*RIBAR UWA* Na Azizat Chapter 01 *Shimfiɗa* Friday 8:12pm in Boston, Massachusetts, USA. Haka kawai jikinta yai sanyi, lokaci guda ta ji komai ya fita a ranta. Hatta littafin da ke hannunta sai da ya faɗi ƙasa saboda yadda hankalinta ya kauce daga karatun. Wani sanyi ne ya shigeta lokaci guda, zuciyarta ya ma ta wani nauyi. Ta dafe ƙirjinta tana maimaita kalmar Hasbunallahu wa ni'imal Wakeel. A hankali ta fara jin sauƙi bayan ta shafe kusan minti biyu tana maimaitawa, duk da haka ba ta dena maimata waɗannan kalmomi ma su ɗimbin lada ba. "Excuse me, are you ok?" muryan wanda ke gefenta ya ankarar da ita daga halin da ta ke ciki. Ta juyar da kanta a hankali zuwa gefen sa tana mai gyaɗa ma sa kai domin ta tabbatar ma sa da lafiyarta ƙalau. Ya miƙa ma ta littafin ta da ya faɗi yana mai nuna littafin yana da daɗi shima ya taɓa karantawa. Ta ƙarɓi littafin tareda furta ma sa kalmar Thanks. Matashin Baturen da ke zaune a gefenta wanda ba zai wuce shekaru talatin da biyar zuwa da takwas ba yai ma ta murmushi sannan ya cigaba da kallon window. Ta maida littafin cikin jakarta domin ba ta ganin za ta iya cigaba da karanta shi a wannan baƙon yanayi da ta tsinci kanta a ciki lokaci guda. Littafin mai suna The catcher in the rye da ta ke karantawa tun kwana huɗu da su ka wuce ba ƙaramin jin daɗin karatun sa ta ke ba, ta yi nisa da karatun dan lokacin da ta shiga motar bus da zai kai ta anguwar ta su ta Mission Hill daga Roxbury ta kusa ƙarisa karanta shi bai fi shafuka shida zuwa biyar ya rage ba amma lokaci guda komai ya chanja ma ta. Baƙon yanayin da ta tsinci kanta a ciki ya sa ta yi kewar gida musamman mahaifiyarta wanda ta ke matuƙar so a rayuwarta. Har aka isa anguwar na su ba ta dena addu'a cikin zuciyarta ba. Ta sauko daga bus ɗin ta dinga takawa a hankali har ta kai gida. Alwala ta yi ta yi sallah sannan ta hau kan gado ta kwanta saboda yadda takejin yanayin jikinta ba daɗi. A hankali bacci mai daɗi yai gaba da ita bayan ta shafa addu'ar bacci... Daddaɗan mafarkin da ta yi a daren na jiya ya sa har kusan makara ta yi da asuba. Lokacin da ta yi sallah ta jima tana yiwa iyayenta addu'a tareda sauran al'ummar musulmi. Ta shirya a gurguje cikin doguwar rigan atamfa wanda ke da kalar blue da fari, ta ɗauki babban mayafi fari ta yane jikinta da shi. Chocolate cornflakes kawai ta haɗa da madara na ruwa ta zauna ta sha kafin ta ɗau jakarta ta wuce makaranta. Ba ƙaramin jin daɗin jikinta ta yi yau ba tana tafiya tana murmushi, duk wani damuwa da ta ke ji jiya da dare ya warware. Haka nan takeji ajikinta yau ranan za ta zo ma ta da alkhairi. Idan ta gama ɗaukan darasin yau tabbas dole ta kira gida ta ji lafiyar mahaifiyarta sannan ta sanar da ita labarin mafarkin da ta yi mai daɗi. Ta kan yi mafarki da mahaifiyar ta lokaci zuwa lokaci amma mafarkin jiya daban ne dana koyaushe mafarkin Aljannah ta yi... Su Ishirin da ɗaya ne a ajin na su kuma su biyu ne kaɗai musulmai, daga ita sai wani ɗan ƙasar Pakistan mai suna Azhar Ali Durrani. A gaba ɗaya ajin kuma su huɗu ne ba 'yan ƙasar na America ba. Ita da ta zo daga Nigeria sai Azhar sannan Audrey mutuniyar Philliphine sai Lee Jung Bo ɗan ƙasar Korea ta Kudu. Tun daga shekarar farko zuwa yanzu da ya saura ƙiris su ƙarisa shekara ta biyu suna tare a ajin tamkar 'yan uwan juna, kowa da ka gani a wajen karatu ne a gaban sa sannan karatun bai hana suna taimakawa junan su ba idan akwai wanda ya ke da rauni wajen fahimtar wani darasi. Daga sun kammala wannan sashi to saura mu su shekara biyu suna zuwa asibiti dan koyon aiki kafin su tafi residency na su... Yau ma tana cikin wanda su ka zo ajin da wurwuri, kaman kullum a gaba ta zauna bayan ta gaisa da sauran mutane bakwai da ta samu a ajin. Ta buɗe littafi tana ɗan dududdubawa kafin malamin ya shigo, yau su na da darasin Professor Umar Audu Bamalli wanda ta san halin shi na yawan tambaya idan yana darasi. Tana jin daɗin darasin sa saboda gaskiya Allah ya bashi baiwar koyarwa gashi kuma ba ƙaramin jin daɗi ta ke yi ba idan ta ga baƙin fata na nuna zarra a ƙasar da ba tashi ba. Prof Bamalli ya yi ƙaurin suna a makarantar na su kuma kasancewar sa baƙin fata kuma ɗan Nigeria ya sa ya ke burgeta sosai kuma ta ƙe ƙara jinjina ma sa. Makarantar su na Harvard Medical school ba ƙaramin ƙaurin suna yai ba a ɓangaren ilimi a duniya baki ɗaya. Idan za ka irga Jami'o'i da su ka yi fice da suna kuma su ka yi zarra a duniya idan ba ka saka Harvard ba kamar lissafin ka bai cika bane. A duk lokacin da aka yi ƙididdiga aka ware Jami'o'i fitattu goma ko fitattu biyar da su ka fi kowanne a duniya sai ka ga sunan Harvard yana zaune ƙyam acikin su. Taimakon Allah da addu'ar Uwa shi ya kawota wannan babbar makaranta da ba kowa ke samun daman shigan sa ba... Ajin na su yai tsit saboda shigowar Prof Bamalli. Kamar yadda ya saba sai da ya gaisa da 'yan ajin kafin ya fara gudanar da darasin. Kusan rabin awa da fara darasin na su ya jefo wata tambaya wanda Jack Stafford yai saurin ɗaga hannu ya amsa ta sai dai kuma amsar ta shi ba dai-dai bane. A maimakon ya gwaleshi ko ya nuna ba dai-dai ba ne sai ya ce "great, but we need something better" Wata baturiya mai suna Emilia ta ɗaga hannu ta sake amsa wannan tambaya sai dai ita ma ɗin ba dai-dai ba ne. Prof yai murmushi ya ce "nice try Miss Stevenson" Ya kalli budurwar da ke gefen Emilia wacce ya sani 'yar ƙasar sa ce kuma ya san ta da ƙoƙari sosai. Hankalinta na kan wayar ta shiyasa ya ɗan kira sunan ta da ɗan ƙarfi. "Pakkari" Budurwar ta yi saurin ɗago idon ta tana ƙoƙarin ba da nitsuwarta ga malamin na su. Ya sake maimaita ma ta tambayar sa ko za ta iya amsawa sai kuwa ta bashi mamaki domin amsar da ta bayar ɗin shi ne dai dai. "Good" ya faɗa sannan ya cigaba da bayanin darasin da ya ke yi. Wata baƙuwar number ne ke kiranta daga Nigeria shi ya ɗauke ma ta hankali ma daga ajin na su. Yadda numban ke kira akan kira ya sa ta yi tunanin ko akwai matsala ne. Ta dai daure ta ba da nitsuwarta a ajin da zimmar ana gamawa za ta kira numbar domin ta ji wanene ke kiran, cikin zuciyarta tana ayyana wa ranta ƙila mahaifiyarta ne ke son gaisawa da ita. Prof Bamalli ya gama darasin sa inda ya ke tsaye domin amsa tambayoyin ɗaliban na sa kamar yadda ya saba a kowani lokaci. Tana son tambayar Prof Bamalli amma kuma ƙaran shigowar text zuwa wayarta ya sa ta maida hankalin ta ga wayan domin ta ga wani irin saƙo ne... Saƙon da ta karanta ne ya sanya numfashinta ya ɗauke na 'yan daƙiƙu. Ta miƙe zumɓur tana faɗin "Ƙarya ne, ƙarya ne" hannunta na rawa ta shiga dialing numbar da ta turo saƙon. Mancewa ta yi da inda ta ke burinta kawai shine ta ji gaskiyan abinda aka turo. Wani bagidajen ne zai tura ma ta saƙon baƙin ciki irin haka, mahaukacin ne ya ke tura saƙon mutuwa haka. Innayi ta rasu shi ne abinda aka turo. Ta ɗara wayan a kunne tana girgiza kai hawaye na zubo ma ta. Wanda ta amsa wayar ne ta sanar da ita abinda ya faru a tsanake. Hakan yai sanadiyar suɓutuwar wayar da ga hannunta ya faɗi ƙasa gamida yin ƙara wanda ya sa hankalin duka 'yan ajin ya tashi domin tunda Raudha Abubakar Pakkari ta miƙe tsaye tana kuka su ka san ba lafiya ba. Tambayarta su ka farayi randomly akan mi ya ke faruwa amma kwata-kwata ba ta jin su balle ta iya ba su amsa. A hankali ta fara takawa tana tafiya hannunta ɗaya a miƙe kaman zata taɓa wani abu. Hawayen da ke ziranya a idon ta ne ya ƙara ingiza yadda ƙwaƙwalwarta ke tuno ma ta lokuta na farin ciki da su ke tare da Innayi... A mafi yawancin lokuta idan ka ji saƙon mutuwar wani na kusa da kai to abu na farko da ka ke tunowa shine kyawawan halayen sa. Za ka dinga tuno su a ranka kamar yau ne abin ya faru, abin zai shiga jikin ka sosai har ka ji duniyar nan fa ba madogara ba ce kuma kaima ɗin lokaci ka ke jira. Amma daga zaran wannan jimami ya huce sai mutum ya shagala da duniya ya manta cewa wannan nakusa da shi da ya mutu yana chan yana cin sakamakon abin da ya yi a duniya haka nan kuma shima ɗin ko ba daɗe ko ba jimawa zai je chan ɗin. Ku biyoni domin jin labarin wata uwa da 'ya'yanta, labari ne mai shiga rai da taɓa zuciya. Labarin da ban rubutashi dan komai ba sai dan ya zama kaman wani hanya na tunasarwa garemu ba ki ɗaya. Burina shine a ƙarshen labarin nan a samu mutum ɗaya ko biyu da su ka gyara zamantakewar su da kuma yadda su ke da iyayen su musamman iyaye mata. Saboda darasin da na ke so na isar ta sigar labari ya sa na ke so dan Allah idan ka karanta ka yaɗa shi saboda wani ma ya samu ko zai ƙaru ko kuma ka baiwa wani labarin a taƙaice ko za a samu wani da zai faɗakantu da wannan labari. Labarin daga farkonsa har ƙarshen sa kyauta ne ga duk wata Uwa da ke doron ƙasa. Its all about motherhood. Allah ka jiƙan iyayen mu ka gafarta mu su amin Wanda na su ke raye a daure a kyautata mu su wanda na su suka rasu a cigaba da mu su addu'a Ta ku Azizat #read #vote #comment #plz share 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 02 (Free book ne) *The bride* Muhammadu Jo'o shi ne ɗa na huɗu a gidan su ya na da yayye mata uku da ƙanne maza uku da autar su Faɗimatu. Da ke auren wuri ake yiwa yara mata a ƙauyen na su shiyasa bai wani shaƙu da su ba, lokacin da ya taso an aurar da 'yar farin su Maimunatu mai bi mata ma ba a jima ba aka aurar da ita. A taƙaice dai ya taso da tsananin son 'yar ƙaramar ƙanwar na su Faɗimatu wanda kuwa duk gidan sun fi kama da juna. Sai dai shekarar Faɗimatu shida a duniya ta rasu sakamakon zazzaɓin cizon sauro. Muhammadu kowa ya shaideshi wajen kyawawan halayen sa da jajircewan sa wajen harkan noma. Yayinda tsaransa ke kora shanu su na tafiya da su Kudu, ma su Noma kuma na saida gonakin su suna shiga birni , shi ya jajirce ne wajen noma sosai yana ƙoƙarin inganta rayuwar sa da ta ƙannen sa. Domin a shekarunsa shashida Allah yai wa mahaifin su rasuwa da ake kira da Baffa Jo'o. Daga wajen mahaifiyar sa ya samu umurni a kan yai aure saboda ya zama yana da iyalin sa, dan ya fi jin daɗin kula da ƙannen sa sosai. *** Aminatu 'ya ce ga Malam Isiyaku Chadi. Malam Isiyaku da iyalen sa su ka zo ƙauyen Tunfure kusan shekaru ashirin da su ka wuce. Ilimin addini da Malam Isiyakun ke da shi ya sa ya samu gindin zama a ƙauyen Tunfure ba tareda mutanen ƙauyen sun damu da rashin sanin asalin sa ba. Malam Isiyaku ya kan ce daga chan gabashin Chadi ya shigo Nigeria inda yai ta yawuce-yawuce kafin har Allah ya sa ya samu gindin zama a Tunfure. Kafin Aminatu, Malam Isiyaku sai da ya busine 'ya'ya takwas sannan Allah ya sa Aminatu ta tsaya, kuma har ya rasu ita kaɗaice 'yar sa... Muhammadu ya yi karatun Allo a gaban Malam Isiyaku ne, inda tun Aminatu na ƙarama ta ke burgeshi. Yana saurayi ɗan shekara shatakwas Aminatu na shaɗaya aka yi auren su bayan an sha fama kafin Goggo Talatu mahaifiyar sa ta amince, dan a da ta nuna ra'ayin ya auri 'yar ƙanwar ta amma ya ƙi saboda soyayyar Aminatu da ya rufe ma sa ido. Shigowar Aminatu gidan kyawawan halayenta da sanyinta ya sa Goggo ta sake jiki da ita har ta fara son ta. Duk da ƙarancin shekarunta tana bin Goggo sau da ƙafa tamkar Goggo ce ta haifeta. Shiru-shiru shekara ɗaya ta shuɗe ba maganar haihuwa ta biyu ma ta shige shiru, hankalin Goggo ya tashi ta fara ƙorafi saboda shekaru biyu ba wasa ba ne a wajenta. Ƙwatsam sai ga ciki ya ɓullo, murna a wajen Muhammadu ba a magana, Goggo ma ta yi farin ciki tunda ya tabbata ɗanta na da lafiya. Tun cikin na ɗan ƙarami ya ke ba wa Aminatu wahala har ta kai da cikin yai nisa. Muhammadu ya nemi a kai Aminatu Asibiti a dubata amma Goggo ta ƙi ta ce lalaci da ragonta ke sa Aminatu wannan tsirfe-tsirfen ciwon, a cewarta komai zai wuce idan cikin ya girma. Cikin na girma Aminatu na ƙara bushewa, ta yi wani fayau da ita kamar ba ta da jini. Ana haka aka wayi gari da rasuwan Malam Isiyaku wanda ya kwana lafiya amma ya mutu cikin baccin sa. Aminatu ta yi baƙin ciki da wannan rashin yayinda ta ke kuma fama da nata ciwon. Sosai Muhammadu ya ke ƙoƙarin kula da ita daidai gwargwado kuma ya damu da rashin lafiyarta. Wani lokacin idan ya shiga garin Misau ya kan siyo wa Aminatu tsire ko balangu ya kawo ma ta a ɓoye ta ci, dan ya kan ji ana cewa idan mace na da ciki ana so ta riƙa cin abu mai daɗi. Har buredi ya ke siyo ma ta idan ya shiga cikin garin na Misau. Ƙarancin shekaru, rashin jini da cutar malaria da typoid da su ka haɗu su ka yiwa Aminatu katutu a jiki ya sa wata rana da safe Aminatu na daka ta faɗi ta suma. Bayan ta farfaɗo naƙuda ta fara gadan-gadan da cikin ta da ke wata takwas. Muhammadu ya tafi ya nemo Amalenke da za a kai Aminatu asibiti dan hankalinsa ya tashi da halin da Aminatun ta shiga. Lokacin da ya shigo gidan ya samu Goggo na rusa kuka yayinda Delu ungozoma ta ke riƙe da jaririyar da Aminatu ta haifa. Bai bi ta kan jaririyar ba ya shiga ɗaki ya tarar da gawar Aminatu kwance cikin jini ya buɗe zanin da Delu ta rufe ma ta yana ganin yadda matar sa kuma masoyiyarsa ke kwance kamar mai bacci amma kuma ba rai. Ya shiga kiran sunan ta da ƙarfi yana faɗin ta tashi ta ma sa magana. Da ƙyar ƙanin sa Habu da abokin sa Iro su ka zo su ka janyeshi a wajen gawar... Inna Hauwa mahaifiyar Aminatu ne ta ke renon jaririyar da ta ci suna Faɗimatu. Baban ta kaɗai ke kiranta da Faɗimatuz zahra yana ma ta kirari da Tauraruwa ta. Koyaushe Muhammadu na maƙale da 'yar sa Faɗima. Maganar ƙara aure da Goggo ke ma sa duk iska ya ke bi domin ya ka sa manta Aminatun sa haka kawai sai ya je maƙabarta ya je wajen Kabarin Aminatu ya zauna ya wuni a chan. A hankali suna ganin abin da wasa har shekaru huɗu amma Muhammadu bai ƙara aure ba, ta kai har Goggo na nema ma sa magani dan gani ta ke ya samu matsalar ƙwaƙwalwa ne musamman idan ta ga irin kulawar da ya ke bawa 'yar sa Faɗimatu. Yana da dogon buri a kan Faɗimatu yana da burin ta yi karatu, tun ranan da ya je asibiti gaida Baffan abokin sa da ba lafiya ya ga wata likita mace musulma amma mutuniyar Minna Banufiya, hankalinsa ya kwaɗaitu da son 'yar sa Faɗimatu ta samu ilimi, har ta kai matakin da Dr Hassana ta kai. Duk da kuwa ya sani abu ne mai wuya musamman yadda a lokacin karatun 'ya'ya maza ma ba kowa ke yi ba balle 'ya'ya mata. A shekaran Faɗimatu na biyar Inna Hauwa ta rasu bayan ta yiwa Muhammadu bayanin asalin su, saboda kar gaba ayiwa Faɗimatu gori. Kamar yadda Malam Isiyaku ya faɗa, su mutanen ƙasar Chad ne daga wani gari da ake cewa Moundou. Mahaifin Malam Isiyaku Allah ya albarkaceshi da arziƙi, yana da mata huɗu kuma dukkan su sun haihu sai dai ciki ya fi son Ruƙayyatu wacce Allah yai wa baiwar kyau da Ilimi na addini kuma haka yaranta su ka taso da kyakykyawar tarbiya da ilimin addini. A hankali a hankali kissa da munafurci tareda mugunta yasa yaranta biyu su ka halaka ya saura Isiyaku kawai, hakan ya sa ta tura Isiyaku Ndjamena wajen yayan mamanta akan ya koyi karatu. A nan Isiyaku yai karatu har ya auri 'yar uwarsa ta ɓangaren uwa. Mutuwar ElHajj Abdoullahe ya sa 'ya'yan sa da matan sa dama 'yan uwan sa su ka fara farautan junan su saboda dukiya, ƙarshe su ka yiwa Ruƙayya asiri har ta kai ta rasu cikin jinya. Hakan ya sa Malam Isma'il ya ba wa Isiyaku shawara akan yai nisa da Chad saboda kar 'yan uwan sa su halaka shi. Wannan ya sa ya ɗau iyalin sa su ka shiga tafiya neman mafaka har Allah ya zaunar da su a ƙauyen Tunfure bayan sun zauna a wajaje da dama... Faɗimatu 'yar gatan Baban ta, duk ƙauyen ba macen da aka sa ta a makarantar boko sai Faɗimatu, inda ta ke tafiya primary school da ke ƙauyen Ajili. Muhammadu shi zai kai ta ya kuma dawo ya ɗauketa ya maidata gida. Tun Goggo na faɗan har ta haƙura ta dangana. Shekarun Faɗima tara Allah yai wa Muhammadu rasuwa. Maciji ne ya sareshi a gona daga haka kuma ya fara jinya har ya rasu. Riƙon Faɗimatu ya dawo hannun ƙanin mahaifinta Baffa Habu. Tunda mahaifinta ya rasu maganar makaranta ya watse tunda Goggo ba ta so duk da kuwa a lokacin an samu ƙarin mata uku da aka sa a makaranta... *** Yau ma garin maganin da Goggo ta ƙarɓo aka jiƙa ma ta ta sha, maganin ba ƙaramin ɗaci ne da shi ba amma haka Faɗima ta shanye shi tas. Shekaru biyu kenan Goggo na nema ma ta magani. Idan watan azumin da za a shiga ya kai ƙarshe aka yi sallah da kwana huɗu to shekara goma shahuɗu za ta cika a duniya kuma har yanzu ba ta fara jini ba. Wannan ne ya hana a mata auren shabiyu sha uku da ake yiwa matan ƙauyen na su. Akwai Sama'ila da ya ke zuwa zance wajenta amma kuma mahaifiyar sa ta ƙi Faɗima saboda wannan lalura na ta. Inna Maimunah da ke aure a cikin Misau ta sha faɗawa Goggo akan ba lalura ba ce Faɗiman ke da shi, halitta ce kawai, wasu matan ba su fara jini da wuri. Kunyar da fulani ke wa 'ya'yan su na fari ya sa duk lokacin da Maimunan ke mata bayani ta ke tashi ta bar wajen cikin fushi tareda yin biris da maganganun 'yar na ta. Ta chanja ma su maganin gargajiya sun yi goma amma shiru ba labarin jini... Cikin azumi jini ya zo ma ta. Ana gab da shan ruwa a ranan azumi na shabiyar. Bayan ta gama toya ƙosai ta tashi kenan Hebbini matar Baffa Habu ta hango jini a bayan zaninta. Da sauri ta zo wajenta ta kamata su ka shiga ɗaki inda ta tabbatar da jinin al'ada ne, cike da murna ta haɗa ma ta ƙunzugu ta ce ta je bayan gida ta saka. Faɗimatu na fita Hebbini ta wuce ɗakin Goggo ta sanar da ita. Goggo ta doka salati tana faɗin dole gobe ta yi sadaka saboda samun lafiyar Faɗimatu... Bayan sallah aka tsaida magana tsakanin Malam Habu Jo'o da kuma Malam Yusufu Pakkari. Ba a wani ɗau lokaci ba aka ɗaura auren Faɗimatu Muhammadu Jo'o da kuma Buba Yusufu Pakkari. Buba ya yi primary daga nan bai cigaba ba. Ya samu aikin Masinja a makarantar Teachers College da ke cikin garin Misau. A lokacin da aka haɗa shi aure da Faɗimatu shekaransa ashirin a duniya ita kuma shahuɗu. Faɗimatu ba ta taɓa ganin Buba ba, shi ɗan asalin ƙauyen Ajili ne, a nan ya taso, yai rayuwar sa kafin ya koma Misau da zama tunda ya samu aiki shekaru uku da su ka wuce. Anyi shagalin biki dai-dai gwargwado kafin aka ɗauki amarya Faɗimatu zuwa gidan mijinta a cikin garin Misau. Cikin quaters na TC ɗin za su zauna. Boys quarter aka ba wa Buba ya zauna da iyalin sa kasancewa shi ɗin ƙaramin ma'aikaci ne. A shekarun ta shahuɗu ba wani ilimi da ta sani gameda aure da ya wuce ta yiwa Buba biyayya sannan ta zama uwar 'ya'yan sa. Hebbini ce ta kowa ma ta wankan tsarki irin na mutanen da ko na ce wanda ke cike da bidi'o'i. Kuma ta ce shi za ta yi a duk lokacin da ta tare da maigidan ta. A ɓangaren ilimi na ƙur'ani kuwa Faɗimah na ɗaya daga cikin 'yan matan da ake kwatance da su a ƙauyen domin duk ajin su ta fi kowa zarra tunda ta haddace suratul Nasi zuwa Suratul Dhuha kuma a rubutu ta kai suratul Yasin. Ko da shekaru uku da ta yi tana zuwa primary school a Ajili sai da ta yi suna saboda ƙwazon ta na ɗaukan darasi da wuri da kuma rashin mantuwa. Sai dai kash! Aure ya katse ma ta duk wani buri nata na cigaba da karatu balle har babban burin mahaifinta ya tabbata... Ba ta iya ɗaga ido ta kalli Buba ba daren ranan da aka kawota saboda kunya ta Fulani, ga kuma tsoro da fargaba da ya cika ta saboda rabuwa da gida da ta yi. Wannan ne karo na farko da ta yi nisa da ƙauyen su, iya kacinta Tunfure da Ajili. Ko irin zuwa hidimar biki ƙauyukan da ke gefen su ba ta yi saboda asalinta ba mai son hayaniya ba ce. Buba bai ja dogon lokaci ba ya tare da ita kuma dayake shima ɗin ba wani ilimin addinin gareshi ba ko sallar nafila ta godiya ba a yi ba balle batun addu'ar saduwa da iyali. Ya dai kawo ma ta tsire da bredi da shayi, wanda ta tsakuri kaɗan ta ci shi kuma ya ƙarisa sauran. Washegari a wahalce ta tashi sai dai ita ɗin dama tun asalinta mai juriya ce. Ta haɗa ice ta ɗaura ruwan zafi ta yi wanka ta gwada gasa jikinta kamar yadda Hebbini ta gaya ma ta. Shi kam Buba tun asubahi ya fita bayan ya tashi Faɗima daga baccin wahala da ta yi. Bai dawo ba sai ƙarfe takwas na safe inda ya taho da kunu mai zafi da ƙosai. Tun a wajen ya sha nashi ya ƙoshi dan haka Faɗima ce kawai ta sha wanda ya kawo. Da rana ta fara girki saboda Buba ya ce zai zo ya ci abinci shi da abokanan sa.... Wata ɗaya kenan da auren Faɗima kuma har lokacin ba ta wani saba ba. Ba abinda ke shiga tsakanin ta da Buba sai dai ta girka ma sa abinci ya ci sannan idan dare ya yi ta bashi hakkin sa, kayan sa yai datti ta wanke. Su na zaune ne matsayin mata da miji amma babu shaƙuwa tsakanin su. Idan magana ta haɗa su to Buba ke buƙatar wani abu, asali dama Faɗima ba mai yawan surutu ba ne ya zo ya haɗu da cewa Buba kuma bai damu da ita ba balle duk lokacin da ya ke gidan ya dinga ma ta hira. Yaran maƙotan su Ma'ulle da Uwani su ke ɗebe wa Faɗima kewa. Yaran sosai su ka shiga ranta, indai sun dawo daga makaranta to gidan ta za su garzayo su dinga ba ta labarin abin da su ka kalla a talabijin ɗin gidan su Zainab, kasancewa mahaifin Zainab ɗin Malami ne ya sa ya zamo ɗaya daga cikin tsirarun mutanen da ke da talabijin a quarters ɗin... Kafin auren Buba da Faɗima, Buba na neman wata bazawara mai suna Harira, tana sai da Masa, shekaru uku da aure ta fito. Bakarkariya ce iyayenta 'yan asalin garin Jalam. Buba ya nace a kanta sosai, sai dai Harira ta rena ma samun sa duk da kuwa ba ƙaramin kuɗi ya ke kashe ma ta ba idan ya zo zance, sannan tana ma sa kallon saurayi kuma yaro, dan shekara ɗaya kawai ya bata a lokacin. Inna Furera mahaifiyar Buba sam ta ƙi zancen sa na auren bazawara kuma Bakarkariya. Shi dai ya nace akan yana son Harira. Sai da ya gama kashewa Harira kuɗi kusan shekara ɗaya da rabi kawai watarana ya je ƙauye ya yi kwana biyu, dawowar da zai yi ya ji labarin Harira ta yi aure har ta tare a gidan mijinta, abin ya ma sa ɗaci sosai. Rashin Harira ya sa ya amince da zaɓin mahaifiyar sa wato Faɗima... Buba ya saba da cin daɗi tun kafin aure shiyasa ko bayan aure kwaɗayin sugar da maiƙo bai barshi ba. Da safe zai je ya sayi shayi da buredi ya karya da rana idan yana wajen aiki zai sayi shinkafa da miya da nama da dare ma sai ya sha shayi kafin ya wuce gida. Yana zuwa kuwa zai tsatstsakuri tuwon da Fatima ta kawo ma sa ya ce ya ƙoshi. Idan ka ga Buba ya ci abincin safe rana da na dare a gida to bashida kuɗi ne kuma ya nemi bashi ya rasa. Faɗima ba ta taɓa damuwa ba ko kuma ta tambayeshi akan ƙin cin abinci da ya ke yi, domin yana daga cikin ladabin da aka ɗaurata ba a yiwa miji ƙwaƙwƙwafi ko shishshigi. Idan ya kawo cefane haka za ta dinga lallaɓawa domin duk lokacin da ya ƙare ta buɗi baki ta ce "Malam ba bu cefane" to ranan haka zai ta masifa ya dinga zaginta akan ba ta tattali. Da ta gane haka sai ta yi shiru har sai ya lura ba komai kafin ya siyo ya kawo. Mahaifin su Ma'ulle gadi ya ke yi a bakin gate amma da ke shi ba kamar Buba ba ne wanda kan sa kawai ya sani ba ya barin iyalinsa cikin ƙunci. Komai a wadace ya ke kawowa duk da kuwa shi ɗin yana da 'ya'ya har uku. Amma su da su ke su biyu sai abu ya gagaresu. A hankali ranaku su ka fara ja, kwanaki su ka zama sati zuwa watanni. Babu wani hali na Buba da bai bayyana ma ta ba, sai dai kamar kowacce Mace da akewa huɗuba da aure sai haƙuri haka itama ta riƙe wannan huɗuba. Domin kuwa tun bayan satin farko na aure to har wa yau zaman haƙuri ta ke da Buba. Abu ɗaya da ya tsaya ma ta a rai shine rashin samun ciki. Lokacin da ƙanwar Buba ta kawo mu su ziyara ta ke tambayarta ya aka yi shiru har yanzu. "Wata takwas fa Faɗima" ta faɗa tana kallon Faɗiman. Ta girmi Rabi ƙanwar Buba da kusan shekara amma da ke ta rigata aure kuma har ta haihu shiyasa Rabin ta ke ma ta kallon kamar ta girmeta. Mi za ta ce ma ta? Ba ita ke ba da haihuwa ba. Abinda ya kamata ta faɗa kenan amma ta yi shiru tana cigaba da sauraron maganganun Rabin... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 03 (Free book ne) *Motherhood* A duk lokacin da aka samu ma'aurata su ka kwana biyu da yin aure, to kowa tsammanin sa shine ya ga an samu albarkar aure. Idan aka ji shiru Mace za a dinga nunawa ana tunanin gazawar da ga gareta ne. A kan manta cewa haihuwa na Allah ne, kuma shi Ubangiji ya kan ba da kyautar haihuwane a lokacin da ya so. Ya gaya ma na cewa wasu zai ba su Maza zalla wasu kuma Mata zalla, wasu ya haɗa musu Maza da Mata wasu kuma haka za su rayu su mutu ba tareda sun samu kyautar haihuwa ba... Tun lokacin da Rabi ta tafi damuwar Faɗima ta ƙaru, babu sallah da za ta yi da ba za ta yi addu'ar Allah ya bata haihuwa ba. A lokacin da ma yanzu gani ake haihuwa shine Ribar aure, idan ka yi aure ba ka haihu ba gani ake ba abinda ka rabauta da shi. A shekarunta shabiyar ta san rashin haihuwa babbar matsalace ga 'ya mace. Ta na fata kada ta zama Gaji da ake labari a ƙauyen su, wanda aka ce kusan shekaru Arba'in da aure amma ba ta taɓa haihuwa ba har ta rasu, kishiyoyinta uku kuwa duka sun hayayyyafa har ma da jikoki. Duk lokacin da mace ba ta haihu ba a ƙauyen su, da labarin Gaji ake tsoratar da ita. A dinga cewa "idan ba ki haihu ba haka za kiyi rayuwar kaɗaici kamar Gaji ki mutu ba tareda kin bar mai mi ki sadaka da addu'a ba". Sai da ta shekara ɗaya da wata uku da aure kafin ta je ƙauye ziyara. Ta na kewar gida amma ba yadda za ta yi, idan mace ta yi aure sai da dalili ta ke zuwa gidan su abinda ta taso da shi kenan. Goggo ce ba lafiya kuma jikin ta yayi tsanani sosai shiyasa Buba ya ce ta je ta yi kwana biyu. Gidan su Buba ta fara zuwa dan ta gaishe su daga nan kuma ta wuce na su ƙauyen. Rashin sakin fiska da ma habaici da ta ci karo da shi a gidan ya sa ta sha jinin jikinta, har ta bar gidan hankalinta a tashe ya ke. A chan ƙauyen su Tunfure kuwa ta samu tarba mai kyau. Goggo ta yi marmarin ganin jikarta sosai wanda rabonta da ita tun da aka kai ta ɗakin miji. Ta na son faɗawa Goggo akan ta nema ma ta maganin haihuwa amma yanayin da ta samu Goggon ya sa ta yi shiru. Tsab Goggo ta karanci damuwar da ke fiskar jikar ta. Yadda itama a baya ta damu lokacin da Aminatu ta wuce shekara ba ta haihu ba, ta san dole ne 'yan uwan Buba su damu. Zurfin cikin Aminatu Faɗiman ta ɗauko, ba za ta taɓa gaya ma ta damuwar ta ba. "Ki yi haƙuri Faɗimatun Baffa. Ina ga jinin Aminatu ki ka ɗauka shiya sa ki ka ji shiru har yanzu. Allah ya sa ina da rabon ganin 'ya'yan ki Faɗima" Faɗima ta amsa da Amin. Dawowar Faɗima Misau da kwana biyar Goggo ta rasu, ta so ta je ta'aziya amma Buba ya hana wai ai ba ta jima da dawowa ba, haka ta haƙura akan sai wani lokaci idan ta je ƙauye sai ta yi mu su ta'aziyar. Mutuwar Goggo ya shigeta sosai saboda shaƙuwar da su ka yi musamman bayan rasuwar Baffan ta, duk soyayyar Goggo ga Muhammadu to ta juyeshi zuwa kan 'yar sa Faɗima... Wasa-wasa shekaru biyu su ka shuɗe babu labarin ciki. Buba dai bai damuba hidimar gaban sa kawai ya ke yi, tunda zai ci ya sha sannan ya tara da iyalin sa ai ba wata matsala. Damuwar rashin haihuwa da kaɗaici ya sa Faɗima ta fige ta lalace, dama ba ƙiba gareta ba sai ta ƙara bushewa. A irin wannan zaman ne Ladi maƙociyar ta ta bata shawaran akan ta dinga sana'a saboda ta rage kaɗaici. Da farko ta yi watsi da shawarar daga baya kuma ta amince, ko dan yadda Buba ke yawan zaginta da rashin tattali. Namiji ke ciyar da mace ya tufatar da ita ya kuma ɗauke duk wata ɗawainiya na ta, sai dai miji kaman Buba wannan haƙƙoƙi da ya rataya a wuyan sa kaman wani nauyi ne da ke hanashi sakewa. Kuɗin da zai fitar dan iyalinsa ta ci ta sha ba ƙaramin takura ya ke yi ba. Za ta yi sana'a ne ba dan ta samu kuɗi ko ta nuna gazawar Buba ba sai dan ta taimaka ma sa. Goggo ta yi sana'ar daddawa kuma ba abinda Faɗiman ba ta sani ba gameda harkan. Hebbini kuma ta yi sana'ar ƙosai wanda shekaru uku kafin aurenta ita ke tuyawa Hebbini ƙosan. Cikin Daddawa da ƙosai da ta iya ta zaɓi ƙosai domin shi zai fi ma ta sauƙi kuma Ladi ta ce za ta fi samun kasuwa. Da ta gama yanke shawara sannan ta tuntuɓi Buba akan ya ba ta izini ta fara sana'ar ƙosai. Ranan kuwa sai da ta ƙwammaci ba ta yi zance mai kaman wannan ba, ta inda Buba ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Ya haɗa da cewa ta san yadda za ta yi ta haihu tun kafin maganganun da ake faɗa akan ta ya tabbata. Kenan shi ma ya damu da rashin haihuwar na ta? Ya za ta yi da ranta ne?, duk magungunan da ake kawo ma ta daga ƙauye babu wanda ba ta sha amma shiru. Ta yi yunƙurin zuwa asibiti Buba ne bai bata dama ba ya ce ba shi da kuɗi... Daga wannan rana ba ta kuma ɗaga zancen sana'a ba, ta fawwalawa Allah lamarinta, idan da rabon za ta haihu to, idan kuma itama haka za ta ƙare rayuwar ta kamar Gaji shikenan, haka Allah ya tsara ma ta. Shekaru uku su ka shige rus ba tareda ta yi ɓatan wata ba. Daga ɓangaren Buba bai ƙara ma ta maganar ba tun ranan da ta ma sa zancen sana'a. Sai dai duk lokacin da dalili ya kawo 'yan uwan sa gidan daga ƙauye to haka za su yi ta hantarar ta. Shekarun ta shabakwai amma gani su ke irin ta kai talatin ɗin nan ba tareda haihuwa ba. Allah ma ji roƙon bawan sa kenan. Acikin shekara na huɗu da auren su sai ga ciki ya ɓullo. Ita kan ta Faɗima ba ta ankara da cewa cikin ba ne lokacin da ta haura sati ba ta ga jinin ta na wata ba. Haka ta tattara ta tafi ƙauye karo na biyu tun aurenta. Auren 'yar Baffa Habu za ayi mai su na Mairo. Cike da tsoro ta tambayi Buba gameda zuwa bikin abin mamaki sai ya amince ma ta. Ta ji daɗi sosai dan rashin zuwa ƙauye ya dameta, tun tana sa ran za ta je ta yi mu su ta'aziyar Goggo har ta haƙura da zancen, gashi Goggo ta kai shekaru biyu da rasuwa. A wajen hidimar bikin ne ta dinga kela amai lokacin da ake kan aikin biki. Umma Asabe ta ja ta gefe tana ma ta tambayoyi. "Anya ba ciki gareki ba Faɗima?" Faɗima ta sunne kanta cikin cinyoyinta tana fata Allah ya sa maganar Umma Asaben gaskiya ce... Haka dai aka yi hidimar biki aka gama wanda Faɗima ta yi ne cikin laulayi. Hatta Hebbini sai da ta tabbatar ma ta da cewa tana da juna biyu amma kunnen ta sun ƙi gaskata zancen duk da kuwa zuciyar ta na son amincewa da maganar ta. Ta koma Misau ta cigaba da hidiman ta, duk da kuwa laulayi ya sa ta a gaba. Sai da Ladi ta tabbatar ma ta da ciki gareta sannan ta amince zuwa lokacin alamu dayawa sun bayyana dan cikin ya shiga wata na uku. Saboda kunya ba ta iya gayawa Buba ba, sai da cikin ya kai wata na biyar kafin ya gane. Shi kam ina ma ya ke tsayawa ya kalleta balle ya dinga lura da chanjawar da ta ke yi. Da dare kuma ana kashe fitila zai ɗaga zani ya raya dare babu maganar wasa balle ya lura da cikinta da ya taso... A hankali cikin Faɗima ya shiga wata tara haihuwa ko yau ko gobe. Cikin gashi tulele da shi, ko sau ɗaya ba ta je asibiti ba duk da alamu sun nuna tana buƙatar hakan amma Buba ba ruwan sa. Matan ƙauye sai su haihu sau goma shabiyu a gida ba tareda sun je Asibiti ba kuma lafiya-lafiya su ke haihuwar su. Abun da ya sa a ran sa kenan. Buba bai wani shiryawa sunan ba dan har tana wata na tara ba abinda ya tanada. Da ta ma sa magana ya ce ai yana sane dan haka ta ja bakinta ta yi shiru. Sai da cikinta ya cika wata goma kafin ta haifi 'yan biyu maza. Ladi da Inna Maimunah ne su ka karɓi haihuwar, sai dai na farkon kuka kawai yai a duniya ya koma. Na biyun ne aka yi sunan sa wanda ya ci su na Hussaini. Idan da ta Buba ne to sai dai Faɗima ta sha kunya dan da ƙyar aka matse shi ya sayi rago bayan nan bai ba da komai ba. `yan uwanta su suka yi rawar gani a hidimar suna musamman Baffa Habu, jikan ɗan uwansa na farko kenan. Su ma a chan Ajili sun yi murna da haihuwar musamman ma da ya ke 'yan biyu ta haifa duk da ɗayan ya koma... Wankan Kwana arba'in Faɗima ta yi a ƙauye kafin ta dawo Misau inda ta cigaba da renon ɗan ta. Duk kunyar da ake yiwa ɗan fari ita kan ta kasa yi, sosai ta ke zagewa ta yi wa ɗan ta wasa. Hussaini na da wata bakwai ya fara rashin lafiya, zazzaɓi da gudawa, daga baya kuma wasu ƙuraje su ka feso ma sa. Tun farko Faɗima sai da ta nemi a kai Hussaini asibiti amma Buba ya ƙi, aka dinga ɗirka ma sa maganin gargajiya. Ranan da jikin Hussaini yai tsanani haka ta ɗauki