yayi babu alamun wasa ya ce "Karba plate ɗin ki fita da shi" karba sultana ta yi ta fita,sultana na fita ya hau jan ruwan allura ganin haka yasa Aziza fashewa da kuka tana ba shi hakuri kar ya mata allura, bata so ko kaɗan karfe ya huɗa jikinta kasancewar tana da jikin maciji hakan zai iya mata illa dan karfe ne zai huɗa jikinta,maciji kuma baya son tab'o, ko kaɗan Nawaz bai damu da kukanta ba duk da yanaji har can kasar zuciyarsa, ya rasa meyasa yake jin tausayin yarinyar, bai so ko kaɗan yana mafarkinta a mugun yanayi, bayan ya saita alluran ya nufeta, da sauri Aziza ta miƙe ta diro a gadon ta hau ja da baya, ihu ta saka zata gudu yasa hannu ya jata, Mom da Sultana da Almazeen da suke parlour suka jiyo ihun Aziza da sauri suka tashi suka yo dakin da gudu, suna shigowa suka samu Aziza da Nawaz sai zagaye daki suke yi, Mom tace "Miye haka me zan gani?" ganin Mom yasa Aziza rugawa da gudu ta buya bayan mom, tsaki Nawaz yayi yasa hannu ya jata a bayan Mom yana fadin "Mom ai kinga irinta, bana son hidiman yarinta wlh,allura fa zan mata amma kalli yadda ta sakani zagaye daki sai kace wacce zan zare ranta!" "Haba Nawaz! Miye haka sai kace ba likita ba, ka lallabata mana ka bita a hankali, Aziza ki tsaya kinji? idan ya miki zakiji sauki, kinga yau kin wuni a daki ga jikinki da zafi, bana son ina ganinki a haka kinji?" girgiza kai Aziza ke yi tana fadin "Mom zai min illa!" "To dan Allah fa kiji mom, wai zai mata illa, taya allura zai miki illa ana shirin nema miki lafiya" yana faɗi ya haɗata da jikinsa ya matseta,a karfinta na nml mutane ta kasa kwace kanta, sadakarwa tayi, jin ya matseta ya danna mata allura yasa ta ƙanƙameshi tana kara sa kuka, allura biyu ya mata kafin ya saketa ya fita a dakin, Al'mazeen wanda ya ƙura mata ido yana kallonta ya fita ya bar su Mom da sultana suna rarrashinta, cikin kuka ta ce "Mom allura karfe ne,kuma jikina na maciji ne, zai min illa" a tare mom da sultana suka zaro ido,mom tace "Aziza meyasa baki gaya mana da wuri ba? Subhanallah! Yanzu me zai faru?" girgiza kai Aziza tayi jiri na dibarta ta zube a jikin mom abun tausayi, hawaye Mom ta goge tace "Ya Allah, kasa abunda yake zuciyata wanda nake shirin haɗawa ya zama alkairi, Allah kasa ya zama jahadi dani da iyalaina, ya zama silar shiganmu aljanna!" "Me kike shirin yi Mom?" "Inaso na saka Yayanki Ya Auri Aziza!" jinjina kai Sultana tayi ta ce "Mom nima na jima da fara wannan tunanin, dan babu wanda zai auresu yayi wannan jahadin idan ba wani ikon Allah ba,mom ya kamata ki gayawa Yaya tun daga yanzu, sannan dan Allah mom a daga bikina zuwa shekara mai zuwa" wani harara mom ta gallawa Sultana sannan tace "To je ki gayawa Nawaz" shuru Sultana tayi dan ko giyar wake take sha ba zata gayawa Yayanta Nawaz a daga bikin ba, yanzu sai ya daki banza. Aziza zazzabi da kaɗan-kaɗan ya fara rufeta, ga shi abunda take so babu shi a cikin gari, furen huriri shine zata jiƙa ko ta tauna ganyensa shi kadai ne zai dawo da ita hayyacinta,amma ina zata samu?" haka ta dinga b'ari. @@@@@@@ A daren yadda Aziza bata rintsa ba,haka ma Nawaz, wanda da ya rufe ido ita yake gani sadda take kuka tana cewa kar ya mata allura, tausayinta ne ya rufe masa zuciya, tashi ya yi ya kalli Almazeen dake bacci, parlor ya fito ya zauna ya riƙe kansa, ji yake kamar yasa kuka, ko yaje ya ganta ko zaiji sauki a ransa, abunda ya shafe wata uku yanaji a ransa bayaso ya tabbata, baya so zuciyarsa ace ta kamu da son wannan jaririyar yarinyar, sannan meyasa yake mafarkinta tun daga ranar da ta shigo rayuwarsa, meyasa yake ganinta a siffar macijiya? Saurin tashi tsaye ya yi, tare da naushin iska, a fili yace "Kamata ya yi ace na tsaneki, dan kin takurawa rayuwata da yawa! Tsawon dare bana bacci duk sabida dake! Why! Why! Why Azizaaa!!" ya faɗa yana rike kansa da yakeji kamar zai rabe gida biyu, anan ya zauna har asuba, bayan Almazeen ya farka ya shiga bathroom yayi alwala ya fito parlor nan ya ga Nawaz yashe a parlor, kallonsa ya yi ba tare da ya yi magana ba yace "Nawaz kayi alwala kazo muje sallah" Almazeen na fadi ya fice, shima Nawaz din alwala ya yi ya bi bayan almazeen bayan sun dawo daga masallaci, Al'mazeen ya hau shiri, yana shiri yana tambayar meke damun Nawaz, Nawaz yace masa ba komai, bai takura ba ya kammala shirinsa, takwas ya shiga ya yiwa mom sallama, mom tace dan Allah kafin ya wuce ya shiga ya duba Aziza ya bata magani dan jiya bata rintsa ba jikin ya yi tsanani,da to Al'mazeen ya amsa. Aziza kwance sai b'ari takeyi jikinta mugun zafi, hannunta Almazeen ya kama ya ga wani zobe a hannunta a ƙaramin yatsarta na karshe, bai damu ba, ya gama dubata ya ajiye mata magunguna sannan yamusu sallama ya tafi. Har wajen mota Nawaz ya raka amininsa tare fadin sai sunyi waya Allah ya tsare, sai da Al'mazeen suka fice kafin Nawaz ya shiga ya gaida mom idonsa a kumbure shima dan baiyi bacci ba ga kansa dake ciwo,cikin kulawa mom ta ce "Nawaz lafiya kuwa?" "Mom kaina ke ciwo jiya banyi bacci ba" "Subhanallah! Sannu Allah ya baka lafiya, ka sha magani ka kwanta" "To Mom" ya faɗa yana tashi, yana so ya tambayeta Aziza amma yakasa,dan haka ya koma part dinsa ya sha magani ya kwanta. bayan ya fice wayar Mom ya dauki ruri, tana dubawa ta ga malamin da tasa ya mata istihara a kan Nawaz da Aziza, da sauri ta daga suka gaisa cikin girmamawa,nan ya shaida mata akwai alkairi mai girma da yardan Allah tsakanin Nawaz da Aziza, shi gwargwadon abunda ya gani kenan, godiya sosai mom ta masa nan ta kara jin karfin guiwa. Dakin Aziza taje ta samu jikin nata ya kara tsanani, sultana idonta ya zazzago tsananin tashin hankali, Sultana tace "Mom a gayawa Yaya ko akwai maganin da zai bata, kar ta mutu" "Sultana shima baya da lafiya idonsa a kumbure da kyar yake budewa shiyasa ban gaya masa na Azizan ba,mu bari nasa ya sauka tukunna" Sultana ta ce "Mom,anya kaddaran Yaya ba a haɗe yake da na Aziza ba kuwa?" shuru Mom tayi, sai zuwa can tace "Allah ka bayyana mana Azima cikin sauki Ya Allah, Allah ka jinkirtawa wannan baiwa taka Aziza,duk da tana karama da kananun shekaru amma tana da hakuri da tawakkali da juriya" hawaye Sultana ta goge ta fice a dakin, khalil ta kira a waya tana kuka tana roƙonsa a kan a daga bikin nan kar ayi nan da wata daya, dalili ya fara tambayarta amma ta kasa gaya masa,inda a karshe ya katse wayarsa dan ya kasa gane me Sultana take nufi ko dai ta daina sonsa ne?. 🐍🐍🐍🐍 Yau fa Azima murna tun daga baka har kunne, Al'mazeen na hanya, bayan su Hadiza sun gama shirya masa abinci ita kuma ta gyara masa part dinsa tas, ta zo shiga cikin kitchen ta hangi Maman Hanan akan abincin Al'mazeen tana barbaɗa masa magani, girgiza kai Azima tayi, ta bar wajan ba tare da maman hanan ta ganta ba,amma tayi alkawari ba zata bari al'mazeen yaci abincin nan ba. Goma da rabi motar Al'mazeen ta yi parking a harabar parker motoci, ya jima a motar yana sauke ajiyar zuciya kafin ya fito, nan ma aikatan gidan suka hau masa sannu da dawowa tare da gaya masa sunyi kewarsa, cikin parlour ya wuce nan Maman Hanan da Maman Beenah suka hau murna suna masa oyoyo, a hankali ya russuna ya basu girmansu ya gaishesu sannan ya fara haurawa samansa, Maman Hanan ta ce "Fuskar mutum kamar fura a dame kullum, Hadiza! Zo ku kai masa abincinsa sama" "Ba zai ci wannan abincin ba, wani zan dafa masa!" saurin juyowa Maman Hanan da Maman Beenah sukayi suna kallon Azima da kanta ke duƙe da lullubi, cak Al'mazeen da zai hau sama yaja ya tsaya jin kamar ya san mai irin muryar, Maman Hanan ta ce "Sabida me ba zai ci ba?" "Sabida bana da bukatar yaci, a bai wa wasu su ci,ko a ajiyewa su Hanif su ci idan sun dawo!" a daqile Azima ke magana, da sauri Al'mazeen ya dawo da baya,nan kuwa ya ganta sanye da bakin abaya itama fuska a lullube, yatsar hannunta ya kalla ya ce "AZIZAAAA!?" a mamakin ce. 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=5️⃣9️⃣↪️6️⃣0️⃣ "To yanzu miye mafita? Wani sharrin satan zamuyi mata?" cewar Maman Hanan, Maman Beenah ta ce "Yanzu ke Maman Hanan idan kikace ta sace miki abu za ace dan ta murɗewa Hanan hannu ne, Al'mazeen ba zai yarda ba, tunda su Sady suna hanya mu jira isowarsa kafin mu yanke shawara" Hanan dake kuka ta ɗago tana kallon hannunta da shati ya fito raɗa-raɗa ta share hawaye tana fadin "Wlh sai na koya mata hankali, zata gane shayi ruwa ne,ita har ta isa! Wacece ita! Waye ubanta! Tana 'yar aiki!" "Bar ta ubanta zamu ci dan naga abun nata ya fara wuce gona da iri" Beenah ta ce "Hummm! Ku ga sadda tazo gidan nan ba ruwanta, amma daga dawowar Al'mazeen sai wani falli take ji da shi, ga shi kullum tana part ɗinsa da yana nan da baya nan, anya kuwa babu wani abunda yake gudana a tsakaninsu?" "Ai dama ba banza ba! kinga dai yadda Al'mazeen ke shakkarmu..." "A'a fa Maman Hanan ba dai shakkarmu ba,yana dai kyalemu kasancewarsa mai biyayya yana shanye duk baƙinciki da takaicin da muke ƙunsa masa" Maman Beenah ta katsewa Maman Hanan hanzari ta hanyar faɗin haka. "To ai ga shi yanzu wannan 'yar banzar mai aikin tana shirin hanamu rawar gaban hantsi 'yan kuɗaɗen da muke karba a wajansa wannan shegiya 'yar banzan tayi ƙyam-ƙyam" Maman beenah zata kuma yin magana suka jiyo sallamarsu Sumy da Sady da karfi sai kace zasu tada gidan, kafin su Maman Hanan su sauko Azima ce ta fara sauƙowa ta fito part din Al'mazeen hannunta dauke da kaskon turaren wuta da alama saka masa tayi, wani kallo Sumy da Sady suka bi Azima da shi har ta gama saukowa tayi hanyar waje ta kofar baya ba tare da tasan Allah ya yi wasu halittu a wajan ba, Sumy ta ce "Tooo! Ina aka samu balarabiya ko ba india?" yatsine fuska Sady tayi ta ce "Oho" saukowarsu Maman Hanan ne ya katsewa su Sumy maganar da sukeyi, nan aka hau musu sannu da zuwa, sai amsawa sukeyi a gadarance,Sumy ce mai gajan hakuri ta ce "Anty (maman Hanan kenan) wacece wata 'yar dogowar yarinya fara ,tasa riga da wando da wani baƙin glass sai kace ba india?" Maman Hanan tayi tsaki tana bin Sumy da Sady da kallo ta ce "Yoo ai ita ce wacce muke gaya muku Azima" "Kan Uba! To ma uwarwa ta yiwa wannan shigan a gida tana mai aiki uban wa ya bata wannan damar!?" cewar Sumy, Hanan ta share hawayen da suka gaza tsayuwa dan ji take kamar hannunta zai fita ta ce "Ba dai yanzu ku ka iso ba? To tunda Al'mazeen ya dawo take ji da iskanci iri da kala" "son Al'mazeen din take yi ne?" cewar Sady tana tabe baki, Beenah tace "Kar dai har kin fara kishinsa?" "Wa? Ni? Allah ya kyauta! Al'mazeen baya raina sam, dan haduwa ya hadu amma ni zan auresa ne dan kudinsa kamar yadda ku ka ce Anty,zamu auresa ne sabida kuɗinsa da mun kwasheshi sai ya sakemu" "Kai kuyi magana a hankali a ƙasa fa muke, kuma wannan shegiyar tana nan, to ma yanzu kin san me ya faru?" cewar Maman Hanan, nan ta basu labarin tsiyar da Azima ke yi a gidan, ta kara da murɗewa Hanan Hannu da Aziman tayi da safe sadda Al'mazeen zaije aiki, har Hanan na nuna musu hannunta da ya kumbura, haɗa baki Sumy da Sady sukayi suna fadin zasu ci Uban Azima, suna kan meeting din yadda zasu korata a satin nan sai gata ta shigo tana shirin sake wucewa kamar dazu Sumy da ta hangeta tun farkon buɗe kofa ta ce "Keee ƙidahumar jeji jikar shanuka! Zo nan" wani birki Azima taci ta tsaya cak ba tare da ta dawo ba, Sady ta ce "Dake ake ballagaza!" cije baki Azima tayi idonta na sake rinewa, rintse ido tayi ta hadiye takaicinta sannan ta dawo da baya ta tako tazo gabansu ta tsaya, Sumy ta ce "Keee! Cire wannan bakin glass din idon naki!" "Ke a wa fa!? idan naki cirewa wata uwar zakiyi!?" Azima ta faɗa tana tinkaro Sumy, ja da baya sumy tayi, ganin haka yasa Maman Beenah faɗin "Kee Azima! ba kya ganin baki ne? Ki dau kayansu ki haura musu da shi sama a wannan dakin da Hadiza ta gyara dazun nan" "Su ɗin kutare ne? ko basu da hannun dauka ne? idan sun ga dama su da kayan nasu su kwana a nan" Azima na gama faɗi ta juya tana taku jikinta na langwasa harta taka step daya ta juyo ta kalli Sumy ta ce "Kee kuma! karki kuma kuskuren fadin cewa na cire wannan madubin, dan kuwa kallo daya ake yiwa idanuna! idan kika kallesa baki kara kallon komai a rayuwarki!" Azima na fadi ta hau sama fuuuu! Aka bar su Maman Hanan a daskare. "Ahaf kun gani da idonku ko?" cewar Maman Beenah, Sumy ta ce "Na san yadda zanyi da shegiya bari Al'mazeen din ya dawo" ta fadi tana hawa sama, Beenah ta kira su Hadiza suka dauki kayan su Sumy suka haura musu da shi tunda Hajiya Azima Banju tace bata hawa da shi. @@@@@ Yau kasancewar ya wuni a office yana tunanin Azima yasa bai yi wani aikin komai ba, ga shi yana son magana da ita kuma ba hali tunda ba waya ne a hannunta ba,kuma tin daga ranar da ya dawo ya fahimci babu jituwa a tsakaninta da mutanen gidan balle yace zai kira alfarma su ba shi Azima yayi magana da ita, shawaran da ya yanke shine idan ya tashi a office ya biya ya siya mata waya sai ya koya mata yadda zata dinga amfani da shi. Bai fara aiki da wuri ba sai wajan hudu ya fara duba marasa lafiya shiyasa yau bai tashi da wuri ba sai wajan takwas da rabi, bayan ya tashi sai da ya biya ya siyawa Azima waya tukunna ya nufi gida. A lokacin Azima na parlour hankalinta tashe tana ta aikin safa da marwa sabida ganin yau Al'mazeen bai dawo da wuri ba, tana cikin wannan zullumi ya yi sallama ya shigo, wani ajiyar zuciya ta sauke wanda bata san lokacin da ya fita ba, da sauri ta karasa gabansa tana tura baki ya ce "Yi hakuri 'yar fullo" "To yau ina ka tsaya kasa duk na damu! Nifa tinda nake a rayuwata ban taba damuwa da damuwar kowa ba sai a kanka na rasa dalili! Ban taba sanin miye tunani ko damuwa ba sai a kanka, abunda na sani a rayiwa shine daukar fansa!" "Fansa kuma!? To kiyi hakuri yau aiki ne ya min yawa a office,nima wuni nayi ina tunaninki kuma babu ta yadda zanyi magana dake shiyasa na siya miki waya da zan dawo, zancan kuma nuna damuwa a kaina ba mamaki ni ɗin na musamman ne!" gaban Azima ne ya faɗi amma da shike tana zumudin waya yasa bata bada hankalinta a kan fadin da ya yi cewa shi ɗin na musamman bane. Wayar ya nuna mata amma yace ba zai bata ba har sai ya mata chajinsa, jakar hannunsa ta karba, ya yi gaba tana binsa a baya idonta kyam a kansa,gani take kamar akwai wani mugun haske dake fita ta ƙeyarsa tare da wani farin mutum na mata kwala "MAGAJI BAWA!" ta faɗa tana shirin kaiwa keyar Al'mazeen duka, juyowar da yayi ne yasa tayi saurin maida hannunta, ya ce "Mene? Waye kuma Magaji Bawa?" haɗe rai Azima tayi ta ce. "Tsohon abokin gabana ne" "Abokin gaba kuma?" Al'mazeen ya faɗa cike da mamaki. "Karka fiye tambaya" ta fada tana wucewa gabansa ta rigasa hawa, duk abunda sukeyi a kan idonsu Sumy:Sady:Maman Hanan:Maman Beenah:Hanan: Sumy tace "Muje kasa ku ga yadda zan tsara wasan nayi cilli da shegiya wajen gate a daren nan" suka sauko a tare, suna saukowa, Sumy ta ware murya tana kwalawa Azima kira sai kace gidan ke ci da wuta, a lokacin Azima na tsaye a kan Al'mazeen dake jona mata wayarta a chaji, jin kira kuma Al'mazeen ya gane murya ya ce "Sumayya? Sun zo ne? To meyasa take kiran Azima haka?" Azima wacce zuciyarta ya tunbatsa jin yadda ake kiran sunanta abun ya bata haushi, a tare suka sauko da Al'mazeen,ya kalli Sumy ya ce "Sumy, Sady, yaushe ku ka zo? Sannan meya faru kike kiran Azima haka?" "E mana,mun zo dazu, da muka zo na ba wa Azima kayana ta haura min da shi sama, na zo da sarƙata ta gwal amma yanzu na duba ban gani ba, da na shiga dakin kuma na ga Azima a jikin kayana ta bude min akwati har nake tambayarta me take yi sai ce min tayi babu komai nayi hakuri, ka dai ni ba saninta nayi ba banda yau" Maman Beenah ta ce "Anjima ana yi mana dauki ɗaɗdai, amma dai bamu taba zarginta ba, kasancewar mun yarda da ita" "Haka ne kam, nima na nemi sarkata wanda ka siya min ɗin nan ban gani ba" cewar Hanan. Al'mazeen a rayiwarsa ya tsani mai halin b'era dan haka ya ɗago ido yana kallon Azima wacce jikinta ke rawa idonta sun ƙanƙace sun kara rinewa, harta hannunta ya fara sab'ulewa yana zama blue, cikin wani irin murya Al'mazeen ya ce "Azima da gaske ne? Kin dauka mata sarƙa?" Wani ihu da gurnani Azima tayi tasa hannu ɗaya ta damƙi wuyar Sumy, nan Sumy ta hau jijjiga kai jin an shaƙe mata magudanar numfashi, cikin daga murya Azima ta ce "Faɗi gaskiya ko yanzu ki jiki a kabari! Kikace na sace miki sarƙa! Nayi miki kama da b'arauniya! Da ku ka sakani daukar kayanku na dauka!?" duk maganar da Azima take yi tana rike da makogoron Sumy wacce ke mutsil-mutsil idonta har ya fara zazzagowa, su Maman Hanan sai dambe sukeyi da hannun Azima a kan ta saki wuyar Sumy amma sun kasa koda motsi ne da hannun Azima, harta Al'mazeen ya kasa b'anb'are Azima daga cikin Sumy, cikin in-ina da shaƙewa gami da fitar hayyaci Sumy murya irinta wa inda suka sha azaba ko suke sha ta ce "Wallahiii.....karya......na.....ke...yi...." 