mayafi ta saɓa ɗan ta a baya ta wuce clinic ɗin makaranta. Su ka dubi yaron su ka dinga faɗa akan miyasa ba a kawoshi da wuri ba sai da ciyo ya ci shi. Ta yi shiru dan ba abinda za ta ce, ba za ta taɓa faɗin gaskiya ba domin kamar ta tona asirin mijin ta ne. Su ka ƙarɓe shi su ka bashi magani tareda faɗin dole a kai shi babban Asibiti. Ta ce sai dai idan Buba ya dawo. A clinic ɗin Buba ya sameta inda likita ya rufeshi da faɗa akan ta ya zai bari ciwo ya ci ɗan sa haka. Dama likitan Bayarabe ne ya haɗa da cewa dama ku Fulani kun fi ba wa saniyar ku daraja fiye da 'ya'yan cikin ku. Buba yai ta ba da haƙuri, daga baya aka basu wata takarda akan gobe da safe su kai Asibiti. Buba ya tisa matarsa gaba su ka dawo gida. Su na zuwa ya titsiyeta a ɗaki ya fara dukan ta wai a dalilin me za ta fita ba tareda izinin sa ba. Bai damu cewa tana cikin damuwar ciwon ɗan ta ba, damuwar sa shine an fita ba a tambayeshi ba. Shi mai girma miji wanda addini ya sa mace a ƙarƙashin ikon sa. Haka ya fice daga gidan ya barta tana kuka. Tun zamanin da chan miji ya bugi matar sa ba a ɗaukar sa a komai, a lokacin na su ma ba komai ba ne balle kuma a zamanin mu na yanzu da abin ya zamo tamkar wani ado ko bajinta. Ta ya za ka daki matar ka kuma ka kwanta lafiya? Ta ya za ka maida mace tamkar Baiwa? Ta ya za ka ɗauki raunin Mace a matsayin hanya ta muzgunawa rayuwar ta? Ta ya za ka daki matar ka wai dan kawai Allah ya ba ka daraja, kana gaba da ita?. Maganar zuwa asibiti haka ta bi iska. Faɗima ta cigaba da ba wa Hussaini maganin da aka ba su a clinic. Ko kaɗan dukan da Buba ya ma ta bai dameta ba damuwarta shine ɗan ta ya samu lafiya. Kwana huɗu da faruwar wannan abu Hussaini ya rasu. Da asubahi ta tashi za ta duba shi ta ga ɗanta kwance jiki a sake, dama daren jiya haka ya wuni da kuka saboda ciwo. Ta ma yi mamaki da bai farka cikin dare ba kamar yadda ya saba, ashe yaro kam ya koma. Buba da ke kwance ta fara bubbugawa tana faɗin "Malam ka tashi ka ga yaro ba ya motsi, dan Allah ka zo ka duba shi" tana maganar tana hawaye. Buba dai da ya ga ta dameshi ya miƙe ya zo ya dubi gawar ɗan na sa. Kallo ɗaya ya ma sa ya tabbatar yaro kam ya tafi sai dai Allah ya sa mai ceto ne. Ya kalli Faɗima da ke zazzare ido tana jiran ya ce wani abu ya ce " sai dai mu yi haƙuri Hussaini ya riga mu gidan gaskiya" Faɗima ta tsugunna ƙasa tana girgiza kai domin ta ka sa gaskata maganar Mijin na ta mai kama da almara, shikenan ta rasa Hassan ta rasa Hussaini ? Kuka mai tsanani ya kufce ma ta... *** Faɗima ta shiga wani yanayi da ake kira da depression a turanci. Bayan rasuwan ɗan ta komai ya fita ma ta akai, ta zabge ta lalace. Haihuwar da ta ke ta kuka a kan sa shine bayan ta samu kuma Allah ya ƙarɓe kayan shi. Ba ta ji mutuwar Hassan kamar yadda ta ji mutuwar Hussaini ba, Hassan ko nonon ta bai taɓa ba amma Hussaini fa? Uwa ita tafi damuwa da mutuwar ɗa, ita ta san zafin haihuwa. Wata goma ta raini cikin su kafin haihuwa, ta zo ta raini Hussaini na wata bakwai da sati uku. Buba dai shima ya ji ba daɗi dan ko ba komai ya sa rai da ɗan na sa amma shi abin bai taɓa shi ba kamar yadda ya taɓa Faɗima, dan shi cikin sati biyu ya koma dai-dai kamar yadda ya ke da. Ita kuwa Faɗima idan Buba ya tafi wajen aiki haka za ta wuni tana kuka tana rungume kayan Hussaini, saboda haka ne ma Ladi ta ke tura su Ma'u lle su je da ƙanin su Kabiru ɗan shekara biyu da rabi. A hakan dai duk sammakal. Ko sati uku ba a cika ba Buba ya nemi matar sa ta bashi hakkin sa. Dan ya gaji da shiru-shiru da ta ke tuntuni, ai mutuwar Hussaini ba zai sa rayuwa ta tsaya ba. Ba abinda ta iya haka ta gyara ma sa ya samu nitsuwar sa... Damuwa kam a hankali Ladi na ma ta nasiha har ta sake ranta ta rungumi ƙaddara. Cikin ikon Allah kuwa wata uku da mutuwar Hussaini ta samu ciki. Duk farin ciki da ɗoki da ta yi a cikin su Hussaini ba ta yi a wannan ba, dan gani ta ke wannan ma haka zai zo ya koma ba tareda ya girma ba. Ciki ya shiga wata tara ta haifi ɗan ta namiji wanda ya ci sunan Adamu (Ado) Kyautar ta bai tsaya haka ba shekaran Adamu ɗaya da rabi ta haifi Ibrahim (Iro). Daga nan haihuwa ta buɗe ma ta, ta sake samun Halimah da Muhammadu da su ke kira da Baffa... Tun bayan haihuwan Halima ta fara sana'ar ƙosai kuma Alhamdulillah tana samun ciniki sosai, haihuwa da ta fara yawa ya sa Buba da kan sa ya ma ta maganar sana'a dan yanzu hidima ta fara ma sa yawa, ga shi har yanzu ba wai ya dena halin sa ba ne na cin abinci a waje. ya gane cewa idan Faɗima na samun wani abu zai tare ma sa wata ƙofar... Ado, Iro da Halima duk sun fara makaranta sai Baffah ne kaɗai ke gida wanda bai gama cika shekara uku ba. Ƙarfe huɗu tana yi za ta tashi ta hau wanke wake tana gamawa za ta fitar da komai da za ta yi amfani da shi tareda ɗaura ruwan wankan yara. Tana idar da sallar asuba za ta ɗaura ɗumamen tuwo yayinda Ado zai ɗau markaɗen wake ya kai gidan Yarabawa, gidan wani Malami kusa da su wanda matar sa ke da injin markaɗe. Yana dawo da markaɗe za ta hau tuya ƙosai, dama ta riga ta yiwa Iro da Halima wanka shima Ado sai ya je ya ɗebi ruwan wanka yai na sa wankan. Kafin ka ce me za ka ji ana sallama ana tambayar ƙosan Sule ɗaya, Sule biyu har ma su ƙosan naira ɗaya. Kan ka ce kobo ƙosai ya ƙare. Tana tattare kayan da ta yi amfani da su wajen tuya ƙosai 'yar ta Halima ta kirata "Innayi ...Innayi" Ba tareda ta juyo ba ta ce "Halime dama ba ki tafi makarantar ba?" "Innayi na tsaya na yi fitsari ne, wai ki ga Baffah zai bini makaranta" Sai alokacin Innayi ta juyo ta kalli Halima da ƙaramin ɗan ta Baffah tana murmushi. Kamar ba yau ne ta ke ganin rayuwar ta baya da ma'ana ba saboda ɗan ta Hussaini da ya rasu gashi yanzu yara ɗai-ɗai har huɗu kuma ba wai ta cire rai da sake haihuwan ba ne. Allah ke nan, mai jinƙan Bayin sa... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 04 (Free book ne) *A man needs many wives* Sana'a sa'a domin kuwa Innayi ta yi sa'a. A gaba ɗaya quarters ɗin makarantan na Teacher's college Misau idan ka na neman ƙosai mai daɗi, mai garɗi to ƙosan Innayi ne. Kuɗin da Innayi ke samu a wata ta hanyar sana'arta ya ninka albashin Buba sau huɗu, ganin matar sa na samu sosai ya sa Buba ya sake ma ta gaba ɗaya ragamar gidan. Ba dama ta tambayi abu sai ya ce ai tanada kuɗi ta yi amfani da shi, haka nan duk wani hidima da ya ke yi da ya rage da kusan kaso saba'in. Idan ya je ya ciwo bashin kuɗi to Innayi ne za ta biya, ba ya kunyar tambayarta kuɗi kamar wanda shi ya ke ma ta wahalar. Duk kuɗin da ya ƙarɓa da sunan aro kuwa babu ranan biyan sa, Kunya da girmamawa ga miji ya sa Innayi ba ta iya tambayarsa kuɗin. Tun tana jira akan zai biya har ta yarda cewa duk kuɗin da Buba ya karɓa to ya zama sadaka. Mutane da dama da su ke ganin cinikin da Innayi ke yi su na mamakin yadda ko kaɗan babu chanji a tattare da ita. Ba ta saka kayan yayi ko kuma ta sayi abun yayi, koyaushe kuɗin ta ya ƙare akan hidimar gidan ta da 'ya'yan ta. A lokacin sallah haka za ta ƙoƙarta ta siyawa yaranta kayan yayi amma idan ka dubata sai ka ga ita ba ta saka irin kaya haka. Kullum aiki ta ke yi babu hutu, mutanen da su ka santa sosai su kan tausaya ma ta domin Innayi mace ce ta ƙwarai sai dai ba ta yi sa'an miji ba. Ɗabi'un Buba ko mutumin da bai taɓa shiga aji ba ba zai yi ba amma shi da ya ke da certificate ɗin primary school idan ka auna ɗabi'unsa abin sai ya baka mamaki. He's selfish and greedy... Innayi na da tsohon ciki mahaifin Buba ya rasu, kafin sati biyu aka raba gado. Buba ne ɗa na biyu kuma su biyu ne maza sannan ɗaya ƙanin sa ya jima da rasuwa, sai mata guda huɗu. Da aka raba gado Buba ya samu gona da shanaye. Wannan gado ya sa Buba ya fara gini a cikin gari, domin wannan ƙaramin boys quarters da su ke ciki ya mu su kaɗan. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarisa ginin saboda dama gini ne da aka fara ba a ƙarisa ba, sai ya siya ya ƙarisa. Yarinya mace Innayi ta haifa wanda ta ci sunan Sa'adatu. Da ke akwai ɗan kuɗi a wajen Buba wannan karan sai ya yi abun kirki, ya sayi kaya sosai lokacin suna. Rabon da ya siyawa Innayi kayan suna haka tun lokacin haihuwar Ado, Atamfofi ma su kyau guda huɗu ya siya ma ta ta yi shigar suna. Ya so ma ace ayi sunan yarinyar a sabon gida amma haka bai yiwu ba dan bai ƙarisa ba. Innayi ta yi farin ciki sosai ganin irin hidimar da yai ma ta har ta ke tunanin Buba ya chanja ne... Kafin rasuwar mahaifin Buba Harira ta fito daga gidan mijin ta, ta fara zawarci a karo na biyu. Akwai matan da kwata-kwata ba su ganin chanja aure a bakin komai, inda za ka ga sai mace ta yi aure ta fito ya fi sau uku. A lokacin da ta ke zawarci Harira ta ji labarin dukiyar da Buba ya samu lokacin da Uban sa ya rasu. Duk da yanzu ba da ba ne hakan bai hana ta ƙoƙarin neman Buba ba. Domin cikin manemanta duk tsofaffi ne 'yan shekaru hamsin zuwa sittin. Wani lokaci maza su kan yi wani abu dan su nuna isa da mulki akan mace. Hakan ce ta faru a wajen Buba domin yana jin labarin auren Harira ya mutu ya danno kai cikin manemanta. So ya ke ya nuna ma ta iyakarta kasancewa ta ƙi shi a baya. Ba a wani ɗau lokaci ba Harira ta amince da Buba inda shi kuma ya kawo kuɗi ma su yawa a matsayin sadaki aka ɗaura mu su aure. Batun tarewa ya ce sai nan da sati uku, zuwa lokacin ya kammala komai na gidan sa. Hakan kuwa aka yi, domin a cikin sati ukun ya kammala komai, yayinda Buba ya kai Harira ta je ta ga gida ta kuma zaɓi ɗakin da ta ke so. Dayawa maza su kan tafka wannan kuskure ko na ce cin fiska. Namiji ne za ka ga yana tareda mace shekara da shekaru, alokacin da ba shi da shi ta zauna da shi ta taimaka ma sa. Amma daga zaran ya samu abun hannunsa sai ya fara maganar ƙara aure, ba anan ne matsalar ba, matsalar shine amarya na zuwa za ka ga ya juyawa Uwargida baya, ya dinga fifita amarya akan uwargida, ya dinga ganin ai Uwargida is outdated. Innayi na zaune tana ba wa Sa'a nono Buba ya shigo da sallama muryarsa ɗauke da annashuwa. Innayi ta ma sa sannu da zuwa cike da ladabi tana tambayarsa ko ta kawo ma sa ruwa ya ce ta barshi. Ledar da ya shigo da shi ya miƙa ma ta ya ce "gashi nan sai ki ɗinka dan ranan Jumma'a za mu tare a sabon gida" Innayi ta amshi ledar tana godiya tareda addu'ar Allah ya sa su tare a sabon gida lafiya. Bayan ta gama shayar da 'yar ta ta fara ƙoƙarin shimfiɗata dan yarinyar ta riga ta yi bacci. Abunka da jariri wanda bai san komai ba sai abinci da bacci. Kaman daga sama ta ji Buba ya ce "Faɗima na yi aure fa" da fillanci ya faɗa duk da kuwa Buba bai cika yin yaren na su na Fulatanci ba, kaso tamanin cikin maganganun sa Hausa ne dan ko a yaran su ma Hausa ya ke mu su. Innayi ce ta dage da yi mu su Fulatanci har ta kai su na ji. Murmushi ta yi mai ciwo ta ce "Allah ya sanya alkhairi" Duk wani abu da ke taso ma ta tana ƙoƙarin danneshi. Ba wai ta sa a ranta ita kaɗai za ta rayu da Buba ba ko kuma tana kishin auren da yai, ko ɗaya ba wannan ba ne. Ɗacin da ta ke ji a ranta shi ne yadda har yanzu Buba bai ɗauketa a bakin komai ba, idan da adalci ai tun kafin ayi auren ya kamata ya sanar da ita, amma kwatsam sai dai kawai ya ce ma ta ya yi aure. Irin rashin adalci da mazaje dayawa ke tafkawa matan su Allah ne kawai zai saka mu su. Daga ƙarshe duk wani zagi da tsinuwa akan mace ake saukewa. Buba bai tsaya a nan ba ya ƙara da cewa "ita Amarya gobe Laraba za ta tare a gidan" Wannan karan ma murmushi Innayi ta yi ta ce Allah ya sa ta tare lafiya. Buba ya amsa da Amin yana murmushi. Wani lokaci idan mace ta fiye sanyi dayawa namiji ya kan ɗau wannan sanyi na ta a matsayin wata ƙofa ce da ya samu domin ya muzguna ma ta. Yayinda mace ta ke da zafi sai ka ga namiji yana kaffa-kaffa da ita. Wannan ya kan sa dayawa mata su zama ba sa iya yin wannan sanyi-sanyi ɗin ko kuma idan ma sun fara sai ka ga daga baya sun dai na. Mutane kaman Innayi kam ba sa iya chanja halin su ko da kuwa za su ƙare rayuwar su da namijin da ba ya ɗaukan su da daraja... Ranan Jumma'a kuwa Innayi da 'ya'yan ta su ka baro quarters su ka dawo cikin gari a gidan Buba da ya gina a Unguwar Kukadi. Innayi da ta zo ta yi tsammanin ta na zuwa za ta ga Amarya budurwa sai ta ga bazawara wacce ta ke gani idan Hariran ba ta fi Buba ba to za su zo dai-dai a shekaru. Sai dai miye na ta a ciki, Buba da ya gani yana so shi ya ɗaukota. Gidan na su ba laifi wadatacce ne domin da ka shigo akwai zaure inda aka yi ɗaki ɗaya sai idan ka shiga cikin gidan kuma akwai ɗakuna biyu a jere sai wasu ɗakuna biyun su ma a jere su na kallon juna. Chan wani fili kuma an fara gina ɗakuna huɗu irin na farkon amma ba a ƙarisa ba. Akwai banɗaki guda biyu akwai kuma ɗakin dafa abinci. Akwai rijiya da kuma ƙatuwar bishiyar dabino. Ɗakin da Buba ke son maidawa na sa saboda ya fi girma shi Harira ta zaɓa dan haka dole ya koma ɗaya ɗakin. Ko kaɗan girman ɗakin Harira bai tsolewa Innayi ido ba ita kan tunda akwai wadataccen wuri Alhamdulillahi. Rayuwa kam ta juyawa Innayi domin a da tana nan ita ɗaya da 'ya'yanta yanzu kuma sun koma su biyu ga Agola guda uku da Harira ta zo da su. Wani lokaci wasu mazan na da sakaci za ka ga 'ya'yan su ba wai yara ba ne sosai amma da zaran sun rabu da mace sai su bari ta tafi da su Agolanci wani gida, ba wai Agolanci ba kyau ba ne A'a amma wani lokaci duk munin gidan Uba ya fi ma akan ka je ka yi zaman Agola a wani gida... Yadda Buba bai daraja Inna yi ba haka Harira ma ba ta daraja ta, ta kowani kafa da ta samu ƙoƙarin muzgunawa Innayi ta ke yi. Ganin Innayin ba ta tanka ma ta ya sa maimakon ta dinga ragewa sai abinma ya dinga gaba-gaba. A haka sai ga labarin Baffa Habu ba lafiya aka aiko wa Innayi akan ta je ƙauye domin Baffa Habu na son ganinta. Innayi ta faɗawa Buba inda ya amince ta je ta yi kwana biyu. Sa'a kawai ta ɗauka ta wuce ƙauye saboda sauran yaran su na zuwa Makaranta. Ko da ta je ƙauye Baffa Habu maganar gado ya ma ta domin tunda aka raba gadon ɗan uwan sa bai damƙawa Faɗima na ta ba saboda ƙarancin shekarunta, ya cigaba da kula ma ta da dukiyarta, gashi yanzu cikin shanayen da aka ba ta har sun hayayyafa sun yi yawa. Gaban sauran 'yan uwan sa Baffa Habu ya sa aka fitar wa Faɗima gadonta, wanda ba ƙaramin mamakin dukiyar ta yi ba. Shanaye talatin da bakwai da kuma gona, ga kuma gida mai ɗakuna biyu wanda cikin gidan gadon su ne dama mahaifinta Muhammadu ya gyara ya zauna da matarsa Aminatu kafin rasuwar ta. Innayi ta yi kuka sosai domin Baffa Habu ya riƙe amana, tunda rainonta ya koma hannun shi bai taɓa banbantata da 'ya'yan sa na cikin sa ba, ga matar sa Hebbini itama Akwai kirki domin ta riƙeta tsakani da Allah... Bayan ta dawo ne ta sanar da Buba duk abinda aka yi. Buba ya sha mamakin dukiyar da Innayi ta samu dan ko shi da ya ke ganin ya gaji dukiya sanda mahaifinsa ya rasu bai kamo rabin abinda Innayi ta samu ba. Wannan dukiya da ya ji labari ya tsolewa Buba ido, nan da nan ya fara shiryawa Innayi magana akan yana so ta bashi aron wasu Shanu ya siyar zai ƙarisa ginin gida da shi idan ya samu kuɗi zai maida ma ta. Poor Innayi ta damƙawa mijinta ragaman dukiyarta, a tarbiyan da aka ɗaurata miji yana da damar da zai yi amfani da dukiyar mace a duk lokacin da ya ke so. Rashin ilimin addini da na zamani yakansa dayawa mazaje su na cutar da matan su simply because matan ba su san hakkin su ba. Buba bai yi batun gini ba ma sai da maganar auren sa ya kankama. Ƙauyen Saɗe ya je ya nemi yarinya budurwa 'yar shekara shabiyar wacce ta ƙarisa makarantar primary, da ke yanzu an fara barin 'ya'ya mata a ƙauye su na karatu musamman primary school ba kaman da ba. Maganar auren ma bai gayawa Innayi ba a bakin Harira ta ji wanda tunda yai ma ta maganar ta tada jijiyar wuya akan ba ta yarda ba. Shi kuwa ya ce mata huɗun nan sai ya cika su rus. The only place da namiji ke iya bugan ƙirji kenan "namiji mijin mace huɗu ne" Bai san hakkin mace ɗaya ba a kan sa balle har mata huɗu, amma haka zai dinga ɗaga kafaɗa yana burga, shi namiji ne, ai zai iya auren mata huɗu. Ya ciyar da su? Ya tufatar da su? ya yi adalci tsakanin su? Duk ba damuwar sa ba ne. Shi dai damuwar sa yana da ƙarfin da zai iya saduwa da mata huɗu dan haka zai auri mata huɗu... Koda daga baya da yai wa Innayi maganan auren itakam addu'a kawai ta ma sa duk da kuwa chan ƙasan ranta ta san Buba da dukiyar ta zai ƙara aure. Ba a ɗau lokaci ba Amarya Aishatu Indo ta tare a gidan. Ƙosai da Innayi ke yi ya fara kasawa, gashi cinikin ba kaman chan quarters ba dan a anguwar ta su gida uku ake tuyan ƙosai. Wannan ya sa ta yiwa Buba magana akan ya siyar ma ta da shanu ta yi jari da shi ta fara sai da wasu abubuwa a gida. Yadda ka san dukiyar sa ne haka ya dinga hura hanci yana kame-kame kafin daga baya ya amince. Dai-dai kuɗin da zai bawa Harira da Indo haka zai ba ta duk ranan girkin ta gashi kuma ita ke da 'ya'ya dayawa dan bayan Sa'a ta sake haihuwan Idrissa. Shiyasa ta ga dole ta ƙara da wani abun dan sana'ar ƙosai ya ja baya... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 05 (Free book ne) *Unwanted child* A hankali rayuwar ta cigaba da tafiya, da daɗi ba daɗi haka iyalen wannan gida ke rayuwa. Innayi kam ta zama mai sana'a goma da ashirin. Ita ce ƙosai, ita ce sai da icce, daddawa, ga kayan miya. Kuma Alhamdulillah akwai Albarka a ciki. Harira ma da ta ga halin Buba ba zai kai ta ba sai ta fara sana'ar ta ta sai da Masa. Indo kuma sana'ar kitso ta ke yi. Zuwa yanzu dukkan su halin Buba ya bayyana mu su, Buba kan sa kawai ya sani, albashin sa bai taka kara ya karya ba amma a hakan ba ya mu su adalci, tun su Harira da Indo na faɗa akan ƙarancin kuɗin cefane da ya ke ba su har su ka haƙura su ka bi sahun Innayi su ka rungumi haƙuri. A gidan yanzu kowa tashi ta fishshe shi su ke. Harira ta haifi ɗa ɗaya mai suna Yusufu, da ke sunan mahaifin Buba ne sai su na kiran shi da Babangida. Ita kuwa Indo yaranta biyu, Rabi da Maryam. Innayi kuma 'ya'ya shida. Ado ya gama secondary school ya samu admission a Teachers College wacce yanzu aka upgrading na ta zuwa AD Rufa'i College for Legal and Islamic studies Misau ( ADR CLIS). Ranan ya zo ya sanar da Buba tareda maganar kuɗin registration da sauran abubuwa. Buba ya hau shi da faɗa akan shi lokacin da ya na shekarun sa ya fara aiki yana ciyar da kan sa amma shi a shekaru shatakwas ba abinda ya sani sai dai a bashi ya kashe. Ya haɗa da cewa Bokon banza Bokon Wofi. Ado ya bar wajen sa cike da ɓacin rai. Kai tsaye wajen Innayi ya nufa ya na ƙorafi, duk abinda bai iya faɗa wa Uban sa ba shi ya ke gayawa Uwar sa tunda dama Uwa Uwa ce. Innayi ta fara bashi haƙuri tareda alƙawarin za ta san yadda za ta yi a samu kuɗin makaranta. Har ranta tana so 'ya'yanta su yi karatu saboda yadda rayuwar ta ke chanjawa. Sai dai duk da haka Ado bai da niyyar taimakon kan sa dan ba sana'ar da ya nema ko kuma ya ke yi. Da farko ma Uban sa ya kaishi shagon ɗinki ya dinga zuwa idan ya dawo daga makaranta amma ya fara zuwa ya ji wahala ya gudu. Ƙanin sa Iro kuwa shi da kan sa ya kai kansa shagon wani bakanikin Mota ya na koya, gashi yanzu sosai ya iya gyaran Mota. Kafin sati Innayi ta harhaɗo kuɗi ta ba wa Ado ya karɓa ya je ya fara registration. Halima ta zama 'yan mata kuma alamu sun nuna aure ta ke so ba Makaranta ba dama Buba ya ce ba yarinyar sa Mace da za ta yi gaba da Sakandare, to Halima kuwa tun tana JSS 2 ta fara tsayawa da Samari. Innayi ta yi ma ta magana akai ta ƙi ji dan haka ta haƙura ta zuba ma ta ido. Ta so ace Halima ta ƙarisa Sakandare ɗin kamar yadda Buba ya ce amma a yadda ta ke yanzu duk ta watsar da karatun ta ma dena zuwa. Farin fata da kyau shi ya ke ruɗar da Halima yadda Samari ke yayinta hakan ya ƙara ma ta falli. Cikin ma su zuwa wajen ta tafi ba wa Alhaji Nuhu mahimmanci saboda duk ya fi sauran arziƙi yana da gida da mota sannan ya je shi Makkah, Ɗan kasuwa ne da ya ke tashe a lokacin. Ganin yadda ake yawan sallama da Halima ya sa Buba ya ce ta tsaida ɗaya aciki ta turo shi saboda ba ya son a ɗau lokaci tunda ta dena zuwa makaranta. Halima ta bi shawarar zuciyar ta da kuma shawarar ƙawayen ta ta amince da Alhaji Nuhu. Innayi da ta ji zaɓinta hankalinta ya tashi domin ta san mutum irin Alhaji Nuhu ba tsakani da Allah ya ke son Halima ba, soyayya ce kawai ta sha'awa ya ke yi ma ta saboda ƙuruciya da kyaun Haliman. "Amma Halimah ni ina guje mi ki auren da babu farin ciki. Idan har za ki bi shawarata ki amince da Malamin makarantar ku" "Allah ya kiyaye Innayi. Mi za ayi da Malam Faruƙ baƙin talaka, malamin primary ne fa. Ni ba zan yi aure na ƙare kamar ki ba kullum ba kwanciyar hankali" Innayi ta yi murmushi ta ce " idan farin ciki ki ke nema, ina da yaƙinin Malam Faruƙ zai faranta mi ki rai har ƙarshen rayuwar ki. Yana da ilimin addini ga na boko ma Alhamdulillah yana da shi, zai riƙe ki da daraja kuma gaba za..." "Dan Allah ki bari haka. Na riga na zaɓi Alhaji Nuhu shikenan, ki min addu'a kawai, idan kuma ba kya son na shiga gidan arziƙi ne sai na ji dalili" Innayi ta girgiza kai kawai tanajin ɗaci a ranta domin ta hango kwaɗayi irin na Buba a tattare da 'yar tata, dalilin kenan da ya sa Halima ta rufe ido a kan sai Alhaji Nuhu. Tun lokacin da Alhaji Nuhu ya fara zuwa Halima ta juyawa Malam Faruƙ baya saboda shi ba ya kashe ma ta kuɗi kamar yadda Alhaji Nuhu ke ma ta. Tun alokacin ta ke yiwa 'yarta nasiha amma sam ta ƙi ji, ga shi Buba ma ɗan kuɗi da Alhaji Nuhun ke sake ma sa idan ya zo ya sa ya fi nuna ra'ayin sa akan Alhaji Nuhun. Ba a ɗau lokaci ba Alhaji Nuhu ya turo mutanen sa aka sa lokacin aure zuwa wata uku. *** Rabon da Buba ya waiwayi shimfiɗar Innayi ya fi wata takwas. Shi ya sa yau ɗin da ya buƙaci hakkin sa ta sha mamaki sosai. Duk ranan girkin ta ba ya kulata, iya ka ci ya ba ta kuɗin cefane, randa tsiyar sa ya tashi kuwa ya ce ba shi da kuɗi. A wajen sa Innayi ta tsufa, ba ta buƙatar namiji, to dama ai buƙatar sa kawai ya ke biya ya tashi ya tafi dan indai batun gamsuwar kwanciyar aure ne to kuwa tun ranar farko har zuwa yau Innayi ba ta taɓa samun wannan gamsuwa ba. A jahilcin ta, ita ta ɗauka dama maganar shimfiɗa to aikin mace shi ne mijinta ya gamsu da ita, ita kuma ta ɗau ciki ta haihu. Ba ta san cewa yadda za ta gamsar da namiji haka shima namiji yana da haƙƙin gamsar da ita. Dayawa maza na wannan kuskuren, da mace ta fara girma sai su dinga ja baya da ita su na ganin kamar ba ta buƙatar kwanciyar aure. Wa su za ka ji su na cewa ai yanzu an girma sai dai a barwa yara wannan. Ko kuma idan mace ta nuna buƙatar ta sai su ce wai ke ba kya girma ne? Ko so ki ke 'ya'yan ki na haihuwa kema ki na yi?. Wasu mazan kuwa ba sa damuwa da gamsar da matan su, su na biyan buƙatar su za su tashi su yi gaba shikenan. Duk da yanzu abun ya fara raguwa amma har wayau wa su mazan ba sa damuwa da shin mace ta gamsu ko ba ta gamsu ba? Indai su sun samu gamsuwa to shikenan an wuce wajen... Kwanci tashi bikin Halima na matsowa ana ta kan shirye-shirye wanda duk da dukiyar Innayi ake yi dan idan ka cire gida to Buba ba shi da komai. Shanun sa gaba ɗaya sun ƙare, hakama gona ya siyar. Ba laifi an yiwa Halima kayan fidda kunya duk da kuwa Alhaji Nuhun ya nuna ba sai anyi ma ta komai ba. Aka yi biki lafiya aka kai Halima ɗakinta tana shekara shashida a duniya. Ba ita ɗaya ce ba dan Alhaji Nuhu na da mata biyu kuma dukkan su sun haihu... Tun ana hidimar biki Innayi ta gane tana da shigar ciki wanda ya sa ta yi mamaki ƙwarai dan autan ta Idrissa ya cika shekara bakwai kenan, har ma gani ta ke ta wuce haihuwa yanzu. Maimakon cikin ya sa ta farin ciki sai ya zama kunyar cikin ta ke yi. Mutanen gidan ba su farga da cikin jikinta ba sai da ya kai wata shida. Harira ce ma ta taɓa tambayarta ko ciki gareta lokacin cikin na wata uku, amma rashin samun amsa daga wajen Innayin ya sa ta watsar da zancen. "Yanzu ke Innayi a wannan talauci ki ke samun ciki. Yo ko Indo ai ta haƙura da haihuwa a gidan nan" Innayi ta sunkuyar da kai cike da kunya ta cigaba da cura daddawa da ta ke yi. Harira kam ba ta yi shiru ba ta cigaba da mita, kafin dare kowa ya san Innayi na da ciki. Wai abin takaici shine Buba da kan sa ya ke zagin Innayi akan ta ɗau ciki bayan ta san ba kuɗi gareshi ba. Hmmm Namiji kenan! A yadda Buba ya ke yanzu yana samun kuɗi kaɗan aure zai ƙara amma shi ne dan za su samu ƙaruwa da uwargidan sa ya ke jin haushi. Haka Innayi ta shanye duk wasu maganganu da ake ta faɗa ta cigaba da renon cikin ta cikin wahala, tunda cikin sana'o'inta ba wanda ta fasa. Ana haka Buba ya fara ciwon ido, tun abun ɗaukan sa wasa yana shan maganin gargajiya har abu ya munana dan yanzu ido ɗaya ba ya gani ɗayan ma ba wai sosai ya ke gani ba. Da ya ga ba Sarki sai Allah sai ya amince ya je asibitin General Hospital Misau wanda su kuma su ka tura shi asibitin Aminu Kano saboda ya ga ƙwararren likitan ido. Jin bayanin kuɗi Buba ya ce a barshi ba inda zai je. Daga baya da aka takurashi sai ya amince amma dai ba shi da kuɗin tafiya sai dai idan za a biya ma sa. Innayi ta ma sa magana akan cikin shanun ta a siyar da wasu ayi kuɗin magani, sai ya hauta da faɗa. "Kina ta maganar shanu, wai shanun nawa ne kam? To bari kiji ba bu ko shanu ɗaya da ya saura. Bikin Halimatu duk da mi aka yi?" Innayi ta danne ɓacin ranta ta fara bashi haƙuri. Saboda gani ta ke babban zunubi za ta samu idan mijinta yai fushi da ita. Sai da ya fice daga ɗakin ta sauke ajiyar zuciya wanda ya sa hawayen da ke maƙale a idonta su ka sauko. Ita kan ta ba lafiyar gareta ba daurewa kawai ta ke yi amma tun lokacin da Buba ya fara ciwon ido ta ke cikin damuwa. Gona guda da ya saura ma ta cikin gadon Uban ta wanda ɗan uwanta Aliyu ya ke noma aciki ta nemi siyarwa shi kuma Aliyun ya siya. Da kuɗin da kuma wasu kuɗaɗen ta na kasuwancin ta ta haɗa ta damƙawa ɗan ta Iro ya wuce da Buba Kano. Iro ya ƙare Sakandare kuma alamu sun nuna ba shi da niyyar cigaba da Boko dan yana tunanin buɗe nashi shagon kanikanci nan ba da jimawa ba. Da su ka je aka duba Buba aka bashi wasu magunguna tareda cewa su dawo nan da sati biyu, saboda za'a gani ko aiki za su ma sa ko kuma za a cigaba da ɗaura shi akan magani... Bayan su Buba sun dawo daga Kano da kwana uku Innayi ta fara naƙuda cikin dare, duka haihuwanta a gida ta ke yin su. Lokacin haihuwan Idrissa kam ita ɗaya ta haihu sai kawai ganin ta aka yi da jariri. Wannan karan ma so ta ke ta gwada haihuwan da kan ta musamman saboda dare ne ba ta son tayarda kowa, balle cikin da kowa baya so, ba ta so ta hanasu bacci saboda shi. Tana jin jiki amma haka ta daure ta cize tana ƙoƙarin ganin ta haihu ita ɗaya. Ta kai awa ɗaya tana jin jiki kafin kyakykyawar jaririyarta ta fito. Ta yi hamdala a ranta tare da ƙoƙarin ɗauko reza dan ta yanke cibiyar yaro amma kawai sai ta sake jiki ta faɗi... Kukan da jaririyar ke tsalawa ya fargar da Harira da ke bacci, da farko ta share kukan daga baya ta tuna ai ba su da jinjiri a gidan sai dai idan Innayi ce ta haihu. Da kukan yai yawa sai ta tashi ta fito tana ƙunƙuni. Tana zuwa ɗakin Innayin yanayin da ta sameta ya tsorata ta, ta rinƙa salati tana kiran sunan Buba da ke ɗakin Indo da kuma Ado da Iro da su ke ɗakin zaure... Kwanaki biyar Innayi ta yi ba ta san inda kan ta ya ke ba, dan ba ta buɗe ido ba ma sai a kwana na huɗu. CS aka yi aka cire ɗaya jinjirin da ke cikin ta wanda ya riga ya mutu a ciki saboda wahala. Likitoci sun yi faɗa sosai dan yadda su ka ga Innayin. Ba dan an kawota asibiti da wuri ba mutuwa za ta yi. Babu jini ajikinta ga kuma haihuwar da ta yi ƙoƙarin yi da kan ta duk ya wahalar da ita. Su kan su 'ya'yanta da kishiyoyinta ba su ɗauka za ta rayu ba sai ga shi Alhamdulillah da ita da 'yarta sun rayu. Ɗaya yaron kuwa ana ciro shi aka je aka ma sa sutura aka bisine shi... Sai da Innayi ta sha jini leda uku kafin ta ɗan fara samun kuzari. A hankali da ta yi kwana goma a asibitin kafin ta iya tunowa da komai har ta tuna cewa fa haihuwa ta yi. Da ke Innayi ba ta da ruwan nono tuni aka ɗaura jinjira akan madara. Har lokacin kuwa ba a raɗawa jinjirar suna ba, balle maganar yanka rago. Ranan da Dr Imtiaz ya ke round ya iso wajen Innayi ya samu tana bawa 'yarta Madara ya tambayi sunan yarinya, Mairo 'yar Baffa Habu da ke jinyar Innayi ta ce ai har yanzu ba a sa ma ta suna ba, Dr Imtiaz wanda balaraben ƙasar Egypt ne ya tambayi dalili. Mairo ta ce ai ba abunda za a yi sunan da shi ne. Dr Imtiaz ya girgiza kai saboda jin wannan tsagoron jahilcin. "Idan na ba ta suna za ku kirata da shi?" Mairo ta kalli Innayi, Innayi ta gyaɗa ma sa kai. Dr Imtiaz ya ƙarɓi yarinya ya ma ta huɗuba da suna RAUDHA "Sunan ƙanwata ce amma Allah ya ma ta rasuwa" Innayi da Mairo su ka ce Allah ya jiƙanta. Ya saba ganin Fulani ma su sakaci da lafiyar su hakanan ya kan nuna ɓacin ran sa garesu amma haka kawai Allah ya haɗa jinin sa da Innayi. Tausayinta ne ya shigeshi tun daren ranan da aka kawota asibitin rai a hannun Allah. Bayan fitar Dr Imtiaz daga ward ɗin Innayi ta dubi jaririyarta, ta kira sunan da aka sa ma ta a hankali RAUDHA... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 06 (Free book ne) *A Mother alone* Al'ada da ake yi da jimawa wanda ya fi ƙauri tsakanin Hausawa da Fulani inda za ka ga idan mace na jinya za ta koma gidan su har sai ta warke, Al'ada ce da kwata-kwata bai kama hankali ba. Idan ina da lafiya mu na tare amma idan jinya mai tsanani ya kamani to sai dai na koma gida wannan kwata-kwata bai dace ba. Amma Alhamdulillah tunda yanzu neman ilimi da ake ya sa an samu massive chanji sosai. Duk jinyar Innayi da ta yi a asibiti 'yan uwanta ne su ka biya kuɗi su ka kuma yi ma ta hidima. Buba kam dama fama ya ke da kan sa balle ma ace zai iya taɓuka wani abu. Daga wajen Alhaji Nuhu mijin Halimah ake tunanin samun kuɗi sai dai ko gaisuwa bai zo ya yi ba balle ya kawo wani abu. Haka Innayi ta yi kwana ashirin da bakwai a asibiti kafin aka sallameta. Zuwa lokacin ta warke sosai kuma ta yi kyan gani, 'yar ta Raudha ma na nan cikin ƙoshin lafiya madaran da ta ke sha sosai ya karɓeta... Bayan Innayi ta dawo aka shiga wani sabon rayuwa. Sosai aka ja ma ta kunne a asibiti akan ta rage ayyukan da ta ke yi idan har ta na son ta samu lafiya. Hakan ya sa ta ajiye sana'ar ƙosai da daddawa a lokacin, sai dai fa abubuwa ba su zo ma ta da sauƙi ba. Domin sai da ta ƙwammaci gara ta koma sana'ar ta saboda asirinta ya rufu da babu da ta ke fama da shi. Mijinta Buba kam tun da ya ji ya fara samun sauƙi ya watsar da maganar komawa asibiti. Dama kuma rashin lafiyar Innayi ya ɗauke hankalin iyalin sa daga batun ciwon idon sa. Raudha Auta, Raudha 'yar gata, Raudha Alkhairi, Raudha haske, kaɗan daga kirarin da Innayi ke wa 'yar tata kenan. Duk da kuwa a zahiri Raudha ba cikin gata ta taso ba, asalima duk cikin yaran Innayi ita kaɗai ce ba a yanka ma ta ragon suna ba balle har ayi wani hidiman suna. Hatta kayan sawa duk kunce ake sa ma ta sai da ta kwana biyu a duniya kafin aka samu kaɗan daga cikin ma su zuwa gaishe da Innayi su ka zo da kyautan kaya wa jinjira. Wata uku da haihuwar Raudha Buba ya makance. Ya fara da ganin biji-biji ne, bayan kwana uku idon ya dena gani gaba ɗaya. Tashin hankali ya shiga wannan gida domin Buba tamkar mahaukaci haka ya dawo lokacin da idon sa ya makance, faɗa ya ke da kowa tareda baiwa iyalensa laifi bisa makantar sa. Anyi ƙoƙari an tara kuɗi an maida shi Kano amma abin duk maganar kuɗi ne, sannan bayan kuɗi an nuna mu su ko da anyi ma sa aikin ba su da cikakken yaƙinin idon sa zai koma gani kamar da. Kuɗi su ka yi wahalar haɗuwa har ta kai 'ya'yan sa su ka yi shawaran sai da ɗaya ɓangaren gidan sa wanda bai ƙarisa ba. Buba yai fir akan shi ba za a saida ma sa gida ba. Daga ƙarshe aka nemo bashi da ƙyar akan za a koma da shi a ma sa aiki. Buba ya ce ya fasa, wai an ma sa kwatancen mai magani a ƙauyen Takadunga chan zai je. Akayi-Akayi da shi ya ƙi zuwa asibiti dan haka aka barshi. Daga ƙauyen Takadunga sai da ya ziyarci ƙauyuka biyar amma still ba maganar sauƙi. Kuɗin da aka ci bashi dan a ma sa aiki a asibiti kaf ya kashe su wajen ma su maganin gargajiya. But still ba abinda ya chanja Buba ya zama makaho. Da ya ga ba shi da sisi sai ya haƙura ya koma zaman gida. Saboda zuwa aiki ba zai yiwu ba ya sa ya yi voluntary retirement ya cigaba da jiran kuɗin pension. A wannan lokaci ne Buba da ya ke ji da ƙarfi da kuma kyau da kwarjinin Fulani ya koma abun tausayi. A lokacin ne ya san cewa gani rahama ne na Ubangiji. Gashi dama lokacin da yana da ido bai jawo kowa ajikin sa ba hakan ya sa yanzu da ya rasa ido ya koma bashida kowa, bashida aboki da zai kira na shi sannan bashi da ikon gane fari ko baƙi. Indo ce ta fara sarewa da shi. Ganin ga Makanta da baƙin hali ya sa ta ce ba za ta iya zaman ba ta nemi ya sawwaƙa ma ta. Sai da aka kai ruwa rana kafin ya amince ya sawwaƙa ma ta. Da za ta tafi ta ɗau yaranta biyu ta yi gaba da su. Ta sani ko ta barsu ma wahala za su sha, Harga Allah ta san Innayi za ta iya riƙe amanar su amma kuma itama fama ta ke da na ta 'ya'yan kuma ba wani samu ta ke ba shiyasa ta zaɓi tafiya da yaran. Harira kam ba ta tafi ba amma kuma darajar Buba kaf ya zube a idonta. Dama tuntuni ta dena ganin sa da kima amma kasancewar sa makaho ya sa ko kaɗan ba shi da wani matsayi a wajen ta. Tun ana rabon kwana tana girki da shi har ta zo ta ce ba za ta iya ciyar da shi ba, idan dai bai ba ta kuɗi ba to ba za ta taɓa zuba ma sa abinci ba. Tun Buba na faɗa har ya gaji da kan sa ya bari, sai dai ya wuni yana zaginta a gidan, wani lokaci ta biyeshi su yi ta yi wani lokaci kuma ta shareshi. Zaman ya koma Harira ke ciyar da kanta da 'ya'yanta ita kuma Innayi na ciyar da Buba da na ta 'ya'yan. Girkin da ba ya son ci lokacin da ya ke da lafiyar sa yanzu kam ba shi da zaɓi dole shi ya ke ci. Batun a je rumfar mai shayi ko rumfar mai tsire duk bai taso ba tunda ba kuɗi sannan ba ido. Innayi ta nemi rancen kuɗi a wajen wani Baffan ta, shi kuma tausayinta ya sa ya ba ta kyautar shanu biyu. Ta siyar da Saniya ɗaya ta sa aka siya ma ta Injin markaɗe, sauran ta zuba a jarin ƙosai, maimakon ƙosai zalla da ta ke yi a da sai ya zamana ta fara yin ƙosai da Koko. A haka rayuwar ta cigaba da tafiya, Da aka fara biyan kuɗin pension Buba ba abinda Buba ya chanja na ha'inci, ya fara ba su kuɗi amma kuɗin da ya ke ba su ba adalci aciki. Kuɗi ne kaɗan zai bayar ya ce ayi cefanen sati da shi, bayan ko cefanen kwana biyu ba zai kai ba. A irin wannan yanayin ne watarana su na masifa kamar yadda su ka saba yiwa junan su Buba ya ɗau sandar sa ya bugawa Harira a wuya. Harira ta sa ihu da kururuwa tana cigaba da zagin Buba tareda faɗin ba dan albarkacin Yusuf da ke tsakanin su ba da ba abinda zai hana ta rama dukan nan. Buba ya harzuƙa ya cigaba da zagi ƙarshe dai sai da ya sa Harira ta tofa ma sa yawu ta fita daga ɗakin tana zage-zage. Tana shiga ɗaki ta fara harhaɗa kayanta shi kuma Buba na ɗaki yana faɗin "Harira ki bar min gida na, tunda ba ki san arziƙi ba ki je chan ki yi iskancin ki a wani gidan ba nan ba. Na rufa miki asiri na aureki shine yanzu za ki min tijara, ki je na sakeki saki uku, Allah ya isa tsakanina da ke" Duk zage-zagen su ba wanda Innayi ta tanka wa acikin su. Markaɗen Gero da ta ke yi nan ta maida hankalinta, lokaci zuwa lokaci kuma tana waiwayan Raudha da ke wasa a ƙofar ɗaki. A ranan kaf kayan Harira sai da ta zo ta kwashe. Abunka da dama ba tsakani da Allah ake zaman ba, Da sana'ar Masa da Harira ke yi ta riga ta sayi fili ta fara gini kuma duk ba tareda Buba ya sani ba. Shiyasa ta ke gani rabuwa da Buba alkhairine ma a gareta dan za ta samu daman ƙarisa gininta ta koma gida ba tareda damuwa da wani Buba ba. Yanzu kam ko da za ta kuma wani auren to a gidan ta za ta zauna sai dai Mijin da ta aura ya dinga zuwa... Babu Indo babu Harira, gidan ya koma na Innayi ita ɗaya kamar farkon auren su, sai dai wannan karan akwai 'ya'ya har bakwai tsakanin su. Wasa wasa rana ɗai ɗai ya haɗu ya zama sati ya zama wata sannan ya zama shekara, daga nan shekaru su ka dinga ja. Abubuwa sun chanja a wannan gida haka nan kuma wasu abubuwan su na nan yadda su ke. Indo ta sake wani aure a garin Darazo, duk lokacin da ta samu zuwa garin Misau ta kan zo su gaisa da Innayi, haka nan za ka ga ta zo ma ta da abun alkhairi wani lokaci sabulu, Omo ko kuma kuɗi. Su biyu ne a wajen Mijinta, kuma ta ga chanji sosai a gidan na ta saɓanin gidan Buba. Mijinta Malam Muhammad sana'ar sai da Kifi ya ke yi kuma yana da tausayi ba kamar Buba ba, yana ƙoƙarin kula da iyalinsa gwargwadon ikon sa, kuma ba laifi masanin addini ne mai son Ibadah. A ɓangaren Harira kuwa ba ta sake wani auren ba. Tana nan a gidan ta da ta gina. Sana'ar ta ta ma sa ta kuma haɓaka, domin yanzu burinta shi ne zuwa Makkah. Ta samu tayin aure a wajen mutane da dama amma ta riga ta ce aure ba ya gabanta yanzu, ko da za ta yi wani auren to sai dai idan ta cika burinta ne na zama Hajiya... Innayi kam tana nan ba wani cigaba a tattare da ita a babin karan kan ta. Tana samun kuɗin amma a wajen 'ya'yanta ya ke tafiya. Ko da Buba zai yi adalci, kuɗin Pension da ya ke samu ba wani abun kirki ba ne, ga shi da ya ke ƙaramin ma'aikaci Masinja, balle kuma shi ɗin ba adali ba ne. Halimah da ta ke tunanin samun arziƙi a gidan Alhaji Nuhu ba abinda ta samu sai tsiya, Alhaji Nuhu irin mazan nan na da za su iya kashewa Mace ko nawane a waje amma da zaran ta shigo to shikenan ita da tsumman goge ƙafa ba maraba. Watannin farkon auren su ta ga gata a wajen sa kamar ba gobe amma tunda ta samu ciki ya fara chanja ma ta. Lokacin haihuwan Raudha da Innayi ta yi kusan wata a Asibiti sau ɗaya ya bari ta je ta ga Mahaifiyarta hakanan ba abunda ya ba ta na alkhairi, haka ta je ta dawo hannu lami. Sai daga baya ne ma ta ɗauki zannuwanta biyu ta siyar a ɓoye ta aikawa Innayi kuɗin. Haihuwa ɗaya biyu duk ta lalace ba wani jin daɗi, musamman gashi ya ƙara aure yana yayin Amarya a lokacin. Shekaran Amarya na uku ne karayar arziƙi ta sameshi, ta kai bai tsira da komai ba sai gidan sa. Taurin ran sa ya kuma ƙaruwa. Gashi ya ƙi sakin ko ɗaya daga cikin matan sa, su kan su matan sun ka sa neman saki a wajen sa duk tsiyar da ya ke mu su, abun dai kamar magani. Sai gashi cikin shekaru goma na aure da ta ke hangowa kan ta zama wata babbar Hajiya sai ga shi ta koma da ita da uwar ta Innayi banbancin kaɗan ne. Har wani lokacin tana tunanin gara Innayi tunda ita tana sana'a tana samu, ita sana'ar ma ta kasa yi saboda tsoron Alhaji Nuhu. Ta yi dana sani a lokacin da ya zame ma ta ƙeya. Ina ma ta ji maganar Innayi, ina ma da Innayi ta yi shawara ba da ƙawaye ba, Inama ta bi maganar Uwarta ba ta bi son zuciyar ta ba. Ba abinda ke ƙara ma ta ɗaci a rayuwar ta irin yadda ta ga lokaci guda Malam Faruƙ da ta rena a baya kasancewar sa Malamin Makarantar Firamare ne, sai ga shi Allah ya ɗaukaka shi. Zuwa yai ya ƙaro karatu da ya dawo aka bashi koyarwa a CLIS. Yanzu ya zama Lecturer yana chan da matar sa hankali kwance. Dama duniya kenan, Allah kaɗai ke ba da arziƙi. Shi ya ke ɗaukaka wanda ya so ya kuma ƙasƙantar da wanda ya so, samu da rashi duk daga gareshi ne... Saɓanin Halima ita Sa'adatu ta so karatu, domin bayan ta ƙare Sakandare ta nuna kwaɗayin cigaba da karatu. Da ke Jamb ɗinta bai yi kyau ba yayanta Ado ya ba da shawaran ta nemi makarantar Health Technology da ke Ningi. Hakan kuwa aka yi ta cika form ɗin ta je ta yi jarabawa ta samu. Da aka zo maganar tafiya ne Buba ya fara faɗa wai taya zai bar 'yar sa mace ta je har wani gari karatu shi lallai bai yarda 'yar sa ta je Ningi ba. A lokacin har Innayi ta nuna rauninta duk da kuwa tafi kowa kwaɗayin 'yarta mace ta yi karatu amma ganin mijinta ba ya so ya sa ta fara ba wa Sa'a haƙuri akan ta haƙura da tafiyar. Magana dai ta kawo cece- kuce har ta kai sai da Baffan Buba ƙanin mahaifinsa wanda ya ke kamar Kakan su Sa'a ya shigo zancen. Daga baya Buba ya ce ya yarda, abin ma har da abin dariya. Babu ko sisin Buba da zai yi ciwo idan Sa'a ta tafi makaranta amma haka nan ya ke ta ɗaga jijiyar wuya akan shi 'yar sa ba za ta cigaba da karatu ba... A wannan gaɓar Innayi tana ɗan samun sauƙin wasu abubuwan saboda Iro ya buɗe shagon gyaran mota yana ɗan samu kuma ba laifi yana kawo wani abu gida. Sai kuma Baffah wanda ya ke aji biyu a ATBU kuma duk lokacin da ya ke gida yana 'yan buga-buga yana samun kuɗi. Duk cikin yaran shine zai iya kashe ko nawa ne saboda Innayi. Yana aji huɗu a sakandare lokacin wani sallan Azumi ya je yai buga-bugan sa ya siyawa Innayi Atamfa ya kawo ma ta tareda hijabi. Ranan Innayi sai da ta yi hawaye, domin ranan ne na farko da ɗaya daga cikin 'ya'yan da ta haifa ya siya ma ta kaya. Ado da ya ke Babba ya ƙare Diploma kuma ya samu koyarwa a wata Sakandare school, duk kuɗin sa tarawa ya ke akan zai yi gini yai aure. Gefen da Mahaifinsa Buba ya ka sa ƙarisawa ne ya siya ya rusa aka fara ma sa ginin zamani na block a wajen. Da an taɓashi maganar kuɗi zai fara cewa "wai bakwa ganin gini na ke yi ne?" Wannan hali na sa ya sa ko da wasa Innayi ba ta taɓa tambayar sa kuɗi ba tunda ta ji yanai wa ƙannen sa irin waɗannan maganganu... Idrissa Buba Pakkari wanda daga shiga aji uku a sakandare ya maida sunan sa zuwa Idris Abubakar Pakkari, hot guy kenan, aka IDAP aka sexyfulani, aka Baban love, aka Babban yaro. Tsayin sa, farin sa, dogon hanci da kuma lallausan baƙin gashin da ke kwance a kan sa, su suka zama abin tinƙahonsa a zamanin da mata ke tururuwa a wajen namiji mai kyau. Ɗan farin Bafulatani mai kyau da kwarjini kenan, ga ilimi ga murya mai zaƙi. Tun yana yaro halayyarsa ta burga ta fara bayyana balle kuma da ya fara girma ya ga yadda mata ke zancensa. Ko kaɗan hidimar gidan su ba ta gaban sa, shi dai ya ci ya sha ya kuma dinga turawa mata wasiƙun soyayya yana haɗa ƙawaye faɗa. Lokacin da ya zama Headboy a makarantar Government Comprehensive Day Secondary School Misau zo ka ga girman kai da ɗagawa. Yadda ya ke yi a waje ka ɗauka ɗan gidan mai martaba Sarkin Misau ne, alhali kuma shi ɗin ɗa ne a wajen Buba Makaho da Innayi mai ƙosai ko Innayi mai Daddawa. Ba ya aikin komai sai dai a bashi ya kashe, duk kuɗin da ya ke tarawa kuwa wajen turare, ƙananun kaya da takalmi ya ke ƙarewa. Cikin ikon Allah bayan ya ƙare secondary school ya samu admission a BUK, wanda lokacin sai da Innayi ta haɗa da sayarda Injin ɗin ta na markaɗe kafin kuɗin makarantar sa su ka haɗu. Da ya je Jami'a idon sa ya kuma buɗewa sai son duniya da girman kai ya ƙaru. Shine kullum cikin yiwa mata hidima, assignment, notes da kuma goya su idan za a yi test ko exam. Indai mace na da kyau ko kuɗi to haka za ka ga Idris yana kaffa-kaffa da ita yana maƙale ma ta kaman chewing gum. Su ma matan dai duk sammakal domin Idris na da kyau ga shi da ilimi shiyasa da mata 'yan ajin su da wanda ba 'yan ajin su ba haka za ka ga ana ta wani shishshige ma sa... *** Buba yana zaune a ɗakin sa yana cin tsire ya ji muryan Raudha na ƙwalawa Innayi kira. "Baba Baba ina Innayi?" Ya jiyo muryan 'yar ta sa tana nufo ɗakin sa. Ya sani za ta iya shigowa ɗakin shiyasa yai saurin tura ledan tsiren ƙarƙashin gado. Yanzu ya fara ci dan yanka uku ya ci gashi yadda ya ji nauyin ledan ya san dayawa aciki dan yana ji Alhaji Yamai ya ce a sawa Buba tsire na ɗari biyu. Ya fita ne wajen Isa mai tsire ya na doddogarawa da sandar sa ya jiyo kamar muryan Alhaji Yamai a wajen sai ya shiga yiwa Alhajin daɗin baki har Alhajin ya ce a sawa Buba tsire, da a wajen zai ci sai ya ji wani a wajen na cewa yawwa Buba ka gyara zama mu sa ma ka albarka, hakan ya sa yai wuf ya ƙarɓi ledan ya ɓoye a rigar sa ya yiwo gida. Normally idan ya je wajen Isa mai tsire haka zai yi ta daɗin baki har Isan ya gaji ya bashi alakoron tsire kaman yanka uku haka. Randa Buban ke da kuɗi kuwa haka zai zauna ya siya ya cinye a wajen kamar yadda ya saba tun ƙuruciyar sa tun kuma yana da lafiyar ido. Duk namijin da ke zuwa gaban mai tsire ko balangu ko mai shayi ko wani abun maƙulashe ya cinye ba tareda ya kaiwa iyalen sa ba Allah ya shiryeshi. Its bad its very bad, mummunan hali ne da kan iya sawa mutum ya samu zunubi a wajen Allah. Za ka ga wasu 24/7 matan su ɗumame su ke ci da safe amma shi 24/7 da safe yana gindin teburin mai shayi yana karyawa. Bai gama tura ledan ba ma Raudha ta shigo ɗakin. "Shegiya 'yar tselen 'wa ko sallama ba za ki yi ba za ki shigo min ɗaki" Da ke ta saba da halin Uban na ta ta murguɗa ma sa baki tunda ba gani zai yi ba ta ce " Baba ashe kana nan, dama Malam Sama'ila ne ya ce a faɗa mu ku Baaba Usaina ta rasu" Ta faɗi mutuwar karangatsau saboda ba ta san zafin mutuwa ba, dan a lokacin shekarunta goma a duniya. Usaina matar Malam Sama'ila maƙocinsa ne. Da kaman zai tsaya ya cinye naman sai kuma ya ce bari sai ya dawo daga jana'iza tukunna. Bayan fitar Raudha daga ɗakin ya sake tura ledar ƙasan gado sosai ya jawo wani wandon sa ya rufe da shi... Buba bai tuna da tsiren nan ba sai washegari da yamma da ya dawo daga zaman makoki. Jiki na rawa ya jawo ledar tsiren yana jin haushin rashin tsayawa da bai yi ya ci tsiren ba jiya. Ya buɗe ya taɓa ya ji tsire ya lalace har ta fara yauƙi-yauƙi. Kaman zai yi hawaye saboda tsabar baƙin ciki, shi damuwar sa ta ya zai zubar da tsiren nan bayan yanka uku kawai ya ci aciki. Ya ɗau yanka ɗaya ya sa a bakin sa ya tauna, taste ɗin dai gashi ga kamar sa amma haka ya daure yai ta ci har ya cinye tas saboda bayason zubar wa. Da tsakar dare ciwon cikin ya ritse Buba ga gudawa, ya lalumi sandarsa yana cakwkwalawa yana sauri tun kafin ya kai banɗakin ya fara zawo a wandon shi. Bai ƙarisa ba ya tsaya a tsakar gidan yana riƙe ciki yana "wayyo wayyo" daga baya kuma ya koma kiran Innayi "Innayi Innayi...Faɗima...wayyo Iro...Ado" Innayi ce ta fara fitowa daga ɗaki tana haska torchlight tana salati ganin mijinta a ƙasa yana juyi yana ihu, Kafin ta ƙarisa wajen sa itama ta fara ƙwala kiran sunan manyan 'ya'yan ta... Kafin gari ya waye ciwon ciki da gudawa yai ajalin Abubakar da aka fi sani da Buba. Buba Yusufu Pakkari mutumin Ajili, uba ga 'ya'ya goma, mijin Faɗima Innayi mai ƙosai. Duniya kenan! yadda ka zo ba komai haka za ka koma ba komai. Daga ƙarshe aikin ka shi zai determining abinda za ka tarar, shiyasa mu dinga tunawa da mutuwa a kowani lokaci domin ita mutuwa ba ta sallama, zuwa ta ke bagtatan, ko da ciwo ko ba ciwo, ko an shirya ko ba a shirya ba... Washe gari da safe aka yi jana'izar sa aka kaishi gidan sa na gaskiya. Mutane na ta al'ajabin abin kamar ba da shi aka yi jana'izar matar maƙocinsa ba ashe shima yana hanya... Innayi tafi kowa shiga damuwa da mutuwar Buba. Gaskiya ne ba ya ma ta komai da ya kamata miji yai wa matar sa amma kasancewar sa raye wani rufin asiri ne gareta sai dai ya za ta yi ita karan kan ta jiran mutuwar ta ke yi. Dukkan 'ya'yan sa sun zo har da 'ya'yan Indo da ke Darazo wacce ɗaya ta yi aure ɗayar kuma tana aji shida a Sakandare. Babangida ɗan Harira ma ya zo anyi zaman makoki da shi. Bayan anyi uku aka fara maganar gado. Buba kam ba shi da komai da ya wuce gidan sa sai kuma kayan sawan sa. A hakan dai sai da aka raba gado da kowa banda Yusuf, wanda uwar sa Hajiya Harira ta ce yafi ƙarfin gadon Buba... Wacce ba ta damu ko kaɗan da mutuwar Buba ba ita ce Raudha wanda dama ko da Buba na raye ita Innayi ce gatan ta, Innayi ce Uwa da Ubanta, Innayi ce komai na ta... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 07 (Free book ne) *A good son and a good daughter* Shekara ɗaya kenan da Raudha ta sa Innayi ta fara zuwa Islamiyya. Da safe take zuwa duk ranan Asabat da Lahdi kuma sosai Innayi ta ke ƙaruwa da wannan Islamiyya. Shekara da shekaru ta na tafka kura-kurai a cikin sallolinta saboda sallan da aka koya ma ta kenan amma yanzu yanayin sallolinta ya gyaru sosai. Ƙaifin ƙwaƙwalwar ba kaman da ba amma a hakan Innayi ta fi mata dayawa a ajin na su ɗaukan karatu. Yau ma daga Islamiyyar ta dawo ƙarfe shabiyu ta ɗan gota. Da sallama ta shiga ɗaki tana ƙoƙarin cire hijabin ta, Raudha na zaune gefen gado tana duba littafi, a hasale ta amsa sallamar ta cigaba da bubbuɗe littafi ran ta ɓace. "Auta lafiya?" Innayi ta faɗa tana matsowa kusa da ita. "Na kasa gane komai, ni dama chemistry wahala ya ke bani. Ba abinda na gane a nan" ta faɗa tana tura littafin gefe Innayi ta ce "darasin ne ba ki gane ba?" "Iyi, kuma gobe mu ke da jarrabawar" Raudha ta faɗa tana ƙara yatsina fiska. Innayi ta ce "da yardar Allah za ki gane, ki bari anjima ki sake dubawa" Raudha ta girgiza kai tana faɗin "gashi Yaya Baffa baya nan balle ya koya min" Innayi ta ce "kar ki damu za ki fahimta Insha Allahu" ... Matsananci shaƙuwa ce ke tsakanin Innayi da autar ta Raudha. Musamman yanzu da ya kasance kusan ita kaɗai ce a gaban ta. Sa'adatu tun kafin ta gama karatu ta haɗu da mijinta Dr Mansoor amma ba ai bikin ba sai da ta ƙare karatu, Dr Mansoor mutumin Bulkachuwa ne amma yana zaune a Azare, yana aiki a asibitin FMC (Federal Medical Centre Azare). Ya auri Sa'a ne a matsayin matar sa ta biyu dan har lokacin da ya auri Sa'an shekaran su bakwai da aure da uwargidan sa amma ba ta taɓa haihuwa ba. Allah da ikon sa a shekaran da aka yi auren su a shekaran Sa'a ta haifi ɗa namiji. Suna zaman lafiya da ita da uwargidan ta hakanan Dr Mansoor ya sama wa Sa'a aiki itama a FMC ɗin. Ado ya yi aure har da 'ya'ya biyu a lokacin. Iro ma shekarar sa ɗaya da aure ya yi gini amma ba a gama ba ya tare da matar sa akan zai ƙarisa ginin a hankali. Baffah kuma ya gama ATBU yana service a jahar Kogi, ya ma kusa gamawa. Shi kuwa Idris yana ajin ƙarshe a BUK. Tunda Innayi ta bawa Raudha labarin mahaifinta Muhammadu wanda yai burin ganin Innayi ta yi karatu mai zurfi har ta zama likita, Raudha ta sa a ranta za ta cika burin Innayi ta kowani hali, tunda 'yar Muhammadu Jo'o ba ta zama likita ba ai jikar sa sai ta zama. Hakan ya sa tana shiga SS 1 ta zaɓi shiga ɓangaren science, duk da kuwa ba wai tana jin daɗin darussan sciences ɗin ba ne... Raudha na tsintar shinkafar da za su dafa da rana sai ga Jamilah matar Ado ta shigo da sallama. Ƙasa-ƙasa Raudhan ta amsa sallamar tana kau da kai gefe. Jamilah ta wuce ɗakin Innayi ba tareda ta yiwa Raudha magana ba, dama yanzu tsakanin su ko gaisuwa babu. Tun tana Amarya su ke faɗa da Raudha, haka Ado zai kama Raudha ya ma ta shegen duka amma gobe ba zai hana ta yi faɗa da Jamilah ba. Musabbabin faɗan ta akan Innayi ne, a rayuwar Raudha idan kana so ka ga faɗan ta cikin sauƙi to ka taɓa Innayi. Tun Jamilar na Amarya ta ke nuna halin ko in kula ga Innayi, ganin uwarmijin na ta ba mai hayaniya ba ne ya sa ta ke ƙoƙarin rena ta sai dai Raudha ba za ta bari ba, dan rana na farko da ta fara yiwa Innayi maganar banza Raudha zuwa ta yi har falonta ta zazzageta duk da kuwa Jamilar ta girmeta da kusan shekara shida. Jamilah na shiga ɗaki ta ajiye ɗan ƙaramin kwanon da ta ke zubawa Innayi abinci ta ce "Innayi zan fita unguwa, ga key nan idan Yaya ya dawo a bashi" Innayi ta amshi key ɗin tareda addu'ar Allah ya dawo da ita lafiya. Bayan Jamilar ta fita Raudha ta shigo ɗakin ta buɗe kwanon da Jamilah ta shigo da shi, ja dogon tsaki bayan ta ga ɗan abincin da aka zuba aciki duk da kuwa ba wai kwanon na da girma ba ne amma abincin ciki ko rabin kwanon bai kai ba. Tun tana Amarya da su ka yi faɗa Raudha ta dena cin abincin ta, ko da Innayi ta yi magana sai cewa ta yi ta yi haƙuri amma ko za ta mutu da yunwa ba za ta ci abincin Jamilah ba. "A dinga zubo abinci kamar wanda za a ba mabarata" ta faɗa tana rufe kwanon. Idan da ta ita ne to so ta ke Innayi ma ta dena cin abincin. Abincin da za a kawo ba nama ba komai idan kuwa aka saka nama to kitse ne ko ƙashi. Kuma na ranan da Yaya Ado baya haɗo cefane da nama ko kifi amma saboda Innayi ce ba ta san daɗi ba shiyasa matar sa ke ƙyashin saka ma ta nama a abinci. "Allah ya dawo da Yaya Baffah lafiya. Ai duk gidan nan ba kamar shi, shiyasan darajan Uwa" Innayi ta amsa da Amin cikin ran ta tana tuno kyawawan halayen Baffan. Shi ne indai yana nan ba sa rasa cin nama ko kifi a abincin su. Watarana haka zai siyo mu su tsire ko balangu da dare ana cin tuwo ana haɗawa da shi. Kayan shayi kuwa indai yana nan ba sa rabuwa da shi dan lokacin har sabo da shayi Raudha ta yi, ko da ɗumame za ta ci da safe to sai ta kora da ruwan shayi... Bayan sun ci abincin rana wanda shinkafa ce da wake da mai da yaji Raudha ta tattaro wankin ta da na Innayi ta je tsakar gida ta ja ruwa a rijiya ta fara wanki. Bayan Innayi ta yi sallar Azahar kamar kullum ta hau addu'o'in da ta saba, tana so ta yiwa Raudha addu'ar gane darasi amma ta manta sunan darasin. Ta ɗan leƙo kan ta ta wajen window ta tambayi Raudha sunan darasin. "Chemistry" "Kamisiri" "Innayi Chemistry fa" Raudha ta faɗa da ɗan ƙarfi. "To na ji" ta amsa tana komawa kan sallayar da ta ke zaune. Ta ɗaga hannu tana yiwa 'yar ta addu'a "Ya Allah ka sa 'yata Raudha ta riƙa fahimtar darasin Kamisiri, Ya Allah ka sa ta dinga fahimtar dukkan darussan da aka koya ma ta. Wannan darasin na Kamisiri da ke ba ta wahala ka sauƙaƙa ma ta shi Ya Allah..." ta jima tana wannan addu'an kafin ta cigaba da sauran kaman yadda ta saba. Ba wai ba ta yiwa 'ya'yan ta addu'a ba ne a da amma tunda a makarantar Islamiyya aka ce addu'ar Uwa ga 'ya'yanta yana saurin karɓuwa ya sa Innayi ta kuma dagewa akan yiwa 'ya'yanta addu'a. Kasancewa zuciya ta fi son wanda ke kyautata ma ta a duk lokacin da Innayi ke addu'a to addu'ar Raudha da Baffa sun fi na kowa. Kuskuren da mu ke yawan yi kenan, ba za mu waiwayi iyayen mu ba sai mu na cikin matsala. Mama dan Allah a tayani da addu'a ina neman kaza. Bayan kuma rabon da ka kyautata ma ta har ka manta, amma saboda kana cikin matsala sai ka tuna cewa addu'ar Uwa yana saurin karɓuwa, wani ba sa tare da mahaifiyar sa amma sai yai sati yai wata bai kira ta ba, sai yana neman abu ka ga jikin sa na rawa zai kira ya fara dan Allah Mama a taya mu da addu'a. Shame on us.... Da dare da Raudha ta sake waiwayan littafinta sai gashi ta iya gane wasu daga cikin abubuwan da aka koya mu su a darasin Chemistry ɗin. Ta je ta ɗakin Baffah ta binciki kayansa ta samo notes ɗin Chemistry ɗin sa lokacin yana Sakandare ta haɗa da nata ta yi karatun da shi sai taga ta gane sosai... *** Sati biyu da gama jarrabawan Raudha Baffah ya dawo, ya gama bautar ƙasa. Abu ne na farin ciki saboda Baffa shine ɗan Innayi na farko da ya kammala degree yai bautar ƙasa, shi Ado diploma kaɗai gareshi ya tsaya. Kamar ya san ba zai yi nisa a duniyar ba ya kira mai hoto gida aka yi hotuna, ya ɗaurawa Innayi facing cap ɗin uniform ɗin sa ita da shi suka riƙe certificate ɗin sa aka ɗaukesu hoto su na murmushi. Ranan Ado da ya ga ƙanin na sa ya kammala degree sai ya ji kishi ya ɗarsu a ransa, dan yana tunanin ya riga shi fara boko amma gashi yanzu ya ma sa nisa. Ranan kam ta zamo wa Innayi rana ta farinciki a rayuwar ta. Kaji biyu Baffah ya yanka aka yi miya da shi, Raudha acicin nama daren ranan baki har kunne saboda yadda ta ga nama dumu-dumu a miyar ta... Kullu yaumin addu'ar Innayi Allah ya ba wa Baffah aiki mai albarka. Yana da buri sosai akan Innayi, shi ne ya fara sa Innayi acikin plan ɗin sa kafin na shi plans ɗin. "Innayi idan Allah ya hore min zan sa a rusa sashen nan kema a miki ginin zamani, Innayi Insha Allah zan kai ki makka" kaɗan daga cikin abubuwan da ya riƙa nanatawa kenan tun ma bai gama karatu ba. Lokacin auren Sa'a yafi kowa zuba kuɗi da ake haɗa kuɗin da za a ma ta kayan ɗaki, duk da kuwa shine bai da aiki a lokacin. A koda yaushe burinshi shine ya samu mace da za ta so Innayi kamar yadda za ta so na ta uwar ko ma fiye. Shiyasa bai sa harkan mata a gaban sa ba tukunna har sai ya kai wani mataki a rayuwar sa. Sai dai ka na naka tsarin ne amma Allah ya riga ya tsara komai da zai faru da kai tun kafin ka zo duniya. Watanni biyu da dawowar shi ya applying wani aiki a Jos inda su ka kirashi interview. Ranan Lahdi ya shirya tafiya akan zai kwana a chan saboda interview ɗin da safe ne sai kuma ya chanja ra'ayi akan zai tafi da sassafiyar Litinin ɗin. Da yamma ya kai ziyara gidan yayar sa Halima da Yayan sa Iro duk da kuwa sun haɗu da Iron da safiyar ranan... Raudha na koyawa Innayi karatun ƙur'ani Baffah ya shigo ɗakin da sallama. "Yaya akawo ma ka tuwon ne?" Ya girgiza kai ya ce " ba na jin cin tuwo yau ƙila gobe na ci ɗumame" "Yaya gobe Litinin fa ko ba za ka ɗauki Azumi ba ne?" Ya ce " af na manta zan ɗauka Insha Allah. Bari mu ga ko zan iya cin tuwon anjima" Raudha ta yi saurin jawo ledar da ya ajiye tana faɗin "Yaya ka san na fi son balangu fa amma ka siyo tsire" "Yi haƙuri Auta balangun ne ya ƙare shiyasa na siyo tsiren" Tana yiwa Innayi karatu tana cin tsiren har su ka gama kafin Innayi ta ci sauran naman wanda kusan Raudha ta cinye fiye da rabi. Innayi ta lura da yadda Baffah yai shiru ba ya magana saɓanin yadda ya saba yi mu su hira idan yana ɗakin. "Baffa na lafiya?" Yai murmushi ya ce " lafiya, kawai ina tunanin aikin nan ne" Raudha ta ce " Yaya ai ka samu aiki angama da yardar Allah. Waya Reza za ka siyamin da albashinka na farko Yaya" Yai dariya ya ce "ki dai dage da karatu ba abinda ba zan siya mi ki ba" Raudha ta ce "yawwa Baffan Innayi" Gaba ɗaya su ka sa dariya. Saboda kar ya ɗaga hankalin Innayi ya sa ya saki ran sa su ka cigaba da hira kamar kullum yayinda Innayi ke ƙara jaddada ma sa zai samu aikin idan ma bai samu ba zai samu wanda ya fi wannan. Ya jima a ɗakin na su dan har sai da Raudha ta yi bacci ta bar su suna hira da Innayi. Kusan ƙarfe shaɗaya na dare ya bar ɗakin bai ci tuwon ba haka ya kwanta. Washe gari da sassafe ya shirya, ƙarfe shida ba ta gama cikawa ba ya fito daga ɗakin sa da ke zaure ya nufi cikin gida. Raudha ta gama wanke wake kenan tana zubawa a roba za ta kai markaɗe ya shigo. Bayan sun gaisa ta ce " Yaya ka yi kyau" Na gode ya amsa sannan ya shiga wajen Innayi. Tana zaune a sallaya tana lazimi ya shigo. Bayan sun gaisa ya miƙa ma ta ɗari biyu kuɗin cefane. "Insha Allahu zan dawo da wuri" ya faɗa a hankali Innayi ta ma sa addu'a tareda fatan Allah ya tsare ma sa hanya. Ya tashi jiki a mace ya fita daga ɗakin, Kiciɓis su ka yi da Raudha za ta shigo har su na bugan juna. "Sorry Yaya" ta faɗa tana kallon sa, gani ta yi ya ma ta kyau sosai, ta fara kallon sa kamar wanda su ka yi shekara basu haɗu ba. "Raudha wannan kallo haka?" Ya faɗa yana murmushi. "Yaya kar fa 'yan matan Jos su sace ka irin wannan gayu haka" Ya ja kunnen ta tareda cewa " na tafi, ki kula da Innayi" Ta gyaɗa ma sa kai ta shige ɗaki shikuma ya fita. Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya leƙo ɗakin ya ce "Auta ki faɗawa Yaya Ado na tafi, bai fito sallar Asuba ba da na ma sa sallama" "Zan gaya ma sa" "Sai na dawo ko" ya faɗa yana murmushi Raudha da Innayi su ka haɗa baki wajen faɗin "Allah ya kiyaye hanya"... Ashe ganin ƙarshe da za su ma sa kenan. Tafiyar Baffah kenan ta har abada, kowa da lokacin da aka ɗiba ma sa a duniyar nan. Wa'adin ka na cika za ka mutu ba tareda ka ƙara ko da daƙiƙa ɗaya ba. Tun kafin su isa Jos motar su ta yi hatsari. An kai su asibitin da ke Toro amma shi Baffah tun kafin a isa asibitin ya cika, cikin motar ta su da shi da wata mata ne su ka rasu sauran sun ji raunuka amma ana tsammanta za su rayu. Tun tafiyar Baffah Innayi ta kasa gane yanayin jikinta hakan ya sa ko fitowa tuya ƙosai ba ta yi ba, Raudha ce ta yi tuyar. Tana gama addu'o'inta ta kwanta daga nan kuma bacci mai nauyi ya ɗauketa. Hayaniya da kururuwa ne ya fargar da ita daga baccin da ta ke yi wanda ba dan koke-koken da ta ke ji ba da sai ta ce baccin da ta yi ya ma ta daɗi sosai. Ƙarfe shaɗaya da wani abu ne na safe lokacin da ta farka. Da sauri ta fito daga ɗakin jin kamar muryan Auta ke kuka. Jamilah ne da Raudha a tsakar gidan yayinda Raudhan ke ta kuka tana birgima ita kuma Jamilar na ƙoƙarin riƙeta. Ɗazu aka kira Ado a waya ake sanar da shi gameda hatsarin shine ya fita dan ya je ya sanar da Iro su je su karɓo gawan Baffah. Fitar shi ke da wuya sai Jamilah ta fito ta samu Raudha a tsakar gida tana wanke-wanke shine ta sanar ma ta, da ta san haka Raudhan za ta birkice da ba ta yi saurin sanar ma ta da wannan mummunan labari ba. "Lafiyah? Miyake faruwa?" Innayi ta faɗa cikin yanayin tsoro. Raudha ta ɗago jajayen idanun ta ta kalli Innayi ta ce "Baf..Baffah, Innayi Baffah" "Mi ya sameshi?" Ta faɗa zuciyarta na bugawa da ƙarfi ƙarfi kamar zai bulluƙo. Tun kafin ace komai idonta ya fara fitar da hawaye domin duk abunda zai sa Raudha irin wannan rikicewan to mummunan abu ne. Da Raudhan da Jamilar duk ka sa furta komai su ka yi yayinda jikin Innayi ya mutu murus, cikin ƙaramar murya ta ce "ba zai dawo ba ko?" Raudha ta faɗa jikinta ta cigaba da kuka... Kafin Yamma an kawo gawan Baffah wanda ya sa gidan ya kuma birkicewa da koke-koke, abin mamaki ba wani ciwo ya ji ba dan buguwa ce yai a kai sai kuma kafaɗarsa da ya ji ciwo. Mutuwa ba ruwanta da ciwo ko rashin ciwo, lokacin mutum na cikawa ta ke ɗaukan sa. Zuwa ƙarfe biyar da rabi aka kai Baffah makwancinsa, har lokacin kuwa ba abinda Innayi ke yi sai hawaye tana faɗin "Baffah na, Muhammadu na, na yafeka duniya da lahira, yadda ka faranta mini rai Allah ya sa Aljannah ce makomarka" Mutane da dama sun ga jarumtar Innayi dan ko kaɗan ba ta yi wani kururuwa ko tashin hankali ba. Idan ana yi ma ta ta'aziya kuwa sai ta fara cewa "shi kan ya huta ai, dama duniya ba ta dameshi ba gashi ya barta lafiya" Raudha ce tafi kowa birkicewa dan lokacin da ta ga gawar Baffah sai da ta suma... Baffah kam ya riga ya tafi sai dai labari. *** Rayuwa ya cigaba da tafiya, yayinda mutuwar ta jijjiga Innayi da Raudha sosai, sauran 'yan uwa da abokan arziƙi sun ma fara mantawa da mutuwar domin kowa ya cigaba da daily activities ɗin sa yadda ya saba... Innayi ta leƙo ɗaki a karo na uku dan ta tashi Raudha wanda take kwance tuntuni ta ƙi fitowa. "Auta dan Allah ki fito ki shirya ki tafi makaranta, sati biyu kenan fa da komawar ku" Daga inda ta ke kwance ta ce "ba zan je ba" Innayi ta sauke ajiyar zuciya ta shigo ɗakin. Ta sani har yanzu mutuwar Baffah bai gama sake jikin Raudha ba dan kusan kullum sai ta yi kuka musamman idan ta tuna irin alkhairin Baffan wanda har yanzu cikin sauran yayunta babu wanda ya kwatanta ko rabin abinda Baffan ke mu su ita da Innayin. "Haba Auta, a haka za ki zama likitan?" "Innayi na yafe zuwa makarantar, ina ce nan nan Baffah ya gama haɗa degree, shekaru biyar cur yai a ATBU ya zo yai bautar ƙasa shekara ɗaya amma ko amfani da bokon bai yi ba ya bar duniyan" Innayi ta yi murmushi mai ciwo wanda ya sa hawaye su ka zubo ma ta. Ta ce "Auta ko bai amfana da boko ba ni na amfanu da shi, kuma duk dan ya faranta min rai ya ke karatun saboda ya cika min burina na samun 'ya'ya ma su ilimin zamani. Har na bar duniya ba zan taɓa manta cewa ɗana mai ilimi ba ne" Kuka ya ci ƙarfinta domin an kwana biyu ba ta yi kuka saboda tunowa da ɗan na ta ba. Raudha ta tashi zaune ta fara sharewa Innayi hawaye ta ce " ki dena kuka dan Allah, zan je makaranta, Insha Allahu zan yi ilimi ni ma kuma za ki yi alfahari da ni"... Sai da ta gama shiryawa kusan ƙarfe goma na safe ta buɗe akwatin kayanta ta ɗauko wani file wanda ajikin file ɗin harda bushashshen jini ajiki. Ta shafa file ɗin tana faɗin "Allah ya haskaka kabarinka Yaya" Takardun bokon Baffa ne a file ɗin tundaga shedar gama primary har zuwa certificate na NYSC. Ta ƙurawa certificate ɗin ido inda sunan Bafffah ke rubuce a jiki ɓaro-ɓaro MUHAMMADU BUBA PAKKARI sai dai shi ma'abocin sunan ba ya duniya wanda ya maida takardar marar amfani, second class ɗin da ya fita dashi a makaranta iya duniya ta tsaya bai kai lahira ba. "Insha Allah zan yi karatu sosai Yaya kuma zan kula da Innayi. Zan gyara ma ta ɗaki kuma zan kai ta Hajji kamar yadda ka ke so" ta kissing takardar ta maidashi cikin file sannan ta sa a akwati