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *JUMMA'@T MUBARAK*🕋 *PAID.* 🅿️=6️⃣1️⃣↪️6️⃣2️⃣ Sakin wuyarta Azima tayi tana huci,tana sakinta Sumy ta zube kasa a sume, cikin tashin hankali suka ɗagota,Beenah wacce saukowarta kenan daga sama dan dama bata nan akayi wannan show din, Mamanta tace "Beenah! Hanzarta dauko ruwa a fridge" ganin Sumy a baje yasa beenah kwasa da gudu taje kitchen ta dauko ruwa aka yayyafawa Sumy, da karfi ta fizgi numfashi, ganin ta saki ajiyar zuciya yasa Al'mazeen ya fizgi Azima ya wanka mata mari, wani gurnani Azima tayi tasa hannu zata shaƙi wuyar Al'mazeen da hannu biyu amma tamkar an daskarar mata da hannu ne ta kasa, cike da mugun zuciya da mugun jin haushin kanta ta yi hanyar waje, ganin haka yasa Al'mazeen dafe kai yana ambatar sunanta amma kamar ba da ita yake yi ba. Gate ta nufa da niyyar barin gidan, dan ta ga Alkadarinta yana gaff da karyewa, kamata ya yi ace ta kashe sumy dan ita duk wanda ya tabata hukuncinsa kisa ne! haka ma Hamma Mazeen da ya mareta, amma ta kasa aiwatar da komai,to me hakan ke nufi? ai gwara ta bar gidan kafin abunda take rayuwa da shi shekara shabiyar zuwa sha shidda a rabata da shi. Al'mazeen ne ya biyota yana kiranta amma kamar ba da ita yakeyi ba dan ta zuciya, karamin kofar gate tasa kafa tayi kwallo da shi,ga mamakin mai gadi sai ganin kofa ya yi a kasa da sauri ya tashi ya matsa ya bata waje, tana sa kafarta a waje da niyyar fita kamar wanda wutar lantarki ta kama haka taji a jikinta, ji tayi kamar an ja kafarta akayi sama da ita sannan aka wurgota cikin gidan, sai da ta yi sama tukunna ta faɗa kan wani dutse kanta ya bugu, zare ido Al'mazeen ya yi yana fadin "Azimaaaa!" da sauri ya yi kanta yasa hannu ya dagota, harta baƙin tabarau dinta sai da ya fadi, a lokacin da Al'mazeen ya matso gareta ta rufe ido jin yadda wani mashahurin jiri dake kwasarta dan kanta ya buge sosai, cikin tashin hankali Al'mazeen ke fadin "Subhanallahi! Azima! Azima! Azima! Dan Allah kiyi hakuri ba da nufi bane,meya sameki?" jinta shuru ba motsi yasa ya dauketa cak ya koma da ita ciki, yana shiga har yanzu ana tsaye a kan sumy wacce bata gama farfaɗowa ta dawo hayyacinta ba. Ganinsa sukayi ya shigo da Azima a hannun sai kace baby yana shirin sa kai ya haura sama,cikin masifa Maman Hanan ta ce "Kai Al'mazeen! Wannan wani irin rashin hankali ne! Ya zaka dauko yar aiki haka a hannunka sai kace matarka!? A gabanka fa ta shaƙe Sumayya tana shirin kasheta amma baka dakatar da ita ba, zata bar gidan ka je ka dawo da ita, ga Sumayya nan dake bukatar taimako amma baka kalleta ba ka wani dauko wannan ƙidahumar jejin matarka ce ko aurenta zakayi! bayan kasan kuma su Sumayya da Sadiyya sune matan da zaka aura ko? ko dai akwai wani abu a tsakaninka da wannan daukar kaddaran ne?" (wai Azima ce daukar kaddara) rai a haɗe Al'mazeen ya juyo ya ce "To auranta zanyi! Ta fiye min su Sumayya da Sadiyya sau dubu! Ina sumayyan ce ta jagaleta? Ita ma Azima ta suma,ku kai sumayyar sama bari na duba Azima tukunna,zan zo na duba Sumayyan daga baya" yana gama fadi ya hau sama ya bar su shanye da baki. A gadonsa ya kwantar da ita yana dubata, gefen kanta ya gani ya ɗan fashe, hannu yasa da niyyar yi mata treatment ji ya yi ta riƙe hannunsa, kallonta ya yi ya ga har yanzu idonta a rintse yake, a hankali ta miƙe ba tare da ta kallesa ba tasa kai zata fita yayi saurin shan gabanta, "Azima yi hakuri! Ki fahimceni ba da nufi na mareki ba, laifinki ne inata miki magana ki saketa amma kin ƙi ki saurareni, taya zaki shaƙeta haka idan ta mutu me kike tunani zai faru? Ba ke kaɗai ba harta ni sai an kulleni dan anyi kisan kai a gidana! da kin kasheta sunanki fa zai koma criminal ne, kuma ba zan so hakan ta faru ba amma kiyi hakuri kinji? karki yi fushi" ya faɗa yana haɗe hannuwansa alamun roƙo,Azima kuwa juya kanta tayi gefe har yanzu taki yarda ta buɗe, yana gama magiyarsa ta rab'a ta gefensa ta fice, riƙe kai Al'mazeen ya yi yana jan ajiyar zuciya,box dinsa ya dauka ya fito yayi side din su Hanan, ya nufi dakin baki wanda su Sumayya suke zama idan suka zo, da sallama ya shiga har zuwa yanzu suna tsaye a kan Sumy, rai a haɗe fuskarsa ba annuri ya shiga, allurai ya yiwa Sumy sannan ya ɗora mata ruwa, nan da nan bacci ya kwasheta, kwashe box dinsa ya yi zai fita Maman Beenah ta ce "Al'mazeen? Amma ina fatan batun auren yarinyar nan kawai ka faɗa ne ba da gaske kakeyi ba?" Cak Al'mazeen ya tsaya ya juyo ya ce "Da gaske nakeyi! Zan aureta! taya zan auri Sumayya? daga zuwanta yau ta bi Azima da sharri! Laifi biyu wanda na tsana a rayuwata! tayiwa Azima ƙarya da ƙazafin abunda bata yi ba,ƙazafin ma kuma na sata!" yana gama fadi ya fice, aka barsu da zare idanu. Part dinsa ya koma, yana tajin babu dadi na ganin Azima tayi fushi, shirin bacci ya yi ya kwanta dan yana tashi sallar dare. @@@@@ Da washe gari kamar yadda Azima ta saba haka ta shigo ta kawo masa abinci amma bayan sallama ko gaishesa taƙiyi, shi kuwa kallonta yakeyi yadda ta duƙar da kai fuska babu rahma ranta a haɗe, ganin har zai fita bata yi masa magana ba ya saka shi fadin "Ba ki huce bane? na fa baki hakuri, ba zaki min magana ba? to ga wayarki, kalli ki ga yadda zakiyi amfani da shi" turo baki tayi tana fadin "Bana so" sannan ta fice, Al'mazeen ya sosa kai ya ce "Tab lallai abun babba ne, duk yadda jiya ta nuna murna da farincikinta akan wayar yanzu kuma tace bata so?" haka yasa kai ya fice, a office sai tunaninta yakeyi, Azima kuwa wuni tayi fuskarta a murtuke dan abunda ya dameta ya dameta, tunda tazo fita akayi sama-sama da ita sannan aka maidota gidan ta rasa inda zata saka kanta. Wasa-wasa Azima ta dauki zafi dan har aka kwashe sati daya bata magana da Al'mazeen tsakaninta da shi sai dai ta kai masa abinci ta gyara masa daki,duk kulawar da take ba shi bata daina ba magana ce dai bata masa, a sati dayan nan kuwa Al'mazeen ya yarda ya kamu da soyayyar Azima, kullum sai ya bata hakuri amma taƙi ta sauraresa dan ita kadai tasan bakincikin da take ciki. Ta bangaren su Aziza sun fara shirin bikin Sultana wanda zai gudana nan da sati biyu ciff, Aziza daurewa kawai takeyi tana abubuwa, amma bata da wani kuzari da karfin dafi. Ana saura sati daya biki duk hankalin sultana a tashe yake. Al'mazeen ya shaidawa Nawaz a kan cewa idan ana saura kwana uku ɗaurin aure zai zo. Ko da Sultana ta kara yiwa Khalil magana a kan tafiyarsu kano yace ta hakura kawai sun yi magana da Al'mazeen yace zai gaya musu ita ba sai taje ba,sultana ji tayi kamar ta kurma ihu dan bakinciki. @@@@@@@ Fitowa daga daki Aziza tayi zata hau sama da wani jiri ya ɗibeta zata fadi dai-dai lokacin da Nawaz ya sawo kai parlorn amma kafin ya iso ya tarota tuni ta fadi kasa,sunanta ya ambata ya dagota yana jijjigata a hankali yana kiran sunan Mom da sultana, da sauri suka sauko kasa suka samu Aziza kamar ta suma ne yaya ne oho "Nawaz me ya sameta!?" mom ta tambaya hankalinta tashe, Nawaz yace "Wlh mom ban sani ba,ina shigowa ne na ganta tana faɗuwa!" Mom ta ce "A gaskiya Nawaz shawaran Malam Yunusa zamu bi, kawai ranar daurin auren sultana a haɗa a daura da naka da Aziza! mu tausayawa yarinyar nan halin da take ciki! Sai daurewa takeyi tana hadiyar zafin ciwo, a kananun shekarunta tayi ƙanƙanta da jurewa!" mom ta fada tana sakin kuka mai ban tausayi, Nawaz wanda shima idonsa ya canza kala ya ce "Duk yadda kikayi dai-dai ne mom" "Ka dauketa ka kaita daki! Sultana ke kuma ki zauna da ita, bari naje na sanar da cewa auren biyu ne" mom ta fada tana hawa sama, shi kuwa Nawaz ya dauki Aziza ya kwantar da ita a daki sannan ya fice yana neman layin Al'mazeen dan ya shaida masa har da shima za a daurawa aure. A cikin ƙanƙanin lokaci mom tayi sanarwan auren Nawaz da Aziza wanda mutane sun sha mamaki, amma da shike ance ba a mamaki da ikon Allah sai kowa ya bi lamarin da fatan alkairi. Sadda Nawaz ke gayawa Al'mazeen akan cewa zai auri Aziza ba karamin mamaki Al'mazeen ya yi ba, har yaushe Nawaz ya fara soyayya da Aziza da har ta kaisu ga maganar aure nan da sati daya? Sannan Nawaz baya son auren yarinya kamar yadda baya son auren babba sosai ,ya tabbata idan Nawaz ne zai iya cewa Aziza tayi masa yarinta, haka dai ya share maganar yana fadin shima ga shi ya kamu da son Azima,yana so ya ba wa Nawaz labarin Azima amma sai yaji kamar an riƙi bakinsa, dan haka ya share maganar gabadaya yana tambayar Nawaz dame-dame zasu shirya da bikin tunda aure yazo a bazata, nan Nawaz ke gaya masa babu wani abunda za ayi wanda ya wuce daurin aure daga shi shikenan, dan harta sultana tace babu abinda zatayi da an daura aure kawai a kaita,babu yadda khalil baiyi da ita ba ko da walima ayi nan ma tace ta yafe, ya fahimci rigima ce kawai take ji da shi amma da ta shigo hannunsa zai sauke mata shi. @@@@@ Da misalin karfe tara hamma mazeen ya kira Hadiza a waya yace ta kirawo masa Azima, Hadiza ta amsa da to sannan taje kiran Azima wacce yanzu dakinta daban ita daya, a lokacin tana kwance a gado ta zama macijiya, Hadiza kuwa tana zuwa ta sako kai ta tura kofa, wani burki tayi turuss! Ganin abunda ko a mafarki bata taba gani ba, shirgiɗeɗen maciji blue sai sheƙi yakeyi, wani mahaukacin ihu Hadiza ta sake tana zubewa a kasa sumammiya, da sauri Azima ta waigo nan tayi saurin komawa mutum ta yo kan Hadiza. Da gudu su Maman Hanan suka fito har da Al'mazeen wanda ya sauko daga part dinsa, dakin Azima suka nufa inda suka ji ihu ya fito, suna shiga suka samu Hadiza a baje Azima na tsaye a kanta, suna shigowa ta duƙar da kai kasa. "Me kika mata!" cewar Maman Beenah hankali tashe, Sumy wacce ta jima da dawowa dai-dai ta ce "Ba mamaki itama an shaƙeta ne! Duk yadda akayi wannan yarinya ta taba zaman prison" Al'mazeen cikin fushi ya kalli Sumy yace "Ban ce duk wanda yake son kansa da zaman lafiya a gidan nan ba ya daina shiga hidimarta!!?" shuru sukayi ya kalli Azima ya ce "Me kika mata?" "Ban mata komai ba,nima daga kewaye nake naji ihu na fito da sauri sai na ganta a sume,idan kuma baku yarda ba idan ta farfaɗo ku tambayeta" Al'mazeen ya kalli Sady yace "Kawo ruwa a yayyafa mata" "Me?" "Nace kawo ruwa a yayyafa mata!" ya faɗa a tsawance Sady ta fice tana yatsine fuska, ruwan ta kawo aka yayyafawa Hadiza a firgice ta farka da karatun ayatul'kursiyyu a bakinta! Nan aka hau tambayarta menene, cikin fitar hayyaci Hadiza ke fadin maciji! maciji! "Maciji!!" Sumy Sady da Hanan da Beenah suka rungumi juna suna ihu,harta su Maman Hanan da Maman Beenah bayan Al'mazeen suka koma jikinsu na kyarma suna tambayar Hadiza ina macijin, yayinda Azima take kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cikin gashin kanta da ta sauko dashi ya rufe mata fuska, Al'mazeen yace maciji dai a dakin nan?" "E wlh nagani! Katon maciji! Ruwan ganye! Babba ya cike wannan gadon! Na ganshi a kan gadon nan! Wlh na gani! Maciji! Babba maciji!" duk a ruɗe Hadiza ke magana,jin abunda take fadi yasa suka maida maganar ta ta shirme ba mamaki tayi gamo ne,su sumy suka hau tsaki "Hanan je ki kirawo Talatu ta zo ta kai Hadiza daki,kafin nan bari nayi mata alluran bacci" ya fada yana ficewa, su ma su Maman Hanan duk ficewar sukayi. Ba jimawa Al'mazeen ya sauko da allura a hannunsa ya zo ya yiwa Hadiza sannan ya ce Talatu ta kaita daki ta kwantar da ita,bayan sun fita Al'mazeen ya kalli Azima wacce kanta ke duƙe yace "Zan sha shayi, za a iya haɗawa a kawo min?" ya tambayeta yana mai ƙura mata ido, gya ɗa masa kai kawai tayi sannan ya fice ita kuma ta nufi kitchen dan haɗa masa. Bayan su Sumy da Sady sun koma daki Sumy ke fadin "Duk lokacin da na kalli wancan jakar yarinya 'yar fulanin can ji nake kamar na kashe shegiya! har yanzu ban manta da kaini kofar lahira da tayi ba" Sady tace "Mu jawo shegiya yau mu ci ubanta a dakin nan kawai" Sumy ta ce "Haka za ayi" fitowa sukayi nan suka hangi Azima da tray a hannunta tana hawa part din Al'mazeen, Sady tace "Kalli Matsiyaciya, mu jira ta dawo mu ja banza muci uwarta!" nan suka tsaya suna jiran saukowar Azima. Da sallama ta tura kofar parlorn a lokacin Al'mazeen suna waya da Nawaz, tana ajiyewa ta tashi ta juya zata fita da sauri Al'mazeen ya ce "Azima tsaya!" Nawaz ya ce "Azima? Azima kuma? Al'mazeen wace Azima?" 🍃🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=6️⃣3️⃣↪️6️⃣4️⃣ "Amm Nawaz ina zuwa zan kiraka" Al'mazeen na faɗi ya ajiye wayar, da kallo Nawaz ya bi wayarsa da shi yana fadin "Azima irin sunan yar uwar Aziza ce fa? anywhere mutane nawa ne masu suna iri daya" daga wannan tunanin ya ajiye wan can a gefe. "Azima pls ki tsaya ki saurareni! Fushin ya isa haka kiyi hakuri dan Allah! Har tsawon wani lokaci zaki dauka kina fushi dani?" ƙin magana tayi yace "To shikenan idan ba zaki min magana ba, ga wayar ki karba,babban aminina Nawaz zaiyi aure shi da kanwarsa yau saura kwana shidda bikin,ni kuma zan tafi nan da kwana uku kafin nan gobe zanyi kwana biyu a asibiti dan akwai mutum bakwai da zan yiwa aiki, ki karbi wayar dan na dinga jin lafiyarki, sannan idan na dawo jibi ba lallai bane mu samu magana da juna ba, dan ba da wuri zan dawo gida ba, da washe garin kuma da wuri zan kama hanyar kaduna" saurin karban wayar tayi tana fadin "Nima zan bi ka bikin" tashi yayi yana fadin "Ba zaki bini ɗin ba, ba fushi kikeyi dani ba ana neman sati uku baki min magana" "To kayi hakuri na daina fushin amma zan bi ka" "To naji, saiki shirya, mutanen gidan nan ma zasuje, idan kika je ma zaki ga wata mai kama dake" "Mai kama dani kuma!? Ni babu wani mai kama dani a duniya! ni ni daya ce" "To naji amma ki dai shirya da wuri,dan inaso ace karfe shidda da rabi mun bar gidan nan" murna ta hauyi tana tsalle zataje yawo, watakila ma daga can ta samu kafar guduwa ta gudu ta huta da ala'ƙaƙai, sai da safe ta masa zata fice ya dakatar da ita, yace "Kina son makaranta?" tabe baki tayi ta girgiza kai, ƙura mata ido yayi yana hango gaskiyarta yace "Kwanaki na tambayeki kin sauke al'kur'ni kika ce min a'a shima nace zaki ci gaba kince bakiso,ke baki san ilmi shine mutum ba?" Azima a ranta ta ce "Humm! Wani karatu ni da ko sallah bane yi" amma a fili da shike tana murnan barin gidan ya sakata fadin "Idan muka dawo daga kaduna na yarda zanyi makarantar" ta faɗa tana murmushi" "Kinyi alkawari?" "E nayi" ta faɗa tana ficewa. da murnanta ta hau saukowa tana zuwa dai-dai step din tsakiya taji an fisgota an shige daki da ita aka wurgata ta fadi kasa, tana daga kai ta ga su Sumy da Sady ,hade rai Azima tayi tana shirin magana sady tace "Inyeee yar banza miye a hannunki? Kinje ya gama kwalularki sai ya baki me?" ta faɗa tana sa hannu ta fizgi wayar daga hannun Azima, tashi tsaye Azima tayi, sumy tasa hannu ta yaye mata mayafi ta jefar,Azima ta duƙar da kai,maganar Al'mazeen ne ya faɗo mata da yake cewa shi a rayuwarsa baya son rigima, sannan yadda yasa doka su daina shiga tsabgar Azima haka itama Aziman yace ta daina shiga tsabgarsu idan kuma maganar aiki ne to yanzu ma shi zata dinga yimawa tinda dama shike biyan duk ma'aikatan gidan, tunowa da haka ya sakata fadin "Kunga bani shiga hidimarku tunda Hamma Mazeen bai son rigima,ku bani wayata!?" Azima ta faɗa tana cije baki gami da miƙa hannu, Sady ce take ƙurewa dalleliyar wayar kallo tace "Inyeee! waya mai tsada wa yar aiki! yar aikin ma ƙidahuma!? To wlh ba zan bayar ba fasawa zanyi sai dai duk abunda zai faru ya faru" da sauri Azima tace "Karki fara wannan kuskuren dan na....." maganarta ne ya tsaya cak sakamakon rutsa wayar da Sady tayi da bango, saurin zuwa daukar wayar Azima tayi jikinta na b'ari alaman b'acin rai, tana daukar wayar ta ga ya ragargaje, bata gama saita b'acin ranta ba taji an jawo wuyar rigarta, waigowa tayi ta ware blue eye dinta a kan Sady, Sady na ganin ido a rine tayi saurin sakin wuyar Azima taja da baya,ihu Azima ta sa ta haɗa hannuwanta biyu ta ɗagasu sama ta tayar da guguwa ya dauki Sady ta dinga bugata da bango, ihu Sady keyi yayinda Azima ta wurga wani bakin abu a kofar shiga daki wanda duk ihu da kacaniyar da za ayi a dakin babu mai ji, nan ta haɗa da sumy ta dinga cin uwarsu,kuka suke suna bata hakuri tare da gaya mata basu san cewa ita ba mutum bace tayi hakuri, Azima da ta kara yin sama da Sady ta buga mata kai a silin fuskar Sady duk jini ta ce "Shin zaki iya maida min wayata ta koma yadda take? Na sha gaya muku karku tunzurani ku ga asalin wacece ni amma kun kasa fahimta! An gaya muku ko wane yake mutum! Balle kuce zaku takasa son ranku!" cikin kuka Sumy tace "Dan Allah Anty Azima kiyi mana rai! Ni wlh yau din nan bana kwanan gidan nan,gobe da sassafe kuma katsina nayi,wlh har ta auren Hamma Mazeen din ma nikam na yafe" Sady ma mai kwasar baƙar wuya tace itama ta yafe, sakinsu Azima tayi suka zubo a kasa sharab kamar an watso kaya, suna faduwa suka hau tattaren kayansu, a daren suka fice ba tare da kowa ya sani ba sai mai gadi da kuma driver da suka ce masa ya kaisu gidan wata kawarsu, Azima sai da ta gargaɗesu da cewa wlh idan suka sake suka gaya ma wani abunda ya faru sai ta maida Sady kunkuru ta maida Sumy gwaɗo, jin haka yasa sukace bakinsu ƙanin kafarsu. Bayan sun tafi Azima ta dau wayarta ta sa hannu ta shafe kayanta ta koma yadda take kamar ba abunda ya same shi tayi hanyar dakinta ta kwanta tana murmushi tana kallon wayar wajan kusan sha biyu da yan mintoci,bayan ta gama daddannawa ta ajiye ta lumshe ido alaman bacci yazo sai taji wayar na ƙara,dubawa tayi tana hararan wayar, to waye kuma a wannan lokacin? Ta tambayi kanta, dagawa tayi kamar yadda Al'mazeen ya nuna mata tasa a kunne, da masifa ta fara tarban wanda yake kan layi "Dalla waye! A wannan lokacin! Baka iya hakura ka kira gobe ne! Ko baka san yau na karbi wayar bane? Idan Hamma Mazeen ya sani ai sai ya kwace! Idan kuma ya kwace ko ma waye kai Allah ko a ina kake sai na maidaka burgu!" dariyan Al'mazeen taji ta zare ido tace "Hamma Mazeen? Dama kai ne? Bakayi bacci ba? Ina dai ba wani abu kakeso ba?" ajiyar zuciya ya sauke mai karfi ya ce "Na kasa baccin ne shine nace bari na kiraki muyi hira" "Oh to inajinka" hira suka hau yi ko wannensu ya saki baki,Al'mazeen yana son gayawa Azima yana sonta amma sanin ba ko da wani lokaci take saiti ba zata iya tsince masa notinan kai ta damka masa a tafin hannunsa, shiyasa ya yi shuru suka ci gaba da hira har wajan biyun dare, harbi suka ji ya fara tashi a gidan, Al'mazeen yace "Ƙaran miye haka? Subhanallahi! ba dai b'arayi ba! Azima karki fito!" "A'a Hamma mazeen kai karka sauƙo" "Azima nace miki karki......" "Na ce maka ka tsaya ko!" ta faɗa a tsawance tana ajiye wayar ta fito, fitowarta ya yi dai-dai da balla kofar parlor da sukayi suka shigo dik da kofar security door ne, suna shigowa da Azima suka fara karo duk sun rufe fuska suna riƙe da bindigogi, Azima suka cafka suna tambayarta ina mai gidan tace baya nan, ogansu ne ya bada umarni a shiga lungu da saƙo na gidan a fito da duk mutanen gidan har da ma'aikata, nan kuwa aka hau fito da ma'aikata sannan aka sauko dasu Maman Hanan da Beenah da Maman Beenah,Hanan da Hanif duk aka fiddo dasu,bindiga aka ɗorawa Maman Hanan a goshi ana tambayarta ina Al'mazeen kafin Maman Hanan tayi magana Azima ta kuma faɗin baya nan da karfi babu alamun tsoro a tattare da ita, Al'mazeen kuwa yana aikin dambe da kofar dakinsa wanda ya kasa buɗewa, Maman Hanan jin bindiga yasata fadin Ai part din Al'mazeen na saman nasu dan haka yana can sama, nan ogan b'arayin yace su hau su duba,dama wa inda suka hau daga farko basu lura da dayar step din ba, wani ke fadin yau zasu cika aljihunsu da kudi a wannan gidan, Azima tace "Idan baka cika aljihunka da kudi ba,ni na maka alkawari zan cika maka cikinka da gubar dafin maciji!" "Kai wannan yarinya bata da kunya! Waike bakinki baya shuru ne zan fasa kanki da bindiga fa!" cewar wani daga cikin b'arayin, ogansu yace ku kyaleta mun san irinsu ai, bari mu karbi abunda ya kawo mu daga nan mu rabata da baki har abada muyi mata fyaɗe muyi gaba, wani kallo Azima ta musu tana shirin magana taga an fito da Al'mazeen ana jansa, ranta ne ya b'aci ganin yadda suke fizgar shi kamar kaza. Gaban ogan aka kawosa ya dago ido yaga ahalin gidansa a zube a kasa an kewayesu da bindiga Azima kuma ana riƙe da ita. "Dan Allah karku yiwa kowa komai plss" Al'mazeen ya faɗa hankalinsa a tashe Wani dariyar mugunta ogansu ya sake ya ce "Abunda ya kawo mu ba mai tsanani bane Kuɗaɗe kawai zaka bamu sannan mu yiwa wannan yarinyar fyaɗe mu kama gabanmu" zare ido Al'mazeen ya yi jin sunce zasu yiwa Azima fyaɗe hakuri ya hau basu amma da shike zuciyarsu ta riga da ta bushe da rashin imani sukace babu abunda ya damesu, Al'mazeen yace Su fadi kudin da zai fanshi Azima,nan suka masa wani zunzurutun kudi wanda idan ya basu ya kwashe kudin acct dinsa kaff kai har ma da gidan da suke ciki a yanzu, zufa ce ta hau wankewa Al'mazeen jiki yace musu baya da wa innan kuɗaɗen a gida, sannan kudinsa na acct bai kai wannan ba sukace karya yake yi,idan babu kudin a gida to ya musu transfer (kai b'arawo da karfin hali yake wlh). "Ko da yana da shi ba zai bayar ba!" Azima ta faɗa jikinta na rawa sabida bakinciki izuwa yanzu yaci ace kaff ta sare b'ayin nan amma fitowar Al'mazeen ya dakatar mata da komai. "Ai kuwa idan bai bayar ba lahira zatayi baƙo, ke kuma zamu yaga-yaga dake! idan kuma kinci musu ya kuma fadin cewa ba shi da kudin da muka tambaya ya gani, dan ko biyar ba zamu rage ba" shuru Al'mazeen ya yi zuwa can suka ce yana bata musu lokaci akwai gidan da zasuje Almazeen yace "Wlh kudina na acct bai kai haka ba,kuyi hakuri na baku kuɗin duka amma bai kai yadda kuke bukata ba" "Amma lallai ka raina mana hankali, a wannan babban gidan naka zakace baka da kudin da muka tambaya ashe kuwa baka son rayiwarka da ta wannan yarinyar!" "Ku kashesa!" ogan b'arayin ya faɗa, daga Al'mazeen akayi aka saita masa bindiga ganin haka yasa da sauri Azima ta rintse ido hannunta ya kama da wuta ta ciki, saurin saketa wanda suka riketa sukayi sakamakon wani bala'in zafi a tafin hannunsu, rintse ido Al'mazeen yayi yana kalman shahada, ji yayi karan an saki kunnamar bindiga, kafin bullet din ya shigo jikinsa Azima ce ta fara shigewa jikinsa bullet din ya shigeta a baya, saurin buɗe ido Mazeen ya yi ga Azima a jikinsa da Alama bullet din jikinta ya shiga! "Azimaaaaa!!" Mazeen ya faɗi hankalinsa tashe da sauri tasa hannu ta shafi fuskarsa nan ya kafe, sannan ta juya ta watsawa su Maman Hanan wani baƙin hayaki nan suma suka kafe sannan ta juyo tana kwashe gashin fuskarta ta nannaɗe ta waro blue eye dinta, dan idan bata ci ubansu ba hankalinta ba zai kwanta ba,bakinciki zai iya sawa ma ta sari kanta ta mutu. Su kuwa b'arayi tsayuwa kallon bala'i da ikon Allah suka yi, wani gurnani Azima tayi ta juya nan ta zama macijiya. Karyan iskanci nan suka saka ihu, ta ce "Kamar yadda baku da imani haka nima ban da shi, nawa kam har ya fi naku! RUWA BIYU! AZIMA! AZIMA BANJU MACIJIYA! NI MACIJIYA CE!" tana faɗi ta hau binsu da sara, sai da ta saresu kaff sannan ta naɗesu kaff dinsu da jelarta ta sulale ta jasu suka bar gidan, b'acewa tayi ta kaisu jeji ta watsar dasu sannan ta koma gidan, nan ta samu mai gadi a sume an harbesa a kafa shima,bata yi ta kansa ba ta koma ciki ta samu har yanzu suna nan a daskare hannu tasa ta shafe jinin dake wajan tass sannan ta watsawa su Maman Hanan wani bakin hayakin nan ta sakesu, Al'mazeen kuwa kara shigewa jikinsa tayi ta shafo fuskarsa nan shima abun ya sakesa a firgici ya riƙo Azima wacce ke sulalewa a jikinsa yayi saurin haɗeta da kirjinsa yana ambatar sunanta, dago kai yayi bai ga kowa ba yaga wayam To meya samesa sai kace wanda komai na jikinsa ya tsaya na wucin gadi. Su Maman Hanan kuwa masu fitsari a jiki da masu kashi duk sunyi, Hadiza kuwa cewa tayi wlh yau gidansu zata tafi dan daren nan babu abunda ta gani sai bala'i ido da ido, Al'mazeen na daukar Azima suka fito gabadaya nan ya iske mai gadi a kwance shima da harbi a kafa, kwashesu yayi duk ya kaisu asibiti a lokacin da ya fito ana kiran sallan assalatu. Bayan sun isa asibitinsa duk yan gidan aka hau basu taimakon gaggawa shi kuwa ya wuce cikin emergency da Azima, shi da kansa ya hau mata aikin cire mata bullet din da ya shiga bayanta,duk abunda yakeyi tanajinsa sarai har ya gama yi mata komai, allura ya dauko zai mata tayi saurin riƙe hannunsa tana girgiza masa kai, da sauri ya hau kiran sunanta,murya can kasa tace "Hamma karka a yi mini allura zai cutar dani, jikina bana allura bane karka mini dan Allah" hawaye Al'mazeen ya goge yana gya ɗa kai alaman ba zai mata ba, duba agogo ya yi ya ga bakwai dan haka ya wuce masallaci dake cikin asibitin ya yi sallah sannan ya koma ya duba lafiyar kowa ya ga kowa lafiya harta mai gadi an cire masa bullet yana zaune, sai a lokacin yaji ya samu natsuwa ya kira jami'an tsaro ya shaida musu duk abunda ya faru, bayan ya gama musu bayani ya tuno da ashe ya bar wayarsa a gida dan da wayar asibiti ya kira jami'an tsaron kasancewar akwai wa inda ya sani a ciki, wayar wata nurse ya karba ya saka lambar Nawaz ya hau kira, sai da ya masa kira uku kafin nawaz ya daga Al'mazeen ya ce "Dude ni ne" "Kai Dude jiya muna magana kace zaka kirani baka kirani ba ni kuwa nata kiranka baka daga ba,ina fata dai komai lafiya?" "E to da sauki dai" nan Al'mazeen ya ba wa Nawaz labarin abunda ya faru, hankali tashe Nawaz yace gashi nan tahowa Kano, Al'mazeen ya ce "Noo! Wlh karka zo don't worry we are safe now alhamdulillah! and Karka gayawa Mom am sure hankalinta zai tashi but still zan taho jibin In sha Allah dan na saka jami'an tsaro a lamarin,pls karka damu ina lafiya" "Pls take care of urself" daga haka sukayi sallama. Sai wajan karfe hudu kafin suka gama watsatstsakewa sannan suka ɗunguma sukayi gida har lokacin yan sanda suna zagaye da gidan,nan maƙota aka hau yiwa su Al'mazeen jaje ana yin Allah ya kiyaye gaba, nan police suka ba wa Al'mazeen rahoton sun san b'arayin sun jima suna aikata b'arna amma yanzu sun nemesu sun rasa amma zasu ci gaba zurfafa bincike, godiya Mazeen ya musu sannan yace yana da bukatar matakan tsaro a gidansa, nan D.P.O. ya shaida masa babu komai, sannan ya kamo Azima wacce ke zaune a mota ya fito da ita suka shiga ciki, dakinta ya kaita ya kwantar da ita ya kalleta yace "Meyasa kika tare min harbi?" "Nima ban san meyasa nayi hakan ba, amma naji a jikina ba zan iya bari a harbeka ka mutu ba" shuru Mazeen ya yi sannan ya tashi ya fita. Sai dare tukunna su Maman Hanan da Maman beenah suka hau neman su Sumy da Sady, ko da aka kira wayarsu cewa sukayi sun jima a katsina, nan aka basu labarin abunda ya faru Sady tace Ashe da rabon ba zamu ga masifa biyu ba,munga daya kun ga daya,maganar auren Almazeen kuwa sun yafe Allah zai bamu wani kar muzo mu bamuci kudi ba mu mutu a banza sai anjima anty suka kashe wayarsu. Bayan kwana biyu Azima ta warware sai shirin tafiya kaduna akeyi gobe, har yanzu kuma ba a samu wani rahoto ba dangane da b'arayin, su Almazeen zasu tafi gobe shida Azima, su Hajiya Lawiza kuma sai ana gobe daurin aure zasu je. Da washe gari kamar yadda Mazeen ya cewa Azima ta shirya akan lokaci hakan ce kuwa ta kasance karfe takwas suka kama hanyar kaduna, gaban Azima sai bugawa yakeyi. Itama Aziza yau da bugun zuciya ta farka dan bata san da maganar aurenta da Nawaz ba duk wannan hidima sai a daren jiya, tun tara suka tafi gidan gyaran jiki da lalle dan idan basuyi yau ba gobe Sultana tace ba fita zatayi ba,kuma mom tace dole ayi walima a goben tunda jibi ne daurin aure jumma'a kenan. Goma da rabi Al'mazeen suka iso, a lokacin gidan ya fara cika da mutane yan biki, yana shiga ciki ya yi parking din motarsa bugun zuciyar Azima ya tsananta,kallonta ya yi ya ce "Menene?" girgiza masa kai tayi alaman babu komai "To fito" suna fitowa Nawaz shima na fitowa daga part dinsa zai shiga wajan mom ta kirasa ya hangi amininsa, da sauri yazo suka rungumi juna ya kara yi masa jaje, bai ma lura da Azima dake maqale kanta na mugun juyawa ba ga jiri ga zufa, har sun fara tafiya Al'mazeen ya waigo ya ce "Azima?" da sauri Nawaz ya juyo ya kalleta tana sanye da black shadow a idonta, fuskar a bude amma tayi rolling din veil mai rufe rabin fuska,ƙura mata ido Nawaz yayi, ya kalli Al'mazeen yace "Who is she?" "I will tell u later, now let's go inside, Azima muje ko?" jinjina kai tayi tana gaishe da Nawaz ya amsa ba yabo ba fallasa suka shiga, suna shiga aka hau yiwa Nawaz tsiya ango ango aure ba shiri a lokaci guda mun zata sai mun buga mata gangan gauro ashe yanzu kuwa wa Almazeenu zamu buga mawa, cewar tsofaffi, su dai dariya sukayi suna hawa sama Azima na kan binsu a baya, dakin mom suka shiga da sallama mom ta amsa tana yiwa Almazeen oyoyo gaisheta yayi ta amsa cikin kulawa tana fadin "Ka ga ikon Allah ko? Abokinka zaiyi aure ,da ina shirin takura muku ashe Allah ya riga da yayi ikonsa, yanzu ma kai zan takura ma wa, naso ace a tare zakuyi aure wlh!" "Mom ba komai ai,komai lokaci ne nima ranata tana zuwa in sha Allah" "Amma dai ba da wannan Alishan ba ko?" Nawaz ya fada yana hararan Mazeen "To wai ina ruwanka?mom ki masa magana" "E kuma gaskiya ne ina ruwanka kai zaka zauna masa da ita ne" mom ta fada tana daga kai ta kalli Azima dake tsaye a bakin kofa kanta a duke jikinta na rawa "Wacece kuma?" "Amm umm e mom tare muka zo da ita, inasu Sultana?" "Ayya sannu da zuwa ɗiyata" Mom ta fada tana kurawa Azima ido ganin wani sirhitaccen kamanni da takeyi da Aziza, duƙawa har kasa Azima tayi ta ce "Ina kwana mom? Mun sameku lafiya?" hakan da tayi ba karamin dadi Almazeen yaji ba, Mom ji tayi muryan ma irin na Aziza amma sai dai Aziza ta fita sanyin murya sosai, "Alhamdulillah! Ga shi kin zo su Sultana sun tafi gidan lalle da gyaran jiki, amma zo na nuna miki dakin sultana sai ki zauna ki jira su, ko kina so a kaiki gidan lallen kema a miki?" "A'a ban taba yi ba ma a rayuwata, zan jira su ɗin kawai" mom tayi murmushi ta kama hannun Azima caraf idonta ya sauka akan zoben hannun Azima iri daya sak da na Aziza,kuma Aziza tace sadda aka haifesu kakansu Arɗo shi ya ba wa Hajjarsu ta saka mu shi a hannu, daurewa Mom tayi ta ce ya sunanki? "AZIMA!" "Ma sha Allah Azima suna mai dadi, Azima wa?" "AZIMA BANJU!!" ba iyakar Mom ba harta Nawaz wanda yake kokonta sai da ya waigo a firgice, da kyar Mom ta iya riƙe kanta tana murmushin yaƙe ta rungumo Azima ta kaita dakin sultana sannan ta koma daki ta samu Almazeen na tambayar Nawaz meke damunsa, Mom Na shigowa Nawaz ya mike yana fadin "Wlh ita ce mom, yar uwar Aziza ce, Allah Alhamdulillahi³!" Mom da Nawaz suke faɗi, Al'mazeen da kansa ya shiga duhu yace "Dan Allah Mom ku min bayani ku fiddani a duhu, dama Aziza tana da yar uwa ne?" mom tace "Dole zamu maka bayani amma kafin nan a ina kasan Azima ina ka sameta?" bai boye musu ba aiki takeyi agidansa a cam ma ya sameta dan tun bayanan su Maman Hanan suka gaya masa an dauke sabuwar mai aiki, har izuwa sadda ya dawo da shakuwar da ta shiga tsakaninsu. "ALLAH KENAN MAI YIN YADDA YA SO, HAKURINKA BAYA FADI KASA BANZA! ALLAH YA TAKAITA MANA WAHALA" cewar Mom tana jinjina kai, zama sukayi nan Mom ta hau warwarewa Al'mazeen komai bata kara ba bata rage ba, Al'mazeen ya zare ido yace "Kenan mom *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE? SANNAN YAN BIYU NE?