ta rufe ta fice daga ɗakin domin ta wuce makaranta... Tundaga wannan rana Raudha ta dage da karatu kuma Alhamdulillah tana ɗauka sosai. Chemistry ɗin da ba ta ganewa yanzu ya zame ma ta favourite subject ɗinta saboda yadda ta ke fahimtar sa sosai... Cikin ikon Allah sai gashi har Raudha ta shiga aji shida har ta fara zana jarrabawar Waec a lokacin ne kuma ake ta kan shirye-shiryen bikin Ado wanda ke shirin ƙara aure. Shi ɗaya ya ke shawara da kan sa shiyasa ko da yai zancen ƙarin auren ba wanda ya tanka ma sa illa addu'ar Allah ya sanya alkhairi da 'yan uwan sa su ka ma sa... Amarya Aisha da ta zo farko-farko ta fara karanbanin yiwa Innayi ladabi da biyayya a shirinta na neman guri a wajen mijin su, sai dai ganin shi Ado baya yabawa da abubuwan da ta ke yiwa Innayin ne ya sa ta fara janye jiki har itama daga baya ta koma kamar uwargidan ta Jamilah. Yanzu kam ma sai sun bushi iska su ke kawo ma ta abinci, ba kamar kullum da rana ba kamar yadda Jamila ke yi da. Hakan ko kaɗan bai dami Innayi ko Raudha ba, dama ita Raudha tun da ta ga take-taken Aishan ma irin na Jamilah ne ta haɗasu duka ta watsar, iya kacin su gaisuwa. Su na tare gida ɗaya amma Raudha sai ta yi wata biyu uku ba ta shiga ɓangaren su ba, idan ma ta shiga to abu ne ya kaita ba wai ta je dan karan kanta ba ne. Duk yadda ta ke da maitar kallo haka ta ke haƙura ta zauna su yi hira da Innayi ko ta ɗau littafin soyayya na Hausa ta yi ta karantawa, hakan ya fi mata akan ta ce za ta shiga gidan Ado yin kallo... Idris na gama bautar ƙasa ya samu aiki a AfriBank da ke Misau. Yadda Baffah ya sha buri a albashinsa na watannin farko lokacin yana raye, shi Idris ba wanda ya gane ma sa. Albashinsa na farko ɗakin su na zaure da ya ke kwana ya gyara aka saka sabbin labulaye aka sake floor ɗin ƙasan ɗakin sannan ya zuba kayan kallo a ciki. Da ƙyar ya iya bawa Innayi ɗari biyar ranan da Innayi ta yi ma sa maganar batun Jamb ɗin da Raudha ke son cikawa. Innayi ta amshi kuɗin ta ma sa addu'a. Dama tun jimawa baya cin abincin gidan shiyasa bai damu da su na da cefane ko basu da cefane ba. Tunda yanzu yana samun kuɗi zai ci mai kyau ya sha mai kyau a duk lokacin da ya ke so. Ko dan Innayin ba ta tambayar su kuɗi ne ya sa su ke kasa bata kuɗi a lokacin da su ke da shi. To wai shin sai mahaifiyar ka ta tambayeka kuɗi kafin ka bata? Wai shin sai ta nuna tana cikin matsala kafin ka yi yunƙurin yi ma ta Alkhairi? *** Dawowar Raudha daga cafe ta zauna a tsakar ɗaki tana kuka a haka Innayi ta shigo ta sameta. Cike da tsoro ta fara tambayarta abinda ya faru. Raudha ta ce ai Jamb ɗinta bai yi kyau ba, ba za ta samu zuwa jami'a ba balle har ta karanci ɓangaren likitanci. "Inba ke ba Auta shine ki ke kuka haka kamar wanda aka yi mutuwa. Ai wata shekaran sai ki zana wani jarrabawan" "Innayi karatun likitanci fa yawa gareshi. Shekaru bakwai za ka yi kafin a kiraka likita, sai na tsofe a gida kenan kafin na yi karatun" ta faɗa tana sake wani sabon kukan wanda ya fi kama da na sakalci. Innayi ta fara rarrashinta wanda da ƙyar ta haƙura ta yi shiru... Ko da ta gayawa Ado cewa yai ta nemi school of nursing ita kuma ta ce ba ta so. Bayan kwana biyu ne Addarta Sa'a ta kawo mu su ziyara inda ta tarar da abinda ke faruwa. Itama shawaran Adon ta bata amma Raudha ta ce ba ta son nursing daga baya kuma Sa'a ta ce mi zai hana ta chanja wani course ɗin wanda ke layin likitancin idan ya so idan ta gama sai ta sake applying DE MBBS. Shima dai shawaran ba ta amince da shi ba har sai da Sa'a ta haɗata da mijinta a waya wanda ya bata labarin wani abokinsa da ya fara karanta Microbiology kafin daga baya ya koma MBBS ganin dai shawaran daga bakin Likita ne ya sa ta amince tunda dai points ɗin na ta ya kai ta samu wani course ɗin. Sa'a ce ta bata kuɗi ta je ta sayi green card ta chanja course daga MBBS zuwa Biochemistry, ta xaɓi Biochemistry ɗin ne saboda gwanancewa da ta yi a chemistry duk dan saboda addu'ar Innayi, wanda har yau duk sallah ba ta fasa addu'ar Allah ya sa Raudha ta fahimci dukkan darussan ta musamman darasin Kamisiri. *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 08 (Free book ne) *A mother to successful children* ABU Zaria Raudha ta cika kuma tun day one da ta sanar da Innayi cewa ga makarantar da ta cika a ranan Innayi ta duƙufa da yiwa Raudha addu'a akan Allah ya sa ta samu. A ka sake first batch babu sunan Raudha hakan ya sa gwiwar Raudha yai sanyi amma ko kaɗan Innayi ba ta gaza ba tunda Raudhan ta ce ma ta sau uku ake sake list ɗin. Innayi ta cigaba da addu'a ba dare ba rana, a second list da aka sake sai ga sunan Raudha Abubakar Pakkari ba ma Raudhan ba ne ta je ta duba saboda ta karaya. Usman yaron maƙotansu da su ka cika tare ne ya duba ma ta sai gashi ita ta samu shi bai samu ba. Farin ciki a wajen Innayi da Raudha ba a magana. Bayan an gama murnan samun admission ne aka shiga lissafin kuɗin da za a kashe a makaranta da abubuwan buƙata idan ta samu hostel. Dama tuntuni Innayi ta fara jefa kuɗi a asusu saboda irin wannan rana. Da su ka fasa asusun su ka irga kuɗin bai kai kuɗin makaranta ba amma ya kusa kaiwa hakan ya sa lokacin da Ado ya shigo washegarin ranan da safe Raudha ta mishi maganar registration. Da Raudha da Innayi haka su ka buɗe ido da baki su na kallon yadda Ado ke banbami saboda kawai an ma sa maganar kuɗi. "Ni ma fa makarantar zan koma na yo degree, albashina bai taka kara ya karya ba ga kuɗin makarantar yara ga hidiman gida. Shi Idrissa da bashida kowa ba za ku tuntuɓeshi ba sai ku tuntuɓeni bayan kun san iyalai biyu na ajiye a gida..." haka yai ta kwarwa babu wanda ya tanka ma sa daga ƙarshe da kan sa yai shiru ya ce zai san ya za a yi idan wata ya ƙare. Bayan ya fita Innayi ta yi murmushi mai ɗaci. Kamar ba yau ne ya zo gabanta kaman zai yi kuka ba saboda ya samu admission Buba ya ce ba shi da kuɗi. Yadda ta shiga ta fita a kan sa haka za ta yi komai saboda karatun Auta. "Innayi ba za ki ma sa magana ba? ya san da zai ƙaro karatun ya ke auran Mata biyu har zai nuna mana shi mai iyalai ne" Innayi ta ce "Auta mi zan ce? Gaskiya ya faɗa ai. Yana da iyali dole mu yi ma sa uzuri, ki tambayi yayanki Idi mu ji mi zai ce" Raudha ta tafa hannu ta ce " Allah ya sawwaƙa. Nan nan zan je zana jarrabawar post UTME na ce ya bani kuɗin mota ya ce wai bai da kuɗi ya bani naira ɗari biyu. Wallahi ko zan mutu ba zan tambayeshi kuɗi ba" Innayi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah shi kyauta"... Lokacin tafiyar Raudha na matsowa Innayi ta saida kajin gida da ta ke kiwo ta haɗa da kuɗin da ke ƙasa. Aka ci sa'a da Iro ya zo gidan ya tarar da zancen tafiyar sai ya ba da wani abu. A haka dai aka haɗa komai Raudha ta je ta yi registration ta dawo. A komawar ta na gaba ɗaya ne Sa'a ta ba ta dubu biyu ta kuma yi ma ta shopping na kayan abinci, yayinda Halimah ta aiko ma ta da dakekken yaji cikin ƙaramin roban custard da naira ɗari biyu. Shi kuma Ado ana gobe za ta wuce ya kawowa Innayi dubu ɗaya wai a ba ta. Bai damu da sanin ya aka yi aka haɗa kuɗin makaranta ba shi dai ya dai ji ana maganar za ta tafin ne wanda he assumes ta riga ta yi registration kenan. Duk yadda Innayi ta yi akan Raudha ta ƙarɓi kuɗin da Ado ya bayar ƙi ta yi, ƙarshe da Innayi ta takura ta ce ta riƙe kawai ta yi amfani da shi dan ko ta karɓa ma sai dai ta yi sadaka da shi. Ya je ya riƙe iyalen sa tunda shi ya fi kowa iyali a duniya. Ta riga ta san halin 'yartata shiyasa ta haƙura ta ajiye kuɗin... Safiyar ranan da za ta tafi ansha kuka kam dan wannan ne karo na farko da Raudha da Innayi za su rabu har na tsawon watanni. Bayan tafiyar Raudha Innayi ta shiga kaɗaici. Ita ɗaya a sashen na ta wanda ya sa ta ƙara ganin faɗin gidan. Ba kasafai jikokin ta ke shigowa ba saboda kallon talabijin da ke ɗauke mu su hankali a duk lokacin da su ke gida, matan 'ya'yanta kuwa sai sun bushi iska su ke shigo ma ta. Da sanyin safiya ta fara aikin wake wanda yanzu sana'ar ƙosai kawai ta ke yi ta dena daddawa ta dena Koko. Rabon da ta wanke wake ta manta saboda Raudha ke wankewa ta yi komai iya kacinta tuyawa wani lokaci idan ba makaranta kuwa Raudhan ta tuya. Da ta gama komai ta saka hijabi ta fita dan ta kai markaɗe daɗin abin ma gidan da ake markaɗen ba nisa da su. Tana wuce zaure kiɗa na tashi a zauren alamun Idris na ciki kenan ta yi ma sa addu'an shiriya dan shikan ba dare ba rana indai a wajen kiɗa ne. Yana gidan amma sai ya ga dama ya ke leƙo ta. Ba ta sanin shigan sa ko fitan sa. Da ta karɓo markaɗe ta shiga fara shirin suya dan har yau a gida ta ke abunta, kuma duk da akwai ma su yi a waje dayawa hakan bai hanata ciniki ba. Musamman saboda kasancewa da wurwuri ta ke farawa kuma ƙosanta akwai daɗi. 'Yan makaranta da masu fita office da sassafe su su ke zuwa su siye, dan kafin bakwai da rabi ya ƙare, randa kasuwa ya ja baya ne za ka ga har ta kai takwas ɗin bai ƙare ba... Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi, ba abinda ke damun Innayi face kewar 'yar autar ta. Wata ɗaya amma gani ta ke kamar shekara. Har lokacin kuwa ba ta bar sana'arta ba dan ba ta so a samu matsala a karatun Auta, yadda ta tallafawa Ado, Sa'a, Baffah da Idris haka za ta yi komai saboda Auta. Da farko ta hango sauƙi a karatun Auta saboda yadda ta ga yayunta su na da rufin asiri za su taimaka amma yadda lamarin ya juye ya sa ta duƙufa da neman kuɗi. Ɗan kwana biyu da ta samu riba ta sayi Akuya ta ɗaure, dama ta kwana biyu ba ta yi kiwon ba. Na baya da ta siyar duk saboda kuɗin makarantar Idris ne. Ranan tana wanki Ado ya shigo yana ƙwala kiran ta. Ta tsame hannu a ruwa ta fara goge hannun a jikin zaninta. "Gashi Raudha ke son magana da ke" ya faɗa yana miƙa ma ta wayar. Jiki na rawa ta amshi wayar ta ƙara a kunne tana murmushi, tana jin muryar Raudha ta fashe da dariya wanda sai da haƙoranta da su ka ɓace da cin goro su ka bayyana. Wayar ƙawarta ta amsa ta kira wayar Ado da shi dan a lokacin ba ta da waya. Da ƙarfi Innayi ke magana dan ita a tunaninta hakan zai sa Raudhan ta ji maganarta sosai. Sun jima su na magana kafin Raudha ta ce Innayi kuɗin zai ƙare sai anjima, Innayi ta ce Allah ya miki albarka. Ta miƙawa Ado waya tana murmushi irin murmushin da rabon da ta yi tun kafin rasuwan Baffah. A wasa Ado ya ce " to Innayi tunda kina son waya da Autar ta ki ki siya ma ta waya mana" ya ƙarisa maganar yana ƙaramar dariya. Innayi ta kalleshi ta ce "Allah ya kawo buɗi" Tunda ta ji muryar Raudha ta ji wani ƙarfi ya shigeta, ƙarfin ta cigaba da fafatawa har Allah ya sa Raudha ta gama karatu lafiya. Sana'ar Daddawa da ta ajiye kusan shekaru huɗu da su ka wuce ta dawo da shi, haka nan ta saro Kuka da Lalle da Borkono tana saidawa. Burinta yanzu shine ta siyawa Raudha waya saboda ta dinga sawa Ado ya kirata duk lokacin da ta yi kewarta... A hankali wata huɗu su ka cika Raudha ta yi exams ɗin ta na farko ta dawo gida. Innayi na bawa raguna abinci ta jiyo sallamar Raudha da ƙarfi daga zaure. Tana juyowa taga Raudha ta saki jaka ta nufota, tana zuwa ta rungumeta tana dariya. A hankali kuma ta dena dariyar yadda ta ji jikin Innayin ya sake bushewa ba kamar yadda ta san ta ba. Ta janye jikinta tana kallon Innayin da kyau, ta rame ta yi baƙi. "Innayi rashin lafiya ki ka yi ne?" Innayi ta girgiza kai tana murmushi. "Allah kin rame" "Ba wani dama haka na ke. Ke ce kika rame sosai, kina cin abinci sosai kuwa?" Raudha ta sake rungumeta tana faɗin " I miss you Innayi na"... Rabon da Jamilah ko Aisha su shigo wajen Innayi sun yi wata amma jin Raudha ta dawo shine su ka jajuɓu jiki wai sun zo barka. A hakan Innayi ta ƙulla mu su dabino da gurasa da Raudha ta kawo tsaraba ta aika mu su. "To duk ki basu ya ƙare, ni a ke kaɗai na kawo ba a kowa ba ehe" "Auta duk wannan sai na ci ni ɗaya? ai sai Allah ya kama ni. Ko ba dan su ba ai dan jikokina zan ba su" "Ni dai ke ki ka sani" ta faɗa tana ƙoƙarin gyara ɗakin Innayin wanda rabonda a gyara shi tun kafin ta tafi makaranta. Lokacin da su na cin tuwon dare ne Raudha ta tambayi batun dabbobi dayawa da ta gani a gidan. "Ba dai duk naki ba ne?" "A'a akwai na Ado da Iro a ciki" "Kutumar chan! Ke ki ke mu su kiwo? lallai rashin kunya. Shi yanzu Yaya Iro ya bar gidan sa ya kawo miki dabbobi saboda kin zama 'yar aikin su" "Kwantar da hankalinki, ni ce na fara kiwo shine su ka ajiye na su a wajen" "Duk ɗaya ne Innayi, ai ganin kina nan ne ya sa su ka kawo miki nan ɗin saboda sun san za ki kula da su tareda na ki" "Ƙyalesu lada na ke samu, kiwon dabbobi akwai lada" Raudha ta girgiza kai ta cigaba da cin abinci ranta a ɓace. Innayi ganin ta yi fushi ya sa ta tashi ta kawo ma ta surprise ɗin da ta tanada ma ta. Raudha ta amshi kwalin wayar tana murna. "Kai Innayi na gode. You're the best" Ƙaramar waya ce Nokia wanda ake wa laƙabi da rakani kashi. Washe gari kuwa Raudha ta je ta sayi layi ta saka... Hutun Raudha a gida ya samar wa Innayi sauƙi dan duk abunda ta ɗauko za ta yi sai ka ga Raudha ta karɓe tana faɗin ki huta tunda ina nan. A hutun ne kuwa Raudha ta lura da ɗingishin da Innayin ke yi, ashe ciwon ƙafa take ji tuntuni ta ke dannewa. Raudha ta sa dole sai da su ka je asibiti inda aka bata magani tareda basu shawaran akan Innayi ta dena aikin wahala. Bayan sun dawo ne su ka tarar da Halimah ta zo, a zaure su ka haɗu dan har za ta tafi da ba ta same su ba. Bayan sun zauna an gaisa ne ta faɗi buƙatan ta na son karɓan aron kuɗi a wajen Innayi. Innayi ta ce " kamar nawa?" "Dubu biyar" Halima ta faɗa Sai alokacin Raudha ta sa baki ta ce " amma Adda kina ji dai na ce miki daga asibiti mu ke amma ki ke maganar a baki aron kuɗi. Idan da tausayi ai ba Innayi za ki tambaya kuɗi ba akwai ƙanin ki ma'aikacin banki sai ki tambayeshi, ko kuma ki nemi yayan ki Malami" "Auta!" Innayi ta faɗa da ɗan ƙarfi. "Bar ta Innayi, ai ta fara jami'a dole ta gwada mana rashin kunya" Halimah ta faɗa ranta ɓace " gaskiya dai da ɗaci ta ke" ta faɗa kafin ta fice daga ɗakin. A hakan sai da Innayi ta lalubo dubu uku ta ba ta kafin ta tafi. Da Raudha ta shigo ɗakin ta yi ta mita tana faɗin ita ba za ta kawo ba amma ta iya zuwa ta karɓa. Kusan kullum hakane dan ko da ba kuɗi ba indai Halimah ta zo gidan sai ta nemi abun tafiya da shi... *** Yau da gobe sai Allah. Haka Innayi ta cigaba da sana'arta tana rufawa kan ta asiri. Ciwon ƙafa da ciwon ido ta ke fama da shi wanda duk aikin wahala ne ya zamo sababin su. Sai dai duk da haka ba ta ji gazawa ba tunda dai duk cikin sauran 'ya'yan ta ba wanda ya iya ɗaukan nauyin karatun Raudhan dole ta ɗau na Auta kamar yadda ta ɗau na sauran. A shekaran Raudha na uku a Jami'a ne Idris yai aure. Zo ka ga ƙarya a wajen ɗan Innayi. Dama duk wani maƙo da Idris ke yi tanadi ya ke yi wa auren sa da matar sa. Shekara ɗaya kafin auren ya samu aiki a Firstbank da ke Bauchi. A nan ya haɗu da Fa'iza wacce 'ya ce ga marigayi Justice Bala Gumau, wanda bai jima da rasuwa ba. Kasancewa Fa'iza 'yar babban gida ne ya sa ya ke ta rawan ƙafa a kanta kar a raina shi. Ba ƙaramin kuɗi ya kashe ba wajen haɗa ma ta kayan lefe a hakan 'yan uwanta sai da su ka raina kayan. Ba su so auren Fa'iza da Idris ba dan dai kawai Fa'izar ta nace akanshi ne. Amma sun so da Kabir ɗan gidan minister ta aura. Anyi bidi'a kala-kala a auren. A lokacin bikin ne Idris ya iya fidda kuɗi ya siyawa Innayi Atamfa guda biyu dan ta yi shigar biki. Sa'a, Halima, matan Ado da matar Iro mai suna Asiya su suka je Bauchi akayi bikin da su, Raudha na makaranta ba inda ta je, ko da kuwa tana gida yadda ba sa shiri da Idris da wuya ta je Bauchi saboda bikin sa... Duk yadda samari ke kawo ma Raudha wargi babu wanda ta bawa dama a cikin su dan karatu ne a gabanta. Dr Ambi shi ne project supervisor na ta kuma jajircewan ta da kamun kan ta ya sa su ka samu shaƙuwa tsakanin su. Lokacin tana hidiman project ɗin ne ya tambayeta mi za ta yi bayan ta gama bautar ƙasa, amsar da ta bashi ne ya sa shi gano ita ɗin mai burin zama likita ce kuma har a lokacin tana son zama ɗin ba ta cire rai ba. Shawara ya bata akan ta nemi scholarshinp a ƙasar waje saboda hakan zai fi ma ta sauƙi, ba lallai ta nemi Direct entry MBSS ta samu ba saboda competition da ke course ɗin. Raudha ta yi dariya ta ce ai idan da halin fita waje itama tana son fita ɗin sai dai babu hali. Ya ce mata wani ɗan yayansa ma da scholarship ya tafi ƙasar canada yai karatu. Ita kan ta bar labarin a ranta ne dan ta san ba mai yiwuwa ba ne. Dan samun scholarship ma a ƙasar ta Nigeria sai a hankali... Raudha Abubakar Pakkari ta fito da first class a ajin su lokacin da ta gama makaranta. Ranan da ta karɓi result haka ta haɗa result ɗinta da na marigayi Baffah tana kallo tana kuma addu'ar Allah ya sa ta yi nisan kwana saboda ta ci amfanin Bokon da ta yi har ta inganta rayuwar mahaifiyarta Innayi... Ranan da ta dawo gida Innayi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farin ciki, finally Auta ta gama makaranta. Dama wuyar karatu fara shi. Bayan 'yan gaisuwa sun tafi kawai Innayi ta fashe da kuka, ba abinda ta tuno irin ɗan ta marigayi. Ta sani da Baffah na raye da ita da Raudhan ba su wahala haka ba. Amma tana addu'ar Allah ya bawa Raudha tsawon rai ya kuma sa ma ta albarka a karatun da ta yi. Raudha ma maimakon ta ba da haƙuri sai ta shiga rera kukan aka rasa mai rarrashin wani... Ga dai 'ya'yan Innayi Shida da su ke raye wanda dukkan su Allah ya wadatasu da ƙoshin lafiya da buɗi. Rayuwar ta zai chanja kuwa? Shin za ta ci riban 'ya'yanta kuwa? Shin waɗannan 'ya'ya za su kula da Innayi a lokacin da tsufa ya kamata ganin yadda kowannen su ya kama gaban sa ya manta da wahalhalun da ta ma sa? Mu kan manta da iyayen mu a lokacin da su ka fi buƙatar kulawan mu. A lokacin da ya kamata su huta sai kaga mun ka sa basu hutun nan, su yi hidima da mu tun muna ciki har kuma iya ƙarshen rayuwar su. Wata simple katin waya ba ta iya tura wa iyayenta, tana jira sai ta zama Hajiya, may be lokacin da ta zama Hajiyar iyayen ta ba sa raye ko kuma suna rayen ma amma ta shagala da duniya ta kasa yi mu su komai. Wani kafin ya kira mahaifiyar sa sai an ja lokaci. Wani matarsa da 'ya'yan sa kawai ya sani ya manta da iyayen sa wanda su ka yi ɗawainiya da shi a lokacin da babu mata kuma babu 'ya'yan. Rashin daraja iyayen mu da kyautata mu su ya kan sa mu samu koma baya a harkokin mu na rayuwa. Ko iyayen ka na da buɗi su na da arziƙi akwai hanyoyi dayawa da za ka nuna musu kulawa garesu. Allah ya sa mu dace amma idan ba mu ba su hutu ba a lokacin da ya dace su huta tabbas muma idan mun tsufan namu 'ya'yan ba za su bari mu huta ba... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@Azi_zat* Chapter 09 (Free book ne) *Raudha* (Ina ba da haƙurin jina da kuka yi shiru kwana biyu) Aikin koyarwa na hucin gadi Raudha ke yi a wasu private school guda biyu kafin ta tafi bautar ƙasa. Duk da albashin bai wani taka kara ya karya ba amma a hakan da shi ta ke samu ta ke kula da kan ta da kuma mahaifiyar ta. Abu na farko da ta farayi bayan dawowan ta gida shine hana Innayi yin aikin wahala. Ta sani suna samun riba sosai a sana'ar ƙosai sai dai lafiyar Innayi ta fi ma ta komai. Bayan ta dawo ne ta lura da ciwon ƙafar da Innayin ke yi hakan ya ƙara ba ta ƙarfin gwiwa wajen hana Innayi ayyukan da ta ke yi na wahala. Dan ta sani ciwon ƙafan ya samo asali ne saboda ayyukan wahala da Innayi ta yi a baya kuma ta ke kan yi har yanzu. Cikin wata biyu Innayi ta samu kwanciyar hankali, duk wani yawan ciwon kai da ciwon jiki da ta ke ji duk ta ji sauƙin su. Wannan nitsuwa ya sa ta maida hankali wajen karatu da ta ke yi, bayan na kwana biyu da ta ke zuwa a ranakun weekend ta shiga Islamiyyar dare wanda ake yi a ta kusa da gidan su. Sau huɗu a sati. Ta dena tunanin komai sai addu'ar Allah ya ba wa Raudha aiki ya kuma ba ta miji na gari domin ta ga tausayi a idon Raudha hakan ya sa ta ke da yaƙinin Raudha za ta kula da ita har iya ƙarshen rayuwar ta... Yammacin ranan wata Lahdi Raudha na zaune tana marking assignment na yara wayarta ya shiga ƙara, Innayi da ke kusa da wajen ta miƙa ma ta wayar. Murmushi ta yi bayan ta ga sunan da ke jikin screen ɗin sannan ta amsa wayar da Sallama. Idan akwai mutumin da za ta kira da Uba to Dr Ambi ne, akan samu malamai dayawa ma su neman ɗaliban su a makaranta amma Dr Ambi baya ciki, kowa ya shaideshi da kyawawan halayensa. Tunda ta bar makarantar lokaci zuwa lokaci yakan kirata su gaisa ko ita ta kirashi. Ya ƙarfafa ma ta gwiwa sosai wajen ganin ta cigaba da karatu. Bayan sun gaisa ne ya ma ta maganar wani scholarship da ake cikawa na wa ta makaranta a Malaysia. Ta ma sa godiya tareda alƙawarin a ranan za ta je cafe ta cika... Ganin yadda ta ke murmushi bayan sun gama wayar ne ya sa Innayi tambayar ko dai sirikinta ne? "Kai kai Innayi rufa min asiri, ni da aure ai sai na zama likita" Innayi ta yi dariya ta ce "Allah ya nuna ma na. Amma auren ma idan ya zo za ayi shi ko?" "Innayi kenan. Wa ki ke ga zai aureni kuma ya bar ni na cigaba da karatu?" Kafin Innayi ta ba ta amsa sai ga Ado ya shigo gidan yana ƙwalawa Raudha kira da ƙarfi "Yaya lafiya?" "Lafiyan uwar ki. Na ce lafiyan uwar ki. Wato Raudha har wuyan ki ya yi ƙwari da har zan yi magana ki tsallake" "Mi na yi kuma?" ta faɗa a kausashe "Dan uwar ki ba na ce ki bar dabbobina a cikin gida ba, miye nufinki da za ki kora min su waje ki ƙi bari su shigo gida jiya?" Miƙewa tsaye ta yi tana kallon Yayan na ta ido cikin ido ta ce " Yaya tun ba yau ba na ce ka nemi mai kula ma ka da dabbobi amma ka ƙi. Yaya Iro da ya ke da zuciya ai ya kwashe na sa, wallahi matuƙar ina gidan nan ba za ka kwaso dabbobi ka ajiye mana da niyyar ni da Innayi ne za mu dinga kula ma ka da su ba" "Haka za ki ce? To wallahi dabbobin nan su na nan gidan ki ka ƙara kora min su waje sai na saɓa miki" "Yaya Ado!" Ta faɗa da ƙarfi har sai da ya ɗan tsorata "Wallahil Azim indai ka ga na bar dabbobin nan a nan to kai ko matarka ko 'ya'yanka za ku dinga shigowa kuna kula da su ne amma idan ba haka ba ba za su zauna a nan ba. Fisabilillahi Yaya wannan adalci ne, ni da Innayi za mu dinga ciyar maka da dabbobi mu na kula ma ka da su, mu ba su ruwa mu share kashin su, ko sisi ba ka taɓa ajiyewa ba. Wallahi..." Saukar mari ya hanata cigaba da maganar. "Raudha ki fita a hancina, dan kina ƙarɓan albashin dubu biyar ɗin ki ba shine zai sa ki ga ina daidai da ke ba" "Innayi ki ja wa 'yar ki kunne dan wallahi zan faffasa ma ta jiki" Raudha ta fusata ta ce "duk abinda za ka yi sai dai ka yi amma dabbobin ka ba za su zauna a cikin gidan nan ba" Mari Ado ya kuma kai ma ta, bai tsaya a nan ba ya shiga dukan ta ta ko'ina. "Ado ka ƙyaleta, Ado, Adamu ka ƙyaleta dan Allah" Innayi ta faɗa da ƙarfi, sai dai kamar a ice ta ke yiwa magana dan ko kula ta bai yi ba ya cigaba da dukan Raudha. Innayi ta shige ɗaki ranta a ɓace, hannunta har rawa ya ke yi. Ta rintse ido tana cigaba da sauraron kukan Raudha... A ranan ya dawo da dabbobin cikin gidan amma kuma yadda Raudha ta rantse haka ta watsar da dabbobin na sa wanda ya haɗa da raguna biyu, tinkiyoyi biyar sai taure ɗaya da akuya ɗaya da ƙananan 'ya'ya biyu. Duk wani dusa ko ƙanzo da ta ke zuba mu su a da ta dena shi. Ta ƙwammaci ta zuba a shara da ta zubawa dabbobin su ci, Innayi kam ba haka ta so ba amma ta yi shiru saboda ta ga har lokacin Raudha fushi ta ke da Yayan ta. Shara kuwa za ta share ko ina amma banda wajen su, gaba ɗaya wajen ya cakuɗe ya zama ba kyan gani ga uban wari. Innayi ce ma ke basu ruwa idan Raudha ba ta nan, bayan kwana huɗu da Ado ya shigo gidan ya ga dabbobin yadda su ka lalace ya sa dole ya nemi Almajiri wanda zai dinga kula ma sa da su safe da yamma... Wata huɗu Raudha ta yi a gida aka tura ta bautar ƙasa a Yobe state har lokacin kuma ba ta samu scholarship ɗin da ta cika ba. Innayi daurewa kawai ta ke yi amma idan da son ran ta ne Raudha kar ta yi nisa da ita. Ba ƙaramin kewarta za ta yi ba idan ta tafi. Raudhan ma ta ji tafiyar a jikin ta sosai musamman idan ta tuna yadda ta dawo ta samu Innayi farkon dawowar ta. "Innayi ban da aikin wahala dan Allah, na yi magana da Salisu zai dinga kawo miki kuɗi duk wata sai ki dinga buƙatun ki da shi. Dan Allah duk lokacin da ki ke da buƙata ki gayawa Salisu shi kuma zai kira ya gayamin sai na turo kuɗi" "Na gode, Allah ya saka miki da alkhairi" Raudha ta amsa da Amin tana danne kukan da ke cin ta. Ranan kusan kwanan zaune ta yi da ita da Innayin na ta su na hira. Washegari Raudha ta wuce Camp a chan Yobe state inda aka losting na ta. Gidan yai wa Innayi faɗi, kaɗaici ya isheta. Ba ta aikin komai daga Islamiyya sai gida, jikokinta ba wani sabawa su ka yi da ita ba, ga gida ga gida amma sai su kwana biyu ba su leƙo ƙakar ta su ba. Musabbabin haka kuwa shine yadda tun farko iyayen su ba su nuna mu su muhimmancin Kakar ta su ba ga uwa uba kuma zamani da ya kawo talabijin wanda ke ɗauke hankulan yara. Ko acikin gida ma yaran sai anyi da gaske su ke zuwa aika indai akwai wuta, idan su ka ƙurawa TV ido za su iya kwana a haka ba su gaji ba. Abinci da matan Ado ke kawowa kuwa tunda Raudha ta hanasu su ka basar, dama abin kamar ba dan Allah su ke ba shiyasa ko bayan ta tafi ba su cigaba da kawowa ba. Salisu ɗan maƙocin su Innayi ne, kusan sa'anni su ke da Raudha, tare su ka ƙare Sakandare amma shi bai cigaba ba, gyaran generator ya ke yi. Raudha na fitowa daga camp aka turata wani secondary school na gwamnati a cikin garin Yobe. Cikin albashin da ake ba su duk wata Raudha ke ware dubu bakwai ta ke turawa account ɗin Salisu dan ya dinga yiwa Innayi cefane sauran kuma ya bata a hannu. Ado ganin Raudha ba ta nan ya sa duk sati ya ke ba wa Innayi dubu ɗaya wato dubu huɗu a wata kenan. A watan Raudha na uku ne watarana ya zo wajen Innayin su ke gaisawa sai ga Salisu ya shigo gidan da sallama. Da ke ɗan gida ne kai tsaye ya shigo ɗakin ya gaida Innayi tareda miƙa ma ta kuɗi saboda bai jima da ciro su ba ma. "Innayi za mu je bikin wani abokinmu a Kaduna shiyasa ban miki cefanen ba amma na gayawa Usman anjima ya zo ya karɓa kuɗi sai ya siyo miki abubuwan da ki ke buƙata" Innayi ta ma sa godiya. Bayan ya tafi ne Ado da ya ƙyalla ido ya ga kuɗin da Salisu ya ba ta ya ce "Innayi ashe kin zama Hajia ba mu sani ba. Raudha ce ta aiko ko?" Innayi ta gyaɗa kai "Ayya! ta yi abun kai" Daga wannan rana Ado ya fara janye jiki daga kuɗin da ya ke ba da wa daga dubu ɗaya ya koma ba ta ɗari biyar a sati har ta kai yanzu kam sai ya bushi Iska ya ke ba ta kuɗi. Zancen Raudha na aikowa Innayi kuɗi ya shiga har kunnen Halima, shikenan kuma ta samu kan Innayi, sai ta daƙonci ƙarshen wata yayi sai ta je gidan ziyara, da sun fara hira sai ta dinga sako zancen ba ta da kuɗi ko kuma yaranta za su sayi kaza a makaranta kuma ba ta da kuɗi gashi yanzu dama ta gama ƙarewa mijinta Alhaji Nuhu. Tausayi irin na Innayi ya sa sai ta ɗau kuɗi ta ba ta wani lokaci har cikin kayan abinci tana ɗeba ma ta. Maimakon ita Haliman ta dinga kawowa mahaifiyarta sai ya zama mahaifiyartan ne ke ba ta. Wani lokaci Sa'a ma kan aiko kuɗi ta wajen Ado a ba wa Innayi amma da kuɗin Sa'an da na Raudhan yanzu ya koma ba ta wani assasa komai da kuɗin, idan Halima ba ta karɓa ba matan Ado za su zo karɓan bashi wanda karɓa su ke yi ba sa maidawa. Shi kan sa Ado wani lokaci idan Sa'an ta turo kuɗi ta wajensa amfani ya ke da su idan ya ga dama ya gayawa Innayi cewa yayi amfani da kuɗin da aka ba ta, idan 'yan iskan na kusa kuwa shikenan. Ai kuɗin uwar sa ce dan ya kashe ba komai ba ne. Raudha bayan wajen da ta ke PPA ɗin ta ta samu waje biyu tana yin lesson ana biyanta. Tunda maganar scholarship ya bi ruwa gara ta fara tara kuɗin da za ta koma makaranta da shi tunda ga yanayin gidan na su kowa nafsi-nafsi ya ke yi, kuma ta sa a ranta har Innayi ta koma ga Allah ba za ta taɓa bari ta yi aikin wahala wai dan ta samu kuɗi ba, duk wahalan da ta yi a baya ya isa yanzu lokacin jin daɗin ta ne... Sau tari mu kan yi wannan kuskuren, wai dan wani ɗan uwan mu yana da kuɗi yana kyautatawa mahaifiyar mu ko na ce mahaifanmu sai mu da mu ke da rufin asiri sai mu ja gefe mu zuba ido mu bar wancan yai ta hidima shi ɗaya. Ai idan shi ɗan uwanmu dubu goma zai bayar mu da bamu da kuɗi ko ɗari biyar mu ka bayar za mu samu lada kuma su ma iyayen na mu za su ji daɗi sosai, tunda sun san bamu da shi amma kuma mu na kyautata mu su... *** Sai da Raudha ta yi wata shida kafin ta zo gida, ba wai ba ta son zuwa ba ne sai dai aikin da ta ke yi ne bai ba ta dama ba, gashi ɗan sarari da ta ke samu tana zuwa wajen wata mata inda ta ke koyon yadda ake ɗinka labule, pillow, bedsheet, duvet da sauran su. Hakanan tunda tana jin muryan Innayi kusan kullum hankalinta a kwance ya ke. Ana gab da sallar Layya ta zo gida, Innayi dai ta yi kyan gani ba kaman kwanakin baya ba duk da kuwa ta ƙara tsofewa ko dan ba ta da jiki ne? Ko kuma dai saboda har yanzu ba ta da kwanciyar hankali... Mamaki ne ya kama Innayi lokacin da Salisu da abokinsa Hassan su ka shigo da ragon da Raudha ta siya na layya. Bayan sun ɗaureta ne Raudha ta tambayi Innayi ko ragon na da kyau? "Gaskiya Auta ragon nan ƙosashshene kuma zai yi mai" Raudha ta yi murmushi ta ce " ragon layyan ki ne" Innayi ta kalli rago sannan ta kalli Raudha sai hawayen farin ciki su ka fara zubo ma ta. Tunda ta ke ba ta taɓa yin layya ba, to ko mijinta Buba na raye ma ba kowani sallah ya ke yin yanka ba balle har ta yi tunanin ita ma zai mata layya. Kowa ya ji labari sai ya dinga nunawa kamar Raudhan ta zaƙe dayawa a kan Innayi, har gani su ke kamar neman suna ta ke yi. Yayinda wasu kuma su ke tunanin wani halin banzan Raudhan ke yi ta ke samun kuɗi. Iro ma da ya ji labari sai da yai mamaki daga baya ya ce ai ba komai bane tunda dai Raudhan ba ta da wani damuwa a kanta shiyasa ta ke da kuɗin yiwa Innayi layya. Shin har akwai wani abun da za ka yiwa iyayenka har yai yawa ne? Shin ko mi za ka mu su za ka iya biyan ɗawainiyan da su ka maka ne?... Ranan sallah kuwa Raudha ta kawowa Innayi kayan sallarta. Wata leshi ne da ake yayin ta a lokacin. Dubu goma shabiyar ake sai da ta, sai dai ita Raudha wata ƙawarta 'yar bautar ƙasa ce ta siyo ma ta a Lagos dubu goma. Ta riga ta sa an ɗinka wa Innayi tun tana Yobe, takalmi mai kyau da hijab da ya tafi da kalar leshin Raudha ta haɗa ma ta da shi. Innayi ba ta san kuɗin lace ɗin ba ta dai ji daɗi sosai da wannan kaya. Tare su ka tafi filin idi wanda tun a hanya ta ke ganin yadda ake kallonta. Duk wanda ka gani da irin lace ɗin to ya kai ne. Innayi ba ta taɓa zuwa sallar idi ba sai bayan rasuwan Buba. Raudha ce ta kwaɗaita ma ta falalar shiyasa ta dage da zuwa. Amma tunda Buba ya taɓa hanata zuwa sau ɗaya ba ta sake tambayarsa ba har ya rasu, shiyasa tana da kaya ba ta da kaya duk ba ta da damuwa tunda duk hidimar sallan a cikin gida za ta ƙare shi. A wajen idin ma chanjin kuɗi naira goma goma sabbi Raudha ta ba ta ta yi sadaka da su. Ba wanda zai gan ta a wajen idin nan ya raina ma ta, kallon wata Hajia ma ake ma ta... Da su ka dawo daga idi, Raudha ta kira Ya'u ɗan anguwan su ya zo ya yankawa Innayi ragon ta. Babbar sallah ta wannan shekara ya matuƙar faranta ran Innayi, Raudha ta ma ta komai, sai godiyar Allah... Bayan sallah da kwana biyar Raudha ta shirya komawa Yobe a lokacin ne kuma Sa'a ta haihu amma ɗan bai zo da rai ba. Da ya ke tun auren Sa'adatun sau ɗaya ta taɓa zuwa ma ta sai kawai ta ce Innayi su je Azare su ma ta gaisuwa kafin ta tafi. Ranan Asabat su ka shirya tafiya da ke tsakanin Misau da Azare ba nisa ba kwana za su yi ba. "Innayi ki sa leshin ki na sallah saboda ki fito a Hajia" Raudha ta yi maganar tana dariya. Innayi ta yi shiru chan ta ce " barin sa wanda yayan ku ya siya min a sallar bara" Yadda ta yi maganar ya tabbatarwa Raudha akwai matsala. "Ba dai kin bawa Adda Halimah ba?" "Aron shi kawai ta yi za ta dawo da shi" Raudha kamar ta yi kuka ta ce " haba Innayi haba Innayi, tunda na ga Adda Halima na ƙwaɗa ɗinkin na san za a rina. Wallahi ko kaffara ba zan yi ba, ba aro ta ɗauka ba ta tafi da shi kenan" "Yo abinki Auta ba na sa ba, ai shikenan" "Shikenan Innayi ba ki isa ki sa abin arziƙi a jikin ki ba sai an miki baƙin ciki, wai hakan ma 'yar cikin ki" Raudha ta ɗau waya ta kira Halima ta zazzageta duk da Innayi ta hana ta kiran amma ba ta saurareta ba, abin ya ba ta haushi kamar ta yi kuka. Duk cikin zannuwan Innayi babu na arziƙi shiyasa wannan karan ta yi ƙoƙari ta siya ma ta abinda kowa ya gani ya san na zamani ne kuma yana da tsada. Har su ka isa gidan Sa'adatu Raudha ba ta bar mita ba, har ƙaran Haliman ta yi a wajen Sa'an a kan ta ma ta faɗa ta dena ɗaukawa Innayi kaya... *** Daf sun kusa ƙare bautar ƙasa Dr Ambi ya cikawa Raudha scholarship na Harvard Medical school. Tareda wata 'yar sa ya cika mu su, kawai kiran ta yai ya ce ta cigaba da addu'a akai ko Allah zai sa ta yi nasara. Raudha ta amsa amma ba ta sa rai a kai ba. Bayan ta dawo gida ne ta gayawa Innayi a wani lokaci da su ka yi hiran batun komawa karatun da za ta yi. Innayi ta dinga maimaita sunan makarantar har sai da ta iya faɗa HABAD a cewarta. Duk sujudin da za ta yi na sallar farilla ko nafila sai ta roƙi Allah ya sa 'yar ta Raudha ta samu tafiya wannan makaranta, yadda Raudhan ke zancen makarantan ya sa ta gane babbar makaranta ce sosai kuma makaranta ce ta mai rabo, amma ta ji a ranta 'yar ta Raudha za ta samu wannan rabo. Haka ta dinga duƙufa da addu'a ba dare ba rana. "Allah ka sa 'ya ta Raudha ta samu tafiya makarantar HABAD"... A wannan lokaci da Raudha ke gida ne samari su ka fara ma ta chaa. Tana da kyau gashi ta haɗa degree a ƙanƙanin lokaci dan kuwa shekarunta ishirin da ɗaya ta gama bautar ƙasa. Cikin wanda su ke nacin neman ta ne Malam Iliyasu wanda lecturer ne a School of Agric da ke Bauchi ya samu daman gabatar da kan sa wajen su Ado. Malam Iliyasu matashi ne dan a lokacin shekarun sa talatin da huɗu yana da mace ɗaya da yara biyu, ɗan asalin cikin Misau ne sai dai shi da iyalin sa su na Bauchi. A lokacin hidimar sallah ya ƙyalla ido ya ga Raudha nan ta ke kuwa soyayyarta ya shigeshi. Ankai ruwa rana tsakanin Raudha da yayun na ta wanda su ke ganin Malam Iliyasu ba shi da aibu ta aureshi. Da ta kawo maganar cigaba da karatu kuwa su ka nuna sam ba su yarda ba gara ta yi aure idan ya so ta yi duk irin karatun da ta ke so a gidan mijin ta. A ɗan hirarrakin da su ka yi da Malam Iliyasu shi namiji ne da bai yarda da aikin mace ba shiyasa koda matar sa tayi diploma amma kwalin na nan ajiye ya hanata neman aiki da shi. Tana da yaƙinin ko ta auri Malam Iliyasu haka itama za ta ajiye kwalinta a ƙasan gado ta dinga jiran man rabbuka, domin iya abinda zai ba ta shi kaɗai zai zama na ta. Ba za ta iya ba, ba ta shirya rabuwa da Innayi haka ba. Da ace ma ita ɗaya za ta zauna sai ta yi tunanin idan ta auri Malam Iliyasu za ta tafi da Innayi gidan ta amma ba ita ɗaya ba ne. Matsin Ado yai yawa har ta kai yana iƙirarin zai karɓi sadakinta a wajen Malam Iliyasu. Da ta ga da gaske su ke ta kai ƙara wajen mai garin Ajili wanda ta ke ganin zai iya shige ma ta gaba a wajen yayun na ta. Mai garin Ajili na lokacin kusan 'ya'yan kawunnai su ke da marigayi Buba. Bayan sun je Ajili anyi zancen ne su ka ba ta wata uku idan ba ta samu makaranta a lokacin ba dole za ta amince ta yi aure... "Innayi idan ki ka ce na yi aure yau yau ɗin nan, zan amince na yi aure ko da ba na so amma idan ki ka amince na cigaba da karatu kamar yadda rai na ke so to kuwa wallahi sai dai kotu ta rabamu amma ba zan bari su Yaya Ado su min auren dole ba" Innayi shiru tana kallon Raudha. Tabbas ta sani duk damuwar Raudha na son cigaba da karatu saboda ita ne, saboda ta inganta rayuwarta. Ta cika alkawarin da marigayi Baffah ya ɗauka ma ta wato ya gina ma ta gida ya kuma kai ta Makkah. "Allah ya mi ki albarka Auta" Raudha ta amsa da amin "Raudha ina miki addu'a kuma na san Allah zai zaɓa miki mafi alkhairi a gareki. Idan cigaba da karatun ki akwai alkhairi a ciki to kafin watanni uku su cika za ki samu tafiya karatu. Idan kuma aure ne mafi alkhairi za ki ga auren zai zo mi ki da sauƙi kuma mijin da Allah zai ba ki zai zamo na gari, mai son ki, mai ƙaunar ki kuma mai tausayin ki" Da wannan Raudha ta amince ta fawwalawa Allah lamarinta. Ana fara cika DE ta cika zuwa ABU tana neman MBBS a karo na biyu. Dr Ambi ya ma ta alkawarin zai yi duk yadda za ayi ta samu admission a ABU. Allah mai jin ƙan bayi kenan, domin addu'ar Innayi ta karɓu Wata biyu da sati ɗaya bayan an gindayawa Raudha sharaɗi. Dr Ambi da kan sa ya zo Misau ya ba wa Raudha labarin alkhairin da ya sameta. Ta samu scholarship na zuwa makarantar Havard. 