* mom ta gya ɗa kai, "Kenan Azima ba Azima bace Banju ne?" mom ta ƙara jinjina kai "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" mom ta kara da cewa "Wannan shine dalilin da yasa auren Nawaz da Aziza ya tashi babu shiri dan yin jahadi ya taimaki Aziza" jinjina kai Al'mazeen yayi ya ce "Idan har Aminina zaiyi wannan aikin ladan ba tare da ya faɗa soyayya ba ina ga ni da na fara son Azima? Sannan ta taimakeni da badin sanadinta ba da yanzu b'arayi sun kasheni!" nan ya bai wa mom labari mom ta hau salati tana sanar da ubangiji, sannan ya kara da cewa "Ta taimakeni! Ta ceci rayuwata yayinda ta saka nata a hatsari! mom ina son Azima! Ina so kuma jibi nima a ɗaura min aure da ita amma karta sani, kamar yadda Banju shaiɗanin aljani ne zai iya kashemu idan har yasan da hakan, sannan ya kamata a gayawa Aziza kar ta dawo gidan nan dan karsu haɗu da Azima har sai bayan an daura aure" Mom tace "Hakan ma wata shawara ce mai kyau,idan yaso aka daura auren da washe gari ranar sai mu shirya tafiya yola,ko kuma da an daura kawai mu wuce tinda Aziza tace cikin daci suke, sai ku shirya mota mai ƙarƙo da zai iya kaimu zamu tafi da Malam Yunusa da ƙanin mahaifinku da kuma Hajiya Lawiza ko kuma Hajiya luba" "E hakan ma yayi mom" cewar nawaz, na suka gama tsara abunda zasuyi. An gama yiwa Aziza lalle tana zaune,ita kuwa Sultana ana wanke mata nata, gajiya da zaman Aziza tayi ta ɗan jinginu tana lumshe ido, tana lumshe ido wa zata gani? Azima ta hanga wani ajiyar zuciya ta sauke da jan numfashi ta buɗe ido tace " *AZIMAA!?"* sultana tace "Azima kuma? Ina kika ganta?" "Wlh na ganta Anty Sulty ina rintse ido na ganta,ina zuwa bari na sake dubawa" rintse ido tayi ta shafo tafin hannunta nan ta hangi Azima kwance a gadon sultana, a hankali ta buɗe ido tace "Azima a gida kuma a dakinki a gadonki?" sultana zatayi magana wayarta ya yi kara, tana dubawa ta ga mom saurin dauka tayi tasa a kunne tayi sallama mom tace saurareni da kyau Sultana" nan mom tayiwa sultana bayanin komai sannan tace Idan sun gama su biya gidan kawarta Hajiya Biba su ajiye Aziza sannan su su dawo, yanzu sultana ki yiwa Aziza bayanin komai yadda na miki, mom na gama fadi ta ajiye waya,sultana ido bude ta kai bakinta saitin kunnen Aziza tayi mata bayani dalla-dalla,itama Azizan ido a waje ta kalli Sultana, sultana ta jinjina mata kai. Basu gama ba sai gaf magriba dan haka ko da suka tashi suka biya suka ajiye Aziza a gidan Hajiya Biba su kuma suka wuce gida. Ko da suka isa Sultana bata nunawa Azima komai ba tayi maraba da ita ta hau janta a jiki. Nan sanarwan aure ya koma na mutum uku. Da washe gari walima Mom ta ba wa Azima haɗaddiyar dogon riga wanda yasha stone, a jiya ne ma da dare tasa aka nemo mata kasancewar ba ayi shiri da ita ba, bata tayi ta saka Azima ta karba ta mata godiya, kasancewar a gidan za ayi walimar a tare kusa da juna Mom ta zaunar da sultana da Azima,itama Aziza ana can anayin nata a gidan kawar mom, sadda aka fara wa'azi dodon kunnenta kamar zai tarwatse ji take har fatarta ƙuna yakeyi dan da karfi Malama Rasheedat Hassan Usman ke fadin Allah yace Annabi Yace. Duk wanda yazo ya tambaya wannan itace amaryan Nawaz din sai mom tace a'a ta Al'mazeen ce, lokacin dasu Maman Hanan suka iso kamar su mutu da bakin ciki dan tun a jiya labari ya iskesu nan suka dinga tsinewa Almazeen da Azima, har suna cewa dama ya sane ya ƙi fada musu zaiyi aure. Anyi walima lafiya aka watse lafiya. Da washe gari karfe sha ɗaya za a daura aure kasancewar su Nawaz zasu kama hanyar yola ne da an daura aure. Tun wayewar gari Azima ta kasa zama ta kasa tsayuwa ta rasa dalili, a gidan Hajiya Biba kuwa itama Aziza ta matsu suyi ido huɗu da Azima. Ma sha Allah sha ɗaya nayi dai-dai aka shaida daurin auren Khalil Alhaji Yaro da Amaryarsa Sultana Alhaji Sardauna, sai kuma na NAWAZ ALHAJI SARDAUNA DA AMARYARSA AZIZA MAGAJI BAWA, SANNAN AKA DAURA NA AL'MAZEEN ALHAJI SAHABI DA AMARYARSA AZIMA MAGAJI BAWA! ana daura aure Azima na zaune a daki da su Sultana da kawayen sultana nan ta riƙe kirjinta ta hau tari, ana gama daura aure Nawaz da Al'mazeen da wasu abokai sukayi gidan Hajiya Biba dan dauko Aziza, da lullubi aka fito da ita kanta na juyawa kasancewar mahaɗi daya suke da Azima wacce take mayuwacin hali a gida su Sultana sun rufo a kanta. Da kyar Aziza ke fizgar numfashi ta gaida su Al'mazeen suka amsa ,hankalin Nawaz na kanta yana lura da halin da take ciki. Suna isowa gida guɗa ya hau tashi ana ga angwaye ga angwaye, Mom tace su hauro sama, Aziza ta taka step jiri ya kwasheta zata fadi da sauri Nawaz ya tallabota nan jama'a aka sa ihu ana musu tafi, shi dai matarsa kawai ya kama suka hau sama, hannun kofar Aziza ta murɗa fuskarta a murtuke, tana tura kofar a lokacin Azima na duƙe sultana na bubbuga bayanta. "AZIMA!" Aziza ta kira sunanta murya a daskare, wani wawan dagowa Azima tayi caraf idonta ya sauka cikin na Aziza wacce Nawaz ke rike da kafaɗunta. 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *WA INDA BASU BIYA BA SUN BIBIYI PAGES BA, CMLPT DCMNT #300 NE, NOR #100.* *PAID.* 🅿️=6️⃣7️⃣↪️6️⃣8️⃣ Murtuƙe fuska Banju ya yi ya ce "Magaji! ba dawowa nayi ba" "Na sani Banju! ba dawowa kayi ba,jarumar 'yata ce ta dawo da kai" "Kaii Magaji! Kunceni! Idan ba haka ba yankin kwana ta koma toka! Dan kasan wanene Banju! Bana da imani! Kasan karonmu da kai!" murmushi Baffa yayi yace "Amma ni Magaji Bawa! ban gudu ba hakane Banju?" haɗe rai Banju yayi baffa ya ci gaba da fadin "A yanzu ko Magajiyata Aziza tsaf zan iya sakata kasheka! amma halin da ka sakani yasa nake son kasheka da hannuna! ka fara ƙirga numfashinka daga yanzu zuwa gobe" dariya Banju ya yi yace "Ashe kuwa idan zaka kasheni zaka haɗa da 'yarka, karka manta gangar jiki daya muke da ita" Baffa shima murmushi ya yi ya ce "Duk makahon da kaji yace ayi wasan jifa yasan ya taka dutse bare mai ido kuma kai ma kasan bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane, a wannan tafiyar kaine makahon inaji ka manta da cewa yanzu haka Azima na da aure ko? mijinta shine zai fiddaka daga jikinta ni kuma na kawo karshenka ta yadda ba zaka kuma dawowa ba, kisan farko da na kasheka ban so ba, amma a yanzu ne zan kau da ka" wani ihu Banju ya yi yana son tsincewa, Baffa yace "Aziza!" juyowa tayi ta kalli Baffa, Baffa ya mata alama da ido, ta gya ɗa masa kai sannan tayi gaban Banju tana shirin sake kafar da shi, da karfi ya furta mata "BAHULAAAAA!!" a kunne yana son tada Bahula dake jikin Aziza, wani ja da baya Aziza tayi ta dafe saitin zuciyarta da kanta, ganin haka yasa Baffa jan Aziza da sauri ya watsa mata wani farin hoda nan Aziza ta sulale zata faɗi Nawaz bai yi kasa a guiwa ba ya tare matarsa, da yatsa daya Baffa ya do ki goshin Banju, kamar anyi ruwa an dauke haka Banju ya tsaya cak, Mom cikin tashin hankali ta kama hannun Aziza wacce take kwance a jikin Nawaz ta ce "Dan Allah Baban Aziza kayi wani abu, Aziza ta sha wuya wlh! Duk wani masifa kanta yake afkawa dan Allah tunda ga Azima a cire mata Banju ko Aziza ta huta, me yasa baka kashesa yanzu ba?" cikin kunya Baffa yace sabida har yanzu yana jikin Azima, idan na kashe Banju a yanzu Azima ma ta tafi!" nan Mom ta gane abunda Baffa ke nufi, ta kalli Hajja wacce ke tsaye a gefe tayi lullubi tana duƙe da kai, Mom ta ce "Nawaz shiga da Aziza cikin gida, Maman Aziza? Dan Allah ki daina ɗaurewa kina wannan kunyar taki, ki saki jiki ki rungumi yarki, an wuce wannan zamanin kunyar, yarki ce fa? Karki cutar da kanki kina son jin dumin yarki amma ki ta rabewa, dan Allah bana son haka, ai gwara ki ja ta a jiki kafin na dauketa" rasssss!! gaban Hajja ya faɗi jin mom tace zata dauke Aziza, amma bata iya furta ko da uhum bane tabi bayan Nawaz da ya shige da Aziza, mom ta ce "Baban Aziza zamu yi magana" Baffa ya ce "To madalla bismillah" gefe suka koma suka kebe, mom ta ce "A ba wa Almazeen matarsa yau suyi mu'amala ta aure dan a kawo karshen wannan masifan, karka ce zaka biyewa kunya, wajan ceton rai babu zan can kunya, a nema masa inda za a kai masa matarsa, a gobe ka kashe Banju,idan kuma hakan ba zai yu ba to a bamu su mu koma birni idan yaso komai ya daidaita a can Banjun ya fita sai a kashesa a can birni sai mu tafi tare da ku, amma ya ka ce?"girgiza kai Baffa ya yi cikin sauri ya ce "Maganar a bar yankin nan a shiga gari akwai matsala, ba zan boye miki ba, Almazeenu zai fuskanci kalubale wajan kusantar Azima, Banju ya wuce duk tunaninki , kuma bayan ya kusanceta zaiyi ciwo, ba lallai bane ku a cikin gari kuna da maganguna irin tamu ta gargajiya, ga misali a kan Aziza haka tayi ta faman ciwo sai da ku ka zo kafin ta samu furen huriri ta warke, a nan aka fara yaƙin a nan kuma nake so a ƙarasata,bana so a kai muku masifa kuna zaman lafiya, burin Banju kenan ya sake barin yankin nan,ni kuwa ba zan bar haka ta faru ba ta yardan Allah, dazu bayan munyi sallar asuba maganar da Baffa Mandi da Arɗo suka min kenan a ba wa Almazeenu Azima yau, akwai wani gida da Arɗo yasa aka zagaye a can kusa da wajan gari, amma akwai tsirarakun fulani a wajan kawai dai gidan ne shi daya, yanzu haka zamu tafi da shi Almazeenu din, kafin nan zan ba shi wasu magunguna da rubutu su sha shi da Nawazu din, dan shi ma yana da bukatar haka tunda miji ne ga Aziza" Mom ta ce "To ba damuwa hakan ma yayi Allah ya iya mana" Baffa ya amsa da amin, mom ta kira Nawaz da Almazeen tace musu su bi Baffa, Malam Yunusa kuma da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami suna tare dasu sarki chubado da mai unguwa ori sai hira sukeyi ana shan damemmen fura da nono, gwanin sha'awa. @@@@@ Gidan suka je, duk da gidan kara ne amma yadda aka shirya gidan ya burge Almazeen, tarko Baffa ya saka a ciki da waje ta yadda ko Banju ya fice a jikin Azima ba iya guduwa zaiyi ba. Sannan Baffa ya ba wa su Almazeen da Nawaz wasu maganguna da rubutu yace su sha, ya basu na kariya da na sha da na wanka da na gogawa dana murzawa dana ɗorawa duka babu wanda bai basu ba, daga nan sukayi wani gida gaba kaɗan da na inda aka ba wa Almazeen, Baffa yace "Nawazu, kai ma a nan zaka zauna ka riƙe Aziza, dan a lokacin da abun da ke jikinta zai fita zata iya shiga wani hali, zata iya fita hayyacinta, idan kuma ta subuce zamu iya rasata na har abada dan babu abunda Banju ba zai yi ba" Nawaz yace "In sha Allah hakan ma ba zata faru ba Baffa, hakuri da gaskiya sune a sama, zamuyi nasara a kan Banju bi'izinillahi ta'ala!" Baffa ya yi murmushi na jin dadin samun sirkai kamarsu Nawaz da Almazeen, haka shi ma wannan gidan ma ya saka matakan tsaro. Wunin ranar kuwa Baffa bai zauna ba shiri yayi sosai ya koma asalin Garkuwa Magaji Bawansa kyakkyawa fari dogon bafulatani mai dogon hanci da halin girma da cikar zati da haiba. Da daddare mom ita ce tayiwa Azima da Aziza komai,ita da Maman Beenah suka raka Azima da Aziza, Almazeen wani irin kunya yakeji, hajja kuwa ta kasa fitowa a bukka tana zaune tana tasbihi ga Allah, tana roƙon mai duka da ya fidda mata yaranta lafiya, hakika ita kam ta ga jarabta. Bayan an mikawa Almazeen Azima wacce take da ita da babu za a iya cewa duk daya, sannan aka wuce aka kai wa Nawaz Aziza duk da shi ba wani abu bane zai wakana a tsakaninsu. Ko da su Mom suka koma itama ba kwanciya tayi ba, alwala tayi ta zauna ta fuskanci gabas, Maman Beenah kuwa gadon kara ta haye tayi kwanciyarta dan tace bacci takeji. Baffa ma uban gayya bai ga ta zama ba balle ya rintsa dan kuwa a tsaye yake kyam. 💕💞💕💞💕 *AL-MAZEEEN DA BANJU AZIMA.* A bukka kuwa Almazeen zama ya yi ya kurawa Azima ido yana kallonta, shi bai ma san ta ina zai fara ba, ya kwashi kusan mintuna talatin yana kallonta daga bisani ya tashi ya ɗauro alwala ya yi sallah raka'a biyu, ya ciro wayarsa ya yi karatun alkur'ani mai girma ya daga hannunsa sama yana adduoi sannan ya shafa ya miƙe a hankali ya fara rage kayan jikinsa, wani magani da Baffa ya basa yace ya shafa a jikinsa idan zai taba Azima, maganin ya shafa a hannunsa da dukkkan jikinsa, yana tabata sai da ta girgiza,kwantar da ita yayi, Banju dake jikinta yana kallon abunda ke faruwa ɗauresa kawai Baffa yayi, wani gurnani ya fara nan ya hau buge-buge, Almazeen da iyakacin karfinsa ya fizgi kayan dake jikin Azima, nan dambe ya kacame duk da banju yana daure amma ba shi ya hanasa kokarin yunkurin kashe Almazeen ba shima Almazeen yaci albarkacin daure Banju da Baffa yayi amma duk da haka yanaji a jikinsa, duk kalman da yazo bakin almazeen indai na salati ne yin shi yake yi ,Banju bai gama sarewa ba sai da ya ga Almazeen ya yiwa Azima kaff da kayan jikinta, yunkurin komawa maciji Banju yayi amma kafin ya fara hakan tuni Almazeen ya karanto adduar saduwa ya fara kokarin shiga jikin Azima, wani sarawa kansa yayi tare da wani wawan jiri dake shirin watsa shi waje daurewa yayi ya riƙe kokaran gadon karan gam jikinsa na kyarma, nan Azima ta fara canzawa tana zama wata halitta daban mai matukar ban tsoro da firgitarwa, kokarin zare jikinsa yayi dan dama bai shigeta sosai ba, tunowa da maganar Baffa na cewa kar ya kuskura ya kyale Azima har sai ta yi attisha sau uku dan duk hanyar da Banju zai bi dan ya ga ya hana Almazeen kusantar Azima zaiyi, daga karshe kuma zai kashesa ya kuma guduwa, tunowa da haka yasa Almazeen ya dage da iyakacin karfinsa sakamakon b'ari da jikinsa ke yi ya shige Azima gabadaya, wani ihuu Azima ta saka da karfi wanda sai da ya karaɗe gefe da kewayen inda suke, ta shaƙo wuyan Almazeen wanda shi kadai yasan abunda yakeji kamar ana zare ransa haka yakeji tsananin azaba dan harta fatarsa ji yakeyi kamar ana soya masa shi, sake damƙar kafaɗun Almazeen Azima tayi ta dage ta saki wani attishawa mai karfin gaske dan kuwa an karya makarin Banju tunda Almazeen ya afka cikinta, tana yin attishawa na ɗaya tayi na biyu, na ukun ne nan wani guɗa ya hau tashi, tana attishawar Banju wanda ya yi tsalle ya fice ta baki da hancin Azima, ƙauuuuu! Azima taji yayinda ta wani firgita tana jan wani numfashi da iskar duniya,da nauyin kai ta hau ware ido da kyar jin idon kamar an liƙe mata su, tana ji tamkar yau ne uwarta ta haifeta, tana gama buɗe ido mutum ta hanga a saman kanta, Almazeen wanda yake gaff da sumewa yana ganin ta bude ido a hankali ya sauke bakinsa saitin kunnenta cikin mayuwacin hali da kyar ya furta "Alhamdulillah! Wlcm back my dear wife, am so happy, u are back! i promise that i wouldn't let any harm attack u, i will sacrifice my life to u, cox I luv u, am really luv u, i fell in luv with u Azima! pls don't leave me alone" Almazeen na faɗi ya hau kokarin zare jikinsa daga na Azima, a lokacin Azima taji wani mugun raɗaɗi ta kasanta hakan ne yasa taja wani numfashin mai cike da azaba, a tare suka suma. Banju dake tsaye yana kallon Almazeen wanda yake son kashesa dan ya lashi takwabin sai ya kashe Almazeen, amma inaaa ya kasa kusantar almazeen balle ya kashesa kasancewar Almzeen mutum ne mai riƙo da ibada baya sanya. 💕💞💕💞 *NAWAZ DA AZIZA.* Sadda aka raka Aziza tsayuwa tayi a bakin bukkar taki karasowa, Nawaz na zaune yana danna wayarsa da tun shigowarsu garin babu network ko ɗigo, ɗaga ido ya yi ya kalleta ya ga jikinta sai rawa yakeyi, da alama tsorata tayi, a hankali ya tashi yaje gabanta bata ma sani ba tayi zurfi a tunani, ji tayi an kama hannunta, a firgice ta dago idonta ya haɗe da na Nawaz, ganin duk ta taburce yasa Nawaz rausaya kai yace "Ya haka? Jaruma a waje, matsoraciya a gabana?" ya faɗa yana matsota sosai, ja da baya tayi tana shirin ficewa yasa hannu ya jata ta shige jikinsa, "Haba jaruma, karki bani kunya mana" mutsu-mutsu ta hau yi tana son kwace jikinta, yasa hannunsa duka biyu ya kewayeta ta kasa kwacewa ya ce "Ko za a watsar dani ne?" nan ma bata masa magana ba, ya ce "Idan baki min magana ba, zan cinye bakinki" mamaki ne ya kama Aziza, oh dama haka Nawaz yake? take tambayar kanta, bata gama yankewa ba sai da taji ya dauketa ya ajiyeta a saman gadon kara yana shirin kwanciya a kanta tayi saurin miƙewa zunbur tana fadin "Sorry Hamma" murmushi ya yi a boye, ya ce "To matso kusa dani, kin san Baffa yace na rikeki da kyau dan haka matso" ya faɗa yana ware mata hannu alaman ta shigo cikin jikinsa, ganin yadda ya sauya fuska ba alaman wasa yasa ta matso a hankali ta shige jikinsa ta kifa kanta a ƙirjinsa, yasa hannu ya rungumeta da kyau yana son fassara me zuciyarsa takeji game da Aziza. A lokacin da Almazeen suka fara dambatuwa da Banju, a lokacin Aziza na kwance a jikin Nawaz, lokaci daya kamar an zabureta haka ta miƙe, cikin hanzari Nawaz ya fizgota ya maidata jikinsa ya matseta dan ya tuno da maganar Baffa da yake cewa idan Aziza ta subuce za a iya rasata shiyasa ya kara matseta sosai a jikinsa, ihu Aziza ta saka jin fatar jikinta na sabulewa, saurin ture Nawaz tayi ta koma gefe tana ƙanƙame jikinta, fuskarta ne ta ji yana b'anb'arewa, hannu biyu tasa tana tare fuskarta tare da ihu, ganin halin da take ciki yasa Nawaz saurin tashi zai zo gareta, nan yabga masifa, daga ƙugunta abunda ya yi sama ta zama macijiya fara sol sai kyalli take yi, sak irin wanda yake gani a mafarkinsa, hannu ta miƙa masa cikin azaba tana fadin "Help me plss! ka taimakeni Hamma Nawaz!" ta faɗa siffar jikinta na ƙasa na haurawa zata zama macijiyar gabadaya, da saurin Nawaz ya rintse ido yaje ya rungumeta ƙaƙam! Yana rungumarta ta tsaya a haka, a lokacin da Banju zai fita a jikin Azima itama Aziza taci azaba dan nan suka hau gwada karfi da Nawaz, hakika shima ya jikata, dan kuwa sadda abun zai fita gani ya yi wani farin abu shi ba dutse ba shi ba tsuntsu ba ya fice ta goshin Aziza, yana fita numfashinta ya tsaya cak yayinda ta koma mutum, haka Nawaz ya zauna riƙe da ita a jikinsa, gab'ob'insa na masa ciwo sosai, har asuba. 💞💞💞💞💞 Sanyin asuba ne ya fara farkar da Almazeen wanda da kyar yake iya buɗe ido sabida nauyin da suka masa, ya jima a haka kafin da layi ya tashi ya janyo kayansa ya saka, ya rufawa Azima jikinta, ya koma ya kwanta a gefenta yana sauke huci mai zafi. Baffa suna idar da sallar asuba Arɗo yace su je a duba yaran nan. Mom aka kira dan da ita za aje Hajja ta ƙi fitowa ƙememe. Suna zuwa gidan Hajja zata shiga da saurin Baffa ya dakatar da ita ya hanata shiga, yace tana shiga Banju zai iya kasheta dan shi yanzu duk wanda ya samu zai kashe ne" Baffa ne ya fara shiga cike da yarda da kansa sabida ya yi imani da Allah ya yi riƙo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam,duk wanda ya yi riƙo dasu baya da fargaba a kan kowa, yana shiga kuwa Banju dake neman hanyar guduwa a gidan tun daren jiya ya kasa sabida Baffa ya ɗaure ko ina da ina, suna ido huɗu Baffa ya daga takwabi, Banju yace "Magaji a gwabza idan ba tsoro! karka kasheni sai mun gwabza!" Baffa ya yi murmushi yace idan ka so haka" "Zan so! amma ka ajiye takwabi" Baffa ya ce "Ba daga yanzu zamu fara ba, kafin nan ga wannan" Baffa na faɗi ya wurgawa Banju wani igiya nan ya daure Banju ya fito da shi, yana fitowa da shi ita kam mom bata iya daga ido ta kalli Banju ba, dan tace mugun ji da mugun gani Allah ya rabamu dasu, Baffa na cewa zata iya shiga da sauri ta wuce shi kuma ya wuce da Banju, mom na shiga ta samesu a yashe, Azima ta jijjiga sannan ta taba Almazeen wanda jikinsa ke rawa alaman ciwo jikinsa zafi raɗauu kamar wuta, na Azima ma akwai zafi amma na Almazeen ya fi nata, babu wani taimako da zata iya masa, amma zata iya taimakawa Azima, dan haka ta fito ta haɗa ƙirare ta tafasa ruwan zafi, kafin ruwan ya gama sai ga jikan Ardo Sanda ya kawo wasu magunguna yace Baffa yace idan su Hamma Almazeen da Azima zasuyi wanka a zuba musu shi a ruwan wankan suyi wanka da shi, wannan kuma su sha, sannan a ba wa Hamma Mazeen wannan,wannan kuma a ba wa Azima" mom ta karba tana masa sannunsa da aika. Mom da kanta ta taimakawa Azima tanuna mata yadda zatayi wankan tsarki, sannan tayiwa mata wanka haka,ita dai Azima wani iri take jin kanta, riƙota mom tayi suka shiga bukkar har yanzu Almazeen ya kasa motsi koda da yatsarsa daya ne, taimakawa Almazeen mom tayo shima ya yi wanka ya yi sallah a zaune ya sha magungunan da Baffa ya bada a ba shi daga nan ya hau bacci,itama Azima maganin ta sha ta hau bacci, haka ma Aziza wanda aka aika aka ba wa Nawaz yasha ita ma ya bata ta sha duk suka buge suka hau bacci. Can wajan dandalin yanki Baffa yaje ya daure Banju, ko kaɗan Banju baida kyawun halitta gani, ga girma katam da shi tamkar basamude ga baƙi fiye da misali, kai babu ta yadda za a sunfanta zubin halittan Banju. Bayan Baffa ya daure Banju yasa maga isar da sakon yankin kwana a kan ya rubuta wasika yayi aike sauran yankuna ana gayyatar su izuwa kallon fafatawa a tsakanin aljani Banju da Baffa bisa umarnin gayyatar sarkin yankin kwana wato sarki chubaɗo, kamar irinsu yankin ja'i da yankin tudu da yankin ja'o da yankin gangare, da yankin shani, da dai sauran yankuna. Sadda wasika ta iskesu sun sha mamaki, kai wannan ai babban fafatawa ne a tsakanin Magaji bawa da Maciji Banju, wanda ya yi b'arna da ta'adi a yankin kwana, wanda ya kashe shahararrun masu kama macizai irinsu jarman macizai dasu Innu maciji, da iro mai maganin macizai da dai sauransu, hakika duk yankuna sun amince zasu zo ganin wannan fafatawar tsakanin mutum da aljan,duk da wannan ba sabon abu bane a wajan Garkuwan Kwana Magaji Bawa Arɗo. Mom ce ta cewa Baffa dan Allah ya taimaka ya raba Aziza da Bahula ta koma asalin cikakkiyar mutun ɗinta ta huta gaba daya, Baffa ya yi murmushi ya ce wannan ba wata matsala ba ce, suka je gidan har zuwa yanzu suna bacci, goshin Aziza Baffa ya riƙe ya rintse ido, attishawa Aziza tayi sannan ta fara hamma, wani farin abu ne ya fito ta bakinta, a hankali farin abun ya koma kamar farin hayaki haka, daga nan abun ya zama mutum wanda ake mata kallon dishi-dishi, Baffa ne kawai yake iya ganinta dan kuwa mom ba ganinta take yi ba, kallon Baffa Bahula tayi tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta dan tasan Baffa kashe mata Yayanta Banju zaiyi dan tasan ko a wasa Yayanta Banju ba zai haɗa karfinsa da kwatan karfin da Magaji ke da shi ba,kawai dai a mugunta ne baya da lamba ta biyu, dukar da kai Baffa yayi, daga haka Bahula ta b'ace, muryan mom Baffa yaji tana magana "Baban Aziza? Yanzu shikenan sun warke babu wata matsala ko?" "In sha Allahu, sun warke, amma wanda ba yanzu zaiji sauki ba wanda shi ba mu san a ya zai farka ba shine Almazeenu, amma harta Azima zata farka lafiya lau,kuma idan ta farka za a gaya mata gaskiyar abunda ya faru kar a boye mata duk da abun da suka faru zata iya gani duk da ta kasance a sume amma zata iya gani kamar mutum mai bacci yana mafarki sabida sun rayu a jiki daya da Banju,jikin ma kuma nata ne, zata tuna komai kuma zata gane komai shiyasa za a gaya mata sabida rashim gaya mata zai iya haifar mata da wani matsala, mom ta gya ɗa kai tana mai tausayawa Almazeen. 🍃🍃🍃🍃 Basu suka farka ba sai lokacin sallar azahar, wani ɗauuuu!! Aziza taji a kunnenta da ta farka, zata fadi da saurin Nawaz ya riƙeta, wanda shima yanzu baya jin komai ciwon jikin nasa ya tafi "Kina lafiya?" Aziza ta gya ɗa kai tana gyara tsayuwarta, zuwa can ta ce "Azima? yar uwata?" ta faɗa zata fice da sauri Nawaz ya rikota yace suyi sallah kafin su tafi, sallan kuwa suka gabatar shi ya jasu sannan suka fita sukayi gidan da Almzeen da Azima suke, mom ma tana gidan tana kula da Almazeen wanda a zaune ma ya ƙara gabatar da sallah, Azima kuwa tunda ta farka har tayi sallah karo na farko a rayuwarta, bata furta ko da uffan bane kallo kawai take bin mutane da shi abubuwa suna dawo mata kamar a mafarki haka take tariyowa, tana zaune a kan sallayar kaba su Nawaz da Aziza suka shigo da sallama, Aziza tana ganin Azima a kan sallaya tasa kukan farinciki tana fadin "Azima?" daidai lokacin su Inna wuro da su Yawuro har ma da Hajja dasu Baffa suka shigo, juyowa Azima tayi tana binsu da kallo, ganin Aziza yasa ta ce "Aziza?" wani kuka Aziza tasa ta ƙaraso da sauri suka rungume juna ƙaƙam "Me ya faru Aziza?" Azima ta tambaya cikin sheshsheƙar kuka " zan gaya miki" cewar Arɗo, nan ya hau yiwa Azima bayani dalla-dalla tun fara kisa da yaƙi da komai da barin yankin kwana har izuwa yanzu, wani kwalalo idanu waje Azima tayi ta hau girgiza kai tana fadin "Ni....ni....ni....ban.....ban....ban...kashe....kowa....ba.....Baffa.......bana....da niyyar kasheka...Hajja ban miki rashin kunya ba.....Aziza...banyi faɗa dake ba.....dan Allah kuyi hakuri..... Ban kashe kowa....ba..." duk Azima ta bi ta ruɗe mom ta jata a jiki ta ringume tace "Mun sani Azima,mun san cewa jinin Magaji da Jamila ba zata aikata hakan ba, kwantar da hankalinki, ba ki kashe kowa ba,mugun nan azzalumin aljani Banju shine ya kashe" ɗago daga jikin mom tayi tana kan ci gaba da kuka, duk da zafi da ciwo da ƙasanta ke mata ba shi ya hanata tashi da gudu ta shige jikin hajja da kuka ba, itama Hajja kukan takeyi, dagowa tayi ta kalli Baffa ta hau girgiza kai da hannu tana fadin. 🍃🍃🍃🍃 GARKUWAN MACIZAI🐍 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=6️⃣5️⃣↪️6️⃣6️⃣ "Aziza?" Azima ta kira sunanta itama murya a sarƙaƙe, Nawaz ne yace kawayen Sultana su fita, da sauri kuwa suka fice,suna fita Al'mazeen ya sawa kofar key, wani kallo Azima ke bin Aziza da shi har ma dasu Mom, Mom ce ta tunkari Azima tana shirin yi mata magana da sauri Aziza ta ce "A'a Mom!" tsayawa cak mom tayi, Aziza ta mata ido a kan taja baya, Al'mazeen ne ya matso kusa da ita ya ce "Azima zan iya ce miki wani abu?" shuru Azima tayi kirjinta na bugawa, "Azima Ina sonki! Kuma na au...." maganar da Al'mazeen bai karasa ba kenan Azima ta saki ihu tana toshe kunne, matsowa kusa da ita Aziza tayi ta duƙa a gabanta tace "Azima? Ohh ina nufin Banju! Ka sa kunne da kyau, yanzu haka yola zamu tafi, yau sai yankin kwana In sha Allahu! zaku haɗe da Baffana! dama kasan karonku dashi ba dadi" wani dariya Azima ta hauyi marar dadin sauti tace "Ke a tunaninki zan yarda na koma ne?" "To taya zaka iya guduwa? Albishirinka! Yanzu haka da aure a kan Azima!" wani zaro ido Banju ya yi yana fadin Sun ci amanarsa sai ya kashe miji waye mijin, Al'mazeen ya amsa da cewa "Ni ne mijin!" wani kururuwa Azima ta saka ta miƙe da karfinta da niyyar zama macijiya dan ta saresu da sauri Aziza tasa hannu da wani farin haske ta tokari goshin Azima nan tayi ɗiff!. "Na kafar da ita zamu iya tafiya" Aziza ta faɗa jiri take ji amma ta rasa yadda zata yi, Mom tace "Nawaz Al'mazeen ku kama matayenku ku saka su a mota, bari na yiwa Umma magana (Umma yaya ce ga Mom wanda itace zata tsaya a karasa biki a kai sultana dakinta) har zasu fita sultana ta fashe da kuka tace "Aziza! Za ki dawo? Kiyi min alkawari zaki dawo?" itama Azizan kuka tasa suka rungumi juna, Nawaz zai ja Aziza mom ta daga masa hannu alamun ya barsu, dagowa Aziza tayi tace "Ban san me zance miki ba Antyna...." "Shiiiii! Yanzu kece Antyna tunda da auren Yayana a kanki" murmushi Aziza tayi hawaye na zuba a idonta tace "Ba a canzawa tuwo suna, ke ɗin antyna ce wacce nake ji da ita sosai, da fari zan fara neman gafararki! aurenki guda amma ta sanadina da yar uwata ba a miki shi yadda ya kamata ba, kiyi hakuri ki yafe mana, ga shi zamu kara tafiya da mom,mu kuwa me zamu ce muku? Sai dai mu muku fatan Allah ya muku sutura ranar lahira, dan kuwa kunyi mana a duniya" Sake rungumeta Sultana tayi ta ce "Ni kam alhamdulillah! Naji dadin aurena,dan kuwa an daura tare da Yayuna, sannan karki damu da batun tafiya da Mom, Umma tamkar mom take har ma taso tafi mom, lafiya za a kaini gidana,ni dai fatana dan Allah kiyi hakuri ki dawo a kan lokaci,kinji?" share hawaye Aziza tayi ba tare da tayi magana ba dan bata sa a ranta zata dawo ba, Nawaz ne ya kama hannun Aziza ya jata ya rabasu da sultana suna kuka suna komai, mom ce ta rufe musu fuska kowa ya kama matarsa a haka suka sauko jama'a sai guɗa ke tashi, da manyan motoci biyu zasu tafi wanda zai juri wahala da afkawa jeji mai gudu, mom da Hajiya Luba Maman Beenah kenan ba dan taso ba haka aka sa ta shiga mota,Maman Hanan kuwa cewa tayi wlh ba zata je ba, da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami da Malam Yunusa abokin Mahaifin su Nawaz. Al'mazeen da Azima suna zaune a bayan mota Nawaz da Aziza suna zaune a gaba,mota daya suke su hudu Nawaz ke driving, Azima tamkar gunki haka ta koma, lokaci zuwa lokaci Al'mazeen zai waiga ya kalleta, sunyi nisa Al'mazeen yace "Aziza? Hope dai Azima lafiya take?" Gya ɗa kai Aziza tayi a sanyaye tace "Lafiya take Hamma Mazeen, kawai na kafar mata da dafi ne idan ba haka ba sunanku gawa dan Banju zai kasheku! Ni ba zata iya kasheni ba, kuma kafin ace nayi kokarin yin wani abu dan dakatar da ita zata iya kashe ko da mutum daya ne ba zan so hakan ba, zamanta a haka shine mafi alkairi har mu isa" jinjina kai Almazeen yayi yana kara maida idonsa kan Azima. Basu isa yola ba sai yamma lilis, dan haka Aziza tace ba zai yu su afka jeji ba su bari su sake yin asubanci gobe, dan haka suka kama hotel inda zasu kwana. A gida kuwa karfe biyu Umma tayi oya-oya aka dauki amarya sultana aka kaita danƙareren gidanta da Khalil dinta ya gina aka ajiyeta, Umma ce tayi mata komai tamkar Mom tana nan, Umma ce ta wakilci mom a komai aka sallami baki da wasu daga cikin yan uwa. Sadda aka ajiye sultana a gidanta za a watse a barta tasha kuka, duk hankalinta da adduarta Allah yasa Aziza ta dawo. Kamar yadda suka ce da washe gari asubanci sukayi, sallar asuba kawai suka yi suka yanki cikin jeji inda zai sadasu da ƙauyen yankin kwana, Aziza ke nuna musu hanya, Nawaz ya kalleta yace "Zamu iya isa a yau?" tace "Hamma Nawaz yadda wannan mota ke gudu kamar a iska inaji nan da yamma zamu isa" "Kai har yamma?" Nawaz ya tambaya a gajiye dan tsakani da Allah ya gaji, yadda ya zare ido ya ba wa Aziza dariya dan haka tayi murmushi, suna tafiya Nawaz ya cewa Mazeen ya musu video recording ɗin hanyar, Mazeen ya ciro waya ya hau musu video ɗin. 