'Yarsa da ya cika mu su tare ba ta samu ba amma Raudha ta samu... Da gudu Raudha ta shigo gida bayan ta gama magana da Dr Ambi da ya ke ƙofar gida. Innayi na Alwala sai ji ta yi an faɗo jikinta ana ihu da dariya. "Innayi na samu admission, na samu scholarship na zuwa Harvard" Innayi ta ɗaga hannu tana faɗin Alhamdulillahi... ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@Azi_zat* Chapter 10 (Free book ne) *A crazy mother* Tafiya ce za ta yi da ba ta san ranan dawowa ba. Duk ɗokin tafiyarta lokacin da abun ya matso sai ta ji ba ta son tafiyar. Innayi ce a ranta, ba lallai ne a kula da ita yadda ya kamata ba. Haka dai ta cigaba da shirye-shiryen tafiya, wani lokaci idan ta fara jimamin abin sai ta zauna ta yi ta kuka. Da taimakon Dr Ambi ta je Abuja ta yi passport ɗin ta cikin sauƙi. Ana saura kwana biyar ta tafi ta je Azare gidan Sa'a. Duk cikin 'yan uwan na ta ita ce ta ke ganin tana da sauƙin kai kuma ta ke tunanin za ta iya fahimtar damuwarta. "Adda kin dai san halin Yaya Ado da Matan sa, ina tsoron kada na tafi Innayi ta shiga wani hali. Ba na so ta koma aikin wahala kamar yadda ta yi a shekarun baya, yanzu yadda Innayi ta ke, tana lokacin da hutu kawai ta ke buƙata da kwanciyar hankali" "Gaskiya ne Raudha, zan yiwa Yaya Ado magana ya matsawa matan sa su dinga kula da Innayi sosai" Idon Raudha ya ciko da hawaye ta ce "Adda idan ba na nan wai wanki da shara Innayi ke yi, sannan sai ita za ta dafa abin da za ta ci. Adda a shekarun Innayi bai ci ace ta dena zuwa gindin murhu ba?" Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka. Jikin Sa'adatu yai sanyi. Itama ba wai tana jin daɗin yadda Innayin ke zama ba ne, amma ya za ta yi tunda ba gari ɗaya su ke ba. "Ki yi haƙuri ki bar kuka zan yiwa Yayan magana Insha Allahu" "Adda ba Yaya kaɗai za ki yiwa magana ba har da Adda Halimah. Za ta zo wajen Innayi ta karɓi kuɗi ta karɓi kayan abinci amma ba abunda ta ke yi mata. Idan da tausayi ai ko Dija 'yar ta za ta dinga turota tana yiwa Innayi wanki duk sati" "Abun kam ba daɗi. Insha Allahu zan kira Yaya Ado inyaso sai ayi fixing meeting mu je a zauna a tattauna komai kafin ki tafi" Raudha ta cigaba da matsar hawaye saboda yadda abin ke ci ma ta rai. *** Meeting dai da aka sa kowa ya hallara banda Idris wanda ya nuna shi ba shi da lokaci duk da kuwa meeting ya kama ranan Asabat ne. Sa'a ce ta ba da shawaran a dinga haɗa kuɗi duk wata dan kula da buƙatun Innayi, Halimah da ke da ƙaramin ƙarfi za ta kawo ɗari biyar a wata, su kuma Sa'a, Ado, Iro da Idris kowa zai dinga kawo naira dubu biyu da ɗari biyar a wata. A hakan sai da aka yi ta ja kafin aka ajiye maganar kuɗi akan kowa zai kawo dubu bibbiyu amma ita Sa'a ta ce dubu biyu da ɗari biyar ɗin za ta bayar, jimillar kuɗi ya tashi dubu tara a wata. Kai Jama'a! Wai mahaifiyar ka ce ba za ka iya cire dubu biyu da ɗari biyar ka ba ta a wata ba. Ƙila a wata kana amfani da adadin kuɗin ko fiye wajen shirme da shirirta ƙila ma harda kashesu a wajen aikata zunubi amma UWA da za ka ba ta ka samu lada sai hakan ya gagareka. *true life story* "Akwai wata Uwa da ta girma za ta kai shekaru 55-60. Sai ya zamana ba ta da lafiya kuma maganin da ake siya ma ta duk wata dubu bakwai ne. Tana da 'ya'ya da su ka manyanta kuma biyu daga ciki su na aiki. Watan farko aka haɗa dubu bakwai da ƙyar aka sayi magani, wata na biyu aka siya ana ƙunƙuni wata na uku aka sayi rabin maganin wato dubu uku da ɗari biyar. Jama'a Wallahil Azim a wata na shida babu wanda ya iya ciro kuɗi dan siyan maganin Uwar da ta tsugunna ta haifeshi. Kowa aka taɓa sai ya fara kukan tsadar rayuwa da kuma babu. Batun sauƙi yana tareda Allah, amma maganar magani wannan Uwa ta rasa mai siya ma ta cikin 'ya'yanta. Da ke sun ga jinyar ya fara sauƙi sai su ka basar, su ka nuna halin ko inkula akan uwar su" A hakan sai mu ce ba ma ganin cigaba a rayuwar mu, a hakan sai mu ce 'ya'yan mu ba sa jin magana, a hakan sai mu ce musiba da fitintinu sun yi yawa. Irin waɗannan abubuwa da mu ke aikatawa muna ganin ba komai ba ne Wallahi babban laifi ne, ba sai UWA ta maka baki ba, ba sai UWA ta maka mummunan addu'a ba. Yadda ka ɓata ma ta rai, ka ƙi ka ji tausayinta haka za ka ga lamurranka su na taɓarɓarewa, kayita addu'a amma kaji shiru, idan aka samu rashin sa'a kuwa kafin ka nemi gafaran iyayen ka Allah ya riga ya karɓi baƙuncin su. Allah ya sa mu gyara amin... *** Kwanaki biyu bayan tafiyar Raudha ƙasar waje Innayi ta fara rashin lafiya. Kewar 'yar ta ne ya sa ta wannan jinya. Ado ya kira wani Nurse da ke anguwar su aka ma ta allura aka ƙara ma ta ruwa, bayan kwana biyar ta warware sosai sai dai har lokacin tana kewar Raudha. Saboda maganar Sa'a sai Ado ya maida yaransa maza biyu manya zuwa cikin gida. Ɗakin Buba na da nan su ke kwana. To abu da yara maza, Innayi ba ta jin ɗuriyar su sai dare idan sun shigo za su kwanta. Abinci kam yanzu safe zuwa dare duk ana kawo ma ta daga gidan Ado sai dai da ka ga abinci da ake zubowa ka san na dole ne ba wai su na so ba. Ko kaɗan hakan bai dami Innayi ba, ita babban damuwarta Raudha. Kullum addu'ar samun nasara da kuma albarka ta ke mata, tana yiwa sauran 'ya'yan na ta addu'a amma na Raudha special ne, sai ta yi minti goma tana nanata addu'a ɗaya a Radha. "Allah ka yiwa 'yata Raudha albarka, Allah ka kareta daga sharri, ka ba ta sa'a a dukkan lamurranta" haka za ta yi ta maimaitawa har sai ta gaji kafin ta cigaba da wasu addu'o'in. Akwai wani addu'a ɗaya da ko farkawa daga bacci ta yi sai ta yi shi, wani lokaci idan tana zaune tana jin rediyo ta ji kaɗaici sai ta tuno da Raudha nan take zata shiga yi ma ta addu'a. "Allah ka bawa Raudha miji na gari, ka ji tausayinta kamar yadda ta ke jin tausayina" Wallahi idan kana kyautatawa iyayenka ba za su taɓa gajiyawa wajen yi maka addu'a ba... Wani sabon salo da aka fito da shi shine sai Innayi na zaman-zamanta sai ka ga Jamilah ta shigo ta zauna ta yi ta kawo gulmar Amaryarta Aisha tana zaginta a gaban Innayi, itama Aishar wani lokaci itama ta shigo wajen Innayi ta faɗi gaskiya da ƙarya akan Uwargidan na ta. Su ka maida wajen Innayi wajen kawo gulma. Asiya matar Iro ma ta shiga sahun wannan gulmar sai dai ita tana aibanta su Jamilah ne saboda tana ganin kamar harda su a wajen son ayi ma ta kishiya, Iro yana neman wata yarinya 'yar uwar su Jamilan. Duk abinda za su zo su faɗawa Innayi ba ta tanka mu su, iya kaci ta basu haƙuri. Ana haka watarana sai ga Asiya ta zo wajen Innayi kuma lokacin Jamilah na wajen ta. Ba a jima ba aka fara cacarbaki ana zage-zage. Innayi ta fara ba su haƙuri saboda yadda su ke masifa kaman za su ci kan su. "Yi mana shiru! Innayi ke ce baƙar munafukar ai, ashe har a wajenki ya fara tara kayan aure ban sani ba amma kullum na zo sai ki dinga kwantar min da hankali kina bani haƙuri kamar baki san komai ba" Idon Innayi ya ciko da hawaye, duk wani zancen neman aure da Iro ke yi ita bai sameta ya ma ta zancen ba a bakin matan 'ya'yan na ta kawai ta ji. "Asiya a ina kika ji wannan maganar?" Ta faɗa tana danne wani ƙunci da ya ke taso ma ta a wuyarta. Maimakon Asiya ta amsa ma ta sai ta kalli Jamilah ta ce " ke kuma wallahi ki cewa 'yar uwarki ta fita a hanyar miji na, yarinyar da Taliya ta ke siyarwa a Tasha ta gama zuwa an lallatsata shine za ta mannewa miji na yanzu" Jamilah ta yi shewa ta ce " daɗin abin kema ɗin Kunu kike sayarwa ya ganki ya auroki. Kuma wallahi sai Hafsatu ta shiga gidan Yaya Iro, idan ma mutuwa za ki yi ki mutu" Haka dai su ka cigaba da zage-zage kamar ma za su bigi juna, daga baya su ka fita. Asiya ce ta fara fita kafin Jamilah ta bi bayan ta, babu wanda ya damu da Innayi balle halin da ta shiga. Innayi zama ta yi a bakin gado tana dafe ƙirjinta saboda zafi da ya ke mata. Maganar Asiya ya shigeta sosai, rabon da wani ya zageta haka tun lokacin zaman su da Harira. Duk yadda ta danne sai da hawaye ya zubo ma ta, tana tsakiyar kukan ne ta ji sallama. Ta yi saurin goge hawaye da gefen zaninta ta fito tana ɗaurawa fiskarta murmushin da bai kai zuci ba... "Lale maraba, Hajiya Harira ce a gidan na mu, sannu da zuwa" Harira ta tsaya tana ƙarewa Innayi kallo. Ko ita da ta girmewa Innayi a shekaru ba ta yi irin tsufan da Innayi ta yi ba. Idan ka haɗasu za ka ce Innayi ta ba wa Harira shekara goma ko ma fiye. "Faɗima haka kika zama?" Innayi ta kuma faɗaɗa murmushinta na bogi ta ce " tunda muna raye sai hamdala ai" Tausayin Innayi ya shiga Harira, a yadda ta kalleta ta san har yanzu ba ta samu jin wani jin daɗi ba. Duk da itama tana fama da na ta 'ya'yan amma Alhamdulillahi babban ɗanta da ya samu aiki a Kaduna yana kula da ita sosai yanzu ma saboda ciwon ta da ke yawan tashi ya sa ya ce ta tattaro ta dawo wajen sa da zama shine ta zo yiwa Innayi sallama, rabon da ta ga Innayi tun da ta zo ma ta barka lokacin da Raudha ta gama bautar ƙasa. "Wai ina Autan ki ne?" Ta faɗa dan ta kawar da shirun da ya ratsa ɗakin. Innayi ta yi murmushi ta ce " ai Auta tana chan ƙasar turawa. Miye ma sunan ƙasar? Ehmmm Amelika, a Amelika ta ke karatu, a wata babban makaranta wai Hawad" Harira ta ce Allah ya dawo da ita lafiya ya sa albarka a karatun ta. Innayi ta amsa da Amin. Bayan sun ɗan taɓa hira ne ta sanar da ita za ta bar Misau za ta koma gidan ɗan ta a Kaduna. Innayi ta tayata murna sosai... Bayan Harira ta tafi ta yi ta jimamin rayuwar Innayi, ko lokacin da su ke auren Buba haka ta rayu cikin ƙunci har Buban ya rasu gashi yanzu ma ba wani cigaban kirki da ta samu. Kafin ta tafi cikin kayayyakin ta da ta ke son kyauta da su ta zaɓi wasu ta aikawa Innayi ta sani ko siyarwa Innayi ta yi za ta samu wani abu. Babban katifa ce da ƙaramin fridge da wasu bokatai da robobi manya- manya wanda ta ke amfani da su da wajen sana'arta ta masa. Ta kira mai mota ya kai gidan Innayi. Innayi da ta ga saƙo sai da ta yi hawaye, a daren ta sa hijabi ta tafi gidan Harira tana ma ta godiya. Harira ta ce ma ta ba komai ai an riga an zama ɗaya... Kaman jira ake yi a kawo kayan dan kuwa ko abu ɗaya Innayi ba ta tsira da shi ba. Halimah ce ta ɗauke fridge da wasu robobi, ita kuwa Jamilah ta wawure katifar wai 'ya'yan ta za su dinga kwana a kai. Ta san da cewa katifar da ke kan gadon Innayi ya lalace amma ba ta damu ba haka ta ɗauke ta tafi dashi, ai ba ruwan tsohuwa da jin daɗi ta cigaba da fama da yarjalelliyar katifa kawai. Ya Allah!😭 Innayi ba ta mu su magana ba ta bisu da ido kawai. Fatan ta a koyaushe Allah ya shiryesu... *** Raudha da ta je Havard kafin ta gane yanayin makarantar sai da ta ɗau lokaci. Bayan komai ya fara dai-dai ta ne ta shiga neman aiki a cikin makaranta saboda ta samu abin aikawa gida dan hankalinta bai kwanta da tsarin Yayun na ta ba... Safiyar wata laraba Innayi tana wajen dabbobi tana shara wani rago ya tunkuyeta ba ta ankara ba ta faɗi ƙasa, ashe faɗuwar da ta yi ta bugu sosai nan ta ke ta suma. Tana kwance a wajen sai da Almajirin da ke zuwa duba dabbobin ya shigo ya sameta a wajen nan ya fara ihu ya shiga gidan Ado ya sanar da su abinda ya gani. Sule Almajiri da ke ba wani biyan sa ake ba abinci kawai ake bashi kuma ya fara girma yana ɗan ji da kan sa shiyasa baya wani kula da dabbobin yadda ya kamata. Wani lokaci sai ya wuni bai leƙo su ba balle har ya mu su wata hidima. Su kuma yaran Ado da ke kwana a wajen Innayi ba damuwa su ka yi da dabbobin ba, kowa tsiyar sa ta isheshi. Idan Sule bai zo ba shine Innayi ke kula da dabbobin wanda har yau ɗin ya zo da tsautsayi... Kwana bakwai Innayi ta yi a asibiti aka sallameta dan bayan buguwa da ta yi jininta ya hau sosai. Zuwan da Sa'a ta yi ne ta dinga faɗa tana tuhumar Ado da rashin kula da Innayi da ya ke yi. Idris bai zo ba da aka faɗa ma sa Innayi ba lafiya amma da Sa'a ta kirashi a waya ta titsiyeshi ta dinga kwarwa dole yammacin ranan Jumu'a ya zo dubiya. Bayan an sallami Innayi ne aka sake zaman meeting, wannan karan kowa ya halarta banda Raudha da ba ta ƙasar. Likita ya ba su shawaran su kai Innayi babban asibiti ta ga ƙwararren Likita saboda a tabbatar da babu matsala a kanta duba da irin buguwar da ta yi. Duk da Innayi na nan lafiya amma Likitan ya ce dole ayi wasu gwaje-gwaje saboda kar gaba a samu matsala. Sa'a ta nuna za su kai Innayi Teaching Hospital da ke Bauchi. Yadda Idris ke wani haɗe rai ka san bayason inda zancen ke dosa. "Ni a shawarata Innayi za ta zauna gidan Idrissa, idan ya so bayan ta samu lafiya sosai sai ta dawo, ko ya kuka gani?" Kafin sauran su sa baki Idris ya ce " ba zai yiwu ba, kun san gidan haya na ke ga kuma aikina baya bani lokaci, ina zan iya da wani jelan asibiti" Wannan karan harta Iro sai da ya ji zafin maganar Idris ɗin. Ya ce " Idris na kwana nawa ne ma za ta gama ganin likita ta dawo, ga matar ka ba za ta rinƙa rakata asibitin ba" "Matata ma'aikaciya ce ba ta da lokaci" ya faɗa kai tsaye. "Ubanka Idrissa, na ce ka ci uban ka da kai da aikin matar na ka. Ɗan Iska wani hidima ka taɓa yiwa Innayi? Ba Innayi kaɗai ba a wa ka taɓa yiwa hidima tunda ka samu aiki? Za ka nuna mana kai da matar ka kuna aiki, to wallahi ba aiki ba Allah ya sa bauta ku ke yi Innayi za ta zauna a wajen ku na iya lokacin da za ta ga Likita" Kamar dama jira su ke nan aka shiga yiwa Idris faɗa musamman yadda bai damu da koɗaya daga cikin 'yan uwan sa ba, tunda ya koma Bauchi da zama sai yai wata uku huɗu bai leƙo Misau ba. Kuma ko ya zo ba abinda ya ke tsinanawa, matar sa kam tunda ya aureta sau ɗaya ya kawota Misau ta gaisa da 'yan uwan sa. Gara Idris yana ɗan kiran 'yan uwansa a waya randa ya bushi iska amma ita matarsa ta watsar da kashin 'yan uwan mijinta ko a waya ba ta neman su. Ganin dai an ma sa taron dangi haka ya haƙura ya amince bayan an nuna ma sa ba shi kaɗai zai kawo kuɗin jigilar asibiti ba.Ranan haka Idris ya bar gidan ran sa a ɓace. Bayan kwana ɗaya aka shirya tafiyan Innayi wanda ya kama ranan Monday. Sa'a da Innayi su ka tafi Bauchi, direct Asibiti su ka je dan ganin likita, bayan an gama mu su komai aka ba su takardar gwaji akan washegari su je a yi ma ta. Sa'a ta kai Innayi gidan Idris kafin ta wuce Azare bayan ta yiwa Idris da matar sa bayanin da likita ya masu tareda basu takardun gwajin da za a yiwa Innayi.... Tunda Idris yai wa Faiza maganar zuwan Innayi gidan su hankalinta ya tashi. Take ta nuna ma sa ba ta son zuwan Innayi, nan ya shiga lallaminta yana faɗa ma ta ai zaman Innayi na lokaci kaɗan ne. Tunda Sa'a ta tafi aka bar Innayi a falo ita kaɗai, sanyin fanka ya ma ta yawa amma haka ta daure tana jiran fitowar su. Ba su fito ba sai da ana kiran maghrib. "Ki shiga ɗakin chan anan za ki kwana" Faiza ta faɗa a yatsine Innayi ta tashi ta shige ɗakin wanda ɗaki ne da su ka mayar ɗakin baƙi. Chan baifi minti biyu ba Innayi ta fito ta samu Faiza na kallo ta ce "dan Allah Maman Mufeedah ina ne banɗaki?" Faiza ta yi kamar ba ta jita ba, Innayi ta sake maimaita tambayarta. Da ƙarfi ta ce " Na ji mana! Ai ni ba kurmiya ba ce. Ki je ƙofar da ke gefen ƙofar da ki ka shiga nan ne banɗaki" Innayi ta juya jiki a sanyaye. Faiza ta harari bayan Innayi tana faɗin " Village Witch"... Innayi ta shiga banɗaki ta yi alwala ta fito, tana son kama ruwa amma ta rasa gane kan banɗakin, ta dai ɗau buta ta yi alwala kawai ta fito. Bayan sallar Isha Faiza ta shigo ɗaki ta kawo ma ta plate ɗin abinci da satchet water ɗaya. Sai da Innayi ta gama addu'o'inta sannan ta buɗe abinci dan ta ci. Fried rice aka yi da coselaw a gefe. Saboda rashin imani abincin rana ne da bai ƙare ba Faiza ta zubowa Innayi. Abincin yayi sanyi salalau ga coselaw ɗin har ya fara ɓacewa. Innayi ta yi Bismisllah ta fara ci, ba ta san coselaw ba dan haka ta turashi gefe ta ci fried rice ɗin kaɗai duk da shima bai mata daɗi a baki ba. Ita tafi gane shinkafa da miya ko da yaji ko jollof ba kasafai ta ke so ba, Raudha ce ma ke yi lokacin da ta ke nan... Ko awa biyu da kwanciya ba ta yi ba cikinta ya hautsine, ta rasa yadda za ta yi. Tun tana jin abin kaɗan-kaɗan har abun ya zama idan fa ta cigaba da matseshi sai dai ya zubo mata ba shiri. Ta yi ƙarfin hali ta je banɗakin da aka nuna ma ta ɗazu duk da ba ta san a ina za ta yi gudawan ba, ta yi ta maza ta zauna akan toilet ɗin ta fara yi. Iya rayuwarta banɗakin gargajiya ta ke amfani da shi shiyasa ganin toilet ɗin na zamani ya zamo ma ta sabon abu. Da ta gama ta yi tsarki ta fito. Daren ranan sai da ta zaga sau uku, gaba ɗaya kunya da tsoro ya kamata dan ganin yadda toilet ɗin ya ɓaci da gudawa gashi ba ta san yadda za ta yi ba. Baccin kirki ba ta yi ba saboda fargaban abinda ta yi (Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Wai UWA ce ta ke fargaba da tsoro a gidan ɗan ta) Da ke a ɗakin Idris akwai banɗaki a nan shi da matarsa su ka yi buƙatun su. Washe gari da sassafe da Faiza ta fito ne ta ji wari hakan ya sa ta buɗe banɗakin da ke gefen ɗakin Innayi. "Darling! Darling !" Ta fara kiran Idris da kakkausan murya. Da gudu ya fito daga ɗakin na su kafin ya zo Innayi ta fito saboda dama tana dakon fitowar su dan ta ja Idris gefe ta ma sa bayanin abinda ya faru. Ganin yadda Faiza ke toshe hanci ya sa jikinta yai sanyi, cikin i'iina ta ce " ki yi haƙuri gudawa ne ya kamani jiya kuma ban san..." "Will you shout up!" Ta dakawa Innayi tsawa dai dai fitowar Idris. Tana tsaye bakin ƙofar banɗakin ta nuna ma sa cikin banɗakin da yatsa tana faɗin " go look at what your crazy mother did" Namiji kenan! Bai fa damu da abinda ta kira uwar sa ba haka ya shiga banɗakin ya je ya gani. Da ya fito ya ce "Innayi ai sai ki kora da ruwa, wannan ai ƙazanta ne" Muryar ta da ke cike da kuka ta ce "ban san ya ake korawa ba ne" Ya jata su ka shiga ya nuna ma ta yadda za ta flushing toilet ɗin. Faiza na waje tana faɗin "Darling wallahi sai dai ta wanke banɗakin dan warin yayi yawa" "Baby kinga ba ta da lafiya, ki bari idan Huwaila ta zo sai ta wanke" Idris ya faɗa cikin rarrashi. Ita dai Faiza sai tsaki ta ke ja tana tottoshe hanci ƙarshe ta je ta ɗauko room freshner ta feshe gidan da shi. Sai da Huwaila mai ma ta aiki ta zo kafin ta rage ƙorafi. Innayi na ɗaki tanajin matar ɗan na ta nata faɗa tana zage-zage ta yi da turanci ta yi da Hausa... Huwaila wata bazawara ce amma ba wata Babba ba ce dan shekarun ta shatara. A chan ƙasan layin su Faizan gidan su ya ke, da sassafe za ta zo ta mata wanke wanke da shara ta yiwa 'yarta Mufeedah wanka ta shiryata. Bayan sun karya sannan ta tafi. Hakanan da yamma ma za ta zo ta yi gyaran gida ta kuma taya Faiza girki, da ke ƙarfe biyu Faiza ke dawowa daga Office. Bayan Huwaila ta gama ayyukan ta ne Faiza ta ba ta biredi da ragowan tea ɗin da su ka sha ita da Mufeedah akan ta kaiwa Innayi. Innayi ta karya a tsorace, ba abinda ke mata daɗi a baki amma haka ta daure ta ci. Tuni Idris ya fita office, da Faiza ta gama shirinta ta ƙwanƙwasa ɗakin Innayi ta ce "idan kin gama ki fito Huwaila ta raka ki asibitin ni na tafi office" Innayi ta amsa da toh. Ita dai Huwaila tana ganin ikon Allah, ko ba a faɗa ma ta ba ta san Innayi ita ce mahaifiyar Idris saboda tsananin kamannin su. Amma yadda Faizar ta yi ka ce Innayi wata boyi- boyi ce a gidan. Huwaila ta nunawa Innayi yadda za ta yi wanka a banɗakin bayan ta sa ma ta ruwan zafi. Da Innayi ta gama shiri sannan su ka fita, da ke an saba bar wa Huwaila Key kawai kulle gida ta yi su ka tafi Asibiti. Su na cikin keke Napep Innayi na sauke ajiyar zuciya. Ba abinda ke ranta irin Raudha... Yadda ka treating iyayenka da 'yan uwanka haka zai sa matarka ta daraja su ko kar ta daraja su... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@Azi_zat* Chapter 11 (Free book ne) *An evil daughter inlaw* Da ke Huwaila ba ta san kan Asibitin ba da ƙyar su ka samu su ka yi gwajin bayan anyi ta mu su kwatance. Daɗin abin Likitan da yai gwajin yana jin Hausa ganin da Huwailan da Innayin duk sammakal ne shiyasa ya mu su bayani dalla-dalla yadda za su gane tareda cewa su dawo washegari su karɓi result ɗin su kaiwa Likitan da ya turo su. Innayi ta ma sa godiya. Lokacin da za su fita ne Likitan ya ce "Mama ina yaranki maza ne su ka barki kina yawo ke ɗaya?" Innayi ta ce " 'ya ta ba ta ƙasar, tana karatu a Hawad" "Hawad?" Likitan ya maimaita dan bai gane ba "A ƙasar Amelika ta ke, makarantan koyon likitanci ne irin na ku" tana maganan ne cike da alfahari, idan akwai wanda ta ke alfahari da shi cikin 'ya'yanta to Raudha ne. Likitan yai murmushi tareda addu'an Allah ya sa 'yarta ta gama karatu lafiya. Bayan fitan su da ɗan mintina yana duba computer kwatsam sai ƙwaƙwalwarsa ta ankaro ma sa ma'anar abinda Innayi ta faɗa wato Hawad, ashe Havard ta ke nufi, yai dariya yana ƙara maimaita sunan... Bayan sun dawo gida Huwaila ta dafa mata spaghetti sannan ta tafi, kafin ta tafi ta ce " Inna sai dai fa ki ƙara haƙuri saboda gaskiya sha'anin Anty Fa'iza sai ahankali. Ba ta da daɗin sha'ani" Innayi ta ce " ba komai, na gode Allah ya saka da alkhairi" Da ƙarfe biyu da rabi Faiza ta dawo gida, ko ta kan Innayi ba ta yi ba. Innayin ne ma ta fito tana ma ta sannu da zuwa wanda ta amsa a fiska ɗaure. 'Yarta Mufeedah ta fara tambayar kowaye Innayi. Da ke rayuwar ƙarya su ka ɗauka wa kan su, da Hausa da Fulatanci duk babu wanda su ka koyawa Mufeedah, turanci su ke mata kuma dashi ta tashi ɗan gara Hausa wani abin ta na ɗan ji amma ba ta iya mayarwa. Maimakon Faiza ta gaya ma ta ko wacece Innayi sai ta ce ma ta ta tambayi Daddyn ta idan ya dawo. Yarinyar ta kalli Innayi ta ce "who are you?" Innayi ta ma ta murmushi ta ce "Allah ya miki albarka"... Da Huwaila ta shigo da yamma ta ma ta bayanin ta dafawa Innayi spaghetti da rana, Faiza ta haɗe rai ta ce kar ta ƙara yi mata girkin da ba ta sa ta ba. "Anty Faiza na ga ba za ki dawo ba sai..." "Huwaila ba na son shishshigi. Ki yi abinda na ce kawai" Huwaila ta ja bakinta ta yi shiru... Ƙarfe shida saura Idris ya shigo gidan amma bai leƙa Innayi ba sai da ya dawo daga sallar Isha. Tambayarta yai ko ta je asibiti, ta gaya ma sa yadda su ka yi da Likita. Ya ce Allah ya ƙara lafiya. Yau dai tuwon Semovita da miyar kuɓewa Faiza ta yi, ta kawo wa Innayi abincin ba yabo ba fallasa. Ko kafin su kwanta sai da ta yiwa Idris ƙorafi akan ita fa ya san yadda zai yi Innayi ta tafi ƙarshen sati dan ba za ta iya ɗawainiyar Uwar sa ba... *** Washegari still Huwaila da Innayi ne su ka je su ka ƙarɓi result su ka kai wajen Likita, amma da ke ba su zo da wuri ba dole sai tafiya su ka yi akan washegari za su dawo. A yammacin ranan ne kuwa Raudha ta kira Idris, da farko Ado ta kira shine ya sanar ma ta abinda ke faruwa, ta ji zafin rashin gaya ma ta da ba su yi ba tun farko, shine ta kira Idris ɗin. Sun jima suna tattaunawa kafin daga baya ta ce idan ya koma gida ya haɗata da Innayi... Daren ranan bakin Innayi har kunne saboda farin ciki. Sosai su ka yi taɗi da Innayi, har ta ke sanar da ita aikin da ta ke yi a free time ɗin ta. Innayi ta rinƙa saka ma ta albarka. Bayan sun gama wayan ne Idris ya tambayeta yadda su ka yi a Asibiti ta sanar da shi ya ce gobe zai haɗa ta da wani saboda ya ji bayanin da Likita zai yi. Innayi ta gyaɗa kai kawai... Da sassafe alert ɗin kuɗin da Raudha ta turo ya shigo, da ke yana da domiciliary account in dollars kuɗin ya shigo, yana ganin kuɗin ya lissafta su a ƙwaƙwalwarsa wanda ya zamo a kuɗin Nigeria dubu goma shatara da ɗari uku. Kai tsaye kitchen ya wuce wajen Faiza yana gaya ma ta adadin kuɗin "Hmmm ko mi ta ke yi har ta ke samun kuɗi haka oho. Ni dai na san karatun Likitanci da wuya ba sa samun lokaci ma bare ace wani aiki ta ke yi" "Honey ƙila gwamnati ke biyan su fa kin san da scholarship ta tafi" Faiza ta ce "Hmmm".... AbdulWahab wani yaron maƙotan su Idris ne yana karatu a Jami'ar ATBU, shi ne ya raka su Innayi da Huwaila asibiti wajen Likita. Likitan ya mu su bayani da cewa gwajin da aka yiwa Innayi ya nuna babu abinda ya samu kan ta sai dai za ta dawo bayan wata uku a sake yi ma ta wani gwajin. Ya jaddada mu su akan lallai Innayi ta cigaba da shan maganin ta na hawan jini sannan ta cire damuwa a ranta. Tun a waya AbdulWahab ya sanar da Idris yadda su ka yi da Likita, Idris ya ma sa godiya. Bayan sun dawo gida Innayi ta haɗa 'yan kayanta dan ta san ba makawa gobe za ta koma Misau idan ya so bayan wata uku da aka ce sai ta sake dawowa. Ta gode Allah da ya sa ma ba su riƙeta a asibitin ba dan ta san yadda Idris da matar sa su ka nuna ma ta tun zuwanta ba lallai su iya yi mata wani jigilar asibiti ba... "Ni da Fa'iza mun tsara za ki zauna a wajen mu har wata uku sannan idan kin koma Asibiti aka sake dubaki sai ki koma Misau" Miyasa da iyayen mu sun girma sai mu dinga yanke mu su shawaran abinda za su yi ba tareda mun shawarce su ba? Innayi ta kalli Idris ta ce "wata uku yayi yawa, ba na son saku cikin ɗawainiyata. Idan Allah ya nufemu wata ukun ya cika, Misau da Bauchi ba nisa sai na dawo" "Ba abinda fa ki ke yi a Misau ɗin. Ga wahala da kikeyi a chan, ba a irin haka ba ne kika samu jinyar. Gara ki zauna da mu a nan, ki ci ki sha ki kwanta" "Ban saba da zaman birni ba Idrissa ka bar ni na koma inda na fi sabawa" "A'a Innayi, yanzu haka kowa zagina zai yi su dinga cewa na koreki na kasa kula da ke, dama Adda Sa'a da Raudha sun min mummunan shaida" Duk yadda Innayi ta yi haka Idris ya ke ja har sai da ta haƙura za ta zauna da su na wata uku... *** Satin farko zaman ba laifi da sauƙi sai dai kewa da ya ke damun Innayi a duk lokacin da su ka fita aiki, ko da su na nan ba wai suna zama su yi hira ba ne amma jin ɗuriyar mutane a gidan yana sa hankalinta ya kyauta. A wannan lokacin ne kuma ta yiwa Idris magana akan ya siya ma ta radio saboda ya dinga ɗebe ma ta kewa. "Innayi ga TV ba za ki fito kiyi kallo ba" Idris ya faɗa yana dariya. Innayi ta ce ba ta saba da TV ba gara radio ɗin. A ranan kuwa ya siya ma ta radio. Duk bayan kwana uku ko huɗu Raudha na kiran wayar Idris ya ba wa Innayi su gaisa. Koyaushe tambayar Raudhan shine ko tana nan lafiya? Ko tana cin abinci sosai? Ko tanajin daɗin zaman Bauchi? Duka amsarta shine "eh" to mi za ta ce tunda dai da Idris ɗin da Raudha duka 'ya'yanta ne... Wata safiyar Lahdi Innayi na ɗaki tana sauraron wani shiri a gidan radion Globe FM ta jiyo hayaniyar Faiza da Idris. "Idan ba za ka faɗa ma ta ba ni zan faɗa ma ta, haka kawai mutum da gidan sa a zo a takurashi. Tun ɗazu na ke son yin bacci amma an hanani, shegen jin radio kamar wata journalist" Innayi ba ta ji mi Idris ke faɗa ba dan da turanci ya ke magana. Ƙarshe dai Innayi ta kashe radio ta turashi gefe tareda sauke ajiyar zuciya. Daga ranan ba ta sake kunna radio ba haka nan shi Idris bai bi bahasin yadda ta dena kunna radio ba... Huwaila ke yiwa Faiza da Mufeedah wanki duk weekend. A sati na biyu ta je ta karɓo kayan Innayi wanda tunda ta zo ba su ga ruwa ba, ba wai Innayi ba ta son wankin ba ne sai dai yadda sirikar na ta ke yi tunda ta zo gidan ya sa ta ke tsoron yi ma ta maganar a bata sabulu. Bayan ta gama yin wankin ne tana ɗauraya bokitai sai ga Faiza ta fito ɗauke da socks. "Huwaila ga socks ɗin Baby ban gani b..." ta tsaya da maganar lokacin da ta hango zannuwan Innayi akan igiyar shanya. "Kayan waye wancan" ta tambaya da kakkausan murya "Na Inna ce" "Wace Innar?" Sai da Huwaila ta yi kasaƙe tana kallon ta