🍃🍃🍃🍃 Yau tinda Hajja ta farka gabanta ke faduwa, ga shi jiya tayi mafarkin Azima da Aziza sun dawo, duk da mafarkin ba sabon abu bane a wajanta. Da yamma ligis wajan irinsu shidda haka Aziza ta shigo yankinta wani murna da annashuwa takeji, yayinda hawaye ya b'alle mata, hakika yanayin al'karyan ya tafi da zuciyar su Nawaz, gari kore shar dashi abun sha'awa ma sha Allah, ga korayen shuke-shuke da 'ya'yan itatuwa, yankin kwana sun ga abunda basu taba gani ba, dan tun farkon shigowar su Nawaz a idon Salti ɗan gidan jauro nan yaje ya baza a gari ya ga wasu sabbin masifa ya shigo musu gari, wasu bayyanannun aljanu,nan yara da manya aka hau bin motar har gaban kofar gidan Baffa, nan aka hau cewa a kofar gidan Magaji masifan ta tsaya, mota na tsayuwa da gudu Aziza ta fito, su ma su mom fitowa sukayi,yayinda Mazeen ya fito da Azima Banju, dasu mom suka rufawa Aziza baya, mutane an cika ana kallon su mom, ko sallama Aziza bata iya yi ba tana shiga ta tsaya turuss tana kallon mahaifiyarta wacce ta rame sosai ta karayin wani fari fal da ita, Hajja na duƙe ta dibi ruwa a kwarya zata zagaya kewaye, su Mom ne suka shigo suma, cikin wani irin kuka da shauki irinta 'ya wanda takeji a kan mahaifiyarta murya na rawa mai fizgar kuka Aziza ta ce "Hajja!" kwass!! Hajja ta saki kwarya ta juyo da sauri, haba duk daren daɗewa muryar Azizanta ba zai goge a kunnuwanta ba, kallon Aziza Hajja ke yi jikinta na rawa tama kasa magana, da kyar Hajja ta ce "Dan Allah Aziza yau karki b'ace ki barni, na yarda zan dinga zama da gizon naki dun Allah karki tafi" da gudu Aziza ta shige cikin hajja ta riƙeta gam-gam suna wani irin kuka mai ban tausayi, harta su Mom suma hawaye sukeyi, Malam Yunusa ya kalli Mom ya ce "Hajiya Kamila(mom)Allah ya saka miki da mafificin alkairi, Nawaz da Al'mazeen Allah ya muku albarka" suka amsa da Amin. Ɗago Aziza daga jikinta Hajja tayi tana shafa fuskarta, Aziza cikin dashashshiyar muryarta tace "Hajja nine na dawo, mun dawo" Hajja na shirin magana sai ga Baffa wujigan a muraran, yana can garkin shanakunsa Salti yaje ya samesa yace ai ya ga bataliyan aljanu sun nufi gidansa yanzu haka aljanun suna gidansa, shiyasa Baffa yazo a hargitse, Baffa na shigowa da sauri Aziza ta zo ta ce "Baffa ni ce Azizanka! Baffa na dawo, kace kar na dawo sai da Azima, Baffa gata nan ga Azima nan" duk irin kunya irinta fulani nan Baffa ya rungume Aziza yasa kuka, an jima ana koke-koke, Sarki Chubaɗo dasu mai unguwa ori dasu Garkuwan yankin kwana, kai duk jama'ar yankin kwana an taro agidan Baffa, sai bayan an gama kuka tukunna aka basu abun zama, Sarki Chubaɗo yace "Kafin a zauna ya kamata mu fara sallar magriba, hakan kuwa akayi, Aziza ta basu ruwa sukayi Alwala suka nufi masallaci. A cikin gida ma Hajja ce ta ba wa Mom da Maman Beenah ruwan alwala, taki yarda ta daga kai ta kallesu sabida kunya irinta fulani, Maman Beenah kuwa ba bakinciki kauyen ya mata kyau ya burgeta. Bayan sun idar da sallar, Hajja na zaune kusa da yaranta nan suka hau gaisawa dasu mom,mom ta kalli Hajja tayi murmushi ta ce "Kyawu! Kyawun hali! Kunya! Natsuwa! Ashe duk ba a banza Aziza ta dauko ba, ta biyo Mahaifiyarta ne, dadtako halin girma! Jarumta a fuska da kuma jiki ta biyo halin mahaifinta ne! Ina tayaku murna da samun 'ya kamar Aziza" Al'mazeen da suke shigowa cikin gidan yace "Kai mom,Aziman fa?" "Har da itama mana" "To kishi kakeyi dan an yabi Aziza?" cewar Nawaz yana hararan Mazeen, murmushi su Arɗo sukayi sannan aka zauna aka hau gabatarwa da juna kai, mom ce tayi musu bayanin komai har izuwa auren da su Azima da Aziza suke da shi a yanzu, sannan ta gabatar da Nawaz a matsayin mijin Aziza ta gabatar da Al-mazeen a matsayin mijin Azima, ta ɗan bada tahirin kansu a gajarce, dago ido baffa yayi ya kalli Al'mazeen ya Kalli Nawaz kawai sai ya fashe da kuka, Baffa Mandi ya hau bubbuga kafadun Baffa yana fadin "Alhamdulillah! Hakika Allah baya bacci,kuma yana tare da masu hakuri da masu jahadi da sadaukarwa, hakika kayi jahadi wa yankuna da dama, kayi sadaukarwa wa yankinka da komai naka, sannan kazo ka kara bi da hakuri da juriya, taya Allah zai barka a haka Magaji? yanzu dubi ka ga mijin da Allah ya bai wa Azima da Aziza, da munata tunani da kokonta wa zai auri Azima da Aziza dan ya kawo mana karshen Banju, sai ga shi Allah ya turo mana mutane daga wasu duniya daban" Sarki Chubaɗo ya ce "Tabbas kuwa Magaji,kai ba mutum bane kamar kowa bane, hakika muna yiwa Allah godiya daku sirakananmu, mun gode da wannan jahadi Allah ya baku lada" aka amsa da amin, nan Sarki Chubado da mai unguwa ori suka bada umarni a shiryawa manyan baƙi kuma sirakanan Magaji Bawa Shugaban garkuwan kwana abinci mai rai da lafiya, nan aka kawo wa su Mom hadaddiyar kindirmo yasha damu, Inna wuro ta ce "Wata kila ba zaku iya cin abincin mu ba" Mom tace "Ai idan muka sha wannan furan wlh alhamdulillah sai kuma gobe" Al'mazeen ya ce "Ana ta magana amma banji anyi maganar matata ba?" Baffa ne ya sunkuyar da kai Hajja kuwa rufe fuska tayi, Arɗo ne yayi murmushi ya ce "Ohh Allah Kaɗo babu kunya, yanzu kai a gabanmu kake maganar matarka?" Almazeen ya sosa keya ya ce "To ai kaka gani nayi to bari dai nayi shuru" aka sa dariya, Baffa yace "Kayi hakuri ɗan nan, sakin matarka ba tare da kayan aiki ba babban hatsari ne ga mutanen yankin nan gabadaya, ka jira har zuwa gobe idan na daure shi tukunna, ai yanzu ba matarka bace katon aljani ne mugu" shuru Almazeen yayi yana kallon Azima wacce ta koma gunki, a hankali Aziza ta miƙe zata shiga bukkarsu, jiri ne ya kwasheta nan ta fadi, kafin kowa yayi kanta Nawaz ya fara dagota, Hajja kuwa ganin su Mom sun rufu a kan Aziza yasa ita taji kunya ta koma gefe tana leken fuskar Aziza, Baffa ne ya kama hannunta ya ce "Ya salam! Aziza an huda jikinki ko?" gya ɗa kai Aziza tayi tana jan numfashi, Baffa yace "Dole sai an nemo furen huriri" "Me hakan yake nufi Baffa?" cewar Almazeen "Ai kasan ita ba asalin mutum bace,maciji kuma baya son tab'o" "Amma an harbi Azima bai bata illa har haka ba?" "E sabida ita Aziza Banju ya rigada da ya maidata macijiya shine dalili, ga shi yanzu dare yayi ina zan samu furen huriri?" tashi Baffa ya yi ya fita zaije jejin kwana ko Allah zai sa ya samu, yana fitowa da Inno Fandi ya hadu ta mika masa furen huriri tace "Ina matukar farin ciki da Allah ya dawo da Azima da Aziza lafiya, sai kuma shirin kashe Banju a gobe ko?" Baffa ya sosa kai yace "Humm Fandi, abun kunya nake jin kunya" Inno Fandi ta gano abunda yake nufi dan haka ta hau masa dariya, dan kunyar kuwa na kusantar Azima da Al'mazeen zaiyi ne,tunda dole sai Almazeen ya kusanci Azima kafin Banju ya fita a jikinta a kashesa. Da sauri Baffa ya koma ciki, Ardo yace "Magaji ina da kaje?" "Da wai zanje jejin kwana ne nemo furen huriri to sai Fandi ta kawo mini" jin sunan Inno Fandi yasa Aziza fara murmushi. Jiƙa mata furen huririn akayi,tana sha ta ware. Su mom sun saki jiki da mutanen yankin kwana sai hira sukeyi kamar an jima da sanin juna. Sai da dare ya tsaga Ardo yace su mom suje su kwanta su huta, su mom gidan Arɗo aka kaisu aka gyara musu wajan kwanciya, su Nawaz kuwa gidan Sarki Chubaɗo aka kaisu. A ranar Aziza da Hajja basuyi bacci ba kwana zaune sukayi suna kuka suna hira, Azima na kafe a gefe, sai da akayi asuba tukunna Aziza ta fara jin bacci Baffa kuma ya ce mata ta fito zai daure Banju sai ta sakesa, Aziza ta miƙe tana hamma dan bacci takeji. Kayan yaki Baffa ya tanada, sai wajan takwas jama'ar yankin kwana suka hallara, Baffa ya kalli Aziza ya mata ido alaman ta saki Azima, gya ɗa kai Aziza tayi tasa hannun ta dafe goshin Azima wani haske na shiga goshin Azima, wani ajiyar zuciya Azima ta sauke, nan ta dawo hayyacinta, idanunsu ne ya sarƙe da na Baffa "MAGAJI BAWA!!?" "na'am BANJU! maraba da dawowa Yankin kwana!" 🍃🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣ "Wlh Baffana bani bace! Wlh ban yi yunkurin kasheka ba!" gya ɗa kai Baffa ya yi yana shafa kan Azima ya ce "Na sani Azima" riƙe Baffa tayi gam tana kan ci gaba kuka, nan al'umman yankin kwana suka hau hamdala ana taya juna murna, wa inda sukayi wauta da farko ta hanyar dukan Aziza suka hau ba wa Baffa hakuri yace shi kam ya wuce a wajansa, nan aka zauna ana ci gaba da jajinta lamarin, lokaci zuwa lokaci Azima tana ɗaga ido ta kalli Almazeen wanda yake lullubi idonsa a lumshe bai san hayaniyar da ake yi ba. Maga isar da sako ne ya shigo da sallama yace Sarakunan Yankuna da Muƙarrabansu sun fara isowa da wani lokaci za a fara fafatawa?" Baffa ya ce "A shirye nake, amma a bar fafatawar sai anyi sallar la'asar da yamma kenan, a ƙara shiryawa mutanen yankuna wajan zama mai kyau da abun motsa baki dan kar su gajiya, sannan a dama musu nono mai kyau a tabbatar an basu isasshe ba ƙasasshe ba" Maga Isar da saƙo ya amsa da to, sannan Baffa yace "Mu tafin ku dan a kara shiri" dukkansu suka fice aka bar Nawaz da Azima da Aziza, Azima idonta na kan Almazeen wanda lokaci daya taji zuciyarta ta harba da shi, a yanzu yana cikin wannan halin ne sabida ita, wani kuka Azima ta kara sakawa tana rufe fuskarta da sauri Aziza tasa hannu ta riƙo hannunta tana fadin "Haba Azima miye haka? Godiya zakiyi wa Allah dasu Mom da Hamma Mazeen" cikin kuka har tana sheshsheƙa ta dago idonta wanda yanzu ya koma daidai amma dik da haka basu da baƙin ido ta kalli Aziza tana girgiza kai ta daga hannuwanta hawaye na zuba ta ce "Aziza! Ni! Wai ni da kaina na ke son kashe mahaifin da ya haifeni! Wai ni da kaina na rayuwa bana bautar wanda ya halicceni! Wai ni da kaina mutane suka shiga masifa da tashin hankali! wai ni da kaina na maida yar uwata ta biyuna macijiya! Wai ni da kaina....!" kuka yaci karfinta da sauri Aziza ta rungumeta tana bubbuga bayanta itama tana kuka "Taya zan manta da wannan abun a rayuwata! Kenan mu haka kaddararmu take!" ɗago fuskarta Aziza tayi tace "Karki yi sab'o, ki godewa Allah, sannan duk abunda kika lissafa ai bake kikayi ba Banju ne ya yi, dan haka ki bar fadin haka Sis" cikin kukan tausayi da Azima ta kasa tsayarwa tace "Amma da jikin wa!? Da fuskar wa?" "Koma da miye ne komai zan zama tahiri, ki ta nanata kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yafi wannan sambatun da kikeyi dan bana so,kina ji na ko?" Azima ta gya ɗa kai hawaye na kan sauka tana kallon Almazeen wanda Nawaz ke riƙe da hannunsa yana ji kamar yasa kuka dan tausayinsa, zuwa can da suka gama kukan Nawaz ya kalli Aziza ya ce "Tashi mu tafi watakila yanzu kam ana can filin yaki, zo muje karo na farko a rayiwata naga yadda ake faɗa tsakanin mutum da aljan" tashi Aziza tayi ta kalli Azima tace "Ki kula da kanki da kuma Hamma Mazeen uhum?" Azima ta gya ɗa kai, Nawaz da Aziza suka fita, suna fita Azima ta miƙe a hankali ta karasa jikin gadon ta kwanta a kusa da Almazeen har yanzu jikinsa da zafi sosai, tana kwantawa ta kama hannunsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta ɗora hannunsa a fuskarta ta lumshe ido. ⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️ Hakika su Mom sun sha mamakin ganin mutane him a wannan alkarya, mutanen yankuna sun zo daga yankuna daban-daban, jama'a an cika ana kallo, Aziza na zaune kusa da mom, Nawaz yana gefen hannun hagunta, ya ce "Mom wlh naso ace sultana tana nan da ta ga abunda take kalla a zahiri a tv" mom tayi murmushi. A hankali Baffa ya fito yana riƙe da zureren takwabinsa wanda ya kashe Banju da shi a karon farko amma wannan karon bai yi amfani da zaren sakar dana ba, dan ko ya koma jejin lore ba ba shi za ayi ba,amma duk da haka yau sai ya kashe Banju da yardan Allah. Kunce Banju Baffa ya yi, Banju yana ganin takwabin hannun Baffa ya ce "Magaji! ka ajiye takwabin nan ba da shi zamu gwabza ba" murmushi Baffa ya yi ya kalli Nawaz ya miƙa masa takwabin, zuwa Nawaz ya yi ya karba yana riƙewa sai da yaji damtsen hannunsa ya girgiza, kara sarawa Baffa Nawaz ya yi sannan ya koma ya zauna. Banju ya kalli Baffa ya ce "Ba kai ka yarda da kanka ba?to inaso ne mu gwabza da karfin-karfi,ni aljani ne faɗa da aljani kuma ba dadi" jan kafa baya Baffa ya yi ya ware hannunsa ya ce "Bar ganin ka ƙereni a tsayi da girman jiki! a haka na daureka na kasheka a farko, ni mutum ne amma ba irin wanda kake tunani ba na san kasan da haka" Baffa na fadi ya hau tada guguwa, ganin haka yasa Banju wani juyi ya koma wani shirgegen Maciji🐉 blue mai matukar kauri da girma, wayyo karka so ka ga yadda wasu daga cikin masu kallo aka watse daga ciki kuwa har da mom, dan tace wlh wannan kallo ba da ita ba. Kokarin sara Banju ya hau kai wa Baffa Baffa na b'acewa a cikin iska, yayinda masu kallo aka kara ja baya ana darewa ana basu fili dan yau abun babba ne, an gwabza sosai tsakanin Baffa da Banju, da ya ga tabbas ba fa zai samu galaba a kan Baffa ba nan ya yanki wajan jama'a yana shirin ya kai musu sara dan kuwa ya tabbatar da Magaji zai kashesa! to dan haka a cikin wa innan dibbannin alumman gwara ya shafe ko da rabi ne, nan ya yi kansu gadan-gadan ganin haka yasa Nawaz fizgar hannun Aziza suka sa gudu tare da mutane, ganin yadda Banju ya yi kan alumma yasa Baffa haɗa hayaki ya kwashe mutanen ya zubar dasu gefe, jelarsa Banju yasa zai kwashi wasu kafin ya kwashe Baffa ya kuma kwashesu, ganin haka yasa ya buɗe bakinsa zaiyi musu b'arin ambaliyar wuta cikin hanzari Baffa yayi wani tsalle ya tashi sama, dan kuwa idan Banju yayi b'arin wutar nan za a mutu dayawa, kafin Banju yayi tuni Baffa ya haye saman kansa tare da zaro wani wuƙa ya dab'awa Banju a tsakiyar kai, cak Banju ya tsaya, a hankali ya fara sulalewa yana zama mutum har ya zama mutum gabadaya, yana gama zama mutum Baffa na zaune a saman wuyarsa da karamin wukar da ya dab'a masa, tsalle Baffa ya yi ya sauka daga wuyar Banju ya dirƙo akan kafafunsa ya juya baya ya maida hannunwansa ya rungume a bayansa. Da kyar Banju ya ce "Wuƙar Dafi!" Banju na faɗi wukar ta narke a cikin kan Banju ta b'ace bat, dan kuwa ba wuƙa bace kamar sauran wuƙaƙe, Baffa ne ya haɗa da hannunsa dan zuwan wannan rana, sharabbbb!! Banju ya zube a kasa, nan take ya kama da wuta har sai da yaci ya ƙone ƙurmuss!! Hamdala da Wani ihu da guɗa da al'umma suka saka suna fadin "Magaji! Magaji! Magaji!" suna daga hannu, wani hawaye ne ya tsiraro daga idon Baffa, da gudu Aziza ta tashi ta zo ta rungume mahaifinta tasa kuka, shima Baffa tamkar an cire masa wuƙa a maƙoro haka yakeji, Nawaz ne ya taso ya zo shima Baffa ha rungumesa, sannan ya karbi wuƙar ya damƙawa Aziza a hannunta yace a mallamaka mata dan tare sukayi yaƙin, nan aka kara sa ihu ana kabbara kafin kace me an daga baffa sama ana ambatar sunansa, sarki chubaɗo mai unguwan yankin kwana ori da kowa na yanki kwana murna sukeyi harda hawayen farinciki, sauran yankuna kuwa ji sukeyi ina ma ace Magaji a yankinsu yake, ko ba komai zasu samu karramawa da girmamawa da daukaka daga sauran manyan yankuna, haka aka dinga miƙawa Baffa hannu ana jinjinawa jarumtarsa. Da kyar suka saffe sukayi sallar magriba, wasu yankuna wa inda basu da nisa sai sun koma yankinsu wasu gobe zasu koma. Ranar yankin kwana wasai, duk majalisa kuwa hiran Magaji Bawa ake yi da yaransa Azima da Aziza, Jauro kuwa dan kunya da tsangwaman da ake masa yasa ya kasa fitowa. Washe gari bayan manyan yankuna sun karrama Baffa nan suka gaya masa ai a yankuna yanzu babban yanki shine yankin kwana, bayan an gama komai suka yi masu sallama, godiya sosai jama'ar kwana sukayi ma wa inda suka samu damar halartan wannan gayyata ta fafatawa. Bayan kwana uku da faruwar hakan komai ya zama daidai alhamdulillah Ma sha Allah. Yanzu Baffa ya maida hankalinsa a wajan yiwa Almazeen magani, sai da Almazeen ya shafe sati curr kafin ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa, a wannan lokacin su mom sunyi sabo da mutanen kauyen kwana fiye da tunanin mai tunani. Washe garin ranar da al'mazeen ya farka nan sarki chubaɗo ya tara su yace yana da magana, bayan kowa ya haɗu nan yake shaida bukatarsa na son sauƙa a kan kujerar mulkin yankin kwana, sannan ya bayyana Baffa a matsayin wanda zai mulke yankin kwana, girgiza kai Baffa ya hau yi kafin yace a'a tuni alumma sukace sunji sun gani, babu yadda Baffa ya iya dan kuwa bai so ba amma kowa ya nuna yana son Baffa ya mulke yankin kwana, haka sarki chubaɗo yasa aka rubuta sakon gayyata inda yankuna suka ce zasu zo, dan za ayi bikin da ba a taba yi ba na al'adun fulani. 