kafin ta ce "Innar gidan nan" "Ka da ki kuskura ki sake haɗa min wanki da ita, infact kada ki sake yi ma ta wanki a bokitina" Huwaila ta zaro ido tana mamakin kalaman Faiza. Innayi fa Uwar mijin ta ne. "Kina ji na?" Huwaila ta gyaɗa kai... *** Kwance ta ke kan wani tsohon gyalenta da ta mayar sallaya tana sallah da shi. Ta jima da yin sallar Azahar ta gama addu'o'inta tana kwance ne tana tuno ƙuruciyarta. Wani waƙa da su ke yi a dandali ta tuno nan ta ke ta fara rerawa, tana waƙar tana ɗan daddanne cikinta da ke kukan yunwa. Tunda ta zo gidan za ta iya irga ranakun da ta ke cin abincin rana. Ranakun Asabat da Lahdi kenan, tana ci ne saboda dukkan su ba sa fita office amma kwana biyar na ranakun aiki daga safe ne sai dare. Wani lokaci saboda tasan za ta ji yunwa da rana sai ta rage biredin ta na safe ta ci sauran da rana. Wani lokaci kuma Huwaila na kawo ma ta abincin rana daga gidan su kafin Faiza ta dawo, dan yanzu Faizar kulle kitchen ta ke idan za ta fita. Tsabar mugunta ko Faiza ta dawo da wuri to ba za ta yi girkin rana ba, idan ka ga tayi to indomie ce za ta bawa Mufeedah ko kuma ta haɗa ma ta cornflakes. A wasu ranakun kuma take away ɗin abinci ta ke siyowa ita da 'yarta su ci, ko leƙa ɗakin Innayi ba za ta yi ba balle har ta kawo ma ta abinci. Abincin safe da na dare ma da ta ke miƙo ma ta ba ƙaramin zafin sa takeji ba. Ita fa kunyar ma azo a ga Innayi a gidanta ta ke ji, wai local Innayi ce Uwar mijinta. Mijin ta handsome ɗan ƙwalisa. Ba dan abinda su ke ci dalilin Innayin ba da ba abinda zai sa ta bar Innayi a gidan ta. Har yau ba wanda ya san da zaman Innayi a gidan su dan ko 'yan uwanta ba ta gayawa ba dan kar su ma ta dariya. Idris kam ya kan ɗan leƙo Innayi su gaisa amma mafiya yawanci lokuta gaisuwan ma daga bakin ƙofa ya ke tsayawa ya yi ta, idan ka ga ya shigo ɗakin to Raudha ce ta kira zai ba wa Innayi su gaisa, da ke ba shi da gaskiya haka zai zauna ya yi ta zazzare idanu yana sauraron maganganun su saboda sabon saran da ya kawo shine ya sa wayar a handsfree saboda ya dinga jin mi Raudhan ke faɗi... Lissafin kwanaki Innayi ta ke yi zuwa lokacin da wata uku zai cika har ta koma Asibiti dan ta samu ta tafi gida. Tun ranan ƙarshe da ta je Asibiti ba ta sake fita ko da ƙofar gida ba. Ranan da ta cika wata uku dai-dai da Idris ya leƙota ta tunasar da shi maganar zuwa Asibiti, shi kam gaba ɗaya ya manta. Ya ce zai ware lokaci su je. Bayan kwana uku ya ɗauketa su ka je asibitin, an sake gwajin kuma an tabbatar ba ta da matsala sai dai jininta ya hau sosai. Amma da Sa'a da Raudha su ka kira shi sai ya ce mu su Likita ya ce ta dinga zuwa check up na wata-wata saboda su monitoring sugar level ɗin ta. Ko yaushe Innayi ta samu sugar oho. Innayi na jiran ta ji an ma ta zancen tafiya sai ta ji shiru, ranan da ta yiwa Idris magana sai ya ce wai ba yanzu ba sai bayan wani wata ukun... Magana ma Rahama ne, rashin magana da kowa ya sawa Innayi wani ƙuncin gashi yanzu sai ayi sati biyu ko uku kafin ta yi waya da Raudha. Ta na yiwa Raudhan uzuri saboda ta san karatu ta ke ba ta taɓa nuna ma ta tana cikin damuwa ba saboda kar ta ɗaga hankalinta... *** "Hello Adda Sa'a" "Mutanen Havard ya kike? ya sanyi na san yanzu lokacin sanyi ne a chan?" "Ina lafiya Adda. Dan Allah yaushe rabon ki yi waya da Innayi?" "Gaskiya an kwana biyu, zai kai kwana tara haka" "Ni fa koyaushe na kira wayan Idris ba ta shiga kuma wallahi kwana biyu ina yawan mafarkin Innayi" "Ayya Autan Innayi! dole kiyi kewa kusan shekara ɗaya da watanni fa. Nima ina son zuwa dubota tun last month to dayake kishiyata ta je Umara shiyasa ban je ba na ce zan je bayan sallah amma ban samu lokaci ba" "Dan Allah ki ƙoƙarta ki je, hankalina Allah a tashe ya ke koyaushe" "Shikenan zan je Insha Allah" *** Watanni biyu su ka shuɗe bayan komawar su Asibiti, a wannan lokacin ne aka yi Azumi har aka yi sallah wanda babu maraba da sauran lokutan a wajen Innayi. Cikin Azumi Innayi ta sha fama da ulcer da gudawa. Sai ta gama Azumi sai a kawo ma ta abincin ƙwalame-ƙwalame na zamani wanda cikinta bai saba da shi ba ta ci ta zo ta yita gudawa. A haka dai ta daddafa ta ƙarisa Azumin. Ranan sallah kuwa duk shige da ficen da ake yi a gidan tana kwance tana fama da zazzaɓi... Yauma wuni ta yi da ciwon ƙirji da ciwon ciki. Tana kwance tana jiyo hiran Faiza da ƙawarta suna hira su na shewa da alama bikin wata ƙawar su za ayi wanda za ta auri wani tsoho. Tana ji ƙawar na cewa Faiza ta yi sa'an miji, miji kamar Idris yana da wuyar samu ga shi da kyau Masha Allahu. Innayi ta cigaba da kallon ceiling kamar yadda ta saba a mafiya yawan lokutan, yau ta yi karatun ta yi waƙan har ta gaji. Sallamar Sa'a ne ya katsewa su Faiza hiran su. Ganin Sa'a ya sa jikinta yai sanyi. Gaisawa su ka yi sannan Faiza ta tashi dan ta ɗauko ma ta ruwa. Sa'a ta kalli Mufeedah da ke assignment a falon ta ce " Mufeedah where's your GrandMa?" Ba tareda ta ɗago ba ta ce "she's inside her room" Sa'a ta ce " go and call her" "She wont come out, she's always inside the room" "Wai haka?" Sa'a ta tambayi Faiza da ta fito ɗauke da tray. "Ina ga bacci ta ke yi" Faiza ta amsa kai tsaye. Sa'a ta tambayi ina ne ɗakin Faiza ta nuna ma ta... Tana buɗe ɗakin ta hango Innayi a kwance tana nishin wahala. "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" Sa'a ta faɗa ta yi wajen Innayi da sauri. Daga inda ta ke kwance a ƙasa ta tallafota. Ta sake firgita da yanayin da ta ga fiskar Innayi, ta ƙyamushe ta bushe, idanunta sun firfito yayinda ƙasan idonta yai wani rami. Yadda ka san wata skeleton haka ta dawo. "Innalillahi! na shiga uku ni Sa'adatu. Innayi ke ce haka?" Sa'adatu ta faɗa tana fashewa da kuka. Innayi ta kalli Sa'adatu da kyau wanda sai da ta ɗau kusan 15seconds kafin ƙwaƙwalwarta ya iya processing ko wacece ke tare da ita. "Sa'adatu" ta furta a hankali tana murmushi... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 12 (Free book ne) *A mother's sad demise* Har lokacin da aka gama sakawa Innayi ruwa Sa'adatu ba ta bar kuka ba. Ba abinda ta ke yi a zuciyar ta sai tsinewa Faiza da Idris. Jinyar jikin Innayi ba na kwana ɗaya ba ne ba na kwana biyu ba, jinya ne da ya ke cin ta tun da jimawa. Lallai a gaishe da Innayi da ƙarfin hali ko sau nawa idan su ka gaisa a waya ba ta nuna ma ta tana da damuwa. Kullum idan ta tambayeta ya jiki cewa ta ke da sauƙi. Bayan nurse ɗin ya tafi ne Innayi ta kalli Sa'a ta ce "miye na kuka kuma? Ba fa mutuwa na yi ba Sa'adatu sa'ar mata" "Yanzu Innnayi haka kike zaune tsawon watanni kina cikin ƙunci ba ki taɓa faɗa ba, Innayi haka za ki yi ta shiru har sai sun kashe ki?" "To mi zan ce?" "Kai Allah ya isa Idrissa, wallahi kai da matarka ba za ku ga alkhairi a rayuwar ku ba" "Kul Sa'a, ka da ki sake mu su mummunan addu'a. Addu'ar shiriya kawai za ki mu su, ita na ke yi mu su tuntuni. Sai da Innayi ta yi bacci kafin Sa'a ta fita ta je wajen Likita dan ta ji bayanin abinda ke damun Innayi. Ba ƙaramin ruɗewa ta yi ba lokacin da aka ce mata Ulcer ce ke damun Innayi da ciwon zuciya. Dama ma su haƙuri irin na Innayi ba sa rasa damuwan zuciya. Ko mi aka mu su suyi shiru su yi ta zurfin ciki, ƙarshe idan akayi rashin sa'a a haka za su mutu da baƙin ciki... Koda Idris ya dawo ya tarar da matarsa tana ta kunfa akan cin mutuncin da Sa'a ta ma ta a gaban ƙawarta da 'yarta. "Darling mari na fa ta yi. Wallahi dan tana yayarka ba shine zai hana in mata rashin mutunci ba. Ka warning ɗinta dan wallahi ba za mu wanye lafiya ba. Haka kawai mutum bai neme su ba su dinga zuwa gidan mutane shishshigi" "Calm down dan Allah, mi ya ke faruwa ne? Nima ta kirani ɗazu tana ta zagi na" Faiza ta tura baki ta ce "wai Innayi ce ba lafiya. To Darling mu muka sa ma ta rashin lafiyar ne? ko ta gaya ma na ba ta da lafiya" "Rashin lafiya kuma? Sanda na leƙata da safe fa lafiyarta ƙalau" "Munafurci mana, munafurci irin na tsofi" Yai ajiyar zuciya sannan ya zauna yana ƙoƙarin kiran numbar Sa'an. Ko kaɗan ba ta saurareshi ba sai ma cigaba da zaginsa da ta dinga yi. Da ya tambayi wani asibiti su ke sai ta kashe wayar. Ranan dai Innayi ba ta kwana gidan su ba, Faiza kan ko ajikinta amma shi Idris ya ji ba daɗi dan kalaman Sa'a sun ɗan tsorata shi... Washegari da safe kusan ƙarfe goma shaɗaya Halima ta iso Bauchi, yadda Sa'a ke maganar halin da ta samu Innayi itama jikinta yai sanyi. Ita kam rabon da ta yi waya da Innayi abin ya fi wata ɗaya tun an kusa fara Azumi. Shirye-shiryen bikin 'yarta da za ayi duk ya mantar da ita komai. Bayan ta zo ne Sa'a ta wuce gida dan ta je ta ɗauko kayan Innayi da ke gidan ta yi magana da Likita za su koma asibitin Azare saboda Innayi ta samu kulawa sosai tunda Sa'a na aiki a chan. Kasancewa Asabat ne ya sa dukkan su suna gida. Faiza na kwance kan Idris tana zuba ma sa shagwaɓa su ka ji sallamar Sa'a. Faiza ta ja dogon tsaki tana faɗin " ba za dai a bar mutum ya huta ba" Idris ne ya tashi ya je ya buɗe ma ta ƙofa. Yana gaisheta ta daka ma sa tsawa " riƙe gaisuwar ka! Dan wallahi zan wankeka da mari " Ya shiru ya bi bayanta da kallo. Ɗakin Innayi ta je ta tattaro kayan ta, ba wasu kayan kirki ba ne iya wanda ta tafi da su ne tun da. Da ta fito ta kalli Idris ta ce "kai kuma za mu yi magana idan Innayi ta samu lafiya" tana faɗin haka ta fice daga gidan. Yana tambayarta wani Asibiti su ke ohoho ko kulashi ba ta yi ba... *** Sati biyu Innayi ta yi a gidan Sa'a kuma Alhamdulillah jikinta da sauƙi sosai. Innayi dai tunda su ka bar Bauchi ta ƙuduri aniyar za ta koma ƙauye, za ta zauna har Raudha ta dawo. A sati na uku ta yiwa Sa'a maganar tafiya. Ba wai dan ba ta samun kulawa a gidan ba sai dan tana jin kunyan zama a gidan Uwar mijin Sa'a na gidan kuma su biyu ne. Hakanan kuma tana son gwada zama a ƙauyen su. Rabon ta da ƙauye bayan rasuwan Baffah ta je sau biyu daga nan ba ta sake zuwa ba. "Innayi ba kya so na samu lada ne? Har yanzu fa ba ki gama warwarewa ba" "Ba abinda zan ce sai dai Allah ya saka miki da alkhairi. Sa'a da kunya na cigaba da zama da ku, ga surukar ki ga kishiyar ki" "A'a Innayi, wallahi Hajiya ba ruwanta da zuwanki, tana ma jin daɗin zaman ki da mu" Innayi ta kama hannun Sa'adatu ta ce "ko da na lokaci kaɗan ne ina son zuwa ƙauye. Ki barni na tafi idan da rabo zan sake dawowa" ta ja dogon numfashi kafin ta ce "Dan Allah ki min alkawarin ba za ki sanar da Auta abinda ya faru ba. Hankalinta zai tashi a inda ta ke kuma bazan ji daɗin haka ba" Sa'a ta zaro ido tana girgiza kai tana faɗin"A'a Innayi, A'a" "Ina so ta kasance cikin farin ciki,ta yi karatu hankali kwance" "Innayi duk wata sai na tura wa Idrissa dubu biyu da ɗari biyar, wata uku da suka wuce na mai da shi dubu uku, ban san ko sauran na tura ma sa kuɗi ba amma na san Raudha na tura ma sa kuɗi itama dan mun taɓa zancen da ita. Wai duk dan kar nauyi ya ma sa yawa shiyasa na ke tura ma sa kuɗi amma ɗan batalikin nan da shi da matarsa su ka maida ke kamar wata Akuya. Ai ko Akuya ka ajiye a gida za ka rinƙa kula da ita balle mutum, balle Uwar da ta haifeka. Dole Raudha ta ji komai dan ita ya fi cin amana. Yarinya na fama da karatu amma a hakan ta ke aiki duk dan ta samu kuɗin da za ta kula da ke" "Sa'a na yafe ma sa. Fatana Allah ya shirya min shi, Dan Allah ki bari Auta ta yi karatunta cikin kwanciyar hankali" Sa'a dai ba haka ta so ba amma ya za ta yi dole ta haƙura ta amince da maganar Innayi. Bayan kwana uku da maganar au aka shirya tafiyan Innayi. Ko da su ka yi magana da Raudha itama ba ta goyi bayan tafiyan Innayi ƙauye ta so gane akwai abinda ya faru amma da Sa'an da Innayi duk su ka nuna ma ta komai lafiya. Sai da ta sa Innayi ta ma ta alkawarin ba za ta jima a ƙauye ba za ta dawo Azare sannan hankalinta ya kwanta... Siyayya na musamman Sa'a ta yiwa Innayi tun daga kayan abinci zuwa situru. Kaya masu kyau kala shida ta ɗinka ma ta da sabbin hijabi da takalmi. Wata biyu ta ce za ta yi a chan za ta dawo, zai yi dai-dai lokacin bikin 'yar Halimah da za ayi nan da wata biyun. Mijin Sa'a ne ya kawo su Misau a motar shi bayan sun ɗau Halimah sai su ka wuce Ajili. Sai da Innayi ta biya gidan su Buba ta gaishe da 'yan uwan sa da su ka rage kafin su ka wuce ƙauyen Tunfure a mashin tunda babu hanyar mota. Sa'a Halima da Innayi ne su ka tafi aka bar Dr Mansoor yana jiran su a Ajili... *** Rayuwar ƙauye akwai daɗi, yanayi na damuna da ake ciki ya ƙara sawa ƙauyen na su ni'ima. Ba hayaniya ba damuwa, duk da shekaru sun ja da ƙuruciyarta a ƙauyen bai hanata tuno abubuwa da dama na ƙauyen ba. Har wayau babu wani chanji na azo a gani a ƙauyen, akwai ƙaramin primary school da aka gina mu su wanda yanzu yara mata da maza su ke zuwa. Su na da dispensary da su ke zuwa a dubasu idan ba lafiya, sai idan babbar jinya ce sai su wuce Babban Asibitin Misau, sai dai har yanzu ba su da wutar NEPA. Gidan su na da ɗin ne dai su ke sai dai an kuma buɗa shi saboda 'ya'ya da jikoki da su ka yi yawa. Cikin ƙannen mahaifin Innayi akwai guda ɗaya da ya rage mu su da su ke kira da Baffa Tsoho. Tun da Ado ya aiko akan Innayi za ta zo ya sa aka gyara ma ta ɗakin Baffanta. Wasu jikokin sa ne ke kwana a ɗakin da amma ya ce su bar ɗakin mai ɗaki za ta zo. Da su Sa'a su ka zo su ka ga ƙyamusashshiyar katifa ce acikin ɗakin shine da za su tafi su ka siyi Katifa a Misau su ka aika ma ta da shi... Alhamdulillah ba ta da wani matsala yanzu, babu cima mai daɗi kamar na gidan Sa'a amma kuma za ta ci ta ƙoshi a wadace, ranan da ta zo ma an karramata sosai dan Kaji biyu Baffa Tsoho ya sa aka yanka. Bayan ta ɗan kwana biyu ne ta ce a bata wasu yara su dinga kwana tare. Kulu da Zahra'u aka ba ta wanda su ke da shekara takwas da kuma shekara goma. Yanzu kam ta rage kaɗaici domin rayuwar ƙauye akwai daɗi, yayinda aka je aka dawo zakaga an zauna ana hira musamman da dare. Wani lokaci haka za su zauna da Baffa Tsoho su yi ta hira ko matar sa Yawuro. Baffa Tsoho ya ɗan kwana biyu dan zai kai shekaru saba'in da takwas zuwa tamanin haka amma yana nan da ƙarfin sa dan har gona yana zuwa. Cikin wata ɗaya da sati biyu Innayi ta murmure, jikinta ya fara kyau, ta sake jiki cikin 'yan uwanta suna rayuwar ƙauye mai daɗi. Ance idan mutuwa tana tunkaranka kana iya jin alamunta, wani lokaci har ka yi wasu abubuwa wanda zai nuna kana bankwana ne da duniyar ƙila sai ka mutu mutane su ankara akan dama abin nan da ka ke yi sallama ce ka ke yi da duniya. Cikin 'yan kwanakin nan Innayi tana yawan yin mafarkin mahaifinta da kuma ɗan ta Baffah akwai ranan da ta yi mahaifiyarta wanda ba ta taɓa ganin kamanninta ba sai a mafarki. Tana kwance akan tabarma a ƙofar ɗaki ta fara kallon yanayin gidan. Abu da Sumaye suna surfen gero su na yi suna waƙa. Chan gefe ga Zaliha na dakan borkono tana yi tana tari. Ta juya gefenta taga Yawuru matar Baffa Tsoho tana tauna goro tanayi tana koran wata Akuya da ke ƙoƙarin cin wani bushashshen tuwo da yara su ka bari a cikin tukunya, ita kan har yau ba ta iya cin goro ba lokacin cikin Idrissa ne ma ya sa ta cin goro. Tunowa da ta yi da Idrissa ya sa hawaye ya ciko a idanun ta, ta yi saurin kawar da tunanin ta hanyar faɗin Allah ya shirya mini ku gaba ɗaya... Zahra'u ta fito daga ɗakin Innayi ɗauke da littafinta na makaranta ta zauna kusa da ita ta buɗe littafin tana rubutu. Chan yarinyar ta fara karatu cikin gurɓatacciyar turanci ta ke maimaita abinda aka koya mu su. "Wat is yor name? My name is Zahara'u. How ol are you? Am am 8 yrs ol" Wannan karatu ya sa Innayi ta tuno da karatun ta na firamare da ta yi kafin aure, ƙila da Baffanta ya yi tsawon rai da ta yi karatu mai zurfi sai dai Allah ne ya tsara komai kuma Alhamdulillahi dan ta sani da yardar sa 'yar ta kuma jikar Muhammadu za ta zama likita. Lokacin da Zahra'u ta sake maimaita "wat is yor name?" Sai Innayi ta furta a fili "My name is Faɗima Muhammadu Jo'o" Zahra'u ta saka dariya tana faɗin " Lah! Innayi ashe kina jin turanci" Innayi ta yi murmushi ta ce "Ina ji kaɗan-kaɗan" Yawuro ta ce " ai lokacin Innayi ce mace ta farko da ta fara yin makarantar Boko a ƙauyen nan, Allah ya jiƙan rai, Baffa shi zai ɗauke ki ya kai ki ayi ta zagin shi amma ko kaɗan bai damu ba" Innayi tayi murmushin jin daɗi tana kuma tuno abun kamar yau ya faru. Yadda Goggo za ta yi ta faɗa idan Baffanta zai kai ta Makaranta... Kiran sallar La'asar da aka yi ya sa Innayi ta miƙe ta je ta zaga kafin ta zo ta yi alwala. Yawuro na cewa " Jumma'a babban rana kenan, yaushe yaushe har la'asar ta yi" "Innayi ta ce ai duniyar gudu ta ke yi, ga mai nisan kwana zai ga ta ma sa nisa amma mai ƙarar kwana nan da nan za ta cimma sa" Yawuro ta ce "Astangafurullahi, bari mu tashi mu yi sallah" Innayi ta tuno itama a da irin abinda ta ke faɗa kenan kafin Raudha ta gyara ma ta. "Innayi ba fa Astangafurullahi ake cewa ba Astagfurullahi ne" ta jiyo muryan Raudha a gefen ta, ta yi saurin juyawa amma wayam babu kowa ta yi murmushin farin ciki, ta juyo dan ta gyarawa Yawuro amma Yawuro ta yi nisa dan wasu raguna da su ka shigo gidan suna shirin sa baki a hatsin da aka surfa ta ke kora. "Astagfirullahi" ta furta a fili... Bayan ta yi sallar la'asar ta jima tana yiwa 'ya'yanta addu'a, addu'ar Allah ya shirya su ya kuma haɗe kan su sannan addu'ar Allah ya bawa Auta miji na gari da 'ya'ya ma su tausayinta. Ta kwanta tana jan carbi tana tuno rayuwar ta, idan ta riƙe lissafin Goggo daidai to yau shekarunta sittin da kwana arba'in da huɗu a duniya. Mi za ta ce ban da Alhamdulillah, a lokacin da ake kukan ba ta fara jini ba Allah ya sa ta fara, a lokacin da ta yi aure ake ganin ba ta haihu ba Allah ya ba ta haihuwa, a lokacin da 'yan biyunta duka su ka rasu Allah ya ba ta wasu 'ya'yan. Akwai ranakun ƙunci da baƙin ciki, Akwai ranakun da ta kwana kuka, Akwai ranakun da ta yi tunanin ya rayuwarta za ta kasance idan Allah bai ba ta haihuwa ba kamar Gaji da ta mutu ba haihuwa. Ta yi murmushi lokacin da ta tuno ɗan ta Baffah. *"Innayi Insha Allahu zan kai ki Makkah, duk wahalhalun da ki ka mana za ki samu hutu idan na fara aiki"* "Allah ya haskaka ƙabarin ka Muhammadu na" ta faɗa hawaye na fita ta gefen idon ta. Ta tuno Raudha da ke fesa ma ta turare ranan sallah bayan ta sa lace ɗin da ta ɗinka ma ta. *"Wato ke fa Innayi da Allah yayiki a gidan masu kuɗi da ba ƙaramin Hajia mai kyau za ayi ba, gashi kin tsufa amma har yanzu ke ɗin Beauty ce"* Innayi ta shafa fiskarta da ya riga ya fara yanƙwanewa ta ɗago hannunta ta kalli yadda su ka koma, anyi zamanin da ta yi ƙosai, daddawa, markaɗe, ɗaukan itace idan anzo siya, ga matsar man gyaɗa da ta yi na lokaci kaɗan kafin daga baya Baffah ya hanata. Ta kai duka hannunta biyu kan cikinta ta shafa har zuwa maranta, haihuwa akwai daɗi akwai kuma wahala. Yau idan babu ita a duniya akwai 'ya'yanta, wannan kaɗai ya isa zama *RIBAR UWA*. Akwai ɗan ta Adamu akwai ɗan ta Ibrahim akwai ɗan ta Idrissa akwai Halimatu akwai Sa'adatu sannan akwai Auta Rhaudatu. "Allah Sarki Rhaudatu na, gashi ke ce ko ragon suna ba a miki ba. Allah ya albarkace ki da ke da zuri'ar ki Amin" Ta yi saurin goge hawayen da ke fiskanta ta sauke ajiyar zuciya tareda rufe idon ta ko za ta samu ta yi bacci aikuwa bacci mai daɗi ne ya tafi da ita bacci na har abada... Lokacin da Kulu ta kawo mu su tuwon dare har lokacin Innayi na bacci an idar da sallar magariba kenan. "Innayi ki tashi mu ci tuwo kar yai sanyi" ta faɗa tana taɓa Innayin ganin ba ta kula ta ba ne ya sa ta fita dan ta ɗebo mu su ruwan sha sai dai a ƙofar ɗakin ta haɗu da Zahra'u da kofi a hannu. Sai dukkansu su ka koma ɗakin. Kulu ta sake taɓa Innayi amma shiru. "Innayi mu kan za mu fara ci" ta faɗa tana komawa wajen 'yar uwarta da tuni ta fara kai loman tuwo. "Zahra'u Innayi ta yi sallar Magariba kuwa? Na ga tun da ta shiga ciki da la'asar ba ta fito ba" muryan mahaifiyar su Sumaye ya katse mu su cin tuwon. Kulu ta ce " bacci ta ke yi" "Amma shine za ku fara ci ba za ku jirata ba" Da ƙatoton lomar tuwo a bakinta ta ce " ta ƙi tashi ne" Sumaye ta shigo ɗakin dan ta tashi Innayi ta sani tunda ta zo ba ta fashin sallah akan lokaci. Ba dan ita ta nemi a dinga haɗa mata abinci da su Kulu ba ma da ba abinda zai sa ta haɗa mu su. "Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'oun, wayyo Allah! Innayi Innayi Innayi" ta shiga bubbuga gawar Innayi. Jin kukanta ne ya sa matan da ke kusa su ka yo ɗakin da gudu. Kafin ka ce me gaba ɗaya gidan ya kaure da koke-koke. Aka je aka sanar da Baffa Tsoho a masallaci. Sai da yai ƙwalla da ya ji wannan labari ashe Innayi ta zo su gana ne na ƙarshe shiyasa ta dawo ƙauye da zama. A daren aka ma ta sutura sannan aka aika Misau akan aje a sanar da 'ya'yanta dan da safe za a kaita. Kusan ƙarfe tara na dare aka kawo saƙon mutuwar Innayi wajen Ado. Yana kallon Ball a falo aka yi sallama shine ya fita. Ganin Harisu da Habu wanda 'ya'yan Baffa Tsoho ne ya sa ya yi mamakin ganin su da dare haka. Sai da su ka gaisa sannan Habu wanda shine Babba ya ce " Hamma Ado Allah yayiwa Innayi rasuwa" Turus ya tsaya lokacin da ya ji abinda Habu ya faɗa. Ya girmi Habu dan da Baffah na da rai to sa'anni su ke da shi. Ya sani Habu ba zai ma sa wasa ba. Cikin i'iina ya ce "mi ka ce?" "Hamma Sai haƙuri amma Innayi rai yayi halinsa. Baffa Tsoho ya ce gobe ƙarfe takwas za ayi jana'izar ta" Ado ya dafe gini hawaye na zubo ma sa ganin sa na ƙarshe da Innayi lokacin da ta ke Azare ne wajen Sa'a, har ga Allah wannan Lahdin ya sa niyyar zai je Tunfure ya dubota ashe ba za ta kai Lahdi ba... Sai da su ka yi ta bashi baki kafin su ka bar wajen bayan sun tabbatar ya dawo hayyacin sa. Haka ya shiga gida ransa a jagule, sai da ya zauna ma tukunna hawaye su ka fara zubowa da dalili ya kusan 30mins kafin ya samu ƙarfin saka kaya ya fita dan ya je ya sanar da Iro dan ba maganar waya ba ce... Washe gari aka je aka taho da gawar Innayi bayan anyi Jana'izar ta a ƙofar gidan Mahaifinta, a tushenta, dama aka ce gida-gida ne. In the end ita ɗin 'ya ce a wajen Muhammadu Jo'o, da wannan aka fara sanin ta, ba da matar Buba ko kuma uwar su Ado ba. Daga Tunfure aka wuce da ita maƙabartar Misau inda aka sa ta a gidan ta na gaskiya. Yadda Idrissa ke kuka a wajen ka ce ya fi kowa son Innayi... *** Fiskar Innayi ta ke gani, tana ma ta murmushi, irin murmushin da ta ke yi a duk lokacin da ta ke cikin farin ciki, irin murmushin da ta ke yi idan Raudha na ba ta labarin makarantar su, irin murmushin da ta keyi idan suna zaune su uku a ɗaki su na cin tsire ko balangun da Baffah ya kawo mu su. Ta kai hannu za ta shafa fiskar lokaci guda kuma fiskar Innayin ya ɓace ma ta da gani, dama she's just hallucinating. *"Innayi ki tsaya dan Allah, Innayi na kar ki tafi please, Innayi Innayi"* ta yi luu za ta faɗi ƙasa yai saurin tarota ta faɗa jikin sa amma tuni ta sume... Mutuwar Innayi ya taɓani ni da na ke rubutawa, infact with tears in my eyes na ke rubutun. character ɗin Innayi kacokam ɗin ta na ɗauko ne daga combination na different mothers da na witnessing irin ƙuncin da su ka shiga sakamakon 'ya'yan su. Da ido na naga 'yar da ke dakawa Uwar ta tsawa to the extend sai da Uwar ta yi hawaye Da ido na naga Uwar da matar ɗan ta ke walaƙantata Da ido na naga Matan 'ya'yan wata Uwa sun haɗu suna zaginta su na kiranta Munafuka Annamimiya wai tana haɗa faɗa tsakanin su (lets say hakan ne tanada irin halin amma a matsayinta na uwar miji a gaban jikokin ta da gaban jama'a ku sata a gaba kuna zagi its totally bad) Da ido na naga Uwa tana kuka saboda 'ya'yan ta sun kasa biya mata buƙatun ta. Da ido na naga ɗa ya ce wa Uwar sa "dalla Mama ki yi mana shiru" Akwai wata 'ya da aka bawa kifi mai yawa tsaraba ta kaiwa Uwar ta. Wannan 'ya ta cinye kifin nan ba tareda ta kaiwa Uwarta ba ba tareda ta kuma gayawa Uwarta maganan kifin ba. Kar ku manta kifin nan an bata nata kafin aka ba da na mahaifiyarta amma haka ta haɗa ta cinye duka. Bayan kamar sati wacce ta tura kifi ta kira dan ta tambaya ko wannan Uwa ta ji daɗin kifin da ta aiko. Uwa ta ce ba ta san maganar kifi ba, da aka kira wancar 'yar sai ta fara kame-kame, Ya Allah! Uwar da ta haifeka. (Dan Allah mu cire mentality na cewa iyayen mu sun tsufa ba za su ci daɗi ba. Indai ba wai abunda zai taɓa lafiyar su ba ne to mu bar su su ci daɗi. Wata tsohuwar kwaɗayin da ba ta yi a ƙuruciya ba sai tsufanta sai ta fara kwaɗayi amma a hakan ka ji 'ya'yanta na zaginta ko su dinga yaɓa ma ta magana, "kai Mama ba dai kwaɗayi ba". Wani lokaci kaya Uwa za ta sa 'ya'yanta su ƙwace su ce ta tsufa, wata takalmi Uwarta ta siya idan ta zo gidan sai ta ɗauke shi. Mu a tunanin mu sun tsufa da saka abu mai kyau ko amfani da abu mai kyau)... Akwai misalai da dama na yadda 'ya'ya ke walaƙanta iyayen su musamman UWA. I'm sure a cikin gidan ku ko a family ɗin ku, ko a anguwar ku ko a garin ku kun ci karo da wata Uwa mai irin 'ya'ya kaman na Innayi ko da 'ya'yanta ba su yi exactly irin abinda 'ya'yan Innayi su ka yi ba, za ka ga sun yi shigen sa. Lokaci ya kawo mu Uwa za ta haifi 'ya'ya goma amma kaga an rasa mai kula da ita yadda ya kamata cikin su, ko kuma kaga cikin goman nan baifi biyu ba ne ma su tausayinta a ciki. Idan ma kina hantarar mahaifiyar ki ko Uwar mijin ki to kiji tsoron Allah ki dena domin akwai ranan da za ki kwanta ki mutu a tuhume ki ayyukan da ki ka aikata a rayuwar ki. Wallahil Azim idan ka zamo mai yawan yiwa iyayenka alkhairi to ko ku talatin ne a gaban su za su fi sanyaka cikin addu'o'in su. Ba wai sai kana da kuɗi za ka kula da su ba, ba sai kana da aure za ka musu abin arziƙi ba. Yau ko lemu ka siya ka bawa Uwar ka za ta ji daɗi ta sa maka albarka balle you can do more than that. Idan ba ka da komai to ka yawaita ziyartar su ko ka kirasu a waya ka gaishesu saboda su ma addu'a, ba wai sai kana da buƙata za ka kira ko ka je ka ce a ma addu'a ba. Ko kira kayi ku ka gaisa idan kun gama magana sai ka ce " To Mama a sa mana albarka" Wallahi addu'arta works like magic. Ga wanda iyayen su suka rasu, ku yawaita yi mu su sadaka da addu'a, a duk inda su ke za a isar mu su. Tunda manzon Allah ya ce addu'ar 'ya'ya ga iyayen su da su ka rasu tana isa garesu, haka idan sun yi mu su sadaka ko sun musu wani aikin alkhairi. Allah ka gafarta ma iyayen mu da mu kan mu baki ɗaya Amin... *** Mutuwa dai ɗaya ce, kullum darasi ta ke ƙara zame mana a rayuwa, kuma idan aka yita ɗanya ta ke komawa. Nasabarka, Arziƙin ka ko Talaucin ka baya hana ka jin raɗaɗin ta, matuƙar lokacin ka yayi to dole sai ka ɗanɗanata. Allah ya sa mutuwa ta zamto darasi garemu, mu gyara ayyukanmu su zamto abin kusanci ga Mahaliccinmu Amin. Damuwar mu a yau shine mu samu duniya. We want all the glitters in this world, komai na yayi shi mu ke so, komai na jin daɗi shi mu ke so. Ba mu san kowa ba sai kawunan mu, ma su ɗan sauƙi sauƙi su ne za su iya jawo kaɗan daga cikin 'yan uwan su na kusa su ci daga arziƙin su. Saboda yadda mu ka bawa duniya mahimmanci shiyasa kowani motsin da za mu yi to na neman duniya ne. Hakan ya sa mu ke bin tafarkin ƙarya duk dan mu samu duniya. Abun ya kai ga idan ba ka bi bokaye da malamai ba to za ka tauye hakkin mutane ka ci dukiyar bayin Allah. Wanda ya ke neman halal ɗin sa kuwa zai rufe ido ya kasa yin sadaka ko kyauta, ko ma ya taimaka wa wani ta hanyar da zai samu ya rufawa kan sa asiri. Abinda ya sani kawai shi ne ya ci shi kaɗai wai yana gutun talauci. Shin mun manta duniyar gaba ɗayanta mai ƙarewa ce, yadda mutanen kirki su ke gushewa haka na banza ke gushewa, amma hakan baya taɓa zama mana izina. Mutuwa aka ce rigar kowa ce. Ko ba daɗe ko ba jimawa wannan rigar za ta hau kan ka ko kan ki. Dukkan mu mutuwa mu ke jira kuma babu wanda ya san gaibun randa zai mutu ko kuma sababin mutuwar sa. Ina Manzanni da Annabawa wanda su ka fi mu daraja da ɗaukaka a wajen Allah? Su ma fa sun mutu sun tafi sun bar mu. Ina Sahabbai da Salihan Bayi? Su ma anyi zamanin su ya shuɗe. Ina manyan kafirai, ƙangararru wanda su ka yi fice a zamanin su kuma har yau sunan su na yawo a doron ƙasa? Kamar Fir'auna, Hamana, da Ƙaruna etc Sun fa halaka tun zamanin da ya shuɗe. Mu gangaro zuwa zamanin mu na yanzu. Manya- manyan celebrities a kowani ɓangare na rayuwa da duniya ta yi yayin su. Yau ina su ke? Ba sa nan fa. To idan har sun shige suma fa na yanzun za su zo su shige ta yadda wasu ne za su maye gurbin su. Amma majority ɗin mu yanzu mun mai da celebrities idol ɗin mu. Rayuwar su mu ke bibiya, rayuwar su mu ke kwaikwayo. Idan ma mutane na ƙwarai ne su ma anyi su sun shuɗe kuma wanda su ka maye gurbin su ba jimawa za su yi ba za su zo su shuɗe a sake maye gurbin su da wasu. Mun maida rayuwar mu daga wani kaya zan saka zuwa wani jaka ake yayi. Mun maida rayuwar mu daga tunanin nawa ne a account ɗina zuwa taya zan ƙara samun kuɗi ta kowani hali. Muna aikata saɓo, muna aikata laifuffuka daga ƙananun har manyan. Amma ba mu damu mu dinga yin ƙananun abubuwa na lada wanda za su kawar mana da saɓon da mukeyi na yau da kullum ba. Ke ce hantarar 'ya'yan kishiyoyin ki Ke ce hana mijinki kula da 'yan uwan sa Ke ce ha'intar maƙotan ki ko ƙawayen ki Ke ce ke hana ruwa gudu a wajen aikin ki da kuma cikin 'yan uwan ki Ke ce yiwa miji asiri Ke ce hana 'yar uwar ki ko ƙawarki samun miji Ke ce bin malamai saboda kasuwan cin ki ya ɗaukaka... Kai ne butulci tsakanin matan ka Kai ne ka ke walaƙanta matar ka Kai ne watsar da 'yan uwan ka a lokacin da ka samu buɗi Kai ne lalata yaran mutane, kana zina da yaran da sun kai ka haifesu Kai ne munafukin anguwa mai haɗa guri Kai ne mai ha'inci a kasuwan cin ka Kai ne za ka ɗale kujeran siyasa ko wani muƙami ka cinye dukiyar jama'a Kai ne malami mai gurɓata tarbiyyan yaran mutane Kai ne neman kuɗi ta hanyar asiri Kai ne neman matsayi a wajen bokaye da malaman tsubbu... Da mu yi mai kyau da kar mu yi, daga ƙarshe dai babu wanda zai tsallake mutuwar sa. A sa mu a kabari a bar mu daga mu sai halin mu. Duk yadda mu ka ji daɗin rayuwa muka yi abun da mu ke so za mu ga sakamakon daga lokacin da Malakul Maut ya ziyar ce mu. A koyaushe mu dinga tunawa cewa akwai ranan hisabi, ranan da babu mai wani iko ko gata ko muƙami, ranan da kowa ke nafsi-nafsi, ranan da Allah kaɗai ne Sarki mai ɗaukaka mabuwayi, wanda zai saka mana gwargwadon abinda mu ka aikata. Idan ka kwatanta daidai ka bi duniya a sannu, Aljannah tana nan an tanada ma ka. Idan ma rayuwar shaƙiyanci, gadara da mugunta ka yi, wutan Jahannama na nan an tanada wa kafirai, mushrikai da munafukai da ma su mugayen hali irin na ka. Mu yawaita tuna wannan: shin mi muka tsinana a rayuwar mu? Shin yau idan mu ka mutu mi muke tunanin za mu tarar a ƙabarin mu? Da mi mutanen duniya za su tuna da mu?, da mi za ayi shedar mu idan muka mutu? Wani aikin alkhairi mu ke yi da mu ke tunanin Allah zai gafarta mana saboda shi? Shin shekarun mu nawa a duniya yanzu? Kuma ko muna da sani gameda iya shekarun da aka ɗeba mana. Mun kusa mutuwa ko kuma dai da saura? So nawa ka ke neman istighfari a rana? So nawa ka ke karatun Qur'ani a rana? Nafila nawa ka ke yi a rana ko a sati? Yaushe rabon da ka yi sadaka ko kyauta? Allah ka bamu ikon gyarawa Amin... Akwai ayyuka guda uku da ladan su baya shiga mizani a ranan alƙiyama saboda girman su: 1- YIN AFUWA GA MUTANE: Allah yana cewa "Duk wanda ya yi afuwa kuma ya kyautata to ladansa yana ga Allah" 2-HAƘURI: Allah bai faɗi iyakar ladan da zai ba wa masu haƙuri ba. "Haƙiƙa ana bai wa ma su haƙuri ladansu ne ba tareda lissafi ba" 3-AZUMI: shima Azumi Allah bai faɗi adadin ladan da zai bayar wa ma su yinsa ba. Manzon Allah ya ce a ranan Alƙiyama wani Mala'ika zai yi kira ya ce " Ina mutanen nan waɗanda ladan su ke wajen Allah?" Nan ta ke ma su haƙuri da ma su afuwa da ma su Azumi sai su fito su tafi wajen karɓan sakamakon su. *Ya Allah ka ƙara mana haƙuri da juna, da haƙuri da ƙaddara da kuma haƙurin biyayyarka. Ya Allah ka sanya mana taushin hali mu dinga yafiya ga junan mu, ka karɓa mana Azumin mu da dukkan Ibadunmu. Amin* Ribar haƙurin Innayi da afuwan ta ga 'ya'yanta yana wajen Allah. A nan na kawo ƙarshen labarin Innayi amma akwai 2-3 pgs da za su biyo baya da za mu ga yadda rayuwan 'ya'yan Innayi ya koma bayan rasuwan mahaifiyar su. *Dan Allah mu daure mu dinga kyautatawa iyayen mu, yanzu da su ka girma ne su ke buƙatan mu, su ke buƙatan tausayinmu da jin ƙan mu. Mu nemi karanta fassaran suratul Isra'i musamman aya ta 23,24,25 da Allah yai magana akan Iyaye* *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 13 (Free book ne) *condolence* Dogon suma Raudha ta yi dan duk taimakon gaggawa da ya bata dan ta farfaɗo ba ta farfaɗo ba hakan yasa ya ɗauketa ya wuce da ita wajen motar sa yayinda Emilia ta bi bayan sa saboda itama ta biyo bayan Raudha ne dan ta bata jakarta da kuma wayarta da ta baro shine ta ga abinda ya faru. Bayan ya shimfiɗa Raudha a kujerar baya yai wa Emilia nuni da ta shigo gaba, ba ta ɓata lokaci ba ta shiga ciki da sauri... A asibitin ma sai da ta kai kusan awa uku kafin ta farfaɗo, bayan wasu daƙiƙai da farfaɗowan ta ta kama kuka. Kukan ne ya ja hankalin Emilia da ke zaune gefenta tana latsa waya. Ta yi ta yi ta sanar da ita abinda ya faru amma ba ta gaya ma ta ba illa cewa da ta ke yi "i want to go home" Emilia ta ɗau wayarta ta kira wanda su ka zo tare. Sallah ya fita yi amma da tare su ke zaune da shi a ɗakin. Bayan ya sanar da ita yana hanya ne ya sa ta kashe wayar ta cigaba da kallon Raudha da ke kuka, ba ƙaramin tausayi ta ba ta ba domin ta san duk abunda zai sa Raudha kuka haka to ba ƙaramin abu ba ne. Ba wai sun shaƙu da Raudha ba ne sosai amma watan da ya wuce da ƙanwar Emilia ta mutu ta je ta ma ta ta'aziyya har gida ita da Azhar hakan ya sa ta ke ƙara ganin Raudhan da daraja, wannan ya sa su ka fara ƙawance. Kafin Prof Bamalli ya iso Raudha ta cire ruwan da aka ɗaura mata wanda saura kaɗan ya ƙare. Ƙoƙarin tashi ta ke yi Emilia ta tareta. "Emilia please let me go" ta faɗa da dasasshshiyar murya Emilia ta girgiza kai. Raudha ta fara ƙoƙarin tureta amma ina Emilia ta fi ƙarfinta. "Rodha calm down, professor Bamly is coming" Ta girgiza kai tana cigaba da tureta, da ƙyar Emilia ta samu Raudha ta nitsu ta zauna a bakin gado ta cigaba da kuka. Turo ƙofar da aka yi ya sa Raudha ta ɗaga idonta ta kalli wajen ƙofar. Professor Bamalli ne ya shigo tareda sallama, ba ta iya amasawa ba sai ma kawai ta sunkuyar da kanta. Emilia ta kissing goshin Raudha ta ce "take care dear, i'll call you later" Bayan Emilia ta fita ne Prof Bamalli ya jawo kujera ya zauna yana fuskantar Raudha. "Raudha" ya kira sunan ta a hankali. Ta ɗago ta kalleshi na ɗan daƙiƙu kafin ta sunkuyar da kai ta cigaba da sheshsheƙar kuka. "Na san ke musulmace Raudha, kuma kin sani yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin cika-ciken musulunci. Saƙon mutuwa akwai ciwo, musamman idan wanda ya rasu makusancin ka ne. Sai dai Allah da ya haliccemu shi ya tsara wa kowa adadin lokacin da zai yi a doron ƙasa, hakan ya sa idan lokaci yai ko second ɗaya ba za ka ƙara ba" Raudha ta ɗan sassauta kukan na ta tana sauraron sa. Prof Bamalli ya cigaba. "Innayi mahaifiyar ki ce ko?" Maimakon ta bashi amsa sai ta kifa kan ta a gwiwowinta tana ƙara sautin kukan ta wanda ke ratsa zuciyar mai sauraro. "A maimakon kuka Raudha addu'ar ki ta ke buƙata yanzu, ki daure ki yi ma ta addu'a" Ta ɗago ido da sauri ta ce "Sir ba ka san Innayi ba ne, ba ka san irin wahalhalun da ta sha a kan mu ba. Bai kamata ta mutu ba, bai kamata ta tafi ba tareda na cika alƙawurran da na ma ta ba. Bai kamata ta tafi ba tareda..." "Manzon Allah da ya fi kowa daraja ya bar duniya Raudha. Babu wani da zai rayu ba tareda ya ɗanɗani zafin mutuwa ba, kisa a ranki mutuwa ita ce hutu gareta. Iya lokacin da aka ɗibar ma ta kenan a duniya. Raudha a duk inda mahaifiyar ki ta ke Insha Allah tana cikin farin ciki" maganar sa ya katseta. Hawaye kawai ta ke yi tana yi tana goge majina da bayan hannun ta. Hakan ya sa Prof Bamalli ya ciro handkerchief ya miƙa ma ta. Nasiha ya cigaba da yi ma ta bayan ya lura ta ɗan nitsu. Ya ƙare da ba ta labarin na sa mahaifiyar. "Ban tashi na ga mahaifiya ta ba. Ance ina ɗan wata goma ta rasu. Yayar Mahaifiyata da ke zawarci Baba na ya aura bisa shawarar 'yan uwan sa, a cewar su za ta kula da ni. Sai dai fa abun bai kasance yadda ake so ba domin tun lokacin da ta shigo ta ke hantara ta, Baba yai faɗan yai masifar amma shiru Umma ba ta kula da ni yadda ya kamata, yadda ta ke mini tamkar ba Uban su ɗaya da Mahaifiyar da ta haifeni ba. Haka na taso a walaƙance tamkar ba a gidan Ubana na ke ba, sai na fi sati ba a min wanka ba, sai Baba ya lura da dauɗan da ke jikina tukunna ya ma ta magana akan ta min wanka, wani lokaci ta yi wani lokaci ta ƙi yi. Ina shekara huɗu ta haihu nan kuwa duk wani kulawa ya koma kan ɗan da ta haifa sai kuma Adama da ta zo da ita gidan. Akwai lokacin da Baba yai yunƙurin ƙara aure saboda ko zai dace a samu wacce za ta riƙe ni amana tunda dai Umma Habiba ta kasa riƙeni amma magana ta zo ta bi ruwa. A haka dai na taso har na kai shekara takwas ba na zuwa makarantar Boko sai dai makarantar Allo idan Umma ta ga dama. Ina girma ina sawa a raina ni ba ɗan gidan ba ne, Yaya ta Adama da ƙannena Sani da Amadu su ne 'yan gida shiyasa Umma ba ta so na. Ina shekara tara a duniya watarana Umma ba ta bani abincin rana ba, na fakaici idon ta na shiga ɗakin da ake dafa abinci na buɗe tukunya na fara ci, rabona da abinci a lokacin tun tuwon dare, dan ɗumamen safe ma ban samu ba. Ina cikin ci Umma ta shigo ta sameni nan kuwa ta hau duka na tana yi tana zagi na. Bayan kwana uku aka kaini wajen Baffa Saleh wanda ya ɗaukeni ya kaini Almajiranci a chan wani gari da ake cewa Yusufari da ke Yobe state yanzu. Ina chan ina karatu da daɗi ba daɗi haka, yadda ba na samun cin abinci da kyau a gidan Uba na haka wajen Malam ma ba na samu, wani lokaci ka samu abinci ka yi hani'an har ka godewa Allah, wani lokaci kuma ka wuni da yunwa. Banfi wata bakwai ba na fara rashin lafiya tun Malamin mu bai damu ba har ya damu ya sa aka fara yi min jiƙo ina sha. Wasa wasa sai ga cikina ya fara kumbura ta kai na kwanta ba na iya ko tashi, hakan ya sa aka kai ni asibiti. Da ganina nurses na wajen su ka yita yiwa Malam faɗa tareda cewa yai gaggawan kai ni Teaching Hospital da ke Maiduguri dan abin ya fi karfin su, idan ya barni haka mutuwa zan yi. Malam dai a tsorace ya lallaɓa ya kai ni chan bayan ya aikawa iyaye na. A ranan da aka kai ni a ranan aka min surgery saboda rashin yin surgery ɗin da wuri na iya sawa na mutu. Typhoid ne ke damuna har ta min katutu a jiki ta fara cin hanjina, rashin abinci mai kyau da kuma jiƙe-jiƙen maganin da aka yi ta bani ya kuma lalata min ciki. Wani Balarabe da ake kira da Dr Fu'ad Hamdan Al Sayyid shine shugaban pediatric a lokacin kuma shi ya jagoranci aikin da aka min. Shi kan sa bai da 100% yaƙinin zan yi rai saboda yadda na galabaita. Ya yi faɗa sosai wa iyayena kan yadda su ka bari har jinya ta ci ni haka. Na yi wata biyu da sati ɗaya kafin na samu sauƙi har ake shirin sallama na a lokacin Dr Fu'ad ya ce indai Almajiranci za a kaini to gara a barni a wajen sa ya sa ni a makaranta. Ba a wani ja lokaci ba Baba ya amince, aka bar ni a Maiduguri wajen Dr Fu'ad. Ina shekara goma na fara aji ɗaya a primary, da ke ina da ƙwazo a aji biyar na zana jarrabawar gama primary na shiga Sakandare, ko da wasa ban taɓa zuwa gida ba saboda yadda na ke jin haushin Mahaifina da Uwar riƙona. Sau ɗaya Baba ya zo ya dubani amma bai sake zuwa ba. Shima ya san zaman wajen Dr Fu'ad ya fi mini a kan gidan sa. Ina aji uku a sakandare mahaifina ya rasu wanda hakan ya sa Dr Fu'ad ya ɗaukeni mu ka je gida ta'aziya. Har lokacin Umma ba ta nuna mini so ba sai ma cewa da ta ke na ƙi asalina ina bin Balarabe har da min addu'ar Allah ya sa na zama ɗan fashi ko ɓarawo, ranan na yi kuka sosai saboda mummunan kalamai da Uwar riƙona kuma yayar mahaifiyata ta yi ta jifana da shi. Bayan mun koma na watsar da kashin su na rungumi Dr Fu'ad wanda ya zame min Uba. Allah bai bawa Dr Fu'ad da matar sa haihuwa ba shiyasa ya ke son yara, kafin ni ya taimakawa yara dayawa ta hanyar inganta rayuwar su. Dr Fu'ad ne ya turani ƙasar America dan na yi karatun Likitanci. Ina nan ina karatu har na kai matakin da na fara yin residency ɗina. A lokacin ne na je Nigeria saboda Dr Fu'ad ba shi da lafiya yana ma shirin komawa ƙasar sa ta Asali wato Egypt. Shi ne ya nuna min akan na je gida na ga 'yan uwa na saboda duk min rashin adalcin su sune Asali na. Bayan na je ne na tarar da Umma a walaƙance, ta lalace sosai, ga jinyar da ya ke cinta ba mai kula da ita. Sai da ta ganni ta fashe da kuka tana neman na yafe ma ta. Ita ta yiwa Baba na asiri ya zamto duk maganar da ta ma sa ba ya iya mu su shiyasa duk abin da ta ke min ba ya iya cewa komai. Ko lokacin da ta ce ya kai ni Almajiranci bai iya musa ma ta ba. Ga uwa uba gadona da su ka cinye ita da 'ya'yanta. Da farko na ƙi na yafe daga baya na ce na yafe ma ta. Ni na kai ta Asibiti na ba da kuɗi aka yi jinyarta yayinda na koma aiki na. Watanni uku bayan dawowa na Dr Fu'ad ya rasu a ƙasar Egypt, sai da na samu lokaci na je na yiwa Matarsa da 'yan uwan sa ta'aziya saboda Dr Fu'ad ya min komai a duniya" Prof Bamalli ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Raudha da ta yi shiru tana sauraron sa dan yanzu ta dena kukan. Ya cigaba da cewa " A lokacin da na samu rufin asiri na kai matsayin da zan iya tallafawa iyayena sai ya zama na ba sa tareda ni. Duk abin da na zama, duk abin da na tara ba zan taɓa iya taimakawa iyayena ba domin ba sa raye. Abu uku zan iya yi mu su yanzu musamman ma mahaifiyata wanda ko kamanninta ban sani ba, abu ukun nan su ne za su zamo ma ta RIBAN kasancewar ta UWA kafin ta rasu. Na farko addu'a da zan dinga yi ma ta. Na biyu Sadaka da ayyukan alkhairi da zan yi da sunan ta. Na uku kasancewata mutum na gari zai zamo ma ta abun alfahari duniya da lahira" Sai da yai shiru na ɗan daƙiƙu kafin ya kira sunan ta "Raudha" Ta amsa a hankali "Na'am " "Ki riƙe abu ukun nan daga yau, domin su ne abun da mahaifiyar ki ke buƙata daga gareki. Ki godewa Allah kin rayu da mahaifiyar ki har tsawon lokaci haka, kin ga fiskar ta, kin ji maganar ta, kin ga murmushin ta, haka nan kin ga fushin ta, ga uwa uba ta yi ta miki addu'a kafin rasuwar ta. Akwai wanda mahaifiyar su ke rasuwa wajen haihuwar su, wasu irin mu kuma su na ƙananun yara su ke rasa ta su, wa su kuma sai sun ɗan girma kafin ta rasu. Almuhim shi ne ko da UWA ba ta raye akwai haƙƙin da ya rataya a kan ka wanda idan ka sauke shi a koda yaushe za a dinga isar mu su da ladan" Wannan karon maganar cikin lallashi ya yi shi "ki yi haƙuri ki dinga yi ma ta addu'a domin abunda ta fi buƙata a wajen ki kenan"... *** Bayan sun bar Asibitin gidan ta ya kaita dan ta ɗauko kayan ta a cewar sa bai kamata ta zauna a gida ita ɗaya ba a wannan lokaci. Ko da ta shiga ɗaki ta ga hoton su da Innayi da ta ajiye a desk ɗin ta kawai sai ta fashe da kuka, kuka ta ke sosai tana ƙanƙame hoton a jikin ta. Prof Bamalli ganin ta fi minti talatin ba ta fito ba ya sa ya shiga cikin gidan dan ya ga ko lafiya. A nan ya samu Raudha riƙe da hoto tana kuka, ta bashi tausayi haka kuma ta sake shiga ran sa. Sai da ya ƙara ma ta nasiha kafin ta haƙura ta shiga ɗaukan kayan da za ta tafi da su... Bayan sun iso gidan sa a hankali ta dinga bin sa a baya har su ka shiga cikin gidan. Wata farar mata tsohuwa guntuwa ce ta tare su da fara'arta. Prof Bamalli ya ce "Hajiya Umma ga Raudha nan" Raudha ta ɗaga ido ta kalli Prof Bamalli wanda yai ma ta alama da ya nuna cewa wannan matar dai ita ce Uwar riƙon sa da ya ba ta labari ɗazu. Hajiya Umma ta kamo hannun ta ta kaita wajen kujera ta zaunar da ita tana tambayarta mi za ta ci, Raudha ta ce a ƙoshe ta ke. Hajiya Umma ma nasiha ta yi ma ta kafin ta nuna ma ta ɗakin da aka shigar ma ta da kayanta ta ce ta je ta yi sallah dan lokacin sallar magariba ya yi. Bayan ta yi sallah ta zauna ta ɗaga hannu tana yiwa Innayi addu'a, tana yi tana hawaye. Ba a jima ba Umma ta zo ta kirata akan ta fito su ci abinci, Rhauda ta ce ta ƙoshi Umma ta ce ba ta yarda ba, dole dai ta fita zuwa dinning ɗin, a nan ta haɗu da yaran Prof Bamalli guda biyu babban Aisha Yusrah za ta kai shekara shabiyu sai ƙaramin mai suna Fou'ad ɗan shekara takwas. Ba wani abincin kirki ta ci ba dan abincin ma ɗaci ya ke ma ta a baki dan ta loosing appetite. Da ta gama tana son tafiya ɗaki Umma ta riƙeta da hira, ta sani duk dan ta kawar ma ta da raɗaɗin mutuwar da ta ke ji ne. Su na zaune a falo Prof Bamalli ya dawo inda ya sanar da ita yayar ta Sa'adatu ta kira kuma sun yi magana da ita. "A ƙauye ta rasu ko?" Ta yi tambayar tana kallon cikin idon Prof Bamalli. "Ki yi haƙuri Raudha" Kawai sai ta fashe da kuka. Nan da nan Umma ta shiga rarrashinta tana ba ta haƙuri. Bayan ta tsagaita kukan ne ta ce za ta je ta kwanta Umma da Prof Bamalli su ka ma ta sai da safe. Tana shiga ɗakin wani sabon kukan ta buɗe tana yi a ciki ciki saboda kar su Umma su jiyota, tana kukan har baccin wahala ya ɗauketa... Washegari ba ta tashi da wuri ba, kuma kasancewar Lahdi ne duk suna gida, bayan sun karya ne Prof Bamalli ya ba wa Raudha wayarta ya ce ta kira Sa'a. Bugu ɗaya aka ɗauka maimakon ta yi magana sai ta fashewa Sa'a da kuka, ita ɗin ma a wajen zaman makokin daurewa kawai ta yi ta shiga ba wa Raudha haƙuri tana danne na ta kukan, bayan ta yi shiru ne su ka yiwa juna ta'aziya kafin ta ba wa Halima wayar dan su gaisa, itama tana magana tana hawaye, Inna Mairo 'yar uwar Innayi ta karɓi wayan itama su ka gaisa, sai aka miƙawa Yawuro wayan dan tun jiya ta ke cewa tana son magana da Raudha. Yawuro ta fara exaggerating mutuwar "Allahu Akabar, Auta Allah bai yi za ki gana da mahaifiyar ki ba. Wallahi Innayi ta yi rabo, tana sallah fa ta rasu. Ta yi sujjada aka ɗau ran ta, ai kinga ta yi rabo. Kai Innayi Allah ya jiƙan ki, Allah ya miki albarka Raudha kafin ta rasu kullum sai ta yi zancen ki, ta ce Allah ya..." Raudha ta fashe da kuka wanda ya sa dole Prof Bamalli ya ƙarɓi wayan ya kashe... *** Duk yadda ta so Prof Bamalli ya bar ta ta zo gida ya ƙi cewa yai komawar ta Nigeria ba zai dawo da Innayi ba, ta bari idan aka yi hutu sai ta je. A haka kwanaki su ka dinga tafiya, tun tana kuka kullum har ta sawa kan ta salama ta daina saboda gaskiyar Prof Bamalli ne kuka ba abinda zai ƙarawa Innayi. Ta kan yi hawaye kam amma banda zama ta yi kuka har na tsawon lokaci kamar yadda ta ke yi farko farkon rasuwan. Ko a aji sai da su ka ga chanji tattare da ita kuma sun tausaya ma ta bayan ta gaya mu su mahaifiyar ta ce ta rasu. Tun sati biyu da faruwan abun ta shirya komawa gidan ta amma Prof ya ƙi ya ce ta je ta kwaso sauran kayan ta daga yanzu ta dena zama ita ɗaya. Ba yadda ta iya dole ta haƙura ta cigaba da zama a gidan sa. A hankali ta lura iya zamanta ba ta taɓa ganin matar Prof ba, ranan ta yi ƙaurin baki ta tambayi Umma wanda ta sanar da ita shekaran matar sa biyar da rasuwa shiyasa ma ya ajiye aikin asibiti ya koma koyarwa dan ya samu lokacin kula da 'ya'yan sa. Sai a lokacin ta ji jikin ta ya yi sanyi, ashe fa yadda ta rasa UWA haka Yusrah da Fou'ad su ka rasa ta su. Gaskiyar Prof ne da ya ce ta godewa Allah, tunda gashi waɗannan yara sun rasa mahaifiyar su da ƙananun shekaru. Ta shiga ba wa yaran kulawa tana jawo su jiki, yanzu kan har ta kai sun saba da ita, za ka ga sun zauna su na taɗi har da dariya. Wasa-wasa har wata biyu ta cika, Raudha su ka fara jarrabawa, duk da dai yanzu ta rage karatun sosai amma duk da haka jarrabawar ta zo ma ta da sauƙi. Yau su ka ƙare jarrabawar su kuma yau ɗin ne ta sanar da Prof a kan za ta je Nigeria. Yana zaune a Library ɗin sa yana karatu ta sameshi da maganar. "Na riga na yi booking, flight ɗin mu Jibi zai tashi" Ta ɗan ɗago ido ta kalleshi da mamaki. "Ni ma zan je ta'aziyar ko ke kaɗai ki ke son ladan?" Raudha ta girgiza kai Har ta tashi za ta tafi ya ce ta zauna. Ya ce " barin ba ki wani labari. Last year na je wani cafe zan haɗu da wani, sai na ɗaga hannu na kira waiter dan ta kawo min coffee. Na kirata ne saboda ƙaramin gyale da ta yane kan ta da shi ya burgeni, ban ɗauka musulma ba ce sai da ta juyo na ga tabon sallah a goshin ta. Da turancin ta na gane cewa ita ɗin 'yar ƙasa ta ce Nigeria kuma a Nigerian ma Arewa. Na karanta tag ɗin da ke jikin apron ɗin da ta sa na ga an rubuta RAP na yi mamakin wannan suna. Bayan ta kawo min coffee ɗin ne na tambayi sunan ta ta gaya min. Ban sake komawa cafe ɗin ba saboda ayyuka da su ka min yawa. Bayan kamar wata uku watarana ni da yarana mun je sallar Jumma'a a masallacin da ke Roxbury na hango yarinyar ranan. Shigar Atamfa da ta yi ne ya banbantata da jerin matan da su ke tare a bakin masallacin. Tun daga lokacin na ke lura da zuwanta masallacin duk Jumma'ah, wani lokaci na ci karo da ita wani lokaci kuma ba na ganin ta. Na je cafe ɗin da ta ke aiki aka ce ta bar aiki a wajen. Ikon Allah sai ga shi farkon shekaran nan da na shiga wani aji zan koyar sa ga yarinyar nan mai yawan murmushi" Tunda ya fara magana Raudha ta sunkuyar da kai tana murmushi. "Tunda na fara koyar mu su ta kuma burgeni saboda ƙwazon ta, lokuta da dama ina son yi ma ta magana amma ina jin tsoron ka da ta fassarani da wata manufa shiyasa na yi shiru na ke son sai na gama karantar ta kafin na gabatar da kai na gareta, kuma Alhamdulillahi na karance ta tsaf" ya ɗanyi shiru yana kallon yadda Raudha ke wasa da yatsunta ya ce "Ban san ko yarinyar nan mai yawan murmushi za ta ba wa tsoho mai 'ya'ya biyu damar gabatar da soyayyarshi gareta ba. Idan son samu ne ya tura magabatan sa wajen 'yan uwan ta" Ai kuwa Raudha ta tashi da sauri ta bar ɗakin tana murmushi. Sai da ta shiga ɗaki ta kwanta a kan gado sannan ta fara jujjuya maganar Prof a ranta. Ta san dai ta taɓa ganin shi a Cafe ɗin da ta fara aiki amma ba ta sake ganin sa ba sai da ya fara koyar da su. Ta sani Professor Umar Audu Bamalli na burgeta, kuma kyautata ma ta da yai a watanni biyun nan sun ƙara ma sa kima a idon ta amma gaskiya ba za ta kira hakan da soyayya ba. Ko kuma dai dan ba ta san SO ba ne? Saƙon sa ya shigo wayar ta a kan ta daure ta bashi amsa. Ta jima tana shawara da zuciyarta kafin ta tura ma sa reply kamar haka "ka bani lokaci zan yi tunani"... Wasan ɓuya ta fara yiwa Prof saboda kunyar sa da ta ke ji har ranan da su ka shirya tafiya Nigeria. A cikin jirgi kujeran su kusa da na juna hakan ya sa duk ta takura da shi. "Na ga alama ɗan tsoho dai sai dai yai haƙuri" Raudha ta ji kaman ta nitse saboda kunya. Ta yi Istikhara akan maganar tun shekaranjiyan da yai maganar amma har yanzu ba ta cimma wani matsaya ba. "Na yi haƙuri ko?" Ya tambaya yana tsareta da ido ta yi saurin girgiza kai Ya ce "Kin amince kenan?" ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya ce "Allah ya shige mana gaba" Ta amsa da Amin... *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 14 (Free book ne) *A bride* Jirgin su ya sauka a Abuja wajajen sallar maghrib, a tunanin Raudha a wannan lokacin za su nemi motan Bauchi ko ma na Jos su ka samu su tafi sai ta ga sun nufi cikin gari. "Hotel a cikin gari akwai tsada" ta faɗa a hankali. Maimakon Prof ya ba ta amsa sai kawai yai murmushi. Maimakon Hotel wani Babban gida su ka nufa a Wuse II. "Gidan abokina ne, tare mu ka yi karatu" ya faɗa dan ya cire ma ta damuwa. Matar Dr Ahmad ta tarɓeta da kyau. Umaimah da Dr Ahmad auren haɗin gida aka mu su kuma dukkan su 'yan boko ne, dan Umaimah chartered accountant ce, mahaifin Dr Ahmad tsohon Minister ne wanda ya rasu shekaru kusan biyar da su ka wuce. Bayan ta ci abinci ta yi sallah su ka ɗan taɓa hira da Umaimah kafin ta kwanta, kusan ƙarfe goma ta gota bacci mai daɗi ya tafi da ita. Washe gari Dr Ahmad ya ba su Driver wanda zai kai su har Misau. Ƙarfe tara na safe su ka kama hanya, sai a lokacin kuma Raudha ta shiga fargaba, bugun zuciyar ta ya ƙaru. Ina ma za ta iya maida hannun agogo baya, ina ma ko da sau ɗaya ne za ta sake ganin Innayi, tana cikin wannan tunani sai hawaye. "Ya Allah! Kin manta alƙawarin da ki ka min kenan?" Prof ya faɗa da sigar lallashi Ta girgiza kai tana ƙoƙarin goge hawaye, tanayi wa su na zubowa. Nasiha prof ya fara ma ta wanda ya sa dole ta haƙura da kukan. Daga baya ma ta sa earpiece a kunne ta kunna ƙur'ani tana sauraro. Tun da su ka iso Jos ta fara bacci ba ta farka ba sai da su ka wuce Bauchi har sun kusa isowa Darazo. "Abban Yusrah ashe na jima ina bacci kaman na ga mun wuce Bauchi ko?" "Da ba ki tashi ba idan mu ka iso goya ki zanyi na shiga da ke ciki. Ta yi saurin rufe fiskarta da gyalenta tana murmushi "Ko na gwada ne idan mun je?" "Kayya ni kam" ta dunƙunƙune gefe tana cigaba da rufe fiskarta... *** Tunda su ka shiga garin na Misau jikinta yai weak, ba ta yi kuka ba amma sai sauke ajiyar zuciya ta ke a kai-akai. Shekara biyu da sati biyar rabonta garin. Akwai 'yan chanje-chanje da ta spotting tun a hanya. Ta dinga yiwa Driver kwatance har su ka iso anguwar su. A dai-dai bakin layin su motar ta tsaya, da ke yamma ne kwalbatin da ke wajen matasa sun kafa majalisa ana ta gulma, ganin dalleliyar motar da ta tsaya gefen su ya sa gaba ɗaya su ka zurawa motar idanu, suna tunanin wa ke da irin motar a garin. "Ni da Malam Isa za mu samu masallaci mu yi sallah, idan na dawo zan kira ki sai ki yiwa Yayan na ki magana mu ƙariso" Ta gyaɗa ma sa kai tana ƙunshe kukan ta. "Please ban da kuka" nan ma gyaɗa ma sa kai ta yi. Da Bismillah ta buɗe ƙofa ta fito tana ƙoƙarin gyara gyalenta tareda maimaita Hasbunallahu wa ni'imal wakil a zuciyarta. "Ehohoho! Wallahi Anty Raudha ce" wani matashi cikin samarin ya faɗa yana tahowa da gudu. Idon matasan chui a kan ƙofar motar lokacin da su ka ga alamun ana buɗewa. Jin Salihu ya ambaci Raudha ya sa su ma su ka sa ihu wasu su ka bi bayan sa. Salihu kaman wani ƙaramin yaro haka ya rungumi Raudha yana murna. Salihu ɗan Yayan ta Ado ne kuma zai kai irin 14-15yrs haka. "Antyn mu sannu da zuwa, sannu mutan America" haka su ke ta faɗa, su ka tisa ta a gaba kamar za su ɗauketa sama, haka su ka rakota har ƙofar gidan na su. Da da ne sashen su za ta fara shiga ta ga Innayinta sai dai yanzu ko ta shiga ba ta san mi za ta tarar ba, ƙila gidan ma ya gama nurƙushewa. Ta daure ta bi Salihu su ka shiga ƙofar Yaya Ado. Tun kafin ta ƙariso Salihu ya ɗaga murya yana shelar isowarta sai ga Matan gidan su na rige-rigen fitowa. Yadda ka san sun shekara goma ba su ganta ba haka su ka rungumeta su na washe baki. Daurewa kawai ta ke yi kar ta yi kuka kamar yadda Prof ya ce. Sai da ta zauna a falo ne Jamilah ke cewa Salihu ya je masallaci ko majalisin su Abban sa ya kira shi. Da ke ta riga ta sanar da zuwanta sun shirya ma ta abin tarba na karramawa. Kan kace me an cika gabanta da maltina, 5alive, ruwa mai sanyi da soyayyar naman kaza. "Zan yi sallah tukunna" ta furta a hankali... Ɗakin Jamilah ta shiga ta gabatar da sallar Azahar da La'asar. Tana cikin addu'a Jamilah ta shigo ta ce " Yaya ya shigo, idan kin gama sai ki fito" Ta gyaɗa ma ta kai... Lokacin da ta fito yana zaune yana amsa waya, kallon sa ta ke yi tana ganin fiskar Innayi a fiskar sa. Da shi da Idris da ita, su ukun nan ne su ka ɗauko kamannin Innayi, duk da su maza ne amma kana ganin su ka kalli Innayi ka san ko shakka babu ita ce uwar su, dan kamannin yai yawa. Yadda ta san shi tun da haka nan ya ke, sai ma gani da ta yi ya ɗan ma ta duhu. "Auta" ya kira a hankali. Ji ta yi kamar Innayi ce ta kirata, maimakon ta bashi amsa sai ta fashe da kuka. Da sauri ya taso ya riƙeta yana ba ta haƙuri " Dan Allah ki dai na kuka, yanzu daga zuwa sai kuka. Innayi fa ta yi rabo saura na mu, wallahi Innayi ta tsira" Yana magana ne a raunane dan shima gani yai mutuwar ta dawo ma sa sabuwa... Bayan ya samu ta yi shiru ne ya ce ina baƙon da su ka zo tare. Ta ce ma sa ya je masallaci. "Yayan ki Iro ma na hanya, Idrissa ma ya ce gobe zai zo" Ta jinjina kai. Ba a fi minti biyu ba sai ga kiran Prof, ta amsa ta ce ma sa za ta turo da yaro ya ƙariso da shi. Ta ƙwallawa Salihu kira ashe ya fita, ana kiran Ridwan ne sai ga Prof ya kuma kira inda ya ce ma ta gasu nan zuwa wani yaro a majalisa ya na rako su. Ta ce shikenan... Babban tabarma aka fita da shi aka shimfiɗa, Ado ya fita ya tare su. Bayan sun gaisa ne Prof da Driver su ka ma sa ta'aziya. Ba a jima ba Iro ya iso da tsohuwar machine ɗin sa, shima ya zauna aka gaggaisa. Daga nan aka fito mu su da abinci dukkan su huɗu su ka ci, ana ci ana hira... Kusan awa ɗaya da zuwan Raudha kafin Halima ta iso, itama dai da ta zo sai da aka koka. Ƙarfe shida Prof ya kira Raudha akan ta fito za su tafi. Wajen da su ka parker mota ta je dan ya ce a mota ya ke jiranta. Tana shiga ta hau yi ma sa godiya dan ɗazu su na tare da Halimah yara su ka shigo da kaya niƙi-niƙi wai baƙon Raudha ya kawo. Yadda idon ta ya ƙanƙance yai ja ya jaddada ma sa ba ƙaramin kuka ta yi ba. "Baby kin saɓa alƙawari, jibi yadda idon ki yai saboda kuka" "Da gaske hawaye kawai nayi ba kuka ba" ta tareshi tun kafin ya fara ma ta faɗa. Sai da ya murmusa kafin ya ce " Raudha zan wuce Zaria, idan Allah ya kaimu ranan talata zan zo saboda Laraba zan wuce Abuja and from there zan koma kin san ku ne da hutu, mu malamai koyaushe muna bakin aiki" "Allah ya kai ku lafiya, ya tsare mu ku hanya" Prof ya amsa da Amin. Shiru ya biyo baya na wasu seconds kafin ya ce "Raudha idan kin amince min zan turo magabatana ranan Lahdi saboda a tsaida magana kafin na tafi kin san ba samun lokaci na ke ina shigowa ƙasar akai-akai ba. Idan son samu ne a ɗaura auren kawai" Ta ƙwalalo ido waje su na haɗa ido sai ya kashe ma ta ido. Ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin rufe fiskarta. "Dan Allah a taimakawa ɗan tsoho, ko zai samu kuzarin komawa gida lafiya" Shiru ba ta ce komai ba. "Raudha kin amince?" Ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofa amma a rufe ta ke. "Yau de ko 'yar Fulani za ta nitse sai ta ba ni amsata, idan ba haka ba ta kwana a cikin mota" Ganin da gaske ya ke ya sa ta ce " zan yiwa Yaya magana idan ya amince zan gaya ma ka" "Na gode Raudha, Insha Allahu ba za ki yi dana sanin amincewa da ni ba" Ta kuma buɗe ƙofan still a rufe. "Saurin mi ki ke yi ne Gimbiya ta. Ko ɗan I love you fa ba ki ce min ba za ki gudu" "Abban Yusrah ba fa mu kaɗai ba ne" Dariya yai kafin ya ce "zan kira ki idan mun isa" Tare su ka fito ya raka ta har ƙofar gida kafin ya juya su ka kama hanya da Driver... Bayan sallar Isha Halimah ta tafi tareda alƙawarin za ta zo gobe tunda gobe za ayi meeting... Kusan ƙarfe shabiyu na dare ta gota kaɗan Prof ya kirata ya sanar da ita sun isa Zaria, dama shi ta ke jira dan haka bayan sun gama wayar ta yi bacci. *** Washegari ƙarfe shaɗaya aka sa meeting ɗin da yaran Innayi za su yi. A cikin gidan sun dai aka shirya yin meeting ɗin. Cikin gidan da ya ajiye tarihi. Ɗakin zaure akwai samari biyu a ciki sauran ɗakunan ciki kuma ba kowa sai dabbobi da aka ajiye. Ƙarfe goma da kwata Sa'adatu ta dira a gidan, tsohon ciki gareta haihuwa ko yau ko gobe. Lokacin mutuwar Innayi cikin da ke jikinta ya sa ta dinga daurewa kar ta sa damuwa a ranta ya taɓa lafiyar cikinta wanda an tabbatar 'yan biyu ne. "Auta haka ki ka zama kamar wata baturiya!" Raudha ta yi dariyan yaƙe dan tun jiya Sa'adatu ta ce idan har ta san za ta ma ta kuka to ba za ta zo ba. Maganar Sa'an yai kama da irin maganar Innayi, tabbas da Innayi na nan itama ɗin sai ta faɗi hakan ko makamancin haka. Ƙarfe shaɗaya da minti arba'in tukunna Idrissa ya iso daga nan aka shiga cikin gida dan a gabatar da meeting ɗin. Tabarma aka shimfiɗa guda biyu, ɗaya mazan su ka zauna ɗayan kuma matan su ka zauna. Raudha na shigowa gidan jikinta ya fara rawa, Sa'a ta riƙeta ta ce "Kul Raudha, ki kwantar da hankalinki. Idan akwai abinda Marigayiya ba ta so to bai wuce tashin hankalin ki ba. Ki daure ki yi haƙuri ki composing kan ki" Ta gyaɗa kai tana goge hawayen da sun riga sun zubo... Bayan an zauna ne Ado ya buɗe taro da addu'a. Sa'a tana ganin Idrissa ta fara aika ma sa harara. Ado ya fara yiwa ƙannen sa Ya haƙurin rashin UWA da su ka yi sannan yai jawabin abinda ya sa ya kira wannan taro. "Da farko barin fara da batun Raudha. Ke ce ƙarama cikin mu, kuma kusan shekaru biyu kenan ba kya tare da mu. Bayan tafiyar ki tun ma kafin rasuwar Innayi anyi ta samuna akan maganar na bar ƙanwata marar aure ta tafi karatu har wata nisan duniya, har ga Allah ba dan Innayi ba da ban amince kin tafi har America karatu ba, duk da kuwa scholarship ki ka samu. Yanzu ma dai a matsayina na Babba zan sanar da ke hukuncin da na yanke wanda ba dan son zuciya na yanke shi ba sai dan kare martabar ki. Ki daure ki fito da miji kafin azumin bana, aure shine rufin asirin mace. Idan ki ka yi aure kin ga za ki dinga zuwa akai-akai ko kuma shi mijin ya dinga zuwa miki har ki Ƙare karatun" "Yaya ba sai ka ja wani dogon turanci ba, Raudha ta samu miji. Infact ya ce idan an bashi dama zai turo magabatansa ranan Lahdi" Raudha ta sunkuyar da kai tana jin kunyan yayun na ta. Tun da Prof ya ma ta magana ta sanar da Sa'a, itace ma ta bata shawaran ta yi istikhara akai. To jiya bayan sun rabu da Prof ta kirata ta gaya ma ta abinda ya ce Sa'a ta ce za ta yiwa Ado magana sai ga shi shima ya Ɗauko zancen auren Raudhan. "Waye shi?" Iro ya tambaya yana kallon Sa'a "Wanda ya kawota jiya. Malamin su" Nan su ka fara washe baki dan tun jiya Prof ya burgesu. Ga shi da kamala da kwarjini, zai girmi Ado da shekara ɗaya ko biyu amma a ido za ka ɗauka Ado ya girmeshi saboda yadda hutu ya ratsa shi ga whether ɗin Massachusetts da ya Ƙarɓeshi. Ado ya ce "Masha Allah. Yanzu sai magana ta gaba, maganar gadon Innayi" Yai shiru yana nazarin fiskokin su. "Tun bayan rasuwanta an tattara abinda ta bari an ware waje guda, duka abinda ta bari gasu nan a rubuce a wajena, za a kaiwa Malami ya raba" Takaici ya cika Raudha. Miye Innayi ta bari a duniya. Ko wata uku ba ta cika ba amma maganar gadonta ake yi. "Kafin aje ga maganar rabon gado, ni ba na son komai na yafe amma ban yafe cin amanar Idrissa ba, ƙwandala ba zan yafe ma sa ba sai ya biya idan ya so a tattara kuɗin ayi wa Innayi sadaka da shi amma sai kuɗin nan sun fito daga wajen shi" tana magana kaman ta je ta bangaje Idrissan. "Sa'adatu kin san ni ne dai Babba ko, ki bari abi maganan a hankali" Idrissa ya fara zuru-zuru da ido. Tun da ya samu labarin rasuwan Innayi har yau bashida kwanciyar hankali. Yayi dana sanin biyema Faiza da yai su ka ci kuɗin Innayi. "Akwai wanda ya yafe gado bayan Sa'adatu?" Idrissa ya ce " na yafe" "Munafuki, ai ko ka ci sai ya tokare ma ka wuya. Mugu Azzalumi" "Sa'a dan Allah ki yi haƙuri" Halima ta faɗa tana kama hannun Sa'an. Raudha dai ba ta fahimci maganar Sa'an ba amma ta ce " nima na yafe amma ina son zoben azurfan Innayi idan kun amince a bar min" Zobe ne na zallar azurfa wanda tun da su ka tashi da shi su ka ganta. Ta taɓa gayawa Raudha cewa zoben na Baffanta ne saboda yawa da ya ma ta ma a babbar yatsa ta ke sa shi. "Ba sai kin roƙa ba zobe na ki ne" Sa'a ta fito da zobe a cikin jakarta ta ce " gashi nan halak malak ɗin ki, ranan da mu ka kai Innayi ƙauye ta cire ta bani ta ce na ajiye miki" Raudha ta karɓi zoben tana jujjuyashi tana tuno abubuwa da dama... Bayan Ado ya sake jawo hankalin kowa ne tukunna ya fara magana da Idrissa inda ya nemi bahasin kuɗi da ake tura ma sa wanda Sa'a ta je ta ga shaida ƙarara ba a kula da Innayi balle ya ce yayi amfani da kuɗin wajen kula da ita. Ado dai duk wata yana tura dubu biyun amma Iro na wata uku ya tura, itama Halima sau ɗaya ta tura ma sa dubu ɗaya ba ta kuma turawa ba. Kan Raudha ya ɗaure jin maganar da ake yi. "Adda ban gane ba" ta faɗa tana kallon Sa'a. Sa'a ta fara ma ta bayanin komai dalla-dalla har zuwa yadda ta samu Innayi da yadda Innayin ta yi jinya a wajen ta. Wani dariyar renin hankali Raudha ta yi. Tana chan tana haɗa karatu da aiki, tana chan tana hana kanta bacci, wani lokaci baccin awa huɗu ko uku kawai ta ke yi da dare duk dan ta samu a ƙarshen wata ta tura wa Innayi wani abu ashe Innayi ba ta ci gumin ta ba. Duk wahalar da ta yi a banza ta yi shi, a Idris da matarsa ta yiwa. Kyawawan maruka guda biyu da Raudhan ta saukewa Idris ne ya fargar da su, dan su na kan alhinin abinda su ka ji Sa'a ta faɗa, sai yanzu jikin su ya kuma sanyi gameda mutuwar mahaifiyar ta su. Ado ya dakawa Raudha tsawa akan ta maida hankalinta ko mi Idrissa yai shi Yayan ta ne, Yayan da ya ba ta kusan shekara takwas. Jikin Raudha ya fara rawa, tana son magana amma ta kasa sai hawaye. A rayuwa mi Innayi ta yiwa Idris da zai ma ta haka. Laifin ta ne ita ɗin bagidajiya ce wacce ba ta yi karatun zamani ba, laifinta ne da ta kasance 'yar ƙauye, ƙauyen ma ƙauye futuk. Laifinta ne da ya kasance ɗa gareta bayan shi ɗin ɗan zamani ne, ɗan ƙasaita mai ji da kan sa. Tun yana yaro ya ke da son nuna shi ɗin wani ne ya ke rena gidan su da kuma iyayen sa. Lokacin da mahaifinsu Buba ya makance ƙyashi ya ke ji a ran sa ace Baban sa makaho ne. Saboda son gayu da Jiji da kai Idrissa Buba Pakkari da aka sa ma sa a makaranta lokacin yana ƙarami ya gyara saboda ya waye, yana son sunan gayu, sunan swagga, daga Idrissa ya koma Idris Abubakar Pakkari. Ya gyara sunan ne ba dan dama haka sunan ya kamata ya zama ba sai dan yana ƙyashin a kira surname ɗin sa da Buba maimakon asalin sunan Abubakar, sannan Idrissa ya yi local dayawa Idrees shi ne sunan zamani. Ta dafe ƙirjinta tana kuka, kuka sosai. Halimah ce ta ƙariso gabanta ta fara lallashinta dan Sa'a kam mita kawai ta ke yi tana nuna dole Idris ya fito da kuɗin nan. Da ƙyar Raudha ta dena kuka ta ce " abu ɗaya na ke so na sani Idrissa" ta cire Yayan da ta ke kiran sa da. Ya ɗago jajen idanuwan sa da su ka ciko da hawaye yana kallon ta. "Mi ka tsinana da kuɗi na?" Kunya, danasani da kuma nadama ya shigeshi lokaci guda. Faiza ce ta bashi gurguwan shawara shi kuma ya hau kai. A niyyar sa idan komai yayi settling zai maida wa Innayi kuɗin. Muryar sa a dashe ya ce " dama na fara gini amma na tsaya saboda ba kuɗi so shine na cigaba da ginin saboda Faiza ta matsa na gama mu koma sabon gida ta gaji da gidan haya" Raudha ta yi murmushin baƙin ciki ta ce " yadda Innayi ba ta ci gumina ba haka kai ma Insha Allahu gumina zai zame ma ka haram, ga ka ga gida a ƙare gini lafiya" Daga haka ta fice a gidan, su Ado na kiran ta haka ta mu su biris ta ƙi dawowa. Sa'a ta ce a barta... Raudha na shiga ɗakin Jamilah ta fashe da kuka, ba abin da ta ke hangowa irin Innayi kwance tana murƙususun yunwa a gidan ɗan da ta haifa. Yanzu ba kukan rasuwan Innayi ta ke yi ba sai kukan wahalan da Innayi ta yi kafin ta mutu. Allah kenan mai yi yadda ya so, wa su kam jin daɗin su sai a Aljannah... *** Gabaɗaya kwana ukun da ta yi garin ya fita ma ta a ka, haushin kowa ta ke ji tareda ita kan ta, tana ganin da ba ta yi nisa da Innayi ba da Innayi ba ta mutu cikin wahala ba. Kamar yadda Prof ya gaya ma ta hakan aka yi, ranan Lahdi magabatansa su ka zo. Ƙanin sa Sani da su ke uba ɗaya ne da Ƙannen Baban sa guda biyu su ka zo tambayan auren Raudha. Bayan an basu su ka ajiye sadaki dubu hamsin tareda neman alfarmar a ɗaura auren ranan Talata tunda Prof zai bar ƙasan ranan Alhamis. Idan ya so ayi sauran bikin ba tareda shi ba. Su Ado ba su yi watawata ba su ka amince sannan su ka tura saƙo Ajili da Tunfure akan za a ɗaura auren Raudha ranan Talata... Tunda Raudha ta ji batun sai wani kewan mahaifiyarta ya taso ma ta, ashe duk burin da ta sha na yadda Innayi za ta shiga ta fita a bikinta ashe hakan ba zai yiwu ba. Ranan Talata da misalin ƙarfe biyu da rabi aka ɗaura auren *Professor Umar Audu Bamalli* da amaryarsa *Raudha Abubakar Pakkari* Aaaf 🤔ashe Prof ma ya kamata ya maida sunan sa na swagga kamar Idris. Doctor kuma Professor *Omarr Abdullah Bamally* 😂 Gaskiya anyiwa Raudha kara domin kuwa mutane dayawa su ka halarci ɗaurin auren. 