🍃🍃🍃🍃🍃 Kamar yadda aka tanada haka kuwa ta kasance wajan karfe goma na safe aka fara bikin naɗa Baffa sarautar kwana, inda manyan yankuna da ƙananun yankuna duk sun zo, anyi walima Baffa ya samu alkairi ba ma iyakar shi daya ba harda jama'ar yankinsa, yankin kwana Allah ya ɗagata sama. Wajan irinsu biyu haka aka kammala taro lafiya, an yanka su shanaye dasu kaji da zabbi an sha kindirmo, kai taro dai tayi saidai muce Allah ya taya Baffa Magaji Bawa Arɗo riƙo. Da yamma Azima da Aziza suna zaune a bukkarsu, hajja kuma suna bukkarta dasu mom, bayan Aziza ta gama koyawa Azima karatu ta kalleta ta ce "Aziza dama ina son na tambayeki" gyara zama Aziza tayi tace "To inajin yar uwata" maganganun da Al'mazeen ya gaya mata a kunne ne take son Aziza ta fassara mata, dan ta kwashe maganganun tsaf a cikin kanta, dan haka ta gayawa Aziza tace ta fassara mata, dariya Aziza ta hau yi har tana riƙe ciki ta ce "Inyee! Kin faɗa soyayya ne?" haɗa rai Azima tayi tace ban son wulakanci idan ba zaki gaya min ba sai naje na tambayi mijinki Hamma Nawaz ko naje na tambayi mom" "Allah ya baki hakuri maida wuƙar" nan ta fassara mata abunda kalmomin ke nufi, wani murmushi Azima tayi tana rufe fuskarta da tafin hannunta, Aziza zatayi magana sukaji sallamarsu Nawaz sai da gabanta ya faɗi, su dai basu fito ba sunajin maganarsu dai a tsakar gida, Almazeen ne ya ce "Mom ya kamata mu koma gida, dan muje mu dubasu mu ga lafiyarsu, barin ma mu da muke da asibiti" mom ta ce "Nima na fara wannan tunani zuwa anjima zamuyi magana da Baban su Azizan" wani zaro ido Azima da Aziza sukayi bama su kadai ba harda Hajja, dan tasan za a kwashesu a tafi dasu ne tunda yara da mazajensu, kuka ta fara haɗiyewa, Almazeen ya kuma cewa "Mom ina yaran naki suke? Ya kamata dai yau su zo su kai mu yawo mu ga gari" mom ta ce "Hakane, Azima! Aziza!" a sanyaye suka amsa da na'am, barin ma Aziza damuwarta yafi bayyana ƙarara a fuskarta, a tare suka fito suka duƙa, mom tace "Ku dauko mayafi kuzo ku kai mazajenku yawon ganin gari" amsawa suka yi da to suka dau mayafin dama dogon abaya ce iri daya a jikinsu, mayafinsa suka dauka suka rufa kansu da shi, a kofar gida suka samu Almazeen da Nawaz sannan suka hau tafiya babu mai cewa qala, duk inda suka wuce sai an bisu da kallon burgewa ganin yadda suke tafiya tamkar wasu taurari masu haska sararin samaniya. Bayan sun kewaya dasu, Azima ta kalli Aziza tace "Ukhty muje rafin jimulo" a sanyaye Aziza ta amsa da to, dan tun lokacin da taji anyi maganar tafiya jikinta yayi sanyi dan idan tace tana son komawa tayi babban karya, suna isa rafin wani iska mai dadi da yake kaɗawa ga ruwa farin sol abun burgewa ga ganyaye kore shar kwance a wajan, "Wowww!" Nawaz da Almazeen suka furta, Azima tana satar kallon Almazeen, hannunta ya kama suka zagaya ta gefen rafin dan yana da bukatar suyi luv, dik da mugun kunyarsa takeji, suna barin wajan Nawaz ya maida idonsa kan Aziza wacce duk ta taburce kamar ma kuka take son yi, dan ita har yanzu bata taba ji Nawaz yace yana sonta ba, dan haka itama ba zata buɗe zuciyarta ba balle ta cutu, hannunta ya kama tayi saurin daga ido ta kallesa, janta yayi ya haɗata da bishiya murya a can kasa ya ce "What's the matter?" girgiza kai tayi sai kuma hawaye suka biyo baya, hannu yasa ya goge mata yace "Ba ki so ki koma ne ko?" shuru tayi, wani murmushi yaƙen takaici ya yi yana sakinta ya juya baya ya ce "Na faɗi daidai shiyasa kika ƙi cewa komai?, karki damu duk yadda kike so kiyi, bcox u are free now" ya faɗa kamar a ɗan zafafe, rungumesa ta baya Aziza tayi tasa kukanta mai sauti, rintse ido ya yi ya ce "Kamar dai na taba gaya miki bana son kuka ko? To sakeni!" sake riƙesa tayi, hannunta yaja suka isa bakin ruwan ya zauna ya zira kafafunsa a ciki, itama zaman tayi kusa da shi ta kamo hannunsa ta kifa kanta a kafadarsa, bata san lokacin da ta furta masa cewa "Hamma Nawaz, ka taba ji kana sona? Ko kawai tausayina kakeji?" ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya fuskanceta yace "Idan har zaki iya karanta abunda yake cikin idona, sannan ki auna bugun zuciyata" ya fada yana ɗora hannunta a saiti zuciyarsa dake bugawa da sauri "Zaki iya ba wa kanki amsa, idan hakan bai samu ba, ki bari idan muka koma kd zaki tabbatar" daga haka bai sake cewa da ita komai ba banda rungumeta da yayi. 💞💞💞💞 Almazeen suna zagayawa baya da Azima ya rungumeta sosai a jikinsa, rufe fuskarta tayi da kirjinsa tana murmushi tanajin wani bakon yanayi a tare da ita, sakinta Mazeen ya yi ya rungumeta ta baya ya ce "Na gama haukacewa na susuce a kan son...." shuru yayi ganin tana ta wani aikin rufe fuska, bakinsa yasa a saitin kunnenta yace "Wai ni wannan kunyar na miye ne? tinda na farka ake guduna, ko dan sabida daren...." bai karasa ba ta jiyo ta sauri ta rike bakinsa tana shigewa jikinsa, murmushi yayi yace to faɗamin "Ana sona?" ɗago kai tayi tasa idonta a na shi ta ce "Idan ban furta hakan ba na zama butulu! wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin tawa, miye ribata idan ban so shi ba, ance tukaicin so kauna, sabida haka ina kaunarka Hamma Mazeen" wani runguma Mazeen yayiwa Azima cike da so, kafin ya haɗe bakinsa da nata ya hau bata hot kiss, Azima tayi alkawari ba zata taba juyawa Mazeen baya ba kamar yadda shi ma bai juya mata ba a lokacin da take abun gudu a wajan mutane, shiyasa ko da yake romantic dinta bata yi yunkurin dakatar da shi ba, tsayuwa ce ta gagaresu suka zube kasa, murzanta yake yi cikin salo da shaukin kauna, Azima ganin hankalinsa ya fara gushewa ne ya sakata zare jikinta daga na shi,yayi saurin riƙota ta ce "Don Allah Hamma, ka duba inda muke,kuma ma ai" sai kuma tayi shuru, saurin saita natsuwarsa Almazeen ya yi, amma gaskiya ba zasu kara sati a garin nan ba zasu koma dan ya samu yaji dadin bai ji ba a daren farko dan wuya kawai yaci. Tashi yayi ya kama hannunta ya ɗagata tsaye, yace "Muje gida" riƙesa tayi tace "Kayi fushi ne?" ɗan murmushi yayi ya girgiza mata kai alaman a'a, wajan su Nawaz suka dawo har yanzu suna zaune a bakin ruwa yana rungume da Aziza, Almazeen ya ce "To romio and Juliet muje gida lokacin sallar magriba yayi" Nawaz yace "Okay Laila da Majnun" dariya Almazeen yayi dan zuciyarsa fari sol. Gida Suka tafi, bayan sallar isha'i mom ke gayawa su Nawaz yadda sukayi da Babansu Aziza kuma itama tayi na'am da maganarsa na cewa a dan barsu Azima da Aziza tukunna, su zasu tafi gobe, Almazeen da Nawaz kamar su kurma ihu, Nawaz da gajen hakuri yace "Har na kwana nawa?" mom tace ungo nan naka🖐🏻 "Har na tsawon wata daya,ni kuma nace a barsu suyi wata biyu tunda alfarma suka nema,kuma ai gaskiya ne tinda sun jima basu ne, yanzu kuma zama na dindindin zasuyi daku" "Haba dan Allah mom, yanzu dake za a yanke wannan shawaran?" cewar mazeen,mom tace bana son rashin kunya, maza ku tashi ku fara shiryawa, a zuciye Nawaz ya fice Almazeen ya bisa a baya. Washe gari asubanci sukayi, kaff jama'ar kwana aka fito yi musu sallama, Almazeen ne kawai yayi sallama da Azima inda ya jima yana tsotsar bakinta, Nawaz kuwa ya ƙi kallon Aziza dan yace itama harda haɗin bakinta dama ba son komawa take yi ba. Baffa ya haɗawa su Mom kaya sha tara ta arziki yayinda suke zubawa juna godiya cikin mutunci da mutuntawa, haka Baffa ya rungumi su Almazeen da Nawaz, sukayi musabaha da Malam Yunusa da Alhaji Karami, su Inna wuro ma sunyi wa mom da Maman beenah abun arziki, mom tace "Dan Allah wata rana ku kawo mana ziyara, da sunyi wata daya kuma mazajensu zasu zo su daukesu" "In sha Allah" mota suka shiga aka dinga ɗaga musu hannu, da gudu Nawaz ya figi motar Aziza ta fito itama da gudu tana daga masa hannu ya hangeta ta glass din mota amma sai ya kara gudun motar, cikin rashin jin dadi tin daga Azima har Azizan suka juya jiki a sanyaye, a ranar haka suka wuni zuciyarsu babu dadi amma suna zuba hira da wasa da dariya da Hajjarsu,yayinda Yawuro ta fara musu gyara tana tsumasu dan tana so ace kafin nan da wata dayan nan sun sama zam-zam dasu, idan mazajensu suka kusancesu basu ba kara tunanin wata mace. @@@@ Sabida gudun da suke yi yasa biyar na yamma suka fice daga jeji suka b'illa titi, yau ma sai da suka kara kwana cikin garin yola kafin da washe gari suka kama hanyar kd, suna isa mom ta kira sultana tace mata sun dawo, wani ihu da murna Sultana tayi a waya mom ta bata labarin abunda ya faru, bata gama ji ba zumudi yasa ta katse wayar ta kalli Khalil dake danna waya tace "Dear su mom sun dawo" da murna a fuskarsa yace "Alhamdulillah" "Dear tashi mu tafi ina son ganin Aziza" "Oh Allah sultana ki bari su huta sai muje da daddare" "O'o ni kawai ka tashi mu tafi yanzu sai ka dawo ka daukeni da daddaren" ta fada tana buga kafafunta a kasa" hararanta yayi yace "ai saiki dauko mayafinki" kiss ta sauke masa akumatu tana godiya da gudu ta hau sama dan dauka mayafinta ta sauko a mota ta samesa ya tada suka nufi gidansu. 🍃🍃🍃🍃 MOMYN AHLAN✍🏻 GARKUWAR MACIZAI🐍😂 [4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *PAID.* 🅿️=7️⃣1️⃣↪️7️⃣2️⃣🔚🔚🔚🔚 ALHAMDULILLAH!. Suna isa da gudu tayi cikin gidan tana fadin "Oyoyo Mom! Oyoyo Anty Aziza!" mom dake zaune a parlour ta ce "Sai dai ni Amma Aziza kam tana garinsu" turus sultana ta tsaya tace "Bangane tana garinsu ba mom? Sakinta Yaya yayi?" "Taya zai saketa? Ba yanzu zasu dawo bane sai sun kwana biyu,mahaifinsu ne ya roƙi alfarma a barsu" cikin rashin jin dadi Sultana ta zauna tace "Wayyo wlh banji dadi ba mom, to ba komai Allah ya dawo dasu lafiya, inasu Yaya Nawaz da Yaya Almazeen?" "Muna isowa basu zauna ba asibiti suka wuce" "Ayya Allah Sarki! Ohh wayyo Mom na bar Khalil a waje ashe" Mom tace "Shi dai yaso zaman waje ai khalil ba baƙo bane" "Wlh kuwa mom kyaleta iyayi take ji da shi waya na tsayayi" cewar khalil da yake shigowa ya duƙa ya gaishe da mom ta amsa tana dariya,sultana tace "Oh wato ma haka zaka ce ko? Ba komai ai" "To dan Allah mom ki ji ni da 'ya fa, to me nace?" mom tace "Ahh kai kam baka ce komai ba" khalil yayi dariya yana fadin "Inasu Nawaz?" "Sunje asibiti,ai muna isowa basu zauna ba" "Ayya Allah Sarki, to bari na wuce mom" "Ah to ita Sultanan fa?" "Zan dawo na dauketa da daddare" khalil ya fada yana ficewa, sultana ta miƙe a dogon kujera tana fadin "Ohh mom korata kikeyi?" "To nan gidanki ne? Me zaki zauna ki min" "To yau ma a nan zan kwana" "ashe da rabon zaki kwana a wajan gate" mom ta fada tana hawa sama, sultana dakin Aziza ta shiga tana tuno abubuwa da dama har bacci ya kwasheta, kamar yadda Khalil ya faɗa bayan isha'i yazo ya dauki sultana, su Nawaz basu dawo ba sai wajan goma, sai da sukayi wanka kafin suka shiga wajan mom a lokacin tana waya a kawo mata 'yar aiki wacce zata dinga tayata aiki da zama dan ita daya ne, sai da ta gama wayarta ta fuskancesu ta ce "Sannunku da dawowa fatan komai lafiya?" Almazeen ne yace "E mom komai lafiya alhamdulillah! Amma muna kewan matayenmu,bamu san halin da suke ciki ba ,su ma basu san wanda muke ciki ba" mom tayi murmushi tace "Haba dai ai wata biyu kamar kwana biyu ne a wajan ubangiji" sai a sannan Nawaz ya yi magana fuskarsa a haɗe "Mom wata biyu kuma? Ba wata daya naji kince ba? Baffa ma fa wata daya naji yace" mom tace "E wata daya ne nice nace suyi wata biyu" tashi Nawaz yayi zai fice mom tace "Akwai abinci a dinning" "Bana jin yunwa" yana gama fadi ya fita, Almazeen shi ma tashi yayi mom tace "Kana nan ne tukunna?" "A'a mom zan tafi gobe naje na duba asibitina nima, ba zan dawo nan kusa ba sai an kwana biyu idan zamuje kwaso matanmu" mom tace "Ya kamata a haɗa musu lefe ayi shagalin biki, ya kasance kafin su dawo an tanada musu komai, da kuma gida wajan zama, shin a gidanka na kano Azima zata zauna? Kasan fa yanzu ba kamar da bane, Aziman yanzu ba jin dadin zama zatayi dasu Hajiya Lawiza da yaransu ba, Azima kuma matarka ce amanace a hannunka a san abun yi gaskiya" komawa Almazeen yayi ya zauna yace "Mom ko da a kano na zauna da Azima wlh su Maman Hanan zasuje su takura mata, inaga gidan dake kasan unguwan nan zanje na taya naji, tunda babu abunda nake yi a kanon idan kuma ta asibitina ne ni zan iya zuwa ina kwana biyu ina dawowa" mom tace "Hanya zai aureka kenan, to ba matsala Allah ya zaba mana abunda yafi alkairi, ka ga shi abokin naka ba shi da matsala a nan zasu zauna dani" Almzeen yace "Ai hakan yafi mom shiyasa nima zan dawo cikin masu sona kawai" mom tayi murmushi, sun jima suna tattaunawa har wajan sha biyu kafin ya yiwa mom sai da safe ya tafi, a kwance ya samu Nawaz ya ɗora hannu a fuskarsa alaman tunani, zama shima ya yi, Nawaz yace "An rabaka da matarka amma me ka zauna mom ke gaya maka? Ai wlh na fahimci mom idam na ci gaba da zama zata iya cewa su yi wata shidda ma" da sauri Almazeen yace "Kamar kuwa ka sani cewa tayi sai sunyi shekara" wani zabura Nawaz ya yi yace "She mene?" "Shekara" Almazeen ya fada yana dariya, tsaki Nawaz ya yi, sai da mazeen ya gama dariyarsa kafin ya basa labarin yadda sukayi da Mom, Allah yasa mu dace, Nawaz ya faɗi tare da shigewa daki ya kwanta, amma kamar jiya ya kasa bacci dan kuwa sun bar wa juna abin tuni. Ta bangarensu Azima da Aziza yadda mazajen nasu ke ji a kansu haka suma suke ji a kansu. Da washe gari Almazeen na wanka dan zai tafi kano yau Nawaz na danna system, wayar Almazeen ne yayi kara yayi kara yana dubawa yaga Alisha "Mayya!" Nawaz ya fadi a fusace yana ci gaba da aikinsa,jin kiran wayar takeyi babu fa shi yasa ya jawo wayar zai daga wata daraba ta faɗo masa, murmushi yayi tunowa da haukan kishin Alisha dan haka Nawaz ya daga kafin Alisha tayi magana yace "Wai ke baki san yayi aure bane?" "What!?" "Yes daidaine abunda kikaji na fadi, yanzu baya yayinki! Idan kuma baki yarda ba zan gwada miki kiji dan ki tabbatar da abunda nake gaya miki sabida...." maganar Nawaz ne ya tsaya sakamakon fitowa da Almazeen yayi, Nawaz yace "Allah ya taimaki Majnun na Azima! wai ni kam ina Alisha ne Almazeen?" mazeen ya riƙe kai yace "Wlh nikam na ma mance da ita" "Kar dai kace min bata san kayi aure ba?" "Wlh bata sani ba,har shakkar gaya mata nake dan ban san yadda zata dau lamarin ba" Nawaz yace "To ai ga shi sai ka gaya mata" ya fada yana mikawa Almazeen waya, wani zare ido Almazeen yayi Nawaz kuwa ko a jikinsa, ba yadda ya iya haka ya karbi wayar yana shirin yi mata bayani ta wankesa tass a kan cewa ya ci amanarta kuma babu ita babu shi, tana gama gaya masa ta ajiye wayarta. "Me kenan kayi haka Nawaz?" "Me kuwa nayi? Ita fa ta kira! Cika min kunne take,kuma ma ai taimakonka nayi" ya fada yana ci gaba da aikinsa, Allah ya kyauta Almazeen ya fadi Nawaz ya amsa da amin, yana gama shirinsa ya shiga ya yiwa mom sallama a lokacin an kawo mata wata mai aiki, Allah ya tsare ta masa ya amsa amin sannan ya shiga motarsa sai kano. 🍃🍃🍃🍃🍃🍃 Haka suka ci gaba da rayuwarsu amma hankalinsu yana kan matayensu wanda suma kullum acikin tunanin mazajensu suke, ga shi babu netwrk babu waya bare a ji muryan juna ko hankali zai kwanta, a daddafe akayi sati biyu, Almazeen yaji ina sam ya kasa hakuri ya tattaro yazo Kd yacewa mom zasu je dauko matayensu Mom tace aa suyi hakuri dai a cike sati biyun, da kyar sukayi sati uku hakurin Nawaz ya kare ya shirya tafiya ya cewa mom zaije kano, mom ta tambayesa lafiya kuwa yace mata lafiya lau kawai zaije bikin wani abokinsu ne dama kuma yana da tiyatan da zaiyi a can, Allah ya kiyaye hanya a dawo lafiya mom ta masa Nawaz yana zuwa kano dama tare suka shirya tafiyarsu shida Mazeen nan suka dauki hanyar yola ba tare da sanin mom ba. Sai da suka kwana da washe gari suka yanki jejin kwana, kasancewar Nawaz ya ƙware a driving musamman ta fannin gudu yasa wajan biyar suna cikin yankin kwana, tun shigowar motarsu yara suka hau bi, a lokacin kuma Azima da Aziza suna kwance a bukka Hajja tana gidan Arɗo, Azima ta tsokani Aziza, Aziza ta hau binta da gudu zata daketa kanta ko dankwali babu, a wannan gudun ne suka fito har waje daidai a kan idon Nawaz da Almazeen, ga shi sun wani kara bulbul dasu sun ciko, wani daci Nawaz ya hadiye yana wurgawa Aziza harara, ganin basu san da zuwan su bane yasa Nawaz danna horn da karfi a firgice suka juyo, ko wacce idonta a cikin na mijinta ya sauka, gaban Aziza ne ya buga ganin hararan da Nawaz ke binta da shi, ita kam shikenan ta shiga uku, ranar da zai tafi ba ayi rabuwar dadi ba, yau kuma ya dawo za a fara rigima,tukunna ma me ya kawosu? Ai ba yau bane ranar da ya kamata ace sunzo daukarsu, Azima ce tayi karfin halin murmushi duk da itama zata iya cewa ba yanzu bane ya kamata ace sun dawo daukarsu ba, Nawaz ne ya hangi wani ɗan fullo rataye da sandarsa a wuyarsa yana tahowa ga Aziza kai ba dankwali tsoro kuma yasa ta kasa gaba ta kasa baya, da sauri Nawaz ya fito a motar yazo ya ja hannun Aziza suka wuce gida, ganin Nawaz ya fita yasa Azima shiga motar da sauri tana yiwa Almazeen oyoyo. yana rungumeta ya saki ni'imartacciyar ajiyar zuciya "I miss u!" yaji ta fadi, saurin sakinta yayi yace "Wow! Aziza ta koya miki kenan!" gya ɗa kai tayi tana murmushi tace "Yanzu nima inajin yaren sosai" "To yayi kyau, ina Baffanmu da Hajjarmu?" "Baffa yana fada,Hajja kuma taje gidan Arɗo, amma na tabbata yanzu labari yaje garesu kunzo yanzu zaka ga hajja har ma da Baffan" "To kafin su zo ,mu sha soyayya a mota tinda Nawaz ya ja Aziza ciki" ya fada yana shirin kama bakinta tace "Amma naga kamar da fushi ya jamin yar uwata,kuma wlh laifi nane, dan tana kwance na tsokaneta" jinjina kai Almazeen yayi yace "Nima naji haushin wannan tsalle-tsallen naku, kawai murna da farincikin ganinki ne ya danne fushina, amma shi baya iya control ɗin fushinsa sam, dan Allah karki sake" a sanyaye Azima tace "To kayi hakuri Hamma Mazeen" "Ai ya wuce" ya faɗa yana shafota. Suna shiga cikin gidan, bukkarsu ya wuce da ita, suna shiga ciki ya saki hannunta a masifance yace "Ashe baki da hankali? Miye haka? Au ashe da bamu nan abunda kukayi kenan? Guje-guje? Wannan ai kauyenci ne! Da Aurenmu a kanku amma kuke guje-guje ga karti na wucewa, ke da shike kece isassa kai ba dankwali ko? Ya miki kyau ki shirya gobe zamu tafi" zaro ido Aziza tayi kwalla na cika a idonta kafin tayi magana yace "Okay wato baki son tafiya sabida can babu maza da guje-guje ko?" yana cikin faɗa da masifa ta rungumesa ta ce "Sorry!" tana fadi kuwa yayi shuru da fadan nasa, yayi missing dinta dan haka yasa hannu ya rungumeta yace "Karki sake, hakan da na gani ya taba min zuciya" "In sha Allah, kayi hakuri" zaiyi magana suka ji sallamarsu Hajja dasu Almazeen da Azima dasu inna wuro, fitowa Nawaz da Aziza sukayi inna wuro tace "Ohh Allah wato kai har ka wuce daki da ita? Wai wai wai kar ayi abun kunya bari Magaji yazo a baku matayenku" Nawaz da Almazeen sukayi murmushi nan aka hau gaisawa, Hajja tana tambaya ya mom, suka amsa da tana lafiya tama ce a gaishesu (kaji su Almazeen da Nawaz da karya mom da bata san sunzo ba). Bayan sun gama gaisawa da matan suka wuce wajan Baffa a fada, nan aka hau gaisawa suka shaidawa Baffa sunzo daukar matansu ne zasu tafi gobe,Baffa Mandi da Ardo da sarkin yankin kwana mai murabus chubado suka hau dariya, ardo yace a basu matansu kawai su tafi, nan suka ce su gobe suke son komawa Baffa yace ba damuwa Allah ya kaimu. Ko da suka zo hira Nawaz da Aziza basu yi wani dogon hira ba ya jaddada mata akan su shirya da wuri, su Almazeen ne da Azima aka sha luv shima ya gaya mata su shirya da wuri. Asubanci suka ku ma yi inda jama'a aka fito rakasu, hajja kam taki fitowa rakasu, Azima da Aziza kuka kamar ransu zai fita,itama Hajja kukan takeyi, su Inna wuro ne suka yi musu nasiha akan su bi Allah da Manzon Allah sannan su bi mazajensu,yi nayi bari na bari shine aure, da haka suka shiga mota ana daga musu hannu nan Nawaz yaja motar da gudu suka hau tafiya, a hanya Almazeen ne ya rarrashi Azimansa, Aziza kuwa da tayi kukanta da kanta ta bawa kanta hakuri tayi shuru. Sai shidda suka fice a jeji, kamar yadda suka saba hotel suka kama, ko a daki Nawaz baccinsa yayi, Azizan ma haka, Almazeen kuwa yaso kashe arnan sama Azima ta hau masa kuka dole ya kyaleta ya lallatsata kawai ya barta, ko da mom sukayi waya da Nawaz da daddare a lokacin suna yola take ce masa ta kirasa bai shiga ba yace mata ai sun shiga tiyata ne gobe ma suna nan dawowa, Allah ya dawo dasu lafiya mom tace. Da safe sai wajan takwas kafin suka sake kama hanya a wannan lokacin anyi canji Almazeen ne ke driving Nawaz na zaune a gefe Azima da Aziza suna zaune a bayan mota, jifa-jifa suna ɗan taba hira. Sai wajan hudu suka shigo garin gwamna, basu zarce ko ina ba sai gida, da sallama suka shiga a lokacin mom na magana da sabuwar mai aikinta Lami taji sallamarsu Nawaz, amsawa tayi tana juyowa sai ganinsu Azima da Aziza tayi, da mugun mamaki mom ke kallonsu kafin tace "Dama dauko su Aziza kukaje yi ne?" Almazeen ya hau sosa kai, Nawaz yace "E wlh mom, cewa akayi Aziza nata kuka tana so ta dawo ta ganni tayi kewarki,ko zakice ba haka bane?" ya fada yana kallon Aziza wacce tayi narai-narai da ido tace "Wlh mom ba haka bane" "Ohh nayi karya kenan?" "Ni dai ban ce ba, amma wlh ni banyi kuka ba ko Azima?" Azima ta kunshe dariya tace "Ni dai ban sani ba" mom tace kyalesu na san ba zaki ce ba, to sannunku da kokari ance ku bar yara suyi wata kunje kun kwasosu ai shikenan, Azima Aziza ku hau sama dakin sultana na da, suka amsa da to sannan suka hau sama, mom tace "Maganar lefensu dama jibi ne za a kawo,shagalin bikin fa?" "Mom dan Allah a bar wani maganar shagali" cewar Nawaz,mom tasan halinsa duk wa innan abubuwan bai damesa ba, mom tace gobe kasa a kwashe kayan part dinka a kawo sabbi dan dama munyi wannan maganar dasu Baffan Aziza da yan uwanta kafin mu dawo, na gaya musu mu yaran kawai mukeso, amma dik da haka mahaifinsu ya bada garken shanu biyu na Azima da kuma Aziza yace dai ba dadi ace yara ba a ga kayan da yan uwansu suka musu ba, bare kuma ace akwai uwa da uba, na karba ne dan ya fimu gaskiya, dan haka Almazeen ya maganar gidan naka?" "Eh mom an gama magana gobe ma za a iya zuwa ayi jere dan haka zamuyi other tare da Nawaz" "Eh hakan ma yayi, ai da wasu daga yan uwansu sunzo sun ga inda yaransu zasu zauna, ko da yake ba damuwa zasu zo wata rana" nan su mom suka gama tattaunawa, bayan sallar magriba Aziza ta cewa mom zataje gidan anty sultana, mom tace je ki tambayi mijinki, dabadin tana son zuwa gidan Sultanan ba da ta hakura, amma haka tayi jahadi taje part dinsa tace masa zataje gidan sultana, ga mamakinta yace mata ta shirya ya kaita, da murna kuwa suka shirya harda Azima, a tare suka je yiwa mom cewa sun tafi,mom tace "Azima kin gayawa Almazeen cewa zakije?" "A'a mom, to karki fita a gidan nan har sai kin gaya masa" "Mom baya nan" Azima ta fada kamar zatayi kuka A waya mom ta kira Almazeen ta gaya masa azima zasuje gidan sultana yace ba komai sai sun dawo, a tare suka fito suka shiga mota dan Nawaz na mota,gidan sultana ya kaisu, da sallama suka shiga sultana na saka turaren wuta ganin Aziza yasa ta saki ihu tana rungumeta cike da kewar juna, haka ma ta rungume Azima,nan suka baje a parlour suna hira sultana ta kawo musu ruwa da lemo nan aka hau labari, har sai da Nawaz yazo daukarsu karfe tara kamar karsu rabu, nan Nawaz suka gaisa da khalil sannan ya cewa su Aziza su shiga su tafi gida. @@@@@@@@ Kamar yadda suka tsara da washe gari aka zo aka canza kayan parlour da daki aka saka sabbi,mom ce ta tambayesu ra'ayin kala, Aziza tace pick Azima tace purple, kai mom tayi kokari sai son barka Ma sha Allah, a ranar da yamma ta kira kawayenta aka zo aka raka Azima gidanta da babu nisa sosai a nan kd dan Mazeen yace ba zai kai Azima can kano ba, bayan an dawo daga rakiyar Azima mom da kanta ta dauki Aziza ta kaita part din Nawaz,kamar yadda tayiwa Azima Nasiha haka ta yiwa Aziza, daga nan ta tashi taje tayi kwanciyarta, mom na fita Aziza ta sulale kafin Nawaz yazo ta koma dakinta na da tare da Lami suka kwana, haka Nawaz yayi neman duniya bai ga Aziza ba. @@@@@@ AL-MAZEEN kuwa yau yake ango dan dadin da baiji ba ranar yau ya shata a wajan Azima dan kuwa ta shayar dashi ni'ima, bai sarara mata ba ko kaɗan ita kam ta miƙa wuya tabi dama kuma sun sha gyara, da washe gari ma haka ta ga tattalin soyayya da kauna. Aziza kuwa wasan boya suka fara da Nawaz a gidan, haka zai wuni bai ganta ba a kwana bai ganta ba, har aka kwashe sati daya yana neman hanyar da zai damƙeta zata gane bata da wayo dan ya ga alama ta rainasa. @@@@@@ Yana kwance waya ta shigo masa yana dubawa ya ga daga outside ne, dagawa yayi nan aka shaida masa ana nemansu a america akwai wani course din da zasu sakeyi na shekara daya, wani tunani ne ya faɗo masa nan yace ya amince zasu zo, Almazeen ya kira ya shaida masa halin da ake ciki, Almazeen ma amincewa yayi, sannan Nawaz yaje ya samu mom da maganar sannan ya gaya mata zasu tafi da matansu, mom tace babu damuwa sai suyi musu passport yaushe ne tafiyar! Nawaz yace nan da sati daya amma ranar labara zasu tafi abuja a can za ayi musu komai, Allah ya kaimu mom tace. Labari ne ya iske su Azima da Aziza zasu tafi america, wai! kirjin Aziza kamar zai faɗo kasa dan firgici, Azima kam an zama yar hannu. Sai ranar da zasu tafi abuja Nawaz ya sa Aziza a idonsa, suna hada ido kwafa ya mata, mom ta rakosu har bakin mota tana musu adduar Allah ya tsare. Awa biyu da rabi ya kaisu Abuja a ranar aka yiwa su Azima da Aziza komai kasancewar da kudi a kasa, da washe gari kuma suka ɗaga kasar waje. @@@@ Sun isa lafiya inda sukayi waya da mom suka ce mata sun isa lafiya, gidan da suka sauka yanzu mai part biyu ne dan haka Almazeen ya ja matarsa suka nufi part daya, Nawaz ma hannun Aziza yaja suka nufi dayan, suna shiga bedroom ya tureta a gado ya bita ya danne yace "Kin rainani ko? Yau zamu raba raini, ki tashi ki watsa ruwa yau zaki bani hakkina!" ido waje Aziza ke kallon Nawaz shi kuwa ya ki yarda ma su haɗa ido. Kamar yadda yace a daren yau ya rafketa, taci bakar wuya a hannunsa dan kuwa bai tausaya mata ba, a ranar shima ya fanshe wahalarsa, sannan ya gaya mata irin buhun kaunar da yake mata. 🔚🔚🔚🔚 Ma sha Allah haka rayuwarsu ta fara a kasar america, suna da sati biyu a kasar suka nema musu skull suka ci gaba da yi har da Azima wacce ita ɗorawa kawai tayi. Soyayya sukeyi mai tsafta mai cike da so da tattali, suna da wata hudu, a tare Azima da Aziza suka fara laulayin ciki, murna a wajansu Almazeen da Nawaz abun ba a cewa komai, kuma basu gayawa mom ba, a wannan wata hudun ne suka samu hutun wata daya suka ce zasu zo su gida nigeria akwai aikin da zasuyi, amma basu taho dasu Azima da Aziza ba sabida skull a can suka barsu. Sai da suka zo sukayi wata dayan nan kafin suka koma suka ci gaba da rainon ciki a tare, ko da wani lokaci suna tare da mom a waya da kuma sultana, yanzu damuwarsu ɗaya shine sunyi kewar Yankin kwana da Baffansu da Hajjarsu. Mom bata san cewa suna da ciki ba har sai da cikin ya shiga watan haihuwarsa tukunna ranar suna video call mom ta ga yara da ciki nan ta rufe su Nawaz da faɗa ta musu kaca-kaca kuma tace maza su dawo dasu su haihu a gida, da washe gari kuwa suka sauka a airport din abuja a ranar suka wuto kaduna, bayan dawowarsu da sati biyu Aziza ce ta fara nakuɗa inda akayi da ita ALWAZ HOSPITAL su Nawaz basu dawo ba suna can, amma jin labarin matarsa na nakuda yace ya bawa kwararrun likitocin asibitinsa umarni dasu tsaya a kan matarsa. Bayan wahalhalun nakuɗa Aziza ta haifo yarta kyakkyawar gaske, murna a wajan mom sai son barka haka akayiwa baby hoto aka turawa babanta,Nawaz kamar ya b'ace ya gansa kusa da matarsa da yarsa, shi kuwa Almazeen yana adduar Allah shi ma ya sauke ta shi matar lafiya, Aziza ta haihu da kwana uku itama Azima nata haihuwar yace ga shi nan tafe, haka itama tasha wahala ta haifi yarta mace kyakkyawa, mom kamar tasa kanta a cikin fridge dan murna. Nan iyayen yara sukace a hada suna ayisa rana daya, mom tace to kawai ayi sunar ranar jumma'a. Ana gobe suna kawai sai ga Al'umma yankin kwana a kaduna, tsananin murna su Azima da Aziza kamar zasuyi hauka, haka suka rungume Hajja gagam a jikinsu, washe gari suna yarinyar Almazeen taci sunan mahafiyarsa Ɗahira amma za a dinga kiranta da AYRAH yarinyar Aziza kuwa sunan mom aka saka mata za a dinga ce mata AYZAH anyi suna lafiya an watsa lafiya sai dai fatan Allah ya raya mana Ayrah da Ayzah, duk yadda ubanninsu suka so zuwa Allah baiyi ba sai nan da wata daya, kafin lokacin yara ai sunyi wayo dama yaran yanzu da wayonsu ake haihuwarsu. Satinsu Hajja biyu nan ma da kyar mom ta sakasu sukayi sannan suka musu sallama suka koma. Haka Azima da Aziza suka ci gaba da rainon yaransu masu kyau dasu kamar iyayensu. Wata daya na cika su Nawaz suka dawo, ranar dasuka ga yaran basu iya bacci ba, dan murna. Haka suka ci gaba da rainon yaransu, sai da Ayrah sukayi wata uku kafin Allah ya sauki sultana ta samu ɗa namiji ranar suna aka saka masa suna Walid. Sai da su Ayrah da Ayzah suka yi wayo sosai kafin suka shirya tafiya yankin kwana harda sultana zasu tafi @@@@@@ Sadda suka isa yola sam ranar basu kama hotel ba, ga mamakin Azima da Aziza yankin da ake yanka a shiga jeji ya koma titi ɗoɗar, mamakinsu bai gama karewa ba sai da suka ga cikin yankinsu ya koma birni ga wutar nepa ga asibiti ga makaranta, wanda yasan yankin kwana a da yazo yace yanzu shine wannan za ace karya ne. Basu gama sarewa ba sai da suka ga mota ya parker a wani hamshakin gida, ashe wai gidan Baffa ne, kamar an kashe fanka haka su Azima da Aziza suka fito a mota, Sultana kuwa sai dariya takeyi tana fadin "Ohh wlh da ace banzo ba kafin ayi wannan aikin ai da na bata" da mamaki Aziza tace "dama kin zo Anty Sulty?" "Eh mana munzo har dasu mom lokacin kuna america dasu Hajja sukazo sukayi kwana biyu a lokacin da za a cire kwalta" Nawaz yace to jawabi zaku shigo ko zaku tsaya surutu" ya fada yana daukar yarsa suka shige, da gudu Azima da Aziza suka rungume Hajja, bayan an gaisa Baffa ya shigo Azima da Aziza suna hada baki wajan tambayar Baffa wannan abun arziki, nan Baffa yake gaya musu ai Mazeen da Nawaz ne sukazo suka maida garin ya zama birni yanzu haka wasu yankuna suna zuwa yankin kwana kallo, duk ta sanadin Magaji Bawa da yaransa Azima da Aziza,harta jauro ya zubar da hassadarsa arziki yake ci, nan Baffa ya dinga gaya musu abun arziki dasu Mazeen da Nawaz sukayi, hakika sunyi farinciki sunyi murna inda son mazajen nasu ke kara ninkuwa a zuciyarsu, sun zama tamkar wasu super'star a yankinsu na kwana. @@@@@@ Sai dare can su Nawaz suka dawo suka cewa su Azima da Aziza su zo su tafi gidansu. Ashe sun gina gida a garin madaidaci idan sunzo hutu nan zasu dinga zama dan zasu dinga zuwa yanzu a kai a kai lokaci zuwa lokaci. Cikin kuka ko wacce ta rungume mijinta tana gaya masa tsananin so da kaunar da take masa, kamar yadda suma mazajen ta bangarensu hakan yake, daga nan ko wanne ya dauki matarsa da 'yarsa sukayi daki. 🍃🍃🍃🍃 TAMMAT BI HAMDULILLAH *ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA DA KA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTAFI ALLAH NA GODE MAKA DA KA BANI IKON GAMATA lafiya, YA ALLAH ABUNDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH KA BAMU LADANTA,KUSKURENA ALLAH YA YAFE MIN.* *INA TAYA YAN UWANA MUSULMAI MURNAN SHIGANMU WANNAN WATA MAI ALBARKA, ALLAH YA YAFE MANA YA AMSHI IBADUNMU, ALLAH YASA A MUYI LAFIA MU GAMA LAFIYA, DAN ISAR ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM* SAI KUNJINI A SABON LITTAFINA BAYAN SALLAH DA SATI DAYA IDAN RAI YA KAIMU IN SHA ALLAH, SUNAN LITTAFIN *AHLAN* AKAN FARASHIN DARI BIYU. BISSALAM. MOMYN AHLAN GARKUWAR MACIZAI🐍🐍