'yan uwan su na Ajili da Tunfure sun zo dayawa. Yayanta Yusuf ma ɗan Hajiya Harira ya zo hakanan Yayunta mata ma na wajen Baba Indo sun zo, duk da ma sai ƙarshen wata za ayi waliman aure, wanda ya kama saura kwana ashirin da huɗu kenan. Ya so ganin Amaryar sa kafin su tafi amma ba hali, a ranan za su koma Zaria kuma ƙofar gidan a cike ya ke balle ya kirata ta fito, dole haka ya haƙura ya bi 'yan uwan sa su ka juya. Da ke ance Prof na da gida a Zaria shiyasa aka shirya kai ma ta kayan ɗakinta chan Zarian. An haɗa kuɗi an ma ta kaya kuma ba laifi sun yi abin kirki. Baffa Tsoho Sa guda ya bayar a yi hidimar biki da shi. Bayan kwana biyar da ɗaura aure Sa'a ta haifi 'yan biyu maza, ta so haihuwan mata dan har yanzu ba ta samu 'ya mace ba, yaranta yanzu sun zama biyar duka maza. Abu ya haɗu ya zamowa Sa'a biyu ga bikin suna ga bikin Raudha da za ayi. Ba laifi an fara yiwa Raudha gyaran jiki wanda Sa'a ce ta haɗata da wata mata da ke yi. Kwana goma da ɗaura aure aka kawo kayan lefe, nan fa aka fara jinjinawa Prof dan ya yi abin kwatance. Akwatuna takwas aka kawo banda jaka manya guda biyu da su ma ke shaƙe da kaya. Tuni Sa'a ta sa aka kai ma ta ɗinki, dan abin ma yai sauri wasu Misau aka ba da wasu Azare wasu a Bauchi. Saboda rashin cika alƙawarin teloli, gashi idan ta tafi chan ba da wuri za ta dawo ba. Duk da haka wasu ba a kai su ɗinki ba. Raudha ba ta da ƙawaye, iya ka ci class mates ɗin ta ne na Sakandare wanda kusan 90% ɗin su sunyi aure sai na ABU. Ta aika wa wanda za ta iya aikawa kuma yawanci sun ba ta haƙuri akan ba za su samu zuwa ba. Wanda ke Misau kam sun nuna za su zo ko dan ayi gulmarta tunda sun ji mijin na ta a chan America ya ke, wasu har sun fara yaɗa gulmar bature za ta aura. Kullum sai sun yi waya da Prof yana ƙara jaddada ma ta soyayyar sa gareta tareda nuna ma ta tsananin kewarta da yai. Ita idan yana magana ma kunyar sa ta ke ji tana tunanin yanzu fa sun zama ɗaya tunda an shafa fatiha. Wani lokaci yakan ba wa Umma da yaran su gaisa... Ranan Jummu'ah aka yi waliman aure, anci an sha kuma anyi sadaka. Tent aka kafa a ƙofar gida aka jera kujerun Roba inda maza da su ka zo su ka ci abinci bayan an sauko daga sallar Jummu'ah abin kamar wani ƙaramin reception. Mata kuma sun cika cikin gida ana ta bidiri. Da yamma aka kira wani Malami yai wa'azi, malamin su Raudhan ne lokacin tana islamiyya. Ranan ta ci kuka kamar ba gobe saboda kewar Innayi, sai dai ƙaddara ta riga fata... Washegari aka kai Amarya Zaria, gida ne Babba da ya ke da komai da komai a ciki. Dan haka kayan ɗakin Raudha ma wani ɗaki aka zuba su aka kulle. Washe gari kowa ya watse bayan anyiwa Raudha nasiha. Da yamma Sani ƙanin Prof da matar sa da wata yarinyar su budurwa su ka kai ta Abuja gidan Dr Ahmad, da ke Sani ya riga Prof aure ɗan sa na fari ma yana shekara shatara yanzu. Jirgin su Raudha bai tashi ba sai ƙarfe goma na daren ranan Litinin. Wayaga Amarya za ta kai kan ta gidan Ango... *** Shi ɗaya ya zo ɗaukanta, ba ta ankara ba sai gashi da yin abinda ya sa ta ji kunya sosai a airport ɗin. Prof yana zuwa ya rungumeta jikinsa yana ma ta sannu da zuwa, duk nuƙu-nuƙunta haka ta barshi sai da ya gaji ya saketa bayan kusan 3minutes yana rungume da ita. "Welcome home my beautiful wife" Ta sunkuyar da kai tana murmushi tareda mugun jin kunyar sa... Da Bismillah ta shiga gidan Prof a karo na biyu, da ta zo a matsayin baƙuwa yanzu kuma ta zo a matsayin Uwargida. Tana ganin Umma ta shiga ɓoye fiska saboda kunyar surikar na ta. Umma kam ba ruwanta domin cike ta ke da farin ciki dan ɗan zaman da su ka yi da Raudha ta karanci tana da hankali za ta iya riƙe amanar 'ya'yan marigayiya. Duk kauɗin Prof dai ya ɗagawa matar ta sa ƙafa saboda shi ba yaro ba ne yasan akwai gajiya a tattare da ita. A yammacin ranan Jumu'ah ne aka gudanar da ƙaramar liyafa a gidan Prof inda abokanan aikinsa lokacin yana asibiti da kuma abokanan sa Malamai da Muslim Community na Boston duk aka hallara aka ci aka sha sannan aka bawa Amarya da Ango gifts. Raudha ma ta gayyaci 'yan ajin su kuma kusan duka sun zo... Ranan Asabat Umma da Yaran su ka tafi ziyaran kwana uku gidan Uncle ɗin Zainab wato marigayiya matar Prof da ke Connecticut. Ta zo karatu ta zauna a wajen ƙanin Babanta har kuma su ka haɗu da Prof lokacin tana ajinta na ƙarshe Allah ya ƙaddara aure tsakanin su. Umma ce ta shirya tafiyar saboda Amarya da Ango su samu su sake. A wannan lokaci ne Prof ya samu damar kula da amaryarsa yadda ya kamata, yai ta lallaɓata a hankali har ya samu kan ta kuma Alhamdulillah ta riƙe tarbiyan da Innayi ta ma ta. Asabat da Lahdi duka Prof na tare da Amaryar sa, ko fita baya yi, yana nan yana lallaɓata, yana nuna ma ta tsantsar soyayyar sa gareta wacce ta ke tsakani da Allah babu Algus. Ranan litinin da yamma su Umma su ka dawo saboda makarantar su Yusrah. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya, tun Raudha na jin kunyar Prof tana ɗari-ɗari da shi har ta zo ta sake jiki dan yanzu kam an riga an zama ɗaya ana batun wata uku da 'yan kai. Da ke yanzu clinical round su ke zuwa ba aji ba, Asibiti mafi kusa da su ta zaɓa ta ke zuwa kuma Alhamdulillah tana fahimtar abubuwan da ake nuna mu su. *RIBAR UWA* *Na...Azizat* *Wattpad@000Azee* Chapter 15 (Free book ne) *Epilogue* Rasuwan Innayi ya zo da sauyi da dama, da masu daɗi da marasa daɗi. Kuma dukkan su babu wanda bai ga darasin rayuwa ba. Raudha tun tana irga watanni da aure har ta fara irga shekara. Kaman Innayi itama ba ta samu haihuwa da wuri ba. Ba ta sa damuwa a ranta ba dan addu'ar ta shine Allah ya bata 'ya'ya ma su albarka 'yan'yan da za su jiƙanta su ji tausayinta, 'ya'yan da za su zamowa musulunci abun alfahari. A ƙarshen shekarar su ta uku da aure ne ita da Prof su ka tafi aikin Hajji. Aikin Hajjin da sai wanda Allah ya kira ya ke zuwa. Duk yadda ita da Baffah su ka ci burin kai mahaifiyar su Hajji Allah bai ƙaddara hakan ba. Bayan dawowar su ne su ka shirya zuwa Nigeria sai dai laulayin ciki da ya sata a gaba ya sa su ka janye tafiyar zuwa wani lokaci. Tundaga laulayi Raudha ta fara jin tsoron haihuwa, ta ke kuma jinjinawa Innayi da ma duk wata Uwa. Ashe ciki da haihuwa ba sauƙi, a hakan ka gama haifan yaro ko yarinya su zo su muzguna ma ka ko kuma su ɗaukeka ba a bakin komai ba. Laulayi tun watan farko har sai da ta shiga wata na biyar kafin ta fara jinta garau. Tana samun kulawa sosai a wajen Mijinta da Umma. Duk wani aure ana samun saɓani itama natan akwai sai dai soyayya, haƙuri da addu'a su suka zaunar da su lafiya ta inda ba a taɓa jin kan su ba. A yayi yawa shine ka ga anyi fushin kwana biyu amma yawanci a yini ake faɗa a kuma shirya. Musabbabin son zuwanta Nigeria ma saboda Idrissa ne. Har ga Allah ba ta ma sa fatan da zai samu iftila'in da ya faɗa ma sa ba sai dai dama hakan yana daga cikin ƙaddarar sa. Prof ya riga ya ɗage tafiyar sai bayan ta haihu amma ta so ta je Nigeria ta ga yadda rayuwa ta juya da ɗan uwan na ta... Tun bayan auren Raudha Idris bai sake zuwa Misau ba. Kunyar 'yan uwan sa ya ke yi yana kuma ƙoƙarin haɗa kuɗin da ya ci. Ita kam Faiza ko ajikinta dan nunawa ta yi ba ta damu ba gida ne dai za su tare tunda an gama. Ba yadda ya iya haka su ka koma gidan watanni goma shaɗaya da rasuwan Innayi kenan. Komawar su ba da jimawaba aka yiwa Idris transfer zuwa Maiduguri, haka ya tafi ya bar Faiza a Bauchi duk ƙarshen wata yana zuwa hutu. A wani hari da 'yan Boko Haram su ka kai wa bankin da Idris ya ke aiki ne iftila'i ta faɗawa Idris. Bomb aka jefa mu su lokacin da ta tashi ta yi awun gaba da rayuwan wasu yayinda wasu kuma su ka rasa wani sassa na jikin su ciki har da Idris wanda ya rasa hannunsa na hagu. Da farko ma da aka ji labarin an ɗauka ya rasu sai daga baya aka gane da ransa. Daga Maiduguri aka fara jinyarsa kafin su Ado su ka dawo da shi Bauchi ƙarshe dai Ado da Iro ne su ka sai da gidan sa aka yi duk wani hidimar asibiti da shi. Sai gashi Idris ɗan gaye ya koma mai hannu ɗaya, ɗaya hannun dumgulmi ne kawai a wajen kafaɗar sa. Tashin hankali Idris ya shiga ba kaɗan ba, ta ina zai fara rayuwa a haka. Bayan an sallameshi Misau aka wuce da shi, ɗakin zaure aka bashi dan ɗakunan ciki an gyara an sa haya a ciki. Tun yana asibiti ya fara ganin izina domin matar sa Faiza 'yar ƙwalisa da ya ke ji da ita kamar zinare ko diamond ita ne dai ta fara nuna ma sa ƙyashi saboda yanzu ya koma mai hannu ɗaya. Ya kirata ta zo Misau amma ta ce ba za ta iya zama a Misau ba ga kuma aikinta. Tunda ya bar Bauchi watanni huɗu da yai a Misau ko mai kamar Faiza bai gani ba. A wata na biyar ne sai ga ɗan saƙo wani ƙanin ta wai ya zo karɓan takardar sakin Faiza. Ya ɗau waya ya kira Faizan dan ya ji dalilin wannan saƙo. "Kai ma Idris tundaga asibiti ya kamata ka sani auren mu ya ƙare kai ne dai ba ka sa shi ya zama offficial ba. Na ɗauka rashin zuwana Misau zai sa ka gane amma ka ƙi, yanzu kam haƙurina ya ƙare ka turo min takardata" Tsabar takaici kasa magana yai sai hawaye. "Ina I love you? I'll never leave you, I promised to be with you till the end of my life ɗin su ka shiga" Dama soyayyar gaskiya ce ke tsayawa through trying times through thick and thin. Kwata kwata ba su gina soyayyar su tsakani da Allah ba. Ita Faiza ta ga ɗan farin bafulatani zubin larabawa shi kuma Idris ya ga wayayyiyar mace 'yar ma su kuɗi. Idris bai ba ta takardar ba sai ma shirya zuwa Bauchin da yai dan ya ga ko dai za ta iya kallon sa ido cikin ido ta ce za ta rabu da shi. Washegari ya wuce Bauchi yanzu har ya fara sabawa da hannu ɗayan. Tarban walaƙanci ya samu a gidan su Faiza domin ko falo ba a shiga da shi ba, a tsaye acikin compound ɗin su Faiza ta fito ta sameshi ta tabbatar ma sa da maganarta na son rabuwa da shi da ta ke yi. Ya ce ma sa ko za su rabu sai dai ta bar ma sa Mufeedah tunda dai ita ɗaya ce rabon da ke tsakanin su. "Mufeedah ba za ta zauna a cikin talauci ba, zan dinga turota hutu ko da na sati ɗaya ne" Idris ya rasa bakin magana domin ba shi da ta cewa, shi ya ba ta soyayya ya ba ta kulawa ya darajata fiye da kowa na sa shiyasa yanzu da ta gujeshi ba shi da ta cewa. A wajen ya furta ma ta saki ɗaya sannan ya bar gidan cike da takaici... Duniya ta koya ma sa darasi, gashi Innayi ta yi ma sa nisa balle ya nemi gafaranta duk da kuwa Sa'a ta nuna ma sa Innayi ta yafe ma sa kafin ta rasu amma har wayau ya kasa samun nitsuwa. Ganin Lafiya ta samu ne ya shiga neman aiki tunda dai tun jinyar sa su Ado ne ke ciyar da shi da kuma buƙatun sa na yau da kullum. Shekaran sa biyu da rasa hannunsa ɗaya ya samu aikin koyarwa ya fara yi, albashin dai bai kai na sa na da ba amma Alhamdulillah he will manage. Wata tara Cif da sakin Faiza ya ji labarin ta yi aure. Ba ma Bauchi mijin ya ke ba a Abuja ya ke dan haka ta tarkata ta tafi ma sa da 'ya chan Abuja. Tun rabuwar su ma sau ɗaya ta sa aka kawo Mufeedah wanda sati ɗaya na cika ta turo aka ɗauketa. Duniya kenan! *** 'Yan biyu Raudha ta haifa mace da namiji, duk da ta samu kulawa sosai daga wajen ƙwararrun likitoci hakan bai hanata jin zafin haihuwan ba. Umma ta shiga kula da ita da yara. Ranan suna Prof ya raɗawa yara sunan Aliyu da Faɗima. Raudha ta ji daɗi sosai dan bai gaya ma ta sunan da yai niyyan sawa ba sai ranan suna. Haidar da Noor ne inkiyar yaran. Yaran su na wata uku su ka je Nigeria dukkan su. A Zaria su ka sauka inda su ka yi sati kafin Raudha ta je Misau. Tana hawaye Idris na yi haka ya riƙe hannunta yana ba ta haƙuri yana neman yafiyarta. Ta nuna ma sa ta yafe wancan maganar da ta yi ma ranan ta yi ne cikin fushi. Sati ɗaya ta yi a Misau kafin ta je Azare ta yi wa sa'a kwana biyu sannan ta koma Zaria, watan su ɗaya su ka koma. Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya... A ɓangaren Ado kuwa a shekarar da Innayi ta rasu a shekarar ya samu lecturing a Legal yana haɗa masters na shi ya samu appointment. Adamu Buba Pakkari yana ji da kan sa a yanzu da ya ke jinsa cikakken mutum da ya bawa arba'in baya. Yadda sabbin lecturers ke kauɗi idan 'yan mata na tururuwan su haka shima Ado bai tsira ba daga wannan hali. Wani jan aji yake yi yana tafiya da tinƙaho da jiji da kai. A shekaru biyar da ya fara lecturing ya shiga neman Sadiya. Shekarun sa arba'in da takwas amma jinsa ya ke kamar ɗan shekara talatin. Sadiya Mustafah ta yi ƙaurin suna cikin ɗalibai, yarinya ce da ta ke ji da kanta a matsayinta na wacce ta yi rayuwa a Abuja. A zahiri a Mararraba su ke zaune amma kullum taɗin ta Abuja su ke a nan aka haifeta a nan ta taso, sau uku da ta taɓa shiga garin Abuja ya sa ta ke taɗi tamkar ta jima a ciki, abu da waya tuni ta browsing sunan anguwanni da manyan wajaje na cikin garin tana yiwa mutane taɗi tana sako su, su kuma na ganin ai ita ɗin a Abujan ma a anguwannin ƙusosin gwamnati su ke. Mahaifinta ɗan Harɗawa ne amma ya jima da komawa Mararraba inda ya ke sai da kifi. Sadiya rayuwar ƙarya ta sawa kan ta shiyasa tun da ƙarancin shekarunta shabakwai ta fara tara samari daga baya ta buge da bin manyan mutane. Tunda dai ta fara shafa mayukan dubu ishirin dubu talatin. Tana da hasken ta amma da ta fara shafa mai sai ta koma ita ba baturiya ba ita ba zabiya ba, fiskan yai wani yellow da shi. Ga wanda bai san kyau ba Sadiya za ta burgeshi amma wanda ya san kyau ya san Sadiyan da ta fi ta yanzu kyau nesa ba kusa ba. Tunda ta shigo CLIS ta ke gwara samari da lecturers. Ado ma ya tsinci kan sa cikin ma su neman ta. Yana da maƙo shiyasa ba sa shiri da ita, abu ɗaya ya sa ta ke biye ma sa shine kyaun sa. Tana bala'in son namiji fari dogo mai dogon hanci sai gashi Ado ya haɗa. Ba dan kyaunsa ba da tuni ta rabu da shi dan baya iya ba ta dubu goma, iya kacin sa dubu biyu dubu biyar ita kuma tafi ƙarfin wannan dan ko kuɗin shower gel da ta ke amfani da shi bai kai ba balle uwa uba mayukan da ta ke shafawa... Yau ma su na tare cikin motar sa yana lallaɓata a kan yaushe zai sake samunta tana gaya ma sa sai wani sati wayar sa ta shiga ringing. Ya duba wayan ya ga sunan Jamilah yai saurin mai da wayar aljihu. "Ka ɗauka mana" Sadiya ta faɗa tana maƙe muryanta "No zan kira idan mun rabu its not important" Namiji kenan. Matar sa da ya bari da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe ya ke cewa not important saboda ya ga budurbazar. Ganin an sake kira ya sa shi sa wayan a silent ya cigaba da lallaɓa Sady har ta haƙura akan za su haɗu jibi, bai tafi ba dan ta fara sarrafa shi yadda zai samu nitsuwa. Yana nishin jin daɗi a cikin mota matar sa na nishin wahala a gida... Jamilah tun safe ta fara naƙuda ta je asibiti amma haihuwan shiru, su ka ce ta koma gida ta yi ɗan exercise zuwa yamma sai ta dawo. Cikin ya ma ta nauyi gashi jiki ya girma dan yanzu haihuwarta na tara kenan za ta yi a shekarunta arba'in da ɗaya. Ta fito da wankinta da na yaran Aisha ta farayi sai da ta gama ta shiga gyaran ɗaki, still har bayan maghrib haihuwan bai zo ba. Ƙarfe tara na dare haihuwan ya tashi gadan-gadan. A lokacin da duk wani miji na ƙwarai indai ba kasuwanci ya ke ba ko aiki ya zama yana tareda iyalinsa shi Ado yana wajen Budurwa yana shan minti. Aisha ce ta ɗau wayar Jamila ta fara kiran mijin na su ko zai zo da mota a kai ta asibiti sai dai ya ƙi ɗauka. Ganin bai ɗauka ba ta ɗauko na ta wayar ta shiga flashing dan ba kuɗi, daga baya ta ci bashin mtn ta shiga kira amma shiru. Da haihuwan ya zo daf ne har ta sa yara su kirayo mai Napep ta fasa saboda kan yaro ya fara fitowa ta ce yara su shiga maƙota su kira Anty Ladi wanda ta girme mu su sosai dan za ta yi shekara hamsin haka. Anty Lahdi da Aisha su ka karɓi haihuwan jaririya, bayan kaman minti shida sai ga wani na shirin fitowa su kan su ba su san 'yan biyu ba ne. Wannan karan Jamilah ta wahala sosai yayinda ta challah ƙara lokacin da jinjirar ta gama fitowa. Suna kan kula da yaran ba su san Jamilah rai ya yi halinsa ba. Sai da Anty Lahdi ta fara magana tana faɗin "Jammy ashe 'yan biyu ne shiyasa cikin ki yai girma" ta tsaya lokacin da ta ga fiskar Jamilar. Ta ɗaga hannun Jamilah ta ji shi yaraf, ta kai kanta daidai ƙirjin Jamilah amma ba alaman bugun zuciya. Ta sa hannun ta a wajen tsintsiyar hannunta ba ta ji motsin jijiya ba. Nan ta saki Innalillahi... Ado sai ƙarfe goma da minti arba'in na dare ya baro bakin hostel bayan Sady ta taimaka ma sa ya yi release. Ya nufo gida zuciyar sa saƙayau yana jin shi lafiyayyen namiji. Sai da ya kusa gida ma ya tuna ashe ɗazu matan sa sun kira shi yai tsaki dan ya san ba zai wuce haihuwa Jamilah za ta yi ba, idan kuwa haka me ai akwai keke Napep da za su iya kira ya kai su Asibiti miye za su wani dameshi da kira. Yana nufo ƙofar gida ya hango Iro da Idrissa da maƙotansa guda biyu. Nan jikin sa yai sanyi. Yai parking mota ya fito a hankali. Iro ne ya tareshi da faɗa akan ina yaje ana ta kiran sa ya ƙi ɗauka. "Mi ya faru ne?" Ya faɗa yana ɗarɗar yayinda zuciyarsa ke gaya ma sa ƙila Jamilah ce ta haihu ɗan ya koma. Malam Shu'aibu da duk ciki ya girme su ne ya zaunar da Ado a kan dakali ya fara ma sa nasiha akan mutuwa sannan ya sanar da shi mummunan labari. Jamilah ta haihu kuma ta rasu, ba nan abin ya tsaya ba duka 'yan biyun sun koma, ɗayar ko minti biyar da rasuwan Jamilah ba ta yi ba ta rasu ɗayar kuma har an yiwa Jamilah da 'yar uwarta wanka itama ta cika a bayan yayar Jamilah da ta goyeta tun zuwan su saboda kuka da ta ke yi. Gumi ya fara ketowa Ado. Ba abinda ya ke tunawa irin yana chan yana saɓon Allah Malakul Maut ya ziyarci gidan sa ya ɗau rayuka uku. Ashe haka ake mutuwa ba sallama. Jamilah Uwargidan sa wanda akan ta ya fara sanin 'ya mace, sai gashi yau tana fama da naƙuda shi ya tura ƙafa ya tafi wajen wata karuwa yana jin daɗi, jin daɗi na lokaci kaɗan na 'yan wasu mintuna da ba su wuce ishirin zuwa talatin ba. Jiki a sanyaye ya shiga gidan tareda Iro da Idris. Yana zuwa ɗakin Jamilah ya ga gawar mutum uku kwance nan ya yanki jiki ya faɗi. Da ya farfaɗo kuka ya ya fara wiwi kamar ƙaramin yaro yana faɗin "kaicona kaicona da son zuciya"... Ba wanda bai ji rasuwan Jamilah ba. Asiya matar Iro kam kusan ƙaramar hauka ta yi dan tuni ta ji tsoron mutuwa ta fara fallasa abin da ta aikata na zuwa wajen boka da ta yi dan ta mallake Iro, shiyasa tun shekaru da su ka wuce da ya taɓa zancen aure ta sa aka rufe bakin sa ya rufe zancen ƙara aure har yau bai ma sha'awar auren. Da ke da sauran imani a zuciyarta ya sa mutuwar ya girgiza ta har ta fallasa kan ta tana neman tuba a wajen Allah da wajen Iro... *** Idan mutuwar Innayi bai ishi Ado ishara ba ga mutuwar Jamilah da 'yan biyunta wanda ya sa yai karatun ta nitsu wa kan sa da duniya wacce ta ke ba matabbata ba. Ba za ace ya dena saɓo ba saboda mu 'yan Adam ne muna da rauni. To amma tun rasuwan Jamilah ya watsar da neman mata da ya ke yi ya rungumi Matar sa Aisha abu da jiki da jini da kuma sabo da mata biyu. Shekaran Jamilah biyu da rasuwa ya auri wata bazawara da mijinta ya rasu, ba wata babba ba ce dan shekarunta ashirin da takwas kuma ɗan ta ɗaya. Iro ya saki Asiya inda ya ƙara aure ya auri budurwa 'yar ƙauyen Baban sa wato Ajili , shekaranta shabakwai, to abu da yarinya da kuma yara har bakwai da Asiya ta bari dole dai ya dawo da Asiya bayan shekaran su ɗaya da rabi da rabuwa. Ta nitsu dan ta rungumi ƙaddararta, tana kaffa da kaffa da mijinta tana kuma ƙoƙarin danne kishinta ga amaryarta Na'ima wacce ke ji da ƙuruciya. Anci sa'a Na'iman ba ta da wani karambani da falli tana mutunta Asiya sosai sai Asiyar itama ta ci girma tana ƙoƙarin tare duk wani kafa da zai jawo matsala tsakanin su. Idris bai yi aure da wuri ba dan sai da yai shekara biyar da rabuwan su da Faiza sannan yai aure. Wata student ɗin sa ya aura wacce ta nace ma sa akan tana son sa, kasancewar sa mai hannu ɗaya bai dameta ba ita dai tsakani da Allah ta ke son sa, tana gama NECO aka yi bikin su gashi yanzu Allah ya azurtasu da ɗiya mace wacce ta ci sunan Innayi suna kiran ta Ummi. Wani madaidaicin gida Idris ya siya a ɗan gefen layin su bayan ya ɗau shekaru yana tara kuɗi. Gidan dai zai kai shekaru goma da gina shi mai gidan ma matsi ce ta sa shi sayar da gidan amma gidan na da kyau, ɗakuna uku manya ne agidan. Su na nan zaune lafiya da matarsa Khadija da baby Ummi. Bayan ya samu iyali ne kuma ya samu gida, ya je Abuja ya karɓo Mufeedah. Ashe Mufeedan ba jin daɗin gidan ta ke yi ba, yaran gidan ba sa son ta kasancewarta Agola sai su dinga hantarar ta. Fa'iza ba ta iya magana dan ba ta da wani daraja a gidan. Alhaji Khalill ba mazauni ba ne kuma ya hanata aiki ga shi tunda ya gane dan kuɗin sa ta aureshi ya ke ma ta walaƙanci, ga uwa uba Uwargidan ta wanda ta ke ji da bala'i. Sau biyu Alhaji Khalil ɗin na ƙara aure tana koran su da masifarta. Wannan Fa'izar ma tayi-tayi ta tafi ta kasa amma ba za ta gushe ba dan sai ta raba auren duk da ma ba ta da damuwa tunda ta san abinda ta yi Fa'iza ba za ta taɓa haihuwa da Khalil ba. Ita ɗin ce dai magajiyar gida mai 'ya'ya biyar, biyu maza uku mata... Shekarar Innayi goma da rasuwa mijin Halimah Alhaji Nuhu ya rasu. Ga shi ba wani abu ya bari ba amma a hakan sai faɗa ake yi akan gadon sa da 'ya'yan da ya bari da 'yan uwa. Su gani su ke Alhaji Nuhu ya ɓoye kadarorinsa a wani waje amma Halima ta san Alhaji Nuhu ba shi da komai, cikin zaman auren su ta gane kuɗin Alhaji Nuhu da yazo lokaci guda yai tashe har ya zo ya gushe ba komai ya ja haka ba sai bin malamai da Alhaji Nuhun yai a ƙuruciyar sa, aka bashi layar da za ta bashi sa'a a kasuwancin sa. Abin ya ma sa amfani amma na lokaci kaɗan dan kwata-kwata arziƙin sa bai wuce na shekaru bakwai ba komai ya rushe ma sa. Abun mamaki ko wata biyu ba ta yi da fita takaba ba ta samu manema. Ciki ta zaɓi Malam Muhammad wanda ya kasance headmaster a Primary school. Rashin haihuwa ya sa duka matan sa ke rabuwa da shi. Ya nemeta ne tunda shi baya haihuwa ita kuma tunda ta riga ta hayyafa rashin haihuwa ba zai dameta ba. Rayuwan su da Malam gwanin sha'awa, shi mutum ne mai riƙo da addini shiyasa tun zuwanta ya duƙufa da koya ma ta karatu saboda ta yaƙi jahilci. Ita kam tunda ta yi aure ba ta sake waiwayar ƙur'ani ba iya kacinta karatun sallah. A lokacin rasuwan Jamilah ma da aka rarraba ƙur'ani dan a karanta ba abin kirki ta yi ba tunda ba iyawa ta yi ba. Sai yanzu ta ke kaicon rashin bin maganar Innayi, ta ƙi karatun Arabi ta ƙi na boko ta buge da guguwar 'yan matanci wanda ya kaita ga ƙarewa da Alhaji Nuhu wanda ko kaɗan bai san darajar ta ba har ya rasu. *** Shirye-shirye su ke na dawowa Nigeria gaba ɗaya. Cikin shekaru goma shabiyu da aure sun samu cigaba da ɗaukaka. Umma ta rasu lokacin 'yan biyun Raudha na shekaru biyu a duniya. Bayan 'yan biyu ta haifi Abdullah sai Muhammad wanda a haihuwar sa ne ta samu complications har aka ba ta shawaran idan da hali ta tsaida haihuwa saboda lafiyarta. Prof bai ɓata lokaci ba ya amince dan lafiyar matarsa ya fi ma sa komai. Itama ɗin yara huɗu kam sai dai godiyar Allah tareda addu'ar Allah ya raya ma ta su da imani. Ko a haka ita UWA ce tunda Allah ya azurtata da haihuwan, wasu nema su ke ruwa a jallo amma Allah bai ba su ba, wasu kuma ɗaya Allah ya mallaka mu su... Last year aka yi bikin Yusrah wanda ɗan ƙanin Baban ta Sani ta aura mai suna Habib. Prof ne ya ɗauko shi karatu shine ya ke zaune da su. Shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin sa da Yusrah ƙarshe ta koma Soyayya. Yusrah ta fara residency ɗin ta dan itama layin Prof da Mom Raudha ta bi ɓangaren Raudhan ma ta ɗauka wato gyneacology. Shima Habib ya samu aiki a inda yai internship na shi dan haka suna zaune da matar sa lafiya. Yana latsa wayar sa yana ganin yadda Raudha ke faman tattara kaya tana yi tana mitar hayaniyar yaran da ta ke ji a ƙasa. "Baby take it easy, tafiyar da saura fa" "Kai ka ke ganin da sauran lokaci 5days fa ya rage gashi ko rabin shiri ba a yi ba" Murmushi yai ya ajiye wayar ya zago bayanta ya rungumeta yana faɗin " ba na so kina ɗaga hankalin ki. All that matters shine Allah ya kaimu gida lafiya. Kin ji Baby Love" Ya ƙarisa maganar yana kissing wuyanta, ganin bai barta ba ne ya sa ta ce "My Ɗan Tsoho akwai aiki a gaba na fa" Prof ya ƙanƙance murya ya ce " to a fara sallama na tukun" Dariya ta yi kafin ta shiga biye ma sa dan ko ta ƙi ma ba bari zai yi ta yi aikin ba. Sai da ya shimfiɗa ta kan gado ya je ya kulle ƙofa dan yaran na su sai a hankali ba dai rigima ba. Ai kuwa suna tsaka da raya sunna Noor ta fara buga ƙofa tana kukan sakalci tana kiran Mom Mom... Jin ba a amsa ma ta ba ya sa ta koma tana cewa Haidar Mom na banɗaki idan ta fito za ta gaya ma ta abinda ya ma ta, kuma sai Mom ta rama ma ta. Shi kuma Haidar na ma ta gwalo yana faɗin sai ta faɗa ɗin shima zai ce ta sha ice cream ɗin da Mom ta ajiye a fridge. Prof da Raudha su ka yi murmushi su ka cigaba da aikin lada... Watan su biyu da settling a Nigeria aka buɗe asibitin Prof wanda dama tun kafin auren su da Raudha ya fara ginin, a hankali a hankali har komai ya kammala aka zuba kayan aiki da duk abubuwan buƙata. Sunan matar sa Zainab ya ke son sawa amma auren Raudha da yai ya sa shi chanja ra'ayin sa. Ita kan ta Raudha ba ta san sunan da zai sa ba kenan sai da ta je bikin buɗe asibitin ta ga sunan da aka rubuta. Duk 'yan uwanta sun halarci Bikin kuma su ma sun yaba da karamcin Prof da wannan suna da ya sawa asibitin sa. Dr Ambi ma ya zo da iyalen sa dan tun bayan aurenta da Prof su ka ƙulla zumunci da shi, matsayin sa na wanda ya taimakawa Raudha ya sa Prof ke darajashi sosai. Ya yi retire ya koma mahaifansa a Kano. *FAƊIMA INNAYI MEMORIAL HOSPITAL* "Ɗan tsoho na" ta kira a hankali hawaye na zubowa a idonta. Prof ya so ta, ya ƙaunaceta, ya darajata, tun da ta aureshi duk Jummu'ah sai ta yiwa Innayi da Baban ta sadaka, tun kafin ta ma sa maganar yin sadaka ma shi ya fara ma ta saboda shima abinda ya ke yiwa na sa iyayen kenan duk Jummu'ar Allah. "Raudha matuƙar Ina raye zan mu su abinda za a tura mu su lada a kabarin su, saboda nima watarana zan je inda su ka je kuma zan ji daɗi ace nawa 'ya'yan su na min sadaƙatul jariya" Ba abinda za ta ce sai dai Allah ya saka ma sa da alkhairi ya sa su tashi a Aljannah a matsayin mata da miji. "Bana son kuka Baby na, idan ba haka ba a gaban mutane zan goyeki na yi ta lallashi" ya faɗa yana share ma ta hawaye da babbar yatsar sa. Ba ta san lokacin da ta saka dariya ba musamman da ta tuno shekarun baya kafin auren su da ya taɓa magana makamancin haka. Shima ya sa dariyan yana hamdala a ransa. Raudha ta zamo ma sa abin tinƙaho, ko da wasa bai taɓa dana sanin aurenta ba sai ma hamdala da ya ke yi da Allah ya bashi ita a matsayin mata... Rayuwa kenan! Addu'ar Innayi ta karɓu a kan 'ya'yan ta, sun fuskanci ƙalubalen rayuwa bayan rasuwan ta amma daga ƙarshe Allah ya shirya ma ta su kaman yadda ta yi ta mu su addu'a a koda yaushe Lokacin da ta ke raye. *ke ma UWA ka da ki gajiya da yiwa 'ya'yan ki addu'an shiriya, ko ba daɗe ko ba jima Allah zai amsa addu'ar ki. May be kina raye, may be kuma sai ba kya nan. Allah ya albarkaci yaran ku amin, muma Allah ya bamu mijin ya kuma azurtamu da 'ya'ya ma su albarka Amin* *Alhamdulillah!* *a nan na kawo ƙarshen labarin RIBAR UWA. Darasin da ke ciki Allah ya bamu ikon waiwayar su mu gyara a cikin tamu rayuwar. Kurakuren da na yi Allah ya yafe min. Duk wanda su ka min addu'a saboda yadda labarin ya shigesu Ina godiya kuma nima ina addu'ar Allah ya biya muku buƙatunku ya kuma gafartawa iyayen ku Amin* *akwai paid story da zan yi nan ba da jimawa ba, ina fata za ku yi supporting ɗina kamar yadda ku ka yi a Sakatariya ta da kuma Tsohuwar Soyayya* *jinjina da godiya ga duk wanda ya karanta labarin nan, haƙiƙa na ji daɗin yadda ku ka yi ta bina da addu'o'in ku. I'm happy* *Ta ku Azizat* ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************